Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai bata haifemu ba,amma uba daya muke ni da........"

"Aliyyu!" Ta kirayeshi da ainihin sunansa

"Banason kaci gaba da gayamin wannan labarin qanzon kuregen......". Yankewa maganar tata tayi sakamakon shigowar kira wayarta.

BIBI ta gani,sai ta dauke dubanta daga kan wayar ta maida akan maina,sanann ta sake kallon wayar a karo na biyu kafin ta daga

"Okay" kawai ta fada a taqaice,sai ta sauke wayar sannan ta maidata gefe ta ajjiye

"Maina" ta kuma kiransa,ba tare da ya amsa ba yayi qas da kansa

"Duka duka shekarunka ashirin da hudu ko da biyar a duniya,karatu nakeso kayi,ka zama mutum kamar kowa,banaso ka harmutsa rayuwarka cikin matsalolin da ba naka bane,bakai bane tilashinsu,kabar masu matsala suji da matsalarsu,so nake kayi karatu,ka zama wani,domin kaine madubin qannenka,kuma kaine gobe na" Yadda tayi maganar kadai zai fahimtar dakai zallar qauna da soyayyar da zuciyarta ke gwada masa. Ya sani,ama tana masa wata soyayya ta daban,wadda tasha banban data qannensa ma,bai sani ba,shin ko soyayyar Wan fari daban take da a zukatan iyayensu?.

Wani qaunar ama ne ya sake saukar masa,tabbas duk abinda takeyi yasan tana yine saboda soyayya da qauna irin ta Wa da uwa,to amma shi Win ta yaya zaya zuba ido ya bari tarbiyyar sultana ta samu rauni?,yarinyar da tunda sanarwar haihuwarta ya shiga kunnuwansa yakeji a jikinsa kamar shine mahaifinta?,kamar rayuwarta da hain kula da ita ya hau kansa kacokam.

"In sha Allah zan kula iya bakin oari na,ba zaki sameni da wani abu da bakiso ba"

"kaje bibin tana kiranka" ta faWa da sautin da zai nuna maka akwai hushi danare cikin ranta.



*ZAFAFA BIYAR FAMILY*>>>>>

=% *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba*

*_ZAFAFA BIYAR_*d'
=%=%d'
=%=%d'
=%=%


d'
=% *_SABUWAR SHEKARA_*

d'
=% *_SABON TSARI_*

d'
=% *_SABBIN LABARAI_*


d'
=% *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_*

d'
=% *_CAKWAKIYA_*

d'
=% *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_*

d'
=% *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_*

d'
=% *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_*

*_KWANTAR DA ZUCIYA_*

*_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_*

*QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA*


*KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo)

*TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul)

*AMEENATU* (Mamuhghee)

*GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma)


*_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_*

*_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_*

*TSARIN SHINE KAMAR HAKA*


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*THANKS FOR CHOOSING US*>>>>





*_GUDUN KADDARA_* <<
@&

*HUGUMA*

PAGE 03

https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz



Har ya kusa fita ya dakata,ya waiwayo yana dubanta. Kallon jaridar kawai takeyi amma da alama bata iya ci gaba da karanta komai ba

"Don Allah ama almu ko atta,wani yayimin kiran najma ta dawo ta sake gyara dakin nan baiyi ba" fararen idanunta ta daga ta kalleshi dasu

"Ba d'iyar wadda zan kira ballantane ayimin gorin rashin diyoyi mata,ko wannan gyaran ma atta na saka yayi maka,suma a hakan zasu koya,tunda ko yanzun ma wasu abubuwan sukeyi min,banga abinda diya mace zatayi wanda zai gagari namiji yayishi ba" Dan qaramin miskilin murmushin nan nasa da yafi kama da motsa baki yayi. Abu guda daya tal da yasan ya jima yana ciwa ama tuwo a qwarya shine rashin haihuwar 'YA MACE,shi kuma ya jima da ciwa kansa wani alwashi game da hakan,alwashin da ita kanta bai sanar mata ba har yanzun

"Kiyi haquri zan saka a turota tazo ta gyara" kai tsaye ta sake dubansa

"Ka wuce ka tafi,kafin ka dawo zan shiga na gyara maka da kaina" kansa ya girgiza da sauri

"Karkiyi wahala,zan sake gyaran"

"Nidai iya abinda nace maka kenan" ta bashi amsa a taqaice tana maida kanta ga jaridarta.

Har ya isa sashen bibi zuciyarsa bata huta da tarin tunani da son gano laifin da nafeesa ta yiwa ama ba wanda har yake shafar SULTANA a wajenta,nafeesar da har tabar duniya bata da abokin fada,nafeesar da har ta gama rayuwarta badai kaji ance an kawo qararta ba,nafeesar da har tabar duniya ko musu bata iya ba bare sa'insa da wani. Laifin nafeesa daya ne LALURARTA indai har lalura da ciwo suna iya zama laifin dan adam......indai har suna iya zama kuskuren mutum da har Allah ya zabi ya dora masa ciwon,banda wannan shikam bazai iya adar da komai ba.

Kaf tunaninsa ya yanke lokacin da ya isa dakin sultana din,ya samu masu aikin gidan da su lamira sun cika dakin suna mata magiyar ta fito. Ransa ya baci lokacin da yaga bibi zaune a gefe,itama tayi magiyar tayi magiyar har ta gaji. Shigowarsa kadai ta sanya muryoyinsu daukewa,kowa ya shiga taitayi da nutsuwar sa. Shurun kuma shi ya isarwa da sultana cewa tabbas maina dinne ya shigo,shi daya ke da wannan fitinanniyar kwarjinin dake karya lagon kowa.

"Ni wallahi bazanji tsoronka ba" ta fada qasa qasa tana jan qwafa hadi da hararar qofar bandakin tamkar shine tsaye a wajen

"Duk ku fita" ya basu umarni yana takawa zuwa bakin bandakin.

"Anyi magiyar anyi lallashin amma taqi ta bude,tunda ta shiga take zaune a ciki,kamar wadda ta samu dakin gyatumarta" bibi ta fada hankalinta adan dage tana kallon maina da ya sanya wani dan scissors yana qoqarin warware lock din qofar. Kanzil bai ce da bibi ba. Sultanan na zaune daga ciki,amma tana iya jin kusur kusur dinsa jikin qofar. Sake hararar qofar tayi,don ta tabbatar bai isa yace zai bude qofar ba muddin idan ba itace tayi ra'ayi ta bude ba.

Kadawa hantar cikinta tayi sanda taga ya tura qofar ya bude,ya kammala warwareta tas kenan.

Tsam ta miqe daga saman toilet seat din tana kallon qwayoyin idanunsa data jima da sanyawa suna da LION EYES,ta fada ta sake fada,a duk sanda yake kallonka irin haka,idanun nasa basa mata kama da idon kowa sai idon zaki sanda yake kallonka cikin fusata,tun ranar da sukaje zoo tace wai ta tantance hakan. Tun su chafa'atu na mata dariya har suma sukayi amannar hakanne.

Yadda ya qureta da kallo ya zuba mata ido itama hakan tayi masa,abinda kaf rayuwarsa yafi tsana kenan,kayi laifi sannan ka tsare mutane da kallo kamar sa'anninka?. Duk wani yaro da ya girma ya taso a gidan yasan baya son wannan dabi'ar,sun kuma kiyaye,abinda ya zaunar dashi da su lafiya kenan

"Zo ki fita a gurin" ya fada mata a tsawace,tsawar da taji kamar zata tarwatse da kwanyarta,ta gigitatata har sai data kulle idanunta gaba daya hadi da qanqame jikinta guri daya. TSAWA na daya daga cikin abinda ta tsana,saboda muddin kayi mata ita ka gama birkitata kenan. Duk da kafiya taurin kai da zafin zuciyarta kuwa.

Idanunsa ya lumshe had'i da budesu,yadda tayi din ya tuna masa da naffeesa,abinda ya sassauta ranshi da zuciyarsa kenan,ya kuma sassauta muryarsa

"Fita nace tun kafin na sake kai hannuna kanki"

"Taho muje,ya isa hakanan" muryar bibi ta ratsa toilet din. Ita ta sanya hannu ta jawota ta fito da ita daga bedroom din,ya tako a hankali ya biyo bayansu yana sake karantar canjin halaye matuqa daga gareta. Musu,taurin kai,tsiwa,rashin kunya da rashin tsoro

"Saketa bibi,ta canza kayanta ta fito taci abinci,kuma wallahi kika wuce minti goma sai na zane miki jikinki,dukan da ban taba kwata yi miki shi ba" ya fada yana juyawa yana fita a dakin.

Da jiqaqqun idanunta ta bishi da harara tana jin kamar zata hadiye da zuciyarta

"Wai shi me nayi masa?,daga dawowarsa yabi ya takura mutane?,kuma ai da ba haka yake ba,salon muguntar da aikin sojin suka fara koya masa kenan?" Dafe goshinta bibi tayi,gaba daya sultana din ciwon kai takeson bata

"Ke bakiga kin canza ba,kin zama mara kunya,ana gaya miki kina musu?,idan akace ki bari ba zaki bari ba,to na godewa Allah da dawowar tasa,shi kadai ne maganinki ai" wani baqinciki ya mamayi zuciyar sultanan,kamar ita za'a ce wai wani zaiyi maganinta?.

"Ki gaya masa ya fita a hanya ta to,ai zama yaya da qanwar ba dole bane,kuma bai isa yayi maganina ba Allah,saidai muyi maganin juna" ta fadi tana soma zare kayan jikinta. Zata shirya taje din bawai don tana tsoronsa ba,saidai don kawai bata qaunar duka,bata qaunar abinda zai taba lafiyarta sam,daga lokacin daka saka hannu a jikinta to ta daura da kai kenan,ba ita babu komai,saidai kuma ka shiga uku a gurinta.

Bibi tana tsaye har ta gama shiryawa abinta,riga da wando ta sanya,skinny jeans mara nauyi,sai shirt dinsa me gajeran hannu,sako sako lallausar sumarta da tsahonta ke sanyawa saidai ta lanqwasa ta sau biyu tayi,don ribbon din dake kantan saboda bala'in da takeji bata ko tsaya gyarashi ba.

Light blue ne kayan,sun yi masifar yi mata kyau,sun haska jar fatarta qwarai,idan ka kalleta zaka dauka ta fito ne daga yankin india ko qasashen larabawa. Tun asali kyan sultana na dabanne,wanda akayi ittifaqin ita daya ce tal ta dauko ainihin kamannin LAILA babar kakanninsu. Har yanzu daidaikun tsofaffi da manyan dake cikin unguwarsu dake tushen jaharsu ta AGADEZ basu manta da LAILA ba,tarihinta bai goge ba,macen data zuba kyau daya banbanta da kyawun kowacce 'ya mace da tayi rayuwa arni guda da ita.

A saman kujerun dining din suke zaune,biyu cikin masu aikin gidan na kaikawon shirya abincin daren a samansa. Ysatsunsa cikin na juna,idanunsa zube fes akan fuskar bibin. Cikin nutsuwar da tun yana mitsitsinsa ta zame masa dabi'a kuma halayyarsa yake magana

"Amma why bibi?,me yasa za'a bari halaye da dabi'unta su canza?,ya akayi sultana ta canza?,ba haka na tafi na bar muku ita ba" ya fada har tsakiyar ransa yana jin radadin rushewar tubalin ginin tarbiyyar da ya fara yi mata,wadda tasha banban data qasarsu.

"Duk wani iya bakin qoqari inayinsa mainassara,to amma kasan komai yana da alaqa da muhalli da kuma abokan mu'amala na yau da gobe" kansa ya girgiza yana furzar da iska me zafi daga bakinsa

"Bibi,goumar ya fara fadamin,mais(but) na dauka kawai surutu ne irin nashi,certainement(definitely)banji dadin abinda idanuna suka tarar ba". Ajiyar zuciya bibi ta saki,itadai ta sani,babu ta inda tayi sake ko saakcin tarbiyyar,tun daga kan uwayensu ma ballantana su,kwadayi da son samun cikakkiyar tarbiyya ya sanya ta yiwa hamidou magana,suka tattara suka bar niamey izuwa maradi,maradinbda take kallo da hangen sunfi kusa,alaqa ta qut da qut da nigeria. A nutse take masa bayanin iya abinda zai iya fahimta. Kansa a duqe yana latsa wayarsa tare da sarrafa maganganun bibi cikin kansa,yana kuma son lanqwashe bakin matsalar da kuma yadda zai bullo mata. Nunfashi ya zuqa yana daga qawatattun idanunsa wadanda suke da wani irin shape,idanun da sultana din ta sakawa suna da yeux de lion(lion eyes) ya zubesu kan tafkekiyar TV plasma din dake maqale a bango,suna haska labaran dare a channel din niger 24tv. K'aramar yarinya ce da bayanta ya mamaye fuskan tv din,tana bayanin yadda wani matashi yayi mata fyade(rape). Kasuwa hankalinsa yayi gida biyu,fiye da rabin hankalinsa yana kan labaran,yayin da wani kaso dan kadan kunnuwansa ke ga bibi.

A hankali wani abu ya soma tsaya masa a rai,bacin rai ya fara sauka a hankali saman zuciyarsa yana mamayeta. Maqurar bacin ran da hatta bibi dake zaune a wajen sai data fahimci hakan.

Wani dogon tsaki mai matuqar sauti ya fidda,dai dai sanda tani shugabar masu kula da sassan bibi ta kawo tray na qarshe ta ajjiye

"Miqo min tlcommande(remote)" cikin girmamawa ta rusuna ta juya ta isa ma'ajiyarsa ta dauko ta miqa masa.

Channel ya canza gaba daya,zuciyarsa na wani irin quna da zafi,babu abinda yafi tsana a duniya a yanzu irin kalmar FYAE. A duk lokacin da aka haska wani mutum dauke da laifin fyaWe,yakanji inama za'a bashi damar hukuntashi,tabbas idan har ace zaya samu irin wannan damar,zaiyi masa hukunci ne mafi tsanani,wanda ko mace akace masa gata zai yanka da gudu ne ya gusa daga wajen,sakamakon azabar da shi daya yasan yadda take da zai WanWana a hannunsa. Harshensa har Waci yakeyi sanda ya buWe baki yana magana da bibi

"majorit ire iren wadan nan abubuwan akwai sakacinmu dake haifar dasu"

"warai kuwa,wasu abubuwan kuma addarar bawa ce daga sarkin mabuwayi" gama maganar bibi yayi dai dai da fitowar sultana. Da ido bibi ta bita tana kallon yadda fuskarta tayi jazur,sai kawai ta miqe a hankali tana sauka daga gurin dining din,abinda ya sanya sultana tsaiwa cak tana kallon bibi din,don ita ba zata yarda ta barsu a wajen daga ita saishi ba,ya sake taba lafiyarta ba gaira ba dalili

"Ina kuma zaki tafi bibi?" Ta tambayeta tana karya wuya,hawaye nason taruwa cikin idanunta

"Qaraso ki zauna" maina da idanunsa yake kanta ya fadi,fuskarsa a matuqar hade,abinda zai alamta maka babu wasa ko misqala zarratin a tattare da shi. Duban cikin idanunsa tayi,niyyarta tace ba zata zauna din ba,to amma kuma sai kalmar ta maqale mata saman harshenta. Kamar ba zata qaraso din ba,amma yadda kaifaffun idanunsa suka ritsata ya sanya ta sauya akalarta zuwa inda yake mata umarnin,zuciyarta kamar zata fashe,duk wani qaunar da take masa taji ta fara raguwa sosai cikin ranta,sai wani haushinsa da takeji. Tana matuqar qaunar lafiyarta,hakanan bata qaunar duk abinda zai taba mata lafiyar. Karo na uku kenan ana sauya mata makaranta saboda attempting din dukanta da aka taba yi sau daya a kowacce makaranta.

Tsaki yaja dai dai sanda ta zauna saman kujerar,ta dafe hannunta tana saman kujerar tana gyara zamanta sosai saboda qafafunta ba zasu kai qasa ba,duk da tana cikin sahun yara masu tsaho. Tsakinsa ya sake qular da ita tare da bata haushi sosai,sai ta juyar da kanta gefe tana murguda bakinta tare da sakin qananun surutai qasa qasa.

"Duba nan" ya fada yana tattara dubansa a kanta. Tilas tabar kallon hagunta ta dawo da kallonta zuwa gareshi

"Wannan kayan.......ban hanaku sakasu ba?,kun dauka a french muke?" Ya tambayeta a kausashe,har cikin ransa yana jin haushi da takaici. Zuwa lokacin alamomin girma sun fara bayyana a jikinta,tana da girman jiki wanda yake da saurin bayyanar da girman d'iya mace,hakan kuma yasan yana da alaqa da rayuwar jin dadi da tsantsar kula da jikinta ke samu na dukkan wani abu da zai inganta lafiyar jiki data fata ya kuma tabbatar da girma na dan adam a lokaci qanqani. Ya sani kusan da madara aka raineta,har ya tafi akan shan madara ya barta,duk da bashi da tabbacin har yanzu tana sha?,yana ji a jikinsa ma lokaci yayi da zata ajjiye duk wasu dabi'u na quruciya,ta fuskanci girma wanda yake dab da iso mata.

"Last zuwan ama Nigeria na qarshe ta kawowa kowaccenku wadatattun atamfofi da zata dinka,sannan dukkaninku kuna da abaya wadatacciya,wannan shine gargadi na farko kuma na qarshe,kada na sake ganinki da irin wadan nan kayan a jikinki" ya fada yana kallon idanuwanta.



*ZAFAFA BIYAR FAMILY*>>>>>

=% *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba*

*_ZAFAFA BIYAR_*d'
=%=%d'
=%=%d'
=%=%


d'
=% *_SABUWAR SHEKARA_*

d'
=% *_SABON TSARI_*

d'
=% *_SABBIN LABARAI_*


d'
=% *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_*

d'
=% *_CAKWAKIYA_*

d'
=% *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_*

d'
=% *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_*

d'
=% *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_*

*_KWANTAR DA ZUCIYA_*

*_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_*

*QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA*


*KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo)

*TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul)

*AMEENATU* (Mamuhghee)

*GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma)


*_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_*

*_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_*

*TSARIN SHINE KAMAR HAKA*


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*THANKS FOR CHOOSING US*

>>>>
*_GUDUN KADDARA_*


*HUGUMA*

Page 04


https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr


Haushi kamar zai kasheta,wai shikam yaa maina yana kallonta ne har yanzu a little sultana da ya bari shekara hudu baya?,itafa ba zata dauki ire iren wadan nan abubuwan ba bayan tana kallon yadda sauran qawayenta na makaranta ke rayuwarsu cikin 'yanci. Kaf cikinsu ma bataga me saka wata aba wai atamfa ba,meye hadinsu ma da ita?,sai ita zai bullowa da sabon tsarin doka?.

"Ni ban iya daura zane ba" ta amsa masa tana turo baki manyan fararen idanunta na kallon shinfidadden gilashin dining din,ji takeyi kaman ta mangareshi,har yanzu tana jin radadin marinsa akan fuskarta.

'Dan dukan table din yayi da tafin hannunsa

"regarder(look),ki iya ko baki iya ba duka zaki koya ne,muddin kinaso kiga ainihin mainassara kici gaba da yimin musu da kuma dan banzan kafiya da taurin kan da kika koyo"

"Kai kuma shegiyar masifa da bala'i da baqinciki da bacin rai kamar tsohon kuturu" ta fada cikin ranta. Baiji abinda tace ba,amma yaga sanda jajayen lips dinta suke motsawa

"Me kika ce?" Ya jefa mata tambayar data kusa sakata fadowa daga kan kujerar da take zaune akai din. Da sauri ta daga fararen idanunta ta kalleshi dasu tana motsa baki

'"ni?,ni bance komai ba" idanunsa ya lumshe kadan ya budesu. Ya tabbatar tayi magana,akwai abinda tace,amma cikin sabon halin da ya fuskanci ta sake kota koya harda iya fadin qarya kanta tsaye. Bayajin zaiyi wuya ya sake tafiya niamy haka ya zauna,gwara duk sati ya dinga tahowa maradi yana hutun qarshen makonsa a nan.

"Dauki abinci kici" ya fada yana nuna mata tsadaddun warmers din dake jere saman dining din

"Mari!,mari!!" Ta fara qwala kiran sunan kamar zata saki kuka. Da kallo ya bita yadda ta narke kamar me ciwo tana kiran sunan mai aiki,tana nufin ita zata zuba mata kenan,zubawar ma bata iyawa?.

"Ya isa haka karki kashemin dodon kunne" ya fada yana wurga mata wata iriyar harara wadda bata taba ganin ya mata irinta ba. Da kallo ta bishi ranta yana baci,sai taji idanunta na marmarin juyewa itama ta mayar masa da hararar da yayi mata din,to amma yana kallonta ta dauke kanta gefe,zuciyarta tana sakeyin zafi,haushinsa na sake cikata

"Nidai wallah ba zai takuramin ba,mutum ba ubanka ba ba komi ba" ta fada qasan ranta.

Plate din ya tura mata maimakon ya jawoshi gabansa ya dinga bata a baki har sai tace ta qoshi kamar yadda ya sabar mata a shekarun baya. Cikin ransa da zuciyarsa yakejin dole ya janye ya kuma rage dukkan wata kulawa da damuwa da yake nuna mata,domin ya fahimci aiki ne jajur a gabansa wajen maido sultana din kan hanya. Don girma ta fara girma,jikinta ma ya nuna hakan,a wannan gabar idan bai tsaya mata sa zafi zafinsa ba a haka zataci gaba da girma a sangarce,bayan kuma gidan wani za'a kaita,ya yiwa nafissa adalci idan hakan ta faru?.

"Oya bismillah" ya fada yana sake turbune fuska,idanunsa akan wayarsa dake ringing. Zai daga ta katse,sai kuma sautin sallama daga can bakin qofa.

Matashin saurayine wanda shekarunsa ba zasu haura sha biyar ba,dogo ne fari,kansa dauke da nannadaddiyar sumar nan ta abzinawa. A fusge yake kama da maina,saidai kuma idan ka kalleshi da kyau zaka fahimci akwai banbacin kamannin.

"Ya maina,ama tana kira" ya fada idanunsa akan fuskar sultana wadda ke kallon abincin gabanta kamar taga wani abun tsoro,fuskar nan a dagule da bacin rai

"D'accord,allons-y(alright, let's go)" miqewa yayi yana gyara shirt dinsa data tattare yana kuma sauke hannun rigarsa da yayi rolling up zuwa gwiwar hannunsa

"Kada na dawo na samu komai a ciki" ya qarashe maganar yana sauke mata kallonsa sai kuma ya dauke kai yana sauka daga dining area din ya nufi qofa.

Da idanu yaron ya bishi,kamar shima jiran fitarsa yakeyi ya dawo da dubansa kan sultana,ya saki dariya yana tattakowa da hanzari zuwa wajenta. Kafin ya iso ta miqe tsaye ma tana shirin barin wajen ba tare da ta sakawa abincin koda yatsarta ba


"Albishirinki,examens lundi(exams monday)" ya fadi yana dariya saboda sanayyar da yayi mata da tsantsar gabar da takewa makaranta.

Harara ta watsa masa kamar zata fiddo fararen idanunta waje

"Kada ka sakemin maganar examens,bazanyi ba,bazanje cole(school)din ba munafuki" ta qarasa fada tana murguda masa baki. Dariya ya sheqe da ita sosai,SADDI mutumin sultana ne qwarai,saidai kuma zaman nasu ayi fada ayi dadi. Yasan duk abinda takeso shi yasa suke shiri,hakanan yana da tarin tsokana da calikanci wanda shike hadasu fada da sultana,saboda ita ba kasafai takeson tsokana ba,saidai akwai dan banzan surutu kamar yadda saddi yake da shi,shi yasa tasu tazo daya da ita sosai.

Waqe ya fara yi mata na gobe ranar makaranta ce cikin harshen farasanci,bata waiwayo ta dubeshi ba bare ta kulashi,saboda bacin ran maina kawai yau ya isheta takaici.

Dakinta ta shige ta kulle abinta tayi kwanciyarta,ko madararta data zame mata qa'idar sha duk dare bata nema ba a yau,don batason ma yazo ya isketa ya sake shiga rayuwarta ya bata ranta.

Tana jin tanja me kula da ita ta musamman da aka ware mata na buga qofa tayi banza da ita. A qalla ta kusa minti talatin tana bugu akan ta bude mata zata shigo ta shirya mata uniform da sauran tarkacen kayan tafiyarta makaranta kamar yadda ta saba duk ranar Sunday war haka amma tayi kunnen uwar shegu da ita har ta gaji tace

"Idan ma bakison zuwa makarantar ne to ki tashi ga lit(madara)dinki,ki kuma yi wanka ki canza kayan kwanciya" hararar qofar tayi ta sake juyawa abinta tana riqe game dinta da kyau tare da sake shiga next level na game din.

Game ce da tayi mugun shiga rayuwarta,muddin kanason ganin nutsuwarta da walwalarta to idan tana yin game dinne,tana bata lokaci da nutsuwarta irin wadda karatunta bai samu koda rabin rabinta ba. Ganin da gaske ba zata bude ko ta magantu ba ya sanya tanja ta haqura. A hanya sukaci karo da bibi

"Ta kwamta ne mutunniyar?" Bibi dake fitowa a kitchen ita da ammara ta fadi tana duban tanja

"Wallahi bibi ta qiya ta bude koda qofar ma,ni zato ma nakeyi fa tayi bacci,da maina zan kira ko zata bude idan ta jishi"

"A'ah,barshi tanja,dama yau sun hau sama sun fado da ita" ido tanja ta zaro,ba ita bama hatta da ammara sai data zare idon itama,kowanne mamaki yana ratsashi.

"Dama akwai ranar da yaa maina zai sab'a da sultana?" Ammara ta riga tanja tambayar bibi. Kai bibi ta kada tana yin gaba,ita kanta ta jinjina al'amarin,koda fada bata zaci maina zai iya daukewa a yiwa sultana a gabansa ba,sai gashi har shine da sanya yatsunsa guda biyar saman fuskarta,abinda ba'a taba yiwa sultana din ba.



Please Login or Register in order to submit comment