Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina ummi take? Dama dr. Ba ya ƙasa ai ko?"

Cikin rashin fahimta ya ce "Ban gane ba, ummi kuma a gidan nan?"

"Eh, jiya ba nan ta zo ba?"

Abdul ya ɗan yi shiru ya ce "Ai ni ban ga ummi a gidan nan ba"

Kamar raihan zai yi kuka ya ce "Dan Allah ka duba mini"

Abdul ya jinjina kai, ya shiga cikin gidan, noor tana ta shirin makaranta, ya kalleta ya ce "Noor, wai ummi ta zo gidan nan ne? Ga raihan can a waje"

Noor ta ce "Jiya ta zo, a waje muka haɗu ma, ta ce mini wai yaya raihan ya saketa, ina ga su maama korarta suka yi, wai ba zata zauna a gidan nan ba".

Abdul ya ce "What! Saki kuma, sai kuma a kore ta daga gidan nan? Ina ta tafi to?"

Noor ta ce "Nima ba ta gaya mini ba"

Abdul ya fita da sauri, ya tarar da raihan na ta zagaye motarsa.

Yana ganin Abdul ya ce "Yauwwa tana ciki ko? Ka ce ta zo mu tafi"

"Me ummi ta yi maka zaka saketa? Ba abu ne da za a iya sasantawa ba? Har ta kai ga saki? Ka bani kunya raihan"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ce muku ta yi na saketa? Abdul ban saketa ba"

"Ba ka sake ta ba, me ta zo yi gida?"

"Ba ta fahimci meyafaru bane? Ka tsaya ka ji, wallahi ba laifina bane ba"

Abdul ya ce "To, koma laifin waye ummi ba ta gidan nan"

"Ba ta zo ba? Ina ta tafi?"

"Ta zo, amma a jiya ta bar gidan nan ban ma san ta zo ba"

Raihan ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ummi meyasa zaki yi mini haka? To ina ka ke ganin za ta tafi, ko gagarawa?"

Abdul ya ce "Bana tunanin ummi za ta je gagarawa, tun da ba shiri suke yi ba, sai dai ko maiduguri"

"Maiduguri ta tafi a daren jiya? Meyasa ta bar nan gidan? Wallahi ban sake ta ba. Dan Allah Abdul ka yi mini wani taimako mana".

"Ina jinka"

"Dan Allah kar ka gaya wa dr. Halin da ake ciki zan nemo ta, dan Allah kar ka gaya masa"

Sai tausayin raihan ya kama Abdul, lallai akwai maƙarƙashiya, sai dai ya san idan dr. Ya ji to ba raihan ba, har maama tana cikin matsala korar ummi da ta yi.

"In sha Allah ba zan gaya masa ba, zan saka a bincika gagarawa, amma ka kira wayarta?"

Raihan ya ce "Wayar a gida ta bar ta"

Abdul ya ce "In sha Allah tana nan lafiya, zan kira gagarawa ka tuntuɓa can maidugurin".

A rikice raihan ya juya ya koma mota, yana salati tare da tunanin in da ummi ta tafi.

A cikin motar ya kira Anty maryam ta can Maiduguri suka gaisa, sai dai yanayin yadda suka gaisa ɗin ya tabattar masa da ummi ba ta je maiduguri ba.

Abdul kuwa da ya koma cikin gida, ya tarar mami ta fito, ya gaisheta sannan ya ce "Mami wai jiya da gaske ummi ta zo?"

"Eh" ta amsa a taƙaice.

"To tana ina?"

"Na koreta, dan ba zan riƙe bazawara har a karo biyu ba, ta koma gidan ubanta".

Ya kalli farida ya ce "Haba maama, da ki ka koreta ina za ta je, ina take da shi da ya wuce nan?"

Farida ta ce "Ta koma gidan ubanta, ko wurin uwarta ta barni na huta a gidan mijina na sake, kuma kar sake yi mini maganarta, kan ranka ya ɓaci" bai sake cewa komai ba, ya fito ya ɗau wayarsa ya kira yaya Hashim can gagarawa.

Suka gaisa sannan ya tambaye shi ko ummi ta je.

"Ai ka san ni yanzu na bar cikin gagarawa, ina dutse ina koyarwa a wata makaranta, har matata muna can, su kuma gagarawa ba kowa yake da waya ba, masu wayar ma sai ka yi ta kira ba ta shiga, saboda rashin caji, amma zan yi duk mai yiwuwa na tuntuɓa na ji, ina fatan dai lafiya ko?"

Abdul ya ce "Eh lafiya ƙalau, na gode sai na ji ka" ya kashe wayar.

Ko da Abdul ya kira raihan ya gaya masa halin da ake ciki hankalinsa ya tashi, ya ce wa Abdul zai je gagarawa da kansa.

Abdul ya ce "Muddin ka je idan ba ta can, dr. Zai iya sanin halin da ake ciki duk da ba ya ƙasar, ka bari mu ji mu tabattar ta je". Da ƙyar ya lallaɓa raihan.

Gashi a iya tunanin sa, ummi ba ta da ƙawaye ko wasu ƴan uwa da za ta je gidan su.

Yana cikin wannan taradaddin, managern su ya sama musu masauki a china, ya kira raihan yake sanar masa, da ummi ta samu kuɗi saboda wannan videos ɗin da suka yi, kuɗi masu yawa.

Raihan sam ba fahimtarsa yake yi ba, ya kashe wayar. Yana kallon kiran mami a wayarsa ya share, ya cigaba da tunanin ina zai ga ummi?.

"Ai garin Allan ya waye ko, sai ki fito ki kama gabanki" Iya ta riƙe ƙugu tana huci.

Ummi ta ƙarewa iya kallo, ta tsufa sosai sai dai zuciyarta babu Allah sam.

"Iya wai me zamana a gidan nan zai rage ki da shi ne?"

"Kar ki sake ki yi mini rashin kunya, ki zo ki fice, ai yanzu kin san in da uwarki take"

Tana cikin maganar sai ga Idris yayi sallama, dan ya zo ya ganewa idonsa da gaske idan ummi ta dawo, an ce masa aurenta ya mutu.

Ita ɗin ce kuwa, kar da ita gwanin sha'awa.

Nana ce ta yi sallama ita ma, tana ganin ummi ta fara murmushi ta ce "laaa ashe ke ce ki ka zo?"

Ummi ta ƙaƙalo murmushi, ga zafin maganganun iya da take ta yaɓa mata babu ƙaƙƙautawa.

Tana dawo da abubuwan da suka wuce, tana sake nanata cewar son zuciyar mariya ne ya kashe bashir ta haukace.

"Ke a duniya har ki na da bakin da zaki cewa wani yana son abun duniya iya? Duk wannan tsanar da ki ke yi mini ta samo asali ne saboda mahaifina ba shi da abun duniya, ki ka riƙe ni da zalunci, ki cutar da ni da dafin harahenki, jikokin ki suka yi mini zalunci kala-kala, ki ka danne ni aka yi mini ɗurar dauɗar gora da ki ke cewa ciki ka sha ta. Iya kema sai na ɗura miki dauɗar gorar nan na ga ko zaki iya shanyeta. Na yi miki uzuri a rayuwa, duk da zaluncin da ki ka yi wa uwata da wanda ki ka yi mini.
Banda zaluncin da jikanki yayi mini, duk ba su isheki ba iya, wallahi tura ta kai bango babu ɗaga ƙafa tsakanina da duk wani mahaluki da yake ganin ni abar banza ce, zan bar gidan nan amma zaki ga abun da zan iya, kuma ba zan bar gidan nan ba sai na kammala abun da na yi niyya, tun da akwai gadon ubana a gidan nan, a da na so in mayar da komai ba komai ba amma a yanzu komai ji nake ya dawo sabo, wallahi iya ki rubuta ki ajiye zalunta ta da ki ka yi da ke da Idris wallahi ba zan taɓa yafewa ba haƙurina ya ƙare mara mutuncin da ki ke so na zama".

Baban su idris ya ce "Ke ummi, shaye-shaye ki ka fara ne? iyan ki ke wa Allah ya isa".

"Lokacin da ɗanka ya keta mini haddi me ta ce, kai me ka yi a kai? Ina da ƙanan shekaru lokacin, abun ya din ga zuwar mini a mafarki na rasa wane irin mafarki nake yi, Iya da bakinta ta goranta mini, ƙarewa da ku ka je karɓar kuɗin aurena har wannan maganar ku ka ɗaukko, kuma dan rashin imani, kun san abun da ya faru bayan na auri Idris ya din ga wulaƙanta ni, baku gaya masa cewar ɗan uwansa Hashim ne ya keta mini haddi ba, duk da yaya magaji yayi iya ƙoƙarin sa dan ya wanke wancan laifin da ya yi. Kuna ina na kwana a waje tsirara ruwa yana dukana, da duk sauran zaluncin da aka yi mini? Wallahi ba zan yafe ba, kuma na shirya tsaf dan aikata abun da ba kwa tunani, sai na tagayyara ku, ba dai kuɗi da son abun duniya ki ka saka a gaba ba, zaki gani"

Tsit aka yi a wurin, dan da yawa ba su san wasu abubuwan sun faru ba, ta yi wa Iya wankin babban bargo.

Haka Ummi ta zaune wa amarya a ɗaki, taƙi tafiya, Iya bata fasa cigaba da cin zarafin ummi ba, duk da irin abubuwan da ummi ta yi mata, ta cigaba da aibata ummi, da cin mutuncnta.

ranar kwanan amarya ya zagayo, ummi ta bar ɗaki ta ce ba zata bari ba".

A kwana na uku, Yaya magaji ya zo gidan, sai dai bai tarar da ummi ba, dan asubar fari aka ce ummin ta bar gidan ba ta yi wa kowa sallama ba.

Gaba ɗaya raihan ya fita hayyacinsa, kwanaki huɗu ba ummi ba labarinta, ya ƙi zuwa gida ya daina zuwa wurin aiki, Alhaji ya kira shi yana tambayarsa ko lafiya ya ce masa ba shi da lafiya ne.

Tun da ummi ta tafi, kullum da ciwon kai yake kwana yake wuni, gashi ba ya iya cin abinci duk ya fita hayyacinsa, kai da ka ganshi ka san baya cikin nutsuwarsa.

Ummi ba ta yi wa ƴan gagarawa sallama ba, sai nemanta suka yi suka rasa.

Kwananta uku da barin gagarawa, wanda yayi dai-dai da kwananta bakwai da barin gidan raihan, aka kaiwa su kawu Ilyasu sammaci daga kotu, ummi ta yi ƙararsu a kan raba gadon kakanta a fitar da na babanta, sannan a bata na ta gadon, da tumunin takabar mahaifiyarta!!!

(Tofa! Ummi ta zama boss😂)

I hit the jackpot with PalmPay! Join PalmPay with my link or my code 'XWPK6722' within 72 hours to help me get my gift! >>https://link.palmpay.com/uwyy6

Team Ummi wanda ba su taɓa cike palmpay ba, dan Allah ga refaral ɗina a bi link a cike mini.

Ayshercool.
08081012143

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
                    CUTARWA!




AYSHERCOOL

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

43

PAID ADVERT

*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*



43

Magaji ya sake duba takardar da aka kawo sammacin ya ce "An ya ummi ce ta kai wannan ƙarar?"

Iya ta ce "Za ta aikata, dan ba ka ga rashin mutuncin da ta tafka a cikin gidan nan ba"

Kawu Ilyasu ya ce "Yanzu ba wannan ne abun yi ba, kai magaji kai ne ka yi boko, yanzu meye abun yi ta yaya zamu shawo kan matsalar nan?"

Kawu Saminu ya ce "meye abun yi magaji?"

Ya numfasa ya ce "Tun jiya nake kiran wayarta a kashe, kamata yayi a fara ganin ummi, amma me aka yi mata har ta kai ga ta aikata haka, ummi da take saliha?"

Babar auwwalu ta ce "Ai ummi ta fetsare, dan ba ka ga rashin mutuncin da ta yi ba, har cewa ta yi ka yi mata fyaɗe iya ta ce ayi shiru da maganar, dauɗar gora ciki ka sha ta, da iya da idris da kai duk ba zata yafe muku ba".

Yayi turus, gabansa yayi mummunar faɗuwa ya ce "Ni kuma? Yaushe na aikata?"

"Oho muku dai, ta ce Iyan ce da kanta ta gaya mata"

Ya kalli iya ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Iya ni kuma? Yaushe? Ban san zancen ba fa sai da na nuna miki ina son auren ummi, ki ka gaya mini cewar ragowa ce, an taɓa yi mata fyaɗe tana yarinya, na ce ina son ta a haka, tun da tana yarinya ne, ki ka ce ba ki yarda ba. Nayi-Nayi ki gaya mini waye yayi mata ki ka ƙi, za ki aura mata idris na ce ki gaya masa abun da ki ka gaya mini, ki ka ce idan na faɗa zaki tsine mini, sai da zaki aurawa Idris ita na ce bai kamata ba ki ka ce dama shi yayi mata, amma ki zagaye ki ce mata ni na yi mata fyaɗe tana yarinya, duk saboda ki kare wanda yayi? Baki yi mini adalci ba, tsawon shekaru ummi kallon macuci take yi mini kenan?"

Iya ta ce "Ni fa ba haka na ce mata ba, na gaya mata hakan ne dan ta yarda da auren Idris a karo na biyu, kar ta auri wanda za ta aura amma kuma taƙi, kuma na yi haka ne dan Idris ya samu dama ta biyu a daidaita zumunci"

Hashim ya ce "Kuma ki ka ce mata ni na yi mata fyaɗe Iya, amma an yi abu ba ta sani ba har ki ka gaya mata? Wace ribar ki ka samu a kan hakan? Kawai ki cuce ni ki ɓata ni a idon yarinya saboda ki kare Idris? Iya meye dalilinki na fifita wani sashe a kan wani a cikin iyalanki ne?" Tuni idonsa yayi jawur, ya jefar da takardar sammacin ya ce "Ku je ku san yadda zaku yi ni ba ruwana"

Kawu Ilyasu ya ce "Idan ka tafi gidan ubanwa zamu koma? Yaya zamu yi da wannan abun? Ta ina za a fara rabon gadon shekara talatin da wani abu baya?"

"Wallahi baba ba saka hannuna, ba zan shiga maganar ba" yayi ficewarsa.

"Iya baki yi mini adalci ba, kin rarraba mini kan yarana kamar yadda ki ka rarraba kan naki yaran saboda son rai, ƙiri-ƙiri babu jituwa tsakanin Idris da magaji saboda ke, ashe wanda ki ke zaluntar da yawa, gashi kin zo kin sake damalmala lamari" cewar babar su Idris.

Kawu Ilyasu ya daka mata tsawa ya ce "Rufe mana baki, da can baki ga hakan ba sai yanzu? Uwar ta mu zaki ci wa mutunci "

"Na faɗa ɗin, tsawon shekaru muna yi mata biyayya ashe cutar mu take yi, ƙiri-ƙiri ta din ga muzgunawa mariya da ƴar ta muna ganin mu take so da ƴaƴanmu ashe zumuncinmu take yi wa illa tana kassaramu, ba ayi mini adalci ba" haka gida ya kacame da hayaniya kamar za a bawa hammata iska.

4YEARS BACK (SHEKARU HUƊU DA SUKA GABATA)

Iya ta kalli ummi ta yatsuna fuska ta ce "Au ke yanzu a yadda ki ke ɗin nan, har wani zaɓi ne da ke? Kin san  dai mutum a hayyacinsa ba zai ce zai aureki ba, dan mazan yanzu fararen mata suke so kyawawa"

Ummi da kanta yake sunkuye ta yi shiru ba ta ce komai ba.

"Hmm ai duk da Idris ya ce ba abun da ya taɓa haɗa ku, ai ba a canzawa tuwo suna, kuma Idiris ɗin da ki ka guda shi ne rufin asirin ki, dan yadda ki ke ganin cewa an zalunceki da ki ka aure shi ai shi aka zalunta ya rufa miki asiri, tun da fanko aka kai masa, gaki fanko ga larura, duk namijin da zai aure ki ko dai a bazawara ko wadda ta zubar da mutuncinta tun a waje" ummi ta ɗaga kai tana kallon iya.

"Eh mana, ai ba ki kai budurci gidan Idris ba, tun kina shekara uku da watanni aka kawar da shi, dan an ƙetare ki"

Gaban ummi yayi mummunar faɗuwa, jikinta na tsuma ta ce "Fyaɗe kenan?"

"Ƙwarai fa, da ki ka fara tasawa ma ai cigaba da biye-biyenki ki ka yi, Idris shi ne wanda ya rufa miki asiri, amma an buɗe ki tuni, dan haka wani zaɓe² ba naki bane, kuma dole a wannan karon ki sake auren Idris"

Ummi ta kalli iya cikin ƙunar zuciya, Idris ɗin da ya kwatsawa duniya cewar ba budruwa ba ce ita, ga kuma ciwon sanyi ya cinye ta, kenan shi tuntuni ya san an yi mata fyaɗe. Sai a lokacin ta tabattar da cewa mafarkin da take yawan yi gaskiya ne.
Tana kwance tana bacci a ɗaki, fitilar ƙwai na ci a cikin ɗakin, jin motsin wani abu ya sa ta buɗe ido, ba ta iya ganin fuskar waye, ya rage hasken fitilar ɗakin, daga nan ba ta iya tuna komai sai muryar iya tana cewa dauɗar gora ciki ka sha ta, duk wanda ya tona wannan sirrin Allah ya isa ban yafe ba, ɗan uwanta idan ba a rufa masa asiri ba, zumunci sai ya lalace.

Ummi cikin wani irin gigitaccen kuka ta ce "Iya dama a gaske abun ya faru, ba Idris ɗin ne ba dai, ina ganin abun a bacci, kuma na yi biye-biye na bi wa?"

Iya ta yi mata wani irin mugun kallo ta ce "Uban waye ya ce miki Idris ne? Shekara uku da rabi ki ke a duniya lokacin, uban me zaki tuna?"

Ummi ta yi shiru sannan ta ce "Dauɗar gora ciki ka sha ta, duk wanda ya tona wannan sirrin ban yafe masa ba, ba haka ki ka ce ba a lokacin? Mama ta din ga kuka a lokacin da daddare, Idris ne mana iya"

Iya ta dafe ƙirji ta ce "An shiga uku, dama na daɗe ina faɗar kina da alaƙa da maita, tayaya zaki tuna abun da ya faru kina shekara uku da rabi? To ba Idris bane ba magaji ne"

Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a Iya Idris ne, dan haryanzu ban manta irin barazanar da yake yi mini ba, da ƙoƙarin sake haike mini, yaya magaji ne yake ƙwatata"

"Sai kuma ki yi, Idris godiya yakamata ki yi masa, dan taimakon ki yayi"

Ummi ta yi kuka kamar ranta zai fita, ta ji zafi da baƙin cikin mummunan labarin da iya ta gaya mata, daga Idris ɗin har hashim wata irin tsanarsu ta shiga ranta, amma ƙasan zuciyarta ya kasa amince mata da yaya magaji zai aikata haka, ta yi ƙoƙari ta din tuna alkhairin sa, hakan ya sanya yin ƙoƙarin ɓoye masa abun da yake ranta game da shi.

Gashi babu wanda za ta tattauna Maganar da shi, dan haka ita kaɗai tayi kukanta ta sha baƙin cikinta, haka zalika maganganun iya ba su yi tasiri a zuciyarta ba, ta ji za ta iya yafewa Idiris zaluncin da ya yi mata ba.

Iya ta faɗa mata haka ne, saboda zafin rashin amincewa da auren Idris a karo na biyu, da kuma yadda Hashim yake ta son nuna shi yake son ya auri ummi lokacin da suka je saukar.

Sai dai hakan bai yi tasiri a zuciyarta ta ji zata sake iya auren Idris ba, shi ne zuwan da suka yi har dr. Ya ce sai an nemi iznin ummi.

Ummi ta ɓata darare da dama tana kuka, tana tunanin babu wani abu mai kama da farinciki da zata samu a rayuwa. Yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ta ƙara tsananta gudun Raihan.

CIGABAN LABARI.

Raihan kamar zai zare saboda neman ummi, duk iya tunaninsa yayi amma ya rasa ina ta shiga.

Gagarawa kuwa Abdul suka kira suka sanar masa da halin da ake ciki, wai sun nemi lambar dr. Sun rasa su zo su kawo musu ɗauki, ummi ta kai ƙarar su kotu.

Abun ya bawa Abdul mamaki, Abdul ya tambayi ina ummin take, suka sanar masa ai ta bar gidan ba su san in da ta koma ba, ya cigaba da matsawa da bincike, dan ya san ummi ba zata aikata irin wannan ɗanyen aikin ba, ya kira Yaya magaji, magaji ya ce an yi haka, amma Iya ce ta kori ummi.

Ya tambaye shi ko ya san in da ummin ta koma, ya ce masa bai sani ba.

Abdul ya tabattar da lallai an kai ummi bango da har ta fara da irin wannan hukunci mai girma.

Kawu Saminu ya din ga nanatawa Abdul, lallai ya sanar da dr. Kan ranar da za a fara shari'ar domin, a kashe maganar.

Abdul ya ce "Kawu ka manta baya ƙasar, babu abun da zai iya yi a kai, kuma yanzu a fara mayar da hankali a samo in da take tukuna, sai a yi wa tufkar hanci, tun da in dai ba ita ta janye ƙarar ba, ba zai yiwu a kashe maganar ba"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma wannan yarinyar an yi sheɗaniyar mara mutunci, maimakon iya mu ta gaya mana ta ce a raba gadonta a bata, sai ta kaimu kotu?"

Ummi kuwa ana gobe za ta bar gidan su Iya, ta karɓi aron wayar amaryar kawu Ilyasu, ta aika nana ta sayo mata kati ta kira yaya magaji.

Suka gaisa ya ce "Ummi layi ki ka canza ne?"

"A'a yaya, akwai matsala ne, ina so ka taimaka mini ina gagarawa yanzu haka"

"Subhanallah, matsalar me kuma?"

Ummi ta ce "Aurena ne ya samu matsala, can gidanmu anty farida ta ce ba zan zauna ba, nan ma Iya ta ce sai na tafi"

Hashim ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mutuwa auren yayi?"

"Eh, mamansa ce ta saka ya sake ni, ba na son zuwa maiduguri in ɗora musu nauyi daga yin aurena, ga dr. Ba ya gari"

"Kin san menene, ni yanzu ina dutse ni da matata, ki saurara da kyau, zan yi miki kwatancen gidana, akwai mukulli a maƙwabta, zan kira su su baki, ki buɗe ki shiga ki zauna, ki bani account number ki in turo miki kuɗi, ko zaki buƙaci wani abun, amma Abdul ya kirani ana nemanki, basu san in da ki ke ba, ai ban san kina gagarawa ba".

Ummi ta ce "Dan girman Allah ko ya sake kiranka kar ka gaya wa kowa ina gagarawa, kuma ba wanda zan gayawa ina gidanka, dan Allah kar ka gayawa kowa idan ku ka dawo zan yi maka bayanin komai"

Ya ce "To shikenan, ki turo mini account number"

"Kar ka damu, akwai isashshen kuɗi a hannuna".

Ana idar da sallar asuba, Ummi ta ɗebi kayanta ta bar gidan iya, sai dai ba ta bar gagarawa ba sai da ta je ta shigar da ƙara a kotu, sannan ta tafi gidan magaji da ba a cikin gagarawa yake ba.

Ko da magaji ya dawo ummi ta kwashe komai ta gaya masa, sai dai ya ji zafin kora da wulaƙanci da Iya ta yi mata, sai dai ba ta gaya masa batun kai ƙara kotu ba, dan haka da ya je gagarawa bai nuna musu ya san meyafaru ba.

Sai dai tun da ya ji ta'asar da Iya ta aikata, ya kasa komawa gidansa, saboda damuwa da fargaba, ya kasa komawa gidansa ya kalli ummi, ashe duk tsawon lokacin nan kallon da take yi masa kenan?.

Ganin ba shi da wani zaɓi, ya sanya ya koma gidan, ya tarar da ummi da matarsa suna hira.

Kamar baƙon munafiki haka yayi sallama idonsa yayi jawur.

Ummi ta ce "Yaya menene? Wani abun suka yi maka?"

Ya girgiza kai ya ce "Ashe kin kai ƙara kotu?"

Ummi ta ce "Eh, dama ina son zan yi maka bayani, na san zaka fuskance ni"

Ya ƙarasa gaban ummi ya zube a kan gwiwoyinsa, sai ga hawaye ya ce "Wallahi! wallahi! wallahi ummi ban aikata abun da Iya ta

Please Login or Register in order to submit comment