Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels A*JININMU DAYA* NA SADIYA IBRAHIM KHALI 1 Godiya Ga Allah(SWT) tsira da aminci sukara tabbata ga Annabi Muhammad(SAW) Godiya har kullum ga mahaifana da 'yan uwana Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi *SADAUKARWA* *Sadaukarwa ga Alhaji Ibrahim Khalil family* *Da 'Danbakane Family* *GARGA'DI* Ban yarda wata ko wani su yi anfani da wani shafi ko littafin gaba daya saida izinina 08144665937 *TUNATARWA* Banyi wannan littafin don cin zarafin wani ko wata ba ta hanyar anfani da suna ko garuruwan dake cikin littafin ba duk wanda littafin yaci karo da rayuwar wata ko wani yayi hakuri arashi ne bawai da sani bane duk kuskuren da nayi a littafin ga wani ko wata bisa rashin sani ya femin domin dan Adam ajizine ina rokon Allah ya femin duk kuskeren da zansamu a rubutun nan *SHINFI'DA* *Kaddara bata taba sauyawa da mizanin rubutun ta saidai addu'a takan jawo zuwanta da sauki 'dan uwa komai yadda abubuwa suka ta'azzara ga juna ba'a canzashi zaka iya canza komai amma banda 'dan uwa karka zamo mai rabon kawunansu 'yan uwa komai tsanani domin shi dan uwa tamkar kashin baya yake duk sanda ka rasa sa to tambar wannan kashin bayannaka ya karye kayi afuwa da rangwame da kyautatawa ga duk yan uwanka ka nufesu da alkhairi domin shi dan kone baya faduwa kasa banza babu riba ga duk wanda yakasa hakuri da dan uwanshi domin karshe danasani zaiyi mara yankewa hakama iyaye sa babu wani mai canza wannan sunan gareku ga 'ya'yanku karkai tsinuwa karka la'ancesa domin dai sunan dai bazai canzama ka haifeshi karkayi fushin da zai jawo rusa kaunar dake tsakaninka da ya'yayennaka domin uwa da uba sune bangon da muma muyi kokarin gyara biyayya ga iyayenmu komai tsanani muddin ba akan sabon Allah sukesan muyi biyayya garesu ba domin sudai iyaye koda daga haifarmu suka yardamu ba abin wulakantawa bane kuma shi kanshi lokacin sakaraine munaji muna gani zaizo yawucemu batareda mun aikata dai-daiba a cikin lokacinmu Kaddara kuma ba abinda bata sauyawa* *TAURARI* *ABDUL-RA'UF* *RUFAIDA* *FARKON LABARI* A nutse ta iso falon ta tsaya bayan kujerar da matashin da zai haura shekaru 33 da yake zaune wani yaro a cinyarsa yana shafa kanshi matashiyar bazata haura shekaru 22 zuwa da 23 ba sai da yaji numfashi a bayansa yasa ya maida dubensa kacokam ga bayan kujerar a tsaye ya sameta ta harde hannayenta tana murmushi ya dan sauke ajiyar zuciya yace Rufaida na lura dai sam yau tsokanata kike ji Rufaida tace bahaka bane Yaya Wahid ya dan juyar dakai yace to ya akai tace dama naga yau kurum ta Yasir kake ni ko kulani ma bakayi Wahid yace to meye damuwar Yasir dai dan kine banasan rigima dawo nan kizauna ya nunamata kujerar da suke ta zauna kusa da yasir tana mai ambatar Bismillah Yasir Ya dan dubi fuskar Rufaida yace Mami kinji Dad sai je Zaria kuma ba zashi daniba Rufaida ta Kalli Ahad tace kaji Dad kurum ka bari wani satin sai mutafi mu duka ya dan marairaice yace Mami kinsan kiran Umma ne gwara na naje wani satin saina kaiku tunda ba kwana zanyi ba tace haba Yaya yaza'ai ka tafi yau ka dawo yau yaushema harkabar Abujar yace ai bawai a motar haya zaniba zan iya kaiwa har na juyo ni narasa Kiranma Umma takemin Rufaida tace ni fatana ma dai har kullum Allah yasa lafiya kalau nima kiran na kasa gano dalilinshi yace to Allah yasa lafiya Rufaida sam bazata iya furtawa mijinta tasan dalilin kiranba da mahaifiyarshi ke masaba don batun yau ba tasan komai tunma kafin aurensu shima Wahid bayajin zai iya furtawa Rufaida dalilin kiran dukda ya tabbatar Rufaida mai hakuri ce sai dai bayasan wani abu yasa zuciyar kuncin da bazata iya furta komai akaiba amma shi bayasan ace daga aurensu ya kara wani auren dukda suna da daya amma duka Yasir nawa yake baikai uku ba har yau to kuma suna zaune lafiya da matarshi meye dalilin kara auren Ruqayya da Umma takeso tayi don baya tunanin zasu zauna lafiya yaji ma da matsalolin aiki kuma yadawo gida ya tarar da wani shiyasa bai fadawa Abba zuwan ba dan yasan ba zai amincemasa yazoba shikuma yanason mahaifiyarsa yaje gareta ya mata magana yadda zata fahimcesa kota samu ta barsa da wannan zancen shi dai har ga Allah baya yiwa Rukayya irin son aure ta kasance abokiyar rayuwarsa sai dai sona zumunci tunda yasan Rufaida tasan komai shiyasa bayason jagwalgwala maganar danshi mutum ne da bayason a dinga tada abin bacin rai,Jin shirun da Wahid yayi yasa Rufaida cewa Yaya koka FASA tafiyar ne lokaci fa baya jira cikin sauri ya dawo daga tunaninsa,yace ai kema kinsan sai an amsa kiran Umma yau Insha Allah,fitowa sukayi shida Rufaida da Yasir har bakin motarsa suka kaishi yace har zai tadane Rufaida tace Yaya Wahid namanta fa zuwanmu gidan Luba yace au nashafa'a jeki ki shirya tace ai Yaya na shirya bara na rufo ciki murmushi yayi yace to suna tsaye da Yasir ta karaso ta shige gidan gaba Yasir yana baya Wahid yana zolayar Rufaida da cewa da ya tafi sai dai tahau taxi murmushi tayi tace ai kudinka ne zai kuka a bakin gate ya tsaya masu gadin Barrack din ya tsaida motar suka gaisa suna yallabai sai ina yace Zariya zanje amma su a gidan abokina Kabir zan saukesu addu'ah suka yimusu kana ya fice daga barrack din 'yan sandan na cikin garin abuja Area1 a Gwarinfa ya saukesu Rufaida har gidan Kabir ya shiga suka gaggaisa da Luba tana baya shigowa sai dai taji firarsu a sitroom yace kusan bana zuwan banzane kinsan shine dalili Rufaida tace ayimasa hakuri zai gyara Yusuf dan Luba yana ganin Yasir suka fice harabar gidan sunata fara wasa,Yace Luba ina abokin nawane yace wallahi ya fita shida Nazir amma bazasu jima ba yace ai ki kyalesa kawai ni tafiya zanyi zanje Zariya zamuyi waya idan naje,bai jira komai ba ya mike Luba tamasa addu'a Allah ya kiyaye hanya yace Amin ya fice daga Falon Rufaida ce tabisa tana masa addu'a sannan tace ya gaida kowa da kowa harda su Gwaggo da Malam da Abba yace aiko da wuya naje gidansu Gwaggo cikin bata fuska tace maiyasa yace saboda kinsan ba kwana zanyi ba tace shikenan amma dai ka daure kaje yace to ranki ya Dade abinda kikace shi za'ayi murmushi tayi tace ko kaifa Yasir ya karaso gurin Babannasa shida Yusuf suna cewa Dad Allah ya tsare Rufaida ma cewa tayi Allah ya tsare Allah ya dawo dakai lafiya a gaida kowa da kowa Wahid ya amsa da amin yana murmushi yaja motar ya fice daga gidan sai da yafita da motar Yasir ya dawo gun Rufaida yana kuka babansa ya ki tafiya dashi Rufaida ce ta shiga lallashin yasir din tana cewa idan baka daina ba Yusuf zai yima dariya ka ganshi can yana kallonka Yusuf can gurin wasa Yasir din ne ya tafi gurin Yusuf din Rufaida murmushi tayi tace kawai ta shige ciki Luba ta kalli Rufaida tace sai yanzu kika barshi ya tafi kenan,Rufaida murmushi tayi tace kai Luba banda sharri yaushe ma muka fita,ni cikina ya fara kiran ciroma goma ta wuce na safe bikinsan mai zaki dafa ba kin daka ta wannan chat din gaskiya Yaya Kabir yana hakuri ace mace bazata gama girki ba sai wajen 4 na yamma Luba tace to hadasu kasa rabasu duka sau nawa kika zo gidan nawa kika tarar bangama abinci ba da wuri wannan chat dinma saikisa a hana mutane Rufaida tace dama yafi Luba tace da kema nasa an hanaki baki Rufaida ta ta'be tace ni kinsan baidame ni ba,Luba tacanza zancen da cewa mutumin kifa yau zanyi Rufaida tace alala gaskiya ki tashi mu dora tun yanzu haka suka mike suka shiga kitchen Bugun Zuciyar Rufaida ne ya karu dole ta bar kitchen din taje falo ta kwanta hakanan yanzu take jin bugun zuciyar batasan daliliba anbatan Allah ta fara yi a cikin zuciyarta,wayarta ta lalubo ta danna tasa a kunne,a daya bangaren murmushi Ahad yayi ganin sunan mai kiran My wife ya daga ya gabatar da sallama ta amsa tana cewa Yaya Ya hanya yace Alhamdulillah nakusa zuwa Kaduna wayar ta ka tse tana masa addu'ar Allah ykiyaye hanya yayi murmushi yana kara jin kaunar matarsa a ransa da haka ya cigaba da tukinsa Wahid bayan barinsa cikin Kaduna yana gaf da shiga Zariya,duk yadda yaso kaucewa motar sai da tazo ta bugi da motarsa nan motar tasa ta dinga mirginawa yanata salati motar man da tayi gefe ta kama da wuta abinka da cikin jama'a yasa dan dan nan gurin ya cika AbdulWahid ake kokarin ceto aka tsaida motar da ta fara shigewa rami kuma mai zurfi dakyar aka fiddoshi daga cikin motar jini yayi kaca kaca da jikinsa bazaka taba shaida cewa wannan fuskar AbdulWahid ne matashi mai kuruciya kyakkyawa lallai duniya ba abakin komai take ba,wayar dake cikin motar da duk ta ragargace police suka dauko suka aka saka sim din a wayar wani daga cikin yan sandan bayan anyi kokarin sasa a motar police din aka bar wasu suna bincika motar tasa nan aka fara kokarin kiran danginsa amma yawanci duk bata shiga ta Rufaida ce kawai ba'a kira ba A abuja Rufaida lafiyarki kalau kuwa kin kasa cin alalan nan kuma bayan nasan kinasan alala Luba ta fada tana dafata damai da fuskarta ga Rufaidan Rufaida tace wallahi Luba wayar Yaya Wahid nake takira naji ko yaje zariyan to da tana shiga baya dagawa yanzu kuma taki shiga gaba daya kuma nasan yaya Ahad baya kin daga wayar Luba tace ki sake kira kiji to yanzu,wayar Rufaidan ta dauka tasake kiran sa anan tayi sa'ata shiga daya daga cikin dan sandan da yake a farfajiyar General hospital na Zaria din ya dubi abokin aikinsa yace yallabai ana kira wancen mai hatsarin naga an rubuta My wife yace,daga kila matarsa ce tunda an kira iyayennasa basu daga ba da ya rubuta hakan da sallama dan sandan ya amsa wayar jin bashine ya amsa wayarba nan Rufaida bugun zuciyarta ya karu dan sandan yace wacece ke a gurinsa tace matarsa dan danan dan sandan ya katse wayar zuciyarsa a raunane domin bazai iya fadama Rufaidan halin da mijinta yake cikiba nan Luba ta kalli Rufaida tace ya akeyi Rufaida tace cikin karayar zuciya tace Luba bana tunanin Yaya lafiyarsa kalau kuwa nan ta labartawa Luba abinda ya faru a wayar da sukayi Luba tace bara na kira baba yusuf nafadamasa ki kwantar da hankalinki ita dai to tace kawai kira daya Luba tayiwa Kabir ya daga yace yana kofar shigowa falon bata aje wayarba ya shigo falon yana riqe da hannunsu Yusuf da Yasir gurin mamarsa ya nufa ya kwanta a cinyarta Rufaida batasan sanda hawaye ya zubo mata ba ta fashe da kuka tana shafa kan Yasir Kabir ya kalli Luba yace Wife mai aka yima Rufaidan ta dan dubesa tace Wallahi abokin nakane Baban Yasir ake ta kiransa yaqi dagawa karshe ma wanine ya daga Kabir yace haba to shine abin kukan bari na kirasa naji yanzu namaga missed call dinsa badamar na daga ina tuki wayar tasa yasa a kunne maganar da yaji anfadamasa a wayar ita ta girgizasa ya dan saki murmushi bayan gama wayar yace,to meye abin damuwar ki shirya yanzu m tafi gidanku ashe aprilfun ya miki ko zariyanma baije ba ita dai Rufaida cikin kasala ta mike tana tunani kala kala to ita tunda take da AbdulWahid baitaba mata wani April fun ba bare kuma yau yayi mata yanzu asalima shi bayasan wannan April fun din tunda ba shi a musulunci shiru tayi ta mike tasa hijibinta tace ta shirya Kabir yace kema wife kije ki dauko hijabinki tace Abban Yusuf kaje kaci abinci mana kafin mu tafi yace kibarshi ni na koshi munje shoprite da Nazir,Luba dai ba tace komai ba dan tasan mijinta baya cin abinci ako ina ba sai gida Hanyar Zaria ya nufa dasu ya hada rai domin karsu tanbayesa ma Rufaida kuwa kukan zuci kawai takeyi dan tariga data yanke tsammani Wani dattijone da zaiyi shekara sittin ne ya shigo babban falon gidan da waya a hannunsa yanasa sallama duk atare suka amsa masa kallon mutanan daake falon yayi kowa yana harkokin gabansa wasu suna kwance wasu suna kallon tashar sunnahTv din da ake karatun alqur'ani wasu suna bin karatun wasu sunacin abinci babu wanda yake surutu dai saboda karatun ina Hajiya Jamila batakai ga cewa gani ba yace lafiyar AbdulWahid kuwa tun dazu yaketa kirana kinsan muna meeting banma shiga da wayarba na barta tana caji a mota sai yanzu dana shigo gida na dauko wayar na duba nagani hajiya jamila tace,ai ina tunanin yau zaizo shine dalilin kiran nima ta yiyu ya kirani nasata a caji wayartawa,dattijon yace bara to na kirasa naji kiran yayi yawa wajen 10 da kira wannan dan sandan ya daga nan ya labartawa masa komi cikin rashin kwarin gwiwa Abba ya katse wayar daya daga cikin matasan yace Abba mai ya faru Abban bai sauraresa ba yace k sameni a waje yayi kofar fita matashin maisuna Abdulmalik da shima ya kidime dan shima ankirasa amma bai daga ba tana dakinsu shikuma yana falo,Hajiya Jamila babu ko mayafi ta fito don ta tabbatar ba lafiya batasan mummunan labarin da zaizo mata ba,Hajiya Kubra ce tayi kokarin mikomata hijabin jikinta Abdulmalik ne yaja ya kaisu asibiti tundaganan Hajiya Jamila ta fara salati tana shikenan na rasa dana motar da Abba yace yaja Emergency da aka kwantar da AbdulWahid suna isa dakin da aka kwantar dashi aka kaisu da taimakon yan sandan da Abba ya kara kiransu babu wanda zaiso kara kalan AbdulAhad rai yana hannun Allah sau daya Abba ya kallesa,Hajiya Jamila kuwa jikinsa ta fada tana kuka mai sauti Abdulmalik ne ya janyeta yayi waje da ita yana lallabata akan zai tashi cuta ba mutuwa bace,Abba shikansa dauriya yake ya kara ga dan nasa mafi kyautatamasa duk a cikin yaran nasa, hannunsa ya kama ya maida dubensa ga fuskar dan nasa yana cewa AbdulAhad kayi addu'a zaka tashi da izinin Allah kaidai ka riqa salati da kalmarshahada yana jin bakinsa alamun magana amma bayaji yaji dai motsi inda ya sa kunnensa a saitin bakin AbdulWahid din yaji dai yana Rufaida Abba,daganan baisake jin komaiba sai motsin da bakinshi yake Abba yana nanatamasa Kalmar Shahada yana ganidai yana motsa bakinsa baisan maizai ceba yadai fi tunanin kalmarshahadar da yake shima yanayi ganin bakin AbduWahid ya daina motsi shine ya tabbatar da cewa AbdulWahid ya rigamu gidan gaskiya dukkan mai rai mamacine koda rasuwar tazo wa kunnen hajiya Jamila sumewa tayi a take anan,saida aka bata taimakon gaggawa ta hanyar fesamata ruwa Abdulmalik gawar dan uwansa ya kama yana kuka shima mai tsuma zuciya,yayi babban rashin da zai wuya yasamu irinsa tun suna yara AbdulWahid yana hakuri da abinsa yabawa Abdulmalik,anan aka gama komai akabasu gawarshi Isarsu cikin asibitin Zariya yayi dai-dai da fitowa da gawar AbdulWahid a motar asibitin ganin motar Abba Bukar na binsu a baya yasa Kabir fasa shiga asibitin don sosai Kabir yasan mortar Abba Bukar kuma yasan Abba Bukar din,dauriya kawai yake yana bin motar har zuwa gidansu AbdulWahid unguwar su dake sabongari Zariya sautin kukan Rufaidah ne ta cika motar domin ta riga ta sadakar da cewa AbdulAhad yayenta yayi tafiya mai nisan da babu waiwaye bayan tafiyar,Yasir ma kukan yake ya makale cinyar mamarsa Luba ma zuciyarta ta karaya itama kukan ta fara Kabir shi kansa kukan yake shirin yi sai dai yakasa yi kukan zuci kawai yake tabbas yasan yarasa aminin aboki shine kadai yake fadawa damuwarsa ya samu sauki bayan iyayensa AbdulWahid mutumin kirki ne yaso ace yazo ya samesa bai rasu ba da zai iya sadaukar da komai don ya rayu muddin zai iya sai dai ina mutuwa bata shawara kuma Idan anyi ba'a dawowa baisan ya karaso gate din gidanba don tukin kawai yake ba tareda yana gane komaiba saida yaji karar bude gate ya tabbatar sunzo Rufaida bata jira yagama parking ba ta fito a lokacin da mutane ke kokarin fito da gawar AbdulWahid daga mota jikin gawar ta ruga ta fada da take haryau da jini tana kuka din tana Ku ajemin miji wallahi bashine ya mutuwa karya ake Ku aje shi mijina bai mutuba yaye fuskarsa tayi shima Yasir da yake abayanta jikin gawar babannasa ya fada da aka a jiyeta a harabar gidan basu kara jin motsinta ba sai kukan Yasir inda Hajiya Kubra tazo tajanyeta amma bata ko motsi anan ta zube ta yi kasa luu alamun suma tayi Yasir kuwa Kabir ne ya janyesa shima Kabir din kukan yake Cikin kankanin lokaci labarin mutuwar AbdulWahid Bukar Bukar (ABB) ya fara zuwa kunnuwan 'yan uwa da abokan arziki da 'yan Unguwa abokansa na cikin unguwa,sukaji mutuwar AbdulWahid din sosai,matashi mai son jama'a bai da abokin fada lallai duniya ba'a bakin komai take ba wanda yayi damara dan ita ya kwance,daganan mutane suka fara tururuwar zuwa jana'iza Wannan zuriyar tabbas sunyi babban rashi kowa kagani a gidan kuka yake wasu idonsu yayi ja jawur a haka aka shirya AbduWahid Hajiya Jamila kasa addu'a tayi bayan gama shiryasa sai kuka itako Rufaidah haryau bata farfadoba sai wasu daga cikin kannensa mata da yan uwansa ne sukayi suma suna kuka suna addu'ar koda aka budesa fuskarsa kai kace zaiyi magana da murmushi akan fuskarsa sai dai har yau jinin dake fitowa a jikinsa bai daina zuba ba daga gefen fuskarsa yake zubowa ba,dukda yadda aka wanke gurin, da haka daukesa aka masa sallah yayi jama'a sosai nan aka dawo aka dan Zauna daga baya duk aka watse domin ka'idar Abba Bukar bayasan wannan zaman na gulma abarsuma da rashin da sukayi yaron sa yataso da son kyautatamusu amma Allah ya karbi abinsa dukda dai akwai wasu yaran amma dai bakamar AbdulWahid din a cikinsu. [4/27, 11:49 PM] Sadiya IB Khali*JININMU 'DAYA* NA Sadiya Ibrahim Khali 2 Ido Rufaidah ta fara bu'dewa a hankali ta saukesu ga mutanan dake cikin falon da take ganin mutanan bishi bishi ta dau tsawan mintina a haka kafin mutanan falon su ankara da yanayinta alamar ta fara farkowa daga doguwar sumar da tadau lokaci bata farko ba tun karfe biyu har yanzu da duhun yamma yayi Gaba daya suka fara yi mata sannu muryoyinsu ne suka fara yi mata amo a kunnenta cikin rashin tsammani wannan yasake tabbatar mata mutuwar AbdulWahid mijinta gaskiya ce idanunta tasake budewa tangaram ta maida dubenta ga Umminta da Gwaggonta da Momynsu sai kuma Luba da Yusuf kekan jinyarta tana jijjigasa dukkansu babu cikakkiyar walwala a fuskarsu Rufaida da sabon kukan da ta fara ya ruda mutanan dake dakin tuni zuciyar Hauwa wato Umminta ya kara tashi wanda dama tun bayyana musu mutuwar AbdulWahid hankalinta yake a tashe har sukazo Zariya da hankalin nata ya sake tsanantar tashi ganin 'diyarta ta Rufaida a cikin mawuyacin hali da yanzu hakan zuciyarta ta karaya na tausayin 'yar ta kuka itama ta fara cikinsu aka rasa mai lallashin 'dan uwansa Gwaggo ce take kokarin lallashinsu tana ban baki tana cewa duk fa wanda ya mutu baya dawowa kuma duk mai rai hakika mamaci ne muma lokaci kowannenmu yake jira hakuri zakuyi da yi masa addu'a halinsa na gari ya bisa danshi AbdulWahid tashi tayi kyau da izinin Allah,da wa'dannan kalaman ta cigaba da lallashinsu har ta fara janyo hankulansu,da haka tasamu kansu hatta Rufaidan shiru ne tayi sai hawayen dake bin kuncinta tanamai sake tuno rabuwarta da mijinta da hirarsu ta karshe yanzu shikenan mutuwa ta yanke kauna itada mijinnata yayi tafiya mai nisan da babu waiwaye tafiyar ta kasance a bigiren da ba'a dawowa har abada ba'a dawowa mutuwa kenan mai yanke buri wani irin hawaye masu dumi suka cigaba da zubo mata lalle mai rai ba a bakin komai yake ba duk wanda yamanta da wannan ranar saidai yayi maza ya koma ga Allah domin yau dai ga wannan bawan Allahn ya tafi ba tareda yasan yau zai mutu ba mutuwa kenan da bata kwankwasa kofa kome kake idan tazo haka zata daukeka Allah yasa idan ta mu tazo mu cika da kyau da imani Bangaren Hajiya Jamila Yasir dake zaune a falo ya takure a tsakanin kujera inda yake kallon Hajiya Jamila da mutane guda biyu dasuke kanne a gareta Kaltume da Haulatu da 'daya take aure a Kaduna daya kuma a makarfi hira suke Hajiya Jamila tana basu labarin yadda taga fuskar dan nata kafin rai yayi halinsa kai baza kace Hajiya Jamila bace da dazu take kururuwar mutuwar amma cikin awannin da busu kai ga kwana ba harta mance tafara bada Labarin mutuwarsa itada 'yan uwanta kuma a gaban karamin yaro,Kaltume ce da itama Umma take cewa Hajiya Jamila a matsayinsu duk ita ta rikesu harta aurar dasu,ni yaron nan bansan kukan da yake ba yabarmu muji da mutuwar da akayi mana yaki,Hajiya Jamila tace yaron da aka cusa masa kiyayyarmu taya zai daina Hajiya Jamila ta fashe da kuka,Haulatu ta miqe tayi kansa taja hannunsa da karfi ta cankadasa kofar da zai sadaka da dakunan gidan Hajiya Kubra da take kokarin fitowa ta zauna falon saboda masu zuwa gaisuwa makofta nan Yasir ya fado jikinta,Hajiya Kubra ta kalli haulatu tace Haulatu mai yayi zafi har haka,sai kace ba jikanku ba kuma maraya Zaki cankadosa yanzu da Allah bai kawoni ba kila har fasa baki zaiyi idan da tsautsayi,Kaltume dake zaune tace Mama sunan da suke fadawa Hajiya Kubra ta cigaba da cewa yaron da mahaifiyarsa da kakanninsa suka cusa masa kiyayyarmu a ransa,Hajiya Kubra tace yanzu dai komai yawuce wanda ake abun danshi yau ina yike bayanan,yanzu cigaba da maganar nan dawo da bara bana ne da jawo Bacin rai yanzu muji da mutuwar da akaimana babu ko daya daga cikinsu da tari ya sille masa saboda koba komai dai mutuwar su akayiwa amma zuciyar ko wannensu da tunanin da yake akan matakin da zasu dauka dan ita bangaren zuciyar Hajiya Jamila yadda zatayi ta fitarda su Rufaida daga rayuwarsu take dukda ga mai hadawa nan Yasir ya riga ya hadasu wanda ko ya mutu acewarta ya mutu ta rayayyun 'ya'yanta take a yanzu domin badan yadda taga gawar AbdulWahid ba to da hankalinta bazai tashi har yasa ta kasa maida raddi ba gurin Hajiya Kubra Hajiya Jamila macace mai matukar son duniya shiyasa ma mutuwar dan nata baisa ta rage kudure kuduren duniya ba da take yi kuma babu daya kwakkwara na gari da za'ace Hannun Yasir Hajiya Kubra ta kama zuwa cikin gidan tana lallashinsa har dakin dasu Rufaida ke ciki ta kaisa inda yana zuwa ya fada jikin Rufaida uwa a garesa yana kuka itama Rufaida hawaye take sai dai bata bari ya gane ba ta cigaba da jijjigasa har barci ya daukesa,nan Hajiya Kubra ta cigaba da yimata nasiha a haka ta fice daga dakin tana goge kwallar tausayin yarinya karama Rufaida gashi ta zama bazawarar da yau Allah ya dauke mata mijinta da yabarta da da da yanzu yazama maraya dukda bazaman farin ciki tayi da mijin nata ba to ina sirikar tabarta tayi haka amma hakan baisa yarinyar korafi ba daidai da rana daya ba hakuri gareta mai yawa dukda wannan abun da yafaru wanda ake danshi baya duniyar baisa kiyayyar da Hajiya Jamila kewa su Rufaida raguwa ba batare da Hajiya Kubra tasan laifi 'daya kwakkwara ba dayaja hakan ba rayuwar dama haka ta gada wasu kome zakamusu bazasu kaunaceka ba Abba Bukar da yake zaune gefen gado wajen karfe tara na dare da haske ya gauraye 'dakin na lantarki Hajiya Kubra ta shigo 'dakin dauke da sallama da Flask riqe a hannunta Abba Bukar ya 'dago fuskarsa da take cikin damuwa ya amsa mata kafin ya maida kansa ga inda yake kallo a kan lokar jikin gadon 'dakin Hajiya Kubra ta zauna ta fara magana cikin sanyin murya da cewa"Abba dukkan mai rai mamacine AbdulWahid ya tafi inda ba'a dawowa damuwar bazata dawo dashi ba Addu'a ce yakamata mudinga yi masa" Kai Abba Bukar ya 'daga alamun ya gamsu da abinda Hajiya Kubra ta fa'da kafin yace" Kubra mutuwar yaron ce tazo shiba ciwo yayi ba rana tsaka yayi hatsarin motar nan ni koma a waya bai fadamin zaizo ba ashe ajali ne yakirasa,gashi kaf cikin yarana babu wanda kai tsaye zakace yabar abu ya bari kai tsaye inbashi ba gashi da kokarin kyautata mana dason yan uwansa"Abba Bukar ya karasa maganar yana zubda hawaye lalle duk abinda zaisa Abba Bukar koda hawayene babban abune tabbas duk abinda Abba Bukar yafada gaskiya ne saidai kuma ya za'ayi wanda yafimu sanshi a amshi abinsa,Hajiya Kubra ke wannan tunanin a cikin ranta Hakuri ta cigaba da basa kafin yace su Haulatu mungaisa sunyimin gaisuwa dazu kuma abin shirmen anan da mazajensu da suka kirani a waya yimin gaisuwa suka fadamin cewa sai anyi bakwai zasu koma saida ma na dinga fada tunda wanda ya mutu bazaidawo ba,amma ko wacce tabaro yaranta ta taho,kuma suda ba jin magana suke ba kafin su koma sai sun hargitsamin gida najima da halin yar uwartasu danike aure wannan ai shirmene da anyi uku duk kowa zai koma gidansa Hajiya Kubra hakuri ta shiga basa Washe gari da wuri Kabir ya shirya zasu koma Abuja shida matarsa sai ana gobe addu'ar uku zasu dawo su kwana ayi addu'a su taho inda Luba zata tahowa Rufaida wasu daga cikin kayan sawarta Yasir ganin Kabir zai tafi yafara cewa Kawu akaini Dady na kukan da Kabir yake maqalewa yafarayi inda tun a falon da yaje musu sallama zuciyarsa ta karye da ya tuna cewa shida AbdulWahid suka saba zuwa muddin wani dalilin yakawosu Kaduna sai sun karaso Zariya kai kobama haka ba gidansu AbdulWahid kamar gidansu Kabir ne tun sanda suka hadu a jami'ar Ahmadu Bello University shiyasa yake tuno falon gidan dakoda yaushe zuri'ar gidan suke zaune a ciki bazaka rasa koda mutum daya ba a kowacce rana ta duniya ba barema zaman ake da yawa ana hira cikin so da kauna harda Abba Bukar uba garesu hakama idan sun biyo da Kaduna a wannan falon zasu zauna aita fira cikin raha da wasa da dariya da girmama juna yau ga yadda abun yakasance gasu a falon amma babu jigon da yayi sanadiyyar sanin wannan a halin da yayi yau yanacan a wani bigiren na daban da muma jiranta muke wannan bigiren na mutuwa da kowa jiran lokaci yake Kabir da harya Shiva mota amma yanajin sautin kukan Yasir nan Abba Bukar da kansa yasa Yasir a mota su tafi tare da shi Koda Labarin mutuwar yazowa gurin aikinsa sunji mutuwar sosai dan AbdulWahid mutumin kirkine yasamu shaida mota sukayi washe gari suka nufo Zariya suda wasu 'yan sandan da suke a cikin barraq din nasu buhun shinkafa katan din taliya couscous da kudi masu yawa suka kawo musu a riqa dafawa wani babba a cikin su nauyin karatun Yasir ya dauka da za'a bashi yaron da yafi kowa son hakan domin duk abinda zaiwa AbdulWahid bazai biyasa shi abinda ya masa ba sanda ya shiga matsala ya taimakamasa sosai sun nuna halalci sosai abokan aikin nasa sosai koda Kabir yakoma abokansa da suke aiki tare haka suka riqa yimasa ta'aziyya kwanansu daya su Kabir suka juyo saida aka lallashi Yasir cewa Abbansa yatafi wani aiki sai yayi girmaan za'a kaishi gurinsa da haka aka samu yafara hakura sai dai jefi jefi idan yana rigima ya riqa maganar mahaifin nas_JININMU DAYA_ (Labari mai dauke da son zuciya) Na Sadiya Ibrahim Khali 3 _A ranar da akayi ukun AbdulWahid ranar Abba Bukar yacewa su Haulatu kowacce tabi mjinta takoma saboda ya fahimci ganin cigaba da zaman nasu zai iya kawo hargitsi,koda Hajiya Jamila taji haka abinda Abba Bukar yace bata tada wata fitinar ba dan a yanzu ne mutuwar 'dan nata take dokarta don tafara zubar da makaman aiki saidai bata zubar dana 'kiyayyar da takewa Rufaida ba har yau kai bama ga ita ba harga jininta kiyayyar ta shafesa,wadda dama 'kiyayyar tadade da wanzuwa,_ _A ranar ukun ne yan uwa da abokan arziki suka zowa Hajiya Jamila gaisuwa daga mahaifarta Nasarawa Lafiya ciki ko harda Ruqayya da a ganinta tafi kowa jin mutuwar AbdulAhad sunzo da niyyar suyi kwana daya su juya dalili mai 'karfi da yakarasa su Kaltume da Haulatu jin haushin tafiyar tasu su da sukaso suyi fira da 'yan uwansu yau amma ga yadda Abba yace banda suna ganin girman Abba da bazasu tafi ba,sai dai matsayin da yake a gurinsu na mahaifi da tunda iyayensu suka rasu suka dawo hannunsa harya aurar dasu bazasu iya ja da maganarsa saboda koba wannan Abba Bukar ba kalar wanda za'ayiwa wargi bane da haka kowacce ta hada kayanta tabi mijinta nata_ _*Abangaren Rufaida*_ _Nasihar da Abbanta Aliyu yake mata sosai take shigarta hawaye take zubarwa daga idanunta dake cikin hijabi,inda shi bai lura ba,dukda shi a karan kansa nasihar yake amma tausayin 'yarsa yana mamaye a zuciyarsa haka ya mike daga 'daya daga cikin kujerun falon 'dakin dasu Rufaidan suke ciki tundaga mutuwar yana yi mata sallama da kyar batare da ta dago kaiba ta iya ma Abbannata addu'a wadda nasihar Abbannata jinta kawai take bata fahimtar komai dan yau mutuwar sabuwa tadawo mata fil gashi yanzu haka kowa watsewa zaiyi a barta cikin tsangwamar da tasan zata riska gurin surikarta akan abinda ba tada masaniya,Da haka Umminta Hauwa'u da Momynta Hajiya Maryam suka fito daga Bedroom din falon da jakunkunasu a hannu kowaccensu fuska babu walwala dasu ma tafiyar zasuyi nan Hajiya Maryam ta kama hannun Rufaida ta 'dago fuskarta ta fara kokarin share mata hawaye kafin tayi mata nasihar itama da haka suka fice suna yi mata Sallama saboda shi kansa Aliyu su yake jira su kama hanyar Kano kodan su isa koda da la'asar ne da haka su Luba da Gwaggo suka fito yi musu rakiya da itama Luba anjima zasu tafi itada Kabir bandama yaje gurin wani abokinsa inda ya tafi da Yasir da Yusuf toda tuni ma sunkusa Abuja Gwaggo kuwa da take a gari sai magriba Abdulmalik zai maida ita gida dukda yadda Abba Bukar yaso Gwaggo ta zauna har Rufaida tafita takaba amma kiri kiri taki amincewa sai dai ta rika zuwa akai akai duba ta_ _Karfe tara na dare gaba daya dakin yayi shiru daga ita Rufaida sai Yasir da yagama rigima yayi barci saiko karar sunnah TV da take sauraron wa'azi saiko wayarta dake gefe da sai yau Luba ta bata da ta kira su Umminta da Momynta Hajiya Maryam sun sauka lafiya nan ummin nata Hauwa'u ta dora da yimata nasiha Luba ma ta kira ta sunje gida lafiya sai kuma kiran kawaye da abokan arziki da 'yan uwa da sukaji mutuwar basu sami damar zuwa ba da take amsawa ganin Number 'din Samiha a screen 'din wayar da take ta gwada number 'din Rufaida tun bayan gaisuwar da tamata a wayar momynsu Maryam da bawani damar yi mata ta'aziyya tasamu ba,sai yau da number din ta kira ta samu ta shiga, ita kanta Samiha taji mutuwar kamar itace mijinta ya rasu dan yadda ta dauki Rufaida a zuciyarta ba abin akwatanta bane badan busu jima da komawaba da saita zo yi mata gaisuwa,da haka Rufaida ta 'daga wayar da muryarta me cike da rauni tayi sallama da kadan ya rage tayi kuka Samiharce ta amsa ta kuma kara yi mata ta'aziyya da cewa "Rufaida Wanda duk ya mutu baya dawowa yanzu Yaya Ahad addu'arki tafi bu'kata damuwa bata maye gurbin komai sai sawa zuciya ciwo domin duk abinda ka rasa bazai dawo ba addu'a itace mafita akan komai" da haka ta cigaba da bata hakuri sosai Rufaida taji da'din wayar tasu tana cewa"nagode Samiha kuma insha Allah zai dauki shawararki yasu Little din da Rufaida karama" cikin farin ciki Samiha tace"duk suna lafiya Ahmad yace yana miki gaisuwa da mundawo gida zamu zo gaisuwa shima yaji mutuwar yace gaisuwar waya ba zata wadatar ba sai anzo har gida"Rufaida ta har ranta taji dadi tace"koma ta hakane tayi ai ina Yaya Ahmad 'din"Samiha tace aiko ba tayi ba ,Yana gurin aikinsu yanacan yauma yana cuku cuku samun takaddar da za'a bashi yadawo gida"Rufaida tace"yanzu bazai hakura ba ai duk dayane nanda shekara biyun da suka cemasa"Samiha tace "wanne duk 'dayane bayan bama ganinku a kusa damu ai bawani cikakken farin ciki ba ahalinka a tare dakai anyi nisan daya wuce na ahau mota sai dai jirgi mai saukar ungulu" da haka suka cigaba da ta'ba hira wadda yasa Rufaida jin da'di dan har ranta matsayin data dau Samiha ya wuce tunanin mai tunani haka sukayi sallama kowannensu a cikin farin ciki_ _koda ta sauke wayar tunani ta cigaba dayi irin yadda rayuwarta takasance kalubalen data riska har kawo yanzu da wannan tunanin barci ya dauke ta_ _'Bangaren Hajiya Jamila_ _Aunty Shema'u da take yaya ga Hajiya Jamila ta dubi Hajiya Jamilar da sauran mutanan 'dakin tana cewa"Wai ita yarinyar nan Rufaida bazata zo gaishemu bane har takwas ta gota komu take nufi zamu je gaisheta yarinya tasamu guru said wulakanci"Hajiya Jamila tace " naga alamar hakan take nufi" nan sauran 'yan uwan Hajiya Jamila suka samu kofar cigaba da magana Mara dadi akan Rufaida dukdai akan dalilinsu nacewa batazo gaishesu da safe ba Aunty Maimuna kanwar Hajiya Jamila ita tasa baki cikin maganar tace" Aunty ai kamata ayi mata uzuri amatsayinta name takaba bakuma asan dalilin nata nakin zuwa ba tunda tasaba zuwa koda banwai Sani ba"wa'danda da suka fara korafin cewa bata zo dinba sai duk suka fara cewa hakane yakamata suje dubata Idan sungama shirin tafiya da sukeyi Aunty Shema'u ta 'dan ta'be baki suka canza fira_ _Hajiya Kubra ta dubi Aunty Amina amaryar Abba Bukar da suke kitchen suna kacaniyar girki su da wata mai tayasu aikace aikace tace" Amarya niko yau banji motsin yarinyar nan Rufaida ba"tace " nifa kinsan bana shiga harkar da baruwana saboda ina tsoron najawa kaina rigima gurin Hajiya Jamila gwara ke manyan 'ya'ya gareki nifa"Murmushi Hajiya Kubra tayi tace"Amarya rufamin asiri yanzu Hassan ya sake Kodan yatsa ya 'daga wa Hajiya Jamila basai ankoremu nidashi a gidanba kinsan Abba bazai 'dau irin wannan ba,Kawai dai gani nayi 'dana kowa ne kuma mahaifiyar yarinyar nan tana ganin girmanmu kuma nidai tunda nike bazance ga abinda sukayi mana ba yakamata muma mukula da ita tunda yanzu ita abar tausayice"Aunty Amina tace " toda wannan amma dai ina tsoron wannan yare yaren" murmushi Hajiya Kubra tayi tace" ashe dama tsoro kawai kikeji ni kinga bari naje dubota" "to sai kindawo" kawai Amarya ta fa'da ta cigaba da aikinta"_ Shiga Hajiya Kubra tayi dakin tana sallama sai dai bataji motsin mutum a falon ba yasata karasa shiga bedroom din a takure jikin gado ta iske Rufaida tana rawar sanyi gefe kuma Yasir ne dayaketa barcinsa babu abinda ke damunsa"Hajiya Kubra tace Subhanallah Rufaida meke damunki"cikin rawar murya tace"Mama zazza'bi nakeji da ciwan kai"Hajiya Kubra tace" amma baki fada ba" tace" yanzu nafara jin zazzabin" Hajiya Kubra tace "hala bakicin abinci haba Rufaida mutuwa fa dole ce Wanda mutu bazai dawoba kuma ke bakaramar yarinya bace da za'atasa ki kici abinci ko aduramiki,bari nakira Hassan idan mota tana hannunsa akaiki asibiti" waya ta 'daga da take hannunta ta lalubo Number Hassan ringing biyu ya 'daga tanbayarsa tayi kana inane yanzu nan yake shaidamata yana bangarensu ko abinci aka gama su fito ci tace a'a Rufaidah ce balafiya ta dauka mota tana hannunsa yace tana hannun Yaya Abdulmalik Abba ya aikesa nan yace Allah ya kara sauki Hajiya Kubra tace Amin ta katse wayar shima Hassan wayar ya aje yana kara tausayin 'yar uwarsa dama haka mace take komawa idan mijinta yarasu lokaci guda Rufaida ta rasa duk walwalarta shi dama za'a bashi ita ba abinda zai hanasa aurenta Koran su rike yaran nan cikin kulawa bazai fahimci yayi rashi ba" Hajiya Kubra AbdulMalik ta kira ganin bai dagaba yasa ta fahimci tuki yake Abba Bukar takira tasanarmasa nan yace bari yashigo dakin ya gaisheta gefen Gado Hajiya Kubra ta zauna ba jimawa ya shigo ya dubata yace idan Abdulmalik yadawo zasu tafi asibiti Yakuma umarci Hajiya Kubra tadauki yasir ayi masa wanka da haka suka bar dakin suna karamata Allah ya kara sauki bayan mikawa yara Yasir ta nufi bangaren Abba Bukar da sallama Hajiya Kubra ta shiga Abba Bukar yadubeta bayan amsa sallama inda tanemi guru gefen gado ta zauna shida yake tsaye jikin Sib yana duba wata takadda da yake nema duk ma'adanar litattafansa yaduba batanan ya dubi Hajiya Kubra da mamaki ganin cewa sun gaisa kuma yanzu suka rabu baidai cemata komaiba yanaso yaji ta bakinta takunna shirun sakanni sukayi kafin Hajiya Kubra tace"Abba dama shawara nakeso na baka amma karkace na Shiga abinda baruwana koya batama rai"murrmushi Abba Bukar yayi yace"Haba Kubra kifadi koma menene bazai batamin rai ba kuma indai dayuyuwa zan dauki shawarar taki" nisawa tayi kafin tace" gani nake gwara yarinyar nan Rufaida takoma gidan Gwaggo zatafi kula da ita amma nan kasan akwai damuwa azamannata saboda kowannenmu bazai kula da ita kamar Gwaggo"Abba bukar ya nisa yace"hakane saidai zaman nata anan zaifi saboda nanne yakamata ta zauna bayan gidan mijinta tunda idan Abujar ne babu wanda tasani kuma nanma koba ta auri danmu ba ai gidansu ne,Kubra daga gareki bana tunanin wata baraka zata taso Dan Allah kirike ta amana har Allah yasa tagama takabar nan takoma gaban iyayenta tunda yar nan kema yar kice kuma da na kowane bakasan wazai taimakeka ba a gaba"Hakane cewar Hajiya Kubra da haka dai suka cigaba da fira Abba Bukar nakarajin kaunar matarsa saboda yadda tafita daban acikinsu badan wata alaqa tasu ba yasa yake kaunartasu ba a'a halayyarta itace dalilinsa babu Wanda cikin nasa zaice ga laifin ta bawai don tasu bace yasa hakanba kawaidai ita bamai son kai bace yana alfahari da matarsa.*JININMU 'DAYA* By Sadiya Ibrahim Khali (Sadiya Khali) 4 Abdulmalik ne ya Shiga dakin Hajiya Jamila cikin saurinsa dako sallama baiba duk ya rude jin rashin lafiyar Rufaida yar uwa a garesa, inda Aunty shema'u da Aunty Maimuna sakonta data ya aje mata ganinsa cikin saurin bako sallama yasa ta tanbayar ko lafiya zai shigo mata daki haka yace "Kiya hakuri Umma Rufaida ce yanzu Abba yake fadamin batajin da'di zamu tafi asibiti"Hajiya Jamila da ranta ya gama baci tace tunda gani uwarka banda lafiya aika rude kakasa yimin sallama wallahi Abdulmalik kashiga hankalinka babban kwabo kawai ko Abdussalam da AbdulJabbar bazasuyi haka ba" AbdulMalik yace "kiya hakuri Umma"Aunty Shema'u da sai yanzu tasa baki tace" toma banda iskanci da raini akanta aka fara cuta"Aunty Maimuna da tasa baki itama tace" Haba dan Allah tunda ya amsa laifinsa ai saiku hakura ku kyalesa"kafin Aunty Maimuna ta fada tana karasa zancen da cewa muje Abdulmalik na dubo jikinta dan balallai kuje asibiti kudawo kusamemu bamu tafi ba"Aunty Shema'u tace"lallai Maimuna wannan dakece babbarmu bamusan ikon da zaki nuna akanmu ba"Maimuna da bata saurari yayartata ba dan tasan rai zai iya baci idan takulata dan ita bata goyan bayan rashin gaskiya suka fice itada AbdulMalik Hajiya Jamila ta kalli Shema'un tace" gaskiya Yaya ,Maimuna bansan ina tasamo wannan halinba bare ace yafi 'dan uwa dama da masu asali ake abin tashiga toda da sauki"Aunty Sha'awa tace "ni bama wannan yafi damuna ba kidubafa kiga yadda Abdulmalik ke rudewa akanta karfa yace shima yarinyar nan yakeso wallahi tun wuri kiyi maganinta kar wannan bakar kayar tasake kutso kai zuriyarki tazo ta sake miki shigar sauri"Hajiya Jamila da sai yanzu hankalinta yakai nan tace hakane Yaya amma daraina bazan amince ba in anyi nafarko anyimin fin karfi wannan bazan bari ba kodan duba da banbancin dake tsakaninmu mai dunbin yawa" da wannan firar tasu ta cigaba da wanzuwa har Rukayya ta shigo dakin da za'a barta anan Aunty Maimuna data kalli Rufaida da take rawar Sanyi tace subhanallah Rufaida zazzabin ne har haka kafin ta bude Sib din jikin bango ta samo mata hijabi tana cewa"anshi maza kisa AbdulMalik yana falo yana jiranki"tare suka fito falon da Rufaida ba wanda take ma iya yiwa magana AbdulMalik cikin nuna tausayi ga matar yayannasu da kasa ta rufesa da take masa takaba yace"Aunty kinga ashe har haka jikin Rufaida yayi zafi"Aunty Maimuna tace"AbdulMalik rasa miji ba abine mai sauki ba dole akwai ciwo da zafi na rabuwa da abokin rayuwarka yanzu dai kayi maza ku tafi asibiti Allah ya bata lafiya idan kun taddamu shikenan"AbdulMalik ya amsa da to Aunty Allah ya saukeku lafiya"duk tare suka fito shida Rufaida sukayi hanyar harabar gidan ya tada mota suka nufi asibitin Da murmushi matashin likitan mai suna Zahraddin ya dago kai daga rubutun da yake zaune a daya daga cikin kujerun office din yana cewa"Malam AbdulMalik lafiya kuwa Zahraddin ya fada yana bawa AbdulMalik hannu da likitan bayan sunyi musabihar ne ,suka zauna a kujerun dake gefen na Zahraddin din kafin AbdulMalik yace"Eh Wallahi zahraddeen nine Matar Yayana da yarasu kwana 4 nakawo bata jin dadi ya nuna masa Rufaida "Zahraddin yace" Allah sarki Mama ta fadamin rasuwar to Jiya nadawo daga Kano shine banzo gaisuwa ba banma ko a waya ba tunda naje ban huta ba wani aiki ne aka turamu Allah ya jikansa ita kuma Allah ya bata lafiya ya fada yana kallen fuskar Rufaida da yaji lokaci guda tausayinta ya kama shi "AbdulMalik yace "Amin abokina babu komai nagode amma ban yarda ba saikazo yimin har gida" Zahraddeen yace" to shikenan zanzo yau din nan ma in Allah ya amince amma waima tsaya kasan da abotar kaki shigowa koka kirani a waya nazo har gida koka fadamin kuna nan a waje nasa a shigo daku yanzu da yadda nace nagama duba kowa da saina fito naganku naji kunya"AbdulMalik yayi murmushi yace"abokina kenan yanzu muka zo badadewa mutane kadan na tarar idan kuma na shigo kaga zan shiga hakkinsu ,idan nayi haka kuma kaga bankyautaba bansan uzurin kowa ba ,kuma bawai alfarmace ko matsayi ace dan kasan wani a guri kai tsaye bawani dalili kazo ka wuce wasu guri kuma bayan sun rigaka zuwa kaga akwai hakkinsu akanmu da munyi hakan"murmushi Zahraddin yayi yace"Uztaz AbdulMalik kenan"AbdulMalik yayi murmushi yace"gaskiya ce ba wani uztaz ni duba min mara lafiyata mu tafi na biyema hirarmu bazata kare ba bare muyi abinda zai anfanemu"Murmushi Zahraddin kawai yayi ya juya ga Rufaida ya mata tanbayoyi ya gwada Blood pressure dinta ya rubuta mata magunguna yace ta rage damuwa sannan ya mata nasihohi kafin su mike su fito Zahraddin yana cewa sai ya karaso zuwa anjima koda yamma ne Daki kawai Rufaida ta shiga bayan fitowarta mota da ledojin magungunan da yoghurt da AbdulMalik ya siya mata da zata sha maganin dashi da tuni lokacin su Aunty Maimuna sun dau hanyar Nasarawa tana shan magungunan gado kawai ta haye ta kwanta AbdulMalik ya da'de a motar kafin ya fito a ranshi yana matukar jin tausauyin Rufaida tunanin da zuciyarsa ta fara shiyashi sakin murmushi ya fito daga motar ya wuce bangaren mahaifinshi don alokacin ya tabbatar su Aunty Maimuna sun tafi don yaga message din data turamasa har ran AbdulMalik yakeso Auntynsu Maimuna saboda tafita daban a cikin yan uwan mahaifiyartashi gwarama Haulatu ba laifi da nata kirkin saidai zugata da yan uwanta keyi shine yake sauya ta dandanan gata da daukar zafi lokaci guda ita ko Aunty Maimuna tana da kafiya akan gaskiya.*JININMU 'DAYA* By Sadiya Ibrahim Khali(Sadiya Khali) 5 AHajiya Jamila ta dan dubi Aunty Amina da Duke zaune Suna karyawa a falo tace Amarya Ruqayya zaki mikawa abincinta kibawa Rufaida ta mika mata"Abba Bukar da baice komai ba sai da yaji karashen maganar Hajiya Jamila yace "kamar ya a mikawa Ruqayya abincinta?ita bazata iya fitowa ta ciba"Hajiya Jamila ta 'dan yatsina kafin tace masa" kasan tunda akayi rasuwar nan yarinyarnan Ruqayya bata cikin nutsuwarta gani take data fito falon na ganin wancen yaron zatayi"Ganin ya gane AbdulAhad take nufi yace mata"dakata Jamila ita Ruqayya AbdulAhad din mijintane ita matartasa daya mutu ya bari take masa takaba ita ta fito take cin abincin da ita yaushe ta warware ince Jiya har asibiti aka kaita"ganin kowa na falon jin amsar zata bayar yake yasata cewa"Ba haka bane Abba kaima kasan akwai banbanci tsakaninta da Rufaida mai tazara saboda ita Rufaida ta auresa tana zaune dashi ita kuma Ruqayya yarasu tana son aurensa"shiru Abba Bukar yayi yana tunanin halayyar matarsa kiri-kiri take fito da komai yace" Wasila jeki kira min Ruqayyan danni tun fil azal iyalina guri 'daya sukecin abinci bakuma za'a ware ba saboda zuwanta ya fada"Wasila datake cin dankali ta ajiye ta mike tana cewa "to Abba "sai da yaga shigowar Rukayyan falo da take ta sissinke kai ya mike yabar dakin da Ruqayyan take gaisheshi ya bita da lafiya lau ya fice daga gidan yaran suna binsa da adawo lafiya Aunty Amina ta bisa yi masa Rakiya Aunty Amina ta dubesa tace"amma Abba abinda Ummansu Abdussalam take sainaga kamar bata kyautawa akan yarinyar nan kuma a gabanta take komu inzamuyi mata kamata yayi ta hanamu tunda koma menene matsayin surikarta take dukda mai rabawa ta raba" nisawa yayi yace "hakane Amina zanyiwa tufkar hanci da wuri kuma kema karki sa baki dukdai kulawar da kukaga yakamata a matsayinku na iyaye gareta Ku bata tunda koba komai Aliyu da Hauwa'u na wane" tace masa hakane Insha Allah zamu kara datse damtse fiye da yanzu"yana murmushin jin da'di yace yawwa Amina"Allah yayi miki Albarka" tace "Amin" da haka yaja motarsa ya fice ya nufi gurin aikinshi. Rufaida da take zaune a gurin tanaji yadda Hajiya Jamila suke fira itada Ruqayya ko daya batasa baki ba dan ko tasama gwaleta zatayi jefi-jefi dai take sauraran firar tasu hirar ragowar yaran dakin take shiga da kusan ta karatu sukeyi hakan yasa ta sake tsunduma cikin tunanin rayuwarta yau babu ginshikan rayuwarta dukda suna raye,amma akwai tazara mai dunbin yawa a tare dasu, Yasir shida Ubaidullah suke wasa 'dan Aunty Amina dukda Ubaidun ya girmema Yasir da wajen shekara 'daya da wani abu,AbdulMalik ya dubi Rufaida yace"kinsha maganinki kuwa" tace "Eh Yaya nasha" yace mata yawwa kinsan Zahraddin yace ki riqa shan magani akan lokaci Allah ya kara sauki dazu da mukayi waya yace a gaisheki"tace"Amin Yaya AbdulMalik to ina amsawa" da haka suka cigaba da firarsu zuwa wani 'dan lokaci. Jingina kansa da jikin kujerar dake office din yayi sanyin Ac na ratsasa yana tuna abun da haryau ya kasa mantawa dashi a rayuwarsa dukda shekarun da suka fara tafiya amma baya tunanin ya manta da wancen ran da yasa shi a sahun mai sa'a a rayuwarsa a hankali ya fara tunano wayarsu da Ahmad da yakasa fahimtar yanzu menene a cikin ransa dukda yadda ya da'de da yanke tsammani kuma har yau baya tsammanin cikar muradinsa ABDURRA'UF RJM kwararran likita MEDICAL DOCTOR kenan matashi mai kimanin shekaru talatin da 33zuwa 34 Mi'kewa yayi da wannan tunanin nasa ganin baida sauran marasa lafiyar da zai duba key din mota ya dauka kawai yana kokarin ficewa daga office 'din yana kallon agogon hannunsa 2:pm dai dai yayi mamakin kaiwarsa karfe 2 bai koma gida ba gurin wayarsa da take caji ya karasa yana kokarin cireta daga cajin yaga kiran Safiyya karasa cirewa yayi inda yayi caraf ya 'daga wayar yana murmushin mugunta dan yasan flashing Safiyyan tayi ako bangarenta cewa tayi cikin yarensu Na India tana cewa" kai Yaya Ra'uf daga flashing harka kama dama ammi ce tace na kiraka karma taho kamanta sakonta"ya dan saki fuska kamar tana kallonsa yace"ai ban ta'ba ganin 'kanwa tana gudun yayanta yaci ku'din wayarta ba sai akanki"jin yaji sakon yasa Safiyya katse wayar tana murmushi shiko Ra'uf da yake jiran amsar Safiyya jin shiru ne yasa shi duba wayar ganin ta katse yasa shi murmushi ya bude kofar office 'din ya fice yana tura kofar office din yasa key ya rufe " a harabar asibitin ya tsaya kiran waya bai jima yana wayarba ya katse ya karasa gun motarsa ya tayar yabar asibitin sa'ko Ammi ya tsaya ya amsa daba komai bane face turare daganan kai tsaye gida ya nufa Da sallama ya isa falon gidan da yaketa kamshi wandaa Key da wayoyinsa suke a hannu sai sakon Ammi da yake hannun nasa"Safiyya da take falon da Pakistan riga da wando a jikinta da dankwalin kayan akanta ta amsa masa sallamar da cewa "a'a Yaya Ra'uf sannu da zuwa kaga yadda kayi kyau kuwa kamar rana bata dokeka ba" Hararar ta yayi yace"banasan raini fa naje aikin na dawo ki fadi haka"tace Allah Yaya dagaske make"yace "to naji ina Ammi" tace masa" tana ciki"da haka ya aje sakon da wayoyinsa anan yace yana zuwa zai watso ruwa Safiyya tana ganin shigewarsa ta 'dauki wayarsa da tasan ba pattern tsaron waya ta fara kiran kawayenta da suka jima busu gaisa ba saboda hutun dasu keyi sai da taji alamun saukowarsa daga saman bene ta ajemasa wayar ta cigaba da kallon da takeyi dashi da Ammi suka sauko inda Ra'uf ya kalli Safiyya ya harareta yace" da ganin fuskarkin kowa yasan kinyi laifi"Ammi ta kallesa tace" kai Ra'uf kadaiji tsoron Allah mai kuma Safiyyar tayi"labari yake bawa Ammin har suka karasa gurin cin abinci suka inda suka fara cin abinci Ra'uf suna cikin cin abincin yace "Ammi yanaga Dady bai dawo ba" Ammi tace "yana hanya nafi tunani" Ra'uf yace "bari dai na kirasa naji ke Safiyya daukon wayata na kira Dady"Safiyyance ta mike daga cin abincin da take ta dauko wayar ta mikawa Ra'uf da hannu biyu da tuni tafara tsorata dan tasan ta cinyewa Ra'uf katinsa Ran Ra'uf inyayi dubu ya 'baci ganin ya kira Dady sun shaidamasa ba kudi shiko yasan da kudi ya aje wayarsa Safiyya ya fara tunanin tacinyemasa kudin duben Safiyya yayi ya ha'da rai yace" wa kika kiramin da waya"cikin tsoro Safiyya tace Yaya kaya ha'kuri 'kawayena ne"yasake cewa "ban hanaki ta'ba min waya ba ke kwata kwata bakyajin magana" cikin tsoron hukuncin Yayannata tace" kaya hakuri bazan kara ba"Ammi tasa baki tace to bata baka hakuri ba ai saika hakura kasa wasu"Ra'uf yace" amma Ammi kina gani fa ta mikon wayar na fara kira maimakon tacemin babu kudi amma taki fa'damin saboda ta rainani"Ammi tace"ai tunda ka kiyin aure 'yar Safiyya ma sai tazo ta rainaka bama Safiyyanba"Safiyya da 'kiris ya rage tayi dariya ganin Ra'uf ya tashi daga gurin yasata yin shiru tana jin bata kyauta ba ganin itace taja abinda ransa ya'baci Safiyya tace cikin Sauri"Yaya kaya hakuri bazan 'karaba" ganin zai karasa matakalar bene murmushi yayi batare daya juyo ba yahaye been ya karasa 'dakinsa kawai ya zauna bisa 'daga cikin kujerun dake falonsa ya jingina kansa da kujerar yana tunanin mikin da aka dasama zuciyarsa babu kwakkwaran hujjar dasawar kuma har yanzu har abada kuma bazai iya mantawa da bigiren ba har wayau kuma bazai ga laifin bigirenba koda duk duniya kowa zai lankaya laifi gashi bigiren ba an shiga rayuwar daya dade yana mafarkin samu ba tareda sanin hujjaba kawai anyi anfani dason zuciya gurin cusguna masa tabbas akwai zalinci mai yawa a wannan rayuwar da ake yi to ta ina zaiyi wata rayuwar da yasan zalintar duk wadda zata zauna dashi zaiyi,babu aure a yanzu haka a tsarinsa koda zaiyi bayanzuba kasancewar yasan tun asalinsa shi bamai sa'a bane da wannan tunanin barci ya daukesa koda dady ya tanbayi Ra'uf Ammi tace da kanwarsa ne ita tamasa laifi ta bashi labari fa'da sosai Dady yama Safiyya tace idan ya fito anjima zata sake basa hakuri da haka hirarsu ta kasance kasan zuciyar Ammi yana tunano wani lamari daya maishe da ',dan nata haka mikin da ya harbi zuciyarsa abunda yafi kama da nuna iko da har yau takasa fahimtar wannan dalilin ikon da aka nuna ga gudan jininta da akai anfani dashi gurin zalintar zuciyarshi da danamasa mikin da har yayi tsamarin da batayi tunanin zaikai haka a zuciyar 'dan cikin nataba.*JININMU 'DAYA* BY Sadiya Khali 6 Bugun 'dakinsa da yaji anayi shine yasa shi farkawa da anbaton Allah a bakinsa,duk jikinsa yayi masa nauyi dan koda can a baya da rayuwar bata kai haka ba jindadi ba shi baisa ba da kwanciya a kujera ba,koda a yanzu tunani yasoma tu'kewa a zuciyarsa har yake neman shafar jin da'di rayuwartasa baisa ya saba makamancin rayuwa Irin wannan ba,jin muryar Ammi tana cewa"wai bazaka bude min kofar ba" ya danyi mi'ka ya mi'ke yana cewa "Ammi a bude fa take" yakarasa jikin kofar ya bu'de matsawa yayi ta karasa shiga ciki ya maida kofar ya rufe kallon Ra'uf Ammi take har tanemi guri saman kujera ta zauna shima kujerar da yatashi ya koma ya zauna Nisawa Ammi tayi kafin tace"Ra'uf yanzu abinda ka za'barwa kanka kana tunanin ya yima kullum kai kenan ka rufe kofa ka zauna kayita tunani bayan komai na duniya hakuri ake dashi duk yadda al'amura suka tu'ke da wanzuwa", Murmushi kawai yayi kafin yacewa mahaifiyartasa"Ammi ni tuni na da'de da barwa Allah komai dukda har yau ban fidda rai ba ga samun waccen sa'ar da nake tunanin ada na rasa ta sai dai yanzu ina mafarkin samun abinda na rasa kona samu Wanda ya fishi" Kai kawai Ammi ta girgiza tana gwada maganganun Ra'uf ama'auni sai dai dukda ta gano abinda yake nufi baisa ta tada maganar ba dan ita ba maison tayadda abinda ya rigada ya wuce bane tun fil azal,Sauya maganar tayi da cewa,"To yanzu maganar aure na lura sai dai an zaboma macen da zaka aura tunda gashi nan shekarunkafa tafiya suke"dan jim yayi kafin ya ce "Ammi ni yanzu banida wani za'bi kiyi duk yadda kikaga ya dace zan amince",Murmushi tayi tace" to Allah yasa karka kara bani kunya,Kamar wancen lokacin Murmushi yayi mai sauti kafin yace"A'a Ammi ai wancen karanma inada dalili mai karfin gaske"ta 'dan murmusa tace"ni banga laifin Intisar ba kai dai kawai kaki ta sai gashi abokin ka ya aureta"yace yawwa Ammi kin gani ko,Inteesar dama tuntuni Shureim yake fadamin son da yake mata kinga kuwa ni din baikamata na cusa kaina ba gwara dai dana barwa aboki na ya muradinsa ya fa'da yana tauna la'b'bansa na 'kasa yana sake tuno wancen mikin da baya kwana bai tuna shi ba abinda yafi kama da al'ajabi da tarin tanbayoyin da bazai gushe ba yana tanbayar kansa ,Ammi tace "to shikenan Allah ya kawo mace tagari" sake maida dubanta tayi ga Ra'uf ta tattara dukkan natsuwarta dukkan nutsuwarta gareshi da alamu maganar mai muhimmanci ce tace "amma Ra'uf mai zai hana ka amince da maganar Dadynku ka auri Safiyya",shiru yayi kana yace" Ammi bawai na'ki bane amma banaso yarinyar nan ta shiga wannan zuriya mai 'dunbin son zuciya da nuna fifiko zatasha wahala duba da ita 'din wacece baikamata nina zama silar cutar da wannan baiwar Allah 'din ba"Shiru Ammi tayi tana sake tunanin maganar Ra'uf datasan gaskiya ce itakanta Ammi ta fiso Safiyya tayi aure a inda zata huta da bazata fahimci ita 'din wacece ba koda har abada bazatasan wacece itanba, Da haka Ammi ta mi'ke da cewa to zan bincikoma tana duben agogon falon ta cigaba da cewa" Safiyya fa ta gama shirin tafiya gidan Shureim kai take jira"ya 'dan saki fuska yace "Ammi na manta gwara da kika tunamin danma banason nakasance mai sa'ba alqawari amma da bazanje ba bare naje da Safiyyan"Ammi tace bamai shiga fa'danku kai da Safiyya idan anshigama aji kunya" Murmushi yayi yace ai kuna gaf da daina jin kunyar "Ammi ta fice tana cewa"kanku dai akeji dai" 'Karfe hu'du na yamma Ra'uf ya sake wani wankan ya shirya cikin kananun kaya ya sauko 'kasa masallaci ya wuce ganin bakowa a falon a masallaci ya ha'du da Dady suka shigo gida tare yana tanbayarsa yanayin aikinsa,a falo suka yada zango inda Dady yake sanarmasa company yabiya da shine dalilin rashin dawowarsa gida da wuri wanda Dady yake da hannun jari a ciki Ra',uf yace "To Dady Allah yayi jagora" yace Amin Babban mutum sunan da Dady yafi kiransa dashi Murmushin sunan da Dady yakirashi dashi yayi yana tuno mai kiransa da sunan da yake tuno rabuwarsu ta 'karshe da ita ya'dan dubi Dady yace" Dady dama maganar kayan da za'a turawa Kawu Mukhtar shine nakeso muyi inasan taimakon kasata yakamata ina bada taimako asibitoci ko yaya ne"Murmushi Dady yayi yace "hakan yana da kyau Ra'uf,Dukda kasartamu akwai arzi'ki amma babu taimako kowa da yasa kansa kawai ya sani rayuwar wani bata damesa ba ,shiyasa har yau 'kasartamu babu cigaba duk mai arzi'ki burinsa sa 'ya'yensa makaranta mai tsada koma subar kasar da karatun gaba 'daya maimakon muyi 'ko'karin bun'kasa 'kananan gurabe zuwa manya manya saboda ko 'kasashen nan damuke ciki ta haka sukayi arzi'ki ,amma saikaga mai arxiki a garinsuma bayason zama da wata 'yar dama tasamesa wani ko gini bazai iyayi a garinsuba, saboda yana tunanin 'kauye ne baya tunanin raya kauyen nasu,wani kuma koda yayi ginin sai yace bazai zauna ba koda aikin gwamnati yayi yayi retire ,ko kuma 'dan kasuwa ne da zai iya zuwa yadawo garinsu,ko kuma wani 'yan mola acewarsa su suka koresa daga garinsu abinda babu mai raba bawa da arziki sai mutuwa,amma sai dai yaje ya raya mahaifar wasu, kuma wasu da yawa idan wata dama tasamesa bazai iya turo ta garinnasu ba ko 'kasarsaba a'a sai dai yabarsu garin wasu kasar wasu Suma marasa 'karfin cikinmu basa baws masu son taimakon cikinmu kwarin gwiwa kuma suma tunaninsu su samu damar suyi fiye da abinda wasu sukeyi shiyasa bama cigaba saboda yadda kowa a yanzu haka kansa ya sani da 'ya'yansa, Nagode wa Allah da 'dana yayi tunanin abu mai kyau Allah ya kara dafamana "Maganar Dady ta shigi Ra'uf sosai yana tunanin rayuwa yadda tazama yanzu ya amsa da cewa" Amin Dady nagode da nasiharka gareni"da wannan zancen Safiyya ta iso falon takatse musu firar ta hanyar sallamarta suka amsa mata ,Inda tana kokarin zama tace Dady shine aka ki kirana muyi fira bakomai zamu rama nida Ammi ,Dady yayi murmushi yace yawwa ai dama munfisan haka gwara kowa ya za'bi gwaninsa" dariya tayi Ra'uf yayi Murmushi yace"ke ina shirin naki "Murmushi tayi tace Yaya nifa nagama shirina dama kainake jira kace nafito" harararta Ra'uf yayi yace"wato nine ma zan je nace miki na shirya?kajitafa Dady",Dady yace"babu ruwa na dashiga zancenku"Ammi ta fito daga kitchen da ruwa na gora a hannunta ta iso da sallama ta zauna kujerar kusa dasu tana kokarin bude gorar take cewa "yanake jiyo hayaniyarku Abban Safiyya ince dai yaran nan ne da basa gajiya da kan kara" wato Ra'uf da Safiyya,Dady yace "kamarko kinsani Asma'u" labari ya bata tace ai saika gaji Indai wa'dannan ne gidan Shureim zasu shine suketa wannan lugyigyita maganar"murmushi Dady yayi yace",ai shine nace bamai shiga fa'dansu"Ammi ta kalli Ra'uf tana canza maganar da cewa "kai wai ina sa'kona" Ra'uf yace "Ammi Safiyya natarar a falo na ajewa"ya kalli Safiyya yace" Baki kaiwa Ammi sakon dana aje ba kuma kinsan na tane"Safiyya tace" Ammi na ajemiki saman madubi danaje 'dakin naga kina barci"Ammi tace" to shikenan jeki ki shirya Ku tafi da haka Safiyya ta mi'ke koda Safiyyan ta iso falon har Ra'uf ya mike tabi bayansa suna yima su Dady sai sundawo. Basu jima suna tafiya ba suka isa gidan Shureim tarba ta musamman aka musu koda cewar su ba baki bane a gidan Irfan Ra'uf ya dauka ya fice shida Shureim daga falon bayan sungama gaisawa suka bar Safiyya da Inteesar. A jikin motar Shureim su Ra'uf da Shureim suka tsaya Shureim da ya 'dan kalli Ra'uf yace"Abokina kai yaushe zakayi aure kadubafa ni gani harda 'da 'daya,Ahmad kuma 'ya'ya biyu haba Ra'uf ka'din baka tunanin kaima kayi aure kobazakayi dan komaiba ai kariqa duba damu abokanka duk munyi amma kaida kurinka bare kace shiya hanaka yi haba Ra'uf har yanzu tunanin wancen mikin nasan shike dawainiya dakai dukda maganar Ahmad bana tunanin a yanzu abin maiyiyuwane dukda kai din banama sha'awar hakan a karo na biyu domin babu tabbacin zama kasamu abin "kalaman Shureim sunkara tasiri garesa bayan na Ammi data masa Saidai shifa har wayau babu wani tunani a ransa na wata budurwa tun bayan abin da yafaru da yake ganinsu kamar yau batare da an shawarceshi ba aka yanke waccen kyakkyawar ala'kar gani yake da yanzune dasai ya yi fito na fito daduk mai gudunsa da wancen ran da yake gani alkhairine a dunbin rayuwarsa da to zan duba yabi Shureim kawai suka kara ta'ba hira daganan suka karasa masallaci said wajen takwas na dare suka yi musu sallama suka koma gida Inda Ra'uf ko a mota bai kula Safiyya ba ita keta zuba surutunta iyakacinsa da ita ey ko a'a har suka isa gida bai tsaya kula kowa a falon ba Ammi tace ga abincin kazo muci yace yaci a gidan Shureim daganan ya haye bene Ammi da Safiyya damai aikinsu basu damu da maganarsaba dan sunsan baida tsawaita magana wani lokacin Safiyya ko zama tayi ta zuba abinci ta fara shiko Ra'uf kai tsaye dakinsa ya sake ya wuce watsa ruwa yayi sallahr isha',i yayi Azkar kawai ya kashe wayoyinsa ya haye gadonsa da yaketa juyi ya kasa barci sai tunani tunanin da kowanne dare saiyayi rabuwa ce ta nuna iko aka yi gurin wanzuwar rabuwar saidai yaci ace yamanta da wannan abun amma Sam yakasa mantawa yakasa manta waccen fuskokin da fuskar da a cikin fiskokin yafi tunawa dama muryar waccen fuskar ya Allah ya furta ya rasa yadda zaiyi ya manta da waccen rayuwar ta baya da abinda yafaru garesa a waccen rayuwar. SADIYA KHALI✍🏽 comment# Share# Vote#*JININMU 'DAYA* By Sadiya Ibrahim Khali 7 Kwanci tashi ba wuya gurin Allah yau AbdulAhad kwanansa Hamsin da rasuwa anyi addu'ar Arba'in da Abba bukar ya hutar dakowa sukayi a masallaci,Rufaida da taji karar wayarta ta duba ganin maikiran yasata 'dagawa karon farko Samiha macen da bazata iya mantata a rayuwarta ba tare sukayi rayuwa mai cike da farin ciki da kaunar juna inda lokaci guda wannan rayuwar tazama tarihi ita 'din Samiha jintatake a zuciyarta fiye da tunani,Da sallama Rufaida ta 'daga wayar da Samiha ta amsa takuma kara da cewa "habawa Rufaida ace sai na kiraki zaki tunani"murmushi Rufaida tayi da ita kadai tasan fassarar abinta tace"a'a Samiha ku'din wayar ne babu na kira bama nida caji sai yau nasamu" cikin firgici Samiha tace" Rufaida meke faruwane kiyimin bayani"hawaye shar sune suka biyo kuncin Rufaida batareda tace komaiba kawai ta katse wayar tana tuno cin fuska da cin zarafin da akemata a gidan kuma bata fuskar kowa ba sai Hajiya Jamila da Ruqayya AbdulMalik da Abba basa zama basusan komaiba cajin waya ma basa bari tayi duk dakin datasa caji sai yara sunbita suna kokawar game kwanakin baya jefarmata ita sukayi ta kara tsagewa,idanko tace wani abu saitaga kamar bata kyautaba tunda 'ya'yan Hajiya Kubra da Aunty Amina ke hakan itako a yadda take daukarsu tamkar umminta Hajiya Jamila da Ruqayya ke mata suke uwa da makarbiya,Dakin Hajiya Jamila da take tunanin sawa don samun sauki to tasan ko giyar wake tasha bazata je da zunmar sa caji ba hakananma idan taje kyara ke hadasu bare kuma taje da zunmar wani abu,dukda itama dakinta akwai komai saidai matsalar dayace babu caza tata tana abuja ,tsangwama gori datake sha ga mutane biyun dukshi yafi damunta mutanan datake samun farinciki a gunsu suma hotone idan mai gidan bayannan dan Hajiya Kubra da Aunty Amina basuda hayaniya shiyasa basa shiga abinda za'ayi wata hayaniyar dasu sai daifa idan sunga abin nanema ya tuke suke uwa makarbiya Samiha data sauke wayar jin Rufaida ta yanke,yasata kurawa wayar ido,tana tunanin mai ake da wacce rayuwar ta baya banda kaddarori mai zaisa ta baro aminiyartata da aka shiga hakkinta gurin lalatamata mafarkinta,kuma akaki sanar da ita dalili dukda batasaniba amma akaran kanta tasan har ya'u akwai tabo a zuciyarta,an zalinci wancen ran,sai dai a yanzu fatanta inganta rayuwar amintacciyarta ta,mai dunbin muhimmanci a rayuwarta tundaga kuruciya har kawo yanzu dukda nisan zangon da sukayi da juna bawai mota ba a'a nisan har tafiya banbancin kasa dake tsakaninsu,Rufaida dataci sunan Rufaida ta fado dakin da take tafa'da jikinta tana cewa Mom Dadynmu yadawo"cikin harshen nasara take maganar dashi suka fi iyawa a yanzu haka,Murmushi Samiha tayi tace to sannunsa da dawowa,Ina Little din"yarinyar ta dan ta'be baki tace yana hannu Dady ni yaqi daukata murmushi Samiha tayi tace mata banda abin Rufaida aike kin girma baki ganki kinkusa fina girma ba" Rufaida ta saki dariya tace Mom ashe nima Little ya kusa fara kirana Mom"tace "sosaima"tana dariya sallamar Ahmad ce ta katsemusu firar sannu da zuwa Samiha ta masa ya amsa da yawwa da murmushi fuskarsa ledar dake hannunsa ta ansa harzata shigar da ledar Kitchen yace tadawo ta zauna zama tayi tsakiyar yaran,da Little ya mika hannu ta daukesa murmushi Ahmad yayi yace" habawa yaro zaka nemi na daukekane nima naki"ya fada yana dungurekan Little yafara alamun kuka ganin haka Rufaida tasa dariya ganin hakan da little yayi 'yar uwarsa tana dariya shima yafara dariyar,suma su samihar dariya abin ya basu ,Ice cream din dake ledar Ahmad yace Samiha ta ciromusu susha ta dauko suka fara sha shida yaran da Samiha tace ita ta koshi,ganin haka yasa Ahmad barwa yaran susha Rufaida itake bawa Little a baki,Kallo Ahmad yabi Samiha dashi jin tace batasha ganin baigano komaiba yasa yace"Samiha maike damunki? kefa kikace da zantafi na tahomiki da Ice cream dinnan" Samiha tace "Eh nice" Ahmad yace "to fadamin maiyasa kikafasa sha" ta dan canza fuska alamun damuwa kafin tace" Dadyn little yanzu mukagama waya da Rufaida da alamu bayan rasuwar mijinta tana cikin damuwa"ya 'dan gyara zamanshi yace "Inajinki damuwa kamar tame"ta basa labarin wayarsu da Rufaida ta kara da cewa masa "nafahimci kamar takuramata ake gidan Abba Bukar" Ahmad da mamaki yace"dama bata Abuja"Samiha tace"Eh kasan Barrack ne gidan ba wanda ta sani sosai acan shiyasa Abba Bukar yace ta zauna harta gama takaba takoma gida"Ahmad yace to gidan iyayentafa ko 'yan uwansu na Zariyan,aita zauna a can badai gidan nasu AbdulAhad ba"Samiha tace"kamanta Abba Bukar yayan Abba ne saidai nikaina saida nayima Momy magana yaza'ayi abarta gidan surikai tayi takaba sai kace batada gidan uba koma gidan Gwaggo ai gwar a takoma Ahmad yace "to tunda duk gidane ai ba matsala kuma kwana nawane"Samiha tace "hakane" nan Samiha ta yanke shawarar turawa Rufaida ku'di ta account koda ka'danne dan itama basu gareta ba dan business din datake nema kudin ke shigo mata"dubu 20K ta turamata acewarta sunyima Rufaida ta wuce karfin kyautar 20k dubu ashirin a wajenta,amma dai tasan sun isheta wasu 'yan bukatun ,dan ita kanta Samiha tasan komai dangane da wannan gadaddar kiyayyar daga Hajiya Jamila,shiko Ahmad tausayin yarinya karama yake kai tsaye batada sa'a a rayuwarta ta 'bangarori da dama zaikirata ,shi kansa da basa tare gari daya abubuwa da dama yasani harma auren nata da AbdulAhad da wani abokinsa Habib yake basa da suke unguwa daya dasu AbdulAhad din"saidai yana mamaki da wuya ko ita Samiha Rufaida ta fadamata abinda akayi mata saita tutance yarinyace mara hayaniya,yana tuno wancen shekarun da yakeji kamar shine a cikin waccen rayuwar Jin karar wani kiran yasa Rufaida yasata duba mai kiran dan tasan idan Samihace bazata dagaba dan tasan tanbayoyin da zata yi mata sunada yawa akan damuwarta itako batasan dagawa aminiyarta hankaki ganin Luba ce mai kiran yasa Rufaida da sauri daga kiran bayan yin sallama suka dan gaggaisa tana tanbayar Luba na tanbayar Rufaida kwana 2 matsalar caji tafadawa Luba Luba da tasan Zariya akwai wuta kawai jin Rufaida tayi dan tasan akwai dalili babba da ita kanta Luba a dan zaman da sukayi da Rufaida tasan zaman hakuri take da surikarta da yan uwan surikartata dukda ba labari take bata ba amma dai tana fahimtane kuma Abban Yusuf wato Kabir yana dan bata labari wani abun kila wayar suka anshemata duk Luba ke wannan tunanin lokaci guda haka dai suka cigaba da gaisawa har zuwa wani lokacin sukayi sallama,jin karar message suna wayar yasa suna gama wayar ta duba mumushi yayi ganin sakon kudin da Samiha ta turomatane ,Allah sarki Samiha Rufaida ta fada a fili tana gama dubawa ta yanke shawarar kiran Abdulmalik ya tawo mata da charger tunda da kudi a account dinta saitamasa transfer da yake tukinsa hankali kwance yaji karar motar ya tsayar ya duba mai kiran ganin Rufaida yasashi katse kiran yabi saida suka kara gaisawa ta fadamasa sakonta da to kawai yabi Rufaida a yakatse wayar yana fadamata tuki yake a ransa yana tunanin Rufaida tasan tanada bukatar wani abu amma bazata fadaba saidai tace a siyo ta bada kudin haba yayima Rufaida siyayya tabasa kudin ai badai shi Abdulmalik ya amsa ba,shi tunaninsa Rufaida tanada komai bakuma zata nema ba shiyasa bama ya siyamata,itako Rufaida tunaninta idan ta tanbayesu mutanen gidan wani abu kamar bata kyautaba ganin batasan aljihun kowannensuba,Kuma ita idanma ba dole ba batasan tayi tanbayar abata abata dukdai Jini daya suke.*JININMU 'DAYA* Sadiya Ibrahim Khali (Sadiya Khali) 8 Rukayya da take zaune a falo itada Hajiya Jamila sauran yara sunyi shirin islamiyya suntafi sai Yasir kadai ya rage a gidan da shiko yana gurin Aunty Amina yanama babynta Ummu kursum da take goyo wasa ,AbdulMalik a haka yashigo yasamesu da sakon Rufaida a hannunsa a leda abindama batace ba saida yasiyomata yayi musu Sallama suka amsa masa Rukayya tace "Sannu da zuwa Yaya Abdulmalik"ya amsa mata kamar anmasa dole da" yawwa"Hajiya Jamila tace "ya aikin naku"yace "Alhamdulillah"daganan yasa kai zai wuce bangarensu ganin sakon Rufaida a hannunsa kuma baiganta a gurinba yasa shi cewa" Umma ina Rufaida naga shiru banji motsinta ba" baki ta ta'be tace "tana kitchen ta doramana abincin dare" ya 'dan juyo ya kalli Ruqayya yace"Umma ita Ruqayya ai yakamata taje suyi tare"tsaki Hajiya Jamila tayi tace"Abdul malik ka kiyayeni fa bandama shirme irin naka ina zaka hada Ruqayya da Rufaida kodai kai wawane sai haka tuntuni nake nunama banbancin dake tsakaninsu"AbdulMalik yace"haba Umma ni haryau bana ganin banbancinsu a zahirin gaskiya ma Rufaida tafi Ruqayya dangantaka da gidannan ta kowacce fuska gaskiya"Hajiya Jamila data fusata tace" to yima Ruqayya gori cewa tazo gidanku cin arziki arzikin da duka yaushe ubannaka yayi kuma kasani komai zakace idan ni kahanani fa'dar banbancin dake tsakaninsu to bazaka hana duniya fada ba,abinda bakowanne biladama zai iya ba saiga wancen matsiyacin yayi da kuma waccen...."AbdulMalik ganin Ummantasu bazata tsaida wannan cin zarafinba yasashi harda saurinsa dan yasan indai zai biyemata tone tone zatayi abinda yasan yana daga cikin kaddarorinsu to akanme za'a dinga jagwalgwala magana dashi haryau yake tantama ga waccen labarin kanzon kuregene da saboda suma suji waccen tsanar kamar yadda ita kiri kiri take nunawa ga wancen rayukan masu matukar muhimmanci a rayuwarsu tabasu labarin da babu kamshin gaskiya a ciki dukda dai mahaifiyarsu ce tabasu,to shi koda ma hakanne shi baiga abin da zaisa yaki 'yan uwansa ba danshi yama jahilci labarin tunfarko kodama gaske ne,Rufaida da take kokarin shigowa falon ta fadawa Hajiya Jamila ta gama abinda tasata mai zata kara dorawa a kunnenta ta fara jiyo maganganun Hajiya Jamila da yaranta data fahimci akanta ake maganar bata karasa jin maganar b takoma kitchen din gudun kada AbdulMalik yazo yasameta anan da haka yasata komawa kitchen din dukda bawai tsaiwar ta gulma bace a'a kowa 'dauka zaiyi itace tana kuma tsoron Hajiya Jamila taji Abdulmalik ya mata magana ta zata ra'be take musu shikenan kuma abin ya zama abin magana a gidan tarasa wannan wanne labari ne kuma wanne tarihi ne dayake shafar rayuwarta har yakawo tsanar da Hajiya Jamila a duk cikin zuriyarsu sai tace tafi nuna musu dukda ita 'din ba zuriyarsu bace kai tsaye a'a aure yakawota zuriyar tasu amma tasan abune babba karon farko ta fahimci shine ya raba wancen ran mai muhimmancin gaske a zuciyarta shine yajawo tafiya mai nisan gaske a tsakaninsu da haryau babu waiwaye,tanbayar zuciyarta take yaushe zatasan labarin waccen rayuwar ta baya da tasan tabbas itace rusa waccen rayuwartata kuma take cigaba da shafar rayuwartata dumin da taji a kuncinta yasata sa hannu ta duba abinda tasan tabbas shine dama ta gani wato hawaye ,tuno waccen rayuwartata dama wadda takeyi yanzu shine abunda a kullum yaake kokarin da gula lissafe lissafen rayuwarta dama tunaninta kai tsaye zama tace Sallamar da taji AbdulMalik yayi kitchen din yasata saurin daidaita nutsuwarta ta goge hawayenta kafin ya karasa shigowa amsa masa sallamar tayi yayi murmushi ya karasa inda take tsaye tana kokarin cemasa "Yaya sannu da zuwa"Ya amsa da" yawwa Rufaida"kafin ya'dan ha'de rai yace "Rufaida"ta amsa da " na'am Yaya"cikin muryar raunana ta amsa masa"ya sake murmushi karo na biyu ganin yadda ta ru'de dagajin kiran sunanta yana mamaki haryau Rufaida bata canza ba daga yadda take,dukda gata da 'da harma ya kusa shekara uku ita kanta a shekaru zata kai 22 a yanzu haka koma da uku amma haryau yarintarta ta rashin son hayaniya da shiga abinda bai dameta da hakurinta yana nan yadai fahimci wannan halayyar a jininta suke"magana AbdulMalik ya cigaba dayi da cewa"yanzu Rufaida Fisabilillah dukda matsayin da kike dashi a gurin mu kinada wata bukatar ta wani abu kudi ko abinci ko abinsha ace bazaki tanbayemu kai tsaye ba muyi miki ba sai kin cemin zakimin transfer haba Rufaida duk abinda muka miki aike din tamuce bama bukatar ki bamu abin hannunki,muddin muna dashi idan bamudashi mumasu tsaya miki ne da karfinmu,bare ina tunanin dubu 2 zuwa uku ko ma fiye da haka ko Abdussalam kika tanbaya ko Hassan ko Hussain ba zata gagare suba haba Rufaida tuntuni kinsan kina bukatar wani karamin abu wato caza danni dai a a karamin abu na dauketa dan inada ita kamar abin banza a dakina tunda nasan zata kai 4 ko 6 duk wayoyin da nayi da caza dinsu a dakina ace bazaki ce na baki ba ko Umma da kike gudun taji kinsan ba zata hana na bayar da abuba tunda kinsan bata hana kabayar da abu bare ma kinada lambar Iowa a gidannan name tunani haba mana ki zama wayayya ta wasu fannonin mana"Rufaida da sai yanzu take ganin laifinta ne dan ita kanta amsar dalilin da zata fadawa Samiha Idan ta sake kiranta jin dalilin kiran nata bata samuntan bazatama iya fadar wancen dalilin ba dan baikai matsayin ka fadawa wani ba tunda akwai hanyoyi da dama na magance waccen matsalar,sai dai ita dalilin kin maganar gani take kamar zata matsawa mutanan gidanne kaita cewa ayima ayima ko abani abani ita bata saba dashiba mijintama da yarasu bata yimasa,bare tayi anan da surikartata bata raina abin magana ,Rufaida tace"Yaya kaya hakuri na daina"yace "Yawwa shikenan ina Yasir din ne ga alewa nan na siyomasa" Rufaida tace" yana can gurin karamar Auntysa Ummu kursum yana mata wasa"AbdulMalik yace "ok to ga naki sakon nan" ya bu'de ledar ya dauki wata ledar ya aje mai dan girman yana cewa bari nakaiwa Yasir nashi"Rufaida tace" Allah ya kara bu'di"AbdulMalik yace "Amin"kafin yace "au na manta ina Inna Lamin" wato mai tayasu aiki Rufaida tace "taje gidan Gwaggo Lariya" AbdulMalik da ya gane Gwaggo Lariyar kanwar kakarsu ce mace yace"lafiya dai ko"Rufaida ta visa da cewa "lafiya lau abincinta ne ba'a kai mata ba har 'yan makaranta suka tafi"yace mata "Ok ", da yasan halin Ummansu Hajiya Jamila sarai ko 'ya'ya zasu fasa gidan indai Inna Lami na gidan aiken duniya ita zata yiwa kaikace Inna Lamin sa'ar tace a haifema Inna lami ta haifi Hajiya Jamilar amma nuna ikon Hajiya Jamila kamar kanwar kanwartama ta maida Inna lamin sai kace ita ta bawa kanta daular da take ciki ba Allah ba itama Inna Lamin sai Allah ya bata Iran yaso hakan da haka yake cigaba da tunanin halayyar mahaifiyartasa datayi sanadiyyar kawosa duniya ,yana kokarin ficewa yaga Rukayya tsaye a bakin kofar kitchen din da Hajiya Jamila tace ta biyo AbdulMalik taji neman maiyakewa Rufaidan ha'de rai AbdulMalik yayi daya ganta cikin rawar jiki na nuna alamun rashin gaskiya tace masa" dama Umma ce tace na samo mata ruwa a kitchen"tsaki AbdulMalik yayi yace" tanbayar ki nayi abinda yakawoki koko yaya?" Rukayya kai ta girgiza alamun a'a wucewa AbdulMalik yayi Inda yana kallon Ruqayya ganin ya tafi yasata bin hanyar komawa falon danko kitchen ma bata waiwaya kai kawai AbdulMalik ya girgiza yana tunanin halin mahaifiyarsa mara kyau wato bata yarda da su ke'be shida Rufaida ',year uwarsa suyi fira ba sai ta sa anjiyo mata,ita batasan shi baya gudun fadan gaskiya ba koma gaban waye ba shifa aransa cewa yake baza'a masa abinda akayiwa yayansuba ya yarda yanzu za'ayi kaca kaca dashi danshi bazaiyi biyayya gurin abinda zak cutu ba kuma za'a cutar da abinda yakeso ba shiyasa yake da kudure kudure aransa da yasan bamai yunkurin hanasa tunda kudurin vamai cutarwa bane da haka ya karasa sashensu da sai ya kammala abinda take zai fito kaiwa Yasir alewarsa Ganin Ruqayya na waigegen bayan shigowarta falon dako sallama babu dan duk adabirce take yasa Hajiya Jamila tanbayarta"ke lafiya "Ruqayya da saida ta zauna a kujera tace" Umma ai Yaya AbdulMalik ne ya kamani ina musu la'be"Hajiya Jamila tace"to saime ince dai ba dukanki yaiba ko?"Ruqayya tace"a'a bai dokina ba,Gaskiya UMMA Yaya AbdulMalik baida mutunci matarsa zatasha wuyar zama dashi kafin tasan halinsa kai kodama tasani idan ta sake ta kuskure masa zatasha bala'i da masifa kings ko yadda yayi min yanzu" labari ta bawa Hajiya Jamila"Hajiya Jamila tayi murmushi tace"to kuma dake zamu aura masa"Rukayya ta zaro ido tace wa waini Umma ko wata dai?indai dan ta nice na yafe akai kasuwa dama dai waccen da yake nuna alamun yanaso Rufaida kika barsa ya aua kodan tasha wuyar sama dan in inbama itan da yakeso ba dawa yake zama yayi magana ta da'din rai mai tsawo sai dai ko Abba dan koke indai yaji kinsa abinda bai masa ba a hirar tuni yake tashi"Hajiya Jamila da ranta ya soma 'baci da maganar Rukayya tace mata "keni rufemin baki tunda kince bazaki aure sa ba saiki bar maganar ,sai shigo da yarinyar da kuke da banbanci maiyawa tsakaninku" Rukayya ta 'dan yatsina fuska tace haka nefa"amma 'kasan ranta addu'a take Allah yasa AbdulMalik ya aureta kodan tasha wuyarsa dan ita gani take ma tafi Hajiya Jamila tsanar Rufaida da kishi da ita tunda ta auri masoyin da taso take karaso har yau wato AbdulAhad shiyasa duk wannan tsanar da take nunawa Rufaida bata shafi Yasir ba dan har wayarta basa take yayi game da take ganin Yasir din kamar AbdulAhad dan ita kanta Rukayya batayi tunanin tanasan AbdulAhad har hakaba sai bayan rasuwarsa ta fahimci haka dukda dai kiyayyar da yake nunamata a fili amma tunaninta data samu ta auresa zai daina anata ganin kenan Hajiya Jamila ta katse shirun da cewa "ni waima na tanbayeki Rukayya wa Rufaida tace ya hanata saka caji nifa shiyasa kin ganni nan banasan zaman ire-iren Aliyu da Hauwa'u a gidan nan indai neman gurin zama ne sun iyashi an musu lecture dinshi" Ruqayya da maganar Rufaida ta fara isarta dan ita duk abinda bataso batasan aita surutunsa kai ko ma dason abin take batasan a dinga damunta da maganar baki ta ta'be tace"Umma bara na 'dauko wayata"daganan tasamu damar tserewa tabar Hajiya Jamila a falon da tunda gari ya waye ko tsinke bata daukaba bare ta wanke ba dukda ranar girkintane ga bayinan tasamu Rufaida da Inna Lami,da sanda ba Rufaida bata gidan wannan bautar ta Inna Lamice sai taga dama sukeyi tare idan taga an kuskure mata ta fara fada kaikace cinye mutum zatayi 'danye Rufaida jin shigowar Inna Lami ta kofar kitchen wadda take ta baya bata falon yasa Rufaida yi mata sannu da zuwa, Inna Lamin ta amsa da dan murmushi fuskarta tace "yawwa Rufaida kinsha wiki Rufaida yakamata kije ki huta ai tunda na dawo" Rufaida tace "haba Inna keda kikasha tafiya ai gwara kibarmin aikin tunda saura karashe shima don baki fadaminba zan tanbayo Umman Yaya AbdulMalik ya shigo kitchen din" Inna Lami tace Allah sarki amma dai kibari na karasa tunda kinga ni aiki name"murmushi jin maganar Inna Lami tayi tana tausayin Inna lami ta fara tsufa amma tana wannan wahalar ta yiyu rashi garesu shine ya janyo hakan kuma sai gashi ta ha'du da muguwar uwargijiya Hajiya Jamila tunda dai kusan aikin gidan da take kusan natane kuma Hajiya Jamilar ce ta samo ta,Rufaida da bayarda ta iya ganin yadda Inna Lamin take ta roqonta da take ji ba dadi ace babba na rokarta da haka yasa Rufaida bar rmata ragowar aikin kayan da AbdulMalik a siyomata ta dauka ta yi hanyar dakinta. SADIYA IBRAHIM KHALI✍🏽*JININMU 'DAYA* HalimatusSadiya Ibrahim Khali (Sadiya Khalii) Page9 Dady da ransa yakai makura gurin 'baci ya soma magana cikin bacin rai yace"Ra'uf abinda kakefa ya fara isata kace bazakayi aure yanzu ba na hakura na qyaleka yanzu kiri kiri ka nuna bazakaje gurin danginka ba Nigeria so kake kayafe zuwanta gaba daya shekarunka nawa da daina zuwa haba Ra'uf yanzu kai sai wani yayi ma fadan abinda yakamata kayi yanzu" Ra'uf yana mamakin fadan Dady akan abinda baikai yakawoba dan kawai yace bazaije Nigeria ba,toma shiko mai zaiyo a Nigeria a yanzu haka yake jin kansa kasar da aka saka masa ciwan da yake damunsa har yau da yasan duk sanda zaije wannan mikin sashen rayuwartasa zasu kara tuno masa abinda yake da tabbacin ku'di martaba duk ahalinsa suna da shi mai kuma yayi saura da har zasu rasa Samar masa farin cikinsa dan shi a yanzu ma koda zaije Nigeria ba wai don waccen rayukan zaijeba sai dai dan rayukan da duk sanda ya kwanta yake tuno su "Ra'uf ya takaita tunanukansa yace "a'a Dady kaima kasan yanayin aiki ne yake hanani zuwa Nigeria" Dady da ya'dan sassauta murya yace "ai kai ne agogon sarkin aiki dama,Ra'uf ko ka'ki koka so bakada kamar mahaifarka ko ta iyayenka amma Yaro ace kiri kiri kaki kasarka duka duka zuwannaka Indian duka yaushe" Ra'uf ya dan kara gyara muryarsa ya nutsu gurin fa'dar cewa"a'a Dady kaima kasan banda yanayin aiki babu abinda zaisa nace bazanjeba"tsaki Dady yaja yace"nikaga kakiyayeni da wannan dadin bakin naka kamar mace,tunda bazaka ba shikenan zanje da Safiyya kawai"shiru Ra'uf yayi yana tunanin halin da Safiyya zata shiga idan aka tafi da ita dan bawai sabawa tayi dasu ba sabodahantarar Safiyyan da suke yi shiyasa babu sabo tsakaninsu wannan shine abinda yasa ma bayasan zuwan Safiyya kwata kwata cikin zuriyar tasu",ya ce "amma Dady a kano za'a bar Safiyyan ko?" Dady da ya gane wancen tunanin nasa sai kawai ya share yace"kamar ya na barta a kano,ita bazataje cikin dangintaba a yanzu haka tanada kamarsu ne fadamin?"Ra'uf yace"a'a Dady"Ra',uf ya sauya maganar da cewa yanzu ranar yaushe zaku tafi?"Dady yace"sai zuwa wani satin nake tunani"Ra'uf yace"to Allah ya kaimu lafiya zan bada sako akaiwa Momy Hannatu"murmushi Dady yayi"yace toni tawa Momyn fa"murmushi shima Ra'uf yayi yace"ni fa tawa Momyn kawai zanyiwa kowa yayi wa momynsa"dariya Dady yayi yace"shikenan tunda abin 'yar hakane"Dady yace "yawwa Ra'uf kunyi waya da Malika kuwa ta fadamin akwai sa'kon da zaka bani na tahomata dashi" Ra'uf yace"Eh Dady ita Safiyya zanbawa sakon ta bata" yace to shikenan dadai haka suka cigaba da firar duk dai akan tafiyar har zuwa wani lokaci" Dan Allah kuya hakuri kuyi maleji✍🏽 SADIYA KHALI✍🏽*JININMU 'DAYA* By Sadiy Khali 10 WAIWAYE Ajin da ya hargitse da surutu kasancewar babu malami 'daliban wasu duk suna saman benci kowa surutu yake maza da mata ko ina an hada group group Rufaida da Samiha da suka hada rukuni na musamman su da suke a gaban layi jin Sallamar Class masters su yasa kowacce daliba rugawa cikin kiftawar ido bencinansu dan sunsan halin Sir Nura wato class mastern su amsa masa sallamar sukayi ya shigo shida wani bakuwar fuska da zai kusa tsarar Sir Nuran ne kallo 'daya Sir Nuran yayi musu ya fahimci basuda gaskiya gashi nan sai kokawa suke gurin gyara zamansu a benci kuma sunayowa birandar ajujuwan sukafara jiyo surutu kuma yasan daliban ajin nasa ne dan yasan duk sunfi rashin ji saidai a ajin bazaice dukansu ba amma dai ana masa kuka da ajin koma malamai,Sir Nura ya 'dan hade rai yana amsa gaisuwar da daliban ke musu shida sabon malamin bayan sungama ya kalli duk daliban ajin kafin ya nunamusu mutumin da suke tare yace"Wannan sunansa AbdurRahman shi 'dalibine a jami'ar BUK yazo Teaching practice yana shekararsa ta Uku a matakin karatu Yana karantar Biology Education yanzu haka...."yana cikin maganar ya jiyo sautin muryar wasu daga cikin daliban tsayawa yayi da maganar yanasan jiyo muryar su waye Rufaida da 'kafa take ta'bo 'yan bayan layin nasu da sune suke surutun alamun suyi shiru amma babu wacce ta fahimta Sir Nura da yagane Su waye masu surutun da busu sam ma yayi shiru ba Sir Nuran hankalinsu nacen wajen hirarsu ya kira sunayensu "Hauwa'u Umar ,Nasiba Abubakar,Ku fito waje Ku fadamin mai kuke fa'de" Cikin rawar jikin suka fito su biyun suna ayyano hukuncin da Sir Nura zaimusu dan baida mutunci ko 'daya a gaban allo suka tsaya suna kukkushe fuska,Tsawa Sir Nura ya dakamasu yace"wato saboda kun raina malamanku ina magana kunayi ko? Kuma bako ma saikun nunamasa halayyarku, to kufadamana muda sauran 'yan aji mai kuke cewa"hakuri suka shiga basa shi kuma ya kafe akan sai sun fadamasa mai yake cewa"nan Nasiba tace Sir cewa nayi sabon malamin da aka kawomana Yana kama da Yayan Rufaida Aliyu Bukar shine Hauwa'u Umar tace itama taga kamar"tsaki yaja Sir Nura bayan ya gama ji yace"Nasiba wato rashin mutuncin naki haryakai ina aji na kawo sabon malami kintafi can yimin hirar kamarshi da wani kin dauke hankalin masu San gane inda maganartawa ta dosa,yanzu haka ma ba haka kikace ba?"Nasiba tace wallahi Sir haka nace,kuma Hauwa'u kawai na fadawa yan aji da sunajin diramar da ake wasu Allah ya kara sukewa Nasibar dan dama duk tafi 'yan ajin rashin kunya da raina malamai da kyar ma idan hakan tace ba fara sawa malamin sunan banzan da dalibai suke sawa malamansu ba to yau ta hadu da Sir Nura dan sunsan yau Allah ne kadai zai kawo silar kwatar Nasiba daga hannun Sir Nura dan bashida mutunci bazai rangwantamata ba Sir Nura yace "su fita waje su tsaya harya fito sukarbi hukuncinsu"karasa maganar yayi da cewa shine zai riqa daukarsu Biology da ayanxu basuda malamin ya tafi karo karatu Sir Nura ne ya fito daga ajin yabar AbdurRahman yana musu tanbayoyi don yaji daga ina zaifara kasancewar dalinan SS3suke sune masu fita a shekarar Sir Nura yana fitowa daga ajin Sir ya kali su Nasiba yace" sakarkaru kawai da bususan darajar malamansu ba bako ma yazo saikun nuna halinku na rashin mutunci tun ba'aje ko ina Ba"nuna Hauwa'u Umar yayi yace" wato kema ina ganinki mai mutunci ashe kinbi sahun wannan sakaryar kawartaki"Nasiba da ranta ya fara 'baci kan kawai tace Sir AbdurRahman yana kama da Yayan Rufaida za'abi a fara cin mutuncinta ita sai yau ta kara tabbatar da rashin mutuncinsa yakai haka ita dai ana cemata"Acid and Base baida mutunci,sunan da aka sa masa kenan saboda tsabar rashin mutuncinsa a makarantar juyar dakai Nasiba tayi tana harare harare ya dakawa Nasiba tsawa da cewa "juyo ki kalleni mara kunyar banza wadda bata da tarbiyya cikakka" AbdurRahman da ya fito daga ajin yace masa Dan Allah ka kyalesu haka daganan Sir Nura ya kyalesu yayi gaba AbduRahman ya dubi Nasiba yace "yanzu abinda kuke baidace ba malami yana magana kuna magana bazasu bari yakai sakon da yakesan isarwa ba yanzu girmankune ace anfito daku waje ana ci muku mutunci bayan kuma duk kune kuke jawa kanku baza kuyi abinda malamanku suka ce kuyi ba" Nasiba tace"Wallahi Sir ba karya muke ba kuna kama da yayan Rufaida A Bukar"AbdurRahman ya girgiza kai ganin su bama tunaninsu sunyi laifi ba yace" waye muke kamar ne " Nasiba tace"wallahi Sir wani yayan 'yar ajinmuce muce Rufaida A Bukar "AbdurRahman yace"a'ina yake fa"Hauwa'u cikin zumudi tace Rijiyar Zaki farko mun dauka ma zakace mana kai 'dan uwansa ne"AbdurRahman yace"Allah sarki a'a kawai kama ce kinsan Khalid Bashar Majiya?"suka cemasa"A'a Sir akwai dai wata 'yar ajinmu a unguwar da yake take kai 'dan sane?"AbdurRahman murmushi kawai yayi batare da ya basu amsa ba ya 'Dora da cewa "amma zanso na ganshi mai kama dani 'din na gani ko haka ne"su Hauwa'u ganin karsu kuresa yasa busuce ya amsa musu ba dole dan daganin AbdurRahman 'dan manyen mutane ne kuma ga sunan mai kudin da aka sanshi sosai tunda manyan kamfanunuwa garesa ya kuma ce ko sun sanshi da gani yanada alaka da Khalid Bashar Majiyan sunmafi tunanin 'dan sane suka ce"wallahi Sir kuna kama daga nesa ma kai kace shine nan makarantar ma ya gama"yace " ok" yasa kai yabi Sir Nura dan shi bai fiye san surutu ba kuma ganin Sir Nura su shiyake jira Sir Nura ya dubi AbdurRahman da suke tafiya yace masa" ai yarannan idan zaka kwana nasiha basaji ko 'daya sunfiso aci nutuncinsu"murmushi AbdurRahman yayi yace"wallahi Sir ni dasuka ce ina kama da wanine ya 'dauremin kai"Dariya Sir Nura yayi yace"lallai AbdurRahman bakasan halin yarannan ba karya cikinsu ba'a magana"suka bada hira yana basu labarin halayyar dalibai ,suko su Nasiba suna shigowa ajin aka fara kus kus ana maganarsu Nasiba ta haye saman bencinsu Rufaida Hauwa'u takoma bencinsu ta zauna Nasiba tace kewai Rufaida bakiga kamar wannan gayen da yayanki ba "Rufaida tace " keni fa bangani ba"Hauwa'u da take baya tace"ke Nasiba ki kyaleta mana kema kinsan Rufaida batasan abin arziki ba,amma yanzu waye zaiga wancen malamin meyema sunanshi kuma ace basa kama da AbdurRafi",Samiha da maganar take cinta ,dan tasan bazasuyi da Rufaida ba, Samiha tace"ke Hauwa jiddah Allah nima nagani ,shiru dai kawai nayi"Rufaida dai tana jin kaya kaya dinsu batace komai ba dukda itamadai taga 'yar kamarsu amma bawai kama suke maiyawa ba amma tasan inta tayasu har atashi ana abu daya fitowar break shine ya watsa group 'din da suka ha'da Samiha ganin anfito Break tace "malama ki fito mufita mai take gaskiya"Rufaida ta dan tabe baki tace" gaskiya yau bazan fita Break ba,ke maii nayi ne na take gaskiya"Samiha tace "hakanan kiri -kiri kince mana sabon malamin nan baya kama da Yaya AbdurRafi bayan nasan karya kike"Rufaida tace" ai nasan halinku da cewa nayi suna kamar da tuni group din nan bai waste ba yanzu kuwa gashi bakowa amma aini ma naga kamar"Samiha tayi tsaki tayiwa Rufaida tace mata kuma"yar rain in hankali kawai,Samiha ta 'Dora da cewa"keni ban shakamiki labari ba"Rufaida ta maida hankalinta ga Samiha tace"shakamin naji kawata"Samiha tace"keni nafasa ma"Rufaida tace "haba Hassanata shakamin dan Allah naji" Samiha tace"ke wani gaye muka ha'du dashi jiya ke kinganshi kuwa kyakkyawa kalar namijin da nakeson aure dogo kyakkyawa"tsaki Rufaida tayi tana dokin jin labari amma Samihan ta tsaya shirmen banza tace"ni fadamin a'ina kuka ha'du yimin bayani naji kinki yimin bayani yadda zan gane "Samiha tace " aike bakya cin ribar zance dama sai kin nuna kin gaji"Rufaida tace"naji dai nidai fa'damin" Samiha tace"na fito Momy ta aikeni gidan su Fahat Hassan na nan ajin"Rufaida tace"Eh naji dai na gane jeki zancenki"Samiha tace"gidan Aunty Ummi na bayani gidanmu a kofar gidan muka ha'du ya tsaidani da kamar bazan tsayaba sai naga baikamata na masa hakaba tunda naga Hanif din Aunty Ummi a hannunsa ,shine na tsaya,muka gaisa,Har yake shaidamin yana sona ganin bankulasa ba shine ya bini gidansu Fahat yacemin Auny Ummi cousin dinsa ce Baban Aunty Ummi da mamarshi wa da 'kanwa ne ,yace yana ganina a unguwar idan yazo yace har a gidan Auny Ummi ya taba ganina ni dake,danshi tunaninsa mu 'yan biyu ne ni dake amma zai shiga mota ya tayar zai fitamu shiyasa bamu gaisa ba dan alokacin mun shiga gidannevgaskiya gayen nan yayi a kasar waje UK yayi karatunsa yace min zaizo gidanmu yau idan ya shigo unguwar da wuri dan yace bays rabo da unguwar"Rufaida tayi murmushi tace "kai amma kawata na tayaki murna Allah ya tabbatar da akkhairi,saidai kibi a hankali karki cika nuna kinasansa ,kuma karki sakankance dashi sosai,ki rika abu da wayewarki" Samiha tace "haka ne " year uwata amma duk ina kikasan wannan sirrikan soyayyar keda bakyayi?i"Rufaida tace"a gurin su Nasiba kinmanta natafi yajin aiki bencinki"Nasiba Shehu Abubakar India batun soyayyah ne ko a ajin azo gurinta yanzu haka ma bikinta za'ayi"Samiha tayi dariya danta tuna sun ta'ba wani fa'da da Rufaida tabar mata bencin Hauwa'u Umar ta koma Samiha tace "kai Rufaida aji tsoron Allah bakya mantuwa kinsan da yanzu ne bazanyi fa'da kan yoghurt ba" Rufaida tace"naga alama fa nidai na baki shawara kibi a hankali ki tsare mutuncinki a gurinshi karki cika nunamasa sosai"Samiha tace"to shikenan kawata,Amma nifa koshi zan aura tare za'ayi bikinmu nidake banaso nayi aure nabark"Dariya maganar taba Rufaida ma tace"banda abin Samiha ai da Allah nima yakawomin kusan hadawa ma za'ayi,yanzu dai Da yaya Saudat za'a ha'daku tsaki Samiha tayi tace "kewai Yaya Saudat zan zauna jira inama saurayin nata ya ta'ba zuwa gidan mu kurum daga haduwa a bikinsu Yaya Samina tace lallai shi take so,ke kin ganshi kuwa kato dashi da gani ma ya fara tsufa" Rufaida tace"kai Samiha banda sharri fa?"Samiha tace"Allah da gaske nake dandai bakije Sokoto bikinba da kinganshi kato tsawo da kiba"Rufaida tace"koma dai ya yake ita tanasan kayanta bare ma dai nasan bahaka bane"Samiha tace"au shigarwa Yaya Saudat yau kike kuma"murmushi Rufaida tayi tace"Eh mana"da haka dai suka kara taba hira har aka dawo break da sabon malaminsu ya shigo Sir AbdurRahman ganin sabon zuwane yasa duk ajin akayi shiru sai yayi tanbaya idan sun sani su bashi amsa don basa so daga zuwan AbdurRahman ya fara fahimtar halinsu gasu Nasiba sun gwangwadamusu cewa shi 'dan babban gidane shiyasa suka fara ganin girmanshi dan Khalid Bashar Majiya ba laifi kam yayi suna a cikin garin Kano. SADIYA KHALI✍🏽*JININMU DAYA* By Sadiya Ibrahim Khaliy(Sadiya Khaliy) 11 Rufaida Aliyu Bukar Hafaffiyar garin Zariya ce da aiki ya dawo da mahaifinta Aliyu Bukar cikin garin Kano yana aiki a babbar makaranta wato jami'ar Bayero University dake Kano wato BUK inda yake zaune a gidansa mallakin kansa dake Rijiyar Zaki shida matarsa 'daya wato Hauwa'u da suke da yaransu shida AbdurRafi shine babba sai Rufaida mai bi masa sai AbdurRashid,Rumaisa,Rafi'a,Ra'is shine karaminsu. Samiha Hashim Sarki 'kawar Rufaida ce tun daga primary har zuwa Secondary da suke tafiya tare aji 'daya benci 'daya dalili mai karfi da ya jawo amintarsu harta zama sun zama kamar 'yan uwa hatta iyayensu wasu 'yan makarantar tasu ma 'daukarsu 'yan uwa ne Samiha hafaffiyar garin Sokoto ce aiki ya maido mahaifinsu Kano Unguwar Nasarawa GRA da mahaifin nasu yake kwararran likita a asibitin Nasarawa matarsa 'daya Hajiya Maryam da yaranta Samira,Samina da sukayi aure,Samir,Saudat,Samiha,Samin,Samima.da a yanzu haka Hajiya Maryam ta aurar da 'ya'ya biyu Samira da Samina kowacce da 'danta 'daya,Sai Samir da yake aboki ga AbdurRafi da suke babbar makaranta Jami' a Yusuf Maitama Sule Northwest dake nan Kano wannan kenan Samiha da take kokarin sa'ba Jakarta a baya ta dubi Rufaida tace "malama ba kyaji antashi kuma kinsan yau juma'a a gidanku zanyi hutun karshen mako" Rufaida da murna batasan sanda tazari jakarta ba saboda murna Aminiyarta zatayi hutun karshen mako a gidansu mikewa tayi tana cewa"Nifa bansan dagaske kike ba"Samiha ta harareta tace"aikema kinsan bana miki karya irin wannan"da haka suka fito ajin da suka hadu da sauran 'yan class dinsu suna firar yadda Sir AbdurRahman ya iya koyarwa suna gane lesson dinshi da shine malaminsu na karshen period yau da wannan firar suka fito zuwa kofar makarantar inda suka hangi motar Abbansu Rufaida dasu yake jira suka karasa sunayiwa abokan tafiyartasu sallama"sauran 'kannen Rufaida har sun shige bayan mota su Rufaida gaban mota suka shige Abba da yake kokarin tada motarsa ya kalli Samiha da take gaishesa ya amsa yacigaba da cewa"wato Samiha mungane saboda kawarki kike zuwa gidanmu duk hutun karshen mako kike yi mana acan?"murmushi Samiha tayi kawai dan tagane Abba ya gano saboda Rufaida take zuwa gidan Abban hutun karshen makon dan ita tana matukar son kawarta da a yanzu take jin Rufaida kamar 'yar uwarta ta jini dan ko Saudat da Samihar ke binta bata saba da ita kamar Rufaida ba ,Samiha ta canza maganar tace "Abba ya maganar Jamb 'din namu" Abba da ya maida hankalinsa ga tuki yace "oh Samiha anfara ne"Rufaida anan tasa baki tace" Wallahi Abba ba'afara ba Samihan ce batada hakuri kofa yau saida ta tanbayi wani malaminmu" Samiha tace" eh mana dole kice banda hakuri tunda ke bakyasan cigaba da karatun yanzu idan bama tunawa Abba har a gama bamuyi ba"Rufaida tace"ba wani nan wallahi ai kinsan Abba baya mantuwa a harkar karatu barema harda Yaya Saudat za'ayi kinsan tunda tayi candy bazai manta ba,ke dai azalzalar kice,"Abba murmushi kawai yake yana jin firar tasu yadda sukeyi wanima sai ya rantse ya da kanwa ne ko 'yan biyu saboda halayyoyinsu da sukazo daya a fisgema har yanayi suke da juna yanason wannan abotar yaran nasa da ta zama yan uwantaka bama gasu ba harga su iyayensu sun hada aminci tsakaninsu kai kace 'yan uwa ne a yanzu haka idan ba har an baka labari ba,Abba yana saukesu d ,yace zaije gurin abokinshi yaje ya dawo su fa'dawa Umminsu a dawo lafiya suka yi masa ya amsa da amin yasakan motarsa yabar gidan su kuma suka shige cikin gidan a fall suka sami Ummi suka yi mata sannu da gida Ra'is mai shekaru biyu yana ganin Samiha yayi gunta da yasaba da ita saboda yadda take masa wasa daukar Ra'is 'din tayi ta haye dashi sama tana mass wasa yana dariya Samiha kaya kawai ta canza ana Rufaida dan girmansu daya hakama kayan sawarsu iri daya ne yawanci saboda yadda iyayensu suke aminta sosai kaya ma kusan tare suke dinka musu Rufaida data fito daga bandaki da towel jikinta ta watso ruwa ta kalli Samiha tace "ya haka ba zakiyi wanka bane" Samiha ta dafe cikinta tace"yunwa nakeji nayi anjima "Rufaida tace" ba wani anjima ,bakyasan yin wanka sai dole kike 'daya badan kinso ba haka Ahmad 'din zai aureki ki bakyason yin wanka wallahi ya daukeki kazama"da Rufaida da tasan sunan Ahmad saboda labarinshi da Samiha take basu nashi kullum indai sun ha'du a makaranta to indai kana ajinsu sai Kasan labarin Ahmad saurayin Samiha a bakin Samihar "Samiha tace to"yi maza ki fadamasa"Samiha ta fice tana jiyo dariyar Rufaida Samihan kai tsaye kitchen ta nufa ta samo abincin rana da miya taliya kawai tagama sai miya da take kan wuta da shigowarsu Ummi ta zuba markadan kayan miyan gurin datasan ana aje ragowar miya ta bude ta diba ta fito kai tsaye babban falo ta karasa bayan fitowarta kitchen din da ta samu AbdurRafi shi ka'dai ta masa sallama AbdurRafi ya amsa mata ya maida dubensa ga kallon ball din daya kori kannensa a falon yanayi ganin ancanza masa tasha ya juyo ya 'dan kalleta da ta zauna a kujerar dake gefen tasa ta tankwashe kafafunta akan kujerar ga remote tana dannawa tana lalubo tashar da takesan kallo yace cikin ha'de rai " waike Samiha ina kallo ya zaki canzamin tasha"Samiha tace"ai kaine Yaya AbdurRafi ko gaishe da nayi kaki amsawa kana can hankalinka yana kan kallon ball"AvdurRafi yace"ke Samiha banafa son karya a ina kika gaishe ni sallama kawai naji kinyi,ke dai kawai kinzo ki takurawa mutane indai kikazo gidan mutum bashida kata'bus"Samiha tace"kai Yaya AbdurRafi gaskiya bakayimin shaida maikyau ba amma bakomai nakusa daina zuwa ai"tsaki AbdurRafi yayi yace"yaushe ai sai dai in anyiwa wadda kike zuwa gunta aure ko an yimiki"Samiha tace"kai nifa Yaya AbdurRafi kadaina maganar idan munyi aure zamu rabu da Rufaida ga gida ga gida zamu zauna"AbdurRafi yace"Ku auri miji 'daya kawai zaifi"Samiha tace"kai Yaya"AbdurRafi yace"eh mana zaifi ai"Samiha ta canza firar da cewa "wai niko Yaya Rufaida ta baka labarin wani saban malaminmu da kuke kama yazo TP da ake turo masu Degree?" Tsaki AbdurRafi yayi yace "ke nifa kinga banasan shirme wallahi ni ka'dai Ummi ta haifa kuma ni ni ka'dai ne bada wanda nake kama a duniyar nan ma gaba 'daya kawai kuje Ku jajubo wani bakusan shi waye ba kuce ina kama dashi?" Samiha tace"haba Yaya AbdurRafi wannan dogon turanci haka daga nace kana kama da wani Allah ya baka hakuri,kuma ka masan shi waye 'dan Khalid Bashar ne" AbdurRafi yace"ke nifa Samiha ki dainamin maganar shi banaso,dama dan haka kikashemin kallon ball din danake"Samiha tace"Allah ya baka hakuri,amma nidai Allah naga kamarku"AbdurRafi ya mike yace"sai kiyi tayi ni kinga tafiya tama yayi gaba ya fara tafiya"Samiha da taga yana kokarin ficewa a falon da taga bayaso ace yana kama da kowa ta tsokanesa tana cewa "Yaya AbdurRafi Allah kuna matukar kama" murmushin mugunta yayi yana tuna abinda zai mata ya karasa ficewa daga falon gaba daya"Samiha ta bishi da dariya Ummi data shigo falon tana lallashin Ra'is da yake kuka taji Samiha na dariya tace"dariyar me kuma kike kuma kike kinje kin bawa yara yaro na sun yarmin dashi shine kike dariya ko?"Samiha tace"Ayya Ummi wallahi Rumaisa ce ta anshe shi da muka hau sama"Ummi Hauwa'u tace"to gashinan dai kin basu yarona sunyi fa'da da Rafi'a sunyarmin dashi,na 'daukama dariyar kike masa"Samiha ta anshi Ra'uf a hannun Ummi Hauwa'u tana lallashinsa tace"Haba Ummi ya kinsan nida Ra'is da amana,Yaya AbdurRafi nakewa dariya saboda nace yana kama da wani malaminmu yake jin haushi bayaso ace yana kama da wani"Ummi Hauwa'u tace"au wai saboda ance yana kama da wani yaji haushin Allah ya kyauta"Samiha tace"Amin dai Ummi" Samihan ta fara lomar abincinta data zubo tana bawa Ra'is Ummi ta wuce kitchen ta cigaba da aikin abincin da take Abba Aliyu ne yashigo gidan da motarsa ganin AbdurRafi ya budemasa gate "yace ya shigo ya shirya su tafi masallaci kasancewar yau Juma'ah yana shigowa falon yayi sallama,Samiha ta amsa masa takuma ce "Abba sannu da zuwa yace" yawwa Samiha ina sauran mutanan gidan" Samiha tace"Suna ciki Ummi kuma na kitchen"Ra'is da yaga Abbansu ya sauka daga hannu Samiha ya tafi gurin Abban nasu,Abba Aliyu ya daukesa yana cewa"nifa Ra'is shirin masallaci zanyi amma bari na tafi dakai na bawa ko Rufaida kai ne ko Rumaisa tunda kunfara batawa da yayartaka" murmushi Samiha tayi kawai ta harari Ra'is da haka Abba Aliyu yayi saman bene dashi 'dakinsu AvdurRashid kai tsaye Abba ya shiga yace ma AbdurRashid yayi shirin masallaci ya bawa Rumaisa Ra'is daya sameta a falon saman AbdurRashid yana fitowa daga dakinsu saboda tafiya masallaci yaga Samiha a falo da kwanon abinci a kan teburin tsakiyar falo tagama ci tana lashe hannu yace" uwar ci 'yanci kawai"Samiha tace"naji dai da ulcer ta kama nifa"AbdurRashid yace"ba wani aike cinki yayi yawa kuma ci babu kuf kullu jiya i......"jin karar takalmi yasa AbdurRashid kin karasa maganr yamayi had ficewa daga falon kar wani ya shigo yaji yana yiwa Samiha rashin kunya Samiha tace zaka dawo kasame nine mara kunya ganin AbdurRafi ne ya shigo falon ya wuce ko Samiha baikula ba tana kunshe dariyarta ganin wai shi ala dole yayi fushi da ita Rufaida tana zura kaya barci ta haye gado barci ya 'dauketa kasancewar basa taya Ummi abinci da rana saboda makaranta. SADIYA KHALIY✍🏽*JININMU 'DAYA*♦️ By Sadiya Ibrahim Khaliy💞 Page 12 Sallamar Samir shi ya dawo dasu Rufaida daga cin abincin ranar da suke tare suka amsa gaba 'dayansu Samir ya gaisheda dasu Ummi Hauwa'u da Abba ALIYU sauran yaran suka gaishesa ya amsa yana murmushi Rufaida da bayan gaisuwar tace "lah yaya Samir yau Kaine a tafe a gidanmu hala makuwa kayi" AbdurRashid yace"Nima "yaya Rufaida na dauka makuwa yayi" Samir ya harari AbdurRashid yacewa Rufaida "ke dai bari Rufaida wannan yarinyar ce tasa saurayinta yazo gidanmu kuma tasan ba'anan take weekend" Abba Aliyu da Ummi Hauwa'u suka ce ai dama munsan ba'a aikin banza a kano banda haka yaushe rabon duniya da ayyaraye"Samir yace "wallahi bahaka bane Abba bahaka bane mutumin nawane AbdurRafi shima baya zuwa inda nake tunda aka samu hutu"AbdurRafi yace" kai Samir kaji tsoron Allah zuwa na nawa nayi gidanku"Ummi Hauwa'u tace kanku dai akeji"ta dora da cewa"AbdurRashid jama yayan naka kujera mana ya zauna yaci abinci shima Samir ya zauna yana cewa" Yawwa AbdurRashid"ya dora da cewa Ummi kamar kinsan banci abinci ba Ahmad yazo Momy tace nataso na rakosa gurin Samiha kinganni ma Ummi bako waya bare key din mota a hannu na sai dai idan mutumin nawa zai kaini gida ya fada yana kallon AbdurRafi da yagama yiwa karya"ganin baice komaiba yafara lomar abincinsa da Ummi ta zuba masa,Abba Aliyu yace "Hauwa'u baki tanbayesa ya budema bakon falon baki"Samir yace "Eh Abba na budemasa" Abba Aliyu yace "yawwa Samir ,Hauwa'u azuba ruwa da lemo akaimasa" Ummi Hauwa'u tace to, da haka Abba Aliyu ya cigaba dacin abincinsa"Samiha da take zaune tana ji duk abinda suke fada bata sa baki ba da tunda aka ce mata Ahmad yazo take cin abinci hankalinta raba da rabi ta qagara Abba ya mike taje taga sahibin ran nata,Jin maganar Ummi yasata tsaida tunanin nata da Ummin ke cewa "Ya haka Samiha ko bakyacine kin koshi kiyi maza ki gama kinga yaron ke yake jira"AbdurRashid yace" Ummi ai dole ma ta koshi ta ci fa 'dazu bandana Yaya Samiha ci gare ta"Ummi tace"AbdurRashid bafa nasan raini kaike kawo abincinne" ya girgiza kai AbdrRafi jin haka yasa sh tuno abinda tayi masa dazu yasa shi cewa"wallahi Ummi Ba Karya AbdurRashid yake ba kifadawa Abba ya karo buhun shinkafa"Ummi ta gallawa AbdurRafi harara,Samiha jin hakan yasata hade rai ta mike ta fara barin falon ta haye sama"Yara ne sukayi dariya Rufaida tace"wa yaran dama kofar guduwa take nema Abba Aliyu da ya gama cin abincinsa ya mike ya bar falon a ransa yana kara jin san iyalensa,da kuma matarsa Hauwa'u ha'ki'ka yayi dacen samun mace tagari, Ummi ta shige kitchen ta shirya kayan da za'a kaiwa Ahmad falon baki ta kira AbdurRashid ya mikamasa Rufaida upstairs saman bene tabi Samiha dakinsu ta tura ta shiga da sallamarta inda ta sami Samiha tanata cacca'ba kwalliya kai kace gidan biki zata"Rufaida tace "Samiha wannan kwalliyar fa harkinyi wankane kinsan dazu fa baki yi ba" Hararar Rufaida tayi tace"waike Rufaida ni kwado ce kamarki zantayin wanka ina laifi nayi daya tunda nayi da zan tafi makaranta ai ya isa" Murmushi Rufaida tayi daga bisani tace mata"ai wanka jindadin jiki ne,kuma ai kinsan fa munshawo rana a makaranta,kyaeje gabansa kita warin rana" Tace"ke ni banshawo wata rana ba,inma nasha haka zan fita,tunda turare yana magani ai" Rufaida tace "nufinki turare na zan baki ki fesa kin da'de wallahi" Samiha tace"kwantar da hankalinki nima inada turaren ai"jakar makarantarta dake kan lokar gado Samiha ta zage ta de'bi turare ta feshe jikinta dashi ta bude Sib ta samo mayafi mai girma kalar kayan jikinta ta yafa" Rufaida da take tsaye tana kallonta Samiha ta kalleta tana bu'de kofa ta kashe mata ido tace"aini ba'ayimin gatse"Rufaida tace" naji kimaza ki tafi kinsan ajan aji ake barin arha,kuma wannan kashe idon ai Yaya Ahmad zaki yiwa"Samiha tace "kuma fa hakane,bari na wuce na tafi said kinzo gaisheshi ko?" Rufaida tace"bafa zanzo ba kigama fa'damin magana"Samiha ta dawo ta dafa Rufaida tace"haba kawata Yar uwata ki taimaka kizo"ganin Samiha zata cigaba da 'batawa kanta lokaci tace"zata zo su gaisa"da haka Samiha ta fice ganin Abba a cikin falon suna hira dasu Samir yasata dan jin kunya ta koma da baya ta tabi ta kitchen zata fita tanan ta wuce Abba Aliyu da idonsa na gun Samihan yayi dariya inda ya tuno halayyar matarsa Hauwa'u tana kama data Samihan amma azamanin baya tunkafin aurensu can yake tunowa sai gashi Rufaida gudan jininta bata biyo cakwakkwayyar Hauwa'unba sai Samiha da babu dangataka ta kusa kota nesa tsakaninsu,Dariyar da Samir keyi ita tadawo da Abba Aliyu daga wancen tunanin nasa"Abba Aliyu ya dubi Samir yace "lafiyarka kuwa Samir" yace "Abba lafiya ta kalau,Samiha ce data ganmu a falo taki wucewa tabi ta kitchen zata wuce tayi arangama da Ummi " murmushi Abba Aliyu yayi yace"kasan yaran suna da kunya duk cakwaikwaiwar Samiha tana da kunya diyartawa"Samir da baice komaiba Dan ya fahimci Abba baisan rashin kunyar da Samiha keyi a gidansu ba akan Ahmad"Abba Aliyu ya tsaida shirun nasa da cewa"Muna magana da Abbanku da muka hadu shekaran jiya yace min yaron ya turo magabantasa to bamu gama maganar ba aka kirani a waya....."Samir yace"Eh wallahi Abba yazo tsaida rana za'ayi Abba yayi bincike akansa baida Matsala babansa shine sabon Commissioner of police a Zariya Road suke da zama"Abba Aliyu da yaji dadin Labarin kamar akan 'diyarsa ya faru ,danshi dama yadda yakeson Rufaida haka yakejin Samiha har aransa baiji bakin ciki ko kyashin wannan labarinba,yace cikin murmushi mai yalwa a fuskarsa"To Masha Allah,ai kaga idan AbdurRafi zai ya tashi tafiya police (Dan sanda)ai bazamusha wuya ba muna da hanya"AbdurRafi da sai yanzu yasa baki yace"Abba yanzu kaima har dakai a tonan nawa" Samir ya kunshe dariyarsa"Abba Aliyu yace"ai kaine Rafi abu ka'dan kace bakaso har kannenka sun ganoka tsokanarka suke da abunda bakaso,kana girma kana kara rashiin wayau"AbdurRafi yace "ni dai Abba Dan Allah a bar maganar ,kai kuma da kake kunshe dariya ka tafi mana kai ga hanya nan" yacewa Samir,Samir,yace"Allah ya huci zuciyar manya musu tsoron training din 'yan sanda"daganan Samir ya gudu ya bar falon yana dariya dan yasan halin abokinsa sarai indai kan ace ya tafi police ne zaku iya yin baran baran,can majalissar unguwa Samir ya shige kasancewar yasan 'yan unguwar wasu saboda akwai abokan karatunsu acan nan ya zauna suna taba fira"AbdurRafi shima binsa yayi yana tunano rashin mutunci da zaiwa Samir saboda yadda ya rainasa dan kawai yace bayason dan sanda saboda training dinsu yanada wuya shiko riqe wannan bindigar aka barshi da shi ai anbarsa da aiki,Abba Aliyu yayi murmushi AbdurRafi da Samir fadansu sai su ba'a shiga koma ka shiga sabaka kunya ya cigaba da kallon da yake a TV Rufaida ko Samiha bata jima da fita ba tasa hijabi mai girma tabi Samiha su gaisa da Ahmad a falon ba'ki ta samesu ta gabatar da sallama suka amsa mata ta shiga" ta zauna kusa da 'kawartata Samiha da take a kujera mai biyu shikuma yana zaune a kujera mai 'daya an ajemasa lemuka a plat da ruwa datasan duk aikin Umminsu ne inda Samiha ta tsiyaya ruwa a kofi Rufaida tace"Yaya Ahmad ina yini"ya 'danyi murmushi yace"lafiya kalau Hussaina,ya juma'ar?" Tace masa" Alhamdulillah Yaya,wato bazaka daina cemin Hussaina ba"wanda tun farkon gaisawarsu da Rufaida da taje gidansu Samiha yace ita Hussainar Samiha ce saboda yadda take basa Labarin Rufaida kona Yaya Saudat bata basa haka,dan shi 'daukarsa suna da ala'ka ma,danshi har kama yaga sunayi,"yace mata "Eh mana ai Ku 'yan biyu ne idan akaga wata za'aga Zahra gashima kuna kama ma inda za'a kara tabbatarwama" ya fadi hakan da sigar zolaya"Rufaida tayi murmushi tace"Samiha kinji fa yaya Ahmad da wani zance"Samiha tace"kema dai kya fa'da nibanga wata kamarmu ba ko 'daya"Ahmad da har yanzu bai fahimci alakarsu ba yace"dama haka zakuce"Rufaida tayi murmushi tace" Ai hakane ma"da haka suka sake ta'ba hira ka'dan sannan Rufaida ta fice daga falon ta basu guri suyi firarsu.*JININMU DA'YA♦️* Sadiya Khaliy💞 Page 13 Samiha ta shigo 'dakin ko sallama babu ta fada gado tareda cire mayafin kanta Rufaida tace" ke lafiya kuwa"Samiha tace"bansaniba wallahi Rufaida Ahmad ya cuceni"Rufaida ta jinjina kai tace mai kuma yayi miki bawan Allah"Samiha ta ta'be baki tace"kinsan tun kwanaki da yacemin zai turo a tsaida magana asa rana"nace masa ya bari keda Yaya Saudat kuma Ku samu miji tukun"ita da Rufaida abinda dariya ya bata ma,Samiha tace"au dariya ma kike ko"Rufaida tace"Ai abin nakine abin dariya banda abinki mainene dan ankawo kudinki muba'a kawo mana ba,kinsan komaifa lokaci ne,kafin ayi naki bikin sai kiga munsamu namu mazajenmu,"da haka dai Samiha tasamu kan Samiha dan ita Samiha dagaske bata yarda ba sai sun samu nasamu mazajen Ahmad ya jira saboda ayi bikin nasu tare Ranar da Weekend ya kare Monday litinin su Rufaida suka shirya Abbansu da zai shiga Makaranta suna wani taro a BUK din ya tsaya ya saukesu a Al'AZHAR har bakin gate din makarantar ya kaisu inda hankalin Samiha ya tafi a motar da aka sauke Sir AbdurRahman motace maikyau da tsada drivernsa ya tsaya ya fito Samiha tace"Abba kalli malaminmu maikama da yaya AbdurRafi"Abba Aliyu da ya 'karasa parking ya dubi AbdurRahman kasancewar ya 'dan juyar da fuska bai ganshi sosai ba ya daiga bayansa saida ya sake kallonsa yaga fuskarsa shidai baiga wata kamarsu ba sai dai a fisge"Samiha tace "yawwa Abba ka ganshi ko?yace mata " Eh a ina yaron yake kunsan shine"Samiha ta cemasa"Khalid Bashar way yake kusa da gidanmu wasu ma cewa suke 'dan sane,TP yazo makarantarmu inda kake lecturing yace yake karatu BUK" Abba Aliyu yace"ok,Allah sarki ba lallai nasan yaron ba akwai daliba da yawa kinsan kuma department department ne "tace " eh hakane"da haka suka fice daga motar sauran yaran suna cewa sumafa basu ga kama ba,Abba Aliyu da shima baiga kamaba yaja motarsa ya bar harabar makarantar,a kofar Gate 'din suka ci karo da Sir Samir suka gaishesa suka shige tare da ya shaida fuskokinsu yaran ne ma baigane ba,saboda baya daukar 'yan ajujuwansu,yace"Health prefect da Labour ne ashe"Rufaida tayi murmushi" Samiha tace"Sir yanzu Abbanmu ya saukemu a mota da har zan kwala ma kira ku gaisa"Rufaida da take zungurar Samiha tayi shiru taki banda shiga ukun Samiha meye na fa'dar hakan bandama koyarwa daganin wannan matashin AbdurRahman zaiyi ji dakai,kuma ga iron motar da aka saukesa da gani dan masu dashine sosai,amma Samiha sai zaqalewa take,tana nema ta wuce gona da iri"AbdurRahman yace"Aiya wani lokacin zamu gaisane"Samiha tace "hakane " tabar maganar daga haka kar dalibai su hangosu a yimata wata fassarar,dan tasan halin 'yan makaranta" Ana gama a assembly malamin biology AbdurRahman ya shigo yafara koyarwa nan aka aiko wata daliba ta kira Rufaida da sallama 'dalibar ta shigo ajin inda AbdurRahman ya tsaya da koyarwar ya amsa 'dalibar tace"Sir ,Sir Nura yace Rufaida Aliyu Bukar tazo"AbdurRahman yace"to kice tana zuwa"ya dawo ya kalli 'daliban yace"wacece Rufaida Aliyu Bukar"Rufaida ta mike tace"Sir gani"AbdurRahman yace "au Health prefect dama kece Rufaida?" Tace masa" Eh"yace "ok,kije Sir Nura ke kiranki kiyi maza kidawo kinga lesson muke"da haka Rufaida ta fito daga bencin tana cewa"to"shi ko AbdurRahman zama yayi akan kujera ya huta kafin Rufaida ta dawo ya cigaba shi sai yanzuma ya tuno Rufaida itace su Nasiba sukace yana kama da wani yayanta,shi kasancewarma baidamu da sabgar ba yama manta gaba 'daya tundaga ranar baisake tunowa ba ,saida ya dawo ya cigaba da lesson 'din harya gama ya fita ya kira Nasiba"ya bata wani class work daya basu ta rubuta a allo period ta gaba da malamin period din baizo makarantarba zaizo ya duba"daliban da sai zagin Sir AbdurRahman suke don ya fiye takura daga fita abada wani aikin aji suna mita suka rubuta suka fara duba test Book 'din biology ita Rufaida key point kawai ta duba tayi taba Samiha tayi ita kanta Nasiba zagin AbdurRahman tafarayi duk shirin da suke da AbdurRahman din don kusan a ajin sunanta yafi riqewa Periof nashiga yana shigowa ajin ya fara da duba litattafan daliban benci benci matanma sunfi mazan kokartawa bencin su Rufaida ya karasa da shine ya bari na karshe duk sunfi sauran kokartawa dan da marking zaiyi sune suka cinye duka tundagan suke 'dan shiri dan shi AbdurRahman yanaso yara masu kwazo Samiha har number dinshi gareta da Ahmad ya kawo mata wayarta mai tsada ba laifi infinix ce da a yanzu haka ansa rana da sunyi candy za'ayi bikin dukda yadda Samiha taso a hada bikin koda na Yaya Saudat ne da yanzu haka tasamu saurayinta mai sonta cousin dinsu a sokoto Mujahid dan tuni ta hakura da wancen da suka hadu a biki dan akarshema wayoyinsa daina shiga sukayi,hakanan Yaya Saudat ta hakura da jiran gawon shanun da take ta amince da Mujaheed Abba Hashim mahaifi ga su Samihan shima kansa ya amince da hadin auren kuma abin yayi masa dadi sosai itako Momy Maryam mahaifiyarsu Samihan da Mujahid din yakasance 'dan yayanta tamafi kowa murna da wannan hadin AbdurRahman ranar da zai gama TP dinsa haka 'yan ajin duk suka ji ba da'di kasancewar sunsan ba lallai su sake cinkaro da Shiba koda a hanya ne don su dai sunsan haduwa da iyalan Khalid Bashar da kamar wuya dan Nasiba Shehu da Hauwa Umar sunada ya kinin gaskiya suka fada musu dukda yawanci yan makarantar 'ya'yan masu da shine amma wasu sunfika kaima kafi wasu sunfika haka rayuwar ke tafiya. AbdurRahman ya kalli su Nasiba gaba 'daya su shida group 'dinsu harda su Rufaida da yake ji a ransa duk ba dadi saboda yadda ya fara sabawa da yaran da yake jinsu har a ransa gasu masu kwazon karatu donshi ko 'yan ajin basu taba masa rashin kunya ba ko zaginsa sai dai ko a bayan idansa shiyasa yake ji babu dadi bayan ya fito daga ajin nasu inda yake tsaye birandar ajin nasu sukuma sun tsugunna a gefe yace"Nasiba Shehu ya maganar karatun naki ne"tace masa"Sir Jamb zamuyi nidasu Zainab Farouk,da Hauwa"AbdurRahman yace"banji kince su Rufaida da Samiha ba"Nasiba tace "lah sir dama banfa'dama su Samiha aure zasuyi ba" ita da Rufaida"Samiha tace"Sir karya fa suke"AbdurRahman yace"to inma shine aiba wani abu bane"Hauwa'u tace"wallahi Sir bama karya muke ba itafa Samiha bayan candynmu da sati biyu za'ayi bikinta,itace dai Rufaida bamu sani ba"AbdurRahman yace "hala wannan yayan Rufaidan da kuke cewa muna kama zasuyi auren zumunci dashi da Samihan,gashima har zan tafi bamu haduba" ya fada da murmushi kan fuskarsa Dan shi ma tunaninsa sunada dangantaka"Aisha Mudassir tace "Eh Sir laifi su Samiha ne basu hadaku kun gaisa ba amma yarone fa koni nakusa girmarsa"Rufaida ta harari Aisha"tace kinma girmesa kawai zakice"AbdurRahman yace"To masu 'dan uwa,don tace ta kusa girmarsa shine harda bakar magana" Rufaida tace"Sir koni fa shekara kusan biyar ya bani inji Umminmu shine zatace ta kusa girmarsa "murmushi AbdurRahman yayi kawai yacanza maganar da cewa"saura kuma kumanta dani lokacin bikin kuki fadamin"duka suka amsa da Insha Allah zasu fadamasa tunda suna da number dinsa da haka ya musu bankwana ya tafi suna kewar juna*JININMU 'DAYA* Sadiya Khaliy💞 Page14 Zaune suke gaba 'daya yaran Abba Aliyu a babban falo da yau yake shirin tafiya zariya da yara hutu Abba Aliyu ya dubi kowa na falon yace"kufa nake jira kowa ya tsaida gidan da zaije hutu kar sai munje Ku batamin lokaci naji Rumaisa tace Kaduna gidan Zainab zatayi hutu shima AbdurRashid yace can zashi"Rufaida jin ba'a anbaceta a tafiyarba dan tagama sakankancewa har da ita tace"Abba yanzu ni banda ni"Ummi Hauwa'u ta harareta tace"bikin Samihan zaki bari ki tafi ko kuwa"Rufaida da ta tuno yanzu dan da tunima anyi bikin bangaren su Ahmad sukace a bari ayi hutun Makaranta sai ayi tace" a'a Ummi"Abba Aliyu da shima ya tuno da bikin yace"ni banda zuwa porthacourt din nan kamar dolece ni aka za'ba naje Hauwa'u bazan 'ketare bikin nanba bikin 'yata sukutun da guda"Ummi Hauwa'u tace"hakane Abban AbdurRafi aiga AbdurRafi zai wakilceka"Abba Aliyu yace "Eh hakane,saura kwana nawa bikin ne Ummi Hauwa'u tace saura sati biyu" Abba Aliyu yace haba harma dawoma"Rufaida tace"Abba kona ha'da kayana naje nima"Ummi Hauwa'u tace "wai Rufaida meke damunki raban IV da zaku fara fa a wannan satinfa,kuma kinsan ranar asabar din nan amarya zatayi yininta a Kano,tunda a sokoto za'ayi bikin akaita daga can"Abba Aliyu da yaga matartasa ta hakikance Rufaida bazata hutu ba kamar ba garinsu zata hutun ba shi abinma dariya ya basa dan yasan badan komai take wannan hanya hanyarba don kartaje ne suma su AbdurRashid dan bayarda zatayi tace bazasu bane shi yarasa maiyasa Hauwa'u takasa manta baya dukda yasan abubuwan da suka faru da aurensu dama bayan aurensu,haryau tsoro take kar nata suje gidan da tasha wahalar rayuwa a ciki,suko yaran da basu fahimci dalilin fa'da Umminsu ba dan cikin fada take maganar abinda basu saba jiba gurin umminsu saifa ta tutance dukda suma suna fuskantar tsangwama amma a gidan Abba Bukar da matarsa ke musu shiyasama ko zuwa zariya zasuyi gidan Gwaggo kakarsu suke zuwa da Malam da Gwaggo suke lalla'basu kamar kwai sai duk jikin yaran yayi sanyi jiki ko harda AbdurRafi da yake tuno wasu abubuwa da suka dinga faruwa a zamansu gidan Abba Bukar kafin Abbansu ya samu aiki yadawo Kano,AbdurRashid ya katse shirun da cewa " Abba na shirya kayana tun jiya kuma mungaisa a waya da Aunty Zainab tun kwanaki a gidanta zanyi hutuna",Abba murmushi kawai yayi don ya fahimci AbdurRashid gudun yin hutunsa yake gidan Abba Bukar,tunda yaron yasan acan zasuyi hutun Abba Bukar nema ya bukaci aje ayi hutu a gidansa danshi Abba Bukar mutum ne mai son danginsa banda Allah ya hadasa da mace mara kirki da kusan Hajiya Jamila ke juya gidan Abba Aliyu yace"shikenan"ke Rumaisa sai kiyi a gidan Abba bukar"Rumaisa ta amsa da"to"badan taso ba ita don itama kanta batasan hutu gidan Abba bukar da tasan can za'a kaita tunda Abba Bukar ta fiso tayi a gidan kanwar babanta Aunty Zainab ko gidan Gwaggo saboda tsangwamar da suke sha indai sukaje hutu gidan Abba bukar gurin Hajiya Jamila saukinsu suje gidan kakarsu Gwaggo "Ummi Hauwa'u bataji da'di ba jin Rumaisa ce zatayi hutu gidan Abba bukar dan bata manta rayuwar da tayi a gidan saidai sam bata nuna koda a fuska ba da haka suka shirya tafiya har bakin mota suka rakasu Abba Aliyu ya bawa Ummi Hauwa'u kudin kashewa ko yaransa ragowar zasu bukata sai kuma kudin cefanan kayan miya abun abinci basuda matsala akwai komai ya sake jaddadamata ta kula masa da yaransa sosai dukda yasan baida matsala ta wannan fannin da Hauwa'u haka ma babban dan nasa AbdurRafi yana kokarin kula da yaran indai Abba Aliyu bayanan kobaya kusa fiyema da shi danshi Aliyu sanyi garesa abunda ko zai batawa Aliyu rai to babbane Ummi Hauwa'u da take zaune bakin gado tana canzawa Ra'is kaya Rufaida ta turo dakin bayan taji Ummi ta amsa masa sallamar da tajira ta amsa tukunno kai dakin Rufaida da Rafi'a mai kusan shekaru biyar ko shida a hannunta ta dubi Umminnasu tace"Ummi nagama shiryawa kudin Napep zaki bamu mu tafi" Ummi Hauwa'u ta dubeta bawata kwalliya fuskarta dan Rufaida ba mace bace mai son kwalliya mai yawa bama taga Rafi'a ba tace"karasa shiryamin Ra'is to na daukomiki "badan tasoba ta zauna gefen gado dan ita macace mai son gayu bataso tayi wanka taga kayanta duk sun cukurku'de sau tari Ummi nace mata zata daina ne data haifi data fara tara yara amsar Ra'is tayi ta fara kokawar sama sa wando Rafi's tana masa wasa ummi Hauwa'u tana kallon yadda take 'bata rai tanasa masa wando sai alokacin ta lura da Rafi'a ta duba inda ta aje kudin tace"har kin shirya Rafi'a ne naga kamar baki mata wanka ba kuma kinsan dai bazata bari ki tafi gidan Momy Maryam ba banda ita kimayi kokarin shiryata kafin ku tafi ko kuma ki tafi da Ra'is" Rufaida tace"Momy biki ga nayi mata kwalliya ba,ai momy gwara yawo ma da Rafi'a dukda surutunta dadai kukan Ra'is yataramin Jama'a ace na satosa"Ummi Hauwa'u tace"ke banfasan wulakanci 'dan autan nawa kike cewa yana kuka ,ta mika mata kudin data dauko taceni anshi kudin ki wuce ku tafi"Rufaida ta dungurar da Ra'is gado ta amshi kudin Napep dari biyar kuka Ra'is ya fara "Ummi wannan mai kai kwal uku shine Autan Ai ko zakiyi auta kyakkyawa ne ""Ummi Hauwa'u ta daukesa tana lallashi tace "ke karfa ki jiwa 'dana ciwo yanzu da akasa yake da tuni ya ji zafi koma yaji ciwo" Rufaida tace"yanxu Ummi daga dungurarwa sai kice da akasa ne saiyaji ciwo tace"eh man baki San tsautsai ba ,kuma ma Ra'is dakike fa'dar muninsa dake yake kama" Rafi'a ta kunshe baki da dariya ta tahomata,Rufaida tace wallahi yarinya kikamin dariya fasa zuwa zanyi dake"Ummi tace"haba yarinya ai baki isa ba kuwa tare zaku itama taje taga kawarta Samima "murmushi Rufaida tayi dan hirarsu da Umminta bata karewa takama hannun Rafi'a suka bar dakin suna cewa da Ummin sun tafi addu'a ta bisu da ita tana kara jin kaunar wannan zuriya tata da Allah ya azurtata da samu*JININMU 'DAYA* By Sadiya Khaliy Page 15 ASuna isowa bakin titi suka tari adaidaita zuwa Nasarawa GRA a flyover wajen bada hannu suka tsaya saboda go slow suna tsayawa Rafi'a da ta fara kalle kalle ta hango wata mota dake 'bangaren hagunsu motar akwai daukar ido sosai matashin cikin motar Rafi'a ta soma nunawa Rufaida tace"Yaya kalli waccen Ash din motar kiga mai kama da Yayanmu"Rufaidsa da take ji mai tace tayi banza da ita dan inta daka ta Rafi'a saita ja musu zagima yanzu saida ta kuma maimaitawa sannan Rufaida ta doke hannunta ta kalli motar da bata kalli na ciki ba tace" nagani wadda bata iya gani ta kyale aike dama matsalar zuwa unguwa dake kenan surutu da kalle kalle yanzu idan mai motar yaga kina nuna safa ba kisan koshi waye ba haka kurum kijamin"Rafi'a tace"Yaya Allah da gaske nake ki kalla mai tuka motar sosai kigani"Rufaida da ranta yafara baci tace naji zan kalla amma kinsan Allah naga akasin haka wallahi saina dokeki idan muka koma gida ko kuma nadaina fita unguwa dake kinyarda "Rafi'a tace "Eh"motar da take nunawa Rufaida ta zuru kanta waje taga matukin motar Kallo 'daya Rufaida ta masa ta fahimci kamarsu sosai da AbdurRafi harma tafi wadda ake ganin AbdurRahman malaminsu yanayi da AbdurRafi dan ita saitace ita bama ta taba ganin kamar AbdurRafi da AbdurRahman ba kurum su Nasiba ke haukansu da Samiha take tayasu,amma wannan matashin na cikin motar banda yanayin shekaru da shi wannan na motar zai iya dara Yayan nasu shekaru ba da kuma yanayin hasken fata da wannan ya 'dara AbdurRafi yayansu haske da sai tace shine ma yayansu" maganar Rafi'a ta dawo daga tunanin data tafi tace"Yaya kema kingani ko ki masa magana koma yayanne"Rufaida tace"banda abin Rafi'a daga kama sai ace lallai wanda kasani ne"Rufaida batayi aune ba taji muryar Rafi'a tana dagawa na motar hannu tana"yaya,yayanmu"Rufaida da zata finciko hannunta mai tuka a daidaita sahun da ya gani ta cikin maduni ya juyo da yake jin duk hirarsu kawai shi bayason shiga hurumin da bana shiba ne "yace haba 'kyaleta mana kikasani ko yayan naku ne"Rufaida da takaici ya fara isarta cikin napep din ta maido kanta tanajin haushi abinda Rafi'a keyi tana kwalawa bawan Allah kira da suna Yaya aranta tanaji ba zata kara yawo konan dacan da Rafi'aba karta dinga jawomata abin magana sai da Rafi'a taga ya juyo ya mata murmushi da shima saurayin matashin maganar da Rafi'a keyi ya fara isarsa har yafara tunanin dashi ake shine dalilin waigowarsa ganin karamar yarinyace mai zubin Hausa Fulani ya sakar mata murmushi ya tada motarsa ganin an fara yi masa horn a baya ma'ana danja ta kawo kenan,Rafi'a ta shigo cikin motar ta sannan mai napep din shima ya tayar Rufaida tace"kingama shirmen naki kenan,zuwa dake kuma unguwa yayi kai ko zanyi sai an dade mai napep din da yake tu',kinsa yace"haba ke kuwa yayanta fa ta gani take kiransa,kinsan harkar yaro sai ana hakuri ,dukansu ba wanda ya kuma tofa alif itama Rafi'a tsoronta kar takuma wani laifin da za'a daina fita unguwa da ita gaba 'daya suna isa Nasarawa GRA ya shiga Latin Khalid Bashar Majiya ya danyi tafiya a layin kadan ya kuma shiga wata kwana nan ya tsaya ya Rufaida ta mikamasa kudinsa bayan ta fito tace " gashi bamu canji"amsa yayi ya duba aljihunsa ya mika mata canjin yayi gaba Rufaida hannun Rafi'a ta kama tanata mata fada akan suruntunta yayi yawa kofar gate din gidansu Samiha suka tsaya suka kwankwasa mai gadi ya karaso kofar yace"waye"Rufaida tace"baba su Rufaida ne"ya bude kofar jikin gate din da ake wucewa yana cewa "ah'ah yau kuma antuna da zumunci kenan" Rufaida da suka shigo ciki race"ai Baba dama munayi ko sati ba'ayi ba da zuwa na aka cemin kaje kauyenku ,yaronka baya jin da'di"yace"wallahi jikata jikin yaron ne usaiba yaki dadi da yaji sauki sai ciwo ya dawo to yanzu dai da sau'ki nazo dashi asibitin cikin birni an dubashi ance typhoid ce da aka rubutan magani Abbanku ne ma ya siya yanzu dai jiki ya fara warkewa"Rufaida da taga ne nufinsa Abba Hashim Abbansu Samiha wato yake nufi" cikin nuna tausayi tace"Baba Allah ya kara lafiya,shi kuma Abba Allah ya kara masa budi"yace amin amin 'yata"Rufaida tace au Baba bamu gaisa ba gaisawar sukayi Rafi'a ma ta gaishesa daganan suka cigaba da tafiya cikin gidan aranta tana tausayin talaka dukda su 'dinma ba masu ku'di bane can dan albashin mahaifin nasu tasan a gurin wasuda yawa masu kudin kudin kashewa ne na siyan kayan kwalliya da kayan saws dukda yawan kudin wasu ma sai an karo linkinsu amma dai sai tace sudai Asirinsu a rufe yake mutum ashirin ma zasu iyaci a karkashinsu da wadannan kudin albashin nasa shima Abbansu akwai tausayin mabukata yana da alkhairi Allah Rufaida take kara godewa da ni'imar da suke a ciki ita a koyaushe na kasa dasu take hanga Da sallamar Rufaida ta shiga falon su Samihan da yasha kayan alatu amma taga har wani gyara ma akai masa da ta tance tundaga kallo daya"Samiha da gudu ta karasa gurin Rufaida ta rungumeta tana Oyo Oyo 'yar uwata ,Rufaida ta tureta daga jikinta tace"keni cikani karkijimin ciwo" Samiha ta dubi kanta"tace ina naga auki banda abinki"Nasiba da tazo gidan tana falon zaune da sauran kawsyensu tace"kema fadamata Rufaida ai bansan yaushe Rufaida zatayi hankali ba abu kamar yaqi yanzu da ta maujeki fa muna haka tayi mana nuna shigowa" Rufaida ta ratsa Samiha ta shige falon ta zauna cikin kawayensu Nasiba shehu Garba da Aisha Mudassir da suke unguwa 'daya su biyun kusan shiyasa duk unguwar da zasu indai gidansu kawayensu na makaranta ne ko kawayen unguwa tare zaka gansu 'dokin ganinsu take dan indai ba Samiha ba bada wadda suke haduwa rabon da duk ta gansu tun Candynsu,hira suka fara yi ta bayan rabuwa, Samiha ta dawo cikinsu ta zauna tana cewa"wato kun manta dani da ko"Aisha tace"haba wazai manta da amarya sukutun da guda"Samiha tace"kwaji da shi dai magulmata"Rufaida ta mike daga zaman da tayi"Nasiba ta dubeta tace "Malama ina zuwa kuma,zamu fara fira kuma kinsan zamuyi rabon IV ma ya'u za'a fara"Rufaida tace" zanje mugaisa da momy ne,kuma bazanje wani raban IV ba,tunda bata fadamin yau ne ba"Samiha taja tsaki tace"kunji tafa Aisha dan Allah da wacce wayar zan mata waya ba waya gare taba,yanzu da muka tsaida magana ayi yau a huta kunaji ina kira Ummi tace sun taho"Rufaida tace"oho miki dai ta haye sama gurin Momy da Rafi'a suna zuwa can ta nufa taje taga Samima autarsu Samiha da suke kawance a makaranta da suke aji 'daya kuma tsararrakin juna ne"Rufaida da saida suka gama gaisawa da Momy tagama bata lokacinta danda batayi niyyar zuwa raba IV 'dinba sai da Nasiba tazo suka yima Momy sai sun dawo addu'a tayi musu tace Musa zai kaisu da yake 'da ga Abba Hashim 'dan qaninsa da Abba Hashim dinne ma ya daukosa yake riqonshi ta aiki Samir da dashi sukayi zai kaisu kai IVn a mota hirarsu duk sukeyi Musa yana tayasu dan shi akwai da barkwanci,Wayar Nasiba ce ta fara ringing ta zira hannunta jikin jakarta ta duba mai kiran AbdurRahman ne malaminsu aiko da murmushi ta kalli sauran kawayen nata Rufaida da Samiha da take tsakiyarsu tace musu"Sir AbdurRahman nefa mai kiran"Samiha tace "Allah sarki sir mun rabu da gaisawa "Aisha da take gaban motar ta juyo tace"Nasiba ko dai dashi za'ayi kinga tuwonmu manmu"harararta Nasiba tayi ta 'daga wayar suka fara gaisawa su Samiha sukayi dariya ,Musa ya kalli Aisha yace"ba ankusa bikin Nasibar ba ne,dawa kuma kuke hadata" Aisha tace"a'a Yaya Musa ba'ako kawo mata kudi ba ,wani malaminmu ne a AL'AZHAR da yazo mana TP"yace "ok inda rabo sai kiga ya aureta"Aisha tace" wallahi kuwa"gaisawa Nasibar suka cigaba dayi da AbdurRahman har take shaidamasa sunzo unguwarsu gidansu Samiha yanzu sunfita rabon IVn bikin anan yake sanarmata sunyi tafiya basa gida baiso bikin Samihar yazo baya nan ba hakuri ya bawa Samiha da Nasiba ta bata wayar su gaisa yake cewa"amma bata fadamata bikin ya matso ba"murmushi tayi kawai ta mikawa Rufaida wayar su gaisa"saida ya tanbayeta ina yayanta da suke cewa yana kama da shi"tace yana lafiya"yake cewa yaso a bikin su ha'du sai dai hakan bai samuba sai dai anata"tayi murmushi ta mikawa Aisha wayar suka gaisa ta mikowa Nasiba inda yace ta turomasa account number din su yanzunnan ,Nasiba suna gama wayar tace "Wallahi Aisha ki rufamin asiri,da maganar Sir AbdurRahman ai kema kinsan bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane ina ni ina 'dan Khalid Bashar ai kema kinsan yafi karfina,irin su Sir AbdurRahman ai saidai 'yar minister" Aisha tsaki tayi ta juyo tace"kamarya na rufa miki asiri,kuma ta ina yafi karfinki kin manta tsarin Allah kenan suma Allah ne ya basu dukiyar Ba karfinsu ba ba dabararsu ba idan mijinkine bawani shi 'dan masu kudi ne ko wani abu indai da soyayyah tsakaninku ki fadama ,kuma kema aiba yar talakawa bace"Su Samiha suka ce yawwa Aisha"fadamata dai,mutum ya dinga yanke tsammani kai tsaye"Nasiba ta 'dan tabe baki alamar bata damu da maganganun nasuba tace"kanku akeji"Musa da yake tukin da yake jin duk abinda suke cewa yace"Nasiba Allah karki yanke tsammani"tayi murmushi tace "Yaya Musa kenan, Dan Allah fadamin Account number din ka mu turamasa"Musan ya fado mata ta rubuta ta turamasa"gidansu wata kawarsu suka fara zuwa suka shiga ya fito ya tsaya bakin motar yana danna wayarsa alert yaji a a wayarsa ya shiga cikin sakunan ya duba sakon AbdurRahman ne ya turo ya turo dubu 100 a account dinsa suna fitowa daga gidan suka Shiga motar kafin ya tada motar ya kalli Nasiba yayi yace"ya turo kudin yanzu dubu dari ne" ido suka zaro su duka suka ce"Yaya Musa dubu 'dari fa dan ba wacce tayi zaton zai turo haka dukda idan yayi ma ba abin mamaki bane dariya a gareshi dariya abin ya bashi yace"dan mai kudi yayi kyautar dubu 'dari aiba wani abu bane linkinsu billion ma zai iya" sukace masa "Eh hakane yaya Musa amma gani mukayi mu dalibansa ne bakomai ba"suna haka kiran AbdurRahman ya shigo wayar Nasiba tanbayarta yayi kudin sun shigo tace masa" Eh"godiya tayi yace babu komai ba yawa ma"ita kam Nasiba gani take dubu dari dukda mahaifinta mai wadatar ne amma dai tasan bazata samu dubu dari ba kai tsaye a hannunsa sai dai ko harkar karatu suna gama wayar Samiha tace ta barwa kawayen nata da yayan nata kudin danko ita batasan mai zatayi dasu ba bata da matsalar komai anyi musu cikin girma iya dai dai karfin mahaifansu kuma Ahmad yana kokari gurin yi mata komai iya arzikinsa kawayen nata ne dai ta fahimci buga buga kawai sukeyi dan ko anko cikinsu ba wadda tayi duka shima yayannata Musa tasan hakanne tunda a karkashin mahaifinta yake har yau karatu ma yake a FCE KANO aiko Samiha tanaji anan take kowacce daga cikinsu ta fara lissafa abinda yakamata tayi da kudin akarshe ma Musa suka barwa sallaho ya siyo musu kayan da suka lissafa da kudin ciki harda gudunmawar da zasu bawa Samiha dan babu boye boye tsakanin Samiha da kawayen nata kaf dinsu sai Yamma lis suka gama raban IVn da mazan ajin nasu suka kira wani daga cikinsu ya ansa zai rabawa sauran har kofar gida Musa yakaisu Nasiba ya sauke ita ko Rufaida bayan sun koma gidansu Samiha Momy maryam cewa tayi ta kwana anan saboda duhun magriba zata kira Ummi Hauwa'u ta fadamata Rafi'a da dama haka takeso murna tayi koda Momy Maryam ta kira Ummi Hauwa'u nunawa tayi babu komai ai duk gidane kuma Rufaida ma 'yar tace bama saita kira ba sosai Momy Maryam taji dadi yadda Hauwa'u take daukarta kai bazakace ba ya da kanwa bane kuma duk wannan zumuncin 'ya'yane silar hadashi. SADIYA KHALIY✍🏽*🔗JININMU 'DAYA🔗* BY SADIYA KHALI🖊️ Page 16📄 AAhmad dake dannawa wayarsa da yake gefen gado zaune ya maida dubensa ga AbdurRa'uf daya kwanta a makeken gado yana lumshe ido yace"yanzu brother bazaka fito koda fall bane muyi fira ba wato dai har yau bazaka canza ba daga wannan tafiyar nasan cewa zakayi ka gaji ne fa"AbdurRa'uf ya bude idanunsa duka ya kalli Ahmad yace"Gaskiya yaron nan ka rainani da yawa yanzu duk a wannin da nayi a jirgi shine zakazo kana takuramin na fito ayi fira ni kaga Malam tashi ka bani guri na huta"Ahmad ya yi murmushi saboda yadda yasan AbdurRa'uf da akwaishi da son girma kamar wasu shekaru ya basa duka duka baifi shekara daya AbdurRa'uf ya bashi ba sassauta murya yayi yayi yace"haba Yaya AbdurRa'uf ayimin afuwa"AbdurRa'uf baki ya yatsina yace"shikenan,in Kasan me kuwa"Ahmad yayi saurin cewa"A'a"AbdurRa'uf yace"Kano ta birgeni sosai babu cikowa daga zuwana na fahimci haka,anya bako a Kano zan nemi mata ba na aura,idan mundawo Nigeria nayi gidana na zauna anan"shi Ahmad ma dariya abin yaba shi amma sai yayi murmushi yace"Mutumina tanbayar da zanma kenan ya kaga garin Kanon,matsalar tsohuwar can ta hanani gini anan wallahi"dariya AvdurRa'uf yayi yace"gaskiya takwareka ka samu mace 'yar Kano amma tahanaka zaman Kano"Ahmad yace "a'a wai Samiha kake nufi ai ba 'yar Kano bace 'yan sokoto ce"to amma ai rainon kano ce ai Malam angama magana,nifa yadda naji kano farar daya garin yayi min hakama matan cikinsa inada yaqini akansu zakaji dadin zama dasu da yardar Allah" Ahmad yace"gaskiya kuwa"amma kasan matar nan dakyar ta amince na aureta ,ai indai matarnan na raye bazata bari muyi abin kanmu ba,wai haka tayiwa su Abba ne"AbdurRa'uf yace" da alama dai hakan tayi musu ai fitinanniyar tsohuwa su Abba Allah ya hadasu da ita"Ahmad yace sosaima kuwa kaima kasan Karimar Baffa Sule takeson hadaka da ita,itama naji ance Karimar tana sonka jira Hajiyar take kazo ayi magana"ido AbdurRa'uf ya zaro yace "to wallahi ba Wanda ya isa yayimin auren dole tun wurima ta canza sheqarta,shiyasa naga tunda Hajiya ta samu labarin zuwana indai na kirata mugaisa saita hadani da Karima mugaisa" Ahmad yasa dariya Abdurra'uf yace"au dariya ma na haka cikin bacin rai" Ahmad ya sassauta murya yace "haba Babban mutum kaima kasan yadda akeji dakai a gidannan Baffa Sule bazai amince ba bare kuma kasan Baffa Alhaji bazai amince ba Indai bakaso"AbdurRa'uf ya dawo da nutsuwarsa da taso gushewa da yace" Eh hakane Ahmad"Ahmad da wayarsa tayi kara yasa shi fasa maganar da yayi niyyar yi ya duba mai kiran ganin sunan da yasawa Samiha yasa shi murmushi ya kara daga ya kara a kunne dan yasan ganin bata kiransa ba hardare yasata kiranshi tunda sukayi magana a WhatsApp tace masa zasu tafi rabon IV ya sauka ba tare ma da yabata amsa ba yafara cikiniyar tarbar Dan uwan nasa AbdurRa'uf Sallamarta ita ta katse masa tunaninsa ya amsa mata ta gaishesa cikin girmamawa ya amsa kana yace Madam ansha yawo yau to ya gajiyar hanya Samiha da take zaune tana duba dinkinsu ita da Rufaida da Rufaidan ke 'dagawa tace masa "aini fushi nake dakai yau gaba 'daya ko Flashing ko text dinka babu a wayata naka" murmushi yayi yace"tuba nake amaryata"itadai Samiha kunyar maganar taji da Ahmad yayi cigaba yayi dacewa,kinsan Yaya AbdurRa'uf yau ya sauka a Nigeria shine dalili"Samiha tace" wallahi na manta shaf kace masa ina masa sannu da zuwa"da murmushi kan fuskar Ahmad yace"zaiji da kyau,gashinan a gefe na"da haka suka cigaba da firarsu "AbdurRa'uf da yaji firar ba mai karewa bace mikewa yayi yana cewa"na lura bazaka daina cikamin kunne ba" Falo ya nufa "da nan 'dinma kayan auren Ahmad da AbdurRa'uf shine ya ha'da komai ya vayar tun wancen satin a kawo su Nigeria sai a jiya suka iso da yanzu shirin mikasu ake gidansu Samihan,haka ya zauna inda kowa yaba kayan yake yasan dama Safiyya da Amminsa ba bayaba gurin iya zaben kaya shidai murmushi yake kawai muryar yakumbonsu yaji tana cewa " Masha Allah Babban Mutum anyi zumunci kaya sunyi Allah ya bar zumunci ya nunamin naka nadau danka"murmushi yayi kawai yace kindaina auren nawa kenan"Dariya tayi tace"kadubeni kaga aina tsufa gwara na barka ka auro budurwa son kowa kin wanda ya rasa,dukda na rasa irin matar dama kaika keso tunda indai India ne akwai kyawawa " murmushi yayi yace "Yakumbo kenan,nifa nafison mai kyakkyawan hali" Momynsu Ahmad sai yanzu tasa baki tace"aiko zaka dade baka samu ba tunda baka nema,kullum mukai waya da Yaya Asma'u saita yimin kukan hakan"Dariya abin yaso basa ma yace"Ai Momy komai lokaci ne,kuma wani jinkirin Alkhairi ne"Yakumbo tace"Hakane amma sai a dage da nema har Allah yasa a dace,amma idan baka nema ai ba lallai ace kasamu kanada ga zaune ba"yace hakane Yakumbo,zan riqa dubawa insha Allah"tace masa yawwa kag shekarun sunfara ja a kalla kayi talatin da doriya"ido ya zaro yace"haba yakumbo har yau ko talatin bankai ba"tace "kaidai kawai yaron zamani da basa san shekaru" Momy tayi dariya tace"A'a Yakumbo ba'kin shekaru suke ba shekarunsa kenan wancen AbdurRa'uf 'din dai kike tuna shekarunsa",Yace yawwa Momyna fadamata gaskiya dai tsohuwar nan ta rikice" "Duban Yakumbo Momy tayi ta suka kalli juna itada AbdurRauf dan sunsan Yakumbo halinta sarai bataso ace ta fara rikicewa Harararsa tayi tace" tsohuwartawa kake ciwa fuska ko harda ta rikice ma ko?" Yace"tuba nake Momy" Yakumbo ta hararesu gaba 'daya tayi ta wasan nan tace"Hannatu harda kallona kafin kiyi magana ja'irar yarinya nasan da bani hardake za'ayi maganar gwara na tattara na koma dan-bat..... Husna data shigo falon ta katse maganar ta zauna kusa da Yakumbo tana dafa ta tana cewa"keda waye haka Yakumbo kike sababi haka harda maganar komawa Dan-batta" "Nida wa'dannan ne ta nuna su Momy da AbdurRa'uf harda kallon juna kafin Hannatu tayi magana,gwara na tattara nakoma inda nafi wayau ai" dariyar abin yaba Husna da itama Yakumbon dan ayi tayi dariyar take wannan maganar"Husna ta juya ga AbdurRa'uf tace"Yaya kaji fa,ina Yaya Ahmad din ne" "Ina jinku,Yana ciki yana amsa waya" "Hala da Samiyy suke wayar ko? "jeki tanbayesa kiji" Tasan bakar magana ya fadamata hakan yasa tayi shiru ta mike ta kunna TV shi ko da Momy suka cigaba da firar zuwansu Ammi cikin wannan satin,dawowa Husna tayi ta zauna tana cewa"amma Yaya harda Safiyya za'azo ko?" Yace "Bansaniba kin kagara tazo kenan ko,a fara Isar mutane gida kamar gidan kallan Kwallo don hayaniya" Dariya tayi tace"ai haka yafi ni ni kadaice gidan bayamin da'di" "Shiyasa kike damin mutane ba" Ahmad da yashigo falon shima ya nemi guri ya zauna suka cigaba da firarsu. LIMAT SADIY 🖊️*🔗JININMU 'DAYA🔗* By Sadiya Ibrahim Khalil🖊️ Hikima writers asso...... 17 "Yakumbo gaskiya kamata yayi kiya hakuri da tafiya mu tafi tare daganan gurin bikin murmushi" Kallon Husna Yakumbo tayi da ita ke maganar kana tace" kyayi kya gama yarinya sauranma sunyi sun gama"Husna ta mike tana 'bata rai" daya daga cikin matasan falon yacewa Husna "Haba Amminmu dawo ki zauna,meye abin fushi, Tace "amma Yaya Bello daga fadar gaskiy.." Yace "kinga kyaleta" Yakumbo data mike tayi hanyar barin falon,dan ta fahimci bata mata lokacin yaran sukesan yi Su AbdurRa'uf da Dady da Momy har bakin mota suka raka Yakumbo Husna ta biyosu da jakar Yakumbo tasa a gidan baya addu'a sukayi musu Allah ya saukesu lafiya suna zolayar Yakumbo"cewa ta kagara taje taga Baffa shiyasa ta damesu da saita koma 'Danbatta yau" Murmushi tayi tace"to meye a ciki tunda Ahmad yafara nuna baya auren dani tun kafin ku juyan baya harda Babban mutum da Bellotu gwara naje nima na rike mai gidana kar matanku su yimin kwace nan gaba "AbdurRa'uf yace" wato Yakumbo hardani duk yadda nake auren nan dake"Bello dake kokarin tada mota yace" Yakumbo cefa ai duk ciki indai akan Baffa ne zata iya dena aure da kowa su Dady murmushi sukeyi su dai da haka motar su tabar gidan ran kowannensu babu dadi ABDURRA'UF JABIR MAHMUD DANBATTA Haifaffen garin Kaduna inda aiki yakai mahaifinsa AMBASSADOR JABIR MAHMUD DANBATTA a matsayin jakadan Nigeria a India da Matarsa daya Asma'u da akayi musu auren zumunci,inda a yanzu suke da zama a New Delhi babban birnin India AbdurRa'uf yayi karatunsa a fannin likitanci ya karanci Medicine a UNIVERSITY OF MEDICAL SCIENCE NEW DELHI yanzu ya zama kwararren likita a asibitin CHAUDHARY BRAHM PRAKASH AYURVED HOSPITAL,asibiti ne babba da yake zaman kansa,AbdurRa'uf shine 'da 'daya tilo gurin Asma'u ta haifi na farko ya rasu daganan ta haifesa ta yi masa kanne wajen hudu duk duk suna rasuwa a karshe haihuwar ta tsaya mata,Safiyya a garesu kuma 'yar riko ce"Shureim Khan Salim Abokin Ra'uf ne a India tare suke a makaranta hakama a gurin aiki Shureim haifaffen dan India ne shi AHMAD USMAN DANBATTA daya kasance Aboki kuma 'dan uwa na jini ga AbdurRa'uf tundaga yarinta har zuwa girma kasancewar halayyarsu da ta zamo daya itace takara assasa abotar dukda da tazarar shekaru daya tsakaninsu bai hana su abota ba tundaga primary har zuwa secondary da suna shekarar karshe a makaranta Jabir yasamu Ambassador USMAN MAHMUD DANBATTA mahaifin Ahmad Kani ne ga Jabir mahaifin AbdurRa'uf uwa daya uba daya yana zaune a cikin garin Kano da aiki ya maidosa Commissioner of Police ICP yana zaune a Zaria Road da Matarsa daya Hannatu da aka musu auren gida na zumunci kanwar Asma'u ce ita Mahaifiyar AbdurRa'uf Ahmad kannensa uku shine babba sai Husna da Ammar,da Abida Ahmad a UK yayi degree dinsa ya samu koyarwa yanzu a haka a Jami'ar Northwest Dady ya dubi Ra'uf da suke su biyu zaune a falon Dady Usman din yace "Ra'uf hidimar nanfa tana yawa banda hidimar kayan lefe ace kuma duk yawan ahalinmu sai ka yi musu kayan anko haba ka riqa rage wani nauyin mana ,da Malika ta shaidamin ba karamin bacin rai raina yayi ba" murmushi yayi yace"Dady indai inadashi banyi muku ba wazan yiwa komai na mallaka naku ne"Eh duk da hakan Ra'uf dawainiyar tana yawa yakamata ka rage,"yace"A'a Dady idan ban mukuba babu wadanda zan yiwa" yace "to shikenan Allah ya kara budi na alkhairi ,yanzu yaushe zaka tafi Kadunan,karfa kasa Hajiya tayo takakka shalelenta yaki tahowa inda take"murmushi yayi yace" Dady kyale Hajiyar nan taku jiya fa nazo saina huta kozan tafi"Yace"duk da hakan ka daure ka tafi akan lokaci,"Yace "to", ya kuma canza Maganar da wata yace"yawwa Dady yaushe za'a kawomin motar tawa inaso nafara sanin gari kafin na tafi Kaduna ko zuwa Juma'a ne idan su Ammin sun isa can" Yace"kai dai kace kanaso kajewa su Hajiya da sabuwar Mota kar Hajiya tace ta daina auren ko"yace"ai Dady dama na dade da sakinta tayimin tsufa"Dariya maganar taba Dady yace "to shikenan itama ta dade da sakinka saki uku," yace "anya kuwa Dady ba gashi ba ta damu naje Kaduna ba,nine dai na saketa",yace "kundaifi kusa ninakema shiga yanzu ,munyi magana da kamfanin motocin ,yau nake saran na tura Mukhtar ya taho da ita" Yace kai "amma Dady nayi murna sosai Allah ya kara tsawan rai" yace masa "Amin" Dady yana jin Dadin addu'ar da ABDUL-RA'UF yake masa ______________ "Rufaida zanyi tafiya ta nabarki, da wannan kwalliyartaki da sai kifi awa kina yi", Abdurrafi ne mai cewa haka cikin nuna 'kosawa. "Yaya gani nan nafito" Rufaida dake 'ko'karin karasa sakkowa daga matakalar bene tace hakan, riga da siket ne a jikinta, saikuma hijabin jikin nata har 'kasa kalar kayan, masu kalar ruwan kasa.bawani kwalliya tayi ba maiyawa dan ita sam batasan yawan kwalliya" " Abdurrafi" da ya maida dubensa ga ummin tasu da take kujerun falon zaune yacewa, "ummi danasan kwalliyar Rufaida kenan da tuni natafi nabarta, har yau taka sa sanin samir , yanzu zataga ya kira waya yacemin an aikesa, tafi kowa sanin da'dewar littafin nan gurin Samir" ummi ce takallesa da harararsa da cewa "yanzu dama ba hidimar biki bace zata kaika sai maganar wani littafi, har kake azalzalal Rufaida ko?" Yace "A'a ummi ba haka bane" kafin Ummi Hauwa'u tace wani abu Abdul -Rafi yayi saurin sake cewa "mudai ummi muntafi", Ummi tace "to Allah ya tsareku, karku manta da sa'kona, akuma gaida momy" Tukin da yake ya tsaida gami da ajiye wayarsa yakalli Rufaida yafara magana, "Rufaida kinjifa samir saboda rainun wayau bama ya gida sunfita dasu momy", dariya ita abin ma yabawa Rufaida, takalli Abdurrafi, tace "yaya fa'danka da yaya Samir wake shiga", yace "wannan karon dagaske nake mun 'bata da samir kinsan ko dad'ewar littafin nan kuwa, bara muje aiken ummin saura kuma kimana kauyanci, haba yaya a shoprite din zanyi kauyanci, kamanta muna zuwa da Abba ne" yace"Au hakane"da haka suka cigaba da hira har suka isa shoprite 'din A harabar shoprite, suka a jiye motar suka fito a tare suka shiga ciki Jin karon da Rufaida tayi da wani abu ne da taji har 'karar abinda ke hannunsa a 'kasa yasata saurin d'ago kai,Ra'uf ne tsaye, Abinda tayar ta du'ka tami 'kamasa da hannu biyu tare da basa ha'kuri, murmuushi AbdulRa'uf yayi yace ba matsala, ya juya ya cigaba da abinda yake itama Rufaida bayan Abdurrafi tabi LIMATU B🖊IndaININMU 'DAYA*🔗 By Sadiya Ibrahim Khalil🖊️ Hikima writers asso..... 18 ___________ "Gaskiya Ahmad nayi gamo fa",Abdurra'uf ya fa'da matashin da zasu iya shekaru d'aya da Ra'uf 'din sannan ga kuma kama da sukeyi. Ya dawo kusa dashi ya zauna saman kujera dake cikin 'dakin gado wanda ada yake 'kokarin ficewa daga dakin, magana matashin ya fara yaya Ra'uf dame kuma kayi gamo,murmushi Abdurra'uf yayi kafin yasoma magana dacewa "yau ne nayi gamo da yarinya mai tarbiyya", Dariya Ahmad yayi kafin yace,haba yaya Ra'uf kasan hajiya bazata yarda ba nima kasan da yadda ta amince da samiha dai, ga uwa uba kai ga karima da takeso ka aureta, murmushi Ra'uf yayi kafin yace kai ni kyaleni da rigimar wannan matar tuni fa karima tafa'damin ita dama tanada saurayi dan kada hajiya taga laifnta ne yasa bata fa'da ba, kuma ai muddin muka biyemata har abada bazamu auri za'bin muba. Labarin ha'duwarsa da Rufaida ya shiga basa, kafin yace kurum matsala 'daya bansaniba ko tana da aure, a'a yaya kada kabari wannan tunanin kabari yadameka insha Allah ma bata da aure da haka Ahmad yamike yana fa'din yaya bara naje wajen Sagiru kan maganar dinku nan mu shima mikewar yayi yace bara naje gurin momy naje maganar da sukayi da Aunty Malika tare suka fito inda suka samu Momy Hannatu suka a falo itada Ammar da yake tayata duba wasu kaya datake zaune 'kasan carpet sallamar da suka yi yasata dago ka ta kallesu da murmushi fuskarta ta amsa musu sallamar kafin tace 'yan biyun Ammi ina zuwa haka, Ra'uf ne ya zauna gefenta yace momy kinga dai mai fitar nan ya nuna Ahmad. Ahmad yace momy cigiyar matar auran da ya samu zanje nemo masa "Momy tace kai fa Ahmad kafiye wasa". Allah momy gaske nake guri Ahmad din yasamu ya cigaba da bata labari. Sai da ya gaji yayi shiru. Momy kuwa tayasa takeyi dan har taji yarinya r tashiga ranta da irin ko'dawar da Ahmad ke sake yimata. Sai da yagama yafice yana fa'din momy zan gangara bakin layi gurin sagiru maganar dinkunan mu. "To a dawo lafiya"momy ta fa'da" Inda Ra'uf shima yacemasa "a dawo lafiya" Ahmad yace"Amin ,ko zamu tafi tare ne" Yace"a'a gadai Ammar ya raka ka" Ammar ya mike yabi bayan Ahmad da yake kokarin barin falo Momy ce ta dubi Ra'uf bayan fitarsu Ahmad tacema sa da gaske ne abinda Ahmad yafa'da kuwa yace mata "eh momy sai dai a tayamu addu'a,tunda har yau bansan gidansu yarinyar ba,banida tabbacinma ba matar aure bace danda wani saurayi nagansu tare a shopping din" "Tace masa" Insha Allah hakan bazai kasance zan cigaba dama addu"ar Allah ya kara haduku ya kuma sa ita Alkhairi ce gareka damu ma" yayi kokarin kar'bewa da "Amin" yanajin dadin addu'ar Momy Hannatu har ransa Bayan shirun wucewar wasu sakunkuna ta sake kallonsa tace masa "Ra'uf yaushe zaka tafi kaduna ne kasan ko yau dady yamin maganar Hajiya ta kirasa a waya ta masa korafin 'kin tahowar ka" Momy gobe nake son tafiya da naje gurin budurwar Ahmad yace narakasa gobe ya kaimata ku'din kunshi da kitso da zasuje gobe, dana dawo daga can saina shirya natafi Tace"to shikkenan Allah yakaimu lafiya",kana tace "aw namanta malika tace an kammala d'inkuna tabawa karima jiya da taje gidan ta ta kaiwa kowa nasa, har da takalman, Ta fa'damin ka kunna wayarka tanaso kuyi waya yau" Yace "Ok momy insha Allah namanta ma tun jiya nakasheta danaga Hajiya tana ta kirana nataho Kaduna" Momy ta amsa masa da cewa" 'kila tama tanadi ne na zuwan ka" Ya amsa da cewa "tanadin magana ba" Dariya ka'dan momy tayi tace "baruwa na kunfi kusa" "Yace wane ni kune 'ya'ya ni a kare nake,Yawwa momy Ammi tafa'damiki ranar juma'a zasu zo itada Safiyya" "Eh tafa'damin amma tace a Kaduna zasu sauka, tunda muma ranar zamu tafi" Yace"Momy banaso Safiyya tazo bikin nan ko daya,kina sane da irin cin fuskar da take sha a gidan nan musamman a gurin Hajiya" Murmushi Momy Hannatu tayi tace"karka damu Ra'uf,ai naji Husna tace gidan Malika zasu sauka"yace Momy "itama Aunty Malikan kinsan halinta sarai" tace"eh duk da haka amma kasan ba zata mataba"yace"Hakane" 'dazu na sayoma yaran dogayen rigunan da sukamin magana suna boot nace mukhtar yabarsu tunda acan za ayi anfani da su, Hajiya ma dasu umma danaku ammi ta fa'damin ta ha'do kayan zata taho dasu" Momy da ta kallesa da cewa "Ra'uf baka gajiya da hidima, eh tafa'damin tace kaman to sune sanda zaka taho, Allah ya'kara bu'di ya ha'daku da masu yimuku" Yace "Amin momy, ina husna ne momy" Ta amsa masa da cewa" kamanta taje gidan Ummi dagacen kasan zasu wuce Kadunar tare". Yace"Eh hakane,nima gobe idan basu tafi ba zan shiga gidan Ummin tunda naji AHMAD yace unguwa daya suke da matar da zai aura"tace "Eh haka ne" Da haka suka cigaba da hirarsu har Dady ya shigo falon da sallamarsa yana tsokanar Ra'uf da cewa babban mutum 'dan mama babban yaya, yaushe zaka je gurin mama da hajiya 'din ne inda yakarasa maganar yana zama kasan carpet din ya jingina kansa da kujera. "Dady sannu da zuwa,gobe nake shirin tafiya tunda an kawomin motar" Yace"Yawwa Ra'uf Wato karkaje Abba yama dariya ko?" Momy Hannatu anan tasa baki tace"Eh mana ina nima zanbari aima 'dana dariya a gansa da tsohon abun hawa kuma ace daga kasar waje yake ai gwara aimasa komai sabo" Murmushi dady yayi yace "guntun gatarinka yafi sari kabani Allah Ra'uf ka daka ta mace bazaka tara komai ba ta fiso komai ita a yimata na gwaninta" Tace"Naji dai tunda kaine ka dauki alkawarin siya masa kuma ka siyamasa shikenan" Dady yace wa "Ra'uf kajita ko bata damu da a ina nasamu kudin siyama ba"dariya shidai Ra'uf yayi Tace " ai saboda nasan a albashinka ka siya masa" Dady shi dai da haka ya mike yana cewa bari na karasa na watso ruwa naga la'asar tayi na fito mu wuce masallaci" Ra'uf yace "to a fito lafiya" ya amsa da Amin yana mai shigewa ciki Rufaida da suka shigo gidan tayo gaba da sakon Ummi ta shigo da sallamarta sai da tayi sau biyu Amma Rafi'a batasan tanayi ba sai da yi magana da karfi tace ke "Rafi'a ina ummi?" Rufaida ta fa'da ta na dungura kan Rafi'a 'din da da take dan na waya tana game, Sai a sannan Rafi'a ta juyo Ta na cewa " Yaya ta na kitchen sannun Ku da zuwa" "Bazan amsa ba" ta fa'da tana cire hijabin kanta gami da zama gefenta tun 'dazu na ke tamiki sallama kika'ki amsawa," tace"yaya ban jiki ba," Dama baza ki jiba ai waya ta dauke miki hankali ta fada fa'da tana mi'kewa "Ummi sannu da aiki"Rufaida ta ambata, Datake 'ko'karin shigewa cikin kitchen 'din, Ummi ce tajuyo tareda cewa badai har kun dawo ba? "Eh ummi su momy 'din duk basa gida" Murmushi ummi tayi kafin tace wani abu Rafi'a tashigo kitchen 'din ummi ta mi'kawa wayar ta tana cewa "ummi ga wayarki momy tana kira. Sai da suka kammala wayar, ummi ta dubi Rufaida "tana cewa momy tace zakuje 'kunshi, Samir zai zo 'daukanki"gobe da safe _________________________ Abdurra'uf yaushe zaka shirya ne? yanzu fa tara ta yi, Bana son tafiya ace baza'a tsireta da wuri ba", Momy ta fa'dawa, Ra'uf da yake kokarin zura takalmi ya fito daga dakinsa yana cewa momy " yanzu zan fito muje gidansu yarinyar nida Ahmad dana dawo sai na zo natafi", To shikkenan inji momy, Naga Ahmad 'din yafita kasamesa Ku wuce, Da "to "ya amsa ya fice "Amarya samiha bata laifi kota kashe 'Dan masu gida", Ra'uf kewa kyakkyawar budurwar kirari dariya kawai tayi tasamu kujera ta zauna dake cikin falon tana fa'din "yaya Ra'uf ai sai dai idan banyi ba" ta 'karasa maganar tana mai gaishesu "Yanzu yaron nan har goma tayi bazai taho su tafi ba yafison sai rana tayi ace za' a tafi guri vaza'a tashi tafiya da wuri ba",dady ne keta sababin fa'dan da ya shigo falon yanzu, momy tace "nima sai da na masa maganar ko da zasu fita", waya dady ya ciro a aljihunsa ya dan na yasa a kunne Jin karar wayar tasa ne yasashi 'dauka cikin gaggawa "dady ganinan zuwa" inji Ra'uf ya katse wayan, yana mai kallon Ahmad yace "dady yana kira na nazo mu tafi",zan biya gidan Ummi daganan zan kira Mukhtar yazo ya daukeni ,"Ga ku'din kunshi nan "ya zaro ku'di masu yawa ya ajiyewa Rufaida a centre table 'din falon godiya Samiha tayi da addu'ar Allah yakaisu lafiya Ahmad ya fito rakasa Dady ne ya kalli momy bayan ya cire wayar daga kunnensa, yana cewa "yanzu da banyi masa waya ba bai da niyyar tahowa, Amma yacemin yanzu gashi nan zuwa". Ahmad da yaraka Ra'uf gate din gidan yace dashi"Sai munyi waya idan kun isa kaje kasha fa'dan Hajiya, Ra'uf yace "ni so nake ma naje naji fa'dan da zan sha gurin Hajiyar da kake fada". "Gaskiya Rufaida kin 'batamin lokaci sosai, Gashi kin barni da Abdur- Rafi sai fa'da ya kemin kamar wanda nama laifi", matashin saurayin dake tu'ka mota ya anbata, "Haba yaya Samir kasan ba laifi na bane, Kasan yau Abbi zai dawo gida shine dalilin da yasa sai da na taya ummi aiki ta 'karasa maganar dacewa fa'danka da yaya Abdur-Rafi babu mai shiga ta fa'd tana murmushi" "Au haka ma za kice to nagode " samir ya fa'da yana cigaba da tu'kinsa Motar Ra'uf da tafito daga layin gidan nasu Samir ya 'dagawa Mukhtar hannu. Ibrahim Khalil Family🖊️🖊️️*🔗JININMU DAYA*🔗 By Sadiya Ibrahim Khalil Hikima writers assoc.... 19 Jin sallamar tasu Rufaida ne yasa su Samima da yaran su Aunty Samira biyu dake cikin falon rugowa gurin Rufaida suka rungumeta, "oyoyo yaya Rufaida", Momy dake daya daga kujerun falon tace, samima kar fa yarda yayar taku,ku kuma Auntynku" Hannunsu takama ta shiga cikin falon da murmushi fuskarta ta mikamusu Biscuit guda uku suka amsa suna godiya suka shige cikin gidan Momy ta kalli Rufaida tana cewa "maraba da zuwa Umminku da nasake kiranta harda cewa da wuri zaki zo" Momyn tace "sai yanzu zaki taho kunshin rana tafara yi da bansa Samir ya 'dauko ki ba zaki zo ba " Murmushi Rufaida tayi tace" haba Momy zanzo Yaya Samir ne baizo da wuri ba dan har nace da baizo ba a napep zantaho ma ,kuma na taya Ummi girki yau Abba zai dawo gida"tace"Bansaniba da nabari sai yammar sai a daukoki tunda naji suna sai yamma karfe hudu za'aje kunshin saboda yanzu mai gyaran jiki tazo,kinsan halin Yayannaku shiriritarsa ya tsaya yi "murmushi Rufaida tayi ta gaida Momy Momyn tace"Samihan tana falon baki Ahmad yazo", kije Ku gaisa "Lallai Rufaida dama kina nan" Ahmad yace bayan ta shigo suna gaisawa, "A'a yaya Ahmad bama ha'duwa ne" Samiha, Ahmad ya kalla "yace haka ne"? Kai ta 'daga masa Samihan dan itama fushi take da Rufaida take ranar Laraba da sukayi bikinsu guduwa tayi tabi su ABDUL-RAFI gida Ahmad yace " kin fitar da ita" Sun 'dan ta'ba hira kafin , Rufaida ta fice daga falon bakin ta koma ciki dakinsu Rufaida ta shiga tasamu Yaya Saudat a ciki da ake mata gyaran jikin amare da ita suka cigaba da hirarsu sai mai gyara da take sa baki a wata hirar ,Shigowar Samiha yasa mai gyara fara yiwa Samihan ta aje musu rafar kudin da Ra'uf ya bata tace"Yaya Saudat gashinan ayi lissafin abinda ba'asiya ba ko sunyi kadan sai aba Driver ko Yaya Musa ya karo"Saudat takalli kudin tace"yanzu duk Ahmad ne yabada wa'dannan kuda'den masu yawa ,ke Samiha ba kya tausayin Ahmad ko "tace" A'a yayan sane ya bayar ,amma shima idan ya bayar ai dolene tunda shi ya tattago yin auren,komai sai kice a riqa tausayawa haka ma kike cewa Yaya Mujahid kenan,bakisan maza ba anuna ana tausayinsuba kusan duk basu da halarci"Murmushi Saudat tayi kawai tace"ke matsalarki kenan a fadamiki goma ki fadi dubu"Rufaida tace"wallahi Yaya Saudat haka take"Samiha ta harari Rufaida tace to aiku gaskiya ne bakwaso a fada"abunda yakamata a siyo ba asiyo ba suka fara rubutawa da yamma suka tafi gurin kunshi da suke saran tafiya Sakoto da asuba saboda daurin auren da za'ayi a can ranar Lahadi da zasuje ana i gobe biki da ranar Laraba sukayi hidimar bikinsu da kawayensu abokan karatunsu maza da mata da angwayen babu wanda yaje dan sai bayan bikin da sai ankai amaren angwayen zasu hada Dinner kowa da shi da Family dinsa banda ma ahalin matan nasu sai tsinta tsinta Saudat cema za'ayi dana ta 'yan uwan kasancewar ita auren zumunci auren gida za'ayi musu ita da Mujahid din nata ABDURRA'UF ya 'dan duba gefen titi da suke tafiya ganin mota a tsaye gefen hanya yace" Mukhtar dan duba Kaga kamar mota na gani a tsaye?ya kamata ka fita kaji lafiya,ni a gajiye nake na dade rabona da tafiya a mota mai nisa"Murmushi Mukhtar yayi ya maida dubensa wajen da Ra'uf yanzu na masa yace "eh nima naganta, Sai dai kuma kana ganin ba matsala Idan mukayi haka, Duba da yadda rayuwar ta zama a yanzu" "Eh babu komai insha Allah sai Alkhairi tunda niyyar taimako mukayi,Allah zai dubi zuciyarmu" Abba Aliyu wato mahaifin Rufaida ne a motar yana kokarin kiran wayarsu Abdul-Ahad da Abba Bukar ya sanarmusu fashewar da tayar motarsa tayi yanzu ko za'asamu mai gyara daga Zaria suzo a tafi da motar da yake ta kiran wayar baya samu Network ya hana ta shiga ,gefensa da ABDUR-RASHID ne da ya biyo ta Kaduna ya dauko ABDUL-RASHID daga gidan ZAINAB Inda mukhtar ya karasa da sallama a bakin sa , Da murmushi ya amsa masa sai da suka gaisa ya kuma mi'kawa ABDUL-RASHID hannu sukayi musabiha, inda mukhtar ke tanbayar ABDUL-RASHID sunansa,ABDUL-RASHID ke shaidamasa sunansa Abdul-Rashid. Kafin mukhtar yace ma Abba Aliyu "yalla'bai mai ke faruwa ne naga kun tsaya a gefen titi ko wani kuke jira yace masa" a'a ko 'daya tayar mota tace ta fashe muna baro cikin garin kaduna yanzu gashi banida wanda na sani mai gyara a cikin Kadunan,kuma banida safayar taya nakira Number din wanda nasani taki shiga " Mukhtar ne yace"Allah ya kara kiyayewa bara nazo" "ya amsa da amin, to nagode" "Mai ya faru ne mukhtar" inji Ra'uf Mukhtar yace"tayarsu suce ta fashe" "Subhanallah ka kira mai gyara bai kamata a barsu a tafi ba, ga abinci ka mikamusu" Abdur-Ra'uf ya fa'di haka tare da mi'kawa Mukhtar abincin dake leda mai 'dan girma Sai da mai gyaran yazo yayi gyaran suka 'karasa kaduna inda Abba ALIYU ke ta Sanya Albarka a garesu tare da addu'oi ma banbanta "Maraba da zuwa mutanan kasar waje" Hajiya take fa'da da murmushi da ya nuna har a saman fuskarta Mama ce da Yakumbo suka 'karaso falon suna nuna murnar ganinsa Inda shi ko Ra'uf yayi 'dai 'dai a kujerar falon yana maida gajiya dan agajiye yake tibis yasha wahalar tafiyar Yakumbo ta ce "wato Hannatu ta ri'ke ka sai yau kataho ko?" ta fa'da tare da 'kara sakin murmushi fuskarta Hajiya tayi saurin karfe zancen da cewa "ahaf ai nasan za'a rina taya zan yarda da maganar ki suwaiba ace har yaron nan yayi sati biyu kice baije gurin hansatu ba, Ai nasan da cewa nice bakwa 'kaunata" Mama ce mai cewa haba "maman jabiru ai kinsan da yaje gurin hafsatu ba ta yadda za'ayi ki'ki sani tun jiya da su Lamido suka fara isowa" "Suwaiba babu ruwanki tun da kinfi kowa sanin abunda yaran nan nawa suke yi min duk akan 'ya'yen Hassatu yanzu zaki zomin da wata gulma" Kafin ta 'kara cewa wani abu gaba 'dayansu suka bar falon Suwaiba ta dubi Yakumbo tana bata ha'kuri "Hansatu kiya hakuri kema kinsan halin yayarki muyi ta yimata addu'a Allah ya shiryeta" "Insha Allah ,amma Halayyar Yaya Hanne, Maman Hamidu badai zance komaiba tunda kince Allah amma abu tunda jajayen sahu ake har zuwa yanzu bata canza ba" inji Yakumbo wadda ita gani take abinda 'ya'yen nata ke ma yayarta ta basa yimata sai dai ita bata gani, Kullum gani take ita ake yiwa batun yanzu ba tuntuni yayarta ta ke ganin haka , kuma ita ina taga Ra'uf 'din da idanunta banda zuwan da tayi ranar da zaizo 'kasar da guntun hawaye ta 'karasa shigewa wani 'daki Shiko Ra'uf kai tsaye 'dakinsa ya shige yanajin shigowar wasu mata falon da suka tarar da banbamin da Hajiyar keyi da cewa "Ai ni dai na kwari kaina da na ha'da zuriya da Hansatu duk an mallakemin 'ya'ya ba jabirun ba ba usman 'din ba Zuga Hajiyar suka shiga yi 'daya a ciki nacewa "Hajiya ai tunda kika bari 'ya'yanki suka auri 'ya'yan Hansatu ai sai dai kiyi ta addu'a Dan kuwa----" Da wannan Ra'uf ya shige cikin daga cikin dakinsa da yake cikin falon ,bai karasa jin maganarsu ba,da baya ma kaunar jinta wato har a gabansa ma maganar mahaifansa za'ayi saboda a nuna isa da fifiko akansa shida mahaifan nasa ,dafe kansa yayi da ya ke matu'kar sara masa, Bai ko tsaya watsa ruwa ba ya fada gado yana danna wayarsa, Sai da yaga kiran momy ya katse yabi kiran suka shiga fira yana bata labarin abubuwan da suka faru bayan zuwan sa Nasiha ta dinga yi masa data sanyaya zuciyar Ra'uf sosai Jin bu'de 'kofar tare da yin sallama yasashi saurin tashi zaune ganin mai sallamar da yake jinta tamkar Ammi da Momy a zuciyarsa,Ga ma kuma kamannin da takeyi dasu,Ba wata bace illah Yakumbo,Sakkowa yayi daga gadon fuska dauke da Fara,a yana kar'bar 'katon farantin hannunta yana cewa"Kai Yakumbo irin wannan kayan sai su ya dake ki jawomana cinya" Dariya Yakumbo tayi tace "Su dai bello sayi badai kaiba" Ra'uf yayi murmushi yace "To ni 'din gunma indiya zamu tafi har ki warke" "Allah ya 'kara kiyayewa" inji YAKUMBO, Ra'uf ya amsa da "Amin dai yakumbo" Abincin ta shiga zuba masa Inda take sanar masa ita tayi girkin Dan shi ka'dai kawai Ra'uf ne ya dubeta bayan yagama cin abincin yace "Gaskiya yakumbo kin iya girki idan nayi aure ke zaki koyama matata irin girkinki" "Kamar gaske auren zaiyi?, Ga dai Ahmad nan zaiyi ya barka saura kuma bello shima, kai ka tsaya ruwan ido, shekarunka yakai talatin yanzu amma ka'ki yin aure, Murmushi yayi ganin Yakumbo so take dai dan dole sai ta cikamasa shekaru takaisa inda baije ba yace " Eh yakumbo da gaske nake nasamu matar da nakeso nima yanzu, na yarda dai Ahmad yarigani aure amma bazan yarda bello yarigani ba insha Allah, ya 'dora dacewa ba ruwan ido na tsaya ba sai dai yanzu ne nasamu wadda tayi daidai da tsarina". Inda ya shiga bawa Yakumbou labarinta, da a koda yaushe yake jin sonta aransa ya kuma kasa daina jinsa. Ita kanta Yakumbo taji lokaci guda ga labarin Rufaidan da ABDUL-RA'UF ya bata ta shiga ranta Karfe Biyar su Ammi suka iso Nigeria Dan-ladi driver yaje daukosu dakai tsaye gidan Malika ya fara kaisu suka aje Safiyya da itama kanta batasan shiga cikin wannan ahalin gudun kar a batawa Safiyya rai yasa Ammi ta yanke shawarar ta zauna gidan Malika duk da anan ma bata tsira ba Safiyyan amma bakamar a gidan Hajiya ba Sunyi murnar zuwan Ammi gaba daya ahalin kasancewarta cikakkiyar yar ahalin musamnan RA'UF kamar ya shekara baiga mahaifiyarsa ba yake jin murna da kowa sai da ya fahimci haka Zaune suke a babban falo wajen large tara na dare da yawanci bakin wasu duk sun kwanta hakan yasa"BAFFA ALHAJI ya zauna a falon cikin 'ya'yensa da matansa da jikokinsa da MA'U ke zaune cikinsu tana bawa kowa tsarabarsa da RA'UF ke taya ta godiya suke sosai "RA'UF da tun 'dazu yake son tanbayar AMMI ina Safiyya ya dan dubi AMMI yace "AMMI ina SAFIYYA ban ganta ba kuma nasan da ita za'a taho "tana gidan Malika " Jin ko haka da Hajiya tayi "yasata bata rai ta fada" wallahi MA'U indai baku fitar da wannan yarinyar daga cikin zuriyarmu ba zan sallama miki JABIRU tunda bashi ka'dai na haifa ba,Kin zamar masa fitina a rayuwarsa kin mallakesa,har wayau bazan daina danasanin ha'da zuriya da HANSATU ba"BAFFA ALHAJI jin maganganun da HAJIYA keyi marasa da'di gaban jikokinta wadanda ma busu San halitta ba da ba'a KADUNA suke zaune ba yace"Haba HANNE irin haka baikamata ba yarinyar nan SAFIYYA itama ta muce kuma 'da na kowa ne bakasan wazai tallafeka ba,kuma komai lalacewa"MA'U ma taki ce ke kina fadar haka a kanta mai zahana ki hana wasu fara"ganin fadan da BAFFA ALHAJI ke mata gaban mutanan falon yasata tashi ta fice fu kamar iska"mutanan falon da duk jikinsu yayi sanyi nan yanayin halayyar Hajiya HANNE da har yau suka kasa sabawa BAFFA ALHAJI,ya shiga kwantar musu da hankalin da nusar dasu ita haka Hajiyar take tuni batun yau ba sai dai su cigaba da hakuri da halayyarta. HAJIYA HANNE ce ta maida dubanta ga Ammi tana cewa "yanzu Ma'u sai an je har Sokkwato saboda d'aurin auren nan?" Ammi ta ce "to ya za'a yi Hajiya? Yanzu haka ma Ra'uf ya fa'damin sun yi nisa, kuma Ahmad ya fad'a min ba 'yan asalin Kano bane, sai dai mu taya su da addu'ar dawowarsu lafiya, amma sun fa'damin da amaryar za'a taho". "Oho musu dai, ace mutum ba zai yi auren zumunci ba sai yaran da ba wanda yasan asalinsu" Ammi ce ta mi'ke wannan hirar tasu da dama gaisheta taje yi ta tareta da wannan zancen tace"Hajiya bari na shiga gurin Maman Karima naji ance acen ake aikin abincin bikin"tace"Eh hakane,ki kiramin NAFI daganan"ta amsa mata "to"da haka ta fice daga dakin tayi hanyar bangaren MAMAN KARIMA 'din*JININMU 'DAYA* Na Sadiya Ibrahim Khalil (Sadiya Khalil) *WANNAN SHAFIN NAKU NE MASOYAN LITTAFIN JININMU 'DAYA SAKON GAISUWARKU YANA ZUWARMIN DA ADDU'AR FATAN ALKHAIRIN DA KUKE MIN ALLAH YA BAR KAUNA😊😊* Page 20 Abba Aliyu da Sallama a bakinsa ya qarasa shiga cikin falonsa kallonsa Ummi Hauwa'u tayi kafin tace "sannu da zuwa Abban ABDUL-RAFI" ya amsa da "yawwa Hauwa"mikewa tayi daga zaman da tayi daga baiwa RA'IS abincin da take ta tashi ta nufi kitchen RA'IS gurin mahaifinsa kai tsaye ya nufa ya daukesa yana masa wasa mintina kalilan UMMI HAUWA'U ta daw falon da sallama da ruwa dauke a hannunta da Kofi saida ya sha ruwan kafin ta kallesa cikin nutsuwa tace " Ya naga ka dawo gida tun yanzu ina meeting(taro)da za kuyi" "Hmm kedai bari,ai sam director bai kyauta ba tun fitar da nayi muna can jiransa,bai zoba sai yanzu yayi mana waya ya fadama bazai samu halartar taronba?" "Kai amma bai kyauta ba amma kila yana da uziri amma da ya fadamuku tun wuri kaga ai da muntafi bikin nan" "Kedai bari HAUWA'U ni kaina abinda ya qara batamin rai kenan naso zuwa daurin auren SAMIHA ko dan yadda iyayenta da ita kanta suka dauke mu" "Wallahi kuwa to ya za'ayi haka Allah yaso,amma gasu ABDUL-RAFI sun wakilcemu ai" "Hakane kunyi ko waya da yaron ma kuwa?" "Eh munyi waya dazu da ABDUL-RAFI yace,a lokacin shirye-shiryen 'daurin auren ake" "Allah sarki ,dama 'daurin auren Safiya ne" "Eh ai naji suna KADUNA za'a kai SAMIHAN kuma da 'yan daurin auren zasu tafi,na dauka kaga Invitation 'din ai,na gansa akan lokar 'dakinka jiya" "A'a bangan shiba ina Sauri zan fita SAMIR ya kawomin , ina ga yaron ne yake aiki acan KADUNAN,amma ai shi iyayen yaron ai anan suke da zama,baban yaron ICP ne na yanzu" Murmushi tayi kawai tace"Eh nagani a Invitation Allah ya sanya Alkhairi,ya basu zaman lafiya" "Amin,ina sauran yaran ne" "Suna ciki amma RUMAISA ta fita na aiketa gidan HAJIYA RABI" "OK" daga haka suka cigaba da firarsu ******** 'Karfe 11 na safe Aka daura auren SAUDAT HASHIM SARKI da MUJAHID AHMAD TIJJANI sai SAMIHA HASHIM SARKI da AHMAD USMAN MAHMUD 'DANBATTA Shigowar amaren cikin falon da suke tare da 'yan uwansu da suke 'yam mata da kawayensu 'dai'daiku da suka taho tare daga kano da a kawayen SAMIHA RUFAIDA ce da NASIBA kawai sukazo bikin,cikin ankonsu suke na atamfa da yayi musu kyau gurin da su MOMY MARYAM suke zaune cikin falon itada 'yan uwa da abokan arziki yasa su karasawa suka gaggashesu amsawa sukayi da murmushi kan fuskar kowaccensu suna yi musu addu'ar fatan Alkhairi da haka suka mike don barin gurin MOMY MARYAM ta tsaida RUFAIDA da cewa"YAYA BILKI kinga 'diyar HAUWA'UN RUFAIDA da nake ce miki kawar SAMIHA" "Masha Allah gatanan 'yar kyakkyawa har kama suke da SAMIHA,banga mamarta taba" mikewa RUFAIDA tayi da wannan zancen ba tare da taji mai MOMY MARYAM da sauran matan dakin zasu fada ba *** Amaren ne suke karasowa jikin motar da angwayen su AHMAD da abokansa ciki yarda RA'UF da suka fito don gaisawa da yi musu iso cikin gidan su SAMIHA suci abinci ayi photuna daganan kasancewar gidansu SAMIHA babban gida ne kuma gidan sarauta mai 'bangare 'bangare *AHMAD RA'UF yake tabawa yana nuna masa amaryar da kawayenta da suke tahowa da ya kasa cire idanunsa ga RUFAIDA da take tsakiyarsu da kallo daya yayi ganeta itace suka taba haduwa waccen ranar a store dan kullum saiya tuno fuskartabanda addu'ar da kullum yake Allah ya qara hadasu ,AHMAD ne kallesa ya katse masa tunanin da take da fadin "YAYA RA'UF ya ya dai meya faru" "Kalli waccen yarinya ta tsakiya da suke tahowa da amaryarka" AHMAD fuskarsa ya 'daga ya kallesu da RUFAIDA ya gani ita ce a tsakiya a layin da suka yi,da kafin yace wani abu suka karaso wajen da sallamarsu,amsa musu sukayi gaba 'dayansu abokan angon gaisawa suka yi da RA'UF ya kafe RUFAIDA da kallo ko 'kiftawa ba yayi tunda suka iso gurin da suke "Amarya bata laifi kota kashe 'dan masu gida"abokan AHMAD suka fa'da cikin tsokana da fara'arsu sukai maganar" Kawayen SAMIHA sukayi saurin cewa "Bata kashe ba dai da har gida za'a korota karewar laifi ma" "Haka dai kuka ce" inji BELLO da yake cikinsu RUFAIDA data 'dago kai taga mai son karyata maganarsu anan suka hada ido da RA'UF taga iron kallon da yake mata tayi saurin dauke kanta zuwa 'kasa" NASIBA da itace tasa baki a maganar yanzu tace "Ai haka ne, yanzu dai mu dai mu shiga daga ciki,kuci abinci da lemo kun shawo tafiya" Murmushi su AHMAD da abokansa sukayi kawai,su RUFAIDA ne da amarya SAMIHA suka yi gaba ,angwayen suka take musu baya da RA'UF a cikinsu gani yake hatta AHMAD bai kai sa murna ba shida yake ango danshi yau muradin zuciyarsa ya gama a nasa tunanin.*JININMU 'DAYA* *SADIYA IBAHIM KHALIL* *(SADIYA KHALIL)* *WANNAN SHAFIN NAKI NE AYISH HUMAIRA MUHAMMAD MY SISI INA MIKI BARKA DA DAWOWA ONLINE KIYI YADDA KIKESO DA WANNAN SHAHIN DONKE AKAI KAWAI* PAGE 21 Zaune suke angwayen a falon hankalin kowa naga abincin da aka kawo musu Friend rice da sinasir sai kayen soyeye soye,Ahmad Ra'uf ya duba da yake kokarin kai ruwa bakinsa yace "AHMAD kasan yarinyar dana nunama 'dazu ta tsakiyar SAMIHA naji har magana kayi mata" yayi maganar yana aje gorar ruwan da ya bude yasha a kasan carpet "Eh nasanta Cousin's din mata tace Rufaida sunanta lafiya maiya faru"ya karasa maganar yana kallon RA'UF kallon rashin fahimtar a inda ya santa" "Bakomai nasanta ne" Murmushi yayi Ahmad kana yace "Malam kodai itace kayi gamo da ita kwanaki kafadamin gaskiya kar naki baka ita tinda kasan kanwar matatace kuma kawarta" "Wallahi baka isa Ba idanma kace haka toni da nake matsayin kaninsa zan tsaya masa ayi komai" cewar Bello dayake kai lomar doughnut bakinsa "Yawwa fadamasa dai ni dan Allah kiramin yarinyarma please (yi hakuri)" Abokan ango sukayi dariya da yawanci abokan sune duka suka ce "Kai Ra'uf ai duk saurin unguwar zoma tabari a haihu" Ahmad yace "Kuma kwa fadamasa dai" "Kaga idan zaka kiramin ita kakirata hakurin kwana nawa kakeso nakuma yi,vayan wanda nayi a baya" Ra'uf ya karasa fadar haka yana daukar wayar Ahmad ya danna yasa a kunne "Tunda bazaka kira ni bari nakira" Abokan nasu dariya suka sa ciki harda Bello da yaji suna neman kwafsa masa ya mike yabar musu falon ya nufi kofar fita daga falon jin an 'daga yasa shi tsayawa daga kofar falon "Assalamu Alaikum,Amarya Samiy" Yayi saurin katse maganar da Samiha keyi A daya bangaren aka fara magana "Wa'alaikumus salam,Yaya Ra'uf" saboda ta fahimci ba Bello bane tasan idanko vashi bane to baya wuce dayan biyu ko Ra'uf Murmushi Ra'uf yayi jin ta gane muryasa ya katse tunaninta da cewa "Dan Allah daya daga cikin kawayenki mukeso tazo" "To shikenan bari naturo ma wata" Da haka ya katse wayar sai da ya katse ya fara tunanin maiyasa ma baice Rufaida yakeso tazo ba tsaki yaja yana addu'ar Allah yasa Rufaida ce zata zo,da wannan tunanin ya koma cikin falon abokan nasu suka cigaba da zolayarsa shi kuma murmushi kawai yake abinsa ***** Rufaida Samiha ta kalla bayan ta gama wayar da take kusa da ita gefen gado dasu biyune kawai a dakin ta soma magana da cewa "Rufy Dan Allah kije gurinsu Ahmad,yanzu Brother dinsa (dan uwansa)ya kirani sunason ganin daya daga cikin kawayena,kinga suku ma sauran sun tafi gidansu Zainab din Momy Balki" "Eh hakane,amma banda haka Allah Ba inda zani" ta karashe maganar tana mikewa "Maiyayi zafi kuma haka Rufaida ko Ahmad yayi miki laifine" "Ko daya wallahi baimin laifi Ba illah dai abokansa kallo garesu musamman wani wanda ya dan darasu haske" Murmushi Samiha tayi tare da fadin "Nidai ki taimaka kije karsu sakemin waya" "Naji" da haka tasakai tavar dakin Samiha ta bita da murmushi har ranta takeson kawarta sai dai gashi sunkusa rabuwa har watarana ta yiyu ko wacce tayi wuyar gani ******** A hankali take tafiya cikin nutsuwa harta kusa isa kofar falon Ra'uf da ya hangota Kasancewarsa yana waje yana amsa waya wayar yayi saurin katsewa ya karaso yasha gabanta da murmushi a fuskarsa da gavatarmata da sallama dago idonta tayi ta dubeshi kallo daya tayi masa ta shaidashi shine mai kallon ta dazu gefe takoma ta amsa masa sallamar ta sake gaishesa karo na biyu ya 'dan murmusa kana ya soma magana "Gimbiya Rufy ya hidindimun biki" "Alhamdulillah" "Kinko shaida fuskata koda yake ta yiyu in ban sace zuciyarki ba, bare harki matsawa zuciyarki gurin neman wannan barawan" Murmushi tayi ka'dan "Gaskiya ban shaidaka ba ,nashiga goma satar me nayi maka dan Allah ka fahimtar dani" Shima murmushi yayi "Kar dai na tsorata Gimbiyar matan ,kin tuna kwanakin baya a store ban riqe dai sunan store din ba, munyi karo dake a lokacin to tundaga nan kikayimin satar zuciyata" Sai a lokacin ta tunosa ta fahimci kallon sani yake mata a dazu sai dai ita a dazu bata ganesa ba" "Naganeka " "Yawwa Rufee,karna cika ki da surutu bari na gabatar miki da kaina ni sunana AbdulRa'uf Jabir Danbatta cousins din Ahmad ne ma'ana dai (Abbansa kanin Abbana ne) haka momynsa kanwar momyna ne ina Delhi da zama da mahaifana kuma ina aiki acan,a takaice kenan ,naganki a tun wannan lokacin naji ina qaunar ki kasance mata a gareni insha Allah ina fatan ki amince dani kuma da yiwa kaina fatan Allah yasa bairigani ba,dukda bazanso haka ba amma dai zan baiwa zuciyata hakuri idan har haka ya kasance" Murmushi ya subuce mata jin karashen maganar tasa tayi shiru ba tare da tace komaiba "Kinyi shiru ko dai zuciyarki bata amince dani" Sauya maganar tayi "Bari na karasa cikin falon,inda ake kira na" Zaro ido yayi "Wato ba zaki amsamin maganarba kika canzamin da wata,to gurin wa zaki cikin bayan ga basaraken dake kiran gimbiyarsa to tunda ta gansa babu abinda yayi saura ko" Jinjina karfin halin Ra'uf itadai Rufaida takeyi wato daga haduwar sau daya zata amince masa "Kinyi shiru gimbiya" "Kaya hakuri..." Bai barta ta karasa maganar ba ya zaro idanunsa duka "Hakurin me harkinsa zuciya tayi raunin" Ita dai murmushi tayi "A'a cewa zanyi zan koma ciki tunda kafadamin sakon" "To naji vani number dinki yanzu" "Banida waya" Bata jira cewarsa ba tabar gurin dan ta lura baida niyyar kyaleta ta tafi Ganin tabar gurin yasa shi murmushi ya kyaleta dan yana ganin alamun nasara ko a yanzu,yana sane da balallai tayi masa doguwar magana ba kasancewar ba gida yazo ya je ya sametaba da haka ya bar gurin ya koma falon ***** "Angon gobe gaskiya gayu bikin Ahmad mu sashi a tarihi" abokansa da suke hangosa shida Rufaida ta kofar falon da take a bude sukayi hanzari fada yana shigowa falon Murmushi yayi "Kai Guys haka zaku ce" "Eh mana haka ne,ko ba haka bane gayu" inji daya daga cikinsu ya fa'di hakan "Khalifa ka kiyayeni" "To tuba nake ranka ya dade" Ahmad da ya shiga firar a yanzu ya soma cewa "Dan uwa Allah kayi sa'ar mace" Khalifa yasa baki karo na biyu "Gaskiya ne Ahmad babyn kyakkyawa tayi ba karya" "To naji dai,yanzu dai ka kira mana amarya muyi hutunan ayi shirin tafiya da amarya na matsu na koma KD" "Kadai fadi gaskiya malam Ra' uf kodai so kake muyi mu koma gobe a dawo bikinka ne"inji Bello Tsaki yayi ya sake ficewa daga falon dan yasan zasu takurasa ne da magana indai ya cigaba da zama sukayi dariya ganin ya bar musu dakin. *SADIYA KHALIL😊😊**JININMU DAYA* By Sadiya Ibrahim khalil (Sadiya Khalil) *Wannan shafin naku ne group mai albarka Sadiya khalil group Allah ya sadamu da alkhairi ya bamu ikon rubuta abinda zai anfanemu duniya da lahira Amin kuyi yadda kukeso da wannan shafin donku akayi*😊 Page 22 arfe 1 na ranar daurin auren aka taho da amarya Samiha da take kuka sosai na rabuwa ita da gida saidai da ziyara haka dai suka taho da yayyenta biyu aunty samira da aunty samina da kannen da yayyyen babanta dana mamarsu biyu da kawayenta cikin harda su Nasiba da Rufaida da bayan gama shagalin bikin da za'ayi a Kaduna yau bayan kai amarya zasu koma kano dasu Aunty Samina duk tare Ra'uf kuwa yayi sa'a motarsa su Rufaida suka hau da Mukhtar yake tuka motar Ra'uf da ya katse shirun motar da fadin " Da alama Mukhtar kurame muka dauko a motar mu" "Nima nafi tunanin hakan kuwa" Mukhtar ya karasa zancen yana maida hankalunsa ga tuki "Saboda me" Nasiba da Zainab suka fa'da itako Rufaida shiru tayi da kwata kwata bata sakewa a motar " "Yawwa to kudai naji magana ku kun fita daga jerin kurame,saura 'yar uwarku"Ra'uf ya karasa zancen yana sake kallon Rufaida ta gilashi Nasiba da ta gano nufinsa ta soma fadin " oh Rufee zakace mana,tana magana sai dai kasan ita sarauniya ce bata magana da kuyanginta matukar bata kama ba amma tunda Sarkin yayi magana to itama ba shakka zatayi" "Hmm haka dai kikace banga alamun zata yi ba,mu muke kidanmu na lura muke rawarmu ni na aje sarautar a yau amma ita na lura ba haka bane anata fannin" Wayar Nasiba da tayi kara yasata kin basa amsa ta duba wayarta ganin mai kiran AbdulRafi ne yasata saurin 'dagawa AbdulRafi yanajin Nasiba ta 'daga ya fara da "Nasiba ina kuke ne kunsan fa yau zamu koma keda Rufaida muke jira" "Yaya AbdulRafi muntaho kawo amarya Samiha,muna tare da Rufaida ma" "Amma buku kyautamin ba kunsan zan jiraku" "Wallahi Momy ce tace mutaho kai amaryar daganan saimu taho dasu Aunty Samina" Tsaki AbdulRafi yayi ya katse Wayar dan bakaramin lokaci suka bata musu ba da tuni sun manta sun bar sokoto dan sunyi dasu tare zasu koma baisan hardasu aka tafi kai amaryarba dole yasa shida Samir suka yi haramar komawa kano Nasiba ce ta dubi Rufaida ta soma fadin "Kin jini da Yayanku ko" "Eh au ke ba yayanki bane" "Sorry sister (yar uwa)yayanane mana" Daganan Rufaida tayi shiru har suka karaso Kaduna bata sake cewa komai ba sai dai Nasiba da Zainab da suke magana tare da Ra'uf ke sa baki a wata firar yana kuma cigaba da aikin kallon Rufaida ta madubi a haka suka karaso Kaduna Isah Kaita Road aka wuce dasu da a unguwar gidan Samiha yake gidan yayi kyau sosai an zuba kudi komai yayi sosai suna isa gidan Samihan suka firfito daga motocin zuwa cikin gidan da mortar amarya aka wuce da ita gidan sirikanta inda daganan sai akawota gidanta Ra'uf ne ya tsaida Nasiba dan ya fahimci tafi sanin Rufaida akan Zainab ita yakeso ta shigar dashi gurinta saida suka gama shiga dakunan gidan da kitchen gidan da yakasance plat saidai yayi kyau dukda babu dorin benen iyayen Samiha ma sunyi kokari sun kashe mata dukiya sosai part biyu ne a gidan nata dana Ahmad din nan suka dawo falo suka zauna suna yaba kyan gidan Ahmad yayi kokari sosai ***** Ra'uf da farin ciki a ransa suka baro gidan shida mukhtar dan ya samu Nasiba ta bashi lambarta zai kirata ta hadashi da Rufaida suna isa gida kai tsaye ta kofar baya ya shige falo saboda mutane dansu a lokacin suke shagalin bikinsu danma akwai 'yan bangaren Kawu Saleh da yawanci daudalar bikin acan sukeyi kai tsaye upstairs (saman bene) ya haye yana takaicin yadda dakinsu a gidan kakanninsu ya kasance a cikin gidan banda akwai dalilin shigowarsa gidan ba abinda zai kawo sama da gidan Abba Hamisu zai bi su Ahmad "Oyoyo Yaya ashe kun iso"jin maganar da turanci yasashi gane mai maganar kasancewar yasan wacece Safiyya ce duk tafi sauran 'yan uwansa sonyin turanci ko indiyanci dan ita bata damu da yin yaran Hausa ba dukda kasancewarsa yaransu shiyasama Hajiya Hanne ta kara kin Sofin dan ita batasan iyayi dukda yadda sofin me girmamata juyowa yayi ya dubeta da murmushi fuskarsa yana fadin "Yawwa Sofee yaushe kikazo gidan" Bata rai Safiyya tayi "Amma Yaya kasan banasan acemin Sofee,yanzu Ammi ce ta kirani nazo gaisheda su Hajiya" Dariya ta basa sai ya gumtse abarsa kar kanwar tasa taji haushi "Yi hakuri Safee, amma Hajiya bata yi miki fa'da ba ko?" "Eh batamin ba ai banmata turanci ba kasan Hajiya shine bataso,da zan fito ma cemin tayi har zan tafi" "Yawwa naji dadi,yanzu ina zaki kuma" "Gidan Aunty Malika zan koma" "OK ki jirani a mota zan dauko wani abu a daki na zamu wuce gidan Abba Hamisu,saimu saukeki a can ita Aunty Malikan batazo bane har yanzu "Tazo takoma yanzu shirin,tafiya Dinner anjima takoma yi" "Ok" ya karasa fadin haka yana karasa wa kofar dakinsa ya shige ita kuma Safiyya ta karasa waje ta isa mota ta shiga suna fira da Mukhtar da haka yazo ya samesu suka bar gidan a motane yake bata labarin Rufaida da ya nuna mata hotonta itada Samiha da sukayi a sokoto da wanda sukayi tare "Wow Yaya ai wannan matar taka ko a indiya samunta sai antona tana da kyau,hala 'yar uwar amaryar Yaya Ahmad ce ko" Murmushi yayi "Eh cousins sister din race" "Ah shiyasa naga suna kama" "Baki cemin tayi miki ba" "Haba Yaya wazaiga wannan yace bata masa ba" "To shikenan naji dadi ko kanwata" Da haka dai suka cigaba da fira yana sanarmata anjima zai hadasu a waya har kofar gidan Aunty Malika suka karasar da ita suka wuce suku ma ****** "Nasiba Allah kina takuramin kan maganar mutumin nan" Rufaida ta fada haka tana kokarin zira rigar material dinsu da suke shirin tafiya dinner da za'ayi da magriba za'a fara tafiya "Ba wani takura kinaso kina kaiwa kasuwa,ni amshi wayar yace zai kuma kira yanzu" Nasiba ta mikamata wayar tabar dakin tana fita Ra'uf ya kira ta saida takusa tsinkewa ta daga Ajiyar zuciya Ra'uf ya sauke jin ta daga wayar "Gimbiya nayi zaton bazaki daga ba" Murmushi tayi tana "Saikace kayimin laifi" "Hmm to bansan laifin ba saidai kona zuciyata data kamu da sonki lokaci guda,idanma laifin ne to itace tayi" "A'a ni bance ba" Murmusawa yayi ya Dora da cewa "Rufaida da gaske nake ina sonki jira nake na koma Kano naje na gabatar da kaina gurin Abba daganan sai su Dady na suzo so nake kafin nakoma Delhi asa ranar bikinmu" Batada yadda zatayi dashi haka ta cigaba da biye masa tana dan amsa masa maganarsa wadda kusan daga eh sai a'a itace maganarta haka sukayi sallama yace zai zo daukarsu anjima fita Rufaida tayi falon gidan Samiha da mai kwalliya tazo yi musu da Ahmad ya daukomusu" *SADIYA KHALILULLAH*🖊*JININMU DAYA* BY SADIYA IBRAHIM KHALIL(SADIYA KHALIL) *TUNATARWA DUK ABINDA KA RUBUTA TO KODA KA GOGE BAI GOGE BA A LITTAFINKA BA MUYI KOKARIN RUBUTA ABINDA ZAI ANFANE MU DUNIYA DA LAHIRA,MATA MUJI TSORON ALLAH KI DINGA TUNANI AKAN MIJIN NOVEL (LITTAFIN HAUSA)BAFA SAMUNSA AKE BA KARKIJI ANCE KYAKYKYAWA MAI KUDI MAI IYA SOYAYYA KI MAI ILIMI KI ZACI ZAKI SAMU IRINSHI KO KIMAIDA MIJINKI IRINSHI ,MUMA MARUBUTAN KI FAHIMCI YA DANGANTA DA IRIN LITTAFIN DA MUKE DA WANNAN WA'AZANTARWA DA NUSARWA KIKESON LITTAFINKI YA BAYAR SHIYASA AKE SA HAKA AMMA KI SA ARANKI MIJINKI KO WANDA ZAKI AURA YA FIYE MIKI MIJIN NOVEL DARI BISA DARI SHI MIJIN NOVEL KI DAUKA DALILIN KASANCEWARSA KYAKKYAWA MAI KUDI MAI ILIMI MAI IYA SOYAYYA DAN LITTAFI YAYI ARMASHI AKE SAWA KUMA KI DINGA DAUKA DUK DA HAKAN KUDIN NASA DA ILIMIN NASA DA KYANSA DA IYA SOYAYYARSA YANADA HALI MARA KYAU DOMIN DAN ADAM TARA YAKE BAI CIKA GOMA BA YANAYIN SAKON DA AKESON A ISAR NE YAKESA AKI SA WANCEN HALIN NASA MARA KYAU,AMMA BADAN A DORAWA YAN MATA DA SAMARI SAMUN MACEN NOVEL BA KO MIJIN NOVEL,DUKDA ANA SAMUN MAI KUDI MAI ILIMI MAI KYAU IDAN DA RABO MACE KUGA TA AURESA AMMA KISA A RANKI KOMAI RABO NE,SUMA YAWANCI MATAN NOVEL DIN SAIDA SUKA CI WUYA SUKA SAMESA AMMA KARKI SAWA RANKI SAMUN WANNAN MIJIN KO SON KI CEWA MIJINKI LALLE SAIYA ZAMA MIJIN NOVEL SAIDAI IDAN KINSAMU DAMA ALLAH YA KADDARAMIKI HAKA AMMA DAI KI FAHIMCI DOLE KISA MESA DA WANI HALI DA BAKYASO MIJINKI YAKASANCE DASHI,AMMA DAI SHAWARA GAREMU MAZA DA MATA MU CIRE WANNAN SHIRMEN NA SAMUN MIJIN NOVEL KO MACEN NOVEL WALLAHI DUK ZANCEN BANZANE MUMA MARUBUTAN BA IRINSU MUKE RAYUWA DA SUBA RAYUWAR WASU MUKE RUBUTAWA BA TAMU BA FADAKARWA MUKE AMMA TA JAN FADAKARWAR HAR ZUWA KARSHEN MASU AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN LITTAFIN MARA KYAU KO MASU HAKURI IRIN NA MUTANEN LITTAFI HAR ZUWA KARSHENSU MAI KYAU KO MUMMUNA KUNGA ANAN SAI MU GYARA RAYUWARMU IDAN MUNA AIKATA MAKAMANCIN AIKINSU MARA KYAU IDAN KUMA MUNA MAI KYAU SAIMU SAKE DAGE DAMTSE ,"DAMA DAGA RAYUWAR WASU MUKE 'DAUKAR DARASIN TAMU* *NAGODE WA MASU COMMENT DA SHARE DA VOTE,MUSAMMAN GROUP DIN JININMU DAYA FAN'S,FATI MANSUR TA GROUP DIN JININMU DAYA NAGA COMMENT DINKI DUK SHAFINKU NE WANNAN KUYI YADDA KUKESO DASHI MASOYAN SADIYA KHALIL* PAGE 23 7pm motoci suka zo daukarsu zuwa wajen da za'ayi dinner din Su Rufaida sunyi kyau sosai cikin ankon material sky blue da touch din baki da browan colour(ruwan sararin samaniya da kwalliyar baki da ruwan toka) sai mayafansu farare ya haska su sunyi uka fito kofar gidan Samiha da Ra'uf ya aje motarsa ya kirasu su fito ya karaso da jakunkunansu na kaya a hannunsu da zasu kwana gidan kanwar mahaifin Rufaida Aunty Zainab da take aure anan Kaduna tana zaune a Bayajidda street ita da mijinta da yaronta 'daya. Ra'uf shima yayi kyau cikin shaddarsa Golden colour yake yasha malum malum dinsa kamar shine angon shine kadai a motar Mukhtar yana can shi zaikaisu Momy Hannatu wajen Dinner din wajen motar suka karaso suka yi masa sallama ya amsa musu ya komar da kansa cikin motar da tunda suka taho yake kallo Rufaida da yake ji sonta yana kara yawa a tare dashi har mamakin kansa yake da farat daya sonta ya shigesa koda yake babu mamaki da ikon Allah kofar motar ya bude musu suka shiga yaja yana yi musu tsiyar sun shanyasa tuntuni yake jiransu wajen Dinner din suka karasa inda suka bar jakunkunansu motar Ra'uf kasancewar a motar zasu koma suka bada pass dinsu suka shiga ciki sun haska a gurin sosai kuma gurin a tsare yake kujerun da aka jera na karfe da aka jera a hall din suka zauna akansu da aka jera musu abinci kala kala da lemuka akan babban teburin jin abinci da kujeru suka zagaye teburin cikin tsari akeyin komai Ra'uf ne ya ja Husna da Safiyya su gaisa da Rufaida da suma suke cikin ankonsu golden colour da kalar ce ankon dangin Ahmad maza da mata gurinta suka karasa da Ra'uf yayi musu jagora cikin mutuntawa suka gaisa kamar ta sansu yaji dadin yadda Rufaida ta mutunta 'yan uwansa suma inda suke zaune suka koma suna koda Rufaida kuma suna fadin kyawunta Ra'uf shima cikin 'yan uwansa maza ya koma bayaso taga kamar yana takuramata basu jima a gurin ba aka kira Rufaida ta ba da labarin yadda amarya takasance ba dan tasaba ba tayi magana da harshen hausa cikin kyawawan lafuza da haka takoma da mutane suka fara maganarta Aunty Malika da su Husna suka nuna mata itace budurwar da Ra'uf keso sosai taji ta shiga ranta har daga kallon farko data yi mata har qaguwa tayi a tashi Dinner din ta je gida ta fadawa Ammin Ra'uf yadda surikartasu take dan kafin a kira Rufaida su Momy Asma'un suka bar wajen Mukhtar ya daukesu a mota zuwa gida. Shima Ra'uf da yake hango sanda take maganganun nata cikin kyawun lafazi sai ya qara jin Rufaidan a ransa itace matar da ya dade yana addu'ar samun irinta tabbas ta hada komai na irin matar da yakeson takasance abokiyar rayuwarsa addu'a daya yake Allah yasa takasance mata a garesa. Sai da aka yi hotuna da amarya da ango sannan aka fara kokarin tashi daga Dinner din. 9pm aka tashi daga Dinner din aka fara dibar mutane zuwa gida a motoci ********* "Nasiba yanzu ina zankaiku naji kince min ba gidan amarya zaku kwana ba" Ra'uf yayi furucin da yake kokarin tada motarsa da yanzu shike tuka motartasa da kansa. "Eh gidan Auntyn su Rufaida zamu je a Bayajidda street take" "Ok kice Auntynmu ba" yayi maganar yana Jan motarsa ba tareda ya kuma magana ba. Da taimakon Rufaida da take masa kwatance ya kaisu har kofar gidan gidanta maikyau da karamin gate dinsa ,yayi parking din motarsa suka fito su Hudu Rufaida,Nasiba,Zainab,Iklima Yatsaida Rufaida daya fito daga motar "Zanje gida zan kiraki wayar Nasiba,ki gaida Aunty idan batayi barci ba idan na kira zaki hadamu" "To Allah ya kaika lafiya" "Amin nagode sarauniyar mata" Da haka tabar gurin tabi bayansu Nasiba Shima murmushi yayi yabi bayanta da kallo yayi waajen motarsa yaja yabar gurin "Yam mata har kungama hirar" Zainab ta furta haka bayan sun kai kofar gidan Aunty Zainab da suke cewa Aunty da Nasiba ke kokarin kiran Aunty Zainab da Ummi Hauwa'u ta turo musu Number dinta. "Zee banasan wulakanci..." Wake wulakancin Aunty Zainab da taji Rufaida na fadar haka da ta fito bude musu kofar gate din,shiga sukayi ta rufo kofar" "Wallahi Aunty Zee ce daga mun gaisa da wani wanda ya kawomu nan yanzu take min maganarsa" Aunty ta 'dan ha'de rai kana ta furta "Ni banasan kula kulan nan na abokan anguna ya wanci dukda matansu wasu kuma da wadanda zasu aura ko idan sunada auran da wadanda zasu kara bakuba sakarci ne yawanci yakesa kawayen amarya soyayya da abokan ango gurin bikin kawarsu har su amince musu kuma yawanci da angama bikin zasu manta da yarinyar idan ta zurfafa ita zata jiyo kusan mutuncin kanku" tana maganar tana kokarin tura kofar falon su Rufaida suna biye da ita Jin tayi shiru yasa Nasiba tayi caraf ta karfe zancen "Aunty saurayin Rufaida ne abokin Ahmad ne,tun kafin biki suka ha'du da shi da bikin ne soyayyarsu ta kara kulluwa" Murmushi Aunty Zainab tayi ranta tana yiwa 'yar dan uwan nata Allah yasa na kirki ne ya kuma tabbatar musu da alkhairi shiga cikin falon sukayi duk suka jefar da jakarsu a saman kujerar falon suna maida gajiya Rufaida tana ganin Asad 'dan Aunty Zainab a falo ta daukesa tana masa wasa Ruwa da abinci ta kawo musu suka ci daganan suka gaishe da Aunty Zainab da take musu tsiyar busu fadamata Dinner din ba aida taje wayar Nasiba ce tayi kara ta mika hannu inda ta aje ta ta duba mai kiran ganin Ra"uf ne yasata mikawa Rufaidha wayar saida sukayi yar fira yace taba Aunty su gaisa sosai Aunty zainab taji Ra'uf ya kwanta mata arai nan ta yi wa Rufaida addua a ranta Allah yasa da gaske yake da aure yazo gareta ya kuma kareta da fadawa tarkon mayaudara suna gama wayar Aunty Zainab tayi zaman dirshan suna fira kamar duka tasansu alhalin Nasiba kawai ta sani bayan Rufaidan da haka mijinta Haris ya shigo ya samesu sannu da zuwa suka masa tare da gaishesa ya amsa fuska sake kana yace wa Rufaida "Ansha Dinner baki gayyace mamarki Ba bare nasa ran zaki gayyace ni ,da mukayi waya da Yaya Aliyu da Mamarku suke sanarda mu zaku zo anjima ku Kwana anan yanzu kuna wajen dinner" "Uncle Haris ayimin afuwa yanzu Aunty taga ma mana maganar walllahi mantawa nayi kuma kaga bamu baro Sokoto da wuri ba" "Zaki tuna ne ai Allah ya sanya Alkhairi" Ya na gama furta haka yabar wajen da Asad a hannunsa da yana shigowa ya daukesa shigewa ciki yayi Aunty Zainab tami ke tabi bayansa Da Amin suka bi addu'arsa suka cigaba da fira Rufaida ta dubi Nasiba ta fara magana "Wai niko Nasiba ina duriyar Sir Abdul-Rahman" "Ke dai bari mun rabu da waya tun waccen ranar amma bari nakira mana shi mugaisa" Ta karashe maganar tana mika hannunta inda ta aje wayarta ta dannan number din Abdul-Rahman Ringing biyu tayi ta katse baifi sakan biyu ba wayarta tayi kara ta duba taga Abdul-Rahman ne ta 'daga ta kunna karar wayar da zolaya ya fara yana "Amare to ya hidindimun biki" "Sir Alhamdulillah,ina yini" "Lafiya lau ya biki" "Alhamdulillah sir" "Ina Amarya" "Wallahi Sir tana gidanta yau aka kawota mukuma muna gidan Kanwar Abbansu Rufaida sai zuwa gobe zamu dawo Kano insha Allah" "To Allah ya tabbatar da Alkhairi ya kaimu naku,ina Rufaidan da take bata" "Amin" Nasiba ta mikawa Rufaida waya suka gaisa sukayi sallama. Aunty Zainab ta dawo falon tace su koma daki suyi shirin kwanciya. *SADIYA KHALILULLAH🖊️*️*JININMU 'DAYA* *BY SADIYA IBRAHIM KHALIL* *(SADIYA KHALIL)* *PAGE 24* *WANNAN SHAFIN NAKUNE SADIYA KHALIL CONVERSATION ROOM,DA JININMU 'DAYA FAN'S GASHINAN KUYI YADDA KUKESO DASHI MASU COMMENT KU CIGABA DA COMMENT'S KU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAHIN🥰🥰SADIYA KHALIL NAGODIYA* *PAGE 24* *** 9am Suka gama shirinsu suka fito kofar gate din gidan da Ra'uf yazo yake jiransu su fito ya kaisu gidan amarya Aunty Zainab itada mijinta Haris har kofar gida sukayi musu rakiya Ra'uf da ya fito ya gaishesu cikin girmamawa da Aunty Zainab taji kunya sosai tunda ya girmeta kuma taji ya kwanta mata a rai haka suka shiga mota ya jasu ran Aunty Zainab ba dadi bataso tafiyarsu ba. Ra'uf suka gaisar ya amsa yana tada motarsa Saida suka soma tafiya ya cewa Nasiba da take gaban motar "Yana ji Rufee Sarauniyar mata shiru kodai kun mata laifi ne" Nasiba ta juya ta kalleta daga bisani ta furta "Ko 'daya ba laifin da aka mata kasan miskilace budurwar taka,saika riqa hakuri" Dariya yayi ya furta "Baruwana keda kawarki kuma tana jinki" "Ai tasan hakane" Rufaida da tana jinsu tayi banza dasu dan Nasiba akwai surutu sunsan halinta Basu jima suna tafiya ba suka karasa Isa kaita Road suka shige kwanar gidan Samiha saida Ra'uf ya fita ya bude gate din gidan kasancewar basuda mai gadi kafin yakoma yaja motar zuwa cikin gidan a harabar gidan suka tarar da su Aunty Samina da har sun shirya tafiya Ahmad ya kira Drivernsu zai maidasu gida Sokoto da Samiha harta fara kuka na tafiyarsu kamar wata yarinyar goye bayan basu duka zasu tafi a lokacinba Sai da suka gaisa kafin Yaya Balki ta furta "Ku kuma sai yanzu zaku dawo kun daka tasu Rufaida da ita Rufaida a gida take" "Mama bahaka bane abokin ango ne baizo da wuri ba"Zainab tayi maganar da sigar tsokana "Ba wani laifinsa basai kun shirya zaku kirasa ba,ku wuce ku shiga mota keda Iklima" Ra'uf yaji dadi da yaga Yaya Balki bata goyi bayansu ba ya kuma fahimci Zainab da wasa tayi maganar dako anan yana kyautata zaton ya samu shiga murmushi yayi Da haka su Zainab suka shige suma sauran matan da Yaya Balki suka shige motar har jikin motarsu su Rufaida sukaje yi musu rakiya sukuma suna zolayar Rufaida said bikinta zasu zo Kano itadai murmushi tayi Ra'uf da matso shima yayiwa su Zainab da iyayensu sallama bayan sunyi ne ya zaro kudi masu yawa ya mika musu sunji godiya suka yi masa da haka motarsu tabar gidan motarsu Cikin gidansu Aunty Samina suka koma da ita da Aunty Samira da Nasiba su sai anjima Ahmad yace musu Ra'uf zai ajesu gida da shima yau zaikoma Kano ******* "Rufaida gaskiya kinyi sa'ar masoyin gaskiya samun masoyi kamar Ra'uf a wannan lokacin abu ne mai matukar wahala Dan inada yakinin da gaskiya yazo aurenki zaiyi dan Allah ki riqesa hannu bibbiyu dan yanada kyakkyawan hali,Ahmad yasha fadamin kyawawan hali irinna Ra'uf kuma yafadamin da gaske yake sonki har sun kira Abbanmu sun shaidamasa zasu je tanbaya kuma yanaso kafin yakoma Delhi ya tura magabatansa asaka rana ayi komai"" Rufaida da take kokarin gyara kayan jakarta takalli Samiha "Gaskiya ne Samiha insha Allah zan riqesa da hannu bibbiyu ina godiya kawata" "Babu komai kawata nidake tamkar abu daya ne,ina tunanin nama fiki jindadin hadin nan" Ido ta zaro "Eh mana dan yaya Ra'uf yace min bakya wani sansa kike nuna masa" "Kijimin da mutumi idan ba goyasa ya keso na riqa yi ba bansan maiyakeso nayi ba" "A to kidai gyara dan gaba kadan mijinki zai zama dan nama rage miki zance ban fadamiki Abba dazu ya kira Ahmad a waya yake shaidamasa Abbanku ya masa izinin zuwa gurinki zance yamace basai sunzo Kanon ba,kinga nanda wata shida zamusha biki ni tuwona maina abu namu" Ni kinga ki kyaleni haka da wannan maganar tayi maganar tana mikewa "Au zamu rabunma shine zaki mike kibani guri" Hannun Rufaidan ta riko "Yi hakuri kawata dawo ki zauna,tunda abin na laifi ne dan na miki maganar rabin ranki kuma gaskiya na fadamiki" "Wani gaskiya indai irin wannan maganarce banaso" "Zaki sone malama ki kyaleta samiy ina tunanin tafara jin kunyar mune shiyasa bata san mu riqa mata maganar Ra'uf din" Nasiba tayi maganar tana karasa zama a bakin gado dan duk tanajin mai suke cewa dan ta shiga bandakine sanda suka fara maganar" "Allah ya kyauta min jin kunyarku ai indai naji kunyarku gaskiya na fado" "Eh lallai fa munyarda,kuma indai ba kunyar bace mai zaisa kice abar maganarsa" Inji Nasiba "Saboda kuna sawa zuciyata da kunnuwana da idanuna son ganinsa dan jin muryarsa da sauraron sakon da zai isar ga zuciyata" Rufaida tayi maganar kamar ba ita tayiba Dan tagaji da maganar Ra'uf da suke mata dukda yadda xuciyarta ta aminta dashi lokaci guda da har mamakin kanta take dukda cewa kuwa tun ranar data taba sasa a idanunta take yabon halayar saurayin a ranta dan ko alamun fushi bata gani ba a fuskarsa ba tadai kawar da mamakin son da take masa da ya shige ta farat daya Dan babu mamaki da ikon Allah,dariyarsu ce ta maidota daga tunanin da take" Dariya maganar tata da tayi ta basu kuma sunga tayi shiru kamar ba ita ta yi maganar ba,nan suka hada baki gurin cewa "Allah ko yayi masoya" "Nasiba ta furta " ni kunga bari nayi sallar walhar nan nayi alwala na zauna fira" ",dadai yafi miki da kin zauna in kunji kunji" Rufaida ta karasa maganar tana kokarin barin dakin *"**"********** Abba Aliyu yayi murmushi bayan ya cire wayarsa daga kunnensa ya maida kallonsa ga Ummi Hauwa'u da Abdul-Rafi da suke saurarensa suji mai zaice musu dan sunsan dai da ganin murmushin fuskarsa akwai magana mai dadi a bakinsa "Hauwa'u kinsan dawa na gama waya,Alhaji Hashim ne yanzu ya kirani ne akan cewa wani abokin Mijin Samiha ya ga Rufaida wajen bikin yace yana sonta to yanzu dai Abba Hashim din yace ya ari bakina ya cumin albasa gurin amincewa yaron fara zuwa zance,su dan fara fahimtar juna kafin ya turo magana Abdul-Rafi ne ya soma magana dalilin da ya sa Ummi Hauwa'u ta maida maganar da take kokarin yi sai dai murmushin farin cikin dake kan fuskarta sai kuma taji Abdul-Rafi 'din yayi wata magana "Allah yasa nagari ne" fadin Abdul-Rafi da tunda aka fara maganar yaji ransa yafara baci da baisan dalilin fadin hakan ba" "Wacce irin magana kake ne wai Abdul" Ummi Hauwa'u tayi maganar tana kallonsa "Ummi addu'a nayi mata fa" Injishi yana kokarin mikewa danko maganar ma saiyaji duk ta gundiresa Abba Aliyu yasa baki a lokacin yana fadin "Saboda haka ake addu'ar dama ko,kai wai maiyasa bakada wani tunani kafin kafurta abu kamar wani karamin yaro,duk fadan da akema bakaji" "Abba kaya hakuri bada wata manufa nayi maganar ba"yana maganar yana karasawa wajen dining " ai dama haka zakace sakarai kawai" Ummi tayi maganar cikin bacin rai "Abdul yana kokarin zama a kujera yaji furucin Ummi Hauwa'u yaji le'ben kasa matukar haushi kalmar Sakaran da ummin nasu takirashi dashi yaji " Haba Hauwa me ye haka ya zaki ce masa sakarai yanzu da a gaban kannensa kika fadamasa ai rainasa zasu yi" Abba Aliyu ya fadi haka. "Allah Abban Abdul yaron ne baida tunani wani lokacin ko daya sai shegiyar wauta ya iya" "To naji dukda haka kidaina cewa yaran nan haka mu riqa musu addu'a" Da haka suka canza babin firarsu ko maganar Rufaidan busu sake bi takan taba 11AM Ra'uf ya fito falo cikin shigarsa ta shaida Ash ruwan toka Hajiya ta dubesa da take zaune a falon itada Yakumbo da Mama da sauran yan biki da busu gama tafiya ba "Kai mai kake nufi ne wai,badai tafiyar zakaiba,wa zaka tarar a gidan idan kaje ca nake ita kanta Hannatun sai zuwa gobe zasu koma" "Mama tasa baki a maganar "Keko Hajiya Hanne banda abinki saurayi kamar Ra'uf kya tanbayesa ina zashi,gida bakowa idan yaje,kika sani ko amarya muka samu a kano zashi gurinta" Murmushi yayi yace "Kamar ko kin sani Mama,na samo muku amarya tunda ku kun tsufa" "Hajiya Hanne ta ha'de rai ta kallesu gami da furta " wanne irin amarya bayan ga Karima nan ban fadama maganar ta ba tun kwanaki" "Eh kin fadamin amma nasamu Karima da maganar tace tanada wanda takeso" "Kodai kai ka fadamata kanada wadda kakeso ba" "Haba Hajiya ku daina gardamar nan kibar kowa da zabinsa mana, mudaiyi musu addu'a Allah yasa Alkhairi a zabin nasu"wata saga ciki tayi maganar mai suna Habi Shikenan Habi wallahi donke kikai maganar nan ne amma kinsan cewa Karimah bazata furta wa Ra'uf tanada wanda takeso ba,sai dai idan shi ya fadamata yanada wanda yakeso dan dama shiba dan mutunci bane uwarsa tagama lalatasa shi kuma ubansa an mallakesa,bare ya tabuka wani abun" Ra'uf ganin bazai iya jure kalaman kakartasa ba yasashi barin falon dan indai ya cigaba da sauraron kalamanta to zai iya fadamata duk maganar da tazo bakinsa,Yakumbo da Mama suma baya suka rufowa jikan nasu da sunaji Hajiya Hanne nace musu munafukai jika dai natane ko mace tace natane to tafi iko dashi bare ma kuma harda su karere wato Mama Suwaiba murmushi sukayi da fitowarsu harabar gidan har Ra'uf ya karasa wajen da motarsu take ajiye dan da saurinsa ya fito falon Mama Suwaiba ce ta kirasa da sunan da ita dince kadai take kiransa da sunan wato Babban mutum,dan sunan babban danta garesa danko da wasu sun fadamasa to gurinta sukaji tana fadamasa suka kwakkwaya ,gurin da suke tsaye ya koma hakuri suka shiga basa akan halin Hajiya Hanne shima hakuri ya basu dan yasan sums suna matukar hakuri da ita fiye dashi namiji tunda shi koda yana kadunan ba zama yake ba a gidan idan sunzo shida Amminsa bare kuma yanzu da basa ma kasar dan Hajiya Hanne wata macace mai wuyar sha'ani halinta kwata kwata babu wani wanda za'a yaba gata da zafin kishi da son zuciya da sonkai da take gaskiya da haka sukayi sallama suka rabu cikin tunanukan rayuwa kala kala haka Mukhtar yaja motar suka bar gidan zuwa Bayajidda street gidan Ahmad suna zuwa daga kofar gidan yacewa Mukhtar ya tsaya anan,wayar Nasiba ya kira yace su fito ba jimawa suka fito harda Samiha da Ahmad inda Ahmad ke masa tsiyar yaki shigowa ciki,ko kulasa baiba shima jin hakan yasan ran mazane ya baci,da haka suka shiga motar Mukhtar ya fito yasa musu kayansu a boot ya hau yana kokarin tada motar Ra'uf yace sai sunyi waya shima a lokacin Ahmad kai ya 'daga Ra'uf ya murmusa dan ya fahimci Ahmad haushi yaji addu'a Samiha take musu da idonta ya cicciko da kwalla da Rufaida gudun kar a banbareta jikin Samiha suna kuka yasata riga kowa shiga motar tanajin sheshshekar Samiha itama ta fashe da kuka a motar a haka suka bar kofar gidan da Ra'uf ya juyo ya kalleta kallo daya ya maida kansa da kukannata baya sansa ko alamu saidai a gaban su Aunty Samira baya tunanin ya iya lallashinta saboda yanada yakinin suma zasu bata hakuri haka ko akayi su Aunty Samina ke kokarin bata hakuri da suma sunsan shaquwar Samiha da Rufaida ranar da daya zai rabu da daya Dole suyi kuka. *LIMATU KHALILULLAH*❤️💞*JININMU 'DAYA* BY SADIYA IBRAHIM KHALIL Wattpad:Sadiya Ibrahim Khalil *PAGE 25* DAN ALLAH KUYI HAKURI KUYI MANAGE BA YAWA MORE COMMENT'S MORE TYPING 3pm suka sauka a Kano kai tsaye gidan Aunty Samina suka ajesu da take a Sharada phase 1 da sai sun huta kowacce zata tafi gida Ra'uf yace wa Rufaida su jira zaizo ya kaisu gida badan taso ba ta amince Ba jimawa da shigarsu gidan Ra'uf ya turo Mukhtar gidan Aunty Samina da lemuka da yoghurt dasu Ice cream Nasiba ce ta fito ta amsa tayi godiya ta koma ciki. Aunty Samina ta dubi himin kayan "Kai wannan hidima haka baya gajiya shidai kiduba Alkhairin da yayiwa su Yaya balki kuma da siyayyar da yayiwa su Khalil (wato tana nufin 'ya'yansu Khalil,Kalim)" "Wallahi kuwa Allah yasa dai yasa ya dore har aurensu ya kuma sa ya kasance mijin nata indan shine mafi alkhairi a gareta amma gaskiya naga alamun yanada kirki" Cewar Aunty Samira Aunty Samina ta amshe da "Amin dai" Itako Nasiba harta bude tafara shan ice cream dan yunwa take ji gashi taga Aunty Saminan batada niyyar cewa su dora girki itako Rufaida Kitchen ta Shiga ta dora girki don gidan Aunty Samina Ba bakonta bane Iran suka zo da Samiha bata musu iyaka da komai dan sun maida Rufaida kamar Samiha su,kuma aranta bata tunanin zata iya cin kayan dan gaskiya yunwa takeji bazasu kosar da ita ba tadaifi gane ko zata cisu sai dai da marmari 5pm Suka shirya suka fito gidan Aunty Samina ita da Aunty Samira da Nasiba da Ra'uf ya turo Mukhtar Driver ya kaisu gida,kasancewar mijin Aunty Samira baya gari a lokacin shine dalilin shiga motar ya ajeta a gidanta da take rijiyar zakin itama da sai ka fara zuwa gidansu Rufaida kafin nata ****** "Oyo oyo Yaya Rufaida munyi kewarki" Su Rafi'a suka cacimeta suna fa'dar haka "Nima nayi kewarku,gashi ba nida waya bare mu riqa gaisawa" "Dama dole kiyi kewarsu gashinan harkuna angijemin dana ba" Ummi Hauwa'u ta karasa maganar tana karasowa gurin da Ra'is yake yana kuka da yake can gefe da shima hardashi a rugowa tarar yayartasu da akayi gefe dashi Daukarsa tayi ta'aje jakar hannunta tana"Ummi yi hakuri kinsan halin dai su Rumaisa da Rafi'a"tayi maganar tana shiga cikin falon da ta zauna kujera "Kodai halinki ba"Ummi Hauwa'u tayi maganar itama ta nemi guri cikin kujerun falon ta zauna Murmushi Rufaida tayi kawai ta gaisheda Ummintasu da Abbansu da shigowarsa gida kenan,Rumaisa kuma ta kinkimi jakar Rufaida tayi Upstairs(saman bene)da ita Da murmushi Abba Aliyu ya dubeta bayan sun amsa gaisuwartata "Wato saida kuka huta gidan Samina kukayo hanyar gida ko saida Umminku tagama girkin tarbarki kika zarce gidan Auntynku" Dariya tayi "ni bangama Yaya Abdul 'din ba" d shine ya kira Nasiba sanda suka dawo har suke shaidamasa suna gidan Aunty Samina, "Eh yanzu suka fita shida Abdul-Rashid Umminku ta aikesu,da naji yana zasu biya daukokuma keda Nasiba" Sallamarsu Abdul ita ta katse maganar da Ummi ke kokarin yi Amsa musu suka yi ya shigo falon Abdul ya dubi Rufaida da take masa sannu da zuwa yana fa'din "Yar rainin wayau bazan amsa miki ba,banda rainin wayau kinsan tahowa zakuyi kika samu wahala kukace zaku jira nazo daukarku saida muka je Aunty Samina tace drivern daya kawoku yadawo kaiku gida" "Yi hakuri Yaya Abdul mun kikkiraka mu fadama bata shigaba" Abdul yace dama mana haka zakice waye yakawoku gidan ne,Aunty Samina tana fadamin ko driven Ra'uf ko waye bandaiji sosaiba" Rufaida tace"Eh drivern gidansu Ahmad ne mijin Samiha" Shiru suka yi nawani lokaci Ummi Hauwa'u ta katse shirun da cewa nasan dai kuncika cikinku gidan Samina bakya bukatar abinci yanzu" Murmushi tayi tace" Wallahi Ummi a cike cikina yake,maikika girkamin" Ummi Hauwa'u tace"Alala" "Allah Ummi zanci zubomin ko dayane" Harararta Ummi Hauwa'u tayi "ni zan zubomiki ma lallai yarinya,nida ko tsaraba baki kawowa 'dana bama" "Rufaida tace" Ummi kinsan banida kudi,yanzu Aunty Samira data siyawa Kalim chocolate a flyover ta bani nakawowa Ra'is tana jaka ta" Abba Aliyu yacewa Abdul-Rafi Kaga Abdul taho mu hau sama naga an manta damu uwa da 'ya sai fira suke ba'asamu ciki" Rufaida tace "Yi hakuri Abba bahaka bane" "Kinga kyalesu Rufaida,muje dining kici abincinki" Cewar Ummi Hauwa'u Abdul dai baice komaiba dan har lokacin Ummi Hauwa'u bata daina fushi da shiba kan maganar da yayi akan saurayin Rufaidan,wanda shikuma a ganinsa addu'a yayi ma yar uwartasa" Maganar Abba Aliyu ita ta katse tunanin Abdul "Shikenan gwara ku tashi kubarmu muyi firarmu muma" Dining Area su Ummi Hauwa'u suka koma Rufaida ta zuba alalan tafaraci suna taba firar da Ummintasu SADIYA KHALIL*JININMU 'DAYA* NA SADIYA IBRAHIM KHALIL Wattpad :Sadiya Ibrahim Khalil 26 *WANNAN SHAFIN NAKI NE AISHA UMAR IBRAHIM(AUI) ALLAH YABADA SA'A YA KARA BASIRA A'I..MARUBUCIYAR ZANJIRATA ,DA NABARWA ZUCIYATA ALLAH YA BAR ZUMUNCI* *Shafi na Ashirin da shidda 26* Sallamar da Rufaida taji Ummi Hauwa'u tayi yasa ta aje Alqur'anin da take Karantawa kan sallayar data idar da sallar isha tayi hanzarin amsa mata ciki ummi Hauwa'u takarasa shigowa ta dubi Rufaida cikin kulawa tace "Tilawa kike ne"tayi karasa maganar tana zama bakin gado" "Eh Ummi" "To Allah ya taimaka su Rumaisa sunyi sallah ko nagansu sun sauka kasa suna kallo" "Eh Ummi sunyi tarema mukayi" "To shikenan kizo Abbanku yana kiranki Ummi Hauwa'u takarasa maganar tana mikewa Rufaida Alqur'an din ta dauke tasa cikin loka tabi bayan Ummin nasu ***** Assalamu Alaikum Rufaida ta gabatar da sallamar a kofar dakin mahaifinsu saida ta jira aka amsa ta tashiga cikin dakin a zaune ta samu Ummi Hauwa'u saman Carpet da shigar ta kenan itama kusada mahaifiyar tata ta zauna tana cewa "Abba Sannu da hutawa" Ya amsa "Yawwa Rufaida" Kafin yayi gyaran murya ya soma magana "Rufaida Alhaji Hashim ya kirani yayimin maganar wani yaro kun hadu wajen bikin Samiha ya nuna yana sanki shine ya kira Alhaji Hashim ya nemar masa izinin fara zuwa fira wajenki,kuma yace daga gobe zai fara zuwa,ina fatan dai da izininki yayi maganar kuma kinasanshi kar azo yafara zuwa zance yayi karfi azo asamu Matsala dukda cewar ba a fatanta" Murmushi tayi bata ce komaiba dan ita bata San mai zatace ba ga dokin San ganin Ra'uf da take don akwana dayan harta fara sabawa dashi saboda ya iya kalamai masu tausasa zuciya Jin tayi shiru yasa Ummi Hauwa'u cewa "Ai Abban Abdul ta amince tunda kaji tayi shiru" Abba Aliyu ya girgiza kai "A'a ki barta dai tayi magana shiru aiba amincewa kadai yake nufi ba akwai shirun da zakayi ba son abinda aka fadama kawai kake nufi ba,ki bata wayarki ta turomin message idan takoma dakinsu" Ummi Hauwa'u tace"to amma wayar na gurin Rumaisa tana game" "Na hanaki bawa yaran nan waya bakyaji ko wacce irin game ace har Rumaisa sai anbata....da wannan fadan da Abbansu yakewa mahaifiyarsu tabar dakin. Kai tsaye kasa ta sauka ta amsa wayar gurin Rumaisa da yaya Abdul ke musu karatun hadisi amma Rumaisan hankalinta nakan waya saida ta mangareta ta amsa wayar danma bataso ta hadata da yaya Abdul din zama tayi nan ta turawa Abba Aliyu text ta amince anan ta cigaba da zama anan karatun da ita a zuciyarta tanajin sha'awar rayuwar gidansu dukda mahaifiyarsu ita kadai gurin iyayenta baisa sun lalatamata tarbiya ba sunbata tarbiya da suma yanzu Ummintasu ce jagaba gurin basu saida Abba Aliyu da yakaranta text message din ya kalli Ummi Hauwa'u data fito bandakin da taje hadawa Abba Aliyu ruwan wanka yace " kinga message (sakon)Rufaida tace ta amince" Itama murmushi tayi tace "Dama nasan da saninta tayi maganar munyi waya da Zainab a jiya da safe tace saurayin Rufaidan sun gaisa da yaxo daukarsu jiya da suka kwana gidanta" "Eh dukda hakan kinsan dai zuciya Hauwah zata iya sauyamata tunani mudai yanzu fatanmu Allah ya tabbatar musu da Alkhairi ya kawar da dukkan sharruka" "Amin ya Allah"cewar Ummi Hauwa'u Jin karar wayar Ummin nasu yasa su gaba dayansu maida dubensu ga wayar da take kusada Rufaida ganin me kiran Yaya Abdul-Ahad be yasata rigasu dauka Yaya Abdul ya dubeta yace mata Wai waye ne mai kiran" Tace masa "Yaya Ahad ne" Ko kallan wayar bai sake yi ba ya cigaba da abinda take Da haka ta daga wayar da Sallamarta shima daya bangaren Ahad jin muryar Rufaida a wayar yasashi amsamata sallamar da murmushi kamar tana ganinsa ta dora da gaishesa ya amsa ya dora da cewa Rufaida 'yan Candy kunyi Candy bamuzo walima ba bai karasa maganar ba Rufaida taji muryar Hajiya Jamila har kunnenta kasancewar yana zaune cikin 'yan uwansa a babban falo suna fira kamar ko yaushe " Cikin fada Hajiya Jamila tace masa "Ahad tanbayar Candy zakayi ko cewa tabawa Hauwa'u wayar kayimata maganar zuwanku gobe, kar a sake kwatanta waccen zuwan fa" Ahad aje wayar yayi saurin yi Wanda atunaninsa ya katse kiran ya aje yace"Umma ki bari mana anajinki fa" Hajiya Jamila tace "ni rufemin baki sakarai ajini mana karyanayi inba tsabar iskanci tasan da zuwanku tasakai tabar gidan itada mijinta,ni mutane naban mamaki da sun samu wata dama saisu fara manta Alkhairi duk abinda mahaifinku yayi musu sun manta shi" Murmushi Rufaida tayi mai ciwo ta kuma kasa cire wayar a kunnents ita ta rasa menene laifinsu me suka aikatawa dangin su suke musu horon aibanta Umminsu tuni batun yau ba bayan itama mahaifiyar tasu 'yar dangi ce ita iya saninta Gwaggo kakarsu data haifi Ummnsu zaune take da kowa lafiya hakama Ummintasu amma haryau takasa fahimtar maiyasa ake cin fuskarsu ake aibatasu ake waresu kowa musamman cin fuskar da zarafin da akewa mahaifiyarsu dasu kansu Hajiya Jamila tafi yin hakan sai a lokacin tayi danasanin 'daga wayar Jin muryar Ahad ta cikin wayar yadawo da ita daga tunaninta "Umma sau nawa zan fadamiki fitarce ta dole har yasa muka je gidan basanan,kuma ai sun dawo kafin mutaho" "Dallah rufemin baki mai kake nufi karesu zakayi took ubanka baka isa ka karesu gurinsa ba akan wannan maganar bare kuma ni da bana kalar dangi ka...." bata karasa jin maganarba ta katse wayar ta ajeta a gefe ta zuba ta gumi hannu biyu ta kuma kife kanta jikin hannuwan nata ita gani take babu wanda yakaisu matsala da 'yan uwansu a ranta tausayin mahaifiyar ta takeji ita kadai ce gurin iyayenta ita kadai tasa ba rayuwa batada abokan shawara sai iyayenta batada yayye ko kanne 'yan uwa kaikace mujiya CE a cikinsu idan ta shiga ko ina Hajiya Jamila ta zauna bata take cikin yan uwa suma da take basanta suke ba saisu yarda tarasa mai Ummintasu ta tserewa Hajiya Jamila gashi tunda mahaifinta ya daina jiran abashi ya daina ci da sha da sutura karkashin wani shikenan tsana da tsangwama garesu ta karu kukane ya kwacewa Rufaida Ummi Hauwa'u data karaso falon ta karasa gurin da Rufaidan ke zaune ta dafata "Ke Rufaida lafiya maike damunki ne" Gaba daya 'yan uwanta suka tsaida abinda suke suka dawo gareta Abdul yace "Ummi daina wahalar da kanki gurin tanbayarta Yaya Ahad ne yakira waya to kila mamarsu yabawa wayar ta fadawa Rufaidan maganganu marasa dadi shine take kukan,har yau takasa dauriya akan abinda banga ranar daina shi ba kishin facala matar wa da kani to ita na mamar Yaya Ahad mai zafi ne Gwaggo tasha fadamana haka" Murmushi Ummi Hauwa'u ta ta dago fuskarta tana goge mata hawaye "Haba Rufaida komai fa lokaci ne wataran zai wuce gaba 'daya yanzu ina waccen rayuwartamu ta baya take da mukayi ba gata ta zama labari ba" Gyada kai Rufaida tayi ta mike tabar falon Ummi Hauwa'u da ido tabi Rufaida ta dau wayar tabi kiran Ahad Ahad dayake zaune kan gadonsa ya zuba tagumi yana tunanin halayyar mahaifiyarsa da baisan randa zata sauya ba yanzu yasamu ya baro mata falon ganin batada niyyar daina maganar karar wayarsa da yaji ya maida kallonsa ga wayar Ringing biyu ana uku ya dauka cikin zullumi maizai faru a idan ya daga dan ya fahimci Rufaida taji duk irin cin mutuncin da mahaifiyarsu ta musu dukda yasan su wacece Ummi Hauwa'u ba tada maida kai ga al'amuran mutane kome zaka mata bata ko nunawa a fuskama bare kaji a furucinta suma kuma 'ya'yan nata irin halin nata gare su yadda ya zata ko hakan yaji gun Ummi Hauwa'u yaji tace "Assalamu Alaikum Babban Yaya" Murmushi yayi a nashi bangaren ya amsa Sallamarta ya gaisheta cikin girmamawa Sun dan taba hira daga bisani tabawa yaran waya duk suka gaisa Ahad bai gigin cewa Ummi ina Rufaida ba ganin cewa dama sun gaisa da haka ya katse wayar bayan Ummi Hauwa'u ta amsa wayar ya sanarmata zuwansa a washe garin da haka sukayi sallama tana cewa ya gaida mutan gidan nasu. SADIYA KHALIL🖊️*JININMU 'DAYA* *NA SADIYA IBRAHIM KHALIL* *SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI 27* *MASU GANIN BANA TYPING KUYI HAKURI KUNSAN TYPING AKWAI CIN RAI WANI SA'ILIN MUSAMMAN KUMA TYPING NA LITTAFI MASOYA LITTAFIN JININMU 'DAYA RUFAIDA NAGAIDAKU ITADA DANTA YASIR DAFATAN BAKU MANTA SHIBA*😊🤔 ******* Yaya Abdul Abdul-Rashid ya kalla da suke Dining suna karin safe su duka yace mass"Yaya ban haka wani kyakkyawan labari ba munje wani boutique nida su Uncle Haris da Aunty naga wani kamarkai" Abdul yace"nine ma mantawa kayi"yayi maganar yana hararar Abdul-Rashid "Allah Yaya nima nida Rafi'a munga wani a mota a flyover kamar kai har Rafi'a ta masa magana"Rufaida tayi maganar da fara'arta "Wallahi kuwa nima Yaya Rufaida har magana mukayi" Abdul-Rashid ya karasa maganar yana tari maganar da yake yanacin abinci ya kawo masa tarin Kallonsu Abba Aliyu yayi ya soma magana "Gashinan kaika shaqe ,bakwa tashi yin magana sai kuna cin abinci,duk fadan da ake muku bakwaji" "Hakuri suka basa suka cigaba da cin abincinsu. Ummi Hauwa'u kuwa ko magana batayi ba saboda sun bata haushi Karar wayar Abba Aliyu yasa Abba Aliyu daukarta da take saman Dining ya duba mai kiran da murmushi ya dauki kiran da Alhaji Hashim ne mai kiran sai da suke gama wayar Abba Aliyu ya dubi Ummi Hauwa'u yace " Alhaji Hashim ne maganar yaron nan saurayin Rufaida ya kira yanzu yana kofar gida Abdul ne ya cire hannunsa a abincin ya kalli agogon hannunsa 11 saura Abba Aliyu ya kalli Abdul "din ya soma magana " yanaga ka cire hannunka a abinci badai harka koshi ba" Yatsina fuska Abdul yayi "Abba na koshi ,lokacin cin abincina ya wuce indai Rufaida ce zatayi batason gamawa da wuri" Ummi Hauwa'u tayi murmushi kana tace "To za'adawo da duty hardakai" "Haba Ummi 23 shekaru nake dasuba yanzu ai na girmi girki da sauran aikin gida sai kace wani dan daudu" "nikaga tashi tunda ka gama kaje ka shigo da bakin nan kakaisu falon baki ke kuma Rufaida kije ki shirya Hauwa ki hadamusu abin tabawa a baki"Abba Aliyu yayi maganar yana mikewa yayi Upstairs Abdul ya fito falon yin abinda Abbansu ya umarceshi. **** Ra'uf ya dubi Mukhtar da suke tsaye jikin motarsu a kofar gidan su Rufaida " Mukhtar kodai Ba kofar gidansu Rufaida tace kasauketa ba jiya daka kawota gida,naga nakira Ahmad run dazu kuma inada yakinin ya kira" "A'a nan ne mujiradai mugani" Mukhtar yayi maganar yana sake kallon kofar gate din Abdul da yakarasa fitowa daga gate din gidan Mukhtar da Ra'uf suka maida kallonsa garesa Ra'uf da kallo daya yayiwa Abdul yaga kamar da yake da Rufaida ganin yana kokarin wucesu yasa Mukhtar saurin yi masa Sallama "Assalamu Alaikum Bawan Allah" Abdul ya juyo da tunda ya fito ya hangosu yadai wuce ne saboda shi kwata kwata busy kwantamasa rai ba dukda yadda ya gansu tsaye jikin mota mai tsada karasowa yayi inda suke da idonsa kyar ya sauka ga Ra'uf da gabansa yaji ya fadi daganin Ra'uf din addu'a yayi ya daure yace musu "Wa'alaikumus salam" Hannu Mukhtar ya mika ma Abdul shima ya mika masa cikin murmushin yake sukayi musabihar Ra"uf shima cikin murmushi ya mika masa hannun suka gaisa "Kune bakin da Abba yace na shugo daku ko" Abdul yayi maganar "Eh mune" Cewar Mukhtar "OK to bari na bude muku gate din ku shigo daga cikin" Abdul yayi maganar yana kokarin barin wajen Suma motar suka shiga Mukhtar ya tayar suka dannan hancin motarsu cikin gidan da Abdul ya wangame musu gate din gidan ya birge Ra'uf sosai duk da bawani mai girma bane amma ginin gidan anyi sa cikin tsari maganar Abdul ta katsewa Ra'uf tunaninsa inda yace musu "Bissimillah ku karaso mana" Bayansa sukabi ya karasar dasu falon baki suka shiga falon "Bissimillah Ku zauna,bari nakarasa ciki nakira muku ita" Abdul yayi maganar yana kokarin barin falon Zama sukayi suna mai ce masa "to" Da sallama Abdul ya karasa falon ya zauna kujera ya kishingi'da Ummi Hauwa'u ta dubesa bayan ta amsa masa sallamar "badai harka kaisuba" "Eh Ummi na kaisu,ina Rufaidan" "Tana ciki ,yanzu zata fito" Sallamar da Rufaida tayi yasa Ummi Hauwa'u amsawa tana cewa da Abdul kaga ta fito ma Gurinsu ta karaso cikin shigar atamfa riga da siket da hijabinta har kasa kalar atamfar. "Ummi saina dawo" Rufaida tayi maganar tana kallon mahaifiyarta "To adawo lafiya ki kula da kanki" "To insha Allah Ummi" Rufaida ta karasa maganar tana kokarin barin falon taji muryar Abdul "Wato ni bazaki cemin Yaya saina dawo ba bakomai kyasami mai shigo mini da bakon naki ai" "Kai Yaya" Rufaida ta karaso maganar tana barin falon da murmushinta Shima Abdul murnushi yayi ya maida kallonsa ga Ummin nasu "Ina ganin wani a waje tayiyuma shine saurayin Rufaidan kinsan mai naji ina kallonsa gabana ne ya fadi" Ummi ta dubesa sosai "Subhanallah Allah yasa dai shigowarsq rayuwarmu da Allah kawosa Alkhairi ne Amma kayi addu'a ko dan Allah kudaina wasa da addu'a" "Amin Ummi Eh Ummi saida manayi na amsa musu sallamarsu", " yawwa Abdul Allah ya kareku daga sharrin duk wata halitta ya shige muku gaba" "Amin ,Ummi saidai wallahi Ummi nifa baikwantamin a raiba ma koda nagansa" "Banasan haka Abdul addu'a zaka riqa ma kanwarka idan shi Alkhairine gareta Allah ya tabbatar da Alkhairi ya kauda fitintinu" "Amin Ummi,karfe nawa su Yaya Ahad zasu zo ne" "Nafi tunanin sun kusa karasowa ma dan wajen 12 zasu karaso ina tunanin don damukai waya bayan fitarka sun cemin saura kadan su shigo Kanon" "Allah ya kawosu lafiya" "Amin yawwa bari kaga katunamin ma bari naba Abdul-Rashid ya siyomin kabeji wanda Abbanku ya siyo Rumaisa tacemin ya kare Kunada lecture ne yau idan zama fita sai ka ajesa a bakin titi" "Wallahi Ummi kin tunamin ma,munada ita 11 na safe zamu shiga yanzu gashi har tayi Abdul ya karasa maganar yana kallon agogon bangon falon. " ato saikayi ka shirya" "Yanzu fa Ummi"Abdul ya karasa maganar yana mikewa" "Kayomin kiran Rumaisa da AbdulRashid ita takaiwa bakon Rufaida ruwa da lemon shi kuma Abdul-Rashid nafadamasa sakon da zan aikesa" "To Ummi Abdul ya amsa mata yana nufar Upstairs. Murmushi Ummi Hauwa'u tabisa dashi kawai. *SADIYA KHALIL*🖊️*JININMU 'DAYA* *NA SADIYA IBRAHIM KHALIL* *SHAFI NA ISHIRIN DA TAKWAS 28* *NOTE:ABDUL-RAFI SHINE ABDUL WATO YAYAN RUFAIDA.FANS INA GODIYA SOSAI* "Assalamu Alaikum" sallamarsu Rufaida ita ta katse firar Ra'uf da Mukhtar "Wa'alaikumus salam" suka amsa mata bakinsu a hade wajen amsawar Jin amsawar yasata kokarin bude kofar ta tura ta shiga Sansanyin kamshin turaren Rufaida yasa Ra'uf dago kai ya kalli fuskar Rufaida matukar kyau tayi masa a yau din kasa Rufaida tayi da kanta ganin idon Ra'uf nakanta harta tako kusa dasu bata dagoba. Cikin girmamawa Rufaidan ta risina ta gaishesu suka amsa Ra'uf da take amsawa yanajin wani dadi a ransa najin muryar Rufaidan. Mukhtar da ya mike yanaso ya basu guri Yace"Matar oga Insha Allah ya gajiyar jiya" Cikin kunshe fuska da alamun kunyar maganar Mukhtar tace masa "Alhamdulillah ,yataku gajiyar" "Tabi lafiya" cewar Mukhtar "Yallabai bari in jiraka a waje" Mukhtar yayi maganar yana bude kofar falon ya fice said a Ra'uf yaji turo kofarsa ya maida kallonsa gareta "Da alama dai gimbiyar nan tawa soja zata tafi" Murmushi tayi kokarin zama kujerar dake kusa dashi. Gaishesa ta sakeyi ya amsa mata cikin nuna kulawa Shiru ya ratsa tsakin kafin Ra'uf yayi murmushi ya dubeta ya fara magana "To ya gajiyarku nasan baki saba tafiya daga wannan state (jaha)zuwa wannan ba" "Murmushi itama tayi " Eh hakane amma dai ina zuwa Zaria da Kaduna lokaci guda" Dariya ta basa "Kinsan fa Kaduna da Zariya ai duk jaha dayane kuma basuda nisa,kunada 'yan uwa a zariya" "Eh hakane,Mamata da Babana duk 'yan Zariya ne Nina acan aka haifeni,aiki ya maido iyayenmu Kano" Kai Ra'uf ya gyada alamun gamsuwa da maganarta "Ashe jahar mu daya nima dai kamar yadda na fadamiki ni dan Kaduna ne amma asalinmu 'yan Kano ne" "Murmushi Rufaida tayi batare da tace komaiba shima baice ba dan baida tacewar shima saboda busu gama sabawa da juna ba,can ya nisa ya soma magana " Gimbiya Rufee biki sanarmin wani abu da ya danganceki ba,vayan ni tuntuni nayi kokarin gavatarmiki da kaina" Wani murmushi ta sake yi da Ra'uf yake hangosa kan fuskarta kuma yake ganin yana kara mata kyau kafin ta nisa ta soma magana jin sallamar Rumaisa yasa ta barin abinda zata fada sukayi kokarin amsa mata sallamar turo kofar Rumaisa tayi ta shigo da plat babba da lemuka da ruwa a ciki teburin tsakiyar dakin takaraso cikin nutsuwa ta a jiye ta tsiyaya masa lemo da ruwan a Kofi sannan ta dago. Rissinawa tayi ta gaisheda Ra'uf ya dago ya kalli Rumaisa da alokacin take da shekaru 14 ya amsa mata da murmushi kan fuskarsa itamadai Ra'uf yana ganinta ya fahimci sunada alakar jini da Rufaidan ganin tana kokarin fita yasa Ra'uf saurin cewa "Haba kanwata ya zaki fita hakanan bayan ko sunanki baki fadamin ba" Murmushi Rumaisa ta juyo ta zauna kusa da Rufaida. "Yi hakuri Yayanmu sunana Rumaisa" "OK ni kuma sunana Ra'uf nasan da wuya yayarki ta fadamiki sunana ba ya fadi hakan yana kallon Rufaida. Murmushi Rumaisa tayi kawa " yace kina tsoron duka ko shiyasa bazaki bani amsa ba ko,to yanzu ya karatu" "Alhamdulillah" "Ya biki je ba yau" "Anyi mana hutu bamu koma ba" "Au namanta,Allah ya taimaka" Daganan Rumaisa ta mike zata bar falon Ra'uf yayi kokarin tsaidata ta hanyar cewa ga wannan kya kashe indan an koma hutu yayi maganar yana zaro kudi a aljihunsa. Murmushi Rumaisa tayi ta kalli kudin masu yawa "Tace Yaya kabarsu nagode tayi maganar tana sakai ta tura kofar falon ta fice dan karma ya roketa ta amsa" Murmushi yayi ya aje kudin kan Centre table yana tunanin lalle bayan wannan ahalin akwai uwa tagari a bayansu da shima burinsa ya samu 'ya garesu wato Rufaida da yake da tabbacin ita dinma ta zarta kanwar tata Rumaisa "Murmushin ya sakeyi ya dago ya kalli Rufaida " kin hanata karbar kudina ko,nagode" "Wallahi baruwana"Rufaida ta karasa maganar tana satar kallon fuskarsa "Banyarda bayan ina kallonki kina harararta karta amsa"yayi maganar cikin wasa " Ni din bani bace" "To naji bake bace,yanzu mu cigaba da hirarmu,ki fadamin ina jiranki" Nisawa tayi tace" Sunana Rufaida Aliyu Bukar ,mu shida ne gurin iyayenmu nice ta biyu akwai Yaya Abdul-Rafi ne babba da muke cemasa Abdul saini daganan Abdul-Rashid,Rumaisa,Rafi'a,Ra'is shine karamin aikine ya maidomu Kano kamar yadda na fadama a baya mu 'yan zariya ne" "Kai ya gyada da alamun gamsuwa da maganar ya gane Abdul din shine ya musu jagora suka shigo gidan amma yafi tunanin akwai tazara sosai a tsakaninsu "na fahimceki inadai fatan nine kawai a zuciyarki babu wani,shine dai biki fadamin ba kawai Murmushi tayi ta maida kanta kasa don batasan me zatace masa ba Shima murmushin yayi don yanada yakinin bazata amsa masa tanbayarsa ba ruwan da Rumaisa ta zuba masa ya dauka ya fara sha **** Abba Aliyu da ya karaso wajen aje motoci da yake azamar tafiya makaranta idansa ya sauka kan Mukhtar da yake cikin mota ya bude kofar motar mutumin da bazai iya manta fuskarsa ba saboda yayi silar taimakonsu a hanyarsu ta dawowa daga Kaduna ya mafi tunanin ko shine saurayin da yakeson 'yar tasa da murmushi Abba Aliyu ya karasa wajen da Mukhtar yake Sallama ya gabatar masa yana mika masa hannu Mukhtar ya dago ya kallesa da kallo daya Mukhtar ya shaidasa shima ya amsa masa sallamar da murmushi kan fuskarsa shima ya mikamasa hannu suka gaisa,saida suka gama gaisawar Abba Aliyu ya kallesa da murmushi saman fuskarsa " Ashe zan iya ganeka,ya bayan rabuwa,ka tafi wancen karan bansan sunankaba" "Wallahi kuwa yallabai bayan rabuwa Alhamdulillah,Sunana Mukhtar yallabai" "Murmushi ya sake Abba Aliyun " Kaine maisan diyartawa ko gaskiya nayi murna kashigo daga ciki mana Abdul baima iso bane" Mukhtar yace "Yallabai bani bane yana can falon bakin na barosa ni driven gidansu ne shine ma a waccen ranar yace na fito naji matsalar motarku harma yasa na kira mai gyaran" Abba Aliyu cikin jin dadi "Amma naji dadi sosai Allah ya tabbatar da Alkhairi bari na kira mai dakina a waya akawoma ko ruwa ne" "To yallabai Allah ya kara girma nagode" cewar Mukhtar da ya yaba da kirkin Abba Aliyu Waya Abba Aliyu yasa kunne ya fadawa Ummi Hauwa'u. Yana gama wayar ya kalli Mukhtar "Zan fita yanzu za'akawo ma yanzu" "To yallavai a dawo lafiya" "Amin,yawwa ya batun karatu fa kayi ne" "Eh yallabai iya secondary na tsaya" "OK bari na baka lambata saika kirani idan ina gida kawomin takaddunka" Mukhtar godiya ya dinga yi ma Abba Aliyu murmushi yayi yana cewa babu komai yiwa kaine daganan ya shiga motarsa ya bar gidan ******* "Sarauniyar mata biki fadamin ina iya karatunki ya tsaya ba"Ra'uf yayi maganar yana kallon Rufaida " iya secondary a wannan shekarar muka yi Candy"tayi maganar tana maida kallonta kan TV "Ki shiyo mana ki kalleni a yanzu fa nine TVnki" "Murmushi tayi kawai Shima murmushin yayi don yasan bazata ce masa komai ba. Daganan ya maida kallonsa ga wayarsa ya danna Lambar Mukhtar ya kirasa ringing biyu ana uku ya dauka sakon da zai fadamasa ya fada masa ya katse wayar ba jimawa Mukhtar ya shigo da ledoji a hannunsa Ra'uf yace ya aje mata Baijira me zatace ba yace " ki kulamin da kanki zan kiraki anjima" daganan ya mike yabar kudin da ya bawa Rumaisa yace wadannan kuma natane bai jira me zatace ba yabi bayan Mukhtar don yanada yakinin bazata amsa ba indai bai saurin fita ba" Jiki bakwari Rufaida ta mike ta kwashi kayan tana tunanin toda wacce wayar zai kirata tabar falon ta jawo ta rufe ****** A gurin aje motocin Ra'uf idanunsa suka sauka kan Ahad da da shigowarsu Ahad din gidan kenan yaji lokaci guda gabansa ya fadi sunan Allah ya fada a ransa yana tunanin to waye shi Ahad din yasan dai wannan ba Abdul bane tayiyu cousin's din sune. Shima Ahad da ya dago kansa ya kalli Ra'uf yana mamakin shi waye a gidan baisan saba,tayiyu dai makwaftansu ne,ko abokin aikin Abba,da alamu dai akwai Wanda yasani agidan, hannu Ahad ya bawa Ra'uf hannu suka gaisa. Daganan Ra'uf ya shige motarsu Mukhtar ya tayar sukayi hanyar gate suka fice da Abdul-Rashid ya bude musu suka fice Ahad yabi motar da kallo harta fice kafin ya dawo suka yi hanyar cikin falon gidan. VOTE☑️ SHARE☑️ COMMENT☑️ LIKE☑️ SADIYA KHALIL🖊️*JININMU 'DAYA* NA SADIYA IBRAHIM KHALIL SHAFI NA ASHIRIN DA TARA 29 A gurin aje motocin Ra'uf idanunsa suka sauka kan Ahad da da shigowarsu Ahad din gidan kenan yaji lokaci guda gabansa ya fadi sunan Allah ya fada a ransa yana tunanin to waye shi Ahad din yasan dai wannan ba Abdul bane tayiyu cousin's din sune. Shima Ahad da ya dago kansa ya kalli Ra'uf yana mamakin shi waye a gidan baisan saba,tayiyu dai makwaftansu ne,ko abokin aikin Abba,da alamu dai akwai Wanda yasani agidan, hannu Ahad ya bawa Ra'uf hannu suka gaisa. Daganan Ra'uf ya shige motarsu Mukhtar ya tayar sukayi hanyar gate suka fice da Abdul-Rashid ya bude musu suka fice Ahad yabi motar da kallo harta fice kafin ya dawo suka yi hanyar cikin falon gidan. "Kai kayan nan sunyi yawa aje Abbanku sai ya dawo an nuna masa idan ya amince a taba shikenan" Ummi Hauwa'u ce tayi wannan furucin "To Ummi nima haka dai nagani ki dubi yawan kudin da za'aba Rumaisa fa"cewar Rumaisa " kinga tashi ki kaisu dakinku ki ajiyesu dai Ummi Hauwa'u tayi firicin" Rufaida na mikewa da kayan a hannunta taji sallamar su Yaya Ahad amsawa tayi kawai ba tare da ta juyo ba tayi hanyar upstairs(saman bene)da murna sosai a ranta ita batasan har sun karaso ba busuyi maganar da Umminsu ba yanzu" Ahad da kallo yabi Rufaida har ya zauna Ummi ta washe baki tana musu sannu da zuwa suma su AbdulMalik duk zama sukayi suna amsawa Ummin da "yawwa" Bayan sun gaisa da Ummi Hauwa'u Su Rufaida suka shigo falon itada su Rumaisa da murmushi fuskarsu "Sannunku da zuwa Yaya" "Yawwa 'yan matan Ummi Hauwa'u" Murmushi sukayi suka gaishesu "AbdulMalik ya kalli Rumaisa yace Momy wannan Rumaisan nan gaba saitafi Rufaida girma gata kuma Copy din Rufaidah" Ummi Hauwa'u tayi murmushi kawai Nan su Rufaida suka shiga kitchen suna jigilar kawo musu abinci Saida suka gama cin abinci suka bude babin hira kafin lokacin sallah yayi suka tafi masallaci suda Abdul-Rashid Suma su Rufaida sama suka koma da Wasila kanwarsu Ahad din suyi sallah Koda su Ahad suka dawo gidan Ummi Hauwa'u suka tarar a falon tana sake gyara falon Zama sukayi suna mata sannu da gida "Abdus-salam yadai ko har yau baka watstsake da gajiyar tafiyar ba"cewar Ummi Hauwa'u tayi maganar tana murmushi Abdussalam dariya yayi yace" wallahi Ummi akwai gajiya" "To kaje ka kwanta dakinsu Abdul-Rashid mana" Hassan yace" kyalesa Ummi ba kwanciyar da zaiyi ba wani gajiya da yayi" Abdussalam baki ya Dan turo jin maganar Hassan din Ummi Hauwa'u "tayi murmushi tace"kai Abdussalam jeka kwanta kayi kwanciyarka ka kyalesu yayan naka" Tashi AbdusSalam yayi yayi hanyar Upstairs Sukuma suka cigaba da firarsu Da Ahad ya kasa hakuri ya tanbayi Ummi Hauwa'u Ra'uf yace"Ummi Hauwa'u dazu muka ci karo da wasu a harabar gidannan zasu fita bansan su ba ,hala makwabtanku ne" Ummi Hauwa'u tayi murmushi "A'a sirikinkune saurayin Rufaida ne" Maganar sosai ta bugi zuciyar Ahad domin shi har cikin ransa tun Rufaida na karama yake sonta amma sai yau da yazowa Rufaida soyayyarsa sai gashi wani ya rigasa tabbas yasan yayi zurfin ciki A hankali ya dawo da tunaninsa gudun kar Ummi Hauwa'u ta fahimci wani abu ya kirkiri murmushi yace "Kai amma Ummi Hauwa'u nayi mata murna,Allah ya tabbatar da Alkhairi" "Ummi Hauwa'u tace"Amin saura ku saika daure kafito da mata a hadaku tare ,tunda dai kayi karatu ka kuma samu aiki kaga babu abinda yayi saura yanzu" Murmushi kawai yayi "Ummi a tayamu da addu'a dai kawai" "Ummi Hauwa'u tace"munayi saidai mu cigaba dayi Allah ya kawo ta gari" "Amin suka amsa gaba daya falon Suna zaune har Abba Aliyi ya dawo suka gaisa suka cigaba da fira Har Abdul ya dawo suka tafi yawo dan ba aranar zasu koma Zariya ba ******** "Kai Hauwa'u kayan nan sunyi yawwa fa ko ma anfani ne da wayar kawai zatayi anfani"Abba Aliyu yake maganar da Ummi Hauwa'u ta kawo masa kayan dakinsa "Nima haka nace saidai tunda ba suttura bace ai ba wani abu idan zatai anfani dasu"inji Ummi Hauwa'u "Kiyi kawai abinda na...wayarsa da tayi kara yasa shi tsaida maganarsa ya dauki wayar ganin mai kiran Abba Bukar ne ya sashi murmushi ya kara wayar a kunne. Saida suka gama gaisawa ya mikawa Ummi Hauwa'u wayar suka gaisa ta sake mika masa wayar suka cigaba da firarsu shid yayan nasa ta kwashi kayan ta bar dakin saboda ya samu damar waya da yayan nasa sosai Wayar kawai taba Rufaida da take kwalinta Iphone ce fara da dama Rufaidan ta hangota a ledojin da Ra'uf ya kawo mata cikin zumudi ta ansa Ummi Hauwa'u na barin dakin ta cirota a kwalinta ta kunnata data sameta a saite take harda Sim **** Ganin kiran Abba Aliyu a wayarta da Ummi Hauwa'u tayi da shigarta dakin kenan ta mike tayi dakin Abba Aliyu Sintiri ta sami Abba Aliyu yanayi a dakinsa jin sallamarta yasa shi juyowa ya kalleta ya amsa mata sallamar ta zauna kujerar dake dakin guda daya da take gefen gado ta kallesa tace " lafiya kuwa Abban Abdul" "To da sauki dai zance" Abba Aliyu yayi maganar yana zama a saman gado" "Meke faruwa kafadamin"Ummi Hauwa'u tayi maganar ranta a dagule" "Abba Bukar ne yanzu yake shaidamin Ashe Ahad ya dade yanason Rufaida zuwan da sukayi ma shi Ahad dansu daidaita da Rufaidan yazo shine nake shaidamasa wani yazo yayi maganar ya biyo ta hanyar Alhj Hashim kuma na cemasa a yau din nayi niyyar sanarmasa lamarin" Ummi Hauwa'u tace "To shikenan tunda ka fadamasa haka" don itadai dama batason hadin Abba Aliyu ya nisa yace "Hauwa'u kinson Abba Bukar yayimin abinda ko iyayenmu sai haka banso hakan ta faru ba,amma tunda an amshi maganar wannan sai a jira aji abinda Allah zaiyi" Ummi Hauwa'u ta cigaba da lallashin Abba Aliyu har yaji yasamu nutsuwa sosai 9:30pm Rufaida da tayi shirin barci ta ji karar wayarta ta jawota jikin madubi ganin mai number din data dade da hardaceta yasata murmushi ta daga tare da da sallama ta dora da cewa "Amarya bakya laifi ko kin kashe 'dan masu gida"ta karasa maganar da da dariyarta Samiha da taji kirarin tayi dariya tace Bandai kashe ba Murmushi Rufaida tayi tace "Aiko kin kashe Yaya Ahmad zai hakura " tsaki Samiha taja tace" Kinga rufani ki saya,waima ba kicemin waya baki number dinki ba" Rufaida tace"ai nasan Yaya Ahmad ne" "Eh shine Yaya Ra'uf ne ya turowa Ahmad yanzu,ke ban fadamiki ba gobe jirginmu zai daga UK kinsan a can Ahmad yayi karatunsa Degree to ya samu admission zai koma yayi Masters,shine zamu tafi tare" Cikin rashin jin dadi Rufaida tace "Yanzu shikenan Samiha zanyi rashinki har ki tafi wata uwa duniya wallahi banji dadi ba naso ya barki ya tafi shi" "Wallahi Rufaida nima dai ganin kudinma ba gari daya muke ba yanzu saima mu shekara bamu haduba shiyasa na amince mutafi tare" Hira suka cigaba dayi kafin suyi sallama zuciyoyinsu ba dadi. Ra'uf ne ya kira Rufaida bayan gama wayarsu da Samiha da yayi mata saving din number din tashi da sunansa ta daga bayan ta kusa yankewa ba tare da tunanin komai ba. Sun jima suna wayar kafin suyi sallama da kusan maganar ta Ra'uf tafi yawa Washe gari su Ahad na gama karyawa suka shirya komawa Zariya dan garin Kanon bayawa Ahad dadi don yaci burin auren Rufaida dukda baya fidda rai amma dai yasan zuciyar Rufaida tana gun wani . Shakuwa mai karfi ke wanzuwa tsakanin Rufaida da Ra'uf har ma yanzu manya ke niyyar shiga maganar don Ra'uf yace sai an tsaida rana zaikoma Delhi su Amminsa da Safiyya ke shirin komawa kawai da itama Ammin Rufaida ta shiga ranta sosai. SADIYA KHALIL😊*JININMU DAYA* NA SADIYA IBRAHIM KHALIL SHAFI NA TALATIN Abba Bukar dake zaune a babban falon gidansu Rufaida ya kalli Ummi yace "Hauwa'u yanzu har dake a masu 'boye min maganar kawo ku'din yarinyar nan da za'a yi yau ko?". Ummi Hauwa'u da take kan carpet zaune tace "Yaya laifin na gurin Abban Abdul da yaron ya shaida zai kawo ku'din aure na ce a fa'da maka shi ne yake sanar min batun zuwanka a ranar da za su zo 'din". Abba bukar ya ce "yanzu da banzo yau din ba to saidai aji kunya kenan shikadai ne zaiyi gaban kansa kenan a fara kokwanto ga 'yarmu ko vata asali irin haka Ai fada ake yanzu da kunfada nima bazanzo nikadai ba ai ko kuma ma aturasu can Zariyan" Ummi Hauwa'u tace "adaimana afuwa Abba Bukar yayi murmushi yace" to Allah ya kawo mana su lafiya". "Amin yaya". Cewar Ummi Hauwa'u Yaran ne suka shigo da 'dokinsu suka ruga gurin Abba Bukar suna cewa "oyoyo Abba". Murmushi ya yi yana cewa Ku 'dagani kar ku 'ballani, tun da kun maida ni abokin wasanku. Hauwa'u ta koya muku wasa da ni ko?" Har dake 'katuwa dake ya nuna Rafi'a ba zaki bar Ra'is yayi ba. Murmushi sukayi suka sauka cinyarsa suka gaishesa suka fice. Ya dubi Ummi bayan sun fita yace "wato dai Hauwa'u kin koyawa yaron nan wasa dani ko?". Ta ce "a'a Yaya laifin yana gurin ka". Ya 'danyi murmushi yace ya canza zancen da cewa "ban ga Abdul..?". bai 'karasa maganar ba suka tsinkayi sallamarsu a falon. Abdul da Rumaisa da suka shigo falo suka ha'da baki gurin fa'din "sannu da zuwa Abba". Amsa musu ya yi da "yawwa". Kusa da ummi suka zauna suka gaishe da Abban, da tambayar sa ya ya baro mutanan gida?. Yace "Lafiya k'alau Abdul-Ahad ma yaso biyo ni to kuma sai ya koma gurin aiki jiya, ya banga Rufaida ba?". Ya karkare maganar da tambaya. Rumaisa tace "tana sama". Rufaida Da take zaune a carpet da littafi a gefenta da take yiwa Rafi'a assignment inda da ya kirata ta ajiye littafin ta dauki wayar da take kusa da ita sunan mai kiran Ra'uf ne Saida ta kusa katsewa ta daga suka gaisa Shi kuwa yana falon 'dakinsa yana kallon TV da ya rage volume yake wayar Ya nisa yace " Allah Rufee na kosa naje su Dady su karaso yanzu suzo sunema min aurenki asa rana ayi komai" Tace "haba dai yaya Ra'uf". "Allah kuwa amma na san ba zaki fahimci 'kaunar da nake miki ba shi yasa". Murmushi ta yi tace "ni kaina Yaya haka ne". "Me kenan? Fa'di muji". Ya fa'di haka wanda dalili mai 'karfi kenan yake 'kara jin sonta a ransa saboda yarinya ce mai kunya Rufaida shi kuma mutum ne mai son mace mai kunya kuma wadda bata saurin furta abu koda tasan dai-dai ne sai tanemi izini. Har da rufe fuskarta kafin tace "ina kaunarka dan Allah har mamakin kaina na keyi". "Rufee kenan kar kiyi mamaki da ikon Allah duk da dai nasan kurum fa'da ki kayi dan ki kwantar min da hankalin cewa kina 'kaunata da kika yi, amma na san nafi k'aunarki fiye da 'kaunar da kike min". "Kar ka fadi haka yaya Ra'uf har cikin raina na fa'di haka". "To Allah yasa" Tace masa "Amin" A haka suka cigaba da hirarsu cikin so da kauna ***** "Abba sannu da zuwa". Rufaida da ta shigo falon ta zauna 'kasan carpet tana gaishe sa wanda yake shi ka'dai zaune a falon ya na ta'ba abincin da aka kawo masa. Gaisawa suka yi ganin shigowar Abba Aliyu yasa Rufaida mi'kewa ta bar falon. Bayan sun gaisa ne Abba bukar ya dubi Abba Aliyu yace "wato Ali kai ka zama babban kanka shikenan har za'a zo neman auren Rufaida ba zaka fa'da min ba ki?". "Yaya da naga kace min zaka zo yau kuma ya yi dai-dai da zuwan su shi yasa ban fa'da maka ba, kuma dama niyyar da nayi suje can a nemi auren a can, sai kuma ranar zuwan nasu ya yi dai-dai da naka zuwan". Wanda zullumin abinda Abba Bukar zaiyi tunanin ganin dansama yanasan Rufaidan idan yafadamasa maganar zuwan baisan ya zai dauki zancenba yasashi kin fadamasa zuwan ganin yayi dai dai da zuwansa. "To ba laifi yaushe ne zasu zo 'din? Dan yau nake shirin komawa gida". "Yanzu Alhaji Hashim ya kirani yacemin Ahmad ya kirasa yace sun taho shima Alhaji Hashim din yaso zuwa aiki gaggawane ya samesa a asibiti" Abba Aliyu ya karasa maganar yana kallon fuskar Abba Bukar ********* Ra'uf ne ya sake kiranta ta mi'ka hannu ta 'dauki wayar da ke gefen gado Rufee su Dady sun taho suna hanya yanzu haka na fa'da musu ace 2week za'a saka ranar bikin so nake kawai mu koma india tare bayan bikin,basai na sake dawowa" Itadai murmushi tayi batace komaiba suka cigaba da wayarsu cikin nishadi da kaunar juna ______________________ Motoci ne guda biyu suka kunno kai cikin gidan nasu Rufaida Dady Usman da sauran mutane uku Abdul ne ya yi musu iso cikin falon bakin a kujerun falon suka zazzauna Abdul ya gaishe su sannan ya bar falon da idon Abba Abdu yanakan Abdul har yabar falon yaron yana da nutsuwa ya fada aransa haka kums yake tama Abdul din kallon sani ******** Rufaida da ta koma ta kwanta bayan ta hango motocin da suka shigo ta taga haka nan ta ji jikinta ya yi sanyi ga kuma bugun zuciyarta da ya karu, Addu'a ta soma yi kafin ta rage jin haka. ********* Ruwan da Dady Usman ya bu'de ya zuba a kofi ya ajiye a centre table Abba Salmanu ya dube shi yace Usman nifa zan tashi dubi fa zaman da mu kayi jiran shigowar mutanan nan tsabar rashin sanin darajar 'dan adam sun'ki koda kallonmu ni shi yasa ba ko wanne neman auren ake zuwa dani ba Dady Usman ya duba agogon hannunsa yace" YAYA mudai kara musu hakuri har yau bamuyi minti ko talatin ba fa" Abba Suleh ne ya mi'ke yana 'ko'karin tashi su Abba suka shigo falon da sallamarsu wanda yasa Abba sulehn komawa ya zauna Cikin firgici a fuskarsu suke kallon juna Abba Bukar da yake kallon fuskar mutanan falon ya mi'ke rai 'bace ya soma magana tare da nu na musu 'kofar fita "Ba zan laminci wula'kanci a gidan 'dan uwa na ba sannan da nasan kune masu Neman auren da buku wahalar da kanku zuwa ba domin dai koda 'dan ku shine ka'dai yayi saura a duniya Rufaida ba zata aure shi ba, indan har nine ma'daurin auren,haka ma indai Aliyu shine uba gareta. Tun kafin ya kai aya a maganar suka mi'ke Abba Suleh ya fara maida martani cikin zafin rai"Ni kaina bana fata ahalina su ha'da jini da ku, koda bayan ranmu kuwa aure nina haramtasa a gare su, da a ce na san da ku 'dan 'kanina ke son ha'da auran nan da hatta wancen auren na baya kuna da ala'ka ta jini da su da bazan bari ahali na ya ha'da ji'ni da masu butulci masu muguwar sakayya irin ahalinku ba da halayyar ahalinku takesha shafar duk wanda ya hada iri daku,mayaudara Maganganu masu zafi suke jifan junansu da shi Da haka su Abba Suleh suka fice daga falon da gidanma baki daya vadan maganganun da suke jifan junansu dasu masu zafi sun kare ba sai dan busuga anfanin cigaba da zama a gidanba __________________________ "Hauwa'u ban ta'ba tunanin da kanki zaki aikata haka ba, kuma daga ke har 'yar taki ku sani kamar yadda kuka turo da mijin da kuke so ta aura ba zata aure shi ba idan har da rayuwata a doron 'kasa Ahad zan aura mata kota naso ko bataso 'dan cikina kuma dan uwanta, domin ni ban manta ba idan ke kin manta" Abba Bukar yake maganar cikin bacin rai karara a fuskarsa da shigowarsa falon kenan da ko sallama ya gagarayi ya tari Ummi Hauwa'u da wa'dannan maganganun. Rufaida da ta tsinci maganar tana 'ko'karin saukowa amsa kiran Ummi 'kafafuwanta ne suka yi mata nauyi kafin bugun zuciyarta ya tsawaita. "ki karaso nan ke da uwarki muji wa ya kira wa'dannan mutanan zuwa ahalinmu,wadanda busu dauki dan adam a bakin komai bare suga darajarsa". Tsintar muryar Abba Bukar da ta yi yasa ta 'karasowa falon ta tsugunna gabansa tana mai da kallonta 'kasa wanda take jin tsananin ciwan kai lokaci guda ya saukar mata. "Kin bani mamaki da har kika biyewa wannan mara sanin mutuncin kanta bare musa ran ko zata san tamu ya nuna Ummi " Kuma ki sani indan kinyi hakan saboda tunaninki mun manta da wancen al'amarin to kin makara ki domin zuriyar Tafida bata canza daga ra'ayintaba har ya'u duk wanda yaketa mutuncin zuriyarmu babu sauran mutunci da zai sake samu a zuriyarmu kuma kiyi gaggawar canza shiri domin koda yaron nan shine ka'dai namiji to baza ta aure shi ba, sai ku sake ha'da wani 'kullin kuma,sannan ki kuka da kanki" ya karasa maganar yana nuna Ummi Hauwa'u da ya tsa. Abdul da ya tarar da zancen bai tsaya saurare ba ya bar gurin, dan shi ba ko wacce magana yake son ji ba,bare shida tun fil-azal Ra'uf bai kwanta masa a raiba "Yaya bukar bani da masaniya a kan Ra'uf ban ta'ba ganin shi ba" cewar Ummi Hauwa'u "Dakata banason sake jin maganar ki amma ki sani ahalinmu ba zasu hada aure da wannan kaskantaccen ahalinba idan da kaddara ta hadamu dasu to yanzu bazan laminta ba matukar ina raye zuriyar Tafida ba zata hada iri da ahalin 'Danbatta ba masu son zuciya da tauye gaskiya ta ko ina akwai banbanci a tsakaninmu" Ummi Hauwa'u da take jin kalaman har cikin kwanyar kanta falon ta bari tana zubda hawaye batasan maiyasa ake ta allaka haduwar Rufaida da Ra'uf tanada masaniya ba. Rufaida ma bayanta tabi. Abba Bukar ya cigaba da fadansa _______________________ Ra'uf da ke falo zaune shi da Momy Hannatu da ya zuba tagumi da hannu biyu , Momy ce ta kalle sa ta ce "lafiya kuwa, Ra'uf?". "Momy zuciyata ce naji duk bata min 'dadi, gashi bugun zuciyar yana 'karuwa". "Ka ri'ka addu'a insha Allah zai ragu, kuma zaka ji komai yazo da sau'ki". "To momy, yauwa Ammi ta ce cikin satin nan zata koma". "Eh ta fa'damin jiya a waya". Abba Sule da bai jira ya 'karasa rufe murfin motarsa ba ya fito ransa a matu'kar bace, Dady Usman da Abba Salmanu da Abba Abdu suna kiran sa amma ko saurarensu bai yi ba ya 'kara sa 'kofar falon ya bu'de ta da karfinsa. SADIYA KHALIL😊🖊️*JININMU DAYA* NA SADIYA IBRAHIM KHALIL SHAFINA 31 Momy Hannatu ta maida dubanta ga Abba Sule wadda take 'ko'karin canza tasha da remote a hannunta, shi kuma Ra'uf yana kwance kan doguwar kujera. Magana ya fara cikin 'daga murya "Wato kai Ra'uf har akwai ranar da kai da kanka zaka nemi wula'kanta mu to wallahi in dai har ka kafe da auran yarinyar nan sai dai mu raba hanya da kai kuma hatta mahaifi a gare ka sai dai ku raba hanya da shi, ko da zaka mutu babu aure haka ko da ita ta yi saura a mata a duniya ba zaka aure ta ba". Su Dady da suke bayansa tsaye suka furta da mun san irin wula'kancin da zamu riska kenan da ba mu yi 'ko'karin zuwa ba, Momy da take 'kokarin furta wani abu, Abba bukar ya dakatar da ita ta hanyar cewa "dakata Hindatu ba na son maganar ki". Ra'uf ba tare da ya furtawa kowa komai ba ya bar falon inda kansa ya yi masa nauyi, da wayarsa ya ci karo a 'dakinsa a centre table 'din falonsa wayar ya 'dauka ya shiga kiran Rufaida Rufaida da ta shigo 'dakinsu gado kawai ta fa'da tana kuka, karar wayar ta da taji ne ya sata mi'ka hannu domin nemo inda take wadda kafin ta hango ta kan drower gefen gado har ta katse ta na dauka kira a kalla goma ta gani da duk dai number 'din Ra'uf ce da ta ganesa da sunan data sa masa YAYA RA'UF, Wani kiran nasa ne ya 'kara shigowa bata tsaya 'bata lokaci ba ta 'dauka muryarsa taji cikin 'bacin rai amma duk da haka yadda yake maganar sa babu hargowa haka yake yin ta a tsanake yace "Rufaida ban ta'ba tunanin ahalina sun cancanci tozartawa a gurin ahalinki ba, sannan ba zan gushe ba face ina miki fatan samuwar rayuwa mai inganci a rayuwar ki ta nan gaba bai saurari wani abu da zata ce ba ya kashe wayarsa gaba 'daya ma duk da ya san Rufaida ba zata kira saba hasali ma yadda ya fahimta ita ba mai damuwa bace da son su ri'ka waya sosai dan sai yace tun da suka fara waya sau 'daya ta kira sa shima Ra'is ne ya dameta ta kira shi su gaisa, yana ajiye wayar sai a sannan hawaye masu zafi suka zubo masa, domin ya san zai yi wuya ya 'kara samun mace kamar Rufaida nutsatstsiya mai sanin ya kamata mai kawaici, tabbas iyayensu basu zamo masu kyautuwa a karon farko a gare shi ba, hawayen nasa ne suka ci gaba da zubowa, daga bisani ya mi'ke ya shiga ban'daki ya 'dauro alwala ya fara nafilfilo da kai kukansa ga mahaliccinmu da neman tuba izuwa ga Allah. Yana idarwa kuma ya fara azkar kafin ya 'dauki alqur'an ya ci gaba da karantawa a hankali yaji damuwarsa tana raguwa, Sai dai kuma garin kano ta masa zafi ba zai iya kwana a cikinta ba a yau , Mukhtar driver ya kira bayan ya shirya kayansa ya zo ya 'dauka yasa a boot, dakin Momy Hannatu kai tsaye Ra'uf ya nufa ya 'kwan'kwasa mata, Ta basa izinin shiga da take a falonta ta zuba ta gumi da alama ita ma tana cikin damuwa, a kujerar dake kusa da Momy ya zauna ya dubi Momy ya na cewa "Momy dan Allah kada damuwar rabuwa ta da Rufaida ta dame ki Allah ne ya ha'damu dama, yanzu kuma Allah bai sa dama zamu yi rayuwa mai tsawo da ita ba, Amma Momy Kano ta yi min zafi haka ma Nigeria na yanke shawarar zan bi Ammi jibi mu koma Delhi tare". "Haka ne Ra'uf Allah ya yi maka albarka, Amma ba na son ka tafi domin shi kansa Dady ba zai so haka ba bare kuma ni" "Amin Momy, sai dai tafiyar tawa itace zata sa na manta da komai in dai Allah ya so na manta 'din dan Allah Momy ki barni na tafi". Ba dan ta so ba ta amince da tafiyar tasa Har mota ta raka sa ita da Husna da take magiyar kar ya tafi kallon Husna ya yi yace "banda abin Husna ai kema Dady zai kawoki Delhi idan jarabawarku ta fito". Motar su ce ta bar gidan Inda Momy ke hawayen rabuwa da Ra'uf 'dan 'yar uwa a gare ta ba tare da ya cika burinsa ba na auren Rufaida, Da take ganin ina ita 'din da namiji ce kuma tana da iko akan aurawa Ra'uf Rufaida da sai ta yi 'ko'karin aura masa Rufaida. "Mukhtar ka yi kwana ina so naje Danbatta yi wa Yakumbo sallama". Ra'uf ya ce haka da sai yanzu ya tuna al'kawarin da ya yi wa Yakumbo cewa zai je mata sallama idan zai koma. SADIYA KHALIL🖊️😊*JININMU 'DAYA* NA SADIYA IBRAHIM KHALIL Wattpad Sadiya Ibrahim Khalil SHAFI NA TALATIN DA BIYU 32 KUYI HAKURI MASOYAN LITTAFIN JININMU DAYA BAZAKU RIKA SAMUN TYPING DINA KO YAUSHE BA,SANNAN A WATTPAD BAN FARA UPDATING BA ANA UKU NAKE A WATTPAD MASU SO DAGA FARKO SU RIKA DUBAWA ACAN.IDAN SUNAYI SABODA ANAMIN MAGANA BANASAMUN DAMAR TUROWA. Minti na da basu wuce arba'in ta sada su da garin Danbatta a, a kofar wani gida suka yi parking 'din motarsu gidan siminti ne sai dai babu shafe a kofar gidan Yara ne suka baibaye motar domin suga mai fitowa a ciki Ra'uf ne ya fito da gudu yaran da suka san shi mata da maza suka baibaye shi suna masa oyoyo, Hannun yaron ya rike suka isa kofar cikin gidan da gidan yake 'bangare uku 'bangaren yakumbo ne farko said 'bangaren kawu sunusi da na kawu Lami'do gidajen ginin zamani ne bangaren Yakumbo ya nufa kai tsaye sai da ya 'kwan'kwasa mata 'kofarta ta 'karaso 'kofar tana fa'din ince dai wannan yaron ba ne Salmanu ta'karasa maganar ta na bu'de 'kofa, Ganin Ra'uf ya sata saurin matsawa ta basa hanya ya shigo ciki cikin 'dakuna ne guda uku a biranda sai kuma kitchen da 'bandak a daga gefe da kuma 'karamin 'daki Cikin fara'a take cewa"lale marhabin da babban ba'ko, a garin Danbatta" Tana ko'karin shinfi'damasa tabarma a saman tiles 'din dake barandar gidan da take share, Tsaftar yakumbo tana birge Ra'uf dan shi dama mutum ne mai son tsafta Zama yayi yana cewa"Yawwa Yakumbo sarkin tsaftar garin Danbatta" "Kai rufamin asiri ina ni ina zama mai tsaftar Danbatta gaba 'daya , Ko ka 'dauka 'kan'kantarta kamar garin jajayen fatar nan ne " A'a Yakumbo Allah Delhi ta lin'ka Danbatta sau million ma" "kada fa karaina Danbatta dan nanne dai asalinka ko ka'ki ko kaso" "Eh haka ne , Amma kuma gaskiya na fa'da ta lin'ka Danbatta sau 'dari ko fiye da haka,Kuma Allah Yakumbon mu mai tsaftace " "Ahaf ka dai fa'di gaskiyya da kace ta linka Danbatta sau million To ai yaro tsafta cikon Addini ce, Allah yasa dai Matar taka mai tsafta ce, Ba irin yaron yanzu ba masu 'dan karon son jiki, Dai dai da abinci ma 'danye suke yin shi, Bare a saran shara da wanke wanke" Bai ce komai ba har yaron da suke shigo da kayan tsarabar da ya tsaya a hanya suka siya da Mukhtar su kashigo da ita , Mukhtar ya na ta yasu, Tsarabar ya bawa yaran suka fice da murnarsu suka nufi gida suna nunawa Sai a sannan suka gaisa da Yakumbo Yake tanbayarta ina Baffa "Tun safe ya tafi gona shida kawunka sai zuwa ya manyar nan muke saran dawowar su" "Allah ya dawo dasu lafiya , Amma ya kama ta Baba ya daina zuwa gona Amma har yau ya'ki ha'kura" "Amin , Kai kajini da yaro idan baya motsa jikinsa wacce lafiya zaiyi jini baya yawo yadda ya kama ta" Mukhtar da ke gefe zaune kusa da Ra'uf dariya yayi Ya gaishe da Yakumbo yana cewa, "Kwarai kuwa yakumbo kin fa'di gaskiyya "Ra'uf yace sai kaje kai ta zuga su" Ruwan hannunsa ya a jiye yana kallon Mukhtar da ke gefen sa saman tabarma yace "Yakumbo bari muje muyi sallar la'asar naga a nata shiga masallaci" "A dawo lafiya " A 'kofar fita gidan suka ci karo da Kawu Lami'do 'kanin mahaifiyarsa, Har 'kasa su ka durkusa gurin gaishe sa, Ya amsa musu cikin sakin fuska "yana cewa a'a Ku tashi", Bayan sun fito gidan Lami'do ya kalli Ra'uf da shima ya fito tafiya masallaci yana cewa "wata saban gani gani yaushe rabanka da zuwa Danbatta sai nace anyi shekara biyu ko anfi haka ma" "A'a kawu shekara biyu kenan" "A fa'dar ka ba", Mukhtar shekara nawa raban Ra'uf da zuwa" Mukhtar yace"Kawu shekara biyu kenan" "Wato kaima ka biye ta tashi kenan, Dan kaima kaga ba zuwa ka ke ba" Da haka suka shiga cikin masallacin da baida nisa da gidan Ra'uf ne ya hangi su Baffa da suke fito wa daga masallaci da fatanya a rataye a kafa'darsu, Saurin 'karasawa gurin su yayi kafin su Mukhtar su 'karasa fitowa gaishe su, cikin ha'din baki suka amsa, Inda Baffa yace "A'a wa nake gani kamar Abdul-Ra'ufu , Sunusi dubamin shi nagani, Baffa ya fa'di haka" "Kwarai kuwa nine babu ko kwanto Baffa" Baffan yace "yaushe Raban duniya da aiya raye", su Kawu Lami'do na 'karasowa, Suka gaisa da Mukhtar su ka shiga cikin gidan" 'Bangaren Baffa suka shiga Fa'da suka sameta ta nayi da yaran da suka shigo 'bangarenta tana cewa su fita karsu 'batama ta gida su koma suyi wasan gurin iyayensu, Ba za'a turo mata su ba su 'bata mata gida ba iyayensu sun gyara nasu gurin, Su ko sunyi shiru suna cigaba da wasa, Da 'kara ta bisu 'kofar 'Bangaren nata inda yayi dai-dai da shigowar su Ra'uf 'din bayan su suka 'boye kada ta dokesu, Karan tayar ta koma ciki, Da yaran suka shigo Baffa da kawu Lami'do suka ajiye fatanyar a biranda, suka shiga falo suka zazzauna, Ra'uf ya kalli yaran da suke zaune kusa da shi da suke su hu'du, mata biyu maza biyu, Yace musu ku Kyale yakumbo idan na sake dawowa tare zamu tafi na maida ku gurin Ammi, Tsalle suka farayi inda Yakumbo ta shigo musu da abinci ta samesu suna tsallen murna tsaki tayi musu tace "Wannan 'kauyawan za'a kai birni" "Kwarai kuwa Yakumbo tunda Ammi bata da 'kananun yara ga shi ba kya barinsu suyi wasa a bangarenki" "Ahaf ai wa'dannan yaron idan ka kaisu wannan 'kasar sai ka kirani ka fa'damin 'barnarsu kuwa" "Ai yakumbo mun daina ki tambayi su umman mu kiji" yaran suka ha'da baki gurin cewa haka Kawu Lami'do yace wato su salmanu ana son tafiya birnin india, ya fa'da yana dariya Abinci suka ci Kafin ya fito su shiga zaga dangi da yawanci suna zaune a kauyen kunya kauyen Danbattan da yake yawanci kauyeb Fulani ne duk inda yaje da irin alkhairun da yake musu da yara ke raka shi a motar sa Yakumbo ce ta kallesa da ta shigo ta zauna a falo inda Ra'uf da Baffa suke ciki Ra'uf ta duba tace "a lallai Ra'uf yau ansha yawo" "Wallahi ko Yakumbo ai yau na zaga gari ji nake kamar duka kunya da Danbatta danginmune" "Baffa yace kai Ra'uf Danbatta fa ba 'kauye bace mai gida nan sai kayi gaba ka tarar da wani,dama kunyan kace saina yadda "Kyalesa dai baffa ni narasa maiyasa yaran nan suka raina Danbatta, Har da fa yaron nan Bello" "A'a Yakumbo Allah ba mu raina Danbatta ba" Hira suka cigaba dayi inda Baffa ya kallesa yace"ya labarin bikin naka yake , wata nawa a ka sa" Kansa yana duban 'kasa da yake 'ko'karin maida hawayensa yace "Baffa ai an fasa biki su Abba Sule sunce bazan aure taba" Baffa da ransa yake 'bace ya soma cewa a kanme bari na kira Sulen naji akan me? shi duk sanda yaran nan zasu nemi aure sai ya kawo wata matsalar ta daban ita kanta yarinyar da Ahmad ya aura sai da yaso kawo wata matsalar mara tushe, To inda baku yi auren ba mai yakeso kuyi" Yakumbo tace "a'a karka kira sa tunda sunfimu iko da yarannan ka barsu kawai mu zuba musu ido sai dai mu tayasa da addu'ar Allah ya ha'dasa da wata ta gari idan kuma da rabo saika ga ya aure ta komai 'kin su da haka" Baffa ya amsa da Amin Tare da kallan Ra'uf ya ce "masa Ra'uf kar kuma hakan ya saka nemi yiwa 'yan uwan mahaifinka da mahaifiyarka rashin kunya ko nuna rashin darajasu domin dai ba kada kamarsu , Kuma kowa ha'kuri yake da halin 'dan uwansa wata rana sai labari" "Insha Allah Baffa bari na je na gaida su Umma ban shiga ba 'dazu kuma gobe na ke son tafiya na kira Bello ya samamin Viza za mu tafi jibi nida Ammi zamu kwana gidan Bello daga nan saimu tafi tunda yacemin jirgin safe za mubi" "To shikenan sai ka fito" Da haka ya mi'ke yabar 'dakin ya sami Mukhtar suka cigaba da fira a dakin da suka sauka*JININMU 'DAYA* NA SADIYA IBRAHIM KHALIL Wattpad SadiyaIbrahimKhali SHAFINA TALATIN DA UKU 33 _Dady ya kalli Momy Hannatu yace ya banga Ra'uf a falon ba ta dubesa tace "ya tafi Kaduna zai bi yaya Ma'u su tafi tare jibi" "Kan wannan abun zai ta fi shikenan to yafi ruwa gudu yaro mara sanin ciwan kansa akan wannan 'karamar magana ya tafi ba sani na idan yana ganin tsira zaiyi idan ya tafi kadunan Momy shiru tayi tana jinjina al'amarin Dady lokaci 'daya ya birkice saboda san zuciya irin nasu sun hana yaro auren za'bin ransa falon Momy Hannatu ta bari ganin zaman ma baida anfani a gurin ta Dan gaskiyya saita fa'di gaskiyya indai ta zauna su kuma ta lura bamai san gaskiya a cikinsu ________________________________ Abba Aliyu da ya sami Ummi Hauwa'u a zaune gefen gado gefenta shima ya samu ya zauna da shigowar sa kenan cikin 'dakin ya dubi ummi Hauwa'un yace " Hauwa'u magana na keso muyi bata wasa ba kuma, yanzu yaya Bukar ya sanarmin zai tafi da Rufaida ko dan ta manta da yaron nan gaba 'daya,kuma su fahimci juna itada Ahad kafin ayi aurennasu. "Amma Abban Abdul ba ayi shawara da niba kwatsam sai azo min da maganar tafiyarta kuma harma da kudurinku na auren Ahad kana sane da kiyayyar da mahaifiyar yaron ke nunamin nida 'ya'ya na "Ki fa'damin wake da iko da yarinyar nan ne wai"Abba Aliyu yayi firicin da alamun ransa ya soma baci "Cikin sanyin murya tace kai ne amma gani nayi kasan komai akan zaman da mukayi nida Hajiya Jamila yanzu kuma ace Rufaida ta auri danta" "Cikin 'bacin rai Abba Aliyu yace"ke harkinada sauran magana akan 'ya'yana kinmanta da abinda kika mana dake danasan da sa hannunki a ciki" *****"*" Ra'uf ya fito Cikin shirin sa shadda milk colour jikinsa 'dinkin mai yalwataccen fa'di da tayi matu'kar yi masa kyau da 'kara haska sa, ya fito da'ki da Mukhtar tuni ya fice da kayan sawarsu yasa a boot da yake waje yana jiran fitowar Ra'uf, da Baffa Ra'uf yaci karo tsakar gida yana 'ko'karin yin alwala "Baffa sallar walhar ce" "Eh Abdur-Ra'uf ba dai har tafiyar ta tashi ba Eh baffa sai dai kuyi mana addu'a Allah ya 'kaddara saduwarmu" "Baffa ya furta amin da ya ajiye butar ya 'karaso gun Ra'uf da yake 'ko'karin su fita tare da Ra'uf, Yakumbo da ta shigo gidan ta dubi Ra'uf da cewa "ba dai har ka fito ba tun yanzu, Wato da tuni sai da nazo na iske tafiyarka daga fita makwabta yi musu barka shiyasa Baraka tace na tashi kar ka tafi yanzuma take shaidamin ashe har gidan ka shiga jiya kayi musu abin arzi'ki " A'a Yakumbo zan Shiga nayiwa su Kawu sallama , Eh mun shiga nida su salmanu da salmanun yace min mu shiga gidan 'kawar Yakumbo, sai dama muka gaisa na gane ta Gwaggo Baraka ce sai dai naga kamar ta fiki tsufa yanzu" "Banga alama ba zaka jira dawo wataba, Abdul-Ra'uf kenan ai Baraka abar a tausaya mata ce musamman yanzu da ta 'kara tsufa a zaman 'kauye kenan da kaya basu lunka ku'din zabi ba kamar yadda suke yi a cikin birnuka,Yaran nata duk sunyi karatu amma ba wanda ya samu abinyi yanzu haka dai iro yana birni ya kammala digri yana tsaron shagon unguwar da ya zauna har ya gama karatun to gaba 'daya ku'din da yake samu basu taka kara sun karya ba kuma a hidimar iyaye suke 'karewa a hakan ma badan sun isa ba" "Da gaske nake yakumbo ina zan tafi ban sake saki a ido ba, To amma Yakumbo mai yasa baki fa'dawa Momy ba tasa Dady ya sama masa aiki" Baffa yace "kaga Abdul-Ra'uf ta ho ka tafi ka daka ta Yakumbon ku ba abinda zaka yi tunda dai ba ka tafi ba ta dawo ai shikenan, ka shiga ka yiwa kawun naka sallama" Suna 'ko'karin fita Yakumbo tace "Ahaf a baki ba amma nasan da tuni ka tafi ba muyi sallama ba" Baffa yace "saiki ta yi dai amma wannan abokin nawa ba haka yake ba" Yakumbo tace"kana dai tare masa ne kafin mu jiku a rana" Da haka suka 'karasa 'bangaren kawu Lami'do da suka tarar suna karyawa gaisawa su kayi sauran yaran kawu biyu duk maza suka koma gefen Ra'uf suka zauna Umma ta ce "Amira jeki kawo wa su Baffa Abincin karin kumallonsu yanzu nake cewa ta je takaimu Ku tace sai tayi karin kumallonta zata kai muku " Baffa yace barshi Zuwaira Yakumbo tun asuba ta 'dora sanwa saboda Abdur-Ra'uf mun 'karya tun 'dazu Allah ya yi muku albarka yasa kuma naku su yi muku" "Umma tace" Amin Baffa" Ra'uf ne ya dubi Amira yace "Umma Amira tayi girma kyau a ha'data aure da Bello sai mu'kara 'karfafa zumunci ni jiya ma banganta ba a gidan" Umma tace "Ai kasan yaran yanzu basa san auren zumunci wani 'dan bayan gidan nan take so,ta je gidan kawu isuhu sai dare ta dawo" "Kin ji Umma shine fa ke sona ba ni ba Amira ta fa'da" Kawu Lamido yace" ina wani so da yake miki tunda kinsan tsinke baya saidawa kin 'ki ha'kura da shi, Ga makaranta saura watanni Ku gama makarantar gaba da fira mare Baffa yace "Bar ta Lami'do da yaron nan abokin Ra'uf na birnin tarayya Abuja da ya sake dawowa zance ya turo magabatansa" Amira ta zun'buri baki tace gaskiya Yaya baka kyautamin ba dan ni bana son wannan abokin yaya Bellon nan Ra'uf yace "kyautawar kenan yarinya , to shikenan tunda ba kya son sa a ha'daki da Bello dan ni banida sha'awar mata biyu ai da nayi ta biyu dake" Amira tace "Allah ya kyauta nayi auren Zumunci, ta 'daya ma ka kasa ka tsaya ruwan ido bare kayi ta biyu dani" Ra'uf yace "eh naji gwara ni keda da zaki ba wan ba 'kanin fa" Baffa ya ce "nidai nagama magana ta Bilal zaki aura abokin Bello" Ra'uf yace dama Bilal ne ai da shi a kayi bikin Ahmad yaje har Sakkwato 'daurin aure yana da kirki sosai Baffa" Amira gurin ta bari saida zasu tafi rakonsa ta fito domin rakonsa 'Bangaren Kawu Sunusi suka shiga harda su Kawu Lami'do basu jima ba a 'bangaren Kawu Sunusi ba suka fito inda suka fito tare domin ganin tafiyar sa har bakin mota suka rakasa kafin motarsu su tashi su juyo gida inda sauran yaran ke cewa yaushe zai zo 'daukarsu, Yace musu sai sun ganshi da sunga yazo tafiya ce Misalin 'karfe biyu suka isa Kaduna ana fitowa daga masallaci Motar su ta dira sai da suka tsaya sukayi sallah a wani masallaci kafin su isa gidan "Horn biyu a ka bu'de musu gate 'din gidan a ' Harabar gidan suka tadda Baffa Alhaji" Da murmushi ya tari Ra'uf yana cewa "maraba da bakano kaje kano ka guji Kaduna garin gwamna" Hakan ne yasa Ra'uf sakin ransa da tunanin ta yiyu baza'a sake masa maganar Rufaida ba yace " yawwa 'Dan tsoho mai ran 'karfe, amma wa zai 'ki Garin Gwamna" Mukhtar ya fito a motar suka gaisa da Baffa Alhaji Kai tsaye yana shiga falon 'dakin Ammi ya shiga da ya yi sa'ar bai sami kowa a falon ba A zaune ya sa meta tana 'ko'karin ha'da kayanta Sallama yayi TaAmsa masa tare da 'dago kanta Kafin tace "wato sai yanzu zaka zo ko ka fison tafiyar dare ko? " a'a Ammi ki yimin afuwa ina Safiiyyan"inda ya 'Dora da gaishe ta amsa gaisuwar ta dora da cewa tana gidan Malika sai zamu tafi zamu dauketa mu wuce,na kirkira ka kashe wayoyinka tun jiya nake 'ko'karin kiranka ba ta shiga ba saboda Momynku ta cemin ka taho" "Eh Ammi na biya ta Danbatta nama su Baffa sallama, tun a Danbattar na kunna wayar da muka je amma babu network mai 'karfin da zai yi kira" Ammi cikin nuna damuwa a kan fuskarsa da tausayin yaron nata mai tsananin biyayya a gare su da bai kamata kan wani banzan dalili a hanasa za'bin ran sa ba da ta tabbatar ba wani 'kau'karar dalili ba ne amma an rabasa da Rufaida saboda suna so suna na isar su akan Ra'uf dan datasan abinda zata tarar ke nan da bata zo nigeria ba magana ta soma yi tana cewa "Ra'uf dan Allah kada Rabuwarka da Rufaida ya janyo wani sauyi daga rayuwarka dama wani lokacin sai ka rasa wani abun kake samun wani abun a rayuwa" "Insha Allah Ammi" Ammi tace "yawwa Ra'uf" Amma Ammi Su Abba Suleh sun fa'damiki wani abu ne da yasa suka hanani auren ta Kai ta girgiza tace "a'a ko 'daya ba su fa'da mana komai ba sunce dai an yi musu wula'kanci da ni narasa kalar wula'kancin amma hajiya ta 'dauki zafi da haka sosai sai dai kayi ha'kuri" SADIYA KHALIL🖊️😊*❣️JININMU 'DAYA*❣️ BY SADIYA IBRAHIM KHALIL HAPPY SALLAH ALL MUSLIM UMMAH ALLAH YA MAIMAITA MANA🤲🏼 34. 34 *Rufaida muddin kikace bazaki bi Abba Bukar ba kinada tabbacin ni zaki jawa zagi bakowa ba,haka koda Aliyu bai kasance miji gareni ba duk abinda na mallaka suka nuna suna so nawa zan basu,saboda sun nunamin soyayya kamar wadanda muke ciki 'daya bare ke din mallakinsuce duk abinda suka yanke gareki bazance don meba" "Rufaida da take zaune jikin mahaifiyarta saman gado da tagama jin kalaman Ummin nasu ta soma magana" "Ummi naji zanbi Abba Bukar amma banason auren Yaya Ahad tunda sunqi aurena da Ra'uf naji na hakura amma wallahi banason auren nan Ummi ,nasan bazanyi auren farin ciki ba don Allah Ummi kice karsu auramin shi"tayi maganar tana fashewa da kuka Lallashinta Ummi Hauwa'u ta fara da itama hawayen take zubarwa ita kanta batason 'yarta tayi rayuwa irin wadda tayi a baya,da tasan saboda Hajiya Jamila ne yasa batason auren na Ahad din badan tana kin Ahad dinba,saida Ummi Hauwa'u taji Rufaida tayi shiru ta soma magana " Haba Rufaida ya kike abu kamar ba musulmaba bakida masaniyar ko Ahad shine zaifi zama miki Alkhairi a rayuwarki tanan gaba idan kina wannan maganar to kenan imaninki ya soma rauni kenan ko,kuma ki tuna da cewa duk Wanda Allah yaso da Alkhairi saikiga ya jarabceshi da wata musibar,idan bakiyi kokari kin cinye jarabawarki ba mai kikeso kiyi a duniya,ko kinfiso ke rayuwarki ta kasance kullum cikin jin dadi ki tuna da za'a tona zukatan wasu aji meke cikinsu da kinyiwa Allah godiya akan ke taki jarabawar,ki fahimci cewa Alkaluma sun riga da sun bushe babu wanda ya isa ya kauda kaddarorin rayuwarsa domin sun rubutu akan alkalamin da baya gogewa,kowa kika gani kafin ya samu abinda yakeso saida yasha wahala ,nasan kinason Ra'uf tuni batun yauba nasan da haka,amma hakuri zakiyi abubuwan da son zuciya ya zama silarsu ya farraqa soyayyarku,maza ki share hawayenki ki cigaba da kaiwa Allah kukanki. "Dago ido Rufaida tayi tana share hawayen fuskarta ta ta jinjina lalle mahaifiyarta uwace mai girma a rayuwarsu lallai mahaifiyarta ta samu tarbiyya daga iyayenta gashi har tasamu nutsuwa da kalaman mahaifiyartata dole mahaifinta ya sota fiye da tunanin dukkan mai tunani da duk wanda ya tabata a dangi to sai Inda karfinsa ya kare dukda dangin nasu dayane,saidai abu daya daya shige mata duhu sanin waye 'Danbatta Family da zuriyarsu basa son haduwa da zuriyar Danbattan. Murmushin karfin hali Rufaida ta qirqira ta dora ido ga mahaifiyartata " Ummi na amince da dukkan maganganunki kuma na yarda da nasiharki gareni,kuma nayi alkawarun bin abinda kikace,saidai ki fadamin maiyasa don Ra'uf ya fito data zuriyar Danbatta bazaku auramin shi ba" Murmushi Ummi Hauwa'u tayi ta dafa Rufaida "Ni kaina bansan dalili ba mahaifinkine da Abba Bukar kawai suka sani amma ki dauka a ranki baki taba jin sunan 'Danbatta Family ba har abada,amma ni bance kimanta da masoyanki na gaskiya ba har karshen rayuwarki ba,kinga maza taso ki shirya kayanki mubar wannan maganar kinsan Abba Bukar bayasan jira. Jiki ba kwari ta mike da tasan lallai akwai rina a kaba Ummince dai bazata Sanar mata ba itama kuma batasan tilastawa Ummin tasu Da haka suka Shiga loda kayannata a trolley da Ummi Hauwa'u ke tayata sunayi tana sake yi mata nasiha 10pm Motar Abba Bukar ta tashi da Rufaida take rungume da Umminsu da Rumaisa da take ji a ranta tamkar rabuwarsu kenan ,bazasu kara haduwa ba,shikansa Abdul kuka yake yanasan kanwarsa gashi an rabata da abinda take so za'a kaita inda ba'asonsu don zalinci ji yake aransa ina ma shi wani ne wallahi da bazata bisu ba hatta Umminsu da kannensa bazasu cigaba da zama a tare da Abbansu ba da sunaji suna gani ake fadawa mahaifiyarsu bakaken maganganu don kawai anga ita din mai hakuri ce. Horn din da Abba Bukar yayi ne yasa Rufaida Shiga gaban motar ya tayar tana hange 'yan uwanta da Umminsu suna hawayen rabuwa da ita da dagamata hannu da hatta mahaifinsu ta hangi siririyar kwallar da dafito daga idanunsa Abdul Rashid daya bude musu gate din Hawayen yake da daga musu hannu har waje ya fito saida yaga baya hangen motarsu ya koma gida itama waigensa take har suna bacewa ganinta sunyi matukar sabo da da 'yan uwanta tare sukai rayuwa tun daga mara dadi har zuwa yanzu da suke ganiyar yin mai dadi da Umminsu take gine dasu ko yaushe akan nuna musu su kaunaci junansu tunanin baya kawai Rufaida ta lula tana hango komai kamar a mafarki. 2pm Suka karaso Zariya da kai tsaye gidan Abba Bukar suka nufa inda yayi horn mai gadi ya bude musu gate din Abba Bukar ya dosa hancin motarsa cikin gidan mai gadi da take masa Sannu da zuwa ya dagawa hannu yayi parking inda aka tanada wajen aje motoci ya fito ba shiri Rufaida ta fito itama tana sake duban gidan da duk sanda ta shigo tarihin rayuwarsu a gidan yake zuwar mata kamar yanzu abin me faruwa tsoro da fargaba ya shiga yawo a cikin zuciyarta to yau karo na biyu da tazo gidan da zama wacce irin rayuwa zatayi kafin lokacin bikin nasu da Ahad yazo tasani ta bayance dai rayuwartasu zatayi koma ta linka ta bayan tunda kaddara tasa zata auri dan matarda take da cikakken iko da isa a gidan na Wan mahaifinnata. Maganar Abba Bukar yasata dawowa daga dogon tunaninta inda yace "Shiga cikin gidan kafin Dan-liti (mai gadi)ya shigo miki da kayan naki" Da to ta bisa dan ta fara tafiya cikin sanyi ta is a kofar falon bata sami kowa a falonba dalilin daya sata jin dadi kenan harta isa kofar da zata sadata da bangaren da shine nasu dasuka zauna a gidan da har yanzu yake nasu da idan sunzo gidan shine gurin zamansu A share bangaren yake kai kace wani na zama a cikinsa. Sallamar Baba Dan-liti da Abba Bukar yayi masa izinin shiga ya kaiwa Rufaida kayanta yasashi shiga,don iyakacin aikinsa gate. Amsa masa Rufaidan tayi ta gaishesa ya amsa ya aje mata kayan a falon ya fito. Jakar dake zagale a kafadarta ta aje saman kujera tareda cire hijabin jikinta ta zauna tana maida gajiya tana mai cigaba da tunanin rayuwa ganin tunanin bazai mata ba yasa ta mike tayo alwala ta tada sallah ta dade tana addu'o'i kafin ta mike tabar dakin da nufar dakin matan gidan gaishesu "Wawa sakarai dama don haka kace bakasan Rukayya don kawai kanason macen da banbanci dake tsakaninku mai girman da bansan adadinsa ba ne, Rufaida da take kokarin tura kofar dakin Hajiya Jamila tajiyo furucin nata da dama tasan fiye da haka saita faru bama ga Ahad dinba har gareta tunda zai aureta,gudun hakan yasa take tsoron auren Ra'uf dukda bawai sonsane itama batayi ba saidai wannan matsalar take hangowa,da ita kullum tunaninta sanin banbancin dake tsakaninsu dasu Ahad da har yau takasa fahimtar menene banbancin jin furucin Ahad ya katse mata tunaninta" "Umma inasan Rufaida tunda tazo duniya banasan Rukayya da soyayyar aure, amma kifadamin banbancin mu ko zaisa ya zama silar hakurata da auren Rufaidan amma ni nasan Rufaida 'yace kamar kowa,bana haufi akan bazata cutar dani ba har ma daku" "Dakata Malam ai banbancinku sananne ne da kowa ma ya sanshi sakarci da wauta ne yasa kaika manta dashi kuma tunda ka kafe sai ka aureni Rufaida to nima zan kafe a au..... Bata tsaya jin karashen maganar Hajiya Jamilarba tabar kofar dakin nata tana kokarin hana hawayen idanunta fitowa, Hajiya Jamila mutuniyar garin Nasarawa state ce acan Abba Bukar da yaje bautar kasarsa ya ganta ya Aurota acan yaranta biyar Abdul-Ahad ne babba a gidanma gaba daya sai,AbdulMalik,Abdul-Jabbar,AbdusSalam,Wasila Kai tsaye dakin Hajiya Kubra ta shiga cikin sakin fuska suka gaisa ta zubo mata abinci taci tana sake nusar da Rufaida yanayin rayuwa Hajiya Kubra mutuniyar kirkice auren zumunci sukayi da Abba Bukar 'yar cikin garin zariyace, kuma aurenso da kauna da ba hadasu akaiba Allah ne ya hadasu da take mutuwar son Abba Bukar dalilin dayasa takesan kowa nasa kenan dukda itada Abba Bukar din abu dayane,amma sonsa ne yake tasiri a zuciyarta dayake kara mata kaunar 'yan uwansa dukda itama din nata ne,amma bata banbanta wadannan sunfi kusanci gareta indai akan abinda ya shafi mai gidan nata ne yaran Hajiya Kubra a lokacin Hassan,Hussaini,Aliyu,Umar,Usman. cikin kwarin gwiwa Rufaida ta fito ta shiga 'dakin Aunty Amina suka gaisa da itama macace mai kirki saidai batada yawan surutu amma dai tanada kirki batada yawan magana bare harta fadawa 'yan uwan Abba Bukar din wata magana mara dadi rashin maganarta ne yasa wasu ke ganin batada kirki amma shi Abba Bukar sam baya ganin haka don ta fadamasa laifin da nasa suka mata to lallai za'a dade yaranta biyu a lokacin don itace amarya Sadiq,Ubaidullah da take goyo Tana fitowa ta shiga dakin Hajiya Jamila da ko sallamar da tayi bata amsa ba haka ma gaisuwarta haka ta gama zama ta fito da Hajiya Jamila ta biyo ta dajan tsaki.*❣️JININMU 'DAYA❣️* BY SADIYA IBRAHIM KHALIL *HAPPY SALLAH ALLAH YA MAIMAITAMANA AMIN* 35 ***** Kukan da take ta tsayar ta maida kallonta ga wayarta ganin number din Samiha yasata saurin daukar wayar da sallamarta saida suka gaisa Samiha tayi gyaran muryar ta soma magana "Rufaida banji dadin abinda su Abba suka ma danginsu Ahmad ba sunsan tun farko yaya Ahad sukeso su aura suka boye masa,bakiji haushin da Ahmad yaji ba dan sai alokacin da aka hana Ra'uf aurenki ya fahimci bamuda alaka dake" Rufaida jin Samiha tayi shiru yasata kokarin cewa "Ni kaina Samiha banso abinda aka ma danginsu Ra'uf ba ga uwa uba inasan Ra'uf amma iyayena sun rusamin burina,batare da nasan dalili ba, sun fadawa Ummi maganganu mara sa dadi sai kace itadin Ba jininsu bace akan kawai suna zargin da hadin bakintama Ra'uf yazo neman aurena,gashi suna kokarin tilastani auren Yaya Ahad dakema kina sane da irin kiyayyar da Umma Jamila ke gwada ma...kukan da take makalewa ne ya kufce mata,Samiha da takejin kukan kawarta ta har saman kanta ta soma rarrashinta " Haba Rufaida kukan meye haka nima Idan kinayi wallahi nima yi zanyi ke kawatace danike jinki a jinin jikina wallahi son danake miki ko Yaya Sauda bana masa kwatankwancinsa yi hakuri daina kukan kinji kawata dan Allah" Kukan Rufaida ta tsayar Kafin ta cigaba da magana "Samiha busu kyautaminba nida Ummi sun rabani da mutumin Dana fara so a duniya akarshe sun yiwa Ummi kazafi sun muzanta ta muna kallo bayadda muka iya nima suna kokarin hadani da wani tashin hankali Abba yanaji bai hana Abba Bukar yanke wannan shawararba gaskiya bazan iya....Samiha bata bari Rufaida takarasa maganar da takeson yiba tayi saurin dakatar da ita da cewa" Haba Rufaida karki furta wata mummunar kalma ga iyayenki dukda nasan busu kyautamiki ba kiyi kokari ki manta komai ki tuno da abubuwan da suka miki tunda ga haihuwarki har zuwa yau sine suka maidake cikakkiyar mutun suka baki tarbiya da har Ra'uf ya ganta tattare dake yaso aureki karki manta hakan ki fadi mumnunan kalma garesu ,nasan abinda suka yiwa Ummin busu kyautaba amma ya zakiyi ita ta suce,saidai fadan ne da sukai mata ni mamaki ma ya bani itada bata sansu ba amma sai a huce akanta amma komai sukayi mata tasu ce dai,sannan batun auren yaya Ahad ki fahimci bad Umma Jamila zaki zauna ba sai kinje inda take ko wani Abu yakawota gunki zata fadamiki wata magana tunda yaya Ahad nasanki ai shikenan. Rufaida da.maganganun Samiha suka shigeta "Gaskiya nagode kawa tagari" Babu komai kinfi ganan Rufaida ke kamar jinin jikina ce"Ahmad da ya samu Samiha a falo yaji tana cewa Rufaida ya fahimci da ita suke wayar ya umarci ta bata wayar su gaisa danshi bayida haufi akan Rufaida yasan bata da laifi Bayan sun gaisa da Rufaida da kamar da zata cewa Samiha karta basa wayar sai kuma taga bata kyautaba tunda shi da akamusu laifi bai kullaceta ba sai ita,jin muryar Ahmad yasata dawowa daga tunaninta "Amaryar Ahad,ashe dama yayanki zaki aura shine aka mana kora da hali ko?" Yadda yayi maganar yasa Rufaida ta fahimci bai dauki zafi ba shi,yasa itama cikin wasa ta mayar masa da amsa "Kai Yaya Ahmad ba laifinmu bane laifin 'Danbata Family ne" Zaro ido yayi baiyi mamakin jin sunan a bakinta ba saboda Samiha "To ke kuma ya sunan naku Family da sainace sune masu laifin" "Tafida, yaji ta fada da tana fadar hakan ta yanke wayar ta daga Koran Ummi da take mata " to sune masu laifin"Ahmad ya fadi hakan,jin bata amsa ba ya sashi duba wayar ganin takatse kiran Samiha ya mikawa wayar "Ungo kawarki ta katse wayar ta soma fahimtar munfisu gaskiya" ya karasa maganar yana murmushi ya shige ciki. Suna gama wayar da Ummi da kannenta da suke fadar yadda sukayi kewarta sakar zuci tafara ta yadda komai ya sauya mata lokaci kankani tunanin Ra'uf shine dankare a zuciyarta sai dai kuma an raba wannan soyayyar data ginu a tafarkin gaskiya tanason ta kirasa taji muryarsa sai dai idan ta kirasa mai zata ce masa ba wani zata aura idan ta kirasa ya daurar kanta zatayi Da wannan tunanin barci ya dauketa *********** Kajan yo ma zuriyarmu wulakancin da babu wani bil adama dan cikin zuriyarmu daya taba janyomana face kai Hajiya Hanne ce take fadar maganar cikin bacin rai wacce take zaune a durowar gefen gado wanda wanda take maganar danshi ke zaune kan gado yana kokawar sa agogon hannunsa Fadan ta cigaba dayi batare da tsayawaba nidai tun lokacin da zuriyata ta hadu da ta hafsatu babu ranar da farin ciki ya wanzarwa zuciya ta iyayenku sun shanyemin 'ya'ya na guda biyu dalili mai karfi da yasa shima dan uwan naka yaje ya auri wadda babu sanayya ko guda daya da na sani game da ita shiyasa kai dinma kaje neman auren irin su saiga irin cin fuskar da kai da karen kanka kajanyoma a halin naka ca nake kai dakanka kafi kowa sanin irin soyayyar da karima ke kokarin gwadama amma kaidin da karan kanka kafurta bakasan 'yar uwar jininka wadda kai kanka kasan tafi yarinya irin mayu aini dai sam banyi sa ar surikai ba daga uwar taka har hannatu yau kimanin shekaru akallah 4 rabon ubanka da zuwa inda nike kuma baidama niyyar zuwa itako uwar taka rabonta da zuwa kaduna tun barinku kasar nan amma inajin labarin bata shekara biyu bata zo taga uwarta ba saboda ni bata daukeni uwa ba duk irin halaccin dana yimusu daga ita har hafsatun wadda a kaf zuriyarmu babu wadda nayima abinda nayima hafsatu a matsayinta na yar uwata mafi kusanci a gareni amma yau ga irin abinda kajanyo ma kanka ka janyo ma zuriyar ka haba *Abdur ra'uf* .jin ta tsagaita maganar tatane yasa shi mikewa yana fadin haba Hajiya duk mai ne ne anfanin fadin haka inji AbdulRra'uf din da yamike yana kokarin daukar wayarsa ya cigaba dacewa tun a lokacin da abun yafaru yakamata aman ta da maganar.hajiyar ce ta kara dacewa naki mantawa da maganar idan kai bakasan ciwan kan zuriyar ka ba aini nasani nasan tozarcin da akamana nidai hada ji'bi da zuriyar hansatu bai kareni da komai ba wato ma kawai nabar maganar . saurin ficewa daga dakin yayi danshi dayasan kalaman na hajiyar yana da cikin mizanin muni nada ga gareshi da baiyi jimirin zama a 'dakin nashiba shidai sam kalaman hajiyar sun masa matukar munin da bazai sake son jinsu ba wadda shidai sam hajiyar bata kasance macen da zai duba amatsayin uwa ga mahaifinsa ba domin da hakan yakasance yasan tabbas bazata zamanto Mai sake kokarin jefa zuciyarsa tasa bisa ga kangin damuwa ba duba da irin kiyayyar da aka nuna masa a bangaren gidansu Rufaida wanda shi yasan ko da bai san dalili ba Ahalin nasane silar rugujewar farin cikin nasa a karo nafarko yarasa yarasa masoyiyarsa mai matukar son farin cikinsa wadda tarbiyyarta ce silar son cigaba da zama da ita na tsawon har abada yana cikin tunanin ne yakarasa bude kofar wani daki yashiga da sallamarsa. Gefen sallayar da yasamu dattijuwar matar fara yazauna yana fadin ammi sannu tasbahar hannunta ta ajiye akasa tana mai amsa masa sallamartasa dafadin yawwa *RA'UF* kafin tadora dacewa sarkin a zama har naga kashirya tun a subar fari tafada tana mai kau da kanta daga kallonsa *RA'UF* 'din ne ya kalleta yana fadin tuba nake *Ammi* tun 'dazu nagama shirya komai wannan rigammiyar tsohuwar ce ta tsaidani nagama shirina ta tsaidani *Ammi* ce ta dubesa tace kaidai kasani yawwa *Ammi Ra'uf* ya anbata dama har yau Hajiya na nan da fadan ta mara karewa idan ta fara Dariya abin yabawa *Ammi* tace sai hakuri zama da hajiya. Ina fata dai ka kammala shirya kayan naka eh ammi danladi ma har yasa su a mota. Ko a jikin motar da hajiya tafito yi musu rakiya ita da sauran mutanan gidan fadan ta hau yi tana fadin idan kakoma kasar fararen motar ka mutu babu aure kannen ka kuma baza su fasa aure ba kamar yadda dai Ahmad yayi kafin tajuya ga Ammi tana fadin ke kuma banaso kodai da rana daya kisake zuwa daga ke har dan nawa dakika shanyeshi kubari sai mutuwata kuzo.ita dai Ammin ba tace ko mai ba sai kanta dake kallon kasa Baffa Alhaji da sai yanzu yasa baki da take gefen hajiyar ne yace haba hannatu kedai sam bakya iya hakuri ne da harkar duniya komai bazaki mikasa ga Allah ba sai kin nemi wani abu da zaki fada akanshi maine laifin yaran nan jabiru bata tsaya jin karshen maganar ba ta bar gurin Mama Suwaiba tace to babban mutum Allah yaki yaye hanya amin umma Ra'uf ya fada yana murmushi dukda yadda zuciyarsa bata masa dadi amma yanajin dadin sunan nan da Mama ke kiransa dashi anan motar ta tasu ta tashi duk zuciyoyi babu wani dadi ba daga shiba har ga zuciyar Ammi da take mahaifiyarsa suna barin gidan Malika suka nufa daganan suka nufa dako zama busu yiba Safiyya ta fito da Jakarta da take ja Aunty Malika da yaranta suka fito musu rakiya harabar gidansu. *** Wayarsa yake dannawa da yake kwance a falon gidan Bello dake Abuja sai dai wayar kawai take dannawa amma tunaninsa naga Rufaida fuskar Rufaida ita yake gani a idanunsa,shi kansa yasan bakaramin so yakewa Rufaida ba Bai saurari lemukan da Bello ya shigo musu da suba ya mike yabar musu falon ya shige ya cigaba da tunaninsa yanasan kiran Rufaida saidai idan ya tuno wayarsu da Ahmad a dazu da yake shaidamasa aure za'a yiwa Rufaida zata auri cousin dinta saiyaga babu anfanin kiran idan yakirama bazai anfanesa ba kiran dalilin da yasa ya hakura yayi kwanciyarsa da addu'o'in kwanciya barci a bakinsa. [8/24, 7:48 PM] Sadiya Ibrahim Khaleel: *JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil😘 *Afuwan masoyan littafin jininmu 'daya kuyi hakuri bisa tsaikonsa ya Allah ka bamu ikon rubuta abinda zai anfanemu duniya da lahira* *Note ABDULAHAD shine ya koma ABDULWAHID* 36 Sai karfe goma saura Rufaida ta kunna wayarta da tagama shirinta na tafiya gidan Gwaggo da Abba Bukar ya umarci ta cigaba da zama har ayi bikin a gidan dan yasan fitinar Hajiya Jamila shi kuma mutum ne mai ra'ayin rikau zai wuya yayi magana ya canzata,jiran Abdulmalik take yazo ya su tafi sai goma saura ya shigo gidan ya dauki kayanta yasa a boot suka nufi gidan Gwaggo A kofar gidan Gwaggon AbdulMalik ya tsaida motarsa da gidan yake ginin blo da blo da a kofar gidan sukaci karo da Malam suna fira da wasu dattawa AbdulMalik ne yayi gaba da kayan Rufaida ta tsaya suna gaisawa Malam shida dattawan cikin wasa da dariya Sallama yayi ya shiga gidan Gwaggo da zaune kujera tana dukar dakanta tana tsintar wake jin muryar AbdulMalik yasata dagowa cikin fara'a ta amsa masa tana yi masa maraba "Amsawa yayi ya aje Jakar ya aje ma Rufaida kofar daki Tsintar waken Gwaggon ta'aje ta mike yayi hanyar daya daga cikin dakunan gidan da suke a Jere tana kokarin shigewa dakin tace "Shigo daga ciki mana" Abdulmalik yace"a'a Gwaggo daukomin tabarma na zauna daga nan ga darbejiya nasha iska naji garin yau antashi da zafi zafi"dakin ta ka rasa shiga ta fito cikin sauri dauke da tabarma a hannunta "Nayi zaton ai kun rikemin jikartawa nayo muku takakka" Gwaggo take fa'dawa AbdulMalik haka da take kokarin yi masa shinfidar tabarmar "Haba wane mu Gwaggo ai Rufaida mallakinkuce keda Malam" AbdulMalik yayi zancen yana aje jakar Rufaida a tsakar gidan ya karasa kan shimfidar da ta masa ya zauna Gwaggo tace "kwarai kuwa fa'di ka kara,ina Rufaidan ne banga ta shigo ba" tayi maganar tana karasa wajen tulun ruwa "Tana can waje Malam ya tsareta da surutu" "Ai ko rabinka baiba India a surutu me nasan" tayi maganar tana karasowa inda AbdulMalik din yake da kwanon silba da cikosa da ruwa takawowa AbdulMalik tanemi guri gefe ta zauna kusa da shi Baikai ga sake yin magana ba suka ji sallamar Rufaida Amsa mata sukayi inda AbdulMalik ya kalleta "Sai yanzu tsohon ya barki ki shigo kenan kinaso ki kwacewa Gwaggo shi ko" Rufaida tace "Ai yayi min tsufa" "Naji dai Ku varmin kayana na ni inasan shi duk tsufanshi" Cewar Gwaggo "Ai Gwaggo dankema kinsan tsohuwar ce"Rufaida tayi maganar tana dariya " sa'arma duk zaku tsufan kuma indai da rayuwa. Abdul malik ya 'dauki ruwan ya'dan kurba ya aje Ya canza maganar yana cewa"wannan ruwa haka Gwaggo sanyinsa kamar na fridge" Gwaggo ta murmusa "Kai AbduMalik banda sharri fa ina zaka hada sanyin tulun ruwa dana fridge kai dai tsokanarka kace" Dariya yayi yace "au Gwaggo bamu gaisa ba" A tare shida Rufaida suka gaisheda Gwaggon Inda AbdulMalik ya cigaba da cewa "ina dumamen tuwon ne yau naji biki min tayi ba" "Gashi can a murhu a sako ma ko" "Anya Gwaggo tuwon nan zai samu shiga naci girkin Mama Kubra ya cikamin ciki kuma sauri nake yau munada lecture karna makara Rufaida da bata ce komaiba tunda suka fara maganar batasa baki ta mike daga zaman da tayi ta shige dakin Gwaggo Gwaggo ta bita da kallo ta juyo ta maida dubenta ga Abdulmalik Shima maida kallonsa yayi ga Rufaida da take kokarin daga labulan dakin Ya maida kallon ga Gwaggon cikin yanayin tausayawa Rufaidan ya dan sassauta murya "Gwaggo ya kamata ku daure ku aura ma Rufaida zabin ranta gudun karta shiga wani hali,duba da ko Yaya Wahid kunsan ta aura bawai da'dinsa zata ji ba saboda Umma kuna sane da duk abinda ke faruwa Murmushin Gwaggo tayi "AbdulMalik kai kanka kasan da inada iko da Bukar da Aliyu in fadamusu suji da sun amince da zabin nata amma kememe sunyi kunnen uwar shegu da maganata suka nuna ban isa dasu ba,ka kyalesu duk abinda suka jawo ma 'yarsu suya shafa" "Hakane Gwaggo amma ina gudun abubuwan da zasu iya zuwa ki dawo kina sane da halin Umma amma kiyi tunani, ni bari na tashi daganan makaranta zan wuce idan nadawo zan biyo" AbdulMalik yayi maganar yana mikewa tsaye. Itama mikewa Gwaggo tayi don ta rakasa" "To Allah ya taimaka aidama nasan tunda 'yar uwarku tana gidannan zamu rika ganinku tunda albarkacin kaza kadangare kansha ruwan kasko" "Au haka kikace Gwaggo nasan da Malam yana nan bazai ce haka ba" "Aiko har gwara ni dashi ma" Takarasa maganar tana kokarin karasa rakashi zauren gidan Har zai fita yace"to Gwaggo tunda tsohon yaji tsoron shigowa bari na samesa a wajen, ita kuma Rufaida tunda ta gudu daki nakawota gida shikenan" Dariya Gwaggo tayi tace "Ai ni Mijina ba matsoraci bane bayaso ya tsorata ka da maganganunsa masu karsashi ka kasa juresu ka gudu dukda yanzu ma da vai shigo ba gashi harka gudu kana tsoron gamuwarku,Rufaida kuma kunfi kusa duk abinda zaka ce mata" "Gwaggo kenan bari dai na tafi saina shigo anjima zan mayarmiki da martaninki"yayi dariya yana karasa ficewa waje Addu'a ta bisa da ita ta dawo cikin gidan datayi kacibis da Rufaida " Lah Gwaggo ina Yaya AbdulMalik 'din na fito da niyar muyi sallama ashe harya tafi"cewar Rufaida "Dake zai zauna zaman jira ana firar arzi'ki kin tashi fu kin shige daki kamar wadda aka tsikara"Gwaggo ta karasa maganar tana cire kofin saman tabarmar ta ajesa gefe ta fara nanna'de tabarmar " Gwaggo shiga nayi amsa waya fa Yaya Abdul ne ya kirani" "Oho miki dai kina kokarin sa damuwa a ranki bayan addu'a ce mafita,ki kuma dauki abinda Allah ya kaddara a rayuwarki yafi duk wannan tarin damuwar" "Hakane Gwaggo kuma insha Allah zanyi yadda kikace dama ba wai kin Yaya Wahid nake ba" "Yawwa jikalli ta ki dinga mi'ka lamuranki ga Allah" Da wannan maganar Gwaggo ta shige daki da tabarma rike a hannunta Rufaida ta nufi kitchen dan marmarin cin tuwon Gwaggo take. *TEAM OF RUFAIDA* *TEAM OF ABDULWAHID* *TEAM OF RA'UF* Muje zuwa anya kuwa....me zai faru a next page ya kuke tunanin Hajiya Jamila zatayi idan taji labarin saka ranar wannan auren 🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️ More comment's more typing [8/24, 10:52 PM] Sadiya Ibrahim Khaleel: *JININMU 'DAYA* BY SADIYA KHALIL 37. "Ina Rufaidan ne yaran nan sai jiranta yake ta shanyasa banda da dare ne ai sai ya bushe" Gwaggo tace "Kwalliya ai take masa karya 'dauketa budurwar kauye yace ya fa.... Gwaggo da bata karasa maganar ba Rufaida ta karasa fitowa daga 'dakin da cikin shigar atamfa riga da siket da hijabinta iya gwiwa da hasken lantarki ya sa Gwaggon hangota daga inda suke zaune itada Malam suna fira Inda suke ta 'karaso tana cewa " kai Gwaggo mai naji kina cewa,Yaya Wahid 'din zan tsaya yi ma kwalliya,kamar bako" Gwaggo tace "Bama dole ba yarinya kar yace ya fasa, kuma ni da ku'di aka ha'dani bazan iya nemo wancen dan kasar turawan yaron ba " Ba tare da Rufaida ta sake furta komai ba tabar wajen su Gwaggon da ko saita dawo bata tsaya ce musu ba dan an ta'bo mata abinda take kokarin mantasa a babin rayuwarta dukda tasan da kamar wuya kaunar Ra'uf daga jininta yake ba daga zuci ba,tasan zata iya auran wani amma kuma bazata iya manta Ra'uf ba dan ya zama kamar 'dan uwa a gareta take ji a ranta Tana jiyo maganar Malam da yake cewa "Haba Zainabu ke maiyasa kika fiye kato 'barar zance kamar yarinya tunda batun yaron nan ya riga da ya wuce" Ba tare da taji mai Gwaggon zata ce ba ta karasa zauren gidan da haske ya gauraye sa sallama ta masa da ta samesa tsaye cikin shigar wando da riga na yadi tazarce kayan isassu ya har'de hannunsa saman 'kirjinsa da ya soma yanke tsammanin fitowar Rufaida dukda bawai lokaci ne ya kure ba sai dai sanin wancen dalilin da yake tunanin zai iya hanata fitowa sai kuma yaga akasin tunaninsa aje wancen tunaninsa yayi ,ya amsa mata sallamar da tayi ya kuma kasa dauke kansa gareta harta karasa shigowa cikin zauren nesa dashi sosai ta tsaya Murmusawa Wahid yayi kafin yace "barka da fitowa Matata Insha Allah" Cikin zaro ido Rufaida ta 'dan kallesa lokaci guda da ta maida kanta 'kasa "Eh mana bikisan ansa ranar bikin mu ba" Cewar AbdulWahid da yaga kallon da Rufaida tayi masa alamun kamar bata yarda ba. "Ina yini" Rufaida tayi maganar tana son a bar waccen firar haka "Lafiya Kalau,amma ya kika canza mana fira,amma dai na kyaleki ko tanbayi Gwaggo idan kin koma ciki" "To" kawai tace kafin Wahid ya maida dubensa ga Rufaida sosai "Rufaida ina sanki tun kafin nayi girman da zan fahimci menene so da kauna nayi tunanin so ne irin na 'yan uwa na jini sai a karshe na fahimci bawai hakan bane,tun tuni naso furta miki sai dai fargabata Umma ya zata dauki lamarinki zata amince dake kuwa,ganin shurun zai soma cutar dani yasani sanar da Abba da ya amshi zancen hannu biyu harma yace naje na nemi soyayyarki indai kin amince shikenan shima ya amince,a lokacin da nazo sanar miki a waccen ranar na tarar wani ashe ya rigani furtawa nayi kukan zuci a wannan ranar karshe dai na hakura na barwa Allah lamura na,saidai bawai bana kishinki ba a lokacin amma hakanan a waccen ranar na yava da zabinki tundaga kallo daya dana masa tabbas nasan idan kika kasance matarsa da inada yakini da kin kasance cikin farin ciki saboda naga alamun kaunarsa a fuskarsa fiye da yadda ni nake kaunarki saboda in 'din mai raunin zuci tamkar wata macen i,hakanan naji a raina,sai dai kuma bansan yadda gobe zatayi ba,wanda zan iya hakurta ma raina ke indai yadawo zai aureki saboda inasan farin cikin kanwata matuka ko ya kikace ya karasa zancen yana sake duben Rufaida Murmushi tayi masa tana son Wahid fiye da son da take tunanin tana masa a baya kasancewarsa dan uwan nata halayoyinsa masu kyaune bayida son kansa sa'banin sauran ahalinta,shi mutum ne mai tsage gaskiya a duk wani hukuncin da zai yanke tuni batun yau ba,tasan tana san shi amma zulliminta 'daya ummansa wannan mataki zata dauka akanta matukar ta aurar mata 'da Jin shirun ya soma yawa yasa AbdulWahid magana "Ya kikayi shiru kin barni na gama zuba zance" Maganarsa ta maidota daga tunanin da take yi "To Yaya Wahid mai zance" Murmushi ya dan sake yi "Au baki san mai zaki ceba,to yardarki nake bukata kin amince dani" Yakarasa maganar yana nuna kansa Bata da wani zabin daya wuce ta amince don tasan da yardarta ko babu aure dai sai an'daura ita da AbdulWahid indai suna raye tunda iyaye sun shiga lamarin auren,bare itama dai bazata ce bata sansa ba dama dai zulliminta guda mahaifiyarsu wahid Hajiya Jamila hakan yasa ta 'daga masa kai Yayi murmushin jin da'di "ina godiya kanwata Allah ya bani ikon riqeqi da amana" A iya fatar bakinta tace Amin ba tare da ta furta ba Ya sake cigaba da magana "Nasan yanzu dai zulliminki Umma ko ki kwantar da hankalinki yanzu Umma ta zubda makaman ya'kinta tabarwa Aunty Amarya da Mama Kubra" Murmushi ta 'danyi ka'dan dan tasan AbdulWahid ya fa'di maganar dan yaji da'din bakinsa zatace banda haka inasu Mama Kubra suke da wani kata'bus a gidan da umarninta ake bi a gidan matukar Abba Bukar yasakai yabar gidan kuma a jiya fa tagama jin maganganun da tayi masa akanta,haka itama ta tabbatar da ta shiga dakinta gaida ita ,shima dai kokarin sa take gani da yau yazo gunta bayan mahaifiyarsa vatasanta bataso ya aureta akan wani shirmen zancen da take da tabbacin baida wata makama dan kawai kanin mijinka yayi aure saika dauki kiyayya ka dorawa matarsa ita ba kishiyar kiva bakomai ba. "Kodai nayi laifi ne kinki sakin jiki muyi fira yau" Maganarsa ta katse tunaninta "Ko 'daya" Agogon hannunsa ya duba ya 'dago da kansa ya dubeta "To shikenan bari zanje gida ni naga lokaci ya fara ja tara tayi harma ta gota kuma gobe nakeson komawa abuja,zan kiraki zuwa anjima" "To Allah ya kiyaye hanya" tayi maganar tana 'dago kanta daga kallon kasan da ta ke. Cikin jin dadin addu'arta ya amsa da "Amin" Da haka sukayi sallama ya tafi Rufaida jiki ba kwari ta koma cikin gidan Da sallama ta shiga cikin gidan inda ta bar su Gwaggo anan ta same su. Amsa mata suka yi Gwaggo tana cewa "wannan zancen haka daga zuwa kodai korarsa kikai ne" "Kai Gwaggo kona koresa ai kinsan bazai tafi ba,tunda gidansu ne"ta karasa maganar tana kokarin cire takalminta ta shige daki Ganin hakan yasa malam gyaran murya " Rufaida zonan" Rufaida da taji maganar malam yasata maida takalminta ta karaso wajen da suke ta zauna "Malam gani" Sake gyaran murya yayi ya soma magana "Rufaida dalilin kiran dana miki shine na sanar miki sa ranar bikinki da iyayenki sukayi sun yanke hukunci nanda wata guda za'ayi,dan Allah kar asami matsala daga gareki ki mika lamuranki ga Allah,Allah yasa hakan yafi zama alkhairi" Gwaggo ta dan dubi Malam ta soma magana "Malam yaushe akasa ranar bikin kuma banida wani labari a matsayinka na uba ga Hauwa'u hatta nima bansani ba,maisu Aliyu da Bukar yaran nan suka maida kansu ne,ace komai isu isu zasu rika yi Malam ya murmusa yace "na samu labarin gurin Ashiru to ni nafadamusu suyi komai saboda kinsan dazu na shiga Kaduna" Rufaida da haka ta mike ta shige daki ta zauna gefen gado ta soma tunanuka mabanbanta a ranta ace har ayi maganar aurenta Malam mahaifin Umminta ba'a fadamasa ba hatta Gwaggo itama da take tasu basu fadamata koda a waya bane takanji labarin matsaloli a cikin Family amma bata ta'ba cin karo da irin nasu matsalolin ba a cikin wadanda takeji ba banda su Gwaggo ta haifi 'ya to da danginsu babu mai saurararsu da komai to yanzu ma gashi sunada 'yar ana kokarin yi musu yadda akaso da 'ya'yenta dukda suke jikokinsu ace hidimarsu ta soma tashi ba'a sakasu a ciki ba suda suke matsayin kakanninsu amma da rashin mutunci ne dangin Abbannasu da Umminsu sunfi kowa yi musu ,dan ba suda banbanci abinda yayi Abbansu shi yayi Ummin nasu duk dangi guda suke dan bata mantawa da Gwaggo da mahaifin Abbansu uwa daya uba daya suke sai dai ita Umminsu mujiya ce a cikin dangin nasu kodan ita ka'dai ce gurin iyayen nata abu saiya taso a danginsu aki fadamata sai Gwaggo taji ta fadamata idan kuwa taje a dinga jifanta da bakaken maganganu tun da suka fara tasowa suke fahimtar haka, suma yau su Gwaggo gashi a aurenta an nuna musu iko. Ganin tunanin ba zai fishsheta ba yasata daukar wayarta ta 'dan nemo littafi ta karanta kota ji sauki a ranta *TEAM OF RUFAIDA* *TEAM OF ABDULRA'UF* TEAM OF ABDULWAHID Ko ya zata kasance dai muje zuwa😊😊😊..ku biyo ni🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️ More comment's more typing *JININMU 'DAYA* BY SADIYA AL-KHALIL 38. ABDULWAHID "Hajiya Jamila ta zauna gefen gadon da ta samu Wahid kai ta cije le'benta na katsa AbdulWahid da tunda ta shigo dakin bayan ya amsa mata sallama yake kallonta saboda yasan babban abu ne zaisa Ummantasu shigowa dakinsa da yake kwana,maganarta ta maidoshi daga wancen tunanin da take " Nasa Abdussalam yayi min kiranka 'dazu yace yazo baka nan" Cike da nuna girmamawa yace "Eh Umma naje gidan su Gwaggo Zainabu ne" "Gurin Rufaida ko" Hajiya Jamilar ta yi maganar ta kuma cigaba da cewa "Wahid maiyasa kakeson abinda raina zai baci" Da sauri ya 'dago ya kalli mahaifiyar tasa Kai ta daga masa ta cigaba da magana "Kwarai kuwa Wahid da bakaso da baka yi gigin kwatanta koda son Rufaida ba bare har kaso aurenta,kana sane da buku dace da juna ba ta kowacce fuska,wannan tunanin da nake yana kara batamin rai idan naji ita kakeso ka aura bayan kai masa nine akan komai,tun farko har zuwa yanzu,ga uwa uba kasan halin munafurcin Hauwa'u da mai goye mata bayan Gwaggo Zainabu shiyasa banasan ka aureta saboda.... "Haba Umma maganar duk ta mecece hakan ,dukdan akan nace inasan Rufaida" AbdulWahid yayi maganar yana kokarin katse maganganun da mahaifiyar tashi keyi. "Murmushin alamun cin nasara da take ganin ta farayi tayi daga visa ni tace " to naji zan daina amma sai kamin alkawarin zaka janye maganar aurenka da Rufaida,ka amince ka auri Rukayya yarinyar nan tana sanka gata mai hankali ga iya zama da mutane,kuma kana sane da irin soyayyar da Yaya Sha'awa(wato mahaifiyar Rukayyan keyi ma tana sanka kamar 'dan cikinta Shiru yayi yana tunanin maganganunta da duk ba gaskiya a cikinsu kafin ya ce "To Umma zanyi tunani" Da fara'a akan fuskarta da jin maganar da yayi tace "Yawwa Wahid Allah yayima albarka amma dai kayi tunani mai kyau" da haka ta mike ta tura masa daki Bayan fitarta ya kwanta yana tunani ,tabbas yasan yanasan Rufaida bayaji zai iya rabuwa da ita,kuma idan ya rabu da ita yasan babu lalle a wannan zamanin ya samu tanada halayya mai kyawun gaske, yasan kawai dan kiyayyar da Ummansa ke musu yasa take alakanta su da munanan zantuka,gaskiya bayaji a ransa zaibi maganar mahaifiyarsa ,saboda nufin Alkhairi ya keson yi,toma idan bai aureta ba Rukayya da takeso ya aura shifa basanta yake ba da aure,batayi masa ba a irin matan da yakeson aura,bata da kunya ga raina mutane to ma shi mai zai kaisa yayi sure a dangin mahaifiyarsa da duk halayyoyinsu daya yawancinsu musamman ma Aunty Sha'awa mahaifiyar Rukayya da ta takasu rashin mutuncin,yana sane da kallon wulakancin da Aunty Sha'awa keyi musu idan sukaje Nasarawa Ummansu tace suje gidanta kasancewar mai kudi take aure ,wanda saida mahaifinsu yayi kudi ta dawo tana kaunarsu,shine yanzu akeso a makala masa Rukayya saboda sunga shima ya dago da arzikinsa,dukda Ummansu batasan wulakancin da Aunty Sha"awa ta riqa musu ba idan sunje gidanta saboda basa fadamata amma su suna sane busu manta ba ,da wannan tunanin ya kwanta ba tare da ya kira Rufaida ba da ya fadamata zai kirata idan ya koma gidan da yana dawowa Umman tasu ta shigo ta tare sa da wannan maganganun. KANO Abba Aliyu da ya fada'da fara'arsa da shigowarsa cikin falon ya tarar da iyalansa guri guda zaune suna fira shima fasa fitar da ya fito da niyyar yi yana kokarin zama "Abba sannu da fitowa" yaran suka hada baki gurin fadar hakan. Da yawwa ya amsa ya zauna kujera yana sauraron firarrakin nasu da kusan duk na yayarsu ne da sai yanzu ya tuna bai fadamusu bikin ta saura sati uku ba da shima jiya Abba Bukar ya kira yake shaida masa dukda baiji dadin abinda Abba Bukar yayi akan 'yar tasa ba ace babu ko shawartarsa a ce za'ayi aure asa biki sati hudu saikace bazawara dukda dai ana hakan amma bawai yanzu ba saboda idan ya shirya shi Uban 'dan to shi bai shirya ba,ga dadin bacin rai shida 'yarsa ba'atashi fadamasa bikin ba sai saura sati uku,saidai inda hankalinsa ya kwanta Abba Bukar din yace shi zai mata komai,shine zuciyarsa ta daina ganin laifin Abba Bukar din,sai dai yanzu zulluminsa guda yadda Hauwa'u zata dauki lamarin da har yau zullumin sanarmata bikin yake,dukda yasan bata kyauta musu ba amma yanzu yana ganin sunfita rashin kyautawa koda ita Rufaida 'yar rikoce gare ta abinda sukayi busu kyauta ba asa ranar 'yarta ba'anemi shawarar ta ba aka zartar da hukunci,sallamar Ummi Hauwa'u ta maidosa daga wancen tunanin nasa,amsa mata sukayi shida yaran suna yi mata sannu da zuwa Rafi'a ta fado jikinta tana yi mata oyoyo Sauran yaran suna dariya suna cewa "Kamar Ummin ta shekara a wani gurin" Hauwa ta hararesu ta riqe hannun Rafi'a suka karaso cikin falon "Ai tafi ku sona ne kuda ko murna bangani kan fuskarku ba" Rumaisa tace "Wallahi Ummi munfi sonki kinga yadda mukai kewarki tanbayi Abba kiji hirarki data Yaya kawai muke tunda kika fita ya jikin Ra'is din namu" Ummi Hauwa'u ta murmusa tana zaunakujerar da mijin nata ke kai sannan tace yana gurin yayanku yaji sauki" "To Allah ya kara sauki" cewar AbdulRashid. "Amin ya rabb Kallonta ta maida ga Abba Aliyu ta dan dubesa ganin fuskarsa babu walwala ba kamar yadda suka barsa ba,gashi bayasa baki a firar tasu. "Abban Abdul anya lafiyarka kalau kuwa" Sai da yaji muryarta sannan ya fahimci ashe harta zauna kusa da shi baisani ba yanacan yana tunani murmushi ya ka kalo "Me kika gani,bayan nine na fara yi miki sannu da zuwa,ina Ra'is din ya jikin nasa" "Hmm,akwai abinda ke damunka nake tunani gashi baka walwala,yana hannun Abdul yanzu zasu shigo a rubuto masa magunguna ,anyi masa allurai,sai dai kudin daka bayar busu isa an siyosu duka ba,ni kuma babu kudi a gu... Bata karasa maganar ba sallamar su Abdul ta katse ta da ya shigo,sabe da Ra'is a kafada da Ra'is din ke shan alawa,daya hannunsa kuma rike da ledar maganin,sallamar suka amsa masa dukansu,kannensa suka masa sannu da zuwa ya amsa ya zauna akan kujera ya sauke Ra'is shima kan kujerar yaran suna yima Ra'is ya jiki Abba Aliyu yayi gyaran murya ,ya kalli Hauwa'u yanasan sanar musu lokacin ranar Rufaida da Abba Bukar yasa,dan boyewar batada anfani tunda Allah ya gani ba shida laifi shi,magana ya soma "Jiya da nayi waya da Yaya Bukar ya shaidamin sun saka ranar Rufaida wancen satin yau saura sati uku nan gaba" Abdul da yaji maganar kamar dirar aradu "What Abba mai kake fada Rufaidan za'ayiwa wannan auran biki wata guda kamar wata bazawara aiko masu kudi da suke tada kai dasu basa irin wannan auran sai.... Abba cikin bacin rai ya soma magana bai bari Abdul ya gama tasa maganar ba don batun yau ba ya fahimci Abdul wata rashim kunya yake ji dashi ma yi masan zaiyi. " Sai Ubanka kome zaka ce ,dan uwarka yarinyar ta samu miji yana santa sai aki aura mata shi,so kake atasa ta a dunga kallo,kota dinga yi mana jajibe jajiben samari wawaye da busu san darajar dan adam ba" Ummi Hauwa'u da take jin maganarsu saidai ta kasa tsaidasu saboda yadda ita ma ranta yake bace a wannan lokacin,ita da 'yarta a dauke mata ita kan kuskuren da ita bata ma gansa ba,dan zuwa yanzu ta fara gajiya da halin Aliyu komai za'ayi baza'a shawarce taba saboda son kai irin nasa Abdul ya dan sassauta murya ganin mahaifin nasa kalaman da yayi masa sun bata ransa har yana zaginsa da kafin kaji Abban nasu yayi zagi to tabbbas zaka dade "Amma Abba ai karatu zata cigaba dayi da mun kyaleta,aure lokaci ne ai koda ma ba karatun zatayi ba, mu ba zamu gaji da ganinta ba dadai auran Yaya Wahid da zatayi gwara ta shekara goma ba aure, kota auri wancen saurayin nata dukda ba'a sansa nake ba,haba Abba maiyasa kake kokarin manta kiyayyyar da Umma Jamila ke gwada ma..." Cikin zafin nama Ummi Hauwa'u ta taso daga Inda take ta rufe bakin Abdul ta wankesa da mari,dan idan tabarsa dukda ita ma ranta a bace yake da Abba Aliyu amma tasan Abba Aliyu uba yake ga Abdul bazata bari ya cigaba da sa'insa da Ubansa ba,dan bats yimasa irin wannan tarbiyyarba ita bata tana sa'insa da Abbansu a gabansa ba,dan yau kenan ka haifesa ne amma baka haifi halinsa ba,gashi a gaban kannensa,hannunsa taja da karfi zuwa upstairs tana magana cikin fada "Abdul baka da hankali mahaifinnaka kake fadawa haka,kamanta duk karkashinsa muke yanada ikon zartar da hukunci akanmu...." Da wannan maganar suka karasa hayewa Upstairs din da Abba Aliyu ya bisu da kallo da ransa ke masa tukuki yanzu ace Abdul shike fadamasa bakaken maganganu har haka gaban sauran kannensa dukda yasan ya musu laifi amma dai abinda Abdul yayi masa ya bata ransa matsayin Abdul na dan cikinsa koshi sa'ansa ne sai haka ,baya tunanin Hauwa'u tanada laifi wajen lalacewar yaran da yake nema yayi yanzu,saidai zai yiwa tufkar hanci,kofa yayiya mike ya duba magunan Ra'is da suke leda ya dauki kati yaje ya ciko masa ragowar magunan da aka rubuta masa Yaran da babu wanda ya shiga maganar da tsoro fal ransu ,dansu basu taba cin karo da wannan matsalar ba bare su saba da ita tunda suka taso a gidansu ba akwai girmama juna atsakaninsu amma lokaci guda gashi ana musayar magana tsakanin Abbansu da Yayansu busu san meke shirin faruwa da suba Ra'is da kowa yaki kulasa kuma yaji hayaniya da baisa ba da jiba ya rushe da kuka Rumaisa ta daukesa tahau lallashi dan ko kusa bata yi gigin kaisa gurin Umminsu ba dan a yadda taga bacin rai a ranta ta iya dukanta ma" Team of Rufaida ,team of AbdulWahid,team of AbdulRa'uf Team of Ra'uf Anya ba za'a yiwa AbdulRa'uf sakiyar da ba ruwa ba koda yake dama dai anmasa saidai ya rungumi sorry Team of Wahid Ya kuke tunanin zata kasance idan Hajiya Jamila taji labarin.wannan bikin anya zata yarda kuwa?kai akwaifa gwarama a gaba nake tunani. Nidai na fece bani na fada ba😂😂🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️ A suburbudo ruwan comments aga typing nagama sa ayau😂😂 basai gobe baFJininmu 'daya By Sadiya Khalil Page 39 "ZARIYA" "Wasila mikomin wayata naga tana kara an kirani" Hajiya Jamila tayi maganar da suke zaune da sauran matan gidan a babban falo suna fira wasila da itace ta rage a gidan bata zuwa makaranta ta dauki wayar tana game Wasilar ta danne wayar silent "Umma bafa kira a kaiba sakone ke shigowa" Aunty Amarya da take kusa da Wasila ta le'ka wayar "Kai Wasila kema kin iya karya ko ga kirannan yana shigowa kin danne wayar a silent" "Hajiya Jamila jin maganar Aunty Amarya yasata mikewa ta anso wayarta da har wani kiran ya shigo wancen ya katse,tsaki tayi ganin mai kiran Gwaggo Lariya ce kanwar surikarsu ,tasan tunda taga kiranta roko zatayi saida takoma ta zauna ta daga wayar da sallamarta saida suka gaisa Gwaggo Lariyar da labari ke cinta ta fara da cewa " Gaskiya Jamila kin bani mamaki duk aminci na dake ace za'akai kayan lefen AbdulWahid saidai naji labari gurin Bukar" Tsaki Hajiya Jamila tayi ka'dan ba tareda Lariyar ta jiba,ita to ta ina zata zama kawar Gwaggo Lariya bare suyi aminci bayan kanwar surikinsu ce itace Autar a gidan su surukin nasu ,shiyasa bata Gwaggo Lariyar bata girmeta ba,kuma Gwaggo lariyar takeso suyi aminci,saidai ita taki jinin mutum mai shishshigin da karya,da son abin hannun mutane, da Gwaggo Lariya dukta kware ta wannan fannin shiyasa yanzu ta kasa gasgata maganar Gwaggo lariyar ta dai daure tace "Wacce irin magana kike ne,wanne irin laife kuma ni bansan wannan zancen ba" Da mamaki sosai jin maganar da Hajiya Jamila tayi Gwaggo Lariya ta cigaba "Kamar ya kina nufin ba kisan auren da Wahid zaiyi ba zai auri Rufaida ta wajen Aliyu" Cikin firgici Hajiya Jamila ta ce "Haba Gwaggo Lariya wacce irin magana ki kene" "Abinda kika ji nace,Wahid zai auri Rufaida yauma su Hauwa'u zasu taho zariya gurin biki nufinki basu fadamiki ba..." Ba tare da Hajiya Jamila takarasa jin zantukan Gwaggo Lariya ba ta kashe wayar ta mike zunbir Mai yafaru ne Maman AbdulMalik ,lefen wa za'a kai" Aunty Amarya tayi maganar cikin rashin sani ,dan itama ko kadan batada masaniya da saka ranar bikin" Wani kallo Hajiya Jamila tayi mata da haka ta shige daki ta dauko hijabi da dan makullin motarta ta dawo falon tana kokarin fita Hajiya Kubra tayi kokarin riketa "Haba Hajiya Jamila komai yayi zafi maganinsa Allah,mai Gwaggo Lariyar tace miki ko mutuwa akayi ne, ki fadamana" Fisge hannun Hajiya Kubra ,Hajiya Jamila tayi daga rikon da ta mata cikin zafin zuciya ta fara magana "Munafuka cikani,kunje an hada baki daku an munafurceni, wallahi yau sai na kashe waccen yarinyar da take kokarin shiga rayuwar dana,saidai nima yau akasheni ,dan dana hada zuriya dasu gwara na hada da kare" Tana kaiwa nan ta fice daga falon gurin motarta ta karasa ta mata key ta bata wuta tavar gidan da wani irin gudu Cikin sanyi jiki Hajiya Kubra ta dawo cikin falon Aunty Amarya ta kalleta bayan ta zauna ta soma magana "Niko Maman Hussaini mu kira Gwaggo Lariyar muji maike faruwa,sai mukira Abban Wahid mu fadamasa,dan a yadda Maman Abdulmalik ta fita kinsan komai zai iya faruwa" "Eh hakane kinyi tunani nima zullimin da nike kenan ,tunda gashi har tana kiranmu da munafukai" Hajiya Kubra ta karasa maganar tana daukar wayarta ta lalubi numbar Gwaggo lariya Wadda Gwaggo Lariyar tana can cikin zullumi dan sai yanzu tayi danasanin katobarar da tayi na fadawa Hajiya Jamilar dan tana tsoron hukuncin da zata dauka kan wannan maganar,tana wannan tunanin haka taji karar wayarta ta bugu daya ta dauka ta kara kunnenta, Hajiya Kubra ta maida wayar a handsfree jin ta saga Magana Gwaggo Lariyar ta fara "Assalamu Alaikum ,Kubra lafiya kuwa,ina Jamilar ,muna waya naji ta katse ,dama batun auren Wahid fa Rufaida muke da za'akai lefe yau...." Hajiya Kubra da bata bari Gwaggo Lariyar ta gama maganar ba tayi hantsarin katse wayar ta sake danna lambar Abba Bukar a kidime tana gudun mai zaije yazo,dan tana da yakinin gidan Gwaggo Zainabu Hajiya Kubra ta nufa shima ringing daya ya dauka da sallamarsa Ba ta jira sallamarsa ba tace masa "Abban Wahid yanzu Gwaggo zainabu ta kiramu,tace ka aje duk abinda kake kaje tana san ganinka" da haka ta katse kiran dan bataso ta fadamasa gaskiyar lamarin saboda gudun kada hankalinsa ya tashi,lamarin suke tattaunawa akai bayan gama wayar tasu dan ko ita Hajiya Kubra ba tasan maike faruwa ba itada take 'yar uwarsa ,a ranta tana fadin amma Gwaggo Lariyar bata kyauta ba ,a matsayinta na kanwar mahaifiyarta shiyasa bata fito ta fadawa Aunty Amaryar ba don kowacce matsayinta daban ne agurinta Tunanin kiran Gwaggo yake da yaga ita bata kirasa ba ta shaidamasa ba,kuma bata Saba yi masa kiranba ma,to mai yake faruwa ganin tunanin ba zai anfanesa ba ya sashi mikewa ya dauki makulle ya fito daga office dinsa ya rufe,massinjansa da ya tare sa,Abba bukar yace "Ba tashi nayi ba,zanje wani guri na dawo,idan anzo ne mana kace ba nisa nayi ba su jira ni" "To Allah ya kiyaye hanya masinjan ya fa da ya koma inda yake zaune" "Amin kawai Abba Bukar ya iya anbata yabar wajen gurin aje motoci ya karasa ya shiga tasa ya tayar ya fito daga cikin makarantar ABU Zaria da a ciki yake aiki da tunani a ransa **** RUFAIDA Rufaida ta kalli himmin fulawar da Gwaggo take so ta kwaba tayin doughnut da cin-cin,da ta tasata saita kwaba zata bar gidan zuwa gidan Gwaggo Hajiya mahaifiyar Hajiya Kubra " Gwaggo Allah na gaji ace aikin nan duk tare za muyi,maimakon ki bari su Aunty Samina su zo tunda yau zasu zo" Rufaida ta karasa maganar tana kunbura baki Gwaggo ta 'dago dakanta daga kwabin alkakin da take ta dubeta taga ta kunboro baki ta ta tabe baki tare da cewa "Yarinya koda ma kuka zaki ba ba kunboro baki ba saidai kiyi,dan sai kin kwaba zaki bar gidan nan" Rufaida ta dan lankwasa murya "To Gwaggona naji zanyi yadda kikace amma dan Allah kiyarda na kira Harira ta tayani,muyi mugama da wuri" Gwaggo ta zaro ido "Wacce Harirar yarinyar da ko uwarta bata mora mata bare ke ta mora miki daga kawancen unguwa kinajin artabun da suke da Mamarsu ta katanga akan aiki,idan Mamarta tace tayi mata" Kasancewar su Harirar makoftansu ne da suke shiri da Harirar a Unguwa itada Rufaida "Eh dukda haka Gwaggo nasan ni zata tayani kinsan muna shiri sosai" Rufaida tayi hanzarin cewa Gwaggo hakan dan karta kuma fadar wani abun "To inanan dai zan jiyo ku ta katanga,dan indai Harira ce kinsan ba shiri ba kome kuke idan vatasa kanta ba saita iya watsa miki kasa a ido" Da haka Rufaida ta mike daga tabarmar da suka shimfida a tsakar gidan ta zura takalmi ta janyo hijabinta jikin igiya tasa tana cewa "Gwaggo saina dawo" "To adawo lafiya'"Gwaggo tayi maganar tana maida kai ga abinda take,a ranta tana tunanin halin Rufaida batasan auren yaron kowa ya sani badan komaiba saidan halin mahaifiyarsa amma ko a fuska vazaka gane ba A bakin kofar zaure Rufaida tayi kicibus Hajiya Jamila da take kokarin shiga ciki hartayi kokarin bangaje Rufaida Rufaida tayi saurin matsamata hanya ta kalli Hajiya Jamilar da kallon daya tayi mata taji gabanta ya fadi ganin yanayin annurin fuskarta babu shi anbaton Allah tayi kafin tayi saurin cewa " Umma sannu da zuwa" Hajiya Jamilar ta kalli mai mata sallamar tayi ido biyu da Rufaida da da idonta ya rufe bata san da mutum a zauren ba dan tunaninta yayi cikin gidan gaba 'daya wata irin fisga Hajiya Jamilar tayi mata zuwa cikin tsakar gidan tana cewa "Wallahi yau sai na kashe ki,dan muddin ina raye dana bazai hada iri da kuba" Jin maganar Hajiya Jamilar ya ankarar da Gwaggo inda a lokacin take kokarin wanke Rufaida da mari gurin Gwaggo ta karaso da niyyar kwace Rufaida Hajiya Jamilar tayi kukan kura ta angije Gwaggo tana cewa cikin 'daga murya" matsanan Munafuka angungunma ca kike yadda kika munafunci 'yan uwanki nima zaki munafunce nine,wallahi sai dai yau na kashe ta inyaso nima akashe ni dan bazan hada zuriya da wannan mazinaciyar uwarta taba ,",ta karasa maganar tana sake kwada wa Rufaida mari daga visa ni ta shake wuyan Rufaida" Ganin haka yasa Gwaggo saka kuru ruwa tana ihu makwabta neman taimako Lokacin yayi dai-dai da karasowar Abba Bukar kofar gidan ganin motar Hajiya Jamilar kofar gidan yasashi saurin kashe motarsa ya rufe ya isa cikin gidan harda gudunsa dan yasan,tunda yaga motar Hajiya Jamilar yasan akwai matsala A lokacin da ya iso Gwaggo ta sake kukan kura ta nufesu tana kokarin cire hannnun Hajiya Jamilar daga wuyan Rufaida amma ta kasa Rufaidan sai zaro ido take "Jamila wallahi idan biki saki wuyan 'yar mutane ba to wallahi a bakin aurenki" Abba Bukar yayi maganar yana karasa shigowa ciki,da babu wanda yaji shigowarsa Badan Hajiya Jamilar taso ba ta saketa Ta kuma cigaba da dukanta,da alokacin makwabta sun fara shigowa jin kururuwar Gwaggon da suke,da kowacce take tsaye tana kallon ikon Allah,mai kuma Rufaidan tayi wake dukanta dan busu shaida fuskar Hajiya Jamila ba saboda ta juya bayanta Gurin da suke Abba Bukar ya karaso ya kwace Rufaida daga hannun Hajiya Jamila da Harira da har da ita a masu shigowar tayi kokarin karasowa gurin Rufaida ta janyeta gefe shiko Abba Bukar Hajiya Jamilar ya nufa da zafin zuciya ya kwashe fuskar da wani gigitaccen mari yayi ball da ita,ya fara dukanta yana cewa "Ke dabba ce 'yar mutanan zaki kashe" ganin yana kokarin cigaba da dukanta yasa Gwaggo rikesa tana basa baki "Kan wannan 'diyar mazinaciyar ka dokeni ko,wadda danginta suka juya mata baya,to wallahi indai kukai kokarin aura mata 'dana saina kashe ta inyaso nima a kasheni" "Da ubanki tayi zinar ko,kuma dangin ubanki ne suka juya mata bayan ko,kuma wallahi aure sai anyi shi ,kuma karki sake ki koma min gida ,na tsaneki da zama dake ,fitinanniya babu abinda auranki ya tsinanamin face asara"Abba Bukar yayi maganar cikin zafin zuciya " Saina koma ,koda saki na zakayi saina zauna nayi zaman 'ya'yana" Cewar Hajiya Jamila tayi maganar tana kokarin tashi tsaye "Abba Bukar yace " Bismillah ki koma wallahi da sai kin yi danasanin da tunda uwarki ta kawoki duniya baki taba yi ba" Rufaida Hajiya Jamila ta nuna da Harira ke bata ruwa tace "Kan wannan,Yarinyar da ko acikin dabbobi tafi su iya dabbaci saboda 'yar mungada ce, ka wulakantani gaban jama'a ko,bismillah Ku daura auran wallahi saikunyi danasani fiye da tunaninku" tayi maganar tana dukawa ta dauki makullin motarta ta soma tafiya "Duk barazanarki ba zata hanani aurawa Wahid Rufaida koda ace vayasonta idan harni inasan ya aureta sai ya aureta,saboda bake kadai keda iko da 'danba" cewar Abba Bukar Kofa Hajiya Jamila tayi ta fice Sai bayan ta fita Abba Bukar ya jiyo ya bawa Gwaggo hakuri shima ya fice yana sanar dasu zai dawo gidan idan ya tashi daga gurin aiki Makwabtanma hakuri suka bawa su Gwaggo suka firfito suna jinjina lamarin masu tsinewa Hajiya Jamila nayi masu zaginta nayi,da kwashe mata albarka,dama mutane jiran suke ayi,dan danki zai auri 'yar uwarsa saitazo tana hauka maiye laifin Rufaidan yarinya mai hankali.*JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil❤️ 40. Hajiya Jamila da tunda ta fito gidan Gwaggo take kuka a cikin motarta bawai kukan danasani ba akan abinda tayi kokarin aikatawa da kuma furucin mijinta akanta ba illa tunaninta 'daya ina zata da wannan abin.kunyar ace dan ta zaiyi aure bata sani ba sai ana saura kwana uku kuma aure ma ya rasa wadda zai jajubo sai 'yar Hauwa'u da kowa yasan kiyayyar da take ma Hauwa'un,ganin tunanin ba shine mafita ba yasata yiwa motarta key tayi gidan Gwaggo Lariya Abba Bukar yana fitowa gidan yatarar da kurar motarta kai ya girgiza ya shiga motarsa da tunanin abinda ya yanke aransa kai tsaye gidan wan mahaifinsa ya wuce Baba Ashiru,Abinda ya faru kaf ya fadamasa da kuma hukuncin da ya yanke a daura auren Wahid da Rufaida saboda baiga alamun Hajiya Jamila zata hakura ayi auren ba Baba Ashiru dubesa "Gaskiya Bukar kayi tunani me kyau,abinda ya kamata ayi kenan,tunda ita Jamila har yau bazata yi hankali ba kamar wadda ake zugawa" "Wallahi Baba babu wata zuga danni sai yanzu nake danasanin aurenta ma.... Baba Ashiru yayi saurin dakatar da Abba Bukar maganar da yake yace "Kul Bukar koba komai ai uwar 'ya'yankace ba kuda wata makankara sai dai muyita yi mata addu'a" Abba Bukar ya mike ya na cewa "Haka ne Baba ni bari zan koma wajen aiki dan Allah ka kira Baba Amadu kasanar masa dan Gwaggo da mukai waya tace gaban kaina na fara yanzu tun busu mutu ba" Baba Ashiru yace "Ina ruwan Zainabu ,to zan sanar masa da dukkan abinda ya faru zan fadamasa hukuncin da ka yanke amma bazan ce kai yanke hukuncin ba karmu sake yin laifi" Abba Bukar ya fito daga dakin Baba Ashirun yana dariya ******* Gwaggo ce tayi kokarin karaso wa inda Rufaida take ganin kowa ya watse daga gidan da ga Rufaida sai Harira da Gwaggon dafata tayi ta soma maganar ba tare da ta damu da Harira dake gurin ba dan abu ne akayi sa ba a boye ba "Haba Rufaida kukan ya isa haka kinemi sakayya gurin Allah kawai" Rufaida ta dan goge hawayenta ta dubi Gwaggo tace "Gwaggo nidai dan Allah a fasa auren nan" Gwaggo ta zaro ido tace "Baki da hankali Rufaida auren za'a fasa saboda wannan shashashar yarinyar tazo tayi haukanta,kenan a fasa taci galaba akanmu,to koda Wahid baya sanki sai anyi auren nan dan akuntata mata" Kuka ta kuma rushewa da shi tare da cewa "Ni dai dan Allah Gwaggo a fasa ,kina gani fa kashe ni Umma taso yi,ga maganganun da take fada akan Umminmu,Gwaggo dan Allah mai muka yi mata" "Kinga bafa za'a fasa ba, ita bata isa ta kashe ki ba haukan banza take,maganganu kuma taje tayi tayi ita ce mara aikin yi,kuma sharrin ta saidai ya bita" Da haka dai Gwaggo ta lalla'beta ta daina kukan suka koma inda suke aikinsu suka cigaba dayi *** Sallamarsu Ummi Hauwa'u ta katse firarrakin da suke jefi jefi suna aiyukansu da gudu Rufaida ta karasa gunsu ta rungume Aunty Samina dukda ba wani kuzari jikinta Gwaggo da Harira suka amsa musu sallamar Ciki suka karaso da fara'arsu suka zauna a babbar tabarmar da aka shinfida Saida suka gaggaisa ,Aunty Samira ta dubi Rufaida tace "Yanaga ba kuzari jikinki kamar kinyi kuka ga idonki duk ya kumbura" Gwaggo tayi saurin cewa "A'a ba wani kuka sauro ne ya ciccijeta jiya bata sa net ba" Aunty samira shiru tayi vadan ta yarda ba Rufaida ta ja hannun su Kalim da Khalil yaransu Aunty Samina dakinsu dan surutun ma batasan shi ko daya Ummi Hauwa'u ta bita da kallo aranta tana tunanin tabbas da abinda ke damun Rufaida zuwa dare zata sameta suyi magana Su Rumaisa ne suke shishshigo da kayan da suka taho dasu da sauran yaran Abdul kuwa da shiya kawosu baima shigo gidanba ya tafi gidan Gwaggo Hajiya gurin abokansa A'a marhavin lale da kanawa,Malam yake maganar da murmushi fuskarsa da shigowarsa gidan kenan ya cikaro dasu Aunty Samina suna aikin doghnut bayan sun huta sunci abinci Da murmushi a kan fuskarsu suka gaishesa ya amsa yana cewa ina su Gwaggon suka ce masa suna daki Dakin ya nufa ya tarar dasu a zazzaune suna nunawa Gwaggo kayayyankin da sukai wa Rufaida Gaishe da Malam sukayi ya amsa yana musu sannu da zuwa Zuwa can ya nisa yace "Yau ne daurin auren fa yanzu Ashiru yake sanarmin ina kokarin shigowa nan gidan ya kirani a waya,shine nazo nasanar muku zance na shirya yanzu ,bayan daura auren zasu kawo lefe" da haka ya mike ya bar dakin dan baya san jin wani zancen su yanzu haka "Wannan wanne irin aure ne Gwaggo daga zuwan mu yau ace yanzu za'a daura"Momy Maryam tayi maganar bayan Malam ya fice daga dakin Gwaggo da ranta ya fara baci ita ma "To ya za'ayi Maryam yadda suka tsara haka za'ayi" "A'a Gwaggo kuma fa kuna da hakkin magana akan 'yar nan ai ba 'yarsu bace su ka'dai,ya daga zuwanmu za'ace yau daurin aure gaskiya babu alamun gaskiya a auren nan" Momy maryam tayi maganar "A'a maryam kar kice haka,mudai yi musu fatan zaman lafiya" Cewar Gwaggo Ummi Hauwa'u bata ce komai ba tana zaune tana saurarensu har suka gama firarsu ******* "Rufaida Dan Allah karki nunama yayyenki ko a fuska akwai abinda ya faru dazu"Harira tayi maganar tana dafa Rufaida da suke daki zaune itada harirar tun da su Aunty Samina suka karbi aikin " Harira ke ma kinsan halina a 'dan zaman da mukai kinsan bazan iya fada ba,abinda kuma Umma tayimin lokaci ne watarana sai labari" Cewar Rufaida "Harira ta nisa tace " nifa matarnan ta bani mamaki kai kace mahaukaciya ce ,kikama 'yar mutane ki shage,shegiyar mata kodaddar banza ita banda farin tama wazai kwasheta mai bakin hali,ai wallahi dan sunga kece shiyasa zasu hadaki aure dashi da wata fitsararriyar suka samu ai bazata yarda ba a rabani da dan arziki a hadani da irin tsiya.... "Kai kai Harira wannan surutu haka kinata kwashe mata zunubi kina dorawa kanki ta hanyar zaginta" "Ai matar ce na lura da cewa cikin dabbobi Kafin asamu irinta za'a yara" Rufaida tayi dariya jin maganar Harira Aunty Samira da take tsaye bakin kofar dakin dasu Rufaida ke ciki azo kiran Harira ta tayasu aikin da suke tayi niyyar shigowa taji suna wannan maganar bata shiga ba ta dawo inda suke aikin tana jinjina lamarin aranta ashe shiyasa suka ga alamun damuwa a gidan da suka zo har Rufaida bata wani nuna murnar zuwansu ba,lallai akwai matsala a wannan auren amma yaza suyi itada ko kusa bataso auren nan Rufaida ba koda ma ba wata matsala dan tana son Rufaida kamar Samiha. Aunty Samina ta kalli Samira tace Yadai Samira maike damunki "Kedai bari kawai Yaya ashe 'dazu surikar Rufaida ce tazo tayi wa Rufaida duka ta shake wuyanta ta kusa kasheta" Maganar suka cigaba da tattaunawa saida Harira ta karaso wajen sukayi shiru ***** Sallamar Abba Bukar a falo yasa kowaccensu amsa masa da kokarin yi masa Sannu da zuwa ya amsawa matan nasa da ko wacce da maganar dake bakinta ga mijin nata ganin vaidawo yadda ya saba dawowa ba dan har hudu ta gota yanzun daya shigo,maganarsa ya dawo dashi daga tunaninsu "Yadai kowacce tayimin kasake kamar nayi tafiyar shekara ba wadda ta iya koda mikewa ta kawon ruwa" yayi maganar da murmushi kan fuskarsa Hajiya Kubra tayi hanzarin cewa "Abban Wahid ka manta yauba girkin daya daga cikinmu na Maman Wahid ne kuma tunda ta fita har yau bata dawo ba" "Kinga Ku share zancen ta" Abinda ya faru ya sanar musu,ya kuma sanar dasu an daura auren Wahid da Rufaida da azahar a babban masallacin Zariya, kowacce ta jinjina lamarin, Ya sake cewa "Har yau babu mai kawan abincin da ruwan" Hajiya Kubra ce ta mike ta kawo masa abincin da ruwan kadan yaci ya aje yakallesu yace "Kayan lefe suna gidan ,Baba Ashiru kuje ku dauka akai musu,nayi wa Wahid magana asabar zaizo ya dauki matarsa kayan dakin kuma acan za'a siya ayi komai" "To Allah ya sanya Alkhairi", suka fada badan sukansu sunji dadin wannan auren ba,da wadannan tunanukan suka shiga ciki su kara shiryawa busu jimaba suka fito suka yi ma Abba bukar sallama da har lokacin yana falo yana yiwa Ubaidullah wasa da shi baya bukatar a kara shiryasa Aunty Amarya ta daukesa suka fita a motar Hajiya Kubra suka fita taja su zuwa gidan Baba Ashiru Kaya kam sunyi kyau da tsari kala arba'in ne akwati 6 su Momy Maryam busu kushe kayan ba sai dai auren ne basa so ko daya da su Aunty Samina suka fada musu abinda ya faru da Aunty Samira taji su Rufaida suna tattauna maganar da Harira, sun bawa masu kawo kayan tukwici mai yawa daganan masu kawo kayan suka tafi da tarin kayan soye soyen da aka hada su dashi da lemuka da Abdul ya siyo musu aka basu.*JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil 41. yanzu Gwaggo Lariya inaji ina gani 'dana ya zai auri irin tsiya" Hajiya Jamila tayi maganar bayan cire hannunta daga abincin da Gwaggo Lariya ta kawo mata. Gwaggo Lariya ta kalleta tare da cewa "Eh to muddin ki ka zauna ba,amma da zaki tashi ki rabawa malamai kudi sai kiga aiki,tunda dai bakyason auren" Hajiya Jamila tayi murmushi tare da cewa "Lariya ke nan kina tunanin kan auran nan nawa ne ban kashe ba,da naji shiru na dauka asirin nawa ya fara aiki amma ashe lamfa lamfa aka yi min" "Gaskiya kuwa dan nima abin ya bani mamaki danaji kai kayan shiyasa na fara shakku akan saninki dan nasan vazaki yarda ba,dan koni ma vazan yarda inaji ina gani surajo ya auri Rufaida ba bare kuma ke" Gwaggo Lariya tayi maganar dan ta sake tunzura Hajiya Jamila Hajiya Jamila tace "Wallahi kuwa Lariya munafuntata sukayi,yanzu nama rasa mafita dan a dazu so nai nakashe banza" Gwaggo Lariya ta jinjina kai daga bisa ni tace "Yanzu dai tunda har yau ba'a daura auran ba yanzu zan hadaki da wata aminiyata tana da shige shigen malamai,nima tana yi min tayin naje nace mata bani da kudin biyen malamai" Hajiya Jamila cikin murna da doki tace "Yaushe zamu je gidan nata,kinga gobe zan tafi Nasarawa da sassafe" Gwaggo Lariya ta nisa tace "Ki bari anjima baban Surajo idan ya dawo saina tanbayesa muje gidan nata" Da haka suka cigaba da fira kafin wayar Gwaggo Lariya tayi kara wayar dake gefenta tasa hannu ta 'dauka ganin mai kiran nata Gwaggo Hajiya yayarta yasata saurin 'dagawa da sallamarta Gwaggo Hajiyar ta amsa saida suka gaisa Gwaggo Hajiyar take cewa" "Ki kira mijinki ki fa'da masa zaki gidan Yaya Ashiru,anjima zamu hadu gurin daurin auren nan Rufaida da Wahid,kuma za'a kai lefe Gwaggo Lariya tayi saurin cewa " Yaya Hajiya ina ce sai wani satin aka ce" "Eh da hakane amma matar Bukar 'dazu tazo 'dazu tayi wa mutane Hauka a gidan Yaya Zainabu,ta kusa kashe 'yar mutane aini bansan munafunki da ya kai mata zancen ba" Gwaggo Lariya ta shiga zaro ido jin zancen Gwaggo Hajiyar harda kiranta munafuka to da tasan itace ta fadi hakan fiye da munafuka fadamata Gwaggo Hajiyar zata yi,da haka dai sukayi sallama da cewar sai tazo Daidaita nutsuwarta tayi bayan katse wayar dan kada Hajiya Jamila ta fahimta da take can daddana wayarta jin Gwaggo Lariya ta gama wayar yasa Hajiya Jamila dago kanta ta kalleta da cewa "Naji kamar unguwa zaki fita" Gwaggo Lariya da sauri tace "Eh wallahi zanje gidan Yaya Hajiya,zamu tafi wata unguwa,amma ba zamu Dade ba zamu dawo yanzu yaro zanyi kira yaje wajen aikin su Baban Surajo ya fada masa",dan tasan muddin ta kuskura bata jeba zarginta za'ayi harda hadin bakinta Hajiya Jamila ta san zancen tunda itama kiri kiri take nuna kiyayyar su Rufaidan,da haka ta mike ta fita daga dakin zuwa wani ba jimawa ta fito kasancewar batada karamin da yanzu haka cikin adonta na kure adaka ta fito ta dawo dakin da tabar Hajiya Jamila data sameta tana waya wayarta ta dauka tana cewa Hajiya Jamila saita dawo ta fice Hajiya Jamila data bita da kallo a ranta tana ayyana tabbas babban abu ake tunda taga Gwaggo Lariya ta caba wannan adon baki ta tabe ta cigaba da wayar da take saida ta gama ta lalubi lambar AbdulWahid amma a kasheta ta sameta dan haka yasa ta hakura da kiran dan tuntuni take kira suna sanarmata akashe wayar take. ****** ABDULWAHID Da farin cikinsa ya kasa boyuwa da albishirin da mahaifinsa ya tare sa dashi dan tun yana Abujar yaso sanar masa to sai ga matsalar Network baya samunsa a waya koda ya daga wayar ta katse ga wadannan kwanakin aiyuka sunsha kan AbdulWahid din kwana biyu Saida aka shiryawa Rufaida gidanta sosai da kayanta masu tsada da Abba Bukar duk shi yayi komai sannan AbdulWahid ya dauki matarsa Rufaida suka tafi tare da wasu daga cikin "yan uwan Rufaidan su Aunty Samina da har kwanakin suna Zaria da zasu ganin gidan Rufaidan Ummi Hauwa'u da ba yadda ta iya ta hakura da irin auren da aka yi wa 'yarta da Gwaggo ta dinga yi mata ban baki kafin ta hakura ***** Gwaggo lariya ta maida dubenta ga Hajiya Jamila " Jamila kiyi hakuri an riga da an 'daura auren,Rufaida da Wahid sai dai mu sauya shiri,fitar da nayi 'dazu najiyo labari gurin Yaya Hajiya" Wani kallo Hajiya Jamila ta yiwa lariya kafin tace "Lariya wannan wanne irin magana kike min ta rainin hankali aure kuma aka daura kuma kicemin baki sani ba aiko a garin mahauta muke bazan yadda ba kikasan maganar kai lefe bare ta aure, ai a dazu na fahimci fitar tafiya kai lefe kikayi ashe ni zaki munafunta nufinki ban fahimci wayar da kikai bane"Hajiya Jamila ba tare da ta jira abinda Gwaggo Lariya ke fada ba ta zari hijabinta da makullanta ta fice tana kokarin ficewa daga gidan gaba daya da har zaure Gwaggo Lariya ta karaso tana bawa Hajiya Jamila baki amma taki koda sauraronta motarta da take kofar gidan ta shiga ta yiwa key tabar gidan ta nufi gidan wata aminiyarta da zata yi kwana daya a gidan daganan ta nufi gidansu nasarawa a ranta tana jinjina halin dangin miji " Yanzu Yaya inaji ina gani 'dana ya auri wannan yarinyar ba yadda na isa nayi,kina gani ko waya raban da AbdulWahid ya kira ni yau ake kwanan sati don karna masa maganar Auren nan,ga uwa uba ubansa ya koreni daga gidansa" Cewar Hajiya Jamila da take zaune a babban falon gidan shema'u take wannan maganar Murmushi Aunty Shema'un tayi kana ta dubi Hajiya Jamila ta soma magana "Ki kwantar da hankalinki Jamila ai idan sunsan wata basu san wata ba,dama nagama yanke shawarar ku tafi Abujar yau keda Rukayya ku zauna acan tunda shi Bukar baida mutunci idan yaji kina can zaice ki koma dakinki dan ba saurara mata zaki ba idan kuka je,tunda gashi Bukar din ya zuga gaba 'daya 'ya'yanki bama Wahid ba tunda kika zo nan waye cikinsu ya kira ki sai munafukan kishiyoyinki da ba kaunar zamanki suke a gidan ba bayan duk arzikin Bukar din dake akasha wahala gurin samu su da suka zo zuwan daga baya" Murmushin jin dadin wannan shawarar da 'yar uwarta ta Hajiya Jamila ta mike tana cewa "Ai Yaya yau ba sai gobe ba zamu tafi" da haka ta shige ciki tana murmushi **** ABDULRA'UF " Ra'uf anya kana da cikakken hankali kuwa"Ra'uf yayi saurin dago kansa daga kwanciyar da yayi saman kujerun falonsu jin maganar da Ammi tayi masa ya soma magana da cewa "Ammi maina aikata kuma?" "Kafi kowa sanin koma maikayi ace daga wannan lamarin yanzu ka daina hatta da zuwa aiki baka yi kadaina walwala bayan Ahmad ya sanarma ita hartayi aurenta ta manta dakai amma kai tana makale a ranka ,tunda muka dawo baka leqa gurin aiki ba" Mikewa yayi daga kwanciyar da yayi ya maida kallonsa ga Ammin nasu yace "Ammi sam yadda kike tunani ba haka bane,wannan maganar ba ita bace ta hanani zuwa aiki ba,kinsan hali na daban manta da itaba bazan hakura ta auri wani ba,kawai dai nasan inajinta a cikin jinin jikina har yanzu" Ammi ta dan tabe baki kana tace "Ai saikai tayi, Shureim ya kirani a waya na lallabeka ka koma gurin aiki dai" Murmushi yayi yace "Ammi kenan,eh gobe dama zan koma,dama hutun dana daukane bai kareba" Murmushi tayi jin abinda Ra'uf ya anbata ta maida duk natsuwarta garesa tare da soma magana " mai zai hana kaje kanemi Auren Inteesar Khan Dawud abokiyar karatun Sophie ina lura da yadda take nuna ma soyayya tun tuni,kaje gurinta a tsaida magana nasan su ba zasu yi mana haka ba" Ido ya zaro Ra'uf tare da jin wata faduwar gaba lokaci guda taziyarcesa ,inteesar din zai nemi aurenta yarinyar da abokinsa Shureim yake fadamasa irin son da yake mata yadai kasa furta mata ne "Ya kayi shiru Ra'uf ko ba kai maraba da shawarata ba"Ammi tayi maganar tana kokarin katse shirun Ra'uf kallon Ammi yayi yace " Ammi shureim ne ke san Inteesar yanzu koda zanje gurinta saidai naje saboda na shigar da soyayyarta gareta" Tsaki Ammin tayi jin gaba daya dan nata har yau hankalinsa baya ga duk zancen da zata yi masa ya karkata ne kawai ga Rufaida,banda haka ina zaice Shureim yana san Inteesar mikewa tayi ta bashi guri rai a bace Da kallo Ra'uf ya bita dukda baya san bacin ran mahaifiyarsa amma dai gaskiya bazai amince da shawarar taba na ya auri Inteesar yarinyar da abokinsa ke so dukda ita bata sani ba amma shi ai ya sani idan yayi masa hakan bai kyauta ba ko 'daya, ga uwa uba shifa a tsarinsa bazai iya auren macen da ba 'yar kasarsa ba. "Ya ko aminci da maganar da kikaje masa da ita"Dady ya tari Ammi da wannan maganar da take kokarin karasa zama gefen gado Da dady yake zaune akai shima " ai dama na fadama bazai amince ba,kaima kasan halin yaron nan da gaddama,tunda ya nuna waccen yarinyar yakeso kuma bai same ta ba zai wuya a yanzu ya amince da wata macen"Ammi ta karasa maganar da alamun bacin rai a fuskarta Dady ya girgiza kai tare da cewa "Wallahi Asma'u ina san farin cikin yaron nan,sai dai a karo na farko nima ba zan amince ya auri yarinyar nan ba,ko ni kaina bama ga Yaya Sule da Yaya Abdu kadai ba suka hana auren ba harda ni kaina mutanan da sukai kokarin lalata mana suna sukai silar rabamu da farin cikinmu rabuwar da sai dai mu kira ta da ta har abada" daga nan Dady Jabir ya fashe da kuka kai kace karamin yaro ne" Ammi ganin mijinta na kuka yasa hankalinta ya tashi da cewa "Haba Abban Safiyya me yayi zafi haka kai ba karamin Yaro ba bakomai ba,addua zaku cigaba dayi tuno da abinda ya wuce ba shine mafita ba" Da wannan kalaman ta cigaba da lallashinsa har ya hakura ***** Yaya yayaa Safiyya take kwalawa Ra'uf kira da baccin ya fara daukarsa Ra'uf da yaji maganar Safiyya kamar a mafarki ya vu'de idanunsa ya mike zaune ya dora idanunsa akanta ya dan harareta da cewa "Sophie Khan ya akai ne,kike kokarin fasamin dodon kunne" Zama tayi kusa dashi tare da cewa "Yaya yanzu Intee ta kira ni sunje Us ita da yayanta ankafe suna taga sunanmu nida Husna" Murmushin Ra'uf yayi tare da cewa "Kai amma ina miki murna sister,kin fadawa Husnan?" Safiyya tayi saurin cewa"A'a Yaya,zuwa nayi ka kira ta a wayarka a fada mata" Ra'uf yace "Ke ina kudin wayar taki?" Safiyya tayi saurin cewa "Yaya ai ba kudi a wayata kamanta ne" Hararar wasa yayiwa Safiyya da cewa "Dady jiya ya sa miki kudi ina kika kaisu" Marairaicewa Safiyya tayi "Na kira kawaye na tun jiyan" Tsaki Ra'uf yayi ya mikamata wayar dan sarai ya gano kudin nata ne batasan kashewa na cikin wayar. Lambar Husna ta kamo ta kira ta shaida mata samun makarantar da sukayi ba karamin murna Husna tayi ba ita ma,daga nan suka cigaba da firarsu saida Ra'uf ya gaji da surutun da Safiyya ke masa a kunne ya anshe wayarsa ya kashe Sadiya Khalil🖤*JININM U 'DAYA* By Sadiya Khalil❤️ 42. Ina yiwa masoya wannan littafin fatan alkhairi a kowanne lokaci ina kuma anfani da wannan damar gurin yiwa 'yar uwata Aisha Umar Ibrahim fatan alkhairi na gama littafinta mai suna ZAN JIRATA lafiya Allah ya hadamu da alkhairan cikin littafin ya kawar damu da akasinsa ya shiryar damu bisa tafarkin tsira ya bamu ikon rubuta abinda zai anfanardamu ko bayan bama raye.Amin 42. ABDULWAHID Cikin kwarewa yake aikinsa da kwanciyar hankali auren Rufaida,bakaramin farin ciki yake da shi ba,tana nuna kulawarta gare sa,aikin da yake ya ajiye gefe,ya dauki wayarsa da take ringing wanda tunaninsa Rufaida ce,ganin tunda ya tafi aiki busu yi waya ba yadda suka saba,sai tunaninsa ya basa ko itace da taga bai kira ta ba ko ta kirasa,duba screen din wayarsa da yayi ya kaudar masa da tunanin sa ganin sunan da yasa wa Ummansu akan screen din itace mai kiran nasa wata irin faduwar gaba yaji ta ziyarce shi tunda yaga kiran Ummansa yasan sai ta yi masa fada sosai don yasa koda bakin aurensa a ranta sai ta masa don rab. an da ya kira ta yau kwana 7,a bakin Abbansu yaji duk abinda ya faru ganin tana kokarin katsewa yasa shi saurin dagawa "Assalamu Alaikum,Umma ina yini,ya su Aunty" Yayi maganar a jere a kuma tsoro ce "Kazo ka shiga damu barrack din ku munzo yanzu nida Ruqayya"ba tare da ta vashi waccen amsar ba ta tare sa da wannan maganar da haka ta katse wayarta AbdulWahid da baida wani zabi da ya wuce yaje tararsu da haka ya mike daga office dinsa ya fito ya fito yaje tarar mahaifiyar tasa ba tare da ya tuna da kiran Rufaida a waya ba ya Shiga motarsa ya fito daga headquarter dinsu RUFAIDA Jin bugun kofar falon nata yasa ta mikewa daga kwanciyar da ta tayi a kujera da barci ya fara daukarta jin an cigaba da bugawa yasa ta mikewa ganin waye cikin tsakar ranar nan yazo gidanta sai da ta leka kofar ganin mijinta tsaye jikin kofar ya sata kokarin bude kofar da murmushi akan fuskarta,ido biyu tayi dasu Hajiya Jamila da suke bayansa da hanzari tayi kokarin basu guri tana cewa " Sannunku da zuwa Umma" Wani banzan kallo suka jefeta da shi,suka karasa shigowa falon wanda da ido suke bin ko ina na kusurwar falon da suke kokarin ganin makusar falon nata Da wani murmushin ta sake cewa "Sannunku da zuwa Umma ku zauna mana kunsha hanya bari na kawo muku ruwa" daga nan ta shige ciki Basu ce da ita komai ba ganin ta wuce yasa suka bita da wani banzan kallo daganan suka zauna a kujerun falon suna ya mutsa baki dukda kayatuwar falon kuwa AbdulWahid katon akwatunsu ya shigo musu da shi da shima ya najin sannu da zuwan da ta musu basu amsa ba,har karo biyu sharewa yayi ya shige da akwatun nasu ciki dan yana ganin akwatun ya fahimci bada tafiya suka zoba da zama suka zo kofar wani corridor na gefen wani daki ya aje kayan ya shige cikin kitchen din da yake tsammanin Rufaidan na ciki jikin kofar kitchen din yayi tsaye yaki karasa shiga ciki da murmushi kan fuskarsa yake kallonta tana kokarin jera lemuka da ruwa akan faranti mai girma ta juyo zata fito idanunta ya sauka cikin nasa murmushi tayi masa inda take ya karaso ya mika mata hannu ganin haka yasa ta gane manufarsa mika masa plat din tayi ya amsa ya rike dubensa tayi kana ta soma magana "Haba Yaya yanzu su Umma zasu zo koka sanarmin gashi sunsha hanya,kuma nasan suna jin yunwa yanzu fa sai sun jira na dora" Murmushi yayi jin kalamanta gaba daya baza kace bata murna da zuwansu ba dukda kuwa yasan hakan ne don koshi da Umma take mahaifiyarsa Rukayya kuma take matsayin kanwarsa baya murna da zuwansu bare kuma ita dan yasan babu alkhairi a zuwan nasu tunanin da yake ya aje gefe kafin yace "Kanwata sai yanzu suka sanarmin da zuwan nasu tuba nake" ya karasa maganar da murmushi "Hm" kawai tace tana kara mika hannu ta amsa tray din "A'a ki kyale zan kai musu ki dauke musu kayan nasu ki kai musu inda kikaga ya kamata su sauka suna corridor" daga nan suka fito daga kitchen din tare Da sallama ya dawo falon da sallamar ta katse musu firar da suke ganinsa dauke da tray da yake kokarin aje musu akan centre table yasa Hajiya Jamila saurin kallonsa tare da kokarin cewa "Wahid me zan gani haka,kaine dan aikin gidan kardai daga auren harka zama mijin tace" Kai ya sosa da kokarin cewa "A'a Umma wanne irin mijin tace taimaka mata nayi fa" "Taimako a haka ake taimakon,dalilin gujema auren nan da nayi kenan,haka kurum kaje ka kwaso irin karuwai,ba dole su mallake ka ba,gashi harsun rabani da kai,ko waya yaushe rabon da ka kira ni" cewar Hajiya Jamila Rukayya tayi saurin cewa "Wallahi kuwa Umma" Hararar Rukayya yayi yace "Ke kuma dake ake magana ya kalli mahaifiyartasa yace mata, "amma ni Umma wannan va mallakewa bace,kowa yasan akwai taimako tsakanin mata da miji sannan,vatun kalmar karuwanci da kike jifansu dashi ,ina jin tsoron mahaifiyata ranar lahira ta tsaya gaban ubangiji ace tazo da wannan shaidar,biki gani ba ba ayi a gabanki ba,to me zaki cewa ubangiji a wannan,sannan ni Umma wallahi ba ruwan Rufaida da kin wayata dake dangataka da ita daban da taki ma haka,ba ruwanta da mahaifiyata,idan ba itama biyayya zata yi miki ba" Hajiya Jamila cikin fusata ta dubesa tare da cewa "To ubana jeramin magana,don ance matarka tana kokarin mallekeka zaka rika jeramin magana" ganin yadda mahaifiyata sa ta fusa ta daga 'yar maganar sa yasa shi sassauta murya gurin cewa "Umma kiyi hakuri" sai a sannan ya gaishe da Umman tasa,kamar ba zata amsa ba tadai daure ta amsa,Rukayya da dakyar ta iya gaishesa don bakara min haushin abinda yayi mata lokacin ta ji ba amsa mata yayi ya mike yabar falon yana kokarin shiga ciki kiran Rufaida jin har lokacin bata fito ba wanda ta tsaya sake gyara dakin da su Umman zasu sauka ne a hanya yaci karo da Rufaidan zata fito falon bayan gamawarta murmushi ya sakar mata don baya so ta fahimci wani abun ita ma murmushin itama tayi don bata so ya fahimci taji duk maganar da sukeyi a kokarin ta na dawowa falon da tayi jin suna magana ya sata kasa karasawa kuma takasa barin gurin kuma maganarma duk dai akanta maganarsa ta katse tunaninta "Dama nazo na sanar miki zan koma vakin aiki,ki fito kuyi fira karki varsu su kadai,sai ma naganki zaki fito din" Ba tare da tace komai ba suka rankayo falon tare Rufaida da suna isowa ta durqusa har kasa tana gaishesu da sake musu sannu da zuwa harda Rukayya ta gaisar da Rufaida bata tunanin Ruqayyan zata iya gaida ita kamar ba zasu amsa ba Hajiya Jamila ta daure tace mata "Lafiya" Daganan ta mike ta nufi Centre table din ta tsiyaya kowacce ruwa da lemo tace musu "Ga ruwa kafin a dora abinci" babu wadda tace mata koda to a cikinsu ita ma batayi tunanin hakan ba daganan ta mike ta basu guri,AbdulWahid dake tsaye jikin TV yana kokarin canza tasha yana jin duk abinda yake faruwa bai sake saurararsu ba yayi hanyar barin falon Yana kallonsu dukansu har Rufaida da ta yiwa kanta matsugunni a wata daga cikin kujerun falon yace musu "Zan koma bakin aiki saina dawo" "Adawo lafiya" Hajiya Jamila ta iya furtawa,Ruqayya ko kallonsa bata yi ba bare tayi masa addu'a Rufaida ta biyo bayansa yi masa rakiya da su Hajiya Jamila suka biyota da wata muguwar harara,musamman Ruqayya dan gani take da tuni ita ce a cikin daularnan fa wannan yarinyar tayi mata shigar sauri a zuciyar AbdulWahid dalilin da yasa take jin wani matsanancin kishi akan Rufaida, har jikin motarsa ta rakasa Wahid da yake kokarin shiga motarsa ya juyo yana Kallonta cikin nuna tausayawa zamansu da mahaifiyar tasa tun kafin aje ko ina yace "My wife kiyi hakuri nasan kemai hakuri ce anma ki cigava dayi karki gaji nasan kinsan halin UMMA bana tunanin zaki sha wuyar zama da ita,dama kafin sanin halin mutum shine wahalar kafin nan dai da Abba ya sauko ta koma dakinta" Murmushi tayi masa ta kallesa "Haba Yaya ai mamarka kamar Ammi ce koda ba muda alaka ni dakai" Ya tari zancenta da cewa "Eh dukda hakan,kinsan zama da uwar wani sai hakuri musamman Umma" "Haba Yaya karka ce haka uwa uwa ce mu cigava da yi mata addu'a Allah ya ganar da ita Rufaida take fadin haka " Hakane my wife,bari na koma aikin,sai na dawo"yayi maganar yana yi mata kallo mai cike da soyayya Kai ta sunkuyar kasa ganin kallon da yake mata Murmushi yayi yace "Badai kunya na baki ba dan na kalli mata ta kallon soyayya,wallahi Rufaida ina sanki kinada halayya mai kyau,da yake karamin sanki koda yaushe,gaki kyakkyawa" yayi maganar yana dariya ya shige mota yana kokarin tayarwa yace "Ya ba kice komai ba" Ta kallesa race " to Yaya mai zance?" Yace mata "kice wani abu nake so" Tace "To ka kulamin da kanka banda kula 'yammata" Ya dan harareta yace "Idan na kifa" "Hmm"kawai tace Yace " kinga uwar kishi ni bani da lokacin kula mace,amma ga babbar wadda zaki kishi da ita nan tazo har gidanki Ruqayya,kibi a hankali dama inason fada miki" "To Yaya insha Allah,ka koma naga lokaci na kurewa"tace masa " to My Special na tafi Yana kokarin tada motarsa tayi kokarin yi masa addu'a "Adawo lafiya Allah ya tsare minkai" Amin ya fadi hakan da murmushi yayi kokarin barin harabar part din nasu. Saida taga wucewarsa tabar wajen ta koma ciki tana murmushi tana san mijinta saboda halayyarsa abar so ce ya iya nuna kulawarsa ga mace,dukda tasan tanasan Ra'uf amma yanzu ta manta dashi,dama addu'arta a kullum Zabin Allah sai gashi yayi mata zabi da Wahid ta kuma rungumi mijinta don dama uwarsa ta jiwa tsoro ba auransa ba amma tunda tanasan zama dashi dole tayi hakuri da mahaifiyarsa domin ance maso uwa taso danta haka ma maso da sai take ga taso uwarsa zaifi,dan da uwar bata haifesa ba ita da bata auresa ba Da sallama ta shiga falon da babu wacce ta amsa mata bata damu da hakan ba ta dubi centre table din yadda ta tsiyaya musu lemukan haka ta tarar dasu Murmushi tayi tace "Umma naga buku sha komai ba anan" "Haka karuwar uwarki ta koya miki bawa baki abinci kenan,amma ta ko yamiki mallake miji ko,to ni bazan jure haka ba saboda akwai banbanci tsakaninmu mu daku,gadon tsiya kawai" Hajiya Jamila tayi maganganun tana sake gyara zamanta Ruqayya shewa ta buga ta ya mutsa fuska tace "Kinga zo ki mikomin ruwan nina sha" Bata ko tankawa Ruqayyan ba ta shige ciki ta barsu,dan Ruqayya bata kai matsayin da zata sata aiki ba ta yi mata saitayi niyyar dukda durqusawa wada ba gajiya bane saboda a girme ta girmi Ruqayyan amma ita Rukayya da izgilanci tayi mata maganar kuma ita bataga laifin taba takawo musu ruwa ta tsiyaya musu,daukarce zata gagaresu,to ko ita 'yar aikice aikinta iya nan zai kare Ruqayyan da kallon mamaki tabi Rufaida don tana da yakinin Rufaida ta fara cin ganye ne. Girki Rufaida ta dora jallop din shinkafa da taji kayan lambu,da suke a fridge,sai kuma lemon abarba data hada,bata yi tsammanin Rukayya zata iya shigowa tayata ba yasa ita ma bata maida kai a hakan ba dan danan ta gama ta zubawa mijinta nasa daban da zai aiko a ansar masa yadda yake yi tun bayan aurensu daganan ta kawo musu nasu ta aje musu a dining ta karaso cikin falon ta sanar musu da ga abincinsu data samesu kowacce ta hakimce a kujera duk sun kwarkwanta suna kallo abinsu sanyin Ac na ratsasu "Umma ga abincinku can a dining kona kawo muku nan" ta furta babu wacce ta kalleta saima dogon tsaki da suka ja mata Ganin haka yasa ta barin inda suke ta ta shige dakinta tayi wanka ta shirya cikin atamfarta kalar lemon green da brown daganan tayi sallah falon dake dakinta ta dawo ta kunna TV ta fara kallo ta dauki wayarta ta kunna data suka fara chat da Nasiba Shehu Garba class mate din ta sosai suke chat suna labarin makaranta,bayan Nasiba ta gama cakakin bata fadamusu bikinta ba sai abakin Samiha suka ji can Nasiba tace "Ke ban baki labari ba Sir Nura ashe Saliha Nasir budurwarsa ce har ankai kudin nagani ina so" Emoji na mamaki Rufaida ta tura mata kafin tace "Ke wai da gaske kike kawata,Saliha dai dana sani" "Kwarai kuwa,Saliha Nasir mutuniya da suke dabi da Sir nura" "To Allah ya sanya Alkhairi,idan sa ranar bikin yayi dai dai da zuwana gida zanje bikin ai Saliha nida ita da amana" Rufaida ta rubuta ta tura mata Nasiba ta turo mata Voice note ta bude taji Nasibar nace wa "Kai da mun jidadi to Allah yasa,baki cemin ina Sir AbdulRahman ba" Voice note din ta mayar mata ita ma da cewa "Ya na ina badai har ansa ranar aurenku keda shi ba" Zuwa can Nasiba ta dawo mata da amsa "A'a ko 'daya,amma dai ansakamin rana a Adamawa zanyi aure, wata makwabciyarmu to dan Yayanta zan aura,da yazo gidanta muka hadu,shima anan Abujar yake aiki a central Bank" Rufaida ta sake tura mata da voice note din "Wow kice gidan kudi burinki ya cika" "Murmushi Nasiba ta turo mata na emoji ta kara yi mata voice "Rufaida kenan kudin da ba baka za" a rikayi kana yawo dasu ba,kedai kawai addu'ar samun miji nagari da kwanciyar hankali bayan auren,danta kudin miji ba kwanciyar hankali aina banza ne gwara ma ace talaka ka aura indai zai mutuntaka" Voice Rufaida ta sake tura mata "Haka ne kawata,Allah ya baku zaman lafiya ya tabbatar da Alkhairinsa" Ganin wayarta na kara alamun kira yana shigowa Wahid ne mai kiran tana kokarin dagawa ta katse " yasa tayi saurin cewa Nasiba zamuyi chat anjima" Nasiba ta rubuto mata "OK akwai labari dama inason fada miki" Da haka ta kashe data tana kokarin bin kiran wani wani ya sake shigowa "Assalamu Alaikum matata" Jin muryarsa ya sata murmushi "Wa'alaikumus salam mai gida ya aiki" "Alhamdulillah,yanzu kofur Bala ya tawo amsar abinci ki hado da Plat da yawa yau Kabir yace da abincin ki zaiyi launch,dafatan kingama aikin lafiya kuma baigaji dake ba" "Murmushi tayi jin maganar mijin nata "To sai yazo nagama komai" "Yawwa farin ciki na da fatan kin Zubawa su Umma tun dazu" Tayi saurin ce masa "Eh ya mijina" Yace ok take care bye ina aiki yanzu" Tace masa"agama lafiya take care to u my regard to Yaya Kabir Da ganan ta katse wayar ta mike ta nufi kitchen ta hada abincin a basket ta dawo falon inda tasa mesu nan ta barsu "Sannu da hutawa Umma" Rufaida tace tana zama kujerar dake gefen tasu ta aje basket din kusa da ita batayi tunanin zasu amsa musu ba ita ma ta share su jin alamar kararrawar kofar falon na motsi ya sata zura hijabin da ta fito dashi a hannu ta dauki basket din sukw gaisa da kofur bala ta mika masa basket din ta dawo ciki ta zauna inda ta tashi tanaji suna yi mata habaici amma bata saurare su ba ta cigaba da kallonta Ruqayya ce cikin tsawa ta fara magana tana kallon Rufaida "Ke yar masu samu tafi iyawa ina ne matsugunnunmu,ko bamu da shi" Rufaida ta kai muryarta kasa dan yanzu taga rashin kyautawar nuna musu masaukinsu amma dai bata ga fuska ba zata iya cewa tace "Kiyi hakuri Ruqayya na manta wallahi da kin shiga ciki kin wuce wani corridor to daki na farko shine naku" Tsaki Ruqayya taja ta mike ta shige ciki Rufaida ma mikewa tayi ta shige ciki,tanason tanbayar Umma ko sun ci abinci amma tana tsoron abinda zaije ya dawo" Bayan wata 8 Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da Rufaida da yanzu take da ciki Na Wata 6 , tsananin hakuri take duk a wannan lokacin da surikartata da kanwar mijinta zaman su da ita kullum dai cin mutunci ne gareta duk yadda take kyautata musu,dan har lokacin basu tafi ba,Ruqayya ce kawai taje gida yin jarabawar jamb tana gamawa kuma ta dawo shikansa Wahid yana kallon abinda akewa matar tasa sau tari sai dai bai isa yace wani abu ba,ba tun hidima iya yi yana yi musu dan albashin na watan da mahaifiyartasa suka zo yana dauka dinkunan sawa yayi wa mahaifiyar tasa dasu,Ruqayya ko duk yadda ta kai da shishshige masa baya koda saurararta don shi soyayya ba ta damesa ba koda ma auren nata zaiyi matar da ya aura ma da yake sonta baiyi soyayya da ita ba ta azo a gani saboda rashin lokaci bare kuma yayi da Ruqayya,Rukayya kuwa tana kara jin son Wahid har ranta ganin yana da halin mai kyau zaman da suke yanzu take kara fahimtarsa, shiyasa take kokarin shige masa ko zai sota dukda tanada samari amma halayyar Wahid tana burgeta musamman yanzu da take ganin zaman su da matar shi tana nuna kulawarsa ga matar tasa,sau tari tana mamakin hakurin Rufaida dan ko ta tarar suna fira da Wahid din da ita suna zaune bata koda saurararsu zata koma ciki abinta wanda gaskiya da ita ce baza ta iya ba,ita ko Rufaida rashin zabi shike sawa ta koma ciki don tanada kishi da idan ta zauna ba zata hakura da abinda zata ga Ruqayya zata riqa ce masa ba a gabanta alhalin bata ga anfanin maganar ba idan tace ba zata hakuran ba don namiji ba'a shaidarsa ko kusa,ba zata ce nata bazai so wata ba bayan ita idan tayi hakan ba ta yiwa kanta adalci ba,yanzu ga cikin jikinta shiyasa ma bata son zama a cikin su saboda karsuyi abinda zai jawo mata bacin rai. ABDULRA'UF Sai a page na gaba zamu waiwaya bangaransa Insha Allah. SadiyaKhalil. Dan Allah Ku rika yin share,wani groups din.*JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil❤️ 43 Wannan page naku ne Amina Muhammad baso Safiyya Galadanci Aisha Umar Ibrahim Nagode da gudunmawarku gareni bisa son cigabana kuyi yadda kuke so da shafin nan Allah ya bar zumunci🖤 ABDULRA'UF "Ra'uf meke damunka" Shureim yayi maganar da yake zaune a kujerar dake kallon ta Ra'uf a office din Ra'uf din Kansa ya dago ya kalli Shureim da murmushinsa yace "Mai ka gani?" Shureim ya girgiza kansa kawai yace "komai ma Ra'uf ,kana tunanin zaka shiga wata damuwa na kasa fahimta,nasan komai damuwarka ta soyayya ce,Ahmad ya fadamin komai,Ra'uf dan Allah ka cire damuwarka,tunda Ahmad ya sanarmin ita ta riga da tayi aurema yarinyar,ka cire ta a zuciyarka please ka samu wata ka aura ga kanwata nan Ruwaydah kaje ka nemi aurenta indai kana santa" Murmushi Ra'uf yayi ya maida dubensa kaco kam ga Shureim ya soma cewa "Shureim ba soyayyar Rufaida ce damuwa ta ba illah iyaka sanin dalilin hanani aurenta shine damuwata,amma ni aure a yanzu haka baya gaba na,sai dai bazan ki Ruwaydah ba amma ba tsari aure yanzu a tsarina sai nan gaba Tausayi Ra'uf ya bawa Shureim saboda shima yanajin zafin soyayya yanzu haka saboda yanasan Inteesar sosai saidai ya kasa furta mata saboda yana tsoron karta ki amincewa da soyayyarsa,ga soyayyarta da ke nuqurqusar zuciyarsa a kullum,dole ya tausayawa Ra'uf danshi sunyi soyayya ma suna da shirin aure aka rabasu ya dai daure ya kauda tunaninsa yace " Eh aboki na nasan da ciwo ravuwa da masoyi amma hakuri zakayi ka cigaba dayi kuma Allah yasa rabuwar tafi zama alkhairi sannan ka cigaba da addu'ar neman zabin Allah a rayuwarka" Ra'uf ya jidadin nasihar abokin nasa Shureim abokine nagari,shiyasa yake alfahari da abokin nasa da murmushi ya kalli Shureim yace "Nagode aboki na" "Haba babu komai aboki na damuwarka ta wace da zan iya fidda ma damuwarka da nayi wallahi amma zan cigaba da tayaka addu'a,tun sanda na fahimci baka da walwala a kwanakin nan kuma naji baka kara yimin maganar budurwarka ta kasarku ba,shine yasa nayi tunanin ko akwai abinda ya faru da soyayyarku shine yasa nakasa hakura har saida na tanbayi Ahmad ko yasan meke damunka ya fadamin shine yasanar dani komai,nasan zafin so Ra'uf nima kullum ina cikinsa zullumi na kar na fadawa Inteesar ta kasa amincewa dani" Shureim ya karasa maganar da rarraunar murya Dafa sa Ra'uf yayi yace "Haba abokina karka damu zata amince dakai yau zanje gidansu Inteesar na sanar mata da soyayyar da kake yi mata nasan zata amince" Shureim ya murmusa yace "Kai abokina ina godiya sosai" "Haba aboki na karka damu komai nayi ma kacancanta da ayi ma ne" Cewar Ra'uf Da haka suka sauya fira ta aiyukansu har zuwa wani lokaci Komai ya sauyawa Ra'uf soyayyar Rufaida koda yaushe ita ke nuqurqusar zuciyarsa sai dai ganin bazai sameta ba yasa shi maida lamuransa kacokam ga ayyukansa yasa kwazo fiye da nada akan aikin nasa,A yanzu haka sunsha hidimar bikin abokinsa Shureim da matarsa Inteesar,da Ra'uf din ne silar auren shi ya shigar da Shureim gurin Inteesar,dan abaya da Ra'uf yaje gurinta kafin ya sanar da ita son da Shureim.ke mata tayi tunanin Ra'uf din ke sonta kamar yadda take sonsa sai taji zance yasha banban ganin bazata iya nunawa Ra'uf batason Shureim ba shi take so,don Ra'uf a matsayin yayanta ta daukesa saboda kawarta Safiyya yasata hakura dan Shureim tasan baida wata makusa,don fannin kyau da kudi Shureim yafi Ra'uf sosai Bangaren Samiha kuwa suna london abinsu acan ta haifi 'yarta mace ,wanda taso kafin haihuwar su dawo gida saidai yanayin karatunsa bai kammala ba a lokacin,shi kuma bayason ta taho kaduna ita kadai ba tare da shiba dom yasan ba wata kulawa 'yan uwansa zasu bata ba tunda yasan a kaduna zata zauna,haka Ahmad din ya nuna bayason wani yazo,ranan suna yarinyar taci sunan Rufaida wanda Samiha ta bukaci Ahmad ya samata yako biye mata yasa mata,don ya fahimci bada wasa Samiha ta dauki Rufaida a zuciyarta ba hakama ya fahimta a bangaren Rufaidan ma haka ne,haka ya jinjina wannan soyayyar tasu sosai a ransa babu wani kusanci na kusa kona nesa tsakaninsu amma suke wannan zumuncin har takai ga sa wa 'ya sunan kawa lalle abun babba ne,koda Ahmad ya fadawa Ra'uf sunan Rufaida yarsa taci ba karamin dadi ya jiba don yakasa mantawa da Rufaida a zuciyarsa har zuwa lokacin ya kuma kasa kula wata ta zama makwafinta a zuciyarsa,takakka yayi ya tafi London daga Delhi shida Sophie da Husna da Husnan ta soma karatunta a Delhi,dukda da yace bazai samu zuwa ba amma jin sunan da Ahmad yasa wa 'yarsa ya sashi tafiya da kayan jaririya masu yawan gaske suka tafi da duk yawan wanda Ammi da Dady suka hada mata saida yakara wasu saboda murnan abinda yayi na saka sunan Rufaida da Ahmad yayi ji yake kamar don shi yasa sunan ga murnar karuwar da suka samu don Ahmad ya wuce amini a garesa, Ammi da ita a lokacin ta ma manta da sunan Rufaida yasa mata fahimci murnar Ra'uf ba,sai tunaninta ya bata saboda Ahmad ya haifi yarinya yake murna don kowa yasan yadda suke da Ahmad din shi yasa babu wanda yakawo komai,bayan shi kuwa murna biyu yake yi RUFAIDA Haka take cigaba da rayuwa da uwar mijinta da Rukayya abun babu dadi,kuma har lokacin Abba Bukar baisan wannan zancen ba,taje Kano tayi Kwana biyu da dakyar Wahid ya barta taje ganin tanada ciki a lokacin shi da kansa Wahid din ya kaita Kanon da shima zaije wata seminar kanon ,bakaramin murna daganinta suka yi ba,ganinta dauke da ciki da kuma ganin babu alamun damuwa a tare da ita don har kiba cikin yasata yasa hankalin Ummi Hauwa'u kwanciya , saida ta zaga gidajen kawayenta ta kuma je gidan Momy maryam tayi kwana daya sannan suka juyo Murnar sawa Rufaida takwara sosai Wahid yayi da Ahmad yake sanar musu bayan dawowarsu Kano da kwana biyu bakaramin kudi Wahid ya tura ba a siyawa baby kayan sawa Rufaida kuwa ranar kwana tayi da farin ciki ta kuma karawa Samiha matsayi a zuciyarta sosai,hakama a bangaren su Ummi Hauwa'u da Momy Maryam sun sallama irin kaunar dake tsakanin Samiha da Rufaida sai da jikin Rufaida yayi wata takwas Abba Bukar yaji labarin zaman da Hajiya Jamila da Rukayya keyi a gidan Wahid da AbdulMalik ya sanar masa da yaje wani aiki abujar yaje gidan,dukda Abba Bukar bayason dawo da Hajiya Jamila don bakaramin dadin zamansa da sauran matansa yake ba tare da Hajiya Jamila ba dama itace damuwarsa,badan yaso ba ya maido da ita ya kuma maida Rukayya nasarawa,saboda yana bukatar zaman lafiyar su Wahid da Rufaida SadiyaIbrahimKhalil❤️ *JININMU 'DAYA* BY Sadiya Khalil 44 *Duk abinda ka rubuta baya gogewa a littafinka koda kai ka goge shi a zahiri* RUFAIDA Bugun wayarta da take ji yasata katse aikin da take na shirya kayanta a drower da take da tsohon cikinta a lokacin ta mika hannu gefen gado ta dauki wayar ganin Samiha ce akan layin yasata saurin dauka da Sallamarta tasa wayar a handsfree ta cigaba da aikin da take ta soma da cewa Samihab "Mai jego ina 'diya ta,takwarata" Samiha da take riqe da Rufaida karama a hannu ta kurawa Rufaidan ido tanaji kamar Rufaida Aminiyarta take kallo ido ta lumshe ta bude kafin ta soma magana "Wato babu wata gaisuwa tsakaninmu ko,bare tanbayar lafiya ta sai tanbayar 'yarki ko?saboda takwararki ce,shiyasa Ahmad yace karna sakawa 'yata sunanki,saboda yasan yadani zakiyi soyayyar da mukewa junanmu ta koma ke Rufaida zaki riqa yiwa" Dariya maganar Samiha ta bata don bata tunanin akwai mahalukin da zai canza soyayyar dake tsakaninta da Rufaida "Au dariya ma kike"Samiha ta fada da ta jiyo dariyar a cikin wayarta Rufaida tace"yi hakuri yar uwata amma wallahi soyayyar da nake miki a jinina take,soyayyar da zanwa Rufaida duk saboda ke zan mata,badan kinmin takwara ba Samiha tace "to naji nima wasa nake miki,ai idan kikaso Rufaida tamkar ni kikaso ne,fatana na rayu da ita domin koda muna nesa da juna dana kalleta na tuno dake" "Hmm to naji 'yar uwata ina godiya da kaunar da kikemin fatana na wanzu gurin yi miki,koda bakya raye zan kula da duk abinda kika mallaka fiye da yadda zan kula da nawa" Rufaida tayi wannan maganar Samiha tace" haba 'yar uwata babu godiya tsakaninmu,ya Yaya Ahmad da baby na Allah dai yasa ki haifi namiji Rufy tayi miji" Dariya maganar taba Rufaida tace "To shikenan,Yana lafiya yana gurin aiki amma nasan yana hanyar dawowa ma baby kuma yana gaisheki,amma ni baby na ba zata auri kaninta ba gaskiya ki bari dai shi sai ki haifar masa mata nan gaba" Murmushi Samiha tayi tace "Aiko ni babyn cikinki na yiwa mata tun kafin yazo duniya,don haka babu fashi, indai namiji kika haifa shine mijin Rufaida,kuma tsiran nasu ba zai kasance mai yawa ba" Rufaida tace "To shikenan wai ma dakata ina Yaya Ahmad din ne" Samiha tace "Hmm ya tafi raka Yaya Ra'uf da su Husna wani store,kinsan su Ra'uf din sunzo daga Delhi,dafa baiyi niyyar zuwa ba yanaji ansa wa baby sunanki yazo,wallahi banyi tunanin har yanzu kina zuciyar Ra'uf ba sai da yace zaizo da kuma ganin kayan da ya siyowa Baby gaskiya ya kashe kudi,Ahmad yace tunda yaki fidda mata tunda kuka rabu yanzu sai ya auri Rufaida karama" Rufaida tayi murmushi kamar tana ganinta tace "Allah sarki,nifa na dauka yayi auren ma,amma ai bazan ba 'yata tsoho ba" Samiha tace "Da yayi aida na sanar miki har yau baiyi ba tunda ya rasa ki ya fidda tsarin aure a ransa tunda idan an masa maganar auren sai yace ba yanzu ba,shi kwata kwata ba tsarin aure yanzu a tare da shi,da Ahmad yace masa ko dai saboda ya rasa ki ne shine yace ko daya yasan dai ya soki amma dai yanzu tunda kinyi aure shikenan,shi dama halayyarki ta rudesa yasa har yaji yanasan yayi aure a baya auren ma kuma ya aureki,tunda kuma iyayenku ke da shi suka nuna basaso ya hakura" Rufaida da maganganun Samiha suke shigar mata zuciya sosai jin Samihan ta dakata da maganarta yasa tace"Kinga aiki nake yanzu zan kiraki anjima" Ba tare da taji mai Samiha zata kara cewa ba ta katse wayar da suke,don baza ta iya jure a rinqa yi mata maganar tsohon saurayinta ba ana tuno mata baya ne da har yau takasa mantawa da ita bakin cikin rayuwarta har yau ya kasa gushewa bawai son Ra'uf take har lokacin ba don yanzu soyayyar ta ta Wahid ce ba ta saka kowa a zuciyarta da sunan so idan ba mijinta ba, sai dai takasa manta yadda suka rabu da iyayen Ra'uf da nata,don tanada yakinin da kalmar karuwa da wasu daga cikin dangin Umminsu ke kiran Ummin nasu dashi a kayi anfani gurin ruguza wancen maganar auren nata,aka hadata da Wahid saukinta guda mijinta na kaunarta,matsalarta a gurin wasu daga cikin 'yan uwansu take da kuma surikarta sa'arta guda ce tayi nisa dasu sai dai duk ranar da suka zo habaici kam ta bani da shi samun daukinta kadai su tafi gida Samiha da take ta magana a wayar jin bata ba ta amsa ba yasa ta duba taga ta katse kiran murmushi tayi ta aje wayar itama tana nazarin dalilin saurin CE mata zasuyi waya anjimar da tayi bakomai bane illa maganar Ra'uf da tayi mata tunda akayi haka ta fahimci Rufaida batasan a yi mata maganar Ra'uf din kwata,koda yake tasan halin Rufaida tun suna 'yam mata bata damu da maganar namiji ba,kota Yaya Abdul ne da Yaya Samir ma ba'ayi take ba su da suke matsayin 'yan uwanta,bare kuma ta saurayi gashi kuma yanzu tana da aure don haka itama Samiha ta dauki alwashin bazata kuma yiwa Rufaida maganar Ra'uf ba idan ba ita ta sako, bare kuma tasan za'a yara kafin tayi maganarsa Wahid da yake tsaye jikin kofar dakin Rufaida da hankalinta nakan wayar da take da Samiha batasan ma ya shigo ba yana kallon yadda yanayin matarsa ya koma bayan ta kammala wayar murmushi yayi ya karaso inda take ya karbe kayan da take kokarin sakawa cikin drower ya riqe hannunta ya zauna gefenta kallon mamaki ta bisa dashi don batasan ya dawo ba, fuskarta ya kalla yace "Waye ya batamin ran mata ta" Sai a yanzu ta iya magana tayi saurin cewa "Babu kowa,mai ka gani" Ya danyi murmushi tukun yace "Ban yadda ba Samiha ta bata ranki saboda tayi miki maganar Ra'uf ko saboda kinason ki manta shi a yanzu haka" Ido ta zaro tace "Yaya waye ya fadama munyi maganar Ra'uf da Samiha?" Ya danyi murmushi yace "Nina jiyewa kunnena babu wanda ya fadamin,na dade tsaye anan,ina jin duk wayarku da Samiha,Rufaida a kullum ina godiya ga Allah dana samu mace ta gari kamarki" "Hmm Yaya kenan maiyasa kace haka" Rufaida tayi wannan maganar" Ya dan kalleta yace "Saboda kin hakura da zabina da Allah yayi miki wato ni baki kasance mai bibiyar tsohon saurayin da kaunarsa nasan ita ta fara linkaya a ruhinki,gashi sai kikayi rashin sa'ar mijinki bai iya soyayya ba,bare lokaci guda ya fitar miki da son Ra'uf a ranki,amma ke din sai kika bada gudunmawar hakan,kinga dole nace nasamu mace ta gari" Murmushi tayi tace "Shikenan ya isa haka mu manta da baya mu tunkari gaba" Yayi saurin ce mata "Hakane mata ta,yanzu mai kika tanadarmin yaufa yunwa nakeji sosai,Kabir ya cinye abincin da kika kawomin office" Ta dan yi masa hararar wasa tace "Duka fa abincin na zubo muku dana girka azo muje dai kitchen kayi girkinka dai,wai shi Yaya Kabir Luba bata iya girki bane?" Yace"Am sorry my wife ki girkamin ko indomie ne,kinsan dai Kabir bayan abincin matarsa bayason cin na kowa saike,Kabir yace abincinki dadinsa daya dana matar Uncle dinsa da take porthacourt,yace gani yake idan yaci abincinki kamar nata yaci" Murmushi Rufaida tayi tace "Kasan dai halin Yaya Kabir kila ma ba haka bane,nidai muje na tayaka kazo nima ka karasa shiryamin kayana" Wahid ya kalleta bayan ta mike yace "Nufinki dai abokina karya garesa ko,ba ruwa na keda luba wallahi,dama yace min yau zata zo, kinga saina fadamata" Zama tayi kokarin yi tare da cewa "OK jeka ka fadamata ni kuma naki tayaka girkin" Wahid da yake kokarin fita yace "Sorry,my wife,wasa nake miki" Da haka ta mike tabi bayansa zuwa kitchen *Bayan wata biyu* A wannan lokacin abubuwa da dama sun faru na farin ciki da akasinsa abun farin cikin harda haihuwar Rufaida ta haifi yaronta kyakkyawa da yaci suna Yasir da yake kama da mahaifansa,Samiha da aka tura mata hoton yaron ba karamin farin ciki tayi ba,kamar ita aka yiwa haihuwar ta kuma turo masa da kaya masu kyau da tsada ba karamin soyayya ake nunawa yaron ba,a gidansu ta haifesa Kano da taje goyon ciki har saida akayi arba'in ta dawo wannan zuwan bakaramin farin ciki Ummi Hauwa'u tayi ba na zuwan 'yarta ta koba komai ta rage jin bacin ran irin auren da akayiwa Rufaidan,ta kuma dora so akan Yasir,da itama Ummi Hauwa'u ta kara wata haihuwar ta haifi 'yarta mace mai suna Amina suna ce mata Rahima a lokacin akayi bikin Nasiba shehu kawa ga Rufaida da duk ta hadu da class mate dinsu da hakan ya tuna musu da rayuwar makaranta Samiha ce kadai bata samu zuwa ba kasancewar Ahmad yace sai ya kammala karatunsa zasu dawo tare,duk yadda taso zuwa haka ta hakura Abdul-Rahman ma yazo bikin dukda baya kasar yana Cyprus saida yazo daurin auren Aisha kasancewar ita ce ta hannun damarsa,haka nan ya dinga tsokanar Rufaida Yasir ya fi ta kyau,Hajiya Jamila badan taso ba tazo ganin da saboda matsawar da Abba Bukar yayi tazo ba tare da ta kawo ko tsinke ba,tana ganin Yasir kuma taji kiyayyarsa ta shiga ranta,da habaice habaice da bakaken maganganu ta baro Kano,wata 1 tayi cur a Kano daganan ta koma Abuja da Luba taje gidan ta gyara mata shi itama a lokacin ta haifi dan ta Yusuf a kwantagora da nanne garinsu Kabir din aiki shima ya maidoshi Abujar da yake matsayin Kwararren likita Share plz kuma kuyi manage *JININMU 'DAYA* By Sadiya Ibrahim Khalil (Sadiya Khalil) 45. Ayi manage please ba yawa *Bayan shekara biyu* Wahid ya dago jajayen idanunsa ya kalli Hajiya Jamila da take zaune saman kujera Wahid yana gefenta kan carpet zaune ya soma magana cikin raunin murya "Mama nifa bana qi auren Ruqayya bane,illa ni dai kawai,bata daga cikin tsarin matan da na keso na aura" Hajiya Jamila cikin zafin zuciya ta kalli Wahid ta soma magana "Na fahimceka Wahid,'yar karuwa wadda banbancinku yafi gaban kwatance har ta fiye ma Ruqayya,to wannan karon muddin baka auri Ruqayya ba sai dai ka saki waccen yarinyar don ba zan bari irin karuwa ta cigaba da haifamin jikoki ba,dan shi kansa wancen 'dan ban yarda naka ne ba ne" Da sauri ya kalli mahaifiyar tasa yace "Haba Umma mai yasa zaki ce haka,dan Allah Umma mu daina tuna baya mu tunkari gaba kawai... Abba bukar da ya dade a tsaye a kofar dakin da yakejin duk abinda suke tattaunawa wanda babu wanda yaji motsinsa a cikinsu yace "Barta ta tuna duk abinda ke ranta Wahid" Muryar Abba Bukar din ce ta katse karashen maganar da yakeson yi Abba Bukar din ya dora da cewa "Jamila tunda har Wahid yace bazai auri Ruqayya ba da bakinsa to nima,bazan amince ba kai koda ma ya amince din,saboda koda ban hada iri da Rufaida ba wallahi ta fiye min ke da yan uwanki" Wata shewa Hajiya Jamila tayi kafin tace "Bari na tuna ma idan ka manta ni din da kake fadar hakan akaina ko makaho ya shinshina yasan cewa nafi wancan dan iskan kanin naka,wanda saboda abun kunya saurayin 'yar da iyayensa suka fasa,sai danni nawa 'dan ya taimaka musu zakayi min maganar banza,me ake da zuriya irin taku Abba Bukar ya tunkaro Hajiya Jamila cikin zafin zuciya zai kai mata duka da take zaune kujera ba tare da tayi koda motsi ba Wahid ya mike ya rike hannun mahaifinnasa yana cewa "Abba kayi hakuri" Abba Bukar da idonsa ya soma ja yace "Wahid yanzu ni Jamila ta ke fadawa wadannan maganganun,ita ta manta abunda ya faru da tata 'yar uwar ranar da ranar aurenta mijin ya fasa ta manta kuma abunda dan uwanta ya aikata da..." Hajiya Jamila sai yanzu ta mike daga kujerar da take ta katse maganar Abba Bukar da cewa "Bukar wallahi karka kusa,ka fadi wata magana akaina idan ba haka wallahi saikayi dana sani mara iyaka" Cikin bacin rai ya kalli Hajiya Jamila yace Wanne dana sani zanyi daya wuce ke wanda zakiyi" Murmushi Hajiya Jamila tayi kafin tace "Aini banida wani danasani,kune kukayi shi,tuntuni bama yanzu ba saboda kuskuren shigowar karuwa kazama cikin..... Wahid ne ya yayi kokarin jan Abba Bukar ganin Ummantasu bazata fasa maganar da take,suka fito daga daki saida suka fito wahid ya dubi Abba Bukar yace "Abba dan Allah kayi hakuri,da abinda Umma tayi yanzu" Abba Bukar dafa kafadar Wahid yayi yace "To ya zanyi Wahid kullum cikin hakuri nake yi,dawowar dana yi mata na dauka abun zaiyi sauki amma abun yafi nada ma,saboda don kawai na hadaka aure Rufaida" Wahid cikin ba ya dubi ABBA Bukar yace "amma Abba menene laifin Rufaida,bata aikata musu komai ba,haka ma ummansu Abba" Abba Bukar yace "To dama mai zata aikata musu Wahid kasan shi makiyi ba ya jira kayi masa laifi yake ba,yanzu ka wuce ku tafi karkuyi dare a hanya" Jiki ba kwari su Wahid suka fito harabar gidan shida Abba Bukar gurin motarsu da Rufaida da sauran matan gidan suke jikin motar sun fito rakiyarsu Haka suka shiga Wahid ya tada motar Rufaida ta shiga tare da Yasir da yayi girma ya fito a kyakkyawan Hausa Fulani da ya debi kamanni mahaifinsa sak Har suka fara tafiya a motar babu wanda cikin Rufaida da Wahid sukayi wa juna magana saidai takan ji firarsu jefi jefi da Yasir don bataji akwai abinda zata iya cewa dashi shi din ma haka ne saboda bayason ta fahimci abinda ya faru shida mahaifiyar tasa a yanayin maganarsa ita dinma bata damu da hakan ba ta bude gidan gaba ta shiga jikinta babu kwari don tasan tabbas akwai abinda ya faru,a shigarsa sa dakin mahaifiyartasa,da niyyarsa tayi mata sallama sai kuma ga wadancen maganganun sun biyo baya **** Marhabin da manyan baki wallahi sam ban tsammaci zuwanku ba"Rufaida ta furta hakan tana kokarin matsawa daga kofar falon da ta bude Luba da ta shigo da Yusuf data riqewa hannu tace "Ai dama haka zaki ce,uwar cika alkawari" Ta karasa maganar tana hararar Rufaida Rufaida tace "Ayi min afuwa matar likita bokan turai kinsan Yasir baiji dadi ba yau kwana 2,yanzu dai ku zauna na kawo muku ruwa" Luba ta zauna kujera tana cewa "Var ruwan nan daga gida muke yanzu Abban Yusuf ya saukemu ya wuce asibiti" Rufaida da take kokarin zama kusa da kujerar dasu Luba kekai tace "Kai Yaya Kabir yana kokari, su likitoci kullum aiki kamar agogo ace har weekend ma" Luba tace "Hmm kedai bari kawai,yanzu aka kirasa waya patient garesu kuma ana bukatar yaje asibitin ya dubashi cikin gaggawa shine muka fito tare" Rufaida tace "OK Allah yabada lafiya"daganan ta maida dubenta ga Yusuf dake ta zaro ido tace "Yusuf zo mugaisa mana ko kula ni yau bazaka yi ba" Kafada Yusuf din ya make ya kwanta jikin Ummansa Rufaida tace "Au bazaka zo ba ko?" Luba tayi dariya tace "ai kema kinsan bazai zo ba tunda yaga baiga Yasir ba,yana inane ko jikin ne yayi zafi" Rufaida tace "Ai na fahimta,yanzu suka fita shida Abbansa,kinsan mara lafiya da kwalama ice cream yakeson sha" Luba tace "A lallai kuwa,nifa na dauka lafiyarsa kalau ashe da gaske baiji dadin ba" Hararar Luba Rufaida tayi ta na kokarin furta wani Abu sukaji sallamar Wahid a falon amsa masa suka yi ya karasa shigowa Yasir da ya hango Yusuf yayi saurin sauka a hannun Abban nasa yayi wajen Yusuf 'din suka fara wasa "Sannu da zuwa" suka yi kokarin hada baki duka gurin ce masa "Yawwa,wa nake gani haka kamar Maman Yusuf hala makuwa kikayi ko?" Wahid yayi maganar da murmushi kan fuskarsa Luba tace "Ai nafi matarka ita ko makuwarma yaushe rabon da tayi tazo gidanmu" Wahid da yake kokarin zama kujerar gefensu yace "Kuma tanbayarta kiji laifinta ne ba nawa ba" Rufaida sai lokacin tasa baki tana dan hararar mijin nata ta wasa tace "Kaji ka da wani zance,dan dan dai banasan tone tone amma da saina ce,anfi kwanan wata ina tanbayarka zani baka bani amsa,sai shekaran jiya kace.min naje,sai Yasir ya tashi da ciwo/a ranar zuwan namu" Wahid ya kalli Rufaida yace "To yanzu duk wannan dogon bayanin,me kikai inba tone tonenba" Dariya sukayi gaba daya Luba tace "Oh Dadyn Yasir bamu gaisa ba hira tayi dadi,ina yini,ya aiki" Wahid yace "Gaskiya kuwa,lafiya Alhamdulillah ya abokin nawa dafatan yana lafiya" "Alhamdulillah,tare muka fito ma yanzu zai karasa asibiti ne"cewar Luba "Ok,sufa aikinsu babu hutu"fadin Wahid " wallahi kuwa,yanzu muka gama maganar da Rufaida,gwara aikinku sosai"fadin Luba "Kai Maman Yusuf babu wani gwara mutum ya fita tun safe shida gida sai yamma"Rufaida ta sa baki a hirartasu,gurin fadin haka Luba ta rike baki tace " iye mai miji yaushe kikeso ya dawo to?" Harararta Rufaida tayi tace "So nake 2ma tayi masa a gida" Tsaki Luba taja mata "Rufaida ta kalli Wahid tace " Dady kaji ta harda tsaki ko nayi laifi ne?" Ya 'dan rausaya kai yace "A'a baki laifi ba,kinga bari nakira Kofur Musa ya karo yawan Ice cream din nan" "Rufaida tace " au dama buku siyo ba?" "Eh mana da baki ga leda a hannu na,muna fita mukayi kicibis da Musa shine ya amshi key din daya motar na masa sautu dan banajin zuwa Shoprite a lokacin shi kuma har can zai karasa, mu kuma Unguwa muka zaga da Yasir" Wahid yayi wannan maganar "Ok,lallai kunsha aiki" Cewar Luba Daganan suka cigaba da firarsu,Wahid ya mike bayan ya gama waya da Musa ya fito waje shida yaran ua barsu a falon suka cigaba da firarsu Sai sannan Luba ta maida dubenta ga Rufaida kacokam ta soma magana "Rufaida yanzu nakejin labari gurin,Kabir cewa AbdulWahid zai kara aure da wannan Ruqayyan da suka zauna da surikarki anan gidan amma Wahid din yace shi sam baya sonta" Jin Luban ta kawo karshen zancenta yasa Rufaida kallonta,dukda bai taba fadamata zancen aurensa ba amma ta dade da sanin zancen Ruqayya tunma kafin suyi aure hakan yasa bata daga hankalinta da taji Luban tayi maganar yanzu kuma bata nuna mata rashin sanin taba tace "Eh haka ne,Luba nidai indai zata zo da Alkhairi ina maraba da ita" Luba ta jinjina kai tana mamakin jin wannan Kalmar daga bakin Rufaida don ita kanta tasan Rukayya ba alkhairi bace muddin ta shigo gidan Rufaida a matsayin kishiya bare kuma Rufaida tayi zaton haka,tun kafinma suyi kishin bata zo da Alkhairi ba bare yanzu da zasuyi zaman kishi,ita kam har mamakin Rufaida take lokuta da dama don gaskiya da itace bazata bari ayi mata haka ba,saboda tana samun wani labarin gurin Kabir mijinta ta dai yi kokarin kauda tunanin nata tace "Hm Rufaida kenan,kina tunanin Rukayya ce Alkhairi,a zamanku kinadai sane da abubuwan da suka riqa faruwa a zamanku dake dasu,nima kuma ina ganin wasu da idona,kedai kiyi fatan Allah ya hadaki da abokiyar zama tagari badai Rukayya ba" Rufaida tayi murmushi tace "Don me za kice ba Ruqayya ba,bakya tunanin ta iya sauyawa idan anyi auren,shifa namiji ne shi zai saita gidansa" Luba ta danyi dariya "Au kina tunanin Rukayya zata canza lokaci guda,kintuna zagin da suka riqa yi miki ta uwa ta uba,da ita da surikarki,kuma ina gidan lokacin,karki yaudari kanki Rufaida, don hatta Abba Bukar yace bai amince da Wahid ya auri Rukayya ba,don shima kansa yana sane da komai" Rufaida tace "Duk da hakan da ya farun kinsan dai,Ruqayya tanasan Yaya Wahid zata daina koma meye,Abba Bukar kuma zai sauko" Luba tace "haka dai kikace,nidai kawai abinda zance miki ki cigaba da addu'a nima kuma zan cigaba da tayaki" Da haka suka cigaba da hirarsu,da sai dare Luba ta bar gidan Rufaida don kawance suke sosai kamar sun dade da sanin juna kasancewarsu hatta a shekarun haihuwarsu daya shiya kara musu karfin kawancensu kuma kowacce ta yaba da halin kowacce" Ayi manage don Allah kunsan yau da gobe sai Allah Kardai ku manta mun dan waiwaya bayane amma next page insha Allah dawo Inda muka tsaya sai a dora insha Allah Nagode masoya a duk inda kuke ina godiya Allah ya bamu iko anfani da sakon da littafin yakeson ya isar Sadiya Ibrahim Khalil (Sadiya Khalil) *JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil 46. Ayi manage don Allah ba yawa kuyi min afuwa nace saura 1page adawo bayan da aka waiwaya yanzu kuma, saura 3page yanzu kuma saura 2page kenan ayi hakuri da spelling mistake Sadiya Ibrahim Khalil (Sadiya Khalil) Jin sallamar Wahid a 'dakin yasata kokarin tashi daga kwanciyar da tayi a gado tana danna wayarta ta tashi zaune tana amsa masa sallamarsa Kallon Rufaidan yayi yana kokarin zama gefen gado yace "Badai har kin kwanta ba" Murmushi tayi ta kallesa "A'a ina kokarin kiran Samiha ne,kuma nagama bata dagawa" Yace "Kila bata kusa da wayar ne" Tace "Eh nima nafi tunanin hakan" Dube dube ya fara kafin yace "Ya banga Yasir din ba" "Gashi nan dakyar na samu ya kwanta bayan ya gama rigimar tafiyar Yusuf" tayi maganar tana nuna masa Yasir din da yake kwance gefenta Murmushi Wahid yayi yace "Ai Yasir da Yusuf shakuwarsu kamar tagwaye" "Gaskiya kuwa" fadin Rufaida Gyara murya Wahid ya danyi ya dubi Rufaida ya soma magana "Dama inaso muyi wata muhimmiyar magana" Kallonta ta maida kacokam garesa tace "Ina saurarenka" Wahid ya gyara zamansa ya soma da cewa "Rufaida,nasan dazu kunyi maganar auren Rukayya da Umma takeso na kara keda Luba sai dai maganar gaskiya bana son aurenta saboda ke irin halarcin da kikayimin da biyayyar da kikayi wa su Abba dan nasan tuntuni ba nine zabin da kike so ba,amma da Allah ya zaba miki ni sai kika hakura,ki amshi zabin da Allah yayi miki da hannu biyu,kuma kika zama mai hakuri da irin barazanar da Umma tasha yi miki,da zagi da cin zarafinki kafin auranmu dukdan saboda kice kin fasa aurena,dama yanayin zaman mu yadda yakasance bayan aurenmu da Umma da Rukayya suka shigo cikin rayuwarmu,kuma suka riqa yi miki abubuwan da zasu bata ranki amma duk kika jure,amma yanzu bana tunanin nayi miki adalci muddin na amince da abinda Umma take so nayi,na auri Rukayya,saboda nasan Rukayya sai tayi barazanar tarwatsa zaman mu,ni kuma banaso na rasa mace kamarki a cikin rayuwata" Murmushi Rufaida tayi jin ya kawo karshen zancensa tace "Karka damu Yaya Wahid,ka aureta din,insha Allah babu abinda zai faru garemu,kuma zata kasance alkhairi a tare damu,zamu rayu nida ita saboda faranta ranka,da tarbiyantar da yaranmu hanya madaidaiciya" Murmushi yayi jin maganar da tayi yace "Haba Rufaida wannan tunanin na kine kawai ba nata ba,ita abinda zai kawota rayuwarmu so take ta wargaza zaman mu ni da ke kamar yadda Umma take so" Murmushi ta sake yi tace "Karka bari wannan tunanin yayi tasiri a zuciyarka domin Allah shine mai gyara ko wanne al'amari ba tare da munyi tunanin hakan ba" "Eh haka ne,mata ta,zan fahimtar da Abba dan shi haryau yakasa amincewa da maganar auren,saboda yana tsoron karsu yima diyarsa wani abu"fadin AbdulWahid Rufaida ta murmusa jin karshen maganar Wahid din tace " Allah yana tare da mai gaskiya,nayi alkawarin zan rike gaskiya a zaman mu,zan kira Abba na sanar masa indai saboda nine bayason ka auri Rukayya toni nace babu komai,saboda inasan mijina ya kasance mai biyayya ga mahaifansa,bana so na zama silar kasawarsa" "Au harda,kinasan mijin naki zaki fadawa Abban" fadin AbdulWahid Rufaida ta 'dan hararesa tace "Eh mana tunda kasan ba nida kunya" Dariya yayi yace "Oh dan kin fadawa Abba irin son da kikewa mijinki shine rashin kunya" Ta sake harararsa tace "Oho ma" Ya dan sake yin murmushi yace "Wallahi Rufaida,ban taba tunanin zaki so ni haka ba a baya can" Ta 'dan zaro ido "Saboda me" "Hmm,saboda ba nine zabin ranki ba" Fadin Wahid "To waye zabin ran nawa bayan gaka" Fadin Rufaida Murmushi yayi jin maganar ta yace " 'dan uwanki shine zabin ranki mana,ni rashin uwa ne yasa akayi uwar daki dani" Murmushi tayi ta dan zaro ido kadan tace "Ko daya kaine dama zabin da Allah ya zaba min,kuma waye dan uwan nawa nufinka Ra'uf ai bamuda dangantaka da shi" Dariya yayi kadan yace "Eh mana dan uwan kine,tunda kun hadu a dangin Annabi Adam" Murmushi tayi tace "Ah to sai dai hakan,yawwa bana fadama,ka dai na min maganar wani tsohon saurayi na ba,bansan mai yasa baka kishi na ba?" "Sorry matata,ina kishinki matukar gaske,amma kuma yanzu ke matata ce babu mai kwace min ke yanzu,ji nayi kawai yau ina sha'awar tuna baya" Ya karasa maganar yana jiran jin amsar da zata basa sai yaji tana cewa "Tuna bayan har saika tuna da Ra'uf kuma bayan babu wata alaka tsakanin mu bare har yasa mu dinga tunawa da shi a cikin bayanmu" "Muna da alaka da shi a bayanmu mana,tunda ya taba shiga cikin rayuwar kanwata" "Hmm to naji,abar maganar tasa Cewar Rufaida " shikenan,amma wallahi ban jidadin abinda ya faru ba da ya zama sanadiyyar baki aure saba,nasan da shine zai kula dake fiye dani" Karar wayar Rufaidan yasa Rufaida maida maganar da take kokarin fada ta maida hankalinta ga wayar ganin Samiha ce yasata sakin murmushi ta nunawa Wahid wayar "Kaga mutuniyar taga kiran ta biyo" daganan ta kara wayar a kunne tare da gabatar da sallama Samihan ta amsa Rufaida ta fara tsokanarta "Uwar biyo ya kike ya ya takwarata,yaya Ahmad" "Wato uwar biyu ko?,Duk muna lafiya yaya Wahid,da surikina" "Eh mana uwar biyu zance tunda ni banida shi,Gashi nan yana jinmu,Yasir kuma ya kwanta" "Zaki yi shine,yawwa bawa Yaya Wahid wayar naji ya akai zai karo mana kishiya" "Gurin wa kikaji wannan zancen" "Kinga nidai bashi wayar muyi magana" Da haka Rufaida ta mika masa wayar tana ce masa "Ungo Samiha tana so ku gaisa" Ya amsa wayar da murmushi kan fuskarsa,yasa a kunne ya fara magana "Assalamu Alaikum uwar biyu" "Wa'alaikumus salam ,au harda kai amasu cemin uwar biyu zan rama ne" Yayi dariya " Eh mana,amma kafin ki rama zaki rame" "Eh amma dai na rama,hmm ba mu gaisa ba Yaya Wahid, ina yini ya aiki ya kawata" "Lafiya Alhamdulillah,ya UK ya maigidan naki ya takwararmu" "duk muna lfy ba lafiya ba" "Subhannallah maiya sameku" "Eh to cutar kishi ke da munmu munaso muji maine kawarmu bata yi maka,har daga aurenku zaka kara mata kishiya" "Au sai mace bata yi ma wani abun zaka kara aure kun manta karin auren Allah ne yace ayi,matukar mutum yana da sararin yi kuma yanada bukatar karawar ,kuma yasan zai iya adalci a tsakaninsu" "Eh hakane amma dai" "Amma me fadi" "Kamata yayi kukai shekara kamar hudu zuwa biyar sai a fara maganar auren" "Nima naso hakan amma Umma ce take so nayi yanzu,saboda Rukayyan ta kusa kammala karatunta,sai tayi service bayan aurenmu,kuma kawarki ta fahimce ni" "To Allah ya tabbatar da Alkhairi yasa ta gari ce" "Amin Samiha,yau ma tukun waya fada miki wannan zancen" "Ai kasan abun duniya baya buya" "Hakane kam,amma dukda hakan ana samun wanda yake fadar wani zancen har wani ya sani" "Eh to haka ne" "To Waya fada miki kodai Kawarta kice?" "Ko daya kaga bata wayar ma" "Au bazaki fadamin ba"daganan ya mikawa Rufaida wayar da take jin abinda suke tattaunawa a wayar dukda batajin abinda Samiha ke fa'da amma ta fahimci akan mai suke tattaunawar yana mika mata wayar ya fice daga dakin Samiha ta soma magana " yanzu Rufaida kina ganin Wahid yayi miki adalci duka yaushe kuka yi aure da zai kara aure,abin ya dauremin kai kodai kina masa wani abu ne" "Babu ko daya Samiha umarnin Ummansa ne karin auren da zai yi wadda zai aura din ma Cousin sister dinshi ce" "Au wai banda kokarin kashe kin data kusa yi kafin auren shine zata hada ki kishi da 'yar uwarta bakin ciki ya kashe ki kenan" Jin furuci Samiha yasa Rufaida ta zaro ido kamar Samihan na ganinta,da alamun mamaki "Waye ya baki wancen labarin ke kuwa" "Aunty Samira ce ta fadamin,tun sanda abin ya faru,ganin baki min maganar ba yasa ta nima ban miki ba,gaskiya Rufaida wannan auren naki hatta Ummi Hauwa'u bata sanshi dandai yazo da rabo ne,amma tun muna yara kike bani labarin abubuwan da Ummansu Wahid take yi muku,kuma nima nasha gani da ji,don wallahi da na isa na fadawa Abbanku da ba zan yarda a aura miki Wahid ba,duk da dai shi yana sanki,amma uwarsa fa,irin wannan abun ake gudu gashi tun ba'aje ko inaba ta sako masa maganar aure so suke su kashe ki" "Haba Samiha maida wukar komai mukaddari ne niba zan sauya komai ba kidai cigaba da tayani addu'a insha Allah babu abinda zai faru dani tunda dai nasan halin Rukayyan ai komai zaizo da sauki" Murmushi Samiha tayi kamar Rufaida na ganinta tace "Kinga Sanin hali bashi ne mafita ba addu'ar dai itace mafita kuma zan ta yaki Insha Allah" "Yawwa nagode kawata" "Babu komai " yar uwa, yawwa kinsan Cousin dinsu Ahmad Nasiba ta aura kuwa,tuntuni inata so na fada miki ina mantawa" "Ke dan Allah fa bansani ba,Nasiba bata fadamin ba" "Wallahi,kuma muna hirar a Group naga bakya duba wane shiyasa,mamar angon yayar surikina ce Ahmad ma yazo daurin aure,saida suka dawo wajen daurin auren da muka yi waya nace masa ya ganki yace a'a baki na Abuja ba,nace masa kinzo goyon ciki a gida kika haihu kuma kina gidan bikin ranar daurin aure,yace min baisaniba aida ya nemeki kun gaisa" Cikin farin ciki Rufaida tace "Ah ashe dai muda Nasiba no parallel" "Eh mana,kece ma mukayi parallel din ma" "To ya za'ayi haka Allah ya tsara,kinga wallahi na fara jin barci fa zan kwanta" Da haka sukayi sallama Rufaida ta aje wayar ta lula duniyar tunanin rayuwarta Bana typing mai tsawo shiyasa wasu zasuga kamar littafin zai yi tsawo Allah ya shiryardamu bisa tafarkin tsira amin*JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil 47 Not edited *RA'UF* "Ammi sannu da gida" Ra'uf yayi maganar yana karasa zama gefen kujerar da Ammin ke kai Ammin ta dubesa ka'dan "Yawwa Ra'uf,yanzu na tanbayi su Husna kana ina suka cemin kaje gidan Shureim" "Eh wallahi Umma can naje naje dakinki na fada miki zan fita na tadda kina barci,a gajiye nake ma" Harararsa Ammi tayi tace " 'yar wannan tafiyar ace harka gaji,dafatan suna lafiya dai ko su Inteesar 'din?" "Eh Ammi lafiyar.su kalau Irfan ne dai bayajin dadi shine naje na dubasa" "Oh Allah ya bashi lafiya,dama yaro da yazo duniya zaka samu ya fara rashin lafiya" "Wallahi kuwa Ammi" "Au kako ji Samihan Ahmad ta haihu yau" Cikin murna Ra'uf yace "A'a Ammi wayata yau gaba daya a kashe take,mai aka samu" "Nima dazu Ahmad ya fadamin yace min ya kira lambarta ka bai samu ba,Namiji aka samu" "Kai Amma Ammi naji dadi mun samu aboki Allah ya raya mana shi" "Amin ya rabb,kai yaushe zaka yi auren ne?" Jin tanbayar da Ammi tayi masa da bai zace taba yasa shi kallonta "Ammi aure kuma?" Cikin karfin gwiwa tace "Eh aure,ko haka kake so kayi ta zama,shekarunka kullum ja suke,amma kai naji ko maganarsa bakayi ga abokanan daga mai 'ya'ya biyu sai mai 'daya" "Ammi ba nida budurwar ne har yau bansamu wacce tayi dai-dai da tsarina ba" "Ai ba zaka samu ba kuwa,tunda ba nema kake ba,nida nayi ma sha'awar kaje kanemi auren Inteesar ba ki kayi ba,sai kaje ka nemawarwa abokinka soyayyarta,gashi nan ya aureta suna zamansu lafiya harda karuwa ma tsakaninsu" "Ammi tayi maganar da nuna bacin rai " amma Ammi na fada miki,Inteesar Shureim ya dade yana fadamin son da yake mata,kinga bai kamata naje na nemi soyayyarta ba" "Amma ai tun a lokacin na fadama kaje ka samu wata ga 'yam mata nan a gari" "Ammi bawai 'yam matanba samun ta gari a wannan zamanin shine aiki,kuma idan nasa mu banaso a sake kwatanta abinda ya faru a baya" Sai yanzu Ammi ta soma fahimtar Ra'uf wato har yau dai bai manta da waccen yarinyar ba kenan bayan ta mayi aurenta ta dai kauda wannan tunanin tace "Ra'uf kenan wato har yau ka kasa manta abunda ya riga da ya wuce,ya kamata ka manta da baya fa a yanzu ka tunkari gaba ka fahimta cewa bafa laifin su Yaya sule bane a waccen abun da ya faru,haka Allah ya kaddara tun fil'azal ita ba matarka bace" "Hakane Ammi,amma na baki damar ki dubomin wata" "To zamuyi magana da Dadynku Allah ya yima albarka" "Amin Ammi na" shiru ne ya biyo baya Shigowarsu Husna ya katse shirunsu "Husna ce ta karasa wajen Tv tana cewa " Ammi sai kace gidan makoki Tv a kashe bari na kunna" Ammi tace "Tunda kinzo sai ki kunna ai uwar iya" Safiyya ta karasa kujerar dake saitin tasu Ammi ta zauna tana cewa da yaran indiyanci da shine yaran da sukeji sosai "Ammi sannu da hutawa,yaya sannu da zuwa" Cikin hadin baki suka ce yawwa Sophie ta karaso tana cewa "Yaya welcome" Da murmushi kan fuskarsa Yace ur welcome Ammi na" Daga haka ta zauna da murmushi kan fuskarta tace "Yaya munfayi 'da" Yace "Eh Ammi ta fadamin" Safiyya tace "amma zamuje wannan karanma ko yaya?" Yace"Anya kuwa Sophie" "Kai Yaya don Allah muje munjema haihuwar Rufaida bare wannan aboki fa kayi"fadin Safiyya Ammi ta harari Safiyya tace " to sarkin da'din baki,karatun fa,kunsan zaku shiga first semester level 400" Husna tace "Kai Ammi kwana biyu fa zamu yi" Harararta Ammin tayi tace "Ba zaku ba fa,karatun zaku bari" Ra'uf yace "Ammi daina wahalar da bakinki nima ba zuwa zanyi ba bare su sa rai" Safiyya ta fara magana kamar zatayi kuka tace "Kai Yaya don Allah kayi hakuri" Dady Jabir da ya karasa falon kowa da upstairs ya karaso falon yana kokarin fita jin hakurin da Safiyya ke bayarwa ya sashi saurin karasowa gurin da suke yace "Ra'uf bazaka kiyayarmin Auta ta kuma kanwata ba mai tayi mana ne" Ra'uf ya harari Safiyya yace "Dady don ance fa bazasu UK ba gurin sunan matar Ahmad shine take ta'bara,kamar ita ka'dai aka hana zuwa" "Kunga ku je ku shirya mu fita mu qyale su" Da sauri suka mike ba sukayi Upstairs Dady ya zauna a kujera yana murmushi ya kalli Ra'uf yace "Ra'u har yau baka sami wacce kake so bane,ga kannenka nan su Husna da sun kammala degree dinsu aure zan musu ga babban wansu a gida ya zama gwauro?" Ammi tace "Wallahi Abban Safiyya nima maganar dana gama masa kenan" Ra'uf yace "Dady zan nemo insha Allah" "Yawwa kayi kokarin hakan kaga Husna tanada saurayinta tsayayye Bello,yanzu saura Safiyya itace bata fito da miji ba,idan kuma kana santa sai ayi 'yar gida"fadin Dady Jabir Ra'uf ya dan bata rai jin maganar Dady yace " kai Dady,badai Safiyya ba zan nemo dai" "To meye aibun Safiyya ne" Ammi tayi maganar tana tsare Ra'uf da ido "Ammi kinsan dai wacece Safiyya kuma kinsan Hajiya bazata yarda ba kuma ma kinsan ko Baff...." Jin sallamrsu Husna yasa shi yin shiru da maganar Dady mikewa yayi ya kalli su Ammi yace "Mu zamu fita" Suka hada baki gurin cewa "Allah ya kiyaye hanya" suka fice Su Ra'uf suka cigaba da firarsu. RUFAIDA Rufaida tana kokarin fitowa daga kitchen taji yo muryar Yasir daga daki yana cewa "Mami,Mami Samiha na waya" Dakin ta shigo da tasa mu Yasir da wayar a kunnensa yana kokarin fitowa kawo mata wayar wayar ta amsa tasa a kunne ta gabatar da sallama Samihan ta amsa tare da ce mata "Oh kin barni da surikina yana ta zuba min gwaranci ko little Rufaida ta fisa iya magana,ina kika je ne" "Dama ina zai hada kansa da.wannan 'yar taki kamar ta saida mutane,wallahi na shiga kitchen ne" "Au haka zaki ce,keba 'yar ki bace,tunda dai takwarar kice ai ba damuwa" "Ato ai ni bana da damai surutu,tunda da 'ya tace bazatayi surutu ba,ya babyboy yanzu shine 'dana yana lafiya,an masa suna yau,naga baki kirani kinji sunan yaron bama" "Sorry Samiha,kokarin da nake kenan dana baro kitchen din sai kuma naga kin kira,ya sunanshi?" "Sunanshi AbdulRa'uf" Jin sunan yasa Rufaida tuno da wancen Ra'uf din Allah sarki rayuwa,jin tayi shiru yasa Samiha cigaba da magana "Ahmad ne yace sunan Ra'uf zaisa tunda nima nasa sunanki,kuma yace yanaso Rufaida da Ra'uf wadannan suyi rayuwa babu rabuwa sai mutuwa tunda sun fito ciki 'daya" Rufaida jin maganar Samiha yasa ta sakin murmushi kamar tana ganinta tace "Gaskiya,bansan irin kaunar da kuke mana ba,a tsawon rayuwarku" "Soyayya ce dan Allah,ina Yaya Wahid din ne ko ya fita aiki ne" "A'a baya jin dadi ne" "Subhanallah kice ina gaidashi,ga Rufaida ku gaisa Little Rufaida da take da surutu ta amshi wayar data matso a bata dama ta fara magana "Mami,ina kwana" "Lafiya kalau,Namesake,ya baby boy" "Gashi nan,yanzu Mami ta daina daukata sai dai ta dauki,Little" Dariya Rufaida tayi tace "To ai yanzu kin zama babba yanzu" "A'a mami ban yarda ba" ta karasa maganar kamar zata yi kuka Dariya Rufaida tayi tace "Ga Yasir nan na miki dariya,Rufaida tayi maganar tana bawa Yasir wayar" Sun jima suna hira akarshe suka yi sallama jin turo kofar dakin nata yasa ta maida kallonta ga kofar dakin ganin Wahid ne ya shigo da shirin fita aiki yasa Rufaida kallonsa da mamaki tace "Badai aiki zaka fita ba ko?" Yayi murmushi ya rungume Yasir da rugo gurinsa yace Dady zan bika "To my son jirani a falo na fito" don yawanci duk fitar da Wahid zeyi da Yasir ne hatta da gurin aikin yana fita da shi lokaaci lokaaci jin Yasir din ya fita ne ya sashi kallonta yace mata "Eh mana My wife ko karna je" "Eh mana,kasan baka jindadi" "To ai nasamu sauki" "A'a gashinan dagani kowa yasan bakada lafiya nasan karfin hali kawai zakayi don Allah ka hakura" Kai ya girgiza yace "kiran gaggawa nasamu a office" "To naji kabari nayi ma driving karkayi da kanka" "A'a my wife kibari na kira kofur Musa yazo ya yii min driving 'din" "Badai kaso nayi kawai zaka ce" "no my wife banaso ki wahala ne,kinsan kece silar haskaka zuciyata fa kinga wazai so hasken rayuwarsa ya wahala" "Hm kaga ma dadin bakinka dai" "To ba kicemin nine haskenki ba?,koda yake nasan bani bane inaji a jikina zaki zauna da mutumin da zai zama sanadiyyar haska rayuwarki" "To ai ba wani bane bayan kai ni Kaine haske na" "Kinga ban yarda ba bani bane" "To waye nidai nasan kaine" yana kokarin cewa wani abu yaji karar wayarsa ya ciro wayar a aljihunsa ya duba ganin lambar kofur Musa yasa Wahid cewa kinga bari naje Kofur Musa ya iso nake tunanin shike kirana yanzu "To Yaya Allah ya kiyaye ya tsaraminkai take care bye" "Amin ya rabb my wife take care too" Da haka ya murda hannun kofar zai fita ya juyo ganin tana zaune yace "Oh yau babu ko rako" "Eh fushi nake dakai" "Baki ya dan tabe yace kina fushin dani kika yi dogon fira dani" "Ke dai kawai bakyason fita waje zaki ce" "Kaje yana jiranka fa?" "Shi waye mai jiran nawa?" "Kofur Musa mana" "Shikenan take care" ya fada da murmushinsa ya fice" Itama kallonta kofar yayi bayan ya FIFA da murmushi akan fuskarta sai tace batajin a yanzu tana da sauran damuwa ta samu miji na gari mai kaunarta damuwarta daya sanin mai Umminsu tayi ta zama saniyar ware a cikin danginsu har ake mata kazafin karuwace don tana da yakinin shine ya ruguza waccen maganar aurenta,sai kuma son da take tasan mainene alakarsu da Danbatta family,dukda wannan yasa take rayuwa da Wahid bawai don soyayyarsa ta mamaye zuciyarta ba illa iyaka yayi mata halarci ya kauda kansa ga wancen abubuwan da ake fada akan mahaifiyarsu ya amince ya aureta dukda yadda ake fadar Umminsun takasance,wasu hawaye masu dumi ta goge wannan shine kawai damuwar da tayi saura a zuciyarta ***** "Ra'uf Koda maganar saka sunansa da Ahmad yayi ga dansa ta riske sa bakaramin farin ciki yayi ba a ransa yana ayyana cewa Rufaida da Ra'uf sun hadu a wata duniyar da babu wanda ya isa ya rabasu saboda sunzo a ciki daya tabbas yasan san Rufaida da kaunarta ba zasu gushe ba a zuciyarsa har zuwa ranar da zaiyi numfashi na karshe ya rasa gane wannan soyayya wacce iri ce,sai dai yace Allah ne ya hadata kawai bawai mutum ba,Dukda yadda iyayensa keso yayi aure yaki yi sam,gani yake baida lokacin ma tsayawa kula wasu 'yammata don gaskiya aure ba shine a gabansa a lokacin ginin asibiti da ya fara a Nigeria yanzu shine a gabansa ba maganar aure ba yanzu abinda ya damesa ya bunkasa kasarsa ta hanyar cigaba ta kowanne fanni shi kuma aure yasa a ransa lokaci ne,yanaso daya kammala gininsa ya koma gida ya samu ya sami nitsatstsiyar mata a kasarsa ya aura don shi gaskiya baya kawo wa ransa zai auri Rufaida saboda tayi aurenta ita tuntuni harma yaga kyakkyawan Baby boy dinta a Dp din Samiha daya na gani yaga kamar yaron da Wahid da bai manta kamanninsa ba shekarun baya da suka wuce ,Husna ta koma Nigeria a can zatayi bautar kasarta,data gama kuma za'ayi bikinta zata auri cousin dinsu Bello,Hajiya tayi tayi Ra'uf yazo Nigeria yaki sam bayajin son zuwa kuma koda ma zashi don su Yakumbo da Mama suwaiba zashi ba dan itaba *********** "Rufaida meyasa ne Umma take so ta matsamin akan auran nan,yanzu fisabillah hakan ya dace" Rufaida jin maganar da Wahid keyi yasa ta aje wayarta gefen gado ta maida kallonta gare sa "To mene ne ya faru kuma?" Yace "Sam ta kasa fahimtata tace min nine na fadawa Abba karya amince da auran nan vayan kuma ,ba mu taba maganar da ta shafi aurena da Ruqayya ba nida Abba,amma zancen da ni ke miki yanzu ya kafe kaida fata ba zan aureta ba,ita kuma Umma ta kafe sai nayi auren nan" "To yanzu ya za'ayi" fadin Rufaida "Ina so zanje gida gobe saboda inaso Umma ta fahimceni maganar waya bazata wadatar ba"fadin wahid " amma Yaya gobe gobe banyi kusa ba" "Wanne kusa kanwata kinsan dai wacece Umma idan banje ba kinsman abinda zaije ya dawo ba karami bane" "Eh da kuma hakan,Allah ya kaimu lafiya" jin karar wayarsa yasa shi mikewa ya karasa inda yasa caji a falon ya dauko wayar ya dawo inda yake,ganin mai kiran ya sashi saurin dagawa ganin Ummansa ce "Assalamu Alaikum Umma ina yini" "Wa'alaikumus salam lafiya lau ya aiki" Bai dama tsammaci za ta ce yasu Rufaida ba hakan yasa shi saurin ce mata "Alhamdulillah ,Umma" "Yawwa dama so nake na fadama inason ganinka gobe,saboda Ina so Bukar ya amince da auran nan kana sane indai ba amincewarsa babu abinda zai yiyu" "Eh hakane,Umma dama yanzu make maganar zuwa na da Rufaida" Jin ya anbaci Rufaida yasa ta jan dogon tsaki dan ita ko sunan Rufaida bata so ma a fadama ta shigar mata cikin rayuwar danta wato ma saboda zaizo gida sai yayi maganar da matarsa kila ma har shawara ya nema,tsaki taja a karo na biyu tace "Ok" Wahid dinne yace "Yasu Wasila da karamar kanwata" "Wacce kanwartaka kuma kana da kanwa da ya wuce Wasila ne" "Eh mana Umma,akwai 'yar Aunty da Mama" Tsaki tayi tace "Naji" "Yawwa,Ummi kema yaushe zaki min kani,ko kanwa" "Kamar ya ai yanzu nabar muku kudai kuyi,yanzu idan ka auri Rukayya,ai shikenan zan fara tara jikoki,kaga ai gwara na bar muku tunda wuri" "Eh hakane gama ,Umma amma ga Yasir nan ai yafara zuwa" Hajiya Jamila jin an sako maganar Rufaida da batasan jinta sam yasa ta cewa "Kaga sai anjima"daga haka sukayi sallama ya katse wayar Ya dubi Rufaida yace " Allah Rufaida banason zuwa Zariya akaran kaina dandai akwai muhimmanci a zuwan nawa,amma inajin kar naje Umma tace min na sake ki,jikina yana bani wani abu zai iya faruwa Indai nasanar da Umma abinda Dady yace" Rufaida ta kallesa da hawaye ya taru a idonta tace "Yaya Wahid,ka daina wannan tunanin ni dakai mutu ka raba,nasan Umma ba zata ce haka ba" "Idan to batace hakan ba, idan kafin goben na mutu fa,Rufaida banaso na mutu na barku" Rufaida da ta fara hawaye tace "Yaya dan Allah ka daina maganar mutuwa,bazaka mutu ba,tare zamu mutu" Murmushi Wahid yayi yace "To zan daina amma kinsan da cewa mutuwa dole ce duk mai rai zai zama gawa,kuma na fiso na rigaki mutuwa saboda ke din yanzu kikasa kafa a cikin rayuwarki ni kuma nafara kwana biyu" "Eh,a'a Yaya ni baka tsufa a guri na ba so nake mu rayu mu mutu tare" Dariya yasa ya nuna ta "Oh kinganki dama kina sona sosai haka" Murmushi tayi tace "Yaya idan banso mijina ba wazan so" "Ra'uf mana ai ni duk a tunani na gangar jikinki na aura" Harararsa tayi tace "Kai Yaya,Wannan Ra'uf yaki fita a ranka shi yana can ya manta da shafin rayuwarmu kaiko kana tason sawo mana shi a cikin rayuwar mu,bayan ba muda alaka dashi" "Rufaida kenan ba zaki fahimci yadda nake son Ra'uf a raina ba inajinsa har a jinin jikina" "To fa saboda me" fadin Rufaida tana zaro ido "Saboda inason abinda kikeso Rufaida nasan kin soshi koda a yanzu baya ranki,kinsan mene fata na" Kai ta girgiza yace "To bazan fada ba ma nafasa" "Yaya Dan Allah ka fadamin" Yayi dariya yace" badai shagwaba zaki ba to dama abinda zance shine koda bana raye ki zauna da mutumin da zai zama sanadiyyar haska rayuwarki" "Oh Yaya kwanaki ma fa ka fadi haka,dan Allah kadaina fadar mutuwa duk sanda bana tare dakai zan zama banida ragowar farin ciki" "Ai hakane Rufaida zaki samu haske da zai haskaka ki a rayuwarki,Rufaida mutuwa dole ce,amma tunda bakyaso na daina fada yanzu dai ina Yasir" Rufaida da murmushinta tace "Ya kwanta a falo,bari naje nadaukosa" "Kyale kawai zanje na daukosa yau ni zan masa shirin barci ma" "Yaushe rabon duniya da ayya raye yau wacce rana m Yace " asabar" yana kokarin fita da dariyarsa *JININMU D'AYA* By Sadiya Khalil 48. DAWOWA LABARI *RUFAIDA POV* Abdul Malik ne ya dubi Rufaida da suke zaune a harabar gidan suna fira kasancewar yau an tashi da zafi garin kuma ba wuta babu inji yara kuma duk sun tafi Islamiyya Tahfiz da yau lahadi babu boko harda Yasir suka tafi Abdulmalik din ya soma magana "Rufaida yau fa naga mai kama dake" "Ni kuma yaya AbdulMalik" Rufaida tayi maganar da mamaki akan fuskarta Ya sake kallonta yace "Kwarai kuwa,da farko dana ganta tana tafiya tunani na bani yayi kece ma,harna fara tunanin maiya faru a kadunan kikazo saida ta juyo da fuskarta naga bake bace,tafiyarku ce sak daya amma a fuska bakwa kama sai dai a fisge" "Oh kodai Samiha ce,ana cewa muna kama nida ita?" Harararta yayi yace "Samihan ce bansani ba" "Aunty Amarya tasa vaki a firartasu tace " oh maiyasa baka tsaya yi mata magana ba,kaga aida ko lambarta saika samowa Rufaidan" AbdulMalik yace"wallahi kuwa Aunty kinga dana hada su kawance,amma zan rika bi ta hanyar kozan sake ganinta,kamar tayi yawa duk da babu a fuska amma akwai a siffar jikinsu" Hajiya Jamila da take jin firarsu tasa baki gurin cewa "ai babu mamaki ko a cikin yawon da akayi ana abun kunya aka sameta" Jin maganar Hajiya Jamila da Rufaida ta jita kamar dirar mikiya yasata mikewa daga gurin gaba 'daya kanta a kasa Ganin Rufaida ta mike daga gurin tayi shigewarta falon gidan kallon data tarar a kunne shi ta kashe tayi kwanciyarta da ita sai yanzu tasan andawo da nepar data san an dawo da wutar ita kam mai zai jama ta zama a can sam shiyasa batasan zama koda a fall ne indai Hajiya Jamila na gurin dan saita fadi bakar magana akanta Ganin Rufaida tabar gurin yasa AbdulMalik kallon Hajiya Jamila ya soma magana "Haba Umma hakan baida ce ba" Hajiya Jamila ta hararesa "To ubanka nace da baida dace ba a cikin maganar,don na fadi gaskiya" AbdulMalik zai sake magana Hajiya Kubra da sai yanzu tasa baki tace "Kaga AbdulMalik kyaleta karka sake yin wata magana" Hajiya Jamila ta harari Hajiya Kubra tace "Kinga nifa banason shishshigi 'dan kine ko nawa,ki barsa ya fadi abinda zai fadama na,a haka a nuna ana sonka sai an ware a fara gulmarka" AbdulMalik ya dubi Hajiya Kubra yace "Mama don Allah kar kice komai" Ya maida dubensa ga Mahaifiyarsa yace "Haba Umma daga ban hakuri" Hajiya Jamila tace "To ubana,hana ni na maida martani" Ganin ba zata fasa maganar ba yasa shi mikewa ya bar gurin don yasan indai yana nan ba zata gaji da magana ba ya nufi falo A falo ya sameta a kwancea a kujera kamar mai varci ammma da gani ba barci take ba zama yayi kujerar dake kusa da wadda take kwance yace "Rufaida kiyi hakuri don Allah,nasan Umma ba ta kyauta ba" Murmushi tayi ta bude idanunta wakeke waken da Rukayya ta fito daga kofar kitchen da Kofi a hannunta tanayi shi ya tsaida maganar da Rufaida Rukayya ta kai kallonta ga Rufaida da take kwance da hankalinta vaikai ga ganin AbdulMalik ba Rukayya ta fara magana cikin bacin rai "Malama ke wacce irin kidahuma ce ya zaki zo ki tarar na kunna kallo ki kashe min ki kuma kwanta wa mutane shame shame a kujera kamar ta gidan ubanki,sakarai kawai ana mata kora da hali kina nacewa mutane..." Ganin Rukayya ba zata yi shiru ba yasa AbdulMalik gyaran murya da zuciyarsa take tukuki jin maganganun Rukayyan Rukayya da sai yanzu ta san AbdulMalik na gurin tuni ta fara zaro ido ta soma magana "Yaya AbdulMalik wa...." cikin bacin rai AbdulMalik ya nuna nuna Ruqayya da ya tsa yace "Ke daka ta munafukar banza ke waya kai kidahumanci,inba kida humanci ba mai zai kawo mace budurwa gidansu saurayin da taso don ya mutu kuma bama zuwa gaisuwa ba a'a zuwa a zauna kamar wadda tarasa mafadi,kuma kenan gidan ubanki ne? da kikazo kikayi shame shame kina cin arziki mai kika hada danan gidan,to ita din ta fiki matsayi da komai anan gidan,donke arzikin Umma kikeci,don koni Rufaida ta fiki matsayi a zuciya ta" Cikin bacin rai da hawaye taf idon Ruqayya tace "Naji ta fini matsayi anan gidan amma ita da ba'ada tabbaci akanta shine,zaka fadamin magana akanta" "Tabbacin ubanki ne va'ada shi akanta,ke ba'ace ba'ada tabbaci akan Ku ba,saike zaki fadawa wata"fadin AbdulMalik "Wallahi mu anada tabbaci akanmu,ita da uwarta take karuwa fa niko mai uwata tayi wallahi muna da banbanci nida ita fiye da tunanin mai tunani" AbdulMalik jin maganar da Rufaida keyi yasa ran Abdulmalik ya kara baci ya mike ya nufi Rukayya zai doketa Rufaida da hawaye ya cika idanunta ganin haka yasa Rufaida mikewa tayi gurinta tace "Yaya AbdulMalik karka doketa kaya hakuri" Hannu AbdulMalik ya dagawa Rufaida ya shiga dukan Rukayya Da kyar Ruqayyan ta kwaci kanta tayi gurinsu Hajiya Jamila tana kuka wiwi Abdulmalik ya bita shima Rufaida ta biyo bayan sa tana kiransa ya dawo amma baya jin ma mai take cewa tana hango Rukayya tana maida lumfashi yayi kanta ya fara dukanta cikin zafin zuciya ba tare da ya bi ta takan mutanan dake rirriqesa ba Tsawar da Abba Bukar ita tasa AbdulMalik sakinta yana maida lumfashi Bai saurari kowa ba ya fara tafiya da niyyar barin gurin Abba Bukar yace "Dawo nan" Dawowa yayi ya sunkuyar da kansa "Rukayya me ya hadaku"cewar Hajiya Jamila Rukayya tana rusa kuka ta dago kanta ta nuna Rufaida wata hararar Rufaida Hajiya Jamila tayi Rufaida ganin haka yasa Rufaida kai kallonta kasa Ganin ta nuna Rufaida Abba Bukar ya kalli Rufaida yace " Rufaida mai ya hadaku da Ruqayya?" Idon Rufaida ne ya ciko da hawaye Abba Bukar yace "Kiyi min bayani ina sauraranki,banaso wani hawayen banza kiyi laifi kizo kina hawaye" Jin maganar Abba Bukar yasa Rufaida goge hawayenta ta zayyana masa duk abinda ya faru Abba Bukar yana gama ji ya dubi Ruqayya cikin bacin rai yace "Yanzu Ruqayya dama baki da mutunci ina ganin kamar zaki fita daban a cikin 'yan uwanki,shiyasa ma ke na amince ki zauna na lokacin da Jamila tace min zaki yi wato ashe har kin fisu ma,dama zaman danki kuntatawa Rufaida kika ce zaki yi" Rukayya tace "Abba dan Allah kaya hakuri ba haka nake ba Aunty Jamila ce take cewa na rika yi mata" Abba Bukar ya jinjina kai yace "Wato ita ke baki labaran karya da karai rayi akan Rufaidan ma ko?" Rukayya ta girgiza kai tana kallon Hajiya Jamila da take girgiza mata kai kar tace ita ce "Ki fadamin gaskiya bana son karya ita ke baki ko kuwa kifadamin wake baki" Abba Bukar yayi maganar yana kallon Hajiya Jamila yadda take girgiza wa Ruqayya kai Rukayya da duk ta tsorata tace "Eh Abba ita ce,tuntuni take bamu wannan labarin" Abba ya jinjina kai ya kalli Hajiya Jamila ya soma magana "Jamila kin bani mamaki amma ba abun mamaki bane nasan fiye da haka ma zaki yi saboda bakya tunani kafin ki aiwatar da abu sannan zai wuya idan kinyi badaidai din ba kiyi danasani,amma nasan akan wannan maganar tabbas zaki yi dana sani koba yanzu ba,sannan babu wani matakin da zan dauka akanki amma tabbas ranar dana sani zata zo miki,sannan yau ba sai gobe ba inaso Rukayya ta barmin gida na dama mahaifinta yayi min waya yanaso Rukayya ta koma gida saboda maganar aurenta da zai aurawa dan abokinsa ita da kune kuke ziga yarinyar karta yarda da auren,batun Rufaida kuma baza ta bar gidan nan ba sai sanda na tsara zata bari" Da wannan maganar Abba Bukar ya maida kallonsa ga Abdulmalik yace "Malik nasha fadama kai ba mace bane ka daina shiga fadan mata,banason karajin irin haka ta faru" Abdulmalik yace cikin ladabi "To Abba zan kiyaye insha Allah" amma a ransa baya tunani zai hakura muddin yaga ana kwarar Rufaida don shi mutum ne da bayason zalinci Da haka Abba Bukar ya bar gurin Abdulmalik da Rufaida suka take masa baya Hajiya Jamila jikinta duk yayi sanyi ta kama hannun Ruqayya,Ruqayya tayi saurin fincikewa daga rikon da Hajiya Jamillar tayi mata ta bar gurin don gani take duk Hajiya Jamila ce ta jawo mata koma mene yanzu ba ta da wata daraja a idon kishiyoyin Hajiya Jamila dama Rufaida ga uwa uba Abba Bukar,da gatanta da komai bawai arziki za'a nunawa mahaifinta ba bakomai ba amma ta ja an yi mata wulakanci har haka kum AbdulMalik ne yayi mata suma sauran matan gidan sumi sumi suka bar wajen aka bar Hajiya Jamila ita kadai ita mikewa tayi ta bar gurin.A daki ta samu Ruqayya tana hada kayanta Hajiya Jamila ta dafa Rukayya tayi saurin cire hannun Hajiya Jamila daga jikinta ta soma magana "Kinga Aunty don Allah ki kyaleni,kinsa an cimin mutunci,nima kuma kina zuga ni na ciwa wata,dama nina gaji da zaman gidan nan koda ba'a koreni ba,tafiya zanyi,gwara naje nabi umarnin Abba da na cigaba da zama anan,ki riqa gulmata na tare a gidan ki bayan wanda nake so dinma baya duniyar,amma kinsa ni na zauna ina goga kishi da matarsa bayan ita bata damu da muba" Hajiya Jamila da ranta ya fara 'baci ta kalli Rukayya tace "Kinga Rukayya a haife dai kinada tabbacin nayi 'yata hudu ma dake,ba zai yiyu ki zauna kina jeramin magana ba nina jawo miki dukan?ince dai ke kika jawo wa kanki,sannan dama fa ba wanda ya rike miki kafa kuma karki min sharri ni bance ki zauna a gidana ba,dama a zagwaigwai dinki ne yasaki zama a gidan nan,amma sanin kanki ne na nuna miki banaso saboda nasan baki da hankalin iya zama da mutane,baki iya rufe sirri ba,kinzo ni kin hadani da miji na cikin kishiyoyi kin kwance min zani" "Au haka zaki ce,kin mata harna hada kayana kila kika ce na zauna,ke ai abinda kika yi na fada nifa kinsa danki ya kwance min zani a kasuwa ya kuma yimin shegen duka kika zaunar dani" "Karfa kimin rashin kunya Rukayya ni zan sa AbdulMalik ya doke ki bakin halinki dai yasa ya doke ki" Dariya Rukayya tayi tace "Su bakin hali manya rashin kunya manya,aishi dama gwano bayajin warin jikinshi,nifa bari kiji baki isa ba wallahi ki fadamin magana na kyaleki,idan kina yiwa Rufaida tana kyaleki,to ni baki samu wannan damar ba ba kuma zaki sameta ba" Haka dai suka cigaba da musayar kalamai tsakanin Ruqayya da Hajiya Jamila saida Hajiya Kubra ta jiyo tazo ta yi musu magana ta kuma shiryawa Rukayya kayanta haka aka rabu da Ruqayya da Hajiya Jamila kaca kaca harda su gore gore (to dama ba dan Allah aka shirya zaman ba) Da Ruqayya ta fito saida ta shiga dakin Rufaida ta shiga da sallamarta Rufaida ta dago da kanta daga kallon wayar da take ta yi murmushi ganin Rukayya ce ta amsa mata sallamar jikin Rukayya a sake ta karaso inda Rufaida take zaune a kujera itama ta zauna kusa da ita ta kalli Rufaidan ta soma magana "Rufaida don Allah ki hakuri ki yafemin abubuwan dana rika yi miki Wallahi Umma ke zuga ni" Murmushi Rufaida tayi tace "Haba Rukayya karki bata bakinki nidama ban taba rikonki da komai ba" "Yawwa Rufaida nagode" "A'a ki daina yimin godiya,yanzu yaushe ne bikin naki ban taba jiba ko a firarku keda Umma" "Hmm kedai bari nice dama banason auren da tuni ma anyi har ankawo kudi fa jin yaya Wahid zai yarda da auren my shine naki yarda asa ranar,to jiya Abba ya kirani yace na shirya na dawo gida,shi bazan bashi kunya ba yasa bikina nanda wata biyu masu zuwa" "Allah sarki,a ina zaki yi auren?" "Adamawa ne" "Lah kinga inada kawa tana aure acan, zan hadaku insha Allah" "OK 'yar inace?" "Kano" "OK,ki bani Lambarta" Rufaida ta duba wayarta ta fado mata lambar Nasiba tasa a tata wayar tayi saving daganan Ruqayya ta amsa ta Rufaidan taayi saving da haka Rukayya ta mike tana cewa "To Rufaida nizan tafi,sai kinzo biki na nasan sannan kin dade da fita takaba tunda yanzu ma baifi saura kwana goma ba ki fita" "Eh hakane,amma kinsan indai na koma Kano ba lallai Abba ya yarda" "Nasan zai yarda insha Allah,sai dai.idan kece bazaki zo ba zaki ce" "A'a zanzo dama yardarshi nakewa kokwanto " "Idan lokacin yayi zan kira ki ki hadani da Ummi kinga saita fadawa Abba" "Murmushi Rufaida ta yi mata tace " to shikenan" "Kinga zan tafi va muyi sallama da yasir ba" "Eh wallahi babu rabo hakanan suka jashi Tahfiz yau din" "Babu komai Idan kunzo biki zan gaji da ganinsa ma indai da zan iya hakan" Dariya Rufaida ta yi tace "Oh saikace idan munzo din shekara za muyi" Da haka Rukayya ta fito sukayi sallama da Rufaida Rukayya tana sake rokar Rufaida ta daure tazo bikinta Bayan fitar Ruqayya Rufaida ta dan goge kwallar data taru a idanunta bata taba tunanin abubuwa zasu sauya lokaci kusa haka va,yanzu ko a mafarki idan aka ce mata Rukayya zata sota sai ta Musa saboda irin kiyayyar da Ruqayya ta rika nuna mata,lallai Allah shine mai juya al'amura tana da yakinin watara na komai zai zama tarihi,insha Allah kamar yadda kiyayyarta da Ruqayya ta zama labari.[9/25, 10:23 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil 49. RA'UF POV "Ammi na yunwa nake ji" Ammi Asma'u ta juyo ta harari Ra'uf ta cigava da tafiyar da take "Ammi magana fa nake,ina jin yunwa,ki samamin abinci na ci" Ra'uf ya sake maimaita maganar Sai sannan tace "Ni zan kawo ma abincin kenan,kana kwance sai dai ayi ma komai" "Oh Ammi yanzu ba zaki kawon ba,shiyasa banso aka tafi da Safiyya ba da tuni ta kawomin" "Ita ce zata jure dama" "Au banda ke Ammi,shikenan bari na kira Dady a waya na fadamasa" "Au Da Dadynku zaka hadani yaro ka dade baka hada muba". Da ganan ta bar gurin Ra'uf ya saki murmushi ya tashi zaune daga ki shingidar da yayi jikin kujera ,wayarsa ya jawo ya danna ya kara a kunne a ringing biyu aka dauka muryar Safiyya ta shiga kunnensa da ta soma magana da yaran indiyanci da kuma turanci "Assalamu Alaikum,my Yaya" "Wa'alaikumus salam,kanwata ya gida da kowa da kowa" "Lafiya kalau" "Ya Nigeria,ina daru Hajiya" "Tana lafiya,amma Hajiya fa ta rage daru,muna zuwa ta fara korafi kai yaushe zaka zo" "Kina nufin bata bata ranki ba" "Eh tanbayarta taka ce kawai muna zuwa" "Kai amma naji dadi" "Yaya ysushe zaka zo,wallahi sun damu kazo Family 'dinka,gaskiya suna sonka sosai, dana ga yadda suka damu dakai nima sai nakeji ina ma ace watarana na hadu da nawa Family..." Ra'uf da hawaye suka tarar masa jin maganar da Safiyya keyi yace "Haba Sophie maiyasa kike da son dawo da abinda ya riga da ya wuce,mune familynki a yanzu haka,dan Allah ki cire komai a ranki" "To shikenan Yaya insha Allah" "Yawwa kanwata,yanzu kina ina ne" "Ina gidan Aunty Malika a can na sauka" "OK ina Auntyn" "Ta shiga kitchen" "Oh shine ba zaki je ki taya ta aiki ba" "Oh yaya kasan nafi iya abincin nan,karna mata jagwalgwalo tace ba dadi" Yayi dariya yace "Oh Safiyya idan kinyi aure fa,kuma kinsan dai a gida za'ami ki aure gwara tin wuri ki sauke wa kanki iyayi" "kai Yaya ba fa iyayi bane" "To menene" Canza maganar tayi tace "Yaya jiya munje asibitin daka gina da Abba ,yayi kyau sosai ni ban dauka yayi kyau haka ba dana gansa a waya sai da naganshi a fili" Dariya Ra'uf yayi yace "Ya kikaga sunan asibitin yayi kyau kuwa" "Sosai ma RJM DANBATTA" Dariya Ra'uf yayi yace "Yawwa kanwata idan zan sake gina wani,SJM DANBATTA zansa" "Kai amma naji dadi Yaya" "OK yaushe zaki tafi Kano" "Abba yace tare zamu tafi,sai ranar Asabar ta sama zai kaini 'danbatta nayi kwana biyu" "Ok Allah ya kaimu" Sun jima suna waya daganan su kayi sallama suna gama wayar kiran Ahmad ya shigo wayarsa ya daga Ahmad yana jin Ra'uf ya daga yace "Oh kodai da budurwa kake waya ne,ina ta kira ana suna nuna min user busy" Ra'uf yayi Dariya yace "Ni budurwa,Safiyya ce muke fira" "Ok sun tafi Nigeria ko?" "Eh mana,kai yaushe zaka koma ne,kaje garin mutane kayi zamanka" "Wallahi sun hanani tafiya sun riqeni" "Oh kai tafiyarka mana" "Eh dama haka kawai za muyi shiryeye muke, Ni kaina nayi kewar gida over" "To yanzu ya little Rufaida ban tanbayeta ba" "Tana lafiya wato bazaka tanbayi little ba sai Rufaida" "Eh mana,ai ita takwarar masoyiyar farko ce,ko zaku bani aurenta tunda na rasa waccen Ahmad yayi dariya yace "Tsohon zan bawa 'yata sai dai kaje kayi zawarci gurin Rufaidan" "Ina ma za'a bani ita yanzu da sai naje wallahi" "Lallai Yaya Ra'uf bazawarar zaka aura,sun hana ka aurenta tana budurwa yanzu kawai tana bazawara kaje ka nemi aurenta" "Eh mana dama Allah yayi bani zan fara aurenta ba ne,kuma laifin fa su Abba Sule ne sune silar da aka hanani aurenta" "Haka dai kake tunani,amma dai sunyi niyyar dama aura mata dan uwanta ne kawai" "Karkayi wannan tunanin Ahmad,haka Allah ya tsara dama" "Haka ne kam,wallahi Yaya Ra'uf Rufaida abar tausayi ce,gaba daya abinda 'yan uwanta ke mata basa kyauta mata gashi Umminta bata isa tayi magana ba,Samiha tana bani labarin komai,kwanaki ma har kudi Samiha tasa na turawa Rufaidan ni na rasa meye matsalar" Ra'uf da jikinsa yayi sanyi yace "Maike faruwa ne Ahmad kayi min bayani ba Rufaidan na kano ba" "Ko d'aya tana Zaria" "Amma su iyayenta sun manta da abubuwan da suka rika faruwa suka barta acan" "Zumunci suke tunani shiyasa suke yin shiru nake tunani" Cikin bacin rai Ra'uf yace "An taba zumunci da zalinci,ni wallahi mutane mamaki suke bani don da bana ka bane idon yana tare dakai kaita zalintarshi" Da haka suka cigaba da tattaunawa akan maganar RUFAIDA AbdulMalik da shigowarsa falon kenan ya idanunsa suka sauka ga Yasir yana zaune shi ka'dai a falon sallama yayi Yasir da yake game a waya ya dago kai yana murmushi yace "Wa'alaikumus salam,oyoyo Dady Malik" AbdulMalik yace "Ina Mamarka AbdulMalik yayi maganar yana kokarin zama a kujerar falon " taje kitchen ta zubo min abinci" "Oh kaifa ina ka baro ci ina zaka ci ne" Yana cikin maganar Rufaida ta dawo falon da plat da abinci a ciki idonta ya sauka ana AbdulMalik AbdulMalik ya sakar mata murmushi itama murmushi tayi masa ta mikewa Yasir abinci ta nemi guri a kasan carpet ta zauna tare da cewa "Sannu da zuwa Yaya Malik,ba dai harka dawo ba?" "Yawwa Rufaida,Eh nadawo yau kinsan friday" "Au nama manta,bari na kawo ma ruwa,a'a bar abinki,na biya gidan Aunty Zainab daga can ma nake nayo Zaria" "Ok" "Baki tanbayeni labarin,mai kama dake ba,munfa sake haduwa yau nagansu ita da Auntyn ta a unguwarsu Aunty Zainab" Murmushi Rufaida da mamaki tace "Dan Allah fa" "Yace " serious har magana mu kayi" "Please ka bani labarin ya akai kuka hadu" Murmushi AbdulMalik yayi yace "Bayan na fita daga gida naje gurin aiki shine nayi kokarin biyawa gidan Aunty Zainab,kafin na shiga Layin su Aunty Zainab na ganta tsaye kofar wani gida a bakin titi shine na tsaida mota ta a kusa da gidan na fito na karasa gurinta na mata sallama,bata yi min magana ba sai dai naga alamun amsawar a labbanta ina cewa Ranki ya dade wata mota ta karaso ta shiga shine na bi bayansu a mota ta har saban kawo" jin yayi shiru yasa Rufaida cewa "Uhmm ina jin ka" "Ke kinga kofar gidan da motarsu ta tayi parking kuwa,ina ganin kyau da tsarin gidan nasan dole yarinyar tayi jin kamshi indai gidan ya kasance gidansu ne,ina gani aka bude musu gate din suka shiga ya rufe ni kuma ina ganin haka na fito a mota ta na kwankwasa kofar gate din maigadin ya leko yace min was nake nema nace masa budurwar da suka shigo nan gidan yanzu a mota,maigadin ya kalleni sosai yace na shigo,gurin kallon gidan na 'bige Rufaida" Rufaida tayi dariya tace "Yanzu akwai gidan da zai rudaka Yaya Malik,bayan kuma gidanku mai kyau ne sosai" "Ke ana miki maganar gaba fa da gabanta akace fa,kuma kinsan komai gareka akwai wanda ya fika haka rayuwa ke tafiya "Eh hakane To cigaba da bani labari na kagu naji koda sunanta ne" Ya cigaba da cewa "Maigadin ne yayi wajensu da har sun fara fitowa daga motar ita magana naga yayi wa wadda nagani din kamar ba zata zoba naga wata mata ta mata magana,sai gata ta biyo bayan maigadin,maigadin daya rigata karasowa yace min cikin girmamawa " yallabai gatanan"yana barin gurin ta karaso tayi min sallama muka gaisa"nace mata Suna na AbdulMalik da wata kanwata dama naga suna kama shine na mata magana"tace min "Ok nagode,amma yanzu ina sauri ne wani lokacin saika hadaDariya kanwarta ka ko a waya ne nace to ai bani da number dinta"shine ta samin ta fadamin sunanta Safiyya amma fa yarinyar batajin Hausa?" Dariya Rufaida tayi tace"sai kaita mata turanci" "Au van dake,anjima zan hadaku a waya" "To Allah ya kaimu lfy" Daganan suka cigaba da firarsu zuwan Hajiya Jamila falon shiya tsaida firarsu,Rufaida ta mike taja hannun Yasir suka zasu bar gurin da ta fara ganin hararar da Hajiya Jamila ke aika mata tun kafin aje ko ina,don tunda abin da ya faru dasu da Rukayya komai ya kara sauyawa don habaici zagi bakar magana shan su take gurinta,da yanzu yau kawai ya rage mata tabar gidan zuwa gobe AbdulMalik ya tsaida Rufaida da cewa "Ina zaki ne,muna fira" "Firar me kukeyi kuma,nifa AbdulMalik vangane maka ba fa"Hajiya Jamila tayi maganar rai bace tana kokarin zama Jin haka yasa Rufaida saurin barin gurin tana ji AbdulMalik na cewa "Kamar ya Umma vaki gane minba" Daganan dakin Hajiya Kubra suka shiga aka bude faifan fira Sadiya Khalil🥰 [9/26, 9:37 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil 50. Masoyan wannan littafin ina godiya gareku,Allah ya hadamu da alkhairan dake kunshe cikin wannan littafin. RUFAIDA POV "Wallahi ina murna yau matuka Samiha Rufaida da take kwance kan gado da waya a hannunta take furta hakan Wayar da take a handsfree Samiha tace " to fa murnar me kike yi" Tsaki Rufaida tayi "Kiji 'yar rainin wayau kin manta gobe zan koma gida" "Na shafa'a 'yar uwa sorry,ke dawa zaki tafi ne?" "Ba muyi maganar da Abba Bukar ba bai shigo gida ba" "Ok to ko Yaya Samir na masa waya ya biyo tanan daga sokoto yazo ku tafi tare" "A'a ki barshi nafi tunanin Abba zaisa Yaya AbdulMalik ya kaini gida" "To badamuwa Allah ya jikan Yaya Wahid yasa can ta fiye masa nan,Rufaida!na rokeki ki cire duk kan damuwar mutuwar nan a ranki duk da nasan dole ki damu tsawan lokaci amma ki tuna da cewa ubangijin da haliccesa yafi ki sanshi shiya karbi kayansa,haka dukkanmu lokaci muke jira shida ya tafi vaiyi gaggawa ba mu da muke raye amu yi jinkiri ba" Jikinta duk yayi sanyi ta fadi "Hakane Samiha,Allah ya sa muyi kyakkyawar cikawa" "Amin kawata, sannan sai maganar aure don Allah idan kin samu miji kin tabbatar da nagartar halayyarsa ki auresa ki zauna gidan mijinki kiyi hakuri bana so rayuwarki ta cigaba da kasancewa kamar ta yanzu inaso ki samu cigaba ko yaya ne"fadin Samiha " Hakane kawata nagode da nasiharki"Rufaida da hawaye ya taru idonta ta fadi haka hakika ita tasan taronsu da Samiha na da ban ne,Samiha ta dace a kirata kawa ta gari,batun yau tasan da hakan ba a'a tuntuni kafin su kai ga aure bayan sunyi saboda kaunar da take mata tasa wa 'yar cikinta sunanta ba tare da tasa na mahaifiya ko 'yan uwa gare ta ba,lallai duk inda kawa ta gari takai Samiha takai harma ta zarce,maganar da Samiha keyi ta katse tunaninta "Godiya ni dake Rufaida ai babu ita,yinta sabo ne fa,idan baki sani ba" Jin maganar Samiha ta karshe yasa murmushi subuce mata tare da cewa "To shikenan kawata,ina takwarata" Batare da taji amsar Samiha ba ta jiyo sallama a falo "Kawata zan sake kiranki anjima" daganan ta katse wayar ta ajiyeta saman drower din gadon ta yafa mayafi ta fito falon tana amsa sallamar Umar ta gani 'dan wajen Hajiya Kubra ya rissina tar da cewa "Yaya Barka da dare" Murmushi tayi "YawwaUmar" Umar yace "Abba ke kiranki yana bangarensa" Tace masa "To muji kawai"tare suka kira har bangaren Abba Bukar din sallama suka yi ya amsa musu tare da yi musu izinin su shigo a falon suka same sa zaune a kujera hankalinsa nakan wa'azin da ake a Tv zama suka yi a kasan carpet Umar ya dago kansa ya kalli Abba bukar "Abba ga yaya Rufaidan nan na kira ta" Sai sannan ya dago kansa daga kallon wayar da yake yace "Yawwa Umar" Umar din yana jin haka ya mike ya basu guri Ganin fitar Umar Abba bukar ya kalli Rufaida ya soma da fadin "Rufaida duk kan mai rai mamaci ne nasan kinyi rashin miji nagari kamar AbdulWahid,sai dai hakuri,da kuma fatan Allah ya sake baki kamarshi ko wanda ya fishi,sannan jiya munyi waya da Kabir akan wani satin zai sa mota ta kawo kayanku kaf na Abujar,kuma ke nasan gobe zaki koma gida,don haka kayanki dana dakinki za'a kawo miki su,ha'de da tumunin takabarki da gadon Yasir duk AbdulMalik zai kawo muku,Abdul saiya cigaba da kularmuku da dukiyar ku tunda yayi girman da zai iya rike dukiya a hannunsa" Rufaida kanta a kasa har sai da taji Abba ya gama maganarsa ta dago tace "To Abba,Allah ya bar zumunci ya jikan wadanda suka rasu" Cikin jin dadi Abba Bukar yake cewa "Amin Rufaida,yawwa batun tafiyarki AbdulMalik yace baya jin dadi,Hassan ko Hussaini sune zasu kaiki Kanon" "To Abba Allah ya kaimu lafiya,shi kuma Allah ya basa lafiya" "Amin Rufaida,kije ki hada kayanki,kar dare ya cika yi"Abba Yayi maganar yana jin dadin yadda Rufaida take bata da fitina balle hayaniya,komai nata mai sanyi ne,shiyasa shima bai ki wa AbdulWahid auren Rufaida ba da ya nuna yana santa saboda yasan ita Alkhairi ce ga rayuwar 'dan nasa,maganar ta ta katse tunaninsa " to Abba sai da safe" "To to mu kwana lafiya" Daganan ta fice tana tura masa kofar karo suka so yi da AbdulMalik da yake kokarin shiga falon shi kuma yayi saurin ja da baya yana dadin "Subhanallah" Daganan ya fara kokarin mur'da hannun kofar falon Rufaida ta kallesa ganin abinda yake kokarin yi tayi saurin fadin "Yaya Barka da dare" Ya 'dan juyo da kallonsa gare ta "Yawwa Rufaida ya Yasir,ya bangansa ba" Murmushi tayi tace "Tara tayi ai ya kwanta" Ok kawai ya iya furtawa Ganin yanayinsa kamar bayasan firar tayi kokarin barin gurin AbdulMalik ya bita da kallo a ransa yana ayyana,anya zai iya barwa Zahraddin abinda yake so tuntuni tausayi da soyayarta suka wanzu a ruhinsa wato Rufaida,wata zuciya tana ayyana masa taya ma zai iya bari abokinsa ya auri Rufaida da shine tunanin Zahraddin da ya kirasa dazu ya fada masa, munufarsa akan Rufaida, saidai yana tunanin Zahraddin abokin sane tun yarinta sunyi rayuwa ta tausayawa juna hawayen idonsa da suka fara ta ruwa idanunsa ya goge yana ayyana yanzu indai ya amince shikenan,ya rasa farin cikinsa,fasa shiga gurin Abba Bukar din yayi ya nufi bangarensu Washe gari Rufaida ta karaso falon cikin shigar leshi ta riga da siket da hijabinta milk colour dogo har kasa da ya haska farar fatarta kyawunta na Hausa fulani ya bayyana sosai hannunta cikin na Yasir da shima ta shirya sa cikin shadda ruwan kasa mai haske sosai "Badai har kun fito sai tafiya Ba,wannan sammako haka" Hajiya Kubra da murmushi fuskarta take fadin haka Hajiya Jamila ta saki dariya ta saka baki "Ke ko Kubra tayi sammako mana tanaso taje ta tarar da karuwar uwarta" Jin maganar Hajiya Jamilar ta dago ta kalleta ta goge hawayenta tanaji yau bazata hakura a cigaba da fadar aibu akan mahaifiyartaba ai uwa uwace ko ya take kuwa, ta dan yi murmushi mai ciwo ta soma fadin "Umma kenan kalmar karuwanci da kike fada Ummin tayi ,mantawa kikayi kece uwar dakinta a can wajen karuwancin" "Hajiya Jamila jin karashen zancen Rufaida yasa ta mike a fusace tana fadin " Allah ya rabani da karuwanci,ni zaki hada da wannan kalmar shaidaniyar yarinya"tana fadin haka tayo kan Rufaidan zata doketa da sauri Hajiya Kubra tasha gabanta "Laifin mai ta yi miki zaki doketa,kina tunanin ko jikar kice zaki riqa fadar wani abu kan mahaifiyarta tun bata tanka wa ai kinsan wata rana dole ta mayar miki da martani,bare ma yarinyar nan ta kawar dakai fiye da tunani"fadin Hajiya Kubra " ki matsa min a hanya na ko muyi fatarta ni da ke,yar da na haifa zata hadani da kalmar karuwa,karuwa fa!,bama karuwa ba nufinta nice uwar karuwan" fadin Hajiya Jamila ta karasa zancen tana nuna kanta Dariya Aunty Amarya tayi da shewar ta kuma ja tsaki "Dan Allah matsa ki bata gurin Maman Umar,naga karyar haukan matar nan,tazo ta tabata idan ban 'balla banza na zubar ba,banda ke din banza ce ai maganar Rufaida ba karya a cikinta,indai bake ce uwar karuwan ba ina kika san Ummi Hauwa'un tayi karuwancin,indai ba an taba yawata duniyar ba kema"fadin ta tana sake cigaba da wata dariyar Kan Aunty Amaryar Hajiya Jamila tayo a fusa ce tana fadin " Amina ni kika samu damar fadawa magana"daganan ta soma kokarin rike hannunta zasuyi danbe Shekeke Aunty Amarya tayi tana kallonta ta janye hannunta daga na Hajiya Jamilar "Kinga malama karki sake hannunki ya taba nawa ma bare harkiyi kokawa dani,don mijinki da kika raina shine dai-dai dake bani Amina ba,don ni ko maganar banza kika fadamin sai kinyi dana sani wallahi,ke kanki kin san niba ajinji bace,dana san haka kike karya da banyi gigin hada gida da keba wallahi,fitinanniya duk halarcin da mijinki ya yi miki ya debo 'yan uwanki ya rike bai ishe ki ki zauna dashi lafiya ba sai kin masa kinwa 'yan uwansa" Hajiya Jamila jikinta duk yayi lakwas don tasan duk da Aunty Amarya ba girma gareta ba sarai zata iya doketa tayar da ita abanza don ita dama ba karfin gare ta ba,kuma ko magana sai Aunty Amarya ta caba mata wadda bata yi tunani ba,don ita dama wanda ta raina take wa wulakancinta Su Hajiya Kubra da suke tsaye circirko Aunty Amarya da take jiran taji Hajiya Jamila ta fada mata wata maganar ganinta tayi shiru kamar gunki, yasa su kokarin fita raka Rufaida harabar gidanku inda zata shiga mota da Rufaida yanzu take jin zuciyarta wasai kamar ta cire dutse a zuciyarta ta,don koba komai yau ta maida martani inda ya dace ace ta dade da mayarwa. AbdulMalik da yake tsaye bayan kujerun falon da tunda aka fara maganganun yake tsaye yana jinsu shi wata maganar ma dariya ta rika basa ya gimtse dariyarsa ya karaso inda suka bar Hajiya Jamila tsaye kamar gunki ya dafa ta yana fadin "Kiyi hakuri Umma ki zauna" Hannunsa ta cire daga kafadarta "Ka gama dariyarka kenan?" Ya dan zaro ido da mamaki kan fuskarsa shi baisan Ummantasu tasan yana gurin ba "Umma dariyar me?" "Ta gidanku ko nace ta ubanka,da ya gama bata ni gurin matansa,nufinka banga sanda kazo nan bane Malik kenan kanaji ana cin mutunci na,maimakon kazo ka shigarmin saika tsaya yimin dariya,saboda baka dauke ni uwaba ko?" Kai girgiza yana cewa "Ko 'daya Umma ai ita uwa uwace,amma dai ni kinsan bana goyon bayan rashin gaskiya tunda ke kika jasu tunda basu saki a maganarsu ba kika shiga,shigarma da kika yi ba Alkhairi kika fada a maganar ki ba,sannan Aunty Amarya ba karya ta fadaba abinda kike wa Abba ta fada kuma a gaban kowa ma yi masa kike,kuma ba ruwan Abba bashi ke fadamusu ba gani suke kinayi" "To Ubana tsare ni kamin fada,wallahi Malik bansan wanne irin da na haifa ba da baya kishi na....." Jin ta fara sababi yasa shi saurin barin falon ya fice harabar gidan da ya tarar Rufaida har ta shige gidan baya Yasir a gaba ,Hassan da da Hussain ne zai kaita suka tafi wata unguwa da Abba Bukar,yana wajen Boot din motar yana kokarin rufewa alamun ya gama zuba kayan Rufaida dana Yasir sai tafiya AbdulMalik ya riko hannun Hassan da yake kokarin bude kofar mota ya masa ra'da Hassan ya dago fuskarsa ya kalli Rufaida yana fadin "Kace ta kusa zama Auntynmu" AbdulMalik ya maka masa a baya duka yace"kaifa matsalarka ba'a sirri dakai Su Hajiya Kubra suka yi dariya sirrin mai za'ayi dani kuwa bayan abin alkhairi ne ya samu,Aunty kinsan mene ya faru"fadin Hassan Aunty Amarya ta girgiza kai Hassan yace na hannun damar Yaya Malik ne Yaya Zahraddeen,yaga Rufaida yace ya 'kyasa idan ba ita ba sai rijiya" Gaba 'daya suka sa dariya banda Hajiya Kubra da Hussain ya sameta da maganar shifa yanason ya auri Rufaida kuma ita ma ta basa goyon vayan hakan saboda yarinyar akwai nutsuwa da sanin yakamata ga rashin hayaniya kuma uwa uba 'yar uwarsa suce ,to kuma yanzu ga wannan ta fara kunno kai duk da tasan baza'aki na gida aba na dawa ba inba daurowa tayi ba,zata fada Hussain yaje mata da soyayyarsa gare ta ko zai dace,ko a ina ma Zahraddin din yaga Rufaida oho Hajiya Kubra tayi wannan tunanin Rufaida da take jin abunda suke fadi ta danyi murmushi kasan ranta tana tuna kamannin Zahraddin kyakkyawane ba laifi,gashi da son barkwanci,sai dai bataji a yanzu zata iya sa wani a zuciyarta guri kusa saboda tayi babban rashi da haryau bata gama jinyar zuciyarta ba ta rasa miji nagari a rayuwarta,saidai tunowa da Nasihar da Samiha ta mata jiya yasa ta kauda wannan tunanin sai dai zatayi addu'ar Allah ya yi mata zabin Alkhairi a rayuwarta jin Hassan ya tada motar da bata ji shigowarsa ba yasa ta dawowa daga tunanin da ta tafi da addu'a su Hajiya Kubra,Aunty Amarya, AbdulMalik suka bisu dashi suna daga musu hannu har ya fara tafiya ya karasa wajen bakin gate maigadi ya bude musu gate din motarsu ta fita ya bisu da addu'a [9/29, 7:00 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil 51 RUFAIDA POV Jin Hassan ya taka burki yasa Rufaida 'dago kai ta kalli gefen titin da takai kallonta gasu Hassan da ya faka motarsa da Yasir keta barcinsa tunda sukaf fara tafiya shi dama Yasir baida wuyar barci ta soma da fadin "Yaya Hassan ya naga ka tsaida motar,a gefen titi lafiya kuwa?" "Eh inaji dai kamar tayar mu ce tayi faci,amma bari na fita nagani Ku zauna basai kunfito ba"yana gama fadin haka bude murfin motar ya fito Rufaida na cewa " to Allah ya tabbatar da lafiya,ya kuma kara tsare mu" "Amin ya rabb" Yana fadin haka ya shiga duba tayoyin motar tasa bai jima yana dubawa ba ya leko da fuskarsa cikin motar daga gefen titin yana fadin "Kamar ko na duba dazu,tayar ce tayi faci ko" "Subhanallah,To yanzu ya za'ayi gashi mun baro zariya" "Zan kira wani mai yi mana gyaran mota sai ya hawo machine ya zo Inda muke da kayan gyaran,dama ban tsaya duba motar ba muka taho"yana fadin haka ya zura hannunsa a aljihu ya fito da wayarsa ya shiga dannawa ya lalubi lambar mai gyaran ya kira sa yayi masa bayani ya sake shigo da kansa cikin motar yace "Ya ce min yana zuwa" "To Allah yasa yazo da wuri" fadin ta "Amin" Sunyi kamar Rabin awa agurin suna jiran mai gyaran amma babu ko alamunsa Ta dan leqo daga cikin motar da Hassan yake waje har lokacin a gurin tana cewa "Yaya Hassan anya zaizo kuwa?" Nima abinda nake tunani kenan,bari na sake tabasa"yana fadin haka ya dauko wayarsa ya soma danna lambarsa "A'a Yaya kawai dai a kira wani Yaya Hassan,yaci ace tun dazu fa yazo" Dariya yayi ka'dan da cewa "Kin ka gara dai,kije kika su Ummi ko?" Murmushi tayi "A'a kawai dai" jin Horn din da ake abayansu yasa Hassan maida abinda yayi niyyar fada cikin bakinsa ya juyo ya kalli motar Prado baka" Ganin ana kokarin fitowa daga motar yasa Hassan fasa karasawar da yayi,Dady Jabir ne ya fito daga motar a mazaunin driver da fara'arsa ya karaso Inda Hassan yake tsaye yayi masa sallama ya mika masa hannu, Hassan da murmushinsa da baikai zuci ba ya amsa sallamar Dady Jabir ya mika.masa hannu sukayi musabiha ,daganan Hassan ya dan rissina cikin nuna girmamawa Hassan ya gaida Jabir din ganinsa matsayin babban mutum,kuma ya girmemasa Dady Jabir,don zai iya sa'an Abba Bukar duk a cikin tunanin Hassan "Yadai 'dan samari maike faruwa, yanzu 'diyata ta hangoku ta cikin glass din mota" fadin Dady Jabir Hassan da maganar ta katse tunaninsa ya dan sake sakin fuska jin maganar da Dady Jabirun yayi yace "Eh dama Yallabai motar muce tayi,faci amma mun kira mai gyaran yace mana yana kan hanya,to mun jima muna jiranshi har yau bai kara soba" "To Allah ya kiyaye gaba,amma wanne gari kuke shirin zuwa?" "Eh kano zan kai kanwata ne" "To Allah ya kara kiyayewa" "Amin" Har Dady Jabir ya juya baya ya soma tafiya ya 'dan dawo da baya yace "Naji kamar kacemin kanwarka zaka kai" "Eh yalla'bai" "To kenan kai rako zaka yi kenan ma?" "Eh to yalla'bai zan iya cewa hakane" "To indai kana ganin babu damuwa,zamu tafi tare,in yaso kai kaje daukarta idan zata dawo" Rufaida da take jiyo maganganunsu Dady Jabir da Hassan da mutumin da yayi mata kwarjini, wanda daga kallo guda idan kayi masa zaka tabbatar kudi da hutu sun ratsashi,haka ma a siffar sa zakasan bafulatani amma jin yace bata san shi ba yace su shiga motarsa ya kaisu Kano yasa jikinta yin sanyi,don yanzu dan adam ba abin yarda ba ne dukda akwai na garih amma sunyi karamci ta tsaya jin mai Yaya Hassan din zaice masa sai kuma taji Hassan din fadin "Yalla'bai ayi haka kuwa,karmu dora ma nauyi mai garan ya kusa zuwa ai" Murmushi yayi kana yace "A'a kaidai kace baka yarda dani ba ko?,nima yarinyata zan kai Kanon gidan kanina,ka ganta can a motar"ya karasa zancen yana nuna masa cikin motar da Safiyya ke zaune ta bude kofar bangaren mai zaman banza da take itama tana hangosu da ga cikin motar " a'a yalla'bai babu alamar rashin yarda a tare dakai ai" Murmushin jin dadin kalmar da Hassan ya fadamasa Dady Jabir yayi,dukda yasan kasan zuciyar Hassan din sam baiyi kama da furucinsa na zahiri da yayi ba,amma bai nuna masa rashin yarda kiri kiri ba,Aljihun gaban rigarsa Dady Jabir ya dauko ya mikawa Hassan "Kaga wannan kati nane, ka ajiyesa a hannunka,har mu isa Kanon,idan kaga wata matsala,ka kira gurin aikina kasanar musu" Katin Hassan yasa hannu ya karba ya fara dubawa saida ya gama karantawa ya dubi Dady Jabir din "Yalla'bai ashe kai jakadanmu ne 'yan Nigeria a India" Ya murmusa yace "kwarai kuwa yanzu to zaka barni na tafi da kanwarka,dan naga kamar a baya kana shakku a kaina" "Ko 'daya yalla'bai bahakabane,bari nayi mata magana" Bai jira amsar da zai basa ba Hassan ya karasa jikin motarsa ya shiga da sallama Rufaida da taga ma jin mai suke cewa ta amsa masa gamida cewa "Yaya Hassan kana gani babu matsala mu bisa" Ya juyo da Kansa yana kallonta "Eh babu wata matsala a katin da yabani akwai address dinsa da komai,kuma bai kamata muyi masa mummunan zato ba daga yi masa kallon farko kinsan duk yadda rayuwa takai da lalacewa akwai na Allah" Tace masa"Eh hakane" "Yawwa kinga muyi addu'a kawai,tunda kinga mai gyaran baida niyyar zuwa ni kuma bansan wani mai gyaran ba bayan shi,ki fito kinga mu yake jira"Hassan na fadin haka ya soma kokarin kinkimar Yasir yayo waje dashi Jikin motar Dady Jabir yayi da shi kai tsaye Rufaida ta fito ta bi bayansu,a bakin motar suka sami Dady Jabir din tsaye yana jiransu idanunsa ne suka kai kan yasir da yake kafadar Hassan,ba tare da yaji gaisuwar da Rufaida ke masa ba yace " ashe ma harda yaro bari na yiwa yarinyarta wa magana ta koma baya sai a kwantar da shi a gaba kaga idan ya farka sai na samu abokin fira"yayi maganar da murnushi bayyane a fuskarsa,cikin motar ya leka yayi wa Safiyya magana,sai gata ta fito daga motar cikin kayanta Pakistan riga da wando sai mayafin kayan Hassan da idanun Safiyya suka sauka akansa tace wa "Morning" Hassan yayi dan murmushi yana kallon Safiyyan yace "Morning 2" Daganan Safiyyan ta bude baya ta shiga Hassan yayi kokarin kwantar da Yasir a gidan gaban "Suna da kaya ne" Dady Jabir yayi maganar yana kallon Hassan, Hassan yace "Eh yalla'bai" "To muje a daukosu" Dady Jabir da suke kokarin brain gurin ya dan kallo Rufaida da kallo guda ya mata ya fahimci yarinyar da alamar nutsuwa tare da ita kuma yaji lokaci guda ta shiga ransa yace "Shiga motar mana,Safiyya bude mata ta shiga" Rufaida ganin an bude mata murfin motar ta shiga da anbatan Bissimillah hadi da yin sallama Safiyya da take can gidan baya ta amsa mata sallamar "Rufaida ta dan waiga ta kalleta tace "Sannu ,Ina kwana" Safiyya tace Yawwa sannu kin tashi lafiya" "Alhamdulillah"fadin Rufaida Daganan Safiyya ta maida hankalinta ga danna wayarta itama Rufaida ta juya tana kallan su Yaya Hassan suna dauko kayanta,saida suka gama Dady Jabir ya shigo motar,Hassan ya leqo da kansa jikin glass din da Rufaida take yana fadin " ki kula da kanki da Yasir,please da kun isa kimin waya" "Insha Yaya Hassan yanzu waye zai kaika gida da motar,zan kira Yaya Malik sai aja motar mu tafi da ita,Allah ya kiyaye hanya ya tsareku" "To shikenan,Amin Yaya Hassan, nagode" Safiyya ta dan murmusa da take jiyo abinda suke cewa ta cigaba da danna wayarsa Daganan ya juya ga Dady Jabir ya yi masa godiya da addu'a ,sai da yaga tashin motarsu sannan ya fara danna wayarsa yasa kunne Rufaida tana hangoshi ta glass din motar da sanyin Ac motar ya fara ratsata tace "Ina kwana Abba" yana murmushi jin Abban data kirasa yace "Lafiya kalau,yayi maganar yana cigaba da tukinsa Sunana Safiyya,kefa Mene ne sunanki" Taji muryar Safiyya na fadar haka "Rufaida" ta fadi haka tana kokarin zage zib din jakarta da take kara alamun kira taji Safiyya ta canza yare zuwa indiyanci da batasan mai take cewa ba Rufaida ta daga wayar ganin mai kiran tayi saurin dagawa tasa handfree da sallama ta dora da cewa"Yaya ina kwana" "Lafiya kalau,kun taho ne?" "Eh Yaya Abdul muna hanya" "Dama Ummi tace na kiraki naji tayi miki alala" "Eh a yimin kasan na dade dama banci shi ba" Tsaki Abdul yayi yana fadin "Yanzu fa za'a fara yi mana alala a gida tunda zaki dawo" "Kai Yaya nifa kadai akewa ko nayi abu na" "A ina,ni kinga ina Yasir yake" "Ya kwanta barci" "To ki kula da kanki,munyi waya da Yaya Hassan yanzu yayi min bayani" "Insha Allah,Allah ya tsare Ku ya kawoku lafiya daganan ya katse wayar Rufaida ta sauke wayar tana murmushi Yasir ne ya tashi barci ya fara waigen Maminsa ganin ya hangota yace Yasa shi kokarin haurawa inda take,Dady Jabir ya kallesa yace "Aboki ina zaka?" Yasir yace "Gurin Mami" Daganan ya haura ya fara waige waige yana cewa "Mami ina Dady Hassan" "Ya koma gida" "Safiyya da idanunta suka sauka kan Yasir tace " wannan kyakkyawan Boy din fa Masha Allah na waye,ko kaninki ne" Murmushi Rufaida tayi kawai "Safiyya tayi dariya tace " yaron kine kenan,kyakkyawa dashi Masha Allah " Ta mika hannu ta dauki Yasir zuwa inda take ta fara ce masa" "Ya sunan ka?" "Yasir" Sunan Abbanka fa jin yayi shiru yasa Safiyya ita ma kyalesa saboda karar wayar ta da taji ta mika hannu ta dauki wayar tasa a kunne Ta fara magana cikin yaran Hausa. [9/30, 7:57 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil🖤 52. Hudu na yamma suka iso Kano Dady Jabir ya kallo Rufaida yana fadin " a wacce unguwa kuke ne" Rufaida da ta soma jin barci taji maganar Dady Jabir din tayi saurin fadin "Muna Rijiyar zaki" "Dady Jabir yace " kash gashi mu a nan Zaria road gidan kanin nawa yake, bari mu fara zuwa kuyi sallah,mu huta sai mu kaiki,tunda unguwarku tana gaba da nan" Rufaida cikin nuna girmamawa tace "A'a Abba dama ka bari saina kira a kaini gida" Yace "A'a ki bari dai muje muga gidansu abokina" Safiyya da take danna wayarta tace "Wallahi kuwa Abba,Dady kaga idan muka ga gidan kafin mu tafi saina je,inason yaron dama ta bamu shi" Dady yayi dariya "To gaki gata in tayarda ta baki babansa ba" Rufaida murmushi takeyi , da take jin maganar da suke tattaunawa A kofar gate din gidan yayi parking yayi Horn maigadin gidan ya bude musu gate din gidan suka shigar da motarsu da 'yan sandan da shigarka cikin gidan zaka tarar dasu zai tabbatarmaka gidan babban dan sanda ne Rufaida da ido take bin ko ina na gidan da kallo Har suka karasa parking space sukayi parking da suke hango mutanan gidan sun fito tarbarsu ta glass din motar Suna fitowa Husna ta rugo ta rungume Safiyya da murnarta Ammar da Abida suka rungume Dady Jabir suna masa oyoyo Daganan suka koma suka rungume Safiyya suna murnar ganinta Momy Hannatu da take gefensu Husnan tace "Yaya Jabir sannu da zuwa" Ya amsa da fadin "yawwa Hannatu" Rufaida da take tsaye tana kallonsu gwanin sha'awa Dady Jabir ya maida duba inda su Rufaidan suke tsaye "Gafa baki nan kunyi,tare muke, kinga wadancen sunyi gaba sun barmu tsaye" yayi maganar yana nuna su Husna da su Abida da su kayi cikin gidan "Momy Hannatu ta dubi inda su Rufaida ke tsaye da taji yarinyar kallo daya da tayi mata ta kwanta a ranta " sannu da zuwa,ku shigo daga ciki,ya 'dan Boy muje ko?"Momy Hannatu tayi maganar tana kama hannun Yasir ta fara tafiya ita dady Jabir zuwa cikin gidan da suke tafe suna fira yana bata labarin haduwar da sukayi dasu Rufaida a hanyarsu ta zuwa kanon Rufaida tabi bayansu har zuwa kofar da zata sadaka da Babban falon gidan Momy Hannatu ta bude kofar falon suka shiga da suka tarar dasu Safiyya a falo sun baja kolin zaman fira Safiyya da taji sallamarsu Momy da Dadyn ta dago kanta ta kai duba ga Yasir tace "Lah Yasir zo nan" "Momy Hannatu ta kai dubenta ga Safiyya ta harari Safiyya tace" " Baya zuwa,wato da baki kuke kika barsu kika shigo abinki ko?" Safiyya tace "Lah Momy Ba haka bane nayi kewar Husna ne shiyasa" Husna ta kai kallonta ga Yasir tace "Sophie ina kuka samo wannan yaron kyakkyawa,ya sunanshi" Safiyya tace "Sunansa yasir,ga mamarsa nan" Taka rasa maganar tana nuna mata Rufaida da take tsaye tana kallon Familyn gwanin sha'awa "Husna tayi kai kallonta ga Rufaida da batayi tunanina Rufaida ce Mamar yasir ba murmushi tayiwa ace " sannu da zuwa ki zauna mana" Rufaida ta mayar mata tace "Yawwa" daga haka ta zauna a manyan kujerun falon kusa da wadda su Husnan kekai" Abida ta ja Yasir gurinta da take da sha'awar yara musamman Yasir da yake kyakkyawa farin bafulatani "Dady Jabir da ya samarwa kansa gurin zama a daya daga cikin kujerun falon yace "Husna kaita dakinku tayi sallah,muci abincin saimu kaita gidansu" Husna tace "To Abba" daganan ta mike ta saki murmushi ta kalli Rufaida tace "Muje ko?" Rufaida ta mike tabi bayan Husna har zuwa ciki" *********** Abida ce da wata mai aiki suka jera abinci kasan carpet din falon Momy hannatu ta mike ta tsiyaya wa Dady Jabir ruwa a kofi ta mika masa "Yaya Jabir ga ruwa"dady Jabir da shigowarsa falon kenan ya shiga masallaci sallar la'asar sunyi azahar a hanya,ya amsa ya fara sha Momy Hannatu takoma ta zauna "Yaya Jabir ina yini,ya hanya,ya kuma gajiya" "Lafiya kalau gajiya tabi lafiya" "Nifa daukata Yaya driver ne zai kawoku,saina ganka da kanka ka tuko motar" "Eh wallahi Hannatu kinsan drivernsu daya ne,kuma ni nafison na rika tuki da kaina ma" "Eh hakane,ya kuka baro su Yaya Asma'u,da Ra'uf "Lafiyarsu kalau,ina Usman din ban ci karo da shiba" "Bai dade da fita ba Safiyya ta yomin waya kun iso fitarma ta dole ce yayi an kirasa a gurin aikinsu ne,bai tsammaci zuwanku yanzu ba,yanzu Dady haka zamu bar yaron nan Ra'uf kiri kiri yaki yin aure" Dady Jabir yayi murmushi yace "Ai halin yaron nan sai shi,Amminsa tace har yau ya kasa mantawa da wannan yarinyar kuma kema kinsan ko giyar wake muka sha ba zamu aura masa yarinyar ba da silar danginta muka rasa farin cikinmu" "Hakane Dady to mai zai hana a hadasa da Safiyyan da Yaya Ma'u tace kun yanke shawarar hakakwanakin baya tunda shi ya tsaya shirme kamar karamin yaro" "Eh to Hannatu kinsan dai matsalar Hajiya ba lallai ta yarda ba" "Ina tunanin zata amince tunda ita ma ta matsa yayi auren yanzu,kuma yanzu Safiyya tana tare damu" "To zan jarraba na gani,ko Allah zaisa a dace" "To Amin" Sallamar su Rufaida ita ta katse hirar dasu Dady keyi suka amsa musu Momy Hannatu ta dubi Rufaida tace "Dama yanzu nake shirin kiranku,kuzo aci abinci" Safiyya tace "Momy ita tafiya zatayi anzo daukarsu" Momy Hannatu tace "Ba Yaya Jabir yace har gida za'a kaiku ba" tayi maganar tana kalon Rufaida "Wallahi Aunty dazu Yayanmu ya kirani waya na masa kwatance unguwar da muke yanzu,shine naba Safiyya waya ta masa kwantance yace yanzu yana kusa da hanyar zai biyo ya tafi damu" Dady Jabir da baiji dadi ba yace "To shikenan amma dai,banso ba naso na kaisu har gidan" Daga haka suka fito rakata Har jikin motar Abdul suka kaita da ya shigo da motarsa ciki Abdul ya fita suka gaggaisa ya kwaso kayan su Rufaida a motar Dady Jabir zuwa motarsu bayan suna kokarin shiga motar Abdul ya dubi Dady Jabir yace "Yalla'bai mungode sosai Allah ya kara girma" Dady Jabir ya dubi Abdul yace Amin,amma kun mana laifi daya fa" Abdul yace "Yallabai laifin me mukayi" " zaku tafi da abokina" "Abdul yayi murmushi " au Yasir,ai yalla'bai zamu zo nan mukawo ma shi" Yace "Nida ba'anan nake ba,saida in zaku barmana shi mu tafi tare,kayima Babansa magana ko zai yarda na tafi da shi,ya shiga ranmu sosai" Abdul yayi murmushi yace "To shikenan yalla'bai" "Ai nasan ba zaku iya ba fade kawai kukayi, nan gidan kanina ina fata zaku cigaba da zumunci tunda garinku daya " "Insha Allah yalla'bai" Husna da take sauraransu tace "Ai Abba ko busu zo ba,mu zamu je kodan Yasir yaron ya shiga ranmu lokaci daya" Abdul yayi murmushi "Haba mai zai hana mu muzo ma" "To Allah yasa" fadin Safiyya Daganan suka shiga motar Rufaida a gaba Yasir ya na baya shikadai yana wasa da motar da Da Dady Jabir ya basa su Rufaida suna ta godiya har Abdul zai tada motar Safiyya tasa kanta cikin glass din motar ta dubi Rufaida tace "Rufee bamu lambarki,saimu rika gaisawa" "Rufaida ta fado mata tasa daganan Abdul ya tada motar suka fara kokarin barin gidan su Husnan suna dagawa Yasir hannu har saida suka ga barinsu gurin Abdul da ya soma tukinsa ya dubi Rufaida da take gaban motar yace " oh Rufaida ban taba tunanin a zamanin nan za'a samu mutane irin wadannan ba,mutanan arziki kiga nifa kamar sun sanmu" "Rufaida tace " wallahi kuwa yaya suna da kirki sosai,Yaya yana ga har kayi kumatu bayan rabuwar mu" Yayi dariya "kai Rufaida banda sharri" "Wallahi Yaya da gaske nake" To nidama kinsan ina da kiba dan duk nafi ku,karatu ne dama ya tsotseni yanzu kuma tunda nagama karatu kuma ina dibar albashi mai tsoka dole na canza" "Eh lallai hakane" "Muje gida kiga abun bazata" "Menene Yaya kodai budurwa kayi ne,tazo tarbata " "Oh budurwa kuma Rufaida" "Eh mana Yaya" "Tab aini ba yanzu zanyi aure ba" "To Allah ya kaimu lokacin ya hadaka da ta gari" Ya amsa da Amim Ya dora da cewa "Oh Rufaida ya zaman naku,keda su Umma, naga ma duk kin rame" "Hmm kaidai bari Yaya ba dadi" "Ai nasan dama bazai dadi ba,Allah dai ya raba ki da auren na kaddara,dan wallahi yanzu ko mai za'ace a kaina bazan yarda karo na biyu ayi wa kanwata wannan auren ba dan saidai muyi fito na fito dasu Abba" Ido ta zaro "Kai Yaya su Abban" "Ko su waye kuwa,kin manta waye Abdul ne ni bana goyon bayan zalinci a rayuwata,dubi fa yadda a kari ka gasa ki kamar biredi,basu a dubi yadda aka rika gasa mu a baya kafin mu samu wannan canjin rayuwar,kina gani yadda har yau ba musan dadin dangi ba,dukda kasancewarsu dangi Ummi da Abba duk daya amma basa nuna kulawarsu gare mu" "Babu komai Allah yaya komai yana gaf da zama tarihi" "Rufaida kenan anya kuwa,kina sane fa ko Abba Bukar ba wani sonmu yake ba,ni tsorona kar abinda ake fada akan Ummi ya zama gaskiya" "Haba Yaya karkai fatan hakan,nina san komai zai wuce" "To Allah yasa Rufaida" Daganan suka cigaba da firarsu har suka isa kofar gate din gidan nasu Horn yayi maigadi ya bude musu gate din suka shiga yana kokarin yi musu sannu da zuwa ****** Gaba 'daya gidan ya rude da murnar dawowar Rufaida kannan nata suka rasa inda zasu sa Rufaida don murna ga Yasir da kowacce kenan nan da shi su Rumaisa an zama 'yan mata tana shirin Candy a lokacin Abdul-Rashid ya tafi gaba da sakandire yana karatunsa a Northwest sai da suka gama murnar suka fara kokarin shigo da kayan Rufaida cikin gidan wannan kenan.[10/3, 10:25 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU D'AYA* Sadiya Khalil 53 Book 2 page 3 Wannan book 2 ne page 3 yakama 53 kenan Safiyar litinin Misalin karfe 11 na safiyar ranar Rufaida tana zaune a falon gidan ita kadai tana kallon wani Film na Sanam teri kasam a Bollywood wayarta ce ta dauki kara ta daga da sallamarta fuskarta da alamun farin cikin ganin mai kiran ta maida wayar a hands free ta cigaba da kallonta "Kanwata kin buya ko flashing bakya yimin" "Kai Yaya Malik haka ma zaka ce" "To ai haka ne ko kina yimin ne,abokina yasa kin mata da 'dan uwanki" "Kai Yaya duka fa jiya muka fara waya da Zahraddin din fa" "Koma yaushe ne nasan dai,zuwa yanzu kinyi na'am da abokina" "Hmm Yaya kenan" "Meye kuma hmm ko baki sonshi ne,karfa ki yaudararmin abokina,wani yazo yayi wuf dake" "Kai Yaya fatan da zaka min kenan" "Ba fata bane Rufaida,nasan irin ku kyawawan mata aurenku rabo ne" "Kai.Yaya Malik ina wani kyau" "Hmm Rufaida kenan,nidai yanzu mu koma batun abokina,please karki kishi Rufaida yace wa Mamarsa inbake ba sai rijiya,sannan kuma ma Zahraddin mutumin kirki ne,haka ma iyayensa nasan zasu rikeki amana" "Insha Allah" "Yawwa kanwata,yawwa na turawa Safiyya photonki yarinyar da nace miki kuna kama kwanaki" "Eh nagane" "Ina turamata photon tace min ta sanki" "Niko a ina tasanni" ta yi maganar tana zaro ido "Ashe kwanaki a motarsu kuka zo Kano" "Dan Allah Yaya Malik,wallahi nima nayi wannan tunanin da naji sunanta,kuma naga yanayinta yayi kama da wadda ka bani labari" "Eh wallahi itace" "Suna da kirki sosai,amma nifa banga kamar mu ba" "Itama tace bata gani ba,amma ni kuma na ganta kune dai kuka kasa gani banda yanayin tafiyarku kuna da siga a fuska ta fannin kalar hancinku" Dariya abin ya bata tace "Yaya Malik kenan kanada zakulo kama wato harta hanci zaka ga kama" "Au dariya na baki ma ko?" "Eh mana ai abin dariyar kayi,don wannan safiyyan ta fini kyau" "Ita din ko kafarki bata kama ba" "Zanfada mata kuwa" "Yi maza kar kuda ya rigaki,kinga ni ina Yasir ne" "Yana can suna wasa da Rahima" "To idan sun shigo falon ki kira ni ki hadamu" Daganan suka yi sallama Rufaida ta maida hankalinta ga kallon da take yi ****** Sallamar Ummi Hauwa'u ya katse tunanin Rufaida da take zaune a dakinsu saman gado Rufaida murmushi ta kakalo ta amsawa Ummin sallamar Ummi Hauwa'u ta karasa shigowa dakin ta zauna gefen gado kusa da inda Rufaida ke zauna "Ummi ina yini" fadin Rufaida tana sinne kai "Da ban wuni ba zaki ganni ne yini ba zaki ganni ne,ace yinin yau baki leqo ko da falo ba,haba Rufaida me ke damunki ne?" "Babu komai Ummi" "Ban yarda ba,nice mahaifiyarki nafi kowa sanin halinki,nasan hakanan bazaki ki fitowa waje ba,Rufaida a yanzu haka baki da wanda ya fini a rayuwarki karki kokarin boyemin damuwarki" Shiru Rufaida tayi zuwa wani lokaci ta soma magana "Ummi jiya Ummansu Yaya Malik ta kira ni a waya tana min barazanar kisa tace na fita harkar danta, muddin na auri danta a karo na biyu sai taga bayana,data hada iri da karuwa wadda iyaye da 'yan uwanta suka sallamata gwara ta kashe ni itama akasheta, muddin tana raye bazata bari ta sake hada iri dake ba" Rufaida takai karshen zancenta tana goge hawayen da suka soma tsiyayowa a idanunta tunowa da kalaman da Hajiya Jamila ta wanzu gurin fadama taajiya ga kuma kalmar sallamawar da aka kira Umminsu dashi da har yau ta kasa manta kalmar wadda a jiya ne kawai ta taba jin wannan kalmar a bakin Umminsu mai Hajiya Jamila take nufi da wannan kalmar nufinta su Gwaggo ne suka sallama Ummi tasu to yaushe abin ya faru bata tunanin abin ya dade da faruwa ta yiyu jiyan nema mai Ummintasu tayi ita kuwa Ummi Hauwa'u ta kalli Rufaida da alamun bacin rai Maganar Ummi Hauwa'u ta katsewa Rufaida tunanin ta "Ke shiga harkar AbdulMalik din kike kenan shiyasa kika ki fitowa waje saboda kun kulla soyayya mahafiyarsa tanason ta rabaku,saboda ke dama wawiya ce,kin manta da abubuwan da suka rika faruwa a baya ban hanaki ki auri AbdulMalik ba dan saboda kina sansa, amma kisa ni muddin kika auri dan ta a karo na biyu ki rubuta ki aje babu ni babu ke"daga fadin hakan Ummi Hauwa'u ta mike tana kokarin fara takawa Rufaida tayi saurin rike hannayenta tana sheshshekar kuka " Ummi yakamata ki fahimceni,wallahi ban taba son Yaya Malik ba,shima bai taba cewa yana sona ba,,sai dai idan a zuciyarsa yabar soyayyar tawa a ransa ya kasa hakuri ya bari abokinsa ya aureni ya fadawa su Abba,amma ni abokinsa ne yace yana sona yanaso ya turo gidanmu,abu daya ne yake damu na tun jiya" Ummi Hauwa'u ta cire hannunta daga na Rufaida ta kalli Rufaida "Mene ne abun" "Ummi ki fadamin maiyasa su Gwaggo suka sallama ki da 'yan uwanki,meye dalili mai kika musu maiyasa ake jifanki da kalmar da hatta masu aikata abun ba saso a kirasu da shi,karuwa nasan wannan kalmar ita ta rusa wancen auren nawa, ta kuma hanayi jin dadin wancen auren nawa,dukda wanda na aura yana sona,yanzu haka nasan hanani wani auren zata yi wannan kalmar muddin mijin auren nawa yaji ni nawa asalin mahaifiya ta karuwace" Ummi Hauwa'u ta daka mata tsawa "Ya ishe ni haka Rufaida,tunda har 'yar cikina ta fara yarda da abinda wasu mutanan suka yarda dashi harma suke kirana da suna karuwa,bayan basu sanni ba,hasali yawancinsu basu san ni wacece ba" "Ummi ki gafarceni ba dan ina zargi gareki na furta hakan ba illah iyaka" kukan da ya kubcewa Rufaida yasata kokarin maida maganar da takeson fada Ummi Hauwa'u da saida ta bari Rufaida ta gama kukanta ba tare da ta lallasheta ba sannan ta komaa ta zauna gefen gadon kusa da Rufaida ta dafa kafadar Rufaidan "Illah kawai kinaso kisan menene dalilin da yasa na amsa suna karuwa ko,amsar ita ce sunan shi ya dace dani musamman duk wanda yayi duba ga wani abu daya wuce ya zama kamar tarihi sai dai har yau ba a fasa jifana da kalmar da take tunomin da wasu abubuwa da suka faru dani a baya ba ,amsar ki ta farko da kike son sanin dalilin anbatonta gare ni itace ni Hauwa'u Mahmud Danbatta ba karuwa bace Rufaida tayi saurin dago da kanta " Ummi Hauwa'u ta daga mata kai "Kwarai ni sunana haka,Malam bashi ya haifeni ba,kaddara ce ta sa ya zamo tamkar uba gare ni,amma Ra'uf saurayinki na farko shi 'dane gare ni,haka ma mijin Samiha da ne gare ni domin su yarane ga yayyena. Ina so a yanzu kafin kisan wani abu game da tarihina ki fahimci cewa ni ban karuwa bace ban taba karuwanci ba ba sha'awarshi ba,tun daga yarintata zuwa fara girma na har zuwa yanzu dukda sunan da aka lakaba min banji ban gani ba, kaddara da tun kafin asan da haihuwarka ita ta yi dalilin anbatonta da wannan sunan LAVARINA YA SAMO ASALI A GARIN DANBATTA KAUYEN KUNYA DA NI DIN GURIN INNATA NA SAMI ASALIN LABARINNAWA [10/5, 11:39 AM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil Book 2 page 4 ALAVARINA YA SAMO ASALI A GARIN DANBATTA KAUYEN KUNYA DA NI DIN GURIN INNATA NA SAMI ASALIN LABARINNAWA Malam Mamuda mutum ne bafulatani dan asalin jihar Kano karkashin wani karamin kauye na fulani kunya dake karkashin karamar hukumar Danbatta iyayensa su uku suka haifa akwai Hadiza da Salamatu shine kadai namiji a cikinsu kuma shine babba, da yana da shekaru goma Allah ya amshi ran mahaifinsa Malam Jauro Inna wuro da take mahaifiya gasu Mamuda, da tun rasuwar mahaifinsu ta zama uwa uba a gare su sai kuma 'yan uwanta da suke kokarin taimaka mata amma banda yan uwan mijinta dukda kasancewarsu 'yan uwanta kasancewar auren zumunci aka yi mata da mijin ta Malam Jauro da asalin sunansa Bello saidai kuma su da suka fi kusa da mahaifin nasu basa taimaka musu, Mijin Inna wuro Malam Jauro nada shekara hudu da rasuwa a lokacin Mamuda yanada shekara 16 da Hadiza a lokacin keda 13 sai Salamatu mai takwas, Allah ya amshi ran Inna wuro sosai 'ya'yan nata suka ji mutuwar mahaifiyartasu shikenan sun rasa uba yanzu sun rasa uwa bayan rasuwarta ne,'yan uwan mijinta suka kwashe 'ya'ya matan suka maidasu hannunsu,'yan uwan Inna wuro da basu so hakan ba,dan sunsan wahala zasu basu tunda suka daukesu, haka dai suka hakura,suka dauke Mamuda shi kadai zuwa gurin kanwar mahaifiyarsa shekarun inna wuro 2 da rasuwa a lokacin shekarunsa goma sha shida wani makwafcinsu da yake zuwa neman kudi Kaduna anan ya bukaci da zai koma a bashi Mamuda ya tafi dashi ya rika tayasa kasuwanci,kasancewar mutumin abokin Malam Jauro mahaifinsu Mamudan ne tundaga yarinta a lokacin ganinsa a matsayin maraya yasa shi sha'awar daukarsa haka Malam Audu ya tafi dashi wannan tafiya ita ta zamewa Mamuda silar arzikinsa Hadiza tana isa aure ta samu mijin ta cikin Danbattan da take kai tallar fura suka hadu a nan da yake dan cikin garin Danbatta ya aureta sai Salamatu da itace karamarsu Mamuda da kudi suka fara zauna masa ya yanke shawarar zaiyi aure kuma ya yanke shawarar diyar Malam Audu da yayi sanadiyyar samun arzikinsa zai aura mai suna Hajara ,yana zuwa da maganar auren da yayi niyyar auren 'yar wajen Malam Audun dangin mahaifinsa suka ki yarda suka ce saidai su zaba masa mata a cikin 'yan uwansa ya aura bazai aure a dawa ba aka aura masa Hanne,ya tafi da ita Kaduna da zamansu shida Hanne daga auren nasu ya fahimci bata da mutunci ko kusa,bata ganin girmansa har suka shekara biyar da aure a lokacin tanada yara uku,Suleiman da suke cewa sule sai yasaka sunan mahaifin Mamudan Malam Jauron da sunansa Bello da ake kiran yaron da Bello sai Inna wuro da asalin sunan Inna wuron Fatima ake cewa da yarinyar Fati Daganan ya yanke shawarar kara aure ya yanke shawarar auren Suwaiba da take 'ya ga kanwar Inna wuro mahaifiyarsa da suma yan uwan nasa basu hana saba hatta dangin Mahaifinsa don kowa yasan halin Hanne a lokacin Suwaiba ita macace mai hakuri da kawaici aurensu da shekara daya ta haifi danta namiji yaci sunan Ubangidan Mamuda da Malam Audu da sunansa cikakke AbdulRa'uf da ake ce masa Abdu Suwaiba ta yi kiransa da suna Babban Mutum, Gwaggo Salamatu a lokacin ciki ya bullu a jikinta hankali dangi duk ya tashi,aka tsareta da tanbayar wanda Yayi mata cikin taki fada,sai da abun yakai da bugunta ta fada Sunusi dan uwan Hanne da suke uwa daya uba daya shine yayi mata da yana jin an fara tuhumar waye yayi mata cikin ya gudu yabar garin ,koda ta fadi Sunusin ne yayi mata babu wanda ya yarda a cikin 'yan uwan nasu dukda sunsan ba ji Sunusin yake ba amma sunyi shaidar baya iskanci da yaran mutane bare ma haryayiwa Salamatun kuma ma sunusin yanzu bama ya garin,acewarsu ita dai ta rasa wanda zata yiwa kazafin ne ta yiwa Sunusi taje wajen tallar furarta amma ta ciki zata zo ta yiwa Sunusin Sharri dukda kasancewarsa dan uwanta,tuni mutanen gari da 'yan uwan Salamatun suka shiga goranta mata,da binta da bakaken maganganu da habaice habaice indai zasu ci karo da Salamatun,wannan bakin cikin yasa Salamatu barin garin su don gujewa maganar mutane akanta da 'yar da zata haifa ko da idan Allah ya nufa Wannan labarin batan Salamatun,ya ba kanta ran zuriyarsu Mamuda ciki harda Mamudan da nai man duniya yayi wa kanwarsa bai sameta ba harya hakura,da saida bacewar salamatun aka sanarmasa dalilin batan kanwar tasa har kuka yayi jin irin kaddara da ta samu kanwarsa kuma ma Sunusi shine yayi mata wannan aikin da shi yanada yakinin Sunusi ne,amma Sunusin ma neman duniya an yimasa ba duriyarsa. ********** Suwaiba a haka suka cigaba da haihuwa kusan a tare da Hanne da Suwaiba Suwaiba nada 'ya'ya biyar a shekarar da bata fi 10 da aurenta ba Abdu,Hamidu,Salamatu,Adam,Karima Hanne tana da yara shida "Sule,Bello,Fati,Jabir,Usman,Asiya Dukkansu kansu a hade yaran suke kasancewar Hanne ke juya gidan shine dalilin zaman yaran inuwa daya Suwaiba kuwa macace mai kawar dakai halin Hanne data sani shiyasa su zama lafiya a gidan kuma matsayin Hanne na 'yar uwarta bazata so su rika hayaniya ba Batun dukiyar Mamuda kuwa kullum bunkasa take yi a lokacin yaje Makkah yakai matansa ma ****** Malam Basiru da matarsa Saude 'yan asalin jihar jigawane karamar hukumar Taura da zama ya kawo su garin Kaduna shida matarsa da Malam Basiru ke sana'ar dukanci a babbar kasuwar Kaduna Central Market rayuwa suke cikin rufin asiri da yaransu uku Aliya,Amina,haladu,daganan haihuwar ta tsaya musu Aliya da itace Babba tana da shekara sha hudu da ta kasance kyakkyawar macace, Samari suka fara nuna aha'awar aurenta amma dukta kisu sai wani mai suna Tijjani da yake kasance dan asalin sokoto sana'ar gini ta maidosa Kaduna,anan Allah ya hadasa da Aliyar da yake a unguwarsu harda shi a masoyan Aliyar da Aliyar duk cikin manemanta shine yafi kwanta mata a rai,dandanan ya fito ganin Aliyar ta amince dashi aka yi musu auren so da kauna Shekara guda da auren Amina ta haifi yaronta namiji mai suna Ahmad. Amina da tasowarta tafi Aliya kyau da farin jini samari suka fara tururuwar son auranta,cikinsu duk Habibu tafi so da yake abokin Tijjani mijin Aliya da Habibun shima magani ne kamar Tijjani Malam Basiru a kullum cewarsa Amina matar manya ce,shiyasa duk yaki bawa manemanta damar turo magabatansa, Allah ya amsa Addu'ar mahaifinta taje sayayya Central Market Allah ya hada ta da Mamuda da taje siyayya shagon nasa Shiko Mamuda yana ganin Amina a shagon nasa da taje siyayyya ganin nutsuwar yarinyar ta kwanta masa a ransa har yaji yana son ya kara aure da ita Abokinsa da suke tare a shagon sanda taje siyayya ya tanbayesa koya santa ganin sunyi magana yace masa "Eh yasanta a unguwarsu take mahaifinta ma a nan kasuwar yake sana"ar dukanci" Sosai abin da abokin nasa ya fadama sa yayi masa dadi ganin yasan ma mahaifin Aminar Malam Basiru mutumin sane ma sai dai bai taba zuwa gidansa ko wani abu ba a iya kasuwar suke hurdarsu anan ya yanke shawarar zai fadawa Malam Basiru yaga yarsa yana son aurenta Malam Basiru da Mamuda yayi masa wannan maganar ba karamin dadi yaji ba,ganin koba komai Amina zata auri babban mutum Kamar Mamuda da yana sane da cewar Mamudan yana da mata biyu da 'ya'ya goma sha daya amma shi koda Mamuda ya fadama sa yawan 'ya'yan nasa da matansa har su biyu bai damu ba,kudi sun rufe idonsa,koda yajewa da Amina da mahaifiyarta batun auren Saude kin amincewa tayi ya za'ayi akai Amina gidan mai mata bama mace daya ba a'a har biyu ga yaran sa 11 da take da tabbacin a 'ya'yan nasa akwai sa'ar Aminar Haka dai Malam Basiru ya shafa wa idanunsa toka yace arziki yana kiran 'yarsu suna gujewa waccen shekarar yaji labari yakai matansa makkah,shine ita Saude zata yiwa 'yarta bakin ciki Saude da har garinsu taje akan maganar auren da yakeso ya yiwa Amina bataso ita Aminar akan a hanasa aurawa Amina Mamuda amma da suka masa magana bai saurare su ba,sam ya ki hangen gaban da su suke masa hange Haka yasa Mamuda ya kawo kudin aure shida makwabtansa suka ansa ba tare da wani dan uwansa ya sani ba,saboda yasan basu son auran Amina da ita ma a bangarenta tunda aka kawo kudin hankalinta ba a kwance yake ba sam ba son Mamuda take ba zuciyarta tana gurin Habibu, Mamuda ko yakan zo zance gurin Amina dukda Aminar bata wani sakin jiki tayi fira da shi saboda yadda zuciyarta bata garesa amma sam shi bai kawo bata san sa ganin yana da duk abinda za'aso shi danshi,kuma ma bai taba ji koda da wasa ba wani yace masa Aminar bata sonsa ba saboda shi soyayyar Aminar ta gama mamaye cikin zuciyarsa jinsa yake a lokacin indai bai aureta ba akwai matsala a rayuwarsa don shi Amina ce daga kallo daya da yayi mata a rayuwarsa yaji yana tsananin sonta fiye da kowacce mace,banda Hajara diyar Alhaji Audu ubangidansa da ya fara so 'yan uwansa suka yi masa auren gida da Hanne dukda bawai sonta yake ba haka ma Suwaiba matarsa ta biyu auren hadi aka musu da ita itama bawai sansu duk yake ba ya auresu Sanda labarin auran da Mamuda ya zowa Hanne gaba daya kiyayyar duniya ta dorawa Amina tun kafin ma taganta haka ta tashi hankalinta ta kuma tashi namijinta, haka ta shiga bin bokaye da malamai akan maganar auren Itako Suwaiba ko a jikinta dan ita dama tasan namiji mijin mace hudu ne,saidai dan kishin da taji dan kadan da baza'a rasa ba ***** Anyi bikin Amina da Mamuda lafiya an gama lafiya Amina ta kasance mai hakuri da zabin mahaifin nata da Allah dama ya riga da ya kaddara auren basu,amma bawai da son ran Saude mahaifiyarta ba dama 'yan uwansu baki daya,haka bada son ran Hanne ba ***** Amina shigarta gidan duk soyayyar duniya Mamuda ya dauketa ya dora mata,bangare guda ya gina mata a matsayinta na Amarya "Wannan ya kara bata ran Hanne ganin duk shige da ficen da take da asarar dukiyarta da take duk a banza suke tafiya,Mamuda yanzu bama ta tasu yake,wannan ya kara hura wutar kiyayyar da Hanne take yiwa Aminar Amma itako Amina tana ganin girman kishiyoyinta da 'ya'yansu sam batada mummunan manufa a ranta game da su Shekara guda da ta zago da auren Amina da Mamuda ta haifi diyarta mace kyakkyawa mai kama da mahaifiyarta sak,tare da kishiyarta Amina ta haihu wato Suwaiba da ta haifi diyarta Malika Safiyyya nada wata shida abubuwa suka fara sauyawa game da zaman Amina da mijin nata babu kwanciyar hankali, dama abokan zama duk ba shiri suke ba dan hatta Suwaiba Hanne ta fara zugeta akan Aminar,saidai ita Suwaiba tunanin da take baza ta ki Hanne da take 'yar uwarta ba tace zatayi shiri da bare da basu da alaka a tsakaninsu,gama halayyar Hannen da ta sani tuni inda ta fahimci shishshigin da take wa Aminar zata iya cewa akwai kullin da suke,ita ko Suwaiba macace mai gudun magana,wannan shine dalilan Suwaiba Malam Basiru tun kafin aje ko ina ya fara dana Sanin aura wa Mamuda 'yarsa Amina don shi tunaninsa yana aurawa Mamuda 'yarsa shikenan sun samu hanyar samu gurin Mamudan,dukda a farko mamudan ya gwada hakan bayan bikinshi da Aminar abinci ake saukewa iyayen Aminar amma yanzu ko ko buhun gishiri basa samu A yanzu haka Malam Basiru gani yake gwara Tijjani mijin Aliya akan Mamuda mijin Amina,saima da Aminar tazo gida bayan komawarta gidan mijinta bayan haihuwar ta da taje gida goyon ciki harta haihu yarinyar tayi wayau ,nan yana ganin Aminar yadda dukta rame daga komarwata gidan daga goyon cikin da tunda Aminar tazo Mamuda ke faman zarya gidan da naman kaji da lemuka amma daga komawarta duk ta rame nan iyayenta suka shiga tanbayar maike faruwa ba ta boye musu komaiba ta fada musu,tunda boyewar mai zatayi bayan ita dama Mamuda ba zabin ta bane,haka Malam Basiru da yasan shine silar auren 'yar tasa, nan ya fara rokon Aminar da mahaifiyarta yafiya Saude tace"ai karshen kwadayinka ne dama yakai ka ya baroka gashinan tun kafin aje ko ina ga yadda ta dawo,kaje ka kai 'yarka cikin kishiyoyi kuma kowacce da 'ya'yanta bayan bata rasa ma rasa matar ba saboda son abin duniya ka manta ubangiji ke azurta bayinsa,amma idonka ya rufe tunaninka ai mijin Aminar shi zai a azurta mu ko ya azurta 'yarta mu,in banda zama babu kwanciyar hankali mai take yi" Wannan abun da Mamuda yake yiwa 'yarsa ya yiwa Malam Basiru ciwo nan ya shiga neman Mamuda a kasuwa akan ya sakar masa 'yarsa amma Mamuda yace shi yana son matarsa ko ina zasu je bazai sake taba haka malam Basiru ya hakura Aliya ma ta sake haihuwar diyarta mace Bilkisu sunan kakarsu Aliyar da ranar da Aliyar ta haihu aka saka wa yarinyarta ta Bilkisu da aikowa da su Aliyar a lokacin da Aliyar ta haihu da kwana daya da rasuwar Bilki kakarsu Aliyar ta wajen uba wannan yasa Tijjani sakawa 'yarsa sunan kakar matar tasa Aliya Wanda bayan haihuwar Aliyar Tijjani ganin sun fara tara 'ya'ya daga daya har suna biyu yanzu ga yanayin yanzu babu wani samun da suke a harkar ginin yasa ya yanke barin anan ya yanke shawarar zai dauki Aliya su koma Sokoto haka yadauketa zuwa sokoton da niyyar Tijjani da duk shekara zai kawo Aliya gida ta ga gida ba dan san ran mahaifan Aliyar da 'yan uwanta ba tabi mijin nata kuma gashi yace zai rika kawota gida wannan yasa shi jin dadi Safiyya na da shekara biyar da haihuwa Amina ta sake haihuwar 'ya mace aka saka mata suna Hauwa'u wato ni da har nafi Safiya kama da mahaifiyarta mu Amina,a lokacin Saude mahaifiyar Amina ta haifi diyarta mace da ita Saude ta fidda rai da haihuwar ma a lokacin dan Haladu yayi shekara goma sha biyar sannan aka yi masa kanwar da taci suna Bilkisu aka sake maida sunan Kakarsu Aminar ga kanwarsu Duk shekara sai su Malam Basiru sun zuba ido ko Aliya zata zo amma babu labarinta bana mijinta har tsawan shekara shida, duk wanda suka tanbaya a abokan Tijjani 'yan Sokoto idan sunje gida maiyasamu Tijjani har aka dauki wannan lokacin bai kawon Aliyar Kaduna ba amsarsu itace aisu Tijjani basu koma Kaduna ba wanda a wannan lokacin ne kuma Allah ya karbi ran Malam Basiru 'yan uwa da abokan arziki sunji mutuwarsa Amina da Mahaifiyar Saude da Haladu har sunfi kowa jin mutuwar Malam Basiru Bilkisu kuwa tana goye a lokacin batasan mahaifin nata ya rasu ba Naji korafin page din danake muku nasan nima yana gajere amma kunsan yanayin rayuwa saboda karna rika barinku shiru yasa nake kokarin turo muku kullum ammah zan rika tsallaken rana indai kunaso sau uku a sati zan rika yi muku amma pages da yawa indai kun amince shikenan. Nagode da yadda kuke nuna soyayyar littafin nan [10/13, 8:18 PM] Sadiya Khalil Muhammad🥰: A*JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil❤ Book 2 5. Shekaru na uku da haihuwa kanwar Mahaifiyarmu ta bace Bilkisu,da take sa'ar haihuwata sakamakon aiken da akayi mata siyo maggin miya shagon unguwa,neman duniya anyi mata amma ko alamun za'asake ganinta babu gidan Radio ba inda ba'a zagaba gurin cigiyarta amma babu duriyarta harma Inna Saude ta fidda rai gaba daya. Batun Hakuri kuwa da Mahaifiyarmu take yi a gidanmu yana da yawa baga kishiyoyi kadai ba a'a har ga mijinta da 'ya'yansu dai dai kune cikin yayyenamu basu kama zugar da Hanne ke musu a kanmu da Mahaifiyarmu ba Kwanaki sunzo sun wuce kamar kiftawar ido dukkanmu a yanzu haka mun soma girma dan Safiyya a yanzu tanada shekaru 11 ni kuma inada 5 Safiyya ta soma girma kuma ta taso da kyawunta Mahaifiyarmu takance ita da yayarta Aliya tafi kama,inda muka tanbayeta ina Umma Aliyar mu bamu santa ba anan ne take sanarmana labarinta haryau babu duriyarta da mijinta Yau da wuri muka dawo makaranta muka shirya zuwa gidan kakarmu nida Yaya Safiya mu amso abincin da muka saba amsowa a kusan kowacce rana ta duniya Tunda mu sam ko abinci bamu samu a gidan namu indai ba Ummanta mu tayi girki ba matan gidan hanamu sukeyi suce badan ita suke girkin ba,idan ta fadawa Baffanmu saiyace shi dai har da ita yake bada kayan abinci don haka ta kwatarwa kanta 'yanci ta rika amsar hakkinta gurin kishiyoyin nata,amma shi sam bazai yi mussu wata magana ba,kuma vazai bata wani abincin baba ta girka ,Ummantamu da tasan ko tayi maganar ba zata samu ba,wannan dalilin yasa duk ranar da ba itace da girki ba gidan Inna Saude zamu tafi mukarbo da ita din abincin saidawa takeyi a lokacin rayuwar tata abin tausayi muda muke a wannan babban gidan da zamu taimaka mata amma muke zuwa amsar taimako "Umma ina kudin machine dinmu" Fadina Umma ta kalleni "Kudin machine kuma Hauwa nan da unguwar Bellon saina baku kudin machine" Safiyya ta harare in "Umma kyaleta,batasan zuwa ne kawai" Muna cikin hakanne yaya Jabir ne ya shigo bangaren namu,da shi da Yaya Usman da Yaya Malika muke shiri,akaf gidan namu da ya turo kofa da sallamarsa muka amsa masa ya na kokarin zama kujera muka gaishesa ya amsa mana da murmushi a fusakarsa ya 'dan kallemu " ina zaku da ranar nan,naji ana cewa wata a cikinku bata da niyyar zuwa,kuma naga yau Alhamis babu makaranta" Yaya Safiyya ta dan sosa kai "Zamu je gidan Inna Saude ne,shine Hauwa tace saidai muje a machine" Umma da take kallonmu ita Yaya Jabir ya kalla "Umma mai zasu yo gidan Inna Saude da tsakar ranar nan,kuma a kafa ai akwai nisa, ko bata jin dadi ne?" Nice nayi saurin yin magana kafin Umma tayi "Yaya Jabir lafiyarta kalau abinci zamu je ansowa" "Abinci kuma wanne irin abinci,kodai abinci zaku kai mata"fadin Yaya yana tsare ni da ido Umma da Yaya Safiya da suke ta hararata ina kallonsu na cigaba da maganata a ganina boyewar mai za muyi "Yaya ai indai ba girki Ummanmu ba bamu samun abinci,gwara ma girkin Mama Suwaiba takan bawa,Yaya Malika ta kawo mana a boye da idan Mama Hanne ta gani bata bari akawo mana" Yaya Jabir da ransa ya baci ya kalli Umman tamu "Yanzu Mama Amina,kuma kika yarda a rika yi miki hakan,ba zaki dauki mataki ba" Umma tayi murmushi "To Jabir mai zan iya yi,tunda bani na girka musu ba,mai gidan ma da nake ga zai iya tsawatar dasu yace bazai yi wata magana ba" "To ai Baffa ba yi da laifi don yace hakan kece mai laifi,tunda yaga ba kisan ki kwatarwa kanki 'yanci ba fiyema da haka ce miki zaiyi, ke zaki kwatarwa kanki 'yanci,idan yaga kin yi jarumartar tararsu da maganar shine zai yi musu magana shima" "To amma taya ya Jabir,kasan sunfi karfina sunfini manyan 'ya'ya ko ku sasa ku dokeni da 'ya'yana"Umma tayi maganar cikin raunin murya Yaya Jabir ya zaro ido " duka kuma Mama Amina wallahi indai ina gidan nan babu mai taba ki,ki cire tsoro kije ki tunkaresu da maganar,ke ranar girkin ki kike girka musu abincin da tarin 'ya'yansu kece suke kyashin baku abincin da bai kai ya kawo ba,haba kema said kace karamar yarinya" Murmushi Umma tayi "Ko 'daya Jabir ni dai banason neman rigima ne" Nayi saurin sa baki da muke har lokacin muna jinsu "Umma wallahi idan ba zaki yi magana ba zanje nayi" Yaya Jabir ya kalleni yadda yaga nayi maganar ba alamu wasa hakan ya bashi dariya "Kyaleta Hauwa'u zama tayi maganar ku je ku debo kwanuka kuje ku kai a zuba muku,idan Gwaggo Larai ta muku magana ku cemata nina ce azuba muku" Haka akayi nice naje nakaiwa kula ta zobo mana abinci,Gwaggo Larai mai yi mana abinci,amma banda ranar girkin Ummanmu duk ranar girkin Ummanmu to ranar hutun Gwaggo Larai ne, haka ta zubo mana abinci mai rai da lafiya da aka dade da gamawa aka rurrufe a kuloli a ciki harda wanda za'a kaiwa makwabta gidajen da suke da karamin karfi a unguwar tamu Koda na dawo Yaya Jabir yana nan sai da ya ga yawan abinci zai ishemu ya mike ya tafi Gwaggo Larai da ina dawowa ,ta nufi bangarensu Mama Hanne ta sanar musu abinda ya faru Yaya Jabir yace a bamu abinci kuma ta zuba mana Cikin bacin rai Mama Hanne ta nufo bangarenmu cikin bacin rai babu ko sallama ta kallemu da muke ta zuba uwar lomar abinci nida Yaya Safiya "Da kyau tsofaffin mayu,kwayi loma mana tunda va'asa ba haduwa ba" Umma ta doka wa Mama Hanne tsaki nayi mamakin tsakin daya fito bakin Ummantamu ganin bata saba yi wa wani tsaki maganar data fadawa Mama Hanne ta kara bani mamaki "Kinga Hanne karki kara cewa 'ya'yana mayu don babu batun maita don sunci abincin gidan ubansu" Mama Hanne da ita ma nasan tayi mamakin maganar Ummantamu ganin bata saba ba "Idan na sake fada musu mai zai faru?" "Zamu kwashi 'yan kallo,saboda yadda kike takama mijinki ya kawo abinci da za'a girka nima miji nane kuma wadannan ta nuna mu 'ya'yansane,don haka banga dalilin kiransu mayu ba,kuma abinci daga yau barar fashin kin zuba musu a gidan nan,tunda suma 'ya'yane"ta fadi haka tana tsare Mama Hanne da ido Mama Hanne tayi dariya "Yayi mai miji,miji da bai damu dake ba baidamu da 'ya'yanki ba harkike tunkawon mijinki ne" Umma ta maida mata da martani "To ai tunda zamansa nake,kuma 'ya'yana nasane to dole na kirasa mai miji na uban 'ya'yana, kuma ni miji na ya damu dani" "Ina damuwar take ni bangani ko a jikinki ba bare a jikin 'ya'yanki" ta karasa zancen tana nuna mu "Ai ni ba so nake ki ganta ba" Fadin Umma ta na cigaba da "Kuma ki fita ki barmin bangare, tun muna mu biyu Ganin yadda Umma ranta ya baci yasa Mama Hanne saurin ficewa don tana tsoron su kwashi 'yan kallon da Ummantamu Tun daga wannan lokacin muka samu saken cin abincin gidanmu amma sai dai wannan abun na kwaranyewa wata rana muna zaune a falo da Ummanmu tana koya mana karatun boko dukda bawai karatun bokon tayi mai zurfi ba ajinta biyar firamare aka yi mata aure amma yadda take da kokari sai kace takai matakin gama sakandire wannan yasa kullum da mundawo islamiyya take zama ta sake koya mana daga na islamiyyar har na bokon Baffa ne ya shigo babu ko sallama da fadansa " yanzu Amina abinda kikai kin kyauta kenan,ace tun daga ranar da nace miki akan abinci ki kwantarwa kanki 'yanci kika daina bawa Malika abinci a gidan nan sai dai ki tasa abincin gaba ke da 'ya'yanki ku ci" Umman ta dago dakanta da idanunta jawur "Amma Baban Sule ya kamata da aka fadama maganar ka zauna kayi nazari ba wai ka yanke min hukunci ba,ni ca nake sanda ba'a kasa abinci dani da 'ya'yana a gidan,duk ranar girki na ban fasa zuba wa diyayoyinsu ba ko su kansu" "Nazarin me kuma zanyi bayan nasan fiye da haka zaki iya,akan wadannan 'ya'yan naki wallahi Amina kiji tsoron Allah,saboda kinga na baki dama shine kike kokarin ki zarce ko?" "Bangane naji tsoron Allah ba da tsoron wa nake ji,kai duk cin zalinmu nida yara na da kake ci baka gani,sai kayi wa matanka suttura biki ko suna ni baka yiwa nawa ko tsinke ba,hatta karatu ma makaranta mai arha kasa su" Umma ta maida masa wannan martanin cikin bacin rai "Lallai Amina wuyanki ya isa yanka ki dubi tsabar idona kice dani haka wato duk kokarin da nake akan 'ya'yanki bakya gani ko,to daga yau dinki ko sallah ce nadaina yiwa 'ya'yanki,makaranta kuma ta gwamnati zan sasu banda ma........." Bai karasa maganar ba Kawu Haladu kanin Umma yayi sallama,mu da muke ta zaro ido muna kallon yadda Umma da Baffa keta fada a gabanmu,jin sallamar Kawu Haladu yasa mu saurin tashi muka karasa bakin kofar da Kawun namu yake muka rungumeshi da fara'arsa shima ya rungume mu sannan ya ruko Hannun mu zuwa cikin falon Baffanmu da yake har lokacin tsaye a gurin Kawu Haladu yana kokarin zama a kujerun falon "Alhaji Ina yini" Tsaki Baffan yaja ya five fuu da daga dakin namu yana banko kofa Baffan na fita Kawu Haladu ya dubi Umma da muke zazzaune kusa dashi "Yaya Amina ina yini" Umman data dawo daga tunaninta jin maganar Haladu "Bazan amsa ba" tayi maganar tana harararsa "Kai Yaya Amina mai kuma nayi" "Kaima kasani ni ban daukama talakawa na ganinku ba" "Wallahi Yaya Amina kinsan yanayin sana'ar tawa yanzu ma wani yaro na bari a gurin" "To Allah ya taimaka" "Amin" Mikewa Umma tayi ta shiga ciki A lokacin muka gaishe muka gaishe da Kawun namu ya amsa yana tanbayarmu karatun mu Muna cikin haka ne Umma ta dawo falon da abinci a plat da ruwa a kofi ta ajiyewa Kawu Haladu "Sannu Yaya kamar ko kinsan banci komaiba,bayan abincin safe,ke din ma ban dauka zan samu gurinki na dan yau ko buga iskar motar da keken kadan akayi,kawai nace bari na zarto nan,na kawo miki cinikin ki sayi wani dan abin bukatar,saina jiyowa inna lafiyarsu Hauwa kwana biyu,basu jeba saima na sameku lafiya" Umma tayi murmushi "Yanzu har yau baka samu aikin ba,duk kudin da akayita caca,ai komai ya sauya muna samun abinci harma mu bada" Sai sannan idon Umma ya sauka kanmu mu tsira musu ido muna saurarensu "Ku tashi ku tafi wasanku,Yanzu nayi baki saina muku fada ku tashi" Kawu Haladu ya katseta "Yaya Amina,don sun zauna ai basu da laifi laifunsu su saka mana baki a maganarmu amma idan yaranmu busu ji matsalarmu ba waye zai ji mana" Mu da muke kokarin tashi muka koma muka zauna,to dama ina zamu gaba daya 'yan gidanmu bamu yawon unguwa harta yayyenmu,imu imu muke wasan mu sai dai mu din a iya bangaren Umma muke wasan mu don dukanmu suke sauran idan mun shiga cikinsu,Umma ganin mun zauna ta bimu da harara "Ai Yaya Amina kinsan aiki sai ka mika kudi to mu ina muke dana mikawar,kudin da aka kashe a karatu basa zama caca ai shi karatu indai kayi ka anfana koda ba kayi aiki ba zai canza ma rayuwa,dama yanzun nake shirin tanbayarmiki maike faruwa ne najiyo hayaniyar ku zan shigo falon kuma naga nagaida Alhaji Mamudan bai amsa ko dai akan abincin ne"fadin Kawu yana kallon Umma "Hmm kai bari Haladu bama batun abincin yake fadan ba,tun ranar dana nuna musu basu isa ba suka soma bamu abincin nan ta bashi labari duk abinda ya farun ta cigaba da " yanzu akan abincin Malika da ban zuba mata ba,bata gidan lokacin ta kwana gidan Alhaji Audu shine ban masan da dawowarta ba,ashe tadawo a dazu,to yanzu matan suka zugosa ya shigo ya fara fada"shine ka taddasa yana wannan banbanmin yace makaranta ma ta gwamnati zai maida su Nana (sunan da take yawan kiran Yaya Safiyya dashi)kan hakan" "Amma Yaya Amina, hakuri zaki rika yi komai yayi kansa amma hayaniya da mijinki ba mafita bace" "Haladu, batun hakuri kam kaima kasan da cewar inayi" labarin duk abinda ya faru da itada mijinnata kafin shigowar Kawu Haladun ta basa "Kai nidai Yaya Amina bansan halin mutumin nan ba,hakuri zaki tayi wata rana sai labari insha Allah komai zai wuce,kinga da kina sana'a da koda ya canza musu makarantar saiki maidasu wata ta kudin,to matsalar babu kudin da zaki ja jari,amma ki barsa ai duk makaranta makaranta ce" "Hakane Haladu,wallahi a kullum yaran nan nake tunani banda haka ba zan iya cigaba da zama da Mamuda ba sabida iya biyayyar aure ina gwada yi masa amshi baya gani" "Hmm Yaya Amina kenan,ai gidan mijinki shine rufin asirinki,duk tsiya gidanki yafi zaman gidanmu,kina gani da ran Baba ma yadda muke rayuwa bare yanzu babu shi,Inna sana'ar saida abinci take idan bake ma so kike ki rika yi ba,hakuri zaki cigaba dayi wata rana sai labari amma ki cigaba da addu'a don ina zargin shiga tsakaninku akayi da mijinki,dan da farko ba haka Alhaji Mamuda yake ba" "Haka ne Haladu,amma wa make tunani zai shiga tsakaninmu,kishiyoyi na ko suwa?,banaso ka rika tunani irin wannan Allah ne mai yin komai babu wanda zai ma wani abu ba Allah ba,mutum sanadiyya yake zamowa,ni na mika lamurana ga Allah kaima inaso ka zamo hakan" "Hakane Yaya Amina,amma kiga yadda Alhaji Mamudan yake nuna kaunarsa gareki kafin aurenku da bayan aurenku dama shine nake tunanin ko kishiyoyinki ne suka shiga tsakaninku amma tunda kin nuna ba haka bane shikenan" "Bawai so ne bana yi ba Haladu,kaima kanka kasan dan Adam yakan boyema halayyarsa,sai daga baya inda tafiya tayi tafiya ka fahimci halayyoyinsa da yake voyema tunani na shima Mamudan haka yayi daga farko" "Eh hakane Yaya amma dukda haka ki cigaba da addu'a a koda yaushe karki rika sake da ita domin ita takobi ce" "Haka ne Haladu" Kallo na Kawu Haladu yayi da tunda suka fara maganar ido na ke kansu dukda na fahimci akan Baffa suke maganarsu kuma ina saurarensun amma bazan iya wani tunani akan maganar ta su ba,tunda shekaru na baikai nan ba, yana dariya ya dubi Ummanmu "Yaya kinga 'yar nan taki ta tsare mu da ido kamar tana fahimtarmu" Itama Umma dariya tayi "Lallai Haladu baka san wayan Hauwa ba,ai sarai tasan maganar Babanta ake tayi tunani inda maganarmu ta sosa sosai ne ba zata iya ba,amma jiya har cemin tayi idan ta girma zata siyamin irin kujerun dakin Mama Hanne dana Mama Suwaiba tunda Baffansu bai siyomin ba,na ce mata ai shima bashi ya siyo musu ba,tace min bata yarda ba tasan shine gashi nan iri daya ne dana dakinshi" Dariya Kawu Haladu yayi "Lallai Hauwa har kin zama kece babba ashe" Dariya nayi Yaya Safiyya da ta kai hannunta baya na ta makan duka Umma da take kallon Yaya Safiya sanda take duka na "Mai tayi miki Nana" Yaya Safiya da idonta ya cicciko da hawaye "Umma tun dazu fa ina kallonta tana murmushi taji ana fadar laifin Baffa a gabanta,yanzu shine zata yi mana dariya" "To sata tayi kuka kamar me tunda,an fadi laifin Baffanku,kuma aiba wani abu akace game da shiba gaskiya aka fada abinda yake ko kar a fada,mai uba" Yaya Safiyya ta girgiza kai kawai ta tashi daga inda muke wannan yasa nima na mike ma bita don nunyi sabon da ba zan iya ganin Yaya Safiya bata guri ni kuma na zauna ba [10/13, 8:18 PM] Sadiya Khalil Muhammad🥰: *JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil Book 2. 6. Bayan watanni uku Alokacin abubuwa da dama sun faru na farin ciki da kasinsa a lokacin ne Baffa ya aurar dasu Yaya Fati da Yaya Umma wato Salamatu,a Danbatta Yaya Umma tayi aure Dan uwansu Baffa ta aura, Yaya Fati kuma anan Kaduna dan kasuwa ta aura a lokacin kuma muka koma sabon gidanmu dake sabon Kawo babban gida yana da bangare akalla uku ,amma na tsakiyar da shine babban ciki a ciki gaba daya bangaren matan Baffanmu suke mu hadu a falo ne sai gefen falon matakalar bene bangaren Baffanmu daga gefe batun ko dai rayuwarmu a gidanmu gaskiya zan iya cewa sam babu dadi musamman yanzu da muka koma rayuwarmu dasu guri daya,indai har muka fito falo mu akaran kanmu wannan yayan namu ya doke mu wannan ya zagemu mune kawai ware a cikin gidanmu muda mahaifiyarmu hatta da Danbatta idan muka tafi nanma hakane babu wani so da suke nuna mana kamar sauran a raina nakance kodan mu bamu mahaifiyarmu ba su da alaka da Baffa ne don itace bare kadai a cikin matansa,amma dai ita ma bafulatanarce daga baya saina fahimci ba haka bane kawai dai ta ko ina Mama Hanne ta batawa Ummanmu suna ne da irin wannan rayuwar muka cigaba da tafiya batun makaranta kuwa tuni an sauya mana an maidamu ta gwamnati amma hakan bai sauya kwakwalwarmu ba muna ganewa sosai da haka har Yaya Safiyya ta kammala Secondary dinta sai ni da nike zuwa ko wacce rana ta duniya,Inna Saude da Kawu Haladu kuwa kullum naje gidan kamar na tasa su na dinga kuka ne gidan da suke ciki duk ya rushe amma Sam mai hayar yaki gyarawa yace basa biyanshi kudi,duk asabar da lahadi na kanje gidan Inna Saude na taya ta mikawa masu siyan wainar da tako ma yi da safe,Umma kuwa ita ba samun wani abu take ba gurin Baffa sai dai matan so su samu,haka zaka jisu a babban falo suna ta yiwa Baffa kidayar kudi da suke so yabasu su da 'ya'yansu amma banda mu tamu mahaifiyar duk ranar da kaji suna magana ta sake tayi masa zance kudi saitayi danasani ranar cin mutunci iri iri yake yi mata saboda har lokacin bai manta son kudin da Babansu Umma ya nuna ba lokacin aurenta ba,Kuka zaka ga muntasa ta muna yi,idan munce tazo mu bar masa gidan ta kance ba muda Inda yafi nan,sai muce garinsu ai yafiye mana nan,murmurshi take yi ta kallemu tace"kuma da zaku taimaka musu so zasuyi,rayuwarsu tafi tamu tausayi,takan ce ko a kauyenmu dangin mahaifina idan munje na kallesu na kalli ragowar na kanga kamar sunfi kowa babu,ku cigaba da hakuri ko vayan bani,batun sana'a Kawu Haladu da yaje garinsu Kuka kubeya dakakkun su barkono kanwa duk ya hadowa Ummanmu ta rika siyarwa ta soma a sa'a tana ciniki amma da matansa suka fahimci haka suka fadawa Baffa yazo ya hadamu duka ya fara mana fada "Ya za'ayi bamu rasa ci da sha da suttura ba,gama yadda yake da arziki mu rasa sana'ar da Umma zata rika yi sai saida su kuka, gaba daya ya kwashe kayan da Umman ke saidawa ya zuba a store dinmu na kayan abinci. Yau kamar kullum da shiri na na makaranta na fito babban falo da na tadda Baffanmu zaune a kujera yana kidayawa Yaya Sule da Yaya Abdu da Yaya Bello kudi na hidindimun bikinsu da za'ayi a wannan watan Gaishe su nayi sannan na kalli Baffa " Baffa na fito kudin tara" Yaya Sule ya duba agogon hannunsa ya kalleni "Yanzu karfe nawa, 8:00 sai yanzu zaki tafi makaranta saboda shashanci...." Baffa ya dakatar da Yaya Sule "Au yanzu Hauwa'u yau ma makarar kikeso kiyi,karfe nawa Larai ke gama muku abinci" Nayi kasa da kaina "Baffa karfe shida da rabi" Baffan ya sake kallo na "Na lura karatun ne bakyaso ko gata ne yayi miki yawa akaiki a mota a dawo dake to yau a kafa zaki tafi haka ma batun dawowa karma kice zaki jira" Jiki babu kwari na mike banma jira kudin tara ba saboda nasan tunda Yaya Sule ya hadani da Baffanmu biyar dinsa baya bani "Na tafi" Nace masu aiko cikinsu ba wanda yayi min koda magana Har na fice **** Ina tafiya ina tunanin rayuwar tsakanin gidanmu da makarantarmu akwai nisa bakadan ba,biyar kuma ba nida ita a jaka ta Horn da naji a baya na yasa ni matsawa gefe Yaya Jabir ya leko da kansa ganin shine yasa ni sauri karasawa inda yake Yaya Jabir ya kalleni "Hauwa yana ganki a kasa yau ina drivern?" "Na makara,shine Baffa yace na tafi a kasa" Yaya Jabir ya girgiza kai ya bude mota "Kinga shigo na kaiki,banda abin Baffa ai yanzu ne ma yafi kamata a kaiki a mota" Daga haka na shige motar Yaya Jabir na zauna gidan gaba,da duk cikin motocin Baffanmu ne ya fito da daya daga ciki Sai da muka fara tafiya Yaya Jabir ya soma magana "Ya yau kika makara ne Hauwah vayan ba halinki bane makara makaranta" Murmushi nayi "Wallahi Yaya Jabir Exam zamu fara na jima ina karatu daga sallar asuba saina koma na kwanta" "To Allah ya taimaka" "Amin" na furta muka cigaba da tafiya Yaya Jabir ya sake kallona "Bari na yima wancen abokin nawa magana" daga haka ya gangara da motarsa gefen titi kusa da inda wani saurayi yake tsaye da alama shine abokin nasa kansa ya zura ta motar "Ibrahim lafiya dai ko?" "Abokin nasa mai suna Ibrahim naga ya waigo ya dubi Yaya Jabir da alama yasanshi ganin ya karaso inda muke ya leko cikin motar yana fadin" "Oga Jabir dama kana gari" Yaya Jabir yayi murmushi "Gani ma" Sai a sannan na gaishe da abokin Yaya Jabir din nayi ba tare dana dago kai na ba Ibrahim din ya amsa da fara'arsa Yaya Jabir ya dora da magana "Ina zaka nufa ne naga alama kamar abin hawa kake jira" "Eh wallahi zanje Mallam Madori Road ne" "Ah to shigo mana na kaika "A'a bana shigo ba naga bakai kadai bane kuma da alama yar makaranta zaka kai" "Badamuwa duk hanya daya ne GGSS Dutsima Road kaga zaina karasa dakai ai can Road din,bari ta koma.baya kai saika shigo gaban" Ni Yaya Jabir ya kalla "Ki fito ki koma baya ya shigo" Babu musu na fito daga motar sai sannan na kalli Ibrahim din yana kokarin shiga motar daganin alamu Ibrahim akwai son gayu Muna fara tafiya makaryaya " jiyo muryar Jabir yana cewa da Ibrahim din "Dama talakawa na ganinku Ibrahim" Ibrahim yace "Kaji ka ai mune talakawan naku" Yaya Jabir yace "Hmm,haka dai kace,ina motar taka yau?" Ibrahim yace "Tana gurin gyara" Ibrahim ya juyo inda nake yana fadin "Yan makaranta ya kike makara makaranta ki daina kin jiko ko karatu bai wuce ki ba za'a doke ki" Murmushi nayi kawai nace nasa "Insha Allah na daina" Daganan ya juya gurin Yaya Jabir "Danbatta ya bansan wannan ba wai itama kanwar kace" Yaya Jabir yace "Eh mana,yanzu bakasan Hauwah ba a gidanmu" Ibrahim yace "Nasan sunan amma bamu taba haduwa da ita ba idan nazo gidanku ba" Yaya Jabir yace "Diyar Mama Amina ce amaryar Baffa" Ibrahim yace "Ah shiyasa duk tafi ku kyau ashe mamarsu ta biyo" Mamaki ya cikani jin maganar Ibrahim ashe har Ummanmu ya sani amma ni ban taba ganinshi ba,wata zuciyar tace.kila sanda yake zuwa gidan namu muna makaranta maganar da naji Yaya Jabir nayi ta katsemin tunani na "Wato mu munana kenan?" Na juyo dariyar Ibrahim ya dora da "Bare ma ni ban ki yaban kyawunku ba,kuma ai kyawawane Fulani,amma dai Hauwah ta daraku" "To ai nace dai naji dama na fiso ta fimu kyawu ai?" Fadin yaya Jabir Da haka suka cigaba da firarsu da take nuni da Ibrahim abokin Yaya Jabir ne sosai.*JININMU 'DAYA* BY Sadiya Khalil Book 2 7. Yau kam saura kwana uku bikinsu Yaya Sule hakan yasa 'yan Danbatta suka fara zuwa a yau din yawanci duk gwaggoninmune daga diyoyin kannen babansu Baffa sai diyoyin kannen su Innarsu Baffanmu dasu da yaransu.hakan yasa yau duk bamu da wani kuzari tunda muka ji zuwansu muke a daki ni guga ma na debo na fara yi Yaya Safiya tana shirya mana a sib ko niyyar zuwa gaishesu ba mayi.Umma ce ta shigo dakin mu da sallamarta a same mu ina cikin gugar kallonmu tayi "Ban gane ba Nana,nufinku ba zakuje gaishe da Gwaggonin naku ba,kuka debo guga kome" "A'a Umma zamu" fadin Yaya Safiya da take kokarin mikewa Dutsen da ke jikin socket na jingine na kalli UMMA "Kai Umma yanzu sai munje wani gaishesu,tunda kinje ba shikenan ba" "Shikenan din wa ni badan ku zani ba dan kuma mahaifinku,da nake auranshi amma ku ai danginku ne dolenku ne" Na zunburi baki nace "Amma Umma bafa da san.... "Umma cikin fada ta katse maganar dana keson fada " Zaki tashi ko ba zaki tashi ba,bafa nasan gaddardami banfi ki sanin komai ba" Badan na soba na mike ina kunburo baki muka fice Umma tabiyo bayanmu. A falo muka tarar da Yaya Jabir zaune a kujera "Umma ta kallesa da fara'arta "Yaushe ka shigo ne Jabir" "Wallahi Mama yanzu na shigo da naga kayan kallo kunne nayi tunanin baki dade da barin gurin ba" fadin Yaya Jabir Umma ta dube mu "Eh Jabir ciki na shiga ciki kiran kannenka suje yiwa gwaggoninku da zuwa su gaisa" Yaya Jabir ya dubemu "To shine,harda batan rai,don ance kuje,kamar wadanda za'a kama "Nace " amma Yaya" "Amma me ku wuce ku tafi" "Umma tace " kaga ni sai gardama nima suke ta yimin" "Daga gaisuwar kuyi ku taso inma busu amsaba kundaije sai duk abinda za'a fada akanku indai kunsan ba haka bane damuwar mai zaku yi,tunda kunsan halinsu kuma Mama saita zuge suma indai baku jeba" Badan munso ba muka bude kofar falo muka fice Muka jiyo Umma na cewa "Yawwa fada musu dai yara sai bakar gardama" A babban falo muka tadda bakin duk kannen iyayen Baffa ne da 'ya'yansu suma dana su 'ya'yan ayari guda sai Gwaggo Hadiza itama da tata gayyar sun bararraje sa falo wasu suna cin abinci wasu kuma suna ta zuba fira cikin fillanci dasu Mama Hanne sallamarmu ta tsaida firarsu Gwaggo Hadiza da idanta ke kanmu har muka tsugunna muna gaishesu da musu sannu da zuwa amma ko kusa Gwaggo Hadiza bata amsaba sai kallonmu da take tayi can muka jiyo muryarta "Sai yanzu Uwarku taga damar barinku kuzo gaidamu,marasa mutuncin banza da wofi" Kanmu muka dago jin kalamin Gwaggo Hadiza Mama Hanne tayi caraf tasa baki tace "Ai kunga halin nasu yanzu da nake fada muku,musamman ke Hadiza kin gaza yadda,ai yanzu ke yarda, Amina yadda ta dauki kanta kamar diyar Dangote tasa diyoyinta suka dauki kansu" Gwaggo Hadiza da Gwaggo Harira suka hada baki gurin cewa "Aiko bata basu tarbiyya ba,ita Aminar 'yar matsiyata ubanta harya mutu da talaucinsa" Mama Hanne ta cigaba da magana jin sun dauki zugarta "Ai Amina makirar macace hatta diyoyinta ta koya masu halinta" Gwaggo Hafsatu da ita ma kanwar Baffa CE abokan wasa suke da Baffa,hakama kanwar Mama Hanne ce tasa baki a maganar "Kunga ku tashi ku tafi" Jiki ba kwari muka mike sakaka muka bar gurin dama munsan fiye da haka zamu tarar Gwaggo Hafsatun muka jiyo tana cewa "Haba Yaya Hanne mai yasa zaki rika irin haka,ko kaffara babu kece makirar" "Ke Hafsatu nice makirar wallahi saikinyi danasanin ce mani makira" muka jiyo muryar Mama Hanne cikin fada Daganan muka bude murfin motar bangaranmu muka shiga Da sallama muka shige falon namu,firar da Umma da Yaya Jabir suke muka katse masu amsa mana suka yi muka zauna kujerar mai biyu mai kallan ta Yaya Jabir Yaya Jabir ya kallemu " badai har kun dawo ba,mai ya bata ranku naga fuskarku haka" Murmushin yake muka yi Yaya Jabir yayi gyaran murya "Hakuri zaku cigaba da yi watarana kowa sai yayi alfahari daku an kuma so ku" Guntun hawayen idona na goge nace "Yaya Jabir hakan bamai yiyuwa bane nake tunani,kaga fa irin kiyayyar da suke nuna mana koda yaushe aita aibata mana uwa" Umma ta kalleni ta soma magana da sai yanzu tasaka baki a maaganarmu tunda shigowarmu "Hauwa'u to meye na damuwar don an aibata ni, duk abinda za'a fada a kaina indai kunsan ba haka bane kudai na damuwa,wata rana bazasu fadamin ba,wata rana sai labari" Na kalli Umma nace "Amma Umma..." Sallamarsu Yaya Malika ta katse maganar da nake son karasawa duk muka maida dubenmu gare su da gudu na karasa na rungume wasu daga cikin yayyena diyoyin Gwaggo Hafsatu suma suka rungume ni da haka muka karaso ciki da Umman mu cikin nuna kulawa take musu Sannu da zuwa Har kasa suka duka suka gaishe da Ummanmu,har raina inasan su Yaya Ma'u da Yaya Hannatu da suka fita daban su da mahaifiyarsu akaf cikin dangin Baffanmu suna nuna soyayyarsu gare mu muddin munje Danbatta kosun zo Kaduna dasu a cikin Danbattan suke zaune shiyasa muka saba sosai. da Yaya Ma'u tsarar Yaya Safiya ce Yaya Hannatu kuma ta girme min da shekara a akalla hudu saboda rashin tazara mai yawa tsakaninsu da Yaya Ma'u don Yaya Ma'u baifi shekara 1 da rabi ta bawa Yaya Hannatu ba,hakan yasa suka taso kamar tagwaye ga kamar da suke da juna. Umma ta katse min tunani na naji tana cewa "Dama har daku a kazo hala dai su Hauwa'u busu ganku ba yanzu suka dawo daga gaishe dasu Mamartaku" Su Yaya Ma'u da suka zazzauna a kujeru Yaya Ma'u tace "Eh wallahi Mama,muna ciki mu,yanzu da naga su Safiya busu shigo ba,nacewa Malika hala busu san da zuwanmu ba,da sun shigo" "Eh gaskiya basu sani ba,to ya hanya yasu Baffanku da sauran mutan gida" Fadin Umma "Yaya Ma'u tace " wallahi duk suna lafiya,su Baffa jibi ranar daurin aure zasu iso" "Allah ya kaimu lafiya" Fadin Umma daganan ta kalli Yaya Jabir suka cigaba da firarsu Yaya Ma'u ta dube ni "Hauwa'u hala duk murnar ce kika tsare mu da ido" Nayi murmushi "Wallahi kuwa Yaya Ma'u kamar ko kin sani, ya hanya" "Alhamdulillah" Fadin Yaya Ma'u tana murmushi Daganan muka mike zuwa dakinmu muka zauna zaman baja kolin fira Zuwa can Yaya Hannatu ta kalli Yaya Malika tace "Yaya Malika wallahi kwadayi nake ji muje bakin titi ko biscuit na siyo" "Yaya Malika tace " aifa kinzo uwar kwadayi,wannan yaya Usman ya bani da kwadayi" Dukkanmu dariya muka yi.Yaya Usman shine saurayin Yaya Hannatu suna matukar son junansu Da zunbula zunbulan hijabanmu muka fito harabar gidanmu muna fira cikin nishadi abakin gate muka ci karo da Yaya Jabir ya kallemu ya dauke kai "Ina zaku je ne?" Nice nayi saurin cewa "Mama Suwaiba ce ta aikemu shago" Kai ya daga muka yi saurin ficewa don nasan indai ba sharara karyar muka yi ba ba zai barmu mu fitan ba muna fita muka sa dariya savoda karyar da na yiwa Yaya Jabir haka.muna kokarin karasawa wani shago da yake jikin wani dan karamin gida mai kyau Yaya Safiya tayi saurin cewa ga wani shagon nesa da wancen muje "Yaya Malika ta tsaya jin maganar Yaya Safiya ta kalleta tace " don me zaki ce muje mai nisa gana kusa,ko basu saida biscuit " Yaya Safiya ta girgiza kai tace "A'a kawai dai" "Kawai me" Yaya Malika ta fadi haka tana cigaba da tafiya muma da muka tsaya muka bi Yaya Malika da sallama muka karasa shagon ba mu samu mutane a shagon ba mai shagon ne kawai kai ya dago yana amsa mana sallamar da murmushi a fuskarsa daganinsa zaka tabbatar bafulatani ne sosai gaishe sa muka yi ya amsa yana bin kowaccenmu da kallo yana jiran jin mai zamu siya "Yaya Hannatu tace " Dan Allah zamu samu Waper ne anan" Murmushi yayi yace "A'a Cabin muke saida wa" Yaya Hannatu tace "Yanzu duk girman shagonnan babu wafer?" Yaya Safiya ta kalli Yaya Hannatu tasa dariya tace "Anyi maganin mai kwadayi" Saurayin ya kalli Yaya Malika yace "Ya kike mata dariya idan ma fiye da wafer ne zata samu anan"yayi maganar yana sake kallen Yaya Ma'u Murmushi Yaya Malika tayi " amma da kace babu" "Eh mana naji kuna tanbaya kamar kun raina shagon shiyasa" ya fadi haka yana karasawa jikin kantocin shagon ya debo mana buskunan kala kala ya zuba a leda ba tare da ya tanbayemu nawa kudinba "Yaya Ma'u ganin ya miko wa Yaya Hannatu ledar ta kallesa " ya zaka bamu kaya haka baka tanbaye mu kudinba,baka tanbayi kalolin da muke soba" "A'a bama saina tanbaya ba na dade da sanin abinda ya cancanceku" " Saurayin yayi maganar yana sakarwa Yaya Safiya murmushi da kanta yake kasa tunda muka zo shagon ina kula da ita "To nawa ne kudin" Fadin Yaya Ma'u tana kokarin bude jakar hannunta ta debo kudi "A'a kubarshi" Godiya muka yi.muna kokarin barin shagon muka jiyo muryarsa yana cewa "Zan zo yau saura kiki fitowa kamar jiya" Yaya Safiya da na fahimci da ita yake tunda muka zo shagon muke kallon yadda yake kallonta nan nayi tunanin ashe shine Hashim din da yazo jiya Yaya Safiya taki fita Saida muka fara tafiya Yaya Malika ta tsaya muma muka ja muka tsaya ta soma magana "Ku Daka ta wai wancen saurayin dawa yake nidai nasan ba dani yake ba" "Yaya Ma'u tace " bare kuma mu,baki" Nima nace " bare kuma ni sai dai koda Yaya Safiya yake,ina kallon irin kallon da yake mata" Duka muka sa dariya Yaya Malika tace "Nima na gani Safiya,she shine na karfen,shiyasa da zaki mana bukulin samun wannan buskunan kyauta" Yaya Safiya tace "Kai Malika nidai ba haka bane" Yaya Ma'u tace "Nufinki bahaka ba saurayin naki bane kome" Yaya Safiya ta daga kai tace Na kalleta nace "Kai Yaya Safiya kiji tsoron Allah jiya fa an aiko kiranki akace inji Hashim kuma baki fita ba" Yaya Safiya ta harare ni "Da tsoron ki nake ji,mara kunya kawai" Zanyi magana Yaya Ma'u tace " kyaleta Hauwa'u mun san komai ai yanzu"dukkanmu muka saka dariya muka cigaba da tafiyarmu A falon bangaren Ummanmu muka baje buskunan Umma da take zaune tana kallo ta kalli buskunan "Usman ne ya siyo muku wannan kayan ko masu yawa" "Yaya Ma'u ta kalli Umma tace " ai dama shine Umma da munji dadi tunda budurwar shi ce mai kwadayin dama,wannan saurayin Safiya ne ya bamu,shagonsa muka je siyayya,wallahi Umma yana da kirki surikin naki" Umma tayi murmushi tace "Tunda zai baku ba,ayi dai a hankali da samari don basu da tabbasa karku zurfafa soyayyar kowanne saurayin Allah ya tabbatar da Alkhairi" Muka amshe da Amin Daganan Umma ta mike tabar mana falon Yaya Safiya kanta a kasa tunda aka fara magana ganin Umma ta bar falon tace "Allah ya shiryi magulmata,harku gwangwadawa Umma" Yaya Ma'u tace "Ba wata gulma indai ba yaudararsa kikeson yi ba gwara mu fada tun wuri kowa ya sani,tunda za'a dashi" Yaya Safiya tace "Kai Ma'u dan baku buskunan har kun yadda dashi" "Kwarai kuwa ai damai bayarwa muke yi,kuma dagani ma yana da kirki" Haka dai muka cigaba da firarmu cikin farin ciki. Umma ce ta leko dakin da muke duk mun kwankwanta har dasu Yaya Ma'u da a dakinmu zasu kwana ni ta kira na fito na sameta a dakinta nace "Umma gani" bayan na zauna kusa da ita Ta dubeni ta soma magana "Hauwa kinsan Ibrahim abokin Jabir" Na daga kai nace "Eh kwanaki mun hadu da Yaya Jabir zai kaini makaranta" Tace "yawwa to shine ya samu Jabir da maganar yana sanki tun kwanakin da kuka hadu, kuma bada wasa yake ba yace wa Jabir ya fadamiki,amma Jabir din yayi shiru yanasan ya sake fahimtar da gaske Ibrahim.din yake ko kuwa,ganin kullum Jabir ya hadu da Ibrahim sai ya masa maganar ki ya sanar miki abinda me ransa hakanne yasa Jabir ya yanke shawarar zai fadamin ni kuma na amince sai dai ko ke din,amma dai Ibrahim mutumin kirkine ina fatan zaki amince dashi" Nayi murmushi da kaina ke kasa harga Allah nima bazance ban amince da Ibrahim ba saboda koba komai abokin Yaya Jabir ne kuma Yaya Jabir mutumin kirki ne inada yakinin abokinsama zai kasance haka.kuma ma yadda na dauki Yaya Jabir ba zai kawo abu na iya bijerewa ba saboda inada yakinin yana kaunarmu fiye da yadda nake tunani yakan dauki matsalarmu kamar tasa.ga uwa uba ma gaskiya ba macen da zata ga Ibrahim indai yace yana santa ba taki amincewa ba" Hakan yasa nace wa Umma na amince daganan na tashi na koma dakinmu na kwanta ina farin cikin da ya kasa boyuwa a zuci har saida fuskata ta muna Ranar Lahadi aka daura auran su Yaya Sule duk diyoyin Alhaji Audu dan uwan Baffanmu ubangidan Baffanmu duk suka aura Yaya Abdu kuma jikar Alhaji Audu ya aura diyar Gwaggo Hajara,Gwaggo Hajarar da Baffa yaso aura a baya anyi bikin cikin tsari dukkansu su Yaya Bello da Yaya Abdu a waje Baffa yayi musu gini Yaya sule ne yace a gida yake son zama wani part aka ware masa shida matarsa.A wannan bikin kuma Yaya Sumusi babban dan Gwaggo Hafsatu yaga Yaya Safiya ya nuna yanasan aurenta harma ya fadawa Baffa re da ya nemi amincewar Yaya Safiya baffa yace babu matsala ya bashi.don shi a tunaninsa Yakumbo Hasiya babu abinda diyoyinta ko jikokinta zasu nema a gurinsa indai yanada shi bai masu ba kasancewar Yakumbo Hasiyar kanwar Malam Jauro mahaifin Baffanmu ga shi kuma Yakumbo Fati surikan Baffa ce mahaifiyar Mama Hanne hakan yasa baiyi tunanin halin da Yaya Safiya zata kasanceba idan ta auri Yaya Sunusin kasancewar kiyayyar da danginsa ke muna mana,kuma Yatya Safiya a lokacin ta amince da Hashim don ta fahimci mutumin kirki .Aiko koda Baffa ya fadawa Umma maganar Yaya Sunusi nan ta sanar masa Yaya Safiya tana da saurayi Hashim Baffa yace saidai Yaya Safiya ta basa hakuri tunda gana gida da Umma takara magana yace abinda ya shirya kenan gwara tun wuri tasa Yaya Safiya ta bawa Hashim hakuri.Mama Hanne da taji labarin Yaya Sunusi nasan Yaya Safiya ba karamin murna tayi ba don indai auran ya tabbatar Kaduna zatace Yaya Sunusi ya dawo ya sauna shida Yaya Safiya ko banza Yaya Safiya ta zama boyi boyinta wannan kenan Yaya Safiya har kuka tayi da aka sanar mata labarin tasan shikenan zata zama abar tausayi tunda har taga Mama Hanne bata hana ba tasan kuwa da cewa akwai abinda suka shirya,ga kuma uwa uba tana matukar son Hashim Wanda Hashim din ya kasance haifaffan Adamawa aikin gidan Radio ya kawo Kawunsa Kaduna ya taho da dashi. koda ta sanarma Hashim din ta bangarensa nuna mata yayi bakomai duk abinda Allah ya tsara shine dai-dai hakan kuma baisa ya daina zuwa gurin Yaya Safiya ba.niko nida Ibrahim muna soyayyarmu cikin girmama juna duk iyayenmu sun sani,don murna sosai yayi don yasan baban Ibrahim sosai shima dan kasuwa ne hakan ya Kara karfafa soyayyarmu jira ake kawai na kammala sakandire a mana aure da lokacin nake aji 3 a sakandiren batun hidima kuwa Ibrahim yana yi mana hakan yasa ba muda wasu matsaloli masu yawa a yanzu sai dai Umma san itada Baffa babu wani mutunci tsakaninta dashi komai ta masa gaban Iowa hantararta yake da fada mata bakaken maganganu Mama Hanne kuma ta dora da NATA kota zuba Baffa amma hakan baisa Umma indai ba Baffa ya kaita makura ba tayi magana ba Allah ya zubawa Umma.hakuri a kullum.na tuno Umma nakan jinjinaa hakurinta ba duka mace za'a samu da shi ba. Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels