Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

labari, ki daina damun kanki ko dan cikin dake jikinki ma" rungume Ummi tayi ta ce "Ina kokarin yin hakan Amma Ummi bana iyawa" Ummi ta ce "Zaki iya Rafi'ah, just forget about Yusuf, ki manta da kin ta6a rayuwa dashi" kwanciya tayi liif a jikin Ummi tana sauke ajiyar zuciya. Karfe 8 Ammi ta karaso asibitin da warmers din abinci, sosai taji dadi ganin Rafi'ah nacin dan wakenta sosai, kunu ne dai bata wani sha ba, da azahar Mami ma sukazo ita da Sadeeq, minti 10 sukai suka koma gida, wajajejn karfe 2 su Umma dasu Anty Rahama suka iso, carton din maltina Umma tasa aka siyo aka ajiye musu. Kwanan Rafi'ah 3 a asibitin aka sallameta bayan an bata magunguna sabi, by now ta dan sake saboda kullum Ameera na zuwa asibiti ita da mamanta, anan take kara kwantar mata da hankali, Mami ma kullum sai tazo ta kawo abinci, haka Ammima itakam safe rana dare sai ta kawo abinci duk da hanata da Ummi take amma bata fasawa, kafin a sallameta 'yan uwa da abokan arziki su kaita zuwa dubata, Yusuf ya sha tsinuwa a gun Gwaggo ba kadan ba, motsi kadan saita tsine masa. Washegarin randa aka sallameta tana zaune a daki ita da Ameera, gaba daya ta damu dan Ameera sallama ke mata zata tafi zaria makaranta ta samu admission, Rafi'ah ta fashe da kuka ta ce "Zanyi missing dinki Ameera, Allah bazanji dadi ba" Ameera ta share mata idanta ta ce "Duk bayan sati biyu zan ringa zuwa, nidai kawai ki daina damuwa ki kula da kanki sosai" Rafi'ah ta kamo hannayenta ta ce "Insha Allah friend, Allah ya bada sa'a yasa ki fara a sa'a" Ameera ta ce "Ameen Fatima" duk jikinta sanyi yayi ganin yadda Rafi'ah ke share hawaye, jin hawaye na zuwa mata tayi saurin daga mata hannu ta fita a dakin, a corridor ta goge idanta sannan ta sakko downstairs, tayi wa Mummy da Ummi sallama, Ummi ta mata fatan alkhairi sannan ta bata leda me dauke da tirare da sleeping dress, da kyar ta kar6a sannan ta kara musu sallama ta tafi, Ummi ta kalli Mummy dake zaune ta ce "Anty bazaki koma gida ba, ai jikinta yayi sauki?" Mummy ta ce "Anjima zan tafi Zainab, Jawad ma yau zai dawo" Ummi ta ce "Allah ya dawo dashi lafiya", tashi Ummi tayi ta ce "Bana leka Rafi'ah ko zata ci abinci" Mummy ta ce "Ohk to" daga haka Ummi ta dauki warmer da plate ta haura sama.


_ALHAMDULILAH, anan na kawo karshen littafin *SHARIK HAYATI* part one, ina rokon Allah ya yafemin kuskuren danayi ya kuma bani ikon rubuta abinda shine dai dai_ 🙏🏻

_Special thanks to the members of my Groups, wallah u people are the best, ina sanku sosai da sosai 💞💞_ _And again my Kk 🥰 i luv u so much sweetheart, u are always supporting me right from the beginning, billahil azeem ina sanki Dije ta, my Jiddah soyayyarki is endless_ 😍, _AISHA SHEHU can't forget with u sister, Fatima is thanking u again and again Allah ya raya Na'eem ya bashi ilimi me inganci_ 😇, _Then my FANS 😇 Billah ina sanku a duk inda kuke sisters, only God knows how much i luv u people, ina muku fatan alkhairi duniya fil akhirah 😘_ .

_08103810398_
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment