Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels KADDARAR SAFWAN! Writing by KHADIJA I Ishak (Oum Ayshat) JAKADIYAR DASHEN ALLAH*_ Call or WhatsApp 08162594440 page 1&2 ____kwance ya ke a kan makeken gadon shi, fari ne sosai kuma dogon saurayi kafafuwan shi sanye da takalma, gado ne na alfarma wanda kwanciya a irin wannan se wanda Naira ta zauna mu su sosai d'aki ne had'ad'd'en gaske mai girma sosai kuma ga komai na more rayuwa ya wadatu a d'akin. Wayan shi da ke can kan drawer ne ta fara ringing tashi ya yi ya zauna, had'e da yin mi'ka, idanun shi a lumshe mi'kewa tsaye yayi domin zuwa ya d'auko wayan tafiya ya ke yana had'a hanya kai da ganin shi kasan baya hayyacin shi, lokacin da ya isa wayan ma ta yanke, wani kiran ne ya sa ke shigowa, wayan ya d'auka hannun shi na rawa da'kyar ya karanta sunan da ke rubuce a jikin BESTY SAFNA d'aukan wayan ya yi ya kara a kunne ya ce "Hello" cikin zazza'kar muryar ta ta ce "Safwan lafiya ba ka zo school ba ga shi har an kusa shiga class?", cikin canza salon murya don karta ga ne halin da yake ciki yace "Saf....Nahhh! ba... najin daɗi ne" maganar ya ke kai da ka ji ma kasan a buge ya ke, Daga can Safna ta ce, "Safwan 'karya za ka yi min?", "a'a ki yi..." dif..! ta kashe wayar bata ma saurari me ze ce mata ba, yayin Safwan hankalin shi ya yi matukar ta shi da fe kan shi ya yi, sannan kuma ya zube anan bacci ya kwashe shi. AHMADU BELLO UNIVERSITY ZARIA Can na le'ko muku abun da ke wakana d'aliban ne ke ta sintiri a cikin faffad'ar makarantar ko wa na sabgar gaban shi, wata matashiyar yarinya wanda baza ta gaza shekara sha ba'kwai ba17 na hanga kan wani dakali ita kad'ai da alama ta yi nisa ne cikin tunani fara ce sosai ga ta kyakykyawa ce sosai, kallo d'aya za ka mata kuma kasan bafulatana ce, wata ce wanda itama baza ta gaza shekarunta ba ta nufo wajen da ta ke zaune, zama ta yi tare da dafa kafad'unta tace "Safnah, me ki ke yi ke kad'ai anan ko kina jiran mutumin na ki ne", wanda aka kira da Safna ta d'ago kai tace "a'a maryam kawai ina hutawa ne kafin mu shiga class, safwan ma na kira shi yace baze zo ba", "to ai se ki ta so mu shiga class don ga sir Deniel can ma ze shiga", da sauri su ka mi'ke su ka nufi ajin don idan ya riga ka shiga baza ka shiga ba. Yana shiga kuma kamar yanda ya saba ya fara lecture don wad'anda su ka zo late kuma se de su ka zauna a waje karatu sosai a kayi, karatun awa1 yayi musu sannan ya bada Assignment yace har wad'anda ba su zo a fad'a musu don shine a matsayinmatsayin C.A d'in su. Bayan ya fita ne kowa yaci gaba da sabgar gaban shi wa su na karatu wasu kuma surutu, Kamal abokin Safwan ne ya ta so ya zo wajen Safnah ya ce mata "Lafiya Safwan be zo ba?", kallon shi ta yi tace "baka kira shi ba ne?", "Ehh", "to ka kira mana kaji", juya wa yayi ya koma ya zauna, ita kuwa safna tsaki ta ja don bata san me yasa bata son kamal d'in nan ba jinin su be had'u ba kwata-kwata. Yau 'karfe sha biyu su ka ta shi makarantar Safnah na hango da 'kawar ta maryam sun jero har zuwa bakin gate d'in makarantar anan ne su ka rabu don yayan Maryam ya zo d'aukan ta kasancewar ta na Dan magaji ne, ita kuma Safnah ta na Samaru gidan su ba nisa sosai da makarantar. Safnah tahowa ta fara yi don ta samu ko keke napep ne ta shiga zuwa gida ga garin yau rana sosai ake yi. ta dad'e sosai awajen sannan ta samu napep ta wuce gida. Har bakin dai-dai madaidaicin gidan na su mai keken ya kaita ta ciro kud'in shi ta ba shi, ya wuce yayin da ta shiga gidan na su dauke da sallama a bakin ta, Anty na zaune a tsakar gida ta na wa Afrah kitso ta amsa cikin fara'a tare da cewa "Safnah kece da wuri haka" "Ehh anty don ma ban samu abun hawa ba da tuni na dawo", "to sannu da hanya", "sannu anty na same ku lafiya?", "lafiya lau", tace. Sannan Safnah ta nufi d'akin ta ta ajiye jakar ta ta fito tayi alwala, kasancewar yanzu kiran sallar 'karfe d'aya 1:00 ake yi, Bayan ta yi sallar ne ta fito ta zauna gefen anty kan tabarman da ta ke zaune, anty ne ta kalle ta tace "Safnah ki zu bo abinci kici mana", "to anty" tace sannan ta nufi kicin d'in, tuwon shinkafa ne da miyar d'anyar kubewa, ya ji man shanu, zama ta yi ta fara ci, Afrah ta kalla tace "ke baki san kin girma ba baza ki de na kukan kitso ba ko", Afrah da a ka kusa gama mata kitso ai kukan ta 'kara yi don bata son magana, dai-dai lokacin sauran yaran su shigo tare da sallama sun dawo school su ma Ibrahim wanda su ke cewa khalil shine Babba se Halima, se Ummar, se Fatima, se khadija wanda su ke cewa Afrah ita ce auta, su biyar. Zuwa su ka yi kamar yadda su saba idan sun dawo makaranta su gaishe da momin su sannan su ka ce "anty Safnah sannu da gida", "yawwa sannu" Safna ta ce musu, khalil ne yace "anty Safnah ya akayi ki ka riga mu dawowa yau", murmushi ta yi tace "ehh yau na riga ku", Sallah su ka yi sannan Safnah ta zubo mu su abinci ta had'a wa mazan matan ma ta had'a musu sannan ta mi'ke tace "anty zan je d'aki na yi karatu" "to Safnah Allah ya taimaka", "Ameen" tace sannan ta juya ta nufi d'akin, d'akin ba lefi ya had'u don komai na masu 'karamin 'karfi an saka mata, don kawun ta na ji da ita sosai. Uwar d'akan ta shiga ta kwanta akan gadon tare da bud'e littafin ta Assignment d'in Sir Daniel ta fara yi don tasan shi ba sau'ki, se da ta kusa gamawa da taimakon wayan ta da kuma fahimtar ta. Aji ye littafin ta yi don wani bacci da ta fara ji kwanciya ta yi duk da tasan Lokacin Islamiyyar su ta kusa. Baccin awa d'aya1 ta yi Afrah ta shigo tashin ta lokacin su har sun shirya ma, Bayin da ke d'akin ta fad'a ta yo alwala ta zo ta yi sallah sannan ta d'auki jakar Islamiyya ta fito, Lokacin ma su khalil sun fita su na jiran ta a waje, anty ta gani zaune a tsakar gida tana gyaran wake, tace "anty mun ta fi" "to Allah ya bada sa'a", "Ameen anty", Fitowa ta yi ta same su a kofar gidan sannan su ka wuce, kasancewar Islamiyyar ta su a cikin anguwan su ta ke amma da d'an tafiya sosai sauri suke yi sosai don sunyi late sosai. Wani d'an zauren gida Safnah ta shiga tare da d'aura nikaf d'in ta, don sun kusa zuwa gidan su Safwan, sannan tace su khalil su yi gaba don bata son ya tsaya bata mata lokacin. Kamar yanda ta zata kuwa Safwan na kofar gidan su yana zaune cikin taron mutanen shi yana sanye da kayan 'kwollo ne Blue ne sunyi matu'kar yi mashi kyau sosai ko da ta iso dai-dai wajen su d'uke kai ta yi don karma ya gane ta don shi idan mutum yasa nikaf be cika gane shi, har ta wuce ta fara nisa, Safwan be ma kula ba Wani da suke kiran shi salman ya ta'bo Safwan yace "Safwan baka ga mutuniyar ta ka ba ne", kallon shi ya kai inda salman ke nuna mai, aiko ya gane ita ce mi'kewa yayi da sauri ya bita. Safnah! Safnah!! Safnah!!! Kamar a mafarki Safnah ta tsinci muryar Safwan na kwala mata kira, abun da ta tsana kuma yasan bata so ne shiyasa, juyowa ta yi ta hango shi can yana tahowa da gudu kallon shi ta tsaya yi har ya 'karaso nikaf d'in ta d'aga tare da kallon shi tace "to mallam makaho ya da kira haka", dariya ya yi sosai yace "se ina?" "Inda ka aike ni", dariya ya ke yi har yanzu ita kuma had'e fuska ta yi, sannan tace "ɗazu me ya naka ka shigowa makaranta", "umm!," rufe ido yayi sannan ya bud'e yace "banjin dad'i ne", "Haba Safwan ka manta nace duk abun da zaka fad'a min ka daina min 'karya" "to momi na ayi hakuri", dariya ta yi sannan tace "ai idan na haifi kamar ka bazan ganu ba tsabar tsufa ka ganni yarinya ta da ni kace min momi", "to naji", "Safwan mubar maganar wasa jiya kaje club ko?" tace, Hannu biyu ya had'a alamar neman gafara yace "kiyi hakuri wallahi kamal ya jani", "igiya ya saka ya jaka ko me, shima giyar Kamal ya d'ura maka ko?, Safwan ina so ka sani ko badan addinin mu ba don lafiyar ka ma ya kamata ka daina shan giya da sauran su Safwan ga addinin mu ma ya yi hani da hakan kai ka sani fa Safwan", "Insha Allah zan yi 'kokarin daina wa", "yafi maka dai, to kasan yau anyi karat ai ko", "na sani har ma naje an koya min kuma na ƙara dubawa a waya", "Assignment d'in fa?" "Har na gama ma", Safnah bata yi mamaki ba don Safwan indai bangaren karatu ne baya wasa ko kad'an ko be zo ba to se ya koye shi, "to ka ga dama nayi latti ga shi ka 'kara sani na 'kara lattin ko", ta fad'a tana yin gaba, tare da cemai "se anjima", "to shikenan", ta wuce cikin sauri ta nufi makarantar. ✍️Khadeejerh Ishaq ce✍️ Comments and share pls _*ƘADDARAR SAFWAN!*_ _*By*_ _*KHADIJA I Ishaq*_ _*(Oum Ayshat)*_ _*JAKADIYAR DASHEN ALLAH*_ Call or WhatsApp 08162594440 _*page*_3&4 Koda ta je su khalil har sun shiga aji an fara karatu, ga kuma wa su wanda su ka yi latti an tara su a waje, ana jiran mallam Ummar ya zo yayi dukan latti, 'karasawa ta yi inda su ke zube suna da d'an yawa, har ta tsaya a wajen kuma se ta nufi ofis d'in malaman mallam umar d'in ne kawai a ofis d'in yana ta aiki gaishe shi ta yi ya amsa cikin fara'a yace "Head girl kema yau kinyi lattin kenan?", "ayi hakuri mallam matsala aka samu" "to dama ke nake jira kiyi musu dukan lattin don lebour be zo ba naje ajin ku ma kema baki zo ba, ni kuma ga shi ina ta aiki, ke kuma gashi kin zo latti", "ayi hakuri mallam", ta ƙara faɗa "to shikenan kije ki ce wa sauran su tafi aji kawai" "to mallam mun gode!" tace sannan ta juyo ta nufi wajen da suke, tace "kowa ya nufi aji" dad'i su ka ji sosai sannan ita ma ta shiga ajin lokacin har Malama ta fara mu su karatu. 'Karfe shida 6:00 ake tashin su Islamiyya su na isowa akayi sallar magriba Mazan masallaci su ka tafi tareda Baban su matan kuma sukayi gida. Basu dawo ba se da akayi isha'i sannan su ka shigo gidan kamar yanda suka saba a Babban falon anty suke had'uwa su ci abincin dare sannan ayi hira kowa se ya wuce ya kwanta. Part ne mai d'an girma sosai d'akuna uku ne aciki d'aya d'akin su Khalil ne d'ayan kuma uwar d'akan anty, se d'ayan kuma d'akin kawu ne, se kuma a waje akwai d'akuna biyu d'aya nan ne d'akin ba'ki yana kallon na Safnah da su Fatima don anan suma su ke kwana. Kamar kullum kowa yana zaune a 'kasa yayin da iyayen na su na zaune akan kujera kowa da filet d'in abincin shi yana ci shinkafa ne da miya yaji nama. Anty ne ta kalli Afrah tace "Je ki kira antyn ki Kice tazo taci abinci" "to mom", tace sannan ta fita zuwa d'akin antyn nata. Ita kuwa Safnah ta na kwance su na waya da Safwan tana cewa "saura gobe kar kazo makarantar", Daga can Safwan yace "ai se na riga ki zuwa ma", "hm zamu gani se na riga ka", "to Allah ya kaimu" "Ameen", "Anty momi na kira" cewar Afrah "to gani nan, Safwan se da safe anty na kira na" "to se anjima" yace sannan ya kashe wayar. 'Dakin antyn ta shigo d'auke da sallama gurin kawun ta ta nufa ta durkusa tace "kawu ina wuni?", "Lafiya lau Safnah ya karatu" "Alhmdllh Kawu", "to ana dagewa ko?", "Ehh sosai ma", "to Allah ya taimaka", "Ameen" tace sannan ta nufi gurin anty ta gaishe ta sannan ta d'auki abincin nata ta fara ci, bayan kowa ya gama ne su ka sha hirar su cike da farin ciki sannan safnah ta yi musu sedasafe suka nufi d'akin su. Washegari Safnah Bayan ta tashi sunyi sallah ta fito kicin ta shiga kamar kullum don kafin anty ta ta so ta gama mata aiyukan ta tas! ruwa ta fara d'urawa wanda zasu yi wanka nan da nan yayi zafi kasancewa Gas ne, Juye wa tayi ta nufi d'aki dashi Afra ta tasa tayi mata sannan tace Fatima ta shiga tayi da ragowar, sannan ta juyo ma halima raguwar, sannan ta mayar mata da na flas wanda zata had'a musu tea da shi ta dawo d'akin lokacin duka sun shirya sun saka uniform d'in su, Halima tace wa jeki d'auko flas a kicin d'in d'aki to anty tace sannan ta nufi d'akin ta d'auko, ta dawo ta bata ruwa ta juye sannan ta mayar da wani sannan ta d'ibo Dankali ta fara ferewa wanda zata soya musu, cikin sauri ta gama fere wa sannan ta daka kayan miya d'an kad'an, ta d'auko kwai ta fasa ta had'a komai na suya sannan ta kira Halima tace je ki ta so min su khalil cikin sauri ta taso su, ta juye musu ruwan sannan ta ta mayar da suyar cikin minti 10 ta gama suyan ta zuba akula sannan ta saka ruwan wankan, d'aki ta shiga da kayan ta jere su a dining sannan ta fito ta shiga d'akin ta ta ciro kayan da zata sa ka da komai nata wanda zata makaranta dashi ta ajiye agefen gado, ta dawo kicin d'in ta juye ruwan nata sannan ta mayar da raguwar shinkafar jiya ta yi 'kasa da gas d'in, ta je ta yi wankan ta ta sa kaya, lokacin da ta fito ma su Halima har sun ta fi d'akin momin su, Bayan ta shirya tsaf ne ta fito itama ta nufi kicin ta sauke shinkafar ta mayar da miyar shima ta d'uma sannan ta kashe gas d'in ta fito zuwa d'akin Antyn nata. Koda ta shiga kowa na kan dining anty har ta yi wankan ta shima kawun nata yana cikin shirin ofis d'in shi ne dama su ad'akin su ke wankan su sede su fito da shirin su. Anty har ta had'a musu shayin Ta zuba musu dankalin su na ta ci, ta 'karaso du'kawa ta yi ta gaishe su sauran yaran ma su ka gaishe ta kawu ne yace "Safnah sannu da 'ko'kari", murmushi kawai tayi sannan ta zauna wajen zamanta kusa da khalil abincin anty ta mi'ka mata ta fara ci. Bayan sun gama cin ne su ka fito lokacin mai Napep d'in da yake kai su ya iso, don Dad su ma tuni ya wuce Hospital don an kira shi akwai mara su lafiya da yawa shiyasa yana gama kari ya wuce, Safnah jakar ta ta d'auko su ka wuce sai da aka safa sauke Safnah sannan ya 'karasa da su don ba wani nisa sosai, Safnah cikin makarantar ta nufa don yanzu 'karfe takwas 8:00, don ma se da rabi zasu shiga class tafiya ta ke yi zuwa cikin makarantar, har ta iso class na su ba wasu mutane a ciki sosai juyawa ta yi can ta hango Safwan zaune da tawagar shi don Safwan akwai mutane sosai, 'karasowa ta yi har inda su ke zaune, mata ne da maza suna ta hirar su. "Good morning my friends", cewar Safnah, Safwan da ke latsa wayar shi jin muryar ta ya d'ago yace "sannu da zuwa ƙawa" kujerar kusa da shi ya nuna mata, zama ta yi tare da gaisawa da sauran mutanen wajen, Sannan su ka cigaba da hirar ta su. Kamal ne ya kalli Safwan yace "lokaci fa na tafiya bamuje mun karya ba Boss", sauran ma su kace "haka ne fa", Kallon Safnah yayi yace "muje mu karya ko?" Ba tare da ta kalle shi ba tace "am okay" mi'kewa su kayi wajen su goma sha biyar 15, su ka nufi wani restaurant da ke kusa da makarantar, Koda su ka shiga kowa zama yayi a kujera ya fad'i abin da za'a kawo mai, shiko Safwan chips kawai yace akawo mai bayan sun gama ci ne aka yi musu total d'in kud'in su dubu ashirin da biyar, kud'i ya ciro a aljihinsa da be san nawa ba ne ya mi'ka wa kamal, 'kar'ba yayi ya biya raguwan saura dubu sha biyar, ya d'auki dubu biyar, ya bawa saura subu goma suka kar'ba su na murna su ka raba, shiyasa su ke son shi don Safwan bashi da rowa indai ka ra'be shi za ka ci kud'in shi sosai shiyasa yake da jama'a sosai kuma kowa na shi ne, duk da bawai mai yawan surutu ba ne amma ze zauna da mutane asha hira, Idan kaga dariyar shi sosai ko surutun shi to shi da Safnah ne, shi yasa kowa yake cewa soyayya su ke yi amma kuma su sunce ba soyayya su ke ba kawai kawance ne da zumunci da Allah ya 'kulla a tsakanin su. Lokacin da su ka shigo 8:29, lokacin ma har mallamin da su ke da shi ya shiga Safnah na zaune su ka shigo, kujerun ajin irin dogayen nan ne, duk guda d'aya mutum biyu su ke zama, Wanda safnah ke zaune Safwan ya je ya zauna don nan ne wajen shi, Kallon shi ta yi tace "se yanzu Kuka dawo?" "Ehh", kawai yace mata, muryar lecturer su ka ji yana cewa, submit your Assignment, Safwan ne ya ta shi ya nufi wajen kamal don jakar shi yana hannun shi, Safnah kuwa se yanzu ta tuna ma da Assignment d'in don ya dad'e, muryar mallam d'in ta ji yana cewa Duk wanda be yi ba ya fita kuma shine CA d'in ku, Safnah sosai hankalin ta ya tashi, wa su ne da basu yi ba su ma su ka fara ba shi hakuri Yace su fita kawai, hakan yasa Safnah mi'kewa don fita dai-dai lokacin Safwan ya dawo da takardar Assignment d'in shi yace "Safna ina zaki?" "Nabar Assignment d'ina ne a gida gashi ance a fita", mi'ka mata takardar hannun shi ya yi ta 'kar'ba sannan yace "ki saka suna a wannan ki bada, kije ki zauna kawai", "amma Safw..... "shiiiii!" yatsan shi ya d'aura a baki alamar ta yi mai shiru, juyawa ta yi ta zauna shi kuma Safwan ya fita waje, Safnah ta shi ta yi ta kai nata. Safwan ko da ya fita sauran sunyi mamakin ganin har da shi be yi ba yace musu ya bar shi a gida ne, Bayan ya gama 'kar'ba ne ya fito waje, wajen wad'an da ba su yi ba, sosai shi kan shi ya yi mamakin ganin Safwan be yi ba, "Muhammad!!" Safwan da yasan Lecturer ne kawai ke kiran shi da haka ya ta so tare da zuwa wajen shi, yace "muhammad ya akayi ba ka yi ba", sunkuyar da kai ya yi yana murmushi sannan yace "Sir na bar shi a gida ne", "ok to gobe kazo min da shi" "to thank sir" yace sannan ya nufi aji, su na had'a ido da Safnah murmushi ya sakar nata ita ma murmushin ta mayar mai sannan ya 'karaso ya zauna, tace "ya akayi ka shigo kuma" dariya yayi yace mata, "ke dai kawai kibar maganar ta wuce amma gobe ki zo da nakin se ki bani" "to" ,tace don ganin lecturer ya dawo karatu ya yi musu sannan ya fita yace anjima ze dawo ya basu takardun su. _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_5&6 Ko da ya fita lokacin 'karfe 9:30 surutu wasu ke yi, wasu kuma su ka fita don su sha iska Kasancewar se 10:00 za su 'kara yin karatu, Safwan ne shima ya tashi ya fita ba tare da yayi wa Safnah magana ba ita ma ba ta ce mai komai ba. Su kamal da ke bayan su ne su ke fira gaba d'aya sun cika mata kunne, Kamal ne ta jiyo ya na cewa "ai gobe akwai shan shagali a club kun san birthday d'in Malika 'yar chairman d'in anguwar mu ga kuma na Zulaihat, ai akwai Holewa" Salman ne yace "ai kuwa fa, amma kasan Boss fa da'kyar ya je kuma kasan idan be je ba abun ba ya dad'i" "haka ne amma kabar min komai kawai zan san yanda zanyi na jawo mana shi" shewa su ka yi na jin dad'i gaba ɗayan su. Safnah ce ta mi'ke ta fito waje can ta hango Safwan zaune a kasan wata bishiya akan kujerar da ke wajen, 'karasawa ta yi ta zauna be kalle ta ba hakan yasa tace "Safwan!" Juyowa ya yi ya kalle ta ba tare da ya amsa ba, "Safwan me yake damun ka naga kamar yau ran ka a bace ya ke" murmushi ya yi yace "ba komai Safnah kawai anty ne ta 'bata min rai kome ma ya wuce" "to shikenan, Safwan ka ci gaba da hakuri wata rana se labari" "to" kawai yace. "Safwan yaushe ne birthday Malika?" Kallon ta ya yi cikin zare idanu da mamaki yace "waye ya fad'a miki za'ayi", "ba ka amsa min ba", "gobe ne", yace, "kuma zaka je ba?" "Ehh mana", Hararar wasa ta yi mai tace "har kana 'kara fad'in Ehh ko!, to shikenan se ka dawo", "to ke ma za kije kenan? Kuma yadda kike mummunan nan, ƙila ki samo saurayi" Kallon shi ta yi ba tare da tace komai ba kawai ta tsira mishi idanun ko kyaftawa wa bata yi, Safwan ku wa Jin ta yi shiru ya juyo ya ga tana kallon shi, d'an matsawa baya ya yi yace "Wayyo!, nace ki daina min irin kallon nan ko", kawar da kai ta yi tace "zaka je, ko ka fasa" "zan je mana, 'yar kauye kawai ke yaushe za ki waye ne ke baza ki je ba amma ki hana mutum zuwa kuma" murmushin jin dad'i ta yi don tasan halin Safwan sarai Idan ya yi mata maganar nan to ba ze je ba ne. amma duk da haka se ta ƙara cewa "Tambayar 'karshe zan maka zaka je ko baza kaje ba", "se na je" yace mata ya na murmushi, mi'kewa ta yi ta nufi aji a zuwan ta yi fushi, kuma ba hakan ba ne don tana da tabbacin ba ze je d'in ba, amma idan yaga ta nuna ta yi fushi Ko da kuwa an zugashi baze jeba. Shi ko koda ta tafi mi'kewa ya yi yana murmushi don wataran ma dariya Safnah ta ke ba shi. Ajin ya shiga don lokacin ma har an fara karatu magana ya yi wa Safnah ta yi banza da shi, kawai se ya kyale ta, don karatu ma ake yi. Yau se 'karfe 2:00 su ka ta shi makarantar yau ita kad'ai ta fito don maryam bata zo ba. Har ta fita bakin gate Safwan da sauri ya shiga motar shi kamal ne ya biyo shi da sauri don wataran Safwan na d'aukan shi Safwan har ya kunna mota kamal ya zo, Hannu Safwan ya saka a aljihun shi ya ciro dubu uku ya mi'kama kamal yace "ga shi ka hau mota yau zan d'auki Besty ne" murmushi kamal ya yi don shi gaba ta kai shi ma don ya samu kud'i. Da sauri Safwan ya ja mota ya fito don yasan halin ta zata iya hawa napep ta ta fi koda ya fito kuwa ya hangota har ta tsayar da Napep d'in, da sauri ya fito ya bawa mai Napep d'in hakuri ya tafi sanna yace "wuce muje", bata yi musu ba ta wuce motar ta bud'e ta shiga, shima shiga ya yi ya fara tafiya bata yi mai magana ba shima haka, ganin shirun yayi yawa ne yace "Haba anty na ki yafe ni kinsan zan iya jure komai amma banda fushin ki a gare ni haba 'yar kanwata anty na kuma" dariya ta yi don yayi ne dama don yasa ka ta dariya, bayan ta gama dariyar ne tace "Safwan kace se ka je ko?, To indai kaje bani ba kai" dariya ya yi sannan yace "to ba shikenan ba waye ze damu, ke za ki damu don ni ko ajiki na ma, don ko school ne ban zo ba kin dinga kira kina cewa yau baka zo ba, tsabar baza ki iya jure rashi na ba, shiyasa ma baki son naje, nasan duk kishi ne kar na je na samo santaleliyar budurwa ko?", Safnah sakin baki ta yi ta na kallon shi se yanzu tace "Allah ya kyauta me zan yi da kai, ba ka san saurayi na ba ne, idan ka gan shi se ka raina kan ka don ya fi ka had'uwa ma sosai, amma jika fa mummuna da kai", Dariya Safwan ya yi yace, "lallai yarinya, kin ga had'ad'ad'en saurayi, ke ba ki ga 'yan mata na ba, ko school guda nawa ne su ke so na, ga anguwan mu ma, ke ko a club ma......" Shiru ya yi ganin ta juyo ta na kallon shi jin ya ambaci club, "ko a club ma miye?" Murmushi ya yi yace "ba komai dai" "shikenan zaka ga saurayina duk lokacin da ku ka had'u ko!, se ka rai na kan ka" Safnah tace Dai-dai lokacin kuma Yayi perking kasancewar an iso gidan su Safnah, dai-dai lokacin mai napep d'in su Khalil shi ma ya kawo su gida Khalil na sauka da gudu ya 'karasa wajen Safwan, Safwan bud'e motar ya yi khalil ne ya 'karaso yace "yaya Safwan ina wuni", "lafiya lau khalil" dai-dai nan su Halima ma su ka 'karaso su ma gaishe shi su ka yi, yace "Sannun ku ya karatu?", "Alhamdulillah" su ka ce atare. Motar shi ya koma ya ciro mu su sweet da coculate, da biscuit da yawa a leda yace "gashi ku je ku ci" 'kar'ba su kayi su ka shiga gida don lokacin ma Safnah har ta shige gidan, koda su ka shiga Safnah na Sallah, Gaishe da anty su ka yi, su ka cire uniform suma su ka yo alwala khalil ne ya mi'kawa Momin su ledar da Safwan ya ba su, yace "momii kin ga yaya safwan ya bamu", "to an gode, Safwan kamar baya nan kwana biyu ko zuwa ma baya yi", "ai yace mu gaishe ki" cewar Afrah "to ina amsawa". Sallah su ka yi sannan su ka zubo abinci su ka fara ci. Waye Safwan waye kuma Safnah. Ku biyo ni don jin labarin su. Taku har kullum Khadeejerh Ishaq ce Comment and share pls ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*7&8 SAFNAH Mallam Suleiman ya kasance haifaffen garin kano ne yana da matar shi guda d'aya Fatima, yaran shi biyu, Al-amin se shamsiyya, su biyu Allah ya ba su. Neman kud'i da karatu ne su ka kawo Al-amin Zaria inda ya ke karantar Doctor, ita kuma Shamsiya, wani mai suna Abdullahi ya fito neman auren ta amma shi d'an katsina ne kuma d'an dangi ne don shine ma auta a d'akin su yana da yayyi maza da mata, Salihu shine Babba ad'akin su akwai zafi sosai don duk ana shakkar shi 'ya'yan 'yan uwa da sauran su, se Aminu, Bashir, sagiru, Mudassir, se kuma mustapha wanda shine autan maza daga shi sai Abdullahi, se kuma matan Aisha saudatu, maryam, ban da wad'an da su ka ra su, su goma ne cif a ɗakin su,. Kasancewar Abdullahi shine auta shiyasa akafi ji da shi ga shi kuma shine ya yi karatu mai zurfi har ya samu aikin gwannati hakan yasa nan da nan kuma ya fara juya kud'in shi nan da nan yayi kud'i sosai duk da Familyn dama da kud'in su don ko wa yana fa sana'ar shi. Ba'a d'auki lokaci ba aka saka ranar Shamsiya da Abdullahi, ba dad'e wa aka yi bikin, aka kaita katsina ba laifi dangin Abdullahi su na son ta amma akwai wad'an da ba su son ta, da ma ba lallai ba ne ace ka samu soyayyar Kowa ba a duniya. Wasa-wasa kud'i sosai Abdullahi ya yi wanda duk Dangin sun huta don su na cikin daula sosai shamsiya ma tana hutawa sosai, ta haifi 'yarta mace suna kiran ta da Safnah. Bayan shekara Biyar da auren Shamsiyya, Al-amin ma yayi aure ya auri matar shi khadija 'yar zaria ce ita acan ma yake zaune, don yanzu ya gama karatun shi yana neman aiki ne kuma yana sana'ar shi, a shekarar ne kuma Mallam suleiman Allah ya yi mai rasuwa inda ya bar matar shi ita kad'ai agidan Al-amin yayi da Innar ta su ta dawo gidan shi da zama amma tace tafi son gidan da take, hakan yasa shi ya siyar da gidan na su dayake yana da girma sosai, ya gina mata d'an madai-daici don waccan ya mata girma ya zuba mata kayan abincin da komai na bu'kata daya ke maman na su akwai son yara shiyasa yaran anguwan su ma suna son ta don idan kazo gidan cike zaka gani da 'yan mata suna ta hira su mata girki da komai ko yaranta se haka, shiyasa ma hankalin Al-amin ya kwanta. Yanzu yarinyar Shamsiya ta girma sosai don tana da shekara Takwas ta na karatun ta don ta gama primary ma yanzu don ta shiga makaranta da wuri. A shekarar ne kuma Su ka shirya zuwa Aikin Hajji na biyu don sun ta'ba zuwa da shamsiya da Abdullahi sun so su tafi da safnah amma ƴan uwa su ka ce abarta kawai, su ka shirya su biyu su ka tafi, sun yi aikin hajji lafiya sun gama a hanyar dawowa su ka yi hatsarin jirgin sama, yayin da jirgin ta 'kone 'kurmus ko gawan su ba'a fitar ba. Sosai aka ji mutuwar su Al-amin ma ya ji mutuwar 'yar uwan shi, Inna ma ta ji mutuwar 'yar ta ta, sosai, haka su ka yi hakuri su ka yi musu addu'a. Safnah ko da ta ji mutuwar iyayen nata sosai abun ya ta'ba ta don se da ta dinga ciwo kamar ma bazata rayu ba, daga nan ta dangana ta na yiwa iyayen ta addu'a, ta na zaune acikin familyn Baban ta, don Al-amin yayi su ba shi ita sun'ki hakan yasa ya hakura. Bayan shekara biyu lokacin Safnah ta na da shekara goma kuma ta shiga jss 1 wata rana ta shirya zuwa ziyara gidan Kawun ta Al-amin, daga sati biyu se da ta yi wata biyu sosai ta ji dad'in zaman gidan don matar kawun nata akwai mutunci ga yaran ta su na da tarbiya sosai don su na girmama ta kamar antyn su wanda su ke ciki d'aya. Da dangin mahaifin ta su kaji shiru ne su kayi tattaki don zuwa d'aukan ta amma fir!, Safnah ta'ki se ma kuka da ta dinga yi musu ta fi son nan hakan yasa aka ce ta 'kara wata d'aya. Bayan wata d'ayan ma dai Safnah ta'ki komawa, ga gidan su gidan kud'i komai akwai gata take samu sosai amma kuma tace ita nan ya fi mata hakan yasa su 'kyaleta se dai ta kai musu ziyara shima se ta shekara bata je ba, ta dawo gidan kawun ta dai da zama yayin da take son su su ke son ta don tun da ta zo khadija ta huta don tun bata iya aikin ba kasancewar bata saba ba har ta kware don ko ta hana ta ma se tayi. Makaranta me tsada kawun nata ya saka ta anan ne kuma su ka had'u da Safwan... SAFWAN Alhaji muhammad (Naira) ya kasance shahararren mai kud'i ne shi d'an asalin zaria ne a Samaru yana zaune da matar shi guda d'aya Maimuna, da yaron su guda d'aya da Allah ya ba su, wanda su ke so fiye da yanda su ke son ran su ma, MUHAMMAD wanda su ke kiran shi (SAFWAN) sunan baban shi yaci kasancewar baban nashi shima sunan Baban shi yaci, sosai Safwan ke samun gata awajen Mahaifan nashi. Safwan yana da shekara goma sha takwas yanzu, yana Jss3 yanzu don be shiga makaranta da wuri ba, lesson akeyi mai a gida kafin ya shiga. Alokacin ne kuma Dad shi iyayen shi su ka matsa mai sai ya 'kara aure don baze zauna da matar da bata haihuwa ba tun da tayi ɗaya kusan shekara goma sha takwas, dama can ba wani son maimuna su ke yi ba kasancewar ita 'yar kano ce ya auro ta ba a garin ta ke ba, nan su ka had'a shi da wata 'yar uwan Dad su Hajara. Hajara irin matan nan ne makirai wanda su ka san kan makirci sosai ga shi tun da ta shigo gidan momim Safwan bata yi kishi da ita ba amma ita bata 'kaunar ganin su a gidan daga ita har d'anta Safwan. Shekarar Hajara Biyu a gidan Ta haifi d'an ta namiji, wanda ya ci suna, mansur, awannan lokacin ne kuma Daddn Safwan ya saki maimuna, (momin Safwan) hakan ya matu'kar 'bata ma Safwan rai sosai momin shi ta koma kano garin su da zama yanzu shi d'aya ne a gidan Dad shi gashi baya zama daga shi sai Hajara da ya ke ce mata anty, tun da momin shi ta bar gidan Hajara kullum da salon zagin da zata yi mai da tsinuwa sosai abun ya ke damun Safwan ya na ta'ba mai zuciya, amma Safwan be cika yanka mata ba, domin yana da haƙuri sosai, amma ba kowa ne se gane hakan ba. Da taimakon abokai da kuma aminin shi kamal Safwan ya fara shaye-shaye, ba irin abun da baya sha, don Kamal ba ƙaramin hatsabibi ba ne, har zuwa club duk Kamal ya koya mai abu d'aya ne dai Safwan ya kasa koya neman mata domin Kamal gwani ne ta nan ma, abun na Safwan wasa-wasa se gaba yake yi, don idan ya sha se dai ma akawo shi gida ko kuma ya shigo a bige, sosai abun ya ke bawa Daddyn shi mamaki wai Safwan ne da wannan d'abi'a, momin shi kuwa da ta samu labari har kuka ta yi, ta cigaba da yi mai addu'a. Ranar da Safnah ta fara zuwa makaranta an saka ta a Jss2 kasancewar ta yi one a garin su, ta fara two d'in ma, sati biyu ta yi ta na zuwa, ta samu kawun ta tace don Allah ayi mata Jumping zuwa Jss3 kasancewar kawun ta yasan wacece Safnah akwai son karatu kuma malamin abokin shi ne kuma yana fad'a mai 'ko'karin Safnah, shiyasa ya yarda aka mata jumping d'in. Ajin su Safwan aka kaita, Su ka dinga raina ta don ganin ta 'yar 'karama, yanzu ta shiga shekara na sha 14 ma, har da Safwan shi ma yana mamakin ganin ta a ajin, duk da akwai yara a ajin amma manyan sun fi yawa. A layin gaba Safnah ta zauna ku sa da wata maryam, har zuwa mallam ya shigo (malamin English), hakan ya sa Safnah ciro littafin English d'in ta, tambaya malamin ya yi wanda al'adar shi ce idan ya shigo sai ya tambayi abun da akayi a ajin baya, kafin ya yi musu sabo, ai ko kowa shiru ya yi aka rasa mai bada amsa, can Safwan ya mi'ke ya fad'a malamin yace ka kusa dai amma akwai gyara, waye ze gyara mishi, Safnah da tun d'azu ta ke son fad'a amma kuma se ta ji kunyar mi'kewa take yi, d'aga hannu ta yi tace "sir", "yes" tashi ta yi ta fad'i malamin ya sa aka tafa mata sannan yace "ke sabuwar zuwa ce ko?", "Ehh!" Safnah tace, yace "ya yi kyau", sannan ya cigaba da tambaya komai ya tambaya se Safnah ta d'aga hannu sosai ta burge 'yan ajin da su na mata kallon rainin wayo yanzu kuma kowa se ya dawo dama za su yi kawance. Ko da malamin math ma ya shigo anan su ka sha mamaki don Safnah akwai math, solving d'in da aka musu jiya malamin yace ayi mai kowa ya kasa, sai Safnah ce ta fito ta Solver gyaran d'aya kawai malamin ya yi mata. Ko da su ka fito break Safnah ita da maryam su ka fito su ka samu guri su ka zauna yayin da Safwan hankalin shi na kan Safnah, haka kawai ya ke jin dad'in kallon ta don Safnah kyakykyawa ce ta 'karshe ita ba fara ba ce sosai amma kuma Ta na da tsantsar kyau sosai. har su ka koma aji. 'Karfe biyu2 aka tashe su gida, Safnah su ka jero da Maryam don zuwa yanzu sun saba sosai da ma Safnah haka ta ke akwai saurin sabo amma idan mutum ya sakin mata fuska, har su ka fito bakin gate Safwan ne ya fito a dalleliyar motar shi ya wuce ta gaban su saura kad'an ma ya taka Safnah, abun ya ba Safnah haushi, maryam ta kalla tace "waye wannan", murmushi maryam ta yi tace "ba ki gan shi a class d'in mu ba, Safwan su nan shi d'an mai kud'i ne sosai, a unguwar ku ma ai yake, ba kin ce Samaru ki ke ba", "Ehh" Safnah ta ce "to ya akayi baki san shi ba?", "Shikenan dai amma haka yake saura kad'an fa ya taka ni, "ki yi hakuri ba halin shi ba ne ina jin be lura ba ne", shiru kawai Safnah ta yi, yayan Maryam ne ya zo d'aukan ta, hakan ya sa su ka yi sallama ita kuma Safnah Napep ta tare ta shiga.  _?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE**BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_9&10 Washe gari Safwan ya samu maryam yace "don Allah ina son 'kawance da sabuwar zuwan nan, ya za'ayi?" Murmushi maryam ta yi sannan tace "to zan mata magana" "wani irin magana kuma!, kar yarinya ta raina ni kawai dai kisan yadda za kiyi amma kar tasan ni nace ina son kawance da ita", "ok, zan gani" tace afili a zuciya kuwa dariya ta ke yi ta na mamakin son girma irin na Safwan da kuma rashin son raini don baya d'aukan rai ni ko kad'an. Safnah ce zaune ita da Maryam a wani ɗan dakali suna hira, kallon Maryam Safnah ta yi tare da cewa "maryam wancan shine wanda ya ku sa ta ka ni jiya ko?" ta ƙarasa tana nuna wajen da Safwan ke zaune shi da Kamal suna hira. "Ehh amma ai komai ya wuce be sani ba ne amma yana da kirki sosai", "ok" kawai Safnah tace sannan Maryam tace ta rakata koyan karatu, ba musu Safnah ta miƙe domin raka ta. Kai tsaye wajen Safwan ta nufa Safnah na biye da ita, waje Maryam ta samu ta zauna, kusa da shi tace "Safwan don Allah math d'in jiya, zaka nunamin" murmushi Safwan ya yi yace, "ki ce kin zo tsokana ta dai maryam, ga ki ga caculator a kusa ki ka zo nan", dariya ta yi tace "waye caculator" "gata nan New comer d'in nan", Dariya Safnah ta yi wai caculator, Sannan tace "ni computer ce ba caculator ba ka ji ko", dariya Safwan yayi sannan yace "ke babbab ce fa", "ko!" Safnah ta ce, yace "Ehh mana" "to yayi kyau", zama su ka yi su ka sha karatu nan da nan su ka saba da Safwan kuma ta yarda jiya be ganta ba ne don da ta zata wulakanci ne na masu kud'i amma Safwan ba ruwan shi. Yau sati d'aya da canzawa Safnah aji yayin da wata irin shakuwa ce ta shigà tsakanin Safwan da Safnah wanda duk dad'ewar da su ka yi da maryam ba su yi irin ta ba, kowa ma kallon soyayya ya ke musu. Safnah yau ta na dawowa gida ta ci abinci ta zauna ta fara ba anty labarin Safwan, anty tace "ai d'an gidan Alhaji muhammad ne, yànà zuwa gidan nan ma kwana2 ne ma na daina ganin shi, Dadyn khalil ai Likitan gidan su ne ya na duba dad shi", mamaki sosai Safnah ta yi a she ma anty ta san shi. Anty ne tace "Safnah miye tsakanin ki da shi?", "anty bakomai kawai abota ne", "Safnah abota da namiji!, amma kinsan Safwan kuwa?, Safwan mutumin kirki ne kafin ya 'bata halin shi da shaye-shaye tun bayan rabuwar momin shi da Dad shi, bayan shaye-shaye da zuwa club kuma bai da wani abu, amma kuma kinsan d'an shaye-shaye ba abun da baze iya yi ba", ita dai Safnah shiru ta yi don sosai abun ya bata mamaki, duk da ƙarancin shekarun ta amma Safnah yarinya ce mai hankali da hangen nesa,yanzu take shekara na 14 amma a yanayin girman jikin ta zaka ce ma ta wuce haka don tana da tsayi ga jiki, jikin ta ya yi sanyi sosai har su ka gama hirar da anty bata sake yin kwakwkwaran magana ba. Washe gari kuwa Safnah ko da taje school Safwan be zo ba ta tambayi Maryam tace mata wallahi bata san me ya hana shi zuwa ba, "gashi bani da number shi", cewar Maryam Wajen kamal ta nufa tace "don Allah number Safwan na ke nema" murmushi ya yi sannan ya bata number kasancewar Maryam tana da waya amma don karatu aka siya mata, kira ta gwada yi taji ya shiga sannan tace "na gode" ta tafi Kira ta 'kara yi amma ba'a d'auka ba, Safnah ce ta ƙarɓi wayar ta ƙara kira tare da ƙarawa a kunne, gaf da wayar zata tsinke aka d'aga sallama ta yi, da'kyar ta ji ya amsa sallamar, sannan ya fara fad'in wa... wa... wa...ye......ne... ? Zama Safnah ta yi kan wani dutse ba ta ma san ta zauna ba kasa magana ma ta yi shi ko Safwan be fasa surutan da ya ke yi ba hawaye ne su ka zubo wa Safnah a ido yayin da ko kasa kashe wayar ta yi shima be kashe ba har tsawon mintina5 sanna ta yanke wayar ta miƙawa Maryam ta tashi na nufi Class gaba d'aya ma bata gane karatun da akayi ba don tunanin da ya yi mata yawa. Ko da Safnah ta koma gida 'karyar ciwon kai ta yi wa anty don ta kasa gane kan ta. Washe gari ko da ta je makaranta a can ta sa mu Safwan, har ya je, yana hangota kuwa ya taso yana kwala mata kira Safnah banza ta yi da shi don haushin shi ma take ji yau, gudu yayi har ya kamota yace "haba Besty ina magana kin kyale ni", ko kallon shi bata yi ba ta yi gaba, be hakura ba binta ya cigaba da yi, har su ka iso wajan zaman su, su maryam duk suna wajen 'karasawa ta yi ta zauna kusa da maryam, zagayowa Safwan ya yi yace "Safnah kin 'ki fad'a min laifin da na miki kinsan bazan iya jure fushin ki ba besty na mutanen da su ke wajen ne su ka kwashe da dariya, wasu har da shewa ma, kallon su Safwan ya yi sannan ya musu alama da su bar wajen. Cikin minti1 Safnah ta ga ba kowa kallon shi ta yi tace "Safwan jiya meyasa baka zo school ba" shiru ya yi sannan yace "banajin dad'i ne" Murmushin takaici Safnah ta yi sannan tace "Safwan jiya fa na kira ka, da safen, Safwan dama abun da aka fad'a min gaskiya ne Safwan kana shan giya", Idon ta taf da ƙwalla take maganar, Hankalin Safwan yayi matu'kar tashi ganin hawaye a fuskar ta Hakuri ya shiga bata cikin kukan Safnah ta ke cewa "Safwan wannan fa halin an ce min da baka yi yanzu me yasa ka d"aura wa kan ka?, Kasan ubangijin mu ya hana fa kai ba jahili ba ne Safwan meyasa ka ke wannan abun Safwan. Safwan ya ma rasa me zece mata don zuciyar shi ta yi mai zafi sosai, shi kan shi besan ya aka yi ya zama d'an giya ba, duk da momin shi na mai fad'a da wa'azi sosai idan yaje mata ziyara amma yau ne karo na farko da ya ji tunanin daina sha ya zo mishi, hakuri ya bata sosai, Safnah tace. "Ni ka daina bani hakuri shawara ce kawai na baka, mi'kewa ta yi zata tafi. "Safnah!" ya kira sunan ta bata juyo ba amma ta tsaya cak, yace "Nagode Allah da yasa ki ka san ba hali na ba ne amma!, amma ina bu'katar addu'an ki domin ni kai na ba'a son rai na na ke sha ba Safnah wataran idan ban sha ba jina nake kamar zan mutu, kaɗaici yayi wa rayuwa ta mamaya, Daddy na da nake matuƙar so baya nan ya zaɓi kasuwanci da zama a nan, momy na rabin raina bata tare dani se nayi dogon tafiya zan je wajen ta, kuma tace na daina yawan zuwa wajen ta, Anty (matar Daddy na) ba ta da maƙiyi da ya wuce ni, to ya zanyi kullum se dai, na je makaranta idan na dawo, ina zaune a ɗaki ko na fito kofar gida yin Ball, ba wanda za bani shawara yace yi wannan ko bar wannan, duk abinda naga dama shi nake yi". se lokacin Safnah ta juyo ta kalle shi idanun shi sunyi jajur tace "Safwan na fahimci damuwar ka amma yaƙi zaka yi da zuciyar ka na ganin ka daina sannan ka dage da Addu'a da karatun Al-qurani, ina maka kyakykyawan zato", Tana fad'in haka ta wuce aji, ta dad'e da shiga amma Safwan be shigo ba yana waje, mi'kewa ta yi ta nemi Izinin fita ta fito waje yana inda ta bar shi ya kifa kan shi, "Safwan!" ta fad'a be d'ago ba 'kara kiran shi ta yi se lokacin ya d'ago ya kalle ta tace "an fara karatu baza ka shiga class ba ne" "Ehh" yace mata, "meyasa?" "Ko na shiga Bazan iya karatu ba Safnah kai na ke ciwo", "to shikenan" Safnah tace, Sannan yace "ki kira Kamal ya kai ni gida" "to" tace sannan ta juya cike da tausayin shi, ta nufi class d'in lokacin ma ba malami a ciki ya fita, Kamal ta kira ya kama shi ya saka shi a mota su ka nufi gidan su, cikin minti10 su ka isa gidan ko da su ka shiga falon Anty na zaune Mansur na gefen ta suna kallo Kamal ne ya shigo da sallama, Ko amsawa bata yi ba tace "to ɗan giyan ne aka dawo da shi ya bugu ko?, kai! Allah ya wadaran naka ya lalace wallahi" Kamal da yasan hali ko kallon ta be yi ba ma ya raka shi d'aki, kwanciya Safwan ya yi sannan yace "Kamal ka koma school ka kulan min da Besty na Don Allah" "ok", yace sannan ya fita Ko da ya fito mansur ne kawai a falo, yace "yaya Kamal yayana bashi da lafiya ne?" "Ehh" kawai Kamal yace, "jikin nashi da sauƙi?" "da sau'ki" Kamal yace mai sannan ya wuce. Safnah ko da aka ta fi da Safwan Ba malamin da ya sa ke shigowa kasancewar ma an kusa ta shi, ta na zaune tana tunani, har aka ta shi ta nufi gida cike da addu'ar Allah ya ba shi lafiya. Washe gari ko da Safnah ta zo Makaranta acan ta Samu Safwan domin ya iya sammako Idan yaga dama, 'karasawa ta yi ta mai ya jiki yace "yayi, sau'ki gani ma kina kallo na", "Allah ya 'kara lafiya", nan dai su ka sha Hirar su sosai. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yayin da Safnah yanzu tana da shekara Goma Sha biyar16 Safwan kuma yana da 24ya bata shekara takwas8 kenan yayinda, suna Ss3 sun kusa ma fita don har sun fara shirin graduation. Yayin da Muguwar shakuwa had'e da soyayya ta shiga tsakanin su a cewa ta da sauran mutane amma su sun ce sam ba soyayya ba ce ba kawai Abota ce, haka dai kowa ya kyale su akan abota ce. Tsarkakakkiyar tarayya suke yi tsakanin su don Safwan ko hannun Safnah be ta'ba ri'kewa ba, sa'banin wasu ko a school d'in na su ma, abun se dai Allah ya kyauta. Safwan yana zuwa gidan su Safnah har d'akin anty kasancewar tun kafin Safnah ma ta zo yana zuwa don Kawun Safnah Likitan Baban shi ne da sauran gidan su ma, za su sha fira sosai, kasancewar Anty da Kawu sun san halin Safwan shiyasa su ka 'kyale Safnah da shi. Da taimakon Safnah kuma duk shaye-shayen da Safwan ya ke yi ya dai na shi se wanda ba'a rasa ba a'boye don Idan ta sani akwai damuwa. Bayan sun gama karatun su ne kuma Kawu yasa Safnah a A B U don ta 'kara karatu yayin da a wannan lokacin ne dangin Mahaifin ta su ka matsa lallai ya ba su 'yar su za su mata aure tunda shi ya barta ta na zaune haka nan ya ba su hakuri ya samu Safnah yace ta fito da miji domin ga abun da Baban ta yace, duk da yasan shima Safnah bata kula samari idan ba Safwan ba, Safnah tace mai bata da saurayi ita karatu za ta yi, "to" kawai Kawu yace ya kyale ta amma a zuciyar shi ya na mamakin Yaran nan, don ya yi ma Safwan magana ma yace mai ai ba soyayya su ke ba, haka dai Kawu ya share maganar. Washe gari su ka had'u a school kamar kullum su na zaune su na hirar su, Safwan ne ya kalli Safnah yace "Safnah ki na so na!?", sosai Safnah ta yi mamakin tambayar a zuciyar ta tace "lallai ma yaron nan wato baze ce ya na so na ba se dai ya tambaye ni Ina son shi", "kinyi shiru", maganar shi ta da wo da ita, "a'a" tace mai, dariya ya yi yace "na zaci ke ki ka fad'a wa Kawu ki na so na", "Allah ya sawwa'ke me zan yi da kai d'an yaron ka da kai duka fa shekara takwas ka ba ni", dariya Safwan ya yi yace "lallai ma ni ne yaron to ki bari ki ga matata wallahi se kin rai na kan ki", "oho dai mu gani a 'kasa, Dady ma baze maka aure yanzu ba ma", "haka ki ke ga ni, to ki dai na wannan tunanin don ko yau nace ma Dady na fito da mata se ya yi min aure", dariya Safnah ta yi tace "yayi kyau mu 'yan shan biki ne dai" haka su kayi ta hirar su. Dad Safwan ya so ya kai shi England domin yayi karatu amma yace shi A B U kawai ya ke so don baze iya nisa ya bar Safnan ba, haka Dad shi ya yi hakuri ya kai shi A B U kuma yayi ma abokin shi da ke koyarwa acan magana yace yasa mai Ido sosai akan shi duk abun da yake ya na Idon shi, don har ya fad'a wa Dad shi maganar Safnah, sosai Dad shi ya ji dad'i. Bayan su Safnah sunyi graduation sunyi hutu hakan yasa suka tafi Kano don gaishe da kakan su tsohuwa mai ran ƙarfe, duka suka tafi har da Kawu, suka yi kwana biyu shi da Anty sannan su ka dawo su ka bar yaran sai sunyi wata ɗaya kafin su dawo, don sun samu hutu mai yawa. Kakan su taji daɗin zuwan su don sun ɗebe mata kewa sosai, Safwan kuwa Kullum se sunyi waya don yanzu tana da ƴar ƙaramar waya a hannun ta, Safwan yana so ya siya mata babban waya amma taƙi yarda, don Kawun ta yace se ta shiga babban makaranta ze siya mata. Yau ma kamar kullum Safnah na kwance a gadon da ya kasance nata ne tunda tazo Kano, waya ne a maƙale a kunnen ta suna magana da Safwan. "Kina ganin wasa ne ko, wallahi gobe ina nan zuwa Kano, se dai idan baki so mu haɗu ba, ki ka ƙi yi min kwatancen gidan" cewar Safwan Dariya sosai Safnah ta yi sannan tace "zaka zo gurin momy kenan" "A'a ni wajen ki zan zo momy na bata son naje wurin ta ma" cikin shagwaɓa yayi maganar hakan yasa Safnah yin dariya sosai sannan tace "Kai ka girma ai dole momy tabar ji da kai" "kina so muyi faɗa ko" "a'a kayi hakuri to" "Shikenan, amma gobe ki tabbatar wayan ki a kunne take" "baka da matsala zaka same ni" "to anjima zamu yi waya kar na kira ban samu ba" "Baza ka samu bama, kai fa ka cika naci tunda nazo kullum se ka kira yafi sau biyar, to kiran na miye, baka gajiya ne kai" shiru taji yayi hakan yasa ta yin dariya "se na kira kawai yace tare da yanke wayar. To a cigaba da labarin mu Kamar kullum bayan su Safnah sun gama cin abinci su ka kwaso littafan su, wanda aka ba su Assignment se Safnah ta ko ya musu, har lokacin Islamiyya ta yi su ka ta fi. Washe gari Safnah ta shirya kamar kullum ta shirya yaran su na zaune kasancewar yau kawun su shi ze kai su don yanzu ya sayi mota kwanan nan Bayan ya kimtsa ne ya fito su ka wuce Safnah ya fara aje wa ya bata d'ari biyar ta yi break Sannan ya ce Idan be zo d'aukan ta ta dawo a napep "to kawu Allah ya tsare", "Ameen Safnah". More comment More typing Ku cigaba da kasancewa tare da ni Taki Khadeejerh Ishaq ✍️  _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*11&12 Safnah sauri take dom ta kusa yin latti ta zo dai-dai shiga ajin su su ka ci karo da wata za ta fito kallon kallo su ka tsaya yi ba lefi yarinyar kyakykyawa ce fara ce kuma, Safnah ce tace "yi hakuri ban gan ki ba" yarinyar da baza ta wuce sa'ar Safnah ba tace "bakomai" Sannan ta mi'ka mata hannu su ka gaisa tace "sunana Salma daga jushi ni sabuwar zuwa ce" "Safnah Daga Samaru" kawai Safnah tace mata tare da wucewa don kawai ta ji yarinyar bata kwanta mata ba, ta na shiga kuma Safwan ya shigo Salma ta ga ni ta shigo ajin kujerar bayan su ta zauna ta na kallon irin kallon da Salma ta ke yi wa Safwan ran ta ba 'karamin 'baci ya yi ba. Bayan an ta shi makaran ta Safnah ta na tsaye ta na jiran shi se hango shi ta yi shi da Salma sun fito se wani yamutsa fuska ta ke kamar ta ga kashi, har ya zo wajen motar shi shiga ya yi Salma kuma ta yi gaba tare da d'aga mai Hannu ta na murmushi, fitowa ya yi dai-dai in da Safnah ta saba jiran shi ya zo ya bud'e mata tare da cewa "ranki ya dad'e amin hakuri na shanya ki ko?, ayi hakuri" ko kallon shi ba ta yi ba ta shige motar su ka fara tafiya juyowa ta yi ta kalle shi tace "yau ne fa" "mene?" Murmushi ta yi tace "oho! ai ka fini sani wallahi kuma kaje ko, hm", dariya sosai Safwan ya yi don har ga Allah ma shi ya manta da wani party da za su, yace "yawwa nagode da tunamin da ma kuwa na manta, na biyo ta gidan ku ne muje", "Ehh mana" Safnah tace, "to 'karfe shida dai zan biyo miki", "to shikenan" Hirar su su ka cigaba da yi har aka iso gidan su Safnah ya sauke ta ya wuce, perking d'in motar shi ya yi ya shiga falon sauri yake domin anty bata falon don yanzu baya son ganin ta ma, d'akin shi ya shiga yayi wanka sannan ya ya bud'e frige ya d'auko lemo da snak ya ci duk da haka yunwa ya ke ji sosai hakan ya sa shi fitowa zuwa kicin Lami mai musu aiki ya samu yace mata "me ki ka dafa?" mamaki ne ya kama Lami ganin Safwan ya zo neman abinci, bayan rabon shi da cin abincin gidan ita kan ta ta manta Idan ba Dadyn shi yana nan ba ne ya kira shi dole ya ci, zubo mai ta yi d'akin shi ya koma don ya ci tsakurar abincin kawai ya yi ya ajiye shi don ya ji ya 'koshi. Sallamar Kamal ya ji daga falon shi, fitowa yayi ya bud'e mai su ka shiga, Kamal ne yace "haba Boss na ji shiru baka yi wata magana ba ne kasan kuma anjima ne fa" murmushi Safwan ya yi sannan yace "Kamal kenan yau bazan samu zuwa ba ka gaishe da kowa a madadi na", "Haba Boss kasan fa idan baka je ba wajen baya dad'i fa", murmushi Safwan ya 'kara yi yace "Kamal yau fa ba zan je ba gaskiya" kud'i ma su yawa ya d'ibo ya bawa Kamal yace ayi komai godiya Kamal ya yi sannan ya fita. Safwan Baccin shi ma ya sha sosai don da ma ya gaji sosai ba shi ya tashi ba se 'karfe5, Cikin sauri yayi alwala yayi Sallah, sannan ya shiga ya 'kara yin wanka, ya fito ya shirya cikin shaddar shi maroon colour da ya yi matu'kar yi mai kyau, sannan ya d'aura agogon shi shima maroon colour mai tsadan gaske, sannan ya Saka takalmin shi shima maroon ne Idan kagan shi yayi masifar kyau sosai fitowa ya yi yaje inda su ke ajiye motoci guda ya zaba wanda sabuwa ce ma ya shiga idan ka gan shi kamar wani sabon ango, kai tsaye gidan su Safnah ya nufa, perking ya yi ya fito wani yaro ya aika gidan yace a kira mai khalil, don yasan yau Juma'a ne ba su da Islamiyya. Su na zaune duka suna hira aka shigo wai khalil ya zo anty ta za ci ma Wani abokin shi tace "to saura a wuce yawo", murmushi khalil ya yi sannan ya fita, yana fitowa kuwa ya ga Safwan murna ne ya kama shi kasancewar su na yi sosai da Safwan zuwa ya yi ya mi'ka mai hannu su ka gaisa don dama sun sa ba, Safwan ne yace, "Anty tana nan?" "Ehh", "kace mata ta yi ba'ko amma kar ka ce ni ne", "to" khalil yace sannan ya nufi gidan da gudu, Yana zuwa yace momi kin yi ba'ko murmushi anty ta yi sannan ta ce "waye?, "ban san shi ba", "ok, kace ya shigo", "to momi" yace sannan ya nufi wajen ya fad'a wa Safwan ya shigo. Safnah da ke zaune kusa da anty jin ance ta yi ba'ko ta mi'ke ta shiga d'akin ta don a tunanin ta 'yan uwan antyn ne Safwan ne ya yi sallama ya shigo gidan anty murmushi ta yi tare da amsawa tace, "Safwan Idon ka kenan?", murmushi ya yi ya na sunkuyar da kai, don shi kan shi kunyar anty ya ke don ya rabu da zuwa gida, d'akin anty ya shiga ya zauna anty ta kawo mai kayan motsa baki ci ya yi sosai don gidan ba bakon shi ba ne, hira su ke yi yayin da Safnah har yanzu bata fito ba, Safwan ne yace "anty wai ina mutuniya ta?" dariya anty ta yi tace "dama wurin ta ka zo kenan?" "wane ni rufa min asiri anty ni ke na zo gaishewa" "to nagode, khalil je ka kira anty Safnah" fad'in anty, da sauri khalil ya mi'ke ya nu fi d'akin Safnah don kiran ta. Akwance ya sameta ta na game a wayar ta, yace "anty ya Safwan na kiran ki" Safnah ta shi ta yi tace "ina yake?" "yana d'akin momi," murmushi ta yi sannan ta ce "ka ce ina zuwa to anty ya ce tare da fita, Riga da wando ne ajikin Safnah hakan ya sa ta d'auko after dres d'inta ta sa ka, ta d'auko hijab d'in ta wanda ya d'an wuce gwiwar ta ta saka sannan ta nufo d'akin Sallama ta yi Safwan da ke facecing ɗin kofar d'akin ya amsa tsayawa ta yi kallon shi don yanda ya had'u sosai don Safwan ba ma'abocin sa ka manyan ka ya ba ne se ta d'auro mai, kuma kyau su ke yimai sosai, sassanyar murmushi Safwan ya sakar ma ta ita ma Murmushin ta mayar mai, har yanzu bata bar kallon shi ba shi ma ita ya ke kallon, anty ce ta tsaya kallon ikon Allah sunyi minti1 a haka sannan Safnah ta shigo d'akin ta zauna tare da cewa "d'an rainin wayo na zaci ai ka ta fi ne ma?" Murmushi ya yi yace "yanzu zan wuce bakin ce na biyo miki ba?" Dariya Safnah ta yi tace "Wannan ba wankan Party ba ne ba", "to ke ai kin yi na Party ke" "to ana zuwa da hijab ne?" "Ehh ma na Idan an je se ku cire a waje ba" "Allah ya tsare ni" "ke kad'ai ban da mu ko?" dariya ta yi tace, "har da ku mana da duk Musulmai" Ameen, Safnah ne ta juya tace "anty kin yi shiru ki na jin mu", murmushi anty ta yi tace "to ba kyale ni ku ka yi ba", "a'a anty ba mu kyale ki ba" cewar Safwan, anty murmushi kawai ta yi, Wayar Safwan da ke Aljihun shi ce ta fara ringing hannu yasa ya fito da wayar, cikin zafin nama Safnah ta kwace wayar ta fita da gudu ta na fad'in "'yan partyn ne ba, to wlh baza ka d'auka ba ma" shi dai Safwan murmushi ya yi kawai su ka ci gaba da hirar su da anty da su khalil da Halima. Ita kuwa Safnah d'akin ta ta shige sannan ta duba sunan mai kiran, SALMA ta ga ni a rubuce, sosai ta yi mamaki kamar baza ta d'auka ba kuma se ta d'auka, shiru ta yi bata yi magana ba, daga can ta juyo muryar Salma na fad'in, "haba Safwan abun da ka ke min ya da ce kenan tun da aka ta shi school na ke kiran ka amma ka'ki d'agawa, hakan na cutar da zuciya ta ga shi baka ba ni amsa ta ba, nace Ina matukar kaunar ka amma kai baka fad'amin ba, zuciyata na azaftuwa da son ka sosai don Allah ka tausaya wa zuciya ta, ka yi magana mana ko zan ji dad'i a raina", Safnah bushewa kawai ta yi awajen don ta yi danasanin d'aga wayar kar ta yi magana tace ta ji mata sirrinkan ta ta yanke kuma tace ya mata wulakan ci, ta na tunanin ne ta ji wayar ta yanke, Hamdala ta yi sannan ta koma d'akin tace "ga wayar ka Sweetyn ka ce ta kira", dariya ya yi yace "wayace to ki d'aga", "babu na yi ra'ayin hakan ne" "ya yi kyau", hira su ka cigaba dayi har gabanin magrib sannan Safwan ya mi'ke don tafiya gida yace wa khalil ya zo ya 'kar'bi tsarabar su, kayan za'ki ne su biskit, coculate, alawa da dai sauran su duk Safwan ya had'a musu, su ka yi sallama Safwan ya nufi gida, Bayan Sati biyu da zuwan Salma makarantar, se faman shigewa Safwan ta ke don son shi ne ya kamata, kuma har ta fad'a mai ta na son shi yayin da shi be bata amsa ba ma amma ta ke ta haukan ta ita budurwan Safwan ce, Salmah irin yaran wa su kud'in nan ne sangartattu ga shi bata da kunya ko kad'an, soyayya ta ke nuna wa Safwan sosai wanda zuwa yanzu Safwan ya fara biye mata yayin da Safnah ke jin haushin hakan. Hakan yasa Safnah ta rage shiga Safgar Safwan shi ma sosai ya shiga tashin Hankali. Kanar kullum Safnah na zaune ita kad'ai don maryam kwana biyu bata zuwa makarantar Safwan kuma ta wuce shi da Salma su na hira, Salma ce tace "wai Safwan har yanzu ba ka ce min ka na so na ba" banza Safwan ya yi da ita, ta cigaba da cewa "Safwan da ace akwai yanda zan cire son ka a raina da tu ni na cire amma wallahi na ka sa don Allah ka tausa ya min", kallon ta Safwan ya yi sannan yace "na fad'a miki amma ina da budurwa ko", "na yarda Safwan ai namiji an bashi damar ya auri mata hud'u ma, duk da bani da ra'ayin zama da kishiya amma indai da kai ne na amince na yarda", shi Safwan abun ma ya fara ba shi mamaki don be iya wulakan ta mace ba da se ya mata wukakan ci ko zata kyale shi, muryar ta ya ji ta na cewa "Safwan ka ba ni soyayyar ka don Allah, ka ba ni dama" "to shikenan", "Nagode" tace sannan ya mi'ke yace "na tafi wajen bestyna", "to a gaishe ta" tace, sannan ya nufi wajen Safnah. kamar daga sama ta ji Sallamar shi Zama yayi ku sa da ita yace "my lovely Besty na kwana biyu kin bar ni cikin damuwa ba ki kula ni", dariya Safnah ta yi tace "to ba kyale ni kayi ba nima", dariya Safwan yayi yace "kodai kishi ki ke na yi budurwa" Murmushi safnah ta yi ta ce, "Allah ya kyauta me ye abun kishi anan yarinya kamar aljana ga shi kamar ka hure ta fad'i 'kasa, se wani jan fuska kamar kosai" dariya sosai Safwan ya yi yace "Kin rai na min budurwa ko to zan ne mi wata" "ya fi maka dai". Tun daga ranar kuma su ka had'e su ka cigaba da abotar su yayin da bangaren Salma ma ta na nan ta li'ke mai kamar manya. yau Safnah ko da ta dawo makaran ta ta samu Kawun ta a gida kallo d'aya ta yi mai ta san ran shi a'bace ya ke, "sannu kawu" tace mai da'kyar ya amsa yace "ki shiga ki shirya ki zo ina da magana da ke" gaban ta yayi mummunar fad'uwa tace "to kawu", cikin sauri ta shirya ko abinci bata ci ba ta zo kallon ta yayi yace "Safnah Allah ya ga ni ina son zama da ke har na ga na aurar da ke amma kuma gaskiya dangin mahaifin ki baza su yarda ba don yau Baba Salihu ya kira ni ya na min wa su maganganu da ba su kamata ba abun ya ba ni haushi ne sosai Safnah", hakuri Safnah ta ba Kawun nata, don ya d'auki zafi, a haka har ya huce, "ba komai Safnah je ki", tashi ta yi ta koma d'akin ta Bayan wata biyu2 su Safnah su na ta karatu sun ku sa fara Exam ma sati me zuwa za su fara Safnah ta dage da karatu sosai Safwan ma ba ba ya ba, Salma ma an dage don Safwan ya had'a su da Safnah ba lefi su na d'an mutunci sosai, amma idan ta ganta da Safwan haushi ta ke ji sosai a ran ta, amma bata bari Safwan ya lura da haka, shi kuma Safwan yanzu gaba d'aya ba ya jin dad'i ya rasa dalilin ba ya son Salma amma kuma yanzu biyayya ta ke yi mai sosai ya lura kuma ta na tsantsar kaunan shi, shiyasa yake ɗan kulata na wani lokaci. Kamar Kullum Safnah na zaune ita da Maryam Salmah ta zo Sallama ta yi musu sannan tace "Sannun ku" Maryam kawai ta amsa mata, ta samu gurin ta zauna tare da cewa "besty ba magana" murmushin ya'ke Safnah ta yi tace "Sannu ina wani tunanin ne daban" "ok" Bayan sun koma aji Safnah can baya 'karshen ajin ta samu ta zauna sa'banin wajen da ta ke zana kusa da Safwan, hakan ya sa Salmah zuwa wajen ta zauna, Safwan ne ya kalleta yace "anan kike zama ne?" "ka yi hakuri na ga ta koma baya ne shiyasa", ta shi ya yi ya koma baya sunan ta ya kira, "Safnah! Safnah!!" d'ago kai ta yi da'kyar don kan ta da yake mata ciwo sosai yace "lafiya?" "kai na ke ciwo", "to ki dawo wajen ki mana" "a'a ka bar ni anan ma" yayi-yayi ta taso amma ta 'ki hakan yasa ya koma ba don ya so ba, Salma da ma ta koma wajen ta kallon ta ya yi ya mata alama da hannu alamar ta zo, tasowa ta yi ta na murmushi ta zauna don ta ji dad'i kallon ta ya yi yace "kinsan bana son surutu ko?" "to ranka ya dad'e", murmushi ya yi dai-dai lokacin kuma Safnah ta d'ago kan ta ba'kin ciki ne ya cika ta wato ya je can har da murmushi be da mu da Ciwon ta ba, shi ko Safwan murmushin ya yi na mamakin Salmah duk class d'in ta ta zu bar ita ce har da fad'in ya yi hakuri. Safnah mi'kewa ta yi ta nufi waje Safwan da tun d'azu hankalin shi na kan ta shi ma ta shi ya yi ya fito office ya ga ta nufa, excuse da ba da akan za ta gida don baza ta iya zama har ta shi ba, fito wa ta yi da sauri ta nufi gate Safwan ne ya biyo ta yana ta kira amma ta yi banza da shi, bin ta ya cigaba da yi ya sha gaban ta yace "Safnah ya akayi ina ta magana kin kyale ni?" "gida za ni" kawai tace, sannan ta juya za ta tafi cikin zafin nama ya ri'ko hannun ta, cikin sauri ta juyo ta kalle shi da mamakin shi, kallon shi ta tsaya yi ko dai baya cikin hayyacin ne, Safwan da se yanzu ya lura da Abun da ya yi da sauri ya saki hannun ta yace "kiyi hakuri Safnah muje na kai ki gida" "ba na so" kawai tace ta juya har da 'karawa da gudun ta, ta na fita kuwa ta samu napep ta tsayar ta mai kwatan ce har gida ya kawo ta ta bud'e jakar ta ta ciro d'ari biyu ta ba shi, tun da ta fito ta ke jin gaban ta na fad'uwa sosai wata jibgegiyar mota ga kuma motar kawu shima a wajen ta gani a 'kofar gidan na su shiga ta yi bakin ta da sallama Anty da ta ke kicin ta amsa mata, "Sannu da gida anty" "yawwa Safnah". Safnah d'aki ta shiga ta aje jakar ta ta fito don kamawa anty aiki don yau ba ta gama ba, fitowa ta yi tace Anty kawo na 'karasa", "a'a Safnah ba ki ga ma munyi ba'ki ba ne", se yanzu Safnah ta kalli d'akin ba'kin ta ga takalma se kuma ta tuna da motar da ta gani a waje "anty waye?" shiru anty ta yi "anty kin yi shiru", "Safnah Baba Salihu ne ya zo tafiya da ke katsina", wayar Safnah da ke hannun ta ne ta fad'i kasa ta ke ta tawarwatse har layin se da ya fita, tace "anty da gaske ki ke?", kafin anty ta yi magana, Baba Salihu ya fito daga d'akin, Cikin rawar murya Safnah tace, "ina....wuni... Baba", "lafiya lau Safnah shiga ki had'o kayan ki Katsina za mu wuce", "Baba don Allah ka barni anan jarabawa za mu fara fa, Next week don Allah ka bari mu gana", tsawa ya daka mata yace "kije ki shirya nace ko ba ki d'auki kaya ba zan aiko a kwasan miki", d'aki Safnah ta nufa yayin da wasu irin zafafan hawaye su ka wanke mata fuska rasa me ma zata yi ta yi se kawai ta zauna kan gado ta fara rusa kuka ga kanta har yanzu kamar ze fashe, Inna Aisha ne ta bud'e kofar tace "Safnah me ki ke yi ne haka muna jiran ki" se yanzu Safnah tasan ma da ita akazo, wato su biyu ne, "Inna don Allah ki ba shi hakuri ki ce ya bari na gama jarabawa" fita ta yi ta kyaleta, Kawu ne ya shigo yace "Safnah ki shirya ki bi su kinji kar ki saka komai a ran ki, Safnah na so na zauna da ke har kiyi aure don idan na ganki ina jin farin ciki kamar 'yar uwata na gani amma Safnah dangin mahaifin ki ba za su yarda ba, tun da na d'auke ki kullum cikin cewa ki dawo su ke bansan me yasa ba su son zaman ki anan ba Safnah, ko da sun ce an barki haka ba aure se karatun boko, kinsan su basu yi ba shiyasa ba su san mahimmancin shi ba, sun ce aure za su miki, Safnah ki yi hakuri amma ni na gama rike ki, ko inna tace nabar musu ke kawai tun da itama ta hakura da ke d'in Safnah ina miki fatan alkhairi kin ji Allah ya miki albarka" Safnah da tun da Kawun nata ya fara magana kukan ta ya tsaya cak, ta na sauraran shi, yanzu dagaske tafiyan zata yi wani marayan kuka ne ya kwace mata kuka take sosai anty ma juyawa ta yi ta bar d'akin don ta fara kwalla itama irin sabon da su kayi da Safnah yanzu idan ta tafi ai zata yi kewar ta sosai. Baba Salihu ne ya dawo yace "ke Safnah ba nace ki fito ba ne ina jiran ki", mi'kewa ta yi ta fito don ba abun da take jin zata iya d'auka anty na tsaye a kofar d'akin ta, Gaban anty Safnah ta zo ta tsaya ta na kallon ta ido cike da kwalla, "Anty... Anty.." Safnah ke fad'i ta kasa yin magana ma rungume ta ta yi nan ta ci gaba da kwalla, anty ma hawaye ne ya fito mata saurin sharewa ta yi, Kawu ne yace "Safnah kukan me ki ke kamar ki na Ban kwanan mutuwa", kasa magana Safnah ta yi se juyawa ta yi ta nufi wajen harta ta fita waje ta dawo da gudu, tace "Anty wayata" da sauri Anty ta d'auko mata, "Anty layin fa?" na duba wajen ban gani ba amma zan duba miki" "to anty" tace sannan ta fita har zata shiga mota ta ga mai napep ya sauke su khalil da sauri ta 'karasa wajen su rungume su ta yi ta na kuka, Khalil ne yace "anty ina za ki?" "Katsina zan ta fi Khalil" "to yaushe zaki dawo?" "bazan dad'e ba zan dawo", "to anty meyasa ki ke kuka?" cewar Halima "ba komai zan yi kewar ku ne kawai, Khalil kace wa Safwan ya yi hakuri d'azu munyi fad'a da shi, sannan kuma kace mai ya ri'ke min al'kawari na, sannan kace mai ina... Ina..." Bata 'karasa ba Inna Aisha ta zo ta kama hannun ta suka nufi motar, Safnah na kuka haka nan ta saka ta amota, su ka nufi katsina, a mota in banda kuka ba abun da Safnah ta ke yi, yayin da su ka kyaleta, har bacci ya kwashe ta.  _‍♂️ƘADDARAR SAFWAN♂️ _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍YAFI TAKOBI️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*13&14 Gaf da magrib su ka isa katsina gidan su yana nan inda ta sani se de an mai gyara sosai ya 'kara masifar kyau horn su ka yi a bakin gate d'in, masu gadi su ka bud'e mu su, su ka shiga ciki, su na perking su ka bud'e su ka fito, wa su 'yan mata da baza su gaza sa'ar Safnah ba naga sun zo da gudu had'e da rungume ta, "sannu da zuwa Safnah" su ka had'a baki su ka ce, Safnah da ta ci kuka har ta gode Allah ta yi shiru, bata ce musu komai ba, hannun ta su ka kama su ka shiga gidan. "Masha Allah" na furta lokacin da na ga falon don katon falo ne sosai ya had'u ya ji kujeru had'ad'd'u sosai, Safnah d'akin su su ka shiga zama ta yi a kujerar da ke d'akin d'ayan ce tace "Safnah kin manta mu, ko magana kin ƙi mana ko?" "banajin dad'i ne" cewar, Safnah. Abinci 'yan matan su ka zubo, Hindatu da Amina, su ka zauna tare da cewa "Safnah ki sauko muci, kai kawai ta d'aga musu don ba su san haushi su ke bata ba idan su na mata magana. Bayan sun gama cin abinci su ka yi Sallah Safnah ta shi ta yi ta fita a d'akin kai tsaye d'akin momin ta ta nufa don baza ta manta da shi ba, murd'a wa ta yi taji a rufe, dai-dai nan kuma Baba mustapha ya zo, yace "Safnah a she har kin zo, yau Su yaya su ke cewa za su d'auko ki ashe har sun dawo", "Ehh" Safnah tace tare da gaishe shi, don tana mutukar son Baba mustapha don shi akwai son yara sosai gashi ya fi sakar musu fuska, gashi kuma shine ke tsantsan kama da Daddyn ta har muryar. "Zaki shiga d'akin ku kenan?" Baba Mustapha ya tambaye ta "Ehh, amma naji a rufe", "Ehh yana rufe ne dama, mukullin na wajen yaya Babba, ki bari gobe zan karban miki, kinje kin gaida Kaka kuwa? Nima wajen ta nazo", 'ta dawo nan ne?" Safnah ta tambaya da muryar ta da tafi kama da ta masu jin bacci, "Ehh, zo muje" cewar Baba Mutapha miƙewa su ka yi zuwa can ciki zuwa wajen kakan na su, a wani d'aki na ga sun tsaya sallama ya yi aka amsa sannan ya shiga, wata 'yar tsohuwa ce wacce a kalla zata kai shekara 87 zaune a kan sallaya da alama sallah ta idar, gaishe ta Yayi ta amsa sannan Safnah ma ta gaishe ta kaka ce tace "wannan wace ce?" "Ai 'yar wajen Abdallah ce" "oho kace Safnatu ce, zo nan Safnah mu gaisa Allah sarki auta na, ka gama wahalar ka tafi gashi se mu muke ci, Allah ya jikan ka" se kuma kuka, Baba mustapha ne yace "Don Allah ki bari kar ki ta so ciwon ki, addu'a za ki cigaba da yi mai muma munanan muna yi". Share hawayen ta yi, sannan su ka d'an yi hira sannan su ka yi Sallama, Safnah ma sallama ta yi mata duk da batasan taka-maiman inda zata kwana ba. ko ina ta shiga kuma kwanciya zata yi, d'akin su Hindatu ta wuce "sannu" kawai tace musu sannan ta hau kujera ta kwanta, Amina, wacce su ke cewa meenal ce tace "Safnah idan Bacci za kiyi ki shiga Bedroom" "to" kawai tace sannan ta nufi uwar d'akan. Masha Allah gaskiya ya had'u sosai Manya-manyan sif ne irin masu guda goman nan masu tsada ne guda, uku a d'akin ga drawer su, ga kuma wasu manyan gado guda biyu ko ba'a fad'a mata ba tasan kowa da gadon shi kenan d'aya ta za'ba tare da hawa ta kwanta, hawaye ne su ka fara bin fuskar ta don tun da ta shigo gidan nan ba abinda ya fad'o mata se Iyayen ta, sabo mutuwar su ta zaman ma ta, se juyi ta ke ta kasa bacci ga tunanin su anty da kawu da su khalil da acan ne ta tabbatar yanzu su na can suna hira, ga uwa uba tunanin Safwan ga kuma irin rabuwar da su ka yi, d'azu a makaranta kuka ta dinga yi har bacci 'barawo ya d'auke ta. A bangaren Safwan tun da Safnah ta tafi, se ya koma Class zuciyar shi a cunkushe, don ya rasa meke yi mai dad'i ma a duniyar, ko da ya shiga shima kifa kan shi ya yi a kan benci, tunani ne su cika mai zuciya har ya rasa wanda ze yi, ana tashi ya hau motar shi se gida, yana perking ya fito da sauri ya nufi d'akin shi, ya kwanta, yana kallon sama yayin da idanun shi ke rufe, Juyo wa yayi laptop d'in da ke ajiye a drawer gefen gadon shi ya jawo tare da kunna ta, shige-shigen shi yayi wajen hotuna na gani ya shiga, hotunan ya tsaya yana gani, hotuna ne da yawan gaske don sunyi d'ari uku300 ko wanne da rubutu a kai, wani hoto ne ya zo kan shi Safna ce, a makaran tasa ka riga da wando ta ɗaura after dress akai ta yafa wani gyale dariya sosai kuma take yi wanda ya fito da tsantsar kyau ta, kallon hoton ya tsaya yi, se da na ƙura ido sosai sannan na iya ganin rubutun dake jikin hoton, "MY LOVELY FOREVER" na gani an rubuta da manyan ba'ki a saman hoton rufe system d'in yayi ba tare ma da ya kashe ba, sannan ya juya ya kwanta wayar shi ya jawo number Safnah ya kira a kashe sosai ya yi mamaki kan shi ya d'aure don Safnah bata barin waya a kashe, se idan ba lafiya, ba, to me ya faru, ko ciwon kai d'in ne, nan da nan tashin hankalin shi ya sake dad'uwa, tunani fal ran shi, bacci ne ya d'auke shi batare da ya zaci zuwan shi bama. A gidan kawu kuwa tun da aka ta fi da Safnan su khalil su ka shigo gida su ka ce "momy ina anty Safnan za ta je?" "ta tafi garin su hutu", "to kukan me take yi", "ba komai kawai dai, ku je ku cire kaya ku zo ga abinci kuci", "to momi" su ka ce, sannan su ka nufi d'akin, Anty cigaba ta yi da neman layin Safnah amma ba ta gan shi ba hakan ya sa ta barshi bayan sunyi Sallah ta zu bo musu abincin su ka zauna su ka ci sannan ko wa ya zauna shiru, Afrah ne ta nufi d'akin Safnah tana fad'in "anty! anty Safnah", anty ne ta rike ta tare da d'auko key ta saka ma d'akin, tace, "Afrah na anty ta tafi anguwa" "to yaushe zata dawo?" "Ta kusa" "kince ta kawo min tsaraba ko", "Ehh", Littafan su su ka d'auko kowa ya duba wanda aka yiwa Assignment anty ta yi nu na mai. A bangaren Safwan be tashi ba se 'karfe 4:30, wanka ya yi sannan ya ya yi Sallah, shirin shi ya yi cikin baƙin wando da kuma jar riga wanda ya yi bala'in yi masa kyau sosai, jikin shi ya feshe da turare mai masifar ƙamshi, falon gidan ya fito ya zauna, tare da kunna tv, tashar kwallo ya kamo kasancewa shi mayen kwallo, Momin Mansur ce ta fito cikin wani dakakken leshi purpule and Blue, se kuma adon ba'ki ajiki, sosai ya yi mata kyau, wajen Safwan ta nufa ta na dariya, "my son har ka fito da yanzu zan aika Mansur ya taso ka naga tun da ka dawo school shiru", mamaki sosai ya kama, Safwan ganin wannan abu, Daddyn shi ya ga ya fito, murmushi ya yi sannan a zuciyar shi, yace "lallai matar nan makira ce", da sauri ya nufi gurin Daddyn shi da ke saukowa daga step rungume shi ya yi, yace "wellcome Dad shine baza ka fad'a min zuwan ka ba se de na ganka", "to ayi min Afuwa my son" "shikenan Dad" jerowa su ka yi su na tahowa falon yanda kasan Hassan da Hussaini don Safwan tsantsar kama ce tsakanin su da Dad shi, se dai Safwan ma ya fi Daddyn shi tsayi da kad'an, Zama Dad ya yi sannan Safwan ya zauna ku sa da shi, "Ya karatu" Dad ya tambaye shi "Alhamdulillah Dad", "yayi kyau to, ya kuma maganar aure" dariya Safwan ya yi yace "Dad aure kuma?" "Ehh mana, Safwan ni nafi son ka yi aure da wuri yanzu shekarun ka ashirin da bakwai fa ka kusa talatin, ya kamata ka yi aure Safwan ka cika min gida da jikokin ka", "to Dad dama ina da budurwa ma" "to masha Allah se ka fad'a min ita sannan naje nema maka auren ta" "to Dad" yace Sannan yace "Dad na tafi kwallo" tare da mi'kewa ya nufi waje, murmushi Dad ya yi yace "to adawo lafiya ka kula dai", "to Dad" Sannan ya fice ya bar su su na hira da momin Mansur. Safwan ko da ya fito tsayawa Yayi jiran wucewar Safnah, se yanzu ma ya tuna da cewa biyar ta wuce, don Safnah ba ta latti, hakan yasa ya wuce filin kwallon kasancewar a hanyar makarantar su ta ke yana yi amma hankalin shi na kan bakin hanya ko ze ganta amma shiru har su ka tashi, lokacin kuma yaga 'yan makarantar an tashe su tsayawa ya yi har su ka wuce amma be ganta ba, ko su Khalil be gani ba gida ya nufo zuciyar shi cike da tunani, kala-kala lokacin an fara kiran Sallar magrib d'akin shi ya wuce da sauri ya d'auko wayar shi ya sake kira amma har yanzu Layin Safnah a kashe sosai hankalin shi ya tashi, to ko ciwon kan ne wata zuciyar ta fad'a mai, abun da be sani ba Safnah ta sauka a katsina a wannan lokacin. Masallacin ƙofar gidan su ya nufa domin yin Sallah Bayan yayi Sallah zama ya yi har se da akayi isha'i sannan ya dawo gidan afalo ya zauna kasantuwar yunwa da yake ji sosai hakan ya sa ya shiga kicin, mai akin su ya gani ya tambaye ta abincin don Safwan ba ya wasa da cikin shi, tace mai ai ta gama ta aje kan dining, dining d'in ya nufa, abincin ya gani kala-kala wanda ze ci ya d'iba ya nufi d'akin shi da shi, ko da ya isa d'akin ajiye abincin yayi Saman gado sannan ya zauna ya fara ci, wayar shi na hannun shi numbar Safnah ya sake kira, har yanzu a kashe, Bayan ya gama cin abincin ne ya koma ya kwanta, to me yake damun Safnah ya zama dole gobe ya je gidan su, ga kuma abun da Dad shi yace, magana ce yake yi a zuciyar shi, "kai lokaci ya yi da zan bayyana wa Safnah sirrin zuciya ta duk da nasan itama tana so na amma ba irin matan da su ke cewa su na so na bace ita baza ta ta'ba fad'a ba, domin Safnah daban take cikin mata, ga kuma wannan fitinanniyar Salma", tunani ya dinga yi har wajen 'karfe biyu sannan bacci ya d'auke shi. Bara mu waiwayi mutan katsina Safnah ko da gari ya waye da ciwon kai ta tashi mai tsananin gaske Sallah ta yi kawai ta kwanta, har wajen 9:00 tana kwance su Hindatu ne su ka zo su ka tashe ta wai Baba babba na kira, mi'kewa ta yi ta fito falon ta gaishe shi Sannan yace "kin ƙarya ne?" "a'a" "to kije dining ga abun karin ki can" "to" kawai tace "sannan idan kin karya kije ki gaishe da mutanen gida don yanzu gidan akwai wasu" "to" tace sannan ta nufi dining d'in su Hindatu ma binta su ka yi, don suma ba su karya ba tana ganin su seda suka cika filet sosai da abinci kuma kada'n su ka rage sun sha ruwan tea da chips na Dankalin turawa kuma, ita ko Safnah tea d'in kawai ta sha sannan ta zuba Dankali d'an kad'an shima bata cinye ba, sannan su ka mi'ke su ka nufi cikin gidan, Hindatu ne tace "Safnah kin ga tsarin gidan ya canza ko, da ku kad'ai ne aciki, amma yanzu an kara part biyu ma wannan da kike gani ta nuna wanda su ka fito, shine akwai d'akin ku na da, to se d'akin mu se kuma d'akin kaka se d'akin ya Abdul d'an Baba Babba ne kuma shi d'in soja ne, sauran d'akin ma ba kowa a ciki, se wancen part d'in ta nuna mata wani part da suke nufa shine na Baba Bashir, d'aya kuma na Baba mudansir, na hannun daman su ka fara shiga wanda shine, na Baba Bashir, irin part d'in su ne dai, se de kayan ciki da ya bambam ta da na su, Shiga falon su ka yi da Sallamar su su ka gaishe da matar Baban na su Hajara wanda su ke ce mata, momin Teemah, kasancewar ta na da yara bakwai Teemah itace ta shida tana da yaya ana kiran shi, marwan, se ƙannen su, Fatima wanda su ke cewa Teemah ita sa'ar su Hindatu ce kuma 'kawar su. "Momi Teemah na nan" cewar, Meenal "Ehh wannan wacece?", "Safnah ce" cewar Hindatu, "Allah sarki Safnah ce ta yi girma haka sosai, ko da ga ku ma ai duk sa'anni ne gara da akace ku fito da miji kuyi aure ma", "kai momi kina goyon bayan su kenan", "Ehh mana", "shikenan", d'akin Teemah su ka nufa, da sauri ta na falon d'akin ta zaune ta na karatun wani littafi, TRUE LOVE su ka shigo da sallamar su, Teemah aje littafin ta yi tana murmushi tace "'yan raini wayo na zaci yau ma baza ku zo bane, ni sedai na dinga zuwa part d'in ku amma ni kun kyale ni baza ku zo ba shiyasa jiya na 'ki zuwa", "ai nace ki dawo part d'in mu kin 'ki", "lallai!, ai wallahi ba ku isa ba, kar ma ku bari Daddy ya ji ma wallahi", "to shikenan" "Bakuwa muka yi ne?", "Safnah ce fa ba ki gane ta ba?", "oyoyo sis, zo ki zauna", hannun Safnah Teemah ta ja ta zauna kasancewar tun da su ka shigo ta na tsaye ne, Safnah kece ki ka yi haka ji ki kin zama wata 'katuwa kin yi kiba, murmushi kawai Safnah ta yi, "Ke ya maganar Baba Babba yace fa ku fito da mazaje a satin nan ba?" cewar Teemah, "aini nawa na nan khalid ke ma kin sani" cewar Hindatu, Meenal kuma cewa ta yi, "nima dai jira na ke yi, ina da nawa", "Lallai yaran nan, ni dai karatu zan yi" cewar Teemah "sannu biro da takarda", cewar Hindatu, ita Safnah jin su kawai ta ke yi. "Safnah ana ta hira ko kin manta mu? ne?" murmushi Safnah ta yi, don duk ba wanda ta manta duk sa'annin ta ne, su na wasa kafin ta tafi, "ta so ki raka mu Part d'in Baba mudan", "to muje" cewar Teemah ta shi su ka yi su ka fito momi lokacin ma bata falo, d'ayan part d'in su ka shiga, shima dai duk irin d'aya ne se kayan ciki, shi kuma yana da yara, tara, Babban d'an shi shine, Ummar, wanda yana, India ya na karatu se kuma, mujahid, se Kamal, se kuma, Sa'adatu, wanda su ke sa'a da su Teemah se ƙannen ta, da Sallama su ka shiga falon, sa'adatu da mujahid su ka tarar a falon, Teemah ce tace "ya mujahid yau ba'a fita ba kenan?" "Ehh zan yi ba'ko ne" "ok ya yi kyau, Sannu 'yar rainin wayo wato ki na nan ko ki zo ki gaishe da mu ko", "ni kuna bani mamaki kuna so a zo muku amma baza ku zo ba, to kowa ya zauna a nashi wajen" cewar Teemah, "Umma bata nan ne?" "tana d'akin ta", "to bara mu gaishe ta" cewar Meenal, d'akin maman sa'adatu su ka nufa wanda su ke cewa Umma, gaishe ta su ka yi su ka fito, ko da su ka fito falon ba sa'adatu, se ya Mujahid da wani, Teemah ce ta 'karasa tace "a'a boss kai ne a gidan namu?", wanda aka kira da boss ya d'ago yana murmushi, Safnah jin an kira boss yasa da sauri ta d'ago don sunan da ake kiran Safwan kenan 'yan makarantar su, idon su ne ya had'u da Boss, d'in ta yi saurin kawar ta kan ta don wani kallo ta ga yana mata, Hindatu ne tace "dama 'kanana na ganin ku?", "to ba gani na zo ba", ya yi kyau ai cewar Meenal sannan yace "kun yi bakuwa kenan?" "A'a 'yar Baban mu marigayi ne" "Allah sarki dama tana ina ne?" "tana Kaduna ne", "yayi kyau", d'akin sa'adatu, su ka nu fa don sun san can ta nufa, aiko nan su ka sameta su ka zauna suna ta hirar su Safnah dai se dai ta yi musu murmushi, Har wajen sha biyu 12:00 na rana su Meenal na part d'in su sa'adatu, Safnah ko bacci ma ta ke yi, don bata saba da irin hirar nan ba kasancewar bata da wa su kawaye, kawar ta d'aya maryan ita ma ba me surutu ba ne, se kuma Safwan kusan ma shine abokin hirar ta, se kuma anty da yaran ta, se da su ka tashi Safnah kafin su ka nufi part d'in su, a hanya su ka ga, Baba Salihu wanda su ke cewa Baba Babba gaishe shi su ka yi, yace "anjima ku shirya ku kai Safnah gidan 'yan uwa, don su gaisa" "to Baba" cewar Meenal, sannan ya wuce, d'akin su su ka nufa don su yi wanka su shirya, Meenal ne ta fara shiga bayin yayin da, Hindatu ta ke d'auko musu kaya, Kujera Safnah ta samu ta kwanta, jakar ta 'yar 'karama da ta zo da shi ta d'auko, ta bud'e wayar ta ta ciro, bud'e wayar ta yi ba layi se memory, kunna wayar ta yi ta ga taci screen sosai don ko fuska ba'a gani, kamar ta kurma ihu, ga layin ta ba'a gani ba, memory ta ajiye a cikin aljihun jakar ta, sannan ta mayar inda ta ajiye, wayan kuma ta aje da niyar zata kai gyara. Karfe, 2:00 su ka fito cikin shirun su sun yi masifar kyau du ka kasancewar su jinin Fulani, Hindatu da Meenal kyawawa ne sosai, amma Teemah ta fi su kyau kuma ta fi su haske ma sosai gashi suna masifar kama da Safnah se dai tafi Safnah haske ne, sa'adatu ma, fara ce amma ba sosai ba ita ma ta na da kyau, sosai kai tsaye d'akin kaka su ka shiga tun da dama a wajen ta su ke ita Hindatu ta kasance 'yar Baba Aminu ce, se kuma Meenal 'yar Inna Aisha, mahaifin ta ya rasu, se ta 'kara aure shi ne ta bar ta a gidan su. 'Dakin kaka su ka shiga tana zaune a kujera, Meenal ce ta karasa da sauri, ta zauna ku sa da ita ta dafa kafad'an ta tare da cewa "tsohuwa mai ran 'karfe kina hutawa ne?" dariya kaka ta yi tace "Ehh se ina haka, naga kun d'au wanka?" "Wallahi yau ziyara ce ta tashi", "ai gara ku dinga ziyara sosai", "to 'yar tsohuwa za'a dinga" cewar Hindatu, Safnah gaishe ta ta yi, ta amsa da fara'ar ta, tace "ki zo ki zauna mana!", "A'a kaka barta sauri mu ke yi wucewa zamu yi muka ce se mun ga kaka don yau bamu had'u, ba" "to sannun ku, waye ze kai ku ziyarar?" "ya mujahid ne don shi ne a gidan", "to ku gaishe da su", "to kaka" cewar, Meenal, sannan su ka fita dining table su ka nufa don har an jere musu abinci kasancewar akwai me musu aiki, wataran kuma su su ke abun su, don komai sun iya, abincin su ka ci sosai Safnah dai bata wani ci ba, ita kan ta ta na mamakin kan ta kamar ba gidan su ba ta ka sa sake wa, amma ita har ga Allah ta fi son gidan Kawun ta, waya Hindatu ta ciro tace "bara na kira Teemah na ji tace zata je", "to" cewar Hindatu, Safnah ce tace, "Hindatu ina wayar ki ki ara min?" "ki je d'aki tana kan kujera na bar ta" ta shi ta yi ta nufi d'akin don dama ta koshi wayar ta d'auka, ba security, Safwan ta ke son kira, amma kuma ta manta number kasancewar sabon la yi ya yi d'ayan kuma ta kira a kashe, sosai ta shiga tashin hankali kuma tana ji ajikin ta yau idan bata ji muryar Safwan ba akwai matsala number anty ta had'a ta kira tana ta ringing bata d'auka ba, dama ta sani don bata d'aga bakuwar number, wani katutun ba'kin ciki ne ya tokare mata zuciya wanda idan bata yi kuka ba ma ba ze daina ba, wa su zafafan hawaye ne su ka wanke mata fuska, ta rasa mafita yanzu ya zata yi ne, muryar su Meenal ta ji za su shigo d'akin da sauri ta share hawayen ta, Mi'ka ma Hindatu wayar ta, gyale su ka d'auko su ka sa ka Meenal ne ta ce "Safnah Hijab za ki saka ko gyale?", "Hijab" tace musu, don ita ba ma'abociyar sa ka gyale bace "to ki za'bo wanda zaki sa ka", wajen kayan nasu ta nufa, d'aya sif d'in na kayan meenal ne shi ta sa ma don meenal ma tana da jiki kamar Safnah, se d'ayan na Hindatu, d'ayan kuma gyalulluka ne, da Hijab, kayan kwalliya da dai sauran su don 'yan matan Familyn su ba dai wanka ba shi yasa Baba babba ma ya sa mu su ido, da ya hana su ma saka gyale ko yanzu ma wataran se yace su cire, Sallamar Teemah su ka ji itama ta shirya tsaf Wani hijab sky blue, Safnah ta d'auko, ya yi mata kyau sosai, "ke wai Hijab za ki saka dama haba dai, kin gan mu fa duk gyale muka saka a'a dai ki cire ki saka gyalen ki" cewar Teemah, tare da bud'e sif d'in wani gyale ta za'bo mata mai masifar kyau, tace "don Allah ki saka shi", Safnah bata so ba haka nan ta kar'ba tare da cire hijab d'in, ta sa gyalen "ku yi sauri ya mujahid na jiran mu, ai se da naje part d'in su na ta so shi tsabar takura wai ace mutum baze yi draving ba se dai a kai shi wallahi haushi abun ke bani ga motoci kuma agida", fita su kayi su ka shiga motar, "ya mujahid boss ya tafi kenan?" cewar, Hindatu, "Ehh tun d'azu ma ya tafi", "yayi kyau" cewar Teemah, gidan Baba Aminu su ka fara zuwa, gidan su Hindatu kenan, Gida ne Babba shi ma mai kyau sosai, Ya na da yara bakwai shi ma, Saddiq shine Babba wanda su ke cewa yaya sadiq shima yana India tare da ya Abdul, se shamsudden, se Majid, se Hindatu, se kanwarta, Fatima, se Rahama, se Hauwa'u ita ce ƙarama a falo su ka tarar da momin Hindatu da ka ga Hindatu ka ga Momin ta don su na bala'in kama da gudu Hindatu taje ta rungumeta, tana cewa "momi na nayi miss d'in ki", "d'aga ni kar ki karya ni" cewar momin, Majid da ke falon dariya ya yi yace, "idan an girma dai asan an girma" "to in ruwanka" cewar Hindatu ta na 'kara ri'ke momin na ta, su Teemah gaishe da momin su ka yi ta amsa cikin fara'a, tace "a ina ku ka samo wannan?", ta na nu na Safnah, "momin 'yar Baba 'karami mai rasuwa ne" "oh! naga kama kuwa wallahi gata nan kamar Shamsiyya", murmushi Safnah ta yi, waje suka samu su ka zauna, sun d'an taba hira sosai musamman Hindatu da 'kannen ta da idan su ka had'u ba su son rabuwa kamar ta dawo gida ta ke ji wataran, amma idan ta dawo zata bar, Meenal ita kad'ai ne. Gidaje da yawa su ka je kuma duka gidajen 'yan uwawa ne, Safnah har se da ta yi mamakin yawan 'yan uwan na su, har se magrib su ka dawo gida a haka ma ba su gama ba se gobe za su sake zuwa, sosai ta ga soyayya awajen 'yan uwan na su, wa su kuma ta ga tsantsar kiyayya, don dama ko a 'yan uwa akwai wanda ba ku cika yi da shi ba. A màtukar gajiye Safnah ta dawo don bata saba irin wannan tafiya ba iyakan ta school se inda ba'a rasa ba se kuma idan ta je garin su kaka, wanka su ka shiga su ka yi su ka fito cikin riga da wando ban da Safnah da ta saka wasu doguwar riga acikin kayan Hindatu. Falo su ka fito bayan sun shirya, dining su ka nu fa su ka cika cikin su,kafin su ka zauna zaman hira, Safnah ne ta 'kara kar'bar wayan Hindatu, anty ta sa ke kira, kira d'aya aka d'auka, " Hello, ta ji ance, muryar khalil ne kuma, tsalle ta da ka ta fita d'akin da gudu tare da cewa, "Khalil Safnah ne" shima ihu ya yi daga can bangaren yace "Halima! Fatima! Ku zo ga anty Safnah", da gudu su ka nufo shi, Safnah ne tace, "Khalil ina anty?" "Bata nan ta je wani waje ne tabar wayan" "to ya kuke ya school?" "lafiya lau Anty mallam Usman na ta tambayar ki", "ka gaishe shi, kace mai ina katsina, Khalil Safwan fa", "Anty yana nan amma tun da ki ka tafi ban gan shi ba" "to kace ina gaishe shi, ka yi Save sannan idan Anty ta zo kace ta kira ni ka ji" "to Anty yaushe za ki dawo?" "Bazan dad'e ba da yardar Allah", "to Allah ya yarda", "Ameen Khalil, seanjima" tace tare da yan ke wayar wani 'bari na zuciyar ta na jin farin ciki, najin muyar 'yan kannen ta da ta yi, wani 'bari kuma na cikin ba'kin ciki na jin tun tafiyar ta Safwan be neme ta ba, falon ta dawo ta bawa Hindatu wayar ta tare da ce mata "na yi Save wani number da Anty na, idan an kira se ki min magana", "to" cewar Hindatu, tana ajiye wayar kira ta shigo, da sauri ta d'auka don daga jin ringing d'in ta ga ne, "yaya Abdul ta fad'a da ƙarfi tare da cewa yakake ya aiki kuma", "aiki ba dad'i" cewar shi, tace "wani irin ba dad'i ya Abdul se kace ba Namiji ba, ko kai ma zaka gudu ne?" dariya yayi yace "wani irin guduwa 'kanwata ai muna nan har 'karshen rayuwa", "to Allah ya baku Nasara", "Ameen 'kanwata", Meenal da tun da ta ji an ambaci ya Abdul ta aje wayar da take chart ta nufo wajen Hindatu, Hindatu ta na cikin waya ta ji an kwace ta na juyowa ta ga Meenal ta ruga da gudu cikin gida, tana fad'in "ya Abdul abun na fifiko ne ni baza ka kira ni ba se Hindatu?", "ki yi hakuri ba haka ba ne na fi samun number Hindatu kinsan inda muke wataran ba service" "to na ji yaushe za ka dawo gida?", "Bazan fad'a muku ba zan mu ku surprises ne amma na kusa" "don Allah ka fad'a mana", "naƙi" cewar shi Hindatu ne ta sake kar'bar wayan tace "ya Abdul tsarabar mu fa kar ka manta", "to bazan manta ba insha Allah" "yawwa" cewar meenal ita ma ta na jaddada mai tsarabar su, Hira su ka yi sosai don sabo ne sosai tsakanin su da Yayan na su, duk da Soja amma be cika d'aure mu su fuska ba sosai, amma kuma akwai tsanani akwai horo idsn su ka yi lefi don manta wa yake da su ne ma. Zaria Washe gari Safwan ya tashi yayi wanka kamar yadda ya saba ya yi shirin school ya fito ya gaishe da Dad shi sannan ya nufi motar da ze tafi da ita ya shiga tare da kunnawa yayi waje, ya so ya fara zuwa gidan su Safnah amma se wata zuciyar ke fad'a masa za su had'u a school, hakan ya sa ya wuce kawai makaran ta, ko da ya isa jama'ar sa na nan zaune su na jiran zuwan sa kafin shiga Class za ma ya yi cikin su su ka gaisa, yace "Safnah fa bata zo ba?" "Ehh bata zo ba" cewar Kamal, sosai hankalin shi ya tashi don yasan indai Safnah ta wuce tara9:00 bata zo ba to baza ta zo bane don bate late gashi tara ta gota. ta shi ya yi bayan ya zube musu kud'i ya nufi can wata kujera da su ke zama, Salmah ya hango ta nufo wajen tsaki yaja a fili sannan yace "wannan kuma fa?", 'karasowa ta yi tare da gaishe shi sannan ta zauna, "Safwan jiya kace min za ka zo gidan mu har na fad'a wa momi na amma kuma ka 'ki zuwa gashi na kira baka d'auka ba" "banajin dad'i ne" ya bata amsa a takaice "Allah ya ba ka lafiya amma idan ka ji sau'ki zaka zo ko?" "Nace miki ban ji sau'ki ba ne, ai idan ban ji sau'ki ba baza ki ganni ba, ina ne anguwar ta ku?", Ta ji haushin tambayar don tun ba yau ba ta ke fad'a mai amma ya manta, "Jushi" tace mai ba tare da ta sake kallon shi ba, "ok anjima zan zo", "dagaske?", "Ehh mana", "amma naji dad'i sosai", tashi su ka yi su ka nufi Class don sun hango Lecturer zai shiga. ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*15&16 Ko da aka tashi school Safwan gidan su Safnah ya fara zuwa don ganin lafiya?, Anty ya samu ta shaida mishi ta tafi Katsina, baza ta dawo ba kad'an ya rage ya fad'i da jin wannan lamari ta shaida mai kuma wayar ta ta fashe, amma bata fad'a mai ta kira ba don Khalil be fad'a mata ba, da'kyar ya iya komawa gida. Bayan sallar la'asar ya yi wanka ya shirya don zaman gidan ma ya ishe shi motar shi ya hau ya nufi Jushi se da ya isa kafin ya kira Salmah akaro na farko da ya ta'ba kiran ta, ta yi mai kwatance. Kafin ya iso ta yi wankan ta ta yi kwalliya sosai ta had'u don Salma ba mummuna ba ce, d'akin momin ta ta nufa da murna tace "momi yana hanya", "to Allah ya kawo shi lafiya, amna Salmah son da kike yi wa yaron nan na sha fad'a miki ki rage don be miki rabin shi amma bakijin magana", "momi kar ki 'bata min rai don Allah ki barni kawai", horn su ka jiyo a bakin kofa Salmah ta zaci shine se da ta le'ka ta window ta ga Daddyn ta ne, shigowa ya yi yace "'yar Baba irin wannan wanka haka ina zuwa?" murmushi ta yi tare da sunkuyar da kai momi ne tace "za ta yi ba'ko ne" "kai! Mamana ki ce suruki na ne zai zo", Dariya Sàlmah ta yi sannan ta nufi d'akin ta, Horn su ka 'kara ji wanda Salmah ta san shine don ta ga kiran shi, da sauri ta fita don taro shi. 'Dakin ba'ki aka kai shi, Safwan se kallon gidan yake ya had'u sosai se dai su zo kai d'aya ma da nasu wajen had'uwa, zama yayi ta jere mai abinci kala-kala da drinks, bud'e d'aya ya yi ya d'auki cokali ya d'iba yakai bakin shi, kallon Salmah ya yi yace "waye ya yi girkin nan?" "Ma su aiki ne" "What! Ke miye àmfanin ki baza ki girka min ba se ma su aiki to bazan ci ba kuma yunwa naje ji", jawo lemon yayi ya bud'e ya fara sha tare da snak, don Safwan ba ya wa sa da cikin shi, ita kuwa ta na zaune ta na kallon shi, har ya gama yace "to ga ni na zo gidan ku ko?", "Ehh nagode sosai, mu je ka gaida momi na to", "ok". Fitowa su ka yi har falon momi na Zaune akan kujera ya durkusa ya gaishe ta momi ne tace "ya hanya?" "Alhamdulillah!" "Madallah!", dai-dai nan kuma Daddyn ta ya fito 'karasowa ya yi yana murmushi yace "mamana ke da surukin nawa ne?", Safwan tun kan ya d'ago ya gane mai muryar nan tabbas kuma ya na d'agowa ya tabbatar shine, "Sannu Daddy ina wuni?", "lafiya lau" cewar Dad ya na zama tare da cewa "Muhammad dama kai ne?", Murmushi Safwan ya yi yace "Ehh Daddy ni ne" "gaskiya wannan abu ya yi min ya Daddyn ka shi ma ya dawo hutu ko?" "Ehh yana nan" "to ka gaishe shi kafin muyi waya" "to ze ji" cewar Safwan yana mi'kewa ya mu su sallama tare da fita Salmah ma mi'kewa ta yi ta bishi har wajen motar shi Sallama su ka yi ta koma cikin gidan. Zama ta zo ta yi kusa da Dad tace "Dad dama kasan Safwan ne?" "Sosai ma kuwa Baban shi abokina ne kuma abokin kasuwanci na ne", dad'i sosai Salmah ta ji momi murmushi ta yi tace "ya aka yi ko bansan shi ba?" "kuma tun muna wancan gidan yana zuwa wataran da Dad shi amma be kai haka ba, yanzu zan samu Daddyn shi mu tsaida magana", "to Allah ya tabbatar da alkhairi" momi tace ta na barin falon ya yin da Salmah ta rungume Daddyn ta "ina son ka Dad", "ba ki da kunya ko mamana?" ta shi ta yi ta shiga d'akin ta da gudu. Safwan ko abun ya bashi mamaki ashe Salmah 'yar aminin Daddyn shi ne, ai ko abun nan ba ze bari Dad shi ya ji ba ko kad'an, haka ya yi ta tunani har ya dawo gida agajiye sosai, ya so kuma ya biya gidan su Safnah a ba shi adireshi don yana son zuwa Katsina ne don ba ze iya jiran dawowar Safnah ba, lokacin da ya isa gida ana kiran sallar magrib ne hakan ya sa yana yin perking ya fito ya nufi masallaci, acan ma ya samu Dad shi, har se da akayi isha'i sannan su ka dawo gida, abinci su ka ci sannan Safwan ya wuce d'akin shi ya cigaba da tunani, Kiran Kamal ya gani, ya shigo wayar shi d'au ka yayi yace "Hello Kamal", dagacan Kamal yace "boss ya kake?" "Lafiya lau" "kwana biyu ba na ganin ka a club me yasa?" "kai dai bari kawai!, ina cikin matsanancin damuwa!" "me ya faru?" "Ba abun da ma be faru ba!, kasan Besty na ta bar garin nan kuma baza ta dawo ba?", "ina ta je?" cewar Kamal ko ajikin shi dad'i ma ya ji don ya na da sanin Safnah ke hana Safwan zuwa club da sauran su, "Katsina ta je" "to miye na damuwa ba ga Salmah ba yarinyar nan ta na son ka sosai amma Safnah kai ka ke son ta" "waye ya gaya maka Safnah bata so na? "Se an fad'a, da ta na son ka ai zata fad'a maka, ka ganni nan bazan auri wacce nake so bata so na ba se dai na auri wacce ta ke so na sosai wallahi za ka ji dad'i", "Dalla mallam kauce!, da irin wannan tunani na ku da na bi ya sa gashi ina shirin rasa Safnah, don haka ko yau da zanga Safnah zan furta mata ina son ta", Dariya Kamal ya yi yace "lallai boss ka shiga hannu!" "Bana son iskancin banza!, me ye ma na kira na ne to?", "Babu!, na kira na gaishe ka ne", "to nagode" sannan su ka yi sallama, kwanciya ya yi amma sam baccin ya 'ki zuwa, tunani ya dinga yi har bacci ya yi gaba da shi. Anty ne zaune da yaran ta da Daddyn su ana cin abinci ana hira, Afrah ne tace "momi yaushe Anty Safnah za ta dawo?" Kallon Dad su ta yi kafin tace "ki tambayi Dad ku", "Dad yaushe za ta dawo?" "Bazata dawo ba ta tafi garin su, amma idan ku na karatu sosai zan kai ku wajen ta", tsalle su ka yi su na murna sosai, Khalid ne yace "momi ranar da ki ka tafi anguwa ki ka bar wayan ki anty Safnah ta kira na yi miki save d'in number ma", "Dagaske?" Cewar anty ta na d'auko wayar ta Daddyn su ne ya 'kar'bi wayar yace "dare ya yi baza ki kira ta ba", "Dad khalid jiya Safwan yazo wai na ba shi adireshin ta a katsina, ko number ta" "kar ki sa ke ki bashi, kinsan halin Safwan ze je, kuma kinsan irin gidan su don haka kibar shi kawai tun da mutunci su ke yi, shikenan tunda ta tafi abar shi haka", "to ai dama bansan ma gidan ba", cewar Anty, kawu ya 'kara da cewa "ko number kar ki bashi nasan ma ba number ta ba ne", "to" Anty tace sannan su ka cigaba da Hirar su ci ke da kewar Safnah. Safwan bacci ya sha sosai don be yi bacci ba se wajen 'karfe uku3, hakan yasa shi makara gashi yau za su fara exam cikin sauri-sauri ya shirya ya nufi makarantar ko karatun Jarabawar be samu sukunin yi ba, shi da ba ya wasa da karatu. Lolacin da ya isa har sun fara jarabawar, da sauri ya yi perking ya fito, lecturer ne yace "Safwan ya aka yi ka yi late?" "wallahi na makara ne!" "to shiga" cewar malamin, jarabawa ta d'auki zafi se fafatawa ake yi yayin da Safwan ya ji saukin ta sosai don shi ya fara gamawa, duk da sun riga shi farawa. KATSINA Yau satin Safnah d'aya a Katsina ya yin da ji take kamar a 'kaya ta ke, gashi yau ta tashi cikin ba'kin ciki sosai don tasan su na can su na jarabawa amma banda ita ta kira number maryam ba ta shiga ta kira Anty shi ma haka, na Safwan kuma bata sani ba, hakan ya sa abun ya mata yawa ta na zaune ita kad'ai a falo don su meenal sun je bikin wata 'kawar su tun 'karfe 10:00 majid ya zo ya kai su don aminiyar su ce sosai su ne manyan 'kawaye, Safnah tace bazata ba don bata son yawo sosai, wanka ta yi ta shirya cikin wata doguwar riga yayi bala'in mata kyau, wani hula ta sa ka mai kama da na sanyi amma mai kyau ne sosai, duk cikin kayan Meenal ne, zama ta yi a falo se tunane- tunane ta ke yi mi'kewa ta yi ta nufi gerden d'in gidan don ta gaji da zama a wajen gashi idan ta je d'akin kaka surutu za ta yi ta sata, yana ta baya ne garden d'in ta 'barayin part d'in su Teemah, tafiya take yi a wajen ba kowa kuma ba motsin komai se kukan tsuntsaye, swimming pool ta hanga a zuciyar ta tace da ta iya da ta shiga, wajen da aka kewaye da shuke+2 ta shiga ayaba ta ciro da mangoro ta zo ta samu wani waje ta zauna ayaban ta 'bare ta gutsira ta fara taunawa, ya nuna sosai ya yi za'ki, ajiye wa ta yi a gefe, tunani ta koma yi duk akan karatun ta ga kuma Safwan da take masifar tunanin sa tasan yana nan da Salmah ya manta da ita wasu zafafan hawaye ne su ka zubo mata, kuka ta fara yi don Safnah ba ta raina abun kuka bare kuma abun ya samu, kuka ta ke a hankali sautin kukan ta ke fita yayin da hawaye ke bin fuskar ta. Cak! ta tsaya da kukan ta jin kamar tsayuwar mutum a bayan ta, tsorata ta yi don tasan ba kowa a gidan se kaka kuma kaka tasan bazata fito ba, a hankali ta fara juyowa, kafar mutum ta gani sanye cikin Kwanbos sama take yi da kanta a hankali takalmin ya kusa gwiwar shi mi'kewa tsaye ta yi zunbur ganin kayan soja, ido biyu su ka yi da shi, dogo ne sosai kuma kyakykyawan saurayi kaman shuwa, shima kallon ta ya yi azuciyar shi ya furta "tabarakallahu ahsanal khali'kin", jikin Safnah ne ya fara rawa don ta na bala'in tsoron soja a rayuwar ta da sauri ta yi hanya za ta gudu cikin zafin nama ya ri'ko hannun ta, kallon shi ta yi tace "don Allah ka yi hakuri" hankicif ya ciro a aljihun shi ya mi'ka mata, tare da cewa "ki goge hawayen fuskar ki" hannunta na rawa ta 'kar'ba ta goge, "me ya same ki? kika zo nan kina kukà tun d'azu nake wajen ina jinki", Safnah rasa mai zata yi tayi se gir-girza kai take yi, ya fahimci tsoron shi take hakan yasa ya sake ta tare da cewa "ke ce Safnah?" d'aga mai kai ta yi, yace "ina su Hindatu?", "sunje biki" ta fad'a "waye ya kai su?" ya sake jefo mata tambayar, "ya majid ne", "to ke me ki ke yi anan ko kukan ne ki ka zo nan yi", "a'a" "to muje" ya fad'a tare da nuna mata hanyan part d'in su, tafiya take yana binta a baya, hànyar d'akin su ta nufa, "ke!" taji yace tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba don tsoron shi take ji, "d'akin kaka" kawai yace mata juyawa ta yi ta nufi d'akin da sauri ta shiga tare da sallama kaka da ke zaune ta amsa tare da cewa "Safnah baki je bikin ba?" "Ehh kaka ba najin dad'i ne" "to Allah ya kawo sau'ki" "Ameen" Safnah tace, shigowa yayi da sallama murmushi yayi tare da cewa "'yar tsohuwa mun same ku lafiya", "lafiya lau mai gida saukan yaushe?", "yau d'in nan ko gida banje ba nayo nan" "to ka kyauta 'kannen naka sun tafi biki se wannan" murmushi ya yi yace "wannan da bata sanni ba, can naganta a gerden", "ikon Allah Safnah baki san Abduljabbar d'in ba?" d'aga kai ta yi alamar Ehh, "ba ki ji su Hindatu na maganar shi ba, shima anan part d'in yake" "Ni yaya Abdul kawai na sa ni su na magana", "gidan ku!, wannan ba shi ne Abdul d'in ba", cewar kaka sunkuyar da kai ta yi tsabar kunya, don tabbas sun mata bayanin Ya Abdul kuma sun ce mata soja ne, amma kaka ne da tace mata Abduljabbar bata gane ba Shiyasa. "Baban ka ya matsa se ta dawo don bata san 'yan uwa ba, wa su ba su san ta ba, amma tun da ta dawo ai zata san su ahankali" murmushi Ya Abdul ya yi sannan yace "kaka bara naje na yi wanka na huta na gaji sosai", "ai da gajiya d'an nan dole ka gaji" murmushi ya yi sannan ya fita, tare da ce wa Safnah "zo muje" tasowa ta yi ta biyo shi, "je kicin ki zibo min abinci", "to" tace sannan ta bi hanyar kicin ɗin, tunda ta zo gidan bata ta'ba zuwa ba se yau, yana da girma sosai ga kaya cike a ciki har da wasu d'akuna aciki duba inda tasan ana aje abincin ta yi amma bata ga komai ba, fitowa ta yi ta tarar da shi zaune a kan kujerar falo, "Ba abinci" tace mai, "to ke baki iya abincin ba ne?", "na iya" "to kije ki min zanyi wanka na dawo" "to" tace sannan ta nufi kicin d'in, ta rasa mai zata dafa mai gashi bata ga komai ba, bud'e d'aya daga cikin d'akunan ta yi, kayan abinci ta gani sosai tun daga kan buhunan shinkafa, kwalayen taliya, na macaroni, na cus-cus da su semonvita, kaya ne sosai komai akwai shi, rufe wa tayi ta bud'e d'ayan d'akin shi kuma Dankali da su doya da kires na kwai, da su kwalayen maggi ne har ta gaji da irgawa, doya ta d'auko, tare da d'ibo kayan miya, da komai da zata bu'kata ta fito fridje d'in da ke kicin d'in ta bud'e kifi da nama ne aciki se su tomatos da peppe da sauran su, doya ta dafa mai da miya yaji nama sosai sannan ta had'a mai juice na karas, dining ta zo ta jere mai sannan ta juya zata nufi d'akin su, "Safnah!" taji ya kwala mata kira juyowa ta yi ya fito daga d'akin sanye cikin wa su 'kananan kayan jar riga ne da ba'kin wando, wandon ba dogo ba ne amma ya wuce gwiwar shi hakan ya bata damar ganin gashin 'kafar shi, ba'ki sid'if, sosai ya kwanta luf a farar fatar kafar shi, "kin gama?" taji muryar shi yana fad'i d'aga mai kai ta yi, "ke wai baki magana ne kike d'aga kai kamar 'kadangaruwa", dariya maganar ta bata dariya ne ya su'buce mata, wanda tundà ta zo gidan bata yi ba kallon ta ya tsaya yi yadda dariya ke bala'in mata kyau sosai ga dimful d'inta ya lotsa, "d'azu kukan me ki ke yi?" kallon shi ta yi, tace "kai na ke ciwo", "to se baza ki fad'a ba ki ke yi ma mutane kuka", shiru ta yi dining d'in ya nufa tare da bud'e kulan da ta saka doya, sannan ya bud'e na miyar, 'kamshi ne ya bugi hancin shi zama yayi ya ja filet d'in ya zuba tare da saka miyar ya fara ci dad'i sosai girkin ya yi mai 'karawa ya yi bayan ya cinye, kad'an ya rage. Safnah tunda ya nufi dining ita kuma ta yi d'akin su don bacci take ji agogo ta duba ta ga kusan 'karfe2:30, Sallah ta fara yi sannan ta yi wanka, sif d'in Meenal ta bud'e ta d'akko wani riga da siket, ta saka sannan ta fito bata ga Abdul ba dad'i ta ji sosai don shima ta lura akwai surutu sosai, dining ta nufa kulolin ta bud'e ta ga saura kad'an dauka ta yi ta mayar kicin ta tattara wajen sannan ta dawo ta zauna, kallo ta saka don rage lokacin don kewa ya ishe ta ga ba wayan ta. ZARIA Safwan yana gama jarabawa ya fito ya samu waje ya zauna, Salmah ya hango ta nufo inda yake kallon ta yake yi har ta iso, sallama ta yi ya amsa sannan tace "zan iya zama?", "Ehh" kawai yace mata waje ta samu ta zauna "Ya gajiyan jiya" shiru yayi mata, ta 'kara cewa "momi tace na gaishe ka da gajiya" "to, dama Wannan ne Daddyn ki?" "Ehh, ya fad'a min Daddy abokin shi ne" hira ta dinga jan shi da shi idan ta yi sa'a yace mata Ehh, ko a'a, har su ka gama jarabawa aka tashe su, Motar shi ya shiga kai tsaye gidan su Safnah ya nufa don Anty ta yi mai adireshin gidan su Safnah, Anty ta shaida mai bata san gidan ba don bata ta'ba zuwa ba ko Dad khalil ma be sani ba haka Safwan ya taho be wani gamsu ba ya za'ace wai ba su sani ba yana jin kunyar anty ne da yace "ta fad'a mai gaskiya", haka ya kamo hanya jiki ba kwari, Perking motar shi yayi a inda ya saba ajiyewa, falon su ya nufa da sallama, Dad shi ya gani yayi ba'ko Gaishe su yayi se da ya juyo kafin ya gane ashe Baban Salmah ne, gaban shi ya yi mummunar fad'uwa, "Safwan!" Yaji Dad shi na kira, dawowa yayi ya zauna a kusa da shi dafa kan shi ya yi yace "Yau karo na farko ka sani farin ciki mara adadi Safwan ashe 'yar aminina kake so, gaskiya na yi matu'kar farin ciki zumuncin mu ze 'kara 'karfi, zan so wannan had'i sosai Safwan dama muna so muyi magana ne a tsayar da rana", Safwan da tun da Dadyn shi ya fara magana ya ke had'a zufa kamar yana gidan buredi, ya ma rasa me zai ce gashi baze iya kallon idon Dad shi yace baya son Salmah ba, ga Dadyn ta a wajen shiru yayi Dadyn shi ne yace "Safwan yaushe kake gani za'a sa ranar tun da duk a shirye mu ke karatu ne kawai ko da aure za'ayi", da'kyar ya iya bud'e baki yace "Daddy duk san da ka saka" "to Safwan Allah ya maka albarka" Dad Salmah yace, sannan ya tashi da'kyar ya iya zuwa d'akin shi saboda tsabar takaiki da 'bacin rai ya rasa mai ke mai dad'i a duniya ya rasa me ze yi ma, number Kamal ya lalubo kira d'aya ya d'aga, ya yace "Hello Kamal ka na ina ne?" "Ina gida ya aka yi?" "yau ba wani labari ne?", "Kamar wanne?" "ka ji d'an rainin wayo wani labari na ke tambayar ka" "ok yau kam akwai wani chasu da aka shirya 'karfe hud'u4:00 ne ma" agogon hannun shi ya duba ya ga 'karfe 3:00 yace "saura awa d'aya kenan" "Ehh" cewar Kamal "to zan shirya ka zo gida ka d'auke ni" "to", Kamal yace cikin farin ciki sosai, sannan su ka yi Sallama wanka Safwan yayi sannan ya yi Sallah da 'kyar don kan shi bala'in ciwo yake mi shi ga tunani da ya addabi zuciyar sa ji yake kamar ze bar duniya ne. Ƙarfe hud'u 4:00 Kamal ya zo ya d'auke shi ko 'kara lokaci be yi ba, kai tsaye club d'in su ka nufa, dondazon maza da mata ne aciki su na ra'kashewa, wa su Hausawa ne wa su kuma yare, wasu 'ya'yan musulmai ne, abun ba kyau ga ni sunyi wata kalar shiga, zama Safwan ya yi, 'yan wajen na gani shi su ka d'au ihu bosss d'aga mu su hannu kawai ya yi kafin kace me aka cika mai gaba da kayan ciye-ciye ga kwalaben giya, kud'i ma su yawa ya bawa Kamal, ya cire na shi sannan ya ba su raguwar, ya shiga filin rawa shi ko Safwan giyar ya bud'e, wata zuciyar ta na fad'in mai ka da ya sha, ba shi da wata mafita da ya wuce ya sha d'aga kwalban ya yi ya fara sha, tun da ya sa abaki be cire ba se kwalbar ya ajiye, ya shanye!, wani ya 'kara d'auka shi ma ya shanye, se da ya sha uku gyatsa ya yi kafin kace me ya fara fita hayyacin shi mi'kewa ya yi yana layi ya nufi wajen rawar, rawar shima ya yi sosai ganin haka yasa na fito don d'auko muku sauran labarin. Safnah ita kad'ai a gidan har se kusan magrib sannan su Meenal su ka dawo, ta yi musu sannu da zuwa sannan su ka shiga su ka yi wanka, falo su ka dawo su ka sameta, zama su kayi Hindatu tace "wallahi yunwa nake ji sosai gashi nasan ba abinci ko?", "Akwai raguwar doya da na dafa d'azu, yau me aikin ma bata zo ba" cewar Safnah, "Ehh ai dama yau bata zuwa weekend", tashi ta yi ta zubo doyar da miya su ka zauna su ka ci ita da Meenal don Safnah a koshe ta ke, sun gama ci su ka mayar da kwanonin sannan Su ka zauna hira su na kallon pictures d'in biki, knocking su ka ji daga kofar falon na su Meenal ta tashi don bud'ewa ta na bud'ewa wa za ta gani "ya Abdul!" ta fad'a tare da rungume shi tana Hindatu ga ya Abdul ita ma da gudu ta zo tare da rungume shi ta na fad'in yaushe ka zo ya Abdul, "d'azu" kawai yace tare da jan jikin shi ya nufi falo, zama ya yi kallon Safnah da ke zaune ya yi yace "ke ba ki iya gaisuwa ba ne?", shiru ta yi bata ce komai ba, "Yaya ina tsarabar mu?" "ta na d'akina" "yawwa ka huta ka d'auko mana" "wa yace miki na ga ji tun Misalin 11:00 na sauka a Katsina, ba ku gida kun je yawo" "yaya biki ne fa mun so ma mu kai amarya amma ya majid ya wani zuwa d'aukan mu", "ai da kun kuskura kun kai Bayan magrib, da da kai na zan zo kuma jiki ze fad'a", "ai ba ayi haka ba ma yaya" cewar Meenal don tasan karon ba dad'i "yaushe Safnah ta zo?" ya tambaye su, "yau satin ta d'aya" Hindatu ta fad'a, "ai Dad ya fad'a min sun d'auko ta, gobe da safe ku shirya akwai in da zamu dukan ku, har ke Safnah" "to" kawai Safnah tace, "bari na koma d'aki akwai abun da zan yi" "to yaya", "Safnah ki dafa min wani abu simple ki kawo min" "to" Safnah tace d'akin shi ya nu fa, Hindatu ne ta kalli Safnah tace, "ke ki ka yi mai girki da rana ko?", "Ehh", cewar, Safnah, dariya ta yi tace "kin zama me mai girki kenan don ya Abdul in dai ki ka mai abu ya ji dad'i to shikenan su nan ki soory, tun da na gyara mai d'aki ya yi mai kyau to kullum ni ke gyara mai har ya koma", "ki tashi muje na ta ya ki" cewar Meenal, kicin d'in su ka nufa, chips na Dankalin turawa, da kwai ta yi mai, se ta had'a mai black tea, falo su ka fito Meenal rike da flat d'in chips d'in Safnah kuma ta rike kofin tea d'in, d'akin su ka nufa har da Hindatu, sanye ya ke cikin jallabiya ba'ki da alama wanka ya yi, ya na zaune bisa kujerar d'akin ya d'aura system akan cinyar shi, da Sallama su ka shigo d'akin ajiye, system d'in ya yi ya mi'ke zuwa center table d'in da su ka aje mai abincin, "sannu da 'ko'kari" ya furta bayan ya bud'e flat d'in, "to yaya se da safe" "to ku shirya da wuri" "to yaya" Hindatu ta fad'a lokacin da ta kai kofa don su sun fita ma, jawo 'kofar ta yi, d'akin su suka nufa, kwanciya su ka yi bayan sun yi sallar isha'i don sun gaji sosai. Taku har kullum Khadeejerh Ishaq ✍️ ce More comment More typing ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*17&18 Washegari Bayan sun tashi sun yi wanka su ka nufi kicin don had'a breakfast, nan da nan su ka gama su ka je su ka gaishe da kaka su ka kai mata nata, sannan su ka kaiwa ya Abdul sannan su ka ci na su, Bayan sun gama ne su ka je suka yi wanka, riga da sket su ka sa ka su ka d'auki gyale, su ka fito falo, ya Abdul su ka tarar a falon sanye yake cikin shadda golden yellow se 'kyalli ya ke, yayi masifar kyau, kallon su yayi yace "ina zuwa haka?" shiru su ka yi su na kallon shi don daga jin maganar sun san ya shirya tafiya ne, "ku koma ku saka hijab" to su ka ce su ka nufi d'akin don sa ko hijab, fitowa su ka yi bayan sun zumbulo hijaban, "Ko ku fa!? Har kun fi kyau, Meenal je ki ce fatima ta fito, sa'adatu ma ki ce ta fito ku yi sauri ku zo tare" "to yaya" tace sannan ta nufi part d'in su Teemah, afalo ta tarar da ita, sanye da gyale da alama ma Part d'in su zata nufa, "to sannu Hajiya Teemah gara ma ki koma ki cire gyaken nan don yaya Abdul na kira", cikin zaro idanu tace "dagaske?" "To tsaya nan" ta faɗa tare da yin gaba zuwa part ɗin su Sa'adatu, ita ma cikin sauri ta fito sanye da hijabin ta Teemah ma hijabin ta koma ta sako sannan suka nufo part ɗin su. Lokacin da suka fito sun samu Hindatu da Safnah tsaye a bakin motar Abdul yayin da shi yake ciki yana ganin ƙarasowar su hakan yasa ya kunna mota Hindatu da Safnah ne suka shiga mazaunin dake tsakiya, yayin da Sa'adatu, Meenal da Teemah suka shiga baya kasancewar motar me sashi uku ne harda na direba, "waye direban ku?" suka jiyo Abdul na faɗa, "Safnah ki koma gaba" cewar Hindatu, Ba tayi musu ba ta koma gaban yayin da Teemah kuma ta dawo ya kasance mutu biyu-biyu ne, jan motar yayi ya bar gidan don tun-tuni ma an buɗe mishi ƙofar gidan. Kai tsaye wani haɗɗen wajen shopping ya kai su, wajen ya haɗu sosai zuwa wajen ma se wanda ya amsa sunan shi mai kuɗi, cikin sauri su Meenal suka fita suka nufi ciki, Safnah ne kawai ta rage don ta ji motar a rufe yasa key, gashi ta kasa yi mai magana ya buɗe mata, "ki je ki ɗauki kaya da yawa don nasan baki taho da kayan ki ba, duk abun da kike so ki ɗauka", ta jiyo muryar ya Abdul yana faɗa, kallo ta bishi dashi bayan ya gama maganar ne ya cilla mata key ɗin motar ɗauka tayi tare da buɗewa, bayan ta fita ne ta ziro hannu ta ajiye key ɗin tare da kama hanya, koda ta shiga su Hindatu har an fara jidan kaya don sun kusa cika Basket ma, zuwa tayi ta ɗauki basket ta fara ɗaukan kaya ita ma. Ta daɗe tana ɗiba amma bata wani tara kaya da yawa ba hakan yasa Teemah taya ta, lokacin Abdul ya shigo, bin kayan da Safnah ta ɗiba yayi da ido sannan shima ya ɗauki basket ya nufi can wani waje yayi nisa da su, a tunanin su kayan shi ze ɗibo shima, se suka ganshi da kayan mata tun daga kan atamfofi Shadda, materials, turaruka, kayan kwalliya da sauran su, "kun gama ɗiban kayan?" Ya jefa musu tambayar, "Ehh" "to muje" yace yana yin gaba mai turo mai kaya na binshi a baya, wajen biyan kuɗi suka zo, koda akayi total kuɗin su wajen 1.5m ba tare da wani jinkiri ba, Abdul ya miƙa Atm card ɗin shi don cire kuɗin. Sai da suka samu wasu suka kwasan musu kayan har zuwa motar su duk girman but ɗin motar seda ta cika dam harda wasu kayan a wajen da suke zaune. Kai tsaye gidan su ya nufa da su gidan Baba babba kenan tun jiya da ya dawo be zo ba se yau don gaishe da matar baban shi Hajiya Safiya wanda suke cewa (anty) don mahaifiyar Abdul ta rasu tun lokacin da ta haifi ƙanwar shi mai suna A'isha gashi yanzu tana da shekara18 ne duk sa'annin su Hindatu ne kuma ƙawar su ce. Hajiya Safiya ta kasance masifffiyar mata ce ta ƙarshe kamar mijin ta don wani abun ma da Baba babba ke yi ana zargin da saka hannun ta, tsantsar kiyayya take nuna wa Abdul da ƙanwar shi A'isha, su biyu mahaifiyar su ta haifa, hakan yasa Abdul ma barin gidan ya koma can, don Abdul mutum ne me wasa da dariya da hakuri kuma duk da kasancewar shi Soja, amma wani lokacin akwai saurin fushi ga zuciya, hakan yasa yayi nisa da Hajiya Safiya don indai yana gidan yana kallon ta to ba zaman lafiya. Koda ya iso gidan perking yayi su Hindatu ne suka fita suka nufi cikin gidan shi kuma yana cikin motar don shi kamar ɗabi'ar shi ce, idan yayi perking mota baze fito ba se yayi wasu ƴan mintuna. Da sallama suka shiga dakin Hajiya Safiya na zaune ta amsa ba-yabo-ba-fallasa ƙarasawa suka yi tare da gaishe da ita, ciki-ciki ta amsa musu guri suka samu suka zauna, jiki a sanyaya don basu ga fuskar hira ba. "Momy A'isha tana nan?" Cewa Teemah don Teemah ba ruwan ta bata shakkar uban kowa bata tsoro kuma jajitacciya ce sosai, ba kamar sauran ba, don ko wani waje ne zasu je kowa na tsoron tambaya Teemah ce mai tambaya musu, don ko ƙofar gida zasu fita se sun tambayi ɗaya daga cikin Babannin nasu. "Ehh tana ɗakin ta" Hajiya Safiya ta faɗa rai a haɗe tashi suka yi suka nufi ɗakin nata, suna shiga Abdul ya shigo falo. "Ina wuni Anty" ya faɗa, wata uwar harara ta wurga mai tare cewa "da ban wuni ba zaka ganni ne?, Tun yaushe ka shigo garin nan amma kafi ƙarfin ka shigo ka gaishe ni saboda ni ba Uwar ka bace ko?, ka kyauta bara Uban naka ya shigo naji ko shi yace kar kazo ka gaishe ni, don shi dai nasan kun haɗu a babban gida". Tunda ta fara masifar Abdul yake binta da kallo har ta gama waje ya samu ya zauna, ba tare da yace mata komai ba, wata yarinya ce ta shigo falon itama mai kimanin shekaru 16, yarinyar Hajiya Safiya ce itace babbar yarinyar ta se maza huɗu. Waje ta samu ta zauna, "ke baki iya gaisuwa bane?" Cewar Abdul "Ehh fa bata iya ba ka koya mata ne?" Hajiya Safiya ta mayar mai da amsa, ita kuwa yarinyar hararar shi ma tayi haɗe da murguɗa mai baki, aiko nan da nan ya hassala cikin zafin Nama ya taso ƙyakykyawan mari ya ɗauke ta da shi wanda se da taga taurari, sannan yace "naga take-taken ki baki da kunya ko wallahi se na gyara miki zama, har ni zaki yi ma wannan kallo?" Ita kuwa Hajiya Safiya tasowa tayi ta nufo shi hakan yasa shi tsayawa kallon ta, ta ƙarasowa ta ɗaga hannu da niyar ta mare shi, beyi ƙoƙarin yin komi ba seda ya bari hannun ta ya kusa kaiwa fuskar shi, cikin zafin nama, ya ɗago hannun shi ya daki hannun ta, wani azababban ihu ta kurma don duka sosai yayi wa hannun nata ihu take riƙe da hannu, da sauri yarinyar nata da ake kira da Hafsat ta ƙaraso ta riƙe momin nata. Da sallama su Hindatu suka shiga ɗakin A'isha ai da gudu ta taso ta rungume su, tana murnar ganin ƴan uwan nata nan da nan aka buɗe shafin hira, Hindatu ce tace "Indo baza ki rinƙa ganin mu a gidan ku ba kinsan Boss tana nan ke ki rinƙa ƙoƙarin tambayar Baba Salihu ki zo mana" "Hindatu kenan baza ki gane bane, kona tambaya base Anty ta yarda ba" "hakane kuma amma da nice a gidan nan se na gyara wa matan nan zama wallahi" cewar Teemah "Hm baki da hankali ma, to Baba Salihu ze barki ki taɓa mai mata ne" cewar Meenal. Suna can suna hirar su basu san me yake faruwa ba a falon. Abdul ɗakin A'isha ya nufa don kiran su Teemah su tafi, be ko kula da halin da Hajiya Safiya ta shiga ba don ni a tunani na ma ta samu karaya a hannun nan. Cikin zafin nama ya buɗe ɗakin don ranshi ya ɓaci sosai"ku taso mu tafi" su kan su sun razana da jin muryar shi, da sauri suka miƙe suka yi waje da sauri A'isha ta ƙaraso ta rungume yayan nata "A'isha zan wuce anjima zamu yi waya" kafin tayi wani maganar har yayi nisa. Su Hindatu a falo suka samu su Hajiya Safiya a ƙasa riƙe da hannu ko ba'a faɗa musu ba sun san aikin Yaya Abdul ne, tunda suka ga ranshi a ɓace fita suka yi suna kunshe dariyar su, seda suka shiga mota sannan suka samu damar yi, amma banda Safnah don ita kamar gangar jikin ta ne a tare da su, amma zuciyar ta na wani wajen, suna cikin dariyar Abdul ya same su hakan yasa su yin shiru, shiga yayi ya ja motar da matuƙar gudu sosai se da suka razana. "Yaya Abdul zaka kashe mu ne?" Cewar Teemah, wani irin birki yaja kiiiiiiiiiit! Kake ji, tuni ƴaƴan cikin su suka kaɗa a tunanin su gun Teemah ze zo. Buɗe ƙofar motar yayi cikin zafin nama tare da rufe ta, wajen wani mota da ta perker yanzu ya nufa, kafin ya ƙarasa aka buɗe ƙofar wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga motar wanda kusan sa'anni ne da Abdul ɗin. "Yaya Sadiq!" Hindatu ta furta cikin tsantsar murna da farin ciki, "yaushe ya dawo ne?" Cewar Meenal "wallahi ban sani ba" Hindatu ta bata amsa. A can waje kuwa bansan me Abdul ya faɗa wa wannan matashin ba, kawai gani nayi ya shiga motar shi shi kuma ya nufo motar da su Hindatu su ke buɗewa yayi ya shiga tare da zama. Gaishe da shi su kayi ya amsa cikin fara'a sosai. "Ya Sadiq yaushe ka dawo?" Cewar Hindatu. "Yau kwana biyu" ya faɗa yana Murmushi, "Shine baka zo wajen mu ba ko, nasan yanzu ma, yaya Abdul ne ya kira ka" "Ehh yace nazo na mayar da ku gida akwai wajen da zai je ne" "Ai gara don kar ya kashe mu da sauran kwanan mu" Cewar Teemah Dariya suka yi dukan su, Ya Sadiq ne yace "kun yi bakuwa ne?" "A'a Safnah ce fa, baka gane ta ba?" "Oho! Dama itace?, Ance min dama ta dawo ai ban san ta ba wallahi" "To gata yanzu ka ganta ai" Cewar Sa'adatu don na lura itama kamar bata cika son magana ba sosai. Ƙarfe3:15 suka dawo gida kowa ya kwashi kayan shi ya mayar sif ya adana shi, ita kuwa Safnah wanda ta ɗibo itama ta kwasa ta ajiye akan gado, "To sauran wa kika bar ma wa" Meenal ta faɗa tana kwasan raguwar nata"ba na yaya Abdul bane?" Safnah ta tambaya "A'a naki ne Safnah" Hindatu ta faɗa "Amma ai sunyi yawa sosai" "Kin ga Malama ki kwashi kaya naki ne, sutura ai baya yawa" Meenal ta faɗa. Su Teemah tun ɗazu sun kwashi na su sun nufi part ɗin su, taya ta kwasa suka yi suka shigan mata da shi don kayan da yawa. Bayan sun gama komai sunyi sallah sunyi wanka suka fito falo don cin abinci kasancewar tun ɗazu mai aikin ta gama girka musu, zama suka yi suka cika cikin su sosai. Yaya Abdul kuwa tunda ya hau mota ya tafi be dawo gidan ba se wajen 6:00 na yamma hannun shi ɗauke da leda ya shigo, kai tsaye ɗakin shi ya nufa don watsa ruwa. Su Hindatu na zaune a falon ɗakin su suna chat don kowa da wayar ta, yayin da Safnah ke zaune tana karanta wani Novels da ta ɗauko a ɗakin Teemah, don Teemah shugaba ce ta karanta Hausa Novels. Kira ne ya shigo wayar Meenal, ɗagawa tayi ta kara a kunne tare da cewa "Hello yaya Abdul" "daga can ɓangaren yace "kun koma lafiya?" "Ehh yaya Abdul" "to yayi, ina Safnah take?" Ɗan kallon Safnah tayi sannan tace "gata nan" "To kice mata ina jin yunwa" Dariya sosai Meenal ta tuntsire dashi, wanda ya ja hankali Hindatu da ta yi nisa wajen chat da Masoyin ta, shi ko Abdul yanke wayar ma yayi. Sai da Meenal ta gama dariyar ta sannan ta kalli Safnah tare da cewa "to Safnah number ki ta fito yaya Abdul fa yana jin yunwa" ita kan ta Safnah maganar ta bata dariya, Murmushi tayi tare da cewa "to ya za'ayi" "Yadda za'ayin kenan shiga kicin ne ya gan ki" cewar Hindatu "Ai na faɗa miki kin zama mai girkin shi daga yau" ta faɗa "Muje to na taya ki koda yanka albasa ne" Meenal ta faɗa tare da yin gaba don tasan idan ba'a yi girkin nan ba akwai matsala don ita yaba saƙon gashi tayi mai dariya a waya abun da ya tsana kenan, tunda taji ya yanke wayar kuma tasan yayi fushi ne. Dama shi Abdul haka yake baya cin abincin mai aiki, se dai ya siyo a restaurant shima bako wanne ba, don yana daga cikin mutane masu zaɓan abincin wanda zasu ci. Haka Safnah ta miƙe suka shiga kicin ɗin jallop ɗin cus-cus tayi mai, mai rai da lafiya, yaji vegetable ga kunun aya da ta haɗa mai ta saka ƙanƙara yayi sanyi sosai, don Safnah ba baya ba wajen iya girki don ita take yiwa Anty ma. Bayan sun gama sun fito ne kiran ya sake shigowa, "lallai ma wannan yana gidan amma ya dinga kiran mutane" ta faɗa a zuciyar ta tare da ɗaga wayan "wai ba'a gama ba ne?" Abinda yace kenan "an gama to ka ƙi fitowa ne ai" "Kice ta kawo min ɗaki na" "Kuma dai!" Meenal ta faɗa ba tare da sanin a fili ta faɗa ba ma, hakan yasa tayi sauri yanke wayar. "Yace ki kai mai ɗakin shi" Meenal ta faɗa tare da yin gaba Tsayawa Safnah tayi a zuciyar ta tace "lallai ma wannan wai a kawo mai" ɗaukan kulan tayi da filet da kuma jug ɗin ta nufi ɗakin shi. Da sallama ta shiga don ƙofar a buɗe take a falon ta same shi kwance akan kujera "Ina wuni" ta faɗa a takaice Se da ya tashi ya zauna sannan ya amsa, ajiye abincin tayi a kujerar dake gaban shi ta juya zata fita "Safnah!" Ya kira sunan ta Tsayawa ta yi cak! Ba tare da ta juyo ba, "ki zo ki zauna za muyi magana ne" ƙarasowa tayi ta zauna can gefe. "Kina so ki zauna a ɗakin su Hindatu ko kuma a baki naki daban?" "Nafi son nawa ni kaɗai" ta bashi amsa "To shikenan akwai ɗakuna se ki zaɓi ɗaya "Ni ɗakin mu nake so, naga ba kowa a ɗakin" "To ba matsala zuwa gobe se ku gyara da su Hindatu, ɗazu kin ga kaya ko?" "Ehh Nagode sosai" "Kar ki sake min godiya" "To" "Shima gobe zasu raka ki, ki kai ɗinki" "To" "Sannan muhimmin maganar da yasa na tsayar dake shine: maganar gadon ki tun lokacin da aka raba yana wajena, an damƙa min ne, na ɗibi rabi ina juya miki sauran kuma suna cikin wani account da na buɗe da sunan ki, sannan akwai gidaje da filaye duk idan na samu lokaci zan kai ki ki gansu" Tunda ta fara magana Safnah kallon shi kawai take yi, har ga Allah ita ta manta ma da wani gado da ake bayarwa don kuɗin basu gaban ta. "Kinyi shiru!" Ya faɗa, hakan ya dawo da ita daga tunanin da take "Yaya Abdul duk yanda kayi dai-dai ne, bi bana buƙatar kuɗi" "A'a ba wani ɗan Adam da zece baya buƙatar kuɗi" ya faɗa tare da miƙewa ya nufi bedroom ɗin shi "To idan buƙatar hakan ta taso zan yi magana" ta faɗa cikin ƙosawa da maganar don tunda tazo gidan bata yi magana daya kai wannan ba. Fitowa yayi ɗauke da leda a hannun shi, miƙa mata yayi tare da cewa "zaki iya tafiya" "to Nagode" tace duk da bata san miye a cikin ledar ba. Hanyar fita ta nufa shi kuma zama yayi ya fara cin abincin shi se santi yake yi. Koda Safnah ta fito bata samu su Hindatu a falo ba, hakan yasa ta wucewa ɗakin su. Da sallama ta shiga ɗakin amsawa suka yi tare da cewa "Safnah se yanzu?" "Ehh ya tsayar da ni ne" "to me kika samo mana" cewar Hindatu Se yanzu Safnah ta tuna da ledar hannun ta don ta manta ma da ita. "Wallahi bansan meye ba ya bani ne kawai" Safnah ta faɗa, rige-rigen ƙarɓar ledan suka fara inda Meenal tayi nasarar kwacewa ita kuwa Safnah zama tayi a kujera. "Masha Allah!" Meenal ta furta lokacin da tayi arba da wata haɗaɗɗiyar waya ƙirar iPhone13 cikin kwalin ta, ta haɗu sosai, cirowa Meenal tayi ta haɗa ta saka layin tare da kunnawa, ƙarar wayar ce ta dawo da Safnah daga tunanin da take yi, zaro idanu tayi tana kallon wayar miƙo mata Meenal tayi, ba musu ta ƙarɓa yayin da farin ciki ya cika mata zuciya ɗon koba komai ta samu wayar da zata dinga kiran Safwan da su, Anty. "Na taya ki murna Safnah" cewar Hindatu "Nagode sosai" Safnah ta faɗa. Tashi sukayi suka nufi bedroom don ɗauro alwala don kiran Magrib ake yi. Khadeejerh Ishaq ✍️ ce More comment More typing Share pls ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_19&20 Washegari se ƙarfe 9:00 suka fito ƙaryawa, suna gana ƙaryawa Safnah ta shiga kicin don yiwa Yaya Abdul nashi abun karin chips ɗin dankalin turawa da kwai tayi mai, haɗe da shayi, tana gamawa kuwa se gashi ya fito mamaki ne ya kama ta ganin shi da kayan soja, don tana tsoron Soja a rayuwar ta, gaishe da shi tayi tare da yi mai godiyar waya, sannan ta kawo mai abun karin, "kije ki kira min su Hindatu" ya faɗa kasancewar basu falon sun shiga ɗaki. Cikin minti ɗaya1 suka fito tare zama su kayi a dining table ɗin, "me kuka koma yi a ɗaki, ke baki ce su taya ki gyara ɗakin bane?" "Ehh babu key ɗin ne ai" Safnah ta bashi amsa "Ok, idan na fita zan aiko Sadiq ya kawo miki, Hindatu ku taya ta ta gyara ɗakin su nan zata koma, sannan anjima Sadiq se zo ya kai ku wajen ɗinki ku bayar harda naku, "To yaya muna godiya" Meenal ta faɗa "Sannan kuma na kira ku nayi muku sallama ne don yanzu zan wuce India" "Yaya! Yau kwanan ka uku ne fa!" Cewar Hindatu cikin zaro idanu "Ehh na sani, Baba babba yace lallai se na koma kun san mun samu matsala da Anty, ta kawo min mari na buge hannunta kaɗan shine wai ta samu gocewar ƙashi" Dariya Meenal ta tuntsire dashi tare da cewa "ashe shiyasa muka ganta riƙe da hannu" "Ehh, ta faɗawa Baba ƙarya da gaskiya shi kuma yace na koma wajen aiki, dama hutun sati ɗaya na samu amma nan da sati biyu zamu sake samun hutu na wata ɗaya nan da sati biyu in sha Allah ina gida" "Yaya za muyi kewar ka sosai Allah ya tsare hanya ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya" Meenal ta faɗa. "Ameen" suka amsa da shi. Miƙewa yayi bayan ya gama cin abincin ya nufi ɗakin shi, cikin minti biyu2 ya fito ɗauke da jakar shi, har wajen mota suka raka shi ya shiga ya bar gidan suna ɗaga mai hannu. Bayan tafiyar shi cikin gida suka shiga part ɗin su Teemah don yin hira. ZARIA Safwan bashi ya dawo gida ba se ƙarfe sha biyu12 na dare Kamal ya kawo shi, don a buge yake sosai, har ɗaki ya kai shi ya kwantar dashi, sannan ya fito ya koma na su gidan. Washegari se ƙarfe 11:13 kafin Safwan ya tashi don ko Sallar Asuba beyi ba cikin sauri ya tashi yayi wanka sannan yayi Sallah har na Magrib da Isha'i yayi na jiya da be samu yi ba. Ƙarfe 12:00 ya fito cikin shirin shi a falo ya samu Daddyn shi, ƙarasawa yayi ya gaishe shi, cikin fara'a ya amsa sannan yace "Safwan mun tsayar da ranar aure wata biyu masu zuwa" Gaban Safwan yayi mummunan faɗuwa, daƙyar ya seta kan shi yace "Daddy nifa bana son yarinyar nan, akwai wacce nake so fa" "Wacece?" Dad ya tambaye shi, kame-kame ya fara yi "Safwan tunda nake da kai ban taɓa neman alfarma a gurin ka ba komai na saka ka zaka yi, to amma yanzu wannan alfarma nake nema a wajen ka" "Haba Daddy wane ni da zaka nemi alfarma a wajena, na yarda" Safwan ya faɗa don baya son ɓacin ran Daddyn shi. "Yawwa Allah yayi maka albarka, in sha Allah zaka ji daɗin auren tunda kayi min biyayya, anjima zan kira Momyn ka na faɗa mata" "Daddy yaushe zaka dawo da momy ne" "Babu rana!" "Daddy ba rana kuma?" "Ehh saboda momyn ka tace min baza ta dawo ba, yanzu haka ma ta kusa yin aure" "Shikenan Daddy zan fita ne dama" "To adawo lafiya, yaushe zaka je gidan su Salmah?" "Se gobe Daddy" "To Allah ya nuna mana, baka gaishe da Antyn ka ba, naga zaka fita" "Mun gaisa ɗazu" Safwan ya faɗa tare da rufo ƙofar da ya fita, yasan idan yaje wajen anty ƙara mai baƙin ciki kawai zata yi, kai tsaye gidan su Kamal ya tafi. KATSINA Yaya Sadiq ya zo ya kai su wajen ɗinkin sun bayar sannan suka shiga ɗakin su Safnah don taya ta gyarawa, ba komai a ɗakin se kujeru a falo da kayan kallo, se ƙaton gado, da manya-manyan sif a Bedroom ɗin, ba wasu tarukuce, gyara ɗakin suka yi tas sannan suka jera mata kayan kwalliya da mayukan shafawa a kan mirror suka zuba kayan ta wanda ba'a kai ɗinki irin su dogayen riguna, riga da siket, da riga da wando, da su gyale don hijaban suna wajen ɗinki kusan goma sha biyu, kaya ne masu yawa kamar na lefen wata, wata ma baza ta samu rabin shi a lefe ba ma. Wanka suka yi bayan sun gama aikin sannan suka kwanta don huta gajiya. Safnah kwance a makeken gadon ta hannun ta ɗauke da waya tana ta gwada number Anty amma bata shiga, abinda Safnah bata sani ba, tun ranar da Safnah ta kira Antyn Kawu ya sani ya ƙarɓi layin ya bata wani sabo. Bayan tayi ta kira bata samu ba, hakan yasa ta shiga facebook domin yin login a account ɗin ta, abun takaici ta manta password ɗin kamar ta kurma ihu haka taji, ta tabbatar indai ta shiga account ɗin zata samu Safwan don suna chart sosai. Wani sabon account ta buɗe tayi ta searching Safwan amma bata same shi ba, kuma tasan baza ta same shi ba, se dai idan shi ya turo mata friend request. WhatsApp ta koma shima ta buɗe sabo ba numbers da yawa a ciki wasu number ne guda uku kawai kuma duka bata san masu shi ba, hotunan dake jiki ta WhatsApp ta duba, ɗaya Yaya Abdul ne da kayan sojoji yayi hoto, ɗaya kuma yaya Sadiq ne don ta san shi sosai yanzu, ɗayan ne bata sani ba. Bayan ta gama abun da zata yi ne ta ajiye wayar tare da kwanciya wani nannauyan bacci ne ya ɗauke ta. ZARIA Safwan bayan yaje gidan su Kamal kai tsaye suka wuce wani wajen shaƙatawa don yanzu baya son zaman gida gashi sunyi hutun school. ********** Kawu ne zaune da iyalen shi ana ta hira cikin nishaɗi "Abban Khalil ya kamata fa muje Katsina domin duba Safnah daga nan akai mata kayan ta" "Wai so nawa zan faɗa miki ba zamu je ba, kuma Safnah bazata dawo gidan nan ba, saboda dangin mahaifin ta sun nuna sunfi ni iko da ita, kuma haka ne, munyi waya da Baban ta Salihu ya shaida min aure za suyi mata ma, sannan kayan ta yace bata buƙatar su, asan yadda za'a yi da su, ke ma ina so ki manta da wata Safnah ta zauna a gidan nan" "Amma ya kamata duk da haka muje mu ga gidan, sannan ga Safwan ya dame mu na bashi adireshin gidan ze je kuma ban sani ba" "Idan ya ƙara tambayar ki ki faɗa masa baki sani ba, kuma Safnah baza ta dawo ba sannan ki faɗa masa tayi aure ma" "To shikenan tunda haka kace" Cewar Anty ba tare da ran ta yayi mata daɗi ba, hakan yasa ta barin wajen gaba ɗaya. Safwan be dawo ba se wajen ƙarfe 9:00 na dare kai tsaye ɗakin shi ya wuce don ba kowa a falon. Direct bayi ya shiga yayi wanka, ɗaure da tawul ya fito mirror ya nufa ya shafa mai haɗe da turaruka masu masifar ƙamshi sannan ya zura wata jallabiya maroon colour yayi mai kyau sosai, saman gadon shi ya dawo ya kwanta, tare da cire wayar shi da yasa caji ya ɗaura a gefen drawer kira ya ɗanna tare da kara wayar a kunnen shi. Har kiran ta katse ba'a ɗauka ba, seda yayi wajen kira uku sannan aka ɗauka, "Assalamu alaikum momy na ykk" Daga can ɓangaren aka ce "Wslm my son ya kake?" "Wallahi momy ba lafiya ba!" "Subhanallahi me ya faru kuma!?" "Komai ma ya faru, momy kin dena son tilon yaron naki ko? Sai da nayi wajen kira uku sannan zaki ɗauka, kuma ko kira na baki yi ma" ya ƙarasa maganar cikin shagwaɓa, dariya momyn tayi tare da cewa"kai Safwan bana son sakarci fa, kai baka san ka girma bane, Dadyn ka ya kira yana faɗa min bikin ka saura two months ma" "Momy ki share wannan maganar, wallahi bana son yarinyar da Daddy ya dage se na aure ta, momy yaushe zaki dawo wai?" "Safwan me yasa ka cika rigima ne, ni bazan dawo gidan nan ba" "What! Momy kar dai abinda Daddy ya faɗa min hakane, Momy yanzu baza ki dawo ba aure zaki sake yi!?" Safwan ya faɗa cikin tsantsar tashin hankali domin yana matuƙar azabtuwa na rashin Momyn shi a kusa da shi sosai. "Tabbas hakane Safwan bazan dawo ba" Momyn ta faɗa. "Yanzu Momy ni kaɗai zaki bari kenan?" "Safwan yanzu fa ka girma gashi har aure zaka yi, ka zauna da matar ka lafiya, sannan ka cigaba da yi wa matar Daddyn ka biyayya kaji!" Wasu zafafan hawaye ne suka fara gangara daga idanun Safwan cikin rawar murya yace "Momyna zanyi abinda kika ce amma duk halin da na faɗa kar ki zarge ni, na kira ki domin ki kwantar min da hankali akan matsalar da nake ciki amma kuma kin ƙi saurarana ma to se anjima momy" ya faɗa tare da kashe wayar yayi wurgi da ita Allah yasa akan kujera ya faɗa da yayi raga-raga. Miƙewa yayi ya nufi firij ɗin dake ɗakin buɗewa yayi ya ɗibo giya har kwalba uku, sannan ya nufo gadon ya zauna tare da buɗewa hawaye nabin fuskar shi, tsurawa kwalbar daya buɗe ido yayi kafin ya fara faɗin "ya Ubangijina kaga halin da nake ciki ka fitar dani, kafi kowa sanin damuwata Allah ka yaye min Allah ka shirye ni, na daina wannan halin, Safnah kiyi hakuri zan ƙarya alƙawarin ki, amma duk lefin ki ne, ki ka yi nisa dani, bayan kinsan bazan iya jure hakan ba. Maganar yake hawaye na bin fuskar shi idan ka ganshi se ka tausaya mai sosai ɗaga kwalbar giyar yayi zuwa bakin shi cikin abinda be fi minti1 ba ya shanye tare da sake ɗaukan ɗaya shima tas! Ya shanye shi. Be yi minti 5 ba bacci mai nauyi ya ɗauke shi. KATSINA Safnah zaune a falon ɗakinta idanunta nakan Tv suna haska shirin Tarkon Ƙauna a tashar Arewa24 amma a zahiri hankalin ta ba akan Tv yake ba don tayi nisa cikin tunani haka yasa bata samu damar jin ƙarar da wayar ta take yi ba, wanda yake nuna kira ne ya shigo, ga kuma ƙarar Tv. Ta daɗe sosai sannan ta dawo hayyacin ta, tashi ta yi ta nufi Bedroom don ɗauro alwala don kiran Sallar la'asar da ake yi. Se da tayi alwala tayi Sallah sannan ta dawo falon wayar ta ta ɗauka, zare idanu tayi gani 2misscall daga Yaya Abdul, mamaki ta shiga yi me yasa kuma ze kira ta. Bayan ta gama tunanin ne ta danna mai kira, har ya katse ba'a ɗauka ba, zata sake kenan se ga kiran shi ya shigo, se da ta dai-daita nutsuwar ta sannan ta ɗaga wayar ta kara a kunne shiru ba'a yi magana ba, hakan yasa ita ma ta yi shiru, har tsawon sakwanni15 sannan ta daure tace "Assalamu alaikum!" "Wa alaikumus-salam" ta ji ya faɗa daga can ɓangaren, "lallai ma wannan mutumin ya kira ya wani yin shiru to me zance mai Oho!" Ta faɗa a zuciyar ta, har zuwa lokacin be sake yin magana ba, "Ina wuni" ta daure daƙyar ta faɗa "lafiya lau, na zaci ai da kurma nake magana" shiru tayi bata ce komai ba"meyasa baki son sakewa a gidan ku, kina yi kamar wata baƙuwa, ranar da na ganki a lambu kina kuka me akayi Miki" "bakomai Yaya Abdul" "ya kamata ki saki jikin ki, ga ƴan uwan ki kuyi hira, ina su Hindatu suke?" Ya ƙarasa maganar tare da jefa mata tambaya"suna ɗakin su" "ke kuma kina ina?" "Ina nawa ɗakin" "To kin ga irin ta ko, ki zauna ke kaɗai cikin tunani, to a ina kike kwana ma" "Ɗakina" ta faɗa kamar zata yi kuka don ta gaji da tambayoyin da yake mata, "To ban yarda ba kije cikin ƴan uwanki ku dinga kwana tare, da rana ma ki kasance tare da su kin ji ko?" "Ehh naji" "to tashi ki tafi ɗakin su" "To seanjima zan tafi" ta faɗa tana shirin yanke wayar. "Kar ki yanke min waya Malama" taji Muryar shi yana faɗa "to zan tafi ɗakin nasu ne fa" ta faɗa cikin shagwaɓa, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mai ba, "Ki tafi da wayar a haka idan kinje ki bawa Hindatu" "to" kawai tace sannan ta miƙe ta nufi ɗakin nasu, a zuciyar ta ta na mamakin wannan abun haka. Da sallama ta shiga ɗakin suna zaune suna hira har da Teemah don tazo part ɗin nasu "Hajiya Safnah ai yanzu nake shirin zuwa ɗakin naki don naji ki shiru, gashi an faɗa min gogan namu har waya ya siya miki ma a kawo mana mu ɗan dangwala" duk surutun da Teemah take yi bata lura da alamar da Safnah take yi mata ba se da ta kai aya. "Safnah Teemah ce ke magana ko?" "Ehh" ta faɗa tare da ƙarasawa wajen Hindatu ta miƙa mata wayar, "me ya faru?" Hindatu ta tambaya bayan ta ƙarɓi wayar, kafin ta bata amsa taji Muryar yaya Abdul yana faɗin "Hindu ki faɗawa Teemah idan na dawo se ta ɗanɗana kuɗar ta" Dariya Hindatu ta sheƙe dashi tare da cewa "yaya Abdul ya kwana biyu 2" jin ta ambaci yaya Abdul yasa Meenal matsowa kusa da ita banda Teemah da ta saki baki ya kasa rufuwa. "Ba wani kwana biyu 2, bayan tunda na tafi ba wanda ya kira ni a cikin ku, se A'isha, wannan ya nuna baku damu dani ba ma" "Haba yaya Abdul wallahi mun damu da kai kawai an samu akasi ne ba mu kira ba, amma kayi hakuri" cewar Meenal, Hindatu ta ɗora da cewa "yaya kayi hakuri bamu so mu takura maka ne gara kayi aikin ka" "To naji nagode, amma meyasa kuke barin Safnah ita ɗaya a ɗaki?" Kallon Safnah tayi da ta tafi duniyar tunani ma sannan tace "yaya kasan halinta har yau ta kasa sakewa damu" "Kuma muma muna so muga muna hira da ita sosai amma bata shiga lamarin mu" Meenal ta faɗa. "To naji dai nace ta daina zaman ɗaki ita kaɗai, idan ta zauna ma ku rinƙa bin ta tunda nasan baza tace ku fita ba" "To yaya za'a kiyaye" cewar Hindatu "Ba Teemah wayar" ya faɗa, "Gashi Teemah" Hindatu ta faɗa tare da bata wayar ba musu ta ƙarɓa ta kara a kunne tare da cewa "Allah ya taimaki babban yaya kwata-kwata da fatan kana lafiya" "ban sani ba, ke wai yaushe zaki yi hankali ne Teemah, baza ki nutsu ba ko?" "Yaya kayi hakuri" "Shikenan kema har da ke ko nema na baku yi ko se ƴaruwa ta kawai" "To afuwan babban yaya" "To bata wayar ta kar ki mata latse-latse naji kina faɗin zaki yi, ko kar ki mata wani ɓarnar" "Su yaya Abdul manya kasan nima wayar nan dai ina da ita, base kunyi min gori ba" Ɗif! Taji ya yanke wayar, ita ma sauke wayar tayi tana dariya tace "Kai!, Allah ya bar mana yaya Abdul namu" "Ameen" duka suka amsa. "Wai wasu sharuɗa naji yana gindaya muku ne?" Cewar Teemah tana ta latse-latse a wayar Safnah don har yanzu yana wajen ta. "Bafa wani sharaɗi bane kawai cewa yayi mu daina barin Safnah ita ɗaya" cewar Meenal"ikon Allah abu ya kan-kama haka akayi!" Cewar Teemah tana zare idanu waje "ke dai kina da matsala wallahi" Hindatu tace, ko bi ta kanta Teemah bata yi ba sema cewa Safnah tayi "La! Ashe kin buɗe facebook da WhatsApp shine ko kiyi adding ɗin mu, ko number mu ma baki dashi" Murmushi Safnah tayi sannan tace "kuyi hakuri ƴanuwana jiya na buɗe kuma bansan sunan da kuke using ba a facebook, ki saka min number ki da na sauran harda na A'isha ma" "To ko ke fa!, "Kai Teemah ba dama, inaji yaya Abdul na miki gargaɗi kar ki mata latse-latse a waya, amma se da kika yi, shima ai yasan hali ne" cewar Hindatu. "To ai mara gaskiya shi yake gudun ayi mai bincike a waya wallahi" cewar Teemah tare da ba Safnah wayan ta, bayan ta saka mata number, sannan tayi searching sunan su a facebook ta tura friend request. Hira suka cigaba da yi se bayan isha'i sannan Teemah ta koma part ɗin su bayan ta cika cikin ta. ZARIA Safwan bashi ya farka ba se ƙarfe 9:00 na safe, da sauri ya tashi ya shiga bayi yayi wanka tare da yin alwala, wata jallabiya fara ya saka sannan ya shinfiɗa darduma ya gabatar da sallar asuba ɗin shi, sannan yayi istigifari tare da addu'o'in Allah ya shirye shi. Bayan ya idar ne ya nufi sif ɗin shi, ƙananun kaya ya fito da su Baƙar wando da jar riga ya saka, sunyi bala'in yi masa kyau, agogo ya ɗaura wa hannun shi tare da ɗaukan wani glass baƙi ya kwama wa fuskar shi, sannan ya ɗauki makullin shi, wanda yake haɗe da na mota da na ɗakin shi ya fita.  ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_21&22 A falo ya samu Daddyn shi da Anty suna hira, zama yayi shima tare da gaishe su, "Babana ina zuwa haka, ko zaka wajen ƴartawa ne" Daddy yace "A'a Daddy ni daga nan Kano na nufa na fito na faɗa maka ne dama" "Kano kuma?" Daddy ya tambaya da alamar mamaki. "Ehh Daddy kasan munyi hutu, kuma na daɗe ban je ba" "To Allah ya dawo da kai lafiya, kwana nawa zaka yi ne" "Daddy gobe zan dawo ma" "To Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya my son" "Ameen Daddy" yace tare da miƙewa ya fita, kai tsaye wajen da motocin shi suke ya nufa wata jar mota ya shiga ya tayar tare da nufan gate ɗin gidan. Katsina Bara mu waiwaya gidan su yaya Abdul Bayan tafiyar Abdul Hajiya Safiya ta bawa yarinyar ta Hafsat wayar ta don ta kira Dadyn ta, ta faɗa mai, aiko ƙarya da gaskiya ta haɗa ta faɗa mai. Ko minti10 ba'ayi ba ya iso gidan, nan da nan aka kira Doctor ya duba ta, ya tabbatar musu ta sami tsagewar ƙashi, ran Daddy ya matuƙar ɓaci sosai, hakan yasa shi yi ma Abdul faɗa tare da cewa ya koma wajen aikin shi. Sai da ya samu Baba Bashir (Baban su Teemah) yayi mai magana ya faɗa mai abinda ke faruwa, shine ya samu Baba Babba ya bashi hakuri sannan ya yarda ya dawo idan sun samu hutu, da yace kar ya sake ya dawo. Hajiya Safiya kuwa wani tsanar Abdul ne ya ƙara shiga ranta haɗe da shakkar sa, don duk abinda take yi mai tana shakkar sa sosai. Yau Safnah suka je suka ƙarɓo ɗinkin ta sunyi kyau sosai, kuma ɗinkin zamani akayi mata, kaya ne masu yawan gaske don ba'a gama ɗinkawa ba ma. Ƙarfe 1:00 Safwan ya isa Kano wata anguwa da ake kira Tarauni, dai-dai wani haɗaɗɗen gida ya tsaya horn ya danna, buɗe mai ƙatoton gate ɗin akayi. Danna hancin motar yayi zuwa cikin gidan, kai tsaye wajen da aka tanada don aje motoci ya nufa ya ajiye nashi motar sannan ya nufi cikin ƙofar falon. Da sallama ya shiga, ba kowa a falon se wata dattijuwar mata, cikin fara'a ta amsa sallamar. Har ƙasa ya duka ya gaishe da ita, cikin fara'a ta amsa tare da cewa "Muhammadu yau kai ne a garin namu" "Ehh kaka ina Momyna" "Sannu mai gidana wato baka yi kewar matar taka ba, se Momyn ka ko?, Ko da ka manta da ni tunda naji ance auren ka ma ya kusa" Dariya yayi tare da cewa "Haba kakana kinsan kina raina, daga ke ba wata" "Yayi kyau, Momyn ka tana nan a waje baku haɗu ba" "A'a Kaka, ban ganta ba ta fita ne?" "A'a tana cikin gidan nan tayi baƙo ne" wani irin bugu zuciyar Safwan tayi, miƙewa yayi ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi waje. Be hango momyn nashi ba, hakan yasa shi zuwa wajen mai gadi ya tambaye shi ina momyn shi, wata mota mai gadi ya nuna mai tare da cewa "tana cikin waccan motar" "Nagode"kawai Safwan yace sannan ya nufi motar. Glass ɗin motar a rufe yake hakan yasa shi yin knocking, buɗe glass ɗin akayi, wata farar mata ce kyakkyawa fuskar ta ɗauke da murmushi tace "my son yaushe ka zo" Shi ko Safwan mutumin da yake cikin motar ya kurawa ido, fari ne sosai kuma ze iya girman Dadyn shi, a zuciyar shi yace "momy ko me ta gani a jikin wannan, dame yafi Daddyna don Allah" "Kai Safwan wannan Wani abu ne ka ƙurawa mutum ido ko gaisuwa babu?" Maganar Momyn shi ta dawo da shi daga tunanin da yake yi don da ƙarfi tayi mai maganar. "Ina wuni" Safwan ya faɗa bayan ya tattara nutsuwar sa. "Lafiya lau, ya hanya" mutumin ya faɗa da murmushi ɗauke a fuskar shi. Safwan be saurari wani magana ba ya koma ciki, be samu kaka a falo ba hakan yasa ya nufi wani ɗaki wanda ya kasance na autan su momyn shi ne mai suna Mubarak, sa'an Safwan ne suna mutunci sosai. Ya same shi zaune a falo yana kallo, gaiswa suka yi sannan yace "Mubarak wai waye suke zance da Momy a waje, "Alhaji Umar ne, shine wanda zai auri Anty, saura 3week ma" Jiri ne ya kwashi Safwan, ba shiri ya zauna a kujerar da yake dafe da ita, cikin tsantsar mamaki yace "Mubarak dama da gaske ne Momyna zata auri wani" Cikin halin ko in kula Mubarak yace "Ehh mana" Tashi Safwan yayi ya fita, falo ya dawo ya samu Kakan nashi na zaune, shima zama yayi, yana zama momyn shi ta shigo da sallama. Kaka ce ta amsa sallamar don Safwan ko sallamar be amsa ba, waje ta samu ta zauna, tare da cewa. "Safwan yaushe ka zama haka, kana gani na da baƙo baka gaishe dashi ba, amma ka ƙura mai ido, waye yace ma kazo wajen?" "Momy ba kiyi farin ciki da zuwa na ba kenan, har kike min faɗa don na kasa hakuri naje na gan ki" "A'a ya za'ayi nace banyi farin ciki da zuwan ka ba, kasan kai ne ɗa guda ɗaya da Allah ya bani" "Shikenan Momy, amma ban ji daɗi ba da baza ki dawo garemu ba, Momy ina matuƙar buƙatar ki a kusa dani" "Safwan nida zuwa Zaria se bikin ka in sha Allah, ya Safnah kuwa?" Wani iri Safwan yake ji, yayi takaicin zuwa Kano ma da yayi yau ɗin nan, "Momy Safnah bata nan tana garin su" "Ayya! Allah ya dawo da ita lafiya" "Ameen" Kawai Safwan yace "Mai gidana ko abinci baka ci bafa ga abincin can a dining" "Na ƙoshi" Safwan yace. Momy kuwa miƙewa tayi ta nufi ɗakin ta, Kallo Safwan ya bita dashi, kafin ya tashi shima ya koma ɗakin Mubarak domin yin Sallah, don yanzu kusan 2:30 ma. Falo ya dawo bayan yayi sallar sunyi hira da Mubarak, ba kowa a falon hakan yasa shi nufar ɗakin Momyn shi. Kwalliya ya samu tana yi, don har ta sake wanka ma, amsa sallamar da yayi tayi, waje ya samu ya zauna tare da cewa "Momyna zaki fita ne?" "Ehh Safwan zan je anguwa ne" "Zan raka ki" Murmushi Momy tayi tare da cewa "Safwan kenan, kana mayar da kan ka yaro, da girman ka yanzu zan tafi da kai anguwa?" Murmushi yayi sannan yace "Momy driving ɗinki fa zanyi" "A'a Safwan ka tafi ɗakin Kaka yanzu zan dawo nima, yaushe zaka koma Zaria?" Tashi Safwan yayi ya fita ba tare da yace komai ba. Kai tsaye tsakar gidan ya nufa wajen da yayi perking motar shi, shiga yayi tare da kunnawa ya bar gidan a guje. KATSINA Safnah ne tare da Hindatu a kicin sun dage se aiki suke, don girkin tarar ya Abdul suke yi, don yana hanya yau, musamman ya kira Safnah ya faɗa mata ta shirya mai girki gashi da abokin shi zasu zo shi ɗan Kaduna ne, tunda Abdul ya tafi kusan-kullum se ya kira Safnah sun gaisa, abun har haushi yake bawa Safnah, don bata son yawan surutu. ********** Safwan kai tsaye Zaria ya nufa don idan ya cigaba da zama a Kano lallai zuciyar shi zata iya tarwatsewa. Ƙarfe 5:30 ya iso Zaria, a matuƙar gajiye ga baƙin ciki da takaici, perking motar shi yayi ya nufi cikin gidan. Da sallama ya shiga falon ganin Daddyn shi a falon, "Sannu da gida Daddy" ya faɗa yana nufar kwanar ɗakin shi, "Safwan!" Daddyn shi ya kira shi, Safwan na shirin shan-kwanar ɗakin yaji kiran Daddyn nashi, yaji haushi sosai na kiran don baya so Daddyn shi ya gane halin da yake ciki. "Safwan ya na ganka yau, kai da kace se gobe zaka dawo" "Ehh Daddy na canza shawara ne" "Ok, wai baka ga munyi baƙuwa bane?" "Ehh, Daddy waye?" "Ƴa ta Salmah mana" "Salmah!" Ya faɗa a zuciyar shi, "Gata can a dining". Duban shi ya kai zuwa dining ɗin, Salmah ya gani fuskar ta ɗauke da murmushi, takaici ne ya cika shi, hanyar ɗakin shi ya nufa ba tare da ya sake kallon ta ba. Yana shiga ɗakin ya faɗa kan kujera dafe da kan shi, da yake mai bala'in ciwo. A falo kuwa Daddy ne yake cewa Salma "Salmah se kinyi haƙuri sosai da Safwan, domin wani irin mutum ne me yuwan sha'ani" "Bakomai Daddy Insha Allah zanyi haƙuri" "Yawwa ƴar albarka, yanzu kije ki same shi ku gaisa se ki fito driver ya kai ki gida" "To Daddy" Salmah ta faɗa tana miƙewa da sauri don tayi kewar Sweet ɗin nata don anyi hutun school" Murɗa kofar tayi taji ta a buɗe, da sallama ta shiga ɗakin, can ta hango shi a kujerar idon shi a rufe, kusa da kujerar ta ƙarasa, "Yaya Safwan!, Yaya Safwan!" Ta kira sunan shi, be amsa ba kuma be ɗago ba. "Yaya Safwannn!!!" Ta faɗa da ɗan ƙarfin ta, Cikin zafin nama ya miƙe tsaye, Ba zato ba tsammani taji ya yarfa mata wani kyakkyawan mari, Wani razanannen ihu ta saki tayi tagal-tagal zata faɗi, cikin zafin nama ya taro ta don akan kwalba zata faɗi wurgi ya ƙara yi da ita wajen ƙofar ɗakin, "Uban waye ya baki damar shigo min ɗaki?, har kina min ihu a kai, ke daƙiƙiyar ina ce?" Salmah miƙewa tayi fa karkaɗe jikin ta, tare da share hawayen da suka wanke mata fuska sannan tace "Yaya Safwan da'ace zan iya cire soyayyar ka a cikin zuciya ta da tuni na cire, domin kaso wanda baya son ka babbar wahala ce, a kullum ina roƙon Allah ya yaye min soyayyar ka duk da anyi mana baiko, amma a kullum kamar ana ƙaramin son ka ne, Ya Safwan miye laifina don zuciyata ta kamu da ƙaunar ka, don Allah ka agaza min ka furta min kalaman so, zuciyata zata yi sanyi, ko so ɗaya ne kace kana so na mana" Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, Jikin Safwan yayi sanyi sosai, don se yanzu ya dawo hayyacin shi. Wajen da take ya ƙarasa tare da cewa "Kiyi hakuri Salmah ina cikin wani hali ne, ki share hawayen nan kar Daddy ya gani don Allah" "To yaya Safwan, amma me yake damunka ne?" "Ba abun da ya shafe ki bane, ki tafi gida za muyi waya anjima" "Ka tabbatar?, Haka kake cewa nayi ta kira baka ɗauka ba kuma" "A'a ni zan kira ki da kai na ma" fara'a ne ya wanzu a fuskar ta Murmushi tayi tare da cewa "to se anjima" sannan ta buɗe ƙofar ta fita, Tsaki Safwan yayi sannan ya nufi Bedroom ɗin shi domin yin Sallar la'asar da ta riske shi a hanya. Yana shiga wayar shi ta ɗauki ƙara alamar shigowar kira, da sauri ya duba don ganin me kiran nashi. MY MOMCY Sunan da ya gani kenan, cigaba da tafiya yayi bayan ya saka wayar a aljihun shi, kira ne ya sake shigowa bayan waccan ya yanke, ciro wayar yayi ya ɗauka tare da kara wa a kunnen shi "Safwan ina ka shiga ne kasa hankalin mu ya tashi" "Momy na taho gida ne" "Wani gidan?" "Momy ina Zaria, na dawo tun ɗazu ma" "Har kake faɗa min kana Zaria, ba sallama ba komai, se dai na neme ka na rasa ko?, hakan ka kyauta kenan Safwan!?" "Haba Momy kiyi hakuri" "Shikenan ka kyauta" tana kaiwa nan ta kashe wayar. Safwan cilli yayi da wayar kan a kan gadon shi, sannan ya nufi toilet ɗin. Minti10 yayi cikakku sannan ya fito ɗaure da tawul, gaban miron da yake ɗakin yaje, mai kawai ya shafa a jikin shi se ya fesa turare sannan ya zura wata baƙar jallabiya, darduma ya shinfiɗa tare da tayar da sallah. *****KATSINA***** Se wajen ƙarfe 2:00 sannan suka gama girkin, a mutuƙar gajiye Safnah ta nufi ɗakin ta domin yin wanka, itama Meenal ɗakin su ta nufa, Hindu kuwa tana part ɗin su Teemah. Safnah tana shiga ɗaki ta zube akan kujera don ji take kamar kanta ze tsage tsabar ciwo da yake mata, bata yi aune ba bacci mai nauyi ya ɗauke ta. Se wajen ƙarfe 3:15 sannan Meenal ta shigo tashin ta. Miƙa Safnah tayi tare da miƙewa ido ta tsurawa Meenal ta kasa magana ma. "Ki zo yaya Abdul yana kira" "Har ya iso ne?" "Ehh tun ɗazu ma". "Don Allah ki jira ni, wanka zanyi tun ɗazu bacci ya kwashe ni, bari nayi shaf-shaf" "To yi sauri". Meenal ta faɗa tana zama a kujerar da yake falon. Cikin mintuna15 Safnah ta fito sanye da doguwar riga Blue colour yayi mata kyau sosai se wani hula da ta ɗaura pink colour mai kamar na sanyi amma kuma shara-shara ne, ko hoda bata shafa ba se man baki da ta saka fuskar ta se tayi fresh sosai. Jerowa suka yi suka fito, can ta hango yaya Abdul ɗin su biyu ne a dining ɗin, basu gan su ba, kasancewar sun juya musu baya ne. Da sallama suka ƙarasa wajen, amsawa sukayi "Ina wuni yaya Abdul" Safnah ta faɗa "Lafiya lau Safnah" juyawa tayi ta gaishe da ɗayan kyakkyawan saurayi ne sosai gashi fari kamar Balarabe, cikin shi da Abdul bansan waye gwanin kyau ba. "Safnah tun ɗazu na iso na tambaya aka ce kina bacci" Safnah bata ce komai se sunkuyar da kai ƙasa tayi, don wata irin kunya take ji kamar ta nutse ga kallon da abokin yaya Abdul yake mata, bata son kallo ko kaɗan. "Safnah wannan shine Umar (Faruq) kuma babban Abokina ne, kuma aminina ne shi, ɗazu baki nan na gabatarwa su Hindatu shi" Safnah bata ce komai ba har yanzu, neman hanyar guduwa ma take yi. "Safnah ki same ni a ɗaki zanje nayi Sallah don naji ana kira" cewar Meenal tana yin gaba. "A'a muje kawai nima banyi ba ai" Safnah tace tare da bin bayan Meenal. "Kai Abokina ƙannen naka har guda nawa ne, naga basu ƙarewa" cewar Faruq. "Kai! Ai a ƙannena baka ga komai ba ma" "Lallai ne babban yaya, ni kuma kaga Ƙanwa ta guda ɗaya ce Ummu Salma, ina son ta Sosai, amma kasan menene aboki?" "A'a se ka faɗa" "Wallahi ƙanwar ka ta tafi dani sosai" "Wacce kenan?" "Wannan da naji ka kira Safnah" "Lallai yaro to wannan anyi mata miji da kake gani" "Kasan yadda zaka yi, ya haƙura ya barmin ita kawai" "Lallai ma to an kusa bikin ma" "Gaskiya a fasa wallahi" dukan wasa Abdul ya kaiwa Faruq tare da cewa"ɗan rainin wayo matar tawa ne kake so" Dariya sosai Faruq yayi sannan yace "dai-dai ma kenan tunda kaine Seka haƙura ka barmin" Dariya Abdul yayi tare da cewa"gaskiya fa ka haƙura domin wannan bazan iya barin maka ita ba, kayi biyayya na baka wata ƙanwar tawa dai" "Yawwa babban yaya wacce a ciki?" "Biyun nan da ka gani Hindatu da Meenal suna da wanda suke so, wata ce anjima zaka ganta" "To shikenan muje muyi sallah nazo na ƙara abincin nan don yayi min daɗi sosai" "Girkin ƙanwata ce" "Ƙarya haramun fa" Faruq ya faɗa, lokacin har sun kai ƙofar fita falon. Basu suka dawo gidan ba se ƙarfe 5:15 lokacin su Safnah duka suna falo suna kallo, ƙarasawa sukayi suka zauna, hira suka cigaba da yi. Abdul ne ya matso saitin kunnen Faruq tare da cewa "Mallam ka daina kallon min mata fa, kar kaji naushi yanzunnan" Dariya Faruq yayi tare da cewa "ayi min afuwa Oga" shi da ƙarfi ya faɗa, saɓanin Abdul da yayi mai raɗa, hankalin shi yana kan Safnah yana lura da halin da take ciki kamar bata da lafiya gashi taƙi sakewa sosai yau. "Hindatu ki je ki kira min Teemah, ku taho tare yanzu fa" "To" Hindatu tace tare da miƙewa ta nufi hanya" "Yaya yaushe zaka koma ne?" Cewar Meenal. "Ai se nayi one month kafin na koma" "Kai naji daɗi sosai amma" "Abba ya faɗa muku za'a yi baikon ku keda Hindatu a cikin wannan satin?" Rufe fuska Meenal tayi, tare da gyaɗa kai alamar Ehh, "To yayi kyau se a cigaba da karatu idan an shiga ɗaki ko" "Insha Allah Yaya, Teemah kuma tace se ta fara karatu kafin nan" "Ki ƙyale ta, tana da taurin kai ne Fatima amma Abba yace duk tare za'a yi nan da two months2" Dafe ƙirji Meenal tayi tare da cewa "yaya two months2 fa, ai yayi kaɗan wallahi". Dariya sosai Abdul yayi sannan yace "lallai ai kuwa Baba babba har ya saka ranar ma" "Ka ga kana da bukukuwa da yawa, ƙanne har nawa, kasan bikin Salmah na saura One month1 shima" cewar Faruq "Kai! Haba ashe biki ya matso" "Ehh mana" Dai-dai lokacin su Teemah da Hindatu suka shigo, da sallama. Amsa musu sallamar suka yi, cikin falon suka ƙaraso, Hindatu ta zauna a inda take, ita kuma Teemah can kusa da yaya Abdul ta nufa cikin fara'a take cewa "Babban yaya kenan, kace har ka iso, to ya hanya kuma ya aiki" "Lafiya lau" Abdul yace. "To naji kira ne, ance kuma idan kaji kira samu ne, tsarabar tawa ce aka kawo?" "Ehh! Amma baza ki iya zama bane kika tsaya min a kai kamar sanda" "Allah ya huci zuciyar babban yaya" Ta faɗa tana yin baya don zama, cikin rashin sani ta zauna a kan Safnah wanda yanzu jikin nata yayi tsanani sosai don ji take kamar kanta ze rabe gida biyu, ƴar ƙaramar ƙara ta saki a wahalce. Dasauri Yaya Abdul ya tashi ya nufo wajen ai kafin ya kawo Teemah ta ruga da gudu tabi hanyar kofa. Muryar shi ta jiyo yana cewa "Teemah idan kika kuskura kika bar falon nan se kin ɗanɗana kuɗar ki wallahi". Cak! Teemah ta tsaya don tasan karon ba daɗi. Safnah kuwa har hawaye sun fara bin fuskar ta, "Sannu Safnah bata ji miki ciwo ba ko?" Gyaɗa kai Safnah tayi, daƙyar tace "zanje nasha ruwa" "Hindu ɗibo mata ruwa tasha" "A'a yaya bari naje" ta faɗa tare da miƙewa cikin sauri har tana haɗa hanya. Sum-Sum Teemah ta fara tahowa don dawowa, har gurin Ya Abdul ta nufa ta duƙa a gaban shi tare da kama kunne tace "yaya Abdul kayi hakuri wallahi ba da sani na ba na zauna a kanta ba, Allah kuwa" "Zamu haɗu ai jeki zauna" waje ta samu ta zauna tana dariya ƙasa-ƙasa, bata san Abdul yana kallon ta ba, har da ɗagawa Meenal gira. Faruq kuwa ya zama kamar kurma se ido ba baki, Teemah kawai yake kallo, Abdul ne ya ɗan taɓa shi ya waigo, da ido yayi mai alama da ya tashi su shiga ciki. Tare suka miƙe suka nufi ɗakin Abdul ɗin. "Ya! Abokina ya ka ganta ne" cewar Abdul yana tura ƙofar. "Kai! Masha Allah wallahi nayi mata in sha Allah tayi sosai, kasan miye ma?" "A'a se ka faɗa" "Wallahi tafi ɗayar nan ma kyau, gata da baki, ni nafi son me baki ma wallahi ba kamar ɗayar ba" "Ai kai kace, amma ni nafi son natsatstsiyar yarinya mai hankali" "Au kana nufin matar tawa ba nitsatstsiya bace kenan" "Kaji wani magana, a ina ta zama Matar taka, kayi biyayya yaro ka samu Teemah, kasan a hannuna komai yake" "To naji babban yaya, yanzu ya za'ayi kenan" "Daɗi na da kai naci da ƙosawa, ka jira zanyi magana da ita" "Matsalata da kai nuƙu-nuƙu da jan magana tayi tsayi, ni ason raina yanzu kawai ka sameta" "Kai dai ka bari gobe in sha Allah zan haɗa ka da ita" "To naji" "Taso mu koma falon" Cewar Abdul, tashi sukayi don dawowa falon. Suna nan zaune a wajen da suka bar su, suna hira, amma Safnah bata dawo ba. "Ina Safnah?" Abdul ya tambaya don be ganta awajen ba. "Bata dawo ba fa" cewar Hindatu. "Jeki ki kira min ita" "To" Hindatu tace tare da miƙewa ta nufi ɗakin Safnah. Safnah kuwa tunda ta bar wajen daƙyar ta ƙaraso ƙofar ɗakinta ma, tana zuwa kuwa jiri ya ɗibeta ta faɗi a kofar, kuka ta saki don ita kaɗai tasan abunda take ji a jikinta, tafi mintuna goma10 a ƙofar kafin daƙyar ta yunƙura ta tashi ta shiga ciki, tana shiga a kujerar falon ma ta zauna, zuciyar ta na wani irin bugu da ƙarfi ga wani tari da ya kamata lokaci guda daƙyar ta miƙe don zuwa ta ɗauko ruwa a firij ɗin dake ɗakin, kafin ta ƙarasa wajen ta zube ƙasa sumammiya. Hindatu na buɗe ɗakin idon ta ya sauka akan Safnah da take ƙasa kamar gawa, da gudu ta ƙarasa wajen, jijjigata ta shiga yi, amma bata ko motsi, cikin tashin hankali ta juya da gudu zuwa falon. Suna zaune a falon har yanzu, suna ganin Hindatu a guje duka suka miƙe tsaye. "Meya faru Hindatu" Cewar Abdul, "Yaya Safnah ta.....!ta.......!" "Ta mene!?" Be tsaya jin me zata ce ba yayi gaba duka suka bishi a baya. "Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un" Abdul ya furta lokacin da ya hango Safnah yashe a ƙasa, dai-dai lokacin su Meenal da Faruq suka ƙaraso, tashin hankali sosai suka shiga suma. "Hindatu ku kama ta ku fito da ita waje, Bara na ɗauko mota" Abdul ya faɗa tare da juyawa da sauri ya nufi waje Faruq ma bin shi yayi. Su uku suka kama Safnah zuwa wajen da motar yake, suna fitowa suka shiga don Abdul ma har ya kunna motar sun shiga, hanyar gate ya nufa da gudun gaske.  ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_23&24 *****Zaria***** Shirye-shirye sosai Daddyn Safwan yake na biki, ana ta gyaran gidan da zasu zauna a unguwar su gidan yake ya haɗu sosai, yanzu ana maganar lefe ne da za'a haɗo nan da sati ɗaya, don yanzu bikin saura sati Uku ne. Shi ko mai gayya mai aiki Safwan ko a jikin shi, don gani yake kamar wasa ne ma wannan auren ba gaskiya bane. Gidan su Salmah ma shiri ake sosai kasancewar ta ƴa ɗaya tilo mace, kuma ga kuɗi da suke da shi. *****KATSINA***** Emergency room aka wuce da Safnah lokacin da suka isa asibitin, kowa ka gani hankalin shi a tashe, Abdul har ya kira Baba Babba da Baba Bashir suna asibitin suma. Har yanzu ba'a buɗe ɗakin da aka shiga da Safnah ba, duk suna zaune suna jira yayin da Abdul zama ya gagare shi, se yawo yake don yafi kowa damuwa. Kusan awa ɗaya1 sannan aka buɗe ɗakin, doctor Nurses suka fito, kai tsaye wajen da suke zaune Dotor ɗin ya nufa. "Waye mahaifi ko mijin mara lafiya ya biyo ni" cewar likitan yana yin gaba. Baba Bashir ne ya tashi ya bishi, mintuna biyu2 bayan shigar shi ya fito ya dawo ya zauna. Abdul yana so ya tambayi Baba Bashir me yake damunta amma ya kasa, gashi yana son sani, wata shawara ce ta zo mai, ƙarasowa yayi wajen da suke yace "Baba an rubuta magunguna ne" "Ehh Abdul ga takardan nan ka je ka siyo" "To" Abdul yace tare da ƙarɓar takardan ya nufi ciki. Kai tsaye ofishin likitan ya shiga da sallamar shi, amsawa likitan yayi tare da yi mai alama da ya zauna. Zama yayi akan kujerar da take kallon likitan sannan yace ."Doctor dama akan mara lafiyar da muka kawo ne, don Allah menene yake damunta?" Ido likitan ya tsira mai na wasu sakonnin sannan yace, "Ai na riga nayi bayani ma wanda ya fita, ba shine mahaifinta ba?" "Ehh shine, amma ni yayanta ne ni, kaga ko ina da hakki na sanin me yake damunta "Ok ƙanwarka jininta ya na gaf da hawa ne sanadiyyar damuwa da take fama dashi, wanda ya haddasa mata barazanar kamuwa da wannan ciwon, kuma idan ba'a ɗauki mataki ba, abun ze cigaba ne har zuwa inda bamu fata, amma idan ta cigaba da shan magungunan da aka rubuta mata zata samu sauƙi sosai. Gumi ne ya ƙaryowa Abdul sosai najin abinda Doctor yace, ya za'ayi ace yarinya kamar Safnah ta gamu da hawan jini. "To Doctor mun gode in sha Allah za'a kiyaye shan magungunan da aka rubuta, Mungode" ya faɗa tare da miƙewa ya nufi waje. Lokacin da ya fito ya samu su Baba na shirin fita har da Faruq, kasancewar kiran sallar Magriba da ake yi, shima bin su yayi don zuwa yin nashi sallar shima. Bayan sun idar su Baba gida suke wuce yayin da Abdul da Faruq suka dawo ɗakin da aka kwantar da Safnah. "Har yanzu bata farfaɗo ba" Abdul ya faɗa yana kallon Teemah da ta tsura mai idanu. "Ehh yaya shiru wallahi har yanzu" Hindatu ta bashi amsa "Yaya ashe Umma ce zata kwana da ita, ta kira ni tace min tana hanya ma" cewar Teemah "Ehh ni na kira ta!, Ku gida zamu wuce da ku, se ku bar ɗaya ta taya Umma kwana" Yana rufe baki kuwa suka ji sallamar Umma (Mahaifiyar Teemah) gaishe da ita su kayi duka, amma banda Faruq kasancewar baya ɗakin. "Ya jikin nata ne Abdul?" Umma ta faɗa fuskarta ɗauke da tsantsar tausayin Safnah. "To Umma gata nan dai!, Da sauƙi za'a ce" "Subhanallahi! Allah ya bata lafiya" "Ameen" Duka suka amsa dashi. Mintuna talatin30 da zuwan Umma suka kama hanya don tafiya gida, lokacin ma kusan ƙarfe 9:12 ne, Hindatu aka bari don taya Umma kwana yayin da suka kamo hanyar gida. Lokacin da suka iso gida 9:30 kowa part ɗin su ya nufa, Teemah taso ta taya Meenal kwana kasancewar Hindu abokiyar ta ta tana asibiti. Meenal kuwa ɗakin Kaka ta nufa don bazata iya kwana ita kaɗai ba, ba abokin hira. "Faruq ina cikin tsantsar damuwa da halin da Safnah take ciki, ina jin yau daƙyar idan zan iya bacci!" Cewar Abdul dake kwance a 3siter da take falon ɗakinshi. Gyara zama Faruq yayi tare da kallon abokin nashi yace "lallai ne abokina ka kamu sosai, amma ina mamakin wannan abu haka, kace Safnah ba a gidan nan ta taso ba, hasalima bata daɗe da dawowa gidan nan ba!" "Faruq kenan!, Baka san so ba, tunda kai ko budurwar ma baka da ita, amma wallahi tun ranar da na fara ɗaura idanuna akan Safnah Bayan dowawar ta matsanancin son ta ya shiga cikin rai na, a da na ɗauka wasa ne, amma yanzu na tabbatar in dai ba Safnah rayuwata tana cikin wani hali" "To Allah ya kyauta!, Amma kuma kace min Safnah bata san cewa kana son ta ba, to baka gani hakan matsala ce!, Duba da kace min duk aure za a musu kaga Safnah na iya bayyana wani ba kai ba, to ƙaddara ma bata da wanda take so, kai kace auren haɗi za'ayi idan mutum be fito da wanda ze aura ba!" Miƙewa Abdul yayi da sauri sakamakon wani tunani da yazo mai, ya tuna wayar da su kayi da Sadiq jiya yake faɗa mai ya samu matar aure a cikin Familyn su. Da sauri Abdul ya jawo wayar shi, Number Sadiq ya lalubo tare da danna mai kira. Gaf da wayar zata yanke Sadiq ya ɗaga "Assalamu alaikum babban yaya" Sadiq ya faɗa daga can bangaren "Sadiq jiya muna waya baka faɗa min wacce yarinya bace kake so ba" Dariya Sadiq yayi daga can sannan yace "Akan wannan ka kira ni babban yaya!" "Sadiq bana son wasa fa tambayar ka nayi" "Saurin me kake yi, zan gabatar da ita ma kowa ranar Family meeting kasan ya kusa" "A'a ni yanzu nake son ji!" "To shikenan ka canka, wacece tafi kowa kyau a cikin matan Familyn mu" Yanke wayar Abdul yayi zuciyar shi na dukan tara-tara, yasan halin Sadiq tunda ya mayar da maganar wasa ba ze faɗa mai ba. "Lafiya Abokina" Faruq ya faɗa ganin yanayin da abokin nashi yake ciki. Labarin yadda suka yi da Sadiq ya bashi ya ƙara mai da cewa "yace wacce tafi kyau a Familyn mu" Da sauri Faruq ya miƙe tare da cewa "kar dai ace Teemahna! Don wallahi tafi kowa kyau duk da ban ga sauran ba" Duk da halin da Abdul yake ciki se da yayi dariya sosai, bayan ya tsaya da dariyar ne yace "Lallai aboki ka faɗa da yawa, kaima kenan yau fa kuka haɗu amma har kake jin tsoron rasa ta!, To ni kuma nace mene?" "To Allah ya kyauta!, Abin yi dai Shine kafin na wuce muje mu samu Sadiq, bayan ya bayyana mana ba ita bace, se na samu gimbiyar tawa, don da dukkan alamu idan na tsaya jiran ka zan rasa Teemah, tunda kaima naga baka ƙarfafa taka soyayyar ba, bare nawa" Faruq ya ƙarasa maganar yana yin dariya. Shima Abdul dariyar yake yi, haka suka cigaba da hirar su cikin nishaɗi, don idan suna tare koda ɗaya yana cikin damuwa, ɗayan ze yi ƙoƙarin mantar da ɗaya damuwarsa. Washe gari Tunda su Abdul suka tashi sallar asuba ya je ɗakin Kaka ya faɗa wa Meenal ta haɗa mu su abun break fast na asibitin, domin zuwa ƙarfe 7:00 su ke son komawa asibitin. Zuwa 7:00 suka fito se da suka karya sannan suka fito suka nufi asibitin. Zuwa ƙarfe 7:25 suka isa asibitin, kai tsaye ɗakin da aka kwantar da Safnah suka nufa da sallamar su. Kai tsaye idanun Abdul suka sauka kan Safnah da Umma ke bata Tea a baki, farin ciki ne ya luluɓe shi, da sauri ya ƙarasa tare da gaishe da Umma, Faruq ma gaishe ta yayi. "Umma ashe ta farka!" "Ehh Abdul!, Tun jiya ma, kun fita ba daɗewa ta tashi" "Safnah ya jiki?" Faruq ya faɗa "Da sauƙi, ina kwanan ku ya Abdul" Safnah ta faɗa da Muryar ta can ciki, irin ta mara lafiya. "Lafiya lau Safnah ya jikin naki?" "Yayi sauƙi" "Umma ga break fast nan, a ina kuka samu kayan Tea" "Sadiq ya kawo, tun jiya ma!" Gaban Abdul ne yayi mummunan faɗuwa, kar dai ace tunanin da yake ya zama gaskiya. Muryar Umma ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, ji yayi tana faɗin "Lokacin da ta farka se tace yunwa take ji, gashi bamu taho da abinci ba, se Hindu ta kira shi ta faɗa mai saboda shine yafi kusa da asibitin, ga kuma dare yayi lokacin" Abdul ya ɗan samu natsuwa kaɗan "amma ya zama dole naga Sadiq yau" ya faɗa a zuciyar shi. *****ZARIA***** Safwan ne shi da Kamal da kuma Daddyn shi suna magana akan bikin shi da yake saura kwana 18 yau. "Daddy nifa bana son ayi wani Event a bikin nan bayan walima" cewar Safwan "To shikenan tunda haka kace, amma son samu ne ace anyi, nasan can gidan su yarinyar baza a rasa shiryawa ba" "Daddy kar ka bi maganar Safwan!, Ya za'ayi ace biki Kamar na Safwan a garin nan ayi shi hakanan ba komai, ai wannan ze iya taɓa darajarmu' cewar Kamal "To Kamal naji naka kaima, ku zauna kuyi shawara duk halin da ake ciki dai kuyi min waya se na turo muku da kuɗin da ze ishe ku, don zuwa jibi in sha Allah nake son wucewa, ina jin kuma zan kai ana saura kwana uku biki kafin na dawo" "To Daddy mun gode" cewar Kamal. Tashi suka yi suka nufi ɗakin Safwan don yin shiri don yau ma akwai wajen da za su je, shine ma makasudin zuwan Kamal gidan. *****KATSINA***** Su Abdul na zaune a asibitin, dangi ne ke ta zuwa gaishe da Safnah, don da yawa basu ji ba se yau, iyayen su da yara duka sun zo sun gaishe da ita, mutum ɗaya ne bata zo ba, Antyn su Abdul (matar Baba Salihu) don ba ko ina take zuwa ba. Abdul ganin mutanen da suka zo yasa su fita kai tsaye gidan su Sadiq suka nufa shi da Faruq. Ba kowa a gidan se Sadiq ɗin don yaran na makaranta momy kuma ta na asibiti wajen. Da sallama suka shiga ɗakin Sadiq ɗin yana zaune gaban system ɗin shi, rufe system ɗin yayi tare da amsa sallamar su fuskar shi ɗauke da Murmushi. "Ɗan rai nin wayo, se yawo da hankali kake min, to gani na zo gidan" Dariya Sadiq yayi tare da cewa "Kai! Babban yaya ko dai ka na son wata ne a cikin Familyn mu" "Ina ruwan ka!" "Ai na riga na ɗano jirgin ka, akwai wacce kake so wallahi, to ni dai Sa'adatu nake so kuma take so na" Ajiyar zuciya Abdul ya sauke tare da mamaki yace "Yaushe har ku ka fara soyayya da Sa'adatu?, Ya akayi kuma babu wanda ya sani" Abdul ya faɗa "Ai tsohon labari ne, don mun fi shekara ɗaya1 muna soyayya, kasan Sa'adatu bata da surutu baza ka taɓa ji a bakin ta ba, amma Momyn su ta sani, se kuma Teemah to su ne kawai suka sani" "To yayi kyau ashe shiyasa nake ga kake yawan zuwa gidan ko?" "Ehh mana, to kai wacce kake so a ciki?" Murmushi Abdul yayi tare da miƙewa yace "zaka gani ba yau ba" "Ok kai ta dama" "Se anjima abinda na zo ji kenan dama" Abdul ya faɗa tare da fita daga ɗakib. Kai tsaye gidan su ya nufa, a falo ya samu su Teemah Hindu da Meenal, har ma da Sa'adatu sun yi shiri da alama akwai wajen da zasu je ne. Gaishe da su su ka yi sannan Abdul yace "Sa'adatu bani wayar ki" Bata yi musu ba ta miƙa mai, ɗakin shi ya nufa tare da faruq. Yana shiga kuwa ya saka Number Sadiq yayi dialing a wayar Sa'adatu "My Husband to be" yaga sunan ta fito, dariya ce ta suɓuce masa ba tare da ya shirya ba, nuna wa Faruq sunan yayi shima dariya yayi. Danna kira yayi ringing ɗaya Sadiq ya ɗaga "Hello my sweet" Sadiq ya faɗa Dariya Abdul yake yi har yanzu, wanda ya tabbatar wa da Sadiq ba sweet bace ta ɗaga wayar. "To Sarkin soyayya ni ne ba Sweet ɗin ba" Abdul ya faɗa "Kai! Amma ka Bala'in rai na min wayo, me ya kawo wayar Babyna hannun ka?" Dariya Abdul yayi tareda cewa "Lallai yaro baka da kunya ni kake ce wa Babyn ka, ashe zan yi sizin ɗin wayar nan" "To se mene, zuwa anjima zaka gan ta da wata" Sadiq ya faɗa tare da yanke wayar. Abdul ma sauke wayar yayi yana dariya Se yanzu ya kai duban shi wajen da Faruq yake zaune wayam! Ya gani bashi, tasowa yayi ya fito falon Sa'adatu ya bawa wayarta bayan ya goge Number Sadiq da ya kira. Har a falon be ga Faruq ba, hakan yasa shi fitowa waje. Can ya hango Faruq shi da Teemah a wajen motar da suka zo gidan, suna hira, sosai abun ya ɗaure mai kai, komawa yayi ba tare da ya bari sun gan shi ba. Ɗaki ya koma cike da tunani iri-iri, Faruq se da ya ɗauki wajen mintuna 25 sannan ya dawo ɗakin da sallamar shi. Zama yayi kusa da Abdul yana waƙar "dama dake na fara haɗuwa da nayi aure tun tuni zama dake akwai ƙaruwa, ni dalling kina burgeni, wayyo!" Abdul idanu ya zuba mai, ba tare da yace komai ba, Se da Fatuq ya gama sannan yace "abokina gaskiya ni mai sa'a ne wallahi, don na riga da na sace zuciyar Teemah" "Kai da gaske kake don Allah?" "Wallahi kuwa ta amince zata aure ni, wayyo daɗi!" "To na taya ka murna, Allah ya tabbatar da alkhairi" "Ameen" "Nima ka taya ni addu'a, Allah yasa Safnah ta ƙarɓi soyayyata" "In sha Allah" Faruq ya faɗa. "Gobe zaka wuce Kaduna ko?" "Ehh wallahi gida an matsa min na dawo, momy bata san na samo mata suruka ba" "Lallai kam! Kaga da'ace lafiya lau da na bi ka mun tafi, amma kafin bikin Salma ina nan zuwa " "To shikenan, momy kuwa tana son mu taho tare wallahi" "Ka bata hakuri kace mata ina nan zuwa" "To shikenan". Zan tsaya anan Ku biyo ni a cikin littafin nan yanzu ma aka fara, shin Safnah zata ƙarɓi Soyayyar Abdul kuwa? To idan ta Karɓi soyayyar shi ya zata yi da Safwan? Maganar auren Safwan ya matso shin za'a yi auren ko kuwa Safwan ze zauna ya jira dawowar Safnah ya faɗa mata yana son ta? Shin wai Safwan da Safnah za su sake haɗuwa ma? Duk amsoshin ku na nan cikin wannan littafi, ku dai ku kasance tare da ni, Nagode Taku har kullum Khadeejerh Ishaq ✍️ ce More comment more typing Share pls ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_25&26 *****ZARIA***** Washegari Faruq sammakon shiri yayi don tafiya gida, kasancewar kwanan shi biyu anan, ƴan gidansu na ta kiran shi, don sunyi kewar shi, watan shi huɗu4 rabon shi da gida. 7:30 su ka fito shi da Abdul, don se sun fara zuwa asibiti sun duba Safnah daga nan se ya wuce. Zuwa 7:45 su ka isa asibitin, Safnah ta ji sauƙi sosai, har yau Umma ne ke tare da ita a asibitin, yayin da su Hindu kuwa asibitin ya zaman mu su wajen zuwa akai-akai. Sun samu Safnah ma tana cin dankali ne haɗe da tea, zama su ka ɗan yi na wa su mintuna, Abdul kuwa se satan kallon Safnah yake don baya gajiya da ganin ta, gashi bashi da hoton ta ko guda ɗaya. Ƙarfe 8:15 su ka baro asibitin, kai tsaye airport su ka nufa kasancewar Faruq jirgi ze bi. Suna isa ana sanarwar tashin jirgin na su nan da mintuna10 hakan ya basu damar tattaunawa. "Faruq ka gaishe da Momy da sauran mutanen gidan, ka bawa momy hakuri kace mata ina nan zuwa nan da two days" "Ok kar ka damu, amma fa idan ka zo se biki zaka dawo ko?" Dariya Abdul yayi tare da cewa "wata ɗaya fa kenan, ai se ku kore ni" "A'a fa ba wata ɗaya ba ne, yau saura 17days ni ne ba na lissafi dai-dai ashe nace maka saura 1month, amma jiya Momy ke faɗa min ai saura 17" "Ok hakanan yayi yawa, se na zo dai" "Ok" Faruq ya faɗa tare da juyawa yana ɗaga mai hannu, shima Abdul hannun ya ɗaga mai, har jirgin su ya tashi, sannan Abdul ya juyo cike da kewar Abokin nashi da yake ji tamkar ɗan uwan shi, kai tsaye gida ya nufo don wani irin bacci yake ji sosai. A falo ya samu su Meenal na hira, gaishe da shi su kayi sannan ya wuce zuwa ɗakin shi. "Meenal yaushe za mu ko ma asibitin ne?" Cewar Hindu. "Ai ki bari kawai ayi sallar azahar, Teemah ma tace zata je" "Ok to shikenan" "Hindu kinsan menene kuwa?" "A'a se kin faɗa!" "Ina wannan abokin yaya Abdul ɗin" "Ehh, Yaya Faruq ki ke magana" "Ehh shi, to shine yake son Teemah" "Keeee! Meenal bana son ƙarya wallahi" "Billahil azimu kuwa!, Ɗazu da muka yi waya take faɗa min, kuma jiya baki gan su suna hira ba?" "A'a hankalina bai kai can ba gaskiya" "To ai Sa'adatu ta gani" "In dai hakane kuwa na taya ta murna!, Domin daga ganin shi mutumin kirki ne wallahi, gashi ya haɗu wallahi" "To kinsan dai halin Teemah, ba lallai ta karɓi soyayyar shi ba" "Ai kuwa da ta yi asara, ai irin shi mata ke rubibin samun, ga kyau ga kyawun hali" "To mu miye amfanin mu indai bamu sakata taso shi ba" "Hakane sister, amma kinsan Teemah da kafiya ko?" "Hakanan dai" Haka suka cigaba da hirar su kasancewar ba aikin da zasu yi, mai aiki ne take mu su girki yau, kuma iya na su ne se kaka, don yaya Abdul bashi a lissafi daƙyar idan ze ci, asibiti kuma abinci ma yayi mu su yawa, don idan suka kai ma za su tarar da abinci kala-kala. *****ZARIA***** Safwan zaune gaban Dadyn shi suna kallon kayan da Anty ta haɗo na lefe, "Safwan kayan sunyi kuwa?" "Ehh Daddy" Safwan yace "To shikenan" amma a zuciyar Daddy har ga Allah ya rai na kaya, amma ya bari a zuciyar shi ne kawai. "Na so a kai kayan yau, amma a barshi kawai se na dawo, saboda ina son na ƙaro wasu" "To Daddy" Safwan ya faɗa tareda miƙewa ya nufi ɗakin shi. Yana shiga ɗakin shi ya faɗa gado, tare da dafe kan shi da yake mai bala'in ciwo, Computer shi ya jawo tareda kunna ta, wajen hotuna ya shiga hotunan Safnah ne birjik! A wajen, kan wani hoto yaje yayi Clicking yana son hoton sosai Safnah sanye cikin Pakistan riga da wando, blue ta yafa farin mayafi, kafarta sanye cikin wani farin takalmi mai ɗan tudu, ta ɗaga hannayen ta duka biyun kamar mai addu'a, ta yi masifar kyau, kamar ba bahaushiya ba. Safwan ya kasa ɗauke idanun shi akan hoton, baze taɓa manta lokacin da yayi mata hoton ba, lokacin da su ka je gidan kakan ta a Kano. "Allah ya mallaka min ke Safnah!, Allah ya dawo min da ke! Ya Allah ka ga zuciyata ya Allah ka yaye min damuwar da nake ciki, ya Allah ka canza min halayena, Allah ka shirye ni" Addu'a Safwan ke ta rero wa, yayin da Zafafan hawaye ke zubowa daga idanun shi, wani irin matsanancin son Safnah ne ke ƙara shiga zuciyar shi, ya rasa inda ze saka kan shi, ya je gidan Anty yafi a ƙirga ta bashi Number Safnah ta faɗa mai bata dashi, kuma ita ce kawai zata iya haɗa shi da Safnah a ganin shi. Number Safnah kuwa a kullum yana kira sau ba adadi amma a kashe, hakan na ƙara mai matuƙar damuwa, yayi rama sosai yayi duhu duk tsabar damuwar da ta addabi zuciyar shi, yana samun sauƙi ne kawai idan ya sha giya ya fita hayyacin shi. Hakan ce ta kasance, yana gama tunanin ya ɗauko kwalaben giyar nashi ya dinga korawa, har ya fita hayyacin shi gaba ɗaya, daga bisani kuma nannauyan bacci ya kwashe shi. *****JUSHI ZARIA***** Ƙarfe 10:00 a gida ta yi wa Faruq, iyalan shi na cikin farin ciki sosai da dawowar shi, don an daɗe ba'a haɗuba. Su huɗu zaune a katafaren falon na su na alfarma, Momyn shi, Daddyn shi, se ƙanwar shi Salmah, da ma su biyu iyayen su suka haifa, hakan yasa suke ganin soyayya sosai a wajen iyayen na su, da dangi gaba ɗaya. "Yaya ina abokin naka kace tare zaku taho?" Salmah ta tambaya. "Ehh mun so mu taho tare, amma kuma se wani abu ya tsare shi" "Allah Sarki Abdul, yaron akwai hankali sosai wallahi ga tarbiyya" cewar Daddyn Faruq. "Ehh wallahi yaron akwai kirki sosai" "Amma yace min zuwa nan da two days ze zo" Cewar Faruq "To yaya, Allah ya kawo shi lafiya" Salmah ta faɗa. "Faruq ka ga ƙanwar ka ta kusa yin aure, kai ma ya kamata ka fito da matar da zaka aura, ka ga ka girma sosai fa" Momyn Faruq ta faɗa Murmushi faruq yayi tare da cewa "Ai momyna ki kwantar da hankalin ki, na samu matar aure" "Masha Allah a ina take?" Daddy ya tambaya. "Daddy a Katsina take, ƙanwar Abdul ce" "Masha Allah, miye sunan ta" "Sunan ta Fatima!" "Yaya kace da walakin, goro a miya, shiyasa kaje kayi zaman ka a gidan mutane ashe ka samo budurwa ne" "Ehh wallahi ƴar uwa, baki ganta ba Masha Allah" "Nuna min hoton ta na gani yaya" Salmah ta faɗa. "To shikenan" Faruq ya faɗa tare da ɗauko wayar shi ya lalubo hotunan da yayi wa Teemah gudu biyu kafin ya taho dama yace zai nuna wa ƴan gidan su ne. Da sauri Salmah ta kwace wayar don ganin Antyn nata. Gaban ta ne yayi mummunan faɗuwa ganin wacce take cikin hoto, ta yi mata kama da wanda ta sani, cigaba da kallon hoton ta yi, nan taga tsantsar kamarta da Safnan Safwan. "To ya akayi haka!, Gashi kuma ance Safnah Katsina ta tafi dama" Maganar da Salmah take yi kenan a cikin zuciyar ta. Kwace wayar da faruq yayi a hannunta, shi ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, miƙawa momy wayar yayi don su ma su ga Sukikar ta su, sannan yace "Sister lafiya kuwa, ko bata miki ba ne" Murmushin dole Salmah ta kirkiro tare da cewa "yaya tayi mana, kuma ta haɗu sosai wlh" "To amma meyasa naga kin tafi tunani?" "Yaya tayi min kama da wata wacce na sani ne" "Tabbas se dai kama kuwa, don baki taɓa zuwa Katsina ba, bare ki san ta" "Ehh yaya" Salmah ta faɗa. "Masha Allah Babana yarinyar ta yi kyau sosai, amma kun gama magana ne?" "Ehh Daddy mun dai-dai ta, maganar aure kawai za'ayi. "Yaran zamani ba kunya, su ke maganar aure a gaban iyayensu, amma mu a da ai ko maganar aure ba muyi a gaban iyayen mu" Momy ta faɗa tana mamakin wannan abu haka. "Ki kyale su zamanin su ne, ai kowa da tashi zamanin" "Hakane kuma" momy ta faɗa tare da miƙewa ita da Daddy su ka nufi ɗaki, suka bar Salmah da Faruq. "Sister har yanzu ban san Ƙanin nawa ba fa! A ina yake?" Murmushi Salmah ta yi tare da rufe fuska, sannan tace "Yaya Safwan ne fa, ɗan gidan abokin Daddyn nan" "Ok! Alhaji Muhammad ko?" "Ehh shine" "Sunan yaron Muhammad ko?" "Ehh yaya, amma Safwan ake kiran shi ai" "Ok da nasan yaron sosai, amma tunda na daina zama sosai se na manta shi, ina jin ko a hanya dakyar zan gane shi, amma a ina ku ka haɗu ne sister?" "Yaya a School" "To Allah ya bada zaman lafiya, to me kike so nayi miki na gudummawar bikin?" "Yaya duk abinda ya samu ina so" "To shikenan bari naje ɗaki nayi wanka na zo na fita naga gari" "To yaya" Salmah tace tare da tashi itama ta nufi nata ɗakin. *****KATSINA***** Jikin Safnah yayi sauƙi sosai hakan yasa ma aka rubuta mata sallama ta koma. Zaune su ke suna hira a part ɗin su Teemah don tunda aka sallami Safnah yau kwana biyu 2 kenan part ɗin take zai ne, don sunyi wani irin sabo da Umma sosai don ji take kamar itace mahaifiyarta, su Hindu ma anan su ke wuni sosai se dare su koma, Safnah kuwa a ɗakin Teemah take kwana. A bangaren ya Abdul hakan yasa har yau be furta kalmar so ga Safnan ba, saboda ba su haɗuwa se dai idan ya je part ɗin Umma, kuma a gurguje yake zuwa. Yau ma kamar kullum Teemah ce da Safnan zaune a ɗakin Teemah suna hira wajen ƙarfe 8:30 na dare, kira ne ya shigo wayar Teemah, cikin sauri ta jawo wayar, don dama jiran kiran take tana jin ringing ɗin kuma ta gane shi ne, wato farin cikin ran ta (Faruq). Ɗaga wayar ta yi fuskar ta ɗauke da Murmushi "Assalamu alaikum gimbiyar mata" Faruq ya faɗa daga can ɓangaren. "Wa-alaikumussalam" Teemah ta faɗa da sassanyar Muryar ta, "Gimbiya ta da fatan kina lafiya?" "Lafiya lau masoyi na ya Momyna" "Momyna lafiya lau ya Ummata?" "Ta na lafiya" Safnah dai bin Teemah kawai take yi da ido tana sauraren hirar ta su, wanda ka na ji kasan tsantsar so da ƙauna sun zauna a wurin. Kusan mintuna talatin30 Teemah ta kwashe suna waya da Habibin nata sannan su kayi sallama. "Safnah kinsan menene?" "A'a se kin faɗa" "Wai dama haka so yake, a da ban taɓa tunanin zan faɗa soyayya nan kusa ba, amma wallahi haɗuwana da Faruq ya canza komai, ya canza min tunani na, ina masifar son shi, ta yadda ba na jin zan iya son wani bayan shi" Maganar da Teemah ta yi ya tono wa Safnah son Safwan da ta samu ya ɗan lafa kwana biyu2 kwalla ne suka cika mata idanu. Cikin ƙoƙarin kawar da kwallar tace "Teemah tabbas so babbar cuta ce, kuma lokaci ɗaya take shigar mutum ba tare da son ran shi ba" Tana ƙarasa maganar kuka ya kwace mata duk da ƙoƙarin da ta yi na danne kukan nata. "Subhanallahi!, Safnah lafiya kuwa?" Safnah bata ba Teemah amsa ba, se ma sautin kukanta da ya ƙaru. Daƙyar Safnah ta samu ta tsayar da kukan da take yi. "Safnan kin taɓa faɗawa tarkon soyayya ne?, Don nasan maganar da nayi ne yasa ki kuka" "Teemah tun zuwa na gidan nan nake fama da tsantsar damuwa na kewar masoyin da ban tabbatar da so na a zuciyarsa ba!, A kullum da tunanin sa nake kwana kuma dashi nake tashi" "Safnan to yaya akayi haka!, Kuma shi ɗin wanene?" "Teemah zuciyata ta amince da ke hankalina ya kwanta dake kuma ke kaɗai zuciyata ta amince da na faɗa wa sirrin da ba kowa ya san shi ba a rayuwana, shi wanda nake faɗa miki abokin karatuna ne kuma abokin shawarana, munyi shakuwa sosai wanda mutane ke cewa soyayya ce, amma kuma bamu yarda da cewa son junanmu muke yi ba, daga baya ne na fara tabbatar da cewa ina son Safwan saboda ko kwana ɗaya idan nayi ban ganshi ba, ba na jin daɗi, amma shi a ɓangaren shi na kasa fahimtar so na yake ko kuwa kawai abota ce" Safnah ta tsaya da maganar har yanzu hawaye na bin fuskarta, Teemah kuwa ta cika da mamakin lamarin Safnah, daurewa tayi tace "Safnan naji labarin soyayyar ki, amma ki sani da ace yana son ki da ze faɗa miki a gani na amma" "Hakane, amma wani ɓari na zuciyata yana faɗa min yana so na" "To shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ya kamata mu kwanta dare yayi, da safe se muyi magana" "To shikenan" Safnah tace tare da kwanciya. A ranar daƙyar bacci ya ɗauketa se tunane-tunane take yi. Zan tsaya anan Kuyi hakuri da wannan in sha Allah gobe zan yi typing da yawa. Ku kasance da ni a cikin wannan littafin nawa don jin yadda zata kaya, yanzu dai aka fara wasan, ina jin daɗin yadda kuke son wannan littafin nawa sosai ina muku fatan alkhairi da fatan anyi sallah lafiya. More comment more typing Khadeejerh Ishaq ✍️ ce  ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_27&28 **Washegari** Safnah ba ita ta tashi bacci ba, se ƙarfe 10:00 tana yin sallar asuba ta koma bacci don bata kwanta da wuri ba. Teemah kuwa tun asuba da ta tashi bata koma bacci ba, Kitchen ta shiga kasancewar ita take musu girki, bata tashi Safnan ba saboda tasan bata kwanta da wuri ba, ga jikinta har yanzu se a hankali bata samu ƙarfin jikinta ba sosai. A ɓangaren part ɗin su Hindu kuwa suna tashi su ma kicin suka nufa don ɗora abin kari suna gamawa kuma suka shiga gyaran babban falon na su da harabar gidan kasancewar yau suna da babban taro wanda suke yi duk bayan wata biyu a Familyn su, ma'ana (Family meeting) kuma a part ɗin su ake gudanar da shi. Ba su wani sha wahalar gyaran gidan ba, kasancewar kullum se an gyara shi dama, kuma su huɗu suka yi aiki, Meenal, Hindatu, se ƴan aikin su guda biyu. Bayan sun kammala ne suka yi wanka tare da shiryawa suka nufo part ɗin su Teemah, kasancewar taron se Ƙarfe 12:00 na rana ne ake farawa har illah Masha Allah, wa su ma anan suke kwana musamman na nesa, haka taron nasu yake kasancewa kamar wani babban biki. Lokacin da suka isa part ɗin su Teemah ƙarfe 10:40 a dining su ka samu Safnan tana ƙaryawa don tashin ta kenan ba daɗewa. Dining ɗin suka nufa ko wacce ta samu kujera ta zauna. "Hajiya Safnah an tashi lafiya?" Hindatu ta faɗa. "Lafiya lau ya kuke" "Lafiya lau, ina Teemah take" "Teemah ta shiga wanka" "Ok, Umma fa?" "Umma tana ɗakinta" "To bari mu gaishe da ita kafin Teemah ta fito" Meenal ta faɗa tare da miƙewa Hindu ma miƙewar ta yi suka nufi ɗakin da ya kasance na Umma ne. "To shikenan" Safnan ta faɗa. Mintuna 5 da shigar su ɗakin su ka fito tare da Umman Teemah sanye take cikin doguwar riga ta shadda blue colour. Falon su ka nufa suka zauna, Safnan ma, ta koma falon don ta gama cin abincin suna hira ne da Teemah don ta fito wanka. Kwalliya sosai ta cancaɓa a fuskar ta, kai ka rantse bikin wata babbar ƙawarta zata je, dama Teemah gwana ce wajen tsara kwalliya a fuskarta, har mutane ma tana mu su idan taga dama. "Su Teemah irin wannan kwalliya haka, kamar ba za'a mutu ba!" Cewar Meenal "Hm ai shine na gani nima, ko dai zai zo ne Teemah?" "Kwa dai ji dashi! Mutum ba ze yi kwalliya ba, se ze tafi wani waje ko za yi baƙo?" "Allah ya huci zuciyar ki amaryar Faruq!" Cewar Meenal Zaro idanu Teemah ta yi tare da kallon Umma, sannan ta juyo ta yi wa Meenal alama da kar Umma ta ji. Amma aikin gama ya gama Umma ta riga da ta ji, don hankalinta yana kan abinda suke cewa, duk da idanunta na kan wayarta ne. "Meenal waye kuma Faruq?" Cewar Umman Gaban Teemah ne yayi mummunan faɗuwa da jin tambayar na Ummanta. Shiru su ka yi daga Meenal har Teemah ba wanda yace komai. "Ba ku bani amsata ba!" Umma ta faɗa "Umm Umma abokin yaya Abdul ɗin nan, da ya zo gidan nan kwanaki" Hindu ta bata amsa don jin duk Sunyi shiru, don ita a tunanin ta ma, Teemah ta faɗawa Umma maganar Faruq. "Wanda suka zo asibiti tare?" Umma ta sake jefo mu su tambaya. "Ehh Umma shine" "To menene tsakanin Teemah da shi?" "Momy Saurayin Teemah ne" Meenal ta faɗa. "Teemah maganar da su ka faɗa min hakane?" Umma ta faɗa tana kallon Teemah da ta sunkuyar da kanta ƙasa alamar jin kunya. Gyaɗawa Umma kai ta yi alamar "Ehh" Murmushi Umman ta yi wanda ka na gani kasan na farin ciki ne, sannan tace "To Teemah ki na son shi ne?" Gyaɗa kai ta sake yi alamar "Ehh" tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana Murmushi. "Masha Allah! Shine baki faɗa min ba Teemah, gaskiya na yi farin ciki da jin wannan lamari, domin na karanci yaron, daga ganin shi yaro ne mai hankali da sanin ya kamata, kuma burin ko wace Uwa ne ta ga ƴarta ta samu miji nagari, kuma aure shine cikar kamalar ƴa mace Teemah, amma da kin dage baza kiyi aure yanzu ba, bayan ga ƴanuwanki duk amsa ranar auren su" Duk shiru suka yi ba wanda ya ƙara magana suna sauraron abinda Umman take faɗa. Wayar Meenal ce ta ɗauki ƙara alamar shigowar kira, da sauri ta jawo wayar tare da ƙarawa a kunne, "Assalamu alaikum Momyna ta kai na" Meenal ta faɗa fuskarta ɗauke da farin ciki da annashuwa. Banji abinda akace a ɗayan ɓangaren ba naji dai Meenal ta ce "Dagaske Momy!, To gani nan zuwa" tare da sauke wayar fuskarta ɗauke da tsantsar farin ciki. "Lafiya ki kuwa?" Hindu ta faɗa ganin irin murnar da Meenal take yi "Momyna ce take faɗa min gata nan har ta zo, tana ɗakin kaka" Meenal ta faɗa tare da miƙewa da gudu tana faɗin "Umma seanjima" Murmushi kawai Umma ta yi, a zuciyarta kuma tace "Allah Sarki Uwa mai daɗi" Su Teemah ma sallama suka yi wa Umma suka fita zuwa part ɗin su Kaka. Meenal bata tsaya da gudun ba har ta shigo part ɗin na su, yaya Abdul ta tarar zaune kan motar shi, shi da yaya Sadiq duk sun ɗauki wanka sunyi masifar kyau duka manyan kaya su ka saka. "Ke kuma lafiya kike faman gudu haka?" Cewar yaya Sadiq, shi ko Abdul bin ta kawai yayi da ido. "Ina kwanan ku yaya Abdul!" Ta faɗa "Lafiya lau, shi aka tambaye ki?" Yaya Abdul ya faɗa. "Yaya momyna na ƙosa na gani wallahi" "To shiga tana ɗakin kaka" Abdul ya faɗa. Da sauri ta shige ɗakin, tsabar saurin da take yi be bata damar ganin mutanen da suke falon ba, kawai ɗakin Kaka ta nufa. Tana shiga kuwa ta hango momynta zaune a kujerar, da gudu ta ƙarasa ta faɗa kan Momyn nata tare da cewa "Momy I miss You so much" Murmushi matar ta yi wanda kamar su ɗaya da Meenal kamar an tsaga ƙara, sannan tace "To tunda kin yi kewata se ki karya ni ki huta!" "A'a momyna bazan karya ki ba, ina su twinse da Zainab?" "Suna falo baki gan su ba ne?" "A'a momy ban lura ba ne" Gaishe da mutanen da ke falon kakan ta yi tare da fita ta yi waje, wajen ƴan ƙannen nata. "Abdul kwana biyu na rasa gane kan ka, kamar ka na cikin damuwa, amma ka ki sanar min" Cewar Abdul tare da saukowa a saman motar da su ke zaune tun ɗazu. "Sadiq kenan!, Wallahi soyayya ce ta yi min mugun kamu" Dariya Sadiq ya tuntsire da shi, sannan yace "ka ce maza an shiga hannu kenan, to kai ko wacce yarinya ce haka take ƙoƙarin baka wahala, kar ka manta kai fa soja ne" Duka Abdul ya kai wa Sadiq tare da cewa "kai fa ɗan iska ne!, Shiyasa wataran gara na bar damuwata, har nayi solving ɗin ta ni kaɗai" "Haba sorry babban yaya!, Yanzu faɗa min wacece?" "Safnah ce!" "Safnan da na sani dai" "Ehh ita" "To ka faɗa mata ne?" "Shine abinda na kasa yi" "To shikenan zanyi maka wani taimako akan haka in sha Allah!" "To Allah yasa!" Suna rufe baki su Teemah su ka shawo kwanan part ɗin, tun daga nesa Abdul ya kafe ta da idanu ba kwalliya ta yi ba, amma ta ƙara masa kyau sosai, ko dan ta daɗe be gan ta ba ne. Abdul be san sun ƙaraso wajen ba don ya tafi duniyar tunani, se da ya tsinkayi muryar Teemah na faɗin "Ina kwana yaya Abdul!" Da sauri ya ɗago kan shi tare da amsawa, Safnah ma gaishe da shi ta yi ya amsa. "Yaya yaushe zaka Kaduna?" Teemah ta faɗa. Shiru yayi bai ce komai ba se tsira mata idanu da yayi ma. "Ki na da saƙo ne zuwa Kaduna?" Sadiq ya faɗa. "Ehh ina da saƙo" Teemah ta faɗa tare da yin gaba don shiga part ɗin don ta ga fuskar yayan na su yau ba alamar wasa, hakan yasa ta shiga taitayinta. "Safnah!" Sadiq ya faɗa lokacin har sun kusa shiga part ɗin. Juyowa Safnah ta yi, alama yayi mata da hannu alamar ta zo. Tahowa Safnah ta yi, Teemah kuma ta wuce part ɗin, "Gani yaya Sadiq!" Safnah ta faɗa lokacin da ta ƙaraso. "Babban yaya ke son magana da ke" Sadiq ya faɗa tare da ƙoƙarin miƙewa, jawo rigar shi Abdul yayi ta baya, alamun ya zauna, sannan ya kalli Safnah yace. "Safnah ya ƙarfin jikin na ki?" "Yayi sauƙi sosai yaya" "Masha Allah!" Ya faɗa ba tare da ya sake yin wata magana ba. Sadiq ne ya kalli Safnah tare da cewa "Safnah akwai wata magana da nake son faɗa miki ne dama!" Dum! Gaban Safnah yayi mummunan bugawa, dakewa Safnah ta yi tace "To yaya ina jin ka!" "Amma kafin nan ina so na tambaye ki, ki na da wani wanda kike so ne, kuma kin taɓa soyayya?" Tara-tara kirjin Safnah ke bugawa, kamar ze fito waje, bata jin zata iya magana hakan yasa ta gyaɗa mai kai alamar a'a. "To Safnah dama akwai wani wanda ya nuna yana son auren ki kuma mutumin kirki ne Safnah, ina fata zakiyi na'am da shi" Shiru Safnah ta yi kanta a ƙasa don bata san me zata ce ba. "Kinyi shiru Safnah!" Sadiq ya faɗa ganin shirin nata yayi yawa. Kafin ya sake cewa wani abu suka ji shigowar motoci guda uku gidan, hakan yasa Sadiq cewa Safnah "ba wani bare ba ne Safnah, a cikin Familyn mu ne, kuma ze bayyana a gare ki anjima kaɗan, zan so ki ƙarɓi tayin soyayyar sa, domin idan ba haka ba, ze shiga wani hali, domin ya narke a son ki Safnah, ki je ciki se mun sake haɗuwa" Sadiq ya faɗa tare da miƙewa don tarbo motocin don Abdul har ya tashi ya tafi wajen. Safnah da gumi ya karyo mata sosai kamar ta shiga ruwa, jan kafarta ta fara yi don zuwa part ɗin don tafiya yana neman gagararta. Mota ɗaya Baba Salihu ne da iyalan gidan sa, ɗayar kuma, Baba Mustapha ne, se ɗayan kuma Baba Sagiru. Gaishe su Suka yi tare da nufar falon dukan su, kai tsaye ɗakin kaka su ka nufa don kowa ya zo can yake zuwa domin gaishe da tsohuwa mai ran ƙarfe. Ƙarfe 11:45 kowa a dangin na su ya hallara, se mutum ɗaya ake jira gwaggon su Maryam, wacce take aure a Zamfara, amma ita ma ta kusa ƙarasowa don har ta shigo cikin garin. Mota gudu uku ne su ka sake shigowa gidan, wanda na abinci ne da akayi odar su, dama duk idan za'ayi wannan taron odar abinci suke yi mai rai da lafiya, kuma mai kyawun gaske kala-kala. Wani babban ɗaki da ya kasance anan ake gudanar da taron nan aka buɗewa masu kawo abinci, shiga dashi sukayi tare da shirya abinci su ka ɗauka akan kujerun da su ke zube a ɗakin masu kama da dining table, ko wanne mazaunin mutum shida6 ne, hakan yasa aka zuba abinci flate shida, da kuma sauran kayan tanɗe-tanɗe. Ƙarfe 12:00 dai-dai aka buɗe musu ɗakin kowa ya shiga, duk Familyn ba wanda be zo ba, har da yara, amma kuma su yaran wanda ba su haura shekara 10 ba ɗakin su daban ne. Kowa a mazaunin da ya saba zama anan ya zauna, Teemah, Sa'adatu, Meenal, Hindatu, Safnah da kuma A'isha kujerar su ɗaya, kamar yadda Abdul, Sadiq, Marwan, Umar, Mujahid da Majid su ma tasu ɗaya, haka dai har iyayen na su mata, da sauran su, amma Mazan kuma su ta su kujerar ita ce a gaba. Kamar yadda suka saba, kowa se ya cika cikin shi kafin su fara gudanar da taron na su. Bayan kowa ya gama cin abincin ne, aka fara da buɗe taro da addu'a wanda Baba Salihu ya gabatar kasancewar shi Babba, daga nan aka shiga tattaunawa akan matsalar da take damun Familyn da kuma yadda za'a magance ta. Dai-dai nan kuma aka tsaya domin lokacin sallah yayi ƙarfe 1:45 kowa tashi yayi don zuwa ya gabatar da salla, za su cigaba ƙarfe 3:00. Bayan anyi sallar ne kuma suka shiga yin hotunan, don dama duk inda dangi suka taru zaka samu suna hotuna domin tarihi. Ƙarfe 3:00 aka dawo aka cigaba zuwa huɗu kuma za su tashi. Baba Bashir ne riƙe da speaker yana magana. "Kamar yadda suka sani abu na ƙarshe da zamu tattauna shine akan auren yaran mu da aka riga aka sanar da sa ranar wasu daga ciki yayin da wasu kuma ba su fito da wanda suke so ba, a zaman da muka yi kafin wannan taron, mun tsayar da cewa duk wanda be fito da wanda zai aura ba, za muyi haɗi ne". Yana kai wa nan ya miƙa abun magana ga Baba Sagiru. "Kamar yadda kuka sani, an sanar da sa ranar, Hindatu da Meenal se kuma Sa'adatu wanda sun dai-dai ta da ɗan uwanta Sadiq, se kuma A'isha, a mata wanda muke sa ran aurar da su a wannan shekarar Fatima da Safnah ne kawai ba su fito mana da wanda suke so, amma Mazan ma Baba Mustapha yace sun faɗa mai, in sha Allah nan da kwana biyu 2 za'a je neman mu su auren, yanzu muna son ganin Fatima da Safnah domin su gabatar mana da na su zaɓin" Safnah tunda aka fara taron dama bata cikin hayyacin ta, tunda ya Sadiq yayi mata magana ɗazu ta birkice ta rasa nutsuwarta, hakan yasa bata samu damar jin me ake cewa ba, saboda hankalinta bashi wajen su, don duk shirme ta ɗauki wannan taro. Teemah ne ta ɗan taɓa ta tare da faɗa mata abinda ke faruwa. Miƙewa su kayi jiki ba ƙwari su ka nufi wajen suna ƙarasawa Baba Mustapha ya ƙarɓi abin maganar tare da cewa "Muna sauraren ku, ku gabatar mana da zaɓin ku" Wata irin kunya ne ta rufe su, sun rasa ma abin faɗa se zare idanu suke yi. Ganin abinda ke shirin faruwa yasa Abdul-jabbar tashi ya nufi wajen da su ke Ƙarasawa yayi tare da cewa Ku biyo ni a kashi na gaba domin jin yadda za ta kasance. Comment ɗin ku shike ƙara min ƙarfin gwiwar yi mu ku Update akai-akai. Taku har kullum Khadeejerh Ishaq ✍️ ce  ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_29&30 Ganin abinda ke shirin faruwa yasa Abdul-jabbar tashi ya nufi wajen da su ke Ƙarasawa yayi tare da cewa "Baba dama akwai maganar da nake so mu yi da kai, kuma akan Teemah da Safnah ne" "To Abdul-jabbar ina jin ka" Baba Mustapha yace Murmushi yayi tare da sosai ƙeya sannan yace "a'a Baba idan an tashi zan sameka se muyi maganar" Murmushi Baba Mustapha yayi tare da cewa "to idan an tashi ka sameni a gidana" "To shikenan" Abdul yace tare da zama a wata kujera da yake gaban, dama an tanade ta domin shi ne, kasancewar shi babban ɗa gaba ɗaya Familyn. Baba Mustapha ne ya umarce su Teemah da su koma su zauna, ba ɓata lokaci su ka koma. Cigaba akayi da gudanar da taron na su mai cike da burgewa da nishaɗi a tsakanin su, har zuwa ƙarfe shida 6:00 na yamma sannan aka rufe taro da addu'a. Wanda suke kusa ne su ka fara haramar tafiya gida kasancewar magriba ta gabato, wanda su ke nesa kuma part ɗin suka koma don anan za su kwana. Wasu ma duk da suna kusa amma a nan za su kwana cikin su har da A'isha da kuma ƙannen Hindatu da sauran su. Su Hindatu part ɗin su Teemah suka nufa don gabatar da sallah sannan su huta. Zaune su ke a ɗakin da ya kasance na mallakin Teemah ne, suna zaune a kujera 3siter dukan su, Meenal ne ta kalli Teemah tareda kwashewa da dariya kana tace "Teemah kinsan menene?, Wallahil ɗazu na so yaya Abdul be je yayi belin ku ba, da na ga yadda za kiyi, ƙaryar rashin kunya ki ke yi" Duka dariya su ka saka amma ban da Teemah da ta ɓata rai kallon su ta yi tare da cewa "ai wallahi kun san ba abu mai yuwa ba ne na fidda kai na, ko shi yaya Abdul ɗin da kuke magana yayi belin mu, wallahi ba don ni yayi ba, yayi ne don wata manufa tashi" Teemah ta faɗa Murmushi ɗauke a fuskarta. "Ba wani nan kawai ya ga baku da mafita ne, kuma ya ga abokin shi ne yake son ki shiyasa" Hindu ta faɗa "To yanzu miye na yin wannan maganar kuma?" A'isha ta faɗa "Kyale su wallahi dai-dai nake da su, duk maganar da za su faɗa ina da amsarta, Ehem!" Duk hirar da su ke Safnah ne kawai bata yi magana ba don kallon su kawai take, hankalinta bashi akan su. "Yawwa kun ce saboda ni budurwar abokin shi ne, to ita Safnah fa?, Kawai abar maganar nan kar ayi tone-tone. "To shikenan yafi muku dai" A'isha tace Da haka suka bar zancen suka kama wata hirar. Wajen ƙarfe 9:00 Meenal tace zata koma part ɗin su saboda tafi son ta kwanta a kusa da momynta, Hindu ma bin ta ta yi su ka koma, ya kasance saura A'isha da Safnah. A ɓangaren Abdul kuwa, ana kammala taron su ka nufi part ɗin shi tareda Sadiq, wanka su ka yi tare da shiryawa, don a daren nan yake son ya samu Baban na su Mustapha akan maganar. Wajen ƙarfe takwas 8:00 su ka kama hanyar gidan. Kasancewar gidan ba nisa zuwa takwas 8:20 su ka isa gidan Baban na su. Ƙaton gida ne sosai haɗaɗɗe, har falon su ka shiga kai tsaye kasancewar gidan ba baƙon su ba ne, domin matar baban na su A'isha akwai kirki da yi mu su mutumci, yana da yara biyar ne. Kamar yadda ta saba tarba mai kyau ta yi mu su, duk da bata daɗe da dawowa gidan ba, kayan ci da na sha ta jere musu sannan ta shiga domin kiran mu su Baban na su. Mintuna biyar da shigarta ya fito, sanye yake cikin farar jallabiya, zama yayi a kujerar. Gaishe da shi su ka yi sannan yace "Abdul har kun zo?, Na zaci ai se gobe" "Ehh Baba har mun zo" Abdul ya faɗa "To inajin ku!" "Baba dama akwai wani abokina ne da ya nuna yana son auren Teemah, kuma mun gama magana dashi, idan anyi mai izini ya fito?" "Masha Allah, naji daɗin wannan maganar, amma a ina yake?" "Shi ɗan Kaduna ne, Zaria" "To yayi kyau zamu bincika mu gani, idan ya cancanta se a bashi izini ya turo, duk da nasan ba zaka yi wa ƙanwar ka zaɓen tumin dare ba, saboda na san waye kai Abdul" Murmushin jin daɗi Abdul yayi tare da cewa "Nagode Baba" "Bakomai, se kuma ita ɗayar wato Safnah na ji baka yi maganar ta bane?" Sunkuyar da kai Abdul yayi yana Murmushi ba tare da yace komai ba, se ɗan taɓa Sadiq yayi alamar yayi magana. Ai ko Sadiq kamar yana jira yace "Baba wannan ai tashi ce, ku kawai yake jira ku ce kun bashi" Murmushi Baba Mustapha yayi tare da cewa "Masha Allah naji daɗi sosai da wannan haɗin, nasan kowa idan yaji ze ji daɗi, wato Abubakar kai ne rasa kunya ko?, Haka kazo ka shaida min abinda ke tsakanin ku da Sa'adatu" Murmushi Sadiq yayi tare da cewa "ba haka bane Baba, gani nayi barin kashi a ciki ai baya maganin yunwa" Sadiq ya faɗa yana sunkuyar da kan shi ƙasa. "To yayi kyau, zan samu Yaya na shaida mai, za'a san yadda za'a yi" "To Baba mun gode sosai" Abdul ya faɗa tare da miƙewa su ka nufi kofar fita falon. Washegari Misalin ƙarfe 10:00 Safnah ta baro part ɗin su Teemah don zuwa ɗakinta, don rabonta da ɗakinta tun ranar da ta fara rashin lafiya. Ɗakin su Hindu ta nufa domin tambayar mulkin nata, a falo ta same su suna hira, ƙarasawa ta yi tare da cewa. "Barkan ku da safiya" "Yawwa Safnah barka ykk?" "Lafiya lau, an nace key ɗin ɗakina yake?" "Yana wajen yaya Abdul" "To shikenan" tace tareda fita waje, a ƙofar ɗakin ta tsaya tana saƙe-saƙe a zuciyarta, ta je ɗakin shi ne, ko kuma ta kira a waya ne. "Safnah me kike yi anan?" Ta ji an faɗa lokacin da ta dannawa yaya Abdul kira, hakan yasa ta yake kiran bayan ya fara ringing. Ɗago da kanta ta yi "ina kwana Baba" ta faɗa lokacin da fuskarta ta yi arba da Baba Mustapha. "Lafiya lau Safnah, ykk?" "Lafiya lau Baba" "Masha Allah, Safnah na ji abinda yake tsakanin ki da Abdul, kuma nayi farin ciki sosai da hakan, Allah ya baku zaman lafiya" Dum! Gaban Safnah yayi wani irin mugun bugawa da jin maganar Baban na su, wanda bata san inda ya dosa ba. Dogon tunani ta shiga wanda yasa bata san ya tafi ba ma, dama kaka ya zo gaisarwa. Ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita daga tunanin da take yi, ko da ta duba yaya Abdul ne, kaman kar ta ɗaga wayar, se kuma dai ta ɗaga tare da karawa a kunne. "Assalamu alaikum" ta ji ya faɗa, daurewa ta yi ta amsa tareda gaishe da shi sannan tace "Yaya key ɗin ɗakina fa?" "Ki zo ki amsa yana wajena" "To" kawai tace tare da yanke wayar, har yanzu bata shiga nutsuwarta ba, ɗakin nashi ta nufa, da sallama ta shiga. Yana zaune yana kallo a Computer shi, "yaya ina key ɗin?" Safnan ta faɗa. "Ki zauna Malama" Abdul ya faɗa ba tarda ya kalleta ba, zama Safnah ta yi a kujerar ta sunkuyar da kanta ƙasa, yayin da zuciyarta ke dukan tara-tara. Kusan mintuna biyar 5 ya ɗauka kafin yace "Safnah me kika fahimta akan maganar da Sadiq yayi miki jiya?" Bugun zuciyarta ne ya ƙaru da jin tambayar nashi, bata samu damar bashi amsa ba, don bata da amsar. Duban shi ya kai wajen da take, tsura mata idanu yayi na wasu sakonnin sannan yace "Safnah bansan yadda zaki ɗauki abun ba, idan nace miki ni ne wanda Sadiq yayi miki magana akai, sannan na ƙara miki da cewa ina matuƙar ƙaunar ki Safnah!" Da sauri Safnah ta ɗago kanta jin abinda yaya Abdul ɗin yake faɗa, ba dai maganar da Baba Mustapha yayi mata ɗazu bace take ƙoƙarin zama gaskiya, in dai hakane kuwa akwai matsala domin bata jin akwai wanda zuciyarta zata amshi tayin soyayyar shi. Mayar da kanta ƙasa ta yi ba tare da tace komai ba "Safnah ina so na ji daga bakin ki shin kin amince da soyayyata?" Gyaɗa kai Safnah ta yi alamar a'a yayin da bugun zuciyarta ya tsananta yanzu. "Safnan ban gane me kike nufi ba, kimin magana, idan ba so ki ke yi zuciyata ta tarwatse ba!" Safnah ta rasa amsar da zata ba Yaya Abdul, hakan yasa ta yin shiru yayinda har hawaye sun wanke mata fuskantarta na jin takaicin abinda ya faɗa mata. "Kin yi shiru Safnah!" Yaya Abdul ya faɗa ganin shirun nata yayi yawa. Daurewa Safnah ta yi tace "Yaya Abdul ka yi hakuri" Tashi tsaye Abdul yayi don maganar Safnah ta bashi mamaki, daurewa yayi yace "Safnah ban fahimci me kike nufi da nayi nakuri ba, baki so na kenan?" Miƙewa tsaye itama tayi tare da cewa Ku biyo ni a kashi na gaba don jin yadda zata kaya. More comment More typing Khadeejerh Ishaq ✍️ ce  ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_ 31&32 Miƙewa ita ma ta yi tare da cewa "Yaya Abdul kayi hakuri, akwai wanda na mallakawa zuciyata" "Safnah waye shi?" Abdul ya faɗa cikin tashin hankali. Shiru ta yi ba tare da tace wani abu ba, takawa yayi har zuwa wajen da take tsaye tare da cewa "Safnah yanzu har akwai wanda zaki so sama da ni ɗan uwanki, nasan ki na faɗa ne kawai, amma rannan ai kin cewa Sadiq baki da wanda kike so!" Juyawa Safnah ta yi ta nufi hanyar fita ɗakin ba tare da ta yi wani magana ba, shi ma Abdul be yi ƙoƙarin dakatar da ita ba yana gani har ta fice daga ɗakin. Hankalin shi ya matuƙar tashi da amsar da Safnah ta bashi, ya rasa ma abunyi yanzu, zama tayi tare da jawo wayar shi. Ita kuwa Safnah kai tsaye part ɗin su Teemah ta nufa, don bata tsaya karɓar key ɗin nata ba ma. Ba kowa a falon hakan yasa ta nufar ɗakin Teemah kai tsaye, a falon ta sameta ta na waya, zama ta yi tana kallon ta. Kimanin mintuna biyar 5 Teemah ta ɗauka sannan ta kammala wayar, kallon Safnah ta yi tare da cewa "Safnah ya naga kin dawo?, Yanzu nake shirin zuwa part ɗin ai" "Teemah akwai matsala fa!" "Subhanallahi!, Wacce irin matsala kuma Safnah?" "Teemah yaya Abdul ne yayi min wata magana da take barazanar tarwatsa zuciyata" Murmushi Teemah tayi sannan tace "Safnah ko baki faɗa min ba, nasan menene, kuma dama na daɗe ina sauraren zuwan wannan rana" Kallon mamaki Safnah ta bi Teemah dashi sannan tace "Ban fahimce ki ba Teemah" "Safnah maganar gaskiya na daɗe da fahimtar yaya Abdul yana son ki, kuma kema da zaki nutsu ki lura zaki gane, a kwayar idon yaya Abdul kaɗai zaki iya hango tsantsar ƙaunar da yake miki Safnah, ranar da ki ka faɗa min cewa akwai wanda ki ke so a can Zaria, yaya Abdul kawai ya faɗo min, kuma na tausaya mai, amma da naji cewa ba tabbatacciyar soyayya ba ce a tsakanin ku naji daɗi sosai, saboda ni kai na nafi son ki da yaya Abdul" Safnah mayar da hankali ta yi sosai kan abinda Teemah take faɗa, kuma ya shiga jikinta. "To yanzu me ki ka ce ma yaya Abdul ɗin?" Teemah ta faɗa ganin Safnan bata da niyyar yin magana "Na faɗa mai ba na son shi" Safnah ta faɗa cikin halin ko-in-kula. "What! Safnah dagaske kike yi don Allah " Teemah ta faɗa cikin tsantsar takaici "Ehh Teemah, kinsan ba wasa a tsakanin mu ai" "Safnah don Allah kar ki ɗaukarwa yaya Abdul wannan ɗanyen hukuncin, ki tausaya masa Safnah, yaya Abdul be taɓa furta kalmar so ga kowa ba se ke Safnah, duk da tarin ƴan matan da suke son shi, don Allah ki kira shi kice mai wasa ki ke yi Safnah" Ita kan ta Safnah ta ji ba daɗi na abinda ta yi wa yaya Abdul, amma abinda ke zuciyarta ne ta faɗa mai. "To Teemah zan kira shi na bashi hakuri, ko na tura mai text" Safnah ta faɗa. "To shikenan, ta so mu tafi part ɗin akwai inda zamu je da su Meenal ne dama" "To" kawai safnah tace tare da miƙewa suka fita. Kai tsaye part ɗin su Hindu suka nufa, a falo suka same su suna ta hira, harda yaya Abdul. Gaban Safnah se da ya faɗi da ganin yaya Abdul ɗin, sanye yake cikin shadda army green yayi masa Bala'in kyau sosai, hira su ke yi kamar ba abinda ya ɓata mai rai ɗazu. Ƙarasawa su ka yi suka zauna "a'ah! yaya Abdul irin wannan wankan se kace yau ne ranar" Teemah ta faɗa lokacin da take ƙoƙarin zama. "To sannu ƴar sa ido, ke baki iya ganin abu kiyi shiru ko?" Abdul ya faɗa tare da kai duban shi inda Safnan take, kanta a ƙasa yake hakan yasa be samu damar ganin kwayar idonta ba. "Kun shirya kuwa?" Teemah ta faɗa tare da kai dubanta wajen da Hindu take. "Ehh mana ke muke jira dama" Hindu ta faɗa. "To sarakan yawo ina zaku? Abdul ya faɗa yana kallon Teemah "Yaya za muje rabon cingam ne na sa ranar su" "Se ki jira idan an saka naki se ku raba gaba ɗaya, amma ba inda zaku?" "Haba yaya Abdul, don Allah ka barmu mana!" Meenal ta faɗa "Yaya don Allah!" Hindu ma ta faɗa Murmushi Abdul yayi tare da cewa "wato ku baku da kunya ko?, Zaku rabon cingam, to Allah ya shirye ku, ku bari jibi za'a kawo na Teemah se ku tafi gaba ɗaya" Gaban Teemah se da ya buga da jin maganar Abdul ɗin, amma bata nuna ba, se cewa ta yi "to yaya tunda wannan fitar ta gagara se ka barmu muje mu sha ice cream" "Ku je ku ɗauko a fridge, ai akwai a gida" Abdul ya faɗa "Ai kuwa dai yaya don Allah ka barmu mu je" Murmushi Abdul yayi a zuciyar shi tace "lallai wannan yaran da son yawo su ke, ko don ba'a barin su fitan ne yasa haka" "Yawwa tunda kuka ga yana murmushin nan ya amince wallahi, ku dai kawai ku taso muje mu sake shiri don shirin zuwa shan ice cream daban yake" Teemah ta faɗa tare da miƙewa su ma suka rufa mata baya da gudu se kace wasu ƙananan yara. A hankali Safnah ma ta miƙe domin bin su, "Safnah!" Taji yaya Abdul ya kira sunanta Tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba, "Safnah abinda kika faɗa min ɗazu shine gaskiyar abinda yake cikin zuciyar ki?" Juyowa Safnah ta yi tare da kallon shi sannan tace "yaya Abdul ka yi hakuri da abinda ya faru ɗazu" "To Safnan ba komai ni yanzu abinda nake son ji a ina ki ka ajiye ni Safnah" "Yaya zan turo maka ta waya" Safnah ta faɗa don bata son ƙara ganin ɓacin ran yaya Abdul ɗin. Murmushi Abdul yayi sannan yace "kije ki shirya zamu fita, sannan kice su kira Sa'adatu ma ta shirya mu tafi" "To yaya" Safnah tace tare da nufar hanyar ɗakin nasu. "Safnah!" Ta ji ya ƙara kiran sunanta Juyowa ta yi don ganin ko dai ba yaya Abdul ɗin ba ne, tsaye ta gan shi yana kallonta. Sassanyar Murmushi ya sakar mata tareda cewa "Safnah ina jiran amsar ki, don Allah ki amince min kin ji ƙanwata ta kaina" Jikin Safnah sanyi yayi sosai da jin maganar yaya Abdul ɗin saboda cikin sigar tausayi yayi maganar tashi. Ɗaga mai kai ta yi alamar "to" sannan ta shige ciki. Da sallama ta shiga ɗakin, "Safnah kiyi sauri ki shirya mu wuce" Teemah ta faɗa bayan ta amsa sallamar ita kaɗaice a falo su Meenal sun shiga ciki don canza kaya. "Ba shirin da zanyi, a haka kawai zan tafi ma" "Ok kun tsaya soyewa kenan da mutumin naki ko?" Teemah ta faɗa Murmushi ɗauke a fuskarta. "Ke dai kin cika neman magana wallahi" Safnah ta faɗa Murmushi Teemaah ta yi ba tare da ta sake cewa komai ba. Dai-dai lokacin su Meenal suka fito sunyi kyau sosai amma fa hijab suka saka. Jerowa suka yi suka fito, ba su samu Abdul a falon ba, hakan yasa su fita tsakar gidan. Can suka hango Sa'adatu da yaya Sadiq sun nufo part ɗin na su, suna tafe suna hira cikin nishaɗi gwanin burgewa. "Idan kun gama kun gama surutun ku taho mu tafi" Su ka jiyo muryar yaya Abdul daga cikin motar shi da take nesa da su kaɗan. Wajen motar suka nufa tare da buɗewa su ka shiga su huɗun. "Ɗaya ta dawo gaba" suka ji yaya Abdul ɗin ya faɗa. Teemah ce ta taso ta koma gaban ta zauna, dai-dai nan su Sadiq su ka ƙaraso. Baya Sa'adatu ta shiga, shi kuma Sadiq ya shiga gaba. "Sannu Anty Sa'adatu" Hindu ta faɗa tana murmushi. murmushi Sa'adatu ta yi tare da cewa "kema sannu Anty" Dariya su kayi sannan Teemah tace "su yaya Sadiq manya, ko kunyar mu baka ji, ka wani jero da ita kuna tafe juna hira ko? To kadai menene ƙawar mu ce ai" "Lallai Teemah rashin kunyar na ki har ya kai ki yi wa matar da zan aura, itafa Antyn ku ce yanzu" Sadiq ya faɗa cikin sigar wasa. Dariya suka kwashe da shi dukan su. Jan motar Abdul yayi ya nufi hanyar fita gidan. Haɗaɗɗen wajen shakatawa su ka je irin na ƴan gayun ƙarshen nan, sun ji daɗin fitar sosai domin sun ga gari kuma sun shaƙata sosai. Se gabanin magriba sannan su ka dawo gidan, duka a part ɗin su Hindu suka sauka har Teemah saboda Ummanta bata nan, ta tafi garin su ɗazu har da ƙannenta ma, hakan yasa ta rufo part ɗin su ta dawo nan, saboda kwana Umman zata yi. Sa'adatu ne kawai ta nufi part ɗin su, yayin da Sadiq suka nufi ɗakin Abdul tare. Safnah ɗakinta ta nufa domin ta yi nasarar ƙarɓar key ɗin a hannun Yaya Abdul ɗazu. Wanka ta yi ta canza kaya tare da dawowa falo ta kwanta tana ta danna wayarta. Knocking ta ji daga bakin ƙofar ɗakin nata kasancewar ta rufe shi ne dama. Miƙewa ta yi ta nufi ƙofar tare da buɗewa su Hindu ta gani tsaye a kofar. "Bismillah ku shigo" ta faɗa tare da shigewa ciki. "Safnah kice kina hutawa ne abunki" Meenal ta faɗa "Ehh wallahi naji ina jin bacci ne sosai na gaji" "Yawwa Safnah ana ta kirana a waya wai wani Khalil daga Zaria kuma yace Safnah yake nema" Zumbur Safnah ta tashi kamar an tsunguleta tare da cewa "don Allah dagaske? Ina Number?" Miƙa mata wayar Hindatu ta yi tare da cewa"nayi saving da Khalil. Da sauri Safnah ta karɓa tare da kwashe number a wayarta, ta fara kira, amma kashhh! Number a kashe take. "Nagode sosai Hindu" Safnah ta faɗa tare da miƙawa Hindu wayarta, hira suka cigaba da yi har tsawon wani lokaci ba tare da sun kwanta ba. ****Washegari**** Misalin ƙarfe 12:15 Safnah ne kwance a kujerar falonta hannun ta riƙe da wata, number nan take ta gwadawa amma taƙi shiga. Tsaki ta yi tare da da yin jifa da wayar kan kujerar, bayan wasu mintuna ta ƙara gwada number. Kira ɗaya ta yi sa'a ta shiga, wayar tana gaf da katsewa aka ɗaga. "Assalamu alaikum" ta ji an faɗa da wata murya wanda kana ji kasan ta yara ce. Amsawa Safnah ta yi tare da cewa "Khalil Safnah ce" "Ba Khalil ba ne abokinshi ne" ta ji an faɗa. "To don Allah ina yake shi?" "Yana gidan su" "To kai a ina kake?" "Ni ina kusa da gidan su ne" "Aminu ne?" Safnah ta tambaya. "Ehh shine" "Don Allah Aminu ka kira shi, amma kar kace waya za muyi kasan Anty bazata bari ba" "To ki kashe bari na kira shi, zamu kira idan ya zo" "To don Allah ka kira shi Aminu" "To zan kira shi yanzu" ya faɗa tare da yanke wayar. Aminu ya kasance abokin Khalil ne kuma kusa da gidan su take, Islamiyyar su ɗaya. "Ko a ina Aminu ya samu waya?" Safnah ta tambayi kanta, sanin bata da amsar tambayar ne yasa ta juya akalar tunaninta zuwa wani wajen. Ƙarar wayarta ya dawo da ita daga tunanin da take yi, koda ta duba number Aminu ce, yankewa ta yi sannan ta kira. "Assalamu alaikum Anty Safnah ya kike?" Ta ji muryar Khalil ya faɗa "Lafiya lau Khalil ya Anty da kawu?" "Lafiyar su ƙalau, Anty kaka fa bata da lafiya tana gidanmu da zama ma yanzu haka" "Subhanallahi! Khalil me yake damunta?" "Wallahil Anty ban sani ba" "Baka ji kawu na faɗin abinda yake damunta ba?" "Ehh Anty" "To Allah ya bata lafiya" Safnah ta faɗa cikin tsantsar tashin hankali. "Anty jiya na ga yaya Safwan, amma ban bari ya ganni ba, saboda kullum maganar ki yake min, to ƙaryata ta ƙare bansan me zan ce mai ba, shiyasa nake ɓuya idan na ganshi" "Khalil meyasa to baka bashi Number ta ba?" "Anty wallahi Momy tace kar na sake na bashi wani bayani da na sani akan ki" "Ya su Halima?" "Suna lafiya, Anty yaushe zaki zo?, Ko se bikin yaya Safwan?" Dum gaban Safnah yayi wani irin mummunan bugawa cikin tashin hankali tace "Khalil wani Safwan ɗin ne ze yi aure" Cikin halin ko ina kula Khalil yace "Anty yaya Safwan dai da kika sani, saura kwana goma ma yau" Zama Safnah ta yi don ta ji kafafunta baza su iya ɗaukanta ba, cikin rawar murya tace "Khalil kasan bana wasa da kai ko? Ka faɗa min dagaske kake yi ko ƙarya" "Anty kinsan bana miki ƙarya wallahi bikin yaya Safwan saura kwana goma kuma Daddy na ji yana faɗa" Wasu zafafan hawaye ne suka wanke wa Safnah fuska daurewa ta yi ta riƙe kukan da yake shirin zuwa mata tace "Khalil gobe za muyi waya, ka kashe" "A'a Anty idan Momy tasan muna yin waya wallahi zata iya dukana musamman ma Daddy, ki bari bayan kwana biyu zan kira ki" "To Khalil wayar waye ne wannan?" "Wayar Aminu ce, yayan shi ya bashi ƴar ƙaramace ma" "To shikenan se anjima" Safnah ta faɗa tare da yanke wayar. Wani marayan kuka Safnah ta fashe da shi na takaici da tsantsar damuwa, yanzu ace Safwan aure ma ze yi, ya manta ma da ita kenan, amma ya barta da tunanin shi ba dare ba rana, lalle bai kyauta mata ba, abinda. Safnah take ta saƙawa kenan a cikin zuciyarta. Ta ci kuka sosai har ta gode Allah, daga bisani bacci mai nauyi ya kwashe ta. Yaya Abdul ne zaune shi da Sadiq suna hira, don indai Abdul na gari to zaka same shi da Sadiq, domin suna bala'in yi dashi, kusan sa'anni suke amma Abdul ya ba Sadiq wata shida6. "Abdul baka faɗa min yadda kuka ƙare da Safnah ba, kace ka faɗa mata" . "Ni kaina amsar nake jira, tace zata tura min ta waya amma tun ɗazu nake zuba idanu shiru" "Hm kace kana cikin jiran tsammani, ai nasan zata amince maka ma babban yaya" "Allah yasa haka" Abdul ya faɗa. A ɓangaren Safnah kuwa knocking ɗin da ake yi a kofar ɗakin nata shi ya tashe ta. Ƙofar ɗakin ta nufa domin buɗewa idanunta gaba ɗaya sun kumbura fuskarta ta yi ja, abinka da jar fata. Teemah ta gani a tsaye lokacin da ta bude ɗakin, shigowa ta yi tare da cewa "Safnah lafiyan ki kuwa?, Tun ɗazu nazo amma ban gan ki ba, har sun gama cin abincin rana, amma sunce ba ki fito ba, gashi yanzu ƙarfe 3:30" ta ƙarasa maganar tare da zama a kujera dake ɗakin. Safnah ma zama ta yi tare da cewa "wallahi bacci ne ya ɗauke ni" "Amma ya naga idanun ki sun kumbura Safnah kamar kinyi kuka?" Duk inda Safnah ta kai ga son riƙe kukan da yake shirin zuwa mata ta kasa, se da ya fito. "Subhanallahi! Safnah kuka? Me ya faru?" Cikin kukan Safnah tace "Teemah wani mummunan labari ne ya sameni ɗazu" "Innalillahi -wa- Inna ilaihi raji'un waye ya rasu Safnah?" "Teemah ba rasuwa akayi ba, wanda na baki labari ina so, shine ze yi aure Teemah" "Gaskiya bai kyauta ba, amma kema ya kamata ki kyale shi, idan yana son ki baze taɓa yin aure ya barki ba" "Hakane Teemah, amma Allah ya gani ina son Safwan sosai, se dai na roƙi Allah ya yaye min son shi a rai na" "Ameen!, Kin ba yaya Abdul hakuri kuwa?" "Ehh, amma ya ƙara cewa na bashi amsar shi, shine nace zan rubuta mai" "To kin rubuta?" "A'a" Safnah ta faɗa tana goge kwallar da take zubo mata da zarar ta goge wasu se wasu su fito. "Safnah ni dai shawarar da zan baki ki amince da soyayyar Yaya Abdul, kin ga wanda ki ke so ɗin ma aure ze yi ya barki, kila ya manta da wata Safnah ma" "Teemah nagode da shawarar ki, kuma zan yi aiki da shi" "To shikenan, yanzu ki tura mai saƙon amincewa da soyayyar shi" Miƙawa Teemah wayarta ta yi tare da cewa "Gashi ki tura mai" Ƙarɓa Teemah ta yi tare da rubuta saƙo kamar haka: "Assalamu alaikum yayana, farin cikina da fatan kana lafiya, yaya Abdul ka yi hakuri da abinda ya faru jiya, amma maganar gaskiya itace na karɓi soyayyar ka hannu bibbiyu, kuma na amince zan aureka idan Allah ya so, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, Ameen!" Abinda Teemah ta rubuta kenan, ba tareda ɓata lokaci ba ta tura. "Duba ki gani na tura" Teemah ta faɗa tare da miƙawa Safnah wayarta. Karɓa Safnah ta yi tare da da dubawa "Kai! Teemah duk wannan kalaman haka, wallahi har kinsa na fara jin kunyar shi kafin na gan shi" Murmushi Teemaah ta yi tare da cewa "lallai ma! su kunya anji jiki!" "Wallahil Teemah da gaske nake bansan ya zanyi ba wajen ganin na mayar da yaya Abdul masoyi, saboda na riga na ɗauke shi a matsayin yayana, kuma ban ji son shi ya shiga rai na ba" "Dama ba lokaci ɗaya soyayya ke shiga zuciya ba, amma akwai wanda lokaci ɗaya zaki ga ya shiga zuciya ya zauna, kamar dai Soyayya ta da Faruq, tun ranar da ya furta min yana so na, na kamu da ƙaunar shi, don a ranar ma kasa bacci nayi se tunanin shi, ki bada lokaci zaki ji kin fara son shi Safnah" "To shikenan Teemah ya na iya zan ɗauki hakan a matsayin ƘADDARATA wacce take bibiyata a kullum" "Kuma kinsan yaya Abdul har ya faɗawa su Baba maganar tsakanin ku, don na ji Faruq yace min gobe iyayen shi za su zo neman aurena, kuma za'a saka ranar ne tare da na yaya Abdul, da na tambaye shi da waye? Shine yace min da Safnan" "Don Allah da gaske kike yi Teemah?" "Wallahi kuwa!" Kafin Safnah tace wani abu ta ji shigowar kira wayarta, ko da ta duba sunan yaya Abdul ta gani. "Teemah yaya Abdul ke kira da!" "To ina ruwana! Idan zaki ɗauka ma ki ɗauka, kinga tafiyata ki sameni a ɗakin su Hindu. Teemah ta faɗa tare da barin ɗakin, lokacin kiran har ya yanke. Wani kira ne ya sake shigowa wayar, se da ya kusa yankewa sannan ta ɗaga. "Assalamu alaikum gimbiyar mata!" Ta ji muryar yaya Abdul ɗin ya faɗa, amsa sallamar ta yi tare da cewa "yaya Abdul ya kake?" "Lafiya lau Safnah, naga saƙon ki, kuma naji daɗi sosai, kin sani farin cikin da na daɗe rabon da nayi irin shi, amma da kinsa zuciyata tana barazanar tarwatsewa" Shiru Safnah ta yi tana sauraren yaya Abdul ɗin yayin da take cike da mamaki, wai yaya Abdul ne ke faɗin irin waɗannan kalaman. "Kin yi shiru!" Ta ji muryar shi yana faɗa "yaya to me zance?" "Ke kike da abin faɗa kuwa, kina ina ne?" "Ina ɗakina" "To ki fito ki sameni a falo yanzu" "To" kawai tace, sannan ya kashe wayar, miƙewa ta yi ta nufi falon. Can ta hango shi a kan kujera shi kaɗai ne a falo, ƙarasawa ta yi har wajen. "To ki zauna mana" Abdul ya faɗa, zama ta yi a kujeran kanta a ƙasa don wani irin kunyar shi take ji sosai. "Ki ɗago ki kalleni mana!" Dan ɗago da kanta ta yi suna haɗa ido ta sunkuyar da kai, murmushi yayi tare da cewa "wai kunyata ki ke ji ne?, To shikenan tashi ki je kimin girki, kinsan nayi kewar daddaɗan girkin ki, kuma baki tambayeni inda nake cin abinci ba ko?" Miƙewa Safnah ta yi tare da cewa "to yaya bara naje nayi maka girkin" Tans faɗa ta nufi ɗakin su Meenal da sauri don ta ga surutun na Abdul bashi da ƙarshe. Zan tsaya a nan se mun haɗu a page na gaba. Ina miƙa gaisuwata ga duk wasu masoya wannan littafin nawa, fatan alkhairi gare ku. More comment More typing Khadeejerh Ishaq ✍️ ce  ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_ 33&34 Da sallama safnah ta shiga ɗakin su Meenal ɗin. Amsa mata su kayi sannan ta samu wuri ta zauna tarada cewa "Yau mai aiki ta yi har da girkin dare ne? Naga har ta tafi" "A'a Safnah!, Na rana kawai ta yi, dama ina jira muyi sallar la'asar ne se mu shiga kicin ɗin" Hindu ta faɗa. "Ok, dama yaya Abdul ne yace nayi masa girki se kawai na haɗa nayi da na daren" "A'a Safnah ki je ki yi mai, ƙila yanzu yake buƙata, dama girkin kashi biyu ne, Meenal za ta yi wa kaka na ta, ni kuma se nayi namu, ke kuma ki je ki yi wa Habibin ki girki kawai" Meenal ta faɗa Hararar wasa Safnah ta jefawa Meenal tare da cewa "se dai mijina ba Hubbina ba!" Ita kan ta Safnah bata san lokacin da maganar ta fito ba. Dariya suka sa duka, Teemah ce ta ce "to kwana nawa ne ya rage ya zama mijin naki Safnah!" "Ai kuwa dai faɗa mata!" Su Meenal su ka faɗa a tare. Safnah shiru ta yi don ta rasa abin cewa ma, "tashi mu je na ta ya ki aiki" Teemah ta faɗa tare da miƙewa tsaye "Ai kwa-bari dai ayi sallar la'asar ko?" Hindu ta faɗa "Ehh!, Kuma hakane, gashi ana kira. Tashi su ka yi duka don zuwa gabatar da sallar. Bayan sun gama ne kuma su ka shiga kicin ɗin dukan su, kasancewar da wuri su ke fara girkin daren su, kasancewar abubuwa da dama suke yi, wataran ma kowa nata za ta yi. BAYAN WASU AWANNI Zaune su ke gaba ɗaya a dining table don cin abinci, kasancewar da sunyi sallar Magriba su ke fara cin abinci, Hindu, Meenal da kuma Safnah Teemah ta koma part ɗin su tun bayan sun gama girkin bayan ta ɗiɓi nata a wani kula, kaka kuma sun kai mata nata, don a ɗakinta take ci, wataran ne take fitowa falo. Bayan sun gama cin abincin ne suka nufi ɗaki don gabatar da sallar isha'i da aka fara kira. Zaune su ke suna hira, bayan idar da sallar ta su. Wayar Safnah ce ta ɗauki ƙara alamar shigowar kira, ko da ta duba yaya Abdul ne, dama tsammanin kiran shi take don tun ƙarfe 5:30 ya kira ta ya faɗa mata ya fita ta ajiye mai abincin, idan ya dawo ze kira ta. Ɗaga wayar ta yi tare da ƙarawa a kunne "Assalamu alaikum" ta ji ya faɗa, amsa mai sallamar ta yi, kafin ya ƙara cewa "ina jiran ki a falo!" "To" kawai tace, sannan ya yanke wayar. "Ku zo muje falo don Allah!" Safnah ta faɗa tare da kallon su Meenal. "Lallai ma! Ki na so yaya Abdul ya ji haushi mu ne!, Ke kaɗai yace kuma baki san me zaku tattauna ba, kila ma sirri ne!" Cewar Meenal "A'a wallahi ba wani sirri, kawai abinci zan saka mai na dawo" "Ok mu je!" Hindu ta ce. Miƙewa su ka yi tare da nufar ƙofar fita. A kujerar falon su ka hangi yaya Abdul ɗin, ƙarasawa su kayi amma ban da Safnah da ta nufi kicin. Mintuna 2 se ga ta ɗauke da babban faranti wanda ta jero mai abincin da kuma drinks da ta haɗa mai. "Sannu da aiki Safnah!" Abdul ya faɗa lokacin da ya ke ƙoƙarin buɗe kular abincin. Zama ita ma tayi a kujerar da Hindu ta zauna. Abdul kuwa ba tare da ɓata lokaci ba ya fara cin abincin shi, don yunwa ya ke ji sosai, rabon da ya ci abinci tun da safe shima tea ne kawai ya sha. Yana cikin cin abincin ne wayar shi ta fara ringing, ko da ya duba, Faruq ya gani hakan yasa shi miƙewa da sauri ya nufi hanyar ɗakin shi. Sai da ya shiga sannan ya ɗaga kiran lokacin ma kiran farko ya yanke wani ne ya sake shigowa. "Assalamu alaikum babban yaya ya kake?" Faruq ya faɗa daga can ɓangaren. "Wa-alaiku-mussalam lafiya lau Alhamdulillah ya Momy?" "Lafiyan ta lau" "To yayi baka tambaye ni ya Teemah ba?" Dariya Faruq yayi tare da ce wa "ai yanzu ko kai wallahi na fi ka sanin lafiyar Teemah!" "Haka zaka ce ko? To ni da muke gida ɗaya ai dole na fi ka sani" "Hmm ba zaka gane ba!, Mu bar maganar kawa, gobe fa su Daddy su na nan zuwa fa?" "To Sarkin azarɓaɓi!, Se ka bari ka ga zuwan na su ai" "Hmm ka bari kawai!, Baka san yadda na ƙosa a mallaka min Teemah ba, gani nake kamar har yanzu akwai wanda ze kwace min ita" "Haba dai! Baka da matsala abokina, ka ƙaddara ka samu Teemah, ka manta nace na baka ita ne?" "To Baba!" Faruq ya faɗa cikin sigar wasa. "Faɗa da babban baƙi!, Kasan ance babban yaya uba!" Dariya Faruq yayi sannan yace "Allah ya biya babban yaya!" "Kai Mallam ka dame ni da surutu abinci nake ci wallahi" "To shikenan!, Se anjima ma yi waya" "Ok, Bye!" Abdul ya ce tare da fitowa waje. Zama yayi ya cigaba da cin abincin shi, su na falo kamar yadda ya tafi ya bar su, ba ya son yin waya a gaban su, don kar su raina shi, musamman idan da faruq ne. "Alhamdulillah!" Abdul ya furta, lokacin da ya kammala cin abincin na shi, kallon su yayi tare da ce wa "kun yiwa Faruq alƙawarin zuwa bikin ƙanwar shi ko, to gashi bikin ya gabato saura kwana goma 10 yau. "Yeah! Yaya Abdul wallahi na ƙosa na je Zaria" Meenal ta faɗa. "Ni ma wallahi na ƙosa mu je!" Hindu ma ta faɗa. Safnah kuwa ido ta bi su da shi jin an ambaci Zaria. "To shikenan, ni zan tafi rana ita yau, ana saura kwana biyu 2 biki, ku kuma ranar biki Sadiq ze kawo ku" "Haba yaya ina laifi mu tafi tare, ana jibi bikin!" Meenal ta faɗa, sannan Hindu ta ƙara da cewe "Ai kuwa dai yaya, mu ya kamata mu fara zuwa, Maza ai nasu ɗaurin aure ne kawai a biki" Murmushi Abdul yayi tare da ce wa "yawwa se ku je gidan mutane ku tare ko? Har kwana uku3, kuma kunsan gidan surukan Teemah ne ko?" "Ehh yaya! Ita Teemah se ta tafi ranar bikin" "Tare za ku tafi!, Ranar bikin" "To shikenan yaya!" Hindu ta faɗa. "Safnah wai ke kurma ne ko?" Abdul ya faɗa yana kallon Safnah da tun ɗazu take bin su da idanu. Murmushi ta yi tare da ce wa "ai duk abinda zan ce sun faɗa yaya" "Au kema ki na bin na su ku tafi ana jibi bikin kenan?" Murmushi Safnah ta yi tare da ɗaga kai alamar"Ehh" Abdul ma murmushin yayi tare da ce wa "to shikenan za ku tafi ana gobe bikin!" "Yawwa yaya!" Su ka faɗa har su na haɗa baki. Hira su ka cigaba da yi, bayan sun gama kuma su ka hau kallo, ba su su ka kwanta ba, se ƙarfe 10:30. *****WASHEGARI***** Shirye-shiryen sa ranar su Abdul da Teemah ake yi, da sauran matasan gidan gaba ɗaya. Iyayen Faruq sun zo, har an tsayar da magana wata uku3, duka rana ɗaya aka saka. Misalin ƙarfe 3:00 iyayen Faruq su ka nufi Zaria, bayan sun gaisa da Teemah ta ga soyayya sosai a wajen su, kuma su ma sun ji daɗin ganin gidan da da yaron na su ya nemi aure, don sun san gidan mutumci ne. Abdul yana cikin tsantsar farin ciki sosai mara musaltuwa, na baiko da akayi mai da Safnah, shi a son ran shi ma wata biyu ya so a saka, a haɗa da na su Hindu, don shi wata biyu aka saka, amma shi ma an ƙara, yanzu an dawo da su ɗaya. Safnah ta ci kuka lokacin da ta ji wai har da ita aka saka ranar, zama ta yi a ɗakinta tun bayan tafiyarsu, ta ci kuka har ta gode Allah. Misalin ƙarfe 5:30 kiran Abdul ya shigo wayanta, ko da ta ɗaga cewa yayi ta same shi a falo. Miƙewa ta yi bayan ta goge ƙwallar da ta zubo mata. A kujerar falon ta same shi, shi kaɗai ne a falon, gaishe da shi ta yi, don wunin yau gaba ɗaya ba su haɗu da shi ba. "Safnah ɗago ki kalleni!" Ya faɗa ganin tunda ta zo kanta a ƙasa ya ke. Ɗagowa ta yi ta kalle shi "me yasa idanun ki, su ka yi ja?, Kin yi kuka ko?" Kai ta gyaɗa mai alamar "a'a" "Kai ki min ƙarya Safnah, kukan me ki ka yi?" Kuka ne ya taho ma Safnah, cikin kukan ta ce "to ba kai ba ne!" Cikin tashin hankali Abdul yace "Subhanallahi! Safnah, me na yi miki?" Shiru ta yi bata bashi amsa ba, se sheshsheƙar kuka take. "Safnan ki yi magana mana!, Don Allah bana son wannan kukan kiyi shiru!" Ganin ya shiga tashin hankali yasa Safnah cewa "to ba kai ne, kace a mana baiko yanzu ba!" Shiru Abdul yayi yana kallon ta daga bisani yace "Safnah ba ni na ce ba, su Baba ne, ko baki ga duka aka saka ranar ba, har da Teemah fa!" Shiru ta yi ba ta yi magana ba, Abdul ne ya sake ce wa "na ce ki yi shiru, ko dai ba ki so na ne Safnah?" Ɗaga kai ta yi alamar "Ehh!" "Ba na son wasa Safnah, kar ki sa hankalina ya tashi!" "To ni ai Soja ne ba na so" Safnah ta faɗa cikin shagwaɓa. "A shirye nake da na ajiye aikin indai baki so Safnah" Ɗago kai ta yi ta kura mai ido na wasu ƴan sakonni, kuma ta ga alamar da gaske yake yi, canza akalar maganar ta yi da cewa "A'a yaya ban ce ka ajiye aikin ka ba, wasa nake maka, amma kuma gaskiyar ranar da aka saka ta yi kaɗan, shekara ɗaya1 ya kamata a saka" Murmushi Abdul yayi tare da ce wa "to ki samu su Baba ki faɗa mu su" "Ai bazan iya ba ne, amma nasan kai za ka iya, kuma za su fi jin maganar ka ma" Murmushi Abdul yayi tare da ce wa"to shikenan!, Zan faɗa mu su" ya faɗi hakane don tabar maganar don baya son ganin damuwarta ko kaɗan. "To se aje ayi min girki ko Madam, zan je gidan su Sadiq na dawo" "To zan yi" kawai Safnah tace, tare da miƙewa ta nufi ɗakinta. "Safnah!" Ta ji yaya Abdul ya faɗa, juyowa ta yi "na yi mantuwa gashi!" Ya faɗa tareda miƙa mata wata baƙar leda babba cike da kaya. "Menene yaya?" Safnah ta faɗa lokacin da ta ƙarɓi ledar. "Alawa ne da cimgum na saka ranar mu" Gaban Safnah se da ya faɗi, dakewa ta yi tare da cewa "to ni waye na sani anan da zan bashi, dama dai a Zaria ne" "Ehh ki je dashi naki ne!" Juyawa ta yi amma ba haka taso ba, taso yace ta je Zaria ne ta raba mu su, amma ta kudirinta a ranta se ta tambaye shi za ta Zaria. *****BAYAN SATI ƊAYA 1***** Abdul zaune da ƴan ƙannen na shi suna hira, don indai ya samu hutu haka mai ɗan yawa ta dawo ba aikin da yake yi se ziyara da kuma hira da ƴan ƙannen na shi. "Yaya wai gobe ne zaka tafi ko?" Teemah ta tambaya, don itama ta na part ɗin na su. "Ehh in sha Allah!, Gobe nake son tafiya" "Amma mu gaskiya se ranar bikin za muje don wallahi kunya ma nake ji, kuma gashi sun damu da na zo, don Salmah kullum se ta kira ni, wai mu taho tare da kai, har an fara Event" "A'a ba zaki je gobe ba!, Se jibi, jibin ma se anyi sallar azahar za ku fita inda zaku isa da yamma ko ma da dare" "To yaya Allah ya kai mu" Hindu ta faɗa. Hira su ka cigaba da yi abun su gwanin burgewa. Bari mu waiwayi mutanen Zaria kuma don jin irin wainar ta ake toyawa. *****ZARIA***** Safwan ne zaune a babban falon su, misalin ƙarfe 12:00 na rana, Daddyn na shi ma, saukar shi kenan a garin yau, don dama yace se bikin two ko three days sannan ze dawo, yau kuma bikin saura kwana uku 3 ne. Tarin kayan lefen da Daddyn shi ya ƙaro suke kallo, don ya ninka wanda Antyn ta haɗo, sau biyu ma, a fili Antyn ta nuna jin daɗinta da kayan da ya ƙaro amma a cikin ranta baƙin ciki ne fal!. "Safwan ka koma ka duba gidan kuwa? Ka tabbatar sun gama komai?" Daddyn Safwan ya faɗa. "Ehh Daddy an gama komai tun last week ma" "To Masha Allah!, Anjima ku na da Event da zaku gabatar ko?" "Ehh Daddy!, Amma ni ban so suka shirya wannan abubuwan ba, ga na can gidan, ga kuma na su Kamal" "Haba Safwan ya ka ke wannan maganar ne?" "To Daddy ayi haƙuri" "Ok, gobe za'a kai lefe fa" Daddy ya faɗa yana kallon Antyn. Murmushin yaƙe ta yi tare da ce wa "to Allah ya nuna mana goben lafiya" "Ameen!" Daddy ya amsa dashi. Shi ko Safwan fita yayi ya bar gidan ma gaba ɗaya. Gidan su Kamal ya nufa, don daga can yake son shiryawa su tafi Event ɗin da za'a yi a gidan su Salmah, daga nan kuma su wuce wanda su ka shirya na dare. Ayi min afuwa zan tsaya anan, sannan ina baran addu'o'in ku saboda ba na jin daɗi, shiyasa kuka ji ne shiru, yau ma na dage ne nayi typing ɗin. Nagode. Comment ɗin ku shine ƙarfin gwiwar mu. ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_35&36 *****Washegari***** *****ZARIA***** Kamar yadda Daddy ya faɗa hakan ce ta kasance, misalin ƙarfe 3:30 na rana aka kai lefen Gidan su Salmah, yau ta kasance Laraba, saura kwana biyu 2 bikin, don ranar juma'a ne bikin zai kasance. Gidan su Safwan har mutane sun ɗan fara zuwa, amma ƴanuwa Daddyn shi ne kawai, a ɓangaren Momyn shi kuwa babu wanda ya zo, ko da mutum ɗaya, Momyn shi ma fushi take yi da shi, saboda be je bikinta ba, tun lokacin da yaje ya dawo ba tare da saninta ba be sake zuwa gidan ba. A ɓangaren gidan su amarya kuwa, cike yake da jama'a ƴan uwa da abokan arziƙi, se hada-hadan biki ake yi, tun ana saura sati ɗaya biki ake Event, Momy da Daddy shiri su ka yi wa bikin sosai, saboda bikin tilon Ƴarsu ne. Safwan kuwa tunda su ka fara Event sau uku ya taɓa zuwa, don wasu ma ba'a buƙatar shi a wurin na iya dangin amarya. *****KATSINA***** Abdul yau yake shirin zuwa Zaria saboda bikin ya kasance jibi ne, misalin ƙarfe 12:00 ya gama shirin shi tsaf, yana zaune a dining table yana cin daddaɗan girkin da ya saka Safnah ta yi mai, gefen shi kuwa Safnah ce da Meenal, suma abincin su ke ci, Hindu ta na ɗaki ta na bacci don bata jin daɗi sosai. "Safnah ina abinda nace ki ɗauko min?" Abdul ya faɗa yana kallon Safnah. Kallon shi Safnah ta yi ba tare da tace mai komai ba, don se yanzu ma ta tuna yace ta bashi hotonta. "Kin manta ko?" Ta ji muryar shi yana faɗa. Gyaɗa mai kai ta yi alamar "Ehh" "To je ki ɗauko min, yanzu kafin na wuce" "To" ta ce tare da miƙewa ta nufi ɗakinta. Zama ta yi a bakin gado tana tunanin ta zo da hoto ma kuwa garin nan, ƴar ƙaramar jakar da tazo da ita ta ɗauko ta fara dubawa, ta samu hoto guda ɗaya, amma kuma hoton be yi kyau ba kuma baza ta iya bashi ba, ajiye wa ta yi tare da fitowa ta dawo wajen. Lokacin da ta dawo ba ta samu Meenal a falon ba, da alama ta shiga ɗakinsu ne. "Ya na ga hannun ki babu komai?" Abdul ya faɗa tun kafin ta ƙaraso wajen shi. "To yaya hotuna na suna Zaria ai ban zo da su ba!" Safnah ta faɗa tare da zaunawa a wajen da ta tashi. "Ok, to ba ni wayar ki" ba musu Safnah ta miƙa mai wayar. Kai tsaye Gallary ya nufa na wayar yayi sa'a kuwa akwai hotuna da Safnah ta yi, kuma duka ranar Family meeting ɗin su ne su ka yi da su Hindu a part ɗin su Teemah. Hotunan sun yi kyau sosai da sosai, murmushi ne ɗauke a fuskar Abdul na ganin hotunan masoyiyar tashi, WhatsApp na wayar Safnah ya shiga tare da yin mark ɗin hotunan ya tura ta number shi, sannan ya kashe mata Data ya miƙa mata wayarta. Ƙarɓa Safnah ta yi ba tare da ta ce komai ba. Miƙewa Abdul yayi tare da cewa "kin san menene Safnah?" "A'a yaya se ka faɗa" "Wallahi ji nake yi kamar na tafi da ke, saboda zan yi kewar ki sosai iya na yau kaɗai" Safnah bata ce komai ba se murmushi ta yi, don bata san me za ta ce ba. "Amma zan yi hakuri har gobe" Abdul ya faɗa tareda nufar ɗakin shi. Mintuna biyu2 da shigar shi ya fito ɗauke da jakar shi, wanda zai tafi da ita. Safnah ta na tsaye a wajen da ya bar ta, ƙarasawa yayi tareda ce wa "Safnah kira su Meenal mu yi sallama na wuce rana ta na ƙara yi" "To yaya" Safnah ta faɗa tare da nufar ɗakin na su. Shi kuwa juyawa yayi ya nufi ɗakin kaka. Da sallama ya shiga ɗakin, a zaune ya sameta ta na cin abinci wanda mai aiki ta kawo mata tun ɗazu. Amsa sallamar ta yi tare da cewa "Kaka na zo miki sallama ne zan wuce" "To Abdul-jabbar a gaishe da su Faruqu da iyayen na shi. "To kaka za su ji, gobe su Hindu za su taho su ma" "To Allah ya kai mu" "Ameen" Abdul yace tare da fita daga ɗakin. A falon ya samu su Meenal ɗin har da Hindu don ta ji sauƙi sosai, har wajen motar shi su ka raka shi, ya shiga tare da barin gidan. A maimakon su koma part ɗin su se kawai su ka nufi na su Teemah. A falo su ka samu Umman Teemah gaishe da ita su kayi sannan su ka nufi ɗakin Teemah. A falon ɗakin na ta su ka same ta ta na waya. "To Sarkin waya!, Kullum ki na maƙale da waya kamar mayya, Allah ya shirye ki dai" Meenal ta faɗa. Da gudu Teemah ta tashi ta nufi uwarɗakar ɗakin nata, don tasan ba za su bar ta ta yi wayar cikin nutsuwa ba, ta na shiga kuwa ta dannawa ƙofar key. "To fa!, Allah ya kyauta" Hindu ta faɗa ganin abinda Teemah ta yi. Zama su ka yi su ka cigaba da hirar su. Bayan mintuna 2 Teemah ta fito ta na faɗin "Allah ya shirye ku, baku san idan mutum yana waya ku yi shiru ba se kun yi mai wannan surutan na ku na banza" "To Inna ayi hakuri ko!" Meenal ta faɗa "HM, ku-ku-ka sani dai" Teemah ta faɗa. "Ke fa ƴar rainin wayo ce wallahi, ke akwai wanda ma ya kai ki yin haka, se dai kice Allah ya shirye ki" Hindatu ta faɗa. "Ni dai yau ba najin surutu ku kyaleni kawai" "Kai! Ku bata hannu Teemah ta fara hankali wallahi, gara ai ki yi hankali saboda gidan wani zaki" Meenal ta faɗa. "Kai bana son iskanci fa!, Yau abun naku kai na ya dawo, wannan ta ce waccen ta ce, to wallahi za mu hau sama mu sauko!" "To fa!, Baza a hau ba ma bare a sauko" Hindu ta faɗa ta na dariya, ita kuwa Teemah haɗa rai ta yi sosai. "Don Allah ku bar wannan zancen haka, kar ya zama faɗa fa" Safnah ta faɗa. "To Anty babba ta yi magana se ku bar surutun haka nan" Meenal ta faɗa. "Ai ko yaya Abdul ɗin ne yayi ya bari" Teemah ta faɗa. "Yau da dukkan alamu Teemah ran ki a ɓace yake waye ya taɓa min ke ne? Haba amarya wajen Faruq bada kanki a sare!" Meenal ta faɗa cikin sigar wasa. Murmushi Teemaah ta yi tare da cewa "wallahi rai na fes!, Ba damuwar komai" "To shine ki ke wani cin magani" Dariya Teemah ta yi tare da cewa "ai ku ne idan ba na fito mu ku a mutum ba ba za mu tafi dai-dai ba, da Momyn Faruq fa mu ke waya amma kuna ta min wasu maganganu" "To Allah ya huci zuciyar ki" Hindu ta faɗa. Hira su ka cigaba da yi abun su, har bayan la'asar sannan su ka dawo part ɗin su domin ɗaura girkin dare. *****ZARIA***** Anty ne zaune ita da kawu a falon na su gefe kuma Kaka ne kwance, kallo ɗaya zaka yi mata kasan ta na jin jiki sosai. "Abban Khalil yanzu haka za mu zura mata ido ka ga fa jikin nata kullum ƙaruwa yake yi" Anty ta faɗa fuskarta ɗauke da tsantsar tausayin halin da kaka take ciki. "To ya za'a yi!, Duk abinda ya kamata ayi mata anyi kuma typhoid ne kawai da maleria ko a asibiti na bar ta iya abinda za'a mata kenan, magani ne, se kuma ruwan da ake saka mata" "To Allah ya bata lafiya!" "Ameen! Shine abin cewa" Kawu ya faɗa. "Amma Abban Khalil ya kamata fa mu waiwayi Safnah, ka ga fa yau wata uku kenan da tafiyar ta, ba mu ƙara jin ɗuriyarta ba, gashi ba number ta bare mu kira mu ji, kuma ka ga yanayin jikin kaka ya kamata ace ta zo ta duba ta" Tunda ta fara maganar kallon ta Kawu kawai ya ke yi se da ta gama sannan yace "To yanzu ya ki ke so ayi?" "Yana wajen ka ai!, Kamar yadda su ke da iko da Safnah kai ma kana da iko da ita, ya kamata ace ta dinga zuwa idan buƙatar hakan ya ta so, kuma akwai muhimman kayan ta a ɗakinta musamman ma na karatu, ya kamata ta zo ta ɗiba ko mu kai mata" "To shikenan zan kira Baban na su" Kawu yace tare da wasu tunane-tunane a cikin zuciyar shi. "To shikenan, na san ba ta san da bikin Safwan ba ma da za ta yi ƙoƙari ta zo" "Ni ba na son ma ta sani, saboda ba amfanin hakan, ina son su rabu gaba ɗaya ne, kar komai ya ƙara shiga tsakanin su" Kawu ya faɗa. Hira su ka cigaba da yi kusan duk akalar hirar ta su ya karkata ne a kan Safnah. Har cikin ran Anty ta na son Safnah ta dawo, domin sun yi sabo sosai, ta so ace aure ne kawai ze raba su da Safnah, Kawu shi ma ya so hakan amma na dole ya hakura. *****KATSINA***** *****Washegari***** Safnan tunda ta tashi gabanta ya ke faɗuwa, ta rasa dalilin hakan, a wani ɓangaren na zuciyarta kuma cike take da farin cikin zuwa Zaria da za su yi don tasan dole ta je gidan Anty kuma za ta haɗu da masoyinta Safwan. Misalin ƙarfe 12:00 na rana Sadiq ya shigo gidan na su tare da cewa su shirya yanzu za su wuce don Abdul ya kira shi yace yazo ya ɗauko su yanzu. Ba ɓata lokaci su ka fara shiri dama sunyi wanka kayan da za su tafi da shi ne kawai suka tsaya kimtsawa, shi kuma Sadiq kai tsaye part ɗin su Sa'adatu ya nufa domin zantawa da sahibar shi, don tun kafin ya taho ya faɗa mata ta shirya, har kayanta ta haɗa zuwan shi kawai take jira dama. Se misalin ƙarfe 1:00 sannan su ka bar gidan, kai tsaye gidan su Abdul su ka nufa domin ɗaukar A'isha, sun sameta ta shirya tsaf, ba tareda ɓata lokaci ba su ka ɗauki hanyar Zaria. To se in ce mu ku a sauka lafiya. ****ZARIA***** Gidan su Safwan se cika yake da jama'a ƴanuwan Daddy da kuma ƴanuwan Anty, musamman ma yau da ya kasance gobe ne za'a ɗaura aure. Duk wannan shagalin da ake yi Mommyn Safwan ba ta zo ba har yau, kuma ba wanda ya bi ta kanta ma, ciki kuwa har da Daddy, Safwan kuwa ko kaɗan be ji daɗin hakan ba, kuma be kira Momyn na shi ba, rabon da su yi waya ma tun ana saura sati biyu biki. *****JUSHI***** Abdul ne shi da Faruq zaune a ɗakin da ya kasance na Faruq ɗin ne su na hutawa, don sun gaji sosai tun safe ba su samu hutu ba se awannin da su ka wuce. "Ka kira ka ji su na ina ne?" Faruq ya faɗa. "Ba zan kira ba, ka jira har lokacin da za su zo, kai ka cika ƙosawa wallahi" "Yayi kyau!, Kasan zan iya kiran Teemah ta faɗa min ai" "Ok kira ta, idan ta san garin kenan" Murmushi Faruq yayi tare da ɗaukar wayar shi, number Teemah ya kira, yayi sa'a kuwa bugu ɗaya ta ɗaga, "Assalamu alaikum!" ya faɗa. "Wa-alaiku-mussalam!, Ya hanya?" "Alhamdulillah!" Teemah ta faɗa. "Ku na ina ne?" "Kasan ai ban san garin ba" "To ki tambayi Sadiq mana" "Yace mun wuce Kaduna tun ɗazu" Teemah ta faɗa bayan ta tambayi Sadiq ɗin. "Ok, se kun ƙaraso" Faruq ya faɗa tare da yanke wayar, sannan ya dubi Abdul yace "sun kusa isowa fa!" "Ok Allah ya kawo su lafiya" Abdul yace. Kafin su ƙara wani magana su ka jiyo ana bugun ƙofar falon, Abdul ne ya tashi ya ya nufi ƙofar domin buɗewa. Salmah ne tsaye a bakin ƙofar lokacin da ya buɗe, Masha Allah! Ta haɗu sosai simple makeup ne a fuskar ta, ta saka kayan Fulani kasancewar yau za su yi funali day, kayan sun amshi jikinta sosai. "Amarya da kanta ne ashe, kin ga yadda ki ka yi kyau kuwa!" Abdul ya faɗa. Murmushi Salmah ta yi tare da cewa "Nagode yaya Abdul" Shigowa ɗakin ta yi tare da cewa "yaya faruq Daddy yace ka zo" "To, ba ku fara ba ne?" "Ehh yaya se anyi Sallar la'asar, kuma gashi ma be zo ba" Duba wayar shi yayi ya ga ƙarfe 3:45, sannan yace "to Allah ya kawo shi" "Yaya na ji shiru ne ba su iso ba" "Yanzu na kira sun kusa isowa" Murmushi Salmah ta yi, sannan tace "to Allah ya kawo su lafiya" "Ameen" su ka amsa. Ta na rufe baki aka yi sallama a ƙofar ɗakin, wata ce wacce za suyi sa'a da Salmah ƴar ƙanwar Momyn su ce, Farida sunan ta. Ƙarasowa ta yi tare da yi wa su Faruq sannu sannan ta ce "Salmah Momy na kiran ki!" "To" Salmah tace tare da nufar ƙofar fita, Farida ta mara mata baya. Su Faruq ma miƙewa su ka yi don amsa kiran Daddy. ********** Safwan ne kwance a bedroom ɗin shi, gefen shi kuma Kamal ne, yayin da falon ɗakin shi ke cike da abokan su, duk sun shirya Safwan kawai su ke jira don zuwa gidan su Salmah. "Safwan wai ka san ƙarfe nawa yanzu kuwa?" Kamal ya faɗa "Na fi ka sani tunda ka ga da agogo a hannu na, kuma ni ba makaho ba ne" "To Allah ya huci zuciyarka, ai ban ce kai makaho ba ne dama" "Ka ji da shi dai!" Safwan ya faɗa tare da miƙewa ya nufi bayin ɗakin nashi. "ka jira ni a waje zan yi wanka" Safwan ya faɗa lokacin da ya kai ƙofar bayin, ba tare da ɓata lokaci ba Kamal ya tashi ya fita. Mintuna 15 Safwan ya ɗauka a bayin kafin ya fito, mayuka ya shafe jikin shi da su da turaruka kafin ya buɗe sif ɗin shi, kayan da aka ɗinka mu su musamman na Fulani day ya ɗauko ya saka, sunyi bala'in yi mishi kyau, se ya zama kamar bashi ba, Wayar shi ya ɗauka tareda mukullin shi ya fita. Su na falon kamar yadda ya bar su harda Kamal "mu je" kawai yace mu su, miƙewa su ka yi gaba ɗaya, su Goma ne har da Safwan da Kamal su ka nufi waje, Safwan rufe ɗakin shi yayi tare da nufar babban falon na su. Mutane ne sosai a falon su na ta hada-hadan bikin, gaishe da su Safwan yayi kafin daga bisani idon shi ya sauka a kan fuskar Momyn shi, Murmushi ne ya faɗaɗa a fuskar shi, da sauri ya ƙarasa tare da ce wa "Momy yaushe ki ka zo?" Murmushi ita ma ta yi sannan ta ce "Safwan ɓan daɗe sosai ba, Masha Allah ka ga yadda ka yi kyau! Se kace Fulanin gaske!" "To Momy ai Fulanin ne" Hira su ka ɗan taɓa da Momyn na shi, kafin ta ce mai "Safwan ka tafi lokaci yana ƙurewa" tashi yayi ya nufi waje don su Kamal tun ɗazu su ke jiran shi a wajen, ka na ganin Safwan za ka ga fuskar shi ɗauke ta farin ciki, wanda ya daɗe be yi kamar shi ba, dama tsakanin uwa da ɗa Allah ne kawai ya sani. Yana fitowa motar shi ya shiga, sauran kuma su na ɗayan motar har da Kamal, kai tsaye gidan su Salmah su ka nufa. ********** Misalin ƙarfe 4:5 su Safnah su ka iso gidan su Salmah, tunda suka shigo gidan bugun zuciyarta ya ƙaru. Perking Sadiq yayi sannan su ka fito daga motar, Farida ce ta zo ta tarbe su, kasancewar Salmah ta na can ana sake mata kwalliya don Safwan ya kirata ya faɗa mata yana hanya dama shi ake jira a fara. Wani ɗaki da aka tanada musamman domin su aka kai su sallah su ka fara yi kafin daga bisani aka gabatar mu su da abinci kala-kala. Su na cikin cin abincin Salmah ta shigo fuskarta ɗauke da fara'a wajen Teemah ta nufa ta rungume ta ta na faɗin "Barka da zuwa Anty Fatima" Safnah kuwa gabanta ne yayi mummunan bugawa da ganin Salmah. "Sannu ku ya hanya?" Muryar Salmah ya dawo da Safnah daga tunanin da ta tafi. Ɗagowa Safnah ta yi tare da cewa "yawwa sannu!" Ita ma Salmah zuciyarta se da ya buga daurewa ta yi tace "Safnah ashe ki na nan" "Ehh ina nan" Safnah ta faɗa daƙyar. "Ku ci abinci se Farida ta kai ku ku gaishe da Momy, mutane sun yi min yawa ne, amma Farida za ta kawo mu ku kaya se ku saka ku fito wajen taron" "To shikenan ba komai" Meenal ta ce. Salmah kuwa juyawa ta yi ta na sake-sake a zuciyarta. Safnan kuwa neman nutsuwarta ta yi ta rasa, hankalinta a matuƙar tashe ya ke, Salmah na fita ba daɗewa su Abdul su shigo ɗakin. Gaishe da su su ka yi, zama su ka yi bayan sun amsa gaisuwar, Abdul idon shi yana kan Safnan ya karanci tsantsar damuwar da take fuskar Safnah. "Ya hanya mutanen Katsina?" Faruq ya faɗa. "Alhamdulillah! Yaya Faruq" Hindu ta faɗa Teemah kuwa sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tun lokacin da su ka shigo ɗakin, Abdul ne ya kalleta tare da cewa "Ke kuma miye haka kamar wata munafuka kin shiga hijabi?" Su Meenal kuwa dariya maganar shi ta ba su, Teemah kuwa haushi ta ji, da za ta nu na rashin kunyarta ta shine na farkon wanda ze mata magana. "Haba Abdul, Teemah ce fa ka ke ce mata haka" Faruq ya faɗa. Dariya Abdul yayi tare da cewa "to kai ba ka ga abinda ta yi ba ne?" "Kunya ce fa!" Hindu ta faɗa. Miƙewa tsaye yayi tare da cewa "ina Sadiq ɗin?" "Tun da mu ka zo ba mu gan shi ba" "To ku yi ku gama cin abincin ku shirya ku fito waje" "To yaya" A'isha ta faɗa. "Safnah ba ko magana?" Faruq ya faɗa ya na kallon Safnah. "Kai kar ka takura mata fa mu je kawai" Abdul ya faɗa ya na jan hannun Faruq zuwa waje. Sai da su ka kai ƙofar sannan Abdul ya juyo ya ce "Safnah zo nan!" "Laaa! Laaa!!! Yaya a gabana ba ka jin kunyata ko?" A'isha ta faɗa, Murmushi yayi tare da jawo ƙofar, Safnah tashi ta yi ta bi shi, su Teemah se tsokanarta su ke yi, don Faruq yana Fita Teemah ta buɗe fuskar ta. A ƙofar ɗakin ta ga Abdul ɗin shi da Faruq, ƙarasawa ta yi tare da cewa "ga ni yaya" "Safnah me yake faruwa ne? Na ga ki na cikin damuwa" "Bakomai yaya" "A'a ban yarda ba, ki faɗa min" "Dagaske babu komai" "To shikenan, amma ki saki ran ki kin ji!, Kin san ba na son na ga fuskar ki da damuwa" "To yaya" Safnah ta ce "To ki koma ku shirya se ku fito bari mu shirya mu ma" Yana faɗin haka ya juya ya nufi ɗakin Faruq, don Faruq tun ɗazu ya wuce. Safnah kuwa bata koma ɗakin ba se fitowa ta yi har zuwa babban falon gidan na su, babu kowa a falon, don duk su na tsakar gida, don har an fara gudanar da Fulani day ɗin. Safnah har ƙofar falon ta zo can ta hango taron mutane sosai. Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa har sai da ta kusa faɗuwa ƙasa, wata mata ce da ta zo wucewa ta riƙeta tare da ce mata "sannu" Safnan kasa magana ta yi se ɗaga kai. Ba komai ya haddasawa Safnah wannan ba, face ganin Safwan riƙe da hannun Salmah a cikin filin rawa. Ku kasance da ni don jin yadda za ta kasance, Na ga addu'o'in ku sosai, kuma ina godiya, Allah ya bar zumunci, ayi min afuwa na ji na shiru, yanayin jikin ne da wasu abubuwan, amma na ji sauƙi sosai, zan cigaba da kawo mu ku. Safnah fa ta ga Safwan! Shin me ze faru idan shi Safwan ya ga Safnan ze fasa auren Salmah ne ko kuma ya za ta kasance? Amsoshin tambayoyin yana cikin wannan ɗan littafin. More comment More typing Khadeejerh Ishaq ✍️ ce ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_37&38 Jingina Safnah ta yi da jikin wani window da ke falon, ka na iya ganin tsakar gidan ta Window kasancewar shi na glass, Kuka mai tsuma zuciya Safnah ta ke yi, ƙara kallon Window ta yi don ganin ko dai gizo idanunta su ke mata, tabbas idanunta ba gizo su ke ba Safwan ne ta gani. "Innalillahi -wa-Inna ilaihi raji'un" Safnah ta furta a fili jin wani irin bugu da zuciyar ta take, muryar Abdul ta jiyo da Faruq alamun fitowa su ke yi, da sauri ta shige wani labule da ke gefe don kar su ganta. Tsayawa ta yi da kukan da take don za su iya ji, sanye su ke cikin kaya irin na Fulani ya yi masifar yi mu su kyau, kamar ba su ba, sun saka hula irin ta Fulani. Ta kusa da Safnah su ka wuce, Allah ya sa ta na cikin labulen da sun gan ta. Jan kafafunta ta yi ta nufi ɗakin da su ka sauka, ta tarar da su duk sun shirya cikin kayan Fulani sun yi kyau sosai, gyale fari su ka ɗaura akan kayan don Abdul se da yayi mu su kashedi kar su fito haka, amma mutane da yawa idan su ka saka kayan ba abinda su ke ɗorawa a kai. "Safnah idan kin gama soyewan se ki zo ki shirya ko?" Meenal ta faɗa. Daƙyar Safnah da daure ta ce "Ku je gani nan zuwa!" "Ai ko ba ki ce ba, don tafiya za mu yi, sahibin na ki se ya zo ya raka ki" Hindatu ta faɗa, Safnah ba ta tanka su ba, ta ƙosa su fita ne ma ta yi kuka ko raɗaɗin da take ji a zuciyarta ze yi sauƙi. Fita su ka yi bayan sun nu na mata kayan ta, su na fita ta durkushe a wajen ta saki kuka mai tsuma zuciya, a hankali sautin kukan nata ya ke tashi. A filin Fulani day kuwa Maza da mata ne su ke cashewa abun su, dangin amarya da na ango don su ma sun samu halartar wannan taro, amarya ma ta na cikin fili ta na rawa, ango kuwa ya fita tun ɗazu, dama Kamal ne ya jawo shi cikin filin don yace ba ya rawa, amma Safwan gwanin rawa ne. A ɓangare guda kuwa Abdul ne da Faruq da kuma Sadiq sun jingina a jiki wata mota suna hira idon su na kan filin, dai-dai lokacin kuma su Hindu su ka fito, Abdul se watsa ido ya ke don ya ga wankan Sahibar shi, amma be gan ta ba, be kawo komai ba, a tunanin shi ko ta riga yin gaba ne began ta ba, don wajen da taron jama'a, su na ƙarasawa kuwa Amarya Salmah ta jawo Teemah ta saka ta a filin rawar fisgewa Teemah take yi amma Salmah ta riƙeta ba don ta so ba ta hakura, saitin kunnen Salmah Teemah ta je tare da cewa "don Allah kar ki faɗa mu su ni ce budurwar Faruq" Don tun ɗazu ta na ji wasu na tambayar ina surukar ta mu?. Dariya Salmah ta yi su ka cigaba da rawar su Hindu ma ba'a bar su a baya ba sun shiga fili kasancewar ƙawayen amarya ne a filin yanzu. Komai da ya ke gudana akan idanun Abdul ake yi da Faruq don Sadiq ma ya bar wajen ya na can wajen ƴan mata, idanun Abdul har yanzu ba su hango mai Safnah ba, taɓo Faruq yayi tare da cewa "zo ka rakani wajen can!" "Ni ma yanzu dama zan je" wajen su ka nufa, Abdul Hindu ya kira tare da tambayarta Safnah, ta faɗa mai ita su ka bari a ƙarshe, shi kuma Faruq wajen mai dije ya nufa. Da sauri Abdul ya nufi ɗakin don ganin abinda ya hana Safnah fitowa, kai tsaye ɗakin ya nufa kasancewar a buɗe ya ke, can ya hangi Safnah ta kifa kai a kujera, zuwa yanzu ta daina kuka se sheshsheƙar kuka ta ke yi. "Safnah!" Abdul ya faɗa cikin ɗaga murya, a firgice ta tashi don ta tsorata sosai, hanjin cikinta se da ya kaɗa. Shi kan shi Abdul be san da karfi ya kira sunanta ba. "Safnah kin ce min ba komai ɗazu, amma yanzu kuka fa ki ke yi" Safnah shiru ta yi, don ta rasa me za ta ce. Ƙarasawa yayi wajen da ta ke yana faɗin "Safnah me ya ke faruwa ne" "Yaya Abdul bakomai kawai kai na ne ya ke ciwo!" "Subhanallahi! Shine ba ki faɗa min tun ɗazu ba, da mun je ko chemist ne ai" "Yaya yayi sauƙi ma yanzu!" "Za ki iya fita wajen yanzu?" Gyaɗa mai kai ta yi alamar Ehh "To tashi ki shirya ina jiran ki a wajen idan an tashi taron se mu je chemist!" "To!" Safnah ta ce tare da miƙewa, shi kuma Abdul ya fita waje. Kayan Safnah ta saka sannan ta ɗauki gyalen ta yafa, ji ta yi ba za ta iya fita a haka ba, cirewa ta yi ta ɗauki wani farin hijabi a cikin kayan ta ta saka. . Zama ta yi ta na sake-sake a zuciyarta don ba ta so Safwan ya gan ta ko kaɗan, gashi idan ta ki zuwa, Abdul ze tambayeta dalilin hakan, bata da wani zaɓi da ya wuce ta fita, miƙewa ta yi ta nufi wajen, ta na buɗe kofar ta ga Abdul a tsaye "Masha Allah wallahi duk kin fi su kyau ma da ki ka saka hijabi, dama wallahi kishin ki fito da gyalen na ke yi!" Safnah ba ta ce komai ba se ƙaƙaro murmushi ta yi. "Mu je to!" Abdul ya faɗa, gaba Safnah ta yi Abdul ya na bin ta a baya. Faruq kuwa ce wa Dj ya yi yace kowa ya bar filin amarya ake son gani da kuma Antyn amarya Fatima. Cak! Kiɗan ya tsaya Dj ya bayarda sanarwar da aka bashi. Teemah har za ta gudu Salamah ta riƙo ta, ba ta da wani mafita se tsayawa ita ma jawo Meenal ta yi, su ka zama su uku ne a filin, Teemah ji ta yi kamar ta nitse a wajen jin mutane sun fara faɗin "ita ce Fatima wanda aka yi mu su baiko da Faruq!" Dai-dai lokacin Abdul ya fito shi da Safnah, tun kafin su ƙaraso wajen Faruq ya je tare da ce mu su "dama ku na ke jira!, Ku shiga fili mu yi rawa!" "Lallai ne, ni ka ga na yi maka kama da mai yin rawa, ita ma ba ta rawa kuma ba ta jin daɗi!" "Kai Mallam kar ka rai na min wayo!, Kai ne ba ka rawa? Kai fa ka koya min fa!" "To amma ka san dai ba zan shiga filin rawa ba ga Teemah, idan akace waccan kuma fa?, Se ace yayanta ne!, Kai ka ga abin yayi dai-dai" dariya Faruq tare da cewa "Gaskiya ne babban yaya!, Antynmu Allah ya baki lafiya" "Ameen Safnah ta faɗa" sannan su ka jero zuwa wajen lokacin har an saki kiɗa, su huɗu ne a filin yanzu da wata ƙanwar Momyn su Faruq (Maman Farida) riƙe da hannun Teemah ta na jujjuyata, Faruq ma filin ya shiga don takawa shi ma, kan kace me fili ya cika da ƴanuwa se takawa ake yi. Abdul kuwa wani waje ya samar wa Safnah ta zauna, shi kuma ya koma daga can gefe in da su ke tsaye ɗazu. Safnah se wurga idanu take yi, amma bata sake ganin Safwan ba, ta na ji dai Dj na faɗin ango ya shirya za'a sake dawo dashi filin. A ɓangaren Safwan wani waje aka tanadar mu su shi da abokan shi gefen filin kaɗan, duk da mutane ma a wajen amma su su na can daga ciki ne. "Safwan ka ɗan ƙara haƙuri mana, an kusa magriba na san yanzu za'a tashi!" "Ni wallahi na gaji kuma tafiya zan yi, na gaji da wannan haukan na su, se wani kiɗe-kiɗe ake yi da raye-raye mara ma'ana!" "To ya mu ka iya zama za muyi dole!" "Gashi wallahi na ji jikina kamar zazzaɓi ne ze kama ni, ga zuciyata se bugawa take yi!" Safwan ya faɗa "Ko ma miye dai zama za ka yi!" Safwan ya na rufe baki Dj ya fara kiran ango da abokan shi, tsaki ya ja tare da miƙewa ya nufi wajen, har ga Allah ya ƙosa ya tafi gida ma. A ɓangaren Safnah kuwa hijabinta ta jawo ta rufe fuska don kar Safwan ya gan ta, ta kusa da ita ya zo ya wuce, ji ta yi kamar ta kwala mai kira ya zo gareta, amma bakinta yayi mata nauyi, kuma zuciyarta ba ta umarce ta da hakan ba, amma idanunta se zubar da kwalla su ke yi. Salmah da Teemah ne har yanzu a filin, ko da Safwan ya ɗora idanun shi akan Teemah se da gaban shi ya yi mummunar faɗuwa. "Safnah!" Ya furta a zuciyarshi lokacin ɗaya kuma duk nutsuwar shi ta rabu da shi, Teemah fita ta yi ta bar su daga Safwan se Salmah don hoto za su yi. A ɓangaren Safnah zuciyarta kamar za ta fito daga ƙirjin ta, tsabar baƙin ciki da ta ke ciki ba ta taɓa tsammanin ganin wannan rana ba ko a cikin mafarkinta. Taro yayi taro an ta shi taro cike da farin ciki a ɓangaren wasu kuma cikin baƙin ciki su ke musamman ma Safnah. Ɗakin da su ka sauka su ka je su ka gabatar da sallar Magriba sannan su ka zauna domin hutawa, ba daɗewa kuma Salmah ta shigo ta kawo mu su abinci mai rai da lafiya, sun cika cikin su sosai, amma banda Safnah don ko kallon abincin ma ba ta yi ba. Misalin ƙarfe 8:25 Abdul ya shigo ya kira Safnah don ya kai ta Chemist, duk da ɗazu ciwon ƙarya ta yi mai, amma zuwa yanzu kan ta kamar zai tsage biyu tsabar ciwo. Wani babban chemist su ka je da ya ke Gaskiya layout Zaria, magunguna aka haɗo mata sosai, sannan ya biya wani super Market yayi mata siyayyan kayan ciye-ciye, sannan su ka nufi gida. Ɗakin da aka sauke su ta nufa, Abdul da Faruq kuma su ka nufi na su ɗakin, ko da Safnah ta shiga kwanciya ta yi bayan ta sha maganin, su Hindu ne su ka cinye duk kayan ciye-ciyen don Safnah ko ta kan shi ba ta bi ba. *****WASHEGARI***** Misalin ƙarfe 2:00pm aka ɗaura auren Muhammad M. (Safwan) da kuma Ummu Salmah Ahmad akan sadaki dubu ɗari biyar 500'000 wanda ya samu halartar dubban Jama'a tun daga kan manyan mutane da kuma ƙanana ma. Zan tsaya a nan Ku cigaba da kasancewa da ni don jin yadda zata kaya a cikin wannan ɗan littafin nawa, Nagode sosai Allah ya bar zumunci, ayi hakuri na ji na shiru kwana biyu2. Ta ku Khadeejerh Ishaq ce ✍️ ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_37&38 Jingina Safnah ta yi da jikin wani window da ke falon, ka na iya ganin tsakar gidan ta Window kasancewar shi na glass, Kuka mai tsuma zuciya Safnah ta ke yi, ƙara kallon Window ta yi don ganin ko dai gizo idanunta su ke mata, tabbas idanunta ba gizo su ke ba Safwan ne ta gani. "Innalillahi -wa-Inna ilaihi raji'un" Safnah ta furta a fili jin wani irin bugu da zuciyar ta take, muryar Abdul ta jiyo da Faruq alamun fitowa su ke yi, da sauri ta shige wani labule da ke gefe don kar su ganta. Tsayawa ta yi da kukan da take don za su iya ji, sanye su ke cikin kaya irin na Fulani ya yi masifar yi mu su kyau, kamar ba su ba, sun saka hula irin ta Fulani. Ta kusa da Safnah su ka wuce, Allah ya sa ta na cikin labulen da sun gan ta. Jan kafafunta ta yi ta nufi ɗakin da su ka sauka, ta tarar da su duk sun shirya cikin kayan Fulani sun yi kyau sosai, gyale fari su ka ɗaura akan kayan don Abdul se da yayi mu su kashedi kar su fito haka, amma mutane da yawa idan su ka saka kayan ba abinda su ke ɗorawa a kai. "Safnah idan kin gama soyewan se ki zo ki shirya ko?" Meenal ta faɗa. Daƙyar Safnah da daure ta ce "Ku je gani nan zuwa!" "Ai ko ba ki ce ba, don tafiya za mu yi, sahibin na ki se ya zo ya raka ki" Hindatu ta faɗa, Safnah ba ta tanka su ba, ta ƙosa su fita ne ma ta yi kuka ko raɗaɗin da take ji a zuciyarta ze yi sauƙi. Fita su ka yi bayan sun nu na mata kayan ta, su na fita ta durkushe a wajen ta saki kuka mai tsuma zuciya, a hankali sautin kukan nata ya ke tashi. A filin Fulani day kuwa Maza da mata ne su ke cashewa abun su, dangin amarya da na ango don su ma sun samu halartar wannan taro, amarya ma ta na cikin fili ta na rawa, ango kuwa ya fita tun ɗazu, dama Kamal ne ya jawo shi cikin filin don yace ba ya rawa, amma Safwan gwanin rawa ne. A ɓangare guda kuwa Abdul ne da Faruq da kuma Sadiq sun jingina a jiki wata mota suna hira idon su na kan filin, dai-dai lokacin kuma su Hindu su ka fito, Abdul se watsa ido ya ke don ya ga wankan Sahibar shi, amma be gan ta ba, be kawo komai ba, a tunanin shi ko ta riga yin gaba ne began ta ba, don wajen da taron jama'a, su na ƙarasawa kuwa Amarya Salmah ta jawo Teemah ta saka ta a filin rawar fisgewa Teemah take yi amma Salmah ta riƙeta ba don ta so ba ta hakura, saitin kunnen Salmah Teemah ta je tare da cewa "don Allah kar ki faɗa mu su ni ce budurwar Faruq" Don tun ɗazu ta na ji wasu na tambayar ina surukar ta mu?. Dariya Salmah ta yi su ka cigaba da rawar su Hindu ma ba'a bar su a baya ba sun shiga fili kasancewar ƙawayen amarya ne a filin yanzu. Komai da ya ke gudana akan idanun Abdul ake yi da Faruq don Sadiq ma ya bar wajen ya na can wajen ƴan mata, idanun Abdul har yanzu ba su hango mai Safnah ba, taɓo Faruq yayi tare da cewa "zo ka rakani wajen can!" "Ni ma yanzu dama zan je" wajen su ka nufa, Abdul Hindu ya kira tare da tambayarta Safnah, ta faɗa mai ita su ka bari a ƙarshe, shi kuma Faruq wajen mai dije ya nufa. Da sauri Abdul ya nufi ɗakin don ganin abinda ya hana Safnah fitowa, kai tsaye ɗakin ya nufa kasancewar a buɗe ya ke, can ya hangi Safnah ta kifa kai a kujera, zuwa yanzu ta daina kuka se sheshsheƙar kuka ta ke yi. "Safnah!" Abdul ya faɗa cikin ɗaga murya, a firgice ta tashi don ta tsorata sosai, hanjin cikinta se da ya kaɗa. Shi kan shi Abdul be san da karfi ya kira sunanta ba. "Safnah kin ce min ba komai ɗazu, amma yanzu kuka fa ki ke yi" Safnah shiru ta yi, don ta rasa me za ta ce. Ƙarasawa yayi wajen da ta ke yana faɗin "Safnah me ya ke faruwa ne" "Yaya Abdul bakomai kawai kai na ne ya ke ciwo!" "Subhanallahi! Shine ba ki faɗa min tun ɗazu ba, da mun je ko chemist ne ai" "Yaya yayi sauƙi ma yanzu!" "Za ki iya fita wajen yanzu?" Gyaɗa mai kai ta yi alamar Ehh "To tashi ki shirya ina jiran ki a wajen idan an tashi taron se mu je chemist!" "To!" Safnah ta ce tare da miƙewa, shi kuma Abdul ya fita waje. Kayan Safnah ta saka sannan ta ɗauki gyalen ta yafa, ji ta yi ba za ta iya fita a haka ba, cirewa ta yi ta ɗauki wani farin hijabi a cikin kayan ta ta saka. . Zama ta yi ta na sake-sake a zuciyarta don ba ta so Safwan ya gan ta ko kaɗan, gashi idan ta ki zuwa, Abdul ze tambayeta dalilin hakan, bata da wani zaɓi da ya wuce ta fita, miƙewa ta yi ta nufi wajen, ta na buɗe kofar ta ga Abdul a tsaye "Masha Allah wallahi duk kin fi su kyau ma da ki ka saka hijabi, dama wallahi kishin ki fito da gyalen na ke yi!" Safnah ba ta ce komai ba se ƙaƙaro murmushi ta yi. "Mu je to!" Abdul ya faɗa, gaba Safnah ta yi Abdul ya na bin ta a baya. Faruq kuwa ce wa Dj ya yi yace kowa ya bar filin amarya ake son gani da kuma Antyn amarya Fatima. Cak! Kiɗan ya tsaya Dj ya bayarda sanarwar da aka bashi. Teemah har za ta gudu Salamah ta riƙo ta, ba ta da wani mafita se tsayawa ita ma jawo Meenal ta yi, su ka zama su uku ne a filin, Teemah ji ta yi kamar ta nitse a wajen jin mutane sun fara faɗin "ita ce Fatima wanda aka yi mu su baiko da Faruq!" Dai-dai lokacin Abdul ya fito shi da Safnah, tun kafin su ƙaraso wajen Faruq ya je tare da ce mu su "dama ku na ke jira!, Ku shiga fili mu yi rawa!" "Lallai ne, ni ka ga na yi maka kama da mai yin rawa, ita ma ba ta rawa kuma ba ta jin daɗi!" "Kai Mallam kar ka rai na min wayo!, Kai ne ba ka rawa? Kai fa ka koya min fa!" "To amma ka san dai ba zan shiga filin rawa ba ga Teemah, idan akace waccan kuma fa?, Se ace yayanta ne!, Kai ka ga abin yayi dai-dai" dariya Faruq tare da cewa "Gaskiya ne babban yaya!, Antynmu Allah ya baki lafiya" "Ameen Safnah ta faɗa" sannan su ka jero zuwa wajen lokacin har an saki kiɗa, su huɗu ne a filin yanzu da wata ƙanwar Momyn su Faruq (Maman Farida) riƙe da hannun Teemah ta na jujjuyata, Faruq ma filin ya shiga don takawa shi ma, kan kace me fili ya cika da ƴanuwa se takawa ake yi. Abdul kuwa wani waje ya samar wa Safnah ta zauna, shi kuma ya koma daga can gefe in da su ke tsaye ɗazu. Safnah se wurga idanu take yi, amma bata sake ganin Safwan ba, ta na ji dai Dj na faɗin ango ya shirya za'a sake dawo dashi filin. A ɓangaren Safwan wani waje aka tanadar mu su shi da abokan shi gefen filin kaɗan, duk da mutane ma a wajen amma su su na can daga ciki ne. "Safwan ka ɗan ƙara haƙuri mana, an kusa magriba na san yanzu za'a tashi!" "Ni wallahi na gaji kuma tafiya zan yi, na gaji da wannan haukan na su, se wani kiɗe-kiɗe ake yi da raye-raye mara ma'ana!" "To ya mu ka iya zama za muyi dole!" "Gashi wallahi na ji jikina kamar zazzaɓi ne ze kama ni, ga zuciyata se bugawa take yi!" Safwan ya faɗa "Ko ma miye dai zama za ka yi!" Safwan ya na rufe baki Dj ya fara kiran ango da abokan shi, tsaki ya ja tare da miƙewa ya nufi wajen, har ga Allah ya ƙosa ya tafi gida ma. A ɓangaren Safnah kuwa hijabinta ta jawo ta rufe fuska don kar Safwan ya gan ta, ta kusa da ita ya zo ya wuce, ji ta yi kamar ta kwala mai kira ya zo gareta, amma bakinta yayi mata nauyi, kuma zuciyarta ba ta umarce ta da hakan ba, amma idanunta se zubar da kwalla su ke yi. Salmah da Teemah ne har yanzu a filin, ko da Safwan ya ɗora idanun shi akan Teemah se da gaban shi ya yi mummunar faɗuwa. "Safnah!" Ya furta a zuciyarshi lokacin ɗaya kuma duk nutsuwar shi ta rabu da shi, Teemah fita ta yi ta bar su daga Safwan se Salmah don hoto za su yi. A ɓangaren Safnah zuciyarta kamar za ta fito daga ƙirjin ta, tsabar baƙin ciki da ta ke ciki ba ta taɓa tsammanin ganin wannan rana ba ko a cikin mafarkinta. Taro yayi taro an ta shi taro cike da farin ciki a ɓangaren wasu kuma cikin baƙin ciki su ke musamman ma Safnah. Ɗakin da su ka sauka su ka je su ka gabatar da sallar Magriba sannan su ka zauna domin hutawa, ba daɗewa kuma Salmah ta shigo ta kawo mu su abinci mai rai da lafiya, sun cika cikin su sosai, amma banda Safnah don ko kallon abincin ma ba ta yi ba. Misalin ƙarfe 8:25 Abdul ya shigo ya kira Safnah don ya kai ta Chemist, duk da ɗazu ciwon ƙarya ta yi mai, amma zuwa yanzu kan ta kamar zai tsage biyu tsabar ciwo. Wani babban chemist su ka je da ya ke Gaskiya layout Zaria, magunguna aka haɗo mata sosai, sannan ya biya wani super Market yayi mata siyayyan kayan ciye-ciye, sannan su ka nufi gida. Ɗakin da aka sauke su ta nufa, Abdul da Faruq kuma su ka nufi na su ɗakin, ko da Safnah ta shiga kwanciya ta yi bayan ta sha maganin, su Hindu ne su ka cinye duk kayan ciye-ciyen don Safnah ko ta kan shi ba ta bi ba. *****WASHEGARI***** Misalin ƙarfe 2:00pm aka ɗaura auren Muhammad M. (Safwan) da kuma Ummu Salmah Ahmad akan sadaki dubu ɗari biyar 500'000 wanda ya samu halartar dubban Jama'a tun daga kan manyan mutane da kuma ƙanana ma. Zan tsaya a nan Ku cigaba da kasancewa da ni don jin yadda zata kaya a cikin wannan ɗan littafin nawa, Nagode sosai Allah ya bar zumunci, ayi hakuri na ji na shiru kwana biyu2. Ta ku Khadeejerh Ishaq ce ✍️  ?????????????????? _*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_ ?????????????????? _*By*_ _*Khadeejerh Ishaq*_ *{Oum Ayshat}* _*Jakadiyar Dashen??Allah*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *DASHEN??AIIAH* *WRITER'S??ASSOCIATION* ```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu``` _*ALLAH SHINE GATAN MU*_ _*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_ *PAGE*_39&40 Biki yayi biki, domin an narka Naira a wannan bikin duka gida biyu, ba zan ce ga wanda su kafi rawar ƙafa a bikin ba, kowa ka gani fuskar shi ɗauke da farin ciki da annashuwa, an ci an sha, ƴan uwa da abokan arziki kamar ƙara watso su ake yi. Yau ne kuma ƴanuwan Momyn Safwan su ka zo, Safwan ya ji daɗin zuwan su sosai, don har ga Allah ya na son ƴanuwan Momyn shi fiye ma da na Daddyn shi. Ɗunguma su ka yi duka su ka nufi gidan da za'a kai Amarya don akwai kwarya-kwaryan Walima da aka shirya misalin ƙarfe huɗu a gidan lokacin kuma za'a kawo Amarya. ********** A ɓangaren gidan su Amarya ma shirin kai Amaryar ake yi domin yanzu ƙarfe 3:00 ne, kuma zuwa ƙarfe huɗu za'a kai ta, su Hindu ma ba'a bar su a baya ba don sun sha wanka iya wanka, amma ban da Safnah da tun wankan da ta yi da safe ta saka kaya bata canza ba, su kuwa kayan jikin su shine na huɗu ma da su ka saka yau don duk Anko ɗin da aka fitar se da Momyn Faruq ta saka aka ɗinka mu su kusan kala biyar. Se misalin ƙarfe 3:45 sannan Safnah ta tashi ta canza kaya shi ma don Abdul ya kirata ya shaida mata gashi nan zuwa za su tafi Walima ne, yau tun safe ba ta gan shi ba ma saboda zirga-zirgan da su ke yi. Wata shadda blue colour ta ɗauka ta saka, duk a cikin Anko ɗin ne, se baƙin takalmi da baƙin jaka, sannan ta ɗora pink ɗin gyale, ta yi masifar kyau duk da ko hoda ba ta shafa ma fuskarta ba. Fitowa daga ɗakin ta yi zuwa babban falon, ba wasu mutane sosai don duka sun tafi wajen Walima se ƴan kaɗan su ma shirin tafiya su ke yi. Ɗakin da ta tabbatar su Hindu na can ta nufa, ɗakin ya kasance na Salmah ne, a can kuwa ta same su su ma su na shirin fitowa har da amarya Salmah. Ƙasa Salmah ta yi da idon ta duk da dama ta na cikin lulluɓi ne, saboda ba ta son su haɗa ido da Safnah don kunyar ta take ji kuma jikinta se yayi sanyi. "Safnah ya jikin na ki?" Hindu ta faɗa tare da kamo hannun Safnah. "Da sauƙi!" Safnah ta faɗa. Sauran ma ya jiki su ka yi mata sannan su ka fito waje, su na fitowa kuwa aka ɗauki guɗa, kai tsaye motar da aka tanada domin Amarya da ƙawayenta aka buɗe mu su su ka shiga amma ban da Safnah don Abdul ya ce kar ta bi kowa shi zai zo su tafi, ta na tsaye a wajen motar ta tashi ta nufi gate ɗin gidan. Motar na fita wata mota ta shigo, har wajen da Safnah ta ke motar ta perker, buɗe glass ɗin motar aka yi, Abdul ne fuskar shi ɗauke da murmushi, alama ya yi ma ta da ta zo, zuwa ta yi tare da buɗe murfin motar ta shiga, kunna motar yayi tareda barin gidan. "Safnah ya jikin na ki!" Abdul ya faɗa tareda kallon Safnah. "Da sauƙi!" Ta ba shi amsa. "To amma kin sha maganin ko?" Gyaɗa mai kai ta yi alamar Ehh, sannan ya ƙara cewa "Shiyasa na ce da kai na zan zo na kai ki, saboda ba na son ayi min gudu da ke a hanya!" "Da nisa ne wajen walimar?" "A'a Samaru ne wai can za'a kai Amaryar" Mummunan bugawa ƙinjin Safnah ya yi jin ya ambaci Samaru "wato gidan su Safwan Salmah za ta zauna ma lal....." "Kin san kuma ban wani sanin wajen ba, karanbani zan yi!, Don mun zo jiya kila na gane" maganar Abdul ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi. Murmushin yaƙe Safnah ta yi, don ta gaji da surutan da Abdul ya ke yi mata. Tafiya su ke yi har Samaru Safnah na hangen gidan Anty don ta kusa da wajen su ka wuce, har gidan su Safwan se da aka wuce, don gidan ya na can cikin anguwar ta su ne. Gidan yayi masifar haɗuwa sosai da sosai, a can ta samu su Hindu har sun isa, har ma an fara Walimar su na wajen, su ma wajen Walimar su ka nufa Safnah a gaba Abdul na biye da ita. Kan ta a ƙasa ta ke tafiyar ta na jan ƙafa, kamar an ce ta ɗago kai su ka haɗa ido da Safwan, zuciyarta se da ta buga, da sauri ta juwo don duk rintsi ba za bari Safwan ya gan ta ba, da alama be gan ta ba, don ko murmushi ne ta san ze yi da ace ya gan ta. "Ya aka yi kuma?" Ta ji Abdul ya faɗa, ita ta ma manta tare su ke tafiya, dabara ce ta zo mata, duƙawa ta yi tare da riƙe ciki tace "yaya Abdul cikina ke ciwo!" "Subhanallahi!, Sannu, za ki iya tafiya kuwa?" Abdul ya faɗa cikin tashin hankali. "Ehh zan iya!" Ta faɗa Mota ya mayar da ita ta zauna sannan ya juya ya na faɗin "bari na kai ma Faruq wannan se na zo mu koma chemist ɗin!" "Yaya Abdul!" Ta kira sunan shi, juyowa ya yi tare da cewa "ya aka yi?" "Yaya don Allah ka bar ni na je gidan Anty mana!" "Wacce Anty?" Ya tambaya "Gidan Kawuna!" "A'a ban yarda ba!, Yanzu ba ki da lafiya ki bari gobe se na kai ki!" Kuka Safnah ta fashe da shi tare da faɗin "yaya Abdul don Allah ka bar ni wallahi na ji sauƙi" "To shikenan kin iya driving ne?" Da sauri ta ce "Ehh na iya!" Tare da share hawayen da su ka wanke mata fuska. Shiru Abdul ya yi ya na tunanin ya rasa gane kan Safnah tun da su ka zo garin nan. "A'a ba ri na kai ki kawai se na dawo!" Abdul ya faɗa bayan ya dawo daga tunanin na shi. Motar ya shiga shi ma tare da kunnawa ya bar gidan. Mintuna biyar 5 ya kawo su gidan Kawun na ta, perking ya yi da sauri Safnah ta ɗauki jakarta za ta fita. "Ba za ki yi min sallama ba ne!" "To se anjima yaya!" "Haka ne sallamar!, To ki gaishe da su, gobe zan zo na ɗauke ki se na shiga na gaishe da su, yanzu Faruq se kirana ya ke yi" "To yaya nagode!" Safnah ta faɗa tare da buɗe motar ta fita. Abdul juyawa ya yi ya koma gidan, Safnah kuwa da mugun sauri ta shiga gidan ta na kwala kiran Anty. Anty da ke tsakar gida ta na aiki da sauri ta ɗago jin muryar Safnah na kwala mata kira, ta na ɗagowa su ka haɗa ido da Safnah, ita a zaton ta gizo kunnuwanta su ke yi ma ta. Da sauri Safnah ta ƙarasa ta rungume Anty tare da fashewa da kuka. "Safnah kukan na miye kuma, ya isa mu shiga ciki" Anty ta faɗa tare da jan hannun Safnah su ka nufi falon, da saurin yaran ma su ka ta so su ka rungume Safnah su na faɗin "oyoyo!, Anty Safnah ta dawo" Cikin farin ciki da Safnah ta manta rabon da ta yi irin shi ta rungume yaran su na murnar ganin juna. "Anty amma ba za ki sake tafiya ki bar mu ba ko?" Afrah ta faɗa. "Ehh ina tare da ku" Safnah ta faɗa da Addu'ar Allah ya sa hakan. "Anty kin je bikin yaya Safwan kuwa?" Halima ta tambaya. Gyaɗa ma ta kai kawai Safnah ta yi alamar a'a don shine kawai amsar da za ta bayar. "Anty bari na ɗauko miki key ɗin ɗakin ki ma!" Khalil ya faɗa tare da miƙewa ya nufi ɗakin shi. Cikin ƴan sakonni ya dawo hannun shi ɗauke da key ɗin, miƙa mata ya yi, da sauri ta ƙarɓa. "To Khalil uban azarɓaɓi ka bari ta huta ai ko!" Anty ta faɗa "A'a Anty ni kai na na yi kewar ɗakina da abinda ya ke ciki!" Safnah ta faɗa tare da karɓar key ɗin ta fita da sauri. Anty kuma uniform ɗin su ta kwaso mu su na Islamiyya su ka saka don lokaci ya yi tun ɗazu ma, se da su ka leƙa ɗakin Safnah su ka mata sallama sannan su ka wuce makarantar ba don son ran su ba, don sun yi kewar Antyn su Safnah sosai. Safnan ko da ta shiga ɗakin fes! Ta gan shi, kamar akwai mutum a ciki, tsayawa ta yi ta ƙare wa ɗakin kallo kafin daga bisani ta shiga uwarɗakar ɗakin nata, fitilar ɗakin ta kunna kasancewar akwai wutar nefa, durowar da ta ke ajiye kayan karatun ta ta nufa tare da buɗewa, computer ta ta fara cin karo da ita a sama, ɗaukowa ta yi tare da komawa ta zauna a kan madaidaicin gadon na ta. Kunnawa ta yi ta dinga shige-shigenta a ciki, hawaye na bin fuskarta na baƙin cikin karatunta da aka daƙile mata, wani ɓangaren na zuciyarta kuma Safwan kawai ta ke tunawa haɗe da jin kishin sa a zuciyarta. Ta yi mintuna 15 ta na kuka a ɗakin na ta kafin ta ji shigowar Anty, har uwarɗakar ta shigo tare da zama a gefen Safnah ta ce "Safnah me ya faru kuma ki ke kuka?" Kara sautin kukanta Safnah ta yi tare da cewa "Anty komai ma ya faru!, Ina cikin damuwa sosai Anty kuma ba bu wanda zan iya faɗawa damuwata, Anty dama ke ce kawai na ke faɗa ma damuwata kuma ki share min hawayena amma kin yi ne sa da ni Anty ko nema na baki yi!" Jikin Anty yayi sanyi sosai, har kwalla sun fara shirin zubo mata na tausayin Safnah, goge kwallar ta yi don ba ta son Safnah ta gani sannan ta ce. "Safnah ki yi hakuri, duk tsanani ya na tare da sauƙi, duk abinda ya dame ki ki cigaba da kai kukan ki wajen Allah domin shi mai ji ne kuma ya na ganin halin da ki ke ciki!, Safnah kinsan ban san gidan ku a Katsina ba, kuma ko na sani Abban su ba ze bar ni na je ba!" "In sha Allah Anty!, Nagode sosai da tunatarwa ki" Safnah ta faɗa tare da share hawayen da su ka wanke mata fuskarta. "To Safnan ya kamata ki faɗa min abinda ya ke faruwa" "Anty kinsan ba ni da burin da ya wuce na ga na yi karatu mai zurfi, amma Anty a can ko maganar karatuna ba su yi se dai maganar aure!" Murmushi Anty ta yi sannan ta ce "Safnah ai shi ma auren abu ne mai kyau, kuma ko da kin yi aure ai za ki cigaba da karatun ki ba matsala ba ne" "Anty ba za ki ga ne ba ne!, Kinsan har baiko fa anyi min nan da Three months fa" Wani iri Anty ta ji a cikin zuciyar ta, amma ta dake ta ce "amma ba mu ji ba, ko Kawun ki na tabbatar shi ma be sa ni ba, amma da waye aka miki baiko?, Ki na cewa ba ki son auren shine daga zuwan ki har kin yi saurayi ko!" "Anty be fi two weeks da yi ba, kuma ɗan Babanmu Salihu ne fa!" "To ki ce auren zumunci ne, Allah ya tabbatar da alkhairi!" Kuka Safnah ta fashe da shi tare da cewa "Anty wallahi ba na son shi, amma shi ya nace wai ya na so na" "Idan na fahimce ki auren dole za su yi miki kenan?" "A'a Anty na ce ina son shi, amma Anty wallahi ba na son shi" Jinjina kai Anty ta yi tare da mamakin wannan lamarin, kallon Safnah ta yi tare da faɗin "amma ba ki faɗa min me ya kawo ki Zaria ba, kuma ke da waye ku ka zo?" "Anty bikin Safwan mu ka zo!, Amma gidan su Amaryar mu ka zo wa bikin, yayan ta shi zai auri wata ƴar uwarmu a Katsina, kuma wanda aka yi min baiko da shi abokin yayan na ta ne, shi ya kawo ni nan ma yanzu se ya wuce gidan da za'a kai Amaryar ana walima ne" "To shine ko ya shigo ya gaishe da mu?" "Anty sauri ya ke yi ana ta kiran shi ne, da ƙyar ma na samu ya kawo ni nan, don da gidan walimar mu ka fara wucewa" "To me yasa ba ki tsaya a wajen walimar ba?" "Anty ba na son Safwan ya ganni ne!" "To saboda mene?, Ba se ki ta ya shi murna ba, bayan tafiyar ki Safwan ya zo nan ya fi a ƙirga ya na neman ki!" "Anty ba zan iya ba ne!, idan na kalle shi baƙin ciki na ke ji sosai a zuciyata!" "Safnah tun farko ku ku ka yaudari kan ku, ta hanyar ɓoye soyayyar junan ku, da kun bayyana da kun daɗe da zama mallakin junan ku" "Anty Safwan be taɓa ce wa ya na so na ba, kin ga ba mutunci ba ne ni na ce ina son shi" "Duk wannan shirmen ku ne!, Amma ko wa ya gan ku zai fahimci soyayyar da ta ke tsakanin ku, musamman Safwan ya na matuƙar ƙaunar ki Safnah, na ji mamaki sosai da aka ce ze yi aure!" Hira su ka cigaba da yi har kusan Magriba sannan su ka fito zuwa falon Antyn lokacin har su Khalil sun dawo daga Islamiyya, se lokacin Safnah ta ke tambayar Anty ina Kawu? Duk da tun da ta shigo ya ke ran ta, amma se yanzu ta tambaya. Se da Anty ta gama jere mu su abinci a tsakar falon sannan ta kalli Safnah ta ce "Safnan Kawun ki ya na asibiti, kinsan Mama ba ta da lafiya ta daɗe a gidan nan, amma zuwa anjima za su dawo" "Allah Sark!, Allah ya ba ta lafiya, ciwon me take yi Anty?" "Typhoid ne da maleria" "To Allah ya ba ta lafiya!" "Ameen!" Su na rufe baki su ka jiyo sallamar Kawu, da sauri Anty ta miƙe don tarbo mijin na ta, a tsakar gida ta gan shi riƙe da Kaka, da sauri ta ƙarasa ta riƙe kaka ta na mata sannu, daƙyar ta iya amsawa, sannan su ka nufi ɗakin, Kawu kuma ya juya domin zuwa masallaci don an fara kiran sallar Magriba tun ɗazu. Zaunar da kaka ta yi a kujera tare da ɗauko abinci ta fara ba ta, don ta ɗan ji sauƙi sosai har ta na iya cin abinci. "Sannu kaka!" Safnan ta faɗa tare da tasowa ta nufo kujerar da su ke zaune" "Yawwa!, Wa na ke gani kamar Safnah?" "Ehh Mama ita ce!" Anty ta faɗa. Ita kuma Safnah murmushi kawai ta yi, don ta ji daɗin ganin jikin kakan na su ya yi sauƙi. "Yaushe ta zo ne?" Kaka ta faɗa. "Yau ta zo, Mama ki bar magana ki ci abinci don Allah" Anty ta faɗa, don tasan idan ta cigaba da maganar damuwa ce kawai za ta dame ta, don ta na yawan yin zancen Safnah. Sosai Kaka ta ci abinci, bayan ta gama ci Anty ba ta ruwa ta sha, tare da sa mata albarka. Dai-dai lokacin Kawu ya shigo ɗauke da sallama, amsa mai sallamar su ka yi ya samu waje ya zauna. "Ina wuni Kawu!" Safnan ta faɗa kan ta a ƙasa. Da sauri ya ɗago daga kishingiɗar da ya yi don jin muryar Safnah, kallon ta ya yi cike da mamaki, don shi kwata-kwata idon shi be kai wajen da ta ke ba ma. "Lafiya lau Safnah!, Yaushe ki ka zo?" "Ɗazu na zo Kawu!" "Kin zo bikin Safwan kenan?" Gyaɗa mai kai ta yi alamar Ehh, sannan ya ƙara ce wa "Ya garin na ku?, Komai lafiya dai ko?" "Ehh Kawai, Alhamdulillah!" Safnah ta faɗa don ba komai ta ke iya faɗawa Kawun na ta ba, saboda ta na jin kunyar shi, amma Anty kuwa ba kunya tsakanin su komai ta na iya faɗa ma ta. "To Masha Allah haka ake so ai, to yaushe za ki koma?" "Kawu ban sani ba, ba ni kaɗai na zo ba" "To shikenan" Wayar Safnah ce ta fara ringing alamar shigowar kira, ko da ta duba Abdul ne, miƙewa ta yi ta nufi ɗakinta don ba za ta iya yin waya a gaban su ba. Lokacin da ta shiga ɗakin har kira ya yanke, wani kira ne ya sake shigowa ɗaukar wayar ta yi tare da kai shi kunnenta. "Assalamu alaikum!" Ta ji muryar shi ya faɗa. "Wa-alaiku-mussalam!" Safnah ta ba shi amsa. "Barka da dare gimbiyata!" "Yawwa barka!" "Ya jikin na ki kuma?" "Alhamdulillah!" "Ina nan zuwa bayan isha'i" "To me za ka zo yi?" Safnah ta faɗa ba tare da sanin maganar ma ta fito ba. "Ɗaukan ki zan zo yi mana!" "Haba yaya!, Ka ce se gobe fa!" Safnah ta faɗa cikin muryar shagwaɓa. "Zan kawo miki maganin ki ne kin manta da shi a can gidan" "To ka bar shi, ni na ji sauƙi ma!" "Ni ki ke faɗa wa haka ko?" "Ka yi hakuri!" "To shikenan na taho ma yanzu, anjima kaɗan dinner za mu tafi" "To se ka zo, ina su Hindu?" "Su na can suna tambayar ki, ana tsaka da biki kin gudu, gobe zamu zo tare da su" "To shikenan" "Ok se na zo" "To" Safnah ta ce tare da yanke wayar, ɗakin Anty ta koma su ka cigaba da hira da yaran don da ta dawo ba ta samu su Kawu ba har Kaka ma ba ta ɗakin. Bayan mintuna biyar5 kiran Abdul ya sake shigowa, ta na ɗagawa ya ce "ina jiran ki a waje!" "To" ta ce sannan ta miƙe tare da cewa "Khalil idan Anty ta fito ka ce mata na je na dawo" "To Anty!" Khalil ya faɗa, Hijabin Anty ta ɗauka ta saka sannan ta nufo kofar gidan. A saitin ƙofar ta ga motar shi yayi perking ɗin ta, ƙarasawa ta yi tare da buɗe motar ta shiga bakinta ɗauke da sallama. "Barka da zuwa!" Abdul ya faɗa kan ta a ƙasa ta bashi amsa da "yawwa ya hanya?" "Lafiya lau, Masha Allah!, Da dukkan alamu kuwa kin ji sauƙi don ga shi na ga alama, gobe misalin ƙarfe 12:00pm zan zo na ɗauke ki" "To" kawai Safnah ta ce ba don ta so hakan ba. Ledar magungunan ya miƙo mata tare da ce wa "mu je na gaishe da mutanen gidan" Da sauri Safnah ta ɗago kai ta kalleshi tare da ce wa "yanzu wai?" "Ehh mana!, Ko kar in je ne?" "A'a mu je" Safnah ta faɗa tare da buɗe motar ta fito, shi ma fitowa yayi su ka jero har zuwa ƙofar gidan. "To ki shiga ki faɗa mu su zuwa na mana!" "To" Safnah ta faɗa tare da nufar cikin gidan, Anty ta tarar a falon tare da yaran ta, zama ta yi tare da ce wa "Anty har kin fito?" "Ehh tun ɗazu ma, ance kin je ki dawo" Sunkuyar da kai Safnah ta yi sannan ta ce "Anty yaya Abdul ne ya zo, kuma ya ce zai shigo yanzu ya gaishe da ku" "To ki ce surukin na mu ne ya zo, to je ki shigo da shi mana!" "To" Safnah ta ce tare da fita suka taho tare da Abdul, iso ta yi mai har zuwa falon Antyn, Anty na zaune a falon ta saka hijabi, har ƙasa Abdul ya duka ya gaishe da ita, cikin fara'a sosai Anty ta amsa gaisuwar shi tare da faɗin "ya hanya!" "Alhamdulillah!" Abdul ya faɗa, gaishe da shi sauran yaran su ka yi tare da miƙewa su ka bar falon dukan su. "Ga waje ka zauna mana ka zauna a ƙasa" Anty ta faɗa ta na kai duban ta wajen da Abdul ya ke zaune a ƙasa. "A'a Anty nan ma ya isa!" Abdul ya faɗa fuskar shi ɗauke da murmushi. Cikin mintuna kaɗan Halima ta cika ma Abdul gaban shi da kayan ciye-ciye da na sha, "Sannu ƴan mata" Abdul ya faɗa yana murmushi don sosai yarinyar ta burge shi, duk da ba ci ze yi ba, amma ya ji daɗin tarbar da aka yi mai sosai. "Bismillah!, Suruki na, bari na kira mai gidan ku gaisa" Anty ta faɗa tare da miƙewa ta yi hanyar ɗakin Kawu. "To se ki zauna ai!' Abdul ya faɗa ya na kai duban shi in da Safnah ta ke tsaye tun shigowar su. Zama ta yi tare da ce wa "yaya yaushe za ku koma?" "Za mu koma ina?" "Katsina mana!" "Ban gane za mu koma ba!" "Yaya don Allah ka bar ni a nan!" Kallon ta ya tsaya yi ba tare da ya ce komai ba, ita kuma sunkuyar da kanta ƙasa ta yi don ba ta son kallo musamman ma na Abdul ɗin. Kafin su sake wata magana su ka ji sallamar Anty da Kawu, waje su ka samu su ka zauna, Abdul ne ya rusuna ya gaishe da Kawu, ba-yabo-ba-fallasa Kawu ya amsa gausuwar ta shi. "Mun same ku lafiya?" Abdul ya sake faɗa. "Alhamdulillah!" Kawu ya faɗa. Sun ɗan taɓa hira kaɗan kafin Abdul ya tafi, bayan ya faɗa mu su maganar sa ranar Safnan, amma be faɗa mu su da waye ba. Kawu ɗakin shi ya koma bayan tafiyar Abdul, daga Safnah se Anty a ɗakin, don yaran ma sunyi bacci. "Safnah wannan shine Abdul ɗin?" "Ehh Anty shi ne" "Amma Safnah ban ga abun ƙi ta tare da shi ba, ƴan matan yanzu sun fi son saurayi mai kyau, kuma wannan ya na da shi, gashi daga ganin shi mutumin kirki ne Safnah!" "Gaskiya ne Anty!, Ko ni idan zan yi adalci zan yi wa Yaya Abdul kyakkyawar shaida, amma Anty kawai ba na son shi ne!" "Safnan ba wai ba ki son shi ba ne!, Zuciyar ki ta na wajen Safwan ne yanzu, shiyasa ba za ki fahimci soyayyar shi ba, amma ki yi ƙoƙarin mantawa da Safwan kwata-kwata, ta haka ne za ki gane ki na son shi. "To Anty nagode sosai!" Hira su ka cigaba da yi har dare ya tsala sosai, sannan su ka nufi ɗakin Anty, don Anty ta ce ta je can su kwanta. *****Washegari ***** Duk yadda Safnah ta so tashi ta ta ya Anty aiki hana ta ta yi, hakan yasa Safnah kwanciya ta sha baccin ta, don tun da su ka zo Zaria ba ta wani samun bacci ba, ga tunani ga kuma hayaniyar gidan biki. Anty ce ta haɗa break fast tare da shirya yaran nata su ka tafi makarantar hadda, sannan ta ta so Kawu don yau bashi da aiki weekend ne, karyawa ya yi shi ma, tare da Kaka, lokacin har ƙarfe 9:00 ta yi, se lokacin Anty ta taso Safnah, wanka ta yi ita ma sannan ta karya. Safnah ɗakin ta ta nufa, ta samu babban akwatin ta ta shiga shirya kayan ta da take buƙatar su, tun daga kan kayan karatun ta, da kayan amfanin ta da sauran su, ba ta ɗauki kayan sawa ba ko guda ɗaya, se da ta cika akwatin sosai da kaya, daƙyar ma ta iya rufe wa, sannan ta jawo akwatin zuwa falon ta. Bayan ta gama ne, kiran Abdul ya shigo, kamar ta fasa ihu haka ta ji don dama a cike take kiris! Ta ke jira ta fashe, abinda ta zata kuwa shine, ta na ɗaga wayar ya ce yana hanya, agogon hannun ta ta duba ta ga 12:15 kuka ta fashe da shi bayan sun gama wayar, ta kai mintuna goma 10 kafin ta share hawayen ta ta fito, Anty na kicin ta na aiki, kicin ɗin Safnah ta shiga tare da ce wa "Sannu da aiki Anty!" "Yawwa Safnah, har kin gama kwashe kayan?" "Ehh Anty!, Yawwa Anty an ga sim ɗin nawa?" "Ehh bari na gama na ɗauko miki" "To Anty, amma kin yi sauri har kin gama shinkafar?" "Ehh mana!, Ba ki ga miyar ma saura kaɗan ba?" "Ehh gashi fa na gani, Anty wai ya na hanya za mu tafi can gidan Amaryar" "To shikenan!, Daga can shikenan kin wuce ko za ki dawo?" "Zan dawo mana Anty!, Ga kayana can ba zan tafi da su ba se gobe" "To shikenan Safnan" Kafin Safnah ta yi wata magana wayar ta ta fara ringing, tsabar takaici ba ta ma ɗaga ba kawai hijabinta ta saka ta nufi waje. Ta same su duk sun fito daga mota su Teemah, ita ta ma manta ya ce za su zo tare, ƙarasawa ta yi ta gaishe da shi, sannan su ka gaisa da su Hindu. "Ku shiga ku gaishe da mutanen gidan se ku zo mu wuce" Abdul ya faɗa tare da komawa cikin motar shi, su kuma su ka nufi cikin gidan. Har cikin ɗakin Anty Safnah ta kai su, su ka zauna sannan ta zo kicin ta shaida wa Anty zuwan su, sauke miyan Anty ta yi tare da kashe Gas ɗin sannan ta nufo ɗakin. Gaisawa su ka yi Safnah ta jere mu su drinks sannan ta fito kicin ta karɓo abincin da Anty ta zuba mu su, ta shigo haɗe da jere mu su a gaban su ta ce "Bismillah!, Ga abincin fa" "Lallai kinsan yaya Abdul na jiran mu shine ki ka wani zubo mana abinci" Meenal ta faɗa. "A'a fa ni se na ci wallahi don ba mu wuce ta yi" Teemah ta faɗa tare da saukowa daga kujera ta jawo filet ɗaya ta hau ci. "Shiyasa na ke son ki Teemah" Safnah ta faɗa. "Ni dai wallahi a ƙoshe nake da na ci" Sa'adatu ta faɗa. "Don Allah ku sauko ku ci mana miye haka, musamman fa na dafa muku saboda yaya Abdul yace tare za ku zo" Safnah ta faɗa don su ci abincin "To ba za mu ba ki kunya ba kuwa bari mu ci!, Amma fa ki je ki faɗawa yaya Abdul mun tsaya ɗa'amun!" Meenal ta faɗa tare da saukowa ita ma. "To ba damuwa, bari na kira shi na faɗa mai" Safnah ta faɗa tare da barin ɗakin, wajen Anty ta dawo ta tarar ta na share kicin. "Safnah ya ki ka fito ki ka bar su kuma?" "Anty na bari su ci abincin ne fa!" "To shikenan" "Anty ɗauko min Sim ɗin kar ki manta!" "To Safnah!, Amma kafin na baki zan miki gargaɗi da ki goge Number Safwan daga ciki!" "To Anty zan goge" Safnan ta faɗa. Ɗaki Anty ta shiga, bayan mintuna biyu2 ta fito ta miƙa mata Sim ɗin, karɓa Safnah ta yi tare da nufar ɗakinta ta saka a cikin kayan da ta haɗa. Ɗakin su ka koma har Anty, hira su ke ɗan yi kaɗan-kaɗan don sun gama cin abincin ma, wayar Safnah ce ta fara ringing ko da ta duba yaya Abdul ne "ku ta so mu je!" Kawai Safnah ta ce ba tare da ta ɗauki wayar ba. Miƙewa su kayi su fito waje, bayan sun yi wa Anty sallama, Safnah se da ta yi wa Anty sallama sannan ta fito su ka nufi ƙofar gidan. A jikin motar su ka samu Abdul ya haɗa rai, ƙarasawa su ka yi wajen tare da buɗe motar su ka shiga amma ban da Safnah, don yana jikin ƙofar da za ta shiga, "Yaya ka yi hakuri, Anty ne ta ce se sun tsaya sun ci abinci" "To shikenan shiga mu je!" Ya faɗa tare da matsa ma ta ta shiga, zagayowa ya yi shi ma ya shiga tare da jan motar, kai tsaye gidan Amarya su ka nufa. Mintuna goma10 ya kai su gidan, fitowa su ka yi ba kowa a tsakar gidan se Sadiq da Faruq da su ka tarar a bakin gate da alama tafiya za su yi, perking Abdul ya yi su ka fita su ka nufi cikin gidan shi kuma ya tsaya a wajen su Sadiq. Sun zo shiga ƙofar falon Safnah ta ga wata ƴar Class ɗin su da alama ta zo wa Salmah biki ne, tsayawa ta yi su ka gaisa, su Teemah kuwa tuni sun shige ciki, Number Safnah ta ba ta sannan su ka yi sallama, tsayawa Safnah ta yi ta na ƙarewa gidan kallo don iya haɗuwa gidan ya haɗu na ƙarshe. "Safnah!" Safnah ta ji an kira sunan ta, gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa don duk duniya ta yi imani mutum ɗaya ne mai wannan Muryar wato Safwan. Ƙasa juyowa ta yi don kafafunta da su ka yi mata nauyi, amma ta na jiyo takun tafiyar shi alamun ya nufo wajen da take. "Safnah ashe ke ce!, Ba gizo idanuwana su ke min ba, Allah na gode maka!" Safwan ya faɗa fuskar shi ɗauke da tsantsar farin ciki. Dakyar Safnah ta daidaita nutsuwarta ta ɗago ta kalle shi, tare da ƙaƙalo murmushin da za'a iya kiran shi da yaƙe ne, ta ce "Ehh Safwan, ya kwana biyu 2" "Lafiya lau, ina ki ka shige ne ko nema na ba ki yi, ba kira ba chat kin sani cikin damuwa!, Kuma me ya kawo ki gidan nan?" "Safwan ashe ba ka manta da ni ba kenan har ka ke tunani na da damuwa akan tafiya ta?" "Haba Safnah ya zan yi na manta da ke!' "Ok!, Na zo bikin Salmah ne dama!" "Salmah kuma?, Miye haɗin ki da ita?" Murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo Safnah ta yi sannan ta daure ta ce "Lefi ne don na zo bikinta?, Kuma na ga ai bikin ka ne kai ma!" "Safnah ki bar wannan magana ki ɗauƙi auren nan a matsayin ba aure ba, saboda ba son rai na aka yi shi ba!" Safwan ya faɗa fuskar shi ɗauke da damuwa. "Safwan kenan! Ban san meyasa ka ke faɗa min haka ba, kamar bansan soyayyar da ta ke tsakanin ku ba tun a School" "A'a Safnah wallahi ban taɓa jin son Salmah a rai na ba ko kaɗan!" "To shikenan!, Ba damuwata ba ce hakan, ni se dai na ce Allah ya ba ku zaman lafiya!" "Safnah ni kuma damuwata ce hakan!, Saboda Safnah ke ce zaɓina, da ke na ke son na ƙare rayuwata!" "Ban fahimci mai ka ke faɗa ba Safwan!, Ka fahimtar da ni!" "Safnah yau ba wani ɓoye-ɓoye don na gaji da dakon son ki da ya ke wahalar da ni, Safnah ina son ki! Ina son ki!! Ina son ki Safnah tun da daɗewa, kuma ke ma na san ki na so na!, Ki daure ki faɗa min haka ko na ji sauƙi a rai na!" Safwan ya faɗa cikin rawar murya kamar mai shirin yin kuka. Ita kuwa Safnah kuka ta fashe da shi mai tsuma zuciya, don zuciyarta ta tsinke, cikin kukan Safnah ta ce "Safwan ba kalmar da na daɗe ina jira ta fito daga bakin ka irin wannan, amma ba ka faɗa min ba!, Safwan nima Ina son ka! Matuƙar so!" Kafin wani ya sake yin magana su ka ji motsin mutum a bayan su, tare da karar faɗin abu. Da sauri su ka juyo a tare, Abdul su ka gani tsaye idanun shi sun kaɗa sun yi jazur, fuskar shi a matuƙar ɗaure kai za ka ce be taɓa dariya ba a rayuwar shi, in da su ke ya nufo a matukar fusace. Zan tsaya anan don ni kai na Abdul ya ba ni tsoro har ta kai alƙalamin rubutu na ya faɗi, amma idan tsoron ya gushe zan ɗauko alƙalamin nawa domin na sanar da ku yadda za ta kasance. Ku kasance da ni har kullum Khadeejerh Ishaq ce ✍️ Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels