Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya
lallausan kallo cikin kwarewa da kissa, ‘yar
zolaya ki zolaye shi cikin sigar wasada dan ba
shi dariya kadan a cikin hira da‘ yar shagwaBa
cikin sigar jan hankali, da kuma kamun kai a
matsayinki na yar
mutunci. Wannan sone kadan daga cikin
abubuwan dake sawa budurwa ta mallake
saurayi, wallahi Saudat da soyayya nake da an
sha kallo".
Saudat ta yi murmushi kafin tace“To me , yasa
ba kiyi?” ’
Shukura ta tabe baki, ta ce
“Wallahi Abba ne bai bari ba, amma duk da haka
ina dan taBa wa sai dai a waya ne kawai, shi ‘
ma Ummi ba ta sani ba, nasan da ta ci ubana
don , har: yanzu ban kammala digiri dina ba fa” .
Saudat ta nufi kewaye tana fadar
~ . :‘Ke kima gode wa Allah kin samu an tsaya
miki kinyi karatun"
-. Ta tuna ita nata ubanda kansa ya hana ta ‘
karatu, yasa‘yar uwarta makaranta tun daga"
firamare har sakandire, amma ita bai saka ta ba.
‘ .Ta lumshe idanuwanta a daidai lokacin da ta
sakar
wa kanta shawer
‘ » Bayan tagamo wankan tafito tasamu har
Shukura ta gama fldda mata kayan da za ta
saka, *
wata hadaddiyar’ doguwar riga ce wadda aka yi
wa adon jajayen fulawowi sannan aka jejjera
ararcn duwarwatsu a ciki, rigar ta yi masifar kyau
irin mai kama mutum ce daga sama daga qasa ta
bude sosai tana da dogayen hannuwa irin masu
tsukewa daga qasa su ma an qawata su da adon
rigar, sai kallabin rigar, Shukura ta hada mata da
wani takalmi fari mai dan tsinin dunduniya kadan.
Saudat ta zauna tana fadar.
“Ke kuma wannan ce ta burge ki?”
Shukura ta ce, “Ai ki sa ki gani ba qammin kyau
za ta yi miki ba
' Saudat ta zauna bakin madubi tana murza mai
a jikinta. . Shukura ta mike tana fadar. ‘ '
“Tsaya ki gani Saudat in miki makeup ” Ba musu
Saudat ta zuba mata idanuwa kawai tana
kallonta, kwalliya sosai ta yi mata da
hodoji da air pencil, air liner, jan baki mascara da
' sauran kayan kwalliya.
Ita kanta Saudat tsaye ta yi tana kallon kanta a
madubi, ta waigo da fara a a fuskarta tana '
kallon Shukura ta ce
“Kai k0 dai kin je makarantari koyon
kwalliya ne? ai wannan k0 shago ba za su nuna
miki komai ba”. ‘
Shukura ta yi dan'dariya kafin ta ce_
“Ke kuma kin hadu kamar sarauniyar qasar waje
Duka suka sa dan'ya, Saudat ta janyo kayan ' za
ta sa, Shukura ta ce
“Ke tsaya-tsaya".
Ta dauko wani sabon turare irin mai laushinnan
mai suna soft ta gogamata a dukkanin gabobin
jikinta har: zuwa bayan kunne wuya, mara da
qirji, sannan ta ce
“Sanya kayan".
Tana sanyawa ta kawo turaren the warior body
Spray ta ba ta ta fesa a can cikin jikinta,
sannan ta mika mata turaren x5 ta fesa wa
,kayanta, ta ba ta qananan ‘yan kunne ta makala’
a kunnenta, sannan ta gwada mata irin nadin da
za ta yi wa gyalen rigar irin na ‘yan matan
jami’a, ita kanta Saudat din ta san ta yi kyau na
ban mamaki, don haka ba ta da bukatar wani ya
Kara fada mata
Shukura ta janyo jakartata ciro mouth freshner
mai qamshin water milon ta feffesa mata a baki
don Kamshi da dauke datti, ita kanta yau Saudat
ba za ta ce ga kalar Kamshin da ta ke ba, tana
cikin sa takalmin Dr‘ Mariya ta leko tana fadar.
‘ “KarBi ga waya ana kiranki”. ‘ Saude ta karba
ita kuma ta juya ta yi gaba abinta, Dr Ahmad ya
ce
“Ga ni a qofar gidanku”.
Saudat ta cr, “To minti biyu”, ‘
Ta kashe wayar tana kallon Shukura ta ce
Yar uwa ga shi a waje”.
Shukura ta mike, “Bari in je in shigo miki da shi".
Saudat ta ce “Yauwa”.
Shukura ta ja qaramin mayafinta ta dora saman
kanta, sannan ta fice, tunda Dr. Ahmad ya. hango
ta zuciyarsa ta ba shi ‘yar uwarta ce saboda
yanayin jilkinsu iri daya ne dogaye duka, amma
basu da kwari sosai, suna da doguwar fuska mai
dauke da dogon hanci da dan siririn baki, don ita
Shukura ma manyan' idanuwa gare ta sosai
masu kalar kyau, farare tas~ tas da su, don dai
ita baqa ce amma irin bakinnan mai haske wato
black beauty kenan, sabanin Saudat dake jajawur
kamar a taBa jini ya' fito.
Shukura ta hango wata tsadaddiyar mota
' mai kyan gaske, sabuwa dal mai kala da
yanayin jirgin sama. Shukura ta ja. ta tsaya don
ba ta taBa
"ganin irin motar ba tunda ta ke a duniya, ga shi
farar motar mai bakin gilashi ce, baka iya ganin *
Wanda ke ciki
Da hanzari ta ga an bude qofar motar kujera mai
zaman banza, wasu mutane su biyu suka fito da
hanzarinsu suka bude gidan baya na motar. " ‘
. A hankali yasA qafarsa guda ta fito
Qasa sosai, sannan ya sauko da gudar ya fito
gaba daya. Shukura ta zuba masa idanuwanta
kyakkyawa ne na qarshe, abin da zuciyarta ta
fada ke nan, ta nufe shi da nutsuwarta tana
fadar. “Sannu da zuwa, ba zaka shigo daga ciki
ba?” ’ . Dr. Ahmad ya girgiza mata kai kafin ya
ce. “Mata: tana da girma ne sosai motar, ba
kowace haraba ba ce za ta isa a yi kwana da ita
a ciki ba, muje kawai”.
Shukura ta yi gaba, ya rufa mata baya har cikin
qawataccen falon, ta yi masa masauki sannan ta
wuce kicin ta yi wa Momy magana ta nufi daki ta
kirawo Saudat wadda ta yi zaune gaban madubi
ta zuba tagumi da hannuwa bibbiyu tana kallon
kanta, amma a zahiri zuciyarta ta lula duniyar Dr.
Ahmad wai yau gani ta ke abubuwan ‘ suna
faruwane kama a cikin mafarki, wai yau ita ce za
su hadu da Dr. Ahmad a matsayin masoya to ke
bata san lokaCin da tayi wani murmuShi ba,
Shukura ta tsaya daga gefenta tana fadar ‘ ‘ ’ “To
saiki tashi yana falo”.
Saudat ta ji wani irin yarr a jikinta, ta ta miqeta
nufi kofa har: za ta fita ta juyo tana kallon
Shukura ta ce
“Don Allah ki zo ku gaisa".
Shukura ta ce, “Ki fara zuwa ina tafe
Ba ta sake magana ba ta juya tafice ta same shi
a hakince saman daya daga cikin kujerun dake
falon, yana latse~latse a wayarsa. Tana shigowa
kamshin turarenta ya daki hancinsa, ya dage da
sauri yana kallon mai tahowar, suka yi ido hudu.
‘ Saudat ta yi wani murmushi ta juya da sauri
ta nufl falou Momy ta fada mata tana nada
kallabin jallabiya a kanta, Saudat ta ce
“Momy ga shi yazo
Tace“Kije yanzu zamu fito da Alhaji sai mu
gaisa”. *_
Saudat ta juya ta yi gaba
A tsaye ta iske shi a yanzu, ya zuba ‘_ hannaye
cikin aljihunsa, Saudat ta Karasa har inda ' yake
ta zube saman gwiwoyinta tana fadar. " "
‘ “Sannu da zuwa Yallabai, barka da ina wuni
Dr Ahmad ya zuba mata kyawawan » idonsa
masu kamar an diga gold yace.
Shi ne ki fito kika koma don kija min 'rai saboda
kin sani sarai ina cikin qishirwar son ganinki k0?
Allah yadda na mike din nan na rantse da sai dai
ki gan ni bayanki”
Ya bude hannayensa
“Taho gareni don Allah Saudat’
; Saudat ta yi saurin rufe bakinta tana dariya, Dr.
Ahmad ya zauna ya tattara nutsuwarsa a kanta,
kafin ya ce
“Saudat kin qara kyau wallahi kamar ba keba,irin
wannan kamshi haka aisaikija intare a nan” .
Murmushi kawai ta yi, Dr. Ahmad ya gyara zama
kafin ya ce
“Wallahi Saudat farin cikina a yau ba zai misaltu
ba, duk yadda zan kwatanta miki ba zaki gane ba,
don Allah ina Momy dinmu in sa ta cikin
idanuwana ko na ji sanyi, wallahi ba kiji da na ji
muryartaba sai na ji kamar da Mom dina nake
magana, wallahi na ji ina qaunarta ni ma”.
Saudat ta yi murmushi tana amsa sallamar
Momy wadda suka shigo cikin falon, Alhaji Ashiru
ya amsa.
“A‘a wa nake gani yau a gidan namu, wai.
Ahmad kai ne da kanka?" Dr Ahmad ya zabura ya
miqe tare da washe bakiyana fadar ‘
Lah wai Daddy da ma nan ne gidanka na
Katsinan ashe?” Alhaji Ashiru ya ce“Ai k0 dai nan
ne ai shi Alhajinka ya sani, don har ya ya taBa
zuwa Dr Ahmad ya ce, “Ikon Allah ashe gidan
Daddyna nazo . ~ Ya durqusa yana gaishe su,
duka dadi ya
cika su don haka cikin fara‘ a suke amsawa.
Alhaji Ashiru ya juya yana kallon Dr Mariya ya ce
“To ai ke wannan tuwona maina ke nan, wannan
dan Yaya Alhaji ne babban wanmu wanda , aka yi
wa aure tun last four years, bai taBa zuwa‘ gidan
nan ba tunda muka yi aure, kullum in nayi
magana sai ya ce kishi yake taya Hajiya, to yau
ga
' shi har cikin falonki tasa ta kawo shi, don haka
kema sai ki Juya kambunki". ‘ Dr. Ahmad yana
murmushi ya ce.
“Lah wallahi kawu ba haka bane kasan abubuwan
ne sai a hankali, amma dai tuba nake ai yanzu
zan rinqa zuwa” . .
Dr Mariya ta ce “Ai dama :zaka rinka . zuwa
mana tunda yanzu taka ta kawo ka” .
' Duka suka sa dariya ban da Saudat wadda
tunda ta sunkuyar da kanta ba ta kara dagowa
ba,
. sai ta koma ita ce sarakuwar. su kuwa hira ce
sosai “suka Barke har Shukura ta shigo aka dasa
da ita, sai
lokacin ne Saudat ke dan sa baki kadan~kadan
har
sai da aka kira sallah, sannan suka fice suka tafi
. don sauke farali. Suna dawowa Momy tasa
Mairo
ta kawo abinci aka da dasa wata hirar a nan
suka"
tsaida ranar zuwa qauye sati mai zuwa don
tsaida , maganar auren.
Dr. Ahmad bai bar gidan ba, sai qarfe goma na
dare, Saudat ta yo masa rakiya har bakin gate,
’ya tsaya yana kallonta muryarsa a sanyaye ya
ce
“Yau zan yi bacci har da munshari Saudat na
tabbatar a wannan karon zan mallaki abin da
zuciyata keso, lallai na yarda babu abin daya fi
qarfin Ubangiji k0 ba haka ba my dear"; ,
Saudat da ke faman wasa da ‘yan yatsun
hannunta ta yi murmushi kawai ba tare da ta
tanka masa ba, Dr. Ahmad ya bi ta da kallo
gabadaya idanuwanta na saman yatsun hannu
nata, ya miqa hannunsa ya riko duka hannayen
ya janyo ‘ ta gabansa.
Da sauri ta waro idanuwa tana kallonsa, ya sakar
mata murmushi tare da hure mata idanuwa' da
sauri ta idanuwanta tana murmushi qasa-qasa “ ‘
ya ce. * . “Ki bari sai kin koma gida kin kwanta
sannan ki bude kin ji? Alkawari?”
’' Ta daga masa kai alamar ta yarda sannan . ya.
sakar mata wani siririn murmushi kafin yace
'Sida safe, ki kular min da
kanki, bacci mai dadi". . Ya shafi kanta daidai
lokacin da ta ke
Qokarin juyawa don haka ta qara sauri yana
kallonta harta bace ya sauke wata nannauyar‘
ajikyar zuciya sannan ya juya ya fice. _ .Bacci ya
kaurace wa idanuwan Saudat, ji ta‘
ke tamkar' ta taka rawar murna duk ta damu
Shukura da juye~juye, sai faman juya takardar da
‘yasa mata ahannunta take koda batasan meye
ya rubuce ba, amma ta san cheque ne na banki,
don
haka yau zuciyarta fes ta kwanta. Tun da gari ya
waye suka hau shirin tafiya
Qauye, Shukura ta shirya cikin wasu riga da siket
na wani swiss‘ lace mai shegen kyau da tsada,
dinkin ya bi jikinta ya hau kalar fatarta
kasancewar leshin light blue mai adonda "ruwan
qasa-kasa, gashin nan ya sha gyara an daure shi
a gefen kunne sannan ta nada daurin kallabinta
mai suna touch Iight irin na ‘yan matan yanzu. .
Gyalenta da takalminta duk farare ne, sai
‘dankunne da sarka na gwal tare da abin
hannunsa ta yi kyau sosai kasancewarta dama .
kyakkyawarce ajin farko ’ Saudat kuwa riga da
siket neta saka dark
brown mai adon yardin gwal a jik; irin na Indiya
.ta gyafa gashin kanta ta daure shi a baya ta
saki jelarsa' a gadon bayanta sannan ta nada
gyalen _ kayan saman kanta ta sake shi bai rufe
kwallliyar kayan ba, siririn dankunnenta na gwal
da abin ‘ hannu wanda mahaiflyar Dr. Tasa ba
tasa abin wuyan ba saboda rigar kayan ta rufe
har wuyanta ta kawo takalminta golden mai
tsinin dunduniya ba qaramin kyau ta yi ba, yar'
indiya sak!
Sannan suka fito falo inda Momy da Alhaji ke
jiransu, Saudat ta bi Momynta da kallo wadda ke
sanye da riga da siket na atamfa sai ta dora '
baqar doguwar riga a sama mai adon jajayen
fulawoyi irin mai tsukakken hannun nan ce
Ta‘ daura kallabin atamfar a kanta sannan ta
dora kallabin rigar a kan nata, ta saka takalmi da
jaka jajaye, hannunta da kunnenta da wuyanta
ma gwal ne mai tsadar gaske. Haka su Nabil da
Nabila sun hade cikin ‘yan kanti kamar ~ ‘ ba"
yan Nageria ba. ’ .
' Dadi ya cilka Saudat, wai nan duk yan uwanta
ne da mahaifiyarta, wayyo rayuwa ke nan, sai da
suka gaisa da Momy da Alhaji sannan ta bawa
Momy cheque din da Dr Ahmad ya bata Momy ta
warware tana dubawa tare da zare ido, ta ce
“Kai wannan kudin Sunyi “yawa is too much, ya
yi yawa abin duba ka gani Alhaji five ,
Hundred thousand fa”.
‘ Alhaji ya ce “Ta gode kwarai ai kyautar soyayya
ba ta yawa; ki bude mata account kawai ki zuba
mata a ciki
. Hajiya ta amsa da, “To”. Sannan suka mike
suka nufi tebur suka karya gabadaya sannan
suka fice su shiga wata Katuwar
motar Alhaji suka tafi humer jeep baka mai kyan
gaske, shi ya ja su da kansa, har zuwa cikin
Dandagoro. Jefi-jefl akan taBa hira inda Saudat
saurarensu kawai take, amma z'uciyarta ’ ta
shiga duniyar tumani da sake-sake ganin
al’amuran ta ke tamkar a cikin mafarkinta suke ,
Faruwa jira kawai take ta farka a kowane
lokaci_ba.
. ‘ALHAMDU LILLAHI Masha Allah.
Mu hadu a littafl na HUDU kuma na karshe ldan
mai kowa mai komaI ya kai mu
NAKU HAR KULUM A,,I,,S
TABA KA LASHE
kadan daga cikin yar tallah book4
Dukkansu suka fito suka shga gidan saudat na
riqe da hannun nabiLa shikura na gefenta sai
nabil a gefen momy alhaji ashiru ya zauna yana
jiransu a mota sallamar da sukene ta janyo
hankalin inna laure take kuryar daki tana tattara
komatsai tayo tsakar gidan tana fadar marabanku
sannunku dai
Turus taja ta tsaya gamida dafe kirji cikin tashin
hankali da kyarmar murya ta soma magana su
waye ku daga ina?
Momy ta gyara tsayuwa gamida cewa ikon allah
abin da mamaki idanni baki ganeniba ai ina
tunanin wannan yarkice kya ganeta tayi maganar
tana nuna saude inna laure ta fadi qasa jabar
kamar an tile kayan wanki tana kwalama malam
bala kira malam bala ya fito daga kewaye a
gigice hannunsa riqe da buta yana fadin kai laure
wannan irin ihu haka ai saikisa juwa ta kwasheni
in fadi babu gaira babu dalili
Inna laure ta dinga nuna masa momy tana fadin
malam dubamin ka gani wacece nake gani kamar
maria
Cikinfirgici malam bala ya siki butar ta fadi facal
yayo kansu yana fadin wacce mariyar kike nufi
‘YAR TALLA- BOOK4
CHAPTER29
ZUciyar Saudat ta shiga duniyar tunani da sake-
sake ganin al’amuran ta ke
tamkar a cikin mafarkinta suke faruwa, kuma har
yanzu ba ta fidda rai ba da za ta farka a kowane
ba lokaci. Minti sha biyar ya kawo su har kofar
gidan Malam Bala, inda Saude ke nuna masa
hanya har suka iso, ya faka motarsa a qofar
tsohon gidan.
Dukkansu suka fito suka nufi gidan, Saudat na
rike da hannun Nabila, Shukura na gefenta, sai
Nabil a gefen Momy, Alhaji Ashiru ya zauna ya
jira su a mota.
Sallamar da suke ce ta janyo hankalin Inna Laure
da ke quryardaki tana tattara komatsai, ta yo
tsakar 'gidan tana fadar, “Marabanku; sannunku
da...”
Turus taja ta tsaya tare da dafe qirji cikin
tsananin tashin hankali da kyarmar murya ta
soma fadar. “Su wayr ku, daga ina?”
Momy ta gyara tsayuwa kafin tace “Ikon Allah
abin da mamaki, idan ni ba ki gane ni ba, ai ina
tunanin wannan ‘yarki cr kya gane ta?”
Ta yi maganar tana nuna Saudat.
Inna Laure ta fadi qasa jaBar kamar an tile kayan
wanki tana kwalla wa Malam Bala kira, dukkansu
suka yi tsaye suna kallonta.
Malam Bala ya fito daga kewaye a gigice,
hannunsa rike da buta yana fadar. “Kai Laure
wannan irin ihu haka ai sai ki sa juwa ta kwashe
ni in fadi ba gaira ba dalili”.
Inna Laure ta rinka nuna masa inda Momy ta‘ ke
tana fadar. “Malam duba min ka gani, wace ce
wannan Kamar Mariya”. ?
Malam Bala ya ajiye butar ya nufo inda suke
yana fadar, “Wacce Mariyar ki ke nufi?”
Yana qarasowa inda suke yaja ya tsaya, suna
kallon-kallo shi da Momy, alamun firgici da
kaduwa sun bayyana cikin idanunsa.
Dr. Mariya ta yi mmmushi kafin ta ce “Kallona da
ka ke tamkar wadda ta fado daga sama, na san
ba :zai rasa nasaba da ganin ba-zatar da nayi
maka ba a lokacin da daga kai har matarka ku ka
saki jiki da na bar muku duniyar shi yasa. ku ka
wofintar da rayuwar bayin Allah, ku ka
gallazamusu, kuka cuta musu don kawai ba su da
kowa, amma me ya sa ku ka manta cewa, duk
abin da kuke Ubangiji na nan Yana kallonku,
kuma duk daren dadewa sai ya saka wa mai
haqqi hakkinsa,
musamman ma bayin Allah wadanda basu da
alhakin kowa?‘
Kuka cuta musu, ku' ka gallaza musu kuka
tozarta rayuwarsu daga qarshe ma ku ka
tarwatsa " . min su kowa ya kama gabansa don
kawai ka tsani
, uawarsu a kan Iaifin daba bata ji ba ba ta gani
ba; wannan shi ne sakamakon soyayyar da
Kaunar da na maka? Lallai da haka shi ne
‘sakamakon . soyayya to da ba ta yi rana ba,
Sai dai da yake Allah ba azzalumin bawansa
bane, sai dai idan shi bawan ya zalunci' kansa,
sai 'ga shi bai bar rayuwata ta tozarta ba kamar
yadda kai kaso, Ya daga daraja ta a duniya, Ya
kuma cika min burina tahanyar azurtanida ilimida
nagartaccen miji Wanda ya fi ka komai a rayuwa,
Ya kuma sake ba ni wasu ‘ya’yan, sannan daga
karshe Ya hada ni da ‘yata gudan jinina, tabbas
babu abin da zance da Ubangiji sai godiya. . ’ '
Abu daya ya kawo ni wurinkn shi ne ka sanar
dani inda dana yake in kuma ba haka ba wallahi
sai na zauna kotu da kai, don sai ka bani‘dana,
cutarwar da kayi musu kuma wannan kai da
Allah, Shi zai yi hisabi a tsakaninku,
-don haka ka sanar dani inda dana yake
. Tsananin firgici da kaduwa su suka girgiza ‘
zuciyar Malam Bala ‘ har ya ji qafafuwansa na
Kokarin gaza daukarsa; ya matsa jikin bango'ya
jingina'yana faman maida numfashi a wahalce"
Laure da ke durqushe a kasa ta zabura ta mike
tsaye cike da qarfin zuciya ta cire kallabin kanta
taci damara kamar irin‘sabbin mahaukatan nan ta
soma magana tana tafa hannaye“Kam babban
abin da malam ya hana, mu za ki gwada wa
qaryar arziki tsohuwar karuwa, kin je kin yo hayar
kaya shi ne za ki zoki mana bariki? To qarya ki
ke, wallahi idan kin fasa zuwa kotun kin raina
Allahn da
ya halicce ki, ke wanda ma ya ba ki hakuri Allah
ya tsine masa, mu din nan sai dai mu ga bayanku
ba dai ku ku ga bayanmu ba
. Dr. Mariya 'ta yi wani qasaitaccen murmushi, ta
cire gilashin da ke manne a fuskarta tana kallon
Laure kafin ta ce, ‘Ai ita da ma . tabarmar kunya
da hauka a ke nade ta, don haka
ban kuma kasa dake ba ballantana har ki kwasa".
Ta juya kan Malam Bala ta ci gaba da fadar,
“Zan tafi Malam, na ba ka nan da sati guda ka
nemo min inda dana yake kafin in dauki mataki,
ga kuma Saude a hannuna Allah ya jefo min
daga sama don haka na rungumi abuna, zan
dawo rana irin ta yau don karbar dana, na barku
lafiya”.
Inna Laure ta yi caraf ta damke hannun Saude
tana fadar, “Wallahi babu inda za ki je da ita, nan
zaki barta a gidan ubanta, don mijinta yazo yace
shi bai sake ta ba, dole kuma'ta koma gidan
mijinta Yanzu-Yanzun nan”.
Ido waje Saude ke kallonta' gabanta na. Faman
bugawa da sauri da sauri, Momy kuwa dariya tayi
cikin ajikafin tace “Kadadai ace shirme da‘
jahilcin' naki har ya fara taba kwakwalwarki? Ai
k0 shi uban da ya haifi Saude bai isa ya hana in
tafi da ita ba ballantana karabiti”. Kamarki ba
1nn Laure ta Kara hayayyakowa tare dA
cukwikwiyo rigar Sauden
Malam Bala yace “Sake ta su tafi” .
Ta juya tana kallonsa a kidime tana fadar
“Wallahi babu inda za ta Malam,Dan duk garinnan
banga ubandaya isa yasa ta tafi da ita ba ,Na ce
ki sake ta k0?” Malam Bala ya fadi a harzuke
fuskarsa dauke da tsananin bacin ran da bata
taba ganin irinsa ba a tare dashi A dole ta saketa
din zuciyarta na barazanar tarwatsewa ta rasa
inda za ta tsoma ranta ta ji sanyi, kawai sai ta
durkushe a Kasa ta rusa wani irin kuka mai ta
hankali.
~ ‘ Momy da Shukura suka tasa Saude a gaba
‘suka fice batareda sunsake bitakantaba. Suna
ficewa daga gidan Malam Bala yaja yan
qafafuwansa ya nufi: hanyar dakinsa, bai ko
kula: Laure ba, abin da ya qara firgitata ke nan
Kara .kidimewa zuciyarta cike da firgicin tonon
asirinta.
Suna fitowa daga gidan suka shiga mota, Alhaji
Ashiru ya ce, “Wai har kun yi me?”
“Momy ta ce, “Mun tafi kawai Alhaji”.
Ya dan waro ido kafin ya ce “Amma na za ta za
ku yi min magana da shi ko da fitowa ce ya yi
mu gaisa, k0 ba ku samu mahaifin nata bane?”
Momy ta kwantar da kanta a kan makarin kujerar
kafin ta ce “Manta da su kawai‘Alhaji, muje ai sai
da mutunci ake zumunci”.
Bai ce komai ba ya yi wa motar key, Momy ta
ce, “Saudat ta nuna musu gidan iyayen Hamid.
Saudat ta’amsa da to jikinta a sanyaye, zuciyarta
cike da kasala.
A Kofar gidan su Hamid maigadi ya sanar musu
iyayen nasa sun yi tafiya zuwa Zaria, sai dai
Hamid din shi kadai, Momy ta ce ya yi musu
magana da shi. Maigadin ya juya ya nufi cikin
gidan, bai jima ba ya dawo ya sanar da su yana
zuwa. Suna nan zaunc cikin mota daga’ gate din
gidan, yana sanye da wani farin yadi mai sheki
ya daura wa wuyan hannunsa wata tsadaddiyar
agogo baka, mai kyan gaske ya dora farin gilashi
saman dogon hancinsa da makullin mota a
hannunsa, da
alama fita zai yi. Kai tsaye wurin motar tasu ya
nufo idonsa a kan Momy tun kafin ya ida
Karasowa
‘ yana isowa ya rusuna ya gaida Daddy, sannan
ya gaishe ta yana fadin, “Doctar kece a
gidanmu?” ~ ‘Dr Mariya ta fadada fara'arta kafin
ta ce “Aiko nice da kaina Malam Hamid, ai dole
ne ma “ inzo ko dan qaunar da ka nuna wa
Saudat ya zame min wajibi inzo in yi maka
godiya, kuma in maka albishir da cewa Saudat
yata ce nice mahaifiyarta nina haife ta da cikina"
Hamid ya waro idanuwa waje yana fadar, “Yarki
kuma DR? Kina nufin dama kece mahaifiyarta‘?” ,
Momy ta amsa da, “Tabbas nina haife ta da dan
uwanta Rabi u”. ~ Wani irin dukulallen farin ciki
daki zuciyar Hamid. ya daga hannunsa sama
yanA yiwa Allah godiya. Saudat kuwa kallonsa
kawai ta ke a . zuciyarta tana jinjina ma soyayyar
da bawannan »ke mata ‘ ‘ Momy“ ta ce “Za mu
tafi Malam Hamid, da fatan zumunci mai Karfi?
zai shiga tsakaninmu” « Hamid ya amsa da
“insha ,Allah"‘ Amma idansa na kan Saudat
wadda ke ta faman haske shi
‘ da lallausan murmushi “ Yace “Mamy ki bani
adireshinku insha Allahu dana dawo daga tafiya
zanzo
Babu musu Momy ta ba shi dan qaramin card din
da ke cikin jakarta wanda ke dauke da adireshin
gidan da lambar gidan, sannan Dady ya ja motar
suka tafi Saudat na daga masa hannu har suka
Bace wa ganinsa. Wani irin abu ya caki zuciyar
Hamid, ya sa dan yatsansa ya lakace ‘yar
guntuwar kwallar da ta taso masa, shi da ya sani
Allah ya jarabce shi da soyayyar Saudat, irin son
da
ba zai iya misaltuwa ba, wai yau Saudat dinsa ce
ta zama haka? Rayuwa kenan.
Ana kiran sallar azahar suka iso gida, don haka
Alhaji Ashiru na sauke su ya wuce masallaci don
ya bada farali, su kuma suka shige gidan, Momy
ta wuce bangarenta su ma suka nufi nasu
Bangaren don gabatar da sallah a cikin lokaci.
Bayan sallar la’ asar kuma Shukura ta koma gida
saboda gobe tana da lecture a school.
Kwanansu uku da dawowa ya kama ranar
alhamis, Saudat na kwance a falonta ita da Nabil
da Nabila tana kallonsu suna home work da aka
ba su daga makaranta, Momy ta shigo felon
kafadarta na rataye da katuwar jaka, ‘sai rigar
likitoci sagale a dayan hannun da alama
dawowarta daga ofis ke nan. Duka yaran suka
zabura suka nufe ta a guje
suna fadar, “Oyoyo my Momy, welcome".
Ita ma da fara‘a a kan fuskarta ta rungume yaran
a jikinta tana shafar kawunnansu.
Saudat ta yunkura ta mike ta nufi inda " ' Momy
ta ke ta karbi jakar hannunta da Iafkwat dinta:
‘da mayafin jikinta ta nufi Sangarenta kai tsaye
kicin ta nufa ta jero kulolin‘ .abinci a babban
faranti tareda kwalin lemo', da ruwa masu sanyi
ta nufo falon, inda ta samu’ . Momy har ta yi wa
kanta masauki saman tallausan ' kafet din falon,
yaran duk sun zagaye ta suna ta_ shirmensu. ‘
Saudat ta ajiye mata kayan abincin a gabanta, ta
soma bude kulolin tana mata sannu da zuwa.
Momy ta rike farantin tana fadar.
“Barshi kawai Saudat, kije falon waje
Hamid nanan ya zo zaku gaisa” . . Saudat ta
washe baki tana fadar. ' ~ “Kai Momy, ashe bai
mance dani ba, yau fa kwana uku . ke nan da
dawowarmu daga -Dandagora, amma bai zoba shi
da ya ce ‘a * washegari zai zo?”
Momy ta ce “Ah to, ni kaina da na ganshi a
yanzu sai da nayi mita, amma dai yace ba ya
garine shi ya sa, dawowarsa kenan. Tashi ki je
kar yaga an barshi shi kadai.
_ ‘ Saudat ta yunkura ta mike ta nufi kan gadonta
ta jawa farin mayafinta ta yafa, ta saka
takalminta flat Shoe shi ma fari
A tsaye ta same shi cikin falon ya nannade
hannayensa a qirji ya zuba wa qaton hoton da ke
jingine a bangon daki ido, na su Nabila da Nabil
ne wanda .aka yi musu a harabar wurin
shakatawa da
ke cikin park dukkansu sun yi matukar
kyau tamkar ‘ya’yan da ke rayuwa cikin dusar
qankara.
Saudat ta qaraso cikin falon da ‘yar siririyan
sallamarta, bakinta na dauke da murmushi.
Hamid ya yi saurin waigowa yana

Please Login or Register in order to submit comment