Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels 🥺🥺🥺🥺🥺🥺 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s . w . t .a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* TAƘABBALALLAHU MINNA WAMIN KUM INA MUKU BARKA DA SALLAH ALLAH YA KARBI IBADUN MU ALLAH YASA MUNA DAGA CIKIN WA ANDA AKA ƳANTA CIKIN WATAN RAMADAN MAI ALBARKA🤲🤲🤲🥰 ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* *page 1* *BATSARI* ƙaramar hukuma ce dake jahar Katsina, garine dake dauke da ƴan boko!, mafi yawancin yan garin suna da ilimi sosai na addini da na zamani. so! suna gabatar da rayuwar su abin sha'awa, dan komai sukan yi shi cikin wayewa... a ƙofar wani matsakaicin gida naga wata matashiyar budurwa, dake tsaye da wani dattijo, da ke ta faman washe haƙora, kamar gonar audiga, yana kallonta kamar ya haɗiye tah, sai kace tsohon maye...... yanayinta kaɗai ya isa, yasa a gane basan tsayuwar take ba. dan da dukkan alamun ma tsoron shi take ji. juyawa baya tayi da sauri , tana mai shigewa cikin gidan kamar zata kifa, dan saurin da take. cikin yanayin kaɗuwa da ɗaga murya take cewa... "innarmu!!! innarmu!!! innar....... " "ke da Allah minene,? kin dameni da wani kira sai kace tsohuwar makauniya.." cewar wata dattijuwa da tafito daga ɗaki, tana wa budurwar da ta shigo gidan, tana faman ƙwala mata kira. kamar wata ƙaramar yarinya... dattijuwar ta cigaba da cewa "haba Asma'u yaushe zakiyi hankali ne, kullum kina girma kuma kina ƙara sakarcewa.." "uhmn.. wllhi innarmu wancen Alhaji Tankon da yazo..., nidai bana sonshi wllhi, in yayi dariya fa kamar wani gwaggwan biri.., ke dan ma baki ganshi ba!!, amma ina zankai wannan tsohon banza.." Asma'u ta faɗa tana mere bakinta.." inna da ta gama ƙuluwa da al'amarin Asma'u, tama rasa mai zata ce mata, can sai ta nisa tace "Asma'u kenan,.. ina lafin wanda yace yana sonki, kuma mah ni wllh banga wani muni da Alhaji tanko yake dashi ba,. kawai de ke kice bakya sonshi ne, amma ba sai kince haka ba.." inna saida tayi ajjiyar zuciya tukun ta cigaba da cewa " kinyi kuskure da har kike jin a wannan shekarun naki, sai kin zaɓi irin mijin da kike so ki aura, shi miji ba yawo ake da shiba, bare adinga ce miki baida kyawu, duba kiga sa'aninki daga mai yara uku sai mai yara huɗu.. ƙannen ki biyu akama aure, amma ke hakan bai dame kiba, shikkenan tunda kin fiso ki zauna a gida muyi ta jera kafaɗa dake.." inna ta ƙare maganar ta cike da tarin damuwa, Asma'u dake tsaye hawaye na shirin zubo mata, ta tare su da hannu zuciyarta na mata zafi, shigewa ɗaki tayi da sauri, inna da tabita da ido tana ayyana abubuwa da dama aranta * * * shi kuwa Alhaji tanko, ganin Ma'u ta shige gida da gudu, hakan yasa shi cikin farin ciki marar misaltuwa, zuciyarsa ƙal yabar ƙofar gidan tare da zumuɗin samun zankaɗeɗiyar budurwa ta bugawa a jarida kuma ta yawo a ko ina dan nuna wa duniya.....✍️ *inga comments fa hakan zaisa ku riƙa ganin post akai akai , ba kama hannun yaro😁* *_more comments_* 😃 *_more typing akai akai_* 🥰💃 ```har kullum taku ce ummussalama s y matar khamis🥰💃``` by *~MRS KHAMIS🥰💃~* [4/29, 5:00 AM] matar khamis🥰💃: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s .w .t .a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* *~GARGADI~* ~ban yarda a juya min littafi na ba, ta ko wacce siga, ko ayi amfani da shi ta wata hanya ba tare da an nemi izinina ba.~ *pls a kiyaye🧏‍♀️* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* *page 2* __________________________________________________________ Bayan magriba Asma'u ce zaune kan katifa ta zabga uban tagumi, kamar wacce akawa mutuwa, Domin kallo ɗaya zaka mata kagane tana da tarin damuwa a ranta.. sosai tayi nisa cikin tinanin data ke, inna ce ta shigo ɗakin, bakinta ɗauke da sallama, har ta zauna amma Asma'u batasan take shigo ba, sai da ta yi dafa ta, tukuna tayi firgigit ta dawo hayyacin ta... cikin kulawa inna tace, "Ma'u menene yasa baki son maganar aure kwata kwata,.? tun samarin suna zuwa yanzu har sun gaji, daga kice Wannan ya miki yaro, sai kice wannan baiyi kala da irin namijin da kike so ki aura ba, to shi wannan namijin ah ina yake..? inna ta ƙare maganar da jero mata tambayoyi... ita de ma'u shiru tayi, ta sunkuyar da kanta,. tin inna na mata magana da lumana, har ta fara mata faɗa faɗa, dan ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ... cigaba inna tayi da cewa "duba kiga shi yanzu kawun ku in yaji kalar cin mutuncin da kika yiwa abokinsa zai ji daɗi.? iyee,? magana fa nake miki!!. kin min shiru...!" daƙyar Asma'u ta ɗago kai tace "innar mu dan Allah kiyi haƙuri," ah ƙufle inna tace "ke za'aba haƙuri tunda mu muka takura maki...." hakade inna ta gama sababinta tukunnan ta fita tabar mata ɗakin.... asukwane ta zamai ta kwanta kan katifar da take kai, wasu zafafan hawaye ne ke zubo mata, wanda takasa tseda su, sai da tayi mai isarta, sannan bacci yayi awon gaba da ita haka ta kwanta cike da tarin damuwa..... cikin bacci taji ana shafa mata face nata, wanda hakan yasa tayi sauri buɗe ido. wanda tayi tinanin ko shine , shine kuwa, tayi tozali da kyakkyawar fuskar sa.. tsadadden murmushinsa ya sakar mata haɗe da miƙa mata hannunsa yana mai mata nuni da ta taho gare shi....... *more comments*😃 *more typing akai akai*🥰💃 ```taku har kullum``` ~ummussalama sy~✍️ *_matar khamis🥰💃_* [5/6, 11:19 AM] matar khamis🥰💃: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *PAGE 3* Da saurinta ta ƙaraso gare shi, janyota yayi zuwa qirjinsa, tare da sakin wata nan nauyar ajjiyar zuciya... saida suka dau tsawon lokaci a haka , sannan Ma'u ta ɗago tana kallon kyakkyawar fuskarsa, cike da shagwaɓa tace "shine ka tafi kabarni ko" tana maganar tana turo baki. tsayawa yayi kallon ɗan mitsilin bakin nata, da yake jin kamar ya cinye shi dan matuƙar birge shin da yake.. Ma'u ganin ya tsaya yana kallon ta, hakan yasa ta cigaba da ƙananun shagwaɓaɓɓunta.. ita kuwa bata san ƙara kunna shi take yi ba... bata ankara ba sai da taji bakinsa cikin nata, lumshe idanuwan ta tayi haɗe da sauke ajjiyar zuciya.. shi kuwa wani zazzafan kissed yake sakan mata, wanda a dalilin haka ne wata nan nauyar kasala ta sakko musu.... saida ya gaji dan kansa tukun ya ƙyale ta , yana maida numfashi.. goshinta ya kaiwa sumba😘, sannan yace "har abada babu batun in tafi, inbarki., duk runtsi, duk wuya, ina tare dake,. bazan taɓa rabuwa dake ba, namiki alƙawari...." sosai Ma'u ta shagala da kallon kyakkyawar fuskar sa, dake ɗauke da wani ainahin sirrin murmushi. azuciyarta tana jin wani irin nishaɗi marar misaltuwa. hura mata iskar bakinsa yayi,. hakan yasa ta dawo daga duniyar tinanin da ta tafi.. saida ya sake sakan mata murmushin sa , mai tsada, sannan yace " *Nurul aini ,..* tinanin mai kike yine haka,? ko kina da buƙatar wani abun ne, ? faɗa minshi indai a kwai shi a duniyan nan, sai na nemo miki shi, da yardar Allah..." saida Ma'u tayi ajjiyar heart, sannan tace "kawai ina tinaninka ne, yadda kadamu dani, kuma kake nuna min soyayya,.. tun ina ƴar ƙaramata kake tare dani , aduk lokacin da na shiga wata matsala ko nake cikin wata damuwa, baza ka gazaba wajen kawo min ɗauki..." mirginawa yayi gefen ta, sannan ya yi matashi da hannuwansa, waje tallabe kansa ... saida ya kuma sakan mata murmushin da a zuwa yanzu na fiskanci ɗabi'ar sane , sannan yace "ina matuƙar sonki Nurul aini, kuma keɗin mallaki na ce ni kaɗai, zan iya komai a kanki, dan ganin babu wanda isa shiga tsakanin mu.." buɗar bakin ta kenan zata bashi amsa, sai kuma taji ana taɓa ƙofar ɗakin , muryar inna taji tana cewa "Asma'u maza ki tashi kiyi sallah, ga kiran sallar asuba can anayi ,.." amsawa tayi da "to innarmu" . juyawa tayi inda yake Amma sai taga baya gurin. cike da mamaki ta furta maganar ta a fili tace " *Hydar* ya tafi kenan.. babu wani alamun damuwa a gareta, ta tashi domin ta gabatar da sallar ta.....✍️ tofa readers waye haidar😳 ni fa har na farajin tsoro🙆🏻‍♀️ 🏃‍♀️🏃‍♀️ku biyoni dan warware muku waye shi ɗin😇 *pls a ƙara yawan comment* *more comment* *more typing* *pls share*🙏 *_MRS KHAMIS CE🥰💃_* [5/7, 10:10 AM] matar khamis🥰💃: 👄👄👄 🥺 *NAMIJIN DARE*🙆‍♀️ _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ 😇 SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 ___________________________________________________________ *page 4* *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ Da marece , Ma'u ce zaune a gindin bishiyar gwaibar dake filin tsakar gidan nasu.. tankaɗen garin masara take, fuskar ta ɗauke da murmushi, da walwala, kai kace an mata albishir da gidan aljanna.. kawu salisu ne ya shigo cikin gidan, bakinsa ɗauke da sallama. kallon Ma'u yayi wace, ke faman gaishe shi, haɗe damai sannu da zuwa, yace, "ya kukayi da Alhaji tanko ne, ɗazu ya kirani yake min maganar shifa a shirye yake, shine nace bari nazo naji ya kukayi ?. azabure Ma'u ta ɗago da fuskar ta, jin an ambaci maganar da tafi tsana fiye da komai. cikin alamun marerecewa tace, "wllhi kawu ni bana son shi, asali ma bamuyi wata magana da shi ba." "kaji mutuniyar banzan ko.!" cewar inna dake fitowa daga cikin ɗaki. Kawu Salisu yace, "to ke Ma'u meyasa baki sonshi,? nidai banga wani dalilin da zaisa ki ƙi shi ba". Ma'u sunkuyar da kai kawai tayi, ganin tarasa abun faɗa yasa inna tace, "Salisu ina ganin kawai kace ya turo, dan in aka biyeta cewa zatayi bata son nashin." Ma'u dake zaune tana zuɓuro baki, cewa tayi , "wllhi bazan auri alhaji tanko bah, saide kusan wadda zaku aura mai." ta tashi da gudu ta shige ɗakinta. Samun *Haidar* tayi zaune kan katifar ta, da hanzari ta faɗa ƙirjinsa, ƙara rushewa da kuka tayi, har da sheshsheƙar ta. bubbuga bayanta yake haɗe da shafawa, sai da ya tabbatar da ta samu natsuwa, sannan ya ɗago da kanta, ido cikin ido yake kallonta, yace " *Nurul'aini* duk duniya bbu wanda ya isa ya aureki, duk wanda yayi taurin kai asan sai ya aureki, ko kuma sai ya aurar da ke, !Na rantse da wanda yake busamin numfashi, sai na kawar da shi, kamar yadda na kawar da wasu a baya." cike da mamakin furucinsa, take bin sa da kallo. abunda yafi komai bata tsoro shine, ganin yadda idanun sa suka rune lokaci ɗaya.. Haidar kuwa ganin Ma'u ta tsorata dashi yasa sai ya rungume ta, tuni wani nan nauyar bacci yayi awon gaba da ita... * * * su kuwa su inna da Ma'u ta shige ɗaki, ta barsu anan, cigaba sukayi da tattauna maganar aurenta da Alhaji tanko,.. Ɓangaren Alhaji tanko kuwa shi a shirye yake kasancewarsa chairman na L.G ɗin , yana da rufin asirin sa, matansa biyu da ƴaƴa goma, wannan dalilin ne yasa ya ware gida daban, wanda zasu zauna shi da Ma'un sa. kamar yau ma yana ta zagaye gidan, don ya duba inda yake da bukatar wani gyaran, dan Ma'u ƴar gayu ce a cewar sa. kamar daga sama yaji an faɗo cikin gidan, juyawa yayi da sauri, ganin mutum tsaye a bayansa yasa yasha kunu, yace "ɗan samari lfy, ka shigo min cikin gida bako sallama, in ma aiki kake nema, to ai sai ka bari sai na fito koh." murmushi saurayin yayi, tare da miƙa mai hannuwansa dan suyi musabiha. shide Alhaji Tanko tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, ganin Alhaji tanko yaƙi mika mai hannun yasa ya janye nasa kallonsa yake cike da tsare gida yace " Suna na *Haidar* kuma nine mijin wadda kake shirrin aure, a tunanin ka wani yana noma ah inda ya kasance mallakin wani.?" ya ƙare maganar yana ƙara haɗe rai, shiru Alhaji Tanko yayi ya tsaya yana mai kallon mamaki.......✍️ *idan naga comment ɗinku , kuma ya burgeni insha allahu zaku samu post da yamma har kullum taku ce ummussalama s y sai na jiku* *more comment* *more typings akai akai🥰* *pls dan Allah ku riƙamin share😞* ~MRS KHAMIS CE~🥰💃 [5/9, 9:22 AM] matar khamis🥰💃: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *page 5* Cike da al'ajabi Alhaji tanko yace, "miji kuma,. yaushe akayi hakan.?" murmushin samun nasara Haidar yayi, sannan yayi taku biyu zuwa uku. saida ya mai kallon irin baka isa ba ɗin nan,.. sannan yace "ba hurumin ka bane wannan, zai fi kyau kabi umarnin da na baka, na fasa auren mata ta.." bushewa da dariya Alhaji tanko yayi, yana nuna shi da hannu, wanda hakan ya fara fusatar da Haidar,. saida yayi mai isar sa, sa'annan ya ya tsuke fuska, kamar bashi yake dariya yanzu ba.. "yaro man kaza, kai a tunanin ka, na tsorata da wannan ƴar burgar da kake min, to barima kaji in faɗa ma,!! Babu abinda zai hanani auren Ma'u, mu duk ina numfashi, dan ma kasani." cewar Alhaji tanko, da yake maganar nan har cikin ransa.. shi kuwa Haidar da ya ga Alhaji tanko ya mai taurin kansu irin na bil'adama,😆sai yayi tafiyar sa a cewar ya san matakin da zai dauka akan sa.... * * * Ita kuwa Ma'u, sai gab da magriba ta tashi daga baccin da ya kwashe ta. kai tsaye tsakar gida ta fito, samun inna tayi tana ƙoƙarin kaɗa miya, sannu da aiki ta mata da ƙyar, domin gaba ɗaya ji take tana jin haushin kowa, ciki kuwa harda innar.. gefe ta samu can kusa da bishiyar dake tsakar gidan ta zauna, haɗe da rafka uban ta gumi kamar wacce aka wa mutuwa... kiran sunan ta inna tayi, tace "Asma'u"!!!, ko gezau batayi ba asalima kamar bata agurin.. saida inna ta kirata, wajen sau biyar, tukunnan ta jiyo. tsurawa inna ido tayi, alamun tana sauraran ta... ƙaramin tsaki inna ta saki, tace kyade ji dashi, dama sallah ce zance kije kiyi, shine kika min shiru, to kar Allah ya sa ki tashi kije kiyi ɗin. auren Alhaji tanko ne dai sai kinyi, saide idan shine yace ya fasa... yau Allah na tuba, mutum yazo taimaka maki ya aure ki, sai kice baki son shi, to wllhi ahirr ɗinki." haka inna tai ta sababi har saida ta gaji dan kanta, tukun nan tai shiru.. afusace Ma'u ta shige ɗaki, faɗawa tayi kan katifarta, haɗe da sakin wani marayan kuka, mai taɓa zuciya...... ita ba komai bane, yafi ɓata mata rai, irin yadda inna take cewa, wai taimaka mata ake so ayi, sai kace wata al'majira.... *WAI SHIN MEYE HAƊIN MA'U DA HAIDAR* ? inna Hajara itace mahaifiyar su Asma'u, inda take da ƴaƴa shida maza biyu sune Auwal da Sani sannan Asma'u sai ƙannanta mata, Aisha da Safiyya, sai kuma auta zahra... Ma'u tunda ta tashi, ta tashi cikin soyayyar iyaye, kasancewar inna, tunda ta haifi Auwal da Sani sai haihuwar ta tsaya mata, saida ta ɗauki shekaru har bakwai, sannan Allah ya bata cikin Ma'u... a lokacin tayi matukar murna sosai, da ɗin daɗin ma, da ta haifi ɗiya mace abinda take matuƙar sha'awa. haka tai ta rainon ɗiyarta yadda yakamata, cikin lokacin ne inna tayi baƙi, sai ta shimfiɗa musu tabarma a tsakar gida, nan suka zauna suna ta hira, yayin da ta kwantar da jaririyar ta Ma'u a cikin ɗaki.. Haidar yazo wucewa ta gurin kenan, sai ya hangi wani kafirin aljani yana ƙoƙarin cutar da ita, kasancewar sa musulmi kuma mai tausayi, yasa yazo ya taimake daga cutarwar wannan kafirin aljanin, tundaga wannan lokacin Haidar ya kasance tare da Ma'u........✍️ *HATTARA IYAYE ANAN YAKAMATA KUSAN CEWA, DUK LOKACIN DA MUKE DA ƘANANAN* *YARA, MUDAINA AJJE SU, A GURI SU KAƊAI BA TARE DA MUNYI MUSU WATA ADDU'A BA , KAWAI MUN BARSU ADUK YADDA MUKA GA DAMA.* *SHIYASA ZAKUGA IYAYEN MU NA DA MUSAMMAN IRIN NA ƘAUYE IN ZASU AJJE JARIRI, SAI ANSA WANI YA ZAUNA A GURI SANNAN UWAR YARO ZATA TASHI, KO KUMA A AJJE MAKAMI KUSA DA JARIRI, WAI DAN YAZAMA KARIYA A GARESHI..* *TO AMMA A GANINA HAKAN DUK BAI YIBA* KAWAI KIYI ADDU 'A KI TOFE YARKI, KO ƊANKI, SHI YAFI ALKAIRI BAMAKAMI BA KO AJJE WANI AKUSA...☹️ *_sannan ina matuƙar godiya da yadda kuka karɓi wannan littafin nawa, jiya da aka jini shiru hakan ya faru ne bisa hutun sati dana keyi na gode_* *more comment* *more typing* *pls share fisabilillah🤩🙏* ~MRS KHAMIS CE🥰💃~ [5/10, 1:19 PM] matar khamis🥰💃: 👄👄👄👄 🥺 *NAMIJIN DARE*🙆‍♀️ _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ________________________________________________________________ *page 6* Tunda ga wannan lokacin, Haidar ya kasance, tare da Ma'u, yana bata kariya... Ko su kansu shaiɗanun, idan suka ga Haidar tare da ita, ko tunkarar inda Ma'u take ba suyi.. Haka Ma'u ta taso, yarinya kyakkyawa, fara doguwa, gata da gashi, kamar ƴar buzuwa, son kowa ƙin wanda yara sa, gata dasan kwalliya gwanin sha'awa, duk wanda yaga Ma'u sai ta burge shi, saide hassada ta mutane.. A lokacin ne Haidar, zuciyarsa ta fara kamuwa da son Ma'u, domin duk abinda take burge shi take, musamman idan tayi kwaliya.. Hakan yasa Haidar yin tinanin bari ya ƙauracewa rayuwar ta, ko ya manta da wata soyayyar ta.. Haka rayuwa tai ta tafiya, abubuwa da dama sun faru, masu daɗi, da marassa dad'i, ciki kuwa harda rasuwar mahaifin su Ma'u.. A lokacin Ma'u an zama ƴan mata, dan tana da shekaru sha bakwai cif cif, komai de na cikakkiyar matashiyar budurwa, ya bayyana gareta.. Dama lokacin, mahifinta yana raye, ya haɗa auren da ɗan ƙanin sa, wato kawu salisu, Ma'u ita da yusif suna soyayyarsu sosai, domin suna matuƙar son juna, dan har lokacin da za'ayi bikin nasu ansa, kawai ana jiran ya gama ginin sa ne sannan ita kuma tayi, Candy.... ★ ★ ★ Ɓangaren Haidar kuwa, tunda ya tafi bashi da wani aiki sai tinanin Ma'u, tun yana daurewa, har ya kai yanzu, baya iya daurewa, dan kullum ciki begen ta yake, kamar yau ma yana zaune shi kaɗai, akan wani tsauni dake tsakiyar ruwa, yanayinsa kaɗai ya isa yasa a gane bawane dake cikin shauƙin soyayya... Ya ɗauki tsawon lokaci agurin, kuma duk abu ɗaya yake wato tinanin bil'adama, ji yayi anda fa sa ta baya, murmushi ya saki ba tare da ya juya ba yace "Iliyas mai kake yi anan! a daidai wannan lokacin?." Dawowa yayi ta gaban sa, haɗe da maida mai martanin murmushin sa, yace "wllhi nazo wucewa ta ƙarshen tsaunin nan, sai na shaƙi kamshin turarenka, kuma nasan bbu mahlukin dake amfani da wannan kamshin, in ba kai ba, shiyasa na zagayo tanan sai gashi na ganka, amma mai kake yi anan!, ka zauna kai kaɗai! lafiyar ka kuwa?.." Numfasawa Haidar yayi, haɗe da sakin wata ajjiyar zuciya mai zafi, yace "wallahi matsalar soyayya ce abokina, wllhi dukan bugun numfashina, da begenta yake bugawa, ji nake bazan iya rayuwa batare da ita ba." Ya ƙare maganar sa, cike da rauni. Da tsantsar tausayi, Iliyas yace "ita ko wannan mace da kake so wace ce, a cikin jinsin jinni ƴar wane haka mai sa'a." Girgiza kai Haidar yayi yace "Ba a cikin ko wani jinsi take ba, face bil'adama." Da mamaki Iliyas yace "bil'adama! bil'adama fa kace, haba Haidar,. mai zakayi da bil'adama, ga jinsinka nan, akwai mata kala-kala, kuma masu kyau, kawai ka rabu da ita.." "Uhmm Iliyas kenan, wannan ba macen da zan iya rabuwa da ita bane, kuma ina sonta kamar numfashi na, zan iya komai akanta." Haidar ya faɗa har cikin ransa... Bushewa da dariya Iliyas yayi, sannan yace "to ita masoyiyar taka tana ina.?" Ya faɗi maganar nan, yana ƙunshe dariyar sa. Ajjiyar zuciya Haidar yayi, yace "yanzu tsawon shekara huɗu rabona da inganta, amma fa ina azabtuwa wllhi abokina." Ƙara kecewa da dariya Iliyas yayi yace "to kai kana nan, kana haukan sonta, wata ƙila ita tana cen tayi aurenta.? A fusace Haidar ya ɗaugo, fuskarsa ta sauya, ta koma wata kala dan ɓacin rai, yace "wllhi duk wanda ya auri masoyiyata, hmm!! sai na ɓatar da rayuwar sa, ta har abada." Miƙewa yayi da sauri, riƙesa Iliyas yayi yace "ina zuwa kuma?. Haidar yace "gurinta zanje naga meke faruwa a rayuwar ta." Da sauri Iliyas, yace "ah ah Haidar! karfa ka manta, cewa ita ɗin bil'adama ce, kuma tana da rauni, kai kuma bil'jinnu ne, kuma kana da ƙarfi, dan Allah! dan Allah! Haidar ka rabu da ita, ka samu wata a jinsinka ka aura, kada ka cutar da ita, kaji tausayin ta Haidar.." A fusace Haidar ya juyo yace " da ace wani ne yake min wannan maganar, da sai ya ɗan ɗana kuɗarsa, kai abokina ne idan baza ka goyamin baya ba, kada ka ƙara min magana mai zafi irin haka, in ba haka ba zamu samu saɓani da kai,.." Haidar ya faɗi haka yana ɓacewa... ★ ★ ★ Acan ɓangaren su Ma'u kuwa, ana ta shirye-shiryen bikinta da Yusuf, dan yanzu haka ma ta dawo daga wurin gyaran jiki, tayi wani fresh da ita, tafito a matsayin ta na amarya, sauri-sauri take ta shiga wanka, kasancewar ana zafi sosai.. A gurguje ta faɗa bayi, dan yin wanka ko taji sauƙin zafin da take ji, Haidar kuwa da ya bayyana a gidan , ganinta cikin bayin tana wanka yasa ya shiga cikin bayin, tsura m halittar ido yayi, yana jin kamar ya haɗiye ta, dan son da yake mata, yayin da ita Ma'u wankanta take cikin kwanciyar hankali, dan har wani lumshe ido take idan ta zuba ruwan ajikin ta, cikin shauƙi da salo take wankan, kamar tasan akwai wata halitta da take kallonta.. Shi kuwa Haidar da ya ƙura mata ido ko ƙiftawa ba yayi, wani yanayi ke fisgarsa, yana jin zai iya kasancewa da ita na har abada........✍️ *ina ta gani ƙorafe-ƙorefen ku dan allah ku riƙamin uziri abubuwa da yawa sunmin yawa ne shiyasa amma insha allah zan ƙoƙarta, ina jin dadin comments ɗinku ina godiya sosai..✍️* *more comment* *more typing* *pls share* ~MRS KHAMIS CE🥰💃~ [5/11, 4:12 PM] matar khamis🥰💃: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *page 7* ________Da wajen magribah, Ma'uce zaune cikin ɗakin inna, tana cin kazar amare, da inna ladidi ƙawar inna ta aiko mata da ita, ci take amma badan ranta yana so ba, asalima ji take kamar zatayi ame.. Yusuf ne ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, guri yasamu kusa da ita ya zauna, leƙa cikin kular yayi haɗe da sakin murmushi, yace "gaskiya ne ƙanwata, ashe ki nan kina cin daɗin ki, kin barni da sanƙamar tuwo." Ya faɗa cikin sigar tsokana, murmushin mugunta tayi tace "bismillah yayana" ƙwace kular yayi yace "saide in cinye duka! dan kede kam kin ci rabon ki." Ido Ma'u kawai ta zuba mai, tana so taga yadda fuskar sa zatayi, yayin da ya fara cin naman kazar, yago wata tsoka yayi ya kai bakinsa, har wani lumshe ido yake, kasancewar nama yaji dahuwar daddawa, yana sawa baki maimakon yaji daɗi, saima wani mugun bauri da ya ziyarci bakinsa, da sauri ya furzar, yana ya mutsa fuska. Ɗagowa yayi, ya kalli Ma'u "sannunki da ƙoƙari, da wani kalar kayan ɗaci aka dafa kazar nan, ya faɗa yana goge bakinsa da hand kichef.. Ma'u kuwa dariya take iya san ranta, sai da ta tsagaita da dariyar, sannan tace ai wllhi yaya Yusuf kwaɗayinka yawa ne dashi, yanzu inda nace bazan baka ba, wallahi sai kaci, shiyasa na bar ka bakinka ya hanaka. Ta ƙare maganar, tana ƙunshe dariyar ta, shagala Yusuf yayi da kallon ta, dan yana matuƙar son Ma'u, kamar ransa. Matsawa kusa da ita yayi, cikin raɗa raɗa yace "na miye ! pls faɗamin ƙanwa ta"? sai da ta ya mutsa fuskarta, sannan tace nima bansan ko na miye ba, kuma inna kusan kullum, sai ta bani irinsa.. Fahimtar ko na miye da yayi ne, yasa ya miƙa mata sauran, yace "gashi ki cinye duka, ai abun na taimakon kaine..." Ya faɗa yana sakin ƙayatacen murmushin da shi kaɗai, yasan ma'anarsa... *** Haidar dake zaune cikin wata sahara, iskar dake kaɗawa, da kuma yanayin ni'imar dake sauka agurin, sai suka haɗu suka saukar mai da shauki, da kuma begen masoyiyar, abin ƙaunar sa... Shafa tafin hannunsa, abun mamaki sai ga Ma'u da Yusuf, suna hirar su ta masoya, cikin kwanciyar hankali, gwanin ban sha'awa.. Wata kururuwa Haidar yayi, haɗe da sakin wani raza nan nan ƙara, wanda ya haddasa wata firgitacciyar guguwa lokaci ɗaya, ɓace yayi ɓat, cikin ƙanƙanin lokaci ya bayyana ɗakin inna, dai-dai lokacin kuma Yusuf ke cewa Ma'u "kinga rana ita yau kina gidana, ba damar ki kore ni, ko kice min bacci kike ji, ya faɗi haka cikin wasa.. Haidar dake tsaye zuciyar sa tana ta tafarfasa, ji yake kamar ya bayyana a garesu, kodan yawa Yusuf lahanin da bazai taɓa moruwa ba..... *_dan Allah kuyi hakuri da wannan ba yawa sakomakon banjin dadi kuma shi jiki da jini sai mun haɗu gobe in Allah ya kaimu_* *more comment* *more typing* *pls share* ~MRS KHAMIS CE~🥰💃 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *Page 8* _________Shirye-shiryen biki yana ta kan kama, inda yau biki ya rage saura kwana ɗaya, sosai ake shagali baka ma hannun yaro, amarya ansha kyau sosai, kasancewar yau suka yi walima, duk tabi ta gaji, tana gabatar da sallah isha'i ta shige ɗakin inna wanda babu mutane da yawa sosai, hayewa can ƙuryar gado tayi, nan ta ƙundundune tuni wani nan nauyan baccin gajiya yayi awon gaba da ita.. zaune suke cikin wani ƙatataccen lambu, cikin nishaɗi da annushuwa, suke hirar su irin ta masoya, wani mutum ne yazo inda suke, kallon yusuf yayi yace "kaide ka nace, sai ka mallaki abinda bai dace ya zama mallakin wani ba, to kasani yau ce rana ta ƙarshe, da zan ƙara ma kashedi akan ka rabu da masoyiyata, idan ba haka ba, zaka tafi inda ba'a dawowa".. Murmushi Yusuf yayi haɗe da kamo hannun Ma'u, ya riƙe shi gam a hannun sa, yace "Babu wanda ya isa ya rabani da Ma'u, sai Allah n da ya halicce mu." Mutumin ƙafa yasa ya hauri Yusuf a ƙirjinsa, tuni ya faɗi ya fara aman jini, Ma'u da take kallon ikon Allah da gudu ta tashi da niyar taje gurin yusuf, amma mai sai mutumin ya riƙe ta, ɗayan hannunsa kuma ya shaƙe Yusuf dashi tun yana motsi har ya daina, kallon ƙasan gurin yayi tuni wani ƙaton rami ya bayyana a gurin, tana ji tana kallo mutumin, ya jefa masoyinta Yusuf a cikin ramin, ita kuma ya wuce da ita yana cewa "keɗin mallaki nace, duk wanda yayi gigin mallakarki, ga irin sakamakon sa.." A firgice Ma'u ta farka daga baccin da take, sakamakon wannan munannan mafarkin da tayi, jiki na karkarwa ta lalabi wayarta da ta kashe lokacin da zata kwanta, gudun kar a dameta.. Number Yusuf ta lalubo, kira take wayar tana ta ringing, amma ba'a ɗaga ba, kira ta sake yi amma still ba'a ɗaga ba, saida ta kira yafi sau bakwai amma shiru, ƙara gigicewa tayi haɗe da sakin kuka tana cewa, "Allah kasa mafarkin nan kar yazama gsky", ta ƙare maganar tana haɗa hannuwanta biyu... Shi kuwa Yusuf a dai-dai lokacin da Ma'u take kiransa, shima yayi mafarki sak irin wanda tayi, amma saide shi ba yau ya fara ba, ya kai sati ɗaya yana irin wannan mafarkin, kuma duk akan barazana ne na ya rabu da Ma'u.. Tashi yayi yaje ya ɗora al'wala sallah yayi raka'a biyu, tare da yin addu'a da neman tsari akan duk wani abin sharri.. Bayan ya gama ne yazo zai kwanta, wayarsa ya ɗauka dan yaga ƙarfe nawa, abin mamaki sai yaga kiran ma'u, da sauri yabi kiran bugu ɗaya ta ɗauka, fashewa da kuka tayi, sannan tace "shine sai kiranka nake, amma kaƙi ɗauka, wllhi kaban tsoro." a kiɗime yace "lafiya! mai ya faru kike kuka!, faɗa min tunkan zuciyata ta buga?." "uhm wllhi yayana ina cikin fargaba, wani mugun mafarki nayi, wai nida kai...." katseta yayi da sauri yace "ba'a faɗan mugun mafarki, saide mafarki na jin daɗi ko na farin ciki, kawai kedai kiyi addu'a, kinji ƙanwata.." Saida ya mata nasiha sosai, tare da nuna mata shi mafarki ba gsky bane, yawanci duka sharrin shaiɗan ne, bai bar ta haka ba, saida ya tabbatar da hankalin ta ya kwanta.. sannan ya ɗora da tsokanarta, duk yawanci wasan da yake mata kunyar sa takeji, hakan yasa ta kashe wayar , haɗe dayin addu'a ta tofa a hannun ta, shafe jikinta tayi sannan ta kwanta abinta. *ASUBA TA GARI MA'U AMARYA* Shi kuwa yusuf kasa komawa yayi, dan jin shi yake kamar bashi da cikakkiyar lafiya, kawai daurewa yake a matsayinsa na namijin gaske, kuma mai dauriya. Yusuf kuwa dake zaune sai gumi yake, ga wani zafi da jikinsa yayi, dan duk wannan shaƙar da Ma'u ta gani acikin mafarkin ta, azahiri yana kwance kan kadon sa, amma a baɗini abinda Ma'u ta gani ya faru da gaske.. Sosai yusuf yake shan azaba a jikinsa, bacci kawai yake so yayi, amma saide bazai samu ba.. A haka har akayi kiran sallar asubar farko, tashi yayi ya ɗora al'wala, fara gabatar da nafilfili yayi, kan ayi kira sallahr shiga Masallaci.. Kafin gari yayi tangararo, ixuwa yanzu yusuf ya jigata ko fita ya kasayi, turo ƙofar akayi , Auwal ne ya shigo wanda ya kasance babban yaya ga Ma'u, hararar Yusuf yayi sannan yace "wato ka barni da wasu shashashan abokananka, shine kazo nan ka kwata, to wllhi maza tashi muje kaji dasu, dan ni nagaji.." Ya ƙare maganar yana cigaba da harararsa, ɗago kai Yusuf yayi yana murmushi yace "kasan wani abu Bros wllhi jiyan ne, in na zauna a wajenku surutun ku yawa zaimin, gashi na dawo nan ɗin ma, amma duk da haka zazzaɓi nake ji." dariya Auwal ya saki yace "to kai gashi baka san surutu, kuma gashi zaka auri Ma'u uwar surutu to ya zakayi, kenan?." "uhmm ai surutun ta na daban, ni bama wannan ba taimaka min da ruwa mai ɗan sanyi nasha, sannan na ɗan shafe jikina dashi, ko naji daɗin jikina kan lokacin ɗaurin aure." Cike da damuwa Auwal ya tashi domin kawo mai ruwan sanyin, fitar sa da ƴan mintina kaɗan ya dawo, hanunsa ɗauke da kwanun ruwa, yace "bros tashi kasha to, sauran sai na shafe ma jikin ka dashi." Yanayin sanyi ruwan ya mai, saboda haka ya sha da yawa, sauran da ya rage ne, Auwal ya karɓa ya shafa masa ajiki, jim kaɗan yaji sanyin ruwan nan ya koma mai kamar ruwan narkarkiyar dalma aka bashi yasha, sauran kuma aka shafe mai jiki dashi, ɗago wa yayi da niyar yama Auwal magana amma sai yaga akasin haka, Haidar ne tsaye a gaban sa, fuskarsa babu ɗigon rahama ko kaɗan, ya haɗe rai yace "ina fatan ka gane ni yanzu, ko sai na gabatar maka da kaina." "Waye kai". Yusuf ya faɗa da ƙyar, murmushin mugunta Haidar yayi yace "suna na Haidar, kuma na kasance ina matuƙar ƙaunar wacce kake shirrin aure, amma saide kasani bazan iya kallo wani bil'adama ya auri masoyiyata ba, ni ba mugu bane kai ka maidani mugu domin ba kalar kashedin da ban ma ba, amma ka nace sai ka aure ta, to kasani mu duk ina doran duniyan nan babu wanda ya isah ya auri Ma'u, ko waye shi.. saida ya kwashe da dariya sannan ya cigaba da cewa "sa'ar ka ɗaya kun haɗa jini da farin cikina, Amma da hukuncin da zan ma, hmmm! Kafin ka mutu sai kayi da nasanin sanin Ma'u a cikin dangin ku. Zan auri Ma'u! sannan nasa taƙi ko wani ɗa namiji, dake duniyar bil'adama." Haidar ya ƙare maganar cike da alfahari, da ƙyar Yusuf ya ɗago yace "ka cuci kanka da har kake jin ka mallaki Ma'u, to ina so kasani, idan Allah ya ƙaddara Ma'u zatayi aure, to wata ran kanaji kana gani wani zai aure ta, kuma ka riƙe wannan idan kana tinanin kai aljani ne kuma Allah ya baka ƙarfi, to kasani a cikin jinsin mutane akwai wanda allah ya halicce su da ƙarfi da tsari da duk wata cutarwa taka bazata yi tasiri ba, kuma insha Allahu irin mutumin nan shine mijin Ma'u da yardar Allah.." Yusuf ya ƙare maganar cikin zafin ciwo. Dariya sosai Haidar yake cike da isgilanci yace "baka tambaye ni mai na baka ba, kasha a matsayin ruwan sanyi, to bari nasanar da kai dan kasan mai zai halaka ka, wani dafin baƙin aljanin miciji ne na baka, kuma ina da ya ƙinin da ƙyar ka rayu, shiyasa na baka kasha, domin kaine mutum ɗayan da inde yana raye bazai barni in mallaki masoyiyata ba.." Yusuf da izuwa yanzu ya fara sakin wani baƙi ame, a wahalce yace "wanin ma Allah zai kawo shin kuma baka isa ka dakatar dashi ba." Shidai Haidar dariyar samun nasara kawai yake, yace "abokina kai ta maimaita kalmar shahada, dan ana so mutum yaci ka da kalmar Gaskiya.." Ya faɗi haka yana ɓacewa.......✍️ *_AFUWA FANS JIYA DA KUKA JINI SHIRU HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON ZAZZAƁIN DA NASHA FAMA DASHI JIYA, ALLAH YA BAWA DUK MARAR LAFIYAR DAKE GIDA DA NA ASIBITI LFY ALLAH YA ZAUNAR DA ƘASAR MU NIGERI'A🇳🇬 LFY DA DUK DUNIYA BAKI ƊAYA_* _💃💃💃💃 Yeeee masu min comment da masu sharhi ina godiya ni daku akwai amana shiyasa nake son ku over🥰_ *masu addu'a kunfi ƴan tanx, masu tnx kunfi masu sitiƙa, masu sitiƙa kunfi ƴan likimo, saide su karanta sunyi shiru🙄 to ni daku ne* *More comments* *More typing*💃💃 *pls kar a manta da share saboda ba kowanne group nake turawa ba, sai da ga baya suyi ta tambaya dan Allah a riƙa tura musu.🙏* ~MRS KHAMIS CE🥰💃~ [5/20, 8:01 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *Page 9* ___________Ɓacewarsa ke da wuya, Yusuf ya fara ƙaƙarin ame wanda ba komai ke fitowa ba, sai wani baƙin gudajin jini.. Auwal ne ya shigo da sauri hannun sa riƙe da ruwan sanyin, da Yusuf yace ya kawo me, ganin halin da yake ciki, yasa ya saki ruwan da hanzari ya ƙaraso gare shi.. Tallabo shi yayi yana tambayar meya same shi, amma yusuf ko bakinsa ya kasa ɗagawa, da gudu Auwal ya fita, jim kaɗan suka shigo tare da kawu Salisu, gani halin da ɗan nasa yake ciki, ya matuƙar bashi tsoro, a kiɗime ya kalli Auwal yace "maza kamashi mu fita dashi," Auwal yace "kawu ina za mu kaishi?" "Asibiti mana! maza tallabo shi". Auwal yace "kawu ka manta yau Lahadi, ƙaramin asibitin can basu fito ba yanzu, kuma in muka ce babban asibiti zamuje, kafin asamu motar ma shine aiki.." "ƙware kuwa, to yanzu ya zamuyi?" kawu ya faɗa yana kallon Yusuf dake kwance cikin wani hali.. da sauri Auwal yace "bari na kira doctor Habu, yau yana gida", fita yayi da gudunsa dan kiran doctor ɗin, shi kuma kawu ya tsaya yana wa Yusuf firfita, ganin yadda yake gumi, taɓa jikinsa yayi amma sai yaji jikin nasa ya ɗau sanyi kamar ƙanƙara, ruwa kawu ya ɗauko addu'a yayi aciki ya tofa, ɗago kan Yusuf yayi, haɗe da bashi ruwan tofin da yayi, da ikon Allah cikin ƴan sakanni sai gashi Yusuf ya ɗan fara dawowa hayyacinsa, saide kawai gumin ne bai daina ba.. Da ƙyar ya ɗago, yace wa kawu "Abba mutuwa zanyi, bazan auri Ma'u ba, amma ina mata fatan Allah ya haɗata da wanda ya fini, kuma jarumi jajirtacce, wanda zai so ta fiye da Yadda nake sonta... Rufe masa baki kawu yayi yace "insha Allahu Yusuf kaine mijin ma'u, ai cuta ba mutuwa bace,.." Auwal ne ya shigo tare da doctor, da sauri kawu yace "yauwa likita dan Allah temaka ka bashi temakon gaggawa, kayan aiki likitan ya fara cirowa amma me lokacin da ya ƙaraso ga Yusuf, samun sa yayi idonsa yana lumshewa yayin da bakinsa yake nanata kalmar shahada.. *Wayyo yusuf rai yayi halinsa, saide muce Allah ya jiƙanka da rahama* 😭 ★★★ Ita kuwa Ma'u tana can ita da ƙawayenta bata san halin da ake ciki ba, kawai shagalin su suke sha.. Lokaci ɗaya taji gabanta yayi mumunan faɗuwa, dafe ƙirjinta tayi haɗe da barin gurin da take, kai tsaye wajen inna tayi, wacce take ta faman sallalami sakamakon yanzu kawu yazo ya faɗa mata abinda ke faruwa, innalillahi wa' inna i'laihir raji un, baƙin ciki ba'a sa masa rana, aranar gidan biki ya koma bikin mutuwa, haka aka suturta Yusuf aka kaisa gidansa na gsky... Ma'u kuwa tunda taji labarin mutuwar sahibinta, ta yanki jiki ta faɗi, bata san inda kanta yake ba, shi kuwa Haidar da yafi uban kowa mugunta, bugar da Ma'u ya ƙarayi, a cewar sa in ta farfaɗo kukan begen saurayinta zata yi tayi... sai da akayi kwana uku sannan ta tashi, ai kuwa tana tashi da kukan mutuwar Yusuf ta farka, kowa kasa rarrashinta yayi, saboda sani shaƙuwa da soyayyar da ke tsakanin su, Allah sarki Ma'u idan ta tuna maganar su ta ƙarshe da Yusuf, sai ta fashe da kuka abin gwanin tausayi.. Haka rayuwa tayi ta tafiya, wata ran farin ciki wata ran baƙin ciki, wanda har yanzu Ma'u ta kasa manta wa da Yusuf, dan kullum cikin tinanin shi take, mane ma aurenta sai zuwa suke, amma ko kallo basu ishe ta ba, shi kuwa Haidar hakan ya masa daɗi, duk dai cewa baso yake ta dinga tinanin Yusuf ɗin ba, kawai dan yaga ba yacce zaiyi ne shiyasa.. A ɓangaren Haidar kuwa, duk wani shirye shiryen sa na yaga ya mallaki Ma'u ne, bi ma'ana ya aure ta, musamman yanzu da yaga ta fara soyayya, da wani malamin islamiyyar su, sunan shi Khalifa, Ma'u tana matuƙar son Khalifa, kasancewar sa shima matashine, kuma yana tafiyar da lokacin sa, dai-dai yadda zamanin yake.. Soyayyar su suke sha gwanin sha'awa, dan maganar Aure har ta shiga a tsakanin su, kawai lokaci ake jira.. Haidar ganin wani yana shirin mallakar Ma'u, yasa ya canja shirin sa, da so yake ya bayyana mata kansa, sannan ya aure ta, amma yanzu gwara ya aure ta ba tare da sanin ta ba, daga baya ya bayyana a gareta... Da sannu saida Haidar ya sanya tsanar Ma'u a zuciyar Khalifa, har an kai kayan lefe aka kai, amma Khalifa ya sa aka karɓo mai akan cewa ya fasa aurenta, Ma'u taji bakin ciki amma sai ta barshi kawai, a matsayin ƙilah hakan shi yafi al'kairi a gareta.. ★★★ A yau Haidar ya ɗaura aure da Ma'u, inda wasu malaman al'janu suka shaida hakan, sai kuma abokin sa I'liyas wanda shi kaɗai, ya goyi bayansa akan auren jinsin bil'adama, shima a zuciyarsa basan hakan yake ba, dan aikata hakan ya saɓawa al'adarsu ta al'janu, musamman da suka kasance musulmai... *To fa reader's ya zata kasance, tsakanin Ma'u da Haidar🤔* *Shin ya Haidar zaiyi mu'amala ta aure da Ma'u🤔* *kuma anya zai barta tayi aure da bil'adama irinta🤔* *duka ku biyoni cikin wannan labarin domin warware rikicin dake ci* *more comments* *more typing* *pls share* ~MRS KHAMIS CE🥰💃~ [5/20, 3:37 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *page 10 & 11* __________Ransa fes yake gudanar da al'amuransa, musamman yanzu da yake jin ya samu nasarar mallakar Ma'u, yanzu duk wani shirinsa shine da yake so ya cimma, shine yaga ya hana ko wani ɗa namiji gaɓar inda Ma'u take.. Haidar bai bar Ma'u haka ba, sai da ya tabbatar da Yasa mata tsoron maza a zuciyar ta, dan duk wata sabga da ake mu duk akwai maza a cikinta, to baza kaganta a gurin ba.. Rayuwa tana ta tafiya Ma'u kullum manema aurenta suna ta zuwa, saide in wani yazo sau ɗaya ba llale ya ƙara zuwa ba, ana cikin haka akayi auren ƙannan ta biyu mata, wanda suke bi mata, kasancewar a dangin su suna auren wuri, dan duk inda yarinya ta kai shekaru sha tara to ta isah aure, saide kawai in bata samu mijin da zai aure tan bane... A yanzu Ma'u tana da shekaru ashirin da uku, kyawun ta da dirinta sun ƙara fitowa, ba shakka yanzu Ma'u take cikakkiyar budurwa, dan ba wani ɗa namiji da zai kalli Ma'u yace bata burge shi ba, dan Allah ya mata kyawu da suffar da ko wani namiji yake da burin yaga ya mallake ta.. Saide kashh! muguntar Haidar tasa ya sanya wa Ma'u kwarjinin da ba ko wani namiji ne yake iya tunkarar Ma'u, yace yana sonta ba, sai wanda ya isah yake jin shi wani ne, a fagen mulki ko kuma a kasuwanci, hakan yasa ƙananun samarin dake da burin zuwa gurin ta, su sha jinin jikin su, suma wanda suke zuwa sai Ma'u tace bata son su, ko kuma de akasin haka, wani lokacin har sai maganar aure ta shiga, cikin ikon Allah saide a rasa ya akayi auren ya warware, Ma'u ita da iyayen ta basu san meye matsalar ba kawai suna ɗauka, lokacin auren ne baiyi ba.... ★★★ Tafiya take kamar tana tausayin ƙasa, sai ka rantse daga gidan wani sarautar ta fito, lalle ba shakka Ma'u akwai iya tafiyar ƙasaita, kanta sunkuye yake tana tafiyar ta cikin natsuwa da kamala.. Bata ankara ba taji tayi karo da mutum, ɗagowa tayi da sauri dan ta bashi haƙuri, amma mai maganar da take niyar mai ce, ta maƙe mata a maƙogwaro, sakamakon ganin kyawun mutumin, da kwarjinin da ya cika mata ido, in-ina ta fara wajen yi masa magana, amma ta kasa furta komai, shi kuwa mutumin duƙawa yayi ya ɗauko mata jakarta da ta yadda, saboda yadda zuciyarta ta tsorata da ganin mutumin, miƙa mata jakar yake yana Binta da wani sihirtaccen kallo.. Gaba ki ɗaya Ma'u ta shiga wani yanayi, mayataccen kallon da yake binta dashi, yasa taji tsikar jikinta tana tashi, hakan yasa ta juya baya da sauri, da niyar barin gurin, dan ita har ga Allah zuciyarta bata kwanta mata, da ganin bawan Allah nan da tayi ba.... Bata ƙara firgita da lamarin mutumin ba, sai da taji ya damƙi hannunta, bin hannun nasa tayi da kallo, har izuwa fuskarsa, hannun nata yake murzawa, yayin da idanunsa suka kasance a kumshe, hakan yaba Ma'u damar ƙare masa kallo, ranta take yaba irin kyawun da yake dashi, dan tana jin bata taɓa ganin wani mutum da yake da kyau irin nasa ba, sai da ta kalle shi up and down, sannan tace a ranta, "Wannan kyawu naka ai yafi kama da na al'janu." Buɗe idanun sa yayi da sauri akan fuskanta, Kamar yasan mai take cewa a zuciyar ta. Ita kuwa Ma'u da ya riƙe mata hannu na ɗan wani lokaci, hakan yasa taji natsuwa yazo mata, kallon shi tayi cike da tsiwa tace, "malam sakan min hannu, ka waniriƙen, sai kace ka Sanni." ta ƙare maganar tana hararsa , shi kuwa murmushi kawai yake, sannan ya sakan mata hannun yace "muje na rakaki inda zaki ɗin" Ƙasa mai musu tayi, hakan yasa tayi gaba, shi kuma yana Binta a baya, saidai tazo inda zata, sannan ta tsaya tace mai "dama nan zanzo." " Ok" kawai yace mata yana shirin juyawa, tana so ta tambaye shi sunan shi amma ta kasa, sakamakon ko shi shima bai tambaye ta sunan ta ba. Ji tayi yace "shine ko ki tambayi sunana" tsorata tayi dan har ga Allah gani take kamar yasan mai take cewa a zuciyar ta.. Tana cikin wannan tunanin taji yace mata "suna na *Haidar* fatan zan iya dawowa na kaiki gida....✍️ *WLLHI IN BA'A MIN COMMENT LITTAFIN NAN YA KUSA DAWOWA NA KUƊI, ,😳* *More comment* *More typing kullum😄* *Pls share* ~MRS KHAMIS CE~🥰💃 [5/23, 8:09 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *Page 12 & 13* __________"Eh." kawai tace tana shirin shiga cikin gida, ji tayi yace " *Asma'ul husnah* Haƙiƙa ina sonki," da sauri ta juyo baya fuskarta shanye da mamaki, ita ba wai cewa da yayi yana sonta ne ba, ya bata mamaki illah da taji ya faɗi, full name ɗin ta.. Saida ta ƙura masa ido na ɗan wani lokaci, sannan tace "amma a ina kasan suna na! Na ga tunda muka taho baka tambayi sunana ba, Gashi kuma naji ka faɗi cikakken sunan." Wani gajeren murmushi yayi, yace "baiwa ta kenan, duk lokacin da na haɗu da mutum, to kai tsaye zan iya ambaton sunan shi." "Uhmm sai kace wani al'jani, baka san mutum ba, amma har zaka iya sanin sunan shi.". Ma'u ta faɗa cikin sigar tsokana... Wani dogon numfashi yaja tukunan yace "oh kina ganin al'jani ne kaɗe yake da wannan baiwar.?" "Eh mana" Ma'u tace ataƙaice, "Ok ko Nima al'janin ne ban sani ba." "Ah ah rabani, ni WLLHI ba haka nake nufi ba, kaga tafiya ta, Allah da aka fara maganar aljanu, har naji tsikar jikina na tashi..". Ma'u ta faɗa haɗe da shigewa cikin gidan... *** Da yamma kuwa Haidar kamar yadda ya ce, sai Gashi yazo, sa yaro yayi yakira masa Ma'u, koda Ma'u ta fito ganin shi ya matuƙar bata mamaki sosai, dan batayi tsammanin dawowarsa ba, tayi tunanin wasa kawai yake mata.... Da murmushi a fuskarsa ya tare ta, yace "muje to Madam." "Uhmm! Madam kuma." Ta faɗa tana ware idanun ta, Hakan da tayi sai ta ƙara birgesa, dan shi komai yaga tayi burgeshi take... Kusa da wata hamshaƙiyar baƙar mota, ya tsaya, saida ya mata key, sannan yace da Ma'u "bissimillah! gimbiyata" Koda Ma'u ta shiga cikin motar yanayin sanyi AC da kuma ƙamshin dake Cikin motar, sai ya saukar mata da wani yanayi, lumshe idonta kawai tayi tana shaƙar ƙamshin dake gurin, jin shiru bai tada motar ba yasa ta buɗe idonta, kamasa da tayi yana kallon ta yasa tace "lfy kuwa." Girgiza mata kai kawai yayi alamun lfy klau, sai da yaja ajiyar zuciya tukunan yace "kinsan wani abu?." "Ah ah". kawai tace ɗorawa yayi da cewa "kin kwa san Yadda kike da kyau, dan ina ganin ko a al'janu babu mai irin kyanki." Dariya Ma'u ta saki sosai sannan tace "tofah kaide kam akwai ka da abun dariya wllhi." Ta faɗa tana ƙara sautin dariyar, tada motar yayi sannan yace "Ko! Ai haka nake so naga kina cikin nishaɗi, shiyasa nake saki safiyar." Tunda suka tafi kuwa Ma'u shiru tayi, aranta tana mamakin yadda aka yi ta sake dashi, kamar wani ta sanshi. Bai gama bata mamaki ba Saida taga yayi paking ɗin motarsa a ƙofar gidan su, cike da al'ajabi Ma'u tace "wai shin dama ka San gidan mu ne?." Yace "Eh mana! ". Ma'u tace "shiyasa naji ka ambaci suna na ɗazu." Saida yayi murmushi sannan yace "ai na sanki tun kina ƴar ƙaramar ki. " Kallon ban yarda ba Ma'u kawai tayi mai, Sannan tace mai bari ta shige gida, sallama suka yi ta shige gida shi kuma yayi tafiyar sa... Koda Ma'u ta shiga cikin gida, ba abinda take tinani illah mutumin da suka haɗu dashi, komai nasa gwanin birgewa, Gashi da abin al'ajabi ga salo, a taƙaice dai Ma'u ta rufta soyayyar wanda bata san ko shi waye ba... Shi kuwa Haidar murucin kan dutse ne, bai fito ba Saida ya shirya, cikin ƙanƙanin lokaci yasa Ma'u ta kamu da soyayyar sa mai tsanani, ta yadda duk ranar da baizo ya ganta ta ganshi ba to sai tayi rashin lafiya... Kamar yau kwanan sa uku bata ganshi ba duk ta wani firgice, tun inna na kulata har ta ƙyaleta gaba ɗaya. Washe gari kuwa Ma'u tana zaune, tana tsefe kanta wani yaro ya shigo, yace ana sallama da ita, da sauri tasa hijab ɗin ta, dan tasan babu wani saurayin da yake zuwa gurin ta, inba Haidar ba. Tana fita shi ɗin kuwa ta gani, murmushi kwance a fuskar sa, dan shi murmushi kamar yazama ɗabi'ar sa, dan ko da yaushe cikin fara'a yake. Ƙara sawa tayi cikin motar fuskanta fal murna yau taga masoyinta, bayan sun gaisane take mai ƙorafin lfy taga ya daina zuwa, "Wallahi lafiya klau nurul aini," ajiyar zuciya Ma'u ta yi harda dafe saitin zuciyar, sannan tace "har hankali na ya kwanta, wllhi dana ga baka zoba, ji nake kamar zan mutu dan Allah karka rabu dani, wllhi ina sonka sosai idan ka rabu sani mutuwa zanyi.." Ma'u ta ƙare wannan maganar har cikin ranta, kamo hannunta Haidar yayi sannan yace "a halitta ta, a ɗabi'a ta, da kuma soyayya ta agreki, baza su taɓa canjawa, na soki tunda daɗewa, kuma babu abinda zai sa na rabu da ke, ina sonki kamar bugun numfashi na, a kanki zan iya aikata komai saboda irin ƙaunar da nake miki, kuma keɗin mallakina ce, babu wanda ya isa ya mallake ki face ni, na miki alƙawarin daga yau bazan ƙara yin wata tafiya ba, da zata nisan tani daga gare ki ba, zan kasance tare dake a koda yaushe, kuma a duk inda kike.....✍️ _A GSKY INA JIN DADIN YADDA KUKE NUNAWA LBRN NAN SOYAYYA, SHIYASA NAKE YIN KU OVER ALLAH YA BARMU TARE_ *LOVE YOU ALL*🥰😘 *More comment* *More typing* *Pls share* ~MRS KHAMIS CE~🥰💃 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *14 & 15* ___________Haka ya cigaba da gaya mata kalamai masu daɗi da kuma ratsa zuciyar mai sauraro, duka a cikin kalaman sa babu wanda suka yi kama da yaudara, ko wacce kalma tana fitowa ne daga zuciyar sa.. Ita kuwa Ma'u ta yarda Haidar masoyinta ne na gaskiya, kuma bata da tamkar shi, shiyasa take masifar sonshi. Abinda Ma'u bata sani ba, a gidan su babu wanda yasan da batun Haidar, asali ma ita kaɗe ke ganin sa, domin duk soyayyar da yake nuna mata yana amfani da tunanin tane.. Yadda yake yi kuwa shine idan yaso ya ganta, zai yi amfani da ƙarfin su irin na al'janu, ya juyar mata da hankalin ta ta yadda komai zata gani kamar komai normal ne.... A zahirin gaskiya kuwa ko innah idan tazo gurin Ma'u, saide ta tarar tana bacci abin ta, domin Haidar yana da wayo sosai, bai bar wata kafa da za'a gane cewa Ma'u al'jani ya aure ta... Zaune suke a tsakar gida misalin wajen bayan isha'i, hira suke jefi-jefi kuma suna shan iska da ke kaɗawa a gurin, kasancewar ana zafi sosai a garin sosai.. Ma'u dake kwance gefe kan shimfiɗar ta, Wayar dake hannun ta ne tayi ƙara, kai duban ta tayi ga inna sai taga ta fara gyangyaɗi kaɗan kaɗan, tashi tayi da sauri haɗe da naɗe shimfiɗar ta ta shige ɗaki.. Faɗawa tayi kan katifar haɗe da ɗaga kiran, cikin zazzaƙar Muryar sa yace "Amincin Allah da yardar sa su tabbata a gare ki ya hasken idaniyata." " Uhmm tare da kai kaima". Ma'u ta faɗa cike da shauƙi, yace "Ameen! Masoyiyata, kinsan wani abu.?" Ma'u tace "ah ah" yace "nayi kewarki wllhi." Murmushi Ma'u tayi mai sauti, sannan tace "nima haka nayi kewar ka sosai." Haka sukayi ta musayar kalamai a tsakanin su har saida Ma'u, ta fara yin shiru alamun bacci take ji, sannan ya rabu da ita, sukayi sallama... ★★★ Zaune take kan ƙayataccen gadon ta na alfarma, wanda babu wacce ta isa ta haushi sai wadda take matsayin ta na amarya, shigowa yayi bakinsa ɗauke da sallama, murmushin dake kan fuskarsa ne ya kasa ɓoyuwa, takowa yayi izuwa gare ta cike da ƙasaita, yayin da annurin fuskarsa yake ƙaruwa... Lulluɓin dake kanta ya yaye a hankali, cikin zumuɗi yake ƙare mata kallo, inda zuciyar sa ke daɗa ta'azzara da begen wannan kyakkyawar halittar dake gaban sa.. Ya tsunsa guda biyu yasa ya ɗago da fuskanta, kyakkyawar fuskanta yake ƙarewa kallo, ji yake kamar ya haɗiyeta dan tsananin son da yake mata, hannunta ya kamo cikin nasa murzawa yake a hankali, cikin kasalaliyar Muryar sa yace "masoyiyata! Gaki a matsayin matata kuma mallakina, wata kulawa zaki bani?, fatan dai baza amin rowa ba." Ya faɗi haka yana ɗaga mata gida, ita kuwa yanayi yadda yayi maganar sai ya bata kunya hakan yasa tasa hannunta ta rufe fuskarta, cikin tsantsar so da begen ta ya matsa kusa da ita, hannun da ta rufe fuskarta dashi ya cire, haɗe fuskarta da tashi yayi, ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi, yayin da yake goga hancinsa akan nata, muryar sa can ciki yace "Nidai gsky bansan wannan kunyar a rage ta, dan ita ke cuta ta pls a rageta," ya ƙare maganar yana shinshinarta.. Ita kuwa da duk tabi ta firgice da irin salon da yake mata, dama shi ya daɗi akan network... Sosai yake sarrafa ta iya son ransa tun ya nabinta a hankali har ya fara da sauri sauri, baibar taba har saida ya cimma burin sa, bayan komai ya lafa ne sai ya rungume ta a jikin sa cikin kunnen ta yake raɗa mata kalamai masu daɗi da sanyaya zuciya.. Ma'u dake kwance take wannan mafarkin, yanayin ya mata daɗi sosai, hakan yasa tayi wata doguwar miƙa, pillon dake kusa da ita ta rungume tsam, kamar ta samu Haidar ɗin ne, wanda a zahirin gsky shi ɗin ne kuwa, Haidar kuwa da yaji ta rungume shi, wani ƙayataccen murmushi ya saki, yana jin bazai taɓa iya rabuwa da ita ba, musamman yanzu da ya sadu da ita, sai yake jin koda mutanen duniya zasu taru dan su raba shi da ita, to bazai rabu da ita ba. Tashi yayi zaune haɗe da tallabe fuskarsa kallon kyakkyawar suffarta yake, ciki da bai yana yiwa kansa fatan kasancewa da ita na har abada.........✍️ *_Tofah Reade's Nima fa na fara tsorata da lamarin Haidar fa😳_* *More comment* *More typing* *Pls share* ~MRS KHAMIS CE🥰💃~ [5/26, 3:11 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *16 & 17* ________washe gari da safe Ma'u da ta tashi Jikin ta duk ba daɗi, asalima ji take kamar bata da lfy, tun asuba da ta fito tayi salla bata ƙara fitowa ba, kwance take a ɗaki amma zuciyar ta maƙale take da tunanin Haidar, tuno mafarkin da tayi jiya ne hakan yasa ta cusa kanta tsakanin filallika, wani kalar yanayi take ji a tattare da ita, hakanan taji son Haidar ya ƙara lunkuwa a zuciyar ta.. Wayar ta dake ƙasan fillonta ta janyo, dubawa tayi taga ko Haidar ya kirata, ganin bai kirata ba hakan yasa ta danna mai kira, amma sai kiran yaƙi tafiya, ajje wayar tayi a gefe tana ɗan sakin ƙaramin tsoki..... Bata daɗe da ajiyewa ba, wayar tayi ƙara jiki na tsuma ta ɗauko wayar ganin Haidar yasa da hanzari ta ɗaga kiran... Cikin kukan shagwaɓa tace "Uhmm! Uhmm,. tun ɗazu nake so naji muryarka, amma kiran yaƙi tafiya saura kiris na fara kuka." Haidar cikin ruɗewa yace "yi haƙuri masoyiyata, wllhi inda nake ne ba network shiyasa, amma ai ina zaune naji zuciya ta ta gayamin kina kewa ta, shiyasa ban yi ƙasa a gwuiwa ba na kira ki, yanzu faɗa min me kike so?, ba tare da ɓata lokaci ba yanzu na miki." Cikin ƙasa da murya tace "kai nake so." Yace "to ai kin daɗe da samuna Nurul aini, ko kina so ki ganni ne."? "Eh mana." "To yanzu zaki ganni ko minti ɗaya ba za'a ƙara ba". Cikin kiɗima Ma'u tace "taya kenan." "Hmm kede rufe idonki zaki gani." Rufe idon Ma'u tayi, cikin ƴan sakanni taji kamar an ɗauke ta kan iska ana tafiya da ita, bayan ƴan wasu sakannin taji komai ya lafa, Muryar Haidar ta tsinkaya yana cewa "to buɗe idonki," a hankali take buɗe idon har ta kammala buɗewa, tsintar kanta tayi a kwance kan wani makeken gado na alfarma, yayin da Haidar yake gefen ta yana aika mata da wani irin saƙonnin kallo iri iri, zuciyar ta na lugude ta tashi zaune cikin tsoro da firgicin me ya kawo ta nan, juyowa tayi da niyar ta tambaye shi ya akayi hakan... Shi kuwa Haidar ganin ta tsorata da yanayin, sai ya janyo ta izuwa jikinsa rugumeta yayi tsam, kamar za'a ƙwace masa ita, ita kuwa Ma'u kicikicin ƙwatar kanta take dan har yanzu tana cikin ruɗu... Ganin ta kasa bashi haɗin kai, hakan yasa yace "kalleni." Kallon sa take irin kallon ƙurulla ɗin nan, yayin da Haidar yake kallon ta wani nau'in abubuwa suna fitowa daga cikin idanunsa suna shiga nata, lokaci ɗaya Ma'u jikinta yayi sanyi jinta ta riƙa yi kamar ba ita ba, wani bacci ne mai nauyi yayi awon gaba da ita, shi kuwa Haidar ganin Ma'u tayi bacci, sai ya saki wani shu'umin murmushi, haɗe da gyara mata kwanciya a jikinsa.. Bai barta haka ba har saida yabiya buƙatarsa, ita kuwa Ma'u bata san abinda ke wakana ba tana can duniyar baccin ta, mafarki ta kumayi irin na jiya wai gashi Haidar yayi amfani da ita.... ★★★ Da misalin ƙarfe sha biyu inna ce zaune a tsakar gida tana tsintar shinkafa, sai faman sababi take tana cewa "haba dan Allah mutum shi sai yayi ta bacci ko gajiya ba yayi, duk baccin da kika yi da dare bai isheki ba, har sai kinyi na safe, na safe ma ba ayi kaɗan a tashi ba a'a har sai anyi na wuccin misali, gashi yanzu rana tayi..." Ganin hakan bai mata ba yasa ta tashi, ta shiga ɗakin da Ma'u take kwance, kiran sunan ta inna take amma shiru Ma'u bata tashi ba, kamar wata matatta.. A fusace inna ta ɗaka mata duka, da hanzari Ma'u ta tashi tana cewa "haba innarmu!, Kede kam baki so kiga mutum yana hutawa, yanzu fa na ɗan kwanta." Inna kuwa dake faman aika mata da harara tace "au yanzu ma kika kwanta ko, to ai sai ki koma ki cigaba da yin baccin, tunda kin zama malalaciya, wllhi duk namijin da ya aure ki idan baya da kuɗi ko wllhi ƙazama zaki koma.." inna ta faɗa tana shirin barin ɗakin, tashi Ma'u tayi da sauri dafo inna tayi ta baya tace "ai wllhi innarmu in na auri mai kuɗi ke kanki saide a miki komai, kawai aikin ki kwanciya ki huta, sai cin abinci sai sallah." Daƙuwa inna tayi mata tace "gidan ku an gaya miki kowa malalacine kamar ki.". Dariyar shaƙiyanci Ma'u tayi tace ai wllhi innarmu har tsintar shinkafa sai kin daina yi, saidai kina zaune inji ya tsince miki shinkafar ki." Cikin dariya inna tace ƙarfi da yaji kin mai dani kakar ki ko,? To nidai fatana Allah ya kawo wannan lokacin, bani da wani buri da ya wuce inga aurenki husnah, Allah ya fito miki da miji nagari da gaggawa..." Inna ta ƙare maganar cikin marereta, Ma'u kuwa bata ce komai ba tayi tsakar gida, ruwa ta ɗiba a botiki zata yi wanka, koda ta cire pant ɗin ta ganin ya ɓaci sosai hakan yasa ta ɗaura niyar wankan janaba, a zuciyar ta tana mamakin yadda akayi dan jiya da dare ma da tayi mafarkin Haidar yayi sex da ita, da asuba saida tayi wanka, yanzu ma wannan dan baccin da tayi, Saida tayi mafarkin yayi sex da ita, a ranta tana so ta tuna wani abu saide ta kasa tunawa, kawai abu ɗaya take tunawa, shine! Daɗin da Haidar yake jiyar da ita da kuma soyayyar da yake nuna mata, murmushi tayi saboda amsar da zuciyar ta, ta bata idan kana son abu komai ma yakan iya faruwa.........✍️ *Mutane da dama suna tambaya ta meye namijin dare, wasu sun sani wasu basu sani ba, To amma insha Allah next page zanyi magana akan shi namijin dare, da kuma alamomin sa, bawai iya mace ke da namijin dare ba, harma maza akwai masu macen dare, kude ku cigaba da biyoni acikin wannan lbr na namijin dare* *_masu min fatan alheri da addu'a ina godiya sosai Allah ya bar zumunci, ga wanda keda tambaya ko wani sharhi zai iya tintiɓata a Whatsapp number na kamar haka. 09137879957_* *Whatsapp only* *More comment* *More typing* *Pls share* ~MRS KHAMIS CE🥰💃~ [5/28, 12:58 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *18 & 19* __________Yau da gobe kullum kwanaki ƙara tsayi suke, yayin da Ma'u tayi matuƙar sabo da Haidar, dan yanzu ako wani lokaci takan iya ganin shi ta kowanne yanayi.. Tun tana ganin wasu abubuwan ban barakwai, har yanzu tazo tayi wani mugun sabo da hakan, ga soyayyar da yake nuna mata mai tsayawa arai.. ★★★ Wasu hamshaƙan motoci ne suka faka a ƙofar gidan su Ma'u, wani dattijo ne mai cike da kamala ya fito daga ɗaya daga cikin motocin, wanda kallo ɗaya zaka mai ka gane hutu dajin daɗi su zauna a jikin sa, ɓangare gidan kawu salisu yayi fuskarsa ɗauke da fara'a..... Shi kuwa kawu Salisu da yake tsugunne a ƙofar gida yana al'wala, mamakine ɗauke a fuskar sa ganin mutum ya nufoshi da murmushi, ƙura masa ido yayi dan bai gano ko waye ba. Saida ya ƙara matsowa kaɗan sannan kawu Salisu ya zabura da sauri yace "Ibrahim! Ashe rai kan ga rai..?" Wanda aka kira da Ibrahim ɗin kuwa murmushi yayi yace " wllhi kuwa ashe rai zai ga rai." Shiga dashi cikin gida kawu Salisu yayi fuskarsa da murnar da takasa ɓoyuwa.. Bayan ya gabatar mai da abinci da ruwan sha, babu ƙyama ko nuna isa Alhaji Ibrahim ya zauna yana cin abincin, bayan ya gama ne sai kuma suka ɓarke da hirar yaushe gamo, wani abun ayi ƙwala wani abun kuma a saki dariya, dan sun kai tsawon shekara sama da talatin basu haɗu ba, anan ne kawu Salisu yake ba Alhaji Ibrahim labarin rasuwar yayansa Bashir wato mahaifin su Ma'u, nan ya jajan tame haɗe dayi mai addu'ar Allah ya jiƙansa... Cigaba suka yi da hirar su, inda suka kwashe tsawon awanni uku suna zantawa, tashi Alhaji Ibrahim yayi yace "To ni yanzu tafiya zanyi fatan dai zamu cigaba da zumuncin mu, ta yadda ko bayan ran mu iyalain mu zasu cigaba dayi.. Fitowa suka daga cikin gidan a tare, yayin da Alhaji Ibrahim yayi wa kawu Salisu sha tara ta arziƙi, har yazo zai shiga Mota sannan ya jiyo yace "amma ina ne gidan marigayi ina son na gaishe da iyalinsa..” kawu Salisu yace ga gidan nan ai a ƙofar gidan ma kuka ajje mota,." Alhaji Ibrahim yace "to masha Allah ai sai ka yi musu magana koh, sai in shiga mu gaisa." Kawu Salisu yace "ah bissimillah ka shigo ai ba wata matsala." Sallama sukayi cikin gidan, Ma'u dake zaune tsakar gida tana dakan barkono ita ta amsa musu sallamar, ganin kawu Salisu da wani Alhaji yasa ta shiga ɗaki ta ɗauko sabuwar tabarma, shimfiɗa musu tayi haɗe da tsugunnawa tana gaishe su, amsawa Alhaji Ibrahim yayi yana ƙare mata kallo, komawa Ma'u tayi ta cigaba da dakan barkonon ta, kawu Salisu ne yace "ke Ma'u ina adda Hajaran take?." Inna da ta fito daga cikin bayi hannunta ɗauke da buta tace "gani nan ina zuwa, ɗaki ta shiga ta ɗauko mayafin ta rufe jikin ta tayi dashi, zuwa tayi ta zauna dab da su gaisawa sukayi inna tana wa Alhaji Ibrahim kallon rashin sani, kawu Salisu kuwa ganin inna bata gane Ibrahim ba, yasa yayi saurin cewa inna "adda Hajara!, Amsawa inna tayi tace "na'am." Kawu Salisu cigaba yayi da cewa "ina wani abokina wanda a lokacin kina amarya, muke zuwa in kinyi abinci mucinye miki.." Shiru inna tayi tana tunanin abun dan anyi wajen shekara arba'in, can inna sai tace "kodai Ibrahim ne." Kawu Salisu yace "eh shine." Fuskar inna da mamaki tace "Allah mai iko! Ibrahim ashe dama kana nan.?" Yace "wllhi kuwa adda yau gani kin ganni." Na suka ɓarke da wata hirar, har saida suka gaji dan kansu sannan Alhaji Ibrahim yayi musu sallama, tare da musu alƙawarin insha Allah zai kawo matarsa da ƴaƴan sa su gansu. Itama inna sha tara ta arziƙi yayi mata kamar yadda yayiwa kawu Salisu, bayan kawu Salisu ya raka shi bakin mota ne sai Alhaji Ibrahim ya lalle shi yace "amma wannan yarinyar budurwa! Ƴar waye.? Kawu Salisu yace "ai ƴar wajen yayana ce itama, itace ƴar adda Hajara ta uku." "Ayya fatan dai ba'a mata miji ba."? Kawu Salisu yace "eh to gsky bata da wani tsayayyen saurayi, dan duk anyi wa ƙannan ta aure, ita ce kawai Allah bai kawo mijin auren ba..." Alhaji Ibrahim yace "to shikenan nidai na yaba da hankalin ta, insha Allah zanyiwa *suraj* magana akan yazo ya ganta, idan ya mata, shima ta masa kaga sai su daidaita kansu... " Sallama sukayi da kawu Salisu sannan escort ɗinsa suka ja motar..... ★★★ *WANENE ALHAJI IBRAHIM* ______Alhaji Ibrahim wani shahararren ɗan kasuwa ne, kuma shahararren ɗan siyasa, dan yanzu haka shike kan kujerar sanata cikin Katsina ta tsakiya. Alhaji Ibrahim aboki ne ga kawu Salisu tun suna yara tare suka taso, abotar su ta koma ƴan uwan taka, dan a ta dalilin abotarsu ne har suka haɗa iyayen su suke zumunci.. Alhaji Ibrahim yana da shekara ashirin da biyar iyayensa suka tashi daga cikin batsari suka koma cikin garin Katsina, kasancewar mahaifinsa ma'aikacin gwamnati ne, amma duk da haka yana ziyartar abokinsa kawu Salisu.. A lokacin ne iyayen Alhaji Ibrahim suka mai aure, harkokin gida da na neman kuɗi suka sa ya rage zuwa batsari... Allah cikin ikon sa ya ɗakaka kasuwanci Alhaji Ibrahim har yazama daga wannan kasar zuwa wannan ƙasar, Alhaji Ibrahim yaran sa uku duka maza babban ɗansa shine suraj sai mai bi masa mubarak sai ƙaramin su Salisu.... WANNAN KENAN Shi kuwa kawu Salisu da yaga Alhaji Ibrahim ya tafi, da sauri yazo yana sanar da inna abinda Ibrahim ɗin ya faɗa, inna tana nuna tsatsar farin cikinta tace "Allah ya tabbatar da hakan, dako nayi farin ciki dan Ibrahim abin a haɗa zuri'a da shi ne, ya cika mutumin kirki.." Kawu Salisu yace "wllhi kuwa! Ni kaina nayi mamakin yadda bai mantani ba." Inna tace "ai kuwa ya kyauta sosai wllhi, Allah dai ya tabbatar mana da alkairi." Kawu Salisu yace "ameen! " Yana shirin barin gurin... Ma'u kuwa dake gefe tana zumɓura baki, ji tayi har ta tsani suraj ɗin da ko sanin shi bata yi ba, tashi tayi ta shige ɗaki tana jin haushin su inna dake neman kai da ita, sai kace an gaji da ita.......✍️ *YAU INSHA ALLAH ZAN CIKA ALƘAWARIN DA NA DAUKA AKAN YIN BAYANI NAMIJIN DARE✍️ *ALAMOMIN NAMIJIN DARE.* _Daga cikin alamomin da mace zata gane tana da wannan matsalar sune:-_ *_Shi wannan shaidanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita acikin barci,yawancin mata suna tsintar kansu cikin wannan yanayi,amma sai su dauka halin mafarkine kawai,to a gaskiya ba haka lamarin yake ba._* *_Yadda lamarin yake shine:-_* _Duk mata ko budurwar da take irin wannan mafarkin zaka sameta tana fama da wadannan matsalolin zatace maka tana fama dasu._ *Gasu kamar hak:-* *_[1]Bacin rai ba tare da anyi mata komaiba,haka kawai taji tanajin haushin kowa har ma mijinta,ko kuma taji kamar mijin nata ya saketa,ita ta gaji da auren,wanda da zaka tambayeta laifin mijin nata bazata iya fadin komaiba akai,kai wata rana ma taji ta tsani y'ay'an data haifa._* _[2]Yawan ciwon kai daga lokacin zuwa lokaci kuma baya jin magani ko kadan._ _[3]Tsananin ciwon kirji da ciwon baya mai tsanani._ _4]Tsananin ciwon mara lokacin jinin al,ada da kuma zubar wani ruwa daga farjin mace,kuma tasan wannan ruwan ba al,adarta bane,_ *kuma ya kasu kamar haka:-* *[a] mai yauki* *[b] marar yauki* *[c] ko mai kauri kamar koko tare da yawan kaikayi* *[d] ko fesowar kuraje masu zafi.* *[5] Idan mijinta yana sauwa da ita sai take jin zafi,ko kuma yana saduwa da ita batajin zafi,amma bata samun biyan bukata.* *[6]Kusan sallar magriba sai ta fara jin zazzabi ko faduwar gaba ko yawa firgita,ko kasala da bacin rai.* *[7]Idan ta dauki al-qur'ani zata karanta,saita rinkajin kasala, da hamma mai sanya hawaye, kuma tanajin barci sosai,amma da zarar ta ajiye Al-qur,anin sai taji ta wartsake kamar ba itace takejin bacci dazu.* *[8]Kuma idan ta kwanta zatayi barci sai ta kasa yin baccin tayi ta juyi akan katifa,idan mijinta yazo kusa da ita sai take jin firgici da tsoro.* *[9]Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga zubewa ko ya canja ya zama jawur,lebenta kuma ya rinka bushewa ko yayi jawur.* *[10]Yawan kaikayin ido da kaikayin kai na amosani,amma ba amosani bane.* *[11]Yawan kaikayin kunne dana hanci kamar mura zata kamata,amma kuma ba mura bace,ko yawan kumburin ciki.* *[12]Yawan zubar da jini wanda ba jinin hailaba,ko hailarta ta dinga yi mata wasa.* _Sannan kuma harma wacce bata da aure budurwa ko bazawara zata iya tsintar kanta acikin wannan matsalar,amma ita ban-bancinta da mai aure._ *shine kamar haka:-* *_[1]Ita marar aure zata kasance duk lokacin da wani yazo wajenta da maganar aure kamar za,ayi sai abin ya lalace daga bangarenta ko bangaren wanda zai aureta._* *_[2]Zata dinga munanan mafarkai tare da ganin wani namiji yana zuwa yana saduwa da ita acikin bacci da fuskar wanda ta sani ko da fuskar yar,uwarta mace._* *_[3]Sannan zata rinka samun cututtuka masu wuyar waraka,kai harma da yawan zubar da jini ko jin ciwo,ko jinin yake zuba amma ba lokacin hailarta ba,ko ta rinka jin kasala ayayin da take karatun al-qur'ani tana fara karatun sai hamma ,kasala su baibayeta,ko kuma idan ana sallama da ita,sai ta rinka jin faduwar gaba ko tsorata._* *_[4]Kuma zata yawaita samun sabani da kiyayya tsakaninta da iyayenta ko 'yan uwanta ko jama'a ko kuma ta zama mai rashin kunya da rashin magana da iyaye da sauran dangi. Allah ya kara tsaremu daga sharrinsu tare da yi mana katangar karfe dasu, amin._* *IN ALLAH YA YARDA NEXT PAGE ZANYI BAYANI AKAN YADDA ZA'A MAGANCE WANNAN MATSALA TA NAMIJIN DARE* *More comment* *More typing* *Pls share* ~MRS KHAMIS CE 🥰💃~ [5/30, 10:32 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *page 20 & 21* _________Cikin ƴan kwanakin nan Ma'u kullum cikin ɓacin rai take, kuma ba komai bane musabbabin haka sai su inna da basu da wata magana sai ta zuwan Suraj, Ma'u a koda yaushe cikin zullumi take, ba maganar da take ɗaga mata hankali sai irin taji an ambaci za'a mata aure.. Shiru shiru Alhaji Ibrahim bai kira kawu Salisu ba akan maganar ɗansa da kuma Ma'u ba, tun yana jira har yabar abun a ƙila ko ɗan nasa ya samu mata shiyasa bai kira sa ba, ko kuma yana jin kunyarsa ne.. Ana haka aka ɗau tsawon watanni, hakan yasa kawu Salisu ya dage da yiwa Ma'u addu'ar, Allah ya kawo mata miji nagari itama ko ta huta... Kasancewar lokacin siyasa ne, duk wani mutum da yake harkar siyasa, to idan lokacin yayi sun fi neman mutane, haka ta kasance ayau , kawu Salisu ne tsaye da chairman ɗin L.G wato Alh Tanko suna tattaunawa, inda kawu Salisu yake ce mai "wato na fahimci cewa ku ƴan siyasa ɗin nan, ba kwa neman mutane sai siyasa ta matso, sai ku fara jan mutane a jikin ku dan wai a zaɓe ku, to ba campaign ɗin da zan ma." Dariya Alh Tanko yayi yace "haba aboki na! Wllhi da alkairi nazo, dama zuwa nayi na cema ka taramin mata wanda mazajen su suka rasu, kuma suke da marayu, akwai wani tallafi da za mu basu suja jari.." Murmushi kawu Salisu yayi sannan yace "ban tarawa! Ni kaina yaushe rabon da ka neme ni, ina ga tun kan ka hau kan kujerar chairman, sai yau kuma da buƙatar ku ta ƴan siyasa ta taso..." Cigaba sukayi da tattaunawa, Ma'u da ta dawo daga aiken da inna tayi mata, ganin kawu Salisu tsaye da baƙonsa hakan yasa ta tsugunna ta gaishe su, shi kuwa Alh Tanko kallo ya bita dashi, saida ta shige cikin gidan sannan ya dawo da kallon sa zuwa ga kawu Salisu yace "wannan kyakkyawar yarinyar fa daga ina.?" Kawu Salisu yace "ƴata ce." Sosa ƙyeya Alh Tanko yayi sannan yace "ko za'a bani auren ta!, idan ba'a mata miji ba.?" Shiru kawu Salisu yayi yana ɗan wani nazari yace "nace ma fa ƴata ce ko!." "Eh ai naji ! Sanin haka yasa na nemi auren ta, kuma nasan kasan waye ni, idan ina da wani mugun halin kasani, idan bani dashi kasani, saide ban sani ba ko baza ka bani ba, idan kuma an mata miji sai ka faɗa min in haƙura.." Kawu Salisu yace "a'a gsky ba'a mata miji ba, zaka iya zuwa idan ta amince da kai to na baka ita.." murmushi Alh Tanko yayi yace "to Masha allah! Allah ya tabbatar mana da alkairi.." "Ameen!." kawu Salisu yace suna yin sallama, bayan Alh Tanko ya tafi sai kawu Salisu ya shiga gidan yana labartawa inna abinda ya faru tsakanin sa da Alh Tanko, cikin murna inna tace "ai kawai kace yazo ya ganta gobe ma inda hali.." _________________________________________ TO FAH READE'S IDAN BAKU MANTA BA FARKON LBRN KENAN INDA ALH TANKO YAZO GURI MA'U YANZU ZAMU DAWO KAN LBRN NE...✍️ ____________________________________ Kwance take kan katifa tayi rufda ciki, sai raira kukanta take gwanin ban tausayi, ita ba komai bane yafi ƙara karyar mata da zuciya ba illah cewa da inna take Alh Tanko taimakon ta yake so yayi, kuma a rasa wanda zai taimake ta sai wannan tsohon banza, ita wllhi ta tsane shi da wani fuskarsa sai kace biri... Ganin kukan bazai mata ba hakan yasa, ta tashi taje tayi al'wala, sallar isha'i ta gabatar, bayan ta idar ne sai ta miƙe da niyar yin nafila Sannan tayi addu'a akan Allah ya kawo mata sauƙin cikin lamarin ta, amma sai ta kasa yi, cire hijabin nata wurgi tayi dashi a ranta tana jin baƙin cikin hakan.. Komawa tayi kan katifar ta kwanta, ba tare da tayi addu'a ba bacci yayi awon gaba da ita... Cikin baccinta take mafarkin Haidar ya kunna wata ga garumar wata wuta, ɗaukar wutar yayi da hannunsa ya jefata a cikin wani gida, lokaci ɗaya gidan ya kama da wuta, jiyo da kallonsa Haidar yayi zuwa ga ma'u yace "duk wanda yayi gingin neman auren ki, kaɗan daga cikin irin hukuncin da zan mai, har sai na tabbatar da baya numfashi a doron duniya........✍️ *AFUWAN KUMIN HAƘURI WLLHI BANDA CIKAKKEN LOKACIN YIN DOGON TYPING AMMA INSHA ALLAH NA SAMU LOKACI ANJIMA ZAKU IYA JINA*🥰 _SANNAN WANDA BASU FARA KARANTA LBRN NAN DAGA FARKO BA , ZASU IYA NEMA DAGA FARKO SU KARANTA SAI SUNFI GANE KAN LBRN_👌 *MORE COMMENTS* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MRS KHAMIS CE~🥰💃 [6/3, 12:23 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *22 & 23* ____________a firgice Ma'u ta tashi daga baccin, nishi take kamar wacce tayi gudun tsawon kilo mita dubu, dafe ƙirjinta tayi tana maida numfashi, a ranta tana ayyana miye fassarar wannan mafarkin da tayi yanzu... Jin kiraye-kirayen sallar asuba da tayi ne, yasa bata koma baccin ba, zama tayi tana ta tinane-tinane, inna ce ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, haske Ma'u tayi da (tochlight) fitila ɗin dake hannun ta, ganin ta zaune sai abun ya bata mamaki.. ,,, Inna tace "lafiyar ki kuwa Ma'u! Na ganki zaune a wannan lokacin.?" Numfasawa Ma'u tayi sannan a hankali tace bakomai innan mu kawai dai naji kiran sallah ne, shine na tashi.." Inna tace "ohhh! Nasha ba lafiya ba, yanzu sài ki tashi kiyi sallah.." inna ta faɗi haka tana barin ɗakin.... Ma'u kuwa tashi tayi tsaye a sanyaye, kamar wacce ƙwai ya fashe wa a ciki, da ƙyar ta idar sallar nan sakamakon wani azababben ciwon kai da ya saukan mata, bayan ta samu ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita... ★★★ Da safe kuwa misalin ƙarfe 7:30 daidai, kawu salisu ya shigo gidan a firgice, inna dake zaune tana haɗa musu abin kari tace "lfy Salisu naga ka shigo ba ko sallama." "Hmmm! Kede bari adda Hajara, yanzu Alh Tanko yamin waya yake cemin jiya gidan sa gobara akayi, suna cikin bacci wuta ta kama, Allah yasa sun tsira da ransu, amma yace bai fitar da komai ba." Kawu Salisu ya ƙare maganar yana cigaba da cewa "Kuma Ni babban abinda yaban mamaki da tu'ajjabi shine, da yake cemin wai ya fasa auren Ma'u, in mun sami wani mu ba shi, amma shi wai ya fasa.." Dare ƙirji inna tayi tace "ohh ni Hajara! yanzu shi Alh Tanko dan ƙaddara ta same shi sai yace ya fasa, Allah ka dubemu ka fitowa da Ma'u mijin aure.." Inna ta faɗa tana ɗaga hannun ta sama.... Ma'u kuwa Allah sarki tana can tana baccinta, bata san abinda ke faruwa ba, sai bayan da ta tashi take jin labarin fasa aurenta da Alh Tanko, da kuma gobarar da yayi, bata san meyasa ba, haka kurum ta tsinci kanta da ji daɗin hakan a zuciyar ta.... Shi kuwa Alh Tanko abinda ya faru dashi shine...... Da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare, kwance yake shi kaɗai a kan gado dama tun da ya zowa da matansa batun auren sa da Ma'u, yaga kowacce cikinsu ta fara kawo masa da maganar rainin wayo, sai ya bi duk ya watsar dasu gefe, saide idan su suka neme shi, juyi yake shi kaɗai a ɗaki jin zafin da ake sai yà tashi dà ñiyar yín wanka bathroom kawai ya shige, koda ya fito kai tsaye kan bed ya nufa dan ya kwanta, jin yayi karo da wani abu yasa da sauri ya ɗago kansa.. Abin mamaki Haidar yagani xaune akan gadonsa, ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya, cike da dauriya Alh Tanko yace "me ya kawoka gidana a halin yanzu! Sannan ma ta ina ka shigo?, Bayan na rufe ƙofar, kodai can dama da kai na rufe...?” Haidar fuskarsa babu alamun rahama yace "kaga nayi ma kama da wanda in zai shigo wuri sai yabi ta ƙofa, ta kowani yanayi nakan iya riskar mutum a duk inda yake.." Alh Tanko yace "to mai kake nufi da haka, ko kana nufin kai al'jani ne..?" Tashi Haidar yayi cikin isah da ƙasaita, yayi taku biyu zuwa uku, yace "naji daɗi da ka fuskanci hakan, ashe dama kai ba daƙiƙi bane, to ma'u ita ɗin mata tace, kuma bazan taɓa barin wani ya aureta ina kallo ba, saboda haka kaje ka janye aurenta da ka nema, inba haka ba zan salwartar da rayuwar ka.." Alh Tanko kuwa kawai binsa da ido yake Sa'annan kuma ya bushe da dariya yace "oh ni ɗan babana! yau wai ni akewa barazana, dan zan auri ƴar baiwar Allah ma'u, to bari kaji in gaya maka wani abu, na daɗai da sanin irin ku a gari, sai kunga yarinyar kirki kyakkyawa kuma mai nasibin samun manyan mutane, sai ta samu mijin aure saiku bi duk hanyar da kuka ga dama, kuyiwa wanda yazo neman aurenta barazana dan ya fasa ko, to kasani ni ba irin barazanar da zakamin wacce zata yi tasiri a gareni ba, kuma banga wanda ya isa ya hanani auren ma'u ba, ba aljani ba ko sarkin aljanu ne kai sai na auri ma'u kayi duk abinda zakayi.." Haidar da ya matuƙar fusata ya jiyo ga Alh tanko ,wata kalar girgiza yayi wacce lokaci ɗaya, halittun sa suka sauya izuwa abin tsoro, yace "dama nazo maka da aminci ne, a tinani na zaka amsawa buƙata ta, amma tunda kace haka bari kaga ƙarfin ikon aljani.." Alh Tanko da ya raɓe jikin bango, ko cikakken motsi ya kasayi, shidai kawai bin Haidar yake da kallo, yana so ya buɗi baki dan yayi magana, amma ya kasa cewa uffan.. Yana ji yana gani Haidar yasawa gidan sa wuta, sannan ne ya samu kƙarfin tashi ya fita da gudu dàn tàimaka ma iyalen sa, da ƙyar suka samu suka fita daga gidan basu cire komai ba.. Da asuba kuwa Haidar ya sake dawowa wajen alh Tanko yace "kaga bala'i na farko kenan, sauran kuma duk baza suma dad'i ba, amma wata alfarma da zan iya ma shine, idan ka janye daga aurenta, kaga wannan gidan naka da ya ƙone zan mallaka maka wani wanda ya fishi sannan na dawo maka da linkin abinda ka rasa.." Shidai alh Tanko shiru kawai yayi, zuciyarsa cike da tausayin ma'u da iyayen ta, haka ya kira su yace ya fasa auren ta. aransa yana mata fatan alheri da kuma fatan Allah ya rabata daga tugun wannan azzalumin shaiɗanin aljanin, da yake iƙirarin cewa shi musulmi ne...... *KWANA BIYU KUNJI NI DAN ALLAH KUMIN AFUWA, NI KAINA BANSO HAKA TA FARU BA SAIDE KOMAI SAI ALLAH YAYI, AMMA INA TARE DAKU MASOYA BOOK ƊIN NAN* *MORE COMMENTS* *MORE TYPING* *PLS KU RIƘA MIN SHARE DAN ALLAH* ~MRS KHAMIS CE~😍💃 [6/5, 10:24 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *24 & 25* __________Washe gari kuwa da yamma, Ma'u ce tsaye ɗauke da botikin wanka, da dukkan alamun bayi zata shiga... Kai tsaye bayin ta shige, ba tare da tayi addu'ar shiga nan ɗaki ba, bayan ta cire kayan tane, fara wankan ta ke da wuya, taji wani sihirtaccen ƙamshi ya cika gurin, sanin mamallakin ƙamashin da tayi ne yasa ta juyo da sauri, hango shi tayi tsaye a jikin bañgon bayin, ya naɗe hannunsa a ƙirjinsa, haɗe da ƙurawa halittun ta ido kamar zai cinye ta, dan ko ƙiftawa ba yayi.... Ganin haka da Ma'u tayi sai tasa hannunta, tana kare ƙirjinta, harararsa take ta ƙasa ƙasan ido, sannan tace "shine ina cikin wanka zaka shigo min ko! ni gaskiya ka juya ka daina kallonsa.." Murmushi yayi,. yana cigaba da kallon nata, matsowa ya fara yi kusa da ita, yayin da yake cigaba da yi mata wani mayen kallo, turo baki Ma'u tayi tana ɗan diddira ƙafafuwan ta, da hanzari ya ƙara so, tare da janyo ta jikinsa, ido cikin ido suke kallon juna kamar ko wannensu zai cinye ɗan uwansa.... Haidar kuwa da yayi nisa a cikin shauƙin begen masoyiyar tasa, yatsa yasa yana ɗan zagaye leɓenta, da suka fi komai jan hankalinsa, da matuƙar birgewa a garesa, a hankali yace "Ina son wannan leɓen! kuma ina kishin su, shiyasa banso inga yana wa kowa magana." Turo leɓen kuwa Ma'u ta ƙara yi, sannan cike da zallar shagwaɓa tace . "Uhmm! Ni ka barni inyi wanka na." Cikin wasa da kwaikwayon muryar ta yace, "Naƙi wayon! saide muje na miki da kaina." Ido Ma'u ta fiddo waje tace "ah ina kuma .?" Yadda ta fiddo idon sai hakan ya burge shi, cikin raɗa-raɗa yace "Ah gida na mana!." Da sauri Ma'u tace "To idan innarmu ta nemeni bata ganni ba fa?." Rungume ta yayi tsam a jikinsa yace "Inna bacci zata yi! Kuma kan ta tashi zan dawo dake.." Ya ƙare maganar yana hura mata iska a kunnenta, lumshe idanunta tayi saboda daɗin hakan da take ji, jinta tayi an tsoma ta a cikin wani ruwa mai daɗin ƙamshi, ga wasu fulawoyi da suka bai baiye saman ruwan, cikin natsuwa da kuma salo yake mata wankan, yayin da Ma'u take jinta kamar wata sarauniya... Haka aka gama wankan nan cike da soyayya, na ɗo ta yayi a towel, ya fito da ita daga bathroom ɗin, shimfiɗeta yayi akan bed ɗin dake cikin ƙayataccen ɗakin, shafe jikinta yake ta ko ina, a haka wani ɓarawon bacci mai ɗan karan daɗi yayi awon gaba da ita.... Bayan Haidar ya samu mutsuwar da yake so ya samu da ita, sai ya mirgina gefen ta yana ƙare mata kallo, cike da tsantsan so da ƙaunarta... Koda Ma'u ta tashi, idonta da Haidar ya fara tozali, murmushi ta sakar mai, shima martanin murmushin ya mayar mata, sa'annan yace "Fatan kin tashi lfy! Gimbiyata kuma sarauniyar da take mulkar zuciya ta." Murmushi Ma'u tayi ta sunkuyar da kai, matsowa Haidar yayi kusa da ita yace "Meye matsalar ki! Yanzu na miki maganin ta, dan zan iya komai akan ki hasken idaniyata.." Ɗagowa Ma'u tayi sannan tace "babu komai! Kawai na tuna mafarkin da nayi jiyane, kana sawa wani gida wuta, kuma da safe a kace gidan Alh Tanko ya ƙone, shin hakane da gaske kai kasa! Ko kuma mafarkin ne kawai..?" Gira ya ɗaga mata alamar eh hakane, sannan yace "Tabbas ni nasawa gidan sa wuta, kuma da ace bai janye maganar aurenki ba, to yau da shi zan ƙona, saboda danni kaɗai aka halicceki, ina ji ina kallo bazan taɓa barin wani namijin bil'adama Ya raɓeki, ke ko al'jani ne ya zo wucewa ta inda kike muduk ya kalleki, to sai na hukunta shi ko waye shi ɗin, kuma ko ɗan waye acikin jinsin al'janu....✍️ *Ina jin koken ku na cewa ya kamata akawo, wanda zai yi maganin haidar* *To koken ya iso gareni amma saide fa kusani Haidar shine lbrn in ba haidar to ba lbr*👌😄 *MORE COMMENT* *MORE TYPING AKAI AKAI*✍️👌 *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/7, 12:41 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *26 & 27* ____________Zuba masa ido kawai Ma'u tayi, tana matuƙar mamakin furucinsa da yake cike da alwashi.... San sanyar ajiyar zuciya Ma'u ta saki a hankali tace "To meyasa zaka aikata hakan..?" Saida yaja dogon numfashi sannan yace "Saboda ina sonki kuma ina ƙaunarki, Wallahi duk duniyar nan babu wanda ya kaini sonki da kishin ki, shiyasa ban ƙaunar inga ko wani ɗa namiji naga ya raɓeki koda kuwa shi waye.." Ita dai Ma'u ido kawai ta zuba mai tana mamakin son da Haidar yake mata, gashi kuma wani ɓangare na zuciyar ta, yana kwaɗaita mata son yin aure ko dan hankalin innarta ya kwanta... Haidar kamar yasan abinda take ayyanawa a ranta, hannunta ya kamo sannan a hankali yace "Husnah ni ban isheki ki ƙare rayuwar ki dani ba?, Zan baki duk wani farin cikin da bil'adama bazai iya baki shiba, zaki kasance a cikin zuciyar da bazata taɓa yi miki kishiya ba, zan nuna miki soyayyar da ba'a taɓa yiwa wata ƴa mace ita ba a cikin duniyar masoya, ki cire tunanin auren wani bil'adama, ni nan kaɗai na isa na baki farin cikin da babu wani mahaluki da zai iya baki shi..." Lumshe ido Ma'u tayi yayin da hawaye yake kwaranyowa daki daki, rungume ta Haidar yayi, yana bubbuga bayanta a hankali alamar rarrashi... Cikin raunin murya Ma'u tace. "Haidar nasan kasan cewa, innarmu bata da wani buri da ya wuce taga nayi aure, kuma gashi..... Yatsar sa yasa a leɓenta yace "Shishhht! Nasan komai basai kin gayamin ba, amma ga tambaya ɗaya zuwa biyu da zan miki, idan na samu amsar ta dai-dai yadda nake so naji to zan yanke hukunci da ya dace.." A hankali Ma'u ta ɗago tana kallon cikin idonsa, duk da dai har yanzu bata iya kallon cikin idonsa, sunkuyar da kanta tayi tana kallon ƙasa.... Ɗago da kanta Haidar yayi sannan yace "ki kalli cikin idona mana, pls mana masoyiya ta." Kallo shi take cikin ido, yayin da take ji duk tsigar jikin ta tana tashi, yanayin salon kallon da Haidar yake mata, sai ya jefata cikin wani yanayi jinta take kamar ba ita ba, Saida ya ɗau wasu ƴan sakanni sannan yace, "Kina sona! Kuma zaki iya rayuwa dani.?" Girgiza kai Ma'u tayi alamar eh, hannunta Haidar ya kamo sannan cikin wani irin salo yace. "Da bakinki nake so naji kin amsa min." Eh kawai Ma'u tace a taƙaice . Cikin murna da zumuɗi Haidar yace "Da gaske! Kuma kinyi alƙawari.?" Ma'u tace "eh mana." Ta faɗa tana murmushi.. Rungume ta Haidar yayi, yana jin farin ciki marar misaltuwa, a ganin sa tunda Ma'u itama tana sonshi to dukan matsalolin sa sunzo ƙarshe.. Haidar bai maida Ma'u ba sai gabda magribah, kai tsaye ɗakinta ya ajje ta... Bayan ta gama shiryawa tsakar gida ta fito, samun zahrah tayi har ta gama girkin dare, kasancewar inna gwana ce wajen koyawa yara girki, ko kaɗan bata so taga yaro ya taso bai iya girki ba... Dundu Ma'u ta kaiwa zahrah a baya, sannan tace "autar mu! ina innarmu take ne". Inna dake fitowa daga cikin ɗaki, fuskarta da alamun bacci tace "Gani wake nema na?". Ma'u tace "nice innarmu." "Ohh Wllhi nasha baƙuwa nayi," Inna ta faɗa tana ɗaukar buta... Zahrah dake durƙushe tana dariya tace "innarmu ina ga baccin bai isheki ba." Guri Ma'u ta samu ta zauna tana cewa "da alama kuwa gaskiya." Haka rayuwa tayi ta tafiya kullum soyayyar Ma'u ƙara lunkuwa take a zuciyar Haidar, musamman yanzu da yake ganin bashi da wani abu da ya shige masa gaba..... Ta ɓangaren Ma'u kuwa saide muce subhanallah, Dan yanzu babu wanda yake zuwa yace yana sonta, ita dama ko a jikin ta dan duk namijin da ta kalla, saide taga ya zaman mata abin tsoro ko taga muninsa, Haidar shi kaɗai take ganin farinsa a doron duniyar s nan, sai ƴan uwanta maza wanda suka kasance muharramanta, amma sauran maza ita dasu *hai hata-hai hata*.......✍️ *More comment* *More typing* *Pls share* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/8, 8:48 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *28 & 29* ____________Haidar ne zaune a cikin wani lambu mai cike da furanni, iskar dake kaɗawa agurin da ƙamshin furannin sai suka haɗu suna bada wani ni'imtaccen yanayin dake sanya nishaɗi.... Babu abinda zuciyar sa ke hararo masa irin masoyiyar sa Ma'u, hannunsa ya shafa abun mamaki sai ga ma'u ta bayyana, ajikin hannun nasa kamar tv, kallon ta yake cike da shauƙi yana murmushi, gani yayi tana cokano baki kamar wata ƴar ƙaramar yarinya, hakan kuma yana matukar birge Haidar, sumbatar ta yayi ta jikin hannun nasa yana cigaba da kallon ta... Ma'u kuwa da taji an sumbaceta sai ta ƙara cunno bakin nata kamar wacce take jiran tsammani....... Haidar da yake kallon ta yana ƙara faɗaɗa murmushin sa, jinsa yake yafi kowa Sa'a a duniya, dan idan yana kallon ta mantawa yake da komai, jin motsi a ta bayan sa yasa da sauri ya shafi hannun sa, tuni hoton Ma'u ya ɓace a hannun nasa.... Abokinsa ne I'liyas, ya ƙara so yana cewa "Toh Mijin bil'adama ashe kana nan! Ko bil'adamar taka kake tinani?." I'liyas ya faɗa cike da tsokana da kuma shaƙiyanci...... Haidar dake kallonsa yana hararar sa yace "Mai zai sa inyi tunanin ta bayan ko da yaushe ina tare da ita, yanzu mah ina cikin ganinta, kazo ka katse min jin daɗi na.." Baki kawai I'liyas ya saki yana kallon sa sannan daga bisani yace "Ni ba wannan ba! ko zaka iya nuna min masoyiyar taka, naga wani irin kyawu gare ta da har ya ja hankalin ka." Shiru Haidar yayi kamar mai tunanin wani abu jim kaɗan kuma sai yace "Gaskiya bazan nuna maka ita ba.." "Saboda me?." I'liyas ya tambaya cikin mamaki, Haidar yace "Saboda ina matuƙar kishin ta sosai, banso inga kowa yana kallonta indai namiji ne.." I'liyas yace "lalle abin naka azimin ne, amma har ni da nake a matsayin abokin ka, baza ka nuna min ba.." Tashi i'liyas yayi zai bar gurin kamar yayi fushi, ganin haka da Haidar yayi sai ya riƙo hannun sa yace "yi haƙuri abokina zo in nuna maka ita." Dawowa i'liyas yayi ya zauna, hannunsa haidar ya shafa sai ga ma'u ta bayyana, sakamakon ɗazu tana bacci yanzu kuma idonta biyu kawai dai tana kwance ne, kamar yadda yace kallo ɗaya i'liyas zai mata, hakan kuwa ta kasance yana kalla Haidar ya janye hannunsa.... I'liyas a ransa yace ba laifi tana da ɗan kyau, amma a fili sai yace wa Haidar "Gaskiya na yarda da ake cewa so makaho ne, to tabbas haka ne! So babbar makanta ce, na farko ni banga wani kyawun da zaija hankalin ka zuwa gare ta ba, wanda har ace babu matan da suka fita kyau ba acikin jinsin al'janu, sannan ƙari wata makantar shine da har idonka ya rufe, ka kasa sanin dai-dai da kuma akasin haka.." Haidar da izuwa yanzu ya fara fusata da abinda I'liyas yake ce mai, cikin fushi yace "to ai bakasan wani abu ba! duk duniya babu wanda nake so yace Nurul aini tana da kyau, hakan da ka faɗa shine daidai, dan da ace cewa kayi tana da kyau to Wallahi da zan iya jin haushin ka, amma da ka faɗi akasin haka naji daɗi sosai, ni kaɗai nake so in yabeta kuma naga kyawunta.." I'liyas yace "lalle kam." "To da kake cewa ma na kasa sanin dai-dai da rashin sa kuma, to ai saika faɗa min mai na aikata na rashin daidai ɗin.." Numfasawa i'liyas yayi sannan yace "Gaskiya baza ɓoye maka ba, kai abokina kuma mai faɗa min gaskiya idan nayi kuskure, ka auri jinsin da ba naka ba kuskure ne abokina, ka killace ta, ka hanata kula kowa, ka ƙi bari jinsin ta ya aure ta, ya kamata kasan cewa hakan da kayi kuskure ne abokina, lokaci yayi da zaka farka daga barci da kake ka fita a rayuwar ta haka nan, ka barta tayi au...." Wata gigitarciyar tsawa da Haidar ya daka mai Saida gurin ya amsa haɗe da bada wata iriyar girgiza, ba shiri, i'liyas yayi shiru daga nasihar da yake mai, wanda hatta tsuntsayen dake gurin Saida suka tsorata da sauran wasu halittu da ke gurin.... Cikin tsantsar fushi Haidar yake cewa "Ba ina sonta bane dan in cutar da ita, ina sonta ne da in bata da farin ciki, kuma ba ina sonta bane dan in haɗa soyayyar ta da kowa ba, haka kuma bazan taɓa jurar na ganta ta haɗani da wa ni ba..." Idanun sa ya Lumshe da suka rine suka koma baƙiƙirin, cigaba yayi da cewa "I'liyas ina so kafin na kefta idanuna, ka ɓacemin da gani, kayi nisa da inda zan iya hangowa, muduk ka bari na ganka sai nama lahanin da har ka ƙare rayuwar ka bazaka manta da shi ba..." Ɓacewa I'liyas yayi kamar yadda haidar ɗin yace, Saida yayi nisa daga inda haidar yake sannan ya bayyana a gurin, saƙa da warwara kawai yake can kuma sai yayi murmushi yace "Wallahi Haidar saina rabaka da bil'adamar da kake iƙirarin cewa matar kace.." Shi kuwa Haidar ganin iliyas ya bar gurin, sai shima ya tashi da niyar barin gurin acewar sa iliyas ya ɓata mai rai bari yaje inda zaiji dama dama...... ★★★ Ɓangaren su Ma'u kuwa zaune suke a tsakar gida, sun shimfiɗa tabarma suna ta hira abin su cikin kwanciyar hankali, kasancewar ƴan uwanta mata sunzo musu ziyara yau, sai hirar su suke gwanin birgewa, Ma'u dake tsakiyar su baza ka taɓa cewa itace yayarsu ba, zakayi tunanin duk sun girmeta... Inna dake gefe tare da ƴan jikokinta, sai wasan su suke abinsu, ɗagowa inna tayi ta kalli Ma'u a ranta ta ayyana cewa Allah sarki kema da kinyi aure da kina nan da ƴaƴan ki, Allah ka dubi wannan baiwa taka ka fito mata da mijin aure nagari tayi auren ta....✍️ *More comment* *More typing* *Pls share* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/8, 7:45 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *30 & 31* *KATSINA CIKIN GARI* ___________A wata ƙasaitacciyar anguwa da tafi kama da ta masu mulki, dukkanin gidajen dake jere a wannan anguwa gaba ɗaya su haɗaɗɗune, idan ka kalli wannan zaka yi tunanin wancan yafi wannan kyau da tsari, amma sai dai kana kallo zaka hango wanda ya fisu.... Wani gida da yafi jan hankali na shi naga an buɗe get ɗin gidan, yayin da motoci na alfarma ke shiga kamar an rako shugaban kasa filin jirgin sama... Bayan motocin sunyi fakin a inda ya dace, ma'aikatan gidan suka taho da hanzarin su, har rige-rigen buɗe Bayan motar suke, wanda hakan ya nuna alamun suna farin ciki da zuwan sa, a hankali aka buɗe murfin motar, tare da zuro ƙafafuwan sa waje, sai ya ɗau wasu ƴan sakanni sannan ya fito gaba ɗayan sa... Alhaji Ibrahim naga ya fito daga cikin tare da wata mata, da dukan alamun dai matar sa ce, sai wasu matasa guda biyu dake binsu a baya, tahowa suke cike da tsantsar farin ciki da murnar ganin juna... Suraj kenan matashi kuma baƙin fata na farko da yake tuƙin jirgin sama, a ƙasashen ture, kyakkyawa ne shi ajin farko ga kuɗi ga jin daɗin duniya duka Allah ya bashi..... Ganin iyayen nasa lafiya hakan ya sashi nishaɗi da farin ciki, jikin ladabi da biyayya ya tsugunna har ƙasa ya gaishar dasu, dan suraj akwai ɗa'a, ƙannen sa suma suka gaishe shi cikin girmamawa suna mai sannu da dawowa..... Ɗunguma sukayi gaba ɗaya suka shiga cikin gidan, a falo suka yada Zango nan suka zauna aka sake wata sabuwar gaisuwar yaushe gamo, haɗe da ƴan hirarraki kaɗan kaɗan.... Momy ce ta kalli mubarak tace "ka cewa yayan ku yaje yayi wanka sai ya fito muci abinci." Shi kuwa Suraj jin tace haka sare yasan dashi take, kawai dai ta fake da mubarak ne, sai yaji bai ji daɗin hakan duk da cewa ya saba da wannan ɗabi'ar ta Hausa Fulani, ace wai uwa baza ta iya kallon ɗan ta na fari ba, bare har tayi doguwar magana dashi.... A sanyaye ya tashi ya shige ciki domin ya watsa ruwa, suma sauran tashi suka yi kasancewar magribah ta gabato, Alhaji Ibrahim ya kalli Momy yace "Wai ina jiddah take ne! Bata zo taga babanta ya dawo bane.." Momy tace "ni Wallahi nama manta in tashe ta Barci take, gashi yamma tayi yanzu, tun ɗazu take jiran dawowar tasa har ta gaji da jira bacci yayi awon gaba da ita.." Daddy yace "to gaskiya je ki tashe ta, daga nan sai ki faɗa mata babanta ya dawo.." Tashi Momy tayi tana dariya tace "yanzu kuwa kaga tsalle tsalle a wajen jiddah.." Hayewa tayi saman bene da shi kuma Daddy ya fice masallaci... ★★★ Bayan magribah kuwa Momy ce ke ta ciku-cikun haɗa musu dinner akan darduma, dan Daddy baison hawa danning ya fison cin abinci a ƙasa wannan yasa har iyalen gidan sa sun saba da hakan.... Wata yarinya ce da baza ta wuce shekara biyar ba, ta fito daga cikin ɗaki da gudu, yarinya sak Suraj kamar yayi kaki ya zubar, cikin Muryar ta ta ƴan yara tace "momy ina Daddyna yake! Kin ce inayi sallah zan ganshi yana ina..?" Momy tace "to Sarkin tambayoyi! Kije yana ɗakinsa, kuma ki tafi a hankali.." Taku uku tayi a hankali sannan ta zuba da gudu. Ɓangaren Daddy nata tayi tana kiran sunan shi... Suraj dake zaune kan sallaya yana zikirin yamma, dan suraj Masha Allah akwai son ibada.... Shigowa tayi da gudu ta, faɗa jikin sa tayi tana ihun murna, rungume ta yayi yana ƙara jin son ƴar tasa da kuma ƙaunar mahaifiyarta, da ta rasu wajen tsawon shekaru biyar kenan, ranar da ta haifi jiddah Allah ya karɓi ranta tun daga nan Suraj bai ƙara yin aure ba, dan ko zancen auren aka mai sai yayi kuka, a ganin sa bazai samu mace tamkar mahaifiyar jiddah ba..... Jiddah ce ta katse masa tinanin da yake wajen cewa "Daddy ka taho min da tsaraba ta.?" "Eh mana sarauniya ta! Yanzu muje gurin momy muci abinci sai mu dawo, na nuna Miki tsarabar ki.." Ɗaukar ta yayi suka wuce babban falon gidan, kasancewar anan suke cin abincin..... Bayan an gama cin abincin ne Alhaji Ibrahim ya kalli Suraj yace "Am!! Suraj ya maganar mu da kai kan ka tafi U.S. , akan zuwa ganin ƴar aminina Salisu, fatan dai baka manta ba.." "Eh Daddy ina sane! Amma yanzu ina ganin kamar za'a iya mata aure, tunda kaga yanzu shekara biyu kenan dayin maganar.." Daddy yace "tabbas hakane insha Allahu gobe sai muje can batsarin, in yaso in an mata aure to dama can ba rabon ka bace ita..." Suraj yace "to Allah ya kaimu.." ya faɗa cikin ladabi, hira suka cigaba da yi ciki nishaɗi har lokacin sallar isha'i yayi, sallar isha'i kuwa kowa yayi nasa gun..... Washe gari kuwa da shirin su, suka tashi sai ƙaramar hukumar batsari........ ★★★ Ɓangaren Ma'u kuwa yau tunda ta tashi take jin faɗuwar gaba, tun tana daurewa har ta gayawa inna halin da take ciki, inna kuwa sai ta kwantar mata da hankalin cewa INSHA ALLAHU alkairi ne Ma'u karki damu kedai kiyi ta addu'a, nima ina miki fatan alheri. A haka har bacci yayi awon gaba da ita, cikin baccin ne take mafarkin wani mutum ya ɗaure Haidar yazo ya jata sun tafi, shi kuma haidar dake ɗaure sai kiran sunan ta yake amma mutumin yaƙi sakar mata hannu, tayi ƙoƙari taga fuskarsa amma ta kasa, a daidai lokacin ne Ma'u ta farka a zabure, tana mamakin wannan mafarkin da tayi, a ko da yaushe saide tayi mafarkin Haidar yana cutar wasu amma yau shi aka cuta......✍️ _alhmdllh yau dai nayi post sau biyu a rana hakan ya faru ne sakamakon comment ɗinku musamman facebook ina yinku ƴan facebook da ace zan iya dana ambaci sunayen ku saide ba lokacin haka amma insha Allah zan ƙoƙarta hakan_ *More comment* *More typing* *Pls share* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/9, 12:37 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *32 & 31* ____________Haka ta tashi tana al'ajabin wannan mafarkin da tayi, ji tayi wani sanyi yana ratsa mata zuciyar ta, sakamakon ɗazu da gabanta yake faɗuwa... Tashi tayi ta fito waje, samun inna tayi zaune tana gyara wake, sai kuma auta zahrah dake wankin uniform ɗinta, sannu da hutawa tayi musu sannan ta zauna, waken da inna take gyarawa Ma'u ta karɓa, cigaba tayi da gyaran suna ɗan taɓa hira jefi-jefi....... Ƙarfe 12:00 daidai suka ji sallamar kawu Salisu da wasu baƙi, ganin Alhaji Ibrahim da inna tayi yasa da sauri ta tashi tana "lale marhaban! sannun ku da zuwa, ku ƙara so ciki.." Cikin ɗakinta inna ta kaisu, tare da shimfiɗa musu ƙatuwar dadduma, nan suka zauna aka fara gaishe gaishe cikin mutunta juna, Alhaji Ibrahim ya gabatarwa da inna Momy da ƴaƴan sa maza guda uku, inna tace "masha allah! Allah yayiwa rayuwa albarka." Gaba ɗaya suka amsa da ameen.... Ma'u dake tsakar gida tana shirya abincin rana, sai kaiwa da komowa take, Dan ma'u gwana ce wajen girki, zahrah ce ta shigo da katan ɗin ruwan gora a hannun ta da ta siyo a shago, da hanzari Ma'u ta karbi ruwan ta ɗauki ƙaramin tire ta ɗora kofuna akai, ta shiga dashi ɗakin da suke...... Koda ta shiga cikin taga sun zuba mata ido, Ma'u dama gata da tsoron mutane Musamman ma taga akwai maza a gurin, a dabur ce ta tsuguna ta gaisher dasu amsawa sukayi gaba ɗaya, suna kallon ta... Shi kuwa Suraj da bai ɗago ba kallon ta yake ta ƙasa ƙasa, idonsa ya faɗa kan ƙafar ta, da take fara sol, kamar bata taka ta a ƙasa, ji yayi ƙafar ta burge shi dan shi yana son yaga ƙafar mace kyakkyawa koda kuwa bata da kyawun fuska... Sauri yayi ya kawar da tunanin da yake a ransa, yana fatan Allah yasa yarinyar da za'a haɗa shi da ita tana da hankali..... Tashi Ma'u tayi ta fita daga ɗakin ta barsu suka cigaba da hirar su da su inna, ganinta da Alhaji Ibrahim yayi sai yaji daɗin hakan, dan haka kurum ta kwanta mai a rai, kuma yana da tabbacin zaman su zai zo ɗaya da Suraj.... Kiran sallar azzhar ne yasa kawu Salisu yaja su zuwa masallaci, a hanyar su ta dawowa ne Alhaji Ibrahim yake cewa kawu Salisu "wannan yarinyar Asma'u! Da nagani yanzu shin maganar mu da kai ta kwanakin baya da suka wuce, tana nan Ko kuwa an mata miji..?" Kawu Salisu yace "ah ah! Ba'a yi mata ba." Nan kawu Salisu ya kwashe dukan abinda ya faru bayan rabuwar su ya faɗa mai, shima Alhaji Ibrahim labarin dalilin da yasa ba su zoba yaba shi, sannan ya ɗora da cewa "yanzu haka ma a shirye suke, dan sunzo da Suraj ne yaga Ma'u, su shirya kansu in sun daidai ta ayi musu aure..... Kawu Salisu yayi murna da hakan, har suka ƙarasa gida kawu Salisu yana murna, bayan sun shigo ne, sannan Ma'u ta gama girkinta zubo musu tayi a kula ta kawo musu, haɗe da kawo musu fulet ɗin da zasu ci tayi waje, zuzzuba musu abincin inna tayi ta miƙa musu, shi kuwa Suraj ganin alale da miya sai yaji bazai iya ciba, kasancewar bai taɓa ciba, amma ba yadda ya iya dole yaci dan yadda yaga mutanen suna da mahimmanci a idon Daddyn sa, idan bai ciba Daddy bazai ji daɗi ba, a hankali ya fara kaiwa bakinsa, yana tinanin yadda zaiji ɗanɗanon abin, amma sai yaji akasin haka za gewa yayi yaci sosai dan yafi kowa ci da yawa.... Kammala cin abincin da kaɗan, Alhaji Ibrahim ya kalli Suraj yace "Son kaje daga waje! Kan mu fito, in yaso sai a turo maka yarinyar yanzu ku gaisa da ita.." Amsawa yayi da " to." Cikin ladabi sannan ya fita daga cikin ɗakin, fitar sa ke da wuya kawu Salisu yace wa inna taje ta tura masa Ma'un... Inna na shiga ɗaki ta samu Ma'u a zaune, dafa ta inna tayi sannan tace "kije daga waje akwai baƙon da zaku gaisa dashi.." Ma'u kuwa jin abinda inna tace sai taji kamar an buga mata guduma, a tsakiyar kanta dafe kan Ma'u tayi sannan ta kalli inna tace "wllhi innarmu kaina ne yake min ciwo bazan iya zuwa ba....." Cike da mamaki inna take kallon ta tace "yanzu na sameki lafiya kalau amma daga yin maganar, kije kiga wani har kai ya fara ciwo, anya Ma'u lafiyar ki kalau kuwa?.." Inna ta tambaye ta tana riƙe baki, cigaba da cewa inna tayi "zaki tashi ki wuce ne! Ko sai na ɓata ranki........✍️ *SHIN MA'U ZATA JE KUWA?*🤔 *WAI INA HAIDAR YAKE NE*😹 *COMMENT*💃❤️ [6/8, 10:30 PM] Matar Khamis,: [6/8, 10:03 PM] +234 703 739 6908: Wow gsky matar khamis duniya ce munajin dadi sosai wlh naji dadin da Suraj yakasance me bautawa Allah akan lokaci naji dadi dayaxama Mai azhkar hakan xaisa ya ci karfin haidar me ikirarin yanason ma'u Allah yakara basira Allah yakaimu gobe muga posting dayawa Allah yakara xakin hannu [6/8, 10:11 PM] +234 906 547 6395: Wayyo Allah alkadarin haidar y karye💃🏻 [6/8, 10:20 PM] +234 703 644 4508: Wow kadarin haidar hakusa karyewa Allah sarki ma'u Allah yakusa rabaki da ala kakai💃💃💃 matar khamis Allah yakara basira muna godiya [6/8, 10:23 PM] +234 906 598 1474: Yau munzama yan gata 2pg arana gaskiya mungodefa matar khamis Allah yabiya muma munayinki over [6/8, 10:24 PM] +234 706 058 4513: Allah ya karawa rayuwa albarka [6/8, 10:31 PM] Matar Khamis,: Bayan Dade wa ta banyi karatun littafin hausa ba.yanzu da na Fara karanta wa ba wani littafi da ya ke min Dadi fiye da wan Nan labari da kike rubutawa some times na Kan rasa Mai zan Cai Miki fatan Alkhairi a ko da yaushai na ke Miki da fatan nasara acikin rayuwa [6/8, 10:36 PM] Matar Khamis,: [6/7, 1:23 PM] +234 906 598 1474: Topah yanxu akafara wasan muna gdy Mrs khamis Allah yabiya [6/7, 7:30 PM] +234 805 056 9109: Masha Allah matar khamis littafi yai Dadi Allah ya Kara basira👍🏾 lallle abun da zai raba ma u da haidar sai Allah!!! [6/8, 9:13 AM] +234 803 777 8216: yau nice 1 matar khamis Allah yakara basira [6/8, 11:30 AM] +234 805 056 9109: Yanzu aka Fara labari .Masha Allah .haidar bai kyauta .Allah sarki mahaifiyar ma u taban tausayi burin kowaccai uwa taga Auran yaran ta ! Shin dangin ma u ba wadda zai Kara tsayuwa akanta ? Ba wadda zaiyi tattamar Anya ma u Bata da wata matsala ? Ina nufin aljanu ko sihiri ko jifa ? Matar khamis Allah ya Kara basira👍🏾zan so jin karshe drama Nan . Lallai haidar shi nai shi nai babban tauraro Amma ya kamata ya samu Abokin gogayya ko da bai Kai shi ba . [6/9, 10:44 AM] Matar Khamis,: Tofa anzo wajan haidar zaigamu da gamonsa Mungode Allah yaqara basira da zakin hannu [6/9, 10:45 AM] Matar Khamis,: Naji dadi ma,u zata fara samu cenji [6/9, 10:46 AM] Matar Khamis,: [6/8, 11:21 PM] +234 803 152 3601: Masha Allah. Allah ya kara basira da hazaka. Ma'u kin kusa hutawa [6/9, 8:53 AM] Alhamdulillah: Wow yanzu akafara munagodiya Allah yakara basira da zakin hannu [6/9, 9:43 AM] +234 916 233 5086: Wow , kai yayai dadi,ni dama naji acukina suraj sai dawo,wayyo haidar har ka ban tausayi, Muna godiya ,Allah ya kara kaifin ido [6/9, 9:59 AM] +234 816 823 8549: Lpy da nisan kwana matar khamis🥰 [6/9, 10:47 AM] Matar Khamis,: [6/7, 6:28 PM] +234 706 363 6092: Kae🙆‍♀️😭😭Allah sarki ma,u Allah yakara basira [6/9, 8:41 AM] +234 706 363 6092: 💃💃💃🤣🤣kae masha Allah da alama wadda xasu papata da hydar yaxo Allah yakara basira _______________________________ _ASHE DAMA HAKA HAIDAR YAKE DA MAƘIYA🤔 NIDAI MATAR KHAMIS BABU RUWA NA IN HAIDAR YA KAMA MUTUM😳🙆🏻‍♀️_ *NAYI NAN 👩🏼‍🦯👩🏼‍🦯* *WALLAHI JIYA COMMENT ƊINKU YA SANI NISHAƊI SOSAI 🥰💃 ALLAH YA BAR ZUMUNCI* *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/10, 7:50 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *34 & 35* _____________Shiru Ma'u tayi ta sunkuyar da kanta ko kallon inna bata yiba, ganin haka da inna tayi yasa ta fara mata magana cikin faɗa-faɗa, tashi Ma'u tayi hankali kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki, bata san mai yasa ba haka nan take jinta kamar ba ita ba, hijab ɗin ta tasa sannan ta fice daga cikin gidan..... Bayan fitar ta kuwa inna wani dogon tagumi taja a ranta tana saƙa abubuwa da yawa, amma ta kasa samun mafita, tashi tayi ta koma ɗakin da ta baro baƙin ta, tana tinane-tinane a zuciyar ta.... Koda Ma'u ta fito samun Suraj tayi a zaune akan dan damalin ƙofar gidan na su, kasancewar kansa a sunkuye yake yana ɗan duba wani abu a wayar sa, bai ji matsin fitowar ta ba shiyasa ma bai ɗago ba, samun guri Ma'u tayi ta tsaya ƙiƙam kamar sojan da yake shirin fareti, kicin-kicin tayi da fuskarta kamar bata taɓa dariya ba, yayin da idonta yake kallon wani gurin daban.... Saida ta ɗauki wajen minti biyar sannan Suraj yaji jikinsa yana basa akwai wani a gurin, ɗagowa yayi a hankali daga kallon wayar da yake, tozali yayi da kyakkyawar fuskanta da take a cirɓine, a ransa ya ayyana cewa da ace zatayi murmushi da sai tafi haka kyau, kawar da tunanin yayi da sauri haɗe da ɗaga kafaɗarsa alamar ko a jikin sa, kallon ta yake tun daga sama har ƙasa haƙiƙa ta haɗu iya haɗuwa, dan bata da makusa ko kaɗan, ta ko ina tayi saide ace masha allah cigaba da kallon ta Suraj yayi baice da ita uffan ba, yana jiran kawai yaga iya gudun ruwan ta, na ƙin mai magana har wani lokaci zata kai a haka... Gajiya da tayi a tsaye yasa ta ɗan jiyo kaɗan, da niyar taga mai ɗan rainin hankalin nan yake, da har yanzu bai ma san da tsayuwar ta ba, idanuwan su ne suka sarƙe da na juna, lokaci ɗaya Ma'u jikinta ya fara karkarwa, baya tayi luuu zata faɗi, wata sufah Suraj yayi ya riƙo hannun ta yana mamakin komai yasa zata faɗi, ganin da yayi kamar bata cikin hayacinta, sai ya ɗauki waya ya kira Daddynsa, sheda masa abinda ke faruwa yayi, cikin al'ajabi dukkanin su suka fito waje ganin halin da Ma'u take ciki sai abun ya basu mamaki... Alhaji Ibrahim yace "Lafiya son me ya faru da ita ne?.." Suraj yace "Wallahi Daddy nima bansan meya faru ba kawai tana tsaye naga zata faɗi." Kawu salisu yace "to kamota mu shiga daga ciki." Ɗaukar ta Suraj yayi cimak kamar wata ƴar baby suka shige gida... Fifita kawai suke mata dan su a tinanin su suma tayi, nan ko basu san kaɗan daga cikin kaidin Haidar ne ba.... Haidar kuwa dake zaune a inda yake yana kallon su, dukkan abinda ke faruwa da saninsa, asalima shi ya bugar da Ma'u a cewar sa bazai lamunci yaga tana yiwa wanin sa magana ba.... Babu abinda yafi komai ɓata masa rai da ɗugunzuma mai hankali, sai yadda yaga Suraj ya haɗa jiki da matarsa, ji yayi wata zazzafar tsanar Suraj tana shiga ta ko ina a jikin sa, kawai tinanin irin hukuncin da zai shiryawa Suraj yake, na taɓa mai masoyiyar sa da yayi, rumtse idanuwan sa yayi, yayin da zuciyar sa da jikinsa yake jin su kamar ana zuba masa ruwan zafi..... Ɓangaren su inna kuwa! Babu abinda ba su yiwa Ma'u ba amma bata tashi ba, hakan yasa momy tace wa inna "Ko asibiti zamu kaita ne! tunda kinga bata tashi ba.." Kawu salisu yace "Ni gani nake kamar abun ba na asibiti ba ne.." Nan dai kowa da abinda yake cewa, Daga ƙarshe dai suka yanke shawarar ayi mata rukiya, ruwa Suraj yasa aka ɗauko a kofi, nan ya karanta ayatul kursiyu da ayoyin farko na suratul bakara, cikin ikon Allah ana shafawa Ma'u sai gashi taja ajiyar zuciya daga bisani bacci yayi awon gaba da ita, sauran ruwan tofin kuwa Suraj yace a ajje mata idan ta tashi sai a bata tasha...... Haka suka zauna har lokacin tafiyar su yayi Ma'u bata tashi ba, tafiya suka akan bayan kwana biyu Suraj ya dawo ya duba ta.... tafiyar su kuwa ko minti biyu ba'a yi ba, sai gashi Ma'u ta tashi daga baccin da take, cigaba tayi da al'amuran ta kamar komai bai faru ba, yayin da inna ta shiga cikin damuwa da kuma rashin sanin madafa........✍️ *More comment* *More typing* *Pls share* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/11, 12:26 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *36 &. 35* ____________Bayan isha'i kuwa inna ce zaune tare da iyalen gidan ta, Zahrah da Ma'u suke hira suke kaɗan kaɗan, ita dai inna saide ta bisu eh ko ah ah, kasancewar jin da take kanta yana matukar mata ciwo, kuma ba komai bane yasa mata ciwon kan, illah tinanin da ta sawa kanta...... Numfasawa inna tayi sannan ta kira sunan zahrah tace "Zahrah kiramin yayanku a waya ince mai in zai biyo ta nan, ya taho min da maganin ciwon kai." Amsawa da "to" zahrah tayi sannan ta ɗauko wayarta dake ɗaki, yaya Auwal ta dannawa kira, bugu ɗaya ya ɗaga haɗe dayin sallama, miƙawa inna wayar zahrah tayi tana cewa "gashi ya ɗaga.." karɓar wayar inna tayi tana karawa a kunnen ta....... Inna kuwa bayan ta gama wayar da yaya Auwal, miƙewa tayi tana ce musu "bari in shiga ciki na kwanta! Kafin yayan naku ya ƙara so." Ta faɗa tana shigewa ɗaki..... kwanciya tayi tana maida numfashi a hankali, da haka har ɗan gyangyaɗi ya fara ɗaukar ta, bata daɗai da fara gyangyaɗin ba, taji kamar motsi a cikin ɗakin, idon ta rufe tace "zahrah kema kwanciyar zakiyi tun yanzu.." Jin shiru ba'a bata amsa ba yasa ta buɗe idonta, taga waye ya shigo cikin ɗakin, maimakon taga zahrah ko Ma'u sai taga akasin haka, dan wani mutum ta gani tsaye a saitin inda take kallo, yanayin halittun sa sun bata tsoro sosai, dan komai nasa ya linka da na bil'adama da ta saba gani ba yau da gobe, inna da take cikin yanayin tsoro da firgicin ganin sa, kawai dauriya take wajen riƙe ihun da take so tayi na akawo mata ɗauki... Kunnuwanta suka jiyo mata awon Muryar sa da tasa saura kaɗan ta saki fitsari, ji tayi yana cewa "Ki kwantar da hankalin ki! Ni banzo dan na cutar dake ba, ko na tsoratar dake, asalima Ni nazo ne dan na tinatar dake, abinda kika kasa fahimta tun da daɗewa..." Inna kawai kallon sa take yayin da tsoron ta yake daɗa ƙaruwa, cigaba yayi da cewa "Ni sunana I'liyas! Kuma Ni al'jani, shin kin taɓa tsayawa kiyi tinanin me ya hana ƴarki Asma'u aure har izuwa yanzu.." Girgiza kai inna tayi, yayin da kanta yake ƙara ɗaurewa... "Nasan kun daɗe kuna tinanin lokacin auren nata ne baiyi ba ko! To abinda baku sani ba shine Akwai wani al'jani, wanda ya kasance daga cikin mu, sunan sa *HAIDAR* shine ya auri ƴar ki Asma'u, kuma ya hana ko wani namiji kusantar inda take, kuma duk wanda yayi gangacin haka yakan sashi cikin bala'i koma ya rasa rayuwar sa gaba ki ɗaya...." Nan dai I'liyas ya kwashe komai tun daga lokacin da Haidar ya kashe Yusif, har izuwa gobarar da Alh Tanko yayi, sannan ya ƙare da cewa "Haidar yafi kowa dake cikin al'janu taurin kai da kafiya, idan yana son abu komai yakan iya aikatawa, abune mai wuya Haidar ya rabu da yarinya ki, Ni dai taimakon da zan iya muku shine kuyi kokarin raba yarinyar nan da wannan *AL'JANIN SOYAYYAR,* idan ba haka ba! ba zai taɓa bari wani namiji ya raɓi inda take ba..." I'liyas yana ƙare maganar da yake, ya ɓace ɓat kamar bai wanzu a gurin ba..... Inna da take cikin tashin hankali da kiɗimewa, sanƙarewa tayi guri guda ko cikakken motsi ta kasa ai watarwa, kawai zufa take keto mata yayin da ta rasa mai ma zata yi, tana cikin wannan halin Auwal ya shigo ya sameta...... Ganin halin da mahaifiyar tasu take ciki abin ya matuƙar ɗaga mai hankali, gaba ki ɗaya jikinta karkarwa yake, tana so tayi wa Auwal magana amma bakinta yaƙi sarrafuwa, da gudu Auwal ya fita daga ɗakin dan kirawo mota, su kuwa su Ma'u ganin yaya Auwal ya fita hankali a tashe, yasa sukayi cikin ɗakin da inna take da gudu, suma halin da suka ganta ya matuƙar basu mamaki, duk da dama ance yanzu yanzu sai Allah.... Kwantar da ita sukayi akan gadon da take suna jera mata sannu, inna kai kawai take ɗaga musu, tana bin Ma'u da idonta, yayin da take jin tausayin Ma'u yana ratsa dukan jijiyoyin jikinta, suna haka ne yaya Auwal ya dawo, kamo inna sukayi suka miƙar da ita tsaye, fita da ita sukayi dan kaita asibiti........ Ɓangaren I'liyas kuwa! bayan ya bar inna tafiya yayi, yana tinanin inda zai iya ɓoyewa azabtarwa da muguntar Haidar, dan yana da tabbacin cewa! Indai Haidar ya gano abinda ya aikata masa, Allah kaɗai ne zai iya karesa daga sharrin Haidar..... Tunowa da wani malamin su dake cikin wani tsibirin dutse da yayi, yasa ya yanke shawarar zuwa can, dan nan gurin ne kaɗai! Haidar bazai iya zuwa ba dan ya cutar da shi... Nufar gurin yayi a zuciyar sa, yana wa Ma'u da iyayen ta fatan samun nasara akan Haidar..........✍️ *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/12, 9:51 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *37 & 38* _____________Ɓangaren su Suraj kuwa! Tunda suka tafi daga batsari babu tinanin da yake sai na Ma'u, haka kurum yaji Allah ya same matuƙar tausayin ta, bai san meyasa ba Amma sai yabar hakan a matsayin, ƙila dan tana da matsalar jinnu ne, har Allah Allah yake ya sake zuwa ko dan ya ganta, a da ya cirewa kansa son yin aure tunda matar sa ta mutu, amma yanzu yana jin lokacin da zai kawowa jiddah uwa yayi, dan yana kallon Ma'u zuciyar sa ta aminta da ita, a matsayin ta kasance uwar ƴaƴan sa na har abada..... ★★★ Likitoci Saida suka duƙufa akan Inna, sannan ta dawo hayyacinta, sosai ina ta tsorata! dan abu biyu ne suka haɗan mata, ga ganin al'jani da tayi kuma ga lamarin da yazo mata da shi kunnuwanta sunyi rauni da sauraron abun, da zarar ta tuno abin sai hankalin ta ya matuƙar tashi, Saida likita ya mata allura sannan ta samu yin bacci..... Yaya Auwal kuwa ganin an kwantar da inna a asibiti, yasa yace "Zahara ke ki zauna a wajen innarmu da goggo ( matar kawu Salisu kenan), ke kuma Ma'u sai mu wuce gida da safe kyadawo.." Ba haka taso ba! amma ba yadda zata iya, dole tabi yaya Auwal da kawu Salisu suka wuce gida... Ba yadda kawu Salisu da yaya Auwal basu yi da itaba akan taje gida kawun su kwana da yara, ko kuma su suzo su tayata kwana, amma taƙi acewar ta zata iya kwana ita kaɗai a gidan, ƙyaleta suka yi ta shigewar ta, su kuma suka ƙara gaba abinsu...... Tana shiga tasa sakata a ƙofa, jin gidan shiru babu motsin kowa, hakan baisa taji tsoron komai ba kai tsaye ɗakin ta nufa da niyar kwanciya, samun Haidar tayi zaune akan katifar ta, ya tanƙwashe ƙafafuwan sa, wani sihirtaccen murmushi yake aiko mata dashi, tare da buɗe hannuwansa alamun ta taho gare shi, da gudu Ma'u ta taho tayi kamar zata faɗa jikinsa, sai kuma ta juya masa baya, táshi yayi ya rungumota ta bayan, haɗe da ɗora kansa a kafaɗarta, cikin kunnenta yace "meye kuma ya faru! Masoyiyata, ko baki yi farin ciki da ganina ba." Cikin sanyi murya Ma'u tace "ah ah innarmu ce bata da lafiya, hankali na ya matuƙar tashi wallahi, saboda innarmu itace komai namu.." Juyo da ita Haidar yayi ta gabansa, ganin tana hawaye sai yasa hannu ya share mata shi, rungume ta yayi yana ɗan buga bayanta a hankali, sannan yace "Ki kwantar da hankalin ki, inna zata samu lafiya insha Allah, kiyi shiru ki daina kuka kinji..." Girgiza kai Ma'u tayi tana cewa "to" Shi kuwa zaunar da ita yayi akan cinyar sa yace "Ina so ki kasance cikin farin ciki a koda yaushe, dan kiyi farin ciki zan iya sadaukar da komai nawa a kanki, wallahi ina sonki kamar bugun numfashi, ina ji rayuwa ta baza ta iya tafiya daidai ba idan ba ke a cikin ta...." Haka yai ta gaya wa Ma'u, kalamai masu tsayawa a rai da ratsa zuciyar mai sauraro, daga ƙarshe kuma ya ɗauketa suka tafi yawon shaƙatawa, bai dawo da ita ba sai gab da asuba, wani nan nauyar bacci yayi awon gaba da Ma'u, cike da mafarkin Haidar masoyin ta, sai ƙarfe takwas saura ta tashi, ganin yadda lokaci ya ƙure gashi ko sallar asuba bata yiba, da hanzari ta tashi tayi bayi tana sauri sauri ta gama abinda take, tana idar da salla ko tsayawa tayi addu'a bata yiba, ta tashi tayi waje tana buɗe ƙofa, tayi karo da yaya Auwal dake ƙoƙarin shigowa tare da anti mardiyya (matarsa kenan) gaishe su tayi tana karɓar kwadon abincin dake hannun anti mardiyyan, wucewa suka yi cikin gidan inda yaya Auwal yasa Ma'u ta ɗaukowa inna wasu kayan, da zata canja sannan suka wuce asibitin...... Koda suka isa asibitin samun inna suka tana bacci, sai kuma zahrah da goggo dake zaune suna karyawa kasancewar kawu Salisu yazo har ya siyo musu abin kari ya tafi wajen aikin sa..... Nan suka zauna aka suna gaishar da gaggo haɗe da tambayar ta ya mai jiki, amsawa tayi tana cewa "da sauƙi! Har ta tashi da asuba tayi Sallah, sai kuma ta koma baccin, Amma likita yace baccin da take shine sauƙin a barta tayi abinta.." Yaya Auwal yace "to madallah bari naje naga likitan, daga nan zan wuce idan kuma ana buƙatar wani abu sai a kira Ni.." Amsawa da "to." Suka yi gaba ɗayan su, sannan shi kuma ya fita dan zuwa ganin likitan....... Alhamdulillah jikin inna yayi sauƙi, kwanan ta biyu aka sallamai ta yayin da kawu Salisu da yaya Auwal suke ta hidima da ita, kasancewar likita yace a daina barinta cikin tinani da damuwa, shiyasa suke ƙoƙarin kulawa da ita yadda ya kamata...... Bayan kwana biyu inna ta kira kawu Salisu da manyan ƴaƴan ta maza yaya Auwal da yaya Sani, Nan ta zayyane musu dukan abinda i'liyas ya gaya mata, game da aljani da yake auren Ma'u, da kuma yadda yake korar mata samari, har idan sun mai gardama yake kashe su ta ƙare da cewa "gobarar ma da Alh Tanko yayi, ashe shi ya assasa komai.." Dukkanin su shiru suka yi sun ma rasa ta inda zasu fara, kawu gumi ya share inda yayi ta maza yace "ba shakka! Lalle biri yayi kama da mutum, wallahi tunda nake ban taɓa jin labari mai kama da irin wannan ba, haƙiƙa al'janin nan ya zalunci Ma'u, da ace anyi wa Ma'u aure akan lokaci, da yanxu ina da tabbacin idan Allah ya bata tana da yara huɗu, tunda gashi yanzu sa'aninta da ƙawayenta daga me yara huɗu sai mai uku, amma yanzu da yardar Allah Ma'u sai ta rabu da wannan azalimin AL'JANIN SOYAYYAR..." Kawu Salisu ya ƙare maganar cike da san kwantar musu da hankali...... ★★★ Ɓangaren HAIDAR kuwa! Duk abinda I'liyas ya sanar da inna, da kuma shirin raba shi da Ma'u da suke, duka yana sane da faruwar hakan, asalima a jiya da i'liyas yazo gidan ya ga zuwan shi, dan ya sawa gidan tsaron da duk abinda ake zaiji kuma zai gani, a duk inda yake, kawai ya ƙyale I'liyas ne dan bai ɗauki hakan a wata matsala ba, kuma shidai abinda ya sani babu wanda ya isa ya raba shi da Ma'u koda kuwa waye a doron kasar nan........✍️ *_Niko nace akwai Allah Haidar saide in bamu haɗa ka da Allah ba_*😒🙄 *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/13, 10:59 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *39 & 40* ______________Yau kawu Salisu tun asuba da ya tashi ya shirya, dan zuwa wani ƙauye da yaji ana labarin wani malami da yake bada maganin al'janu, tafiyar sa yayi ko inna bai gayawa zai je wani gurin ba, dan ya ɗauki aniyar nemawa Ma'u magani koda Kuwa nawa yake.... Wajen ƙarfe 12:00 daidai ya ƙarasa cikin ƙauyen, tambayar gidan da mai maganin yake yayi, nan ya samu wani yaro ya raka shi har inda mai maganin yake, mutane ya samu da yawa kuma dukkanninsu kowa yazo da matsalar shine dan ya samu waraka idan Allah ya yarda, samun guri kawu Salisu yayi ya ɗan raɓe anan, da haka har layi yazo kansa, Shiga cikin shagon da mai maganin yake yayi, bakinsa ɗauke da sallama...... Wani babban mutum ne a zaune mai cike da kwarjinin da kamala, da ka gansa kaga malamin addinin saboda yanayin sa kaɗai ya isa ya nuna haka, bayan sun gaisa ne kawu Salisu ya zayyane masa dukkan abinda yake tafe da shi, gama maganarsa ke da wuya malamin yace "Ya Salam! Inalillahi wa ina ilaihir raji'un, haƙiƙa kuma kuna da naku laifin, yarinya taƙi samu mijin aure, ko kuma sai an zo yin aure abu ya lalace, ko manemin aure ya gudu, ko wani abu ya faru dashi, ko kuma ita tace bata sonshi ga alamomi nan da yawa wanda kace duk suna faruwa, to ku meyása baza kusa ayar tambaya ba.. " Numfashi malamin yaja yana girgiza kanshi domin yaji matsalar da bai taɓa jin irin ta ba, cigaba yayi da cewa "Kafin a raba wannan yarinyar da mugun AL'JANIN SOYAYYAR sai an sha wuya, saboda ya daɗai tare da ita, kuma ya kamata ita kanta yarinyar tasan da wanda take mu'amala, dan zata iya yiwuwa yayi amfani da ƙarfin su na al'janu yasa mata soyayyar sa, dole sai kunyi ƙoƙarin sanar da ita abinda ya aikata mata, inba haka ba abune mai wuya aci galaba akan shi.." Haka malamin nan yayi tawa kawu Salisu bayanin yadda za suyi, da kuma basu shawarwari akan yadda za'a taimaki Ma'u, daga ƙarshe kuma ya bashi maganin da za'a ba Ma'u, nasha daban na wanka ma daban, har da wanda zata turare jikinta...... Bai iso gida ba sai wajen la'asar, kai tsaye gidan inna ya shige, inna dake zaune tsakar gida, jin sallama yasa ta amsa tana bada izinin shigowa, ganin kawu Salisu ne ya shigo a sukwane, da mamaki inna take tambayar sa "daga ina haka! Naganka kamar a gajiye." "Hmm kede bari! Wallahi wani ƙauye naje, tun asuba sai yanzu na dawo, gashi ko abinci ban iya zama naci ba... Ina Ma'u take ne?.." Kawu Salisu ya ƙare maganar yana tambayar. Inna tace "kasan ta ita ƴar ɗaki ce, ko gajiya da zama ita kaɗai a ɗaki bata yi, ni Wallahi da ma zafi bai damun ta.." "Ai kuwa lokacin daina zama ita kaɗai a guri yazo, dan yanzu ko kwanciya zatayi da dare ku riƙa haɗuwa duka a ɗaki ɗaya kuna kwana, sannan ki riƙa sata a koda yaushe ta kasance cikin tsarki, da yawan karatun Alkur'ani, da kuma yin addu'a idan zata kwanta bacci, yanzu ga magani nan na karɓo mata, malamin yace INSHA ALLAHU za'a dace..." Cikin murna inna ta karɓi ledar magani, yayin da take ƙara ganin girman kawu Salisu a idanun ta, dan shi ɗin mutum ɗaya ne tamkar da dubu, yasan takan riƙe zumunci da amana a zuciyar ta kawai addu'a take ta faman zuba masa...... A fili kuwa rasa maima zata ce mai tayi dan ta rasa da wani harshe zata mai godiyar abinda yake musu, a hankali inna tace "Salisu a koda yaushe kana kula dani da ƴaƴana kuma hakan bai taɓa gajiyar da kai ba, na rasa da wata kalma zan yi ma godiyar abinda kake mana, koda mahaifinsu yana raye iyakar abinda zai mana kenan, Allah ya jiɓinci lamarinka a ko ina..." Girgiza kai kawai kawu Salisu yayi sannan yace "Adda Hajara kenan! Ni kaina nasan ina da tabbacin cewa, da ace nine na mutu yaya yake raye to zai yiwa iyalaina fiye da abinda kike ganin ina muku, ƴaƴan ki ƴaƴana ne suma babu wani bambanci, dan haka ki daina damuwa..." Bayanin yadda za'ayi amfani da maganin ya mata, sannan yayi kiran Ma'u yana ce mata "ki tabbatar duka wannan maganin kiyi amfani dashi Yadda ya dace, kuma wallahi naji labarin ba kyasha, ko akasin haka sai ranki yayi mummunan ɓaci.." Amsawa da "to kawu." Ma'u tayi tana mamakin maganin meye kuma aka kawo... Yana fita inna ta jiƙa maganin da Za'a sha a kwano, bayan ya jiƙu taba Ma'u tasha tana cewa "kiyi bissimillah.." Karɓar maganin Ma'u tayi takai bakinta tana ambaton sunan Allah.... Haidar kuwa! A daidai lokacin da Ma'u zata sha maganin nan, lumshe idonsa yayi, dan ganin wani kalar maganine ake bata, dama aduk lokacin da yake so yaga wani abu, da ya lumshe idonsa zai gano ko meye... Ya ɗauki ƴan sakkani idonsa a rufe, daga bisani ya buɗe su cike da ɓaci rai, dan gaba ki ɗaya idanuwan sun canza kala, da niyar zubar da maganin ya tankwaɓi hannun Ma'u, kufcewa kwanun maganin yayi daga hannun Ma'u, da sauri inna tasa nata ta tare, tana aikawa da Ma'u wata iriyar harara tace "Da mugunta zubar da maganin zakiyi koh, bayan kina kallo duka na jiƙe, to ai saiki tashi ki ɗauko ƙaramin kofi na ɗiban Miki Kisha.." Tashi Ma'u tayi ta ɗauko kofin, zuba mata inna tayi ta bata, Sha take tana ya mutsa fuskarta, kwata kwata maganin bai mata daɗi ba, kawai dan ba yadda zata yi ne dole sai tasha, ko minti ɗaya batayi da sha ba ta amayar dashi, inna tace ajedai tunda kin sha.... Shi kuwa Haidar da shi yasa Ma'u ta amayar da maganin, amma duk da haka Saida wani ya tsaya a cikin ta, tashi tsaye yayi ciki fushi yana ambatan sunan i'liyas, a cewar sa shi ya jamai wannan bala'in, gashi ana banka mata wasu banzayen magani, rufe idonsa yayi yana binciken inda i'liyas yake, da ƙyar ya gano asalin inda i'liyas ɗin ya ɓoye, ware idanuwan sa yayi yana murmushin mugunta, sannan ya furta a fili "I'liyas gani nan zuwa gare ka.." ya faɗa yana ɓacewa...... Bai bayyana a ko ina ba sai a wani tsaunin fararen duwatsu, gaba ki ɗaya gurin cike yake da wasu duwatsu manya manya manya, wanda yafi ko wanne girma HAIDAR ya nufa kai tsaye, ko da yazo bakin ƙofar wasu samudawan dakaru na gani tsaye a bakin ƙofar, suna gadin ta babu wanda ya isa ya kyata wannan gurin sai wanda suka aminta dashi..... Wannan gurin kuwa ya kasance mallakin Sarkin malamen al'janu, dukkan wani ilimi na addini da na rayuwa har ma da dubarun da al'janu, suke dashi shi yake koya musu haidar ya kasance ɗaya daga cikin ɗaliban wannan malamin aljani, wannan dalili yasa i'liyas yayi tinanin zuwa gurin, dan Haidar yana matuƙar jin kunyar aikata wani abu a gaban malamin, kuma yana jin maganar sa fiye da iyayen sa....... Shiga gurin yayi kai tsaye ba tare da sun ce mai komai ba, kasancewar shi ɗin sananne ne a wajen, haƙiƙa zan iya cewa cikin yafi waje girma dan halittun dake gurin nan Allah kaɗai yasan yawan su, hango iliyas yayi zaune yana koyawa wasu yaran al'janu karatun Alkur'ani, kasancewar malamin baya nan ya tafi umara, ganin Haidar da i'liyas yayi ba ƙaramin tsorata yayi ba, baisan lokacin da ya miƙa tsaye ba yana kallon sa, rai a haɗe Haidar yace "ina so zan yi magana da kai, inda halin haka.." Haidar ya faɗa yana yin gaba i'liyas da gabaki ɗaya ya gama tsorata da lamarin Haidar, da ƙyar ya aro jarumta yasa wa kansa, gudun kar Haidar ya gano ya tsorata da shi, binsa yayi a baya yana addu'ar Allah ya kuɓutar dashi daga sharrin Haidar........ Wani guri da babu kowa nan HAIDAR ya tsaya tare da juya bayansa, iliyas da ya ƙara so cikin ƙarfin hali yace "gani.." Saida Haidar ya daɗai bai ce uffan ba, sannan yaja numfashi yace "I'liyas...! Me na aikata maka, kuma meye ribarka, da har zaka je kaci amanata..." Shiru i'liyas yayi yana girgiza kai dan bashi da bakin da zaiwa Haidar magana kuma duk abinda zai cemai, bazai taɓa fahimtar saba..... Cigaba Haidar yayi da cewa "Gashi a dalilin maganar da kaje ka faɗa, sun fara ɗura mata wasu banzayen magunguna, nidai nasan wannan maganin da suke bata babu abinda zai sauya Dan yanzu ma na fara sonta, amma abinda nake so kasani, Ma'u tana da cikina, na tsawon wata ɗaya da sati biyu, kuma muduk suka ci gaba da bata wannan maganin, zai iya barar mun da cikina, kuma na rantse da Allah cikin nan ya bare kayi kuka da kanka, domin duk abinda nama kai kaja, kuma shi kanshi wanda ya bada maganin ma bazan ƙyale shiba, bare kuma kai da ka kasance kaine sila..........✍️ *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/15, 1:46 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________________ *41 & 42* _____________I'liyas kuwa dake tsaye yana kallon Haidar, kasa furta komai yayi, dan yana da tabbacin indai yayi magana, to zai iya ƙara tunzura Haidar, shiyasa yayi shiru, har ya gama banbamin sa ya tafi..... ★★★ Yau Suraj tun safe yake shirye-shiryen zuwa batsari, kasancewar Daddynsa yace yana son ayi auren akan lokaci, kawai idan zai koma U.K sai ya wuce da matar sa.... Cikin wani yadi fari ya shirya, kayan sun matuƙar karɓar sa, dan ba ƙaramin kyau yayi ba, wata baƙar hula ya ɗora a kansa, kasancewar sa fari, sai hakan ya ƙara fito da asalin kyansa, gaba ki ɗaya shigar baƙi da fari yayi dan hatta takalmin sa da agogonsa baƙaƙe ne..... Fitowa yayi yana zuba ƙamshi, kai tsaye gurin mommy ya nufa dan ya sanar da ita tafiyar sa, mommy dake zaune tana kallo a T.V, hango Suraj da mommy tayi addu'a kawai take a zuciyar, bata son lokacin da a fili ta furta "fa subhanallahi ahassanal kali qin." Ƙarasowa yayi haɗe da tsugunnawa, mommy ya yiwa sannu sannan yace "Na shirya mommy! Ni zan wuce, sai na dawo..." Mommy da fara'ar ta tace "to Allah ya kai ka lafiya, Allah ya kare ka daga sharrin masu sharri, kuma Allah Ubangiji ya baka nasara akan duk abinda ya kasance alkairi a gare ka.." Amsawa yayi da ameen yana matukar jin daɗin addu'ar da mommy tamai, har ya tafi yana jin nishaɗi a zuciyarsa..... Saida sukayi tafiyar waje awa ɗaya da rabi sannan suka ƙarasa, kasancewar akwai ƴar tazara sosai tsakanin cikin Katsina da kuma ƙaramar hukumar ta batsarin....... Darek wajen aikin su kawu Salisu yayi, nan suka taho tare zuwa gidan su innan... Kawu Salisu ne ya fara shiga yana cewa "bari nama iso koh.." Ya faɗa yana shigewa, samun inna yayi a ɗaki a zaune, labarta mata zuwan Suraj yayi, sannan yace mata "yana zaure ma a tsaye.." Riƙe haɓa inna tayi tana cewa "Wallahi har ga zuciya ta, ina farin ciki da zuwan Suraj! Saidai wani ɓangare na zuciya ta yana fargabar abinda zai iya faruwa dashi, sakomakon auren Ma'u da yake son yi, wallahi ina tsoron wani abu ya sami wannan ɗa.." Jan numfashi kawu salisu yayi sannan yace "Haba adda Hajara! Komai fa kika ga ya samu bawa, to dama rubutacce ne a wajen Ubangiji, karki jingina hakan da wani abu kedai kawai kiyi fatan alheri.." "Uhmm! Uhmm!! Uhmm fa, Salisu ina ga kawai ka shigo da yaron nan, in mai cikakken bayanin abinda ke akwai, in yaso sai muji daga bakinsa..." Fita kawu Salisu yayi ya shigo da Suraj ɗakin inna, bayan sun gaisa ne inna ta fara mai bayanin abinda yake wakana..... Ma'u dake tsugunne tana wankin under wear's, ganin omon da take wankin ya ƙare ,sai tazo wajen window inna, dan ba'a rasa omo ko sabulu a gurin, jin da tayi inna ta ambaci masoyinta yusif, yasa ta tsaya taji mai ake cewa..... Dafe ƙirji Ma'u tayi tana magana a hankali, "Haidar dama kai ka kashe min Yusuf ɗina,? dama kaika Hanani nayi aure kamar yadda kowa yake yi,? mai na aikata maka?...." Shi kuwa Suraj ganin inna ta gama bayanin ta, yasa ya saki murmushi yace. "Babu wani halitta da ya isa ya cutar da wani halittan, face Allah ya riga da ya rubuta a kundin ƙaddararsa, so! ni abinda nake so kusani, suma sauran Allah ya rubuta ƙaddarar cewa a ta dalilin haka, wani abu zai faru dasu, wallahi inna! Yanzu da kika bani labarin abinda ke faruwa da Ma'u, sai naji duk duniya babu macen da nake so sama da ita, ada na zone saboda umarnin mahaifina, amma daga yanzu duk zuwan da zanyi zazone bisa matuƙar son da nake mata, kuma insha Allahu nine mijin ta, inna ki daina damuwa, Allah ba zai taɓa barin wani ya aikatawa bawansa wani abu ba, kuma idan wani abu ya faru dani ki ƙaddara Allah ne ya ɗoramin....." Inna kawai murmushin su manya tayi, tana wa suraj fatan samun nasara a rayuwar sa... Ma'u dake tsaye a bakin window, kasa motsawa tayi musamman da taji kalaman da suke fitowa daga bakin suraj, wani girman sa da ƙimarsa taji suna shiga cikin zuciyarta, a ranta ta ayyana. "lokaci yazo da zan rabu da kai Haidar, in fuskanci rayuwar da ta dace dani, in rabu da zalunci da kake min, kuma kana fakewa wajen cewa kana tsananin soma.." Ɗaukar omon tayi ta ƙara gaba abin.... Fitowa inna tayi tsakar gida, tabar kawu Salisu da suraj a ɗaki, suna cigaba da tattaunawa sai da suka gama sannan kawu Salisu ya fito yana ce mai "bari a turo maka da ma'u.." Ya faɗa yana fita daga ɗakin...... Inna kuwa dama tunda ta fita ta samu ma'u, akan taje ta ɗan kimtsa ga baƙo tayi, babu wani musu ko ɓaci rai Ma'u ta shiga ɗaki dan kimtsa wa, ba ƙaramin daɗi inna taji ba, har tana cewa lalle maganin malamin nan yana aiki, har an fara samun sauyi.... Ta ɓangaren Ma'u kuwa, abin ba haka yake ba, dan har wani duhu duhu take gani, ga wani azababben ciwon kai dake sauko mata lokaci ɗaya, kawai dai dauriya take dan yanzu tana jin lokaci yayi, wanda zata yi fito na fito da haidar...... Ɗaukar hoda tayi da niyar ta shafa a fuskarta da ɗan man leɓe, madubi ta ɗauka, maimakon taga fuskar tata ko hasken madubin, sai taga gaba ki ɗaya yayi baƙiƙƙirin, ajje shi kawai tasa hijab ɗin ta.... Tana fitowa inna tace ki ɗan shigan mai da ruwa ko, da to ta amsa, sannan ta ɗauko wani sabon jug da inna ta siyo, ruwan randar inna ta zuba mai sanyi, ta wuce ɗakin da yake a zaune....... Shiga tayi ɗakin bakinta ɗauke da sallama, samun sa tayi zaune a kan dardumar tsakar ɗakin inna, kansa sunkuye yana daddanna wayar sa, Ma'u a ranta tace shi kullum yana danna waya ko gajiya ba yayi, ɗagowa yayi suka haɗa ido, da sauri Ma'u ta sunkuyar da kanta tana ambaton sunan Allah, jin jikinta yana karkarwa, bata san meyasa ba ko sunan Suraj taji an ambata, sai taji jikinta yana tsuma..... "Are you ok?." Muryar sa Ma'u taji tana huda dodon kunnen ta, cikin in ina Ma'u tace "yeh... Yeah.." Yace "kin tabbatar.." Girgiza kai Ma'u tayi, sannan ta ajje ruwan haɗe da tsiyaya mai a ƙaramin kofi, ganin hannun ta Suraj yayi yana rawa, dan saura kiris ta zubar da ruwan, karɓar yayi ya ƙara sa zubawan, yana kai ruwa bakin sa, kaɗan ya kurɓa ya ajje kofin.... Sautin siririyar muryarta ya tsinkaya tana cewa "ina yini..!" "Lafiya ƙlau.." Suraj yace a taƙaice . Shiru ne ya ratsa gurin kowa yana tinanin mai zaice, can kuma sai Ma'u tace "Ya su inna.." Dariya Suraj yayi sannan yace "Mu bamu da inna saide mommy.." Taɓe baki Ma'u tayi tana cewa "Amma ai duk ɗaya ne ko.." "Eh mana! Sosai ma." Shiru ne ya ƙara ratsa gurin, dan har Ma'u ta gundura da zaman kawai Allah Allah take ya bata dama ta wuce, ji take kamar tana zaune a kan ƙaya, bata yi aune ba taji muryarsa yana cewa "Shekarar ki nawa..?" Ƙara maimaita tambayar Ma'u tayi a ranta, tana cewa ko ina ruwansa da shekaru na, ciki ciki tace "Ashirin da tara.." Gyaɗa kai Suraj yayi yana cewa "Anya kin kai haka kuwa, Ni kallon ƴar 19 nake.." Ma'u kuwa da take da shegen son girma, jin ya maidata ƴar sha tara, a zuciyar ta tace ji kuma wani ranin hankalin, amma a fili sai tace "Uhmmm!." Cigaba yayi da cewa "matakin karatu fa! Ina nufin a ina kika tsaya.." Cikin gajiya da amsa tambayoyin nasa ma'u tace "Secondary school.." Yace "kuma kina da buƙatar ki cigaba ko kuma kawai hakan ma ya isa.. " A hankali Ma'u tace "ina so mana.." Cigaba yayi da janta hira tun Ma'u tana ɗan nuna rashin sabo, har tazo ta sake dashi..... Dazai tafi kuwa ɗayar wayar dake hannun sa, ya bata a cewar zasu riƙa gaisawa ta cikin wayar......✍️ *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/17, 10:54 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________ *43 & 44* _____________Ƙin karɓa ma'u tayi tana mai godiya, hakan ya ba suraj mamaki dan shi a rayuwar sa, babu abinda yafi ƙi irin yama kyauta kaƙi karɓa, ƙyaleta yayi kawai ya fita daga ɗakin.... Tsakar gida ya samu inna a zaune nan ya mata sallama akan zai wuce, inna tace "bari na baka saƙo ka kaiwa Momyn ka.." ɗaki inna ta shiga ta fito da leda ɗauke a hannun ta, ganin baya tsakar gidan yasa inna tayi kiran ma'u da sauri... Fitowa ma'u tayi tana zumɓura baki kamar wata ƙaramar yarinya, lallashinta inna ta fara, dan yanzu inna ta daina jin haushin ma'u, tunda tasan lalurar da take damunta, janta take a jiki haɗe da kuma nuna mata soyayya... cikin rarrashi inna tace "Ma'un inna! Ungo nan kai masa yana waje yana jiranki, in mutum yayi baƙo in zai tafi rakashi ake kinji koh.." Amsawa da "to." Ma'u tayi tana karɓar ledar hannun inna, tana fita ta same shi zaune a bayan mota da dukan alamun dama ita yake jira, dan hatta mirfin motar a buɗe ya barshi, ƙarasawa tayi tana tuttura baki, wai ita a dole an takura mata.... Alama ya mata da ta shigo cikin motar, ba haka ma'u taso ba dandai kawai bata san yi mai musu ne, zaunawa tayi kan kujerar amma ƙafafuwan ta suna daga waje, miƙo masa ledar da inna ta bata tayi tana cewa "Gashi inji inna tace kaba momy.." Ƙin karba yayi yana binta da wani irin kallo, ita kanta Ma'u sai da taji kunyar kalar kallon da yake mata, cikin sanyin murya Ma'u tace "Lafiya..!" Murmushi Suraj yayi sannan yace "ba komai! Kawai naga kin min kyau ne.." "Uhmm! Ina so in shiga gida pls.." Ma'u ta faɗa cike da shagwaɓa Cikin nuna kulawa Suraj yace "Kodai kin gaji dani ba! Shiyasa kike so in tafi.." Dariya Ma'u tayi tana cewa "Ah ah wallahi! Kawai dai ina da ɗan wani aiki ne a cikin gida.." Murmushi yayi kawai, sannan ya ɗauko wata ledar shopping yana miƙo mata, tsayawa Ma'u tayi tana kallon sa, Suraj kuwa ganin bata karɓa ba, yasa cikin tsare gida yace "Karɓi mana!" Ya faɗa yana ƙura mata ido... Kwarjinin da ya mata ne yasa ta karɓa tana yi mai godiya, tashi tayi a sanyaye sannan tace "Allah ya tsare hanya! A gaishar da mutanen gidan.." "Ameen." Yace yana Binta da kallo, Saida yaga ta shige gidan sannan yawa direban sa magana suka wuce...... Ma'u kuwa tana shiga cikin gidan wajen inna tayi, tana miƙa mata ledar da Suraj ya bata, karɓa inna tayi tana cewa "Na miye wannan ɗin." Buɗe wa Ma'u tayi, nan taga kayan lashe lashe ne da kuma na tanɗe tanɗe, sai kuma wayar da ya bata, bata karɓa ba. Ɗauka tayi tana jujjuya wayar cike da mamaki ganin wata ƴar takarda a jikin wayar, yasa da sauri ta buɗe, ƙaramin note ne kamar haka *"Pls Husnah ki ɗauki wayar nan! Zan kira ki anjima, in na koma gida.."* Ɗaukar wayar tayi tana murmushi, taji daɗin kiranta da Husnah da yayi, sai hakan ya tina mata da yayanta yusif, dan shi kaɗai ke ce mata Husnah... ★★★ Da misalin wajen ƙarfe tara na dare, Ma'u taji wayar da Suraj ya bata tana ringing, saida kiran ya katse sau wajen uku sannan Ma'u ta ɗaga kiran, cikin zazzaƙar muryarta tace "Assalamu alaikum." "Wa'alaikis salam! Ranki ya daɗe fatan dai kina cikin ƙoshin lafiya.." Jin satin muryarsa da ma'u tayi yasa ta gane shine, da sauri tace "Lafiya kalau! Ya kaje gida lafiya.." "Alhamdulillah! Sun ce ma suna gaishar dake.." Dariya Ma'u tayi mai sauti sannan tace "Ina amsawa.." Nan Suraj yaja ta da hirar soyayya, ita dai Ma'u saide kawai ta bishi eh ko ah ah, bai kawo komai ba tunda yasan harda rashin sabo da take da shi akan al'amarin... Cikin farin ciki da jin daɗi suka gama wayar, dan ita kanta Ma'u baza ta iya cewa bata sonshi ba, haka kuma bazata iya cewa ba ta fara sonshi, ita dai kawai yana burgeta ne ga rayuwar sa yana tafi da ita yadda Yakamata, ko kaɗan baya da girman kai, ko jin shi ɗin wani ne, ita dai rayuwar sa ta mata..... Tana cikin wannan tunanin ne, taji wayar tayi ƙara alamar shigowar saƙo, tana dubawa taga an rubuta *"Matata insha Allah!* *Ina so ki tashi kije kiyi al'wala, kizo kiyi sallah koda raka'a biyu ne, sannan kiyi mana addu'a sosai, INA SONKI..* Murmushi Ma'u tayi tana maimata saƙon, kallon su inna tayi, nan taga inna har ta fara bacci ita kuma zahrah tana chart da wayar ta, dama yanzu tunda inna ta san lalurar Ma'u, suke kwana tare a ɗaki ɗaya, duk dan ta gujewa mu'amala da Haidar..... Saukowa daga kan gadon inna Ma'u tayi a hankali, fita tayi tsakar gida dan ta ɗoro al'wala, har ta tsuguna da niyar al'walar sai taji tana jin fitsari, da sauri ta shige toilet ba tare da tayi addu'a ba, tana tsugunnawa taji motsi a bayanta, da sauri ta juya cikin tsoro, ganin wajen tayi wayam alamun ba kowa, da hanzari tayi tsarki tana shirin barin bayin, dan Allah Allah take tabar gurin, gaba ki ɗaya ta tsorata da yanayin, ji tayi anyi sama da ita, kama akan iska haka take jinta, lokaci ɗaya ta fita a hayacinta Bama tasan inda kanta yake ba, Saida ta ɗauki tsawon lokaci, sannan ta dawo hayacinta, samun kanta tayi akan wani ƙayataccen gado yayin da haidar yake zaune a gefe ya juya mata baya, yana kallon tarin hannunsa.... Cikin tsiwa da rashin kunya Ma'u tace "Meye na kawo ni nan! Ni ka mai dani inda ka ɗauko ni..." Ganin ya mata shiru kamar ba da shi take magana, hakan sai ya ƙara ƙule Ma'u, cikin fushi Ma'u tasa hannu da niyar fisgoshi, ko gezau bai yiba asali ma yana nan a yadda yake kamar ba wanda ya taɓa shi, sai ita da tazo fisgoshi sai taji kamar ita aka fisgah, ta sowa tayi ta zagayo ta gaban shi, kallon shi take tana jin zuciyar ta kamar zata fashe da tsoron shi, ita wallahi ko can dama da tasan haidar al'jani ne, bata ji tsoron shi ba kamar yadda take ji a halin yanzu, bin hannun nasa tayi da kallo, ganin ya ƙura mai ido ko ƙiftawa ba yayi, yasa ta leƙa kanta abinda ta ganine yasa ta zaro idonta.........✍️ *MORE COMMENT* *TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/18, 9:51 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* __________________________________________________ *45 & 46* _____________Ba komai ta gani ba illah, Suraj zaune kan dadduma sai ƙur'ani mai girma da ke gaban shi da dukan alamun dai karantawa yake... Da sauri Ma'u ta buɗi baki da niyar yin magana, amma sai Haidar yasa yatsan sa a leɓenta yace "Shishhht!! Kar inji bakin ki yanzu, a gaba in dawo ta kanki.." Allah sarki Ma'u sai ta koma gefe ta zauna, yayin da ta rafka uban tagumi wani tsoron Haidar take ji, yana shiga lugu da saƙo na zuciyar ta, cigaba yayi da kallon Suraj ta tafin hannunsa.. Saida ya ɗauki tsawon lokaci sannan ya ɗago, kallon Ma'u yayi fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Masoyiyata taho gareni.." Shiru Ma'u tayi tana binsa kawai da ido a zuciyar ta kuwa, sunan Allah kawai take ambato dan shine kaɗai zai kawo mata ɗauki, game da azzalumi HAIDAR.. Tsinkayar muryar sa tayi yana cewa "baki ta so ba fa.." A hankali Ma'u ta so har ta ƙara so gaban shi, tsugunnawa tayi a gaban shi cikin kuka Ma'u tace "Haidar! Dan girman Allah karka cutar da sur...." "Shishsht! Bana ce Miki ba kar inji bakin ki anan ba, kiyimin shiru.." Ido kawai ta zura mai tunda ya hanata tayi magana da bakinta... Janyo ta jikinsa yayi ya rungume ta tsam, kamar za'a ƙwace masa ita sai faman jera ajjiyar zuciya yake kamar wanda yayi tseren gudu, magana ya fara cike da rauni yace "Wallahi Ma'u! Badan sonki da ƙaunar da nake Miki ba, wallahi banga dalilin da zai hana na miki hukuncin abinda kika min a yau ba, meye shi wannan bil'adama yake da shi wanda ni bani dashi, ki duba fa na fishi kyau nafishi sonki ke na fishi komai, meyasa lokaci ɗaya zaki sauya ra'ayi,? meyasa..?" Ya ƙare maganar yana ƙura mata ido.. Shiru Ma'u tayi haɗe da sunkuyar da kanta, a zuciyar ta kuwa nemon temakon Allah take ta kowanne yanayi... Cigaba Haidar yayi da cewa "Ko kin manta alƙawarin ki a gareni, na zaki kasance tare dani a kodayaushe..?" Nan ma shiru Ma'u tayi me, sai kuma can ta saki kuka tana cewa "Ni ka maidani gidan mu bansan ganinka, na daina sonka ɗin, kawai ka maidani inda ka ɗauko ni.." Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka.... Sakinta haidar yayi, yayin da idanunsa suka rine baƙiƙƙirin, dan ɓacin ran da yake ciki, komawa gefe yayi ya zauna yana kallon Ma'u da take kuka, kamar ance mata uwarta ta mutu.... Jin kukan nata yake har cikin ƙoƙon zuciyar sa, saidai bazai iya hanata yiba, saboda ko da wasa baijin zai iya rabuwa da ita ba.... Ta ɗau tsawon lokaci tana kukan har Saida ta gaji dan kanta, sannan ta taso.. zuwa tayi gaban Haidar ta durƙusa, kama ƙafafuwan sa tayi tana cewa "Ina mai haɗaka da Allah da Annabi Haidar ka fita daga rayuwata ko na samu salamah, kabarni in auri jinsi nah, nayi rayuwa ta kamar yadda kowa yake yi, Haidar pls kaji tausayina....." Ta faɗa tana haɗa hannayen ta...... Kauda kansa Haidar yayi yace "Bazan iya ba! Saboda ina sonki, in na rabu dake ni kuma sai inyi yaya da rayuwata..." "To kabarni in auri jinsi na! Kodan farin cikin iyaye na.." "Shima bazan iya ba! Saboda ina matuƙar kishin ki, kuma ma naga ai yanzun ma kina da aure, tunda kina dani, ko akwai wani abu da na tauye miki a rayuwar mu ta aure ne..?" Ihun baƙin ciki Ma'u ta kurma, da kuma na rashin sanin madafa...... ★★★ Ɓangaren su inna kuwa da inna ta tashi da asuba, ganin bata ga ma'u ba hakan yasa tayi tunanin ko tana bayi, jiranta tayi akan in ta fito itama sai ta shiga ta kama ruwa, shiru shiru Ma'u bata fito ba, hakan yasa inna fitowa tazo wajen bayin tana kiran Ma'un.... Jin shiru bata amsa ba, yasa inna ta fara sababin ta "Waike Ma'u uwar mai kike yi a bayin da har baza ki fito ba, na hanaki daɗewa a bayi, amma kinƙi ji ko Allah yasa na shigo na sameki anan ciki wallahi sai ranki ya ɓaci..." Jin shirun yayi yawa gashi kuma bata jin motsin kowa, sai ta tura ƙofar bata ga komai ba, saima butar da ma'u ta shiga da ita jiya da dare, bata kawo komai ba, tayi abinda zata yi ta fito tayi al'walar ta, ta shige ɗauki abinta.... Saida inna ta idar da sallar tukunan ta tashi, zahrah tana ce mata "Maza tashi kizo kiyi sallah, daga nan ki tashi Ma'u ina ga ɗakin can ta koma ta kwanta, tashi zahrah tayi ta fita, Saida ta kammala al'walarta, sannan ta tunkaro ɗakin ƙwanƙwasawa tayi tana kiran sunan Ma'u, shiru bata amsa ba, hakan yasa zahrah tura ɗakin, wayam babu Ma'u cikin tashin hankali zahrah ta ƙwalawa inna kira.... Da hanzari inna ta fito tana cewa "Lafiyar ki kuwa zahrah da sanyin asuban nan, zaki riƙa wa mutane ihu.." "Wallahi innarmu adda Ma'u bata cikin ɗakin nan.." "Kamar ya bata ciki! Inba ta ciki ina zata shiga to..?" Saida suka leƙa ko wani lungu da saƙo dake cikin gidan, amma basu ga ma'u ba, cikin tashin hankali inna tasa zahrah ta kira kawu Salisu, shima da yazo ya shiga cikin tashin hankali, ace babban mutum a neme shi an rasa to ina Ma'u kuma tayi...... Sosai hankalin su ya tashi, dan sun rasa ta ina ma zasu fara neman ta... ★★★ Suraj kuwa tun da asuba da ya tashi ya kira wayar hannun Ma'u, jin ba'a ɗaga ba yasa yayi tinanin ko bata tashi ba, ko kuma bata kusa da wayar ne.... Duka iyalen gidan Daddy zaune suke suna breakfast, bayan sun kammala ne Daddy ya kira Suraj yana tambayar sa yadda suka yi da ma'un, nan Suraj ya labarta mai komai ciki kuwa harda lalurar da aka ce Ma'u tana da ita, kawai abinda ya ɓoye mai shine bai bashi labarin cewa AL'JANIN Ma'u yana kashe mata samari in sun nace sai sun aureta, kuma ko su su inna ya riƙe su akan subar wannan abun a matsayin sirri, bai so su ƙara gayawa kowa... Nan Daddy yace "Gaskiya wannan yarinya tana da babbar lalura, Allah Ubangiji ya zaɓa mana abinda yafi alkairi, amma Salisu bai taɓa gayamin ba wallahi.." Suraj yace "ai da yake suma kwanan nan suka fahimci tana da NAMIJIN DAREN, amma yanzu sun fara nema mata magani..." Daddy yace "to Allah ya kawo mafita insha Allahu, anjima zan kira shi salisun mu tattauna akan maganar auren.........✍️ [6/17, 7:27 PM] Matar Khamis,: Haidar Wallahi duk nacinka Sai ka rabu da Ma'u.haka kawai ka hanata Aure,Ina ake aure tsakanin mutum da Aljan indai ba Mugunta ba,to wannan Karon dolenka ka hakura.muna gdy sosai Allah ya Kara basira yasa kifi haka.much love for you Sis.🥰🥰👍 [6/17, 7:29 PM] Matar Khamis,: [6/17, 11:17 AM] Marichou: Kai Masha Allah Allah ya kara basira Ko meye Ma'u ta gano😳😳😳😳 [6/17, 11:41 AM] +234 906 547 6395: Nashiga fargabar abinda ma'u tagani [6/17, 11:41 AM] +234 906 547 6395: Allah y kara basira d alama haidar bacin ransa na rashin nasara ne [6/17, 11:48 AM] +234 816 328 3548: Masha Allah matar khamis Allah yakara basira dakarfin ido dazakin hanu munagodiya Allah yabarki da khamis har aljanna🤣🤣🤣🤣💃💃💃 [6/17, 12:16 PM] Ummu Khalid: Da alama soyayyar Suraj tayi nasara haidar kowa ya hango faduwa! Hmmm kishi da mutum ya Kare balle halittar da baka gani! Ga Dan Adam da shagala! Kishi tsakanin Suraj da Haidar! Bafa sai na fada muku duk Kan ahli biyu suna farinciki ba 😁domin Suraj mutum nai da matar sa ta mutu Yan gidan su suna ta so suga yayi aurai😄ma u ta Jima Bata shiga daga ciki ba😄 Ga haidar Aljanin soyayya!!! Haidar zaka Bari muji yadda yadda a Yi kayataccen biki 💃💃💃😁 ko aa? Da alama fa Suraj dan soyayya nai😍 shin Mai haidar yake so ya nunawa mau? Mrs khamis muje zuwa Allah ya kara fasaha👍🏾 [6/17, 1:25 PM] Fateemah Adam: Muna gdy Allah yakara basira kifi yadda kike yanzu yabiya maki bukatunki na alkhairi damu baki daya [6/17, 2:21 PM] +234 916 233 5086: Toh me taga ni ? Munje zuwa...muna godia Mrs khamis [6/17, 7:30 PM] Matar Khamis,: [6/17, 12:03 PM] Ummu Abno: Allah ya qwaci Suraj yau a hnnun haidar ita kanta ma'u tashiga taskun shi Allah y qwacesu 🤲🏻 [6/17, 2:10 PM] Maman Khairat: Allah yakara basira da zakin hannu to ma'u kema Allah ya qwace ki [6/17, 5:48 PM] +234 806 548 4348: Tab🤔narasa me dance dan tsoro [6/17, 6:30 PM] +234 913 122 9563: Dakyau soRaj ka iyaya soyayya tunda gashi ma'u tafara manta haidar matar khamis Allah y Kara zakinhannu tareda basira _comment ɗin ku fa yana ƙara fasamin kai, ku taimake ni kar kan ya dagargaje😹_ _yan facebook groups Ni daku akwai amana cau cau💪💃_ _Ƴan group dina na Whatsapp ina yinku over kunfi kowa búrgeni yacin🥰💃😹_ *ALLAH DAI YA BARMU TARE* *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/20, 4:18 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________ *47 & 48* ______________Suraj ya kira wayar hannun Ma'u sau ba adadi, amma shiru ba'a ɗaga ba hakan ya matuƙar ɗaga mai hankali, kawai sai ya yanke shawarar kiran kawu Salisu dan yaji ko lafiya, shima Saida ya kira shi sau wajen uku sannan ya ɗaga..... Bayan sun gaisa ne kawu Salisu yake sanar da shi abinda ke faruwa, cikin kiɗimewa Suraj yace "Yaushe kuma aka sace tan! Ko jiya da dare fa munyi waya da ita...." Kawu Salisu yace "Wallahi kuwa dai! Saida safe muka nemeta muka rasa, amma muna tunanin ko ƴan kidnaping ne suka ɗauketa ..." Cikin damuwa Suraj yace "Tabbas haka zata iya faruwa, kasan yanzu yadda ƙasar tamu take, Allah dai ya kawo mana ɗauki..." "Ameen ya Allah! Insha Allahu muna nan, muna tayin addu'a da yardar Allah Ma'u zata bayyana.." Kawu Salisu ya faɗi haka cikin rauni, a sanyaye Suraj ya ajje wayar zuciyar sa cike da damuwa, a iya jiya ne kawai ya keɓe da ma'u, amma ba ƙaramin jinta yake a zuciyarsa ba, ta riga da ta zama shi ya zama ita, sosai ya damu da ita da al'amarin ta, hakanan yaji Allah ya sa mai tausayinta da kuma tsantsar ƙaunar ta acikin zuciyar sa... Dogon numfashi yaja yana jin ransa yana ƙuna, ayyana abubuwa da yawa yake a ransa, ganin hakan bazai fushshe shi ba, sai ya tashi da sauri jin kiran salhar azzhar, al'wala yayi ya wuce masallaci, bayan idar da sallar kuwa, ya daɗai a zaune yana addu'o'in Allah ya bayyana Ma'u cikin aminci...... Da yamma kuwa da Daddy ya dawo daga office, nan yake wa Suraj faɗa akan meyasa bai biyosa office ba, tunda yanzu kana hutu kan ya koma ai sai ya riƙa zuwa yana taya shi aiki.. Cikin ladabi suraj yace "wallahi Daddy yau ɗin ne nake jina wani kala, gashi kuma ɗazu kawu Salisu yake sanar dani ƴan kidnaping sun ɗauke Husnah.." "Subhanallahi!! Kaji baƙaƙen mugayen ko, Allah ya mana katangar ƙarfe dasu, Allah Ubangiji ya mana maganinsu.." Suraj yace "Ameen ya Allah.." Kai tsaye Daddy kawu Salisu ya kira bayan sun tattauna akan abun, sai Daddy yace "indai har sun kira to kuyi min magana dan Allah.." Kawu Salisu yace "Allah yasa to su kira yau.." Daddy yace "ameen.." Ɓangaren inna kuwa ta shiga tashin hankali dan bazai misaltuba, Ko abinci ta kasaci, sallah kaɗai ke tadata, amma ko ƙwaƙwaran magana bata iya yi, sai Allah da take kaiwa kukanta dan shi kaɗai zai kawo mata mafita acikin lamurran ta..... ★★★ Ma'u kuwa tun tana kukan har ta gaji, bacci yayi awon gaba da ita anan inda take a durƙushe, shi kuwa Haidar dake zaune yana kallon ta, ji yake zuciyar sa tana ƙuna sosai, musamman idan ya tina yadda Ma'u take cemai, bata sonshi, wani take so, kuma ya fita daga rayuwar ta, sai yaji kamar ya shaƙe kansa ko ya huta.... Duk wani kalar hukunci da ya shirya yiwa Suraj, sai yaji gabaki ɗaya hukunci ya mai kaɗan, dan duk shine silar sa shi cikin wannan yanayin.. Ɗaukar Ma'u yayi ya kwantar da ita kan bed ɗin, yadda take turo baki alamun shagwaɓa take ji, sai hakan ya matuƙar birge shi, ƙura mata ido yayi yana kallon leɓen nata da suka fi komai jan hankalinsa, yadda ya shagala da shauƙin kallon kyakkyawar surar ta, bai san lokacin da ya fara kissing ɗin bakin ta, shashshafata yake ta ko ina, yayin da yake ƙara dulmiya cikin shauƙin ƙaunar ta da kuma tsantsar sha'awar ta... Cikin bacci Ma'u take jin wani baƙon yanayi a tattare da ita, ƙara shigewa jikinsa tayi, tana ƙara banƙaro masa ƙirjinta, farkawa tayi da sauri kamar ance ta buɗe idonta, kawai sai taga Haidar a kanta yana ƙoƙarin yin sex da ita, sunan Allah ta fara kira, haɗe da sakin a'uziyyah da ƙarfinta, sannan ta fashe da wani marayan kuka....... Lallashinta haidar ya fara yana cewa "Haba Ma'u meye haka ɗin! Yau ni kike neman tsari dani, sai kace kinga shaiɗani..."? Cikin kuka Ma'u tace "Wallahi Haidar kai kafi shaiɗanin ma! Inba haka ba mai na maka da ka'adabi rayuwa ta, ka rabu dani mana, ka mai dani gidan mu, kuma kabarni in auri Suraj shi nake so yanzu.." Haidar da yakai ƙololuwar fusata, yanayin sa da kamanninsa gabaki ɗaya sun sauya, saboda ɓacin ran da yake ciki, tashi yayi yabar mata ɗakin dan muduk ya cigaba da zama kusa da ma'u, to zata cigaba da ce mai Suraj take so, shi kuma bazai iya jurar haka ba, gwara ya fita yabar mata gurin gaba ki ɗaya..... Ma'u kuwa da taga ya fita, haɗa kanta tayi da gwuiwa ta cigaba da rera kukanta.... Washe gari kuwa da safe, Ma'u koda ta tashi bata ga Haidar ba, gashi tana so tayi al'wala tayi sallar asuba, sai dai bata ga ruwa ba, bare kuma taga bayin da zata shiga..... A fili ta furta "Allah yasa ma yanayin salsallar Ta faɗa tana hararar ɗakin sai kace shine Haidar ɗin, _niko nace kai Ma'u karki yiwa Haidar ɗin mu sharri, dan kinga yana sonki_ 😏🏃‍♀️ tana cikin wannan tunanin, sai taga kamar an ajje ruwa a kusa da ita, tashi tayi ta dauki ruwan, waige waige ta fara, nan taga wata ƙofa ta buɗe, shiga tayi ba tare da taji tsoro ba, dan yanzu lamarin Haidar ya daina bata tsoro, koda ta idar da sallar kasa yin ko wacce addu'a tayi, kuka ta saki dan shi kaɗai ne take yi a halin yanzu taji ɗan sauƙi, komawa kan bed ɗin tayi tana cigaba da kukan ga wata uwar yunwa da take cinta, tana cikin wannan kukan ne taji an dafa ta da sauri ta juyo, ganin haidar ne yasa ta mai da kanta yadda yake, tana cigaba da abinda take... Ɗaukar ta cimak haidar yayi ya ɗora ta akan cinyar sa, cikin son rarrarashinta yake mata raɗa a kunne "Pls kiyi shiru kinji! Kina so na maida ki gida ko.?" Ɗaga kai Ma'u tayi da sauri alamar tana so.. "Ok!! Indai kina so to ga abinci nan ki cinye duka, sannan na maidaki gidan ku.." Bata abincin yake a baki, Ma'u badan tana so taci ba take ci, saidan kawai ya maidata gun innarta, bai barta ba Saida yaga zata yi ame sannan ya ƙyale ta, tashi Ma'u tayi tana cewa.. "Tunda na gama ci kazo ka maidani.." Shiru ya mata haɗe da zuba mata ƙwala ƙwalan idanuwan sa, ƙara maimaita masa abinda tace Ma'u tayi, Saida yaja numfashi sannan yace "Zan maidaki! Amma sai kin yarda da sharuɗɗa biyu.." Ma'u tace "ina jin ka faɗe su naji.." "Sharaɗi na farko shine! Dole zaki daina shan maganin da inna take baki, saboda cikina dake jikin ki kar ya zube, na biyu kuma shine, dole sai kin min alƙawarin zaki rabu da Suraj..." Jin haka da Ma'u tayi yasa ta Sandare a tsaye, ta rasa ma mai zata ce wa haidar, cikin tashin hankali Ma'u ta furta a fili, "Ciki.!! Ciki fa kace gareni haidar,? Kuma waima naka..? Na shiga uku ni Ma'u.." Ta faɗi haka tana ɗora hannunta a kanta🙆‍♀️......................✍️ [6/18, 11:04 AM] Matar Khamis,: Masha Allah Allah ya biya Haidar kano kona mun rai haba irin wannan naci inaga suraj shine maganin ka [6/18, 11:06 AM] Matar Khamis,: [6/18, 10:17 AM] Haskenah: Ikon Allah waikam haidar meyake nufi ne kam wlh karya yake baison ma' u dayanasonta baxai hanata aureba baxai aureta ba saide yake kulawa da ita koda wasu mugayen mutane xasu cutar da ita shikuma sai ya ankarar da ita Amma kwatakwata. Narasa gane meyake nema awajen ma'u tinda duk abinda yake nema ai yasamu sai yarabu da ita🤨🤨 jinjina gareki uwar gida kuma Amarya agidan Mr khamis fatan alkhairi fatan nasara agareki muna fatan Allah yabaki ikon gama wannan littafin cikin koshin lfy Allah yakara basira Allah yakara nisan kwana Mai albarka👌👌 [6/18, 11:05 AM] Matar Khamis,: Ameen ya Allah [6/18, 11:06 AM] Matar Khamis,: [6/18, 10:43 AM] +234 813 069 6464: Allah yakara karfin ido [6/18, 10:54 AM] +234 906 547 6395: Haidar sorrynka fa ma'u ta dena sonka dama zalunci baya dorewa Allah y kara basira mrs khamis suraj Allah y baka nasara wlh ina karantawa kamar kar page din y kare hk nakeji😍✌🏻 [6/18, 11:50 AM] Matar Khamis,: [6/18, 10:54 AM] +234 906 547 6395: Haidar sorrynka fa ma'u ta dena sonka dama zalunci baya dorewa Allah y kara basira mrs khamis suraj Allah y baka nasara wlh ina karantawa kamar kar page din y kare hk nakeji😍✌🏻 [6/18, 11:41 AM] Fateemah Adam: Topah wata sabuwa azzalumi shine kasaceta to Allah yanaganinka munafiki insha Allahu saura kiris muga bayanka domin ruwa batsaran kwando bane matar khamis munayinki over Allah yabarmu tare yahadamu a aljannah yakara soyayyarki azuciyan khamis [6/18, 11:48 AM] Ummu Khalid: Lallai zalinci haidar yayi yawa😭 To ta Allah ba taka ba!!! Shin Mai haidar ya ke son ai watar wa akan Suraj? Da ya ke wani bibiyar sa ? Allah sarki 😢 innah da " Yan gidan su mau .shin gidan su Suraj zasu bar shi ya auri ma u ko sai an Kai ruwa rana! Matar khamis Allah ya Kara basira👍🏾 [6/18, 11:55 AM] Matar Khamis,: [6/18, 11:39 AM] Ummu Khalid: Shin za a ganai caiwa haidar nai ya sacai ma u kuwa? Lallai so makaho Suraj wato har da boyai Ana kashai Mata samari!!! Shin wani irin mataki haidar ya ke son dauka akan 1 Suraj 2 ma u 3 kawu salisu ( Mai naimo malami da kawowa) Ina labarin aljani Abokin haidar Mai tona Masa asiri! Matar khamis Allah ya Kara wa rayuwa Albarka muje zuwa😄🥰👍🏾 [6/18, 11:41 AM] Matar Khamis,: Ameen ya Allah [6/18, 11:57 AM] Matar Khamis,: Masha Allah Allah ya biya Haidar kano kona mun rai haba irin wannan naci inaga suraj shine maganin ka [6/18, 12:44 PM] Matar Khamis,: [6/18, 12:27 PM] Marichou: Haidar ka zama sorry🤪🤪🤪 Ma'u dai ta dena sanka😜 Kuma insha Allah☝️ sai ka rabuda ita, han'a kujimin aljani mai nacin tsiya🤭👉 bari nai shiru kar ya jini🤣🤣 Allah ya kara basira da zakin hannu Aunty [6/18, 12:36 PM] Sadiya: Sis gaskiya inajin dadin wannan lbr naki sosai kuma ina ilmantuwa Allah ya saka da alkhairi [6/18, 12:39 PM] Ummulkairi: Inayimiki matar khamis💯Allah yakara basira [6/18, 2:48 PM] Matar Khamis,: Tofa jama'a me Wannan mugun yake nufi daya sace ma'u?wato kagane cewa Sooraj yafi karfika shine ka bullo ta wannan haryar,to Aradun Allah Sai karabu da ita.itama yanzu Bata sonka kaje kanemi Aljana 'yaruwarka Dan Rainin hankali kawai.Matar khamis gdy trillion Allah ya biyamiki dukkan bukatunki na Alkhairi,inayinki over Wallahi. [6/18, 6:28 PM] Matar Khamis,: [6/18, 3:14 PM] +234 706 058 4513: Shi zalinci ai baya dorewa Matar khamis Allah ubangiji ya kara basira da nisan kwana mai albarka [6/18, 5:43 PM] Maman Samhat: To masha Allah littafi yana tafiya yadda yakamata Allah ubangiji yataimakeki yakareki [6/18, 5:45 PM] +234 901 266 9279: allah yasaka mrs khamis munajin dadin littafin sosai allah kara zakin hannu *More comment* *More typing* *Pls share* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/21, 10:06 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ___________________________________________________ *49 &. 50* ________________"Dan girman Allah Haidar ka taimaka, ka cire min cikin nan, wallahi bana son shi, na tsane shi.." Maimakon yaji haushin ta, saima dariya da ta bashi irin yadda ta ruɗe tana roƙonsa, tashi yayi tsaye yana cigaba da dariyarsa yace "Ah wannan baki shirya zuwa gida ba.." Ya faɗa yana barin ɗakin, ita kuwa Ma'u durƙushewa tayi anan gurin tana rusa kukanta, wani abin baƙin cikin ma sai ta tuna wai tana da cikin Haidar al'jani, ko taya zata haifi ɗan al'jani, oho.... Wasa wasa Saida akayi tsawon kwanaki uku, shiru ba Ma'u ba labarinta, tun suna tsumayin za'a kira su ace anga Ma'u ko a mace ko a raye, amma shiru kake ji, hakan ya matuƙar ɗagawa inna hankali, haka duk wani masoyin inna ko Ma'u ya shiga damuwa, saide roƙon Allah kawai da suka dage suna yi.... Hatta Suraj malamai ya sanya suyi saukar alƙur'ani mai girma, da nufin indai Ma'u tana raye Allah ya bayyana ta..... Dan shima ya damu sosai kullum yana Hanyar zuwa batsari, yau kam da yaje ya samu jikin inna sai a hankali, ɗauko ta yasa akayi aka kawo ta wani babban asibiti, dake cikin garin katsina ana kula da lafiyar ta... Momy da Daddy ma suma suna iya bakin ƙoƙarin su wajen kula da inna, dake kwance a asibiti, yayin da su kawu Salisu suke batsari suna jiran tsammanin ganin ta inda za'a ce anga Ma'u..... Yau Suraj a gajiye yake kasancewar, yadda yake faman zirga-zirga daga batsari zuwa cikin Katsina, Da wuri ya gama dukkan wasu al'adu da ya saba yi in zai kwanta bacci, kwanciya yayi zuciyar sa cike da tunanin Ma'u a fili ya furta "Allah sarki ko kina cikin wani yanayi a halin yanzu..?" "Tana cikin aminci.." Daga bayan sa yaji an bashi amsa.. Juyawa yayi da sauri, idanuwan sa suka yi mai tozali da wani saurayi fari tas kyakkyawa, farinsa har ɗaukar ido yake, ga manyan idanuwa da suka kasance fari fes, bakin idon sa kuwa, duk iya dauriyar ka baza ka iya haɗa ido da Haidar ba, haƙiƙa Haidar kyakkyawane ko acikin al'janu ba kamar sa... Cikin murmushi ya ƙara so kusa da Suraj yace "Nasan zuciyar ka cike take da tambayoyin cewa wanene Ni koh, to na hutar dakai ba sai ka tambaya ba, Ni suna na Haidar kuma nine mijin Asma'u, wacce kake so ka aura, fatan ka fahimci abinda nake gaya maka..." Shiru Suraj yayi yana ɗan nazarin sa, tashi yayi zaune haɗe da jingina bayan sa da a jikin filon, sama da ƙasa yake ƙarewa Haidar kallo, yayin da yake jin wani kishi a tare dashi, musamman da yaji Haidar na iƙirarin cewa, Ma'u matar sa ce, basarwa yayi haɗe da sakin murmushi yace.. "Dama Husnah tana da wani mijin da ya wuce ni kuma, ai a sanina dai nine mijin da zata aura, kuma ina da tabbacin Itama tana sona sosai, kuma insha Allahu nine uban ƴaƴan ta.." Suraj ya ƙare maganar yana shafa Sajen sa, haɗe da sakin ƙayataccen murmushi.... Tsuke fuska Haidar yayi, ganin kamar Suraj yama raina mai wayo, cikin isa da taƙama ya cemai "Kasan waye ni kuwa!" "Uhmm!! Nasan waye kai mana, ka wuce wani bawa daga cikin bayin Allah.." Haidar kuwa da ya matuƙar fusata, da halin ko in kula ɗin da Suraj yake nuna masa, gashi nan dai sai yin wani abu yake kamar baisan komai ba, yazo masa a yanayin da indai ba al'jani ba, babu mai irin wannan yanayi, amma shi Suraj nunawa yake ko a jikin sa, cikin ɓacin rai haidar ya soma magana, "A dah kan inzo wajen ka, nayi tinanin zaka fahimce Ni kasan meye matsala ta, ashe kaima daƙiƙi ne kamar sauran wasu mazan da suke Son auran Ma'u, to Ni ba wai nazo bane dan muyi gardama da kai, ko wani abu daban ba, nazo ne dan in maka kashedi, da kuma baka shawara akan tun lokaci bai ƙure maka ba, to ka janye auren matata da kake son yi, idan kuma ba haka ba, to na rantse da girman Allah saina lahanta ka, na ɓatar da kai acikin wannan duniyar, sai ka yi da nasani kasancewar ka acikin wannan rayuwar, kuma ka sani! Ma'u tana gurina ina kula da ita cikin aminci, muduk kana so in dawo da ita, to kabi shawarar da nazo maka da ita..." Suraj kuwa da yake kallon Haidar yana murmushi, tashi tsaye yayi! Saida yayi taku uku zuwa huɗu, sannan ya ƙaraso kusa da Haidar, cikin isa da taƙamar sa irin ta bil'adama yace "Haidar ko kace min! To ni zan baka umarni mai cike da gargaɗi, kuma ya zama dole kabi wannan umarnin da gargaɗin da zan baka..... Saida Suraj yaja numfashi sannan ya cigaba da cewa "Na baka nan da kwana biyu! Kayi gaggawar dawo min da matata, dan ina son muyi auren mu akan lokaci, idan kuma baka dawo min da Husnah ba, to Wallahi cikin yardar Allah, sai kayi da nasanin addabar rayuwar husnah da kayi, tunkan lokaci ya ƙure maka, to kayi gaggawar dawo min da matata..." Wata razananniyar tsawa Haidar ya dakawa Suraj, wanda Saida wayata ta suɓuce da har zan gudu amma sai na dawo, nace ai indai da Suraj to Haidar saide ya ganni ya barni, 🤗✍️ Shi kuwa Suraj ko a jikin sa saima kauda kansa da yayi gefe yana cewa "Zaka iya tafiya! Dan ina son in kwanta na ɗan huta, kaga gobe sai ka dawo mu ƙarasa maganar koh.." Cike da mamaki Haidar yake kallon sa, a ransa kuwa ayyana ƙarfin halin Suraj yake, kwata kwata basirarsa toshe wa take, a duk lokacin da yake kimtsawa Suraj wani tuggun, to wai shin mai ma Suraj ya taka ne yake jayayya da al'jani.. Ɓacewa Haidar yayi zuciyar sa cike da baƙin ciki, da alwashin yiwa Suraj lahanin da bazai taɓa moruwa ba...........✍️ _Wllhi comment ɗinku yana min kaɗan fa😣👩🏼‍🦯👩🏼‍🦯_ *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/23, 8:17 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ___________________________________________________ *51 &. 52* ___________Washe gari kuwa da safe a gurguje Suraj ya tashi, Saida ya kammala dukan abinda yake sannan ya wuce asibiti, dan duba jikin inna, Alhamdulillah jikin nata da ɗan sauƙi, saidai abinda ba'a rasa ba, ganin momyn sa tana gurin yasa bai cewa inna komai ba, dan yana matuƙar gudun ƴan gidan su suji matsalar dake tattare da ma'u, dan Kar a samu wata mishikilah, game da auren nasu, sallama Suraj yayi musu ya fita daga gurin...... Kai tsaye gida ya koma dan ya sanar da Daddy zai tafi batsari, koda ya isa samun Daddy yayi zaune yana hutawa, bayan ya sanar da shine Daddy yace "Ai tare zamu tafi! Tunda kaga ya week end ne, sai mu wuce kawai, bari na shirya koh,.." Ba yadda Suraj ya iya dole suka wuce tare da Daddyn sa.... Basu ɗau wani lokaci ba suka ƙara sa cikin garin, kasancewar kawu salisu yana gida shi ya tarbe su, bayan sun gabatar da gaishe gaishe ne, suka ɗora da jajantawa juna akan ɓatan Ma'u, Suraj kuwa yanzu da yasan komai, shiru yayi yana nazarin yadda zai sanar da kawu salisu, abinda ya faru dashi tsakanin sa da Haidar, ga kuma Daddy yana gurin, cigaba yake da saƙa da warwara, sallama akayi da kawu Salisusai ya fita yaga waye, fitar sa ke da wuya Suraj shima ya tashi yana cewa Daddy. "Bari na amsa waya! Naga kamar ɗakin ba network.." "Ok." Kawai Daddy yace Fita Suraj yayi! Nan suka ci karo da kawu Salisu yana ƙoƙarin dawowa, da sauri Suraj yace "Am...! Kawu ina da magana.." Amsawa to kawu yayi, Sannan suka raɓe gefe yana sauraren abinda Suraj ɗin yake gaya mai, sosai kawu Salisu ya firgita da jin abinda Suraj ɗin yace , cikin ɗimuwa kawu Salisu yace "Gaskiya Suraj wannan ba abu bane, wanda za'a ɓoye ma iyayen ka ba, idan wani abu ya same ka baza yafewa kaina ba, dan kaima Tamkar ɗa kake a wajena..." Kawu Salisu ya faɗa yana jan Suraj cikin gidan.. Ta ɓangaren Suraj kuwa tsoro yake kar iyayen sa, su tsorata da lamarin Haidar, su hana ya auri Ma'u, shi kuma abinda bazai iya ba kenan, dan ji yake kamar idan bai aureta ba mutuwa zai yi... Suna shiga ɗakin kawu salisu ya zayyanewa, Daddy dukan abinda ke faruwa harda wanda aka ɓoye mai, sannan ya ɗora da cewa abinda yasa ba'a faɗa maku ba, Suraj ne ya nemi alfarma akan abar wannan abun a matsayin sirri, kar a sanar daku... Kallon Suraj Daddy yayi sosai sannan yace "Anya Suraj kasan wace alaqa ke tsakani na da mutanen nan kuwa, da har kake ganin akwai wata lalura da zata sa in guje su, Nima Asma'u ƴata ce! Kuma duk inda magani yake, dani za'a nemo mata.." Sunkuyar da kai Suraj yayi yana cewa "Daddy kayi haƙuri insha Allahu bazan sake ba.." Gyaɗa kai kawai Daddy yayi yana maida kallonsa ga kawu Salisu yace. "Yanzu shi wanda ka karɓo mata magani kwanaki a ina yake..?" Kawu Salisu yace "Nan wani ƙauye ne ba nisa..!" Daddy yace "Ai kawai tashi zaka yi muje wurin malamin.." Kawu Salisu yace "Tun Yanzu kuma..?" "Ƙware kuwa! Kasan da zafi zafi ake kunna wuta.." Daddy ya faɗa yana miƙewa tsaye... Mota suka shige dukan su, Suraj shi da direba a gaba, sai kuma Daddy da kawu Salisu a baya, tafiya suke suna cigaba da tattaunawa akan wannan matsalar, da Haka har suka iso gidan mai maganin.... Bayan an musu isone suka shiga daga ciki, samun mai maganin suka yi kwance bayada lafiya, dan ko tashi baya iya yi, Saida wani yaronsa ya ɗago shi daƙyar, Yana ganin kawu Salisu ya saki murmushi yace "Bawan Allah kaine ka dawo! Gaskiya naji daɗin zuwanka, kullum addu'a ta kan Allah ya karɓi raina ka dawo, dan in sanar ma da wani abu.." Cike da ruɗewa kawu Salisu yake kallon mai maganin, yayin da ya kasa furta komai.. Daddy ne yayi ƙarfin halin cewa "Malam fatan dai lafiya! Kaike neman shi gaggawa haka..?" Cikin Muryar wanda yake jin tsananin ciwo malam ya cigaba da cewa "Lafiya ba lafiya ba! Wato kam bayan zuwan ka da kwana uku, misalin ƙarfe sha biyu na dare, sai ga wannan AL'JANIN da ya auri yarka ya zo min, a tunani na aikina ne ya fara cin nasara akan sa, shine yazo ya bani haƙuri bisa abinda ya aikata, ashe abin ba haka bane yazo dan ya min kashedi akan inbar yin aiki akan saina raba shi da ƴarka, idan ba haka ba kuma zai illatani..." Numfashi yaja sannan ya cigaba da cewa ''Nan muka fara jayayya dashi, har ina tilasta masa sai ya rabu da ita, bai cemin komai ba sai murmushi da ya saki, sannan ya fesamin wani abu a jikina, yana cewa wannan hukuncin da nama, nayi maka ne saboda maganin da ka bada ake bawa matata, yana barazanar zubar da cikina da ke jikinta, kuma wallahi idan cikin nan ya zube saina kashe ka..." Sai da ya kuma jan doguwar ajjiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa "To kunji abinda ya faru tsakani na dashi, kuma tun daga wannan Lokacin nake kwance bani da lafiya, shima bai ƙara dawowa gare ni ba...." Dukkanin su tsuru tsuru suka yi suna kallon malam ɗin, fuskar su shanye da mamaki, cikin sanyin murya kawu Salisu ya kwashe dukan abinda ya faru ya gayawa malam ɗin har da ɓatan Ma'u da kuma zuwa da Haidar yayi gurin Suraj ya mai barazana... Girgiza kai kawai malam yayi yana murmushi yace "Tabbas wannan anyi shaiɗanin al'jani, wato kam da yaga rashin nasara a tattare da shi sai ya ɗauke yarinya, amma insha Allahu sai anci nasara akan sa, yanzu taimakon da zanyi muku, zan haɗa ku da wani ɗan uwana cikakken mafaraucine yakan iya ganawa da ko wani irin al'jani, kuma duk hatsabibancin al'jani yana iyawa Dashi..." Kiran wani yaro yayi yana ce mai, "malam muddasir kuwa yana gida..?" Shiru yaron yayi can kuma sai yace "eh ɗazu kamar naga ya dawo daga farauta..." "Yauwa!! Yi sauri ka raka bayin Allah nan wajen sa, kace mai ni na turo su gurin sa.." Tashi suka yi suna mai godiya, Daddy kuwa rafar yan dubu dubu, guda biyu ya ajje mai yana cewa gashi kayi hidimar gida..." Godiya sosai malam ya mai haɗe da nuna mai jin daɗin sa, fatan Samun nasara ya musu, sannan suka mai sallama..... Basu daɗe suna tafiya ba, suka ƙaraso gidan malam muddasir ɗin, kasancewa babu wani nisa sosai tsakanin gidan sa da gidan wancan malamin... Yaron da ya rako sune ya shiga gidan, can kuma sai ya fito yana cewa "yace ku shigo.." Shiga sukayi bakin su ɗauke da sallama, wani dattijo ne da yake sanye Da Kayan farauta, ya amsa musu sallamar tasu, Izini ya musu da su shigo daga cikin ɗakin, bayan su zauna ne yake tambayar su mai ke tafe da su, dukkanin su mamakine kwance a fuskar su don basu yi tunanin shine mai maganin ba, dan Ko kaɗan baiyi kama da mai farauta, bare ace yana magana da aljanu ba, komai nasa a natse yake yinsa..... Kawu Salisu ne yamai bayanin dukan abinda yake tafe da su, cike da mamaki malam muddasir yace "A gaskiya tunda nake ban taɓa haɗuwa da matsala irin wannan ba, amma da yardar Allah bazata gagareni ba...." Kallon Suraj yayi yace "kaine wanda kake son yarinyar ko..?" "Eh ." Suraj yace Ɗauko wani abu yayi a cikin kwalba ya miƙawa Suraj yana cewa "karɓi wannan maganin ka shafa a jikin ka, insha Allahu babu abinda zai iya maka saidai ya ganka ya barka, yadda ka dogara da Allah, da kuma zikirorin da kake a kodayaushe, bazai taɓa tashi a Banza, insha Allah ita ma yarinyar yanzu za'a san yadda za'a kawo min ita nan...........✍️ _Wayyo mura nake😤🤧 sosai, jiya naso inyi muku post, saidai hakan bai yiwu ba, amma insha Allahu zaku jini zuwa yamma_ *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/23, 7:46 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* __________________________________________________ *53 &. 54* ______________Rufe idanuwan sa yayi yana karanta wasu ɗalasimai, da in yana son ganawa da aljanu yake karanta su, ya ɗau tsawon lokaci yana wannan abun, daga bisani kuma ya buɗe idon sa yana kallon su yace "A gaskiya samun nasara akan Haidar, abu ne mai wuya saidai mubi hanyar ta cin amana da kuma yaudara..." Kawu Salisu yace "Kamar ya kenan.?" Malam muddasir yace "Dole in Muna so a ɗauko Ma'u daga inda Haidar ya ɓoye ta, to sai mun nemi taimakon abokin sa i'liyas, dan ina da tabbacin shi kaɗai ne yasan inda Haidar yake..." Daddy yace "indai hakan ba zai yiwu kawai ina ga ayi..." Kirari malam muddasir ya fara yi, wanda zai isa ga iliyas da sauri kuma aduk inda yake zai san ana buƙatar taimakon sa... ★★★ I'liyas kuwa dake zaune a cikin tsanin farin Dutse, tun laifin da ya aikatawa Haidar, har yanzu ya kasa fita daga cikin gurin, dan yana da tabbacin Haidar bazai taɓa ƙyalesa ba, abisa cin amanar da ya mai, wannan dalilin yasa ya ƙi fita daga wajen dan gujewa cutarwar haidar a gare shi.... Ji yayi ana kiran sa da gaggawa, alamar ana buƙatar taimakon sa, tashi yayi daga inda yake, wajen wani tsohon aljani dake zaune yana karatun Alqur'ani mai girma yazo, durƙusawa yayi yana miƙa mai gaisuwa cike da girmamawa, amsawa al'janin yayi fuskarsa cike da kamala yace. "Yadai i'liyas!! Lafiya naga kamar kana cikin damuwa.." Cikin girmamawa i'liyas yace "Wallahi yallaɓe!! A wani wajen ne, na duniyar bil'adama ake da buƙatar taimako na, kuma gashi ba zan iya fita ba dan taimaka musu..." "To me yasa baza ka iya fita ba..?" Duƙar da kai iliyas yayi sannan yace "Allah ya gafarceka!. A gaskiya ba wai nazo nan bane dan ɗaukar darasi ko wani abun, illah nazo ne dan na gujewa Haidar daga laifin da na aikata masa, nan i'liyas ya kwashe dukan abinda ya faru ya faɗa wa wannan tsohon, girgiza kai kawai tsohon nan yake har I'liyas ya dasa aya a maganar sa, cikin fushi wannan tsohon aljanin yace "Lalle Haidar ya tafka babban kuskure, sa'ar sa ɗaya da bansan wannan lamari tun fari ba, kuma Wallahi sai ya fuskanci hukunci na, yanzu zan je a madadinka dan in taimaki waɗanda suke neman ka...... Ɓangaren malam muddasir kuwa, sai faman kiran iliyas yake amma shiru bai bayyana ba, dakatawa yayi da kiranyen da yake mai yana mamakin meyasa bai zo ba, zai ƙara yi kenan yaji wata guguwa tana doso inda suke, lokaci guda ɗakin ya rune da duhu ba'a ganin komai, cikin ƴan sakanni komai ya lafa, saiga wannan tsohon aljanin ya bayyana a dakin, tsorone ya kamasu gabaki ɗaya, dan hatta shi kanshi Malam muddasir saida ya tsorata da ganin wannan tsohon aljanin, cikin san kwantar musu da hankali yace "Sunana Shaikh ibn muzzafar! Kuma nine Sarkin malamain aljanu na musulmi, Nazo ne dan na taimaka muku, abisa neman taimako da kukayi a wajen I'liyas, saidai shi yana cikin wani uzuri ne da bazai iya zuwa ba, amma gani nazo a madadin sa.." cike da girmamawa malam muddasir ya farawa ibn muzzafar kirari, dakatar da shi yayi yana cewa "Bana buƙatar wannan abun, kawai ka faɗi wani kalar taimako kuke da buƙata a gareni, yanzu inyi muku shi.." Nan malam muddasir ya kora masa dukkan abinda yake wakana..... Cike da mamakin abinda suka faɗa mai, dan yayi daidai da abinda I'liyas ya sheda masa, da sauri yace "Insha Allahu yanzu zan kawo ƙarshen wannan lamarin.." Ya faɗa yana ƙesta Yatsun sa, kafin ƙiftawa da bissimillah, sai ga wasu samudawan aljanu su uku sun bayyana, hannun ɗaya ɗauke da wata kujerar zinare, ajje ta yayi kusa da ibn muzzafar dan ya zauna, zama yayi yana kallon wannan samudawan aljanu, cikin bada umarni ya kalli guda biyun yana ce musu "Kuje duk inda Haidar yake ku kawo min shi nan..." Cikin girmamawa suka ce "angama ya Shaikh..." Suna faɗin haka suka ɓace ɓat.. Kallon ɗayan yayi shima yace mai "Kaje gidan Haidar! dake ƙasan ruwa yarinyar da ka gani a cikin gidan ka ɗauko mini ita.." Duƙar da kai yayi yana cewa "an gama ya Shaikh.." Ya faɗi haka shima yana ɓacewa... Sudai su kawu Salisu zubawa sarautar Allah suka yi ido, dan wannan lamarin yafi ƙarfin su, hatta shi kanshi Malam muddasir shiru yayi yàna mamakin abun kamar a Film, ga shi dai cikin sauƙin shugaban malamain aljanu zai magance wannan matsalar koya zata kaya..............✍️ _zanso inga ko Haidar zai rabu da ma'u,🤔🤔_ *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/24, 10:19 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* __________________________________________________ *55 & 56* ______________Ma'u kuwa dake zaune tunani ne fal a ranta, musamman yanzu yadda Haidar ya killace ta a guri ɗaya, babu motsin wanda take ji bare taji sanyi a ranta, kullum sai ya mata alƙawarin maidata gida amma sai ya saɓa mata alƙawarin da ya mata, a fili ta furta "Haidar yaushe ne zaka maidani cikin ƴan uwana.." Ta ƙare maganar tana sakin kuka gwanin ban tausayi.... Tana cikin wannan tunanin ne taji anyi sama da ita cikin iska, kasa tantance a wani yanayi take, cikin firgici take Ambaton sunan Allah dan neman tsarinsa, daga dukan wani abun halitta, cikin ƙanƙanin lokaci taji an ajje ta akan doron kasa, ƙara tsorata tayi sosai hakan yasa ta rumtse idanuwan ta..... Su kuwa su kawu Salisu ganin an ajje Ma'u, hakan ba ƙaramin basu mamaki yayi ba, cikin zumuɗi da murna kawu Salisu yace "Ma'u kece...!?" Da sauri Ma'u ta buɗe idonta tana binsu da kallo, ganin kawu Salisu da kuma Daddy har ma da Suraj, sai kuma wasu da bata san ko su waye ba, cikin jin daɗin Ma'u ta ƙarasa kusa da kawu Salisu, hannunsa ta riƙo tana ƙara fashewa da kuka, cikin gunjin kuka Ma'u tace "Wallahi kawu haidar azzalumi ne shi ya hanani in kula kowa, kuma ya hana kowa ya raɓe ni....." Lallashinta kawu Salisu ya fara yi, amma kamar ba da ita yake yiba.. Kallon Suraj Ma'u tayi, cike da fitar hayyaci ta faɗa jikinsa, tana cewa "Yace kaima sai ya kashe ka! Kuma wallahi idan ya kashe ka Nima mutuwa zanyi, dan wallahi ina sonka..." Allah sarki Suraj! Da yaga kamar bata cikin hayacinta, sai ya rungumo ta jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta, a hankali ta fara yin shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa akai akai....... Haidar ne tare da waɗanda Shaikh ibn muzzafar ya aika su kawo shi suka bayyana a gurin, idon haidar bai sauka akan kowa ba, sai kan Ma'u da take rungume jikin suraj, cikin fushi da tsananin kishi haidar ya tunkare su, hannu yasa da niyar ya funciki Ma'u daga jikin suraj, bai kai ga ƙara sa hannun nasa ba yaji andaka masa tsawa da sauri ya juya, ganin ibn muzzafar ne yasa ya duƙar da kansa alamar girmamawa, amma duk da haka zuciyar sa da tunanin sa, yana gurin Ma'u dake jikin suraj, magana ibn muzzafar yake mai amma ko kaɗan baya jin sa, asali ma idonsa ya rufe ba abinda yake gani sai ma'un sa dake jikin wanin sa wanda bashi ba....... Yadda yake jin zuciyar sa tana suya, yasa ya kasa haƙuri, Ɗayan hannun Ma'u ya kama ya fisgota, Suraj kuwa da yake ankare da shi, sai shima ya riƙe hannun nata ɗaya, idan Haidar ya jata, sai shima ya jata, aka rasa waye zai haƙura ya sake ta, Ma'u kuwa kuka kawai take tana so ta ƙwace daga riƙon da Haidar ya mata amma yaƙi sakinta..... Ibn muzzafar kuwa dake zaune yana kallon yadda Haidar yake ja inja da bil'adama, sai abin ya matuƙar bashi mamaki, lalle Haidar ya daɗe da makancewa a soyayyar bil'adama, wata tsawa ya sake daka mai a karo na biyu, da sauri Haidar ya sha jinin jikin sa amma bai saki hannun Ma'u ba, cike da isa ibn muzzafar yace "Haidar!!!! Ina mai umartarka da ka sakin mata hannun ta..." Sakin hannun Ma'u haidar yayi yana aikawa da Suraj wani irin mugun kallo, mayar masa da martani Suraj yayi a ransa yana ayyana "ai ba tsoron ka nake ji ba.." *Kai Suraj kodan kaga da ibn muzzafar ne a kusa🤔dan shi kanshi haidar ba kanwar lasa bane😹* Gyaran murya ibn muzzafar yayi Yana kallon haidar daga bisani kuma yace "Nasan izuwa yanzu ka fahimci cewa, nasan komai kuma nazo ne dan na kawo ƙarshe al'amarin.. Haidar yaushe ka zama mai zalunci.? Yaushe ka zama mai tauye haƙƙin rai.? Shin ko ka manta cewa hakan da ka aikata ya saɓawa al'adar mu da addinin mu, kuma sai ka fuskanci hukunci na dai dai da abinda ka aikata, saboda haka ina mai umartarka a karo na biyu, da ka rabu da wannan bil'adamar tayi rayuwar ta cikin salama, kazo cikin jinsin ka nama alƙawarin duk wacce kace kana so, ko ƴar waye acikin duniyar aljanu zan nema maka auren ta..." Durƙusawa haidar yayi cike da rauni yace "Allah ya gafarceka! Na yarda da duk hukuncin da zaka min, amma dan Allah kar kace sai na rabu da ita, wallahi ina sonta fiye da rayuwa ta, bazan taɓa barinta ba koda da daƙiƙa ɗaya ne..." Ibn muzzafar yace "Ba wai na tambaye ka abinda ke cikin zuciyar ka bane, umarni ne na baka ba shawara ba, ina so ka furta da bakin ka cewa ka rabu da ita.." Cikin dagiya da taurin kai Haidar yace "Allah ya gafarceka! Ban fara sonta ba dan in rabu da ita, na fara son tane dan in dauwama da sonta na har abada...." Fusata ibn muzzafar yayi da yadda Haidar ya ke mai jayayya, cikin tsawa yace "A karo na ƙarshe haidar Ina umartarka da ka rabu da ita..." Miƙewa tsaye Haidar yayi ido cikin ido yake kallon ibn muzzafar yace "Gaskiya bazan rabu da ita ba, kawai ka cire kanka a wannan al'amarin, dan zan iya fito na fito da koma waye, kuma zan iya faɗa da koma waye a kanta..." Nuna Suraj yayi da ɗan yatsarsa yace "Kayi gaggawar sakin hannun matata, idan ba haka ba zan illataka anan gurin.." Ibn muzzafar ne ya nuna haidar da wata sanda dake hannun sa, take anas sarƙa ta bayyana jikin Haidar duk ta ɗaɗɗaure shi, fisge fisge Haidar ya fara nasan ya ga ya fidda sarƙar daga jikin sa, amma ya kasa, ɗagowa yayi yana kallon ibn muzzafar kallo irin na tuhuma, takowa ibn muzzafar yayi har ya ƙara so kusa da Haidar, sannan yace "Ina ga kamanta cewa duk wani hatsabibanci da shu'umanci da kake taƙama da shi, a gurina ka ɗauki darrusa.. Saboda da haka dole ka rabu da ita ko ka ƙi ko ka so.." "Ya Shaikh!! Karka aikata haka, ina sonta itama tana sona, kar ka shiga tsakanin masoya biyu.." Shanye da mamaki ibn muzzafar ya kalli Ma'u yace "Yarinya wai haka ne..?" Girgiza kai Ma'u tayi alamar a'a, ibn muzzafar yace "magana zakiyi yarinya.." A hankali Ma'u tace "A'a ni ba muyi haka da shi ba...." Ibn muzzafar yace "To kaji dai.." Cike da rauni Haidar yake kallon Ma'u yana girgiza kanshi yace "Haba Nurul aini! Karki aikata haka, zaki yi babban kuskure...." Cikin kuka Ma'u take girgiza wa Haidar kai tace "Kayi haƙuri Haidar! Hakan da nayi shine dai dai, ka barni haka dan Allah inyi rayuwata kamar yadda kowa yake yi.." Ƙiyasta yatsu ibn muzzafar yayi, take anas waɗannan samudawan aljanu suka matso suna jiran umarni, kallon Haidar yayi sannan yace "Har yanzu kana nan akan bakan ka? Ko kuwa ka yanke shawarar rabuwa da ita.." Cikin kafiya Haidar yace "ina nan kan bakana.." "Anya kuwa kasan wani kalar hukunci zan yi maka...?" Cikin rashin tsoro Haidar yace "nasani kuma na Amince.." Kallon waɗannan samudawan aljanu ibn muzzafar yayi sannan yace "Ku kai Haidar cikin kogon dutse mai feshin wuta, a tsare shi a ciki na tsawon wata huɗu baci ba sha, kuma muduk bai furta zai rabu da wannan bil'adamar ba, har wata huɗun nan ya cika to za'a sashi acikin ruwan narkakkiyar dalma, har tsawon shekaru biyu..." Haidar kuwa ko ajikin sa, asali ma sai murmushi yayi mai ciwo yana bin Ma'u da kallo, ta sowa Ma'u tayi da gudu tana dafa ƙafar Haidar cikin roƙonsa tace "Dan Allah haidar ka amince, banso a ta dalilina ka shiga cikin wata wahala.." Murmushi ya ƙara saki mai ciwo yace "A kanki zan iya jure ko wacce azaba da wahala, kuma duk mun daren daɗewa sai na dawo gare ki..." Yana gama faɗa ya ɓacewa ganinta tare da samudawan aljanun nan................✍️ *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [6/27, 5:06 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* __________________________________________________ *57 & 58* ________________Durƙushewa Ma'u tayi a ƙasa tana sakin wani kuka mai sautin gaske, Ba haka taso ba, taso ace Haidar ya amince da umarnin da aka bashi, saidai shi ɗin rayuwar sa ba kamar ta kowa take ba, ko a cikin jinsin al'janu haidar daban yake, duk da cewa ya zalunce ta amma har yanzu akwai ɓarɓashin sonshi a zuciyarta, baza taso ace a ta dalilinta wani abu mummuna ya same shi ba...... Tana cikin wannan yanayin taji andafata ta baya, ɗagowa tayi a hankali yayin da idanun ta ke zubar ruwa, Suraj ta gani durƙushe a kusa da ita yana girgiza mata kansa, share hawayen ta tayi tana sakin ajiyar zuciya..... Ibn muzzafar kuwa da ya ƙurawa Ma'u ido yana nazartar ta, gyaran murya yayi sannan ya kalli Ma'u yana cewa "Yarinya kije kuyi auren ku cikin kwanciyar hankali, insha Allahu ina mai tabbatar muku Haidar bazan taɓa sakin shi ba, har sai ya janye a ƙudirinsa, saboda haka keda iyayenki ku kwantar da hankalin ku, daga yanzu baku da wata matsala, *NI NABARKU LAFIYA* " Ya faɗa yana ɓacewa ganin su..... Cikin farin ciki da tsananin murna malam muddasir yace, "kunga ikon Allah koh! Cikin ƙanƙanin lokaci gashi komai zai zama tarihi.." Kawu Salisu da Daddy suma cikin murna Da farin ciki, suke godewa Allah abisa kawo musu ƙarshen Wannan al'amari da yayi, can kuma sai kawu Salisu yace "to amma wani hanzari ba gudu ba, shine batun cikin da ma'u take da shi na wannan *AL'JANIN SOYAYYAR*..." Murmushi malam muddasir yayi sannan yace "Ai cikin al'jani ne! Kaga Bana mutum Ba, saboda haka wannan ba wata matsala bace, da zarar anyi mata aure mijinta ya yi mu'amalar Aure da ita, to insha Allahu cikin nan zai zama tarihi..." Nan suka cigaba da tattaunawa akan Maganar, daga ƙarshe Malam muddasir ya basu wasu magunguna da za'a bawa, Ma'u ta riƙa sha...... Shi kuwa Suraj yana ganin an kammala komai, ya janye Ma'u suka yi waje cikin mota..... Sosai yake nazarin ta ganin kamar tana cikin damuwa, yasa ya riƙo hannuwanta yana cewa "Husnah meye yake faruwa ne naga kamar kina cikin damuwa.." Ɗago da kanta Ma'u tayi idonta cike da hawaye, girgiza kai kawai tayi alamun babu komai... "Ah ah! Sai kin faɗa min, gashi nan yanayin ki kaɗai! ya isa yasa a gane cewa kina cikin damuwa...." Hawayen da take ƙoƙarin maida wane suka zubo, hannu tasa ta share sannan tace "Wallahi yaya Suraj! sai nake ganin kamar hukuncin da aka yiwa Haidar yayi tsauri.." Sakin baki Suraj yayi yana kallon ta cike da mamaki, rasa abin faɗa yayi! Can kuma sai yace "Yanzu ke kina ganin hukuncin da aka yi mai yayi Tsauri, karfa ki manta Haidar shi ya kashe miki yusif ɗinki, kuma ma ko ba haka ba ai shi Haidar al'jani ne, duk wata azaba da za'a yi mai to mai sauƙi ce a gurinsu su al'janu, ba kamar mu bil'adama ba..." Ajiyar zuciya Ma'u tayi tana cewa "haka ne kuma." Suna cikin hakan ne su Daddy suka fito tare da malam muddasir, sosai Daddy yayi wa malam muddasir alheri mai yawan gaske, a cewar sa ai duk a ta dalilin sa ne komai yazo ƙarshe... Sallama suka yiwa juna cike da mutuntawa, kai tsaye cikin garin Katsina suka nufa, kasancewar inna da take kwance a asibitin cikin garin.... Murna gurin inna kuwa! faɗa ma ɓata baki ne, yaji daɗin labarin da su kawu Salisu suka zo mata da shi, aikuwa ba shiri inna ta miƙe, Dama ciwon nata na ɓatan Ma'u ne, yanzu kuwa tunda taga Ma'u cikin kwanciyar hankali ta samu lafiya.... Bayan likita ya bata sallama suka ɗunguma sai gidan Daddy, anan suka yi kwana biyu, tukunan aka sa ranar bikin Ma'u da Suraj Sati biyu, momy kuwa tuburewa tayi sai an bar mata Ma'u, ba haka inna taso ba, taso ace ta tafi da ma'u kodan ta gyara ƴarta tsab, haka su inna suka wuce batsari Suka bar Ma'u a wajen momy........ Zaman Ma'u a gidan yasa wata shaƙuwa da soyayya a tsakanin su ita da Suraj, sosai suke nunawa junan su kulawa da tsantsar soyayya, batun Haidar kuwa ya zama tarihi a zuciyar Ma'u, musamman yanzu da ta samu Suraj, kasancewar shima baƙaramin ɗan soyayya bane..... Mai gyaran jiki ta musamman momy tasa aka kawo mata tun daga nijar, sosai Ma'u take shan gyara ciki da waje, sam ba kama hannun yaro, abinka ga farar fata tuni gyara ya ɗau jiki, sai ta zama kamar wata sarauniya...... ★★★ Ma'u ce zaune a falo baƙi tare da Suraj, suna hirar su ta masoya gwanin birgewa, tsura mata ido Suraj yayi ko ƙiftawa baya yi, haɗa ido sukayi da ma'u, sai ta Sunkuyar da kanta cike da jin kunya, ita wallahi in yana mata irin wannan kallon, sai ta ganshi kamar wani mayen dake shirin cinye ta, ɗagowa tayi tana mai hararar wasa sannan tace "Wannan kallon fa.." Murmushi ya sakan mata cike da shauƙin ƙaunar ta yace "Kawai naga ƙin ƙara kyau ne, kin kalli kanki kuwa a madubi (mirror), wallahi ki zama wata tauraruwa acikin taurari, faɗa min meye sirrin....?" Ya ƙare maganar yana matso da kansa, shiru Ma'u tayi tana wasa da ƴan yatsun hannunta, cigaba Suraj yayi da cewa "Kodai duk a cikin gyaran jikin ne...." Gira kawai Ma'u ta ɗaga mai alamar eh, "Gaskiya ne! Amma momy tamin ƙoƙari Allah ya biyata, nasan duk dan farin ciki na ake wannan gyaran, Nima zansa akawo min mai gyaran jiki na musamman na maza, yazo ya gyara ni tunda ba wanda ya kula dani....." Maganar sa ta ƙarshe ta matukar ba Ma'u dariya, hakan yasa ta dara abinta. Shagala Suraj yayi da kallon ta, ganin yadda take dariya cikin natsuwa, sai hakan ya matuƙar birge shi, gimtse dariyar Ma'u tayi tana cewa "Gaskiya yaya Suraj kana da abin dariya, a ina ka taɓa jin ana yiwa namiji gyaran jiki..?" Murmushi Suraj ya saki mai tsada sannan yace "To za'a fara a kaina! amma kin san wani abu.?" Ma'u tace "a'a sai ka faɗa.." "To nidai gaskiya bansan yaya Suraj ɗin nan ya kamata a canza min suna, idan ba haka ba zanyi hukunci.." Da sauri Ma'u ta kama kunnen ta tana cewa "Afuwan ya *ZAUJIY*." murmushi Suraj yaƙara saki sannan yace "maimaita naji.." A hankali Ma'u ta ƙara cewa "Afuwan ya*zaujiy*." "Wow!! Gaskiya sunan yamin daɗi ya *ƙalbiy* Haka sukayi ta hirar su gwanin sha'awa, kamar bazasu rabu ba............ *AFUWAN KUN JINI SHIRU KWANA BIYU KO, WLLHI HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON BANI DA LAFIYA AMMA YANZU DA SAUƘI, KUMA NA GODE MUKU SOSAI DA IRIN ADDU'O'INKU A GARENI, DA MASU KIRA NA DA MASU TURO MIN DA SAKO DUKA INA GODIYA.* *ALLAH UBANGIJI YABA MARARSA LAFIYA NA GIDA DA NA ASIBITI LAFIYA DA ABINDA LAFIYAR ZATA AMFANA DASHI...* *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* *Kar fa amanta da share dan Allah a riƙa yimin share zuwa wasu group din* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [7/1, 8:33 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ____________________________________________________ *59 &. 60* ____________Shirye-shiryen biki na ta kankama, inda ayau ta kama ranar kamu, yayin da ake komai cikin wadata, babban hall suka kama wanda za'a gabatar da kamun amarya....... Ma'u amarya tayi matuƙar kyau wanda bazai misaltuba, sanye take cikin wani ash colour ɗin materials da yake da ɗan ratsin baƙi-baƙi, Yayin da aka ɗaura mata baƙin gwaggwaro, sai abin yafawa ma shima baƙi, kasancewar ta fara tas, sai kayan suka matuƙar amsar yanayin jikinta... Ta ɓangaren ango ma, shima ya haɗu matuƙar haɗuwa saide muce masha Allah, a haka aka gudanar da kamun nan cikin kwanciyar hankali da birgewa, har aka tashi kowa ya koma gida.... Washe gari kuwa akayi walima kasancewar Ma'u tace ita ba sai anyi wata bidi'a ba a bikin ta kawai ayi walima ma ta wadatar, Suraj kuwa yaji daɗin hakan da Ma'u tace, kasancewar sa shima baya da wannan ra'ayin, ranar Lahadi kuwa dubbanni mutane suka sheda auren SURAJ IBRAHIM SENATOR DA ASMA'U BASHIR BATSARI, akan sadaki dubu ɗari biyu, Alhamdulillah biki yayi biki, saide muce Allah ya bada zaman lafiya..... Farin cikin da inna take ciki kuwa, faɗa ma ɓata baki ne, dan wuni tayi tana sallar godiya ga Allah, da ya nuna mata wannan rana mai albarka, duk wani masoyin Ma'u ya taya ta farin ciki da wannan ranar, ita kanta Ma'u da aka ce mata an ɗaura auren, ɗaki ta shige ta kulle kanta tana kukan murna, a fili take furta "ashe haka ake ji idan aka ɗaurawa mutum aure?, da raban nima ashe zanyi aure.." Ta ƙare maganar tana ƙara sakin kuka, ganin hakan bazai fishshe taba, yasa ta tashi ta shiga bathroom, al'wala ta ɗoro ta gabatar da sallar nafila raka'a biyu, ta daɗe a zaune tana addu'o'i na neman tsari da kuma sharrin shaiɗan, sannan ta ƙare addu'ar da yi musu fatan zaman lafiya na har abada, ita da Suraj ɗin ta...... Bayan ta idar ne taji wayarta tana ringing, da sauri ta ɗaya kiran ganin momy ce, murya a dashe tayi sallama sakamakon kukan da tasha, cike da kulawa momy tace "Asma'u ina kika shige ne! Ina ta faman neman ki..?" "Ina cikin ɗaki.." "Ok! Ina zuwa jira ni anan.." Ba'a ɗau lokaci ba Momy ta turo ƙofar ɗakin, hannunta riƙe da kofi, zaunawa tayi tana dafa kafaɗar Ma'u cikin kulawa tace "lafiya naga kamar kinyi kuka." A hankali Ma'u tace "Ah ah ba kuka nayi ba! Kawai kaina ne yake min ciwo.." "Ayyah! Allah ya sawaƙe, karɓi wannan ki shanye, kafin na kawo Miki maganin ciwon kan.." Momy ta faɗa tana miƙa mata ruwan markaɗeɗɗan zogale da madara, karba Ma'u tayi tana sha haɗe da ya mutsa fuskarta, fita Momy tayi daga ɗakin tana cewa "ki kwanta ki ɗan huta ko! Nasan hayaniyar biki ce ta gajiyar dake.." Bayan kwana biyu da gama sha'anin biki, Daddy yasa akai Ma'u batsari wajen su inna, kasancewar nan da sati ɗaya zasu wuce America, tunda a can Suraj yake da zama, shiyasa aka bari in sunje can sa tare... Ɓangaren Suraj kuwa ba haka ba yaso, ya so ace an bashi matar sa ya nuna mata kulawa, in yaso kafin su tafi ya kaita batsarin tayi bankwana da ƴan uwanta, amma ba yadda ya iya dole ya bi Abinda Daddy yace.... Inna kuwa ba ƙaramin daɗi taji ba, hakan yasa Ma'u tana zuwa ta shirye gyare-gyaren su na gargajiya dan yiwa Ma'u, badan ta raina ƙoƙarin momy ba, kawai tana son ƙanƙarowa ƴarta daraja da martaba a gidan mijine.. Cikin sati ɗayan nan kuwa inna ba ƙaramin dagewa tayi ba, wajen gyaran Ma'u dan hatta ruwan wanka na musamman inna take dafawa Ma'u da lallen hausa.. Ranar da ma'u zata wuce kuwa, kuzo kuga kukan rabuwa da inna da ƙyar aka ƙanƙareta daga jikin inna, ƴan uwa da abokan arziƙi kowa yana kukan rabuwa da ma'u, haka aka wuce da ita sai gidan Daddy...... Bayan magribah kuwa! Dukkanin su suna zaune a falo, Daddy da kawu Salisu sai momy da goggo (matar kawu Salisu) sai Suraj da Ma'u dake durƙushe a ƙasa, bayan kawu Salisu ya buɗe gurin da addu'a, sannan ya ɗora da yi musu nasiha mai ratsa jiki, sosai dukkanin su jikinsu yayi sanyi, bayan ya ƙare ne Daddy ya ɗora da cewa "To Suraj gadai Asma'u nan! Mun baka ita amana, idan ka tafi da ita to kasani cewa, bata da kowa sai kai, kaine komain ta, dan Allah ina roƙonka da ka zama mijin marainiya a gare ta, kaji tausayin ta in tana cikin damuwa, kazama kaine gatan ta a ko wani yanayi..." "Insha Allahu Daddy! Bazan baka kunya ba.." Suraj ya faɗa cike da ladabi. Daddy yace "ƙarfe nawa jirgin naku zai tashi.." "Na ƙarfe 8.00 pm ne." Suraj ya faɗa yana duba agogon hannunsa.. Daddy yace "ai lokacin ma ya kusa, bari mu tashi mu shirya koh.." Nan suka ɗunguma gaba ki ɗaya suka wuce airport, Ma'u kuwa hannun ta na cikin na momy, har Saida aka zo shiga cikin jirgin, sannan momy ta kamo hannu Suraj ta haɗa da na ma'u tana cewa "to son ga ma'u Nan na baka ita, kar inji kar ingani, ina so ta kasance cikin farin ciki a koda yaushe.." Rungume Ma'u tayi tana ce mata "Asma'u kema ki kasance mai ambaton Allah a ko wani hali, kar ki bar karatun Alqur'ani da nafilfili, sannan kiyi wa mijinki ladabi da biyaya, duk abinda yake so kiyi masa bakin gwargwado, inde bai wuce ƙa'idar addinin Musulunci ba, kuje Allah yayi muku albarka, insha Allahu zamu ziyarce ku nan da wata uku, har da innarki zamu taho ki daina kuka kinji.." Kama hannun ta Suraj yayi suka fara hawa matattakalar jirgin, kasancewar an bada sanarwar shiga cikin jirgin, su Daddy basu tafi ba har Saida jirgin su Suraj ya ɗaga... Suraj kuwa ganin irin Yadda Ma'u take zaune a cikin jirgin, duk tabi tayi tsuru tsuru alamun rashin sabo, rungumota Suraj yayi jikinsa, yana ɗan shafa bayan ta alamun rarrashi, numfashi take saukewa haɗe da nan nauyar ajiyar zuciya, bata daɗe ba bacci yayi awon gaba da ita......... _ANA TA SHAGALIN BIKI KO INA HAIDAR 🤔_ *MORE COMMENT* *MORE TYPING* *PLS SHARE* ~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~ [7/2, 7:11 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄 *NAMIJIN DARE* _aljanin soyayya_✍️ ```story and writing``` *by* *_ummy mrs khamis_* 09137879957 ________________________________________________________________________________ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *short story* *TSOKACI* : ```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️``` ```bissimillahir rahamanur rahim``` *_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_* ______________________________________ SADAUKARWA!! ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃 *bissimillahir rahmanir rahim* ___________________________________________________ *THE END* 💃💃💃💃💃💃 ________Misalin ƙarfe sha biyu na rana jirgin su, ya sauka a ƙasar America, mayan motoci na alfarma suka zo tarfansu dan ɗaukar Suraj, yadda turawan suke bawa Suraj girma, hakan kaɗai ya isa a gane cewa ba ƙaramin mahimmanci yake dashi ba a gurin su, saukowa yake daga matattakalar jirgin, hannun sa riƙe da na Ma'u, ita kuwa Ma'u ganin yadda turawan suka tsura musu ido, suna kallon su, duk sai tabi ta tsargu, dan saura kiris tayi tuntuɓe ta faɗi, rungumeta Suraj yayi a jikin sa, a haka suka ƙara so jikin motar da zasu shiga, buɗe mata motar yayi da kansa ta shiga, sannan shima ya shiga cikin motar, ita kuwa Ma'u sunkuyar da kanta tayi tana wasa da ƴan yatsun hannunta, a hankali Suraj yace "Madam!! What happened..?" Yayi maganar cikin raɗa, rufe fuskarta Ma'u tayi da tafukan hannayen ta, sannan tace "Ba komai fa.." Murmushi yayi mai ƙayatarwa, haɗe da matso da fuskarsa zuwa gare ta, cikin wani salo yake goga karan hancinsa akan nata, murya a sanyaye Suraj yace "Wannan kunyar taki! Ita kaɗai ce zata hanani rawar gaban hantsi, pls dan Allah a rage ta.." Ma'u kuwa da take jin kamar ƙasa ta tsage, kodan ta shige ta ɓoye wa rashin kunyar Suraj, tun jiya ta lura da take-taken sa a cikin jirgi, sai wani abu yake gwanin ban kunya🙈, gashi a fuska kamar bazai aikata ba, ƙwace fuskarta Ma'u tayi tana mai da numfashi, ganin yana ƙoƙarin kissen ɗinta, hararar wasa ta mai tana nuna mai direba da yake tuƙinsa kamar ma baisan da zaman su ba, noƙe kafaɗa Suraj yayi alamun naƙi wayon, kallon ta yake kamar wani tsohon maye, ita kanta Ma'u idan taga Suraj yana mata irin wannan kallon, gabanta har faɗuwa yake, amma inda take jin daɗin abun ya iya takunsa sosai, a haka har direba ya ƙaraso gidan suraj wanda zan iya wa lakabi da aljannar duniya, haƙiƙa gidan ya haɗu iya haɗawa, saide muce Masha Allah... Fitowa Suraj yayi haɗe da zagayawa ya buɗewa Ma'u ƙofa, tana fitowa ya cicciɓeta yayi sama da ita yana cewa "Amarya tazo gidanta.." Be direta ba a ko ina sai da yazo bakin ƙofa ya ajje ta, yana cewa "To bissimillah!! Ki shiga gidan ki da ƙafarki ta dama, sannan kiyi addu'a da bakinki mai albarka.." Shiga Ma'u tayi da ƙafar daman tana karanta wannan addu'ar a zuciyar ta...👇 رب انزلن منزلً مبارك وانت خيرٌ منزلي. sau bakwai 7 Bin bayan ta suraj yayi hade da kamo hannun ta, wani bedroom ya shiga da ita, da dukan alamun dai nasa ne, zaunar da ita yayi a kan gadon sannan ya kalleta cike da kulawa yace "Me kika fi buƙata a halin yanzu! Wanka ko abinci, ko hutawa." "Uhmm! Gaskiya nafi bukatar wanka da hutawa.." "Ok! Yayi kyau.." Ya faɗa yana tashi, rage kayan jikinsa ya fara yi, iya boxe kawai ya bari sannan ya kamo hannun ma'u yana ƙoƙarin cire mata kayan jikinta, noƙewa ma'u tayi alamar bata so, ƙyele ta suraj yayi ta cire da kanta sannan ya janyo ta yana cewa "taho to muje muyi wankan ko.." Cikin shagwaɓa ma'u tace "ah ah kaje kayi! In ka fito sai na shiga nayi nima.." Kallon ta yayi da kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, a sanyaye ya shige cikin bathroom ɗin, ganin kamar baiji daɗin haka ba yasa ta bishi cikin bathroom ɗin tana sanɗa kamar ɓarauniya..... Saida suka gabatar da sallolin su tukunnan suka kwanta, basu tashi ba sai wajen gab da magribah, a gurguje suka yi wanka suka shirya, wata baturiya ce ta shigo dan yiwa ma'u make up, kasancewar abokanansa na nan sun haɗa musu wani shagali, sosai ma'u tayi kyau cikin farar doguwar riga ta amaren turawa, itama sai ta fito sak a baturiyar ta, haka ma ɓangaren suraj shima sak ya fito a matsayin Bature ango, shagalin su suka sha cikin kwanciyar hankali da birgewa, ba'a tashi ba har sai waje sha ɗaya na dare, sannan amarya da ango suka sami nutsuwa, wanka ma'u tayi haɗe da ɗoro al'wala dan yin sallar isha'i, shima suraj wankan yayi haɗe da ɗoro al'walar, bayan sun idar da sallar ne, suraj yayi wa ma'u umarnin da ta tashi suyi sallar nafila, bayan sun idar ne, ya gabatar da addu'ar samun zaman lafiya da zuri'a ɗayibba. Daga ƙarshe ya dafa kan ma'u haɗe da karanto addu'ar da annabin mu ya koyar da duk wani sabon ango.... Fita suraj yayi daga ɗakin, jim kadan kuma ya shigo hannun sa riƙe da ƙaramin filet, ajjewa yayi sannan ya buɗe ƙaramin frij ɗin dake ɗakin, yoghrt da lemun sha,ya ɗauka haɗe da kofina, fidding ɗin ma'u yake cike da soyayya, har saida ya tabbatar da ta ƙoshi sannan ya ƙyaleta haka, tashi ma'u tayi taje tayi brush, sannan tazo ta hau kan bed ta kudundune.. Suraj kuwa bai tashi ba har saida ya cika cikin sa nak, sannan yaje yayi brush, bayan ya fito bai hau gadon ba saida ya feshe jikin sa da turaruka masu kamshi, sannan ya hau kan bed ɗin, rungumota yayi jikin sa, setin kunnen ta ya mata magana cikin raɗa, yace "Zo muyi wasan amarya da ango.." *NI KUWA GANIN YA FARA TAKURA MATA YASA NA HITA WAJE IN JIRASU ACAN*👩🏻‍🦯👩🏻‍🦯 Suraj bai bar ma'u ba, sai wajen ƙarfe huɗu na asuba, wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, shi kuwa suraj rungume ta yayi tsam kamar za'a ƙwace masa ita, wani tsarkakaken sonta da ƙaunarta yake ji suna ratsa duk wasu gaɓoɓin jikin sa, ada ji yake yana sonta da tausayinta, amma a yanzu jinsa yake ita ce mahaɗin rayuwar sa, idan babu ita bazai taɓa iya gudanar da rayuwar sa ba.... Yana cikin wannan tunanin shima wani daddaɗan bacci yayi awon gaba da shi.. Misalin ƙarfe bakwai na safe suraj ya buɗe idonsa, ganin yadda lokaci ya ƙare yasa ya tashi da hanzari ya shige bathroom, wanka yayi haɗe da ɗoro al'wala, sallar asuba yayi sannan ya dawo kan bed ɗin, shafa fuskar ma'u yake a hankali yana cewa *"MY LIFE*." Buɗe idonta tayi a hankali, suna haɗa ido da suraj taja bargo da sauri tana rufe fuskanta, murmushi suraj yayi yana cewa "ai aikin gama ya riga da ya gama yarinya.." Ya faɗa yana sunkutar ta, haɗa ruwan ɗumi yayi ya sata aciki, wankan tsarki ya sata tayi sannan ta ɗora alwala suka fito daga cikin bathroom ɗin.... Ma'u tana idar da salla tazo gaban suraj ta tsuguna, tace "Mijina ka tashi lafiya..?" Cike da jin daɗi suraj yace "Lafiya kalau matata! Fatan kema haka..?" Gyaɗa kai Ma'u tayi cike da jin kunya.. Janyo ta suraj yayi jikin sa yana shinshinar kamshin jikinta, cikin wata kalar murya yace "Husnah ina so ki faɗa min! Duk duniyar nan me kike so Inyi miki, wallahi koda zan ƙarar da duk wani abu da na mallaka ne, ni kuma sai na miki shi.." Murmushi ma'u tayi tana kallon sa, cike da tsantsan so tace "Kai nake buƙata! Ina so inyi rayuwata tare da kai har mutuwa ta.." "Kin same ni kuwa! Soyayyar ki da ita aka halicce ni, babu abinda zaisa inji na gajiya da zama dake bare har na rabu dake.." Rungume juna suka yi cike da tsantsan soyayya, kowa yana faɗawa ɗan uwansa yadda yake sonsa... Wajen aikin su suraj kuwa hutun sati biyu suka ƙara mai, sannan ya koma bakin aikinsa, sosai shaƙuwa da soyayya ta ƙara ninkuwa a tsakanin su, tsantsan kulawa suke nuna wa juna, kowa bai son ɓacin ran ɗan uwansa, soyayyar su suke sha mai cike da tsabta... Bayan wata huɗu su daddy suka zo har da inna da auta zahrah, harma da kawu Salisu, murna gurin ma'u kuwa ba'a cewa komai, satin su ɗaya suraj ya biya musu umarah, suka wuce Saudi Arabia, suje su sauke farali.. Ita kuwa ma'u da take laulayi yanzu, yace idan ta haihu saje aikin hajji, ana cewa ko harshe da haƙori ana samun saɓani, to su wannan ma'auratan ba haka ba yake a gurin su, dan zallar soyayyar su suke sha mai tsabta..... ★★★ Haidar kuwa tunda ibn muzaffar yasa aka tafi dashi, ake gana mai azaba, amma bakinsa sunan ma'u kawai yake kira, ganin haka da ibn muzaffar yayi yasa aka linka azabtarwar da ake mai, amma duk a banza dan kullum cikin begen masoyiyar sa ma'u yake, babu wanda yake tausaya mai sai Iliyas, ba irin roƙon da Iliyas bai mai ba, akan ya furta ya rabu da ma'u, amma fa fur yaƙi amincewa, duk wata wahala da ake bashi shi ake bawa, amma Iliyas shike jin raɗaɗin azabar, dan Iliyas aboki na gari ne... Tsawon shekara ɗaya ana abi ɗaya, amma kamar ana ƙarara Haidar son ma'u a zuciyarsa... Iliyas ne durƙushe a gaban ibn muzaffar, cike da ladabi yace "Ya Shaikh! Alfarma nazo nema, Allah yasa hakan ba zaisa inyi kuskure ba.." "Ina jinka mana Iliyas! Faɗi abinda kake son fada muku in zai yiwu.." "Allah ya huci zuciyar ka! Allah ya gafarceka, dama Alfarma nake nemawa Haidar, akan a rangwanta mai, a duba lamarin sa, yana cikin tsananin ciwon so, a halin da yake ciki a yanzu, ina ga azaba baza ta sauya masa ra'ayi ba, dan kullum burinsa ya fita daga wurin nan ya koma gurin bil'adamar nan, nidai alfarma da nake nema, shin mai zai hana ba za'a haɗa dayi masa wa'azi ba, da ƴan nasihohi, sannan a zaburar da shi dokokin Allah, ina ga kamar hakan zaiyi tasiri.." Girgiza kai ibn muzaffar yayi, cike da gamsuwa da abinda Iliyas ɗin ya faɗa. "Gaskiya ne Iliyas! Tabbas da ace azaba zata yi tasiri akan Haidar, da izuwa yanzu ya gundura da azabtarwar da ake mai, Ni kaina ina matuƙar tausaya mai, saboda na san illar soyayya, kuma INSHA ALLAHU zamu gwada yadda kace ɗin.." Kamar yadda Iliyas ya nemi alfarma, hakan ce ta faru, kuma an dace sosai dan hakan yayi matuƙar tasiri a zuciyar Haidar, sosai jikin sa yayi sanyi, dukan wasu makaman yaƙin sa saida ya zubar da su, amma soyayyar ma'u tana nan a cikin zuciyar sa, kullum ƙara sabunta take..... ★★★ Ma'u ce ta fito daga ɗakin suraj sanye da riga da wando, na mutanen ƙasar fakistan, jidda ce zaune a falo, tana yiwa wata ƙaramar yarinya da bazata wuce shekara ɗaya ba wasa, ƙarasowa tayi wajen su da murmushi tace "to jidda wasa kike keda ƙanwar taki..?" Ta faɗa tana karɓar ta. Rawa ta fara yiwa yarinya haɗe da waƙa, "Ah ah momyna yunwa take ji.." Ta faɗa haɗe da fiddo nono tana fidding ɗin yarinya, da take tsantsan kama da ma'u, kamar an tsaga kara.. Bayan ta gama fidding ɗin nata ne, ta miƙe tsaye haɗe da kamo hannun jidda, tana cewa "ohhyah muje gurin daddy.." Zaune suraj yake kan dadduma yana rera karatun Alqur'ani mai girma, ganin sun shigo yasa ya rufe Alqur'anin yana murmushi, da gudu jidda ta faɗa jikin sa tana ihun murna, yarinya ma dake hannun sai zillo take alamun tana son zuwa gurin daddynta miƙa masa ita ma'u tayi, sannan ta koma gefen sa haɗe da ɗora kanta jikin kafaɗarsa, marairaice fuskanta ma'u tayi cike da shagwaɓa, cikin kulawa suraj yace "yadai Madam..?" Cikin shagwaɓa ma'u tace muje gidan su Momy, daga nan mu wuce shopping.." Amsawa yayi da "to madam! Yadda kika ce haka za'a yi.." Cikin murna ma'u ta tashi harda ɗan tsallanta, kamar wata ƙaramar yarinya, kissing ɗin suraj tayi a goshi😘, jidda ita ma cikin shagwaɓa tace momy nima, mucch😘 ma'u tayi mata a goshi, kairat wadda taci sunan inna, itama tsalle ta fara alamun ita ma ayi mata, dukkanin su dariya suka fashe dashi sannan ma'u takai mata mucch 😘 a goshi, fita ma'u tayi daga ɗakin tana cewa "bari naje na shirya...." A gurguje ta shiga wanka ta fito ɗaure da towel a jikin ta, tsane ruwan dake jikin gashinta take da wani ƙaramin towel ɗin dake hannun ta, kwalliya ta fara tsantsarawa cikin nutsuwa, wajen minti 30 tana zaune gaban mirror sannan ta kammala kwalliyar, miƙewar da zata yi kenan, ta hangi kamar akwai wani a bayan ta, da sauri ma'u ta juya haɗe da zaro idonta, ganin Haidar ne yasa jikinta ya fara karkarwa, batasan lokacin da ta saki towel ɗin dake ɗaure a jikin ta, gaba ki ɗaya a tsorace take da ganin Haidar, takowa yayi cike da ƙasaita yana sakin mata ƙayataccen murmushin sa, ɗaukar towel ɗin da ta yarda a ƙasa yayi, haɗe da kauda kansa gefe yana miƙa mata, karɓa ma'u tayi amma ta kasa ɗorawa, murya cikin sarsarfa Haidar yace "ki ɗaura mana.." Ɗaurawa ma'u tayi haɗe da tsugunnawa a gaban Haidar ta fara magana cikin kuka.. "Ina zaune da mijina da ƴata da na haifa cikin kwanciyar hankali, dan girman Allah Haidar kayi nesa da rayuwa ta, kabarni in huta haka, idan ban manta ba ka taɓa cewa Zaka iya sadaukar da komai akan soyayyar da kake mini, ina mai roƙon ka da Allah, dan girman soyayyar da kake iƙirarin kana min ka barni, inyi rayuwar aure da mijina, saboda ina sonshi.." Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka.. Ɗagota Haidar yayi haɗe da rungume ta, yana bubbuga bayan cikin lallashi yace *"ASMA'UL HUSNAH* tabbas nayi alƙawarin sadaukar da komai dan farin ciki, kuma Insha Allahu bazan ƙara cutar da rayuwar ki ba, a tsakanina dake daga yau saide taimako, saboda sonki acikin jinina yake, kuma zan cigaba da sonki har duniya ta naɗe........... *TAMMAT BIL HAMMDULILLAH*..... ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO ƘARSHEN WANNAN LITTAFIN, KURAKUREN DAKE CIKI INA ROƘON ALLAH YA YAFE MIN, ABINDA NA AIKATA NA ƘARUWA ALLAH YASA A AMFANA DA SHI, ALLAH UBANGIJI YA GAFARTA MANA ZUNUBANMU ALLAH YA SAKAWA IYAYEN MU DA ALKAIRI MAFIFICI.... RUBUTU DA LABARI MALLAKIN *UMMUSSALAMA S YAHYA* (MATAR KHAMIS)✍️ Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels