Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya'ta batada tarbiya? Bayan kin haifi Abinda yafi karfin ki bayajin maganar ki, ai shine Abun tir ba Salifa ba yakawo santaleliyar yarinya ya Ajiye ba biyan bukata me kikeso tayi inbatasha Abinda zai cire mata damuwa ba, don haka bani wuri in kintsa abata kina wani toshe hanci kamar kinga kashi. Takasa cewa komai kawai fita tayi domin tafita masifa
Tana ayyana dole ta nemi mafita don bazata Y'ar da da wannan iya shegen nasu ba, tana fita momyn salifa ta kulle kofar ta dawo tareda bata fas a kumatu, zabura tayi dauke da Ashar" kutumar ubancan wane shegen...... Tayi ido biyu da momyn ta, " momy meye haka don Allah Ina bacci na mai dadi kizo ki tasheni da Mari meyakawo ki gidan suruki early morning please?
"Ubanki dake kabari yakawoni Y'ar banza, wato bazaki daina daga kwalbar nan cikin gidan nan bako, nace ki hakura da duk wani iskanci har burin mu ya cika Amma kina wannan Rayuwar a gaban idanun shi yazai zauna dake? Zama tayi tareda kallon Aman, ta kwalawa maid dinta Kira, " clean this mess ta wuce tabar momy, tashi tayi tabita tana bambami " wato na zama karya inyita haushi ko? Kwabewa tayi tsirara agaban uwar Wanda ba wani Abu bane a wurinta tace " tunda gani dutse ba namiji ba chilling ba kwalba bazan iyaba. " kice dai ba y'an iskan kawayen ki y'an madigo, salifa tanbadewar ki tayi yawa wallahi ki rage kodan y'an cutukan nan. "Kinfa shiga rayuwa ta ne because of your greediness, meye bandashi you have money momy me zakiyi da kudi, inada big girls a kasashe masu kudi dake da burin mallakamin duk Abinda nakeso a fadin duniyar nan kin nace sai na Auri wannan mugun d'an wulakancin, Momy I don't want to deceive myself , that guy hate me with passion yasan ni munsha haduwa a bangkok with my girlfriends, I can't west my precious life here. "Oh baby na daura towel din tom kije kiyi wanka kifito muyi magana. " nop Ina fitowa zanfita niba dutse bace inada appointment. "Ok ba kince kina sonshi ba? Shiru tayi kadan tana kallon momy, " meye amfanin son? Abinda nakeso bazan samuba guduna ma yakeyi tun zuwa sau biyu nasa shi a ido na. "Jiya yashigo shi ya ganki a wannan halin uwar tafada min komai, kinga ga dama tasamu kin yi sake da lokacin da ya shigo kin samu kinja hankalin shi kin shafa wannan turaren da bazai kuma tsallake dakin ki ba Amma kinja mana asara. " oh Momy nida nasa wannan turaren har dakin shi naje ba Abinda ya faru sai don yazo nan? " kinga halin ki ko, wayace ki saka kifita waje wani yaji kamshin? Keda akace miki shikadai zai shaka Amma kinje kinyi min Asarar kusan million a banza batareda ribar ko dubu daya ba, mtsww kinada kayan haushi ni natafi kiyi duk tsiyar da kikaga zaki yi tunda bakida ganewa Abinda kikesha duk ya sa kwakwal war ki bata aiki.
Haka ta tafiyar ta batareda ta nemi Momy ba, Wanda tabar salifa da cizon yatsa, da ace jiya bata kwafsa ba da ta rage mugun zafin data dauka nashi koda ta hanyar yimai fyade ne domin tasan y'an da zatayi seducing dinshi dole ya biye mata kobaya so Indai ya kawo kanshi har wurinta, saidai Kash ta kwafsa. Haka ta sheka wanka cikin kana nan kaya kamar zataje club ta maka katon space tareda d'an wani yalolon gyale ta dauki key din motar ta tafice.

Karfe shadaya tagama shiryawa cikin wata doguwar riga Y'ar saudiya mai shegen kyau taji stones tana sheki, ta yana gyalen ta tafito kamar balarabiya, takwashe lokaci mai tsawo kafin ta gama shiryawa saboda kawai ta burgeshi,Wanda Aunty ta yaba, tace " kaga madam khaleel gaskiya zaki rikitashi irin wannan ado haka, ga kirjin sun kunburo hips dinta d'an dai dai ya bayyana saboda shape din rigar duk da bawai takamata bane Amma tafito da perfect figure dinta,
Karfe shabiyu dai dai ya Kira wayar ta, lokacin tana shan wani hadi mai shegen dadi da Aunty tabata, na Zuma da kanun Fari da kuma mazarkwaila ga dadi ga aiki mata. Ganin kiranshi yasa ta Ajiye cup din tayi picking " Ina waje let go. Ya datse kiran, mikewa tayi tace "Aunty yazo.
Wani turare ta dakko mata domin ita batasan Ina zasuje ba, ta ce ta shafa,

Tun daga nesa ya zuba mata ido ganin y'an da take tafiya cikin natsuwa, saida ya kalli ko Ina yaga ba idanun mutane yasamu natsuwar kare mata kallo, har ta iso bakin motar, batareda ya motsa ba, ita sam bata ganin shi ta rasa dalilin da yasa duk motocin shi kamar na matsafa saboda tinted glasses danna motar yayi tareda bude mata, dukawa tayi ta shiga, ya juyo da kyau ya zuba mata ido itama ta kalleshi cikin adon manyan kaya, yayi matukar haduwa harda hula wadda sai jefi jefi zaka ganshi da ita, idanun shi dauke da katon eye glass daya karamai haiba da kyau, batasan lokacin da ta shagala da kallon shiba, shima kare mata kallo yakeyi shikadai yasan me yakeji, baiki ya kwantar da kujerar motar nan yayi mata kaca kaca ba domin tasa mai zafi, numfashi ya fesar mai zafi, " don't dress like this inkin san ba agidan mu mukeba, I feel like striping you necked right now. Ya fada muryar shi a shake. Kunya taji ta dawo hayyacin ta tareda gaida shi, ya amsa "mubar nan kafin inyi miki tsirara anan gidan surukai.
Tayarda motar yayi tareda riko hannun ta gam da dayan hannun shi domin rage zafi y'an da yake murza hannun ma nasa taji wani iri a jikinta ga hannun shi laushi kamar na mace, domin baya wahala, waka ya saki na su p square na no one be like you yana bin wakar a natse cikin kwarewa tareda d'an juyowa yana kallon ta, turo baki tayi domin wannan glass din da yasa haushi yake bata yanzu duk da yayi mai kyau ita burinta taga kwayar idanun shi da yanda yake aika mata da kallon shi mai cikeda tasiri a zuciya da gangan jikinta. Yana ganin reaction dinta baice uffan ba har suka isa kofar gidan malam Wanda tundaga nesa ya faka ganin cin cirindon mutane ya zare glass din " oh god zamu juya fa. Yafada yana matse rai, Wanda ita dai murna takeyi tazo gida zataga Inna, jin kalmar shi yasa tayi saurin juyawa, " saboda me? " can't you see, maza cike yazan bari kifita cikin wannan adon su kalleki?
"Almajiran gidan mune sun sanni batun yauba meye a ciki please don Allah muje. Tafada cikin marai raice wa, " excuse me, kikace sun sanki? Ba Wanda ya sanki sai Ibrahim khaleel, don haka if you want to go in call Shukrah ta kawo miki katon hijab if possible harda nikab am not a fool.
"Don Allah meye haka? " kishin iyalina.
Yafada tareda gyara zama yana cewa " call her or mu juya yanzu we have a plight to catch time is going.
Wayarta ta daga domin Allah yagani bataga samu taga rashi ba don haka ta Kira Shukrah tace don Allah takawo mata hijabi tana waje, karbar wayar yayi jin Shukrah na tanbaya wane irin hijabi kuma meke faruwa? " Shukrah ki kawo mata please muna jira harda nikab please. Dariya Shukrah tayi tareda mikewa tana cewa "Aunty kinyi Aure. saida ta dakko mata kato cikin kayanta nagida sabo tareda nikab domin tanada su tafadawa inna tana zuwa Yaya khaleel nakiranta a waje.
Fitowa tayi tana kunshe dariya harta matso gaban motar ya zuge glass yace " Shukrah tank you for saving her da bazataga Inna ba yau. Gaidashi Shukrah tayi tareda mika mai ya karba ya mika mata tana tura baki ta zura, gefen ta shukrah ta zagaya tace "Aunty kece da irin wannan shigar yanzu Yaya khaleel ya taimake ki da keda malam ma. " Shukrah kyaleta saboda tasamun hawan jini yasa takeson fita a haka yanzu. Ya bude motar yafito tareda zagayo wa gefen su harta daura nikab din ya bude mata ta fito, yace "wow koke fa yanzu? Harara ta watsa mai cikin wasa yace "I will pay for that look letter. Yayi gaba yana murmushi, matsowa Shukrah tayi tareda cewa "Aunty wannan irin love, when how? Gaskiya kunfi matching da Yaya khaleel look at him, inama kinki Y'ar da, Dana shige ni. Tafada cikeda tsokana, ta kai mata Dan dukan wasa, har suka isa kofar gidan ta wuce Abunta ciki shikuwa yayi wurin da malam yake da manyan Almajiran shi,

Tana shiga ta kwalawa Inna Kira cikeda doki da kewa, tana zaune tana kulle kullen ta tace "Aa Amare da rana?
Zama tayi suka gaisa Shukrah ta kawo mata zobon Inna mai sanyi tasha tana lumshe idanun ta "I miss this. Inna fuskar ta dauke da walwala da farin ciki, tace "Y'ar nan kina can kinyi shar dake ni Ina nan kullum tunanin ki tunda nasan bakiso wannan Auren ba Naziya, da Alama wannan Khaleel yana kulamin dake tunda har kinsaki jiki kinyi fes, kai Alhamdulillahi. Murmushi kawai tayi tareda dukar da kai saboda kunya, haka suka shigo tareda malam ya gaida Inna cikin girma mawa kafin malam yace "sunzo yimana sallama ne zasuje can kasar waje. Saurin kallon shi tayi Wanda idanun shi na kanta kur ko kunya baiji aganshi, ya kashe mata ido daya, wato tafiya zasuyi shiyasa yake neman hoto,
Wanda duk batasan shirin shi ba,
Sunkai karfe hudu a unguwar barinta ciki yayi shikuma ya fita waje wurin malam saida ya kirata ta mike batareda ta gaji ba tayi missing Inna, Shukrah ta rakata bayan tasha nasihohi wurin Inna da malam, yabawa malam kudi sosai yace akarawa Almajirai Abinci, domin yasan in shi zaibawa bazai karba ba, Shukrah ma yabata yace tasiya kayan kwalliya, wayar hannun Naziya ya karba ya mika mata bayan ya cire layin yace " kiyi manage kafin inkawo miki sabuwa. Tayi tsalle tana godiya domin ta mugun lora wayar tunda taganta, murmushi Naziya tayi tareda karajin shi cikin zuciyar ta yanda yake sakin jiki da yan uwanta All that ego da take tunanin yanada yau bata gani,
Haka suka tafi fuskar ta kamar gonar Auduga tana Kara daura damara,
Gidan kawu sukaje Wanda ta yaba da karamcin su, sun karbeta hannu biyu, hardai uwar gidan da taji dama haka Momy takeyi da ita. Sunyi mata shatara ta Arziki kafin yace tafito sutafi, kamar karta tafi ga y'an matan da dama sun d'an saba tun lokacin Ahmed.
Karfe biyar da rabi suka isa ainihin kofar gidan su Wanda bai shiga ciki ba yace ta jirashi ya dakko kaya, ido tabishi da shi, har ya shiga katon gate din, bai wani dauki lokaciba ya fito dauke da akwati madai daiciya, ya saka a bayan motar, "nakira Aunty nafada mata sai mundawo jirgin mu yakusa tashi.
Yafada yana tayarda motar, tareda kiran manager dinsu yace su hadu Aminu kano Airport yanzu,

Abun kamar wasa taganta a filin jirgin Wanda all her life bata taba mafarkin zuwa ba, yau gata wai jirgi zata hau zuwa wata kasa, ta zubawa sarautar Allah ido, suna isa manager na isowa, yace "naso muyi wanka before going Amma har anfara announcing, hanata fitowa yayi ya bashi envelope ya kaiwa momy gobe da key din motar if he needs him zai kirashi. Saida yaji ana Kara Announcing yace ta fito baida yanda zaiyi,
Fitowa tayi still da katon hijab dinta saidai ta cire nikab din yanzu domin tagaji, suka gaisa da shi sama sama kafin ya sallameshi ya rike hannun ta suka wuce.
Wai yau ita naziya ce zaune a cikin jirgi first class seat tunda jirgin na y'an kasuwa ne, yana zaune a gefen ta ba wasu mutane sosai a wurin ya daura mata belt tareda d'an saka hannu ya rungume ta domin supporting dinta don yasan karon ta nafarko kenan, Wanda tayi matukar kokari wajen natsa kanta da dauriya karta nuna kauyancin ta,
Sai gasu a sararin samaniya, jirginsu ya daga, taso tayi sallama da Aunty Raliya Amma yabawa Shukrah wayarta, sai muyi musu fatan sauka lafiya........ 🖊



Me kuke ganin zaifaru da rayuwar momy masoya, ga khaleel ya tsallake ta batareda tasani ba ya dauki Y'ar da bataso ya bar kasar, ga momy nan dauke da sabon shirin kashe Auren shi tareda nemo mai wata Matar, muje zuwa dai ankusa isa, inda nakeson kaiku da Yar dar Allah.


*Matar Soja*






5⃣1⃣&5⃣2⃣

*Alhamdulillah naga masoya na Asali, naga kuma masu mugun gajen hakuri, yau ba bawa mai hankali da zaiyi wa kanshi fatan ciwo, tsawon lokacin da nafara rubutu inba wani kwakkwran dalili ba bana kaunar infara typing in tsaya, na rubuta littafi bakwai wnn ne na takwas hakan bai taba faruwa ba, nafada nakuma nafada nabada hakuri mutanen da sukasan halin da nake ciki sunfito sunyi bayani, Amma wai duk da haka wasu zasu rika daukar waya suna tanbaya ta Ina posting dinmu Ina update sister kin ajiyemu kin kyale mu, kuma abin mamaki masu complain din duk wainda suka biya dari biyar ne, Allah sarki akwai sister da tabiya dubu uku Ana bata prvt wlh tun ranar da ta tanbaya nafada mata banda lfy bata kuma bina tace update ba, haka akwai masu dubu biyu dubu daya duk ba wadda tayi complain saboda lfy itace komai idan ba lfy ba Abinda bawa zai iya yi a rayuwa, kuma ciwo inba na Ajali bane yanada iyaka don haka masoya nagode sosai da sosai masu complain kuma Allah ya baku hakuri bazance komai ba*


08032252760
08175479641contact this numbers for more information



...............Bacci tasha sosai a kafadar shi, Wanda ya raba dare yana kare mata kallo, wani irin farin ciki yake jin shi a ciki, finally zai kasance tare da ita, zasu rayu su biyu ba wani shamaki ba Wanda zai hanasu sakewa.
Washe gari tunda safe sakon shi ya iso wurin Momy lokacin ta shirya fita aiki, cikin adonta na manyan mata, taci karo da manager din khaleel, yace "ga sako inji mai gida Hajiya. Ya shigo da motar tana sake da baki ya faka wajen Ajiyar motocin su, saurin bude takardar tayi taga Atm din Ahmed da nashi na gida tareda takardun gidan dana company, wani irin faduwa gabanta yayi, me wannan sakon ke nufi? Saurin kiran manager tayi ganin zai fita tace " kai zo Ina mai gidan naka da yabaka wannan sakon?
"Hajiya ai tunjiya yabar Nigeria bai fadamin inda zaije ba tareda madam dinshi. Ya fita Abinshi domin shidai ya isar da sakon.
Dafe kai tayi tareda jan kafa takoma cikin gidan, tana shiga falon ta zube, " shikenan ya tafi ya koma, Wayyo Allah na ni balkisu
Nashiga uku na. Tasa kuka mai karfi, Wanda saida masu aiki suka firfito a rude suna tanbayar lafiya?
"Duk ku wuce kubani wuri munafukai magulmata. Da gudu suka koma, Wanda yayi dai dai da shigowar salifa cikin wasu arnan kaya duk jikinta a bayyane, "yau kin tunada mutuwar Ahmed ne Momy? Tafada cikin izgili, "mutuwar ubanki natuna mai farar kafa, yakamata ingano cewa keba Alkhairi bace a rayuwar ya'yana Amma nakasa gano hakan saida nayi sanadin d'ana ya gudu yabarni, nashiga uku na ni balkisu.
Matsowa tayi a fusace ta shake wuyan Momy batareda duba girma ko shekarun taba, " ubana sa'an iskancin kine? Eh, kuma yanzu ne kika gano cewar ni ba Alkhairi bace a rayuwar ki, kina tunanin don Allah na Auri d'an ki tunfarko? Dukiyar nan mukewa bawani Abu ba, tunda bazan samu kan mijin ba meye amfanin Auren. Dakyar ta kwaci kanta tana jan numfashi da kyar tasamu ya dai dai ta, Wanda lokacin har idon Salifa yakai kan takardun dake zube akasa, saurin kwashe wa tayi tana dubawa " kawosu nan dukiyar ya'ya na ce bakida hakki a ciki. "Hhhh niko keda hakki da Dukiyar mazaje na, Ina tuminin takaba na na Ahmed? Yanzu shima wannan kisa kawai ya mutu domin bazai dawo miki ba, tunda nikuma nasamu wannan yanzu kinga gida ya zama nawa office company motoci.
Tashi tayi tareda kallon ta " sharia kuma tazama banza kenan da zaki mallaki Dukiyar mijina da ya'ya na daga sama ni balkisu Ina kallon ki. "Watch and see Hajiya balkisu zan nuna miki inada manya asama, Wanda zai tsaya miki kinja ya gudu don haka bakida wani gata, kibini in labaki cikin gidan nan ko kina kuskure wa in watsaki waje couse this is all my property. Tafada tana juyi tareda kada jiki, ta fice Abinta, cikin kaduwa ta dafe baki "na janyo ruwan kashe kaina. ranar ba inda ta iya zuwa, koda ta Kira kawarta kin dagawa tayi domin Y'ar ta tashafa mata komai, don haka ta tattaro inata inata tayo gidan, suka baje a side din salifar suna y'an da sukaso batareda sanin momy ba. Domin kirjin ta ciwo yakeyi tana cikin tsananin tashin hankali, kanta har wani nauyi yake mata, waye zata fadawa ya taimake ta yadawo mata da Khaleel? Modu, tayi saurin mikewa tareda daukar key tayi waje cikin sauri, ta manta ranarda kafarta ta taka zuwa gidan shi Amma yau batada wani zabi dole taje.
Saida tafito taga motar kawar tata, batabi takaiba domin khaleel ne damuwar ta idan yana nan komai zai dawo dai dai don haka dole tasa yadawo kota halin yaya.

Shikan shi Alhaji yayi mamakin ganin ta yau a gidan shi, saidai yanda ta saukar da kai yafi bashi mamaki" Baban yara shin ko kasan da tafiyar khaleel? Shine maganar ta tafarko bayan sun gaisa, yace mata "ya akayi Hajiya balkisu? Nayi matukar mamaki da na ganki gidana yau. "Nidai bashine matsala taba, Ina so inji in kasan inda yarona yaje? "Bansani ba toh, ai d'an ki ne kece uwar shi kinfini Iko da mulki akanshi don haka kike zuba sarautarki a matsayin ki na uwa, yau ya akayi kike neman shi a wurina? Kije ki nemeshi duk inda yaje. Wani irin takaici taji y'an da yake fada mata magana a kai kaice, " toh ai kaima akwai hakki a wuyan ka tunda Amana d'an uwan ka yabar maka, don kasa ga rufemai idanu shine zaka bari zuri'ar shi ta watse, shi wancan ya tafi, wannan kuma ya gudu yabarni, don girman Allah nidai kafadamin inkasan inda yaje.
"Bansani ba kitashi kibani wuri, kedaman matsalar ki jahilci kije ki nemi ilimin addini kafin ki mutu cikin duhu domin kalaman ki Sam bana mai ilimi bane, da kinada kwakwal wa da kin gano mugun halinki duk shine ya janyo miki halin da kike ciki, kuma bakiga komai ba inda wainnan mutanen banzan da kike tareda sune, kije sune zasu cire ma Y'ar mutane hakki da kika tsana kika hanata sakewa da mijin ta tunfarko kuma Allah ya nuna miki Aya akan dole dai saita rayu da jinin naki da bakya kauna, meye laifin talauci ke kika bawa kanki Arziki? Ko ke cikin Arzikin aka haifeki, saboda kawai kinshigo cikin zuri'ar mu kin lashi jar miya kinfi uban kowa daga kafada..... Kuka tasa mai ciwo tareda mikewa " basai kaci mutunci naba modu, basai katuna min da Asalina ba, nasan duk inda nafito Amma kasani inda sa hannun ka dana yabarni sai Allah yasakamin. Ta juya tafita tana kuka, a hanya ta Kira zarah tasa kuka, ko bayani takasa yimata, " Aunty lafiya yada kuka kuma? " Ina cikin masifa zarah khaleel ya dauke Naziya yabarmin kasar baki daya sannan yanzu wannan tsinanniyar itada uwar ta sun tare min agida..... Ta kora mata komai. tasa salati, tareda cewa Ina zuwa Aunty Anjima ki kwantar da hankalin ki.
Kuka takeyi sosai yanzu take nadama mara Amfani tunba aje ko Ina ba, domin babu abin tashin hankali a wurin ta sama ga tafiyar khaleel.


Sun sauka lafiya Wanda cab ke jiransu already a filin jirgin, tayi matukar gajiya tayi bacci harta gaji, tundaga filin jirgin take baza idanun ta domin tasan wannan kasa tanada cigaba sosai a fadin duniyar nan, domin ta hada al umma daban daban yare Kala Kala, dafa kafadar ta yayi tareda cewa " welcome to bangkok madam. Fuskar shi dauke da murmushin farin ciki, kallon gajiya tayimai ya ce " sorry muje ga mota. Ya bawa driver umarni ya kwashe kayan su suka shige baya yana kwakume da ita, kallon bakin shi takeyi Wanda take mamakin y'an da yake zuba yaran Japanese da driver kamar yaren da aka haifeshi dashi, saida yaga tana kallon shi yayi murmushi tareda cewa " zankoya miki different language anan Chinese Japanese harma Hungarian language Wanda duk sun tattara a wannan kasa, kuma idan bakin sani ba bazaka banbance suba domin kusan duk kalar idanun su daya da. Dora kanta tayi a kafadar shi domin wata irin kasala takeji wadda bata taba jin irin taba a jikin ta.
Yasaka hannu tare da rungume ta, ba Abinda yakai mai wannan dadi a rayuwar shi, ganin shi tareda ita a wannan kasa da yake mafarkin ganin ta a ciki, burin shi yagama cika a rayuwa, sai Ajiyar zuciya yake yi, ita kuwa kallon hanya takeyi tana shakar iskar wannan kasa mai matukar burgewa, ko Ina tsab tsab har suka isa unguwar da yake zama, gidajene kamar quarters ba wani hayaniya sai kukan tsuntsaye, cab din na tsayawa ya saketa tareda bude kofar yace " let go madam we are home our small world. Fitowa tayi tana kallon KO Ina, gidan ba wani kato bane akan gidan su dake kano, Amma tasani a irin wannan kasar wannan gidan kudin shi sai yafi karfin wancan, gashi yaji fulawoyi masu bansha'awa da furanni,
Masu sanyin kanshi, fitowar wata mata Y'ar China ne daga cikin gidan zata iya kaiwa kimanin shekara arba'in tana sanye da afron na girki, fuskar ta sake tana mai welcome da yaren sinanci ya amsa tareda nuna mata madam dinshi, da gudu ta Kara so tana rungume ta tareda zuba mata yaran da ko zo inkasheki bazata jiba, kayansu ya shigar ita kuma ta rakota har ciki jikinta na rawa, kamar rakumi da akala haka ta bita,
Kamar yanda kasashen na waje suke basa cika tarkace a cikin gidajen su haka shima nashi simple ba wani hayaniya sai sai dai kasan koma meye kudi ne a ciki, saida ya shigar da trolley da Jakar shi ta laptop ya dawo tareda cewa ta hado musu Abinci madam is hungry yace ta shigo bedroom ta yi fresh up su rsma sallolin su, dama akagare take da wanna Matar me shegen zuba da bata gane komai, tuni ta cire hijabin jikinta suna shiga ta ga kujera ta zube kwance domin tayi mugun gajiya jikin ta kamar anyi mata duka, kwabewa shima yayi tareda daura towel ya juyo, yaga yanda ta kwanta tana shirin yin bacci, murmushi yayi mai d'an sauti, ya matso tareda tsugunawa gaban ta, ya dukar da kanshi dai dai bakinta ya bata light kiss, tayi saurin bude idanun ta, murmushi ya sake mata kafin yace " bacci? Wani irin lumshe idanun ta takeyi gwanin sha'awa, Abun ya burgeshi sosai yaji tsigar jikin shi na Tashi Wanda ya dade yana controlling tareda Addu'ar neman dama, yau gashi gata a cikin gidan su sukadai, harshen shi ya Dora saman girar ta ya lasa tareda matsawa har kan hancin ta ya gangara lips dinta ya rike na kasan gam yana Ajiyar numfashi, bajewa yayi zaune akasan tareda rungumota zuwa jikin shi, zare bakin ta tayi cikin kasalar da yasakar mata tace " bacci nakeji, kuma bamuyi sallah ba. "Uhmm. Kawai ya iya cewa tareda saka hannu ya dago doguwar rigar dake jikinta ya zare ta ya wurgar, jikinshi har wani irin mazari yakeyi kamar mayunwacin zaki, " zakiyi bacci letter baby sallah kuma zamuyi yanzu, na matsu da yawa

Please Login or Register in order to submit comment