Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko ina a jikinta amma fuskarta a bude, cikin wasu masu tsaron gidanne suka bi bayanta aka bude masu kofa,suka shiga wasu runfuna inda taron mata yake kusa da gidan yarin tun tahowarta yan jarida keta daukar hotunanta da videos dinta kai tsaye bisa minbari ta nufa tahau tare da daukar lasifika, tana goge hawayen idonta ta nunanin yanzu duk wannan alummar don ita suka taru sukeson jin abunda zata fada.



Kara kallonsu tayi tayi karfin halin bude taro da addu'a da sallah ya musulmai sannan ta bude baki tace"iyayena, yayyena, kannena kuji tsoran Allah, kune jigon gida kuyi ilimi ku bada tarbiyya, duniya ba matabbata bace, kada ku sayar da lahirarku akan kyalekyalen duniya, Allah daya haliccemu yayi mune domin bauta masa, ku dauka duniya jarabawace kukeyi zakuje inda zasu iske sakamakonku da gidan zamanku nahar abada, ki sani idan kikayi gudunmawar bacewar rayuwar yaranki ko kannenki ko jikokinki to Allah bazai barkiba, zai bi masu hakkinsu a ranar da babu tsimi babu diba, kada ki zama jahilar uwa da zata koyi yayanta da shan giya kwayoyi shigar banza zinace zinace, ku sani alfarman manzonmu mukeci da tuni an dade da juyar da duniyarmu, ke kanki in aka saba maki ko aka yimaki kishiya kina fushi da neman hukunci inaga anyi hakan ga mahalliccin, kada Kiyi koyi da kazamar rayuwar Khadija ta farko wanda iyayenta suka tarwatsa mata farin cikinta, abun takaici batasan ADDININTA ba bare tasan mahalkiccinta bare kuma ta bauta masa, Allah ina rokonka daka bamu iyaye na gari masu ilimi da fita hakkinmu da sanin ya dace, a fannin boko za'a iya kashe dubunnai har kasar a bari, amma a islamiyyah ana kyashin kashe dubu daya, ko'a takura wa yaro yayi karatun ADDINI, mu sani kiwo muke kuma ababen tambayane ranar gobe kiyama, ya kamata musan kanmu muyi bauta ga Allah mubawa yaronmu tarbiyya kada mu kaskantar da rayuwarmu sannan mu likata gawai kaddarace, kaddarace wannan ko sakaci, Ya Allah kasa mu hadu dakai muna masu imani a gareka da kuma kwadayin haduwa dakai, mu hadu dakai zukatanmu da gangar jikinmu suna shaukin isa gareka, Ya Allah ka bamu damar abunda muka karanta dayi maka biyayya".


Kukane yaci karfinta sosai har tana neman shidewa ajiye lasifikan tayi ta kuma fashewa da kuka saida su Asiya suka kamata zuwa ciki dominko tsayuwa gagararta tayi bata komai sai fitar da kuka yayinda zuciyarta ke matukar kuna da tsanar rayuwar duniya gaba daya.


Duk wanda ya halarci wannan taron kuka yake, hankalin kowa ya tashi jikin kowa ya mutu indai kana da ragowar imani a tare dakai.


Aysha dake kallah a TV kuka take kamar ranta zai fita, ga soyayyar yar tata dake kuma azazzalar zuciyarta.


Khadija kam kan bed ta fada tana kuka tare da kaico da irin rayuwarta ta baya ga wani irin ciwan kai daya kawo mata ziyarar, alwala tayi taci gaba da jero nafilfili da istig fari na neman yafiyar ubangiji.



Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karsheπŸ‘πŸ»


Emm Iyy luv




*ADDINI NA*
*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*
*BY MARYAM ISMAIL*

*INKA KARANTA KA TURA WASU GROUPS DON ALLAH HAR FACEBOOK*
*TRUE LIFE STORY*
9
Tana haka wahallan bacci yayi awan gaba da ita, Asiyace ta gyara mata kwanciyar tayi ficewarta, duk wata mace da tazo wa'azin ranar ta koma gida cike da dumbin imani da tausayi tabbas wa'azinta yayi nasarar canza mata da dama wanda suka afka kogin nadama da kuma jin tausayin rayuwarta gata yarinya karama saidai abubuwan duniya sun rikitar da ita.


Wani hadden gida da ni'imomi iriri da duk wani abu najin dadi an tarasa a cikin tankameman gida wani irin sanyin dadi da kamshi ke ratsata wanda tunda take a rayuwarta bata tabajin irinsaba ga wata natsuwa da kwanciyar hankali dake ratsata ko ina ka kallah sai kaji natsuwa ta ziyarceka, murya taji kamar daga sama ana fadin *nanne gidanki ki taho, kiji dadin da baki taba jinsaba*. Firgigit ta farka daga mafarkin da takeyi da addu'ar tashi bacci a bakinta, cikin tsananin mamaki Khadija ke zagaye dakin nata da kallo duktayi zufa addu'a tayi ta tashi ta nufi wurin karatunta amma ta boye sirrin wannan mafarkin da tayi.


Kamar wasa Khadija ko baccin minti biyu ya dauketa sai tayi wannan mafarkin ana kuma kawata mata da disa mata soyayyar wannan gida da take gani, saidai in bata kwantaba a matsayinta na malama tasan fassarar mafalkinta, kuma sai a sannan laifin data aekata ya fado mata a rai kuma tasan hukuncinta a musulunci, gyada kanta tayi cike da kwarin gwaiwa da aminta da shawarar da zuciyarta ke bata mikewa tayi cike da taurin zuciya da rashin tsoro ta saka hijab dinta tasa aka nema mata iso wurin malam liman, ba dadewa akace ta shiga.

Tana shiga ta zauna nesa dashi bayan sun gaesa tace "Baba so nake ka fadamun laifin me nayi aka kawoni nan? "

Murmushi yayi yace"Khadija an kamaki da laifin kashe abokinki Sadiq kuma kin ansa laifinki shiyasa aka yanke maki hukunci".


Girgiza kai tayi tace"tabbas nina kasheshi da hannuna, Baba kaika koyar dani ka bani tarbiya wacce na gagara samu daga iyayena, baka gujeniba ka tallafeni kamar y'arda ka haifa, kasa nayi karatu mai zurfi da sanin hukunce hukunce, inaso ka fadamun meye hukuncin wanda yayi kisa a ADDINI NA"


Izuwa yanzu kam jikin malam liman yayi sanyi don dukta rikitashi da wannan tambayoyin nata wanda yasan ta sani cikin kwarin gwaiwa yace"Khadija wanda ya kashe a kasheshi, amma kisa Kala biyune akwai na ganganci sannan akwai na tsautsayi, inka kashe da gangan a kasheka, in na tsautsayi ne kamar accident to kayi azumi sittin a jere".

Murmushi tayi tace"Baba nina kashe Sadiq da gangan inason zuwa kotun musulunci donko na ansa laifina, ta yankemin hukunci daidai da ADDINI donna isa ga ubangijina inada tsarki bani da wani laifi gara amin hukunci a duniya ba sai naje lahira ba".


Tunda ta fara magana hankalin malam ya matukar tashi a rude yake kallonta yace"kina cikin hankalinki kuwa, kinsan me kike fada".

Sai a lokacin ta dago ido ta kallesa fuskarta cike da fara'a tace"na sani mana, duniya jin dadi ne mai yankewa, dama zuwa nayi ganin gari to lokacin komawata gidana na Asali yayi kaika karantar dani to banaso yanzu lokacin amfanin karatun yazo ka hanani, kuma hukunci na yanke kayi hakuri Baba banason shawarar kowa akan abunda na aekata"tana zuwa nan ta masa sallama tayi gaba.


Tabbas abunda ta fada gaskiyane babu yanda ya iya dole ya fadawa na gaba dashi, mikewa yayi cike da al-ajabi yaje ya isar da sakonta, zuga guda akayo don lallashinta amma fir Khadija ta bijire taki sauraron kowa kai karshema kuka tasa masu ta tada hankalin kowa, dole sukabi yacce take so aka tattara kundinta aka kaita kotun musulunci, suka tsaida ranar juma'a itace za'a saurari karar Khadija.


Ba karamin farin ciki tayi ba dajin wannan batu, murna take juma'a tazo, don kwata kwata duniyar ta fice mata akai bata kaunar zamanta cikinta, sosai ta dage da addu'o'i da ibada baji ba gani.



Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karsheπŸ‘πŸ»

Emm Iyy lov



*ADDINI NA*
*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*
*BY MARYAM ISMAIL*

*IDAN KA KARANTA KA TURA WASU GROUPS*
*TRUE LIFE STORY*
09030953294.
πŸ”šπŸ”š10πŸ”šπŸ”š

*HUKUNCIN KHADIJA A KOTU*
Yau ya kasance juma'a motocine jere guda biyu daya tasu malam liman daya kuma yan sanda ana jiran fitowar Khadija, itako daga wanka ta fito tana tsane gashin kanta da yake jike da ruwa alamun wankan tsarki tayi bata kula Asiya ba da taga tanatana faman sharbar hawaye, shiri tayi cikin shigarta ta mutunci tayi sallah raka'a biyu sannan tazo da murmushi ta kama hannun Asiya tace"banason wannan kukan naki, yanzu addu'arku nake bukata, kuma zan roka a barmu mu tafi tare don muyi bankwana, murna ya kamata kiyimin zan hadu da ubangijina"hijab ta sakawa Asiya ta jawo hannunta suka fito waje, roka tayi a barta su tafi da Asiya sai a dawo da ita, kowa yan gidan kabbara suke tare da zubar da hawaye, cikin dakiyar murya tace"duk Wanda nawa laifi ya yafemin, sai wata rana Allah ya hadamu a aljanna madaukakiya, nidai na yafewa duk Wanda ya batamun"tana zuwa nan ta kutsa kanta cikin motar akaja sukabar gidan, mutanan gidan kuwa basa komai sai kuka da rokawa Khadija gafara.


Kallon mutanen dake damke da kotun take ga yan jarida da gidajen TV sun cika wurin, kamar wurin ya bare da kyar aka samu damar shiga da ita cikin kotun, aka tare yan jaridar daketa faman jefo mata tambayoyi.


Lokacin da Alkali ya shigo kotun tayi tsit aka karanto laifin Khadija tare da mika takardar ga alkali, kallah yayi sannan ya dago da idonsa ya kalli Khadija yace"Khadija kinji laifinki kina daja ko karin bayani? ".


Cike da ladabi tace"bana daja yamai shari'a nina kashe Sadiq da hannuna, shine nazo a yankemin hukunci daidai da yadda shari'a ta tanada.

Allahu akbar mutan kotun ke fada tare da jinjina imani irin na Khadija Wanda ba'a samun mai Shi.

Yan rubuce rubuce alkali yayi sannan ya dago ya fara magana kamar haka"a bisa ansa laifin da Khadija tayi hukunci a addini shine Wanda ya kashe a kasheshi, inba da ganganba to kayi azumin kaffara, itako tayi kisanne tana sane, hukuncinta ya kama kamar haka kotu ta yankewa Khadija jabir kisa ta hanyar fille wuya nanda awa biyu"buga tebur yayi ya fice daga wurin, bakajin komai sai ihun mutane da koke kokensu kowa da abunda yake fada, tun anan aka rufe mata fuska da bakin kyalle aka sakata mota aka nufi inda za'a zartar da hukunci yayinda dubban mutane suka bisu ciki hardasu malan liman da iyayenta da suka fara zaucewa.


Filin zagaye yake anyi tsit, Asiya kam ta kasa rarrashin zuciyarta don kuka take kamar ranta zai fita, nan aka shigo da Khadija filin tare da dukar da ita, hannu tasa ta yaye rufin da akama fuskarta tace"kuban mintuna kadan nayi wasiyya".

Gyada mata kai kawai sukayi ta mike cikin natsuwa tace"ya jama'atul Muslim, kullun maganata ta farko itace kuji tsoran Allah, kusan me kuke aekatawa kuyi kwadayin neman rahmarsa dan Adam ba a bakin komai yakeba nasiha karama dazan muku itace rayuwa cike take da jarrabawa, duk mumini Wanda yayi imani da Allah ya tabbatar sai an jarabesa, wannan fadar Allah S A W ce, kuna tunanin shikenan tunda kunyi imani ba jarabawa?, wallahi sai an jarrabemu hagunmu ko damanmu, samanmu ko kasanmu, hanya dayace ta kubuta shine mu karbi jarrabawarmu da hannu biyu, muyi imani da kaddara mai kyau ko marar kyau, duniya jin dadice mai yankewa kasan meka aekata kafin haduwarka da Allah, mutuwa bata sallama ko bankwana"hawaye kebin fuskarta "ina kuka badon hukuncinaba saidon murnar barin gidan wahala da bakin cikin duniya, yau Khadija ce tsaye a gabanku take bankwana da neman gafarar Wanda ta batawa, inna mutu kuyimin wanka ku sallaceni ku gaggauta kaini makwancina babana(malam liman shina yarda ya sani a kabari) ku yafeman". Tana zuwa nan ta dauki butan gabanta tayi alwala da sallah raka'a biyu.


Har malam kuka yake daduk Wanda ke wurin musamman Asiya da iyayenta.

Kai tsaye zuwa tayi ta duka inda za'a yanke mata wuya ta daga hannu sama tace"ya Allah ni baiwarka ce ya Allah, kuma kana bima Wanda aka zalunta hakkinsa, Allah na kawo karar iyayena Inaso kabimin hakkina ka mani sakayya ranar gobe, kayi masu yadda suka yimin ka hanasu jin dadin duniya ya Allah ka kuntata masu, wasiyyata ta karshe kada kubar iyeyena su kusanci gawata"dora kanta tayi tana furta " *la'ila ha illallah* "daidai nan aka sare mata wuya jini yai tsartuwa ya fara malala ta fadi kasa ragwab idanuwanta na kallon sama fuskarta sai kyalli take da alamun farin ciki.

Kuka sosai mutane keyi, Asiya kam sumewa tayi ita da Aysha, su Aliyu kam mutuwar tsaye sukayi.

Da kyar malan liman ya furta"Allah ya karbi bakuncinki Khadija".


Sosai mutane ke fada kan Wanda zasuyi mata wanka, da kyar aka samu masalaha aka shiryata, kwata kwata an hana iyayenta da abokanta kusantarta, malan liman da kansa ya sakata kabari, akayi addu'a kowa ya watse.


*ya Allah inda nayi kuskure ka yafemun, ka bamu ikon fahimtar sakon dake ciki, ka daukaka littafin nan yaje har inda banyi tunani ba, ka yafe mana kurakuranmu ka bamu ilimi mai amfani, ka gafarta mamu, mu hadu dakai muna shauki da imaninka a tare damu ya Allah*


😭😭😭😭nayi kuka iya kuka a labarin nan, kuma na tsinci abubuwa da dama


09030953294.


Emm Iyy luv
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment