Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

ο»ΏCompiled by Umar Dalha Funtua.

πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
AUREN SIRRI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



Bismillahirahmanurrahim


Aysha A bagudo



Page 1-2


Lekki Unguwace mai dauke da karancin mutane da suke rayuwa acikinta ,a silent place, saboda bata cika hayaniya mutane ba , dauke da tarin sanyin ni'ima mai dadi sakamakon kusancinsu da ruwan teku" unguwace da tattara kan manya ma'aikata da kusoshin gwanati, hade da manyan masu kudi ,ga tarin yan yahoo boy'z domin mafi yawancisu sunfi sha'awar zama acikinta. rayuwar mutane unguwar abin sha'awa bbu ruwan wani da wani domin suna rayuwasu ne tamkar a kasar waje .


PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE

Estate ne mai dauke da tarin dangi acikinta , hadin kai tattare da zaman lfy, Sam bbu hayaniya acikin wannan family kowa kagani cikin nishadi da farinciki zaka gansa ,ga tsantsar fahimtar juna dake tsakanin wannan family. kwakkywan family ne masu matukar kaunar junansu .


Let alh Muhammed bello khaliyal ,haifafen garin Lagos ne ,Amman asalinsa fulanin khaliyal ne dake jahar kebbi. sananne mai kudi ne yayi tashe tun alokacin da duniya ke kwance. sannan kuma take zaman lfy, marigayi Muhammed bello soldier ne daya taka rawar Gani a kasar nan .
ya rike mukamai da dama a wancan lokacin. ya rasu yabar tarin dukiya da da ya'ya da jikoki bila adade.
gabadaya family Muhammed bello bbu talaka aciki domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsu .

kafin rasuwarsa dake shine babba a dakinsu kuma Allah yabashi tarin dukiya da en'uwan , dan ganin ya inganta rayuwar kannensa kafin daga baya ya Gina wannan katanfarin estate din mai mazan kanta.
ya tattara kan yan'uwasa suna zaune a ciki ,yana da mata hudu hjy shema'u wacce aka musu aure tun saurayi da budurwa tana da ya'ya goma Sha biyu, mata takwas maza hudu sai hjy hauwa mai dauke da ya'ya goma maza biyar mata biyar ,sai hajiya rabi mai ya'ya takwas maza biyar mata uku sai hajiya Fatima wacce suke kira da hjy shuwa itama tana da yaya takwas mata bakwai namiji daya .
bbu abinda bbu acikin wannan estate din kama daga makarantar islamiyya wajen wasa buga kwallo wajajen exercise wajen swimming pool library Sannan ga wani katanfarin Holl dake gefe wanda aka shiryashi da kayan kyale kyale zagaye da kujerun zama . an ginashine saboda taron sada zumunci , wanda zasu dinga yi a duk karshen wata .

haka suka taso har zuwa girmansu cike da son junansu .
anan cikin dangi mazan suka zabi matan suma matan suka zaba akayi bikinsu anan cikin estate din suka zauna tare da iyalinsu har zuwa sanda tsufa yacima marigayi Muhammed bello yayi retire.
yayinda ya'yansa da ya'yan en uwa suka cigaba da kula da estate din .
a lokacin aliyu da habib ne kadai suka rage da basuyi aure ba saboda karatu .

Byn rasuwar marigayi bello ne aka raba gado aliyu ya dukufa gurin juya dukiyarsa ,ba abinda yasaka a gaba sai neman kudi wanda acikin kankani lokaci ya gawurta yayi fice yayi suna a duniya, yayiwa sauran yan'uwansa zarra aliyu ya mallaki tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. hade da tarin compenis a Lagos da kudancin Nigeria yana da gidajen saida man petir Bila adadi shine mallakin aliyu airlines yana da hannu jari da dama a compenis na kasashen duniya yana da gidaje a abuja da sauran garuruwa .
tsananin neman kudinsa ne yasa bai ajiye iyali da wuri ba ,burinsa bai wuce ya auri mace mai matukar kyau da tarin illimi ba .

Garin neman kudinsa ne ya hadu da fadila a india tun daga lokacin da aliyu ya daura idanunshi akanta "ya dauki son duniya ya daura mata kasancewarta kyakkywa gaske ga tarin illimi . fadila itace Diya ta biyu a gurin iyayenta su uku ne , ahmed ne babba sai ita sai farida , kin amincewa iyayenta sukayi da auren shi a cewarsu bako ne sannan kuma bakin fata. sai da aka kai ruwa rana dasu sannan suka amince da auren .
koda yazo daita Nigeria ma bata wani sha wuyan zama cikin family dinsa ba .
kasancewarta mace mai tsananin son jama'a da son yara cikin lokaci kadan tashaku da sulaiman da mahamud ya'ya ne ga yayyen aliyu sun shaku matuka da yaran ta daukesu tamkar ya'yan data haifa acikinta .
suma kuma suna maseefar kaunarta dan haka suke kiranta da ummi ,duk abinda suke so itace take musu bata ragesu da komai ba saboda bata da rowa hakan ne yasa ta sake janyo mata soyayya ta daban a gurin iyayensu.

shekarata biyar da aure mutuwar mahaifiyar ta risketa ,zuwan datayi indiya ne dazata dawo tazo da kanwarta fadila ta hada dasu Mahmoud tacigaba da rikonsu .
sai da fadila ta dauki sama da shekara takwas da aure sannan tasamu cikin murna a wajen wannan family bai faduwa .
cikinta na da wata tara cif ta haifi NASURUDEEN daga ita har aliyu suna matukar son DEENI tamkar numfashinsu DEENI yataso cikin gata da kulawar iyayensa, da dangi gabadaya suna nuna masa tsansar gata da soyayya fiyye da tunanin mai karatu .
shiyasa yataso a shagwabe a sangartacce saboda kaf estate din kowa yasan da zaman DEENI babbar matsalar da suka fara fuskanta da deeni , shine rashin magana da bai yi ,da farko fadila ta dauka ko kurma ne sai daga baya tagane tsabar miskilanci ne kawai yayi masa yawa .
duk tarin ya'yan dake cikin wannan estate din DEENI yafita dabam acikinsu, bashida aboki ,.
gabadaya baya yarda da kowa koda yaushe yana tare da umminsa ko farida ko su Mahmoud tun tasowarsa yake da burin son zama soldier yayinda ummi take bashi goyon baya wajen kiransa soja .
Domin wani lokacin zai je yatasa hotonta marigayi kakansa dake manne a falonsu gaba yayi ta kallo yana shafa fuskar tsohon yana murmushin ,Sam shi bashi da fara'a ballanantana sakin fuska koda yaushe fuska nan tashi a hade take tamkar hadari , .DEENI Nada shekara takwas byn yakare primary school aka sai mishi form din shiga makarantar sojoji ba'awani samu wata matsala ba yasamu sakamakon matsayin mahaifinsa da kakansa. sabanin wayanda basu da gata.
domin a wanan lokacin idan dai kai bawani bane ko dan wani ba ko bakada hanya a military school ,sunanka sorry.
Domin kuwa kana ji kana Gani military school zai gareka shiga .

byn wani lokacin farida ta samu miji anan cikin estate din wanda shima yakasance "Da"ne ga marigayi Muhammad bello wato habibu ubansu daya da aliyu mahaifin ga DEENI .
duk da fadila ta nuna rashin amincewarta matuka , da nuna wa er'uwartata illar aurenta da Habib Amman sai taga yarinya ta nuna tana so abunta ,dan haka ta kyaleta kuma da kunya dai ta fito fili tace batason jinin aliyu ,wanda itama kanta tasan hakan ba mai yiwu bane . itama ba wai shi din ne bataso ba ,halinsa ta tsana ,
Amman shi babban ma'aikace gwanati ne, director of land and housing & same na Lagos state gabadaya. yana da mata biyu da yaya bakwai farida ce ta uku .
Ko alokaci daya auri farida takasance mace ce mai tsananin hakuri .
duk da mijin nata Vai kasance mutun mai adalci ga iyalansa ba. Amman bata taba kawo kararshi ga ummi ba domin tasan halin ummi Sam bata son raini .

Shekarar da aka yiwa sulaiman da mahamud aure shekarace Allah yayiwa mijin ummi rasuwa wato alh aliyu Muhammad bello sunji matuwar farar daya , mutuwar tayi matukar gigita ummi dan byn ya dawo daga sallah asuba ne yayi irin kishingide nan yana lazimi koda ummi taji shiru shiru bai sake fitowa ba Sannan bai nemeta ba kmr yadda ya saba , wanda aldarsa ce da zarar gari yayi sha ...yake fitowa ko yakirata a waya Amman taji shr .
tashiga dakin nasa ta tarar dashi kishingide da carbi a hannunsa .
da fari ta dauka ko bacci yakeyi sai tayi nufin ta tasheshi yakoma kan gado.
Ammai sai taga alamun rashin motse atare dashi takai hannuta wajen hancinsa da karjinsa a lokacin daya taji baya numfashi.
take ta zube anan ta sume.
har a kashare zaman makoki ummi batasan a wani hali take ba ,dan bata cikin haiyacinta' koda ta farfado ma sai da akayi ta hadawa da addu'a Sannan aka samu kanta ta dawo daidai , dan mutuwar ta girgiza har ta kusan zarar daita .

Byn wani lokacin su sulaiman suka cigaba da tallafawa ummi da DEENI a lokacin farida na dauke da tsohon ciki duk da itama ta dan jima bata haihuwa ba, kuma har lokacin ummi bata san er'uwarta tana cikin matsala ba ,sai byn data haihu" lokacin ne ummi taga komai bbu alhalin ga tarin dukiya kmr zai kashe habibu , gashi yasake kara wani sabon auren matansa sun cike hudu cif .
ummi tayi kuka kmr may gashi tana cikin danginsu da suke tamkar tsiya madauri daya.
ba daman tace zata dauki wani mataki akan haka .
dan tasan yadda kansu yake a hade .
dan haka taci kukanta takoshi ita da er uwarta ahankali take furta kalmar shiyasa tun farko naki amincewa da auren nan naki da habibu ,ba dan komai ba sai dan irin haka Amman kika nace ,ga irin abinda nake gudar miki kennan Amman kika kiji , sai kuma ta tsagaita da kukanta ahankali tace ba yadda zamuyi da ikon Allah ,sannan ga rabo a tsakani.
Amman duk da haka sai da ummi tayi masa tatas saboda daman ita bawani sakar masa fuska take ba kuma yana shakkata.
kullum ummi acan take wuni har ranar suna yarinya tace sunan mahaifiyarsu ummi wato muzeenat , shima habibu yayi hakan ne saboda ya wanke kansa a wajen ummi,kuma yayi nasara domin hakan da yayi yasa ummi taji dadi Sosai aranta har ta dan rage jin zafinsa .
sannan bakaramin kudi ummi takashewa bby ba. haka ma ranar suna ummi Tayi rawar Gani sosai .
byn anyi suna ne ummi tasamu habibu akan dan Allah ya dinga kula da farida dan ita kadai gareta bata da kowa duk fadin Nigeria sai ita, idan ma bazai damu ba, zata bashi Rabin dukiyarta yakara akan nashi da duk wani abinda yake so, ita dai burinta kawai ya kular mata da er,uwa ,yayi murmushi kawai hade da ce mata yaji .

Byn wani lokacin farida ta kuma samun wani ciki wanda tun yana karami take fama da laulayi tun lokacin ummi tadawo da zeenat wajenta ,
a kwana a tashi bbu wuya a gurin Allah har cikin farida ya isa haihuwa gurin haihuwar ne taji jiki sosai .
koda ta haifi yaron ma bbu rai sannan itama tace ga garinku .
mutuwar ta shigi habibu matuka yayi kuka tamkar ransa zai fita ,dan shi kansa yasan yayi babbar rashin da ba zai taba maida irinsa ba.
yayi rashin mata mai tsananin kirki da hakuri da sanin darajar miji . Allah sarki ummi kusan har tafi habibu jin mutuwar tilon er'uwarta ta ,.
a wannan Lokacin ne rikon zeenat ya dawo dindindin gurin ummi ta dauki soyayyar duniya ta daurawa zeenat tana mugun ji da Yarinyar tamkar ranta kwata kwata bata son abinda zai rabata da zeenat Sannan kuma tana debe mata kewar er'uwarta .
lokacin shi DEENI na ss1 a NMS, Nigeria military school dake zariya.
yayinda DEENI Sam ba halinsu daya da ummi ba koda yaushe kagansa fuskar nan tasa a daure a cunkushi bbu wani fara'a ga shegen miskilanci tsiya sai dai mugun kyakkyawa ne na karshe . ajin farko, wato first class ,gashi da maseefar iya sa kaya kallo daya zaka masa ya gigitaka kaji yashiga ranka farar daya saboda tsabar kyawunsa sai shegen shiga ran mutane domin kusan yan'mata cikin estate din suna maseefar son sa yayinda yake girma kyawunsa na sake bayyana hade da miskilancinsa .

Tunda zeenat ta dawo gidan magana bata taba hadasu ba ko gaisheshi Tayi baya amsawa in dai bayaga idanun ummi ba yana da matsanancin tsafta wanda kusan a wajen ummi yagada .
Cikin haka ya kammala karatunsa na secondary school ya wuce NDA burinsa kennan nason zama cikakken soja itama ummi kuwa nasake karfafamasa gwiwa da bashi goyon baya yana karantar science ne ,wato likitan soja .
bansan yadda zan kwatanta muka halinsa ba Amman yakasance mutun ne shi mai bambanci ra,ayi.
byn yakare karatunsa ya fito da mukami second lieutenant star biyu kennan .

Zaune zeenat take a falo tana kallon wani serisfilm a zeeword my let home Tayi zurfi cikin kallon film din gabadaya attention dinta naga kallon ita kadai ce ummi tashiga cikin estate din yin barka taji karar Bell wanda shine kusan karo na hudu da taji ana dannawa. cikin jin haushi ta mike dan bata son abinda zai dagata daga kallon datakeyi , tana bude door din bata tsaya ganin kowaye ba ta juya abinta takoma mazauninta sallama taji hade da shigowa ta dago kanta kennan da niyar amsa sallama sai taga mutun tsaye kikam sanye da sabon kayansu na sojoji gabadaya zeenat ta gigice hade da rikicewa tsabar tsoro dan ita Allah yayita da maseefar jin tsoron soja take cikinta ya dauki kugi Amman still idanunta na kansa ta tsaresa da kallo .
in ina tasoma yi wa..wa.. waalai....ya dakatar daita da hannushi, yana zabga mata wata uwar harara muryasa a kwasashe yace yau ne kika fara ganina da har zaki wani tsareni da idanu Kona canza miki ne ?da sauri tasoma girgiza masa kai. Kai tsaye dakin ummi ya nufa tunda bai ganta a parlour ba yasan tana dakinta tana kallonsa ta kasa dauke idanunta daga garesa har sanda ya dawo fuskar nan tasa a hade yace ke.....dan iskanci kina kallon mutune bazaki iya cewa ummi bata nan ba kin wani tsare mutun da idanuwa tamkar na maciji ,dayake bawani manyan idanu gareta , da sauri bakinta na rawa tace dan Allah kayi hakuri mantawa nayi ko kallonta bai sake yi ba yaja tsarki yayi hanyar dakinsa ta tabe baki hade dacewa jarababbe kawai ai yadawo kennan, itama taja tsaki ta juya tacigaba da kallonta ..


MMN SUDAIS CE
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
AUREN SIRRI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—



Aysha A bagudo



Page 3-4

Sai da tagama kallonta tsab Sannan ta canza Chennal hade da tashige kitchen dan daura abinci abincin dare
bakin kofar kitchen din ta dawo Tayi tsaye abunta tana cigaba da kallonta Chennal data canza, ajima ajima tana zuwa tana duba abinda ta daura.
Karar bell taji ba kaukautawa shiyasa da sauri taje ta bude gudun maseefar DEENi dan tasan muddin yana gida baya son yawan hayaniya , yanzu ne zai gama daita, Maryam tagani tsaye da wasu en school dinsu su biyu tuni murna yakama zeenat ,ta rungume su daya bayan daya tana musu sannu da zuwa hade da basu hanya "suka shigo har cikin main parlour din hade da Sallamar su .
waje ta nuna musu da hunnu kuzauna mana suka zauna ita kuma takoma kitchen ta duba abinda ta daura taga yayi ta kashe gas din sannan ta dawo inda tabarsu hade da kawo musu drunks mai tsanyi da snacks ta ajiye agabasun .
gabadaya hayaniyya ce ta barke a atsakaninsu da murna ganin juna ,zeenat ta kalli su Sumy hade dayin kasa kasa da muryata tace kuyi magana ahankali fa sannan tace kun kyauta sai yau kuka ga damar zuwar mana , Sumy tace ba gara mu ba muna zuwa time to time.
kufa sai aikin sa rana kullum, hira suka shiga .
a inda Maryam ta dube zeenat tace wai nan fa IV suka kawo mana na birth din rukky, zeenat ta zaro idanu waje I ....me Maryam tace IV .
zeenat Tayi dariya hade da cewa uhmm badani ba" kema kinsa sarai baza'a taba barinmu zuwa wani birthday party ba " Sumy Tayi murmushi sannan tace ai sai da nagaya rukky Amman tace ga zance ga magana " gashi nan, ni ai nasan bazakuyi attending birthday party dinta ba ,da day itace sarkin shishigi da neman suna , zeenat tace kmr kinsani ,duk abinda ya wuce cikin gidan nan namu "ta girgiza kanta baza'a taba barinmu ba ,ki bata hakuri kawai Amman wlh har ga Allah naso zuwa ko dan rukky Sumy tace to why nut ku sace hanya kuje a boye batare da kowa yasani ba ... zeenat ta kalli Sumy fuskarta a hade tace kefa kin cika matsala fa wlh.
kmr bada hausa nake miki magana ba.
ta bude bakinta kennan da niyar sake balbale summy.
sai ga DEENi ya sake fitowa parlour jikinsa sanye da jallabiya marun colour may maseefar kyau sai kyalli take zuwa ga kamshin turarensa mai mugun sanyi dadi wanda tun tasowar zeenat ta sanshi da auren Hamilton har yanzu fuskarsa a daure take tam .. kmr koda yaushe " take ta hadiye maganarta batare da tasan Tayi hakan ba ,ta zuba masa idanu tana kallon kwayar idanunshi, sai data ya hararata, sannan ta dauke idanunta ,ta maida kallonta da hankalinta kacukam a kansu Sumy dake zaune surusuru. Yayinda gabadaya Maryam duk ta fisu tsurewa ko dan ita Yar gidan ce oho..
cikin wata irin murya mai sanyi dadi tamkar ba soja ba yace ke......ta juyo ta ahankali ta sake zuba masa idanunta dan tasan dai daita yake dan haka tabada duk attention dinta garesa.
bakisan kibawa mutun abinci bane ? Dan iskanci sai an roka ,zatayi magana ya katseta a fusace , ai ba tun yanzu nasan ke muguwar rowa ce dake ba Tayi surusuru da idanu ,da sauri tace kayi hakuri dan Allah nayi zaton ko kana azumi ne "naga kullum kana yi "
yace "oh "dama kinsa min ido ne har kinsa cewa azumi nake kullum ?
Jikin Maryam har rawa yake ,a hankali tace wayoo Allah ashe ya dawo ,bari in gudu tun bai gama daita ya da kanmu ba , zeenat tayi shr har sanda ya sake maimaita tambayarsa hade da cewa dan ubanki bada ke nake ba kike bina da idanu kmr zaki cinyeni" ta sake girgiza masa kai,. Tana bashi hakuri
marowaciyace banza kawai mai mugun gado. shiru yayi na dan wani lokaci hade da sauke numfashi .
Sannan can kuma yace ai idan bakiyi rowa ba sai Allah ya tambayeki" km baza'asan ke...Yar uncle Habib bace .
kin taba ganin barewa Tayi gudu danta yakasa rarrafe" zeenat ta sake girgiza kai da sauri ,yace OK ashe dai kema kinsa gaskiya dole kiyi gadon rowa.
Ganin haka yasa su sumy suka nemi sulalewa duk yana kallonsu sai daya ga Maryam na shirin gudu itama dan har summy ta daura hannuta kan handle din kofar ,ya dakatar dasu da hannusa , sannan yacigaba duban zeenat yace barikiji da kyau yana mai nuna da yatsansa" nan ba gidan marowata bane gidan masu bayarwa ne aci . yace menace ? Da sauri tace gidan masu bayarwa ne.
yace gud daga yau bama ni ba ,ko wani ki kaga yazo gidan nan ki bashi ruwa da abinci yaci dan ba naki bane.
ya sake jiho mata wata tambayar yace ko abincin naki ne?, da sauri ta girgiza masa kai dan gabadaya ta sure ta kasa kwakwaran motsi sai ajiye zuciya kawai take yi , yace" baki da baki ne kike kadawa mutane kai , tace naji kayi hakuri dan Allah. Sannan ya juya kan Maryam da kadan ya rage ta fashe da kuka , ya zuba musu ritattun idanunsa da suka fi kama da mage masu saurin raunana mutun kai tsaye , yace ku kuma en iskanci banza kun wani cikawa mutane kunne da hayaniya tamkar kuna club ,kallo daya yayi musu kowace tabawa kafarta iska yaja tsaki ya juya ya nufi dakinsa.

ahankali zeenat take sauke ajiyar zuciya hade da dafe kirjinta , batasan meyasa ba ,idan har Yaya DEENI yana guri Sam bata samun cikakkiyar natsuwa "sai tarinka ganin duk yacika guri ga tsananin tsoransa da take ji yana mamaye zuciyarta . Maryam har da kuka tayi byn sun fita dan daman can ita haka take ,shegen tsoro gareta aiko, su sumy suka ce mezasu ba dariya ba dariya suka dinga yi har da rike ciki suna nuna ta aiko tace yau sai da suyi ta zama a estate din dan bazata rakasu gun securities ba sai da sukayi ta bata hakuri sannan suka jera suna hirar abunda ya faru.

Ko lokacin da ummi tadawo tuni murna da farinciki Ganin tilon "dan " nata yamamayeta zuciyarta nan suka zauna a parlour suna hira cikin hirar ne ummi take masa maganar aure in da tace masa yakamata yanemi mata yayi aure kasan shekararka nawa kuwa yanzu ?yayi murmushi ai dole nasan shekaruna ,muke nan kullum cikin rubuta date of birth ,talatin da biyu ne kawai fa ummi Tayi dariya 32 din ne kawai kusan duk sa'annin haihuwar ka duk sunyi aure acikin estate din nan gasu yasir nan ma duk ansa musu rana dan haka kaima ka fidda mata kafin azumi DEENI yazaro idannu yana bin ummi da kallo a shagwabe yace haba first love dan sunan da yake kiranta dashi kennan tun tasowarsa .... ni din guda nawa nake da zakice inyi wani aure yanzu. Dan Allah kiyi hakuri my first lov zuwa wani lokaci ,duk hirar da suke zeenat na zaune tana jinsu haka kawai taji gabanta na faduwa lokacin da taji abinda ummi tace ,Amma jin amsar da yaya DEENI yabata yasa taji wani irin sanyi na ratsa zuciyarta .
kmr ance ya dago idanunsa suka sauka cikin nata harararta yayi yace kallon

Please Login or Register in order to submit comment