Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels 01/07/2019 à 15:27 - Les messages envoyés dans cette discussion et les appels sont désormais protégés avec le chiffrement de bout en bout. Appuyez pour plus d'informations. 01/07/2019 à 15:27 - Cette discussion est entre vous et un compte professionnel. Appuyez pour plus d'informations. 21/07/2019 à 11:47 - Cette discussion est entre vous et un compte professionnel. Appuyez pour plus d'informations. 05/08/2019 à 12:54 - Cette discussion est entre vous et un compte professionnel. Appuyez pour plus d'informations. 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHEEM* *DUKKAN GODIYA DA YABO SUN TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DA YA BANI IKON DAWOWA CIKIN WANI SABON LITTAFIN, TSIRA DA AMINCI SU K'ARA TABBATA GA ANNIBINMU FARKON K'AGA K'ARSHEN AIKA WATO ANNABI MUHAMMDU S.A.W*. *WANNAN LABARIN K'IRK'IRARRAN LABARINE BANYISHI DAN WATA KO WANI BA, DAN HAKA A KIYAYE JUYA MIN LABARI TA KO WANI IRIN SIGA* ```WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA CE GAREKU MASOYAN K'WARAI, FAUZIYYA MUHAMMAD WAKILI, SHAFA'ATU BALA BABA, AISHA NICHOI, MAMAN LABYB MAMIENMU, ADAMA TANIMU A BIYE, HAK'IK'I KUNA NUNAWA RAHEENAT SOYAYYA, DAN HAKA LITTAFIN NAKU NE.``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 1 Tafe suke a mota sai rusan kuka takeyi kamar wanda aka ce mata mahaifiyarta ta mutu, yanda na lura da kukan nata harda na shagwab'a ma, shi ko duk da kasancewar yana jin kukan nata har k'asan ransa bai saka ya daina tuk'in nasa ba ko kuma yayi yunk'urin rarrashinta, dan abinda ya sakata kukan shi nashi b'angaren farin ciki ya saka shi. Jin kukan nata bana k'are bane yasa ya taka wani mahaukacin birki wanda sai da *Meenat* wanda take kuka ta hantsila sannan ta dawo ta zauna a mazauninta, take kuma kukan da take ya tsaya cak ta zaro manyan idanunta waje saboda tsananin tsoro. Ganin yanda ta firgita yasa *Al'ameen* fashewa da dariya yace "ya kika bar kukan kuma, ai da kin ci gaba da kukanki tinda Abbie ne ya mutu. " Wani kukan ta fashe dashi tana kai masa bugu, shi ko me zaiyi in ba dariya ba, dariya yakeyi yana fad'in "dukeni *Meenat* indai zai saka kiji sanyi a ranki. " Sai da taji hannunta ya fara zafi sannan tabar dukanshi tare da jingina kanta a kafad'arsa tana sakin ajiyar zuciya, a hankali ta bud'e baki tace "yah *Al'ameen* wai baka tausayi na ne.?" Ajiyar zuciya ya sauke ya d'ago da kanta ya kalli cikin idanunta sannan yace " *Meenat* me yasa zanji tausayinki bayan kina kuka ne akan abinda ya kamata kiyi farin ciki. " *Meenat* tace "farin ciki?!! Farin ciki fa kake cewa inyi yah *Al'ameen*, ta yaya zanyi farin ciki bayan wanda nake so ya bar ni, wanda nake so ne fa aka rabamu dashi, shine kake cewa nayi farin ciki, shine kake cewa kar nayi kuka.?" Murmushi *Al'ameen* yayi yace "to gani nayi fa mahaifiyarshi ce tace bata sonshi dake, k'iri-k'iri ta nuna miki k'iyayya, to dan yanzu ya kiraki yace an saka masa ranar aure da y'ar uwarsa sai ya zama abin kuka ? Ni zatona kuka ba naki bane, saboda ko aurensa kikayi ba zakiyi farin ciki ba, ni wallahi murna ma nayi miki, gara yaje can ya auri 'yar uwarsan, uwarsa kuwa taje ta bak'in halinta badai k'anwata ba. " Shagwab'e fuska *Meenat* tayi tace "to amma ai shi yana sona ni ma ina sonsa." Cike da jin haushi *Al'ameen* ya tayar da motan yana fad'in "to ai sai kije ki auresa, kuma wallahi kika k'ara cika min kunni da kukanki sai na tsayar da motar a ajiyeki sai dai ki nemi taxi ya k'araso dake gida. " Turo baki tayi gaba cike da shagab'a tace "yah *Al'ameen* kai baka san soyayya bane shi yasa. " *Al'ameen* bai san sanda ya k'ara taka wani Burkina ba ya kalleta yace "bansan soyayya ba kika ce *Meenat*,? To kallo ni nan. " Kamar yanda yace aiko ta d'ago ta zuba masa ido shima d'in kuma ita yake kallo, cikin wata irin murya yace "me kika gani cikin idanuna.?" Kau da kanta gefe tayi saboda irin tasirin da idanunsa yakeyi mata ajiki a duk lokacin da ta kallesa tace "ni ban ga komai ba. " Murmushi yayi ya tayar da motar yana fad'in "k'arya kike wallahi" Tab'e baki tayi tace "to ai kai idanun naka ko yaushe a haka suke, mutum ba zai iya kallonsu na mintuna biyu ba ma saboda tsaban kwarjininsu. " "Ashe dai ki ce gwarjinin sukayi miki kika kasa ka gano abinda suke cikinsu. " *Meenat* tace "ni dan Allah k'aleni naji da abinda yake damuna. " Murmushi *Al'ameen* yayi ba tare da ya k'ara cewa komai ba ya ci gaba da tuk'insa. Kaitsaye unguwar nasara g.r.a suka nufa, daidai k'ofar wani tamfatsetsen gida naga yayi horn, me gadi ne ya lek'o ganin motar *Al'ameen* ne yasa ya koma ya bud'e masa da sauri shi kuma ya danna hancin motar nasa cikin gidan. Suna shiga ko parking bai gama yi ba *Meenat* ta bud'e ta fice da gudu tayi cikin gidan ko tsaya ta d'auki kayan siyayyar da suka siyo ba tayi ba, girgiza kai *Al'ameen* yayi ya bita da kallo sannan ya k'arasa gyara parking ya d'auki ledan kayan shima ya fito ya nufi cikin gida. Da sallama ya shiga falon gidan, *Ummi* da take zaune a falon ne ta amsa masa sallamar tana fad'in "d'ana har kun dawo. ?" Zama yayi saman kujera yana fad'in "eh mun dawo *Ummi*. " "To sannunku da dawowa, amma me ya sami mutuniyar taka ne naga ta zo ta wuce ranta a b'ace ina mata magana amma ko ta kulani. ?" Murmushi *Al'ameen* yayi yace "hmmm *Ummi* kinsan halin rigimar *Meenat* sarai dai, kawai muna kan hanyar dawowa ne *Salis* ya kirata yake fad'a mata an saka ranar aurensa da 'yar uwarsa nan da sati biyu shine fa ta d'aga hankalinta take tayi min kuka. " Tsaki *Ummi* tayi tace "au akan hakan ne take wannan kumburin, ni ai gara hakan ma, dama ni ba sonta dashi nakeyi ba, dan ko ta auresa mahaifiyarsa ba zata barsu suyi farin ciki ba tunda bata sonta. " *Al'ameen* yace "nima haka na fad'a mata, amma ita so ya rufe mata ido." "Allah ya kyauta" cewar *Ummi* Ameen *Al'ameen* yace yana mik'ewa, sannan yace " *Ummi* ga kayan nan ki bata ni zan shiga gida, sai zuwa anjuma zan dawo na k'ara rarrashinta domin nasan yanzu ba zata saurareni ba. " Murmushi *Ummi* tayi tace "da kanta ma zata biyoka na sani, domin shak'uwarku da juna ya wuce misali, ka gaida min da Ummar taka in ka shiga gidan. " Murmushi shima yayi ya nufi hanyar fita yana fad'in "zata ji *Ummi*. " ************* *Al'ameen* yana fitowa gidan dake manne dana su *Meenat* na ga ya shiga, gidan bashi da banbanci dana su *Meenat* hatta da fenti kuwa, tagwayen gida kenan wanda mamallakanta suma suka kasance tagwaye. Da sallama ya shiga k'ayatatcen falon wanda bashi da banbanci dana gidansu *Meenat*, komai na falon irin d'aya ne da wancen, in ka shiga wancen gidan ka dawo ka shiga wannan ba zaka banbaceau ba, cewa zakayi gida d'aya ka shiga. *Umma* ce da take fitowa daga kitchen ta amsa masa sallamar tana fad'in "ina ka bar min d'iyar tawa ne. ?" Fad'awa *Al'ameen* yayi saman kujera yana fad'in "d'iyarki ko y'ar rigima, tana can tana kukan an sakawa *Salis* ranar aure. " Ajiye abincin hannunta Umma tayi a saman dining sannan tace "ni bansan maitan me *Meenat* takeyi ba akan wannan yaron, inda aka ce ba'a sonka to meye na tusa kai.?" Tab'e baki *Al'ameen* yayi yace "ohon mata." Cikie da jimami Umma tace "amma saboda Allah tana kuka shine ka tawo ka barta ba ka tsaya ka rarrasheta ba. ?" Mik'ewa yayi tsaye yace "Umma kin sani sarai bana son damuwar *Meenat* bare har naga hawayenta, amma a wannan gab'ar ba zan iya rarrashinta ba, saboda ni banga abin da zai sa ta d'aga hankalinta ba, in ta hak'ura da kanta zata tawo nemana, bari naje nayi wanka na d'an kwanta na huta *Umma*. " Yana gama fad'in hakan ya nufi hanyar d'akinsa. Da kallo Umma ta bishi tana fad'i afili "ni har yanzu na kasa gane wani irin so yaran nan sukeyiwa junansu, in kayi zargin soyayya tsakaninsu sai su zo su kifar da kai ka kasa gane komai kuma. " Ta dad'e a tsaye tana sak'e-sak'e kafin tace "Allah ya kyauta." Ta nufi kitchen tana me ci gaba da aikinta. ********** *Al'ameen* yana shiga d'aki toilet ya fad'a ya shek'o wanka abinsa, yana fitowa gaban dressing mirror ya nufa yayi shafe-shafensa sannan ya nufi closet d'insa ya bud'a ya d'auko wani wando three quarter da wata riga singlet ya sanya, yana kammala ya koma gaban mirror ya fashe jikinsa da turaruka sannan ya d'auki computer d'insa da take saman wani d'an k'aramin tebur ya haye gado. Yana bud'e computer d'in hoton *Meenat* ce ya bayyana saman screen d'in computern tana dariya, shima bai san lokacin daya saki murmushi ba ya kai hannu ya shafi fuskarta yace "I love you so much my *Meenat*" tayi kyau sosai cikin hoton, sanye take da k'ananun kaya riga da wando kanta babu d'ankwali k'ananun kitson kanta sun zubo saman kafad'unta, daga ganin hoton an d'aukesa ne cikin yanayin farin ciki. Ya jima yana kallon hoton kafin ya shiga ya fara abinda zaiyi... Muje zuwa🥰 More comment more typing *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ _WAYYO DAD'I KARKA KASHENI😄 BARNI DA RAINA NA CI GABA DA GANIN COMMENT D'IN MASOYANA😂, HAK'IK'A NI RAHEENAT YAU NA GA RUWAN COMMENT TARE DA ADDU'OINKU READER'S, KUMA HAKAN BA K'ARAMIN DAD'I YAYI MIN BA WALLAHI, INA SONKU MASOYANA, KU CI GABA DA SAMBAD'O COMMENT NI KUMA NAYI ALK'AWARIN SAMB'A MUKU TYPING AKAI AKAI🥰😁_ SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB* *(MAMIEN MU)* *FAUZIYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 2 Yana cikin aikinsa a computer yaji a turo k'ofar d'akin an shiga da sallama, d'ago kai yayi ya zuba mata ido yana kallo, sanye take cikin wasu riga da wando yar kanti, rigar har gwiwa take yayin da wandon ya kasance fencil ne, wandon fari ne k'ar yayin da rigar kuma pink colour ne mai adon fari, wani siririn gyale ne ta rataya akanta fari, tayi kyau sosai cikin katan yayin da fuskarta tayi fayau kasancewar babu komai cikinta, ma'ana ba tayi makeup ba. Takowa ta farayi a hankali gurin gadon tana turo baki gaba alamar shagwab'a, shiko *Al'ameen* har lokacin idanunsa na kanta, zama taje tayi gefensa ba tare da tace dashi komai ba. Ajiyar zuciya ya sauke yace "my *Meena* fushi kikeyi da yayan naki.?" D'ago manyan idonta tayi ta watsa masa su ba tare da tayi magana ba, rufe computern yayi ya juyo sosai ya fuskanceta cikin taushin murya yace " *Meenat* shirunki na iya tarwatsa zuciyar *Al'ameen*, dan Allah kice wani abu. " Hawaye ne suka fara zuba mata, cikin wani irin rud'ewa wanda ni raheenat yayi matuk'ar bani mamaki naga *Al'ameen* ya kai hannu yana share mata hawayen yana fad'in "dan Allah kibar zubar min da wad'annan tsadaddun hawayen, kin kuwa san zubar hawayenki kamar zubar ruwan dalma ne a zuciyata, daina kuka my meenat fad'a min damuwarki. " Cikin muryar kuka tace "kar ka rink'ayi kamar baka san komai ba mana yah *Al'ameen*, me yasa ne kuka kasa fahimtar irin rad'ad'in da na keji a zuciyata ce ? Yah *Al'ameen* ina son *Salis* amma an rabamu da k'arfi da yaji, ku kuma kun kasa fahimtar halin da zuciyata take ciki, dan dama ba sona kukeyi dashi ba, ya kuke so nayi yah *Al'ameen*, me yasa aka kasa samun wanda zai taushi zuciyata cikinku ? Har dakai ma yayah wanda nake ganin in kowa ba zai fahimceni ba kai zaka fahimceni." Hannunta *Al'ameen* ya kamo ya rik'e yana kallon cikin idanta yace "yanzu na fahimceki *Meenat*, ina so ki sakawa zuciyarki hak'uri dan Allah, ki sani komai da kika ga ya faru da sanin Allah, in *Salis* mijinki ne wallahi komai rintsi sai kin aureshi, ko kin manta babu mai auren matar wani ne ?, to da wannan nake son ki ajiye komai gefe ki rungumi k'addara, in Allah yayi da aure tsakaninki da *Salis* kina zaman zamanki zaki ga ya dawo gareki, in kuma babu aure tsakaninki dashi sai kiga ya fito miki da wani zarkad'ed'an saurayin kamar yayanki, ko bakya son miji irina.?" Ya k'arasa maganar da sigar zolaya. Murmushi ta saki tare da kai masa bugun wasa tace "kai!!! Yayah ai kai mijin manyan mata ne ba irina y'an sakayau ba. " Ta k'arasa maganar da dariya. Had'e fuska *Al'ameen* yayi yana hararanta, saurin gintse dariyarta tayi tana fad'in "sorry yayah." Murd'a kunninta yayi yace "nak'i sorryn." "Wayyo kunnina, yayah da zafi fa. " Murmushi yayi yace "ai nasan da zafin nayi miki, ke in kika samu miji kamata ma ai kin more, amma saboda kin rainani sai ki rink'a fad'a min duk abinda yazo bakinki. " Turo baki tayi gaba cikin shagwab'a tace "wallahi da gaske nakeyi yayah kayi min girma, kalleni fa. " Ta mik'e tana juya jikinta a gabansa cikin sangarta da tab'ara, dan bana ce yarinta ba, wai ita a dole ya kalleta ya gani. Shi ko *Al'ameen* gaba d'aya ya shagalta gurin kallonta, zuciyarsa na k'ara narkuwa cikin soyayyarta wanda ita ta kasa gane hakan. Rintse idonsa yayi yana ya mutsa gashin kansa cikin wani irin yanayi, har *Meenat* tazo ta zauna kusa dashi bai sani ba, muryarta yaji kawai tana cewa "yah *Al'ameen* lafiya.?" Bud'e idonsa yayi ya kalleta yace "ina sonki my meenat. " Murmushi tayi tace "nima ina sonka yayana. " Wani irin murmushi yayi tare da lumshe idanunsa, ita kuwa *Meenat* ko ajikinta saboda ba yau ne suka saba irin wannan ba, tun tana yarinya take jin kalmar so daga bakin *Al'ameen*, kuma a kullum in ya fad'a mata ba ta d'aukarsa da wani abu face soyayyar jini d'aya. _Niko nace kinyi kuskuren fahimta Ameenatu😄_ *Meenat* ce tace "yah *Al'ameen* bani wayarka na buga game d'in nan..." Murmushi yayi yana yi mata nuni da wayar nashi dake kan seat-drower da hannunsa. Mik'ewa tayi ta d'auko ta dawo ta zauna ta fara buga game d'in cike da nishad'i. Shiko Al'ameen kallonta yayi a ransa yace "Meenat kenan, yanzu har ta manta da damuwarta. " Girgiza kai yayi yana murmushi ya janyo computer d'insa ya ci gaba da aikinsa yanayi yana kallon Meenat lokaci zuwa lokaci wacce ta mayar da hankalinta kacokan kan game d'in da take bugawa. Kiran sallar magriba ne yasa *Meenat* ajiye wayar ta mik'e ta kalli *Al'ameen* tace "yayah ga wayarka nan ni zanje nayi sallah. " Shima mik'ewan yayi ya nufi hanyar toilet yana fad'in "ajiyeshi inda kika d'auka nima alola zanyi na wuce masallaci. " Ajiyewa tayi kamar yanda yace sannan ta fice daga d'akin. Tana fitowa suka ci karo da *Abba* wanda ya fito zaije masallaci, gaisheshi *Meenat* tayi tare dayi masa sannu da zuwa dan tasan bai jima da dawowa ba, amsa mata yayi cikin sakin fuska yana fad'in "maza kije kiyi sallah *Meenat* ni na tafi masallaci gashi can za'a tayar. " To tace ta nufi d'akin *Umma* shi kuma *Abba* ya fice da d'an saurinsa. Kan sallaya ta taras da *Umma* ta tayar da sallah, dan haka itama sai ta nufi toilet ta d'auro alolan tazo ta saka hijjabin *Umma* ta kabbara nata sallar. Sunanan zaune suna lazimi aka kira isha'i, nan suka mik'e suka kawo nasu, sai da sukayi shafa'i da wutiri tare da addu'oi sannan suka mik'e suka fito zuwa dining. Zaune suka samu *Al'ameen* a dining d'in yana danne-dannan wayarsa, ganinsu ne yasa ya ajiye wayar yace "sannu da fitowa *Umma* " Jan kujera tayi ta zauna sannan tace "yauwa sannu *Al'ameen,* ina ka baro Abban naka da sauran 'yan uwanka.?" Ya bud'e baki zaiyi magana kenan sai suka jiyo sallamar Abban da Usman da Aliyu k'anninsa. Amsa musu sallamar sukayi sannan suka k'araso suka zazzauna suma. Meenat ce ta fara saving d'insu d'aya bayan d'aya tana turawa kowa gabanshi, sai da ta kammala sannan ta zuba nata ta zauna ta fara ci itama. ******* Suna kammala cin abincin *Meenat* ta mik'e tace "Abba Umma ni na tafi saida safenku. " Kallonta sukayi da murmushi a fuskarsu Umma ce tace "mu kwana lafiya Meenat. " Abba ma dai cewa yayi "sai da safe yar gidan Abbinta. " Murmushi tayi ta kalli su Usman tace "yah Usman yah Aliyu mu kwana lafiyanku. " Tana gama fad'in hakan ta nufi hanyar k'ofa. Had'a baki sukayi gurin cewa "Allah ya tashe mu lafiya Meenat." Al'ameen ne ya mik'e yabi bayanta yana cewa "wato ni ba za kiyi min sai da safen ba kenan.?" D'an d'aga murya tayi tace "to ai nasan kai d'an rakiya nane. " Da sauri ya taka ya bita yana cewa "tsaya ki fad'a min waye d'an rakiyar naki. " Tana jinsa a bayanta ta kwasa a guje ya rufa mata baya, su kuwa su Abba da kallo suka bisu sunayi musu dariya... Muje zuwa🥰 Ga mai k'orafi ko wani gyara yayi min magana ta wanann layin👇 07033643262 A shirye nake da amsar gyaranku ko k'orafinku readers🥰😘 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 3 Da gudun tare da sallama a bakinsu suka shiga falon su Meenat, Abby da Ummi da sauran y'an uwan Meenat da suke zaune suna hira ne suka bisu da kallo, domin hakan ba bak'on abu bane a gurin su, Abba ne ya fara magana yace "Al'ameen sai yaushe zaka girma kabar wasan yara da k'anwar naka ne wai.?" Murmushi Ummi tayi tace "hmmm ai banga wannan ranar ba kuwa, dan kullum k'ara girma yakeyi amma yana biyewa Meenat suna shirme. " Murmushi *Al'ameen* yayi yana sosa kansa cikin jin nauyi ya nemi guri ya zauna yace "Ummi ita ce fa ta kirani da d'an rakiya. " Girgiza kai Ummi tayi tace "shine kai kuma ka biyota a guje ko. ?" Dariya yayi yace "a'a Ummi ita ce dai ta fara gudu." Abba ya amshe da cewa "kai kuma sai ka biye mata ko.?" Dariya k'annin Meenat suka kwashe dashi, shi kuma Al'ameen ya had'e gira irin ba wasa d'in nan yace "ina wasa daku ne.?" Aiko nan take suka gintse dariyarsu suna zare idanu, domin sun san yah Al'ameen babu wasa yanzu zai masge yaro, dan shi iya wasansa da shiriritarsa akan Meenat ce kad'ai, sauran k'anninsa kuwa tsoronsa su keji sosai. Abba da Ummi ne suka mik'e suka shige ciki, nan suma su Isma'il suka mik'e suka nufi d'akunansu aka bar Meenat da Al'ameen zaune su kad'ai, kusa dashi Meenat ta koma ta zauna suka ci gaba da hirarsu har zuwa k'arfe 10:00pm, Al'ameen ne ya mik'e yana hamma yace "ni zan shiga gida na kwanta. " Itama Meenat mik'ewar tayi tace "ok, muje na rakaka dan nima baccin nake ji. " Baice komai ba sai nufar k'ofa da yayi ta mara masa baya, daidai get taja ta tsaya tace "to sai da safenmu yayah. " Kallonta yayi yace "mu kwana lafiya k'anwata, gobe ki shirya da wuri karki saka nayi latti gurin aiki. " Meenat tace "to yayah. " Hannunta ya kamo ya sumbata yace "kiyi mafarkina bye. " Murmushi tayi ta juya ta fara tafiya, har ta d'anyi nisa taji Al'ameen yace "Meenat!!" Juyowa tayi tana kallonsa ba tare da tayi magana ba, shima kallontan yakeyi yace "dama cewa zanyi karki manta da addu'a. " Wani murmushi ta sakin masa tace "insha Allah ba zan manta ba yayah. " Tana gama fad'in hakan ta juya ta ci gaba da tafiya, sai da Al'ameen ya ga shigarta cikin gidan sannan ya fice daga gidan ya nufi nasu gidan. ************* Washe gari misalin k'arfe bakwai da mintuna arba'in na safe Al'ameen ne ya fito cikin shirinshi na tafiya aiki, sallama yayi wa Umma wacce ke zaune a falo tana kallon sunna tv tayi masa addu'ar tsarewa dana dawowa lafiya sannan ya fice daga gidan. Yana fitowa gidansu Meenat ya shige, da sallama ya shiga falon, Meenat ce ta amsa masa wacce take zaune saman dining tana break, k'arasawa yayi dining d'in yana fad'in "ke sai yanzu ne kike naki break d'in. ?" Mik'ewa tayi tare da d'aukar jakarta dake saman dining d'in tace "ai nama gama muje kawai. " "Ok, ina Ummi take.?" "Ummi ba ta dad'e da hawa uptsar ba." Be k'ara magana ba sai hanyar fita da ya nufa tabi bayansa. Gurin motarsa da ya ajiye jiya ya nufa ya bud'e ya shiga, itama Meenat bud'ewa tayi ta shiga ta zauna, sai da ya tayar da motar nasa yayi ribas ya nufi get sannan Meeenat tace "good morning yah Al'ameen." Kallonta yayi yace "morning how are you. ?" "Am verry fine yayana. " Murmushi yayi daidai lokacin da mai gadi ya bud'e mana get yace "k'arfe nawa zaku shiga lecture.?" Meenat tace "k'arfe 9:00 ne. " Agogon hannunsa ya kalla yace "da sauran time ashe. " Babu wanda ya k'ara magana cikinsu har motarsu ta daidaita saman kwalta. ************* Suna tafe Meenat nayi masa hira har suka isa B.U.K, parking Al'ameen yayi gurin ajiye motocin makarantar yana kallon agogon hannunsa, "k'arfe takwas da talatin da biyar. " Al'ameen ya fad'a a fili, sannan ya kalleta yace "to ni zan wuce asibiti k'arfe nawa zaku tashi na zo na d'aukeki.?" Fari tayi da idanunta sannan tace "sai k'arfe biyu zan bar makaranta, yanzu zamu shiga 9 to 11, sannan 12 to 2. " "Ok, zuwa k'arfen biyun zan zo. " D'aukar jakarta tayi ta fice tana fad'in "sai ka zo, Allah ya kiyaye hanya. " Ameen yace yana tayar da motarsa ya nufi inda suka fito, wato ya koma zoo road Inda asibitinsa yake. ********** Duk da tarin aikin da yake dashi a asibitin amma yana ganin k'arfe biyu tayi ya ajiye komai ya rufo office d'in nasa ya shiga motarsa ya fice daga asibitin, kai tsaye b.u.k ya nufa, da zuwansa ya iske Meenat ita da wata k'awarta mai suna Suhailat tsaye bakin get tana jiransa, tana ganinsa tayiwa Suhailat sallama ta shiga suka kama hanya. Suna tafe Meenat ta kalli Al'ameen tace "yah Al'ameen banyi tsammanin zaka dawo ba fa, dan nasan kana da aiki sosai a asibiti. " Murmushi yayi yana ci gaba da tuk'insa yace "ai duk aikin da nake dashi ba zai hanani zuwa na kaiki gida ba, kinsan fa bana son direba yana kaiki ko da unguwa ne. " Murmushi tayi cike da jin dad'in kulawar da yake bata tace "shi yasa kake da babban matsayi a zuciyata yah Al'ameen. " Kallonta yayi ta gefen ido sannan yace "har yau Meenat baki bani matsayin da nake son kaiwa ba a zuciyarki. " Da mamaki ta kallesa tace "wani irin matsayi kake son na baka bayan wanda na baka yayah.?" Waigowa yayi ya kalleta sosai sannan yace "bar maganar kawai zan gaya miki nan gaba kad'an. " Turo baki tayi gaba cikin shagwab'a tace "nidai yanzu nake son ka fad'a min. " Wani siririn dariya yayi yace "Meenat rigima. " *Wai shin su waye ma wannan family d'in ne ??* Muje zuwa🥰 _Kuyi hak'uri da wannan yau na yini bb chaji ne_ *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Wattpad @rahinamustapha *GASKIYA INA JIN DAD'IN COMMENT D'INKU READER'S🥰😍* MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 4 Alhaji Hassan da Alhaji Husaini 'yay'a ne ga Alhaji Sabi'u da hajiya Suwaiba, Alhaji Sabi'u haifaffan garin maiduri ne iyaye da kakanni kuma shuwa arab ne su, su uku iyayensu suka haifa Sabi'u, Hajara, Halimatu, Sabi'u da Hajara da Halimatu sun taso da matuk'ar k'aunar junansu, lokacin da aka aurar da Halimatu da Hajara lokacin ne Allah yayiwa iyayan nasu rasuwa, Sabi'u ya taso yaro mai k'wazo da neman na kansa, tunda iyayansa suka rasu ya k'ara dagewa gurin karatu da neman na kansa domin inganta rayuwarsa da kuma taimakawa k'anninsa duk da cewa suna gidajen mazajensu, da taimakon 'yan uwan mahaifinsu ya samu ya kammala digiri d'insa har ya samu aiki a wani kampanin sarrafa abinci dana sha dake garin kano matsayin manager, wannan ne dalilinsa na dawowa kano da zama gaba d'aya, sai dai yana yawan zuwa maiduguri gaida dangi, ana cikin hakane ya had'u da Suwaiba, Suwaiba y'ar nan maiduguri ce itama, wani zuwa da yayi gaida y'an uwa ne Allah ya had'ashi da ita, Suwaiba yarinya ce kyakkyawa kuma mai tarbiyya, kanuriya ce ita, ba a d'auki wani dogon lokaci ba manya suka shiga al'amarin aka d'aura musu aure, bayan auren kano ya kawota ya ajiye, haka suke zamansu zama na lafiya tare da soyayya, saida suka d'auki shekaru bakwai da aure sannan Allah yabawa Suwaiba ciki, zo kaga murna gurinsu, y'an uwa ma sun tayasu murna sosai. Nan suka fara rainon cikin nasu cikin kulawa, watan haihu na tsayawa Suwaiba ta haifo 'ya biyu duka maza, murnar gurin Sabi'u da 'yan uwansa kamar anyi musu bishara da gidan aljanna, ranar suna na zagayowa aka sanyawa yara Hassan da Husaini, Hassan da Husaini sun taso cikin tsananin soyayyar iyayansu tare da kulawa, iyayansu suna matuk'ar k'aunarsu, duk soyayyar duniya sun d'auka sun d'aura akansu, wani ikon Allah kuma tun da ga kansu Allah bai kuma bawa Suwaiba wani haihuwa ba. Hassan da Husaini sun taso komai tare sukeyinsa, makaranta tare suke tafiya tare suke dawowa, sutura iri d'aya suke sakawa, ko unguwa d'aya zaije tare zasu tafi, sai kayi mugun saninsu zaka iya banbancesu saboda tsananin kamamninsu da juna, lokacin da suka shiga jami'a kuwa mata kamar zasu d'aukesu su kaisu gidajensu saboda so, su kuwa wannan damar suka samu suke gwara kan y'an mata yanda ransu keso, na farko Allah yayi musu arzik'i daidai gwarwado mahaifinsu na dashi, na biyu ga kyawu da Allah ta'ala ya hore musu wanda yake k'ara dulmiya y'an mata cikin kogin soyayyarsu. Bayan sun kammala jami'a suka fara aiki akan abinda suka karanta wato business, da farko dai shiga da fitarwa sukeyi daga gida najeria zuwa wasu k'asashen haka ma daga wasu k'ashashen zuwa gida najeria, kuma cikin hakan ne suka had'u da masoyan zuciyoyinsu. Asma'u da Fateema k'awayen juna ne na k'ut da k'ut, a unguwa d'aya suke zaune, zan iya cewa ma tare suka taso kasancewar gidansu na kusa dana juna, iyayensu kuma aminan juna ne, suna da kyansu daidai misali, cikkaku kanawa ne su, kuma babu laifi iyayansu na da kud'i daidai gwargwado, sun had'u dasu Hassan ne a super market sunje siyayya, sun zo fito kenan suka ci karo da Hassan da Asma'u, nan take kayan hannunta ta watse, kasancewar ita ce ta bangajeshi yasa ta bashi hak'uri tana mai duk'awa ta fara tattara kayan, shima duk'awa yayi ya tayata kwashe kayan yana binta da kallo domin yarinyar ta tafi dashi sosai, d'agowa sukayi a tare bayan sun gama kwashe kayan sai suka ga Husaini da Fateema tsaye a kansu, kallon kallo sukayi tsakaninsu sai kuma suka saki murmushi, a wannan rana su Husaini suka bayyana soyayyarsu gasu Asma'u, nan take su kuma suka amsa masu. Tun daga wannan rana soyayya me k'arfi ta k'ullu tsakaninsu, ba'a d'auki wani dogon lokaci ba aka sanya ranar aurensu, nan aka fara shirye shiryen biki gadan-gadan, lokaci nayi aka d'aura auren Asma'u da Hassan, da Fateema da Husaini, bikine na y'an gata akayisa a wannan lokacin, sun ajiye matan nasu ne a gida d'aya, wato gidan da Dadynsu ya gina musu a hotoro. Zamana na lafiya da tsantsan soyayya suke gudanarwa a tsakaninsu, yayin da b'angare d'aya arzik'i ke ta k'ara hab'b'aka musu, muje muje har yakai ga sun bud'e wani katafaren companyn da yake sarrafa zannuwa da jakunkuna. Shekararsu biyu da aure Asma'u ta haifi Al'ameen, Al'ameen kyakkyawa ne sosai domin babanshi ne sak, kana kallonshi kaga jinin shuwa, ita kuwa Fateema har lokacin bata da ciki, tafi-tafi shekaru nata ja har Asma'u ta k'ara haihuwa biyu Fateema har lokacin bata da ciki, kuma hakan bai sa ta damu ba, tunda mijinta ma bai tab'a nuna mata damuwarsa ba, bayan Al'ameen Umma ta haifi Aisha da Bilkisu, Al'ameen tunda ya fara wayau yana gurin Ummi wato Fateema, yayi matuk'ar shak'uwa ta ita fiye da Ummanshi, itama sosai take son yaron a ranta, hakan ne yasa Umma take ce mashi d'an Ummi. Umma na da cikin Aliyu wata hud'u Ummi ta fara laulayin ciki, murna gurinsu ba'a magana, kuma a wannan lokacin ne suka tare a tamfatsa-tamfatsan gidajensu da suka gina nasarawa g.r.a, gini ne na gani a fad'a, gidajen jere suke da juna komai iri d'aya, kowa yaga gidajen nan sai sun burgeshi. Laulayi sosai Fateema takeyi kamar ba zata sha ba, cikin ikon Allah cikin na shiga wata biyar tabar laulayi, lokacin kuwa Umma ta haihu yaronta namiji mai suna Aliyu, haka dai Fateema ta ci gaba da rainon cikinta har watan haihuwa ya kama ranar wata juma'a ta tashi da nuk'uda, haka aka d'auketa akayi asibiti da ita, basu jima da zuwa asibitin ba ta haifi y'arta kyakkyawa mai kama da ubanta, kowa yaga yarinyar babu abinda yake fad'i sai masha Allah, tunda Al'ameen yayi arba da babyn nan yake manne da ita, ya hana kowa d'aukarta. Bayan Ummi ta huta aka sallamosu suka dawo gida, tunda suka dawo gida 'yan uwa da abokanan arzik'i suke zuwa barka, kowa yazo sai ya fad'i kyawun yarinyar. Sati na zagayowa yarinya taci suna Ameenatu, Al'ameen shine wanda ya fara kiranta da Meenat nan kowa ya kama, sosai Al'ameen yake son Meenat tun tana jaririyarta, sam baya son kukanta, ko wanka ake mata yaji tana kuka zai fara rok'on Ummi ta k'yaleta, in kuwa kukan rigima takeyi tare sukeyi, dan in ya rarrasheta tak'i shiru shima sai ya fashe da kuka, komai ya samo na Meenat ce, ko makaranta yaje duk abinda yaci sai ya rago mata, itama Meenat ko da ta fara wayo komai yayah Al'ameen, shak'uwarsu har mamaki yake bama iyayansu, babu mai son damuwar d'an uwansa, kuma basa tab'a fushi da juna, kome ya had'asu to basa wuce mintuna sha biyar suna fushi da junansu, duk inda Al'ameen zaije yana manne da Meenat d'in shi, lokacin da Meenat ta fara zuwa makaranta shi yana jss 1 ne, amma haka zai jira a shiryata su tafi tare, sai ya ga shigarta har ajinsu sannan zai dawo ya shiga mota a wuce dashi nasu makarantar, shak'uwace tare da soyayya bana wasa ba a tsakaninsu, suna girma kuma shak'uwarsu na k'ara k'arfi, duk kuma inda suka shiga anga yayah da k'anwarsa saboda kamarsu da juna, Al'ameen bai san ya kamu dumu dumu cikin soyayyar k'anwar nashi ba sai lokacin da yake shekararshi ta k'arshe a jami'a, a lokacin shekarunsa ashirin ne da shida ita kuma Meenat tana shekara sha shida aji biyar a secondary, a lokacin sam bata son yaga wani namiji ya rab'eta ko kad'an, bayan kammala karatunsa na likita Abba ya sama mishi addimition a k'asar India dan yaje ya k'aro karatu akan abinda ya karanta, amma fafur Al'ameen yace ba zaije ba, dan ba zai iya tafiya yabar Meenat ba, dole Abba ya hak'ura ya k'yalesa ya d'aura karatun nasa anan gida najeria yayin da b'angare d'aya kuma ya fara aiki a asibtin malam Aminu kano (A.K.T.H). Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Al'ameen na b'oyewa Meenat soyayar da yake mata duk da cewa wasu lokutan yana kwatanta kansa a matsayin mijin aurenta cikin wasa, ita kuma tana cewa yayi mata girma, dan gaskiya Al'ameen dogo ne me d'an jiki, ga faffad'ar k'irji, namiji ne me k'iran k'arfi a tsaye yake kana kallonsa ka ga jarumin namiji, ita kuwa Meenat siririya ce amma ba can ba, doguwa ce itama d'in sai dai Allah ya hore mata k'ira da duk mace zatayi fatan samunsa. Cikin hakan ne Meenat ta kammala karatunta na secondary, kuma a lokacin ne Abbie wato baban Meenat ya mallakawa Al'ameen katafaren asibiti da ya gina masa mai suna twins Hospital, asibiti ne da ya bashi kyauta halak malak, shigar Meenat university babu dad'ewa Allah ya had'ata da Salis, lokacin da ta zo wa Al'ameen da maganar Salis hankalinsa ya tashi sosai matuk'a da gaske, amma tsaban mazantaka ya dake ya nuna mata farin cikinsa, tare da k'arfin gwiwarsa ta fara soyayya da Salis, sun d'auki watanni hud'u tare Salis ya buk'aci turo magabatansa, nan Meenat tazo ta gayawa Al'ameen, lokacin ma hankalinshi k'ara tashi yayi yana ganin zai rasa Meenat d'inshi, kuma ya kasa fad'a mata sirrin zuciyarsa saboda ta riga ta kashe masa jiki da kalamanta na cewa shi mijin manyan mata ne😄, haka dai Al'ameen yayiwa su Abba maganar Salis, nan su ka bashi damar turowa. Sati d'aya da ba Salis dama amma shiru bai turo ba, hakan yasa Meenat tambayarsa dalili, nan ya fara yi mata y'an kame kame, daga k'arshe dai ya fad'a mata mahaifiyarsa ce tace ba zai auri bare ba sai y'ar uwarsa, hankalin Meenat ya tashi domin kuwa tana son Salis, nan tazo ta fad'awa Al'ameen abinda ke faruwa, shi kuma hakan ba k'aramin dad'i yayi masa a ransa ba, nan ya nuna mata ta hak'ura da Salis kawai tunda Mahaifiyarsa bata son bare, amma Meenat ta dage ita fa tana son Salis, shima b'angaren Salis ya nata fama da mahaifiyarsa amma tak'i yarda masa sam, ana hakane ya d'auki Meenat ya kaita ta gaisheta, habawa ranar sunyi dana sanin zuwa, domin kuwa a fili ta nuna k'iyayyar Meenat sannan ta rok'eta da tabar mata d'anta ta riga tayi masa mata, da taga Salis ya duk'a gabanta yana rok'o da magiya tabarsa ya auri Meenat sai ko ta mik'e ta fara jan Meenat har sai da ta fito da ita bakin get tace tabar musu gida basa buk'atarta matsayin suruka, abin nan yayiwa Meenat ciwo sosai, ko sauraran Salis ba ta tsaya yi ba wanda yake rok'on ta tsaya ya d'auko mota ya kaita gida ta tari taxi ta nufi gida. Da zuwanta d'akin Al'ameen ta nufa tana kuka, cikin rud'ewa ya mik'e ya rik'ota yana tambayarta abinda ke faruwa, nan ta fad'a masa komai, haushin mahaifiyar Salis tare da ita Meenat d'in ne ya kamasa, cikin fushi yace "to ke me ta kaiki gidansu, Meenat wai me yasa bakya jin magna ne, ki rabu da wannan yaron yaje yabi zab'in mahaifiyarsa tace bata sonki to dole ne sai kin tusa kanki inda ba'a sonki. ?" Aiko sai Meenat ta k'ara fashe masa da kuka, wannan rana Al'ameen rufe ido yayi yayi tayi mata fad'a cikin b'acin rai, daga baya kuma ya dawo yana rarrashinta, to tun daga wannan rana Meenat ta fara ja baya da Salis, amma dai soyayyarsa yana nan a ranta, suma su Umma da suka ji batun fad'a sukayi mata sosai akan ta rabu dashi, ana cikin wannan halin ne kuma sun dawo daga shopping ita da Al'ameen Salis ya kirata a waya yake fad'a mata an sanya masa ranar aure da y'ar uwarsa, shine fa ranar ta dinga kuka Al'ameen yayi burus da ita domin kuwa yaji duk abinda Salis ya gaya mata da yake a hand-free ta saka wayar. To ga dai yi nan yanzu kamar Meenat taji maganar Al'ameen, domin bata kara maganar Salis ba, kuma tsakanin jiya da yau ya kira wayarta yafi a k'irga tak'i ta d'aga masa. Yanzu haka Al'ameen yana da shekara talatin a duniya ita kuma Meenat tana da shekara ashirin yanzu haka tana shekara ta uku a jami'a tana karantar likitanci domin tace yayanta zata gada.😁 *Back to story* Daidai k'ofar get d'in gidansu Al'ameen ya faka motarsa har lokacin Meenat na zuba mashi shagwab'a wai sai ya fad'a mata wani irin matsayi yake so ta bashi, shi kuma yak'i fad'a mata yace da akwai lokacin da zai fad'a mata. Kallonta yayi yace "to Ameenatuwa sauka ki shiga gida ni zan koma asibiti na bar aiyuka da yawa. " Turo baki tayi cikin shagwab'a tace "kaima yayah Ameenatuwan zaka ce kamar yanda Mama (kakarsu mahaifiyar su Abby) take fad'a min sai kace wata tsohuwa. ?" Rik'e kunninsa yayi yace "sorry meenat d'ina sub'utar baki ne. " Murmushi tayi tace "na hak'ura sai ka dawo. " Tana gama fad'in haka ta bud'e motar ta fice tana d'aga masa hannu, shima hannun yake d'aga mata har ta shige gida sannan yaja motarsa ya koma asibiti zuciyarsa cike da nishad'i, hak'ik'a in yana tare da Meenat yana samun kansa cikin farin ciki mara musultuwa, yana so ya sanar mata soyayyarsa amma ya rasa ta inda zai b'ullo mata, dan shi sam baya son abinda zai b'atawa Meenat rai, yayiwa kansa alk'awari duk randa ya fad'a mata soyayyarsa tace bata sonsa ba zai mata dole ba. Muje zuwa😍 _A shirye Raheenat take da amsar gyara ko wani kuskure da kuka gani reader's😊🥰👇_ 07033643262 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Whattpad @rahinamustapha _WANNAN PAGE NAKI NE ALAWIYYA QANIN MIJI FANS GROUP, WLH INA MATUK'AR JIN DAD'IN COMMEN D'INKI, KI SANI RAHEENAT NA YINKI😘, KI HUTA KAWAI KIJI DAD'INKI🥰_ MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 5 Sai k'arfe biyar da rabi Al'ameen ya baro asibitin, kafin ya kamo hanyar gida sai da ya biya ya siyowa Meenat abinda yasan tana matuk'ar so wato shawarma sannan ya nufi gida. Ya fito kenan daga motar sai ga Meenat da gudunta ta fad'in "oyoyo yah Al'ameen, tun d'azun nake jiran dawowarka kuma nayi ta kiran wayarka a kashe. " Ta k'arasa maganar tana b'ata fuska alamun bata ji dad'in nan ba. Dafe kai Al'ameen yayi yace "oh sorry my Meenat wallahi aiki ne yayi min yawa shi yasa na kashe wayar, I hope kina lafiya. ?" Wani juya ido tayi sannan ta rik'o hannunsa tace "lafiyata k'alau, dama nima ina son naji ko kana lafiya ne nayi ta kiran wayarka a kashe. " Murmushi yayi yace "lafiya k'alau neke Meenatuna aiki ne kawai yasha kaina, dan yau an kawo marasa lafiya da yawa. " Meenat tace "shi yasa ai na k'osa na kammala karatuna na zo na rink'a tayaka aiki. " Cikin jin dad'i yace "Allah ya nuna mana lokacin Meenatu na. " Meenat tace "ameen yayana. " Al'ameen ne ya kalleta yace "kinsan me na siyo miki kuwa. ?" Girgiza kai tayi alamar a'a, murmushi yayi yace "ina zuwa. " Bud'a motar yayi ya d'auko ledar shawarman da ya siyo mata ya mik'a mata, tun kafin ta bud'e tasan meye a ciki, aiko sai ta doka tsalle tare da rungume yayan nata tana fad'in "thank you yayah Al'ameen, Allah ya baka abinda kake so kaima kamar yanda kake k'ok'ari gurin siya min abinda nake so, ina sonka yayana. " Tana gama fad'in hakan ta sakeshi ta fara k'ok'arin bud'e ledar. Al'ameen dai ya sandare a tsaye saboda rungumar bazata da Meenat tayi masa, wani irin yanayi ne yaji a cikin jikinsa, dak'yar ya daidaita nutsuwarsa ya kalli Meenat dake k'ok'arin kai shawarma bakinta yace "Meenatu wai anan kike ci. ?" Saida ta saka a bakinta ta tauna sannan tace "yawuna ne ya tsinke wallahi yayah, zo muje ciki kaga kaima abinda na tanadar maka. " Tayi maganar tana jan hannunsa zuwa cikin gida. Abba ne dake tsaye saman bene tun tsayuwar motar Al'ameen ya saki murmushi bayan ganin sun shige ciki, yana matuk'ar jin dad'in yanda Al'ameen da Meenat suke nunawa juna k'auna, abin na burgeshi har yake fata a ranshi su zama miji da mata, sai dai al'k'awari ne ya d'aukarwa kanshi ba zai tab'a had'asu aure ba har sai in sune suka ce suna so. ************** Kai tsaye dining Meenat ta nufa da Al'ameen ta ja masa kujera ya zauna, k'ok'arin bubbud'a abincin dake dinning d'in ta farayi Al'ameen ya rik'e hannunta tare da kasheta da idanunsa, d'ago ido tayi tana kallonshi da alamar tambaya, langwab'e kai yayi kamar wani k'aramin yaro yace "Meenatuna zakiyi min alfarma na fara wanka kafin abincin nan please. " Murmushi ta saki wanda yake k'ara mata kyau tace "gani nayi kana tare da yunwa shi yasa zan fara baka abinci kafin kayi wanka, amma in wanka kakeso ka fara shikenan. " Shima murmushi yayi mata yace "gaskiya nafi buk'atar wankan. " "To shikenan tashi kaje kayi ka dawo." Tayi maganar tana zama akan kujera tare da janyo ledar shawarmanta. " Al'ameen ne yace "au yau kuma baza a had'a min ruwan wankan ba.?" Kallonsa tayi cikin wasa tace "so nakeyi na fara sabarwa kaina barin aiyukan nan kafin matarka ta zo, dan had'a maka ruwan wanka da dafa maka abinci duk aikinta ne bana Meenat ba. " Waro ido Al'ameen yayi yace "kina nufin zaki baryi min komai.?" "Eh mana, so nakeyi ka saba dayi da kanka dan nan da d'an lokaci zanyi aure na barka, dan kai banga kana niyar aure yanzun ba. " Sakin baki Al'ameen yayi yana kallon Meenat, ita kuwa sai kai shawarma take bakinta kamar ba ita tayi maganar ba. Bud'e baki Al'ameen yayi yace "Meenat ni kike fad'awa zakiyi aure ki bari, ashe zaki iya nesanta kanki da yayanki.?" Har ga Allah Meenat da wasa tayi maganarta, amma maganr Al'ameen yayi matuk'ar shiga jikinta, sai yanzu zuciyarta ya hasasho mata aurenta zai iya nesantata da yayanta, k'walla ne suka ciko mata idanu, cikin rawar murya tace "ba zan iya barinka ba yayah Al'ameen, wasa kawai nakeyi, *ni da yayah Al'ameen* mutuwa ce kawai zata raba mu. " Ajiyar zuciya Al'ameen ya sauke me k'arfi sannan yace "to in hakane tashi muje ki had'a min ruwan wankan. " Mik'ewa tayi ba tare da musu ba ta nufi hanyar d'akinsa shima mik'ewar yayi yabi bayanta. ******** Saida ta had'a masa ruwan wankan sannan ta fito daga toilet d'in, Al'ameen da dama jiranta take yana ganin ta fito ya shige, ita kuma wardrobe d'insa ta nufa ta ciro masa kayan da tasan yafi son sakawa a irin wannan lokaci, wato three-queter da yar k'aramar riga, ta feshe masa da turare ta ajiye akan gadonsa ta fice daga d'akin. Al'ameen na fitowa ya shirya cikin kayan da Meenat ta fito masa dasu ya k'ara feshe jikinsa da turare ya fito zuwa dining d'in domin cin abinci. na biyu wato me bin Isma'il me suna Habiba, sorry reader's na mance ban ce muku Ummi ta k'ara haihuwa hud'u bayan Meenat ba, Isma'il, Habiba, Saudat sai auta Faruk. Kallonta Al'ameen yayi bayan ya zauna yace "ina Meenat d'in take ne.?" Cikin nutsuwa tare da girmamawa Habiba tace "Ummi ce tace na zo na kirata ta tayata su k'arasa aiki a kitchen, shine Aunty Meenat tace na zauna nayi saving d'inka. " "Ok" kawai yace ba tare da ya k'ara magana ba, nan ko Habiba ta mik'e ta fara saving nashi. ********* *Bayan kwana biyu* Zaune Meenat suke ita da k'awarta Suhailat suna hira bayan fitowarsu daga lecture, Suhailat ce ta kalle Meenat tace "ni ko Meenat ina son na tambayeki. " Kallonta Meenat tayi tace "Allah yasa nasan amsar tambayar naki Suhailat. " D'an murmushi Suhailat tayi tace "kin sani mana Meenat. " "To ina jinki " cewar Meenat. Gyara zama Suhailat tayi tace "dama tambayarki zanyi dan Allah meye tsakaninki da yayanki Al'ameen. ?" Wani irin kallo Meenat tayi wa Suhailat sannan tace "ban gane me kike nufi meye tsakaninmu ba.?" Suhailat tace "a'a maida wuk'ar Meenat, ba da wani manufa nayi tambayar ba, nufina wai akwai soyayya ne tsakaninku. ?" Dariya Meenat ta kwashe dashi tace "soyayya!! Wai *ni da yah Al'ameen*? Hmmm ni babu wata soyayya tsanina da yayah Al'ameen da ya wuce soyayyar *jini d'aya*, kawai munyi matuk'ar *shak'uwa ce* dashi fiye da zaton me zato, yana sona nima ina sonsa, yana bani kulawa nima ina bashi kulawa, bacin wannan babu wani abu tsanani dashi, *ni da yayah Al'ameen* ba soyayya na aure tsakaninmu sai dai na y'an uwa. " Ajiyar zuciya Suhailat ta sauke tace "in ko hakane kice nayi so a inda ya dace. " Kallonta Meenat tayi cikin rashin fahimta tace "ban gane me kike son fad'a ba Suhailat." Murmushi tayi tace "ina nufin ina son yayanki Al'ameen so bana wasa ba, tun ranar dana fara ganinshi naji babu wani d'a namijin da nakeso sai shi, na mayar da maitata ce lokacin dana ga irin kulawar da kuke nunawa junanku wanda babu wanda zai ganku yace ba soyayya kukeyi ba, gashi ke k'awata ce dana ke matuk'ar so, dan haka na bawa zuciyata hak'uri, to yanzu kuwa da kika sanar min ba soyayya kukeyi ba sai naji k'arfin gwiwan tinkararsa da soyayyat..." Meenat bata barta ta k'arasa ta d'aga mata hannu tare da fad'in "ya isa haka Suhailat, ke a zatonki yayah Al'ameen zai soki.?" Cike da k'arfin gwiwa Suhailat tace "me zai hana kuwa ya soni, nima fa macece, kuma ina da kyan nan daidai misali. " Meenat cikin jin haushi wanda bata san ko na miye ba tace "to ai sai kije ki kai tallar kanki, yo talla mana tunda bai zo yace yana sonki ba. " Kallonta Suhailat tayi da mamaki tace "Meenat wai bakya sona da yayanki ne.?" Cikin nuna basarwa tace "a'a, kawai dai naga zubar da aji ne kace ma namiji kana sonsa. " "Kenan ba zaki taimaka min ba. ?" Meenat tace "ni wai, banyi miki alk'awari ba gaskiya, dan yayah Al'ameen murd'ad'dan namiji ne, kwanaki ma ce min yayi shi ba zaiyi aure yanzun ba sai nan da shekara goma . " _Ni ko raheenat nace kaji Meenat da sharri😂_ Kallonta Suhailat takeyi da mamaki, kishi ne ta gani k'arara a idanun Meenat, a ranta tace "hmm wannan shak'uwar naku ba banza ba dama, kuna son junanku ba tare da kun sani ba, ni na hak'ura dama tuni na bawa zuciyata hak'uri. " _na ce ke Suhailat waya fad'a miki Al'ameen be san yana son meenatunsa ba🤔 ita ce dai ta kasa ganewa, kuma gara da kika hak'ura dan gaskiya Al'ameen na Ameenatu ne ko ba haka ba reader's😄_ Mik'ewa Meenat tayi ta kalli Suhailat tace "ni zanje aji kaina ciwo ya keyi min. " Murmushi Suhailat tayi tace "ok, muje to. " Aji suka nufa gaba d'aya Meenat tana cika tana batsewa dan haka kawai taji tana jin haushin Suhailat tunda tace tana son yayanta Al'ameen, ita kuwa Suhailat dariya ma abin ya rink'a bata... Muje zuwa🥰 More comment more typing😁 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 6 Har lokacin Al'ameen yazo d'aukarta cika take tana batsewa, bayan sun d'au hanya ne ya kalleta cike da kulawa yace "waye tab'a gimbiyar Al'ameen ne take fushi haka.?" Kallonsa tayi sannan ta kau da aki gefe tare da sakin wani dogon tsaki tace "aikin banza, ni wallahi bana son zub da aji, ai wannan zubar da aji ne da kimar ya mace. " Shi dai Al'ameen ya tabbatar ko giyar wake Meenat tasha ba zata fad'a masa wannan maganar ba, dan haka yace "dawa akeyi kuma my meenat.? " Turo baki gaba tayi wanda ya riga ya zamar mata jiki dan Meenat shagwab'ab'b'iya ce number d'aya tace "Suhailat ce mana. " D'an k'ara girman idonsa yayi yace "yau kuma me ya had'aku da aminiyar taki.?" Tsaki ta k'ara ja tare ta cewa "rabu da ita kawai yayah, to wai nima ina ruwana ne dan tace ..." Sai kuma tayi shiru. Al'ameen yace "dan tace me.?" Shiru tayi zuwa can kuma tace "babu komai. " Murmushi Al'ameen yayi yace "ni dai nasan k'anwata bata b'oye min komai, wannan d'in ma ina zaman zamana nasan za a gaya min. " Murmushi itama tayi ba tare da tayi magana ba, haka suka ci gaba da tafiya babu wanda ya k'ara magana cikinsu har suka k'araso gida. *************** Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, kwanaki suna shud'ewa suna zama sati, sati yana zama satittika a haka aka kwashi watanni biyu da rabuwar Salis da Meenat, zuwa lokacin Meenat tuni ta cire wani Salis a babin rayuwarta, yayin da b'angare d'aya kuma shak'uwa tare da soyayya ke k'ara k'arfi tsakaninta da yayanta, ana cikin hakane kuma ta haɗu da wani guy me suna Kamal, sun haɗu da Kamal ne a sahad store taje siyayya, ranar basu fita da Al'ameen ba direba ne ya kaita sakamakon aiki da ya riƙesa a hospital, tunda Kamal ya ɗaura idonsa akan Meenat yaji ya kamu da sonta, be tsaya ɓata lokaci ba ya tinkareta, farko dai Meenat taƙi sauraransa, dadai ya isheta da naci ne ta sauraresa har ma ta basa number wayarta, nan suka rabu yace zai kirata, koda Meenat ta dawo bata faɗawa Al'ameen haɗuwarta da Kamal ba, dan haka kawai taji ba ta son faɗa masa yanzu. A wannan daran Kamal ya kira wayarta, kuma wasa wasa sun ɗauki lokaci dashi suna waya, sosai Meenat ta saki jikinta dashi kai kace sun daɗe da haɗuwa ne. Yau ta kama asabar Al'ameen ne tare da Meenat suka fito cikin shiga iri d'aya, wata arniyar shadda ce coffee colour ajikinsu me d'an karan kud'i, d'inkin da akayi ma shaddar kad'ai ka kalla kasan kud'i yayi kuka a gurin nan. Ita Meenat doguwar rigace akayi mata yayin da ya zauna ajikinta d'as, ba k'aramin kyau yayi mata ba, shi ko Al'ameen d'inkin samarin zamani akayi masa, kayan sunyi matuk'ar yi musu kyau abinka da farare, Umma ce dake zaune a falo ta d'ago ta kallesu tace "y'ata har kun fito. ?" Murmushi Meenat tayi tace "eh min fito Umma. " "To Allah ya kiyaye hanya ku gaida min da Bilkisun da kyau in kun isa. " Meenat ce cike da d'oki tace "zata ji Umma, yah Al'ameen zo mu tafi " tare da kama hannun Saudat k'anwarta da yake da ita zasu je. Al'ameen bayansu yabi yana cewa "Umma sai mun dawo" dan har meenat ta kai k'ofa, "a dawo lafiya, Allah ya kiyaye" cewar Umma. Ziyara zasu kaiwa Bilkisu k'anwar Al'ameen dake aure a garin Zaria. Sai da Al'ameen ya shiga yayiwa Ummin Meenat sallama sannan ya fito suka d'au hanyar Zaria. ************ Zaune suke a falon Bilkisu yayin da aka cika musu gabansu da abin ciye-ciye, firar zumunci sukeyi abinsu cike da nishad'i, fuskar Bilkisu sam yak'i ɓoye farin cikinta. Kallon Al'ameen Bilkisu tayi tace "yayanmu, (da yake haka suke kiran Al'ameen) wai sai yaushe za kayi aure ne.?" Ido Meenat ta zuba mishi dan jin amsar da zai bayar, shiko Al'ameen ɗan haɗe fuska yayi yace "ina ruwanki da aure na ne, gidanki nake zaune balle kice kin gaji da ganina koko kina ciyar dani ne balle kice kin gaji.?" Murmushi Bilkisu tayi dan tasan halin Al'ameen sarai tace "babu ko ɗaya ciki yayanmu, kawai dai naga shekaru ne na ta tafiya. " Wani kallo yayi mata yace "ko dai zakiyi min auren ne a huta.?" Dariya ta ɗanyi tace "wallahi yayanmu kana cewa kana so zanyi maka, dan dai sadaki da kayan lefe da abincin biki zan ɗauke maka. " Al'ameen yace "saboda ni bani dashi ko.?" Shiru Bilkisu tayi dan tasan tana ƙara magana ranta zai iya ɓaci, Allah ya gani bata da wani buri da ya wuce taga yayantan yayi aure, kuma ba matar da takeyi mashi ƙwaɗayin samu sai Meenat. Meenat dai dariya tayi tace "yayah fa ko budurwa bashi da ita, shi yasa rannan nace mishi bai san yanda soyayya take ba. " Wani kallo ya jefeta dashi wanda yasa tayi saurin yin ƙasa da kanta ba ta ƙara magana ba. Nan dai suka ci gaba da hirar zumuncinsu, a nan gidan Bilkisu suka kwana, Al'ameen ɗakin baƙi ya kwana, su kuma su Meenat a ɗakin bilkisu, washe gari da sassafe suka juya kano, Bilkisu ji tayi kamar kar su tafi. *Bayan wata biyu* Zaune suke cikin lambun gidan suna shan iska, Al'ameen ne ya kalli Meenat wacce take shan ice-cream yace "Meenat ina son na faɗa miki wata magana maimahimmanci. " Tsaida shan ice-cream ɗin tayi tare da ɗago da fararen idunta ta kallesa tace "ina jinka yayah. " Ajiyar zuciya ya sauke ya fuskanceta sosai yace "Meenat na daɗe ina son faɗa miki sirrin zuciyata amma na rasa ta ina zan fara, kullum zuciyata tana cike da tsoro tare da fargaban faɗa miki saboda bansan ta yaya zaki amsheta ba, saboda kullum baki kallon yayanki matsayin mijin aurenki, kullum kaƙƙon yaya kike yi min, Meenat ina sonki, na fara sonki tun baki san wacece ke ba, Meenat ina yi miki so na aure, dan Allah ki amshi soyayyata mu ci gaba da rayuwarmu cikin soyayya kamar yanda muka saba. " Tunda Al'ameen ya fara magana Meenat take kallonsa cikin wani irin yanayi har ya saka aya, buɗe baki tayi muryarta na rawa ƙirjinta na bugawa tace ".... _Kuyi min afuwa yau ban samu sukuni bane.👏_ Muje zuwa🥰 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NIDA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga duk wani makarancin littafin nan na baku shi kyauta Raheenat nayi muku fatan alkhairi a duk inda kuke. Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 7 Tace "yayah kana sona da aure kace.?" "Eh Meenat, ko ke bakya sona.?" Hawayene suka fara sauko mata murya na rawa tace "yayah wallahi ni ban taɓa kallonka a matsayin mijin aure ba, kallon yayana nakeyi maka, ina sonka yaya amma soyayya na jini ɗaya, yayah kamar yanda nake faɗa maka ne wallahi kafi ƙarfina, yayah ban masan ta wacce fuska zan kalleka a matsayin miji ba, yayah ina amshi soyayyarka yanzu me kake tunanin zan faɗawa Kamal, so kake ya kirani da mayaudariyya ? Yaya kana da babban matsayi a zuciyata, ina yi maka son da ko ƴan uwana da muka fito ciki ɗaya ba nayi musu irinsa, Yayana dan Allah ina roƙonka kabar maganar soyayya tsakaninmu mu ci gaba a yanda muke."👏 Idanun Al'ameen ne suka kawo ruwa, amma sai yayi ta maza ya mayar dasu, kallon Meenat yayi wacce take hawaye zuciyarsa nayi masa zafi da kalamanta, shi a tunaninsa a yanda suke da Meenat duk lokacin da yazo mata da buƙatarsa ba zata juya masa baya ba, ashe yayi kuskure, ashe da gaske takeyi ba zata iya aurensa ba ? To wai duk soyayyar da take nuna masa tare da kulawa na menene ? yana cikin tunanin nan yaji Meenat ta riƙo hannunsa tare da duƙawa gabansa tana cewa "yayana dan Allah ka fahimci ƙanwarka, dan Allah kar kayi fushi dani, wallahi ba zan iya juran fushinka gareni ba, ina ji a jikina zaka samu matar da tafini komai, wacce zata kula min da kai sosai. " Ta ƙarasa maganar tana ɗaura kanta saman cinyarsa tana ci gaba da shashsheƙa. Hannu Al'ameen yakai ya ɗago da ita cikin nuna jarumta ya sakar mata murmushi yace "is ok my meenat stop craying, alƙawarin zuciyata ce bazan taɓa tursasaki ki soni ba, sannan ba zan taɓa aurenki ba tare da yardanki ba, Meenat duk da son da nakeyi miki wallahi zan haƙura tunda ke bakya ra'ayin aurena, ina da tabbacin in najewa su Abba da maganar ina son aurenki zasu aura min ke, amma ba zanyi hakan ba tunda zuciyarki bata buƙatar hakan, Meenat zan iya sadaukar da farin cikina dan ke kiyi farin ciki, farin cikinki kawai ya isheni farin ciki, Meenat ki saka a ranki daga yau yayanki ba zai ƙara yi miki maganar soyayya ba, na haƙura, na sadaukar da soyayyata domin farin cikinki, na san kina son Kamal ina fatan ya sakaki farin ciki ƙanwata, hakan kawai in yayi ya isheni. " Ya ƙarasa maganar ƙwalla na ciko idanunsa, faɗawa jikinsa Meenat tayi tana kuka faɗi take "kayi haƙuri yayah, kayi haƙuri, bansan me yasa na kasa amsar buƙatarka ba yaya. " Murmushi ƙarfin hali yayi yace "kibar kuka dan Allah, kukanki na taɓa min zuciya. " Da ƙyar ya lallasheta ta bar kukan suka miƙe sukayi cikin gida. Tun daga wannan rana Meenat take cikin ƙuncin zuciya, gaba ɗaya ji takeyi ta tsani kanta da ta kasa amsar soyayyar yayanta, me yasa zuciyarta ta kasa yiwa yayanta alfarman soyayya, me yasa ne zuciyarta ta kamu da soyayyar Kamal wanda take ji ba zata iya rabuwa dashi tabawa yayanta soyayya ba, why, why ? Tambayar da takeyi wa kanta kenan duk lokacin da take ɓance ita ɗaya, haka zataci kukanta ta ƙoshi, ga wani abu dake addaban zuciyarta game da yayan nata wanda bata san ko meye ba, shiko ɓangaren Al'ameen ko a fuska bai sauya mata ba, duk wani abu da yakeyi mata bai fasa ba sai ma ƙarawa da yayi, kullum shine ke kaita makaranta kuma yaje ya ɗaukota komin aikin da yake dashi kuwa, sai dai in ya shiga ɗaki yana kuka, kuka me tsanani domin son da yakeyiwa Meenat ba sone na wasa ba, so ne wanda Allah ya halicci zuciyarshi da ita haka dai zaiyi kukansa ya share hawayensa, iyayansu kuwa basu fahimci komai ba tsakaninsu, saidai Meenat wani kunyar yayan nata ne takeji yanzu, sam bata iya haɗa ido dashi, ita kanta tasan bata kyauta ba, amma ya zatayi, in ta amshi soyayyarsa to bata san ina zata kai son da takeyi wa Kamal ba. Yau ma kamar kullum tafe suke a hanyarsu ta dawowa daga makaranta, Al'ameen ne ya kalleta yace "meenatuwan yayanta meke damunki ne naga kwana biyun nan kin zama wata iri.?" Idanunta ne ya ciko da ƙwalla bata yarda sun haɗa ido ba tace "babu komai yayah, kawai karatune ya fara zafi. " Murmushi yayi yace "gaskiya fa karatun likitanci babu sauƙi, amma ai kina tare dani, karki damu kanki insha Allahu komai zaizo miki da sauƙi. " Hawayen da suka zo mata ne ta share ba tare da ya lura ba tace "Allah yasa, yayah ka wuce dani gidan Mama kaka kawai in ka taso daga asibiti sai ka biyo ka ɗaukeni. " Al'ameen yace "ok, kice yau ziyara zaki kaiwa tsohuwa. " Murmushi Meenat tayi tace "babu ruwana in Mama kaka ta jika, kasan bata son kace mata tsohuwa. " Murmushi shima yayi yace "wannan tsohuwa badai rigima ba wallahi. " Da ire-iren wannan hirar suka isa gidan Mama kaka dake Hotoro. A ƙofar get ya ajiyeta ya juya ya tafi, a ƙayataccen falon ta iske ƴar tsohuwar matar zaune tana jan carbi, da gudu Meenat taje ta faɗa jikinta, tureta Mama kaka tayi tace "ni ɗaga ni karki ƙarasani uwar son jiki. " Turo baki Meenat tayi tace "to in na ƙarasakin meye, ina ce kwasanki kawai zamuyi mu kaiki ƙabari mu rufe. " Bugu Mama kaka takai mata ta goce tana dariya tace "au nafa manta ƴar tsohuwar bata son mutuwa. " Dan Alƙah kuyi min haƙuri naso yi muku da yawa wlh amma jikina yau banjin daɗinsa sosai wlh👏 Muje zuwa🥰 Zaku iya turo da ra'ayinku ta 👇 07033643262 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Wannan page naki ne Alawiyya, gaskiya muna matuƙar jin daɗin comment ɗinki ni da masoyiya Meera, hakiƙa bazan taɓa gajiyawa da baki kyautar page ba, saboda ke ɗin tadabance cikin fans ɗinmu, muna godiya sosai da adduoinki garemu Allahu ya amsa🤲 kina cikin❤ɗin Raheenat kawai ki huta kiji daɗinki Allah ya amintar dake. Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 8 Mama kaka tace "Babu me son mutuwa ai dama, amma duk ƙinka da ita sai ta ɗaukeka da zaran lokacinka yayi, fata dai Allah yasa mu cika da imani. " Meenat tace "ameen dai kakus. " Mama kaka ce tace "ki tashi ki shiga kitchen ki ɗibo abinci kici nasan kina jin yunwa, dan da gani ba sai na tambaya ba daga makaranta kike. " Miƙewa Meenat tayi ta nufi hanyar kitchen ɗin tana cewa "wallahi kuwa ina jin yunwa sosai, tun karin safe ban ƙara kai komai cikina ba. " Taɓe baki Mama kaka tayi tace "ku dai kuka sani da wasa da cikinku, in ciwon yunwa ya kama mutum shi zaiji a jikansa ai. " Murmushi Meenat kawai tayi ta shiga kitchen ɗin ta ɗebo abincin ta fito tazo ta zauna kusa da Mama kaka tana ci suna hirarsu irinta jika da kaka. Sai bayan magriba Al'ameen yazo ya ɗauki Meenat suka kama hanyar gida, suna tafe a hanya babu me magana cikinsu wayar Al'ameen ta fara ruri, miƙa hannu yayi ya ɗauki wayar ya ƙara a kunninsa yace "Assalamu alaikhi yah ruhin Al'ameen. " Ai Meenat da sauri ta ɗago kai ta kallesa gabanta na wani irin bugawa, shiko Al'ameen hankalinsa na ga tuƙi ya ci gaba da faɗin "eh mana kece ruhina Basma, bansan lokacin da soyayyarki tayiwa zuciyata mugun kamu ba, da banyi tsammanin zan iya son wata ɗiya mace nan kusa ba, sai kuma gashi da haɗuwarmu dake zuciyata ta mace a soyayyarki, ji nakeyi kamar mun shekara tare ba sati ɗaya ba. Ɗan shiru yayi alamu yana saurare daga ɗaya ɓangaren, zuwa can yayi dariya yace "dan kina son ganina shine sai kin roƙoni, nifa naki ne, karki damu zuwa 8:pm ki zuba idan ganina. " Shiru ya kuma yi sannan yace "ok bye love you. " Sumbatar wayar yayi sannan ya mayar ya ajiye. Meenat kuwa hankalinta in yayi dubu to ya tashi, tunda Al'ameen ya fara waya take ji kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito dan taƙaici, ji takeyi kamar ta ƙwace wayar ta bugata da ƙasa ko kuma ta gaura masa lafiyayyan mari amma babu halin yin hakan, haka kawai taji hawaye suna zubo mata, saurin saka hannu tayi tana sharewa, amma sam sun kasa tsayuwa, Al'ameen kuwa da yake kallonta ta gefen idanunsa jin hawayen nata yakeyi kamar zuban ruwan zafi a jikinsa, to hawayen me takeyi kuma daga jin yana waya ? ya tambayi kanshi, tsaida motar yayi, Meenat najin ya tsayar da motar tayi saurin juyowa tana kallonsa dan ganin me ya tsayar dashi, shima ita yake kallo, saurin yin ƙasa tayi da kanta saboda yanda ya ke kallonta, cikin wani voice yace "Meenat me yasa ki kuka ne.?" Ba tare da ta ɗago da kanta ba tace "babu komai. " Al'ameen yace "kamar ya babu komai.?" Kukan ta ƙara fashewa dashi tare da faɗawa jikinsa tana shashsheƙa, ƙara rungumeta yayi sosai a jikinsa yana faɗin "is ok Meenat, ya isa haka dan Allah, yi shiru ki faɗawa yayanki damuwarki. " Shirun tayi tana ajiyar zuciya ba tare da tace komai ba, cikin damuwa Al'ameen yace "faɗa min meke damunki mana Meenatuna. " Cikin muryar kuka tace "bani da lafiya yayana, zuciyata nayi min ciwo, zafi takeyi min wallahi yayah." Shiru yayi yana kallonta tare dana nazartanta, wasu hawayen ne suke sake zuba mata, hannu ya kai a hankali ya fara share mata hawayen, kafin yace wani abu sai haƙoran Meenat suka fara haɗuwa da juna, ga jikinta daya ɗauki zafi, cikin ruɗewa Al'ameen ya ɗagota yana cewa "lafiya Meenat, me ke damunki. ?" Be jira amsarta ba ya rabata da jikinsa ya kwantar da ita kan seat ya tada motar ya nufi hanyar gida hankinsa a matuƙar tashe, yana tuƙi yana kallonta, ita kuwa lumshe ido tayi hawaye na ci gaba da zuba mata ga kuma haƙoranta da basu bar haɗuwa da juna ba, tambayar kanta takeyi "meke shirin faruwa dani ne, meke damun zuciyata ne game da yayah Al'ameen ? Wayyo ni Meenat Allah karka ɗauro min abinda zaifi ƙarfina. " Cikin mintuna kaɗan suka iso gida, Al'ameen na paka motar ya fito ya buɗe ƙofar seat ɗin Meenat ya ɗauketa yayi cikin gida da ita da sauri, Umma dake zaune a falo ne ta miƙe tana tambayarsa lafiya, hanyar ɗakinsa ya nufa da ita yana faɗin "bata da lafiya ne Umma. " Bayansa Umma tabi tana cewa "subhanallahi meke damunta ne. ?" Al'ameen dai be ce komai ba sai kwantar da Meenat da yayi kan gadonsa ya ɗauko wani akwati ya buɗa fara bata taimakon gaggawa, gwaje-gwaje yayi mata nan ya gano damuwa ce ke damunta har ya janyo mata zazzaɓi, tambayar kansa yakeyi "to damuwar me Meenat ta saka a ranta ne da yake neman janyo mata matsala.?" Haka dai yayi mata allurai har ya samu bacci ya ɗauketa, zama yayi kusa da ita yana kallon kyakkyawan fuskarta, Umma ce dake gefe ta kallesa tace "meke damunta ne Al'ameen.?" Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Umma yace "zazzaɓi ne kawai Umma. " Itama Umman ajiyar zuciyar ta sauke tace "to Allah ya bata lafiya. " Matsawa tayi jikin gadon takai hannu ta shafi wuyar Meenat taji har yanzu jikin nata da zafi saidai be kai time ɗin da suka shigo ba, kallon Al'ameen tayi tace "bari naje nayi sallar isha'i sai na girka mata wani abu me ɗan ruwa ruwa kafin ta tashi. " "To Umma" Al'ameen ya faɗi yana mayar da kallonsa kan Meenat. Bayan fitar Umma ya daɗe zaune yana kallonta tare da saƙa abubuwa da dama kafin ya tashi ya shiga toilet ya ɗauro alola yazo ya kabbara sallah. Yana idar da sallar yaji sallamar Ummi da Abby tare da Abba sun shigo ɗakin, miƙewa yayi yana cewa "barkanku da dare Abby. " Murmushi Abby yayi yace "yauwa barkan ka dai Aminullah, ya me jikin.?" Kallonsa ya kai ga Meenat dake bacci har yanzun yace "jiki da sauƙi Abby. " Ƙarasawa sukayi jikin gadon suna kallon fuskarta, Ummi ce ta kallesa tace "Al'ameen menene ke damunta ne. ?" Ɗan sosa kai yayi yace "wallahi Ummi zazzaɓi ne kawai, muna hanyar dawowa daga gidan Mama kaka kawai sai naga ta fara rawar sanyi shikenan kuma sai zazzaɓi ya rufeta. " Abba ne yace "ayya, sannu kinji ƴata. " Ya faɗa yana shafa kan Meenat dake baccinta. Umma ce ta shigo da sallama hannunta rike da tire ɗauke da abincin da ta girkawa Meenat, ajiyewa tayi sannan tace "har yanzun bata farka ba.?" Ummi ce tace "bata farka ba Umman Meenat. " Murmushi Umma tayi domin tana jin daɗin Ummi ta kirata da Umman Meenat, kallon Al'ameen tayi tace "halan dai kayi mata allurar bacci ne.?" "Eh Umma nayi mata dan ta samu hutu. " Umma tace "yayi kyau, Allah dai ya bata lafiya. " Duka suka amsa da ameen, shiru ɗakin ya ɗauka babu me magana kowa ya zubawa Meenat ido, suna haka sai ga su Aliyu da sauran ƙannin Meenat sun shigo ɗakin da sallama, amsa musu sallamar su Umma sukayi. Dukkansu jikin gadon suka je suna kallon ƴar uwar tasu cike da tausayawa, kowa addu'a samun lafiya yakeyi mata, haka dai suka ta sata a gaba su duka suna jiran farkawanta, daga ƴaƴan har iyayan babu wanda ya iya motsawa. Al'ameen kuwa yama manta da batun zuwa gurin Basma sam, duk kiran da takeyi wa wayarsa bai san ma tanayi ba, hankalinsa da nutsuwarsa duk suna ga ƴar lelen ƙanwarsa Meenat. Sai misalin ƙarfe tara Meenat ta buɗe idanunta, mutanen ɗakin ta fara bi da kallo tana son ta tuno abinda ya sameta, tuno abinda ya faru da tayi ne ya saka hawaye ya fara gangaro mata, da sauri sukayi kanta sunayi mata sannu da jiki, Al'ameen ko jiki na rawa ya fara taɓa jikinta yana cewa "Meenat inane keyi miki ciwo yanzun.?" Girgiza kai tayi alamar babu tana binsa da wani irin kallon tuhuma, murmushi yayi gano inda kallon nata ya dosa ya shafi fuskarta yace "sannu ko ƙanwata, Allah ya ƙara miki lafiya." Ameen su Abba suka amsa dashi yayin da ita kuma ta kasa buɗe baki tayi magana sai binsu da kallo da takeyi, Umma ce ta riƙota tace "taso muje ki wanke bakinki sai kici abinci kisha magani ƴata. " Murya a sanyaye tace "zanyi sallah Ummana. " Murmushi Umma tayi tace "to miƙe mu tafi ɗakina kiyi. " Taimaka mata Umma tayi ta riƙo hannunta ta miƙe suka nufi hanyar fita dafa ɗakin, ƴan uwanta kuwa sai sannu suke jera mata tare da mara musu baya suma suka fice daga ɗakin. Bayan fitarsu Al'ameen zama yayi bakin gado yana tunanin wani irin damuwa ce Meenat ta saka a ranta da har yake neman yi mata illah ? Ganin tunanin bazai kaishi bane ya sa ya miƙe ya je yayi wanka tare da ɗauro alola yazo ya fara jera lafilfili, yanayi wa ƙanwar tashi addu'a tare da kuma addu'ar Allah ya mallaka masa ita matsayin matar aurenshi indai rabonshi ne, dan yau ya hango kishinsa cikin idanun Meenat. Be kwanta bacci ba sai da yaje ya ƙara duba jikin Meenat dake ɗakin Umma dan bata koma gidansu ba. ************** Washe gari jikin Meenat yayi ras har ma ta shirya zuwa makaranta, tafe suke a hanya Al'ameen da yake tuƙi ba tare da ya kalleta ba yace "Meenat damuwar me kika saka a ranki ne haka.?" Kallonsa Meenat tayi taga ba ita yake kallo ba hankalinsa naga tuƙinsa, itama mayar da kallonta tayi ga titi ba tare da tace dashi komai ba, dan bata san me zata ce masa ba, dan itama kanta bata san meke damun nata ba, ita dai kawai abinda ta sani shine tun daga ranar da taƙi amsar tayin soyayyar yayan nata take jin zuciyarta babu daɗi, ga wani abu da yazo ya tokare mata zuci wanda ta kasa gane meye shi, so da dama sai tayi kuka takejin daɗin zuciyarta, kullum dare sai taci kukanta me isarta take iya bacci, bata san meye ke damunta ba balle ta faɗawa wani, wasu hawayene ma a yanzu suke neman sauko mata, da sauri ta mayar dasu. Al'ameen ko da yaji taƙi magana kallota yayi yace "ba kiji abinda nace bane Meenat.?" Itama kallonsa tayi tace "ni babu abinda na saka a raina yayah, yauwa yayah jiya da dare munyi magana da Kamal yake cewa nayiwa su Abba magana zai turo iyayansa. " Tayi maganar ne dan ta kawar da wancen maganar, amma ita ba shi taso faɗawa maganar ba, Umma taso ta samu ta faɗawa sai ta faɗawa Abba, dan yanzu nauyin yayan nata takeji. Al'ameen kuwa jin maganar Meenat yayi kamar saukar aradu, be san lokacin daya saki sitiyarin motar ba, nan suka fara tangal-tangal a saman titi, Meenat babu abinda takeyi sai salati. Cike da kwarewa ya kama sitiyarin ya daidaita motar kan kwalta, yana wani irin huci, Meenat kuwa banda zare ido babu abinda takeyi, har ta jiyo ƙamshin ƙiyama. Babu wanda ya ƙara magana cikinsu har suka isa makarantar, yana paka motar Meenat ta buɗe ta fice da sauri, shima yana ganin ta fita yaja motar a gudun tsiya yabar makarantar. Da kallo Meenat tabi motar har ya fice, hawayen da suka zubo mata tayi saurin sharewa ta nufi aji tana nadamar maganar da ta faɗawa yayanta. Al'ameen kuwa Allah ne kaɗai ya kaisa asibitin lafiya, yana isa ya shige office ɗinsa ya kulle yace wa masinjarsa duk wanda yazo ace baya nan. ********* Bayan kwana biyu Al'ameen da Meenat ɗinsa sun ɗinke abinsu kamar babu komai tsakaninsu, sai dai kowa na zuci na zuci, dan babu wanda zaice babu abinda ke damunsa a zuciyarsa, sai dai Al'ameen koda wasa be faɗawa su Abba kamal yace zai turo ba, itama Meenat ganin beyi mata magana ba ne ga kuma Kamal yana ta takurata yasa taje ta samu Umma ta sanar da ita, koda Umma ta faɗawa Abba cewa yayi ta jira zai ƙara bincike sosai a kansa, bayan Abba yasa anyi masa bincike yace ace masa an bashi dama ya turo, ranar dai da aka faɗawa Meenat rasa meke damunta tayi ita dai bata farin ciki haka bata baƙin ciki, koda ta faɗawa Kamal murna yayi sosai, kwana biyu tsakani iyayansa suka zo, nan akayi komai aka gama aka saka ranar aure wata biyu masu zuwa, nan fa aka fara shirye shirye, Al'ameen ko zama yayi kamar wani mara lafiya, koda iyayan suka tambayesa meke damunsa sai yace babu komai, sai su kuma suka ɗauki hakan a matsayin ya fara kewar ƙanwar tashi ce dan shaƙuwarsu ta wuce misali. Ɓangaren soyayyarsa da Basma kuwa sai abinda ya ƙaru, har zuciyar Al'ameen ba wani son Basma yakeyi ba, kawai dai yana ƙoƙarin cusawa kanshi itane dan yana ganin ƙanwarsa ta kusa yi masa nisa. *Bayan wata ɗaya* Haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya kwanaki na ta ƙaratowa, Meenat tun tana ɗari ɗari har ta saki jikinta ta fara shirye shiryen bikin, domin ita har zuciyarta tana son Kamal, Al'ameen ganin yanda take farin cikine yasa shima ya saki jiki ya tayata, komai ya zama tare dashi sukeyi, shine ya zama kamar ƙawayenta, Suhailat kanta ƴar kallo ta koma. Ana saura sati uku biki Al'ameen ya ɗauketa suka shiga kasuwa yayo mata siyayya na fitar hankali, bata dama yayi ta ɗauki duk abinda yayi mata, haka sukayo siyayya sosai sannan suka dawo gida. Ana saura sati biyi biki, zaune Meenat take da Kamal a farfajiyar gidan su Al'ameen suna hirar yanda bikinsu zai kasance, duk fuskokinsu cike yake da annuri, motar Al'ameen ne ta shigo cikin gidan, tunda ya hangosu zaune yaji zuciyarsa tana yi masa zafi, Allah ya gani yana son Meenat yana kuma kishinta babu yanda zaiyi ne dole yasa ya haƙura dan farin cikinta. Itama Meenat tunda taga shigowar motar nashi hankalinta ya koma kanshi, idanunta ƙyar akan motar har Al'ameen har ya buɗe ya fito, Kamal sai magana yakeyi mata amma hankalinta ya tafi ga yayanta. Murmushi Al'ameen ya sakar mata lokacin da suka haɗa ido, itama murmushin ta sakar masa wanda ya bayyana fararen haƙoranta, miƙewa tayi ta fara takawa tana isa gareshi, shima takowar yakeyi, suna zuwa kusan juna suka ja suka tsaya suka zubawa juna ido cike da ƙauna, Meenat ce ta kai hannu ta kamo hannun Al'ameen tana faɗin "sannu da dawowa yayana, tawo muje ku gaisa da Kamal. " Binta yayi suka nufi inda Kamal ke zaune hannunsu sarƙe da juna. Muje zuwa🥰 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 My Bk ina tayaki murnar kammala littafinki me suna *NA BAKI RAYUWATA* haƙiƙa littafin ya faɗakar kuma ya ilmantar sannan ya taɓa zuciyar me karatu, Allah ya baki ladar faɗakarwa ya yafe miki kurakuren ciki, fatan alkhairi gareki Raheenat na yinki kuma tana ƙaunarki❤ Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 9 Shiko Kamal ido ya zuba musu yana kallo har suka ƙaraso gabansa, ransa ne ya ɓaci da ganin yanda Meenat ta riƙe hannun Al'ameen, kishin Al'ameen ya keji har ƙasan ransa. _Ni ko nace kayi a banza_ Hannu Al'ameen ya miƙa masa suka gaisa fuska ɗauke da fara'a, shiko babu yabo ba fallasa ya amsa, kallon Meenat Al'ameen yayi wacce take riƙe da hannunsa har lokacin yace "Meenatu na bari na shiga ciki na watsa ruwa. " Kallon Kamal tayi ba tare da ta saki hannun Al'ameen ba tace "Kamal bari naje na haɗawa yayana ruwan wanka na basa abinci na dawo. " Zunbur ya miƙe tsaye yace "tafiya ma zanyi yanzu, ma ƙarasa maganar tamu ta waya kawai." Meenat tace "ok sai munyi wayar, yayah zo muje. " Tana gama faɗin haka taja hannun Al'ameen sukayi cikin gida suka bar Kamal tsaye. Da ido Kamal ya bisu da kallo, sai da ga shigewarsu sannan ya juya ya shiga motarsa ransa a ɓace, tun ba yau ba yake kishin Al'ameen, saboda yawan ambatonsa da Meenat takeyi a duk lokacin da suke tare. ******* Su kuwa su Meenat suna shiga ɗakinsa ta sake hannun Al'ameen taje ta haɗa masa ruwan wanka kamar yanda ta saba, fitowa tayi ta kallesa tace "yaya na haɗa, bani wayarka nayi game. " Murmushi yayi ya saka hannu a aljihu ya ciro wayarsa ya miƙa mata yana faɗin "Meenat kenan sarkin game. " Murmushi tayi tana cire key ɗin wayar tace "kayi wankar ka fito ina jiranka a falo. " Tana gama faɗin hakan ta fito a bedroom ɗin nasa ta dawo falonsa ta zauna saman kujera ta hau buga game ɗinta cikin farin ciki. Tana tsaka da buga game ɗin wayar ta fara ruri, *my love* shine sunan da ya bayyana saman screen ɗin wayar, nan take annurin fuskar Meenat ya ɗauke, ranta ne taji ya ɓaci, kallon wayar takeyi ba tare da tayi yinƙurin ɗauka ko kashewa ba har kiran ya yanke, wani kiran ne ya ƙara shigowa again nan ma bata ɗauka ba sai kallo wayar da takeyi zuciyarta nayi mata zafi, kira na uku na shigowa wayar ta ɗauka a fusace tace "ke wata irin wawiya ce wai, kin kira sau biyu ba a ɗaga ba amma ba zaki haƙura ba sai kin ƙara kira, to ne wayar baya kusa banza mayya kawai. " Tana gama faɗin haka ta yanke kiran tana huci ita ɗaya. Ɓangaren Basma kuwa sandarewa tayi zaune ta kasa cire wayar a kunninta, mamaki da al'ajabine ya kamata, "to wacece wannan ta ɗaga wayar Al'ameen har take zaginta, Ita ce wawiya kuma mayya? Me yakai wayar Al'ameen hannun mace ? Take taji itama ranta ya ɓace, zagin da Meenat tayi mata yafi komai ɓata ranta, lallai Al'ameen yama raina mata wayo. Meenat kuwa miƙewa tayi cikin ɓacin rai ta koma cikin bedroom ɗin, tana shiga Al'ameen na fitowa daga toilet ɗaure da towel, da saurin ta juya masa baya tana kallon ƙofa ta miƙo masa wayarsa tace "ga wayarka ana kiranka." Takawa yayi ya buɗe wardrobe ɗinsa ya ciro wata jallabiya ya zura sannan yace "to juyo ki bani wayar. " Juyowa tayi tana turo baki gaba ta miƙa masa wayar, amsa yayi yana kallon fuskarta, ba ta jira komai ba ta juya da sauri tabar ɗakin tare da bugo masa ƙofa da ƙarfi, da kallo ya bita har ta fice sannan ya dawo da kallonsa ga wayar yana duba wanda ya kirasa, ganin kiran daga Basma ce yasa ya saki murmushi yana ƙara kallon ƙofa. Zama yayi bakin gado ya dannawa number Basma kira, cikin sauri ta ɗaga zatonta yarinyar da ta ɗaga ɗazun ne dan ta shirya cin mutuncinta, jin muryar Al'ameen ne ya sakata saurarawa, ba jira uzirin ta yake karanta mata ba ta jefo masa tambayar "wacece ta ɗaga wayarka ɗazun dana kira.?" Ɗan jim yayi kafin yace "ina ganin Meenat ce ta ɗaga kiran." "Meenat!!" ta maimaita. "Eh Meenat nace." "Wacece Meenat ɗin.?" Basma ta tambaya. Murmushi Al'ameen yayi yace "ƙanwata ce, ta faɗa miki wani abu ne.?" Saurin cewa a'a Basma tayi saboda wani tunani da tayi sannan tace "amma zan so ganinta. " Murmushi yayi me sauti yace "aiko zan kawo miki Meenat ɗina ki ganta. " Itama murmushin tayi tace "yanda na lura kamar kana son ƙanwar nan taka. " Lumshe ido Al'ameen yayi ya buɗe yace "kamar raina haka nake sonta. " Ɗif Basma tayi na ƴan sakwanni kafin tace "kai irin wannan soyayya haka, kuma ɗakinku ɗaya.?" Ɗan murmushi yayi yace "ƙwarai ma kuwa. " Wani irin ajiyar zuciya Basma ta sauke wanda saida Al'ameen yaji sautinta, murmushi ya kuma yi sannan yace "zan kiraki zuwa anjuma. " "Ok bye" tace sukayi sallama suka ajiye wayar. Al'ameen yana ajiye wayar ya miƙe ya fara shiryawa yana tunanin yanda Meenat ta fita ɗakin da ta bashi wayar. ************ *Bayan kwana biyu* Shirye shiryen biki na ci gaba da tafiya yanda ya kamata yayin da bikin ya rage saura kwana goma sha biyu, kwanakin auren na matsowa Al'ameen na kallon Meenat ɗinsa tana ƙara yi masa nisa, kuma cikin kwanakin ne gidan su Basma suka buƙaci daya turo magabatansa, jin abin yakeyi kamar a mafarki, dan haka ya kasa tunkarar su Abby da maganar, ganin dai lokaci na tafiya kuma ba samun Meenat zaiyi ba yasa kawai ya tunkari iyayan da maganar, Abba yayi farin ciki sosai dan dama ya ƙosa ɗan nasa yayi aure, yace masa Abba yayi yace mata ta gaya mu iyayan nata suyi haƙuri a gama hidimar bikin ƙanwarsa sai suje ayi komai, dan lokacin ya rage saura kwana takwas ne bikin Meenat. Meenat ko da taji labarin gidansu budurwar yayanta sunce ya turo gaba ɗaya yinin ranar ba tayi sa cikin farin ciki ba, cikin damuwa da ƙuncin rai ta yini, ko magana ranar taƙiyi wa Al'ameen wai ita tana fushi dashi. _Ni ko raheenat nace ashe babu daɗi Meenat, Allah ya bawa yayah Al'ameen haƙuri_ Da yamma misalin ƙarfe huɗu zaune suke inda suka saba zama da Kamal in ya zo, hirar bikinsu kawai sukeyi da irin event ɗin da za suyi, duk da cewa Meenat ɗin ba amsashi takeyi sosai ba, dan gaba ɗaya hankalinta ya tafi wani gurin ne daban. Shigowar Al'ameen gidan ne ya ɗauki hankalinta, sanye yake cikin ƙananun kaya wanda sukayi matuƙar yi masa kyau, ko kallon inda suke beyi ba ya nufi cikin gidan, ita kuwa shi take kallo kamar zata haɗiyesa, nan take zuciyar Kamal ta harzuƙa, cikin ɓacin rai yace "Meenat!!" Yanda ya kira sunantan ne da ƙarfi yasa ta juyo da sauri tana kallonsa tare ta cewa "lafiya.?" Wani kallo ya jefeta dashi sannan ya miƙe tsaye yace "lafiyarce ta kawo haka, ni na rasa gane meye tsakaninki da yayanki da kina ganinsa kika susucewa ki fita a haiyacinki, koni bakya susucewa in kin ganni kamar yanda kikeyi in kin ganshi, na gaji wallahi, haba na gaji!!. " Kallonsa ta ci gaba dayi da mamaki ba tare da tayi magana ba, shiko hakan ba ƙaramin harzuƙasa ya ƙarayi ba, dogon tsaki yaja ya juya a fusace ya nufi gurin motarsa, Meenat ba tayi yunƙurin dakatar dashi ba ko yi masa magana ba sai kallo da ta bisa dashi har ya shiga motarshi ya fice daga gidan, jikinta a matuƙar sanyaye ta miƙe ta nufi cikin gida itama tana tunanin maganganun Kamal. Da dare suna zaune a falo suna hira, Meenat dake kusan Al'ameen wayarta ce a hannunta tana daddannawa duk da har lokacin jikinta a sanyaye yake, tambayar duniya su Umma suyi mata tace babu komai, haka suka gaji suka ƙyaleta. Ba tare da zato ba kawai sai gani sukayi Meenat ta saki wayarta ƙasa tare da sakin wani ƙara ta zube gurin sumammiya, Al'ameen dake kusanta ne yayi saurin yin kanta yana kiran sunanta tare da jijjigata, gaba ɗaya mutanen falon hankalinsu yayi masifar tashi, Abby ne cike da ruɗewa yake faɗin "Al'ameen ɗauketa muje asibiti. " Ɗaukar wayarta yayi wacce take kusa da ita sannan ya saɓeta da sauri yayi waje da ita, duka mutanen falon suka rufa masa baya, a mota ya sakata su Abby suka shiga yaja suka nufi asibitinsa. Da zuwansu likitoci suka karɓeta suka shige da ita, Al'ameen baiyi yinƙurin binsu ba danshi a ruɗe yake yasan ko ya shiga bazai iya komai ba, kai kawo sukeyi gaba ɗaya a bakin ɗakin hankali a tashe, Al'ameen ne ya ciro wayar Meenat dake aljihunsa ya fara dubawa dan shi yasan ko meye ya firgita Meenat to daga wayar ya fito domin shine a hannunta lokacin da abin ya faru. Yana buɗawa ya ci karo da wani saƙo, duba numbern da ya turo saƙon yayi sannan ya fara karantawa kamar haka..... Muje zuwa🥰 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 10 _Meenat!!, ina so kiyi haƙuri da abinda zai fito daga bakina, nasan ba lale yayi miki daɗi ba, amma ya zama dole na faɗa miki, gaskiya Meenat bazan iya aurenki ba a halin da ake ciki yanzu, badan komai ba sai dan gano akwai wani halaƙa me girma tsakaninki da yayanki, ba tun yau ba nake karanto wasu abubuwa a cikin idanunku ke dashi, nasha zama nayi tunani to soyayya kukeyi ne da juna ? Sai zuciyata ta bani amsa da cewa a'a, domin da soyayya kukeyi ba zaki amshi soyayyata ba, to kuma in son junanku kukeyi ai yaci ace kun bayyana wa kanku sirrin zuciyoyinku dan ba yau kuke tare ba, domin in wani cikinku ya kasa gane kuna son junane wani zai gane, in nayi wannan tunanin sai naji zuciyata na raya min abubuwa masu yawa, har zuciyata ta fara zargi akanku anya babu wani alaƙa a tsakainku kuwa, domin kuwa shaƙuwar taku tayi yawa, zuciyata bata ƙara tabbatar min da zargina ba sai ranar da kike cemin zaki je ki haɗa masa ruwan wanka, wani abune naji cikin raina, akan me zaki rinƙa haɗa masa ruwan wanka alhali shi ba mijinki bane yayanki ne kawai, tun daga wannan rana zuciyata take ƙara zarginku, to yau dai Meenat zuciyata ta gama tabbatar min da zargina kuna wani mummunan mu'amula ne da yanyanki a ɓoye shi yasa bakwa son damuwar juna, shi yasa kuke bawa junanku kulawa tare da nuna tsantsan soyayya wa junanku, to ni dai bazan iya auren ragowar wani ba, ina yi miku fatan yin aure da ke da yayanki ko kwabar fasiƙanci da juna, Allah ya shiryaku yasa ku gane, na yafe miki komai da na kawo domin aurenki, in yayanki zai iya kwansanki sai ya aura na bar masa ke ba wai dan bana sonki ba, aa sai dan bazan iya auren matar da ta rasa darajarta ba_ Daga Kamal Zuciyar Al'ameen ne ke tafasa, saƙon ba ƙaramin tunzura shi yayi ba, ji yakeyi ina ma Kamal ɗin na gabansa ne yayi wannan maganganun, da wallahi yau me ƙwatansa a hannunsa sai Allah, ya rasa irin zargin da zaiyi musu shi da ƙanwarsa sai zargin zina, zinan ma wai da Meenat, idanunsa ne suka haɗa sukayi jajir jijiyoyin kansa suka miƙe, kulle idonsa yayi ƙam yana jin ziciyarsa nayi masa zafi, muryar wani daga cikin doctors ɗinsa yaji yana cewa "doctor ta farfaɗo. " Da sauri ya buɗe idanunsa waɗanda sukayi jajur, be jira kuma me wannan doctor zai ƙara faɗa ba ya nufi ɗakin da sauri su Abba suka mara masa baya suma. Da sauri ya isa gadon da Meenat ke kwance tana rusan kuka, tana ganin yayan nata tayi saurin mikewa ta faɗa jikinsa ta ƙara fashewa da wani kukan, shafa bayanta kawai Al'ameen yakeyi ya kasa magana, jin kukanta yakeyi har ƙasan ransa, suko su Umma tsayawa sukayi suna kallonsu babu wanda yayi magana, domin sun san tsakanin Al'ameen da Meenat sai Allah, cikin kukan Meenat take faɗin "yayah Al'ameen Kamal yace ya fasa aurena, kuma be tsaya a nan ba sai da..da...da...yac..." Al'ameen ne yayi saurin rufe mata baki dan baya son su Abba suji yace "Shiiiiiii..., nasan komai ƙanwata, Allah ne kawai zaiyi mana sakayya, shima insha Allahu sai ayi masa abinda yayi mana. " Kuka Meenat takeyi sosai tace "yaya dama mutane kallon da sukeyi mana kenan dan kawa dan kawai mun shaƙu da juna.?" Girgiza mata kai Al'ameen yayi saurin yi yana cewa "a'a ƙanwata a'a, shima ɗin mummunar zato ne, kiyi shiru kibar kuka dan Allah. " Abba ne ya kallesu cikin ɗaurewar kai yace "me nake ji kuna faɗa ne wai, Kamal ɗin ne ya faɗa da bakinsa ya fasa aurenta.?" Al'ameen ne ya raba Meenat da jikinsa ya nufi kan gadon da ita ya zaunar, sannan ya kalli Abba yace "eh Abba, Saƙo ya turo mata akan ya fasa auren, sannan kuma ya ƙara da cewa wai..." sai kuma yayi shiru. "Wai mene?" cewar Abby yana tsare Al'ameen da ido rai a ɓace. Haɗiye wani mugun yawu Al'ameen yayi yace "wai shi ba zai iya aurenta ba saboda yana tunanin wani takeso ba shi ba. " Cikin ɓacin rai da ƙunar zuci Abba yace "aikin banza aikin wofi, kaji wani maganar banza anan, in ba ta sonsa zata kawosa ne har ayi maganar aure, kawai dai yace shi ɗan ƙananun mutane ne wanda basu san darajan ɗan adam ba. " Umma itama cike da takaicin abinda Kamal yayi tace "ƙwarai kuwa, amma in ba haka ba menene, kawai dan tana son wani sai yace ya fasa aurenta, wannan ma ai sakarci ne. " Matsawa Abba yayi kusa da gadon yace "kiyi haƙuri ƴata ki bar kuka, insha Allahu babu abinda zai hana auren ki, in shi yace baya so akwai masu so da yawa, insha Allahu nan da kwana takwas za a ɗaura auren kamar yanda aka saka. " Kallonsa su Abby sukeyi da mamaki, yayin da Abby ya buɗe baki yace "dawa kenan za'a ɗaura yaya.?" Murmushi Abba yayi yace "da wanda ya dace mana, kuma wanda yake sonta, zan zaɓawa ƴata miji wanda ya dace da ita wanda zai riƙeta da amana ya bata kulawa ko bayan ba ranmu, in ma kunya yake son bamu to yayi ƙarya. " Ajiyar zuciya Abbyn Meenat ya sauke zuciyarsa na saƙa masa abubuwa masu yawa, ba tare da ya ƙara cewa yayan nasa komai ba, itama Umma da nata tunanin sai dai ba tace komai ba, domin tasan halin Abba sarai in yayi ƙudiri babu me sauya masa ƙudirinsa. Kallon kallo akeyi tsakanin Al'ameen da Meenat, yayin da gaban Al'ameen ke dukan tara-tara. Umma ce ta riƙo hannun Meenat tace "sannu ƴata, kiyi haƙuri kinji. " Ɗaga wa Umma kai tayi har lokacin hawaye na zuba mata dan ƙazafin da Kamal yayi mata da yayanta yana yi mata zafi a ranta, ga kuma Abba da ke neman ƙara sakata cikin wani cakwakiya ko dawa zai ɗaura mata aure oho, Umma ce ta kalli Al'ameen da yake cikin tunanin waye Abba zai bawa Meenat tace "Al'ameen zamu iya tafiya gida ai ko.?" Da sauri ya ɗago kai yace "eh Umma." Riƙo hannun Meenat tayi ta tayar da ita tace "miƙe a hankali muje ƴata. " **************** Bayan sun isa gida ne Abby ya samu Abba a ɗakinsa yace "Yaya wai waye kake son bawa auren Meenat ne.?" Kallon Husainin nasa sosai Abba yayi yace "Husaini ina tunanin tun ɗazun na baka amsa, nace maka zan zaɓa mata mijin da ya dace da ita, koko kana son ka nuna min Meenat ƴarka ce.?" Murmushi Abby yayi yace "haba dai yaya, ni ai bani da wata ƴa, kawai dai ina son nace ne a ganina babu wanda ya dace da Meenat kamar Al'ameen, shine wanda yakeyi mata son da bazai taɓa barin wani abu ya cutar da ita ba, kuma shine nake da tabbacin ko bayan ranmu zai riƙe Meenat ba zai wulaƙantata ba. " Murmushi Abba yayi me ɗauke da ma'anoni yace "shi Al'ameen da kansa yace maka yana son auren Meenat, ya taɓa zuwa ya tunkare ɗaya daga cikin mu ya nuna masa yana sha'awar ya aureta ? Amsa a'a, kenan hakan ya nuna baya son aurenta, soyayyar da sukeyi wa junansu na ƴan uwantaka ne da kuma tsantsan shaƙuwa, kana kallo Meenat ta kawo mana wannan yaron matsayin mijin da takeson ta aura amma hakan be saka Al'ameen yazo ya nuna yana son aurenta ba ko dan tsoran karya rasata, to a hakan ne kake cewa na basa ƴata ? Al'ameen baya son Meenat so na aure Husaini, dan haka ina son kabar maganar nan anan, akwai mijin dana zaɓawar ƴata kuma insha Allahu ba za a ɗaga ko a rage ranar ba daga yanda aka saka ba kawai dai kuje a ci gaba da shirye shirye. " Shiru Abby yayi yana jujjuya maganar Abba, kafin ya nisa yace "amma yaya duk da haka Al'ameen shine wanda ya dace da auren Meenat, ba tun yau zuciyata ke sha'awar haka ba, amma rashin nuna mana da yaran ba suyi suna son auren juna ba yasa nayi shiru, to yanzu kuma dama ta bada me zai hana ba zamu basa ba.?" Jingina kansa Abba yayi da kujerar da yake zaune yace "Husaini ni dai na gama maganata. " Badan ran Abby yaso ba ya miƙe yace "shikenan yaya tunda haka kace. " Yana gama faɗar hakan ya fice daga ɗakin. ******* Ɓangaren Al'ameen da Meenat kuwa gaba ɗayansu sun shiga tsaka me wuya, kowa ya shiga tunanin waye Abba zai haɗa Meenat dashi, ita Meenat hankalinta a tashe yake bata san waye za'a bata a matsayin miji ba, shi kuma Al'ameen tsoro ya shiga kar a bawa Meenat wani ba shi ba, dan sai da wannan abin ya faru ne yake jin ƙarin soyayyar ƙanwarsa tare da karfin gwiwar aurenta. Da dare ya samu kira daga gurin Abby, ba tare da ɓata lokaci ba yaje domin jin kiran da yakeyi masa, bayan ya zauna ne Abby ya kallesa yace "Al'ameen kasan abinda yasa na kiraka.?" Cikin girmamawa yace "a'a Abby." Gyara zama Abby yayi yace "to abinda yasa na kiraka tambayarka nake sonyi kana son Meenat so na aure.?" Da sauri Al'ameen ya ɗago kai ya kalli Abby sannan yayi ƙasa da kansa cikin jin kunya yace "eh Abby ina sonta." Kallonsa sosai Abby yayi sannan yace "kana sonta ne amma duk tsawon lokacin nan baka taɓa magana ba, kasan abinda rashin bayyanarka ya janyo maka kuwa. ?" Kansa na ƙasa still yace "Abby na faɗawa Meenat ina sonta, amma sai ita ta nuna bata son aurena, to ni kuma nafi son farin cikin Meenat fiye da komai shi yasa nayi shiru ban faɗa muku ba. " Kallonsa Abba yayi da mamaki yace "ai wannan shirme ne, ta yaya zaka biye mata ka cutar da kanka, to ai gashinan kana gaf da rasata, domin koda abin nan ya faru nayi tunanin haɗaku aure amma yaya yace sam be san wannan magana ba, kuma kai kafi kowa sanin bana taɓa musu da duk abinda yaya ya yanke kamar yanda nima in na kawo abu baya musawa, shawara zan baka yanzu kaje ka samesa ka roƙesa ya baka auren Meenat, domin ni nafi son Meenat da kai, ta hakan ne kaɗai nake ganin yaya zai yarda ya aura maka Meenat. " Al'ameen cike da jin daɗin shawarar Abby yayi godiya ya miƙe ya fice, da kallo Abby ya bisa tare da fatan Abba ya yarda ya basa auren Meenat domin yasan yaran suna son junansu sosai. *********** Al'ameen be samu zuwa ga Abba ba sai washe gari da safe, bayan ya samu Abba da batun yana son Meenat, mursisi Abba ya shafa wa idanunsa toka yace bazai bashi ba sai dai yayi haƙuri, domin kuwa ya riga da ya sanarwa wanda yayi niyar bawa auren Meenat tun jiya, dan haka shi ba zai zama ƙaramin mutum ba, ba zaiyi magana ya sauya ba, magiya Al'ameen yakeyi sosai amma Abba yace be san wannan ba yayi haƙuri kawai, me yasa tun farko be nuna yana son aure nata ba sai yanzu, har da tambayarsa da Kamal be ce ya fasa ba to ya zaiyi kenan, Al'ameen kuwa da idanunsa suka kawo ruwa yace "dama zan barta ta auresa ne domin farin cikinta dan farin cikinta yafi min komai Abba. " Murmushi Abba yayi yace "to yanzun ma sai ka ƙyaleta a karo na biyu domin farin cikin nata, dan nasan mijin dana zaɓa mata zatayi farin ciki sosai dashi. " Hawaye suka zubo wa Al'ameen yayi saurin sharewa ya kalli Abban nasa yace "Abba in dai har Meenat zatayi farin ciki wallahi na sadaukar da soyayyata domin farin cikinta, tayi farin ciki Abba, hakan kawai ya ishi Al'ameen. " Yana gama faɗin hakan ya miƙe ya fice daga ɗakin yana layi, cike da tausayi Abba yabi ɗan nasa da kallo har ya fice, shi kansa yana son auren Al'ameen da Meenat sai dai aikin gama ya riga ya gama. ********** Tun daga wannan rana Al'ameen ya zama bashi da wani walwala, gaba ɗaya ya zama wani iri, kallo ɗaya zakayi masa kasan yana cikin damuwa matsananci. Meenat ma dai a nata ɓangaren tana cikin mawuyacin hali, abubuwa ne da dama suka haɗu suka haɗe mata, na farko ga rabuwarta da Kamal duk da cewa a yanzu tsanansa takeji fiye da komai da kowa saboda zargin da yakeyi mata ita ta yayanta, na biyu kuma ga rashin sanin waye za'a ɗaura mata aure dashi har yau da ya kasance saura kwana huɗu bikin, ga kuma soyayyar yayanta da yanzu ta tabbatar ta kamu dashi, kamu bana wasa ba, ga kuma halin da take ganin yayan nata a ciki, dan gurin Umma ta samu labarin duk yanda sukayi shi da Abba, yanzu ma kwance take kan gado tana rusan kuka kamar ranta zai fita, yanzu tafi buƙatar mutuwanta fiye da komai dan tana gani shine kawai zai rabata da soyayyar yayan nata. Tana jin motsin buɗe ƙofar ɗakin amma ko ta ɗago da kanta, kukanta kawai take ci gaba dayi, Suhailat da ta shigo tsayawa tayi tana kallonta kafin ta taka a hankali jiki a matuƙar sanyaye ta zauna bakin gadon ta kira sunanta, bata amsa ba kuna bata daina kukan ba, ajiyar zuciya Suhailat ta sauke cikin matuƙar tausayin ƙawar nata tace "dan Allah Meenat kiyi haƙuri ki daina kukan nan, kuka fa babu abinda zaiyi miki. " Ɗago da jajayen idonta tayi ta kalli Suhailat tace "kuka kam yana magani Suhailat, in abu ya isheka sai kayi kukan kake samun sausauci, Suhailat ki faɗa min ya zaiyi da raina, ina zai kai soyayyar yaya Al'ameen ?" hawaye ne suka ciko wa Suhailat a ido cikin rawar murya tace "kiyi haƙuri Meenat " da ƙarfi tace "haƙuri!! Haƙuri fa kike cewa nayi Suhailat, ta yaya zan iya haƙuri da soyayyar yayana Al'ameen, ko kin manta ne *ni da yaya Al'ameen* jininmu ɗaya ne, tare muka tashi tare muke komai .?" buga kanta tayi da ƙarfi jikin gado tana faɗin "me yasa ne sai da lokaci ya ƙure min na gane ina son yayah Al'ameen, me yasa zai da ake gaf da raba mu na keji ba zan iya rayuwa da ko wani ɗa namiji ba sai shi, me yasa ban gane ina yiwa yayana son da zan iya bada rayuwata saboda shi ba sai yanzu ? Me yasa, me yasa,? Lallai ni na cika babban shashasha wawiya, wayyo ni Meenat ina san saka rayuwata ne. ?" Riƙota Suhailat tayi itama tana kuka tana faɗin "dan Allah meenat ki dawo haiyacinki, ya kike abu ne kamar wata mara ilimi. " Faɗawa tayi jikin ƙawar tata tana ci gaba da gunjin kuka.... Nima dai hawaye yaƙi barina na ci gaba da yi muku typing readers😭😭😭, Allar sarki Ameenatuna kiyi haƙuri ƙaddararku kenan hakan.😭 Muje zuwa 🥰 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 11 Da ƙyar Suhailat ta samu ta rarrashi Meenat tabar kukan, sai ajiyar zuciya kawai take saukewa, a hankali ta miƙe ta shige toilet. Ta daɗe tana wanka kafin ta fito ta saka wata doguwar riga, ko mai bata shafa ba ta nufi ƙofa, Suhailat da take zaune ne tace "ina zaki je Meenat.?" Waigowa tayi ta kalleta da idanunta da sukayi luwu-luwu saboda kukan da tayi, cikin sanyin murya tace "zanje na ga yah Al'ameen ne, nasan yau lahadi be fita asibiti ba. " Ajiyar zuciya Suhailat ta sauke cike da tausayin ƙawar nata tace "to ni bari na wuce gida, sai gobe zan dawo mu tattauna akan abinda ya kamata muyi." Tare suka fito ɗakin Suhailat tayiwa Ummi sallama sannan suka fito, gidansu Al'ameen Meenat ta shiga ita kuma Suhailat ta kama hanya domin tafiya gida. ******* Da sallama ta tura ƙofar falon nashi ta shiga, zaune yake yana aiki a computer ɗinsa, ɗagowa yayi yana kallonta har ta ƙaraso kusa dashi ta zauna, ajiyar zuciya Al'ameen ya sauke tare da mayar da hankalinsa kan computernsa ya ci gaba da abinda yakeyi ba tare da yace mata komai ba, wasu ƙwalla ne suka ciko idanunta tayi saurin mayar dasu tace "sannu da aiki yayah. " Be ɗago ba yace "yauwa." Ƙara matsawa tayi kusa dashi tace "yayah ya yafe min laifina dan Allah. " Still be ɗago ba yace "laifin me.?" Shiru tayi ta kasa magana kuma, ɗan ɗago da kansa yayi ya kalleta sai kuma ya mayar ya ci gaba da abinda yakeyi, hawaye Meenat ta fara cikin muryar kuka tace "yayah baka sona yanzu ko, kana ji a ranka ka tsaneni ko, ba ka son na zo kusa da kai ko.?" Yanayin yanda tayi tambayar yaso bawa Al'ameen dariya duk da yanda yake jin zuciyarsa kuwa, rufe computern yayi ya ajiye ya juyo yana kallonta sosai, hannu yasa yana share mata hawayen cike da kulawa yace "ko ɗaya Meenat, sam yayanki be tsaneki ba, kuma be daina sonki ba, Meenat in dai zan iya daina sonki to tabbas zan iya daina son kaina, sai dai bazan ɓoye miki ba Meenat ina jin haushinki sosai saboda kece kika jawo mana komai, da a lokacin da na zo miki da soyayyata kin amsa da yanzu na tabbatar mun zama mata da miji, amma babu komai Meenat, na yarda da ƙaddara, nasan komai na Allah ne, Allah ne ya ƙaddaro haka, dama can ya rubuta hakan sai ya faru, Meenat ina son farin cikinki fiye da yanda nake sonki, na barwa Kamal ke ne dan ina tsammanin zakiyi farin ciki da aurenshi, sai kuma Allah ya juya al'amarinsa, yanzu Meenat kin zama allurar cikin ruwa me rabo ka ɗauka, duk da ta wani ɓangaren ba zance haka ba, saboda Abba yace ya zaɓa miki miji, kenan wanda aka zaɓa mikin shine be rabon, Meenat ina sonki ba kuma zan taɓa daina sonki ba sai ranar da numfashina ya bar gangar jikina, soyayyarki a cikin jinina yake, inayi miki fatan samun farin ciki tare da soyayya ga duk mijin da zai aureki. " Ya kai ƙarshen maganar hawaye na zubo masa. Faɗawa jikinsa Meenat tayi tana sakin kuka me taɓa zuciyar me sauraranta, cikin kukan tace "yaya ina sonka, ina ganin in dai ban sameka ba sonka shine zai zamo ajalina, wallahi yaya jin zuciyata nakeyi kamar zata fashe, yaya kayi wani abu dan Allah kar ka bari a rabamu, pleace yaya pleace." Rungumeta shima yayi sosai a jikinta yana kukan, faɗi yakeyi "bazan iya komai ba Meenat, ba zan iya ba, Abby ma ya kasa balle ni Meenat. " Haka dai sukayi ta kukansu abinsu babu me rarrashin wani, da kansu suka bawa kansu haƙuri sukayi shiru suna ajiyar zuciya, ita ko Meenat wani a zababben ciwon kaine tare da zazzaɓi ya rufeta, Al'ameen ne ya taimaka mata da magani ta sha har bacci ya ɗauketa a jikinsa, ƙara rungumeta yayi a jikinsa yana kallon fuskarta zuciyarsa na harbawa da ƙarfi. ********** Haka dai aka ci gaba da shirye shiryen bikin cikin rashin armashi, domin kuwa fitullun gidan basa cikin farin ciki, dan haka rashin walwalarsu ta shafi kowa, shi kansa Abba baya jin daɗin yanda yake ganin mutanen gidan, domin fuskar kowa zaka kalla ka ga rashin walwala. Aisha da bilkisu (ƙannin Al'ameen) da Umma ne zaune a falo suna hira, Aunty Aisha ce tace "ni wallahi sam bana farin ciki da wannan biki na Meenat. " Cikin nuna alhini Bilkisu tace "to waye kika ga yana farin ciki da bikin Aunty Aisha ? Gara ma lokacin da auren da waccen ɗan iskan za'ayi kowa be nuna damuwarsa ba saboda ita ta kawo tace tana so, kuma lokacin yah Al'ameen be nuna komai ba, amma yanzu babu wanda yasan dawa za'a haɗata sai shi Abba, kuma gashi ita da yah Al'ameen suna cikin wani hali, ni wallahi Abba mamaki yake bani, ƙiri-ƙiri kaƙi ɗanka ka bawa wani. " Murmushi Umma tayi tace "ƙila shi da abinda ya hango wanda mu ba mu hango ba. " Cikin ɓacin rai Aisha tace "wani abu ne zai hango Ummi ? Wallahi babu wani abinda ya hango kawai dai dama be niyar bawa yah Al'ameen ba ne. " Umma ce tace "to koma dai miye ai ya riga ya yanke hukunci ko, kuma babu wanda ya isa ya sauya masa, Al'ameen dai da Meenat ƴaƴansa ne kuma yana da ikon yin komai a kansu. " Tana gama faɗin haka ta miƙe ta nufi ɗakinta ta barsu suna ci gaba da tattaunawa akan al'amarin. ********** Juma'a ana ya gobe ɗaurin aure aka gabatar da shagalin al'adar shuwa, shagali akeyi da amarya kaɗai ba tare da ango ba saboda wani uziri nasa daya gabatar, abin ya ƙayatar matuƙa sai dai duk abinda akeyi fuskar amarya babu wani ɗigo na farin ciki a cikinsa. Da dare misalin ƙarfe tara Abba ne ke kai komo a ƙayatatcen falonsa fuskarsa cike da ɓacin rai yayin da Abby ke zaune saman kujera ya zubawa Hassan ɗin nasa ido yana jira yaji meye dalilin kiran da yayi masa. Ganin kai kawon yaƙi ƙarewa ne yasa ya buɗi baki yace....." Wash na gaji _Yau dai wlh banyi niyar typing ba kwata kwata saboda wasu dalilai, amma saboda masu tambayar ni da yaya Al'ameen sunyi yawa yasa nace bari na tafa muku ko kaɗan ne, dan hausawa kance da babu gwara ba daɗi🤣_ Muje zuwa tare da ƴar mutan zazzau😘🌹 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga dukannin makaranta littafin ni da yaya Al'ameen, kusani raheenat na yinku a duk inda kuke ku huta kuji daɗinku kawai guys🤝💘 Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 12 Ganin kai kawon yaƙi ƙarewa ne yasa Abby ya buɗi baki yace "wai yaya me ke faruwa ne.?" Tsayawa Abba yayi cak ya kalli Abby fuskarsa har lokacin na nuna ɓacin rai yace "nayi kuskure Husaini da naƙi ɗana naso ɗan wani, wai ace kamar ni Alhaji Musbahu zai watsawa ƙasa a ido. ?" Da mamaki Abby ke kallon Abba yace "nifa ban gane inda ka dosa ba yaya, me Alhaji Musbahun yayi maka ne.?" Zama yayi saman kujerar da take fuskantar Abby yace "dama ɗansa Ibrahim na bawa auren Meenat saboda nuna sha'awarsa da hakan ta yayi, da kansa yazo nan ya roƙeni na haɗa auren ɗansa da Meenat, to lokacin an ruga anyi maganar Kamal, shine na basa haƙuri, to da Kamal yace ya fasa sai naga ya dace na ba wa ɗansa tunda ya nuna sha'awa dama can, kuma ko ba komai shi ɗin aminina ne, na kuma yarda da tarbiyar ɗansa ɗari bisa ɗari, yayi farin ciki sosai da naje na samesa da maganar, nan mu kayi komai muka gama, bayan nan ne fa Al'ameen yazo min da batun yana son auren Meenat, ni kuma naga bazan iya zama ƙaramin mutum ba nace yayi haƙuri, duk irin wannan halaccin da na nunawa Musbahu shine yau yake kirana yake gaya min wai ɗansa yace baya son auren Meenat ko kunyata be ji ba, da na nuna masa ai mu muka haifesu zamu iya tanƙwasasu suyi abinda muke so sai ce min yayi shi bazai yiwa ɗansa dole ba, kenan nine na zama shashasha ko, har nake shirin ɗaura wa ɗiyata aure da wanda bata sani ba. " Abba ya ƙarasa maganar yana sakin ƙwafa, ransa a matuƙar ɓace. Murmushin jin daɗi Abby yayi yace "to aini banga abin ɓacin rai ba anan, ni wallahi naji daɗin fasawar da sukayi, dama can Meenat rabon ɗana ne, dama ana cewa rabon mutum ko ya hau sama sai ya sauko. " Abba be san sanda ya saki murmushi ba yace "wato kai Husaini murna ma kakeyi an fasa auren ƴarka.?" Ƴar dariya yayi yace "sosai ma kuwa Hasanu saboda ɗana dama can shine mijin. " Ɗan haɗe rai Abba yayi yace "Hasanu.?" Dariya Abby yayi yace "tuno da school nayi ai, katuna Fateeme ƴar nufawa.?" Dariya Abba yayi sosai yace "kai Hassan baka mantuwa, Allah sarki Fateeme ko tana ina yanzu ? Rayuwa kenan. " Abby yace "dama haka rayuwar take, sai tazo ta wuce kamar ba'ayi ba. " Abba yace "Allah dai yasa mu cika da imani, yanzu ya zamuyi da batun ɗaurin auren nan kenan.?" Ajiyar zuciya Abby yayi yace "ɗaurin aure nan yanda yake mana, ni zan wakilci ɗana kai dama kaine waliyyin ƴarka. " Murmushi Abba yayi yace "kai dai yanzu da ƙargi da yaji kabawa ɗanka auren nan, zan iya cewa fa bazan bashi ba naga yanda zakuyi. " Ɗan harararsa Abby yayi yace "kama isa ka hana ɗana, ai ko da sai inda ƙarfina ya kare. " Dariya Abba yayi yace "to ko za'a gwadane mu gani.?" Shima Abby dariyar yayi yace "a'a ba sai an gwadan ba dai a barsa haka ma. " Ɗan murmushi Abba yayi yace "to ina so ya zamo sirri har zuwa lokacin da za'a ɗaura auren kar wanda yasan dawa za'a ɗaura kamar yanda dama basu san dawa za'a ɗaura ba. " Murmushi Abby yayi yace "to shikenan, ni dama buƙata a ɗaura da ɗana. " Nan dai suka ƙara tattaunawa akan batun kafin Abby yayiwa Abba sai da safe ya nufi gidansa. ********** *Rana bata ƙarya* Yau asabar yau ne ta kama ranar ɗaurin aure, gaba ɗaya gida ya kacame, ƴan uwa da abokan arziƙi cike suke da gida, amarya kuwa na can ɗaki da ƙawayenta zaune ana fama da ita ta je tayi wanka taƙi, banda kuka babu abinda takeyi tun daran jiya. Can ƙofar gida kuwa maza ne suka fara cika unguwan ƴan ɗaurin aure, motoci da babura a kan layin kamar an buɗe kamfaninsu, cikin babban masallacin unguwar kuwa Abba ne da Abby da wasu mutanen ana ta shirin ɗaura aure. Al'ameen ko na can cikin gida kwance ko niyar fitowa bashi dashi, kuma cikin ƴan uwansa babu wanda yace masa ya fito zuwa gurin ɗaurin aure domin suma suna tayashi baƙin cikin rasa menatuwallensa😀 Ƙarfe 10:00am daidai dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren *Al'ameen Hassan* da amaryarsa *Ameenatu Husaini* ɗaurin auren da yabawa mutane da dama mamaki, domin sam ba suyi tsammanin ɗaurin auren da Al'ameen bane, wanda aka bawa IV ɗin auren abin ɗaure musu kai yayi saboda ba sunan Al'ameen suka gani ba jin katin, nan ko maroƙi ya fara ihu yana shela. Ƴan uwan Al'ameen maza wato Aliyu da Usman sandarewa sukayi a tsaye saboda mamaki, farin ciki ne ya lulluɓe zuciyarsu da sukaji da ɗan uwansu aka ɗaura auren, ai da gudu Aliyu ya kukkutsa cikin jama'a ya nufi cikin gida, a farfajiyar gidan yaci karo da Umma, yana haki yaci burki gabanta yana faɗin "wallahi Umma da yah Al'ameen aka ɗaura auren. " Cikin nuna tsantsan farin ciki Umma tace "da gaske kakeyi Aliyu. ?" "Wallahi Umma da gaske ne, ina yah Aliyu yake ne nayi masa albishir. ?" Murmushi Umma tayi tace "bari ni da kaina zanyi masa albishir ɗinnan. " Tana gama faɗin haka ta nufi cikin gidan da sassarfa, shima Aliyu baya ya mara mata zuwa cikin gidan. ************** Meenat na kwance tana rusan kuka ƙaninta Isma'il wanda yake bi mata ya shigo da gudu ɗakin, be damu da mutanen da suke cikin ɗakin ba shi dai buƙatarsa ya isa ga yayan nasa, aiko kanta ya faɗa yana dariya. Cikin fusata ta miƙe da niyar masifeshi, amma furucin da Isma'il yakeyi cikin nuna tsantsan murna ne ya dakatar da ita faɗi yakeyi "Aunty Meenat wallahi da yah Al'ameen aka ɗaura aurenki, muna wajen masallaci naji maroƙi yana faɗin an ɗaura auren Ameenatu Husaini da angonta Al'ameen Hassan akan sadak..." Ai Meenat bata bari ya ƙarasa faɗi ba ta buga tsalle ta rungumi Isma'il da ƙarfinta tana faɗin "da gaske kakeyi Isma'il, da gaske *ni da yah Al'ameen* an ɗaura mana aure. ?" Isma'il da yasha matsa gurin Meenat yace "eh da gaske nakeyi, amma cikani dan Allah kin matseni da yawa. " Saurin cikasa tayi ta zube ƙasa tayi sujjadar godiya ga Allah, tana miƙewa ta faɗa toilet da gudu cikin matsanancin farin ciki. Ƙawayenta kuwa da suke zaune tun ɗazun suna aikin rarrashi da kallo suka bita baki sake. Ni raheenat nace congrat my Meenat💃💃🤝 *********** A hankali Umma ta tura ƙofar ɗakin Al'ameen fuskarta ɗauke da tsantsan farin ciki........ Manage dis page pleace reader's👏 _Ku sani masoya a duk inda kuke raheenat na yinku kuma tana sonku, burina shine farin cikinku, nasan page ɗin yau zan faranta muku rai sosai🥰😁, no complain pleace👏❤_ Muje zuwa🥰 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:59 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Ina yinku masoya a duk inda kuke❤💘 ````Sister Alawiyya kina da girma da matsayi a gurina, dan haka na amshi roƙonki akan ƙara yawan typing, insha Allahu daga yau no complain indai akan hakan ne, love you my sister💘❤``` *AUNTYNA MARYAM GITAL, INA MISSING NAKI SOSAI WALLAHI😭 KWANAKIN NAN SAM BAMU SAMUN TIME NAKI KAMAR DA, NA SAN AUNTYNA TANA DA UZURIRRIKA NE, KUMA DA DA YANZU BA ƊAYA BANE, TO RAHEEENAT NAYI MIKI FATAN ALKHAIRI, KI SANI RAHEENAT NAYI MIKI SO IRIN NA JINI ƊAYA, KOMAI WUYA INA TARE DAKE, WALLAHI KO BANA TARE DAKE SOYAYYARKI NA CIKIN ZUCIYATA KUMA BAZAN TAƁA MANTAWA DAKE BA, ALLAH YA AMINTAR DAKE YA YARA MIKI ZURIA YA BARKI DA YAYANA, YA KAWO MANA ƳAN BIYU🤭 AU AFUWAN MY AUNTY ASHE DAI NAYI KATOƁARA🙈😃, FATAN ALKHAIRI A DUK INDA KIKE ALLAH YA SADA FUSKOKINMU DA ALKHAIRI AUNTƳNA, LOVE YOU TOO ALL MY HEART.💘❤🥰* Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 13 A kwance ta taras dashi saman gado daga shi sai singilet da gajeran wando kansa na kallon bango, ɗakin take bi da kallo ko ina anyi kaca-kaca dashi babu kintsi. Al'ameen duk da yaji shigowar mutum be saka ya juyo dan ganin waye ba, domin yanzu hakan da yake kwance hawaye yakeyi, waɗanda tun jiya sunƙi tsayuwa masa. Takawa Umma tayi a hankali ta zauna bakin gadon, hannu ta saka ta taɓashi tare da kiran sunansa a hankali "Ameenullah." Jin muryar Ummansa ne yasa yayi saurin miƙewa yana share hawayen da suka tawo masa yace "Umma dama kece.?" Murmushi tayi tace "nine Al'ameen, ya baka shirya ya tafi gurin ɗaurin auren ƙanwar naka ba. ?" Rintse ido tayi yana jin wani raɗaɗi a zuciyarsa saboda ambatan ɗaurin auren ƙanwarsa da Umma tayi, buɗe idon yayi wanda har sun kaɗa sunyi jajir ya kalli Umma, cikin dakushashshen murya yace "Umma me zanje nayi kuma a gurin, ita kanta ƙanwar tawa bata farin ciki da auren, dama tana farin ciki ne zanje kodan farin cikinta. " Murmushi Umma ta kumayi tace "to naji, yanzu dai miƙe kaje kayi wanka ka shirya ka fito sai muyi magana. " Lumshe ido yayi yace "Umma bana musu da maganarki, amma yau dan Allah kiyi min afuwa domin bazan iya fita gurin ɗaurin auren Meenat da wani ba." Kallonsa Umma tayi tace "koda da kai ka ɗaura aure.?" Waro manyan idanunsa yayi waɗanda suke firgita ƴan mata ya kana kallon Umma dasu, kau da kai gefe Umma tayi domin yanda ya waro idanun nasa ya tuno mata da baya😁, ƙara lumshe idan yayi yayi murmushin kan labɓa yace "bama za'a ɗaura danin ba, Umma me yasa kike son zolaya ne a irin wannan lokacin. ?" Kallonsa Umma tayi sosai tace "babu zolaya Al'ameen, domin a halin da ake ciki yanzu Meenat matarka ce, da kai ka ɗaura ba da kowa ba. " Wani irin durowar bazata Al'ameen yayi daga kan gadon wanda Umma sai da ta zabura ta miƙe dan zatonta wani abu ne ya cijesa, amma ganin ya rungumeta fuskarsa na nuna tsantsan farin ciki yana faɗin "nasan Ummata bata ƙarya, kuma ba zatayi wasa da zuciyar ɗanta ba, wayyo Ummana me zan baki ne a matsayin tuƙwuci wanda zai nuna miki nayi farin ciki ?, Umma na baki kyautar mota da gidana da yake rijiyar lemo, hakan yayi miki Ummana.?" yasa ta saki ajiyar zuciya tare da bubbuga bayansa fuskarta ɗauke da tattausar murmushi tace "nagode ɗana da wannan gagarumin kyautar da kayi min. " Murmushi yayi yana sakin Umman yace "girma da matsayin albishir ɗin da kikayi min Umma yafi ƙarfin kyautar dana baki, ki jira ƙari na nan zuwa, bari naje nayi wanka na fito. " Yana gama faɗin haka ya nufi toilet da sauri fuskarsa ɗauke da wani irin annuri, Allah kaɗai yasan irin farin cikin da yakeji a zuciyarsa❤ Da kallo Umma ta bishi har shige toilet ɗin tana jin wani irin farin ciki, Allah ya gani soyayyar Al'ameen da Meenat daban yake a zuciyar ahalin gidan, shi yasa kowa yake farin ciki da farin cikinsu tare da baƙin ciki da baƙin cikinsu. Juyawa tayi tabar ɗakin fuskarta ɗauke ta murmushi wanda ya kasa gushewa, a kullum mamakin soyayyar Al'ameen da Meenat takeyi, wani irin so ne yaran sukeyi wa junansu?? Shine tambayar da takeyiwa kanta a kullum. _Ni dai Raheenat Nace so wanda ɗaya zai iya mutuwa saboda ɗaya, na faɗi daidai readers koko akwai me gyara❓😃🥰_ ************** Tuni batun da Al'ameen aka ɗaura aure ya karaɗe cikin gidan, nan fa ƴan uwa suka cika da farin ciki, dan ko babu komai zumunci zai ƙara ƙarfi, a cewarsu fa ba cewar Raheenat ba😁 Ƴan uwan Al'ameen kuwa ƙungiya sukayi gaba ɗayansu suka nufo ɗakin Al'ameen domin tayashi murna. Suna shiga suka iskeshi ya fito daga toilet kenan ɗaure da towel a ƙugunsa, turus sukayi suna kallon kallo tsakaninsu, sai kuma suka juya suka nufi ƙofa, fuskarsa ɗauke da fara'a yace "ina zaku je kuma, ina ce kunzo ku tayani murna ne.?" Juyowa sukayi su duka fuskarsu ɗauke da Murmushi tare da haɗa baki gurin faɗin "eh yayanmu. " Shima murmushin yayi yace "to ku zauna na gama shiryawa mana. " Falo suka koma kowa ya nema guri yayi ya zauna shiko Al'ameen ba tare da ɓata lokaci ba ya fara shiryawa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama shirinshi tsaf cikin wata haɗaɗɗiyar shadda ruwan zuma wacce akayi mata aiki da zare coffee color, da hular da ya ɗaura a kansa zuwa takalminsa duk coffee color ne, sosai yayi kyau cikin shigar sai ya fito a angonsa sak, fuskarsa banda annuri babu abinda yake fitarwa. Ƙamshin turarensa ne ya sanar da ƴan uwansa zuwansa, aiko nan suka juyi suna kallonsa, aiko Aunty Aisha da Bilkisu sai suka saki buɗa, faɗi suke "ka ga ango, ango na Meenat ba gaba da gaba ba, domin ko ta baya sai an shirya, gaskiya ƙanwarmu tayi dacen miji sankaɗi. " Sai suka ƙara sakin wata buɗar. Al'ameen ko sai ya zaro kuɗi a aljihunsa ya hau zuba musu, domin yau rana ce ta farin ciki a garesa, komai sukayi daidai ne. Saida ya sake musu bandir ɗin ƴan dubu tas a gurin sannan ya nufi ƙofa, godiya suke ta zubawa har ya fice daga ɗakin, tattara kuɗin sukayi suka haɗa kansu dubu ɗari cas, kasafi sukayi a tsakaninsu kuwa ya ɗauki nashi, duk fita sukayi daga ɗakin ya rage daga Aisha sai Bilkisu suka fara gyara masa ɗakin. ******** Al'ameen na fitowa falon mutanen falon suka fara sake masa buɗa suna wasa shi, shiko sai buɗe baki yakeyi yana dariya, nan ma dai ruwan kuɗin yayi musu kafin ya samu ya fice daƙyar. Abinda ya bashi mamaki yana fitowa haraban gidan ya ga abokansa tsaye, cikin sauri Miftahu abokinsa kuma abokin aikinsa ya nufosa yana faɗin "ango, ango, amma wallahi babu ɗan iska irinka, yau ace yau ana ɗaura aurenka ko labari, sai Aliyu ne ya kira wayana yake cemin an ɗaura aurenka yau, shine fa ba tare da shiri ba na fara kiran abokanayenmu ina tambayarsu, kowa sai cemin yakeyi be sani ba shima, ni wallahi ɗauka nayi ƙarya ne, nace dai bari na zo nagani ko da gaske ne, ina zuwa naga taron mutane, wallahi naso na juya sai kuma nace bari na barka da halinka. " Murmushi Al'ameen yayi yace "gara dai da kabarni da halin nawa, amma shi Aliyun be faɗa maka yanda akai auren bane. " Ɗaga kafaɗu Muftahu yayi yace "ni dai yana gaya min an ɗaura maka aure ya kashe wayar, na bisa da kira wayar taƙi tafiya. " Al'ameen yace "to nima ban san dani za'a ɗaura ba, sai bayan an ɗaura na sani, zan baka labarin yanda akayi, yanzu tawo muje girinsu Auwal mun barsu tsaye, ya akayi ne su suka zo.?" "Ni na gayyato maka su da ƙarfin tsiya." Muftahu ta faɗa yana bin bayan Al'ameen da ya fara tafiya. Murmushi Al'ameen yayi yace "ka kyauta." Suna ƙarasawa suka kaure da hayaniya, duka kuma tsiya ne sukeyiwa Al'ameen, daƙyar ya samu ya wanke kansa, nan Muftahu yace anjuma misalin ƙarfe 8:00pm da akwai paty wanda shine zai ɗauki nauyin komai, Al'ameen na jinsu be ce komai ba saboda a yanzu hankalinsa ya koma kan Meenat ɗinsa ne, ita kawai yake burin gani, wayarsa ne ta fara ringi, curota yayi ya duba sai yaga sunan Abba. Ɓangaren Meenat kuwa tana fitowa wanka ta shirya cikin wata ɗan ubansun shadda, abinda yabani mamaki shine ganin shaddar iri ɗaya ne da wanda Al'ameen ya saka, ƙwalliya tayi na kece raini tare da taimakon ƙawarta Suhailat, nan take Meenat ta fito, kowa sai yaba wankan nata yakeyi, hotuna suka fara ɗauka ita da ƙawayenta. Suna cikin hoton sai ga ƙanwar Ummi tare da Umman Al'ameen sun shigo ɗakin, sauri nutsuwa sukayi daga karaɗin da suka cika ɗakin dashi, Umma ce ta ƙaraso kusa da Meenat fuskarta cike da fara'a ta riƙo hannunta tace "ƴata kinyi kyau sosai, kin ganki kuwa.?" Kunya ce ta kama Meenat tayi ƙasa da kanta tana murza yatsunta wanda suka sha lalle, wanda daƙyar ta yarda akayi mata shi, murmushi Umma tayi tace "kunya ta kuma akeji yau ƴata.?" Meenat dai bata ce kanzil ba kuma bata ɗago kanta ba, Umma tace "to shikenan tunda ƴar tawa suruka zatayi dani ba uwa ba, dama Abbanku ne yake kiranku shine nazo tafiya dake. " Cikin jin kunya Meenat tace "to Umma. " Bawa ƙawayen nata haƙuri Umma tayi ta riƙe ta hannunta suka fice daga ɗakin. _Kuyi haƙuri dan Allah, wallahi ba haka naso ba, chajina ne ya kare ina kan typing, kuma unguwarmu bamu da wuta yanzu, kullum chaji nake kaiwa, amma nayi muku alƙawari insha Allahu daga yau ba zan ƙara typing kaɗan ba._ 06/08/2019 à 10:59 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 14 Tsit falon ya ɗauka bayan kowa ya zauna, Abba da Abby zaune suke a kujera two seater, Umma kuma da Ummi suna zaune a three seatern dake fuskantar nasu Abba, Al'ameen kuma ta Meenat waɗanda suke satan kallon juna tare da aikawa juna saƙonni ta cikin idanunsu zaune suke saman kafet kansu a ƙasa. Abba ne yayi gyaran murya ya fara da cewa "godiya ta tabbata ga Allah da ya nuna mana wannan rana, haƙiƙa ban taɓa zato ko tsammanin auren nan zai juye ya dawo kanka ba Al'ameen, amma cikin iko na ubangiji sai ya gashi an ɗaura da kai, dama ance matar mutum ƙabarinsa, haƙiƙa gaskiya ne ba me auran matar da ba tashi ba, to ba komai yasa na taraku anan ba sai dan na tunatar daku tare da yi muku na sihohi, da farko zan fara dakai Ameenu domin kaine babba, da da yanzu ba ɗaya bane, yanzu wani nauyi me girma ya hau kanka, ka tashi daga sawun yara ka shiga sawun manya, da yanzu duk wani nauyin Ameenatu ya tashi akanmu ya koma kanka, cinta, shanta, suturarta, lafiyarta samar mata makwanci duk kaine yanzu, ya zama maka dole ka sauke duk wannan nauyin a matsayinka na miji gareta, sannan ka zama me tausayinta tare da yi mata uziri koda tayi maka ba daidai ba, domin su mata an haliccesu ne da ƙashin haƙarƙarinmu mu maza, annabi s.a.w da kanshi yake cewa ina yi muku wasicci da mata, domin su mata an haliccesu ne da ƙashin haƙarƙarinku, kuma a karkace suke, yace idan kuka tafi zaku miƙar dasu sai su karye, in kuma kuka barsu baza su gushe ba suna a karkace, kenan anan annabi yana magana ne akan mubi su a hankali karmu ce zamu rinƙa takurasu, sannan kuma kar mu zuba masu ido akan komai ba tare da mun tsawata su ba, tsakatsaki kenan, to ina so kaima ka kasance me bin matarka a hankali, komai in tayi mata ka zaunar da ita ka nusar da ita daidanta darashin daidanta, bawai ka hau mata faɗa ba, hakan ba zai janyo komai ba sai dai ta rainaka kuma ba zaka samu yanda kakeso a tare da ita ba, ina yi maka nasiha ka zama namiji adali meyiwa matarshi adalci akan komai, na sanka nasan halinka, nasan abinda zaka iya da wanda ba zaka iya ba, to dan haka karka sauya akan yanda na sanka da kuma tarbiyar da mukayi muku, tarbiyarka dana matarka ɗaya ne, domin abinda yayi Ameena shi yayi ka, kafini sanin wacece Ameenatu, domin Ameena rainonka ce, tare kuka tashi kusan zan iya cewa tarbiyarka ce ita ɗin, to kaga kenan basai ma faɗa maka ta inda zaka dasa daga tarbiyarta ba, kayi haƙuri, kayi haƙuri, kayi haƙuri, domin saida haƙuri komai zai tafi daidai, ina fatan Allah ya baku zaman lafiya kai kuma ya baka ikon sauke nauyin da ya ɗora maka ya kuma baka ikon riƙeta da amana. " Ameen su Umma suka faɗi, sauke numfashi Abba yayi sannan ya ɗaura "to ke kuma na dawo kanki Ameena, na sanki da girmama na gaba dake tare da biyayya, to ina so ki ɗaura akan hakan, kiyi wa mijinki biyayya yi nayi bari na bari, ki kasance macen da duk inda mijinki zai shiga zai zamo yana tuno dake tare da alfahari dake, rayuwar gidan aure ba rayuwar sharholiyya bace da yanci kamar yanda wasu suke ɗauka, shi rayuwar aure ibada ne wanda zai kaika aljanna, kuma aljannar nan bafa zata samu daga kwance ne ba har sai mutum yayi abinda ya kamata, ba sai na faɗa miki ba, kina dai ganin yanda iyayanki sukeyi mana, to ina so ke kifi haka, ki zamo farin cikin mijinki, in yana farin ciki to ki fishi farin ciki, in yana baƙin ciki ki fishi baƙin ciki, in ya kawo abu yana so to ki fishi son abin, abinda be so kuma ki fishi ƙin abin, ki nuna masa kina tare dashi duk komai wuya, yanzu shine komai naki, duk wani damuwa naki shi zaki dosa da ita domin yanzu shine yafi kowa kusanci dake, ki riƙe sirrin mijinki, karki zamo mace me fallasa sirrin mijinta, ko mahaifiyarki ba kome ne zaki faɗa mata ba, kuma ina miki nasiha ki kasance me haƙuri da juriya, domin da haƙuri ne zaki kai ga cin nasara ga rayuwar aurenki, sai kin kasance me haƙuri sannan zaki iya yiwa mijinki biyayya, yanzu kin tashi a budurwa kin zama matar aure, wasu abubuwa da zakiyi da yanzu ba zakiyi su ba, sannan ina miki nasiha kar ki zamo me ɗaga muryarki sama da na mijinki, in ya ɗau zafi ke ki kasance me sanyi, ko faɗa yakeyi miki to kiyi shiru har ya gama sannan sai ki bashi haƙuri, in kuma kina da abin faɗi sai ki faɗa, ba wai yana faɗa kina faɗa ba, sannan banda bin zugar ƙawaye, domin wasu ƙawayen basu da buri sai ganin sun fitar dakai gidan mijinka musamman ma in sunga kana jin daɗi, Allah yayi muku albarka ya albarkaci aurenku, ya baku zuri'a ta gari, ya kau ta fitina tsakani, ya baku haƙurin zama tare. " "Ameen ameen. " su Abby suka faɗa, murmushi Abba yayi ya kalli Abba yace "Husaini kana da abin da zaka ce musu ne.?" Murmushi Abby yayi yace "ai duk abinda zan faɗi ka gama faɗinsa yaya, sai dai na ƙara akan wanda ka faɗa, Al'ameen, Ameenatu kamar yanda Abbanku yace ne sai kunyi haƙuri, domin yanzu da da ba ɗaya bane, zaku ga wani abubuwa daban cikin sabuwar rayuwar da kuka shiga wanda kuma dole sai anyi haƙuri, Allah yayi muku albarka ya baku zaman lafiya. " "Ameen" suka amsa dashi kansu na ƙasa. Abba ne ya kalli Umma yace "to mu mun gama namu saura ku. " Murmushi Umma tayi tace "ai kun riga kun rufe bakinmu, abinda ya rage mana yanzu kawai mu saka albarka tare da addua." Dariya Abba yayi yace "aiko kuna da sauran abin cewa, in zaku buɗe baki kuyi magana kawai kuyi. " Dariya sukayi gaba ɗayansu, nan dai suma su Umma da Ummi suka tofa albarkacin bakinsu tare da addu'oin zaman lafiya tare da saka ma auren albarka tare da masu auren, nan dai Abba ya sallame su. Miƙewa sukayi cikin sanyin jiki suka fito daga falon, suna fitowa suka tsaya kallon kallo tsakaninsu, Al'ameen beyi wata wata ba yaja hannunta ya nufi hanyar ɗakinsa da ita, Meenat dai kallonsa takeyi har suka shiga ɗakinsa. Sake hannunta yayi yaje ya rufe ƙofar ya dawo ya tsaya a gabanta ya zuba mata idanu, ƙasa tayi saurinyi da kanta saboda wani kunyarsa da taji ya kamata, murmushi ya saki yace "naga ƙanwar tawa yau ta sauya min ne gaba ɗaya kodai an canza min ne da wata Ameenar. ?" Ɗago ido Meenat tayi tana kallonsa da alamun tambaya a hankali ta buɗi baki tace "wani irin sauyawa nayi. " Hannunta yaja ya zaunar saman kujera shi kuma ya duƙa a gabanta cikin taushin murya yace "kin ƙara kyau, sai wani sheƙi da haske kikeyi kamar wata ɗan daran sallah. " Saurin rufe fuskarta Meenat tayi ta tafin hannunta cike da kunya, cikin dariya tace "kai ma halan baka duba madubi bane ka ganka, ai kafini yin kyau sosai. " Tsura mata ido Al'ameen yayi cike da shauƙi yace "da gaske.?" Meenat tace "sosai ma. " Hannu ya kai ya cire mata hannun ta ta rufe fuskarta dashi ya tsura wa fuskar nata ido yana kallo, itama ɗin shi take kallo cike da shauƙin junansu, a hankali Al'ameen ya buɗe baki yace "amma ƙanwar tawa tace nayi mata girma to yaya zatayi dani kenan yanzu.?" Waro ido tayi cike da jin kunya ta faɗa jikinsa tace "wayyo yaya dan Allah kayi haƙuri kabar maganar nan ta wuce. " Murmushi yayi yace "a'a fa be wuce ba, saboda da bakinki kika ce nayi miki girma. " Turo baki tayi cikin shagwaɓa tace "to to ai lokacin da na faɗi bani da wayo kuma bani da girma, kaga kuwa yanzu nayi wayo kuma na girma " Dariya ta bawa Al'ameen sosai saboda yanayin yanda tayi maganar, cikin dariyar yace "Allah ko.?" Ɗaga kai tayi tace "sosai ma, baka ga yanzu na girma ba. " Murmushi Al'ameen yayi ya ɗago da ita daga jikinsa yace "gaskiya yanzu Meenat ɗita ta girma, dan yau na hango kunyata a cikin idanunta. " Ƙara sunne kai tayi a ƙirjinsa tana dariya ƙasa-ƙasa, a hankali tace "a da nayi wauta me girma da naƙi amsar soyayyarka yayana, da na rasaka da bansan halin da zan shiga ba, ina matuƙar ƙaunarka yayana. " Janyota sosai Al'ameen yayi cikin jikinsa ya rungume yace "Meenat na yarda komai rabo ne, kuma duk abinda ya kasance rabonka wallahi duk inda kake sai yazo ya sameka, har wayiwar garin yau ban saka a raina zaki zamo matata ba, sai gashi ina kwance kan gadona a kazo kayi min albishir wacce nake matuƙar so da ƙauna ta zamo matata mallakina, Meenat da ban sameki ba bansan yanda rayuwata zata kasance ba, bansan cewa ina miki so me tsanani ba sai daga jiya zuwa yau da naga da gaske zan iya rasaki, i really love you my Meenat. " Ƙara shigewa jikinsa Meenat tayi tace "mee too yayana. " Wani abu Al'ameen yaji yana masa yawo wanda be taɓa jinsa a jikinsa ba duk rungumar da yasha yiwa Meenat a baya, be san lokacin da ya ɗagota daga jikinsa ya haɗe bakinsu guri ɗaya ba. Gaba ɗaya sun shiga wata duniya na daban wanda dukkansu biyu basu taɓa shiga makamancinsa ba, Al'ameen dai ya samu alawa me zaƙi sai tsotsa yakeyi lol😃🙈 Ringin ɗin wayar Al'ameen ne ya kashe musu jin daɗi, a hankali ya rabata da jikinsa yana maida numfashi ya ciro wayar daga aljihunsa ya duba me kiran, ganin Muftahu ke kira yasa ya ɗaga cikin kasalalliyar murya yace "hello Muftahu ya akayi ne.?" Daga can ɓangaren Muftahu yace "wai Al'ameen ina ka tafi ne ? Tun ɗazun fa akai muke jira. " Lumshe ido yayi ya buɗe yace "ganinan fitowa yanzu. " Yana gama faɗin haka ya kashe wayar, kallon Meenat yayi wacce kanta ke ƙasa yayi murmushi yace "my blood bari inje su Muftahu na jirana. " Cikin jin kunyarsa Meenat tace "dama nima tafiya zanyi nasan su Suhailat na can suna jirana. " Miƙewa Al'ameen yayi yana faɗin "ok taso muje to. " Meenat tace "a'a kaje zan tawo. " Murmushi yayi kawai ya ɗauki hularsa ya sanya ya fice daga ɗakin, ajiyar zuciya Meenat ta sauke tare da lumshe ido a fili tace "Allah ya taimakeni. " Ta faɗin haka ta miƙe ta ɗauki gyalenta tare da gyara ɗaurin ɗan kwalinta ta fito ta rufo masa ɗakin ta koma cikin gidansu. ********* Haka dai aka ci gaba da gudanar da shagalin bikin cikin farin ciki, ƙarfe huɗu daidai Umma ta haɗa wani gagarumin walima ana farfajiyar gidan nasu, anyi wa'azi tare da nasihohi sosai sannan aka ci aka sha tare da rarraba kyaututtuka sannan aka watse. Ƙarfe 8:00 daidai aka zo aka kwashi ƴan zuwa party, amarya a moto ɗaya da angonta aka ɗaukesu, sun sha kyau cikin shiga irin na shuwan asali da sukayi su duka. A gurguje Partyn ya ƙayatar sosai matuƙa, an tafiyar da partyn cikin nuna ƙwarewa babu hayaniya, komai dai masha Allah, abinci dai gashinan baja baja, can na hango ƴan grp's ɗina suna takai lomar rangyam da kaza😁 My meera, my bk, my lissa, my hajjata cemer, Fauxiya s madaki, Aisha, momyn sultan, Ameena Muhammad, maman khairat, Adabiyya isa, Hauwa'u, Fusaina surukata, Mman Ishaq, sis alawiyya, Aisha nichoi, Adama tanimu a biye, Fauziyya wakili, maman labyb, Shafa'atu bala baba, Naja'atu nura, Sareena, Safiya bello k, maman dady, beebat, nana khadija, Mom haneef, memeey, lubabatu shehu shayi, Zainab Abdullahi, Ashmar, Amina Abubuakar, Mmn Yasmin, fatima maihadisi, dadai sauransu yawanku ba zai bari na ambatoku duka ba, amma ku sani kuna zuciyar raheenat. Zuwa 9 aka tashi daga partyn kai tsaye daga gurin partyn gidan amarya aka wuce dake unguwar zoo road, ba'a koma gidansu da ita ba, tanƙamemen gida ne wanda ya amsa sunansa gida, ya haɗu iya haɗuwa, farin fanti akayiwa gidan ko'in ƙal-ƙal sai haskawa yakeyi, kana shiga gidan zaka san ka shiga gidan likitoci. Suna isa suka iske gangin su Ummi da Abby a can, nan aka dasa wani sabon walimar, abin birgewar a ciki shine karatun alqur'ani me girma aka gabatar, kowa aka raba masa izun da zaiyi, saida suka sauke alqur'ani sannan aka rufe da addu'a, amarya da ango sun sha ruwan addu'oi abin dai gwanin birgewa, sai ƙarfe 11:00pm aka tashi daga walimar kowa ya kama gabansa, nan ne fa Meenat ido ya raina fata ganin an watse babu kowa sao ita ɗaya, ƙudundunewa tayi cikin hijjabinta ta kwanta zuciyarta cike da tsoro. Ba'afi minti goma ba tsakani taji an turo ƙofar ɗakin da sallama, saurin miƙewa tayi taje ta rungume Al'ameen tana sauke ajiyar zuciya, shafa bayanta Al'ameen yayi cikin taushin murya yace "ya akayi ne my blood.?" Ɗago da kanta tayi daga ƙirjinsa cikin shagwaɓa tace "tsoro naji ganin an barni ni kaɗai. " Murmushi yayi yaja hannunta zuwa ciki yana faɗin "to ai gani na zo tsoro sai ya ƙare. " Murmushi tayi ba ta ƙara cewa komai ba, zaunar da ita yayi bakin gado ya kalleta yace "nasan kina jin yunwa ko.?" Ɗaga kanta tayi alamar eh, murmushi yayi ya miƙe yace "to ina zuwa yanzu. " Yana gama faɗin haka ya nufi ƙofa, riƙo rigarsa Meenat tayi cikin shagwaɓa tace "ina zaka je kuma ka barni. ?" "Abinci zanje na kawo miki fa. " Miƙewa tayi tace "to muje tare. " Dariya taso bashi ganin yanda ita wai bil-haƙƙi tsoro take ji, shi dai a iya sanin da yayiwa Meenat bata da tsoro, murmushi yayi ya kamo hannunta ya riƙe yace "muje. " Tare suka shiga kitchen suka ɗauko plate da cup's tare da ƴar ƙaramar knife suka dawo falo, kajin da ya shigo da su ya juye a plate ɗin suka zauna suka ci suka ƙoshi sannan suka kora da madarar holandia domin Meenat na son madarar sosai. Mayar da Plate da cups ɗin kitchen sukayi sauran kazar suka zuba a firiza sannan ya kama hannun Meenat suka nufa ɗaki. Suna shiga toilet suka shiga sukayi brush, Al'ameen barin Meenat yayi yace tayi wanka yana zuwa, ɗakinsa ya koma shima yayi wanka ya shiryo cikin kayan bacci ya dawo ɗakinta, samunta yayi har ta kwanta, wutar ɗakin ya kashe shima ya haye gadon ya janyota jikinsa, ba su jima ba bacci yayi gaba dasu domin a gajiye suke sosai. _Asuba ta gari Al'ameenat_ ********** Washe gari Al'ameen ya riga Meenat farkawa, duba agogon dake jikin gadon yayi yaga ƙarfi biyar, a hanzarce ya tashi ya faɗa toilet ya ɗauro alola, yana fitowa ya tashi Meenat, yana ganin ta tashi ya fice daga ɗakin da sauri ya nufi ɗakinsa dan shirin zuwa masallaci.. Sai shida da ƴan mintuna ya shigo gidan, kai tsaye ɗakin Meenat ya nufa, da sallama ya tura ƙofar ɗakin, Meenat dake kan sallaya har yanzu tana Azkar ɗagowa tayi tana kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi tare da amsa masa sallamar, har kusa da ita Al'ameen yaje ya zauna yana murmushin shima. Meenat ce tace "an tashi lafiya heart-beat. ?" "Lafiya ƙalau my blood, ya kwanan baƙunta. " Cikin shagwaɓa tace "ni banyi kwanan baƙunta ba, gidan yayana na kwana fa. " ƴar siririyar dariya Al'ameen yayi yace "hakane fa, ai mantawa nayi. " Ɗan hararar wasa tayi masa tace "to ni ban manta ba. " Tallafo fuskarta yayi ya kai mata sumba a ɗan ƙaramin bakinta sannan yace "kin gama ne ki zo mu shiga kitchen mu samarwa kanmu abin break-fast.?" Ɗaga masa kai kawai ta iyayi saboda jikinta da taji yayi mata sanyi, miƙewa yayi yana faɗin "oyo miƙe muje to. " Miƙewar tayi ta naɗe sallayar shi kuma ya ɗauki littafin addu'oin ya ajiye a ma'ajiyarsu sannan suka nufi kitchen ɗin. Cikin ƙanƙanin lokaci suka dafa ruwan zafi sannan suka soya ƙwai da Arish suka ajiye saman dining, ɗaki suka koma domin yin wanka.. Muje zuwa🥰 _Kuyi min afuwa na rashin updating jiya, lokacin da naso yi muku lokacin chajin wayata ya ƙare👏_ *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:59 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 15 Kusan tare suka fito kowa cikin shirinsa, shi Al'ameen cikin ƙananun kaya ya shirya ita kuma cikin wata riga da siket da atamfa, ɗinkin ya zauna mata ɗas a jikinta, hakan yasa kayan sukayi mata kyau sosai. Daning suka nufa Meenat taja wa Al'ameen kujera ya zauna, ba tare da ta zauna ba ta fara haɗa masa tea, tana gama haɗawa ta ɗauki plate ta zuba masa dankalin da kwai tare da buredin da suka soya cikin kwai ta tura masa gabansa, sannan taja kujera ta zauna zata fara haɗa nata, duk abinda takeyi idanun Al'ameen a kanta har ta gama. "Taso ki zauna a nan. " Al'ameen ya faɗa idanunsa na kanta. Ba tare da musu ba ta miƙe ta zauna saman cinyarsa da ya nuna mata, cup ɗin tea ɗin ya ɗauka ya kai bakinta ba musu ta buɗe baki ta fara amsa, a haka tana zaune saman cinyarsa ya ciyar da ita har ta ƙoshi, ba tare da ya sauketa ba ya haɗa wa kanshi ya fara sha, kallonsa kawai Meenat takeyi cike da so da ƙauna, cikin ranta take faɗin "gaskiya da ban auri yah Al'ameen ba da nayi asara babba. " Ɗaga mata gira Al'ameen yayi yace "ya dai irin wannan kallo haka?" Murmushi tayi tace "ina kallon kyakkyawan yayana kuma mijina ne ko nayi laifi.?" Murmushi yayi lokacin da yake ajiye cup ɗin tea ɗin ya kalleta yace "ba kiyi laifi ba my jinin jiki, kalleni son ranki ni naki ne. " Kwantar da kanta tayi a ƙirjinsa tana sakin tattausar murmushi a hankali tace "yau an wayi gari *ni da yaya Al'ameen* a matsayin miji da mata abinda ko a mafarkina ban taɓa kawo hakan ba. " Al'ameen yace "ni kuma kullum mafarkina kenan, burina kenan, muradina kenan, sannan kuma tunanina kenan, bani da wani buri sai naga na auri ƙanwata wanda nake matuƙar so, muradina na ganta matsayin matata, tunanina kuma yanda zamu tafiyar da zaman aurenmu, sai na rinƙa ganin abun cikin idanuna gani ga ƙanwata a gidana muna rayuwa ta aure tare da ƴaƴanmu da muka haifa, ana haka ƙanwar tawa ta rusa min duk wani mafarkina da muradina lokacin da na riga na sallama mata rayuwata, ashe dai kuma ita ɗin tawa ce rabona ce ina kwance aka bani ita, sai yanzu nake ƙara tabbatarwa babu wawa mara sa'a irin Kamal, sai da yake gab da mallakarki kika suɓuce masa, sannan a karo na biyu shima Ibrahim cikin rashin sa'a yace ba yayi, koda yake ke ɗin ba tasu bace dama nawa ne, domin ni kaɗai aka halicce ki, ina sonki Meenat, *na baki rayuwata* my blood. " littafin masoyiya (my bk) Har yanzu kanta na manne a ƙirjinsa tace "tunda aka haifeni yayana yake nuna min ƙauna be bari nayi kuka, be taɓa bari na nema wani abu na rasa ba, komai nakeso shi yakeyi min, duk abinda na wayi gari nace ina so komai wahalarsa zaije ya nemo ya kawo min, be son ɓacin raina ko kaɗan, kulum burinsa ya ganni ina farin ciki, to ko wannan na duba ya isheni gane tsantsan ƙaunar da yayana yakeyi min, wallahi yah ko ba ka ƙara furtawa Meenat kalmar so ba ba zatayi complain ba, domin ƙaunar da ka nuna min tun ina jaririya kaɗai ma ya isheni, domin ina da tabbacin kome zanyiwa yayana ba zai fushi dani ba balle har ya tsaneni, *ni da yaya Al'ameen* soyayyarmu a cikin jininmu yake, sai dai na zama babban shashasha da ada na kasa gane so da nakeyiwa yayana ba soyayyar ƴan uwantaka bane kaɗai so ne da aka halicci zuciyata da ita, so ne wanda indan babu shi rayuwa zata zama me matuƙar wahala ga Meenat, so ne wanda Meenat zata iya bada rayuwarta saboda yayanta, ina ƙara neman gafararka yayana, ina ƙaunarka *raina fansa ne gareka* yayana." Ta ƙarasa maganar tana ƙara shigewa jikinsa sosai. Shafa bayanta Al'ameen yakeyi cikin wani irin yanayi wanda ya kasa fassarashi, cikin wani irin voice be tada tsigar jiki ya raɗa mata a kunni "kome kikayiwa yayanki ya yafe miki tuntuni, sannan yayanki ba zai taɓa barin furta miki kalmar so ba har ranar da numfashinshi zai bar gangar-jikinsa, ki sani son da yayanki yakeyi miki so ne wanda bakinsa ba zan taɓa gajiyawa gurin furta miki shi ba. " Ya ƙarasa maganar yana goga mata hancinsa a wuyarta. Nan fa batu ya fara canzawa, domin Al'ameen kiss ya fara kaiwa Meenat duk inda ya bakinsa ya kai a jikinta. Ita ko Meenat ƙara lafewa tayi a jikinsa tana ƙarɓan saƙon. _Ganin abun na nema ya wuce gona da iri ne yasa na fito a guje na bar musu gidan, dan gani nayi Al'ameen ya ɗauketa cak ya nufi hanyar ɗakinsa da ita, nace abin babba ne😁._ ************* Yinin wannan ranar su Al'ameen sunyisa ne cikin farin ciki da annashuwa, abincin rana ma tare suka shiga suka girka, ƙarfe biyu daidai ƴan uwa suka cika gidan wanda ya tilastawa Al'ameen fita, wasu sallama suka zo yi musu zasu koma inda suka fito wasu kuma ganin ɗakin amarya suka zoyi. Sai misalin ƙarfe biyar kowa ya watse ya rage saura Aunty Aisha da Bilkisu ne sai ƙanwar Meenat Habiba, su suka ƙara gyara mata gidan suka ɗaura mata girkin dare. Sai bayan isha'i sukayi mata sallama suka bar gidan, Meenat ji take kamar kar su tafi, da ta roƙi ma su bar mata Habiba Aunty Aisha harararta tayi tace "amma ke baki da hankali. " Turo baki Meenat tayi cikin shagwaɓar da ya zamar mata jiki tace "to meye abin rashin hankalin anan dan Allah Aunty Aisha. " "Oh ke baki gani ba ko ? To in ke baki da hankalin mu muna dashi, Habiba kinji wuce mu tafi. " Haka dai tana ji tana gani suka tafi suka barta, komawa tayi ciki tana ta kumburi ita ɗaya, basu daɗe da fita ba Al'ameen ya shigo gidan, da gudu kamar yanda ya zama sabonta ta zo ta rungumeshi tana faɗin "oyoyo yayana. " Cike da farin ciki Al'ameen yace "oyoyo my blood, da fatan kina lafiya. ?" Raba jikinta tayi da nasa ta amshi ledar hannunshi tana murmushi tace "lafiya ƙalau nake kamar yanda nake fatan kaima lafiya kake. " Murmushi Al'ameen yayi ya riƙo hannunta suka ƙarasa cikin falon yace "lau nake my blood, kinsan me nake buƙata yanzu. ?" "A'a sai ka faɗa. " Meenat tace tana kallonsa. "Ruwan wanka. " Murmushi tayi tace "an gama Nurul qalɓi, bari naje na haɗa maka. " Tana gama faɗar haka ta nufi hanyar ɗakinsa, shima miƙewa yayi ya mara mata baya. ********* Wata jallabiyya me gajerar hannu ya saka bayan ya fito daga wankan, kallonsa ya kai ga Meenat dake zaune bakin gadonsa tana buga mutuninta, wato game yace "my blood jeki ɗauro alola ki zo muyi sallah. " Ɗago ido tayi ta kallesa tace "ina da alola ai yah." Al'ameen yace "ok, to ɗauko hijjabinki ki zo. " To tace ta fito daga ɗakin nasa taje ta ɗauko hijjab a ɗakinta ta dawo, tada sallah sukayi sukayi raka'a biyu, bayan sun idar Al'ameen ya daɗe riƙe da kan Meenat yana kwararo addu'a kafin ya miƙe yana hamma. Kallonsa Meenat tayi tace "yunwa ko yayah. ?" Ba ta jira amsarsa ba ta riƙo hannunsa zuwa dining ta ja masa kujera ya zauna, abinci ta zuba masa ta tura masa gabansa, kallonta yayi yace "zauna mu ci to. " Fari tayi da idanunta tace "ni na ƙoshi, ɗazun munci abinci dasu Aunty Bilkisu. " Yasan halin Meenat sarai ba cin abincin zatayi ba ko ya dage dan haka yace "ok, to zo nan ki zauna. " Yayi mata nuni da cinyarsa. Kallon ciyar tayi sannan ta kallesa tace "sorry, kaci abincinka ne zanje nayi wanka ne yanzu. " Kallonta yayi sosai da mamaki, sanye take cikin wata farar Top sai baƙin wando wanda ya kamata daga sama daga ƙasa kuma ya buɗe kaɗan, fuskar nan nata yasha makeup yace "bayan wankan da kikayi kuma. ?" Turo baki tayi tace "wannan wankan kai nayi wa, to tunda ka gani yanzu kuma wanda zanyi na kwanciya bacci ne. " Ajiyar zuciya Al'ameen ya sauke fuskarsa ɗauke da murmushi tace "ok na gane, jeki. " Aiko bata saurari komai ba ta nufi hanyar ɗakinta shi kuma ya rakata da idanu sai da yabar ganinta kafin ya dawo da hankalinsa kan abincinsa. Meenat na shiga ɗaki ta faɗa toilet, wanka sosai tayi duk da be daɗe ba tayi wani wankan sannan ta fito, gaban mirror ta nufa ta tana goge jikinta, wani mai ta ɗauka ta fara shafe jikinta dashi, ta ɗauki sama da mintuna goma gaban mirror tana shafa wannan ta goga wancen a jikinta sannan ta taka a hankali ta buɗa gurin kayanta ta ɗauko bras da pant ta fara sanyawa. Wata arniya kuma fitinanniyar rigar bacci ta ɗauko ta sanya a jikinta kalar pink, rigar shara shara take dan babu abinda ba a gani a jikinta, iya gwiwarta rigar ta tsaya mata, gaban mirror ta dawo ta tsaya tana kallon kanta, a fili ta furta "wayyo ni Meenat anya zan iya tsayuwa gaban yah Al'ameen da kayan nan,?" yamutsa fuska tayi tace "to amma Aunty Aisha kuma tace kar naji kunyar komai na daure na saka, kai abin akwai kunya wallahi. " Hannu takai ta fara tattare gashin kanta ta ci gaba da magana ita ɗaya, ribbon ɗin da ta ɗauko kalar kayan baccin nata ta ɗauka ta kama gashin dashi, daidai nan taji an turo ƙofar ɗakin da sallama, da sauri ta juyo tana kallon ƙofar, Al'ameen da ya shigo ɗakin shima cikin kayan bacci sumar tsaye yayi domin be taɓa ganin Meenatuwan nasa a irin wannan shigar ba tunda suke, ita kuwa Meenat wani irin kunya ce ya kamata da yasa tayi mutuwar tsaye a gurin ta kasa motsawa tare da saurin yin ƙasa da kanta, takowa Al'ameen ya farayi yana kusanta kansa da ita, Meenat kuwa rintse idanunta tayi ƙam ta kasa koda motsawa. Ji kawai tayi Al'ameen ya rungumeta a jikinsa, runguma irin wanda be taɓa yi mata irinsa ba, can kuma sai taji hannunsa ya fara yawo a cikin jikinta yana shafo duk inda yaso, nan fa jikin Meenat ya fara rawa, Al'ameen beyi wata wata ba ya jata suka faɗa gaɗo, nan ya haɗe bakinsu guri ɗaya kuma hannunsa be bar yawo a jikinta ba har ya kai ga dukiyar fulaninta ya fara latsasu cikin wani irin salo. Al'ameen dai gaba ɗaya ya gama rikita Meenat ɗin tasa dashi kanshi ma, domin gaba ɗayansu sun fara fita a hayyacinsu, dan cikin ƙwarewa da sanin logon mace Al'ameen yake sarrafa Meenat. Ni dai ganin Al'ameen ya fara ƙoƙarin ya kicewa Meenat rigar jikinta ne yasa na fito daga ɗakin da gudu dan kar na gano abinda yafi ƙarfina. Kukan Meenat kawai nake iya jiyo ina daga falo zaune tanayiwa yayan nata magiya ya ƙyaleta, su Umma da Ummi da Abba da Abby kuwa sunsha kira, to dama dai Meenat shagwaɓaɓɓiya ce ko ba ayi mata komai ba balle ta samu dalili. Da naji kukan na Meenat yaƙi ƙarewa ni Raheenat ina daga zaune cike da tsausayinta nace anya ba maganar Meenat gaskiya bace da tace yayan nata yafi ƙarfinta😢🤣🏃🏻‍♀ Duk wannan kuka da magiyar da Meenat takeyi Al'ameen be saurara mata ba saboda bama ya cikin haiyacinsa, domin ya shiga duniyar maji daɗi🤭🙈, sai da ya samu nutsuwa sannan ya gane aika aikan da tayiwa ƴar gudaliyar ƙanwar tasa. Da sauri ya rungumota jikinsa yana yi mata sannu tare da saka mata albarka, Meenat dai banda shashsheƙar kuka babu abinda takeyi domin kuwa tasha wuya sosai, da sauri Al'ameen ya raba jikinsa da nata ya sauka akan gadon ya faɗa toilet, cikin gaggawa ya tsarkake jikinsa sannan ya haɗa wa Meenat ruwa me ɗumi, fitowa yayi ya ɗauketa ya koma toilet ɗin da ita, cikin ruwan ɗumin da ya haɗa mata ya sakata, kawai sai Meenat sa sake masa ihu tana niman miƙewa, dannata yayi ta koma ta zauna jikin ruwan, riƙo sosai yayi mata saida ya tabbatar ruwan ya ratsata sosai sannan yace ta fito, buɗewa yayi ruwan ya wuce ya ƙara tara wani, shima yasha darga da ita kafin ta yarda ta ƙara zama cikin ruwan ɗumin, daya tabbatar da taji daɗin jikinta ne ya fito yabarta yace tayi tsarki. Yanan zaune Meenat ta fito ɗaure da towel sai matsan hawaye takeyi, saurin miƙewa yayi ya riƙota ya zaunar da ita bakin gadon, da kansa ya ciro mata wasu kayan bacci riga da wando ya taimaka mata ta saka sannan ya bata wasu ƙwayoyi ta haɗiya sannan suka haye gadon suka kwanta yaja musu blaket ya rungumota jikinshi. Asuba ta gari Al'ameenat🥰 ********* Washe gari ko kaɗan Al'ameen be bar Meenat tayi aiki ba, shi yayi musu komai ya bata abincin a baki, ita kuwa sai shagwaɓa take zuba mishi son ranta, shima yana biye mata, gaba ɗaya wayoyinsa kashesu yayi saboda kar a takura masa. Haka dai sukayi ta cin amarcinsu tare da nunawa juna soyayya kamar zasu cinye juna, Meenat har mamakin yayan nata takeyi in yayi mata wasu abubuwan, sam bata tsammaci Al'ameen a hakan ba, ashe dai ɗan soyayya ne no 1, itama ba abarta a baya ba ta zage tana nuna masa itama fa no 1 ɗince a wannan fagen, abin nasu dai gwanin burgewa. A gurguje Bayan sati ɗaya Zaune yake a office ɗinsa yana wani aiki a laptop, yau ɗin ma da dole ne yasa ya fito yabar Meenat ɗinsa a gida saboda kiran da ya samu an kawo wata mara lafiya kuma dole ana buƙatarsa a gurin, yanzu ma bayan ya gama duba mara lafiyar ne ya dawo office yana ƙara bincike akan lallurar matar, ƙofar office ɗin yaji an turo an shigo, ɗago ido yayi domin yaga wanene, ido huɗu sukayi da Basma... Muje zuwa😘 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:59 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ *GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI GAREKU MASOYA, NI RAHEENAT INA BAKU HAƘURI NA RASHIN POST AKAI AKAI YANZU, WALLAHI ABUBUWA NE SAI A HANKULA GA RASHIN WUTAR DA MUKE FAMA DA ITA DATA FARA SHIGA RAYUWARMU😭, KU DAI KU CI GABA DA HAƘURI RAHEENAT NA TARE DAKU, INA YINKU MASOYA😘❤* ```MY BK INA KIKA SHIGENE KWANA DA YAWA, ALLAH YASA KINA CIKIN ƘOSHIN LAFIYA, RAHEENAT NA KEWARKI SOSAI😭``` *MY ƘANWA KEMA INA KIKA SHIGA NE WAI, WALLAHI NAYI KEWARKI SOSAI, AISHA ISA MUMMY'S FRIEND ALLAH YASA KEMA KINA LAFIYA YASA ALKHAIRI NE YA ƁOYE MANA KE MUNA KEWARKI SOSAI DA SOSAI😭, KIYI SAURI KI DAWO DAN ALLAH😭* Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 16 Murmushi Al'ameen ya sakar mata yana faɗin "Basma kece yau a office ɗina.?" Ya tsina fuska Basma tayi tana bin ƙayataccen office ɗin da kallo, yau ne farkon zuwanta office ɗin Dr Al'ameen, idanta ne ya faɗa kan wani tanƙamemen hoton Al'ameen da Meenat dake manne a bangon office ɗin, Meenat ta kwanto ta bayan Al'ameen aka ɗauke su hoton, dukkansu suna dariya, dammm! Taji gabanta ya buga tare da wani irin kishi da taji, tsananin kyawun da sukayi a hoton kanshi ya bugeta, to dama ai masu kyan ne😀😘 Muryar Al'ameen ta sake ji yana cewa "zauna mana Basma ga gurinan" saurin ɗauke kanta tayi daga kallon hoton ta dawo dashi kan Al'ameen tana ci gaba da ya tsinar fuska, kujerar daya nuna mata taja ta zauna, nan ma sai idanunta sukayi arba da wani hoton a saman tebur ɗin gabansa, shima su biyun ne da Meenat ɗinsa, wannan hoton yafi bawa Basma haushi saboda an ɗaukesu ne suka kallon juna tare da sakarwa junansu murmushi, kai kana kallon hoton ba sai ka tambaya ba kasan akwai tsantsan ƙauna tsakanin mutanen jikin hoton. Ajiye lemon da Al'ameen yayi a gabanta ne ya dawo da ita daga hayyacinta tare da saki wani irin ajiyar zuciya, murmushi Al'ameen yayi lokacin da yake tsiyaya mata lemon a cikin cup yana faɗin "nafa yi mamakin ganinki irin wannan lokaci Basma. " Kallonsa tayi tace "ba abin mamaki bane Dr Al'ameen dan ka ganni a office naka, dole ce ta saka nazo domin na tabbatar da gaskiyar labarin da nake ji a gari. " Komawa mazauninsa Al'ameen yayi ya zauna yana kallonta yace "wani irin labari kenan Basma. ?" Wani irin kallo ta jefeshi dashi kafin tace "na aurenka mana, " idanunta ne suka kawo ruwa ta ci gaba "da gaske ne wai kayi aure Doctor.?" Lumshe idanu Al'ameen yayi ya buɗe ya kalli Basma cike da tausayinta yace "am sorry Basma, gaskiya ne an ɗaura min aure satin da ya wuce. " Hawayen idanunta ne suka ida zubowa cikin rawar murya tace "wannan dalilin ne dama ya saka ka kashe dukkan wayoyinka ? Wannan dalilin ne yasa ko nemana ba kayi ? Sam ban zaci yaudara daga gareka ba dr Al'ameen, ɗauka nayi soyayyar da kakeyi min na gaskiya ce, ashe ban sani ba yaudarata kakeyi, kaico dani Basma da na yarda dakai har na baka soyayyata, me yasa zakayi min haka Al'ameen, me nayi maka wanda na cancanci ka yaudari raunanniyar zuciyata. ?" Ta ƙarashe maganar tana rushewa da kuka. Tasowa Al'ameen yayi ya dawo kujerar da yake fuskantarta ya zauna cikin sanyin murya yace "Basma ba yaudaranki nayi ba, wallahi daidai da minti ɗaya ban taɓa niyar yaudararki ba, ki sani shi bawa baya da ikon tsarawa kanshi rayuwa sai yanda Allah ya tsaro masa, ni kaina banyi tsammanin Meenat zata zamo mata gareni ba, na riga da na sakankance na rasata sai kuma Allah yayi ikonsa a kanmu ya mallakamin ita, Basma ko lokacin dana fara sonki ina tare da soyayyar Meenat, Meenat tun tana jaririya Allah ya saka min sonta a cikin zuciyata, ba wai dan nabar sonta bane yasa na fara nimanki, a'a kawai dan ina tunanin zan rasa Meenat ce, kuma shekarauna suna tafiya ya kamata ace nayi aure, domin a lokacin na riga da na sadaukar da soyayyata, sai kuma soyayyata ta dawo min a lokacin da banyi tsammani ba, Basma kina son sanin su waye Al'ameen da Meenat.?" Ɗaga kai tayi alamar eh hawaye na ci gaba da zuba mata, daga maganganunsa ta fahimci ƙanwarsa da yake bata labari ne ya aura wacce ta taɓa zaginta lokacin da ta kirashi a waya, kuma babu shakka ita ce a jikin hotunan nan, zata so sanin cikakkiyar tarihinsu da irin soyayya da sukeyiwa juna, duk da cewa zuciyarta nayi mata raɗaɗi na rashin Al'ameen da take tunanin tayi a halin yanzu. Ajiyar zuciya Al'ameen ya sauke ya miƙa mata hanky yace ta share hawayenta, amsa tayi ta fara share hawayen idanunta amma wasu suna ƙara zuba. Al'ameen ne yace "Basma bamu wani daɗe tare dake ba bare nace kinsan waye Al'ameen sosai, hasali ma zan iya cewa baki wani sanina ba saboda ban baki damar hakan ba, sai dai zan iya cewa kisan matsayin Meenat a gurin Al'ameen saboda irin yawan ambatanta da nakeyi in ina tare dake, to ina so kisan waye Meenat da Al'ameen a yau domin kibar zargin cewa ni Al'ameen na yaudareki...." nan Al'ameen ya fara bata tarihin rayuwarsu daga one har end, bai ɓoye mata komai ba game da soyayyarsu da Meenat da shaƙuwar da sukayi da juna, samarin da tayi yanda aurenta ta watse ya dawo kansa, yana kai aya ya kalli Basma sosai wacce ta zuba na mujiya tana sauraronsa yace "Basma kinji tarihinmu, anan ina so ki yanke min hukunci na yaudareki ? Ni wallahi ko da na fara da nemanki da niyar aurenki na zo ba da komai ba, Allah ne kawai ya juya Al'amarin. " Ajiyar zuciya Basma ta sauke tana jinjina soyayyar da sukewa juna shi da Meenat, abin yayi matuƙar burgeta sai dai kuma ta wani ɓangare tana jin takaici tare da kishin Meenat, cikin sanyin murya tace "na yarda baka yaudareni ba Al'ameen, amma me yasa baka kirani ko kazo gida ka faɗa min komai ba, sai dai naji a gari wai kayi aure.?" Murmushi Al'ameen yayi yace "wallahi Basma ina da niyar hakan, lokaci ne kawai ban samu ba. " "Hmmm,! Al'ameen kenan, amma fa har yanzu kana da damar aurena, saboda kai mijin mace huɗu ne, ni kuma nayi alƙawarin zama da ƙanwarka duk da nasan son da kake mata ko rabin rabinsa ba zan samu ba, Al'ameen wallahi ina sonka sosai. " Ajiyar zuciya Al'ameen yayi yace "gaskiya Basma banyi miki alƙwarin aure ba, saboda a halin da ake yanzu bana tunanin zan iya haɗa Meenat da wata mace. " Cikin jin haushi tace "kana nufin ba zakayi mata kishiya ba kenan.?" Murmushi Al'ameen yayi ya gyara zamansa sosai saman kujerar da yake yace "ko ɗaya, banyi alƙwarin ba zanyi wa Meenat kishiya ba saboda bansan me ƙaddara zatayi ba a gaba, sai dai bana tunanin hakan anan kusa, domin ko nan da shekara goma bana ganin zan iya haɗa Meenat da wata, ita kaɗai ce macen da nakeji zanyi rayuwa da ita ba tare da na taɓa gajiyawa da zama da ita ko soyayyarta ya ragu ba. " Lumshe ido Basma tayi wasu hawaye suka sauko mata tace "kana dai nufin na haƙora dakai kenan Dr Al'ameen. ?" Al'ameen yace "in dai gaskiya zan faɗa miki ba yaudararki zanyi ba to kiyi haƙuri Basma, tabbas da ban samu Meenat ba zan aureki, amma yanzu sai dai mace kiyi haƙuri ki kuma yafe min wasting time ɗinki da nayi, ina yi miki fatan samun miji wanda ya fini Basma. " Share hawayen idanunta tayi ta miƙe ta ɗauki jakarta ta kallesa tace "kaima ina yi maka fatan zaman lafiya kai da matarka, haƙuri ya zamar min dole doctor, ko ba komai ba zanyi ƙoƙarin tusa kai tsakanin irin wannan soyayyar ba, maganar samun miji wanda ya fika kuma anya kuwa a irin wannan zamanin da muke ciki zan samu namiji irinka wanda zaiyi min so tsakani da Allah, wanda baya da shakkar faɗin gaskiyarsa ko da ba zaiyiwa mutum daɗi ba. ?" Murmushi Al'ameen yayi yace "insha Allahu zaki samu wanda ya fini Basma ko dan kyawawan halayyarki, nayi burin samunki matsayin mata Basma, saboda kina da halayyar da duk namiji zaiyi fahari da samunki sai dai kash Meenat ta rufe zuciyata ta cillar da makullin a cikin takun maliya. " Murmushin kan laɓɓa Basma tayi tace "Allah ya amsa bakinka doctor, na barka cikin aminci sai na zo gida ganin amarya bye. " Tana faɗin hakan ta nufi ƙofa zuciyarta na mata zafi, amma ba yanda ta iya dole ta haƙura da soyayyar doctor Al'ameen ko tana ƙi ko tana so. Da kallo Al'ameen ya bita cike da tausayinta yana yi mata fatan alkhairi a cikin ransa, haƙiƙa Basma macece me sanyin hali da sauƙim kai matuƙa, baya mance ranar da suka fara haɗu da ita. Ranar ya dawo daga gurin aiki ne, kamar yanda ya saba tsayawa siyawa Meenat shawarma haka ma ranar ya kasance, bayan me shawarman ya miƙo masa ya saka hannu a aljihunsa ya fito da ƴan dubu guda uku ya bashi, sai me shawarman yace baya da chanji, shima Al'ameen sai ya ƙara laluba aljihunsa ko zai samu ɗari biyar, amma babu sai ƴan dubu kamar yanda yayi tunani, sai ya kalli me shawaman yace "gashi nima babu chanji anan, kawai ka bar..." be kai ƙarshen maganar ba yaji muryar Basma wacce take tsaye itama zata siya gashshen kilishi tace "bashi dubu ɗaya ga ɗari biyar na cika masa. " Kallonta Al'ameen yayi cikin murmushi yace "ayi haka ƙanwata, ai da kin barshi kawai ya riƙe chanji kawai. " Murmushi tayi tace "nasan duk yanda akayi kai costomarn sa ne amma ya kasa barin maka ɗari biyar, to kai a wani dalili zaka bar masa. " Ta ƙarasa maganar tana hararar me shawaman. Dariya ta bawa Al'ameen sosai cikin dariyar yace "to tunda ke gashi baki sanni ba kin iya min kyautar ɗari biyar to ni ma na baki kyautar ki amshi 1000 ɗin kawai ki riƙe a gunki. " Waro ido tayi tare da turo baki cikin shagwaɓa tace "naƙi wayon, wato baka son na samu ladan sai kai ko. ?" Cikin murmushi Al'ameen yace "waneni, ai an riga an baki ladan tuni. " Itama murmushi tayi tace "bayan ka dawo da kyautar kaina kuma. " Hannu Al'ameen ya saka ya amshi dubun yace "to nagode, ina ce shikenan yanzu ke ne da ladan. " Murmushin jin daɗi tayi tace "yauwa ko kai fa, har naji daɗi. " Shi dai me shawarma kallonsu kawai yakeyi yana murmushi, Al'ameen ne ya ƙara sakin murmushi yace "nagode sosai fa ƙanwata, sai gani na biyu. " Yana faɗin haka ya juya ya bar gurin, murmushi Basma tayi tace "da alkhairi" ta juya tana cewa me shawarman ya bata kilishi na dubu uku. Al'ameen har ya ɗanyi nisa da tafiyarsa ya juya yace "ba ki ji ba!" Juyowa Basma tayi tana kallonsa, yace "baki faɗa min sunanki ba kuma. " Amsar kilishin da me shawarman ya miƙo mata tayi ta tako a hankali ta iso gurin Al'ameen, sai da ta zo kusa dashi sannan tace "sunana Basma. " "Basma" Al'ameen ya maimaita sannan yace "nice name. " Murmushi tayi tace "nagode kai ya sunanka.?" Nufar motarsa yayi yana faɗin "Dr Al'ameen Hassan. " Itama dai maimaita sunan nasa tayi ta bisa da kallo har ya shige motarsa, har Al'ameen yayi ribas zai fita daga gurin ya leƙo yace "na ga kamar baki da abin hawa ko zaki zo na rage miki hanya ne.?" Cikin jin daɗi Basma ta nufi motar tana faɗin "aiko naji daɗi wallahi, dama ina tunanin yanda zan koma gida dan yamma tayi masu taxi wuya sukeyi. " Nan dai ta buɗe gaba ta shiga ta rufe shi kuma yaja motar suka fice daga gurin, sai da ya hau ƙwalta sannan yace mata ina zai kaita nan tace masa rijiyar zaki, sai da Al'ameen ya sauketa har ƙofar gidansu sannan ya juya kan motarsa ya nufi nasu unguwar bayan sunyi musayar numbern wa juna, to tun daga wannan rana alaƙarsu ta faro, da a gaisuwa na yaya da ƙanwa ya rikiɗe ya koma na saurayi da budurwa. _Wannan kenan_ Ajiyar zuciya Al'ameen ya sauke lokacin da ya dawo daga duniyar tunanin daya faɗa, miƙewa yayi ya tattara komatsensa ya fito daga office ɗin ya silale ba tare da ya bari kowa ya gansa ba ya nufi gida, dan babu abinda yake buƙata a halin yanzu irin yayi tozali da meenat ɗinsa. Bayan getman ya buɗe masa get ɗin adana motar yayi cikin parking space sannan ya ɗauki briefcase ɗinsa ya buɗe motar ya fito ya mayar da murfin motar ya nufi cikin gidan cikin takunsa na zaratan maza, da sallama ya murɗa ƙofar falon ya shiga. Meenat dake zaune a falon ɗauke da wani ƙaton littafi tana dubawa tsilli tayi da littafin ta tafi da gudu ta ɗaneshi ɗaf, cikin nishaɗi Al'ameen ya fara juyi da ita a tsakiyar falon suna ƙyaƙyata dariya, to dama dai Meenat ba wani nauyi ke gareta ba abinka da siririya. Be direta a ko ina ba sai saman kujerar falon suna dariya tare da maida numfashi, cikin murmushi Meenat ta kallesa tace "barka da dawowa my habibi ya aikin.? " Shafar fuskarta Al'ameen yayi cike da ƙaunarta yace "barka da gida my blood, i hope kin yini cikin ƙoshin lafiya.?" Wani irin juya idanu Meenat tayi wanda ya tafi da imanin Al'ameen tace "ina ko zan kasance cikin ƙoshin lafiya alhalin ruhina baya tare dani. " Ɗan murmushi Al'ameen yayi yaja kumatunta yace "to gani na dawo my blood komai normal ko. ?" Ɗaga masa gira tayi tace "yes sir, ruwan wanka da abincinka is ready. " Sumbatar bakinta yayi ya lumshe ido yace "so sweet my baby. " Be buɗe idanunsa ba yaji Meenat ta haɗe bakinta da nashi ta fara tsotsa tare da zura hannunta cikin rigarshi tana shafar lallausar gashin ƙirjinsa, tuni ta gigita Al'ameen, nan ya fara maida mata da martani, nan fa komai ya kwance musu suka shiga duniyar maji daɗi, a hankali Al'ameen yakai hannu saman dukiyar fulanin Meenat ya fara murzasu ba tare da yabar tsotsan bakinta ba suna musayar yawu wa juna, banda nishi babu abinda sukeyi. Ganin haka yasa na siɗaɗa a hankali naja musu ƙofar na fice daga falon, nace su kuma waɗannan haka akeyi🤔 Daƙyar suka rabu da juna Al'ameen ya rungumota jikinsa suna maida numfashe, idanun Meenat a rufe tace "my ƙalbi tashi muje kayi wanka kazo kaci abinci. " Daƙyar Al'ameen ya buɗe baki yace "to my sweet muje. " Yunƙurawa yayi da ita ajikinsa suka nufi hanyar ɗakinsa, tare sukayi wankan sannan suka fito, shiryawa Al'ameen yayi cikin three quater da ƴar ƙaramar riga Meenat ma dai wata rigarsa da saka wacce ta tsaya mata iya cinya dan ba kayan da zata saka a ɗakin, a haka suka fito zuwa dining, saving ɗinsa tayi sannan ta zauna ta fara bashi a baki, tare suka ci abincin yana bata tana bashi har suka ƙoshi, tattara kwanukan sukayi suka je kitchen suka wanke sannan suka dawo falo suka zauna tare da kunna wani india flim suna kallo. Ku ci gaba da haƙuri da Raheenat pleace reader's👏 Muje zuwa🥰 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 10:59 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 17 Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya musu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, masoyan suna iya ƙoƙarinsu na ganin sun faranta ran juna, Meenat duk wani abu da tasan yayanta yana so shi takeyi masa, yanda baya son ɓacin ranta haka itama take gudun nasa ɓacin ran, zaman nasu dai gwanin burgewa daban sha'awa. *Bayan sati uku* Da gudu ta fito saɓe da jakarta ta buɗe motar ta shiga ta zauna tana haƙi, kallon Al'ameen tayi wanda har ya data motar sai dariya yakeyi mata tace "yanzu nurul ayni da gaske zaka iya ka tafi ka barni. ?" Wani kallo Al'ameen yayi mata yace "me zai hanani tafiya kuwa kina neman sakani latti gurin aiki, tun jiya da dare ake shirin nan amma har gari ya waye yaƙi ƙarewa, daga zaki koma makaranta yau sai kuma ni nayi lattin zuwa aiki, ba sai nayi tafiyata ba kya hau taxi. " Cikin wani salon tace "ai kaine dajin kunya in na hau taxi ɗin, cewa za a dinga yi matar doctor Al'ameen tazo a taxi duk da tarin motocinsa. " Dariya Al'ameen yayi lokacin da yake fita daga get ɗin gidan bayan getman ya buɗe masa get, yace "ko ke kiji kunya ba, saboda ƙiri-ƙiri kin kasa iya moto balle ki tuƙa kanki, Isma'il yanzu babu inda ba zai shiga da mota ba amma ke ƙatuwa dake ko sitiyarin ba zaki iya riƙewa ba. " Taɓe baki tayi tace "banyi ra'ayi bane kawai kai kanka ka sani, amma zaka sha mamaki kwanan nan zan fara tuƙa mota, kaga sai na taimaka maka na rinƙa kaika gurin aiki sannan ina wuce makaranta. " Dariya Al'ameen yayi yace "da yake na zama ke ko. " "Kamar ya ka zama ni.?" Al'ameen yace "ina nufin nima ban iya motar ba ne kamar ke balle in jira sai kin saukeni. " Gyara zama tayi a mazauninta tana kallonsa tace "wato kenan ni ɗin taimaka min kakeyi.?" Gintse dariyarsa yayi yace "kusan hakan. " Ƙwafa Meenat ta saki tace "aiko zan baka mamaki, in dai taimaka min dama kakeyi to ka kusa bari. " Al'ameen hankalinsa na kan kwalta yace "da kin birge kuwa. " Meenat bata ƙara magana ba sai ciro wani littafi da tayi tana dubawa tare da ƙudurawa a ranta zata dage ta koyi mota cikin sati biyu saboda ta bawa Al'ameen mamaki, ba yana mata gori ba, kuma tasan da gangar yakeyi mata, dan tun tana kan ƙuruciyarta yake binta tazo ya koya mata mota, lokacin sai dai tayi dariya tace "wani koyan mota kuma zanyi ina dakai yaya, nasan duk inda zani zaka kaini to ai ba sai na koya ba. " Murɗa kunninta ya kanyi duk sanda tace haka yace "wato gani direbanki ko.?" Dariya takeyi masa tace "sosai ma kuwa. " To nan fa zata kwasa a guje shi kuma ya rufa mata baya suyi ta zagaye gidan wai ta kirasa direba. A haka har suka isa makarantar ya paka motarsa a parking space na makarantar ya kalleta yace "to Ameenatuwa ayi karatu sosai, kinsan dai yanzu kun kai level ɗin da karatunku baya son wasa ko ?" Turo baki tayi gaba cikin shagwaɓa tace "da wani suna ka kirani yanzu.?" Murmushi yayi yace "meenatuna nace ina ganin ko.?" Hararar wasa tayi masa tace "ka tuna dai. " Murmushi yayi ya shafi fuskarta yace "ina sonki my blood, ki kula min da kanki sosai har lokacin da zan dawo ɗaukarki kinji. ?" Murmushi tayi tace "insha Allah, kaima ka kula min da kanka, duk wacce ta kalleka ban yafe mata ba. " Dariya Al'ameen yayi tare da waro manyan idanunsa yace "to taya zan hana mata kallona su da idanunsu. " "Au haka ma zaka ce? To shikenan kaje suyi ta kallonka, ni dai nace ban yafe wa duk wanda ta kallar min miji ba. " Tana gama faɗar haka ta buɗe motar zata fice, riƙo hannunta Al'ameen yayi ya dakatar da ita daga fitar, juyowa tayi tana kallonsa, bakinsa ya kai ya sumbaci goshinta sannan ya sumbashi bakinta yace "ba kiyi min addua ba fa yau kuma zaki tafi. " Lumshe ido tayi ta buɗe tana murmushi tace "Allah ya kiyaye ya tsare min ke da dukkan abin ƙi, yanda ka tafi cikin ƙoshin lafiya ya dawo min dakai cikin ƙoshin lafiya, ya buɗa maka ƙofofin nemanka ya kuma tsareka daga faɗawa hanyar da bata dace ba, Allah baka dukkan abinda kake nema ya ɗauraka akan maƙiyyarka kafi ƙarfinsu. " Cikin jin daɗi Al'ameen yace "ameen ameen my meenat, nagode da addua. " Murmushi tayi ta shafi sajensa tace "karka damu haƙƙina ne yi maka addu'a, bye. " Tana faɗin haka ya fice daga motar tana ɗaga masa hannu, shima hannun yake ɗaga mata sannan ya tada motar ya fice daga school ɗin, sai da taga fitarsa sannnan ta nufi hanyar class ɗinsu. *Note* _Ya kamata ace mata muna yiwa mazajenmu addu'a a duk lokacin da zasu fita gurin nemansu, domin hakan na ƙara soyayya tsakanin mata da miji, wallahi har yaje ya dawo ba zai manta da addua'rki ba, kuma ko kin manta addu'ar mata ga mijinta karɓaɓɓe ne gurin ubangiji ?, bance duka ba mayi ba, amma wallahi da yawanmu in miji zai fita basu san suyi masa addu'a ba, me dama dama ce kawai za tace a dawo lafiya ko sai ka dawo, wata ko Allah Allah takeyi mijin ma ya fita ya bata guri, zaka ji da yace wance ni zan fita sai tace to sai ka dawo, to ya dawo yayi miki me ? Nifa ban ɗauki sai ka dawo matsayin addu'a ba, ai ko mutumba kice ba in Allah yaso zai dawo, magana ana shine miji yace wance sai na dawo mace tace to Allah ya dawo da kai lafiya ya tsare min kai ya baka abinda ka fita nema, Allah ya azurtaka da halas ɗinka ya tsareka daga cin haram, dadai makamancinsu cikin tausasa lafazi da nuna zakiyi kewarsa, to shi kansa zaiji daɗi ya fita cikin farin ciki, amma wata ma tana daga kwance kan gadonta zaka ji tana cewa sai ka dawo, yana juyawa ya fita za tace gara ma ka fita na huta, wata ko ko kallo ma mijin be isheta ba in zai fita ko sai ka dawon ma ba zai samu daga gareta ba, to me kike zato ? Wallahi ba zai fita yana tunaninki ba balle har in ya tuno dake yaji farin ciki, me makon farin ciki in ya tuno dake sai dai yayi baƙin ciki, Wallahi naga wata mata da mijinta in zai fita yace mata sai ya dawo sai dai tace yanda ka fita haka zaka je ka dawo, insha Allahu babu abinda zaka samo, kuma wallahi da wahala yaje ɗin ya samo, saidai ta nemi abinda zata ci ita da ƴaƴanta a aljihunta, to dan Allah wa ya kwana a ciki ? Kuma badan komai take masa haka ba sai dan baya dashi, to wallahi tallahi na tabbatar da zata bisa da kyakkyawar addu'a lokacin da zai fita kuma da zuciyarta ɗaya to wallahi cikin hukuncin ubangiji sai ya samo abinda za suci, amma jahilci da rashin sanin darajar miji ya sakata hauka, Allah yasa mu gane kuma mu gyara, domin addu'ar mata ga mijinta babban garkuwa ce garesa, Allah ya bamu ikon yiwa mazajenmu addu'a a dukkan sallolinmu da lokacin fita nemansu, ya rabamu da son zuciyarmu ya karemu ya kare zuri'armu, ameen👏_ ************ Yinin wannan ranar Al'ameen yana aikinsa ne yana tuno da Meenat ɗinsa, a duk lokacin da ya tuno da ita sai dai kawai ka ga Al'ameen ya saki murmushi shi kaɗai kamar wani taɓaɓɓe. _Hhhhhh, reader's karfa kuga laifin Al'ameen, ba iya soyayyar da yakeyiwa Meenat bane yake sakasa nishaɗi in ya tuno da ita, har ma ta tsaban kulawar da take bashi tare da mayar dashi kamar yaron goye da tayi tsaban tattali da nuna soyayya._ A haka a daddafe ya iya kai ƙarfe ɗaya da rabi a asibitin, cikin hanzari ya fito ya shiga motarsa ya nufi makaranta dan ɗauko rabin ran nasa dan yasan zuwa yanzu ta fito daga lectur tana jiransa. Aiko yana isa ya sameta bakin get tsaye da Suhailat suna hira, tana ganin motarsa ta saki murmushi ta kalli Suhailat tace "ga sanyin idaniyata nan kuma mintin zuciyata ya ƙaraso. " Ɗan harararta Suhailat tayi tace "kefa Meenat baki da kunyar kirar yah Al'ameen da ko wani irin suna gaban koma waye. " Itama hararar Suhailat ɗin tayi tace "kunya wa to zanji, ƙarya nakeyi ne, a duk sunan da zan kira yah Al'ameen dashi ya cancanceshi ne, ni kinga tafiyata sai gobe kar na ɓatawa lolipop ɗina time. " Tana faɗin hakan ta nufi motarshi da sauri. Murmushi Suhailat tayi tare da girgiza kai tabi Meenat da kallo har ta shige motar Al'ameen, haƙiƙa soyayyarsu yana matuƙar burgeta, tana fata da addu'ar samun miji da zai muna mata soyayya da kulawa ko rabin wanda Al'ameen ke nunawa Meenat ne. Meenat kuwa da sallama ta shiga motar tare da faɗin "barka da rana masoyina ya aiki.?" Al'ameen yana kallonta yace "barka dai my blood, aiki alhmdllh, ya karatun.?" Yamutsa fuska tayi tace "karatu fa babu daɗi my happiness. " Cikin nuna tausayawa yace "am sorry my ni, nasan karatun likitanci akwai wahala sosai, yanzu muje gida ki ci abinci sai ki kwanta ki huta ko. " Shagwaɓe fuska Meenat tayi tace "na gaji sosai fa, ba zan iya girka komai ba ko mun isa, kuma kasan bamu da abinci. " Tada motar yayi yana faɗin "karki damu, sai mu biya mu siya abincin sannan mu wuce gida, dan nima ba zan koma asibitin ba sai kuma Allah ya kaimu gobe. " "Allah ya nuna mana " cewar Meenat tare da kwantar da kanta jikin seat ɗin tana lumshe idanu. ********** Haka ko akayi, sai da suƙa biya sukayi take-away sannan suka nufi gida, ko da suka isa gida abincin kawai Meenat taci tayi wanka ta haye gado sai bacci, dan kamar yanda tace ne ta gaji, domin lecture ɗin yau ya chaza mata kai da yawa, shima Al'ameen bayan yayi wankan bayanta yabi shima ya kwanta. ***** *Bayan wata bakwai* Meenat ce na hango zaune saman kafet tayi zaman dirshan ta tasa zogale gabanta sai aikawa baka takeyi kamar tana gudun wani ya ƙwace mata. Al'ameen dake zaune gabanta ya zuba mata ido yana kallon yanda take cin zogalen cikin sauri yace "kiyi a hankali mana my Meenat karki ƙware, ke kaɗai fa kike ci ba da wani ba, kuma in kin cinye be isheki ba zan ƙaro miki wani. " Lomar da ta ɗibo takai bakinta ta tauna sannan ta kallesa tace "ba zaka gane bane Nurul hayat, zogale daɗi ne dashi sosai kamar zuma, kai yama fi zuma daɗi." Dariya Al'ameen yayi yace "tabbas yafi zuma daɗi a gurin irinki masu ciki. " Cikin shagwaɓa tace "nifa cikina na cin abinci ne tam. " Murmushi Al'ameen yayi yace "ai daga nacin abincin ne yake zama na ɗa. " Ajiye plate ɗin zogalen tayi bayan ta cinye tace "kasan me nake son cin yanzu .?" Kallonta Al'ameen yayi yace "sai kin faɗa. " Mere baki Meenat tayi tace "wainar fulawa nake so. " Murmushi Al'ameen yayi yace "an gama uwan biyu. " Yana faɗi ya miƙe yayi hanyar kitchen. Muryar Meenat yaji tana faɗin "kar ka saka ƙwai a ciki yayah, zallar fulawar nake so. " Al'ameen be juyo ba yace "baki da matsala dani tawa. " ************ Cikin minti goma sha biyar sai ga Al'ameen ya fito ɗauke da plate tare da robar yaji ya dire gaban Meenat, aiko ba ta jira komai ba ta hau cin abinta tana cewa "Allah yayi maka albarka yayana, shi yasa fa kullum nake ƙara sonka. " Murmushi kawai Al'ameen yayi ya nufi fridge ya ɗauko ruwa ya ajiye mata a gaba, dan tunda Meenat tayi ciki bata shan lemo ko wani irine, abinci ma ba ko wanne take ci ba, barta dai gurin ƙwaɗayi, kuma matuƙar akayi abu a gabanta taji ƙamshinsa komin sonta dashi ba zata iya ci ba, shi yasa duk abinda tace tana so Al'ameen in dai ya iya sarrafashi to zai shiga kitchen yayi mata ya kawo mata, in be iya ba yaje Umma tayo mata ko kuma ya siyo a restaurant Tas ta cinye tasha ruwa, hamma ta fara yi tana miƙa, kallonta Al'ameen yayi yace "ya dai.?" Cikin kasalalliyar murya tace "bacci. " "To miƙe muje kiyi brush sai ki kwanta ko. " Yayi maganar yana kamo hannunta ya miƙar da ita tsaye, ganin cikin da nayi ya fara turo riga ne yasa na waro ido nace oh ni Raheena yaushe cikin Meenat ya girma ne bani da labari🤔, wani harara Al'ameen ya jefo min yace "kya dai ji da gulmarki. " Nima hararar na dalla masa nace "to ni nasan sanda kayi cikin ne balle nasan girmansa da kake wani hararata. " Murmushi kawai yayi ya riƙe Meenatunsa yana cewa "my Meena zo kinji muje ki mu ƙyale wannan uwar bin ƙwaƙƙwafin. " Bayansu nabi da harara nace "naji ɗin, da ban bin ƙwaƙƙwafin ai da reader's ba suji labarinku ba. " Ku ya kuka ce reader's😉 Sai da yayi mata brush sannan ya kaita har gado ya kwantar da ita, lumshe idanta ta farayi a hankali a haka bacci me daɗi ya ɗauketa, tsura mata ido Al'ameen yayi yana kallo cike da tsantsan ƙaunarta, shafan fuskarta yayi yace "Allah ya saukeki lafiya ƙanwata ki haifo min yaro ko yarinya me kama dake. " Nidai nace ameen. Yana nan zaune yana gadinta kamar an ce masa wani zai saceta😏 Shima baccin yayi gaba dashi daga zaune, can kuma ya ɓingira ya gyara kwanciyarsa saman gadon... Muje zuwa😘 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 11:00 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ *INA MIƘA SAƘON GAISUWA TARE DA FATAN ALKHAIRI GA DUK MAKARANTA LITTAFIN NI DA YAYA AL'AMEEN, HAƘIƘA KUN NUNAWA RAHEENAT SOYAYYA, WALLAHI HAR CIKIN RAINA INA JIN DAƊIN YANDA KUKEYI MIN ADDUA TARE DA BIBIYAR NOVEL ƊINA, DAGA FARA WANNAN NOVEL ƊIN ZUWA YANZU BA ZAN IYA CEWA GA ADADIN SAƘONNIN DANA AMSA GAREKU BA READER'S, KUMA DA YAWANSU JINJINA CE TARE DA ADDU'OI, GASKIYA BAKINA BA ZAI IYA FAƊIN IRIN FARIN CIKIN DA NAKEYI BA ADUK LOKACIN DA NAYI ARBA DA SAƘONNIN MASOYA💘, SAI DAI KAWAI NACE MUKU INA FARIN CIKI MATUƘA, NI RAHEENAT KO DA MAFARKI BAN TAƁA TSAMMANIN LITTAFAINA ZASU SAMU ƊAUKAKA IRIN HAKA BA WALLAHI, SAI GASHI ALLAH YA ƊAUKAKANI TARE DA LITTAFAINA. ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN🥰* _BAZAN MANTA DAKU BA MASOYAN ƘWARAI, DUK INDA RAHEENAT TA SHIGA A DUNIYA KUNA MAƘALE CIKIN RANTA SABODA GIRMAN MATSAYIN DA KUKE DASHI A GARETA, KUMA RAHEENAT TANA DA TABBACI A GAREKU SO KUKEYI MATA DOMIN ALLAH_ AUNTYNA MARYAM A.I GITAL SAMEERA HARUONA (MY MEERA) BILKISU Z. YA'U (MY BK) MUGIRAT MUSA (MY MUGITA) KAWAI KU HUTA KUJI DAƊINKU RAHEENAT NA YINKU, LOVE YOU TO ALL MY HEART ALLAH YA AMINTAR DAKU😘🤝 Ban mance daku ba kuma Fauziyya Muhammad wakili Shafa'atu Bala Baba Maman labyb Adama Tanimu A biye Safiya bello Fauziya s madaki Hauwa Jamil kakud ɗita ba😘 Aisha nichoi Sameera My Beebar Alawiyya Maman khairat Amina Muhammad maiduguri (one love) Kuɗin na daban ne ƴan hannuna, ku sani Raheenat na yinku, tabbas soyayyar da kuke nunawa Raheenat zan iya cewa babu wani fans ɗina da yake nuna min irin haka, hakan yasa nake sakaku cikin masoyana sahun farko, nasan so ne kukeyiwa raheenat badan littafanta ba, wallahi rahina na yinku kuma tana sonku da zuciyarta ɗaya💘, kawai ku huta kuji daɗinku😘 *MY MATAR ABOKIN MIJI, BASAI NA ANBACI SUNA BA NASAN KINSAN DAKE NAKEYI😘, SOYAYYARMU HAƊINE KAWAI DAGA RABBI, BA SAI NACE KINA YIN RAHEENA BA, SABODA FAƊAMA ƁATAWA NE, TO KI SANI RAHEENA NA YINKI FIYE DA YANDA KIKE YINTA. LOVE YOU MY MATAR ABOKIN MIJI💘,KI HUTA KAWAI KIJI DAƊINKI ALLAH YA ƊAURAR MIKI DA LAFIYA YASA ABINDA MUKE NEMA NE YA SAMU🥰🤝* Duk yanda akaje ka dawo raheena ba ta mancewa da masonta koda bada gaske yakeyi ba, to matuƙar dai yace yana sonta ya zauna cikin zuciyarta kenan, to balle ku da ko yaushe bakwa gajiya da bibiyar novel ɗina tare da yaba min, to ban mance daku ba musamman Aisha Idris Aysha Ahmad Jawahir Gombe Nafisa Abubakar Farida Abudoul kader Hanipha Muhd Kabir Memeey Zarah A musty Harazimiyya lagos Bilkisu Abubakar Lashminzy Maman Yasmin Mummyn sultan Maman Abulkhairi Hafsat A.A Hafsatou Adabiyya Isa Aysha Hafsat B Umar Ruƙayya Yareemerh Fatee shehu (my fatee) Oum Ayeesh Miss fansy Sauderth Ummi Kabir Ummu akram Maman Husna Mareeya Bilkisu Karouna Saudatu Lawal Ruƙayyat Ad Baffa Maijidda Khadija ringim Khadija A hamza darazo Khadija Abdullahi Meenat Isma'il Maman Ameera Zinatu Aliyu Hamza Fatee barde Maman Ihsan Fusaina Mustapha (surukata) Mummyn Yasmin Habiba ɗantakai Nanah Firdausi Quren zee Sadiya Tanko Amina muhammad (dotana) Fatima haruna Bint abiha Madaniyya Hajara inuwa Queen zarah Auntancy Bilkissa Aisha eesha Deeja suraj Ummu rauda Zahara zinariya Momyn Khadija Momin nihlat Rashyda Miss Xerks Hafsat hamza maman ahmed Ummu eman Ruƙayyah Nafisat Fareeda ya'u Zainab Abdullahi Zainab m Kabir Zainab sarki Ameenatu Naseer Maman Abbulkhairi Ummiter Darmah Kausar sidibasha maiduguri Aisha Abdullahi kaduna Sareena N@j@'@tu Nur@ Masha Allah Bilkisu Aliyu skt Xee saleh Maman nazir Mama Khaleefa Fatima muhammad Raheeda Bara Maman dady Mom muheep Fatima maihadisi Mmn Auwal Saratu balarabe Kgadija Deey Oum Sadeeq Maryam Abacha Jeeddah adamawa Amatullah Khadeey Saudat b chiroma Beebat Amina Abubakar Aishmar Hauwa s. Yahanasu Abubakar Rabi'at Yusuf Nana Khadijat Maman Sauban Lubabatu Shehu shayi Salmat Nafusat Abba Yasmina Shamseeya street Hauwa Ibrahim Teemah Suleman Hauwa kaseem Maman Faruk Maman farouq Tauraruwa Zainab Abdullahi Bintu Umar Aisha Musa Zainab hassainu u.d Aisha yero Ummu farhan Ummu basma Amina tambuwal Elusmay ( Aunty Fatee ƴar sudan😁) Chappa Ƴar mulki Feenah ƙamshi Princess deejert Miss fancy Ku huta kwai kuji daɗinku Raheenat na yinku irin sosai ɗinnan fa😘 *KO WANI IRIN MATSAYI NA TAKA A RAYUWA WALLAHI BAZAN MANCE DA IRIN GUDUMMUWAR DA KIKA BANI A RAYUWA BA BILKISU Z. YA'U, HAƘIƘA KIN TAKA MUHIMMIYAR RAWA KAFIN RAHEENAT TA FARA RUBUTU, NIKO ME ZAI SAKA NA MANCE DA WANNAN?, AIKO DA NA ZAMA BUTULU INDAI NA MANCE DA WANNAN, KECE ƘARFIN GWIWAR RAHEENAT KUMA MADUBIN DUBAWANTA KUMA FITILAR DAKE HASKAKA MATA HANYA, INA MIƘA TARIN GODIYATA GAREKI TARE DA FATAN ALKHAIRI, ALLAH YA TSAREKI YA KAREMIN KE, ALLAH YA BAKI LAFIYA INGANTACCIYA YA KAWO MIKI MIJI NA GARI, KI SANI RAHEENAT NA SONKI KUMA TANA YINKI, ALLAH YA AMINTAR DAKE👏😘* Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 18 Sai misalin ƙarfe huɗu Al'ameen ya farka, miƙa yayi tare da salati sannan ya miƙe, kallo Meenat yayi wacce har yanzu take sharrar baccinta bata farka ba, murmushi yayi sannan ya sauko daga kan gadon a hankali ya nufi toilet, alola ya ɗauro sannan ya fito ya shimfiɗa sallaya ya kabbara sallah. Ya idar kenan ya zaune yana addu'oi Meenat ta farka da salati a bakinta, juyowa yayi yana kallonta, nan take suka sakarwa juna murmushi, Al'ameen ne ya fara magana yace "kin tashi my blood. ?" Lumshe ido tayi ta buɗe alamun eh ba tare da tayi magana ba, murmushi ya kumayi yace "na zo ne na taimaka miki.?" Girgiza kai tayi tare da sakar masa harara tana me sauko da ƙafafunta daga kan gadon, sai da miƙe tsaye sannan tayi magana tace "tunda nayi ciki ka mayar dani malalaciyar ƙarfi da yaji, komai sai kace zakayi min kamar an gaya maka ba zan iya ba, sam baka son na motsa jikina kamar ba likita kake ba. " Ta ƙarasa maganar tana masa wani irin kallo harara harara love love tare da nufar toilet. Dariya Al'ameen yayi yace "Allah ya baki haƙuri gimbiyata, naga kamar dai da rigima aka tashi baccin nan. " Ba ƙara tankasa ba ta shige toilet abinta. Yana nan zaune ta fito ta saka hijjabi ta fara sallar, daƙyar daƙyar take sallar har ta kammala, saboda cikin nata ba ƙaramin girma yayi ba, watanshi bakwai kenan yanzu. Kallonta Al'ameen yakeyi cike da tausayi har ta idar, matsawa yayi ya fara daddan na mata ƙafafunta da ta miƙar dasu bayan kammala sallar saboda kunburi da sukeyi mata. Kallonsa kawai Meenat takeyi har ya kammala matsa mata ƙafafun yana faɗin "wannan kumburin ƙafar yaƙi ya barki my blood, kuma iya bincike sai dai ya nuna babu komai. " Murmushi tayi tace "to ai ba sayi min ciwo meye abin damuwar, wani lokacin a kaina na lura mancewa kakeyi kai doctor ne. " Kallonta yayi yace "kinsan yanda na keji a raina kuwa, wallahi da akwai yanda zanyi cikin ya dawo jikina da nayi my blood, ina matuƙar tausaya miki. " Shafar fuskarsa Meenat tayi tana murmushi tace "karka damu kanka my habibi, bana jin wani ciwo ajikina, kawai dai cikin ne ya fiye girma da yawa. " Ta ƙarasa maganar tana kallon cikin. Shima cikin yabi da kallo tare da kai hannu ya shafashi yace "Allah ya rabaki da cikin nan dai lafiya, ni girmanshi har tsoro yake bani saboda ɗa ɗaya yake nunawa a duk skyning ɗin da akayi. " Ameen Meenat tace tana ƙara kallon titsetsen cikin nata kamar wanda ya haura watan haihuwa. Al'ameen ne yace "my blood me zaki ci naje na ɗaura miki. ?" Shiru ta ɗanyi alamun tunani, can ta kallesa tace "ɗan wake nake son ci, amma na Ummana nakeso ba naka ba. " Dariya yayi yace "yau kuma.?" Juya idanunta tayi tace "eh mana. " "To miƙe muje nayi miki wanka muje gidan kici a can. " Aiko cike da ɗoki ta yunƙura zata miƙe da sauri ya riƙota yana faɗin "bi a hankali mana my blood. " Miƙar da ita yayi ya nufi toilet ɗin da ita, cikin ƙanƙanin lokaci ya wanke abinsa tas ya ɗauro mata towel ya taimaka ya riƙota suka fito, bakin gado ya zaunar da ita ya ɗauko manta ya shafa mata, ya ɗauko hoda zai sanya mata ta riƙe hannunsa tare da girgiza masa kai tace "bana sonta shafa min lip gloss kaɗai ya isa. " Kamar yanda tace haka yayi mata, kayanta ya je ya buɗe ya ɗauko mata wata doguwar riga ya sanya mata, dan yanzu dogayen riguna ne kaɗai suke shigarta ta daɗin rai, suma ba ko wanne ba. Bayan ya gama shiryata kallonta yayi yace "to nima bari naje nayi nawa wankan nazo ko. ?" Riƙo hannunsa tayi tace "muje ɗakin naka tare, bana son zama ni ɗaya. " "To taso muje " ya faɗa yana taimaka mata ta miƙe, hannunta ya kama suka fito daga nata ɗakin suka nufi ɗakinsa. ********** Wanka yayi ya fito ya shirya cikin ƙananun kaya Meenat na kallonsa har ya gama shiryawa, kusa da ita ya matso yace "to tashi muje ko my blood. " Miƙewa tayi daƙyar ta fito, shi kuma ya ɗauko makullin motarsa tare da rufo ƙofar ɗakin ya riƙo hannunta cikin nasa suka fito daga cikin gidan, saida ya rufe ƙofar falon sannan suka nufi parking space, da kanshi ya buɗe mata gidan gaba ta shiga sannan ya zagayo ya buɗe mazaunin direba ya zauna ya tada motar. Get man ne ya buɗe musa get ya fice daga gidan suka nufi nasarawa g.r.a. ************ Suna isa Meenat ta buɗe motar da sauri ta fito, kallonta Al'ameen yayi bayan shima ya fito yace "dan Allah kiyi a hankali my blood. " Ko kallonsa Meenat ba tayi ba ta nufi cikin gidan, murmushi yayi yabi bayanta da sauri tare da riƙo hannunta, a haka suka shiga cikin falon bakinsu ɗauke da sallama, Umma dake zaune akan kujera two seater ne ta amsa musu cikin fara'a tare da miƙewa ta riƙo hannun Meenat tana faɗin "ga ƴata ga ƴata. " Murmushi Meenat takeyi kawai har suka zauna, kallonta Umma tayi tace "sannu ƴata." Cikin jin kunya Meenat tace "ina wuni Umma. " Fuska fal murmushi Umma tace "lafiya ƙalau ƴata, ya nauyi jiki kuma. ?" Meenat bata amsa ba sai ƙasa da tayi da kanta, Al'ameen ne da shima ya nemi guri ya zauna yace "ina wuni Umma.?" Sai lokacin Umma ta dawo da kallonta gareshi tace "lafiya ƙalau Al'ameen, ya kuke.?" "Lafiya ƙalau wlh Umma, yanzu ma Meenat ce tace tana son cin ɗan wake, kuma wai naki, shine na ɗaukota muka tawo. " Murmushi Umma tayi ta kalli Meenat tace "in dai wannan ne an gama ai, yanzun nan zan saka miki ɗan wake kici har ki ture ƴata, bani minti goma ina zuwa. " Tana gama faɗin hakan ta miƙe ta nufi hanyar kitchen da saurinta. Al'ameen yana ganin shigewar Umma ya dawo kusa da Meenat ya zauna yana cewa "shikenan hankali ya kwanta ko.?" Meenat tace "be kwanta ba tukunna dai, dan har sai naci ɗan wake hankali zai kwanta. " Dariya yayi yace "ai yanzu zaki ci insha Allah. " Nan dai suka ci gaba da hirarsu jifa jifa, cikin mintoci kaɗan sai ga Umma ta fito da plate shaƙe da ɗan wake wanda yaji salat da dafaffen ƙwai ta ajiyeshi gaban Meenat tana faɗin "sauko ƙasa ƴata ko zaki fi jin daɗin ci. " Aiko sauko Meenat tayi tayi zaman dirshan ta fara aikawa da ɗan waken nan kamar ta samu nama, kallonta Umma da Al'ameen kawai sukeyi ganin yanda take masa cin ƙwan mahaukaciya. Tas ta cinye ɗan waken nan, ruwan da Umma ta ajiye mata ta ɗauka tasha sannan ta saki wani irin ajiyar zuciya tare da faɗin "Alhamdulillahi, Ummana na ƙoshi. " Murmushi Umma tayi tace "sannu ƴata da ƙoƙari, Allah dai ya rabaki da cikin nan lafiya. " Al'ameen ne kawai yace ameen, ita Meenat murmushi kawai tayi, Umma ce ta miƙe ta ɗauki plate ɗin da robar yajin ta mayar dasu kitchen sannan ta dawo falon ta zauna. Al'ameen ne ya miƙe yace "bari naje na gaishe da Ummina na dawo. " Kallonsa Meenat tayi tace "ka gaisheta, ni sai zamu tafi zan shiga." To kawai yace ya sa kai ya fice daga falon, Meenat da Umma kuwa shafin hira suka buɗe. ********* Sai bayan sallar isha'i su Al'ameen suka nufi hanyar gida bayan Meenat ta shiga ta gaida Umminta, suna isa gida wanka Meenat ta shiga, tana fitowa ta sanya kayan bacci ta haye gado, domin ba ƙaramin bacci taje ji ba. Ko da Al'ameen ya shigo ɗakin har tayi bacci, murmushi yayi ya taka ya haye gadon ya kwanta tare da rungumota jikinsa yana faɗin "Meenatuna dai ta zama kasan ƙarfi da yaji. " Shima be daɗe ba baccin yayi gaba dashi. _Asuba ta gari Al'ameenat_ ******** A gurguje *Bayan wata biyu* Zaune Meenat take ta miƙe ƙafafunta Al'ameen na aikin matsa mata su, sai lumshe ido takeyi alamun tana jin daɗin matsan da yakeyi mata, a hankali ta fara yatsina fuska tana cije laɓe, kallonta Al'ameen yayi sosai yace "lafiya my blood.?" Murmushin ƙarfin hali ta sakar masa saboda wani irin murɗa ta keji mararta nayi mata, ga bayanta da yayi wani irin riƙewa tace "lafiya ƙalau my one. " "Kamar ya lafiya ƙalau.?" Al'ameen ya faɗa yana kallonta, rintse ido tayi tare da dafe mararta ba tare da ta shiryawa hakan ba, tsura mata ido yayi yana kallo, matsayinsa na likita yasa tuni ya gano naƙuda ce, miƙewa yayi ba tare da yayi magana ba ya nufi hanyar wani ɗaki dake cikin falon, dafe mararta da bayanta Meenat tayi tana faɗin "wayyo bayana wayyo marata!" be daɗe ba sai gashi ya fito, lokacin Meenat duk ta haɗa gumi sai murƙususu take, kusa da ita yazo ya duƙa ba tare da yace mata komai ba ya sunkuceta ya nufi hanyar ɗakin da ya fito, be direta a ko'ina ba sai saman wani gado dake cikin wannan ɗakin, kallo nabi ɗakin dashi, ɗakin bashi da maraba da ɗan ƙaramin ɗakin shan magani, duk wani magunguna da kayan aiki na likitoci an tanadesu a cikin wannan ɗakin, ga wannan gado ta aka ƙawatashi da gani an ajiyeshi a ɗakin ne dan ɗaura mara lafiya a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Be tsaya wata wata ba ya fara dubata domin ganin haihuwar nata ya matso ne ko da saura, ko wani lokaci zata iya haihuwa, hakan ne yasa Al'ameen be tsaya ɓata lokaci ba fara yi mata duk wani abu da yasan zata haihu cikin sauƙi, Meenat ko kira take "mutuwa zanyi yayana, wayyo bayana wayyo marana" sai aikin jera mata sannu Al'ameen yakeyi, yana faɗin "insha Allahu babu abinda zai sameki my blood, zaki haihu lafiya, ki daure kinji, sannu, sannu, ƙoƙarta dai, sannu my blood, ba zaki mutu ba insha Allahu. "shi kanshi kallo ɗaya zakayi masa kasan yana cikin wani yanayi, ita kuwa Meenat banda salati ta kiran sunansa babu abinda takeyi. ******** Kukan jaririyar da na jiyo ne yasa na daka tsalle na koma ɗakin, aiko da shigata naga Al'ameen ɗauke da wata santaleliyar jaririya a hannunshi fuskarshi ɗauke da annuri, kafin kace wane wannan lebo ya dawo sabo ga Meenat, ai Al'meen be san sanda ya saka min jaririyar a hannuna ba ya ƙara komawa kan Meenatuwallansa ba, cikin ƙanƙanin lokaci sai ga wata babyn ta faɗo, kafin Al'ameen yayi wani yunƙuri sai ga kan wata ma ya danno, waro ido nayi waje ina daga tsaye nace "3 babys lokaci guda Ameenatu.?" Al'ameen kuwa mamaki da al'ajabi ne ya kamasa, bayan ɗayar babyn ta faɗo ita ma, Meenat ko ta galabaita matuƙa, kallon yaran yakeyi yana kallon Meenat wacce sai sauke numfashi takeyi wanda daƙyar ma yake fita, cikin ƙanƙanin lokaci ya goge ma jariran jikinsu su duka ya lullɓesu cikin wani towel me ɗan karan laushi da kyawo ya kwantar dasu, sannan ya koma kan Mommynsu domin taimaka mata ta gyara jikinta, sannu dai yaƙi ƙarewa a gurin Al'ameen, sai faɗi yakeyi "kin biyani my Meenat, yau kin haifa min sanyin idaniyata, Allah yayi miki albarka." Cikin ƙanƙanin lokaci yayi mata duk wani abu da ya dace yayi mata a matsayinsa na doctor, wayarsa ya koma falo ya ɗauka ya dannawa Umma kira, Umma na zaune tana duba wani littafin addu'oi taji wayarta na ringi, dubawa tayi taga sunan Al'ameen, da sauri ta ɗauka ta kara a kunninta tare da sallama, cike da ɗauki Al'ameen yace "ina kwana Umma.?" Saida tayi duba da tanƙamemen agogon dake maƙale a falon taga ya nuna ƙarfe 10:35am, sannan tace "lafiya ƙalau Aminu, an tashi lafiya.?" Cikin farin cikin da yake ciki yace "lafiya ƙalau Umma, ƴarki dai ta haihu yanzun nan. " Cikin tsananin farin ciki Umma tace "masha Allah! Me aka samu ne Ameenullahi.?" Shima fuska fal murmushi yace "Umma yara uku ta haifa min fa duka mata kuma. " Waro ido Umma tayi tace "da gaske kakeyi ko wasa Al'ameen.?" "Wallahi da gaske Umma." Umma tace "kai masha Allah, gaskiya nayi farin ciki sosai, ganinan tafe yanzun nan insha Allahu, ka kula min da ƴata sosai kafin na zo, sannan kayi mata sannu. " To Al'ameen yace daga haka suka kashe wayar, nan ya fara kiran ƴan uwa yana faɗa musu haihuwar Meenat, ɓangaren Umma ma haka abin yake, cike da zumuɗi ta shiga ta faɗawa Ummin Meenat haihuwar, sosai itama tayi murna ta haihuwar ɗiyar nata, sai dai sam bata nuna zaƙewarta ba saboda kara da kunya da take nunawa Umma akan Meenat, Umma bata tsaya wani ɓata lokaci ba ta shirya ta nufi gidan su Meenat, da kanta ta tuƙa kanta bata saurari direba ba. Tana isa ta iske Meenat zaune cikin kamala tana shan shayi, yayin da Al'ameen ya ta sata a gaba ita da jariran yana kallo fuskarsa taƙi ɓoye farin cikinsa, itama zama tayi tanayi wa Meenat sannu, cikin kunya Meenat take amsawa kanta na ƙasa, kallon kyakwawan jariran Umma tayi waɗanda Al'ameen ya shirya cikin wasu kaya masu ɗan karan kyau sai harba ƙafafu sukeyi alamun lafiya, ɗaya bayan ɗaya ta bisu ta ɗauka tana me saka musu albarka, bata tsaya wani ɓata lokaci ba ta miƙe ta shiga kitchen ta ɗaura ruwan zafi, yana ta fasa ta zo ta fara yiwa jariran wanka, sai da ta gaba shiryasu tsab sannan taje ta juye ruwa ta kaishi toilet ɗin falon tazo ta tisa Meenat gaba su kaje tayi mata wanka, bayan nan Umma kitchen ta koma ta fara ƙoƙarin tuƙawa Meenat tuwo miyar kuka. Cikin ƙanƙanin lokaci Umma ta kammala tuwan nan, miyar tasha man shanu da naman rago, zubowa Meenat tayi ta kawo mata, aiko Meenat ba wasa ta zage taci tuwan nan me isarta. Zuwa ƙarfe ɗaya gida ya cika da ƴan uwa da abokanan arziƙi, har tsohowa me ran ƙarfe ta zo, wato Mama kaka, taga ƴaƴa taga jikoki yau ga ta ga tattaɓa kunni😁, kowa sai masha Allah yake faɗi in yaga jariran nan, yarane barakallah, ba zaka ɗauka ƴan uku bane in ka gansu, saboda ɓul-ɓul suke manya dasu gwanin sha'awa. Kwana uku da haihuwa Bilkisu dake Zaria ta zo, Aunty Aisha kuwa kullum tana gidan tunda akayi haihuwar sai dare take komawa, da yake ita anan kanon take aure, cikin Abba da Abby ko babu wanda be zo yaga ƴan jikokinshi ba, Abba ma shi zuwansa biyu, Ummi ce dai har yanzu bata zo ba, wai tana jin kunya, balle Mama kaka tana gidan har yanzu, itace me kulawa da Meenat. ********** A gurguje hilis Sati na zagayowa akayi gagarimin sunan da ko biki albarka, suna ne da aka kashe masa maƙudan kuɗaɗe gurin hidima, shanu uku aka kada, komai baja baja a bikin sunan nan kamar ba'asan zafin neman kuɗi ba, uwar suna kuwa ta kashe kala a wannan rana iya kala, yara sunci sunan da suka zo dashi, dan Umma ce ma tace kar su wani sauya wa yara suna, hakan ne yasa aka barsu da Hassana da husaina gambonsu kuwa aka sanya mata *Husna*, sunan ƴan uku dai yayi armashi, kowa yaci yasha masha Allah, abinci dai duk wanda yazo yaci ya barshi, haka aka watse taron sunan nan cikin farin ciki. Bayan sati biyar Mama kaka ce take zaune da Meenat har tayi arba'in, rashin kunya dai kala-kala ta ganshi gurin Al'ameen da Meenat, dan babu ruwansu a gabanta suke zuba love ɗinsu, tsiya ko iri iri sunsha shi gurin ƴar tsohowan nan, har zuwa ranar da Meenat tayi arba'in, bata bari ko kwana ɗaya ta ƙara ba ta tattara komatsenta ta koma gidanta, dan cewa tayi in bata tafi ta basu guri ba zasu haƙewa juna a gabanta🤣 _Ni ko nace ai ko da rashin kunyar nasu ya kai lawaula_ Ranar da Kaka Mama ta tafi da dare Al'ameen ne ya shigo ɗakin Meenat da sallama, isketa zaune yayi tana ƙoƙarin sanyawa su Husna kaya, yaran sai ƴan rigiggimunsu sukeyi, ƙarasawa yayi ya zauna bakin gadon ya tayata suka saka musu, ajiyar zuciya ta sauke bayan taga sun kammala shiryasu, kallonta Al'ameen yayi tare da ɗaga mata gira yace "yaya dai.?" kwaɓe fuska tayi kamar zatayi kuka tace "gaskiya raino akwai wahala yayana, yau ɗaya da tafiyar Kaka mama yaran nan sun kusa haukatani. " Dariya Al'ameen ya kwashe mata dashi, duka ta kai masa tana fashewa da kukan shagwaɓa, tsagaitawa yayi da dariyar yana faɗin "sorry, sorry, to ai kene da abin dariya, wai sun kusa haukataki, tun yanzu ma kenan ina ga nan gaba. ?" Turo baki tayi gaba cikin shagwaɓa tace "to wa yace kayi min cikin na haifi ƴaƴa uku?, bafa ɗaya ba ba biyu ba uku, ai wallahi gida zan koma nayi rainonsu a can. " Cikin dariya Al'ameen yace "to naji tunda ni nayi cikin zan ɗinga tayaki rainonsu, ina ce dai ba shi kenan ba. " Cikin turo bakin still Meenat tace "ni dai ban yarda ba sai dai kai ka raini abinka kai ɗaya, yanzun ma ka fara sasu suyi bacci tukunna dai. " Girgiza kai yayi yana dariya yace "to naji, yanzu ƙara basu nono su tsotsa to. " "Tun ɗazun suke tsotseni wallahi, in na biye musu watarana ƙamewa zanyi a tsaye. " Dariya Al'ameen yayi yace "to ina madararsu a ƙara musu dashi, ni ban maga abin damuwa ba yara ba rigima sukeyi ba ba komai ba. " "Ai nasan dama haka zaka ce, to ni dai yanzu kawai ka saka suyi bacci shine burina. " Ɗan risunawa Al'ameen yayi alamun girmamawa yace "an gama ranki shi daɗe. " Juyar da kai Meenat tayi gefe tana murmushi. Muje zuwa🥰 *Heenat ce💋* 06/08/2019 à 11:00 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *NI DA YAYA AL'AMEEN* 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾 *STORY AND WRITING* BY *RAHEENAT M ABBAKAR* _(Heenat)_ ```WANNAN PAGE ƊIN SADAUKARWA CE GAREKU``` HAlissa adamou (my lissa) Maman Sabeer (Raheenat m kk fans) Mummyn Al'ameen (Raheenat m kk fans) Ummu Affan (Ni da yaya Al'ameen fans1) Zainab Abdurrahaman (Ni da yaya Al'ameen fans1) Maman jidda ɗiyar kirki taƙwacen miji fans Sayyada taƙwacen miji fans Big Mummy beneficial writers Maman Baffa Beneficial writers Abdullahizainab340 beneficial writers Bilkisu Abubakar Na baku shi kyauta kuyi yanda kuke so dashi, ku sani raheenat na yinku irin sosai ɗin nan fa🥰❤ *ƊINBIN GODIYA TARE DA FATAN ALKHAIRI GA WAƊANNAN GROUP'S ƊIN* RAHEENAT M KK FANS GRP NI DA YAYA AL'AMEEN FANS 1&2 JIHADI FANS GRP JININANE REAL FANS HAUWA SARKI NOVEL GRP HAFEEZA HALAWATY FANS BINEFICIAL WRITER'S FANS CLUP GITAL NOVEL GROUP LISSA NOVELS GROUP SHARHI DA TAMBAYOYI MRS SARDAUNA FANS MEERAGEE FANS FILIN LITTATTAFAN HAUSA ZEEY HAUSA NOVELS UMMU FATEEMA CONVERSATION ONLINE WRITER'S ONLY ZUMUNCIN MARUBUTA HOME OF HAUSA NOVELS ƘADDARATA FANS TAƘWACEN MIJI FANS ZAN SOKA A HAKA FANS BK FANS GROUP INA JIN DAƊI MATUƘA ZAMA TARE DAKU, DAMA GROUP ƊIN DA BAN AMBATABA, KU SANI RAHEENAT NA YINKU😘 Whattpad @rahinamustapha MARUBUCIYAR *1 KOMAI YAYI FARKO....* *2 HALIN RAYUWA* *3 RAYUWAR SAUDA* *4 RAYUWAR HANEEFA* *5 MAHAK'URCI....* *6 RUK'AYYATU* *7 RAINA FANSA NE GARETA* Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN* SADAUKARWA GA *MAMAN LABYB (MAMIEN MU)* *FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI* *SHAFA'ATU BALA BABA* *ADAMA TANIMU A BIYE* *AISHA NICHOI* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *(Z.A W)* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛``` Page 19 -20 🔚🔚 Madarar yaran ya ɗauko ya haɗa ya fara basu ɗaya bayan ɗaya cike da nutsuwa, Meenat tana zaune tana kallonshi har ya kammala, kafin ya gama bawa Husna har tayi bacci, ajiye fidar yayi ya ɗauki Hassana yana jijjigata, yanda yake girgiza yarinyar cikin ƙwarewa za kasan tabbas ba yau ne ya fara raino ba, cikin kwanciyar hankali itama tayi bacci zuwa yayi ya shimfiɗar da ita kan gadonsu dake ɗakin wanda aka ƙawatasa gwanin birgewa, itama Husna ɗaukarta yayi ya kwantar, sannan ya dawo ya ɗauke Husaina wacce take lumshe ido alamar itama baccin zatayi, a hankali yake girgizata har baccin nata ya fara nisa a hankali ya kwantar da ita kusa da ƴan uwanta sannan ya duka ya tofesu da addu'oi tare da shafar fuskar ko wannensu yace "Allah ya albarkaci rayuwarku ƴaƴana. " Duk wannan abin Meenat tana zaune tana kallonsa, takowa yayi ya zauna kusa da ita yace "ya kika gani ? Gashi dai cikin ƙanƙanin lokaci duk na sakasu sunyi bacci, to na raini mamansu ba bare su, kamar yanda kika ga nayi musu to kema haka nakeyi miki lokacin kina kamarsu, da zaran kin dami Ummi da kuka to nine zan rarrasheki har kiyi bacci, Ummi har mamaki takeyi a lokacin." Kwantar da kanta tayi saman kafaɗarsa tana murmushi tace "duk abinda yayana ya faɗi nasan yayi ma fiye da haka wa Meenat, ai Meenat na yah Al'ameen ne, Al'ameen ya raini Meenat a hannunshi, ya goyeta a bayanshi, yau gashi yana rainon ƴaƴanta, ina matuƙar ƙaunarka yayana. " Rungumota yayi sosai a jikinshi yana shaƙar ƙamshinta yace "mee too my blood. " A hankali Meenat ta ɗago kai ta kalleshi tace "yayana zai iya bani damar naje nayi wanka.?" Murmushi yayi yace "me zai hana?, har ma da wanke ƴar ƙanwar nashi ta kansa, ko yau ƙanwar tawa bata son yayanta yayi mata wanka.?" Lafewa ta ƙarayi a ƙirjinshi tace "in dai yayana nason hakan to ƙanwarshi ta bashi dama, domin shine me ita, ita bata da iko da kanta. " Kiss ya kai mata a wuyanta ya tare da miƙewa da ita a jikinshi ya nufi toilet ɗin da ita. Tare sukayi wankan, ya wanketa ta wankeshi cikin so da ƙaunar junansu, dukkansu ɗaure da towel suka fito suna goge jikinsu, gaban mirror Meenat ta nufa tana ci gaba da goge jikinta, wani mai ta janyo ta fara shafawa a jikinta, ji tayi an rike hannunta, ɗago idanunta tayi ta saukesu cikin idanun Al'ameen tana aika masa da wani irin kallo, lakatar man yayi da hannunsa ya mutstsika a hannunsa sannan ya nufi jikinta ya fara shafa mata. Hannunsa ne ya fara yawo a duk wani sassan jikinta, daga bayanta ya fara shafowa yayo saman wuyarta, a hankali hannunsa ya gangaro ƙirjinta, saman dukiyar fulaninta yayi burki ya fara shafasu cikin wani irin salo, lumshe ido Meenat tayi saboda wani maganaɗisu da ya ziyarceta har tsakar kanta, duk da irin zafin da nonon nata sukeyi mata saboda cika da sukayi da ruwa ga tsotson ƴan uku da suke yini yi, amma saukar hannun Al'ameen a kansu ya tafiyar da dukkan zafin nan ya maye gurbin da wani irin sanyin daɗi tare da hmmmm... Ba abakin raheenat zaku ji ba, Meenat ce kawai taza iya faɗin muku😉. Be tsaya nan ba ya haɗa bakinsa da nata yayin da ɗayan hannun nasa yayi ƙas...., tsayuwar ne ya fara gagaransu su duka, a hankali Al'ameen yajata suka faɗa saman gado, nan ya ci gaba da sarrafata son ranshi, itama Meenat bata tsaya wata wata ba ta fara maida masa da martani, domin tayi kewar mijin nata matuƙa. Ganin hakan yasa na lallaɓa na fito daga ɗakin. A wannan daran sun gurji junansu iya gurza, Al'ameen jin Meenat ɗin nasa yayi kamar an sauya mashi ita saboda wani irin ni'ima da yaji ta ƙara , haka yayi ta sumbatu yana sanya mata albarka. ************* Washe gari da safe kamar haɗin baki tare suka farka, Al'ameen ne ya fara buɗe idanunsa sai itama Meenat ɗin ta farka, kallon juna sukayi suka sakarwa juna murmushi, shafar fuskarshi tayi tana wani lumshe ido alamun wanda bacci be isheta ba tace "barka da tashi sanyin idaniyar Meenat. " Hannunta da ta shafi fuskarshi dashi ya riƙe yana murzawa yace "yauwa barka farin cikin Al'ameen. " A tare suka ƙara sakin murmushi sannan suka yunƙura suka sauko daga gadon, toilet suka nufa domin tsarkake jikinsu. Bayan sunyi tsarki wanka sukayi sannan suka fito daga toilet ɗin wanda yayi daidai da kiran sallar asubahi a masallacin jikin gidan, wardrop Meenat ta nufa ta ciro musu jallabiyya, sai da ta feshesu da turare sannan ta miƙawa Al'ameen nasa tana faɗin "my one gashi ka hanzarta an kusa shiga sallah. " amsa yayi saka sannan ya nufi gadon triples, yaran har lokacin suna baccinsu cike da nutsuwa, shafa fuskar ko wannensu yayi yana murmushi sannan ya fice da sauri saboda ji an tada sallah da yayi, itama Meenat saka nata jallabiyar tayi bayan ta shafe ko wani gaɓa na jikinta da turaruka sannan ta fuskanci gabas domin sauke farali. Tana zaune ta karatun alqur'ani Al'ameen ya dawo daga masallaci, zama yayi kusa da ita shima ya fara binta karatun, sai da suka kai ƙarshen suratul baƙara sannan sukayi addu'a suka shafa, mikewa sukayi Meenat ta mayar da qur'anin ma'ajiyarta sannan ta naɗe sallayar, daidai nan kuma Hassana ta motsa, kamar saura ita suka jira suma sai suka tashi, nufar gadon Al'ameen yayi ya saka hannu ya ɗauki Hassana yana faɗin "barka da tashi yaran albarka. " Ƙarasowa Meenat tayi bakin gadon ta saka hannu ta ɗauki Husna tana faɗin "sun tashi kenan kuma, da zaran ɗaya ta tashi to duka sai sun tashi, ko kuka ɗaya ta fara to suma saura zasu fara, in dare yayi ji nakeyi kamar kar gari ya waye wallahi. " Dariya Al'ameen yayi yana saɓa Hassana a kafaɗarshi sannan ya ɗauki Husaina da ɗayan hannunshi ita ya saɓata a kafaɗa ya nufi bakin gado ya zauna yana faɗin "yara kuna jin abinda Mummynku take faɗi ko. ?" Kusa dashi Meenat ta zo ta zauna ta fara ƙoƙarin basu nono saboda tasan abinda zasu fara buƙata kenan yanzu, in ba haka ba kuwa yanzu zasu nemi ɗaga mata hankali da kukansu. Da taimakon Al'ameen ta basu nonon su duka suka sha, tana kammala basu ta kalli Al'ameen tace "kasan abinda za'ayi yanzu.?" Girgiza mata kai yayi yana kallonta, murmushi tayi tace "wanka zakayi musu ka shiryasu, ni kuma sai na shiga kitchen na haɗa mana abin karyawa. " Wani kallon Al'ameen yayi mata sannan yace "ke kiyi masu wankan ni zanje na haɗa mana break ɗin. " Miƙewa Meenat tayi ta saka masa Husaina dake hannunta a saman cinyarshi tana faɗin "naka wasa ne, bari ka gani. " Tana faɗin haka ta fara ƙokarin cire kayan jikinta ya rage daga ita sai bras da pant, wata riga me ƙaramar hannu ta ɗauko ta saka da wani wando da ko cinyoyinta be rufe mata ba, duk abinda takeyi idanun Al'ameen a kanta yana haɗiyar yawu, shi dai da zaran idanunsa zai ga Meenat babu kaya jikinta be sanin sanda yake susucewa ya rasa duk wani nutsuwarshi, tana gamawa ta tako tazo kusa dashi tace "ni na gama shirin shiga kitchen my dear, kai kuma kayi ƙoƙari kafin na kammala mana kayi musu wanka ka shiryasu. " Ta ƙarasa maganar tana shafar fuskarshi da hannunta tare da kashe masa ido. Baki da hanci Al'ameen ya sake yana kallonta, shi ƙirjinta da sukayo waje tamtsantamtsan dasu gwanin sha'awa su sukafi tafiya da imaninsa, idansa ƙar a kansu, lura da hakan da Meenat tayi ne ta ƙara juya masa su kusa da fuskarsa sannan ta nufi ƙofa ta fice ta barshi da binta da kallo. Ajiyar zuciya ya sauke bayan ficewarta a fili yace "wayyo ni Al'ameen Meenat zata kasheni da raina. " Shimfiɗe yaran yayi su duka a kan gadon sannan ya miƙe ya nufi toilet ya ɗauko bawon wankansu ya ajiye, bokiti ya ɗauka ya ɗebo ruwan zafi ya sirkashi daidai wankan yaran ya fito ya fara ƙoƙarin yi musu wankan. ************ Bayan Meenat ta kammala da komai da zasu karya dashi jere saman dining ɗaki ta nufa dan ƙarayin wanka. Tana shiga ta iske Al'ameen yana ƙarasa wanke Husna, duk ya jiƙa jikinsa sharkaf da ruwa, ga kumfa duk fuskarshi, bata san sanda dariya ya ƙwace mata ba, ɗagowa yayi yana kallonta bayan ya naɗe Husna a towel yace "me kikeyi ma dariya kuma.?" Cikin dariyar tace "kalleka fa yaya👈" Tana faɗa tana nunashi tare da ƙara fashewa da dariya, mikewa yayi ya kwantar da Husna kusa da ƴan uwanta yace "to shine meye ? Ban mayi ƙokari ba da na iya musu wankan. " Tana ci gaba da dariyar tace "a kayi ƙoƙari sosai fa, kuma tun ɗazun akan wankansu kake.?" Ɗan harararta yayi yace "ke kin gama haɗa break ɗin ne.?" "Tun ɗazun ma. " Ta faɗa tana ɗaukar ruwan bawon da yayi musu wakan ta nufi toilet tana faɗin "yau fa an bawa maza aiki, saura shiryasu kuma ya rage maka, ni yanzu wanka zanyi. " Ɗan ɗaga murya Al'ameen yayi yace "wallahi ki shiga ki fito ki tayani mu shiryasu, ke fa kinsan ƴaƴa uku ba ɗa ɗaya bane. " Dariya Meenat tayi lokacin da ta shige toilet ɗin tana faɗin "yanda baka tayani aikina ba kaima ba zan taya ka ba, da ga yau mun raba aiki, ni girki kai hidiman yara. " "Aiko baki isa ba, dole mu zauna a sake shawara." Cewar Al'ameen lokacin da ya lakata mai ya fara shafawa Hassana. Meenat dai bata ƙara magana ba ta fara cire kayan jikinta dan yin wanka. Lokacin da ta fito har ya kammala shiryasu cikin wasu kaya ƴar kanti iri ɗaya, yaran sunyi kyau sosai cikin kayan, kallonsa tayi tana murmushi tace "sannu da aiki Dadyn uku. " Ɗan hararar wasa yayi mata yace "zakiyi bayani ne ai. " Gaban mirror ta nufa tana cewa "babu wani bayanin da zanyi, yanzu dai kawai ka tashi kayi wanka kazo muyi break. " Miƙewa yayi ya nufa gaban mirrorn, ta bayanta yaje ya rungumota suna kallon kansu ta mirror, a kunninta ya raɗa mata "kina rikitani da yawa fa a duk lokacin da na ganki a haka my Meenat, me zan samu yanzu. ?" Murmushi kawai tayi ta fara ƙoƙarin shafa mai a jikinta ba tare da tace masa komai ba, riƙe hannunta yayi yace "can help you.?" Lumshe ido tayi ta buɗe tace "yes" Ba su ƙara magana ba ya fara shafa mata man, har hoda shi ya shafa mata tana zaune tana kallonsa, ya ɗauko jan baki zai sanya mata ta riƙe hannunsa tace "is ok " Ajiyewa yayi ya langwaɓe kansa kamar ƙaramin yaro yace "to ni kuma waye zaiyi min wanka. ?" Kallonsa Meenat tayi tana murmushi tace "ba gani ba. " Murmushi yayi ya sumbaci goshinta yace "a'a ki huta bari naje na watsa da sauri na fito, give me ten mint. " Yana faɗa ya nufi ƙofa da sauri. "Na baka 20. " Cewar Meenat tana miƙewa ta nufi wardrop domin ɗauko kayan da zata saka. ******** A gurguje hilis Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya musu cikin kwanciyar hankali, soyayyarsu kuwa sai abinda ya ƙaru, suna bawa ƴan uku kulawa sosai abinka da likitoci, yaran sai ƙiba sukeyi abinsu, in ka gansu ɓul-ɓul dasu gwanin ban sha'awa, Meenat ta koma makaranta abinta, sai dai yaran ba ƙaramin takura mata sukeyi ba ta fannin karatunta, ga hidimar gida gana Al'ameen gana karatunta ga na yara, danma Al'ameen yana ƙokari sosai gurin ganin ya rage mata wasu aiyukan, Umma tace zata samar musu ƴar aiki yace baya so, ganin gaba ɗaya bata samun sukuni ne yasa Al'ameen yaje ya roƙi Abby ya basu Habiba ƙanwar Meenat da tazo ta zauna dasu kodan taimakawa ƴar uwarta, zuwan Habiba gidan ba ƙaramin sassauci Meenat ta samu ba, dan ko makaranta zata shiga bata zuwa da yaran barinsu takeyi gurin Habiba har taje ta dawo, da yake Habiban ta fara zama budurwa rainon nasu be bata wani wuya, yanzu tana shekara na sha baƙwai ne, hakan ne ma yasa har wani aiki na gida take taya Meenat, sosai Meenat take jin daɗin zaman ƴar uwar nata tare dasu. ********* Yau ta kama weekend hakan ne yasa Al'ameen ɗaukarsu zuwa super market dan suyi siyayya, bayan sun gama siyayyarsu tsab sun zo fito Meenat taci karo da wani mutum, da sauri taja da baya tana bashi haƙuri tare da faɗin "wallahi ban lura da zuwanka bane yi haƙuri dan All..." Maganar nata ne ya maƙale lokacin da idanunsu suka haɗu da wanda ta bigen, Kamal ne ba kowa ba. Saurin kawar dakai Meenat tayi daga kallonsa ta raɓa ta gefensa zata wuce tana faɗin "Habiba zo muje kinji. " Da yake sun bar Al'ameen a ciki. Saurin taran gabanta Kamal yayi yana cewa "haba Meenat ya zaki tafi kuma ko gaisawa ba zaki tsaya muyi ba." Wani shegen kallo Meenat ta wurga masa tace "ina da wani haɗi ne da kai da zan gaisa da kai. ?" Sosa kai ya ɗanyi cikin jin kunya yace "a'a, amma ai.... " Cikin ɗaga murya Meenat tace "amma ai me Kamal, so kakeyi ka ƙara jaddada min saƙon cin zarafina ni da yayana daka turo min shekara ɗaya daya gabata ko me ? A iya sanina in ba wannan zaka ƙara jaddada min ba babu kuma wani abu da zaka faɗa min yanzu, kuma kamar yanda kace in yayana zai iya aurena ya aureni to ya aureni, saboda duk duniya babu wanda ya cancanta da Meenat irin yayanta Al'ameen, dan haka dan Allah bani hanya na wuce. " Kamal cikin jin kunyar abinda ya aikata da kuma nadama yace "dan Allah Meenat kiyi haƙuri, nasan nayi kuskure kuma nayi nadama, wallahi ba komai ya rufe min ido ba a wannan lokacin sai kishinki, saboda bana hango komai a idanunku ku duka sai tsantsan soyayyar junanku, ni na sani Kamal be cancanci Meenat ba, shi yasa ma na haƙura dake a wannan lokacin, saidai kuskurena ɗaya da nayi mummunar furuci akanku, dan Allah ku yafeni, sai bayan na faɗi hakan naga be dace ba, kuma a lokacin naso nazo na baku haƙuri sai dai kishinki ta soyayyar da nakeyi miki ba zai barni nazo gareki ba, ki gafarceni dan Allah. " Wani irin kallo Meenat ta aika masa tace "hmmm, Kamal kenan, ai duk wanda yayi nagari ya sani, kaje Allah ya yafe mana gaba ɗaya, " tana faɗin haka ta raɓe ta gefensa ta wuce abinta Habiba ta bi bayanta, kuma daidai lokacin ne Al'ameen ya fito daga cikin super market ɗin, kallon kallo sukeyi tsakanin kamal da Al'ameen, Kamal ne yayi saurin miƙawa Al'ameen hannu suka gaisa, ba yabo ba fallasa Al'ameen ya amsa masa, nan Kamal ya shiga basa haƙuri akan abinda ya faru yana me nuna nadamarsa, murmushi Al'ameen yayi yace "komai ai ya wuce Kamal, saidai Allah ya yafe mana gaba ɗaya, ni ai banji haushin abinda kayi ba saboda hakanne ya zamo sanadin samun abinda nekeso. " Nan dai sukayi sallama Al'ameen ya nufi motarsu dan tuni su Meenat sun shige, Kamal ko da kallo ya bisu tare da yaran hannunsu, a ranshi yake cewa "ba dai ƴan uku Meenat ta haifa ba ? Inko hakane nayi wa kaika asara. " _Niko nace kaji wawa, wa ya gaya maka ana haifan ma wani ƴaƴan da ba nasa ba, kamar yanda ba me auren matar da ba nashi ba, to haka ba a taɓa haihuwar maka ƴaƴan da ba ƴaƴanka ba, ko wani ɗa da ubanshi😃_ Tsakanin Al'ameen da Meenat babu wanda yayi maganar Kamal, sai ma wani hirar da suka ɗauko har suka isa gida. *********** Rayuwa tana tafiya musu yanda ya kamata, yara sai wayau sukeyi abinsu, suna da shekara ɗaya Suhailat ƙawar Meenat ta samu mjin aure, anyi biki ankai amarya kaduna dan anan mijin nata ke aiki, haka ƴan kai amarya suka dawo suka bar amarya daga ita sai halayyarta, ba aɗauki dogon lokaci ba Habiba ta samu miji itama, Meenat da Al'ameen sune jagaba akan komai na bikin nan. *********** Bayan shekara takwas Zaune take a ƙayataccen office ɗinta tana duba wasu takardu, sanye take cikin shiga irin na likitoci fuskarta ɗauke da wani farin glass wanda ya ƙara fito mata kyawun fuskarta, gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan takardun gabanta kwnoking ɗin ƙofar da kayi ne yasa tace "come in. " Ba tare da ta ɗago da kanta ba. A hankali ya turo ƙofar office ɗin ya shigo shima cikin shigar likitocin, ƙamshin turarensa ne da ya daki hancinta yasa ta ɗago da fafaren idanunta ta sauri, murmushin da bata shirya masa bane ya ƙawace mata tare da saurin miƙewa tana faɗin "doctor kai da kanka ka zo kuma.?" Murmushi yayi yaja kujera ya zauna yace "to naga ke ba zaki zo bane, gashi idanuna sun matsu suyi tozali da kyakkyawar fuskar nan taki. " Komawa mazauninta tayi ta zauna tana murmushi tace "kaji ka, kamar ba kwana kayi kana kallon fuskar ba, kuma ba ƙin zuwa nayi ba, aikin da ke gabana nake son hattamawa domin nasan matuƙar Al'ameenat suka haɗu duk wani aiki ya ƙare. " Wani kallo yayi mata yace "ke waya ce miki Al'ameen yana gajiya da kallon Meenat ɗinsa ? Har abada ba zan gaji ba, maganar aiki kuwa yanzun ma ta ƙare dan tashi zakiyi mu wuce mu ɗauki yara daga makaranta daga nan kuma mu wuce gida. " Kallon agogo tayi taga ƙarfe 5:55pm, ɗan waro idanunta tayi tace "yaushe time ya tafi haka ne ban sani ba. ?" Miƙewa tsaye yayi yace "yaushe zaki sani tunda kin zama agogo. " Itama miƙewa tayi tana tattare kayanta tana faɗin "wallahi ban ɗauka lokaci ya tafi haka ba, yara ma yau sai sunyi ƙorafin Mom a Dad sunyi latti gurin zuwa ɗaukarsu. " Jakarta hannunta ya Al'ameen ya amsa yana faɗin "ai duk laifin na Momynsu ne. " Murmushi Meenat tayi tace "naji mu dai je. " Basu ƙara magana ba sai ficewa da sukayi daga office ɗin tare da rufowa, kai tsaye gurin motarsu suka nufa, Meenat ce ta shiga ma zaunin direba kasancewar da zasu fito da safe Al'ameen ne ya jasu, kujerar me zaman banza Al'ameen ya shiga taja motar ta fice daga asibitin a guje. Kai tsaye hanyar makarantar yaran ta nufa, da yake makarantar in an tafi ƙarfe 7:30 na safe sai 6:00pm na yamma ake tashin yara, sai dai yaronki ya tafi da abincinshi, arabic and boko ne makarantar. Da isarsu kuwa suka iske yaran suna zaune suna jiransu, Abdul-Jalal ƙaraminsu yana ganin tsayuwar motar dadynsu ya mike a guje yana faɗin "oyoyo Dad and Mom. " Suma sauran yaran miƙewa sukayi cike da farin ciki suka nufi motar, fitowa Meenat tayi ta ɗauki Abduljalal ta rungume tana faɗin "oyoyo autan Mom. " Wani kallo Al'ameen ya jefa mata jin tace auta, kau da kanta tayi kamar bata gani ba, su Hassana suna isowa suka duƙa har ƙasa suka haɗa bakinsu gurin cewa "mun yini lafiya Dad and Mom. " Murmushi iyayan nasu sukayi suka ce "lafiya ƙalau yaran albarka, ya makarantar.?" Lafiya ƙalau suka ce suna miƙewa, Meenat ce tace "ku shiga muje ko. " To suka ce suna shishshiga motar, suma shiga sukayi ta tada motar suka kama hanyar gida, suna tafiya ne Umar yace "Dady yau auntynmu ta bani home work. " Husna ce ta harareshi tace "sarkin surutu ai ka bari muje gida tukunna. " Shima hararar nata yayi yace "ba zan barin ba dake nayi. " Al'ameen ne yace "ya isa hakanan, Husna bana faɗa miki ki bar irin haka ba, so kike ƙanninki su rainaki ko yaya?" Husna tace "sorry Dady ba zan ƙara ba. " Shiru motar ya ɗauka baɓu wanda ya ƙara magana har suka isa gida. Fitowa sukayi gaba ɗaya sukayi cikin gidan bayan Meenat ta paka motar a parking space na gidan. Suna shiga Meenat ta kalli su Hassana tace "kuje ɗakinku kuyi wanka ku sai kuzo ku ci abinci, kuyi home work ɗinku. " "To Mom" Cewar Hassana. Kar sun nufi hanyar ɗakinsu Meenat tace "am Hassana. " Juyowa yarinyar tayi tace "na'am Mom. " Meenat tace "ki yiwa Abduljalal wankan ki saka masa kayansa kinji. " "To Mom" Hannun yaron rmta riƙe tace "zo muje yaron Mummy. " Meenat yara biyu ta ƙara haifa bayan yan uku, yanzu ƴan uku suna da shekara tara da wasu watanni sai Umar me shekara bakwai sai Abduljalal me shekara huɗu. Meenat tana ganin shigewar yaran ta kallo Al'ameen tace "oga me kakeso ne yanzu.?" Ƙashe mata ido yayi yace "ke nake so tawa. " Murmushi tayi dan tasan manufarsa, kamo hannusa tayi tace "in dai nine ka samu tawan, mu shiga ciki. " Suna shiga ɗakinsa ta zaunar dashi bakin gado ta nufi hayar toilet dan haɗa mashi ruwan wanka, hannunta ya janyo ta faɗo kansa, cakulkuli ya fara yi mata aiko Meenat ta fara ƙyaƙyata dariya, rungumota yayi jikinsa sosai ya raɗa mata a kunni "ina sonki Menatuwallena. " Dariya ta saki tace "nima ina sonka Ameenuna. " Ciza kunninta yayi a hankali, aiko sai Meenat ta saki ƴar ƙara tana cewa "Wayyo kunnina, da zafi fa yah. " Wura mata iska ya farayi a kunnin yana faɗin "sorry my meena. " Ɗago ido tayi tana kallonsa cike da ƙaunarsa, shima ita yake kallo, sun daɗe cikin kallon juna kafin Meenat tace "abin kamar ba gaske ba. " "Me kenan ?" Al'ameen ya tambaya yana tsareta da idanunsa. Ƙwantar da kanta tayi a saman ƙirjinsa tana shafa gashin ƙirjin da hannunta tace "wai *ni da yaya Al'ameen* ne a matsayin ma'aurata kuma har da ƴaƴa biyar, sai na rinƙa ganin abin kamar ba gaske ba. " Murmushi yayi yana shafa gashin kanta yace "abin Allah kenan dama, kibar ganin abin kamar ba gaske ba, gaskiyane ke da yayanki Al'ameen matsayin miji da mata tare da albarkar ƴaƴa," shafa cikinta yayi ya ci gaba da cewa yanzu haka ina da tabbacin akwai ɗa ko ƴa na shida a cikin wannan cikin. " Lumshe ido Meenat tayi tana murmushi tace "haƙiƙa soyayyarmu da yah Al'ameen haɗi ne daga Allah, *ni da yaya Al'ameen* mutuwa ce zata rabamu da yardan me duka. " Kyakkyawa sumbata Al'ameen yakai mata kumatunta, nan ya ci gaba da bata sumba ta ko'ina, daga nan kuma sai batu ya sauya suka lula duniyar ma'aurata, nima ganin haka nace to Al'ameenat na barku cikin aminci....... Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, dukkan godiya ya tabbata ga Allah da ya bani ikon ganin ƙarshe littafin nan lafiya, tsira da aminci su ƙara tabbata ga annabinmu farko ƙaga ƙarshen aika, ina miƙa godiyata ga duk makaranta littafin nan wanda na sani da wanda ban sani ba da ƙoƙarin jimirin bibiyata da sukayi nagode nagode nagode. *HAƘIƘA KOMAI KA GA KA SAMU A RAYUWA TO RABONKA NE, DUK ABINDA BAKA SAMESHI BA TO TABBAS BA RABONKA BANE, RABON MUTUM DUK INDA YAKE WALLAHI SAI YAZO YA SAMESHI, KUMA BABU ME AUREN MATAR WANI, KOWA KAGA YA AURI MACE TO MATARSHI CE DAMA, INA FATAN MAKATANTA SUN FAHIMCI MANUFATA👏, NA BARKU CIKIN AMINCI SAI ALLAH ME KOWA ME KOMAI YA ƘARA HAƊAMU CIKIN WANI LABARIN NAWA IN YA NUFENI DA RUBUTAWA, AMMA KAFIN NAN INA CEWA MAKARANTA SU CI GABA DA BIBIYARMU A CIKIN LITTAFINMU NA ƘANGIN RAYUWA TARE DA MASOYIYATA SAMEERA HAROUNA (MY MEERA), INA TABBATAR MUKU AKWAI DARASI SOSAI CIKIN LABARIN TARE DA ILMANTUWA DA FAƊAKARWA KAI HARMA DA NISHAƊANTARWA KUDAI KU BIYO MEERAHEENAT KAWAI.* _Subhana kallahumma wabi hamdika ashhadu anla ilah ha'illa anta astagafiruka wa'atubu ilaika👏👏_ Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels