Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels FATAUCIN BAYI MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071 Haƙƙin mallaka Mansur Usman Sufi Shekarar bugu 2023 GARGAƊI Ban yarda wani ya sarrafa min littafi ba ta hanyar yaɗa shi a soshiyal midiya, karantawa a rediyo ko manhajar YouTube, website da sauran su ba tare da izina na ba, yin hakan zai kai mu zuwa ga hukuma a kiyaye. Ko kuwa zuwa babban mai sakamako Allah (SWT). Sako daga Sarkin Marubutan Yaƙi GODIYA Ta tabbata ga Allah SWT bisa iko da ya ba ni na rubuta wannan littafi mai taken FATAUCIN BAYI. Tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama da iyalanshi tsarkaka. SADAUKARWA Na sadaukar da wannan littafi ga dukkanin masoyan Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama a ko ina suke a faɗin duniya. Bugawa da yaɗawa SUFI PUBLISHING COMPANY R/lemo Kano state Nigeria 08137237071 BABI NA ƊAYA Ƙasaitaccen jirgin ruwa ne da aka cika shi maƙil da fursunoni maza da mata, manya da yara, gaba ɗaya an ɗaure hannayen da waɗansu irin murtuka-murtukan sarƙoƙi kuma an haɗa da katakon jirgin an ɗaure tamau, ta yadda babu mai iya tserewa daga cikin su. Duba ɗaya za ka yiwa fursunonin ka fahimci cewa sun kasance jama'ar ƙabila ɗaya, abin da zai tabbatar maka da hakan shi ne yanayin ƙirar jikkunansu da kamanni gami da tufafin su iri ɗaya ne sak! A wannan lokaci jirgin ruwan na tafiya ne a saman wani makeken teku, a kowace kusurwa a jirgin an zuba dakaru masu tarin yawa, suna shirye suke cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu ɗauke da miyagun makamai, suna ta kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro. Sai da jirgin ya shafe tsawon sa'a biyu da daƙiƙa ɗari biyu yana tafiya a saman tekun ba tare da watsala ba, shi dai tekun ana yi mashi laƙabi da Baharul-sawara. Ana cikin wannan tafiya ne wani garjejen ƙato daga cikin dakarun ya dubi wani badakare wanda da alama shine shugaban su ya risina a gare shi sannan ya buɗi baki ya ce "ya shugaba na ina ganin ya kamata a kwance waɗannan fursunonin a basu abinci domin sun galabaitu ainun, haƙiƙa a koda yaushe za su iya rasa rayuwar su, kuma sanin kan ka ne cewa mutuwar ɗaya daga cikin fursunonin tamkar rasa rayukanmu ne baki ɗaya''. koda jin wannan batu daga bakin badakare Sharkar sai shugaba Yasiran ya dube shi cikin alamun matuƙar damuwa cikin wata irin kakkausar murya mai tattare da jarumtaka ya ce "ya kai Sharkar tabbas ka zo da shawara mai kyau, amma fa wani hanzari ba gudu ba, shin ba ka tsoron kwance fursunonin zai bada matsala a tare damu? Koda jin wannan tambaya sai Sharkar ya bushe da dariya ya ce ''haba ya shugabana ka duba fa ka ga irin tsananin yawan mu, ta ya ya kake tsammanin cewa akwai wanda ya isa ya tsere mana. Yanzu mafita ɗaya ce ta rage mana, ko dai mu bawa waɗannan fursunonin abinci domin su rayu, ko kuma mu ƙyale su yunwa da ƙishirwa su zamo ajalin su". Sa'adda shugaba Yasiran ya ji wannan batu daga bakin Sharkar sai ya ce "tabbas zancen ka dutse ya kai Sharkar ya zama wajibi mu yi amfani da wannan shawara da ka kawo". Yana gama faɗin hakan ya umarci waɗansu dakaru mutum arba'in suka kwance fursunonin mutum ɗari biyu, sannan suka rarraba masu wata bushasshiyar gurasa gami da wani ruwa mai yauƙi a matsayin abin kalacin su. Dakarun na cikin aiwatar da hakanne wani badakare ya miƙawa wata yarinya gurasar. Kafin hannunshi ya kai inda take, sai kawai ta shammace shi ta ciri wata siriyar wuƙa a damtsen shi ta soka mashi a marainanshi, sannan ta sanya ƙafafuwanta biyu ta daki a ƙirji, take ya hantsila izuwa cikin tekun yana mai tsandara ihu Al'amarin da ya janyo hankulan sauran dakarun kenan, suka zubar da abincin suka zare makamansu suka ruga izuwa inda yarinyar take. koda ganin hakan sai yarinyar ta ɗauko wata doguwar igiya cikin wani irin zafin nama ta yiwa igiyar wasu ƙulluna barkatai ta jefawa dakarun, sannan ta daka wawan tsalle ta faɗa izuwa cikin tekun tana riƙe da sauran igiyar a hannun ta, take igiyar ta zarge kafafuwan dakarun ta ja su izuwa cikin tekun. Koda ganin hakan sai Sharkar ya dakawa sauran dakarun tsawa da su sake ɗaure fursunonin, kuma aka umarci masu tuƙin jirgin su tsayar da tafiya, sannan ya yiwa dakaru hamsin inkiya da hannu da su biyo bayan shi suka ruga izuwa bakin jirgin. Ai kuwa koda tsayuwar su sai suka yi arba da gawarwakin 'yan uwansu dakarun da suka faɗa sun taso izuwa saman ruwa, gaba ɗayan su an yi masu yankan rago, Al'amarin da ya yi matuƙar ba su mamaki kenan kuma ya harzuƙa su. Abin da ya ba su mamaki shine ya za ayi a ce yarinya ƙarama ta samu ƙarfin damtsen da za ta yiwa zaratan dakaru sha biyar yankan rago. Cikin matuƙar fushi Sharkar ya umarci dakaru goma waɗanda suka ƙware wajen iya ninƙaya a ruwa, suka faɗa izuwa cikin tekun domin laluben inda yarinyar ta shiga. Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, domin da a ce waɗannan dabaru sun san abin da zai biyo baya da ba su gangancin faɗawa tekun ba, domin abin da ba su sani ba shi ne lokacin da suka faɗa tekun wani ƙaton kifi ya wangame bakinshi, yana hamma ai kuwa bisa sa'a sai suka faɗa ciki, kawai sai ya lamushe su ya yi loma ɗaya da su sannan ya yi nutso izuwa cikin tekun. Nan fa ya zamana cewa Sharkar ya tura gaba ɗaya dakaru hamsin dake biye da shi izuwa cikin tekun, amma ɗayan su bai taso a raye ba. Kwatsam Sai aka ga gawarwakin dakarun birjik sun taso daga ƙarƙashin tekun. Al'amarin da ya ƙara firgita shugaba Yasiran da Sharkar kenan. Kawai sai shugaba Yasiran ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu, sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da WASIƙAR MUTUWA, sannan ya buɗe bakinshi yana mai karanta waɗansu dalasiman tsafi, gami da yin nuni da ɗan yatsanshi izuwa saitin inda fursunar yarinyar ta faɗa.Take ruwan wajen ya daskare ya zama ƙanƙara, kawai sai ya zare waɗansu zabga-zabgan takubba a godon bayanshi, sannan ya dako wawan tsalle ya faɗa tekun yana mai yin nitso izuwa ƙarƙashin ta, A dai-dai wannan lokaci ne rana ta take kuma ta yi zafi ainun, nan fa gaba ɗaya fursunonin suka shiga cikin mawuyacin hali, musamman ƙananan yara, suka fara faɗuwa ƙasa sumammu, wasu ma na sheƙawa barzahu, nanfa iyaye matan da 'ya'yansu suka mutu suka shiga rusa kukan baƙin ciki. Inda a ce mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da wannan al'amari ke faruwa, dole ne tausayi ya kama shi ya zubar da hawaye. Al'amarin shugaba Yasiran kuwa lokacin da ya yi nutso izuwa ƙarƙashin tekun Baharul-sawara, domin ya lalubo yarinyar fursunar da ta faɗa cikin tekun, sai ya shafe tsawon rabin sa'a yana dube-dube da kalle-kalle, amma bai ga inda ta shiga ba. Al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan kuma ya fusata shi, ya cigaba da yin nutson. Lokacin da ya zamana ya shafe sa'a biyu cur! Yana wannan bincike, kwatsam bazato babu tsammani sai ya ji an kirɓa mashi wawan naushi a wuya. Saboda ƙarfin naushin sai da ya yi katantanwa sau uku, ya saki takubban dake hannunshi yana mai kurma wawan ihu. Cikin baƙin zafin nama ya juya domin ya ga wanda ya naushe shi ɗin. Ai kuwa sai ya yi turus bakomai ya gani ba face yarinyar 'yar shekaru sha biyar, hannayen ta ɗauke zaratan takubban da suka suɓuce daga hannun shi. Abu na farko da ya bashi mamaki shine ya aka yi wannan yarinya ta samu ƙarfin damtsen da ta hallaka dakarun tamkar takasance basadaukiya mace mai kamar maza. Koda ya zo nan a tunanin shi sai jikinshi ya kama tsuma yana ƙyarma, idanunshi suka kaɗa suka yi jajur, gashin jikinshi ya mimmiƙe. Kawai sai ya zare waɗansu takubban na daban a damtsen shi, yana mai yin iyo ya durfafi inda take yana shaƙar numfashi ta hanyar amfani ƙarfin sihiri. Koda ganin hakan sai yarinyar ta gyara riƙon wani mazirari a bakinta da take amfani da shi wajen shaƙar iska. Lokacin da suka haɗu sai suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban al'ajabi. Shugaba Yasiran da fursunar suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA ta ban mamaki. Babu abin da zai burge mutum ga jaruman biyu irin yadda suka kaiwa juna hare-hare cikin zafin nama tamkar na'ura ce ke sarrafa su. A wasu lokutan sai kaga sun taso izuwa saman tekun. A cikin jirgin ruwa kuwa koda sadauki Sharkar ya ga an shafe tsawon sa'a biyu bai ji ɗuriyar shugaba Yasiran, kuma ya ga yadda fursunonin na sheƙawa barzahu sai hankalinshi ya dugunzuma ainun, ya rasa abin da yake yi mashi daɗi, domin hakan za su iya rasa rayuwar su baki ɗaya idan har su ka isa ga sarki. Nan take ya faɗa izuwa kogin tunani domin samun mafita, abu na farko da ya faɗo masshi shine, shin yanzu zai sake ƙwance fursunonin ne ya ba su abinci da ruwan sha domin su rayu? Ko zai ƙyale su, sannan ma yanzu za su cigaba da tafiya ne ko kuwa za su jira fitowar shugaba Yasiran daga cikin tekun. Sa'adda Sharkar ya zo nan a tunanin shi, sai kwakwalwarshi ta saƙe dagulewa, da ƙyar da siɗin goshi ya samu mafita. Koda samun mafitar sa kawai ya juya ya nufi wani ɓangaren a jirgin, ya umarci waɗansu dakaru mutum ashirin ya ce su buɗe wani katon murfi, take dakarun su ka cika aikin su suka murfin, sai ga wata matattakala guda goma ta bayyana wacce ta zata shigar da mutum zuwa ƙasan jirgin, sannan Sharkar ya yiwa dakarun wata inkiya ta wutsiyar idanu. Kawai sai suka kwance fursunonin suka shigar da su izuwa ƙarƙashin cjirgin, sannan ya yi umarni da a basu abinci da abin sha. Sannan ya juya yana hangen inda shugaba Yasiran ya yi nutso izuwa cikin tekun Baharul-sawara. A ɓangaren shugaba Yasiran da wannan fursuna kuwa, sun wanzu suna bawa hamata iska suna kaiwa juna hare-hare, gaskiyar masu iya magana da suka ce, duk wanda ya riga ka kwana dole ne ya riga ka tashi. Nan fa yazamana idan shugaba Yasiran ya kaiwa yarinyar hari idan ta kare harin da takubbanta sai ka ga ta durkushe ta nutson izuwa ƙasa, amma ta sake taso sama, nan fa ya zamana ta fara galabaita ainun, ya zamana bata iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kanta, domin daƙyar take iya shaƙar iska. Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne Yasiran ya shamma ce ta ya yanke ta da takobinshi a gadon bayanta. Nan take inda ya yanke ta ya haddasa wani lafcecen rauni, jini ya kwaranya, saboda tsananin zafi da zugi sai da ta tsandara ihu. Sannan ta saki takubban dake hannunta, jikinta ya sandare tamkar babu rai tare da ita. Al'amarin waɗannan dakaru kuwa suna cikin rabawa fursunonin abincin ne sai waɗansu zaratan yan mata guda ashirin waɗanda suka ƙware ainun a fagen sarrafa takobi da sanin dubarun yaƙi, su ka shammaci dakarun suka afka masu da yaƙi, cikin ƙanƙanin lokaci suka hallaka dakarun ta hanyar murɗe masu wuya. Koda samun wannan nasara sai wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa mai annurin fuska da kwarjini daga cikin 'yan matan, ta dubi wasu 'yan matan daban a cikin fursunonin ta ce da su "ina so ku cigaba da baiwa jama'ar mu wannan sauran abinci, kuma ko me zai faru dar ku kuskura ku fito daga cikin wannan ɗaki, ko ku kira sunayenmu, kawai ku kira sunayen ababan bautarmu. Ina so ku yi sani cewa ɗayan mu ba zai dawo nan ba face mun tserar da sauran rayukan jama'ar birnin mu kuma mun ɗauki fansa akan sarki Husnalu". Koda kyakkyawar budurwar ta zo nan azancenta sai jama'ar suka cika da matuƙar farin ciki mara musaltuwa. Sannan budurwar ta zira hannunta a aljihun riga ta ɗauko hodar banju ta miƙa wa sauran 'yan matan ta ce da su "wannan hodar zamu yi amfani da ita ne kafin mu kai ga ɗaukar makaman yaƙi ina fatan kun fahimce ni, tana gama faɗin hanak sai ta juya ta shige ba sauran suka mara mata baya. Su na fita sai suka shiga yin sanɗa da laɓe-laɓe, suka nufi madafa. Lokacin da kyakkyawar budurwa da ake kira Nabihat suka iso izuwa bakin madafar, sai Nabihat ta ɗauko hodar banju a cikin aljihun rigarta ta busa ta izuwa ciki, jim! Kaɗan sai suka kunna kai ciki suna shiga suka tarar dakaru masu dafa abinci sun kama barci mai nauyi. kawai sai suka cire tufafin su suka maye da na dakarun, sannan suka rufe fusakunsu da hulunan ƙarfe. Kawai sai suka matsa izuwa inda dakarun suka ɗora sanwa akan wuta suka buɗe murafun tukunyoyin suka zazzaga wannan hodar banju a cikin, sannan suka mayar suka rufe ruf. Bayan shuɗewar daƙiƙa goma sai suka zuzzuba abincin a cikin waɗansu ƙananan akushi, suka ɗora akan farantai na azurfa, sannan juya suka fice daga tantunan suka shiga rarrabawa dakarun dake cikin jirgin ruwan abincin mai dauke da hodar banjun har suka iso izuwa inda wani sadauki yake. Nabihat ta ɗauki akushi ɗaya ta miƙa mashi ya karɓa ya bude ya sanya hannunshi ya yi loma ɗaya, kawai sai ya dubi Nabihat ya ce "ya kai Himairu ya aka yi abincin nan ya yi ɗan karen daɗi haka? Koda jin wannan tambaya sai Nabihat ta yi murmushi gami da gyaɗa kai, kawai sai ta huce gaba ba tare da bawa sadaukin amsar tambayar shi ba. Haka dai suka cigaba da rabawa dakarun abincin, har suka iso inda suka bar saduki Hushaibu. Nabihat ta ɗauki akushin ta miƙa mashi ya karɓa. Har Hushaibu ya buɗe da nufin cin abincin kwai ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi, kawai sai ya yi jifa da akushin ya durfafi madafa cikin hanzari. A dai-dai lokacinne su jaruma Nabihat suka kammala raba abincin suka samu wata maɓuya a cikin jirgin suka laɓe. A fusace Hushaibu ya kunna kai izuwa cikin tantin, ai kuwa sai ya yi arba da masu dafa abincin kwance suna sharar barci babu tufafi a tare da su. Cikin matuƙar fushi gami da tashin hankali ya zare takobinshi ya ruga izuwa waje yana mai ƙwallawa sauran dakarun kira. Al'amarin da ya janyo hankalin sadauki Sharkar kenan ya zare takobinshi da nufin dakawa dakarun tsawa. A dai-dai wannan lokaci ne hodar banjun da su Nabihat suka zuba a cikin abincin ta fara bugar da dakarun suna ɓingirewa kasa suna sharar barci. Kafin Sharkar da Hushaibu su farga fiye da rabin dakarun dake cikin jirgin ruwan sun kamu da barci mai nauyin gaske, cikin matuƙar kaɗuwa gami da tashin hankali sadauki Sharkar ya cigaba da falfala azababban gudu, yana mai kurma wawan ihu Nan fa sauran dakarun da ba su kai ga cin abincin ba suka firgice suka ɗauko makaman yaƙin suka dinga fitowa daga kowace kusurwa a jirgin. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga su jaruma Nabihat da sauran 'yan matan fursunonin sun yo fitar burgu daga maɓuyar su suna, suka yi ɗauki izuwa kan dakarun suna ihu da kururuwa mai firgitarwa. Koda ganin hakan sai dakarun suka yi ɗauki kansu suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a filin daga. Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan zaratan 'yan mata su ashirin kacal! Suka tunkari ɗaruruwan dakarun dole ne ya cika da mamaki kuma ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA, mata masu kamar maza. Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro daban al'ajabi. Nan fa gaba ɗaya jirgin ruwan ya yamutse da ƙarar haɗuwar makaman yaƙi, gami da ihu da kururuwar mazaje. Nanfa Nabihat da 'yan matan fursunonin suka wanzu suna kaiwa dakarun sara da suka cikin matuƙar zafin nama tamkar jikkunan ba su kasance na jini da tsoka ba. Cikin abin da bai gaza daƙiƙa arba'in ya zamana cewa sun samu nasarar hallaka fiye da mutum hamsin na dakarun sun rauna ta fiye da ɗari biyu. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin dakarun kenan kuma ya fusata su ainun, bisa ganin cewa a matsayin su na GWARAZAN MAYAƘA, amma a ce 'yan mata sun zame masu alaƙaƙai kuma GOBARAR ANNOBA. Nan fa dakarun suka ZAGE DAMTSE wajen kaiwa su Nabihat miyagun hare-hare. Ana cikin wannan artabu ne wani garjejen sadauki, ya kaiwa wata daga cikin 'yan matan wani wawan sara, da nufin tsinke mata wuya amma budurwa ta sunkuiya cikin zafin nama, takobin sadauki ta sari iska. Kafin ya sake mayar da martani, budurwar ta cire wata siriyar wuƙa a damtsenta s caka mashi a maƙogaranshi, sannan ta sanya ƙafarta ɗaya ta daki ƙirjin shi da dukkan ƙarfin ta. Saboda da matuƙar ƙarfin dukan sai da ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya ya faɗa cikin tekun yana mai tsandara ihu. Kawai sai budurwar ta sake afkawa cikin dakarun ta ci-gaba da saran su. Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne SADAUKi Sharkar ya samu nasarar make Nabihat ta faɗi ƙasa, magashiyan nunfashin ta na fita daƙyar, kawai sai ya sanya hannunshi ya damƙo wuyanta ya tattare dukkanin karfinshi da nufin karya wuyan Nabihat. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Nabihat ta dunƙule hannayen ta biyu ta girɓawa sharkar naushi a fuska. Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da ya yi katantanwa a sama sau uku, sannan ya kife a ƙasa, yana mai tsandara ihu sakamakon zafi da zugin da ya ji, haƙorinshi guda ɗaya ya yi fitar burgu daga cikin bakinshi jini ya yi tsartuwa. Amma saboda karfin zuciya gami da juriya irin ta manyan GWARAZAN JIYA sai ya miƙe tsaye zumbur yana mai goge jinin dake bakinshi yana mai gyara tsayuwa. A dai-dai lokacin da Nabihat ta miƙe tsaye zumbur, aka sake sabon kallon kallo, sannan suka sake afkawa junan da yaƙi, ana fara wannan arbu ne Nabihat ta shammaci Sharkar ta gabza mashi naushi a kirjinshi da kafafuwanta biyu, saboda ƙarfin naushin sai da ya yi sama ta tamkar an janye shi da ƙungiya sannan ya faɗa izuwa tekun Baharul-sawara. Koda samun wannan gagarumar nasara sai jaruma Nabihat ta ruga izuwa inda 'yan uwanta suke ta kai masu ɗauki su ka cigaba da ragargazar dakarun.Cikin kankanin lokaci suka hallaka su baki ɗaya. Kawa sai Nabihat ta umarci 'yan mata uku da su tuƙa jirgin ruwan a cigaba da tafiya Cikin matuƙar kaɗuwa ɗaya daga cikin fursunonin ta dubi Nabihat cikin tashin hankali ta ce '' ya ke Nabihat ta ya ya zamu cigaba da tafiya bayan cewa yarinya Lazimat na cikin wannan teku, kuma bamu da tabbacin a wane hali take ciki tana raye ne ko ta mutu. Koda jin wannan batu daga bakin Sharimat sai idanun Nabihat su ka ciko da ƙwalla, ta dube ta ta ce "ya ke Shamirat tabbas a yanzu ba ni da tabbacin yarinya Lazimat na raye, shin yanzu zamu tsaya neman ta ne? Ko kuwa zamu cigaba da tuƙa wannan jirgin ruwa domin ceto daruruwan jama'armu da suka haɗar da yara ƙanana da mata gami da tsofaffi,'? Ina so ki kwantar da hankalinki idan har yarinya Lazimat na raye zamu sake saduwa da ita". Koda jin wannan batu daga bakin Nabihat sai Shamirat ta gyaɗa kai cikin alamun matuƙar damuwa ta matsa kusa da 'yan uwanta, suka shiga tuƙa jirgin ruwan domin koma izuwa birnin su. A dai-dai wannan lokaci ne shugaba Yasiran ya taso daga ƙarƙashin tekun fuskarshi a murtuke babu annuri, tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta, gundulmin hannunshi da Lazimat ta sare mashi na zubar da jini. Sa'adda jaruma Nabihat ta cigaba da jagorantar sauran 'yan uwanta fursunoni, a bisa jirgin ruwan dake tafiya akan tekun Baharul-sawara, domin gudun TSIRA DAGA HAKA. Sai suka shafe tsawon sa'a biyu suna tafiya babu sassauci. Lokacin da ya zamana an shafe sa'a ɗaya ana tafiyar sai jaruma Nabihat ta yi umarni aka shiga ɗakin sirri dake ƙarƙashin jirgin ruwan, aka ɗauka gurasar gami taceccen ruwan inabi, aka shiga rarrabawa jama'arsu domin kowa ya kimtsa cikinshi. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka hango waɗansu tawagar jiragen ruwa kimanin guda ashirin, sun bayyana a saman tekun a kowa ce kusurwa, wato gabas, yamma, kudu da Arewa, Cikin matukar kaɗuwa gami da tashin hankali Nabihat ta yi umarni aka tsayar da tafiya, kawai sai 'yan matan suka ruga izuwa wani ɓangare a jirgin suka ɗebo makaman yaƙi, sannan suka ruga izuwa tsakiyar birnin suna masu gyara tsayuwar su zukatansu cike da matuƙar firgici. Ya yin da ya zamana cewa jiragen ruwan sun matso daf juna, sai Nabihat ta sake ɗimauce wa, su dai jiragen ruwan suna ɗauke ne da waɗansu irin zaratan dakaru masu ƙirar samudawan farko, suna sanye cikin sulken yaƙi na baƙin ƙarfe, ɗauke da miyagun MAKAMAN ƘARE DANGI. Kaico! Haƙiƙa waɗannan dakaru sun kasance masu ban tsoro, domin babu halitta da za ta yi arba da su face ta yi nadamar wanzuwar ta a doran ƙasa. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Nabihat da tawagar dakarun. Tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali, a lokacin ne su Nabihat suka hango shugaba Yasiran a ɗaya daga cikin jiragen ruwan, shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannunshi ɗaya ɗauke da wata sharbebiyar takobi, ɗayan kuwa da ya yi dungulmi ya naɗe shi da wani farin ƙyalle, fuskarshi a murtuke babu annuri har gyatsune take saboda matuƙar fushi. Al'marin da ya yi matuƙar ba su mamaki kenan, suka tambayi kansu a cikin ransu suna masu cewa, ya aka yi Yasiran ya rayu shin ina yarinya Lazimat take tana raye ne ko kuwa ta mutu? Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kawunansu kenan. Kawai sai Nabihat su ka hango dakaru masu tarin yawa suna dako tsalle daga inda suke suna sauka akan jirgin da suke suna shawagi a sama tamkar tsuntsaye, suna ihu da kururuwa mai firgitarwa. Koda ganin hakan sai Nabihat ta ɗaga takobinta sama cikin ƙarfin hali gami da ƙarfafawa sauran 'yan matan gwiwa ta falfala da gudu izuwa kan dakarun. Ya yin da 'yan matan suka ga haka sai suka yi koyi da ita, suna masu mara mata baya. Tabbas shi ƙarfi a zuciya yake ba wai a girman jiki ba, domin idan ba haka ba taya ya mutum ashirin za su za su tunkari ɗaruruwa. Amma dai masu iya magana na cewa shi bala'i kafin ya zo ne ake neman mafita, amma idan yazo babu abin da ya rage face a karɓe shi hannu biyu. In da a ce mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan dubban dakarun suka yunƙura kan su jaruma Nabihat, sai ya yi zaton DANDAZON zakuna ne suka farwa barewa guda ɗaya jal, saboda matuƙar kwarjinin su. Ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar firgici da ban tsoro. Ƙarar haɗuwar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne. Ana fara wannan artabu ne su jaruma Nabihat suka fara gane cewa sun haɗu da gamon su. Domin kuwa koda ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza, kuma ruwa ba sa'an kwando ba ne. Domin a zahiri dakarun sun ninka su a ƘARFIN DAMTSE gami da zafin nama nesa ba kusa ba. Sai da aka shafe sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari biyu ana wannan baƙin artabu, kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI sai ya zamana dakarun sun yi masu miyagun raunuka suna zubar da jini, bisa hakan ya sanya suka faɗi ƙasa a sune. Koda samun wannan gagarumar nasara sai dakarun suka sake ɗaure fursunonin da waɗansu irin murtuka-murtukan sarƙoƙi. Koda aiwatar da hakan sai waɗansu dakaru na musamman suka shiga tuƙa jirgin ruwan aka cigaba da tafiya, sauran jiragen tawagar guda ashirin suka mara masu baya. Tafiyar sa'a uku kacal suka yi aka iso izuwa gaɓar tekun, take dakarun suka fito da su Nabihat daga jirgin ruwan, nesa kaɗan da inda aka sauka wani ƙasaitaccen birni mai dogayen gine gine, masu tsari da kyawu. Kallo ɗaya za ka yiwa birnin ka fahimci cewa an kashe dukiya mai tarin yawa wajen ƙawata shi. Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka tusa ƙeyar fursunonin izuwa birnin su su Nabihat kuwa sai aka ɗora su a bisa kan keken doki. Nan fa tsananin wahala ya sanya sauran jama'ar su Nabihat suka dunga yanke jiki suna faɗuwa ƙasa, sakamakon matuƙar zafin rana amma a haka dakarun suka cigaba da jan su a ƙasa. Komai rashin tausayin mutum idan ya yi arba da halin da ƙananan yara da mata ke ciki dole ne ya zubar da hawayen tausayi. Domin wasu lokutan idan mutum ya faɗi ƙasa sai dakarun su zabga mashi wata murtukekiyar bulala, take inda ya daka ɗin zai fashe jini ya yi tsartuwa. Tun kafin a iso kofar birnin waɗansu girɗa-girɗan dakaru suka wangame makekiyar kofar birnin, suna zuwa suka kunna kai izuwa ciki. Daga ciki birnin ya kasance tafkeke na gaban kwatance, gaba ɗaya gine-ginen shi an yi su ne bisa tsari mai ban sha'awa, duk inda mutum ya kalla jama'a ne rututu na kai komo suna gudanar da ayyukan su na yau da kullum, haka dai su shugaba Yasiran suka ci-gaba da tafiya a cikin birnin, duk inda jama'a suka hango su sai ka ga sun dare sun buɗa masu hanya. Kai tsaye aka shiga izuwa fadar birnin wacce ta kasance ƙasaitacciya da aka ƙawata da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, kai tsayawa musalta tsaruwa da ƙawatuwar fadar zai iya zama ƙauyanci sai dai abin da idanu suka gani kawai. A wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a maza, mata yara da manya tare da yan majalisa. Zaune a bisa wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'anta ta da ƙarfen jauhari aka yi mata feshin da ruwan zinare. Wani garjejen mutum ne mai kimanin shekaru talatin da ɗoriya, yana sanye cikin tufafin alfarma irin na hamshaƙan sarakai, kanshi sanye da KAMBUN SARAUTA. Kallo ɗaya zaka yiwa mutumin ka ji baka marmarin sake haɗa idanu dashi, saboda matuƙar munin fuskarshi tamkar murmushi bai taɓa wanzu akan ta ba. Ba wani bane wannan mutum ba face sarki Uhaisu ibn Falluz. A gefen hannunshi na dama bisa wata ƙasaitacciyar kujera wani kyakkyawan saurayi ne ma'abocin kwarjini da haiba, ya caɓa ado irin hamshaƙin BASARAKE, babban abin da ya ƙara tona asirin kyawun shi shine saje da gemunshi da suka kasance baƙaƙe siɗik. Ba wani ba ne kyakkyawan saurayin ba face yarima Zafiyar ibnu Uhaisu, wanda ya kasance ɗa guda ɗaya tilo ga sarki Uhaisu. Sarki Uhaisu ibn Falluz ya kasance GWARZON DUNIYA a fagen jarumtaka gami da sanin ilimin tsafi, daɗin daɗawa kuma ya kasance AZZALUMI na gaban kwatance. Tun yana da shekara goma sha biyar ya hau bisa karagar mulki, duk da yana da ƙarancin shekaru amma sai jama'a suka ga yana gudanar da sha'anin mulki cikin tsari fiye da na mahaifinshi marigayi sarki Falluz. Lokacin da sarki Uhaisu ya cika shekaru ashirin a bisa kan gadon sarauta, sai ya zamana cewa ya fara kai mamayar bazato izuwa ƙauyuka da biranen dake maƙwabtaka da shi, ana farauto mashi bayi gami dukiya mai tarin yawa. Cikin ƙanƙanin lokaci Uhaisu ya zama mashahurin attajiri da babu tamkar shi a nahiyar. Da wannan dukiya da ya tara yake siyo manyan sadaukai daga sassan duniya domin su taimaka mashi wajen FATAUCIN BAYI. Shin mene ne dalilin da ya sanya su jaruma Nabihat suka baro birninsu har aka farauto su a cikin wannan jirgin ruwan? Amsar hakan kuwa shi ne kamar haka:- BABI NA BIYU Wata rana daga cikin ranakun da sarki Uhaisu ke kai FARMAKIN BAZATO izuwa birane da ƙauyuka domin FATAUCIN BAYI. Yana zaune a cikin lambun shaƙatawar shi sanye da riga 'yar shara irin ta hamshaƙan sarakai, waɗansu irin tsala-tsalan kyawawan kuyangi na shayar da shi taceccen ruwan inibi da barasa a bisa waɗansu kofuna na zinare, a gefe guda kuwa waɗansu kuyangi ne sanye da tufafi mai bayyana tsiraicinsu. Babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da su face hankalinshi ya tashi. Su na yiwa sarki Uhaisu tausa tamkar wani jariri, shi kuwa yana kallon korayen tsirrai gami da waɗansu irin tsuntsaye dake shawagi a wajen, su suna fitar da wani irin sautin kuka mai daɗin saurare. Zuciyarshi cike da matuƙar farin ciki, yana cikin wannan hali ne kawai sai ya ɗauko madubin tsafinshi ya shafe shi da hannunshi na hagu ya fara gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi. Kamar yadda a duk sa'adda zai kai farmakin yana gudanar da bincike ne domin ya gano birnin da zai kai aiwatar da hakan, Tsawon daƙiƙa hamsin yana gudanar da binciken sannan ya gano wani baƙon birni dake iyaka da tekun Baharul-sawara wato birnin DARUL-IMFAL, Abin da ya firgita shi a binciken shi ne, tabbas a wannan birni ne za a samu mahalukin da zai kawo ƙarshen mulkin zaluncin shi a doran ƙasa. Kooda ganin hakan sai sarki Uhaisu ya miƙe tsaye zumbur yana mai kurma wawan ihu, ihun na shi ya firgita kuyangin dake yi mashi hidima, gami da tsuntsayen dake lambun suka tashi sama furrrr!. Al'amarin da ya janyo hankulann dakarun dake gidan sarautar kenan suka rugo izuwa lambun ɗauke da makamai. Amma koda suka yi arba da sarki Uhaisu a tsaye tsam! fuskarshi a murtuke babu annuri tamkar an watsa mashi garwashin wuta a kan ta, kuma idanuwanshi sun kaɗa sunyi jajur. Sai suka yi turus! Kowa ya kasa isa izuwa inda yake, cikin matuƙar fushi sarki Uhaisu ya ƙwallawa wani badakare kira mai suna Hushaibu. Kafin ya gama rufe bakinshi Hushaibu ya bayyana a gare shi ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa jikinshi na ƙyarma saboda tsananin tsoro. Cikin matuƙar fushi sarki Uhaisu ya dakawa kuyangin dake yi mashi hidima tsawa da su fice daga cikin lambu, sannan ya mayar da uban shi ga Hushaibu cikin kakkausar murya ya sune shi ya ce "ya kai Hushaibu ka yi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira ka nan ba sai domin ina son ka hanzarta kira min sadauki Yasiran''. Muryar Hushaibu na rawa ya ce "An gama ya shugabana, yana gama faɗin hakan sai ya miƙe tsaye ya fice daga cikin lambun da sauri. Jim kaɗan sai ga Yesiran ya bayyana gareshi, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance SADAUKIN SADAUKAI, mai tarwatsa maza a filin daga. Sarki ya dubi Yesiran ya ce "ya kai Yasiran ka yi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka tafi izuwa wani birni dake iyaka da tekun Baharul-sawara, ana kiran birnin da suna DARUL-IMFAL ina so gaba daya mazajen birnin su zamo matattu, sannan ka kawo min matayensu da dukiyoyin su cikin ƙoshin lafiya, sai dai ina son kayi sani cewa kuɓucewar ɗaya daga fursunonin dai-dai yake da rasa rayuwar ka baki ɗaya''. Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Uhaisu sai Yesiran ya ce "ya shugabana ai wannan aiki abu mai sauƙi a gare ni tamkar kurɓar ruwa, na rantse da ƙarfi mulkin ka sai na kawo maka matayen birnin DARUL-IMFAL cikin ƙoshin lafiya''; Koda jin wannan batu daga bakin Yesiran sai Uhaisu ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. Kafin sarki Uhaisu ya sake furta wani abu Yesiran ya miƙe tsaye zumbur ya fice daga lambun. Kamar yadda sadauki Yesiran ya yiwa sarki Sarki Uhaisu alƙawari haka al'amarin ya kasance, a in da yana fita ya ɗebi dakarun yaƙi guda dubu hamsin, suka durfafi hanyar da za ta sada su da birnin DARUL-IMFAL bisa wani makeken jiragen ruwa. Da la'asar sakaliya, sadauki Yesiran da rundunar mayaƙanshi, suka iso gaɓar tekun Baharul-sawara sakamakon hango kofar birnin DARUL-IMFAL da su kayi. A wannan lokaci jama'ar birnin DARUL-IMFAL na gudanar da ayyukan su na yau da kullum cikin walwala da jin daɗi, hakan ya faru ne sakamakon saukar ruwan sama a daren jiya. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ji ihu da kururuwar dakaru masu tsaron ƙofar gari, kafin ka ce me, gari ya hargitse da guje-gujen jama'a gami da ifice-ifice, yara da manya mata da maza, Nan take dakarun sadauki Yesiran suka afkawa jama'ar birnin da masifaffan yaƙi, nan fa mazaje suka dunga yin MUTUWAR JARUMTA, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, ƙarar karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje gami da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne. Kaico! Haƙiƙa yaƙi abin tausayi ne in da a ce mutum zai ga yadda dakarun Yesiran ke hallaka mazajen birnin ba ji ba gani, dole ne ya zubar da hawayen tausayi domin hatta ƙananan yara maza kashewa suke yi, koda kuwa jariri ne sabuwar haihuwa ba su ƙyale ba. Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN KARFI sai ya zamana dakarun Yesiran sun kashe gaba ɗaya mazajen birni ɗayan su bai tsira da rayuwar shi ba. Nan fa ƙananan yara da mata suka dunga rusa kuka mai matuƙar ban tausayi da narkar da zuciya, wasu na kuka ne bisa rasa mazajensu, wasu 'ya'yensu, wasu 'yan uwansu. Bayan sadauki Yasiran ya kashe sarkin dake mulkin birnin wani dattijo mai suna Sha'aran sai ya yi umarni aka kwashe baki ɗaya dukiyar dake birnin, aka sanya matayen birnin da suka rage a raye sasari na baƙin karfe, bayan an fice daga birnin sai waɗansu dakaru suka bankawa gidadanjiin birnin wuta, take aka nufi gaɓar teku aka sanya ɗora dukkanin jama'ar a bisa wannan makeken jirgin ruwa. Lokacin da aka ɗora su jama'ar a bisa jirgin ruwan suka hango yadda birninsu ke ci da wuta, kuma an mayar da da yawa daga cikin su zaurawan yara kuwa sun zamo marayu. Sai suka fashe da matsanancin kukan takaici da baƙin ciki. Ba tare da wani ɓata lokaci ba sadauki Yesiran ya yi umarni aka tuƙa jirgin ruwan a aka cigaba da tafiya zuciyarshi cike da matuƙar farin ciki da samun wannan nasara. Wannan shi ne dalilin da ya sanya sarki Uhaisu ya farauto su jaruma Nabihat daga birnin DARUL-IMFAL dake iyaka da tekun Baharul-sawara. BABI NA UKU Al'amarin shugaba Yesiran kuwa, lokacin da ya gabatar da su Nabihat da sauran jama'ar birninsu gami da dukiyar ganima a gaban sarki Uhaisu sai sarki ya dube shi a lokacin da yake durƙushe a gaban shi ya buɗi baki cikin alfahari da BAƘAR IZZA ya ce ''ya kai Yesiran haƙiƙa kayi aiki mai kyau yadda na buƙata saboda ina mai tabbatar maka da cewa zaka samu gwaggwaɓan kaso daga cikin ganimar dukiyar da aka farauto. Yanzu abin da nake ya kamata ayi shine a tafi da dukkanin fursunonin izuwa kurkuku a ajiye su a ɓangaren BAUTAR MUTUWA". Koda yarima Zafiyar da ya kafa idanuwanshi akan jarumai jaruma Nabihat dake cikin halin suma, ya ji wannan batu daga bakin mahaifinshi sai ya yi caraf ya tari numfashin shi ya ce "ya abbana ina neman alfarma a gare ka da abar fursunonin a hannuna har izuwa lokacin da za'a yanke hukunci akan su." Da jin wannan batu daga bakin yarima sai sarki ya juya ya dube shi yana mai fahimtar wani abu akan fuskarshi, sannan ya yi tattaunawar murmushi a gare shi ya ce "ya abin alfaharina kuma muradin zuciyata kayi sani cewa babu wani abu da zaka nema a gare ni face na baka shi koda kuwa raina ne, amma akwai buƙatar ka ba ni lokaci na yi nazari, domin bisa binciken da na gudanar ya tabbatar min da cewa a cikin jama'ar za a samu wanda zai kawo ƙarshen mulki na". Sa'adda yarima ya ji wannan batu daga bakin sarki sai ya gyaɗa kai cikin alamun matuƙar damuwa, domin wannanne karo na farko a rayuwarshi da ya ji ya kamu da matuƙar tausayin bayin da mahaifinshi ke farautowa. Koda gama wannan tattaunawa sai shugaba Yesiran ya huce kai tsaye izuwa hanyar da za ta sada su da kurkukun birnin, koda isowar su sai masu gadin suka wangame makekiyar ƙofar shiga, suna masu risinawa ga shugaba a gare shi. Daga ciki kurkukun ya kasance tafkeke tamkar gari guda, katangun shi sun kasance masu matuƙar tsawo da aka yi su da zallar duwatsun wuta masu ƙwarin gaske. Duk inda mutum ya kai duban shi a ciki bayi ne maza da mata, yara da manya na ta gudanar da ayyukan bauta nau'i daban-daban, waɗansu na aikin farfasa duwatsun wuta da manyan gudumun ƙarfe, wasu na ɗinka kayan adon dawakai da tufafin sarauta. Koda shigowar shugaba Yesiran cikin kurkukun sai gaba ɗaya bayin su ka dunga a jiye aiyukan su suna zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa a gare shi, cikin hanzari shugaban dake kula da kurkukun ya karɓi su jaruma Nabihat ya yi umarni aka rarraba jama'ar su a cikin waɗansu ɗakunan na musamman. Koda jama'ar dake wajen suka ga cewa an shigar da su jaruma Nabihat izuwa ɓangaren da ake yiwa laƙabi da BAUTAR MUTUWA, sai suka cika da matuƙar tausayin su. Domin kuwa duk wanda aka shiga da shi izuwa ɗakin BAUTAR MUTUWA baya fitowa a raye sai daigawar shi. Sa'adda jama'ar su Nabihat suka tsinci kansu a cikin ɗakunan sai suka fashe da kukan baƙin ciki mai matuƙar tsuma zuciya. Wannan shine abin da ya faru da su Jaruma Nabihat ya yin da aka isa da su izuwa kurkuku. Al'amarin wannan yarinya fursuna da ta fafata yaƙi da shugaba Yesiran a ƙarƙashin tekun Baharul-sawara kuwa, bayan ta samu nasarar datse nashi hannunshi ɗaya, shi kuma ya samu nasarar yi mata miyagun raunuka, ɗaya a gadon bayanta na biyu a cinya na ukun kuwa a damtsen ta na hagu. Saboda yawan jinin dake zuba a jikinta take numfashinshi ya ɗauke, kuma ta taso izuwa saman tekun igiyar ruwa ta cigaba da tafiya da ita, har ta kawo ta izuwa gaɓar tekun ta ɓangaren yamma maso kudu. A dai-dai wannan lokaci ne wani mafarauci da matarshi suka nufo gaɓar tekun ɗauke da bahon ɗibar ruwa. Sa'adda suka yi arba da ita kwance babu alamun rai a tare da ita ga manyan raunika a jikinta sai suka yi turus! cikin kaɗuwa suka matsa inda take. Ba tare da wani ɓata lokaci ba suka ajiye bahon ruwan dake hannunsu, mafaraucin ya ɗauki yarinyar ya saɓa ta a kafaɗarshi. Cikin hanzari suka juya suka durfafi hanyar da zata sada su da dajin da suka fito. Tafiyar daƙiƙa latalin kacal suka yi suka iso wani gida a dajin. Gidan an gina shi ne da zallar duwatsun wuta, kai tsaye suka kunna kai izuwa gidan. Daga ciki gidan ya kasance mai kyawun tsari yana ɗauke da ɗakuna guda biyu da makewayi ɗaya sai wani madaidaicin fili da aka kafa turken dabbobi wata saniya guda ɗaya fara sol tana cin ciyawa a cikin wani bawon kaba. Cikin hanzari matar mafaraucin ta shimfiɗe yarinya Lazimat a bisa wani madaidaicin gado da aka yi shi da zallar itace aka shimfiɗe shi da kilishi mai taushi, bayan ta kwantar da ita sai ta shiga danna ƙirjinta cikin matuƙar tashin hankali. Shi kuwa mafaraucin sai ya fice daga ɗakin, jim kaɗan sai ga shi ya dawo ɗauke da tafashasshen ruwan zafi gami da tacecciyar madarar shanu, a ɗayan hannunshi kuwa yana ɗauke da wata jakar fata, kawai sai ya shiga ɗauko waɗansu magunguna a cikin jakar ya na haɗa su a cikin wani akushi mai ɗauke da ruwa. Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya Lazimat bata farfaɗo daga dogon suman da tayi ba. Sai daga bisani ne ta buɗe idanuwanta tana mai jan gwaron numfashi, nan fa suka cika da matuƙar farin ciki bisa ginin farfaɗowarta, ba tare da wani ɓata lokaci ba matar ta shiga sanya mata magani a raunikan ta. Bayan ta kammala ne sai ta tashe ta zaune ta shiga bata wannan madarar shanu a baki tana kurɓa, sai da tasha ta ƙoshi sannan ta bata waɗannan magunguna da maigidanta ya haɗa a cikin wannan akushi. Kana daga bisani mafaraucin ya dubi matarshi fuskarshi cike da annuri gami da tsantsar so da kauna ya ce "ya uwar 'ya'yana ina mai ba Ni farin ciki, kiyi sani cewa ina ji a jikina wannan yarinya da muka tsinta za ta maye mana gurbin da raɗaɗin 'yarmu da muka rasa. Kuma na ji a jikina cewa za ta zamto silar da zamu ɗauki fansa akan sarki Uhaisu". Koda jin wannan batu daga bakin mai gidannata sai ta cika da matuƙar farin ciki ta ce "maganar ka haƙƙun ya abin bege na tabbas alamun nasara sun fara bayyana a gare mu"; Mafaraucin ya ce "yanzu zan ɗan shiga izuwa daji, domin na farauto mana abin da zamu yi kalaci sai ki kula da ita har naje na dawo". Yana gama faɗin hakan sai kawai ya miƙe tsaye ya fice daga ɗakin ya na mai waigen matarshi suna jifan juna da tsantsar so da ƙauna, yana fita ya sake kunna kai izuwa cikin daji . Jim kaɗan bayan shuɗewar waɗansu daƙiƙu matar mafaraucin na zaune a gaban Lazimat ta ƙura mata idanu sai kawai ta jiyo ƙarar takun sawaye gami da gurnani mai matuƙar ban tsoro, ya cika dajin baki ɗaya. Koda jin hakan sai kawai ta ɗauko wata takobi a gefen gadonta ta miƙe tsaye zumbur ta ruga izuwa ƙofar gidan, ai kuwa tana fita sai tayi arba da waɗansu irin ayarin gabza-gabzan birrai su kimanin guda ɗari biyu. Birran sun kasance masu matuƙar tsawo, girma, kwarjini gami da muni, a hannayensu na ɗauke da wani irin sungumi mai waɗansu irin tsinika a jikin shi tamkar zarto, Wannan shi ne abin da ya faru da mafarauci da matarshi da suka tsinci yarinya Lazimat. Kallo ne ya wakana tsakanin kilimat matar wannan mafarauci da ayarin gwaggwan birran na ɗan wani lokaci. Daga can sai birran su kayi wani mahaukacin gurnani mai matuƙar ban tsoro mai ɗimauta duk wata halitta numfashi, bishiyu suka dunga rangaji suna karairayewa suna faɗuwa kasa. Wani daga cikin birran wanda alama shi ne shugaban su ya daka masu wata tsawa dake nuna cewa su afkawa matar, ai kuwa sai su ka yi ɗauki kanta suna masu daga makamansu suna ihu da kururuwa mai firgitarwa. Shi kuwa shugaban birran sai ya samu wani ɗan faffaɗan dutse ya zauna a a kai yana mai harɗe kafafuwanshi yana mai zuba idanu domin ya ga yadda artabun zai wakana. Koda ganin hakan sai uwar gidan mafaraucin ta ɗaga takobinta sama sannan ta ruga izuwa kan birran tana ihu da kururuwa mai firgitarwa ta far masu da sara da suka, su kuwa suka shiga kai mata duka da bugu da sungumin su cikin wani irin zafin nama, duk sa'adda takobinta ta sari jikkunan birran sai ta ji kamar dutse ta sara domin ko gezau ba su yi Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin ta kenan, yazamana ta canza salon fadan ta a in da ta dunga saran su gami amfani da hannunta ɗayan tana gabza masu naushi da bugu da dukkan ƙarfin ta. Gaskiyar masu iya magana da suka ce "Idan kiɗa ya canja dole ne rawa ma ta canja, nan fa ya zamana cewa ta fara samun galaba akan birran, domin duk wanda ta gabza masu naushin sai ka ji ya tsandara ihu ya ya faɗi ƙasa yif!. Koda ta fahimci cewa ƘARFIN DAMTSE ya fi tasiri akan su sai kawai ta yi jifa da takobinta ta shiga amfani da hannayenta duka biyun gami da kafafu wajen kai farmaki. Duk in da ta sanya a gaba sai dai kaga gawarwakin birran na zube kasa matattu. Wohoho! Tabbas ƙarfi da jarumtaka ba a siyan su da kuɗi face baiwa daga Allah, Komai tsakanin hassadar mutum idan ya ga yadda kilimat ke ragargazar birran dole ne ya jinjina mata ya san cewa ta ciri tuta a cikin jerin manyan JARUMAN DUNIYA. Nan fa kururuwa gami da hargagin su ya cika dajin baki ɗaya, jini ya dunga tsartuwa yana kwaranya a kasa, haƙiƙa waɗannan birrai suna ganin tashin hankalin da basu taɓa ganin irin shi ba. Domin ta zame mssu alaƙaƙai, kuma ƙadangaren bakin tulu, cikin abin da bai gaza daƙiƙa ɗari biyu ba ta kashe fiye da kaso biyu bisa uku na birran. Sa'adda shugaban birran ya ga irin muguwar ɓarnar da matar mafaraucin ke yi mashi sai ya cika da matuƙar mamaki kuma ya fusata ainun, domin fiye da shekaru ashirin suna zaune a wannan daji ba su taɓa ganin bil'adama da ya yi masu hasara kamar haka ba. Nan take zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone, kawai sai ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu da sanya bishiyu suka dunga ƙarye suna faɗuwa ƙasa, duwatsu suna karo da juna su na yin bindiga, kawai sai sauran birran da ke yaƙin suka zubar da makaman su suka ruga izuwa bayan bishiyu su ka ɓuya A lokaci guda shugaban ya tsuke bakinshi sannan ya dako wawan tsalle daga inda yake zaune ya durfafi inda take, ya yin da ya isa gare ta nan take ta zamto 'yar mitsitsiya tamkar an ajiye ɓera a gaban giwa, saboda matuƙar tsawo da girman shi. Kafin ta yi wani yunƙuri shugaban ya shammace ta ya gabza mata wawan naushi a fuska da hannunshi ɗaya. Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da tayi katantanwa a sama sau uku sannan ta faɗo ƙasa tim! A matuƙar galabai ce, cikin ƙarfin hali ta yunƙura ta miƙe tsaye da nufin ta mayar da martani amma sai ya damƙe ta da hannunshi ɗaya ya matse ta ya shiga yi mata lugudan naushi a fuska nan take fuskarta ta kumbura, tayi kaca-kaca da jini da majina kuma numfashinta na fita samas-sama. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai ya ji ta ƙwalla ƙara ta suɓuce daga hannunshi sannan ta gabza mashi naushi a idonshi ɗaya. Take ya fashe wani koren ruwa gami da jini ya dunga kwaranya da ga ciki, nan fa shugaban ya dunga ihu da kururuwar neman taimako, kafin ya sake wani yunƙuri matar mafaraucin ta cire wata 'yar karamar wuƙa ta caka mashi a maƙogaronshi, nan take ya faɗi kasa rikica! Yana shure-shuren mutuwa kafin wani lokaci ya sheƙa barzahu. A dai-dai wannan lokaci ne mai gidanta ya rugo izuwa wajen, koda ya yi arba da gawarwakin birran sai kawai ya rungume matarshi cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa bisa ganin cewa tana raye bata mutu ba. Sai daga can ne ya janye jikinshi daga na ta, a lokacinne ya lura cewa ta samu manyan raunika, sai kawai ya ɗauke ta ya shiga da ita izuwa cikin gida cikin matuƙar tashin hankali. Lokacin da ya isa sai ya shimfiɗe ta a bisa wani gadon na musamman dake cikin turakarshi ya shiga bata taimakon gaggawa,to ta hanyar sanya mata magani a raunikan ta, inda jini ya taru ya gasa mata da ruwan ɗumi. Har a wannan lokaci yarinya Lazimat ba ta farfaɗo ba tana kwance tana sharar barci sakamakon maganin barci da aka bata. Ana cikin wannan hali ne sai kawai ya ga uwargidanta shi ta buɗe idanuwanta tana mai yi masa wani murmushin karfin hali, cikin tattausan murya ta buɗi baki ta ce "ya uban 'ya'yana shin mene ne ya sanya zaka saka kan ka a damuwa bayan cewa mun samu abin da zai share mana hawaye, kuma gani a raye ban mutu ba? Mai gidan nata ya dube ta cikin tsantsar tausayi da so da ƙauna ya ce "zancen ki haƙƙun ya abar kaunata, amma ina so kiyi sani cewa tsananin kaunar da nake yi miki ne ta tayar min da hankali. Koda jin wannan batu sai su duka biyun suka bushe da yar karamar dariyar murna suna yiwa junan su wani irin kallo mai tattare da tsananin begen juna Sai aka shafe kwanaki uku mafaraucin yana jinyar matar shi da yarinya lazimat. A wata rana matar mafaraucin na bawa yarinya lazyimat horan yaƙi, bayan ta kammala bata horan yaƙin sai ta ta ja hannunta izuwa kan wani faffaɗan dutse suka zauna tare a kan shi, sannan ta sanya hannayenta biyu ta ɗora a kan kafaɗunta dube ta cikin nutsuwa ta yi gyaran murya ta ce "ya ke wannan yarinya shin mene ne sunan ki da labarin rayuwar ki?. Koda jin wannan tambaya daga bakin matar sai hawaye suka kwaranyo daga idanun Lazimat tana mai fashewa da kuka mai tsuma zuciya. Al'amarin da ya yi matuƙar bata mamaki kenan kuma ya dugunzuma hankalinta dube ta ta ce "shin ina dalilin wannan kuka naki? Ki sani cewa sanar da ni labarin ki shi ne zai bamu damar taimaka wa rayuwar ki. Da jin haka sai Lazimat ta share hawayen dake fuskarta ta buɗi baki daƙyar ta ce "da farko ni suna Zalimat bintu Haiman mahaifina ya kasance GWARZON DUNIYA mai tarwatsa maza a filin daga, Bisa wannan dalili ne ya sanya jama'ar birninmu ke matuƙar kaunar shi domin yana bayar da gagarumar gudummawa wajen kare martabar birninmu daga harin bazato. Daga wannan ne lazimat ta kwashe labarin farmakin da sarki Uhaisu ya kai birnin su bisa jagorancin shugaba Yesiran,dama abin da ya faru tsakaninta da dakarun jirgin ruwan da ya ɗauko su a saman tekun Baharul-sawara, daaga farko har ƙarshe ta zayyane mata. Sa'adda da yarinya lazimat tazo nan a labarin ta sai ta sake fashewa da wani matsanancin kuka mai ban tausayi , Saboda matuƙar tausayi da matar mafaraucin ta ji bata san lokacin da hawaye ya zubo mata ba ta rungume ta a kirjinta su duka biyun suka fashe da matsanancin kuka, sai da suka ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani ta janye jikinta daga na Lazimat suka fuskanci juna. Idanu sharkab da hawaye ta dube ta ce "ya ke Lazimat haƙiƙa sarki Uhaisu baƙaramin AZZALUMI ba ne, tun da ya raba ki da iyayen ki dangi da yan uwanki ya mayar dake marainiya. Ina so ki kwantar da hankalin ki domin ni da mai gidana mun yi miki alƙawarin sai mun ɗauko miki fansa akan sarki Uhaisu, kuma sai mun ceto sauran jama'ar ku ina so ki ɗauke mu tamkar iyayenki"; Koda jin wannan batu sai Lazimat ta cika da matuƙar farin ciki ta dube ta ce "ya ummina ba ki sanar da ni sunanki da na abbana ba da ma labarin ta ku rayuwar? Da jin wannan tambaya sai matar mafaraucin ta yi murmushi mai taushi a gare ta ta ce "mai gidana ana kiranshi da suna Najwas ibnu Naufal, ni kuwa ana yi min laƙabi da Kilimat bintu kurbas, ya 'yata ki yi sani cewa a halin yanzu ba zan ba ki labarin rayuwar mu ba, kasancewar na ki labarin ya yi min fami a zuciyata, amma na yi miki alƙawarin zan ba ki anan gaba". Koda Kilimat bintu kurbas ta zo nan a zancen ta sai suka hango mafarauci Najwas ya dawo daga farauta, cikin matuƙar farin ciki suka miƙe tsaye suka je suka tarbe shi, Kilimat ta riƙe mashi dabbar da ita kuwa yarinya Lazimat sai ta karɓi salkar ruwa da jakar dake rataye a gadon bayanshi suka dunguma izuwa cikin gida. Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya lazimat bayan ta samu lafiya a hannun mafarauci Najwas da uwar gidanshi. BABI NA HUƊU Ƙasaitacciyar turaka ce da aka ƙawatata da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, gaba ɗaya tana shimfiɗe da wani irin kilishi mai matuƙar taushi,wanda idan mutum ya taka shi sai ya ji tamakar kafafuwanshi za su shige ciki, ku san dukkanin abin da ke turakar an sana'anta shi ne da zallar ƙarfen jauhari da yaƙutu, waɗansu irin fitilu masu matuƙar haske sun ƙara fito da kyawun tuarakar. Kai tsaya wa musalta tsaruwa da kawatuwar turakar ya huce hankali sai dai abin da idanu suka gani kawai. A wannan lokaci dare ya tsala babu abin da kunne ke ji face kukan gyare gami da haushi karnuka tsilli-tsilli,i' idan mai kallo ya kai duban shi a tsakiyar turakar zai yi arba da wani mutum sanye da riga 'yar shara da wando irin na hamshaƙan sarakai yana kai komo tamkar wanda ya yiwa sarki ƙarya. Ba wani ba ne face sarki Uhaisu, a wannan lokacin bakomai ne ya hana Uhaisu barci ba face tunanin buƙatar da ɗanshi yarima Zafiyar ya nema a wajen shi, ta ya amince mashi ya zamo mai kula dasu jaruma Nabihat. An ya kuwa yarima ba saboda zuciyarshi ta kamu da soyayyar Nabihat ba ne yasanya ya ce a ba shi ikon kulawa da su ɗin ba? Yanzu idan har ya yi ganganci soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin su ta ya ya zai iya zartar da hukuncin kisa akan su Nabihat tun da halarar tsafi ta bayyana mashi cewa sune za su kawo ƙarshen MULKIN ZALUNCIn shi daga doran ƙasa. Sa'adda sarki Uhaisu ya zo nan a tunanin shi sai hankalin shi ya dugunzuma fiye da ko yaushe. Yana Cikin wannan hali ne wani tunani ya faɗo mashi wanda ya sanya shi farin ciki. Tunanin kuwa shi ne ai ya umarci sadauki Yesiran akan ya kai su Nabihat izuwa ɓangaren BAUTAR MUTUWA dake kurkukun, tabbas yunwa ce zata zamo ajalin su. Koda ya zo nan a tunanin sai ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Uhaisu bayan ya baro fada, ya kaɗaita a cikin turakarshi. Kashe gari tun da duku-dukun safiya kafin hudowar rana aka fito dasu jaruma Nabihat daga cikin ɗakunan da aka kulle su a ɓangaren BAUTAR MUTUWA, dake cikin kurkukun Mautul- shammar, aka rarraba masu aikin farfasa duwatsu, da yake yanayin garin ana cikin wunturu, nan take tsananin sanyi ya addabi ƙananan yara da tsofaffi, saboda ba sa sanye pda tufafi masu nauyi, Sai da suka wuni cur suna aiki sannan dakaru suka sake mayar da su izuwa cikin ɗakunan su ba tare da an bawa ɗayan su koda loma ɗaya ta abinci ba. Tun da duku-dukun safiya fadar sarki Uhaisu ta cika ta batse da jama'ar gari gami da fadawa, bayan kowa ya hallara ne sai sarki ya miƙe tsaye daga kan karagar shi ta mulki ya fuskanci jama'a ya buɗi baki cikin tunƙaho da baƙar uzza ya ce "ya ku jama'ar wannan fada mai albarka ku yi sani cewa ba komai ya sanya na tara ku anan ba sai domin sai ku ganewa da idanuwanku yadda zan yanke wa jama'ar birnin DARUL-IMFAL hukunci, domin a cikin su ne za a samu tsageran da zai kawo ƙarshen mulkina, ina so hukuncin ya zamo darasi ga duk wani mai ƙarar kwana irin su"; Koda gama faɗin hakan ya koma kan karagarshi ya zauna, take fadar ta kaure da ce kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka hango shugaba Yesiran ya tuso ƙeyar su jaruma Nabihat sanye cikin sasari na baƙin ƙarfe, dakaru na take masa baya sun Kunno kai cikin fadar, sai da Yesiran da fursunonin ashirin suka iso izuwa wani dogon tudu,sannan ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa ga sarki, kana ya miƙe tsaye ya juya ya yi wani badakare inkiya ta wutsiyar idanu. Kawai sai badakaren ya tusa ƙeyar jaruma Nabihat izuwa kan wannan gayayyen tudu mai matattakala ta hau ta tsaya kuma ya ɗaure idanuwan ta wani baƙin ƙyalle. Daga can sai wani badakare ya ratso daga cikin dakarun fadar ya fito waje yana taka tafka-tafkan ƙafafuwanshi. Badakaren ya kasance garjejen kato mai ƙirar samudawan farko, yana da manyan damatsa ya tara kwanji, cikinshi runtumeme ne tamkar an kifa ƙwarya, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa zuciyarshi a ƙeƙashe take da tsantsar zalunci. Kai tsaye ya durfafi inda jaruma Nabihat take yana mai zare wata sharbebiyar takobi a cikin kubenta, yana wani irin huci tamkar kububuwa ya ɗaga takobin sama domin ya datse mata wuya. Kafin KAIFIN TAKOBIN ya ratsa wuyan Nabihat Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu kyawawan jarumai biyu mace da namiji da gami da wata yarinya 'yar kimanin shekaru goma sha biyu sun kutso izuwa cikin fadar shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensi rike da miyagun makamai, ba wasu ba ne waɗannan jarumai ba face mafarauci Najwas da uwargidanshi Kilimat tare da yarinya Lazimat. Har dakarun dake fadar sun yunƙura za su afka masu a kacame da azababban yaƙi sai sarki Uhaisu ya daka mssu tsawa su ka ja da baya, cikin matuƙar fushi ya miƙe tsaye zumbur! Daga kan karagar mulkinshi yana mai zare takobinshi gami da kwarara uban ihu, sannan ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye tamkar an harbo shi daga cikin baka, Yana saman ya kaiwa mafarauci Najwas wawan sara da nufin tsinke mashi wuya. Cikin ƙwarewa gami da zafin nama Najwas ya sanya takobinshi ya kare harin, Uhaisu ya dira bisa turba aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro. Koda ganin hakan sai yarinyar Lazimat ta ruga izuwa inda su jaruma Nabihat suke ta sanya takobi ta sare sarƙoƙin da aks ɗaure su. Nan fa Nabihat da sauran 'yan matan su sha tara suka rungume yarinya Lazimat suna masu fashewa da kukan farin ciki. Suna cikin wannan hali ne suka hango shugaba Yesiran da dakarun shi sun ya rugo izuwa kan su, koda ganin hakan sai suka yi wuf suka juya suka fuskance su aka yi karon battar ƙarfe aka kacame da azababban yaƙi. Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin mafarauci Najwas da sarki Uhaisu, su jaruma Nabihat da shugaba Yesiran da dakarun shi. Sai karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne, Najwas da kilimat suka wanzu suna kare hare-haren da Sarki Uhaisu gami da mayar da martani. Wohoho! Haƙiƙa wanda ya iya ya huta, kuma faɗan gwani da gwani daɗin kallo gare shi,in da ace mutum ya na tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan ZARATAN MAYAƘA uku ke kaiwa juna hare hare domin hallaka juna dole ne ya jinjina masu ya kira su da JARUMAN DUNIYA. Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari da arba'in ana wannan fafatawa amma ɗayan su bai samu nasarar yiwa abokin gwamin shi koda kwarzane ba. A zahiri ga wanda yake kallon artabun zai lura sarki Uhaisu ya ninka su jarumi Najwas a ƘARFIN DAMTSE, sai dai su nuna mashi ƙwarewar yaƙi. Al'amarin da ya fusata sarki Uhaisu kenan kuma ya cika da matuƙar mamaki, domin a tarihin jarumtakar shi tai taɓa yin GABA DA GABA da wani jarumi ba face ya kai shi ƙasa, abin tambaya ana shi ne ya aka yi ya kasa samun nasara akan su? Shin wai su waye ma waɗannan jarumai Kuma daga ina su ka fito? Amsar tambayoyin da ya kasa bawa kanshi kenan, kawai sai ya ja da baya sannan ya yi kururuwa ya sa ke afkawa masu yana mai canza salon faɗan shi. Ashe Najwas da Kilimat sun lura da abin da sarki Uhaisu ya yi, don haka su ma sai su ka koyi da shi suka canza salon artabun nasu. Wohoho! Gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya sauya dole ne rawa ta sauya salo. Nan fa yaz' zamana su sarki Uhaisu sun lalata dukkanin makaman yaƙinsu, sun zubar da su aƙas sun shiga amfani da tsagwaron ƘARFIN DAMTSE suna kaiwa juna naushi da bugu hannu da ƙafa. Nan fa labari ya sha bamban domin a yanzu Najwas da kilimat basa iya kare naushin Uhaisu. Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne sarki Uhaisu ya shammace su gabza masu wawan naushi a fuska a lokacin da suka dako tsalle sama, take su kayi saman tamkar an janye su da ƙugiya, sannan su ka rikito ƙasa hancinsu na yoyon jini. A ɓangaren su jaruma Nabihat kuwa ba haka al'amarin yake ba, domin kuwa sun zamewa shugaba Yesiran alaƙaƙai ya rasa yadda zai su da su, duk inda su ka sanya a gaba sai dai kaga MAZAJE na zubewa ƙasa matattu tamakar ana sassabe a gonar auduga. A ɓangaren yarinya Lazimat kuwa, ta zamo tamkar shaiɗaniya a tsakiyar dakarun, ta wanzu tana aika rayukansu barzahu ta hanyar amfani da KWARI DA BAKAnta, Ya zamana cewa duk hare-haren da ake kawo mata tana kare wa, tare da mayar da martani cikin zafin nama na ban al'ajabi, ta wanzu wajen ragargazar dakarun, a cikin wannan hali ne sai ta hango shugaba Yesiran ya rugo izuwa inda take hannunshi riƙe wata zabgegiyar adda mai baki biyu, Koda ganin hakan sai tayi wata katantanwa a tsakiyar dakarun tayi fanka tana mai dukan ƙafafuwansu, a lokaci guda suka zube a ƙasa magashiyan suna aman jini, sannan ta gyara tsayuwar ta tana mai jiran isowar shi, Ya yin da rage saura taku goma tsakanin su sai shugaba Yesiran ya ja ya tsaya aka yi kallon-kallo na wani lokaci. Yesiran ya jijjiga addar dake hannunshi sannan ya duba ɗayan da ya zama dungulmi, take abubuwan da suka faru tsakanin shi da yarinya Lazimat a ƙarƙashin tekun Baharul-sawara, ya dunga dawo masa a cikin kwanyarshi. Daga can sai hawayen baƙin ciki su ka kwaranyo daga idanuwan shi, kawai sai ya taƙarƙare ya kwarara ihu ya afkawa Lazimat da dukkanin ƙarfin shi suka garƙame da masifaffan yaƙi. Lokacin da su mafarauci Najwas suka fahimci cewa wankin hula zai kai su dare, idan aka cigaba da wannan yaƙi a haka za'a iya yin ragas ko ayi kare jini biri jini. Sai su ka zurfafa izuwa cikin kogin tunani domin samun mafita. Koda samun mafitar sai suka ja da baya sannan suka rugo da gudu suka haɗa ƙarfin su waje guda suka gabzawa sarki Uhaisu wawan naushi a fuska da hannayensu biyu, saboda ƙarfin naushin sai da sarki Uhaisu ya tuntsira baya har sau uku ya kife a ƙasa yana aman jini, sannan suka shiga da naushi. Nan fa Uhaisu ya dunga kwarara wawan ihu sakamakon naushin dake ratsa sassan ƙasusuwan jikinshi, fuskarshi duk ta daddauje jini na zuba. A ɓangaren Lazimat da shugaba Yesiran kuwa sun cigaba da kaiwa juna miyagun hare-hare da niyar hallaka juna, Idan Yesiran ya kaiwa Lazimat sara da addarshi, idan ta kare harin sai ta durkushe ƙasa saboda bambancin ƙarfin a bayyane yake, Ana cikin wannan yaƙi ne Yesiran ya shammaci Lazimat ya yanke ta da addarshi a kwiɓin cinyarta ta dama jini ya yi tsartuwa. Lazimat ta ƙwalla ƙara sakamakon zafi da raɗaɗin da ta ji. Sannan ta mayar da martani cikin gwanin ta, nan take ta yanki Yesiran a damtsen cinyarshi ta hagu jini ya kwaranya. Haka su ka cigaba da wannan ɗauki ba daɗi ya zamana cewa sun yiwa junan su rauni fiye da biyar dukkanin su jiri na ɗibar su suka kife a ƙasa magashiyan, ma'ana dai an yi RAGAS tsakanin su A dai-dai wannan lokaci ne Nabihat suka samu nasarar hallaka gaba ɗaya dakarun dake fadar, ya yin da Nabihat ta hango halin da Lazimat ke ciki sai ta ruga izuwa inda take kwance ta ɗauke ta ta goyata a gadon bayanta, sannan ta kama ingarmar doki ta haye 'yan matan fursunonin suka yi koyi da ita, suka sakar masu linzami suka sukwane su a guje suna masu ficewa daga fadar. A dai-dai wannan lokaci ne mafarauci Najwas da matarshi kilimat suka dako wawan tsalle daga kan ruwan cikin sarki Uhaisu suka dira a can gefe, cikin wani irin baƙin zafin nama suka kama dawakai suka haye suka rufawa su Nabihat baya suka fice daga fadar. Lokacin da mafarauci Najwas suka samu nasarar tserar da rayuwar su jaruma Nabihat daga fadar sarki Uhaisu, sai suka wanzu suna ratsa layuka da unguwannin birnin har suka samu nasarar ficewa daga birnin baki ɗaya, suka nausa izuwa cikin daji suna tsala azababban gudu a bisa dawakansu. Tafiyar daƙiƙa arba'in kacal suka yi suka iso wata mararrabar hanya guda biyu a dajin, hanyar ta farko ta gangara ne izuwa wani waje mai ɗauke da kwazazzabai, ta biyun kuwa ta durfafi wata sahara. Ya yin da aka ga waɗannan hanyoyi biyu sai aka ja linzamin dawakai aka tsaya cak! da tafiya, mafarauci Najwas ya buɗi baki ya yi gyaran murya ya dubi jaruma Nabihat cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "ya ku wadannan jarumai yanzu ga shi mun iso mararrabar hanya shin yanzu wacce ya kamata mu bi? Koda jin wannan tambaya sai kowa ya yi shiru aka rasa wanda zai ce kala, sai daga bisani ne jaruma Nabihat ta buɗi baki cikin damuwa ta ce "waccan hanya mai ɗauke da sahara babu alkairi a cikinta, domin ba za mu damu ruwan sha, da 'ya'yan itace da zamu yi kalaci ba. Ita kuwa mai ɗauke da kwazazzabai dole ne a samu halittu masu cutar wa a cikin ta ba, amma dole ita za mu bi''. Koda jin wannan batu daga bakin Nabihat sai kowa ya na'am da hakan, aka sakarwa dawakai linzami aka cigaba da tafiya, ana cikin wannan tafiya ne aka iso wani waje mai tattare da duhuwa a dajin, kwatsam! Sai aka ga ganyayyakin bishiyun motsawa, alamun dake nuni da wani abu mai rai na shirin bayyana. kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin mutane bila-adadin suna fitowa daga duhuwar bishiyun suna masu yiwa su Najwas ƙawanya. Sa'adda su mafarauci Najwas su ka yi arba da mutanen sai suka raza ainun, domin a iya tsawon rayuwar su ba su taɓa ganin dakaru masu kwarjini tamkar su ba. Su dai mutane sun kasance girɗa-girɗa masu ƙirar samudawan farko, suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, fusakunsu a murtuke suke tamkar ba su taɓa dariya ba, hannayensu rike da makamai dangin gatari, majaujawa, al'amudi da takobi. Haƙiƙa waɗannan dakaru sun cika ababan tsoro. Domin ƙaramin jarumi ba zai iya haɗa idanu da su ba face JARUMIN ƘWARAI mai dakakkiyar zuciya, a hankali mayaƙan su ka cigaba da matsowa kusa da su Najwas sai da ya rage saura kamar taku goma sannan su ka ja suka tsaya cak! Sannan suka dare gida biyu suka buɗe wata 'yar siririyar hanya a tsakiyar su, Jim kaɗan sai ga wani garjejen ƙato ya da nunka sauran dakarun girma da kwarjini gami da cika idanu. Idununshi ɗaya a makance yake ya jirkice ya zama fari gaba ɗaya. Ya fito gaban dakarun yana mai tako lafka-lafkan kafafuwanshi. Sannan ya ja ya tsaya cak yana mai ƙarewa su Najwas kallo, kawai sai ya bushe da dariyar mugunta sannan daga bisani kuma ya murtuke fuska tamkar an ai ko mashi da WASIƘAR MUTUWA ya shaƙi iska da manyan ƙofofin hancinshi masu kamar da mazirari ya busar, sannan ya buɗe tafkeken bakinshi mai kama ƙofar gari cikin wata irin kakkausar murya ya ce " shin wane rashin sani ne yasa ku shigowa wannan daji, shin ba ku da labarin cewa nan ce fadar sarkin ɓarayi na wannan nahiya baki ɗaya. Kuma alamu sun nuna cewa ku ba fatake ba ne bakwa ɗauke da wani abu da ya danganci dukiya ko da za a amfana da shi, hakan ya tabbatar min da cewa kenan ɗayan ku ba zai tsira da rayuwarshi ba''. Koda jin wannan batu daga bakin shugaban dakarun sai mafarauci Najwas ya tari numfashinshi yana mai daka mashi tsawa cikin ƙarfin hali ya dube shi ya ce ''shin wane ne kai a jerin JARUMAN DUNIYA da har za ka kira kanka da shugaban 'yan fashin wannan nahiya, ka sani cewa kawar da mu ba abu ne mai sauƙi ba''. Da jin wannan batu daga bakin Najwas sai badakaren ya fusata ainun ya dakawa mashi tsawa wacce ta firgita dukkan wata halitta dake wajen, sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA ya dubi Najwas ya ce "tabɗijan! Wai yanzu a duniyar nan har an samu jarumin da zai tsaya a gaba na yana faɗa min baƙaƙen maganganu, ya kai wannan jarumi tabbas ka sayi ajalinka da kuɗinka, Amma kafin hakan zan sanar da kai ko ni wane ne kamar yadda ka buƙata. Suna na Mazabir ibn Sharr shugaban 'yan fashin wannan nahiya baki ɗaya. Koda gama faɗin hakan sai sadauki Mazabir ya shammaci mafarauci Najwas ya gabza masa wawan naushi a fuska, take Najwas ya sulalo ƙasa daga kan dokinshi yana mai aman jini. Al'amarin da ya harzuƙa zuciyar kilimat da su jaruma Nabihat kenan suka zare makaman su domin su afkawa sadauki Mazabir. Amma sai suka ga Najwas ya daga masu hannu yana mai nuna cewa su dakata. Sannan ya yunƙura ya miƙe tsaye yana gyara tsayuwarshi da riƙon takobin dake hannunshi, sannan ya furzar da gudan jini daga bakinshi ya dubi Mazabir ya ce "ya kai Mazabir ka yi sani cewa ni kaɗai zan iya kashe yaranka baki ɗaya ba tare da ka samu nasarar taɓa lafiyar ɗaya daga cikin 'yan uwana ba''. Koda jin wannan batu daga bakin Najwas sai Mazabir ya bushe da dariyar mugunta ya dubi Najwas a karo na biyu ya ce "dakyau SARKIN SADAUKAI haƙiƙa ka tabbatar min da cewa kai GWARZON NAMIJI ne, to ai ga fili ga mai doki, kuma sai an gwada akan san na ƙwarai''. Koda gama faɗin hakan sai shugaban 'yan fashi Mazabir ya yi wa yaran shi inkiya ta wutsiyar idanu dake nuna cewa kada su kuskura su yaƙi su jaruma Nabihat. Take dakarun suka ja da baya suka buɗe masu wani fili, kamar haɗin baki Najwas da Mazabir suka ruga izuwa kan juna suna ihu da kururuwa mai firgitarwa. Lokacin da ya zamana cewa saura taku goma a tsakanin su nan take Najwas ya zamo ɗan wada a gaban Mazabir, saboda yadda Mazabir ya nunka shi a girma da tsawo. Mazabir ya zare wani al'amudi a jikinshi. Ana haɗuwa aka rincaɓe da masifaffan artabu, suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA ta ban mamaki, sai da aka shafe sa'a ɗaya cur ana wannan fafatawa amma babu nasara ga ZARATAN MAYAKAn biyu. Al'amarin da yayi matuƙar ɗaurewa shugaban 'yan fashi Mazabir kai kenan kuma ya ba shi mamaki, domin fiye da shekaru ashirin suna gudanar da wannan sana'a ta su ta fashi da makami, amma bai taɓa haɗuwa da jarumi mai zafin nama da juriya tamkar Najwas ba. Haƙiƙa yau ya gamu da gamon shi. Sa'adda Mazabir ya zo nan a tunanin shi sai zuciyar shi ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone ta faso ƙirjinshi ta fito waje, sai kawai ya sake zare wani makami a jikinshi mai kama da lauje mai matuƙar tsawo gami da kaifin tsiya ya cigaba da kaiwa Najwas sara da suka ta ko ina. Sa'adda kilimat, Nabihat da sauran fursunonin su ka ga yadda shugaban 'yan fashi Mazabir ke kaiwa Najwas miyagun hare-hare sai hankulan su su ka dugunzuma ainun. An cikin wannan hali ne Mazabir ya shammaci mafarauci Najwas ya danƙara mashi wani sara da wannan makami na shi a cinyarshi ta dama, jini yayi tsartuwa Najwas na ƙwalla ƙara sakamakon zafi zugi da raɗaɗin da ya ji a cinyarshi. Kafin Najwas ya sake wani yunƙuri Mazabir ya sake kafta mashi wani saran a karo na biyu a hannunshi jini ya zuba. Ya yin da Najwas ya ga halin da yake ciki sai ya faɗa izuwa Kogin tunani domin samun mafita. Koda samun mafitar sai kawai aka ga ya daka tsalle sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan ya ya sanya ƙotar takobin shi ya daki kan Mazabir da dukkan ƙarfin shi, saboda ƙarfin dukan sai da Mazabir ya kurma ihu sannan ya runtuma da ƙasa, amma saboda juriya da nacin tsiya sai ya zumbur ya miƙe tsaye. Cikin gwanin ta Najwas ya kama reshen wata bishiya a lokacin da ya yi ƙasa zai faɗi, sannan ya yi sufa yana riƙe da reshen ya durfafo inda Mazabir ya ke ya shammace shi ya sake maka mashi ƙotar takobin a ƙeyarshi Mazabir ya kurma wawan ihu ya faɗi ƙasa da rubda ciki. A dai-dai lokacin da Najwas ya dira a gadon bayanshi ya riƙe hannayenshi ya banƙara su ta baya. Nan fa Mazabir ya shiga ƙoƙarin ƙwacewa daga hannun Najwas amma sai abu ya gagara ya ci-gaba da kurma wawan ihu domin ji yake tamkar najwas zai ɓalla masjid hannaye. Tabbas in da a ce mutum ya na tsaye a wannan waje ya ga irin bajintar da Najwas ya yi dole ne ya jinjina mashi, bisa ganin yadda ya danne garjejen basamuden ƙato ya hana shi rawar gaban hantsi, Ya yin da Mazabir ya ga cewa Najwas yana yunƙurin yanka mashi wuya ta baya da wata 'yar siririyar wuƙa, sai ya buɗi baki cikin matuƙar galabaita ya ce "ina roƙon ka ya kai wannan jarumi da kar ka kashe ni na yarda cewa kai shugaba na ne kuma duk abin da kake so shi za'a yi nayi maka rantsuwa da rayuwa ta. Koda jin wannan batu daga bakin Mazabir sai Najwas ya ce "bazan yarda da abin da ka faɗa ba har sai ka umarci yaranka da su zubar da makamansu. Da jin hakan sai Mazabir ya ɗaga kanshi kaɗan yana daga kwancen a lokacin da idanuwanshi suka kaɗa suka yi jajur tamkar garwashin wuta, cikin kakkausar murya ya dubi yaranshi ya ce "na umarce ku da ku zubar da makamanku''. Koda jin wannan batu daga bakin shugaba Mazabir sai gaba ɗaya 'yan fashin suka ajiye makaman su suka durƙusa a ƙasa bisa gwiwoyin su suna masu yin MUBAYA'A. Ya yin da Najwas ya ga cewa dukkanin 'yan fashin sun miƙa wuya sai ya tashi daga kan gadon bayan Mazabir ya na mai duban kilimat da su Nabihat yana mai yi masu murmushin samun nasara. Da ya ke a wannan lokaci duhun magariba ya fara kawo kai sai Mazabir ya umarci yaranshi suka sanyawa Najwas magani a raunukan sa, da yarinya Lazimat dake cikin mawuyacin hali sakamakon artabun da ta fafata da shugaba Yesiran a can fadar sarki Uhaisu. Duk wani abu da su Najwas suke buƙata 'yan fashin ke kawo masu hatta abin kalaci da taceccen ruwan sha. Shi kuma shugaban 'yan fashi Mazabir sai ya shiga aikin nemo manyan itace aka haɗa su Najwas tafkeken ɗaki domin su shiga ciki su huta, sannan ya rarraba 'yaran a kowacce kusurwa a dajin domin tabbatar da cikakken tsaro, shi kuma sai ya tsaya a ƙofar ɗakin da su Najwas ke ciki ya shiga yin rangadi, hannunshi riƙe da wata sharbebiyar Adda, ɗayan kuwa riƙe da wutar ice domin haskawa. Yana cikin wannan hali ne sai ya hango mafarauci Najwas ya tawo gare shi. Koda ya iso daf da shi sai Mazabir ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa. Najwas ya dube shi a nutse sannan ya yi gyaran murya ya ce "shin wane azzzalumin sarki ne ake kiran shi da suna Uhaisu? Koda jin wannan tambaya daga bakin Najwas sai fuskar Mazabir ta murtuke tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA, ya dubi Najwas ya ce "ya shugabana ai wannan sarki da ka ambata babban abokin gabar mu ne, babu aminci ko yarda tsakanin mu da shi face yaƙi''. Da jin wannan batu sai Najwas ya kwashe labarin da yarinya Lazimat ta ba su, da kuma abin da ya faru da su a fadar sarki Uhaisu lokacin da suka ceto su jaruma Nabihat tun daga farko har ƙarshe ya zayyanewa Mazabir. Sa'adda Mazabir ya ji wannan batu daga bakin Najwas sai ya cika da matuƙar mamaki ya yi ajiyar zuciya ya ce "ya shugabana haƙiƙa ka zo mani da labarin da muka daɗe muna jira, wato hanyar da zamu bi wajen ɗaukar fansa akan sarki Uhaisu. Ya shugabana tun da dai yanzu babban burin ku shine kawar da sarki Uhaisu, tabbas zama bai same mu yanzu zan haɗa dakarun yaƙi domin kai FARMAKIN BAZATO izuwa kurkukun Uhaisu domin mu ceto sauran fursunoni 'yan uwan su Nabihat. Za mu bar yarinya Lazimat da 'yan uwanta biyu su kula da lafiyar ta, sauran dakarun mu za su yi gadin su, ka sani cewa babu abin da zai same ta a wannan daji. Koda kuwa dakarun sarki Uhaisu ne domin akwai iyaka tsakanin mu dasu, haƙiƙa na san duk wata hanya da za mubi wajen shiga kurkukun ba tare da mun sha wata wahala ba, da zarar sun ceto fursunonin, sai kuma mu fara shirin yaƙi domin kuwa dole ne sarki Uhaisu ya kawo mana FARMAKIN BAZATO''. Sa'adda Najwas ya ji wannan batu daga bakin Mazabir sai Najwas ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. Ba tare da wani ɓata lokaci ba Najwas ya juya ya shige izuwa cikin wannan ɗaki na su, shi kuwa Mazabir sai ya ƙwallawa wani badakare kira mai suna Hidairu. Hidairu ya bayyana a gare shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa, Mazabir ya dube shi ya ce "ya kai Hidairu ayi maza a shirya mana dakarun yaƙi mutum dubu biyar domin zamu kai wata mamayar bazato"; Koda jin wannan umarni sai barde Hidairu ya ce "an gama ya shugabana". Yana gama faɗin hakan ya miƙe tsaye zumbur ya ruga izuwa wani ɓangare a dajin, jim kaɗan sai ga shi ya dawo tare da waɗansu ZARATAN MAYAƘA shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu riƙe da miyagun makamai suna zaune a bisa dawakai fusakunsu rufe ruf da hulunan ƙarfe. A dai-dai wannan lokaci ne mafarauci Najwas tare da matarshi Kilimat, jaruma Nabihat da mutum uku daga cikin waɗannan 'yan matan fursunonin shirye cikin shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro suka durfafo wajen. Koda ganin hakan sai wani barde dake tsaye a can gefe guda hannunshi riƙe da takobi, ya janyo wani ingarmar doki ya kawowa su Najwas da Mazabir suka kama suka haye. Cikin hanzari Najwas da Mazabir suka sakarwa dawakansu linzami suka shige gaba, Kilimat, jaruma Nabihat da 'yan mata uku suka mara masu baya dakaru a ƙarshe, aka fara tsala azababban gudu na keta sa'a ana ratsa duhuwar bishiyu gami da ƙoramu da kwazazzabai. Da yake a wannan lokaci dare ya tsala akwai matuƙar duhu, sai wa su daga cikin dakarun suka kunna fitilar ice suka riƙe a hannayensu. Lokacin da aka iso wani waje mai tattare da waɗansu duwatsu 'yan madaidaita sai Mazabir ya ja linzamin dokinshi ya tsaya ya kama ya sakko ƙasa, take kowa ya yi koyi da shi aka tsayar da tafiya. Mazabir ya tsugunna ƙasa ya sanya hannayenshi ya ɗauke waɗansu duwatsu dake wajen ya shiga kwashe ƙasar wajen, jim kaɗan da fara aiwatar da hakan sai ga wata makeken murfi ya bayyana a wajen da aka yi shi da zallar baƙin ƙarfe. Cikin baƙin zafin nama Mazabir ya sanya hannayenshi biyu ya buɗe murfin, sai ga wata matattakala da zata shiga izuwa ƙarƙashin ƙasa, nan fa su Najwas suka cika da matuƙar mamaki maral-musaltuwa. Mazabir ya juya ya dubi Najwas da mutum dubu uku daga cikin yaranshi ya ce "duka za ku ajiye dawakan ku anan mu shiga izuwa wannan ƙofa, sannan ya dubi sauran yaran ya ce "Ku kuma ku tsaya anan ku jira har mu fito daga wannan ƙofa ina jan kunnenku da ku kiyayi saɓawa umarni na. Gama faɗin hakan ke da wuya sai Mazabir ya shiga cikin wannan kofa yana mai taka matattakalar. Najwas, kilimat, 'yan matan uku da dakaru suka mara mashi baya, suna masu kunna kai cikin Kofar, tafiyar daƙiƙa latalin kacal aka yi aka iso ƙarshen matattakalar. Nan take aka yi arba da wata ƙatuwar ƙofa Mazabir ya matsa daf da ita ya ƙwanƙwasa sau biyu. Daga can sai wata 'yar siririyar taga ta buɗe a saman ƙofar wani badakare mai turɓunanniyar fuska ya leƙo da kanshi ya buɗi baki da nufin ya ce wani abu sai Mazabir ya cire hular ƙarfen dake kanshi, Koda badakaren ya yi arba da fuskar Mazabir sai ya sakar mashi wani ƙeƙashasshen murmushi da ya ƙara wa fuskarshi muni cikin wata irin kakkausar murya ya ce mai kama da haushi kare ya ce "barka da zuwa ya shugabana". Badakaren ya mayar da kanshi ciki, jim kaɗan sai aka ji ƙarar zare sakatun kofar, zuwa can sai ta buɗe. Mazabir, Najwas, kilimat, yan mata uku wato Shamirat, Luwaisat, Zulfirat da dakaru dubu uku suka kunna kai izuwa ciki aka cigaba da tafiya, duk inda suka huce sai kaga dakaru na zube kasa suna kwasar gaisuwa ga Mazabir. Nan fa su Najwas suka cika da matuƙar mamaki da al'ajabi, bisa ganin yadda Mazabir ya tsara wannan hanya ta cikin ƙarƙashin ƙasa domin kawai yana shirya hanyar da zai bi wajen ɗaukar fansa akan sarki Uhaisu. Haka dai aka cigaba da wannan tafiya har ya zamana an kawo ƙarshen wannan hanya an tarar da wata ƙofa. Cikin hanzari waɗansu ZARATAN MAYAƘA suka buɗe ƙofar aka fita izuwa waje. Ya yin da aka fito nan take aka tsinci kai a cikin birnin Darul-kashmal, kuma a kayi arba da kurkukun Mautul-shammar. Mazabir ya yi gyaran murya umh! Sannan ya dubi Najwas ya ce "yanzu ga shi mun iso kurkukun Mautul-shammar, ya zama wajibi mu zage damtse wajen yaƙar dakarun kurkukun, mu ceci rayuwar al'ummar su Nabihat, mu koma izuwa sansanin mu domin mu sake sabon shirin yaƙi a gobe. Koda jin wannan batu daga bakin Mazabir sai Najwas ya gyaɗa kai, sannan ya zare wata sharbebiyar takobi daga cikin kuben ta ya durfafi ƙofar kurkukun. Mafarauci Najwas, Kilimat, Nabihat, Shamirat, Luwaisat, Zulfirat da dakaru dubu uku suka yi koyi da shi suka zare makamansu suka rufa mashi baya. Lokacin da ya zamana saura kamar taku goma tsakanin su da kurkukun, su Najwas suka yi arba da dakarun dake tsaron kurkukun sai suka firgice ainun, su dai waɗannan dakarun sun kasance zabga-zabga tamkar samudawan farko, suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, hannayensu ɗauke da waɗansu miyagun makamai, suna ta kai komo tamkar za su ci babu. Mazabir ya ɗaga takobinshi sama yana mai yiwa dakarunshi wata inkiya, kawai sai dakarun suka zaro kibiya suka saka a cikin bakansu suka ja suka ɗame sannan suka harba su izuwa dakarun dake saman ganuwar ƙofar kurkukun. Nan take suka hallaka fiye da rabin dakarun, kuma fitilun dake wajen suka ɗauke, wajen ya yi duhu dunɗum! Ta yadda mutum ba zai iya hango wanda ke nesa da shi ba, a dai-dai wannan lokaci ne su Najwas suka ƙarasa ƙofar kurkukun suka hallaka dakarun ta hanyar yi masu kisan sunƙuru, suka murɗe masu wuya ba tare da dakarun dake cikin kurkukun sun ji ihun su ko wani sautin ƙara ba. Kafin cikar rabin sa'a sun hallaka dakarun sun ɓalle ƙofar kurkukun ta ƙarfin tsiya suka kunna kai ciki. Ya yin da dakarun kurkukun suka yi arba da su Najwas sai suka zare makaman su suna ihu da kururuwa mai firgitarwa suka rugo izuwa kan su. Ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro. Ɓangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance. Ana fara wannan arbu ne dakarun suka fahimci cewa tabbas yau sun haɗu da gamon su, domin su Najwas sun wanzu suna aika rayukansu barzahu babu sassauci. Duk inda Mazabir, Kilimat, Najwas, Nabihat, Zulfirat, Shamirat da Luwaisat suka sanya a gaba sai dai ka ga dakarun na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga. Nan fa sassan jikkunan bil'adama suka dunga shawagi a sararin samaniya suna zubowa ƙasa, jini yana kwarara, feshi gami da tsartuwa tamkar an balle ƙorama. Wohoho! Haƙiƙa MANYAN JARUMAI sune waɗanda suka saba yin KARO DA MAZA komai tsakanin yawan su, kuma su ne waɗanda TSANANI DA UKUBA basa saka su gudu a FAGEN GUMURZU sai dai su yi MUTUWAR JARUMTA. Sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ana wannan ɗauki ba daɗi tsakanin su Mazabir da dakarun kurkukun. Ya zamana cewa su Najwas sun kashe kaso bakwai bisa goma na dakarun, amma su dakarun ba su samu damar kashe ɗaya daga cikin su Nabihat ba sai raunika da suka samu. Duk da cewar dakarun sun firgita da irin mugun kisan da su Nabihat ke yi masu amma sai suka cigaba da kai sara da suka saboda naci da taurin kan tsiya. Koda shugaban 'yan fashi Mazabir ya ga cewa tabbas idan aka cigaba da wannan yaƙi a haka wankin hula zai kai su dare, sai kawai suka ci-gaba da yaƙar dakarun suna masu ƙutsa kai izuwa ɓangare BAUTAR MUTUWA in da aka ajiye jama'ar su Nabihat. A wannan lokaci gaba ɗaya fursunonin kurkukun suna sharar barci ba su san abin da ke faruwa ba. Koda suka jiyo kurkukun ya hautsine sai su ka dunga fitowa daga cikin ɗakunan su. Yayin da suka ga cewa su jaruma Nabihat ne ke yaƙar dakaru, sai suka shiga make dakarun ta hanyar amfani da itace da gudumun da suke amfani da su wajen farfasa duwatsu domin dai taimakon su Nabihat. Da wannan dama su Mazabir suka samu nasarar fito da jama'ar Nabihat. Lokacin da aka zo fitowa sai dakarun Mazabir yi kuri suka saka su a tsakiya su kayi masu ƙawanya domin kada wani abu ya taɓa lafiyar su. Haka dai aka cigaba da wannan yaƙi fursunonin sun taimaki su Nabihat har aka samu isa inda wannan ƙofa, take suka shige izuwa cikin wannan ƙofa tekun mai ɗauke da siririyar hanya ta cikin karkashin kasa. Lokacin da aka fito izuwa inda aka bar sauran dakaru da dawakai, sai Mazabir ya yi umarni aka ɗora jama'ar su Nabihat akan dawakan dakaru aka sake nausawa izuwa cikin daji cikin matuƙar farin ciki maras musaltuwa. Kashe gari tun da duku-dukun safiya su jarumi Najwas suka kammala shiri tsaf A wannan karon dakaru dubu huɗu aka ɗauka sannan aka ƙara samu waɗansu gwarazan 'yan mata mutum shida daga cikin jama'ar su Nabihat da aka ceto suma suka shiga sahun MAYAƘA Wato jaruma AMATULLAH, KHADIJAH, SAFNA, jaruma FATIMAH, Basadaukiya TEEMERH, da KHADIJAH bintu Yahya, Jaruma Nabihat tayi matuƙar mamakin yadda akayi sunayen yan uwannata ya canja zuwa masu daɗi haka. Amma sai ɗaya daga cikin su wacce ta kasance kyakyawa ta gaban kwatance mai suna AMATULLAH ta bayyana mata cewa Sunayen nasu sun sauya ne sakamakon sun karɓi addinin Musulunci a hannun wani fursuna da ake yiwa laƙabi da sheik ABDULLAH IBN ZAID. Bisa wannan dalili ne ya sanya sunayen na su suka canja. Tun a daren jiya jaruma Nabihat da gaba ɗaya fursunonin jama'arta har Mazabir da dakarunshi suka ƙarbi addinin Musulunci suka bayar da gaskiya da Ubangijin talikai. A wannan lokaci inda ace mutum zai ga irin shigar da jaruma Nabihat da sauran 'yan matan su kayi dole abin ya burge shi gwanin ban sha'awa. Shigar fararen tufafi na sulken ƙarfe su kayi tun daga ƙasa har sama, sun rufe fusakunsu da koren rawani, idanuwansu kaɗai ake gani, hatta dawakan da suka hau ingarmu ne farare sol! Ita kam yarinya Lazimat shiga tayi cikin ayarin ta na rataye da kwari da bakanta. Bayan an kammala yin kalaci sai aka ɗauki hanya aka durfafi zuwa birnin Darul-kashmal qka wanzu ana ratsa duhuwar bishiyu da kwazazzabai haɗe da sarƙaƙiya a bisa dawakai cikin matsanancin gudu na keta sa'a, tafiyar sa'a ɗaya kacal aka yi aka iso ƙofar birnin. Tamkar sarki Uhaisu jira yake su iso tuni ya gama shirin yaƙi tsaf. Koda tsayuwar su jaruma Nabihat a wajen sai aka ga Ƙofar birnin ta buɗe sai ga dakaru na tuttuɗowa wasu a bisa dawakai, giwaye, raƙuma wasu a ƙafa. Tsamanin yawan su ya huce misali, duk inda mutum ya kalla makaman yaƙinsu ne birjik. Bayan dakarun sun yi sahu-sahu a filin daga. Sai aka hango sarki Uhaisu ya saki linzamin dokinshi ya durfafo inda suke, yana sanye cikin gagarumar shigar yaƙi ta baƙin sulke mai matuƙar kwarjini da ban tsoro tamkar wani ifritu. A gefen hannunshi na hagu kuwa shugaba Yesiran ne shirye cikin gagarumar shigar yaƙi, a dama kuwa yarima Shaiban ne cikin shigar yaƙi. Lokacin da ya zamana cewa tazarar da ke tsakanin su bata huce taku goma sha biyu ba sai kowa ya ja linzamin dokinshi ya tsaya cak! Aka shiga yin kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu, Sa'adda shugaba Yesiran ya yi arba da yarinya Lazimat sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone ya na mai duban dungulmi hannunshi ɗaya da ta sake mashi . Shi kuwa yarima Shaiban ya shagaltu da kallon kyakkyawar surar jaruma Nabihat, tsakanin ƙaunar ta na ƙara ruruwa a zuciyarshi, har sai da Nabihat ta galla mashi harara sannan ya kawar da kanshi. Sarki Uhaisu da shugaban 'yan fashi Mazabir da Najwas haɗe da kilimat kuwa, wani irin kallo su ke wa junan su mai cike da matuƙar ƙiyayyar da mugun tanadi. Sarki Uhaisu ya ce a cikin zuciyarshi "ya aka yi sadauki Mazabir ya haɗa kai da abokan gaba ta? Shin dama har yanzu mazabir na raye bai mutu ba? Lallai babu tantama shi ne ya jagoranci rundunar mayaƙa a daren jiya suka ce ci rayuwar jama'ar su Nabihat Sa'adda Sarki Uhaisu ya zo nan a tunanin shi sai takaici gami da baƙin ciki suka turnuƙe zuciyarshi. Daga can ne sai sarki Uhaisu ya zare takobinshi ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu sannan ya ruga izuwa kan su Najwas. Koda ganin hakan sai Najwas da Mazabir suka sakarwa dawakansu linzami suka yunƙura kan shi. Shugaba Yesiran ya durfafi yarinya Lazimat, ana haɗuwa sai aka ruguntsume da azababban yaƙi suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA. Sa'adda dakarun ɓangarorin biyu suka ga cewa shuwagabannin su sun kacame da yaƙi, sai kowanne su ya yi kukan kura ya afkawa abokin gabar shi aka yamutse da masifaffan yaƙi. Koda ganin hakan sai jaruma AMATULLAH, KHADIJAH bintu Muhammad, SAFNA, jaruma FATIMAH bintu Yahya da Basadaukiya TEEMERH suka ƙwala kabbara da ƙarfi suka zare takubbansu suka kutsa izuwa cikin dakarun kafirai aka cigaba da artabu. Wohoho! Haƙiƙa wannan rana ƙasa ta jiƙu da jinin bil'adam, kaico! Tabbas yaƙi abin tashin hankali da ban tsoro wanda bai san shi ba shi ne yake fatan zuwan shi Duk inda su jaruma SAFNA suka sa a gaba sai dai ka ga dakarun arna na zubewa ƙasa matattu. Wani sadauki mai ƙarfi na Allah ya isa ya kaiwa jaruma AMATULLAH wani wawan sara da takobin shi, cikin baƙin zafin nama AMATULLAH ta sunkuiya takobin sadaukin ta sari iska, Kafin ya sake dawo da martani AMATULLAH ta kafta mashi wani sara a wuya take ta tsinke jijiyar wuyanshi ya faɗi ƙasa yana shure-shuren mutuwa. Jaruma FATIMAH kuwa ta zamto tamkar shaiɗaniya a tsakanin mayaƙan sarki Uhaisu, Khadijat kuwa da ƙarfin damtsen ta take ragargazar dakarun babu sassauci. A ɓangaren yarinya Lazimat da shugaba Yesiran kuwa sun wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin JURIYA DA BAJINTA gami da baƙin zafin nama tamkar za su cinye junan su. A ɓangaren manyan GWARAZAN SADAUKAI, sarki Uhaisu, Mafarauci Najwas da shugaban 'yan fashi Mazabir kuwa. Tuni labarin ya sha banbam, domin kuwa sai da suka lalata gaba ɗaya makaman yaƙinsu suka yi jifa da su suka dira ƙasa daga kan dawakansu bisa turba suka shiga kaiwa juna naushi da bugu cikin juriya da nacin tsiya. Nan fa ya zamana cewa idan Najwas da Mazabir suka nushi Sarki Uhaisu sai su ji tamakar buhun hatsi suka daka domin ko gezau ba ya yi sai ƙura ce kawai ke tashi. Idan kuwa Sarki Uhaisu ne ya naushi ɗaya daga cikin su sai kaga ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan ya faɗo kasa tim! Nan fa yazamana cewa Uhaisu ya tara masu jini kuma ba sa iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kai, sa'adda su Najwas suka fahimci halin da suke ciki sai kawai su shiga neman Ubangijin musulunci a cikin zukatansu, ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai suka fara samun nasara akan Uhaisu ya zamana cewa suna haɗa ƙarfin su waje guda su gabza mashi naushi. Kafin cikar rabin sa'a sunyi mashi jina-jina ya zamana cewa ya faɗi ƙasa daƙyar yake numfashi yana kakarin mutuwa. Kawai sai Mazabir ya yi wuf ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a jikin wani badakare ya datse wuyan Sarki Uhaisu. Kaico! Inda a ce mutum ya na wannan waje lokacin da Sarki Uhaisu ya yi irin wannan mutuwar ta wulakanci dole ne ya yi farin ciki ya yiwa Allah godiya bisa ganin mutuwar AZZALUMI. A dai-dai lokacin ne yarinya Lazimat ta samu nasarar hallaka shugaba Yesiran ta hanyar soka mashi kibiya a kan ƙahon zuciyarshi ya yi mutuwar banza. Sa'adda dakarun marigayi Uhaisu suka yi arba da gawar jagoran su sai suka zubar da makamansu suka miƙa wuya. A wannan rana aka shiga izuwa birnin Darul-kashmal aka musuluntar da gaba ɗaya jama'ar birnin, aka fito da dukkan fursunonin dake kurkukun, aka karya gumaka da ababan bauta. Tsawon kwani uku aka shafe kowa ya yi jinyar raunin dake jikinshi. Sannan aka ɗora yarima Shaiban abisa karagar mulki, bayan an ɗaura auren shi da da Jaruma Nabihat da Jaruma Zulfirat. Najwas kuwa ya zamo angon 'yan mata uku wato Khadijah, Luwaisat da Shamirat, kuma yazamo waziri ga yarima Shaiban. Mafarauci Najwas kuwa ya zamo shugaban majalisar dokokin birnin Darul-kashmal. Sheikh ABDULLAH IBN zayyad yazamo jagoran harkar addinin musulunci da amsa fatawa na birnin. Yarinya Lazimat kuwa ta zamo wacce zata gaji sarkin yaƙin birnin wato shugaba Yesiran. Tun daga wannan rana aka kawo ƙarshen FATAUCIN BAYI a nahiyar baki ɗaya addinin Musulunci ya mamaye ko ina, sarakunan dake nahiyar da kansu suke zuwa su miƙa wuya su karɓi addinin Musulunci, saboda mulkin adalci da yarima Shaiban ke gudanarwa saboda HASKEN MUSULMI. Ƙarshe ALHAMDULLILAHI A nan na kawo ƙarshen wannan ƙasaitaccen littafi nawa mai taken FATAUCIN BAYI. Ubangiji ya haɗa mu cikin laɗan, ya yafe mana kusakuren da muka yi. Zaku iya samun litattafan mu a yanar gizo (Google) idan kuka rubuta SUFINOVELS.COM Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels