Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* PAGE 1️⃣➡️2️⃣ *Federal University dutsinma* Wata y'ar madai-daiciyar mota ce ta tsaya cikin filin school d'in bud'e marfin motar akai cike da takon k'asaita take ta fito daga cikin motar bak'in gilas d'in dage manne da fuskarta ta cire tana bin school d'in da kallo kasancewar zuwanta ne na farko. Can ta tsinkaye wata murya na faman kiranta cike da murna taji an rungumeta da sauri ta waigo tana yamutse fuska da sauri ganin yadda duk suka rirrik'eta ta k'ara b'ata fuska ta ce "wai Bilki dake da Nawwara wai yaushe zaku canza ne shi yasa fa ban so zuwa school d'aya daku ba shi yasa again na ce ku fara yo gaba nabi bayanku shine daga isowata duk kunbi zaku wani kada ni", ta idasa maganar tana k'ara bin school d'in da kallo yadda taga duk Arna sunyi yawa a cikinta da sauri Nawwara ta d'an saketa ta ce "kai Surayya kefa akwai yarfa mutum wallahi mufa murnar zuwanki ne yasa kinga bamu san kowa ba a cikin school d'in nan", Bilki ce ta amshe da cewa "kai gaskiya Surayya daba dan mu k'awaye bane tun na yarinta da tuni mun barki da halinki akwai ki da murd'and'an hali". Ganin kamar sunyi fushi yasa Surayya cewa "kufa dad'i daku akwai saurin fassara mutum nidai kun sani sai kuna hakuri dani school d'in ce kamar b'ata kwanta min a rai ba", ta idasa maganar tana tafiya kamar ba ita tayi maganar ba ganin tabi wata hanya yasa da sauri Nawwara ta ce "Surayya ki tsaya ba'a cika bi ta wannan hanyar bafa tana da matsala", d'an dakatawa tayi da tafiya tana waigowa ta ce "to sabon salo ai na ce dai ana bi dai ko kuma zata iya kaini a inda nake so ina ce hakane?", d'aga mata kai sukai cike da d'an tsoro Bilki ta ce "dan Allah Surayya kiyiwa Allah karki bi ta wannan hanyar akwai tantiran makaranta dake zama ta wajan nan duk school d'in an sansu kuma ana tsoron su ba wadda bai san tarihin su ba". Surayya kuwa tsaki taja tana ci gaba da tafiya tana cewa "zan so jin tarihin mi suka aikata har ake jin tsoron su, to daga yau za'a sake kafa wani tarihin cewa ga wadda bata shakkar kuwa dan banga wadda ya isa ya hanani zaga ko ina ko shiga wani waje dage cikin school d'in nan ba indai zuciyata taso hakan", ta idasa maganar tana shan wata kwana da sauri su Bilki suka rufa mata baya suna mamakin rashin tsoro da kafiya irin na Surayya. Koda tasha kwanar idonta ya gane mata dan-dazon maza sun kai su bakwai sai zuk'ar sugari suke zuciyarta ta buga dumm dammm dakewa tayi tana tafiya irin ko a jikinta tana niyar wuce su da sauri wani cikin y'an iskan dake zaune wajan ya ce "Oga Goga ga wata mai rabon shan duka ta biyo da hanyarka miya kamata muyi mata danna tabbata an sanar da ita waye kai", ya idasa maganar yana kallon Goge dage kallon Surayya da wani salon iskance ya ce "barni da ita wannan daga gani kalar mu ce", ya idasa maganar yana yin wata shegiyar mik'a ya nufi wajanta. Surayya kuwa batai aune ba taga mutum a gabanta ganin sa gaf da ita kamar zai shige jikinta yasa da sauri tad'an matsa tana tushe hancinta saboda warin giyar da yake. Wani murmushin gefan baki yayi yana fiddo harshan sa yana lashe bakinsa kamar tsohon maye yana kallon gefe yana cewa "da alama baki san ana tsoron biyowa ta nan hanyar ba ko? kuma baki san waye Goga ba baki binciki tarihin sa ba dami-dami ya aikata harya kawo wannan matsayin ba kohhh?", ya idasa maganar ya ware mata jajayen idonsa. Da sauri Surayya ta d'an k'ara matsawa cike da k'arfin hali ta dake tana aikwata da wata shegiyar hararara kamar idonta zasu fad'u ta ce "waye kai kuwa inbanda bawan Allah kuma an gaya min ina sane na biyo hanyar tunda naga ai ba wani ya gina hanyar ba kowa nada ikon wucewa in...... Kamin ta idasa maganar ya daka mata wata uwar tsawa da cewa "keeee y'ar gidan abun wacece ke koh y'ar gidan wacece bata isa ina fad'a tana fad'a ba ba'a yota ba kuma baza a tab'a yinta ba", dai-dai lokacin su Bilki suka k'ara su suna tsaye gefe sai ba abinda jikinsu yake sai kyarma na tsananin tsoro. Goga ya bud'e baki da bud'ad'd'iyar muryarsa ya ce "kai gayu ku d'akko min ita sana ku had'a da y'an matan can", wata irin zufa ce ta hanko ma su Nawwara suna fashewa da kuka suna cewa "Surayya kinga abinda kika zamana ko?". Suna gaf da isa inda su Bilki suke Surayya ta saki wata irin dariya mai amsa kuwwa wadda tasa gaba d'aya wajan amsawa d'an gyalan dage jikinta ne ya cire daga kanta gashinta ya sauka har gadon bayanta ya rufe mata fuska ta duk'ar da kanta, cike da mamaki su Nawwara ke dubanta. Goga kuwa dariya shak'iyanci yayi ya ce "mu zaki firgita da aljanun k'arya kai ku dagata bari na d'akkota da kaina", da sauri wadda suka nufi inda Surayya take suka tsaya dan ba k'aramar girgiza su tayi ba dariyar ko dai Goga baiji dariyar da kyau bane kamar fa bata mutane ba ce kai wannan dariyar tafi k'arfin mutum yayi ta. Kamin ya kai gare ta Surayya ta wata irin murya wadda kwata-kwata ba tata bace ta ce "da alama har yanzu Goga baka daddara ba baka daina abinda kake can baya ba dama irin wannan yarinyar nake so tazo wacce bata da tsoro da ita zanyi anfani na shiga jikinta naci ubanku hankali kwance bazan tab'a kashe ka ba dan yanzu ba Goga saina gana ma azabar da sai ka gwamce mutuwa da rayuwa tunda kayi SILAR MUTUWA ta nida wadda nake k'auna", wata irin zabura yayi jin muryar wadda har duniya ta nad'e bazai mance mai ita ba hantar cikinsa ce ta kad'a wata irin zufa ce ke hanko mai kota ina sai zazzare ido yake su kansu wadda suke bimai baya ganin kamar suna Shirin tsire wa yasa ta k'ara sakin wata irin dariya mai firgita ruhin d'an Adam ta nuna inda suke niyar guduwa da hannu dan da nan wasu irin halittu suka bayyana masu mummunar kama fuskar su ba kyan gani suna zaro zungureran harshan su ga wasu zafga-zafgan bulali a hannunsu kamar na k'arfe umarni ta basu kan su fara aiki ai ko ba shiri suka fara zafga masu bulali wata irin azaba suke ji ihu suke babu mai jin su baka Jin k'arar komai sai na ihun su da k'arar bulala. Juyawa tayi tana shak'ama su Nawwara wani farin abu nan take wani nandauyan bacci ya sure su tana sa hannunta ta shafe su b'at suka b'ace daga wajan. Goga kuwa da yayi suman zaune ganinta gabansa tana wata y'ar iskar dariya gashinta ne yayi baya mummunar fuskar ta bayya na da tasa Goga sakin fitsari ganin rabin fuskarta naman dake wajan duk ya zaizaye tsutsotsi na bin wajan idonta ya koma fari fari fat ko d'igon baki babu bakinta wasu irin hak'ora ne y'an guntaye masu masifar sini wani irin jini kalar ruwan ganye ke zubowa tana lashe baki...........✍️ *ZAHRA ROYAL STAR CE* Share fisabilillahi🙏🥰 *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* PAGE 3️⃣➡️4️⃣ Wani irin jini kalar ruwan ganye ke zubowa tana lashe baki, nuna sa tayi da hannunta wani farin haske ya fito ya shigi Goga wata irin zabura yayi yana makyarkyata kamar wanda wutar neper ta kama sai da taga ya wahalu sana ta saki wata irin dariya mai k'arar gaske sana ta b'ace b'at sai dariyar da tayi ce ta karad'e lungu da sako na wajan wata irin amsawa kuwwa dariyar ke yi kamar yanzu ne take dariyar. Su Goga kuwa ganin sun tsira ba wadda ya tsaya d'aukar wanni abu suka arce da mugun gudu yadda kasan ita ce ta biyo su a baya. Basu sauka a ko ina ba sai a wani rub'ab'b'an gida wadda suke kwana kai daka kalle su kasan sun jiga tu wani daga cikin su ya ce "kai Oga na kasa tuna miye ma ya faru a wajan shin muryar wacece muka ji ne?", Kowa shuru yayi dan kwata-kwata kamar anyi masu yasa a cikin kwanyarsu sun kasa tuna shin muryar wacece ma suka da ainahin miye ya faru abinda baza su manta dashi ba dai shine sunsan sun tare wata budurwa ita kanta sun kasa tuna fuskarta, share abun sukai duk dukan da suka sha suka fara jinya ba k'aramar jinya sukai ba suna suka wartsake suka koma fagen shashancin su. A wajan su Surayya kuwa tsintar kansu su kai a gidan da suka kama na wajan makarantar a cikin d'aki sai sharar bacci suke koda suka farka basu kowa komai a ransu ba dan kwata-kwata suma ba'a basu damar su tuna wani abun ba. Zaune Surayya take suna waya da Ammee tana mata fad'an danmi bata Kira su ba data isa ta sanar dasu isarta gashi kinsa mijinki cikin damuwa, dan kuwa Surayya nada aure karatu ne ya kawota an d'aura auran ne a bisa sharad'in saita gama karatu zata tare. Zunb'uro baki Surayya tayi ta ce "Ammee amma ba sai ya kira ni ba sai yaje ya data miki hankali yana ganin ke kad'ai kika rage min Allah sarki Daddy na Allah ya jik'an sa da rahma ina kewar Daddy", ta idasa maganar wasu hawaye na neman kumce mata ita kanta Ammee cikin raunin murya ta ce "kin ganki ko zaki sa zuciyoyinmu karyewa abinda nake so dake yanzu shi SADEEQ mijinki yasa an samar mai aiki a nan school d'in taku zai rink'a koyarwa har ki gama dan saboda ke yasa a samar masa aikin nan", cike da kid'ima Surayya da d'an kishi-kishi ta ce "amma Ammee miye da sai yazo nan wallahi Ammee karki ga school d'in duk Arna sunfi yawa ga y'an mata wadda kwata-kwata basu da kintsi bare kamun kai d'ai-d'aiku ne zaki ga yarinya ta zauna tayi abinda ya kawo ta in...... Kamin ta idasa maganar Ammee ra tare ta da cewa "kinfa San waye mijinki kinsan yafi k'arfin ya zauna yana koyarwa kinsan waye shi a k'asar nan kema Allah ne ya inganta rayuwarki kuma ya dasa masa soyayyar ki kin manta irin wahalar da kika sha na soyayyar ku aka rasa wazai furta yana san wani cikin ku shi girman kai kema haka duk da ya kasance d'an uwa a gare ki duk sadda yazo gidan nan danke yake zuwa amma saiya wani share yayi kamar badan ke yazo ba, to taya za'ai mai irin wannan hali kike zaton ya kalli wata mace yadda ma yake sonki ke kinsan hakan ma bazai yuwu ba", kunya ce ta kama Surayya yadda Ammee ta fahimci kishi ke damunta Ammee ta k'ara mata fad'a kan cewa "Surayya ki kama kanki karki ga cewa ai gaku waje d'aya ki basa kanki tun kan a kaiki d'akinsa ki kankaro ma kanki daraja again kuma ki kama kanki Kinga ke matar aure ce koda yake tunda Sadeeg na kusa nasan shi shima da d'an banzan kishin tsiya dole nasan zuwansa sai kafa miki doka ni wallahi yayi min dai-dai ma daya biyo kin", ta idasa maganar tana sauraron yadda Surayya ke zuba shagwab'a ita fa za'a takura mata, bayan sunyi sallama da Ammee . Su Nawwara dake yankan kayan miya sun d'ora abinci Bilki ta ce "ai wallahi Ammee gaskiya take fad'a miki ni Sadeeg yamin dai-dai daya biyo bayanki ni dama nasan Allah tsawon shekaru bazai iya hakurin rashinki ba bare baya ganinki", Surayya ta d'an gyara zama akan katifar da take ta ce "ni ba wannan ba kawai dai school d'in nan akwai k'ura dan na rantse duk wacce ta shiga harkar miji na kunsan Allah zan iya mata koma miye indai akan Sadeeg ne dan haka za'a sha kallo wallahi", ta idasa maganar tana tab'e baki Nawwara ce ta ce "hmm shi kansa saiya miki shamaki da kowanne d'a namiji ko gaisawa kuwa wadda shi yama fiki kishi GARKUWA kai zafa asha kallo wani ma tab'a zaton zaiga Garkuwa da idonsa ba amma ta dalilinki zai gansa duk Najeria fa ansan mijinki Garkuwa ai wallahi Surayya ki k'ara godema Allah, ai kawai dai Allah ya kyauta ni ban tab'a ganin soyayya irin taku ba". Washe gari tun wajan k'arfe 8:00am dai-dai suka fita lecture da yake duk abu d'aya suke karanta suna cikin class kowa na harkar gabansa ana jiran Malamin da zai shigo na gaba wasu na wajen class ba zato ba tsammani wani arnan k'amshi yayima gaba d'aya class d'in sallama duka mutanan dake ajin har rige-rigen waigawa suke suka wannan wane sabon Malami ne aka kawo musu, ita kuwa Surayya da tun isowar k'amshin a hancinta tasan waye zuciyarta sai bugawa take jinin jikinta na gudu lumshe idonta tayi tana da tabbacin kenan shi ne wadda zai d'auke su English tab ta tab'e baki tana bin y'an matan ajin da kallo yadda ko wacce har suna rige-rigen furta "WOW", kai bama mata ba hatta maza sai da suka sarama Sadeeg. Tafiya yake cikin k'asaita harya isa gaban allo tsaya yayi yana juyowa gaba d'ayan sa gaba d'aya y'an matan dake ajin sai da sukai MUTUWAR zaune d'an kuwa kyan sa da kwarjininsa ba k'ara min tafiya yayi da imaninsu ba sanye yake da wata arniyar shadda ruwan sararin samaniya da hular zanna bukar dake zaune a kansa dogo ne ba irin sosai d'in nan ba yana k'irar k'arfi daka kalli damtsin hannunsa kasan cewar yana motsa jiki gaba d'aya jikinsa a murd'e yake yana da yawan gashin gira girarsa har had'ewa take idonunsa kuwa hmmm wai wai wai Allah yayi halitta tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan halitta mai tsananin kyau da kwarji idonsa daga cikinsa kalar ruwan k'asa ne sosai har wani shek'i suke fari kal dasu in aka zo fagen hanci kuwa ba'a magana dan hancinsa dogo ne daga k'asansa ya d'an bud'e kad'an saiya k'ara ma fuskar sa cikar zati idan aka zo wajan bakinsa kuwa kai ya Allah ba'a cewa komai bakinsa mai zanan love ne d'an k'ara mi dashi daga saman lab'b'ansa sai ka rantse yasa janbaki ne amma ainahin kalar su ce jawur dasu. Babu abinda y'an matan ke furtawa sai Masha Allah ko wacce tana addu'ar inama ace wannan bawan Allah ya zamo miji a gare ta ai basu k'ara shiga wani shauk'in ba sai da suka tsinkayi muryarsa mai matuk'ar zak'in gaske da dad'in sauraro turanci yake yadda kasan na k'asashen k'etare suman zaune sukai jin irin turancin dake fitowa daga bakin sa da k'arin mamakin wai shi zai d'auke su English basu k'ara shiga tsananin mamaki sai dai sukaji sunan sa Ahmed Sadeeg Garkuwa, waye bai san Garkuwa a Najeria ba Garkuwar tallakawa tun sunan Mahaifinsa ne tun asali Mahaifinsa mai tsananin taimakon na k'asa dashi ne shi yasa mutane suka sa mai Garkuwar talaka Mahaifinsa mai kud'in gaske ne shi kad'ai Allah ya basa tun yana k'ara mi iyayansa suka rasu baki d'aya y'an uwa sukayi ma dukiyar sa caaa kowa yana buk'atar ace shi zai gaje ta yasha wahalar rayuwa wajan dangi dan sai da suka ga dukiyar ta tafi k'arewa suka guje shi sai dai Allah mai iko ne sadda Sadeeg zai taso ya samu sukula ship aka d'au nauyinsa zuwa k'asar India a Indiar ma yasha wahalar karatu dan kuwa akwai wani d'an k'asar daya fahimci Sadeeg Garkuwa nada mugun k'ok'ari ya sako shi gaba tunda Sadeeg yana yo first class a school d'in kamin zuwan Sadeeg Garkuwa shike yo first class hakan yasa hassada ta shiga tsakanin su ya hassala har mahaifinshi zuwa yayi mai gargad'i mai zafi wadda yasa ba k'aramar rigima suka sha ba har Sadeeg nada zafin zuciya Allah yayosa da shegen k'arfi hakan yasa yayi ma y'an baradan sa mugun duka. Suna gaf da kama karatu aka kira Sadeeg kan cewa za'a basa aiki yana gama karatun sa kasancewar shi ke yo first class a inda ya ce shi bazai amshi aikinsu ba sai ma shine zai basu aiki dan shi ya taso da hazak'ar k'irk'irar abu su kansu turawan sunyi mamakin jin furicinsa yana bak'ar fata sai girman kai ya ce musu shi ba girman kai yake nuna musu ba sai gaba tar masu da wani Application daya k'irk'ira da kansa sunyi mamaki d'an Najeria ne zai iya k'irk'irar wani application, ai basu k'ara tsure da tsananin mamaki ba sai da ranar da zasu kammala school d'in aka tara duban jama'a a yadda ya gabatar masu da irin app d'in daya k'irk'ira sunyi mamaki wadda har yasa suka kasa cewa komai ba k'ananan kud'i ya samu ba wani ma kyauta zai bashi inda wadda suke takun saka dashi shi kansa sai da ya jinjina masa shi da Mahaifinsa ko ina basa girma ake cikin k'asar India bai baro k'asar India ba sai da ya bud'e kanfani har uku wadda yake mallakin sa sana a dawo Najeria to a k'asar sa ma bai zauna nan ba sai da ya tabbatar ya bud'e kanfani har hud'u wadda suka fi na Indiar ma ya d'auki talakawa wadda suke neman aiki inda sunan Garkuwa ya k'ara binsa duk inda ya zaga Garkuwar talaka hatta lambar motarsa Ahmad Sadeeg Garkuwa talaka ba inda ba'a sansa ba a k'asa Najeria harma da k'asashen k'etare y'an mata kuwa suna mahaukacin son sa sai dai akwai shi da kwarji bare wata ta kawo mai wargi a sadda ya fara ganin Surayya yaje kaima Ammee ziyara dan ya kasance d'an uwa ne a gare su ta b'an garan Uban Surayya ba abinda ya fara had'a su sai rashin jituwa shi kuma tunda ya fara ganinta yadda ta nuna kwata-kwata bata tsoron sa ko shakkar sa dama macen daya ke son samu kenan wadda bata shakkar kallon idonsa tayi magana wadda zata kama kanta wadda take da class shi kansa sai da ya jinjina ma Surayya yadda duk da tana mahaukacin sonsa bata fito ta sanar dashi ba har sai da yazo da kansa ya furta harya nemi auranta..............✍️ *ZAHRA ROYAL STAR CE* Share fisabilillahi🥰🙏 *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* PAGE 3️⃣➡️4️⃣ Wani irin jini kalar ruwan ganye ke zubowa tana lashe baki, nuna sa tayi da hannunta wani farin haske ya fito ya shigi Goga wata irin zabura yayi yana makyarkyata kamar wanda wutar neper ta kama sai da taga ya wahalu sana ta saki wata irin dariya mai k'arar gaske sana ta b'ace b'at sai dariyar da tayi ce ta karad'e lungu da sako na wajan wata irin amsawa kuwwa dariyar ke yi kamar yanzu ne take dariyar. Su Goga kuwa ganin sun tsira ba wadda ya tsaya d'aukar wanni abu suka arce da mugun gudu yadda kasan ita ce ta biyo su a baya. Basu sauka a ko ina ba sai a wani rub'ab'b'an gida wadda suke kwana kai daka kalle su kasan sun jiga tu wani daga cikin su ya ce "kai Oga na kasa tuna miye ma ya faru a wajan shin muryar wacece muka ji ne?", Kowa shuru yayi dan kwata-kwata kamar anyi masu yasa a cikin kwanyarsu sun kasa tuna shin muryar wacece ma suka da ainahin miye ya faru abinda baza su manta dashi ba dai shine sunsan sun tare wata budurwa ita kanta sun kasa tuna fuskarta, share abun sukai duk dukan da suka sha suka fara jinya ba k'aramar jinya sukai ba suna suka wartsake suka koma fagen shashancin su. A wajan su Surayya kuwa tsintar kansu su kai a gidan da suka kama na wajan makarantar a cikin d'aki sai sharar bacci suke koda suka farka basu kowa komai a ransu ba dan kwata-kwata suma ba'a basu damar su tuna wani abun ba. Zaune Surayya take suna waya da Ammee tana mata fad'an danmi bata Kira su ba data isa ta sanar dasu isarta gashi kinsa mijinki cikin damuwa, dan kuwa Surayya nada aure karatu ne ya kawota an d'aura auran ne a bisa sharad'in saita gama karatu zata tare. Zunb'uro baki Surayya tayi ta ce "Ammee amma ba sai ya kira ni ba sai yaje ya data miki hankali yana ganin ke kad'ai kika rage min Allah sarki Daddy na Allah ya jik'an sa da rahma ina kewar Daddy", ta idasa maganar wasu hawaye na neman kumce mata ita kanta Ammee cikin raunin murya ta ce "kin ganki ko zaki sa zuciyoyinmu karyewa abinda nake so dake yanzu shi SADEEQ mijinki yasa an samar mai aiki a nan school d'in taku zai rink'a koyarwa har ki gama dan saboda ke yasa a samar masa aikin nan", cike da kid'ima Surayya da d'an kishi-kishi ta ce "amma Ammee miye da sai yazo nan wallahi Ammee karki ga school d'in duk Arna sunfi yawa ga y'an mata wadda kwata-kwata basu da kintsi bare kamun kai d'ai-d'aiku ne zaki ga yarinya ta zauna tayi abinda ya kawo ta in...... Kamin ta idasa maganar Ammee ra tare ta da cewa "kinfa San waye mijinki kinsan yafi k'arfin ya zauna yana koyarwa kinsan waye shi a k'asar nan kema Allah ne ya inganta rayuwarki kuma ya dasa masa soyayyar ki kin manta irin wahalar da kika sha na soyayyar ku aka rasa wazai furta yana san wani cikin ku shi girman kai kema haka duk da ya kasance d'an uwa a gare ki duk sadda yazo gidan nan danke yake zuwa amma saiya wani share yayi kamar badan ke yazo ba, to taya za'ai mai irin wannan hali kike zaton ya kalli wata mace yadda ma yake sonki ke kinsan hakan ma bazai yuwu ba", kunya ce ta kama Surayya yadda Ammee ta fahimci kishi ke damunta Ammee ta k'ara mata fad'a kan cewa "Surayya ki kama kanki karki ga cewa ai gaku waje d'aya ki basa kanki tun kan a kaiki d'akinsa ki kankaro ma kanki daraja again kuma ki kama kanki Kinga ke matar aure ce koda yake tunda Sadeeg na kusa nasan shi shima da d'an banzan kishin tsiya dole nasan zuwansa sai kafa miki doka ni wallahi yayi min dai-dai ma daya biyo kin", ta idasa maganar tana sauraron yadda Surayya ke zuba shagwab'a ita fa za'a takura mata, bayan sunyi sallama da Ammee . Su Nawwara dake yankan kayan miya sun d'ora abinci Bilki ta ce "ai wallahi Ammee gaskiya take fad'a miki ni Sadeeg yamin dai-dai daya biyo bayanki ni dama nasan Allah tsawon shekaru bazai iya hakurin rashinki ba bare baya ganinki", Surayya ta d'an gyara zama akan katifar da take ta ce "ni ba wannan ba kawai dai school d'in nan akwai k'ura dan na rantse duk wacce ta shiga harkar miji na kunsan Allah zan iya mata koma miye indai akan Sadeeg ne dan haka za'a sha kallo wallahi", ta idasa maganar tana tab'e baki Nawwara ce ta ce "hmm shi kansa saiya miki shamaki da kowanne d'a namiji ko gaisawa kuwa wadda shi yama fiki kishi GARKUWA kai zafa asha kallo wani ma tab'a zaton zaiga Garkuwa da idonsa ba amma ta dalilinki zai gansa duk Najeria fa ansan mijinki Garkuwa ai wallahi Surayya ki k'ara godema Allah, ai kawai dai Allah ya kyauta ni ban tab'a ganin soyayya irin taku ba". Washe gari tun wajan k'arfe 8:00am dai-dai suka fita lecture da yake duk abu d'aya suke karanta suna cikin class kowa na harkar gabansa ana jiran Malamin da zai shigo na gaba wasu na wajen class ba zato ba tsammani wani arnan k'amshi yayima gaba d'aya class d'in sallama duka mutanan dake ajin har rige-rigen waigawa suke suka wannan wane sabon Malami ne aka kawo musu, ita kuwa Surayya da tun isowar k'amshin a hancinta tasan waye zuciyarta sai bugawa take jinin jikinta na gudu lumshe idonta tayi tana da tabbacin kenan shi ne wadda zai d'auke su English tab ta tab'e baki tana bin y'an matan ajin da kallo yadda ko wacce har suna rige-rigen furta "WOW", kai bama mata ba hatta maza sai da suka sarama Sadeeg. Tafiya yake cikin k'asaita harya isa gaban allo tsaya yayi yana juyowa gaba d'ayan sa gaba d'aya y'an matan dake ajin sai da sukai MUTUWAR zaune d'an kuwa kyan sa da kwarjininsa ba k'ara min tafiya yayi da imaninsu ba sanye yake da wata arniyar shadda ruwan sararin samaniya da hular zanna bukar dake zaune a kansa dogo ne ba irin sosai d'in nan ba yana k'irar k'arfi daka kalli damtsin hannunsa kasan cewar yana motsa jiki gaba d'aya jikinsa a murd'e yake yana da yawan gashin gira girarsa har had'ewa take idonunsa kuwa hmmm wai wai wai Allah yayi halitta tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan halitta mai tsananin kyau da kwarji idonsa daga cikinsa kalar ruwan k'asa ne sosai har wani shek'i suke fari kal dasu in aka zo fagen hanci kuwa ba'a magana dan hancinsa dogo ne daga k'asansa ya d'an bud'e kad'an saiya k'ara ma fuskar sa cikar zati idan aka zo wajan bakinsa kuwa kai ya Allah ba'a cewa komai bakinsa mai zanan love ne d'an k'ara mi dashi daga saman lab'b'ansa sai ka rantse yasa janbaki ne amma ainahin kalar su ce jawur dasu. Babu abinda y'an matan ke furtawa sai Masha Allah ko wacce tana addu'ar inama ace wannan bawan Allah ya zamo miji a gare ta ai basu k'ara shiga wani shauk'in ba sai da suka tsinkayi muryarsa mai matuk'ar zak'in gaske da dad'in sauraro turanci yake yadda kasan na k'asashen k'etare suman zaune sukai jin irin turancin dake fitowa daga bakin sa da k'arin mamakin wai shi zai d'auke su English basu k'ara shiga tsananin mamaki sai dai sukaji sunan sa Ahmed Sadeeg Garkuwa, waye bai san Garkuwa a Najeria ba Garkuwar tallakawa tun sunan Mahaifinsa ne tun asali Mahaifinsa mai tsananin taimakon na k'asa dashi ne shi yasa mutane suka sa mai Garkuwar talaka Mahaifinsa mai kud'in gaske ne shi kad'ai Allah ya basa tun yana k'ara mi iyayansa suka rasu baki d'aya y'an uwa sukayi ma dukiyar sa caaa kowa yana buk'atar ace shi zai gaje ta yasha wahalar rayuwa wajan dangi dan sai da suka ga dukiyar ta tafi k'arewa suka guje shi sai dai Allah mai iko ne sadda Sadeeg zai taso ya samu sukula ship aka d'au nauyinsa zuwa k'asar India a Indiar ma yasha wahalar karatu dan kuwa akwai wani d'an k'asar daya fahimci Sadeeg Garkuwa nada mugun k'ok'ari ya sako shi gaba tunda Sadeeg yana yo first class a school d'in kamin zuwan Sadeeg Garkuwa shike yo first class hakan yasa hassada ta shiga tsakanin su ya hassala har mahaifinshi zuwa yayi mai gargad'i mai zafi wadda yasa ba k'aramar rigima suka sha ba har Sadeeg nada zafin zuciya Allah yayosa da shegen k'arfi hakan yasa yayi ma y'an baradan sa mugun duka. Suna gaf da gama karatu aka kira Sadeeg kan cewa za'a basa aiki yana gama karatun sa kasancewar shi ke yo first class a inda ya ce shi bazai amshi aikinsu ba sai ma shine zai basu aiki dan shi ya taso da hazak'ar k'irk'irar abu su kansu turawan sunyi mamakin jin furicinsa yana bak'ar fata sai girman kai ya ce musu shi ba girman kai yake nuna musu ba sai gaba tar masu da wani Application daya k'irk'ira da kansa sunyi mamaki d'an Najeria ne zai iya k'irk'irar wani application, ai basu k'ara tsure da tsananin mamaki ba sai da ranar da zasu kammala school d'in aka tara duban jama'a a yadda ya gabatar masu da irin app d'in daya k'irk'ira sunyi mamaki wadda har yasa suka kasa cewa komai ba k'ananan kud'i ya samu ba wani ma kyauta zai bashi inda wadda suke takun saka dashi shi kansa sai da ya jinjina masa shi da Mahaifinsa ko ina basa girma ake cikin k'asar India bai baro k'asar India ba sai da ya bud'e kanfani har uku wadda yake mallakin sa sana a dawo Najeria to a k'asar sa ma bai zauna nan ba sai da ya tabbatar ya bud'e kanfani har hud'u wadda suka fi na Indiar ma ya d'auki talakawa wadda suke neman aiki inda sunan Garkuwa ya k'ara binsa duk inda ya zaga Garkuwar talaka hatta lambar motarsa Ahmad Sadeeg Garkuwa talaka ba inda ba'a sansa ba a k'asa Najeria harma da k'asashen k'etare y'an mata kuwa suna mahaukacin son sa sai dai akwai shi da kwarji bare wata ta kawo mai wargi a sadda ya fara ganin Surayya yaje kaima Ammee ziyara dan ya kasance d'an uwa ne a gare su ta b'an garan Uban Surayya ba abinda ya fara had'a su sai rashin jituwa shi kuma tunda ya fara ganinta yadda ta nuna kwata-kwata bata tsoron sa ko shakkar sa dama macen daya ke son samu kenan wadda bata shakkar kallon idonsa tayi magana wadda zata kama kanta wadda take da class shi kansa sai da ya jinjina ma Surayya yadda duk da tana mahaukacin sonsa bata fito ta sanar dashi ba har sai da yazo da kansa ya furta harya nemi auranta..............✍️ *ZAHRA ROYAL STAR CE* Share fisabilillahi🥰🙏 *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* PAGE 5️⃣➡️6️⃣ Dalla-dallah ya fara masu lasin cikin turancin sa mai dad'in sauraro harda hausa yake had'awa domin afi ganewa. Yana gamawa ya jefo wata tabbaya shuru ajin yayi baka jin ko tari tsit kallon y'an ajin yake da idonsa masu matuk'ar shek'i da hannunsa yayi manuniya ya ce "you", ya nuna Surayya wani irin rass taji gabanta yayi wata irin bugawa dama tasan za'a rina nunawa zaiyi kamar bai tab'a ganinta ba da harshan turancin ya ce ta fito gaban allo jikinta ne ya fara rawa da kyar ta fito idon mutane yayi mata caaa hararara kawai take aika mai baima san tana yi ba abunda ya k'ara bata mamaki data tsinkayi muryarsa wai minene sunanta wani miyau ta had'iye a hankali ta basa amsa wata tabbaya ya jefo mata ya ce ta juya taba y'an class amsa. Kowa ita yake sauraro jikinta inba kyarma dan yawan idonun mutane yayi mata yawa wasu ma haushinta suke ji har sun fara kishi a kanta ko wacce tasu ita aka tabbaya koda bata sani ba ai ko sunan ta ya sani tayi sa'a. Wasu basuyi tsammani ba suka fara jin wani daddad'an turanci har yana so yafi nasa zaki, kunsa muryar mace sosai take bayani wadda tasa gaba d'aya mutane suman zaune harda shi kansa Ogan shi dama yana so yaga shin tana maida hankali tunda a secondary kokuwa. Tana idasawa aka fara tafi da yawan mazan ajin ta birgesu tana kallonsa da idanuwata ita masu girman gaske wani murmushi ta jefa mai wadda ya kusa sashi zuzucewa da sauri kuma ya maze kamar bashi ba ta koma ta zauna tana sauke wata irin ajiyar zuciya yana gamawa ya fice yadda kasan ya tafi da zuciyar y'an matan ajin wasu yana fita kamar jira suke suka fara zancan sa. Cike da jin d'an haushi Surayya taja su Nawwara suka fice daga ajin domin zuwa masallaci yin sallah domin k'arfe d'aya har tayi ta gaji dajin yadda ko wacce banza ke zuzuta mijinta zuciyarta har wani motsawa take. Suna fitowa daga masallaci bayan sunyi sallar taji wayar ta na k'ara d'akkowa tayi ganin sunan Hubby yasa ta murgud'a ma wayar baki kamar yana gabanta su Nawwara kuwa sai dariya suke mata kamar baza ta d'au wayar ba tana gaf da tsinkewa ta d'auka ta k'ara a kunne daga sallamar da tayi bata k'ara cewa komai ba tana sauraron muryarsa mai sata shiga wani shauk'in k'aunarsa taji ya ce "ina office kizo ki same ni", turo baki tayi cike da shagwab'a ta ce "amma lecture zamu shiga fa", cikin harshan turancin ya ce mata "bana son gaddama fa kin sani zan iya zuwa har class d'in naku na d'auke ki Allah kinsan zan iya ko in......kamin yama idasa maganar da yake son fad'a ta yanke wayar tana nufar office d'in nashi a zuciya kuwa cewa take kad'an daga aikin Sadeeg Garkuwa tsaf zai iya barinta da jin kunyar jama'a, sai da tayi tabbaya taje ga office d'in dan iyanzu ba wadda bai sheda wanzuwarshu a school d'in ba yadda aka basa babban matsayi shi kansa Office d'in nasa abin kallo ne dan sauran Malamai ba k'ara min ji suke dashi ba har cewa suke su ai gaba ta kai su ko banza makarantar su ta kafa tarihi na zuwan Garkuwa cikinta, ba yadda ba taiba su Nawwara su rakata sukak'iya suka ce "ina zamu shiga tsakanin mata da miji yana buk'atar ganinki ne shi yasa sai kin dawo", cike da jin haushi tabarsu kamar ta d'ora hannu akai ta zunduma ihu haka take ji. Shigarta Office d'in abinda tagani ne yasa taja turus ta tsaya ganin wata mace tasha wasu shegun kaya daga gani ma wannan ba dai d'aliba ba sai dai ko Mlm ce wani irin kishi ne ya rufe Surayya duk da tasan halin mijinta kuma taga shi Sadeeg bata ita yake ba nunwa ma yayi kamar ba kowa a gabansa, aikin gabansa kawai yake ganin shigowar ta yasa ya tashi kad'an ya saki fuskarsa cikin harshan turanci ya ce "Dr Zuby zaki d'an iya bamu waje nida halali na", wani irin dammm dumm taji gabanta ya fad'i juyowa tayi tana kallon Surayya, mi yake nufi ne ba dai matarsa yake nufin wannan y'ar abar ita ce ba kenan duk burin data ci ya rushe kenan. Tashi tayi jiki ba kwari ta fice daga Office d'in zuciyarta na zafi. Tana fita Surayya ta juya cike da fushi zata fice tana turo baki da sauri ya sha gabanta yana turata jikin bango kallonta yake da rikitattun idonsa k'asa tayi da kanta dan kwata-kwata yau d'in wani irin kwarjini yayi mata zata bud'e baki tayi magana tana faman turo baki bata zata ko tsammani ba ya had'e bakinsu waje d'aya jikinta ne ya kama kyarma kamar wacce aka jonama lantarki kwata-kwata ta kasa d'aukar abun saboda bata tab'a yi ba ganin yadda jikinta ke kyarma yasa a hankali ya zare bakinsa cikin tana ya juyawa ya koma kan kujerar dake office d'in yana cewa "hukuncin ki kenan idan kika k'ara min kaddama ban sallame ki zaki fita", ya idasa maganar yana shar mur, irin baya son raini yadda kasan bashi ya gama kiss d'in ta ba. Cikin sanyin jiki take binsa da kallo ganin yana nuna mata kujera yasa dole ta zauna a hankali kamar wadda aka cirema lakka k'asa tayi da kanta can ta tsinkaye muryarsa yana cewa "ki tabbatar gobe ki sanyo hijab inda hali ma kisa abun rufe fuska bana son kina sa gyalan nan kin sani, dan haka daga yau bana son in k'ara ganin wani wai shi gyale a jikinki kinji?", Da sauri da d'ago tana kallonsa cike da mamaki tasan za'a rina ita wallahi takura mata zaiyi zuwanshi school d'in nan haba ta idasa maganar a zuci can taji muryarsa ya ce "zan takura miki kike cewa ko?", Da sauri ta k'ara dubansa cike da mamakinsa wai shi kamar wani aljani. Ganin kallon da take mai yasa yashi yin wani shegen murmushi na gefen baki wadda ya k'ara ma fuskarsa tsananin kyau ya ce "zaki iya tafiya ba abinda kuke buk'ata na anfani keda k'awayan naki?", Tashi tayi dan dama a k'agare take tana cewa "a'a babu abinda muke buk'ata akwai komai idan ma akwai wani abun zan sanar da kai", tana maganar tana niyar barin Office d'in tana gaf da ficewa ya ce "daka ta", tsayawa tayi bata waiga ba, jinsa tayi a bayanta ya rungumeta ta baya yana fesa mata hucin numfashinsa wata irin zubura tayi da sauri ya k'ara rik'e ta yana k'ara mannata a jikinsa jikinta dan da nan ya fara rawa kai daka kalla kasan bata saba kasancewa da wani d'a namiji a irin wannan yana yin ba. Sakinta yayi yana nuna mata hanya kan zata iya fita ai da sauri harda had'awa da d'an gudu ta fice shi kuwa dariya ma ta bashi, murmushi yayi yana shafa lanlausan sajansa wadda yake zagaye da kyakkyawar fuskarsa gashi ya k'ara mai wani sahihin kyau mai fisgar mutum, wani irin nishad'i yake ji idan yana tare da Surayya yasan Surayya ta daban ce. Sadda zata fito yamma tayi sosai sai ya kasance d'ai-d'aiku ne a school d'in can kamar ance ta waiga taga su Goga sunyi ma wata yarinya caaa sai mutumcinta suke ci wani irin abu ne taji ya shege ta idonta yayi jajawur hankalinta ya gushe jikinta har wani kyarma yake na b'acin rai. Su Goga basuyi tsammani ba kawai suga ka mutum a gabansu a yanzu sanye take da fararan kaya kanta a k'asa cike da wata irin murya ta ce "wato kudai bazaku tab'a dai na cin zarafin mace ba ko ni kuma bazan gaji da gana muku azaba ba ina mantar daku gobe ku k'ara na sake k'ara muku wata azabar, har sai Goga ka kai kanka koto ta bimini hakki na, na kashe min abin k'aunata da kayi can baya an danne min hakki ba'a yi muku komai ba to wannan na rantse da sarkin da ya halicci ni sai kakai kanka da kanka koto an yanke maka hukuncin dai-dai da abinda ka shuka lokaci na nan tafe da zansa a wannan baiwar Allah da nake jikinta zansa ta bin ciko abinda kayi min a rayuwa Goga bazan tab'a yafe ma ba bazan tab'a bari ka zauna lafiya baaaaa", ta idasa maganar cike da wata irin murya mai amsa kuwwa muryar har wani rarrabuwa take kashi kashi. Wata irin zubura su Goga su kai suna shirin arcewa da mugun gudu, wadda suke ma cin mutumci kuwa tuni an gusar mata da hankali an kaida ta daga wajan su kuwa suna k'ok'arin guduwa ta nuna bayansu da zungureran hannunta da yayi tsawo kamar shantu dan-danan wasu irin karnuka suka wanzu a wajan karnukan ba kyan gani bakinsu zak'o-zak'o da wasu irin hakura bakinsu na zubar da wani jini mai shegen kauri kallon fuskasu kuwa saita sa mutum zaucewa, umarni ta basu kamin kace kwabo sun bisu a goje gudu suke suna neman ceto babu ma mai jinsu bare ya gansu kwata-kwata an kaida hankalin mutane daga gare su sai da karnukan nan sukayi masu kaca-kaca da jiki duk sun raunata su sana suka b'ace b'at kamar ba'a yi wanzuwarsu a duran duniya ba. Basu daina gudu ba har sai da suka isa gidan da suke inda suke kwana suna shiga wani babban parlo nasu duk tarkacan shaye-shaye ne cike da parlon suna faman ihu da kuka kamar k'ananan yara dan kuwa wani irin rad'ad'i suke ji a jikinsu inda karnukan suka yayyage su ji suke yadda kasan ana zuba masu gishiri akan ciwon sai birgima suke a k'asa bare Goga kamar da gayya Karan da aka turo mai yafi mai lahani.......✍️ *ZAHRA ROYAL STAR CE* Share fisabilillahi🥰🙏 *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* PAGE 7️⃣➡️8️⃣ Suna cikin shan wannan azaba suka tsinkayi wata murya mai amsa kuwwa harda wata irin dariya aka ce "wai ku nufin kun tsere kenan ai yau azabar ku ta daban ce hahahaha", aka idasa maganar da wata irin dariya dariyar na rarrabuwa kashi-kashi. Wata irin zabura sukai suna shirin arcewa a guje tana daga zaune akanta a k'asa wani irin gashi ne a tsakiyar kanta wuta na faman cinsa yana k'unewa wani na tsirowa hatta jikinta gashi ne kamar biranya wani irin shegen kallo take musu ganin suna kaiwa k'ofar ta datse gam. Tsayawa sukai sai rawar d'ari suke suna hawaye mutanan naku Goga harda sakin fitsari wata dariyar tayi tana kallon wani faranti shak'e da wiwi kallonsa tayi tana lauyar da kai nunasa tayi da yatsa nan take cikin farantin ya koma cike da wasu irin tsutsotsi marassa kyan gani juyowa tayi ta ce "bismillah ku fara ci yanzu na ceeee", ta idasa maganar cike da bada umarni, ai dan da nan jikinsu ya kama wata irin kyarma suna zubewa k'asa har suna had'a baki wajan cewa "dan girman Allah kuke ganinmu bamu muke ganin ku ba kiwa Allah ki yafe mana ai in muka ci wannan irin abincin naku ai sai dai wasunmu badai mu ba", dariya ta kece da ita tana d'aga kanta sama tsananin dariyar da take ce d'akin ya fara wata irin girgiza kamar zai tashi daga inda aka gina sa. Had'ewa sukai suka cure waje d'aya dariyar ba k'aramar firgita su tayi ba d'agowa tayi tana bin su da kallo cikin tulun gashin dayayi ma fuskarta kawanya ta ce "ashe har kunsan Allah dan ubanku zaka fara ci ko kowa sai na fara d'aukar ranku d'ai-d'ai da d'ai-d'ai", ai har suna rige-rigen jawo filat d'in kuka suke kamar mi ai suna had'a ido na tsutsotsin nan yadda suka ga kamar hararara suke aika musu yasa wasunsu fara sumewa a nan take wani irin kuka ne suka fara ji kamar na jarirrai ga wata irin iska data mamaye ilahirin parlon ji sukai kamar ana zagaye su ana wata irin magana cikin wani irin yare maganar na fitowa kamar ana rad'a ga wata irin dariya kamar ta jinjirin jaki ga parlon duhu ya mamaye shi sauran daba su sume ba tuni suma sun riga da sun sume hankalinsu yabar jikinsu. Surayya kuwa bata tashi tsintar kanta ba sai a d'akinsu sallar asubahi su Nawwara suka tashi suka ga ita ce ta tada su sunyi mamaki suna son tabbayar ta amma sun kasa idan ita kanta tashi tayi sallar ta ganta kwance a kan gadonta. Gari na idasa wayewa suka shirya suka nufi cikin school suna tafiya sanye take da hijab har k'asa dan taji gargad'in Sadeeg inya fad'i abu yafi so ayi nan take tafiya take waya manne a kunanta tana waya da Ammee tana sanar da ita semester ta kusa k'arewa suna shirin fara exams dan kuwa school d'insu karantunsu gudu yake amma suna mugun kada d'alibai tana sauke wayar taga wasu y'an mata sunsha gaban su daka kalle su kasan y'an tasha ne dan kuwa sai wani kallo suke aika musu suna faman taunar chingum, Bilki ce ta ce "bayin Allah lafiya dai?", da sauri wata tasha gaban Surayya ganin zata rab'a su ta wuce dan ita bata ga anfanin tsayawa da wa'innan matan ba marassa kamun kai zaro ido Surayya tayi tana bin wadda tasha gabanta ta ce "ina kuma zaki baki ji miya kawo mu ba", Surayya kuwa wani murmushi tayi maisa ma wadda akai danshi jin haushi dan kuwa na rainin wayo ne ta ce "to mi zan tsaya naji inba shirman Dr Zuby data baku labari na shine kuka kwaso k'afa domin wai ku jamin kunne akan saita auri Sadeeg Garkuwa hmm to tun wuri ku fad'a mata cewar Ahmad Sadeeg Garkuwa na Surayya ne ita kad'ai taje ta binciki waye shi in banda ni ita bata isa ta ganshi ba bare harta yi tink'aho wai saita shigo rayuwarmu da alama har yanzu bata san waye Garkuwa ba", kallonta suke cike da tsananin mamaki kamar wata aljana ya akai tasan komai da suka zo sanar da ita wata daga cikin ta ce "koma dai miye ki shirya amsar ta ai ba dan ke kad'ai aka haifi shi Sadeeg Garkuwan ba yana da ikon yayi mata har hud'u sabo...... Kamin ta idasa maganar Surayya ta daka mata tsawa da yasa su firgita ta ce "ke ba sa'ar yina bace idan ta isa tazo da kanta kuma kuce mata duk inda zata taje domin mallakar Garkuwa na bata dama inta isa duk wajan bokayan da zata ko malamai taje bana shakka ko tsoro da alama bata san wacece Mrs Ahmad Sadeeg Garkuwa ba", ta idasa maganar tana masu kallon banza rab'a su tayi zata wuce wadda tafi su rashin kunya da alama yadda suke kama da Dr Zuby ba tantama k'anwarta ce ta jawo hijabin Surayya cike da isgilanci. Batai aune ba taji saukar mari tassss tassss duka kumatunta Surayya ta sharara mata mari mai zafin gaske tana fisge hijab d'in ta ta ce "ke da alama wata ce wajan Zuby ko ke nifa akan mijina wallahi zan iya komai dan haka ku kama kanku kusan dawa kuke magana", tana nuna su da yatsa su Nawwara kuwa murna suke suna cewa "maganinku kenan indai Surayya ce ba kanwar lasa bace", suna maganar suna bin bayan ta suka barsu sake da baki......✍️ *ZAHRA ROYAL STAR CE* Share fisabilillahi🥰🙏 *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* PAGE 9️⃣➡️1️⃣0️⃣ Su Goga sanyin asuba ne ya tada su jikinsu yayi tsami da kyar Goga ya d'auki waya ya kira likita koshi doctor d'in ya girgiza da ganin irin ciwokan dake jikinsu da kyar yasa mu ya gyara musu ciwon ya basu magani ya tafi ya barsu da tsananin jinya. Kusan satinsu d'aya y'an school basu ji d'iroyar su Goga ba y'an makaranta sai murna suke kwana biyu sun d'an sarara duk inda ka zaga maganar su Goga ce kwana biyu an huta. Su Surayya bayan sun gama lecture fitowa su kai duk ranta a b'ace ba taima su Nawwara magana ba ta nufi office d'in Sadeeg girgiza kai Bilki tayi ta ce "kai yaufa akwai rigima ni nasan dama sai anyi haka d'an gayu da ga kyau ga kud'i ai dole a samu y'an matan da basu da class su kai kansu gare shi", sauk'e ajiyar zuciya Nawwara tayi tana juyawa ga Bilki ta ce "ai wallahi banga laifin su ba tsananin kyau irin na Ahmed Sadeeg Garkuwa wai a haka ma dan bai taho da masu bashi tsaro ba a hakan ma again a nan ba wani nuna kud'i yake ba har yanzu basu san shi d'in wanene ba kinsan Allah Bilki da zai nuna ainahin kalarsa wata mace bata isa kawo mai raini ba koda yake ma ko yanzu sai dai suzo wajan Surayyar ba dai wajan sa ba ina ji fa jiya wata wadda ba y'ar department d'in mu ba suna maganar sa amma kwarjinin sa da haibarsa sun kasa tun kararsa kinsan Allah wasu matan banzaye ne da sun kalli Ahmed Sadeeg Garkuwa ai sunsan na gaba yayi gaba na baya sai labari", Bilki ta ce "wannan maganar taki gaskiya ce zaka iyayin komai indai akan irin su Garkuwa ne Allah dai ya raba Surayya da shirrin mutane muje kawai mu jirata wajan cin abinci dan yinwa nake ji", Bilki na idasa maganar suka bar wajan. A wajan Surayya kuwa tana shiga Office d'in wani irin matsifaffen k'amshi ne yayi mata ziyara da wani sanyi maisa natsuwa lumshe idonta tayi duk matsifar data zo ta ita tana had'a ido dashi ta nemeta ta rasa, yadda yake kallonta yayi bala'in kyau sanye yake da wani irin arnan yadi kalar sararin samaniya ba k'aramin kyau yayi mata ba kullum indai zata sa Sadeeg a idonta to sonshi da kishin shi ne ke k'arowa a zuciyarta. A hankali take nufar wajansa tasowa yayi ya jawota jikinsa da sauri zata zame ya ce "Ohh shat wai ke sai kace y'ar k'auya, sai kace baki waye ba wai kefa halali na ce bana son irin haka fa", turo baki Surayya tayi, sa hannunsa ya d'alle mata baki da sauri tasa hannunta hawaye na b'alle mata cikin y'ar rud'ewa ya ce "minene nasan dai wannan a hankali nayi miki akwai wani abu please mike faruwa?", fad'awa tayi jikinsa tana k'ara fashewa da kuka da sauri ya k'ara rungumeta yana shafa bayanta alamar lallashi sai da ya bari ta gama kukan ya d'agota batayi aune ba yasa harshan sa yana lashe hawayen kallonta yake da idonsa masu kaifi k'asa tayi da kanta cikin zazzak'ar muryarsa ya ce "kinsan yadda nake jin kukan ki kuwa a zuciyata zuciyata zafi take minene ke faruwa", da kyar ta bud'e baki ta fara bashi labarin abinda ya faru kamin ta kai maganar ma ya jawota ya had'e bakinsu waje d'aya dole tasa tayi shuru tana zaune kamar gunki sai da ya gaji dan kansa sana ya zare bakinsa cikin nata idonsa harya canza kala cikin sanyin murya ya ce "ki daina sama kanki damuwa kinsan waye mijinki so please kima daina biye masu kinji", da kyar ta d'aga mai kai sun dad'e sosai a haka har sai da yaga hankalinta ya kwanta inka gansu a yanzu yadda suke wasa da dari saika rantse kamar ba masoya ba sai kace abokan wasa ne ita kad'ai yake ma wannan abun dan Sadeeg Garkuwa baya da wasa ita kanta wani lokacin inya birki ce mata bata iya gane kansa danma ita ke iya sakko dashi ko in yayi fushi ko wani abu ya shige mai duhu cike da farin ciki ta bar office d'in nashi. Sadda zata fito ganin yawan d'alibai sun ragu yasa ta wuce inda gidan da suke kwana dan kuwa jibi zasu fara exams yauma sai da sukai text abubuwa sun fara yawa danma a CBT zasuyi wata. A sadda ta isa d'akinsu harsu Nawwara sun gama abinci suna karatu ko wacce da littafi a hannunta da handing out suna ganinta yadda ta saki ranta suka fara tsokanar ta sharesu tayi ta cire kayanta tabar y'ar wata riga, yadda surar jikinta ta fito kai gaskiya Surayya kyakkyawa ce ta k'arshe gata da k'ugu da manyan cinyoyi da Hips kamar su fad'u in tana tafiya gata nonuwa y'an dai-dai ba irin masu mugun girman nan ba amma a tsaitsaye suke ko a cikin riga zaka iya lura da hakan gasu tabarkalla cike suke kamar balan-balan, tana da tsawo amma ba can ba fara ce tas hancinta ba irin dogon nan bane matsakai ci ne fuskarta dogowa ce sai bakinta d'an mitsitsi kamar na tsuntsu jawur dashi kamar na jariri, dan ba laifi ana zafi saida taci abinci itama sana ta d'akko handing out domin yin karatu kwanciya tayi rufda ciki tana cikin karatu sai kuma ta d'ago ta ce "wai ni kuwa Nawwara da Bilki a cikin school baku ji anata maganar wani waishi Goga ba kamar fa nasan shi ina tunanin kamar wata y'ar tsama ta tab'a had'a ni dashi ina so nasan miye ya aikata da yasa school d'in ake zancan sa naji kwanansa biyu bai shigo ba mutune sai murna suke da alama ba k'aramin tantiri bane", da sauri su Nawwara har suna had'a baki wajan cewa "kai Surayya ke kuwa mi zai had'a ki da Goga shu'umi abokin shaid'an muma kanmu muna son sanin miye ya aikata da ake ta zan cansa kuma in ka tabbayi wasu kamar basu son baka labarin sai kika zuciyarsu ta sosu da alama labarin akwai sosa zuciya ya kamata gobe ko jibi in mun fito exams mu fara binciken tarihin su k'ila mu d'au darasi cikin labarin", "tabbas kuwa haka za'ai ai ko indai su Goga ya kasance laifin da suka aikita babba ne wallahi ko wanene ko na ce wacece suka aikita ma laifin zan tsaya tsayin daka zan sanar da Sadeeg domin a maka su a koto dan banga ma anfanin barin irin su Goga cikin jama'a ba har abarsu suyi karatu ai hakan babbar barazana ce ga al'ummah"..........✍️ *ZAHRA ROYAL STAR CE* Share fisabilillahi🥰🙏 *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* PAGE 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣ Bayan kwana biyu izuwa yanzu exams d'in su Nawwara tayi nisa sosai sun tari mutane da dama domin jin labarin su Goga wasu ana tabbayar su kuka suke saki wasu kuwa fuskarsu ce zata canza daga farin cikin da suke ciki zuwa damuwa yau saura kwana d'aya su idasa exams d'insu suna shirin komawa gida duk da hutun semester ba wani mai yawa bane sati d'aya ne da y'an kwanaki sun samu wata mai suna Teemah ta ce zata sanar dasu ainahin abinda ya faru a yau shi yasa su dukansu da zumud'i suka fito suka nufi Teemah dake k'ark'ashin bishiya itama fitowarta kenan daga jarabawar dama su take jira suna zuwa suka zagaye ta ta ce "kun shirya jin labarin dake sa kuka domin kuwa labarin nan ba wani yawa ne dashi ba amma kawai ban tausayi", ta idasa maganar hawaye na wanke mata fuska su duka jikinsu harya fara sanyi da sauri Surayya ta ce "please Teemah karki karyar mana da zuciya tun yanzu mana muna sauraranki", gyara zama Teemah tayi ta ce "Shekara hud'u da suka wuce ko na ce biyar, ni na kasance k'awa ga Khairat, mutuniyar kirki ce sadda ta fara shigowa school d'in nan, tafiya take tana ta waige-waige domin kuwa zuwanta ne na fari, tuntub'e tayi littatafan dake hannunta suka watse a k'asa tana niyar kai hannu domin kwashe su idonta yayi mata tozali da hannun na miji a hankali ta d'aga kanta harta sauke idonta akan kyakkyawar fuskarsa kallonsa take cike da mamaki da kuma kallon rashin sani da sauri ya idasa kwashe book's d'in ya mik'a mata ya ce "sorry fa ni sunana Anwar tunda kika shigo school d'in nan naji ina son abota dake zamu iya zama abokai", idasa maganar yana aika mata da murmushin nasa wadda baya barin fuskarsa ita dai Khairat murmushi ta d'anyi mai ganin Teemah na tahowa yasa ta wuce sa bata ce komai ba shi kuwa girgiza kansa ya d'an yi yana cewa "kai mata komai sai anja aji", jin sunanta Teemah na cewa "lah Khairat kece haka da ranar nan Ohh keda Anwar ne can, ai Anwar ba ruwansa wallahi, yana da kirki ga son jama'a gashi da k'ok'ari yana k'ara koyar damu idan Malamai sun fita yana k'ara ganar damu bashi da matsala wallahi", da sauri Khairat ta ce "to fad'i ba'a tabbaye ki ba, na ce ki fad'a min ya halinsa yake ne daga ganin mutum kawai saina saki jiki dashi nidai wuce muje", dariya Teemah tayi ta ce "hmm kinfa sakko da kanki dan kuwa Anwar na fad'a na k'ara fad'a bashi da matsala Allah sarki bawan Allah bashi da kowa d'an talakawa ne a cikin garin katsina yake kinsan zakiyi mamakin idan ya koma katsina adai-daita saho yake ja domin rufawa kai asiri duk iyayansa sun raso shi ke d'au nauyin karantunsa da kansa wallahi mugun tausayi yake bani, dan Allah Khairat idan ma cewa yayi yana sonki karkiyi mai wulak'anci baki san nan gaba mi zai zama ba please na rok'eki", ta idasa maganar tana had'a hannuwanta waje d'aya alamar rok'o Khairat kuwa tuni hawaye sun wanke mata fuska da sauri ta juya inda ta barshi bata gansa ba sai dai bayansa data hanga yayi nisa dasu kamar ya sani ya waigo daga inda yake hana faman mata murmushi, itama murmushin ta mayar mai lokaci guda taji bala'in tausayin Anwar ya shiga zuciyarta. Fita sukai wajan school d'in kad'an da yake nan aka kama masu gida da yake Federal University Dutsanma bata da hostel a cikinta. Washe gari ita da Teemah suka shigo school d'in suna cikin tafiya suka hango su Goga suna nufo inda suke tafiya da sauri Teemah ta ce "kinga Khairat zomu koma in suka wuce sai mu wuce dan wannan mutanan suna da had'ari", "had'ari kuma Teemah to mi yasa aka barso suna shigowa school d'in?", cewar Khairat girgiza kai Teemah tayi ta ce "kamar baki san a cikin Najeria kike ba to shima mai kud'i ne yana da kud'i sosai kud'in sa basu anfane sa da komai ba sai shaye-shaye da tara y'an iska yana k'ara lalatasu, ubansa ya mutu yabar mai mak'udan kud'ad'e sana d'an siyasa ne yasan mutune da yawa koda yayi laifi ba'a gani sai a boye kinga zo mu wuce dan Allah karma su ganmu", ai kami ta rufe baki Goga da bud'ad'd'iyar muryarsa ya ce "ku dakata daga nan idan kuma kuka matsa na rantse da Allah sai na keta mutumcinku", jikin Teemah ne ya kama rawa gabanta yayi wata irin mummunar fad'uwa jin abinda Goga ya ce. Goga na k'arasowa ya tsaya akan Khairat data rungume hannu duk da itama taji shakkarsa dakewa kawai tayi, kallonta yake har yana wani karkace baki yana fiddo harsha irin na y'an iska kawai basuyi tsammanin maganar da zata fito bakinsa kenan ba ya ce "ina sonki", ya fad'a yana kallon Khairat wani kallon banza tayi masa wani murmushi tayi ganin Anwar na nufo wajansu da sauri bawan Allah har yana had'awa da gudu yana isowa yaji Khairat ta ce "ni ga wadda nake so nan ya k'ara so", ta idasa maganar tana matsawa inda Anwar yake tsaye yayi mutuwar tsaye wata irin shegiyar dariya Goga ya saki ya ce "tabbas ina sonki kuma sha'awarki nake duk wadda ya ce zai shiga gonata to sai nayi SILAR MUTUWAR SA kima sa wannan a ranki shi kuma sakaran da keki so kece zaki ceceshi daga halaka", yana idasa maganar yaja y'an koransa suka bar wajan kuka Khairat ta saki ita da Teemah da sauri Anwar ya ce dan Allah ku daina kuka haka nan Insha Allah ba abinda zai iyayi inba abinda Allah ya rubuta a cikin littafin K'ADDARAR MU ba", share hawaye Teemah tayi ta ce "hakane amma har yanzu baku san waye Goga ba ina tsoron abinda zaije ya dawo wallahi", da sauri Anwar ya ce "babu abinda zamu gani sai alkhairi kunga kuzo mu wuce class kubar wannan maganar ma please", badan maganar zata iya fita a ransu ba suka shiga aji haka dai aka gama lecture's har uku ba abinda suka gane daga su har Anwar d'in dan kuwa damuwa ce dank'are akan fuskarsu dan yau Anwar ko tsayawa koyar da d'alibai bai ba suma kansu sunga yana cikin damuwa. Har tsawon sati uku basu k'ara ganin Goga ba har hankalinsu ya d'an kwanta har soyayyar Anwar tayi tasiri a zuciyar Khairat soyayya suke mai cike da nutsuwa abinda basu sani ba shine Goga bawai kyale su yayi ba zuba musu ido yayi kuma yana sa y'an baradansa suna sa mai ido akan Anwar da kuma Khairat zuciyar Goga a bushe take kamar tsohon arne kwata-kwata ba Allah a cikinta bare imani shed'an yana nan yana kitsamai mugun abun daya shirya musu dan har cewa yake "indai bazau d'an d'ana zumar Khairat ba ya rantse da sarkin dake bosa mai lumfashi sai dai kowa ya rasa zai iya hallaka kowa akanta kai harma da ita inta k'i basa had'in kai............✍️ *ZAHRA ROYAL STAR CE* share fisabilillahi🥰🙏 *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* PAGE 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣ Bak'ar rana ita ce ranar da Federal University Dutsanma da yawa wadda suke cikinta kai harma da cikin gari baza su manta da ita ba. Washe gari cike da nutsuwa Khairat da Anwar suke tafiya dan Teemah bata samu shigowa school d'in ba dan kwata-kwata bata jin dad'i. Kamar an jefoshi ya shiga gaban su yana zazzare idonsa irin na y'an shaye-shaye cike da muryarsa irin ta y'an iska ya ce "Khairat bazaki rabu da wannan malohon ba dai ko na rantse da wadda raina ke hannunsa idan baki rabu dashi ba nine zan zama SILAR MUTUWARSA indai a kanki ne kai kuma", ya idasa maganar yana kai dubansa kan Anwar yana tsaye ko gezar bai ba sai ma ya b'ude baki cike da rainin wayo ya ce "kai harka isa ka raba ni da RAYUWATA inba Allah ba koda yake kufa ba sanin Allan kukai ba ban tab'a ganin dabba...... Kamin ya idasa maganar Goga ya kai mai wani shegin naushi yana cikumo wuyan rigar sa, cike da tsananin tashin hankali da tsananin tsoro Khairat ta rushe da kuka tabbas babu abinda Goga bazai iyayi ba a kanta da sauri ta nufi inda suke da sauri Goga ya waiga yana ware mata jajayen idonsa ya ce "tabbas kin jamai mutuwa dan ba abinda zai hana ban hallaka sa ba ke indai ban same ki ba sai dai kowa ya rasa harke zan iya d'aukar RAYUWARKI", wani irin ras taji gabanta yayi wata mummunar fad'uwa har tana yin baya ta fad'i k'asa hawaye na k'ara b'alle mata wannan wacce irin k'addara ce haka take shirin faruwa da ita. Da kyar mutane suka b'anb'are Anwar jikin Goga da kyar ya samu wunyansa ya dawo dai-dai dan ba k'aramar shak'a yayi mai ba, da sauri Khairat ta ce "dan darajar Allah Anwar kabar makarantar nan yau-yau d'in nan ina gudun abinda zaije ya dawo bazan tab'a yafe ma kaina ba idan wani abu ya same ka", "karma kice haka babu inda zani", yana idasa maganar ya tashi ya fice daga school dan kwata-kwata baya ma jin dad'in abinda ke faru dan dai ba yadda zaiyi ne har k'arar Goga yasha kaiwa amma babu abinda akeyi sai kaga kamar da gaske za'a d'au mataki amma sai dai kaji shuru. Khairat kuwa ganin dare ya fara yi dan da k'arfe shadda tayi rana ke fad'uwa duhun dare ke mamaye ilahirin garin cike da tsananin tsoro take tafiya har tana hard'ewa dai-dai zata sha wata kwana wata bak'ar mota ta zo da gudu kamin tayi wani yink'uri suka jata da tsiya suka tusata cikin motar tana niyar ihu duk da school d'in sai mutune dai-dai ku kuma dai-dai kwanar ba'a cika binta ba saboda school akwai girma, suka sa tsunma suka d'aure mata baki hawaye ne kawai ke zuba ta idon Khairat kamar fanfo. A wajan Anwar yana zaune a shi kad'ai domin d'ebe kad'ai ci ga gabansa dake fad'uwa kawai yaga dan-dazon maza a kansa rik'e da wuk'ak'e da sandina kamin ya ce tak suka rufesa da Uban duka kota ina baji ba gani baka jin k'arar komai sai na dukan da suke mai sai na ihunsa tun yana motsi har ya daina sai da suka duba ganin baya motsi da sauri wani cikin su ya ce "kai gayis kamar fa ya mutu muyi maza mubar gun nan ku tabbatar baku bar wata shaidar da za'a gane mune ba", sai da suka tabbatar sun kwashe duk wani k'arfe nashi sana suka ajiye shi tsakiyar titi dan ayi zargin mota ce ta bank'e sa dan irin bugun da zuka mai yadda kasan tirera ce tabi ta kansa Anwar kuwa dama rai tuni yayi halinsa tun farkon bugun da suka kaima dama ransa na gaf da fita sai ya zama sune sanadi. A wajan Khairat kuwa bata tsinci kanta a ko ina ba sai a gaban Goga, zaune yake kan kuje wata irin dariya yayi yana cewa "yanzu akwai wadda zai iya cecanki wadda kike tak'ama kina so tuni yanzu na sani yayi bankwana da duniya kuma yaune zan cika buri na a kanki", wata irin zabura Khairat tayi tana zubewa k'asa wani irin kuka ta saki tana cewa "Wai kai wani irin bawa ne marar imani badai sawa kayi a kashe Anwar ba to wallahi dana bari ka keta mutumci na gara na mutu nima nabi masoyina na rantse bazaka tab'a cika burinka a kaina ba", Goga tashi yayi a zuciye yana kai mata wani bahagon mari ji kake tassss har saida Khairat ta kifa a k'asa tashi tayi tana dafe kumatunta iyanzu zuciyarta ta bushe bata ma tsoronsa k'ugunta ya kamo da sauri tasa hannunta domin hankad'e sa sai dai ina yayi mata mugun ruk'o, miyau ta tattaro ta tofa mai a fuska, runtse idonsa yayi cike jin haushinta ya k'ara kai mata wani marin har guda biyu tassss tassss tassss kake ji kamo gashin kanta yayi dake cikin hijab da k'arfi wata y'ar k'ara ta saki tana kallonsa da idonta da sukai jawur sai da ta dai-dai ci wajan mafitsarar sa tasa k'afarta da k'arfi ta daddage tana kaima wajan wani shegen naushi ba shiri Goga ya saketa yana sakin k'ara ai kamin kace mi ta d'auki wani k'aton k'arfe ta bibbigi duk wadda yasha gabanta da sauri ta b'alle K'ofar gidan tana fice da gudu hawaye take tana wani abun gudu gasu Goga dake binta a baya yana cewa "ku tabbatar bata shaba inba haka ba wallahi dukanku saina yanke muku mummunan hukunci", jin abinda ya ce suka k'ara k'aimi dan sunsan Goga kamar mai zuciyar fir'auna bashi da imani ko kad'an, gudu take tana waige harta hau babban titi bata sani ba wata babbar mota ce ta taho gadan-gadan kanta ga mai motar nata so ya kawuce mata amma ina sunzo gaf da juna Goga ne ya fasa wata irin k'ara yana faman cewa "keee Khairat baki da hankali mota ce fa gabanki", wata irin dariya ta saki tana cewa "ai dana bari ka kassara rayuwata gara mutuwa ta cinmini a yanzu kayi SILAR MUTUWAR masoyi na ka rubuta ka aje zaka girbi abinda ka shuka nan bada dad'ewa ba in...... Kamin ta idasa maganar ma motar tayi gaba da ita ba k'aramar banka ce akai ma Khairat ba dan sadda zata dawo k'asan titin kanta ne ya fashe dan har kana iya hangen tsakiyar kanta, shi kansa Goga ya girgiza da sauri suka bar wajan mai motar shima bai tsaya ba guduwa yayi (kai Allah ka kasa mufi k'arfin zuciyarmu Najeria kenan). Wayewar gari ba k'ara min tashin hankali garin Dutsanma da kewaye aka tashi dashi ba Teemah kuwa kasa d'aukar maganar kanta da tunaninta yayi suma ta rink'a yi har saida akayi asibiti da ita sadda dangin Khairat zasu k'araso nanma sabon tashin hankali ya k'ara b'arkewa kuka kam ba'a magana duk wadda ke cikin school d'in nan indai mai tausayi ne sai da yayi kuka imani ya k'ara shigarsa har mutuwar Anwar an danganta tane da had'ari yayi makarantar kanta ta girgiza har saida aka daka ta da komai na kwana biyu. A sadda Teemah zata farka kuka take tana cewa "wallahi Allah ba mutuwar Allah da Annabi ce sukayi ba kashe su akai" ba wadda ya d'au maganar da mahimmaci saima aka dankanta da hakan da cewa mutuwar ce ta zautata ba k'aramar jinya Teemah tayi ba k'arshe ma karatun katseshi tayi ta ce ta hakura da karatun, sai dai abinda ya dakatar da Teemah daga barin school d'in duk sadda nayi niyar barin school d'in nan ina yawan wasu irin mafarkai masu rikita min tunaninta a cikin mafarkin ina yawan ganin Khairat tana cewa "in daina sa damuwa a raina kuma kar nabar karatu na akan wannan abun k'arshen Goga bazai kyau ba in zauna a cikin makarantar nan zanga yadda Allah zaiyi ikonsa akan Goga". Teemah ta idasa maganar tana kallon su Surayya yadda kowa daga cikinsu tunkan aje k'arshen labarin suke kuka harda shashsheka ita kanta kuka take Surayya ta share hawayen tana tashi tsaye kamar wani abu ya shiga jikinta muryarta ta koma wata iri ta ce "tabbas saina sa su Goga cikin uk'uba da kansu zasu kai kansu koto kuma dole a yanke musu hukunci dai-dai da laifinsu", cike da mamaki suke kallonta har Teemah kamin suyi magana suka nemi Surayya suka rasa sama ko k'asa babu ita kamar ba'ayi wanzuwarta a wajanba sosai suka shiga tashin hankali anya Surayya ita d'aya ce kuwa.......✍️ *ZAHRA ROYAL STAR CE* Share fisabilillahi🥰🙏 *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* PAGE 1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣ Wani irin daji ne mai duhun gaske su Goga suna tashi suka tsinci kansu a ciki ga wasu irin koke-koke ba dad'in ji, wata irin dariya suka ji daga bayansu dariyar na wata irin tashi gaba d'aya kogunan dake dajin da bishiyoyi har wani amsawa suke suna wata irin girgiza waigawar da zasuyi suka ga wata mace sanye da take da wasu bak'ak'en kaya fuskarta rabi a k'one idonta ko d'igon baki babu gashin kanta na tashi sama kamar iska na hurasa sosai suka tsoron ta suka fara ja baya Goga ne mai k'arfin halin bud'e baki ya ce "bawar Allah shin wai ke wacece da kiketa azaftar damu haka?", wata dariyar ta sake yi wata irin murya bud'ad'd'iyar muryar ba dad'in sauraro ta cika musu kunne har saida suka runtse ido muryar na fitowa a rarrabe ta ce "harka manta da abinda kayi duniya to shine yanzu kuke girbar abinda ka shuka kaida mutanan ka wallahi Goga kamin in bari kaje wajan shari'a su yanke ma hukunci saika d'and'ana kud'arka", zubewa Goga yayi a k'asa ya fashe da kuka kamar yaron goye yana cewa "kayiwa Allah kabar mu haka wallahi munyi laushi kuma nida kaina zanje kotu domin yanke min hukuncin abinda nayiwa Khairat ne nasan cewa shine yake biya-biyata", wata dariyar ta sake kecewa da ita mai ban tsoro ta buga mai wata irin tsawa ta ce "kai har kasan Allah sadda zaka cuci mutane ai sun had'a ka da Allan ka kyale su ne dan haka yanzu ma sai kunyi muguwar nadamar da har abada bazakuyi marmarin cutar wani ba har abadan kuwaaaaa", ta idasa maganar tana buga wata sadda dan danan wasu irin namun daji masu had'arin gaske suka wanzu a wajan. Kamin kace mi su Goga sun arce da mugun gudu cikin jejin umarni taba namun daji ai kuwa kamin ta rufe baki sun bisu da mugun gudu su Goga ganin yadda suke gudu namun dajin gudun nasu kamar walk'iya haka suke gudun. Gudu suke suna k'ara nausawa cikin jejin ko kallon gabansu basa yi ga namun dajin dake binsu masu had'arin gaske da yawa cikin mutanan Goga sun fara gajiya da gudun kuma ba damar tsayawa shi kansa Gogan numfashinsa har d'aukewa yake mak'oshin sa ya bushe k'amas wata irin k'ishir ruwa yake ji kamar zai mutu tuntub'e yayi da wani mugun icce ya buge kansa yana fad'uwa k'asa wata irin juyawa kansa yayi yana sarawa kamar zai rabe gida biyu zubewa yayi a wajan numfashinsa na barazanar d'aukewa su kansu mutanan Gogan zubewa sukai suna faman sauk'e numfashi sun riga sun sadak'ar namun dajin na k'arasowa zasu cinye su. Sai dai namun dajin na k'arasowa suka b'ace b'at kamar babu kowa cikin jejin dajin ne yayi cit baka jin ko tari wata irin ajiyar zuciya suka sauke. Wata irin k'ara daga cikinsu wani ya saki da sauri su Goga suka matsa kusa dashi hankalinsu yayi mugun tashi ganin wata shirgegiyar mage bak'a wulik girmanta ya wuce misali sai tayi girman wani jaririn ta kama k'afarsa da wasu irin farce zak'o-zak'o ta karceshi da k'arfin tsiya shi kuwa sai birgima yake dan wani irin azaba yake ji kamar ana yankan naman jikinsa, kallonsu take da jajayen idonta masu firgitarwa kamin suyi wani yink'uri ta b'ace b'at wani irin tsoro ne ya dirar masu ganin babu magen babu alamarta sukam sun shiga uku wannan waccce irin masifa ce haka. Basu k'ara tsurewa ba sai da suka ga d'an uwansu wadda magen ta yakusa yana wata irin girgiza da wani irin gurnani kamar mage ta samu nama matsawa sukai kusa dashi domin basa taimako sai dai mi. Wata irin zabura sukai ganin idonsa ya koma fari fat tsakiyar bak'in ya koma wata irin kala hakuran bakinsa sun koma irin na masu shan jini masu tsinin gaske jikinsa na wata irin babbank'arewa kamar ana kakkarya k'asusuwan jikinsa wata irin mik'ewa yayi kamar an basa umarni yana wani irin gurnani. A wajan su Zuby kuwa k'awayanta na komawa gida sukaita zuga Zuby akan cewa akwai wani boka mai aiki kamar yankan wuk'a, sha yanzu magani yanzu aikinsa ba k'arya yana yi k'anwarta ta ce "ai Aunty wallahi idan baki shiga gidan Ahmed Sadeeg Garkuwa ba sai na ce kinyi asara babba kuwa, koni na samu saina shiga wallahi had'uwa irinta Garkuwa ba abinda bazaka iyayi kan wannan bawan Allan ba kai ai Allah ya zuba halitta ga wanga mutune inji sakwatawa, wai ga kud'i ga kyau komai ya had'a ai dole ayi hauka a kansa ita kuma waccar banzar Surayyar harta isa ta ce ita d'aya keda shi ina tama shirya yanzu aka fara wasan muda ita", da sauri Zuby ta ce "kware kuwa hakane babu abinda bazaka iya ba akan irin su Garkuwa yanzu yaushe zaku raka ni wajan bokan a shirye nake nayi komai na kashe ko nawa ne", da sauri cikin k'awayan nata guda biyu wata ta ce "ai ko yanzu inkin shirya kina da uwar kud'in ki zamu iya zuwa", da sauri suka mik'e Zuby na cewa "ku tashi mu tafi da zafi-zafi ake bugun k'arfe ai ba zama inta kwana a zaune ni a tsaye na kwana tunda ta bari na kyalle ido naga Garkuwa hmm kota halin yaya saina same shi"...........✍️ *ZAHRA ROYAL STAR CE* Share fisabilillahi🥰🙏 *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* PAGE 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣ Kamin sunyi wani yink'uri ya kaima d'aya daga cikinsu cafka ya kada shi k'asa yana wani irin gurnani yana niyyar kai mai cizo kokowa suka farayi da sauri Goga ya d'auki wani itace ya kaimai duka a kai. Sakinsa yayi da sauri yana fad'uwa k'asa ya rik'e kansa yana sakin wata irin k'ara da gurnani. Da sauri Goga yaja d'ayan suka fara gudu ganin yadda ya tashi kamar ba'a kaimai duka ba ya fara binsu a bayansu yana shin-shine shin-shine gudu suke suna waigen bayansu ganinsa suke kamar walk'iya yana matsowa gare su. Goga ne ya saki wata irin k'ara yana zubewa k'asa k'afarsa ya kama ganin wata irin k'aya mai tsinin gaske ta cakesa a tafin k'afarsa harta b'illo saman k'afar tasa da sauri sauran mutanan sa suka matso gare sa suna tabbayar lafiya yayi sauri su cigaba da gudu dan gaf yake da isowa gare su. Da kyar Goga yasa hannunsa ya runtse idonsa yana cire k'ayar da sauri wata irin k'ara ya saki ta azaba wani irin zafi yake ji har tsakiyar kansa. Ba yadda ya iya haka suka tashi yana d'angyashi suka cigaba da gudu. Jan birki su kai su dukansu ganin gabansu wani irin ruwa mai shegen yawa ya tare musu hanya ruwan duk ya cinye hanyar ruwan sai yayi girman wani garin waigawa su kai ganin ba kowa dage binsu abin mamaki ma sai suka tsinci muryar wadda ya zama horror ya dawo dai-dai yana cikinsu cike da tsananin tsoro da mamaki suka bisa da kallo kauda mamakin su kai ai babu abinda ba zasu iya gani ba. Da saui Goga ya ce "ga mai buk'atar shan ruwa yayi maza yasha kamin mubar wajan nan dan ruwan nan yadda yake da yawan nan zai iya anbaliya ya cinye mu gaba d'aya", ai da sauri suka duk'a domin shan ruwan sai dai mi ruwan ne ya zama wani irin jini mai kaurin gaske da kakai hannunka jini ne zaka d'ebo inka cika matsawa jikin ruwan kuwa ji zakayi kamar za'a kawoka ciki, da sauri suka tashi suna zare ido y'an hanjin cikinsu na hautsinawa iyanzu da yawa cikin su sai tsinewa Goga suke suna danasanin kasancewa tare dashi amma tsoro ya hana su nunawa a zahiri sai dai a zuci da yawa cikin sun fidda rai da fita wannan jeji anya ma za'a maida su cikin gari kuwa irin wannan jejin ko a film basu tab'a ganin irinsa ba wasu daga cikinsu zubewa sukai suka fara durzar kuka kamar wasu mata. A wajan su Nawwara kuwa sun kasa zaune bare tsaye gashi sun kasa gayama Garkuwa dan mugun shakkar gaya mai suke to su cemai mi ma matarsa ta b'ace kai abinma ba tsari kamar an datse musu baki sai zarya suke cikin dare har gari ya waye da kyar suka shiga exam d'in k'arshe suna jimamin Surayya kar ta rasa wannan damar sai dai abinda ya basu mamaki suna shiga class d'in suka ganta zaune har Teemah ta girgiza da ganin ta a cikin class d'in a inda ta sab'a zama a nan suka hangeta suna fitowa exams d'in kuma kamar an yashe musu duk wata tabbaya duke dank'are cikin ransu murna ma suka kamayi da murnar zuwa gida. Basu b'ata lokaci ba sukayi sallama da Teema inda Surayya ta ce "karki damu Teemah damun dawo hutu zakiji an yankewa su Goga hukunci Insha Allah", su duka mamaki sukai sun kuma kasa tabbayar tayaya hakan zai faru a cikin zuciyar Surayya kuwa cewa take a sadda zamu dawo su Goga sun d'and'ana kud'arsu sun kai k'arshen wahaluwa a dajin k'are kukanka, wata dariya ta saki a cikin zuciyarta dan yanzu ita kanta tasan akwai wani abu dake shiga jikinta kuma har magana sunyi kuma ta d'au mata alk'awarin ta cigaba da zama jikinta har sai an yanke ma su Goga hukunci. Garkuwa ne ya aiko da mota y'ar ubansu wadda zata kai su Surayya Katsina dan duk a nan suke shi kuma ya riga su tafiya yahau jirgi zuwa Abuja a nan komai nasa yake kuma a nan yake zaune. Surayya sai hushi take danmi zai tafi baisuyi sallama ba shima kansa yasan yayi laifi jira yake ta d'an huce tukun ya hau aikin lallashi, a sadda suka isa Kt sai da aka sauk'e su Nawwara sana aka wuce da Surayya unguwar sabon titin kwad'o unguwa ce sabuwar unguwa masu kud'i suka fara gini a cikinta ta zama unguwa ta masu dashi a nan aka sauk'e Surayya dai-dai wani gida mai shegen kyau da tsari da gudu ta shiga cikin gidan tana kiran Ammee ita kanta Ammee da sauri ta fito tana rungume d'iyar tata suna murnar ganin juna. A wajan su Zuby kuwa wani irin dokar daji ne cikin wani mugun k'auye gidaje jefi-jefi har saida suka daina ganin tsilli-tsillin gidajen rugar sana suka aje motarsu gefan titin garin daba wani titi bane birji ne kawai, suka fara kutsa kansu cikin dokar dajin ko tsoro babu a ransu sai da sukayi tafiya mai nisa harsun jigata ba'a saba da wahala ba, sana suka hango wata bukka daga gefe wata wuta ce ke ci sai wata kwarya dake gefe tana fitar da hayaki. Daga nesa aka buga musu wata irin tsawa aka ce "ku dakata daga nan la'anannun Allah nasan abinda yake tafe daku kina su ki mallaki Ahmed Sadeeg Garkuwa ko ba haka bane?", Da sauri bakinta har kyarma yake ta ce "hakane boka ina so a mantar dashi Surayya ya manta da ita kwata-kwata a rayuwarsa a tusa mai soyayyata cikin ransa sai abinda nake so zaiyi", boka ya fara dube-dube da sauri ya daka masu wata irin tsawa har suna zabura ya ce "dakata wannan abinda kike so ayi ba mai yiwuwa bane ban tab'a ganin aiki mai hatsari irin naki ba karki k'ara kiran sunan Surayya a nan shi kansa Garkuwar yana da kariya a jikinsa alwala bata sub'oce mai daga jikinsa kuma yana yawan azzakar dan haka ba abinda zamu iyayi a kansu", "amma boka itafa Surayyar" cewar Zuby zuciyarta cike da k'unci wata irin dariya ya saki har dajin na girgiza sun tsorota da dariyar har suna rungume juna sai zare ido suke tsawar da ya buga musu ce yasa suka k'ara had'ewa waje d'aya ya ce "ba na ce karki k'ara kiran sunanta a nan ba inba so kike dagani har ku mu shiga cikin wahala ba ku tashi ku fice min a nan kona sa aljanu su fitar min daku kuma ku sani duk inda zakuje duk wani boka wadda yake ji da tsafi magana d'aya ce zai sanar daku shi ne wannan amsar dana baku sai dai in kud'inku zaici ku tashi in daina ganinku daga nan", ya idasa maganar a tsawace. Ai da gudu suka fito daga dokar dajin suna sauk'e numfashi da sauri k'anwar Zuby mai suna Shahida ta ce "amma wallahi wannan bokan baisan aikinsa ba haba ai wallahi sai mun k'ara zuwa wani wajan Aunty ya kika ce", d'auketa tayi da mari ji kake tassss tassss tana kallonta da jajayen idonta dan saura kad'an ta fashe da kuka ta ce "ashe baki da hankali Shahida ku duba irin wannan bokan har akwai wadda yafi shi ko bakiji miya ce bane ai tunda bokan nan ya kasa na hakura da shiga gidan Garkuwa nima zanje na nemi wadda ya dace dani ai Allah ma yana sona daya fahimtar dani tun wuri wahala kawai zansha tunda Garkuwa bazai tab'a sona dan Allah ba...........✍️ *ZAHRA ROYAL STAR CE* Share fisabilillahi🥰🙏 *💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔 (Horror Story) ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️ *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI* *END END END END* PAGE 1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣ Zaune take a d'akinta tana waya da Garkuwa sai shagwab'a take zuba mai yana aikin lallashi daga can cikin wayar naji ya ce "kinsan Allah Noor zanzo ayi komai a bani ke dan gaskiya a matse nake yanzu haka duk kin susuta ni ina zan iya d'aukar rigimarki baki kusa dani", Surayya kuwa duk kunya ta cikata ta kasa cewa k'ala ji tayi ya hura mata iska ta cikin wayar da sauri ta sauk'e ajiyar zuciya ta fara dire-diren kafafu na tsananin shagwab'ar da ita kanta bata san ta iya ba sai a gaban Sadeeg da sauri ya dafe kansa ya ce "ya salam dan Allah nidai ki bari zaki fara ko kinsan halin da nake shiga kuwa Surayya", ya idasa maganar da kiran sunanta lumshe idonta tayi jin yadda ya kira sunan nata yayi mata mugun dad'i a bakinsa kamar kar ya daina kiran sunan nata ita kanta wani irin yanayi take ciki tana buk'atar mijinta amma tana bala'in tsoron Sadeeg dan ita shaida ce idan ya kamata bafa zai sarara mata ba sauk'e numfashi sukai a tare ji yake kamar ya janyota cikin wayar ta fito ya rungumeta ko zai samu sukuni zaune yake cikin Office d'insa dake Abuja aiki ne a gabansa amma kwata-kwata ya kasa komai duk ta dagulamai lissafi "yarinyar nan k'arshe ce wallahi", ya furta can k'asan mak'oshin sa, tasan komai na lagon Sadeeg tasan komai da zata susutashi nan take shi yasa kullum sonta k'arowa yake a zuciyarsa da gaggar jikinsa, cike da tsananin kewar juna sukai sallama dan saura kwana biyu su koma school. Bayan kwana biyu Surayya ce tsaye ta rungume Ammee sai hawaye take a ranar da aka koma ta shirya domin bazata k'ara ko kwana d'aya ba tana son isa da wuri domin kai su Goga ga shari'a inko sukayi mata hauka taci Ubansu, so take kamin su Teemah su dawo sai dai suji an yankewa su Goga hukunci, sauk'e ajiyar zuciya Ammee tayi ta ce "ni duk kin rikita min lissafi kiji yarinya kina son sani kuka nima kefa kikace ke da wuri zaki koma ko kwana d'aya bazaki k'ara ba to kuma miye na kukan?", Ammee ta idasa maganar tana kallonta da sauri Surayya ta ce "a'a Ammee kewarki harta fara damuna", Ammee kallonta tayi sai kuma ta ce "anya Surayya baza ai daga dake ba wajan kaiki gidan miji ga abu sai matsowa yake", dan da nan hawaye suka k'ara b'allewa Surayya data tuno da wannan rana kwata-kwata bata son wannan rana tazo tana ji tana gani za'a rabata da Ammee ta. Da kyar suka rabo cike da kewar juna Suna isa school d'in da yawa duk ba'a dawo sai y'an nesa wadda wasu ma ba hutun suka yafi ba dan wani inya zo irin y'an kudun nan wani ma saiya gama karantunsa baki d'aya tukun zai koma gida school d'in shuru duk sai taji babu dad'i daga shigowarta garin ta fara tsintar maganar wai su Goga sun b'ata sama da k'asa ba'a gansu ba mutane kuwa murna ma suke da b'atan su Goga dan ba cikin makaranta ba har cikin gari sun addabi bayin Allah. A wajan su Goga kuwa iya azaba sun azaftu so suke kawai tazo ta fidda su sukam a yanke masu hukuncin nan sunfi buk'atar hukuncin koto akan hukuncin nan da take musu idan suka k'ara kwana ko d'aya ne a wannan dajin mai sark'ak'iyar gaske to ba shakka mutu zasuyi tsawon kwanakin nan basu cin komai sai ganyen dake cikin dajin tun suna ci suna amai har fara zama a cikin su in suna so su shi ruwa kuwa sai dai wani tafashashshan ruwa da suke ganin an aje musu kan hanya dole su dauka su sha bakin da harshan su kamar zasu cire dan azaba haka suke rayuwa tsawon kwanakin nan. Kwance suke suna wani irin numfashi sama-sama kamar ransu zai fita Inka kalli fuskokinsu hawaye ne ke zuba ta idanuwansu iya nadama sunyi nadama. Basu sammanin zuwanta dan yanzu ba kawai sukaji wata irin mahaukaciyar dariya ta kauraye ilahirin dajin cike da k'arfin hali suka mimmik'e suna tangali kamar zasu kifa a k'asa ganinta sukai cikin wata mummunar kama wadda yasa hantar cikinsu kad'awa ba shiri suka cure waje d'aya jikinsu na mazari sai kace ba maza ba wata dariyar ta k'ara kecewa da ita dajin har wani rugugi yake kamar aradu zata fad'u, ta buka masu wata irin tsawa ta ce "kun shirya amsar hukunci a koto ko kowa an barku kud'an k'ara kwanaki a cikin jejin k'are kukanka", cikin zuciyar su kuwa cewa suke a lallai yaci sunansa dajin k'are kukanka to komai zakai ba ubanda zai jika bare yasan da kai ya kawo ma d'auki, da sauri har suna rige-rigen cewa "dan girman Allah mukam ki fidda mu daga wannan dokar dajin munji mun yarda mudai a yanke mana hukuncin koto yafi wallahi da irin wannan azabar", wata irin guguwa ce ta turnik'e wajan da sauri suka rufe idanunsu gabansu na tsananta fad'uwa wata irin dariya suke ji a rarrabe kashi-kashi da wasu irin surutai jin shuru yayi yawa sai k'ara ababan hawa da suke jiyowa da sauri suka bud'e idonsu idonsune yayi musu tozali da koto ta ciki tayi fam kamar dama jiran su ake jinransun kuwa ake dan kuwa babu abinda Surayya bata yi ba ko nace abinda ke jikinta tuni an shigar da k'ara lauyan da yake tsayama mata shi kansa ba mutum bane inda koto ta nemi shaidar zargin da sukema su Goga koto ta bada damar a nemo su Goga duk inda suke sai gashi kamar kyaftawa da bismillah aka tsinci su Goga a cikin koto mutane da yawa sun girgiza jin abinda su Goga suka aikta da yawa kuwa basuyi wani mamaki ba inda aka tabbaye su dasu amsa laifinsu nan take bada wata gargada ba suka amsa laifinsu basu ba koto wahala ba al'k'ali ya yanke musu hukuncin rai da rai a gidan yari da aiki mai tsanani nan take koto ta buga gudumarta ta tashi. Sai barka akema wadda ya tsayama shari'ar anata sa mai albarka. Bayan kwana biyu su Nawwara da Teemah suka diro cikin school d'in tun kamin su isa gidan da suke suka ji wannan labari mai dad'i ai da sauri suna isa gidan suka rungume Surayya Teemah harda kuka, iyayan Khairat kuwa harda su akayi zaman koto da dangin Anwar ba k'aramin kuka suka sha ba suna tsine ma su Goga suna ta ma duk wadda ya binciko abinda Goga yayima yaran nasu addu'a ba k'ak'k'autawa zuciyarsu sai yanzu ta samu sukuni . A wajan Surayya kuwa sunyi magana da Aljanin dake jikin Khairat tun tana da rai tana da aljanu jikinta ashe shine ya dawo domin d'aukar ma wa'innan masoya FANSAAA ya ce ma Surayya "Insha Allah zai saka mata itama zai kasance tare da ita duk wani abu na cutarwa inya tunkarota zaiyi iya bakin k'ok'arinsa dan ganin abin cutarwar nan bai iso gareta ba" amma Surayya ta nuna mai ai Allah na tare da ita sai aljanin ya ce ai Allah shine ya turo sa domin taimakon bayin Allah dan haka bazai rabo da ita ba dan har abada ba zai bari a cutar da ita ba, a haka suka rabo da Surayya. Rayuwa taja yanzu babu abinda ke gaban su Surayya sai shirye-shiryen gama makarantar su sosai Garkuwa shima ya d'auki nauyin wasu abubuwan domin kuwa shi yad'au nauyin kyatuttukan da za'a ba hazak'an d'alibai, sosai aka gudanar da bikin graduation mai k'ayatarwa wadda aka ba kyatuttuka harda su Surayya dasu Nawwara sosai Sadeeg yayi alfahari da matar tasa inda ya gayyaci da yawa cikin Malamai zuwa bikin da za'a gudanar domin tarewar Surayya za'a had'a dinner guda d'aya daga can za'a wuce da Surayya gidanta dake garin Abuja a jirgi za'a d'au amarya Mlm sunji dad'in karmawar da yayi musu na gayyatarsu bikinsa da yayi ai wannan abun al'faharin su ne. Rana bata k'arya sosai akai taro na gani na fad'a harda su Teemah wajan zuwa a Abuja a jirgi duk mai buk'atar zuwa su Bilki kuwa sune iyayan biki ranar sun kasa zaune sun kasa tsaye inda Surayya da kyar aka rabata daga jikin Ammee kuka tayi shi kamar ba gobe ita kanta Ammee sai da aka wuce da Surayya sana ta kama share hawaye a b'oye. A Abujar ma saida aka had'a dinner wadda taba mutune mamaki irin su Zuby da muk'arabanta sosai ta girgiza lallai sun shaida Surayya tayi sa'a ita kam Zuby tasan na gaba yayi gaba na baya sai labari domin ganin kwaf har saida sukaje akayi komai dasu waketa tasu ma. Gidan Surayya kuwa tofa nanne kallo ya koma sama kai yadda zan fasallata gidanma kansa sai a b'ata shafi guda babuce kawai babu a gidan nan kai gidan nan kona shugan k'asa iya abinda za'ayi kenan gida fa ya amsa sunansa gidan Ahmed Sadeeg Garkuwa duk wadda zaiga wannan gida bazai mamaki ba domin kuwa indai Garkuwa ne zaiyi hin mahiyinsa ma. Kowa sai da ya tabbatar ya an maida shi inda yake cike da abun arzik'i duk wadda yazo bikin nan sai da ya shaida yazo bikin Ahmed Sadeeg Garkuwa wasu ma haka nan ba'a San dasu ba zasuzo kowa cike da farin ciki ya koma gida. Zaune Surayya take ita d'aya akan tangamemen gadonta sai hawaye take sharewa tunda aka rabota da Ammee hawaye sunki tsayawa a idonta, wani sanyayyan k'amshi ne taji ya bigi ancinta da sauri ta d'ago tana kai dubanta a Sadeeg sanye yake da wata farar shadda y'ar ubansu sai shayinin take wani shu'umin murmushi ya sakar mata wadda ya kusa sa Surayya fita daga nutsuwarta k'asa tayi da kanta dan yau wani irin kwarji yayi mata, can ta tsinkaye muryarsa yana cewa "my Noor tashi ki d'auro alwalla ina jiranki domin na gaji da yawa kwanciya nake so nayi", da sauri takai dubanta garesa sai kuma ta sauk'e ajiyar zuciya tashi tayi a hankali ta shige toilet alwallar tayi ta fito ta samesa harya ya rage kayan jikinsa daga shi sai jallabiya mai shegen kyau ga wani k'amshi mai kwantar da hankali dake fita daga jikinsa. Sallah suka gabatar raka'a biyu sosai yayi masu addu'ar zaman lafiya ya tabbayeta game da addininta sosai ta basa amsa sosai yayi farin ciki da samun Surayya a matsayin mata Ammee ta jajirce akan ilimin addini dan bata wasa sai da taga Surayya ta sauk'e tasan wasu abubuwa wadda ya wajaba akan musulmi sana ta bari ta cigaba da karatun bokon. Garkuwa kuwa sosai ya jijina ma Ammee duk da Abban Surayya baya raye hakan baisa ta saki Surayyar sakaka ba ta lalace tasan komai game da addininta. Yana fita daga d'akin ta tashi ta rage kayan jikinta wanka tayi ta fito daga ita sai wani k'aramin tawul tana cikin shafa turare taji ya turo k'ofa da sauri ta tashi zuciyarta na bugawa zata d'auki hijab kamin ma tasa hijab d'in ya fisge ta yana mata wani shu'umin kallo da sauri ta k'ak'k'ame jikinta cike da tsananin tsoro take binsa da kallo duk sai taga ya susuce daga ganinta a haka batayi aune ba ya sureta kamar baby kukan shagwab'a ta sakar mai, shi kuwa runtse idonsa yayi dan bata san wannan shagwab'ar tata k'ara kunno mai wata wutar sha'awa take ba. Bai direta a ko ina ba sai kan gadonta kwantar da ita yayi yana kwanciya shima a jikinta wutsil-wutsil ta fara mai a jiki da sauri ya had'e bakinsu waje d'aya shuru tayi tana amsar sak'onsa har cikin kwanyarta wani irin abo suke ji yana taso musu daga tafin k'afarsu har tsakiyar kansu su duka sun hargitse sun fita hayyacinsu dan Surayya ita ba daga baya ba wajan fitina gashi dama ko yaya Sadeeg ya tab'a ta wata irin sha'awar sa da sun kasancewa tare shi take tsintar kanta a ciki. Tawul d'in dake jikinta ne ya cire na shanonta suka bayyana jikin Sadeeg har wani kyarma yake duk duniya idan akwai abinda yake sa ya rasa natsuwarsa to sune da sauri ya kai bakinsa kansu wata irin zabura tayi tana sakar mai kukan dad'i shi kuwa in akwai abinda yake k'ara susuta shi ana cikin wannan yanayin yana bala'in son mace ta rink'a mai kuka koda na shagwab'a kona kissa ne duk tabi ta susuta Sadeeg Garkuwa tun yana iya jurewa a sadda ya shigeta wata irin k'ara ta saki ta azaba wani irin rad'ad'i take ji shi kuwa kuka ya sakar mata dan wata irin duniya yake ciki jinshi yake kamar yana yawo a gajimare tsabar yadda yake jin wani irin bala'in dad'i dake kaimai har tsakiyar kansa sai da yayi kusan awa biyar ko nace shidda a kanta sana ya sarara mata duk abinda ya tara ya a mararsa saida ya juye mata shi tas, sakayau ya jisa kamar an cire mai wani dutse sosai ya bata taimako ya gasata sosai taji dad'in jikinta kamin safiya jikinta yayi garau sai k'asanta dake d'an mata rad'ad'i. Haka suke cigaba da gudanar da rayuwarsu cike da farin ciki da tausayin na k'asa dasu ga tsananin taimako ga duk wadda yazo neman taimako wajansu gidan marayu kuwa Garkuwa ya ganasu ba adadi kota ina ka zaga sunan Ahmed Sadeeg Garkuwar talaka ita kanta Surayya bata bar y'an uwanta a haka kawaii ba su Nawwara kai bama su ba duk wadda yake tare da ita sai da ta basa jari mai tsokar gaske dan mijinta abin hannunsa bai tsone masa ido ba shi yasa koda yaushe dukiyar sa k'ara bunk'asa take........ *Alhmdllhi Alhmdllhi Alhmdllhi Alhmdllhi* *Duka-duka anan na kawo k'arshen wannan d'an tak'aitaccen labari nawa Ubangiji Allah na godemaka daka bani aron lokaci da dama harna kammala wannan book nawa darasin dake ciki Allah yasa ayi nafani dashi* *Nice dai taku ZAHRA ROYAL STAR CE sai kun sake jina a sabon novel nawa Insha Allahu ina k'aunar masoya na a duk inda suke* *Wannan labari true life story ne da gaske anyisa game buk'atar tabbaya game da book d'in zai iya min magana ta wannan number dake k'asa* 👇 08130479973 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels