Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallahr Azahar yayi ya tashi ya fita, Yana dawowa daga masallaci yaji wayan shi na ringing duba wa yayi yaga waye, Hameeda dum dum dum k'irjin shi yace da kaman bazai d'auka ba sai kuma ya d'auka.

Hameeda muryan ta na rawa tace "hello"

Sai da ya Dan ciza labb'an shi sannan yace "hello"


Hameeda ta fashe da kuka, tama kasa magana sai kukan kawai da take yi

Yace "ayya Hameeda kiyi hak'uri ki daina kuka Ni nasan ba da San ranki bane hakan ya faru Amma Dan Allah kiyi shuru Allah na tare damu pls Hameedan Hamed"


"Cikin shashek'ar kuka tace my Hamed yanxu kana nufin kaji ance za'a min aure my Hamed mutuwa zanyi"

"Haba Hameeda kiyiwa iyayan ki biy'aya haka k'addarar mu take Amma Allah yasa muci wannan jarabawar pls karki sa kanki a damuwa kinji Hameedan Hamed" ya k'ara she zance cikin zulaya Dan dai karta gane Yana cikin damuwa


"To my Hamed insha Allah zan daina damuwa Amma kuma na maka alkawari Ni taka ce, ba wani namijin da ya isa ya mallake Ni in ba Kai ba, Kai d'aya namawa ta najin jiki na"


"Hmmmmmmmmm" kawai Hamed yace dan yasan wannan magana Bata bazai tab'a yiwuwa ba Dan ba namijin da zai aura Hameeda yace ya tsaya yana kallon.

"My Hamed ya naji kayi shuru"


Yace "Aa Hameeda ba shuru nayi ba sai anjima Dan zan shiga gida yanxu"

Tace "to sai anjima" wani irin dadi taji dan Bata Sha Hamed zai fahince ta ba wani irin son shi na qara shaga Mata zuciya...




****************

Bayan wata d'aya





_Kuyi hkr yau ban samu Daman yi muku typing da yawa ba kunsan ance jiki da jini_🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀




I love you all my fan's😍😍😍🥰







*comment*
*share*







Aunty Baby✍🏻

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺
🌺



💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA* 💅🏻




®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼





*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻






*Bismillahir rahmanir rahim*





*page* 3⃣2⃣to3⃣3⃣




Shirye- shiryan biki ake sosai an fito da anko kala-kala sai Wanda ka zab'a, gyara kuwa su Hameeda nashan shi duk da dai ita Hameeda ba wani tsayawa take ba sai Momy ta Mata Jan ido tukun na, aunty amarya ummin Fadila kenan ta d'auko musu wata mai gyaran jiki 'Yar maiduguri sosai take gyara su, Nusaiba kon uwarta ta Hana ta zuwa, Fadila da Hameeda kawai ake ma wa, Hameeda ta qara kyau sosai tayi fari Amma ta rame sosai bata cin abincin in ba an titseyeta ba....



Yanxu haka suna d'akin da ake gyara su Fadila ake shafawa wani had'in magana na fata Hameeda kon na zaune tana karanta wani novel mai suna *SAUDALA* na Neat Lady dariya take sosai, Fadila tace

"Wai Hameeda mai kike wa dariya ni raban da in ga kina dariya kaman haka har na manta"


Dariya Hameeda ta k'ara yi sannan tace "Wallahi buk din nan namin dadi saudala tana wulakanci ta".

Fadila tace "tab Ni karatun novel bawai ya damai ni bane Amma zan fara ko dan kula da my yaya Areef".


Murmushi mai musu gyara tayi sannan tace.
"Ai kuwa kin burgeni Wallahi gwara ki kula da mijin ki kafin k'adangarun barike su kwace miki shi, Yan matan yanxu basu san kula da miji ba su dai burin su kawai a Sha magani su burge miji da dare Amma basu San yanda za su kula da tsafta girki kwailiya iya daukan wanka iya magana iya tafiya ke abubuwa da yawa Wanda ba sai kasha maganin Mata, ba baka San daga Ina aka yi shi ba kai dai kawai ka dauka kasha wai da duk ka burge miji kuma hakan bazai hana ya wulakanta ka ba, Ina mai baku shawara Kar ku biye wa Yan matan yanxu na shaye- shayan maganin Mata, ko Kai da kanka zaka iya had'a abinda zai amfane ki Wanda bazai cutar da Kai ba irin su, dabino, aya, ko kayan fruit suna gyara jiki da duk abinda kike so".

Kallon ta Hameeda tayi sannan "tace hmmmmmm aunty Rawan kenan ke yanxu duk Ina kika San wa'innan abubuwan Naga dai baki dad'e da aure ba"? .


Tace "ummmmh Hameeda zauna ganin ruwa kwado ya miki k'afa ai yanxu dole ka kula da kanka saboda 'yan Mata yanxu bin maza suke ba maza ne ke binsu ba, dan haka ku dage wajan gyara jikin ku d'akunan ku girki shine adon mace duk mace da Bata iya girki da kwaliya ba to Wallahi sunan ta sorry".


Murmushi Fadila tayi sannan tace "Wallahi aunty Rawan mijin ki yayi dace gashi kin iya gyaran jiki kin iya kwalliya kin iya girki to ai kin more" .



Tace "keko ba dole in iya ba ko so kike ai min abunda Mata suka tsana"?.



Dariya sukai dukan su, haka dai ta cigaba da koya musu abubuwa kala-kala ita dai Hameeda ba d'auka take ba dan tace ba Wanda zata je tana ma gyara, dan ita Hamed kawai ta tana darwa kan ta.........

******************


Maman Nusaiba ce zaune gidan Haj zuwaira suna magana yanda zasu tsara bikin su dan a cewar su Nusaiba sai tafi kowa had'uwa a gurin bikin, Haj zuwaira tace

"Haba Haj yanxu shi Nabil din yake Bata kud'in to Wallahi tun wuri gwara mu datse mai baki sai yanda tayi dashi in ba haka ba nan gama mun shiga uku, dan zamu siyar da akuya ne da dawo tana ci mana danga"


Tace "Hmmmmmm ke dai bari Haj zuwaira wannan yaro daga ganin shi bashi da kirki, wai cewa nayi tace ya bata ko dubu d'ari biyu ne a k'ara a cikin shagalin bikin na Amma ya k'i to Wallahi ta bakin nake dole mu d'aure mai baki in ba haka ba zafi karfin mu wata ran"



Haj zuwaira tace "haba Haj ai qarki damu nice ba Haj zuwaira, dole ma ya sakin Mata hannu"


Haka dai suke ta kule kuken su........


***********

Yanxu baki sauran sati biyu,kuma yau ne suka gama exam din su gaba daya, yaya Areef ya had'a musu party a cikin gida suke abin su k'awayan su gaba d'aya sun zo ana ta cashewa, fadila duk ta gaya musu bikin su sauran sati biyu, akwai suna ta murna zasu Sha biki haka aka tashi cikin farin ciki.......


Washe gari

Big Daddy duk ya tara su yace Areef zai zauna a gidan shi dake malali kaduna, shi kuma Yaya Yazeed Abbu ya siyan mai wani gida a GRA, sosai sukai murna sanna sukayi godiya, yaya Areef ya mik'awa yaya Yazeed IV yace gashi Nan ya d'ibar wa Hameeda, shikuma zai ba Nusaiba da Fadila, yaya Yazeed yace ai da biyi bama yasa ayi, yay Areef yace kawai yace a barshi tinda yayi, iyayan su suka sa musu albarka sannan yay Yazeed yace abokanan shi sun had'a dinner, kuma harda iyaye za'a je, suka ce to ba matsala Allah ya kaimu........






***********



Kaya sosai a haka had'a na amare, kuma duk big Daddy ne yayi Hameeda akwatuna goma Sha biyu ita ma Fadila haka sai dai kayan cikin da ya banbanta dan Meme ba qaramin kudi ta narka a kayan Hameeda ba, ita ma Nusaiba yau za'a kawo nata shiyasa gidan ya tashi da shirye- shirye.......



Karfe 4:23 motan iyayan Nabil suka zo kawo kaya, part din haj jadda suka Kai Dan nasu Hameeda ma duk Yana can, akwatuna ne gwada takwas sai kit daya kayan sunyi ba qarya, Amma ita uwar amarya sai ta buge da zage-zage wai anyi San Kai su, su Hameeda an musu goma Sha biyu ita kuma yarta an kawo Mata takwas, haka dai tayi ta fad'an ta.......



*************
Yanxu an shiga satin biki, in gaka su Hameeda baza ka iya gane su ba sunyi kyau, barin ma hameeda kaman ka sace ta ka gudu, su Fadila duk sau shirya abun da za'a yi, ranar laraba za'a fara shakali za'a fara da walima ne sai ranar alhamis ayi Arab night sai ranar juma'at ayi kamu ranar asabar kuma daurin aure da dinner,



Hameeda ce kwance tana tinanin yanxu fa auran nan za'a yi da gaske, Fadila da Zarah ne suka katse Mata tinanin da d'aka Mata duka Zarah tace.

"Waya gaya miki amarya na bacci ki tashi yanxu aunty Rawan zata xo ta miki dilka"


Mtswwwwww taja tsaki sannan tace "haka kurin Ina bacci ba mai dadi Kun xo Kun tashe ni"


Fadila tace "lallai ma yariyar Nan ana miki gyara kina fushi Wallahi wata ran zaki ga amfanin shi"


"Wallahi bazan taba ganin amfanin shi ba tinda ba Hamed nayiwa ba"

Zarah tace"oho miki dai"


Nusaiba kon ba abunda uwarta ke Bata sai maganin Mata Dan tace shine gyara mai kyau ba irin Wanda ake wa su Hameeda ba, akwai tayi wani himmm da ita ta qara ciki kaman ba ita ba......





Hamed kon har yanxu Yana son cire Hameeda a rain shi Amma ya qasa, Amma dai yanxu Yana Dan sakewa da Hanifa dan umma ta Mata bayani komai kuma ita hanifan tace ta yarda zata aure shi murna kam sosai umma tayi Dan Bata Sha zata yarda ba (Ni kon nace Daman tana son abunta🤣) shiyasa yanxu tana kula da shi sosai, yanxu bikin su ma sauran 1month haka daman kawun Hamed wata daya da rabi yasa.........





Yau ta kama laraba kuma yau ake musu lalle, karfe 4 za'a yi waliman shiyasa aka fara musu da wuri, an gamawa Fadila da Nusaiba sauran Hameeda ita ma an kusa gama mata, bakin lalle ne da ja aka musu yayi masifar kyau da yake sun iya masu yin,



Su Momy kam ana cikin jama'a Dan Yan uwanta sun zo su aunty Hiba aunty Yasmeen aunty Sakinat duk sun zo...


Ita ma Meme part dinna nata ba masaka sinke Yan uwanta kowa ya zo tinda Bata tab'a auran wa ba sai akan Yazeed kuma shi daya Ni ba wani shiyasa mutane.....



Maman Nusaiba ma dai hakan take yaran ta duk sun zo su aunty Nafisat da aunty shamsiya...



Aunty Amarya ma haka take, gida dai ya cika tam,
part din Haj jadda ma dai shima mutanan ne Yan Zaria duka......




Ana gamawa Hameeda aunty Rawan ta zo ta tafi da su D'aki ta qara turare musu k'unshin sai kamshi suke zubawa, ko ruwan wankan da za suyi ita ke hada musu da turarukan kamshi, yanxu ma haka ita da hada musu dan karfe 4 ta kusa an fara cewa suyi sauri, suna fitowa dakan wanka sai da ta qara musu wani turaran sannan ta musu kwaliya, wasu dugayan riguna ne da Aunty amarya ta siyo musu suka sa rigan Hameeda pink ce sai dan ratsin blue daga sama ta matse sai kuma kasa aka sake ta ta zauna daram a jikin ta sai dan qaramin gyalen rigan da shi aka yafa mata, ita kuma Fadila fari ne sai ratsin black iri daya ce dai da ta Hameeda kala ne kawai suka banbanta, sunyi matukar kyau Dan sun Sha make-up, aunty amarya ce ta shigo D'aki sannan tace.

"Wai ku har yanxu baku gama Shirin bane kunsan fa karfe 4 aka ce za'a waliman Nan Amma Kun tsaya sai faman nuku-nuku kuke"


"Aunty amarya mun gama fa cewar" Hameeda

"To ku fito mu tafi"

Takalman su suka sa shima dai irin rigan ne haka suka fito, a cikin gidan za'a yi waliman Dan anyi decoration din gidan yayi kyau sai fararan kujeru da aka shirya......



K'wance yake abin shi zakace na angon kwana biyu da zasu su ba, wayan shine yayi ringing Yana cikin bacci ya d'auka ba tare da sani waye ba, yace "hello"


Daga can yace "Amma Kai dan i'ska ne daga ji ma bacci kake sai kace ba ango ba wani irin bacci kuma yanxu"


Yaya Yazeed yace "safwan yane Wallahi bacci ne a ido na kasan jiya banyi ba ina asbiti duba patient"

Safwan yace "lallai ne ango to Wallahi d'azun nan Yusura ta zo baka nan naso na gaya Mata bikin ka Amma na fasa"


Yace "Ni Dan Allah bar wannan mgn yanxu dai menene ka kira ni"?

Safwan yace "daman kan mgn abokan mu ne an manta ba'a sa karfe nawa za'a yi dinner Nan ba a iv"


Mtswwwwww yaja tsaki sannan yace "Daman akan mgn Nan zaka tashe ni to ka Bari sai na fito anjima mayi mgn" ya fada tare da Kashe wayan ko tsayan amsan shi beyi ba.


Safwan yace "Allah ya shirye ka Yazeed"




An fara walima sosai malaman ke wa'azi aka aure, jikin su duk yayi sanyi a haka har aka tashi a gun sannan suka koma part din Aunty amarya, ita Daman Nusaiba Bata je ba tana can tare da k'awayan ta suna party.


Washe gari suka tapi salon aka musu gyaran Kai karfe biyu suka dawo, aka fara Shirin kamu kuma gashi harda angwaye za'a yi. Amaran gaba daya lifaya za su sa su kuma angwaye suit zasu sa, shima kamun ana cikin gida za'a yi Amma an canja Yana yin decoration din.


Su Nabil ma sun shirya zasu tahu, yay Areef shima yay Yazeed ne kawai sai yanxu da su safwan suka zo ya shirya.


Anyi wajan zaman amarya da ango duka su ukun sannan na mutane, su Hameeda an musu kwaliyan su an yafa musu lifaya ga gyaran kan da aka musu sai qara feshe su da turarukan ake , Kai fadab kywun da sukayi Bata lkc ne bazan iya musarta muku ba kawai ku aiyana a xuciyan ku, Nusaiba ma irin ta aka Mata tayi kyau ita ma.

Motar su Nabil na qarasowa Suma su yay Areef suka zo yay Yazeed ma shima suka fito, gaskiya angwaye sunyi kyau iya kyau.

Aunty Yasmeen qarwan Momy tace a Bari amaran su zo sai su huce gun zaman su tare, haka kon aka yi su Fadila na fito yay Areef yace ya reko hannun ta Yana takar Mata murmushin.

Shima Nabil hakan nan ya je ya riko tashi Nusaiba.

Yay Yazeed kuwa...............





To fa ko mai yay Yazeed zaiyi 🤷‍♀






*comment*
*share*





*Aunty* *baby* ✍🏻
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment