Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da halayenta..sai malamin yace "shin akwai Wanda yake Binta bashi? Aka ce "a'ah daga karshe dai basu gano laifinta bah,malamin ya tamabaya ko rashin lfy tayi nan aka sanar dashi ta haihu har anyi suna angama lfy..malam yace "wannan kayan sunan su suka hanata kwanciyar kabari" jama'a suna mamaki , malam ya cigaba da cewa "wasu matan suna bayar da kaya ne tamkar bashi suna sa ran cewa idan sun haihu xaa biyasu ko fiye da Wanda suka kai..donhaka a maidawa kowacce kayan da ta kawo a bar na iyayenta da kuma na mijinta, saboda wannan kayan tamkar bashine a gareta idan bata biya bah xata hadu da axaba..bishara ce Allah ya nuna musu" hakan kuwa akayi aka maidowa kowacce kayanta wasu sun karba wasu ko sunce sun yafe daga nan aka binne matar ba tare da fuskantar matsala bah .. *true life story*..Allah yasa mugane..wllhi daya wa mata basa yin Abu don Allah suna yi ne don idon jama'a ko don a maida musu makamancin Wanda suka bayar ko fiye da haka.hakan ya taba faruwa a unguwar mu inda wata mata ta kaiwa makociyarta turmin xani, ita kuwa makociyar ta kai mata zani 2 nan aka fara kananan maganganu..Allah yasa mu dace ..amin )
Ruhaimat bata gayyaci jama'a bah duk Wanda yaxo don kansa shikenan, haka suka gama taro lfy bayan ta gama wanka ta shirya ta koma Abuja don sadeeq ya koma can da aikinsa imran da Ibrahim su suke kula da *amz* na yola.

*Reefat ce*😘😘😘😘

πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž
*75*
By *Reefat yahya*

*an imaginary Lov story*
πŸ”šπŸ”šπŸ”š

_Alhamdulillah..godiya ta tabbata ga Allah ( s.w.t ) da ya bani ikon kammala wannan labarin Allah yasa mu dace amin_ *godiya gareku masoyana Allah yabar mu tare Lov u all*😘😘😘

Ruhaimat ta koma Abuja lfy haka suka cigaba da rayuwarsu ckn jin dadi da kwanciyar hankali suna matukar nuna wa juna so, basu rabuwa sai idan sadeeq ya tafi wajen aiki kullum suna makale da juna ga yaransu gwanin sha'awa Mimi an girma tana matukar kama da baba karami tamkar an tsaga kara.
****Xaune suke a falon mami gaba dayansu Mimi Ya'r shekara 7 ta juya gun mami tace "mami nafi Abba kyau koh" dariya suke Ruhaimat ta juya tana kallon Abban nata Dan shekara 2 tace "don't mind her Abba Nah..duk gidan nan ka fisu kyau" murmushn jin dadi yake dama basa shiri da Mimi ko kadan suna matukar kishin juna , sadeeq yace "mmi Nah tafi kyau don tana kama da ni" Mimi tayi carab tace "yawwa dad Shiyasa aka ce kuma kama da little baba koh" kai ya gyada mata cike da jin dadi ta juya tana yiwa Abba gwalo nan ya fashe da kuka sadeeq ya jawosa "sorry sadeeq Dan sadeeq jikan sadeeq kafi kowa kyau duk duniya babu Wanda yafi ka kyau ok" haka ya fara rarrashinsa mami tace "oh..shi wannan babu inda yabar mahaifiyarsa wato har wannan shagwaba saida ya dauka" dariya Ruhaimat take dai2* nan baba ya shigo tare da sallama yaran suka ruga suna masa oyoyo nan ya xauna aka cigaba da hira.da safe sadeeq yace Ruhaimat ta shirya xata raka shi unguwa nan ta dauki dogon hijabinta ta sanya daga nan suka fita sun bar yaran gun babah larai , tafiya mai nisa sukayi sannan yayi parking dai2* wani kayataccen gini aka wangale gate suka shiga ciki ..wow..masha Allah filin ya hadu wani katafaren story building mai kyawun gaske ya bude mota ya fito ya xagaya bangaren ta ya bude mata.tsayawa tayi tana kallon building din yafi amz company haduwa wajen shiru alamar babu mutane a ciki sai masu gadi "ina ne nan kismat?" Murmushi yayi tare da cewa "cloz ur eyes" haka ta rufe idanunta ya rike mata hannu sunyi tafiya kadan yace ta bude ido tana bude wa taci karo da rubutu ckn manyan harufa *AA JADA COLLEGE OF ISLAMIC STUDIES N RESEARCH CENTRE* ta juya tana kallonsa murmushi ya sakar mata tare da rike hannunta yana wasa dashi yace " Ruhaimat kin bani komai na rayuwa kina sona fiye da yanda kike son kanki ..kina bani kulawa ta musamman..kina kyautatawa iyayena da yan uwana kina matukar girmamasu..kina sona ba don wani Abu nawa bah..baki taba bude baki ki rokeni wani Abu bah duk da nasan kina bukata...kin bani dukkan farin ciki na Rayuwa don haka na Gina miki wannan makarantar na mallaka miki shi har abada ko bayan raina wannan baya ckn gado tnx for evrytin I Lov u so much" hawaye ne ke xuba a fuskarta bata da bakin da xatayi amfani dashi wajen yin godiya don haka ta fada jikinsa ta dinga rusa kuka dakyar ya rarrasheta daga nan yabi ya nuna mata koina ckn fadin makarantar abun ba'a cewa komai don karshen tsaruwa kam ya tsaru.bayan sun koma gida ta sanar da mami da baba ta kara musu godiya daga nan ta fara bugawa yan uwanta waya tana shaida musu, a wanna ranar sadeeq ya samu kyauta ta musamman ..hmmm abar kaza ckn gashinta.bayan sati 2 anfara bada admission a makarantar ckn kankanin lokaci yaran masu hannu da shuni suka cika makarantar a yayinda ta bada admission 200 kyauta ga marayu , manyan malamai masu ilimi aka dauko daga kasace daban2* masana addinin islama har da yan kasar mu Nigeria nan aka sa ranar bude makarantar. Yan uwa da abokan arxiki babu Wanda baizo bah ranar bikin bude makarantar, Abba umma Hajja Dada yasmeen imran Ibrahim momin imran da dadynsa da iyayen yasmeen meenah Ameena ya Yusuf anty maryam anty Xee da sauran yan uwa da kuma danginsu na kano duk sun halarta,manyan kusocin gwamnati da manyan yan kasuwa dakuma talakawan gari duk sun hallara a wajen nan Ruhaimat ta fara gabatarwa da harshen larabci daga bisani tayi da turanci tunda ta fara magana ake jinjina mata har ta gama..haka dai aka cigaba da gudanar da programs daga karshe aka tashi da adua.bayan sun koma gida bakin na masauki Ruhaimat na xaune ckn yan uwanta ta chaba ado tayi kyau sosai anty maryam ta tabe baki tace "oh duniya..Ruhaimat da nake rainawa nake mata kallon bagidajiya Yau ita ta xame mana abar alfahari a duk fadin danginmu" yasmeen tace "hmm kedai bari kawai ni xan baki wannan labarin" anty Xee ta kyalkyale da dariya tace "abunda ka shuka shi xaka girba..hijabin nan dai da kuke raina wa Yau shiya saye mata girma da daukaka a idon duniya" karar wayar Ruhaimat ne ya katse musu hirar daga nan ta tashi tace " *mai sona* yana son ganina na barku lfy" "mu bamu sonki kenan" meenah ta fada ckn xolaya dariya tayi ta fice daga dakin. Kwance yake bisa darduma hannu ya mika mata nan ya jawota ta fada saman kirjinsa " I miss u so much maini" "miss u more mai sona" "my Dil ( xuciya) my pretty i Lov u" "mai sona my kismat my sadeeq my Bbn sadeeq ina matukar kaunar ka Allah yabarmu tare har abada har a gidan aljanna Allah yasa Kaine mijina" "ameen maini..I Lov u more Dan anything in dis world" "Lov u more *mai sona*"
*TAMMAT BIHAMDILLAH* _anan na kawo karshen labarin mai sona abubuwan da na rubuta bisa kuskure Allah ya yafe min , wannan labarin kirkirarre ne banyi shi don cin zarafin wani ko wata bah Allah ya ganar damu yasa mu dace ameen Lov u all_😍😍😍
*littafan Reefat yahya*
~shine zabina~
~nida shugaban kasa~
~mai sona~

*Gareku masoyana*
_Gidan gyara_
_professional writers_
_manshart novel_
_duniya novels_
_xahra bukar novels_
_home of novels_
_matan arewa_
_manyan mata novels_
_Hausa novels_ da sauran groups da ban lissafa bah..Lov u all😘😘

*cutee* *manshart( kishias)😜😜 Nah* *mjay Nah* *billy s fari* *miss xoxo* *hafsy rano* *little princess* *daso ( miemie b)* *billy Ibrahim* n masoyiyata *laurex😜 ( billy losh)* *ayusha iliya* *rabia SK* *Xee yabour* *badiat ib* Lov all

_maman haisam_
_maman afra_
_hasmad_
_only bro Auwal_
N my _fine fine bobo haneef_ Lov u wujiga wujiga
😍😍😍

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment