Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

TYPING 📲Fri, Dec 13/24 4:51pm YUSRAH MUSA ABUBAKAR✨✨✨.





💕MÏÑÏSTËR ÄSHRÄF💕





WHATSAPP NO:+234 8160983083
yusrahmusaabubakar@gmail.com



A*W*A
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan karbar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan.

____________________
____________________________
___________________________________




STÔRY WRITTEN ND EDITING
YUSRAH MUSA ABUBAKAR
✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë.




¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶
I'm here to make you happy educated domin nifa I have no girman kai if you fushi dani to wallahi you are just 6atawa kan k lokaci.




THINK BEFORE YOU DO
Always be watchful don't take risk don't try to get lost try to protect your life always, be good be helpful people will like u to be a happy child like my daughter Fatima Zarah Ilham little Zarahn Aunty people will like u.



°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
📿BISMILLLAHIR RAHMANUR RAHIM📿


In the name of Allah the must benefits and the must merciful ALLAH THE MOST HIGH DOESN'T SLEEP ALLAH THE MOST HIGH IS PURE HE ACCEPT ONLY WHAT IS PURE we love our NABI no success without him he's the light of every darkness he's the mirror of our life he's the answer to every question he've no limits, ya rasulullah muna sonka fiye darai da iyaye da dukiya muna sonka fiye da dukka muradi na zuciya ANNABI mu mu ganka shine buri na zuciya lamince mu ganka ya mai salsabil da khausara.

÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷
SHORT STÔRY
÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷


💦Yüsëëñ Sïr Äl-ämëëñ çë💦
PG____01&02
Zaune wani kyakkyawan farin mutum yake a wani office da takardu a gabansa yana dubawa a shekaru zai Kai shekara arba'in da biyar fari ne kamar ka ta'ba jikinsa jini ya fita a saman sa akwai katon photon sa banne a jikin bangon yana tsaye kamar ka kirashi ya amsa a qasan photon an rubuta sunansa da manyan ba'ki ASHRAF AHMAD da kyakkyawan murmushi na kwatance akan kyakkyawar fuskarsa sa, aiki kawai yake baya ko d'auke hannunsa ya huta sai lokacin da akai Kiran wayarsa sannan ya d'ago yana kallon wayar tasa ganin me kiran yasa yadan ja tsaki batare daya d'aga ba ya mayar da hankalinsa kan abinda yake yi har Kiran ya katse wani ya shigo amma ko inda wayar take bai sake kalla ba balle ya damu da ya d'auka saima saka wayar dayai a silent dan kada ringtone d'in yasa yayi mistake kawai yaci gaba da aikinsa.

Tsaye wata cikakkiyar mace take tasha ado ta soke d'aurin kwali kallo d'aya zakai mata kasan yar duniya ce ranta a'bace tana kallon wayar dake hannunta gashi Kiran yana zuwa amma ba'a d'agawa Kuma tasan yana gurin yana ganin kiran huci ta fitar daidai ta sake Kira ya katse tai jifa da wayar tana zama akan kujera tare da dafe kanta tace.

"Wai meyasa Alhaji Ashraf yake min haka wannan ai wulakanci ne nasan yana ganin kiran amma ya'ki d'agawa dan ya 6ata min rai meyasa zai min haka kodan yaga na damu dashi humm dole zan dau mataki a kansa kafin ya haukata min 'kwa'kwalwata haba wacce irin masifa ce wannan"?.

Ta'be baki hajiya Bilkisu dake gefe tai tana kallon yadda fuskar qawar tata take dan'kare da ba'kin ciki da damuwa tace "kema wallahi Hajiya Sadiya kina da abun mamaki dole dan zamuyi tafiya saikin sanar masa kamar wani mijinki ina ruwansa da wannan harkar ki share shi mu tafi idan mun dawo koma menene saiki je har office din nasa ki same shi".

Kai Hajiya Sadiya ta girgiza tare da furzar da huci tana cire glass d'in idonta tace "amma dai Bilkisu ke kanki sheda ce irin son da nakewa Ashraf ji nake kamar nayi hauka taya bazan damu da halin ko in kular da yake nuna min ba yadda nake binsa sau da qafa dan ya aureni ko ubana iyakaci kenan amma baya gani kullum labarin daya ne taya kike tunanin zan samu nutsuwa idan bai saurare niba"? Rausaya kai Hajiya Bilkisu tai tana cewa.

"Humm kece fa kika d'au abun nan da zafi wallahi yadda Alhaji Ashraf yake bazai ta'ba sauraron kiba a haka kinsan meyasa? Ta fad'a tana kallon Hajiya Sadiya wacce ta zuba Mata ido jiran amsa cigaba hajiya Bilkisu tai da cewa "saboda kina yawan zubar da kimar ki a gabansa kina nuna masa kamar baki da aji kin zauce kin susuce da ace zaki iya da kin d'auke masa wuta kona wata biyu zuwa uku ne ki daina kiransa ki daina zuwa nemasa wallahi Ina fad'a Miki da kansa zaki ji ya kira wayarki yana tambayar kina lafiya amma kullum kina kiransa kina zarya a office dinsa taya kuwa bazai Miki wulakanci ba"?.

Sauke numfashi Hajiya Sadiya tai tana kallon hajiya Bilkisu tace "amma taya kike tunanin zan iya share Alhaji Ashraf na wata uku batare Dana kirasa ba? Humm aiko kwana uku bazan iya ba balle wata uku so kike na mutu? domin ko sati nayi ban ganshi ko naji muryarsa sainayi rashin lafiya to kuma me kike zato idan aka ce yau rana ta fito ban daga waya na kirashi ba saidai a d'auke ni zuwa asibiti Bilkisu ni kaina bansan wanne irin so nake yiwa Ashraf ba hankali bazai kwatanto shiba misali bazai iya musalta shiba sannan kalmomi bazasu iya fad'ar saba kawai ki kyale ni nayi gwagwarmaya ta na samu soyayyar sa kuma burina a kansa shine na aure shi" tana rufe baki hajiya Bilkisu ta she'ke da dariya tana tafa mata tace "gaskiya ne saida ke qawata to Allah ya taimake ki ya soki nikam ina ganin hakan abu ne mai wuya domin kina kallon yadda naci ba'kar azabar soyayyar Alhaji Mukhtar amma qarshe ya barni ya auri wata balle ke da Alhaji Ashraf bai baki goyon baya ba ina tunanin yadda abun zai kasance da kamar wuya fa" ta karasa maganar tana yiwa Hajiya Sadiya kallon babu nasara a gabanta Kuma hakan zahiri ne a bayyane yake abunda take yi Mata hasashe gaskiya ne Alhaji Ashraf yasan Hajiya Sadiya da irin kalar rayuwar barikin da take na zaman kanta sannan dama gata babbar yar siyasa ce ko ina da ita ake shiga a fita dukkan wasu halayenta saidai ya baiwa wani labari shiyasa ko kad'an bai sake mata balle tayi tunanin zata samu fuskar dazai amsa mata gaisuwarta ma ko tayi zaton a gaba zata samu shiga a gurin sa inaaa!!! Never in history...............

Ganin yadda tayi nisa cikin tunani yasa hajiya Bilkisu dafa kafad'arta tana d'an girgiza ta da sauri Hajiya Sadiya ta dawo daga tunanin da take tana kallon Hajiya Bilkisu wacce ta d'age mata gira tana cewa "wato kema kin fahimci hakan bazai ta'ba kasancewa gaskiya ba ko? To yanzu ya kamata ki daina wahalar da kanki a kansa ki tsaya ki saita rayuwarki ki kama kasuwancin ki kawai".

Kai Hajiya Sadiya ta girgiza jikinta yana qara yin sanyi da karya mata gwiwar da hajiya Bilkisu take yi cikin rashin jin dad'i da walwala tace "a'a dan Allah Bilkisu kiyi shiru haka ki daina fad'a kar kisa zuciyata tai bindiga ko hawan jini ya kama ni abinda nace zai kasance alkhairi muna nan dake saina auri Ashraf ko yana so ko baya so ta hanyar halak ko haram tunda ni Ina sons........ shiru Hajiya Sadiya tai bata karasa ba sakamakon jin qarar takalmi ana saukowa daga upstairs tasan maybe Husnah ce ta shirya zata tafi school Kuma bata so ta ri'ka riskarta tana irin wad'annan maganganun juyawa tai tana kallon budurwar data sauko tasha kwalliya da handbag a hannunta bata rataya a kafad'a ba karasowa cikin parlon tai itama tana kallon Hajiya Sadiyan tace.

"Momy zan je school".

Kaita d'aga mata tana cewa "ok Husnah sai kin dawo".

Bangaren da hajiya Bilkisu take xaune ta juya tana cewa "Ina kwanan Momyn Meelat"? Da fara'a hajiya Bilkisu tace "lafiya kalau Husnah ya kike"? "Ina lafiya Momyn Meelat" ta fad'a daidai zata wuce Hajiya Sadiya ta dakatar da ita da cewa "am Husnah zamuyi tafiya yau nida hajiya Bilkisu idan kin dawo daga school ki wuce gidan Hajiya Maryam ki zauna tare da ita idan mun dawo next week zan Kira ki a waya saiki dawo Kinga babu dad'i ki zauna a gida ke kad'ai" jin abinda Hajiya Sadiyan ke cewa yasa Husnah ta juyo fuska ba walwala tana cewa "Momy Ina Kuma zakuje har sati guda baku dawo ba dan Allah Momy ki rage fita da wannan yawace yawacen".

Tana rufe baki Hajiya Sadiya ta sakar mata wata zazzafar harara tana cewa "kinga Husnah ki kiyaye ni akan irin wannan tambayar taki mara tushe Ina ruwanki da inda zanje wato abinda nake fad'a miki dabam kema wanda kike fad'a min dabam ko? Humm Husnah ke 'yata ce bana son ki ri'ka nuna kamar kina zargina dan haka ki kama kanki! ki kama kanki!! ki kama kanki!!! Sau uku na fad'a miki ko? Idan kunne yaji jiki ya tsira get to the point" ta karasa maganar cikin tsawa tana nuna mata kofar fita da hannu jikin a sanyaye Husnah ta juya ranta a'bace ta fice a parlon yayin da Hajiya Sadiya ta hau bala'i iri iri.

"Ji yarinya da rainin hankali wato kenan maganata ta tabbata zargina take da wani abu nake aikatawa a 6oye ko? Tunda gashi harta fad'a lallai Husnah kina gaf dana 6alla miki qafa kici gaba da samun ido zanyi maganinki saina fasa idon gulmar inga da abunda zaki saka min idon haba ba dama kayi abun arziki idon yarinya yana kai kamar itace ta haifeka mutwww".

Mi'kewa Hajiya Bilkisu tai tana gyara d'aurin kwali ta sake turo shi gaba ganin abun bana qarewa bane Hajiya Sadiya ta riga ta hauro tad'au xafi tace "kinga dan Allah d'auko gyalen ki mu fita hakan da kike sake 6ata mana lokaci kike yi ita wacce kike fadan a kanta batasan kina yi ba tunda ta fice saiki ha'kuri mu tafi kar lokacin mu ya fita" ta karasa maganar tana kallon yadda Hajiya Sadiyan take qara fusata sai data sake dannawa Husnah d'anyar ashar kafin ta juya tana hawa stairs d'in ta d'auko mayafinta da handbag suka fita a gidan.

F.U.D
~🏙️Federal University Dutse🏙️~
D'alibai ne keta faman shiga maza da mata ta kowacce kofa dake school d'in daidai Husnah tayi parking wata farar mota mai qirar Mercedes-Benz mai ba'kin glass itama tai parking a kusa da ita kallon motar Husnah tai tana murmushi kafin ta bud'e kofa ta fita kusan tare suka fito da mamallakiyar motar hummm wata zu'ke'kiyar kyakkyawar budurwa ce sanye da bakar tsadaddiyar doguwar riga mai adon stone tayi Mata mugun kyau fara ce 'kar 'kar Kuma beauty no filter bata da qiba siririya ce amma ba irin can d'in nan ba tana da shape sosai a shekaru zatai ashirin da d'aya fuskarta sanye da qaramin farin glass wanda yasa fuskar tata ta sake kyau ga ba'kin gashi me kamar saje kwance a gefe da gefen fuskarta ta sanya lipstick mai walwali ko yaya ta motsa bakinta sai she'ki ga uwa uba dogon hanci da dimple duka 6arikan kumatu biyun suna lotsawa ko batai magana ba, bata tsaya rufe murfin motar ba da sauri ta taho yayin da Husnah itama da murnarta ta tafi gurin ta suna had'uwa suka rungume juna cike da farin ciki Husnah ta d'ago tana cewa.

"Ke Nabilah Tajuddeen kin ganki kuwa"?.

Ta fad'a harda d'an zaro ido murmushi Nabilah tai tana cewa "meya faru"?.

"Babu komai kawai gani nayi yau har kinfi kullum ma kyau anya kuwa Nabilah ba akwai wani sirrin da kike yiba fad'a min Nima na fara" dariya Nabilah tai jin abinda Husnan tace yasa ta kalleta tana cewa "kai Husnah kina da abun dariya me zanyi kuwa ba wani sirri wallahi da nake yi ni dama haka nake" kai Husnah ta girgiza tana cewa "a'a ba haka kike ba Beelat gaskiya yau kin zarta ko yaushe Allah ba da wasa nake miki ba yau kinfi kyau" murmushi Nabilah tai tana cewa "to nagode qawata muje ko" ta fad'a tana komata gaban motarta ta d'auko key da wayarta da kuma handbag d'inta suka shiga cikin school d'in tafiya mai nisa sukai kafin su shiga department d'insu fal suka samu gurin da d'alibai kowa ya inda yake zaune shiru hankalinsu nakan karatu sakamakon exam da za'ai musu suma zama sukai batare dasun kula kowa ba suka fara karatun karasowar wani lecturer tare da wata babbar malama itama kallon Nabilah yayi da d'an murmushi a fuskarsa yace.

"Nabilah Sïr Tajuddeen".

A bazata taji an Kira sunanta saidai tad'au murya domin babu a inda zaiyi magana bata ganeshi ba d'agowa tai tana kallon sa da ido yai mata magana d'an 6ata fuska tai a ranta tace "gaskiya gayen nan yaja yana matsa min fa bana son yawan maganar da yake min" daidai sun wuce ta bishi da kallo kafin taja qaramin tsaki tana cire glass d'in idonta ta mayar dashi cikin handbag d'inta tana mi'kewa ta kalli Husnah wacce itama ta d'ago tana kallon ta da mamaki tace "wai Beelat zuwa zakiyi"?

Kaita d'aga tana cewa "eh zuwa zanyi amma wannan shine karo na qarshe da zanyi masa gargad'in kada ya sake kulani domin na fuskanci take-taken wannan lecturer saina fito na nuna masa 6acin raina a fili maybe daya rabu dani".

Sauke ajiyar zuciya tai jin abinda Nabilan tace yasa ta mi'ke itama tana daukar tata handbag d'in ta rataya tana cewa "ok indai haka ne bake kad'ai zakije ba tunda kince Kinga alamar take-taken sa bai kamata ace na bari kin had'u dashi ku biyu ba Nabilah ina sonki kamar jini na bazan so wani abun cutarwa ya sameki ba" kai Nabilah ta jinjina cikin jin dad'in nuna kulawarta da Husnah keyi ta saki murmushi tana cewa.

"Shikenan muje"

Tafiya sukai suna zancen su da nishad'i harda dariya kamar wanda zasu kar'bo gift har suka karasa inda yace yana zaune ya d'ora kafa d'aya kan d'aya karasawa sukai da sallama ganinsu biyu ne yasa ya had'e rai ya d'aure fuska tamm ya kumbura kamar fulawar da yis ya mata yawa ya fara harare harare da muzurai alamar Husnah ta d'an basu gurin amma yafi karfin bud'e baki yace ta d'an basu gurin itama taga hakan amma ta share tana d'auke kai sake gyara zama yayi yana qare cika da batsewa wanda suma a nasu bangaren sunja sun tsaya kowacce ranta a 'bace musamman Husnah da kwata kwata bai kwanta mata arai ba har tafi Nabilan fusata ganin lokaci yana qurewa bai fad'a mata dalilin kiranta ba sannan su basu tafi sunyi karatunsu ba yasa Nabilah tace.

"Sir Ahmad gani".

Banza yayi ya'ki magana kusan mintu biyar ya sharesu had'a ido sukai suna kallon juna da idon sukai magana a tare suka kuya zasu bar wajen da sauri domin suje suyi abinda ke gabansu ko bari suyi taku baiyi ba muryarsa a hasale yace.

"Nabilah come back here" ya fad'a cikin tsawa wanda yasa gabadayan su suka juyo suna binsa da kallon mamaki daidai ya taso yana gyara agogon hannunsa ya karaso ransa a mugun had'e yace "bamu wuri zamuyi magana" Husnah tasan da ita yake amma saita dake tana cewa "sister nace fa Sir Ahmad".

"Ko wacece taki nace ki bamu guri".

Tsaki Husnah taja a ranta kamar bazata bar gurin ba saboda yadda take matukar jin haushin sa amma sai ta juya tana barin gurin saida yaga wucewarta yaja tsuka yana mayar da kallonsa kan Nabilah wacce tai bala'in d'auke kai ta murtuke fuskarta yace.

"Nabilah what is it"?.

Shiru tai masa ko inda yake bata kallo saboda takaici saida ya sake tambayar ta karo na biyu amsar farko da zata bashi tace.

"Sir Ahmad nifa Ina da wanda zan aura dan Allah ka rabu dani" ta fad'a tana sake had'e fuska zuba mata ido yayi yana kallon ta har kallon ya wuce misali ganin kawai lokaci zai 6ata mata tace "zan tafi" zata juya ya dakatar da ita "Nabilah" tsayawa tai a fusace ta juyo zatai magana ya girgiza mata Kai yana kara matsowa inda take kamar me shirin ri'ke mata hannu da sauri ta sake matsawa ya kuma binta karo na biyu ganin idan tai sake masa zai iya taba mata jiki yasa kamar walkiya ta juya fiiiii kafin ya farga har tayi nisa yaso yabita a baya amma saiya tsaya yana hard'e hannunsa ya zuba mata ido harta 'kule kafin yayi murmushi yana jinjina kai a ransa yana ji yana son yarinyar nan da aure da zata amince masa amma zai lalla6ata idan ta'ki hummm that mean war kenan dan wallahi bazai iya ha'kura da ita ba dole zaisan yadda zaiyi ko bai aureta ba zaiyi kokari yaga ya samu abinda yake so a wajenta juyawa yayi shima yana barin gurin.

Husnah tana tsaye a bayan block d'in tana jiran Nabilah sai kuma ta ganta ta 6ullo a fusace tana sauri gyaran murya tai mata wanda yasa ta juyo da sauri tana kallon ta tare da sauke ajiyar zuciya ta waiga baya ko Sir Ahmad ya biyota karasowa Husnah tai fuskarta ba walwala tace.

"Wai nikam dan Allah me Sir Ahmad d'in nan yake nufi bake da yake takurawa Beelat ni kaina na fara gajiya da wannan aikin banzar nasa kullum bazai bari kiyi abun arziki ba idan munzo school daga Kira sai Kira tsabar bulkumanci da sakalci Allah daga yau bazaki sake zuwa inda yake ba kome zaiyi domin naga d'anyar kan nasa ya wuce inda nake tunani haba jama'a" tsaki Nabilah tai tana cewa.

"Share sa muje kawai indai yana da zuciya daga yau bazai sake kulani ba wallahi so yake yayi asarar takardar aikinsa domin matukar yaci gaba da matsa min zan hadashi da Daddy kawai ya dauka min mataki" Kai Husnah ta d'aga tana cewa "basai yaci gaba da matsa miki lamba ba kawai ki sanar masa a d'au mataki idan ma za'a bashi transfer lokacinsa baiyi ba saiya sani aikinsa zai 6ata muje kawai kar a shiga mana exam d'in ma muna nan" wucewa sukai kamar sun sani kuwa suna zuwa daidai lokacin shiga ko zama basuyi ba suka zarce cikin class d'insu,,,basu fito daga jarrabawar ba sai kusan karfe d'aya da rabi a ranar suna fitowa kowa ya fara alwala suna tafiya sukai sallah su Nabilah sun jima a gurin sallar domin saida la'asar tazo sukayi sannan suka taso Kai tsaye gurin motarsu suka nufa saida sukai sallama Nabilah harta bud'e mota zata shiga ta tsaya tana cewa.

"Husnah dan Allah karki manta gobe ki fito da wuri tunda naji kince gidan kanwar Momyn zaki tafi" Kai Husnah ta d'aga tana cewa "ok sai Allah ya kaimu gobe ki gaida mun da Mum sosai Beelat" "ok bye" Nabilah ta fad'a tana shiga motarta itama saida ta Husnah ta wuce sannan tabi bayanta ita ta nufi Yalwawa Nabilah Kuma ta nufi Yadi ko a hanya tunanin yadda zata 6ullowa da al'amarin Sir Ähmäd takeyi amma ta bari a ranta tunda yau ta fad'a masa ya rabu da ita idan yaji shikenan idan baiji ba koda za'a 6ata masa paper saita fad'awa Daddy domin ya d'aukar mata mataki irin su Sir Ahmad ba mutanen da za'a zubawa ido bane domin shi mutum ne d'anye kuma ga6o ta tabbata matukar ta share bata fad'a anyi maganinsa ba uhmm tana tsoron abinda zai faru a gaba Allah ma ya kiyaye.

Horn tayi a kofar gate d'insu me gadin dake zaune ta ciki ya tashi ya bud'e mata ta shiga sakamakon tana sa rai maybe zata fita da yamma yasa bata Kai motarta cikin rumfar parking d'in motoci ta barta a baya baya ta kasheta tana fitowa ta shiga ciki tsit parlon kamar ba kowa sakamakon Hajiya Fatima tana bedroom kuma TV ba'a kunne yake ba shiyasa parlon yad'au wani irin shiru shirun ma har yayi waya part d'inta ta wuce domin haka kawai taji jikinta na mata ciwo saida ta had'a ruwa me zafi tayi wanka ta sake sabon shiri cikin dinkin wata kyakkyawar atamfa anyi mata dinkin buba yasha stone yanata walwala ta kashe d'auri ta dau'ki agogo ta saka da takalmi harda d'an kunne da sarka kamar wacce zatai ba'ko ta feshe jikinta da daddad'an turare sannan ta dau'ki phone d'inta ta dawo parlor ganin kiran Husnah yasa tai murmushi tasan abinda zata tambaye ta amma sakamakon yanxu Hajiya Fatima ta fito tana parlon yasa bata bi kiran ba ta bari saita koma part d'inta yadda xatafi yin wayar a sake karasowa tai tana zama ta kalli Hajiya Fatima dake binta sa kallo tace.

"Barka da gida Mami na fatan kin wuni lafiya"?.

Kai Hajiya Fatima ta d'aga tana cewa "lafiya kalau na wuni ya gajiyar school ya exam"? "Alhamdulillah Mami ina Daddy ko bai dawo ba"?.

"A'a ya dawo da wuri ma wanka yayi dai ya fita a gidan" ok kawai Nabilah tace tana d'age kafafunta daga kan carpet ta maida kan kujera ta tan'kwashe su bata sake cewa komai ba hankalinta nakan waya tana chatting d'agowa Hajiya Fatima tai tana cewa "amma Nabilah bakici abinci ba tun breakfast d'in safe shine kin dawo d'inma basaki mayar da hankali kici ba sai ulcer ta kama ki" murmushi Nabilah tai tana girgiza kai tace.

"Ai Mami ulcer bazata ta'ba kama niba".

Da mamaki Hajiya Fatima tace "meyasa bazata kamaki ba saboda da tana tsoron ki"? Dariya Nabilah tai tana cewa "a'a saboda 'kawata ce mun riga mun saba" "uhmmm" kawai shine abinda Hajiya Fatima tace tana kallon Nabilan wacce da gaske bazata ci abincin ba ta sake gyara zama tana mayar da hankalinta kan secreen d'in wayar tace.

"Nabilah d'azu Daddyn ki yazo yana nemanki nace kina school amma ya aje Miki kyautar daya kawo miki gashi can akan dinning banma d'auke sa nasa a fridge ba sai kinzo ki gani da kanki yaso kin dawo kun gaisa har yace zai jira ki taso sai kuma akai kiransa a waya shine suka fita tare da Daddyn naki".

Murmushi Nabilah tai tana d'agowa kalle ta domin tunda taji tace Daddyn ta tasan wa take nufi aje wayar tai cikin zumud'i ta mi'ke tana zuwa ta d'auko kyakkyawar ledar dake she'kin tabuntaka balle kumà abinda yake ciki ta dawo tana zama har lokacin da murmushi akan fuskarta ganin kayayyakin da suke ciki yasa ta sake fad'ad'a murmushin ta cikin walwala tace.

"Wai Mami kina nufin Daddy Ash yazo gidan nan yau? Wayyo gashi bana nan".

Zaro ido Hajiya Fatima tai tana kallon ta da mamaki tace "Daddy Ash kuma Nabilah abokin uban naki guda kike kira da Ash"? Dariya Nabilah tai tana cewa "to Mami ba sunan shi bane"?.

"A'a ba sunan shi bane tunda ba Ashraf kika ce ba shi kuma sunansa kenan".

"Ai Mami da Ash da Ashraf duk d'aya ne".

"A gurinki ba amma ba d'aya bane tunda shifa ba yaro bane da saurayi ne saiki kirashi da hakan amma ubanki guda"?.

"To Mami bakiji akace dakai wasa da baban wani gara kayi da naka ba shiyasa nayi hakan".

"Au haba kenan yanzu zaki iya kiran naki tsohon da Daddy Taj ko? Tunda ai shima Tajuddeen yake".

Hhhh dariya Nabilah tai tana fiffito da kayan zallar chocolates ne kala kala sai yogurts da ice cream da tsadaddun biscuits humm Hajiya Fatima bata bud'a taga mene a ciki ba amma tasan za'a rina kallon Nabilah wacce ta 6are wata babbar chocolate tana sha tayi ta d'an girgiza kai tana cewa "wai mutum ya girma shekara ashirin da yan kai amma saboda babu qani yasa suke shagwa'ba ki yanzu irin wannan kayan za'ki haka kamar 'yar yaye"? Dariya Nabilah tai tana mi'ko mata guda d'aya tace "Mami kema gashi ki sha wadannan chocolates d'in na dabam ne bana yara bane" kai Hajiya Fatima ta girgiza "a'a nikam bazan sha zaki ba kema da kike wadansu abubuwan ganin ba wani sai kene da kina da qani ko qanwa baza kiyi wani abun ba koda kud'i" murmushi Nabilah tai tana hade kayayyakin ta mayar dasu cikin ledar tace.

"Shiyasa ya Sultan yake cewa wai Daddy's dina sune suka 6ata ni dashan abubuwa shiyasa ban damu da abinci ba shikam bazai yarda da wannan shaye shayen kayan za'kin ba dole ya koya min cin abinci".

Jin abinda Nabilan tace

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment