Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taka mata hannu harsaida yay 'kara yafice fuuuu...wata galabaitacciyar 'kara tasaki dan azaba, babu wanda yay yun'kurin taimakonta, bayan wasu 'yan mintuna saiga dady da gayyar 'yan sanda, yayibarsu aka sakeyi su bakwai akai ciki dasu.

Bayan wasu 'yan awanni komai ya natsa, Ameeda tabasu labarin halin data tsinci kanta awajensu iya abu da yanda rayuwa tamai da ita adalilin Naseer, kuka suke sosai cike da tausayinta, ta ce, "ashe inada gata bansaniba??, ashe su ba iyayena bane?, shiyyasa suke cutar dani ta hanyar lalatamin tarbiyya, shiyyasa basu ta6a damuwaba da halin dana tsinci kaiana, ya Muzzaffar haďuwata dakai alkairine, bazan ta6a mantawa dakaiba, kataimakeni kataimaki rayuwata kacetota daga hali irinna gur6atattun mutane, ngd ngd ngd yayana abin alfaharina...ta kara rushewa da kuka, dady dake kusada ita yarungumeta yana lallashi saikace wata karamar yarinya.
    Tabasu tausayi kwarai da gsk, amma babu komai zasu sharemata hawayen shekara ashirin da biyu dataketa zubarwa, zasu maida ita 'yar gata kuma mai gata.
   Tun aranar tafara ganin gata na musamman ga iyayen nata, komai saidai ayimata, jinta take tamkar awata (SABUWAR DUNIYA littafina mai zuwa), lallai tayarda ita 'yar gatace kuma a bar so ga kowa, ranar agidan kaka ta kwana, tasha tarairaya.

RAYUWAR AMEEDA A SABUWAR DUNIYA.
     tana zaune afalo cikin 'kayatacciyar kwalliya ta burgewa, 'yan tagwayen yarannan dabamusan ko 'ya'yan waye ba har yanzu suna gefenta suna mata surutu sai faman murmushi take dan tanason yara, ita indai yaro baida fitina to xata iya zama dashi, ya Muzzaffar yashigo falon da sallama, ta ďago manyan idanunta tana amsa masa, fuskarta cike da murmushi.
   Dagudu yaranan sukaje suka tarosa, ya tarbesu shima da farinciki, kusada ameeda ya zauna datake binsu da kallo cikin sha'awa da matu'kar birgewa zuciyarta na kissima mata abubuwa dayawan gsk, har yazauna kusada ita bata saniba, ya hura idananunta dake tsaye 'kyam awaje guda.
   Ajiyar zuciya tasaki tana murmushi, saikuma ta shagwa6e fuska kai yaya sokake idanuna su bushe??.
   Yay murmushinsa mai 'kayatarwa tareda juyowa sosai suna fuskantar juna, ya sanyaya muryarsa tareda faďin khadijah na mikike runanine??.
   Hannu tasaka tana rufe fuska ta ce, "babu komai.
   Hummm niko kinga nasan abinda kike tunani, taďago kai da sauri tana kallonsa to faďi naji idan kacanki gsky.
   Yaďan jinjina kai tareda latse baki, idan na faďa minene tukuycina??, ta rausayar da kai gefe duk abinda kabukata indai bai sa6ama shiri'a ba kuma inadashi zan maka, yasake yin murmushi mai sauti, kina tunanin inama ace su 'yan biyu 'ya'yanmune na cikinmu ya 'kare maganar da kashe mata ido ďaya, idanu ta zaro lah yaya nidai babu ruwana kuma ba haka nake tunaninba.
   Ya ce, "uhhmyiiim ban yardaba, kirantse indai ba haka bane, tashitai da niyyar guduwa yay saurin dam'ke hannunta, saikuma yay saurin saki, tajuyo ahankali tana kallonsa, saikuma ta tuna rayuwarta da Naseer, tatuna babu abinda yafi bu'kata arayuwarsa irin jikinta, kullum burinsa yaza'ayi ya mallaketa, ashe akwai sauran mutane masujin tsoron ALLAH da tsare dokokinsa??, ashe akwai masu gudun aikata alfasha komin 'kan'kantarta, jiki asanyaye takoma ta zauna, cikin sayin murya ta ce, "yayana inasonka ina 'kaunarka, kaine mutum nafarko dana faraso amatsayin masoyi, kaine mijin daya dace da rayuwata, kaine kaďai zaka iya saita sauran halayena dasuka nemi ku6cemin.....ta rushe da kuka mai tsuma zuciya.
   Xamowa yayi daga kujerar, ya tsuginna agabanta, banason ganin kukanki khadija nima nadaďe ma'kale da 'kaunarki araina kawai dan baki bani dama bane, nasan alokacin kina tsoron Naseee ne kawai, amma inaji araina kece uwar 'ya'yana, ahankali yakai hannu yana share mata hawayenta.
   Su momy dake la6e suna kallonsu cikin farinci da jin daďi, jisuke tamkar su tashi sama dan daďi, lalai za ayi bikin 'yan gata.........wata sallamace ta katse musu farincikin nasu, gaba ďaya sukajuyo suna kallonsa cikin mamaki da al'ajabi.
    Wani saurayine baki, dakagansa kasan arikice yake; kodai abuge kokuma yanada ta6un hankali, hannunsa rikeda bindiga..................

Ku biyomu.




©2017

Hikayarmu!!!!!.
abba gana
      bilyn Abdul
[11/03 10:45] bilyn Abdul: KUKAN KURCIYA.........





              NA
MUH'D ABBA GANA
                 &
BILKISA IBRAHIM
  (☆bilyn Abdul☆)


Zaku iya samun book's ďin bilyn Abdul a blog kamar haka.
https://Mrsbilkina.blogspot.com


  🔚
Page2⃣7⃣&2⃣8⃣

........Arikice Ameeda da ya Muzzaffar suke kallonsa, bindigarsa ya saita sosai akan ya Muzzaffar da Ameeda, hazbinallahu wani'imal wakil kawai suke ambata a zuciyarsu, ya Muzzaffar yay 'karfin halin faďin Sayeed mimuka yimaka? Yaushema kadawo 'kasar??.
     Cikin sanďa  daddy yabiyo ta bayansa ya daki bindigar ta faďi (karku manta daddy babban ďan sandane) mari ya wankama sayeed ya'kara wanka masa wani, tuni sayeed yazube awajen saboda zafin mari, da'kyar momy da Ya Muzzaffar suka ri'keshi saboda sai kaima Sayeed duka yake tako ina.
    Ya ce, "ku 'kyaleni harni wannan ďan iskan yaron zai shigoma gida da bindiga?, to anufinsa nizai kashe kenan ko iyalina??, Sayeed ya fashe da kuka yana faďin nibanzo danna kashe kowaba dady, kaduba kagani babu bulet cikin bindigar, nazone gareka domin nayi maka godiya nakuma baka ha'kuri akan abinda maciya amana sukai maka.
    Tuni jikin daddy yayi sanyi da abinda yayma Sayeed, ya kamoshi dakansa yatayar zaune, to amma Sayeed miyasa zaka shigo da bindiga??, yanzu dakasa nayi maka abinda yafi haka aiban 'kyautaba.
   Murmushi Sayeed yayi karka damu daddy nayi maka uzuri, kobaka aikata komai akainaba 'yan sanda zasuzo su kamani yanzu babu daďewa.
    Atare suka ce, "yan sanda kuma???........ kafin surufe baki wayar daddy tafara wringing yaďaga tareda sallama, basu san mi akace masaba sungadai ya ajiye wayar.
    Yadawo da kallonsa ga sayeed, sayeed mika aikatane haka da zafi??, murmushi Sayeed yayi ya ce, "daddy nakafama maciya amana tarihine, na nuna musu kuskurensune, na harbi 'kafafunsu mamane da waďanda sukace su iyayenane, harda ďan iska Naseer.
   Harbi sayeed miyasa ka aikata haka??.
   Dady hakane yadace dasu, domin nina sun taka rawar gani wajen lalata min rayuwa nida 'kanina, munaji muna gani Sadiq yazama ri'kakken ďan iska, nikuma kuga yanda rayuwa ta maidani, shaye2 ya lalatani, babu abinda nake aturmrai sai iskanci da shan giya da koken, yafashe da kuka, daddy su mama masifane adoron 'kada, sonaima nafasa kawunansu da bulet suyi mutuwar jakuna abola, amma saina canja shawara na hahharbe musu 'kafafu da hannuwa ta yanda bazasu sake moruwaba, koda wanan ba'kincikin nabarsu zanji sanyi, dan haka dady dan ALLAH ko ankamani karkayi belina kabarni acan na 'kare rayuwata gabaďaya, banaso kokaďan wani yasake taimakona, ya mi'ke dazummar ficewa amma sai ya Muzzaffar ya ri'keshi, haba Sayeed baikamata ka yankema kanka irin wanan hukuncinba.....murmushi Sayeed yayi tareda dafa kafaďar ya Muzzaffar ya ce, karka damu Muzzaffar abinda yadace damai irin halina kenan.
    Tun farko iyayena sunrigaya sun ruguzamu, sun sayar da rayuwarmu akan kuďi kuďinma daba nasuba, wlhy daza abarni ayanzu saina ida ďauke ragowar Numfashinsu kowa ya huta...ya fisge hannunsa yafice.
   Basuda za6i face take masa baya, yana fita 'yansanda suka cikuykuyesa, suma su dady mota suka shiga suka bisu.

Tuni ankwashi su iya abu zuwa asibiti dan sayeed ya faffasa musu kafafu da hannaye da bulet abun babu 'kyawun gani, sai kuka da dana sani suke, nikam gsky banji tausayinsuba saima ALLAH ya'kara danayimusu.
    Su daddyma asibitin suka Nufa hankalinsu yatashi daganin 6arnar da Sayeed yayi, (lallai KUKAN KURCIYA JAWABINE, sun raini abunda zai halakasu, sun gina ramin muguntar saka wani, sai duk suka afka batareda sun saniba, ALLAH sarki dady shine yabiya akai musu aikin cire bulet ďin.

Bayan kwana biyu daddy yayi ciku2 aka fito da sayeed, saidai kasha Sayeed ya rasu, batareda kowa yasan yanda abun yafaruba, ALLAH sarki gsky bamuso hakaba domindai Sayeed abin tausayine ALLAH ya yafe masa), agidan dady akai masa sutura ananma akai zaman makokinsa, to ALLAH yaji'kan musulmai.

BAYAN lafawar komai aka shiga shirin bikin su ya Muzzaffar da Ameeda, lallai naga bikin 'yan gata kam, dan shiri ake bana wasaba.
     Zuwa sanan an sallami su haj hassana daga asibiti, saidai suduka sun rasa 'kafa da hannu, lallai suna danasani akan 6arnar dasuka aikata, kukakam sunyi harsun rasa hawaye.
  ALLAH yataimakesu ma haj kaka tahana daddy yakaisu kotu, amma kamar yanda Naseer yay hasashe hakane tafaru, domin kuwa abokan daddy duksun rasa aikinsu, ga haj hassana takar6i takardarta sakinta uku ahannu, komaidai ya lalace musu basuga tsuntsu basuga tarko, su iya abu kam aisunfi kowa asara, domin sun rasa 'ya'yansu duka biyu, Sayeed ya rasu Sadiq kam bama asan inda yakeba saidai gyaran ALLAH.

   BIKI BUDURI.
   dahaka dai aka fara shagalin bikin su Ameeda, Naseer yayi kuka sosai na kubcewar Ameeda daga gareshi, har kano Ameeda taje ta gayyato Falmata, wadda itama ayanzu ta yanke shawarar yin aure, harma tafara istibira'i.
    Bikidai ya kankama don yaune aka ďaura aure, bayyana muku yanda ake shagalinma aii 6ata lokacine ammafa anan kwasar shoki, bakin ango da amarya yaki rufuwa, hakama dady da momy daduk wani masoyinsu, aranar da daddare aka sada amarya da ďakin mijinta ya Muzzaffar.
    To masha ALLAH komaidai yayi dai dai dominko amarya da ango sun riski rana mai cike da farinci saimuce ALLAH yasanya alkairi.
   Itamaidai falmata ALLAH ya haďata da abokin ya Muzzafar wato Ahmad kuma sunyanke shawarar yin aure, dan haka dady yahanata komawa kano yari'keta awajensa, idan biki yataho zasuje har Barno wajen mahaifinta.
    To saimuce ALLAH yasanya alkairi baki ďaya.

BAYAN WASU SHEKARU.
    Mun isa gidansu ameeda domin ziyara, amma sai abubuwa dayawa suka bamu mamaki, domin kuwa mun tarar da ameeda da yara har huďu duk tagwaye, mace da namiji sai maza kuma, abin sai wanda yagani yara 'kyawawa abin sha'awa da birgewa, muna nan zaune saiga falmata itama danata yaran har uku, lallai masha ALLAH aure yayi riba.
   Saimuce ALLAH yabar zaman tare da 'kaunar juna.

A6angaren su iya abu kuwa komai ya lalace, dan tuni malam dauda yasaketa yakoma 'kyauyensu, itakam tana kano tana bara dan tazama gurguwa, hajiya hassana kam ciwon 6arin jikine ya kamata saboda ba'kincikin rashin cimma burinta, to saimuce ALLAH yakara, dama ance idan zaka gina ramin mugunta to saika ginashi gajere dan bakasan mai faďawaba, kuma KUKAN KURCIYA JAWABINE......

TAMMAT BI HAMDULLAH.

Nan muka kawo 'karshen wanan ďan takai taccen labari namu, ALLAH yabamu ladar abinda mukayi dai2, Wanda mukayi kuskure ALLAH ka yafe mana.
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment