Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta har da kukan su,kuma suka ba Fatima hakuri akan sukayi mata.



Tace babu komai kuma har da ita ta tayasu ba Daddy haƙuri amma yayi kamar bai san sunayi ba daga baya ma tashi yayi ya bar musu gida.





Abu kamar wasa ba irin magiyar da baayi ba Daddy ya maida Mumy amma yaƙi dan yanzu har da Hajiya Saa tayi masa magana amma yaƙi ko ya saurare ta inda akan maganar ne.




Itako Mumy ba wanda bata aiko masa ba amma yaƙi ya saurare shi ba irin magiyar da bata yi ba.





Fatima ce data Daddy bashida niyar maida Mumy dan haka itama ta bar masa gidan sa tace bazata dawo ba har sai ya maida Mumy ɗakin ta.




Dan yanzu Mumy abar tausayi ce dan yanzu idan ka ganta sai kayi mamaki sosai ta sauya dan a islimiya ta haɗu da ƙawaya masu ɗaura ta kan hanya sosai take jin dadin mu'amala dasu.




Ko da Fatima ta koma gida da ƙyar aka samu Daddy ya aminta zai maida ta amma da sharaɗi daya ga abunda bai yadda dashi ba zai kura ta.




Kuma ta yadda da abun da yace.



Ba aɗau lokaci ba Mumy ta koma amma yanzu ba gida ɗaya suke da Fatima ba,dan ita Mumy wancan gidan ta koma ita ko Fatima ya kata wani fantamemin gida da yagina mata da farko tace bata yadda da haka ba gwanda ya game su amma daga baya da yace inta aminta da haka zai maida Mumy inko bata yarda ba to sai da Mumy tayi tazama agida.




Da haka Fatima tabyadda ta zauna a wannan gidan.



Mumy ta dawo kamar wata malama dan Daddy har gwada ta yayi tayi har kawo mata yaran yake suna zomata lokaci-lokaci sosai Mumy take sasu ajikin ta dan yanzu Hasan da Husaini sun fin son zama wajan Mumy dan haka Fatima ta haɗe musu kayan su suka dawo nan da zama kuma idan ga gansu ayanzu zaka ce Mumy ce ta haifesu.




Abun Nabila yaƙi ƙarewa dan yanzu mijin ta aure zai ƙara Nabila tayi kuka har ta gaji.




Lokacin da suka je gidan Fatima suna fira har suka bata labarin abnda ake ciki sosai ta nuna rashin jin daɗin ta akan haka.





Shawara Fatima ta basu tace abari agwada na hausa ko Allah nasa adace ,sosai suka ji daɗin shawar ta.



Koda suka faɗa ma Mumy itama tayi na'am da haka Fatima ta shirya taje ita dasu wajan Malamin su na isilamiya ta faɗa masa abunda ake ciki.




Magani ya haɗama Nabila yace taje tayi affani dashi bayan kwana biyu ta dawo.



Haka akayi kafin ma tagama anfani da shi aljanin dake jinkin ta ya bayya na.
1/23/20, 11:50 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦









*ƘAWAR ƳATA CE*
*1441H/2020M.*
*RABI'U II/JAN.*



®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍?*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira}_



```🎐G•W•A🎐```
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE?*_





Story & Written
By
*SUMMY M NA'IGE*✍?



_Alhmdulillahi,Alhmdulillahi, hausawa sunka ce laihin daɗi ƙarewa, kamar yau ne anka fara labaringa na *ƘAWAR ƳATA CE* amma gashi yau ya ƙare, *LABARI* daya zo mana akan *MOMMY,FATIMA, da DADDY*..... wato har yau mata da yawa saboda *ZAFIN KISHI* sukan kasa yarda cewa shifa *AURE* lamari ne na ubangiji bana ɗan adam ba, abu ne wanda tini ubangiji ya rigada ya rubuta shi sai anyi, idan ya nufi mijinki da yayi to tabbas babu tsuminki babu dabararki sai anyi auren nan, mijinki na halin ƙari baki isa ki hanasa ba tinda Allah ya umarce dayi, mace tayi ta faman tada hankali tana shiga malamai ta maida kanta mushirika saboda kawai miji zai ƙara aure, ƙarshe duk abinda kika aikata ya zama a banza a wofi dan auren da ubanigiji ya shirya bashi da fashi, tsabagen son zuciya mace ta manta da faɗin ubangiji da yace yana yafe kowanne kuskure da bawansa ya aikata a garesa matsawar ya nemi gafararsa amma banda abu guda wato *SHIRKA* ,amma akan wata banza kishiyar da idan tazo ba zama zatayi akanki ba, ba ƙwace miki miji zatayi ba sai dai idan ke kika so, kije ki jefa kanki ga *HALAKA* kina aikata saɓon Allah kina *SHIRKA*, mai-makon mace ta kawai Allah kukanta wato ta dage da *ADU'A* shine kawai zai zamar mata mafita saboda babu wani abinda ya gagari adu'a wlh sai dai idan baki yi ba, ƙarshe kizo kina dana sanin da bashi da amfani saboda bazaki taɓa tashi ganewa ba sai lokaci ya ƙure maki, muna mantawa da mutuwa, muna mantawa da mutuwa,waya izubillah,duniya tana ruɗarmu mu mance da abu uku da suke *GASKIYA* muna mance faɗin Allah mu ɗauki huɗubar sheɗan, *ƘAWAYE* suyi mana banzar huɗu ba, *MUTUWA, ZAMAN ƘABARI da HISABI* sun zama dole amma *RUƊIN DUNIYA* da *SON ZUCIYA* suke mantar damu su, a banza ilimin da tinanin mata ya gushe, idan kin hana mijinki aure a nan duniya ai baki isa ki hana shi a *ALJANNAH* ba, gidan da za'a bashi *HURUL-EN*._


ga dai yanzu darasi mun ɗauka akan Mommy, duk yanda taso ta raba tsakanin Fatima da Daddy amma haƙarta taƙi cimma ruwa, hakan ya nuna mana kenan matsawar ba aikin ƙwarai kasa a gaba ba to hanya bata taɓa ɓulle maka indai akan na sharri ne,Allah yasa mu amfana da wannan faɗakarwar taki Sumayya.


Sumy Nah ina mai tayaki murna tare da farin cikin kammalla wannan *NAGARTACCEN* labari naki mai cike da ɗumbin *DARASI* tare da *FAƊAKARWA* na rayuwa, Allah ya baki ladan faɗakarwar da kika yi ya kuma yafe maki kuskuren da kika aikata aciki,sai mun sake jinki a sabon novel naki na gaba mai ƙayatarwa wanda zai nusar da al'umma zuwa ga amfana,muna godia sose da sose sakillahu biljanna,Allah ya raya zuri'a ya kuma ƙara danƙon ƙauna ga tsakani ga mai gida._




*MISS XERKS✍️.*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment