Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 _____________________________________ *Writing by*✍🏻 *Hajara L Sadeq* *Miss hajo*🖤 ~marubuciyar~ *KOMAI MUKADDARI NE* *K'ADDARAR SOYAYYA TA* ~And now~ *NAJMAT ABIY* _____________________________________ 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* ~*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*~ *Da sunan ALLAh Mai Rahama Mai jin k'ai Ina godiya ga ALLAH SWA da ya bani ikon fara rubuta littafin nan Mai suna NAJMAT ABIY K'irk'irarren labari ne da yazo da nashi salon na musamman Wanda na tabbatar zai nishada'antar da Mai karatu ban yarda wata ko wani su juyamun labari ba LITTAFINE Mai d'auke da darussa da Dama a cikinshi Wanda inkuna biye Dani zakuji sak'on da littafin ke tafe dashi Ina rokon ALLAH yanda na fara shi lafiya Allah yasa na gamashi lafiya ALLAH tsari alkalami na da rubuta abunda yake ba ALKHAIRI ba Free book ne comment dinku da sharhi kawai nake buk'ata kamar yanda kuka karb'i KOMAI MUKADDARI NE ina fatan Shima zaku karb'eshi hannu bibbiyu har kullun burina baiwuce naga na faranta muku my sweethearts* *I LOVE YOU ALL MY FANS K'AUNAR KU A JINI TAKE SWEETHEARTS* Sakon gaisuwa da godiya da jinjina gareku y'an uwa kuma masoya k'aunar ku a jini take. 👇🏿 *Ummu maheer* *Momyn shukura* *Nearnah M sha'aban* *Hafsat Zubair (Muhsat)* *FREE BOOK*📒 ___________________________________ *PAGE 01 & 02* ____________________________________ *INDIA*🇮🇳 *NEW DELHI* *HIGH GARDEN REAL ESTATE* Naga an rubuta a jikin katafaren get din da shi kanshi abun kallo ne. Tun daga shigar ka estate d'in zaka tabbatar ba ta k'ananun mutane bace duba da yanayin tsaruwar gine_ginen dake cikinta. Gidajene na alfarma dukkaninsu iri Daya girman estate din ya wuce misali Dan Bakama iya k'irga yawan gidajen dake cikin ta ba gari gudace Fadar tsaruwar ta B'ata Baki ne kowane gida da get d'inshi da komai a ciki na more rayuwa. Akwai pack a cikinta inda yara suke wasansu Babu abunda Babu cikin pack din tundaga kan swimming pool da sauran kayan more rayuwa sannan akwai makaranta tun daga primary har secondry duka y'ay'an dake cikin estate din a nan suke karatunsu hankali kwance ga kuma kwararrun ma aikata haka zalika akwai hospital cikin Estate din Shima Mai d'auke da k'wararrun ma aikatan kiwon lafiya. indai takaice muku Mai karatu duk inda za Akira waje Aljannar duniya tofa estate d,innan takai a kirata Aljannar duniya Dan tunda nake bantab'a ganin estate Mai kyan taba. D'aya daga cikin gidajen wannan katafariyar estate d'in na kutsa kaina ciki Wanda bakin get d'inta ma shak'e yake da security. Zaune suke a katafaren palour na alfarma wanda shak'e yake da kayan more rayuwa Babu abunda Babu najin dad'in rayuwa. "please ABIY don't say no I wan't see her I love her so much ABIY or only once have see it" ta Ida fad'a idanunta na cikowa da ruwa kamar zatayi kuka *NAJMAT* kenan y'ar shekaru takwas da haihuwa kyakyawar yarinya NAJMAT fara ce sosai farinta irin na yaran turawa Mai kyau d'in nan round face d'inta. Dogon hancin ta ga kuma k'aramun bakin ta da yayi das da kyakyawar Fuskanta dimple d'inta Wanda yake ko batayi magana ba a lotse yake Y'ar wushiryarta data Kara fito Mata da asalin kyanta NAJMAT yarinya ce kyakyawa duk da karancin shekarunta Bai hana kyanta fitowa ba Bata k'iba kuma bazaka.kirata da Siririya ba y'ar chakwas d'in yaran naj ce Durk'ushe take gaban mahaifinta tana Mai magiya akan ya taimaka ya kaita taga mahaifiyarta ko da sau d'aya ne ita dai burinta taganta a rayuwar ta ko sau d'aya ne. Maganganun Nan na tilon d'iyar tashi ba k'aramun sosa mashi zuciya suke ba jawota yayi jikinshi tare da rungumeta tare da Fara lallashin ta saboda a duniya Babu abunda ya tsana sama da b'acin ran NAJMAT. Ko kad'an bayason Yaga kukan tilon d'iyar tashi ga kuma takaicinshi na Son ganin Mahaifiyarta da ta dameshi dashi kwanannan yasan Babu abunda NAJMAT zata nema a wajenshi ya gaza Mata a rayuwa amma.kuma wannan Karin bazai îya cika Mata burintaba saboda Alk,'awari ne ya d'aukarwa kanshi har abada bazai tab'a had"a ta da mahaifiyarta ba Harya Koma ga mahaliccinshi maganganun Nan nata suna k'ara sosa Mai tsohon raunin da ke cikin zuciyar shi. Cikin sigar lallashi yace "My Najma" d'ago dara Daran idanun ta tayi da ya cika da k'walla tace yes My ABIY "do you wan't. Upset me?ya fad'a fuskanshi na Nuna alamun damuwa. Girgiza Kai ta fara cikin Y'ar in Ina tace "No ABIY "Shafa kanta yayi tare da sakar mata Murmushi yace ,"if you don't like my frustrations don't talk to me about your mom as from to day " Goge k'wallarta tayi tare da sakarmashi Murmushi ta gyad'a Kai alamaun ta fahimta Dan itama Babu abunda ta tsana sama da b'acin ran ABIY. "Yawwa *NAJMAT ABIY* d'inta GOD bless you dariya NAJMAT tayi jin ABIY ya kirata da sunan da tafi k,'aunar a kirata dashi rungumeshi tayi tare da cewa"Amen my ABIY I love you so much"I love you more my daughter ya fad'a Yana Shafa kanta . Cikin hausarta da Bata gama Nuna ba tace "ABIY innasin janze gidan su Amera , " "inye my baby tafara iya hausa "dariya tayi tare da lafewa jikin shi D'aukarta yayi Suka fito don ya kâita gidan su Amera Kamar yanda ta b,uk'ata Shima gidan cikin Estate dinne hakan. Yasa suka tafi a k'asa Saida ya kâita har cikin gidan Saida Yaga shigarta sannan ya juya da niyyar bayan magriba yadawo ya d'auke ta. Tana shiga palour Mamy kad'ai ta iske yatsarta tasanya ta fara tsotsa tana waige waige inda zataga Amera *NAJMAT* Ba magana cewar Mamy "mak,'ale kafad'a tayi alamun bazatayi magana ba "Murmushi mamy tayi Dan tasan miskilancin NAJMAT Cigaba tayi da waige waigenta chan dai ta gaji ta zauna Tana cigaba da Shan yatsanta Mamy ce tace "Dear bana hanaki tsòtsan yatsa ba"Turo Baki tayi tare da shagwab'a fuska ta cire yatsan Yaudai miskilancin kike ji bazamuyi hira ba kenan? Cewar Mamy gyad'a Mata kai Najmat tayi alamun Eh. Murmushi Ummy tayi kawai taci gaba da kallon news d'in da take. Amera ce ta fito daga bedroom d'insu tana ganin NAJMAT a palourn da gudu ta ruga tare da rungumeta Nan suka.hau tsalle tsalle da wasansu kamar yanda suka Saba sannan suka fara buga game d'insu a Tab Sunayi Mamy tana gefe tayi Murmushi tana Yaba wannan tsantsar k'aunar dake tsakanin NAJMAT da AMERA kamar Wanda suka fito ciki D'aya. Magriba ABIY yazo domin d'aukar NAJMAT Nan suka had'u da Abba Yana Shirin shiga Gida mik'awa juna Hannu sukayi suka gaisa ABIY ne yace "Ina wuni Alhaji an dawo lafiya " "lafiya qalau abu NAJMAT ya harkoki " Alhamdulillah"Masha Allah"Sannan yace Daman NAJMAT na zo d'auka Murmushi Abba yayi yace Baka barta ta kwana ba "d'an Murmushi ABIY yayi Yana d'an sadda Kai yace "Kar Kuma tayi kuka"Murmushi Abba yayi Dan yasan Daman ABIY bazai îya ba Sannan yace to bari na turo Maka ita har yayi gaba sai Kuma ya juyo yace " gobe idan Allah ya kaimu Ina son magana da Kai Muhammad"To shikenan Alhaji Allah ya kaimu ". Abba Yana shiga ya iskesu suna wasa suna ganinshi Suka ruga a guje tare da hug d'inshi D'aukarsu yayi d',aya bayan d'aya Sannan yacewa NAJMAT ABIY na waje Yana jiranki. Da gudu tayi hanyar k'ofa Mamy ce tace "Ba Sallama Najma Dariya Abba yayi yace "Bama mugaisa ba shine Zaki tafi ko Daughter"y'ar dariya NAJMAT tayi sannan tayi musu gwalo tare da d'agawa Amera hannu tace "God bye my friend until tomorrow when we meet at school" tayi waje dukansu Saida suka dara tana fita Rugawa tayi ta fad'a jikinshi d'aukanta Yayi Yana Mata Murmushi. Suna isa gida bayan yayi Mata wanka Boxes kawai ya Sanya Mata Sannan ya Bata abinci Saida ta k'oshi sannan yakaita ta kwanta Saida ya tabbatar da Tayi bacci sannan ya Koma d'akinshi Shima ya kwanta.......✍🏻 *Sai naji ruwan comment tukwana zanci gaba idan banji comment ba zan dakata* 🙅🏼‍♀️ *Hmm my sweethearts ya kukaji salon labarin* *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *GOD WE REPENT* 🤲🏼 *_Miss Hajo ce_* 🤙🏿 [9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 _____________________________________ *Writing by*✍🏻 *Hajara L Sadeq* *Miss Hajo*🖤 _____________________________________ https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *FREE BOOK*📒 _____________________________________ *PAGE 05 & 06* _____________________________________ "Ma'ana.Tauraruwar mahaifinta Najma tauraruwa ce a gareni Bata da kowa a duniyar nan sama Dani haka Nima a halin yanzu bani da kowa sama da ita itace komai nawa shiysa nake tausaya Mata ranar da babu ni....kasa k"arasa maganar yayi sakamakon zafin da zuciyarshi ke mashi." Dafa kafadarshi Abba yayi yace"Muhammad a da ne baka da kowa Amma a yanzu kad'auka kana da kowa inajinka Kai da Najma har cikin zuciya ta Ina maka kallon k'ane ne Wanda muka fito ciki d'aya insha Allahu indai Ina raye Najma bazatayi kukan rashin uwa ba "Tausayin NAJMAT ne ya tsargu a Zuciyar Abba Yana tausaya Mata na maraicin da ta tsinta kanta tun k'uruciya. Shawara Abba yabawa ABIY akan ya kamata yayi aure ko Dan saboda Najma amsa mashi yayi da to Amma ba Dan zai aikata hakan ba Dan yanda yake ji a game da tsanar da yayi wa Mata bayajin zai iya K'ara yin aure har abada a rayuwarshi . NAJMAT ce da Amera sai k'awarsu Simi zaune a compound d'in school d'insu Kasancewar an tashi gashi har yanzu ba a zo an d'auke su ba. Kasancewar mazajen Estate d'in duk ma aikata ne hakan yasa iyayen su Mata suke zuwa d'aukansu NAJMAT idonta nakan yaran da ake ta zuwa d'auka kowa saitaga mamanshi tazo ta d'aukesu hakan ba k'aramun Bata sha'awa yake ba jikinta ne duk yayi sanyi ji take inama ita ce. K,'walla ce ta fara zubowa daga idanun ta Bata da wani buri da yawuce itama ta ganta tare da mahaifiyarta suna rayuwa kamar yanda kowace y'a ke rayuwa da iyayenta. Maman Simi ce itama tazo d'aukanta Rugawa da gudu Simi tayi tare da rungumeta itama rungume y'ar tata tayi tare da Bata peck a kumatu K'walla NAJMAT ta fara Simi ce cikin harshen Hindu tace "Momy ga friends d'ina Najma and Amera. "hug d'insu d'aya bayan d'aya Maman simi Tayi gaisheta suka Yi ta amsa tare da tambayarsu ya akayi ba azo aka d'auke su ba "Simi ce Kasancewar ta Mai Surutu ta ce, "Moma NAJMAT ai Bata da moma bantab'aganin. maman ta ba ,ABIY kad'ai Gareta Amera Kuma driver su zaizo ya d'aukesu su" Kuka NAJMAT ta fàshe dashi jin abinda Simi ta fad'a lallashin ta Amera ta Fara tace "Sorry my dusti Babu ruwanmu da Simi daga yau sannan ta gallawa Simi Harara tace tunda kikasa Dusti ta kuka Babu ruwanmu dake ke yanzu ba friends d'inmu bace, ,"sorry my friends bazan sake ba Amma karkuce ni ba k'awarku bace sannan ta Fara kuka itama" . Hak'uri Maman Simi tabasu sannan taja hannun y'arta tare da ce Mata karta sake irin wannan maganan.(karku manta duk cikin harshen Hindu suke maganganun Nan) . ba irin lallashin da Amera batayiwa NAJMAT ba Amma tak'iyin shiru Suna haka Aunty nafesa tazo D'aukarsu da gudu Amera ta ruga wajenta tace "Aunty Dosti tun dazu take kuka tak'iyin shiru please Aunty kice tayi shiru Nima zanyi kukan idan batayi shiruba". A d'an rud'e aunty nafesa tayi wajen Najma tare da D'agata ta fara lallashin ta kamar k'ara zugata take Aunty nafesa ce tace "amera me akayiwa Najma . Amera da idanun ta suka ciko da k'walla " tace "Simi ce tace Mata Wai Bata da mama Kuma nace Mata ba ruwanmu da ita yanzu ita ba k'awarmu bace" Saida jikin Aunty nafesa yayi sanyi jin maganan nan tasan a lokacin nan Najma na buk'atar kulawar uwa tun sanda Abba ya fad'a musu Najma marainiya ce take tausayinta Kuma tayi Alk'awarin saita zamewa Najma uwa bazata tab'a rashin uwa ba inhar tana raye Dan tanajin Najma ne tamkar y'ar da ta Haifa a cikin ta . dakyal ta samu ta lallashi ta suka koma gida tun daga ranar aunty nafesa ta ninka kulawar da take bawa NAJMAT b'angaren ABIY Yana jin dad'in kulawar da aunty nafesa ke bawa y'arshi b'angaren Najma kuwa Damuwa ce tayi katutu a cikin zuciyarta dukda kulawar da Aunty nafesa ke Bata Kuma itama tasan tana son aunty nafesa Amma a zuciyarta tana son taga yau itama ga mahaifiyarta wacce ta haifeta. Hakan yasa ta zamto kullun silent ta rage hayaniya da kuzari musamman a makaranta ta rage K'ok'arin Dan tun da Najma tashiga school Bata tab'a zuwa da second position ba Koda yaushe first position take zuwa dashi Najma nada k'ok'ari sosai k'ok'arin ta na baiwane saboda gifted ce ta bugawa a jarida hakan yasa teachers din gaba d'aya suke ji da ita a school d'in Hakan ne yasa ma suka Yi Mata jumping yanzu tana jss one ne. A tak'aice dai. Najma da Amera aminai ne tun da suka shiga school din jininsu ya had'u gashi shekarunsu sukaso d'aya koda akayiwa Najma jumping itama Amera kuka tasa akan itafa sai an hada ta Dusti bayanda aka iya itama Amera aka Mata jumping din dukda itama ba laifi tana da kokari. Shakuwace sosai tsakanin Najma da Amera hakan yasa Koda yaushe a gida Amera Bata da zance idan ba na Dusti ba Haka Najma Bata da zancen da ya wuce na Amera dukansu a cikin Estate Daya suke Koda NAJMAT ta bukaci ABIY ya kâita gidan su Amera Bai Musa ba tun lokacin da Najma ta fara zuwa gidan su Amera y'an gidan su Amera suka d'auki son duniya d'orawa NAJMAT jinta suke tamkar y'arsu. Musamman Abba dan tunda yaganta ita da Abiy Kasancewar Najmat kamarta Daya da abiy kàmar an tsaga Kara an karya Yaga suna Mai mugun kama da k'anwarshi hau'wa'u ga kuma yanayi da take Mai da babbar y'arshi data rasu Amina Hakan yasa yakejin najmat a ranshi kamar amina ce ta dawo aunty nafesa k'anwar Ummy ce uwa Daya uba Daya budurwace tagama karatunta na deegree a wajen Ummy take da zama. Ummy da Abba suna da yara Ukku dukansu Mata ,babbar y'arsu Amina Allah yayi Mata rasuwa sai Sarat ita yanzu tana Nigeria wajen Mahaifiyar Abba take sai autar su hauwa'u suna kiranta da Amera Asalin su y'an Nigeria ne aiki ne.ya kawo Abba India Inda ya saya gida a Estate din yake zaune da iyalanshi. shak'uwa ce sosai tsakanin Najma da gidan su Amera musamman Aunty nafesa Hakan yasa Koda yaushe tana gidan su Amera da andawo daga school tana chan. ABIY Yana aiki ne.a Babban Componyn sarrafa manya manyan motoci a new Delhi shine C E O a componyn mutum ne Mai Amana baya tab'a cin Haram halal d'inshi yake ci Hakan yasa shugaban componyn yake ji dashi Kuma yakemai alheri sosai ga albashin shi Mai tsoka sosai yanzu haka Abiy Yana da componyn shaddoji da lessusuka nashi na kanshi guda Biyu ga ya mallaki gidaje da Dama a garin New Delhi ciki harda gidan shi da yake ciki ga manya manyan motoci Kuma duk halal d'inshi ce mutum ne Mai Kirki da Kamala ga îya zama da mutane. NAJMAT ita kad'ai ce Y'ar da Allah ya mallaka mashi Yana son Najma fiye da komai Baya yarda Najma na shiga damuwa Tun da Najma take Bata san mahaifiyarta ta ba tunda ta tashi a rayuwarta da ABIY ta tashi Bata son meye dad'in uwa ba gashi kuma ABIY yaki hada ta mahaifiyarta gata ,da soyayya ba abunda Najma ta nema ta rasa daga wajen ABIY Amma duk da haka soyayyar mahaifiyarta da Bata San ko wacece ba ta na Nan mak'ale a cikin zuciyar ta shakuwace Mai k'arfi tsakaninta da Abiy suna matuk'ar son junansu dukansu biyun basason suga dayan su Cikin damuwa a ta'kaice dai wannan kenan......✍🏻 *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *GOD WE REPENT* 🤲🏼 *_Miss Hajo ce_*🤙🏿 [9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 _____________________________________ *Writing by*✍🏻 *Hajara L Sadeq* *Miss hajo*🖤 _____________________________________ https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* _____________________________________ *FREE BOOK*📒 _____________________________________ *PAGE 03 & 04* _____________________________________ washegari Around 6am ya tada NAJMAT yayi Mata wanka ya Mata Shirin makaranta riga da d'an k'aramun siket d'in bakin k,'ugu sai Doguwar safa ya gyara Mata two babies d"in gashin ta bayan tayi breakfast ya zuba Mata a basket d'inta Shima shiryawa yayi cikin Shirin tafiya wajen aikinshi tare suka fito da NAJMAT a hannunshi mota suka shiga driver ya jasu Saida ya biya ya Fara Kai NAJMAT sannan ya wuce Kai ABIY compony. 2:00pm Aka tashi su NAJMAT daga makaranta kamar kullum driver d'in su Amera yazo ya d'aukesu suna shiga palour Aunty nafesa suka tarar fad'awa jikinta sukayi dukan su wayyo baby's zaku karyani fa k'ara hayewa chinyarta sukayi suna dariya NAJMAT hada k'ara dira wa Saida suka gaji Dan kansu tukwana suka sauka "Wayyo baby's Kun Karyanu"dariya suka hau Mata " Najma ce cikin shagwab'a tace "Aunty yunwa nakeji" Abincinku Yana dining a red cooler d'in chan d'ayan na Su Ummy karku tab'ashi kunji NAJMAT ta fara Rugawa sannan Amera ta bita harsun fara cin abincin Ganin Aunty nafesa tabar palourn Aiko suka d,'ad'aga Wanda ta hanasu d'in suka sa duka hannuwansu biyu suka hau shagwalgwala shi suna watsashi a gurin. salati aunty Nafisa ta fara fitowarta taga yanda suka wulak'anta abincin "me nake gani Amera Najma sauran. abincin Ummy da Abban ne kuka lalata juyowa sukayi Suna kallonta Amera tace "Sorry Aunty we will not do it again "Turo Baki NAJMAT tayi taci gaba da watsa abincin tana jagolgolashi kamar badasu take ba. Tafa hannu Aunty nafisa tayi tace "watau NAJMAT inama magana kina cigaba ko ta fad'a a d'an tsawace Dan taji ciwon lalata abincin da sukayi Dan Tasha wahala kafin ta girka. "Kuka da dira k'afa Najmat ta fara saboda ita Babu abunda ta tsana sama da ace tayi ba daidai ba musamman a Mata fad'a komai take Kar amata magana yanda ABIY d'inta ke Mata baya tab'a hanata b,'arna shiyasa in tanayi tofa ba a isa amata magana ba . haka Mamy ta shigo ta iskesu dawo warta kenan daga office Kallon NAJMAT tayi tana kuka kallon Aunty Nafisa tayi tace "me akayi Mata nafesa ". "wallahi Aunty Abincin ne suka lalata ita da Amera shine daga musu d'an fad'a ta hau kuka"NAJMA rigima inji Ummy sannan tace "Keda daughter ki da Bata laifi bazan shiga fad'an da zanji kunya ba ta fad'a tana barin wajen,Dan tasan Inma tashiga kunya zataji dan tskanin NAJMAT da Aunty nafesa ba a shiga. Hanyar k'ofa NAJMAT tayi zata fita tana kuka da gudu Aunty nafesa ta tare ta tare da d'aukanta wutsil wutsiltun ta fara Aunty nafesa tace "Haba My Habibty fushi zakiyi Dani sorry my baby I will not tell you again indai kinajin magana ta bazan dinga maki fad'a ba". Lafewa jikinta NAJMA tayi tana sauke ajiyar zuciya "Daddab'ata taci gaba dayi tana lallashi "Haba my sweet daughter kin tab'a ga inda Daughter tayi fushi da Momynta"haka dai Aunty nafesa tayi ta lallashinta harta samu ta hak'ura bacci ya kwashe ta a cinyarta gyara Mata kwanciyarta tayi kan cinyartata tare da Shafa Mata fuskarta Ita kanta aunty nafesa wani Karin har mamakin son da take yiwa NAJMAT take Nan Ummy tafito ta iskesu Murmushi tayi tace "har an shirya kenan dariya Aunty nafesa tayi tace "Dan dak'yal ai Babyn tawace ba dai rigimaba. "Muhammad yanzu dai a iya zamanmu daku kusan shekaru Biyar anriga an zama d'aya Ina d'aukar ka ne matsayin d'an uwa uwa uba Addini mu d'aya haka zalika k'asar mu d'aya Kuma Allah ya hadamu waje d'aya Saidai kamar har yanzu ,Ina ganin baka gama sakin jiki damu ba kamar yanda muka saki jiki dakai", Abba ne ke maganarnan suna Zaune a garden d'inshi bayan ya Kira Abu NAJMAT "Nima haka nake d'aukarku Alhaji da Kai da iyalanka bansan da wani irin Baki zan iya gode muku bisa ga yanda kuke hidima damu ni da y'ata Saidai ince kawai Allah ya biyaku da mafificin ALKHAIRI"Babu komai Muhammad Najma ai y'a take.a wajenmu dalilin da yasa na nemu magana dakai illa inason sanin takaitaccen tarihinka da Kuma dalilin da yasa kake zaune Babu Mata da ga Kai Sai y'arka abun Nan yajima Yana daure mun Kai ., Yanayin Abiy gaba d'aya Saida ya chanza saboda maganar Tarihin shi da yayi mashi ga kuma bak'incikin tado mishi da zancen Mahaifiyar NAJMAT da yayi Wanda baya k'aunar tunowa da ita ko misk'ala zarratin saboda Yana k'ara sosa mai zafin radad'in ciwon dake cikin zuciyar shi Dan ajiyar zuciya ya sauke Dan bayajin zai iya fad'a wa kowa Gaskiya game.da tarihinshi idan ma yace zai fa'da to ta Yama zai fara Dan shi kanshima har yanzu cikin duhu yake hakan ya sashi cewa. "a takaice suna na Muhammad haifaffen garin gombe Iyaye na sun rasu tun ban girma ba nayi Auren soyayya da Mahaifiyar NAJMAT wajen haihuwar NAJMAT Allah yayi Mata rasuwa Nina cigaba da kula da Najma tun tana jinjira Ina son NAJMAT fiye da yanda nake son Kaina zan iya Sadaukar da komai Akan NAJMAT Najma ita nake kallo naji sanyi a Raina Najma itace tauraruwata Najma ta zame mun. matsayin uwa ,uba,d'an uwa,y'ar uwa,aminiya,hakane ya sanya nake Kiran ta da *NAJMAT ABIY* ..........✍🏻 *idan kun karanta dan girman Allah kuyimun sharing fisabilillah* ~*GOD WE REPENT*~👏 *_Miss hajo ce_* 🤙🏿 [9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 _____________________________________ *Writing by*✍🏻 *Hajara L Sadeq* *Miss Hajo*🖤 _____________________________________ https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *FREE BOOK*📒 _____________________________________ *PAGE 7 & 8* _____________________________________ Yau ta kama end of 3rd term Wanda da sun dawo Hutu su NAJMAT zasu shiga Jss two. Abun. Mamaki NAJMAT dake zuwa first position itace wannan Karin tazo 3rd potision malaman kansu sunyi mamakin lamarin Nan. Hakan yasa suka sanar da ABIY ya binciki NAJMAT cikin kwanakin nan sun lura akwai abun da ke damun ta. Shima ABIY ya lura da hakan dan ta chanza sosai ta rage kazar-kazartu abun Yana damunshi sosai. Koda ya tambayeta me ke damunta Bata fad'a Mai dalilin ba saboda tun ranar da yace karta Kuma Mai magana game da mamanta Bata sakemai ba saboda a duniya Babu abunda ta tsana sama da b'acin ran ABIY. Wata Rana da magriba ABIY yaje d'aukar NAJMAT Nan suka had'u da Abba suka fara tattauna wa game da lamarin Najma. Muhammad akwai wuni hukunci danake son yankewa kokuma ince shawara a matsayi na na d'an uwa Dan yanzu an riga an zama d'aya to bansan b,'angaren ka ya zaka d'auki lamarin ba ". Saida gaban ABIY ya fad'i amman ya fusge yace ,"inaji Abban Amera insha Allahu zanyi Amfani da shawararka ". "Wani nazari ne nayi Duba da shak'uwar dake tsakanin nafisa da NAJMAT nake ganin mezai hana ka Auri nafisa na tabbatar nafisa zata rik'e NAJMAT da amana haka Kuma Najma yanda ta d'auki nafisa tamkar uwar da ta haifeta Ina ganin Hakan zai yiwa NAJMAT dad'i Kuma zatayi farincikin zama da nafisa Ina ganin hakan itace kad'ai mafitar da Najmat zata dawo da walwalarta kamar da Koma Fiye da da. Tun da Abba ya fara maganganun Nan Wata uwar zufa ta jika ABIY a zuciyarshi yace ,"ya zakayi mun haka Abban amira Kodan bakasan halin da na shiga a rayuwata ta baya bakasan Azabtuwar danayi ba ta dalilin mace baka san illar da mace ta aikata mun ba Da bazaka bani shawarar K'ara kallon Wata mace ba bare har Takai ga aure banajin zan iya K'ara rayuwar aure da wata mace a duniya Illar da Mahaifiyar NAJMAT ma kad'ai tayimun a rayuwa ta isheni". Kasancewar kwarjinin da Abba yayi mishi da Kuma Ganin kimar Abba dayakeyi bazai îya Musa Mai Kai tsaye ba da k'yal ya iya daidaita nutsuwar shi yace "To shikenan Alhaji Insha Allahu zanyi shawara sannan sukayi musabaha Abba yayi gida da niyyar kirawowa ABIY NAJMAT. Duk maganar Nan da su Abba sukayi akan kunnan Amera da Najmat Sunfito wasa kenan suka lab'e sunajin su Wara idanu Najma da Amera sukayi a tare saikuma suka saki Murmushi Najma tace "da zanfi kowa farinciki idan ABIY ya Auri aunty Nafisa lokaci guda Kuma ta had'e Rai tace To idan Kuma Aunty Nafisa tace batason ABIY na fa ,"Amira ce tace "Ai Dole ma musanya ta soshi tab'awa sukayi tare da kashewa juna Ido ganin Abba yataso ya Sanya su Rugawa da gudu suna dariya Kai tsaye bedroom din Aunty nafesa sukayi. Kwance suka tadda ita tana charting hayewa kanta sukayi Murmushin kawai tayi Dan ta Saba da hayewar yaran nata Nan ta biyesu sukayi ta shiririta. Abba ne ya Kira Aunty Nafisa a palour ta fita ta iskeshi Najma da Amera suna jin Kiran suka lab'e Dan suji Wata amsa aunty Nafisa zata ba Abba Najma addu'a kawai take Allah yasa Aunty Nafisa tayi accepted. Shiru sukayi na d'an wani lokaci Ummy Abba sai Aunty nafesa Nan Abba ya korawa Aunty Nafisa buk'atar dake tafe dashi. Dan danan Aunty Nafisa ta tada hankalinta Wata uwar zufa ta keto Mata Dan Bata da burin Auren Wanda ya manyanta a tsarinta dukda ABIY baiyi wani girma ba dan Bai wuce 40years. Abba ne ya lura yace "karki k'wari kanki Nafisa ba umarni nake Baki ba shawara ce idan kinsan bakiso kifad'a mun kawai ba wata damuwa . Dan Jim Aunty Nafisa tayi har zuciyarta Bata son ABIY Hakan kawai yasata fito da gaskiyarta a Fili ta ce ''gaskiya Abba ban sonshi".........✍🏻 *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *GOD WE REPENT*🤲🏼 _*Miss hajo ce*_ 🤙🏿 [9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 _____________________________________ *Writing by*✍🏻 *Hajara L Sadeq* *Miss Hajo*🖤 _____________________________________ https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *Shafin Nan sadaukarwane gareku NAJMAT ABIY Fans Ina Jin dad'in comment dinku da sharhi fiye da yanda kuke zato Ina alfari daku my sweethearts Love you wujiga wujiga wallahi Shafin Nan nakune kuyi yanda kukeso dashi Ina alfahari daku* *FREE BOOK*📒 __________________________________ *PAGE 9 & 10* __________________________________ "Oh my GOD" NAJMAT ta fad'a tana dafe goshi kamar wata babba k'wallace ta fara kwaranya daga idanunta Amera ta maza ta goge Mata tace "Banason kina kuka fa Dusti you forgot we are claver ? Don't mind Dusti now our game will begin". ta fad'a tana kashewa Najma Ido dariya k'asa k'asa Najma tayi tace "it's true Dusti" . Ummy bataji dad'in abunda Nafisa tace ba koba Komai kodan saboda Najma yaci ta amince Aiko Nan ta hau ta fad'a Saida Abba yayiwa Ummy magana yace ta k'yaleta ai ba tilastata za a yiba. Tun daga ranar Najma da Amera suka Mayar da hankalinsu akan yanda zasuyi su had'a soyayya tsakanin. Abiy da Aunty Nafisa Duk sun shiga busy cikin kwanakin nan tunanin su kawai yatafine akan game d',in da suke shiryawa. B,'angaren ABIY Kasancewar Bai Bawa Abun mahimmanci ba Hakan yasa Yama mance da zance ya shiga harkar gabanshi Da misalin 8pm kwance take ta d'ora kanta cinyar ABIY tana buga game a Tab d'in ta suna hira da ABIY d'inta. Cikin hirar ne tace "ABIY gobe inason ka kaini shopping Teddie's d'ina sun lalace Kuma Coculate d"Ina ma sun kusa,k'arewa" "To daughtern ABIY d'inta zan kaiki duk inda kikeson zuwa Amma zakimun Alk'awari d'aya"wani Alk'awari ABIY "Zaki dage a makaranta kamar yanda kike da Ina son ma kifi da k'ok'ari Kede kike so ki zama doctor in saya Miki k'atoton hospital kema kidinga yiwa mutane allura ko bakiso. "washe Baki NAJMAT tayi tana dariya tace Ina so ABIY Kuma Na maka Alk'awari ABIY na Zan dage inzama doctor Nima nadingayiwa mutane allura Kuma saina rama allurar da doctor Kharena tayi mun dariya ABIY yayi yace "yawwa My lovely daughter na. "NAJMAT tun tana yarinya take son ta zama doctor tun lokacin tana shekaru hud'u tayi zazzab'i aka kâita asibiti doctor Kharena tayi Mata allura tayi ta kuka tun daga lokacin tad'au Alk'awarin itama saita zama doctor tana yiwa mutane allura Kuma saita rama allurar da doctor Kharena tayi Mata har yanzu ta kasa mancewa ". "Abiy nima inason zakayimun wani Alk'awari "Shafa kanta yayi yace Alk'awarin me dear "d'an Murmushi tayi tace kaidai ABIY kawai kayimun Alk'awarin duk abunda na rok'eka zaka amince Kai tsaye " Murmushi yayi ya na lakutar kumatun ta Dan yasan Najma da iyayi kamar wata babba k'ilama wani iyayin nata ne hakan yasashi cewa "nayi Miki Alk'awarin"Murmushi tayi tace "Promise ABIY nasan kasan dai girman Alk'awari da illar k"in cika Alk'awari". Dariya ABIY yayi yace "oh Najma badai iyayi ba Sannan yace eh. Naji na yarda shikenan dariya itama tayi tare da wara hannu tace "shikenan ABIY na"lakutar kumatun ta yayi yace "iyayi babe "dariya tayi a zuciyarta tana murnar burinta ya kusa cika . Washegari kamar yanda Najma ta buk'ata wajejen 4pm suka shirya ita da ABIY sanye take cikin gajeriyar y'ar kanti d'inta pink anmata parking gashin ta sai shek'i da walkiya yake Tasha kyau sosai kamar ka sace ka ruga. Har sun shiga Mota ABIY ya tuk'a Dan Najma tace shi zai tuk'a ba driver ba harsun fito get d'insu tace Yakaita gidan su Amera tare zasu tafi ba musu ya karkata motar shi ya kâita chan tana shiga ta iske Aunty nafesa tace . "ta taho ABIY yace zata rakasu shopping ita da Amira har ta Musa Ummy ta harareta ba musu ta tashi ta shirya cikin Doguwar riga abaya Tasha kyau Kasancewar ta black beauty' ce Amira da Najma suka fara yin gaba da gudu suka shige back sit tare da SA lock ba yanda aunty nafesa ta iya sai front sit ta shiga tana Hararar su Najma Yar dariya sukayi Mata. A gajarce tace wa ABIY "Ina yini"ba tare da ya kalleta ba yace Lafiya qalau ygd "Alhmdllh ta fad'a haka sukaje sukayi shipping, sosai su Aunty Nafisa ma ABIY yasa suyi Amma ita batayiba Amera kad'ai tayi ganin Hakan yasa yayi Mata da kanshi sosai ya saya Mata Kayayyaki Dan ko ba komai yanajin dad'in yanda take Nuna kulawa ga y'arshi.da soyayyar da take Nuna ma Najma (kunsan me d'a). Hakan kuwa yayiwa Aunty Nafisa dad'i saitaji kunyar kin amincewa da soyayyar shi da tayi (Abba ya ce Mata ne ABIY ya ce yana sonta Dan karta k'i saurin amincewa). Najma ko Amira cikin sauri suka gama daidaita plane d'insu cikin wayau Najma ta kwafe number Aunty Nafisa tayi save a wayar ABIY. Bayan sun Koma An sauke su Amira da aunty Nafisa Saida Anty Nafisa tayi hug d'in Najma tare da ce Mata "Good bye My Dear ki kulamun da kanki "sannan tayiwa ABIY godiya ta wuce. Suna komawa gida bayan sun huta after isha'i Nan Najma tace ABIY ya ara Mata wayarshi ba musu ya ara Mata Dan duk abunda Najma takeso tofa saiya Mata. Whats app ta shiga ta yi sauri tayi search d'in aunty Nafisa da tayi save dazu Salam tayi Mata cikin sa a ta sameta Online tayi wslm Murmushin da ya fito Mata da fararen hak'oranta Najma tayi a Zuciyar ta tace "plane d'inmu Yana tafiya a daidai'' Nan suka Fara chat da Najmat kamar da ABIY take chatting Aunty Nafisa kanta Saida tayi Mamakin Abu Najma d'in da ko magana bayayi shine suke surutun Nan dashi a chat daga k'arshe ne Najma tace "Auntyn Najma Ina fatan sak'o na ya iso gareki fatan Zaki karb,'eni hannu bibbiyu" Daram gaban Aunty nafesa ya fad'i ta d'an turamai da sticker dariya Mayar Mata Najma tayi da sticker Harara tare da cewa "Haba auntyn Najma ko ba Dan niba kodan soyayyar da kike yiwa najma yaci ace kin sammani ko kad'an ce daga cikin tata badon saboda ni ba please saboda Najma zakiyi jahadin Nan kinsan Najma tana buk'atar kulawarki a matsayin ki da uwa Gareta" Karo da wannan sakon ya Sanya Aunty nafesa Murmushi lokaci guda taji Kuma tana son Auren ABIY ko Dan saboda Najma d'in Daya ambata ga wani dad'i da taji jin ya kirata mahaifiyar Najma hakan ya sata maida refly da ''uhm ba komai ABIY NAJMAT zanyi tunani insha Allahu. "Zuwa yaushe kenan kinsan bana son a d'au nisa"Dan Murmushi tayi tatura Mai da "Gobe kamar haka insha Allahu "farinciki gurin Najma kamar ta kwala ihu a zuciyarta tace "NAGAMA dake Kuma aunty nafesa saura ABIY nasan bani da matsala da ABIY Saida ta goge chat din gaba d'aya sannan ta samu ABIY a d'akinshi ta mik'a Mai wayar Murmushi yayi yace angama game d"in kenan" Gyda'a mashi kai tayi tace "ABIY promise d'in da kamun gobe ne fa zan fad'a Maka please ABIY karkace mun a a a komai zance kace mun ka amunce jawota jikinshi yayi yace "insha Allahu iyayi babe d'ina na amince Murmushi tayi tare da lafewa jikinshi ita kad'ai tasan farincikin da take ciki. washegari Najma da ABIY suna garden Najma ce tace "ABIY nafad'a Maka Dan Allah kace eh "Murmushi yayi yace inajinki daughter"ABIY Dan Allah ka Auri aunty Nafisa please ABIY Ina sonta Ina son ta zama mamana Dan Allah kada kace a a "What ABIY ya fad'a Yace Najma a Ina kikasan wani Aure harkikemun maganar na Auri Wata to bazan aureta ba Kuma nakarajin Kinkuma maganar aure saina Sab'a Miki". najma Bata tab'a ganin ABIY yayi Mata haka ba Aiko take ta rud'e tasa kuka da gudu ta nufi cikin gida tana kuka "dafe goshi ABIY yayi yace "meyasa nayima daughter tsawa sannan ya nufi hanyar data bi Dan ya Bata hak'uri Koda ya isketa palour ya taddata tana kuka lallashinta ya Fara Amma ta tubure tace Ita baruwanta dashi tunda bazai Auri aunty ta ba "Nan hankalin ABIY ya tashi saboda a rayuwar shi Babu abunda ya tsana sama da kukan Najma ko b'acin ranta Hakan ya sashi cewa . "idan na amince shikenan kin hak'ura cikin kuka tace eh"Na amince Najma zan auri auntyn ki saboda farincikinki "lokaci guda Najma ta d'àgo tace "da gaske ABIY na"gyad'a Mata kai yayi yace "da gaske Daughter tunda Hakan zai maki dad'i na amince". da gudu Najma ta fad'a jikin ABIY tare da cewa "I love you my ABIY"I love You More Daughter ABIY ya fad'a Yana D'agata sama Nan ya hau Mata wasa Saida ya sata farinciki sosai. Najma ce ta bukaci da yataho su Tafi gidan su Amera yafadawa Aunty Nafisa Yana sonta wara idanu ABIY yayi yace "Again Kuma daughter"cikin shagwab'a tace eh Mana ABIY nidai saimunje " ta fad'a tana kamo hannunshi ba yanda ABIY ya iya yabi ta saboda Yana k'aunar farincikin Najmat zai iya Sadaukar da komai Akan farincikin tilon y'ar tashi. suna isa Najmat ta fara yin gaba Murmushi kawai ABIY yayi Yana mamakin iyayi irin na Najma tana shiga da Amira tafara cin Karo rungume juna sukayi Suna tsalle Najma tace "Albishirinki Dusti "...✍🏻 *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *GOD WE REPENT* 🤲🏼 _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 _____________________________________ *Writing by*✍🏻 *Hajara L Sadeq* *Miss Hajo*🖤 _____________________________________ https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *FREE BOOK*📒 _____________________________________ *PAGE 11 & 12* _____________________________________ "Goro"inji Amera "ABIY ya amince"wara idanunta Amira tayi tace da gaske Dusti"eh Mana Dosti yanzu Ina Aunty Nafisa"tana palour inji Amira a palour suka iske Aunty Nafisa da Ummy suna Zaune"fad'awa jikinta NAJMA tayi tace ''i miss you my mom"miss you too daughter" Aunty nafesa tafad'a tana Shafa kanta. Najma ce tace "Aunty ABIY na waje yace na kiraki"aunty Nafisa tayi mamaki kallon ummy tayi gyad'a Mata kai Ummy tayi tace jeki''. Tana fita a Baki gate din gidan ta sameshi Bayan sun gaisa Kamar yanda Najma ta fad'a Mai haka yayi badon Yana son Aunty nafesa ba Saidan farincikin Najma Ba B'ata lokaci Aunty Nafisa tayi accepted d'inshi. Abiy ya samu Abba yafad'a Mai ya amince haka Aunty Nafisa ma tace Mai ta amince Abba shi kad'ai yasan farincikin Daya shiga ba b'ata lokaci cikin Wata biyu Aka gama komai da komai na biki cikin Wata na ukku aka d'aura auran Aunty nafesa da ABIY Wanda Abba ne ya wakilce Aunty Nafisa ABIY kuwa shugaban componyn su Kasancewar musulmi ne ba ayi wani shagali ba ranar juma a aka mik'a aunty nafesa d'akin mijin ta. Farincikin wajen Najma ba amagana Koda Ummy tace ta zauna wajensu k'iyawa tayi ita tana wajen ABIY d'inta da Aunty nafisar ta. Kulawa ta musamman aunty Nafisa take bawa Najma ga wata shakuwa data Kara shigarsu ABIY tun baya son Nafisa dalilin kulawar da Yaga tana bawa y'arshi yaji ya Fara sonta haka suka ci gaba da rayuwa cikin tsaftattaciyar soyayya Mai birgewa. B'angaren Najmat karatun ta take hankali kwance cikin nutsuwa Kokarin ta ya dawo kamar da Dan ta Koma d'aukar na d'ayanta. Kwana a tashi ba wuya a gurin Allah ranaku naja haka watanni shekaru sunja Najmat sun kammala secondary school d'insu inda suka fito da Results Mai kyau yanzu haka Abiy Yana nema musu admissions ne ita da Amira. Duk wani girma da budurtaka ya fara bayyana jikin Najma ga wani kyau data k'ara fuskarnan tayi fresh hancinta zuwad ga d'an k'aramun bakinta mai matuk'ar d'aukar ido Dara-daran maganan ta da su ne suka k'ara fito Mata da asalin kyawunta kallo d'aya zaka Mata kaga cikakkar. Y'ar Hutu da gayu ga class sanye cikin wasu English wears riga da wando tayi parking gashin ta gwanin sha'awa sai k'yalli yake zaune take a garden ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana kurb'ar drink hankalinta kwance. Bugun dataji anyi Mata ta baya ya sata cewa "Wayyo Dusti Zaki jimun ciwo fa "dan tasan amira ce kad'ai ke mata haka juyowa gabanta Amira tayi itama taxama matashiyar budurwa kamar Najma Amera tana da kyau itama fara ce Saidai Bata Kai Najma ba jikinsu da tsawonta kamar na Najma shiyasama wasu dasun gansu suke cemusu twins ne ,"harararta Amira tayi tace''Tun d'azu nake nemanki Aunty Nafisa tace mun kina Nan ,"Murmushi Najma tayi tace "Allah sarki dusty sorry na walalar dake". "Amira ce tace Wai ya Maganar koyon driving d'in da kikace zamuyi kinsan admissions d'inmu Yana gab da fitowa ,"Wallahi Dusti nayima ABIY magana so yace zaiyiwa Wanda zai koya manan magana Kinga yau Friday to Monday yace zaizo ya fara koya Mana kinsan bazaiyu ace kamar mu classic Ladies bamu iya driving ba "Dariya Amira tayi tab'awa sukayi "Najma tace ai harna k'agara mu shiga school d'innan zamu Basu wuta "sosai ma dusti,"inji Amira Nan suka zauna suka cigaba da tattaunawarsu akan Show d'in da zasuyi a university. Sai yamma likis suka koma cikin gida a kitchen suka tarar da Aunty Nafisa tana abincin dinner"sorry momyna kawo mu k'arasa jeki ki Huta "cewar Najma tana Amsar tray d'in maggi a hannun aunty Nafisa Murmushi aunty tayi tace "ai nama kusa Karasawa daughter kawai barshi jeku ku d'an gyara mun palour"to suka Amsa a tare sannan sukaje suka gyara palour suna gamawa ana Kiran Salla. suna gama Sallah Aunty Nafisa ma tayi Nan suka zauna Aunty Nafisa ta fara Yi musu k'arin q'ur'anin da take musu kafin malamin su yazo sun iya dayake malami yake zuwa har gida ABIY ya d'aukeshi yake koya musu karatu ita da Amira Dan yanzu Amira tadawo gidan Dan bazata iya zama gidan su ba ba Aunty Nafisa ba Najma Ummy ba yanda ta iya sai hak'ura sukayi Amma kullun suna zuwa gidan rabi suna gidansu Amira rabi suna gidansu najma. Tana gama musu k'arin ABIY yashigo da gudu Najma kamar yarinya ta ruga ta rungumeshi tace "wellcome my ABIY"Murmushi yayi tare da yayi kamar zai D'agata ya kasa Aiko Nan suka kwashe da dariya duka palourn "ABIY ma dariya yayi yace kinyi nauyi daughter"cikin shagwab'a tace "ABIY ni saika d'agani"dariya yayi yace "Jiya ba yau ba daughtern ABIY bakiga kingirma"hararar wasa Aunty Nafisa tayi Mata tace ",Daga dawowarshi Baki bari ya huta Zaki fara ko''d'an turo Baki Najma tayi tace "to Aunty na barshi ya huta shikenan dai ko''dariya aunty Nafisa da Amira sukayi....✍🏻 *Dan girman Allah idan kun karanta kiuyimun sharing fisabilillah* *GOD WE REPENT* 🤲🏼 _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 _____________________________________ *Writing by*✍🏻 *Hajara L Sadeq* *Miss Hajo*🖤 _____________________________________ https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *FREE BOOK*📒 _____________________________________ *PAGE 13 & 14* _____________________________________ Bayan aunty Nafisa tayiwa ABIY sannu da zuwa rakashi tayi d'akinshi tare da taimaka Mai yayi wanka Sai Sanya Mata albarka yake Nan suka fito sukayi dinner d'insu gabak'i Dayansu gwanin sha'awa. Saida Najma da Amira suka Kara yima ABIY magana akan koyan driving d'in Nan ya shaida musu Monday su shirya zai kaisu makarantar koyo 2 weeks sun k'ware murna gurin Najma da Amira ba amagana aunty Nafisa ce tace. ''Allah ABIY Kai kake D'aure ma yaran Nan gindi duka nawa suke 16years in Banda iyayi irin nasu zasu fara wani driving"Bata Rai najma da Amira sukayi Najma tace "Aunty kullun saiki dinga Mana kallon yara bayan mu manya ne university fa zamu shiga. "Hararar wasa Aunty tayi tace "Ina girman yake Wanda har yanzu Shan yatsa kike"dariya Najma tayi tace "ai yanzu nadaina ko my ABIY"Murmushi ABIY yayi Mata yace "gaskiya ne daughter yanzu kungirma kunzama manyan yara "dariya sukayi Najma tana jin dad'in yanda ABIY ke kod'asu. Ranar Monday kamar yanda ABIY ya fad'a haka yaje yayi musu registration a makarantar koyon driving hankali kwance aka fara koya musu Dan a ranar ma sun iya abubuwa sosai. *NIGERIA*🇳🇬 *KADUNA* Farin matashin saurayine Wanda a sheekaru bazai wuce shekaru talatin ba kykkyawane ajin farko farine irin farin Nan Mai kyau ga bakin sajenshi Daya k'ara fito mashi da kyawunshi duk inda karshen kyau yake tofa Yakai akirashi Dashi gashi da murdaddan jiki Ga fad'addan k'irji. Sanye yake cikin k'ananan kaya sunyi mugun k'arb'arshi tuk'i yake cikin nutsuwa yazo daidai wajen Bada hannu an tsaidashi waigawar da zaiyi ya hango Sa'adatu na driving itama an tsaidasu gefenta ya hango khairat. "what khairat da Sa'adatu watau duk kashedin da nayiwa yarinyar can na ta rabu da waccen Yar iskar bataji ba kenan dandanan Ranshi yayi mugun b'aci yau shikadai yasan irin rashin mutuncin da zai kirtawa khairat idan suka koma gida Mai rabashi da ita sai Allah saboda a duniya babu abunda ya tsana sama da ya hana mutum abun sannan ya aikata a ganin shi wannan karshen raini ne. Ana Basu hannu Kai tsaye gidansu dake G R A ya nufa daidai wani katafaren gida Mai matuk'ar girma da tsaruwa Wanda kaf ilahirin manyan manyan gidajen area ya keresu a kyau da tsaruwa horn yayi security d'in bakin k'ofar suka wangale Mai gate Yana shiga katafaren parking space din gidan ya nufa Wanda tamk'e yake da manya manyan motoci na alfarma. Fitowa yake cikin takun k'asaita kallo d'aya zaka Mai kasan ranshi yayi k'ololuwar b'aci Kai tsaye part d'in aunty Amarya ya nufa Yana danna belt Wata kyakyawar yarinya da Baza wuce shekaru hud'u ba ta fito tana kallonshi tayi Murmushi tace ,"sannu da zuwa Yaya"yawwa sannu fena ya fad'a Yana Kama hannunta suka shiga. Zaune ya iske Aunty Amarya a kan sofa sanye da glass medical cikin shigarta ta alfarma kallo d'aya zaka Mata kaga chikkar Yar boko da gayu tana duba wasu takaddu Jin sallamarshi yasanyata d'agowa tare da fad'ad'a fara'arta tace. "Likita bokan turai har andawo kenan"wallahi ko aunty nadawo Nakwaso gajiya Allah sa akwai fruit salad ya fad'a Yana zama kan sofa" Murmushi aunty Amarya tayi tace "Sannu son daga gani kashawo gajiya ai Aikinku ai ladar ku Allah ne kawai zai iya biyanku sannan tace "Ai fruit salad kodan saboda Kai dole na ajeshi sannan tace "fena jeki kan dining ga Jug chan daukoma yayanku. "Allah sarki my aunty shiyasa nake sonki Allah barmanake Auntynmu"Murmushi tayi tace "amen son" bayan fena ta d'auko Mashi fruit salad d'in cikin nutsuwa yagama Sha sannan ya tashi yace Naji amfara Kiran magriba bari naje nayi salla na wuce b'angaren umma Murmushi kawai tayi tace Agaishesu. Yana fita masallacin gidan yaje ana gama Sallah b'angaren Umma ya nufa dubawa yayi ko zaiga motar dasu khairat suka fita da ita kosun dawo Yaga basudawo ba hmmm yafad'a Dan shi kad'ai yasan irin rashin mutuncin da zaiwa khairat danshi Babu ruwanshi da Sa'adatu duk iskancin da zatayi tayi ita kad'ai Amma bazai yarda Ya zuba Ido ta lalata mai k'anwa ba. A palour ya tarar da Umma tana kallonshi ta kauda Kai tare da Jan tsaki har k,'asa ya tsugunna yace "umma Ina yini"Tsaki ta Kuma ja tare da juyowa tace "da ban wuni ba ka ganni eh *NAJIB* nace Ina buk'atar gaisuwar ka ne Watau har waccen matsiyaciyar juyar mayyar tafini daraja da matsayi a wajenka saika fara zuwa gaisheta tukwana ni to bana buk'atar gaisuwar taka Ka Koma wajen uwar taka Ka had'a Mata da tawa bana buk'atar gaisuwar taka maza Koma wajen uwar taka *NAJIB* kaima na barmata ta zama uwarka .......✍🏻 *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *GOD WE REPENT* 🤲🏼 _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 _____________________________________ *Writing by*✍🏻 *Hajara L Sadeq* *Miss Hajo*🖤 _____________________________________ https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *FREE BOOK*📒 _____________________________________ *PAGE 15 & 16* _____________________________________ Dukanku na hakura daku fad'a kawai take Inda ta shiga ba tanan take fita ba shidai NAJIB yayi shiru dan Idan da sabo ya Saba da fad'an Umma harta gama fad'an ta baice uffan ba tunda ya bata hak'uri sau d'aya Bai Kuma magana haka tagama ta gaji Dan kanta Murmushi kawai yayi yace "Umma zanwuce Saida safe Bata ko d'ago ta kalleshi ba har ya wuce. Koda ya dawo daga isha 'i Saida ya hanga ko zaiga motar dasu khairat suka tafi da ita Amma baigantaba duba agogo yayi Yaga har 9 "shikadai yasan irin hukuncin dazai yankewa khairat. Washegari around 7am ya fito cikin shigar k'ananan kaya da sukayi mugun karb,'arshi yayi bala in kyau bayan yaje ya gaishe da Umma dukda ciki_ciki ta amsa Yana Shirin shiga Mota ya hango Aunty Amarya ta fito da alamar wajen aiki zataje. Karasawa yayi har kasa ya gaisheta ta amsa cikin fara'arta motarta ta shiga ta wuce Shima motar ya shiga a bakin gate ya tambayi security d'in akan Saida yaushe su Sa'adatu suka dawo d'an Jim bala yayi yace "Gaskiya inaga lokacin 12 ta kusa"bai bashi Amsa ba ya wuce Yana Jinjina sakacin da umma ta tarka har 12 yara na waje ko a kanta. katafaren clinic Ne Mai matuk'ar tsaruwa da girma Yana Daya daga cikin manyan asibitocin da ake ji dasu a jijar KADUNA. Saboda akwai k'wararrun likitoci cikinshi *N.A.N.SPECIAL HOSPITAL KADUNA* tun daga shigowar motarshi tun kafin ya fito ake mik'omai gaisuwa d'aga musu hannu kawai yake Har ya shiga office d'inshi gaisheshi ake. Zaune yake.yana wani bincike a laptop Habib ya shigo d'ago kanshi kawai yayi yamaida ga Aikin da yake tsaki NAJIB yaja yace ,"mutum sai d'an banzan miskilanci dariya ma mutum bayayi Dan mugun Hali sai Jan aci kamar mace "ko kallonshi najib baiyiba Dan yasan dashi yake Saida yace "Akwai patient da za ayiwa aiki yanzu sai sannan Yad'ago yace "okay kuje kushirya ganin Nan zuwa "NAJIB ne yace "Okay Amma abokina Kamar yau da abunda ke damuka" "Me ka gani inji NAJIB"kawai naga kamar ranka a b'ace "Bakomai Cewar NAJIB sannan ya tashi Dan yayi Shirin Shiga aikin. 4pm ya dawo gida Kasancewar yau ba ba ayi aiki da yawa ba Yana dawowa bayan ya watsa ruwa Kai tsaye b,'angaren Umma ya nufa Yana shiga palour yadanyi Murmushi yace ,"Ummana sannu da hutawa"itama Dan Murmushi tayi Dan bazata iya fushi da first born din nata ba "tace yawwa har andawo ya Aikin alhmdllh Umma to Allah ya tsare ya Kara karkun Kai amen ya fad'a dan yaji dad'i saukowar tata da wuri dukda sun Saba irin haka Kuma ta sauko. Sa'adatu ke gaisheshi ko kallon inda take baiba bare ta sa ran ansawa Hakan ba k'aramun ciwo yake Mata ba tarasa me tayiwa Yaya NAJIB ya tsaneta haka gashi ita.kuma.har kullun wutar sonshi k'ara ruwawa take a cikin zuciyarshi Umma ce tace "Uban bakin Hali bakaji Yar uwar ka na gaidaka ba shi haushi ma yaji da Umma ta kirata da Yar uwar shi Bai amsa Mata ba sai cewa yayi"Ina khairat yafad'a Yana kallon Sa'adatu Babu alamun wasa a fuskarshi "Ta na d,'aki ta fad'a Dan taji dad'in Tambayar tata ma da yayi a zuciyarta tana tsoron kome zaiwa khairat yake tambayarta Dan tasan Daya tambayi mutum tofa laifi ne. Tashi yayi ya nufi bedroom d'in su khairat A kwance ya sameta tana waya Daman ya nad'e belt d'inshi Aiko ya zaro batayi aune ba tafara Jin saukar belt ihu take baimasan tanayiba zuba Mata kawai yake tako ina. Nan su umma sukayo dakin Jin ihun da khairat dasukajiyo "salati Umma Tayi tace "uban Me ta maka Dan ubanka zaka haumun d'iya da duka "baimasan Umma nayiba laftar khairat kawai yake rikeshi Umma ta fara tana karka kashemun y'a NAJIB Amma baima saurareta ba Dan yau saiya koyawa khairat hankali kuka.umma ta fàshe dashi tace "NAJIB ka hada Dani ni zaka daka ba itaba Saida khairat ta Suma Nan Umma ta buga K'ara Nan ne NAJIB ya k'yaleta sai huci yake Bugunshi da hannu Umma ta fara tace ka kasheta hankalinka ya kwanta da gudu sa adatu taje ta d'auko ruwa ta yayyafa Mata dandanan ta kawo ajiyar zuciya tana daga Ido tafara kuka tana "Yaya Dan Allah kayi hak'uri ta fad'a tana boyewa bayan sa,'adatu. Umma ce tace ficemun daga da'ki NAJIB ficemun da ganin ko Kuma Nima dukan nawa zakayi dakayimun tsaye "kiyi hak'uri Umma zan fita sannan ya Koma kallonshi gurin khairat yace "Wallahi kad'an na Miki mudddin bazaki chanza haliba nafara jibgarki kenan kamar jaka.a gidannan sannan ya gallawa Sa'adatu harara yace "ke Kuma wallahi daga yau na k'ara ganin kin fita keda khairat ko wani a gidannan saina Miki abunda yafi nata daga yau na rabaki da ita Babu ita Babu ke ko d'aki na raba muku kuma wallahi na Kuma Ganin Wata mu'amula ta shiga tsakanin ku ni kadai nasan irin. Hukuncin da zan yanke muku ke Kuma khairat bakin get ma na samu labarin kin lek'a hmmm kinsan sauran. "Salati Umma tayi tace "shikenan Shima an raba ni dashi To wallahi baka isaba baka isa ka rabata da Yar uwata ba ,tunda kai baka da kirki bakada mutunci, shege Mai irin halin ubanshi da mugun Hali to ya tsaya iya kanka Amma baka Isa ka hana sauran y'ay'a na zumunci da Yan uwansu ba tunda kai bazakayi zumunci dasuba tofa baka Isa ka hana sauran suyi da Yan uwansu ba Karyarka shege salamamme waccen y',ar iskar tsinanniyar juyar mayyar ta cinye Maka kurwa kaida salammamn ubanka yanda ta gama da ubanka shine kaima yanzu ta had'a dakai. sannan ta fàshe da kuka tace "Allah ya isa tsakani na.dake Amina kin rabani da mijina da d'ana jaraba kawai Umma take Inda tashiga ba tanan take fitaba NAJIB ko ranshi yayi matuk'ar b'aci Yana son gyarawa kannanshi tarbiya umma tana daure musu gindi ita kawai kishi ya rufe Mata Ido komai saita daura wa aunty Amarya itada ba ruwanta ranshi a matuk'ar bace kamar zai tashi sama ya nufi part d'inshi zuciyarshi na mashi radad'in sauyawar halin Nan na Mahaifiyar shi Kuma yasan Babu Mai zuga Umma irin Aunty asiya (Maman sa'datu) Babban takaicinshi yanda aunty asiya ke juya Umma itace kanwarta Amma sai abunda tace Mata Kuma yasan ba son tsakani da Allah sukewa Umma ba ta ciki na ciki gashi Umma tak'i ta fahimta zurmiyata kawai suke tak'i ta fahimta Hakan yasa ya tsani aunty asiya da diyanta saboda juya mai da hankalin uwa da sukayi. Nan Umma da SA adatu dukda sa adatu ta tsorata Dan tasan halin Yaya NAJIB ya Kama mutum Jibgashi yake kamar Dabba gashi tasan baida wasa haka yasa duk ta tsorata Umma ce tace "kyaleshi Bai Isa ya raba ki da yar uwarkiba sannan tace taimaka mata Ki gaggasa Mata jikinta zanje nadawo kuka kawai khairat take Dan ta jibgu ba kad'an ba Umma ko fuuu da d'auki makullin mota Kai tsaye gidan Asiya ta nufa. Tana kuka tace "Asiya kina gani Shima NAJIB din ta raba ni dashi Nan tana kuka ta kwashe komai ta fadawa kanwar tata. "to ai laifin kine aunty Jidda nace Miki ga inda zamuje a fitar Miki da wannan annobar Amma kin'iki to ai ga abunda nake fad'a Maki Nan kinaji kina gani Suma sauran khairat da Khadijar zata mallake mikisu"Gaskiya asiya yanda kikeso din bazanyu ba ko bakinciki zai kasheni bazan sabawa mahallicinna ba Kede kawai ki kawo Wata shawarar ni wallahi fena ma nakeson karb'owa tsorona kawai Kar Alhaji ya samu labari Dan wancen Karin Kinga irin wulak'anci da yamun". Tsaki asiya taja a Zuciyar ta tanajin haushin yanda har yanzu Umma tak'i amincewa da zuwa wajen malamin ji take kamar ta mangareta Dan haushi saboda tana ruguza Mata Shirin da take ''to tsaya ta k'wace gidan ita Bata Haihuwa ke ki Mata Haihuwa Nan asiya tayi ta zuga Umma akan ta amso Fena Shikuma NAJIB ta rabu dashi akwai tunanin datake nashi Mai saukine Saida Asiya ta zuzzuga Umma sannan Umma tabaro gidan da niyyar kome zai faru ya faru Amma saita amso Fena Kuma tasan matakin da zata d'auka akan NAJIB. *INDIA*🇮🇳 *NEW DELHI* Najma ce kwance ta d'ora kanta Kan cinyar aunty Nafisa tana gyara Mata gashinta Amira.kuma tana kitchen tana girki Dan Aunty Nafisa yau ta tashi batajin dad'i ABIY ne ya shigo "sannu da zuwa my ABIY" yawwa *NAJMAT ABIY* D'ina sannan aunty Nafisa tace "sannu da zuwa Dear"yawwa Momyn Najma ya jikin dasauki tafad'a "ko zamuje asibiti dai""Murmushi tayi tace ". a a a dear dasauki fa"to Allah Kara sauki Sweetheart"ameeen inji Aunty Nafisa. "ABIY ne yace wa Najma Albishirinki daughter"goro Amira tafara tana fitowa Dariya ABIY yayi yace "yawwa daughter kezan farawa Albishirin ma Cikin shagwab'a Najma tace "ABIY nid'infa "Amira ce tace "yawwa "ABIY ni Zaka fara bawa"to shikenan bari nabaku a tare ya fad'a Yana mik'a musu admissions. Suna dagawa sukaga admissions ne ihu suka buga a tare da da rungume juna da daka wani uban tsalle A tare ganin sunan makarantar da ABIY zaikaisu bakinsu game sukace *GOLGOTIAS UNIVERSITY GREATER NOIDA* Ba k'aramun surprised d'insu ABIY yayi ba Basu taba tunanin zai sama musu admissions a wannan katafariyar makarantar Mai mugun tsada wadda ta d'iya shuwagabannin k'asashshece rungume ABIY sukayi Tare da fara sambada Mai albarka. Duk sun rude Dan murna Aunty Nafisa dariya kawai take musu tace,"Gaskiya yau sai an had'a walima a gidannan"aunty ai dole yau ayi walima agidannan inji Najma Tafada tare da da Kara rungume ABIY tace I Love you so much my I ABIY I love you more my ABIY Allah Saka ka a ALJANNA Allah Kara Maka ARZIK'I Ameeen daughtern ABIY ya fada Yana Shafa kanta ranar haka suka yini cikin farinciki Dan Najma a iya rayuwarta ita da Amira Basu taba shiga farinciki irin na yau ba........✍🏻 *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *_Miss Hajo ce_* 🤙🏿 [10/2, 1:37 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* ____________________________ *PAGE 17 & 18* ____________________________ *NIGERIA*🇳🇬 *KADUNA* Washegari kamar yanda Umma ta Innata amso fena haka taje b'angaren Aunty Amarya ba ko Sallama ta banka k'ofar dakin cike da. Masifa da bala'i tace "Ina kike Yar gidan matsiyata "fitowa tayi daga bedroom d'inta tare da yin fara a tace "Aunty lafiya". Tsaki taja cike da bala I da masifa Tace "lafiya ta Isa ta kawoni wajenki Amina, Y'ata nazo amsa tunda ba uban wani yayimun nak'udar haihuwarta ba ,"Kasancewar Amina ba mace ce Mai son fitana ba kawai cewa tayi "Amma saiki bari Wanda ya bani ita yaZo ya amsheta da kanshi shiyake da alhakin Amsar Fena ba ke ba tunda shiya bani ita da hannunshi ba keba", "Kutumar ubannan Amina harkin samu bakin da Zaki fad'i mun magana to wallahi bari kiji yau Babu wani mutunci a tattare Dani wallahi gwara tun Muna mu biyu ki fitomun da y'ata tunda bake kikamun nak'udar haihuwarta ba ko ke kika haifamun ita kujimun karfin hali''Umma tafad'a tana huci. "Aunty Amarya da Abun ya kâita bango daki ta shiga ta tattarowa Umma kayan Fena tana kuka saboda ba k'aramun Shak'uwa sukayi da Fena ba Tana son yarinyar Amma dole ta hak'ura da ita kodan Tijarar uwarta Saida ta gama tattara Mata kayan ta sannan ta sungumeta a kan bed tana ma bacci lokacin A palour ta tarar da Umma rik'e da k'ugu sai jijjiga take Kayan ta mik'a mata tare da Fena tace "ga y'artaki Ina fatan d'aga ita daga ita Babu Kuma wani abun ". Tsaki taja tare da wartar Fena tace "idan fitsari banzane kaza tayi mugani Mana "fuuu tayi waje da yarta Fena ko sai kuka take Dan ita batason bin Umma tafison zama wajen auntynta Suna fita Nan ta durk'ushe gurin tare da sakin marayan kuka Mai tab'a zuciya. Sanye yake cikin lapcoat ba k'aramun kyau sukayi mashi ba zaune yake a office d'inshi Yana Tunanin yanda zai bullowa lamarin khairat dangane da mu'amular su da SA adatu Dan idan yayi sake Yana hango babbar marsala Habib ne yashigo saida ya tab'a shi sannan ya dawo cikin hayyacinshi "b'ata Rai yayi yace "zaka fara ko"dariya Habib yayi yace "waini abokina kwana biyu sai tunane tunane kake ko ka fad'a soyayya ne" tsaki najib yaja yace"Matsalata dakai kenan sa Ido wallahi , kana ganin har akwai macen da ta Isa na sota a fad'in duniyar Nan Babu ita wallahi wannan shirman soyayyar sai ku "yafad'a Yana Jan tsaki. Dariya Habib yay yace "Hmmmmm haka kake fad'a kullun harna k'agara naga lokacin dazaka fad'a soyayya irinku masu cika bakin Nan Kune.masuyiwa Mata kuka"Duk inda k'uluwa take najib ya kulu Jin abinda Habib yafad'a yanda yakejin da kanshi har akwai mace data Isa a fad'in duniyar Nan ya furtawa kalmar Yana sonta Jin haushin maganganun abokin nashi ya sashi tashi dan ya Bata Mai Rai yace "yallab'ai ni zan wuce saika barmun office ''yafada Yana kichin-kichin da fuska". Dariya Habib yayi ganin yanda ya daure fuska lokaci guda sannan yace "yau Kuma ni kake.kora najib"tsaki yaja sannan Tafita tare da tilla Mai makullin Office din yace idan kagama shirman naka saika rufe mun sannan ya fice dariya Habib yayi Yana Jinjina Hali irin na najib. Kai tsaye najib gida ya nufa Kai tsaye b'angaren Umma ya nufa a palour ya tarar da ita sai sa adatu gefenta sai khairat na gefe tana latsa waya suna ganinshi gaban su yafadi musamman Khairat Dan yanzu ta Kara tsorata da Yayan nata . Bayan ta gaishe da Umma ta amsa mashi cikin sakin fuska Nan khairat da Sa'adatu suka gaishesu ko Kallonsu baiyiba saima.latsa wayarshi da yake. Khairat ce ta tsorata ta maza ta tashi har tafara hawa stairs yace "dawo ki zauna"Har lokacin Bai d'ago kanshiba kamar bashi yayi maganar ba. Sim sim ta dawo ta zauna "Saida tayi minti biyar da zama sannan Yad'ago fuskarshi Babu alamun wasa yacw " Ina fatan kina sane da dawowar Abba ranar Friday"Daram gabanta ya fad'i tace "a a Yaya"to ai yanzu kinsani Kuma ki shirya da Shirin zan sanar dashi duk rashin tarbiyarki da lalacewar da kike Neman Yi Kuma kishirya na Baki sati biyu daga Nan zuwa sati biyu ki fito da mijin aure idan ba haka ba zan aura Miki Koma wanene ko Mai gadi ta kama shizan aura Miki *Yana gama fad'in haka ya ta tashi ya fice a palour. Yana fita kuka khairat ta fàshe dashi wiwi tare da rungume Umma tace. " nashiga ukku Umma Dan Allah ki hanashi Umma wallahi ni Babu abunda nake na banza wallahi Umma banason aure Dan Allah kibashi hak'uri yafasa Sambatu kawai take Umma tana lallashinta tace "insha Allahu Babu abunda zaimiki karki damu "sa adatu ce ta taso tare da dafa ta tace "sorry sis insha Allahu da wasa yake"bangajeta tayi ta karfi tace "da Allah ni sakarni duk ba ke kika jamun ba ke gakinan hankalinki kwance ni kin barni Da jaraba "Tsaki Sa'adatu taja a Zuciyar ta tace kedai kika sani banxa sannan ta cewa Umma zataje gaishe da mamanta "kigaishemun da ita Kuma kice mata gobe Ina son ganinta Dan Allah "to sa adatu tafad'a sannan tabar gidan Kai tsaye gidansu dake rigasa ta nufa madaidaicin gidane Mai Dan kyau ba laifi Babu get sai k'ofa da Sallama ta shiga . Babanta ta iske Yana wanke wanke mamanta Kuma tana zaune tana Shan kankana B'ata Rai tayi tace "wai mama har yaushe xaikibar baba ya huta ne yanzu fisabilillah abokananmu suka shigo ai abun kunya ne.wlh. Sannan ta juya wajen babanta tace baba bar wanken_wanken Nan tazo ta k'arasa Yana karkarwa yace "A a a sa'adatuna ba ita ta Sanya niba nice naga ta gaji na tayata Ai Sunna ce sa 'adena ki bari ta huta ta gaji,''duk Yana karkarwa yake fadar maganar Nan "Girgiza kai kawai Sa'adatu tayi Nan mamanta fuuu taja hannunta sukayi d'aki. "B'ata Rai sa'adatu tayi tana fuskantar maman tata tace "Mama yanzu fisabilillah haka zakiyi ta juya baba kamar wani d'anki"bansan iskanci Sa'adatu ni sa'arkice wai duk maganar datazo bakinki ki fad'a mun bansan fitsara inbanda na gama da uban naki da kinaji kina gani zakiji ana ayyiri,an yiwa uwarki kishiya,shine hankalinki zaikwanta ko "asiya ta fad'a ajiyar zuciya Sa'adatu ta sauke tace "shikenan mama abar maganar "dadai yafi Cewar Asiya. "daman mama magana akan Yaya najib ce ta kawoni, mama kince kinsan yanda zakiyi ya aure ni har ya so ni, Amma kin kasa komai, Kuma kinsan duk duniya Babu Wanda nake so sama dashi please mama Dan Allah kiyi abun Yi wlh kullun tsanata k'ara ninkuwa take a cikin zuciyarshi nikuma kullun soyayyarshi k'ara ruruwa take a cikin zuciya" ta Ida da ida fad'a tana kama.hannun Maman tata. "Haba sa'ade na karki damu aikinsan komai a hankali ake.binshi kisa a ranki kin auri najib kin gama nan da d'an wani lokaci"Sanyi Sa'adatu taji a zuciyarta Dan tasan Mamanta tafad'a magana saita cikata ko ta halin k'ak'a Hakan yasanyata jin sanyi a zuciyarta. Sa'adatu ce tace "yawwa mama na manta ban fada maki ba kince idan Abba zaizo na fad'a Miki to jibi Friday zaizo" sannan ta Bata Rai tace "Mama Kuma Wai Yaya najib yace Khairat zaiyiwa aure please mama kisa Umma ta hana kinsan Ina bak'incikin khairat tayi aure batare da tayi cikin shege ba Umma ta goya"Dariya asiya ta kece da ita ta mugunta tare da shewa tace "shegiya kinyo halin uwarki Baki d'auka a k'as ba karki damu sa'adane na duk zansan abunyi Bada jimawa ba "dariya Sa'adatu tayi tace ''sai mama "Asiya ce ta d'auko Mata wasu layu da magunguna tace "tasan yanda zatayi ta tutsa layun k'ark'ashin gadon.umma duk yanda zatayi tayi wannan Aikin tofa tayi sannan tabata wani magani tace ta dinga barbad'awa Umma a shayi kullun Harya k'are"Saida dai suka gama k'ulle_k'ullensu sannan Sa'adatu ta Koma gidan Da niyyar aiwatar da aikin da mamanta ta sanyata. *INDIA*🇮🇳 *NEW DELHI* Najma ita da Amira shirye shiryen fara zuwa school kawai suke duk sun shiga busy kullun suna shopping sayayya Dan abiy ya D'aure musu gindi A T M ma ya Basu su saya abunda sukeso sukam mutanen namu kunsan ba wasa Aiko jibgo kaya kawai suke kamar ba gobe Dan sund'au Alk'awarin harsu gama school din bazasu maimaita kayaba. Aiko kaya kawai suke jibgowa yawaicinsu duk manya manyan dogayen riguna ne sai top sai English wears had'addu na gayu ba mtsatsuba Wanda zasu iya yawo ma dasu hankali kwance Abba har fad'a yakewa Abiy akan ya sake musu Kud'i da yawa"shidai Abiy Saidai yayi Murmushi Dan indai akan farincikin Najma ne zai iya Sadaukar ma da dukiyarshi gabak'i d'aya bare wannan d'an Abun danshi d'an Abu ma ya d'aukeshi. Yauma kamar kullun sundawo daga shopping Amera na driving d'insu Najma sai sauke ajiyar zuciya take a cewarta ta gaji har suka isa gida bayan sunyi parking a had'ad'd'en parking space din dake gidan Abiy Kai tsaye parlour suka nufa bayan sunsa ma'aikatan gidan su kwaso musu kayansu su shigo musu dashi. Tun a palour suke jiyo kakarin aman Aunty nafisa ta gudu suka nufi toilet din da suke jiyowa Nan suka iske Aunty Nafisa Duk ta galabaita iya rud'ewa Najma ta rude Dan hada kuka Saida Aunty nafisata lallashe tace dasauki sannan ta samu taji dan sanyi. Saida suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan Najma ta maza takira ABIY cikin k'ank'anin lokaci Abiy ya iso Kai tsaye asibitin dake Estate din suka nufa gwajin farko ya tabbatar da Aunty Nafisa nadauke da juna biyu. zo kuga murna wajen Najma kamar ta zubda ruwa a kasa Tasha Aunty Nafisa ma tayi farincikin Samun cikin nata tsawon shekaru takwas da aure ta godewa Allah sosai Abiy ma yayi farinciki sosai Najma ko hada rawa Tundaga ranar da aka Ce aunty Nafisa nada ciki Najma ta d'auki son duniya ta d'orawa cikin ga wani tattalin Aunty Nafisa da take ko kuda Bata barin ya tab'a ta . Abun har mamaki yake bawa mutane yauma kamar kullun bayan sati biyu aunty Nafisa taji sauki sosai Ganin Najma duk ta hanata aiki Aiko tana ganin sun fita shopping Dan saura kwana biyu su fara attending lectures, Aiko tana ganin fitarsu tayi Maza ta Afka kitchen hada sauri ABIY har dariya yake Mata tace "aikasan Babyn tawace y'ar rigima gwara na maza nayi sauri nayi kafin su dawo"dariya ABIY yayi yace Aiko kiyi sauri karta ritsaki Dan Babu ruwana". Aiko su Najma Basu jima ba suka dawo tana dawowa taga Abiy a palour yana ganinta yayi Dariya"najmace tace. Abiy Ina Aunty''kitchen ya Nuna Mata wara idanu tayi tace "What ABIY kitchen fa Bana hana ta aiki ba ohh shine Dan mun fita tashiga kenan Daman haka take Mani idan munfita kenan Aiko zan dinga kunnan ctv camera". Abiy da Amira me zasuyi inbanda Dariya Ummy ma da shigowar ta kenan taga yanda Najma ke iyayi dariya tayi b'ata Rai tayi tayi hanyar kitchen din zama Ummy tayi tana dariya tace ''bari muyi kallon game din uwa da y'a Dan tazo K'ara duba lafiyar k'anwar ta,ta''sai sannan Abiy ya lura da ita gaisheta yayi har kasa ta amsa cikin fara a. Najma na shiga kitchen amshe Kayan aikin tayi tana Bata Rai "tace "Daman Aunty kenan wayau kikemun idan natafi bayan na hanaki Komai to daga yau bazaki sake mun wayau ba Sannan ta kashe gas d'in tace tunda bakison kuku na Aikin shikenan daga yau ba a Kara shiga kitchen order za a dingayi. "sorry my daughter baxan sake ba kinji yaudinma naji saukine shysa"haka tayi ta lallashinta tun a kitchen har suka fito suna fitowa Najma ta kulle kitchen din ta zare key d'in mamaki duk yagama.kama Aunty Nafisa tanaso tayi dariya tana tsoro lallashi kawai take har suka fito. Suna fitowa Aunty Nafisa tacewa Abiy"Abu Najma Dan Allah ka tayani Bata hak'uri tafa rufe kitchen din"dariya ABIY yayi yace ba ruwana kunfi kusa "Dariya Ummy kawai take Najma ko murtukewa tayi tace ,"Abiy daga yau baza a sake girki a gidannan ba sai Aunty haifamun babyna Idan tana shiga kitchen zafin zaidinga Shafanmu k'ani Kuma ma bak'i zaiyi Daga yau order za adinga Yi . "dariya Ummy tayi tace "su Najma manya daga shiga kitchen sai baby yayi bak'i"Bata Rai tayi cikin shagwab'a tace "Ai Ummy na hanata tak'ijin magana ta shiysa"mezasuyi inbanda Dariya Dan har Aunty Nafisa dariyar take Abiy ko tausaya Najma yayi a zuciyarshi yace ,"Allah sarki my Najma ke Baki Samu kwantar wannan gatan daga mahaifiyaba Amma kina bawa k'anin dako duniya baizoba A zuciyarshi yace "har abada Babu y'ar da zan Haifa namata kwatankwacin soyayyar danake Miki my najma.ranar dai haka aka yini ana dramar aunty Nafisa da Najma yau ta kama Monday su Najma zasu fara attending lectures a School....✍🏿 *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *GOD WE REPENT* 🤲🏼 *_Mhiss Hajo ce_*🤙🏿 [10/5, 9:47 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *Shafin Nan sadaukarwa ne GAREKI Maman nusaiba my momcy kiyi yanda kikeso dashi my lovely mom k'aunarki a jini take Ki huta kiyi shekaru irin na dabinon*😝 ________________________ *PAGE 19 & 20* ________________________ Tun Asuba da suka tashi Basu Koma ba suka fara shiri Dan 7 am lectures din bayan sunyi wanka Najma ce zaune gaban mirror Tana tsara kwalliya Kasancewar ita simple make up take Aiko Nan tafara tsarawa Had'addiyar light gira tayi sai had'addiyar hodar datayiwa farar lallausar fatar ta kyau ta shafa sai Dan light jambaki dabai fitowa sosai ta goga wa iya zubilllahi shine abunda na ambata ba k'aramun kyau tayiba ita kanta Saida ta Yaba kanta tasan tayi kyau. Wata bak'ar Doguwar riga (Abaya) tasanya Mai shegen kyau jikinta duk tsararrun stones ne rigar tayi iya haduwa Sannan ta d'auko belt din rigar ta nadashi nadin larabawa sak Najma tafito balarabiya ita ba balarabiya ba ita ba bafullatana ba ita ba baturiya ba haka ba bahaushiyaba nama kasa gane da wata kala tayi kama Dan iya haduwa ta zubu. "wow tafad'a data Duba kanta a madubi ''gaskiya nayi kyau ta fad'a tana Murmushin Daya lotsarda dimple d'inta turarruka Kala-kala ta feshewa jikinta masu sanyi k'amshi Kasancewar Najma mace ce Mai son k'amshi Nan ta d'auko takalmin ta Mai Dan tudu ta sanya. Palour ta fito Dan Amira tarigata fita cikin takunta na k'asaita kamar batason ta taka k'asa "Wow daughter Ammafa kin had'u Aunty Nafisa tafad'a tare da tasowa tayi hug d'inta Murmushi Najma tayi tace thanks my mom Abiy ne ya fito Shima ya Yaba kwalliyarta Sannan suka jera ita da Abiy suka nufi hanyar dazai sadasu da inda driver yake jiransu bayan sunyiwa Aunty Nafisa bye bye. Suna Isa Abiy ya shiga Front sit Najma da Amira suka shiga back seat driver ya jasu ''jiyowa Amira tayi tace ''wow Dusti kinyi kyau"Murmushi Najma tayi tace ''thnks Dusti like you kema kinyi kyau"Murmushi Amira tayi tace "Ai bankaikiba haka sukaci gaba da hirarsu jefi jefi har Abiy Har suka isa makarantar. Saida Abiy ya tsaye aka gama musu komai da cike cike Sannan kowa yayi department d'insu Kasancewar ba course d'aya zasu karanta ba Najmat zata karanci permancy itakuma Amira Economic zata karanta. Tunda suka shiga school din kallo ya Koma wajensu musamman Najma wasu har tuntub'e suke Dan kallonta Tatafi da imanin su musamman samarin school din Hatta Yan Matan Saida ta burgesu. Mutane suna son tunkaranta hatta Mata suna son suyi friendship da ita Amma ganin yanda take Jiji dakai da daddaurewa Dan sun lura yarinyar tana ji da class bama kad'anba Basu tunkareta ba. Koda 2pm tayi tagama lectures d'inta bayan tafito Amira takira ring biyu tayi picking"Dusti Kun tashi kuwa tafad'a cikin cool vooice d'inta "eh Dusti ai tun 1 muka tashi harna Kira driver inama cikin mota "okay to ganinan tafad'a Dan tagane inda driver yayi parking kai tsaye chan ta nufa tana shiga driver yaja suka tafi. Haka rayuwa taci gaba Najma da Amira sun maida hankalinsu sosai akan karantunsu ba wasa musamman Najma Dan yanzu kullun cikin karatu take da bincike da course d'insu akwai wahala Harkar gabanta kawai take a school din samari da Dama sun kwata suna sonta masu kasada harsu tunkareta Amma ko kallo Bata ishesuba Dan kwata kwata soyayya Bata gabanta ita dai burinta taga ta kammala karatunta ta zama kwararriya Likita Kawa d'aya tayi tunda tashiga Mai suna Raliya Yar Ghana ce itama Dan taga tana da hankali da nutsuwa ga kuma itama karatu yakaita Hakan yasa suke friendship da Najmat Najmat Kam ba abunda zatace sai Alhamdulillah Dan tana ganewa sosai da sosai Dan kaf department d'insu yanzu haka ba Mai k'ok'arinta Dan ko tambaya akayi kowa sai kasa Bada amsa Amma Najma zata tashi ta bada Hakan yasa ko a class din suke ji da ita Dan tana mugun burgesu wasu har haka suke cewa ga kyau ga ilimi ga gayu komai ta had'a. Hakan yasa kowa yake jida ita tun Bata sakewa mutane fuska harta dawo tana sake musu saboda ganin yanda suke Nuna mata kauna Amma Bata sake musu irin dai wasan wannan da maza da mata suke tsakanin dalibai dadai sauran su a a a mu'amula suke Mai cike da tsafta yawaicima duk akan harkan karatunsu ce. *NIGERIA*🇳🇬 *KADUNA* Kamar yanda mahaifiyarta ta umarceta Haka sa adatu tayi hankali kwance batare da wani zargiba Dan tana da freedom a gidan Nan ko Ina shiga take bangaren Yaya najib ne kawai bama ta tarki tinkaraba dan Babu wasa. Yau Friday Abba yadawo daga china Babban danshi mafi soyuwa a wajenshi yakira ya d'aukeshi haka har suka isa suna hira gwanin Sha''awa Kasancewar Umma take.dashi ya sashi Fara nufar b'angaren Aunty Amarya. Yasamu tarba ta musamman daga wajen Amaryar tashi Dan Amina badai biyayya ba Hakan yasa Abba yake matuk'ar sonta Sai bayan magriba ya nufi b'angaren Umma . Khairat ce ta Fara mashi sannu da zuwa Tare rungumarshi Tana Mai sannu Nan ma sa adatu tayi Mai sannu da zuwa ya amsa Mata cikin sakin fuska Umma ko ko kallonshi batayi ba dan taga lokacin Daya shiga b'angaren Amina. "Uwar gida sarautargida" Abba yafad'a Yana zama kusa da ita bayan su khairat sun Basu waje murtukewa Umma tayi tace "Ba wani dad'in baki saika koma inda kafito''murnushi kawai Abba yayi Dan yasan halin mutumniyar Tashi indai akan Amina ne Nan dai ya basar yayi ta lallashinta har ya samu ta sauko Bayan sun Tab'a hira a palour Nan Abba yace yagaji baccci zaiyi daki Umma ta rakashi tare da jera Mai sannu Yana Sanya Mata albarka toilet ta shiga ta had'a Mai ruwa wanka shikuma yazauna kan gado Yana zauniya yaji kanshi yayi wani mugun sarawa dafe goshinshi yayi Dan wani juyamai yake Umma tana fitowa salati tayi tace Abban NAJIB lafiya ". Tsaki yaja Dan Yana ganinta yaji yayi wani mugun tsanarta tashi yayi yayi hanyar Kofa binshi Umma tayi tace Ina zaka Abban NAJIB ya Muna Zaune lafiya lokaci guda ka sauya"Tsaki yaja yace Karki sake ki biyoni jidda kawai ji nayi bazan iya kwana a D'akin Nan nakiba Ina ganinki naji kawai na tsaneki "ya fad'a Yana nufar Kofa kuka Umma ta Fasa tace ",nashiga ukku Amina Allah ya isa tsakani na dake nasan ke kad'aice macen da zata rabani da mijina Amina sakayyata dake sai Allah tsinewa Amina Umma kawai take. Abba Kai tsaye b'angaren Aunty Amarya ya nufa ita kanta tayi Mamakin ganin nashi Ganin Harya kwanta ya sanyata Mai magana akan wajen Umma yake ba yanda batayi dashiba ya koma yakiya karshe tsawa ma ya daka Mata ba arziki taja bakinta tayi shiru tare da komawa bedroom d'inta ta kwanta cike da tunannika. Tun daga ranar Nan Abba Bai Kara shiga b'angaren Umma ba Aunty Amarya Tasha wa azin da nasiha Amma a banzan Wata Rana kuka ta Sanya Mai tace Dan Allah ya taimaketa wannan abun da yake Yana k'ara ruruwar rashin jituwar dake tsakanin ta da Umma Karshe Chayai ta Kara Mai maganar Umma zai mugun Sab'a Mata saijan bakinta tayi shiru amma tana addu'a komene ya shiga tsakaninsu Allah ya daidaitasu. A haka har sati biyu b'angaren Umma duk ta rame abun na mugun damunta kullun cikin addu'a take Allah karkato Mata hankalin mijinta a zuciyarta kuwa tsanar Amina ce kawai Dan ita take da tabbacin tashiga ta fita ta rabata da mijinta da abundai ya dameta. Wata Rana ta shirya ta tafi gidan kanwarta Asiya Tana kuka ta kwashe komai ta fad'a mata asiya ko a Zuciyarta kamar ta tsala guda Dan farinciki Amma a Fili hada k'wallarta tace "wallahi Aunty Jidda Babu Mai rabaki da Alhaji sai Amina yanda Alhaji yake mugun sonki tunda kike dashi Bai tab'a Koda fushi dake ba Amma kiga wai har sati biyu Yana gida baixo inda kike ba,ai na fad'a Miki Amina muguwar Yar bin bokayece. "Nan dai Asiya tayi ta zagin Amina daga k'arshe tace ''yanzu mafita daya ce kawai tashi zakiyi muje wajen malam barau indai mukaje wajenshi magana takare "ta Ida fad'a azuciyarta tana adduar Allah sa ta amince. Jim Umma tayi sannan tace ""Gsky asiya kisamo Wata mafitar Amma wannan baxanyiba nayi Alk'awarin bazan tab'a shirkaba harna Koma ga mahaliccina,"a Zuciyar asiya ji take kamar ta shake Umma da haushi Amma a Fili tace to Shikenan Aunty Allah kawo Mana Mafitar amen Umma tafad'a sannan ta Koma gida asiya ko tana fita taja tsaki tace watau duk mugun cin Dana Baki har yanzu bakiyi lakwas ba Harkina da bakin yimun gaddama sannan tace ,"tunda Babban aikin yaci ai alhhmdlhh Sannan Tayi shewa tace shegiya kwanannan Zaki fara zawarci kinkusa fitowa Daga daularnan kina ganin ke ga matar Mai Kud'i Muna zuwa kina bamu dubu Dari dubu hamsin ai Wallahi saimun daidaice Koma mu fiki ai karyane ki fimu wlh......✍🏿 *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *_Miss Hajo ce_*🤙🏿 [10/6, 7:22 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *Shafin Nan sadaukarwa ne gareki sis quen pherdaus kiyi yanda kikeso dashi inajin dad'in sharhinki over love u wujiga wujiga*😅 _________________________________ *PAGE 21 & 22* _________________________________ Najib ne zaune a palourn Aunty Amarya suna fira jefi jefi Amma ya lura kamar da abunda ke damunta Koda ya tambayeta Murmushi kawai tayi tace ,,"bakomai son". Najib ne yace "Aunty Dan Allah wani taimako zakiyimun game da khairat,inajinka son "Saida ya Dan numfasa sannan yace ''Aunty bazan boye maki ba wannan sa'adatun da take tare da khairat ban yarda da tarbiyarta ba dukda tana Yar uwata Amma bazan bari ta lalatamun. K'anwa ba saboda Wata kusar tafi Wata Aunty yanzu na lura Khairat Kamar ba lokacin dawowa daga school take dawowa ba Kuma na lura Time d'in da take school Sa'adatu yawaici Bata gida Aunty Dan Allah kutaimaka mun muyi yak'in Nan tare Ina hango babbar matsala game da mu'amular su. Shiru Aunty tayi Dan a gaskiya bazaiyu ta b'oye Mai wani Abu ba Hakan yasata fito da gaskiyarta tace "Gaskiya zan fad'a Maka najib Amma Dan Allah karka dake ta akwai shawarar dazan baka tafi duka mahimmanci. "sannan ta d'ora da cewa"cikin satuttukan Nan biyu gaskiya yarinyar Nan Sa'adatu tana zuwa school a mota tana d'aukarta Kuma lokacin da zan dawo gida bana ganin dawowarsu Nima ban yarda da tarbiyarta ba Amma Aikin Nan Mai sauk'i ne khairat batayi gaurin da za a kasa lank'wasata ba Dan gaskiya Ina yimusu lectures sosai bantabajin ance ga matsalarta ba Amma ayi sauri a rabata da wannan yarinyar Dan zata iya gurb,'ata Mata tarbiya". "Innalillahi kawai najib ke ambata Dan Kanshi yagama daurewa Lallashinshi aunty Amarya tafara tace karka damu son Zan taimaka matuka Ai khairat y'ace a wajena zanbaka gudummawa sosai "yawwa Aunty inajinki Dan kaina yagama kullewa wallahi da khairat harararta nayi tabar Abu Amma zuwan yarinyar Nan nema take ta rikitamana family wallahi. "Allah kyauta kawai tace sannan tadora da cewa"zan kawo Maka time table d'insu Lokacin zuwa da lokacin dawowa kaga kasan lokacin 2zuwan ta da dawowa saika bawa driver Time table din kaima ka rik'e "> "Gaskiya Aunty kin kawo shawara Mai kyau Dan wlh da niyar aurar da ita nake Dan nagaji karatunma da barinshi zatayi wallahi" Murmushi Aunty tayi tace ,"sorry babban Yaya"sannan yace "Amma aunty shawarar Dana yanke zan maida ita gidan Hajiya da zama. ""Shikenan Magana ta kare abunda nake Shirin cewa kenan kamaida ita haka yafi dadai Nan dai suka cigaba da tattaunawarsu gwanin sha'awa kamar d'a da uwa. Kamar yanda sukayi shawara da Aunty Amarya haka ko akai yasa khairat ta had'a kayanta sannan yayi mata kashedin wlh tasake tafadawa sa'adatu ga inda zai kâita zaiya mugun Sab'a mata Umma da Abba Kawai yafadawa Abba ma yayi na am Umma kam cewa tayi Allah kiyaye Dan Bata da matsala da gidan hajiyarta. Sai da yasa ta had'o kayanta gabak'i d'aya Dazasu wuce Saida ya biya b'angaren Aunty Amarya Nan ta bashi turaren wuta da Turarruka masu tsada tace ya kaiwa Hajiya sannan ya gaishe Mata ita. A palour suka tarar da Hajiya akan carpet khady na Mata dannar k'afa da fara arta Hajiya ta tarbesu tace "yau inada manyan Bak'i kenan Masu bakin Hali biyu a gidana". Murtukewa najib yayi yace "ai Shiyasa na daina zuwa gidanki yanzuma sai na Koma ai"haba Mai gidan wasa ne fa Nina Isa sannunku da zuwa khairat ko sai murtukewa take tanajin haushin maidota gidan Hajiya da yaya najib yayi tadawo kurkuku kawai Dan Hajiya badai tsaro ba" harira bak'in halin ne Zaki fara ko Hajiya tafad'a tana kallon khairat,". Duk inda Khairat takai shak'uwa ta shak'u Dan ba sunan data tsana a kirata dashi irin real name d'inta a zuciyarta tace Nidai an cuceni da akasamun sunan Nan sunan Mahaifiyar babansu ce Aiko ta shaku tace "Kinga dalilin dayasa banason zuwa gidanki Nafad'a Miki bansson sunan Nan inbanda ke Babu Mai fadamun tafada tana tashi tanufi bedroom d'insu Nan tahadu da Yar uwarta kawarta Kuma sarat Aiko kankace me sun rungume juna suna hirar yaushe Gamo. Hajiya ko tab'e Baki tayi tace " kinji dashi Malalaciya sannan tace "Kai yanzu Najib haka zakayi ta zama ba Mata duba fa kaga sa'anninka wasu hada y'ay'a,najib yaushe zakayi hankali wai,Ace duk fad'in Matan k'asarnan kace ba wadda tayi Maka haba Najib kayiwa kanka fad'a kafin duniya tayi maka ni gaskiyace nake fad'a muku saikuji haushi ku tafi Kuna cewa ni fad'a a yau mai Maka fad'a masoyinka ne NAJIB wani Neman Mai mashi ma yake Amma ya rasa Dan Allah najib Kar nabar duniya Banga auranka ba ka haba Najib kamar Kai ace ko budurwa baka da ita ". Shiru najib yayi Yana sauraran Hajiya Saida tagama fadan ta hak'uri kawai Yabata yace "insha Allahu Hajiya Zanyi komai lokaci ne"sannan ya d'auko sakon Aunty Amarya Yabata Kuma yace tace tana gaisheki. "Allah sarki Amina yarinyar arziki wannan yarinyar Samun irinta sai an tona Allah dai ubangiji Yayi Mata albarka Yazaunar da ita gidanta lafiya ai Wallahi Jidda tayi sa'ar kishiya Amma malalaciyar Bata da mak'iyar da ta fita Ai Jidda yanzu nema take tafi k'arfina najib kadufa fa kaga Jidda Bata da Masoyan da sukafi makiyana Wanda basa kaunata basa kaunar Mai kaunata Haule. Da d'iyanta ,(uwar su asiya) Yanda ta d'auki Haule da daraja koni Dana dukursa na haifeta Bata d'aukeni da daraja ba fada kawai Hajiya take hada k'wallarta najib ko hak'uri kawai yake Bata sannan sukayi bankwana yanufi wajen aiki. Sa'adatu ta nemi Khairat ta rasa takirata tak'i d'agawa Taje school d'insu yafi a k'irga amma Bata Samun ganinta Hakan ba k'aramun dakula Mata lissafi yayi ba ganin dai ba alamun Nasara Akan Khairat yasanyata janye makaman aikinta. Tana kuka ta samu mamanta tace "Allah mama idan bakiyi maganar aurena da yaya najib ba Zaki nemi ni ki rasa haba mama nagaji wallahi nidai kawai ayi auran Nan kowama ya huta kuka kawai take . Asiya duk ta rud'e Hakan yasata lallashin Yar tata tare da shaida Mata gobe zataje gidan tayi magana da Umma Kawai Daman yanzu ne lokacin da take jira. Kamar yanda asiya tafada haka washegari Taje har gida ta samu Umma da maganar hada Auren najib da Sa'adatu Umma tayi na'am sosai da wannan Maganar Kuma taga dacewar Hakan a hadasu Auren zumunci Dan. Itama ta gaji da ganin Najib haka ba Aure Saida suka gama shawarar su sannan suka fito Umma ta rakota . Asiya ce ta hangi Aunty Amarya na Shirin shiga Mota Aiko da gudu tayi baya tare da boyewa bayan flowers gabanta in. Banda dufduf ba Abu da yake Dan yau da ace sunyi Ido hud'u da Amina Aida tata ta kare Saida taga fitar motar ta sannan ta fito tana huci Umma da abun yagama Bata mamaki ta lura duk tsawon zaman Amina a gidan Asiya Bata tab'a yarda suka haduba data ganta take boyewa. Tambayarta Umma tayi tace Anya asiya Babu abunda ke tsakaninki da Amina kuwa"basarwa Asiya tayi tace bakomai wallahi aunty kinsan nafad'a Miki mayya ce to tsoro nake karta cinye ni ,"Amma Aida mayyace asiya Dani da diyana zata fara lashewa kafin ku na waje uwa ubama Fena da tsawon shekaru ukku a wajenta ,"Cewar Umma "Aunty bazaki gane bane kinsan ni tsoron mayu gareni tab'e Baki Umma kawai tayi ba don ta yarda da zancen Asiya ba Cewar Amina mayyace Dan idan mayyace ai su zata fara cinyewa kafin na waje asiya ko harta fita gabanta fad'uwa yake Dan yau ta auna rijiya da baibai dan yanda takeji da Amina ta ganta gwara tayi Gamo da rundunar aljannu Ido da Ido......✍🏿 *Tofa meye ke tsakanin Amina da asiya da take tsoron had'uwarsu haka*🤔 *Ya kenan Najib zaiyarda da had'in wannan kuwa tsanar da yayiwa Sa'adatu zata bari ya yarda ya aure ta kuwa*🤔 *Shin wai menene ma asalin Tarihin su najib* *Amsoshin Nan duka suna next page kudai kuci gaba da bibiyata Dan wasan baima fara ba tukwana ba ayi komai ba* *Najmat abiy fans zanyi tankad'e da rauraya Dan gaskiya duk Wanda yaga na cireshi baya comment ne idan kasan kana karanta book d'innan baka comment ku gyara please Dan duk Wanda na cire ya fita kenan bazaiyu Ina Bata lokaci wajen typing Kuma ka karanta just comment ya gagara please Cwthearts agyra Dan ina da uzurirrikan danake saki ina muku typing yanzu haka haihuwa aka mana amma dan na faranta muku bandaina typing ba idan naga baku gyara ba Nima zan hutashshe da kaina nadaina typing huta roro*😊 *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *_Mhiss Hajo ce_*🤙🏿 [10/11, 11:06 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* ___________________________________ *PAGE 23 & 24* ___________________________________ *INDIA*🇮🇳 *NEW DELHI* su NAJMAT karatu Ake Babu kama hannun yaro Dan yanzu haka sun shiga level 2 Aunty Nafisa ta haihu inda ta haifo santalelen.baby boy d'inta Wanda yaci suna Umar Faruq sunan Abban.su Amira aka.sanya Mai matuk'ar kama da mamansa zo kuga murna.wajen su Najmat yaron Kam Yana shan.gata da soyayya wajen yayartashi Dan indai tadawo daga school tofa Yana hannunta Yana Shan wasa haka. Rayuwar wannan family taci gaba gwanin sha',awa Aunty Nafisa da Abiy sai yanzu suke Kara fariincikin hada aurannan da Abba yayi suka k'ara jinjina lamarin ubangiji inda aka fayyace musu Najma da Amira suka Ida hadawa Aiko sunsha Shan albarka su Najma agurin Abiy da Aunty Nafisa Abba da Ummy ma sunyi farincki matuk'a Wanda har yanzu Najmat Cikin zuciyarta tana mak'ale da tunanin mahaifiyarta da Bata San wacece ba. *NIGERIA*🇳🇬 *KADUNA* *WANENE NAJIB* Alhaji abubakar najib shine mahaifinshi hamshak'in Mai arzik'ine da yayi suna a ciki da wajen jahar kaduna shahararran d'an kasuwa ne Wanda yawaicin harkokinshi a kasashen waje yakeyinsu mutum Mai tafiye tafiye Wanda tafiye tafiyen nashi akan kasuwancinshi ne NAJIB ne babban danshi Wanda yake matukar ji dashi Hakan yasa ya Sanya mashi sunan mahaifinshi najib tunda ya tashi miskiline Wanda idan kaga maganarshi ko dariyarshi tofa Yana gaban umman shine ko abbanshi yataso Cikin gata da soyayyar iyaye ga farinjinin jama'a yayi saukar alkqur',ani Mai girma har saubiyu yayi karatunshi tundaga kan pri har degree dinshi inda ya Yi karatunshi a America ya karanci medicine Kasancewar tun Yana yaro yake mugun son ya zama doctor. alhmdllh Kuma burinshi ya cika tunda Yana gama karatunshi mahaifinshi ya gina.mai katafaren asibiti ya kashe mak'udan kud'ad'e Wajen Gina kanshi asibitin inda aka sanyawa asibitin SUNA * N A N SPECIAL HOSPITAL KADUNA* Ma'ana *NAJIB ABUBAKAR NAJIB*. Najib Koda yayi karatunshi Baitaba budurwa ba saboda yanda Yan Mata ke rud"ewa idan suka ganshi saboda Najib saurayine kyakyawan gaske Dan kyanshi har tsorata mutane yake hakan yasa Yan Mata suke rububinshi Wanda ko kallo basu isheshi ba. Hakan yasa ya tsani Yan Mata saboda gani yake duka haka suke Basu da class shiko.a tsarinshi bazai Auri mace marar Aji ba yanda yake ji da kanshi bayajin zai Auri ballagaza Wanda yanzu haka shekaru talatin da d'aya garai Amma har yanzu Bai da ko budurwa saboda bayajin akwai macen da ta Isa ya sota a tsarin rayuwarshi ma shi Babu soyayya Habib abokinshine tare sukayi secondry school Shima yakaranci b'angaren lafiya ne Hakan yasa suna gamawa Najib ya d'aukeshi aiki inda suke gudanar da Al"amuransu tare ba a tab'ajin kansuba tunda suka taso Saika rantse ma Yan uwa ne Shima dai Habib har yanzu baiyi aure ba amma Yana da budurwa. Najib k'annanshi ukku Khairat sunanta harira sunan Mahaifiyar babansu ce tana da shekaru 19 a yanzu sai khadija Mai shekaru 16 wacce take zaune ne a gidan kakarta ta wajen uwa sannan autarsu da har an cire rai Allah yabasu Mai suna Nafisa suna ce Mata Fena Ganin Aunty Amarya tunda aka aurota Bata tab'a Haihuwa ba gashi tana mugun son yara Hakan yasa Abba ana yaye Fena yabawa Aunty Amarya ita halak malak ansha ko bala I wajen Umma ba irin ruwan masifar da batayiba Amma Abba yaki sauraranta Haka Fena taci gaba da rayuwa b'angaren Aunty Amarya sun shaku kamar ita. Ta haifeta Tana Bata kulawa sosai da sosai Hakan ko ba k'aramun dad'i yakewa Abba ba danko Umma bazatabawa Fena kulawar da Amina ke Bata ba b'angaren Fena ma tana mugun son Aunty Amarya Dan Umma ta tab'a kwata Amsar Fena inda ba irin ruwan tijarar da batayiwa Amina.ba Ashe Abba Yana jinta har sanda take ce Mata juya maganar Tayi mugun tab'a Mai zuciya. Aiko Tasha wulak'anci wajen Abba Dan har marinta yayi Aiko tundaga lokacin ta K'ara tsanar Amina tanace Mata ita tayi asiri ta rabata da mijinta . Yaran gidan sun tasone cikin had'in Kai da k'aunar juna suna mugun tsoron Yaya NAJIB Dan baya musu wasa Ko kad'an Mahaifiyar su Hawwa'u Jidda Macece Mai bala'in kishi Dan Bata tab'a zaton Alhaji zai k'ara aure ba kwatsam saigashi ya k'aro aure fadar tashin hankalin da Umma ta shiga Bata bakine tunda aka Auro Amina gidannan Bata da kwanciyar hankali ta tsani Amina Bata k'aunarta Amina kwata kwata Amina ko daidai gwargwado tanayiwa Umma biyayya ummako kullun kiyayyarta Kara ninkuwa take a cikin zuciyarta. Amina lecturer ce a KASU kaduna macece Mai tsananin kyau ,ilimi ladabi ,biyayya uwa uba tarbiya ga son yara jininsu yazo Daya da najib saikace uwa da d'a idan suna fira duk miskilancin najib Amma bayayiwa aunty Amarya Kasancewar haka yaran gidan suke ce Mata. Khairat da ta tarki yiwa Aunty Amarya rashin kunya tunda NAJIB ya taka Mata burki Bata sakeba itama khairat a kasu take karatu yanzu haka tana level 2. Asiya kanwar Umma ce ubansu Daya Umma batajin maganar kowa idan Bata asiya ba da uwarta Asiya da Mahaifiyar ta da Yan uwanta basa kaunar Umma DA mahaifiyarta saboda basuyi zaman dadiba musamman umma sun tsaneta saboda tafisu rufin asiri tafisu dacen Miji dukansu Amma a Fili basa Nuna Mata yanda suke Nuna.mata sunfi kowa k'aunarta amma a zuciyarsu ji suke kamar su cinna Mata wuta itako Umma ta d'auka duka kenan Dan ita da zuciya d'aya take zaune dasu. Asiya bayanda batayi da Umma ba akan tarakata wajen Boka a fitar Mata da Amina Amma Umma ta k'iya sabida macece Mai tsananin tsoron Allah tana da fad'a sosai Amma Kuma fad'an ta iya Baki ya tsaya Dan kome zai sameta tofa tana fallamawa Allah komai. Asiya muguwar makira ce ta bugawa a jarida ta kware wajen hada makirci kashe aure kuwa a wajen ta kamar kashe tururuwa ne gashi Bata da godiyar ubangiji Dan mijinta D'ansanda ne sunyi zaman garuruwa sosai inda Duk garin DA suka zauna saita ha'da makirci.daidai gwargwado Bata nemi komai ta rasaba Amma Bata hangen nata na wani take hange ta Raina rufin asirinta Mijinta malam Sani ta mallakeshe ta gama dashi sai abunda tace Mai Dan Tama rabashi da danginshi tunda Allah yasa aka maidoshi kaduna da aiki tsawon shekaru goma Sha hudu Amma baitaba waiwayen iyayenshiba Dan Yama manta dasu ita kuwa Hakan yamata dad'i saboda ta dawo mahaifarta. Sa'adatu ce babbar diyarsu Sa'adatu tun tana secondry ta lalace Dan shekararsu ta karshe akayi Mata ciki gudun asirinsu karya Tonu Tadaina zuwa makaranta inda Dak'yal suka samu suka subar da cikin daga Nan Bata Koma makaranta ba Dan ko jarabawa batayi ba nanko ta cigaba da Yawon bin mazan ta da Yan mata Dan Sa'adatu ba iya maza ta tsaya harta Mata suna lesbian dasu kwararriyar Yar iskace. Tunda ta tashi take mugun son Yaya NAJIB b'angaren shiko Babu wacce ya tsana sama da ita Irin son da take Maine yasanyata komawa gidansu da zama duk Dan taja hankalinshi amma a banza Dan ko kallo Bata ishe shiba hakan ko ba k'aramun bakanta Mata Rai yake ba haka dai take har hak'uri har lokacin Da burinta zai cika na auranshi. Kasancewar khairat age mate d'inta ce Hakan yasa tunda ta dawo suka kulla kawance duk yanda Sa'adatu zatayi taja Ra'ayin Khairat tayi Amma abun ya gagara tana son Khairat ne itama ta lalace kamar yanda ta lalace Amma ba yanda batayiba Khairat tak'i lalacewa taso Tasanyata a harkansu ta y'an lesbian Shima Hakan ya gagara Hakan yasa ta sauya dabara take yawo da ita wajajan kawayenta na banza Koda haka zaija ra'ayinta cikin ikon Allah Najib ya shiga lamarin inda ya tarwatsa Mata shirinta hakanko ba k'aramun ciwo yayi Mata ba yanda take murnar Khairat takusa zowa hannu Gashi ya ruguza Mata shirinta Hakan yasa ta aje makaman aikinta akan Khairat kafin tasan abunyi. Asiya burinsu baiwuce suga Umma ta wulak'anta ba Ita da y'ay'anta Hakan yasa suke banka Mata mugun asiri tanaci yanda duk abunda suka Sanya ta bazata bijire musu ba gashi duk kud'in da asiya ke so da ta tambayi Umma tana sauri zata mik'a mata a tak'aice dai Asiya ita ke juya Umma kamar waina.a tanda Wanda itake Kara chusa Mata k'iyayyar Amina a cikin zuciyarta Wanda har yanzu tsawon shekaru bakwai da Auro.amina tunda Asiya taga.amina ranar da aka kawota cikin gidan Kasancewar basuyi ido hud'u ba Aiko tundaga ranar asiya Bata bari su had'u Dan kosun.hadu saitasan yanda tayi basuyi ido hud'u ba Wanda abun tun yanabawa Umma mamaki harta dawo Tadaina mamakin. *DAWOWA LABARI* Sanye yake Cikin k'ananun kaya yayi bala'in kyau sajen Nan nashi yasha gyara k'amshin turarenshine kawai ke tashi a palourn Dan Najib ma'abucin son turare ne Yana mugun son k',amshi Hakan yasa ko Dan yaushe baya rabuwa fa kamshi Duk inda kamshi yake Yana son wajen Hakan yasa yake yawan shiga bangaren Aunty amarya Dan itama ma,'abuciyar son k'amshin ce. zaune yake a Palournshi dayaji kayan alatu Gyare Yake tsaf Kasancewar kullun sai masu aiki sun gyara k'aramun bowl ne hannunshi Yana Shan fruit salad d'in da aunty Amarya tahada Mai sai wani lumshe Ido yake Dan ba k'aramun dad'in shi yake jiba. Fena ce ta shigo tafad'a Mai Umma na kiranshi yana gamawa tare suka tafi da Fena sai Surutu take zubamai suna shiga a palour suka tarar da Umma bayan ya gaishe ta da fara'arta ta amsa Najib kanshi yayi mamakin fara'ar Mahaifiyar tashi Dan rabon da Yaga tana fara'a har ya manta. Sund'au minti biyar Sanna Umma ta juyo tace "Najib Ina son ka Bud'e kunnenka da kyau ka ji abunda zan Fad'a Maka ka saurareni da kunnen basira ba shawara zanbakaba umarni ne a matsayina na mahaifiyarka wacce tayi nak'udar haihuwarka ta kawoka duniya. Tunda tafara maganar najib gabanshi yaji yafadi Amma kasancewar mutum.ne Wanda bai fiya nuna damuwarshi a fili ya sashi cewa "inajinki Umma Kuma insha Allahu zanbi umarninki matsayina na d'anki Mai biyayya a gareki". Murmushi Umma tayi tace "ai daman nasan bazaka bani kunya ba najib Allah yayi Maka albarka,ameeen ya amsa sannan ta d'ora da cewa ,"Daman munyi shawara ce da y',ar uwata Najib nagaji da ganinka haka ba Mata Hakan. Yasa muka Yanke shawara da Asiya akan zamu had'aku Auren zumunci kaida,y',ar uwarka sa',adatu Kuma Alhmdllh munyi magana da sa',adatu ta amince " Tunda Umma ta fara maganar Najib yayi sakato Yana kallon umman tashi Dan Jin maganganunta yake kamar a mafarki me Umma take nufi wai,sannan ya d'ago runannun idanun shi da sukayi ja tsabar b'acin Rai yace "Umma wai kina nufin zaku had'ani aure da Sa'adatu Koko Kunne na ne ya juyamun ba daidai ba ko mafarki nake . "Umma ce tace ohh so kake na maimaita Maka ne ba mafarki kake ba gaskiya ne zamu had'aku Auren zumunci da SA'a Kuma ba fashi. "innalillahi wa inna ilaihiraji un Umma kina nufin zaku had'ani aure da wacce ta gama lalacewa a titi waccce maza suka gama lalatata zaku ce na aura Umma ba sab"awa umarninki zanyi ba Ina Mai Baku hak'uri Amma wallahi bazan yarda da had'in Nan ba Sa'a ba class Dina bace ba itace zab'ina ba Bata da d',Aya daga cikin halayyar kalar matar da nake son aura Umma bazan Auri ballagaza marar kamun Kai ba haba Umma kamarni zan auri mace marar Aji marar ilimin boko Dana addini hasalima Kuma karuwar gida.....Bai k,'arasa maganar ba sakamakon saukar Marin da yaji Umma ce ta wankeshi da Mari sai huci take tace "najib ni kake.fadawa maganganun Nan harka Kai matsayin da zaka musamun har yaushe kayi girman dazaka fad'a mun magana A gaba na kake.cewa y'ar y'ar uwata karuwa agabana kake.fadawa y'ar zumu na.wannan maganganun to wallahi kaji ni dakyau komai zaka fad'a Saidai ka fad'a Amma aure ba fashi inko kaga an Fasa auran Nan tofa Saidai ka biyani nono na da kasha Dan akan maganar nan wallahi zan iya tsine maka Kabi duniya ". Duk inda tashin hankali yake najib ya shigeshi Dan tunda yake tsawon rayuwarshi baitaba shiga tashin hankali irin na wannan lokacin gashi Abba jiya yayi tafiya bare ya sanar dashi halin da ake ciki Dan shine zai iyabmagancemai matsalarnan cikin Sauk'i. Baima tsaya Ida sauraran fad'an Umma ba ya tashi ranshi a matuk'ar b'ace kamar zai tashi sama yayi part d'inshi ji yake kamar ya kurma ihu koya rage rad'ad'in dayakeji a cikin zuciyarshi Dan wallahi Daya auri Sa'adatu gwara ya mutu Babu Mata ga Kuma tashin hankalin umma Wai yau itace har ta d'aga hannu ta mareshi Kuma har take ikirarin zata tsine Mai akan waccen Yar iskan yarinyar Tsanar sa'adatu ce ta K'ara nunkuwa a cikin zuciyarshi ita DA mahaifiyarta ranar haka ya kwana ko rintsawa baisamu yayi ba........✍🏿 *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *_Mhiss Hajo ce_* 🤙🏿 [10/17, 8:22 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* ________________________________ *PAGE 25 & 26* ________________________________ Tundaga lokacin nan Najib yashiga damuwa DA tashin hankali ko wajen aiki ya daina zuwa Habib Shima ya Taya abokinnashi bak'in ciki Dan koshi bazai yarda DA had'in nan ba lallashin Najib kawai yake Yana bashi baki Najib ba irin Hak'urin DA bai Bata ba Amma tatubure karshe ma chatai ya K'ara Musa Mata akan auran nan Bata yafe mashi ba zokuga tashin hankalin wajen Najib ranar har wani zazzabi ya kamashi. Yauma kamar kullun Habib ne ke gefenshi a palourn Shi Yana bashi baki ,"abokina Dan Allah ka cire damuwar abun nan cikin ranka ka Barwa Allah komai shizai magance maka"cewar Habib. Murmushin takaici yayi yace "watau Habib bazaka gane bane kafi kowa sanin Hali na Kasan Sa'adatu ba tsara ta bace Kuma kafi kowa sanin Yanda na tsani k'azamar yarinyar nan Kuma shine yanzu za a lak'ama mun ita haba Ni.wallahi kainama ya gama kullewa". Cike DA tausayin abokin nashi Habib yace "Abokina GA wata shawara Ina tsammanin zata taimaka.mana me zai Hana muje mu sanarwa da hajiya maganar nan Na tabbatar bazata Bada goyon bayan abun nan ba,. "Cikin sauri Najib ya juyo yace "Kai amma.abokina kaid'in k'warone.wallahi Duk tunanina baizo nanba na tabbatar hajiya bazata yarda maganar nan ba sannan ya.mike.tare DA d'aukar key d'in.mota dariya Habib yayi yace "DA sauri sauri haka "Ehmana Ai kasan DA sammako ake.kamun kifi har suka Isa gidan hajiya Habib namai tsiya. A palour suka Tarar DA hajiya na Sallah Zaunawa sukayi harsaida tagama suka gaisheta ta amsa cikin sakin fuska sannan ta tambayesu ya y,'an gida lafiya qalau suka amsa nan suka Shiga fira DA Habib Saboda mutumin hajiya ne daman. Najib ne yayi gyaran murya yace "hajiya daman.magana ce ke.tafe damu Kokuma ince taimakonki.muke.nema nan hajiya tace inajinku nan suka kwashe abunda Ke faruwa suka fad'a Mata tare DA rok'onta Dan Allah karta yarda lamarin nan ya faru. Salati hajiya tayi ta salamce tace Ni Amina na Shiga ukku me jidda take neman ta zama ne watau abun ya wuce iya kanta ya Fara biyo y'ay',a kenan to bazata sab'uba bazan tab,'a lamunta DA wannan shirmen banzan ba "Allah yayi muku Albarka DA Kuka sanar Dani halin DA AKE ciki tunda ita malalaciyar bankai matsayin dazata sanar Dani ba fad'a hajiya take inda take shiga Bata nan take fita ba. "Bangaren Najib wani sanyi ne ya ziyarci zuciyarshi koba komai yasan hajiya bazata yarda DA auran nan ba, Hajiya ce tace "Maza Maza yanzunnan ka kiramun jidda Saida gaban Najib ya Fadi yasan halin umma Sarai zatace yazo ya had'ata da mahaifiyarta Saida hajiya Tak'ara mik'amai tace ''nace ka kiramun jidda sannan ya amsa ya kirawo umma ring ukku ta d'aga hajiya ta amsa. Hajiya bama ta tsaya Amsa gaisuwarta ba tace "Ina son ganinki yanzu yanzunnan.kome.kike.ki saki.kizo Idan na.isa dake Dan yanzu lamarin naki yafi k'arfina Idan Kinga Dama kizo minti ashirin na baki "sannan ta katse Kiran. Habib garin dai Maganace ta family d'insu ya Sanya Shi tafiya tare yimusu bankwana nan hajiya ta had'oshi DA tsintsiyar kamshi ya kaiwa hajiyarshi sannan ta gaishe su godiya yayi ya amsa Kashewa Najib ido yayi tare DA yimai Saida safe Yana b'oye dariyarshi ganin yanda ya rikice lokaci guda. Cikin minti baiyi ashirin ba kasancewar ba nisa sosai tsakaninsu umma ta iso suna hada ido DA Najib gabanshi yayi mugun fad'uwa ganin irin kallon DA take Mai ya Sanya Shi tsurewa. Har k'asa ta duk'ursa ta gaishe DA hajiya batare DA hajiya ta amsa ba tace "Ni bana buk'atar gaisuwarki jidda yaushe Har Nakai matsayin DA Zaki gaisheni a a ki Aje gaisuwar taki iya iyayennaki na gaskiya sannan ta d'ora DA cewa,Bari kiji jidda Duk irin abunda kike Ina sane k'yalekine kawai nake Dan karmuba Duniya dariya jidda baki d'aukeni a bakin.komai ba to Bari kiji wallahi kinji na rantse Duk shirmanku da kuke bantab'a Shiga ba KO?to wannan nashiga wallahi muddin baki janye maganar had'a Auren sa'adatu da Yaron nan ba ban yafe Maki hak'k'in haihuwarki DA nayi ba ke ni.wallahi dakike ganin wannan yaron yafiyemunke so dubu Nafi sonshi akanki yanda Aka sukukutaki shine Shima Zaki kaishi a lalatamai rayuwa tun yana k'uruciya to wallahi bazan yarda ba ke jidda fa Bari kiji wallahi Akan maganar auran nan zan iya tsine Miki ki Ida lalacewa na gaji DA bak'in cikin ki sannan ta fashe DA Kuka tace "kasheni kikeso kiyi bakincikinki kawai nake k'unsa Yaudai na gaji jidda keni karki k'arama zomun gida na hak'ura dake wallahi nabarwa su haule ke Dame zanji DA bak'incikin wad'annan mutanen DA suka gama chusamun Wanda Har yanzu bai warke ba zanji Koko DA bak'incikin ki zanji ,"Duk cikin kuka take maganar nan Ba kan umma kad'ai ba hatta Najib Saida ya firgita d'ajin maganganun hajiya Dan yasan hajiya Idan tana fad'a Komai fad'a take Sai yaji haushin ma fad'a matan DA yayi. innalillahi wa Inna ilahiraji un kawai yake ambata ummako k'wallace ta zubo Mata juyowa tayi Kallonta wajen Najib tace "watau Najib Ni kazo ka had'a DA mahaifiyata KO akanka kaja ta furtamun Kalmar DA KO a mafarki bantab'a tsammaninta daga wajentaba Najib babu abunda zance Maka Kuma ka kyauta ammafa ka sani daga yau babu ni babu kai na yafe ka a Jerin y'ay'a na.kaje ka Nemi.wata uwar Amma baniba kamar yanda kaja mahaifiyata tayimun baki Nima nayi Maka Babu Ni Babu kai Babu Ni Babu kai ''Umma Dan Girman Allah kiyi Hak'uri ki yafemun Wallahi Bada niyyar had'a ki DA hajiya nazoba Dan Allah kiyafemun umma bazanga daidai ba muddin kina fushi dani ya ida fad'a Yana kama k'afafuwanta idanuwanshi sunyi jajur. Warce.kafarta umma tayi tare DA Jan Jakarta tayi haryar fita Binta Najib yayi kamar zaiyi Kuka Dan Shi Babu Wanda ya tab'a ganin hawayanshi saidai kukan zuci. Tsinkayo muryar hajiya sukayi DA cewa "Kika Saka k'afa kika fita daga gidan batare da kinyafewa Yaron DA baiji baiganiba ban yafe maki hak'k'in haihuwarki DA nayiba Kuma saikin.biyani nono na DA kikasha yau d'innan....✍🏿 *Dan Girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *_Mhiss Hajo ce_*🤙🏿 [10/17, 8:23 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* _____________________________ *PAGE 27 & 28* _____________________________ A tare Najib Da umma suka juya suka Kalli Hajiya kallo d'aya zakayi musu dukansu kasan suna cikin tashin hankali Kuka umma ta fashe dashi tare DA rugawa ta rungumi hajiya cikin kuka tace "Dan Allah hajiya kiyi Hak'uri ki yafemun Idan ma Ina Maki laifi cikin Rashin Sanine kiyafemun Ko zanyi rayuwa Mai dad'i nasan fushin kine Ke jefani cikin masifa Kala Kala hajiya kiyafemun Dan Girman Allah. Allah Sarki kunsan uwa DA D'a itama hajiya rungumeta tayi tace "Nayafe Maki Jidda Kidaina Kuka daman ba fushi nake dake ba kawai chanjawar halinkine lokaci guda yasa bama jituwa " Goge hawayen ta umma tayi sannan tace "nagode hajiyata insha Allahu Zanyi iya kokarina wajen ganin nadaina B'ata Maki Rai Sannan ta Kalli Najib tace "Na yafe Maka Duniya DA lahira Allah yayi Maka Albarka a cikin Dukkan al'amuranka Maganar aure Kuma Na janye tunda hajiya ta nuna Bata so Allah zab'a abunda yafi alkhairi" wani sanyine ya ziyarci zuciyar Najib a zuciyarshi ya furta Alhamdulillahi sannan yaje ya rungume umma Sai godiya yake zuba Mata Itama tana Sanya Mai Albarka Hajiya taji dadi sosai Murmushi tayi a zuciyarta tace "Allah K'ara karkatomun DA hankalinki y'ata"ranar har magriba su umma Na gidan hajiya Dan rabonta DA gidan takai wata biyu Sai bayan Isha'i tukwana suka Baro gidan hajiya Najib yadauki umma kasancewar driver ya kawo ta Kuma ya koma. Tunda suka Shiga Mota Najib yaga ta murtuke Takoma ummar ta DA "Hak'uri Najib yakarabawa umma "murmushin takaici tayi tace "aini Na riga Na yafe Maka ammafa ka sani Auren nan ba fashi Na janye ne kawai a gaban hajiya Dan taji dad'i sabida haka kasanma Duk yanda zakayi DA kanka zakaje kacewa hajiya kai kakeson auran "Najib Ji yayi kamar ya k'wala ihu Dan takaici zaiyi magana umma ta katseshi tace "banson Jin komai "ba Wanda ya sake magana harsuka Isa gida tukwana kowa yayi sharanshi. "Oh my god umma yakuke so nayi ne Wai DA rayuwa ta fad'a Yana buga kanshi DA hannu " Ranar baisamu yayi bacci ba ya durk'ufa tunanin mafitar DA Zai samawa kanshi Chan wata dabara ta zomai Yes ya fad'a yana k'usha DA hannu. Bayan sati biyu Abbansu Najib ya dawo daga Lagos din dayaje wani babban metting Nasu Na y'an kasuwa alhmdllh wannan karin kam yasamu Shiga bangaren umma Wanda aunty Amarya ce ta tilastamai Akan saiya Shiga Saidai suna had'a ido ya karajin ya tsaneta dakyal dai ya iya Zama harma ya amsa Mata gaisheshin DA take daga gaisuwar nan ba maganar DA ta Kuma Shiga tsakaninsu Dan umma akwai zuciya ba kad'an ba. Suna haka Najib ya Shigo Sannu DA zuwa yayiwa abban nashi tare DA Rungumeshi Nan suka Shiga firarraki Wanda Duk Akan aikin Najib ne Abba Ke tambayarshi. Cikin hirar ne Najib yace "Abba daman inason nayi shawara dakai Ina son zuwa India zank'aro karatu Ina son zanyi masters ne Akan aikina Dan Na K'ara k'warewa. "Dafashi Abba yayi yace wow son Ai Bama saika nemi shawara ba Na amince Maka son Wannan tunani ne Mai kyau Allah ubangiji ya bada sa'a ya Sanyawa karatun ka albarka "ameeen Abba najib yafad'a Yana kallon Umma yaji ko me zatace Harara Yaga ta gallamai sadda Kai yayi Umma ko a Zuciyarta cewa tayi kenan duk Dan gujewa auran Nan ne ya tarki tafiya to ai kaje ka dawo ka sameni duk inda zakaje. Cikin Wata biyu Abba yagamawa najib Komai Kasancewar ta online sukayi Komai da registration Yanzu haka tafiyar ta rage saura kwana biyu Duk yaje yayi bankwana dasu Hajiya da su khairat Umma ma tun tana fushin harta sauko tasanya Mai albarka tare da fatan Nasara Akan karatun. B'angaren Sa'adatu hauka ne kawai batayi ba Jin tafiyar da najib zaiyi mema amfanin zamanta a gidan Hakan yasa ta had'a kayanta ta Koma gidansu kota rage rad'ad'in da takeji Asiya ma bataji dad'in tafiyar da najib zaiyi ba Amma dai Koma meye tasan zaidawo kuma had'in Auren Nan ba fashi. Yau takama tafiyar Najib India Wanda jirginsu cikin dare zai tashi k'arfe Ukkun dare Hakan yasa da dare yagama had'a kayanshi yasa komai a boot Wajen k'arfe takwas ya shiga b'angaren Aunty Amarya Dan Yi Mata bankwana. Bai iske kowa a palour ba Hakan yasashi jira Baijimaba saigata ta fito daga kitchen "sannu da fitowa my mum"yafad'a Yana kallon ta "B'ata Rai tayi tace "haba son Ina Nan ina jimamin tafiyarka gaskiya inaga sainafi kowa yin kewa"Shima Bata Rai yayi yace "Nima Aunty zanyi missing naki irin sosai d'innan ji nakema kamar na Fasa tafiyar" a a son Ai Abu Mai mahimmanci ne zaka Allah ubangiji ya taimaka ya bada sa'ar abunda akaje nema "sun d'an jima suna hira Saida zai tafi tukwana ta d'aukomai Turarruka masu mugun k'amshi sannan alkqur'ani da wata had'ad'd'iyar zobanya ta gold sai shek'i take . Tace "gashi son duk inda zakaje kada ka manta da karatun alkqur'ani Mai girma karkayi sake da addini kamar yanda na sanka mutumin kirki kacigaba da rik'e mutuncinka Karkayi sake da azhkar safe da yamma goge hawayen Daya zubo mata tayi sannan ta mik'a Mai had'ad'd'iyar zoben gold din sai d'aukar ido take Sanya Mai tayi a k'aramar yatsanshi. kasa tsaida hawayenta tayi tana hawaye tace ,"Najib zoben Nan ka rik'eta da kyau zobe ce da na jima Ina tanadinta akan idan Allah ya azurtani da Samun Haihuwa zansanyawa y'ata ko d'ana Saidai Allah Bai nufa ba Allah baisa zanga k'wai na a duniya ba najib Likita ya tabbatarmun bazan tab,'a haihuwaba Hakan yasa na baka ita kaid'in inajinka ne tamkar d'an Dana Haifa najib nasan kaima ka d'aukeni a matsayin uwa Dan Allah najib ka cigaba da d'aukata a matsayin uwa Allah yayi Maka albarka yasanya albarka akan abunda zakaje nema". Ba k'aramun tausayin auntyn. Tashi ba ya kamashi "Kama hannunta yayi yace "insha Allahu Aunty zan Rik,'e duk abunda kika fad'amun da mahimmanci nagode my cwt mom kidaina damuwa Aunty banason kinacewa Baki da y'ay'a mud'in fa ,mufa y'ay'ankine banajin dad'in hakan da kikecewa please Aunty kidaina Nid'in d'anki ne Kuma zanci gaba da zama d'anki har karshen rayuwa ,". Abba Dayana jinsu Saida ya goge k'walla saboda ba k'aramun tausayin Amina yake ba yasan rashin Haihuwa Babu dad'i musamman ita da Aka tabbatarmusu da bazata tab'a haihuwaba Hakan yasa yake mugun tausayinta shiyasa yake kyautata Mata. Daga b'angaren Aunty Amarya b'angaren Umma ya nufa Chanma ta Sanya Mai albarka Itama hada kukanta Dan ba k'aramun missing d'in Najib zatayiba sabida duk cikin y'a y'anta babu Wanda take yiwa son da takeyiwa NAJIB sannan ta bashi tsarabar dazai tafi Da ita. K'arfe 2 pm Abba ya raka najib airport Saida yaga tashin jirginsu sannan ya Koma cike da kewar d'an nashi mafi soyuwa a wajenshi. *INDIA*🇮🇳 *NEW DELHI* Cikin sauri suka gama breakfast din kasancewar sun makara Goge bakinta tayi DA tissue paper cikin sauri ta tashi Sanye take cikin wasu had',ad'd'un English wears pink din riga me umbrella a gaban rigar an rubuta pretty Wandon jikinta black Sai head data d'aura Shima black ba make up fuskanta Amma sainaga ba make up ma tafi kyau natural beauty face d'intane matsakaicin pink d'in takalmine jikinta Wanda baida tsawo sosai takalmin kanshi abun kallo ne. Bugu a baya Najmat takaiwa Amira datake cigaba DA breakfast d'inta tace"acici dalla ki tashi mutafi time Na tafiya kinsan yau Ina DA lectures D'in safe kin tsaya kina bautawa ciki mutum saici kamar kaza"chabd'i Ni kika cewa Kamar kaza Aiko wallahi saikin San wakika cewa haka kuma saina Rama tuluk'in DA kikamun" Amira tafad'a tana nufar Najmat DA niyyar kaimata duka. A guje Najma tayi palour Bata tsaya Ko Ina ba Sai bayan Aunty nafisa ta b'oye biyota Amira tayi nan ta kankame Aunty nafisa tace "Sorry my Dusti Dan Allah kibiyoni bashi Nayarda ki Rama Please ba yanzu ba wallahi sanyi fasamun fata zakiyi haba my love amirata haba my sweety Na kiyi Hak'uri bazan sake ba"Dariya Amira tayi tace "Mutum Sai tsoro.amma ya iya Jan fad'a kinci sa'ar Munyi latti amma wlh DA saina Rama tafad'a tana rataye Jakarta ,gwalo Najma tayi wa Amira Aiko DA gudu Amira tayo.kanta DA karfi Najma ta kankame Aunty nafisa tace "wayyyo Aunty Dan Allah ki Bata Hak'uri nifa Bada ita nake ba"Aunty nafisa ce tace "kudai bakwa girma wallahi kullun Abu daya Saida suka gama shiriritarsu tukwana Najma ta d'auki key tare DA hug din Aunty nafisa DA little faruq DA yanzu harya Fara rarrafe tukwana suka tafi School a guje Najmat taja motar suka tafi Dan Najma gudu gareta a Mota Amira tun tana Mata fadan harta hak'ura. Around 2pm Najma tafito daga lectures a cikin Mota ta Tarar DA Amira Dan tarigata gama lectures "sorry Dia kingaji DA jira lectures d'ince yau tayi zafi kinsan Sai yau nayi submitted din assignment d'innan tafad'a tana zagayawa ta Shiga driver seat ta zauna tare DA tada Mota suka d'auki hanya suna cikin tafiya Kira yashigo wayar Amira ganin Abba ne Mai Kiran yasanyata saurin d'agawa. "Hello Abba "Dayan bangaren Abba yace "Amira tabawa Najma wayar amsa Najma tayi bayan ta gaishe DA Abba Yace Mata "Dan Allah daughter ku wuce Airport yanzu akwai d'an sister ta daya iso yanzu Yana airport kuje ku d'aukoshi daga nan saiku taho gida kubi a hankali"murmushi Najma tayi tace ,"to my Abba nan Abba yayi musu kwatancen yanda xasu Ganshi DA sunan airport d,,'in, Kai tsaye *Indira Gandhi international airport* suka nufa Kamar yanda abba yasanar musu Suna Isa Najma taja tayi parking juyawa tayi ta Kalli Amira tace ''dusti jeki ki taho dashi nagaji wallahi "Tsaki Amira taja tace kedai kin Shiga ukku raguwa kawai "eh naji dai Najma tafad'a tana dariya. Amira tana fita tsaye ta hango Shi Sanye yake cikin wasu Ash colour d'in k'ananan Kaya Wanda sukayi mugun karbarshi sumar gashin. Nan nashi kwance Lufluf sajenshi dayasha mugun gyara Kai tsaye wajenshi Amira ta nufa Dan tabbas tasan shine Dan tatab'a ganin Shi a hoto dukda Basu taba had'uwaba kasancewar zuwanta Nigeria d'aya Shima tun tana yarinya. "Assalamu alaikum Amira tafad'a lokacin data Isa wajenshi d'ago kanshi yayi daga latsa wayar DA yake yace "wa'alaikumussalam"Ina yini anzo lafiya,mune Wanda Abba ya turo kud'aukeka' "Amira ta fad'a Duk a jere "Alhamdulillahi kawai yace sannan yace okay muje ya fad'a Wana ware hannu Yana wani Had'e gira. Daga haka Amira Bata Kuma cewa komai ba Dan talura guy d'in yanaji Da Girman kai DA rainin hankali a zuciyarta tace "daman kyawawan mazan nan haka suke y'an rainin wayau Wai Na gaisheshima ya amsa mun a Raine DA wannan tunanin Amira Har suka Isa inda Najma tayi parking back seat ta nuna Mai ya Shiga tsayawa Amira tayi gyara takalminta. Tsaki Najma taja tace "hurry up Mana so everyone knows I don't wan't to wait"Tsaki itama amirar taja sannan ta Shiga Dan a k'ule take . Tab'e baki Najmat tayi batama tsaya Ta Kalli Wanda suka d'auko ba ta fusgi motar DA k'arfin gaske Najib kanshi Saida yad'an firgita Dan a rayuwarshi Babu abunda ya tsana sama DA gudu a Mota so yake.yaga fuskarta a zuciyarshi yace " wannan wace ,irin fitsararriyar yarinya ce Ko gaisuwa Bata iya ba tazo tana Mana kasada DA rai "Tsaki yaja a fili a zuciyarshi yace "kodan yaran turawan nan ba tarbiya ta ishesu ba Ji wasu tsinannun Kaya jikinsu Har Amira Da take bahaushiya mamaki yake yanda uncle Umar Shima ya b'iyewa al'adar turawa Har yabar y',arshi tana yawo DA wannan shaggun Kayan cigaba DA danna wayarshi yayi dan ba damuwarshi bane. Bangaren Najma ma Tsaki taja DA k'arfi a zuciyarta tace shikuma wannan Ko WANI irin marar tarbiyar ne ya shigowa mutane Mota Ko gaishesu baiyiba (kunsan Najma DA tsagwaron iyayi DA son girma) sannan ta Kuma Jan Tsaki a fili a zuciyarta tace "kodan y'an Nigeria d'innan daman ba tarbiyar kirki ce ta ishesu ba (nikam.nace Najma wlh ki iya bakinki Harkin Isa ki kushe mana k'asa) Wanda Har lokacin Bata Ganshi ba. Har suka Isa cikinsu bamai cewa uffan Najma tana Jin haushin Bai gaishe ta Amira tana Jin haushin amsa gaisuwarta DA yayi a wulakance Najib ko Danne Danne wayarshi kawai yake Suna Isa gida Tana parking Amira ta Fara fita Tana kunburi cikin sauri tayi part d'insu Sannan Najma itama tafito Ko rufe k'ofar motar batayi ba Shima Najib fitowa yayi cikin nutsuwa Juyawar DA Najmat tayi zata bar wajen shikuma ya fito daga Mota Ji kake gam sunyi Karo. Cike DA masifa Najma ta d'ago zata balbaleshi tare DA dafe goshinta DA hannu Dan taji mugun zafin Karon Shima d'agowa yayi cike dajin haushi Idonsu ne ya Sark'e cikin Na juna a tare kallon juna suka tsayayi kallon mamaki kowannensu Ke yiwa d'an uwanshi musamman Najib baiko k'iftaba Kara wara idanunshi yake wajen K'ara kallonta mamakine dank'are a cikin zuciyarshi Dan tunda yake cikin family d'insu Ko cikinsu y'ay'an ummanshi Ko y'ay'an family Bai tab'a ganin Mai kama da umman Shi Rai DA Rai ba sama DA yarinyar nan dake tsaye gabanshi Duk yanda mutane Ke cewa Yana kama da umma ganin wannan yarinyar dake tsaye gabanshi ta Dame kamannin tsakin DA Najmat ta Jane ya MAIDO dashi Daga duniyar tunanin DA ya Lula kallonta ya tsayayi ganin Har yanda ta HAD'E fuska take kunburi Sak umma Har irin yanda umma Ke b'acin ranta ganin yanda ya kafeta DA idanu ne yayi mugun b'atawa Najma Rai gashi taga baida niyyar Matsa Mata ta wuce haka ya Sanyata d'aga baki cike DA tsiwa DA masifa tace ..........✍🏿 *Congratulations my cwt mommah Ina tayaki murnar kammala littafinki Mai suna Amer Da Amera Allah bawa al'umma damar aiki DA fadakarwar DA littafin Ke tafe dashi Ina tayaki murna Sosai mom nusy uwa ta gari*💃🏽💃🏽 *Ga long page nan Asha karatu lafiya Na kwana ukku ne*😂😊 *Kardai a gaji DA sharing Dan girman Allah Bani DA groups sosai ne shiyasa cwthearhs Kar a gaji damun sharing fisabilillah*😊 *_Mhixx Hajo ce_*🤙🏿 [10/20, 7:36 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* _____________________________ *PAGE 29 & 30* _____________________________ "Tumpaaree Koee aankh Nahin hai ya aap pooree Tarah Se andhe Hain Mujhe baahar jaane Ke lie de do" (Kai dalla baka da ido ne Ko kai makaho ne zaka zo kamun Karo maimakon ka Bani hak'uriba a a kawai zakazo ka kafeni Da wannan idanun naka abun tsoro Kamar Na mujiya , jibeshi Da Allah ya wani Tara bak'in Abu a fuska Kamar Zaki (sajenshi) dallah Ni Bani hanya Na wuce )Duk cikin harshen Hindi take maganar nan Dan tayi zaton bayajin yaren Saboda Tasan Abbansu Amira d'an Nigeria ne to Yace d'an k'anwarshine Hakan yasa ta balbaleshi son ranta Harwani watsa hannu take irin masifar nan tayi yawa. Duk maganar da take Najib Yana jinta Saboda ya iya yaren Hindi tun yana yaro Shi mutum ne Mai kaifin basira Duk abunda yasa Burin iyashi tofa saiya koya ya koyi yaren Hindi ne ta dalilin wani abokin karatunshi murza Course mate dinshine shiya koya mashi harshen Hindi sosai Babu abunda bayaji haka kuma Zai iya mayarwa. Nuna Mata yayi kamar baisan abunda tace ba Amma a zuciyarshi ba k'aramun ciwo maganganun nata sukayimai ba Tsaki yaja a ranshi yace shiyasa bana Shiga sabgar Mata Duk inda suke matsalace wlh jibi wannan k'ank'anuwar yarinyar DA a auran wuri Na haifeta Amma take fad'amun irin wannan maganar Tsaki yaja tare DA barin wajen a ranshi Yana K'ara Tsanar harka DA Mata Dan ba k'aramun B'ata Mai Rai figigiyar marar tarbiyar yarinyar can tayi ba. Najmat Ko tana ganin yabar wajen baisan abunda tace ba Dariya ta k'yalk'yale Da ita tace d'an rainin hankali yawani shigowa mutane Mota ba gaisuwa aigashinan Na zazzageka baka San me nace ba Dariya kawai Take sosai a haka ta Shiga palour tana dariya. Kafad'ar Aunty nafisa ta d'aura kanta tare DA cewa"wash Aunty Na gaji"shafa kanta tayi tace "ayya sorry my dear kije kiyi wanka kifito Kiyi lunch Na tanadar Maki Abu Mai dad'i "d'agowa tayi murmushi dauke DA fuskarta tace "Wow my Aunty thnks u so much my lovely mom Kamar kinsan Na Kwaso yunwa sannan ta Bata Peck a kumatu ta tashi hada gudunta ta Haye stairs. Zaune suke a palourn Abba Ummy Najib Sai Amira dake zaune tana latsa waya Hirar yaushe gamo Abba DA ummy sukeyiwa Najib Abba ne yace "wato son Har yanzu kana nan DA mugun miskilancin nan naka Na tsiya Ko"murmushin DA inba lura Kayi ba bazakagane murmushi ne yake ba yayi yace"Uncle ba haka bane Kawai gajiya ce "Ummy ce tace "gaskiya kam akwai gajiya kam sannan tace ya su hajiya Da Su Jidda "Lafiyansu Qalau Duk sunce a gaishe ku "sannan ya d'auko musu tsarabar DA umma tabada a kawo musu Wanda yawaici duk kayan bahaushe ne Wanda su Basu dashi sunji dadin tsarabar sosai. Saida suka Sha Hira tun Najib baya sakin jiki Har yazo ya saki sai wajen 10pm ya koma masaukinshi had'adden bedroom dinshi Mai matukar girma DA tsaruwa komai akwai a ciki na bukata d'akin Shima cikin gidan yake kasancewar gidajen Ko Wani Daki saika b'ulla ta palour Amma akwai k'ofar DA Zai iya Shiga ya fita batare DA yashigo ta palour ba Kuma Zai iya Shiga ya fita ta palourn gidan. Ruwa ya watsa sannan ya dawo gado ya kwanta Bai jimaba bacci yayi awon gaba dashi Dan ya shawo gajiya ba kad'anba. Bayan kwana biyu Najib ya saki DA mutanen gidan kasancewar ba wani Sabo sukayi dasu ba Dan basufiya zuwa Nigeria ba saisuyi 5yrs Har Fima Hakan yasa basuyi Sabo Dasu ba. Zaune yake a garden d'in gidan Yana Shan dad'd'an Iskan wajen ba k'aramun dad'in iskan wajen yake Jiba qur'anin DA Aunty amarya ta bashine hannunnshi yake karantawa cikin zazzak'ar qiri'arshi Mai dadin sauraro. Kamar kullum Sanye take cikin k'anan kaya faruq Na hannunta tana bashi biscuit Sai dariya yake yiwa Auntyn nashi itama tana mashi murmushi tana mishi fira Shima Yana Mata gwalamgwalamtunsu Na yara Hanyar gidan su Amira ta nufa kai tsaye . Tana knocking Amira ta fito ta bud'e rungume juna sukayi Najmat tace "Haba Dusti Wai meyasa two days kika Baro gida kika dawo nan kinsan bazan juri missing d'inki ba "harararta Amira tayi tace ''eh mana Nima Na dawo gidanmu tunda Aiba haka muka tsaraba Idan yau munkwana Chan gobe mukwana nan Amma kika watsar kullun saidai muyi ta kwana gidanku shiyasa Nima Na dawo gidanmu "sorry Dusti tohm shikenan Nayarda Amma kiyi Hak'uri daga gobe Sai a Fara "kallon bakida wayau Amira tayi Mata tace "nak'i Wayan Ummy tace two Weeks zamuyi Mata tukwana murmushi Najma tayi tace to Naji nan Amira taji sanyi palour suka nufa hug din ummy Najma tayi tare DA gaisheta. Nan Amira Da Najma suka Hau shiriritarsu Faruq Yana hannun ummy a palour. Gajiya sukayi DA Zama cikin gidan haka yasa suka fito Dan su tafi garden Faruq Yana ganin fitowar Najma zasu fita Aiko yasa Kuka tare DA Fara Mika hannu "Lallai Yaron nan watau Kaga yayarka shine zaka rikicemun Ko to Ai zanga Mai d'aukarka Idan Suna makaranta "Dariya Najma tayi tace "karkiga laifinshi ummy Kinsan ance Babbar Yaya uwa Bani abuna muje mu shak'ata tare "Murmushi ummy tayi tace "ummm su uwa Manya ga abunnakine Chan kuje kuyi shiriritartaku tare Dan Shima Naga kin Fara bashi training irin naki tafad'a tana dungurar kan faruq"Uhm uhm ummy kidaina dakarmun boy Kuma ma bazai K'ara zuwa wajenki ba daman ya fad'a mun dukanshi kike shine kikayi a gabana to baxai K'ara zuwaba "tafad'a tana d'aukar kaninta tabi Amira Dan hartayi gaba . Kai tsaye garden d'in gidan suka nufa Basu ma lura DA Najib dayake gefe ba zaune kan chairs kai tsaye wajen table tennis suka nufa nan Aje faruq tare Da ajemai kayan Wasa suka tafi suka Fara buga wasansu cikin. K'warewa ita DA Amira Kallo d'aya zakayi musu kasan ba abunda Ke damunsu Suna cikin Jin dadin rayuwa. Najib DA tun shigowar su yagansu baiko d'ago ya kallesu ba Saidaga baya ya d'aga idanunshi ya kallesu yanda suke buga wasansu hankali kwance Tsaki yaja Ganin Hada figaggiyar marar kunyar Chan )Dan haka yasawa Najmat )Amma Saida gabanshi ya K'ara fad'uwa Kara ganinta Karo Na biyu har murmushinta Sak irin Na umma dimple ne kawai umma Bata DA Shi itakuma Najmat Har two side shagala yayi DA kallonta Yana K'ara ganin. Tsantsar kamanninta DA umma ta yayinda Dimple d'inta Ke lotsawa tana murmushi Yana tsalle tsalle dimple d'inta ya tsaya kallo Sak Kuma Sai yaga dimple d'inta irin Na aunty amarya yanda ya lotsad'in sosai Tsaki yaja a fili sannan yayi saurin kauda tunanin nan a cikin ranshi ya d'auki Hakan a matsayin kamannin halittar Allah ce kawai daman ance mutum Yana DA Mai kama dashi.. Najmat DA suka gaji DA table tennis din nan suka Hau Tsaren gudu ita DA Amira Suna zagaye garden d'in DA niyyar exercise. Faruq daya gaji da Zama nan ya Fara Kuka sosai Najma DA Amira Bama Susan yanayi ba Dan nishad'insu kawai suke faruq Ko rarrafe yake kawai Yana Kuka. Najib ne yajiyo Kukan Yaro bayanshi juyawa yayi yaga Yaro Na rarrafe Yana Kuka ga alamun d'auka yakeso Tashi yayi daga zaman Da yayi tare DA nufar inda Yaron yake DA niyyar d'aukarshi Shima faruq d'in wajenshi yake nufowa DA niyyar ya d'aukeshi. Durk'usawa yayi DA niyyar d'aukar fine boy d'in Dan Yana ganin Yaron yaji yaburgeshj kasancewar Najib mutum ne Mai son yara nan ya duk'a ya daukeshi ya koma wajen xamanshi DA faruq a hannunnshi Yana daukarshi yaji Yaron yayi shiru Sai kallonshi yake nan yashiga mashi Wasa faruq Ko Sai dariya yake Dan yaro ne Mai yawan dariya nan yashiga Wasa DA sajenshi Yana shafawa Yana dariya....✍🏿 *Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *_Miss Hajo ce_* 🤙🏿 [10/22, 7:02 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *This page is for you sis Amina Yusuf bawale Ina Jin dadin comments DA sharhin d'inki over thnks for ur love shafin nan nakine kiyi yanda kike so dashi*💃🏽💃🏽🌹🌹🌹🌹 _________________________________ *PAGE 31 & 32* _________________________________ Saida suka gama exercise d'insu tukwana suka tsaya Suna gama gumi Nan Najmat tahau waiwayen inda ta ajje faruq bataganshiba kasancewar Garden d'in baida wani girma sosai Hakan yasa tayi saurin hangosu Tsaki taja Ganin faruq hannun wancen mutumin a fili tace "Wai meya kai faruq hannun wancen marar tarbiyar d'an Nigerian sanadin ya lalatamun yaro "Harara Amira ta Galla Mata tace "Banson iskanci Najma dad'in abun kema Dai Y'ar Nigerian ce Kuma wancen DA kike cewa marar tarbiyar d'an k'anwar Abba ne Aunty jidda wacce aka Sanya Mata sunana ki iya bakinki "sannan tace. Kodan ma nalura d'an wulakancine shiyasama Ni tunda yazo Banshiga harkarshi "tab'e baki Najma tayi tace ''uhm kede kika sani Naji me d'an uwa Nikuma DA Bani dasu Ko to yayi Mai d'an k'anwar Abba. Sorry Dusti wallahi ba haka bane Dan Allah kiyi Hak'uri bansan zakiji haushi ba kiyi Hak'uri kawai nafada ne Nima. Ba saninsu nayi sosai ba aini kece Y'ar uwata wancen mutumin DA tsawo Kamar poll Ni tsoroma yake Bani jibeshi Da Allah daga gani baida mutunci Ko dariya bayayi "Dariya Najmat tayi tace ,"Kai Dusti Dan uwan naki kikewa ba,'a sannan ta sake dariya tace kumafa hakane nan Najmat tabawa Amira yanda sukayi Jiya me Amira zatayi inbanda dariya tace "dusti wallahi kinyimun daidai Nima kinkoyamun Idan zaimun rainin hankali Nima saina balbaleshi DA yaren DA bayaji dariya Najmat tayi tace "Ai haka zamuyi tamai Har mu bashi tarbiya D'an rainin hankali nan sukayi ta gulmanshi Har suka kusa inda yake. ja Najmat tayi ta tsaya tace Amira ta amso Faruq su wuce itama amirar tsayawa tayi tace "wlh saidai Ke ki amshoshi aike kika ajeshi Tsaki Najmat taja Dan batasan Jan dogon magana ya sata nufar Shi ja tayi ta tsaye tare Da murtukewa Kamar Bata tab'a dariya ba ta kama k'ugu Dan a tunaninta tasan bazaiji me tace ba yasata cewa cikin harshen hindi (Hey d'an raino na Bani baby Na kazo ka wani d'aukarwa mutane yaro aika Bari muyi ciniki dakai sannan ta k'yalk'yale Da dariya tace "Kodan Naga Kayi kama Da Mai Reno karka damu zaka dinga yimun rainon Shi ,kaji Amma kafin nan saika dinga gaishe Dani Ko dayaushe inba haka ba Na fasa) ta ida fad'a tana wani yatsine fuska Kamar taga Kashi. Najib Yana jinta ya nuna Kamar baijiba kawai ya Mika Mata Yaron Amma a zuciyarshi yaji haushinta DA tsanarta lokaci guda Dan a rayuwarshi ya tsani Rashin kunya gashi ya lura yarinyar kwata_kwata Bata DA kunya kanta a tsakar ka yake Tsaki yaja yace nalura itama k'awar Tata irintace (Amira Kenan)tab'e baki yayi yace "Ina ruwana ma yafad'a Yana ware hannu sannan yaci gaba DA harkar gabansa a zuciyarshi Yana karajin Tsanar Mata. Yau Monday Najib Zai Fara attending lectures a school din daya Shiga abun mamaki Kuma Ashe makarantar su Najmat ce Shima yashiga Hakan Ko yayiwa Abba Dadi Dan daman anfadamai yanda yaran Ke sharara Gudu a Mota Hakan yasa yayi shawara DA Abiy Akan Najib Zai dinga tafiya dasu Yana maidosu Sai Suna tafiya tare. Abiy yaji dadin Hakan sosai inda ya bukaci DA Abba ya hadashi DA Najib su gaisa nan Ko Abba ya hadasu Lokaci guda Abiy yaji tarbiyar Yaron DA nutsuwarshi ta kwanta mashi a Rai Bangaren Najib ma hakane ga Kuma Karin mamakinshi Na ganin tsantsar Mai kama Da ummanshi Sak Ko ba a fad'a Mai ba yasan wannan mahaifin Najma ne. Nan Abiy yayi Mai magana Akan Shi zaidinga tafiya dasu makaranta Amma kafin kagane Hanyar Najma Ko amira zata dinga tafiya dakai lokacin daka gama gane hanyoyin saika dinga kaisu kawai Idan time d'in lectures d'inku yazo d'aya. Najib yaji Babu Dadi Saboda ya tsani abunda Zai had'ashi Sabga DA Mata Amma kwarjinin DA Abiy yayimai ya sanyashi amincewa Amma a zuciyarshi Sam baiji Dadi ba musamman had'ashi DA marar tarbiyar yaran can Ga Kuma mamakinshi Na yanda yaji Hausa rad'am a bakin Abiy Kuma yalura mutumin yanada tsakaninin kirki haka yasa yacewa Abiy ba damuwa nan Abiy ya Shiga domin kiramai su Najmat SU tafi. Sanye suke cikin Wata blue d'in gown iri d'aya fuskarsu Kamar kullun Babu make up Sai d'an yafa k'aramun belt d'in rigar DA sukayi ba k'aramun kyau sukayi ba Kallo d'aya zakayi musu kayi tunanin two wins ne Dan hatta yanayin Girman jikinsu iri d,'aya A waiting palour suka had,'u Da Abiy "morning my twins" Abiy ya fad'a Yana ware musu hannaye Daya bayan d'aya Sukayi hug dinshi Najma Ko Sai shagwab'a take zubamai Kamar jaririya shiko Sai biye ta yake a haka suka fito compound d',in gidan Najmat Na mak'ale jikin Abiy. Najib dake tsaye tunda ya hangosu ya ja Tsaki tare DA kauda kai yanajin haushin had'ashi Da yaran nan daza ayi. Abiy ne yace "Sannu son GA sunan sun fito Ina tunanin zaku iya tafiya Allah kiyaye "Sannan ya ya Kalli Najmat Yace"My dear GA yayankunan daga yanzu tare zaku dinga tafiya zaku gwada Mai hanya zuwa Konan DA one week ne saiya dinga tafiya daku Allah muku Albarka. Wara manyan idanun ta Najma tayi tare Da saukesu Akan mutumin data Kira Da marar tarbiyar Nigeria Abiy ta Kalla tare fito Da dara_daran idanun ta didddira k'afa DA kukan shagwab'a ta Sanya cikin zazzak'ar muryarta Mai Hade DA maganar shagwab'ab'b'u tace.....✍🏿 *Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [10/23, 9:18 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* _______________________________ *PAGE 33 ,& 34* _______________________________ Nidai wallahi Abiy bazan yarda ba Taya xa ayi ace wannan mutumin Zai dinga tafiya damu school Ni wallahi ban yarda ba saidai na fasa makarantar gaba d'aya ta ida fad'a tana Sanya musu kukan tab'ara ." "Sorry my dear calm down mana ba abun rigima bane.daugher kinfi Kowa sanin bana son ganin hawayenki my beautiful angel Dina kiyi Hak'uri shid'in yayanku ne zakuji dad'in tafiya tare"Abiy yafad'a Yana bubbuga bayanta alamun rarrashi. "Uhm uhm uhm Abiy nidai Allah banaso Kowa a bashi motar Shi kawai "shafa kanta Abiy yayi cikin sigar lallashi yace "To shikenan Goge hawayen Na yarda za a bawa Kowa motar Shi Amma Ku Fara nuna Mai hanya tukwana kinji *NAJMAT ABIY* D'inta nasan bakya yiwa Abiy musu Akan komai". Cikin sauri ta goge hawayenta tare DA sakin murmushi lokaci guda Jin dad'in Abiy ya kirata DA sunan DA tafi k'aunar a kirata tace "to my Abiy Na yarda tafad'a tana rik'e hannunnshi "Yawwa my daughter Ko kefa Kinga kin goge kwalliyar Taki Ko Na d'auko Maki Hoda ki shafa "Ba Najma ba hatta Amira dariya ta Sanya tana dariya tace "a a my Abiy ba saina shafa ba. Najib Ko sank'arewa a wajen yayi Yana kallon ikon Allah a zaton Shi tsawatar Mata zaiyi Amma saiyaga Yana lallashinta Kamar wata baby Yana Dai tsaye Yana kallon tsantsar soyayyar dake tsakanin uba da y'a Dan wannan kad'ai ya tabbatar Mai DA akwai soyayya DA shak'uwa Mai tsanani tsakaninsu tab'e baki yayi a ranshi yace "ah lallai wannan Dole kiyi Rashin kunya Babanki ya sangartaki DA yawa ga Kuma mamakinshi Na yanda yaji Hausa rad'am a bakinta Dan Duk daukanshi batajin Hausa ". DA lallab'o Dai Abiy ya samu Najma ta Shiga Mota Amira ta Shiga front seat Najmat tana driver seat Cike da Jin haushi Najib ya Shiga Back seat Sannan ta jasu suka tafi Tunda suka Shiga ba Mai cewa uffan a haka Har suka Isa school d'in kasancewar makarantar Nada girma sosai Hakan ya sata tsaida motar tare DA juyowa baya Shima d'ago wa yayi Dan tunda suka taho baima d'ago ba Saida yaji alamun tsaida Mota idanunsu ne suka sartse cikin Na juna Sai yanzu Najma ta k'are Mai kallo ganinshi tayi Fari kyakyawan gaske ga bak'in sajenshi Daya K'ara fito da hasken fuskanshi Sexy eyes d'inshi dashi yake Kara rikita Mai kallonshi Kwantaccen sumarshi Da Tasha gyara ta kwanta lufff Kamar ana Sanya Mata Mai nan Ko tsabar tsaftace DA gayu Sanye yake cikin wasu had'addun Kaya shirt din rigarshi pink Sai bak'in Wando Duk cikin second baifi biyu ba ta k'are Mai kallo saitaga lokaci guda yayi Mata kwarjini tayi niyyar Mai Rashin kunya Amma kawai saitaji ta kãsa Saboda four eyes din DA sukayi cikin sweet voice d'inta tace "Ina ne department d'in naku". Najib Yi yayi Kamar badashi take ba Hakan Ko ba. K'aramun ciwo yayi Mata ba Tsaki taja ba tare DA ta sani ba ta juya Amira ce tace ''Yaya Najib DA kai take ina ne department d'inku"Ba tare DA ya d'ago ya Kalli Daya daga cikin su ba yace "ya Isa nan zank'arasa ya fad'a Yana Bude motar tare DA fita . Najmat tanajin fitarshi Tsaki ta Kuma ja k'asa_k'asa tace "Aikin banza kak'i cewa da kanka zakazo tun a gida ba Saida muka kawo ka ba "Najib ya jita sarai danshi koya kayi magana saiya jika "wucewarshi yayi ba tare da ya Kula ta ba Dan ya lura kwata_kwata yarinyar ta rainashi mamaki yake a rayuwarshi Babu macen DA zata iya hararanshi Bare Har akai GA fadin magana Hasalima tsoronshi Ake DA shakkarshi Duk inda yaje Amma yalura kwata_kwata yarinyar Bata tsoronshi Ko shakkarshi Tsaki yaja tare DA aniyar koya mata hankali Dan bazai iya d'aukar raini Daga wajen Ko Wani irin mutum ba musamman ma mace Da Bata isheshi Kallo ba. Jin abunda Najmat tace dariya Amira taja tace "kai Dusti wallahi bakyajin magana Kin raina Yaya Najib "tab'e bak'i Najma tayi tare DA kwaikwayar Amira waiwani "Yaya Najib"Su Yaya manya sannan taja Tsaki "dariya Amira tayi kamar ta tuno DA Wani Abu Mai mahimmanci tace lah Dusti kinsanme "A a Dusti saikin fad'a Najmat tafad'a tana zumudin Jin Sabon labari "Wallahi Sunanku yayi matching *NAJIB* And *NAJMAT* Wow Dusti Kuma wallahi a fuska ma kunyi matching Har wani kama Kuke gaskiya ba k'aramun dacewa kukayi DA soyayya ba tundaga sunayenku Har Fuskokinku. Duk inda kololuwar b'acin Rai Yakai Najma ranta ya baci batasan lokaci DA ta tik'awa Amira k'ulli a baya ba cike DA masifa tace " ba a tab'a cimun mutunci irin Na yau ba yanda kika cimun Dusti wallahi Kinyi mugun gamawa Dani ki rasa Wanda Zaki had'ani dashi Sai wannan sunduk'in kinmayi mugun rainamin wayau "Ta ida fad'a tana Shirin kai Mata Wani tuluk'in Amira tayi Maza tabude Kofa tana dariya tayi waje tare DA cewa "Sorry babyn sunduk'i Bye Sai anjima tafad'a tana cigaba da dariya tare DA barin wajen Najmat cike da haushi ta fito tana cewa "Ai zamu Hade kinsan bashi kikaci wallahi. A ranar Najib ya ida cike_cikenshi yafara attending lectures Around 3:00pm ya gama lectures dinshi kai tsaye capteria ya nufa Dan yad'an Sanyawa cikinshi Wani Abu. Tun Daga shigarshi wajen y'an matan dake wajen suke kallonshi Suna Yaba kyawun halitta irin Tashi Tsaki yaja a ranshi Dan ya tsani irin.kallon DA mutane Ke mashi Zaunawa yayi nan ma'aikatan wajen sukazo. Suka tambayeshi Akan me yake so. Snacks Da juice kawai ya bukata Ba Bata lokaci aka kawomai abunda ya bukata. Najmat sai 3:00pm suka gama lectures kasancewar sund'an tsaya practical a matukar gajiye take Ga yunwar data ciwota kai tsaye capteria ta nufa. Batare da ta lura DA mutumin dake zaune ba taja kujera ta zauna tare DA bukatar akawo Mata abunda take so. Ba Bata lokaci aka kawo Mata tafara CI tun zamanta Najib yaganta Bai tanka Mata ba Saboda baya son abunda Zai had'ashi Da marar kunyar yarinyar can wayarshi ce tayi ringing dubawa yayi yaga Habib ne me Kiran Tashi yayi Dan ya Matsa tare DA cup d'in juice a hannunnshi ringing d'in wayar yajawo hankalin Najmat wajenshi kallonshi tayi Tsaki taja a ranta tace Kome ma yasa Na zauna kusa DA Yaron nan yazo zaiwuce ta gefenta cike DA mugunta Najmat tasa k'afarta Dan ta tad'e Shi ya Fadi mutane suyimai dariya koya rage fad'in ran nan Aiko ta samai k'afa Kenan maimakon yafadi Sai akayi Rashin sa'a lemon hannunnshi ya kauce dukanshi ya kwarare a jikin Najmat tundaga fuskarta Har kayanta gabaki d'aya ya kwarare.......✍🏿 *Masoyan asali kardai a gaji DA sharing fisabilillah*😄 _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [10/27, 8:58 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* ________________________________ *PAGE 35 & 36* ________________________________ Tashin hankali ba agwada Maka Rana Najma Ba k'aramun rudewa DA rikicewa tayi ba d'ago rinannun idanunta DA sukayi ja Tsabar b'acin Rai ta saukesu akanshi tare DA nuna kanta DA yatsa tace "Ni ka zubama lemo a jiki Kai mahaukacin Ina ne Ko kai makaho ne baka Da hankali ne Ko me stupid kawai Kuma yau sainaga Wanda ya tsaye Maka a garinannan. "Najib DA ranshi yayi kololuwar baci Har wannan karamar marar kunya yarinyarnan zata zaga Aiko baisan sanda ya d'aga hannu Zai wanke ta DA Mari ba Yaji an rik'emai hannu. Cike DA b'acin Rai ya Kalli Wanda ya rik'e Mai hannu yace"sakemun hannu malam"mutumin ne yace "Haba aboki kayi Hak'uri Kar zuciya ta rudeka harka biyewa mace Kuna sa'insa Ka Danne fushinka kayi Hak'uri kai "Najmat ce tace "Ai DA baka rikeshi ba Da Ka bari ya mare Ni din Ai wallahi DA Koda Wasa kayi gigin Mari Na Da saikayi nadamar zuwanka Duniya sannan taja tsuka Fuuuu tayi waje Kamar zata Tashi sama Tsabar b'acin Rai Dan iya rayuwarta ba a tab'a Bata Mata Rai irin Na yau ba. Najib Ko Hak'uri mutumin. Nan yabashj Amma a ranshi Shikadai. Yasan k'unar DA yakeji ganin hankalin mutane ya Fara dawowa wajensu Shima fita yayi cike DA b'acin Rai Baima saurare Suba kai tsaye abokinshi murxa ya Kira Akan yazo ya. D'auke shi. Najmat Ko kai tsaye inda tayi .parking ta nufa ba tare ta jira Amira Bama ta fisgi.mota ta tafi cike DA b'acin rai. Tundaga abunnan yafaru Najib Bai sake Shiga motar Najmat ba haka Najmat Bata sake Shiga sabgarshiba Shima ta bangaren Shi haka Dan Ko ganinta Baya son yi haka rayuwa taci gaba Suna gudanar DA karatunsu kowannensu cikin. Kwanciyar hankali. *5months later* Zaune suke Suna dinner Abiy Najmat Aunty Nafisa Sai faruq Abiy ne yace "Daughter kina sane Dai DA tafiyarmu Umrah Jibi ne kuwa naso mutafi tare Amma Kinga jarabawa kuke Idan Kuka gama Kema saikuje"Murmushi Najmat tayi tace "Ina sane Abiy Allah Dai ya kaiku lafiya ya maidoku lafiya "murmushi yayi yace "ameeeen my angel kidai CI gaba DA Maida hankalinki Akan karatu DA jarabawar DA zakuyi sannan kinsan gidan Abban Amira Zaki zauna Ki Kula DA kanki "Gabanta ne yafadi Jin Abiy yace gidan su Amira zata zauna tunowa datayi Da marar tarbiyar Nigeria d'innan Dan ita Ko sunanshi Bata rik'e ba Dan harma ta manta dashi Saboda ba had'uwa sukeba kowannensu ya toshe Hanyar DA zasu had'u Dan sabida Shi Ko gidansu Amira tadaina zuwa Hakan yasa Amira tayi fushi ta kwashen kayanta ta koma gidansu gaba daya a zuciyarta bataji dadin zaman DA zatayi gidansu ba Amma ba yanda zatayi dole Dai gidan su amirar zata zauna sabida tasan Basu Da Kowa a garin nan gashi tana son tambayar Abiy game DA asalinshi DA iyayenshi Amma tana tsoron karyayi fushi. Tafin DA Aunty nafisa tayi Mata ce ya Maido DA ita Daga duniyar tunanin data Lula Aunty nafisa ce tace ''yadai dear tunanin Me.kike"Murmushi Najma ta k,,'ak'uro tace "Bakomai aunty kawai tunanin missing d'inku ne nake"hmmmm Daughter Kenan yanzu two weeks din dazamuyi shine Zaki Shiga damuwa to kodai mu fasa tafiyar ne.lokacin Da kika gama jarabawar saimu tafi tare "dariya Najmat tayi tace a a a Aunty kuyi tafiyarku Bani DA damuwa fa fatana Dai Allah kaiku lafiya ya maidomunku lafiya ''Ameeeeen dear Abiy DA Aunty nafisa suka fad'a. Ranar alhamis haka su Abiy DA aunty nafisa tare DA faruq DA Har an yayeshi suka d'aga zuwa kasa Mai tsarki domin gudanar Da ibadar Umra Wanda Har airport SU Najmat suka raka su Saida suka ga tafiyarsu tukwana suka dawo gida cike DA kewar family din nata. DA misalin karfe takwas Na Dare kwance take tana chat a wayarta Tana Hira DA sababbin friends d',inta na school Sanye take cikin Riga DA Wando Na baccci Yunwace ta faraji ya Sanyata Tashi tare DA Aje wayar Da niyyar tafita ta samawa kanta abunda zataci dukansu Yan gidan Suna palour hatta Najib Dan yanzu ya Saba dasu ummy DA Abba Duk dare Yana nan Suna tab'a Hira dukda ba magana ya fiyaba"Ummy ce tace "Ummm su Najmat Ogannin chat anfito Kenan"murmushi tayi tace "kai ummy Ai yanzu na rage chat fa yawaici karatu nake a wayarfa "Abba ne yace "Eh Yana dakyau kuwa Daughter Kucigaba Da dagewa Dai so Nike Naganki Kunzama k'wararriyar likita wadda Zamuyi alfahari DA ita Sannan yayi murmushin Su na manya yace ''Ya maganar Rama allurar DA zakiyiwa Doctor kharina Idan kika Zama likita Ko Harkin yafe"Dariya Najmat tayi tace "Abba Ashe kana sane Ai ban yafe ba Ko Rannnan Saida nayi Mata tuni Dan ta shirya ta kanta zan Fara Amira ce tace ,"Kafin ki Fara ta kanta nizan Fara ta kanki yarinya "Harararta Najmat tayi tace "Ke Idan manya Na magana kidaina sanya mana baki kina yarinya dake Ko mema ya Hada economic DA allura "chab yarinyar nan nalura fa kinrainani Nikike cewa yarinya Kuma ma Ai Na girmeta Ko Abba "Amira ta fad'a tana kallon Abba "Kunga Babu ruwana Da wannan gardamar Taku wacce Bata k'arewa Ko wannenku Sai son Girman Tsiya Ummy ce tace ''kaima Dai ka fad'a Abban Sarat "Najma ce ta Gallawa Amira Harara tace dagayau Aunty zakidinga cemun "Lallai kam SU Aunty ansha wuya "Najib Yana zaune Yana jinsu Dan tunda Ta Shigo d'akin Bai sake.magana ba Yana jinsu Yayi Kamar ma Baya. D'akin Sai Tsaki yakeja a ranshi yace "Na rasa ta inda Uncle Umar ya Had'o dasu najmat yalura Suma saiwani Ji suke.da ita Tsaki yaja aranshi Dan Saboda yarinyar nan Yama k'agara yagama karatun Daya kawoshi ya koma gida. Washegari Najmat ta tashi DA Wani zafaffan zazzabi Gidan Duk sun rikice gashi ba yanda ba ayi DA ita ba Akan akaita asibiti ta kiya Saboda a rayuwarta Babu abunda ta tsana sama DA allura Ko Karin ruwa hakan yasa ta tubure ita baza a Kaita asibiti ba Gashi Taki Shan magani Har Isha'i Najmat zazzabi Bai sauka ba Gashi Duk ta Fara galabaita Amira ce Yar jinya dukta rikice Sai sannu take jera Mata Yanzu ma Amira ce gefenta tana lallashinta Akan ta tashi Ko ruwan tea ne Tasha Amma Ta k'i Tashi "Tashi Amira tayi tayi Dusti waiso.kike.ki.illata kanki ne.ance Kisha magani.kin'kiya ance akaiki asibiti kin k'iya gashi ba abunda Kikaci tunyau ki daure Ko tea ne Kisha banza Najmat tayi Mata tana jinta Dan yanda takeji bazata iya Cin komaiba Tashi Amira tayi tace ''bari naje nakira Abba tunda kin k'iya Dole akaiki asibiti"sannan tafita a palour ta Tarar DA Abba Sai Najib Zuwa wajenshi tayi tace "Abba Najmat fa Har yanzu zazzabin yak'i sauka gashi tak'icin komai tun safe please Abba mukaita asibiti ,"Cike DA nuna.damuwa Abba Yace "jeki ki lallasheta taci Wani Abu saimu tafi asibitin" Tunowa Abba yayi DA Najib doctor ya sashi cewa "son Na manta fa Ashe Muna DA doctor a gidan Dan Allah Ko zaka Shiga ka duba ta " Wace ba lafiya cewar Najib"Abba ne yace "Yarinyatace Najmat tun safe take kwance Dan Allah Shiga ka dubata Ko allurar ta kama kayi.mata Tunda ba Shan magani take ba kartayi ta Zama DA ciwo". "To shikenan Abba Bari naje naduba ta Amira tamai jagora Har d'akin Najmat kwance cikin bargo ya hangota Tsaki yayi a zuciyarshi yace "gwara DA aka damkeki Yanzu Kuma muga ta Rashin kunya"Bakin gadon yaja ya zauna tare DA Hade Rai Kamar Bai tab'a dariya ba amirace ta taimaka Mata ta zaunar DA ita Kan gadon juyawa Najmat tayi idonta ya sauka Kan Najib Daya Hade Rai Kallon Amira tayi cike DA mamaki tayiwa Amira alamar me yakeyi a d'akinsu Amirace tace ,"Doctor ne duba ki zaiyi Ji sukayi Najib ya jefo Mata tambaya"me yake damunki"Kamar bazatayi magana ba hakanan Dai ta Danne zuciyarta tace "zazzabi Sai ciwon kai "Batare Daya Kalle Ko Daya daga cikinsu ba ya tashi baiyi minti biyar ba ya dawo d'auke DA akwatin first aid box Najma Dai tana kwance tanajira taga Ikon Allah batare DA ya kulasu ba yafara Hada allurarshi Saida yagama tukwana ya Kalli Amira yace "Kiyi Mata magana ta shirya allura za Amata "okay Amira tafad'a sannan tace dusti Tashi ki daure"Gwalo idanu Najmat tayi tare DA Tashi zaune tayi kamar Abun tausayi tace "Dan Allah Yayan Nigeria kataimaka ka Maida allurar nan wallahi Bana sonta namaji Sauk'i Dan Allah Kayi Hak'uri ka Maida ita "tafad'a Kamar zatayi Kuka Dan ta lura akwai alamar mugunta Zai Mata Musamman abunda ya hadasu a baya "Shi Najib ma abun dariya yaso ya bashi Amma ya fusge yace "to Idan ba ayi Miki allura ba me Xa ayi Miki ni allura nakeyiwa patients Dan haka Kijuya Ko Kuma so kike Sai an rik'e munke",Amira abun dariya ma Yabata barinsu tayi tace ''bari taje na Hada Mata tea kada ayi allurar ta d'auketa Dan bataci komai ba sannan tafita Dan ta Hada Mata tea Mai kauri. "Uhm uhm Nafa warke yayan.nigeria Nahakura zansha magani Amma a daure a Maida allurar nan "tafad'a tana muzurai tare DA neman Hanyar DA zata tsere Dan bazata tab'a yadda mutumin nan yayi Mata allura ba "Najib Tsaki yaja a ranshi yace" Ashe Duk Rashin kunyar Tata ta iskanci ce jifa yanda ta rikice Akan.allura "Najmat ganin Dai DA gaske allura za ayi Mata Aiko batasan Sanda wata jarumta tazo Mata ba Da gudu ta sauko Daga gado zata Arce hannu Daya Najib yasanya ya fardo Aiko take ta Fad'o jikinshi rigijib saigasu a gado Yana kasa tana Samar kirjinshi Ko wannensu Sai Maida numfashi suke Hakan yayi daidai DA shigowar Abba Dan ya Shigo yak'araganin jikin nata.........✍🏿 *SAUYIN ZUCIYA* *Littafin kuɗi ne!* *It's all about Love, dislike nd romantic story💋* *Nrml grp 300, Vip grp 600, Speacial grp 1k* *Duk da kasancewarsa bawanta ne! amman tun kallon farko da tayi masa taji ta tsaneshi bata son ganinshi ko kaɗan! har ta kai ga wata rana ta saka ƙanwarsa mai suna ifteehal ta gyara turakar Gimbiya Abeela! yayarta ce ta samu matsala a kwakwalwarta sanadiyar hatsarin da sukayi, bata iya tuna komai! Ifteehal kwata-kwata bata huce shekara biyu ba! ko da ta dawo ta tarar da Ifteehal ta rufewa Gimbiya Abeela ido da ɗankwalinta suna wasan ɓuya, Gimbiya Abeela ta zame ta faɗi, ganin haka yasa ta kama Ifteehal ta dinga buga kanta da tiles* *Shin Ifteehal mutuwa za ta yi! ko kuma za ta rayu?* *Shin Bassim wane yanayin zai shiga idan yaji abun da Gimbiya Afsheen tayi wa ƴar uwarsa?* *Idan Ifteehal ta mutuwa ya zai yi da rayuwarsa? ba shi da kowa sai ita! yana da shekara takwas ita kuma Ifteehal tana jaririya aka tsincesu a bola, haka suka taso cikin baƙin ciki da ƙuncin rayuwa! yau kuma ace an wayi gari! ƴar uwarsa da ta rage masa ta mutu ta barsa* *Ana haka Gimbiya Abeela tayi tozali da Bassim! babu abun da bakinta ya fara faɗa sai kiran Bassim da tayi da mijinta! shin ya Gimbiya Afsheen za ta ji al'amarin nan ita da mai martaba tunda halinsu ɗaya dashi* *Gimbiya Abeela za ta auri Bassim ko kuma ba za ta aureshi ba?* *Ana wata ga wata! Hajiya Asabe matar ƙanin mai martaba wacce take da yara guda biyu mace da namiji gaba ɗayansu ƴan fancy life ne! babu abun da suka iya sai yawon club dan ita Iklima har mata nema take🥺basu da wani buri irin su ga bayan mai martaba da iyalansa babban ɗanta wanda ya zama kamar bunsuru wajen neman mata take so ta ga an haɗa a matsayin sarki* *Shin burinsu zai cika kuwa?* *Gimbiya Afsheen zata ankare da shirinsu kuwa? tunda ita gaba ɗaya hankalinta yana kan Bassim dan bata da wani buri irin ta ga bayansa shi da ƙanwarsa! to gashi ita ma ana so a ga bayanta ita da iyayenta da ƴan uwanta* *Labari ne mai dogon zango, wanda tsayawa nayi muku bayanin yadda yake to zamu daɗe ban gama ba, idan kuna buƙatar karantashi ku turo kuɗinku ta wannan account number 0017770369, Aisha muhammad Yusuf, Unity bank, sai ku turo shaidarku ta 08122188717 ko kuma hoton kati ta number ban da vtu plss* *Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [10/30, 7:30 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* _______________________________ *PAGE 37 & 38* ________________________________ Turus yayi ganin wannan bakin tashin hankalin a gidanshi a zuciyarshi yace "watau yaran nan daman irin abunda suke Kenan Amma a fili su nunawa mutane basa jituwa lallai yaran nan suna mana Wasa DA hankali lallai Yaran zamaninnan a Gansu a kyalesu Amma Idan kunsan wata bakusan wata ba sannan ya juya Dan bazai juri ganin abun. Takaicin wannan ba. Najmat DA Najib DA basusan Bama za wanzuwar Abba a wajen harya tafi kowannensu sauke ajiyar zuciya kawai suke kowannensu ya kafe Dan uwanshi DA kallo Kamar su cinye juna Najmat ce tayi karfin halin cewa " Dan Allah ka tadani nauyi "Sai sannan Najib yatuna Akan ta yake Tsaki yaja sannan ya Mike itama ta Mike tana gunguni DA turo baki. Najib ne ya ce "Karamar marar kunya kina Bata mun time Bana Bata lokaci na a banza Dan haka ki nutsu nayi Maki inada aikin Yi "Turo baki tayi tare DA kauda kai tace "Ai ba cewa nayi kaduba niba Ko nace Ina bukatar taimakonka Kuma allurace banaso Ko ana dole kujimun naci Wanda za ayiwa Abu yace Baya so to dole ne "ta ida fad'a tana murguda baki. Najib. Tsayawa yayi Yana kallon ikon Allah a zuciyarshi yace "watau yarinyarsam Bata DA mutunci Ko kadan "Yace "Okay haka kika ce Ko"Murguda baki tayi tace "Eh din"Bata rufe bakiba taji ya damkar Mata hannu tare DA juyata ya kwantar DA ita rubda ciki Kan gado ya Danne Mata hannu Da k'afa Kuka ta fashe dashi tare DA ihu baima San tanayiba Take Ko ya Danna Mata sirinji Hada muguntarshi Ihu Najma tasa Saida yagama tukwana ya tadata tare Da Jan Tsaki yace "Duk Rashin kunyar Taki ta banza ce Ashe matsoraciya kawai common allura Amma Ji yanda tarikice Kamar wacce akace za a kashe "Cikin kuka tace Allah ya isa mugu kawai Kuma anyidin Azzalumi Allah saiya sakamun,"Wara idanu yayi tare DA nuna kanshi yace "Dani kike"Eh din dakai din Ake me zaka iya"Zako kiga abunda zan iya yafad'a Yana nufarta DA allura gadan gadan Aiko DA gudu Ta Arce tayi waje A palour ta Tarar DA Ummy DA Abba nan tafad'a cinyarta tana Mata Kuka ummy dukta rikice tana tambayarta lafiya ta kyaleta Najib ne yafito cikin tafiyarshi ta kasaitattun maza masu Ji DA kansu ta fito baiko Kalli gefen taba yasamu wuri ya zauna Abba Ko kallonsu baiyi ba musamman Najib Dan a k'ule yake dashi. Najmat tanaga shigowarshi palour tace "Ummy Wai Dan Allah yaushe mutumin nan Zaibar gidan nan Wallahi Ni Na k'agara Yatafi Mugu ne ta ida fad'a tana jefa mishi Harara"Murmushi ummy tayi tace "Kee Najmat bansan Rashin kunya fa Baki ganin ya girmeku Kuma Babu inda zashi Shima yayanku ne Yana nan tare damu"Najib Ko baiko d'ago ya kallesu ba bare har suyi tunanin Zai tanka Saima Danne Danne wayarshi Daya Fara Karshema ficewa yayi a palourn. Cikin 4days Najmat taji Sauk'i sosai Ba abunda Ke damunta Kamar kullum.tana Tashi Bayan tayi wanka tayi brush ta wanke kanta Gaban mirror tazauna tare DA kunna hand drayer ta busar Da lausassan bakin gashinta Mai matukar baki DA silbi Ga tsawo Parking dinshi tayi a kasa tare DA shafeshi Da mayuyyukan gyaran gashi masu dadin kamshi lotion ta shafa sannan tadanyi simple make up bamai wata hayaniya ba hadaddiyar doguwar Rigarta Abaya brown ta d'auko ta Sanya Sannan ta yafa k'aramin belt d'in rigar turarurrukanta masu mugun kamshi Ta feffesa inbanda sihirtaccen kamshi ba abunda Ke Tashi daga.wajen ta Koban fad'a ba Mai karatu kunsan Irin haduwar DA tayi ma B'ata baki ne wayarta kirar iPhone 12 pro max ta d'auka sannan tafice Dan sauri take kartayi latti Saboda Amira yau tana gida Bata DA lectures. Abba DA Ummy ta Tarar a palourn Hug d'insu Daya bayan d'aya tayi tare DA gaishesu tayi suka amsa Mata cike DA kulawa Kai tsaye dining area ta nufa Tare Da Jan 'Daya daga cikin chairs d'in kujerar Ta zauna d'ago idonta tayi ta kalleshi Sanye yake cikin bak'ar suit Sai Wando White Sumarnan Tashi lufluf gwanin sha'awa waya mak'ale a kunnenshi Duk kusancinta dashi ba tajin abunda yake cewa Sosai Sai murmushi yake DA alamar Yanajin dadin hirar DA suke Tsaki taja kasa_kasa tace "mutum yayi ta Wani mak'ale murya Kamar wata mace tafad'a tare DA Fara Breakfast dinta. Najib Ko Yana jinta Dan Koya kayi magana Sai yajika Shi yanzu Shirmen yarinyar nan ya rage bashi haushi ma Dariya ta koma bashi Aunty amarya ce suke waya tanacemai tayi missing nashi Shima yace nayi missing naki Over my mom ''daga bangarenta tace "son yafa kamata ace kazo ka kawo mana ziyara karkaga Babu kai gidan ba Dadi ,"shagwabe Face yayi yace "Karki damu Mom Ai shekara biyu Kamar Sati biyu ne Kamar Wasa zakiji Ance nagama"Son Kenan wayau zakamun Sannan. Tace "Patan Dai kana yawaita karatun alk'ur'ani sannan zoben nan Dana baka Fatan Tana hannunka kasan Ba a Wasa DA kyautar iyaye "Murmushinshi Mai tsada ya saki sannan ya murza zoben hannunnshi yace "Mom kinganta nan ma Hannuna Koda yaushe ita nake kallo sainaji Kamar kece a gabana Ai bazanyi Wasa Da special Abu Daga wajen Mama Na ba"Murmushi Dayan bangaren tayi tace "Allah yayi Albarka son Ya baka Mata tagari Murmushi kawai yayi yace Sai anjima.mom sannan sukayi bankwana. "Najmat tana jinsu Duk abunda sukecewa Daga Karshe kasancewar sunyi kusa DA yawa Lura DA tayi DA mahaifiyarshi ce yake waya Duk tana sauraren hirarsu gwanin sha'awa abun saiya burgeta tayi inama ace itace Ke haka Da mahaifiyarta Ko a waya ne Hakan yasa zuciyarta saurin Karaya Batasan lokacin DA wasu zafaffun hawaye suka zubo Mata ba Jin an ambaci zobe ya Sanyata d'agowa Idonta ne ya sauka a Hadaddiyar zoben zinaren dake hannunnshi Sai walk'iya take Ji tayi a Duniya Babu Abunda take so sama DA zoben dake hannunnshi Kafe zoben Tayi DA kallo ba Ko kiftawa gabantane ya tsananta fad'uwa ba tasan lokacin DA hawaye Ke zuba Daga idanunta ba Kuma Taki kauda idonta Daga Kan zoben Saboda batajin zata iya gajiya DA kallonta Najib Duk Yana Lura DA sauyawar yanayin nata DA Kuma hawayen nata lokaci guda Shi Abun mamakima ya bashi ganin. Lokaci guda mood d'inta ya chanza ta Zama wata kalar tausayi gashi yalura DA yanda ta Kafe zoben hannunnshi DA kallo bako kiftawa Lokaci guda kallon zoben yayi sannan ya kalleta d'auke hannunnshi yayi Daga Kan table din dining ya maidashi gefen Shi Amma ga mamakinshi Sai Yaga Ta koma kallonta saitin inda hannun nashi yake Gyaran murya yayi Wanda shiya maido DA Najmat Daga duniyar tunanin data Lula Sai yanzu ta tuna zoben a hannun .Wanda take Ba tare DA tagama breakfast dinba Dan gaba d'aya hankalinta Baya jikinta ta Tashi tare DA ficewa DA niyyar Kota halin k'ak'a zoben .nan saitazo hannunta hakanan.kawai taji tana k'aunar zoben Dukda zobayen gold d'in dake hannayanta wadda dayar ma Abiy ne ya Saya Mata Amma batajin tana sonsu Rabin yanda takeson ta hannun marar tarbiyar d'an Nigeria d'inchan Kamar yanda tasa mashi Suna a haka harta Shiga Mota DA tunanin yanda zatayi zoben can tazo hannunta ...✍🏿 *Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [11/2, 7:47 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *Shafin nan sadaukarwane gareki Maman siddiqa hakika comment d'inki ba k'aramun karfafamun guiwa yake ba Shafin nan nakine kiyi yanda kikeso dashi love you wujiga wujiga wollah*😄 ._________________________________ *PAGE 39 & 40* ___________________________________ Najib Ko d'age kafad'a yayi tare DA Tashi ya tafi school Dan yanzu dakanshi yake zuwa yagane hanyoyin. Suna gama lectures kai tsaye inda tayi parking ta nufa taja motarta ta tafi Tazo daidai wata unguwa a hanyarta ta zuwa gida kawai taji motar ta ta tsaya Tayi_tayi ta tada ita Amma tak'i Tashi Gashi ta kãsa gane inda matsalan take fitowa tayi Daga motar gashi ta lura unguwar tsit ce bakajin Karan komai Sai tsintsaye Ko wucewar mutane Ko motoci Bata gani Saboda ba afiyabin Hanyar ba itama tana bine Saboda tafi Mata saukin zuwa gida sabida kwata kwata anguwar kamarma a daji ne take Dan gidajenma basufi Goma ba Shima a ciccire Chan gida saikayi Nisa ka hango Wani gidan. "Waige waige kawai take Ko zata samu Wanda Zai taimaka Mata Amma Bata samu ba Gashi Har yamma Tayi tsorone Da Fargaba suka ziyarceta Dan ita kanta ta Fara tsorata DA wajen Addu'a kawai take ta neman d'auki gashi wayarta ta Mutu Babu chaji bare takira gida azo a tafi Da ita GA magriba Na gabatowa Har k',Walla tafara Tana Haka ta hango wasu Maza su biyu Na fitowa Daga Wani gidajen dake cikin anguwar . "Alhmdllh tafad'a Suna hangota kai tsaye wajenta suka nufa d'aya yayi dariyar mugunta cikin harshensu Na Hindi yacema d'an uwanshi "Rohan see this beautiful baby gaskiya yau munyi babban kamu"Daya ne yayi dariya Shima yace "Ai saina rigaka d'anata Waccen dagaci zatayi sugar harsuka Isa wajen DA take Suna firarsu ta iskanci. Suna Isa gab Da ita d'aya yace "Hey Baby barka DA hutawa"Kallonsu Najmat tayi lokaci guda tsoro ya tsargu a cikin zuciyarta ganin irin kallon DA suke Mata tare DA nufota Tafara ja baya dariya suka kece DA ita tare DA nuna ta sukace "Ke har kina Da Hanyar tsarewa a wajen nan Ai Babu Mai iya Cetonki Y'ar budurwa gwarama ki bamu had'inkai ba Wani Abu zayi Miki ba Muna gamawa zamu barki kitafi. "innalillahi wa Inna ilahiraji un Tafad'a tana runtse idonta tace auzubillahi Zata iya cewa a iya rayuwarta Bata tab'a Shiga tashin hankalin data tsinta kanta cikinshi ba Bude idanunta tayi DA suka ciko DA kwalla tace "don't touch me please karkumun komai Niba Y'ar iska bace Dan Allah "Dariya suka Kara kacewa Daya ya damki hannunta Yace "Haba y'an Mata Ina ganinki wayayya Yazakina mana maganar gidadawa Iya karfinta ta fusge hannunta tare DA cewa. "Tunda Na Biku DA laluma kunkiya to Bari kuji wallahi Wani yayi gigin tab'ani saina kasheshi banzaye y'an iskanbanza Ta ida fad'a Ranta a matukar b'ace "Maimakon Suji haushi Dariya suka Kara kecewa D'aya ya damketa Zai d'auketa Aiko Iya karfinta ta fusge tare Da rugawa a guje Binta sukayi Suma a guje gudu kawai take batare DA tasan inda ta nufa ba Suma Binta suke kasancewar gudun mace Da Namiji ba Daya Ba Aiko batayi Nisa ba suka chafkota Ihu NAJMAT tasa Aiko nan suka rirriketa Daga ya sungumeta wutsil wutsiltu take tana ihu tana neman dauki suko dariya suke Suna cewa "keda kike DA karfin guduwa yanzunma Sai karfinki ya kwaceki. Sai wajen 6 ya fito daga lectures Yana Shiga Mota zaitada motarshi yaji wayarshi Na ringing d'agawa yayi yaga murza ne Ke Kiran Bayan sun gaisa nan murza Ke fadamai Allah yayiwa mahaifinshi rasuwa kwana biyu Da suka wuce "Subhanallahi Najib yafad'a tare DA cewa ,"Shine baka sanar Daniba dawuri sannu brother Allah ubangiji yajikanshi yasa ya huta Gani nan zuwa yanzu nayi muku ta Aziya ". Daga nan kai tsaye ma unguwar SU murza ya nufa Dan ya rik'e unguwar tun zuwanshi Na farko kasancewar hanyarshi ce ta komawa. Yana zuwa yayi musu ta Aziya baijimaba ya fito a lokacin ana Kiran magriba murxa yabukaci DA yayi Sallah saiya wuce Hakan akayi Saida yayi Sallah tukwana sukayi bankwana Tafiya Yake cikin Mota bakajin komai Sai k'aran AC tuk'i yake cikin nutsuwa yayi Nisa nan yafara jiyo Kukan mace Da ihunta Kamar tana neman d'auki Nan yafara waige waige Chan ya hango wasu Maza biyu D'aya sungume Da wata budurwa dake wutsil wutsiltu DA neman d'auki Da ihu Harzai wuce Saboda Yana tsoron taimako a zamaninnan Amma yaji zuciyarshi ta kãsa koba komai Saboda Allah zaiyi Kuma ya lura yarinyar Na bukatar taimakonshi Parking yayi tare DA nufar wajensu cike DA b'acin Rai sunzo daidai zasu Shiga Wani gida DA ita ga alamun gidansune Yayi saurin Shan gabansu tare DA wanke d'aya Da Mari D'agowa yayi tare DA shak'arshi ganin Hakan yasa d'aya sakinta Tsabar rud'u Nan tafad'i wajen sumammiya Dan Tariga ta sadak'as Da rayuwa Najib baimabi ta kan yarinyar ba dasu ya Fara Aiko nan yahau Naushinsu ba k'akkautawa Duk ya lakata SU ganin Dai mutumin nan yafi k',arfinsu ya sasu rugawa gidansu tare Da Saka key . Najib Ko Allah wadarai yayi DA halinsu tare Da Maida Kallonshi ga yarinyar dake kwance a sume Gashin kanta ya rufe Mata fuska Rasa yanda zaiyi DA ita yayi Gashi Babu halin Ya Barta a wajen hakan yasashi kawai d'auksrta tare DA nufa DA ita Mota front seat ya ajeta Tare Da d'auko ruwa Ya yayyafa Mata Firgit ta Tashi tare da sakin Kuka tace "Dan Allah karkumin.komai wallahi niba Yar iska bace Karku illatani Idanunta a rufe take maganar nan Dan Bata son ta d'aga su ma. "mamaki yakama Najib Dan bazai tab'a manta muryar marar kunyar yarinyar nan ba Kamar yanda Shima yasa Mata Suna mamaki ya kamashi Meya kawo ta nan wajen a wannan lokacin Yana haka yaji ta Bude idanunta tare DA saukesu akanshi DA Shima ita yake kallo DA mamakinta tace "Najib "Karo Na farko Data tab'a Kiran sunanshi Kenan''Shima.kallonta yayi yace "why are you here ''Goge hawayenta tayi tace ''Mota tace ta lalace a hanya "shine wasu suka Biyoni ''ta Ida fad'a tana hawaye. "Allah kiyaye gaba yafad'a tare DA cewa Ina motar taki "Kasancewar a tsorace Take sosai yasata cewa "Gatachan Dan Allah mu Barta ka maidani gida Dan Girman Allah kada ka barni a wajen nan nasan Idan ka tuno DA abinda nayi Maka a baya zaisa Ka barni SU b'atamun rayuwa Dan Allah ka taimakamun "ta ida fad'a tana sakin Kuka. "Girgiza kai kawai Najib yayi Dan ya lura sha'anin yarinyar akwai tsantsar yarinta Dan son kwantar Mata DA hankali.ya sashi cewa ,''kinga kiyi shiru bazan barki anan wajenba Koda ace bansankiba zantaimakeki Allah kiyaye gaba Dai kidinga kiyayewa yafad'a Yana kokarin tada motarshi. Mamaki yacika Najmat Jin kalamanshi Dan a zatonta Irin Cin fuskar DA tamai a baya bazai Bari ya taimake taba Sai yanzu take nadamar irin abunda tamai Ashe mutum Amfaninshi yawa gareshi bantab'a tunanin mutumin nan Zai taimakeni DA komai ba Ashe ba haka bane mutum Babbar daraja ce dashi Dan ba a wulakantashi ita Duk kunya ma ta cikata a sanyayae tace "Nagode bansan Da Wasu Kalamai zanyi amfani wajen gode Maka ba ka taimakeni a daidai lokacin DA nafi bukatar taimako ka tseratarmun DA mutuncina Dan Allah Kayi Hak'urin Duk irin abunda nayi Maka a baya kayafemun Sharrin shai'dan ne ". "Karo Na farko Kenan DA mace tayi Abu ya burge Shi Yana son mutum Mai saurin Bada Hak'uri Akan laifin DA yayi batare da Girman kai ba burgewa na biyu kuma DA yanda tayi kokarin Kare mutunci ta Kenan akwai sauran kamulallun Mata a zamanin nan danshi Duk kud'in Goro yake musu yalura yarinyar Rashin kunyace kawai DA ita Amma tana Da tsananin kamun kai Da tarbiya Dan ya lura DA mu'amularta DA mutane Ko a makaranta DA yanda mutane Ke respected d'inta Saiyaji d'abi'unta sun burgeshi Batare Daya d'ago Ido ya kalleta ba yace "Kidainayimun godiya Allah zakiyiwa godiya danshi Yakawoni harna taimakeki maganar abunda yafaru a baya Kuma ya wuce ". Harsuka Isa gida ba Mai magana Kowa DA tunanin DA yake Suna Isa Najib yafara fita sannan Najmat ta fita Haryayi gaba ta Ruga DA gudu tare DA Shan gabanshi ta Hada hannayenta biyu tace " don't tell Abba please if the shaulder of the knower will tell my Abiy" "Kallonta yayi yace "Why? Saboda me bakyason abin naki ya sani'' "Cike DA muryarta Da ta saba DA shagwab'a tace "Hankalinshi Zai Tashi Nikuma banason abunda Zai tada Mai hankali Kuma Zai iya cewa ya sauyamun school Koya hadani DA bodyguards nikuma banaso''. "D'an wara idanu Najib yayi Yace "Sabida wannan abun zaisa yayi haka "Gyad'a kai tayi tace "Eh nasan Abiy Zai iyama fin haka""Gyad'a kai kawai yayi yace bamaiji "Murmushi tayi tace ,"nagode sannan ta wuce gida Shima Najib ya Shige room dinshi ta k'ofar Baya. Koda suka tambayeta me ya tsaidata ta fad'a musu ne kawai Motartace ta samu matsala a hanya saita barota ta hayo napep. DA misalin karfe Tara Na dare kwance take idanunta lumshe Kamar Mai bcci alhalin ba bacci take ba tunanin irin abubuwan datayiwa Najib tayi tayi dadinta Daya DA Allah yasa lokacin DA tadinga cimai fuska batayi DA yaren dazai gane ba hakan yasa taji sanyi a ranta. Amirace ta Shigo tace "Dusti Wai yau meke damunki tunda kika dawo daga school Naga yanayinki ya chanza Ko Magana bakya sonmu "Batare DA ta Bude idanunta ba tace "nothing Dusti I just don't wan't to talk ne kawai"Hmmm yau Kuma kece bakison Magana kodai Wani abun yafaru ne kike b'oyemun "Gajiya Da maganganun Amira yasanyata juyawa tare DA cewa "good night". Washe gari Najma Bayan tagama shirinta Na school DA misalin 9 am itada Amira a palour suka Tarar DA Najib Na gaisawa dasu Abba ga alamun Shima makaranta Zai wuce "good morning yaya Najmat tafad'a tana kallonshi " Amira mamaki Duk ya gama cikata Najmat ce yau ta gaishe DA Najib Shima kanshi yayi mamaki Cike DA nuna kulawa yace "morning kintashi lfy"Steady tafad'a ganin Zai fita gashi ta tsorata Dan bazata Kara bin Hanyar ita kad'ai ba yasa ta cewa "Dan Allah Ko zaka saukemu "Murmushi Jin Dadi ummy tayi ganin yanda Najma yau Ke respected din Najib "Okay follow me "Najib yafada tare DA ficewa parking space Suma binshi sukayi Amira Dai ta Zama Kamar gunki kallon Najma kawai take Dan taga yanda tayi mugun sauyawa Hakan yasata cewa "Dusti Wai Ko kinshirya DA Yaya Najib ne"Harararta Najmat tayi tace "Kede kinshiga ukku DA gulma "Dariya Amira tayi tace "eh naji nidai fad'amun ''badai zakijiba Najmat tafad'a tana Shiga back seat Sannan Amira ta Shiga front seat suka tafi . Wajen dawowama Suna gama lectures suka nufi inda yayi parking Basu jimaba sukaga tahowarshi tare DA Wani course mate d'inshi Suna Hira harsuka iso Inda suke Suna Magana DA yaren Hindi Tsayawa Najma DA Amira sukayi kallon Najib dake ta Magana DA harshen Hindi saika rantse daman yarenshi ne kallon kallo Najma DA Amira suka shigayi kasa daurewa Najmat tayi Kenan Daman yanajin Duk abubuwan DA nake cemai ganin wancen Yatafi ya sata kallonshi tace "Daman kanajin Harshen Hindi ne Murmushinshi Mai tsada ya saki tare Da d'age Mata gira yace "Tun aashcharyachakit ho" (Kina mamaki ne) wara idanunta tayi tace "main ek pankti mein teen hoon Aur jitane shabdeein"(Na Shiga ukku Kenan Duk maganar Dana fad'a Maka kwanaki kanajina kayi shiru) Dan shafa sajenshi yayi tare DA sakin wani rikitaccen Murmushi ya Dan sake D'age gira yace " Agar nabhee abhee Nahin to ham bhaasha bolate hain (Idan banjiki ba a lokacin yanzu Har zanji abunda kikace)...✍🏿 *Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *_Miss Hajo ce_*🤙🏿 [11/3, 11:30 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* _________________________________ *PAGE 41 & 42* __________________________________ Najmat DA kunya tagama rufeta Kenan Duk yaji irin tijarar DA tamai Kenan sadda kanta tayi tace Dan.....katseta yayi DA cewa banason wata doguwar Magana Kushiga mu wuce D'agowa tayi tana Dan Marairaice fuska tace Amma yakamata Na Baka Hak'.....K'ara katseta yayi ta Hanyar cewa kin manta nace komai ya wuce "Batare Da ta Bari sun sake had'a Ido ba tayi sauri zata Shiga back seat Amira ta Rigata tana Mata dariya Harararta tayi tare DA karkada Mata yatsa sannan ta Shiga front seat Shima ya zagaya yashiga yajasu suka tafi. Tunda suka d'au hanya ba Mai magana ganin yanda Najmat ta takura Tayi sanyi ya sanyashi Janta Da Hira yace "ya school din Fatan Kuna Maida hankali''murmushi tayi tare DA sadda kai tana Wasa DA zoben yatsarta cikin zazzak'ar muryarta Mai rikita Mai sauraro tace "Alhamdulillahi"Masha Allah kawai yace sannan yace Allah Bada SA ar jarabawar "Ameeen ''ta amsa Har lokacin kanta sadde Dan Wani mugun. Nauyinshi take Ji. Suna Isa Najma Bata Bari sun Hada idoba tayi sauri ta fita Har tuntube taso tayi Dan sauri girgiza kai kawai Najib yayi. A palour Amira ta sameta dariya Amira ta Hauyi ba kakkautawa tace "Ashe dusty kinsan Jin kunya Ji yanda kike Wani sassada kai Kamar ta kirki"sannan tace Amma fa bake ba dusty koni Saida Naji kunya "Tab'e baki Najmat tayi tace "Saida kika gamamun dariyar sannan tace hmmmmm kede Bari Wallahi Ji nayi Kamar in. Nutse Dan kunya Duk a takure nadawo "Amirace. Tace "kaico Ashe Yana jinki Gaskiya yanama DA Hak'uri kam Ina ganinshi Kamar Mai mugun Hali Ashe Yana DA saukin kai"hmmm Ai ya koya mana hankali Najmat tafada tana nufar dining Dan DA yunwa ta dawo. Kasancewar yau weekend Kuma Basu Da exams yasanyasu Sai wajen 1 suka Tashi Daga bacci Bayan Sallar asuba Najmat ce ta Tashi Da Bakar yunwa tana Tashi ta fito daga ita Sai gajeruwar doguwar rigar bacci fitowa tayi Dan samawa kanta abunda zataci Bata Tarar DA Kowa ba a palour dining taje ta duba Babu Abinci Tana turo Baki ta Shiga kitchen Dan Har wani bibbiyu take Gani ba Bata lokaci ta Had'a ruwan tea Da wainar k'wai sannan ta fito ta zauna a dining tafara Ci Tana cikinci taga fitowar Najib Daga bedroom dinshi GA alamun Shima yunwar yakeji Sadda kai tayi Dan Har yanzu kunyar had'a Ido dashi take. Kan Sopa ya zauna Yana d'an Danna waya Batare Daya Kalle taba yace "Akwai Abinci ne?itama d'agowa tayi tace "A a saidai in nahad'a Maka ruwan tea"Okay thnks "Yafad'a tana gamawa ta Had'a Mai ta mik'amai tazo wucewa yace ,"yadai Naga Kinyi shiru Ko baki DA lafiya"dan murmushi Tayi tace Bakomai kawai dai "kawai dai Me yafad'a Yana kurbar ruwan tea din data hadomai "Uhm Bafa komai tafad'a cikin Y'ar shagwab'a ,''gyada kai kawai yayi. Tun Daga lokacin nan Shiri ya shiga tsakanin Najmat DA Najib sosai suke zaunawa suyi Hira sometimes DA yamma zasu zauna a Garden suna hirar rayuwa yauma kamar kullum zaune take a harabar gidan ita kad'ai tana tunanin mahaifiyarta Dan cikin kwanakin nan tana yawan mafarkinta Wai tana kuka tana Bude Mata hannayenta tazo gareta Amma Nisan dake tsakaninsu sun kasa had'uwa Lurar DA tayi Duk inda mahaifiyarta take lallai tana buk'atar ganin ta k'walla ce ta zubo Mata batare DA ta saniba. Najib ne ya hangota Wajen yanufa Yajima tsaye Amma batasan DA zuwanshiba Sabida tayi Nisa DA lulawa duniyar tunanin Tab'i ya Mata shiya fargar DA ita ganinshi tsaye ya Hade Rai ya Sanyata K'ik'irar murmushi tace "ka fito Kenan"Harararta yayi yace "tunanin me kike tun dazu nake tsaye bakisan DA zuwa Na ba "Tunani Kuma "Tafad'a Tana nuna alamun bakomai"Zaunawa yayi kusa da ita tare DA cewa "Eh Tunani Na sameki kinayi"Dan son barin. Zancen ya sata cewa "Gobe fa su Abiy zasu dawo karkaga yanda nayi missing d'insu "D'an wara idanu yayi yace "Haba kice gobe Muna DA Manyan bak'i "Murmushi tayi tace "Sosai ma gobe zanga Abiy na ,Nasan Yana Chan Yana missing d'ina"Dan hararanta yayi yace "inye Y'ar Abiy Ai nasan ma ya manta dake ba Wani kewanki Da zaiyi,"Shagwab'a fuska tayi tace "uhm Allah kadaina cewa ya manta Dani Abiy bazai manta Daniba tafad'a tana turo baki''dariya yayi yace "Injiwa Ai zamu Gani goben Idan ya dawo "Didddira k'afa tafara cikin shagwab'a Kamar zatayi Kuka tace "Allah Ni kadainacewa haka inba haka ba zamu b,ata ''Sorrry *NAJMAT ABIY* d'inta Wasa nake Maki yaza ayi Abiy ya manta da Tauraruwarshi."yafad'a Yana d'an murmushi. Lokaci guda ta saki murmushi Jin yakirata DA. Sunan datafi kauna tace "Waya fad'a Maka sunan Dana fiso *NAJMAT ABIY* d'an mak'ale kafada yayi yace "bazan fad'a ba "Uhm uhm Dan Allah fa nace Badan Halina ba " "hmmm lokacin Dakikayi ta borin bazan Hau Miki Mota ba Lokacin Naji Ankiraki DA sunan kin hak'ura"Dariya tayi tare DA rufe fuska tace "ohhh Na tuna ," Shiru yayi Itama daganan Bata sake magana ba Idonta ne ya kai Kan zoben hannunnshi k'ure zoben Tayi ta Kallo bako k'autawa Jin shiru yasanya Najib juyawa ya kalleta yaga zoben hannunnshi take kallo tayi 5 minutes tana kallo batare Da k'ak'ak'autawaba Hakan yasashi gyaran murya yace "Kar a cinyemun zobe fa"Sai sannan hankalinta yadawo tadanyi murmushi tare DA sadda kai tace "Zoben ce ta burgeni Dan Allah Ko zaka Bani Shan Miya" Cikin zolaya yace "a a a bazan baki ita ba Ko kallanmunma Da kikayi batare DA Izini Na ba ya Isa "d'an shagwab'a fuska tayi tace "Dan Allah to ka sayarmun da ita" batare DA ya kalletaba yace "Ba ta sayar wa bace kintab'a Ganin ansayar DA kyautar DA akayi Maka kyautarma ta zobe Daga waje Mai mahimmanci "Uhm to waya Baka Ko Auntyn mu Tabaka "Tafad'a cike DA zallar k'uruciya "murmushi yayi yace "Auntynku Kuma wa Kenan" nufina girl friend d'inka Ko Wife d'inka ,"girgiza Mata kai yayi yace"A a a Dan yafara gajiya DA Surutunta". "To waya Baka "tafad'a tana d'an Marairaice fuska "gajiya Da Surutunta ya sashi cewa "Mahaifiyata tace ta Bani ita dazan taho tace Nadinga kallonta Kamar itace gabana Kinga Bai kamata ta fita Daga hannu Naba Kamar Na sab'a Mata alkawari ne Kuma kinsan ba 'a Wasa Da kyautar iyaye koke Idan mamanki tamiki kyauta zakiba Wani ne ". Tunda ya Fara maganar zuciyarta Ta Karaya Yana k'arasawa ta Gyad'a Mai kai alamun ta fahimta sannan tad'an sadda kanta sakamakon kukan dayaci k'arfinta ganin. Kamar DA gangam ya fad'a Mata maganganunan Gani take gorine yake Mata Tashi tayi tana Kuka tare DA rugawa tayi cikin. Gida Mamaki Duk yagama cika Najib to me akayi. Mata Na Kuka anan Hakan ya Sanya Shi Tashi tare DA Binta Koda ya Shiga palour Bai isketaba Amira ya Tarar. Kallonta yayi yace "Najmat ta wuce nan "Kallonshi tayi tace "eh Yanzu ta wuce tana Kuka bansan me aka Mata ba Na bita Kuma ta Sanya key ,"Tsaki yaja tare DA Zama Kan sofa "Amirace tace Yaya Ko Wani yayi Mata Wani abun "Tsaki ya kumaja yace "Daga Muna Hira shine tahau Kuka ta rugo DA gudu" d'an Tunani Amira tayi tace ''to Daga Hira me zaisanyata kuka sannan ta cija yatsa alamun Tunani Kamar ta tuno.wani .Abu tace "To Ko cikin hirar kayi Mata zancen mahaifiyarka Ko tayi Maka zancen"d'agowa yayi yace "Tabbas anyi haka akwai damuwanei'?" Amirace tace "Ayya dole tayi Kuka ,ba ayi Mata zancen uwa Saitaga Kamar Gori ne Ake Mata "DA mamaki Najib yace Gori Kuma ,?,to ita Ina mahaifiyar Tata . Cike DA tausayin aminiyar Tata tace "Mamanta ta rasu tun wajen haihuwarta Amma Har yanzu Wai Bata yarda DA tarasu ba shiyasa "lokaci guda Najib yaji ta bashi tausayi Saboda Yana mugun tausayin maraya musamman Wanda ya rasa uwa Saiyaji ta bashi tausayi cike DA tausayawa yace "Allahsarki Allah yājikanta sannan yace Dan Allah jeki ki lallasheta ''murmushi Amira tayi tace "to "Sannan ta Tashi Shima yabar d'akin cike DA tausayin halin maraicin data tsinci kanta tun. K'uruciya Saiyaji baiji dadin maganar DA ya Mata ba. Dakyal Amira ta samu Najmat ta Bude k'ofar dakyal ta samu ta lallasheta Har tayi shiru Amma a zuciyar Najma ta innata Babu ruwanta DA Najib tunda yayi Mata wannan cin fuskar Dan a tunaninta DA gangam yayi Mata. Yau SU Abiy suka dawo sun samu tarba ta musamman Daga wajensu ummy Najmat Ko Dadi Kamar Sallah tana mak'ale DA Abiy tana.mai shagwab'a Yana biyemata "Tace Abiy Dina nayi.missing d'inka sosaifa ''shafa kanta yayi yace "Nima.nayi kewanki soosai daughtern Abiy Saida natafi Naji Daman Na Bari Kingama jarabawar mutafi tare Dan kullun DA tunanin Ko daughtern Abiy ya take nake "murmushin Jin dad'i tayi tace "Nima haka kullun tunanin ya Abiy Na yake Sannan tace "Me Abiy ya rokamun ne"murmushinsu Na manya yayi yace "Miji Na gari Na rok'ama *NAJMAT ABIY* D'inta sannan yace Har yanzu Dai kink'i kawomun sirikina ''yafada DA sigar zolaya. Rufe fuska tayi tare DA sinne kai a kafadarshi "Dariya yayi yace ''yau Kuma Abiy akejin Kunya "Kara rufe fuska tayi tace "uhm uhm uhm Abiy Nifa yarinyace Har yanzu "Jaririyama kuwa Aunty nafisa tafad'a tana saukawo Daga Kan stairs"Dariya Najma tayi tace ''yawwa auntyna fad'a masa Dai"Hararta Aunty nafisa tayi tace ''Ai Maganace Na fad'a Maki Nimadai Nakagara Naga bikin daughter''Uhm uhm Aunty kema haka zakice Ko Ko tokuma daina tunanin wannan Dan Babu inda zani Na barku ."Aunty nafisa ce tace "Aiko saimu Gani kina Gama makaranta zan aurar dake "dariya Najmat tayi tace ,"to saimu Gani Ai knocking din DA akayi yakatse musu hirarsu NAJMAT ce ta Tashi taje ta Bude ''Najib ne tagani tsaye Sanye cikin farar suit Bata Rai tayi tare DA matsamai Shima batare Da ya bi ta kantaba ya wuce Daman Abiy yazoyiwa sannu DA zuwa Shima Saida Abba ya tilastamai Najmat Ko dakinta ta wuce Dan batason abunda Zai sake had'ata dashi tunda yayi Mata Gori . NAJIB Bayan sun gaisa dasu Abiy yayi musu sannu Da zuwa suka Ansamai cikin sakin fuska DA Fara a "Abiy yace ya karatu Fatan ana Maida hankali"Kanshi. Sadde yace alhmdllh''To madalla Allah yataimaka "Ameen Najib yafada yace ,"Allah huta gajiya Saida safe yafad'a Yana Tashi nan Aunty nafisa ta tsaidashi ta d'aukomai tsarabar dabino DA zamzam godiya yayi Mata sannan yawuce . Najmat wasan buya take DA Najib Dan batason abunda Zai had'ata dashi Daman Abba yasama musu driver yanzu shike kaisu school Ko taganshi a hanya zata sauya hanya yauma kamar Kullum gidansu Amira ta nufa Dan tarage zuwa ma Saboda karta had'u dashi yaumad'in Dan Kar Amira tayi fushi yasata Shiga tana Shiga ta iske bakowa a palourn Nan Mai aikinsu Ke shaida Mata Sunfita unguwa juyawa tayi DA niyyar komawa gida tunda basanan ta zo fitowa Najib nashirin shigowa Kadan ya Hana suyi Karo saurin matsawa tayi batare DA tamai Magana ba Alamun ya wuce shigowa yayi tare Da jingina jikin k'ofar ''Kallonshi tayi tace "Zan wuce "Kallonta Shima yayi Babu Wasa a fuskarshi. Kamar Dai tsohon Najib din dabaya dariya yace "Jeki zauna Magana nakeson muyi''sakamakon kwarjinin DA yayi. Mata yasata. Kasa. Musamai Samun guri tayi a one seater ta zauna Shima zaunawa yayi kusa DA kujerarta Saida yadauki kusan two minutes ba tare DA yayi Magana ba Najma haushi Duk ya cikata a zuciyarta tace jifa rainin hankali juyowa yayi tare DA kallonta yace .....✍🏿 *Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* *_Miss Hajo ce_*🤙🏿 [11/5, 5:13 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* *SAK'ON GAISUWA DA JINJINA GAREKU MASOYAN ASALI NAJMAT ABIY FANS INA JIN DAD'IN COMMENT,D'INKU DA SHARHI INA GODIYA DA ADDUO'INKU GARENI INAYINKU OVER Y'AN WAJENA*😎 ________________________________ *PAGE 43 & 44* ________________________________ I am sorry Akan maganar Dana fad'a Maki bansan mamanki ta rasu ba Kiyi Hak'uri kidinga Yi Mata addu'a Allah ya jikanta. Najmat Ranta a b'ace tace "wayace. Maka mamana ta rasu ne kai ka kasheta Ne,Ni mamana Bata Mutu ba Kuma insha Allahu saina ganta "ta ida fad'a tana fashewa Da Kuka. Tausayinta ne ya K'ara nunkuwa a cikin zuciyarshi Hakan yasashi cewa "To kiyi Hak'uri kibar Kukan nan indai kinason ganinta Zan kaiki wajenta "yafad'a Dan son kwantar Mata DA hankali. Lokaci guda ta d'ago idanunta DA sukayi ja tace "DA gaske zaka kaini wajenta"D'aga Mata kai yayi yace "Sure "Goge hawayenta tayi tace "To tayaya Zaka kaini wajenta Bayan Nima bansan inda take ba "Ga mamakinshi ya kalleta yace "Kinsan inda danginta suke'' girgizamai kai tayi tace "Babu Kowa Nawa Dana Sani DA Abiy kad'ai Na Tashi bansan Kowa Nawaba tundaga Kan dangin uwa Da uba Kuma nasha tambayar Abiy yasanar Dani Amma yak,'i fad'amun Hasalima ranshi baci yake Kuma yace Karna k'aramai maganar. Mamaki ne ya cika Najib Dan son Jin labarinta Dan ya lura Kamar akwai wani b'oyayyan al'amari cikin labarin yace "To ya fad'a Maki k'asarsu Da garinsu ma'ana inda aka haifeshi "Gyad'a mishi kai tayi tace "Eh Shi d'an Nigeria ne a Gombe state Amma Daga haka baik'ara Bani labarin komaiba Baifadamun garin Ko k'asar Da mamana take ba ". Nauyayyan ajiyar zuciya Najib ya sauke tukwana yace "To ya akayi yace mahaifiyarki ta rasu Kuma"Cikin shahshek'ar Kuka tace "Wallahi mamana Bata rasu ba Saboda bazan manta ba tun Ina yarinya Idan nayi mashi maganarta Saiyadinga lallashina yace zaikaini wajenta Harnafara wayau ganin Na takura mashi Da zancenta Wani time din yakan cemun kada Na k'aramai maganarta bazai had'ani DA itaba kozan Mutu Nasan lokacin DA yacewa su Abba ta rasu Amma wallahi Bata Mutu ba tafad'a tana rushewa DA Kuka. "Najib jikinshi ne Duk yayi sanyi Jin labarin ya lura DA Kamar akwai abunda Abiy Ke boyewa Wani tunani.yayi yace to Ko ba y'arshi bace wata zuciyar Kuma tace "Kamanninsu tafi karfin Wasa Tabbas mahaifinta ne Amma Kuma meyasa yake b'oye asalinshi. Jin kukan nata yayi yawa ya sashi Had'e Rai yace "Wallahi Idan bakiyi shiruba Zan fasa taimaka Maki ki had'u Da mahaifiyartaki''Lokaci guda ta had'iye kukan tare Da cewa "Dan Allah Kayi Hak'uri nayi shiru to".handkerchief ya mik',a Mata yace "goge hawayen "ba musu ta amsa Ta goge Tana shak'ar dad,'ad'an k'amshin dake jikin.handkerchiep d'in "Tashi yayi yace "Muje Na Rakaki''Murmushi tayi tace to tare DA Tashi suka jera suka Tafi. Daidai gate d'insu ya tsaya yace "zanwuce Bani Handkerchie d'ina "mak'e kafad'a tayi tare DA rugawa tayi bakin get d'insu ta juyo tana dariya tace "goodbye handkerchief Dai ya Zama Nawa "ta ida fad'a tana shigewa gida tana dariya. murmushi kawai yayi Yana jinjina k'uruciya irin ta Najmat Kamar ba itace ta gama Shan Kuka ba juyawa yayi Yana murmushi Shi kad'ai. Washegari wajen 6:Pm zaune suke a garden d'in d'in gidan su Amira ,"Najmat ce tace ''Yaya Bani labarin Nigeria"Yana Danna waya Batare Da ya d'agoba yace "Bazan bayarba baki tab'a zuwa bane"B'ata Rai tayi tace "Uhm Dan Allah Yaya Bani bantab'a zuwa ba Kuma Ina son zuwa"ban iya Bada labari ba yafad'a Yana Mai kallonta "Itama kallonshi tayi cikin shagwab'a tace "To fad'amun Sunan state d'in dake Nigeria da sunan garuruwan'' Tsayawa yayi kallon ta baitab'a ganin wacce shagwab'a keyiwa kyauba Kamar Najmat shagala yayi DA kallonta Yana K'ara ganin tsantsar Kamarta DA Ummanshi 'hure Mai Idon DA tayi ne ya fargar dashi fusgewa yayi ''yace kinfasa shopping d'in dakikace zakije. "Lah ,Na manta Duk kai katsaidani tafad'a tana Tashi tace Bari naje nashirya ka Rakani Bata jira amsarshiba ta fice tayi part d'insu cikin minti baifi Goma ba ta shirya ta fito cikin Arabian gown black tayi nadin labarawa tunda Ta tunkaro wajen Najib Ke kallonta bako kiftawa baitab'a ganin macen DA Duk shigar DA tayi kyau take Kamar Najmat ba yashagala sosai DA kallonta Saida yaga tazo gab dashi tukwana ya fusge Yana kallon Wani wuri Dan Kar yarinya ma ta rainashi. Shike driving tana front seat tana Mai dariya Wai shikenan Daga yanzu yazama driver d'inta Murtukewa yayi yace "Allah zakija Na koma''hade hannu biyu tayi tace "Sorry my friend bazan sake ba"Murmushi yayi yaci gaba DA tuk'i yace "Amirar fa "murmushin DA ya lotsar DA dimple d'inta tayi tace "Ai yanzu fushi take damu Wai kayi Mata k'wacen k'awa yanzu dakai nake Abota "Murmushi kawai yayi baice komai ba harsuka Isa. A Mota ya jirata Dan bayason fita " Saida tagama shopping d'inta Tazo wajen biyan kud'i ta d'aga Jakarta ta d'auko A T M d'inta tana mik'a musu Taji ance "Anbiya "Tambayarsu tayi waya biya Mata nuna Mata Wani matashin saurayi sukayi ''Kallonshi tayi cikin harshen Hindi tace ''Wayace ka biyamun Zan biya DA kaina"Murmushi yayi Mata yace "I am sorry""Tab'e baki tayi tare DA.maida a t m d'inta tace "Thnks "sannan ta nufi Hanyar fita Binta yayi Yana Mata magiya akan ta bashi number wayarta Amma ta hanashi Ba irin rokon DA Bai mataba Amma fir tace Bata DA waya ganin Zai janyo hankalin mutane wajensu yasata tsayawa tare DA bashi whorng number godiya yayi Mata Yana murnar Jin Dadi Dan ba k'aramun tafiya DA Imaninshi babe d'in tayi ba Najib dake Mota tunda yaga fitowarta yaga saurayin dake Binta a Baya Yana Mata magana Har zuwa lokacin data bashi number hakanan kawai yaji ranshi ya b',aci Dan ya tsani yaga namiji Nabin.mace tsaki yaja a ranshi yace "itama Ina ganinta Mai hankali harta tsaya Bawa Wani sakarai number" cigaba Da Danna wayarshi kawai yayi. Tunda tashigo taga ya sauya tayi Mai magana yace bakomai Har suka Isa gida baimata Magana ba Saida zata fita tace "Dan Allah me namaka "Murmushi ya k'irkiro yace bakomai kiyi Maza ki Shiga gida Kar Abiy yayi Maki fad'a '', murmushi kawai tayi tace "Goodnight"Have a nice dream yafad'a Shima Yana barin wajen. Shak,'uwace sosai ta k,'ara Shiga tsakanin Najib Da Najmat Wanda ba Wanda baisani ba cikin Gidan nan hatta Abiy Dan su d'aukarsu ma soyayya ce suke Amma su bangarensu kawai Abota ce suke yanzu yarage saura y'an satittika Najib ya gama Masters dinshi Wanda su Najmat Kuma Suna level 3 zasu Shiga 4. Da misalin karfe ,8pm Kwance take cinyar Ummy Najmat ce tace "Ummy Wai yaushe Zaku Nigeria "Shafa kanta ummy tayi tace "nan Da 1 months kinsan bikin Sarat Da khairat saura Shati shidda "Tashi Najmat tayi tana kallon ummy tace "Lah ummy Kuma Lokacin Muna hutu Wanda damun Koma zamu Shiga level 4"DA Fara arta ummy tace "Kai Masha Allah Kinga DA Abiy zaiyarda saimu tafi tare tunda Kinga DA Dustinki zamu tafi''Najmat Kamar zatayi Kuka tace "Ummy Dan Allah kiyimai Magana yabarni mutafi tare inason zuwa k'asar "Amirace ta fito daga kitchen tace ''Eh wallahi Dusti Ni Idan bazai barki Bama Nima Na fasa zuwan saimu zauna kawai "Ummy ce tace Ku kwantar DA hankalinku insha Allahu Zai yarda mutafi taren Amma Najmat kifara mashi maganar kiji Idan Zai Bari kafin muyi Mai maganar. Murmushi Najmat tayi tace to ummy yanzu ma zanje nafada Mai tafad'a tana Tashi "Dariya ummy tace kajimun sarkin zumud'i "Dariya Najmat tayi tace "Ai ummy kinsan komai DA zafi_zafi yafi "Amirace tace "Allah sa ya yarda Dai "ameeen Najmat tafada tana ficewa. Najmat ta Samu Abiy Har dakinshi Yana zaune Yana Aiki DA laptop Bayan tagaisheshi ya amsa cikin so da k'aunar Y'ar Tashi nan Najmat take fadamai tana son Binsu ummy Nigeria Idan zasu tafi. Ganin irin kallon Da Abiy Ke Mata yasata Shan jinin jikinta tace "Abiy Daman Saifa Idan ka yarda Idan baka yarda ba saina hak'ura"ta ida fad'a Kamar zatayi Kuka " Abiy dake Kan gado laptop Na hannunnshi sake duban Najmat yayi dake durkushe k'asar carpet din gadon yace "To ban yarda ba Babu inda Zaki Karki sake zomun Da maganar wannan kowace irin k'asa kikeson zuwa a fad'in duniyar nan kifad'amun zankaiki Koda kuwa kwana d'aya zakidingayi kina dawowa Amma Banda Nigeria Karki K'ara kawomun shirmen maganar nan hope kinfaminceni''Gyada Mai kai tayi kawai Dan Idan tace zatayi Magana zata iya Kuka ficewa tayi Daga d'akin Saida tafita ta fashe da Kuka tare DA rugawa bedroom d'inta ranar kwana tayi tana Kuka. Washegari Duk Wanda yaganta yasan Tasha Kuka tana Tashi Bayan tayi wanka tayi Sallah tan a break fast Aunty nafisa Na kallonta tace "Dear Naga idanunki sun kumbura Ko Kuka kikayi"girgiza kai tayi tace "a a kaina Ke ciwo"Subhanallahi Aunty nafisa tafad'a Sannan tace "Kinsha magani kuwa?, Gyad'a Mata kai tayi tace eh nasha "to Allah ya sawwake "Ameen Najmat tafada tana Gama breakfast Wanda lakutar abincin kawai take ta Tashi tace" aunty Bari naje gidansu Amira Gyad'a Mata kai kawai tayi tace "Adawo lafiya. A compound din gidansu Amira ta Tarar DA Najib Na Shanya Kaya "k'arasawa tayi wajenshi bailura Da itaba ta d',Aiko haki a hankali ta d'osanamai a Bayan wuya SA Yad'an firgita dariya tasanya tace "Namiji DA tsoro"Hararta yayi yace "Kinrainani Ko Najmat ,"Dariya tayi tace "a a a nidai banceba sannan tace wanki kake Kenan "Yana Shanya kayan yace "wallahi Ko Wai Saboda exercise "Gyad'a kai tayi tace ''Maimakon ka kirani na tayaka "tafad'a tana Amsar bucket d'in hannunnshi taci gaba DA Shanya kayan Suna Hira Abba ne ya hangosu yayi murmushi Yana Raya Wani Abu a ranshi. Saida ta gama shanyawa ya kalleta yace"Yadai Naga idanunki sunyi ja Kuka kikayi ne? kanta sadde tace " a a a "B'ata Rai yayi Yace "Zaki b'oyemun Wani Abu NE GA idonki nan ya kumbura Daga Gani Kuka kikasha ',fad'amun waya tab'aki Ko yayi Miki Wani abun'', Cikin murya Kamar zatayi Kuka tace "to ba Abiy bane ''saikuma tayi Shiru ta sadda kai ''d'ago Mata kanta yayi yace ''Abiy yayi me "Kuka ta fashe dashi tace "Shine yace Wai bazanbi su Ummy bikin DA zasu Nigeria ba Kuma inason inje"ta ida fad'a tana rushewa DA Kuka. Ganin irin Kukan DA take Har cikin ranshi yake jinshi baisan lokacin Daya janyota jikinshi ba tare Da Fara bubbuga bayanta cikin sigar lallashi yace "Calm down my friend kibar Kukannan haka yafad'a Yana K'ara daddaba bayanta Kamar yanda Ake lallashin jariri. NAJMAT shiru tayi Sai ajiyar zuciyar kawai Take saukewa ajere-ajere K'ara lafewa tayi jikinshi tanajin daddad'an k'amshin turarenshi Mai Wani sihirtaccen k'amshi lokaci guda Taji wata nutsuwa Na ratsata Najib Ko wata kasalace saukar mashi sunkai 5 minutes a haka batare DA Kowa ya sake cewa uffanba........✍🏿 *Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [11/7, 8:13 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{ *Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa* }_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* ___________________________________ *PAGE 45 & 46* ____________________________________ Gyaran muryar Da sukaji ya fargar dasu Najmat ce tafara zamewa cike DA Jin kunya sannan Shima ya zame Amira suka gani kansu itama tana d'an sadda kai alamun Kamar dariya take Harara Najib ya Galla Mata yace ''ubanme kike anan''d'an marairaicewa tayi tace ''Uhm Yaya Daman dusty nazo Nema"tsaki yaja tare DA Tashi yawuce. Saida Amira taga yayi Nisa tukwana tasa dariya tace "jibeshi Da Allah waini zaigwadawa borin kunya"Najmat ce ta Tashi tace"kede wallahi Kinshiga ukku DA gulma "Dariya Amira tayi tace "Kai dusty Amma fa kunfad'a DA yæwa"cikin Rashin fahimta Najmat tace "Kamarya"Amira Na dariya tazauna kusa DA ita tace "keda Yaya Najib mana"Lokaci guda Najmat ta Hade Rai tace "me kike nufi" Dan daidaita dariyarta Amira tayi tace''Soyayya kuke kidaina ma Wani b,'oye b'oye najima DA Gano Ku"Lokaci guda Najmat ta had',e Rai tace "dusty bansan iskanci tun ba yau ba nafada Maki kidainacewa Muna soyayya DA Yaya Najib Ni friendship ne kawai muke Amma ba soyayya ba meye wata soyayya shirme kawai tafad'a tana Jan tsuka"Danne dariyarta Amira tayi tare DA tab'e baki tace "Uhm in tayi tsami Maji sannan tace "Wai ya kukayi Da Abiy yabarki kuwa". Kamar zatayi kuka tace"Ya Hana"Subhanallahi Amira tafad'a tace "kai Amma banji Dadi ba sannan tace muje kifadawa ummy nasan k'ila Idan tayi Mai magana yabari . A palour suka Tarar DA Ummy tana Breakfast"gaisheta Najmat tayi Ta amsa Mata tare DA cewa "Ya y'an gidan naku''Lafiyansu qalau Najmat tafada tana Zama Kan sofa "madalla ummy yafad'a "Amirace tace ''ummy Wai Abiy yace bazatajeba "Ikon Allah ummy tace sannan tace "to shikenan tunda Bai bariba Najmat kiyi Hak'uri Ai akwai next time. Kuka Najmat Tasa tace "Ummy Dan Allah kiyimai Magana wallahi inason zuwa "Ajiyar zuciya ummy ta sauke tace "to zanjaraba Karki damu . Ya rage saura kwana biyu tafiyar su Ummy 9ja Wanda lokacin Najib yagama Masters dinshi Da Sati biyu Wanda tare zasu tafi Duk sunyi parking komai Najmat Duk tayi sanyi , zaune suke a palourn ummy "ummy ce tace "Dear Ko baki Da lafiya Naga Kinyi sanyi tun Jiya"Batare Da ta d'ago kantaba Saboda hawayen dake k'ok'arin zubomata tana kokari maidasu Amma ta kãsa"Ya Allah Najmat Kuka Ko ummy yafad'a tana Zama kusa DA ita tare DA tallabota . ,"kukan DA Najmat Ke rik'ewane ya zubo Mata lallashinta Ummy tafara tace "ya Isa haka meye damuwarki Najma kike.kuka ,"cikin shahshek'ar Kuka Najmat tace "Ummy shikenan tafiya zakuyi Ku barni nikadai ba dusty Dan Allah kiyiwa Abiy Magana nasan zaiji maganarki"Daddaba bayanta ummy tayi tace "toyi shiru Bari Na Samu Abba nafada Mai zaiyi Mai magana kinji "Gyad'a Mata kai Najmat tayi. Abba Na dawowa ummy ta fad'a Mai Najmat Nason zuwa Amma Abiy ya Hana ''cike DA b'acin Rai Abba Yace "dayake sayar Mai DA Y'ar za ayi Dan tace tanason zuwa zaihana Ai yayima Kara dakanshi yace atafi DA ita Dan Rashin yarda Ai Anriga anzama daya sannan yace zansameshi gobe Idan nadawo. Daga aiki. Har gida Abba ya samu Abiy yace "Haba Muhammad Yanzu Dan Najmat tace zatabi su Amira 9ja Zaka Hana saikace za'a sayar Maka DA y'a Koko Har yanzu Babu yarda tsakanin mu a Tunani Na Anriga anzama d'aya tunda Har mun Hada zuri'a a Tunani Na Ina DA Iko Akan ka DA y'ay'anka Amma tunda ka gwadamana iyakarmu bakomai. Abiy ne yace ''Abban Amira bahaka bane wallahi kana DA Ikon komai Akan Najmat Dan Allah Kayi Hak'uri Na yarda SU tafi d'in Allah kiyaye hanya ya kaisu lafiya ya maidosu lfy, " Abba ne yace "yawwa haka nake sonji tunda tana so taje Ko kaifa daganan sukayi musabaha. Kwance take ta d'ora kanta cinyar Aunty nafisa Abiy ya Shigo Sannu DA zuwa Aunty nafisa tayi Mai Sannn Najmat tace "Abiy sannu DA zuwa "kallonta yayi yace "Ke yanzu Najma Dan nace bazakije 9ja ba shine zakije ki had'ani dasu Abba Ai kin kyauta "NAJMAT Kamar zatayi Kuka tace ''dan Alla Abiy kayi Hak'uri aitunda kace bazanjeba Nama hak'ura Dan Allah Kar ranka ya b'aci Kar Kayi fushi dani "yaso yayi Mata fad'a Amma ya fasa Saboda yanda yasan Najmat Ke kiyaye b'acin ranshi DA Kuma yanda take Mai biyayya Hakan yasashi k'irkirar murmushi yace. "Taya za ayi. Abiy yayi fushi DA Najmat dinshi "Tashi Najmat tayi tare DA rungume Abiy tace "Thnks you uba Na gari"Shafa kanta yayi yace "Na Bari ki bisu Allah ya kiyaye hanya "Zaro idanu tayi tace "DA gaske Abiy ,"Gyad'a Mata kai yayi Yana. Murmushi K'ara Rungumeshi tayi tace "wow Abiy I am very joyful nagode my Abiy Allah ya barmun kai Allah Saka Maka DA alkhairi"Cike dajin dad'in addu'ar y'artashi yace "Ameeen daughtern Abiy Allah yayi Miki Albarka. Aunty nafisa Dai murmushi kawai tayi tace "To konima nabisu Abiy Najmat"Harararta yayi yace "ohhh wayau zakumun Kenan Duka Ku tafi Ku barni to ban yarda ba "Dariya Najmat tayi tace "Gaskiya aunty ban yarda ba a tafi abar Abiy Na Shi kad'ai a gida "Pillow Aunty nafisa ta tilla Mata tace "Ohhh Ke Zaki tafi Niko oho Ko?Dariya Najmat tayi tare dayiwa aunty nafisa Gwalo tace "Badai inda Zaki bimu Kina gida tafad'a tana rugawa dariya Abiy yayi yace "yawwa shikenan ma Najmat ta Hana Kinga ba inda Zaki "B'ata Rai Aunty nafisa tayi cikin shagwab'atace "To Ai satin bikin ka barni muje plx abban Faruq"murmushi kawai yayi yace "kema rigimarce irin ta Najmat Ko "uhm Dan Allah abu Najmat kasan baikamata ace Banje bikin ba Kuma kaga Nadad'e Banje gida ba " Abiy ne yace "zolayanki nake aidole kije yaza ayi Na hanaki zuwa Allah ya kaimu lokacin. Najmat DA gudu ta nufi gidansu amira DA zumud'inta Dan tayimata albishir "A bakin gate taci Karo DA Najib baya tayi Tana huci tace "Sorry ban Lura DA kai bane,"Yana kallonta yace ''gudun Me kike Kamar wata yarinya"tana huci tace ''Yaya Amira zanyiwa albishir Abiy ya yarda za a tafi Dani 9ja "inye kaji bak'auya zataje 9ja''ciikin shagwab'a tace ''Uhm nidai Allah ba bak'auya bace ,Kuma ma Ai India tafi 9ja komai"wara manyan idanunshi yayi yace "A Ina India tafi Nigeria k',asar da Duk inda kayi saikaci Karo Da gumaka"Dariya Najmat tayi tace "mu Ina ruwanmu Da shaggun gumakansu sannan tace ''Ina Zaka naganka DA key ". Unguwa zani Ko Zaki Rakani ?Gyad'a kai tayi tace "Eh; muje"tafad'a tana binshi parking space juyowa yayi ya kalletata yaga Daga ita Sai doguwar rigar bacci Harararta yayi yace ",wazakibi a haka"kallon jikinta tayi taga normal take cewa tayi ,"me Kuma nayi,''"A haka DA wannan tsinannun Kayan Zaki bini''kara duba kayan jikinta tayi cikin shagwab'a tace "to me kayan nau sukayi Kuma "Tsaki yaja yace "to bazakibini ba ''turo baki tayi tace ''aidaman Bani nace zanbikaba kai kace Na rakaka "Murtukewa yayi yace ''gidan ubanwa nace ki Rakani "K'ara turo Baki tayi tace "ba asaniba mutum Sai zagi Kamar babaguje(Bamaguje ne takeson tace Dan Taji Wani time din Idan Amira tayi zagi ummy saitacemata wannan zagin saikace maguzawa shine itama take so tace ) "Wara idanu yayi yace Dani kike "Tsaki taja tace "Ehd'in tafad'a tare Da murgud'a baki tabar wajen tayi cikin gidan. tsaye yayi a wajen tare DA Jan Tsaki yace "Mai Hali Baya fasa halinshi Yana.mamakin yanda kwata_kwata yarinyar Bata tsoronshi Ko kad'an Bata shakkar gayamai Magana sannan yakuma Jan tsakin haushin yanda suke shigar turawa Ko ajikinsu sun d'auki al'adar wasu sunmaidata tasu. NAJMAT tana Shiga tayiwa Amira DA Ummy albishir Abiy ya Barta zokuga murna wajen Amira Hada Rawa ummy Dai dariya kawai take musu. Yau ta kama tafiyarsu 9ja Wanda jirgin K'arfe Goma Na safe zasu Hau sungama parking d'insu Na komai Najib ma yagama parking dinshi haka su Najmat Abiy ya zuba Mata kud'i sosai a account d'inta Koda zata buƙata Haka sukayi bankwana dasu Abiy DA Aunty nafisa Ji take Kamar tabisu Najmat Sai murna take yau zataje k'asarta ta Haihuwa Najib ma daka Ganshi kasan Yana cikin farinciki dukda baka fiya ganin fara'arshi ba haka Amira DA rabonta DA ƙasar tun tana yarinya haka ummy ma Abba DA Abiy sukayi musu rakiya Har airport Najmat taso. Tambayar Abiy Koda d'aya Daga cikin danginshi yafad'a Mata ta had'u dasu Amma tana tsoron ɓacin ranshi Hakan yasa tayi Shiru DA bakinta tunda Dai tasamu ya Barta Zatajema alhmdllh . Saida su Abba DA Abiy sukaga tashin jirginsu tukwana suka Koma gida sabida Abba Sai ana Fara bikin Shima zaitafi cike DA kewar ƴarshi Abiy ya koma gida. Tafiyar 24hours takaisu Nigeria NAJMAT Suna sauka Bayan sunfito Daga jirgi Sanye suke cikin Wata mayyar pink din Abaya itada Amira sunyafa k',aramin belt din rigar kallo ɗaya Zaka musu kasan Suna cikin farinciki sunyi kyau dukda gajiyar dake tattare dasu kallon Wurin ta tsayayi tana murmushi Ta furta Alhamdulillahi wata nutsuwace ta saukar Mata lokaci gudaWani farinciki ya mamayeta Annashuwa kawai take tare godewa Allah Daya kawota ƙasar ta Haihuwa . Kai tsaye gidan Hajiya suka nufa Bayan driver yazo ya d'aukesu Najmat Dai tun a Mota suke ƙarewa garin kallo itada Amira Ummy Dai dariya tayi musu tace "Suna Mata k'auyanci ". D'aid'aya suka Fara Shiga Palourn Najib ne yafara Shiga hajiya cike DA farinciki ta taryashe tare DA rungumeshi Dan ba ƙaraamun kewanshi tayi ba nan ummy ma tashigo ita DA Amira hajiya Sai sannu DA zuwa takeyimusu itama Dai Daka ganta kasan tana cikin farinciki. ganin Mai shigowa ta k'arshece ta Sanya hajiya yin saranda kallonta ta tsayayi bako k'iftawa Itama Najmat Kallon ta ta tsayayi Najib. DA Ummy Zama sukayi DAn sunsan anrina "Cikin ƙarfin Hali hajiya.ta Matsa kusa da ita Wanda DA ƙyal take iya ɗaga ƙafafunta dafo ta tayi tare DA shafa fuskarta ta murza idonta taga Ko idonta ne Keyi Mata Gizo Dan Sak jidda take Gani gabanta lokaci Da take budurwa. Najmat Dai tsaye tayi Don tun shigowarta Ido hud'u DA tsohuwar datayi Taji Kamar ta had'u Da wani gudan jininta ƙara shafa fuskar Najmat hajiya tayi cike DA mamaki tace Jidda....✍🏿 *Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [11/9, 9:07 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{ *Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa* }_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *⚜️©J.A.W📚🖌️* ________________________________ *PAGE 47 & 48* ________________________________ "Jidda Kuma "Najmat ta fad'a a ranta Ummy ce tana Murmushi tace"Hajiya Jidda Kuma tayaya Jidda zata Koma haka "juyowa Hajiya tayi tace "ohhh Ashe fa Jidda nace Allah Mai iko naga kamarne tayi yawa ''itadai Najmat tsaye tayi tana tunanin wace Jidda ce Ake cewa suna kama . Ummy ce tace "kawai kamar halittar Allah ce sannan tace daughter ku k'araso kuzauna kunyi tsaitsaye sai sannan su Najmat suka Samu suka zauna cike da girmamawa Najmat da Amira suka gaishe da Hajiya ta amsa musu tare da cewa "ya gajiyar Hanya"Alhamdulillah suka fad'a a tare Hajiya dai har lokacin idonta nakan Najmat kallo Ummy tayi tace ''waiko hauwa'u ce ta girma Haka Ta Koma kamannin takwararta. "Dariya Ummy tayi tace "Hajiya Wannan ba Amira bace sunanta Najmat sannan ta Nuna Mata Amira dake gefen. Najmat tace ,"Kinga Amira nan''Ohh Allah Mai iko Dan Kar ace tafiya magana taja bakinta tayi shiru. Najib ne yace "My Amarya me kika tanadarwa me gidan ne "Murmushinsu na Manya Hajiya tayi tace "Ai komai ma na tanadarwa Mai gida guda ''d'an Murmushinshi na gefen Baki yayi tare da Shafa sajenji yace "Kice yau d'an gata nake sannan yace Wai Ina yaran Nan"Ai idan da abunda yafi d'an gata ma yau Kaine Mai gidan sannan ta tab'e Baki tace "Malalatan yarannan dai zakace suna ciki suna baccin Asarar da suka Saba tunda ka kawomun wannan shegiyar harirar Ta lalatamun sauran Khadijar da saratun Ba tsiyar da suke tsinanamun Saidai su ci suyi bacci Ai Saida ka tafi naga mugun amfanin ka nasan da kana Nan da Kai kad'ai zakayimun maganinsu. Hajiya Bata rufe Baki ba Khairat ta fito tana hammar yunwa "Nuna ma najib khairat Hajiya tayi tace "kagani dai da idonka ko?Sai sannan khairat ta lura da mutanen palourn fad'ad'a fara'arta tayi tare da cewa "Lah Yaya yaushe kukazo sannunku da zuwa tafad'a tana nufar wajen da Ummy ke zaune "Kallonta yayi ya tab'e Baki yace "Lafiya"Jan bakinta tayi shiru a zuciyarta tanaa mamaki Hali irin na yayannata sai bak'in Ran tsiya tafad'a a zuciyarta sannan ta gaishe da ummy "lafiya qalau Amarya ya muka sameku"Murmushi kawai tayi tace "Lafiya qalau ummy Ina su Amira., Amira gatanan "tafad'a tana Nuna Mata Amira datayi lik'is duk ta gaji "Murmushi Khairat tayi tace "Ah yau Muna da manyan Bak'i gidan Nan gaskiya Sannan tace Ummy k'anwar tamu tayi saurin girma fa ''D'agowa Amira tayi ta kalleta tare da Galla Mata Harara tace "Son girma yayi Miki yawa matar Nan nice yarinyar "Lallai Kam rashin kunyar da kikemun a waya ne zakimun a Fil....,muryartace ta sarke sakamakon ganin Mai tsananin kama da ummanta da tayi kamar antsaga Kara an karya kallonta ta tsayayi ta kalli Ummy tace. "Ummy bayan Amira kinsake Haihuwa Dama "Dariya Ummy tayi tace '"Eh Baki sani ba "B'ata Rai Khairat tayi tace "Kai Ummy Kuma shine Baki fad'amanaba Kinhaifo Mana Mai kama da Umma Sannan ta kalli Najmat tace "Sannu da zuwa sister "Murmushi Najmat tayi Mata tace ''yawwa"Yagida "Alhmdllh sister Mai kama da Umma "Murmushi Najmat tayi Mata Dan ba fahimtar zancensu take ba"najib Ne ya gallawa khairat Harara tare da cewa "yanzu Zaki fara zubar kamar aku mahaukaciya"Simsim taja gefe ta zauna Tana gunguni a zuciyarta tace "mutum sai masifar tsiya daga dawowarshi ko na marmarima Babu "Najmat ko tab'e Baki tayi a zuciyarta tace "Kenan shi jarabar tashi har y',an uwanshi Bai bari ba". Sarat da khady ne suka fito Wanda kansu d'aya a guje Sarat tayi gun Ummy tare da rungumeta tsam itama Ummy rungumeta tayi Dan ba k'aramun kewar y'ar tata tayiba Nan suka shiga gaisawa cike da kewar juna. Hajiya ce tace "gaisawar ta Isa haka kuu barsu su huta NAJMAT Daman haka takeso Dan ta gaji Abinciccika kala-kala.aka jejjera musu a dining bayan kowannensu yaje yayi wanka Amira da Najmat sun shirya cikin ankonsu kamar yanda suka Saba khady da Sarat so suke su tambayi Ummy wacece Najmat Dan Suma sunga Kamar ta b'aci Saida suka gama cin abinci tukwana Hajiya tasa su Khairat su Rakasu d'akinsu haka ko akayi Najmat da Amira Daman a mugun gajiye suke ba b'ata lokaci bacci yayi awon gaba dasu. "Palour yarage daga Ummy sai Hajiya sai su Khairat da Sarat da khady Sai najib dake Shirin tafiya gidansu Dan ya k'agara ya gansu ba k'aramun kewansu yayi ba. Hajiyace ta kalli Ummy tace "Habiba wannan yarinyar fa "Sauke ajiyar zuciya Ummy tayi Nan tabasu labarin had'uwarsu dasu har zuwa Auren Aunty Nafisa da babanta da Kuma shak'uwar su da Amira da tak'aitacce tarinsu kamar yanda ABIY yafad'a musu". Ba Hajiya ba hatta su Khairat yara Saida sukayi mamaki Babu dangantakar komai tsakaninsu Amma wannan tsananin kama haka aita b'aci "Hajiya ce tace "Allah Mai iko tunda nazo duniya bantab'a ganin tsananin.kama haka ba Kuma kuji ikon allah ba dangin iya bana baba"Murmushi Ummy tayi tace."wallahi ko Hajiya Ai danma bakiga uban nata ba Ai sak kamarshice Tayo Shima sak kamarshi d'aya da Jidda saidai.kice anfi ganin Kamannin nata Dan ita macece. Gaban Hajiya ne ya Bada Daram tace "Habiba kina nufin itama uban nata Kamarshi d'aya da Jidda"wallahi ko Hajiya Konima Saida kamar tabani tsoro najib yafad'a "Hajiya ce tace "Dan Allah ku nunamun hotonshi?Najib ne yace ''nidai bani da hotonshi Sannan Ummy ma tace Nima banida hotonshi". Tagumi Hajiya tayi kamar Mai tunanin wani Abu saikuma chan tace "Habiba kardai ace d'ana adamune baban yarinyar Nan Daman Nasha mafarkinshi Bai mutuba"Tab'e Baki najib yayi yace "Hajiya yanzu Zaki fara sambatun ko taya za ayi babanta yaxama Adamunki bayan shi sunanshima Muhammad Kuma ma Adamunki Daya jima da rasuwa zakice wai Adamunki har yanzu bazakibar Sambatu akanshib" Kuka Hajiya tafara Tace "Nidai kawai hakanan jikina yake bani adamu na na raye Allah ya isa tsakani na da Wanda sukayi sanadiyar rabuwata da d'ana wallahi inbanda zargi haramun da sainace da SA hannun Haule a sace adamu na wallahi harna koma.ga mahaliccina bazan tab'a yafe musu ba".duk cikin kuka take maganar Nan tana shaftar majina. Tashi najib yayi.don yasan Hajiya tafara zancen adamun Nan nata Sai Allah Ummy ce tayi ta lallsshin Hajiya harta samu tayi shiru. Najib yasamu tarba ta musamman daga family d'in nashi Babban farincikinshi Kuma yanda ya Samu Umma da Abba sunkoma rayuwarsu kamar da wannan abun yafi Mai dad'i Umma ta tarbi d'an nata sosai Tashiryamai kayan ciye ciye harsaida ya ture hirar uwa da d'a sukayi tayi har yamma yanason.lek'awa b'angaren Aunty Amarya Yana tsoron Umma sai da akayi Sallar magriba ne bayan ya dawo daga masallaci ya Samu yashiga b'angaren nata batare da ya bari kowa ya ganshiba. Zokuga farinciki wajen aunty Amarya dayake Daman tasan da zuwan nashi Nan tashiga jeramai Kayayyaki"Dariya najib yayi yace "Aunty duk Ina zankaisu"Murmushi kawai take Dan Baki yak'i rifuwa tace "Aiko saika cinye su tas"wara idanu yayi yace "duka"Ehmana ko sunyi kad'an a k'aro''Marairace fuska yayi kamar k'aramun yaro yace "Haba my big mom karkuma cikin ya fàshe"Dariya tayi tace "Sai a d'inke ai "Murmushi kawai yayi da fruit salad ya fara Nan har bayan isha'i Yana sashen aunty Amarya suna hirar yaushe Gamo. Cikin kwana biyu Najmat da Amira suka Saba da mutanen gidan sosai Najmat tashiga ran y'an gidan musamman Hajiya Dan jinta take har cikin ranta haka su Khairat dasu sarat. Najib tunda ya tafi baidawo gidan Hajiya ba Sai a kwana na ukku yazo shida ummanshi "Sosai Umma tayi Mamakin ganin Najmat Dan ita kanta kamannin sun Bata tsoro Itama Najmat b'angaren ta hakane sosai ta tsorata da ganin Kamannin su. Bayan Umma tazauna kallon ummy tayi ta kauda Kai batare da ta Mata magana ba abun ya daurewa kowa Kai yanda Umma da Ummy ke shiri insuka had'u kamar Sunfito ciki d'aya Hajiyace tace ''ke wai bakiga su Habiba bane"Turo Baki gaba tayi kamar wata yarinya batare da ta kalletaba tace "Sannu"Yawwa ya muka sameku"lafiya''umma ta Bata amsa a tak'aice"Madallah "Ummy tafad'a tare da tashi tabar ma palourn. NAJMAT ce tace "Ina yini"lafiya kalau y'an Mata"Sannan Amira ta gaisheta ta amsa tashi NAJMAT sukayi da Amira suka koma d'aki suna shiga Najmat ta kalli amira tace "Dusti wacece wannan bantab'a ganin Mai kama Dani hakaba ke ko Abiy bama kama kamar wannan matar''Iwallahi ko Dusti Nima bantab'a ganin Mai kama dake haka ba Sannan ta tab'a Baki tace "mamar wancen mutumin ne"Wani mutumin Cewar Najmat tana hayewa Gado"Yaya najib Mana "Tab'e Baki Najma tayi tace "unhum,Dan ta lura matar batada mutunci ganin yanda take amsawa Ummy magana a wulakance Amira kanta batajin dad'in hakan ba. sannan taja bargo tayi kwanciyarta baccin Rana itama Amira gado ta haye dansu Khairat suna makaranta saura su biyu ba jimawa bacci yayi awon gaba dasu. "Haba Jidda banji dad'in yanda kika gaishe da matar yayanki ba meye laifin Habiba a iya tunani na da ba haka kukeba Kuna mutunci sosai Amma ko bakisantaba yau kika ganta ai bakya Mata magana haka ba haba Jidda waike wani irin hali gareki ne kamar me aljannu tukunnama me habibar tayi Miki?. Umma ce tace "Haba hajiya me Kuma nayi Dan girman Allah"dak'uwa Hajiya tayi Mata tace ''ungo gidanku Dan iskanci ina.miki.magana kina me kikayi Nace Meya had'aku da Habiba ". "Hajiya ni ba abunda ya had'ani da ita kawai narabu da ita saboda munafuka ce !"Munafurcin me ta Miki?,Kamar zatayi kuka tace "haba hajiya wai bakya ganine y'ar uwartace fa Alhaji ya Aura Tunda nake da mijina baitab'amun kishiyaba shekara da shekaru sai akan Amina wadda taso ta rabani da mijina k'arfin addu'a ya maido da hankalin Alhaji kaina kinmanta y'ar uwar habibace da baban Amina da Maman Habiba uwarsu d'aya ubansu d'aya a fa gidan Hadiza babbar yayar su Habiba Alhaji yaganta ya aurota afa gidan akayi bikin Dan tsabar Munafurcin Dan haka yasa na rabu da ita saboda bazanyi tare da Y'ar uwar mak'iyata ba", Salati Hajiya tayi ta Salamce tace "Kai kedai anyi Malalaciya wallhi waida wananne kawai dalili to wai inama ruwan Habiba da Miki kishiya dakike magana ince dai ba Habiba ta had'asu ba yamasan y'ar uwar habibace ba Saida akayi auran bama kokuma Kinga Habiba ne wajen bikin yaushe rabon Habiba da k,'asar nan ma barekice ta Saka anyi Miki kishiya kede wallahi kinshiga ukku da wannan bak'in kishin da kika d'orawa ranki kin d'auki tsanar duniya kin d'orawa baiwar Allah wallahi Jidda Ina rabaki da halin Nan Kar hak'k'in baiwar Allah ya tambayeki ni Banga laifin yarinyar Nan Amina ba yarinyar ARZIK'I y'ar mutunci ba ayi Wata ba Nan tazo gaisheni dubu goma sukutum ta d'auka ta bani ke Dan bak'in Rai bakima raga Mata kodan saboda kyautatawar da takewa mahaifiyarki kodan ai ba Haule tayiwa ba bare kiji dad'i.ta Ida fad'a cikin masifa. Umma kamar tayi kuka haka takeji Dan ta tsani fad'an da Hajiya ke Mata Kuma batajin kunyar agaban y'ay'ana ta rufeni da fad'a Ga Kuma haushin ta na yanda Umma ke yabon Amina jitake kamar ta kurma ihu Dan takaici Amma tayi shiru harta gama fad'anta batace uffan ba. Dan son barin zancen ya Sanya Umma cewa "Hajiya wai yarinyar Nan Dana gani d'azu wacece" tare suke dasu Habiba yarinyar mijin nafisarta ne Amma Jidda bakiga yanda kuke kama ba kuwa"Aishiyasa na tambayeki Hajiya naga kamar tayi yawa to Kuma Baku da dangantaka dasu kuwa?"Wallahi ko Jidda kema Kya fad'a ba dangantaka kota kwabo Dan Habiba tacemun.mahaifinta d'an gombe ne haka mahaifiyarta tama rasu tonikuma na duba naga ko dange dange bamu dasu a garin gombe Ko almajirin gidana baitab'a xuwa gombe ba bareni harnasamu dangi a gombe"tab'e Baki Umma tayi tace "To Allah kyauta Hajiya zanwuce"to Allah kiyaye " najib ya maida ita gida Shima kanshi Yana mamakin zafin kishi irin na.ummannashi Dan baiji dad'i abunda tayiwa Ummy ba. Bayan tafiyar Umma Hajiya takira Ummy tabata hak'uri akan bataji dad'in abunda Jidda tamata ba Nan Hajiya tace "waifa akan Amina ne tamiki wannan abun Dan kina y'ar uwarta oh ni Saratu bantab'a ganin Mai zafin kishin Jidda ba addu'a dai nake Allah yaye Mata. ,''bakomai Hajiya "Cewar Ummy ita kanta mamakin kishin Umma take wai akan Amina zata daina Mata magana aminar da bama wani zumunci suke a da ita ba sosai inbanda dawowarta gidan Aunty Hadiza karatu bama tasan da auran ba sai bayan Nan Ake fad'amata a zuciyarta tace "kenan shiyasa Kona kirata Bata d'agawa tsaki taja a ranta tace ikon Allah iska Yana wahalar damai kayan Kara Niko tunda kika gwadamun haka to yanzu natashi zumuncin da Amina muga ta tsiya. Washegari su Khairat da Sarat sai khady sungama shirinsu na tafiya makaranta Wanda yanzu khairat na level 4 Sarat da khady na level two bayan tafiyar Najib khairat da Sarat suka Samu mazaje Wanda aka had'e bikin tare zasu cigaba da karatunsu bayan auran. Najmat ce tace Gaskiya nagaji da zaman Nan wallahi mutafi tare itama Amira tace eh wallahi Dusti mubisu mu maza mushirya "Yawwa sisters Daman friends d'ina nasan ganinku yanda nake Basu labarinku Cewar khairat. Cikin k'alilan mintina Suka gama shirinsu cikin k'ana Nan kaya rigar iyakar gwuiwa green sai wandonta red sai hed d'in kayan red simple make up sukayi zokuga yanda sukayi wani masifar kyau musamman Najmat Dan sak Takoma kamar baturiya bayan sun fesa turarruka masu mugun k'amshi. a Palour suka tarar dasu suna jiransu kowannensu masha Allah sukecewa Dan sunyi musu mugun Kyau. Hajiyace tace ''ku yanzu a haka zaku fita kamar d'iyar arna "Dariya sukayi Najmat tace ,"Hajiya me.kayan sukayi munfa yafa gyale"khairat ce tace "da Allah ku k'yaleta wannan tsohuwar meta sani tafad'a tana jansu a ,Sukayi waje. Mota suka shiga driver ya jasu tun shigowarsu makarantar kallo ya Koma wajensu Musamman Najma kowa da abunda yake cewa Dan ba k'aramun burgesu tayi ba ganin Hakan yasanya khairat Janta Tayi class d'insu da ita Dan khairat akwai son y'an gayu shysa tunda Najmat tazo jininsu yayi wani mugun had'uwa Dan taga yarinyar classic Ajebo ce ga maganartama ta Isa ta rikitaka uwa uba tafiyarta yanda take taku kamar wata jinin sarauta uwa uba kyau komai ta had'a. Suna shiga department d'in duk kallo yakoma wajen Najmat Nan khairat tadinga fad'awa k'awayenta ai cousin sister d'intace dake India sukazo biki Nan k'awayenta suka dinga cewa tafisu kyau dayake Najmat tana da warka ba laifi Nan sukahau fira da friends d'in Khairat Suko hada amsar number ta Dan sosai mutane keson suyi friendship da ita. Basu jimaba lecturer ta shigo domin Fara musu lectures sadda Kai NAJMAT tayi tana danne _dannen wayarta yayinda duka class d'in suka Bata attention d'insu ga abunda Ake koya musu Dan sosai sukejin dad'in lectures d'in m. Amina ga Bata da tsanani. Cikin lesson d'ine m. Amina tayi Wata tsatsaurar tambaya kowa class d'in baisaniba Kowa yayi shiru ya kasa Bada amsa Najmat datana danna waya Amma Hankalinta nakan abunda Ake koya musu dukda har lokacin kanta na sadde Jin k'ara maimaita Tambayar yasanyata tunowa ai tun a s s two ankoya musu haka yasata tashi tare da d'aga hannu idontane ya sauka ga kyakyawar Matashiyar matar da bazata wuce shekaru 35 ba sanye take cikin wani had'ad'ad'an lace ubansu anyi Mata Doguwar riga d'inkin ya zauna das a jikinta Tayafa gyale matching color Sannan k'aramin medical glass d'inta dayayi Mata mugun Kyau Tasha d'aurin zarah buhari Bazaka tab'a cewa takai shekarun ba duba da yanda gayu ya zauna Mata uwa uba kyau ga dimple d'inta side biyu Daya lotsa Lokaci guda kawai Najmat taji gabanta yabada Daram. Hakan takansance wajen Aunty Amina itama Lokacin da idonta ya sauka ga kyakyawar budurwar data mik'e ta d'aga hannu Babu dalili kawai taji gabanta ya fad'i a sanyaye Tabata umarni data fito ta rubuta Mata Amsar Dan calculation ne Mai mugun zafi. Cikin takunta na k'asaita da aji ta fito kowa hankalinsu nakanta wasu na gulma da tab'e Baki suna cewa daga zuwanta bakuwa harzara tinkari wannan caculation d'in da ko me masters albarka . Tana Isa gaban hall d',in Murmushin Daya fito Mata da wushiryarta da Kuma hak'orin makkarta Daya k'ara Mata kyau aunty Amina tayi Mata tare da mik'a mata maker d'in itama Najmat Murmushin Daya lotsar da dimples d'inta tasaki idonta nakan matar a sanyaye kamar wacce aka zarewa lakka ta Amshi maker d'in tare da zuwa gaban white board d'in tafara calculation d'in. Cikin minti biyu tagama Tare da mik'a.mata maker har lokacin Amina batabar kallontaba Gabanta na tsananta fad'uwa Tana juyawa ta karanta Abunda ta rubuta taga correctly bako kuskure d'aya Wow tafad'a tana kallon NAJMAT ba k'aramun burgeta Tayiba sabida a rayuwarta tana son Taga intelligent Dan tasan ba k'aramun Mai ilimi bane zai iya ansa tambayarnanba. Murmushi tayi tare da juyawa ta kalli d'aliban tace "Clamp for her"Duka Hall d'in ya hau tab'i su kansu sunyi mamakin k'ok'arin yarinyar ba k'aramun burgesu tayi ba. Aunty Amina batasan lokacin data rungume NAJMAT ba itama Najmat rungumeta tayi A tare sukaji Wata nutsuwa ta sauko musu Najma ji tayi tunda take Bata tab'a Jin Dad'in runguma ba irin yanda matar Nan ta rungume ta itama Hakan takansance wajen Aunty Amarya ga wata nustuwa data saukar Mata ga kuma gabanta da ya tsananta fad'uwa NAJMAT ji tayi Kamar su dawwama a haka rungume da juna Jin d'umin da Bata tab'ajin irinshi a rayuwarta ba Sunyi minti biyu a haka Kwata kwata Aunty Amarya Tama mance da Cikin Class suke Jin hayaniya ya sanyata rage rungumar datayiwa Najmat Tare da kallonta itama Najmat d'agowa tayi ta kalleta kafe juna sukayi da Idanu bako k'iftawa Aunty Amarya ce tayi Murmushi tare da Shafa fuskarta tace..✍🏿 *Tofa waiya abun yake ne niduk sun gama rikitani fa*😢 *Idan banji ruwan comment ba Yasin zakujini shiru atoh idan Kuma naji ruwan sharhi tohm zakujini ga long page nan na kwana biyu ne wollah*😉 *Kardai agaji da sharing fisabilillah Masoyan asali bani da grps ne* _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [11/13, 8:44 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴 🪴 🪴 *NAJMAT ABIY* 🪴 🪴 🪴 *Story and writing* *By* *Hajara L Sadeq* ( *Mhiss Hajo*🖤) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{ *Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa* }_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *⚜️©J.A.W📚🖌️* *Ina Mai Baku hak'urin Jina shiru dakukeyi kucigaba da hak'uri ba kullun zansamu Daman muku typing ba idan nasamu Dama zakujini kullum idan Kuma Hakan baisamu ba to duk bayan kwana d'aya zaku dinga jina ma'ana yau idan nayi gobe bazanyiba*😢 _______________________________ *PAGE 49 & 50* ________________________________ What is your name pretty? Cikin sweet voice d'inta tace " *NAJMAT* Wow is so sweet name Murmushi Najmat tayi cikin sanyi tace "Thanks " "Nan department d'in kike Daman" Girgiza Mata Kai NAJMAT tayi tace"no " Tunawa da cikin class suke yasanya aunty Amarya musu bankwana Daman tagama musu lectures d'in kama hannun Najmat tayi sukayi waje Dan sosai takeson yin magana da yarinyar . b'angaren Najmat ma haka ta kasance batare da tunanin komai ba tabita a wani bench dake gaban department d'insu khairat suka zauna Aunty Amarya ce tace "Amma ba school d'in Nan kike ba,",. Murmushi Najmat tayi tace ,,"Eh rakiya nayi"Dafa ta aunty Amarya tayi tace ,"Nayi mamakin yanda kika ansa question d'innan kinburgeni sosai y'ata Ina son naga yaro da k'ok'ari but wace school kike?,. Murmushi tayi Mata tace "Thanks you aunty Ina karatu ne GOLGOTIAS UNIVERSITY GREATER NOIDA" Wara idanu tayi cike da mamaki tace "wow India ko? Murmushi Najma tayi tace "Eh"Masha Allah Allah Miki albarka ya taimaka ya sanyawa karatunki albarka "Wani sanyi Najmat taji har cikin zuciyarta cike da farinciki tace "Ameeen nagode"Murmushi Aunty Amarya tayi Mata Itama a zuciyarta tana ganin tsantsar kamar Yarinyar da kishiyarta. Dubu biyar da zaro a jakarta ta mik'awa Najmat "k'in amsa tayi tace "a a Aunty nagode"b'ata Rai aunty Amarya tayi tace "Ki amsa bakyau maida hannun kyauta baya idan Baki amsa ba bazanji dad'i ba ko ". Girgiza kai Najmat tayi tace "Allah aunty ba haka bane idan na amsa banmasan ya zanyi dasu ba ban iya kashe Kud',in 9ja ba Kuma tun Ina yarinya Abiy ya hana ni Amsar kud'in mutane shiyasa bana ansa" Cike da mamaki Aunty Amarya tace "Daman ba Nan k'asar kike ba ?gyad'a Mata kai tayi tace "Eh India nake wannan ne ma first zuwa na 9ja bantab'a zuwa ba"ga mamakin Aunty Amarya tace "ikon Allah nad'auka karatu ne yakaiki india ya Kuma naji hausa rad'am a bakinki" . Dariya Najmat tayi sosai ganin yanda ta rik'e Baki ,"b'ata Rai Aunty Amarya tayi tace "Dariya ma kikemun ko"Kama hannunta Najmat tayi tace "Sorry Aunty yanda kikayi.maganan ne yabani dariya''to naji fad'amun ya akayi kika.iya hausa haka". "Abiy na bayamun ko wani yare idan ba hausa ba shiyasa natashi da yaren "gaban. Aunty Amarya ne yafadi Dan son gaskata abunda zuciyarta ta Innata Mata tun farkon ganin yarinyar tace "Shi mahaifin.naki d'an Ina ne Ma'ana wani gari yake ko wace k'asa yake". Hartazo zatace Gombe "saita tuna kashedin da Abiy yayi Mata ana gobe zasu tafi na cewa kada ta sake ta fad'awa kowa garin da yake ko ta nunawa wani hotonshi Hakan ya sata saurin cewa "Shima d'an India ne tafad'a tana Dan rawar Baki. India ? Aunty Amarya ta maimata cikin ranta sannan tace "Kuma kince shiya koya Miki hausa ,"rashin sabo da k'arya ya Sanya Najmat d'an rud'ewa zatayi magana Wanda Batasanma me zatace ba wayar aunty Amarya tayi ringing d'aga Mata hannu tayi tace "Ina zuwa pretty bari na amsa waya nadawo ajiyar zuciya Najmat ta sauke tare da mata Murmushi Jin Dad'in sunan data kirata sosai sunan yayi Mata dad'i tana Murmushi tace to saikin dawo" a zuciyarta ta maimaita pretty Murmushi tayi sosai auntyn ta iya fad'an pretty. Aunty Amarya na barin wajen Dan amsa waya Najmat ta tashi ta Koma class d'in su khairat Dan tsoron Kar idan tadawo tacigaba da Mata tambaya ta k'ureta Amma badan tagaji da hira da ita ba sosai matar ta kwanta Mata arai. Aunty Amarya Koda ta dawo Bata iske Najmat ba bataji dad'i ba office d'inta ta Koma tunane tunane tayi tayi ganin kanta ya fara ciwo ya sanyata komawa gida cike da tunanin pretty kamar yanda tasa Mata suna Bata tab'a ganin yarinyar da ta kwanta Mata a Rai lokaci guda ta shiga ranta sama da yarinyar Nan. Sai bayan azahar su Najmat suka koma gida kafinsu Tafi ba irin Neman da batayiwa Aunty ba kamar yanda itama tasa Mata suna Amma Bata ganta ba sai hak'ura tayi cike da Jin haushin kanta na tahowa d',azu da tayi cike da tunanin matar da batasan sunan tabama suka koma gida. Sa'adatu tunda ta Samu labarin NAJIB yadawo ji tayi Kamar ta zubda ruwa a k'asa ta Sha Dan dad'i Tattara kayanta tayi ta Koma gidansu najib Ko zata samu ta shawo kanshi ta haka Amma me ko kallonta bayayi ko tamai magana baya amsa gaisuwarta ba k'aramun haushinta najib yake ba. Rayuwar Najmat gidan Hajiya sosai tamata dad'i Kullum suna waya da Abiy da Aunty Nafisa ana saura kwana ukku a fara biki aunty Nafisa da Abba suka iso 9ja.sosai Najmat taji dad'in zuwan su musamman auntyn tata da Kuma lil bro d'in nata da take matuk'ar ji dashi. Tunda sukazo 9ja magana Bata sake had'a najib da Najmat ba ko sun had'u zata shareshi Shima haka yake shareta Amma a zuciyarshi bayajin dad'in hakan Saidai Kar yarinya ta rainashi ya Sanya yake shareta Shima. Da misalin k'arfe Shida na yamma Gajiya da zaman cikin gidan Najmat tayi Hakan ya sanyata fitowa compound d'in Kasancewar Yana da fad'in gaske Daidai k'asar bishiyar mangoro tazauna sosai iskan yayi Mata dad'i sanye take cikin Doguwar riga gown Black ta d'aura belt d'in rigar kanta sosai rigar tayi Mata kyau chatting take da wayarta tana Murmushi ita kad'ai sosai chat d'in ke Mata dad'i itada friends d'inta na school. Najib ne yashigo da motarshi bayan yayi parking hangota yayi waya na hannunta sai Murmushi take ita kad'ai harzaiwuce saikuma yayi wajenta tare da zama gefenta hakanan ya sauke girman kanshi yace "y'an Matan Abiy iska akesha''juyowa tayi ta kalleshi Saitaga ya K'ara haske da kyau kwana biyun da Bata ganshi ba . 'turo Baki tayi ta juya taci gaba da chat d'inta "maimakon yaji haushi sai Murmushi yayi Dan yanzu komai zatayi saiyaji bayajin haushinta saima dariya da take bashi kokuma Yaga abun ya Mata kyau musamman yanda take shagwab'a. "Wai me nayiwa y'an Matan Abiy ne take fushi Dani haka har take share best friend d'in nata"k'ara turo Baki tayi cikin shagwab'a tace "Kamanta mun b'ata dakai fushi nake dakai kaida kayimun tsawa Kuma kacemun ubanwa yace na rakaka". Dariya yayi danshi Harya manta ma "Ohhh wai wannan abun ne yasa kike fushi dani.kenan har bakya mun magana?gyad'a Kai tayi tace "eh Mana aimun b,'ata had'e hannayenshi yayi waje guda Yace ''to kiyi hak'uri bazan sake ba "turo Baki gaba tayi tace "Ni ba ruwana dakai ka fiya fad'a'". wara idanu yayi yace "Nid'in "gyad'a Mai Kai tayi tace eh Mana "Murmushi yayi yace "to na Baki hak'uri fa ai kin hak'ura ko *NAJMAT ABIY* d'inta Dan yasan sunan dazai kirata kenan Tahak'ura. Lokaci guda tayi Murmushi tace "Nahak'ura ,''tare da mik'a mai k'aramar yatsanta alamun su shirya "Badan ya so ba ya mik'a mata hannu Dan bayason jikinsu na had'uwa. Idonta ne ya Kai ga zoben hannunshi da harta manta Murmushin mugunta tayi Dan tayi Alk'awarin kota halin k'ak'a sai zoben Nan yazama nata suka shirya ta sakar Mai fuska sukayi ta hira Tana bashi labarin Wuraren data je a kaduna Yana Murmushi. Khairat ce da Amira da khady sundawo daga anso anko Dan Najmat tace bazatajeba kewarsuce ma tasata fitowa Ga mamaki khady da ita ta fara hangosu ta tsaya tana kallon NAJMAT da Najib kama hannun Khairat tayi tace "Yaya khairat kalli Yaya najib da Najmat "wara idanu Khairat tayi Dan iya rayuwar tata zatace Bata tab'a ganin fara'ar Yayan nata ba sai yau cike da mamaki suka tsaya kallon ikon Allah Amira ce tayi dariya tace "wai mamakin me kuke"badole muyi mamakiba Amira jibi Yaya yanda yake Murmushi hada rank'wafawa Bantab'a ganin Murmushinshi haka ba "Cewar khairat Murmushi Amira tayi tace "Ai Baku ga komai ba indai Najmat da najib ne wai Kuma saisu rainawa mutane wayau suce ba soyayya suke ba bayan na riga da ganosu. Wara idanu Khairat da Khady sukayi tare sukace "Soyayya"dariya Amira tayi tace "kuna mamaki ne"Ba dole muyi mamaki ba Amira Yayan da ko kallo mace Bata isheshiba hasalima haushinsu yakeji bantab'ajin Yaya yayi budurwa ba masu soyayya ma shi haushinsu yakeji zakiji Yana cewa basuda aikinyi kwata_kwata fa ya tsani y'an Mata ko kallo basu isheshi ba bare ya tsaya suna magana karkiga yanda yake takura Mana ko hak'oranshi bama Gani Amma jibi yanda yake Mata Murmushi Kinga Aiko dole muyi mamaki"Cewar Khairat. Dariya Amira tayi tace "Chab ku yake rainama wayau "Aiko dagayau yadaina cika Mana Baki cewar Khairat tana dariya "Kumafa kinsan me sisters Cewar khady saikin fad'a suka fad'a a tare. Hhh dariya tayi tace "kinmanta lokacin da yake cewa Hajiya shi ko aure zaiyi bazai Auri yarinya ba wacce a Haihuwa ya haifeta ta rainamai wayau Sai babba waddaa. Ta mallaki hankalinta Koma zaiyi Auren. "Dariya Sosai khairat da Amira suka shigayi khairat tace "Aiko alhmdllh Allah na gode Maka gashinan y'ar jaririya tayi wuufff dashi Amma fa ba k'aramun matching sukayi ba "sosai suka shiga Mai tsiya tare da lab'ewa suna Kallonsu wai suga k'arshen love. Najib da Najmat da basusan da wanzuwarsuba hirarsu kawai suke Inda Najmat ke cewa "Ita tagaji tundazu suka tafi suka barta najib ne yace to ko yawo kikeso gyadamai Kai tayi tace "eh wallahi"Murmushi yayi yace "to ko Zaki rakani gida anjima saina maidoki "Murmushi tayi tace "eh muje "Tashi yayi itama ta mike "harararta yayi yace ''to yafa gyalan ''warwareshi tayi ta yafa sannan ta bishi suka tafi parking space ya zagaya ya shiga driver seat. itama tashiga front seat horn yayi get man yafito ya Bud'e musu suka tafi. Ihu su Khairat sukasa ganin fitarsu khady tace ''shegiya love Baki da wasa kin damk'i Yaya najib da yawa wallahi ba k'aramun dacewa sukayi ba Yaya yayi Babban kamu wallahi"Dariya Khairat tayi tare da wak'ar "soyayya ruwan Zuma "haka sukayi da Mai shak'iyanci. Kai tsaye gidansu najib suka nufa Horn yayi get man yafito ya Bud'e suka shiga bayan Sunfito sai hira suke suna Murmushi a lokacin har amfara kiraye kirayen magriba. Hakan yayi daidai da fitowar sa'adatu zata fita Yawon banxanta data Saba tayi wannan mugun ganin Yaya najib da wata.ta fad'a a Fili cike da mamaki Harsuka kusa zuwa inda take tana Kallonsu zuciyarta na matuk'ar tafasa ganin kyakyawar budurwar dasuka fito tare tasan bama zata iya had'a kanta da yarinyar ba tafita komai batasan lokacin da wasu zafaffun hawaye suka zubo mata ba a guje ta Koma part d'in Umma ta rufe bakin ta da hannunta Dan rik'e kukan Daya taho Mata Amma ya gagara sosai ta fàshe da kuka kamar wacce akace uwarta da ubanta sunmutu lokaci Daya . Tab'e Baki najib yayi a zuciyarshi yace "'sakarai y'ar wahala "Tambayar shi Najmat tayi tace "wacece ko kanwarkace ? girgixa Mata Kai yayi yace "y'ar aiki ce'' Dan sosai yakejin haushin a Kira banzar yarinyar chan da k'anwarshi shikadai yasan bakin cikin dayakeji Dan sosai ya tsani Sa'adatu bakomai yasanya hakanba sai lalacewarta a rayuwarshi ya tsani Yaga y'ar iska ko d'an iska sosai yake k,'yamatarsu Babban abunda ya K'ara sawa ya tsaneta labarin daya samu cewa Sa'adatu y'ar mad'igoce Babu abunda ya tsana a rayuwarshi sama da wannan abun Hakan yakara ninka tsanar ta a cikin zuciyarshi ga kuma k'yamatarta da yake Dan zai iya rantsewa Koda Kud'i bazai îya cin abun hannunta ba Kuma bawai Bata da tsafta bane kawai shi haka yake da kyamatar Dan Iska . Hakan ya sashi cewa Najmat"y'ar Aikinsu ce"Gyad'a Kai NAJMAT kawai tayi part aunty Amarya suka nufa yace Mata "Bari na kaiki b'angaren auntyna kugaisa sainaje nayi sallah kema kiyi . to tace sannan suka nufi part d,'in door belt ya danna aunty Amarya tafito ta Bud'e musu turus tayi ganin Najmat gabanta cike da mamaki tace "pretty"Itama Najmat cike da mamakin ganin matar data jima tana burin sake ganinta tace "Aunty tare da nufarta cike da farincikin sake ganinta tayi hugging d'inta itama hugging d'inta Aunty Amarya tayi cike da mamaki najib ya tsaya Yana Kallonsu a zuciyarshi yace "Sun San juna daman''. Sunjuma rungume da juna sannan suka shiga Kowannensu fuskarshi d'auke da tambayoyi najib ne ya kasa daurewa bayan sun zauna yace "Aunty Daman kin Santa ne daman........✍🏿 *Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah* _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels