Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH *♡SPECIAL☆* _Ta daban_ *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ ~Na Maryam Naseer Mirrah~ _AMMEY LAYLERH_ Page 1&2 _ƊAN ƊANO_ *NA'EEMA SULAIMAN SARAUTA*. _NIMCY LUV_ Ban manta kalan gudun mawar da kika ringa bani ba a littafi na na baya wato MIKIYA. TO haka za wannan ma da Salonta labarin ze fara SEY MA SHA ALLAH.Na sadaukar miki da wanan littafin, this novel is for you my humi darling, my Mummy'na, my support system, my role model, i love you_ *_Special Thanks to:_* Masoya masu bibiyana ina alfahari daku a ko ina a kowacce duniya kuke Love you all 💞💖💘💗💝 ♡♡♡♡♡♡♡ The official trailer for *SPECIAL* {Ta daban} (2025) introduces Novelist to a chilling😄💃, suspense-filled Power Romance thriller set in an isolated, post world. Directed by MARYAM NASEER MIRRAH *AMMEYLAYLERH* SHEIKH JURAIJ THABIT JT follows. *♡SPECIAL☆*must evade capture while uncovering hidden truths about her past and her connection to the cult’s terrifying leader. The trailer teases In a world where trust is a luxury and survival is the only rule. Alhamdulillah masoya na Asali am back dawo muku da wani fitacce kuma ƙayatacce ƙasaitaccen labarin dazai ƙayatar daku💃, Bazan iya misalta muku meya ƙunsa ba sai inhar kun biyo alƙalamin AMMEY LAYLERHbAnan ne kaɗai zaku fashimta inane alqamin ya dosa🪷, fatar baku manta da ƙayatattun littatafan nan nata ba irin su. *MIKIYA* *KAREN BANA* *JALAAL AREEF* *ƘAUNA BIYU* *SANYI YA HAIFA WUTA* And Ongoing *♡SPECIAL☆* Fatan baku manta da yadda kuke nishanɗan tuwa da duka littatafaina na baya ba. Iyaka waɗan da suka karanta littafinta na MIKIYA to kuwa sune zasu fi kowa bada yadda waccen tafiyar ya kaya. Se dai wannan ma is not free book shima yazo ne a paid amma kafin nan akwai free page da zan ba *MASOYA* Masu bibiyana. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ *_KADUNA MARAFA_* ~012 Alongside films shot~ Cike ƙaton hall ɗin yake da mutane babu ko masakar tsinke.kowa ka kalla zakaga fuskansa na ɗauke da annurine. Dan kuwa kalla ɗaya zaka ma fuskokin nasu ka gane lallai suna cikin farin ciki ne matuƙa. Se dai wasu tsirari daga cikin jama'ar dake cike tab da hall ɗin suka soma kallar wrist watch ɗin dake ɗaure da hannayensu suna jan tsuƙa can ciki ciki. Wasu kuwa suna a cikin yanayi ne na shiru fuskansa suma yana fara sanjawa zuwa na damuwa. Domin kuwa idan har akace yauma Babbar jaruma kuma fitacciyar ƴar wasan Hausan nan wato *DIAMOND MEESHERH* ba zata samu halartar wannan shooting trailers ɗin ba Lallai kuwa da akwai babbar damuwa. duka mutanen dake zaune a hall ɗin zaka kalla lallai yakai ya kawo ya kuma taka wani matsayine tabbas, ko daga yanayin murjewan jikkunansu da kuma uwa uba tsarin da hall yake da. Wani shahararren tallane na ADD companies Wanda manyan ƙusoshi suka haɗaka wajen gina shi, Tsaye tsammm shi kansa shugaba a companies ɗin ya miƙe ganin wasu har ransu ya soma ɓaci. Ehhhh lallai tabbas kuwa da haushi ace yau har kimanin kwanaki uku kullum a jere suna taruwa iwar haka amma haka suke bajewa ba tare da an gudanar da TRAILER na ADD companies ɗin ba. A dai-dai loƙacin ne kuma wata farar mota samfurin ƙirar Toyota Highlander ta yi parking a harabar hall ɗin. Cikin yanayi na sauri² wata farar matashiya amma ba can ba ta fito daga cikin motar tana sanye cikin wani baƙar pleate skirt sai farar oxford shirt wadda ta ɗora maroon suit a kai,wuyanta saƙale da tie se silver band ɗin dake kanta, gashin kanta wanda ya ji gyara an ɗaureshi cikin pony rail ya zubo har gadon bayanta. ƙafafunta sanye cikin baƙaƙen sneakers. A kuma daidai loƙacinne hall ɗin ya ɗauka wani kalan ihu na tarin masoyanta, har wasu na tsalle wanda suke daga waje basa da ikon shiga ainihin inda za'a gudanar da Trailer ɗin.Hotuna wasu suka fara ɗaukanta wasu na aikin video wasu na ɗaga takardu masu ɗauke da sunanta me haɗi da tallar ADD companies.ɗaya daga cikin security female ɗin dake zagaye da wurin ne tayi saurin isa ga DIAMOND MEESHERH tana saƙala mata Symbol na tallar da zata gudanar. Cike da mutsuwa take tafiya Fuskarta rufe da mask, ta rufe fuskar ne kuma saboda bata son takurawar jama'a, duk da kasancewarta mutum me nuna so da ƙauna ga masoyanta, Fuskanta da kai tsaye ba'a gani ta zare mask ɗin dake kan fuskan nata ganin ta faranta wa masoyanta Rai. Wani twisting na ihun murna mutanen suka sake saki suna jin ƙaunarta na sake ratsasu. A natse cikin wannan ɗan banzar izza da mulkin da duk wani ahali daya kasance ɗaya daga cikin ahali na *JEDAANS POWER MENTION* to kuwa kowa yasan *_Respect and peace_* ake ƙiran duk wanda ya fito daga wannan Ahalin. Tafiya taci gaba dayi harta dangana da kan stage na hall ɗin. Tun kamin ta kai ga shigar manyan mara masu gwara kan nera yaran ajebor suka ɗauka wani kalan ihu suma harda ma waɗan da suka ɗan manyan ta bi ma'ana dattijai masu rukunin ADD companies kenan. Microphone ɗin da wannan macen security ta farko ta sake maƙale mata ne ya sanya sakin kyakkyawan murmushi tan nan me kyau. Nan aka soma gudanar da duk abinda ya tara sun bayan ta nemi afwan su akan cewa wani uzirine me girma ya ɗan riƙe ta. Seda ta ɗan rumtse idanunta sakamakon tunowa da musabbabin hanata fitan kai tsaye. Bayan masu camera's sun gama haskata kana suka buƙaci data ɗan gudanar musu da show haka koda ba me yawa bane. Cike da wannan fara'an da son farantama masoyanta Kamar yadda suma suke faranta nata ranta ta soma gudanar musu da wani zazzafan show ɗin daya sake haukata ƙaton hall ɗin. tana tsaka da gudanar da show ɗin ne kuma Moh Saif Ameen turaki ya bayyana shima cikin hall ɗin nan sukaci gaba da gudanar da show ɗin a tare. Sosae yanayin ya musu daɗi Kamar yadda suma fam nasu suke jin daɗin show ɗin na yau, dan burin ransu ne ya cika A yau gasu ga manyan masoyansu,Suna gudanar musu da show a tare wato *DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS* da kuma *MOH SAIF AMEERN JEDAANS* Cike da jin daɗi da kuma farin cikin kasancewar su a tare Masoya suka shiga ihun murna. Tsitttt kuma hall ɗin yay sakamon tsaya wa da sukay suna kallon masoyan nasu. Ihun murna masoyansu sukaci gaba dayi haka har taron ya tashi, Moh Saif ne ya zagayo ta inda Diamond Meesherh ke tsaye bayanta zagaye da security. Hannunta ya kama bayan mutane sun gama murnar yin pisc dasu kai tsaye har inda tay parking car nata ya kaita seda ya tabbatar da shiganta kana shima ya koma yana jan tashi motar ya rufa mata baya. Sun zo daidai shan kwanar Mobil filling station na round about wani shegen goslow yay blocking na hanyan. Ɗan tsuki kaɗan tayi tana jin gundura da zaman motarn baki ɗaya hakan ne kuma ya sanya Meesherh Jedaans fita don ganin ko me yay blocking hanyan har haka. Duk da kasancewar face nata rufe yake cikin mask amma hakan be hana wasu ƴan mata biyu da suke cikin napep kasa gane taba. Wacce face nata ke waje tana leƙen woje ta window'n napep ɗin ta furta "Laaa A'isha kalla can ki ga kamar Diamond Meesherh Fa?” ta faɗi cike da ɗaukin ganin babbar jaruma kuma sananniya a duniya. Da sauri wacce aka ƙira da A'ishan itama ta dawo da kanta setin inda ake nuna matan, "Wllh kuwa Rumaisa itane da da gaske!" Ta faɗi tana ɗan zaro idonta woje alamun mamaki. Cike da zumuɗi wacce aka ƙira da Rumaisa ta sake furta. "Kinga tashi don Allah muje muy photo" Ɗan numfasawa A'ishah tayi tana sauƙe numfashi tare da duban Rumaisa tana me furta. "Ki na ganin zata yarda kuwa Rumaisa? Karfa ki manta cewa Diamond Meesherh ⭐ Cikakken sunanta *Meesherh Sameer Jadeens* wannan shine full name nata bayan haka kuma role models da duniya jeji da ita gaba da baya. A yanzu haka ita kanta Meesherh Jadeens na ɗaya daga cikin world billionaires da duniya ke ji dasu ta gama zama cikakkiyarn attajira a loƙacin data mallaki manyan company's dake tashe a ƙasashe daban daban. Bare azo ga ahalinta kai tsaye kuma. Kana ƴa ce ga Sameer Jedaans Kuma sanin kankine kamar cewar Meesherh Sameer itace zuciyar duka alhalin Jedaans baki ɗaya! taya kike tunanin ma zata tankamu bare ma harta kula mu?.Sannan kuma kin manta cewan duka wasu campanies da zaki kalla na *MEESHERH LUXURY PRODUCT* Ina nufin M.L.P fa nata ne ko kin manta kamfanine da suka lashe maƙudan dukiya wajen ƙirƙiran campanies ɗin kawai. Wanda bako wanne kamfani yasamu irin wannan shaharar ba bayan latex cars da campanies nata suke ƙera ma duniya. Kana tana da hannun jari da wannan shegen campanies ɗin nan da ake sarrafa laptops, iPhones da suke ƙerama duniya da duk wasu nau'o'in na'urori kolo daban daban. Wato babban Ɗa ga JEDAANS kuma me Jedaans ɗin baki ɗaya wato *SHEIKH JURAIJ THABIT JADEENS*" A'isha ta ƙarishe maganan tana fesar da numfashi me ɗan zafi daga bakinta. "Wllh naji mutane kam na yabonta sosae A'isha wllh kamar ba ruwanta" Sake fuskantar Rumaisa A'ishah tayi kafin ta furta."To shikenan mu gwada sa'ar mu! Allah yasa mu dace" ta furta suna ɗaukan eskis wa me napep ɗin. Tana dab da shiga motan nata da ɗaya daga cikin securities ya buɗe mata Cike da ɗoki da zumuɗi Rumaisa ta isa gareta.tana me furta "Amm.... Am don Allah Sis kozan.... Securities ɗin da suka dakatar da itane suka sanya Jikin Rumaisa yin sanyi sosae tana jin tamkar ta muzanta kanta, kana tayi kutse wa matsayin da tasan ita bata isa takai koda kwatar wurin bane. "Ku..ku yi haƙuri amma dama photo ne kawai zamu ɗauka dama" Ɗaya daga cikin securities ne ya sake doka musu tsawa cikin buɗaɗɗiyar muryarsa yana furta. "ku ɓace min a wurin nan, ko kunga Hajiya tayi kolo da ƴaƴan talak.... Shiru yay sakamon tsawar da shima Meesherh Jedaans ta kotsa masa. A tare securities ɗin duka suka juya suna kallonta. Mask da kuma Baƙin shade ɗin idonta ta zare tana watsawama securities ɗin kallon me yasa kunnenku har abada baya ji?. Kana ta juyo da dubanta zuwa ga ƴan matan biyu fuskanta ɗauke da wannan murmushin nata wanda yake ƙaramar fuskanta kyau. Ta sakar musu tana amsan woyan dake riƙe a hannun A'isha ƙurar OPPO tana furta. "Ayya I'm a so sorry sister's Password fa?" Ta faɗi cikin muryanta me shegen daɗi. Jikinsu har rawa yake suka bata password na woyar ta buɗe tana nemo camera na woyar. kana ta matso tana shiga tsaƙiyansu ta dafa duka shoulder's na ƴan matan tana ɗaukan su photo. Kuma duk ta ɗauka ne suna kallonta irin na mamakin nan lol. Wayar ta sauƙe bayan ta gama musu pisc ɗin kana ta koma motarta bayan ta mayda mask ɗinta fuska, Har driver na shirin tada car ɗin tayi saurin dakatar dashi magana tasa ya mata da ƴan matan ID card nata me ɗauke da phone nata da kuma full address ta basu kana ta amshi phone na ɗaya daga cikinsu tana faɗin idan ta sama free time haka zata neme su. Mamaki, Al'ajabi sune suka bi suka sake daskarar dasu Rumaisa a wurin, wuri kuwa tuni ya cika sedai ita kamm har tayi saurin ba driver umarnin suje kawai don hayaniyan mutanen harsun fara hawan mata ka. Kai tsaye katafaren dogon ginin da kai tsaye zamu iya ƙura da da aljannar duniya suka nufa, Mention ne babba domin kuwa *_Respect and peace_* Gidane babba wanda a yanzu haka yana daga cikin best and top mansions dasuke most expensive and attractive a cikin faɗin Nagerian kai harma da duniyan baki ɗaya.Faɗin irin tsarinsa da haduwarsa ma ɓata time ne abinda kawai zance na sani shine cewan gidane haɗaɗɗe tsararre kuma ƙerarren dayake gari guda a girma. Sam bata leƙa ko inda Mah take ba kasancewar a gajiye ta dawo, kai tsaye samanta ta wuce kasancewan dama bata tarar da kowa ba a parlour'n. Bata fito Sai bayan anyi sallar Isha'i kana ta saƙko daga saman stairs nata.A loƙacin dakkanin jama'ar gidan suna kammale ne a babban parlour'n gidan domin yin dinner. Kai tsaye inda Abbie'nta ke zaune ta nufa fuskanta a ɗaure taki sakinta don ma gudun kada wani daga cikin mutanen parlour'n ya kawo mata wargi.B Tana sanye ne wannan karon cikin wani Turkey gown Wacce ta fidda shape ɗinta kai tsaye sosai, inda ta yi rolling gyalen a kanta.Ba laifi kuma tayi kyau sosai cikin shigar illa kawai shape ɗin ta daya fita sosai ne kawai matsalan shigan nata. Iyaka iyayensu mata ne a wurin kai tsaye jikin Mah ta faɗa tana maƙaleta "Mah yau duk a gajiye na dawo amma ko nemana bakiy ba" ta faɗi tana tura bakinta gaba. Bakin data tura matan Mah ta ɗan mirza ba da yawaba "Ni kuma duk yau na wuni aikine gyaran room na babyn daddy" Sautin tsuƙin da aka jane ya sanya su su duka kalla duk da kuwa sun riga da sun san ko wace ɗin tay kai tsaye. Basu wani tanka ba haka har metres ɗin dake aikin ta na saving kowa dinner tazo ta jerema kowa abinda yake so. pancake breakfast ɗin da ta fi so with honey aka jere a gabanta, kasancewar harta da metres na gidan sun san Diamond Meesherh bata cika son abu me nauyi ba. Ta gefen idon taga sadda ya shigo parlour'n,Nan parlour'n ya sake ɗaukan shiru kowa na rige rigen gaida babban yayan nasu wato *SHEIKH JURAIJ THABIT TURAKI* Kanta ta ɗauke ko kaɗan bata nuna wata alamar ta kula da shi ba har kuwa loƙacin daya kai zaune daidai kujerarn dake pacing nata. Cikin sauri Annie ta miƙe fuskanta babu alamun Rahman ko kaɗan. "JURAIJ tashi dawo nan!" Wani irin Shiru daƙin ya ɗauka na wani ɗan loƙaci kafin ka fara jin sauƙe numfashin wasu mara sauti sosai Domin kuwa kowa ya riga da yasan halin Annie akan rashin son zamar lafiyanta, da kuma kalan tsanan da tama Meesherh ɗin. Me ran ƙarfe Jedaans Turaki na shanu dake dap da shigowa parlour'n ne ya ƙarasa shigowa cikin ɗan hanzarin Sameer Jadeens ya ja may Sofa yana kaiwa zaune. Wani ɓoyayyen numfashi Sheikh juraij ɗin ya sauƙe mara sauti numfashin sa na cunkushewa da bugun zuciyarsa, ba tare da yace komi ba ya miƙe da niyar komawa inda mahaifiyarsan ta bashi umarni Jedaans Turaki na shanu ya ɗauke fuskansa daga kallon bugun zuciyar nashi Sheikh. "Koma zaune a idda kake" Haka kowa yaji sauƙan muryan tsohon, Mah ce ta miƙe da niyar barin wurin domin ita zuciyanta bame iya jure ana wulaƙanta nata bane ta ƙyale. Shirun kuma da tay tsumawa kawai namomin jikinta keyi ta kuma yunƙuro ne da niyar medama Annie da zazzafan martanin da ke kusan halaƙa nata zuciyan Muryan tsoho Jedaans ya katse mata tunani. "Kin yi lonch da zaki tashi ne Zulfa'u?" Haka ta sake tsinkayar Muryan tsohon a karo na biyu. Chakkk ta tsaya ba tare data juyo ba ta furta. "Ina da buƙatar na kaɗaice kainane kawai Baaba!" "Da akay mike mene?" Kai tsaye ya wulla mata tambayrn shima. Shiru tay taƙi bashi amsa zuciyanta na sake turara da wutar tsanar duk wani JINI daya danganci Annie. wata kyakkyawar ijiyar zuciya me nauyi tsohon ya kawo yana jin abu ɗaya shine zeyi maganin duk wannan matsalan {*AURE*} zuciyarsa ya furta mashi idan yace zuciyarsa seda yau tsalle to kuwa tabbas beyi ƙarya ba. Wani bahagon murmushi kuma ya saki daidai da Shigowan zaratan magidan tan gidan guda biyar. THABIT JADEENS, AMEERN JEDAANS,SAMEER JEDAANS,JAMAAL JEDAANS,EL-MUAZ JEDAANS. A natse suka ƙara shugowan kowa na nemar inda ya dace ya zauna, Baaba suka fara gaidawa kafin daga baya nan ɗaya bayan ɗayan yaran gidan suka fara gaida iyayen nasu cike da girma mawa. Wancan maganar tuni ya fice suna me fuskantan yin dinner nasu kawai. Sedai a wasu zukatan lamarin kuwa be shuɗe ba yana nan daram matankwacin yadda ake ɗora kwarya a gurbinta. Sheikh juraij Jedaans da yafisu ƙarfin halin danne abu a zuciyarsa ne ya fara miƙewa zuwa balcony na side ɗinsa. Idonsa toshe da bakin gilashi ajiyan zuciya ya saki abinda ya danne ƙirjinsa da daɗewa yaji ya yana ɗan lafa masa yana jin ɗan sassaucin ba kamar ɗazun ba. Shiru yay yana tsaye daga jikin doguwar Sofa irinta hutawar nan, lumsassun fararen idanuwansa ya buɗe yana fesar da wani abu me kama da ɓacin rai. Mohan Sameer Jedaans da tun ɗazun yake tsaye a bayansa ne yay gyaran murya domin lura da yay kamar juraij ɗin ma be san da tsaiwarsa wurin ba. Wata coffee cough ya janyo ya ajiye seti da inda Juraij ɗin ke tsaye yana ɗora ƙafansa kan ɗaya yana tallafar kuncinsa da left hand nashi. A hankali cikin tsanani na nisan kiwon dayay a duniyar tunani ya buɗe fararen idanuwansa da haskensu ya ɗan ragu na ɓacin ran daya ɗan wanzu ya sauƙe akan Mohan ɗin wanda babu kamannin kowa akan fuskansa kai tsaye sena Diamond Meesherh Sameer Jadeens. "Yaayaa sheikh beci ace har zuwan yanzun kana barin damuwowi irin haka suna brain out naka har haka ba" Mohan Sameer Jedaans ya furta yana jin shima ƙunci da damuwar gakan na sake mamaye zuciyarsa. Bayansa ya juya may don a yanzun baison yin magana da kowa hakan da yay ne ya sanya Mohan fahimtar mi hakan yake nufi. Wani abu me raɗaɗi Mohan ɗin ya haɗiye kafin ya buɗe bakinsa ya furta. "Idan Yaayaa Sheikh ya dawo daidai ko zuwa safiya ne inason magana da shine kai tsaye. Hannunsa yaɗan wara may alamun yaje yana jin sadda Mohan ɗin yay may nisa da barin balcony ɗin ya buɗe fararen idanuwan san yana me bin bayansa da kallo. ★ *Meesherh* Bayan bajewan kowa a dining room ɗin ne suka tattauna irin maganganunsu da ya shafi iyaka su tsakaninta da tsohon daga haka tamay sallama tana wucewanta zuwa nasu ainihin Passes ɗin. Tana dap da shiga Annie kuma na kawo kai zata fito daga sassan da tayi niyar janye wa amma da taga matar ne se kawai ta sa kai tana tafiyar ta. Daga inda yake tsayen yake kallar komai hakan yasa shi ɗauke idonsa akansu yana jin wani abu me kama da gazawa ko kasawa na son wanzuwa a ransa. Ganin yana wa'azi domin al'umma dama duniya su zauna ƙalau da juna se gashi a familynsa sam hakan yana ƙoƙarin ruguzuwa. Zuciyarsa yaji tana sake cunkushewa da wasu tarin abubuwa maban banta. Wasu shuɗaɗɗun al'amurra da suka jima da shuɗewa na ƙoƙarin zeroying mind nashi. Zaune takai gefen bed nata tana duba tarin reports na acct histories na duka companies nata tana ganin yanda komai ke sake haɓaka kansa, Wasu rubutu masu ɗan tsayi tay kafin ta miƙe akan laptop ɗin tana faɗawa toilet. Da alwula ta fito duk da kasancewar tasan ba sallah zatay ba amma kuma hakan ya riga ya gama zama ɗabi'anta tun tana ƙanƙanuwanta, tun tana ƴar renonsa shi da kansa ya ɗora ta akan duka tsarikansa. Kafin wani rubutaccen Al'amari me kama da walƙiya yazo ya gitta wannan shaƙuwar. Ko bayan faruwan komai taso ta yafitar duka al'adunsa sedai wasu kammm samm basu yakitun ba. Saurin kawar da wancan tunanin tay tana tofe ko ina nata da addaan bacci. A hankali Moh Ameern ya rufe ƙofar ya mayar sam babu ƙarar takun sa ko kaɗan akan floor ɗin, shi yasa kuma bata lura ya ƙaraso har gaban gadon ba kasancewar ta riga da ta kashe bals, bata rufe bedroom nata sauda dama amma kuma saran shigo mata room Kai tsaye da Moh Ameern ɗin ya kowa ne ya tilasta fara rufe room nata. Ko a yau ɗin ba mantawa tay bata rufen ba bayan fitar wata mets data biyota da cup me ɗauke da tea party bata na al'ada wanda shi kansa hakan taso yakitarwa sedai shima hakan yaƙi yakituwan. Zamansa ya bakin bed ɗin harma yana ƙoƙarin yaya blanket data rufa dashi shine ya farkar da ita daga gajeren bacci daya soma ɗaukanta kasancewanta mutum bame wuyar bacci ba haka kuma bame wuyar tashi ba. Zaune tay saurin tashi tana kunna bedside lam ɗin dake gefen gadonta. Ta cikin ɗan hasken daya haska room ɗin ba da yawa ba ta nuna may hanyar fita a room ɗin tana me furta "Out Moh!!!" Cikin mugun ɓacin rai. Hannunta yake ƙoƙarin ganin ya lalabo "kinga rilax beb wani aikine yanzu aka turomin ta email address shine nake son nuna miki ba komi ba!" Ya furta yana sake matsota, "Amma get out nace ma ko?, Ko WhatsApp ba amfaninsa hakan ba da seka ratso har room nawa? Kodan kawai kaga ina baka fuska shine a kullum kake sake bayyanar min da munanan halayenka na ɓoye?" Ta furta da ƙarajin da badan ace ƙofa ce mara fidda sauri da kuwa tsaff kowa da kowa dake a side ɗin na iya jiwota. A sanyaye ya miƙe yana kama hanyar barin ɗakin. Ak'adansa ne kullum se yayi zagaye don tabbatar da komi na dede ko wanne matashi kuma na a makwancinsa. Yazo seti da window'n room nata yaji kamar ihun faɗarta, Hakan ya sanya shi zagayowa domin ganin komi ke faruwa duk kuwa da yadda zuciyansa ke gargaɗansa akan aikata hakan. Gilmawar inuwar kawai ya gani amma kasancewar mutum mai kaifin brain da kuma karantar halayyar ɗan adam kai tsaye ya gane ko wanne ya gilma ɗin. Dummmm haka yaji kansa ya bada sautin yanajin zuciyan sa kamar ana sauƙeta a ƙasa, sassan jikin sa kuma tamkar ana kwara musu ruwan suna suna tashi a aikinsu. Da ba ya baya ya shiga komawa cikin kamalallar takunsa har dogon wandon farar shaddar jikinsa na neman shatalarsa. Da bibbiyu bibbiyu idonsa suke gani haka harya kaishi ga dangana da sashinsa, jagwab ya kai zaune amma kuma cikin nutsuwansa da kuma cikakkar kamalarsa yay hakan. "Kamar Yadda Allah yake juya dare zuwa Rana. Ya Ubangiji na roƙe ka ka juyar da damuwarmu zuwa farin Cikinmu🙏 domin na san cewa ƙaddarorin yanzu ne suka fara! Yanzu ne LABARINMU zai soma......" *By Ammeylaylerh* 08104493215 _Tofa Fan's shi kuma wannan nashi salon kenan, da wannan muka fara_ _Jedaans Mention yau kuma ta kansu Labarin ze soma_ _to my fam nawa idan kunason ayi tafiyan daku seku biyo NI AMMEY LAYLERH domin jin yadda wannan zazzafar tafiyar zata kaya_ _Karfa ku manta sunan wannan littafin TA DABAN, to wai ma wace ta daban ɗin kowa dai a karan kansa yasan cewar ai shi na daban ne, to kuma ga wata AMMEY'NKU LAYLERH tace wai ita ɗin SPECIAL ce ta daban...._ _to ya kuke kallon wasan ze kaya? Ya kuma kukaji salon rubutun wannan karon? _ _Ni ban ze ce ma kowa komi ba kawai dai nasan zance mu haɗu a kashi na gaba domin jin yadda zata kaya_ https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH ༺༻ *♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆* ༺༻ _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ_ *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ 𝙉𝙖 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 ᴺᵃˢᵉᵉʳ ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _AMMEY LAYLERH_ BOOK ONE…………񆬍✍ Page 3&4 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ _015/01/2025_ Paid Book *Maman Ihsan tawa duka wannan page ɗin na sadaukar miki dashi kiyi yadda kike so dashi idan ma kinso ki hana kowa ciki kuwa har dani AMMEY LAYLERH* *MIKIYA* *KAREN BANA* *JALAAL AREEF* *ƘAUNA BIYU* *SANYI YA HAIFA WUTA* ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ # Ⲛᕪᐜ Ⲩᕪᵃʳ'ˢ # 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ # SoulmateVibes # DeeplyInLove # TogetherForever # UnbreakableBond # Endless Love # SilentLoveAffair # HiddenHeart # ForeverAndAlways # Ɩ૦𝚅𝞔 Ʀ૦Ꮇ𝔸𝑵ᑕ𝞔 𝗕𝔸𝗕Ⲩ # ɑ.𝚔.ɑ 𝔸ɱɱҽ𝑦 ʟɑ𝑦ʟҽ𝔯һ 👇 https://t.me/+ISpf1lql0GwyNmJk Duk me neman AMMEYLAYLERH ganan link nawa na Telegram Wanda kai tsaye idan kabi link ɗin ze dinga kaika ga post namu kai tsaye. 👇 https://www.facebook.com/share/1A1gMDViUG/ Sannan kuma ganan na facebook don samun post nawa kai tsaye shima. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ .... Tun da ta mai da doorhandle ɗin ta koma ta jingina da jikin ƙofan abubuwa da yawo na son dawo mata. tun da ga loƙacin da tafiyar su tasha banban da juna wacce wata shuɗaɗɗiyar Ƙaddara tazo ta ratsa tsakani. Haka kuma idan taso wannan ita dai ƙaddarar itane zata zo ta sake haɗe giɓin data riga da raba shekaru da ɗan dama.A zahirance duk inda Kalmar KADDARA take to kuwa kowa yasan kalma ce dake motsa zuciyar ko wanne bawa domin kuwa tabbas wannan kalmar ta KADDARA kalmace me girma da faɗi wacce ta ƙunshi abubuwa masu yawan gaske. domin kuwa Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwa juna.haka kuma kowacce rayuwa tafe take da nata salon ƙaddarar. Idan har bawa zeyi haƙuri wajen jure wannan tarin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin kowanne rai mai numfashi game da duk abinda ALLAH ya riga da ya ƙaddara a cikin rayuwarshi,To kuwa duk ALLAH Ya zaɓa maka shi ne mafi alkhayri agareka. ♡ Wani kalan Runtse rinannun idonta tayi sakamon kanta da taji ya wani kalan mugun sara mata da tsanin ciwo. Zaune takai bakin bed haryanzun hannuwanta riƙe da saman kanta dake jujjaya mata. Alamun zurfi datai a tunani nason haifar mata da wani damuwan. Wani kalan zazzafan numfashi ta fesar tana hana kanta bama damar tunanin. Domin kuwa ita ɗin mutumce me tsananin taurin kai da kuma ƙarfin zuciya. Ba kowanne abu take bama yay crossed mind nata ba, Wanda kai tsaye duk ta koya hakan ne daga garesa kasancewarta renonshi ce ita ɗin. Ƙin bama ko wacce ƙofa dama tayi na zurfi a tunanin dake son bijiro mata. Knocking doorhandle ɗin da akai ne ya katse mata tunani, zuwa loƙacin jikinta har rawa yake a mugun wahalce ta nufi doorhandle ɗin tana buɗe. Mah ce Mah ɗin ta ce dama ta sani tasan itace don kuwa bata iya kwanciya duk daren duniya se tazo taga Meesherh ɗin. Saurin rungumata Mah ɗin tay "Subhanallahi Meeshel ɗin Papiey'nta What wrong? Me ke damun ki?" Duk kuma seta bi ta ruɗe kasancewanta auta kuma ƴa mafi soyuwa a zukatan iyayen nata. Ganin duk yacce Mah ɗin tabi ta ruɗe ne ya sanya Meesherh ɗan janye jikinta ana Mah ɗin tare da ƙaƙaro murmushin dole tana furta. "Headache ne kawai fa Maayh, Don't worry karki woni damu" ta furta wai duk a sonta na kwantarma Mah ɗin nata hankali. "A ahhh ban Isa ba wllh Meesherh dole ko dactor Asia tazo ta duba min ke" tay maganan ne kuma tana laluben number na dact ɗin, Maganan second sukai ta datse ƙiran. Kai tsaye kuma ta maida akalan ƙiran kan Billionaire Sameer Jadeens. Se dai jin ring na woyar dap da ƙofarn shigowane ya sanyata katse ƙiran, Cikin yanayi na nutsuwa da hutu da wayewa suka gama ratsawa ya sanyo kansa bedroom ɗin. Yana sanye cikin kamilallar shiga ta blue in jallabiya ta maza se hular nan irin ta kafiye nacin nan. Zama yay a gefe da daman Meesherh ɗin suka sanyata a tsaƙiyansu. "Ꮇҽ𝚔ҽ ᙏα𝓶αɳα ђ𝔞қ𝔞?" Kai tsaye prof 𝙎𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 Jedaans ya tambayi Meesherh daidai yana kai hannunsa saman goshinta. Maganan dayay shirin yine ya tsaya may a maƙoshinsa sakamakon knocking door ɗin da akai. Umarnin shigowa kai tsaye suka bada don sun san Dr Asia jamaal ce ta ƙara so. A natsenta ta shigo har cikin bedroom ɗin, gaidasu tay cike da mutumci da girmamawa take kuma ta shiga duddubata Injection ta mata tare da ajje mata magunguna ganin ba normal damuwa bane ya sanya Dr ɗin duban su Mah tare da furta. "Don't think about it totally don't worry, the only stress paining her Ina ganin da zarar ta ɗan sama natsuwa shikenan zata warware Insha Allahu" daga haka Dr ɗin ta musu sallama ta tafi bayan sun mata godiya.Ring ɗin da woyarta a ɗauka ne ya sanya ta duba me ƙiran. Yayartace Ummetah mebin Mohan Sameer Jedaans se ita kuma data kasance autarsu, "Meesherh kince zaki ƙirani baki ƙirani ba tun ɗazun right?" Cikin muryan da yay low Sosai ta furta. "I'm sick fa Aunt" "Subhanallahi Meeshel baki da lafiya amma baki sanar min ba?" "No karki woni damu headache ne kawai da wata ƴar damuwa ya haifar min hakan" daga ta can ɓangaren Aunty'n nata ta furta. "Bara na barki kiyi bacci se zuwa tomorrow morning Insha Allah" daga haka suka yanke woyan tana me sake komawa jikin Mah ta kwanta abinta.Duka da kallo suke binta a loƙacin da suka gama tabbatar ma cewan tayi baccin. "Allah ya inganta min rayuwar ki Meeshel!, Allah ya dafa muku gaba ɗaya daga ke har ƴan uwanki ya kuma raba min ku daga sharrin masharranta cikin gida dana woje" tayi maganar tare da jaho hannun Meeshel ɗin ta haɗe da ƙirjinta ta rungume,prof kuwa sai wani kalan murmushi kawai yake saki. Shima jikin Mah ɗin yaɗan motsa kaɗan yana kwantar da kansa setin shoulder nata. Yana rungumeta Ya jima sosai rungume da Mah ɗin,Nan ya shiga musu addu'a shima Mah ɗin na amsawa da ameen. Seda suka gama tabbatar ma da kansu cewan baccin yay mata nisa sosai kana suka ja mata duvet suna rufeta kana suka fita bayan Prof Sameer ya sake mata adda'an bacci. ★ The great Billionaire juraij Jedaans ne zaune kan wata ƙerarriyar cough yana snye ne cikin wata rantsatstsiyar lallausan farin yadi wanda yake lafe a farar shiny skin nashi wanda kai tsaye ke bayyanar da asalin hutu da luxurious life ɗin dayake cikinsa. Fuskansa sakaye cikin wani yankakken farin gilashi, System ce a gabansa ya zuba mata fararen idanuwansa wanda a zahirin gaskiya bawai kallon nata yake ba ya tafi ne duniya irin ta tunani. Wani zazzafan numfashi mara sauti ya fesar jin yanda zuciyarsa ta sake karta masa a karo na ba adadi.Yasan kaff duniya haka kuma kaff rayuwar Sheikh juraij Jedaans babu abinda yake haɗawa da bautama ubangijinsa haka kuma shi kaɗai ne abinda keda tsananin mahimmanci da girgiza dakkakiyar zuciyarsa. Me bi ma hakan baya kuma ita ce Zuciyarsa! Bugun numfashin sa *MEESHERH SAMEER JEDAANS* domin ita ɗin ta kasance tamkar renonsa ce. Duk da cewar Ƙaddara ta riga da ta buɗe tafin hannun kowannensu ta masa zanen rubutacciyar ƙaddararsa, wanda har hakan kai tsaye yay sanadiyar ban bancin ra'ayin su koma yace rabuwar su. Hakan ba shike nuna cewar ze barta har abada ba, kana hakan ba shike bayyana cewar ze barta taci gaba dayin duk kalan abinda taga dama, sosai yaji ransa ya sosu da ganin fitar Moh Saif Ameen a ɗakin nata wanda Allah ne kaɗai yasan yadda ya kwana da wani kalan masifan ɓacin ran hakan a daren jiya. Wani gauron numfashi ya kawo yana sake zubama laptop nashi farare ƙal ɗin idanuwansa. Pisc na Meesherh yake kalla a cikin laptop ɗin idanuwansa har kalan bala'i bala'in yaji suke mai na ɓacin ran ganinta cikin wasu shegun riga da wando outpit. Wanda kai tsaye yake tabbatar da cewan a shooting film ne tayi koda ma a cikin Film ɗin ko waƙa. Ya rasa me Meesherh take nema a duniyar ta rasa dahar ta jefa kanta cikin shirin fina finan Hausa. Idan suna take da buƙatar yi ya tabbata Kaff Duniya babu inda sunan *JEDAANS POWER MENTION 💪 PEACE and RESPECT* be gama zagaya da kareɗe wa ba a duniya. Haka kuma Idan kuɗi take da buƙatar ya tabbata ita kanta tana da dukiyar da bata san iyakarta. To amma me take da buƙata a wasan Hausa? A har kullum kwanan duniyar shine tambayar daya rasa amarya har zuwa yanzun kuwa da yake a zaune gaban System nashi. Idan kuma yay duba da yadda Ubangiji yake juya lamuransa daga kyawawa zuwa munana se ya sake jinjina lamarin ubangijin da babu kamarsa a duniya dan kuwa shine kaɗai wanda ya isa yayi abinda babu wanda ya isa juya hakan. dan yana da tabbacin idan wani na juya ƙaddarar wani da tuni ya jima da juya ƙaddarar Meesherh, A kaf cikin duniyar nan ya tabbata babu abinda ya rasa a rayuwa hakama babu abinda bazai iya zubar wa domin ganin ya dawo da Meesherh kan hanya se dai wannan maganar ta *TUN RAN GINI* da tsarin ƙaddararta ya daɗe da rubuta komai da ze wakana da rayuwar ko wanne bawa nashi. Amma duk da haka bazai gajiya ba wajen kaima Allah kukansa kan ya dawo mai da Meeshel ɗin sa hanyar daidai. Janye fararen idanuwansa da sukai ja yayi a kan laptop ɗin a sanyaye kuma ya maida ya rufe yana sauƙe numfashi me zafin gaske. Knocking ɗin da aka danna ne ya sanya shi dawowa duka cikakken tunaninsa. "Yes Come In" cikin wannan kamilallar muryan ya bada izinin shigowa. Mohan Sameer Jedaans ne ya shigo hannunsa riƙe da wani kyakkyawan farin yaro mai tsananin kamanni da ubansa,shi kuma uban me irin kamanni ɗaya Meesherh Sameer Jadeens. A natse ya iso har inda yake Sheikh ɗin yake zaune,zama yay natse domin badan ban bancin kamanni ba da babu abinda zai hana ace uwa ɗaya uba ɗaya ne suka haife su ba. Yanayin sanyinsu iri ɗaya da yanayin shiru shiru ɗin su da kamala, wannan kamannin banbanci shi ne kaɗai ze nuna maka cewan ba uwa ɗayan ce ta haifesu ba, sedai duk da haka suna fisgen kamanni na alaƙar jini me ƙarfin da yake gudana a tsakan kaninsu. soft Fararen hannuwansa ya miƙama yaron daya kasance me sunan shi, domin Mohan Sameer Jedaans kai tsaye sunan Sheikh juraij ɗin ya sakama yaron. Wanda Sheikh kema wani kalan mahaukacin so na tashin hankali,Yes shi kansa yasan yana son yara sedai tayaya me zeyi auren bare har a haifar mishi yaran? A kullum kwanan duniya shine tambayar dake addaban zuciyarsa. So da Ƙaunarsa a gun mace ɗaya yake baida feelings akan ko wacce irin macece koda kuwa zatay yawo tsirarane a gabansa. Sedai a yanzu yasan wannan ɗin ya zama kamar tarihine don ko kyauta aka bashi baya jin ze ko iya kallonta a matsayin mace, macen ma kuma ta aurensa. tun iyayensa na damuwa da rashin aurensa har suka tattara lamuran suka miƙa buƙatunsu wurin me du ka me kowa me komai wato ALLAH. Ɗan gyaran muryan da Mohan yay a karo na biyu ne ya dawo dashi daidai ɗin sa. Magana ne sukai akan zaman meeting ɗin da yake da shi da ƙarfe 11:30 na yau. Daganan suka ɗan tattauna maganganu akan yadda al'amuran kasuwancin nasu yake tafiya. ★Araund 7:50 kowa na gidan ya gama kammala kansa a babban dining room na gidan inda room ɗin yake ɗauke da rassa daban daban na dining table. Meesherh itane ƙarshen fitowa kuma dama kusan kullum itane last, zama tafi fuskan nan ta kan daren jiya kan wayewar yau ta sake yin fiyau. Bata ɗaga kanta ta kalla kowa ba bare ma woni yay tunanin kawo mata wargi, kamar kuma yadda bata gaida kowa dake room ɗin ba. Annie ce ta dubeta cike da jin zafin da bata san kona miye ba ta furta. "To Ishashshiya tunda babu tarbiyyar girmama na gaba dakai se a tashi ayi saving namu dinner,Mutum kuma in yaji haushi ya ajje aikin shirmen da yake ya koma Islamiyya kodan sanin yadda ake girman na gaba dakai" Idan ƙasar dake wurin tayi motsi to kuwa tabbas Meesherh ɗin ta yi itama. Don haka wurin ya ɗauka wani kalan mugun shiru kowa na kissima abubuwa maban banta a cikin rayukansu. Papiey' ne kawai yay ƙarfin halin duban inda Meesher'n take bawai don beji zafin maganan da annien tay akan gudan jinin nasa ba. A ahhh sedai kara da kawaicin da ya saba ma yayyensa iyayen su juraij ɗin kenan. kasancewar shi autan su kuma mutum mafi haƙuri da jure ko wanne kalan ƙalubale daga Ahalin nasu. Ɗan zafawa yay tare da furta. "Mamana bata ji ana magana ba ne?" Prof Sameer Jadeens yay maganan yana duban inda Meesherh ke zaune. Cike da rashin haƙurin da mijinta Sameer Jadeens yaga ta kowa take dubansa, domin kuwa ita ɗin ba sakar ya bace da zata ji ana muzanta jinin ta kuma tai shiru, "Amma ai Papiey'n Meeshel kadai fi kowa sanin cewan Meesherh bata da lafiya? Ko duk ba gasu Nainerh nan ba, su Aysha su Nanameerah su Salma ba se ita kaɗai za'a kalla ace tayi saving namu dinner" Ya buɗe baki kenan da nufin mata magana Jedaans turaki ya katse shi ta hanyar masa nuni da eat kawai don wannan loƙacin dinner nasu ne. Kafin kowa ya miƙe Annie ta miƙe ranta na mata suyar ƙin tanka tan da Meesherh tayi. Hakan ya sanya cike da fusata ta furta, "A dai koma Islamiyya ko a samu rabon kusanta kai ga Allah" wani irin shiru mai saka duk wanda ya shiga mutuwar jiki gurin ya ɗauka, Don hatta metres sarvice ɗin dake ta aikin kai da koma a wajen tsit sukai.Kallo ɗaya Maminsu Moh Saif Ameen tama ma'aikatan wurin suka tare duka a take. Ajiyar zuciya me ɗan ɗumi Sheikh ya sauƙe a natse, se kuma ya miƙe tsammm a wurin se dayay taku ɗaya ana biyun a dakata. Cikin wannan natsatstsen low tong voice nashi ya furta. "Kiyi haƙuri Annie Amma kai tsaye daga yau na soke duk wata magana da zata fito daga bakin ki akan baby da Mah, Indai bame daɗi bace kai tsaye da yawun bakin Abbie nay magana" daga hakan ya sanya kansa yana barin room ɗin baki ɗaya, yanajin hankalinsa na dawowa jikinsa kodan umarnin abbiensa daya cika akan annie'nsa. ɗago idanuwanta rinannu tai da sukai laushi ta kalla Eng Thabit Jedaans wanda shima juyowa yayi ya kalleta da idanuwansa da suka nuna babu wasa ko wargi a cikinsa.wata bahaguwar ijiyar zuciya ta sauƙe ahankali tana matse hannuwanta duka biyu a wuri guda.Ga Wani kalan shegen sanyin da taji yana ratsa ilaihir gangar jikinta. Wani kyakykyawan murmushi tsohon ya saki wanda ya fito da ƙananun teeth nashi farare tasss kamar ba na tsoho ba. Kai tsaye zaratan magidan tan ƴaƴan nashi suka bishi da ido. Wani murmushin ya sakar musu na badai zaku fahimtar komai ba. Daga haka ya miƙe tsaye da ƴar sandarsa ta narkakken zinare me sheƙi yana barin parlour'n baki ɗaya ma. Daga haka suma kowa ya miƙe kasancewar sun san lalle kenan akwai abinda tsohon yake shirin aikata koma yana dap da aikatawar. *Sheikh juraij* Kai tsaye katafaren dogon ginin sa ya nufa ba hasalin wanda yake a ciki yanzun ba. A cikin can ƙasan zuciyarsa yake furta. "Hamdan,khathiran,ɗayyuban barrakhallahufihi!!!" Domin ma ya rasa abin magana akan Anniensa ya kuma rasa wanda kalan tunanin ya kamata yayi. Nosemask ɗin dake cikin aljihun farin dogon yaɗin jikinsa ya ɗauko yana sakayawa a face nashi. duk rabin face nashi a rufe da nose mask ɗin se glass ɗin daya sanya. Amma hakan ba shi ne zai hana ka gane cewan shi ɗin kyakkyawa ne ajin farko ba, Yana da murɗaɗen jiki haɗi da murjewan fata,yana da wani irin faffaɗan ƙirji tamkar irin India actor's ɗin nan.Damtsen hannun san nan tamkar sa fashe saboda training gym da yake yi a ko wacce safiyar duniya. duk girman wajen shiru babu motsin ko wanne rai me numfashi, dama haka yake sau da dama yakan zo sa'i zuwa sa'i don kaɗaita kansa daga kowa musamman idan yana hali na damuwa.zaune yakai kan wata fara tas ɗin sofa. jikin nan nasa se glowing na ƙyau da kyau kawai yake kai ka rantse da Allah bai taɓa taka koda ƙasa bane, Saboda tsananin laushinta da kuma yadda take ɗaukan ido na tsantsan kyau. Gashin nan a kwance luff luff tamkar wani renon larabawa ko turawa.Duk inda kaji an ce Sheikh juraij thabit Jedaans to ana nufin wannan Kyakkyawan farin matashin malamin ne mai jini a jika, sosai yake da hasken fata da kallo ɗaya mutane suke bashi sunan 𝑩𝒂𝒕𝒖𝒓𝒆 ko 𝘽𝙖𝙡𝙖𝙧𝙖𝙗𝙚. dogone cikakken namiji me cikqkkan wayewa na addinin Islama daya gama ratsa jinanen jikinsa, yana da faffaɗan ƙirji wanda yasa kai tsaye muscles nashi bayyanuwa sosai. Wannan kyakykyawar Innocent face ɗin nashi ɗauke take da dogon hancin da ya ƙara wa fuskarsa wani kalan kyau da zati, ɗan karamin bakinsa ɗauke yake da kyakkyawan Pink lips kalan masu shining ɗin nan tamkar wanda ake goga musu lipstick. Wanda hakan ba ƙaramin kyau ya ma ɗan ƙaramin bakinsa ba ta hanyar masa ƙawanya. A hankali ya ɗago da dara daran fararen idanuwansa masu kama da ana musu ɗuren madara masu shegen kyau kamar yasa musu ƙyalli, kwayar idanuwansa da ta kasance light irin me tsananin hasken nan mai ɗaukar ido, idan kayiwa idon na shi kallo a fusge sai kaga kamar ruwane suka tarun masa a cikin eyes ɗin nashi. Don kuwa sedai a fisgen don da matuƙar wuya kace ka taɓa iya haɗa ido dashi koda na tsawon 1 mints ne. Don wani irin kwrjinine dashi na Zati da kuma girman da musulinci ya bashi, kai tsaye idan da za'a faɗa maka yawan shekarun Sheikh juraij thabit Jedaans to lallai tabbas zaka Musa ne. Don wani kalan kyakykyawan ginannen jiki me kyau da tsada Ubangiji ya ba shi, kai bakace wannan first born ɗin bane na JEDAANS wanda yake matakin girma na shekaru ɗai ɗai har shekaru 47 year's. Kai tsaye kai a naka lissafin zaka iya bashi shekaru kamar irin 31/32 ɗin nan ne. Kai bakace ma ya haura 30 year's ba shugaban 𝙏𝙐𝙕𝙐𝙍𝘼𝙉 𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼 𝗞𝞔𝑵𝔸𝑵. A hankali ya fara motsa idanuwansa da suke a ɗan lumshe har dogayan eye Lashes ɗinsa na motsawa suma sosai ,wanda hakan ya sanya sosai girarsa take a cike itama motsawa da haɗewa sabida cikarta ya sanya motsa fuskan nashi dayay suka haɗe da juna, gefe da gefen fuskar sa duk gargasar gashi ne da yasha gyara irin me luff luwai ɗin nan kuma veey mood for anything, A natse ya ɗan kai hannunsa ya shafi kyakkyawar dark brown hair nashi fuskar nan ɗaure take tamau kamar bai san me dariya ba ma a duniya.Wani irin ƙamshinsa ne baki ɗaya ya gama gauraye ilahirin gurin hutawan. Wanda kai tsaye kowanne hanci dake shaƙan ƙamshin yake masa laƙabi da na musamman, don tsadansa da kuma ƙamshinsa ya banbanta da wasu ƙamshin sbd kai tsaye shi nashi ƙamshin cikin sanyi me nutsuwa yake shiga ya wuce zuciya mutum kai tsaye. Jin motsin shigowar Personal person ɗinsa wato Al-Ameen Hafeez gurin ne kuma ya sanya buɗe idon kai tsaye yana sauƙewa akansa. Waya ya shigo yana yi wanda kai tsaye akan zuwan su Lagos ne da zasu wanda wasu manyan malaman can ɗin suka turo masa gatin gayyatarsa ta cikin email address nashi dama saƙon kai tsaye. Tun kamin ya ƙara so inda yake ya kashe wayarsa ya ƙaraso har inda Sheikh ɗin ke zaune, Nuni ya masa daya zaune daga kujeran hutawan dake gefen sa, System nashi ya buɗe directly a gaban Sheikh ɗin nan ya shiga gabatar masa da yadda tsarin tafiyan nasu ze kaya da booking flights ɗin daya riga tun daren jiya ya musu. Sosai ya gamsu da jawaban Al'ameen ɗin kuma nan da 45 minutes jirgin nasu ma ze tashi kasancewan a yau ɗin suke zon zuwa Lagos ɗin kuma su dawo a yau ɗin. Daga nan Personal person ɗin nashi ya fice shi kuma ya miƙe yana shigewa zuwa ɗaya daga cikin ɗakunan palonsa ya zauna ahankali akan 2 seater ta turkish luxury sofas dake palon ya zauna, wanda ƙamshi da sanyin ac/n suka gama ratsawa.Wayarsa dake gefensa ajiye ya kai dogon hannunsa fari tas ya ɗauka yana cireta daga flight mode ɗin daya sata kai tsaye yana calling wata No. Maganan seconds sukai ya ma kashe woyan baki ɗaya a natsensa ya miƙe bedroom dake palon ya faɗa. Minti kaɗan ya fito cikin wata shigar ta daban, Ta can wata sihirtacciyar hanya yabi domin sauƙaƙama kansa tafiyan. Apartment na iyayensa ya yaje ya musu sallama don tsaff yake da shirinsa na tafiya Lagos ɗin. Adda'a Abbiensa ya may Annie'nsa kamm ko inda yake bata kalla ba, Se kuma yaji duk babu daɗin hakan har yaji tafiyan ma nason fita masa a rai gaba ɗaya, ganin yanayinsa take ya sanja ne ya sanya Abbie ƙarfafa masa gwiwa harda ma daɗin yar nasiharsa bayan anniey tabar palon. ♡ Kai tsaye inda manyan jibga jibgan motocin sa suke a Parker ya nufa,da guda ɗaya ya fita kasancewar airport ne kawai zasu kaishi. Sedai hakan be hana wasu daga cikin securities na gidan rufa masa baya ba. Suna zuwa befi da 3 mints ba girginsu yay landing zuwa garin Lagos. A Wani babban wuri wanda ake tanajarshi kawai domin yaɗa aikin ALLAH suka sauƙa. Fuskansa da tsananin haiba da kuma tsananin kwarjinin dake firgita magautanshi ya fara tafiya akan sawayensa. Yana Sanye cikin shigan nan ta al'farma shigar dake nuna nasabarsa ta kowacce sashi,Wanda madarar ilimin addinin daya gama kwankwaɗar romansa. A natsensa ya zaune a inda aka tanajar masa se gefinsa kuma Personal person ɗin sane tsaye cakk tamkar woni dogari. Cikin rahama da ni'imar da ubangiji (S.W.T) yau ma wannan bayan nashi ta iya sarrafa harshe da tausasan laffuza, ya soma da gabatar da adda'o'in zaman lafiya wa ƙasar mu Nigeria. Wani kalan Shiru mutanen dake cike da wurin suka ɗauka kamilallar muryan san nan na ratsa musu har jinin jikinsu. Bayan ya kammala tarin Adda'o'in sa A hankali kuma yasa hannunshi yana gyara zaman Microphone ɗin dake maƙale wacce ta zagayo harta bayan ƙeyarsa, wanda hakan ya zamewar kamar ƙarin ƙawata adon nashi ne. A hankali ya lumshe idanunshi kana yayi ƙasa da kanshi cikin yanayin nitsuwarsa ya buɗe pink lips nashi cikin zazzaƙan sautin muryarsa bayan ya gama kawo jawabansa akan *MUTUWAR ZUCIYA* yaci gaba da furta. "Idan kana karanta littattafan tarihi to tabbas za ka ga a kowane zamani bayin da ake bautatarwa sun rabuwa kashi biyu ne!. Akwai bayin da ake azabtar da su!, Kana akwai kuma bayin da suke jin daɗin kasancewarsu bayi a ƙarƙashin wasu, waɗanɗa zuciyarsu ta gama mutuwa murus,ba sa tunanin ƴancin kansu Alal misali...... Zamanin da aka kwashi baƙaƙen fata daga nahiyar Afirka zuwa Amurika da Turai da sunan bayi, ana bautar da su.Wanda Bayin sun kasu kashi biyune, Bayin Gona da kuma bayin gida. Bayin Gona su ne masu yin aikin noma da sauran ayyukan wahala,kai tsaye su ne waɗanda ake azabtarwa Su kuma bayin gida su ne waɗan da suke gidajen masu gidansu fararen fata, suna yi musu aikin bauta suna cin abincin da suka rage, da sanya tsofaffin tufafinsu. da kwana a gidajensu suma waɗan nan bayin gidan suna jin daɗin bautar sune har ta kai ga ba sa tunanin samun ƴancin kansu da kuma rayuwarsu. Su kuma bayin gona waɗan da suke cikin azaba sune wanda kullum suna tunani tare da ƙoƙarin samun ƴanci daga ƙangin bautar da suke cikin ta. Idan bayin gona suka nemi haɗin kan bayin gida domin gwagwarmayar neman ƴancin kai da kai sai waɗan nan bayin gidan su ƙalubalance su, Kana su ƙi ba su haɗin kai! sa'an nan kuma sai suje su gaya ma iyayen gidansu sirrin bayin gona na yin tawaye da neman ƴancinsu. Su kuma sai masu gidan su daƙile shirin bayin gona na neman ƴancin kai da kai bayan sun sake ninka musu bautar da suke musu akan ta baya........Su bayin gidan masu moruwa da fararen fata, suna rusa shirin yan'uwansu ne wajen neman ƴanci ba don wata hikima ko wata manufa ba, a'a, sai don kawai tsoron yankewar ragowar abinci da tsofaffin tufafin da suke samu daga masu gidajen nasu. Su a wajensu wannan ragowar abinci da tsimmokarar sun fi ƴancinsu muhimmanci. Irin waɗan nan bayin gidan su ne musabbabin rashin nasararsu wajen neman ƴanci a duk lokacin da mutanen da ake zalunta suka yunƙura. Akwai kalar mutanen da sun saba da rayuwar bauta,Waɗan da zuciyoyinsa suka riga da suka gama mutuwa ƙurmus murus, wanda suke jin kansu ba za su iya rayuwa ba a ƙarƙashin wani ba, yau da za a yi ruwan ƴanci da da lema za su riƙa yawo. Duk lokacin da waɗan da ake zalunta suka yunƙura, su waɗan nan bayin gidan ne za su ƙalubalance su. Sai ka ga azzalumi ya harɗe ƙafa bisa karaga yana kallon bayinsa na gida suna tare masa faɗa daga bayinsa na gona, don haka ya yan uwana Musulmi ya kamata ace munbar wannan mutuwar zuciyar da take neman aurenmu, Wanda muke jin ai seda wane ko wance kana ni zan kai labari!!!...... A ahhhhh ba haka bane kai kanka ba zaka gane hakan ba se loƙacin da kaganka a tsayayyen ingarman Namijinka sannan zaka tabbatar da cewan lallai ba seda wani wanin yake rayuwa. Ka sama kanka yaƙini da ƴancin cewar ehhhhhh lallai tabbas zaka iya💪. To da ga nan ne se Ubangiji ya jiɓanci dukkan lamuranka da kasa gaba, se kaga ya zaman kama wasu zarra da nisan kiwon da koda gudun ceton rai aka haɗa shi be Isa kamo koda kamu ɗaya bane. Don haka har gaban abada zuciyar kowannenmu ta kasance jajirtacciyace me jin zata iya. Ya kori wannan nakasar dake bisne cikin zuciyarsa domin Ba kasawa bace...." Ƙiran sallar la'asar da aka ƙirane ya sanya Sheikh juraij thabit tsayawa chakkk, daga ta cikin zuciyarsa kuma yana me ambatar wannan addu'ar ta ƙiran sallah. Kowa dake wurin be so ba haka suna ji suna gani sheshin malamin ya kuma gudanar da addu'ar tashi bayan ya musu alƙawarin Inda Rai da Rabo wata rana INSHA ALLAH zasu ɗora daga inda suka tsaya. Sahu ya biyo shima kamar yacce al'adansa yake bawai irin al'adan wasu daga cikin manyan malaman mu na yanzu ba. Ko nace masu mulki da wasu masu kuɗin, Yazo dap da wasu matasa biyu karaf buɗaɗɗun kunnuwansa suke nan kamar na maciji suka jiyo masa wasu munanan kalmomi daga gare su....... .........kunsan dama ance ɗan Adam ba'a iya masa?_ _Yaya kuke tunanin wasan ze kaya?, Gadai sheik juraij thabit Jedaans nan ga kuma waɗan nan samarin nan_ *BY AMMEY LAYLERH* 08104493215 Byeeee https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH ༺༻ *♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆* ༺༻ _ °♡◦༺ _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ_ °࿐_ 𝙉𝙖 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 ᴺᵃˢᵉᵉʳ ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _AMMEY LAYLERH_ *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *Happy juma'art mufeedah in advance to all Muslims 💅* BOOK ONE…………񆬍✍ Page 5&6 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Paid Book 07085041758 The Writer's of *MIKIYA* *KAREN BANA* *JALAAL AREEF* *ƘAUNA BIYU* *And Ongoing 𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵* ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ # Ⲛᕪᐜ Ⲩᕪᵃʳ'ˢ # 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ # SoulmateVibes # DeeplyInLove # TogetherForever # UnbreakableBond # Endless Love # SilentLoveAffair # HiddenHeart # ForeverAndAlways # Ɩ૦𝚅𝞔 Ʀ૦Ꮇ𝔸𝑵ᑕ𝞔 𝗕𝔸𝗕Ⲩ # Hot Romance scene # Real life # Hot love scene # A.k.a AMMEYLAYLERH👍👉 👇 https://t.me/+ISpf1lql0GwyNmJk Duk me neman AMMEYLAYLERH ganan link nawa na Telegram Wanda kai tsaye idan kabi link ɗin ze dinga kaika ga post namu kai tsaye. 👇 https://www.facebook.com/share/1A1gMDViUG/ Sannan kuma ganan na facebook don samun post nawa kai tsaye shima. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ "_Wato mutumina nifa lamarin wasu mutanen tsoro ma yake bani,Kai ban da ma iyayi da rainin hankali irin na wannan malamin ya za'ai gashi nan ƙannensa a gidansu ƙarƙashin su' suna aikata abinda suka ga dama be hana su ba se mu! Ta ya be fara gyaran gidansu ba yake tunanin ze gyara waje in banda rainin wayo. Kai nifa Maganar gaskiya ma saboda kawai naji wannan zazzaƙar muryan nashi kawai nake jin wa'azin sa bawai zanyi amfani da abinda yake faɗi ba.Nifa mutumina wllh ma se nake ga kamar dani ma kawai yake........ Be tsaya ƙarasa sauraron yaran ba yay gaba abinsa ba tare dama sun san shi ɗin bane. Bayan an idar da sallar zaman ganawa kawai yay da wasu Manyan malaman Lagos ɗin daga nan suka sake biyu jirgin yamma liss zuwa Kd,Manyan motocin da suka zo ɗaukarsa sune suka maida su har airport. Daga nan jirginsu ya lula yana keta sararin samaniya, tafiyan awanni kaɗan ce ta kawo su babban airport ɗin ★Tun da jirgin su yay landing a babban filin jirgin suka fito har suka fara tafiya Kansa a ƙasa yake hannuwansa kuma tttare cikin cashmere ɗin dake jikinsa, Taku yake yi cikin natsuwa sai dai kallo ɗaya zaka mashi kasan cewa ehhhh lallai Sheikh juraij jarumin namiji ne sosai mai jini a jika wanda kyaun jikinsa ke ɓoye hasalin shekarunsa. duba da yadda yake a buɗe kuma yana tafiya ne da jikinsa sosai, ba shi da kiɓa sosai sedai yanayin murjewan fata dana jiki kawai wanda hasalin Luxury da Luxury suka gama ratsawa,SE dai Yanayinsa kaɗai zaka kalla ka tabbatar da cewan lallai ba lafiya ba.Amma wannan karamci da kuma tsananin kwarjinin sa suka shanye yanayin san na ɓacin rai, Cikin hanzari Personal person ɗin sa Al-Ameen Hafeez yay gaggawan buɗe masa Toyota Avalon ɗin da yake da tabbacin itan ze shiga. Yana shiga shima yay hanzarin shiga yana amsan driving ɗin daga hannun. Mustapha Haroon da yazo ɗaukan su tare da rakiyan bodyguard nashi. ♡ Se wajajen yamma liss Meesherh ta fito dan tana da wani zaman meeting da company'n *MEESHERH LUXURY PRODUCT* {M.L.P} Wanda tun safe aka so gudanar da zaman meeting ɗin, sedai kasancewar bata tashi da lafiya bane ya sanyata ɗaukan Excuse tun a daren jiya. Sosai Meesherh tasha kwalliyarta cikin wasu dogon wando da riga, malesian dress wandon yana da faɗi sosai kamar palazo, rigar kuma ya fitar mata da shape ɗin ta sosai,Inda rigan yakai har zuwa gwiwanta ya tsaya, sai ɗan ƙaramin veils ɗin sa data rolling sannan rigan irin me igiyar nan ce ta wajen cikinta,se ta ɗaure igiyar a baya hakan yasa rigar ta kara fito mata da shape ɗin ta sosai, flat tummyn nan nata shape nasa ya bayyana, Sosai tai kyau sedai matsalan shape ɗin ta daya fita sosai shi ne ya ɓata mata kwalliyan nata. Cikin yanayin ɗan jin ƙarfin jiki take saƙƙowa daga stairs nata, a parlour'n ta tarar da mahaifiyar nata zaune kan Sofa se kayan fruits veggies in dake gabanta. "Ahhhhh Masha Allah Baby,kice sauƙi ya samu tunda har kika sama daman fita" Mah ɗin tay maganan fuskanta ɗauke da murmushin ƙaunan yarinyan nata. Ɗan zama tai gefe da ita Apple ɗin dake gaban Mah ta ɗauka tana cin kaɗan. "Ehhhh naji sauƙi sosae Mah! Kinsan yau ina da meeting shi ne ya sanya dole zan fitan" shafa kanta Mah ɗin tayi tare da mata adda'an dawowa lafiya da kuma cimma nasarar ta a koda yaushe. Ita kaɗai ta fita duk da securities ɗin Papiey'nta sun so bin bayanta amma ta buga musu shegen warning akan karsu daddara su bita. A kuma daidai loƙacinne shima Moh Ameern Saif ke fitowa daga nasu ɓangaren da shirin fitansa tsaff, magana ya soma mata sedai samm ita Bama ta jishi ba haka yata buga mata uban horn amma sam bata san da cewan itane akema hong ɗin ba. Wayarsa dake gaban motar yay saurin ɗauka yana dokama lambarta ƙira bakinsa cike taff da addu'ar ALLAH yasa ta cira, ai kuwa adda'an nashin ta karɓu don ring ɗaya ta daga, wani kasaitaccen murmushi yay tare da sanya woyan a amsa kuwwa yana me furta. "Meesherh Sameer Jadeens laifin me nayi dana cancanci wannan horon?, Tun jiyan kin sanya zuciyata a tsoron kodai na aikata ba daidai gareki ba!" Wani Banzan numfashi irin na ɓacin ran nan ta fesar still taƙi yin magana. Shi kuma hakan ne ya sanya shi sake furta "Meesherh" "Naam" Ta amsa a karon farko tunda farkon fara woyan nasu. "Pls ki tsaya muyi magana don Allah" kitt kitt kitt haka yaji ƙaran kashe masa woya da tay. Samm bata san biye yake da ita ba kamar yadda bata san shine ya ƙirata ba kasancewan amsa woyan kawai tay ba tare data ko duba me ƙiran ba. Cikin wani kalan ɗan iskan driving taci gaba da mirza steering car nata hankali kwance, idan ka ɗauke ɗan ciwo² da kanta ke mata har yanzun amma bada yawa ba kaɗan kaɗan yake harba mata. A kyakykyawan Parking car ɗin da aka tanaja domin Parking motaci ta Parker nata motan. Tun kamin ta gama daidai ta Parking motan ta ma'aikatan wurin suka zagaye motan ta cike da girmamawa. Iyaka Lugagge bag nata dake ɗauke da system nata ta ɗauka a motan, se eye glasses ɗin ta data maida saman face nata, Cike da kuzarinta da kuma kwarin gwiwan ta ta ziro da fararen sawayenta tana fitowa gaba ɗayanta. Fitowan ta a car in kenan taku ɗaya tay ana biyun taji an wani irin riƙo Hannuwanta. Ai a wani irin fusace cike da tsantsan ɓacin rai da tashin hankali ta jiwo don ganin uban daya aikata mata hakan. Sedai idanunta be sauƙa ana kowa ba se akan Moh Ameern Saif. Aikuwa Babu tantamar komi ta wanke kyakykyawan fuskanshi da marin daya cilas tashi janye hannunsa dake cikin nata. A kausashe a kuma faɗace ta shiga nunnunashi da manuniyar yatsarta. "Ina son wannan ya zama shine karo na ƙarshe da gangar jikinka zata ci gaba da baka haɗin kan sake kusanta kanka gareni Mohammed Ameern Saif" ta ambaci full cikakken sunan shi. Wani kalan shegen kill smile ya saki ya ɗan yin luuuu da idonsu da suka jaaaa na ɓacin ran shima, Sake matsowa dap da ita yay tamkar ze shige jikinta se kuma ya sake sakin wani shegen murmushin irin na cikakkun ƴan barikin nan masu aji. "Na sani! Na sani!! Na sani ba sekin sake maimaita min ba Meesherh Sameer Jadeens tana dakon soyayyar wanda yake mantawa da itama a tashi rayuwan, nasan duk waɗan nan abubuwan da kike yi pretend ne kawai kike a gaban mutane sedai ki sani rainin hankalinki samm ba zai yi tasiri a gareni ba, saboda ina son ki tuna da cewan tare kike da Moh Ameern Saif Jedaans wanda ya gama sanin sirrinki tsafff don haka care your manner take a good calamity" yay maganan da raɓata yana komawa cikin car nashi fuskansa ɗauke da Murmushin cimma nasarar shi gareta. A hankali cike da jin ciwon abinda ya aikata mata haka taci gaba da ratsa cikin company'n, cikin yanayin nutsuwan data zame mata dabi'a,tana takawa a hankali ƙamshinta da kuma yadda shigar ta amsheta kaɗai na sake jan hankulan jama'arn dake cikin company'n. Yadda take ɗaukan hankulansu haka kwarjininta ke sake baibaye masu kallon nata, gashi dai a zahirance dai ita ce Wannan shahrriyar jarumar da kullum suke kallonta a poster ko a photo ko video, sedai yau da sukai ido biyu da ita duk se wasu da suke jin suna da kwarin gwiwan mata magana da haɗa ido da ita harma da tarar ta se kowa ya gaza yin hakan. Saboda yadda tsananin kwarjinin ta ya riga da ya gama baybayesu da ɗi da ƙari yadda fuskanta take a tamke. Tamkar irin kunun ƙanwar nan da aka dama ba'a haɗa shi ba haka fuskanta yake a wannan loƙacin. Tun daga nesa ta hangi Muhsin Aliey Yahaya zaune cikin tanfatsesiyar car nashi, ya zubo kafafunsa woje hannunsa riƙe da kwalbar da ta tabbatar da cewan wine ce. Sosai taji ranta ya saƙe ɓaci a karo na biyu tana jin mi yasa abubuwa da yawa ke son yawo da kuma wajiga rayuwanta haka?. Tamkar bata san da wanzuwarsa a wurin ba haka tazo ta gitta shi ta fice abinta. Sedai shi ɗin ma ko taku cikakken uku batay da gitta shin ba yasha gabanta. Tun daga sama har ƙasa ya shiga binta da fitinannun shegun idanunsa haka harya sauƙe daman ƙirjinta da kuma cikinta dake lafe cikin shigan riga da wandon dake jikinta. Wani shegen numfashi yaje a sanda ya shaƙi ƙamshin mayen tularenta da yake bala'i bala'in ƙauna kamar me, cikin dakakken sautin amsa amo da kuma kuwwa ta furta. "Muhsin Aliey bani hanya na ce!!!" Ja baya yay kafin a hankali ya fara motsi da jajayen laɓɓansa, cikin muryan da ya fara tafiya da maye yake furta. "Meesherh kince na baki loƙaci na baki, kince na kaucewa ganinki a ko ina na kauce kince kince kince abubuwa da ya wa duk nabiatakan amma kuma loƙacin da kika ɗibar min sun cika kuma kinƙi bani damar taya kike tunanin zan baki amsa ba tare da kin amshi tayin soyayyar da nake mahaukacin yi miki ba!" Kanta ta kawar gefe zuciyanta na tafar fasa kamar me don wani loƙacin ita kanta bata san yadda ake take gaza sarrafa fushinta akan koma waye ba, kamar few minutes ɗin nan data ɗauke fuskan Moh da zazzafan marinta da babu wasa. Babu zata haka ta fisgen kwalbar wine ɗin dake riƙe a hannun sa tana buga mai a fuska tana raɓa gefen sa ta wuce bayan tama security ɗin umarnin su fitar dashi a company'n kar kuma su bar kome kama dashi ya sake shigowa. "Meesherh don nace ina sonki shine har kike jin kina da kwarin gwiwan wulaƙanta Ni Muhsin Aliey Yahaya jarmai, to wllh kin yi kuskure mafi muni a cikin rayuwankin kan wulaƙanta nin da kikai" daga haka yay wurgi da securities ɗin ya faɗa Motarsa yana ɗibarta da gudun hauka ya fice gaba ɗaya daga harabar company'n. ***Daga Inda yake tsayen yay wani kalan Runtse fararen idanunsa da suka masifar kaɗewa irin mai ban tsoro ɗin. Yana jin zuciyarsa tamkar zata ɓallo ko ta faso rufin fata bakwai ɗin dake ƙirjin ta fito. Wani hucin numfashin azaba ya fesar yana soma taka stairs ɗin bibbiyu yana yowa ƙasa. Tana isa babban office nata daya ƙawatu sosai da kayan mo re rayuwa takai zaune saman cough ɗin dake gaban table editing chiers ɗin, tare da zube manyan wayoyinta tare da Lugagge bag nata. Ijiyar zuciya me ƙarfi ta sauƙe tana me tallafar kanta da duka hannuwanta biyun, Mayataccen ƙamshin da taji ya soma shiga hancinta ne ya sanya ta Cikin nutsuwarta da rashin rawarn kai ta ɗago idanunta kaɗan tana bin ƙofan shigowa office ɗin da kallo, dan wannan shegen unique ƙamshine da baya taɓa ɓacewa daga cikin rai da tunaninta. Daidai ganinta na sauƙa daga inda yake tsaye jingine da bayan ƙofarn. ƙirjinta taji yay wani irin motsawan tsoron biyo bayan tan da yay. Dan a Jinin jikinta tasan cewan dama yana cikin company'n. Sosai taji ƙirjinta na amsan dakan uku ukun da yake mata, zuba masa idonta tay tana masa kallo irin na mamaki ko ruɗani ma zamuce ne oho. Amma kasancewarnta mutum bame barin ko wanne irin hali take bayyana bane ya sanyata majewa. fuskarnta na a daken alamun babu wani shock da taji ta tsinta kanta a ciki. Ya sani ze kuma iya rantse yafi kowanne mutum na cikin duniyar sanin halinta ciki da bai kasancewanta renonshi ce.Nunawa tay bata damu da yadda ya tsareta da idon ba se ma janye idanun ta da tay slowly tana maidawa gefe daban. Gently shima ya lumshe nashi fararen idanuwan san da kalan ɓacin ransu ke a bayyane. Ahankali ya shiga motsawa gabanta hannuwansa biyu ya sanya yana dafe table editing chiers ɗin dake gabanta. Se da ya ɗauka sama da 5 minutes tamkar me rowan yin maganan, kafin kuma cikin ɗan kaushi kaushin murya ya furta. "Babyyy!!!" Se kuma ya ga za ci gaba da maganar da yay niyan faɗin mata. Wani irin bugawa gabanta yay, a raunace ta ɗago da kanta tana zuba idanuwanta cikin ysakiyar nashi idanun. A tare kuma kamar an tunasar dasu wani abu suka janye daga kallon junansu. Ƙasa tay da kanta tanajin gabanta naci gaba da bugun da yake mata, Soft fararen zara zaran yatsun hannunsa uku ya sanya yana me ɗago fuskan nata.★ Lumshe idanunshi yay yana sake shaƙar sassanyar iskar dake kaɗawa me garwaye da daɗdan ƙamshinta da yake shigan masa hanci. har zuwa lokacin kuma shi be janye idanun nasa a kanta ba Runtse idanunta a karo na biyu tai tana ƙoƙarin kwatar numfashin ta dake barazana wa gangar jikinta. danne dukkan abinda ke yunƙuro mata a kan shi tay. A natse lips inta har na ɗan rawa a ƙoƙarin ta na ganin ta ambaci kalmar Pa'apah kaɗai. Sedai laɓɓantan sun mata nauyi sun gaza bata haɗin kai wurin yin maganan tan yadda ya kamata. Lips natan dake motsa ya zuba idanunsa har adams apple ɗinsa na ɗan motsawa a maƙoshinsa."Me yasa Babyn pa'apah bata jin magana kamar yadda ta dena jin tausayinsa" A tsanake yay maganan Slowly yana janye idanunsa daga kallon lips. A hankali a hankali yake yin baya baya yana ƙoƙarin danne abinda ke yunƙuro masa game da Babyn tashi. ƴar kuma rikicin sa Meesherh, da idanunta da suka fara ƙyalli alamar taruwar hawayen da suka tara.tana jin yadda jinin jikinta ke wani irin harmutsawa tamkar ana aza wuta a jinin jikintan haka take ji, da idon taci gaba da binsa tana jin wani abu me kama da bijirewa kowa da zuciyarta akansa na ƙoƙarin ingiza ɗan ƙaramin lissafin ta. Yana fita ruwan da suka cika idanunta na zubowa da taji bala'i bala'in zafi da ƙunar da suka haifar mata. "I hate that bai ci ace zuciyana kinci gaba da yaudarana akan shi ba, and I LOVE YOU pa'apah dika nake son jin tsanar ka da kuma ƙaunarka, Inson jin tsanarka kan ƙoƙarin shata min layi da kuma buri na da kai ƙoƙarin yi tun a baya, ina kuma ci gaba da son jin S0 da kuma ƘAUNARKA a matsayin ka na pa'apah Naaaaa dikaaaa!!!" Haka dai ta shiga surkullen maganganun ta tana yin fatali da duk wani abu me amfani dake cikin babban office ɗin nata. A haka seda ta gama hargitsa komai, Babban P'A ɗin ta Tanim teddy ne ya shigo da shirin faɗin mata ta fito ya tarar da ita cikin wannan halin. A take ya ƙira Iklima wata ma'aikaciyace itama a cikin company'n, itane tay ƙoƙarin dakatar da Meesherh ɗin shi kuma ya shiga tattare komai yana killacewa wuri guda, marassa amfanin wanda suka tashi a aiki yana fita dasu. Tun a take yay ordering daga ɗayan company'n suka zo suka sake docoret na office ɗin. Zaman meeting ɗin da ba'ai ba kenan a ranar Iklimar ce ma ta taimaka mata wajen dawo da ita gida. Kasancewar da night bayan sun dawo a sallah al'adanshi ne se yaje yayo sabon wanka ne yake sanya shi zuwa dining room din a ƙurarren loƙaci kullum.Fararen riga da wando na fendi masu azabar laushii da kwanciya a jikin mutum ne a jikinsa. Fararen sawayensa kuma suna sanye cikin Blue Lorenzo's slippers masu taushi, ga wannan mayen ƙamshinsa dake rige rigen kaima hancinansu ziyara tun kafin isowansa parlour'n. Wani irin tsalle taji zuciyarta yayi a karo na biyu,iyaka ƙamshinsa kaɗai karyar mata da zuciya yake, se dai kwarai da gaske tana ƙoƙari wajen shanye hakan,Cikin irin jarumtar da take da ne ya sanya kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta tana ci gaba da sipping coffee creamer ɗin ta. A cikin zuciyarta ayyanawa take ehhhhhh lallai Pa'apanta na daban ne kuma me kyau ne da kuma tsafta. Wanda indai magana ake ta wanka yabi jiki to kuwa ba tantama tasan pa'apanta ƙarshe ne. Sam babu ko ɗigon annuri a kyakykyawan farar fuskan shi haka babu wasa ko alamarsa a saman fuskarsa nashi da tai wani kalan fayau, wanda kai tsaye ita tasan dalilin daya haddasa may hakan. Don kamar yadda yasan duka halayensa haka itama ta san duka halayensa da kuma kalan damuwan da yake shiga ko akasin hakan. Kowa dake parlour'n wani kalan shiru yay har ya gama saƙƙowa,kallon kowa baiyi a cikin parlour'n ba saima ta bayan parlour'n daya zaga yana shigewa cikin balcony in da kai tsaye nan ake jera may abu mara nauyi duk daren duniya ba tare da su yake yin lonch ba. Wayane maƙale a kunnensa wanda da dukkan alamu wata wayace yake yi muhimmanci. yana yin wayar ne kuma hannunsa na ɗauke da wani haɗaɗɗen glass cup mai ɗauke da Whipped cream a ciki yana sha. Gefensa kuma Mohan ne da bay jima da biyo bayansa ba shima zaune saman sofa se woyansa da yake aikin dannawa wanda alamu suka nuna kai tsaye chatting ne yake yi. Shima nashi hannun ɗauke da Extreme milk shakes ɗin dake a saman ɗan table ɗin dake gaban Sheikh juraij ɗin. ★ Bayan ya kammala woyan kai tsaye ya maida kallonsa ga Mohan ɗin. "Yaya abubuwa sosae suke yin kyau game da binciken sirrin da muke yi kamar yadda ka buƙatan ama. To Alhamdulillh se dai mu ce Masha Allah" Gefin lips nashi ya ɗan ciza kaɗan se kuma ya furta "don't worry zamu magana daga baya ina buƙatan hutawa yanzu" kansa ya gyaɗa may yana miƙewa harya fara tafiya kuma ya tsinkayi muryan babban yayan nasu yana ambatar sunan shi kai tsaye da *Mohan Sameer* chakk ya tsaye tare da waigowa alamar gaskata in ƙiran ne ya koma. nodding Kansa yay alaman ehhhhhh ƙiran yay, baya ya dawo yana zama inda ya tashi. Magana yake son may game da Meesherh amma bakinsa ya masa nauyi se kawai ya fiddo da wani kyakkyawan ƙaramin kwali me kyau da ɗaukan hankali "Na lil juraij Mohan ne" amsa yay fuskansa ƙawace da murmushin jin daɗin kulawan da Sheikh ɗin kema yaron san, duk da yasan kome yake da buƙata shima a cikin duniyar yakan iya narka kuɗaɗen sa wajen siyan ko miye se dai ita kyauta ɗaya ce kuma daban take. Duk yawan tarin dukiyar da kake da to fa idan wani ze ciri wani abu ya baka as matsayin kyautatawa wani kalan jin daɗi kake. Kwarai kyauta Rahma ce kuma takan sanya mutum yaji daɗi da shauƙin kyautan da aka masa. Godiya ya may cike da fara'a yana barin wurin gaba ɗaya don bashi space ɗin kamar yadda ya buƙata. A ƙalla seda ya debi wasu ƴan lukuta masu tsayi kana ya miƙe yana bin ƙofan fita wajen parlour'n ta baya. Ji yay a jikinsa tamkar ana kallonsa loƙacin da yake tafiya domin nufar ɓangaren sa, tana tsaye cikin kayan shan iska amma ba masu nuna tsiracin mutum ba kanta babu cap hannunta riƙe da woya tana daddannawa. Ido biyu sukai tay saurin janye nata tamkar dama can ba shi take kallo. Se hakan ya Hasko wani abu daga cikin memory'n baya cann. Ko me ya tuno kuma oho amma kome ya tuni me girma ne dan wani kalan tattausan Murmushin gefin baki ya saki yana wucewar sa kai tsaye. Wani kalan luuuuuuu da nata idanun itama tayy tana yin bayaaaaaa...... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* More Information 08104493215 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ༺༻ *♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆* ༺༻ _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ_ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 Naseer ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _AMMEY LAYLERH_ Page 7&8 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Ƙafar benen tay hanzarin kamawa tana sakin wata munafukar ɓoyayyar ijiyar zuciya ta saki acan ƙasan ranta. Juyowar da zatai tay ido biyu da Mammanta wacce ta tsarera da ido, Ɗan faɗuwa taji gabanta yayi ganin yadda Mah ɗin ta wani kalan tsareta da idanunta."Me ki ke yi anan?" kai tsaye Mah ta cilla mata tambayar fuskanta babu alamun wasa don ita mace ce bame son ɗaukan wargi ba ko daga yaran natane kuwa. "Ina shan iska ne maah" Rolex watch ɗin dake daure a tsintsiyar hannun ta Mah ɗin ta kalla tana furta. "Kalla ki gani ƙarfe nawa yanzun da kike nan tsaye har yanzun baki kwanta ba?" Kanta ta ɗan rausayar gefe ba tare data ko sake furta wata magana ba Mah ta kama hannunta tana kaita har bakin ƙofar parlour'n ta. Ita kuwa Meesherh Koda ta shige room ɗin nata ma bata shige bedroom nata ba kwance kawai tay anan bisa 3 str daga ita sai wata yellow ɗin doguwar rigar baccin dake jikinta irin me santsin nan me kuma bin jikin mutum.Sai wata tattausar hular sanyin dake kanta yellow, yayinda himilin gashinta yayi luf luf yana kwanciya har gadon bayanta se dai ba can ba, don da kaɗan ya zarce kafaɗunta. Sosai tay wani kalan masifar kyau duk da kasancewar kayan bacci ne a jikinta,kasancewar ita ɗin me kyau ce wanda shi wannan kyaun ya haɗu da aji da kuma tsantsar hutu da jin daɗin Rayuwa. Har ta kama doorhandle na ƙofar parlour'n ta seta juyo da baya tana jin kamar ba daidai ba, kodan kasancewar ta auta ne ya sanya duk daren duniya bata taɓa iya bacci ba tare da ita taga baccin babyn nata ba. Kamar yadda take a kwance a parlour'n haka Mah ta tarar da ita kwance hankalin kwance kuma take baccin abinta.Gashin kanta dake ɗaure cikin jan riboms ƙwara ɗaya ya zame yayi nashi wuri, se hakan ya bama gashin damar bajewa akan 3 str ɗin da take kwance akai.Se sheƙi da walainiyar kyau yake gwanin birgewa. Zama tay gefenta farar fuskanta irin ta Mahaifinta Sameer Jedaans sak ta ɗan shafa,sauƙe ajiyar zuciya tay tana zuba mata idanu sosai, A natse kuma ta shiga tashinta ba yadda zata firgita kota tsorata ba. Idanunta ta baccin sosai ya fara cin ƙarfin su ta ware akan mahaifiyar nata. Ɗan Murmushi me laushi ta sakar mata tana kamata ta mikar da ita tsaye. Kasancewar ta bame nauyin bacci sosai bace ya sanyata miƙewa Mah na taimaka mata wajen soma tafiya da ita. Akan lallausan gadonta ta kwantar da ita haɗi da tattare mata gashin tan wuri guda tana sake ɗaure mata shi da ribboms ɗin cen ƙasan ƙeyarta don karya dameta wajen baccin. Adda'an barci ta mata haɗi da neman tsari kafin ta tsareta da ido a cikin ranta kuwa faɗi take {ya Allah ga baiwar ka nan Meesherh ka kula min da ita cikin amincinka da buwayarka, kaci gaba da tseratar min da ita daga duk wasu masu nufarta da mugun nufi. Na bayyane da na ɓoye, ya Ilahi ya mujibud da'awati karkaci gaba dabe kowa damar sake cutatarmaka da wannan bewar take me raunin zuciya!!! Ya Allah} Se kuma A hankali ta ja abin rufa ta rufe mata daidai saman ƙirjinta haɗi da ɗan ɗukawa tana manna mata kiss a goshinta. "Ya Allah kamar yadda ka raba tsakani idan har babu Alkhairi karka kuma jarabtar wannan baiwa taka da wani abu na daban" wannan karon kam a bayyane tay maganar Jiki sanyaye ta juya tana barin bedroom ɗin. Itama jikinta sanye da kayan bacin dogon wando da riga sakake sosai da riga buɗaɗɗiya sosai irin fararen nan masu faɗi dai haka sosai. Kamar yadda ta fita haka ta dawo ta tarar da prof Sameer Jedaans yana nan zaune gaban System nashi sai faman aikin sarrafata yake idanunsa sanye da farin gilashi, bare daya ɗago ba ya furta "Se yanzun kike dawowa? Kin gama lallaɓa Babyn taki kenan har tayi baccin!" Murmushi kawai ta yi ba tare da tace komai ba ta wuce Bathroom don haɗa masa ruwan wanka me ɗumi da ƙamshi. Don al'adansane baya taɓa kwanciya har se yayi wanka. Zama tay kusa dashi tare da ɗan Murmushi ɗauke saman fuskarta. Kanta ta kwantar da kanta saman shoulder nashi, "Papiey'n Meeshel ruwan wankanka is ready" Kansa kawai Papiey'n ya ɗan girgiza yana lumshe idannuwansa ƙaunar matarshin abin sonshi na sake ratsa shi. Kayan jikinsa ya rage yana faɗawa bayin. Bayan ya fito ɗaure da alwulan da al'adan gidan ne ba'a kwanciya ba tare da alwulan ba, sedai wasu sukan yi wasu kuma basu yi haka nan tsarin yake. Ko kafin ya fito tuni Mah ta sake gyare bed ɗin daga nan suka kwanta abinsu se bacci. ☆☆☆☆ Ance wai dare mahutar bawa, kamar ko wanne rai me numfashi ke kwance domin samun hutu ga rayuwarsa cikin kwanciyar hankali yana barcinsa, Se dai a dai-dai wannan loƙacin Sheikh juraij thabit ke zaune saman darduma yana rera karatun Al- Qur'ani mai girma,Cikin wani irin amo madaidaiciyar muryarsa mai daɗin sauraro da sanya ma zuciyoyi nutsuwa yake raira karatun. Idanunsa lumshe suke daga can cikin ƙasan ƙasan zuciyarsa karatun ke fitowa. Wani kalan Nunfashi mai nauyi Abba dake tsaye tun da jimawa a ƙofar shigowa parlour'n yaron nasa yaja. kana ya fesar tare da cike da sanyin jiki ya turo ƙofar ya shigo a natse. Jin motsin ne ya sanya Sheikh juraij buɗe idanunsa da suke a lumshe har zuwa loƙacin. Akan Abbansa ya sauƙe ganinsa kai tsaye, saurin tashi tsaye yay yana me nufo abban. Sanya hannun sa masu taushi yay yana kama na sheik ɗin cikin nashi, bakin bed ɗin Sheikh ɗin Abba ya zaunar dashi shima yana zama kusa dashi. Se daya ɗan ja wasu second haka kafin cike da tsananin tausayin yaron nashi ya furta. "JURAIJ akwai wata alfarma da nake nema awajenka!" Cike da wani Irin baƙon yanayin da zuciya ke ɗauka a bazata ya ɗago kansa yana kallon Abban cike da girmamawa ya furta. "Abba kawai kace wani Umarni zaka bani amma ba alfarma zaka nema daga gareni ba. Saboda kafi ƙarfin neman alfarma awajena sai dai ka bani Umarninka kawai, Ni kuma a koda yaushe me biyayya ne ga dukkanin umarninka" Zama da kyau Abba ya gyara kana ya fuskancesa da kyau cikin raunin zuciya da amincin da yakeji akan Sheikh juraij ɗin yace. "Um-um Juraij alfarmar dai kam nake nema" Cikin jin nauyin mahaifin nashi da ganin kimansa ya sake risinar da kansa ƙasa, muryan sa har na shirin karyewan raunin da tay ya furta. "Idan har Abbana ya zaman yana nema alfarma daga gareni to ni a gun waye zan nemi ta wa alfarmar, idan kana faɗin hakan Abba kunya nake ji duk loƙacin da naji kana furta kalmar neman alfarma daga gareni Abbana" Kai Abban ya ɗan girgiza cikin sauƙe wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya furta. "Sai alfarmar da zan nema daga wurinka inason ya kasance iyaka ni da kaine, a iyaka mu nake son maganar ya tsaya" kansa yake geɗawa Abban tamkar irin wanda bay maganan nan. Kafin cikin wani irin yanayi mai gauraye da damuwa da rauni ya furta. "Insha Allah Abba a koda yaushe ni me bin umarnin kane kamar yadda ni me riƙe maka sirrinka ne" "Meesherh!!!, Meesherh itane damuwar juraij tare da Mahaifiyar ka na rasa ta yadda zan fuskanci wannan al'amari Juraij....." Daga nan suka juye baki zuwa wani yare na daban wanda Ni AMMEY LAYLERH'NKU banjin duk abinda suke faɗi ɗin kuwa. Sun ɗauki a ƙalla sama da 40 minutes suna magana kuma cikin wannan juyayyen harshen da suka juyemin. Kafin daga bisani Abban ya miƙe cikin yanayi na ƴar damuwa Sheikh ɗin na biye a bayansa. Da sauri Inuwar da tun farkon fara zancen nasu take tsaye ta gilma alamar ta kauce. Kafe wurin da ido Sheikh juraij yay zuciyan sa na beating na ɓacin ran hakan da aka jima ana mai wato laɓe.... *Around 4:20 Am* Ƙarar Alarm ɗin data sets duk asubahin duniya shi ne ya farkar da ita. A hankali ta shiga ware lumsassun idanunta da suke cike da barci har yanzun kana suka mata nauyi.da adda'an tashi a bacci ta tashi a bakinta. A natse ta ziro fararen santala santalan sawayenta kan tattausan canies carpet ɗin dake gaban gadon, ɗan miƙa tayi haɗi da shigewa cikin bathroom. Alwula ta ɗauro tazo ta fara gabatar da raka'atanil fijr,tana nan zaune da Rabbana Arba'in riƙe a hannun ta na Adda'o'i taji wannan amintaccen sautin nashi na ratsa duka cikin jikinta. Cike da tarin nutsuwa take binsu sallar subhi ɗin. Bayan an idar komawarta kwance tay tana sake shigewa cikin lallausan duvet ɗin ta. Ba itane ta farka se wajajen 11:40 kasancewar weekend ce, Kai tsaye bathroom ta shige tana sakar ma kanta shower. Se da ta ɗauki sama da 40mins a cikin bayin kana ta fito jikinta sanye da peach cobbler bathrobe a jikinta, Kanta kuma na cikin fari tass ɗin towel mini. A kan stool in dake gaban 1 mirro'rnta ta zaune kanta ta fara busarwa, kana ta shiga tsane ruwan jikinta. very expensive lotions ɗinta ta ɗauka take levelling lower skin ɗin nan nata me kala dana new born baby Wanda hasalin Luxury da Luxury ya gaka ratsawa. Farar powder me hasalin maiƙo ta shafa a face nata daga haka kuma ta shige cikin closet nata don shiryawa. Sanye ta fito cikin wani mahaukacin milk and coffee colours One Millions all stones yaɗi halp bubu, Yaɗine me shegen kyau da kuma tsada na manyan yaran ƴaƴan gata. Siririn mayanin yadin ta ɗora iyaka gefen shoulder nata na dama.Kai tsaye Phone nata dake jikin Rinlight already ta nufa. Seta cameras na woyan tay ta cikin tiktok nata. Wannan fitacciyar wakar da tay trend a media ta saki ta Ƴar Arewa. Wacce jarumi Sadeeq sale ya saki, har wani ɗan lullumshewa idanunta keyi. Tana gama yin Vedio'n tayi posting nata a duka pages nata na media, take mutane suka ringa likes kan videos ɗin nata kamar kullum. Daga haka ta nufo ƙasa ta sauƙo kamar yadda ta zata duk iyayentan suna babban parlour'n gidan ne. Tun kamin ta iso wannan shegen ƙamshin tan nan ya gama sanar musu cewar me zuciyar j̶e̶d̶a̶a̶n̶s̶ ce gaba ɗaya ke tafe wato 𝘿𝙄𝘼𝙈𝙊𝙉 Ꮇ𝞔𝞔𝘚Η𝞔Ʀ 𝙎𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝕁𝔼ᴰᴬᴬᴺˢ. Daga gefen Mah ta zauna bayan ta gaida kowa dake dining room ɗin. plate ɗin dake ɗauke da donut, pizza se picanto taja gabanta tare da ɗauka tana ɗora shi kan cinyarta tare. Metres sarvice ɗin dake aikin shirya kitchen Meesherh ta kwalama ƙira tana bata umarnin kawo mata fruits. Babu jimawa kuwa se gata hannunta riƙe da plate da yankakkun fruits ɗin a ciki masu sanyi, da akama yanka ƙananu². Nanameerah ce ta ɗan kalla inda Meesherh ke zaune ƙanwa Moh Ameern Saif ta furta wallh Aunty Meesherh kalan yadda kike gudanar da acting naki wurin aikin ku na burgeni wllh" Ɗan murmushi me faɗi tay tana kallon Nanameerah'n itama tare da furta. "Sosai mutane ke faɗin wllh aikin mu film na burgesu sosaifa Nanameerah" a tare kuma suka saki murmushi wa junan su cike da shaƙuwa. Annie ce ta kalla sashin da Meesherh ɗin take tare da furta. "Aikin me? Ke yanzu har wani abun kirki da alfahari kika ɗauki sana'ar taki, Ko da yake aifa aikin tallata jiki a yanzun kam shine babbar sana'a a Nigeria" A rene cikin wani ɗan iskan renin wayo da rainin hankali ba tare data ko kalla inda Annien take ba ta furta "Nagode!" Tsaye ta miƙe da niyar barin dining room ɗin. Abba ne ya kalleta da alamun damuwa a ranshi ya furta. "Mamana ina kuma zaki bayan baki ko kammala yin dinner naki ba?" Shafafen cikinta da ba kamar yanzu ta gama cin donut da pizza haɗi da picanto ba sam kai ba kace ma kwai ƴaƴan hanji a cikin cikin nata ba. Ɗan shafa cikin nata tay tare da furta. "Alhamdulilah na ƙoshi ne Abba" "Ok shikenan Mamana Ubangiji yay Miki Albarka, da ameen ta amsa bayan ta sake musu sallama don yau tana da wani shooting film da za'a ɗauka wanda Film ɗin tane itane da kanta ta tsara abinta.Har taje bakin ƙofar parlour'n kamar daga sama ta tsinkayi muryawan Ama tana me furta. "Takwarata taimaka ki sauƙe min yayanku a gidan gwaggo Haleemah" Cike da ɓacin Ran daya kasa dannuwa Annie ke kallon Ama data kasance surukuwa a gare su kafin cikin hucin ɓacin rai ta furta "Haba ama bayan batama zuri'armu suna da tay, duk hakan be isheku ba sema ƙoƙarin dan gan tata da Mutum tsarkakakke kamar juraij da kuke! Don me ake min haka ne eye? Kodan kawai kina matsayin Yaya ga Mahaifiyata? To ni wllh na gaji nima kawai daga yau ki dawo yimin kallon surukuwarki ba ƴar ki b...... "Zeynab!!!" Abba ya wani irin ƙira sunanta a mugun tsawacen da ya sanya kowa rawan jiki a wurin. Don ba abu bane daya taɓa faruwa a zahirance duk kuwa irin tijara da jalalar da Annie'n keyi akan duk wani abu daya danganci Meesherh ɗin. I'm sorry Abban jur..." Ta furta muryan ta na rawa. "I said get out my friend!" ya sake buga mata wata uwar tsawar da tafi ta farko ba shiri ta haɗiye maganar da bata ƙarasa taba tana barin wurin don A yadda ta ji muryarsa a kausashe kam ta tabbata babu wasa a cikinta. Jiki a sanyaye kowa ya shiga darewa banda Mah da jikinta har wani jijjiga jijjigan ɓacin rai da baƙin cike take yi, Sa'ar ta ɗaya sunan ALLAH ne ya fara zuwa bakinta kafin komi shi yasa ta dinga nanata sunayen ALLAH'n a bakinta. Meesherh kuwa tana fitowa compound na gidan ta tsaya tare da ɗan sa hannunta na dama tana riƙe ƙugunta. Nainarh ce tsaye ƙaramar autarsu Sheikh juraij jingine da jikin motar ta. Wani irin kallo Nainerh take watsama Meesher'n tare da furta. "Har ke wa ce ce a cikin gidan nan da har zaki ringa mahaifana meda yawu akan ki gaban mutane?" Wani kalan sheƙeƙe Meesherh ta mata "Kin ga kenan ke da kanki kin ba kanki cikakkiyar amsarn cewa Ni ɗin wata aba ce me girma a cikin gidan nan, Idan kin gama bani hanya ta zan wuce" Tay maganar tana kama murfin car nata tana ɗora haɓarta akai, ta buɗe baki kenan da nufin sake watsoma Meesherh ɗin wata rashin kunyar idanunta ya sauƙa akan babban yaya wato Sheikh juraij thabit Jedaans. Babu shiri ta gimtse bakinta tana haɗiye sauran maganar data saura a cikin bakinta. Tamkar kiftar ido haka Nainerh ta ɓace a wurin. Zuciyanta a cunkushe ta shige Motan tana zama mazaunin Driver yayin da ya zauna gefen mai zaman banza. A natse tasa hannunta farare ta kunna motar cikin yanayin nutsuwa take driving nata, Yayin da shi kuma yake gefenta zaune. Ahankali yake ƙarema zara-zaran yatsun hannunta dake kan stearing tana juyawa kallo,me kama da kalan nashi don sosai abubuwan su suke ɗibar kamanni harta da sawayenta kalan nashi ne futiƙ,wani ɗan numfashi ya fesar tare da furta. "Bani motar nan b.... Ji yay ya tsinta kansa da kasa ƙarasa sunan Babyn da yay niyar faɗi.Se ma lumshe idanunsa dayay tare da shaƙan ƙamshin humranta daya cika motar. Ita kuwa bata kawo komi a ranta ba sema kallon yanda ya lumshe idanunsa tay se taga ba ƙaramin kyau ya mata ba. A jikinsa yaji kallonsa take se kawai ya gyara fuskan da kyau yana jingina kansa da jikin motar, Kamar kuma ba zai yi magana ba buɗe lips inshi a hankali yay tare da furta. "Kallon fa?" Kanta ta ɗauke wani munafikin murmushi ɗauke saman fuskanta. "Pa'apahh!!!" Ta ƙira hasalin ainihin cikakken sunan shi gareta tun yarinta.Hakan ne ya sanya Idanunsa dake lumshe ya shiga motsasu ahankali yana son buɗe su tare da faɗin. "Buddies kiyi abinda ke gabanki, ko kiban motan!" Buɗe idon ta da yanzu ne ta lumshe su dama tare da juyowa ta kalli inda yake zaune, iyaka muryansa kaɗai da taji ya sauƙar mata da samun nutsuwa. "Pa'apahh to kace ka yafe min pls" tay maganan da alamun rauni sosai tattare da ita. "Da ki kamin me kenan fa?" Yay maganan cikin ko in kula. "Everything forget itt" Kansa ya dauke a kallonta yana maida shi can kusa da closed windown motar, Itama se bata sake furta komai ba don tasan bayi son maganar kenan.Nuvel script ɗin ta dake gefe ta ciro me ɗauke da photon'nta tana budewa ta ɗaura shi saman gaban motar. A duka sassan jikinsa ya soma jin banbancin yanayi. Sake buɗe idanunsa calmly akanta yay, wacce ta nutsu wurin driving nata a kuma daidai loƙacin suka kawo ƙofar get na wani makeken ƙaton get. nitsatsassun fararen idanuwan ta da suke nan sakk nashi kawai ta zuba akansa. tamkar wacce bata da wata matsala a rayuwarta tamkar babu abinda ke damun zuciyarta ta furta. "Pa'ap.... Bai bata wani dama na ƙara sa ambatar sunan shi da tay shirin yiba ya fi ce a motar. Wani irin shiru tay tana me binsa da kallo da raunatattun idanunta. dan Shiru tayi na wani loƙaci kana taja kan motar ta tay reverse tana shan kwanar da zata bi. Cikin son shanye komi cike da nitsuwa take ci gaba da tafiyanta kamar daga sama taga wata babbar mota tayo kanta. Tamkar wacce aka bugama guduma haka taji amon muryansa cikin wani shuɗaɗɗen lamari yana furta "Babyyyyyy..... A wani irin tsiyace ta taka wani mahaukacin birki tare da juya kan motar ta zuwa ɓangaren gabas, wannan babbar motar da tayo kanta na bugar wata motar daban ba ita ba. ★★ Slowly ta shiga buɗe idanunta da taji sun mata nauyi loƙaci guda, ɗan lumshesu ta sake yi tana ƙoƙarin saita kanta dan koda wasa batai tunanin zerewa motar ba. Wata ƙatuwar Ajiyar zuciya ta sauƙe me nauyi. Tana ambatar sunan ALLAH cikin rai da ruhinta. ★ Ɓangaren Sheikh juraij kuwa a natse ya sanya kansa cikin ƙaton parlour'n gidan, da gwaggo Haleemah wacce ta kasance kaka a gareshi ya fara cin karo. Gwaggo Haleemah yaya ce ga Ama kuma ita kaɗai take da ita ƴar uwa anan kusa idan ka cire dangin su dake saudia. "Aaaahhh lale marabu da babban angona, Juraij yau kuma kaine da kanka?, Kodai ɓatan hanya kayi Ni Ko nace banda wajen zaman masu ɓatan hanyar?" Tay maganar da murmushi kwance saman fuskarta. Zama yay daga saman 1str ɗin dake kusanta. Zamansa babu daɗewa kamar an cillota Samha ta shigo cikin parlour'n zaram tamkar ana tunkuɗota. Samha ƴa ce ga Surayya ƙanwa ga Annie kenan wacce kuma suke ƙoƙarin haɗa aurentane kuma da juraij ɗin, sedai sam yarinyan bata da kamun kai amma su basa ganin hakan babban burinsu kawai auren ya haɗu. Se data ta shigo kuma cikin mugun bariki da kisisina ta wani sinne kanta ƙasa tana furta. "Laaaah dama uncle kaine? To sannu da zuwa Bara a kawo maka juice" da hannu ya mata halaman bai buƙata. Dan faɗa fuska tayi tare da duban gwaggo Haleemah tana furta, "Gaskiya gwaggo ki ma Uncle juh magana! Shikenan yazo shi kullum ba zai ci abincin mu ba inda Ni ce na ce zan kawo mishi" Dan murmushi irin nasu na manya gwaggo Haleemah ta yi tana furta "Yo in banda abin kima Samha kwana nawa ya rage miki, ku ce kan kita masa girkin kalan wanda yake so, kuma dai kinsan juraij bai fiye son komai a sake ba, amma idan da gake se shi ne seki ta lallaɓa kayanki ko" ta ƙarishe maganan da Murmushin nan ɗauke saman fuskarta. Dariya ta saki tana rufe idonta wai ita ala nan dole an bata kunya.Daga haka ta shige dayan parlour'n dake kusa da wannan ɗin shi kuwa a natse yaja fruits ɗin dake gaban gwaggo'n apple ya ɗauka ya ɗan ci kaɗan. Bayan bata saƙon da yay ya miƙe da shirin tafiya. Suraj ne ya shigo parlour'n da yake shima jika ne ga gwaggo Haleemah'n. Gefensa ɗan wani matashin saurayi ne suna tafe gwanin birgewa. "Ahhhh yau wa nake gani kamar babban malami" ya fadi a washe hakwaronsa farare tasss waje, Bai bi ta kan iya shegen da suraj ɗin ya soma mashi ba yana bama matashin hannun suyi masabaha. Don ya san idan ya biye ma suraj ɗin babu ruwansa kunya ne kawai ze bashi. Ita kuwa gwaggo Haleemah bin bayan Samha tay, zama tay gefenta suka soma fira cikin dabara gwaggo take dan son lurar da Samha'n kan lamarin Sheikh juraij ɗin da ake shirin aura masa dap. Sedai maganan bawai tama ko fita bane iyaka yasu ya sune suke ƙusƙus dinsu tsakani. Sosai firan da gwaggo take mata akan juraij ɗin ke mata daɗi da sanyata nishaɗi ♡ Rasss gabanta ya mugun buga mata don ganin drector Muhsin Aliey Yahaya tsaye da wasu yara wanda kana kallon su kwanyarka zata Hasko maka cewan ƴan daba ne. Sedai shanye tsoron nata bayyanuwa tay tana karasa fitowa a motar nata kai tsaye ba tare data kalla inda yake ba ta shigewanta inda zasu gabatar da shooting film ɗin ta na. ★TAURARUWA♡ Film ne da take son yin cleaning up nashi Kan yadda waɗanda taurarinsa suke Haskawa a cikin duniyar suke wulaƙanta mabiya dama masoyansa. Tana shiga hall ɗin Hotels din da za'a gudanar da shot ɗin suka dauki sowa da ihun ƙiran sunanta. Kanta ta ɗauke daga kallon Moh Ameern Saif daya kafeta da ido. Nan aka soma gudanar da shirin cike da birgewa. Ba itane ta sama kanta ba se wajajen 5:40 pm. A matuƙar gajiye lilis ta fito daga cikin hall ɗin tana jin matuƙar haushin kanta na kin tahowa da ko gurds ɗaya da batay ba. Jingina da jikin Railer'n dake gaban hall ɗin tay idanunta lumshe. Ko dinner gaza yi tayi haka har wata actress me suna Khadija Yobe ta fito itama ta sameta. "Meesherh lafiyan ki kuwa?" "Hummm kedai Khadijah kyaleni wllh duk a gajiye nake jima nake kamar bazan iya driving ɗin nan bane ma wllh" "Me zai hana idan har babu damuwa na miƙaƙi gidan" ɗan numfashi ta fesar tana furta "No ba ma se kin hawal da kanki ba na kira ayrah amoh nace ta biyo ta nan ta tafi dani" "Kuma kina ganin har loƙaci bazai ƙure miki ba kanta ƙara so?" Khadijah yoben ta tambaye ta ko kafin ma ta bata amsar sega wata arniyar farar Roy *R* Rayce nan na danno Kanta cikin Hotels ɗin. Har gab dasu motar ta ƙaraso kafin a natse aka soma yin kasa da glass na motar, wani kalan zaro fararen idanuwanta woje tay don ganin.............. To ai Shikenan muma semu gimtse 👌 *BY AMMEY LAYLERH* Chat mee view My phone 07085041758 Or 08104493215 Don son magana dani AMMEY LAYLERH chart Mee or call a wannan No ɗin 08104493215 Masu neman *MIKIYA* ma har yanzun ƙofarku a buɗe take har yanzu yana nan akan farashin sa na ₦ 500 ban ƙara ba kamar yacce na ce a baya. https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ༺༻ *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 9&10 ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* *𝙄 𝘿𝙀𝘿𝙄𝘾𝘼𝙏𝙀𝘿 𝙏𝙊 𝙂𝙊𝙑𝙀𝙍𝙉𝙈𝙀𝙉𝙏 𝙂𝙄𝙍𝙇 𝙐𝙉𝙄𝙏𝙔 𝙎𝙀𝘾𝙊𝙉𝘿𝘼𝙍𝙔 𝙎𝘾𝙃𝙊𝙊𝙇 𝙈𝘼𝙇𝘼𝙈 𝙈𝘼𝘿𝙊𝙍𝙄 𝙋𝙈𝘽 001* ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Don ganin Papiey'nta da tai zaune cikin car ɗin, duk da cewan ba abin mamaki bane a wurinta amma na yau ɗin se ya fi koda yaushe bata mamaki. Wata kyakykyawar ajiyar zuciya ta sauƙe me ɗan ƙarfi tare da nufo car ɗin ita da jaruma Khadijah yobe. Itane ta buɗe mata gaban motar kusa da Papiey'nta ta, car key nata ta miƙa mata bayan ta gaida Papiey'n tare da cewa tayo dropping car ɗin zuwa gidan su tun da dama ba sa da woni tazara sosai. Itama Khadijah yobe ƴar masu hannu da maiƙo ce sedai idan dasu Meesherh Jedaans a wuri babu Powerful ɗin kowa da ke aiki a kafff ma faɗin garin Kd da zagayenta. "Papiey yau ka tuna dani kenan?" Shi ne tambayar data fara jefa ma mahaifin nata Duk da tasan cewan tasan kwanan zancen ba zai wuce sake kwantar mata da zuciya da zai yi ba. Left hand nashi da baya driving dashi ya sanya yana kama nata tafin tare da jimƙewa a cikin nashi, cikin tsananin jarumta da ƙarfin hali da kuma son kwantar mata da hankali ya furta. "Baby ita Rayuwa da kike kallo komai yana zuwarma bawa ne ga bisa umarnin abinda ya tsara a cikin tarin Rayuwarka! Ina son kici gaba da shanye komai da zakici gaba da fuskanta daga can gida, amma ba ta yadda komai ɗin ze zama illa wa taki Rayuwar ba. Insha Allah wannan karan komai ya kusa daidaita da yardan me du ka wato Ilahu Sarki ALLAH, Sarkin da babu kamarsa buwayi gagara misali ina..jin... Ina...jin...ina.........jin matuƙar ciwo sosai da ɗaci kan aibantamin MY BABY'n Papiey da ake... Muryan shi ce ta soma rawa da ƙoƙarin karyewa dan haka yay shiru yana sake damqe hannuwan Meesherh ɗin da ɗan ƙarfi yana qasa da idanuwansa da suke neman cikowa da hawaye. Don sosai Maganan Anniey ya buge shi se dai samm baya taɓa damuwan komi akan face nashi kan duk wani mahluki dake cikin estate ɗin nasu koma na ce family. Jin rauni ya wanzu a cikin muryan papiey ne ya sanya ta itama ɗin sake kame hannuwansa cikin nata ta na kasa cewa komai dan tasan kuma ba zai iya ci gaba da maganan ba kenan. Ɗan lumshe fararen idanuwanta tayi A bayyane kuma ta shiga furta adda'ar "Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir³ Ra rabbi inni magalubun fantasir³ la haula wala quwwati illa billahil aliyal azeem³, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³" haka ta shiga ambata tare da sauran adda'o'in da duk suka zo cikin bakinta. Ajiyar zuciya me sanyi papiey ɗin ya sauƙe a natse yanajin hankalinsa na dawowa jikinsa take yaji dacin zuciyarsa ya ragu sbd yadda adda'o'in data karanto ɗin suka ratsa shi sosai tare da zuciyarsa. slowly kuma ta shiga ware idanunta tare da sake sanya hannunta tana jinginar da kanta jikin papiey ɗin nata, daga haka tafiyan nasu ya koma na kurame har suka ƙara so mahaukacin estate ɗin su, Shi ya fara fita jikinsa duk a wani kalan amma yadda yake tafiyan cikin nutsuwa kai kace babu abinda ke damun Rayuwar sa nan. Lugagge bag na papiey kawai ta dauke se handbag nata tana bin bayan mahaifin nata. tana tafiyar ne kuma tana ɗan shedding tears nata zuciyan ta na ƙara yin nauyin abubuwa da yawa da suka kanainaye cikin rayuwarta. A bakin entry na babban parlour'n gidan sukayi kiciɓus da Moh Ameern Saif inda ita ta tura shi kuma ya turo. Kin sakin ƙofan tayi tana kuma ƙin kallonsa, sake murɗa handle door ɗin yay yana jan ƙofar baya ya kuma ja ya tsaye yana ƙare mata kallo tun daga samanta zuwa ƙasa. A ɗan kausashe ta furta "Moh Bani hanya" Ɗan girgiza kai yayi kawai tare da ɗan taunar lisp nashi, Wani shegen killer smile yayi tare da ɗan shafar gashin ƙeyarsa yana me furta "Ohh Ohhh beb wai cikin sauƙi haka?" Yay tambayan cikin ɗan iskan salon jan hankali da kuma rashin mutumci. Chakkk ta tsaya daga ƙoƙarin raɓa gefen Moh Ameern ɗin da take niyar yi. Sakamakon tausasan hannuwan da taji ya raba tsakanin su ta hanyar janye ta daga niyar shigan, ko bata juyo ba ZUCIYAR TA ta riga da ta gama sanar mata ko wa ne ne. Hakan yasa ta jan idanunta ta lumshe su gaba ɗaya. Moh Ameern daya ƙame cike da tsoro da kuma kafe Sheikh juraij ɗin da ido yake kallonsa, Shima idanuwansa da suke a rufen ya buɗe tarrr akan Moh Ameern. Kafin ya saki wani murmushin rainin wayo tare da zamar da ƙasan lips nashi ya furta. "Shi kuma wannan ko a cikin wanne hadisin ne ko sura ohooooo, amma ko ba komi abin ya bada gitta da ƙyau Sheikh babban salo!!!" Haka muryan juraij ɗin ya dake shi Sheikh juraij ɗin. A natse ba tare da garajen komi ba ya rabata da jikinsa yana jefawa Moh Ameern ɗin wani kalan mugun kallo me tattare da cikakken gargaɗi. Ita ne ta fara barin wurin tana jin yadda ƙirjinta ya ɗan ƙare mata tare da mata wani kalan nauyi wanda dama har yanzun bawai ta gama warkewa bane rass. ★A ƙaton parlour'n su wanda yake ɗauke da duk wani nau'in jin daɗin rayuwa ta tarar da duka su Maamah har dama ƙarin babbar yayarsu ummeterh. Da sauri ummeterh ta nufo ta tare da riƙe hannunta fuskanta ɗauke da kyakykyawan Murmushin da ya sake fidda tsananin kamanninsu kasancewar su duka Ukun kamanninsu ɗaya. "Ma sha ALLAH Dear lallai jiki yayi sauƙi tunda har aka iya fita shooting yau" ɗan murmushin yaƙe tayi tana shafa kan baby'n nuwaira da ita ma ta nufo su fuskanta cike da farin cikin ganin Aunty Meesherh ɗin. "Dama ay duk laifin Maamah ne banda haka ai naji sauƙin sosai!" Maama'n da itama ta taso daga idda take zaune ne ta dawo ɗayan gefen Meesherh'n ta zauna ahankali tare da dafata fuskan ta da ɗan murmushi ta furta "Ko yanzu nasan babay'n papah ba ta da cikakken lafiya kawai dai kina danne hakan ne na sani" "To banda abinki Mamman'su Karfa ki manta Meesherh fa ita ma ce ce wata rana haihuwa zatay, tun daga yanxun idan bata koyi ƙarfin hali ba se yaushe kike son ta koya?" Papah ya bata amsa da hakan yana hayewansa sama. Mohan Sameer da shigowansa kenan parlour'n shima yama kansa mazauni akan ɗaya daga cikin expensive chairs da suka ma parlour'n ƙawanya. Yana ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana fuskantansu su duka cike da farin cikin ganinsu su dukansu. Aunty Ummeterh ya fara gaisarwa kana ya sake gaida Maamah duk da kuwa cewan babu jimawa suka Hausa ɗin. Lil juraij dake riƙe da hannun Mohan ɗin ne ya zame cikin wayonsu irin na yara kai tsaye ya nufi inda Meesherh take, duk kuwa da yadda take ƙoƙarin ɗauke fuska daga yaron,cikin muryan gyaranci ba sosai ba ya ce "Otty kin ga ni paap ne ya bani kuma yace karna fatawa kowa ma" yay maganan cikin gwaranci ba sosai yana mata nuna da wani Rolex watch na diamond gold me kyau kalan na yaran nan me shegen tsada da kyau. Ɗan taɓe baki Maamah tayi tana juyar da kanta daga kallon yaron tana maidawa kansu Ummeterh da Mohan da suke wata maganar daban. Miƙewa tayi da niyar tafiya amma lil juraij ya maƙale mata duk yacce ta so data yagar dashi kuwa. Gashi zuwa loƙacin kanta sosai taji yana juya mata gashi wasu masallatan harsun fara ƙiran sallah, dole dashi ta tafi sama yana maƙale da ita. Duk da ido suka bita kafin Mohan ya kalla Maamah tare da furta "Maamah don ALLAH Meesherh ta dakata da aikin nata don yanzu kamata yay ace tana gidan aurenta, Ki duba fa tana age na 24 year's ba ai yaci ace ma tana da nata babay'n itama" tunda ya soma maganar Maamah ta kafe shi da ido ko ƙiftawa batayi seda ta tabbar da ya gama ta furta. "To sannu ubana da wannan ai kamata kawai yay ka bani umarni, ka ga Mohan ka fita ido na In rufe idan har kaima ba zaka iya bin Meesherh da fatan Alkhairi ba to kamata yayi kaima ka janye idanuwanka daga gare ta" ta ƙarasa maganan a fusace tana miƙewa tare da barin parlour'n baki ɗaya, don Maamah irin iyayen nan ne masu shegen S0n ƴaƴansu wanda basu ganin laifinsu ko kaɗan, se dai sammm bata barin ko waye daga cikin yaran nata ya aikata ba daidai ba kuma ita mutum ce da bata iya ƙunbiya ƙunbiya da abu ba ita ɗin karan tsaye ce ƴar kai tsaye me gaɓa². Ko waye ya taka ta to kuwa lallai itama zata taka shi don bata ɗaukar raini kamar yacce itama bata raina kowa se har in mutum shi ne ya fara shiga hurumin ta da wata sigar ta daban, to kuwa lallai anan ne zaka gane ko kai ɗin wane ne. Ajiyar zuciya me tattare da damuwa Ummeterh da Mohan Sameer suka sauƙe kusan loƙaci guda kan kalaman mahaifiyar nasu, duk kuwa da cewan ba yau bane suka saba fuskantar hakan daga gareta. kawai abinda suka sani suke kuma so shi ne suga sun inganta rayuwar Autar nasu, sun gaji da ce ce kucen da ake akan Meesherh ɗin daga media harma da nan cikin gidan nasu kuwa. Tabbas hakan na masu ciwo da kuma matuƙar ƙona musu zuciya. † *Sheikh juraij* Tunda yabar wurin kai tsaye cikin garden yay shigewansa, sanyi da kuma iskan dake kaɗawa a wurin na ratsashi wanda har yake jin kamar fatar jikinsa ce ta bude kai tsaye sanyin yake ratsa masa ko wanne sassa na jikinshi yana daskarar da duk wata magudanar jini ta jikinsa, kamar kullum yana sanye cikin shigar farin yadi me azabar laushi da tsada ɗinkin jumper cables irin na zamanin nan amma kuma ba masu sherp da yawa ba irin na matasan yanzu. Sumar nan tasha gyara na musamman se fidda daɗdan ƙamshin take yi gami da daukar ido. Sajen nan yay luf luf abunsa har wani kalan shine blue yake bayarwa daga nesa. Sanyi haɗi da daɗin iskar ne ya sanya shi kasa zama wuri guda don haka ya shiga zagaye cikin garden ɗin,Hannuwansa goye a bayansa daga can ƙasan zuciyarsa kuwa yake furta. _Subhanallah,wal hamdu lillah, wala'ila ha ilallahu wallahu akhbar³_ Da dai duk sauran adda'o'in da duk suka zo bakinsa, kai tsaye ba zaka taɓa fuskantan tasbihi yake ba sedai ka kalla fatar lips nashi kaɗan tana motsawa. Sammm yama rigada ya manta da abinda ya farun yanzu ko na ce dazu. Ganin loƙacin ƙiran sallah yayi ne ya sanya shi fita, se da ya fara shiga bedroom nashi kana ya fito kai tsaye yana shigewa cikin babban masallacin dake cikin anguwarsu. Shi ne ya ƙira sallar ya kuma ja jami'i cikin wannan daddaɗan sautin nashi da sauraran yanda yake fidda tajweed nashi yake sanya mutane cika masallacin duk kuwa kalan girman da yake da. Dama shi ka'idan sane baya shigowa se bayan sallar Isha'i sosai shi yasa kowa na gidan ke riga shi kammaluwa a dining room ɗin,duk da kasancewar tonight baya zaman dining room ɗin amma kuma hakan jiran shigowarn nashi ya zama kamar al'adan kowa. Iyayensu mata kawai ya gaida kasancewar sun gaisa da iyayensu maza tun a can cikin masjid ɗin.Nan ƙannashi maza da matan suka gaida shi shima,A natsensa ya amsa su yana kallar bakin Meesherh da kuma Moh Ameern Saif da babu su a cikin jadawalin gaisuwar. Directly balcony ɗin da ya saba zama kai tsaye wuce maids ɗin dake aikin shirya dinner ɗin na binsa da tea plask ɗin dake ɗauke da zazzafan tea wanda duk daren duniya shi ne kawai yake sha. Jere mishi tay daga inda yake idanunsa lumshe yana ambatar sunan ALLAH acan ƙasan ranshi. Se da ya tabbatar ta bar wurin kana ya buɗe idon yana jan tea plask gabansa. A natse yake sipping tea ɗin abinsa daga gefe dashi kuma System nashi ce yake aikin sarrafa ta. Yau be daɗe a wurin ba kamar kullum ya tashi ya tafi don yana da abinda zeyi a daren. Ga yawan bugun da zuciyarsa ke mai akai akai yana jin tamkar wani abu mara daɗi na dab da faruwa dashi, Amma sosai yay ƙoƙarin danne hakan se adda'o'in sa da yaci gaba dayi yana adda'an koma miye zai faru dashi to Ubangiji ya kawo shi cikin sauki ya kuma takai ta ma masa ɗin, da haka yanar wurin yana daura alwula tare da fara jero nafil fili wa mahalicci'nsa... ☆ Meesherh kuwa koda ta koma bedroom nata wanka tayo ta shirya kanta cikin singlet ta mata da wando. Army green da farar singlet inda tayi stocking singlet ɗin cikin wandon ta ɗaure da beld. Sai light green ɗin top wadda ta ɓalle duka maɓallanta ta barta a buɗe, Iskar da ake kaɗawa a gurin na diban rigar nata tana kamar zata cire,gaba ɗaya rigar tabar jikinta sai singlet ɗin kawai, tsaye take daga jikin window na bedroom ɗin ta tayi crossing ƙafafunta suna a harɗe. Sosae iskar dake shigowa ta cikin window'n ɗakin ke mata daɗin shaƙa tare da ƙamshin flowering dake ata bayan window nan suke sake bata nishaɗi da jin cikakkiyar nutsuwa, saima taji ta nema ciwon kan data shigo dashi ta ne meshi ta rasa.♡ Shi yasa most especially Idan tana cikin yanayi mara daɗi idan bata son fita balcony takan tsaya a wurin ne ta yaye duka labulayen wurin nan take samun cikakken nishaɗi sosai. ☆ Lumshe fararen idanuwanta tayi tare da faɗawa wata duniyar ta daban, tunani take akan baya idan tace baya tana tunanin Baya cann da dadewa kafin rugujewar komi. A cikin idanunta dake lumshe komai daya faru yake dawo mata daki daki tamkar komai daya faru ne a waɗan can loƙutan haka komai ya Shiga zeroying mind nata. Saurin dawowa hayyacinta tayi sakamon zuciyan ta da taji tana son maido mata da hannun agogo baya, Bayan nan da har gaban abada bata fata da burin dawowarta cikin rayuwarta koda a matsayin mahaifin ne a gareta. Domin mahaifiyarsa ta rigada ta gama ɓata komi tun a wancen loƙacin. A yadda ta tashi ta tashi ne ta buɗe Ido da shi, Shi ne mutum na farko data fara ƙira da pa'apahh........... Akan shi ta fara koyan magana tana yima kowa ƙyuwwa amma banda shi ciki kuwa har da Maamah'nta. Domin matukar Meesherh tana wurin juraij bata yarda da kowa bata kuma zuwa wurin kowa se pa'apahh'nta juraij. Ta kai ta kawo ko bacci zatay se da shi a gefenta, shi ke maga wanka ya wanke mata fufu idan tayi, ya goye ta a gadon bayansa da zani irin yanda uwa kewa ɗan ta, a loƙacin shi yana da shekaru sha bakwai a duniya ita kuma tana da 1 year's a cikin duniyar, Shi ne ya Renata yaci kashinta yaci fitsarinta har zuwa sanda ta shekara biyar a duniya, A kuma daidai loƙacinne abubuwa suka soma Sanja kansu, suka kuma soma samun saɓani wanda shi ne farkon jinin tubalin da har ya kai su ga irin wannan matakin da suke kai a yanzu. ♡ Duk wasu ɗabi'iu kalan nashi take yi masu kyau a da can baya kai takai ta kawo ko cima bata cin abinda baya ci, iyaka abinda pa'apahh'nta yake ci itama shi take ci. Saɓanin farko da suka fara samu a cikin rayuwarsu shi ne tun da ta ɗan ƙara wasu shekaru a cikin shida zuwa tara/goma ya fuskanta ita ɗin mayyar jin kiɗe-kiɗe da waƙe waƙe ce, ga shegen son kallon tsiya a wurin ta kamar me, duk yacce zeyi don ganin ya cire mata hakan abin yaci tu ra. Har yakai ga ya dena shiga lamuranta na wasu ƴan loƙuta haka zata zo ta shige jikinsa tayi ta masa koke koken banza har se ya dawo ya kula ta, Amma hakan bazai hana gobe ta sake kunna casunta ba, haka zata sa ata sawo mata irin kayan indiyawa sune kayan sawanta. Ya tattare ya ƙone amma haka Maama zata sake sawo mata wasu. Kai har takai ta kawo Meesherh ta dena shiga cikin duk wasu lamura na Juraij ta dena tsoronsa ta dena ƙiransa da sunan data bashi na pa'apahh wanda a da yayyenta shi kuma ƙannensa koda mutum ne yay kuskuren ƙiran sunan shi da sunan da ita kaɗai take son take ƙiransa da abinda to kuwa ranan wunin rigima zata wuni tana yi. Amma se gashi sannu a hankali komi nasu na sake samun saɓanin ra'ayi. Se kuma a karo na biyu loƙacin da ya fahimta Film ta karanta, wannan shi ne tushen komi... Shi ne tubalin dayay sanadiyyar rugujewa da watsewar komi don a nan ne Mahaifansu suka samu babban saɓani na farko kowa ya nuna nashi na shi ne. Daga nan komi ya tsaya musu cakkkk kowa ya fita a rayuwar kowa fita wacce suke jin fita ce ta har gaban abada abadan. ☆ ★Wani gauron numfashi ta kawo me kyau lokacin data tuno kaɗan daga cikin wani sashi na rayuwar da suka shuɗe na baya. Tsaye ta miƙa daga zaunen data kai gefen bed nata zuciyarta na wani kalan bugu very slowly ta miƙe. Waƙar (pareshanura ) ta cikin film ɗin Dhruva na jarumi _Ram Charan_ Wacce sukai da _Rakul preet_ ta kunna tana ƙure volume ɗin. Waƙar na sata shiga wani yanayi mai wuyar fassara tare da ɗebe wan can tunanin nata tana ta rawa tana juyi abinta. Ita ta bari on repeat tayi ta kuma dawowa daga nan ta koma waƙar *BAD BOY* ta cikin film ɗin _Saaho_ wacce jarumi _Prabhas_ tare da _Jacqueline fernandez_ kai da kaga yacce take rawan zaka tabbatar da cewan ehhhhhh lallai wannan dole a ƙira ta da TA DABAN ɗin, don kai tsaye kai baka isa cewan ba ita ne ta hau waƙoƙin ba kai tsaye bare kai duba da kalan shigar dake jikinta. Shigowan Maamah'nta shi ne ya katse ta don loƙacin 11:30 na dare harya gota. Kwantar da ita Maamah tayi bayan ta tofeta da adda'an bacci,seda ta ƙara kamar 15 minute kana ta fita a daƙin a tunaninta bacci Meesherh'n ta samu, sedai bata sani ba idonta biyu tana fita ta tashi zaune wani abu na mata suka a cikin zuciyarta. Wanda take yawan jin hakan a da a yanzu ma shike ƙoƙarin gaza control nata. ☆Around 11:30. Kwance take saman ƙayataccen bed ɗin ta da ya gama jin haɗuwar duniya da kuma wani irin gyara na musamman, kai ba kace Mutum ne me Numfashi ke rayuwa a gadon ba. Ɗan juyi ba da yawa ba tayi kaɗan kafin Ahankali ta shiga ware sleeping eyes nata da suka mata wani kalan nauyi kana kuma suka ƙanƙance, dishi dishin da take gani acikin su ne ya sanya ta maidasu ta kulle, sosai taji kanta na wani kalan bala'in sara mata, wanda take da ta cikakken tabbacin rashin baccin da bata samu ba ne a daren jiya ya haifar da hakan. dan haka take jin gaba ɗaya jikinta yayi weak haɗi da kasalan jiki ga kanta da taji ya dawo mata da wani kalan fitinannen ciwo. Hannu tasa tana ɗan dafe kan dake mata ciwo kaman zai rabe biyu,still idanunta masu kama da na mashayiya ko kalan like irin wanda aka janye su ɗin nan, Ahankali ta ɗan motsa jikinta tare da soma ƙoƙarin ɗaga kanta da takejin yayi mata nauyi sosai,jingina bayanta da jikin fuskar gadon tayi tare da sakin ajiyar zuciya tana miƙewa da ƙyar tare da nufar bathroom ɗin dake cikin bedroom nata. Shower kawai ta sakarma kanta tare da tokare hannuwanta duka biyu da jikin toiletry ɗin. haka ruwan shower'n ya shiga dukan jiki da kuma kanta, jin numfashinta na neman sarƙewa ne ya sanya ta janye jikinta da ƙyar. idanunta da suka sha ruwa sosai ta buɗe tana furzar da ruwan cikinsu. Ahankali ta ziro fararen sawayenta daga cikin bathroom ɗin, Sanye da rigan wanka ta fito komi ahankali takeyinsa, Anutsenta tazauna gaban mirror kan stool, blow drying gashin kanta tayi tai parking nashi a ƙasan ƙeyarta, ta ɗauki wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta feffesa ma gashin,kai tsaye ta nufi wurin clothing nata da jibgin kayanta ke ciki, walking slowly take tafiyan fuskar nan babu walwala samm ko kaɗan a saman kyakkyawar fuskar tan,Bakar doguwar rigan Arabian jallabiya ta mata ta sanya. Hannunta riƙe da car key. Bata tarar da Papiey'n taba ya fita wurin aiki amma kafin ya fita seda ya leƙata a loƙacin tana bacci kasancewan se dab da asuba bacci gwanin iya sata yay nasararn sace ta. Maamah na kallonta ta tabbatar ba lafiya ba. Zama tay a kusa da Maamah ɗin tana furta "Maamah kaina kamar ze fashe ciwo ciwo ciwoooo yake min sosai!!!" Saurin tarota jikinta Maamah ɗin tayi jikinta harna rawa wajen furta "Subhanallahi amma kuma shi ne kika kwana a haka? Meesherh har yaushe kike son zanci gaba da miki magana akan lafiyar jikinki?" Se kuma ta ɗan numfasa tare da furta "Shi ke nan tashi muje Hospital don ni ban woni yarda da cewan azo gida a duba ki ba nima duk yau haka haka nake ji ma wllh ba daɗi" tsaye ta miƙe a sanyayen itama tana furta "A ahh Maah kiyi zaman ki bara yanzu zanje na dawo IN SHA ALLAH" "Ke Meesherh anya kuwa duba fa yanayin ki sosai baki da lafiya kidai bari ko driver ne yayi driving naki" Dan murmushi tayi tana ficewa da tsokanar Maah ɗin. A Parking car na gidan suka haɗu da shi kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa yana sake jin bugun zuciyarsa da fitowan nata. Akan Idonsa ta shige car nata tayi reverse tana janta tare da barin gidan ba tare data ko kalla inda yake ba. Cikin nitsuwa shima ya shige tashi motar sanye yake da fararen kayansa kamar kullum. Security's ne suka hanzarin buɗe may mitar ya shige personal person ɗinsa na jan motar suna barin gidan. Dummmmmmm haka yaji zuciyarsa ya buga shan kwanar da zata sada su da inda suka nufa ganin dandazon mutane fiye da dari kewaye a wuri guda. Cikin bugawar zuciya ya bama driver umarnin su tsaya. Cikin kamala da tattako ya nufi wurin cikin cikakken takun ƙarfi na hasali zaka san cewar ehhhh lallai shi ɗin Matashi ne mai ji da lafiya irin ta da namiji, se hakan ya ɓoye yawan shekarun sa don idan ka kallashi befi ka bashi irin 35 year's ɗin nan ba a duniya, nan kuwa yakai 55 year's a duniyar. Kowa dake wurin ya gaza taɓa komai dake wurin se jinin dake malala ta ƙarƙashin motar data kife kirif da duk wanda yake a cikin ta. Wani irin jiri yaji ya ɗauke sa loƙacin da idanunsa sukai masa arba da car ɗin kokkomeɗe a wurin. Chakkk yaji numfashin sa ya tsaya amma yay ƙoƙarin taro shi domin bazai iya taɓa barin nashi numfashin ya fita ba tare daya tallafi Tata rayuwar ba..... 😔😔😔😔😔😔 _Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un 3 meya faru? Meke shirin faruwa damu haka?_ The comments are dropping. 😔 ko dai baya muku daɗi ne? Naga ba comments ba reactions naku. LPlease don't be a silent reader. Comment, vote and share. Thank you. Love you all my mutanena ƴan Amana😘 _Put a smile on my face please. Vote, comment, and share My lovely friend's ana tare_ # Voice of the innocence # Team Sheikh juraij _Team juraij meke meke shirin faruwa daku haka?_ _Laaaaa wayyoooooo wayyo wayyoooooo Meesherh ɗin mu😳😳😳😳_ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 07085041758 *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 11&12 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ ☆༻ Hakan ya sanya cikin wani kalan sassarfar dashi kansa be san yana da itaba ya Isa ga car ɗin. Idanunsa na rarrabe masa be ma san sanda ya zare babban ƴar cikin rigarsa yay jifa da ita ba. Shi kansa ba zai iya cewa ga sanda ya isa ga motar ba abinda kawai ya sani shidai ya ganshi ɗauke da Meesherh ɗin cikin jini kuma bata numfashi, kana duk da kasancewan shi ba me gyaran karaya bane amma yana da tabbacin kusan duka sassan jikin ta a kareraye suke. Ko kallon gabansa bayyi taku kawai yake a farfajiyan filin wurin da mutanen suka zagaye. Idanunsa da farat ɗaya suka sanja ya ɗago yana watsawa wasu daga cikin tsirarin mutanen da suke faɗin kada ya taɓa ta ya sauƙe ta ya bari police suzo. Ko kafin ya isa ga motar'nshi tuni Personal person ɗin sa ya buɗe may motar. Yana ƙoƙarin shiga ya dakatar da shi ba tare daya furta masa ko ƙala ba. Da wani kalan bala'in gudu na fita hayyaci ya fige motar wanda harya tsorata Personal person ɗin sa Al'ameen Hafeez dama wasu daga gurin, tun da ya taka kan motar yake wani irin bata wuta na fita a hankali. Kai tsaye S Power specialist hospital ya nufa, A wani kalan tashin hankali ya taka motar yana fitowa a tsiyace. Cikin tafasar jini yake takunsa Meesherh ɗauke a hannayensa ganan jini se malali yake daga jikinta. Amma hakan sammm be dame shi duk nurse ɗin da yaci karo da ita tayi ƙoƙarin amsanta amma seya kauce ma hakan amma basa daddara haka wasun su ke sake nufo shi kasancewar sa sanannen mutum da gari dama duniyar ke wani irin karrama shi da girmama shi a matsayin sa na babban malami. Shi kansa ba zai ce ga randa ya taɓa shiga tashin hankali kwatankwacin wannan ba. Ko cikakken 30 mints ba'ai ba zaratan matasan Jedaans Mention suka cika hospital din, Wanda Kai tsaye Personal person ɗin juraij ɗin ne ya ƙira thabit Jedaans da kuma Sameer Jedaans. Wanda kusan loƙaci guda Manyan mazajen suka shigo Hospital ɗin. Iyaka yanayin tsaron dake zagaye da Hospital ɗin kaɗai ya tada hankalin su ba kaɗan. Bare kuma azo kan yadda tun kamin ka shiga room ɗin da Meesherh ɗin ke kwance cikin hali na Rai ko mutuwa ƙara da bututun na'urorin dake tashi kaɗai tashin hankali ne. Hakan yayi dai da loƙacin da zuciyar prof Sameer Jedaans Turaki tay wani kyakkyawan bugu na tashin hankalin ganin a yadda yanayin Meesherh yake. ☆Wani irin numfashi Prof Sameer Jedaans ya fidda yana runtse idanuwanshi kamun kuma ya sake buɗe ganinsa Ahankali tar akan Shalelen Rayuwarsa. Billionaire juraij thabit Jedaans kam daina motsi yayi se Idanuwanshi shi ma daya kafe Meesherh ɗin dashi amma baya fahimtar komai dake wakana a cikin duniyar. Mohan Sameer Jedaans da bai daɗe da shigowa bane shima ya tsinta kansa da tsayawa wuri ɗaya chakkk. Don bai tsammaci abin yayi tsanani har haka ba duk kuwa da cewar babu da wanda yayi magana cikin su, Amman yanayinsu da yanda sukai shiru ɗin kawai ya kalla ya gama karantar komi dake shirin faruwa dasu wato rasa Meeshel ɗin su, Rayuwar su. A take shima yaji iskar wajen na canza masa da kalan tashin hankali. A natse ya miƙe yana barin accident & emergency room ɗin gaba ɗaya, daga yanayin yadda yake takunsa da cikakken ƙarfi na hasali zaka san cewar ehhhh lallai shi ɗin matashi ne mai ji da lafiya kuma cikakken namiji ne. Hannunsa ɗaya da yaji an kamane ya sanya shi tsayawa chakkk,juyowa yayi don ganin ko waye ganin Sameer Jedaans ne tsaye daga bayansa ya sanya shi risinar da kansa ƙasa sosai. Cikin muryan rauni sosai ya furta "Ina kuma zakaje bayan ana buƙatan ganin mahaifi'n Meesherh?" Yana furta hakan ya saki hannun Sheikh juraij ɗin tare da komawa cikin room ɗin da ya fito. Wani irin daskarewa a wurin yayi yana rasa mi ma ya kamata yayi. Tamkar wanda ake ja d linzami haka ya koma inda ya fito ɗin kai tsaye ya shige Room ɗin da dactor ke son ganinsa. A natse ya tura babban office ɗin da yake ƙaton gaske tamkar parlour'n wata matar, da hannu Dr Anas Mansur Ma'aji yama Sheikh nunin ya zaune shima ya ɗan fara manyan ta don har ya kusan fin Sheikh ɗin ma a haife. Idanunsa ya janye akan Sheikh ɗin tare da tura may file ɗin dake ɗauke da sakamon gwajin Meesherh wanda Taɓo da lamba da kuma hatsari dake jikin Rubutun ne ya sanya shi kasa iya furta masa komi.sabida nauyi da kuma kunyarsa da yake ji me tsanani, Hannunsa na rawa zuciyarsa na wani kalan mahaukacin bugu ya ɗauka file ɗin. Tun daga layin farko daya Runtse fararen idanuwan sa be yarda ya sake buɗe suba. Su kuwa acan woje duk suma hankalinsu ba'a kwance ba ganin shirun Sheikh ɗin yayi yawa. A ƙalla su Sameer Jedaans sun kusan zaman kusan awa ɗaya zuwa biyu a wurin kuma har zuwa loƙacin basu ga fitowar Sheikh juraij ɗin ba daga cikin office ɗin. Hakan shike sake tada musu da hankali. Cikin tsananin ɗaci da damuwar zuciya ya fito ya fito daga ɗakin yana sauƙe numfashi me tsananin zafi zaune yakai akan kujeran da take kallan su daddy'n kafin ya ɗago idanuwansa kai tsaye yana sauƙe su akan Sameer Jedaans turaki. ★Thabit Jedaans kam kasa zama yayi saboda kansa da yaji ya masa wani kalan dummmm kafin nauyin hakan ya biyo baya ya danne. Shigowan Moh Ameern Saif sanye da riga da wando na bacci long sleeve daidai da miƙewa tsayen da Sameer Jedaans Turaki yayi a mugun kiɗime don shine ƙarshen duban file ɗin. Idanuwansa da sukafi na kowannensu sauyawa ya ɗago ya kalli kowannensu kafin ya dawo da kallonsa kan Sheikh juraij thabit a cikin su yana neman wanda ze bashi kwarin gwiwa akan hakan. Tun kamin ya iya furta komai juraij ɗin yay hanzarin miƙewa yana ficewa zuwa ɗakin da Meesherh ɗin take, tana kwance sanɓal kai baka isa tantance a wanne condition take ba illa kawai abinda zuciyan ka zata iya Hasko maka akanta wato Rigar kowa Mutuwa. A natse thabit Jedaans da ya biyo bayan juraij ɗin ya sauƙe ijiyan zuciyan ɓoyayya ganin inda juraij ɗin ya nufa. Daidai kuma da shigowan Maah tare da ihun kururwan data buga na ganin halin da Meesherh'n take. Ita kanta da da farko bata gane ta don farko kamar gezau idanunta suka hasko mata ita. Tana kallan itane kuwa ta fasa wata uwar kururwan ƙara tare da zubewa ƙasa sumammiya itama, Shigowan Sameer Jedaans Kenan ya fahimci akwai wani abin kenan a kuma kwai abinda ba daidai yake tafiya ba. Ajiyar zuciya da numfashi kawai ya sauƙe tare da kaiwa ƙasa daidai inda Maah take. Kowane ya fice a room ɗin ana barinsu su kaɗai se kuwa majinyaciyar dama bata san inda kanta yake a ciba. Da kyar ya samu ta kawo numfashi tana buɗar idanunta kuwa akan shi ta kife kanta a ƙirjinsa ta shiga riskar kuka na tsantsan tashin hankali. Cikin kulawa da nuna tausayawa sosai da nutsuwa da kuma sanyi a cikin muryan'shi ya furta. "Ba kuka ya kamaci ace kin tsaya zaman yiba Mamansu! Duk da nasan hakan da ciwo amma a wannan condition ɗin da Meesherh'n mu ke ciki adda'an mu da fatan Alkhairinmu kawai take da buƙata" daga haka ya miƙe jikinsa matuƙar sanyaye yana barin ɗakin. Farar takardar data faɗo daga jikinsa tay hanzarin kaiwa hannuwanta tana rarumarta. Bibbiyu idonta suka fara kallon ƙaddararren rubutun da yake tun daga rabbil izzati jalla wa'allah. Hakan ya sanya idanunta fara ganin dishi dishi sedai kasancewanta mutum me taurin Rai ya sanya taƙi aminta ta sake komawa duniyar sumewa a karo na biyu. Hakan ne yay sanadiyyar miƙewanta a razane tana fita kanta na jujjayawa la yi na kuma na ɗibarta tamkar ze yasar a ƙasa. Duk suna inda suke tsaitsaye harda ƙarin wosu ma, Tana zuwa idanun ya rine yayi jajur ta shiga nuna ma papiey takar cikin muryan da ma sammm bata san da ma wanne kalan yare daidai koba daidai ba ta shiga furta. "Papiey'n Meesherh?" Se kuma ta dakata tare da ɗago rinannun idanunta a karo na biyu ta ƙirayi sunan shi kai tsaye. "SAMEER!! Wannan file ɗin na wanene? Gashi dai ina kallon takardar sakkk me irin sunan Meesherl ɗin mu, 😳 amma sedai ita wannan wai naga ta samu lack of memory (wato tabuwar ƙwaƙwalwa), kuma a jikin file ɗin naga kamar ansa Mahaifarta tayi damege ba zata iya haihuwa ko ɗaukan ciki bafa..... ALLAH Sarki baiwar Allah" Ta yi maganar wasu hawayen da bata san da suba na zubo mata. Da baya da baya kowa na dake wurin ya shiga ja, kowa najin zuciyarsa ba zata iya ɗaukan wannan babban lamarin dake tunkaro su ba. Hannuwan Ummeterh na rawa jiki sanyaye idanunta jawur ta sanya tana riƙo hannun mahaifiyarta dake ƙarƙashin sakin file ɗin ƙass. Saurin taro file ɗin tayi tare da haɗawa da hannun Maah ɗin tana jimƙesu wuri guda. "Maahhhhh wannan ba file bane da zaki saki a ƙass iska ta tafi dashi, daganan masu shara su shara su tafi dashi bola.... Wannan ɗin *GABA ƊAYA RAYUWAR Ꮇ𝞔𝞔𝘚Η𝞔Ʀh 𝙎𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝕁𝔼ᴰᴬᴬᴺˢ ce wallafe a cikinta, wanda ƙaddara ta kaita ga zuwa wannan matakin!!!" Se kuma kuka ya sarƙe mata jikinta na rawa dama duk wanda basu san ainihin takamaiman abinda ke faruwa da Rayuwar Meesherh Jedaans ba. Ɗagowa Maah ɗin tayi tare da kallon Ummeterh ɗin wacce ta gyaɗa mata kai alamar ehhhhhh lallai tabbacin maganar kenan. Amma duk da haka bata gasgata taba hakan ne ya sanya ta kwace hannunta a cikin na ummeterh tan tare da saurin riƙo na papiey. Cikin idanuwan sa ta jefa nata kwayar idanun can tsakiyar su, shima kan kawai ya iya ɗaga mata wasu hawayen da tun farko suka ƙi zuwar masa na saƙƙo masa. Hakan ne ya sanya bama tasan sanda ta zare hannunta cikin na papiey'n ba tana juyawa ga ummeterh'tan tare da sauƙe mata wani bahagon marin da ya ratsa zuciyar kowa dake wurin. "Ashe dama ke ma bame hankalin bace Ummeterh? Me yasa sai kece wacce zata fara taryana da wannan mugun labarin. Ko dan kawai kunga ina ƙaunarku da yawa da yawa da yawa..... Amma ai duk da haka ban cancanta irin wannan wasan ba, naji Meesherh tayi accident amma iyaka yau ɗaya ai baici ace duk taji waɗan nan abubuwan ko?" Tai maganan kanta na tangal tangal ganinta kai tsaye na sauƙa akan juraij dake tsaye nesa dasu kaɗan kansa kuma ƙasa babu me iya fuskan tan ainihin yanayin da yake a ciki. Wani murmushi wanda ake ƙira da kafi kuka ciwo ta saki tare da buɗe baki da niyar magana taji tamkar an buga mata abu a tsakar kanta itama hakan ya tilas ta mata haɗiye maganar makut babu shiri tana riƙe kanta ƙam ƙam. Cikin abinda bai wuce kiɓtar idanu ba Sameer Jedaans Turaki yai hanzarin taro matarsa zuwa jikinsa tana karasa somewar jikinsa. Yana saurin nufar emagency room yay da ita. Dagowa Mohan Sameer Jedaans yayi tare da buɗe idanunsa don shima se sannan yasan ko me ke faruwa da Rayuwar Meesherh ɗin tasu. Bayan Mahaifinsa yabi da kallo zuciyarsa shima najin yadda tazo ta toƙare nashi ƙirjin. Maah kuwa daga nan bata sake sanin abinda ya sake faruwa a wurin ba, se buɗe ido tai ta ganta kwance itama a nata gadon majinyatan cikin Hospital ɗin. "Mohan?" Sheikh juraij ya ambata sunan ganin yadda idanunsa ke janyewa shima. "Are You okay?" Ya sake tambayansa se kuma hankalin kowa ya sake tashi ganin uku na ƙoƙarin haɗuwa duk ata dalilin numfashin mutum ɗaya rakkk. "Don ALLAH Yaya Mohan ka daure ka jure kaima karka kwanta wllh³ kana kwanciya nima duk binku zanyi.d0n ALLAH ka tsaya mu rarrashi juna" Ummeterh ta fadi tana rushewa da wani sabon kukan me ƙarfin daya san Sheikh juraij barin wurin a sukwane yana wani kalan fesar da numfashi. Tallafar kanta Mohan Sameer yayi yana ɗan bubbuga bayanta yana me kasa yin magana ko yaya ce. *Maah* Bayan ta farka A loƙacin ne ta sake gaskata ma al'amarin lallai ƙaddara ba ta kaɗan ba ta yawa. In banda haka wllh da tasan abinda zai faru da ɗiyar tan kenan kara ita tayi zamanta gida ita kuma ta fita abinda ya faru da Meesherh ɗin ya faru da ita in yaso. Sadda kanta kawai ƙasa tayi not saying anything saidai ita kaɗai tasan irin halin da zuciyarta take ciki da irin ɗacin dake danƙare acen cikin tsakiyar ƙirjinta. A hankali ta maida idanunta ta lumshe tana haɗiye yawun daya tokare makoshinta, zafi mai mugun raɗaɗi na dada game ilahirin zuciyarta ji take kamar ana gasa mata zuciyar a oven ne kuma a tarfa mata narkakkan dalma. Hakan ya sanya Ahankali ta shiga ɗan bugun gadon da take kwance akai comfortably tana streaming ya Rayuwar Meesherh ɗin ta zata kaya a kuma wanne mataki take zuwa yanzun? Prof Sameer Jedaans da ya zuba mata idanunsa tun farkon farkawan nata ne ya ɗan shiga takawa zuwa a hankali zuwa gareta jiki a matuƙar sanyaya. "Ita ƙaddara da kike kalla Haleematu wajibatunce akan ko wane bawa kuma mumini mai iman!. Domin Allah baya taɓa ɗorama bawansa ƙaddarar da bazai iya ɗauka ba. Kana ita ƙaddara da kike gani rubutacciya ce tun daga rabbis samawati! Me yasa kike ma taki ƙaddarar kuka?. Idan muka sanya ma zuciyarsa mu nasibi da miƙa al'amurra ga Sarkin da shi kaɗai ne buwayi gagara misali sai kiga ya sauƙaƙa mana tarin ƙalubalen dake cikin makauniyar ƙaddarar SAMEESHERH. Ya kuma kawo mana mafita akan lamarin da take ciki,Kuma bawai sun ce lalli kwakwalwanta ya gama samun matsala bane suna hasashene akan hakan shi yasa ma suka bada izinin saka hannu domin sake binciko ainihin abinda ke faruwa da ita , kanta ne ya bugu sosai inda har suke hasashen kwakwalwanta ya haɗu da jini. Marar ta kuma wani abu ne daga cikin karafen motan ya daki wurin tare da hudawa ya faso..... Ki daure ki daure ki daure kiyi haƙuri Hali dubu na manzon Allah" Itakam tama gaza yin maganan se kawai wani kalan shiru da tayi ga idanunta da suka janye farat ɗaya. *All-day diner* Tsaye yake se famar kaiwa da koma yake wani irin zafi na sukarar zuciyarsa, Yasan tunda yaji shiru ba'a haskaka labaran mutuwar Meesherh ba to kuwa tabbas da sauran ranta kenan bata mutu ba. Amma a yadda ya ganta ɗin a dagargaje be ɗauka cewan zata kawo har yanzun bata mutu ba.kasancewan shi ma yana ɗaya daga cikin mutanen da suka je a matsayin ƴan kallo, Shi ya hana kowa ma tunkarar inda take a cewarsa har se hukuma tazo wurin. kuma akan idon sane Sheikh juraij ya ɗauka Meesherh'n jikinta na yalalar da jini sosai. Zuciyan sa yaji ta sake kunbura da ɓacin ran da yake ciki. Sama sama cikin sautin ban haƙuri ya fara jiyo muryan virus yana me bashi haƙuri akan wllh sunyi iyakar yinsu kumama a yadda dai jikinta yake gaskiya be zama lallai Meesherh ɗin ta kai labari. Hakan ne ya sanya shi juyowa a mugun fusace tare da wanke fuskar virus ɗin da wani shegen azababben mari na tashin hankali tare da furta. "Will you shut that your dirty mouth up!, are you stupid Ina magana kana yimin zancen banza da wofi, kodai ka sama taɓin hankaline ban sani ba ko bana da labari Impossible wannan abu bamai yiyuwa bane.... to ni a yanzu babu abinda nake da muradin ji da gani illa naga ana haskaka labaran Mutuwar Meesherh Sameer Jedaans a ko ina a kowacce kafa ta sada zumunta" Yadda ya hayayyaƙo musu ɗin yana masifar kadai zai shaida cewan lalle a mugun fusace yake. "Boss ka yarda damu na rantse da uban daya haifi ubana seda mukayi raga raga da motar yarin yar nan kuma wllh wllh be zama lallai ta kai labari ba, idan kuwa takai to tabbas ba zata warke garau kamar yadda take a da ɗin taba" Kaifi yayi maganan a wannan karon yana wani zazzaro jajayen idanuwansa irin na shegu. "Stop your dirty mouth all over again" daga haka ya fice a room ɗin da suke ciki kai tsaye yana nufar gaban Motarsa dayay Parking nata. Kai tsaye woyansa ya fiddo bayan ya tada motar tare da dokama lambar Moh Ameern Saif ƙira. "Hello Moh Ameern yanzu nake tsintar wani labari wai Diamond Meesherh Jadeens ce ta sama accident right?" Daga ta can ɓangaren me ƙiran kuwa ɗan lumshe ido Moh yayi duk jikinsa sanyaye babu daɗi ya furta. "Wllh Meesherh tana cikin wani yanayi sosai director muhsin se dai a taya mu da adda'a" yana katse ƙiran ya fesar da wani zazzafan numfashin da ya sanya Mohan Sameer Jedaans dubansa yana tambayar ko lafiya? Amsa ya bashi kan abinda Muhsin ɗin ya tambaye shi. Chakkk Sheikh juraij thabit dake woya ya tsaya chakkk na wosu mintinan, kafin yay saurin ɗauke kansa daga garesu jin tambayar da Mohan Sameer ya cillama Moh Ameern ɗin. "Amma daamaki taya maganar da bata fita ba har shi yasan abinda ke faruwa da Meesherh ɗin?" Panping hand nashi yay irin oho ɗin nan.☆ ☆Umarnin kowa ya tafi haka nan Sheikh juraij ya bayar ganin har zuwa loƙacin bata farfaɗo ba wanda kuma dama can basu sanya Rai da hakan ba kodan a yanayin da take a ciki, Domin maƙil suka cika Hospital ɗin da duka ajalinsa babu wanda be zoba har na nesa kuwa masu aure a garuruwa daban daban amma banda Anniey. Bisa dole don sun nan ba'a wasa da umarnin Sheikh ɗin ya sanya wasu tafiya wasu kuwa sunja sun kafe kan dole suna nan kodan shige da ficen su Maah ɗin. Haka aka ɗin ga ɗibansu a lafiyayyun manyan motoci ana tafiya dasu can Jedaans Mention ɗin. A fusace thabit Jedaans daddy'n juraij ya shigo gidan zaune ya tarar da Madam anniey da kayan maƙulashe gabanta cikin shiga ta alfarma. "Yanzu ke A'isha abinda kike aikatawa kina kallon ya kamata kenan? Ke kuwa me wannan yarinya da uwarta suka aikata miki da zafi har haka? Koma dai miye jinya ta kori komi da kike ji da gani Wllh. Domin ita gata can bamuma tunanin zata rayu amma ki kasa sanya ƙafarki asibitin wllh rashin imanin ki kullum sake gaba gaba yake A'isha na rasa wacce kalan zuciya garek. ki sani Allah (S.W.T) da kansa yace karmu tsani kowa a Rayuwa" Zamanta ta gyara sosai tare da fuskantar mijin nata kana ta furta " Amma ai yace mu naisanta kammu ga waɗan da zasuci zarafinmu ko mutuncinmu, kaga kenan bana da laifi akan hakan ko?kuma shi da kansa yace kada ka damu da wanda bai damu dakai ba,kana yace kada ka matsanta son wanda baya sonka!! Shi kenan dan banje asibitin suba kenan nayi laifi? Sanin kanka ne ba ƙaunata Haleema takeyi dan me ni zan kaunaceta duniya ai cewa tai kaso duk wanda ya nuna maka ƙauna ka nesanci duk wanda baya ƙaunar ka amma ka kaucewa nuna wanda baya sonka ƙauna ta hanyar shishshigi dan banyi hakan ba shikenan nayi laifi" tana gama faɗin hakan tayi tafiyarta a wurin. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe shima yana nufar bangarensa yana jin sammm babu daɗi hakan har can kasan zuciyarsa. Daga haka kowa ya kwanta wasu zuciyoyin duk babu daɗi da masu akasin hakan. Tun kan 10 na safe ya cika wasu suka soma tafiya Hospital ɗin. Sheikh juraij kamm seda ya tabbatar da cewan kowa na gidan ya fita kana ya nufi ɓangaren mahaifiyarsa don jiya da dare daddy'n sa ya ƙira shi kan dan ALLAH ya gwada sa'ar sa ko ALLAH zai sa a dace ya lallashi Anniey'nsa ko za'a dace ta yarda yau taje asibitin. Tana zaune cikin ado tamkar jiyan se baza ƙamshi take kai ba kace itane ta haifa bazaraten saurayi kamar Sheikh juraij ɗin ba. Zaman shima yay a gabanta tare da tonƙoshe ƙafafu yana jan ƙafarta tare da fara matsa mata su. Gaisheta yay Cike da kulawa kalan na kowacce uwa da ɗan ta. Bayan ta amsa shi fuskanta babu walwala sosai. Seda yaja numfashi kana ya fuskanceta cikin wannan nutsuwarsan da Ubangiji ya masa ya shiga furta. ☆ "_Duk yadda ka kai da kyautatama mutane ba kowa ne zai soka ba.kamar duk yacce kakai da nuna ƙi wa mutum ba. Domin da abinda wani ya soka shi ne dalilin da wani zai ƙi ka, abu mai muhimmanci a nan shi ne ka kyautata niyar ka akan komai, domin gobe bata da tabbas, sai iya ka abinda ka gani kawai. Don haka ake son ka koyi yin tsari a rayuwar ka da samawa kanka mafita me kyau, sune zasu taimaka wajen samun alkiblarka domin sanin abinda ya kamata kayi a duk minti guda na kwanan duniya. Anniey bawai ina faɗin hakan bane wai don son raina sedan faɗin Annabin ALLAH ne.Nauyi na kara hawa kan ko wanne bawa ne a duk loƙacin da yake ƙara shekaru. Wato babu ranar da za a wayi gari face nauyin da ka sauƙe jiya yafi sauki akan wanda ke tafe a gobe'nka. Wannan nauyin ko ya haɗa da nauyin da ya zamar maka wajibi da na wanda ba dole ba. Kamar na iyaye, ƴan uwa, makwafta, abokai har dama wanda baka sani ba. To amma ana son a kullum mutum ya zamo me yawan sassauci'n zuciya to da yiwuwar ka dinga jin abinda kakeji akan waninka yazo maka da sauki. Don shi Loƙaci baya taɓa jira sedai a jira shi ma'ana duk minti guda na rayuwarka da baka amfane shi ba, to kayi asarar shi kenan har gaban abada. Don haka zaman kullatar wani a cikin zuciyarka ba komi zai haifar maka ba fa ce ɓata shi wannan loƙacin da baya jira!!!. Mafi mahimmancin shi wannan loƙacin da zaka mora to fa shi ne kake ka faɗa wajen riƙon wani. Anniey komai na duniya da kike gani ba mai ɗorewa bane farin ciki ko akasinsa. To mafita anan shi ne ka yadda da ƙaddara ka kuma ringa karɓar kuskuren ka a koda yaushe kuma ka ringa ƙarɓar sauyi ta yadda ko wani zamani zai tafi da kai. Kamar Kyautata alaƙar ka da kowa yana da matuƙar muhimmanci a wannan gaɓar, kuma duk hakan yana nuni ne akan haƙurin zama da mutane. Ka Kuma fahimci cewa ko wanne ɗan Adam zai iya maka rana_" ya ƙara sa maganan kansa a kasa shiru ne ya ratsa wurin na kamar minti biyar. Ijiyan zuciya ya sauƙe loƙacin da yaji Anniey ta zame ƙafafunta tana karkaɗe jikinta tamkar dai yacce tama daddy. Idanunsa shima yaka ya lumshe jim kaɗan kuma ya ɗauki Littafin Ayoodah na tsofin labaran gaskiya dana zahiri dake hannunsa ya buɗe. Don yana san damuwar da yake a ciki yaɗan sassauta. Lumshe manyan fararen idanunsa yay kalmomin da yanzun nan ya karanta su na sake amsa kuwwa a tsakar kansa. _Kamata yay ace dukkan wata alaƙa ta kasance kamar Hannaye da Idanu. Idan hannaye su ka ji ciwo idanu su zub da hawaye idan kuma idanu suka zub da hawaye hannaye su share hawayen_ Abinda wannan kalma ke nufi se yake kallan tamkar akan kansa ne aka gina maganar da mahaifiyarsa, domin kuwa kalmar na nuni ne akan cewa a duk loƙacin da ɗa ya nema kaucewa daga tafarkin da ba na daidai ba uwa itace mutum ta farko daya kamata ta fara dawo da shi wannan dan nata zuwa kan hanyar daidai. Amma shi se gashi shi ne wanda a kullum yake ƙoƙarin ganin ya seto da Rayuwar tashi mahaifiyar kan hanyar dede bawai kuma dan bata da ilimi na addinin bane. Sedan hakan dole yana daga cikin jarrabobin rayuwarta da kuma son zuciya ta biye mata da tsananin rashin rabo. Tsamm ya mike jin zuciyan da yake son ya sama sallama ta na ƙoƙarin sake kumbura. Kai tsaye ya fice a gidan ma baki ɗaya yana me nufar Hospital ɗin. _To fa lallai wannan shi ne ana wata ga wata_ _lalai akwai ƙura kenan a cikin tafiyar wanda kawai da me tsananin Rabo ne Za ai tafiyar tamkar da littafin MIKIYA,don shima se masu rabo ne suka dinga samu_ _lallai aka ce idan da ranka kasha kallo kuma na zaune be ga zama inji masu azancin magana_ _to se ku buyo Ni AMMEY LAYLERH don jin yacce tafiyan zata kaya, kuma kada ku manta nace duk yacce kuka tunani to kuwa tabbas Ni AMMEY LAYLERH nace ba haka tafiyan yake ba🤗_ *BY AMMEY LAYLARH ✍️* *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 13&14 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ A Parking car na gidan ya haɗu da Nainerh tamkar yacce ya bata umarni tana tsaye hannunta riƙe da basket. Buɗe car ɗin yayi da kansa yana shigewa mazaunin driver ita ma buɗe motar tayi ta shige tana zama side da inda yake. Gaidashi tayi ya amsa har ya kunna car ɗin yayi yana ƙoƙarin yin reverse Anniey ta ƙara so wurin ba ta yi masa magana ba ta buɗe kujerar baya ta shige tana ɗauke kanta.Motar yaja da hanzari yana barin harabar gidan don yasan adda'ar sace ta karɓu tunda har Annie ta yarda zaraje Hospital ɗin. A hankali yake jan motar kasancewansa bame garaje a komin saba, Shiru motan ta ɗauka haka har suka isa Hospital ɗin loƙacin kuma wajen Sha ɗaya da wasu mintoci ake magana, Ita ce ta fara fita a motan Nainerh nabin bayan ta shi ne na ƙarshe kuma seya tsaya da wasu cikin dactor's ɗin donjin yadda suka kaya.Anan suke sanar dashi lallai da akwai gagarumar matsala don duk yacce suke tunanin abin to kuwa abin ya wuce saninsu. Har yanzu numfashin ta yana a mataki na 0-6 ne wanda kuma hakan shike tabbar musu da cewan lallai akwai matsala kenan. Kana a daren jiya kwana sukai basu bacci ba akan binciken kwallkwalwarta da suka kwana yi. Don haka dolen dole se an fita da ita woje don mata aiki. So d0n haka ma suka ƙira prof Sameer tun a daren jiyan suka sanar masa da komi yanzu haka ma ya shirya musu fita waje can ƙasar Spain daga can su wuce Madina. Kansa ya ɗago fararen idanuwansa da sukai nauyi kana suka ɗan sanja ya kalla likitan da kallo ɗaya ya ɗauke kansa daga kallonshi yana soma takawa ya zuwa ainihin cikin room ɗin da Meesherh take yana tafiya yana s nazarin maganar fitan dole wanda yake sake ƙoƙarin nazartan ma'anar fitan damuwa na sake wanzuwa akan fuskarshi'n. ba dan kai tsaye wani na iya karantarn yanayi na damuwar akan fuskarshi'n ba,Dan shi samm baya yadda da damuwa akan face nashi dan ba mutum bane me barin damuwan wani abu ya wanzu a face nashi ba. ★ Wannan maganar fitan da yaje kunnan Maah itace ta sake saka zuciyarta damuwa da ɗaukan wani irin nauyi tamkar wata zararra haka take jin kanta gani take yi tamkar komi ba a zahiri yake ba, gani take data rufe ido ta buɗe komi ze dawo mata Normal Kamar ba'ataɓa yinsa ba.a take takejin komi na shirin kwace mata kanta kuma na mata wani irin bala'in sara mata, ita kanta bata san sanda ta fasa kukan da babu mai jinsa ba bayan Allah da take fatan ya sassauta ma Rayuwar Meesherh. Don haka dole take son ƙarfafa jikinta kodan ai tafiyarn da ita don tasan halin Sameer akan taurin rai tsaf zaice bazata jeva, ita kuwa a wannan halin da Meesherh'n take ciki bata ga uban da isa hana mata binsu zuwa ko wacce ƙasa bace. Dake dama already an riga an shirya fitan tun a daren jiya ya sanya babu ɓata loƙacin komi aka fara shirye shiyen tafiyan. Daidai da shigan sa cikin room ɗin daidai ake gangaro gadon da take kwance sanɓal ana tura ta dashi, komai nata a rufe ko fuskanta ba'a iya gani saboda kwata kwata tun jiyan ko motsi babu inda yayi a jikinta.yadda jikinta kuwa ya koma iyaka na jikinta kaɗai sune suke iya gane ta, domin kuwa duk kamanninta sun ɓace ɓat.Wani kalan rumtse idanuwansa yayi da suke sake sauyawa ƙirjinsa na wani irin bugu gaske ganin yau wacce yake ma kallon tamkar duniyarsa ce kwance a hali na mutuwa irin wannan, wanda idan aka ɗauke mahaifiya mahaifi a gareshi to kuwa Meesherh itace abu na farko da yake so fiyeda komai a rayuwarsa da komai daya mallaka, duk kuwa da cewan a yanzun duk babu wannan amma yana da tabbacin har yanzu zuciyarsu da ruhiznsu a tare suke rayuwa. Jin yayi zuciyarsa na neman bugawa dan haka ya sauƙe wani irin numfashi me zafin gaske ya ɗago ahankali ya zubama Gadon da yay masa nisa idanuwansa sai yaji zuciyarsa na sake ƙoƙarin bajewa a wurin.Da hannu yama masu tura gadon alamun su dakata, a gabanta ya tsaya su kuma yana basu umarnin tafiya. zubawa fuskanta da yanzun ya ɗan zama ido yayi yana mata wani irin kallo me cike da tsantsan tausayawa,ƙauna, soyayyar da yake tunanin ta jima da mutuwa babu ita. Tin daga fuskanta yake kallon har zuwa iyaka shahsin daya buɗe ji yayi zuciyarsa na nauyi da kallonta a hakan, ashe dama bugun zuciyar daya taji akan tane kenan? Ashe wannan mummunan ƙaddarrar ce zata faru da ita shi yasa ya gaza runtsawa a daren wancan ranan? Ashe dama ashe dama ashe dama abubuwan da yawa har haka? Ashe ƙaddarorin masu girma ne har haka. Ta ita ya fara tafiya yana gungura gadon yana wuce sauran family's nasu. Duk suka rufa mashi baya suna jin tamkar abu mafi muhimmanci na shirin rabuwa dasu ne na har abada. acikin series car aka jagoranci tafiyan nasu su uku kawai, Shi kansa uban gayyar se kuma Maah data dage dole itama se taje. Thabit Jedaans ne yace ma Sameer Jedaans ɗin kawai a tafi da ita daga nan se itama a duba ta tunda jikin nata babu daɗi itama. Hakan kuwa akai kai tsaye ta Lagos jirgin nasu ze tashi tacan jirginsu ze lula zuwa ƙasar Spain ɗin. Seda gaba ɗaya katafanin ahalinn Jedaans suka ma su Prof Sameer Jedaans rakiya har Lagos. Buɗe idanuwansa yayi ahankali tareda zubawa jirgin su daya fara landing na tashi yana kasa tantance a wanne mataki ya kamaci ace ya dauki hakan. Zurfafawan da dole dole yake son zurfafa Kansa ne ya sanya Wani irin ciwon kai dirar masa irin na loƙaci gudan nan. lumshe idanuwansa da suke masa zafi yay Mohan Sameer ne ya taimaka mashi wurin kaisa cikin car ɗin ♡ Tunda suka baro cikin airport ɗin ya kwantar da kansa jikin kujera yay shiru idanunsa dake da cikar baƙin gashi da gira a sama suna a lumshe suma. Bakinsa ne kawai ke motsawa alamun tasbihi yake a cikin zuciyarsa.         Duk yanayin da yake a ciki Mohan na kula ta cikin mirror'n hakanne ya sake sanyaya zuciyarsa akan du abubuwan da suka ringa faruwa. Haka dai sukaci gaba da tafiya kowa da abinda yake saƙawa a cikin rai da ruhinsa.Hakan ne ya sanya Mohan sake gudun motarsu sosai kai kace Jigawa suka nufa ba Kaduna ba. Tun kan 4pm tayi suka isa gida kai tsaye seda ya fara biyawa ɓangaren anniey kai tsaye loƙacin tana sama wurin Daddy, se kawai yay kwanciyar sa kan lallausar doguwar kujerar parlour'n ya fidda woyarsa yana saka ƙiran Hafeez Al'ameen a woyan. Babu jimawa kuma sega Anniey'n ta fito daga saman sanye cikin shiga ta alfarma kamar koda yaushe. Zaune ya tashi daga kwancen da yake gaidata yay ta amsa shi sama sama, daga haka taja bakinta tayi shiru se can kuma tamkar wacce aka tsikara ta ɗan dubeshi tare da sake tamke fuskanta me kyau sakk kalan tashi ta furta. "A ina maganar mu ta kwana" wani irin janye idanunsa daga kanta yayi yana jin yadda tambayar Anniey'n ta taɓa har cikin tsaƙiyar ƙirjinsa, uwa uba ga ciwon da kansa ke mai. "Anniey pls mubar wancan maganan don ALLAH!!!" Ya kai ƙarshen maganan cikin raunin murya sosai. "Auren Ƴar ƙanwar tawa kake cewa na ƙyale juraij, to wllh³ bara kaji na rantse sau uku to wllh seka auri Samha kuma nan da kwana kusa" fuuuuuu tabar wurin don sosai kanwar nata keta faman mata naci akan batun tare da sake hurata da rura mata wutar tsanar Meesherh da uwarta a cikin zuriyar ta. Sheikh kan tun da ya fita a gidan be sake dawowa ba se araoun 10pm wanka ko zaman dinner yau be yi ba tunda be shigo gidan bama. Ransa a jagule haka ya shigo gidan ko inda sassan mahaifansa suke bai nufa ba yay wucewansa nashi ɓangaren. Tura ƙofar bedroom nashi yayi ahankali sanyin a/cn da kuma ƙamshin turarensa da baya taɓa ɓacewa na sake gauraye room ɗin baki ɗaya, kai tsaye bathroom ya wuce ya shower ya sakarma kansa ya fito jikinsa sanye da bathrobe. Fararen riga da wando na bacci dogaye ya sanya kai tsaye kan lafiyayyan gadonsa ya yay kwanciyansa yana dunƙulewa cikin fari ƙal ɗin duvet cover. Kafin kuma Ahankali ya sanya hannunsa ɗaya ya janyo ɗayan pilonsa ba tareda ya buɗe idanunsa ba ya toshe kunnuwansa dashi saboda yadda kawai yanayin jikinta ke sake damun zuciyarsa, wajen karfe biyu da rabi na dare ake magana amma ya gaza yin bacci don haka ɗaura alwula ya dinga jera nafilfili tare da jera mata adda'o'in samun sassauci wa rayuwarta, ƙarfin ciwon da kansa ke masa na sake hauhawa. ~012 Alongside films shot~ *G 9 building* 4:22pm ✯ Zaune duka manyan director's dama ƙananun producer's suke cikin keɓan taccen wurin da suke gudanar da wasu manyan meeting nasu iyaka su yasu na. To yauma kamar kullum zaunen suke suna tattaunawa akan lamarin daya faru da ɗaya daga cikin manyan jarumansu wato *DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS* Se anan ne ma wasu ke jin abinda ya farun da itan. Tattaunawa sosai sukai director Abdulazeez Dakata daya kasance shi ne shugaban duka masana'antar shirya fina finan Hausa ne ya fara miƙewa daga nan se Muhsin Aliey Yahya shida Moh Ameern Saif. Mohan dake gabana ya juyo Yana kallon inda muhsin ke tsaye daga bayansa, hannuwansa cikin aljihun bakaken coat ɗin dake jikinsa. Iska se baza gashin kansa take har yana rufe may fuska. "Aikin ka na kyau babban abokin harƙalla" Moh Ameern Saif Jedaans ya faɗi da irin jinjinawar nan. Dan gyara tsaiwarsa muhsin yay tare da fuskantar Moh Ameern ɗin se kuma ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya yana furta, "Ai tun ta gama nuna mana ita ɗin ƴar zafin kaice dole mu sauƙe mata shi right?" Shima dariyar Moh ameen saif ya fashe da ita tare da furta. "Mutumina baka da kyau fa ko kayi wanka!!!" Moh Ameern ya faɗi yana sake kashewa da wata mahaukaciyar dariyan."Jirgi ɗaya ne ya kwaso mu nida kai, kaidai kawai ALLAH yakai damo ga harbawa ko be ciba zeyi birgima" chakk kuma Moh ɗin ya tsaye da dariyan da yake tare da furta,"Se dai ban fahimci wannan hausan ba muhsin?" Don yasan halin Muhsin ɗin tsafff na cin amanar ko waye a masana'antar.(Idan na gama da ita banzar zan dake kanka nake nufi) ya furta a cikin ransa a baɗini kuma yana kama kafadar Moh ɗin suka ci gaba da tafiya, "Daɗi na da Moh tsoro tamkar ba namiji ba, ace kana gafjejen namiji kamar haka 👌 baka san wannan karin maganar ta ALLAH yakai damo ga harbawa ko be ciba zeyi birgima ba na jinjina maka" shima ya faɗi yana zaro wayarsa ƙirar apple tare da faɗin "Inji alert" ɗan hararan keyansa Moh Ameern yay a ransa yana ayyana kaima ka kusa barin duniyar ai.transper ya masa na 1:ml. A take yay hanzarin duba alert na kuɗin da suka shigo masa. _Debit: 320XXXX397 Amt: NGN1000,000 Date: 03-MAR-2025 19:28:33 Desc: QS894:DT/101300014444937337/234703638033. Bal: NGN5,5000000 Dial *894*11# to get loan_ wani ɗan banzan kallo ya cillama Moh Ameern ɗin yana me furta. "Kasan kuwa abinda ka tura min Moh? One million kawai fa ka tura wanda iyaka kafin alƙalami ma ni tashin farko 2 billion na bama yaran da suka mana wannan aikin, amma kai da ka tashi seka tura min One kawai" Wani ɗan zame jajayen laɓɓansa Moh yayi tare da furta. "Iyaka haka naga dama kuma iyaka hakan zan bada, ba kuma wai don bana shi ba A ahhh sai don kawai hakan na ga damar baka domin kai kanka kansa koda harafin Bb ba zaka taɓa samu a cikin zuriyar mu har ƙarshen rayuwarmu kuwa" "to kuwa wllh zan tone gaskiyan abinda muka bisne Ashe Moh" "Idan ka fasa ba ɗan halak uwa da ubanka suka haifa ba, wa ya faɗa na ana wa ire irenmu barazana? Stop your dirty mouth all over again" daga haka ya tafiyarsan yana barin Muhsin da saƙar jaki. Khadijah yobe ce ta ƙara so wurin bayan data gama tabbatar da barin Moh daga masana'antar baki ɗaya. Ta na sanye ne cikin Wando palazzo pink colour da Shirt Navy blue , ta yi Rolling wani veil navy blue a kan ta shi ma, se ƴar karamar bag black Itama dake rataye a kafadarta, hannun kuma ɗauke da wayarta. Skin nata ba Farar nan ce kal ba dark skin gareta kalan Wanda ake yayi ɗin nan. Kana tana da manyan idanu ma su ɗaukar hankali wanda cikinsu yake farare ƙal ba laifi. Ta na da shape irin me ƙirar coca cola ɗin nan wato hips da breast din ta cike su ke bamm. Ta ɗan ɗauka loƙaci tana nazartan yanayinsa kafin ta saki ƴar siriryar dariya tana dawowa ta gabansa tare da furta. "Da dukkan alamu wannan Moh Ameern ɗin na son kawo ma aikin mu wargi" Fesar da wata zazzafar iska ta bakinsa yayi yana naɗe hannuwansa saman shoulder nashi tare da furta. "Yobe pls I hate this.. a yanzun kawai hutu nake da buƙata ba ƙarin wata damuwar ba" yana faɗin hakan yau tafiyansa yana barin ta wurin tsaye, Miƙewa itama tayi tana rufa masa baya tana me furta "Muhsin can pls I promise me you'll wllh nayi alƙawarin tayaka kawo karshen waɗan can wawayen JEDAANS ɗin can Moh Ameern da kuma Meesherh cikin sauƙi" tayi maganan tanason cimmasa don ganin kamar ba zai tsaya ɗin ba, baki ta buɗe da nufin yin wota maganar ya riga ta ta hanyar furta. "Kin tabbata?" "Yes I promise I will" ta amsa daidai loƙacin da take cimmasan. "Thank you Yobe Naaaaa'' ya faɗi tare da kyakykyawan murmushi saman fuskansa. Wata Ajiyar zuciya tasaki loƙacin da yake mata magana kan ta shiga cikin car nashi. Cigarettes ya zaro a cikin gidanta seda ya kunna ta da lighter kana ya tada kan motar yana yin reverse tare da ficewa a wurin baki ɗaya. *SPAIN* Flight ɗinsu yana landing motor Ambulance ta Hospital ɗin tazo ta ɗaukesu. *Welcome to Spain and Portugal Specialist hospital analyzing*   Dake magana ake ta kuɗi da kuɗi kai tsaye tun a daren ranan aka wuce da ita special screening room da ita. Dr John Amaan shi ne kan gaba wajen fara aikin. Dr Maheer Osman da ya kasance bahaushen ƙasar Nigeria ne tare suka ringa duk wani shirye-shiryen fara ma Meesherh aiki. Farin glass ɗin dake sanye a idanunsa Dr Masheer Osman ya gyara tare da kallar inda Dr John Amaan yake tsaye yana ƙoƙarin haɗa wata ruwan Injection."No Dr ba buƙatan wannan Injection ɗin! *Keep him under anesthesia"* wani kalan waro idanunsa waje Dr John Amaan yayi cikin kamilallen English ɗin daya gama riƙa a bakinsa ya furta. "Amma His life'd be in danger if we give him an overdose I can'ttake that risk, don haka ba zanyi mata wannan allurarn ba" Wani shegen murmurshi Dr Masheer yayi saying tare da furta "Do as I say?" Kallonsa da jajayen idonsa da suka surku da ɓacin rai Dr John Amaan yayi tare da furta. "Watch and See, it will be really fun and hilarious, Maheer reshe ne zai juye da mujiya kikayi kuma ya koma kan masheƙi,don baka san match ɗin da kake shirin taroma kanka bane. Kasan kuwa ita ɗin wacece? Kasan kuwa ko su waye Asalin JEDAANS!!!?" Tsaye Maheer ya miƙe tareda murtuke fuska ya furta "Enough... Enough is enough! Enough of it Mana kada fa ka nemi raina min wayo anan john kaine ma wato zaka faɗa min ko su waye JEDAANS ɗin?, To ƙarewanta daga tacan familyn JEDAANS ɗin ne aka bani maƙudan kuɗaɗe dan kawai na kawar da rayuwar yarinyar" "Uhmmm kaifa Maheer na gama lura baki ɗaya baka san zuru ba" Ɗan ware idonsa Maheer yayi tare da furta "Lallai ba shakka kuwa da dukkan alamu kaima wani daga cikin su ya maka tayin babban kamu ne duk yacce akai" Shima cikin ɓacin rai da ɗaga murya cike da ihu yace. "But you are the causer Maheer bcoz at ever never naci amanan wani Kona ha'ince woni" Da sauri  Maheer ya ɗan girgiza kai tare da kwantar da murya yana furta "Cool down John please ni nasan hanyar da  zamu bi muyi handling ɗin yarinyan ba tare da barin wata ƙofar da za'a iya zargan woni abu ba kawai mu fara aikin" "Maheer zaka fara  ko? Okay then mu buga wasan aka wanda zai cin ye" ♡ A can masauƙin su Prof Sameer kuwa suna isa aka shige dasu wani lafiyayyan parlour'n jira ko wannensu zama yayi cikin yanayi mara daɗi da yanayi na cunkushewar zuciya. Prof ne ya fara miƙewa tare da dauro alwula ya fara kai kukansa ga mahaliccin sa akan neman sassauci daga garesa, ganin hakan ya sanya ita ma Maah tashi ta fara gabatar da nata duk da bata a mood me daɗi, ko wannensu da abinda zuciyarsa ke saƙa masa. ♡ Around 5:15 Bayan kusan kwanan tsayen da sukai akan Meesherh suka samu numfashin ta ya yakawo sau ɗaya. fitan su da kamar 15 minute wata muguwar ƙara ta karaɗe iyaka room ɗin da Meesherh take. Hakan ya sanya a guje duk wasu manyan dactor's sukai room ɗin a guje. Turus John Amaan ya tsaya yana kallon Maheer dake tsaye kan Meesherh wacce kallo ɗaya zaka mata indai kai cikakken dactor ne kasan cewan tabbas babu numfashi tare da ita. ♡ Kallon me kake nufi John yake ma Maheer Scowl ɗin dake fuskarshi yana ƙara zurfafa, da kuma fuskan mamaki John ɗin ya ɗora da faɗin. "Maheer me ne kai ma patient ɗina?" Da kalan kallon Mamaki da kuma rainin Hankali Maheer ke jifan John tare da kuma da furta "What is with the look? Kana mun kaman baka san da komi ba? Bayan kuma kaine kace mu buga wasan, toni yanzu ne nawan ya soma don haka in kana dawowa da wanda ya riga ya sheƙa numfashi seka dawo mata dashi ba iyaka allurar anesthesia na mata ba harda crecenial risk na mata" Girgiza ma Maheer kai John yake yana ja baya. A cikin zuciyar kuma yana tabbata lallai duk inda ƙarshen mara Imani yake to kuwa ga babansa don a yau ya sake tabbatarma da kansa cewan Maheer samm baya da zuciya a cikin ƙirjinsa, don ko shi da yake Christian wllh ba zai taɓa iyama ko dabba bane wannan allurar. Cikin wannan goggagan turancin irin wanda se a ƙasar turawa kawai zaka iya jinsa,Dr John Amaan ya juye baki da muryarsa mai tafiyar da yannayin halitar zafin sa kai tsaye irin na ƴaƴan arna ya shiga balbale Dr Maheer da ruwan masifa, domin dama Maheer ya daɗi yana musu irin wannan ɓarnar don kawai saboda wasu ƴan kuɗaɗe da yake amsa. Abu ɗaya ne kawai ya Dr John Amaan ke rufa masa asiri shi ne tsoratamar hukuncin ƙasar su da yake. Amma yanzu tunda shi bai san zuru INSHA ALLAH daga kan wannan patiend ɗin ba zai sake ƙoƙarin aikata woni kuskuren ba. Don haka ya bama Dr *Randeep Hooda* da *Dr Jackie Shroff* umarnin su kama Maheer ɗin. A natse cike da cikata aikin ogansu a fannin aiki suka sanya ƙiran Hukumar Asibitin suka zo suka tafi da Maheer ɗin. Amma dake ɗan bala'i ne memakon kaga ladamar hakan a ransa sema baki da ya taɓe tare da kallon Dr John ɗin yana furta masa zasu haɗe. Kallonsa shima yayi tare da sauran ma'aikatansu da yannayi na Expression ɗin fuskarsa ya furta "Ban sanya an kama ka don aikata S0n raina bane maheer, kawai dai na yi mamaki ne a matsayinsa na jinin Musulmai kuma a same ka da aikata babbar ɓarna irin haka wajen taɓarɓare addininku, da kuma rugujewar tarbiyar irin ta ƴayán Hausa. Musulunci'n da ya riga da ya gama gina tarbiyyar ƴaƴansa wanda har sauran wasu yaren ke sha'awan shiga cikin ku, saboda yadda tsarin addinin Musulincin ke burge su, to kuwa tabbas irinkune masu danne niyar masu son musulinta da masu muguwar zuciya irin taku" Ya ajiye maganarsa hankali kwance yana ƙoƙarin ganin ya haɗa wata ruwan allurar da iyaka ita kaɗai idan kaji kuɗinta kan ruguza ƴaƴan hanjinka. Kana ya buɗe wata na'urar computer'n da suka gama rufewa a ɗazun. Kasancewarsa babban likitan da ko a sauran ƙasashe ji ake dashi ya fara sarrafa wasu abubuwa daga cikin ta. tsari irin na wanda ya gama laƙantar abin ya shiga sarrafa ta,seda ya ɗauka wasu lokuta masu ɗan nauyi kana ya rufe yana sharce zubar data gama jiƙa gaban goshinsa wata ƙatotuwar damuwa na rufe shi.    Kusan a tare Prof Sameer da kuma Maah suka miƙe tsaye ƙirjinsu na wani irin bugawa, jin wannan ƙarar data karaɗe ilahirin cikin Hospital ɗin.Allah sarki cike da raunin rai dana ruhi suka kalli juna sai dai duk cikin su babu wanda ya iya furta wani abu. Kai tsaye suka nufa room ɗin zuwansu daidai loƙacin da kunnuwan Maah da papiey suka jiyo masu wannan mummunan tashin hankalin. A take anan Maah ta zube sumammiya cikin sauri nurse's suka dauketa suna shiga wani room na daban da ita. A hankali Maah shiga buɗe idanunta da take kallon komi dishi dishi. Hannunta ɗaya ta ɗaga da ƙyar ta kamo na Prof Sameer wasu zafafan hawaye na silalo mata daga cikin idanunta. Cikin rawar murya ta shiga furta ,"Da gaske mun rasata ko? Da gaske mun rasa Meesherh ɗin mu ko" sai kuma ta taci gaba da hawaye tana ɗan jujjaya kanta.         Ƙasa papiey yay da kansa shima hawayen na ƙoƙarin ciko nasa idanunn. dan baya da tabbacin Meesherh ɗin tana a raye ne ko a mace,Cike da matsanancin tausayin kansu da kansu ya zame hannunsa daga cikin na Maah ɗin ya miƙe. Saurin riƙosa Maah tayi tana girgiza masa kai. "Please Prof ka faɗamin gaskiya wllh ba zan yi komai ba bazanyi kuka ba kaji na rantse ko? Wllh ka faɗa min gaskiya ba kuka zanyi ba"       Kai papiey ɗin ya shiga girgiza mata cike da damuwa ya shiga faɗin. "Basu ce mana komai ba har yanzun Mamamsu. Tun da aka kawo ki nan suka sake komawa ɗakin har yanzu basu fitoba kuma.... Tun kafin ya ida maganar Maah ta miƙe da sauri, Sai dai ta yi saurin komawa zaune tare da dafe kanta da hannuwanta saboda tsananin sara matan da yayi. Saurin riƙota papiey yayi yana me furta "Please cool down Maah"       Kanta ta ke jujjaya masa tamkar kuma wacce aka zaburo ta furta, "Bazan iya ba Papiey'n Meesherh inaso zanje na ganta ne a duk yanayin da take a ciki zan iya jurewa Meesherh ta kawai nake da buƙatar gani a halin yanzu!"        Duk yanda papiey yaso Maah ta haƙura taƙi ta saurarensa sam, dole ya taimaka mata suka fito a ɗakin da aka kwantar da ita tana dafe da kanta,Sai dai dole a ƙofar ɗakin aka tsayar dasu kasancewar doka ce babu me shiga se nan da farfaɗowan patient din. Wani ɗan abu dake a jikin Computer ɗin dake maƙale a bangon ɗakin ɗaya daga cikin dactor's ɗin dake zagaye da wurin ya danns, seda ƙofar ta ɗauka kamar mintuna uku zuwa huɗu haka kana ƙofar wata gilashi ta zuge. A kwance duk suka hangota harma tafi sanda suka kawo ta kyan gani sosai. Ai daga papiey har Maah babu me ƙarfin zuciyar da a cikin su ya iya tare hawaye da suka zuba musu.          Da ƙyar suka shiga ringa ja da baya ƙafarsu na musu nauyi tsoro da fargaban rasa Meesherh ɗin na sake riskarsu. A tare duk Doctors ɗin suka juyo suna kallonsu domin abin a tausamane. Don su gani suke sun ma gama yarda kawai sun ma rasata ne, Dan haka duka su biyun suke tafiya da baya da bayan hawaye naci gaba da gangaro musu a saman fuskokinsu. A hankali Dr John Amaan daya fito ya tsaya Cak da ga yunƙurin fitowa daga cikin room ɗin da yake, Sai kawai ya tsinta kansa da kasa juyowa ya haɗa ido dasu. da ƙyar ya iya ƙaƙaro murmushin yaƙe yana samun kwarin gwiwan nufosu murmushin ɗauke a saman fuskanshi. ✯      "Smiles pls INSHA ALLAH PATIEND namu a koda yaushe zata iya farkawa kuma cikin hankalinta ba tare da wota damuwa, kawai ku taya ta da adda'an ku" Yay maganar yana jin kwarin gwiwan yin hakan kodan ransu ya kwanta. ✯ "Amma John nake kallon kamar ka bar maganan Maheer haka nan" yay maganan Slowly yana duban John ɗin. Kasancewar sa shi mutun ne me tsananin riƙo da gaskiyar sa da kuma amana ya sanya sammm baison yaga woni na aikata ba daidai ba kuma ya iya kyalewa, Yabi Maheer da nasiha akan ya dena wancan banzan halin nashi amma ya ƙi denawa don haka yake jin a wannan karon dole a nunama kurciya baka ko ta shiga taitayinta. Hannunsa ya cira may tare da furta ✯ " Kaga raina a bace yake Randeep. Don't just don't wllh Raina bazaiyi sanyi ba Randeep har se na kalla an hukunta duk wasu masu hannu a cikin wannan case ɗin. Dr John ya faɗi yana jin ze iya Shari'a da kowa akan Ahalin JEDAANS. Mayar da bakinshi yayi ya rufe yana bin John ɗin da kallo don yasan ko waye shi akan riƙo da ɗabi'unsa. Haka harya ɓace ma ganinsa sauƙe numfashi Dr Randeep yayi badon maganar daya faɗi ɗin ba har ransa ba shima. Acan ɓangaren su Maah kuwa da kyar suka kai kansu room ɗin da suke cikin kwarin gwiwa da kuma ƙarfin zuciyan da Papiey'n yafi Maah ya dube ta tare da furta........ To ai shikenan semu bari mu haɗe a page na gaba, don wllh hannuna ya gama nuna da ɗan banzan ciwoooo. *BY AMMEY LAYLARH ✍️*             *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 15&16 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Waɗanda suke buƙatar samun litattafan *AMEEY LAYLERH* za ku iya shiga shafin ta na Telegram don samun su kai tsaye daga wurin ta. Ga link nan ga masu buƙatar shiga 👉https://t.me/ammeylaylerh_novel ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ "Ita Rayuwar duniya da kike kallo tana iya juyama ko wanne baya ajin da yake tamkar yacce Rayuwar mutane ita take iya sauyamana a duk lokacin datay niyar sanjawar, People change, things go wrong. Just remember life goes on Sauyi na rayuwa yakan zo loƙaci ɗaya ne. Wasu loƙuttan kuma sauyin kan zo ma na da yarin ƙalunale n rayuwa ne. No one is born with Positive Passion. This Power is ignited by Inspiration!Komai na da alaƙa da yanda tsarin ƙaddararmu take. Ko yatsun hannuwanmu idan kika duba suna da banbanci da junansu. Saboda me mu zamu tsaya ɓatama kanmu loƙaci wajen ja da kaddararmu data zamo iri ɗayace. Gode wa ALLAH ya kamata muyi yayin samu ko rashi. Don bamu isa ja da hukuncin Ubangiji ba, Amma idan mukai haƙuri Allah na tare damu a ko wanne yanayi adda'an mu SAMEESHERH take da buƙata bawai kuka ba!!. Silalewa a wurin Maah tayi hannuwanta da ƙafafunta na rawa ta zame ƙasa tana son tayi koda numfashi me ƙarfi ne amma ƙirjinta ya toshe ya tsaya mata cak wani abu me nauyin gaske na danne mata ƙirji zuwa maƙoshinta. Paah kuwa Idanuwansa ne suka wani irin ja yana kasa hana hawayen sa zuba sosai shima.A cikin su biyun duk aka rasa me rarrashin wani ko me be wani kwarin gwiwa a cikin su, domin kuka suke sosai suna haɗe kansu a wuri guda suna riskar kuka, cikin kukan Maah take furta "Meesherh dan ALLAH karki tafi ki barmu kece sanyin idaniyanmu ya Rabb ka kawo mana ɗauki Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³" Jajur idanunsa suka se a yanzu ma yake tunowa da gida dan haka kai tsaye woyan sa ya ciro yana ƙiran babban yayansa thabit Jedaans. Sanar musu yay halin da ake ciki suma se hankalinsu duk suma ɗin ya tashi don haka suna yanke woyar a washe garin ranar su daddy dama duka sauran families suka biyu Flight zuwa ƙasar SPAIN ɗin. Se ganinsu kawai su Prof ɗin sukai amma juraij be zo ba kasancewan ma ashe shi baya a ƙasar ne ma. A kuma washe garin ranar wanda yay daidai da kwanan Meesherh biyar kenan a kasar aka shiga da ita aikin daya gama kassara jikin kowa. A kuma daren ranan ne Sheikh juraij thabit Jedaans ya dira a ƙasar spain ɗin wanda babu wanda yayi tsammanin ganinsa. Domin kuwa can Ƙasar Sudan ya tafi, tun a daren aka fara mata aikin har zuwa ƙarfe 5:30 na asuba. Kum Alhamdulillh aiki yayi kyau sosai sai fatan farfaɗowanta lafiya da kuma adda'ar ta tashi lafiya ƙalau IN SHA ALLAH. Haka suka dinga fitowa fuskansu ɗauke da murmushin cimma nasara a aikin nasu.Suna fitowa baki ɗaya duka Family'n JEDAANS sune cike a compound na hospital ɗin tamkar wanda suke a Nigeria. Dr John Amaan ne cikin murmushin jin daɗi da kuma ƙaunar Ahalin JEDAANS ɗin ya miƙa ma Prof Sameer hannu yana furta. "Congratulations Sir anyi aiki cikin nasara da kuma dacewa IN SHA ALLAH zata farka cikin hayyaci da nutsiwanta, kana anyi mata gyaran karayan da tayi se nan da Awa shida zuwa bakwai za'a fiddota, daga nan se adda'an fatan farfaɗowarta gaba ɗaya kuma" hannun Dr John Amaan ɗin sosai papiey ya riƙe ya kasa saki yanaji tamkar Meesherh ɗin ce ma gabansa tsaye haka. Dr John na barin wurin su daddy suka ringa rungume ɗan uwan nasu suna taya kansu murna. Ganin irin farin cikin dake kwance tattare da fuskokin kowannensu ne ya sanya wasu hawaye wanko fuskan prof Sameer ɗin. Daddy ne ya ƙira gida Nigeria yana sanarma Ama da kuma JEDAANS TURAKI nasararn aikin da akay.♡   ✯ Ranta a mugun ɓace bayan ta zagaya ta bayan asibitin ta ɗauki woyanta kai tsaye tana dokama Dr Maheer da yake can a tsare ƙira.Domin kuwa sunyi da shi lallai Meesherh bazata tashi ba se kuma gashi taga saɓanin hakan. dan sun gama yi dashi zaiyi duk abinda zaiyi ya kasheta tun a wajen aikin. Sai dai har wayar ta katse ba'a ɗauka ba. Maida akalar ƙiran kan wata nurse da zasu aikin tare tayi tana jin yadda zuciyar ta ke tafasa, Ba ƙaramin sake haukacewa Mameey tayi ba kuwa ganin itama ba amsa. Hakan ya sanya ta ringa zazzaga bala'i, Ita da tazo ganin yadda iyayen yarinya'n zasu zauce hankalindu ya tashi daga nan suma in yaso su haɗiyi zuciya su mutu, Domin ita macece data rayu da tsantsan kishin Maah da papiey, kasamcewarn sune gaba ɗaya ƙarfin tattalin JEDAANS ɗin. Kana sunfi kowa Power a cikin family dama sauran dangi duka. Wannan shi ne dalilin da ya sanya ta rayuwa da ƙiyayyar Maah da papiey, dama sauran yaran da suka haifa se kuma akalar tsanan nata ya koma kan Meesherh a loƙacin data gama fahimtar Meesherh ce ta kasance zuciyar kowa daga cikin Jedaans ɗin. Hakan ne ma ya sanya ta cusa babban ɗan ta Moh Ameern Saif shiga ƙarƙashin Meesherh ɗin shi kansa ba tare da yasan mi hakan ke nufi ba, domin Mameey irin makiran matan nanne masu shegen iya takunsu da taka tsantsan wajen iya tuggunsu. A zahiri ma idan kai rayuwa a JEDAANS kai tsaye itace mace ta farko da zaka fara sheda da cewar ita kaɗai ce mace ta kirki akan sauran matan. A loƙacin da ta buɗi ido kuwa taga kalan shaƙuwan dake tsakanin juraij da Meesherh zaucewane kawai batayi ba. Tun daga loƙacin ta shiga ta fita seda taga ta raba ƙarfin alaƙar dake tsakanin su kana hankalinta ya kwanta. Itace nan ta sanya a kan garar mata da Meesherh ɗin hakan be yiyuwa ba, shi ne ta sanya aka ɗora mata masifan don kiɗe kiɗe kuma bayan hakan bawai ta barta bane don so tayi ma ta zama tantiriyar karuwa lamba ɗaya,Sai dai kuma shi UBANGIJI alhakimu ne kuma ba azzalumin bawan sa bane, dan hakan data aikata sai hakan beyi tasiri akan Meesherh ɗin ba. Bata so hakan ba amma ya ta iya dole ta haƙura. Kuma itace take sake sanya muguwar tsana me ƙarfi tsakanin Maah da kuma anniey To yanzu kuwa inhar ba ganin gawar Meesherh tayi ba to kuwa lallai zuciyarta ba zata huta mata ba. Tun Meesherh na yarinya Mameey ta gama ruguza rayuwarta wanda badan tsarewar Ubangiji ba da tuni wani zancen ake ba wannan ɗin ba. Don bayan a sanya mata jin tsanar juraij ɗin harda taurin kai na bugawa a jarida yadda zata gallabi kowa Mameey ta sanya a sakawa Meesherh ɗin duk ita kaɗai. Duk loƙacin da taga ƙarfin aikinta ya soma rawa zuwa take ta sanya a sake rura wutar tsanar dake tsakanin juraij da Meesherh, Anniey da Maah, sedai bokan nata sau tari yakan faɗa mata cewar destiny ɗin Meesherh da juraij a sarƙe suke kuma daɗi da ƙari shi duk wani aiki da za'a buga a kansa baya ko tunkarar inda yake balle har yay tasiri akansa, Sedai sunyi amfani da rashin jin maganar ta da kuma daɗe gangarar da Iran da suke shi ne salon aikin kawai dake tasiri a cikin aikin juraij ɗin yana sake jin Meesherh ɗin na ficewa a ransa gaba ɗaya. Da yadda itama baza'a bari ta so shi kamar dai baya koda kuwa na minti guda ne, Kai hatta mahaifinta mameey bata bari ba seda taso sanya mishi tsanar ƴarsa ta cikinsa wanda jinin dake gudana a nashi jinin shi ne ke gudana a cikin nata jinin jiki. Dan haka ƙarfin jinin dake yawo yana zagaya tsakanin su ya hana mata cimma burin ta, se gashi ma a maimakon kowa yaƙi Meesherh ɗin se ya kasance kowa tamkar an buɗe zuciyarsa ne an ɗiga masa mugun ƙaunar Meesherh ɗin ne, dan ta kasance ma tamkar itane zuciyar JEDAANS ɗin baki ɗaya. Sa'ar ta ɗaya shi ne kawai dama can akwai ƴar tsama tsakanin Maah da kuma anniey wanda kuma dama irin dan faccalanci ɗin nan ne haka, se tay amfani da wannan damar ta sake rura musu wutar tsanar junansu haka kawai, sedai aikin ma kusan zamu iya cewa iyaka akan Anniey'n ne ke tasiri kawai don ita Maah bawai tsanar Anniey'n take ji ba abinda kawai bata so shi ne a wulaƙanta ko yaranta. Wanda dama hakan kuma can ɗabi'ar Anniey'n ne kodan ita ta kasance jinin Ama ce oho wacce take ganin ai ita dasu daddy'n duk abu ɗaya ne,tunda mahaifiyarta ita ce ta kasan yaya ga Ama ɗin dan hatta Auren ta da Daddy Ama ɗin ce ta haɗa, kasancewarn daddy'n Juraij ba mutum bane shi me ƙin biyayya ga mahaifansa hakan ne ya sanya shi amsan Auren Anniey'n babu musu. Da shigowarta gidan ita kuma ganin ƴar uwace garesu ya sanya take son seta mulki sauran matan dake gidan tunda ita ɗin jinin suce. Saurin dafe kanta haɗi da dawowa daga duniyar tunanin data yafi mameey'n tayi jin numfashinta na ƙoƙarin fara seizing. Tuno wasu abubuwan da suka riga suka shuɗe datay. Wanda kuma take jin har a yanzun bawai ta saduda bane se dan ma tanajin har a yanzun tana kan bakarta bawai ta gajiya bane. Cikin iya taku da kuma yaudarar data saba tamkar koda yaushe tana komawa cikin room ɗin. {Anan ina son haska mana wata ƴar hanya ce ta cewar. Ba kowa bane ze nuna maka soyayya a fili kuma har a zuciyarsa ta kasance hakan ba, haka kuma ba kowa bane ze nuna tsanarka a fili ya kasance kuma har cikin zuciyarshi haka ɗin abun yake ba. Kuma karka yadda zuciyan ka haka kawai taka rudarka akan haka kawai kaji ka tsani wancan ko kaji seka mulki wannan haka nan. Don haka karka yadda ka taɓa judging mutum by cover ba tare da ka tsaya ka gama karantar ya yanayin sa yake ba. Kuma kun ga anan ALLAH nason nuna mana cewan Meesherh yarinya ce kafin Allah, ba don Allah na tare da ita ba da yanzu ba wannan zancen ake ba} ✯ Alhamdulillah yau kwanaki uku kenan ciff da yima Meesherh aiki. A kuma yau ɗin ne kowa ke sanya rai da farfaɗowanta, dan haka tun sha biyu na daren yau ɗin kowa da kowa zuciyarsa take a cikin zullimi da kuma fargaban abinda ka iya zuwa yaje. Ƙarfe shida na safiyar ranar dayay daidai da Ranar juma'a Meesherh ta farka, Gaba ɗaya dactor's ɗin da suka mata aikin ne zagaye da ita suna fatan ta farka a gaban su ba tare da wota matsala ko damuwa game da aikin nasu ba, Se kuwa paah da Maah da suke cikin room ɗin suma, domin suma suna son ganin farkawan Shalelen nasu akan idonsu. Shi kaɗai ne ya lura da ɗan motsawan da yatsarta ƙwara ɗaya yay.hakan ya sanya shi kafe yatsar cak da kyawawan idanunsa akan yatsun ƙafarta nata dake motsawa, haka har zuwa hannayenta biyu da suma ke motsin. A hankali kuma gashin idanunta suma ke motsawarn kafin a hankali numfashin ta ke sauya salon fita daga na duniyar sumewa zuwa na wadda take a cikin duniyar rayayyu.       Da farko bata iya ganin komai ba se taci gaba da motsa idanun sannu a hankali har ta fara ganin jama'ar dake kewaye da dakin dishi dishi. Idanun ta maida ta rufe tana ɗan matse fuska tare da daƙuneta, jin yadda Gefen ciki da kuma kanta suka mata wani kalan kummmmm, Ahankali ta shiga ƙoƙarin ɗaga hannunta dake ɗaure da canular tana son dafe kai da kuma cikin nata. Se a sannan kowa dake room ɗin ya lura da farkawan nata. Tana kuma sake jarraba bude idon nata wanda kai tsaye ganinta akan Dr John Amaan ya fara sauƙa. tayi kusan sakan sha biyar tana kallonsa kafin ta janye kanta a hankali zuwa ga na kusa da ita.Kai tsaye basu faɗa ko ina ba se cikin Idanuwan Sheikh juraij lumshe idon tayi ta sake buɗesu akan Sheikh juraij ɗin still. Yanda take kallonsa haka shima yake kallonta cike da fargaban ALLAH yasa tana a taytayinta ne, Tafi tsayin 10 minutes tana masa kallon ƙurullah da duk ya ba kowa dake room ɗin tsoro, dan tamkar tana masa kallo ne me kama da rashin sanin nan. Ɗauke kanta dake ɗan jujjaya mata tai tana maidawa ga Maah. Gaban Maah ne yay wani kalan bugawa ganin yacce itama ta ƙureta da idon tamkar ya ce ta ƙure Sheikh juraij da Dr John Amaan. Kan papiey ta sake maida kallonta sema kawai ta meda idanunta tana kullesu don tamkar wacce ake mata kiɗa da ihu haka takeji a cikin kanta.       Gaba ɗaya se duka jikinsu yayi sanyi har likitocin, dan da alama ta manta komai ɗin kenan. Tamkar kuma daga sama a bazata sukaji ta furta.       "Pa'apahh!!!" Shi kansa dukan kansa ƙiranyan sunan shin datay yayi. Janye fararen idanuwan sa yayi yana lumshe su da kyau a kuma nutse yana lafewa jikin cough ɗin dake room ɗin. Duk da maganar tan da ƙyar ta fita amma duk sunjita kowa da kowa duk da cewan a hankali ne tayi maganan murya cen ƙasa. Rikicewa duk sukai da farin cikin jin har ta iya sheda woni a cikin su, su kansu dr's ɗin sunyi murna sosai. "Pa'apahh nan a ina muke?" Ta sake yin maganan muryanta cen kasan dai. Papiey ne ya bata amsa da cewan "$halele ki daina magana haka muna asibiti ne mun kawo ki baki da lfy" Ɗan maida idanunta tayi ta kulle acan ƙasan ranta tana me furta. {Ohhhh GOD!) Ta furta tana ɗan Runtse idanunta da ƙarfi. Ummeterh tace tayi saurin tashi tana taro kan Meesherh ɗin tana haɗawa da nata wasu zafafan hawaye na kwaranya a cikin idanunta. Sauƙar ruwan hawayen da Meesherh taji na ƴar uwan nata shi ya sanya nata idanun cika da kwallar itama da bata san kota miye ba amma kawai abinda ta sani tana jin kanta tamkar wata sabuwar halitta kodai akwai abubuwan da suka sanja a cikin jikinta. Kuka sosai Ummeterh take na tsananin tausayin Meesherh ɗin duk da kasancewan hasashe ne kawai har yanzun dr's keyi akan matsalan mahaifan Meesherh ɗin. Amma duk da haka da tausayi abun ace Tun kamin yarinya tayi Aure ta fara fuskantan manyan ƙalubale irin wannan. Mohan Sameer ne ya matso kusa dasu tare da sanya hannayensa duka biyun yana zagayesu suma yana ɗora kansa tsaƙiyarsu tare da furta. "Please mu daina kuka domin ba'a yima ƙaddara kuka. A duk loƙacin da Allah ya jarrabi wani bawa nashi da wata ƙaddara to ba kuka ya kamaci ace ya tsaya zaman yiba, Alƙibla ze fuskanta yayima ALLAH godiya domin baya taɓa jarrabar wani baya nashi face a ƙarƙashin ita wannan ƙaddara akwai ɓoyayyen wani abu bayan hakan! Kuma ita wannan ƙaddarar tamkar Inuwa ce domin kowa yana da nashi salon ƙaddarar. A kuma koda yaushe tana bibiye da mune matuƙar kar wai kaga ƙaddarar wani ka masa dariya domin kaima bakasan me gobenka zata haifar maka ba. Kalmar ƙaddara! Kalma ce mai ɗauke da rassa biyu walau ƙaddara mai kyau ko Akasinta. Ƙaddara abokiyar tagwaitakar inuwa ce domin bawa ba ya taɓa shallake ma tarin ƙaddarorinsa, Duk iya gudun ka duk iya saurinka baka isa kujema tarin ƙaddarar da ubangijin ya ƙaddaro taka bace, Dan Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwan haka suke, tamkar yadda kowacce Rayuwa take tafe da tarin ƙalubale a cikin. A kullum kwanan duniya sake canjama bawa ajin karatunsa take domin yau ɗin kace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙaddarar jiyanka!. Rayuwa mataki biyu ce Acikin kowacce duniya duk wacce kaddararka ta zabar maka zata kaika ne zuwa makomarta, sabanin shine kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurbatacciya don haka godema ALLAH ya kamata ace munyi Ummeterh, Matsalan da muke tunanin Meesherh tana da bashi ze sanya mu sata gaba muyi ta kuka ba" Ya kare maganan cikin muryan kukan shima, bawai don bayajin ciwo ko daci da raɗaɗin hakan a cikin zuciyarsa ba sedan kawai kwarara ita kanta Meesherh ɗin. ♡ A hankali Meesherh ɗin ta ɗago manyan fararen idanunta tare da kallon cikin tsakiyar idanun yayyen nata. Haka nan take jin wani irin abu a cikin jinin jikinta, Ji takeyi tamkar akwai wani abu da yake tafiya ba daidai ba, Numfashi me sanyi ta fesar tare da ƙara lumshe manyan idanunta tana jin yadda zuciyarta ke sake bugawa tana hautsinawa bugunta na sake gudu bayan hannunta ta sanya a sace tana share ruwan hawayen tare da sakin ɓoyayyar ijiyar zuciya tana son tantance a wanne mataki gudun zuciyarta yake?. Don sanin zata iya ɗauka ko fuskanta ko shanye wacce irin ƙaddara ce wannan dake tunkaro cikin rayuwarta. ♡ "Alhamdulillh!!!, Duk da bansan ko wacce irin ƙaddara bace take kewaye dani a yanzun haka? amma ina fata da kuma burin me sauƙi ce a gareni" Meesherh ta furta wasu siraran hawaye na saƙko mata kafin taci gaba da furta. "Ya Rabbi ya zul'arsheem majeed kaci gaba da jiɓantar dukkan lamari Naaaaa!!!. Kaci gaba da bani kwarin zuciyan dazan ci gaba da amsar duka jarabawowinka gareni Alhamdulillah ALLAH na gode da tarin ni'imominka gareni" ta faɗi tana kife kanta saman tafin hannuwanta ruwan hawayen na taruwa a cikin hannuwanta tana sake wanko fuskanta dasu. Da rarrafe Maah da ƙara sa garesu tana zuwa ta haɗesu duka su ukun ita cikon ta haɗu suka sake fashewa da kukan. Kafin a hankali ta shiga tapping gadon bayansu dukansu na sakin ijiyan zuciya. Kowa dake Room din ne jikinsa yay sanyi masu raunin zuciyan cikinsu har wasu na hawaye. Mammey ce ta mike tsammm dare da kara woya a kunnen nata like irin an ƙira tan nan tana son amsa woyan. Kai tsaye nesa can ta cikin asibitin ta fita.  A loƙacin da Mameey ta sama ganin nurse amalya yousouf kuwa rufeta tayi da faɗa tamkar irin uwar tan nan.          Don hatta gaida tan da nurse ɗin keyi mammey bata bari ta amsa ba ta rufeta da jarabar miyasa sunsan bazasu iya aikinba suka amsa mata cewan zasu iya? Bayan kuma har maƙudan manyan kuɗaɗe ta riga data narka musu.           Nurse amalya dai kallon mammey kawai takeyi sai waige waigen kar wani ya gansu take yi, don kunsan ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yake. Ga kuma tsoron garƙame Dr Maheer da akai hakan ya sanya cikin son ta raba tafiyan sun tare da ɗan ja baya tana me kafe mammey'n da ido tare da soma faɗin. "Ni de yanzu ma na lura da cewan tamkar ƙwalwarki bata aiki da ƙyau Hajiya. Wannan ƙasar da kike gani ba irin africa ɗinku bace da kuka saba aikata ɓarna irin haka da kuma ɗaukar ran mutum ba abakin komai ba!. Sannan mutanen mu ba wawaye bane irinku da suke abu da ka babu wata ƙa'ida ko sanya idon wani akan ka. Duk da aikine mai haɗarin gaske amma a hakan abokin aikina yay ƙoƙarin gwada sa'ar sa sedai sa'ar bata je ko ina ba don a yanzu haka zancen da nake miki Dr Maheer na tsare a hannun hukuma, domin ƙirir ƙiri aka kama shi da ƙoƙarin kisan kai wa patiend namu. Ni ma ALLAH ne ya rufa min bargon asiri dan bansan cewan a ranar bane bama za'a ma ita patiend ɗin namu shi wannan aikin ba, SO dan haka ma ni ina gida bansan wainar da ake toyawaba, Ashe ni hakan ma taimkone a gareni domin kaff duniyar babu wanda besan su waye *peace and respect* wato _JEDAANS Power_ wai tunda kika shigo cikin asibitin nan baki ga yacce yake bala'i bala'in duka families ɗin naku ba?. dan mutane ne masu matuƙar mutunci karamci da kuma mutunci haɗi da ƙarfin iko a kowace duniya ba iyaka a wannan asibitin ba. So Please inason kiyi wani tunani akan kisan yarinyar data kasance jinin JEDAANS"          A rikice Mameey ta furta "Ban gane duka maganganun ki Amalya kuna nufin kunci kuɗaɗena a banza kenan?"        "A wofi ma kuwa Madame Fateemah Usman Sannan kuma shawaran da zan baki shi ne karki yadda kiyi ko gangancin saka wani wannan aikin domin kuwa tsaff asirinki zai tonu. Abu na ƙarshe dazan sanar miki kuma shi ne zagaye patient ɗin take da securitys ta ko ta ina bisa karrama wa Ahalin JEDAANS dama Me JEDAANS ɗin baki ɗaya wato SHEIKH JURAIJ THABIT JADEENS. Dan tunda kowa ya fahimci wannan patient ɗin tana da haɗi da mutum me girma irinsa kowa na cikin Hospital din suke wani kalan sake bata kariya da kuma sake ninka kulawarsu fiye data farko a gareta. Kana ita kanta yarinyan a ƙasashe'n ketaren ma ƙasa kaɗan ce basu san ko wacece DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS ba. Don haka I DON'T CARE YOUR MANNERS na barki lafiya" ta kare maganar da wani kaɗa ma mameey'n yatsun hannunta guda biyu tare da kashe ido mata idonta ɗaya cikin wani shegen murmushi. Tayi taku ɗaya ana biyu chakk ta tsaya sakamakon tsinkayar muryan Mameey'n da tay tana na furta. "Yaro duk inda yake akace yaro ne!A lallai ruɗin Kuruciya tana kararrawa a kanki amalya yousouf ji da kay kuma yana fusganki shekarunki ƙananune shi yasa ba zaki fahimta a irin ramin damisar da kike shirin jefa kanki ba amalya"         Kallon ɗaya ta mata tana ci gaba da tafiyanta domin dai tasan tabbas data buga wasa da ƴar prof Sameer Jedaans Turaki kara ta buga da Fateemah Usman ɗin wacce ta kasance ita mata ce kawai a Jedaans ɗin. Wacce a koda yaushe tana iya tafiya itakuwa fa jinin gidan ake magana, bare uwa uba taga wannan Billionaire's ɗin wato SHEIKH JURAIJ THABIT JADEENS. Alhamdulillh haka jikin Meesherh keta daɗa samun sauƙi zuwa loƙacin kuma tuni duk su Ummeterh sun koma dama kowa da kowa ciki kuwa harda Prof Sameer Jedaans, se ya rage iyaka Maah ce se kuma mohan. Haka sukaci gaba da kulawa da Meesherh harta worwore duk wasu karayas nata na daɗe samun sauki sosai tare da sauran raunikan datay. Sedai muce Alhamdulillh komi yayi daidai, Mameey kuwa ta tafi ne cike da sake cin alwashi akan ganin bayan Meesherh ɗin amma a zahiri kuwa kusan zamu iya cewa ma tafi kowa farin ciki da samun sauƙin Meesherh ɗin.         *FEW MONTHS EARLIER*         Ƙarfe huɗu da mintuna ashirin da biyar na yammacin ranar Alhamis cifcif jirgin daya taso daga ƙasar SPAIN ya yayi dirar MIKIYA a cikin babban airport na Kd. Cikin nutsuwa duk wani passenger dake a cikin jirgin suka fara fitowa sannu a sannu, A mugun natse DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS tare da mahaifiyarta da kuma yayanta da suke zaune daga ɓangaren privete section na cikin jirgin suka miƙe suma suna sanyo kansu suma cikin jerin masu fitowar. Meesherh itace ƙarshen miƙewa a wurin tana sanye ne cikin shigar ɓakar abaya se Rolling Vail pink mai haske da tay wanda yay dai-dai da kalar rigar jikinta datay Rolling din a saman kanta ya matuƙar sake ƙawata adon nata da fidda zagayayyar fuskarta data sake wani kalan fresh.A hankali itama ta miƙe tana ɗan wani ɓata fuska tamkar irin mai jin baccin nan. Yanda ta rufe idanunta da eyeglasses blue kuwa ba ƙaramin ƙara saka fuskarta kwarjini da bayyana ƙyawunta mai sanyi hakan yayi ba, sam fuskarta babu alamar wata Rama bare ma kayi tunanin daga wata jinya me zafi ta tashi.Don a kallo ɗaya zaka ɗauka cewan ma irin daga hutun nan ta dawo. A hankali ta fesar da sassayan numfashi dai-dai loƙacin data fara taka step na forko wanda ta fito da kanta zuwa sararin garin Nigeria tana shakar yancin iskar ƙasar ta me ƴanci. "Yah Salam!" Ta furta Sabida wani irin ni'imtaccen iskar kasar ta mai daɗi mai cike da salama data shaƙa wanda take shiga duk ta inda wata hudar gashi take a jikinta. Wani rin amintaccen numfashin mai cike da yanayin sauƙe ajiyar zuciya ta sauƙe like irin wanda baya tare da natshwar nan yau kuma ya sama cikakkiyar nutsuwar. A hankali taci gaba da taka steps na benen tana saƙƙowa zuwa ƙasa. tana jan ƙaramin tsaki dai-dai tana kare fuskanta da hannuwanta. Haka taci gaba da saƙƙowa ƙasa yanda take taku tsinin fararen takalminta irin me gammo gammon naɗin igiyoyin nan na bada sauti na jan magana,ga sautin madaidaiciyar bag Lugagge nata da take ja, wanda dama Meesherh badai iya ɗaukar magana ba. Wani irin saurin runtse idanunta tayi loƙacin da hasken Camera's suka ɗauke fuskan ta da hasken su. Wanda suka cika cika filin jirgin tun kamin su sauƙa. Nan fa suka sama aikin yi domin kuwa haska dawowan DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS a kafar sada labaran su tamkar haska ɗaukaka da kuma nasarar sune. Wasu shegun haɗadɗun dunkulallun manyan luzury car's ne suka kutso kansu cikin airprt ɗin wanda suka kasance mallakin JEDAANS ne. Wanda ko wacce bayan mota me makon lamba ɗauke suke da sunan *JEDAANS POWER*. Domin kuwa ba'a taɓa ganin motocin da suka kasance mallakin JEDAANS ɗauke da lamba irin ta sauran motoci. Wanda kai tsaye kowa ta sunan ne yake sanin mamallakan motocin ko mallakin su waye?. PROF SAMEER JEDAANS ne da kansa yazo ɗaukar Shalelen nashi cikin rakiyar sauran jama'ar gidan. Da yar sassarfa Meesherh ta tafi loƙacin da tayi ido biyu da Paah ɗin ta tare da hugging na shi. Moh Ameern Saif dake tsaye daga bayan paah ɗin ne ya ɗan yi gyaran murya tare da furta "Ur well come 2 u in my country Sweetie, tunda idanunki iyaka paah suka gane miki" Shi kuwa Prof ɗan bubbuga bayansa Meesherh ɗin yake tare da furta "Well come to the world my shalele hppy for the well coming back again I'm so excited" paah ya faɗi yana sake rungume Shalelen nashi. Sake hugging nashi zaid yayi kana ya isa ga arms daya kasance amini a gareshi shima yayi hugging nashi. Sake hugging papa'n tayi itama kafin su nufi wurin dunkulallun motocin dake jiransun. Ƴan media kuwa tuni suka yaɗa dawowan DIAMOND MEESHERH'n cikin aminci na Ubangiji dan danan ko ina ya ɗauki pisc na dawowan DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS ɗin ya zama latest version. Kan kace me maganar dawowantan yayi spreading tamkar gobara a bushashshen ciyayi. Cikin gida wata jarida ta *ZAMANI TV* Wacce ta wallafa nata salon Rubutun da yasha ban ban dana sauran kai tsaye su kuma ne suka wallafa. ~Ur well come 2 u in my country 𝘿𝙄𝘼𝙈𝙊𝙉 Ꮇ𝞔𝞔𝘚Η𝞔Ʀh 𝙎𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝕁𝔼ᴰᴬᴬᴺˢ~ꨄ *_𝘿𝙄𝘼𝙈𝙊𝙉 Ꮇ𝞔𝞔𝘚Η𝞔Ʀh 𝙎𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 Singh_* ꨄ _ꨄꨄꨄ_ _ꨄShin ko kunsan cewa anyima Diamond Meesherh Jadeens tayin Aiki acikin film ɗin *LOƘACI RIGA*. A Loƙacin da ake tsaka da shirya film ɗin?. Amma taƙi amsa saboda yanayin time na Shooting kuma a sannan tana tsaka da aiki akan wannan FITACCEN Film ɗin nata ne me suna, *TAURARUWA* Da kuma wasu ayyuka nata da take kan shirye shiryen su.ꨄ A Loƙacin ne kuma aka sanya Khadija yobe babbar Aminiya a gareta. Wannan shi ne dalilin da yasa bamu ganta a cikin film na *LOƘACI RIGA* Ba Kuma ta bayyana cewa tayi nadamar hakan ba ganin Irin yadda film ɗin ya samu Amsuwan ga Al'umma ba. A Ƙarshe dai an ɗauki Khadijah yobe wacce ta taka rawa a film ɗin A Maimakon Diamond Meesherh din. ꨄ𝘿𝙄𝘼𝙈𝙊𝙉 Kenan Wannan Aƙidar nata shi yake ƙara birge dubban jama'a a tare da Ita, Babu ruwanta da duba waye Jarumi ko kuma Director wajen Amsan Script kai tsaye tana amsan abinda yayi daidai da Ra'ayinta Ne ❤️😍🥰_ *_ꨄJa Muje 𝘿𝙄𝘼𝙈𝙊𝙉 Ꮇ𝞔𝞔𝘚Η𝞔Ʀh 𝙎𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝕁𝔼ᴰᴬᴬᴺˢ😎 𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ_* Wannan shine kyakykyawan rubutun daya sha ban ban ya kuma ɗauki hazo a duniyar ta gajimare wato media..... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 17&18 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Waɗanda suke buƙatar samun litattafan *AMEEY LAYLERH* za ku iya shiga shafin ta na Telegram don samun su kai tsaye daga wurin ta. Ga link nan ga masu buƙatar shiga 👉https://t.me/ammeylaylerh_novel ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ ♡ Tunda suka ɗauka hanya ta sake nutsewa cikin kujerar motan tare da lafewa luff tana jin yadda bugun zuciyarta ke ta faman kai da kom0. Kai tsaye a gaban tafkeken gidansu daya gama amsa sunansa gida duka car's ɗin suka shiga buga hong da sauri get man yazo ya buɗe musu get ɗin farko na cikin Mention ɗin, kafin su kuma shimgiɗe motocin nasu saman kwaltar dake malale a gaba ɗaya kata fanin gidan. Gaban get na biyu suka kuma danna hong shima get man yazo ya buɗe musu, wanda wasu kattin manyan soldier's ke harabar wurin zagaye da ko ina na gidan wanda inhar ba sani kayi ba tabbas zaka daɗe kuwa kana ƙiran *JEDAANS MENTION* da *SOLDIER'S HOUSE*ne. Domin irin sojojin dake ta kai kawo a duka harabar gudan,A get na uku ma dai hakan take bayan sunyi tafiya mai ɗan nisa kaɗan kafin suka Isa wurin hasalin cikin gidan, direct parking deposit car suka nufa duka motocin suna kutsa kansu har zuwa Parking car na gidan, Anan duka driver's ɗin suka parker manyan luzurie's car nasu. Gaba ɗaya Jama'ar gidan baki ɗayansu suna tsaitsaye ne suna ganin motocin na gama daidaita parking nasu dukan su suka nufo motocin.Kusan Mameey ce gaba ita da Ummeterh kafin sauran matasan gidan su biyo baya daidai kuma loqacin da aka fara bubbuɗe musu motocin, Motar da Meesherh take kai tsaye Ummeterh ta nufa tana buɗe motar sunan ALLAH ɗauke a bakinta, tare da sanya hannuwanta ta kamo na Meesherh ɗin, ɗago kanta tayi don ganin wanda ya taɓa tan. Numfashi ta sauƙe don ganin Yayarta Ummeterh da tay itane ta fito da suna rungume juna kai tsaye. Welcoming nata tayi cikin tsantsan farin cikin ganinta tsaye tar Kan diga diganta. Saurin kawar da kanta daga kallon Aunty Ummeterh tan tayi domin kai tsaye taji abubuwa da yawa nason suyi crosing mind nata marasa daɗin da suka rigada suka faru. Idanunta ta lumshe tare da buɗesu tana fata da burin Ubangiji yaci gaba da bata kwarin gwiwan shanye komi, haka suka dinga rungumarta ɗaya bayan ɗaya. Duk wasu maids dake aiki suma a gidan hana suka zo suma suka gaidata da mata ya jiki. Daga nan suka nufi katafaren parlour'n gidan, Hajiya Ama ce zaune akan kujera 2str hannunta riƙe da tasbaha tana ja. Kai tsaye wajenta Meesherh ta nufa tana zuwa ta rungume tsohuwar. Kanta Hajiya Ama ta shiga shafawa tare da buɗe bakinta cikin kamala ta shiga faɗin. "ALLAH kai ne ALLAH. ALLAH Mun yi tawassali da sunayenka tsarkaka, ALLAH don soyayyar ka da Habibinka, ALLAH don alfarmar annabawa da manzanninka, ALLAH don isar ka da ikon ka, ALLAH don matsayin Alkur'ani Littafin ka, ALLAH ba don halayenmu ba ALLAH kai ne mai amsa adda'ar bayin ka, ALLAH mu masu rauni da yawan zunubai ne, ALLAH kawunanmu a ƙasa hannayenmu a sama mukeyin wannan roƙo. ALLAH kai ne ka faɗa mana inna ma al'usru yusrah ALLAH ka kawo mana sauƙi a bayan wannan tsananin jarabar da muke ciki. ALLAH kafimu sanin daidai Allah karka barmu da son zuciyarmu. Allah Kai ne Allah kai kaɗai ne zaka iya maganin matsalolin mu ka kuma share hawayenmu a wannan loƙacin ma ALLAH ga SAMEESHERH nan ya ALLAH!!!" Se kuma kuka ya sarke Ama dama duka jama'ar dake kewaye da parlour'n. Daddy ne yazo ya janye Meesherh shima yana ɗauke guntuwar kwallar data sauƙo masa. Cikin aro jarumtaka daddy'n ya raɗa mata cewan "Kin ga shalele dena biye Hajiya je yanzu maza kiyo wanka ki fito akwai suprise na musamman dana tanajar miki"     "Thanks you sweet daddy" Ta faɗi tana ɗan rungumesa da sumbatar hannunsa kana nufi hanyar hayewa sama Ahankali Meesherh ta dakata daga tafiyan da tai niyan yi tana tsayawa charkk tare da ɗago fararen idanuwanta dasuke sak da nasa tana waiwayo cikin sanyi hancinta na shaƙo mata kalan ƙamshinsan da tun tana zanin goyonta ta gama haddcesa fiye da komi a cikin rayuwarta. Wanda a wurin sane kaɗai take iya jin wannan unique ƙamshin. Inda take kallon duka mutanen wuri suka juya suna kalla suma nasu hancinan na shaƙo musu ƙamshinsan tamkar dai ita. Daidai loƙacin da yake ƙara sako kansa a natse cikin wani irin kwarjinin daya sanya kowa ɗauke kallonsa daga gareshi cike da girmamawa a gareshi saboda da tsananin kwarjinins, kai hatta hasken fatarsa dake wani irin shining na hutu da kwanciyar hankali tareda daula lafiyayyar fatar ke samu ya saka kyansa yin yawa sosai irin over ɗin nan. A hankali ta janye idanunta a kallansa tana jin dukkanin jikinta na mutuwa wani sanyi yana sauƙa zuciyarta yana mamayewa, tabbas har zuwa wannan loƙacin babu abinda yafi mata daɗin kallo a rayuwarta sama da kallansa pa'apahh'nta tun tana ƙanƙanuwarta. Kyansa da asalin kamannin dake tsakanin su iri ɗaya komai da komai ɗin su. Shima itan yakeb kalla cike da wata irin kewanta dake cinsa da yay kaman cikin kansa zai kunce amma kai tsaye babu wanda ya isa karantar yanayin da yake ciki. Ɗauke kansa daga kallon ta yayi hasken idanuwanta zuwa dogon hancinta na sake nakastar da kwarin gwiwa da jarumtakarshi. A sannu yaji wata nutsuwa na zuwar masa acen ƙasar zuciyan sa yake godewa Allah da dawowantan cikin aminci da kuma karamcinsa. Ahankali ya buɗe bakinsa cikin sauti me nutsuwa da rashin hayaniya ya furta. "Yaya jikinki" loƙacin da yake ƙara sa saƙƙowa cikin parlour'n. Kallansa kowa yayi dukkaninsu duk da ba sauti yayi maganar cikin natsatstsen Sautin sa. Ɗauke kanta Maah tayi tana miƙewa ta nufi upsaid nata. "Mama kun dawo lafiya? Ya kuma sauƙin jikinta" haka ta tsinta muryansa da ameen kawai ta amsa tana ƙara sa barin wurin. Mameey ce ta zo ta kama hannun Meesherh'n dake daskare a wurin tana haurawa sama da ita, don wani mugun baƙin cikene taji ya turniƙeta ganin yau dai a gaban idanunta bayan tsayin shekaru masu ɗan dama sun yi magana, wanda a da ko gaisuwa bata haɗa su. Kai tsaye bata zauna a ƙayatacen falonta da aka sake gyara mata shi ba ya gama tsaruwa ba ta nufi bedroom nata kai tsaye. Ita kuma Mameey'n tana fita zuciyan ta na raya mata kamar tabi Meesherh ɗin kawai ma ta shaƙeta harse ta mutu. Duguwan rigan jikinta kawai ta sutale tana faɗa cikin Lafiyayyan toilet nata da yake da girma sosai komai kuma a tsare, ƙamshi ne me sanyin daɗi da nutsuwa yake tashi a cikinsa. Ruwa masu ɗumi ta haɗawa kanta tana fara yin wankan a natse ƙamshin shower gel ɗinta me kyau da tsada yana sake tashi, haka harta gama wankan ta kashe shower ɗin tare da miƙa hannu ta janyo towel ta ɗauro a jikinta ta fito cikin Lafiyayyar bathtub ɗin ta nufi gaban mirror'n daya kusan cike rabin bangon toilet din ta tsaya cak ta zubawa kanta fararen idanuwanta da suka sanja sakamakon ruwan da suka shiga cikin su. Hannunta na dama ta sanya ahankali ta dora daidai setin Heart nata tana jin zuciyarta dake bugawa akan a hankali. lumshe fararen kyawawan idanuwanta tayi tana sauƙe numfashi ahankali me dumi. ɗaure da fari ƙal ɗin towel me ɗan girma a jikinta ta fito, Anutsen ta ta zauna kan stool na mirror, blow drying gashin kanta fara yi tana kama lallausan gashin kanta tayi parking nashi cikin woni mini riboms, wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta ɗauka ta feffesa ma gashin, sannan cikin sanyin da jikinta yayi ta shafa lotion masu sanya laushi tayi. Ko inda parfumes suke bata kalla ba domin bata a mood me daɗin da zata iya tsayawa zaman sanya wan. Cikin clothes na kayanta ta shige wasu nude riga da wando dogwaye masu ɗan faɗi ta sanya. Wow ko Ni AMMEY LAYLERH saida nace ma sha ALLAH dan there’s no way idan ka kalleta baza kaso ɗauke Idonka akan ta ba, don wani kalam masifar ƙyau tayi cikin kayan tamkar wacce taje hutun honeymoon ta dawo dan yadda farar lafiyayyar fatar ta ke ƙyalli cikin kayan, tabbas Meesherh me ƙyau ce idan nace ƙyau ina nufin ƙarshe maƙura kenan. Kan lafiyayyan gadon ta kwanta tana Sake lafewa a cikin lallausan fari ƙal ɗin duvet cover ɗin ta. Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauƙe loƙacin da taji abinda yay mata tsai a zuciya na komawa ya kwanta luff cikin tsaƙiyar Heart nata. Moh Ameern ne ya shigo har cikin bedroom ɗin kasancewan se yanzu ne shi yake dawowa daga wurin aiki. Zama yayi dap da ita sosai yana ƙoƙarin yaye duvet ɗin da take ciki. Saurin ƙanƙame duvet ɗin tayi se a yanzu nema take sanin da mutum ya shigo mata ɗakin. Cikin matuƙar ɓacin rai da gajiya da ire-iren abubuwan da Moh ɗin ke mata ta furta. "Shin babu zuciyane a ƙirjinka wai Moh Ameern? kokuwa dai kana tunani da zuciyar takane bada ƙwaƙwalwa ba?, Ji ina ƙarshen haɗuwana dakai last worning na ƙarshe dana maka akan kusanta kanka gareni ne! Na ce ma banaso banso bana so to ka ƙyaleni mana" Meesherh ta faɗi fuskanta ɗauke da mugun ɓacin rai. Kafe ta yay da idanunsa da suke kamanceceniya da nata kasancewar kusan duka family's din kwayar idonsu kala ɗaya ne fara ƙal seda na wani yafi na wani haske. Kallonta yake daga sama har ƙasa ta cikin shegen eye glasess ɗin da manne idonsa dashi, ba tare da yama nuna alamar ya fahimta yaren da take maganar da shiba ko nuna yama ji zafin maganar nata se ma furta. "Hope jikinki yayi sauƙi kenan tunda har kika sama bakin tsiya haka"Ya sake faɗa a hankali yana janye idanunsa akanta. Kin sake yanka shi tayi sai kawai ma woyanta data ɗauka tana manna Bluetooth a kunnenta ta doka ƙiran syster Ashley Agar da tayi babbar aminiyar datai acan ƙasar SPAIN. Woyarta ta shiga yi da Syster Ashley Agar tana ma mantawa da woni halitta kusa da ita. Shigowan Maah ɗauke da plate na farfesun tsokar Mana datai ne ya sanya Moh Ameern tafiya.itama ta sanja kayanta daga wanda tazo dashi zuwa plat riga da zani na less mara nauyi ko kaɗan.zama tayi kusanta tana ɗan rungumo Meesherh ɗin zuwa jikinta, woyar ta nuna mata alamar woya take. Sunan kuma Ashley datay ne ya sanya murmushin Maah sake faɗaɗa domin Ashley da families nata ba mutane bane da zasu iya mancewa dasu cikin sauki don sune suka maye musu gurbin Family'n JEDAANS tattare dasu. Amsan woyan Maah tay tana furta. "Ashley doter se kika fara ƙiran bestie Mee taki kenan kafin Maah ɗin ko?" Har yanzu fuskanta ɗauke da murmushin. "Wllh Maah ba haka bane Besty Mee ita ne ta ƙirani Maah tambayar ta kiji ma" dariya kaɗan Maah ɗin tayi nan dai suka ɗan tattauna dangane da yanayin jikin Meesherh din. Daga nan suka yanke woyan ita da kanta Maah ta tayar da Meesherh ɗin zaune toilet ta kaita ta sake ɗaurayo mata bakinta ta sake dawo da ita tana bata naman a baki. A haka papiey ya shigo ya tarar dasu tare da tsokanar Meesherh ɗin da Shalelen kowa. Murmushi kawai tayi ƙaunar mahaifin nata da duka Family'n tan ma na sake zagayeta da jin alfahari dasu a ko ina take kuwa. ♡ Se bayan sallar Isha'i kowa da kowa ya sake fitowa zuwa babban parlour'n gidan. Ƙamshinta kawai da take fitarwa me yawa ne ya janyo hankalin duk wani dake zaune a parlour'n, ciki kuwa harda juraij sedai shi be juya ba tamkar yadda sauran su suka juya. Zama tay cike da gadara dajin kan daya kasance a cikin jinin jikinta yake, wanda ba koda yaushe ƴan jiji dakan ke tashi ba se ko in woni ya taɓo ta koya ɓata mata rai. To kuwa duk yanayin da take a ciki bata jumrewa se asalin jiji da kan na da gadarar sun motsa tabbas. ƙafarta ta ɗauka ta ɗora ɗaya kan daya tana jan idanunta ta lumshe su luff tana jiran taji me mata magana daga cikin tsageru da marasa haƙurin gidan tsaff ta tsefe su don daidai take jin kanta dasu. Wani shegen murmushin Mugunta anniey a zuciyarta ta saki a cikin ranta tana furta.(shegiya dan ubanki yanzu kuwa zanyi maganin ki, dama wannan ranar nake ta dokon jira). Kallon inda juraij ɗin yake zaune tayi cikin son ta ɓakanta ran Meesherh da uwarta ta furta. "JURAIJ amma yau ya kamata ka leƙa gidansu Matarka *SAMHA* ko?" Ta ƙare da alamar tambaya. Duk parlour'n babu wanda be ɗago ya kalleta ba idan ka ɗauke Maah dama ita kanta Meesherh'n, bawai don maganar bata shige ta ba a ahhh wani irin mugun bala'in bugun zuciya hakan ya haifar mata wanda har kusan sarƙewa numfashinta yayi amma ta yi saurin daidai ta kanta, Shi kuwa juraij yi yay tamkar bema jita ba hakan kuma dayay seyama daddy daɗi, don ba ƙaramin kunya Anniey'n ta bashi ba gaban Prof ɗin duk da kasancewan ƙani yake gare shi amma ai ba daɗi hakan. Duba da cewan a yau ne ƴarsa ta dawo daga zaman jinya har wata ƙasa, dan dama already kowa da kowa dake gidan ya rigada ya san da zancen Auren juraij ɗin, wanda uwarsa ce ta jajirjice har seda maganan tayi ƙarfi. Idan ka ɗauke Meesherh da uwar dan hatta Mohan Sameer yasan da maganar auren Sheikh din. Kuma wani tsantsan rashin kunyan ma ga anniey a loƙacin data tunkari mijinta da maganar ya mummunan ɓata mata rai akan kada ta yarda ta sake tararsa da zance me colour da wannan yayi, seta koma gun papiey'n Meesherh.wanda shi ne ya shige gaba akan komai har aka tsaida maganar watanni biyar masu zuwa gashi yau har anci kusan 3 Months kenan, wanda a lissafi bikin befi saura nan da 2 Months ba inma ze zarta to da ƴan sati kai ne. A natse ya miƙe daga zaman cikin tafiyarsan a natse ta zallar nutsuwar da ALLAH (S .W. T) yamar ya fice daga parlour'n baki ɗaya. Wanda har Annie ta so yimay magana amma wani kallo da Daddy ya mata ya sanya ta gimtse bakinta ba shiri. Don ba haka taso wasan ya tsaya haka nan ba. ~012 Alongside films shot~ *G 9 building* 4:22pm ✯ Yau kwanaki biyu 2 Kenan da haskaka wannan zazzafan film ɗin na *LOƘACI RIGA* wanda sammm jama'ar da suka kalla be woni karɓu sosai a wurinsu ba, domin sammm acress ɗin da aka bama role ma Bata ɗau ko hanyar iyawa ba. a kuma daren jiya ne suka saka Film ɗin wa duniya baki ɗaya wanda jaruman ciki suka kasance Khadijah yobe ce tare muhsin Aliey Yahya se kuma wani jarumi London boy tare da Naveen Wanda duniya ta san shi da can baya, se kuma gashi kwasam a daren jiyan sun sake ganinshi a cikin shirin *LOƘACI RIGA* wanda dama can baya da woni farin jini. Wanda tun a daren jiyan suke amsan ƙorafe ƙorafe daga jama'a da dama kan yadda film ɗin be fita ba kana kwata kwata be kuma fidda wota ma'anar komi ba. Wanda dama tun daga tallan Film ɗin wasu suka fara ƙorafin a sanya musu cikakkiyar jarumarsu wato 𝘿𝙄𝘼𝙈𝙊𝙉 Ꮇ𝞔𝞔𝘚Η𝞔Ʀh 𝕁𝔼ᴰᴬᴬᴺˢ, wanda ata sanadiyyar hakan ne komi daya faru da ita ya farun. Don su masana'antar ana su tunanin suna son dena aiki da Meesherh ɗin ne kawai wacce basu san cewan itace haske a cikin masana'antar tasu ba. Kacaniyace me ƙarfin gaske ta sake ɓallewa wanda ya sanya har wasu daga cikin tsirarin mutanen kewaye Industry ɗin. Dalili hakan ya sake jefa zuciyar muhsin Aliey cikin kunci da kuma hasalashi. Har yaji yana son sake kallar film ɗin tare da bi ɗaya bayan ɗaya yana karanta ƙorafi akan hakan. Zaman meeting na gaggawa Abdulazeez Dakata ya haɗa a take a wurin tare da direktocin da suka tace Film ɗin dama screen pleyar's da suka tace labarin. Wani gauran numfashi Abdulazeez Dakata ya sauƙe yana jingina kansa da jikin doguwar kujerar da yake kai yana duban duka kowa da kowa dake wurin tare da furta. "Ni kaina nayi mamaki da ganin hakan domin shi ne shirin Film na farko da aka taɓa aiwatar da irin wannan cakwakiya, Amma kuma idan mutum ya zauna ya nutsu ya kalla da kyau tabbas Film ɗin ya fidda ma'ana me kyau,amma kuma kafin nan ina son ganin marubucin labarin?" Ya faɗi kansa na sake juyewa da labarin sosai. Tsaye muhsin ya miƙe se wani kunbura dacin magani yake ya furta. "Idan na haɗu dashi ba" Hakan ya sanya kowa juyowa yana kallonsa da alamar tambayar suma. Kansa ya jijjaga alamar hakan se kuma ya furta. "Ni babu wani Writer daya min rubuta nida director Kamaal Jigawa muka rubuta muka kuma tsara labarin mu" se kuma kowa ya shiga sakin ijiyar zuciyan jin abinda muhsin ɗin ya faɗi. Daga nan suka sake tattauna wa akan wasu muhimman abubuwan da suka shafa Film ɗin. Amma duk da haka hazon be dena tashi a sama ta sake zama spreading tamkar gobara a bushashshen ciyayi. Wannan al'amari shi ne dalilin daya sanya har Meesherh da har yanzu take killace cikin gida ta magantu. Wani shahararren matashin tictoker Abis fulani shi ne ya fara ganin new video na Diamond Meesherh Jadeens. Ba tare da ko ya buɗe video'n ba kai tsaye yay Repost na video'n da Rubutu kamar haka..... *TURN ON THE LIGHT* Kan kace meee sega View's na mutane fiye da 1.5m sun kalla. Cikin ƙanƙanin loƙaci gaba ɗaya media ta sake hargitsewa da kwarabniyar dawowan Meesherh. Inda video'n nata kai tsaye befi na wasu ƴan minutes ba. Ga abinda video'n ya ɗauka. Tana tsaye jingine da jikin Railer na upstairs nata, kayan dake sanye a jikinta kuwa ba wasu masu hayaniya bane riga da wando ne kawai marasa nauyi se covering face nata da tay da marsk. _Ɗaukakar jaruma ko sunan datay ba shi ne kaɗai abinda masu kallo ya kamata su fara fahimta tattare da ita jarumar ba_ Gyara tsaiwarnta tayi tare da crossing ƙafafunta kana taci gaba da furta. _Abinda masu kallo ya kamata su fara lura tattare da jarumarsu shi ne yaya Qualities nata yake? Amma kafin nan ma d0n ALLAH ina da wata tambaya?_ Ta sake fatar maganar tana ɗauke mask ɗin dake saman kyakykyawar beautiful Innocent face nata tare da harɗe hannuwanta a ƙirji kana tana me ci gaba da fadin. _Wai don ALLAH maimaita jaruma guda ɗaya a kowanne Film baya gundurar masu kallo ne?_ Se kuma ta sauƙe ijiyan zuciya tare da matso da face nata wurin video'n sosai ta furta. _Na faɗi hakan ne bawai don son ɓatama mabiyana rai ba A ahhhhhh se dan magana ake ta gaskiya da gaskiya, wanda kuma wannan gaskiya take fitowa tun daga ƙarƙashin ƙasan zuciyata. Kamata yay ace sunan jaruma ko kuma ɗaukakarta ba sune abubuwan da ya kamata kuna crossing failure na wasu jaruman ba, shi kansa yawan maimaita Film da jaruman da kuka fiye yawan gani koda yaushe a kowanne Film kan sanya masu kallo suji sun fara gmgundira dashi. Anan abinda nake son faɗi shi ne a duk loƙacin dakika taka wata *NASARA TA RAYUWA* To ƴan bayanki ya kamata jarumar ta fara waige, dalili na anan shi ne se ta ɗan bama sabbin fuskoki ƙofa suma su sanu sosai kafin kuma loƙaci ɗaya tay dirar MIKIYA ta dawo_ _Tamkar dai yadda cikakkun jaruman India keyi irin su PRABHAS sharukhan Rama Charan like haka, idan suka tashi dawowa kuma_ Se kuma ta ɗan buga ƙafa tare da furta _"WOhoho!!!, To anan ne ita kanta wannan jarumar zata gane me ake nufi da hasalin soyayyar Fan's, duk ma mu bar wannan maganar kai tsaye mu tafi kan maganar mu, Ni kaina na kalla Film na *LOƘACI RIGA* kuma tabbas Film ɗin ya fita sedai abu ɗaya ne kawai mutane ke da buƙata shi ne DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS. POWER Kenan to IN SHA ALLAH Meesherh Jedaans tayi alƙawarin sake wanko muku Film na LOƘACI RIGA duk da cewan ata sanadiyyar Film ɗin komai daya faru ya riga da ya faru kuma akwai abubbuwan ban mamakin da zato bai zace su ba Nagode ƙwarai. don haka akwai 🔥 Fire🔥🔥🔥🔥🔥🔥 a gaba amma a cikin Film nawa me suna *_☆TAURARUWAꨄ_* _Don haka Aaaaaaahhh gimtse👌😜_ Ta ƙara sa faɗin hakan da kashe Ido ɗaya daga nan kuma vedio'n ya ƙare. Wai WOhoho zokaga yadda ake hasalin tada hazo a yanar gizo gizo, daganan aka saki komai waɗan nan kalamai na Meesherh shi ne ya gigita Media ɗin ma baki ɗaya ba Tiktok kawai ba. Kai har matan aure a gidajensu zancen kawai suke wasu na faɗin abinda jarumar tayi daidai ne wasu na faɗin tsabar iyayi ne kawai don tasan ta gama daukaka ne. Kuma dama kunsan dole a sama hakan tsakanin mutane. Don duk inda mutane ya kai ga iya taku da taka tsantsan ɗin sa be isa yace ze haskaka duniya shi kadai ba, abinda kai wasu sukani sonka to kuwa wasu wannan abinda dakay wasun suka soka su kuma a shi ne zasu ƙiƙa haka taken wannan maganar yake. Don haka wata se mutane suka fara Repost na wasu paya payan video nata na baya masu shige da kalan waɗan nan kalaman. Kamar irin su inda take furta. _Kada ka yarda da kowa ka yarda da kanka kai kaɗai ɗin ka inda ka yarda da kanka to koma waye kada ka yarda dashi illah ka zama naka kai kaɗai.Yare ɗaya ne a duniyar nan wanda kowa yafi fahimtarsa, shi ne kada ka yarda da kowa wannan shi ne_ To fa kunsan dama haka media take da zarar an ɗan samu wani sabon update se a saki wanda ake kanyi a kama sabo, haka dai aka ci gaba da kaftawa wasu na goyan bayan maganganun Meesherh wasu kuma na kushewa. A loƙacin da wasu daga cikin jaruman fina finan suka kalla wasu da yawa ta birgesu tamkar yadda wasu da yawa bata birgesu ba ,don su gani kawai suke danta fito daga babban gida ne kuma dama duk wata fira da za'a i da ita idan aka tambaye ta menene dalilin daya sanya ta shigo kannywood amsar ɗaya ce shine *RA'AYI* Bawai don ta ɗauka hakan a matsayin sana'ar ta bane kawai Ra'ayin da ta ce to kuwa ra'ayin ne, don sun san in suna take nema to kuwa iyaka ƙarfin dukiyarsu ya gama zage ko ina bare kuma JEDAANS FAMILY. Wanda kowa babban fata da kuma burin sa shi ne JEDAANS FAMILY. *BY AMMEY LAYLARH ✍️* *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 19&20 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Waɗanda suke buƙatar samun litattafan *AMEEY LAYLERH* za ku iya shiga shafin ta na Telegram don samun su kai tsaye daga wurin ta. Ga link nan ga masu buƙatar shiga 👉https://t.me/ammeylaylerh_novel ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ ꨄ_The third season of *Winter Wonderland # JEDAANS FAMILY* has kicked off, offering a unique winter experience that combines entertainment and fun activities for the entire family_ ꨄ Gaba ɗaya ɗakin tsit yake daga sautin karatun Sheikh juraij thabit ɗin daya sanya bakajin komai a room ɗin sai na sanyin AC kawai kakeji. Sai wani irin ƙamshin Air freshsheners da turarukaan wuta masu daɗi, Ɗakine me girman gaske dake ɗauke da setin royel furnitures masu tsananin kyawun gaske White colour sai ɗan adon milk da aka musu. Daga ta nan bakin bed ɗin wani haɗaɗɗen Islamabab carpet ne me tsananin laushi da aka shimfiɗa wanda yakai har tsaƙiyar room ɗin, daga gefen window's kuma wata keɓantacciyar Luxury sofa ce Ajiye da ƙaramin fridge. daga ta gefen mirror kuma wani babban table ne da aka jera littattafan Addini shimili guda gasunan, daga ta gefen gabas akayi wani zagayyen wuri na musamman wanda ke shimefiɗe da wata kalan lallausan praymed me taushin tsiya, sai wasu zagayayyun EGYPTANI'AN decoration's irin masu haskaka room ɗin na, sammm ɗakin baya da woni tarkace haka yake simple gwanin birgewa wanda mutum zaiyi normal real life nashi cike da bada cikakkar nutsuwa. Agogon ɗakin ne ya buga ƙarfe 10:31 daidai da Mirza handle na ƙofar bathroom ɗin da Sheikh juraij thabit Jedaans da yayi, Anutse ya fara ɗora santaleliyar ƙafarsa me cike da gargasan gashi baƙi siɗik akan ƙaramin carpet ɗin dake shimfiɗe bakin ƙofar bathroom ɗin. kafin ya Ida fitowa gaba ɗayansa a nutse ya fara taka sawayensa cike da nutsuwa take ɗakin ya gauraye da ƙamshin shower jurl ɗin da yayi wanka dashi. Ahankali ya nufi gaban dressing mirror yana sanye da rigan wanka navy blue wanda ya tsaya iyaka singallinsa sai wani milk saman wuyansa yana goge ruwan jikinsa dake yarara saman fatarsa da kai tsaye yake nuna cewa shi ɗin tsayayyen namiji ne me jini a jika sai faman walainiya fatar nan take tamkar woni beby sabuwan haihuwa. Wannan fuskar da cikar kamala mai nuna barazana wa maƙiyinsa a tinƙe ɗifff tun a daren jiya wanda dole ne ma mutum ya yarda yaci wannan suna na jarumi kuma ingarman namiji me ji dantashen samartaka wanda hasalin jin daɗin rayuwa ya gama ginashi, .wanda kai tsaye a cikin bathrobe ɗin se ya ɓoye asalin n manyantan da ya fara yi kaɗan. wanda kuma na tabbatar da zallar hutu da kuma jin daɗine suke sake ɓoye manyan tan nashi. Cikin wani irin tafiyan ɗaukan hankali ya fara tafiya da zaratan sawayensa, Komai yake yi cikin tacin zuciya yake tsafff ya gama shirya kansa cikin wasu sky blue cashmere se hular daya mirza saman kanshi inda ta haska farar lafayayyar cutie face nashi ta ƙara fidda ainihin taswirar kyawu da kuma zatinsa. A natse ya isa gaban Iphone nashi inda sautin karatun ke fita take karatun kuma ya tsaya sakamakon shigowan ƙira ɗan lumshe Ido yayi ya kuma sake buɗewa ya kalli agogon dake manne jikin bango, red lips nashi na motsawa kadan alaman tasbihi yake yana ɗaukan phone in dama yasan ƙiran bazai wuce Anniey'n shi bace, ba tare daya ɗauka wayan ba ya nufi hanyan fita, kamar yadda yana yinsa na rashin fara'a yake haka yafito daga cikin ɗakin hannunsa riƙe da key nashi na car. A nutsensa ciki wannan yanayin na kamewa da yan muskilanci da ya motsa yau yake saƙƙowa daga saman stairs ɗin,Directly Sassanta ya fara nufa tamkar yacce yayi zata kuwa tana zaune akan wata royal sofa ruwan zuma, tayi crossing ƙafafunta tana watching wani series film. Zana yayi a kusanta yanayin fuskan shi na sake sanjawa da ganin abinda take kallan. "Kafito kenan?" ta faɗi tana kallonsa itama tata fuskar a gimtse. Gaida ya fara yi kafin nan ya bata amsa da cewan wurin aiki ya nufa. Kai tsaye umarnin zuwa wurin Samha ta bashi tare da tura may wata leda kan ya bama Samha ɗin da hannuwansa. Seda ya ɗan dafe kansa zuciyan sa na kin amsan abinda woni sashe na daga cikin ta keson bijiro mishi dashi wato jin ba daɗi abinda Anniey'n kemai. Saurin istgfar ya fara a ranshi. Ba tare daya tsaya zaman diner tamkar yacce take may tayin ba yay fitansa. Inda kai tsaye mahaukacin street house parking loot na adana motocin gidan ya nufa Mai karatu idan nace zan tsaya zayyano muku adadin kuɗi masu tarin yawan da kawai aka narka wajen zuba ado a departmen house kawai na adana motocin ma wani sabon ɓatama kai loƙacinne sabo ma kuwa. Get uku ne a gidan kuma kowanne get akwai wuraren Parking car's, sedai gaba ɗaya wannan shi ne ƙarshe a komai wajen haɗuwa. Daga nan ya fice a gidan yana ɗaukan hanyan gidan gwaggo Haleemah don cika umarnin anniey. _ꨄ *Meesherh* Zaune take kan wata arniyar farar cough ta a sanye da top irin wannan wanda daga ƙasansu ake ɗinkewa sai crazy 3½, se kanta da yasha gyara sosai na musamman inda ke tubke cikin wata trap band. iPhone nata ne a hannunta tana duba irin yadda mutane keta sake kallar video'nta, da kuma irin ƙalubalantan ta da mutane ke sake yi. Ƙara lafewa cikin cough ɗin tay tare da ɗora wani ɗan ƙaramin rubutu kamar haka. 0o 0o 0o 0o 0o ꨄ _ꨄThank you for sharing your Videos with the world and enriching our lives with your beautiful FAN'S💃💐. May this special day bring you as much happiness as you bring to others. Wishing you endless love, success and fulfillment in all that you do. ❤️ All my love 😍_ tana ɗora rubutun tun kamin ta fita ta fara ganin kalan yacce mutane suka fara kallar short Rubutun tare da dawoata da amsa. Sharewa tayi tana mike ta nufa cikin domin cikin na kukan yunwa ya fara mata. A hankali take tafiyan tana jin yadda sanyin tyles ɗin da take takawa na ratsa mata ƙafafu. Kai tsaye kitchen ta nufa tana fitowa hannunta ɗauke da chocolate na day&night simsek tare da peanut chocolate ɗin dai tamkar ba mutumiyar dake jin yunwa ba. Zaman tay a wurin hankalinta kwance ta ɓare chocolate ɗin ta fara cin abinta har wani ɗan lullumshe idanunta keyi. Haka ta shirirince a wurin har wajen rana daga nan ta miƙe take ta wo wanka, bayan ta fito ne kuma ta nufa shashen mahaifinta. A zaune ta tatar dashi gaban tv screen yana kallln tashar sunan tv, zama tay kusa dashi tana tura dan cuwal ɗin bakinta gaba, "Me ake ma Autana kuma shalelena ne taga se kumbura take ita kaɗai?" Sake tsuke fuska tayi tana amsa remote ɗin dake hannunsa tana sanja channel zuwa wata tashar ta daban. Bayan ta sanja ne kuma ta duba mahaifin nata tare da furta. "Alhamdulillh papiey yanzu kamm jikina ya gama worworewa inas0n zan koma bakin aiki ne!" Ɗan jim papiey ɗin yayi yana auna maganartan a mizanin daya kamata, don ko shi gaskiya a yanzun ya fara gajiyawa da Film ɗin da take yi ɗin. Amma kuma idan yay duba da kamar cewa Aikin Film ɗin nata tamkar shi ne woni kaso mafi rinjaye na farin ciki daga cikin rayuwarta se yaji sammm baya iya hanata Film ɗin. Ijiyan zuciya ya ɗan sauke yana dubanta kaɗan tare da furta. "Dadai shalele ta bari jikinta ya sake hutawa sosai ba da gaggawa haka ba" shi ma yay maganan da son ta yarda da tsarin nashi. Amma samm taƙi ya wanda hakan ya sanya dole papiey yin magana harda Uncle's ɗin ta JAMAAL JEDAANS dama EL-MUAZ JEDAANS mata magana duk da kasancewan su bama sa ƙasar ne, shi Uncle Jameel Yana Islamabad shi kuma uncle El-muaz yaka ƙasar India acan yake da zama. Wanda dama su biyun ne basu zaman Nigeria sosai su kuma ukun sunfi zaman Nigeria daddy'n Juraij se daddy'n Moh Ameern, se Papiey'n Meesherh ɗin. Sunyi ta lallashinta amma da kyar ta haƙura se nan da kamar 2 Week's haka amma tana fita loƙaci bayan loƙaci zuwa *M.L.P MEESHERH LUXURY PRODUCT* har ranar yau data kasance abokan kasuwanci ta sun shirya mata kwarya kwaryar shagalin samun lafiyanta da kuma murnan dawowanta bakin aiki. Tsaye take a wurin da gurds nata sukai parking tsadaddun motocinta daga ta can harabar Hall ɗin da taron zai kasance, Shigowar Diamond Meesherh cikin hall ɗin shi ya sake haukata hall ɗin da sake ɗaukar hankalin kowa suna sake fasa ihun murna na wanzuwar ta kawai tsaye akan diga diganta. cikin takun ta me kama dana ƙasaita take tafiyar fuskarta me ɗauke da shade Glasses yalwace cikin kyakykyawan annuri. Duk wasu wanda suka kamata suna zaune ne a first cough na wurin don kawai kallar yadda Meesherh zata gudanar da Shooting show nata kawai na celebrate ɗin samun lafiyanta da wasu ƙusoshi suka shirya mata. Gaba ɗaya duk kowa da kowa sun bada hankulansu ne ga Diamond Meesherh Jadeens, A natse aka fara gudanar da wasan bayan ta gabatar da kanta tare da jinjina da tarin godiya wa mabiyanta datai cikin harshen English se ɗan sirkin Hausa kaɗan data ɗan hada. Tuni show ɗin ya fara ɗaukar ɗumi fa, masu aikin videorizing kuwa suma nata fama dama photographer da suke ta aikin yin pisc. Gaba ɗaya wurin ya sake ɗaukan shiru kowa hankali da tunanin sa naga Diamond ne. Wasu shigarta kawai datay suke kalla wacce take nan tamkar ƴar sarkin Islamabad ce, saboda yadda tafi kama da ƴan can hakan, domin kuwa dama su ba ƴan hasalin Nigeria bane. Hasalin shi Jedaans ɗin haifaffen ƙasar swizland ne wanda harkan kasuwanci ta kawo shi kasar Nigeria ɗin. Daga nan yazo ya kafa iyalansa dama da komai da komai, amma zaman Lagos suka fara SO kuma dai daga baya me ya dawo Kd ɗin da zama. Cikin salo na jan hankali da tafiya da imani Diamond taci gaba da gabatar da wasan ta tamkar kullum tamkar yadda ta saba, sedai a jinin jikinta yau ɗin take jin wannan Meesherh Sameer Jadeens ɗin dake tsaye gaban dubban al'umma ba waccen Meesherh ɗin ba ce wannan wata sabuwar halitta ce tsaye gabansu. Amma dake abune daya riga da ya zama Real life nata takejin shauƙi da kasancewarta hakan na har abada. Ƙarfe ɗaya da kwata daidai wasan ya tashi kasancewar komi ake yi indai da ita ciki to kuwa indai loƙacin sallah yayi to kuwa tabar ko miye ɗin. Kana tana da wani ɗabi'a sammm ita nata tsarin babu wannan yawace yawancen kwanan su Hotel's haka dadai sauran wurare da wasu actress ɗin keyi samm ita babu wannan a cikin tsarin jaddawalinta. Daga nan masu aikin jaridu da videorizing suka ci gama da naɗar komai har akai komai aka gama aka kuma bata award ɗin da suka shirya mata. Daga nan wasan ya tashi bayan ta ɗan yi dogon bayani da da harshen turanci na godiya wa mutanen da suka shirya mata taron tare da FAN'S nata. Kai tsaye ta sanya aka wuce da ita gida tare da jibgin gifs nata data sama. ♡ Wani irin uban ihu A'isha ta saki wanda ya janyo hankalin Rumaisa dake wanke kanta daga can baya kaɗan dasu. "A'isha kefa yanzu a rayuwa baki ɗaya baki da hankali notikan kanki sun gama kwancewa yaseen" Rumaisa ta faɗi tana maida kanta tare da jan tsuƙa. "Hmmmmm Rumaisa ba zaki gane ba ne kawai wllh amma fa A gaskiya wannan show ɗin ya ƙayatar ya kuma tafi dani sosai, Bara ma ki gani Wllh yanzun zan ɗaura a account nawa na Tiktok da Facebook kai wllh harma da Instragram duk saina ɗaura ɗaukar nan saboda abin sosai ya tafi dani" Wata tsokar Rumaisa taja tana furta. "Ai wllh dama na sani tunda naji kinyi ihun nan nasan cewan bazai wuce akan wannan Meesherh ɗin ba, Matar dake cewa zata ƙira ƙi se yau tashin zance karyar banza kawai" "Ke wllh ni da banji haushin taba ai irin waɗan nan mutanen uziri ake musu kodan ayyukansu da baya karewa, buhh ALLAH Sarki Wllh haushin kaina da kaina ma Ni nake ji da ban ko duba matar nan ba wllh, abin da ciwo sosai." Tana fadar hakan ne kuma tare duba wayarta wanda yayi daidai da sake sakin uban ihun murnar data saki me ƙarfi a karo na biyu, sakamakon duba wayartan da tayi taga yadda cikin ƙanƙanin lokaci hakaa amma mutane sama da 1k sun mata like harda masu comments ma akan video'n Meesherh kawai data ɗora. Kamar kuma da wasa kamar a mafarki taga Diamond Meesherh Jedaans cikin jerin masu mata like harda ɗan takaitaccen comment. Kafin ta wani yi baya luuuuuu kamar zata faɗi kwance daga zaunen da take tana dafe setin Heart nata, da ƙarfi kuma kamar wacce aka zabura ta furta. "Na shiga ɗaka na kasa fitowa ni A'isha yau wacce kalan Sa'a gareni Umma! Umma!! Umma!!!" Haka ta shiga kwalama mahaifiyanta ƙira kafin kuma tamkar wata filfilwa ta falla a guje har tana kusa kaɗe mahaifiyanta da itama ta fito ɗin a tsorace jin uban ƙiran da ƴar nata ke mata tamkar tashin duniya. Har rige rigen ƙarasawa gurin ta Ummih da Kilan keyi domin ganin abin da ke cikin wayar nata da ya sakata ihun murna haka. wani cafka Kilan takaima woyar dake a hannun Aysha ɗin, dake dama already tana cikin Tiktok ɗin ne ya sanya Kilan ƙanwarta me bi mata kallon komi. Wata nannauyar ajiyar zuciya Ummih ta sauke lokacin da take kallan abinda ya sanya ƴar uwar nata murna da ihu haka loƙaci guda Ita dai Ummah tana daga gefe tana kallon ikon Allah don ma ta gaza ƙarasowa. Ƙara zaro idanu woje Kilan tayi ganin uban likes da comments ɗin da yayar nata keta ƙara samu a take se sake shigowa suke babu ƙaƙƙautawa. "Aunty Aysha Ina harda FB kika daura kamar dama Instagram ma ko?" Da kai kawai ta mata alaman ehhhhhh ita kuma tana shiga sema taga ashe likes da comments ɗin dake cikin facebook da Instagram ɗin ma har na neman fin na Tiktok ɗin kuma dai shima Diamond Meesherh Jadeens tayi mata like duka. Ɗagowa tayi cike da zallan farin ciki ta buɗe baki kenan da niyar yin magana ta hango Ummah tsaye daga inda take daskare tamkar wacce akayi Freezing nata. Da hanzarin ta kilan ta ƙara sa ga umman tana me furta "Ummah wllh zo kiga Ikon Allah" tsoki kawai ummansu A'isha'n ta buga itama kamar dai Rumaisa ɗin tana komawarta inda ta fito, don dama tana kitchen ne tasha ma wani mummunan abun ne ya faru lokacin dataji irin uban ƙiran da ake kwakwara mata. 4:15 duk zaman ya ishe ta haka nan kawai taji tana son zuwa park ta hutawanta, tamkar kuma wacce ake umarta haka ta sama kanta da cll na No ɗin yarin yan Ranar data amsa tun a wancen ranan, tamkar almara tamkar a mafarki haka A'isha da take zaune tana ta aikin dudduba yawan like da comments na jama'a taga ƙira na shigo woyanta me ɗauke da sunan *Sweet Diamond* tun a wancen ranar data bata Id card nata tayi saving da hakan, hannunta har rawa yake wurin amsa call ɗin tare da manna woyar da kunnenta cikin rashin gaza samun cikakken nutsuwa ta mata sallama. Daga ta can kuwa ɗan murmushi mara sauti Meesherh ta saki tana furta. "Kodai an sama matsala row number ne!?" Ai cikin wani irin sauri A'isha ta furta. "A ahhhhhh wllh Aunty Meesherh ba row number bace Ni ce! Ni ce A'isha'r da kika bama N0 naki!" "OK dama nace idan ba damuwa musha ice cream a park na lelewal Jedaans" wani kalan waro idanuwanta woje tayi tare da rufe bakinta gudun hana ihunta fitowa tana furta "okk aunty Meesherh da kamar ƙarfe nawa kenan?" Amsa ta bata da cewan 4:40 kasanwan dama shirye take ita tuni, cikin wani sauri A'isha ta nufi ummanta tare da kunna mata Voice recording ɗin da tay na wayanta da Meesherh ɗin yanzu yanzu. Se kuma ummman jikinta yay sanyi tare da mata adda'an fatan Alkhairi. Daga nan ta shige gidan su Rumaisa da suke makwaftan juna wanda ba bata dade da fita a gidan su A'isha'nba ɗazu. Itama kunna mata tayi kamar yacce ta kunnama ummanta na ƴan gidan su Rumaisa ɗin suka dinga zuwa suna jin wai yau ga A'isha'n Rumaisa nayin waya da JEDAANS Sa'a kenan. Wata yarinya ce ƴar matashiya me suna Baby'n Nuwaira tace "Amma adda A'isha'n Rumaisa idan zaku tafi se kuje gidansu yaya Baby ku aro kayanta ku saka don karta renaku kota muku kallon ƙananun yara" Wani mugun kallo A'isha'n ta wurga mata tana me bata amsa da cewan. "Ai idan kana son mutum dan ALLAH da kuma zuciya ɗaya to zaka so shi ne bawai don ka nuna fariya kodai wani abu dan shi wannan abun ya soka ba, IN SHA ALLAH tamkar yadda muka sota dan ALLAH itama haka zata somu dan ALLAH bawai don komi ba.... Tun kan ta rufe bakinta kishiyar babar Rumaisa ɗin ta tarya numfashin ta da futta, "Yo ai gaskiya Baby'n Nuwaira ta faɗa muku ita kanta Rayuwar duniyar ta koma ƙarya ce yanzu idan zaka nuna kanka as ɗan wani ne kai tofa yanzu zaka zama na kowa, kowa kuma ya dinga rubibinka, amma idan zaka bayyana mutane dama duniyar kanka as ɗan Malam Shehu wllh abotar ma seka rasa da wanda zakayi saboda kowa ze dinga gudun kane..... Itama taryan numfashin nata tay ta hanyar furta. "Amma fa karda ki manta Aunty Mardiya ita duniyar ba taruwa duka tayi aka zama ɗaya ba, kowa ba kamar yacce kike tunani bane! Kuma wllh babu aron kayan da zamuyi duk gamunan da kayan har se mun tafi woni aron kaya dan kawai zamuje wurin Meesherh Jedaans" tun kamin kowa ya sake cewa komai A'isha'n tay ficewanta bayan tace Rumaisa ɗin ta shirya itama ta tafi shiryawan. Se gashi kusan lokaci guda suka gimtsa, ita A'isha'n na sanye cikin doguwar rigar kimono blue black ita kuma Rumaisa sanye cikin riga da sket na wani shadda lece me bala'in kyau kalan pink. Ita Rolling Vail nata tay sakamon ita da tayi Normal yafi da mayafin shadda lace ɗin. Sallama suka sake ma umma harsun fito tay kiransu ta basu 1k tace su hau napep. Godiya suka mata suna tagiya. Ƙarfe 4:40 me napep ɗin daya kwaso su ya sauke su a park ɗin daya kasance mallakin JEDAANS ne. Seda aka musu duk wasu aune aune da tsarin dokar wurin kenan ba'a shiga se anyi check out mutum, ɗan dube dube suka shiga suna son kallar ta inda zasu hango Meesherh ɗin. Wani maaikaci ne a wurin ya ƙaraso yana furta "Are people's that you are talking with madame?" saurin geda masa kai sukai suna furta. "Yeah" Iso ya mudu har zuwa woni tsararren wurin da tamkar ba'a cikin park ɗin yake ba. Kamin gilmawan ido se gashi an cika musu gabansu da kayan motsa baki. 4:57 Diamond Meesherh Jadeens ta bayyana a wurin wanda dama already ta riga da yasan wurin da suken tunda itane ta ware musu wurin zaman ta sanar tun a woya. Suna kallon isowanta duk suka miƙe tsaye suna ganin kamar ba haka bane kamar zata ce ne bata sansu ba ko kuma ta ƙirasu ne d0n buga musu mugun worning akanta. Duk dai jikinsu ba kwarin gwiwa haka harta ƙara so garesu, inda take sanye cikin wasu Fendi riga da wando na mata lightgreen colour. Se fancy goggles ɗin dake manne a idanunta ruwan makuba.Musamman yanda ƙaton gilashin data sanya ya kusan mamaye rabin fuskar tata da sake haskaka farar fatarta. Se wasu shegun fitinannun Heels ɗin dake sanye cikin fararen sawayenta irin me igiyoyin nan ya dauku ba ƙarya, Sosai tayi wani kalan masifan kyau na bugawa a mujalla. "Peace be open you my friends " ta firta cikin daddaɗan Sweet voice nata. A natse cikin kama kansu suka amsa mata suna jin tamkar tasu kolliyar a bola suke dan kawai iyaka Heels ɗin dake ƙafarta sun san sai ya sayi suturar dake jikin kowannen ninki uku uku wai ma fa kar ace sunyi ƙarya ne hakan. Santalelen farin hannunta ta miƙa musu sukayi musabiha, da Rumaisa suka fara yin Musabihan se A'isha'n wacce take ta noƙe hannunta jin da tayi hannun Meesherh'n ɗin wani kalan laushin da yake da ga woni gumi gumin da taji hannun na tarawa, hakan ne ya sanya tay ta ƙoƙarin janye nata amma Meesherh taki sakin mata hannu, se kawai ta ceci kanta ta hanyar furta"Aunty Meesherh barka da yamma" ɗan murmushi tayi tana zama kan royal blue royal icing chairs ɗin da suka zagaye inda suke zaune. Gefe kuma ga tight securities na gidansu dake zagaye da wurin dan tsoron lafiyan Diamond Meesherh. Sosai suka gaisa a mutumce cikin girmamawa daga nan suka ɗan taɓa abubuwan da aka jere a wurin wanda bisa tilas tawan Meesherh ɗin ne ma har suka ci Chocolate tare da juice. Daga nan ita da kanta tayi musu pisc tare da video a woyanta wasu sabbin kwalaye guda biyu ta ciro cikin hand bag nata tare da tura duka pisc da video's din ta cikinsu tabe ko wannensu sabuwan iPhone Wanda ya sanya jikkunansu daukan rawa a tare a lokacin da take sanar musu Gifs nasu ne ta basu suma cikin abinda ta samu a yau ɗin wurin taron da aka hada mata, zamansu babu jimawa wasu arnayen manyan motaci kusan guda biyar suka danno kansu Cikin wurin. Tun daga yadda taji yanayin bugun numfashin ta na sanjawa tasan cewan shi ne ya zo wurin. Daidai lokacin da ya sako kai a natse yana fitowa a car din cikin wani irin kamewa da kwarjinin da yake da, wanda duk girman mutum idan Sheikh juraij na tsaye wuri baka isa ɗaya ido kai masa kallon Ido cikin Ido ba.cike da girmamawa kowa dake wurin sukai ƙasa da kawunansu hatta kuwa securities ɗin dake zagaye da wurin saboda tsananin kwarjinin da yake da kuma tsananin girmamawa a gareshi. Ita kaɗai ce wacce bata janye kallanta a kansa ba sema wani abu me kama da sanyi da taji yana sauƙa a zuciyanta yana mamaye ko ina nata kamar koda yaushe. Domin kaff duniya bata da abinda ya fiye mata kallon pa'apahh ɗin ta daɗin kallo fiye dashi Wani kalan rintse idanuwanta tayi ahankali wani mashi me tsananin zafi na sukar tsaƙiyar ƙirjinta ganin wata koɗaɗɗiyar budurwa ta fito a cikin motar biye dashi tamkar wata bindi ata bayansa. Hakan ne ya nema toshewan numfashin ta ƙirjinta na da zafi da neman jin numfashinta tamkar ya na neman yankewa ne da gangar jikinta Idanuwanta kuma na mata wani kalan yaji yaji, akan kirjinta ta ɗora hannunta ahankali tana karɓan azaba da gashin da zuciyan ta ke mata. Amma duk iya bi kokof ɗin ka baka isa fahimtar ko a wanne yanayi take a ciki ba, hatta kuwa su wanda suke tare da ita harda ma isowan Sadja data kasance tamkar Aminiya ƙwara ɗaya da take da. Cikin tarin nutsuwarsa yake tafiyan zuwa inda babu hayaniyar jama'a sosai kafin ta gama sayayyar da Anniey'n shi ce dole ta tilas mata se yazo lallai lallai ya kawo Samha ɗin. Ta seti da inda suke zaune yazo ze gitta ba tare daya ko san su waye a zaune wurin ba kasan cewan idanunsa ba a kan kallon kowa yake ba. Cike da girmamawa da rawar jiki kaman zasuyi masa sujjada su duka suka miƙe tsaye suna gaida shi cikin nuna girmamawansu gare shi. Dai dai isowan Samha ɗin wurin don ta dudduba bata ganshi ba ita kuma yau ɗin take son burge ƙawayenta da nuna musu cewan lallai Sheikh juraij Jedaans mallakin tane ita kaɗai shi ya sanya ta saka Mommah nata dole ƙiran ƙanwar nata akan cewan lallai maza maza jurai ɗin yazo yakai Samha ƙarashen sayayyar da ba'a mata ba ko park na Jedaans ne. Ai kuwa tana kallonsa tsaye a wurin ta wani taho a fusace tare da tarin friends nata dake take mata baya zuwa inda juraij ke tsaye harma yana niyar tafiya. Ganin Meesherh wurin shi ya sake hassala Samha ɗin domin kuwa kaff rashin jituwar dake tsakanin su ta sani haka ma duk soyayyar dake tsakanin su tun ta yarinta duk tana da labari akan haka. Fuskan Meesherh ɗin kuwa ba ɓoyayya bace a gareta duba da cewan ita ƴar Film ce yar wasan hausa. Tana zuwa babu wota wota ta ɗauke fuskan Meesherh Jedaans da wani kalan shegen marin daya gigita su Aysha da Rumaisa har dama Sadja. Kafin ace Samha ta sake yunƙurin komai taji Saukar mata lafiyayyan marin akan kuncinta tasss, kafin ta dawo hayyacinta ta sake jin an sake wanke ta da woni lafiyayyen marin daya kusan tashin duniyarta. "Babbar magana" Cewar Sadja tana miƙewa tsaye. dafe da kuncinta ta ɗago tana sauƙe idonta a cikin na Meesherh dake jifanta da wani shegen kallo na gargaɗi. Mamaki al'ajab da tsantsar ruɗanin su suka taru suka hana su Aysha cewa komai don ma duk jikkunansu rawa ya shiga yi. hatta ita uwar gayyar kuwa wutar kanta ɗaukewa tayi domin abinda batayi zata bane idan tay duba da yacce kowa ke yabon Meesherh ɗin ana faɗin babu ruwanta ita samm. Hakan ya sanya A fusace Samha ɗin ta sake kai hannu da nufin shaƙota Meesherh ɗin, Aikuwa wani shegen kallo ta sake watsa mata tana riƙe hannun dayay niyar shaƙota hankali kwance babu alamar tsoro kona sisi a idanunta. Cikin zafin rai disgin da yau ne ta taɓa riska kaff cikin rayuwarta ta shiga nuna Meesherh da yatsa cike da tafasan zuciya take furta. "Ke har kin Isa ki raɓe inda Mijina yake har kiyi tunanin tsaiwa dashi!? Wato anga an gama yawon tsaface tsafacen duk babu riba shi ne kike son ɓata masa suna ta wannan hanyar ko? To wllh kinyi kaɗan da ɓata sunan Mijina to ki sani niba takalmi bace ballantana ƙafafunki suyi tunanin takawa a duk sanda kikaga dama dani da Mijina munfi ƙarfin karamar ƴar duniya irin ki wllh" ta faɗi tana wani huci tare da ƙoƙarin son kwace hannunta a cikin na Meesherh ɗin data gasa amsa. Da wani shegen kallon sama da ƙasa Meesherh tabi yarinyan da aƙalla zata girme mata da kamar shekaru biyar zuwa hudu haka. Kafin ta janye kanta wata dariya nason kwace mata don wllh ita sema a yanzu ne ta gane fuskan wato Samha ce wacce ta sani tun basu kai haka ba. "Ohhhh Ashe fa kene wacce aka ce ana daurama pa'apahh Naaaaa Aure dashi buhh congratulations Amma kafin nan Respect your self ok? Don bar ganin kina a matsayin wacce pa'apahh Naaaaa zai aure tsaf idan kika min ba daidai ba zan wulaƙanta ki. Tana cilli da hannun tare da surarn hand bag nata tare da furta. "Hi my enemy friends ku muje ko?" Tayi maganan tana yin gaba cikin takun izza... Ita kuwa Samha tamkar gunkin da aka dasa haka ta kasance tsaye tana bin Meesherh'n da kallo, dan da gaske wutar kanta ce ta ɗauke baki ɗaya har tama rasa hukuncin da zatai mata, ganin tana shirin ɓacema ganin tane ya sanya ta furta. "Ke karamar ƙaruwa idan har kin haifu yau a cikin ubanki SAMEER JEDAANS ki tsaya a idd...... Ai bata ƙara sa ba Meesherh tayo wani kalan zaburowa da nufin tafiyar ruwa da Samha ɗin. Domin ita ba mutum bace sakarya da zata ji ana zagar mata iyaye ta iya jumrewa. Se dai kuma chark ta tsaya sakamakon riƙe tsintsiyar hannunta da taji anyi. Hakan ya sanya ido rufe ta buɗe baki tana antaya bala'in koma waye ita ya sake ta, duk da cewan zuciyan ta ya rigada ya gama sanar mata cewan ko waye ɗin kuwa, amma haka ta shiga shure shure tana furta ya sake ta ya barta ta tafi. Be sake ɗin ba sema sake damƙar hannunta. Bakinta dake maganar yake kalla yana ɗan lumshe idanuwansa yayi tare da buɗe su ahankali yana zuba mata su cikin wani kalan sanyi.. Itama idanuwantan masu shegen kaifi a gareshi da yanke haƙuri da duk wani kamewansa akanta ta zuba mishi uwa uba kuma ga numfashinta dake daf da nashi me gauraye da ƙamshin turarenta na tafiya kai tsaye i zuwa cikinsa, Ita kanta ajiyan zuciyan take sauƙewa mara sauti tana rufe idanuwanta ahankali batareda ta motsa ba, domin wannan wani abu ne da tunda ta mallaka hankalin kanta bai taɓa faruwa da ita ba. Saida suka kusan yin mintina biyu a hakan kafin ya juyo da ita ahankali zuwa gabansa chak yana tsaidata kan ƙafafunta tare da zubawa fuskanta nasa Idon yanajin abinda baima San meye yake ji ba, Kansa gaba ɗaya kuncewa yaji yana naiman hakan ya sanya shi ja baya yana raɓata a hankali da nutsuwansa yana barin wurin. Kafe bayansa da idonta da suka kusan tara ruwan hawaye tayi tana kallonsa a hankali cikin yanayin daya sanya numfashinta neman yankewa Amma tana danne hakan a natsen ta kuma ta janye. Tuni Samha kuwa cikin wani irin uban tashin hankalin abinda ya faru da maganar da Sheikh juraij ɗin ya yanka mata akan taɓa koda da farcen karen gidan daya kasance ahalinsa ne ta sake yin ƙurinyi to kuwa tabbas anan ne kaɗai zata gane cewan me aka nufi da hasalin ƙure haƙurin me haƙuri da kaishi bango. Ta bangaren Meesherh kuwa kota kan banzar bata sake biba sema su Aysha da tama magana tare da basu wata farar envelope tace su hau machine. Tunda suka ɗauki hanya suke maida zancen yadda abin ya faru. "Wai kinsan wllh a loƙacin nan har wani zazzaɓi naji na neman rufeni kuwa take?" Caraf Rumaisa ta amshe da cewa "ayke zazzaɓi ma kikace da sauƙi Aysha ni wllh Jima nayi kamar nayi fitsari a wurin ashe haka ta iya wanza almasifatu itama. kai jama'a yaseen ALLAH ka rabamu dayin amai mu lashe abinmu jiday woni faɗan rashin gaskiya a wurin matar cen fa" Rumaisan ta karasa da alamun mamaki tattare da ita. "Wai kam nace ni baki lura da kamar cewa ita ɗayar tamkar tana kishi ne da Aunty Meesherh'n bane? Cewar aysha'n. "Nifa tsaya kiji ma A'isha wllh se da nai tantamar wai wannan itace matar da ze Aura, ke kina ganin ta wllh kinga wankakkiyar ƴar duniya wllh samm basu ma dace ba dan se sukafi ma dacewa da Aunty Meesherh'n" hmmmmm A'isha'n ta kawo ijiyar zuciya tare da furta "Kinga forko dai shi mutum ne wanda ubangijin yayi mishi baiwar ilimin addini dana zamani.kana yana ɗaya daga cikin manyan malam da Afirka kai dama duniyar baki ɗaya ke ji dashi. Sabida a duk ƙiyasin malamai babu yaro matashi mai jini a jika da tarin ilimin addini kamarshi suka gama ratsashi wanda akace tun yana da ƙananun shekaru ya gama haddace al'ƙur'ani mai girma a kansa.kana ga jibgin littatufan dake kansa suma da yake da haddarsu suma a kanshi fiye da zaton me tunani.ga tarin baiwa daraja ɗaukaka amma kuma a ce ya ƙare a wannan abar!?, Ni wllh sammm banma ji ta ko kwanta min a raina ba. Kifa duba kaff girman Kaduna babu malami babba kamarsa daga nan har Lagos kai harda ma sauran garuruwa Kinga nasaba kan nasaba kenan. In kyau ne kuwa na halitta babu ta inda ta isa ta ko kamo tafin ƙafar sane, In kuwa kuɗine ai base an baki labarin ko su waye JEDAANS ba, Shi mutun ne wanda ya gama samun kekykyawan zato a wurin mutanen duniya baki ɗaya, to kuwa kinga tako ta ina ya tserema tsararta kuma bazance wannan aikin asiri bane don wllh ko kaffara bazan yiba duk da ance asiri gaskiyar me shi wanda ko Annabin ALLAH be kauce masa ba amma kuma IN SHA ALLAH wannan asiri bazai taɓa kama shi ba don shi ɗin. SPECIAL ne" Duka a tare suka sauke ajiyan zuciya suna yin shiru kuma suna rasa abin faɗa ma baki ɗaya. ꨄ Sosai aka shiga shirye shiryen yadda ɗaurin Auren Sheykh da Samha zai kasance a duka family biyun,Inda amarya Samha se wani jiji da akai ake za'a auri babban mutum kamar Sheikh juraij Jedaans uwa uba kuma tarin dukiyan dashi kansa bema San adadin tashi ba bare aje kan ta ahalin kuma. Sosai shirye shiryen komai ya gama kankama cikin ƙanƙanin lokacin daya musu saura, iyayen Samha kuwa se aikin banka mata magungunan mata suke. Banda wanda ita kanta Samha'n take banka da ƙawayenta suke kawo mata tsadaddu masu shegiyar tsada. Mayuka kamm na bleaching ai ba'a magana wai duk suma a cikin kaya na gyaran jiki suke. Wanda kuma Ayau ne gidansu su juraij suka kai kayan lefe gidansu Samha, Inda suka sami tarɓa ta girma da girmamawa. Inda babu kunya samha ta fito tare da tarin ƙawayenta da suka cika gidan kallon kaya tun a gaban su ƴan gidan. Yayinda su papiey ke can suna tattauna yadda ɗaurin auren ze kaya. Wanda cikin masu kai kayan harda Aunty Ummeterh Amma Maah bata je ba. Ita dai Aunty Ummeterh a ranta take ayyana lallai akwai gyara a lamarin wannan amarya, duk da kuwa kasancewar itama kamar ƴar gida ce dan sun santa sosai, don wllh ita har cikin ranta take jin tausayin Sheikh ɗin kasancewarsa bai wani cika zafi da yawan magana ba'a mafi yawan lokuta. Ita kuwa Samha se wani gani gani take ma Aunty Ummeterh ta dan itama tun kan haka take jin ta tsani duk wani wanda suka haɗa jini da Meesherh haka kawai. Wando da riga ne a jikinta ƙirar ƙasar kuwait inda farin nan ko nace jan nan har wani shuni shuni yake irin me ɗaukan idon nan . ꨄ Ata ɓangaren Meesherh kuwa gaba ɗaya tayi sanyi sosai da zancen Auren ganin dai tabbas gadan gadan kullum maganar da ranakun ƙara kusanto kansu suke se kawai ta ware kanta ta a komawa rayuwarta ita kaɗai babu ruwanta da kowa, sema harkan Film ɗin da take son ta saki a cikin satin da suke ciki shi ya sake dauke hankalinta daga bikin. *BY AMMEY LAYLERH ✍️* ꨄ *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 21&22 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Waɗanda suke buƙatar samun litattafan *AMEEY LAYLERH* za ku iya shiga shafin ta na Telegram don samun su kai tsaye daga wurin ta. Ga link nan ga masu buƙatar shiga 👉https://t.me/ammeylaylerh_novel ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Masu iya magana sukace wai Rana bata ƙarya, tabbas wannan karin magana haka take don kuwa a yau ne ranar asabar dubban jama'a suka shaida ɗaurin Sheikh juraij thabit Jedaans tare da amaryarsa Samha Abdulkareem Wada a babban masallacin dake nan cikin anguwarsu. Biki da bidi'a sosai dangin amarya suka shirya wanda suka san ko guguwar me Sheikh ya sha sun san bazai jeba. Haka suka inga gudanar da taron bikinsu Amarya Samha kuwa ba'a cewa komi. Don wani irin zumuɗi take yi na bikin. Wanda kuma a daren ranan ne aka dangan tata da gidan Sheikh ɗin, dake sun san tsarinsa babu bidi'a ko kaɗan ya sanya baffanta da kanta ya kai ta har ɗakin mijin nata. Sedai ya tarar da wasu dangin mahaifiyarta a gidan shidai seda ya tabbatar ya danganata da ɗakin mijinta kana ya mata yar nashiharsa kan tabi mijinta kar kuma ta ɗauka halin mahaifiyarta. Fitowarsa daga wanko kenan ta shigo kamar an jehota room ɗin. Kawai sai sauƙar hannuwanta yaji saman fresh naked skin ɗin sa, farko seda gabansa yaji ya may wani mummunan bugu amma yana jinta bai ko motsa bare  ta saka ran zai tanka ta, cik6 nutsensa ya zame hannuwanta data zagaye shi yana zaunar da ita gefe da bed ɗin. Kai tsaye kayansa na bacci farare ya kwasa yana komawa bethroom ɗin daya fito ya kimtso kansa cikin dogayen lallausan kayan baccinsa na long sleeve pyjamas, seda ya gabatar da nafilfili kana ya dawo kan gadon yana kwanciya don shi shafff ma ya manda da wata ana Samha zaune a dakin. Daga inda take zaune ta miƙa hannunta a bayansa kasancewar rufda ciki ya yi slowry ta fara shafa bayansa she's try to make him feel emotions for her, da wani irin tarin mamaki al'ajabi ya yayi saurin juyowa yana sauƙe kallonsa a kanta. "YA SHEIKH BACCI" ta furta cikin wata shegiyar murya wai irin zata rinjaye shi ɗin nan tare da sake ɗora hannunta a waist ɗinsa ta zagaye ƙugunsa da duka hannuwantan, duk abinda dake mishi yana jinta sai dai he's not interested bai da feelings ko guda a kanta bare ta yi tunanin zai ji wani abu dangane da abinda take masan, abinda kawai ya sani feelings nashi yana jin sane kawai akan mutum ɗaya wanda a farko ma shi yasa kota kota baida cikakken lafiyane irin na kowanne cikakken ɗa namiji. Se daga baya ya gane ba haka hasalin karatun yake ba shi wannan feelings ɗin akan tane kaɗai yake tasiri domin duk inda cikar mace takai mace to ko ɗan yatsar ƙafarsa bai harbawa bare har aje garin jin feelings a knata. shiru kawai yayi yana jinta yana son mata magana Amma kuma baison shiga haƙƙinta gudun kar ALLAH ya kamashi da laifin rashin kyautatawa a gareta tunda yanzu mallakinsa ce ta zama matarsa ta sunna. Daɗi da ƙari baison hayaniyar komi saboda yadda yaji gaba daya komi da komi na sire mishi kansa kuma kamar zai fashe ya tsage gida biyu,jin tana ƙoƙarin sanya hannunta cikin bxer ɗinsa ne ya sanya ya yi saurin haɗe ƙafafunsa tare da mirginawa ya ware fararen idanunsa a kanta, ita kuwa samha jin ya dakatar da itane ya sanya ta buɗe idanunta don ta riga da ta gama sakawa ranta cewan yau zata kwashi romonsa. Jikinsa har wata tsuma tsuma yake ya mike tsaye tare da mata nuni ta fita. Ƙi yawa tayi sema sake ƙoƙarin rarumarsa da take sake niyan yi hakan ya sanya shi miƙewa tsaye yana furta "pls Samh kije bana cikin ko wanne kalan mood moment ne" cikin wata maraitacciyar murya ta furta "Please jurh ka saurare ni wllh I love you to the rest of my life,kai kawai nake gani na ji farinciki,I want to stay with you forever! I want to stand by your side Ina sonka wllh na yarda zan kwana anan ba tare da munyi komi ba" Wani irin yunƙuri yaji zuciyansa ta masa wanda yake ƙoƙarin danne ɓacin ransa a kanta amma duk yacce yakai ga hakan hakan seda ya gagara hakan ya sanya shi nufar inda take cikin tafasar zuciya amma a normal nashi yake.haka ya ja hannunta kiiiiiiiiiiiy har nakin doorhandle na room ɗin ya a cillata woje tare da rufe ƙofar yana jingina da jikinta, yana jin tamkar ana gasa kanshi ne a cikin ovan, daga ta cen ƙasan zuciyarsa kuma yana jin tamkar hakan dayay ya saɓa wota lamba ce, yana jin tamkar ya aykata ma abu mafi soyuwa a cikin zuciyarsa wani abu ba daidai ba. Yana jin idan da ace itace yau a matsayin mallakinsa kuma halaliyara a yau zata kwana a gidansa matsayin matarsa to kuwa da babu abinda ze hana komai faruwa a wannan daren. Don yana mata wani irin Mahaukacin S0 ne wanda ko a baki aka tambayeshi wanne irin so yake mata bazai taɓa iya furta shi ba abinda kawai ya sani yasan He luv her more & more & more for ever never. Se dai kashhhh idan ya tuna a yanzu ko wacece ita wani irin zafine ke yankar zuciyarsa da ƙirjinsa na irin yacce take gudanar da rayuwarta yanda take so, Ya so ta taso killace a kamile cikin kamalar rayuwa bawai ta zamo me talla wa jikinta ga wasu mazajen duniya na amma wannan kalma ta ƙaddara ta riga fata, ta riga ta gama yima kanta gurbi daram a cikin babin ƙaddarorinsu da haka ALLAH ya rigada ya gama tsaro musu, wanda sau da dama idan ya tuna yacce take mu'amulantar jama'a yakanji ma kwata kwata tama gama sirewa a kansa, amma dake ance so jarabta ne so masifa ne duk yacce yakai ga munana ta a cikin zuciya dama kwayar idonsa da ruhinsa se abin yaƙi tasirantuwa a cikin brain nashi. Innalillahi ya shiga natata yana jin tamkar yana masa dakan ɗaka ne a cikin taaƙiyar ƙirjinsa. ✯ Washe garin ranar. Zaune take akan sofar dake parlon hannunta ɗauke da wayarta tana ƙoƙarin saka ƙiran mahaifiyarta kana ganin yanayinta kasan She is not felling Wall,Idonta ya kumbura sosai saboda kukan data kwana ta nayi a daren jiya lips nata har tashi yayi saboda tsaban kukan data kwana da kuma irin yadda mararta ta azabtar da ita. Shi kuma Sheikh ya rufe mata ƙofa tayi bugun duniyar yaƙi buɗe mata kofa tunda ya hankaɗota wojen nan.Jin kamar an zauna kusa da ita ne yasa ta ɗaga rinannu idanunta tare da sauƙewa akan Sheikh wanda ya zuba mata ido tare da furta. "Are you Okay?" Zuba masa idanun nata tayi jin har yana da bakin da zai iya tambayan abinda ke damunta se kawai ta fashe da kuka wanda ya sanya Sheikh Runtse fararen idanunsa domin ya tsani yaji ana kuka kusa dashi, kukan ma ace na mace, macen ba kuma wacce take matsayin mallakinsa. gyara zaman sa yayi har laps nasu na gogan juna wanda ita hakan ya sanya tsikan jikinta wani kalan zubawa, shi kuwa babu abinda yaji. Yana ƙoƙarin sake mata magana kawai ta faɗa jikinsa tare da ƙanƙameshi tana sake sakin woni kukan tare da cusa kanta cikin tsaƙiyar ƙirjinsa. Wani irin yankewa yaji gabansa yayi ya faɗi kansa na sarar masa loƙaci guda.ita kuwa Samha jinta cikin jikinsa ya sanya ta ƙara ƙanƙameshi tana jin kamar tayi may faɗe. Se kuma cikin muryan kuka ta furta"Kai ne! Ba kai bane jiya ka rufe ɗakin ka ba nayi ta bugu kaƙi ka buɗe min kuma" wani kalan dafe kansa yay domin shi sammm hakan ya ɗauka ba woni matsala bane. Ƙoƙarin janye ta a jikinsa yake tare da furta "OK shi ne kawai matsalan?" Kanta ta jinjina masa tana sake maƙaleshi. Sadda kansa ƙasa kawai yayi haɗe da lumshe fararen manyan Idonsa haɗi da ɗan taunar gefin lips nashi ba da yawa ba yana jan idanunsa ya lumshe saboda yadda yaji zuciyansa na bada bugu da ƙarfi har yana iya jin yanayin yadda gudun zuciyar san ke ƙaruwa. wani wahalallen numfashi yaja sleep'yn eyes nashi wanda suke koda yaushe lumshe na sake janyewa yana amsan yadda bugun zuciyarsa ke ƙara tsanananta. ♡ A mugun firgice ta farka daga ɗan baccin data samu ya ɗauketa bayan tayi sallarn subhi, wanda kwana tayi bata runtsa ba data rufe idanunta pisc na shi kawai ke mata gizo a tsakar kanta tare da wata macen rungume a jikinsa.wani kalan cukukkuye jikinta wuri guda tayi tare da sakin Shassheƙar kukan da bata san sadda ya zo mata ba har eyes ball ɗin ta na ƙanƙancewa jikinta kuma ya shiga rawa jijiyoyin ƙanta na tashi da ƙyar ta samu cikin wani tear out voice ɗinta dake creating ta furta "I don't love him anymore, My life is nothing for him, ba haka ya kamata kamin ba, ba yadda nai zata na samu ba WHO? why? Why pa'apahh da zaka ma zuciyana irin wannan mummunan horon da kai tsaye ze iya illatar da ita. Sake lafewa tay tana maƙale jikin fuskar gadon tare da rufe idanunta tana jin kamar shi ne ya shigo wai yazo ze rarrasheta. Hakan ya sa cikin cira sauti ta furta "Ahhhhhhhh A ahhhh don't touch me! Don't touch me pls paah ka fita a rayuwana kamar baya bana so bana son duk hakan in ba haka ba wllh zan haukace kowa ma ya huta I hate all off you about....... Sosai zucyarta ke beating very fass,gefe guda kuma ji take kamar ana buga mata wani abu a tsakiyar kanta,dalilin hakan yasa jijiyoyin kanta sukai raɗa² yayinda jikinta ya shiga rawa take ta fara wata irin jijjaga ta fitar hankali. Shi kuwa can ɓangaren Sheikh juraij duk abinda Samha take masa kawai ƙyaleta yayi tunda kamar yaga hakan take buƙata bawai dan yana jin komai dangane da hakan bane, amma fa duk sadda hannunta ze sauƙa a wani sashi na jikinsa ji yake tamkar narkakken dalma take ɗiga masa a wurin. wani kalan jakin numfashi ne so sarƙe shi zuciyarsa na kamar zata faso ƙirjinsa ta fito da gudun bala'i, ga wani mugun kalan zafin dake daɗa mamaye tsakiyar ƙirjinsa, tamkar wacce aka zabureshi haka ya wani kalan janyeta da ƙarfin bala'i daga jikinsa yana miƙewa tsaye tare da fara ja da baya baya yana ficewa a parlour'n kai tsaye ya nufa inda indara Land cruiser car nashi take. Wani irin gudu na ceton numfashi ya shiga gudu na tashin hankali. ALLAH ne kaɗai ya kawo shi gidansu lafiya dan wani irin gudun tashin duniya yayi wanda tunda yake a rayuwarsa ba zai iya r̃iƙe rana me kamar haka dayay kalan wannan gudun ba. Loƙacin daya shiga gidan daidai da sanda Meesherh ke duƙe gaban Railer'n parlour'n ta. "Baby!!!" Sheikh ya ƙi rayi sunan da kaf duniya shi kaɗai ne me ƙiranta da wannan sunan idanunsa zube a kanta, ganin yacce take a duƙe a wurin hakan ya sanya shi nufota. Cike da wani kalan kwarin gwiwan da ita kanta bata san tana dashi bane ya sanya ta miƙewa a mugun hargitse tamkar wanda tayi tozali da dodo, tunkararta yake tana dada ja baya tana ƙokarin ganin ta miƙe ta gudu domin iyaka ganinshi wani shegen zafin zuciya yake haifar mata. Taku ɗaya ana biyu ya sanya hannunsa yana jawota yana tsaidata kan ƙafafunta, Innalillahi! Ya amtabata a cikin zuciyarsa don ganin yacce idanunta suka yi wani kalan ja da kuma tashin da sukai alamun taci kuka sosai harta gode ALLAH. Zuciyar sa ce yaji ta fara rawa tana wani irin yunƙuro masa domin har maƙoshinsa yake jin numfashinsa na kawowa, sake ware idanunsa akanta sosai yayi don yanajin yadda ƙafafunsa ke gaza ɗaukar gangar jikinsa. "What brought you here Baby?" Ƙara ja baya tayi tana matsawa can nesa dashi da hannu take masa alamun ya dakata kada ya motsa inda take tana yi tana girgiza masa kai irin ya dakata ɗin nan, he just trying to get more close to her. a gigice kuma ta furta "Stop Stop Stop it pa'apahh, Don't touch meeee!!!" jikinta duka rawa yake domin tamkar gani take shikenan pa'apahh'n nata ya rigada ya gama cin amanar tane. Ita kanta bata san sanda wasu wahalallun hawaye suka shiga zuba mata ba daga cikin idanunta sai da ta ji sauƙan lallausan tafin hannunsa kan fuskanta yana share mata hawayen dake zubo mata. Kanta ta ɗago a raunace tana kallonsa amma ga mamakinta se taga ya sakar mata woni kyakykyawan murmushin da zata iya rantsewa rabonta dashi tun tana ƴar yarinyantan. Tamkar wota baby'n kuwa haka ya ɗauke ta cilak yana nufar bedroom nata. Kai tsaye a katafaren gadonta ya kwantar da ita komai bai ce mata ba ya juya yana barin bedroom ɗin. Zaune take tsakiyar royal bed nata tun fitar shi ta gaza taɓuka komi sema curewa waje guda da tay banda sauƙe numfashi babu abinda take,sai yalwataccen gashinta wanda ya rufe duka fuskanta. A hankali ta ɗago lulu eyes ɗinta wanda suke always sleepyn ta zubasu kan oval face ɗinsa mai matuƙar kyau da kuma tsari Allah yay masa baiwar kyau da kuma kwarjinin da ba zaka taɓa iya yin 4eyes dashi ba, a pisc ne amma se take kallan tamkar yana a gaban tane dubanta takai kan faffaɗan ƙirjinsa wanda yake yalwace da kwantaccen baƙi siɗik ɗin gashi mai sheƙi,Wasu siraran hawaye ne suka shiga zubo mata tuno da cewan wata ta rigada ta mata shamaki da abinda kaff duniyar tafi ƙauna fiye da komai dake cikin ta idan aka ɗauke iyayenta. Jinta take tamkar wata zautacciya irin wacce take daf da kamuwa da ciwon haukar nan. A matuƙar galaɓaice ta mike tsaye ta shiga cilli da duk wani abu data ci karo da shi, kafin takai zaune yaraf kan tsakiyar gadon ta dafe saitin Heart nata ta shiga furta. _Na yarda da shiiiii! sabo dani dashiiii,kaga ni dakai ɗaya na dogara ba rabuwa da kai.... _ Ta faɗi wasu hawaye masu zafin azaba na zubo mata, sake matse jikinta wuri guda tayi tare ware hannuwanta tana buɗe idanunta gaba ɗaya da dira gwiwowinta kan tsakiyar bed ɗin taci gaba da furta _Ni ba haka ya kamata kai min baaa, ba yanda nai zato na samu ba fiye da haka ɗan uwanaaaa fiye da haka pa'apahh Naaaaa..._ Taunar gefin lips nata tayi da ƙarfin daya sets taji a jikinta amma kuma bata damu ba taci da rera waƙar ta. _Ashe sabo shi haka yake, yasa zuciyata ta tsiƙe gaɓoɓin jikina su sake,silar kaneeee silar kaneeee, kullum da s0n ka zuciyata ta kwana kai kai kaɗai nake ba loƙacina tunaninka ne kawai a gabana. Dan deda s0 a ɗau kiyayya da zafi....._ _fiye da hakaaaaa.kada kai hakaaaa kada kai haka._ Ta furta tane riƙe kanta da take jin kamar ze tarwaste gida biyu. _Duka kakkausan lafuzanka zanji taushinsu, na baka kaina kaima kamin biyan bashi!, kome kake S0 ♥️ ka ambaceshi zan yishi, da haka na fige fiffiken s0nka ba batun tashi_ ta faɗi kamar zata zata tashin sedai tana kasawa hakan tamkar yana a gabanta ta nuna pisc nashi dake gabanta ta furta. _Na baka yardaaaa, na baka yarda na duka_ Tana jin yadda zuciyan ta ke barazana wa rayuwanta ta furta. _Niii! baka haka ya kamata kai min baaaa!, duk da hakan ma ban raina ba ka wuce hakaaaa ɗan uwana Naaaaaa fiye da haka jinin jiki Naaaaa_ se kuma tunani shi tana me ambatar. _Komai na faɗa kana jinaaa! na gane kana fahimtana, kaban madaraaaa kanan madara na ɗan ƙurfa ka bani cikon muradinaaaa....._ Ta furta hakan numfashin ta na tsayawa da aikinsa cakkkk. Tun misalin ƙarfe 4:55 ta gama shiryawa cikin shigarta ta alfmar inda tayi wani irin sahihin yau na gaske gashinta ya sauƙa har gadon bayanta kasancewar vail ɗin da tay Rolling dashi ƙaramine, se hand bag nata dake gefenta. Ɗan sake duban wrist watch ɗin dake hannunta tayi a karo na biyu, Fitowan Maah da kuma papiey'nta ne ya saka ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, domin ALLAH ² take tayi tabar gidan ma baki ɗaya kai harda garin ma tun da yau ne zataje Lagos inda wasu manyan jarumai da kuma wasu ƙushoshin kasar suka roƙi da taje a fara haska wannan zazzafan Film ɗin nata na TAURARUWA a gidan Cineme mar dake Lagos ɗin, inda da taƙi yarda da tsarin nasu se kuma wannan abin na daren jiya ya sanya ta amincewa ko nauyin dake danƙare a cikin zuciyarta ze ragu. Maah ce ta fara kaiwa zaune saman sofar parlour'n kafin papiey shima, ɗan murmushi tayi cikin tsananin ƙaunar Meesherh ɗin tare da furta "inyeeeeeee ƴen Matan ma'ama ɗin ta har an gama shiryawa kenan? Wato irin an matsu abar nan ko?" Ɗan murmushi itama tayi tare ɗan jingina kanta a jikin Maah ɗin tana furta. "A ahhh Maah, papiey kaji ma ko?" Saman fuskanta me ƙawace da murmushi papiey'n ya dan shafa tare da faɗin, "Babu komi manana rabu da wannan Moh ɗin naki kedai Ubangiji ALLAH ya sauƙeku lafiya........ Da ameen ta amsa tama miƙewa tsaye gudun kada tayi lett jirginsu ya tashi, kiss ta mannawa Maah tare da papiey tana furta. "Thanks 💐 My humi darling friends" har compund na gidan suka rakata inda motoci uku ne zasu mata raƙiya zuwa airport. Bai ma san woinar da ake toyawa ba shigowan sa kenan ya hangi papiey da kuma Maah ɗin tsaye a compound na gidan har dama sauran tsirarin ƴan matan gidan su Nainerh Nanameerah da Salma, hakan ya sanya shi fitowa a natse yana me nufar inda suke tsayen ita kuwa harma ta shige car se Lugagge bag nata da Maah ke ƙoƙarin miƙa mata.da sallama ɗauke a bakinsa ya isa wurin cikin girmamawa yana gaida papiey'n tare da Maah data wani irin ɗauke kanta gefe, Amma duk da haka ne sanya Sheikh sake gaidata da ban ba, a fisge ta amsa da lafiya lou daga haka taja bakinta ta gimtse gamm. "Abba ko lafiya naga kamar wani abu na faruwa?" Ya tambayi papiey'n risine, ita kuwa tun kamin ya iso wurin zuciyan ta ya gama tabbatar mata da lallai shi ne tafe. Haka iyaka muryansa da taji seda kusan bugar mata da zuciya. Papiey ne ya bashi amsa da cewan "Meesherh ce zata je Lagos aiki kwana biyu...... Ai tun kamin ya karasa yaji zuciyansa ta wani irin yanka masa, Amma se ya daure yana dafa jikin car ɗin da already ta gama shiga ciki, cikin kamilallar muryan san ya furta. "Amma Abba loƙaci bay yiba daaaaaa...... Se kuma yay Shiru yana gaza furta sunan Babyn da yaso ambata. "Ba komi Habeebty tama kusa dena aikin nan kota kota Ni kaina a yanzu babban burina bai wuce ace yau naga me Sunan Mama ɗakin mijinta ba, wllh kullum raina ba'a konce ba inajin tamkar har yanzu akwai abinda yamin saura daga cikin rayuwan Meesherh ɗin" ɗan numfasawa yayi da niyan sake furta woni abu, Amma komi be ce ba Maah ta taryi numfashin sa ta hanyar faɗin. "Papiey lokaci na sake ja kar Sweetie ta missing Flight nata" Tayi maganan ne kuma tare da tura murfin motan.Idanunta da tun wanzuwar sa a wurin suke a kulle ta buɗe tana me wa motar key tana kanta da mugun speed. Wanda ya sanya papiey da Maah saurin runtse idanunsu duk a loƙaci guda domin kuwa ba zasu manta ba last driving nata ne wannan mummunan haɗarin ya faru da ita. Tashin wata motar da suka ji ne ya sanya su buɗe idanunsu a ɗan tsorace, Sheikh juraij suka kalla shi ma ya ɗebi nashi car ɗin da mugun speed da zama su iya cewa yafi nata. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya papiey yaja Maah kuwa ƙirjinta ta dafe tana son abinda ya taso mata ya koma. Isanta airport ɗin yayi daidai da lokacin da aka far kiran passengers da zasu tashi. Masu gadin wurin ta bama car key na motan ta. Tsakanin airport da Hotel ɗin da suka kama ba wota tafiya bace me zurfi. Tarɓa mai burgewa da aji akayima su Meesherh a Lagos ɗin tare da luxury masauƙin daya kasance Hotel ƴan wasan suka tanadar mu su,kasancewan ba ita kaɗai bace tare da wasu jarumansu ne harda ma ƙarin wasu fitattu guda huɗu daga kano uku maza ɗaya mace Queen beebee. Ita kuma a nata ɓangaren tana tare ne da Sadja se Bishop tare da London boy da ya kasance shi ne kamar babban yaronta kuma babban amininta a harkan kannywood ɗin dan idan Moh Ameern Saif baya ƙasar to kuwa London boy shike maye mata gurbin Moh, to se gashi ma baya ƙasar baki ɗaya kuma se itama hakan ya mata daɗi duba da irin yadda suke samun saɓanin tsakanin su. Duk wannan abin da ake idanunta na a lumshe ne tanajin yadda motocin da suka ɗakko su ke tsuga uban gudu a saman kwaltan. zubewa a saman lafayayyar kujerarn dake parlour'n ta na danƙareren hotel ɗin da suka kama tayi lumsansun idanunta na'a lumshe wanda suka ɗan canja launi kada, abubuwa da dama sun haɗu sun  mata yawa a kwakwalwarta ga kuma ƙarin tafiyan da yake tattare da gajiya. buɗe idanunta ta yi tana mai furzar da iskan bakinta haɗe da yamusta fuskanta, zuciyarta na son sake dawo mata da wasu emojis cikin kwakwalwanta, lumshe idanu ta yi ta shiga karanto addu'ar samun nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin zuciyarta _"Allahmma inni as'lukas sabbas fil amr, wal azimatu alar rushdi, wa as'aluka shukra ni'matika wa husna ibdatika,wa as'aluka kalban saliman wa lisaanan sadiƙan, wa as'aluka min khairi ma ta'alam wa a'uzubika min sharri ma ta'lam wa astgfruka lima ta'lam innaka anta allumul gayub"_ Sannu a hankali kuwa damuwan dake damun zuciyarta taji suna raguwa cikin kaso mafi rinjayen damuwarta. Daga nan ta miƙe a kasalance tana shigewa bedroom na room hotel ɗin, amma kafin tayi amfani da komai seda ta tabbatar babu damuwan komi irinsu cctv Camera's da wasu Hotel's din ke sanya wa. Daga nan ta faɗa tayi wonko tunda a daren za'a fara shirye shiryen yacce za'a fara gudanar da ayyukan haska Film ɗin. A daren ranar ne kuma da misalin ƙarfe 8:20pm suka fita zuwa dan shaƙatawa bisa jagoranci mutanen Lagos ɗin tare da rakiyan abokan sana'ar ta. A wani kyakkyawan ~*PLEX INSURANCE*~ suka yada zango, a ƙayatattun wuraren daya kasance na manya ne dama aka musu masauƙi, inda tuni jama'a dama tarin yan mata da ƴan samari suka kewaye inda suke zaunen, kowa cike da murnan ganin manyan jaruman hausa. bayyanar waɗansu haɗadɗu fitattun manyan motoci guda bakwai A farfajiyar Plex Insurance ɗin suna shigowa a jere ne ya sanya mafi akasarin mutanen meda hankalinsu kan tarin car's ɗin, kowacce motar kuma ɗauke da tint glass a jikinta yadda na waje bai isa ganin na ciki ba. Kafin kiftar idanu duka ƙofofin motocin suka shiga buɗewa ta hagu da dama. Kamar da kusan 5 minute wani bazaraten matashin chocolate ɗin guys ne ya sanyo sawayen sa woje tare da ziro fuskarsa dake sakaye da face mask woje. Daga yanayin suturan jikinsa kaɗai ya isa sanar maka ko shi ɗin wanene bare kuma azo kan yanayin yadda tafiyarsa take to anan ne kaɗai zaka gane shi ɗin wani ne ta fannin aljihu sannan kuma da alamun sun zarce shekarun samartaka. Tunda daga yanayin yadda zaratan soldier's ke kewaye dashi suna sanya shi tsaƙiyarsu. Haske daya haskake wurin ne ya sake sanadiyyar bayyanuwar irin kyawun da yake da. A jere kamar masu yin layi haka zaratan soldier's ɗin suka rufa masab baya har zuwa cikin ainihin wurin. Kanta sam sam ba'a wurin yake ba domin hankalinta yana ba'a wurin bane, Harya gitta ta gefensu yaji zuciyarsa tayi masa wani irin bugu, hakan yasa yau sanadiyyar tsaiwarsa chakkk a wurin daidai da lokacin da Meesherh ke ɗago kanta a natse da niyar yima Queen beebee magana. Shanyayyun idanunsa da kusan suke a lumshe ya zuba mata zuciyarsa na aiyana masa anya kuwa itace? Da hannu yama tarin soldier's nashi alaman su je. Shi kuma yana komawa da baya tare da tsaiwa daga seti da inda Meesherh ke zaune. Kusan a tare kowa dake wurin ya wani irin zaro ido alaman mamakin ganinsa a wurin. Sallama ya musu tare da ɗan ɗukawa daga inda take kyakykyawar chocolate Innocent face nashi na bayyanuwa ta hanyar janye facemask ɗin da yayi. Tare da furta "ALLAH yasa banyi gaggawa ko ko kutse a cikin daddaɗan yanayin zaiyi kyau wa Masoya, duk da kuwa cewan niba ba sabon masoyi bane a gareki Meesherh, domin kuwa wannan zuciyar dake manne cikin ƙirjin Ahmed xm ta kamu da SO da tsananin ƙaunarki a rana ta farko dana fara ganinki cikin wani Film na *GANSHEƘA* tun daga ranar wannan zuciyar ta kamu da wata kalar azabbiyar SO da ƙaunarki Ms Jedaans!." Wani ɗan iskan kallo ta jefa masa irin na ka kama kan kan nan kafin ta buɗi baki cikin muryanta me nutsuwa ba tarin hayaniya ta ce. "kai ɗin wanene? How dare you talk about my life menene haɗin ka da rayuwana Ms Jedaans?" Meesherh ta faɗi zuciyan ta na wani irin tafarfasa. tamkar yasan abinda ke kai kawo a cikin zuciyar nata se ya ɗan rage tsahonsa da yake da tare da furta. "Cikin gaggawa haka Cwty?..... Yay maganar kyakykyawan murmushi shimfiɗe a saman lafayayyar fuskansa, wanda hakan ne ya bama Meesherh mamaki tare da ɗan runtse idanunta kaɗan cikin salon da yafi kama da lumshesu tayi kana ta buɗesu kai tsaye tana zubesu saman fuskar matashin Chocolate beauty ɗin dake duƙe a seti da inda take. Shi kuwa yadda ta tsaida fararen idanuwan tan cikin tsaƙiyar nasa idanunn ne ya sanya shi janye kallonsa daga gare ta. Wani irin kwarjininta me tarin yawa na bebayeshi karon farko kenan da ya fara jin irin haka kaf tsayin rayuwarshi mace ta masa kwarjini, ɗan numfashi ya fesar kyaunta a zahiri na sake kashesa domin kenan ita Camera's na ƙarama wasu kyau to yau yaga ainihin inda Camera's ke rage kyaun mutum shida akan Diamond Meesherh Jadeens yayi imanin a irin kyan da ALLAH yayi mata ba kowanne namiji bane zai iya tunkararta da sunan Love. "I'm so sorry Cwty mebi banzo a loƙacin daya dace bane dan haka ki tsimayi dawowana gareki a ko wanne loƙaci" ya faɗi hakan ne yana ajje mata rafas na Dollars. Yana ɗara wurin Sadja tayi saurin motsowa kusa da Meesherh ɗin tana furta. "Ahmed xm Mahmoud Abbas kin san waye shi kuwa? Ai nasam Sadja ta jefa mata tambayar cikin kwantar da murya da salon da babu maiji sai su ya su. Tamkar ba zata tanka mata ba sai kuma ta motsa laɓɓanta a hankali bayan ta kafe Sadja ɗin da idanunta kyawawa. "Ban damu da nasan koshi waye ba! Haka kuma bana buƙatar na sani ɗin Sadja right?" Ta yi maganan a sadda take janye idanunta akan Sadja ɗin. "Amma gaskiya kyautu ace kin disga mutum kamar Ahmed xm Mahmoud ba....." Ta gaji da saurarn zancen Sadja ɗin da haka ya miƙe tsaye tare ɗaukan pakega na Chocolate peanut brittle. Inda kyakykyawan farar ƙafarta dake fes ta bayyana.....      _Wannan labari ne da kuka daɗe ba kuci karo da irin sa ba, don kuwa wannan labarin ƙaddarar ne akan wata irin soyayya me tsayawa a zuciya da kuma saka shauƙi a duk a zuƙatan masu karatun amma fa bayan mun gama shan ubanmu ato kaidai kawai abinda zan iya cema shi ne kawai tsammaci abin da baka tsammata ba inji malam bahaushe. Don wannan karon ma AMMEY'NKU tafe take muku da wani salon Rubutun na musamman💐💐💐💪 Heart beat♥️ Heart attach💔 Heart broke 💘_ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 23&24 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfan xz iti da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Waɗanda suke buƙatar samun litattafan *AMEEY LAYLERH* za ku iya shiga shafin ta na Telegram don samun su kai tsaye daga wurin ta. Ga link nan ga masu buƙatar shiga 👉https://t.me/ammeylaylerh_novel ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Ɓangaren su Aysha kuwa tare da Rumaisa me napep ɗin nan na sauƙe su sukai cikin gidan su Rumaisa ɗin kai tsaye. Da aunty'n Rumaisa suka fara cin karo se kuma baby'n Nuwaira. Cike da murmushin jin daɗi suke kallon Aunty ɗin tamkar yacce baby'n Nuwaira ke kallonsa da murmushin itama. "ALLAH yayi aure da mara kobo dai Aunty Amaryar mu🤗 fine dai Diamond Meesherh Jedaans ta amshe mu da hannu bibbiyu ba tare da duba da yanayi ko suturar dake jikku nan muba,ganan ma harda ƙarin tsaraba" Aysha ta faɗi take dama ba'a kasheta a zance a kwana ƙalau bare ayi tunanin zaunawa lafiya. Woyoyin hannuwan nasu dake bi da kallo da kuma uban kuɗin da ya kusa tashin kanta. "Bara ki kalla Aunty gudun kokonta" Rumaisa ta faɗi kai tsaye tana buɗe wayanta tare da shiga cikin Mx pleyar nata dake pisc da video's ɗin da Meesherh tayi tare da sune kaɗai ya sanya bama tasha woni wohalan nema ba da pisc ta fara tun a na farkon Aunty Amaryar ta wani kalan zaro ido woje tana toshe bakinta da hannuwanta alamaun mamaki me girman gaske na ratsata. Haka ta ci gaba nunnunamata har zuwa kan video's ɗin da duk ta musu. Wani ihun tsalla baby'n Nuwaira ta saki tana furta "Yes wllh taci sunanta wato *SPECIAL* _TA DABAN_ kenan kalla nima a yau na zama shaidar hakan don kuwa ganau ce ba jiyau baaa...." Daga haka ta falla ana kare zuwa gidan su Aysha ɗin tun kafin ta isa. Nan ma da ihun murnan ta isa Umman Aysha ɗin wacce ke alwulan ƙiran magriba da taji an fara yi a wosu masallatan dake kusa. Miƙewanta daidai da loƙacin da Aysha da Rumaisan na shigowa, itama nuna mata sukai wanda hakan ya wanzar da murmushi kwance saman fuskarta me taushi. "Ubangiji ALLAH ya bata abinda take nema duniya da kuma lahirarta! Ya kuma saka mata da gidan ALLAH mafi tsada ya kauda ita daga duk wani sharri dake shirin tunkarota ko wanda suke tare da ita badan ALLAH ba, Ubangiji ya biyata da mafificin Alkhairinsa tamkar yacce itama take Alkhairan wa mutane" duk da amenn suka amsa suna jin ƙaunar Meesherh ɗin na sake kanainaye ko ina na cikin jikinsu. Alwalan itama Rumaisa ta kama ita kuwa Aysha dake fashin Sallah ƙasan bishiyan dake tsakar gidan ta nema tana zama. Deta nata ta kunna kai tsaye tana buɗe Gmail address tare da shiga cikin pley store nata, kai tsaye app's ta shige sauƙewa wtsp lite se Tiktok da dai sauran app's masu muhimmanci. Tiktok ta fara bude da nem account nata inda ta buɗe da *ƳAR LELEN MEESHERH JEDAANS* haka ta ringa buɗe app's da sunayen ƴar lelen Meesherh ɗin har zuwa kan wtsp nata. A kuma duka dp profile nata pisc nata tare da Meesherh'n take sanyawa. Se bayan data gama seta komai tayo send's na duka abubuwan ta zuwa new Phone nata samsum galaxy me shegiyar camera kamar me. Ɗora duk wasu pisc da videa na Meesherh ta fara ta ringa post har zuwa kan wanda sukayi tare. Wanda hakan ya ɗauke ta ɗan lokaci me sawo. Cikin ƙanƙanin lokaci Aysha ta sama mabiya sama da dubu biyu da wani abu, wai ma hakan iyaka yau kenan seya school Meta nata wanda a da suke discount nata nata following nata ciki kuwa harda masu ƙarfin halin mata magana. Ita ma Rumaisa buɗe komai tayi sedai ita da sunan Rushuna person ta buɗe tare da baza pisc da video na Meesherh. Dan da nan itama se gata a media tana shawagi. Cikin ƙanƙanin lokacin yaran suka yara wasu mahaukatan FAN'S su kansu. ꨄ Zaune take kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun dake jere a gaban Railer'n Hotel ɗin ta harɗe ƙafafunta tana ɗan duba ipad nata fuskarta se hasken ipad ɗin ya sake haskaka kyakkyawar Innocent face nata. Cikin takunsa na ƙasaita yake tunkaro inda take zaunen idanunsa lumsassun nan na yawo akanta wanda suke a janye se kuma hakan yamai yanayi da kamar yana jin bacci ne baƙin sajen daya gama sake ƙawata kyakykyawar chocolate fuskarsa kyau yana nan kwance luff-luff haka ma bakinsa da hancinsa  mai kyau wanda ya dace da fuskar sa, sanye yake cikin jeans da riga masu kyan gaske designers,tinda ya tunkaro inda yake ta ɗauke kanta a gareshi, Ta inda ta juya kan nata ya juyo yana ɗan rankofowa gareta kafin a hankali cikin dakakken sautin sa me class yace. "Cwty barka da hutawa!" A fusace Meesherh ta miƙe daga zaunen da take  ta ce " Wai kai wane irin banza ne mara hankali daƙiƙi mara aji?, Idan kai baka da tunani me kyau ne to inason daga yau kayi gaggawan fita a cikin rayuna all of you. Ko kai a naka daƙiƙin tunanin zaka iya ja da Meesherh Jedaans ne?" Nose Mask na shi da kusan ya zama shi ne ɗabiansa ya zame jajayen tausasan laɓɓanshi masu wani irin ɗaukan hankalin mace na bayyana haɗe da tsayayyen hancinshi.fararen shanyayyun idanuwanshi ne suka ɗan rine ruwan hawaye na taruwa a cikinsu na ɓacin rai, sedai tsananin SO da ƙaunar da yake mata shi ya gaza bayyana ɓacin ran nasa bayyana. Hakan ya sanya a mugun fusace ya kaima iska naushi cikin tafasarn zuciya yana barin wurin baki ɗaya. Duk ma se taji baki ɗaya garin na fita a ranta iyaka jiya da yau kaɗai. Wanda kuma a yau ne dama za'a haska Film ɗin wanda ya kama da gobe kenan zasu koma gida. Wata nannauyar ajiyar zuciya take sauƙewa sanda ta gama tabbatar da cewan ya bar wurin. Duk wani shiri akan lounch Film ɗin an gama hakan ya sanya ƙarfe 8:15 na cika daidai duk wanda yake a cikin list na lounch Film ɗin bayyana, ciki kuwa harda ita uwar gayyar. Tsit kowa yay baki ɗaya suna maida hankali da nutsuwansu akan Gellary Odyssey screen ɗin dake shafe da bangon wurin. Tunda suka fara kallar Film ɗin wani kalan shauƙi shauƙi ke ɗiban masu kallon. Wani kalan gentle classic life aka shimfiɗa a cikin Film ɗin wanda haɗewa da kyansa har ya gama yin yawa. 12:20 cif cif aka gama kallar Film ɗin inda wanda sukay lounch na Film ɗin suka suka Bama Meesherh kyauta na wasu mahaukatan kuɗaɗe maƙudai na tashin kai, sedai ita a gareta ba komai bane domin ko ita kanta tana iyama mutum kyautan nin kuɗin sau goma ba tare data ko girgiza ba. Tun a daren dama an gama tanaja musu komi na komawa wanda tafiyan nasu ze kama ne se yamma bayan an sake tattauna akan Film ɗin da kuma yacce za'a sake shi kai tsaye a duniya. kwanan su uku a Lagos ɗin suka tattara suna barin Lagos zuwa kd kai tsaye ita daga gida masu shegun bugaggun manyan car's guda uku ne suka zo suka ɗauke ta se gida. A cikin gidan kuwa su Ummeterh ne tare da sauran ƴan matan gidan suka shiga murna da ɗan ƙaramin shagali na dawowan Meesherh Jadeens lafiya gida. Bayan sun gama murnan first abinda ta fara yi shi ne Wonka,daga nan ta fito akayi diner duka daga can part nasu Ama ta nupa kasancewan dama su ba kullum bane suke fitowan. A zaune ta tarar da Ama ɗin ƙafafunta mike turaki na daga gefenta shima kishin giɗe. Tana zuwa ta rungume turaki tare da gaida su cike da tsantsan SO da ƙaunarsu tana kwanciya kan ƙafafun Ama ba yanda zata sakar mata nauyinta ba. Albarka da adda'an dacewa da kuma gamawa da duniya lafiya Ama suka shiga mata tana amsawa da ameen daga nan ta nasu tsaraban da tazo musu dashi. Wani irin rass haka taji ƙirjinta ya buga dan Sosai tayi ƙoƙari wajen mantawa da Sheikh ɗin. Kuma Alhamdulillh sosai se ta manta dashi dama auren nasa baki ɗaya tana mantawa dasu tun a daren ranar data bar kd. Cikin nutsuwa da kuma kwarjinin ya kutso kansa cikin parlour'n cike da wani irin majestic takunsa. Tinda ya tinkarota parlour'n taji numfashinta na fita da sauri bugun zuciyarta na ƙaruwa ahankali idanuwanta na kasa ɗaukewa daga kansa, Wannan nutsatstsen ƙamshin nasa mai sanyin daɗi da kai tsaye yake tabbatar da tsadarsa a shaƙa ɗaya na gwamewa da sanyin ac/n daya taho da ƙamshin nasa kai tsaye yana shige mata hanci yana sauya numfashin main babban palon gaba ɗaya da kamshinsa. Sake buɗe kyawawan idanuwanta a kanshi tayi tana kallo tin daga fararen yatsun ƙafarsa dasuke wani irin fes kaman baya fita dasu sanye cikin versace shoes. Yana sanye cikin shigar lallausan cashmere fuskansa datake wani irin fresh na sake shining. Hannuwansa dake cikin aljihun cashmere ɗin jikinsa ya zare Cikin sakewan fuska dake tafe da girmamawa ya furta. "Ama barka da dare" Yana zaunawa bayan yama inda take kwance kallo ɗaya yana ɗauke idanuwansa akanta, sakamakon raight jeans ɗin daya lafe jikinta da white Cardigan ɗin dake jikinta masu kauri. Janye idanunta itama tayi ahankali tana ƙoƙarin danne ganinsan da tay. Wani numfashi me ɗan nauyi ta haɗiye tareda danne ruɗewanta tana sanya dogayen yatsun hannunta farare tana kare fuskanta. Duk da yacce zuciyan sa ke sake ingiza shi akan sake kallon nata amma samm ya ƙiyama hakan tunda yasan haramcin kallon daya fiye ɗaya tattare da hakan. "Ƴar lelen pa'apahh'nta banji kin gaida pa'apahh ɗin naki ba?" Ama tayi maganan da biyu don son ganin reactions na kowa a cikin su. Shi idanunsa yaja yana lumshewa ita kuma tana saurin barin parlour'n a mugun guje. Wanda hakan ya saka wani Kyakkyawan murmushi kwacema tsoffin biyu dukansu don kuwa duk ɓoye ɓoyen da kowannensu keyi akan kowa an kare suke da hakan. Kuma dama alƙawarin Aure ne tsakanin su sedai duk sanda suka so bayyanar da maganan se woni abu ya faru mara kyau koma suji suna mantawa da zancen amren. *Down town mall* Akai Akai take yawan duba hanyar mall ɗin da sama da 50 minutes. Wanda kai tsaye Aunty Ummeterh ce da take shirin komawa garinda da take da aure tace Meesherh ɗin ta kaita mall don ALLAH. Tun da ta kawota taƙi motsawa ko ina wanda ada zaune take a cikin car ɗin saɓanin yanzu da take jinge da jikin car nata. Sanye take da wata tattausar exclusive atamfa da bata tara yawan tarkacen kololi ba,hatta da zanen jikinta kuwa baida wata hayaniya sosai SO simple ne, Sai kalolin da suka dace da yanayin jikinta da aka raɓama atamfar, ɗinkin doguwar riga ne daya buɗe sosai daga ƙasa,daga saman kuma ya zauna mata cas kamar dama can don ita kaɗai aka halicci atamfar dama ɗinkin jikintan gaba ɗaya. Ta lulluɓe kanta da wani madaidaicin mayafi wanda yayi set da kalan shigan dake jikinta, Amma duk da hakan sai da Wannan kwantaccen gashin dake zagaye daga gaban kanta ya fito luf luf abinsa,wanda duk bayan minti ɗaya zuwa biyu take sanya zara zara yatsun hannunta tana jan mayafin tana sake rufe gaban kan nata da kyau, domin ita ba mutum bace me son bayyana gashin kanta wai don ado ba. Wannan hali nata na tsantsan tsare dokokin ALLAH shi kaɗai ke sanyaya zuciyan duk woni Masoyinta dake mata soyayya ta don ALLAH. Wasu lafiyayyun plate shoes ne a ƙafarta Heels masu shegen kyau da matuƙar tsada mahaɗin ƙaramarn handbag ɗin dake a hannunta ne wanda suke mahaɗin company guda na Dior lv. Tana tsaye jingine da jikin car nata hannunta ɗaya na riƙe da wayanta amma duk da hakan bai hanata harɗe hannayen taba a ƙirji, kyakkyawar fuskar nan babu digon fara'a ko kaɗan sai ma ɗan ƙaramin bakinta da take motsawa kaɗan bada yawa ba, alamun dake nuni da cewan magana take yi amma kuma cikin bakinta dake mamulawa. Har yanzun guri ɗaya idanuwanta suke kalla ba tare data barsu sun gusa da kallon wurin da take ba har ranta na neman ɓaci, domin a rayuwanta abu mafi muni da tafi tsana shi ne wasting time. Wanda take jin wllh badon Ummeterh bane da tuni ta bar wurin shi yasa ita samm bata sayayyar kai tsayen nan tafi son komai tayo oder nashi tana kwance daga cikin gidansu. Cikin abinda bai wuce 20 minutes ba sega wata rantsatstsar black RR car nan ta shigo cikin wurin. Wani irin harbawa taji zuciyanta yayi a take hakan yasa bama tasan lokacin data lula Duniyar tunani ba, Sai kawai wannan unique ƙamshin da tun garkon haɗuwansu na farko ta gaza mance kalansa ba ne ya bugo yana kawo mata ziyararn kai tsaye. ɗago idanuwanta masu kyau tai tana kallonsa. Sanye yake da Ash balmains na wata crazy shirt me shegiyar tsada da straight wando sai tsadaddun cover shoes ɗin dake ƙafarnsa na ballies wanda kodan yawan sanyasu ɗin da yake ne ya sa kai tsaye zaka gane cewan shi ɗin soldier ne. ɗauke kanta take son yi daga face nashi, sedai ta gaza hakan don wani irin sabon kyaun da take daɗa iya kalla me kyau, wanda kyaun yafi yanayi da irin morning beauty ɗin nan ko ko dai muce morning freshness. Duk yacce taso ɗauke kanta daga kallonsa gaza hakan tayi domin kuwa fin ƙarfinta zuciyarta tai ta kasa ɗauke fararen idanuwanta akansa tana masa wani irin kallan da ita kanta bama tasan tana masa ba. Shi kuwa tunda yay tozali da kyakkyawan face nata tsananin azabtuwan da zuciyarsa yay akan sonta da yaƙi barin Heart nashi ne ya sa ya kasa ɗauke idanuwansa daga gareta harya yana ƙoƙarin loosing control nashi gurin bayyanar da hakan har idanuwansa nason cikowa da wani abu da yafi kama da hawaye kai tsaye. Fitowan Aunty Ummeterh daga cikin mall ɗin ne ya katse shi daga buɗe bakin dayay da niyan mata magana ita kuwa Aunty Ummeterh'n ba tare da tama lura da wanda ke tsayen ba ne ya sanya tace "I'm so sorry bestie mun tsaida k...... Se dai bakinta yay shiru ganin wani a tare da Meesherh ɗin, hakan ya sanya ta naɗe sauran maganan datay niyan yi ɗin kuwa. Shi kuwa Ahmed xm kallo ɗaya yama Ummeterh ɗin ya fahimta cewan Aunty nata ne don haka cikin wayewa da class me aji ya gaida Aunty Ummeterh'n tana amsawa tare da kallon Ummeterh ɗin tana furta. "Meesherh wannan kuma fa?"Cikin basarwa ta furta "Ban sani ba aunt nima kawai ganinsa tsayen nai kamar yacce kika ganshi" Tayi maganan tana mai sake ignoring nashi Dawn. ꨄ *Sheikh juraij* Farkawan kenan daga baccin bayan la'asar ɗin data konta hakan ya sanya ta tashi a ɗan hanzarce don sanin yanzu duk inda yake ya dawo. Duka ɗakunan gidan ta shiga dubawa sedai babu shi hakan ya sanya ta leƙa compound, sesai ganin car nashi daya fita da itane ya sanya ta sake komawa tama sake dudduba sauran ɗakunan. Da kyar ta sama ganinsa a cikin wani Master bedroom nashi tayi masararn samun shi wanda yake kwance kan tsakiyar Raoun bed nashi me tsananin laushin da kai tsaye idan mutum ya kwanta yake yin luf ya lafe cikin bed ɗin. Kana sanya ƙafarka kuwa a cikin parlour'n abu na farko da zai fara maka maraba, Shi ne sassanyan ƙamshin turaren da humidifier ke bayarwa. Wani gajeren numfashi Samha ta ja yana nufar kan bed ɗin. Har zata tashe shi se kuma ta tuna da ya hana mata tashinsa se kawai ta juya bayan ta gama bin jikinsa da mayen kallon da bata sama gani ba dake lulluɓe da dubet tabar room ɗin. Shi kuwa ashe duk abinda take yana jinta kawai ya sama kan sane a wani yanayi na daban wanda tun jiya Meesherh taƙi barin tunani da kuma kansa. Inda yaki wani mayen feelings nata kamar ze kashe shi amma ya danne hakan. So da dama har gani yake kamar shiya ɗorama kansa hakan na rashin feelings ko wacce macen dake duniya se ita kaɗai. Gani yake kamar ALLAH se iya tashinsa da laifi akan hakan, wanda a daren jiya bayan ya dawo shi da kansa yake har room nata da niyar kasancewa da ita tunda yaji feelings nashi ya motsa. Sedai tamkar abin asiri yana shiga room ɗin nata kallo ɗaya kawai ya mata yaji farar ɗaya feelings ɗin na ɓacewa ɓatt. Wanda hakan yaso tashin hankalin sa sosai domin yana tsoron ALLAH ya kamashi da hakkin Samha a kan sa, Shi ne abinda ya hana shi fita duk a ranar yau ɗin. Kuma da ko tuna sunan Meesherl ɗin yayi se yaji abun ya motsa masa kamar ya karshi. Bayan fitan ta da kamar 15 minutes ya miƙe a natse bada garaje ba yana faɗawa cikin toilet. Kayan dake jikinsa ya zare lafiyayyar farar fatarsa na bayyana tana ɗaukan ido saboda samun hutu da tsadaddiyar gyara da original skin products masu tsada da kyau da yake amfani dasu. shower ya sakarma kansa ruwan dumi yana rufe idanuwansa ruwan na sauƙa akan fuskansa suna ganganrawa jikinsa suna dumama jikinsa a hankali. Ya jima sosai sosai yana wankan kafin ya fito ɗaure da babban towel me kauri brown jikinsa na fidda ƙamshin shower Soap ɗinsa na Ocean seaweed. Da Mini clean blue towel ya shiga tsane jikinsa a natse. kafin ya shiga shafe jikinsa da bodymilk da mix na oils na diamon dia da suke saka jikinsa glowing da kyan gani da wani irin soft ya shafa perfs dasu bodyMist da sauransu, kafin ya gyara fuskansa yai brushing gashin kansa dayake a kwance da santsi irin na asalin ustazan larabawa. Bai woni ɗauki loƙaci ba sosai ya shirya kansa cikin wani brawn cashmere daya nutsu a jikinsa saboda tasan kuɗin da ya lasa. A cikin tarin tsadaddun designer agogayensa dake jere a doguwar glass drawer'n ya buɗe yana ɗaukan ɗaya ya saka a hannunsa da gargasa ke kwance luf luf gwanin birgewa. A natse ya fito shirye fess zuwa ainihin parlour'n sa da ko ina a parlour'n yake neat ba hayaniyar komai a parlon komai is so gentle unique simple and luxuries ne kawai ke magana a parlour'n kawai. A babban parlour'n ya yada zango yana ɗaukan ipad nashi ya shiga duba jerin schedule ɗin da aka turo masa ta cikin Gmail nashi. Anan yaci karo da bayanan da ya bada cikin sirru a duba masa dangane da accident ɗin daya faru da Meesherh. Duba komai yayi zuciyan sa na ƙona ganin sunan Moh Ameern dumu dumu a cikin jerin list na wanda aka lissafo masu hannu a cikin case na accident ɗin. Idanunsa yaja yana lumshewa abinda ke ƙoƙarin taso masa yana maidasa da ƙarfin adda'a. ꨄ Kwanci tashi akace asaran me rai haka Ahmed xm ya dinga bibiyan Meesherh har seda ta fara kulashi, wanda cikin ƙanƙanin lokaci wata soyayya me zafi ta shiga tsakaninsu su. Amma yasha fama tabbas ba laifi don wai duk dan ya guje mata har Matsalan ta da In banda su Family'n babu wanda ya sani seda ta faɗin meshi cewan barata taɓa haihuwa ba. Amma amsan daya bata shi ne dalilin daya sanya kai tsaye ita kuma ta buɗe masa zuciyan ta. "Meesherh be wai haihuwanki ko rashin haihuwan ki nake SO ba ke zatinki nake SO har cikin zuciya da ruhina kuma na yarda in aure ki a hakan in yasa mu mutu hakan ba tare da tunanin samun haihuwa ba Cwty..." Wannan maganan nashi dama wanda yakan faɗin mata makamantansu sune suka rinjayeta a kansa. Wanda yakai a yanzu har gidama amsan da maganar Ahmed xm ɗin. An kuma saki Film nata a duniya wanda yaja wani irin ƙura a duniya don kuwa duk inda ka gilma maganar Film ɗin ake wanda ya fita da wani irin zafi na garari. A wannan karon kamm har gida Jedaans Aysha suka zo suka kawoma Babbar Role model nasu ziyara. Inda suma suka zama manyan yara sosai wanda a yanzu suke yawan ganin Meesherh ɗin akai akai. Suma kansu sunan su wani irin fice yay a duniyar gajimare. Wanda suke nasu video's ɗin suna ɗaurawa amma ba wanda zeja magana ba masu nutsuwa suke yi cikin aji. Kowa yana da salon nashi masoyan wanda idan ka leƙa shafin Aysha se kaga kamar tafi Rushuna person sunan, itan ma da ka shiga shafin Rushuna person ɗin saka kalla tamkar ma tafi Aysha ɗin suna. Wannan abu ma daɗa Hargitsa masoya mabiyansa. Kasancewar shirye shiryen azuma ya gabato ya sanya uncle El-muaz da Uncle jamaal Jedaans dawowa Nigeria wanda duk shekararn duniya haka suke a gida suke azumi da kuma sallah. Inda dawowan nasu shi ne ya zama mabuɗin komai cikin sauri amma ba irin na garajeba. Dan kai tsaye a cikin ƴan tsakanin Awwb El-muaz Jedaans ya bayyana soyayyar sa ga Meesherh wanda dama sosai yake sonta amma ganin kamar da wota alaƙarn soyayya tsakanin ta da Sheikh juraij ne ya sanya shi kin bayyana mata love nashi. Amma da suka zo wannan zuwan se kawai ya buɗe mata zuciyan sa wanda ita kuma a lokacin da riga ta kamu da love ɗin Ahmed xm. Amma da akace jininka duk inda yake jinin kane se cikin ƙanƙanin lokaci ya rinjayeta akan soyayyar sa me tsafta da yake mata. Wanda tama iyayen dadi dan kuwa dama kowannensu auren Meesherh ɗin yake da burin ganin. Se dai wani matsalan da kai tsaye aka samu shi ne mahaifiyan Awwb ɗin Mum Khadija don kai tsaye tace bata yarda ba ba kuma da yawon taba. Da me yasa tun a azziƙi basu bashi auren Meesherh ɗin ba har se data sama matsala akan haihuwa a sannan ne kuma za'a liƙa ma ɗan ta to wllh bata yarda ba. Shi kuma El-muaz Jedaans Turaki ya ce mazawar ta hana auren Awwb El-muaz Jedaans da Meesherh Sameer Jadeens to taje itama a bakin nata auren. Sosai hankalin mum Khadija yake a tashe wanda take cike da tsabar baƙin ciki da takaicin zuwansun Nigeria'n kasancewan ita ƴer cen Islamabad ɗin ce. Alhamdulillh kuma haka aka shiga watan azumi lafiya cikin salama da buwayer Ubangijin al'arshi. Wanda kuma kai tsaye aka tsaida maganar auren bayan salla da sati ɗaya, ita kanta Maah bawai tana son auren ba har ma se tabi jin kwara Ahmed xm ɗin akan duk Family'n JEDAANS ɗin. ALLAH Sarki shi kuwa bawan Allah yana can bama ya kasar yana cen ƙasar saudia. besan wainan da ake toyawa ba. Dake komai na alaƙansu bawai sauyawa yayiba komai na alaƙansu nanan sedai ta gaza sanar masa da abinda yake faruwa domin wani mugun tausayi taji yana bata. Haka kwanakin azumin ke tafiya ayi ba ayi ba har kaci karfin watan azumin wanda mafi yawan dake ribanta da irin yadda wannan shahararren malamin Sheikh juraij thabit Jedaans duk wani masoyi bemin fejin nashi dama wanda suke samun tafsr nashi basu son watan azumin ya ƙare. Domin wata irin nutsuwa ne ke zaunar musu da kuma karuwa daga irin yadda yake farke gaskiya akan komai ya kuma dilmiya masoyansa ji da son kasancewan Ina sune shi. Dan kallon ɗan baiwa haihuwan Sa'a kawai suke mai.inda iyaka aikin ladan da yake bazama jama'a kaɗai suke ƙara rikicewa akansa da ƙaunar sa. Banda gidajen marayu gidajen marasa ƙarfi kai dama kowa da kowa. Dan kawai ribata da watan me tarin falala da tarin alkairuka. Kuma har zuwa wannan lokacin babu abinda ya shiga tsakaninsa da Samha wanda a cikin watan azumin har kukansa yakai wa mahaliccin sa akan ya bashi feelings ɗin da zai iya fuskantan matarshi Samha ɗin. Kuma yanzu sosai yake ƙoƙarin ganin ya faranta mata kuma ƙoƙarin janyo ta jikinsa wanda wani bin har kwana sukanyi tare amma ba tare data taɓa kallon ko satin cibiyoyin sa bane bare kuma jikinsa. Ita kanta yanzu duk wani rawan kai nata se ta nema shi ta rasa ga uwarta data sako ta gaba akan lallai tasan duk yacce zatai tayi ta sama ciki ko cikin watan azumin nan ne. Sedai takai ta kawo woyar mahaifiyanta ma ta dena dauka a takaice don wllh ita tama fara gajiyawa. Sema kawai taji auren Sheikh din na fita a kanta. Wanda take jin tana gan da zuwa ta bayyana ma iyayensa cewan shi ɗin ba cikakken namiji bane in yaso komai ze faru ya faru. Se shima sannu a hankali ta fara janye masa wanda koba komi se hakan ya masa daɗi. Gefe guda kuma har yanzun yana nan akan case na accident ɗin Meesherh,wanda ya gama kammala komai akan case ɗin bayan sallar yake jira akan ya dokasu a kotu. A ranar da aka kai azumi na ashirin cif a ranar ne Prof Sameer Jedaans ya bama Sheikh juraij waliyyin da zai ɗaurama Meesherh Jadeens ɗin aure. Wanda iyaka waliyyin da aka bashi Anniey ta ringa surfa balai da masifan hakan har seda itama daddy ya taka mata birki kana ta shiga hankalinta amma kuma bawai ta haƙura tana ji tana gani a kaƙaba ma danta waliyyin auren Meesherh ɗin bane........ _ALHAMDULILLAH,ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH 🙏 🙏!!! Anan zamu dakata a book One na wannan littafi mai suna TA DABAN sai kuma Allah ya haɗamu da masu rabo a book two_ ★Tofa masu karatu yaya take ne?. Ni dai AMMEY LAYLERH nace lallei akwai kallo gaba_ _don tabbas Sheikh juraij zubama kowa ido yay ya gama tsalle tsallensa ya aiwatar da shirinsa da ya jima da kullawa_ _to ku a ganinku meke shirin faruwa ne wai......?_ _Shin ya kuke tunanin zata kaya tsakanin Anniey da kuma Sheikh juraij,gefe guda kuma ga Diamond Meesherh ɗin mu?_ _Mike shirin faruwa?, Shin wanda tsalle tsalle ne Sheikh juraij ya barmu mu gama ya aiwatar da shirin?_ _★Magana fa ake ta aure sora befi 3 weeks ba Amma kuma hhhhhh Meta fharu Bara dai nai shiru?_ _★Hhhhh masu karatu akwaifa gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon shima. Hargitsi da cakwakiyar dake cikinsa kuwa ai ba'a magana wanda a da naso labarin ya kasance dogo kamar MIKIYA amma kuwa wasu abubuwa dana hango ya sanya ni yanke labarin yadda zefe shigar masu karatu, don wani lokacin ma yawan dogon rubutun kan gundira Reader's koba haka ba?_ _★Kai kar dai na cikaku da surutu ku shirya kawai tsaff domin warware muku zare da abawar dake cakude cikin wannan littafin_ _Duk zamu samu amsoshin wad'annan tambaya idan mun shiga book 2 da yardar Allah. Nan muka kawo k'arshen BOOK 1 NA SPECIAL Ta daban Wanda basu biya ba su hanzarta don kar ayi tafiyar babu su littafin TA DABAN Naira 500 ne kacal babu yawa_ _Ga duk mai son biya zai tuntuɓeni a wannan number_ 👇 08104493215 Wanda suke sun biya zasu turo kuɗin su cikin wannan asusun bankin 👇 3206656358 Maryam Nasiru First Bank A turo shedar biya ta wannan number 08107880451 *_Kardai ku manta this one ma is not for free zaku Antayo darinku biyar ta Asusun banki na 3206656358 Maryam Nasiru first Bank ko katin mtn ta wannan number 08104493215 vip suma is 700 kamar yanda kuka sani masoya I no kuna bani goyon baya fiye da yanda nake tunani don haka ina ma kowa fatan Alkhairi don haka kar ku tsaya jiran ayi posting a sato muku na BABA NA BATI ku Antayo kuɗin ku karanta Cikin farin ciki da salama yanda kuke so sai najiku masoya karku sake ayi tafiyar PART 2 na SPECIAL BA TARE DAKE BA HAJIYATA by AMMEY'N LAYLERH'NKU me ƘAUNAR KU FAKA FAKA_* _wanda a da naso littafin ya kasance ne akan 1k amma ganin na rage labarin ne ya sanya ni barinsa a 500 kacal_ *Byeeeeeeeee my Re@l f@ns sai mun sake haduwa a cikin PART 2 gamai Rabo. Dan koda kuɗinka Saida rabonka littafin TA DABAN ba hhhhhhhhhhh To ai shikenan sai a gimtse koooo?_ _A gimtse kawai baaaaa._ _ Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels