Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da nan mama ta dunke fuska
kusa da Alhj ta zauna nima na zauna kasa gefen
mama,sai baba yace uwata zo nan kusa dani mana ,na
dubi mama sai naga bata kalleni ba dan haka sai na nufi
babana kasa na zauna ya jawo ni kaina ya dora kan
gwiwowinshi naji wani irin muguwar soyayya irin ta da da
mahaifi na ratsani kawu malam ne ya soma magana
Habiba ga uban Amina ya zo bada hakuri akan irin
kuskuren da ya aikata a can baya,mama tace ai bai min
komai ba,babana yayi karfin hali yace haba Habiba nasan
nayi maki kuskure dan Allah ki yafe ni nasan baki da
ruko habiba,mama tace ai ni Idris dan ka sakeni ba laifi
kayi ba tunda halas ne sannan Allah ya bani wani mijin
wanda yafi ka komai nima sakamakon hakurina kenan,na
dubi mama banji dadin maganar data fada ba babana
akafi?na kuma gyara kwanciyata a jikin shi ni ina sonshi
nace a raina,kawu malam yace yanzu dai yace ki yafe
mashi babna yace yauwa nidai kimin aikin gafara mama
tayi shiru sauran mutanen sukayi tasa baki mama tace
meyasa sanda ya zalunceni ba wanda ya bada baki sai
yanzu da ya milla da kanshi zaizo ya wani ce wai na
yafe mishi,kai Idris kai ne mutumin da banyi tunanin yi
maka afuwa ba,ta soma hawaye kai ne ka aure ni tun
baka da komai kai ne ka fara sanina ya mace kai na fara
haifa ma 'ya amma daga karshe ka ce na tafi da yata kai
kafi son 'ya'ya maza daga tsatson fati ka manta?dan
haka ynxu ma sai kaje gurinta
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347








Tawa Tasameni 2-02
Posted by ANaM Dorayi on 08:27 PM, 03-Jan-16
Under: TAWA TASAMENI
__________NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI________
Tunda muke da kai ko ince tunda muka rabu da kai ka
taba kawo daidai da pant aba Iman,Alhj yace kiyi hakuri
Habiba ya wuce kice kin yafe masa,mama tana kuka
Alhj da sauran mutane ma suna bata hakuri kawu
malam ya soma mata fada to tunda duk nan ba mu isa
ba shi kenan karki yafe ko Allah ana mishi laifi yana
kuma yafewa bare ke,ganin ran kawu ya soma baci sai
tace shi kenan ya wuce ya shiga godiya yace Alhj
Mukhtar kaima na gode da irin rikon da kaima uwata
Allah ya saka da alheri ya dubeni uwata ynxu wacce
makaranta aka gama?ko shirin aure akeyi?na boye
fuskata a gwiwarshi,Alhj yace sun kammala sec bara to
paper din tata batayi kyau bane shine zata gyara
sannan asan abinyi, babana yace to batun miji fa? Alhj
ya ce eh akwai wani Adamu abokin Abdulrahim tare
suke sana'ar tasu can a England shi nake zaton take
so,amma sai mun gama bincike mutumin Ghana ne ina
da abokin kasuwanci a can binciken ba zai bamu
wahala ba tunda Abdulrahim yace min game da halayen
Adamu babu matsala karatun ma yace a can zatayi shi
ne nace ya nemi iso gurinta,babana ya dubeni uwata
kina sonshi?na kada kai alamar eh sannan na boye
fuska ina kuka dan na san ba shi nake so ba,babana
yace Alhj kaga wani sakarci?wai kuma kuka take
yi,mama dama tuni ta tafi nima na tashi zan tafi
babana yace uwata wai yaushe zaki zo mana kwana
biyu ne?na ce sai na tamabayi mama Alhj yace ko
zuwa jibi ne ai na kawota dan Habiba sai da lallashi
yanzu, babana yace ba komai kasan fushin irin na mai
hakuri bai iya ba har na fita babana ni yake kallo
bakinshi yaki rufuwa.
Goman dare ina kwance kan gadon na murna duk ta
cika ni don munyi settling da babana wayata ta soma
ruri na duba Adams ne na danyi tsaki sannan na dauka
yace yar gidana ya garin?nace yana hannunku yan
England to haka ne ni dai na kira ne inji batunmu na
runtse ido raina a jagule nace Adam na yarda zan
aureka da karfi yace da gaske kikeyi?nace kwarae
kuwa,ashe kina sona Maska yace min ba kya sona karo
na farko kenan da Maska yayi min karya,na numfasa
sannan nace zancen so ai ya kare ko ina sonka ko
bana sonka tun da dai nace zan aureka ai shi kenan
sannan kayi hakuri Adams ina son barci ne shima sai
naji muryarshi tayi sanyi ya bar murnar yace to sai da
safe na kiraki kinji?to na gode na tsaya ya kashe wayar
sannan na ajiye,daren nayi kuka sosai ba kukan komai
nayi ba sai na rasa abin sona shi kenan Adams ne
rabona zan auri Adams dan in nuna ma yaynmu cewa
tunanin shi ba gasky bane tunda baya sona ne da dai
yana sona ne da sai na tabbatar mishi da cewa nima
ina sonshi.Washe gari ina zaune akan kujera karama a
nan kkfar dakinmu sauran mutanen gida kowa yana yan
harkokinsa safa da pant dinsu jamila nake wankewa
Sa'a da Bilki suna lido a kofar dakin su mami haj shuwa
ce da girki dan haka tana ta kaiwa da komawa,lami mai
aiki kuma tana wanke wanke anty mimi ta shigo tayi
sallama ban san mai yasa ba duk sanda zanga anty
mimi sai gabana ya fadi ita kuma a nata bangaren haka
ne abin yake muna hada ido sai ta daure fuska gami da
jan tsaki sannan ta kauda kai,su Bilki da Sa'a suka rugo
suka rungumeta suna mata sannu da zuwa ta durkusa
tana gaida haj shuwa sai ga yaynmu shima yayi
sallama daidai sanda na gama shanya pant din ina
wanke nawa pantys din,tun shigowarshi idonshi na
kaina ni kuma duk da son ganinshi da nakeyi sai naki
dubanshi dan ga matarshi kusa da inda nake zaune ya
tsaya suna gaisawa da haj shuwa anty mimi kuma ta
shiga dakin su mami dan gaida haj kulu,ba kya
gaisuwa?ban dubeshi ba nace ina yini?yace ba zan
amsa ba tun da ko kallo ban isheki ba bai san duk
haushin su nake ji ba shi da matar shi ba,menene
wannan kike wankewa a gaban mutane?sai naji kunya
duk ta kamani,anty mimi ta fito daga dakknsu mami
zata wuce sai yaynmu yace mimi baki gaida maman
sagir ba ranta bai so ba haka ta shiga dakinmu data
fito yace ta gaida ni na kwanta asibiti tayi jim can tace
ya jiki?tayi gaba nima sai nace da sauki shima ya shiga
ya gaida mama ya fito lokacin su bilki sunbi anty mimi
dakin haj yaya sai haj shuwa a kicin ya dan duka saitin
kunnena baa wanke irin wadannan abin a waje sai
atoilet kin ji ko?ya wuce na bishi da kallon mamaki na
rasa mai yasa yanzu duk ya canza min baya jin nauyin
yi min wasu maganganun daidai zai shiga dakin
hajyarshi sai ya juyo muna hada ido sai ya kashe min
ido daya ya shige dakin na kasa ci gabada wankin dan
duk ya saukar min da kasala kamshinshi kawai nake
shaka raina yayi fari tas na tattara na koma toilet dana
gama kan gadona na haye na dau wayata na kunna dan
kasheta nayi saboda ban san Adams na kirana duk sai
inji na tsaneshi,text ya shigo min na bude sai naga
show message i love you forever na duba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Yauma kamar kullum zai kai kusan sati biyu kullum sai
an min wannan short msg na rasa waye?amma ina
ganin Adams ne sai ya wani boye no naja tsaki ya
karata nidai ba zan nuna mishi nasan yana yi ba ina yan
fadace fadace na sai call ya shigo na duba sai naga
yaynmu ne da sauri na dauka hello ki samenj dakin
Kabir,hijabi na saka na fito falo mama yaynmu na
kirana zai aikeni,to tace min
Na fita zaune kan kujera na sameshi da remote a hannu
gani na fada ina fubanshi sai naga ya daure fuska dan
haka sai nima na shiga taitayina cikin dakewa da
miskilanci na shi yace zauna,na zauna ya dubeni da
farko ina maki murnar daidaitawa da mahaifinki da
fatan ki zama mai mishi biyayya ya cigaba da cewa naji
batun Adam's da kuma na gyara papers dinki kin zabga
karya kince kina son shi ya harareni ya harareni
makaryaciyar banza innaso in miki gata ki samu krt ko
da Degree ne ynxu kuma baki son krt ko?nayi shiru ya
daka min tsawa bakya jina?bakina na rawa na ce ina
son krt mana yace karya ne da kina son krt da kin
tsaya kan ra'ayina na sonki yi krt amma sai kika ki kika
dauki son aurr kika dora a ranki to muddin kikayi aure
ba wani krt da zakiyi lokacin kiyi kuka da kanki ba da ni
ba,na dube shi ai Adam's yace zan ci gaba da krtna ya
harareni wannan ra'ayin shi ne ina sonki san cewa ba
dole bane Adams ya zama mijinki,don ba shi zuciyarki
take so ba,haushi ya kamani nace ina sonshi yayanmu
ya fusata zan mareki fa,karya na maki kenan?gara ma
ki fito ki fadi wa wanda kike so ko zai taimaka miki da
sauri na dubeshi yace shiii yi min shiru kin san siyasa
na karanta ko?ya cigaba in ina son bararda Adams a
wajen su a
Alhj a guna abu mai sauki ne sai dai ba halina bane
yanzu zan fada miki sirrin zuciyarki,kin kamu da ciwon
son wanda kike so tun shekarun baya sai dai baki da
tabbacin ko yana sonki dalilin shi ne kika kamu da
ciwon zuciya dan kin kasa neman shawara ko mafita
kar ki min musu kuma kar kiyi mamaki mutane da
dama suna zaton na karanci halayyar dan Adam ne
saboda yanda Allah yayi min baiwar saurin fahimtar
mutane kin yarda ko har yanzu kina nan kina nan kan
cewa ba haka bane?wata zuciyar tace min ki fada mishi
gsky wata kuma tace kar ki bada kai,sai nace ni fa ba
wanda na taba so ni Adams kawai nake so,ya zuba min
ido ranshi in yayi dubu ya bace shi in ban dama yana
ganin zubar da girma ne yace yana son yarinyar nan da
dai ta yarda da abinda yace to sai ya nuna mata cewa
zai taimaka ya aureta dan dai shi ba zai taba cewa
yana sonta ba ta raina shi,to ita kuma ga shegen taurin
kai ynxu yaya zaiyi kenan?kai shi ai daya san inda ake
ajiye so da ya cire inda nata yake ya yar ya huta ya
mike tsaye yana dubana sannan yace na zone nayi
sallama dake don gobe kamar yanzu muna hanya duk
yanda kika ga dama kiyi sai dai zan fada miki wani abu
komai ya biyo baya kiyi kuka da kanki zan maimaita
miki kiyi kuka da kanki yace kina iya tashi ki tafi
sannan in kina bukatar taimako ko na menene kina iya
nemana ta waya jikina babu karfi na mike a raina na
raya bari na mishi kallon karshe dan haka sai na dube
ahi shima ni yake kallo na juya daidai kofar fita na
kuma juyowa na dubeshi sannan na fita,gidansu Amira
na nufa tana kwance tama aikin karanta littafi kanta na
dafaa ina kuka tayi jifa da littafin hannunta ta juyo lfy
Iman?me ya faru?cikin kuka nace shi kenan mun rabu
tace dawa?nace da yayanmu,sannu kan hankali na
zayyane mata komai ta ce kash! Kinyi wauta dakin sani
kince mishi kina sonshi menene?ba zan iya ba Amira
tunda shifa ba sona ya keyi ba cewa fa yayi wanda
nake son zai taimaka min gara na hakura sam ya ma ki
nuna cewa shi nake so da kyar Amira ta lallasheni
sannan na dawo gida.
Kwana biyu duk na rame na fita hayyacina saukin tama
naje gidan Babana kamar yanda Alhj yayi alkawari gata
dai na duniya ba irin wanda ban gani ba har kasuwa
yaje dani can naga yaya Abubkr da yaya Ibrahim don
ynxu sun kyaleni,kyauta dai na sameta gurin abokan
babana yace yaya Ibrahim ya dawo dani gida ya maida
ni Anty Fati sai huci take yi niko ko kallonta banyi ba
Anty Maijidda itace matar da babana ya sake aura
itama yar cikin kano ce shekara biyu kenan da
auran,itama dai shiru ba haihuwa tana da kirki sosai
kuma ta nuna tana sona har kitso tayi min dan haka sai
nake gurinta,da babana ya dawo kuma sai na koma
gurin shi tare muke cin abinci muyi hira ya kan
tambaye ni me nafi so ko kuma me na ke so ya sai
min?na dinga mishi lissafi ranar da zan dawo sai da
muka shiga kasuwa dashi siyayya har ta banza kuma
daga kan sutura kayan shafe shafe turarurruka da
takalma su Jamila da Sagir kai har su Mami sai da nayi
musu tasu tsarabar,Mama da Alhj turare na sai musu
sai kace daga wani gari na dawo da ya kawo ni gida
kamar kar mu rabu nace zan kuma zuwa ai ya kara
bani wata wayar yace shi kadai zai dinga kirana ya
samin layin glo ya zuba min no dinshi da ta tsohuwa
kakata yace na kira nace zai kawo ni na kwana biyu
nace babana na tafi ka gaida Anty Maijidda ta bani
tirare tace na ba Mama yace shine baki fadamin ba?
nace ita tace kar na fada maka yace to zan mata
godiya ki ce ina gaida Habiba har na kai bakin kofa sai
yace kin manta da tsarabarki nace lah na mance na
dawo ya kwaso min, duk wani motsina idonshi yana
kaina kai Babana na sona matukar so..
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Kwanaki suna shudewa,Lokaci na kara wucewa mun
gama Diploma a Comp, sannan munyi jarabawa sai dai
jiran abin da zai biyo baya Adams yana kirana a waya
duk da bani sonshi a raina ina dan sauraranshi yaynmu
kam bai taba kirana ba sonshi dai yana nan makale a
raina ,Alhj da Babana sunyi bincike akan Adams ashe
ma mahaifin shi abokin Alhaji Adamu garko ne me
gidan Babana dan haka basu sha wata wahala ba wurin
bincike sun shirya magana tasu ta manya sannan sunce
sai sunji ta bakin Adams sun kira shi sun mishi bayani
yayi murna sannan sun bukaci ya fadi daidai lokacin da
yake son a sa bikin yace su bashi kwana biyu zai sanar
dasu, a son Alhj ayi bikinmu rana daya dasu Mami da
Sa'a da Bilki,to amma da kyar hakan zata samu.
Yau laraba zaune nake gonar kawu kabiru kanin mama
a kauye gefena Jimmala ce kanwar yaya Ibrahim tunda
naje kauye kullum sai naje gona kota dangin mama ko
ta dangin babana,daga inda nake ina hangen kawuna
yana bawa masara ruwa wayata ta soma ringn Adams
ne na sani dan haka sai na dauka gami da sallama yar
gidana na jima ina nemanki ban same ki ba?nace
matsalar ntwk ne yace to ya gari?nace gari na
hannunku mutanen England yayi dariya,to yaya?na me?
na zancen mu mana kinsan yau ne na yanke musu zan
sanar dasu date din daya kamata a sa fa,na dan
yatsina baki nace kai yaushe kake so,nafi so asa watan
goma kin ga yanzu muna watan hudu nan da wata
shida kenan ko?nace to hakan ma yayi daidai, su Mami
zasu rigamu dan su saura wata biyu yace insha Allah
dani za'ayi bikinsu Mami,Amira fa?nace ita sai tayi
HND tukunna yace Ok! to duk yanda sukayi zan kiraki
nace kai yaushe zaka zo yace sai bikin su mami zamu
zo tare da yaynku ne,gabana ya fadi sam bana son
tuna shi dan yaynmu shi kadai nake so so mai tsanani
rabona da ganin shi tun bankwanan nan da mukayi
yace kina jina?nace ina jinka Adams wai dan Allah kuna
shiri da yaynmu?yace sosai ma dashine muka sa date
din bikinmu gabana ya fadi nace haba yace Allah gaske
ne fa nace suna lfy yace kalau shine ma ya tsaida date
don nace nan da four month yace gara six din,nace
Allah ya kaimu yace amin...
Adams kan abin motsa jiki yaynmu ne ya hada zufa
tamkar mai tukin mota yanata faman yi can ya dubi
agogon dake manne jikin bangon dakin karfe takwas na
safe ya jawo tawul ya soma share gumin da ke zubo
mishi sannan yasa baki ya kira Mimi,Mimi ta shigo da
sauri gani ya dubeta ina shayin wai yaushe ne zaki koyi
yanda ake kula da miji ne?kin san kawo shayin nan
aikin ki ne daidai wannan lokacin amma kullum sai
nace ki kawo?to za kije ki kawo din koko?kin tsaya min
akai,ta juya shi kuma ya ja tsaki sannan ya sauka daga
kan abin motsa jikin ya hau kan wata kujera a gefe ya
zauna yaci gaba da share zufar,ta shigo rike da kofin
tangaran babba da karami,ta ja wani dan tebur ta tura
mishi ta juya ba tare da magana ba ya bita da kallo
sannan ya girgiza kai sam Mimi bata dace dashi ba ta
kowanne fanni sannan yana son a inganta mishi ciki
dan kowa ya san yan kwallo da cin abinci,ya kurbi
ruwan na lipton mai hade da wasu ganyayyaki can sam
sai yaji komai ya ishe shi ya kwana biyu kenan baya
cin wani abin kirki tunda Adams yazo mishi da zancen
sa ranar shi da Iman ya kuma nemi shawarar sa ya
bashi shawara ya bari sai nan da watan goma ne dan
yana son ya nemi mafita sam ba zai bari adams ya auri
yarinyar da yake masifar so ba,so mai tsanani sannan
yasan tana sonshi taurin kaine yasa taki fadi to shima
yayi alkawarin sai ya aureta muddin yana numfashi a
doron kasa,yayi lissafi Mimi tana da ciki wata biyu zata
haihu watan sha daya yana son sai mimi ta haihu
sannan ayi bikin nashi ,amma ba zai yiwu ba,ya danyi
shiru na wani dan lokaci sannan yace na san abinyi ya
mike tsaye ya fita bayi ya shiga a cikin dakin shi ya
hada ruwa yayi wanka a gagauce ya shirya cikin JC
blue da ratsin fari ya daura takalmi mimi ta shigo kana
da bako,ya dubeta wanene?ta dan tsina baki ko Adams
yake ne oho?haushi ya kama shi me yasa yarinyar nan
batada kunya ne yanxu?amma zaiyi maganainta yace
fita anan banza kawai ni zaki cewa baki san Adams ba?
ta fita tana yin kuna kunai na gaji da wulakancinka
komai kace sai an maka ni ko gsky ko a gidanmu ban
kauda tsinke bare wani girki ina dan wanda zan iya kai
kuma kana ganin kasa wata yana jiyota sai dai bai san
me take fada ba yace zaki gane kuskurenki.Ya sami
Adams zaune shima da shiga irin ta Maska Adams ya
dubeahi kace ka shirya Maska ya zauna sai dai ban
karya ba,haba baka karya ba kai da kake da iyali
ma,Maska yace kasan bata da lfy gata dama da son jiki
sam bata son aiki Adams yace sai hakuri nidai Allah
yasa nayi dace in har ka dace ka sameta din to Adams
kar kayi shakka zaka sami yanda kake so,Adams ya ce
ya kake cewa in har na sameta?kana ma shakka
kenan?kar ka manta fa har na biya sadaki an sa mana
rana kuma kaine ma ka tsaida min har na sanar da
manya,Maska yayi wani murmushi Adams ya kalleshi
Maska bana son wannan murmushin naka fa tuni na sa
mashi suna murmushin mugunta dan ko a fili muke
gurin wasa abokan wasa suka sako mu a gaba kana
irin wannan murmushin sai kaga Allah ya bamu
nasara,Maska yace tashi mu tafi a can zan yi break
kafin mu shiga fili. Ni kam lokacin ina kauye ranar
kwana na sha takwas daga sati daya ina jikin tsohuwa
kakata tana fadin daga ni takwara kar ki karasa ni nace
kai dan Allah ki barni na dan huta mana infa na tafi sai
na dade zan zo tace ai ba zaki kawo min Adamu mu
gaisa ba?nace ni ina naga wani Adamu yana can
kasashen turawa yana kwallo tace ai Ball yake?ynxu
dan Ball din zai rike ki?nace to ai tasu ta gaske ne ba
irin ta nan ba,ta tureni ke ja can da ban haushi baga su
nan muma muna dasu ba yan bal din yanxu jibi yaron
nan na gurin karima shima aikinshi kenan bal asubar
fari yasa gajeran wando da wani kwandallelen takalmi
raf raf ya tafi bal kusan shekara biyar ance har yau baa
taba nuno shi a cikin talabijin ba shi bai tsaya yayi
noma ba shi kuma bai tafi rani ba,sai dai yau yana
waccan unguwa gobe yana waccan yawon bal,tunda ta
soma magana nake dariya,tace dariya ma na baki?
dama wannan shirmen Adamun keyi shine za'a bashi
mata?ko mu da muke karkara dan gidan karima an
hanashi mata,na kuma tuntsurewa da dariya ta dau
mafici ta bini kki bani guri ta kai min duka da gudu na
fita ina kwasa dariya sai naji tsayuwar mota da sauri na
leka motar babana na gani da gudu na fita na
taroshi,Ya kira wasu yan samari suka shigo da kayan
abinci na rike mishi hannu muka shigo, dakin Baba ya
soma shiga kafin ya shiga dakin Tsohuwa na nufi
madafi na dauko masa abinci a kwano na debo masa
ruwa a randa na aje a gabanshi ina fadin Babana kamar
nasan zaka zo na yi abinci da yawa,yace to na
gode,nace yasu Mama?yace suna lfy sune ma suka
matsa min akan na daukoki daga sati har kin kusa wata
jiya Alhj ya kirani a waya yace in mashi kwatance yaje
ya daukeki,nadan yatsina fuska nace ni ban son tfy
tsohuwa tace to ai ya zama dole nace muna gama
bikin su Mami zan taho nan,baba yace a'a muma muna
son ki zo mana kafin bikinki daga nan nayi shiru ban
sake magana ba,tsohuwa tayi caaraf tace yawwa ashe
kai yanzu Adamun dan bal ne?shi ne zaku bashi yar?
Babana yayi dariya sannan yace ai sana'a ce sosai
suna samun kudi fa shima dan mai gidan Habiba
kwallon yake tare ma suke, ai shi kenan amma ko ga
tarihi bal ance bata da kyau,yace to ai wasu malaman
sunce za'a iya yi in ta zama lalura saboda kishin kasa
tace tunda kuna so ai komi ma cewa zakuyi ni dai ina
jin su har suka gama.
Adamssalin tara text din da aka saba yi min tsawon
watanni kullum ba fashi ya shigo,very soon zamu
kasance tare domin nasan i am always lucky akan duka
abinda nakeso,ban ma gama dubawa ba na kashe yau
kamna gane Adams ne yake min text yana boye no
haushin shi ya kara kamani na hau fada ina cewa nufin
shi sai ya min haka zan so shi?to yayi kuskure ni ba
sonshi nakeyi ba zan dai aure shi ne dan hujjar da na
ba yaynmu nace kai bari ma in mashi karara don ya
daina damuna na soma neman layinshi ai cikin sa'a na
sameahi ashe lokacin suna tare da yaynmu a wani club
ya dubi yaynmu yace ga yar gidana sannan ya dauka,in
kaga yaynmu zaka dauka bai damu da wayar da Adams
keyi ba amma ya tattara dukkan hankalinshi gurin
sauraron Adams dan ta maganr da Adams keyi zaka
gane me nace,ni kam Adams na dauka nace hello
Adams menene na boye no kana yi min text in ma kana
yi ne dan ka birgeni to wllh haushi ma kake bani,tunda
na soma maganar bai tare ni ba sai da nayi shiru,yace
calm down my wife wllh ba ni bane ba ban ma taba yi
maki text ba nace to wanene?ina zan sani inji adams
sannan yace don Allah kiyi hakuri karki damu kanki
kashe na kiraki,nace yanzu zanyi shafai da wutiri ne sai
da safe yace sai da safen yanda ya amsa har tausayi
ya bani,Maska ya dubi Adams dan san jin karin
bayani,Adams me Iman tace maka ne?Adams yace wai
cewa tayi ina boye no ina kiranta wai bata so Maska
yayi murmushi to dama kai kake mata ko?Adams yace
bani bane Allah maska yayi tsaki sannan yace kaga
abinda nake gaya maku ko ku nemi manyan babys ynxu
gashi kana yi ma yar cikinka rantsuwa ita kuma sai
masifa take maka ynxu ina girma?babu babba wani
abun ma sai taga gadon kwananka Adams yayi
murmushi yace wannan ra'ayinka ne kawai niko ina son
in auri yarinyar dan na more sadakina da kyau Maska
yace in ka samu big girl shine zaka more sadaki Adams
yace mu bar zancen haka Maska yace kai dai ka sani
yaushe zan bar yar yarinya ta juyani? ai ni in babbar ce
ma sai ta raina kanta in tace zata kawo min iskanci
Adams yace in baka sonta ba ba in kana sonta komai
zatayi maka zaka jure sai kaga karamar ta juya ka
babbar bata juya ka ba,tsaki Maska yayi sannan yace
baka gama sani na ba har ynxu don ina son mace tayi
kadan na jure iskanci, sannan ya mike ya tafi Adams na
mishi dariya.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Muna zaune a dakinmu muna aikin gyaran katunan
bikin su Mami yau saura kwana takwas bikin kuma
yaune su yayanmu zasu iso shine babban abokin ango
kuma babban yayan Amare,na dubi Mami nace ya kan
Badarawa,Malali,da Unguwar sarki ya kamata muje dan
yan skull zamu gayyace sosai mun dade bamu hadu ba
mami tace haka ne yi sauri mu biyama Amira,tare
muka shiga gari sai magriba muka dawo sai dai in
lokcin sallah yayi mana mu tsaya muyi,shirye shirye
sunki karewa saboda wasu abubuwan bada su Sa'a
zamu hada ba walima ce kawai tare sai Sisters day da
su Anty Mariya suka shirya a gidan yaynmu in sun iso a
Yakubu Avenue amma mu zamuyi lunchn sannan
angwaye sun shirya dinner,mun dawo mun sami yaynmu
ya iso saboda gidansu sai an gyara da yan share share
gurin su Sagir na sami lbr isowarsu sai ga kuma wayar
Adams yana ce min sun iso ynxu suna tare da ango
nace to sannu da zuwa me zan shirya maka?yace
komai ma nace to an gama nadai daure ne nayi
wannan maganar dan kar ya ce ban yi murna da
zuwansa ba amma zahiri hankalina yana kan yayanmu
da kuma masifar son ganinshi,nan na dan yi girke girke
na san Adams na zaci zan sameshi tare da yaynmu a
dakin yaya kabir din ina sai shi kadai na samu dan haka
shi kadai yayi ta surutanshi Adams ya dubeni kin kara
cika fa yar gidana ina son Maska ya ganki shi da yake
cewa zan auri yar cikina nace um! Sama sama mukayi
hira sannan na koma gida shi kuma ya nufi gidan Nasir
har ramar lalle banga yaynmu ba ko anty mimi ban
gani ba mu da yake gidansu Amira

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment