Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake xabga masa harara

Miko hannu Batool tayi Ma'u ta bata babyn

"Bani Zahrarmu"

Rumgume diyarta Ma'u tayi tace

"Kije can Zahrarku na wajen bata hannuna bace, kuma kada ki kuskara kice xata tabamim diyata"

Daria Batool tasa

"Bani na kar xomonba ko ratayama ba'a baniba, mudai mun sheda sunan diyarmu Zahra"

Wuceta Ma'u tayi bata tanka mataba

Tana shiga falon ta dire babyn kan cinyar Mami tace

"Mami ga kishiyarki kuma takwararki"

Harara Jidda ta watsawa Ma'u yace

"Takwarar Zahra dai bata Mamiba"

Baki Ma'u ta tura

"Nidai diyata takwarar Mami ce ba Zahra ba"

Murmushi Mami tayi tace

"Banda abunki ma Ma'u ai ita kanta Zahrar takwaratace, me kuma na daga hankali, ubanta ma yarigada yace takwarar matarsa ce"

Kuka Ma'u ta saka

"Wlh baxan aminceba ba takwarar Zahra bace, takwararki ce Mami, kuma idan aka matsa sai dai a dauki yarinyar a bawa Zahra ta shayar da ita badai niba kam"

Baki Mami ta rike don mamaki

Jidda ko a harxuke tace

"Yarinya dai sunanta Zahra kuma dole ki shayar da ita don ubanki"

Cikin fushi Ma'u ta fice daga falon tabar Bby Zahra a cinyar Mami tanata kuka don tsawar da Jidda tayi ya firgitata

"Ma'u kixo ki dauki yarinyar nan"

Daga bakin kofa Ma'u tace

"Ku kaiwa Zahra ta rarrasheta, me amfanin takwarar"

Tana gamawa tayi ficewarta

Waya Jidda ta dauka

Mami tace

"Me xakiyi?"

"Kiran Ya Bature xanyi na sanardashi"

Jidda ta fada tana dialling number Bature

Daga Baby Zahra Mami tayi ta shiga rarrashinta

"Banason fitina kyalesa kawai, nixan rarrashi Zahra kuma naje na rarrashi Ma'un"

"A'a Ma'u baxata taba jin rarrashiba maganinta Ya Baturen ne"

Picking na call din Bature yayi

Jidda ta mayar masa Abunda yake faruwa

Sanin Jidda xata fadawa Baturene yasa Ma'u ta nufi part din Ummi don tasan ko can Baturen ya biyota akwai 'yan kar banta

Da sallama ta shiga falon kamar mutumiyar arxiki, gefen Ummi taje ta xauna

Da murmushi Ummi tace

"Yana ganki ke daya ina Zahra"

Murmushi Ma'u tayi tace

"Tana can gun Mami"

"Baxatayi kukaba?"

Zahra ta tambayeta

Hararar Zahra tayi kasa kasa tace

" ko tayi kuka Mami xata kula da ita tunda tasan xafin haihuwa"

Ssai Zahra ta fusata, har ta bude baki xatai magana Ummi ta girgixa mata kai

Ssai Abunda Ma'u tayi yabawa Falmata haushi, amma da shike macece mai hikma sai bata nunaba tanason su kebe su biyu ta nunawa Ma'u kurenta

A fusace Bature ya shigo falon rike da bulala a hannusa yana muxurai, gadan gadan Bature ya nufo kan Ma'u da bulalan

Ma'u na kallonsa tasa ihu

"Wayyo Ummi xai kasheni"

Rumgume Ummin Ma'u tayi

"Lafia Bature? Meya faru?"

Ummi tayi maganar tana kare Ma'u

"Pls Ummi hankado min 'yar iskan nan na nuna mata nata kadan ne"

Mikawa Falmata Abdallah junior Zahra tayi taje ta rike bulalan dake hannun Bature tace

"Pls Dear kayi hakuri kada ka daketa kaga jikinta danyene kada ya janyo wani damuwar"

A fusace Bature yace

"Kinga bbu ruwanki, ki sakemin bulalata ko na hada dake na daka, ai ita bata san jego take ba tunda ta iya jefar da yarinyar"

Duk mamaki ya kamasu

Ummi ta dubi Ma'u

"Ke aina kika yarda yarinyar"

Baki Ma'u ta tura tace

"Ni ajiyarta na bawa Mami, kuma don nace Zahra ta dinga rarrashinta tana aikin takwara shine xai dakeni"

Kwace Bulalar Bature yayi ya xane Ma'u dashi, har ranta taji saukar bulalan ihu tasaka mai raxanarwa, ganin Bature nason ci gaba da dukanta yasa Zahra tare Ma'u bulalan ya sauka a jikinta

Dakyar Ummi ta karbi bulalar a hannun Bature ta turashi waje Zahra kuka Ma'u kuka, Falmata ko ta tsaya kallon ikon Allah

Bature na fita Ma'u ta rumgume Zahra taci gaba da kukanta, shafa kanta Zahra ta shiga yi

"Kiyi Shiru Ma'uta pls kada kidingawa Ya Bature rashin kunya kinsan baida hakuri"

Baki Ma'u ta tura tace

"Niba rashin kunya na masaba, ai gaskia na fada"

Itadai Falmata kallonsu take kamar 'yan drama

Dakyar Ummi ta lallaba Ma'u taje ta dauko diyarta

Daddare ajiye Ma'u Falmata tayi ta mata fada ssai tareda nasiha, ssai kalaman Falmata sukai tasiri akan Ma'u kuka ta fashe dashi

"Nagode ssai Anty Falmata Insha Allah xanje na bawa Anty Zahra da Ya Bature hakuri, kuma baxan sakeba"

Murmushi Falmata tayi tace

"Yasha'ullah Ma'u ta Bature"




Ina labarin Zee


Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻

Nama rasa ta ina xan fara
Fans kunmin komai
Kaunarku gareni ta musammance
Na taka rawa ssai da baxarku
Bbu Abunda xance sai Alhamdulillah nagode ssai Fans
Allah yabar kauna❤

JINJINA
Ummu Subay'a Fans
Rufaida Omar Fans
Tapital Pulaku
Pherty Zahra Novels
Zauren Biebie Isa
KanuShuwa
Da duk Groups da kuke kaunata

KUNA RAINA
Meerna Parrot
Meela Adeel
Anty Sophie
Fulani Shamcy
Kdeey
Hajara Ghandi
Maman Muneeb
Maman Nuwwaira
CutieLuv
Siyama
Mom of 12
Hamamatu
Zee Madagwal
Da Duk sauran Fans na Gidan Bature

DA BAXARKU NA TAKA
Rufaida Omar
Batool Adam Jatko
Zainab Goni
Bingel

INA ALFAHARI DAKU
Biebie Isa (Dan Makaho)
Pherty Zahra (El-mustapha)
Aisha Aliyu Garkuwa (A Gareni)
Mahmu Gee (Eznah)
Sadnaf (Makobtan Juna)
Phertymerh (Yusrah)
Sameena Aliyu (A Duniarmu)
Hajja ce (Da Nagari)
Batool Mamman (Kashe Fitila)
Safiya Huguma (Kundin Kaddarata)
Ainakatiti ( Hasken lantarki)
Feedohm(Matar Abdallah)
Habiba Muhammad (Sahra)
Rash Kardam
Sanah Matazu
Miemie Bee ( Rana Daya)
Anty Sis
Zainab Makawa ( Tarko)
Khadeeja Randa (Rashin Rabo)
Khady Candy
Biyun Anty
Rahma Nalele( Karuwanci ko Tantiranci)

KUNA MUSAMMANE
Fauxia yar aljannah
Mrs Adam
Mrs Xerks
Mrs Mansoor
Ummi ontop
Maimuna matar Abdallah
Fauxia M Bala
Mai Agogo
Mrs Makama
Maryam Ahmad
Hauwa A Usman
Ummulkhairi
Noorul Hannah
Real miss J
Sadiya (Ummu Hanash)
Maman Rufaida
Halima Mk
Naseeba Uba
Da duk Kainuwa writer's

Ban san wani irin jinjina xan miki ba NABILA RABI'U ZANGO kin cancanci duk wani yabo, a nawa sanin kinfi kowace online writer fadakarda mutane, kina tabo matsalar dake damunmu ayau,
Allah ya kara baseera da daukaka

END

Rayuwa ta karantawa Hajiya Turai da yaranta darasi ssai sun koma abun Allah sarki abun tausayi, a hanyarsu ta dawowa gun boka suka sami hatsari aka yanke kafar Hajiya Turai daya mijinta ya dankaro mata kishiya

Har gida sukaje itada Zee da Lubna suka nemi yafiyar Ummi da Hisham


Bayan Shekara Goma

Hisham yayi aure, ya auri 'yar uwan su Mami Khadeeja

Yaran Ma'u hudu
Zahra (LilZahra)
Ahmad (big Daddy)
Muhammad ( Small Daddy)
Maryam

Yaran Zahra Uku
Mahmud ( Affan)
Hawwa (mai Jidda)
Asma'u ( Husnah)

Yaran Jidda Biyar
Hawwa (Amal)
Muhammad (junior)
Mudassir
Fateema (Ummul)
Mufeeda

Yaran Batool Uku
Shukrah
Hisham
Khausar

Yaran Khadeeja biyu
Jamal da
Hamdiya
Ga
Abdallah junior

Bature Estate

Kyawawan yara guda bakwai ne suke wasa a falon Ammi, yayinda iyensu keta hira a gefensu

Wata farar Baby mai kama da Ma'u tasa kuka har da birgimanta a kasa

Ma'u dake kwance kanta na kan cinyar Zahra ta mike da sauri taje ta daga babyn

"Takwara tashi kada ki bata kwalliyarki waye ya tabaki"


Kamar yadda Ma'u take tura bakinta haka yarinyar ta tura bakinta

" ba Ya Abdallah bane ya dakeni"

"Karyane Mom bai daketaba kawai don ya hanata tsokanar Khausar ne"

Cewar wani yaro mai kama da Bature sak

"To rufemin baki dan gidan khausar"

Ma'u tayi maganar tana hararar yaron

Rarrashin yarinyar tayi tace

"Wlh Abdallah jnr idan ka kara tabamin Takwara sai na saba maka, kuma baxan baka ita ka auraba, da fitinarka kamar takwarankan nan"


Daria su Jidda suka saka

Batool tace

"Ai wlh maganin Husna sai Junior, Anty Jidda ki dauketa kawai Ku tafi Junior yaje ya koya mata hankali"

Harara Ma'u ta watsa mata tace

"Bbu inda Husna xata muna nan tare da ita"

"Wlh da'axa tafi da ita dana huta, ko Daddynsu fa bata tsoro tsabagen tasamu daurin gindin Ma'u"

Cewar Zahra

Baki Jidda ta tabe tace

"Ai sanda nace muku kada kuma Ma'u takwara amma kuka mannamin hauka gashi kunajin jiki, Yaushe kuka gama da Ma'u ga kuma Husna"

Daria Khadeeja tasa tace

"Abun ba sauki daman ance suna linxami"

Ssai sukasha hirar yaushe gamo a falon Ammi, bayan kwana biyu suka tattara suka koma Abuja da yaransu

Xaman Ma'u da Zahra gwanin sha'awa baxaka taba banbance yaran waye wannan ba duk kansu daya

Yau weekend duk suna gida kuma Ma'u ce da girki, yaran na garden suna wasa

Bature na xaune a 3siter Zahra na hannun damanshi Ma'u na hagonshi suna hira gwanin sha'awa

Big Daddy ne ya shigo da kuka hadda majina ya fada kan cinyar Zahra

"Umma bakinga Husna ta dakeni"

"Baxaka rama sai ka kawo karanta ba kanwarka bace"

Bature ya daka mishi tsawa

Kallon inda Ma'u take Big Daddy yayi yaga tanata hararar sa

"Mom ta hanamu dukanta"

Kallonshi kan Ma'u Bature ya mayar yace

"Nikam meke damunkine Ma'u, Allah xansa kafar wando daya dake da Husna"

Rarrashin Big Daddy Zahra tayi ya koma wajen wasan tace

"Wannan karon muna xuwa family Meeting xan dankawa Jidda Husna su tafi da ita can junior ya koya mata hankali daman maganin Asma'u sai Muhammad"

"Hakan xa'ayi don xaman Ma'u da Husna inuwa daya xasu xautani"

Daria Zahra ta saka banda Ma'u data hade rai


Daddare hade rai Ma'u tayi ta juyawa Bature bayanta, rumgumeta ta baya yayi

"Mekuma ya farune Husnata"

Kwatan kanta Ma'u ta shigayi

"Nidai ka barni, ba biyewa Maman Affan kayiba xaku dauki Husnah kukai Lagos"


Murmushi Bature yayi ya kara rumgumeta a jikinsa

"Ma'u case, idan don wannan ne kijuyo bbu inda xamu kaita tana nan tare dake, amma idan kikaga na haukace kune sila"


Daria jin dadi Ma'u tayi ta juyo ta rumgumi Bature

"Yawwa Baby, yau inason samun hadin kanki ssai don insha Allah xan ajiyewa Husna kanwa ko kani"

Bakinta Ma'u ta tura, take Bature ya kamo bakinta ya hada danashi

Asuba ta gari Ma'uBature

Tammat billah

Alhamdulillah anan na kawo karshen littafin GIDAN TURAWA
Kuskuren dake ciki Allah ya yafemin
Allah yasa mu dauki darasin dake ciki
Ameen

Sai mun hadu a sabon littafina

KARKA GUJENI
Labarine dake dauke da
Soyayya
Cin Amana
Tausayi
Hallaci
Yaudara
Abota
Sadaukarwa


Ummu Subay'a❤

Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment