Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk abinda nakeyi wanda yakamata yake kaina zai iya sannan ya cancanta don haka zansa ayi shela agari kowa yasanda wannan rana

FAATU tace "To amma Takawa kana ganin wannan abun dakayi bazai kawo rabuwar kai atsakaninsa da Dan,uwansa yarima ba mahaifiyar safa ta kudurci dantane zai zama sarki natabbata zataji ba dadi koma tayi bore

Sarki yace "Nike da iko da komai daga kan mutan gari da bayi da ku kanku iyalaina da dukuma Sarautar kanta Dan haka babu me canzamin zabin da nayiwa Garina

Ckn biyayya FAATU tace " angama ranka ya Dade Allah yaja kwana yakara lfy

Yace "Amin Fatima. Inkin futa kituromin LAMIDO

tace "To.

Bayan futarta tazarce Dakin MAMAH domin takai mata wannan batu sbd duk abinda take ciki saita sanarta kuma bata zartar da komai saida izininta

Jakadiya na zaune kusa da MAMAH tana mata hira

Shigowar FAATU yasa ta tsahirta tareda gaisata

FAATU ta amsa tareda zama kusada MAMAH

Ta zayyanewa MAMAH komai na abinda Mai martaba yatsara na bikin LAMIDO da *KUYANGA* Da kuma bikin nada LAMIDO Sarki da za,ayi

Jakadiya na qunsa tafuce da rawar jiki ta nufi dakin UMMAH Donkai mata Rahoto

UMMAH taga shigowar Jakadiya hankali atashe

Ranta yai matuqar baci dajin wannan kalami daga bakin Jakadiya kamar ta Dora hannu aka tayi kuka taji

Inama tana da damar da zata hana wannan Nadi

Jakadiya tace "Kibar komai ahannuna domin nima bazanso adora Lamido INA gani ba zanso ace Yarima ne zaizama sarkinmu

UMMAH ta gyada kanta tana fadin "Nagode jakadiya nasan ke me qaunata CE

Jakadiya taxo futa adakin kenan sukai kicibus da Yarima shima yashigo dakin UMMAH

Kallon kallo sukaiwa juna ko gaidashi Jakadiya ba tayiba kowa aransa akwai abinda yake ayyanawa akansu

Yaxauna akan kushin yana fadin "UMMAH naxo gaya mikine zantafi turai nan da kwana biyu nagaji da zama agarinnan babu masu sona

Tace "Kamar yaya babu masu sonka baya gamu nida mahaifinka

Yace "Hhhmmm adane kike sona amma ayanzu kam dagake har TAKAWA babu me kaunata kinrabani da gudan jinina kinkuma ki sanyawa Takawa ya yafemin yafaina fushi dani

Tace "YARIMA kai kake janyo komai gashi yanzuma zaka tafi kuma kasan bason tafiyarka yakeyiba Danhaka tafiyarka daidai take da karin wani laifin kanka sannan kuma abinda nayi daidaine agunmu nidakai domin inhar Yaron ya girma xai iya tasowa ackn wani yanaya na mugayen halayya ko kuma muzama abin kwatance

Inaso kacireshi aranka kafuskanci abinda ke shirin Kasantomu na Nadin Sarauta da mai martaba zaiyi akan kaninka LAMIDO

Yarima ya gyara zama da firgici akan fuskarsa yace "Da gaske UMMAH yanzu haka Takawa zaimini SBD yabakanta min rai. Tabbas saina dauki mataki sosai akai

Waye ya kawo miki wannan labarin?

Tace "JAKADIYA CE

yace "shikenan.


Yafuta yanufi Dakinsa yadebo kudi masu yawa aljihunsa yafito yanufi sashin da Jakadiya take

Cikin ikon Allah Yatararta Ita kadai kuwa

Tanaganinsa gabanta yafadi ganin irin kallon da yayi mata dazu tana ganin ko akwai manufarsa ta hakan

Yakalleta ba fara,a afuskarsa ya mika mata kudi ahannunsa yace "Karbi wannan !
Jiki na tsuma ta karba

Tace "na menene wannan?

Yace "Nakine aiki zansaki

Tace '"aikin meye hakan? Wannan uban kudi yafi karfina

Yace "Yanda kika zama makisiya shine nakeso ki kashemin wani nima

Ta zabura "Baxan iya ba walh

Yadaka mata tsawa "zaki iya !! Waishinma kinji kowaye?

Tace "waxan kashe?

Kaitsaye yace mata "LAMIDO!!

taji dirar Kalmar akunnenta tadira gefe tana miko masa kudin "karbi kudinka bazan iya kashe LAMIDO ba ka kaiwa wadanda sukai maka aiki akan MAHBUB suyi walh bazan iyaba

Yadaka mata harara yace "babu Wanda zansa yayi saike don haka kisani k'in yinki yana daidai da tonuwar asirinki

Yana gama fadin haka yajuya yabar ta tsaye atsorace take da wannan lamari ina ita ina iya kashe LAMIDO to yanzu yazatayi gashi tana bukatar kudin sbd yawansu yakai ace tagina kanta da rayuwarta na wasu shekaru toshin yanzu Yaya zatayi ? Rana zafi inuwa Quna!!

Mafita ce tazo mata arai gara taraba kudin biyu taje tasami Fadawan da taga yasa su kashe MAHBUB tabasu sutayata aikin


******

Abin Duniya yadami Yarima gashi da gasken Gaske Mai martaba yajuya masa baya ko gaisuwarsa baya amsa masa don hakan ma ya qudiri niyyar kawar da LAMIDO domin yazamo dolen sarki yanad'ashi agaba yakuma Auri *KUYANGA*

Shawara ya yanke natafiya Turai tun agobe domin in aka kashe LAMIDO kada adora zargi akansa gara ayi bayanan

Da safiyar Lahadi ya daga ko sallama da Mahaifinsa baije yayiba yabarwa UMMAH sallahun tagaya masa

Itako dama ranta baiso ba

Da kuwa taje ga sarki tagaya masa ko uffan baice mataba shiru yayi mata dole tabar maganar yariman ta tafi

Amma ta qudurci yin aikin Asiri atsakaninsu domin janyo soyayyar yariman azuciyar sarkin


Yarima Yana dira akasar waje Allah yahadashi da wata bakar fata Ta nuna tana muradinsa azahiri bama tasan shidin Dan sarki bane saida taga alamomi a Dan zaman da sukayi na mintina a Airport

Hindu "Yar Minister ce a jahar Kaduna mahaifinta me kudine sananne Alh Khalid Baffanyo

"Yar boko ce gata da jijji da kai da dagawa Amma yau sai Allah ya damketa duk yanda take wulakanta samari a garinsu sai gashi ayau Allah yasa mata Soyayyar Saurayin da batasan asalin saba tashi guda

Dayake yariman ma na mamajo ne tuni ya afka cikin sonta shima taringa kanainaya da kissa don yasota takuma yi sa,a

Har rakiyarta yanema gidansa takuma bishi


Saidataje gidansa ta tabbatar shidin Dan babban gidane ta gane dawa take tare Domin tafahimci da alamar Dan gatane kamar yadda take yar gatan babanta

Saida suka kadaita sannan yahau tambayarta meya kawota England ?

Tace masa tazo Hutu ne gun kawunta Wanda shiya riketa alokacin datayi karatunta acan

Takuma gaya masa asalinta da matsayin data taka na aiki domin tana aiki da Ministry of Health itace Director asashen kula da Asibitocin Shiyyar Su


Ya jinjina kai yace " Ina sonki zaki Aureni?

Da zakuwa tace "Kwarai kuwa inhar da Gaske kake na amince maka amma kada ka yaudareni bani da dadi

Yayi dariya yace " nima ba Dadin gareniba.

Tayi dariya kawai

Aranar ta tayashi kwana agidan sunyi romance amma basu zarta nan ba don ya ayyana aransa ita zai aura takwanta masa

Aranar sun tsaida magana zaizo nanda sati biyu Kaduna yagaida iyayanta zai kuma tura magabatansa

Tunda suka tsaida magana da Hindu shikenan soyayya ta dinke atsakaninsu akullum suna tare awaya ba dare ba rana

Shaquwa sukai sosai in basuji muryar juna ba basajin dadi

Tana daga Kaduna amma kowa nata yasan da Fara soyayyarta da yarima

Iyayanta harsun San da sunansa domin ta gaya musu tuni

Dama ita kadai suka Haifa itace shalele sunaji da ita basa son bacin ranta


Yarima yakasa sakat tuni yahado kayansa sai Nigeria

Amaimakon yadiro Kano saiya zarce Kaduna

Kai tsaye yabi kwatancen d tayi masa

Ta aika da mota aka daukoshi aka kaishi gidan

Yaji Dadin tarbar da tayi masa da yan gidan

Yai mamakin ganin shankwamen gidansu kamar gidan Gwamna ga tarin motoci kamar ana saidasu

Akaita kawo masa gaisuwa ma,aikatan gidan aka cika gabansa da kayan ciye ciye

A main falour aka saukeshi

Mahaifiyarta taje takuma yaba da zabin diyar tata

Saida yajira mahaifinta Alh baffanyo yadawo suka gaisa ckn mutunci

Dayake mutumne wayyaye tuni yace yabashi ita yakuma bashi sati yaturo magabatansa

Yarima yai na,am

Sunyi soyayya kafin yatafi da yamma yai mata sallama yabi jirgi yataho Kano


Yaringajin kamar karsu rabu tamkar Wanda tayi masa asiri yaringaji

Ransa Dari qal yasami Matar Aure yasan yanzu dole maimartaba zai sauko inyaji zaiyi Aure


Muje zuwa fans
[8/12, 10:51 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA* 📿





*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*HAPPY SALLAH*
Eid⁠-Mubarak to all the muslims all around the world. May Allah SWT grant us the ability to make the most of this years.




*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)



95-100

Da Isar yarima gida kai tsaye gun mahaifiyarsa ya nufa

Tayi mamakin zuwansa bai sanar mata ba

Yana murmushi yace "UMMAH dawowar gaggawace tasameni adalilin Matar Aure dana gamu da ita

UMMAH da mamaki tace " Matar Aure kuma yarima ?a INA?

Yagyara zama yazayyane mata komai

Tahau gyada kai tana jin farin ciki aranta domin jin yarinyar yar masu dashine kuma hakan yayi mata arai tafiso shima yariman yayi Aure kamar yadda LAMIDO zaiyi domin Aure yana karawa mutum martaba da kima a idon Al,umma abin tinkahon tane ace tayi suruka Yar babban gida ba "yar Bayi ba dama

Tasawa abin albarka tareda karfafa masa guiwa " na amince maka kayi Aure adaidai wannan lokaci Yarima domin makiya suji kunyar abinda ake shirin maka tunda nasan duk don abakanta maka aka shiryi Auren su balle anga kafito da maitarka karara ka watsar dasu zuwa gaba mushirya kutunguila akansu inhar Aka nada LAMIDO sarautar domin baxamu barsuba

Ya gyada kai yace "Nima akwai shirin Dana shirya akan LAMIDON, UMMAH saidai zan ajiye komai agefe sai bayan nayi Auren tukunna amma kiyi kokari Takawa ya karbi abin da muhimmanci ahada ayi tareda na LAMIDON domin iyayan yarinyar da Gaske suke asatinnan zasu Zuba idon ganina

UMMAH tace " kada kaji komai Aure fa kamar anyi Angama

******
Koda UMMAH tajewa da Mai martaba wannan zance Murna ma yayi domin yasan yin Auren Yariman kamar wata hanyace zatazo masa ta shiriya don haka saiya nuna amincewarsa da gaggawa tareda tsayar mata da maganar zai tura aje akai kudin Aure tareda tsaida musu rana daidai Dana LAMIDO

Taji dadi tayi masa godiya takoma yiwa Yariman Albishir

Da farin ciki yakwana jin antsaida masa ranar Aure sati uku masu zuwa

Yaiwa Amarya Hindu albishir

Ai ihu taringayi Dan dadi da farin cikin data tsinci kanta aciki

Tuni ta gayawa iyayanta tamkar suma sungaji da itan saigashi suma suna murnar

Ackn Satin kuwa Mai martaba ya Aiko batun nan Aure

Galadima ne da Liman Amintattun Sarki sukaje kai kudin Aure Dubu Dari biyar

Da kwatance suka sami gidan domin mahaifin Hindu fitaccene babu Wanda baisan Gidan Minista ba a A T/wada Kaduna



Anbasu an amince musu nanda sati ukun Dayake kanin mahaifinsa ne da Yayan mahaifin nata da Amininsa suka karbesu agidan Ministan

Anbasu tukuici me tsoka tareda karramawa domin da tsaraba aka rakosu da zasu koma

Kaji da cake da lemuka da turarika da shaddoji haka aka zubasu a but din motarsu

Koda suka koma suka rattabasa sarki abinda suka gano cewar iyayan yarintafa Sunada mutumci da Halin girma

Sarki yaji dadi yasawa abin Albarka

Zancen Auren yarima da LAMIDO yazagaya gari anata irgen kwanakin dasuka rage sbd irin shagulgulan da aka shiryi yi sbd nad'in da za,aiwa LAMIDO na zama sarki da zaiyi


Lefe ma yarima A England yatafi yahado

Shiko LAMIDO dayaje gun *KUYANGA* tambayarta yayi

"Gimbiya!

Takalleshi da murmushi kan fuskarta tana murza zoben hannunta da MAHBUB yabata kafin yarasu

Tace ahankali
" Harna zama gimbiyar ?ai naga Gimbiya Matar Sarkice wacce yakeso kuma

Yayi murmushi dama shidin ma,abocin murmushine yace "Zeenatu kenan ai kamar kinzamane Tunda saura kwanaki daga lokacin da Aka daura mana Aure nima naxama Sarki Kema kinzama Gimbiya tunda aranar za,ai Nadi

Ta gyada kai tanajin annashuwa aranta da kuma sonshi ackn zcyrta

Shima hakan yakeji aransa agame da itan

Yakatse shirun nata dacewa " Awace kasa kikeso ahado miki lefe?

Takama baki "Ni na isa? Wacece ni tab ahado anan

Yasha mur! Yace " keko kika isa kuma ke me matsayice da kima don haka daga yau kidaina ma daukar kanki maqasqanciya agidannan domin kintashi daga *KUYANGA* kindawo *GIMBIYA ZEENATU*

Tayi murmushi ita kanta sunan yayi mata dadi

Yaci gaba da fadin"kinaji ko zamuje Sudan ko Dubai inhado miki komai acan nida Abokina Safwan tare mukai karatu dashi acan mahaifinsa ne liman na gidannan tare TAKAWA ya biya mana zaizo kugaisa

Takawa yana sonki Zeenatu ki godewa Allah jarabtar da Allah yayi mk arayuwa tazame miki riba da ci gaba domin ayau yakirani yakaramin kudi akan Wanda yabamu na siyayya nida yarima yace ke tadabance inyi miki siyayya mekyau

Yakarasa maganar yana kallon kyakykyawar fuskarta yana murmushi

Itama murmushin takeyi tana fadin "Naji dadi nagode ayiwa takawa godiya

Yace " To ni zankoma

Tayi masa yar rakiya da baifi taku biyar ba ta koma tana waigensa

LAMIDO ya burgeta tabbas yanada aji ga iya magana da kalami duk macen dayace yanaso dole ta amsa domin shi din abin sone

Tana shiga Daki tafada akan gado tana fara,a

Zulaihat tabita da kallo tana fadin "Yarinya tashiga kogin soyayya tafito

Dafatan kinyo iyo kinkamo kifi?

*KUYANGA* tayi murmushi tareda tashi tazauna tana fadin "Zulaihat kifaye ma nakamo ba kifiba tabbas LAMIDO yatafi dani kamar yadda nima natafi dashi


Allah nake godewa da yabani wannan baiwar ta zama matarsa gashi Yace Takawa yana sona yakara masa kudi akan Wanda yabasu da yarima na soyayyar lefe

Mahaifiyarsa kawai nakeji bansaniba ko itama tana sona kamar yadda Sarkin ke sona?

Zulaihat tace "Hhhhmm Zeenatu kenan aike abar soce itama banajin zataki sonki tunda ta tako har gidannan tazo miki barka da gaisuwa Dan haka kigodewa Allah kawai

" Allah nagode maka.cewar *KUYANGA*

Zulaihat tace "Ga magunguna can inji Iya Sha,awa tace kada kiyi sake da kowanne masu kyaune akwai nasha da nono dakuma nasha da Zuma anjima zata kawo miki na tsugunno

*KUYANGA* takama baki " oh maganin mata kuma tun yanzun?

Zulaihat tace "Eh aishine daidai hakan kinga abin xaifi kamaki Sosai

" Hhhmmm Allah dai yasa ba daci

Zulaita tace "koma me gareshi haka zakisha tunda kinsan Halin tsoffin nan insuka bada Abu ba,ashaba fada zasuyi suce suna mana gata muna gocewa

*KUYANGA* Tayi murmushi tadauki magungunan tafara hada wa xatasha

******
Yarima yadauki wayarsa yalalubo nambar abokinsa SAHABI da suka Dade basuyi wayaba

Acan bangaren SAHABI yana ganin kiran Yariman yayi murmushi yadaga yana fadin" Dama kana da nambata kamance dani

Yarima yace "inada ita mana fushi nayi dakai na abinda kayimin amma yanzu na huce Dan haka Ina gayyatarka Aurena karshen wata

SAHABI yayi murmushi yace " Allah yasanya Alkairi nima Auren zanyi nanda sati mezuwa kafin nakama

Yarima yace "Shegen kaya wato banda nakira bazanjiba kenan ?lallai na yarda karikeni aranka SAHABI

SAHABI yace " ba haka bane yarima Aurenne ba Wanda nakeso ba Hadani akai da yarinyar diyar kanin mahaifina ce ita ke sona

Dariya yarima yabushe masa yace "sunmin daidai walh domin insun kyaleka " yar talakawa zaka dauko musu banza me sakaran ra,ayi

Sahabi yace "kai " yar INA zaka aura?

Yarima yabashi labarin Hindu da yanda suka hadu a Airport a England

SAHABI yace "Hhhmmm to bagiringirin ba dai tayi mai

Yarima yace " oho dai nafika tunda ni Auran Soyayya zamuyi

"Nima bawai kinta nakeba tunda yar 'uwa tace

Ina Zeenatu naji ance abinda ta Haifa yarasu

Yarima yace " Eh, Sunkusa Aure da LAMIDO...

SAHABI yakatseshi da sauri "ya akai hakan dama soyayya sukeyi?

Nan yarima yazayyane masa komai

SAHABI yace " Gud ammafa naji dadi LAMIDO yaburgeni Allah yasanya Alheri

Yarima baikulaba yai masa sallama

Acan kasan ransa soyayyar Zeenatu na nan baxai mantawa

******
Anata shirye shiryen biki akowane bangaren

Shi yarima agidansa na cikin gari zai zauna baiyda ra,ayin zama acikin gidansu wai kada atakura masa shida amaryarsa

Shiko LAMIDO sashi guda aka gyara masa agidan me dauke da dakuna agidan gidan yasha gyara babbane dama ba kowa ciki

Aka zuba komai na alfarma agidan

Lefe yazo daga Dubai akwatuna goma Sha biyu cike fal da kaya tsadaddu

Komai dozinne ciki koina acikin gidan da wajen gidan zancen kayan lefensa akeyi domin sunhadu sunburge kowa

Saida aka kaiwa takawa yagani yace sunyi yasa albarka kana mata suka hadu suka dauka bayan Su MAMAH DA FAATU sun gani aka kaiwa KUYANGA

Tsoffinsu sunsaka albarka sunyaba Angyagije Zeenatu anfiddata kunya dukda sunsan arina

Shiko Yarima karya yahada ackn kayan duk don ace nashi sunfi na LAMIDO

Harda key din mota yasaka akan lefen mahaifiyarsa ta saka takardun gida duk akan lefen gudummawarta duk don mutane suga na LAMIDO lami ne sannan su burge mutan Kaduna



Amarya anata rawar kai anatashan magungunan karin Ni,IMA da tsukewa sbd gurin anshigeshi

Tun fara karatunta a Abroad tayi soyayya da wani Anwar yamaisheta tamkar mata ta amince masa daga baya ya yaudareta yana gama karatu yakoma kasarsu yamance da ita

Shiyasa data hadu da yarima takasa ta tsare saida taga natsaida lokacin Aure sannan hankalinta yakwanta

Duk kashe kudin da akai alefenta baisa sunyi rawar jiki ko an yababa tunda su ba farin shigar komai bane ita kanta motocinta biyu na hawa tanada gidaje kuma

Aiko dai yan kawo kaya suka koma jiki asanyaye danma anbasu tukuici me tsoka

Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya

Allah yakawomu wannan rana

Ranar Asabar takama ranar daurin Auren da nadin sarautar

Ancika agdn sarki anata kade kade da bushe Bushe da algaita LAMIDO yasha kwalliyar sarakai

Yayinda yarima yai tashi ta angwaye daidai misali ba yabo ba fallasa yasha tsadaddiyar shadda babbar Riga d yar ciki

Saida akayi nadi LAMIDO yazama sarki sannan aka daura auransa da KUYANGA kana akayi shagulgula sannan wasu suka dunguma da angoma Yarima suka tafi daurin Aurensa Kaduna

Andauro Aure antaho da Amarya a ranar domin sai dare suka iso aka ajiyeta a gidansa dake GRA

Itako KUYANGA data tashi daga wannan suna daga yau ta tare ackn gidan sarkin A gidan mijinta LAMIDO daya zamo sarki ayau



To fans saimu Tara a page din gaba *GIMBIYA ZEENATU* Cigaban KUYANGA


Wanda zakuji badaqala da cakwakiya ackn Wanda nake muku zaton yafi wannan Dan haka kada kubari abaku labari

Taku har kullum Auntyn Sayyada da Shahida
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment