Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

malama daina tazar nan zan ci abinci, kada ki jefa min gashi a ciki”.
Sai ta kame gashin ta daure da ribbon ba ta ce komi ba. Sai ya ji dan tausayi ya kama shi, saboda tunda suka zo bai yi mata magana ta dadin rai ba, alhalin ya rabota da wadanda ke sata farin ciki suna tarairayarta (Daddy da Inna).
Yana kuma sane da cewa cikin bacin rai da kawa-zucin karatun ta da ya rabota da shi take. Yayi sanyi gabadaya yace a hankali,
“Rayhanah idan ba za ki daina yi min abubuwan da kike yi min din nan ba, ba zamu shirya ba. Kin kama bakinki kin dinke, ina ta magana ba za ki amsa ni ba.
Rayhanah ko a dawo lafiya baki ce min ba, dazu da zan fita, baki tambaye ni ina ne dakin ki ba, na dawo ko sannu da zuwa baki ce min ba. Kina jin yunwa ba za ki gaya min ba.
Ba sai kin yi hakan za ki nuna min cewa Khalipha kike so ba ni ba….”
Bai kai karshen maganarsa ba sai ga hawaye sun biyo kuncinta…… bai damu ba ya ci gaba da fadin.
“Ba dama in fadi Khalipha sai ki sa min kuka, idan shi kika aura za ki yi mishi wannan shakulatin bangaron da ni kike mini? Ko ko don ni lika miki aka yi?
Kina bakin ciki an raba ki da farin Balarabe an daura miki baki a kafa.... to dai ai gara ni sau dubu da wannan bakar fuskar taki da kike min rowarta.
In don dan kiss din da nake roka ne a wajenki na bari, na zo inda zan samu a bagas, ba sai na biki ina lallashi ba.
Kin ga mukulli nan, dauki ki tattara koma tsani ki kama hanyar dakin ki wancan dake kallon nawa, ranar da kika shirya karbata a mijin aurenki, sai ki zo nan inda nake….. have your way out…..!!!”
Ya fadi da dan daga murya yana nuna mata kofa. Ta sulale a kan kafafunta tana kuka sosai ba ta fitan ba. Sai ya ja wani mugun tsaki ya mike ya yi fatali da abincin nasa ya suri mukullin mota ya yi waje.
Tana jin tashin motarsa daga inda take, sai ta ji zuciyarta kamar ta fashe. Ta yi kukanta mai isarta, babu mai lallashi babu wanda ya san tana yi. Fitar hawayenta a ganinta shi ne hukunta zuciyarta da ta ki yin farin ciki da Ibraheem a matsayin miji. Amma kuma take KISHINSA!.
Abincin da ya tankwabar ta bi ta tsittsince ta yi kokari ta ci amma ta kasa. Rabon ta da abinci tun a cikin jirgi, da ta tabbatar ba za ta iya ci din ba, tunda wanda ya sayo da kudinsa bakin cikinta yasa ya kasa ci bai ci ba, ya fita yana mai fushi da ita.
Ya kasa ganeta ne, ita ba ta da yawan magana, yawancin abubuwa ma in ya fadi mata ba ta san amsar da za ta ba shi bane, shi yasa take yin shiru.
Shima kuma da yana Kano ai haka yake, ba ta san yaushe ya koyi son surutu ba, abu kadan ya ce Khalipha wanda dare daya ta nemi gurbin da ta saka shi a ciki a zuciyarta ta rasa. Ya shafe kamar ba a yi shi ba (Son).
Me yasa yake yi mata duka wadannan tuhume-tuhumen marasa amfani a gareshi? Abin da ya wuce, ya wuce a zuciyar Rayhanah……..
Har wata shukar ta dasu, tana so ta fidda rassa, ta yi sabuwar yabanya. Wannan bishiyar kuma ba wata ba ce illa dan tsiron da Allah ya dasa tsakanin mace da mijinta na sunna, ba irin na saurayi da budurwa ba.
Idan ya ci gaba da zarginta a kan Khalipha babu shakka yana daukar alhakin ta, ina ruwansa da abin da ya gabata a wata rayuwa can da ta shude wadda ba shi da hurumi a ciki? Abin haushin ma wai a kan Yayansa ciki daya.
Rayhanah ba ta san cewa da matacce ma mai sonka na kishi balle rayayye. Karfin kishin miji a kan matarsa na da nasaba da adadin soyayyarsa gareta. Don haka ita ma ta yi fushin, ta tattara inata-inata da mukullin da ya jefar mata ta yi dakin da ya batan.
Ta so ne ta shirya kayanta cikin cupboard amma ta kasa. Yunwa ta ci karfinta, damuwa da fushin nasa ya fi nata fushin. Sai ta kasa hassala komai ta yi tagumi a gefen lafiyayyen gadonta ta rasa abin da ke mata dadi.
Dakin kawai take kallo da kayatuwar zamanancinsa. A yau ne Rayhanah ta taba sha’awar Allah ya ba ta ‘ya’ya, ko ba komai su din sanyin zuciya ne a lokacin da ubansu ya hutsance, sannan abebaden debe kewa ne.
Har agogon bango ya buga karfe goma sha biyun dare a Chicago ba ta ji shigowar motar Ibrahim ba.
Sai ta fara sana’ar tata wato (kuka) har da addu’ar Allah ya sanyaya zuciyar IBRAHEEM. Har da jan Ayar “qul yaa Naaru kuuni Bardan wa Salamun alaa Ibrahimu...”
Me ke faruwa da ita ne haka a kan Ya Himu? Da fushinsa ya tafi da dukkan farin cikinta? Walwalarta da bukatun rayuwarta ta dan Adam (barci da abinci).
Wadannan alamu ne na wani mutum da ka damu da shi matuka. Ibrahim ya zo ya yi karan-tsaye a rayuwarta da zuciyarta. Ta yadda har bacin ransa ya tafi da sukunin zuciyarta da kuzarin gangar jikinta gaba daya.
Dungurgur Rayhanah ke zaune, duk iya sata irin ta barci ya kasa sace Rayhanah. A kan idonta lokacin sallar asubahi ya yi, ta yi sai ta ci gaba da zama a inda ta yi sallar, a lokacin ne barci mai nauyi ya dauke ta.
Ba ta farka ba sai a dalilin tashin kira’a daga redio dake fitowa daga falo, wannan ya tabbatar mata Ibrahim din ya dawo. Kuma da gaske yake sai ranar da ta shirya karbarshi a matsayin miji zai sauko daga fushinsa tunda ga shi bai kwana gidan ba, ya dawo kuma bai nemi inda take ba.
Yaushe ce wannan ranar? Me za ta yi din ya nuna ta karbe shin? Ita tun ranar da ta san Ibrahim aka aura mata ta karbi yin Allah, babu komai cikin zuciyarta a yanzu sai so da kauna irin na mace da mijin da suka yi aure bisa tubalin soyayya.
To shirin da yake nufi din ne ba ta gane ba, in dai hira ce da surutu ba ta iya su ba, ta san kuma shima din bai iya ba, banda yanzu da bakinshi ya bude. Mai zai hana suyi zamansu yadda Allah ya haliccesu? Su yi magana a inda hakan ya zamo dole, kuma mai muhimmanci? Tunanin Rayhanah kenan.
*****
[12/28/2019, 19:06] Takori: Toilet din dake makale da dakinta ta shiga hajijiya na dibarta saboda yunwa wadda ta haifar mata da ciwon kai. Wanka ta yi a daddafe, ta yi brush ta kuskure da listerine, sannan ta fito.
Kayan da ta dauka riga da wando ne suit na mata masu kauri da dogon hannu maroon kala, ‘yan gidan ‘george’. Ta bi ta feshe ilahirin gabobi da kusurwoyin jikinta da deo-spray din rexona, ta cakuda da turarenta na din-din-din (Makhmariyyah wa lamsa nectar), ta tausasa labbanta da vaseline din avon ta murda kofa ta fito falon.

Yana kwance ruf da ciki a doguwar kujera, exercise wears ne a jikinsa. Da alama ya yi exercise din ne ya gaji yake hutawa. Ta karasa ta zauna a kujerar gefensa kanta a kasa ta yi shiru.
Ya ji bude kofarta da fitowarta amma bai juyo ba, don ya san ba wani abu za ta ce masa ba, shima bai san me zai ce mata ba.
Amma ga mamakinsa sai ya ji ta zauna a kasan kujerar da yake kwance muryarta na dan rawa ta ce,
“Don Allah don Annabi ka yi hakuri Ya Himu, Allah ni ban san abin da zan dinga ce maka bane shi yasa nake yin shirun..”
Ya yi shiru bai tanka mata ba. Sai ta sake cewa cikin damuwa ta gaske,
“Ka gaya min abinda kake so in dinga gaya maka din, sai in gaya maka…”
Bai juyo ba amma dariya ce ta kama shi, a kalla ta nuna ba ta da wani ra’ayi nata na kashin kanta sai nasa.
Ya mike gaba daya ya zauna sosai a kujerar ya mike santala-santalan kafafunsa a kan tebirin gilashi, ga alama ya yi matukar yin sabo da irin wannan zaman.
Ya dube ta a hankali ta sadda kai tana share hawaye ya ce,
“Yaa Ladif! Ke kam baki da aiki sai kuka kamar matar mamaci? To ai kinga abin da bana so din kenan, kukan.
Rayhanah ya za ayi na ga farin ciki da walwala a fuskarki? Bayan Daddy ya ce min kina hira har da dariya, ko duk a cikin rashin son nawa ne Rayhanah? Me zan yi ki saki jiki dani ki daina sani a gaba kina min kukan nan?”
A hankali amma da alamar fusata cikin consonants and vowels din sentence din da zai fito daga bakinta tace,
“Ka daina tuhumata a kan Yaya Khalipha!”.
“Saboda kada in taso miki da son da kike masa?”
“Ka ga abin da bana so din kenan”.
“Sai in yi shiru, ni ina aurenki kina tunanin wani can?”
“Ni na ce maka ina tunanin sa?”
Ta fada muryar na kara yin rawa.
“Kada ki yi min kukan saurara….. dago ido ki dube ni…..”
Ta kasa dagowar sai da ya sake maimaitawa a dan zafafe.
Cike da nauyi, da tsoro da firgita ta daga idanunta a hankali ta dube shi.

Abin da ta gani cikin idanun Ibraheem din suna da yawa, ga kishi, ga rikici, ga neman rigima, ga neman tada zaune tsaye….. sannan ga so da kauna mai yawa….. so yake ayi ta rikici kada a daina ba shi da alamun saukowa idan ba a fadi yadda yake so ba.
Sai ta mike ta yi dakinta da sauri-sauri da gudu-gudu don zuciyarta da gangar jikinta ba za su iya jure rikicin nasa ba. Shine bai son a zauna lafiya sai dai ya yi ta tone-tone kamar kaza, to ita ina yake so ta jefa ranta?
Eh, da gaske ta so Khalipha domin mutum ne mai kyautata mata, mai son ganin walwala da farin ciki a fuskarta da zuciyarta…. Mai son inganta rayuwarta, mai darajata a duk lokacin da Abida ta wulakantata.
Mai nuna mata cewa nakasa ba hujjaba ga jera kafada da sauran mutane! Yaya Khalipha yace da ita a lokuta da dama “You are only disabled if you truely believed you are .........!! He’ll stand by her even when the whole world turns its back on her..... he's indeed her pace-setter!!!
To mai yi maka wannan ya za ayi ba za ka so shi ba? Tunda ita zuciya an halicceta ne da son mai kyautata mata???
To Allah mai juya al’amura bai nufi za su yi aure ba, ya canza mata da shi, kuma ta karbi canjin, ta gane abubuwa da yawa wadanda a da ba haka suke ba.
Wato sai da Ibrahim ya zo ne da ‘yar mu’amalarsu ta tsahon lokacin nan ta soma rarrabe abubuwa. Ta fahimci ta so Khalipha so ba irin wannan da take yi a yanzu ba. So ne na rama halacci ga wanda ya yi maka alheri.
So ne wanda ba ta taba jin tana sha’awar hada jiki da Khalipha ba, zuciyarta ba ta taba rikicewa don ta ga Khalipha ba, ko don ya kalle ta. Amma shi wannan (Ya Himu) ….... ??? Ta girgiza kai.
Ba za ta iya fassara abubuwan da take ji a zuciya da gangar jikinta a kansa ba. Shine ke gigitata, shine ko magana ya yi mata ko ina a jikinta sai ya amsa. Shine bacin ransa ke kassarata ya sanyata kasa yin komai including barci da cin abinci dolen dan adam.
Shine mutum na farko da ya rungumeta ya hada da jikinsa da nata ya zuba mata wasu chemicals cikin bakinta da sassan jikinta gaba daya, da suka karkashe kwayoyin son Khalipha da birbishinsu daga kowane sako da kowanne lungu da kusurwa na jiki da zuciyarta.
Suka dasa wata bishiyar, wadda ta yi sauri ta fidda rassa da korran ganyayyaki suka yi girman da suka rufe kofar zuciyarta ruf, daga tunanin kowanne Da namiji cikin dan lokaci kadan, suka shimfida tasu katuwar dardumar suka zauna suka baje, suka yi kane-kane suka kankane ko ina, suka yi babakere a kowanne angle. (Kusurwa).
Wannan shine matsayin Ya Himun a yanzu da ba za ta iya fassara masa ba. Ba ta san kuma wata hanya da za ta bi ta nuna masa hakan ba. Ta yarda ya ci gaba da zargin nata da tone-tonen nasa in sha Allahu ta daina damuwa, in ba haka ba Himun so yake ya tarwatsa mata zuciya.
Sai ta soma nemawa kanta abin debe kewa don ta raba kanta da damuwa da fitinar Ibrahim, kawai sai ta dauko biro da exercise book ta ce
“Bari in fara RUBUTU!”
Sunan farko da ya fado mata a zuciyarta shine, bari in sawa littafin suna RAYUWAR RAYHANAH! Bari in rubuta labarin rayuwata tun daga kauye zuwa birni. Bari in bawa ‘yan’uwana mata da masu irin lalurata labarina ko sa sanyawa zuciyarsu hope da salama… (kada su fidda rai da rahamar Ubangiji (waraka) domin shine mai sanya cuta mai kuma yayeta a sanda ya so.
Babu wata cuta da aka saukar a bayan kasa ba tareda an saukar da ita tareda maganinta ba. Cuta lokaci daya take shiga, amma waraka sai lokacin da Allah YA so. Duk kudin ka duk mulkin ka, lafiya ta Allah ce.
Rai dai, baya rabuwa da rabo, saidai idan ya kare!
Cikin littafin nan ba zan manta da mutum biyu masu muhimmanci ga rayuwata ba. (DADDY) Dacta Mansur Balarabe Takai da Abdullahi Mansur Takai (YAYA KHALIPHA…..) ba zan manta da IYA BILKI ba, da ADO da ya yi sanadiyyar da na fito daga kauye har a yau na samu alfarmar zamantowa barin rayuwar YA HIMU na mallakeshi a matsayin MIJI NA.
Really it’s a blessing….. a mysterious miracle ba isa ta ce ba dabara ta ba......!!!
Watakila idan na rubuta yadda nake son YA HIMU zai fi fahimta ya yarda dani ya daina zargina a kan Yaya Khalipha........
Ya daina azabtar dani da fushinsa, wanda ya fi zafin bulala a dukkan jikina….......
Ba zan manta da Jawahir ba…. Ita ma MAMI ba zan taba mantawa da ita ba. Na yi mata uzuri sau (70) a bisa yadda rabuwar mu ta kasance, domin a da, ba haka take ba…. “
Haka ta yi ta rubutu tana tsiyayar da ruwan biro. Sallah da wanka, shan tea, cake da juice dake cikin firij a kicin dinsu kadai ke tada ita tsawon kwana uku.
Ta tattara Ibrahim da iyayen cefanensa ta watsar, ko tattasai daya ba ta taba ba. Daga baya ta fahimci ya samu kuku da mai gyaran gida duka Turawan Ohio ne. Taji yana kiransa Benjamin.
Idan ya gama girkin yana aje mata a dining ya kuma danna mata intercom ya sanar da ita, ‘to’ kawai take cewa, amma yadda ya aje haka yake daukar abinsa.
Ibrahim ya soma damuwa, me yarinyar nan take yi a daki tsayin kwana hudu ba ci ba sha? Kada fa yaje wani abu ya sameta, ga shi ta garkame kofa da mukulli ta ki cire shi daga jikin kofar.
Wai ita ma nan fushi ta yi kenan? Ban da ya damu da rashin cin abincin ta Allah sai dai ta yi ta gaji ta fito ko sati daya ne.
Dawowarsa kenan daga asibitinsu ko farar rigar likitocin dake jikinsa da abin wuyan sa bai cire ba ya doso dakin nata, da karfi yake bugawa sosai yana fadin
"Ba za ki bude ba Rayhanah?"
Banza ta yi da shi ta ci gaba da rubutunta. Tana fadi cikin ranta,
"Idan ka balla kofar ai taka ce ni ina ruwana?".
Bugun duniya Ibrahim ya yi amaryar ta ki budewa, har hannayensa sun fara zafi. sai ya juya ya nemo sikundireba da wuka ya zo yana kwance kofar. Ita dai ta ji dan sukur-sukur amma ba ta kawowa ranta kofar yake kwancewa ba.
Ibraheem so ya yi ya bata bahagon mari hagu da dama, amma a yadda ya risketan bisa study table tana ta rubutu sanye da belted- waist –shirt din da ya fara ganinta da ita a singapore, ta yiwa gashin kanta tufka mai kauri guda biyu ta makalesu da farin dutse (bead) ta zama kamar wani fure da mutum zai so daukewa ya gudu ko ba’a bashi ba, sai ya daskare a tsaye.
Rayhanah ta ji ya kwance kofar ya kuma shigo, amma juyowa wannan ba ta yi ba. Ya tabbatar ba za ta kalle shi ba, ba za ta yi mishi magana ba.
Sai ya tabbatar lallai fushin nata na gaske ne. Wace irin miskilar mata Allah ya hada shi da ita haka!
Allah sarki Doctor I.M Takai, komi nasa kwancewa ya yi ya kasa marin da ya shigo da niyyar yi, ya jingina da kofar sakamakon kafafunsa da suka ce; ba za su iya daukar nauyin gangar jikinsa ba.

"Rayhanah!"
Ya fada a hankali cikin kwantaccen sauti da tausasawa mai nuna amsar laifi. Amma ba ta juyo ba. Rubutu kawai take ta yi kamar SUMAYYAH TAKORI.
A lokacin ne kuma hawayen da suka cika mata ido suka mirgino a kan takardunta..... ta zari tissue guda daya tana tsane su da hannun dama tana ci gaba da rubutunta da hannun hagun (lefter) ce.
Ya sake kira, wannan karon da rawar murya
"Rayhanah….. Rayhanah...... Rayhanah, am your husband…… kin zabi azabar Allah ta tabbata a kanki ta hanyar wulakantani………..???”
Da sauri ta dago fuskarta jike da hawaye ta dube shi. Sun dade suna kallon juna kafin Ibrahim yayo tattaki ya zo dan tebirin nata ya rungumeta gabadaya ta baya, ya rufe idonsa sosai yana ajiyar zuciya kafin ya bude idonsa a kan takardun nata.
Hawayen da suka jika mata fuska, da kuma saukar su a kan katoton exercise book din, suna jika shi, da kuma rungumar da Ibrahim yayi mata daga bayanta bai hanata ci gaba da yin rubutun da take yi ba, don gudun kada ta manta. Duk da cewa ya dora mata nauyinsa kadan. Idona akan takardun nata. Dai-dai sanda take rubuta;
“.......he didn’t trust me anymore........
Yana referring kowanne motion na zuciyata a kansa da KARYA… Bayan kuma sau tari tsoron kar ya ce na yi KARYAR yake kidima ni in yi masa shiru. Idan ni munafuka ce don ina son YAYA KHALIPHA, nayi zaton an halicci zuciya ne da soyayyar mai kyautata mata? Shi da yake sanya zargi a cikin AURE ya ya sunan sa.......???????

Fizge littafin ya yi ya keta shi gida biyu…. Bude baki ta yi cikin takaici, haushi da tsoro duka a lokaci daya, ta kuma mike tsaye da nufin fita ta bar mishi dakin tun da wuri, sabida ganin wani irin temper da ya samu kansa a ciki, sai ya fizgo hannunta da azama ta fado jikinsa. Shima bashi da kwarin, don haka gadon suka fada baki daya kamar jikakkun tsummokara.
Sai da ya tabbatar ya kanainayeta ya boyeta sosai ajikinsa, ya hanata yin koda kwakkwaran motsi don ta kwaci kanta, ya hanata yin kukan ta hanyar rufe bakinsa da nata. Kissing din da yake gudanarwa ga RAYHANAH zazzafa ne sosai, shi kansa bai san zai iya yinsu ba in real life ga kowacce diya mace a duniya saidai cikin kintace (imaginations).
Domin sumbace dake wanzuwa kadai a bisa umarnin zuciya da jagorancin so da kauna da kuma bukatar gangar jiki na miji ga matar da yake mutuwar so..... dying for her......!!!
Rayhanah ta rasa inda za ta sa kanta da sabon al’amarin da ya tunkaro ta a yau. Har sai da GIRMA ya risketa. Girman da take zaton shekaru sune shi, ashe basu bane. Girman diya mace daban ne.
A yau ta tabbatar ta bi sahun sauran mata, sai dai nata GIRMAN da wahalar da ta ci kafin ta same shi daban ne da na sauran mata.
Domin nata mijin ko a cikin MAZA sunansa MAZAJE….. ya kuma nuna mata bambancin sa da sauran maza….. ta hanyar sauke mata gaba dayan kauna da soyayyar shekara da shekaru da ya adanawa matarsa. Da shi kansa baisan wacece ba. Wanda ke nufin, ita din, ita tayi nasarar mallakar gurbin UWAR IYALIN.
Ko da za a karo wata daga baya, to ba za ta samu komai ba, sai burbushi ko ragowar IBRAHEEM MANSUR TAKAI (leftover). In ma akwai burbushin da ragowar kenan. Tayi amanna da cewa Ibraheem ya mallaka mata zuciya da gangar jikinsa gaba daya.
Ko da ya samu nutsuwa bai rabata da katafaren kirjinsa ba, domin shi kansa ya san ba karamar azaba ya gana mata ba. Sannan ya ki bada damar ta yi kuka, a doke ka a hanaka kuka!
Shi kansa ya san bai bi a hankali ba don shima al’amarin sabo ne a gareshi. Wanda ya jima yana tsimayen ranar zuwansa, ya sha kissima a yadda zai zo, da wadda zata amsheshi, would she be fresh on it kamar shi? Wani abu ne da ya fi karfinsa, ya fi karfin duk yadda ya zace shi.
Ya tabbata Rayhanah is his first luv..… ya so ta tun tana ‘yar Takai…. Ya so ta a sanda Daddy ya maida ta ‘yarsa….. ya so ta a sanda Abida ke wulakantata ta yadda har yau babu alaka mai dadi tsakaninsa da Abida…
Haka ya so ta a ‘yar Baba Dacta mai hearing-aid da har yau bai san ina ya tafi ba. Ya so ta son da ya tabbata Khalipha bai yi mata shi

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment