Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajiyar tayi magana ba ya mayar da idanun sa kan Usman dake tsaye har yanzu kansa a ƙasa, "fitar min a gida dan uban ka, kai wato baka da mutunci ko Ban isa da kai ba? Wuyan ka yayi kaurin da har zamu zaɓa maka abu, amma ka ce mun yi kaɗan, dole sai ka nuna mana iyakan mu, to, saƙon da ka aiko ta tafaɗa mana ta sanar mana, cewa "sai mun yi dana-sani ko?" Eh tabbas mun yi dana-sani wlh ba sau ɗaya ba, yanzu zaman uban me kake min a wajen nan?"


Sumui-sumui Usman yazo zai wuce ya fice


Big Dady ya dakatar dashi, "dan uban ka ina takardan nata?"


Shiru yayi


Nan kuwa Big Dady ya zuciya ya daka masa tsawa, "da kai nake magana kayi min shiru?"


Cikin sanyin murya yace, "ban rubuta ba".


Ƙwafa yayi kafin ya zauna yana cewa, "kar ka sake in sake maka magana a karo na biyu".


Juya wa Usman ɗin yayi ya fice.



             Hajiya dake tsaye duk ranta babu daɗi, ta san dama za'a rina duk da tabbas kamar yanda Usman ke hasashe ne fushin da suka ɗauka sun huce, amma da a lokacin ne ta san faɗan da zai sha sai ya fi haka, tana matuƙar son Usman duk cikin yaran ta, shiyasa ko kaɗan ba ta ƙaunar wani abu ya shiga tsakanin su da mahaifin sa, duk da shi ya jawa kansa. Ajiyan zuciya ta sauke kana ta sami wuri ta zauna tana kallon Dadyn, tace, "Dadyn Zainab don Allah ka sassauta wa wannan yaron, abinda ya faru ya rigada ya faru, yanzu sai dai mu ce Allah ya kyauta na gaba.."


Katse ta yayi da faɗin, "dalla rufe min baki, duk ba ke kike ɗaure wa yaron nan gindi ba, kar ki manta fa duk wani rashin ƙaunar auren nan da kike yi a baya yana raina kuma ban manta ba, ta yiwu da haɗin bakin ki yayi ma Daughter wannan abun da yayi". Ya ƙare maganar yana miƙe wa cikin zafi ya wuce ɗakin sa


Sosai Hajiya ta shiga damuwa da jin zancen sa, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yanzu Ni yake zargi na saka Usman abinda yayi?" Shiru tayi kawai duk jikin ta yayi sanyi domin ta kasa tashi ma tayi abinda ke gaban ta, zuciyar ta na nadamar abinda ta aikata tun farko na nuna ƙiyayyar auren, yanzu ga shi hakan na son jawo mata matsala da mijin ta, yana zargin ta da ita ce ta ziga Usman, kuma babu yanda za'a yi ta kare kanta tunda tun farko ta nuna ba ta ƙaunar auren.





                 ⚫⚫⚫

            Usman kuwa yana fita gida ya koma ya ɗauki motan sa ya fice, be damu da dauɗan motan ba so yake yi kawai ya samu relif a zuciyar sa, gaba ɗaya yanzu jin sa yake yi wani iri, abinda yake ji a ƙasar zuciyar sa dake buga wa tana sake taso masa tana mamaye zuciyar, tsaki yaja a ransa yace, "kai fa kace zaka iya ɗaukar duk wani abinda zai faru? Ba ga shi yanzu faɗan Dadyn naka ya wuce ba, saura kuma nasu Kaka suyi nasu su gama". Da wannan tunanin nasa ya ɗan samu ƙwarin gwiwa, sai dai yanayin da yake ji a zuciyar sa kwata-kwata ba ya jin daɗi, ya fi jin hakan duk sanda ya haɗu da wancan yarinyan (yana nufin Ɗahira. Fargaba da tsoro a zuciyar sa) amma abun mamaki yau kuma ba ta kusa dashi amma yake ji. Kamar an ce ya wulƙa idanun sa gefen daman sa, ai kuwa sai ga ta tazo ta wuce sa a motan ta, be yarda ita bace sai da yabi motan da kallo ta mirror, kuma tabbatas ya gane ita ce tunda ya ga fuskar ta, sosai ya haɗe rai ganin motan nata ta faka a bakin titi, sai ya ɗauke kai yana jin kamar ya koma ya sanar mata tun yanzu ya sake ta, sai dai kuma ba ya ƙaunar ganin fuskar ta, gwara idan ya koma gida ya rubuta sakin ya miƙa wa Dady, haka ya ƙara wa motan wuta yana jin kamar ya ciro zuciyar sa ya jefar tsaban abinda yake ji.






               ⚫⚫⚫⚫⚫⚫


              Ɗahira kuwa da ta faka motan ta a bakin titi fito wa tayi, duba tayan ta soma yi abinda take zargi ne tayi faci, sai taja dogon tsaki cike da takaici, "oh Allah ka taimake Ni, wlh motan nan kin yi min wulaƙanci tunda kika tsaya min a hanya, yanzu ya zan yi?" Sai ta sake jan tsaki tana koma wa cikin motan, wayanta ta ɗauka tana neman Numban bakaniken su, amma a kashe ake ce mata, maida akalan kiran tayi kan Numban Baffa, shi kuma ba service, gaba ɗaya duk ta damu domin ta san ruwa zai iya riskan ta a nan, dole ta yanke shawaran hawa keke napep ya ƙarisa da ita gida, inyaso ta bar motan a nan me gyara yazo ya gyara. Jakan ta ta ɗauka ta fito ta rufe motan da keey, kana ta ƙarisa bakin titin sosai don ta samu abun hawa, kasancewar hanyar babban titi ne ba kasafai suke tsaya wa ba, duk yawanci ma akwai mutane shiyasa tasha wahalan samu. Tana nan tsaye sai mota ta faka a ɗan nesa da ita kaɗan, kallon motan tayi da kyau, ta gane ko na wane ne, na Dr. Said ne tunda yanzu ma kafin ta fito sai da suka yi sallama dashi a wajen motan nasa, kafin ma ta gama tunanin nata


Sai gani tayi Abokin sa Dr. Sabo ya leƙo yana mata alama da hannu ta taho


Nufan wajen tayi kanta tsaye, tana isa sai ta leƙa gaban domin tayi masa magana, sai dai ba shi ne a motan ba, wani mutum ne sai Dr. Sabo a gaban, murmushi tayi tace, "sannu Doctor ai nayi zaton Dr. Said na ciki ne?"


Shima yana murmushi yace, "a'a ba ya ciki, amma ki shiga sai mu sauke ki ko? Ina ce motan taki ce ta samu matsala?"


Gyaɗa kai tayi tace, "eh tayi faci ne".


"Ok ki shiga kawai mu sauke ki".


Godiya tayi masa ta buɗe baya ta shige, suna jan motan suka tafi.


             Usman da yaje ya kewayo zai koma gida duk a kan idanun sa Ɗahiran ta shiga cikin motan, taɓe baki yayi yana bin bayan su, a ransa yana mamakin "ita wannan yarinyan har yanzu bata dena abun tsiyan nata ba?" Tsaki yaja a fili ya furta "karya kawai, idan da kun san abinda na sani a game da halin ta wlh da baku yi fushi dani ba". (iyayen sa) Yayi maganar yana sake haɗe ransa tamkar da wani yake yi a gaban sa.



Sanda suka isa layin anguwar su memakon yaga motan ta shiga cikin anguwan nasu, sai yaga taci gaba da tafiya, be yi mamakin hakan ba illa shige wa layin gidan su da yayi, amma a ransa sai yayi tunanin "why not yau ya samu hujjar da zai gabatar wa iyayen sa a matsayin abinda ya saka yaƙi yarda da zaɓin su? Idan ya bi su ya gano abinda suke yi sai ya ɗauka a waya ya nuna musu". Wannan shawaran ta zuciyar sa ita yayi na'am dashi a lokaci guda, sai ya juya motan nasa nan da nan yabi hanyar da suka bi, ko kaɗan ba ya hango motan tasu, hakan yasa ya ƙara Speed sosai, ai kuwa sai ga su har ya kamo su yana bin su a baya ba tare da sun sani ba.






                 ****** *******

               A cikin motan kuwa tunda Ɗahira ta shiga ciki bata yi tunanin akwai kuma wani a baya ba, sai da ta zauna kafin ta kula dashi, har taji tsoro tana shirin magana ya rufe mata hanci da baki da handkerchief, Lokaci ɗaya numfashin ta ya ɗauke tayi luuu ta zube jikin sa


Dariya suka kwashe dashi duk kan su, shi kuma yana gyara mata zaman ta da kyau


Wanda ke tuƙin yana ci gaba da dariyan yace, "ai wlh aikin nan da muka yiwa Dacta dole sai ya ƙaro farashi, don bazai yiwu ba muna ganin wannan zuƙeƙiyar budurwan kyakykyawa da ita muna gani mu barta ba tare da mun dangwali fa'ida ba".


Dr. Sabo yace, "kai ina ruwan ka? Kana ji fa ya ce auren ta zai yi idan sun tafi can, ka dena haka don Allah".


"Ai don na san yace hakan ne shiyasa baza mu siɗe masa kwanon ba, dole ne fa ya ƙaro mana kuɗi idan dai muka kai ta, domin duk wanda muka yi masa wannan aikin yana barin mana siɗi, amma shi babu abinda zai bar mana".


Na bayan yace, "haka ne wlh, domin wlh oga wannan yarinyan tana da farashi kamar yanda kace, ka ganta kuwa?". Ya ƙare maganar yana shafa fuskar Ɗahira da bata san ma yana yi ba


Dr. Sabo dai be ce musu komi ba illa ƙoƙarin kiran Dr. Said da yake yi, sai dai layin ba ya shiga saboda yanzu hadari sosai ya haɗu, garin yayi duhu sai iska da aka fara, ɗagowa yayi yana kallon me tuƙin yace, "layin sa fa ya ƙi shiga, ina yace zamu same sa a hanyan?"


"A'a ai be faɗa mana ba, sai dai idan zamu juya da ita mu kai ta gidan da muka haɗu dashi".


Shiru dai Dr. Sabo yayi yana ci gaba da gwada layin, sai kuma yace, "wlh ka san Allah ba don ta ganni cikin motan nan ba baza ta hau ba, komawan mu akwai matsala, kawai ka faka a can mu nemi service mu rabu da alaƙaƙai tun kafin ƴan sanda su cafke mu, Ni wlh ban ma san ya aka yi na biye wa Dr. Said a wannan shirin nasa ba, da ya zo yayi kayan sa da kansa".


Faka motan suka yi a gefen titi, domin har sun kusa fita cikin gari sun tasar wa hanyar Zaria, dama a hanya suka yi da Dr. Said ɗin zai amshi Ɗahiran ya wuce da ita Zaria, a can iyalan sa suke, daga can yake zuwa nan aiki, shirin da suka yi ya saka a sato masa Ɗahira ne domin yaje ya ajiye ta a wani gidan sa da yake dashi a Zarian ba inda matar sa take zaune ba, dawowar Ɗahiran a bakin aikin ta ya sake shige mata sai da suka ƙulla alaƙa, domin tun sanda ya sake ganin ta burin da ke ransa ya sake taso wa, dama yana kwaɗayin ta sosai, sai kuma zuciyar sa ta raya masa why not ya sace ta ta zama nasa kawai? Da taimakon wani abokin sa ya ba shi ƙwarin gwiwan ya sace Ɗahira ya ajiye ta a ɓoye ta zama tamkar matar sa, kuma zai riƙa zuwa wajen ta ne ba tare da ta san shi ne ba. Hakan yasa ya faɗa wa Dr. Sabo ƙudurin sa, shi kuma ya samo masa waɗannan mutanen domin su yi masa aikin, tunda dama kidnapping shi ne sana'ar su, da kuma yiwa yaran mutane Fyaɗe idan sun sace su.







******

              Usman dake bayan su yana ganin duk abinda ke faruwa, da tsayar da motan nasu da kuma fitowar da suka yi har su uku, suka ɗan yi gaba suna ɗaga wayoyin su, hakan ya gane suna neman service ne, sosai wannan abun ya ba shi mamaki, har a ransa ya ɗarsa zargin su lokaci ɗaya, "kar dai ace kidnappers ne su? To me zai saka taje wajen su da kanta?" Wani zuciyar nasa tace masa, "ta yiwu neman taimako take a wajen su tunda motan ta tayi faci". Sai yayi shiru kawai yana tunanin abun yi, duk yana kallon su, kuma be damu su juyo su hange sa ba, tunda tazaran su babu nisa da inda yayi parking


Lokaci ɗaya yabi shawaran zuciyar sa, sai ya fito ya nufe su, ba tare da fargaba ko wani tsoro ba, shima wayan sa na hannun sa yana shirin neman layin wani daga cikin ƴan gidan su ya sanar musu da abinda ke faruwa, amma kuma wayan babu service, gaba ɗaya kiran da yake yi taƙi zuwa. Yana isa wajen motan duk basu san da zuwan sa ba tunda suna ta gaban motan ne sun juya wa motan baya. Leƙa motan yayi, ilai kuwa zargin da yake yi haka ne, kwance ya ganta tamkar matacciya ba ta numfashi, lokaci ɗaya ya saka hannu ya janyo ta tare da saɓata a kafaɗa yana juya wa da sauri ya nufi motan sa


A lokacin ne aka saki ruwa me ƙarfi wanda yaja mutanen suka juyo don shiga motan su su samu mafaka, kawai sai suka hangi Usman har ya kusa isa motan sa ɗauke da Ɗahira a hannun sa, basu tabbatar ba sai da suka duba cikin motan suka tabbatar da ita ce, ai kuwa nan suka bi bayan sa da gudu, ɗaya daga cikin su ya ciro bindiga ya soma harba masa


Take a nan Usman ya ƙara da gudu, yana isa motan ya buɗe ya ajiye ta a wajen me zaman banza, shi kuma ya zagaya ɗaya side ɗin da gudu yana duƙa wa don kar su same sa ya shige yaja motan, saboda ruɗewa ma kasa yin reverse yayi sai ya Yi kansu


Ganin haka sai suka dare don neman ceton ransu


Shi kuma tuni ya yanki jeji da gudu


Ɗaya daga ciki yace, "Mu bi shi mana me muke jira? Kaji min ɗan isa har yana da ƙarfin halin biyo mu ya ɗauke ta?".


Tuni sun isa motan su sun shige, amma Dr. Sabo ya kasa bin su, gaba ɗaya ya ruɗe domin gani yake yi asirin su ya tonu, duk da be gane Usman bane amma ya san cewa duk wanda ya biyo bayan su ya san su, shiyasa duk ya ruɗe


Su kuwa tuni sun tafi sun bar shi a wurin sun bi bayan Usman


Usman dake tuƙi a cikin sunkuru, neman hanyar da zai yi ya fita titi yake yi, sai buga uban tsaki yake yi cike da dana-sanin abinda yayi, sai yanzu ma hankalin sa ya dawo jikin sa ya tuna wacce yazo ceto, maƙiyiyar sa wacce ya tsana a duk faɗin duniyar nan, ji yake yi kamar ya tsaya ya buɗe motan ya jefar da ita don haushi, sai dai yana tsoron kar su kama sa su harbe sa tunda yana hangen sun kusa kamo shi ma, sosai yake gudu a sunkurun ga ruwa da ake zuƙa wa a yanzu ɗin, titi ya nufa da gudun sa ko kaɗan be damu da ruwan ba, fatan sa kawai ya fita titi don yaji daɗin guje musu, sai dai be kula ba ashe ta wajen gada ya biyo, babban magudanan ruwa ne a wurin. santsin ruwa dana ciyayi suka ja shi ya karkace hanya lokaci ɗaya motar tasa ta gangara ƙasan gadan dake cike da ruwa, duk ƙoƙarin da yayi don ganin ya samu ya fita kafin motan ta shige sosai amma ya kasa, lokaci ɗaya suka afka ciki ji kake yi cindimm..



Ba don Allah yasa su ma sun ja wawan burki ba, da tuni tasu motan su ma ta afka, domin uban gudun da suka shanyo, dole suka ja birki lokaci ɗaya, ganin motan Usman har ta nitse ai tuni sun juyar da nasu sun bar wurin, inda Dr. Sabo yake suka je suka ɗauke shi suka gudu.
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_




        *EPISODE Fifty Three*


         Aunty Amarya shiru-shiru taji yau Ɗahira bata dawo kamar yanda ta saba ba, domin tunda ta koma bakin aiki, to, ba ta wuce 05:30pm. Take dawowa gida, ko shida ba ta kaiwa yanzu, bare yau ana ruwa tayi tunanin zata dawo da wuri. hankalin ta duk ya tashi hakan yasa bayan ta idar da sallan magriba sai ta fito Parlour ko cire hijabin jikin ta bata yi ba, zama tayi tana jiran Abbu ya dawo masallaci sai ta sanar masa, dayake wayan ta ta lalace kwana biyu, to, bata samu an gyara mata ba


Zaman ta babu daɗe wa Fadil ya shigo da sallaman sa


Tana amsa mishi sai tace, "yauwa Auta zo ka kira min Numban Yayar ka, har yanzu bata dawo ba ban san me ya tsayar da ita ba".


"To Aunty bari in ɗauko wayan a ɗakin Umma na bar ta da zan je Masallaci". Wuce ta yayi da sauri ya shiga ɗakin Umma dake sallah ya dauko ya dawo


Koda ya kira wayan a kashe ne, yayi try har sau biyu a kashe ake ce masa, sai ya kalli Aunty Amarya dake kallon sa ko ƙyafta idanu ba ta yi, duk da tana jin an ce wayan a kashe, amma ta kasa magana, yace da ita, "Aunty a kashe ne fa".


"Sake kira min, me ya sami wayan nata da zata kashe? Ai yaci ace ta dawo yanzu ko?"


"Haka ne Aunty, yanzun ma ga shi a kashe".


A lokacin Abbu yayi sallama ya shigo parlour'n


Duk suka amsa mishi suna bin shi da kallo


Shima ganin su cirko-cirko sai yace, "lafiya me ke faruwa?"


"Wlh ba lafiya ba Abbun Zulaiha, Ɗahira CE har yanzu bata shigo ba, kuma na san idan wani wuri taje dole zata faɗa mana, sannan wayan ta ba ya shiga ma".


"To fa subhanallah.. amma kin san halin ta akwai son aiki, yanzu haka ta samu wata patient ne hakan ya tsayar da ita wajen duba ta, kin san ta ai".


"To yanzu shikenan Abbun su baza a bincika a gani ba? ka san fa bata taɓa kaiwa haka ba, yanzu ana shirin kiran sallan isha'i fa". Cewar Aunty Amarya cike da damuwa


Abbu yace, "ki kwantar da hankalin ki don Allah, bari in saka takwara ya bi ta ya gano mana ko lafiya, kai Fadil kira min Baffa".


"To Abbu". Fadil ya amsa mishi yana fice wa


Itama Umma a lokacin ta fito tana tambayar abinda ke faruwa


Aunty Amarya ta sanar mata


Sai cewa tayi, "to Allah ya kyauta, Allah yasa dai lafiya".


"Amin". Inji aunty Amarya tana zama, tunda tun sanda aka soma zancen ta tashi tsaye


Shima Abbu zaman yayi yana ɗaukan wayan sa don ya gwada kiran ta


Yayinda Umma ta wuce kichen don kwaso abinci ta shirya a dainning.


       Sanda Baffa yazo, Abbu ya sanar masa "yabi bayan Ɗahira asibiti ya dubo ta".


Da Fadil suka tafi a lokacin ruwan ya ɗan tsakaita. sun je har asibitin an tabbatar musu da tafiyan ta, hankalin su sosai ya tashi da jin ta daɗe da tafiya ma tun biyar da ashirin yau ta fice.



      Sanda za su dawo gida ne Baffa ya hangi motan ta a kan hanya, tunda da za su je be kula ba saboda ba ta side ɗin suka biyo ba, nan suka fito da sauri suka nufi motan, duk sun duba babu ita ga shi motan ma a rufe ne, a nan ne hankalin nasu ya sake tashi ainun


Cikin sauri Baffa yace wa Fadil, "su yi maza su wuce gida".


Da sauri suka shige motan ya figa suka yi gida, suna isa suka tarar da Abbu ma a haraban gidan yana waya


Saurin katse wayan yayi ya nufe su yana tambayar Baffa "kun ganta? Ina take?"


Nan Baffa ya sanar masa da komi


Ai nan Abbu shima ya ruɗe yana faɗin, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. me ke faruwa ne?"


Su Big Dady da suka fito za su tafi masjid, suka tambayi ba'asi, da jin abinda ke faruwa su ma hankalin su ya tashi ainun, Abba dake da Numban wani abokin sa ɗan sanda, tuni ya kira shi ya sanar mishi abinda ke faruwa.



     Kan kace me kowa yaji labarin rashin dawowar Ɗahira, nan da nan Hankula suka sake tashi, ba kamar Kaka duk ya gama ruɗe wa, basu so ma faɗa mishi ba, amma kuma ganin har ƙarfe goma tayi babu labarin ta duk inda aka je, dole suka faɗa mishi. Gida dai ya rikice ana neman Ɗahira babu ita babu labarin ta, duk an kira dangi "ko sun ganta?" amma babu wanda yace, "ta zo", hanya an bi ya kai sau goma amma babu ita, ƴan sanda kurɗa-kurɗa an baza su amma ba'a dace ba


Sai da wajen sha daya tayi kafin Hajiya ta lura shima Usman be dawo ba, dayake mutanen gidan har yanzu basu ji labarin dawowar sa ba, Big Dady be sanar musu ba, sai nan itama Hajiya ta ruɗe ta soma kiran layin sa, amma shiru shima a kashe, ta kira Big Dady ta sanar mishi


Shima tun yana ɗaukan abun da wasa, domin ko kallon inda take be yi ba sanda ta sanar masa, sai kuma abun ya soma damun sa ganin lokaci na ja, a nan ne yake sanar ma su Abba "ai shima Usman be dawo ba".


Duk sun yi mamakin maganar nasa, basu kai ga magana ba Hajiya ta ƙariso wajen tana kuka tana sanar wa Big Dady "har yanzu ta kasa samun layin Usman, kuma ta je gidan shi babu motan shi babu shi a ciki".


Abba yace, "dama ya dawo ne ashe?"


Sai a nan Big Dady ya tuna basu sani ba su, shi ne yake sanar musu da dawowar sa ɗazu.




       Abu kamar almara an nemi su Usman ba'a samu ba, a wannan daren babu wanda ya runtsa a gidan nan sabida tashin hankali, kowa tunanin yanda mutane biyu aka rasa su a lokaci ɗaya, sai kuma duk tunanin su Big Dady suka koma kan "ko dai Usman ne ya ɗauke ta suka koma can Turkay ɗin?" Wannan tunanin yasa Big Dady safiyar Allah na yi yace, "zai je domin yaci uban sa a can, wlh idan har da gaske ne tunanin nan nasu Usman ya kaɗe a wurin shi," sosai ransa ya ɓaci sai faɗa yake yi


Ganin haka yasa Kaka yace, "kar yaje, Baffa yaje shi ya gano musu".


Wannan dalilin ne yasa Baffa ya shirya aka nema masa jirgi na ƙarfe 10:00am a ranan ya wuce TURKEY.






⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫


          Duk yanda ya so ya buɗe ƙofan motan ya fice ya kasa, har sai da motan ta gama nitsewa zuwa ƙasa, kokuwa yayi ta yi amma ya gaza, ba don Allah yasa ya iya ruwa ba da tuni babu numfashin sa, amma duk da haka yanayin awannin da suka ɗauka a haka cikin motan babu jan numfashi bare iska sai duk ya galabaita, ya rasa ya zai yi har numfashin sa ɗauke wa yake yi kamar zai shiɗe


daƙyar da siɗin goshi ya samu ya buɗe ƙofan motan, har zai fice ya tuna da ita, nan ya dawo ya janyo ta suka fito daga cikin motan, sai dai yanda ake tsula ruwa ya kasa yanda zai yi ma yayi iyo, take a Nan ruwan yayi gaba dasu saboda yanda ruwan yake gudu sosai, ta cikin gadan wajen yabi dasu yay gaba dasu, dayake wajen makwararan ruwa ne na sassa-sassa dake tafiya ya isa babban kogin dake can wani yankin jeji dake cikin Kadunan.


      Tun Usman na sanin halin da yake ciki, har shima numfashin sa ya ɗauke gaba ɗaya


Ita kuwa Ɗahira har yanzu bata farka ba ma bare tasan inda take.


      A haka har garin Allah ya waye, inda wajen hantsi wani Tsohon Mutum yazo gaɓar ruwa zai ɗiba ruwan a tulu, a nan ya tsince su tamkar matattu ruwa ya fito da su bakin gaɓar ruwan, sosai hankalin tsohon nan ya tashi, nan ya nufe su cike da mamakin ganin su, sai da ya gama taɓa su ya tabbatar da tabbas suna da rai, sannan ne ya koma cikin ɗan ƙaramin ƙauyen nasu, ya kira wasu samari suka zo suka taimaka masa ya kai su gidan shi, aka zube su cikin ɗaya

Please Login or Register in order to submit comment