Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels  Na farfado ne daga dogon suman da na yi na jini Jike sharkaf da ruwa da yawun addu'o'in da akc tofa min ina Kwancc jikin Antina wacce tuni idanuwanrta suka yi luhu-luhu saboda haka na kalli baba babba wanda har lokacin bai gaji da karanto addu'o'i yana tofa min ba na yi karfin hali da kyar na iya bude bakina saboda nauyin da ya yi min ga sarawar da kaina yake yi na ce baba cikın sauri ya amsa na'am Badi'atu na ce da gaske ne Muktar ya yi haisarin jirgin sama ko kuwa mafarki nake yi? Ya gyada kai tarc da cewa E Bad 'atu abinda suka sanar damu kenan kuma a halin da ake ciki tuni har an iso da gawarwarkin mutanne biyar daga cikin bakwai dake cikin jirgin na dora hannu biyu na dafe kaina saboda jin shi nake tamkar zai arwatsc na shiga halin kidima da dimauta na rasa abinda zan yi in ji saukin bakin cikin dana tsınci kaina a yau sai kawai na kurma ihu ina cewa wayyo ni Badi'atu wayyo na ga ta kaina wayyo na rasa Muktar na shiga kuka haka kuwa ma tsananı 1arc da tsima zuciya da bada tausayı Antuna da Hajiya Mariya suma tayani kukan suka yi ina kuka ina sambatu me na yiwa Muktar? Me na yi mishi da zai bari su kasheshi bayan ya yi min alkawarin in har na yi mishi alkawarin kame kaina in tsare mnishi mutuncina shi kuwa zai yi duk yanda zai yi ya ga ya dawo gida mun ci gaba da rayuwarmu mu biyu don ya ga ya yiwa suaran maza kwalele a kaina Joda ta dora tafin hannunta a bakina ta rufe da karfi cikin kuka take ce min yi shiru Badi'atu daina yi magana don kar ki yi sabo, ni kam a kidime nake na kasa mallakar komai nawa shi kan shi baba hankalınshi ya kai matuka wajen tashi sai salati yake yi yana karawa Gali da Nai11u suka shigo sun dawo daga inda suka je duba gawarwakin da aka kawo su dukansu biyun tamkar an zare musu laka baba ya bisu da kallo cikin matsanancin soro da racana jikinshi har bari yake yi cikin Rarfin hali ya tambayesu kun ganshi a cikinsu ko? Gali ya ce a'a ba ya cikinsu, baba ya sake tambaya kun duba da kyau kuwa? Ya ce e, baya ciukikafafuwansu muka duba muna nan cikin wani hali da ba zan iya kwantawa ba wajen karie biyar na yamma aka sake aikowa wai ga wata gawar an kawo su Gali da Nafi'u suka ruga suka tafi gani muka shiga jira, jiran da na rinka ganin tamkar na walanni ne saboda kidima jimawa can suka dawo suna zama Nafi'u ya fashe da kuka wiwi gaba daya muka tsare sai Gali ya shiga yi mishi fada me ye haka Nafi'u zaka 1sorata mutane baba ba shi bane Major Balogun ne na zaro ido lare da dora hannu biyu kaina na kurma ihu ina birgima gaba daya dakin kowa kuka yake yi baba yana salati hawaye suna zuba a idonshiGali ne kawai yake durkushc a gaban baba yake aikin báshi hakuri yana cewa har yanzu bamu tabbatar Muktar ya rasu ba, baba ya ce gaba Gali an kawo mutum shida cikin bakwai kuma daga cikin wadanda aka kawo din nan har da Balogun abokin aikinshi na kut da kut, ai kuma shi kenan "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un Allah ban yi kukan rasa dana don butulci a gareka ba sai don zuciyata bata da karfi kan abinda ya shafeshi na yi burin Muktar ya yi min rakiya ta karshe zuwa kushewata ashe ba haka aka shiryo ba Allah mun gode maka da ka bamu shi a lokacin da bamu sani ba ke ni'imtanmu da rayuwarshi ka karbeshi a lokacin da ka yi niyya tsarki ya tabbata a garcka ya Ubangiji wadannan su ne jein kalaman da ke fitowa daga bakin baba ko baka san Muktar ba ganin baba kawai zai.iya sanya dan adam zubar da hawaye kiran sallar isha'i da aka yi shi ya dawo damu cikin nutsuwa kowa ya nufi wurin sallah tsawon dare ran nan Nafi'u da Gali suma officc din G.0.C. suan kokarin wai a taimakesu a sanyasu cikin sojojin da za a sake turawa Libcria saboda an samu labarin har lokacin ba a san inda Muktar yake ba yana da ra ko ya mutu ba a sani ba, wajen hudu na asuba su Nafi'u suka dawo dukanmu kuwa babu wanda ya runtsa muna hallare a lalon Muktar mun yi zugun kowa da abinda zuciyarshi ke raya mish Gali ya cewa Baba bayan sun zauna mun yi sa a baba an amince da tatiyar mutum daya a cikinmu kuma dama akwai karin sojoji mtasu taiiya gobe su yi canjin masu dawowa har da Brigedier Kabir a masu tafiya shi nc ma ya yi mana kokari aka yarda da tafiyar mutum dayan baba ya ce haka matarshi ta gaya mana dazu da zata koma gida cewar in banda tafiyar tashi da anan ta kwana to yanzu ya ya waye mai tafiyar? Gali ya ce ni nc baba na bayar da sunana baba ya zuba mishi ido da baka bar.....cikin sauri Gali ya katseshi a'a baba ni ne nafi kowa cancantar in bi Muktar do haka ni ne zan tafi ya mike ya shiga dakin da yake sauka idan ya zo gidan jimawa kadan ya fito cikin shirin tafiyar kananan kayane a jikin bai rike da komai a hannunshi ya zo ya durkusa a gaban baba ya ce zan bi bayan Muktar baba in har yana raye da izinin Allah zamu dawo tare ka yi hakuri bisa abinda ya samemu cikin sauri baba ya dafa kafadarshi ya ce Allah ya yi maka albarka Gali Allah ya tsareka ya dawo da kai lafiya da haka Gali ya fita ya bar gidan daidai karfe biyar na asubahi abin mamaki gari yana wayewa sai kawai ga abokan Muktar suna ta isowa daga wurare daban-daban har daga Benin Legos da Sakkwato wurare masu nisa amma wai har sunyi mafi yawanci kuwa sukan isone tare da matansu nan da nan gida ya zama babu masaka tsinke wannan yazo wannan ya tafi kwana biyu da faruwar al'amarin ran nan cikin dare muna daki na a kwance duk da dai ba barci muka yi ba misalin daya da rabi na dare Nali'u ya zo ya yi magana kusa da ko far dakina Anti kar ku ji mun fita a mota ku damu zamu kai baba asibitine cikin sauri ni da Anti muka fito muna rige-rigen shiga falon Muktar, mutumin da muke makwabtaka dashi wanda suke matukar zama lafiya da Muktar Major Amadu yana rike da baba yayin da Uzairu yake rike da wata.tasa jini yana zuba ta hancinshi tamkar mai habo sai dai yanda jinin.yake gudu abin ya fi karfin ace mishi habo, ni da Anti zubewa a kasa muka yi muna ta aikin kuka a haka suka fita da baba wanda ya zama tamkar wanda ya dade yana jinya. Suka tafi suka bar mu muka zauna anan ni da Anti muka yi kuka har muka gode Allah Uzairu ya shigo muka bishi da kallo na.neman bayani sai ya ce ni fa dama basu tafi dani ba ina nan a waj ina tsayc Uzairu ya wuce zai shiga dakin baki na sashin Muktar yana cewa Anti hakuri fa kawai zamu yi don kuwa babban al'amarn ya samu zuriyar mu sai dai kawai mu yi ta rokon Allah sauki. Har wajen tara na safe kafin Nafi'u da Major Amadu suka dawo muka tambayeshi jikin nashi? Sai Nafi'u ya ce mana da sauki amma baba karami ya zo ya tafi dashi Zaria Anti ta ce dama kun gaya musu ne? Naft'u ya ce e sai da na yi mishi waya na gaya mishi nai da yake ciki da asibitin da muke shirin kai shi sannan na yi muku sallama kuma tun shida da rabi ya iso garin nan shi ne ya ce a sallameshi su tafi gida kawai zai fi samun nutsuwa tafiyar baba babba ya sanya zuwan babanlungu don wai ba za a bar gidan babu wani babba ba shi ne wakilin baba babba saboda yanda mutane ke ta zuwa daga wurare daban-daban zuwan baba al'amura suka sanya daga zaman karbar jaje ya koma karbar gaisuwa wai bai kamata a biye min a ki yiwa Muktar abinda ya kamata ba wai ashe su dama a Zaria zaman karbar gaisuwa suke yi tuni na ji na gundura da zuwan nashi muka samu rashin fahimtar juna ni da Antina don so take in yarda takaba nake yi ana gobe Muktar zai cika kwana bakwai da yin hatsari da safe Antina wai tana min bayani tana so in amince da shirin su baba na yi mishi sadakar bakwai. Na ce ba zai yiwu ba nan gidana ne tunda gidan mujina ne na ce bana son gorin ana yi mishi sadakar bakwai anan aje Zaria inda ak a yi mishi sadakar uku a yi mishi na bakwai din Anti ta zuba min ido cikin bacin rai ta ce rashin kunya zaki kawo mana tana shirin fara yi min lada na yi maza na jawo waya na buga lambobin baba babba na ji maganarshi cikin kuka na fara mishi bayani ina gaya mishi baba da Antina da babanlungu basa mu'amalla dani b1sa kyautatawa, a hankali ya tambayeni me suke miki? Na shiga yi mishi bayaní saida na gama sai na ji ya ce daina kuka ki ji abinda zan gaya miki na sassauta kukan da nake yi sai na ji an ce ki kyalesu su yi abinda suka ga ya yi musu daidai yin hakan ba zai hanashi dawowa ba in har yana raye in kuwa baya raye kinga babu mamaki abinda kike kokarin hanawar ya amfaneshi a halin da Alhaji yake ciki a yanzu bana so ke ko wanı ku yi mishi maganar da ta shafi yaron nan don kuwa bai da lafiya tun safe yau bana zaton Albaji ya san wanda yake tsaye a kanshi cikin sanyin jiki na maida wayar na ajiye sai a lokacin na fahimci da baba karami nake magana na dago ido na kalli Antina tausayınta ya kamani na matsa kusa da ita na kwanta a jikinta ki yi hakuri Anti abinda kawai na iya fada mata kenan na soma kuka muka rungume juna ni da ita muka yi kuka har muka gaji muka yi shiru tunda mu biyu ne a dakın ma kwancea jikınta na.ce mata kenan na soma kuka muka rungume juna ni da ita muka yi kuka har muka gaji muka yi shıru tunda mu biyune a dakin ina kwancea jikinta na ce mata Antı kije gida kije ki smau baba babba ki bashi hakuri a yanzu babu wani wanda zai iya kwantar mishi da hankali in bake bace ta cc to ke fa Badi'atu? Na ce bar ni kawai Anti ki je wajenshi ni da na soma son Muktar a kwanan nan ma na ga musiba kari abinda ya sameshi ballc baba da tun ranar da Muktar ya zo duniya yake son abinshi na shiga wani sabon kukan, Anti ta amsa sallamar da aka yi da ita ta tashi ta fita na bita da kallo katon cikin da take tarawa nake kallo tare da tunanin Ubangiji ya kiyaycta daga fadawa halin da nake cikin tunda ga halin da baba yake ciki yanzu ma kenan ran da aka zo mishi da gawar Muktar ko me zai faru oho? Tunani mai nisa na yi sai kuma na ga to ai ita Antina tata da sauki ko yau aka ce babu ran mijinta dan dakc cikinta na bakwai nc bakin cikinta da sauki baba ya bar baya ni kuwa fa? Su kansu su baba inda nikc tarc da cikin da Anti ke dashi da abin ya fi musu sauki 6acin rai don sau biyu suna sawa Anti tana tambayata wai ko ina da ciki? In cc a'a in na yi wani tunanin sai in ga wata kila ni ce na hana Muktar barin kwanshi a duniya da na bashi hadin kai kila da yanzu tsohon cikine dani shike nan sai masoyanshi su yi ta zuba idon ganin isowar dan shi zuwa cikin wannan duniyar wacce bata da tabbas, Anti ta dawo tabbas, Anti ta dawo tana kai kawonta a dakin na ce Anti dazu ina kokarin ajiye wayar nan na ji kamar baba karami yana cc min innarsu Wasıla tana kan hanyar zuwa ko zaki shirya ne in sun zo sai kawai ku koma tare? Ta ce mun to bayan sallar Azahar ina zaune gaban inna tana min nasiha ni kam cikin zuciyata magana nake yi ina cewa yau ne zuwanta gidan Muktar na farko sai dai kuma bata zo a dadin rai ba ta gama yi mun nasiha ni kuma na yi mata bayanin a binda ake ciki na matsa min da ake yi wai in an yi bakwai in koma Zaria na gaya mata abinda Muktar ya gaya min cewar duk abinda ya faru bai yarda in je ko ina ba in hakura har sai ya dawo, ta ce to zan yi magana akan hakan tunda ga umarnin da mijinki ya baki da yamma suka tafi bayan ta ce in an yi sadakar bakwai dinni a bar ni in zauna a dakina tafiyar Antina sai na shiga wani hali na karin tsanani don kuma Antina mai sona ne mai tausayına mai tattalina a yanzu ta bami tare da Joda wacce take so ta ga na bi ka'idojin yin takaba ana ta fahimtar muna cikin wannan zaman da ita sai ga baba Sabuwa mahaifiyarsu Gali ta zo da niyyar yi mun kwanaki wai babansu Galin ne ya turota da ya ji Komawar Anti gida ya ce bai kamata a barni daga ni sai Joda da masu aiki ba, ita ce ta ceceni wurin Joda ta ce in yarinyar nan nunda bata son kira mata takabar nana kyaleta kawai babu wani abinda take yi na sabawa shari'a ita ba fita take yi ba, ba surutu ba, kowane lokaci tana kudundune in ba bakine suka zo ba, kowae iokaci a azumin nafila da salloli sanda da jan kafa ahankali da ake cewa mai takaba ta rinka yi wannan camfine babu shi a Musulunci Joda ta ce to ai shi kenanan daga nan kuwa ta fita harkata sai mu'amalar arziki, kullum na Kai azumi baba Sabuwa zata shirya min kayan buda baki in na ki ci sai tace to zaki yi bakin ciki da abinda Ubangyi ya dora miki nc? Kin cin abinci shi kuma ame yake? Wannan abinda ya samemu ba wai Ubangiji yana kinmu bane jarrabawane ya kuma jarrabi manyan bayin Allah ki duba ki ga tarihin shugabanmu Annabi Ayuba ta shiga kawo min tarihin rayuwarsa da wasu bayin Allah na kwarai wadanda suka gamu da jarrabawa iri-iri a rayuwarsu har sai taga ta kwantar min da hankalı in kuwa ta riganı tashi cikin dare don yin nafila sai ki ji tana tashina tashi ki yi sallah Badi'atu kar gari ya waye baki samu alheri ba. Baba Sabuwa ta nutsar min da zuciyata, kwanan Muktar goma sha daya Nafi'u ya koma kaduna gun aikinshi ya bar Uzaıru wanda aka ce shi ya zauna ya kula da gidan satinmu biyu da baba Sahura ran nan nace mata baba ina ganin gara ku koma gida tunda a yanzu bani da damuwa tace kin dai samu nutsuwa Bad'atu, amma damuwa kam ai da ganinki an san kina cikinta kin ga kuwa yanda kika zama? Komai na jikinki ya zagwanye kin zama tamkar alli saboda sirantaka ni in banda ma dai haramun ne mace ta aske gashin kanta da na yanke miki gashin nan don sai ina ganin kamar yana damunki ko kuma zo ki gani na matsa kusa da ita ta rabashi biyu ta kitse sannan ta hada wuri daya ta daure Uzairu ya yi waya aka turo direba daga Zaria ya tafi da ita baba Sabuwa tana taiiya na shiga damuwa saboda ina jin dadin ama da ita na soma zargin kaina me yasa nace ta tafi? Sai kuma naji wani sashin na zuciyata yana gaya min gara da kika yi haka Badi'atu tilas ne ki zama jarumar kanki don ba zai yiwu ace kullum sai an tayaki zama a gidan mijinki ba. Satin Muktar uku muna zaune a falon ni da Uzairu da Joda bayan tafiyar 'yan jami'armu da suka zo rokona wai inci gaba da zuwa daukar karatuna hakan zai rage min damuwar da nake ciki nace musu to amma zan jira in ga dawowar Gali tukuna, muna zaune muna Magana ace dai muga Gali da Muktar tafdi in ji Uzairu da sai nayi azumin talatin a jeer nace ni kuwa sai Joda ta katseni kar dai ku yi alkawarin da bazaku iya cikawa bay a dawo din ku kasa kafin ince komai sai aka ce wai ana sallama da Badi'atu inji Barrister Kamal wai yazo mata gaisuwa gaba daya muka kalli juna.ni da Uzairu nace me mutumin nan yake nufi? Zuwanshi gidan nan yau na uku kenan, Uzairu ya mike ya fita bai yi minti biyu bay a dawo muka kuma ji tatiyar motar Kamal, nace me ka gaya mish1? Yace cewa nayi ya yi a hankali zansa ido kwarai a kanshi don haka yayi maza ya bace mana daga nan in har ba wulakanci yazo.nemarwa kansa ba. Nace gara da kayi mishi hakan, sau da yawa.idan muna zaune da Uzairu hakuri yake bani haka nan halayenshi da yawan aikinshi kan yi min shigen halin Muktar ko da yake dama sunfi kama da juna a kira na jiki Muktar ya cika kwana shirin da bakwai ran nan da safe ina dakina ina karatun Alkur'ani maigirma ina addu'ar Ubangiji ya kaiwa Muktar ladan a inda yake don nima na fara debe tsammani sai ga Joda ta shigo ta sanar dani Zuwan baba babba da baba karami cikin sauri na shafa fatiha nace ta gayawa wacce take kicın a kai musu abin karyawa tace to na kintsa tsaf cikin doguwar riga da hijab a zuciyata ina cewa dauriya zanyi ba zanyi kuka a gabansu ba don baba babba yaji dadi yaga na kwantar da henkalina na 1sa falon nayi sallama suka amsa na shiga na durkusa da nufin gaishesu amma na kasa, saboda ganin baba babba ya zama tamkar bashi ba, ya rame ya tsuke, ya motes ya zama tamkar wanda aka sanyashi cikin wata na'ura ta tsotse mishi Jini da ruwa ta barshi daga kashı, sai fata, ya zama tamkar tsohon da ya doshi shekaru tamanin bayan ada kalin wannan tashin hankalin ya auku in ba kasanshi ne wan mahaifin Muktar ba babu yanda za a yi ka yarda ya wuce shekaru hamshin a duniya saboda kyan jikinshi, gaba daya ya zama tsoho cikin wata guda duk gemunshi yayi fari Sol muna hada ido dashi nikam kuka na farayi kuka kuwa mai tsanani shima kuma bai hanani ba sauri kawai yayi ya dauko hankacif dinshi ya shiga goge fuska wanda na san wata hikimace ta hana aga hawayenshi. Baba karamine mai bamu hakuri ko da dai shima asirin zuciyarshi ya tonu don kuwa yayi zuru-zuru alamar rama sai dai shi baya nuna damuwarshi kokari yake yana nuna bashi da ita na share hawayena bayan nayi kukan ya isheni sannan muka gaisa dasu sannu Badi'atu, sannu da kokari kin ji? Ki yi ta hakuri wata rana sai labari kalaman da baba babba yake min kenan nace mishi to ya dan muskuta ya gyara zama yace min nazo ne in ji ko akwai wani ibu na bashi da kika sani tsakanin Muktar da mutane? A zuciyata naj haushin kaina na yiwa kaina gori na zauna da mijina ban taba kula harkashi ba balle in san mu'amallarshi da mutane haushin kaina ya kamani nace ban san komai ba baba mai kawo mana kajine dai na san tunda ya tafi kawowa kawai yake yi ban taba bashi kudi ba.wannan kuwa umarnin Muktar din ne na bi yace to maza ki aki Uzairu ya kirashi, nace to na aikeshi na dawo na zauna a kasa, mun kamala bincike ta can Zaria na kuma sa Nafi'u yaji min tsakaninshi da abokanshi babu wata mas'ala sai ma wasu mutane biyu da suka ce ya basu jari bisa alkawarin da suka yin a zasu rika raba ribar dashi, to amma ribar farko da suka kawo mishi bai karba ba sai yace su koma dasu su ci gaba da sai an shekara su zo su yi mishi bayani to gashi ba a shekarar bag a abinda ya faru don haka in basu lokaci zasu yi kokari su ga sun dawo da kudin nace musu a'a su barsu in Allah yasa ya dawo in aka sbekara suje su sameshi in bai dawo ba tunda yayi musu hakan ne don ya taimakesu tunda su suka rokeshi to su rike su ciyar da iyalinsu Ubangiji ya bashi ladan abinda yayı nace amin, Uzairu da mai kaji suka shigo bayan an gaisa Baba yayi mishi bayanin abinda yasa ya kirashi mai kaji ya sunkuyar da kai kasa hawaye sura zuba yace baba ni Allah ne ya hadani da yallabai wata rananc nayi rashin hakuri na shiga gonar wasu mutane bisa tsautsayi na karyi masara na zuba cikin buhu ina nufin kaiwa gida saboda iyali sai aka kamani aka kuwa rufeni da duka kamar za a kasheni yazo wucewa a motarshi yaga cincirindon jama'a ya tsaya don ganin abinda ya faru shi ya kwaceni a hannun mutanen yace suyi kudin masara ya biya su ya sanyani a motarshi zai saukeni a inda zan yi nisa da mutanen nan akan hanya ya tambayeni n wane bata basirar ne ya kaini ta ba abinda ba nawa ban ace mishi yallabai wallahi ba halina bane 'ya' ya shida ne dani da matata bakwai an koreni a aiki bani dia wata sana'a gani a gidan haya tun safe na bar gida ban bar musu kGRmai ba gashi rana tana shirin faduwa ban samu abinda zan kai musu ba, da wannan dalili ne kawai shaidan ya rinjayeni in karyi masarar in kai musu Su dafa su ci, bai ce mnin komai ba said a zai saukenı sai ya kawo kudi ya bani yace in yiwa iyalina cefane shi yanzu tafiya zai yi amma bayan kwana uku in sameshi ya bani adireshinsa bayan kwana ukun nan kuwa dana tashi uwa sai na zo mishi da ya'yana guda shida da matata don ya kara gaskatani nan lalon ya shigo damu iokacin nan bai yi aurc bay a kawo kudi masu yavwa ya bani yacc in je in biya haya, in yiwa iyalina alheri in rinka yin cefane in kuma duba sana'ar da zan iya yi inzo in gaya mishi at da imatata kuka muka rinkayi sati guda bayan nan na dawo aka ce min baya nan ya tafi Benin wai dama daga can ya dawo nan bai me kama aiki ba tukuna nace ikon Allah na tafi na kara yin sati na dawo ta Samestu a gaya mishi zanyi sana'ar kaji da kwaidon duk kwanakia nan da baya nan a kasuwar kaji nake wuni naga yanda suke taliyar da al'amuransu yacc to in jirashi a waje na tashi na fita jimawa kadan sai gashi ya fito ya bani kunshn leda said a naje gida naga yawan abinda ya banı na fara zuwa ina saro kaji ina sayarwa, ran nan 1azo gaisheshi naz0 mishi da guda goma wadanda na riga nasa aka yankasu aka gyarasu yayi murna kwarai yace yanzu wadannan kana sayar dasu kamar nawa na gaya mishi da zan tafi sai ya kawo kudinsu ya bani nace a'a wannan kyauta na kawo mishi yayi murmushi yace a'a in aka yi haka ai sai in karyaka karbi kudinka daga yau kuma cduk sati ka kawo min kamar haka, ina daga lokacin kuwa duk sati ko yana nan ko baya nan zan kawowa masu aikinshi har kuma ita Hajiya taz0 a lokacin bikinta ma duk kajin da aka ct ni na kawo a guna ya saya kuka sosai mai kaji yake yi, Allah ne kadai ya san irin taictakno la yallabai yayi min don haka kudin kajin dana kawo mishi a ar su kawai Allah kuma ya dawo mana dashi lafiya in kuwa ta riga ta kasance Aliah ya rahamsheshi mukace amin. Baba yace to harkar kyauta ko alheri daban ciniki ma daban Uzairu tayashi yayi lissafin kudinshi a bashi suka fita suka gama Uzairu ya shigo ya gaya mishi ya mika mishi mukulli yace a cikin but din motarshi akwat kudi ya kirga ya bashi. Baba yayi min bayanin komai da ya sani na gae da Muktar abindaya fahumtar dani suma sun soma hakura da dawowarshi da zasu tali sai na durkusa gaban baba babba bayan baba karami ya fita ya barmu mu biyu nace mishi baba nag ode maka bisa alherin da kayi ka rikeni bisa kyautatawa kayı min gatan da baka yiwa wata 'ya a gidanka ba don kuwa ka hadani da danka wanda kake so fiye da komai a duniya kamar yanda ya rokeka ka tayashi kishin abinda yake so ko bayan ranshi a yau nima zan rokeka ka tsare mishi ni kar ka sake hadani da kowa ka barni in yi zamana har kafin nima nawa ajalin ya sameni, shiru baba yayi yana kallona da kyar ya iya bude baki yace min ki yi hakuri Badi'atu ya lashi ya fita ya barni ina tambayar kaina wannan irin hakuri da yakc bani ni dashi kowa yafi cancantar ayi ta bashi hakurin oho? Tun bayan tafiyarsu baba ran nan ina dakina na rufe kaina ina kwance kan gadona tunda ba sallah nake ba ni kaina ban san tunanin me nake ba sai dai kuma ba barci nake yi bas au biyu Joda tana min Magana akawo miki abincine nan? In ce a'a zan fito in ce har dare ina nan a haka har aka shiga kwanciya dare ya yi nisa na rasa abidna ke min dadi na tashi na fito babu kowa na nufi kofa zan bude sai naji muryar Uzairu yana tambayata ina zaki in kin bude kofar? Karfe biyun dare ne fa, na juyo na kalleshi yace ki koma dakinki kawai ki yi hakuri in aka bar wa Ubangiji al'amarin sai kiga yayi maganinshi na koma dakina jimawa can na sake fitowa don kuwa ji nake tamkar in sulale in tafi Liberia in je in gani abinda ke faruwa tunda gashi kusan sati hudu da tafiyar Gali babu shi babu Muktar abin yana nema ya zama biyu babu wai kamun gafiyar Baidu. Na zauna a falon ina tunanin Muktar mutumiun dana rayu a da ina tsanarshi ina kinshi ina kuma kyamarshi saboda daukarshi danayi a matsayin mugu a dalilin yawan tsoronshi da muke ji sanda muke yara da kuma kama mana kunne da yake yi in mun yi laifi, kyamarshi kuwa ya farone tun sanda naga kwalbar barasa a motashi dana zauna dashi a matsayın mata da miji kuwa rashun fahimtar juna dake tsakanınmu ya sanya nan da nan na gane shi din mutum ne mai yawan hulda da'yan mata to amma duk da haka a yau na ganc Muktar mutumin kirkine mai tausayi mai taimako mai ibada mai kuma girmama yaye mutum ne wanda ya samu farin jini Wurin jama'a saboda yawan alherinshi na ganin ko baba babba bai san alherin dan nashi ya kai haka ba sai bayan aukuwar wannan al' amarin day a ga irin cincirindon mutane da suka rinka zuwa kuma kowa yazo da abin da zaice Muktar din ya tabal mshi na alheri wanda ba zai taba mantawa ba, ni kaina zaman da muka yi dashi tun sanda muke fafata tsiya ina gida da kuma bayan mun yi aure nasan ya min alheri da yawa sai dai in hana zuciyata ganin alherin ta hanyar lassarashi a matsayın mayaudari gashi a yau ina cikin nadamar abinda na rinkayi mishi na cutarwa da gangan gashi babu shi balle in gyara kuskurena, hakika na zalunci Muktar na kuma zalunci kaina na bijire mishi na ki yarda mu yi mu'amallar aure dashi da yanzu in ma ban haihu ba ina da tsohon ciki tunda duk sa'o'in aurenmu sun haihu ga Wasila ma bayan 6ari yanzu tana goyon 'yarta mnace ni kuwa wayam babu komai ga Titi ta taso da wani rikici wai dan da take dashi Muktar ne ubanshi har taje Zaria ta kaiwa baba babba shi ko da yake baba ya kori zancen ya kuma yi mata kashedin kart a kara tuntubarshi kan wannan zancen. Titin tayi barazanar bugawa a jarida wai tana da da tare da Col. Muktar Zubairu abinda yayi matukar tayar da hankalin baba da 'yan uwan Muktar har ma Naliu ya shiga shirye-shiryen kai karar Titi kotu kan kokarin da take yi a iata sunan dan uwansh to da ni ked a wannan dan fa? Tambayar da nayiwa kaina kenan tabbas day a zama dan lelen zuriyarsu hinda magajin Muktar ne a da ina ganin tsiyar da nake yi Muktar nake yiwa a yanzu kam na gane kaina na yIwa na CUci kana wayyo! Alah na ban san lokacın da kalmar ta fito Bakina bada karfi sai ganin Joda da Uzairu nayi suna rige-rigen zuwa kaina ni kuwa ban fasa birgimar da nake yi ba Subhanallahi kalmar da Joda take ta nanatawa kenan tana kokann rungumeni shi kuwa Uzairu cewa yake yi gaskiya Anti idan ba zaki rin ka hakuri ba tilas ne mu koma aria dukanmu don kuwa zamanki muke yi kuma maimakon ki zama jaruma don muma na kasa dake mu samu kwanciyar hankali ina kuka a hankali ina kallonsu cikin Zuciyata kuma cewa take vi kin zauna kina hukunta Muktar kan laifuffukanshi guda biyu da kika sani kin ki waiwayawa ki dubi dimbin alherinshi ko ki yi bincike kan naki laifin tunda Hausawa sun ce wai laifi tudu nc taka naka ka hango na wani. Gari na wayewa Uzairu ya dauko Dr. Lami ta zo ta dubani ta bani magunguna kwana biyu a jeer na dan samu nutsuwa, saboda yawan barcin da nake yi a dalilin magungunan da nake sha, kwanan Muktar talatin da daya ina tsaye jikin window ina kallon tausari da yanda komai ya yi tsit saboda nisan da dare yayi na tuna 'yan awowi dan da suka wuce zirga-zirga da motsi da kaiwa da kawowa duniya ke ciki yanzu kuwa komai ya nutsu a zuciyata nace wannan kadai ya isa dan adam ya ji tsoron Ubangijin dake jujjuya wadannan al'amura, ina cikin haka naga wata bus ta doso gidanmu tana tafiya cikin nutsuwa tamkar tana dauke da kwai, ko kuma basu Son aji motsin sune oho? Na ce in dai barayıne suke wannan sandar to sun yi kuskure don kuwa wautace babba su ce zasu yi batan kai su zo barıkın soja don yin sata, har suka tsaya a kofar gidanmu ina tsaye a inda nake mutumin day a fara fitowa daga cikin motar shi ne ya sanyani faduwar gaba naji tamkar zan shide don kaduwa karshcn tika-tika tik. Badi'atu abinda zuciyata take gaya min kcnan ina ganin ya doso kofar falon zai buga nayi maza na bude bai iso ba sai ya juya da sauri suka bude bayan motar suna jawo shimfidadden gadon asibiti mara kafa yau kam ga gawar mijinki an kawo miki abinda nake gayawa kaina kenan, kusan suma nayi a tsaye kaucec mana daga hannya kalmar da la dawo dani cikin hankalina kenan ban kuma shaida wanda yayi maganar ba sai kuma naji muryar Uzairu yana waya, su yaya Galine suka dawo, baba ya dan saurara kadan sai naji yace to ban sani ba gashi nan dai ana kokarin shigowa dashi a shimiide kan wani gado ku ajiycshi anan kawai sumane in ii likitan dake biyc dasu kalmar da Uzairu yaji kcnan ya cewa baba da rasnı baba da ranshi ya nanata fadin hakan babu adadi na durkusa gaban Muktar wanda bai san inda yake ba ni kaina ban san me nakc yi a gaban nashi ba kowa yayi cirko-cirko yana tsaye sai Major Amadu yace to me yasa aka kawoshi nan a haka? Gali yace tunda muka ganoshi magana guda daya da ya yi ita ce in Alah yasa mun dawo gida yana raye a lara kainshi gidanshi don matarshi ta ganshi in kuma ya cika a hanya nan ma a kaiwa matarshi gawarshi ta gani kalin a kaishi inda za a ajiyeshi, Major Amadu da Gali suka sa hannu suka suri gadon suka fita dashi lokacin ne nayi kokarin fitowa don in bisu koma kawai Badi'atu motar da muka zo a diki ambulance ce shi da likita da direba ne kawai suka shiga cikin sauriu kuma suka tafi Major Amadu ya fito da mota ya dauki Uzairu da wasu mutane da suka nemi binsu dukansu maza suka bi bayansu, Joda ta rikoni muka shigo falo ta zaunar dani kan kujera tana raashina hakuri kawai za ki yi yanzu Badi'atu tunda Allah ya riga ya rula miki asiri ya dawo yana raye na kallo Joda a hankalia zuciyata nace anya wannan ba ta lcko ta koma bane? Hawaye suka zubo na tuna yanda naga kamannin Muktar mummunan kumburne a kanshi ga habarshi ta karkacc ta kauce gaba daya daga mazauninta na asali don ko alama bata hade da'yar uwarta hannunshi na dama kuwa a karye yake karayar da ban san iyakatarta ba don kuwa gaba daya ya juya sama ya dawo kasa, ciki ya zama baya wannan abinda na gani kenan na zahıri ban san abinda ke cikinshi ba Joda tana bani hakuri naga kuka ba zai fissheni ba, na tashi na dauko mukullin motata ina zaki? in ji Joda nace zan bi bayansu ta ce ai baki san inda suka tafi ba nace asibitinsu na sojoji zasu kaishi na fita ina tayar da mota Joda ta fito ta shiga muka tafi muna isa asibitin naga Major Amadu a tsaye yace min kun zo? Na ce e, ya ce sun riga sun shiga dshi tiyata tun 1sowarmu don an riga an sanar da likitocin su suka tura ambulance ta dauko shi a airport nace Gali fa? Yace yana can dakın ana mishi treatment don shima ya zo da raunuka, kusan awa guda muna wurin kafin Gali ya fito da sauri na nufi wajenshi muka tsaya nace Gali ya yi murmushi Badi'atu sannunku yaya gida? Muka koma kan wasu kujcru muka zauna kasa ce mishi komai nayi shima gab yakc da fita hayyactnshi ramar da ya yi tafi gaban a yi magana ga raunuka har da dinki a dantsen hannunshi sannu Gali suka gaisa da Joda mun godc Allah da ya dawo mana daku, Gali yace gaskiyanc Allah shi ne abin godiya shi ne kuma ya nufemu da dawowa gida, karfe biyar na asuba Nafi'u ya iso asibitin daga Kaduna ko minti talatun bai yi da zuwa ba sai ga su baba sun iso, ni na fara ganinsu don a lokacin su Gali da Nafi'u suna tare da wani likita da ya fito daga dakin da ake yiwa Muktar aiki da sauri na isa wurin su baba shida babanlungu tun kafin in yi musu sannu da zuwa yace Badi'atu Muktar ya dawo ko? Nace e, baba sai dai...ya katscni babu komai da izinin Allah kije gida kawai in an fito dashi daga tiyata zan turo a daukoki nace to ni da Joda muka dawo gida gari ya waye har sha biyu shiru na tura Daniel ya dubo shima shiru kamar an aiki bawa garinsu ina zaune har Azahar kamar n koma sai na ga kamar baba zai ce ban ji abinda ya gaya min ba, na yiwa Nafi'u waya don in ji abinda ak eciki yace har yanzu basu fito dashi ba, nace yana na kuwa? Naff'u yace yana nan abinda wani likita da aka canza dazu ya gaya min kenan nace Nafiu kafin incc komai ya ce ki kwantar da hankalinki kawai a ganina tunda ya iso da ranshi to da Izinin Allah zai rayu, wahala ce kawai zai sha za kuma ta wucc, ina zaune a falona nama rasa abinda zai faranta min rai sa'ar da na ya ma itace tun safe makwabta jama'ar bariki sai shigo min murnar Mukta ya dawo suke yi na idar da sallar La'asar kenan sai ga su Antina, Hajiya Murja da kuma Wasila sun iso na kankame Anti ina kuka ta ce tunda Muktar ya dawo ai kuma kuka ya karc Badi'atu nace Anti kin ga yanda ya iso kuwa? Na bata labarin irin yanda na ganshi dana gama sai tace to ai wai yana da karayama a hakarkarinshi yanzu daga can muke ta shiga bani labarin raunukan da aka gano a jikın nashı ta ce to amma wnanan duk in aka yi la'akari da irin jejin da Gali ke bayar da labarin sun ganoshi sai aga ba komai bane Ubangijin da ya fiddoshi da ranshi daga can shi nc a yanzu ma muke rokon ya warkar dashi na dan ji dadin zancen Anti muka gaisa dasu naje na kawo musu abinci suka ci suka huta, sai nace Wasila ina ganin ki shiga kICin ki tayasu aiki don a gama da wuri akai asibiti kawo bebin ta miko min ita na karbeta ta tafi wajen takwas da rabi na darc sai ga Uzairu da saurinshi ku zo mu je sun fito dashi yanzu cikin sauri da rawar jiki muka bishi zuwa asibiti Muktar yana shimfide kan gado ya zama tamkar ba shi ba, saboda sirantaka da baki an yi bandejin wuyanshi gaba daya har kan habarshi hakanan kirjinshi a daure yake hannunshi da ya karye shima an yi mishi filasta, tun daga mahadar hammatarshi har uwa tsintsiyar hannunshi ana yi mishi karin jini ta jikin kafarshi ta dama mutane da yawa muka tara a' dakin wanda yake na kwanciyar mutum daya ne, sai dai dukansu yan uwane na jiki na isa gadon da yake kwancen bayan na gaida mutanen dana samu a dakin kasumbar da ta cika mishi fuska ta bani tausayi ina kallon Muktar ina kuma jin Gali yana cewa in kaga jejin da Muktar ya kwana talatin a ciki yana raye baba sai abin ya baka tsoro da mamaki kuma yana da kuzarinshi muka sameshi don shi ne ma yake magana yana fadin inda yake tunda muka daukeshi ne dai a helikofta tun kafin mu iso sansani ya soma suma yana farfadowa, ya sake har Zuwa lokacin damuka 1so gida, kwana biyu da wuni uku Muktar yana barci bai farka ba, don haka aka sanya mishi roba ta hanci don bada magani da abinci mai ruwa-ruwa barcin har ya gundurt jama'a an matsu kwarai a ga Muktar ya bude ido ranar da ya cika kwana uku da barcin misalin karfe goma na dare har muna shirin tahowa gida sai kawai muka ji Muktar ya kwallara wata irin kara mai tsananin firgitarwa kan kacc meye wannan tuni ya buge Uzairu dake tsaye kusa dashi da hannunshi mai lafiya har ya kifar dashi a kasa cikin zafin nama su Nafi'u, Gaii da Major Amadu da duk wasu majiya karfi dake wurin suka nuii kanshi suka daddaneshi ihu yake yi yana yunkuri ya finciko karyayyen hannun nashi dake sagale ya tsinka abinda aka rataye hannun dashi na kankamc Hajiya Mariya dake saye ksua dani ina cewa wayyo Mami zai bata duk aikin da aka yi mishi na soma kuka a hankali likitoci biyu suka shigo tare da wanda yaje kiransu ku dan ragu umarnin da suka fara bayarwa kenan muka fito kin cika kuka Badi'atu matar soja kuwa-sojace zama jaruma take saboda tana koyon jaruntakar wurin mijinta ina kuka nace mata ai ni Muktar bai koya min komai na jaruntakar ba ni yanda zan yi in soni ya koya min duk da bacin ran dake bayyane a fuskata sai da ayi murmushin maganar da nayi iikitoci suna fita ni da ita muka sake shiga su Gali suna tsattsaye a kanshi baba sai karanto addu'o'i yake yi yana tofa mishi ta ko ina an dadfaureshi jikinshi sai bari yake yana kaduwa tamkar mai yın sharo ta ko ina gumi ya feso mishi Hajiya Mariya tace me suka yi mishi? Gali ya ce allurar barci ne kawai kwana biyu a jcre abinda ya rinka fauwa da Muktar kenan hankali ya tashi don kuwa kowa da abinda yake fadi kan abinda yake yi din wasu suce kwankwamai ne wasu su ce kila ya kashe dabbobi masu kwari wa1 suke mishi gizo yayin da wasu ke cewva mafarkin jejin da ya zauna a cikI yake y1 nan da nan baba ya yi taike wurare daban-daban ana kuma karbo magungunan gargajiya duk da kashedin da likitoci ke yi kan bashi maganin gargajiya bayan suna' nasu aikin fakon idonsu ak cyi ana dura mishi magani ta baki a hankali yana dan hadiyewa a jiki na gari a shafe mishi jiki a kuma gunbuda mishi hayaki ya turnikeshi ya yi ta atri ni kam har na rasa me zan yi akan halin da Muktar din yake ciki in ban da addu'o'i babu abinda nake yi in naje gida kwanan Muktar a asibiti biyar ran nan naje asibitin da sale muna cikin gaisawa da baba babba sai muka ji Muktar a hankali yana cewa "Hasbinal lahu wa ni imal wakil, da sauri su baba suka nufi kanshi Muktar baba yana kiran sunanshi Muhammadu Muktar ya sake kira kusa da kunnenshi, Muktar ya fara maganganu dake nuna bai san abinda yake fada ba abinda ke zuciyarshi kawai yake fitarwa ni tausayın babana nake ji sai kuma kishin matata na san masu sonta sarai, Gali da Nafiu sukacewva wadanda suke wurin mu dan tsaya a waje gaba daya suka tita suka barmu daga ni sai baba, baba ya kara matsawa jikinshi ya ce Muktar ga matarka kusa da kai babu mai taba maka ita tunda Allah ya rufa mana asibiri ya dawo mana da kai lafiya pga matarka nan tabashi da hannunki ya ji Badi'atu na yi maza na dora hannayena a jikinshi ian shafashi tuni ya shiga fadin magangau irin wadanda na tabbatar in yana cikin hankalinshi babu yanda za a yi ya fadesu, yaancin maganganun damuwoWinshi a kaina da wasu babu wata damwarshi a kaina da bata fito ba har da rowar kaina da nake mishi ni kuma na rasa inda zan sa kaina don in atunanin yanda baba ai dauken sai na ji baban ya na gaya mishi duk ta daina Muktar ke Badi'atu bashi hakuri ki gaya mishi kin daina irin wadannan abubuwan masu bata mishi rai, na yi maza na sunkuyo da kana wajen kunnenshi na dama a hankali na kira sunanshi Muktar ka yi hakuri kaji, ba zan sake sabawa umarninka ba tuni na yiwa Ubangiji alkawarin in har ya maido min da kai gida lafiya zan zama mace mai biyayya ga mijinta, tausayin Muktar ya amani na tabbatar inda ya mutu a dajin nan zai mutu nc da damuwata a cikin zuciyarshi, na kasa hana kaina kuka lamkar na mancc ni da babanc a wurin a gefen kirjinshi na kwantar da kaina kuka sosai na rinka yi jimawa can sai muka ji yacc daina kuka ki yi min addu'a. Baba ya kara matsuwa tana maka addu'a Muktar kowa yana yi maka bamu san adadin mutancn dakc tayamu yi maka addu'a ba budc idonka mana Muktar kwana da kwanaki muna fatan ganin ka budc ido, budesu ka gani mutancn da kafi sone suke tare da kai bude, ka ji Muhammadu Muktar, a hankali tamkar ya mance yanda ake bude sun ya bude yana kallon rufin dakin. Muklar, baba ya kirashi ya juyar da idanunshi a hankali ya dubeshi ka gancni? Baba ya tambaycshi ya dan gyada kai alamar c, ya cc to gaya min ni wayc? Kainc babana, ya bashi amsa, 1o wancan fa? Ya nuna mishi ni ya cc Badi'atu ce, godiya 1a tabbata garcka Allah da ka tsare min rayuwata ka kuma maidoni gida lafiya, AIlah na gide maka ya ci gaba da fadi kafin ya sake lumshe idonshi ya yi shiru ya dauki lokaci kadan ya sakc bude ido ina su baba? Ya tambaya, baba yacc babu wanda banzo ganinka ba a cikinsu mutanen da ka sani dama wadanda baka sani ba sun zo ganinka Muktar kowa yana addu'ar Allah ya baka lafiya, 'yan uwanka ma suna nan tarc da kai cikin sauri ya leka ya ce duk ku shigo gaba daya aka kewaye gadon Muktar kowa na kokarin gaisheshi ya kalli Naff'u yacc Nali'u cire min robar nan ta hanci ta dame ni, Nafi'u ya sunkuya kusa dashi yana mishi magana a hankali likitocin da suka yi maka aiki dukansu sun ce kar a cire ta sun yi aiki a habarka sun ce tanan za a rinka baka abinci, cire min kawai Nafi'u ka rabu dasu kudurar Ubangiji ce ta kawoni wannan lokacin ba likitoci ba Nafi'u ya ce to bari in kirasu su zo su cire cikin sauri ya fita suka dawo tarc da babban likitan da ya jagoranci aikin da aka yiwa Muktar din cikin turanci ya ce Col. Muktar Zubair ya dawo cikinmu mun gode maka Allah, Muktar din ma murmushi ya yi ya gama aunc-auncnshi sai ya ce zaka kara hakuri da zaman robar don bama son kana motsa habarka launa ko magana har sai mun ga aikin ya yi kyau ya juya wurin Gali ya cc kai nafi samu a wurinshi daga yanzu a daina barin mutane da yawa suna shigowa don kar a rinka sanyashi yin magana dama mun bari ne don ya rinka jin maganganun mutane kusa dashi don zai taimaka wajen dawowar hankalinshi da tunaninshi garemu ya gama bayani ya fita, baba yace Nafi'u tunda Muktar ya farfado sai ka koria gun aikinka yau kwananka biyar kenan, anan kaima Uzairu takardunka na hidimar kasa sun fito ban yi maka zancen bane kawai don ga abinda muke ciki, baba ya yi ta sallamar jama'a suna tafiya. Galim a baba ya ce ya kamata ya je gida su sadu da jama'a su gaisa kuma ya dan huta, ya ce ai sun zo mun gaisa baba gara dai ina kusa dashi Gali in ji baba kwana biyu a jere Muktar yana rokon abinci, likitoci sun hana wai sai dai ayi ta dura mishi ta hanci ga matsananclin zazzabin dake damunshi kowane lokaci yana cikın rawar sanyi, sannan duk da ya dawo cikin hayyacinsa jifa-jila in yana barci yana yin irin wannan ihun da buge-bugen in kuwa zai yi magana to ciki biyune zai fadi daya ko dai yace ku taimakeni ku bani abinci ko yace robar nan ta dameni a cire min ita, in kuwa yaji an fara bashi hakuri sai ya lumshe idonshi kawai ya yi shiru, ran nan ni kadai ce a dakin ina goge mishi jikinshi da tawul da ruwan zafi don ya ji saukin dankon datti sai ya bude ido ya kalleni ya ce cire min robar hancin nan Badi'atu na tsaya ina bashi hakuri tare da bayanin abinda aysa aka sanya mishi ita ya daka min tsawa tare da zare min ido ki cire min ita nace nasa hannu na kama ga zatona ina janta zata kare sai naga ashe doguwa ce sosai jikina ya dauki rawa don na ji tsoro ya ce figcta kawai da sauri ki wurgar da kyar na daure na karasa janta ta lito ina goge mishi dan jinin da ya biyo bayanta sai ga Gali ya shigo yana gani ya ce lah lah lah irin abinda zaki rinka yi kenan Badi'atu? To lallai kuwa yau zaki bar asibitin nan ba kuma zaki sake zuwa ba sai ya warke ya zo ya sameki a gida, na ce ka yi hakuri Gali, Gali ya murtukc fuska ya ce ba zan yi ba, dauki jakarki ki fita daga nan na soma yin kuka ina bashi hakuri ya ce fita kawai wato ke ga mai miji duk abinda yake so sbı zaki mishi ba kya tunanin abinda hakan zai iya zama na ga da aka gaya miki abinda ya sameshi suma kika rinkayi ana kwara miki ruwa amma yanzu ya dawo ba zaki taimaka a ga ya samu lafiya ba sai dai ki yi mishi yanda zai ji dadi ya isa Gali in ji Muktar Gali ya ce a har da magana kake y1? Lailin nata ya zama biyu ta saka ka yi magana na kuma kamata ta zare maka robar da likita ya ce kar a cire. Baba babba ya dawo daga sallar Azahar yacc me ya faru ne? Gali ya ce laifi ta yi baba nacc ta tafi gida shi ne take kuka, Baba ya cc to ka yi hakuri Gali ka barta tunda na sa baki, ya cc to ya fita ya kira likita ya zo ya duba ya ce a barshi kawai sai a rinka bashi ta baki da cokali amma banda abinda zai sashi tauna mai karfi na ce kenan zan iya tuka mishi tuwo mai laushi, ya cc kwarai kuwa mika hannu na kawai na yi na surn jakata da sauri na nufi inda motata take ina isa gida kicin na nufa Joda ta biyoni, yau dai da alama maigidan zai fara cin abinci? Ina murmushi nace kwarai kuwa Joda sai dai kin san yana da matsalar tauna shi ne nakc tunanin abinda zan girka mishi ko in yi mishi semobita nc? Tacc ai kuwa ina ganin tuwon dawa miyar kuka zai fi sai a yi shi mai taushi kwarai, miko min tukunyar kasar can sai in yi mishi tuwon ke ki yi miyar don mu yi sauri, nace to Joda da naman kaza na yi sanwar miyar sai da ta nuna ta farfashe na tsame kashin ta sannan nasa maburgi na kada miyar na barta ta nuna ga kuma 'finnishi fish. soup' dana shirya nishi sai da na yi wanka na shirya tsaf yau ne ranar farko da na yi kwalli tunda naga wasikar da Muktar ya bar min watanni bakwai da suka wuce, na fito sai kamshi nakc yi Joda ta kalleni ta ce kwanciyar hankali dai shi ne wani abu gashi dai jinyar mijinki kike yi amma har kin fara murmurcwa haka Alhaji babban ma na yi murmushi kawai na kwaso kayan abincin Muktar da kuma nasu Gali wanda mecu cikin gidan suka yi muka isa asibiti wasu bakin abokan Muktar nc a aicki muka gaisa suka yi sallama suka tafi Joda ta gaisheshi itama ta fita na matsa kusa dashi zan fara bashi finnishi fish soup din sai ya kalleni yace abincin ma a daure zanci? Naje wajen hannun nashi mai lafiya dake daure na kwance ya yi kokarin tashi zaune ya ji ba zai iya ba sai na sanya mishi filoli ya jingina a jiki ina bashi miyar da cokali yana sha Gali ya shigo ya ganmu ya ce ai har kwanccshi kika yi? CIkins auri nace abinci zai ci yace oho In kin ga dama in ya gama ki sake daure hannun in kuma kin tausaya mishi ki bar hannun kawai ke zai fi shafa don ke kika fi kowa kusa dashi, Muktar va bishi da harara ni kam dana ga zai fita sai nace akwai tuwon baba cikin farin food flast din nan. Gali ya ce to an kawo min farfesun kayan cikin? Nacc e, ya tafi tas Muktar ya cinye tuwon dawar nan ya ce ban miyar in shanye na rinka diba da cokali ina bashi yana sha har ya shanycta na bashi ruwa kuskure bakinshi, ya koam ya kwanta daurc hannun ya mikeshi daidar inda ake daurewar nacce barshi kawai kaji ai ba ka dawwama a daure kenan ba. Gali ya sake shigowa ina fata dai ba hira kuke yi ba? Tunda kin san har yanzu ba a baiwa Muktar umarnin yin surutu ba, kai Gali in ji Muktar cikin sauri Galin ya katscshi in ka yi magana ban koreta daga asibitin don ta sanyaka ka saba doka tunda in ba ita ce kusa da kai ba duk abinda ake yi baka tsoma baki ni kam na kwashi kayana na yiwa Muktar sallama zani jami'a daukar karatuna sai na dawo ya gyada kai saboda tsoron masifar Gali tunda aka baiwa Muktar izinin cin abinci mai saukin tauna kullum cikin shirya mishi garar abinci nake kala-kala kullum kuwa na kawowa Muktar abincin dana shirya mishi shi da baba, don larc nake musu baban ya rinka sanya min albarka kcnan, ran nan kawowa Muktar din abinci ina bashi sai ya kalleni ya ce kishinki nake yi Badi'atu, sanda nake Cikin jejin nan in na tunaki sai inji wani irın ciwo a cikin kirjina in ji kamar in farkc kirjin nawa in ciro zuciyar dake damuna da ciwo in wurgar da ita in huta da azabar da take gana min, na cc kai Muktar ba zaka hakura da magana kaja bakinka ka yi shiru ba sai Gali ya shigo? Ya mana masifa ko ya koreni tukuna rabu dashi kin ji Badi'atu kin san shi Gali bai san soyayya ba balle ya san yanda masoya suke ji, na yi murmushi nace Muktar kenan Gali mutumin da ake shirin daura mishi aure nan da 'yan watanni shi ne zaka ce bai san so ba? Muktar ya langabar da kai gefe daya nuna alamar tausayawa yace aiya ai auren doie za a yi mishi Haushi da takaicI suka turnikeni har ban san sanda na gallawa Muktar harara na kuma ja mishi wani dan banzan sakı ba nace wato ku dukanku aurcn dole za a muku? Ya ce a'a ai ni ba auren dole aka yi min ba ni dama auren gala nake cewa babana zai yi min yana cikin gaya min tsakanin ali da yarinyar da za a aura mishi sai ga Galin ya shigo gaba daya ni dashi muka yi tsuru-tsuru sai bin Galin da kallo muke yi muna sauraron irin masifar da zai yi tunda ya kamamu muna maganar sai da ya gama abinda zai yi ya nu kofa zai fita sai ya ce kai ku yi zanccnku tun shekaran jiya da aka yi hoto dama likita yacc in gaya maka komai ma kana iya yi da bakinka ko da kuwa launar kashi ne mantawa na yi ban gaya maka ba, haushi ya kama Muktar ya cc kai dai mugu ne maketaci kawai Gali ya yi murmushi ya fita ya barmu. Ina sonki Badi'atu kin yarda? Ya tambaycni nace na yarda mana Muktar ran nan duk abincin dana shiryawa Muktar da nama ne don kuwa shi mutum ne ma'abocin cin nama tun ma ba kaza ba, ranar Lahadi ran nan tunda naje na baiwa Muktar abin karyawa na dawo na hau gadona na kwanta ban farka ba sai wa jcn sha daya da rabi na safe na tarar tuni su Barratu sun soma aikın abincin rana sia da na karya sannan na shiga kicin wajen karfe daya na soma aikin abıncin Muktar ke nan suka ce min sun kammala nace to ku je ku kai musu in na gama nashi zan tafi dashi suka cc min to. Kwallıya sosai na yi bayan gama girkin na zuba wara-warai da zobuna ina kamshi lokacin dana isa asibitin na tarar kuma ana cike su Naliu, Umar, Uzairu da abokan Muktar daga Kaduna ga baba su Gali ma ya zo tare da mahaifiyarsa Baba Sabuwa ina shiga ta tarei cikin fara'a da barkwanci Allah sarki Badi'atuna miji ya dawo kuka kuma ya Kare, gaba daya aka yi dariya, ni kam kunya ta kamani na sunkuya na gaishesu cikin girmamawa na tarar suna hira da aka natsa sai babansu Gali Alhaji Abdulwahab ya ce muna jn ka Muktar. Muktar ya ce baba ba nike tukin jirgi ba ai ni sojan kasa ne ni dai akwai aikin da ya sa na bisu wanda na sirrinc jirgin kuma ma bana kai hari bane, muna shawagi ne a yankin dake hannun 'yan tawaye sai suka harbo jirgin namu ganin da na yi geien jirgin ya kama da wuta ya sanyani yin amfani da, rigar lema na ficc daga ciki bayan na kasa taimakon Balogun saboda irin kidimewar da ya yi 'yan second kadan ne kawai da ficewata jirgıin ya tarwatse ina ganinshi saboda na yi kokarin ganin na fita lare da Balogun iska ma sannain karfi dake tsananin kadawa a loacin shi yá sa sanya ban sama saka a kusa ba na lada Cikin wani munmunan daji dake tsakanin iheria da kasar SierraLeone na yi nisa kwarai ga shi inda na saukan babu sabis na yi kokarin saduwa da sansaninmu n gaya musu abinda nake ciki babu hali tilas na shiga yawo cikin dajin nan ba ba ina ncman inda zan samu hanyar sadarwa, ka dai sauka lafiya kenan in ji babansu Gali. Muktar ya gyara zama ya ce lafiya kalau na sauka amma tun kafin in wartsake daga bakin Cikin halin da na samu kaina ga kuma nadamar rasa abokan aikina da na yi cikinsu kuwa iai da Balugun mutumin da tun muna N.D.A. muka saba da juna sai kawai na bude ido naga wasu namun daji sun kewaycni suna kokarin su fara yagata ta ko ina ya dan yi shiru kadan sai kuma ya yi murmushi ya ce baba ko kadan ban san zan sakc dawowa gida arayc ba, duk kokarin dana rinkayi akan rayuwata na rinkayi ne ina addu'ar Ubangiji ya karb1 rayuwa1a a inda za a ga gawata a dawo da ita gida ku ganni don ku samu kwanciyar hankali wannan shi ne ya hanani iya yin hakuri in kyalc dabbobin da suka yi ta bar/anar cinyen Cimma burınsu amma wani lokaci idan azabar yunwa da bakin ciki gami da kadaicin da nake ciki suka addaben sai in ga to ai in na mutu na huta da duk wahalar da nake ciki sai kuma in tambayi kaina anya in har babana bai ganni a shimfide gabanshi babu numfashi ba zai hakura da nemana? Kwanaki ashirin da biyar ina yawo baba kafin Allah ya kawo ni inda na smau na yi magana da sansaninmu na gaya musu ina nan a raye na kwantanta musu yanda yanayin dajin da nake ciki yake a lokacıin nan kuwa na kai matuka wajen wahala raunukan dake jikina ma kadai sun addabcni gashi bani da kayan fada harsashi ya kare ni kaina karfina ya kare, karlin hali kawai nake yi ina amfani da 'yar wukar dake jikin bindigata na wuni na kwana ina jiran ganin anzo daukana ba a zo ba na tabbatar ba a gane inda nake bane, na rasa yanda zan yi ni ba abin in canza wuriba ina tsoron kar in je inda babu hanyar sadarwa gashi inda nake din akwai wasu irin shakiyan birurruka in guda daya ya ganka sai ya wuce kamar bai ganka ba baka ankara ba sai ka ganshi ya yiwu gayyar yan uwanshi su zagayeka, ganin halin da nake ciki ya sanyani yanke shawarar hawa wata katuwar bishiya mai duhuwa sosai na zauna na hakura na zauna ina gayawa Ubangiji karfina ya kare ya Allah babu wani taimako da zan iya yiwa kaina sai yanda ka yi dani Allah, a wannan bishiyar na wuni na kwana gari ya waye wajen karfe tara na sale sai naga kamar wulgawar mutum abinda ban taba gani ba cikin kwanakin nan a zuciyata na yi nagana dasu safiyar sun tabbatar min ba a ganc inda nake ba, juyowar da mutumin ya yi sai naga kamar Gali sai kawai na yankewa zuciyala ko aljaninc ya zo min cikin siffar Gali zan iya mika kaina gareshi sai na kira Gali bayan na karanta addu'o'in neman isarı kowa ya yi tsit kallon Muktar kawai ake yi sanda yake bayar da labarin nan kowa kuma yans fadin albarkacin bakinshi ni kam ajiyar zuciya na yi cikin zuciyata ina yiwa Ubangiji godiya da ya kubutar da shi daga musibar daya fada Muktar ya soma samun laliya sosai duk aikin da aka yi mishi an yi shi cikin nasara ya yi kyau sosai nan da nan ya soma murmurewa, yana maida jikinshi satinshi uku a asibilin ran nan na dawo daga jami'a sai na zarce asibiu tun kafin in je gida wata mace a samu a dakin nashi suna hira tana ganina ta mike wai dama tafiya zata yi ina ciki muna magana sai ga Titi ta shigo suna cikin gaisawa Uzairu ya shigo sai ya ce mishi yiwa Titi rakiya in akwai abinda ya kawota ta gaya maka na galls mishi harara bayan fitarsu na yi tsaki nace dama ban san komai bare ya yi nurinushi ya ce me kiak sani zo ki gaya min yana shirıin kanmo hannuna sai aka turo kofa gaba daya muka juya don ganin mai shigowa wata farar maccce yana ganinta ya ce Hello Juli sai yau kıka ga damar zuwa dubani? Ya nunoni da hannushi Meet my wifc Badi'atu ban jira na amsa gaisuwar da take min din ba na suri jakata na tafi gida ban sake dawowa ba abincin ma da nake mishi ban yi ba washe garima haka ina kwance a dakina sai ga Gali, Badi'atu wai ki zo mu je tare in ji baba, na yi maza na tashi muka tafi a motar da yazo na shiga dakin Muktar ni kadai nacewa Gali ina baba ya ce yaje sallah dama Muktar ne yace in zo in dauko mishi ke ya ji abinda ya sa bakya kawo mishi abinci ba baki zo dubashi ba nace ai karuwanku suna zuwa su rinka kawo abincin mana ya ce haba Badi'atu ana fada a asibiti ne? Nacc me' zar hana ai na rantse Mul1ar zai gamu da bacin rai irin wanda bai taba zato ba ba dai ya ce shil na-inanmajo ane? arai ya kama naman cinyata ya matse na kwallara kara mat tsane ai saboda zafin da na ji na kuma shiga kuka baba ya shigo yana jan carbinshi yana ganina ya tsaya cikin kaduwa menene ye faru? Ina share hawaye nace mishi baba Muktar ne ya mintsineni ya dauke aiin fata, akan wane dalili? Ya juya kan Muktara hankali ya ce zagina ta yi ta zagcka ta ce me? Ya ce ce min ta yi nsmamajo. Baha ya tunzur ya ce an ce maka na-mamajon shakivancin banza shakiyancin wofi. In bata ce maka na mamajo me zata kiraka Gaya min sunan ya kake son sanya maka? Ai ban san shakiyancinku ya kai haka ba sai bayan faruwa wannan abin Galiyana makale bayan gadon Muktar ya ce amma baba abokan aikine kawai baba ya kara tunzura ya ce kai Gali ranku zai baci in kuka ce zaku kawo min rainin hankalia abokan aikin daka kawo min da aka ce na Muktar ne? To bari ku ji da kyau ko bayan ranmu kuka shigo mana da shege cikin zuri'armu bamu yafe ba, dama jira nake yi a fita daga asibiti mu gamu daku tsawon lokaci baba yana fada da ya dan saurara sai Muktar ya ce ka yi hakuri baba na daina da izinin Allah bayarn sake ba na tuba ina rokon Allah ya yafe min kuma don Allah ka yi hakuri ka yafe min bacin ran dana sanyaka nan da nan sai kuma baba ya bar fushi ya shiga sanya musu albarka, na ce uh baba da sauri ya juyo gareni menene Badi'atu? Na ce saura abin nan kalin in ada sai aka yi sallama dashi ya fita cikin sauri Gali ya tambayeni da me zaki gaya mishi? Na yi murmushi na ce dama zance mishi ne kuma shan ruwan London menene ruwan London? Na ce tä farin dokin nan Gali yace kanki daya kuwa? Kina so ki ja mana bacin ran baba ne? Muktar kuwa kafa min ido ya yi yana kallona da alama nasa abin yi ya yi na juya zan tafi sa1 ya ce ina zakı? Na ce gida baki wuce ba kenan? Ya sake tambaya na ce me ka yi da zan huce? Gali ya yi sauri ya ce ai sai ka bata hakuri kawai don a zauna lafiya kasan an ce wai durkusawa wada ba gajiyawa bane. Muktar ya ce to ki yi hakuri Badi'atu' yan mata dai kına yi na ce bani basu na daina ke ni zunubi nå gangacina, duk zan daina abinda na gani da idona yana da yawa kin ji? Na ce giya fa? Ko ita ba ta ganganci bane? Galiu ya ceda daina ambatan sunanta kika yiu kar baba ya ji ki Muktar ya ce barta kawai Gali so take ya ji naga kuma shi lamarin duniya al'a hankali ake binshi me zaki shiryo mana na abinci? Na yi kunyar gwasaleshi tunda na ce na daina na ce me kake son ci Muktar? Ya yi murmushi ya ce ni baki san kunyar da kike bani ba idan kina rangada min sunana a gaban babana na yi kamar ban ji ba don na san magana kawai yake nema kwanaki talatin cif Muktar ya yi kafin likita ya yarda zai sallamemu shima don Muktar din ya matsawa likitan ne da tambaya zaka sallameni ne likita ko kafi so in gudu in bar muku asibitin? Baba babba yana hira da Brigedicr KabirIsyaku wanda ya dawo daga Liberia a dalilin raunukan da ya samu ni kam ina jinsu ina kuma aikin harhada kayayyakin mu da suka tara tamkar mun shekara a asibitin sai ga Gali ya shiga da saurinshi yana rike da takardu a hannunshi kai Muktar sun fa kafe kan sai na sake yin hutu nan kalin su sanya hannu a saliamar wai suna son su kara ganin hakarkarinka da haba tukuna sai kuma su ragc maka bandein dake hannunka Muktar ya yi tsaki ya sauko daga gadon suka fita tare da Gali suka nufi wajen yin hoto Brigedier ya bisu da kallo sai da suka fice ya dawo da kallonshi cikin dakin ya ce baba Gali jarumin yaro ne na yi sha'awar ya bar aikin da yake yi, yazo mu bashi kakin soja ya tayamu zaman bariki ya shiga baiwa baba labarin jaruntakar da Galin ya nuna wajen neman Muktar inda ya tabbatar wa Baba cewar Galin ne mutum na farko da ya fara ficewa daga cikin helikoftar dake shawagin neman Muktar ya sauka cikin dajin nan a lokacin da shi din ya bada umarnin a sauka baba ya yi murmushin jin dadi ya shiga baiwa Brigedier labarin yanda Muktar da Gali suka taso suna kaunar juna tun suna 'yan yara yanda suka zama dalilin shiryawarshi da Alhaji Abdulwahab bayan sun kasance kwatar dake tsakaninsu takan hadasu rikici gashi a yau bani da wani ain da ya wuce Alhaji Abdulwahab isawon lokaci yana bashi labari ya ce ba zai manta be rikicin karshe da suka yi akan kwatar nan nuna cikin sa in sa ana bamu hakuri sai wani dattijo a lokacin ya cewa mai basu hakurin kai ka kyalesu su yi musu abin kunya ku rinka kira musu 'ya'yansu suna rabasu rigima baba ya ce shi dai ran nan tunda ya shiga gida bai sake fitowa ba sai da sallar isha'i saboda lokacin duhu ya yi don kunya ya JC ya samu dattijon nan ya bashi hakuri sai dattijon ya Ce mishil ai ya kira Muk tar ya sanyashi ya kwashe kwantar ya kumna gaya mishi tunda tana hada iyayensu rigima, to ya dauki nauyin kwasheta duk sati, su baba suna ta hirarsu nima ina aikina har su Muktar suka dawo Gali yana murmushi hankali ya kwanta yau su Badi'atiu zasu gida sun yi sallamar? Baba ya tambaya Gali ya amsa E baba, ya ce to ai shi kenan ni kam zan taii dama na tsayar da Umar in an yi sallamar sai ya kaini gida na yiwa Baba sallama yana ta samun albarka su Muktar da Brigedier suka yi mishi rakiya shima Brigedier daga can ya tafi Galima saukemu a gida kawai ya yi ya ce shi kam zai nufi Zaria ya yi kwana biyu sannan ya koma Legos inda yake aiki akan iyakar Nigeria da Benin kasancewarshi costum tunda Muktar ya fito daga wankan bayan isowarmu gida ya fita falonshi don ganin masu sallama dashi bai sake samun lokacin kanshi ba, saboda jama'ar dake zuwa mishi murnar dawowa gida lafiya har dare nima ban sake ganinshi ba duk girkc-girken da nake shirya mishi ina aikewadashi ne can atrc da wanda su Barratu suke yi don jama'a da daddare bayan na yi sallar isha'i na yi wanka don Muktar karo na farko dana yi nufin bin Muktar dakinshi don faranta mishi rai rigar barcin da na sanya wata 'yar shimice kawai kamshi sosai nake yi lokacin dana shiga dakin Muktar ranar farko dana hau gadon Muktar na kwanta na kuma ji dadin yin hakan har barci ya daukeni bai shigo ba, ban san ma lokacin daya shigo din ba, farkawa na yi na ga Muktar yana sallah, na mika hannu na dauko agogonshi dake ajiye akan dirowar gadon na duba lokaci hudu da rabi ne na mayar na ajiye na gyara kwancyata na koma barcina sai da aka yi sallar asuba ya tashen, tashi ki yi sallah Badi'atu ki shirya cikin sauri ki rakani Zaria. Nan da nan na warisake na cc Zaria Mukta? In ce ko lafiya? Ya ce lafiya kalau t unda na dawo mahailiyata baia zo ta ganni oa saboda kawaicI irin na iyayenmu zan je mu sadu sannan na yi wa Ubangiji alkawari zan je in cikashi na ce to dama zaka karya ya ce a Zaria zanu karya sallah kawai za ki yi ki yi wanka ki zo mu tafi tun mutane hasu fara zuwa sun tsaremu ba. Na ce to na idar da sallah na yi wanka na yi shafa sosai, kwaliyar da na yi ba wata mai tsasada bace amma tana da ban sha'awa Fwnrai, rigar leshi ce a jikına dinkin Buba kalarta mai ruwan hoda, zanin shadda na daura shima mai ruwan hoda, an yi mishi ado jefi-jcfi da irin yadin rigar leshin dake jikina na daura dan kwalın ashoke a kaina, shima mai ruwan hoda ga yan kunnc sarka, wara-warai zobuna da agogona sal daukar ido sukc yi don dukansu zinarene takalmin kafata mai tsinine sosai shi da jakarshi kuwa sun dacc da kayan jikina na kuma toshe idona da madubin ido'spider' shima mai ruwan hoda ni kaina na san ba karamin kyau na yi ba, ina kara fesa turarc ina tunanin yau ne uwana zaria na farko fun bayan yin aurcna don haka na jawo wata katuwar jaka na soma jibga tsarabar da zan yiwa mutane a ciki. Muktar ya shigo shima ya yi kwalliya babbar-riga 'yar ciki da wando na yadin shadda mai ruwan kasa ne a jikinshi hularshi zannan Zarcnta irin kayan jikinshi bakin takalmi sau ciki ne a kafarshi ga agogonshi da zobc sai walainiya suke yi ga wani Jalausan kamshi dake fitowa daga jikinshi ya zuba min ido yana nin wani irin kallo dake bayyana asinin uciyarshi ke dai kullum ba kya gajiya da dogaycn takalma duk da isayin nan naki ya kara matsowa kusa dann yana murmushi imma tsayina kikc son kamowa to har yanzu da sauranki kin gani? Ya matso wai yana gwada mana tsayi ba don kar in isotsi bakinki ki ce na lashe miji janbakinki ba sai kin sakc shafawa ba da na yi Badi'atu kwalliyar ta bani sha'awa, na yi.murmushi kawai na ce da wannan hannun Muktar ya ya zaka yi da babbar rigar? Ya ce to yaya zan yi Badi'atu? Zan je gidane gaban iyayenmu da kananan kaya? Motar Muktar Mercedes 190 golden kala ita ce zamu yi tafiyar a ciki yana kokarin tayar da motar ina mishi magana da hannu daya zaka yi tuki har Zaria? Ya kallcni da gefen ido ya yi murmushi na san abinda ya sa kike raina hannun nan guda daya don jiya kın ga ya kyalcki ne bai tabaki ba, na ja bakina na yi shiru "Bismillah." Abinda ya fada kenan a bayyance lokacin da motar ta fara tafiya kwalliyar nan. taki ta mun kyau sai dai yaicn ashoken bai gamsar dani ba tunda babu lullubi bari in zuge gilasan sama funda tintet ne zasu hana a rinka ganinki daga waje ban yi magana ba ina kokarin sanya kaset cikin rikodar motar kaset din na 'Cclinc Dion Ne a cikin wakarta "I'm alibe' 1aliya sosai Muklar ya yi tamkar yana tsere da iska ko da yake wata kila shi haka lukinshi vake na dai kasa yin shiru na ce tafiyar ta yi yawa ya yi murynushi ya ce hala tsoro kike i? Na ki yin magana ya ce lo tsoron nie za ki ii tunda in ma tafiyar ce da kanmu zamu 1afi ya dan rage gudun yana kuma ban labarar karo na farko da nake tafiya larc dash1 muke kuma hirar farantawva juna rai. Karfe tara da 'yan mintuna Muktar ya tsaya kofar gdanmu, ana ganinishi gaba daya yaran unguwarmu suka taso suna ihun Yaya Muktar oyoyo, ni kam na yi maza na shige Cikin gida falon baba babba a nike da jama'a watakila masu tayashi murnar samun lafiyar Muktar ne don haka kai tsaye sashin Innarsu Wasila na wuce tunda ita ce dalilin zuwanmu Zaria tana can cikin dakinta na yi sailama ta amsa cikin nuna alamar mamakı Badi'atu me ya fito dake yau. cikin ladabi da girmamawa na cc Inna ni da Muktar ne tare muke ya zo gaishcki ta juya tana min sannu da zuwa, can cikin dakinta ta shiga can nima na bita muna cikin gaisawa zainab suka shigo da gudu suna Anti oyoyo Zainab 1a ce ina Yaya Muktar ya ji sauki? Na ce gashi can a waje mutanen unguwar suka tsareshi da gudu suka fita muna cikin hira Antina ma ta shigo lafiya dai ko Badi'atu abinda ta fara tambayata kenan na yi murmushi na ce kalau Anti Muktar ne ya ce in rako shi zai zo gaida Inna ta ce af to sannunku da zuwa na ce yawwa Uzairu ya shigo da sauri yana mana da Anti. Anti ina makullan wajensu yaya Muktar? Ta ce ai a gyare wajen yake tun jiya da Alhaji ya dawo ya sa aka gyara ya ce ya san Muktar zai iya zuwa gida a kowane lokaci sai dai ka budemusu kawai ya ce to Muktar ya yi sallama a kofa Anti ta amsa tana mishi sannu da zuwa ta kuma bashi izinin shigowa ya zauna kan wata shimfidediyar darduma ka samu fitowa Muktar, ya amsa cikin ladabi barka da arziki ta wuce ta fita ni kam ina zaune cikin ladabi Muktar ya gaida Inna ita kuma tana amsa cikin yanayinta na kowane lokaci da suka gama gaisuwa sai ta ce da haka kuma wannan tafiyar ta zo muku? Cikin ladabi Muktar ya sake sassauta murya ce Inna rahamar Ubangiji ya sanya ya amsa addu'o'in da kuke mana shi yasa na dawo shi ya sa na taho in rokeku Inna ku kara yi mana addu'a daga nan kuma in cika alkawarind a na yi wa Ubangji sanda nake cikin dajin nan na yi alkawarin in har ya sake dawo dani gabanku ina raye zan gina masallacin Juma'a tare da makaranta don karantar da Alkur'ani mai girma tsawon lokaci tana sauraron bayanin da yake mata da ya gama sai ta yi mishi addu'ar Ubangji ya bashi ikon kammala aikin da zai faranta kuma shiga yi mishi nasihar da ta sanya Muktar ya rinka share gumi don kuwa hannunka mai sanda ne kam asirinsa da Titi ta tona na cewar danta nashi ne ku yi hakurn Inna da ikon ALlah hakan ba zai sake laruwa ba Babanlungu ya tsaya a kofar falon Inna ya ce Muktar yana Cikıne da Sauri ya amsa c gani Baba ya ce to gara ka hanzarta fitowa don uwa dattawan unguwa suna nan sun taru a falon Alhaji suna son ku gaisa cikin ladabi ya amsa to baba gani filowa bayan tafiyarshi Muktar ya ce Inna zanje mu gaisa dasu ta ce to ya fita ni kam anan wurin Innar na karya muna 'tyar hira na lura kuma kamar ta kara tarairayata su Zainaba suka sake shigowa na ce musu mu je ku rakani mu gaida mutanen gida sai da na gama gaida mutanen gidan babu sashcn da ban je ba sai namu shma don naga abokan Muktar sun fara cikashi duk da cCwar shi din yana wajen su Baba, sannan na iso wurin Antina tana ciki tana magana da masu aikinta guda biyu da alama umarni take basu na Karasa can cikin dakinta da gudu na yi tsalle na fada kan gadonta ina cewa wayyo ni Badi'atu na yi kewar gadon Antina mai dadi ta tsaya tana kallona tare da salati, wa to kenan har yanzu ba ki yi hankalin da za ki daina tsalle akan gado ba? Na ce Allah Anti akan wannan kawai nake yi ta zauna a bakin gadon na matso jikinta na yi fito da cinyar duk da katon cikin nata tana kallona cikin murmushi da fara'a cikin nuna alamar farin cikin ta ce oh Allah ya rufa mana asiri Badi'atu ya dawo mana da Muktar na yi murmushi na ce Muktar ya dawo Anti taimakeni ki gaya min mc zan yi mishi ya so ni? So nake in mallakeshi ni kadai, ta saki wani lallausan murmushi ta ce bayan wanda yake miki? Na ce kai Anti n aji tsoron al'amarin Mukiar zuwana gidanshi ban san adadin 'yan matanshi dana gani ba, ta ce ya yiwa babanshi alkawarin ya bari na kuma sani zai yi maukar kiyayewa, in har ba kcce kika ingizashi ga komawa ba, don' kema abin haushinki yana da yawa in ba haka ba da Muktar bai samu jarumtakar da zai rinka kawo 'yan matashin kana idonki ba, kina da kyau na jan hankalin da namiji Badi'atu kin iya girki kin iya kwalliya in kika kyautata mishi kika tarairayeshi kika jawoshi a jikinki kika mallaka mishi kanki kika yi amfani da hikima tare da hila irin wanda Allah ya bamu bana zaton Muktarvzai ci gaba da kallon wasu mata bayan ya san ke din tashi ce ban amince da aurar dake gareshi ba duk da na san irin kiyayyar da yake miki sai don na san in har aka barku gdia daya ku biyu to duk siyarshi zai shiga hannunki tunda dolc idonshi zai ga nan mishi kyanki 1sawon lokaci tana bayyana mun dalilinta na son aurcna da Muktar ta tashi zata fita don ganin aikin da ake yi na bita zuwa kicin din girkc-girken da ake yi din tamkar na gidan bikina daga inda muke muna jin hayaniyar jama'a alamar dai gidan a cike yake na ce oh ni 'yasu ina jin har yanzu Muktar bai karya ba Anti ta ce to a laifinki ne kema kin san a dadewar da Muktar ya yi bai zo gida ba ga kuma wannan abinda ya sameshi ai dolc ya gamu da jama'a ina taya Anti aiki tana min fada nan gaba komai sammako ki tabbatar kin shiryawa mijinki abin karyawa har ma ki tanadar mishi a foodflast ya tafi dashi na ce to Muktar bai samu shigowa wajen Anti ba sai bayan sallar Isha'i ya shigo kanshi babu hula 'yar ciki da wando ne kawai a jikinshi da ganinshi ka san a gajiyeyake Anti ta ce sannu Muktar yau dai kam ka sha magana, ya yi murmushi kawai ya shiga gaisheta tana amsawa suna gama gaisuwar bata bari wata magana ta shigo ba sai ta ce gara ka koma wajenku Muktar ka samu kadan huta bai yi musu ba ya ce to yana fita ta ce miun tashi ki bishi akwai gasasshiyar kaza a kicin ki daukar muku na tashi na ce sai da safe zan fila, ta ce zo Badí'atu je ki cikin wancan kit din akwai sauran abin nan din da 'yar Sakkwato ke kawo min dauko ki sha dama anasha ne awa biyu kaíín lokacin....Kunyar Anti ta kamani na ce kai Anti barshi kawai abinda ma bai gama warkewa ba tukuna ta galla min harara ta ce sakarya na yi murmushi kawai na fito na barta na samu Muktar a falona yana zaune shiru falon ya yi matukar burgeni lamkar ban taba sanin kayan da aka jera min din ba wanda duka Antina ce ta yi min duk da ce matan da Muktar ya yi wai ya hutar da ita bata amince ba, na kalleshi cikin sakin fuska na ce gajiya ce damuwar? Ko yunwa? Ko hannunka ka fama? Ya yi murmushi ya ce malata nake son gani in gaya mata na da matsala na je na zauna kusa dashi na budc kazar da na zo da ita kalilon da yayi mata ya tabbatar min yana da bukatarta na shiga yagarta ina bashi har sai da ya ce ya Koshi ha mika mishi ruwa mai sanyi ya sha ya yi hamdala, sannan na tambaycshi zaka yi wanka ne ko sai na ji matsalar taka ya ce zan yi wanka na shiga na hada mishi ruwan wanka ya shiga ya gama ya fito ba tarc da ya shafa mai ba kawai ya sanya rigar barcinshi ya fito ya samcni a falona na ce mu je wanjcnka ko? Ya daga kafada nuna alamar duk daya na wuce ya biyoni dama kuwa na riga na feshe ko ina da turare sai kamshi kake ji muna zaune a falonshi na ce menene abinda kakc son gaya min? Ya dan kallen a hankali ya cc ina son Badi'atu ina kuma son in kara sonki sai dai tsoronki nake ji. idan na tuna yanda kika rinka azabtar dani ta hanyar hanani jikinki yanzu kuma na sa rai na saki jikı in kika min rowar kanki ya ya zan yi? Kin san ance wai sa rai ga ci shi ke kawo jin yunwa, na cc uhum wato kana tuna abinda ni na yi maka har kana tsorona amma ni baka tuna irin wanda ni ka yımin? Ya dan yi murmushi ya cc ni in kin ga ina da kuzarin yi mıki tsiya ai naga kina mun ne in miki ki j1i in da dadi amma in na san kına son ganina kusa dake Badi'atu ai sai kawia in kwantar da kai in sha gara, na yi murmushin jin maganar shi na ce Muktar ban sake hanaka jikina tunda kana so ya miko hannu zai taba nayi caraf na rikice hannunshi na cc barı sai hannunka ya warke cıkın sauri ya ce ai na warke Badi'atu babu abinda ba zan iya ba da hannun kin gani, ya jawoni yana kokarin cusa hannunshi cikin rigata wai zai taba nono ban san yanda ya yi ba surta kawai naga yayi ya nufi dakinshi dani baka fa da lafiya Muktar hannunka abinda na ce mishi kenan lokacin dana ga wasan nashi zai wuce yanda na yi zato. Duk da kokarin da na yi na in zama jaruma in bar Muktar yayi yanda yake so dani kasa hakuri na yi ni kam ban ganc bambancin yau dana Tanar da ya kawar da budurcina ba don haka duk da ban nemi hanashi biyan bukatarshi ba, amma ya sha mita de korafi da kuma roko ina makalw jikinshi bayan ya gama biyan bukatarshi sumbata yake yi ta ko ina yana fadin maganganun da bai kamata in fadesu wani ya ji ba, a haka barci ya daukeni wani irin nannauyan barci na yi mai niisuwa ban farka ba sai da Muktar ya tashenı har ya yi wanka ya yi kwalliya yana sanyc da wando Chinose T.H. baki ngar jikinshi shirt ce short slccbe light brown ga kanshi saisaye irin askin da ya saba sai kamshi yakc yi yayi min kyau kwarai na bata fuska na ce lah shi ne ka tashi ka yi saliah ka barni a kwance? Ya vi murmushi ya Zaunar danı ya zauna muna fuskantar una na tasheki Badi'atu baki ji bane, sai na ga bari in kyalcki ki kara don na san barcin gajiyar abin nan e na yi saurin rufe tdn da tatikan hannune ya mike tsaye na zuba miki ruvwan wanka ni zan je gut su baba fta san da kyar zan iya shigowa da sauri in kin gama säi Ki jiki gau su Baba Sabuwa da sauri ki dawo kin san yau zamu koma ko? Na ce to na gama shirywa cikin wata atamfa'yar Holland mai ruwan mallo znai da riga da dankwali ta yi min kyau kwarai na nufi sashin Innarsu Wasila na gaisheta tun daga nan na san Muktar ya yi rabon tsaraba saboda yanda na ga kaya a jibge kan kujerarta na san na yan uwantanc dake nesa na gaida Inna na zauna anan na karya na kuma gaya mata zani in gaida su Baba Sabuwa, ta ce to in gaishesu, a lalon Antina na samu ne tana akin rabon tsaraba gidajen makwabta na gaisheta na jawo jakata dana tarar an shigo min da ita na bude na Ciro lesuka guda biyu iri daya na hada da atamfofin Holland biyu suma irı daya na ce Anti wannan naki ne ke da Innarsu Wasila turarraruka guda uku Baba Babba baba karami da babanlungu Ieshin nan guda biyu Hajiya Murja da Baba Sabuwa amma Baba Sabuwa zan hada mata da wannan atamfar ita da baba karama amaryarta shinma baban gidansu turare gashi sauran kayan dake cikin jakar ke kika san wadanda ya kamata ki rabawa a cikin gdian nan Anti tayi murna ta yi ta sanya mana albarka ni da Muktar na kama hannun Zainab da Luba suka rakoni gidansu Gali tunda na shiga gidan na soma gamuwa da oyoyo wurin yara har muka iso falon Baba Sabuwa na yi sallama ta amsa na shiga suka biyoni kowa da abinda yake gaya min na ce ku yi shiru ku yi shiru ku ji suka dakata na cc Amir maza kira min Usaina ku zo tare ya fita da gudu suka dawo tare Anti sannu da zuwa ina gogewa Baba karama dakine ban san kın zo ba na yi murmushi na ce nima yanzu na shigo Usaina na bude jakata na dcbo kudi ban ma san yawansu ba na bata na ce maza kaisu kantin Garba kowa ki saya masa abinda yake so ta ce to ku zo mu je su dukansu suka bita da gudu, lokacin ne na amsa sannu da zuwan da baba Sabuwa ke min na kuma kalli budurwar dake kwance muna hada ido ta saki murmushi ta kuma tashi zuane sannu da zuwa Baba Sabuwa ta.ce kar ki amsa gaisuwar da zata yimiki. Badi'atu babu yanda ban yi da ita ba ta je ta gaida mijinki kin ganta nan kememe ta ki zuwa cikin shagaba ta soma magana cewa na yi Inna sai an sallameshi ya koma gidanshi na ce to shi kenan randa kika zo gidan nashi kika gaisheshi na huce in amsa gaisuwar ta ki. Gaba daya muka yi murmushi daure ki kira min Larai ta kawowa Badi'atu abin karyawa abinda na ji baba Sabuwa ta ce mata kenan ta ce zan ma kawo ta mike tana tafiya cikin wani yanayi na lankwasa da iya taku sai dai da gani ka san ba koyo ta yi ba halitta ne ni kam lalacewa na yi wajen binta da kallo kyan yarınyar ya wuce a tsaya bayanı ta dawo ta ajiye kayana a gabana ta tsuguna tana shirya min na cc kadan zan sha na riga na karya ta juya ta kalli Baba Sabuwa ta ce la Inna kin ji wai kadan zata sha, Baba a yi murmushi ta cc zuba mata kadan din ai ba bakuwa ba cc ta zuba min ta koma jikin Baba ta kwanta tana ccwa nima in nazo gidanki kadan zan ce ki zuba min kafinin bata amsa sai Gali yayi sallama na amsa ya shigo ya tsuguna gcfe daya gani Umma ta dan sha mur kadan kalin ta yi magana ta ce har yanzu baka je ka sayo maganin Nuwaira ba? Cikin ladabi ya amsa yanzu zan sayo ya mike bari in dawo mu gaisa Badi'atu na ce to muka gaisa da Baba muna hira mutanen gidan ma suka zo muka gaisa na kawo tsarabar dana zo musu da ita na bata tana sanya mana albarka ni da Muktar tana ce jiya da daddarc Muktar ya lullubcmu da aike kaya da kudi ke kuma yanzu ga naki nuwaira ta cc Inna ai kyauta miji daban taka daba a'a duk dayanc in ji Baba Sabuwa ni kam murmushi na yi Gali ya shigo ya basu magungunan ta ce mu je in kaiki gida Badi'atu na ce to na yi musu sallama muka fito ni da Gali har muka iso bai ce mun komai ba alamar dai yana da 'yar matsala muna shigowa lalona muka tarar da Muktar yana kintsa wurin alamar ya gama shirin taliya Gali yana zama ya ja tsaki ya ce kai Muktar yau zan bar garin nan. Muktar ya ce Haba Gali yau Juma'a ku bari jibi lahadi ka tafi mana. Gali ya ce uh uh zan tafi kawai ka riga ka san in har sakaryar yarinyan na tana gidan nan to ni kuwa ban da sauran hutu. Muktar ya ce me aka maka na rashin hutu? Galı ya yi tsaki ya ce yanzun nan daga sayo mata magani na dawo, jiya da daddare kuwa karfe daua Umma tasa aka tasheni wai cikinta uana ciwo in je in dauko musu likita na je na kawoshi tunda na shiga na tarar tana kuka Umma wai tana fyace mata majina na fito na tsaya a tsakar gida, don kar takaici ya sani yin magana Umma ta ci mutuncina ni kam dariya na yi jin bayanin da Gali ke yi yanzu ne kuma na kara gane wacece Nuwaira? Muktar ya kalleshi ya ce wai kai har yanzu kana nan akan ba zaka aureta bane? Gali ya ce haba Muktar ai in na auri yarinyar nan to ni kuma na ga ta kaina kenan in na fita aiki in yi ten aiki, in na dawo gida in lalace wajen tarairayar tunda ita dai kowane lokaci a kwance take a jikin Umma ni har mamaki nake ji yanda ake yi take karatu don in tana turanci sai ka yi zaton a turai ta girma kuma baka san abinda ya fi kona min rai ba wai tafiyar nan da na yi dubu abında ya samemu amma wai bata samu damar bude baki ta ce min a'a ashe abinda ya sameku kenan? Allah ya kiyaye to ko kalmar sannu bata hadani da ita ba amam ni cikin dare an katse min barcina saboda ita ni yanzu addu'a nake yi Allah ya taimakeni takardun tafiya kos dina Ingila su fito kafin su sake tayar da maganar Inna samu na tati sai sun gaji da jirana sun auarar da ita kafin in dawo kasar nan, Muktar ya ce to ka san dai iyayenmu ba abokan wasanmu bane, Gali ya ce e, ya tashi zai fita yana cewa Badi'atu ki shirya abincin dare duk dani a gidanku zan kwana, cikin sauri Muktar ya ce a'a au babu wurin kwana a gidanmu amarci muke yi ba kuma zaka zo ka takura mana ba, Gali ya tuntsire da dariya ya ce ai kun makara ga abokan aurenku tun wata hudu da suka wuce suke ta haihuwa matar Umar ma jiya ta haili 'ya mace sia da muka yi sallama da duk mutanen gidan kafin muka shiga falon baba babba ni da Muktar muna zaunea kasa.cikin ladabi baba yana kan kujera na kalleshi ba tare da ya san na kalleshin ba cikin zuciyata na ce oh wai har baba ya murmure daga masifaffiyar ramar data sameshi ya gama amsa gaisuar sai ya ce min Allah ya vi muku albarka Badi'atu ku yi liakuri da juna ku zauna lafiya Allah kuma ya albarkaceku da samun 2uriya dayvaba, adanda zasu zamo masu biyayya a garcku kamar yadda kuka yi1 mana Muktar ne ya ce anmin, Muktar ya miki bayanin ya bayar da aikin ginin masallacin Juma'a tare da makaranta ko? Na ce e, baba ya ce to ya kuma ce in shirya tunda Nafi'u zai ara hutu a satin nan sai yayi min rakiya zuwa Jiddah don a duba lafiyata saboda hawan jinin da aka ce ina dashi don bamu taba sanin akwai shi din ba sai a lokacin na ce to baba Allah ya dawo daku lafiya muna shirin tashi kenan sai ga Uzairu ya gaida Baba ya zauna yana soshe-soshe baba ya ce lafiya dai Uzairu? Uzairu ya ce lafiya baba yaya Muktar ne nake so ya ganni don kauyen nan da suka turani ya ji shiru yana dan sauraro baba ya yi murmushi ya ce ya kara ganinka kenan muka yi sallama da baba muka fito Uzairu ya budewa Muktar kofar mota ya shiga ya zauna ya rufe mishi ya kalleshi yana murmushi dama antinka ka budewa kofar da kafin samun wani abu don ni kam yanzu ina jin ko ası bani dashi a jakarta na samu kudin mand ake je ka sawo mun aa motar nan. Uzairu ya kalenı yana murmushin sakarci ya ce Antice yau muzurai take min Muktar yana kokarin tayar da motar yana cewa laifi kenan ka yi mata? Ya ce c to ni ko ma ban yi laifin ba na tuba Muktar ya yi yar dariya ya ce nima na tayaka tuban Uzairu ta yi hakuri ta ganka ya dawo wajena yana murmushi Allah anti yau zani Soban in kai sakon jiyan nan aikine ya mun yawan na kai dai gashi na riga nasan alkawarinka na karyanc tunda ka ce zaka yi arumi ma ban ga ka yi ba, Cikin sauri ya ce na yi shima yaya Muktar ya san na yi azumi talatin yana asibili tun washe garin dawowarshi na fara na ce to un go na mika mishı bandil din dari bıbbiyu guda daya ya ce na gode Allah ya kara girma Muktar ya ja mota ya fara tafiya yana dariya irin rungumar da Uzairu ya yiwa kudin da na bashi ya ce kai Uzairu da son kudi saukın abin dai jarumı ne zai iya nemansu sai da muka biya na yiwa ma tar Umar barka sannan muka wuce muna isa gida su goda suka tarycmu cikin murna Daniel kuma ya kawowa Muktar littafi mai dauke da sunayen mutancn da suka zo baya nan da daddare ganin yawan mutanen dake tare dashida na yi wankana sai kawai na yi kwanciyata a dakina wajen goma da rabi Muktar ya shigo dakin cikin shirin kwanciya yana dora kaladarshi ya jawoni jikinshi ya dora bakinshi kan nonona guda daya hannunshi mai lafiyar kuma yana kan dayan yayin da ya rungumeni da hannunshi mai bandejin gaba daya ya kidimani, na kasa tsayawa wun daya sai zillo nake yi ina bashi hakuri da kyar na samu ya sakeni yana kallona cikin murmushi na ce gaskiya Muktar yau kam a'a ya yi murmushin shagwaba ya ce yi hakuri Badi'atu ni kam e, zan yi magana ya Earn kankameni a jikinshi come on Badi'atu kar ki zama raguwa mana 2 wuce ki ce jIya kaza da kaza ba na ce a'a to kullum De? Yace e. mana in dai naga zna iya zo ki ji? Yand Rokarn. Juyo dani in fuskanceshu kin dai san juyawa iuji baya tu.ou kyau? Na ce uh, to juyo nan ki gani da haka ya shawo kaina na hakura na bashi hadin kai, watanni shida da dawowar Muktar ina zaune gaban madubi ina shafa mai tare da kallon katon cikin dake gabana Muktar ya fito bandakin dake dakin yana goge hannunshi da tawul kananan kayanä dana jika a jiki ya wanke min ya kalleni ya ce Badi'atu an ya cikin nan bai wuce lissafin da dake mishi ba kuwa? Na kalleshi na ce to ya kai nawa kai a ganinka? Ya dan karkata kai ya kara kallonshi ya ce wata takwas na yi murmushi na ce to kai kuma wa tanka nawa da dawowa? Ya ce shida na ce ato, ya miko min riga ina sanyawa ya karbi tawul din danake daure dashi ya mayar mazaunnshi ya dawo na ce Muktar satin nan ne fa bikin Asma'u Adam ya yi amza ya sha mur ya ce babu inda zaki da wannan cikin yanzu ke kin ga yanda kike ma kuwa? zani daurinaure Anti zata je musu biki shi kenan ya wadatar ban yi magana ba na dai zobara baki alamar ban ji dadi ba ya kalleni yana tambayata ga jakarki ko kuwa in rike miki? Na ce uh uh bari ita na karba asibiti muka nufa yin scanning saboda Dr Lami ta ce bata gane kan awon da take min ba ina kwance kan gadon asibiti ana ta goga min wani abu a ciki likitoci biyu tare da Dr. Lami suna kokarin gano abinda computer take.nuna musu tsawon lokaci suna kokari kafin suka tsaya daya daga cikinsu ya ce 'yan biyune duhansu maza sai dai daya daga cikinsu hannu ukune dashi, dayan kuwa cewa ya yi.a'a shi wannan hannun a ganina zaman kanshi yake yi, 'yan biyune da kuma hannu daya daban, kafin in wartsake daga faduwar gaban dana samu sai kawai na ga Muktar ya fige soket din ya kashe na'ura, dakata yallabai in ji daya mutumin Muktar ya ce a'a a barshi kawai to in kuwa wani abu ya laru babu ruwanmu in ji likita. Muktar ya wulwulo wani irin ashar ya kunduma mishi na razana har ban san lokacuin da na tashi zaune ba don ban taba jin shi yana yin ashar ba, ya kamani ya sauko dani da ka yi hakurı an sake yin scanning din don mu gani in Ji Dr. Lamı ya ce a'a a barshi kawai zo mu Badi'atu ya rike hannuna da hannunshi dama na hagun kuwa yana rike da jaka har muka isa inda ya yi parking ya bude min kofa na shiga na zauna ina kuka ya rufent ya juya wajenshi shima ya zaune yana tayar da motar basu 1ya komai ba wadannan likitocin kin taba ganin mutum da hannu uku? Y an abu kazan uba ya sake wani ashar din na ce to mu koma mana su gano ko meye? Ya ce bana so na barwa Allah al'amarin kuma kema gareshi ya kamata ki dogara ki daina wannan kukan da kike yi cikina ya shiga wata na takwas a lokacin nan girman cikin ya kai matuka har ba a magana gaba dayan hankalin Muktar a kaina yake a wannan lokacin ne ya shiga shirye-shiryen haihuwata ya gyara, dakin dake kusa da nawa ya zuba kayan yara tun daga gadaje har kayan wasa komai bibiyu ya saka a wannan lokacin hatta abincin da muke ci ni dashi shi yake mana sauran mutuncin gidan kuwa Barratu ke musu ina zaune a kasa gaban Muktar latsa kumburin kafafuwana yake yi me suka ce game da kumburin? Na ce wai babu damuwa sai dai yau ma likitan da ta min awon ta sake yin magana wai in sake yın scanning Muktar ya zuba min ido Badi'atu ba na ce a'a ba? Na ce e, ya ce to na sake cewa a'a kuma kar ki sake min maganar kina tsammanin akwai mai canzawa Ubangiji shirinsa ne? Na ce a'a ya ce to shi kcnan kina Zuwa awo don ban iya ba ban san komai game da yanda ake kula da lafiyar mace mai juna biyu ba haka nan ban iya karbar haihuwa ba don haka nake kai ki don kula da lafiyarki ke da abinda ke cikinki amma ba don su shiga cikin lamarin da ba nasu bane, to ya shiga matsa min kafafuwan yana gaya min in Allah ya yarda lafiya zaki haifan mana 'ya'yanmu suma kuma laliya na ce Allah ya sa ya ce amin Daniel ya shigo yana gayawa Muktar an yi bako daga Zaria ya ce ya shigo dashi ya juya ya fita sai gashi atre da Saminu. Muktar ya daga ido ya kalleshi ya ce Saminu yau kuma wani shakiyanci ne haka? Sai ka turo an yi ruaka iso ba zaka yi sallama ka shigo ba. Saminu ya ce ka yi hakuri Yaya shi mutumin ne ya tsayar dani wai sai ya gaya maka. cikin ladabi ya gaida Muktar nima ya gaishcni na kira Barratu ta kaow mishi abin tabawa yana ci Muktar yana tambayarshi lafiyar mutanen gida yana gaya mishi, wato kai daka dage sai ka zama dan sanda ko? Saminu ya yi murmushi na zo gdia baba take ce min wai ka samu Police Academic ta nan Zaria na ce hala rike kulkin nan nasu ne yake burgeka don akwai wani dan sanda da da yake yawan zuwa kofar gidanmu kullum da rullum nake ganinshi Saminu da bai san inda zancen Muktar ya nufa ba ya tsaya yana gayawa Muktar dalilınshi na son zama dan sai da ni kam ina jinsu sai da ya gama sai Muktar din ya ce mishi yana da kyau Saminu dan sanda ai abokin jama'a yaya baba? Saminuya ce shine ya aikoni wai in gaya maka an sanya bikin Yaya Gali da Nuwaira 21 ga watan Sha'aban shi ne ranar daurin aure wai in kuna da magana sai ka zo ka sameshi cikin sauri Muktar ya ce bamu da magana saminu sai dai Zan zo godiya yaushe ne watan zai kama? Na ce gobe Muktar ya tashi va shiga dakinshi ya to wasu laliyayyun shaddoji kala uku yana kaje ka bada dinki ka ei biki ya kuma bashi dubu ashirin wai ya biya kudin dinkin. Sami nu ya yi godiya ya tashi ya tafi fitarshi ke da wuya ya danna lambot in Galia can London, Allah ya ja zamanin ango abinda ya fara ga'a mishi kenan ban ji abnda ya ce ba sai na ji Muktar ya ce mu ture zancen wasa Gali yanzun nan Saminu ya bar gidan nan, ya yı misbi bayınin abinda ya kawo Saminu, shiru ya yi yana sauraron abinda Galin ke fadi sai ya ce e, bamu san abinda ya dace damu ba kuma iko da fin karti da ka ce iyayen nu suna nuna mana gata ne, ba 2amu kara gane hakan ba sai a ranar da muka rasa masu yi mana irin wannan gatan a hanyar nuna isuwarsu a akumu bi kam gobe zan isa Zaria Zan je in tsaya n ga an yi komai ruwanka ne ka is gida a yi biki da kai in kuma ka ga zaka tsaya ka nuna musu sun haifcka amma basu Isa da kai ba to shi kenan sai dai abinda nake so in tuna maka shi ne addu'o'insu da albarkar da suke sanya mana sune jagorar nasarorin mu a rayuwa ban $an me Galin ay ce ba na dai ga fuskar Mukiar ta nuna alamar farin ciki sai naji ya ce to ai ni yanzu ma baka Sa damuwata ba ya shiga basni lahnriu iaiun da nake ciki ya dan yi shiru yana sauraro sai kuma ya ce ai ni asalin nauyin Badi'atu dana sani shi ne kilo arba' in da biyar da digo uku to amma a yau nauyinta da aka gwada shine kilo saba'in da daya tana kuma da sauran sati uku zuwa hudu nan gaba kafin ta haihu, kaga kenan babu mamaki ta cike kilo dari Koda ban sani ba Gali dariya ya yi kafin yayı magana, don shima Muktar din murmushi ya yi, sai ya ce a'a na san nauyinta na farkon zuwanta gidan nan mana ai kasan gwanacc kwarai wajen horon miji da yunwa, awancan lokacin da take yin girki ta cinye ita kadai ni ta hana ni nakan barı sai ta gama cinye abincin natata Roshi sai in sa hannu in sureta in je in do:ata a sikeiin gwada nauyi in nuna mata matsayın nauyinta ita da abincin data ci ta koshi, sannan in sauketa nima in hau in nuna mata nawa nauyin a ban ci komai ba, in ajin yunwa don ta san abin kawai na Allah ne ba wai yawan ci banc, dariyar da Galiya yi ba karamar ba ce, don sai da na jita a inda nake zaune suka gama maganarsu ya aj!ye wayar ya juyo ya kalleni, yana dariyar zolaya, ban da ia kai na ba kuwa Badi'atu? Cikin sauri na tambayeshi da aka yi me? Ya ce to ga bikin Gali ga halin da kike ciki ba sai na gaya miki matsay in Gali a wurina ba kin san komai na ce me damuwarka? ya ce zan so zuwa bikin tare da matata zan so ace kece zakı hadamun kayan auren da zan shrya mishi don ki hada min komai kamar yadda aka hada naki na ce in ai don wannan ne baka ga ta kanka ba Muktar zan hada kayan aure zan bika bikin amininka in ma na haihua a can bai baci ba a gaban yayenmu ne, ya yi murmushin farin ciki ya kwanto da kanshi jikina. Washe gari Muktar ya nufi Zaria nima na dauki matar Major Amadu ta yi min rakiya zuwa kasuwa don sayayyar kayan aure Gali kwana uku Muktar yana Zaria, nima ina gida ina aikin sayayya, muka kammala komai na hada komai yadda aka yi nawa, hatta Zinaren dake cikin kayan auren irin nawa ne haka yawansu ma daidai da nawa ne, da daddare Muktar ya dawo Allah ya saka miki da alheri abinda ya gaya min kenan bayan ya gama kallon kayan ranar itinin ina isa Zaria da kayan auren Gali tare da llari maar Major Amadu da iyalan gidana duk sai da su baba suka ga kayan Sannan su Anti da Hajiya Murja suka nuka kayan ga iyaycn Gaklt don su shirya kaiwa gidan Amarya? Wasiie gari da safe muka nufi Soba ni da Antina da ilari saboda na ji kewar iyayena tun zuwan da Suka yi ganin jikin Muktar bamu sake saduwa ba, ran nan kuwa a gidanmu farin cikin da aka yi na ganina ba kadan bane, ana iin labarin zuwana gidan ya cika da makobta muka yi' ta hira da daddare kuwa s$ai da muka 1asa kwanon abinCin da zamu ci saboda yawan abincin da makwabta suka tara mana Hari ta ce wato dai Badi'atu har yanzu iyayenmu suna nan da irin wdlifidi Katar ? Na ce kwarai kuwa babana kuwa wayyo Allah kamar ya lasheni don dadi kwana daya muka yi da zmau yi sallama da baba sai ya ke ce min wannan aiken da mijinki ya baki ya ce ki kawo mana kadan ce kwarai akan irin aiken da yake mana don haka in kin je gida godiya sosai za ki yi mishi, na ce to baba. Mun dawo Zaria Anti ta gama shirya kayan sa lalle wanda shima aikin Muktar ne har dani aka nufi Hunkuri kai kayan saura kwana biyu a daura auren ni da Hlari muka je ganin sabon gidan da Gali ya fara ginawa ya bar aikin shima Muktar ne yake aikin gamashi komai ya kammala ya kuma yi kyau kwarai a lokacin da muka je kwayayen fitilu muka tarar ana ta aikin daurawa ana gobe daurin aure da daddare na dawo daga Hunkuri inda na je kawai amarya kayan da na bayar aka dinka mata na cin bikin shima umarnin Muktar na cika gajiya ta hanani karasawa gida na hau gadon baba Sabuwa na yi kwanciyata da nufin hutawa anan barci ya daukeni ni dana kwanta tun takwas ban farka ba sai sha daya na tashi zaune ina salati na fito falo, baba Sabuwa da wata mata su biyu kin tashi Badi'atu? Na ce e, me kike so na ce gida zani ta ce a'a ai sai mu kwana kawai don kuwa dare ya yiı na ce to zan yi wanka, ta ce to ta zo ta shiga bandakinta ta shirya min ruwa na yi na fito na yi sallar shafa'i da wutiri ina addu'a sai na ji ta ce in kin idar fito nan Badi'a ni kadai ce, na shafa fatiha na fito na zauna ia shirya min tea ta miko min gasasshen naman rago mai zafi gashi yaji yaji na soma ci tana tambayata wai yaya naga Nuwaira don shekaran jiya ta tafi tana mura ta ce kalau dinta suna ta hidima da kawayena Muktar ya yi sallama a kofar falon cikin hanzari Baba Sabuwa ta amsa tare da bashi 1zinin shigowa ya shigo Gali yana biye dashi, na rike baki cikin murmushi ina kara jawo kayan cin akusa danı, Baba Sabuwa ta rage fara'a ganin Gali. Na ce angon ya iso ne? Basu amsa ba, saboda suna cikin nutsuwa, kwarai Muktar ne ya fara gaisheta kafin gali da suka gama gaisawa sai Muktar ya ce ku yi hakuri Ummaa hazo ne ya hana Gali isowa shekaranjiya sai da asubahin yau bata amsa ba yana cikin yi mata bayani babansu Gali ya kirata ta tashi ta fita suka dan sake. Yaya dai Badi'atu? Muktar ya Tambayeni na ce kalau ashe ango ya iso? Muktar ya yi murmushi ya ce ya iso har mun sanyashi a lalle, na ce haba gaskiya na ganshi yana kyalli. Gali ya dan yi murmushi ya sunkuyar da kanshi kasa kema wai sai da kika zo wannan bikin? Sai da suka jira ta dawo sannan suka yi mata sallama suka tafi. Washe gari tun sassafe na sha kwalliya cikin wani shegen leshi baki mai shara-shara da laushi ya sha duwatsu, gashibashi da nauyi ko kadan dinkin siket ne mai fadi da katuwar riga da aka yi ta tamkar malum-malum turmi biyu Muktar ya saya aka yi min amfani da yadi bakwai na baiwa 'yar gidan Wasila yadi ukun, na yi matukar yin kyau ga zinarai sun kama jikina sai walkiya nake yi ina gama karyawa na nufi sashin baba karama don a can ake aikin bikin, ita baba Sabuwa sashinta ya cika da'yan uwanta wadanda kuma sunc iyayen Nuwaira, ina gaida baba karama na nufi kicin don in sa ido kan aikin da ake yi hidimar aikin sosai na shiga tamkar ba tsohon cikine a jikina ba duk. lokacin da Baba karama ta zo wucewa zaka ji tana ce min ki fa rinka zama Badi'atu in yi murmushi in ce mata tio kafin karfe daya aikin ciccika manyan kuloli da abinci muke yi ana kai wa wajen mutane ana zuba musu na ware wasu manya guda uku na shakesu da farar shinkafa guda daya na cikashi da soyayyen naman saniya guda biyu na cikasu da kunun gyada sannan na kawo wata katuwar kwalla na cikala da miyar tumatur wacce baba damna ka sanya ludayi cikınta sai ka debo naman kaji na hada na ce a kaiwa angwayc kafin su nuf wurin daurin aure na dawo sashın baba Sabuwa na tarar da su Antina da Innarsu Wasila da Hajiya Murja har da Hari suna wajen na cc lah kun zo ashe kuna nan na tsuguna na gaishesu na ce gaskiya Anti ba bikin Gali kuka zo ba nan ai dangin amaryane gaba daya aka yi dariya na ce zo mu je Hari, Wasila ma tana can muka taho tare na zo na shirya abincin da muka yi har da masa da miyar taushe ya kuma sha tantakwashi da naman rago na jera kan wani katon tirc na dauka na je na kai musu na ce akwai fruit salad da 41 zobo da kunun zaki har ma da alala bari in je in kawo muku, Henya Murja ta ce ke Badi'atu samu wuri ki huta kin ga yadda kike digar gumi kuwa? Samu Wasila ki sata ta kawo mana na ce a1 tana cikin kicin ne zan dai turo duk wanda na samu. Kawai Baba Sabuwa 1a ce in banda karfin halima wannan ciki na Badi atu in ta zauna a1 sau au dagata. anti ta ce itama bhaka take, na yi maza na bar wurın don ban son jin tonon asirin da take shirin yi min. Wajen karfe uku da rabi na fito daga wanka na sake wata kwallıyar want leshin na s ake sakawa sky blue dinkinshi irin na safen ne yan kunnayen dake Jikina ma ba sune na yi amfani dasu a safiyar ba. Saminu ya le:ko ina Anti Badi'atu? Wuce tana can ciki Hajiya Murja ta bashi um rni ya miko min wani kunshi mai girma na goro da dabino murza murza wai gashi in ji Yaya Muktar an daura auren Yaya Gali da Nuwaira gaba daya muka ce Allah ya sanya alheri na tire na zu ba na fito dashi inda iyayenmu suke zaune na ajiye musu a tsakar gi da ma sai raba goro da dabinon akeyi ana sanar da Jama'a an dau ra auren Gali da Nuwaira tsofaffi kuwa sai rangwada guda suke y1 Saminu ya sake shigowa yana fadin akwai ltyafar cin abinci yanzt a Zaria hotel duk mai son zuwa ga motoci nan a ko far gida da daddare ni ban je daukar amarya ba, baba Sabuwa ce ta hana ta ce wai in dai ba so ake in je in haihu a hanya ba Den haka na zauna cikin masu tarbar amarya su Wasila da su Hari suka tafi amarya ta 1so bayan sallar 1shai ga alama kuwa'yar dangice don kuwa jama'ar da suka rakote ba kadan bane ta sauka a sashinta wanda aka vi matukar kayatar dashi aka kuma nuna mata gata ta wajen kayatar dashi da kayan alatu ko da yake Antina ta ce min gaba duyan abiada na gani a wurin aikin baba Sabuwa ne na rike baki nuna alamar mimaki na ce lallai baba Se buwa tana ji da ita. Anti ta rike baki ta ce ai kanwar baba Sabuvar ne ta haifeta a hannunta kuma ta girma don tarc aka kawoe ta y1 nata zaman daki data girma tä aurar da ila ta baiwa kaninta abokin wasansu shi ne ta haifi Nuwaira na ce to yanzu tana ina? Ta ce Allah sark ai tn nahuwar Nuwairan ta rasu tausayi ya kamani na kara jin mamakin shakiyancin Gali na ce wato dai Gali so ya y1 ya tsokano sama da tsinke da vake cewa ba zai aur Nuwaira ba Anti ta ce rabu dashi ja'ir washegari a wurın liyafar 42 kuwa komai ya tsaru ango da amarya sai kyalli ske yi kana shiga wurin zaka gane irin ta'adin da aka yiwa turare kafin azo ina zaune gefen Muktar muma mun sha kwalliya anko muka yi. Hari tana kusa dani Major Amadu yana can gefenta don tunda ya zo daurin aure bai tafi ba. flari ta rada min a kunne ta ce kai wannan amarya akwai ta da kyau, dubi yanda ta zama cikin kawayen nata tamkar wata a Cikin taurarı, na yi murmushi na ce kin ganta ko? Ta yi.saurin amsawa e, na ce to kema dai sheda ce makaranciyar alkur'ani ce tunda a gabanki aka yi mata sauka, ta ce kwarai, na ce bayan haka tana da diploma a Home Management daga kaduna Polytechnic, ta ce eyc, na ce to auren dolc aka yiwa Gali ta rike baki nuna alamar yin mamaki, na ce amam fa nima fin karfin Muktar aka yi aka bashi ni, ta kyalkyale da dariya ta cc ke kice abotar tasu ta yi matukar daccwa na ce uh kwarai kuwa, ta ce to amma fa babu laiti suna da biyayyar iyaye na ce c to da wannan kam, kawar amaryace ta mike take karanto tarihin amaryar lokacin da na ji wata irin masokiya ta sokc sai da na ce wayyo Allah na saurin abin Muktar ne kawai ya ji cikin hanzari ya juyo gareni menene Badi'atu? Na ce bana jin dadin zaman kujerar ta matseni dubi duk matan da suke wurin nan Muktar ni kadaice mai katon ciki dukansu kwalliyarsu gwanin sha'awa da sauri ya ce min wa ya ce miki kwalliyarsu tafi taki kyau? Katon cikinki abin takamarki ne, don kema kowa ya ganki ya san mijinki yana sonki. Ni in kika kyalcni ma sai in ce miki dukan su sha'awarki suke ji, na dai yi murmushi kawai na hakura, an gama ciye-ciye da tande-tande an kuma gama jawa bai har an karbi kyaututtuka ni kam ban iya tashi bayar da kyautar ma ba saboda yanda cikina ya dun kule wuri daya sai Muktar ne ya bayar mana da namu, taro ya kusa tashi Muktar ya mike yana Karanta jawabin godiya yana gamawa aka rufc taron da addu'a, muka dawo gida wajen sha biyu Muktar ya dawo gida don ya tsaya raka ango dakin amaryarshi da asuba muna idar da sallah Muktar ya shiga kinisa wuri cikin shirin tafiya sammako zamu yi don mun kwana bamu yi barci ba saboda ciwon bayan daya addabeni ina can Cikin dakin Muktar ina fama da cikina wanda ya dunkule wuri daya naji shigowar Gali falon Muktar din lafiya ka zo mana gida yanzu? Gali ya yi tsaki daidai lokacin da na ji zamanshi kan kujera, to yaya zan yi? Mata sun cika min gida? Ya sake wani tsakin, yarinyar nan bata barni na yi barci ba kwana ta yi tana kuka, to kai me ya kaika wurinta? In ji Muktar, Gali ya sake jan wani tsakin wai daga naji zan mata sai da safe kar ace an bani amana ban rikc da kyau ba sai kuma na kasa fitowa daga dakin. Muktar ya fita tsakar gida ba tare da ya yi magana ba ya sake shigowa Gali ya ce yarinyar nan fa budurwace sai da naji faduwar gaba jin maganar Gali shi kuwa Muktar tsaki ya yi ya ce haba Gali ka ja bakinka ka yi shiru kar mutane su ji wannan abin kunya da ka yi su yi maka dariya, ya ce Allah ina jin da addu'o'in da Umma ta tofa mata shi yasa dana ganta na kasa hakuri ai ba jiyan na soma ganinta ba ko zaka tura Badí'atu ta gaisheta? Ya ce to ya leko dakin ya ce Badi'atu yi kokari ki je ki yiwa su nna sallama yanzu zan zo mu tali, na ce to na fito da kyar nake iya daga kala katuwar rigace a jikina ina rikc da gyalcna a hannu na ce ina kwana Gali? Fara'ar dake fuskarshi ita tafi komai bani mamakı ya amsa yana tambayar ko dai asibiti zamu kaita Muktar. Ya ce a'a gidanmu zmau tafi in Allah ya yarda sai mun isa ta haihu na shiga wurin Innar su Wasila tana falonta ta bini da kallo anya wannan tatiyar kuwa zata yiwu? Na yi murmushi kawai na zauna na gaishcta. Muktar ya shigo cikin ladabi ya gaisheta ya kuma yi mata sallama sai ta ce-mishi ka bar Badi'atu anan in ta haihu ta yi wanka sai a kawota ya ce to ya fita har na dan ji dadi don kuwa ni kadai na san abinda nake ji sai ga Naff'u da sauri shima shirin tafiya yake yi ya zo ya zauna cikin ladabı ya ce Inna wal Badi'atu ta fito su tafi in ji Baba babba, ta ce to tashi ku je, na tashi na yi mata sallama ko wurin Antina ban shiga ba, a kofar gida bab babba yana tsaye ya sha manyan kaya tamkar wani mai mulki saboda kwarjini shi kuwa Muktar yana jikin motarshi ku je gida Badt'atu Allah ya kaiku lafiya, na cc amin na je na shiga mota na zauna na ji Muktar yana cewa buba Babba idan abokina ya kawo matarshi yimu uku sallama a hadosu da goggo Uwale su zo, ya ce to In Allah ya yarda zasu zo, wata inin tafiya mai matukar wahala na yi sai dai cikin yardar Ubangiji mun isa lafiya mun isa kuwa kayan haihuwa kawai Muktar ya dauka ya nufi asibiti dani mun yi sa'a Dr Lami tana nan ita ta karbeni, ta gama dubani ta cewa Muktar in yana da abin da zai lya tafiya don kuwa ko zan haihu zan kai wajen magariba, na kalli agogon dake dakin naga lokaci a zuciyata na ce wato kusan awa takwas kenan daga yanzu lallai kuwa za a taba jifa-jifa Muktar kan dawo ya dubani na rinka ganin awa takwas din nan da likita ta diba tamkar ba za su taba zuwa ba saboda wahalar da nake ciki sannu a hankali sai gashi sun cika ban halhuwa ba suka fara wucewa azaba ta gallabeni na shiga wani hali na gajiyar da azabar da nake ciki na rasa inda zan tsoma rayuwata in ji dadi, tun bayan sallar isha'i nake tare da Muktar a dakin haihuwa har wajen hudun asuba na kalieshi lokacın da yake ta aikin goge min gumi na ce Muktar a kira min Antina kawai ina ganin mutuwa zan yi cikin sauri ya ce stop it Badi' atu ya kankameni yana min magana a kunne yana kara karfala min gwiwa kar ki ji tsoro kar ki karaya haka iyayenmu suka wahala kafin suka haifemu shi yasa ya zama tilas mu yi musu biyayya muryata tana rawa na cc Muktar zan mutu ya kara kankamcni daina Badi'atu daina fadin haka ba zaki mutu ki barni ba na riko Ubangiji in har zan rayu to ya rayani tare da ke ne ki yi hakuri ki yi hakuri kin ji? Yi nishi Badi'atu umarnin da likita ta bani kenan Muktar yana rike dani don kara min karfi yana min magana daure ki yi nishi Badi'atu ko ma samu Allah ya taimakemu ki huta da wannan wahalar da iya karfina na kc nishin na ji tahowar wani abu na ji tamkar kokarin rabani biyu yake yi jikina sai bari yake y na kidine saboda azabar da nake ciki na saki komai na koma kiran Ubangji ina cewa "Hasbuneliahu wa ni'imal wakil a haka na haihuwa, Muktar yana gopge mii gimı da gcien rigarshi yana fadin Alhamdu lillahi kin haifi daya saura daya, duba mana ka gani Muktar ko Shine mai hannu ukun abinda na fara gaya mishi kenan da sauri ya nufi gun likita wacce ka gwade nauyin jaririn ya karbeshi ya zo dashi wurina hannu biyunc dashi' Badiatu kin ganshi? Dogone Sambalcle kyakkyawa kaleshi ki gaya min dawa kika ga ya yi Kama? Duk da ban gama wartsakewa ba sai da na yi murmushi ya Bama tofeshi da addu'o'i ya mikawa nurse din da tazo karbarshi, su Hari da Goggo Uwale suka aiko min da gaisuwa na ee ina amsawa a gajiye kwarai na haifi daya yaron don kuwa shima na wabala kafin in haifeshi cikin matsananciyar murna Muktar ya shaida min shima hannu biyu ne dashi Badi' atu kin ganshi komai nashi irin na dan uwanshi ne har nauyinsu, sa mnusu shaida don mu ganc na farko da na biyu ya umarci nurse din likita ta ciro min mahaifa ta kuma shi latsa cikina a kokarın da taek yi na gano hannun da suka ce sun gani, mawa kadan sai ta cewWa Muktar akwai sauran da acikin an na in numfashi flasbunallahu wani imal wakil, in ji Muktar ni kam kidimewa na yi na shiga halin targaba saboda tsoron wahalar da zan sake shiga shi kuwa yana ta gaya min kalmomin karfafa gwiwa ciwo ya taso na ji tamkar ya zarce duk wanda na yi a baya tunda yanzu kam jina ya yi tsami duk idna aka taba min sai in ji tamkar famani akayi na rasa inda zan sa kaina Hafsa ma'aunin likita kin yarda na yi a dora min shi a cikin rarrashina Muktar yake yi yana bani hakuri yi nishi Badi'atu in ji Likita ta fadi hakan ya fi sau ashirin shima Muktar ya yi iyakar taimakonshi na kasa, Badi'atu zaki kashe yaron fa gashi ya sauko ki yi nishi ta fito mana Dr. Lami take gaya min a firgice, hankalın Muktar ya kai matuka wajen tashi ya yi duk abinda zai yi na kasa nishı ji yake. yi tamkar shi ya yi min nishin babu hałi, yana rike dani sai bari jikinshi yake yi yi kokari Badi'atu a hankali na dago idona na kalleshi da kyar na iya buda bakina na cc mishi ka yi hakuri Muktar karfina ya kare ji nake tamkar numlashina zai tsaya ka yale min laifutfukan da na yi maka na sake lumshe idona saboda jinn dake dibana da gwiwoyinshi biyu ya durkusa a kasa ya kifa fuskarshi akan tawa yana sissika tamkar mai yin kuka yana fadin ya Allah abinda na saui kawai shi ne na ji lokacin da Dr. 1Lami ta ke kokarin tura min injun din da zai taimaka musu Ciro yaron da aka cc ya saura a cikina na dawo cikin nayyacina, na ganni cikin wani dakin na daban Muktar yana zaunce Kan kujera yana rike da hannuna da ake min karın ruwa ta jikinsn Antina kuwa tana tsayC sai faman lyacc majina take yi Innalila Wa inna ilaihir raji'un abinda na fara fada kenan Muktar da An Kamar rigc-rigcn kiran sunana suke yi sannu Badi'atu na kallcshiu a hankali shima ya yi muzai-muzai kamar tare muka yi nakudar na ce Sun Cire yaron ko har yanzu tana cikina? Cikin sauri ya ce sun cire Badi'atu mace muka samu sai dai itama kamar ke ta wahala da yawa dukansu suna dakın renon jarirai wasu hawaye da ban san dalilınsu ba suka gangaro min Antina ta matso kusa dani kar ki yi kuka Badi'atu ki yiwa Allah godiya ya yi miki kyautar da bai yiwa dubban mata ba, 'ya'ya uku kika haifa lokaci daya na zuba mata ido ina kallonta ta sake kusantoni yau ke da Muktar 'ya'yanku uku kuyi farin ciki ku yiwa Allah godiya na ce to Anti kafin yamma asibitin ya cika kwarai da jama'a masu taya mu murnar samun yan uku. Dr Lami ta shigo tana auna jinina bata da wata matsala sai na karfin jiki ina ganin tunda kuna son ta koma gida sai ku tafin kawai, nurse din da kace in samo maka akwai kanwata ta gama karatunta na nursing bata samu aiki ba sai ta zo ta kula maka dasu Muktar ya ce na gode, Dr Allah ya saka da alheri ta yi murmushi ta kalleni to Badi'atu sai na zo gida ganinki da yaran ko? Na ce to Dr mun gode, mun iso gida Antina tana rikc dani saboda rashin karfin jiki su I lari suna rungume da yawan muna isa hanyar da ta raba sashina dana kicin ma hango Nuwaira a ciki tana ta aikin girkin abincin dare tamkar ita ce matar gidan. Anti tana gyara min kwanciya Nuwaira ta shigo tana murmushi na ce amarya ce da aiki haka kace-kace? Ta ce to amarya ta samu 'ya'ya uku ras ina ta ga ta zama, gaba daya aka yi dariya, na cc ke da wa kika zo? Ta yi wani irin lallausan murmushi da nake zaton in a gaban Cali ta yi kila sai ya kusa shidewa, don dadi ta ce ni da ango saukeni ya yi ya shiga kasuwa, wai zai yiwa babin da ya buya musu nata sayayyar me zan kawo miki1? Na ce Nuwaira da masu aiki a gidan nan kar ki wahalar da kanki ta kalleni la ce ni fa mijina ya cc in na zo gidan Muktar in maida gidan tamkar nashi na yi dariya na ce gaskiya ya gaya miki Nuwaira to kafin in ci komai ina so in yi wanka, cikin sauri ta je ta juyc min ruwa, gaba daya hidimar Muktar da abokanshi Nuwaira ta dauke gata itama gwanace kwarai wajen iya girkI gata gwanar karbar baki duk yawansu ta san yanda zata yi dasu ni kam sai binta nakc yi da kallio ina tunanin sakarcinta da Gali yake bani labari da yamma Dr. Lami ta kawo mana nurse yarinya nulsattsiya kyakkyawa da ita ga kunya da girmama mutane nan da nan ta kama aikinta tana maganar yaran suna bukatar hutu a daina yawan daukosu don baki sun zo a rinka akai bakin dakinsu suna ganinsu, da daddare Anti da sauran bakin da zasu'kwana suna dakin baki ni da Nuwaira ne mu biyu tana kallona tana kara gaya min mamakinta kan haihuwar ya'ya uku da na yi, na ji karar waya nasa hannu na dauka na ce hello Gali ne yake magana cikın wata irin murya da ban taba sanin yana da itaba a marairaice ya ce haba Nuwaira ni da ke ta ba yara bane kanana, na yi saurn katseshi da gaya mishi ba Nuwaira ba ce ya cc at mai jego ce? Toya ya karfin ikin naki? Na ce da sauki na mikawa Nuwaira ban san me yake gaya mata ba na dan ji tana cewa aa ba zai yiwu ba, ta sake sauraronshi tsawon lokaci sai kuma ta ce ka gayawa Anti fa ka ce? Ban san abinda ya cc ba sai ta ce to gaya mata mana ai itama ta san dole aka maka ka karbcni balle ko acc in hakura da takurawarka saboda kana sona ta aiyc wayar na kallcta a hankali na ce ina zata zaki br umarnin da ya y miki takalleni ta yi wani lallausan murmushi ta ce na gode maka Alah da ka nuna min karshen tsiyar Gali na bita da kallo na cc Nuwaira in tambayeki mana? 1a sake wani murmushin ta ce tambayeni ni kuma in gaya miki gaskiya, na ce amma ke dai ba tulastaki auren Gali aka yi ba ko? Ta yi wani murmushin tare, da cewa ban gane ba? Na ce ina nufin dama kina sonsh1, ta ce uyh to haka ne ba haka bane na ce ban gane wannan amsar ba, ta ce gaskiya a larkona ban taba kallonshi da wani nufi ba face na yan uUwantakar dake tsakanina dashi, to amma alokacin da na lara girma na tara samarı mutane suka yi ta fitowa suna nuna kaunarsu a gareni na shiga turasu wajen Inna ta gansu su gaisheta sai na lura hakan yana bata mata rai, wata rana na je Zaria gaisheta sai ta ce min ni kuwa Nuwara da zaki yarda ki mun wani alberi da zan ji dadi kwarai na ce na mcnenc Inna? Ta ce bana son ganinki da samari don ni na sha' awar aurenki da wannan yaron tun kina yar jaririya na yi burin hakan wannan shi nc dalilin da ya sma na reneki ba tare da.na shayar dake nonona ba, nan take na ce mata daga yau ba zan sakc yn samari ba, Inna ta ce Allah ba yi miki albarka, tun daga nan ban sake sauraron wani saurayi ba, ba kuma sai na gaya ba kcma kin san tilas zan y1 masoya sai dai kawai in ki bayar da hadin kai, na ce haka ne ta ce to zuciyata ta kamu da son Gali saboda dalila1 da yawa na farko Inna ta ce ta haifeshi a rayuwata kuwa ina ganin babu wani wanda ya fita sona, na rayuwa gabanta ba tare da na san ni din marainiyacc ba, a lokacin da mahaifina ya karbeni daga hannunta na dauka riko aka bayar dani don na sha gudowa in dawo wurinta ya biyoni ya tafi danı ni da ita mu yi ta kuka, sai daga baya na ganc Hunkuri din na da nake zaton riko aka kaini nan ne gidan mu, mahaifiyata kuwa babana ne ya shaida min cewar tun ranar data haifen ta bar duniya na kuma gane yana matukar sonta don kullum zai ambaci sunanta Fatimah, yayi mata addu'a shima yana sona ni ce'yarshi ta fari saboda haka duk da bana jin dadin zama da maatrshi sai na hakura na zauna sai dai akai-akai ina zuwa gun Innata dana samu labarin abinda Gali ya fada a kaina kuwa wai bai sona saboda ni a ruga nake a cewarshi duk da an sanyani a makaranta ba zan yi wayewar da yakc son matarshi ta yi ba bayan haka kuma wai ni shagwababbiya ce shi kuwa bashi da lokacın tarairayar mace yana ririlata, ban yi shiru ba na yiwa Inna magana, na ce to ki zan ci gaba da yin samarınanc? La ce kar in sake kula zancenshi da sannu wata rana zai shiga hannuna in juyashi yanda naga dama sai dail in na tuna dan uwanane in yi mishi sassauci na ce to sai dai duk zaman da muka yi dashi ban yarda ya gane yana da wani mnatsayi a zuciyata ba don ko kallon inda yake bana yi a ranar dana zowa Innata sallama kuwa na koma gidanmu aka sanyani a lalle ita ce ta min hudubar inna je gidanshi kar in yarda tsiyarshi ta yi yawa in yi kokarın kawo karshenta, na ce to don haka ni na yi mishi shigo-shigo ba zurit na kuma yi mishi saki kecece ta yanda ya kasa fita daga dakin, bar san lokacin da na kyalkyale da dariya ba, Jin maganar Nuwaira, ta sake wan murmushi ta ce ai indar za a so hutawa a tare dake na ganin karshen kiyayya kuma uz0 ta sake lumshc ido ta ce ina son Gali Badi'atu dan uwanane jarumine mutum ne me yawan alhere bayan haka kuma yakkyawar halitiar da aka yi mishi wayar Gali ta sake shigowa la amsa ba atre da ta dauki kan wayar ba don haka ina Jinsu Allah Nuwaira ina sonki ni in banda tsiyarkima dana gaya miki wani shirme dana rayu ina yi ban sani ba, ta ce gaya min ai bani da wata tsiya da zan yi ma ba ahannunka nake ba? Ya ce a'a ni ne dai a hannunki da gaske Nuwaira na zamo mai sha'awar zana surorin kyawawan mata don haka a duk lokacin da nake cikin hishadi na kan yi irin wannan zanen sai dai baki sanı ba, a duk lokacin dana takarkare na yi irin wannan zanen ban iya zan akowa sai ke ta ce ga alama dai kai kadai ne a dakin ya ce e, kin san Muktar Jiya ya taya matarshi nakuda ya shige dakinshi ya kwanta ganin haka yasa kowa ya kama gabanshi sai mi kadai, ta ce to gani nan zuwa ta tashi ta shiga wanka tsawon lokaci bata fito ba ya sake waya Nuwaira kina kallon agogo kuwa? Na cc wanka take yi ta fita tana shafa ina kallonta a raina na ce lallai Gali ya mori mace sai da ta gama ta fita sannan Antina ta shigo tana murmushi ta ce ai na gode Allah da ya hada Gali da maganinshi na yi barci sosai kafin Anti ta tashen ta ce llalima tana maganar ki je ki baiwa yaran nan nono na ce to muka fito tare dakin yaran ya yi matukar tsaruwa komai a cikinshi uku-uku ne ga rubutacciyar Ayatul Kursiyua dukkan kusurwowin dakin na kana wata takarda dake reto a tsakiya dakin ga abinda na gani a rubuce: To Mr. & Mrs Col Muktar Zubair The joy of this day is like a dream we do very litle to get it but the memories will last a life time, may Allah in his never falling way be ever present you more conmfortable, guide you help you through-out the life of the children may He bless the family more joy more happiness. Congratulations and say welcome to the triplet babies. Brigedier General Kabir Isiyaku & Family Na zauna Halima tana miko min su daya bayan daya ina shayar dasu nono har sai da sukä koshi muna shirin fita sai ga Muktar ya shigo, ganin Antu ya sa ya ja zai koma ta ce a'a shigo abinka ni dama yanzu zan fita, sai da ta ita ya shigo ya kalleni yana munnushi ya ce maman'yan uku na ce kai kumma la Ya ce ni sunana mjin maman yan uku. kina yawan cewa Alhamdulillahi kuwa? Na ce kwarai kuwa. Washe gari da safe Gali ya nuti SSakkwato ya bar Nuwaira wai ta taya mu aikin jego sal ana gobc suna zai dawo, da daddarc muna kwaace ni da Nuwaira akan gadona ni kam har na lara barci sai na ji waya, Nuwaira ta yi maza ta dauka wata kila ta san mijinta ne na ji tana cewa a kwance nake ina shiria yin barci, sha daya ne fa, yanzu, ta dan yi sauraro kafin na ga ta yi nurmushi sannan ta ce haba yaya Gali auren yan kwanaki kadan shi ne kewata zata dameka? Ta sake yin shiru sannan na ji tana cewa to a yi hakuri na daina cewa yayan, amma wannan sunan da kakeso in kiraka sai a gida don kar aj1 mu ace mun cika zumudi, kwanan yara uku ran nan da sassafe sai ga su baba babba Nafi'u ne ya kawo su shi ne ma ya shigo ya fita musu da yaran Suka gansu daga nan suka yi musu huduba shi Nafi'un ne kuma ya zabi sunayen da za a sanya musu Muktar da abokanshi sun yi hidima ta ban mamaki a Zaria aka rada sunan yaran Umar, Usman da Ummulkusum shima Muktar din ya halarci radin sunan da yamma kuma suka iso Abuja suka halarci hyafar cin abincin dare nima anan gida kawayena irinsu Asma'u Adam, Barira Inuwa dasu Hari da Nuwaira sun kayatar da mata da liya la a ranar sunan da yamma ina zaune a dakina da daddarce ranar sunan sai walkiya nake yi Joda ce lake tambayata ni sunan suwa aka sanyawa yaran nan? Na ce Umar sunan baba babbane Usman sunan baba Soba, Ummu Kulsum kuwa sunan Baba Sabuwa, mahailiyar Gali, Joda ta rike baki at ce kai amma Nafiu ya yi bikıma wajen zabar musu sunayen. Washe garin suna da yamma duk jama'ar da suka balarci suna sun koma gidajensu daga ni sai yaran sai goggo Uwale da Joda da Muktar ya roki ta zauna ta taimaka mana kula dayara sai Halima nurse dinsu sai su Barratu dama su yan gidane muna tare, Nuwaira kuwa da ta tsaya kints amin gida tana falon Muktar don Gali yana nan a gidan, na fito daga wanka na yi shafa na shirya tsaf, na dauko Suwaita na sanya saboda sanyin da ake yi na shiga kicin na duba aikin da ake yi na dibi dambun nama a plate na je falo wai in kai musu Gali da Nuwaira suna gefe daya ta shirya mishi salad yana ci, Muktar yana can gefe shi kadai ya zubawa talabijin ido yana kallon tashar Aljazira, nima kallonsu kawai na yi na wuce naje wunn Muktar na bi Idonshi da kallo don in ga abinda ya ja mishi hankali haka sojojina Amcrica ne a cikin tsaunukan kasar Aganistan wai suna farautar Usama Bin Ladin na firgita kwarai da ganin inn neman da suke mishi na ce anya ba zasu ganshi ba kuwa Muktar? Ya kallcni a hankali ya ce al'amarin ba na allah banc? Na yi hanzarin amsawa kwarai kuwa, na matsa kusa dashi na ajiye mishi dambun na,man ya soma ci yana kall kallona ai yanzu nake tunaninki a zuciyala na ce to ita mai jego bana ga in an yi suna tana firtowa ba' Amma shru ko kuwa don an samu yara sai Kuma a mance da wanda ya yi sanadin zuwansu? Na yi murmushi na ce kai babansu Abba kar su Gali su ji abinda kake fada ko da yake hankalinsu baya nan, Muktar ya ja tsaki ya ce ai ni Gali kunya yake bani ya karbi mata da kyar gashi ccikin sati biyu kawai ta kidimashi Gali ya juyo ya kallemu ya ya na ji kamar ana ambaton sunanmu? Muktar ya sha mur ya ce a'a me kuka yi da za a ambaci sunanku? Ya ci gaba da cin dambun namanshi Nuwaira je ki kicin ki debo miun dambun nama kin ji? Ta kalleshe tana murmushinta na hila yi hakuri yayana sai an jima ka ci sakwara da rana yanzu ka ci salad ina ganin a bar dambun naman sai an jima, ya ce to shi kenan ni da Muktar muka kalli juna muka yi dariya cikin sati shida yaran dukkansu tubarkallah, kowaya gansu sai ya ce kainononki yana da kyau Badi'atu, dubi yanda suka yi kiba, gashi kuma kin ce nonon kadai kike shayar dasu, in ce e, wata na biyu da haihuwa aka yiwa Brigedier General Kabir Isiyaku transfer daga nan Abacha Barrack zuwa barikin Dodon a Legos, abinda ya yi matukar tayar min da hankali saboda yanda muka shaku dashi ban wartsake daga kewarsu ba sai kuma umarni ya fito cewar Muktar Zubair yana cikin sojojin da zasu lafi kos na watanni takwas a kasar North Korea don koyon sabbin dabarun aikin soja, na kammala shirina da daddare bayan na je na baiwa yara nono na kuma shaidawa Halima kar ta nemeni cikin dare zan zo da kaina ta ce to na kammala feshe jikina da. turare na ja kofata na nufi wajen Mukta ina tunanin kwankwasa kofa zan yi ko me zan y1? Tunda yau ne ranar farko da zani dakinshi tunda na haihu ina murda kofar na jita a budeahankali na shiga na laluba gadonshi na hau don fitilar dakin a kashe take ya mika hannu ya jawoni jikinshi yana cewa uh na ji kamshun dana dade ban ji ba na yi kewarki Badi'atu, gadon nan ma da yana da baki daya ce ya yi kewarki ya kara cusa hancinshr cikn gashin kaina yana shakar kamshin ya.ce uhbh na godewa babaua da ya bani ke Baui aiu, gashi baki gaya min kina zuwa yau ba balle in shirya miki sauka arama bani in miki wacce ta samu ya sanya bakinshi a nawa muka shiga tsotson juna tsawon lokaci tsawon dare ran nan ni da Muktar a makale da juna muka don kuwa mu dukaninu niun ji kewar juna wajen karfe ukun dare ina kwance a jikinshi wadansu irin kalamai masu dadin ji da sauraro yake gaya min da ya yi sbiru sai na ce mishi Muktar ya kalleni a hankali ya sake jawo bakina ya tsota kalin ya ce min babansu Abba sunana Badi'atu na yi murmushi na ce to babansu Abba ya ce uhun ina jinki menene? Na ce so nake ka tafi dani Korea, ya yi shiru nuna alamar a tunani kafin ya ce ko meye dalili? Na dan yi ajiyar zuciya ce watannin sun yi yawa kuma ni ina jin isoro ya kara kankameni ya juyani daya geten gaya rnin gaskiya meye damuwar ki ban in ga idonki don in kara gasgata abinda zaki gaya min ya sa hannu ya kunna fitia haske ya bayyana na kare idona da dantsen hannuna saboda kallon da yake min ina suararonki na boye fuskata a jikinsbi kafin na iya cewa gaskiya ni Muklar na kishu, watanni takwas sun yi yawa na yanda zaka iya yi kai kadai ya yi murmushi ya ce Badi'atu kenan akwai abinda nake so mu sanya ya zamo shi ne jagoran zamannu, yarda da kumna amincewa juna, kin gane? Ni kam bankalina a kwance kwarai yake har abada na san da izinin Allah na san ba zaki ta ba bayar da kanki ga wani ba, ni ra so k Yarda cewar ni mutum nc wanda ban yiwa Allah alkawari in saba, Da ce na tauba bazan sake aikata zina ba, zan fi kowa farin cikin ace na tafi dake to amma yaya zan yiin tafi dake da jarnrai guda uku? Ya zuiba min ido yana kallona na kwanatr da kaina a kiriinshi dukkanmu shiru muka yi na wani lokaci kafin ya sake cewa ina ganio hakuri kawai zamu yi kamar yanzu ne zaki ga najc na dawo, na ce Allah ya dawo dakai laliya, ya ce amin, na tashr na dauki rigar barcina ina sanyawa ya kalleni ina zaki kuma? Na cc zan baiwa yara nono ya ce jirani in rakaki sai da ya shiga ya yi wanka ya iito sannan muka je, ni kam har kulium ina mamakin dabi' un Muktar babu yanda Za a yi komai sauri ka ga ya yarda ya li1ta dakinshi da datti. Bai damu ba a cikin dare ya yi wanka sau biyu ko ma fiye da bakan amma in dai zai ita, to zai yi wanka in ya so in ya dawo ua sake yin abinda zai sake sanyashi wankan sati uku da aka baiwa su Muktar na kanmmala shirye shirycnsucikin wadannan kwanakin babu abinda ban yi ba don ganin na faranta mishi rai ana saura kwana uku su tafi na yi mishi rakiya zuwa Zaria, falon baba babba muka fara sauka don shi akdaine a ciki har gabanshi Muktar ya je ya ajiye mishi Ummu ya yi sauri ya karbeta yana dariya wai wannan kiba da yaran ke yi inda mnulum daya ne yake shan nonon zai ganu kuwa? A Soba ma da muka jc abin gwanin dadi inna sai murmushi lake yi tana cewa Allah gwanin Badi'atu na ta zam maman 'yan uku, Muktar ya yi murmushi ye ce inna ba ia ta son a rinka kiranta da wanan sunam Ipna t nkehakinuna alarnar mamaka ta ce to akan me? Mata nawa kika gani da yan uku? Daga Soban bar Zaria kwana daya muka vi muka wuce Sakkwaio wur in da Gali yakc a yanzu muna shiga gidanni kam ban san sanda na kyaIkyale da danya ba wai Galine a kicin yana daure da (Apron) rngar da masu girke ke ratayawa a wuyansu don kare kayan jikinsu daga lalacewa ya dage sai kokarin tuka tuwo yake yi, ita kuwa gimbiyar na hangeta cikin falo kwance shame-shame kan doguwar kujera gabanta kuwa kayan ciye-ciyene iri-iri in ta mika hannu sai ta dauka ta sanya a baki tana daga kwance. Muktar ya iso yana rungume da su Abba a kirjinshi ya kulli Gali rike da muciya ya ce yallabai barka da aiki, Gali ya juya suka hada ido Muktar ya Ryalkyale da dariya, to meye abin dariyar in ji Gali, bani yaran ka shiga ka dauko mun tukunyar miyar, Muktar ya mika mishi su ya wuce zuwa falo yana cewa Allah ya sawwake ai ni rabona da ina taba tukunya na manta ba kuma zan taba ba yau don na zo gidanka a falo da kyar Nuwaira ta iya mikewa ta karbi Ummu tana cewa mamana Gali ya zauna yana rungume da yaran yana magana tun jIya Nuwaira take son cin tuwon masara miyar kuka Kande ta y mata jiya bai gamsar da ita ba, shi ne na ce bari ni in yi mata ko zai mata. Muktar ya ce ai sai ka kawo mata tun bai yi sanyi ba, Gali ya ajiye yaran kusa da Nuwaira ya nufi kicin ya kawo abinci a tire, ya ajiyewa Nuwara nata yazo gabanmu yana ajiyewa, Mukta ya girgiza kar nuna alamar a'a ya ce mu kam mun gode a yanzu a koshe muke a kira Kande kawaio ta yi mana girki. Gali ya galla mishi harara ba dai zaka ce bai yi dadi ba, malmala ne kawai bai yi kyau ba ni dai ina hira da Nuwaira ina kurna kokarin hana kaina dariyar fadan Gali da Muktar akan tuwonshi Nuwaira ta gama cin tuwon Gali ta yamutsa fuska tuwon ya yi dadi amma zuciyata tana tashi, cikin saun ya zo yana shaf amata kijinta wai zai kwantar mata da hankali ta wankeshi da amai, Muktar ya ce wai lalle ana renon ciki a gidan nan da kaina na tashi na tsaftace wurin shi kuwa Gali da Nuwaira suka nufi daki don tsaftace kansu kwana muka yi muna hira bayan mun kammala cin abincin dare wanda ni na yi mana washe gari kuwa muka taho gida kwana daya muka yi ne sake yiwa Muktar rakiya zuwa Legos inda zai kwana daya washe gari su tashi a gidan su Mami Hajiya Mariya muka yi hira kafin muka isa hotel dinmu da safe kuwa a kan idona jirginsu Muktar ya tashi zuwa kasar Korea ta Arewa na dawo gida zuciyata cike da begen Muktar sai dai ban yarda begen nashi ya hanani aiwatar da abinda ya zama wajibi a kaina ba a yanzu gidana a cike yake da jama'a gaya' yana uku rus ga masu tayani hidimarsu ga karatuna da yaek gab da karewa, wata biyu da tafiyar Muktar muka yi bikin Nati'u da 'yar wani commissioner na yan sanda daga Katsina State safiyah sanin da na yi idan Muktar yanabnan shi zai dauki nauyin shirya kayan auren ya sa na tsaya na shirya akwatuna guda hudu da kit na aike dasu zaria tun kafin ni in je a bikin muka hadu dasu Nuwaira cikinta har ya fara dan fitowa Uzairu ma ya kammala hidimar kasa har ya kama aiki a Benuc Cement Company ni da yaran dukanmu lafiya karatuna yana gab da karewa, ina shirye-shiryen zana jarrabawata ta karshe a jami'a don samun takardar shaidar digiri kan ilimin na'ura mai kwakwalwa wato 'computer ina zaune da Nafi'u a falona wanda tun tafiyar Muktar ya dauki matakin zuwa duba yara duk sati biyu hira muke yi yaran kuwa suna ta kokawarsu don su dukansu a yanzu tafiya suke yi Umar ya turmushe Ummu a kasa da sauri Nalfru ya tashi ya je ya dagashi yana cewa haba Malam ba a fa san babba da cin zali ba, na kamo Ummu zan bata nono don in rabata dasu kememe ta ki yarda Nafi'u ya yi murmushi ya ce da kin ajiyeta ta je cikin yan uwanta, na ce wahala suke bata duk wanda ya tashi cin zalinshi 1ta yake dannewa, amma ita bata son rabuwa dasu. Nafi'u ya yi dariya ya ce ai niAnti da akiban yaran nan da kin burgeni, wallahi na harareshi na ce wato ni ce ma zan baka su'? Ya yi murmushi ya ce a'a ai ni kece matsalata ayya Muktar ai ba zai hanani ya yanshi ba na ce haka kake gani? Ya ce kwarai sati biyu kafin in fara jarrabawata ta karshe a jami'a aka aiko min da labarin haihuwar Nuwaira a Sakkwato inda ta samu'ya mace, haka na tsallake dimbin karatun dakc gabana na nufi Sakkwato daga ni har ya'yana su Joda da hari muka tafi suna tuna ana saura kwana biyu suna, ina rungume da jarunyar wacce komai nata irin na uwarta ne, na kall Nuwaira na ce ke kam kin ji dadi kin samu mai kama da ke, amam ni dubu na haili ya' ya amma aka rasa wanda zai min kara ya biyoni duk sai suka bi Muklar, ta kyalkyale da dariya te ce to ai gara haka Muktar din bai fi ki kyau ba? Nace Ia ila ha illallahu, ban taba jin wanda ya yi min wannan zagin ba sai ke yau ta sake kyalkyale da dariya Gali ya shigo muka gaisa na kalleshi na ce rashin lafiya ka yi ne ko? Ya ce uh uh fargaba ne kawai ai mun ji jiki da cikin nan mun dai gode Allah an rabu lafiya, na yi darıya na ce to Allah ya kara rufa asiri, ya ce amin, gagarumar hidima Gali ya yi a sunan nan Kiris ya rage a sanyawa jaririyar sunan baba Sabuwa, sai ga aikenta kan wai a radawa yarinyar Fatima sunan mahaifiyar Nuwaira, hakan aka yi Suna da kwana biyu na shaidawa Gali gobe zamu koma ya ce to tunda ga jarrabawa a gabana in bar musu yaran su yi musu bakunta na ce ai ban yayesu ba, ya ce a yayesu anan goggo Uwale da Halima su zauna tare dasu ni da Joda da Hari mu koma gida in zai taho Zaria zai zo min dasu lokacin na kammala jarrabawata, na ce mishi to ina zaune a dakina kan dardumar dana idar da sallolin nafilar godiya ga Ubangii bisa kammaluwar jarrabawata tunanin mijina ya tsaya mun wata tara yau da tafiyarshi bayan an ce mun wata takwas zai yi na dai sarnu wayarshi gab da zai cika wata takwas din hakuri ya banu kan wai an yi musu karin kwanaki arba'in akan wata takwas din saboda wasu dalilai da ba zai yiwu ya gaya min a waya ba to gashi lokacin ya yi kome zai ce min yanzu kuma obo? Ranar Litinin da safe ina ta kaiwa da kawowaa gida kewace ta fi komai damuna ya'yana watansu biyu a Sakkwato ga Muktar shitu ga karatuna ya kare bani da abin yi in banda zama na koma aikin girkin gidan na hutar da Barratu amma hakan bai debe min kewar da nake eiki ba, na yiwa Uzainu waya ya je Sakkwato ya debo min yara ya ce in yi hakuri amma shi ba zai aya zuwa ya cewa yaya Gali wai ya bada yara ba, shma Nafi'u dana mishi maganar ya je ya debo min yaran murmushi ya yi ya co wai kyan wannan in je da kaina ni kaina na rasa yanda zan yi in je gidan gali don in debo ya' yan Muktar, ina kwance kan gadona ni kadai na lulluba da bargo barci ya ki daukata duk da matsanancin ruwan saman da ake zabgaa kamar da bakin kwarya ga walkiya da cida, na ji wayar dake dakin ta yi kara na mika bannu na dauka na ce wanene? Muryar Muktar na ji don Allah ki yi hakuri Badi'atu mutanen nan sun sake kara mana sati biyar da karfi na kurma mishi ihu wayyo Allah na ni badi atu na ga ta kaina, na saka mishi kuka ina cewa ni na gaji wataani takwas sun zo sun wuce da kyar an kara sati shida, surma na daurs sun cika har sun fara wucewa yanzu zaka sake kira uin sali biyar to ba zan iya ba in kai baka damu ba ni wahaia ta ishepi, dakata-dakata mana ki ji da kyar na iya yin shin haba maman'yan uku ke kina kuka yaran kuma ta? Na ce oho suma sun san kewar upansu ta dameni, to ke dai bude min kofa, cikin saurn na ce eye, ya ce btude min aana Badiatu ru wa la yana dukana, na tabbatar da gasken don in zolayala yakc bai yiwuwa ya san ana ruwa anan da gudu ni fita na bude kofar falonshi yana tsaye sai digar ruwa yake yi tsalle na yi na makaios1sbima ya kankameni ya sureni da gudu sai dakinshi dama kuwa kullum a cikin tsaftaceshi nake sai kamshi yake yi ba tare da mun cewa juna komai ba Muktar ya shiga tu6eni nima ina tubesti saboda tsananin matsuwa da juna da muka yi sai na ji tamkar ba mu taba mu'amala mai dadin na ran nan ba ina kwance a jikin Muktar yana maida numfashi a hankali ya ce ya'yana fa Badi'atu ina son ganinsu na kara kwanciya mishi sosai na bashi labarin haihuwar Nuwaira zuwanmu suna da yanda Gali ya ce abar mishi yaran har gayawa su Uzairu su dauko min yaran na yi sai dana gaya mishi ya yi murmushi ya ce da kin yi abin kunya Badi'atu kuma a tsiyar Gali dana sani ba zai bada su ba in ya ga dama kuma ya ki dawo dasu ni kuma kin san ba zani in ce aka wo su ba tsawon lokaci muna hira ina bashi labarin abidna ya faru bayanshi shima ya gaya min yanda ya yi koos dinshi da irin kewata da yara da ya yi gab da ruwa zai dauke muka Iito bayan mun yi wanka, ni na shiga kicin shi kuwa ya shiga amsa gaisuwar masu zuwa mishi sannu da zuwa kunun gyada na fara dama mishi na kai mishi ka lin in gana mishi abunci na koma kicin na shiryawa muklar kuskus da miyar taushe mai wadataccen naman saniya da tantakwashi sai kuma na shirya mishi york shire pudding da roast beel, ga abubuwan da na yi amlani dasu:- flour, kara, madarar ruwa, man gyada sai gishiri dan kadan shi kuwa roast beef din namnan cinyar saniya na yanka mai nauyin kilo daya na hudashi ta kusurwa biyu ya bullo ta kusurwa biyu na daureshi da irin jijiyar nan da aka samu a kings way ta yin gashin nama na dauko bluc band din dana riga na cakuda da garin maggi da kori da barkono da gishiri dan kadan na yi ta murzawa naman nan ina cusashi ta wacec käla na samu kusan minti goma aikin da nake yi kenan sai da naman nan ya nade blue band din nan tas na sanyashi cikin oben na daidaita mishi wuta na koma kan lour da na riga na kwaba na shiga suyan yorkshire pudding da mangyada yana fitowa bisa tsarin yankan dana mishi tamkar kwabo-kwabo sai da na kammala soyashi na je dakına na yi wanka na zauna na lailaye jikina na yiwa Muktar kwalliyar sannu da zuwa, sannan na dauki abincin dana shirya mishi na je na kai mishi yawancin mutane da Suka shigo sun tafi sai Major Amadu suna hira muka gaisa ya tayani murnar dawowar Muktar na ajiye abincin na koma kusa da Muktar na zuba mishi abincinshi a plate yana cin kuskus din ina aikin yankan naman nan ina nadewa cikin failan yorkshire pudding ya ture platdin kuskus ya shiga soke shi da cokali mal yaisu yana ci shima Major Amadu yana yin yanda ya ga ina yi yäna CA SAuna kuma hurarsu yawanci akan abinda ya shafi aikinsu na soja, ni kam ina jinsu ban kuma tsoma musu baki suna gab da gama cin abincin na ji Major Amadu ya cewa muktar anya yallabai mace gwanar girki zata yiwa mijinta laifi kuwa? Muktar yana taunar yorkshire a bakinshi ya yi murmushi ya ce kasan yau da gobe Major Amadu ya ce ammna za a yi saurin yafe mata don kuwa kauma tana faranta maka, a yanda kake da yaWan bakin nan in banda kana da wannan rulin asirin al da Tanka ya baci ya sake mumushi yace yallabai ai Wa tal lokaci na kap yi tunanin in banda a bariki kake da gidanka ya zama matattarar jama'a Muktar ya yi murmushi ya ce aine la dan fan a wurin iyayena maza guda uku kannena kadai Sun fi arba' in na zubawa Muktar ruwan matsattsen lemo na mika mishi ya karba ya mikawa Major Amadu na sake zuba wani na ajiye mishi na kwashi kwanukan na tafi na barsu suna ira, daren ran nan ko rintsawa ni da shi bamu yi ba washe gari da safe na kammala shirya mishi abin karyawa misalin tara da rabi na safe na je na yi wanka n ayı kwalliya cikin wata riga da Muktar ya riko nmin ita a yar karamar jakar da ya zo da ita a hannunshi rigar ta karbeni ba karamin kyau na yi ba, ga kamshi mai dadin ji dake tashi a jikina, ina cikin shirya kayan a falon Muktar kafin in je dakinshi in taso shi Daniel ya zo ya shaida min isowar baba babba da babanlungu na je na bude musu kofar falonshi suka shigo na zauna cikin ladabi na gaishesu baba ya min murnar Muktar ya dawo ban yi magana ba murmushi kawai na yi ya fita ne? Baba ya tambayeni na ce a'a yana dakinshi na shiga na tasoshi ya fito sanye da rigar barcin a kasa ya zauna yagaishesu, cikin ladabi baba ya ce sia kuma ka-kayi ya Muktar ya ce e, wallabi baba mun samu Fatimab, to yaushe 2aka ganinsu? Ya dan yi shuru kadan sai ya ce in banda su Abba suna can ai da gobe na je ganinta, Baba ya ce su Umar ai suna tare da babansu a London Gali ya tafi dasu da Uwale. Halima kuwa tana tare da maijego a Sakkwato ita da Hajiya Sabuwa bayan haka Murja ma ta haihu an samu da namiji ni da Muktar muka yi murna muka ce Allah ya raya baba ya cc amin Muktar ya ce to gobe in Allah ya yarda zan fito zan je Kaduna in ga iyalin Nafi'u daga nan in iso Zaria ganin sabon yaro sai in wuce Sakkwato wuria Nana Fatimah in ganta na koma wajna na barsu suna karyawa har sar da na kammala abincin rana na kai musu na samesu hira ta y musu dadi bayan sallar La'asar suka tafi. Washe gari misalin bakwai da rabi na safe na kammala mana shirye-shirye bar abincin da zamu ci a wunin ran nan na shirya mapa a manyan foodflast kwalliya sosai na yi na yafc jikina da lafaya irin ta bare-bari sai kuwa Muktar manyan kayane a jikinshi D Class Combatable one door Ita ce motar Muktar da zamu yi tafiyar a ciki kusan ma wannan ita ce tafiyar da za a yi da ita na farko don bai dade da saenta ba, ya tafi kasar North Korea da wuri kwarai muka isa Kaduna gidan Nafi'u tarbar da Nafi'u ya yi mana ba Karama ba' ce, a yau ne na kara gane kaunar dake tsakann Nafiu da Mukatar don kuwa saukar gimamawar da ya yi mishi tana da yawa, matar ce dai ban ga kamar ta iya karba baki ba, ko kuma don yau ne zuwana na farko tun bayan bikinta oho, ruwan tea kawai Muktar ya sha na kuma san don Nafi'u ya sha ni kuwa tunda na ga matar bata iya fara'a ba na ce a koshe nake. Awa biyu cif Muktar da Nafi'u suka yi suna ganawa ni kuwa muna falon amarya Safiyah muna zaman jugum-Jugum jilfa jifa dai na kan dan nermata da magana cikin zuciyata kuwa ina cewa uh uh uhum gida har gida maigidama haka sai dai matar gidan ne cikas, da zamu tafi kyautar sarkar diamond sigen wacce Muktar ya bani daren jtya ita ma ye bata akan hanyarmu la zuwa zaria muna hira na sako zancen yanayin gidan Nafiu dana gani tun kafin in gama gaya mishi ya shamur ya dan hararcni zaki koma gidansu da zamane? Na ce a'a ya ce to babu ruwanki da halin matarshi, kin girmeta a shckaru kin girmcta ta wajen ke matar wanshi ce doa haka ki kama girmanki, na coe to a Zaria kuwa sashin babanlungu muka tara sauka ganin majego da danta dukansu gwanin sha'awa dasu lafiyar kalau tubarkallah muna Zana har sai da muka yi sallar La'asar uku da rabi muka mika hanyar luntuwa kan hanyarta zuwa Gusau daga nan mu wuce Sakkwato a farkon taliyar kaset din 'Celine Dion cikin wakar A new day has come ne ya debe mana kewar zaman shiru saboda taliyar ta yi karfi da yawa, daga Rersbe kuwa na sanya mana Power of love shima dai Celine Dion Muktar ya kalleni cikin murmushi ya ce kc dai kina son matar nan na tayashi mummushin na ce a1 ni a wajena ita ce uwar mawaRa, ya sake mumushi ai ni ma kin koyan sonta a tafiyar nan da na yi duk lokacin da kewarki ta dameni man shalawarki nake daukowa dove 1n tsiyaya a haununa in ji karmshinshi sar in ji kamarjikinki nake sunsuna in kuma na saaya kaset din Celine 1Dion din sai ini kamar muna tare tunda ba kya rabo da jin wakokinta dadi ya kamani cikn uciyata na ce ashe dai Muktar ya yi ba duk da tsayuwa da muka yi a hanya har sau biyu a gidan galli muka yi sallar isha'i falon ya sha ado hotunansu Abba kowa nashi shi kadai sai kuma aka sake yi musu su ukun tarc Muktar yana rungume da yarinyar addu'o'iyake ta karantowa yana tola mata tsawon lokaci kafin ya dago ya kallemu ya ce Aah ya yi mata albarka na ce amin suka shiga gaisawa da Nuwaira suka shiga hira jimawa can na ce baka fa je ka gaida Baba Sabuwa ba, ya ce Nuwaira gaya mata zaan shigo mun gaisa shi a Nuwaira suka shiga ni kuwa Halima ta zo wajena.muna kara gaisawa da tambayarta labarin bayan saduwa sai da ta fita sannan na bi bayansu na samu Muktar yana cevwa ato Umma ai laifin mamun nasun ne da ta haifo na ce guda daya da biyu ne kinga da bata hadasu rigima, na ce to ai sai ta karo daya kafin badi su zama 'yan mata biyu Nuwaira ta galla mun harara akwati na uku shake da kayan jarirai ya kuwa yiwa Nuwaira na kyautar mota Honda Prelude sabuwa dal mai Rofa daya a Sakkwaton ma ya sayeta kwananmu biyu muka dawo Abuja, watanni biyu da dawowar Muktar ina dakinshi ina shirya mishi jakar da zai yi tafiya da ita shi kuwa yana kokarin karasa kwalliyar shi takalmi black mocasin ne a kafarshi farin wando chınnose poduct din D.K.N.Y ya sanya rigar T. shirt baka nike ya dora shirt akanta short sleave beach wear milk clour agogon hannunshi kuwa rolex sai daukar ido yake yi ya kammala ta je gashin kanshi ya ce ya ya dai Madam na cinye? na kalleshi na yi murmushi kafin in yi magana ne jero atishawa har sau biyar ya kalleni cikin tausayawa 'yar hamakillah, na amsa mishi. Ta hanyar rama mishi addu'ar da ya yi mun yace an ya Badi'atu wannan. murar taki banine sanadinta ba kuwa? Na kalleshi. kamar yaya? ya yi murmushi ya ce to naga taku karewa duk magungunan da kika sha ko a jikinta na yi kamar ban gane abinda yake nufi ba na ci gaba da kokarin rufe mishi jakar, kwanan Muktar hudu a Lagos kan wani aiki da aka turashi inda zai yi sati guda ni kadaice a falo sanda aka yi sanarwar shugaban kasa mai ci wanda yake soja ne mai mukamin General wanda kuma yake da matukar larin jini wurin talakawa don shirye-shiryen da ya gabatarwa na kawowa talaka sassauci zai gabatar da jawabi na mika hannu na dauki remot na kara maganar daidai an soma kada taken Nigeria ya soma jawabinne da gaisuwa ga yan Nigerna sai ya Ci gaba yana gaya mana halin da kasamu ke ciki matsayin tattalin arzikinta a jiyarta a bankin duniya abinda ake binta bashi da abinda ta biya tun hawanshi kan karagar mulki nasarori da kurakurai daya samu tun hawanshi ya kuma rokijama'ar Rasa da su kara hakuri da juriya don gwammanti ta samu ta ida manufofinta don samun cimma bukata cikin gaggawa majalisar koli ta soja tayi taro inda ta zartar da yin wasu canje-canja a jihohi an canzawawasu gwamnoni wuraren aiki yayin da aka nada wasu sabbi ya soma fadin wadanda aka yiwa canji yana kammalawa sai ya shiga fadin sabbin gwamnonin da aka nada "Col Muktar Zubair is the new military administrator of Adamawa State" Abidna na ji shugaban kasa ya fadi kenan kan in yı komai da gudu Joda ta fito daga dakinta inda take nata kallon Badi' atu na ji kamar shugaban kasa ya kra suna maigidannan me ya y1? Na ce an nada Muktar Joda ya zama gwamnan Adamawa, Joda ta kidime cikin farin ciki gida ya kaure da sowar murna da gudu Hari ta shigo ta rungumeni tana murna ta ko ina makobta sai shigowa suke yi na ce Hári ki lura dasu a raba musu lemo su sha akwai fivealive a sito, ta ce to ni kuma na amsa wayar dake ta kara, muryar Gali na juyo daga London Your Excellency Congratulations" na ce kai Gali ni ce ma your excellency din? Ya ce e, mana gashi kuma an kaishi jiharku ta Adamawa ina ganin ma da biyu aka yi hakan na yi dariya na ce na rasa dalilin da kullum kuke turawa mutanen Adamawa ni bari zage-zagi su ji ku tunda Adamawa dai garin kawunnai na ne Gali ya kyalkyale da dariya kafin yayi magana sai na ce to ga nauyi yana shirin hawa kanku ya ce e, wallahi na ce to Allah ya layaku rnko ya ce to amin amin ni ma gani nan zuwa yana Legos ko? Na ce e, ya ce toina jin zamu iso tare na ce Allah ya kawoku lafiya, ina ajiye wayar Gali sai ga su Nafi'u Congratulations Anti na ce kaima haka Nafi'u ya ce yanzu zani Zaria in yiwa su Baba murna gobe sai mu iso ABuja cikin kungiyar abokanshi da kuma mutanen Zaria da za su zo taryen maigirma gwamna na ce to Nali'u saikun zo, ina ajiye wannan sai ga wayar Asma'u Adam ihu take yi har na hangoki a Government House,.na ce ai sai ki yi na katse layın don ganin shigowar lambobin Wasila har cikin dare jama'a isowa suke yi ban samu sassauci ba sai da dare ya yi nisa na yi maza na yi alwala na yi nalila na gabatar da addu'ar godiya ga Ubangiji da ya ni' imta mijina da zama gwamnan Adamawa na kalli agogo dare ya riga ya yi nisa, ban samu wayar Muktar ba a yau na Kuma san jama'a ne don haka nima ban nemeshi ba washe pgari da asuba ina idar da sallah Zaria na yi waya don in yiwa iyayenmu murna Innasu Wasila ce ta dauka na gaishesta cikin girmamawa na ce inna kunKuma Muktar ya zama gwamna ce e, haka al'amarin Allah yake ta Ko ina in ya ga dama sai ya jarrabeka na tausaya muku kwarai ganin yadda ake cincirindon tayaku murna alhalin hatsarin da kuke shiin Shiga a yanzu ya fi hatsarin da ya fada sanda yake jeji mulki da kuke gani in ka samcshi ba abin ayi la tsalle ana murna bane shugaba a ranar alkiyama zai zo gaban Ubangiji ne a daure cikin sarkar wuta sai adalcinsa ne kawai zai iya kwanceshi ku yi kokari ku yi abinda aldalcinku zai kwaceku a wannan ranar in ba haka ba kuwa to kua ga ta kanku, ta katse layin ni kam ajiye wayar na yi na shiga kuka saboda taysayi, tun daga ran nan kuwa kullum na yi sallah ga addu;ar da nake yiwa mijina "Ubangiji kaine ka baiwa Muktar mulki shi bawankane mai tawali'u a gareka ka fini sanin tsakaninka dashi Allah domin kaine ka halicceshi na rokeka ka kara mishi jin tsoronka ka kara mishi karfin zuciya da jaruntakar tsayawa kan gaskiya ka kurna bashi mafita kan nauyin jama'a bayinka da ka dora mishi" wurin ran nansu Wasila da Asma'u Adam da Barira da Hari da su Nuwaira sune suka yi ta kula abincin da ake shiryawa don baRi masu zuwa mana murna da kuma Isowar mai girma gwamna, Muktar ya iso bayan La'asar cikin tawagar.Jama'a masu dimbin yawa da suka tareshi dakuma wadanda suka rakoshi daga can cikin masu rakoshin kuwa har da ya'yanshi guda uku da amininshi na kut da kut wanda ya zama danuwa a gareshi Gal AbdulWahab, ban samu ganin Muktar ba har na hakura na kwanta barci cikin barcinane kawai na ji kara waya na yi kokarin dauka na kei kunnena muryar Muktar na ji barci kike yi Badi'atu? Na ce, nauyin jama'a.yana shirin hawa kanmu kina irin wannan barcin Badi'atu? Ban zama abin tausayi a gareki ba? Bann taba sha'awar mulki ba, bana son shi saboda na san hatsarinshi tausayin Muktar ya kara kamani cikin sauri na ajiye wayar na ja mayafi na rufe jikina na nufi dakin Muktar yana zaune kan dardumar da ya idar da sallolin nafila yaran kuwa ya kwantar dasu kan gadonshi su dukansu barci suke yi durkusawa na yia gabanshi ya jawoni jikinshi ya kankameni Badi'at nafi sha'awar zamana soja kawai a maimakon a dora mun nauyin jama'a akaina na sassauta murya a hankali na ce Muktar godiya ga Ubangji ya kamata ka yi ba ka shiga damuwa ba yada sbugabanni ke saurin kai shugabannin da basu da adalci wuta hakannan yake saurin samarwa shugaban mai adalci matsayi mai girma a wurin Ubangiji samina da kai din jarumine mai gaskiya da rikon amana har kullum a cikin taimakon na kasa da kai kake aka da kishin kasarka a ganina shugabanci a wurinka alheri ne don kuwa zaka yi abinda in Allah ya yarda zaka samu mafita a gobe kiyama ya zuba mun ido yana kallona sai na ce da zaka bar abu guda daya Muktar ina ganin da baka da sauran matsala a hankali ya kalleni.menen shi Badi'atu? Na ce ka bar barasa Muktar ko da kake cewa baka sha ka bugu anya Muktar ana yiwa Allah hikima ne kan abinda ya ce kar a yi? A hankali ya ce na barta Badi'atu na daina shanta fitar mun da.kwalbar dake dakin nan kar su Abba su tashi su ganta, a fadar.shugaban kasa ina tare da Muktar lokacin da aka rantsar dashi a matsayin gwamnan Adamawa daganan kuwa bai dawo gida ba airport ya wuce tare da yan rakiyarshi mutum biyu ya hau jirg1 Zuwa Yola headkwatar Adamawa, nima na dawo gida na shiga shirun taliya Yoola kafin in tafin kuwa sia da na kaiwa iyayenmu ziyara Zaria soba da hunkurn wurin iyayen Nuwaira na isa Yola sati biyu da isar Muktar na.samu iyalina da suka rigani zuwa kalau dinsu sai dai Muktar yana cikin matsanancin aiki saboda yanda al'amura suka cabe ga dimbin bashin da ake bin jihar ga yajin aikin malaman makaranta da malaman unguwar zoma ga yan kwangila sunyi aiki ba abiyasu ba, farkon abinda Muktar ya yi sbi ne zabge kudaden da ake baiwa matar gwamna a matsayin kudin aiwatar da hidimar gida abina ya shali har gidajen manyan ma'aikata a jawabinsa na farko ga al'ummar jihar ya gaya musu halin da jigar ke ciki ya yi alkawarin yin aiki tukunu don ganin ya fitar da jihar daga halin da take ciki, sai ya nemi hadin kai a wurin sarakuna wadanda suke sune iyayen kasa da kuma sauran jama'a baki daya, a lokacin da Muktar yake cikin wannan aikini kama gida harkata bude mun kyaututtuka ta ko ina sai zuwa mun suke yi daga wurin jama'amasu kamun kafar abasu commisinoni wasu kuwa yan kwangilane dake son Muktar yana Zama sosai ya bada izinin biyansu kudadensu cikin kwana asbirin da zuwana Adamawa dukiyar dana tara ba kadan bace matsalar kawat bar yanzu ban samu zama da Muktar ba ballc in gayaa mishi mutanen la nake so ya baiwa commisinoni don wani tokacin kusan kwana a 0flice yake yi ran nan dai na jira dawowarshi wajen karfe daya da kwata na dare na shiga dakinshi cikin kwalliya sosai don ya san da gaske na zama matar gwamna sai a na fara mishi mita kan rashin ganinshi ni da yara da bama y ya bani1 hakuri ya ce shima abin ya fi karfinshi ne, na auna na bashi bayanin irin alherin da nake samu tun zuwana da sSunaye mulanen da nake so ya nada commisinoni tagumi ya yi dla hannu biyu ya ce ni Muktar naga ta kaina gani gareka Allah ka taimaken1 na kalleshi fuskata a daure na ce me Kuma ya samcka., ya mike tsaye ya nui can cikin dakinshi ba tare da ya ce min komai ba kusan miinti talain ina zaune anan wurin na mike na bishi dakin yana kwanc akan gadonshi ya yi rigingine yana kallon sama ya dora hannayenshi guda biyu kan cikinshi daya kan daya haushi ya kamani yanda har na shiga dakın bai motsa ba, na ce wani sabon wulakancinne kuma haka? Ka san kwanciya zaka yi ba zaka gaya min ba sai ka barni ina zaman jiranka? Na soma zazzago mishi tsiya yana kwance bai ce min komai ba har na gaji da magana na koma kuka da dai na ga ba zai yi magana ba na fita na nuti sashina ina tunanin zaman Muktar gwamna ya soma canza hali tunda gashi ya soma wulakantani kwana biyu da faruwar wannan al'amarin ina kallon talabijin tashar N.T.A. Yola naga sanarwa daga gidan gwamnati Muktar ya harantawa masu zuwa gidanshi yin hakan wadanda suke son ganinshi ko bashi shawara su yi hakan tahanyar samunshi a office daga.karshe aka ce yana fatan za a kiyaye don kiyaye bacin ran hukuma, ina zuane ina tunanin manufofin Muktar a kaina na kasa ganewa gani dai.da ilimi har na digiri amma yayi kememe ya ki yarda in zama shugaba a kungiyar mata kamar yadda sauran matan gwamnoni suke yi, tsawon lokaci muna zaman tsama ni ashi abinda bai taba faruwa ba tun bayan shiryawarmu shekaru uku har da watani ina kwance a dakina a lokacin nan cikina wata bakwai ne gashi dai an gaya min 'yan tagwaye zan sake haifa amma ban gayawa Muktar ba saboda ni dashi kowa harkar gabashi yake yi har na soma gundura da zamanshi gwamna tunda dai canza min hali zai yi na shiga tunanin kan karar Muktar wurin baba babba kanabubuwan da yake min sia gashi ya shigo Badi'atu yaya dai? Na kalleshi a lalace na ce kamar yaya kuwa? ya ce wai lafiyarki nake tambaya na ce kalau dina ya ce to Alhamdulillahi dama zuwa na yi in rokeki ki taimakeni ki tsaya ki ga su Halima sun kintsa akan lokacin don yau su Abba zasu koma Kaduna gidan nafi'u da zama za kuma su tafi tare a masu kula dasu Halima da goggo Uwalc, ban san lokacin da na mike daga kwanciyar danke yi ba, na ce amma tun ran nan da ka gaya min na ce ban yarda ba, ya kalleni cikin nuna alamar mamaki ya Ce ni fa bana ganeki Badi'atu wadannan yaran naki ne? Da zan gaya miki kanina ya roki in bashi su ki ce min baki yarda ba? Nac in ba nawa bane ai kuma ba amansu ka yi ba nina haifesu, ya ja min kofa ya fita na bi bayanshi zuwa dakinshi ban ganshi ba na konna wajen yaran na sameshi ya tarasu dukansu ukun akan cinyarshi yana gaya musu yau zaku konma gidan babanku Nafi'u ba sai na gaya muku yana sonku ba Kuma kun sani shi ne yake kaiku Legos ku je ku ga beach, shi ne ya Kaiku Daura kuka ga rijiyar kusurgu, shi ya kaiku Sakkwato wajen Nana Fatima da maminku Nuwaira, Ummu ta yi maza ta ce e, baba yama kaimu Zaria da Soba Muktar ya yi maza ya ce yawwa Ummu kema kin tuna ba. 1a ce e, su Umar da Usman suma suka yi ta Iisšafi abinda Suke rike dashi na alherin nafiu a garesu da suka yi shiru sai ya ce to zaku koma gidanshi ku zauna zaku yi karatu a can Adamawa ba garina bane Umar ya ce amma garinsu maman mune, Muktar ya dan sha mur garın mamanku bashi ne garinku ba babana ka jiko? Usman ya ce e, babamu Zaria ne garinmu Muktar ya ce very good, baba ya jawoshi jikinshi in kun je can akwai Anti Safiyah matar babankuce ku yi mata ladabi Ummu tace bata..shiii ya katseta ku yi abinda nace muku gaba daya suka amsa to baba ina Halima? Cikin sauri ta zo cikin ladabi ta ce gata ya ce maza ku j ku gama karfe goma direba za1 kaiku airport Nafiu zai tareku a Kaduna, ta cc to ta kama hanounsu da gudu suka tali tana zolayarsu don ta iya kula da yara, na kalieshi cikin bacin rai na ce wai kai kana nufin dolc sai ka bayar dasu nc? Ya ce ki yi hakuri kar ki biyoni gaban ya yana ki zageni yafita ga zatona dakınshi zashi in bishi can mu yi wacce zamu yi sai kawai naga yayi waje yana tita na ji a. tayar da jiniya alamar office dinshi zai tafi na dawo dakina na rasa abin yi sai kawai na jawo wayana buga zuwa Zaria don in gayawa Baba babba 1rin kama karyar da Muktar yake min sai na samu Antina sai dana gama gaya mata komai Sai na ji ta ce yaran da kuke rigima ke dashi akansu nakinc? Ko dasu kika je mishi gidan? Ke Badi'atu bana son rashin kunya da dibar albarka ya'yan larin kike yiwa tashin hankali? Haka kika ga iyayenmu sun sa ido akanmu? To kar ki ji dawai zan je Soba in gayawa Inna abinda kike yi na ce Anti ba haka bane ni zamansu da Safiyan ne ki duba ki gani fa manya ma in suka je gidan nan in dai ta ga zasu dade sai ki ga zaman bar yi dadi ba balle 'yan yara haushi ga kara kama Antina ta ce in su je gidan kaga zamansu ya isheta ta hura wula ta jefasu a ciki ina abinda ya dameki? Sakarya mara kunya in yaran nan basu iso Kaduna yau ba ni da kene da yau zani Soba na fasa Kaduna zani in ga zuwan yaran ta, katse layin na kwanta ina kuka Anti kullum a bayan su Muktar take share hawayena na yi nuka yi Sallama dasu suka tali, kwana bi1yu ina zazzabı na kuwa san bakin cikin rabani da 'ya'yana da aka yi ne, tun ranar dana biyo Muktar ya fita ba are dana samu na gaya mishi abinda zan gaya mishi ba ban sake ganinshi ba sai a talab1jin na ganshi wai yana rangadin jihar Adamawa don saduwa da jama'a ya gama rangadin da sati daya a labaran N. T.A. Yola na ji sunayen sabbin commissinoni da Muktar ya nada babu ko cdaya cikin sunayen dana bashi haka nan bai saka ko daya cikin dangina ba abinda nake ganin akalla ya saka kawunaina biyu na kara kulewa da Muktar bai dai ce mishi komaiba to ina na n aganshi balle in ce mishi? Muna nan ahaka har ran nan na wayi gari ina nakuda e lokacin nan kuwa wata shida ne da hawan Muktar gwamnan Adanawa ya shigo dakin kafin ya fita dama kuwa kullum haka yake yi ina kwana Badi'atu? na ce lafiya ba tare da na kalli inda yake ba, ba dai matsala ko? Na ce babu ya juya zai fita ya ce to ni na tafi office zani wurin kaza da kaza zan kaddamar da rijiyar burtsatse a wuri kaza da kaza na ce sai ka dawo bai yi minti talatin da tafiya ba na baifi'yan tagwayena macee da namiji, Joda da sauran mutancn dake gidan suka yi ta tsalle suna murna nan da nan tunda lafiyata kalau ni da yarana ga kuma kulawar likitoci muka yi Lsab da daddare Muktar ya shigo zai gaya min dawowarshi ya ganni da yan tagwayena a sanyaye ya matso Jikin gadon ya zauna ya sa hannu ya daukesu sai da ya tubesu ya gama kallonsu ya tofesu da addu'a sannan ya mayar musu da kayansu ya kwantar dasu ya kalleni cikin nutsuwa ya ce kin yi nakuda ba ki gaya min ba, kin haihu baki bari an sanar dani alherin da ya sameni ba, me na yi miki Badi'atu kike jin haushina? Na ji kamar ba dani yake maganar ba, ban dauka zamu sake irin wannan zaman na rashin fahimta ba, ni da ke na dauka abinda muka yi a baya ya wuce har abaa, sai gashi muna yin wanda ya fishi munı don giman Allah gaya min laifina a wurinki na ce kai zan tambaya tunda kaine ka fara canzawa ya ce ban canza komai ba Badi'atuu in kuma na canza gaya min na soma lissafi mishi tun daga ranar dana sameshi adalci da bayanin alherin da na samu da commisiononin da nake so a nada har kawio nadin da ya yi bai sa nawa ko daya ba ya kaileni ya ce tun farko sai da nace miki ba zan iya mulki ba kika ce zan iya sai gashi mun zo kina kokarin taimakon maso son ingizani cikin rami su yi galaba a kaina akan maganar yara kuwa ke baki fini son su ba baki fini son ama dasu ba amma yaya zan yi tuna Nafi'u yana son in bashi nkonsu ba zan iya cewa a'a ba ni a gianmu ban ga iyayenmu suna sa ido akan 'ya'yansu ba ni na san mahailina ne kawal la sunanshi da nake amsawa amma ba wai ta mu'amallar da da mahaifiba in ta wannan nc babana na sani kuma ke kanki Badi'atu in banda kara da kawaici irin na iyayenmu da baki zo gidanmuba, to kina nulin hakan a suke yi basu sonmu ne? Na girgiza kai nuna alamar a'a ya ce to me yasa ba zamu yi Koyi dasu ba? Ina laifin wanda ya tayaka son abinka? Na zobara baki na ce to ai baka min wannan bayanin ba a lokacin sai ka nuna wai kai kana da iko da ka zo nada commissinoni kuma ka ki nada min kawuna Yero, Muktar ya yi murmushi ya ce ikon dmanake dashi ya wuceki kirashi wai domin Allah ne ya baiwa uba karfin mallakar ya' ya su kawu Yero kuwa na yi musu abinda zan yi musu shi ne in basu hakkinsu na sun haifi'yarsu na aura, isowata jihar nan ban soma aiwatar da komai ba sai dana bisu duk yawansu na gaishesu na gaya musu zuwana na kuma rokesu su taimaka mana da addu'a ya sake wani mumushin ya ce kai Badi'atu ke dai har yanzu yarinya ce ko don ke yar autace ya sa kike yin haka oho? Na harareshi na ce ma autan yay1? Ya ce to a sanina dai ana cewa dan auta ya fi dan fari wayo maimakon ni in yi irin autarmu ta yan fari in debo kawunan naki in dorasu kan mukamai ke ki mun fada ki ce a'a Muktarkar ka yi haka abokan adawa zasu kulla maka sharri su ce ka debo dangin matarka kana nadasu a mukamai sai kuma wai kece kike so in yi hakan, abubuwan da kika yi min a zuwanmujihar nan sa'a kika ce na fanshi zuciyata saboda tausayinki da nake ji in banda haka.da na hadaki da malam lokacin da naje Soba, sai naga gaki da tsohon cikin in zo kuma ina yi miki sanadin 6acin rai shi yasa na kyalcki, na ce to ka yi hakuri babansu Abba yayi murmushin jin dadi don na dade ban kirashi da wanan sunan ba, ya ce yawwa to yanzu kika yi maganar sulhu amma kafin mu gama sasantawa zaki mayarwa mutanen da kika kar6i kyaututtukansu kudadensu tuna ni dai ban sanya kowa cikinsu a gwarunatin ba 'yan kwangila masu neman in biyasu kuwa na kafa kwamiti wanda zai yi bincike kan aikin da yan kwangila suka yi kowa ya yi da kyau za a biyashi kudinshi amma ba zai yiwu ka yi aikin banza ka zo ka ce in kwashi kudin talakawa in baka ba, na dan bata fuska na ce ai ni wadannan kudaden na gama kashesu ya ce a'a to ai kina da kadarori sai insa a sayar da wani abu naki a mayar musu da sanin halin Muktar da na yi ya sanyani yin murmushi na ce haba babansu Abba kayi hakuri ka biya min mana, ya ce to ki rubuto a lissafe in gani na ce to Muktar bai yarda an yi shagalin suna a Yola ba cewa ya yi a yi komai a gidansu sunayen yara kawai ya gaya min da safe. Zubair da Zara'u na ce Allah ya rayasu ya ce amin, shekara guda da hawan Muktar kujerar mulkin jihar Adamawa, jihar ta samu ci gabn da ya baiwa jama'a mamaki tsofaffi sai sa mishi albarka suke yi matasa Suna yabo, 'yan mata suna mishi waka, yan jaridu suka rinka kiranshi da gwamnan gwamnon a wannan lokacin ne kuma maigima shugaban kasa ya kawo ziyarar aiki jihar ta Adamawa, abubuwan daya ganarwa idonshi sun yi matukar kayatar dashi don kuwa a jawabinshi bayan ya kammala rangadin adamawa cikin kwanaki biyun da ya yi a jihar ya bayyana Muktar a jarumin soja gwaninki mai kamanta gaskiya da rikon amana, ni kam a wannan lokacin alfahari nake yi da mijina bisa yabon da ake yi msihi na godewa Allah da bai zamo mai son zuciya ba Muktar ya yi bikin cika shekaru biyu a jihar Adamawa da sati uku a lokacin nan kuwa ina goyon mai sunan Innarsu Wasila Nafisatu ina zaune ina shayar da ita nono tare da sauraron jawabin shugaban kasa sai kawai na ji wai an dauke Muktar daga jihar Adamawa an mayar dashi Bayelsa tare da karin girma a mukaminshi na soja daga zuwa Brigedier Muktar Zubair daga karshe kuma'ya yi alkawarin bayar da mulki ga gwamnatin farar hula nan da shekara daya da rabi don haka an cire takunkumin hana harkokin siyasa ni kamn dafe kaina na yi da hannu biyu na ce ALlah sarki Muktar ya gama shan wabalar Adamawa al'amura sun fara gyaruwa mishi za a daukeshi a kanshi cikin wata damuwar nan danan wayoyi suka yi ta shigowa ana taya mu murnar karin girman da Muktar.ya samu tare da yi mishi fatan alheri a jihar da zai koma. A wannan lokacin muna cikin shirin tafiya Bayelsa Nafi'u ya kawo yara taya babansu mnurna da yi mishi fatan alheri, dukkansu sun girma ba kadan ba, ga nutsuwa da hankali gasu in ka ji suna rera karatun Alkur'ani tamkar 'ya'yan Larabawa a bangaren karaun bokon ma baka ita kanta Halima ta Kara gogewa ta kara kyau ta yi mul mul gwanin sha'awa na raka yaran falon babansu shi da Nafi'u ne a ciki cikin tafiyar soja Usman ya isa gaban Muktar ya sara mishi tare da kamewa irin ta soja Muktar ya yi maza shima ya sara mishi ya kuma Jinjina mishr ya ce na yarda baba kai soja ne sannan ya jawoshi jikinshi ya zaunar, Umar ya mika mishi hannu suka yi musabaha ya ce baba ni Lawyer nake son zama ko dan sanda, Muktar ya kalleshi ya dan daure fuska kadan ya ce mamanka ce ta zabar maka wannan aikin ko? Don ita ce naga lana shaawar irinsu Umar ya yi dariya ya ce a'a baba ban gaya mata abinda nake son zama ba, ni ina son zama dan sanda don bana son masu laifi, zan kamasu baba da karfi Umar ya ce hatc criminals" Muktar ya kyalkyale da dariya ya rungume Umar yana shala kanshi da hannunshi ya ce na yarda da kai babana kai ba dan sandan rike kulki zaka zama ba dan sanda mai maganin masu laifi zaka zama ke fa Ummu itama ya jawota tun kafin in yi magana suka kwashe da dariya suna cewa wai teacher zata zama baba, Muktar ya kalleta yana murmushi ya ce ai duk tafi ku wayo in babu teacher ai ba za a samu soja ko dan sanda ba, ni da Nafi'u sai kallonsu muke yi muna dariya dai dai da dai dai suka taya Muktar murnar karin girma da ya samu suka yi mishi fatan alheri a Bayelsa ya sallamesu suka tafi sai ya kalli Naffu ya ce ba fa zai yiwu Halima tayi ta zama babu aure saboda yaran nan ba ka nemi mai kula maka dasu iyayenta suna son aurar daita, a hankalibNafi'u ya ce to su bani ita mana, ya ce haka ake yi don tana maka renon yara ka jJi za a yi aurenta sai ak ce abaka? Cikin ladabi Nafi'u ya ce wallabi ina son ta na kuma riga na shaida nmata ina ganin kuma ka amince ban yi maka maganar bane, saboda ina ganin kamar za a tashi auren nata ba, ya ce to sai ka samu su baba su yiwa iyayenta bayani, mun isa yenagua babban birnin Bayclsa ko kwana talatin bamu yi ba aka yi bikın Nafi'u da lIalima gidanta daban ya ajiycta ya kuma ncmi sabbin masu renon su Abba sati guda da gama bikin su Nali'u ina kallon labaran kasa sai kawai ga deputy controller costumc na kasa baki daya Alhaji Gali Abdulwahab yana mika takardunshi na ajiye ailki wai zai fsunduma cikin harkokin siyasa na ce naga ta kaina ni Badi'atu.me ya kar Gali kuma Siyasa? A kidime na yiwa Nuwaia waya ina tambayarta ina dalilin wannan aikin bayan Gali yana gab da kure mukaminsu zai ce ya ajiye aiki? Sai kawai na ji ta yi dariya wai alamar ita bata cikin damuwar da nake ciki ta ce ba zaki gane ba don ke yanzu kakin sojane kawai ba kya sanyawa amma tunaninki da halinki inin na Su ne, na ce to Allah ya rufa asiri ina babangida? Ta ce ya yi barci na ajiye wayar, nan da nan jama'ar kasa suka amsa kiran da shugaban kasa ya yi musu na su fito su kafa jam'iyyun siyasa, guguwar siyasa ta motsata ko ina sabbin kungiyoyi kakc ji wadanda ake fatan ayi musu rijistar su zama jam'iyyu watani uku bayan nan ayi rijiyar jam'iyyu guda hudu cikinsu akwai jam'iyyar talakawan kasa wacce Gali ya ke ciki yan kwanaki kadan da yin rijiyar jam'iyyu aka nuno Gali a Sakkwato wajen da suke yi convention dinsu wai ya lashe zaben zama shugaban jam'iyyar tasu a lokacin kuma Muktar yana wurin taron gwamnoni na buga waya Kaduna inda ayanzu Gali da iyalinshi suke da zama don in tayasu murna cikin hargowar jama'a take 'yan taya murnar Gali ya zama shugaban jam'iyyar talakawa na kasa baki daya sun ciki gida na sake yiwa Muktar waya na shaida mishi nasarar da Gali ya yi a Zaben zama shugaban jam'iyya yayi dariya ya ce yanzu na gama tayashi murna ya dawo gida da kwana biyu muka nufi Zaria tafiyarta gaggawace don amsa kiran baba babba ya yi muna zaunc a kasa a gabanbaba wanda ya zama tamkar a tabashi da tsinke jini ya tsirto saboda kyan jiki ya mulmule ya yi gwanin sha'awa furfurarshi sai sheki take yi Anti ta shigo tana rike da kwano ta ajiyc gabanshi ta budc mishi shake yake da farfesun kaji cikin zuciyata na ce watakila wurin baba Muktar ya koyi cin kaji sannu Shema'u Allah ya yi miki albarka, Anti ta yi murmushi ta ce mishi amin La fita baba ya soma magana Muklar kuwa ya Rkara sunkuyar da kanshi Rasa nuna ladabi da sauraro na kiraka ne Muktar don in damka maka kanncnka a hannunka ko da yake dama nauyin komai akanka yake na hidimar mu dukanmu amma umamin yi ko hanawa ko zariar da hukunci ni ke wannan to na mika maka daga yau ya koma kanka cikin ladabi Muktar ya lambayeshi baba wani abu yana mak ciwo ne? Baba babba ya yi murmushi ya cc lafiyata kalau Muktar to amma duk yadda na kai da lafiya da karli ai na san yamma la yi mun ranata ta doshi faduwa tunda Manzo S.A.W. ya gaya mana cewar shckarun al'ummarshi sittin ne ko saba'in kadan ne kwarai suke zarce hakan ta ni ina cikin 'yan kadan din da suka zarce don a yau ina da shekaru saba'in da biyar ne a duniya kai kuwa shekaran jiya ka yi arba'in da biyu, Muktar ya ce e, baba ni ma har na manta ban tuna ba sai dana dawo gida cikin darc na samu Badi'atu a zaune tana jirana na tambayeta abinda yahanata kwanciya, ta ce min jirana take yi ta tuna min na cika shekaru arba'in da biyu a duniya baba ya yi murmushi ya ce to ko sanda aka haifcka shckaru talatin da biyar nc dani shekaru goma sha udu kcnan da yin aurcna don ni ba Zubairu ne kanina mai bina ba akwai wasu su uku basu rayu bance tsawon lokaci baba yana bamu labari daya gama sai ya cc Badi'atu al'amarin kannenku zai kara komawa hannunku gaba daya sai ku kara hakuri akan wanda dama kuke dashi, Muktar ya ce baba ina ganim Anti tayi maka rakiya zuwa Jidda a duba lafiyarka daga nan sai ka yi ummara, baba ya yi murmushi ya ce to Muktar amma abinda nake so ka sani shi ne yanda duk ka kai da kula alafiyata hakan ba zai hana ajali zuwa ba, shckara daya na mulkin Muktar a Bayclsa ranar na wuni ina saduwa da kungiyoyin mata daga kabilu daban aban na jihar da suke zuwa tayani murnar nasarar mijina a shekara daya da ya yi akan mulkin jiharsu na fito daga dakin dana gama saduwa dasu na dawo falon Muktar don in ga bakon da aka sanar dani zuwanshi Uzairu na samu a zaune ya zama wani kato pashi ya ajiye kasumba kai in ka ganshi sai ka ce shi ne gaba da su Muktar din na ce haka ka zama Uzairu? Ai ka tsufa, ya yi dariya ya ce haba Anti zaki sa gabana ya ladi, na zauna muka gaisa na ce ka samu ganin maigirma gwamna kuwa? Ya cc mun gaisa sai dai ina ganin kamar yana fushi dani don bai wani amsa da kyau ba balle in yi mishi wata magana, na ce ato tsawon lokaci muna hira da Uzairu kafin Muktar ya shigo zai wuce dakinshi ne alamar zai kwanta Uzairu ya ce your excellency da ina son magana ne Muktar ya sha mur ya ce amma yanzu nina kiraka maganar da ta sani kiranka kawai zan gaya maka in ka samu lokaci ka dawo sai ka gaya min maganar aka zan sanya bikin su Zainab karshen watan nan in na je Zaria daga wurinmu uwa wunn babanlungu 'yan mata biyar za a aurar samarı uku zasu auro na ura yayen wadancan su sanya tasu ranar don mu daidaita namu lokacin duk masu yin auren nan ka girmesu shi ne nake so in ji abinda kake ciki, Uzairu ya dan sunkuyar da kai a hankali ya ce ina dan dubawa ne a hankali ban samu ba tukuna, Muktar ya cc to ka je ka samu Hindatu ku daidaita, wacce Hindatu? Uzairu ya tambaya na ce Hindatun baba Sabuwa ko? Ina kallon Muktar, Muktar ya kara daure fuskaya ce shima ya san ita nake nufi yana sha'awar yin wasa dani ne, Uzairu ya kara nutsuwa jin maganar Muktar cikin ladabi ya ce ba haka bane our excelleney ka yi hakuri ya dan saki rai ya ce in ka ganta kun daidaita sai ka je Kaduna ka samu Gali ku gayamishi ba kuma na ce ka je ka ganta bane don ka dawo ka ce min baku daidaita ba, ya wuce dakinshi na sallami Uzairu ya iso masaukinshi ni kuwa na dawo na shige gun mijina washegari da sale misalin goma muna karyawa da Uzairu ya ce min ina son ganin maigimma gwamna kafin ya je office na ce Muktar yanzu yana Abuja tun takwas da rabi ya bargarin nan akwai mitin din gwamnoni da shugaban kasa bisa shirye-shiryen ba yar da mulki da ake yi ya ce to amma Anti yarinyar nan bata mn Kankanta bakuwa? Tsananinta fa sha bakwai ko sha takwas, na harareshi na ce to a daura maka da Joda mana ko goggo Uwale ya yi murmushi ya ce zan tafi da Umminmu la yi mun hutu na ce Allah ya kiyaye dayake kaga ni da ake zuwa wa gwauro hutu na mike tsaye na suri gyalena dake ajiye kusa da jakata ian gyara lullubina ina gaya mishi in ka tafi ka gaida gida, mutune suna jirana zani ziyartar yara a asibitoci da gidajen marayu kasan yau ranar yara ce ta duninya, ashinn da bakwai ga watan biyar ya mike tsaye zai mun rakiya zuwa inda 1awagata take yana cewa Anti ba a taba bani kujerar Makka ba la, sa1 dai in ji ana ta rabo, na ce ba irinka yake baiwa ba Uzairu kai kana da hali baka ga damar zuwa banc, gaba daya yaran Muktar ya sanya ranar bikinsu 21/7/ wanda ya 2o daidai da ranar A sabar ni da Nuwaira mun kasance cikin shin mai yawa ni dai ta bangarcna banda kasancewar Muktar zai yi bikin kannenshi guda tara mata biyar maza hudu uku cikin yaran nan ya yan Antina ne da ta haifanwa baba babba wannan kuma shi ne lokaci na farko da Anti da baba zasu yi bikin 'ya'yansu na cikinsu duk hidimar bikin da suke yi a baya ya'yan 'yan uwanc sai yanzu ne zasu ga bikin Abdulwahab baban Anti da Zainab da Saliha wadanda suka zama kansu daya lamkar yan tagwayc don haka aka hada su shi baban Anti ina dai Innala ce ta hada na shi auren da yar kaninta na Yola kawu Yero bayan ya kammala karatunshi a makarantar koyon tukin jiragen sama dake Zaria, ila kuwa Zainab wani abokin Gali Dr. Manniru zata aura a gidan Galin ma ya ganta a Kaduna don haka zata Gali nc a matsayin mace ta biyu sai Saliha ita kam auren soyayyanc ita ta kawo mijinta don haka ina cikin matsanancin shiri ita kuwa Nuwaira 1ana zumudin innar zata aurar da yar autarta Hindatu, ni kam tun sati biyu kafin bikin zaman Bayelsa ya gagareni na koma zaryar Zaria, Soba, Yola da Kaduna a ranar daurin auren kuwa a gabansu baba babba Muktar ya daur auren 'yan mats shida don itama Dintadu babansu Gali Muktar ya baiwa waliccin aurenta don haka shi ya daura auren baba babba ya karbarwa Uzairu yana gama bayar da nashi kannen ya nufi Yola don karbarwa baban Anti auren Bintu yar kawuna Yero ya kuma wakilta Gali da Nafi'u suka je karbarwa sauran yaran maza guda biyu na dawo daga Kaduna inda aka yi budar kai Zainaba a gidan Dr. Mannir ina yiwa Antina bayanin abinda ya wakana Wasila ta leko tana cewa ina kirjin biki, na yi kamar ban ji a ba, sauran mutancn dake lalon Anti suka yi dariya Wasila ta shigo ana gaya min yaya Muktar ya yiwa Inna waya dazu ya ce ta gaya miki ki bar komai ki isa Bayelsa gobe don ki samu halariar bikin da matan kabilar wawan ke yi sbekara shekara wai sun roki ki zama musu babbar bakuwa a wurin, na ce irkashi to rakanı gidan su Luba in zaga su kafin in tafi goben. Ina Bayelsa na haifi mai sunan Antina Shema'u, duk da a Zana aka yi suna liyala sosai matan garin suka shirya don tayamu murnar karuwar da muak samu, siyasa ta kankama sosai har an fara gudanar da za6a66uka yau ma ranar zabece da wurio Muktar ya tasani a gaba muka je muka jefa kuri'ar mu a mazaba ta 4 dakc garın ycnagua, indá aka yi mana rijista mun dawo gida ni da shi muna zaune a falonshi na yi waya Kaduna don taya su Abba murnar cika shekaru bakwai bakwai a duniya Ummuce ta fara magan da alama tana cikin farin ciki salamu alaikum baba abinda ta fara fada kcnan, amin wa alaikum salam Muktar ya amsa barka Ummu da cikarku shckaru bakwai ta ce yawwa baba mun gode, amma bakwai da yawa kuwa baba? Cikin sauri Muktar ya ce da yawa kai Ummu daga daya fa aka faro har kun zo bakwai ai Kun kama hanyar girma, ta cc to kai shckarunka nawa? Yace ni yanzu ina da arba'in da uku watanni kadan ne babu ibu ta saka mishi arba'in da auku fa ka ce baba muka yi tayi kara alamar an fige wayar daga hannunta, ni ne. soja baba na saramaka baka ganni banc Muktar ya yi maza ya sara cikin murmushi ya ce nima na sara maka baba don na yi yanda ka bugi kasa da kafarka sai dai mc yasa ka kwace waya a hannun 'yar uwarka? ya cc ta cika surutu baba zata bata mun lokaci Muktar ya ce to kun cika shckara bakwai yau ko? Ya ce e, amma ni zance babanmu ya kara mun nawa tunda Nafisu karfi dukansu na iya kayar dasu na kuma fisu iya gudu da tsalle, ni kam dariya nake yi Muktar kuwa ko a jikinshi sai ya ce yi hakuri ku tafi tare kawai baba hakan bawai yana nufinka fisu shckaru banc sai dai alamune na kai din sojane rikici ya kaure tsakaninshi da Umar akan karbar wayar Muktar ya ce kai soja baiwa dan uwanka wayar nan shima mu yi magana, Umar yana karba ya ce baba shi karfi da tsalle ya fini ni kuma na fishi kokari a aji na wuceshi a karatun Alkur'ani ni na yi haddar izufi goma sha bakwai shi ya yi sha biyar wel done babana to ai dama kaine babbain ji Muktar kuma yau da sassafe da babanmu ya kaimu gidan baban Sakkwato mu gaya mishi shekarunmu bakwai ni ya baiwa kyautar mu da ya bamu na rike to ai kaine babban Muktar ya sake fadi yanzu an jima zamu ziyarci gidan marayu babanmu zai kaimu da yamma zamu yi gasar karatun Alkur'ani kuma ni zan cinye gobe kuma za mu je Zana da Soba shi kenan jibi zamu koma makaranta Muktar ya ce na gode muku dukanku Allah ya yi muku albarka suka amsa amin, ya katse layin ni kam a yanzu nafi kowa murnar zamansu Abbawurin Nafiu gaba daya lokacin shi na yaran ne ga cikakkiyar tarbiyar da yake basu, sakamakon zabe ya fito jan'iyyarsu Gali batayi nasara ba sai dai sun samu gwamnoni goma sha biyu daga cikin talatin da shida jam'iyyar da ta yi nasarar tana a gwamnoni sha biyar nc sauran jam'iyyu biyun suka sauran gwamnonin a tsakaninsu talakawa Sun zabi wani raba, shugabane da ya yi alkawarin larlado da taltalin arzikin kasa, darajar naira la bunkasa ya wadata asibitoci da magunguna, kyauta ya magance matsalar dauke wutar lantarki ya bayar da ruwan sha mai tsafta kai alkawura dai masu dadin to Allah ya yi mun nikawa farar hula mulki mun dawo barikin soja da zama Muktar ya zama Bnigodicr Gencral ko wata shida bamu yi ba a Rukuba Barrack dake Jos aka turashi Bakassi cikin sojojin da aka dora musu nauyin lura da yanda za a mika wurin ga Cameroun, yana can bai dawo ba wani umarnin ya sakc fitowa cewar ya nuli kasar Indiya don yin kos na watanni shida kan aikinshi dai na soja, yana dawowa ya zama shugaban rundunar ta 4 ta askarawan Nigeria dake Bauchi mun sbekara a Bauchi aka cc ya nufi jaji ya zama shugaban makarantar borar da hafsoshin soja dake can muna jaji shekararmu daya da wata biyu a lokacin ina goton Muhd Gali, Muktar ya zama Major Gencral a duk lokacin a mukc cikin wadannan ayyuka da canjc-canjc Gali yana can yana fafatawa cikin harkokin siyasa, kasa tana ncma ta rikice al'amura sun cabe komai ya ta barbare Gali kullum yana cikin babatu a gidajcn jaridu da talabijin kullum cikin kushe yanda gwamnati take tafiyar da al'amuran kasa yake, tun jama'a suna ganin adawa ce tasa Gali iin wadannan maganganun har dai aka gano gaskiya yake fadi, gwamnati sai almubazzaranci da dukiyar kasa take yi cin hanci da rashawa ya yi katutu an kasa biyan ma'aikata hakkinsu, masu fansho kuwa tuni suka shiga halin ha'ula'i farashin man fetur sai tangal-tangal yake yi wai an bar yan kasuwa su yi yanda suka ga dama, gwamnati ta cire tallafin da take yiwa man, tuni talakawan kasa suka soma fadin sun ga ta kansu. Ran nan Muktar ya dawo daga kasar Germany tafiyar shi ce ta kashin kanshi ya yi ind aya tafi da Ummi Nafisatu da Nana Fatima suka yi mishi rakiya ya dawo da sati biyu ina gida na amsa wayarshi daga office shirya maza Badi'atu gani nan zuwa zaki rakani Zaria yanzu sa ce lafiya ya ce lafiya mun isa Zaria kusan sallar La'asar ne yana cikin falonshi can muka sameshi ni dia Muktar mun nutsu sosai don oima maganar da Muktar din ke yi ta kashe min jiki kwarai baba babba ya gyara rikon da ya yiwa baban yara ko Gali ya ce amma a matsayinka na yanzu ka bar aikin soja Muktar? Ai na dauka zaka bari ka kai matsayin General tunda kana gab da kaiwa Muktar ya kara sunkuyar da kai ya ce burina kenan amma abinda nakc hange ya sanyani bakura da hakan in dai ba kainc ka ce baka amince da barin aikin nawa ba, don na shiga wani hali na canka-cakare, ko da Muktar bai furta ba daga ni har baba mun fabimci akwai wani abind aya hango nan da nan baba ya amince da barin sojan Muktar ya shiga yi mishi fatan alheri wata hudu kaca idan wannan maganar sai ganmu a sabon gidanmu na Kaduna Muktar ya zama ritaya Major General yan uwa da abokan arziki sai zuwa mana murna ake yi Muktar ya fita aikin soja lafiya, nan da nan ya shiga shirye-shiryen abinda zai yi cikin kankanin lokaci ya bude kamfanin sufurin jiragen sama mai suna ZU U MA AIRLINE, ina tare da Muktar a ranar da aka kaddamar da jiragen muna barin wajen Zaria muka nufa don shaidawa baba babba jirgin ZU'UMAN ya tashi na shiga dakin Antina ina mata sallama zamu tafi, anti ta kalleni ta ce ke dai kullurm daga ciki sai goyo wahalar nakuda bata damunka nayi murmushi na ce Ant.i kowa da irin zuwanshi da kuma arzikinshi ni kuma kin ga wannan din London Muktar ya ce zani awonshi ta ce ai sai ku yi ta yi na yi dariya kawai na tafi muna kwance cikin dare ni da Muktar wasanninmu muke yi na farantawa juna rai rabon damu mallakawa juna kanmu irin na yanzu tun kafin Muktar ya zama gwamnan Adamawaa a yanzu ni dashi mun zama tamkar amare ko ina zashi ni ce 'yar rakiyarshi in kuwa kwanciya zai yi zai ce bar abinda kike yi ki zo ki mun tausa, in ce to, karar waya ce ta damemu Muktar ya mika hannu ya dauka, hello na ga alamar fuskarshi ta canza, na ji yana cewa yanzu? Wanc asibitin zaku kaishi? Ganinan 2uwa yanzu, da sauri Muktar ya dira daga gadon ya shiga bandaki wanka mai sauri ya yi ya fito yana sanya kayanshi yana bani amsar tambayar dana yi mishi babana bashi da iafiya Badi'atu, abinda babanlungu ya gaya min kenan wai yana ciwon habo, na ce irinshi ya taba yi Muktar sanda baka nan kana dajin nan biyo Muktar na yi ina mishi wannan bayanin don tuni har ya shige motarshi yana kokarin fita daga gidan ba zan iya jiranki ba da safe kawai ki zo na ce to Allah sawwake na dawo dakinshi na kwanta barcin da na yin ba mai dadi bane daga idar da salla ta na shirya cikin motata na nufi Zaria daga ni sai Gali karami mu biyu ina isa kofar gidanmu na ga motoci sai isowa suke yi na kauce don in yi parking gefe daya sai kawai naga Muktar kanshi babu hula kafarfshi babu takalmi shi da wasu mutane suna kokarin fito da makara daga ciki Tukuna A ranar kaddamar da littafin a jihar bayelsa Wanda yayi daidai da ranar da mukhtar ke cika shekaru hamsin cif a duniya zan iya cewa gaba d'aya Nigeria ta taru a bayelsa, shugaban kasa da mataimakinsa suna can ministoci gwamnoni da sarakuna da duk wani mai fad'a aji ya zo uzairu na zab'a chief launcher don shi ke shagabancin zuuma airline, Alhaji Gali Abdulwahab uban taro, mai masaukin bak'i gwamnan bayelsa, Ina zaune cikin hijabi da bak'in madubi kusa da mijina masu jawabi suna ta yi, yabona suke yi suna fadin namijin kokarin da nayi wajen kammala tarihin da nayi da aka gama jawabai sai aka shiga lunching, Ni kam da naji abinda uzairu ya bayar rike baki nayi, jama'a suka yi ta fadin abinda suka bayar, jihar adamawa ce take fadin yawan littafin da ta saya akan miliyoyin nairori a lokacin da mukhtar ya juyo yana tambaya ta ranki ya dade wadanannan miliyoyin da ake Tara Miki me zaki yi dasu? Ko zaki ajiyesu ne ki yi ta shirya min gara Ina Sha , in yi ta cin Bean And meat casserole? Nayi murmushi nace your Excellency zaka Sha gara ne inka in ka warware bakin aljihunka, wadanannan makudan kudaden da kake magana a kansu zasu tafi ne wajen aiwatar da shirina na taimakon yara qanana masu fama da ciwon zuciya, samar musu magani kyauta da Kuma daukar nauyinsu zuwa kasashen waje in har hakan zai Zama shine hanyar warkewarsu. Mukhtar ya kama hannuna ya rike da karfi ya ce Badi'atu, a lokacin da Babana ya bani ke biyayya da gudun bacin Rai ne yasa na karbeki a yau Ina alfahari da kasancewata d'a mai biyayya ga iyaye don Kuma hakan ya sani na samu abunda nayi ta roko tun Ina d'an k'arami shi ne ubangiji ya azurtani samun mace ta kirki. Shekaru hudun mulkin mukhtar sun kusa cika jama'ar k'asa sai Kira suke yi mukhtar ya sake fitowa su zabeshi ya ci gaba da mulkinsa saboda a zamaninsa kasa ta yalwata zaman lfy ya tabbata jama'ar k'asa sun samu kwanciyar hankali an raba su day talauci da wahala an rabasu da ambaton kalmar *NAGA TA KAINA!* sai anjima Taku Hafsat sodangi Sai mun sake haduwa a wani littafin. Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels