Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba d'aya hankalin NAFI'U shi ma yana kan su jin IMRAN zai dubo ta ne sai yayi kamar bai jiba..

IMRAN na fita Adda ta bi bayan sa da harara a zuciyar ta tace"zama ka dawo sarkin iyayi." ta fad'a tana wani saki murmushi.

Shashin su yaje, yana ta kiran ta, da duduba wa ko zan hange ta, shi ne taik'a can d'aga can, duk inda yake saka ran gani bata wajen, gaba d'aya hankalin sa ya tashi, sai zufa yake yana haki, yazo komawa babban falon ne dan sheda musu, sai yaji karar fad'uwar abu kamar k'arfe ta bangaren Addan jameela, haka kawai yaji hankalin sa bai kwanta ba dan haka yace"waye a nan ?" ya fad'a dan k'arfi.
shiru babu amsa, har ya fara takawa zai shiga shashin yaji murya Adda ta bayan sa tace"IMRAN tana ina kuma naga zaka shiga nan?" ta fad'a tana kallon bayan sa.

Shi ma kallon ta yayi yace"bangan ta a can bane shi ne na fito na fad'a miki, ko kinga wani ya d'auke ta a cikin su khadija? "

Zainab tayi d'an shiru can tace"aa gaba d'ayan su suna zaune babu wanda yaje ko ina, amma tsaya na duba waje ko ta fita.""
tana fad'ar haka ta fice daga wajen da sauri.

shima falon ya koma bai shiga sashin ADDAN ba.

Gayen dake tsaye jikin labulayen d'akin rik'a da JAWAHIR jin sun matsa daga wajen, ya sauke wata wawuyar a jiyar zuciya, kana ya mai da duban sa ga yarinyar da ta jima da suma tun matsi mata baki da yayi, cikin sauri yayi hanyar kicin din gidan dan tana ne kawai zai samu hanyar wuce wa, ba tare da an kama shi ba.


hankali a tashe yace"Baffa na ba'aga JAWAHIR ba fa har yanzu." ya fad'a cikin sammatsi.

gaba d'aya mutane falon suka mi'ke tsaya ido waje cikin had'in baki suka ce"me!!?"

"ce Baffa's tun d'azu nake duba ta, kuma na duba ko ina bangan ta ba wallahi ina ga kamar hannu ne ya d'auke ta."

kafin kowa yayi magana ADDA Mairo tace"kaji yaro da wata magana duk tsagerancin mutun ai bazai shigo har cikin wannan tangamemen gidan ma cike da matak'an tsaro ya saka hannu ya d'auke yarinyar ba, ka dai ka sake duba wa da kyau me yuwa ta shiga wani wajen ta kasa fito wa." ta fad'a cikin manyen ce.

Adam yace"kware kuwa da ido na, naga wuce war ta, ta nan waje ka shiga sashin ADDA SAMIRA dan nan naga ta nufa." ta fad'a yana nuna mai da hannu.

Samira taji kamar ta k'utuntumawa Adam zagi, amma sai ta d'aure tace"ta iya yuwa yaro kuma, shi ga ka duba ko nace muje tare naga ko ta shige waje ne." ta fad'a tana yi gaba su Baffa na bitan a baya, har suka shigo falon ta, IMRAN bai jira cewar kowa ba ya fara k'walla mata kira da *k'albi na!!* kina ina!! ? *k'albi na!!*." yana maganar yana duba duk inda yaci karo dashi,

IMRAN babu ko kara har cikin d'akin barci su ya shige yana duba ta, had'i da 'kwalla mata kira, amma shiru kuke ji tamkar bata wajen, aiko hankalin sa ya tashi jijiyoyin kan sa suka furfuto, gaba d'aya ya hautsine a d'an k'an'kanin lokaci idanun sa su kayi jawar dasu, babu wanda bai tsorata da yanayi da ya shiga ba, sun duba ko ina bata wajen.

hankalin kowa ya sake tashi Baffa ya gigice ya manta da yar fari ce, bako kunyar yayin sa yace"na shiga uku yanzu ina kuma yarinyar ta sake shiga, haka ma fa kwanaki aka d'auke ta kuma har d'akin barcin ta, yanzu ba dare bane bare nace, ana nema ta an rasa YaYa Abdullahi ku taimaka mini kar na sake rasa ta a rako na biyo, su biyu gare ni a rayuwa ta." ya fad'a cikin gigita.

Abdullahi ya kama shi yana girgiza mai kai yace"ka nutsu Nafi'u ina ji a jiki na 'yata tana cikin gidan nan babu abinda zai faru kaji zamu gan ta." ya fad'a da sigar kwantar mai da hankali.

Adam dai babu bakin magana dan har ga Allah yana son Jawahir, jin ta yake kamar khadija.

gaba d'aya sun suka fito daga shashin, suka nufi na ADAM lokacin Zainab ta dawo nan ta tare da mumunan labari Allah yaso ta fad'a ma'aikatan gida kuma sun bazu a ko ina na gida har ta bayan gidan kuwa, duk nacin mutun da taurin ran sa bai isa ya wuce ba tare da angan shi ba.

ko da suka duba na ADAM nan ma bata ciki, dan har kicin suka shiga ba su ganta ba.

IMARN yayi shiru na d'an wani lokaci yace"ina zuwa." yana fad'ar haka ya wuce da sauri sai shashin su jameela, yana shiga bai zarce ko ina sai kicin dan nan ne basu shiga ba, cak ya tsaya ganin hular ta ya she a k'asa babu komai a kicin din sai hayak'i da turiri da ya rasa ko na menene. gaba d'aya ji yayi kafar sa ta kasa d'aukar gangar jikin sa, cikin tashin hankali da rud'e wa, ya zube a wajen yana fitar da wasu zafafan hawaye, zuwa can ya zafga wani mahaucin ihu!! game da k'walla mata kira cikin hargitsi da tsabar rud'u.

gaba d'aya mutane gida wajen sa su kayo hankali tashe.

jikin Baffa har ruwa yake sabida tsabar rud'ewa, Adam ne ya shige gaba ganin kowa ya gara duba wa, cak ya tsaya cikin tsantsar kid'ema da rawar jiki.......


*a nan zan daka ta sai naga comment din ku sannan zan ci gaba*

Comment
And
Share
Please

Mrs Abubakar ce
[7/29, 1:25 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( _cutar ka za suyi_ )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*








LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...


_Rashin comment din ku ya fara yawa gaskiya_ 😒😒
8⃣➖9⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

A sandare take, a kasa babu alamar rai a tare da ita, tayi wani duhu a cikin d'an k'ank'anin lokaci, Baffa Adam ya kasa k'arasawa gare ta, banda rawa babu abinda jikin sa yake, gani haka ya sa kawu Abdullahi 5a kawa a hankali kamar wanda k'wai ya fashe mai a ciki ya k'arasa gare ta, gani halin da take ciki, jiki na rawa ya d'auko ta bakin sa na ambata sunnan Allah, bai jira cewar kowa ba yayi waje da ita cikin sauri da mazarin jiki.

sai da ya kai waje sannan ya bud'e murya yana kiran IMRAN da k'arfi, kafin ya gama sauke numfashin sa, har ya iso waje duk da irin kukan da yake kuwa, ba su zarce ko ina ba sai asibiti gaba d'aya gidan sunyi carko-carko a bakin d'akin da aka shiga da ita, sun d'auki lokaci mai tsaho sannan Doctor ya fito yana share gumin da ya zubo mai, office ya wuce suka bi shi a baya, sai da yayi wasu yan rubuce-rubuce, kana ya d'ago rai a b'acce yace"maganar gaskiya ban ji dadi yanda akayi sakaci da yarinyar k'arama irin haka ba, yanzu ba dan Allah yayi tana da saurin numfashi a duniya ba, dashi kenan sai da ace tsautsayi ne, bayan babban ganganci aka mata...."

IMRAN yayi sauri k'atse shi ta hanyar cewa"daka ta dcotor ina so naji tana raye ko-ko, ban son d'ogon zance, yanzu in tana raye menene abinda ya same ta?" ya fad'a dan son sani abinda ya faru da ita.

Dcotor ya sau'ke a jiyar zuciya kana yace"binciken mu ya nuna mana, ta jima da suma ta sanadin taushe mata hanci da baki da akayi, dan ko ba'a fad'a kuna kallon fuskar ta za ku gane haka, duk da babu shatin hannu a jikin face din ta, da alama anyi amfanin da wani abu ne, sannan an sake yun'kurin cutar da ita ta hanyar sha'ke mata wuya wanda har sai da ta farfad'o ta sake d'ogon suma, wanna shine abin da muka gani kuma muka shida dan Allah a kiyayye domin tasha wuya da yawa." yana maganar ne lokacin da yake k'ok'arin fita a office d'in.

IMRAN ya saki wata muguwar kara yana cewa"Ya rabbi, wai me yarinyar nan ta tsare musu ne? ko da yaushe basu da burin da ya wuce su cutar mini da ita, da zan kama mutun ko waye da hannu zan harb'e shi, wallahi da bazan raga mai ba ko k'ank'ani ne." ya fad'a cikin muryar nan tasa me dad'in sauraro duk da yana cikin tashin hankali amma hakan bai hanata dadi ba..

Adda samira tayi mai wani kallo sannan ta kawar da kan ta gefe, ta sake d'ago tana kallon sa, ta kasa jurewa har da tayi magana tace"umm ni kam IMRAN abi ka yana d'aure mini kai mutuk'a, haka kuma bazan boye maka ina gani kamar da sa hannu ka a sace yarinyar nan da ake..." maganar ce ta mak'ali gani irin kallon da kowa yake mata...


Abdullahi yayi mata wani mugun kallo kana yace"ke!! har kina da baki magana akan haka? amma tukuna dai menene dalilin ki na fad'ar hakan?" ya fad'a rai a mutu'kar b'ace..

"kayi hakuri Baffa jameela kawai na kasa yarda ne da abin da zuciya ta take raya mini har sai da na maganun, a cikin gidan nan dai gamu nan da yawa mu, kuma ba ita d'aya yarinya ba, ga su jameela da khadija amma tunda nake da su ba a tab'a d'aukar ko d'aya daga cikin su sai ita, kuma duk lokacin da wani abu zai faru to shine yake zuwa dashi akan bai ganta ba, ko yace an sace ta, haka kuma shine yake nemo ta, abin duba wa nan mudin ba wai ya san inda take ba ya akayi yake d'auko ko? kuma ya akayi ya san an sace? gaskiya yana da kyau a bincike shi, dan ni sam nafara zarewa da alamarin sa, kullum shi ne yake fito mana da matsala kuma in an duba sai aga haka ne, tabbas akwai ayar tambaya a tare dashi." ta fad'a cike da ya'kini.

IMRAN kukan sa ya tsaya tunanin sa ya tsaya gaba d'aya ya rasa inda kalaman ta suka nufa, haka kowa na d'aki ya mayar da kallon sa gare shi, ana mai kallo zargi.

Abdullahi yayi wani murmushi irin nasu na manya yace"ai in da wanda ya cancanci a saka ma ido, bai wuce ke ba domin duk lokacin da wani abu zai faru to a part din ki ake samun ta, yarinyar nan tun kan tayi kafa ana same ta a part din ki ya kai sau biyar kuma duk cikin mumunan yanayi, kin ko kece alamarin ki akwai abin duba wa a cikin sa, dama shi gwano bai jin warin jikin sa, amma ba damuwa kin d'aura mu akan hanya zamu bincika kamar yanda kike ce tunda shawara ce kika bayar.?" ya fad'a yana mata murmushi..

ADDA SAMIRA bata yi tsamani akwai wanda zai zarge ta ko yayi tunanin ita ce ke kula komai ba,, bare kuma har a fad'a mata irin abinda mijin ta ya fad'a mata, a yanzu take taji cikin ta yayi wata irin hautsi nawa, cikin kid'ema tace"me kuma zai kawo wannan maganar tsakanin da Allah, banda abin ka me zan ci a jikin wannan yar miniyar yarinyar? ni wallahi a matsayi d'aya nake d'aukar ta ita da jameela, kawai tsautsayi ne yake kawo ta part din na kamar yanda na fad'a a kwana kin baya.." ta fad'a cikin dakak'iyar zuciya, wanda duk kutullar mutun bai isa ya gano ainahin halin da take ci ba, dan har d'an b'acin rain ta nuna...

Abdullahi yayi mata shiru yana ci gaba da tunanin mafita, babu wanda ya kulla da lokacin da IMRAN yaje gaba ta sai ji akayi yace"kin san irin kaunar da nake mata kuwa? shin kin san yanda nake jin ta a zuciya ta, karfa ki manta ita din jini nace, menene ribata in na cutar da k'anwa ta!? farin ciki na, wallahi zan iya komai akan ta, karki ji nace komai kiyi tunanin d'an k'aramin abu, ki sa a ran ki komai fa nake nufi."" hannu ta ya kama yayi waje da ita, bai zarce da ita ko ina ba sai d'akin da aka kwantar da JAWAHIR hannun ta ya d'aura d'aya a saitin zuciyar jawahir, sannan ya d'aga wanda ke hannu sa ya d'aura akan saitin tashi zuciyar yace"maza fad'a mini gaskiyar abinda kika ji? kin yarda ita din bugun numfashi na ce? kina tunanin zan iya cutar da rayuwa ta ne? to tun wurin ma ki d'ai na, ki cire haka a ran ki domin jawahir rayuwa tace ita din, dan haka babu yanda zaayi na cutar da iya, kuma a yau nayi miki alkawari duk wanda na kama da alhakin cutar mini da ita wallahi, wallahi azeem sai na b'atar dashi, sai na gigita rayuwar sa fiyya da tsamani duk me ko'konto." yana gama fad'ar haka yayi wurgi da hannun gefe sannan ya rab'e ta ya wuce abin sa..

Su Baffa dake tsaye bakin 'kofa suka bashi hanya babu wanda ya tsawatar mai dan sun san gaskiya ya fad'a.

Adda Samira ta tsaya cak a inda take idon ta na kawo k'wallar bakin ciki, da tsantsar mamaki tabbas babu karya a cikin zance sa dugun zuciyar su lokaci d'aya suke yin sa, musamma yanzu da suke cikin tashin hankali, ta mayar da kallon ta ga Jawahir dake kwance, har yanzu hannun ta yana kan kirjin ta, ji tayi ta sauke wata ajiyar zuciya, cikin tsananin tsoro da fargaba ta d'auke hannun ta da sauri kamar wace ta tab'a garwashi, tana wani duba hannun da kuma kallan inda jawahir din take.

Abdullahi yayi mai yan uwan sa inkiya da suje waje, iko babu musu su ka fice, shi kuma ya shiga ciki.

cikin sauti tafiyar sa yasa tayi sautin d'akewa tana aro face din tsusayi tana sama face din ta, sannan ta juyo tana kallon sa kamar tayi kuka tace"Baffan jameela ka tayi ni neman gafar yaro na, tabbas nayi ba dai-dai ba kuma naga kamar ya dau zafi dani, sharin shedan ne bazan kara ba." ta fad'a tana fad'awa jikin sa.

Abdullahi yayi murmushi gefen baki yace"a'a ki dai fad'i gaskiya kin tsora ta ko? fad'a da aljanin sam babu riba, karki manta na san komai da kike shirya, abun ki ya fara yawa su yara ne basu san komai ya kamata ki ajiye makaman yakin ki, in ba haka ba ke za'a bari da jin kunyar mutane, ni kai na kike ishe ni angulu zata kuma gidan ta na tsamiya." ya fad'a yana mata wani mugun murmushi.

take jikin ta ya d'auki rawa, da yake makirace uwar makiraru, sai ta sake kuka tace"yanzu dama dan Allah Baffa jameela abin da dakake fad'a d'azu da gaske ne, karfa ka manta jawahir yarinyar ce kuma 'yata ce, ya zanyi na cutar da ita wallahi ban tab tunani kallon zargi kake mini sai yanzu, ina rokon Allah mudin ina da saka hannun akan abinda yake faru, Allah ya tuna mini asiri kowa ya gani.." ta fad'a cikin shasha'ka.

tace Allah sai jikin sa yayi sanyi, kawai sai ya tsanci kan da cewa"to Ameen tunda haka kika zab'a, amma karki manta shi shari d'an aike ne, ki rik'e wannan a ranki."" yana fad'ar haka ya ture ta a jikin sa ya fice.

bayan sa tabi da kallo wani kululun bakin ciki na tukare ta, tabbas dole ta d'aga k'afa akan komai, amma kar ya manta shi kan sa bai ci bulus ba, duk kan su sai tayi maganin su, sannan ta kallen gadon da jawahir take a fili tace"duk kece matsala shegiyar yarinyar." ji tayi tamakar ta sha'keta ta huta a lokacin...


Jawahir sai da ta shafafe kwana uku a kwace asibiti gaba d'aya hankali mutane gidan yana kan ta, haka Adda Samira ta ishishire a wajen, inda Abdullahi yasa mata ido sosai duk wani mutsin ta yana kallo,,, IMRAN bai barin Asibiti sai Baffa Nafi'u yayi da gaske sanna yake zuwa ya dan huta sannan ya dawo, a haka har aka sallamo ta.



_gaskiya bazan boye muku ba rashin comment din ku yana damu na, kar kuga na dae na typing kuji haushi ne._


Mrs Abubakar ce
[8/1, 2:18 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...

*kuyi hakuri na rashin jina da ku kayi hakan ya faru ne, sabida wani dalili nawa daban na ga sa'kon ni ku na gode.*



1⃣0⃣➖1⃣1⃣


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Ko da suka dawo gida, haka aka ci gaba da jiyar Jawahir inda Adda Samira ta d'auke ta zuwa part din ta, tana kula da ita sosai ga soyayya da take nuna mata.


Jawahir tana k'arama taga abubuwa da yawa, a rayuwar ta domin haka aka dinga farautar rayuwar ta, da taimakon ALLAH da na IMRAN, ta dinga k'ub'ata.

Bayan shekaru 18, JAWAHIR ta zama budurwa hasken ta ya sake fito wa, ga wata haiba da take da shi, kyau iya kyau ya sake baiyana a gare ta, ga wata irin shak'uwa dake tsakanin su da Imran, babu wanda baya mamaki sha'kuwar dake tsakanin su.

Jameela tunda ta girma ta zama budurwa bata da burin da ya wuce ace Imran ya zama mallakin ta, kullum burin ta bai wuce a gan su tare a inuwa d'aya ba, amma matsalar ta d'aya shine Jawahir,, a duniya tana so taga yana mata yanda suke da jawahir ko khadija, amma a banza kamar yau.


A palo ta isake shi, yana zaune yana latsi-latsi a waya, ta shigo palo cikin shigar ta ta fitar da tsireci, cikin takun jan hankali, ta isa gare shi tana wani nark'ar da ido kamar me jin barci, kusa dashi kad'ai ta zauna, tana wani karya jiki, murya na raurauwa tace"YAH IMRAN sannu da huta."

muryar ta kawai ta sheda mai, ko wacece, bai d'ago ba yace"yauwa sister sannu da fito wa." ya fad'a cikin isa.

ta kalle shi zuciyar ta nayi mata wani irim zullo, sabida tsananin shau'kin da take ji duk lokacin da za su had'u, a hankali ta sake matsowa kusa dashi, tana wani kashe ido tace"YAH me kake yi ne haka?" ta fad'a tana haye wa jikin sa gaba d'aya..

IMRAN ran shi ya sake b'acci, amma sai ya d'aure cikin dabara ya zare ta daga jikin sa, yana mata wani murmushi wanda shi d'aya yasan ma'anar sa, yace"nutsu mana 'yar k'anwa ta, kin san yayan naki bai cika k'wari ba, tsaf zai karye." yayi maganar yana tura ta gefe cikin hikima...


sam bata ji dadi ba, dan duk lokaci da zata zo jikin sa, sai ya san abinda zai fad'a mata, dan kawai ya ture ta, amma sai ta d'aure, tana ya'ke yafi kuka ciwo tace"sorry na manta yayan nawa ba jarime bane ashe." ta fad'a tana kallo face sai dan ganin yanayin da zai shiga, abin takaici har yanzu bai kalle inda take ba,, haka kuma bai sake tanka mata ba, shiru ne ya biyo baya zuwa can sai ga Jawahir ta shigo cikin nutsuwa da ka mun kai, bakin ta d'auke da sallama..

da sauri IMRAN ya d'ago yana mata wani kallo, kana ya amsa salamar ta game da ware mata hannuwan sa, cikin jin nauyin sa ta iso gare shi amma sai tak'i rungume shi ta zaune gaf dashi tana wani sunna kai tace"My!! dama kana nan naje d'akin ka ina ta neman ka." ta fad'a cikin shagwab'a fusaka, kamar za tayi kuka duk da tana cikin nutsuwar ta.

IMRAN ya sauke wata ajiyar zuciya, cikin isa da iza yace"Sorry k'albi na! ai kin san duk inda nake ina nan din na." ya fad'a yana tab'a saitin heart din sa.

ta wani tsumshe ido kana ta ware su akan face din sa, tana wani karkatar da kai gefe them tana kallon sa, tace" nafi kowa sani haka, tunda duk jini d'aya ne, amma fa sai gaya mini me yasa yanzu ka ke tafiya ka bar ni?" tana turo baki gaba, had'i da duga kafa a kasa.

IMRAN yayi wani k'asaitacen murmushi, yace"'kanwa ta ina tausaya wa mijin da zaki aure, dan sai kin kusa kashe shi da wani shagwab'ar taki." yayi maganar yana tal'kace mata hanci.

ga mamaki sa kawai sai yaga ta fara fitar da k'walla hawaye wuwi.

Aiko gaba d'aya sa ya hargitsi a lokaci d'aya shi ma yana wani rawar jiki, game da kamo hannun ta cikin nasa ya matse da kyau yace"haba k'albi na, sani kan ki ne, duk duniya babu abinda nafi tsana sama da gani ki cikin kunci, bare kuma zubar hawaye ki, fad'a mini dalili wannan hawayen ki, ni kuma nayi miki alkwari da yarda Allah ko menene mudin bai zarce kima ba zanyi miki shi insha Allah..


Jameela ta gama cika da bakin ciki, domin ji take zuciyar ta tamkar wace aka watsawa, garwashe sabida tsananin kunar da take mata, tana cikin wannan yanayi ne na bakin ciki ta hango abinda zai tarwatsa mata zuciya..


Jawahir ta zamo daga kan kujera, gwiwowin ta a kasa har yanzu tana hawaya tace"ban san da irin kalmomin da zanyi gode ya a gare ka ba My!, ka nuna mini dukan gata kula wa soyayya da k'auna, gashi ko da yaushe burin ka ka sani a cikin farin ciki, kanayi komai domin nema mini farin ciki, gaba d'aya komai naka domin na kake yin sa, ni ko da me zan saka maka wanda nan gaba za kayi alhari da hakan? tabbas kai din ka cika cikaken masoyi na, na har abada wanda bazan

Please Login or Register in order to submit comment