Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daureta dayawa.

Yaci gaba da cewa"Abinda na fahimta zuwan yarinyar nan yana so ya canza kyawawan halayenki na Arziki haba me Babban suna,ina hankalinki yake? ni ayanzun da kika ganni murna nake na samu diya mace agabana da nake da muradin samunta tuntuni,kinfi kowa sanin yanda nake kaunar naga inada 'ya mace amma Allah bai bani ba,walh a yanxun haka bana yiwa yarinyar nan kallon matar Aure na sai 'yar cikina,Amana kuma take agurina atunani na fa nayi tsammanin zaki tayani rikon Amanar nan,kuma azahiri kina nuna mata kaunar zama da ita da hakan yasa itama ta saki jiki dake umman ta,sai gashi a bayan idonta kina nuna fuska biyu,nafiso kitsaya aguri daya ki nuna mata kauna ta fisabilillahi ko kya shiga Aljanna salin alin babu zunubinta akanki,ki daure ki cije kamar yanda nasanki tun afarko da dauriya akan kishi.....tayi saurin dakatar dashi "walh ni ba kishinta fa nakeyi ba akwai babban dalilin dayasa nake hakan.

yace"to meye dalilin da baza'a iya gayamin ba,nifa babban masoyin ki ne,abokin shawararki uban yaronki kuma dan,uwa agunki haba uwar gidana me halin kwarai bana jin dadin yanda kika birkice min akwana biyun nan fa.

har ga Allah tanajin dadin yabon da yake mata ita anan ma yake samo lagonta don duk yanda takejin zafin abu daya kalailayeta shikenan take hkr ta saki.

murmushi tayi tace"to nidai ko ma meye abar wannan batu kuma kasa aranka nima bana kishi da 'yar gudullen taka.

Shima murmushin yayi yace"Inama kema zaki dawo fada mata wannan suna da naji dadin hakan da kin kara faranta min sosai matata.

Tace"ikon Allah wai to meye dalilin wannan sunan,?

ya gyara zama yace"Badda bami nakeso nayiwa jama'a inaso kowa yasan ina son Jiddah agidannan amtsayin 'ya.inaso itama tasan a matsayin 'ya nake kallonta wannan shine dabarata kuma nasaka gobe idan an sauko sallar juma,a ayi shelar sunan jiddah ya dawo 'Yar gudullen sarki, wato gudaliyata da nake jinta araina daya tilo agareni.

murmushi tasakeyi tace"Lallai kana so ka haifar da wani kishin anan gaba kashi biyu.

Da mamaki yace mata"Kamar yaya kashi biyu,?to da ina da ina?

itama gyara zaman tayi tace"na farko kasan matarka Iyami tana da tsananin kishi zata iya tsangwamar 'yar taka.sannan kuma yarima idan yadawo yatarar ka canza soyayyar da kake masa da ta gudaliyar taka to tabbas bazaiji dadi ba tunda a yanda ka daukaki abin sai ayi zaton baka da d'a ko 'ya ne aduniya sai ita kawai.

girgiza kai yahauyi yana fadin"wannan ba dalili bane dole zaiyi uzuri idan ya fahimta nasan yana da hankali bare yanzun yakaro hankali da ilimin zaman takewa haka zalika yarima me tausayi ne idan yadawo yaji batun gudullena na maraici natabbata zai tausaya mata.

Tahau gyada kai tana fadin"Haka ne na yarda da batunka amma matarka fa,?

yace"to ai ita ba komai bace akan sabgar gidana tunda bata nuna kulawarta akaina da soyayyarta akaina sai sarautar kawai take so da arzikin gidan duk rufin asirin iyayenta amma tana hangen wani tamkar bata taso cikin arzikin ba,kuma indai tace zata takurawa gudullena to tabbas nima saina takura mata don bazan dauka ba.

Fulani tace"hhhuum Maganar karatun da nakeso atura gudullen taka nakeson jin ina aka kwana,ka gama yanke shawarar ne ko yaya,? saboda munyi magana da yarinya ta nuna tana son tayi dogon karatu arayuwarta kuma kasar da yarima yake takeso.

Kura mata ido yayi kana yaja ajiyar zcy sannan yace"wannan nasan duk shirin kine kuma ban amince ba,idan ina bin abinda kikeso nima dole kibi abinda nakeso nima,na gama kansile maganar babu inda gudullena zataje so nake na jajirce na tsaya tsayin daka naga ta sami tarbiyya agaba,inyaso idan ta girma takai munzali sai in sahale mata Auren kaina inbata wanda takeso inta fito dashi amma yin nesanta damu za.a iya samun matsala arayuwarta kuma Allah mu zai tambaya akan tarbiyyarta kuma kema kinsan da hakan dan haka dan Allah fulani kibar maganar nan kitayani renonta kafin girmanta.

Fulani tace"to naji na kuma yarda na bar zancen saidai inaso ka kara gaskata min kalmar daka faranta min rai da ita har zcyrka ka fada kuwa ko kawai ka fadane dan inji dadi zaka sahale mata Auren naka agaba kayi Alqawari,?

ya gyada mata kai yana fadin "Nayi Alqawari duk rintsi duk tsanani bazan karyaba.

tace"To Alhamdulillah nikuma insha Allahu zan yar da komai intayaka renon yr rikon taka zan dage wajen baiwa Yar gudullen taka tarbiyya kamar yanda ka roka.

yace"to nagode Allah yatayamu riko yabamu ikon cika Alqawarin.

Tace "Amin.

*********
Kamar yanda Takawa ya fada ya kuma Rattabawa jama,arsa cewar ayi sanarwar jiddah ta dawo 'yar gudullensa haka kuwa akayi ana idar da sallar Juma,a akai shela akan canjin sunanta.

kuma a yammacin aka tashi mutum uku cikin fadawa suka shishshiga lungu da saqo na cikin gari cewar Jiddah 'Yar sarki dayake riko diyar Dan'uwansa anyi mata canjin suna ta dawo 'Yar GUDULLEN SARKI kamar yanda sarki ya biɗa aringa gaya mata saboda soyayyarsa gareta da matsayin 'yar cikinsa da tadawo.

haka kuwa lamarin ya juye akoina zancen kenan har wasu suna ganin zata iya kwace soyayyar da sarki kewa D'ansa yarima.

A cikin gidan sarki kuwa a bangaren Amarya Iyami wannan abu bai mata dadi ba don tayi fassara akan hakan kala kala.

har bore taje yiwa sarki akan ta kansile wannan sunan.

baice mata uffan ba kam saida tagama maganganunta da koke kokenta akan ita yarinyar nan batayi mata ba.

ya jinjina kansa yace"nikuma yarinyar tafi gaban kowa agidan nan akanta zan iya yiwa mutum komai,Yar gudullena daya take tamkar da dubu wanda duk keson bacin ransa to yaringa tabo ta yagani.

tayi kwafa tace "kana nufin kenan daga zuwanta gidan tafini matsayi kake nufi,kawai naga alamar dan ban taba haihuwa ba shiyasa ban isa komai agun ka ba to walh na fada na kara na tsani yarinyar nan.

ya dago a fusace yai mata kallon banza.

ta tashi da jan ido ta fuce fuuuu


tayi sashinta ranta na mata quna.

daga can nesa Jakadiyarta ta hangota aiko da sauri ta nufi bangaren uwar dakin nata don jin meya fusata ta haka a wannan lokaci data san yau ita ke da sarki amma alamu na nuna ansamu saɓani.

Tana zuwa ta tarar da ita ta zabga tagumi tana ta goge hawaye.

gurfana tayi agabanta tana zuba mata banbadanci da rarrashin ta "ranki ya dade hankalina yatashi ganin yanayinki awannan hali,Allah ya huci zcyrki uwar dakina kiyi hkr ki kwantar da hankalinki kinsan dai kinada hawan jini banason damuwarki ko kadan daure ki gayamin meya faru dake wala Allah insamo mana mafita uwar dakina.

ajiyar zcy taja tace"jakadiya Takawa baya darajtani akan yarinyar can komai ya fito bakinsa gaya min yake sbd bantaba haihuwa ba walh da ace kudi na siyen haihuwa da tuni na tara yara agidannan da ba,ai min cin fuska akan wata shegiyar yarinyar karereba.

jakadiya tayi saurin dora hannunta aka kirjinta na firgici tace"badai 'Yar gudullen sarki ba.

cikin jin haushin sunan dai tace mata"ita mana, walh jakadiya na tsaneta sosai ba da wasa ba zan iya salwantar da rayuwarta walh sbd naga zata iya zamemin masifa agidan nan akanta sarki zai iya sakina nasan da hakan ya kuma nunamin azahiri nagani.dan haka kibani mafita jakadiya inba haka ba zan iya hadiyar zcy inmutu akan yarinyar nan.

jakadiya taja ajiyar zcy tace"wannan abune me sauqi kwantar da hankalinki uwar dakina akwai mafita akusa ma kuwa muda muke da bokanya GOGAL muke da Malam Buba me gani har hanji haba uwar dakina kinsan fa komai kikeso ayi miki akanta zasui miki akan lokaci kalilan.

ajiyar zcy taja tace"naji jakadiya,yaushe yakamata muje gurinsu dukan ayi min maganinta dan rubdugu nakeso ayi a aikin agigita ta fice agarin gabaki daya.

jakadiya tayi dariyar mugunta wawulanta ya bayyana tace"Ai ko ayanzun kikace aje a shirye nake uwar dakina.

Amarya iyami ta gyara zama tace"Hhuumm mubari gobe mufita yanzun bani da damar zuwa tambayar fita gun takawa sai ya huce.

*******
adaren iyami na so taje ta sami mai martaba kan tana son fita amma batasami damar nan ba sbd tana shiga take tarar dashi shida 'Yar gudullen tasa yana mata hira ta ba dariya ita kuwa tana ta kyalkyalawa

sau biyu taje adaren amma bata sami damar zama dashi ba tana shiga yake hade rai haka zalika gudaliya ko kallonta batayi canza fuska ma takeyi kamar zatayi kuka gashi takawa yaqi cewa ta fita

hakan yasa a zuwanta na karshe data gaji da zama ta tashi fuuu tafuce afusace.

shikuwa ko ajikinsa dan dama ba wai ta saba bashi kulawa tayi ba bare ya damu shikuma aduk lokacin dayake zaune yana hira da yar gudullensa yana cikin nishadi baya son tsahirtawa.

ko Fulani ayanxun intashigo ta tararsu suna hira da yar tashi tayasu takeyi in tatsuniya yake mata itama tsoma baki takeyi ayi da ita,ta fahimci yin hakan ne kadai ke faranta ransa shiyasa ta zubda makaman.

Sarki nayiwa Yar gudullensa wani azababben so wanda ko yarima baijin yatabayiwa hakan amma duk wannan abu dayakeji akanta bawai son sha'awa ko dan da auransa akanta ba bane Aa yanayine kawai sbd sabo da haduwar jini kuma yanayi matakallon 'yar cikinsa.

A cikin satin yarima kuma yayo wayar cewar zai zo gida hutu zaiyi wata guda idan yazo din, wanda idan yakoma ne zasu gama karatun duka yadawo gida.

aiko gida yadau murna duk iyayen nasa suka shiga shirye shiryen Zuwan d'an nasu

Yar Gudullen sarki tafi kowa zakwadi da murna mafarkin yayan nata dama takeyi kullum.

burinta akullum dama ace Yaya yarimanta zai dawo.

dayake kusan kullum sai Ummanta ta hadasu awaya sunsha hira tayi ta masa surutai na son zuwa kasar dayake itama tayi karatu ko taita bashi labarin kawayenta data baro na garinsu shidai biye mata kawai yake sbd surutunta dayanda take nuna tana son ganinshi ke burgeshi yanajin dadin hakan.

sunyi sabo ta waya gashi tasanshi a hoto amma shikam bai san fuskar kanwar tashi ba

acan bangaren nashi shima yana dokin dawowar tashi kasar don Ganin sabuwar kanwar tasa wato 'yar Gudullen Sarki.

muje zuwa.....



Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group

WHATSAPP NO:+2349030159301


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment