Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels Gubar Rayuwata By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) _____________________________________ Wannan Labarin kagagge ne da babu duban yadda wani yake rayuwarshi aka tsara shi, amma wanda yaji kamar dashi ake to ba nayi dan tozartashiba, kuma ni bansan dashi ba. Page 1 & 2 Cikin wata babbar makaranta ce ta kud'i da ke cike da kayan wasanni na yara kala-kala , wannan makarantar ba kowacce makaranta ba ce face . DR DD SECONDARY SCHOOL. Uncle Yahaya ne zaune a cikin staff na malamai yana making d'in wasu littattafan d'alubai. Wayarshi ce ta fara ringin , kawai yana kallon wayar ya ga Harun ne ke kira murmushi ya yi yana cewa, "Zaka dame ni Harun." Har kiran ya yanke Uncle Yahaya bai d'auki kiran ba . A karo na biyu dai Harun ya sake kiran wayar uncle Yahaya ya 'ki dauka , Harun bai sake kira ba. Hakan yaba Uncle Yahaya damar cigaba da aikinsa. Anan cikin wani babban gida kuwa , Zainab da Ahmad ne zaune cikin falo , Zainab ce ta kalli Yayannata Ahmad tana cewa, "Yaya Ahmad! Abokinka Harun ya zo nemanka." Da sauri Ahmad ya kalleta yana cewa, "Da gaske , ai na yi zaton ya mance dani zasu zana jarabawar sojoji." Zainab cikin zumud'i ta kalleshi tana cewa, "Da gaske , to dan Allah yayana ka gayyato mana shi cin abinci, wallahi yana da kirki sosai." Wani zumm Ahmad yaji a ransa , ya kalleta ya yi murmushi yana cewa, "Zancen ki ya yi tsari kuma zan gayyatoshi." Zainab tai godiya , a jiyar zuciya Ahmad ya sauke yana satar kallonta gumi ya had'u masa , ga dukkan alamu Ahmad ba ya san zuwan Harun cikin gidansu. Iyalan Alaji Kabiru ke nan , babban mutum d'an kasuwa da ya san ya kamata . Anan cikin gidan Alaji Idris kuma abin har yafi na can , domin gida ne babba da babu makosa a jikinsa , yaran Alaji Kabiru guda uku ne , Kalisa , Jafar sai Nabila , sai matarsa Hajjiya Maryam . Alaji Idris yana kaunar yaransa matukar gaya , duk yadda zai don si farin ciki yana musu, hakan ya sa su ma yaran suke kaunar iyayensu. Zaune take cikin doguwar riga mai launin d'awisu tana waya cikin farin ciki , da wanda take kauna wato Umar, kai da ka ganta zakasan matukar farin ciki yake sata , musamman taji labarin zai zana jarabawar sojoji , Alaji Idris ne ya shigo d'akin , tai saurin sauke wayar kasa tana kallon mahaifinnasu , Alaji Idris ya samu guri ya zauna kusa da ita yana kokarin fara magana, ganin haka yasa Kalisa saurin kara wayar a kunnenta tana cewa da Umar zasi magana . Fuskantan mahaifinta ta yi sosai Kalisa cikin girmamawa Alajin ya kalleta yana cewa, "Wato Kalisa a kullum wannan rayuwar gudu take mana , bani da burin da ya wuce naga walwala a tare daku , a dan haka naga lokaci ya yi da zan samar miki da abokin rayuwa , wanda ko bayan bama nan za ki alfahari da shi ." Da sauri Kalisa ta d'aga kai tana kallon mahaifinta hakan yasa Alji Idris cewa , "Karki damu ba shi da wani aibu." Ya karasa maganar yana tashi , da hanzari Kalisa ta riko hannusa tana cewa, "waye shi dady." Alaji Kabiru ya yi murmushi yana shafa kanta yana cewa, "Zai zo Kalisa." Ya fita waje , ajiyar zuciya ta sauke tana binsa da kallo . Harun ne a kan hanyarsa ta zuwa gidansu Ahmad , yana tafe cikin ransa yana tunani a zuciyarsa , "Kai yau kuma koda wacce macen zan kwana oho, ni wallahi matan ne ma duk ba tsafta garesu ba , kai gaskiya mata sun yi arayuwa , dubi dai ta ranar juma'ar nan yarinyar nan ta susuta ni ta sumar dani, Haba malam yanzu nasan ina rayuwa, amma dah na fashe a Tiga Dam ba inda nake zuwa." Sauri ya yi ya matsa sakamakon wani mai keke zai cusa masa taya , hakan yasa ya yi tsaki yana ," idan da wannan banzan ya gyaran mota ta ai bazan taho a kafa ba ." Yaja tsaki yana kokarin tsai da abin hawa . Anan kuma Zainab ta matsu da isowar Harun , sakamakon ta yi masa girki kala-kala aiko tana zaune a falo sai ga Harun ya shigo da sallama yayin da Ahmad a lokacin ya fito daga d'akinsa . Mutuwar tsaye Harun ya yi yana kallon Zainab cikin mamaki, a cikin ransa yace , "Wow kyakykyawar yarinya kuma karshe." Ahmad ne ya katse sa yana cewa, "Karaso mana Harun." Harun ya yi murmushi yana kallonsu tare da karasowa cikin falon "To Zainab ga Harun yazo." Ahmad ya fad'a yana kallon Harun da murmushi Zainab cikin wata siririyar ta kalli Harun tana cewa, "Sannu da zuwa yayana, ya hanyar fatan kazo lafiya." Murmushi ya sake yi yana jin dad'in maganarta yace ,"Nazo lafiya Zainab, fatan kin mini girki mai dad'i domin ni indai akwai abinci to ba matsala." Dariya tasa tana nuna teburin cin abinci tana cewa, "Na yi ma girki mai dad'i sosai." Ta mai jagora zuwa teburin yayin dashi Ahmad har ya ruga da ya zauna a wajen yana danna ayarsa . Harun yana isa wajen ya saki murya yana cewa, "Gaskiya wannan abinci ya yi kyau sosai, amma bai kai wacce ta had'a shi ba ko kad'an." Ahmad ne ya yi sauri ya kallesa yana cewa, "Hmmm." Ya ci gaba da danna wayarsa yayin da Zainab ta kuma murmushi bayan ya zauna ta fara zuba musu abincin , tana zubawa Harun ya satar kallonta yana kallon duk kan jikinta yana girgiza kai , shi Ahmad sam baisan abin dake faruwa ba, bayan ta gama tace dasu bismillah , aiko duk suka maida hankali kan abincin , wanda lokacin ne Alji Kabiru da Hajjiya suka shigo falon. Anan cikin DR DD kuwa uncle Yahaya ne cikin staff room shi da wata d'aluba mai suna Laila , Uncle Yahaya ya kalli Laila cikin soyayya yana cewa, "Me yasa jiya ina kiranki ki tsaya mu tafi gida ba ki tsaya ba."? Laila ta d'ago fararan idanunta tana kallon Uncle d'insu tana cewa, " ba komai." Ya yi murmushi yana cewa, "Tom ni dai gaskiya kalaman soyayya nake so ki mini." Zaro idanunta ta yi tana kallonsa ,"Uncle ni ban iya kalaman soyayya ba gaskiya. " Ta fad'a cikin shagwa'ba Murmushi ya yi tare da jin dad'in yanayin yana cewa, "To gaskiya kije koya ina so , ki ringa rubuto mini a takarda ina karantawa ina jin dad'i." Laila tace ,"To." Yace" za ki iya tafiya lailata". Laila ta mike ta fita tana tunanin ta ina ma zata farayiwa Uncle Yahaya kalaman soyayya saiga wata d'aluba 'kawar Laila tazo tasha gabanta tana cewa, "Ta Uncle har an gama love d'in ." Murmushi Laila ta yi tana cewa, "Wai kalaman soyayya yake so, kuma ni ban iya ba Khadija ki taimakan ." Khadija taja da ba ya tana cewa ,"To nima wallahi ban iya ba Laila yanzu ya zami to." Laila idanunta sun ciko da ruwa ta kalli Khadija tana cewa, "Wallahi ina son Uncle zan iya mutuwa zuciyata ta buga a kan shi ." Kawai Khadija ta jefa mata wata harara . Wayar Uncle Yahaya ce ta fara ringin , Harun ne dai ya d'auki kiran "Kai shegen duniya har yau zuwa legos d'in bai zo ba ne ." Harun ya tambayi Uncle Yahaya, Uncle Yahaya yaja doguwar a jiyar zuciya yana cewa, "To ina ruwanka ko ance ma ni neman mata zani , biki ne fa ." Harun ya kwashe da dariya yana cewa, "Wallahi mutumina ba da ban ina aiki ba , nima binka zan kawai naje na shanawata da manyan mata. To ya Tiga ya mutanen garin." Uncle Yahaya dai mazaunin garin Tiga dam ne , ba shi da kowa sai kakarshi tsuhuwa ce da yake kira da kaka , yana koyarwa cikin private school ta DR DD haka kuma yana soyayya da wata yarinya Laila mai kimanin aji 5 na babbar secondary, Laila Adam mahaifinta lauya ne babba , ita kawai Allah ya ba shi a matsayin 'yarsa hakan yasa yake matukar sonta. A bangaren Harun kuma iyayensa suna a Tiga , shi kuma ya shiga cikin kano yana rayuwarshi a can yana d'an guba gubarsa ta neman kudi , kuma yana cin mutuncin mata da su . Duk sun hallara a teburin cin abinci amma banda Kalisa. Alaji Idris ne ya kalli a gogon hannunsa yana cewa , "Har 8:05 ina Kalisa ne." cike da shagwaba ta fito tana jan jiki ta zauna kan kujera tana cewa, "Ni wallahi dady na gaji da abincin gida." Alaji Idris cikin rarrashi yace ,"To me kike so ayi yanzu." "Kawai mu tafi restaurant dady." Jafar ya fad'a Alaji ya kalli autarsa Nabila yana cewa, "Wai haka my baby." Nabila tace, "Eh." Hajjiya ta had'e rai tana cewa, "Haba Alaji ya ku ke son nayi da wannan abincin kuma , wallahi ka dena yiwa yarannan haka , sanda babu kai ya kake so su yi." Alaji Idris ya kalli Hajjiya yana cewa, "Dakata Hajjiya! Kema in kina so kawai ki taso mu tafi , kuma da kike maganar idan ba nanan to ba mutuwa zan ba ni na barsu." Alaji ya kallesu yana cewa, "Kai kona mutu ku d'ebi kud'i ku yi duk abin da kuke so, idan ban yi muku ba wa ku ke dashi." Ba tare da Hajjiya taso ba suka tafi suka ci duk abin da suke so , domin saida Alaji ya kashe kud'i ki manin dubu talatin sannan suka dawo gida. A halin yanzu Harun ya rasa ta yadda zai gabatarwa da Zainab cewa yana sonta ,Harun ba karamin d'an iska bane , aiko duk yadda zai ya samu Zainab nasan zai aikata. Wajejen yammaci yana kofar gidansu budurwarsa Rufaida suna cikin mota suna hira , wani langwa'be mata ya yi yana cewa, "Please Rufaida kizo muje gidana mu huta ." Wani fad'uwar gaba taji a ranta , ta kalleshi tana cewa, "Ni fa babu inda zani , yanzu zaka ga an aiko ma na koma gida ". " To har kafin a aiko ma munje mun dawo rakani za ki fa." Ya karasa maganar kamar zai had'e jikinsa da nata, Murmushin ya'ke ta yi tana cewa, "A'a gaskiya baby." Had'e rai ya yi sosai yana cewa, "To Gaskiya na yi fishi." Rufaida tace, "Yi hakuri to ka fad'i wani abin da zanma sai ka hakura." Cikin fushin Harun ya kalleta yana cewa, "Abu daya za ki mini ." Ta sake fuskantarsa tana cewa, "ina ji." Yace ,"To rufe idanunki." Rufaida ta rufe idanunta tana murmushi, ba zato ba tsammani kawai taji Harun ya cafki bakinta yana tsotsa Furgita tayi tana ture shi tare da saurin fita daga motar shima sauri ya yi ya fito yana cewa, "Haba mene hakan kuma." Ta kaici ya hana Rufaida cewa komai kawai yawu take tofarwa tana share bakinta "Ai ni dama na dad'e da sanin ba sona kake ba kawai kanason lalata dani ne Harun." Ta sake tofar da yawu tana cewa, "To wallahi indai ni ce daga sama na har kasana haramun ne a gare ka, kwarton banza mahaukaci , malalaci kawai ." Ta tofa masa sauran yawun dake bakinta tai shigewarta gida . Share yawun ya yi yana cewa ,"Na kwafsa na yi gaggawa ,amma shi ke nan." Ya shige motarsa ya tafi . Ma daidaici ne mai fad'in jiki wasu sa iya kiransa da kyakykyawa, yana zaune cikin falon Alaji Idris, yana kallon yadda wannan gidan ya burgesa , bayan su gaisa da dukkan mutanen gidan ne , sai suka tashi suka bashi guri shi da Kalisa. kallon Kalisa ya yi ya kuma yana kwarai da gaske kyakykyawa ce , "Kamar yadda dai kika sani suna na Sahid , sannan ina aiki ko ince ni ne manager company na Alaji Tasi'u mai turare." Kalisa da zancen Sahid ya isheta ta bukaci komawa cikin gida , aiko hakan yasa Sahid komawa gidansu. SAHID Sahid dai d'an abokin Alji Idris, kuma Amininsa wato malam Aminu , a kwai matukar Amana a tsakaninsu , kuma Alaji Idris ya yi wa Sahid sanin mutumci da tarbiya, ga tsoron Allah da sanin ya kamata , hakan yasa dukkan wasu kadarori daga abin da ya shafi ,gonaki , filaye gidaje da sauransu na Alaji Idris suna karkashin kulawar Sahid , domin Alaji kallon d'an cikinsa yake masa, hakan yasa yake son ya ba shi auren Kalisa domin yana da ya'kinin zata samu farin ciki, saidai Kalisa babu wanda ta mallakawa zuciyarta sai Umar. Anan gidan Alaji Kabiru , Zainab ce kwance a kan gadonta tana karanta littafin Hausa wato novel, hangen wayarta tai ta kawo haske , hakan ya tabbatar mata da message ne ya shigo , ta mike ta ciro wayar a caji tana kokarin ganin message d'in da ya shigo mata . Share and comment...📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta). _________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Editing❌ Page 3 & 4 Number ta gani babu suna an rubuta ,"masoyiya ya kike ? ya gida Allah yasa kina lafiya." A zuciyarta tace to waye wannan ni dai nasan ba yaya Mahmud ba ne . Typing ta fara tana mayar masa da cewa ,"lafiya kalau nake amma waye ."? Harun da ganin sakonta ya zabura yana murna ya sake maida mata da cewa, "Bani da suna amma mafi yawanci ana kirana da mai kaunar Zainab." Murmushi tasa da ganin ganin sakon nashi , kafin ta sake turawa ya turo mata cewa,"Mai kaunar Zainab da fatan rayuwa da ita har abada ". Kawai Zainab tai a jiyar zuciya. " Yanzu Uncle tafiya zakai." Laila ta fad'a cikin damuwa Uncle Yahaya ya kalleta yana cewa, "Haba Laila kwana biyu ne fa , ni dai kawai idan na dawo ina san kalamaina masu dad'i." Laila tai murmushi, saida ya sake komawa gidansu ya sake sallama da kakarshi sannan ya tafi. Ita kuwa Laila sai 'ku'kewa take tana had'o masa kalamai. tana cikin yin ne Khadija tazo ta warta, aiko ta bita . Yau ma Sahid yaje gidan Alaji Idris, saidai ita Kalisa har yanzu bata jinshi a zuciyarta, kullum saidai Umar kuma ta'ki fito mana da Umar mu ganshi. Alaji Idris yana cikin a zaune, sai ga Garba nan ya shigo Alaji ya kalleshi yana cewa, "Ahh, haba Garba sai kace ba ka garin , nan da nan baza a ringa zuumunci ba ko na yi laifine." Garba da sauri da Girmamawa ya fara cewa, "Haba Alaji, wallahi babu abin da kai mini , kasan zaman birni , motar tawa ce ta lalace shi yasa ba a ganina har saida aka gyarata." Alaji Idris ya had'e rai yana cewa, "Haba Garba yanzu motar taka ta lalace amma ba za ka sanar dani ba , to mene amfanin ...." Dakatar dashi Garba ya yi yana cewa, "Haba Alaji , Yanzu ni saboda abin kunya da raashin tausayi , motar tawa ta lalace shi ne sai na jira ka gyara mini . To mene amfanin kud'in da nake hayar da ita ." Garba ya sake gyara zama cikin tausayi da girmama Alaji yana cewa, "Haba ! Ai wallahi bazan mance da abin da kai mini ba , ka kawoni birni ka bani sana'a ka ko ya mini zama da mutane, ka se mini..." Alaji Idris ya dakatar dashi yana cewa, "Karna sake jin kana fad'e , to mene 'yan uwanta kar GARBA." Garba yace ,"Gaskiya ne ." Nan dai suka gaggaisa Garba ya koma , domin gidansa yana cikin gidan Alajin daga wajen gefen gate , ya dauko shi daga 'kauye ya ba shi mota ya ara masa gida , domin Garba da Alji Idris 'yan uwa ne , mahaifinsu d'ya wanda yanzu basu da kowa. Ahmad ne zaune kan kujera , Zainab kuma na kwance kan 'kafar yayannata suna hira, hirarsu suke cikin kwanciyar hankali da farin ciki , ga shi kuma anata 'kwad'o sallama amma babu wanda yaji a cikinsu , saida Hajjiya Salima ta fito daga d'akin girki ta tsaya kansu cikin b'acin rai sannan suka san halin da ake ciki , Kafin su ce komai Hajjiya Salima ta je ta b'ud'e kofar Yaya Aminu da Yaya Mahmud ne Hajjiya ta dawo gabansu Ahmad tana cewa, "Kuna ji ana sallama amma kun yi shiru ." Zainab ta tashi kan 'kafar Ahmad yayin da Ahmad yake cewa, "Wallahi momy bamu jisu ba ko kad'an." Mahmud da ke tsaye ya kalli Zainab yana cewa, "Taya za ai kuji , kullum ba ka da aiki sai shagwa'ba wannan yarinyar." Da sauri Ahmad ya cafe yana cewa, "Haba Mahmud kasan bani da kowa , sai ita kawai , ai dole na sota na nuna mata soyayya kafin ta barni , kuma momy ta'ki haifo wasu." Dariya yaya Aminu yasa ya kallon Zainab Hajjiya ce ta kalli Ahmad tana cewa, "To aku , sai kai musu shiru ai su zauna su huta ko ." Duk dariya suka saka yayin dasu Aminu suka zauna . Aminu da Mahmud kamar 'ya'ya suke wajen Alaji Kabiru, domin dukkansu 'ya 'yan kannensa ne da suke zaune a Kaduna, wanda Yanzu sun kawo musu ziyara ne . Aka kawo musu kayan motsa baki masu da kyau suka ci suka sha, yayin da wata iska ke shigarsu suka fara hira. Mahmud ne ya kalli Zainab yana cewa, "Su Zainab'yan mata." Wani kallo ta jefa masa tana cewa, "Uhum." Wayarta ce ta nuna mata alamar sa'ko hakan yasa ta 'bud'e wayar tana karantawa,"Dan Allah my life ki amshi soyayyar da nake miki dan Allah. " Zainab ta mayar masa da , "Bana san zancen banza koma waye kai ka fito fili mana ." Su kam su Aminu hirarsu kawai suke , amma Mahmud rabin hankalinshi yana wajen Zainab da ba ta sauraransu. Harun ya dawo mata da amsa, "Idan kin shirya ina son mu had'u gobe ." "Ina zamu had'u." Ta tura masa . "Gidan abincin dake bayan gidanku da karfe 11na safe." Kawai ajiyar zuciya ta yi ta mi'ke zata shiga d'akin ta, Mahmud ne ya dakatar da ita da kiran sunanta ,"Zainab. " Ta juyo tana kallonsa sannan yace , "Ina son gobe da safe za ki rakani asubiti zan je wani aiki." Tsayawa tai tana cewa, "Gobe kuma da safe." Mahmud yace ,"Eh." Saida ta d'anyi jimmm sannan tace ,"To Allah ya kaimu." Ta shige cikin d'akinta . Yau Alaji Idris shi da Hajjiya Maryam ziyara ya kai wa wani tsohon abokinsa . a hanyar dawowa ne ya kad'e wani yaro wanda yake tafe da kakarshi , aiko hankalin Alaji ya matukar tashi sosai , hakan yasa ya garzaya asubiti da yaron , sai dai ina rai ya yi halinsa domin yaron ya rugamu gidan Gaskiya, Hankalin kowa ya matukar tashi sosai , aiko Alaji Idris ganin cewa wannan tsohuwa bata da gata yasa ya taho da ita gidansa , ta tabbatar musu yaron jikanta ne da iyayensa duk suka rasu , su kad'ai suke zama . Tare da gawar yaron ya taho gidansa , anan akai masa komai aka kaisa makwancinsa. Bayan Uncle Yahaya ya isa legos , sun yi biki , aiko suka ringa yawon bud'e ido da abokansa , a garin yawon ne Allah ya had'ashi da wata karuwa wacce ta manne masa . Yanzu haka yana zaune da wani abokinshi ranshi a matukar 'bace yace , "Ni wallahi Shu'aibu zuwa na legos bai amfane ni da komai ba sai masifa." Shu'aibu ya kalli Uncle Yahaya yana cewa, "Haba !Karka bada maza mana , kawai don yarinya ta mannema shi ne masifa , to wallahi kafin ka tafi ka amince mata kawai inba haka ba Wallahi za kai asara." Cikin haushi Uncle Yahaya ya kalli Shu'aibu yana cewa, "Wai wannan banzar yarinyar , sanin kanka ne karuwa ce , me zan samu a gunta." Dariya Shu'aibu ya kwashe da ita yana cewa, "Wallahi ina ma ni ne , ai ko ita ce zaka samu wani abu agunta kana ganin yarinya cikakkiya , ai wallahi dani take so tuni an wuce gun , kuma wallahi babbar karuwa ce , domin ko kud'in yaharta bani da shi." Dogon tsaki Uncle Yahaya yaja yana cewa, "Dama dai sona take da gaske shi ne , amma kana ji fa , wai gayyatata take na kwana a d'akinta fa." Kafin ya rufe baki ya hangota tana tahowa inda suke kawai Uncle Yahaya ya juyar da kanshi yana tsaki , hakan yasa Shu'aibu kallon inda take yana sakin baki , riga da wando tasa wanda suka kama jikinta sosai , tun daga nesa Shu'aibu yake jin kamar ya rungumota , bari ma lokacin data 'karaso bada ban ya daure ba da Fa'iza taji wani abu😂. ,"Haba Yahaya, sai ne manka nake a cikin garin nan ." Uncle Yahaya ya yi mata shiru ko kallonta bai ba , ta sake cewa, "Na yi maka girki jazo muje ." Kallon wayarta tai dake hannunta sakamakon kiran da ya shigo, Abdul Salim , kawai ta kashe wayar tana cewa, "Da kai fa nake magana Yahaya." Uncle Yahaya yaja dogon tsaki yana cewa, "Ke ni fa babu inda zani , baza ki ta'ba samun abin da ki ke so ba , kawai dan kinga kirjinki dam -dam shi ne za ki tunanin za ki rud'eni." Ya sake jan dogon tsaki ya bar waje , shi kuwa Shu'aibu ya tsaya yana kallonta dama shi ne . Fa'iza cikin ranta tace, "To wallahi matukar na cika karuwai gaske sai na jawo Yahaya jikina, mu zuba mu gani ." A'a ni ko na ce Allah ya ba mai rabo sa'a . Uncle Yahaya a yau ya shirya ya baro legos, lokacin da dare ya yi tazo ta sami Shu'aibu, yake tabbatar mata da Uncle Yahaya ya koma Kano , aiko ta yi takaici , kawai ta amshi numbarsa ta koma. Zainab da Mahmud ne a kan hanyarsu ta zuwa asubiti, Mah.mud ya kalli Zainab wanda duk hankalinta yake kan had'uwarsu da Harun yana cewa, "Kin san wazan dubu ." Zainab tace, "A'a Yaya Mahmud." Mahmud ya jawo hannunta ya ri'ke , hakan yasa Zainab tsayawa tana kallonshi , shi ma ya kalleta yana cewa, "A haka zamu taafi." Tai ajiyar zuciya suka ci gaba da tafiya badan taso ba . Sisters kar a manta comment dina a private za a ajen. Share , like and comment.........📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano ( Autar marubuta ) _________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Page 5&6 Shigarsu asubitin ke nan Mahmud ya saki hannun Zainab yana nuna mata guri yace ta zauna ta jirashi . Tsayawa tai tana kallon shi , yayin dashi kuma ya shige d'akin gwajin cuta mai karya garkuwa jiki , Zainab hankalinta ya sake tashi ta kasa zama tanata sake-sake a ranta har Mahmud ya fito tasha gabansa da sauri tana cewa, "Wai me yake faruwa? mene ne ka yo a ciki , nifa ka fara bani tsoro ." Mahmud ya yi murmushi yana cewa, "Babu komai kawai ki taho." yasa kai ya fita waje yana cewa, "Harun zan kasheka." Zainab sauri tai tasha gabansa tana cewa, "Ni gaskiya yaya ka fad'a mini abin dake faruwa." Mahmud ya yi ajiyar zuciya yana cewa, "Budurwata ce Maryam, ake jita-jitar tana da HIV, kuma an tabbatar mini da anan take ansar magani, a halin yanzu ina cikin mummunan yanayi, na ro'ki alfarma a bincika mini , sun ce kuma zasu kirani ." Ya kauda kanshi yana cewa, "Harun idan tana da wannan cutar zan kasheka ." Cikin tsananin fusata ya yi maganar har saida idanunsa ya yi jah , Zainab ta kalleshi tana cewa, "Yaya kamar kana magana ko gaskiya kana cikin damuwa." Mahmud yace ,"A'a ba komai mu tafi kawai ." Suka d'auko hanya Bayan sun zo gida 1:25 hakan yasa Zainab ta kaici rashin samun da mar fita , kafin ta Zauna Harun ya turo mata sa'ko cewa zai zo har gidansu wani lokacin. Bayan Mahmud ya koma bai sanar da Ahmad komai ba, a kan zan cen Harun , amma abin yana matukar cinsa. Alaji Idris kuma yana 'ko'karin fara azumi , wanda fad'ar Allah ce domin yaron da ya kad'e ya rasu . Kakar yaron mai suna Baba anje a halin yanzu ta dawo gidan Alaji Idris da rayuwa, har zuwa lokacin da Allah zai raba , bayan haka ta sanarwa da Alaji Idris cewa bata bukatar diyyar yaron kawai Allah yasa mai ceto ne . A halin yanzu Harun ya sami labarin zuwan Mahmud, hakan yasa yake Shankar zuwa gidan . Yana zaune daga cikin harabar gidan ganin fuskarshi kawai zaka gane yana cikin damuwa, Zainab ce ta zo tana kiran sunanshi hakan yasa Mahmud d'ago kai yana kallonta da murmushi "Haba Yaya ka yi hakuri da tunani , to Yanzu tun ba a sanar maka tana da cutar ba kana haka , idan aka fad'a fa." Mahmud ya kalleta yayin da yake tuna tsohuwar soyayyar su yana cewa, "Mene kuwa ai ke zan aura ." Saukar maganar taji kawai a kunnuwanta Zainab tasa idanunta cikin nashi tana kallon shi, "Kina mamaki ne ."? Ya fad'a yana kallonta Kawai ta juya ta shige cikin gida , Mahmud yana cewa," ko da Maryam ko ba Maryam kaunarki a cikin jinina take kuma bazan sarara b." . Uncle Yahaya ne zaune cikin staff room a cikin makaranta babu abin da yake sakamakon a halin yanzu d'alubai sun fito break. Wayarshi ce ta fara ringing ya kalli wayar a sa'ilin da ya ga ba suna, d'auka ya yi yana karawa a kunnensa yana cewa, "Hello." Daga can 'bangaren yaji wata siririyar murya mai cike da yaudara ana cewa, "Hi Yahaya daga legos ne ." Wani fargaba yaji da tashin hankali sun ziyarce shi , hakan yasa shi ajiyar zuciya yana cewa, "Wai ke wacce irin ce ne." Ajiyar zuciya Fa'iza ta yi tana cewa, "Haba Yahaya, wai mene laifin mai son ka ne , wai duk irin abin da nake ma ka'ki yadda dani mene haka to." Uncle Yahaya yaja dogon tsaki yana cewa, "Tukun nama waye ya baki number har za ki kirani." cewa tai ,"Uhum to number ka ai bata da wahala kamar yadda zan taho kano kwanannan." Zaro idanu ya yi yana cewa, "me za ki zo yi a kano bana san shirme." Fa'iza tai dariya tana cewa, "To waye nake dashi a kano , gurinka zanzo mana ." Kawai ya kashe wayar yana tsaki Ya lalu'bo takardar da Laila ta kawo masa yana karantawa, kamalan soyayya masu dad'i da suka ja hankalinsa sosai kuma yaji sun fi na kullum dad'i hakan yasa ya yi godiya ga Allah. Yau Alaji Idris ya gudanar da azuminsa na goma ,aiko saiga Garba d'an uwanshj ya zo masa da labarin an sace masa mota , nan Alaji Idris ya ba shi hakuri yace masa insha Allah yana gama azumi zai siya masa sabuwar mota ya cigaba da sana'arsa, aiko Garba harda kukan farin ciki da matukar ganin girman Alaji. Lokacin da Alaji Idris ya ci dabino da ruwan shayi ne ya zauna ya yi tagumi, Hajjiya Maryam data shigo ta kalli Alajin tana cewa,"Lafiya kuwa Alaji. " Ko motsawa baiyi ba ga dukkan alamu bai san tana yi ba ,"Alaji lafiya. ". Ta sake fad'e matsawa tai tana shafa fuskarshi hakan yasa Alaji Idris ya dawo hayyacinsa , Kauda kai ta yi tana cewa," Innalillahi , wai ya haka ne Alaji, kana sawa kanka damuwa ." Ajiyar zuciya ya yi yana tashi tsaye yana cewa, "Wallahi Hajjiya yadda mahassada suke nuna mana 'kiyayya shi ne damuwata , kawai dan Allah ya fifita mu a cikinsu ." Hajjiya Maryam ta kama hannun Alaji Idris tana cewa, "A kullum ina fad'a ma , addu'ar da muke yi , ita ce Allah yake hanasu yi maka wasu abubuwan , mu da muke da Allah, Wallahi duk sharrinsu a kan zu zai tattare , kawai addu'a zamu cigaba da yi." Alaji ya girgiza mata kai alamun yaji dad'in zancen ta yana cewa, "Gaskiya ne." Kalisa ce ta shigo ta katse su da cewa ,"Momy Dady , abinci ya kammala ku taho ." Alaji ne ya kalleta cikin kauna yana cewa, "Tom Kalisa Yanzu zamu taho." Matsowa ta sake yi tana cewa, "Haba Dady tsawon yini fa kana azumi, kuma babu abin da kaci , ka dena biyewa momy ka taho mu tafi ." Ta ja masa hannu ya bita suka fita yana yiwa Hajjiya Maryam murmushi. Ita ma murmushi tai ta bi bayansu. Duk sun zazzauna su baba anje , Nabila, Jafar , Alaji na fitowa gun kawai duk suka d'auke wuta kowa ya yi shiru , su Hajjiya Maryam su ma suka zauna , aka fara cin abinci amma abin mamaki da tambaya kowa shuru ya yi kamar wanda aka aikowa da mutuwa , jikinsu duk kasala ta ziyarcesa bayan sun gama cin abinci sai aka fara kallon-kallo ba tare da kowa ya bar wajen ba . Alaji Idris ne ya bud'i baki yana cewa, "Kalisa gobe ki sanar da Sahid ina san ganinshi." Wani fad'uwar gaba taji ba zato ta shiga yanayi tana tunanin ba dai dady zai maganar aure ba . "Kalisa ba ki ji mene na ce ba ne ". Alaji ya fad'a Da sauri ta kalleshi tana cewa," Naji dady ." Sannan ya d'auke kai a gunta yana cewa, " Idan Allah ya kaimu gobe ,ina son magana da kowa da me nan bayan kun yi break fast. " Maganar suka ji wani iri harsun fara tunanin meke damun Alaji yau . Kawai ya tashi ya nufi d'akinsa , Hajjiya Maryam ajiyar zuciya tai tana binshi da kallo Nabila ce ta kalli Jafar tana cewa, "Mene dady zai fad'a mana gobe , nifa har na fara jin tsoro ." Baba Anje tace ,"Too Allah masani ku bari goben ta yi , Allah ya kai mu , mu kuma ji alheri." Suka ce ,"Amin." Washe gari da safe Aminu ya fara shirya kayansa domin komawa Adamawa inda yake karatu , bayan ya shirya kayanshi tsaf Hajjiya da Alaji Kabiru suka fito sukai sallama har Alaji ya ba shi wasu kud'i Sai Ahmad da Mahmud suka d'auki kayansa domin rakashi Zainab ta kalli Aminu tana cewa, "To yaya Aminu Allah ya tsare hanya ya kula mana da kai ." Aminu yace ,"Amin Zainabu ta." Hararar kauna Mahmud ya jefa mata yana cewa,"Ni ba za a mini addu'a ba." . Murmushi tai mai jan hankali tana cewa, "To kai yaushe zaka tafi yaya Mahmud." .Zaro idanu ya yi yana cewa, "Laaaaah ashe korata kike so ki yi ."? Dariya tai tana cewa," Wallahi a'a yaya bari na koma ciki ." Ta tafi yana bin ta da wani kallo.... Fitarsu ke nan sai ga Harun ya shigo aiko Zainab tana zaune taji sako ya shigo mata, "Ki fito gani a harabar gidanku." Murmushi tai tana cewa, "Ya Allah, yau zan ga waye mai wasa da hankalina ." Ta tashi ta sa hijab ta fita duk ta duba harabar gidan amma babu kowa hakan yasa ranta matukar'baci cikin ranta take cewa aikin banza kawai ta juya zata shiga gida ." Jin murya tai ance ,"Ina za ki kuma gani a Bayan ki." Tai sauri ta waiga don ganin wayeeeeee. Comment d'ina a zube shi a private Share , like and comment.................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano ( Autar marubuta ) _________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Page 5&6 Shigarsu asubitin ke nan Mahmud ya saki hannun Zainab yana nuna mata guri yace ta zauna ta jirashi . Tsayawa tai tana kallon shi , yayin dashi kuma ya shige d'akin gwajin cuta mai karya garkuwa jiki , Zainab hankalinta ya sake tashi ta kasa zama tanata sake-sake a ranta har Mahmud ya fito tasha gabansa da sauri tana cewa, "Wai me yake faruwa? mene ne ka yo a ciki , nifa ka fara bani tsoro ." Mahmud ya yi murmushi yana cewa, "Babu komai kawai ki taho." yasa kai ya fita waje yana cewa, "Harun zan kasheka." Zainab sauri tai tasha gabansa tana cewa, "Ni gaskiya yaya ka fad'a mini abin dake faruwa." Mahmud ya yi ajiyar zuciya yana cewa, "Budurwata ce Maryam, ake jita-jitar tana da HIV, kuma an tabbatar mini da anan take ansar magani, a halin yanzu ina cikin mummunan yanayi, na ro'ki alfarma a bincika mini , sun ce kuma zasu kirani ." Ya kauda kanshi yana cewa, "Harun idan tana da wannan cutar zan kasheka ." Cikin tsananin fusata ya yi maganar har saida idanunsa ya yi jah , Zainab ta kalleshi tana cewa, "Yaya kamar kana magana ko gaskiya kana cikin damuwa." Mahmud yace ,"A'a ba komai mu tafi kawai ." Suka d'auko hanya Bayan sun zo gida 1:25 hakan yasa Zainab ta kaici rashin samun da mar fita , kafin ta Zauna Harun ya turo mata sa'ko cewa zai zo har gidansu wani lokacin. Bayan Mahmud ya koma bai sanar da Ahmad komai ba, a kan zan cen Harun , amma abin yana matukar cinsa. Alaji Idris kuma yana 'ko'karin fara azumi , wanda fad'ar Allah ce domin yaron da ya kad'e ya rasu . Kakar yaron mai suna Baba anje a halin yanzu ta dawo gidan Alaji Idris da rayuwa, har zuwa lokacin da Allah zai raba , bayan haka ta sanarwa da Alaji Idris cewa bata bukatar diyyar yaron kawai Allah yasa mai ceto ne . A halin yanzu Harun ya sami labarin zuwan Mahmud, hakan yasa yake Shankar zuwa gidan . Yana zaune daga cikin harabar gidan ganin fuskarshi kawai zaka gane yana cikin damuwa, Zainab ce ta zo tana kiran sunanshi hakan yasa Mahmud d'ago kai yana kallonta da murmushi "Haba Yaya ka yi hakuri da tunani , to Yanzu tun ba a sanar maka tana da cutar ba kana haka , idan aka fad'a fa." Mahmud ya kalleta yayin da yake tuna tsohuwar soyayyar su yana cewa, "Mene kuwa ai ke zan aura ." Saukar maganar taji kawai a kunnuwanta Zainab tasa idanunta cikin nashi tana kallon shi, "Kina mamaki ne ."? Ya fad'a yana kallonta Kawai ta juya ta shige cikin gida , Mahmud yana cewa," ko da Maryam ko ba Maryam kaunarki a cikin jinina take kuma bazan sarara b." . Uncle Yahaya ne zaune cikin staff room a cikin makaranta babu abin da yake sakamakon a halin yanzu d'alubai sun fito break. Wayarshi ce ta fara ringing ya kalli wayar a sa'ilin da ya ga ba suna, d'auka ya yi yana karawa a kunnensa yana cewa, "Hello." Daga can 'bangaren yaji wata siririyar murya mai cike da yaudara ana cewa, "Hi Yahaya daga legos ne ." Wani fargaba yaji da tashin hankali sun ziyarce shi , hakan yasa shi ajiyar zuciya yana cewa, "Wai ke wacce irin ce ne." Ajiyar zuciya Fa'iza ta yi tana cewa, "Haba Yahaya, wai mene laifin mai son ka ne , wai duk irin abin da nake ma ka'ki yadda dani mene haka to." Uncle Yahaya yaja dogon tsaki yana cewa, "Tukun nama waye ya baki number har za ki kirani." cewa tai ,"Uhum to number ka ai bata da wahala kamar yadda zan taho kano kwanannan." Zaro idanu ya yi yana cewa, "me za ki zo yi a kano bana san shirme." Fa'iza tai dariya tana cewa, "To waye nake dashi a kano , gurinka zanzo mana ." Kawai ya kashe wayar yana tsaki Ya lalu'bo takardar da Laila ta kawo masa yana karantawa, kamalan soyayya masu dad'i da suka ja hankalinsa sosai kuma yaji sun fi na kullum dad'i hakan yasa ya yi godiya ga Allah. Yau Alaji Idris ya gudanar da azuminsa na goma ,aiko saiga Garba d'an uwanshj ya zo masa da labarin an sace masa mota , nan Alaji Idris ya ba shi hakuri yace masa insha Allah yana gama azumi zai siya masa sabuwar mota ya cigaba da sana'arsa, aiko Garba harda kukan farin ciki da matukar ganin girman Alaji. Lokacin da Alaji Idris ya ci dabino da ruwan shayi ne ya zauna ya yi tagumi, Hajjiya Maryam data shigo ta kalli Alajin tana cewa,"Lafiya kuwa Alaji. " Ko motsawa baiyi ba ga dukkan alamu bai san tana yi ba ,"Alaji lafiya. ". Ta sake fad'e matsawa tai tana shafa fuskarshi hakan yasa Alaji Idris ya dawo hayyacinsa , Kauda kai ta yi tana cewa," Innalillahi , wai ya haka ne Alaji, kana sawa kanka damuwa ." Ajiyar zuciya ya yi yana tashi tsaye yana cewa, "Wallahi Hajjiya yadda mahassada suke nuna mana 'kiyayya shi ne damuwata , kawai dan Allah ya fifita mu a cikinsu ." Hajjiya Maryam ta kama hannun Alaji Idris tana cewa, "A kullum ina fad'a ma , addu'ar da muke yi , ita ce Allah yake hanasu yi maka wasu abubuwan , mu da muke da Allah, Wallahi duk sharrinsu a kan zu zai tattare , kawai addu'a zamu cigaba da yi." Alaji ya girgiza mata kai alamun yaji dad'in zancen ta yana cewa, "Gaskiya ne." Kalisa ce ta shigo ta katse su da cewa ,"Momy Dady , abinci ya kammala ku taho ." Alaji ne ya kalleta cikin kauna yana cewa, "Tom Kalisa Yanzu zamu taho." Matsowa ta sake yi tana cewa, "Haba Dady tsawon yini fa kana azumi, kuma babu abin da kaci , ka dena biyewa momy ka taho mu tafi ." Ta ja masa hannu ya bita suka fita yana yiwa Hajjiya Maryam murmushi. Ita ma murmushi tai ta bi bayansu. Duk sun zazzauna su baba anje , Nabila, Jafar , Alaji na fitowa gun kawai duk suka d'auke wuta kowa ya yi shiru , su Hajjiya Maryam su ma suka zauna , aka fara cin abinci amma abin mamaki da tambaya kowa shuru ya yi kamar wanda aka aikowa da mutuwa , jikinsu duk kasala ta ziyarcesa bayan sun gama cin abinci sai aka fara kallon-kallo ba tare da kowa ya bar wajen ba . Alaji Idris ne ya bud'i baki yana cewa, "Kalisa gobe ki sanar da Sahid ina san ganinshi." Wani fad'uwar gaba taji ba zato ta shiga yanayi tana tunanin ba dai dady zai maganar aure ba . "Kalisa ba ki ji mene na ce ba ne ". Alaji ya fad'a Da sauri ta kalleshi tana cewa," Naji dady ." Sannan ya d'auke kai a gunta yana cewa, " Idan Allah ya kaimu gobe ,ina son magana da kowa da me nan bayan kun yi break fast. " Maganar suka ji wani iri harsun fara tunanin meke damun Alaji yau . Kawai ya tashi ya nufi d'akinsa , Hajjiya Maryam ajiyar zuciya tai tana binshi da kallo Nabila ce ta kalli Jafar tana cewa, "Mene dady zai fad'a mana gobe , nifa har na fara jin tsoro ." Baba Anje tace ,"Too Allah masani ku bari goben ta yi , Allah ya kai mu , mu kuma ji alheri." Suka ce ,"Amin." Washe gari da safe Aminu ya fara shirya kayansa domin komawa Adamawa inda yake karatu , bayan ya shirya kayanshi tsaf Hajjiya da Alaji Kabiru suka fito sukai sallama har Alaji ya ba shi wasu kud'i Sai Ahmad da Mahmud suka d'auki kayansa domin rakashi Zainab ta kalli Aminu tana cewa, "To yaya Aminu Allah ya tsare hanya ya kula mana da kai ." Aminu yace ,"Amin Zainabu ta." Hararar kauna Mahmud ya jefa mata yana cewa,"Ni ba za a mini addu'a ba." . Murmushi tai mai jan hankali tana cewa, "To kai yaushe zaka tafi yaya Mahmud." .Zaro idanu ya yi yana cewa, "Laaaaah ashe korata kike so ki yi ."? Dariya tai tana cewa," Wallahi a'a yaya bari na koma ciki ." Ta tafi yana bin ta da wani kallo.... Fitarsu ke nan sai ga Harun ya shigo aiko Zainab tana zaune taji sako ya shigo mata, "Ki fito gani a harabar gidanku." Murmushi tai tana cewa, "Ya Allah, yau zan ga waye mai wasa da hankalina ." Ta tashi ta sa hijab ta fita duk ta duba harabar gidan amma babu kowa hakan yasa ranta matukar'baci cikin ranta take cewa aikin banza kawai ta juya zata shiga gida ." Jin murya tai ance ,"Ina za ki kuma gani a Bayan ki." Tai sauri ta waiga don ganin wayeeeeee. Comment d'ina a zube shi a private Share , like and comment.................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano ( Autar marubuta ) editing❌ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Page 9&10 "Dan Allah malam yi hakuri". Yarinyar ta fad'a tana kallon Mahmud Murmushi ya yi yana cewa, " Babu komai laifina ne , kema ki hakuri, na gaji ne ga ciwon kai ." Murmushi ta sake yi tana cewa, "Allah sarki , to idan ba damuwa ka shigo na rage maka hanya tunda naga kai ma hanyar tawa kayi ." Mahmud ya ce ,"A'a wallahi karna bata miki Lokaci nan babban titi zan gangara." Tace ,"Haba babban titi ai da sauran tafiya ka shigo kawai." Ya bud'e kofar ya shiga tare da rufewa yana ajiyar zuciya babu wanda ya ce da wani komai , har saida motar ta tsaya , ta fita ta bud'e gaban motar domin ganin matsalar, dogon tsaki ta saki , hakan ya sa Mahmud fitowa yana duba mata ,"Na ce da dady na tsani motar nan amma ya'ki saurarana ."Tai maganar cikin damuwa . A lokacin Mahmud ya rufe gaban motar yana cewa, "Karki damu , shiga ki tayar mu ga ." Ta shiga tasa key , aiko mota ta tashi suka ci gaba da tafiya "Ki sauke ni anan ". Mahmud ya fad'a Murmushi tai ta fara kokarin parking,bayan tayi burki ne ta kalli Mahmud tana cewa," Sai dai bansan sunanka ba ." "Sunana Mahmud. ke kuma fa ." Ajiyar numfashi tai tana cewa, "Ni suna na Hauwa Muhammad Sadiq, ni 'yar gidan lu'utanan Muhammad Sadiq ce ." Mahmud ya kafeta da idanun mamaki Lokaci guda kuma yana cewa, "Gaskiya na gode Hauwa Muhammad, amma idan ba za ki damu ba , ko zaki ban number ki ." ya mika mata wayarsa Ta amsa tare da aje masa number ta a cikin wayar , Mahmud ya fito ya sake godiya ta tafi Mi'ka ya yi yana cewa, "Tabb ka ga wata mota , yaran manyan ke nan ." Ya yi murmushi ya gangara domin tafiya gida. Zainab ce kwance a kan kujerar falo suna waya da Harun , yake sanar mata fa zai jarabawar sojoji ta taya shi da addu'a Ganin shigowar Mahmud cikin yanayin da bata saba gani ba ya sa ta tashi zaune , tare da sanarwa Harun zata kirashi . Mahmud kusa da ita ya zo ya zauna , ya jingina kanshi a kujera tare da ajiyar zuciya . "Yaya Mahmud lafiya kuwa." Mahmud ya kalli Zainab da cewa ,"Zainab daga asubiti nake, wallahi tana da cutar nan." ya karasa maganar cikin yanayin damuwa "Ina Ahmad."? Ya kalleta yana tambaya Cikin jimami ita ma Zainab ta ce ," Wallahi bansan inda yayi ba , naga ya hau mota ya fita . To amma Yaya Mahmud yanzu mene abin yi ." Mahmud ya gyara zama yana kallon Zainab ya ce ,"Zaki aure ni Zainab, kina so na."? Jitai zuciyar ta tai wani irin bugawar tsoro "Ni dai ina son ki , amma kiyi tunani." Ya tashi ya shiga cikin d'akinshi , Zainab tana bin shi da kallo "Me ya sa yaya Mahmud yake mini haka , duk abin dake ranshi kawai fad'a mini yake ko kunya." Zainab tai maganar tana mamaki tare da sake kallon kofar d'akinshi Kiran Harun ne ya katse mata tunani, ta tashi ta shige d'akinta, kai tsaye kan gado ta fad'a ta cigaba da waya dashi. A halin yanzu Alaji Idris ya yi azumi guda 58 yana zaune a falo shida Hajjiya suna hira "Wato Hajjiya kinga a kwana a tashi na kusan kammala azumi na , Allah ne abin godiya." Hajjiya tai murmushi tana cewa, "Wallahi kuwa Alaji ai wata rana sai labari." "Wallahi Hajjiya na yi dace da samunki a matata , duk wanda bai samu mace kamar ke ba , to abin tausayi ne ." Dariya Hajjiya tai tana cewa, "Alaji ke nan ai ni ce na yi dacen miji wallahi , ni dai fatana Allah ya barni da kai." Alaji Idris ya zaro mata idanu yana cewa, "A barki dawa? ai ko Allah bazai barni ba , sai dai kiji wufff na mutu ." Ya karasa maganar yana dariya Ita ma Hajjiya dariya tai tana cewa, "To ai shi ke nan kowa na haka ne . To amma Alaji me zai hana kasha ruwa muje kauye a gaidasu , domin mun kwana biyu bamu je ba ." Alaji Idris ya ce ,"Eh gaskiya ne wannan in sha Allah zamu je kuwa ." ..... Yanzu karfe 12 na dare , sai yanzu Uncle Yahaha ya tashi a bacci daga d'akin Fa'iza, yana tashi a firgice ya sakko daga kan gadon , Fa'iza dake kan kujeara sauri tai ta tashi tana kallonshi da cewa ,"Lafiya kuma ." Ajiyar zuciya ya yi , sannan ya ce ,"Bansan zan yi bacci haka ba , ga shi dare ya yi , tafiya zan yi gaskiya. " Ganin yana kokarin sa takalmi Fa'iza da sauri tasha gabanshi tana cewa, "Haba Yahaha dan Allah wanne irin tafiya kuma bayan dare ya yi haka kawai ka bari saida safe ." Ganin yadda take kwarkwasa ya sa yasha jinin jikinshi , ya fara mata magana cikin nutsuwa. "Haba dai safiya , na bar kakata a gida ita kadai, kuma ban sanar mata zan kwana a waje ba , ni ban ta'ba kwana a hotel ba , kuma bugu da kari da mace ." Shagwa'ba ta fara tana bubbuga kafafunta a kasa tare da girgiza jiki, "Ni gaskiya ka zauna ." Shi kuma banza Uncle ya koma gado ya zauna jabar , "To shi ke nan na fasa tafiya , amma da sassafe zan tafi." Wani dad'i ya kashe Fa'iza a tsaye ta karasa ta d'auko masa abinci . Bayan ya gama cin abincin na wajen wasu mintina . Fa'iza ta tashi ta jawo akwatinta rigar jikinta ta fara kokarin cirewa hakan ya sa uncle Yahaya saurin kauda kai ya kalli fuskar gado . 😂 dariya ta yi tana kallonshi , tsat ta cire doguwar rigar , sannan tasa wacce bata kai wacce ta cire arziki ba , gadon ta hau ta zauna tana kallon Uncle Uncle Yahaya yaji wani yarrr ,"Haba mene nasa irin wannan kayan kuma." Dariya tai tana cewa, "Baby bana san yarinta , sai ka ce ba wani mara ilmi." Hard'o wuyanshi tai tana cewa, "Wallahi ina san ka Yahaya aure nake son mu yi." Duk ya rasa yadda zai da ita jikinshi ya fara rawa "To shi ke nan naji sake ni." Fa'iza ta sake shi tana murmushi Lokacin da safiya tai , su Uncle Yahaya harda yin wanka sannan ya tafi gida wajen kakarshi domin ita kadai yake da ita. Yana fita wayar fa'iza ta fara ringin tsaki taja sannan ta d'auki kiran . "Yaya haka haba my baby zaki tafiya baki sanar dani ba , me ya sa ." Daga can bangaren aka fad'a Tsaki Fa'iza tai tai tana cewa, "Dole idan zani waje sai ka sani ne ." Daga dayan bangaren cikin mamaki ya sake cewa ,"Kai Fa'iza ni ne fa , Abdul Salim ne ." Dariya ta kwashe da ita tana sake tuntsurawa tana cewa dashi ,"To kana tunanin muryarka zata buya ne ,koba komai ai na yi saving numbobinka nasan kuma kai ne ." Ya yi ajiyar zuciya tare da cewa ,"OK yaushe zaki dawo to." Gaskiya ba yanzu zan dawo ba , domin babu kud'i a hannuna kuma ina san zan se wasu abubuwan in taho dasu ." Abdul Salim ya yi murmushi yana fadin ,"Zan turo miki dubu dari ki yi hakuri da ita." Fa'iza ta ce ,"Shi ke nan to ina jira ." Abdul ya ce ,"To ko dai siyayyar aurenmu zaki fara ne." Fa'iza tai tsaki tana cewa, "Wanne irin aure kuma , ni dai kasa min kud'in , sauran maganar sai na dawo." Ya ce ,"To ba komai I love you. " Ya kashe wayar . Shi Abdul Salim haifaffen dan legos ne da yake da gata , kuma dan masu fad'e aji dan manya, Yana son ya auri Fa'iza, bai taba lalata da ita ba , amma Fa'iza ba sonshi take ba , ya yi mata komai hatta gidan da take ciki a can shi ne ya siya , Saidai ba cikakken hankali gare shi ba , yana shaye-shaye , Kuma baya barin duk wanda ya zo masa da rainin wayo. Harun ne zaune shi da Zainab a restaurant Tun da ya sa idanunshi cikin nata bai cire ba , sai tunani yake kala-kala Shin Zainab kuwa zata ba shi kanta , ko kuma maganar aure zai je da ita , to amma yasan Mahmud ba zai bari ba , hakan ya sa kawai yake jin gara ya yaudareta kamar yadda ya saba yiwa sauran 'yan mata. Tom ni dai comment din na PC , share, like ...........📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano ( Autar marubuta ) *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Page 11&12 Zainab ganin yadda kallon ya mata ñauyi , ya sa ta ta fara tsarguwa , ta kasa zama daidai . "Harun lafiya kuwa kake mini irin wannan kallon." Murmushi ya yi mara kunyan yana cewa, "Haba Zainab akwai abin da nake son sanar dake ." Zainab murmushi ta yi tare da gyara zaman mayafin dake jikinta tana cewa, "To ka fad'a mini mana baby." "Tom fatan kin shirya ji domin kalmar tana da zafi." "Zafi kuma." Zainab ta fad'a cikin mamaki "Ina san ki." Zainab ta kau da kai tana dariya yayin da Harun ya ce ,"Ba fa abin dariya ba ne , Ina jin san ki a raina kamar zai fasa zuciya ta ya fito , Ina kaunar ki da dukkan yakini da sadaukarwa, fatan zan same ki cikin girmama soyayya ta da bata kulawa." Ya karasa maganar yana duban cikin idanunta "Ni ma ina san ka Harun , soyayyar da uwa takewa yaronta , soyayyar da bata da karshe kuma bata da misali , domin kai din Rayuwata ne ." Murmushin farin ciki ya yi da jin wannan batun na Zainab hakan ya sa ya fara fadin , "Gaskiya naji dadi Zainab amma ina mai sanar dake cewa Gobe zan yi tafiya zuwa gida wato garin Tiga zan gaida iyayena, domin fa kinsan anan gidan kanin ummanmu nake." Murmushi ta yi Zainab da ya matukar kara fito da kyanta tana ce masa , "Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya , a kuma gashshemin da Umma ta." "Karki damu my baby za su ji gaisuwarki Sarauniyar soja." Ya yi maganar yana sara mata , ita kam ta yi masa dariya Bayan malamin lissafi ya fita daga ajinsu Khadija Ajin ya rufe da surutu yayin da wasu suke yin bitar lissafin Laila ko rubutun ma batai ba ta yi tagumi idanunta sun kawo ruwa Khadija ce ta dungureta tare da cewa ,"Haba Laila Adam mene yake damunki ne ." Laila ta kalli Khadija tana cewa, "Wallahi ke ma kinsan Uncle ne , wallahi ina son shi , amma yanzu duk ba ya kulani , ko gani na ba ya yi , so yake ya juya mini baya , wallahi ina san uncle Khadija." Khadija ta ce ,"Kuma babu abin da kika yi masa ." Laila ta ce ,"Babu abin da nai masa Khadija, duk fa ya juyan baya." Khadija ta ce ,"To ki bari anjuma ki same shi mana ." Laila cikin fushi da bacin rai tace wallahi ko ganina fa ba ya san yi ." Khadija ta ce ,"Tabbb ki ce dai akwai matsala. " Yanzu dai Uncle Yahaya ko d'ar ba ya ji idan zai tafi hotel wajen Fa'iza Domin kafin ya tafi makaranta ma ya sanar da kakarshi cewa ba zai kwana a gida ba yau , domin akwai aikin da zai , haka ta yi masa addu'a tare da fatan alheri.... Duk iyalan Alaji Idris zaune suke suna karyawa cikin farin ciki , domin Allah ya sauki Alaji Idris lafiya ya kammala azumi wajen kwana uku ke nan "Hajjiya kin san yau ne fa zami tafiyar nan zuwa kauye , da safiyar nan zamu tafi domin kinsan gari ne mai nisa kuma hanyar ba kyau ne da ita ba ." Hajjiya Maryam ta ce ,"Alaji ke nan , ai na fika zumudi , domin tun dazu nasa Musa driver ya wanke mota , kuma ya zuba duk kayan abincin da za a kai musu." Alaji Idris ya yi dariya yana cewa, "Eh lallai ki ce abin na yi ne , amma baba anje ba za ki ba ne ."? Hajjiya tayi dariya tana cewa" Tabb ka ji Alaji da zance , baba mai jikin tsufa ina zata wannan garin , ai kam tayi zazzabi." Dariya baba anje ta yi tana cewa, "Gaskiya kam ku je Allah ya dawo daku lafiya , ina nan dasu Nabila." Jafar ya ce ,"Ai ko dai baba ki yi zamanki wannan garin ba abin zuwa ba ne kuma kauye ne." "Ka ci gidan ku. Ina ce dangin ku ne ." Hajjiya ta yi maganar Kalisa ce ta zumburo baki tana cewa, "Ni dai ina san zuwa momy." Hajjiya ta ce ,"Ai na sani Kalisa danta Jafar da Nabila baza ai zumunci ba . Alaji Idris ya mike da cewa ,"Hajjiya ki tashi mu shirya ina san har na dawo naje office. " Ya shige ciki . Bayan duk sun shirya suka fito harabar gidan Duk suna musu a dawo lafiya "Baba dan Allah karki bari yarannan su fita yawo , a kula dasu." Hajjiya tai maganar cikin girmamawa tare da shigewa cikin mota Sukai sallama suka tafi yayin dasu kuma suka koma gida Bayan wajen minti goma da fitarsu , sai ga GARBA ya shigo Suke tabbatar masa Alaji sun tafi kauye Garba ya koma yana takaicin rashin ganinsu domin ya basu sako zuwa wajen Shehu . Bayan sun fito break Laila ta nufi staff don ganin uncle Yahaya aiko yana zaune suna hira da wasu tsurarun malaman wanda duk kusan sa'anninshi ne yana ganin Laila ta shigo ya had'e rai , hakan ya sa Laila Adam tasha jinin jikinta da 'ker ta karasa wajen shi ta tsuguna Tun kafin ta kawowa ranta ta yadda za ta masa magana taji yana cewa, "Tashi ki tafi baki ganni da malamai ba ne." Sau dubu nawa yake kiranta a gaban malamai ,amma yau yake wannan maganar, abin da ya zo mata kai ke nan Cikin nutsuwa ta kalli cikin idanunshi da fuskar maraici ta fara magana da turanci ."Uncle dan Allah, wallahi na matukar damuwa da kai , mene na yi maka ." Uncle Yahaya ya tashi ya fita waje wani abu taji ya turnuke mata zuciya ta kalli sauran malaman wanda duk hankalinsu ba ya kanta , sannan ta tashi ta fita Uncle yana can gefe yana waya ga dukkan alamu koma wayar me yake da mace yake yi Laila ta sawa zuciyar ta wannan maganar zafafan hawaye ne suka zubo mata , hakan ya sa ta kasa daurewa ta nufi aji tana kuka , kafin ta karasa ta ci karo da Khadija "Mene ya faru kuma".? Khadija tai tambayar tana jawota jikinta cikin kuka Laila ta fara magana ," Khadija kin san ya nake son uncle kuwa , me ya sa yake min haka , ni ce fa Lailanshi , wallahi zuciya ta zata buga a kan shi , zan tarwatsa zuciya ta idan ya rabu dani. " Duk d'alubai sai hankalinsu ya fara yowa kansu "Mene yake damun Laila? waye ya dake ta? Me ya faru ?...." Sunata tambaya da turanci yayin da wasu suke yin Hausa Khadija ta kallesu tare da basu amsa guda cikin yaren Hausa "Bata ta lafiya ne." Suka mata fatan lafiya wasu suka bar wajen , Khadija ta ja Laila suka koma aji "Wata kila fa Uncle wannan kalaman naki ne basi masa ba." Khadija ta fad'a Laila da idanun kuka tace ,"To ai sai ya fad'a mini ko , zan yi wa Uncle kalaman da ban taba yi masa ba na ba shi , matukar bai dawo yadda yake ba to ya dena sona, kuma Khadija ciwo ne zai kashe ni." Khadija tai ajiyar zuciya tana takaici . Kalisa da Nabila ne suke girki yayin da baba anje take daki shi kuma Jafar yana falo "Aunty tin d'àzu gabana yake fad'uwa wallahi." Nabila ta yi maganar Kalisa ba tare da tace mata komai ba ta nufi wayarta sakamakon kiran Umar da ya shigo . Saukarsu Alaji Idris cikin kauyen driver ya fito da kayan abincin yana shiga dasu cikin babban gidan . Sai ga yaran gari riiiiiiii sun nufo Alaji domin basu dari bibbiyun da ya saba basu duk zuwa , aiko sai da ya sallami kowanne yaro , sannan ya samu nutsuwa Malam Shehu ya yi musu jagora cikin mutunci da tarbar arziki zuwa cikin gidan , kowa kuma sai murna , kafin ka ce komai a kawo musu nau'ikan abinci daga kowanne sashi na gidan , dambu fate , dashishi, dahuwa, da dai sauran su da dama sun ci sunsha sosai kafin matan gidan Alaji ya sallamesu sun yi matukar farin ciki . Uncle Yahaya ana tashi daga makaranta ya wuce wajen Fa'iza Zaune take cikin wata mara kunyar doguwar riga fara shara-shara , bayan wannan rigar jikinta babu komai data sanya domin kana hango dukkan surar jikinta , bayan ma dai Fa'iza karuwa ce to 'yar iska ce ta gaske😂 waya take yi da wata kawarta ," Aisha ya kike so na yi da Abdul ne dan Allah, ni fa wallahi bazan aure shi ba ai na fado." Fa'iza tai maganar cikin fada hakan ya hassala Aisha ta fara cewa ,"Sannu sara ,idan banda Abdul Salim wane yake sonki da gaske, to kuwa wallahi sai ki dena ci masa kudi , ki fada masa gaskiya, ai wallahi ma shi ne zai rufa muki asiri , to wallahi kiji tsoron Allah kiyi aure , ni yanzu tunda na samu masoyin gaskiya nayi aurena ba abin dana rasa." Fa'iza ta ce "Ke ni zan kashe waya ai gobe zan dawo." Ta kashe wayar tana tsaki A lokacin Uncle Yahaya ya turo kofa ya shigo Fa'iza ta mike domin taro shi ." Share, like and comment..............📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Editing❌ page 13&14 Hannayena biyu ta rike tana cewa "Tun dazu nake jiranka fa baby sai yanzu." Uncle bata rai ya yi yana cewa, "Me ya sa zaki sa wannan kayan yanzu, kin san dai bana san haka sai da daddare ko." Sakin hannayensa tai ta hardo wuyanshi , yayin da Uncle Yahaya ya ke sake kallon cikin jikinta yana ajiyar zuciya. " "Nasan kana jin yunwa muje mi wanka sannan muci abinci." Duk uncle ya kasa cewa komai kawai kallonta yake ...... kakartashi ma a halin yanzu bata da lafiya ga gidan ba kowa . Anan gidan Alaji Kabiru Zainab na falo a zaune , a lokacin Mahmud ya shigo yana kallonta kujerar da take zaune shi ma ya zauna yana cewa, "kawo mini ruwa Zainab." Ta tashi ta kawo kamar yadda ya ce tana mika masa tai hanyar d'akinta "Ina zaki zo mana." Ta juyo tana cewa, "Uhum." Murmushi ya yi mata yana cewa, "Gobe ina san zamu fita." Tasa kai tana cewa, "Allah ya kaimu ." "Kaii! Lallai ma yarinyar nan ba komai." Ya girgiza kai wayarshi ya ciro a aljihu ya nufi numbar Hauwa "Bari na kira yarinyar nan mu gaisa." Mahmud ya yi maganar yana danna kiran har ta tsinke ba a da ga ba , ya sake kira amma shiru wayar ya aje a gefenshi tare da cewa "Ai shi ke nan ." Ya kashe kujerar ya kwanta , wajen wucewar minutes 3 sai ka kira ya shigo masa , ba wata-wata ya daukin kiran "Hello 'yan mata ya kike ya gida."? Cikin muryar rashin sanin waye Hauwa ta ba shi amsa jin hakan ya sa Mahmud cewa ," Kamar baki gane waye ba KO."? Murmushi tai tana cewa, "Eh gaskiya ban gane waye ba." "To Mahmud ne." Ya fad'a kai tsaye dariya ta saki tana cewa, "Gaskiya ne wallahi ban dauki murya ba , ya kake ya gidan ya su momy."? Mahmud ya bata amsa cikin girmamawa nan su ka yi hirar da bata kai minutes 6 ba sukai sallama da juna . Yayin da Mahmud ya fara bacci bisa kujerar da ya kwanta. Tun tuni su Alaji Idris sun baro kauye sun nufo hanyar gida....... Wayar Kalisa ce ta fara ruri , hakan ya sa baba anje dake kusa da wayar tana caji ta fara kiran sunan Kalisa kafin ta iso kiran ya yanke, " Kaiii ai dady ne ya kira." Ta yi maganar tana kokarin bin kiran , sai dai kafin ta kira ya sake kira "Gaskiya aunty Kalisa girkin nan ya yi dadi." Nabila ta shigo falon tana fad'a Jafar ya harareta yana cewa, "Wannan wanne irin abinci ne tun d'azu ba a gama ba." Kalisa ta kara wayar a kunnenta tana cewa, "Hello dady har kun dawo."? Wata kakkausar murya taji tana cewa,"ke ce Kalisa."? Jin hakan ya sa duk hankalinta ya tashi " Eh ni ce ina dadyna fa." Daga can bangaren aka sake fadin ,"Sun sami accident, yanzu haka suna asubitin dake Kuje Abuja." Wani mummunan faduwar gaba taji tare da mugun jiri ya ziyarceta ta sullubar da wayar cikin mugun yanayi Duk su baba anje suka yo kanta tare da matukar damuwa da tambayoyi Daurewa tai ta basu amsa da cewa "Su momy ne sukai accident, suna Kuje hospital." Idanunta matukar ruwa suka kawo , yayin da ita Nabila ma ta bud'e bakin kuka . Jafar bai ce komai ba kawai tsaye ya yi ya kasa motsi Baba anje cikin tashin hankali ta ce da Jafar , "Jeka sanarwa Garba , ya zo yanzu mu je musan halin da suke ciki." Jafar ya fita da ker ya shiga gidan Garba , aiko yana sanar masa ya fito cikin tashin hankali, duk suka rankaya suka nufi asubitin Bayan sun je asubiti, suka sami doctor suke sanar dashi akwai wanda aka kawo sun yi accident likitan cikin far a ya kalli nurse din dake gefenshi sannan ya kallesu yana cewa, "Ai karku damu mun yi musu aiki nan da anjuma zaku gansu." "Alhamdulillah." Garba ya fad'afad'a Nurse din ce ta kalli doctor tana cewa, "Dactor ina tunanin fa , wanda aka yiwa aiki , ba su ne 'yan uwansu ba , kuma accident biyu ne ya faru yau wanda muka ansa a nan." Wani firgici suka sake shiga dajin batun nurse Likitan ya cire tabarau din sa yana cewa cikin turanci ,"Haka ne ." Ya kalli Garba ya ce ,"ku ne masu mata biyu.? wanda aka yiwa aiki. "? Cikin gagarumin matsanaicin kuka Kalisa ta ce ," No dactor mu fa kiranmu akai d'azu." Likitan ya maida gilashinsa yana cewa "Okay sorry, police ne suka kira ku , ina mai baku hakuri, ku je mutuware." Yana gama magana ya wuce Tashin hankali😿 Mutuwaren suka ne ma cikin mummunan yanayi , suna isa suka tarar da police men . "Wai da gaske sun mutu." GARBA ya tambayi daya daga cikin police din cikin tashin hankali nan aka tabbatar musu duk sun ruga mu gidan gaskiya har driver. Nan ne fa wani kuka da zaucewa ya same su , "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'u, la'ila ha illallah...." Nabila tana fad'e cikin tashin hankali Jafar ya kalli yayarshi Kalisa dake tsaye tana kallon gawarsu kawai yaji wani kuka ya kuf ce masa ya fadi kasa yana kiran sunan Allah a sannan Kalisa ita ma ta sake fashewa da kuka ta nufi gawawwakin tana cewa ,"Kun gani momy , ku dubi Nabila da Jafar irin halin da suka shiga , ko dan haka karku mutu , ba dan ni ba , momy dan Allah wannan wacce irin mutuwa ce." Ta kwanta jikin Alaji Idris tana kuka baba anje gefe taja tana salati,tana kuka har da majina Garba kuwa Allah ya kawo masa dakewa a halin yanzu amma yana matukar tashin hankali kallon su ya yi yana cewa, "Ku yi kuka wallahi, ku yi kuka , Allah ya kawo mana jaraba." Idanunshi sun yi jajir mota suka hau tare da su domin zuwa ai musu suttura ana cikin motar ana tafiya, Garba ya ciro wayarshi ya fara sanar da mutane lokacin da ya zo kan numbar malam Shehu ya fashe da kuka yana cewa, "Yanzu su Alaji sun baro kauye lafiya, Yanzu kuma na sanar musu da mutuwarsa, innalillahi wa Inna ilaihir raji'un."😭 Wayar ta zame a hannunshi tai kasa ya cigaba da kuka , hakan ya sanar da malam Shehu nan shi ma ya rikice ya kid'ime da jin zancen, shi ma ya sanarwa da sauran mutane ai kuwa kafin ka ce komai su ka yo zuga suka taho cikin jimami . Bayan an isa gida babu abin da ya canza na tashin hankali haka akai musu wanka , tare da dukkan abin da addini ya tanadarwa mamaci sannan aka kaisu ,wajejen magariba. Allah ya sa mu dace . Bayan idar da sallar magariba, Mahmud yana zaune yana jiran dawowar Ahmad mota yaji daga can harabar gidan, hakan ya sa ya yi sauri ya fito " Me zan gani"? Mahmud ya tambayi kanshi cikin tsananin fusata Harun ne ya fito daga motarshi yana murmushi ga Mahmud, hakan ya sake hassala Mahmud ya nufi wajen shi "Gurin wa ka zo a nan gidan? , na ce gurin waye."? Ya yi maganar cikin huci yana niyyar naushinsa cikin gadara da isa da samun guri Harun ya ce ," A'a gurin budurwata na zo mana Zainab. " Hannu Mahmud ya kai jikinsa ya sha'ke wuyansa ,"Harun zan kashe ka , ka fita daga rayuwar Zainab, ba irinka ba ce , ka lalata mini Asma'u , Zainab kuma kanwata ce ka rabu da ita Harun, wallahi ba zan barka haka kawai ba." "Kamar ya , Yaya Mahmud mene haka , ka sake shi." Zainab ta karaso tana fad'a cikin bakin ciki Mahmud ya kalli Zainab yana cewa, " Me ya sa haka Zainab, karki fad'a tarkon sa , Harun mayaudari ne , azzalumi mara tausayi , shi ne wanda ya lalata mini Asma'u." Ya aje maganar yana huci "Harun mutumin kirki ne , ba shi da wani aibu , kawai kana kishi dashi ne." Zainab ta aje maganar cikin 'bacin rai da jin haushin Mahmud. Ina jiran comment a private mara adadi fa 😎 saina jiku Share and comment and like..........📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> page 15& 16 Wani abu Mahmud yaji ya tokare masa zuciya hakan ya sa duk ya rasa kalaman bakinsa Cikin nutsuwa da sanyin murya ya fara cewa ,"Kishi kuma , Harun Guba ne mai girma , yana da illa , Zainab karshen magana manemin maza ne ." Da sauri Zainab ta kalli Harun cikin tashin fahimtar abin da Mahmud yake fad'a hakan ya sa Harun saurin faraiwa Zainab magana ,"Wannan ba gaskiya ba ne Zainab, Mahmud ka ji tsoron Allah mene na tare maka." Wani bacin rai ne ya tokare Mahmud "Minutes biyu na baka , ka fita daga gidan nan , karka sake kula Zainab ka fita daga rayuwar Zainab." "Dakata yaya Mahmud, ba ruwanka dani , ni shi nake so , ai ba haka ya kamata ka nuna kishinka ba , kuma dan kana yayana baka da wannan damar a Rayuwata." Zainab ta fad'a cikin bacin rai Cikin mamaki da takaicin kalamanta ya fara magana "Matsayina ya wuce haka a rayuwarki, kuma ban damu da gun uban wa ya zo ba , dole ya fita yanzu, kuma ko ba komai ni na isa nayi hukunci a gidan nan ." Ya koma ya kalli Harun yana cewa, "Minutes daya na baka , wallahi idan baka fita ba sai na fasa motarka." Harun yanayin Mahmud ya razana shi , hakan ya sa ya hau mota ya fita , Zainab na kiranshi . Bayan Ahmad ya dawo Mahmud ya sanar dashi komai , tun daga Asma'u har ranar yau . Ahmad ya ce ,"Ni wallahi na yi zaton ya canja halinsa , shi ya sa na yadda har yake rabata , tabbas dole ya bar Zainab kuma zan sameta . Abin mamaki yana nan da halinsa." Ahmad dai abin ya taba shi sosai ya ba shi mamaki Anan kuwa cikin hotel Fa'iza da Uncle Yahaya sai wanda ya gani tana kwance jikinsa yana shafa kanta tare da cewa ,"Ni dai na shiga uku , idan kin tafi gobe ya zan yi." Dariya Fa'iza tai tana fad'in ,"Wallahi ka shirya mu tafi tare , domin ni wallahi bana iya zaman kano ta ishe ni , dama soyayyarka na zo nema kuma na samu." Uncle Yahaya ya ce ,"Kin samu kuwa , domin ni duk bana ganin wasu mata sai ke Ina matukar son ki baby." Fa'iza ta tashi zaune tana masa wani irin kallo . Yanayin kallon ya sa yaji...... Laila tana matukar cikin damuwa da rashin kulawar uncle Yahaya, ga shi ita ba waya gareta ba , zaune ta ke ta yi tagumi cikin falon gidansu hawaye fal cikin idanunta tana tambayar kanta ,"Wai shin Uncle me ya sa haka , wallahi zuciya ta , ta damu da kai sosai , me ya sa nake kaunar ka haka , ya Allah ka dawo da Uncle gare ni." Daga wajen gida taji karar motar shigowar barrister Adam , wato mahaifinta hakan ya sa ta sami nutsuwa. Washe gari da safe Fa'iza ta koma legos, Uncle Yahaya dai ko kadan bai ji dadi ba , yana komawa gida ya sami kakarshi cikin mugun yanayi na zazzabi, wanda dole sai da suka tafi asubiti. Yau kwana guda ke nan da rashinsu Alaji Idris, duk rayuwar su babu dadi, babu farin ciki , mutane suna girgiza idan suka ji wannan zancen mutuwa, haka Umar abin ya taba shi sosai , musamman ganin Kalisa cikin yanayi mara kyau. Haka Sahid da mahaifinsa malam Aminu abin ya bige su . ⚡🌹⚡ Tom ni Fatima Abdallaah kano Ina sanar daku akwai masu yawo suna 'bata mata suna wato ana bud'e group na batsa na iskanci ana dora novels din mu jikin wannan link ana share. zaki shiga d nufin samun novels, tom sai ki ga ba haka ba dan haka muna sanar d ku ba mu bane ba kuma zamu yafewa wanda suke shirin 'bata mn suna ba A kiyaye ⚡🌹⚡ A ranar yau kakar Uncle Yahaya ta rasu , tabbas ya ci kuka sosai , haka aka shirya daluban makarantar DR .D.D suka je gaisuwa. Allah ya jikan musulmi Harun yana matukar takaici da abin da Mahmud ya yi masa amma babban farin cikin da yake samu Zainab sam bata yadda ba , hakan ya ke faranta masa rai . Sun zana jarabawarsu , wanda hadda Umar Ahmad ya sami Zainab ya mata fad'a sosai a kan Harun, ta ga bacin ran sa , wanda sai da ya yi niyyar sanar da Alaji Kabiru mahaifinsu , amma Mahmud ya ce kar ya sanar dashi tukun zata gyara . Yadda Zainab take ganin Mahmud ya shiga tsakaninta da Ahmad ya sa ta dena kulashi , tana matukar jin haushinsa, kuma ta sanar masa ba za ta rabu da Harun ba. Yau an gabatar da addu'ar bakwai ta su Alaji, mutanen kauye sun zo da matukar yawansu, wajen yamma kuwa kowa ya watse in ka cire mutanen anguwa dake shigowa jefi-jjefi su yi gaisuwa Iyalan Garba ne shirye tsaf sun fito harabar gidan, Kalisa ce ta kalli Garba tana cewa ,"Dan Allah Baba Garba kai ma tafiyar za kai , ka bar mu , ai muna jin dadin zama dakai." Nabila ce ta ce ,"Haka ne wallahi mun jin sauki idan kana nan." Baba anje da Jafar basu ce komai ba dai , face tsayawa suna sauraron abin da kowa yake fad'a cikin kasalalliyar murya da rashin kwarin gwiwa Garba ya fara magana "To ya zami da mutuwa, ta tozarta mu babu yadda muka iya , kuma ni ba kud'i ne gare ni ba , zamana daku wahala zai ja , gatana Alaji ne , kuma yanzu babu shi , mota ta an sace Allah bai nufi ya canza mini ba , ya rasu , bani da komai , gara na koma kauyen zan fi nutsuwa." Ya aje maganar cikin rauni d'aga kai ya yi yana sake cewa ,"Duk abin da ya taso da kuke da bukatata , ku kirani." Baba anje ya kalla yana cewa, "Dan Allah Baba, kiyi hakurin zama da ...." Baba anje dakatar dashi tai tana cewa, "Haba Garba , yaran nan sun zama amana a gare ni , babu yadda na iya , Alaji da Hajjiya sun wuce haka , kuma ta su ta yi kyau , sai dai mu ce Allah ya jikansu da rahma ya kuma sa mu dace mu ma ." Matar Garba ce ta ce ,"Ameen ya Allah. " Haka su kai sallama da juna Garba ya tafi . A yanzu dai Uncle Yahaya sai Allah, domin tun tafiyar Fa'iza ya haukace da neman mata , lokacin da ba ya goyawa Harun ba ya a kan hakan fad'a suke , amma yanzu Uncle Yahaya sanda Harun ya kirashi ya masa gaisuwar kakarshi , yake ba shi labarin yadda yake fantamawa da karuwai , Allah ya sa mu dace Yau Laila tana cikin farin ciki ta yi wa Uncle Yahaya kalamai wanda ba ta taba masa ba , ta tabbatar wa kanta Uncle zai sakko daga yajin da ya yi mata , hakan ya sa ta tafi makaranta cikin kwarin gwiwa. Cikin zumudinta ta aikawa da uncle wannan wasika mai matukar dadi da kwantar da hankali har Khadija na tsokanarta yau uncle zai susuce dariya laila ta yi tana cewa, "Zuciyata tare data Uncle take bugawa da zarar ya barni to zata tarwatse." Dariya Khadija tai mata tana cewa, "An fa kusa tashi ga shi Uncle bai kiraki ba." A lokacin ta ji karar kararrawar makaranta, Laila ta 'bata rai tana cewa, "Aikin banza , wai ina Uncle ya shiga." Khadija tashi tai ta dauki Jakarta tana cewa, "Wallahi ba zan jiraki ba, indai sai kin tsaya wajen shi ." Laila ganin Khadija zata tafi ta barta ya sa ta fasa ganin Uncle ba dan taso ba , Cikin matukar bacin rai Uncle ya koma gida "Wannan yarinyar ni zata wani rubuta wa kalamai , to ni yanzu har akwai yarinyar da zan tsaya ina soyayya da ita , Allah ya kaimu gobe , zata gane kuskurenta kuwa , ga mata nan wacce nake so ita zan samu , zan yi maganinki." Kiran wayar Fa'iza ne ya sa ya sarara da maganar ya dauki kiran. Har dare ya yi Laila da matukar shaukin Uncle ta kwanta A washe gari da safe ta shirya cikin uniform din makaranta ta tafi Sakamakon yau talata d'alubai suna ta mamaki da aka ce su fito assembly, shi kan shi shugabàn makaranta duk sun fito da sauran malamai haka Laila ta ringa amfani da wannan damar tana hango Uncle Yahaya tana kallonshi tana jin dadi .Sai dai shi Ko ta tata ba ya yi , sai dai ma idan ka kula kana iya ganin tsantsar rashin mutunci a idanunsa . A lokacin Uncle Yahaya ya fara magana cikin muryarsa mai dadi ga kunnen Laila. "A yau cikin wannan makaranta." Uncle ya fara magana yana kallon malamai da d'alubai . Washhh Allah na kuna sa ina dena typing da rashin like d comments wallahi🙏 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Page 17&18 "Akwai wata sabuwar d'abi'a da d'alubai suka shigo da ita , wanda hakan yana jawo raini da lalacewar tarbiya, to gaskiya ba za mu yadda da wannan abin ba , kuma zamu fara hukunci a yau ga irin wannan d'alubai." Wani fad'uwar gaba Khadija ta ji ya bugar mata zuciya, ta kalli Laila , amma ita Laila sam babu wannan yanayin a tare da ita "Mene Uncle ya ke nufi."? Khadija ta tambayi kanta cikin tashin hankali, Lokaci guda kuma tana tana maida hankali ga Uncle Yahaya da ya cigaba da magana. " Laila Adam. Fito waje." Uncle Yahaya ya yi maganar da turanci Sai a lokacin Laila wani firgici ya sameta , tashin hankali ta sami kanta tare da tunani kala-kala, a kan Uncle ko dai ba lafiya yake ba . Jin ya sake magana ne ya sa ta sake furgita ta fara takowa domin fitowa Saman gurin ta hau tana raba idanu "Kun san mene ta aikata." Uncle Yahaya ya tambayi d'alubai d turanci . Suma cikin irin harshen suka ce masa "A'a." "Yanzu zata fad'a muku abin data aikata , kuma duk wacce take shirin aikatawa, ita ma hukunci zai biyo baya ." Shugaban makaranta dake zaune yana saurara ya ce ,"Gaskiya ne ." Khadija wani yanayi ta shiga na matukar damuwa , haka Laila mamaki ya isheta Takardar ya amsa wajen shugaban makaranta ya mikawa Laila Adam Rassss taji zuciyar ta ta bada tare da wani saurin bugawa da take yi Kallonshi tai cikin tashin hankali ba tare da ta amshi takardarba "Karbi mana ki karanta musu abin da kika aikata." Yadda ya yi maganar cikin tsawa ya sa ta saurin amsa hannunta na rawa a lokacin data amsa ya tabbatar mata wannan takardar data yi masa kalaman soyayya ce "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un. mafarkina nake yi ko zahirin Rayuwata ne." Laila ta fad'a cikin zuciyarta Wani Uncle Sani ne ya daka mata tsawa da cewa ,"Yi sauri mana bamu da Lokacin batawa zamu shiga aji." Hannunta rawa yake sosai jikinta na 'bari ta fara bud'e takardar bayan ta bude ta zuba mata idanu tare da kallon Uncle Khadija kuwa Allah ne yasan abin dake ranta na bacin rai da kakkausar murya ya ce ,"Fara mana." Da malamai da d'alubai duk ita suke saurara , ta fara karanta takardar wacce ta kasa riketa da hannu biyunta . "Assalamu alaikum my Uncle, fatan kana lafiya kamar yadda nake bukata,masoyin raina ." Da sauri ta d'aga kai ta kalli Uncle Yahaya da matukar mamaki da wani mummunan yanayi, wata Aunty ce ta ce ,"Baki ji kunyar rubuta masa ba , sai kunyar karantawa cigaba dallah izina ga masu son aikatawa. " Laila ta maida kanta ga takardar wanda hawaye suka ciko mata fal har bata iya ganin rubutun da kyau . "Masoyina kafi na kowa , ina san ka fiye da komai, kai ne dadin duniyata kuma muradina a duk Lokacin da nake cikin damuwa kai ne nake son gani domin yayewarta , Ina maka san da baka tunani, son da uwa take yi wa danta, soyayya mara gushewa , abu ne mai sauki zuciya ta ta buga a kanka". Hawaye ta share yayin da wasu masu yawa suke zubo mata suna sauka a kan takardar idanunta sun yi jajir , jijiyoyin kanta duk sun tashi , ita ma Khadija ta shiga wani yanayi " Bani da burin barinka domin kai ne mahadin zuciyata, Rayuwata taka ce , na yi tanadin kauna da soyayya saboda kai , bada kwakwalwa nake son ka ba , bada zuciya nake son ka ba , da raina nake kaunar ka , Ina tunanin ka da kwakwalwata , ina rikonka da zuciya."😭 Kuka ta sake fashewa da shi mai matukar ban tausayi kowa ya yi shiru yana sauraranta Khadija kuka take kamar ba gobe Laila kam wani jiri take ji yana dibarta , tana kallon takardar idanunta amma bata iya ganin komai Sai ji suke timmmm Laila ta fadi kasa , ko shurawa ba tai ba Da gudu Khadija ta nufo ta tana kuka haka malamai duk hankali ya tashi "Dama tana da aljanu ne." Shugaban makaranta ya fad'a Cikin tsananin fusata Khadija ta nuna shi da yatsa tana cewa, "Zaka ga aljanu , ko numfashi bata yi , Allah ya sa ta mutu." Ta fashe da kuka "Ke shugaba kike fad'awa wannan maganar." wani a cikin malamai ya fada Yayin da sauran malamai suka fara kora d'alubai aji Lokacin da malamin lafiya ya zo aka duba Laila, amma ya tabbatar musu sai an tafi asubiti a sannan shugaban makarantar ya tabbatar ya ya yi kuskuren barin wannan abin da ya faru Kneel down aka sa Khadija a gefe guda yayin da suke shirin kai Laila asubiti mikewa tai Khadija ta nufi hanyar fita daga makaranta da gudu tana kuka ta nufi gidansu Laila yayin da duk malaman mamaki ya matukar kamasu da fitar ta hakan ya sa aka tura malamai mata biyu suka bita, domin a zatonsu aljanu ne Bayan sun isa asubiti aka kwantar da Laila dake asubitin gwamnati ne kuma babu wadatattun ma aikata likita daya aka samu ya yo kanta . Khadija tana shiga gidansu Laila ta sanar da mahaifiyar ta , ita ma da sauri tayiwa Barrister waya kafin ka ce komai sai ga shi ya dawo cikin tashin hankali sauran malaman da suke tafe da Khadija suka nufi asubitin sakamakon barrister Adam yana zuwa matarshi da Khadija ya dauka suka tafi . Yana zuwa ya ga da gaske Laila ce cikin mummunan yanayi, bai ce da kowa uffan ba ya dauketa ya sata a mota .A Lokacin malaman suka ringa kokarin yi masa magana , amma babu wanda ya kula a cikinsu ya shiga mota ya nufi babban asubitin yayanshi . Suma suka bi bayan shi. Tom ni Fatima Abdallaah kano Ina sanar daku akwai masu yawo suna 'bata mata suna wato ana bud'e group na batsa na iskanci ana dora novels din mu jikin wannan link ana share. zaki shiga d nufin samun novels, tom sai ki ga ba haka ba dan haka muna sanar d ku ba mu bane ba kuma zamu yafewa wanda suke shirin 'bata mn suna ba A kiyaye Kalisa ce cikin d'akin mahaifiyarsu cikin tsananin kadaici da kewa , bayan tasha kuka ta more , sannan ta zauna kan gado , wata loka dake kusa da gadon ta jawo , haka idanunta suka kai kan wasu takardu d'ebosu tai kallo guda tai musu ta ji jikinta ya mutu , a sa'ilin data fahimci takardun gidan Hajjiya ne wanda Alaji ya bata , ta mayar ta aje Wayarta ce ta fara ringin ta dauki wayar ba tare da yanayin ta ya canza ba ta ce ,"My Umar har ka zo." Umar ya yi ajiyar zuciya yana cewa, "Haba My Kalisa ta ya zan yi wasa da lafiyarki , bayan an ce yau ne dactor zai zo , kawai maza ki fito mu tafi ." Kalisa ta ce ,"Tom shi ke nan." Ta aje wayar ta fita tana fita falo ta yi sallama dasu baba anje , suka mata fatan samun lafiya sannan ta fita , tana fita Umar suka nufi asubitin,sakamakon ba nisa ne dashi ba , a kafa suka isa suna hira . Doctor jamil ne zaune cikin office dinsa tare da laptop a gabanshi , a lokacin sukai sallama suka shiga . Cikin girmamawa doctor ya tashi ya taro su , sa'ilin da ya basu wajen zama "Sannunku fa , wato Umar duk an mance damu." Doctor Jamil ya yi maganar cikin kyakykyawan yanayi Umar ya mai da masa da cewa ,"Kai fa ka fiye surutu dan Allah haba naga kusan kullum muna gaisawa a online. " Jamil ya ja tsaki yana kallon Kalisa da cewa ,"Kalisa ya karin hakuri. "? " Mun gode Allah dactor. " Kalisa ta ba shi amsa a lokacin wata nurse ta shigo , yayin da Doctor ya kalleta tare da mika mata wata takarda yana cewa,"Ku je tare da Kalisa ai mata wannan gwaje-gwajen , yanzu fa ." Nurse din ta amsa yayin da Kalisa ta bi bayanta . Umar suna zaune suna hira ba jimawa Kalisa ta shigo da takardar binciken lafiyar da aka mata. Ta mikawa dactor sannan ta zauna tana kallon Umar yana mata murmushi. Bayan dactor ya bude sakamakon ya yi ajiyar zuciya yana kallon Kalisa .Wanda duk hankalinasu ya koma ga dactor Jamil . A zube min comment a private mu had'u next page. Share, like and comment.........,📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Page 19&20 Ba editing "Wato Kalisa zahirin gaskiya wannan ciwon naki , sai an miki aiki , domin a halin yanzu ma hunhunta ya samu matsala." Ya karasa maganar yana kallon Umar wani faduwar gaba Umar ya ji ya bigi zuciyarsa , "Kuma gaskiya wannan aikin na gaggawa ne , don haka zan yi magana da dactor Aisha dake babban asubiti, zan tura ku can ." Doctor ya kuma fade Kalisa cikin mutuwar jiki ta kalli Umar tana cewa, "Ka ga ni ko Umar , na kusan mutuwa." "Haba Kalisa ai cuta ba mutuwa ba ce , an yi wa mutane da yawa aikin kuma sun sami lafiya dan haka kema insha Allah zaki warke , saidai aikin gaskiya akwai kud'i sosai ,duk da nasan baku da matsalar sa ." Umar ya ce "Yanzu dai yaushe ne za mu je asubitin."..... Ahmad ne yake wa Zainab fad'a sosai a kan Harun, amma sai kare shi take tana nuna Mahmud ne yake son bata masa suna , Ahmad saida ya matukar yi mata gargadi tare da mata barazanar sanar da Alaji abin dake faruwa duk da hakan dai har zuciyarta bata shirin barin Harun . Kalisa har sun je wajen doctor Aisha a yau , nan ta tabbatar musu da dinbin kud'in da aikin zai ci . Bayan sun dawo gida suka sanar da baba anje komai . Nan akai waya suka sanar da Sahid halin da Kalisa ke ciki ga kuma irin kudaden da ake bukata Nan ya tabbatar musu ba wata matsala zai turo da kud'in har yake sanar musu ma zai basu dukiyarsu ta dawo wajensu. Amma har washe gari shiru , Sahid bai ce komai ba , wayarshi ma a kashe Jafar ya je companin da Sahid yake aiki amma bai samu ganin shi ba . A halin yanzu Laila ta sami lafiya, amma har yanzu Barrister Adam bai ce da makarantar DR.DD komai ba Ansha matukar jinya kuma ana kansha a kan ciwon Laila , barrister yana kashe kud'i sosai babban abin da ya ke ci masa rai wai Laila 'yarshi za a wa wannan tozarci har hakan ya jawo mata ciwon zuciya. Rashin sanin irin matakin da zai dauka a kan makarantar ya sa har yanzu bai ce komai a kan lamarin ba . Su ma malaman makaranta sun shiga rudani , musamman ma shugaban , yarinya ta kamu da ciwon zuciya lokaci guda , to da zuciyar bugawa tai ta mutu fa . wannan kaddara ce ta shigo masa makaranta, kuma yadda ya biyewa Uncle Yahaya har hakan ta faru . "Wai Khadija yaushe zaki dawo makaranta". Wata Zainab kawarta ta fad'a Khadija ta kalleta tana ta'be baki ta ce ," Ni na bar wannan makarantar wallahi, domin dady ma ba zai takurani ba." Zainab ta ce "To Allah ya kyauta ya bawa Laila lafiya, ni Wallahi ma abin da yake bani mamaki ashe da gaske Laila haka take son Uncle, ki dubi yadda zuciyarta ta so bugawa. ai wallahi Allah zai saka mata." Khadija da duk kan 'bacin rai ta kalli Zainab ta fara magana, "Ai wallahi Uncle ya yi asara , kuma jira nake kawai dadyn Laila ya yi magana." Zainab ta ce ,"Allah dai ya kyauta." Cikin tsananin fad'a baba anje take magana "Wannan ai wulakanci ne , haka ake yaron nan ya bamu kud'i amma har yau shiru , tun yaushe ake masa magana kuma kullum ciwon Kalisa girma yake." Umar dake zaune a gefe guda cikin falon ya girgiza kai alamun goyon bayan abin da baba anje take fad'e Jafar ne ya ce ,"Gaskiya kam dai Sahid bai kyauta ba kaka , to mene abin yi." Kalisa ta ce ,"Me zai hana muje gidansu yanzu Umar, kasan babanshi abokin dady ne, kuma da zarar mun je zai masa magana. " Baba anje ta ce "Eh gaskiya ne Umar ku tashi ku je yanzu domin wannan lamarin bana zama ba ne ." Kalisa cike da kwalla ta kalli baba anje tana cewa ," Muna matukar godiya Baba anje , kina tsayawa da nuna damuwa a kan lamuranmu Allah ya baki.......". Dakatar da ita tai tana cewa, "Haba Kalisa ai zan tsayawa lamarin ku bakin rai bakin fama ku amana ne gare ni . Tashi ku je kawai a dawo lafiya ." Umar ya tashi yayin da Kalisa tabi bayanshi , sannan ta juyo ta kalli Jafar tana cewa, "Bari na tafi da mota jafar." Jafar ya ce "To a dawo lafiya daman akwai mai a ciki ai." Suka nufi harabar gidan ita da Umar. Anan kuwa cikin makaranta duk kan malamai sun had'u suna tattaunawa a kan matsalolin makaranta, ana cikin haka wani mutum ya shigo a mashin guri ya samu ya yi burki sannan ya sauka ya nufi ofishin shugaban makaranta, ai kuwa duk malamai suna cikin office din mutumin karasawa ya yi yana gaida shugaba, sannan ya mika masa sako ya fito , bai jira cewar komai ba ya fito ya hau mashin din sa ya tafi . "Ikon Allah". wani a cikin malamai ya fad'a, Uncle Yahaya ma yana zaune shugaban makarantar ya bud'e takardar jin abin da Dr Dauda ya fad'a yasa duk hankalin malaman tashi Cikin yaren turanci wata malama yare ta ce ," Me ke faruwa sir." Sauran malaman kunne suka kasa domin jin amsar da zata fito daga gareshi , domin a halin yanzu suma ita ce damuwarsu Ido ya kafa wa uncle Yahaya cikin tashin hankali, hakan ya sa Uncle tsarguwa yana cewa ,"Shugaba lafiya kuwa." Cikin zafi shugaban makarantar ya tashi tsaye yana cewa, "Barrister Adam ya shigar damu kotu , wannan takardar tuhuma ce ." Ya karasa maganar yana cillawa Uncle Yahaya takardar Wani tsoro da mamaki ne ya ziyarci malaman Dr. Dauda ya zauna yana kifa kansa kasa yana cewa, "Innalillahi, yanzu sunan wannan makarantar zai baci a idon duniya , na tabbatar har mane ma labarai za su yad'a wannan case a labaransu , innalillahi wa Inna.....". Uncle Sani ya kalli sauran malamai yana cewa," To yanzu mene abin yi , ya kamata a nemi mafita wallahi. " Dacter ya dago kai yana magana cikin tsafi ,"To yanzu mene mafitar." Yanayin yadda ya yi maganar suka sha jinin jikinsu , musamman ma Uncle Yahaya. Tafiya suke cikin mota , Umar yana tu'ka su kallon Kalisa ya yi yana cewa, "Ki ce dai gidan nasu da nisa. ga shi kauye, to ina zai aje min ke saboda rashin kunya." Dariya Kalisa tai tana cewa, "Wallahi kuwa da nisa." Umar ya yi tsaki yana cewa "Ai wallahi ya bani mamaki, dama fa shi dan kauye bai san arziki ba , sai ka yi masa rana ya tashi ya yi maka dare , yanzu ina amfanin wannan, garin nasu duk daji." Wani gau suka ji wata babbar mota ta bige su , a sa'ilin da sam ba su ganta ba hakan ya sa motar ta su ta kwace ta nufi daji "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un, abin da suke fad'a ke nan Umar ya bude murfin kofa da nufin su fi ce a irin wannan gudun da motar take " Kalisa fita , fita kar kiji tsoron komai. " Amma ina Kalisa duk ta rude rigarta ta makale " Kai ka fita Umar ka fitaaaaaaa". Kalisa ta karasa maganar a yanayin firgici da ta ga sun kusa dukan wani dutse . Kauuuu motar ta bigi dutse ta tashi sama , a lokacin suka fado kasa dukkansu , yayin da motar ta kama da wuta tun daga saman sannan ta fad'o kasa . Kalisa ko shurawa ba tai ba matukin waccen motar yana ganin haka ta faru kawai ya gudu abin sa ya bar su .Duk da shima yaji rauni . Cikin mummunan yanayi Umar ya tashi kanshi duk jini , yana tashi ya fad'i kasa yaja jikinshi da kyer ya nufi Kalisa. Yanayin tashin da ya yi mata ya tabbatar masa fa ta mutu bugu da kari wani karfe da ya gani a cikin gwiwarta ya tsagata . Wani tashin hankali ne ya ziyarce sa ya kwalla ihu yana kiran sunanta da dukkan muryar da Allah ya hore masa. Share ,like and comment...........📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano ( Autar marubuta) *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Page 21&22 Cikin tsantsar mazantaaka Umar ya yi jarumta ya nemi mutane Allah ya taimaa ka wasu mutane suka kawo dauki .Wanda har motar asubiti da 'yan sanda suka karaso Yadda Umar ya ga an dauki Kalisa ya sake tabbatar masa Kalisa ta tafi ta barshi Timm ya fadi kasa kamar matacce , asubitin cikin gari aka karasa dasu , tare da turasu emergency Sai ga su Nabila sha'be -sha'be cikin kuka da matukar tashin hankali suna isa wajen doctor ya fito daga d'akin Umar da sauri suka tare shi , Jafar ne ya ce "Ya jikin na su likita."? Baba Anje cikin damuwa ta kallo likita tana sauran amsa " Ita macen tana ICU room, gaskiya akwai bukatar a yi mata aiki, shi na mijin yana sume , amma nan da anjuma..... " Likita maganar da yaji a bayansa ne ya sa su duk baba anje saurin juyawa "Likita ya jikin Kalisa ta." Umar ya fad'a cikin wasu ruwan hawaye dake shirin zubo masa "Haba malam ka koma ka kwanta , komai zai iya faruwa da kai a wannan yanayi kana bukatar hutu da kulawa." Dactor ya yi maganar yana kallon Umar Umar ya karaso gabansu , kawai Nabila ta fashe da kuka ta rungume Jafar ita ma baba anje duk tausayin Umar ya rufe ta da ganin ciwon dake tare dashi "Dan Allah yaya Umar ka je ka huta a halin yanzu kaji abin da doctor ya ce ." Jafar ya yi maganar Nabila kwance a kirjinsa yana rike da hannun Umar. Umar ya janye hannunshi tare da fara cewa ," Ni bana jin komai Jafar , yanzu kawai Kalisa ce damuwar , domin karku mance akwai bukatar yi mata aiki tun kafin wannan accident din." Wasu zafafan hawaye suka zubo masa sannan ya ci gaba da cewa ,"Na ga karfe ya huda gwiwar Kalisa, na ji zafi a zuciyata kuma na bayar ta rasu , yanzu kawai lafiya zamu nema mata. " Baba anje cikin tashin hankali ta ce "Gaskiya ne , innalillahi wa inna'ilaihir raji'un." Dactor ya ce "Tom gaskiya ciwonta ni bazan iya dubata ba , ku jira kwana biyu likita yana zuwa." Yana gama maganar ya wuce Ba zato sukaji Umar ya shako sa ,"Kai wanne mara hankali ne , har gobe zamu jira tana cikin wannan yanayin, ina imaninka da tausayinka ka je fa su."? Likita da ya ji shakar sa ta yi yawa cikin wahala ya fisge ya hankade Umar "Kai mahaukacin ina ne , bari na kira security su fitar da kai." Dactor din ya karasa maganar ya nufi wajen masu gadi Umar ya ce , "Mu dauki Kalisa mu koma babban asubitin dactor Aisha hakan zai fi." Nabila ta yi ajiyar zuciya tana kiran sunan Allah . Mahmud ne ya fito waje yana duban yanayin anguwar yadda tsarinta kullum yake sake burgeshi , duba ga manyan gidaje da sanyin anguwar hakan ya sa har yau ya kasa komawa gida, har Aminu ya koma , amma shi ba shi da niyya , amma babban dalilin 'kin komawarsa a kan Zainab ne . Sake bude idanunshi ya yi yana sake kallon abin da ya hango daga gefe , kofar gidan wani mutum malam na lado , wanda har almajirai yana dasu Mahmud ido ya sake zubawa yana kallon ikon Allah "Mene Harun yake yi anan". Mahmud ya tambayi kanshi . Daga bisani lokacin da Harun ya kula da Mahmud ya yi murmushi ya nufo wajensa. " Malam Mahmud me ake kuma anan." Harun ya tambaya lokacin da ya karaso gaban shi Mahmud zuciyarshi wata irin tafasa take masa kamar ya kai masa duka, amma ya daure ya kalle shi yana cewa "Mene ka zo yi a wannan anguwar."? Harun ya sheke da dariya har da tafawa , sannan ya ce ," Mahmud ni wallahi ma dariya kake bani , to mene ya dameka dani, sannan kuma kar ka yi zaton na bar Zainab, Wallahi ban bar ta ba , kai ne kamin shamaki da ita , amma wallahi kasa a ranka da zarar na zama soja wallahi sai na kawar da kai dan na samu Zainab, ka rubuta ka aji ye ni Harun ni ne ajalinka. " Ajiyar zuciya Mahmud ya yi yana cewa, " Mu yi mu gani , kar kai tunanin dan ka 'bata Asma'u na ya zamo ina jin tsoron ka......." Mahmud bai karasa maganar ba Harun ya dakatar dashi da cewa ,"Zan yi wulakanci idan nasa kaki , wallahi Mahmud sai na wulakantaka, zaka gani." Ya wuce ya yi tafiyarsa Ran Mahmud ya matukar baci sosai , gida ya shiga cikin bacin rai , ya shiga cikin lambu ya kasa tsaye ya kasa zaune , kawai maganar Harun ce take masa yawo , cikin ranshi yake sake nanata zancen "Tabbas Harun azzalumi ne , zai aikata duk abin da yake so, yanzu mene mafita."? Mahmud ya dafa kanshi da ya farai masa ciwo " To ko dai na shigar dashi kara. "? Ya tambayi kanshi , tare da bada amsa kuma " Gaskiya 'a'a wannan ba shawara ba ce ." Ya tsuguna kamar mai shirin yin kuka , sannan ya tashi tsaye yana kallon sararin sama yana ajiyar zuciya. Da sauri ya dawo da kanshi kasa tare da rudewa da farin cikin shawarar da ta zo masa, da sauri ya shiga cikin gidan ya wuce d'akinshi ya dauko wayarshi dake caji ya zauna a bakin gado . Sannan ya fara danna wayar yana cewa, "Hhh kwananka ya kare Harun." A daidai lokacin yana kiran numbar Hauwa 'yar gidan lu'utanal Kamar jira take karaf ta dauki kiran "Ya Mahmud manyan gari kwana biyu." Ta yi maganar cikin yaren turanci Murmushi Mahmud ya farayi sannan ya ce "Ke dai bari Hauwa ai kasar ta ku ce , wallahi ina cikin tashin hankali." "Subhanallahi yayana meke damunka." Hauwa tai maganar cikin tsantsar kulawa Nan take Mahmud ya fara zuba kai tsaye "Wallahi Hauwa Harun ba shi da imani mazunaci ne yadda kika san ba dan halak ba , azzalumi ne , mata yake lalatawa ke har HIV yana d ita ." Jin ya yi shiru ne ya sa ta kwashe da dariya 😂 "Au dariya zaki mini." Ya yi maganar cikin haushi Hauwa cikin dariya ta ce ,"Yi hakuri, nasan daga ji haushin sa kake ji , domin nasan da yana kusa da kai sai Allah. To amma ni mene nawa a ciki." Mahmud ya sanar mata da komai tun daga waye Harun , har zuwa yau din nan , tare da neman alfarma ta sanar d mahaifin ta Lu'utanan nan Hauwa ita ma ranta ya baci ta kashe waya ta fita falo Mahaifiyarta Hajjiya Bilkisu na zaune ta fad'a jikinta ta kamata . "To mene kuma ko sirikin nawa ne." Hajjiyan ta fad'a Hauwa ta tashi ta bata rai tana cewa "Momy wani ne ..." Lu"utanan Sadik ya shigo ya tari numfashinta yana cewa "Ya taba ki ko me? fad'a min mamana." "Dady a cikin sojojin da zaku diba akwai Haruna Sani mu'a zu , irin wannan d'auri ne ya dace dasu." Ta karasa maganar cikin kwalla Hakan ya sa Lu'utanal hankalinsa ya tashi "Manana waye ne shi mene ya miki." Nan ta fad'a masa waye Harun kuma da kalar barnar da yake da kuma wacce zai idan ya samu aikin soja . Nan ita ma Hajjiya Bilkisu tai Allah wadai dashi yayin da Lu'utanal Sadiq Muhammad ya tabbatar wa Hauwa za ai bincike a kan shi . "Yawwa dady ina so zanje gidansu Surayya, domin tun da ta dawo daga America bamu had'u ba." "Okay gidan ambassador koh."? Lu'utanal ya tambaya. " Eh can dady." "To ki bari idan na samu lokaci sai mu je tare." Hauwa ta ce ,"Okay dady." .A halin yanzu Kalisa ta dawo hayyacinta , doctor Aisha tana iya yinta domin samawa Kalisa lafiya , sai dai ta tabbatar musu fitar da ita ne kawai mafita . Jafar har gida ya je neman Sahid sai dai tun jiya mahaifinsa ya tabbatar ba ya nan , sannan dukkan SMS din sa basa tafiya . Ran malam Aminu ya yi matukar baci sosai dana mahaifiyarsa, musamman jin halin da Kalisa ke ciki ma ya tabbatar musu gobe zai zo garin ya ga jikin nata , kuma zai nemo Sahid din in sha Allah, Jafar jikinsa duk ba dadi ya koma asubitin. Shugaban makaranta ne da Uncle Yahaya da bayis tare da wasu malamai biyu zaune a falonsu Laila. Gefe guda kuma ga Laila da mahaifiyarta zaune ,ga kuma barrister Adam ran shi bace . "Dan Allah barrister Adam ka duba wannan lamarin, mun yi kuskure sosai wanda a tarihin DR.DD ba a taba irin sa ba , amma a matsayin mu na masu ilmi mu yi sulhu dan Allah barrister." Shugaban makarantar ya aje maganar cikin tausayin kanshi . Amma barrister Adam kamar sun sake fama masa ciwo haka ya fara magana. "A she kuna da ilmin kuka aikata hakan , ni fa na gama magana kawai ku je ku nemi lauyan da zai tsaya muku , dan haka ku fitar mini a gida kawai." Idanun shugaban makarantar ya ciko da ruwa ya kalli barrister yana cewa, "Wannan makaranta ita ce cigabana rufin asirina wallahi sunan ta zai baci barrister ka taimake ni." Barrister tsaye ya tashi yana cewa "Ciwon zuciya ne ya sameta yanzu a kan ku , ta ya zan share wannan lamarin kamar ba kaunar ta nake ba ko ina jin tsoron ku." Uncle Yahaya ya yi kasa da kai cikin jin haushin kansa. Laila kuwa ganin yadda shugaban nasu Doctor Dauda ya shiga wani yanayi ya sa taji duk tausayinshi ya kamata, cikin sanyin murya Laila ta ce ,"Dady."! Barrister Adam ya kalleta yayin da duk kowa ya maida hankali gare ta . "Ni ce aka yi wa komai dady amma abin kai ne ya shafa , bani da wani farin ciki sama da kai, hakan ya sa wannan ciwon dole ya barni tun da ina tare da kai." Tai ajiyar zuciya tana sake cewa "Ina matukar girmama shugaba kuma wannan tarbiyar ku ce Duk abin da ya faru da kai wanda ba za ka taba mancewa dashi ba kuma idan ka tuna kanajin ciwonsa to wannan shi ne Gubar Rayuwarka." Ta aje maganar tana kallon uncle Yahaya ,yayin da ya yi kasa da kanshi . Mahaifinta ta kalla barrister Adam tana cewa "Dady dacter ba shi da laifi dan Allah ka janye karar." Kowa ya kalleta cikin mamaki tare da sa'ke-sa'ke kala-kala da kowa ya ke yi a ransa. Cikin wani Murmushin ta kaici barrister Adam ya ce "Babu ruwanki Laila wannan maganar kar na sake jinta a bakin ki , dole ne na dauki mataki, shin ko baki san wanne kalar jiwo suka jawo miki ba ne , ke ce kawai Allah ya bani kuma duk wanda ya yi kuskure irin wannan dole hankali na ya tashi idan ban dauki mataki ba Laila." Cikin hawaye Laila ta tashi tsaye tana kallon barrister da dukkan girmamawa ta fara magana. "Dady ni kaina nasan kana kaunata , amma wannan shi ne Gubar Rayuwata domin ba zan taba mancewa ba amma dan Allah dady ka janye karar." Ta karasa maganar yayin da wasu hawaye suka zubo mata. Hakan ya sa barrister Adam ya kalli Uncle Yahaya yana cewa . Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Page 23 & 24 "Laila ina kaunar ta." Ya fad'awa Yahaya sannan ya kalli doctor ya ce "Na janye karar tare da sharadin matukar Laila ta mutu sanadin wannan ciwon to akwai babban tashin hankali." "Babu abin da zai samu Laila in sha Allah barrister, sannan na yi alkawarin duk in da magani yake zan ke nema mata har ta sami lafiya." Shugaban ya yi maganar cikin tashin hankali da rawar murya "Lafiya ta Allah ce kuma ni zan cigaba da nema mata magani , dan haka zaku iya tafiya nasan kun bar d'alubai a makaranta." Barrister Adam yana gama maganar ya shige ciki . Sannan suka yi sallama da Hajjiya da Laila suka fito DR Dauda cikin fusata ya fito ranshi matukar bace suka dauki hanyar makaranta, babu wanda ya ce da kowa komai har suka isa makarantar Suna shiga shugaba ya sa a fito assembly hakan ya sa wasu malaman mamaki da tunani Bayan kowa ya fito suma malaman suka hallara Kowa yana iya ganin 'bacin rai da damuwa a fuskar dactor, Bai jira wani gabatar da abin da aka saba ba ya fara magana "Wato duk kun debi zancen Laila kun yada a gari ta fadi ta kamu da ciwo , shi ke nan ina jan kunnenku da duk yarinyar da wani malami ya ce yana sonta suka fara soyayya zamu dauki mummunan mataki wallahi a kan su." Ya kalli Uncle Yahaya sannan ya ce " Daga yau mun sallami Yahaya a wannan makaranta, babu wanda zaike kawo mana farmaki ba mu dakatar dashi ba , idan kunne yaji ." 'Dalubai suka karasa masa maganar cikin murya mai karfi Wani abu ne ya tirnike zuciyar uncle Yahaya da abin da shugaba ya yi masa . Hakan ya sa bayan ya koma office ya je ya same shi "Shugaba sallama ta fa kayi gaban d'alubai." Uncle Yahaya ya yi maganar cikin maraici haka shi ma shugaba ya fara magana "Hukuncin da zan maka ke nan domin haka ne ya dace da kai , kuma kaji ka sani ko albashi ba zan biyaka ba , zan yi amfani dashi na gyara 'barnar da kamin cikin makaranta, fitar mini a office." Uncle Yahaya ya fita cikin damuwa ya nufi gida . koda yaje gidan ya ga ya masa duhu kakarshi ta bar masa duniya , babu wani hanyar samun kud'i da yake dashi yanzu, bare ya nemi matan da ya saba , duk yaji duniya ta masa zafi sosai . Yana cikin wannan yanayin ne sai ga kiran Fa'iza ya shigo masa , ba tare da ya boye yanayin da yake ciki ba ya fara magana da ita . Da baba anje da Nabila ne zaune a d'akin Kalisa dake asubiti, a wannan lokacin ne baba ta kàlli Kalisa tana cewa "Yau dai Kalisa na ga jikin naki da sauki Allah ya dorar dashi." Kalisa cikin zuciyar ta ta ayyana cewa "Kawai dauriya nake baba , amma Allah ne yasan abin da nake ji." Nabila ce ta ce "Amma aunty Kalisa cikin ba ya ciwo ko."? Kalisa tai murmushi kawai Umar da Jafar ne suka shigo a lokacin tare da sallama " Ina kuka shiga ne haka tun safe."? Baba anje ta fad'a bayan ta amsa sallamar Umar ne ya fara magana yana kallon Kalisa cikin kauns "Tun da har yau babu labarin Sahid a kan me zamu zauna to baba , mun fita neman kud'in da za a mata aiki , kuma a halin yanzu mun sami dubu dari biyar ." Nabila ce ta ce "To yaya Jafar me zai hana mu siyar da gidan da muke ciki." Jafar yayi ajiyar zuciya tare da cewa "Nabila komai fa yana hannun wannan azzalumin babu takardun gidan ." Umar ya yi ajiyar zuciya Kalisa ce cikin wata muryar tsananin wahala ta ce "Akwai takardun wani gidan momy da dady ya bata , nasan zamu sami kudaden da zasu isa idan aka siyar." "Alhamdulillah Allah mun gode maka." Baba ta yi maganar Jafar ya ce aiko ba wasa za a yi ba yau za a siyar dashi in sha Allah komai zai tafi daidai." Umar ya ce "In sha Allah kuwa." Kalisa ta kira Umar kusa da ita cikin kasa da murya ta ce "Ina matukar kaunar ka." Koda yaji hakan sai ya ja da baya cikin tausayi da wasu hawaye a cikin idanunsa Sannan ya dago ya kalleta ya ce "Ni ma ina kaunar ki Kalisa zaki samu lafiya in sha Allah." Baba anje ta ce "Allah kai ne abin godiya, ka bawa Kalisa lafiya." Nabila ta amsa da "Amenn." tare da sake cewa "A gaskiya ya kamata a sanar da baba Garba duk ba su san abin dake faruwa ba." Baba anje ta ce "Gaskiya ne za a sanar dasu." Sallama da aka yi ne ya sa duk hankulansu ya koma kan kofar Mahaifan Sahid ne suka shigo nan aka basu wajen zama zamansu ke nan Kalisa ta fara shure- shure hakan ya tayar da hankalin kowa saida aka kira dactor Aisha bayan ta zo ta mata abin da ya dace har ta samu bacci . Cikin tashin hankali malam Aminu yake tambayar dactor "Yarinya meke damunta haka." "Baba tana dauke da mummunan ciwo a cikinta, kuma kullum tsanani yake karawa , sannan da fari kasar waje za a kaita , amma a halin yanzu an sami asubitin da za mata aikin , kud'in ne ba su samu ba , kuma ni gaskiya babu abin da zan iya mata kawai aiki take bukata , sannan a gwajin da mukai dalilin accident din nan karfen da ya tsagata ta sami cancer., Amma in sha Allah da zarar an mata aiki komai mai wucewa ne ." Bayan ta gama ta musu sallama ta fita Malam Aminu ya ce "In sha Allah." Umar ya yi ajiyar zuciya yana cewa da Jafar "Mu je a nemi dillalai wannan ba abin zama ba ne Jafar." Jafar ya ce "To yaya Umar." Ya tashi cikin kasala da matukar damuwar da yake ciki . Kafin su kai ga hanyar fita wani saurayi ya shigo cikin d'akin tare da sallama, nan take malam Aminu ya shaida shi ya caf ki sunan shi "Sani." Saurayin ya amsa tare da gashshe shi , sannan ya kalli Jafar yana cewa "Don Allah ka yi hakuri tun shekaran jiya MD Sahid ya bani sako a company amma ban kawo ba na mance ." Ya Ka rasa maganar yana ciro wata takarda da aka sata a gidan sirri ya ba shi . Ya musu sallama ya fita, kowa mamaki ne ya rufe shi har Kalisa da ba komai take iya ganewa ba. Bayan ya bud'e takardar ya karanta a zuciyar shi , bayan ya gama ya yi shiru , yayin da ya barsu cikin tashin hankali dalili kuwa sun ga tashin hankali a tare dashi . Mahaifiyar Sahid ce ta bude baki tana cewa dashi "Yaro mene a ciki me ya aiko haka." Jafar ya kalli Kalisa cikin tsananin tashin hankali Yadda Umar abin ya yi masa ciwo kawai ya karbi takardar ya fara karantawa shima a zuciyar sa Bayan ya gama irin yanayin da ya shiga har yafi na Jafar "Haba dan Allah wai mene wannan yaron ya rubuto kun yi mana shiru." Cewar mahaifiyar Sahid Baba anje ta karbi takardar ta bawa Nabila. "Nabila dan Allah karanta mana sun bar mu a duhu." Baba ta yi maganar cikin damuwa Idanunta fal da hawaye ta karbi takardar cikin rawar jiki muryarta na rawa ta fara da cewa "Assalamu alaikum. Kalisa ku yi hakuri amma a halin yanzu babu wani kud'i da zaku samu duk da naku ne , ba zan baku komai ba balle ku fita kasar waje, a halin yanzu nayi biza ina birtàniya kuma ina da hakki cikin dukiyar Alaji Idris don haka na tafi na ci nawa .Sai wata rana." Cikin mummunan yanayi Nabila ta aje karatun tare da tashin hankali "Na yi asarar haihuwa , Sahid mutumin banza ne wallahi, Allah wadaran ka." Mahaifinsa ya yi maganar cikin kuka lokaci guda kuma ya fad'i kasa Hankalin matarshi ya tashi , hakan ya sa duk su Umar suka yo kanshi , da gudu Nabila ta fita kiran likita tana zuwa wajen doctor Aisha ta turo wasu nurse zuwa wajen shi . Bayan sun kanshi daki cikin hanzari ita ma dactor ta shigo dakin domin taimakon gaggawa . Zuuuu duk suka fita Nabila da Kalisa aka bari a dakin . Lamarin yana dukansu , a can daga waje kuwa mahaifiyar Sahid kuka take tana cewa, "Wallahi shi ke nan malam mutuwa zai , zuciyar shi ta buga , yaron nan duk irin hidimar da Alaji Idris ya mana bai gani ba , Allah wadaranka Sahid, ka yi asara ka kashe mahaifin ka , wallahi ba zan yafe maka ba." Baba anje ce ta fara bata hakuri cikin rarrashi "Ki yi hakuri , ba mutuwa zai ba , babu abin da zai same shi ." Ta fusge jikinta a jikin baba anje tana cewa "Ni nasan halin malam wallahi, shi ke nan malam sai mun taho." Tana gigicewa da kuka Ran Umar da Jafar duk ba dadi , Allah ne yasan ciwon dake ransu . Dactor Aisha tana nuna kwarewa , yayin da tai saurin masa abin da yake bukata hakan ya tabbatar mata yana da rai . Yayin da daya a cikin nurse din ke shiran sa masa ruwa ne , ya fara fisge fisge sai aman jini. Nan doctor Aisha ta dawo kanshi . Anan waje kuka kawai matarshi take , cikin kukan ta kira yayan Sahid take fad'a masa malam Aminu ya mutu, cikin tashin hankali ya fanno asubitin. Zama ta yi dirshen tana ta kukanta , har baba ta gaji da rarrashi . Sannan sai doctor Aisha ta fito tare da nurse din . "Ba sai kin fad'a mini ba nasan ya mutu 😭 jeki abin ki." Matarshi ta yi maganar cikin kuka "Likita ya ake ciki ya jikin nashi ."? Jafar ya tambaya yayin dasu baba duk suke jiran amsa likita Aisha ta fara magana" Ku yi hakuri Jafar , mun yi iya yin mu dan cetar ransa , amma Allah ya amshi abinsa." Dauuuuu suka ji zuciyoyinsu na wani dukan dubu dubu na tsantsar tashin hankali. Aisha suka wuce suka basu guri . "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un.Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un. Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un" Baba anje ta fada cikin tashin hankali, su Umar duk sun kasa cewa komai Ba a dade ba danta Jibrin ya karaso asubitin, shi ma , aiko su Jafar cikin wannan tashin hankali suka bisu kauye har saida aka shiryashi aka sallace shi sannan da aka kaishi suka dawo wajen dare. Allah ya sa mu dace Share and comment..........................,..📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) ___________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Page 25 & 26 Duk da Kalisa ba ta ce komai ba amma tabbas zuciyar ta babu dadi tun d'azu take kuka , anata rarrashinta amma ta kasa iya dena kuka . A washe gari bayan sun sayar da gidan , dactor Aisha take tabbatar musu dole Kalisa a fitar da ita domin da tun da fari a matakin ciwon na farko an san abinyi shi ne za a mata aikin anan. Haka dai basu ji dadi ba , amma gwarin gwiwar da suke samu Kalisa zata samu lafiya , Duk yau wani farin ciki suke yi domin zuwa gobe Kalisa za a fitar da ita India wajejen yamma kuwa sai ga Baba Garba , aiko nan ya yi ta musu fad'a a kan rashin sanar dashi da wuri . Jibril magana d babarshi a kan Sahid Bayan magariba ta dauko kai Baba anje da farin cikinta ta ce "Nabila ta shi ki tafi gida ki shiryawa muku duk kayan da zaku bukata domin kinsan jirgi ba ya jira ." Nabila ta ce "To baba bari naje gidan , su ka yi sallama tafi. Yau dai a 'kallah duk sun sami farin ciki , domin yadda suka saki fuskokinsu abin farin ciki ne , sai dai ma mutuwar mlm Aminu ce duk wani bacin ran. 10:02 na dare Baba anje ta fad'a a ranta " Nabila dai gida zata kwana ke nan , to Allah ya sa ta zo da wuri , ai Jafar ma na gidan shi da Garba ." Jafar ma yana komawa gida babu wata-wata ya kwanta domin ya matukar gajiya . Washe gari da safe Laila ta samu lafiya har barrister Adam ya sama mata makaranta ta ci gaba , haka ta ci gaba da Rayuwar ta cikin aminci da kaunar iyayenta . A 'bangaren Uncle Yahaya kuwa shiri yake zai koma Lagos wajen Fa'iza, domin ya sanar da ita halin da yake ciki , hakan ya sa ta turo masa kud'i domin ya koma kusa da ita , tun da dai yanzu ba kowa yake dashi ba . Aiko yau din nan zan tafi lagos 🚴😂 "Karfe nawa jirgin zai ta shi." ? Baba ta tambaya "11." Jafar ya bata amsa a gajarce "To amma Nabila ina ta shiga ne , ko abinci take yi ne , tun jiya ban zata zata kwana a gida ba sai ga shi ta kwana kuma har karfe 9 shiru." Baba anje ke nan Jafar ya ce "Ai na yi zaton ma anan ta kwana domin jiya banganta ba ." Darammm a zuciyar Kalisa da Baba anje Kowa shiru ya yi yana sake-sake cikin ranshi , Jafar ya ciro wayarsa a aljihu ya ya nufi numbar Nabila domin kira, wayar ko shiga ba tai ba balle ya sa ran jinta Jin sallama duk ya sa hankalinsu ya koma kofar shigowa "Assalamu alaikum". Suka amsa sallamar tare da wani yanayi a cikin furkarsu Baba garba ne ya shigo , shi ma yadda ya gansu ne ya sashi tambaya " Ya haka , ko lafiya na ganku haka."? Ya karasa maganar ya na zuzzura musu idanu, "Nabila ce ba a ganta ba." Jafar ya ba shi amsa "Subhanallahi kamar ya kuma Jafar."? Tun kafin Baba Garba ya yi magana , Umar ya shigo yana tambaya Duk shiru sukai kawai suna jin abin a ransu, " Bata kwana a gidan ba ne ko ya". ? Baba Garba ya yi maganar yayin da ya katse musu sake -saken su." A wannan karon ma dai Jafar ne ya fara magana "Ni wallahi ban sani ba , jiya na gaji hakan ya sa ina shiga gida na kwanta." "Kuma ba ta makota."? Baba anje ta jefawa Jafar tambaya Jafar cikin takaicin yadda kowa shi yake tuhuma ya fara cewa " Ba mu tabbatar ba kawai mu fita mu duba." Ya karasa maganar tare da fita bai jira kowa ba . A jiyar zuciya Kalisa tai , ba tare da ta ce komai ba amma kana iya hangar tashin hankalinta a furkarta . Bayan Uncle Yahaya ya sauka a legos, yabi wannan adireshi na Fa'iza ,wato inda gidanta yake , babu jan lokaci ya sami gidan "Assalamu alaikum." Uncle Yahaya ya yi sallamar a gidan Fa'iza tare da takatsan-tsan din kamar ba gidan ba ne , ba tare da ya kuma sallama ba ya ringa duban gidan yana lekawa Jin muryarta ne ya tabbatar masa tabbas ya zo gidan masoyiya "Haba baby, ni daya ce fa a gidan , daga ni sai kai , sannu da zuwa." Ta karasa maganar yayin data aje buta tare da jan bandakin data fito . Ajiyar zuciyar farin ciki ya yi yana gyarawa jakar kafadarsa zama yana cewa "Ga kyakykyawata farin cikina yau a gabana." Wani irin kallo Fa'iza tai masa tare da kashe ido , lokaci guda kuma tana kai hannu tana karbar jakar tashi." Suka nufi daki suna shiga dakin wayarta ta fara ruri , tabbas tasan Abdul ne , hakan ya sa bata bi ta kanta ba , shi ma Yahaya ko tayin daukar kiran bai mata ba , domin ga dukkan alamu bai ma jiba , saboda wani shegen kallo da yake binta dashi . To ga dai Uncle Yahaya a lagos Ko ta ina zai fara , kuma ya zai rayu Ga kuma bangaren Kalisa, har yanzu babu labarin Nabila, da Sahid, ga ciwonta kullum abin tafiya yake , ko Kalisa zata sami lafiya? Ga kuma bangaren Zainab da Mahmud, ga mutumin ku Harun . Tofa duk ba za mu ji yadda abin zai kasance ba ,sai mun had'u a A tare da ni Fatima Abdallaah kano Wato Auta ga marubuta Mu had'u a kashi na biyu karku mance fa 👇 Share and comment..................................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano . (Autar marubuta) ______________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Page 27 & 28 Duk hankalinsu ya gama tashi matukar gaske, har magariba ta yi amma babu labarin Nabila , da tananan sun tabbatar yanzu Kalisa tana India, amma duk inda ya dace a duba kuma a tambaya an yi , sai dai babu wani cigaba. Allah ya kawo sauki da mafita , haka rayuwar take, kowa da kalar tashi kaddarar. Washe gari Jibril ne zaune kusa da mahaifiyar shi yana rarrashinta , tun da garin Allah ya waye take kuka Cikin tausayin mahaifiyar tashi Jibril ya ce "Babata dan Allah ki jure wannan jarabawar , wallahi komai mai wucewa ne ." Cikin rashin gwarin gwiwa ya karasa maganar Cikin kuka tana face majina tana gogewa da zaninta ta ce "Wallahi Jibril kaninka ya yi asara duniya d lahira , domin ba zan yafe masa, ya je indai duniya ce , wanda ba su zo ba ma jiransu take , sai ta sashi kukan da babu hankicin da zai share masa."😭 Ta kuma fashewa da kuka Jibril duk ya kasa cewa komai domin zuciyar shi shi daya yasan zugin da take masa . Kasar waje Sahid ne ya fito daga asubitin kashi yana dingishi , guri ya samu ya zauna iska mai dadin gaske ce ke kai wa tana dawowa , ga duk kan alamu yana jin dadinta fiye da su mazauna kasar Lokaci guda kuma ya hade rai yana magana shi daya , yayin da ya hango wani gurgu bisa keke ana turashi " Allah ka raba mu da wannan masifar kawai a yankewa mutum kafarsa , wannan asubitin za su min komai ba sai na koma Nigeria ba , Allah sarki babata da na ce ciwo zata daukon magani , ni da na koma Nigeria sai na yi aure na haihu da baturiya ,daga nan ma Pakistan zan wuce." Ya aje maganar yana kallon ambulance din da suka shigo asubitin. A d'azu jikin Kalisa ya rikice sosai da sosai , nan hankalinsu ya tashi sun yi kokarin fitar da ita , amma Kalisa ta ce bazata bar kasar nan ba ba tare da tasan halin da kanwarta ke ciki ba . Duk da an sanar da 'yan sanda amma har yanzu ba ta sauya zani ba Fitar kannen Umar ke nan daga asubitin , su biyu mace dana miji macen tana kuka da wannan yanayi data gansu a ciki. To ya za ai da lamarin ubangiji Umar ya matukar ramewa sosai , su baba anje ma ba a cewa komai ga su Jafar da Garba , abin dai sai wanda ya gani. Jingum suka yi duk din su a dakin wayar Jafar da take ruri ne kawai ya sa ake jin wani sauti da kasala ya cirota a aljihunsa tare d amsa kiran yana karawa a kunne . Koda jin wata kakkausar murya ce ke magana hakan ya sa ya tashi tsaye , yayin da duk hankulansu suka dawo wajenshi Da alamar magana da kai Umar yake tambaya ko lafiya, hakan ya sa Jafar ya sata a sautin da kowa kan iya jin abin da ake cewa "Na ce kai ne Jafar." Aka fad'a cikin muryar rashin girmamawa, cikin faduwar gaba Jafar ya amsa da shi ne Aka ci gaba da magana kamar haka "To wallahi mu harkar mu babu karanta , da zarar mun baka lokaci ba kai amfani da shi ba komai na faruwa, mu ne muka dauke kanwarka , kud'in fansa muke so , idan kuma ka shigo da 'yan sanda cikin kasuwancin mu to ku shirya jana'izarta." Yana gama maganar ya kashe wayar Tare da dukkan tashin hankali da matukar hanzari duk suka tashi , su baba anje da Garba tare da salati suna kiran sunan Allah suka tashi . Kalisa ma kana iya hangen mummunan tashin hankali a kan idanunta, cikin tsananin ciwo da fargaba tare da tashin hankali gami da juriya ta fara magana. "Mun shiga uku Jafar , ka dubi rayuwar data riskemu a bayansu momy, Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un." Ta karasa maganar cikin ciwo tana Ajiyar zuciya tare da hawaye . Yadda Umar ya kalli masoyiyarshi Kalisa duk wani tausayin ta ya kama shi , duk da bata da lafiya sannan ga baba anje ga Garba, amma tana daukar lamarin 'yan uwanta a kanta .Matsawa ya yi kusa da ita a sa'ilin da yake jin kamar ya sa hannu ya goge hawayen dake gangaro mata kana ya rungumeta ya rarrasheta . Amma ina duk ya kasa ma cewa da ita komai ya juya ya fita. Tun da lamarin ya faru babu wanda ya yi wani yunkuri , domin yadda Kalisa ta damu da lamarin Nabila duk abin sai ya sake d'aga musu hankali. Babu inda kowa ya motsa har dare ya yi , idan ka ga wani a cikinsu ya fita ,to bai wuce ya nuna damuwar shi a waje ba , sannan ya dawo , domin duk dakon kiran kidnappers din suke . Ai kuwa wajen karfe goman dare , sai ga wata sabuwar number ana kiran Jafar, hakan ya sa duk suka mayar da hankali ga kiran, sannan Garba ya ce ya saka a speaker. "Kana jina." Ha kan da aka fad'a ya tabbatar musu muryar wannan azzalumin ce ta d'azu Cikin rawar murya Jafar ya ce "Ina jin ka." "Zuwa gobe na baku, da karfe 4 na yamma, idan baku amsheta ba , zamu hada ta cikin masu bakuntar lahira gobe , Million 3 za ku aiko." Ya kashe wayar daga can bangaren . "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un, yanzu ya zami , kud'in aikin Kalisa ne kawai damu bayan fafutukar da akai aka had'a su , ina zamu sa kanmu 😭 Yanzu da Sahid ya bamu kud'i ko million dari ce ai ba wahala za tai fa." Baba anje ta yi maganar tana rushewa da kuka . "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un." Garba ya fad'a yana samun guri ya zauna Cikin rawar murya tare da fargabar abubuwan da suke faruwa Jafar ya ce "Dole a fitar da Kalisa baba Garba, tun da wannan kudin...." Kalisa ce ta dakatar da Jafar cikin ciwo tana cewa "Babu inda zani sai Nabila ta dawo , dukkan abin da aka tara dan zuwa neman lafiya ta ,a halin yanzu Nabila ce mabukaci , ita jini na ce ,dan haka kawai ku karbota Jafar." Ta aje maganar tana wani irin nishi . Baba anje kuka ta sake fashewa dashi tana neman taimakon Allah. Baba Garba ma ya kasa cewa komai , KANO Mahmud ne a zaune a falo kamar kullum, cikin zuciyar shi ya fara tunanin ya kamata ya koma gida, domin wani abokin sa ya tabbatar masa aikin da suka nema koyaushe za a iya kiransu . Zainab ce dake kwas kwas kwas da takalmi ta dawo dashi cikin hayyacinsa .ko kallon inda yake bata yi ba ta wuce ta gabanshi . Ganin suturar dake jikinta ya tabbatar masa fita za tai zama ya gyara yayin da ta kai bakin kofa tana kokarin budewa ya ce "Ina zuwa."? Wani zafin takaici ta ji a ranta " Zan je gidansu wata ne , kuma momy ta sani , ba sai ka tuhume ni ba." Duk jikin Mahmud wani iri ya masa domin ya tabbatar Zainab ba gaskiya ta fad'a masa ba , wajen Harun zata ,haka zuciyar shi ta ba shi. "A dawo lafiya". Abin da ya fada ke nan ya koma ya yi lakaf kamar ya saduda . Hakan ya sa Zainab ta fita Zumbur ya yi ya tashi kamar wanda aka tsikara ya zura wayarshi a aljihu ya fita ya bi bayanta. Yana binta a baya- a baya har tasha kwana ta nufi bayan gidansu , wanda hakan ya tabbatar wa da Mahmud abin da yake tunani, tana tsallaka titi ya ga ta doshi wani babban gidan abinci da hutawa mai suna Shuwa Love , mamaki ne ya sake rufe shi ya ci gaba da binta , wanda harta shiga ciki bata san yana bibiyarta ba . Sahun kujera number ta goma sha bakwai ta hangi Harun yana zaune yana jiranta, hakan ya sa ta nufi wajen shi cikin farin ciki. " Ohh Zainab! Wajen wannan wawan kika sake zuwa ya Allah. " Ya yi maganar cikin tsananin haushi da bacin rai . Daga inda yake labe yake hangosu ya kalli hagu da damar sa , sannan ya nufi inda suke Zainab wani yarrrr take ji duba da yadda Harun yake kallonta kamar mai shirin fada mata kah yana daga zaune "Masoyi wannan wanne irin kallo ne."? Zainab ta tambayi Harun cikin ya'ke tare da murmushi wanda lokaci guda zaka gane duk hankalinta bai kwanta da kallon ba . Ajiyar zuciya ya yi yana kokarin fara magana , sai dai kafin ya kai ga cewa komai Mahmud ya tsaya 'kyem a kansu rike da kugunsa Duk mikewa tsaye sukai suna kallonshi , ba tare da ya bari wani a cikinsu ya ce komai ba , ya fara magana "Sannu ku, ashe nan kika taho." Tare da duk bacin rai Zainab ta fara magana"Wato bibiya ta kake , amma wallahi ka bani kunya , wannan wacce irin. ".. " Shiru mara kunya." Mahmud ya fada cikin zafi da hassala, ni yayanki ne , amma ni kike fadawa wannan maganganun , saboda duk kin ga na zama wani zato . Rashin hankalinki ya wuce tunanina , kwakwalwarki ta dena aiki , kin zabi mutumin da yake da burin kashe ni ." Sauri Harun ya yi ya tari numfashin Mahmud, wanda a wannan lokaci duk mutanen dake zaune a wajen hankalinsu yana wajensu suna ji da kallon hayaniyar tasu . "Ta ya zan kashe ka Mahmud, ai ko ba komai kai abokina ne kuma yayan Zainab, ka dena min kazafi dan baka so na ." Ya yi maganar cikin muryar tausayi da marairaicewa . Hakan ne ya matukar hassala Mahmud, cikin fusata ya yi sauri ya daki kirjin Harun da hannu biyunsa , wanda sai da ya kai kasa har kasan rigarshi ya yage , sakamakon kujerar da ya bige ta rike shi . "Nasan duk abin da kike dan bamu sanar da dady ba ne , kuma wallahi yau sai ya san komai." Mahmud ya fada yana nuna Zainab da yatsa "ka fada mana, ko tsoron hakan nake ka dameni ka ishi Rayuwata, kai azzalumi ne mara tausayi." Wani saukar mari da taji a fuskarta ya sa tai shiru ta rike gurin , tana kallon Mahmud da mamakin ya mare ta . Kafin ta ce komai taji muryar Harun yana cewa "Security ga shi nan." Yana nunawa security na kula da gidan Mahmud. Suka sashi gaba domin ya fita a gurin , kawai kallon Harun ya yi , ya wuce ya fita . Share and comment...............................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) No editing _______________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Page 29 & 30 Cikin mummunan 'bacin rai Mahmud ya fito , duk ya rasa mene yake masa dadi , kawai ya nufi gida kanshi tsaye , har ya isa gida yanayin shi bai canza ba , yana shiga falo ya ci karo da Alaji Kabiru shi da Ahmad suna zaune. Yanayin yadda ya musu sallama a ciki ya sa suka tambayi mene yake faruwa . Bai boyewa Alaji komai ba , haka shi ma Ahmad ya sake bada tabbacin abin da Mahmud ya fada . Cikin bacin rai Alaji Kabiru ya kallesu yana cewa "Mutanen banza ku tashi Ku bani guri , duk kunsan da wannan baku fada mini ba saida abin ya kai haka ." Ya karasa maganar lokacin da Hajjiya ta shigo , "A yi hakuri dady , mun yi zaton zata gyara ne ." Mahmud ya bada hakuri. "Zaku bani guri ko sai na ci mutuncinku ." Suka tashi ya yin da kafin su fita suna iya jin karashen maganar tasa "Ta zo ta same ni , ina nan ina zaman jiranta ."... LEGOS Abokan Abdul Salim ne a d'akinshi suna ta shaye shayensu da bushe bushe . Wani daga cikin su da ba ya iya magana sai ya karkata baki ya ce " Kai Abdul yarinyar nan taka fa , naji an ce ta aje kato a gidanta ." Abdul na kokarin jan shisha ya ce "Ai na sani dan uwanta ne , ta fada mini komai." "Kai dama baka da kishi ai koda yake ita karuwa ina ruwanta koma waye." Mari ya ji an d'auke shi dashi , yayin da duk abokan suka razana . "Kar ka kuma kiran matar da zan aura karuwa, da yau a ce Fa'iza ba za ta aure ni ba , sai na wulakantata , amma tana sona, kar na sake ji ." Kowa yasha jinin jikinshi, su abokanshi sun sani sarai ba sanshi take ba , amma sun bari duniya ta fada masa domin ba zai yadda dasu ba . Uncle Yahaya dai asara ta tabbata , ba shi da abin yi , hatta kudin kashewa Fa'iza ke ba shi amma a haka suna shirin yin aure , ba tare da Abdul ya sani ba , Mu je zuwa Fa'iza zancen duniya ba ya buya. ABUJA Har yanzu sai dai saukin Allah, jikinta babu dadi Nabila ce rike da ita tana tsala kukan bakin ciki "Aunty Kalisa wallahi lafiyarki tafi komai a kan mene zaki bari a karbo ni , bayan bama da wasu kudaden , ke ce damuwarmu , amma yanzu bamu da wata dama." Rurutaccen kuka suke yi baki da yansu, sai dai abin da basu sani sani ba a halin yanzu Kalisa bata iya magana. Tsanani ya kai ya wuce tunaninsu , ita kanta dactor Aisha tana mamakin yadda Kalisa ta kai har yanzu a raye, bayan tsananin da matakin da ciwonta ya haura. "Likita , Likita likita ." Jafar da Nabila suka fita da gudu suna kiran dactor, wasu nurse ne su biyu suka shigo sukayi kan ita Kalisa data sassan kare , Umar ganin bai gamsu da nurse dinta ba fita neman doctor Aisha da gaggawa Aisha ta taho gurin Kalisa, ya yin da taci karo da wannan nurse din su biyu , nan take suka ja baya suka bata guri . "Baba Yaya Kalisa mutuwa za tai." Nabila ta yi maganar tana rushewa da kuka , baba anje bata iya cewa komai ba , domin a yadda take kallon Kalisa yanzu ita ma ta cire rai , domin a halin yanzu numfashi ya gagara , cikin kokari da sanin aiki na dactor Aisha aka sawa Kalisa oxygen machine , wanda daga nan ne aka samu sauki ta koma kamar matacciya . "A gaskiya ku dauketa ku koma gida , tunda har yau fitar da ita ya gagara , nasan halin da kuke ciki , amma hakan ba yana nufin ku zuba idanu ba , domin taya Allah kiyo yafi Allah na nan , ciwonta ya wuce duk yadda kuke tunani , musamman ma cancer dake kafarta wacce take cigaba da yawo." Doctor Aisha ta yi maganar tana kallon kowanne a cikin su . Ba tare data jira wani ya ce komai ba ta fita yayin da wannan nurses din suma suka fita da fatan samun lafiya . Baba Garba ya kalli , baba anje yana cewa "Gaskiya ne wannan, duk abin da yake faruwa daga Allah ne , ya kamata mu tashi zuwa jibi a fitar da Kalisa a samo mata lafiya." Baba anje dai ta kasa cewa komai, sai wani ajiyar zuciya da ta yi mai cike da fargaba tana kallon Kalisa. "Zan je na sayar da gadon gidanmu , amma ba wani kud'i ba ne mai yawa." Umar ya yi maganar yana kallon Baba Garba Baba Garba ya mayar masa da cewa "Ni ma yau zan tafi kauye, zan tattaro duk abin kadara ta da kiyo , a siyar dasu in sha Allah." Ya mike yana cewa "Bari na tafi ba a bori da sanyin jiki , zan kuma tun-tu'bi duk mutanen kirki cikin 'yan uwa zasi wani abun." Ya aje maganar lokacin da yakai kofar fita nan sukai masa sallama da fatan alheri ajiyar zuciya Jafar ya yi tare da kallon can gefe guda idanunsa kamar zai yi kuka, sallamar da aka shigo ana yi ne ya sa ya dawo da kallon sa bakin kofa "Ahh Jibril kai ne." Cewar Umar Jibril ya gaida baba anje ,Wanda nan suma suka sami damar yi masa ta'aziyya ya kalli Kalisa dake kwance da oxygen idanu a rufe yana cewa "Allah ya bata lafiya dan annabi." Duk tare suka amsa da amin , wanda ya kalli Nabila yana sake cewa "Sannu ke ma Nabila, haka Allah yake kudurarsa , amma da wannan azzalumin Sahid ya bada kud'i n nan ai na tabbatar komai zai zo da sauki." "Haka ne ." Jafar ya fada a takaice yana kallon Kalisa yayarshi wacce bata san inda kanta yake ba kwana guda babu abinci. A lokacin Jibril ya kalli Jafar lokaci guda yana had'a kallo da baba anje yana cewa "Sahid jinin mu ne babu yadda muka iya , kuma bamu da bakin ba ku hakuri ku dauki duk matakin da ya dace dashi." Ya ciro wasu makudan kudade daga jikinshi yana ajiyewa gaban baba anje yana cewa "Wannan ku had'a ayi amfani dashi wajen lafiyarta amma babu yawa." "Allah sarki, Allah ya saka muku da alheri." Baba anje ke nan Jafar ya kai ido kan kudaden wanda kallo guda ya musu ya gane dubu dari biyu ne, Sannan shi ma ya mika godiya, shi ma Umar haka ......... Haka har wajen dare Kalisa jiki babu dadi , su ma Umar da Jafar a wannan dare suna ta kokarin samo wannan kud'i, haka bangaren baba garba kowa yana ta kokarin sa . 🌹Rayawa da kashewa duk na Allah ne, kuma duk yadda ya yi babu mai tuhuma , amma muna yiwa Kalisa fatan samun lafiya ta dawo kamar yadda take dah.🌹 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) No editing __ _____________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><> Page 31 & 32 A wannan daren Zainab ta ci matukar kuka , duk ranta babu dadi , domin Alaji Kabiru ya matukar taka mata burki ya mata abin da yake mata ciwo , babban abin da yake mata ciwo take yawan tunawa wai ita dady yau , ya mara ya kuma kirata da sha sha sha, bugu da kari ya amshi wayarta duk saboda Mahmud, sannan aka yabi Mahmud , abin yana mata ciwo ta ci kuka har gari ya waye . Da safiya ta yi , ta fito cikin lambun gidan nasu ko taji wani saukin , yadda ta ga Mahmud yana motsa jiki cikin lambun tare da kwanciyar hankali ya sa ta ji duk ta kuma tsanar shi. "Hankalin ka ya kwanta ." Ta yi maganar lokacin data sha gabanshi Mahmud dakatawa ya yi yana fuskantarta, wanda wannan lokacin ne da ya dubi idanunta ya san taci matukar kuka, amma ba tare da ya bayyana mata ya gane ba ya fara cewa "Eh kam na ji dadi , tun da yanzu bakya cikin hadari irin na Harun." Ya karasa maganar yana korawa da ruwan jarkar dake hannunshi . Wata sabuwar 'kufula Zainab ttaa sake yi da jin hakan "Ka rabani da farin cikina , kasa dady ya mareni , kasa yayana Ahmad ya dena kulani , wallahi kai masifa ne , dan Allah ka koma garin ku kai ma ka yi rayuwarka haba ." Cikin bacin rai Zainab ta karasa maganar Mutuwar tsaye ya yi shi kuwa Mahmud, mamaki ya cikashi da jin wannan zance na Zainab, komai yaji ya sire masa , wai shi ne masifa "Zainab na yi miki gata .Amma sam ba za ki gane hakan ba yanzu, ni yayanki ne , ko ba komai ban can can ci wannan kalaman naki ba ." Bai jira komai daga gareta ba , domin shi ma ba iya abin dake bakinsa ba ke nan , amma ya wuce ya tafi, ya barta a gun , . Zuciyar shi cikin kuna da tunanin irin maganar data fadaa masa ya fara shirya kayanshi a jaka, babu bata lokaci ya shirya tsaf , sannan ya fita domin yin sallama da mutanen gida . A lokacin Hajjiya tana shirya break fast , ya fito , mamaki ya cikata , haka data sanar da Alaji Kabiru, shi ma . uzururruka ya basu sosai wanda ya kirkiro , sannan suka barshi ya tafi bayan ya karya , Ahmad ya hau mota ya rakashi zuwa......... Abdul ne yake kwala sallama gidan Fa'iza , Ni ko na ce ashe yana da hankali irin haka har baya fada mata gida 😤 Suna kwance tare da Uncle Yahyah a cikin bargo , da jin sallamar Uncle yaja dogon tsaki tare da sakinta daga rungumar da ya yi mata ."Yi hakuri baby , kasan Abdul ba hankali gare shi ba bari naje. " Ta sakko daga gadon tare da daukar kaya zata ,sa kawai ta fasa ta aje tasa wani dogon farin hijab ta fita Yana tsaye rai a bace , yana ganin ta ya fara masifa "Ni fa tunda wannan dan uwannaki ya zo bana ganewa , me ya ke faruwa ."? A jiyar zuciya ta yi cikin murya mai dadi tana cewa" Haba baby tun yaushe wai ya tafi ne. " Wani dadi Abdul Salim yaji ya rufe shi tare da nuna yadda yaji dadin maganar ya fara magana , "A gaskiya Fa'iza na matsu mu yi aure , ko ba komai ki dena zama haka domin kinsan ina son ki." Ya aje maganar yana kallon cikin idanunta. A jiyar zuciya ta yi , kana ta fara cewa , "Na sani Abdul, amma fa banajin za a bari ka aure ni , sannan kuma...." Yadda ya dakatar da ita da maganar ne ya sa ta yi shiru tana saurararsa "Haba waye ya isa , ai duk fadin legos...." Shiru ya yi ,wanda a lokacin ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa ,sakamakon kiran da ya shigo masa . Yana kara wayar a kunnen shi bai fi wasu sakanni ba , sannan ya aje cikin gaggawa yana cewa da Fa'iza "Bari na je , zan kira ki mu ci gaba da magana." Ba tare da ya jira jin wani abu daga Fa'iza ba ya tafi hakan ya sa Fa'iza ta koma ciki , tana shiga dakin ta cire hijab din dake jikinta, kana ta zauna bakin gado , ya yin da uncle yahaya yake zuba mata kallo , lokaci guda kuma yana kai hannu jikinta . "Gaskiya akwai matsala." Fa'iza ta fada tana ture hannun Uncle a jikinta "Mene kuma ."? Uncle ya yi maganar da takaicin yadda ta hana shi abin da yake yi . Ba tare da ta jira ba ta fara da cewa " Wannan gidan , gidan Abdul ne , sannan aure yake so mu yi , bansan mene zan yi ba ." Had'e rai ya yi Uncle yana cewa "Aure kuma da wannan. To ni kuma fa."? " Nima shi ne abin dake damuna ai , ya zan yi."? Fa'iza ta fada tana kallon uncle "Fa'iza sanin kan ki ne bani da kud'i , bani da gida ke ce kike ciyar dani. Amma wallahi ko kin auri wannan Abdul din , to har gida zan na biyo ki . Gara ma karki fara kisa Allah ya konamu." Dariya Fa'iza ta kwashe da ita tana cewa, "Kana nufin yanzu kai Allah ba zai kona ka ba Yahaya , ka sabawa Allah ba mace daya ka nema ba fa." "Ki bar Wannan maganar, ai Allah mai gafara ne, kawai ki fada masa ni zaki aura in sha Allah ba zan baki kunya ba ." Fa'iza ta kalli Uncle yahaya tana cewa " Kar fa wallahi ka ci amanata Yahaya." Ta'be baki ya yi Sannan ya ce "Ni da ke mutu karaba Fa'iza." Ya jawota jikinshi lokacin da ya gama maganar. Yadda Fa'iza taji dadin yanayin ya sa ta fara cewa "Amma kasan kana da HIV ko." Rassss . Abin da Uncle ya ji ke nan a zuciyar shi , ya cireta a jikinsa yana cewa "Amma wasa ki ke koh."? Tintsirewa ta yi tana muguwar dariya lokaci guda kuma cikin dariyar ta fara magana " Sannu san banza , ka yi irin Wannan shanawar sannan ka tsira ko. To wallahi cutar HIV ta wajen shekara biyu , kuma ko matan kano din ma da kaje gunsu ai suna da ita . Kawai ka shirya muje asubiti asan matsayin taka , shi ne kawai ." Cikin dariya ta karasa maganar. Tashi tsaye ya yi cikin tashin hankali yana kallon Fa'iza "Fa'iza bana san irin wannan wasan wallahi, ki dena har duniya ta tashi babu ni ba wannan cutar." Ganin yadda Fa'iza ta lura dashi dari bisa dari bai yadda yana da Hiv ba ta tashi tsaye. "Haba dan Allah sai ka ce wani yaro , HIV ai ruwan dare ce , to wallahi kana da ita sannu dan san banza." Cikin tsaki da harara ta aje maganar, tare da juya masa baya tana zama bakin gadon . Timmmmm, abin da taji ke nan wanda hankalinta ya bata fad'uwa ce . Cikin sauri ta juyo , ai kuwa sai ga Uncle Yahaya a kasa kamar matacce . Da firgici ta yi kanshi tana jijjigashi tana kiran sunan shi . Yadda ta ga alamun kamar ya mutu ne ya sa ta tashi , ta sanya kaya riga da wando , sannan tasa hijab ta fita neman taimako. Koda ta fita babu kowa a wajen , domin anguwa ce bata mutane ba , sa 'a ta ci Allah ya kawo wani mai napep sannan ta kira shi , suka dauki uncle suka tafi asubiti. Tare da dukkan tashin hankali, Fa'iza domin tunaninta Uncle Yahaya ya mutu kawai , to idan Uncle ya mutu Allah ya jikanshi , dama kowa na haka ne. A halin yanzu Likitoci suna kan Kalisa domin tunda garin Allah ya waye suma basu samu damar ganinta ba , abin dai ba a cewa komai . Baba Garba ya musu waya cewa ya taho da million biyu , yana hanya, haka suma akwai wasu kudaden da suka samu daga al'uma . Bayan likitocin sun fito tare da dukkan tashin hankali su Umar suka tambayi jikinta nata. Yadda doctor ta tabbatar musu ba mutuwa tai ba wani sashi daga zuciyar su ya yi fari . "To zamu iya shiga gurinta."? Nabila ta tambayi Aisha likita " Me zai hana. " Ta bata amsa , hakan ya sa suka shige baki dayansu . Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa dactor Aisha, tana sharewa amma sun ki dena kwararowa "Da kun san matakin jiwonta , duk wannan kwarin gwiwar ba za ku same shi ba , ta ya zan fara fada muku wannan bayan kun kasa fitar da ita." Aisha ta karasa maganar tana dena kallon kofar dakin Kalisa tare da tafiya tana share hawaye. Cuta ba mutuwa ba ce . Share and comment..........................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) No editing _________________________________________ Page 33 & 34 Ba yadda Fa'iza ta iya da Uncle, gida suka dawo bayan likita ya tabbatar mata da ciwon barin jiki ne ya kamashi wato paralysis. Ta shiga rudani tun a asubitin, bata da kudin jinyarshi ya sa ta dawo gida , wani abin takaicin da yake damunta tun a asubiti ya fara bata aiki , domin wata gudawa da yake yi abin ba a magana , haka bayan ta dawo gida bai fasa ba , amma likita ya bata magunguna duk da haka abin bai lafa ba , yau ta sha bacin rai . Ido ta zuba musu tana kowanne su, yadda abin ya basu mamaki rabon da manyan idanunta su bude irin haka tun tana da lafiya "Kalisa ki daure ki ci abinci yaufa kwana biyu baki ci komai ba." Baba anje ta yi maganar tana rike hannun Kalisa. "Ku yi hakuri, na wahalar daku." Kalisa ta fada da kyer "Sahid ya ci amanar dady ." Kalisa ta kuma fada "Yi hakuri Kalisa da Wannan maganar, baba garba ya taho da kud'i yana hanya." Kalisa ta yi murmushi Umar ne ya ce "Dan ma yau juma'a ne da tuni ya karaso." Yadda Kalisa take wani mike mike ya sa duk hankalinsu ya tashi Da sauri Nabila ta kira Aisha, koda aka kirata kawai a jikinta ta ji Kalisa mutuwa za tai tana karasowa tare da wasu nurse aka fara buga mata iska tana haki Kalisa tana wahala tana jan wani numfashi tana mikewa wata doguwar ajiyar zuciya taja , sannan tai shiru , hakan ya sa suka dena buga mata iskar Doctor Aisha ta cire dukkan masu machine da aka sanyawa Kalisa. Yana yin yadda suka ga tashin hankali a fuskar dactor ya sa duk suka tsure . babu wanda ya iya tambaya wanne hali ne Kalisa ke ciki , duk da taja malullubi ta rufe fuskarta ,sai da doctor Aisha ta juyo ta kallesu tare da girgiza musu kai , wanda hakan yake tabbatar musu babu ranta . "Me ki ke nufi ne."? Umar ya sha gabanta yana tambaya a bisa yanayin rashin ganewa " Ku yi hakuri, ta rugamu gidan gaskiya. "🙊 Aisha ta fada cikin matukar tausayi tare da fita , waje , fitar ta ke nan Garba ya shigo cikin daki ya ci karo da gawar Kalisa. Kacokan din su suka rufe ta , abin yana dukansu , Nabila ta bude fuskar Kalisa, " Haba dan Allah aunty Kalisa, ke ma kin san a'a ne , mutuwarki tashi kawai." Cikin matukar zautuwa Nabila take jawo Kalisa domin ta tashi . Ganin haka ya sa Jafar ya fara janyeta ta karfi yana kuka . A wannan lokacin Umar Allah ne kawai yasan zuciyar shi , domin kawai wasu hawaye ne suke zubo masa yayin da ya kafa mata idanu. Baba anje kawai sunan Allah take kira jikinta na rawa kamar mai shirin zaucewa . Allah sarki Garba tun da ya yi burki , ya yi mutuwar tsaye ya rungume jakar kud'in da ya zo da ita . "Haka Allah ya kadarto , amma Sahid tabbas ka cutar damu." Umar yake yin maganar lokacin da hawaye suke zuba jikin malullubin da aka rufe Kalisa "Shi ke nan . Kin barni Kalisa, kin tafi inda ba a dawowa." Ya sake fashewa da kuka yana zube gwiwowinsa a kasa cikin karyayyar zuciya. A Wannan lokacin Nabila ta fad'a jikin Kalisa "Haba dan Allah, Haba dan Allah." Tana ta kuka mai gwanin ban tausayin gaske. "Baba ya kamata mu tafi kawai." Jafar tare da dukkan rauni ya kalli Garba ya yi maganar. innalillahi wa inna'ilaihir raji'un. Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un Kowa na haka ne daman sannan mutuwa dole ce ga kowa , kawai kowa da hanyar ajalinsa . Mu dai muna addu'a ya Allah👐 ka kashe mu bisa hanya ta addini, ka jikanmu taji tausanmu ya Allah. Haka suka koma gida ,wanda duk kafin su isa an sanarwa da kowa , domin da zarar wani yaji labarin zai kira ya sanar da wani .Haka suma mutanen kauye , abin ya girgiza su sosai . "'Yar uwata ce fa ita , da farko momy da dady yanzu kuma ita , ban yi tunanin shiga irin wannan yanayi ba , wannan shi ne Guba mafi girma da bazan mance ba a Rayuwata har ranar da Allah zai dauki raina . Allah ya jikanku aunty ku yafe mini." Maganar Nabila ke nan yayin da aka aka fito da gawar Kalisa za a tafi "Nabila ki yi hakuri kina yin salatin annabi, addu'a kawai Kalisa ke so yanzu." Cewar wata baba Ramma da ta zo daga kauye . Nabila dai ba a magana, saima lokacin da aka isa makabarta , Jafar da Umar 😭 Abin dai sai mazan wajen da suka gani😭 Allah ya sa mu dace A bangaren Fa'iza kuwa a halin yanzu rayuwata kawai wahala take sha kullum cikin bacin rai da masifa take wa Uncle , fitowar ta daga toilet ke nan ta nufo daki tana shigo wa ta toshe hanci cikin bacin rai tana kallon uncle tana cewa "Haba dan Allah, wannan, wanne irin wulakanci ne , na ce maka duk sanda kaji kashi kana mini magana, amma sai kana yi a kwance kamar wani yaro , to wallahi na gaji , na gaji da wannan masifar gaskiya mwtss." Ta fita cikin bacin rai ta barshi a dakin A jiyar zuciya ya yi yana daga kwance ya fara cewa "Rayuwata ke nan , kasan farkon ka baka san karshe ba , wallahi alhakin Laila Adam ne wannan, alhakin ta ne , in banda haka saurayi kamar ni Yahaya da wannan cutar , Allah ka bani ikon cinye ta ." Kun ji fa uncle, sai yanzu yasan haka . Ita Laila ma a halin yanzu tana makaranta, domin Allah ya bata lafiya . Fa'iza na daga tsakar gida tana tunanin yadda za tai da Uncle ta fara jin sallama. Ranta sake baci ya yi da jin hakan , ba tare da ta yafa komai ba ta fita rai turbine . Koda Abdul ya ganta haka , sai ya tambaya ko lafiya "Ka ga dan Allah mene ya kawo ka Abdul kana bani matsala fa." Ta yi maganar da dukkan d'aga murya tare da fushi mamaki ya rufe Abdul da jin haka "Mene kuma haka ni ne fa Abdul Salim naki , mai shirin zama angonki fa." Fa'iza ta kalleshi da takaici tana cewa "Allah ya sauwake wallahi, ni ba auren ka zan yi ba , ai ba hauka nake ba mwtss." Matukar mamaki ne ya rufe Abdul , yasan Fa'iza ba za ta masa haka ba , hakan ya sa ya maida abin wasa yana cewa "Haba Fa'iza na , a dena wasa mana ." Wata muguwar harara ta buga masa tana cewa "Wasa kuma , aikin banza , ai wallahi banga abin aura a gun ka ba gara ma ka sani." "Okay haka kika ce."? Abdul ya fad'a Fa'iza ta ce " Haka kaji , kuma haka na fad'a." Ya ce "Okay shi ke nan ." Ya kama hanya ya tafi , yayin data samu damar shiga gida Tana shiga gida taci karo da wayarta ta gama ruri sakamakon kiran wata kawarta , wacce take son ta da Abdul wato Zuby wacce tun tuni ta yi aure ta tuba . "Gayyar hauka." Fa'iza ta fad'a yayin da taga ita ce ta kira. Harun ne tsaye kofar gidan malam na lado , wato anguwarsu Zainab ke nan yana tsaye yana jiran fitowar Maryam, a yadda yake yatsine fuska zaka gane cewa almajiran dake kofar gidan suke karatu sun dame shi , lokaci guda kuma yana iya saurara duba ga malam na lado yana cikin gida . Lokacin da Maryam ta sako kai zata fito ya zuba mata idanu kamar kullum , Allah ne yasan karatun kurma , amma zuciyar Harun cike take da sha'awar Maryam tana karasowa kusa da motar shi ya fara tsarata kamar kullum yana shiryata , Allah ma ya sani Maryam ta kamu da son shi , domin tun da aka masa iya ka da Zainab ya dawo wajenta ka'in dana 'in "Gaskiya nifa ina shan kalamai shi ya sa kullum kake sake shiga zuciya ta ." Cikin murya mai dadi Maryam ta yi maganar. "To baby naji , amma yaushe zamu je ki gaida momy , domin kullum maganar ki take fa, Gaskiya ya kamata ki shirya na kaiki ." Ya karasa maganar yana mata wani shegen kallo, lokaci guda kuma yana sauraran jin amsarta." Share and comment.....................................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano ( Autar marubuta) No editing _____________________________________ Page 35 & 36 Kafin Maryam ta kai ga bude baki ta yi magana malam na lado ya fito da babbar riga da hula tare da allo da carbi . Ganin Maryam da Harun tsaye ya nufi wajensu , Harun ya yi saurin kai wa kasa yana gash she shi , bayan sun gaisa yana daga kasa Malam ya fara cewa "Kai ka sanar da iyayenka a zo anema maka aurenta , bana san wasa ." Harun ya ce "To baba in sha Allah zan sanar dasu yau ma kuwa." Malam na lado ya nufi wajen almajiransa ya zauna . Sannan Harun ya tashi yana ajiyar zuciya yana cewa "To kin ji ba , sai ki shirya kin kusa zama amarya." Ya yi maganar yana yatsine fuska , kunya ce ta rufe Maryam da jin hakan "To kinga gaskiya naji dadin jin wanna maganar ta baba , don haka gobe ki shirya zan zo mu tafi shop domin ina son faranta miki baby ." Maryam ta ce "A gaskiya zan fi kowa farin ciki Allah ya kai mu."...... Yau ne aka gudanar da addu'ar bakwai ta Kalisa Duk sun matukar jin jiki wallahi, sun rame kowannensu rashin ne yana matukar taba su , ba a gama nasu Alaji Idris ba , Kalisa ma ta zo ta tafi . To babu yadda aka iya dama kowa na haka ne . Har aka gabatar da addu'ar 40 babu abin da ya canza domin mutuwa mummunan tabo ce , wannan lamarin ya zame musu Gubar Rayuwa babu yadda suka iya. Wani mahaukacin bugun kofa Fa'iza taji ana mata , lokaci guda kuma ana cewa " Kina ina mara mutunci." A yadda taji tabbas ba mutum daya ba ne , ba kuma ta shaida murya ba duk tabi ta rude tana tunanin ita dai batai fad'a da kowa ba , bare a zo kamata , tana yin wannan tunanin ta saka hijab ta fita . Koda ta fita ajiyar zuciya ta yi ganin Abdul ne da abokanshi "Haba dan Allah mene haka." Ta yi maganar tana kallon Abdul da fuskarshi babu wani annuri . Ragowar cigari din dake hannunsa ya jefar tare da take ta , kana yana wasa da makulli da kwadon gida , wanda da gani sabo ne da ke hannunshi yana cewa "Ki tattara kayanki , zamanki ya kare , ki shiga na baki minti biyu ." Wani rass Fa'iza taji a ranta "Haba Abdul lafiya kuma."? Abdul ya kalli abokanshi yana cewa " Ku shiga jiki , domin idan ita ta shiga zata bata mana lokaci, duk ku yo wurgi da kayanta ." Cikin masifa Fa'iza ta fara cewa "Haba Abdul wannan ai cin mutunci ne ." Ba tare da ya saurareta ba ya fara cewa "Duk abin dake cikin gidannan ni na siya , dan haka abin da nasan bani na siya ba , daga akwatinta sai bahon wanka , da tukunya , ku shiga ku fito mata dasu." Babu wata-wata suka shige gidan domin aikatawa Zuciyar Fa'iza kamar ta fashe ta kasa motsi ta kasa cewa komai, tana tsaye taji an wurgo mata takalmi,wanda sai da ya sameta a goshi taji zafi wani takalmi ne mai tsini ruwan zuma ta kalli takalmin ta kau da kai , yayin da tana kau da kai idanunta suka kai inda aka wurgo mata tukunya da soson wanka da baho. Bayan su gama fito mata da kayan suka tsaya carko carko kamar masu shirin dukanta "Ya ka ce mi mata shegen duka mana." Wani a cikinsu ya fada yana kallon Abdul. Abdul ya ce "A'a ku barta kawai , domin duk abin dana ba ta na karba , dama taimakonta zan na aura , tana karuwa waya san cutukan dake jikinta .Ai yanzu na gane Allah ya yaye mini wahala." Fa'iza duk ta rasa inda yake mata dadi ta kasa cewa komai Abdul ya mika musu wannan kwadon gidan yana cewa "Rufe min gidana mu tafi." "Kai Abdul akwai wani gardi fa a gidan kamar bacci yake ma." Wani a gefenshi ya yi maganar yana nuna gidan Abdul da ranshi ya yi matukar baci ya kallesu yana cewa "To uban me ya sa bai fito ba ku koroshi tunda ba gidanshi ba ne ." Kamar suna rige -rige suka fada Cikin gidan kai tsaye sukai dakin Uncle duk yabi ya tsure ganinsu a kanshi "Ba yin Allah lafiya ." Uncle ya yi maganar yana kallonsu daga kwance "Tashi ka fita dan uwarka , kwarto kawai . Ita ma kwartuwar taka mun am she gidan mu." Haka Uncle taji an fada , ba tare da ya gane wane ya yi maganar ba . "Dan Allah ku yi hakuri, wallahi cutar barin jiki gare ni bana iya tashi." Ba tare da sun ce komai ba suka dauko shi su su hudu , biyu sun rike hannaye , biyu sun rike kafafu . Haka suka fito suka wurgo Uncle waje "Kan uban can dama har yau wannan yana nan , to Allah ya kuma tonaki ." Abdul ya karasa maganar yana kallon Uncle da yaji wurgi yana kwance a kasa Suka rufe gidan suka hau mota sukai tafiyarsu . Cikin mummunan takaici Fa'iza ta fara tattara kayan da aka watso mata , waje guda ta had'a su tana kallon tare da tunanin sauran kayan dake ciki, a cikin ranta ta lissafa yadda zata dauki kayan a hannunta ba tare dasun mata yawa ba . A lokacin kuma hankalinta ya kai ga uncle yahaya da yake zararar da hawaye . Wanda sa'ilin ta kuma kula da yadda gari ke rugugi sakamakon had'owar hadari . Had'e rai ta yi tana kallon Uncle tare da matsawa kusa dashi tana cewa "Ni zan tafi , domin babu inda nake dashi bare na je dakai ." Cikin tashin hankali Uncle yahaya ya zaro idanunsa ya fara magana a yanayin wahala. "Ya za ai ki barni a nan Fa'iza, ga hadari , ina zan sa kaina , ban zata zaki mini haka ba." Ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce ,"Ka so gaskiya mana Yahaya ina ne zan kai ka , dama kowa yana da kaddarar shi , to ka dauki wannan matsayin abin da ba za ka ta'ba mancewa ba , shi ne Gubar Rayuwarka." Tana gama magana ta juya da sauri tana kwashe kayanta , sakamakon tsawa da iska da aka fara. Ba tare da ta ko kalli Yahaya ba tasa kai cikin sauri ta fara tafiya, sakin baki ya yi yana kallonta cikin mamaki ganin cewa da gaske fa tafiya ta yi ta barshi . Wasu hawaye ne suka zubo masa yayin da ya fara ba za idanu da nufin neman wani ya taimake shi , amma babu wanda ya gani sai wani yaro dake gudu a keke sakamakon yayyafin da aka fara . "Yanzu ya zan yi , wallahi da nasan abin da zai faru ke nan bazan zo legos ba , basu da mutunci yanzu sai su kone ni a gun nan ." Uncle cikin kuka ya sauke maganar yayin da aka tsuge da ruwan sama .Domin ko ita Fa'iza kafin taje inda zata wannan ruwan ya dake ta , bare Uncle naku dake guri daya. Yau tun da gari ya waye Maryam take murna da fitar da zasi da Harun , mahaifiyar ta kawai ta sanar wa da wannan labarin , domin ta san malam na lado mahaifinta idan ya ji bazai yadda da wannan shirme ba , A tsakanin uwa da 'yah haka sukai maganar su , nan ta ba ta goyon baya tare da umarnin karta jima har Mlm ya tambaye ta. Doya da kwai take soyawa , daga gefe kuma kana iya hangar wani kunu na gero wanda yasha kayan kamshi. "Wai Nabila har yanzu ba a gama girki ba yunwa fa nake ji nasan ita ma Baba haka ." Jafar ya shigo madafa yana wa Nabila maganar cikin mita , "Hmmm ." Kawai abin da Nabila ta iya fad'a ke nan Jafar ba tare da hakan ya dameshi ba ya sake cewa "Kin san dai yau ne Yaya Umar ya ce zai kawo 'kannenshi ko , to ki musu girki dan Allah." Ta kalleshi tana cewa, "Ban fa mance ba Yaya Jafar." Ya karaso yana daukar doyar da zummar d'and'anawa. Bayan Harun ya iso ba 'ba ta lokaci Maryam ta fita suka tafi "Ya kamata mu biya ki gaida momy na fa." Harun ya yi maganar yana kallon Maryam Cikin shagwa'ba Maryam ta kalleshi tana cewa. Share , like and comment......................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) Editing❌ ________________________________________ Page 37 & 38 "Amma gaskiya ba za mu dad'e ba." Harun wani dad'i yaji ya rufe shi dajin amincewarta , hakan ya sa ya ce ,"Haba sarauniyata yadda ki ke so ai haka za ai besty na." Cikin 'kwarewa da farin ciki ya cigaba da tuki ya nufi gidan da yake kiran gidansu. Wani gida ne babba suka shiga , Harun yana mata kalamai masu kwantar da zuciya har suka shiga cikin falo. Maryam dakatawa tai cakk , sakamakon duhun da ta gani a cikin falon , saida Harun ya kunna haske sannan ta ji hankalinta ya kwanta . "Duk kin wani furgita zauna mana baby bari shaf-shaf na shiga ciki na kira momy." Harun ya yi maganar yana shige wa ciki. Nabila kam tasha aiki sosai ta yi girke girke , duk saboda 'kannen Umar da zasu kawo musu ziyara . Wajen minti biyar Harun ya yi bai fito daga dakin ba , Hakan ya sa Maryam ta yi shiru tana sa'ke-sa'ke cikin zuciyar ta ba ta gama tunanin abin da ya rike su a ciki ba , sai ga Harun ya shigo jikinshi duk a mace ."Mene kuma ya faru."? Maryam ta yi maganar tare da tashi tsaye "Ina shiga ciki, na ga momy kwance wallahi hawan jininta ya tashi." Inji Harun "Subhanallahi." Maryam ta fad'a "Amma karki damu , ki shiga ciki ki kula da ita dan Allah, ki kula min da mahaifiyata zan kira likita." Da sauri Maryam ta fad'a dakin cikin tausayin Harun. Duhu ta kuma gani cikin dakin , amma ba tare da ta nemi inda glove yake ba , ta nufi gadon wanda tana iya ganin mutum a kudundune a kai. "Mama , Mama." Tana ta'ba mahaifiyar Harun tana kiran sunanta . Wani tashin hankali ne ya bigi zuciyar Maryam tare da tsoro , sakamakon yadda taji tulin kayan Harun ne a kan gadon ba wai mahaifiyar shi ba ce . Da firgici ta tashi tana shirin fitowa taji an rike ta. "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un." Maryam ta fad'a sa'ilin da take da tabbacin Harun ne a gabanta Dauuuuuu ya kunna glove din dakin yayin da yake rike da hannunta yana dariya. A yadda mamaki ya kasheta ne ya sa ta kasa cewa komai, zuciyar ta tamkar ta fito musamman jin yadda ya fara magana. "Kin ga yadda shiri na ya yi koh. Ga ki gare ni yau Maryam zaki ga irin san da nake muki , babu kowa a gidan nan daga ni sai ke yawan." Ya karasa maganar yana fincike mayafin dake jikinta . "Inna'ilaihir wa inna'ilaihir raji'un Harun , kaji tsoron Allah, na roke ka karka rabani da mutunci na , dan Allah." Cikin matukar kuka da firgici Maryam ta yi magana. Dariya ya yi yana cewa ,"Haba Maryam, karki zama yarinya mana , wallahi tun lokacin da nake zuwa wajenki Wannan ranar nake jira , ban samu Zainab ba , domin na so mu shiga irin wannan yanayin da ita ,amma shegen yayan ta Mahmud ya hana.".... "Dan Allah Harun kar ka cutar dani, wallahi bazan jure ba." Ya tunkud'eta ta fad'a kan gadon , haka har mai faruwa ta faru . Sannan Harun yaji dadin rayuwar shi . Bayansu su Umar sun shigo suka zauna a falo nan suka fara hira dasu Jafar da baba anje Ya yin da Nabila ta fito daga wanka tana shiryawa. Da siririyar murya kanwar Umar Salma , wacce take kusa da yayanta Nasir ta ce ,"Wai ina Nabilan ne to."? Jafar ya ce ,"Ta na zuwa yanzu. " Nabila ta karaso cikin falon sanye da wata doguwar riga abaya , wacce taji ado ga launi mai matukar kyau. Tun daga 'bullowarta Nasir ya kasa jire idanunshi a kanta , har ta karaso ta zauna "Ya ya Umar har kun zo."? Nabila ta yi maganar da Umar yayin da kuma ta ke kallon Nasir da Salma " Kanwata mun iso, yau dai ga salma nan." Ya yi maganar yana nunawa Nabila kanwar shi . Murmushi Nabila ta yi tana cewa, "Eh yayana ka cika alkawari kuma naji dadi." Nasir ne ya 'ba ta rai yana kallon Umar da cewa ,"Haba Yaya Umar to ni ba za a gabatar dani ba." Jin hakan ya sa kowa ya kalleshi suna masa Murmushi. Umar tsaki ya yi yana cewa, "Nabila wannan matumburin kanina ne sunan shi Nasir." "Haba Yaya Umar matumburi kuma." Nasir yayi maganar yana kallon shi . Dariya suka kwashe da ita baki dayansu har da Umar yayin da ya ce ,"Ai Nasir din ne ya cika zance wallahi. " Nasir ya kalli Nabila yana cewa ,"Baki gabatar mana da kanki ba sister. " Cikin haushi Umar ya Had'e rai yana cewa, "Kun ji ba , baka ji an ce Nabila sunanta ba ,banan surutu bama kasan mene za ka na tambaya ba." Dariya suka kuma yi wacce tafi ta d'azu , har ita Nabilan ya yin da Nasir yake kallon yadda dariya take mata kyau. Sannan ta tashi ta nufi dakin girki domin kawo musu abinci , Nasir harda lekenta . Lomar farko ta Nasir ya ce ,"Gaskiya Nabila kin iya girki sosai , sai ka ce a Australia. " Wata harara Umar ya watsa masa tare da cewa ,"Su Australian girki suka iya? dan Allah ka yi hakuri ka yi shiru haba." Dariya suka sake yi a karo na ba adadi haka suka gama cin abincin cikin farin ciki da walwala . Bayan su kammala suka tashi tafiya, nan ne Nasir ya karbi number Nabila sannan suka yi sallama. Sun matukar jin dadin wannan ziyara baki dayansu." Fa'iza a gidan kawarta ta samu guri , inda ta tabbatar wa da kawarta zuwa gobe zata koma garinsu . Tana tsakar gida a zaune ta yi tagumi , a lokacin ne wannan kawarta ta ta fito daga daki . yadda ta ga Fa'iza ta yi tagumi tana kallon taurarin dake sama ya sa kawarta cewa ,"Haba Fa'iza lafiya , kin zauna a farin wata kuma kina kallon sama ." Fa'iza ta yi ajiyar zuciya tare da cire hannu daga tagumin da ta yi "Ki dena damun kanki fa dan Allah." Cewar kawarta Ajiyar zuciya Fa'iza ta kuma yi tana cewa, "A kwai abin da ban fad'a miki ba kawata, kuma nasan yanzu duk wannan ruwan saman da akai ga dare yana kwance a wajen nan." "Topha waye ke nan." Cewar kawarta Fa'iza ta fara bata labarin halin da Uncle yahaya yake ciki da kuma yadda ta baro shi . "To yanzu ya kike so a yi masa Fa'iza, ki rabu dashi kawai , idan ya mutu Allah ya jikanshi , kema shawara nake baki tun kina da lokaci ki tuba wallahi, domin ya zama izina gare ki ga yadda Yahayan nan ya samu kanshi , ki manta da komai ki koma ga Allah domin shi mai gafara ne , kuma ba damuwarki ba ce idan Yahaya ya mutu , nan zasu sa wuta su kona shi , idan kuma yana raye to rayuwa ce zai gani ya more duk yadda Allah ya yi daidai ne ." Yanayin zazzakar muryarta ya sa Fa'iza ta gamsu da zancen kawartata . Fa'iza ta ce ,"Haka ne kawata , in sha Allah bana komawa karuwanci domin gobe ma yobe zan koma, Allah ya yafe mana. " Kawarta ta ce ,"Yawwa Fa'iza ki je kawai ki kwanta saida safe. " Fa'iza ta shige dakinta ta rufo ta kwanta . Washe Gari Hauwa ce zaune tana karyawa a lokacin mahaifin ta lu'utanal ya shigo "Dady har yau baka samu time ba ni gaskiya yau zanje na ga Surayya." Kai tsaye Hauwa ta yi maganar Murmushi ya yi yana cewa, "Ehh gaskiya ne , ban samu lokacin ba kije abinki ki gaida mini da ambassador." "Thanks dady." Maryam babu wanda ta sanarwa da abin da ya faru , gashi tana cikin halin rashin lafiya , tun da Harun ya samu abin da yake so bai kuma waiwayarta ba , Allah sarki. Tuni ya barta har ya samu wata , wacce yake da irin wannan nufi a gunta , amma abun da yake ba shi tsoro yadda babanta yake babban mutum ambassador, Amma sai ya samu salama da ya yi tunanin ya ta'ba'yar malami ma ya zauna lafiya, bare yaran manya da suke chilling suke shoshalewa tabbas cikin sauki zai samu abin da yake so . Umar ne bayan ya amsa wata waya da akai kiranshi ya tashi da sauri ya fita , a karshe gudu yasa kamar mai shirin tashi sama , yana sake nanata sakon da aka isar masa cikin wayar . Jafar da Nabila ne zaune , sai baba anje , bayan sun gama karyawa "Gaba na fad'uwa yake Yaya Jafar." Nabila ta yi maganar cikin damuwa. Share and comment...................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) Editing❌ _________________________________________ Page 39 & 40 Jafar ya kalli kanwar tashi yana cewa," nima haka Nabila, tun jiya da daddare ma kuwa." Baba anje ta ce ,"Tofa! Ikon Allah, Allah ya sa alheri ne yake tunkaro mu." Kafin su kai ga cewa Amin suka Umar kamar an wantsiloshi ya shigo yana haki idanunsa sun yi jajir , ga dukkan alamu akwai damuwa. Duk tashi tsaye su kai kafin kowa ya ce komai yana ta sake saken abin da ya shigar da Umar wannan hali . "Tantancewar sojin da akai babu shi ne ? Amma hakan ba zai tada hankalin Umar ba ." Jafar yake fada cikin zuciyar shi . "Bai zo ba."??? Umar ya yi musu tambayar cikin tsananin jiran amsa . Kallon juna suka yi alamun samm basu gane mene yake nufi ba . Jafar ya karasa kusa dashi da cewa ," Kwantar da hankalin ka Umar, mene yake faruwa ne ." Daga can wajen gidan kuwa wani saurayi ne mai jiki wanda ya ginu ya wadatu da farar fata, ya nufo gidan yana d'ingisawa , yayin da yake tafiya cikin isa yana tattare farar jallabiyar dake jikinshi . "Sahid nake magana akai domin ya dawo Nigeria a daren jiya , kuma duk inda yake zanje na nemo shi." Umar ya fada tare da matukar nuna kiyayyar Sahid a zahiri Duk wani tashin hankali suka ji ya sake bugar musu zuciya da kiran sunan maci amanarsu "Assalamu alaikum." Sautin sallamar da suka ji ke nan wacce ta daskarar dasu a tsaye Tabbas yau idanunsu sun ga abin mamaki domin kuwa Sahid ne tsaye a gabansu , yayi wani kyau dashi yayi kiba . Wasu zafafan hawaye suka zubo wa Nabila masu matukar ciwo Umar ya kasa cewa komai domin zuciyar shi tana ayyana masa mummunan abu a kan Sahid, hakan ya sa yake 'kokarin sarrafa kanshi "SAHID". Jafar ya kira sunan shi ," Na'am Jafar, na sani cewa bani da bakin magana a gabanku , amma ba a son raina komai ya faru ba , na yi tafiya Britannia, jiya da na dawo nake jin labarin mutuwar Kalisa. " 'Kuummmm Wani wawan duka da Umar ya kai masa , ya fadi ya bige da bango, Umar ya taso shi cikin tsananin takaici ya cigaba da dukanshi . "Me nai maka ne , haka , mutuwar Kalisa ai haka Allah ya tsaro me ya sa za ka doran laifi." Cewar Sahid ke nan yayin da Umar yake bibbige shi . "Jafar ka yi masa magana mana ya dena dukana , ina ciwon kafa." Jafar ya nufi bayan Umar ya ture Umar ya amshi Sahid. Yadda Sahid ya ganshi a tsaye ya fara ajiyar zuciya da samun 'yancin da ya yi . Ba tare da ya ankara Jafar ya kwarfe shi ya fadi ya bugu da bango, ya taso shi ya ma'kure shi kana ya fara magana. "Burinka ya cika ba , Kalisa ta rasu , kuma ka zaune dukiyarmu." Gummmm Ya bugashi jikin wani karfe , sai jini . "Jafar ku bari karku kashe shi mana , ya jigata sosai." Baba anje ta yi maganar tana kokarin kwace Sahid a hannun Jafar. Jafar bai san lokacin da ya ture baba anje ba , Allah ya sa bafa fadi ba , ya kalleta cikin takaici da tarin hawayen dake idanunshi , yana cewa. "Shin baki tuna lokacin da Kalisa take kwance ba ? ko kin manta sanda muka tashi aka yi garkuwa da Nabila, kin mance ranar da Kalisa tai Allah wadai dashi , mu bamu jigata ba ne baba ? ko kuwa bamu ga tashin hankali ba ." Ya aje maganar cikin wasu zafafan hawaye da suka zubo masa , sannan ya maida kallon shi ga Sahid yana cewa, "Kai azzalumi ne mayaudari ka kashe Kalisa ka kashe mahaifin ka ." Ya tun kude shi gefe Sahid yana jiri ya ya tashi ya nemi hanyar fita ya hau mota ya tafi .Kai tsaye masaukinshi ya nufa wato hotel ya gyara jikinsa ya sauya kaya, kana yasha magani. Kwanciya ya yi da nufin hutawa sai maganar Jafar take fado masa tana masa amsa kuwa . "Kai azzalumi ne mayaudari ka kashe Kalisa ka kashe mahaifin ka." Ya yi ajiyar zuciya ya tashi zaune, ya dauki mukullin motar shi da kafar shi mara lafiya da taji duka ya nufi gidan nasu . Zuciyoyin su jafar tafasa suke yi matukar gaske, hakan ya sa suka fita domin daukar matakin da ya dace a kan Sahid. Hauwa ce cikin wani babban falo suna hira da kawarta surayya Hauwa ta zubawa Surayya idanu tana cewa, "Allah koh , ki ce sabon saurayi kika yi , shi kuma Faruk din fa." Surayya ta kalli Hauwa tare da jefa mata wata harara tana cewa, "Shi fa soja ne, kuma wallahi ya kwanta mini a rai domin gaye ne Hauwa." Hauwa ta ta'be baki tare da tashi tsaye tana cewa, "Kin ga ni tafiya zan yi , har akwai wani gaye da zai kuma shiga zuciyar ki bayan Faruk, wallahi kin bani kunya." Surayya cikin dariya da zolaya ita ma ta ta shi tsaye tana cewa, "Wallahi duk sanda ya zo san had'aku ku gaisa besty ta." "Mtwss." Hauwa ta ja tsaki tare ta bud'e kofar falon . Lokacin ne wani farin mutum lukuti mai sanye da farar shadda ya turo kai , ba kowa ba ne kuwa fa ce ambassador. Nan Hauwa ta gaidashi har yake tambayar mahaifin ta , nan take sanar masa yana gaida shi, shima ambassador ya sake aika masa da sakon gaisuwa. Haka Hauwa ta dawo gida......... Anan bangaren su Zainab kuwa Suna zaune a falo ita da yayan nata Ahmad, laptop ce a gabanshi yana dannawa Zainab ta ce ,"Yaya Ahmad dan Allah ka yi hakuri ka bawa daddy hakuri, ka amson wayata, wallahi na tuba na canza." Ahmad ya kalleta ya ta'be baki ya ci gaba da aikinsa "Haba yayana Ahmad, wallahi na tuba ka kula ni mana , har abada babu ni ba HARUN." Tsaki Ahmad yaja yana wurga mata harara "Dan Allah ki barni na yi aikina , ki bari ki kuma hankali da kanshi Dady zai baki." Wayar Ahmad ce ta fara ruri , yana ganin mai kira ya dauka cikin farin ciki. A yadda Zainab ta ga yayan nata yana waya tasan cewa Mahmud ne . hakan ya sa yana gama wayar ta titsiye shi da tambaya, "Wa ne Yaya."? Ahmad cikin farin ciki da washe baki ya ce ," Wallahi Mahmud ne , yana sanar min ya samu aiki a matatar mai ta kasa, abin ya farantan rai ." Zainab ta yi murmushi tana cewa, "To yaushe zai zo."? Ahmad ya jefa mata wani kallo yana cewa," To sannu , ke da ganin Mahmud sai Allah, sai dai ke ki shirya kije." Ya cigaba da aikinshi Duk atake Zainab ta shiga damuwa . Bayan ya yi burkin motar shi a kofar gidansu, ya fito da kyer ya shiga cikin gidan . "Assalamu alaikum." Sahid ya yi sallamar a cikin gidan , wanda bai ga komai ba sai tabar ma a tsakar gidan , sallama ya sake yi a karo na biyu babu amsa . Yanayin yadda yaji karshi shi na masa zugi da zafi ya sa ya nufi tabarmar da shirin zama "Kar ka sake ka zauna mini a gida mugu azzalumi." Cewar mahaifiyar shi data fito daga daki , a lokacin ne shima Jibril ya fito daga wanka . Tsololo Sahid ya yi da baki yana kallan mahaifiyar shi dajin wannan furuci da ta yi masa "Ka gaggauta fita a cikin gidan nan Sahid." Ta kuma fada cikin kunci Sahid ya daure ya ce ,"Mama da gaske ne baba ya rasu."? Jibril dai bai ce komai kawai yana sauraransu "Sahid ni mahaifiyar ka Binta , babu abin da zance maka tsakanina da kai , abu guda dana sani ka ci amana, kuma tana tafe domin cinka , ka je za ka gani." Tana gama magana ta shige daki , Jibril ma ya shige dakinshi ya sanya kaya ya fita , yana fita ya ci karo da 'yan sanda tare da Umar da Jafar . Kafin su yi masa tambayar ina Sahid, Sahid ya fito suka sashi a mota suka tafi . Share and comment...............................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) Editing❌ _________________________________________ Page 41 & 42 Hankalin Harun duk yabi ya tashi ganin yadda wasu abokanshi da dama an turo musu sakon ni da yake tabbatar zasu tafi training amma shi Harun bai ga wannan sako ba ko tuntuba, hakan ya sa yake bibiyar inda matsalar take . Anan ma Umar Allah ya ba shi sa'a sai dai ba ya so ya tafi training ba tare da yaga yadda kotu za tai ga Sahid ba , sai dai jafar ya tabbatar masa babu abin da zai gagare shi , tun da suna da kwararran lauya , ga kuma baba GARBA shi ma ya zo. Haka dai Umar ya hakura ya tafi kaduna ba tare da ya so ba. Maryam ce ta fito da gudu daga daki tana sheka amai , tana gama amai ta malale a wajen tana shure-shure . Haka cikin gaggawa mahaifiyar ta , ta kira malam na lado suka tafi asubiti. Yadda alakar Harun da surayya take , lokacin da yake sanar da ita matsalar da ya samu , har an tafi training babu shi , ya roki surayya alfarma data mika takardunshi ga mahaifin ta ambassador, domin ya yi magana da lu'utanal a kan shi. Haka kuwa aka yi surayya ta karba , domin a halin yanzu ma takardun suna hannun mahaifin ta , amma har yau bai samu damar magana da lu utanal ba . Allah sarki Maryam, lamarin dai har yanzu babu dadi , malam na lado da babarta sun shiga damuwa , haka dai dactor ya sa akai mata gwaje-gwaje , daga bisani ta samu bacci Lokacin dasu Hajjiya, matar Alaji Kabiru da zainab suka zo dubata , har suka dawo bata farka ba, Zainab dai ta ji tausayin kawartata tana kuma mata fatan samun lafiya.. Fitowar ambassador ke nan daga gidansu Surayya, ya hau mota rike da wasu takardu a hannunshi, sannan driver ya ja mota suka tafi . Ambassador sake kallon wannan takardun na hannunshi ya ke yi , lokaci guda kuma yana sake mamakin yadda saurayin 'yar tashi Harun ya zama mai irin wannan mummunan hali da lu'utanal ya sanar masa. Wanda lokaci guda yana sake tuna maganar da tafi tsaya masa a rai , da lu'utanal ya fada kamar haka . "Lokacin da Hauwa ta zo min da zancen, sai da muka bibiyi rayuwar shi , muka tabbatar da zargin da ake masa sannan muka hana shi wannan dama , irin Harun mummunan tashin hankali ne zamansu cikin al'uma, kuma bugu da kari mu kara ba su gwarin gwiwa tare da basu aiki irin na soja , ambassador hakan ba mai faruwa ba ne." Ambassador ya yi ajiyar zuciya bayan tunanin da ya gama . Har suka isa cikin gida, ambassador jefi jefi abin yana damunshi , daga karshe yana shiga cikin gidan ya zauna a falo Yadda matarshi ta ganshi haka , ya sa ta fara tambayar ko lafiya, nan take ya sa ta kira masa surayya. Bayan surayya ta zo ya mika mata takardun Harun yana cewa "Ki maza ki kira wannan yaron ki ba shi , kar na sake jin komai daga gare shi , hatta mu'amalar ku na wargaza ta." Dauuu ta ji gabanta ya fadi "Rabuwa da Harun kuma yanzu." Surayya ta fad'a a cikin ranta ta kalli ambassador tana cewa cikin harshen turanci , "Dady me ya sa kuma ? Me yake faruwa."? Nan take ambassador ya sanar wa da Surayya komai , da irin binciken da lu'utanal sukai a kan shi , har suka haram ta masa aikin soja." Surayya ta yi matukar mamaki da jin hakan , abin ya matukar d'aure mata kai. Tashi ta yi ta shiga daki da nufin kiran Harun , Amma sai ta fasa , ta kira Hauwa ta ce ta zo tana ji ranta. Bayan Hauwa ta Harun Surayya ta sanar mata halin da take ciki , nan Hauwa ta sake tabbatar mata da waye Harun, ta tabbatar mata yaudara ce ta kawo shi, babu yadda Surayya ta iya , Ta kalli Hauwa tana cewa, "To yanzu mene abin yi Hauwa." Hauwa ta ce , "Ki kira shi ya zo." Ko awa daya Harun bai 'ba ta ba ya karaso Ya shigo yayi parking da motar shi , sannan ya dauki waya ya kira Surayya. "Ya zo." Surayya ta yi maganar sa'ilin da ta kashe wayar tana kallon Hauwa. Hauwa ta ce , "Ta shi mu je." Surayya ta kwashi takardun suka fita . Tun da ya hango su ya fara washe baki domin a lissafinsa Surayya zata gabatar masa da kawarta ne , ya sa suka taho tare . Suna karasowa Surayya ta sake had'e ranta , ammo sam Harun bai lura da hakan ba, domin yadda ya ga kawartata Hauwa zazzafa ya sa hankalin shi ya koma kanta yana kallonta sama da kasa. Yadda Surayya ta lura da hakan ya sa ta sake jin tsanarshi ta kuma yadda da abin da aka fada mata. Lokaci guda ya maida kallon shi ga Surayya yana cewa "Annurin Rayuwata, barka da fitowa." Tasssssss Ya ji saukar mari a fuskarshi Da gigicewa da tsananin jin zafin marin da mamaki ya kalli Surayya , hannun shi dafe a kuncinsa . Cikin turanci Surayya ta fara magana, "Kalle ni da kyau mayaudari, azzalumi ,na tsaneka Harun ." Ta d'ago hannunta na hagu da ta rike takardun ta watsa masa Sannan da yaren Hausa ta cigaba da cewa , "Sai ka kwashe su , kuma kai da aikin soja har abada. Allah ya mana tsari da kai yi waje ." "Haba Surayya waya shiga tsakaninmu haka , ban yi muki komai ba , amma...." Kafin ya karasa maganar ta sake shara masa mari tana cewa, "Matukar baka fita a gidan nan ba ka sake magana sai na sa an kulle ka." Harun matukar mamaki ya rufe shi ya kasa gane dalili, idan ma shi mayaudari ne ta ya ta sani. Abin ya d'aure masa kai sosai. Ya durkusa ya d'ebi takardunsa ya shiga mota ya tafi . Surayya ta yi ajiyar zuciya tana kallon Hauwa. Malam na lado yana Cikin tashin hankali , jikin Maryam babu kyau , gida suka koma sakamakon tabbatarwar likita cewa Maryam tana da ciki , sun shiga tashin hankali sosai Tana matukar jin jiki sosai ko magana bata iya wa amma haka Malam na lado ya tsaya a kanta yana mata tsawa yana tambayar wanda ya yi mata ciki . "Maryam yanzu wannan shi ne abin da zaki bar mana , cikin shege gidan malam guda." Mahaifiyar ta ta karasa maganar cikin kuka "Wallahi kin bamu kunya kin cutar damu." Maryam cikin radadi tana kuka tana kokarin magana ta fara neman yafiyarsu tana sanar dasu ba ba halinta ba ne ba kuma lefinta ba ne. "To waye ya yi miki ciki Maryam." ?Malam ya tambaya cikin zafi . Maryam tana gumi cikin jinya tana kuka ta fada musu yadda Harun ya yaudare ta . "Lallai wannan yaron baisan gidan da ya zo ba , zan kuwa nuna masa ni Malam na lado malumtata ba a banza take ba." Cikin huci ya karasa maganar "Wallahi baba sam ba zan yi abin da zai cutar daku ba , daga karshe ake tabbatar min haka halinshi yake , ya yaudari mata da yawa, dah nasan zanga irin wannan ranar da na kashe kai na kafin ta zo." Maryam ce ta yi maganar tana kuka , yayin da mahaifinta ya yaji duk tausayinta ya kamashi. Haka ma mahaifiyarta ita ma ta fashe da kuka tana rarrashin Maryam. "Allah ka gani na yi kokarin tsare amanar da ka bani ta Maryam, amma ga yadda ka tsaro lamarin ka." Malam na lado ya fada cikin matukar rauni Sannan ya kalli Maryam yana cewa, "Shi ya sa naso ya turo iyayensa , amma tabbas na yi sakaci , na yi babban kuskuren da bazan yafe wa kaina ba." Share and comment...........................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) Editing❌ _________________________________________ Page 43 & 44 Anan kuma cikin kotu an yi zama na farko tare da karanta irin tuhumar da ake wa Sahid, amma ya'ki yadda da wannan tuhuma , yana sanar da kotu babu wata cin amana da zai iya aikatawa ko handuma ,wanda har zata yi sanadin mutuwar Kalisa. Jibril da babarshi ko kotun ba su halatta ba , haka alkali ya d'age shari'ar zuwa wani lokaci, tare da ba da belin Sahid. Hauwa ce kwance kan kafar Hajjiya. Hajjiya ta ce ,"Wai yaushe ne Abdallaah zai dawo daga Germany zamanshi ne fa ya sa bikin ku har yau ba rana. " Hauwa ta yi Murmushi tana cewa, "Ai momy ya kusan dawowa, shi ma ya damu ya dawo fa." Hajjiya ta ce ,"Ai gara dai ayi -ayi a wuce gun." Hauwa ta ce ,"Yawwa momy kinga ashe wannan yaron Harun, wanda abokina Mahmud ya yi magana a kan shi , har Surayya yaje gunta." Hajjiya ta yi dariya tana cewa, "Tabbb amma wannan yaro ko d'anbanza, yanzu shi ina Mahmud din." Hauwa ta ce ,"Ba ya nan , amma ya ce idan ya shigo gari zai zo ya gaida Dady." Hajjiya ta ce ,"To Allah ya kawo shi." A halin yanzu kowa yana ta magana masu gulma da yamad'd'i suna ta yi cewa Maryam yar Malam na lado ta yi cikin shege , daga wanda zasu zagi ta da iyayenta sai masu Allah ya kyauta da fatan shiriya....... Musamman yadda abin ya yi tsamari da suka koma asubiti aka tabbatar musu tana da cuta mai karya garkuwar jiki , nan malam hankalin shi ya sake tashi , haka suma almajiran malam duk abin bai yi musu dadi ba. Haka ita ma Zainab ta sami wannan labarin, kuma an tabbatar mata da Harun shi ne wanda ya aikata mata wannan abu. Zainab ta shiga wani hali tana ta kuka , yayin data tuna Lokacin da Mahmud yake shirin rabata da Harun take masa wani kallo, har ya kai ta wulakantashi , haka ta ringa kuka tsawon yini guda tana nadama . A Yanzu babu wanda take son ji da gani idan ba Mahmud ba , amma yadda ta ga ba ta da damar , ya sa hankalinta ya sake tashi , cikin kuka ta nufi wajen Hajjiya ta sanar da ita komai kuma ta roketa da ta 'kar'bo mata wayarta wajen Alaji....... "Umma yau ne za a zaman kotu na biyu." Jibril ya sanar da mahaifiyar shi cikin mummunan 'bacin rai ta kalleshi tana cewa, "To mene."? " Ba komai. " Ya ba ta amsa "Ni tsakanina da Sahid kawai Allah ne zai mana hisabi , idan ma kotu ta sake shi ya dawo gidan nan ya ci gaba da zama , amman a ranar gobe akwai tsaiwa tsakanina dashi da mahaifin sa." Jibril ya yi ajiyar zuciya yana jinjina dajin tsoron maganar mahaifiyar tasu." Anan cikin kotu Lauyoyi sai musayar hujjoji suke , domin lauyan Sahid ya yi iya yinshi , har ya ke son gamsar da kotu cewa Sahid sam ba mai laifi ba ne bai kuma aikata wannan tuhuma da ake masa ba . Nan Lauyansu Jafar ya fara sanar da kotu manyan shaidu da kotu ta gamsu dasu , daga karshe haka Sahid ya rasa ta cewa har ya amsa tuhumar, yayin da lauyanshi bai iya kare shi ba . Daga karshe lauyansu Umar ya nemi kotu data umarci Sahid da ya fito da dukkan dukiya da kadarori mallakin wannan marayu har wanda ya kashe ya fita birtaniya , Sannan lauyan ya mikawa kotu adadin kudade da kadarori da Sahid ya zaune." Bayan alkali ya gamsu ya sanarwa da Sahid umarnin kawo wannan kadarori a zaman kotu na gaba........ Ana tashi daga zaman kotu Sahid asubiti ya wuce sakamakon ciwon kafarshi , Umar dai yana can , amma duk sanda akai zaman kotun yana bibiyar yaji yadda aka tsaya , wannan babbar shari'ar har gidan radio ake saurara.. "Malam wannan wacce irin rayuwa ce na shiga uku malam." Mahaifiyar Maryam take fada cikin kuka yayin da take rike da gawar Maryam a hannunta . "Malam Maryam ta rasu ta bar mana duniyar , ina zansa kaina , wallahi bazan yafewa wannan yaron ba , ya Allah ka ga yadda ya yi mana..." Ba tare data karasa maganar ba ta sake rushewa da kuka mai matukar gwanin ban tausayi . Malam na lado shi ma baisan lokacin da wasu hawaye suka zu'bo masa ba , ya kalli gawar Maryam yana cewa, "Na yafe miki Maryam." Ya yi sauri ya fita waje yana kuka . Zainab hankalinta ya kuma matukar tashi sosai dajin labarin mutuwar kawarta Maryam, aiko cikin radadi da nadama ta dauki wayarta ta kira Mahmud amma bai dauka ba kira uku ta yi amma tana shiga ba tare da ya d'auka ba. Ta jefar da wayar gefe cikin kuka tana cewa, "Ya yi fishi dani, ba laifin ka ba ne dole ka tsaneni." Ta sake fashewa da kuka tana cewa "Na juya maka ba ya na cutar da kai,na cancanci duk wani hukunci yaya Mahmud.wallahi yanzu na yi nadama." Ta sake 'kan'kame fulo tana kuka kimanin minti biyar tana kuka tana tunanin Mahmud ta ji wayarta ta fara ringin Cikin jajayen idanunta na kuka da dake ganin dishi-dishi taja wo wayar Yadda idanunta suka nuna mata tai saurin share hawayen tana tashi zaune "Yaya Mahmud." Ta fad'a da mamakin ganin kiranshi Ta kara wayar a kunne tare da sallama Bayan Mahmud ya amsa ta ce ,"Yaya fishi kake yi dani koh , dan Allah ka yi hakuri ka yafe min." Wata karamar dariyar shi taji a can kasa kafin ya ce ,"Haba 'kanwata ni ban yi fishi dake ba , domin babu abin da kika min." Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce ,"Dan Allah yayana ka yafe min , nasan na yi maka ba daidai ba lokuta da yawa."....... Ba tare data karasa maganar ba ya dakatar da ita yana cewa, "Hmmm Zainab ke nan to na yafe miki." "To yaushe zaka zo."? Ta yi tambayar tana ajiyar zuciya Mahmud ya ce ," Zuwa kuma , ai gaskiya ba ranar zuwa domin ayyuka sun min yawan." Cikin muryar shagwa'ba Zainab ta ce ,"Auu baka da lokacin masoyiyarka." Mahmud yaji wani zummm da shaukin yadda ya yi maganar ya ce ,"Ai masoyiyar ba ta sona, har yau, hakan ya sa na mance da ita." Zainab ta fara kukan shagwa'ba da yake jin sautin sa yana masa dadi tana cewa, "Wai Yaya ka dena sona koh." Mahmud ya yi dariya sannan ya ce ,"Ina kika ta'ba jin Yaya ya ce ba ya son kanwarshi , ai har abada bazan dena san ki ba Zainab. " Zainab ta ji dadin maganar matukar gaske cikin shaukin soyayyar shi ta ce ,"To idan haka ne ka zo kano ina jiranka. " "Gaskiya babu lokacin Zainab." Ya fad'a kai tsaye "To gaskiya ni idan baka zo ba a cikin satin nan na yi fushi kuma rijiya zan fad'a." Mahmud dariya ya kuma yi mata yana cewa, "Kanwatyna zan zo kinji na yi alkawari, amma ina Harun yake." Wani yarrrr ta ji da kiran sunan Harun , baki daya sai ta koma sabon yanayi mara dadi ................. "Tun da Maryam ta rasu malam dai kun ga ba shi da lafiya,kuma hakan ya tsayar mana da karatu , gashi malam bai d'au mataki a kan shi wannan mutumin ba." Wani daga cikin almajiran malam na lado mai suna Garzali yana karantawa sauran gardawan su uku abokan karatun shi . Wani mai suna Allaro ne ya ce ,"Ai wallahi ko ni bazan yafe masa ba ." Nazifi ne ya kalli Musa yana cewa, "Kaji su , to ai ba ido zamu zuba ba , tun da aunty Maryam ta rasu shi wanda ya kashe tan ma ko gaisuwa bai zo ba ." Garzali ya ce ,"Ai wallahi da munsan inda zamu ganshi sai ya gane ba shi da hankali, sai mun masa shegen duka wallahi. " Musa ya ce ,"Allah sarki aunty Maryam. Allah ya sa kin huta Allah ya jikanki .".. Harun yana jin jita jitar Allah ya yi wa Maryam rasuwa sai dai bai yadda ba domin bai samu tabbaci ba . Malam na lado ne kwance a daki cikin zazzabi Matarshi ta zauna kusa dashi tana cewa, "Malam yanzu babu abin da zaka yi wa wannan yaron Haruna , kai fa malami ne ko yanzu yana daga d'aki zaka iya kashe shi , amma ka ki aikata komai akai , ka ki daukar mana fansa ." Ta yi maganar cikin ciwo da matukar damuwar rashin 'yar ta . Share, comment and like ................................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) Editing❌ ________________________________________ Page 45 & 46 Malam na lado ya kalli matarshi tare da cewa , "Ubangiji Allah shi ne mai rayawa da kashewa haka ya kaddarowa Maryam rayuwarta , ke ma ina baki shawara ki fawwalawa Allah komai, domin ni na bar shi da Allah, a ranar gobe su tsaya da Maryam su yi Shari'a dan haka babu abin da zan yi a kai wannan shari'ar sai a lahira ." Ta fashe da kuka tana cewa, "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un Allah ya jikan ki Maryam." Malam ya yi ajiyar zuciya. Bayan alkali ya yi rubutu ya ci gaba da sauraran lauyoyi duk kan shaidun lauyansu Umar sun gamsar da kotu , sannan Sahid ya gabatar da wannan kadarori Daga bisani ne alkali ya du'kufa yana rubutu , Yayin da kotu ta yi shiru , lauyoyi suna tattaunawa kowa yana jiran hukuncin da kotu zata yankewa Sahid Bayan alkali ya gama rubutu ya d'ago ya fara gabatar da hukunci .......... Ana fitowa daga kotu Nabila ta fara kiran wayar Umar, domin tana son sanar dashi irin nasarar da suka samu a kotu amma bai dauki kiran ba Haka suka tafi gida suna ta murna da farin ciki ,har da su baba Garba wanda bayan sun koma gida ya wuce 'kauye cikin farin ciki . Bayan wani lokaci ne Umar ya biyo kiran Nabila, nan suke sanar dashi irin nasarar da akai . Ya yi matukar farin ciki sosai da sosai "Mama Allah ya sa mu dace Allah ya jikan baban mu , kin ga ita gaskiya ba ta 'ya'ya yanzu ga shi Sahid ya rasa komai sai gidan bursun aka tura shi." Jibril ya karasa maganar yana kallon mahaifiyarshi Mahaifiyarshi ta yi ajiyar zuciya tana cewa, "Farin ciki na kawai yaran nan an mayar musu da dukiyarsu, shi kuma da aka tura shi kurkuku Allah ya shirye shi , Allah ya sa mu dace." Jibril ya ce ,"Amen mama." Su Garzali ne zaune suna karatu , Musa ya fado kansu cikin gudu yana haki Allaro ne cikin fargaba ya tambaya, "Mene ya ke faruwa jikin malam d'in ne."? Musa cikin wata murya kamar yana barbara ya ce ," Ku taso muje ga wanda ya sanadin mutuwar aunty Maryam can na ganshi a bayan layi." Garzali ya ce ,"To mene zami masa kada malam ya sani fa.' Musa ya ce ,"Babu yadda za ai ya sani kawai ku taho." Suka shiga suka d'e'bo sanduna suka fita da gudu Sauran almajiran 'kolawa suna kallon su . Da gudu suka nufi inda Harun ya ke yana tare da motar shi a kofar wani gida kafin ya an kara ya fara jin saukar duka ta ko'ina, ya fara ihu , dukanshi suke dauu dauu dass dasss har ya kai kasa ba su dena dukanshi ba har suka fara fasa masa jiki , ganin ya kai kasa ba ya motsi Musa ya ce ,"Ku taho mu tafi mu bar maye anan." Garzali ya d'aga sanda ya makawa gilass din motar na baya sannan ya sake 'kwalawa Harun sanda suka gudu. Buja-buja suka koma gida alamun su duk mara sa gaskiya "To idan ya mutu fa .Ya zami mun kashe rai." Allaro ya yi maganar yana kallon su Musa ya ce ,"Wallahi ba zai mutu ba , amma wata kila ya karye." suka kwashe da dariya Musa ya ce ,"Tsoron da nake kada malam ya samu labari." "Ba ta yadda za ai ya samu." Cewar Allaro Mutanen anguwa ne suka taimaki Harun suka kaishi asubiti bayan ya samu kanshi ya kira wani abokin shi Jamilu "Yanzu wane ya maka wannan abin da Allah Harun." Harun cikin zafin ciwo ya ce ,"To Allah ne masani ai domin wallahi ta baya naji an rufe ni da duka ban san komai ba banga kowa ba." Jamilu ya ce ,"Wallahi dukan mutuwa su kai maka dubi kunne ka amma Likita ya ce ba matsala koh."? Harun ya yi ajiyar zuciya tare da cewa ,"wallahi matukar ciwo wannan kunnen yake min , ni bama wannan ba so na ke na koma gida yau ." Jamilu ya ce ,"Wai Tiga kake magana.Ka bari ka warke mana." Harun ya ce ,"Ka ga idan zaka kai ni tom idan ba za ka kaini ba saina kira Yahaya duk da ina ta kiran wayarshi a kashe." "Dan Allah ka bari kaji sauki mana haba Harun ." Cikin bacin rai Harun ya ce ,"Wato na zauna sai yau a biyo dare a kashe ni koh ? Wallahi yau gida zan koma." Jamilu ya ce ,"To ai shi ke nan Allah ya kyauta." Yau dai Mahmud ya shigo kano, Zainab ta matukar farin ciki sosai ya ga kauna da soyayya a zahiri wajen Zainab, Daga karshe har gidansu Hauwa yaje ya gaida mahaifinta wanda shi lu'utanal da kanshi ya ba shi invitation na bikin Hauwa ya sanar dashi yana gayyatar shi. Sahid yana can yana fama da rayuwa sai yanzu yasan da cewa tabbas ba shi da gata ya yi matukar shiga tashin hankali yayin da ya lura tabbas hakkin mahaifishi sai ya bishi , Ga ciwon kafa da yake matukar fama da ita , a cikin satin ne da likita ya je bursun din aka duba masa ita aka kuma tabbatar cancer ce ta kama kafar tashi.Nan hankalin Sahid ya sake tashi matukar gaske . ___________________________________________ Yau su jafar duk suka shirya domin tafiya ta ya Umar murna na passing out din da zasi Nasir da Salma , Nabila, Jafar da Baba anje suka tafi Soyayyar Nabila da Nasir ta yi matukar nisa sosai Umar farin ciki kamar ya kashe shi amma yana ganinsu ya fashe da kuka mai matukar gwanin ban tausayi "Haba Yaya Umar mene haka kuma." Jafar ya yi maganar yayin da ya rungume shi Umar kuka wiwi tare da hawaye Duk sai jikinsu ya yi sanyi Umar cikin kukan ya fara musu magana, "Wallahi tun jiya nake jiran ku Jafar cikin matukar shauki , lokacin dana hango ku Kalisa na gano a tare daku tana ta min murmushi sai da kuka karaso na ga Nabila ce." Wani tausayi suka ji ya sake rufe su mummunan Nabila data fara kuka . Salma ta ce ,"Ku yi hakuri dan Allah Yaya , dama aunty Kalisa ai tana tare da kai addu'a kawai zamu cigaba da yi mata. " Baba anje ta ce ,"Haka ne a dena kukan haka dan Allah domin farin ciki ne ya kawo mu." "Yi hakuri Nabila, inajin zafi da wannan kukan da kike, ki dena baby dan Allah." Nasir yake yiwa Nabila magana yayin da ba kowa ke jin maganar ba . Umar ya yi musu iso zuwa ciki , suka sami guri , ana ta gaisawa nan farin ciki ya karu aka ci aka sha cikin farin ciki . Harun dai ya koma Tiga , nan iyayensa lamarin ya d'aga musu hankali, musamman jin bai samu aikin soja ba, ga kuma abin da ya faru dashi, haka sukai hakuri suka kuma fara nema masa magani , domin kunnenshi ba a cewa komai . Bayan wani lokaci. Wani irin kallo Zainab take yiwa Mahmud, Mahmud ya yi murmushi yana cewa, "Mene kuma Zainab." Zainab ta ce ,"Yaushe ne auren mu yaya Mahmud. " Mahmud ya rike baki cikin mamaki yana cewa, "Eh tabbas kanwata ta girma har aure ma take so." Ta ta'be baki tare shagwa'ba tana cewa, "Ni fa da gaske nake yaya Mahmud." Mahmud murmushi ya sake yi yana kallonta yana gyara zaman hular dake kanshi yana cewa, "Ni ma Zainab wannan ranar nake jira , domin..." Bai karasa maganar ba Ahmad ya shigo falon yana cewa, "Tashi mu tafi." Mahmud ya kalleshi sannan ya tashi tsaye yana kallon Zainab. "Amma zaka dawo ko."? Zainab ta yi wa Mahmud tambaya ajiyar zuciya ya yi kana ya ce da ita ," Gaskiya Zainab bazan dawo ba , da zarar an d'aura auren zan wuce ba sai na dawo baya ba." Zainab ba tare da taji dad'i ba , ba kuma ta so hakan ba ta yi musu sallama suka tafi Mahmud da Ahmad suka nufi d'aurin auren Hauwa, eh tabbas an yi buduri an yi wasa da kud'i mu dai sai dai muce Allah ya sanya alheri. Umar ne ya nufo gidan su Jafar sanye da kayan sojoji yana tura kofar gidan ya ci karo da Nabila da Nasir suna hira, Umar ya yi sand'a ya lalla'ba ta bayansu ba tare dasun sani ba . Share, like and comment......................📚 Gubar Rayuwata⚡🌹 By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) Editing❌ Page 47 & 48 A hankali ya karasa bayan Nasir yayin da yaji yana cewa da Nabila ,"Tun da komai ya yi daidai a gaskiya sai a daura mana aure domin a halin yanzu babu wata..." Kafin ya 'karasa yaji an tallafe masa 'keya, yana juyowa ya ga Umar Duk kunya sai ta rufe Nabila musamman jin maganar da Umar ya fara ,"Eh lallai yaron nan wato ka girma harda zance aure , to ai sai ka bari ta gama makaranta, kai ma ka tsaya da kafafunka kafin ka yi maganar aure ko , amma ka ban mamaki Nasiru." Umar ya karasa maganar yana rike ha'ba Dariya suka yi a tare yayin da Nasir ya bawa Umar hanya domin ya wuce ciki Wani mamaki ne ya kama Umar "Me kake nufi." Ya tambayi Nasir "Yaya ina ce wucewa zakai ciki." Dariya Umar ya sa yana sake kaiwa kanin nashi duka yana cewa, "Dallah wuce muje ciki babu wata sauran soyyaya tunda na zo ." Nabila da gudu tasa kai ta shige ciki , yayin da Umar ya dafa 'kanin nashi suka nufi cikin gidan . Yauu tunda Harun ya tashi ya kasa gane inda yake masa ciwo , hakan ya sa ya yi 'kokari ya nufi asubiti wajen wani abokinshi Dactor Sa'id Yana isa asubitin ya nufi office din shi yana bude kofa kuwa ya ganshi zaune yana cike wasu takardu "Ahhh Aboki Harun kai ne tafe , masha Allah karaso." Cikin farin ciki doctor ya yi maganar Harun yana zama doctor ya kula da tabbas ba shi da lafiya mussaman ganin Fuskarshi a kunbure ga kuma rama hakan ya sa kafin ma su gaisa ya fara cewa "Kaiiiii Harun sannu , baka da lafiya haka ."? Ajiyar zuciya ta takaici Harun ya yi sannan ya ce ," Bari kawai Sa"id , ina cikin wani hali. " Shima doctor ajiyar zuciya ya yi yana cewa, "Meke damunka haka dan Allah." "Abokina ka ga ina fama da ciwuka da bansan daga ina suke ba , domin ka ga ina ciwon kunne." Dactor , ya ce ,"Eh tabbas ga shi na ga yana ruwa." Harun ya cigaba da cewa ,"Ciwon ciki , kasala , kai hatta futsarina ya canja , dama kuwa HIV ba bakuwata ba ce ." Da mamaki abokinshi ya ce ,"Kana nufin kana da ita Harun wa'iyazubillah." Harun ya had'e rai yana cewa, "Ka ga ni dai bana san wani iyayi kawai ka bani magani." Murmushi Dactor ya yi yana cewa, "Gashi ma ko gaisawa bami ba , amma bari na kira nurse ummi taje ta raka ka a yi maka gwaji , shi kuma kunnen naka gaskiya sai ranar da dactor ya zo." Harun ya ce ,"Okay ." Likitan ya d'auki waya ya kira nurse sannan ya durkusa yana rubutu a cikin takarda lokaci guda kuma yana cewa, "Idan ka je a kai maka sai ka dawo mu yi hira kafin result din ya fito." Yana rufe baki Ummi tana turo kofa ta shigo Wani shegen kallo Harun ya zuba mata , sakamakon yadda ta shigo wani sindi-sindin da wani karamin hijabi Had'iye yawu ya yi yanayin shi duk ya canja Sa'id ya bata takardar yana cewa, "Ummi ki kai shi a dubashi bako na ne , idan result ya fito sai ki kawo min ." "Okay sir ." Shi ne abin data fad'a Tana fita Harun yabi bayanta , harda hard'ewa da tuntu'be yana tafiya , yadda ya ga ta ba shi baya tana tafiya yaji kamar ya yi abin da ya saba , domin ta matukar shiga ranshi a wannan yanayi Jitai an sa hannu ana shafa mata baya cikin wani salo , hakan ya sa taji wani yarrrr ta juyo cikin tsananin mamaki da tashin hankali Harun ta gani yana mata wani murmushi, hakan ya sake fusatata "Kutumar uba .Kai wanne irin d'an iska ne wawa shasha ." "Allah ya baki hakuri." Ya yi magana yana duban da hange karta tara masa mutane "Allah wadaran jahili irin ka , baza ka gama da duniya lafiya ba wallahi Allah ya isa. Wallahi ba da ban doctor Sa" id bane ya had'a ni da kai sai ka ga abin da zan maka ". Ta buga wani tsaki tare da harara ta cigaba da tafiya Ana yiwa Harun wannan gwaji ya koma wajen doctor kamar yadda ya ce " Sannu Harun ." In ji abokinshi "To ya kake ya kwanaki ai wallahi na yi zaton zaka dawo da kakin soji." Harun ya ce ,"Ina ta lafiyata ina wani maganar kakin sojoji , wallahi kunne na kamar , kaiii ina shan wahala dactor. " "To Allah ya sauwake yanzu ya ake ciki ne ."? Cewar dactor Sa'id Harun ya gyara zama yana cewa," Yawwa ni abin dake damuna ma wallahi Yahaya ne , domin na jima banajin shi , ga shi har na dawo an ce wai ya tafi legos. ". Ya karasa maganar cikin tsananin son jin Sa'id ya yi magna a kai Sa'id ya ce ," Allah sarki Yahaya , ai wallahi bamu da labarin shi tunda ya tafi legos, bamu san halin da yake ciki ba ." Cikin damuwa Harun ya ce ,"Gaskiya ya kamata mu san halin da yake ciki doctor. " Sa'id ya ce ,"Insha Allah zan sa a bincika mana legos din , domin akwai wani abokinshi Shu'ai bu." A lokacin Ummi ta shigo ta mikawa dactor result din Harun Yayin da ta zo fita ya sake 'kura mata idanu ta jefeshi da wata harara ta fita Bayan ya bude sakamakon ya tabbatar wa Harun yana d'auke da ciwon hanta Amma Harun bai damu ba , sai da doctor ya tabbatar masa ciwon hantarshi mai tsanani da muni ne , domin a kan mutuwa lokaci guda ko kuma hantar mutum ta dan'kare waje daya. Sannan ne hankalin Harun ya yi matukar tashin gaske , nan ya nemi matakan kula d kanshi da magunguna ,bayan ya koma gida ma dai jikin nashi ya sake matsawa sosai musamman ciwon kunnenshi da yake fitar da ruwa mai warin gaske , iyayenshi suna matukar iya yinsu domin samun lafiyarshi amma har yau Allah bai yadda ba . Haka anan cikin gidan yari Sahid rayuwa ta juya masa baya , ya matukar yin nadama yadda ya kula ba shi da wani gata , mahaifinshi babu , mahaifiyar shi bata tare dashi ga kuma wannan ciwon kafar da a halin yanzu zuwa anjuma za a yanketa , innalillahi wa innailaihir raji'un Baya jin dadin rayuwarshi ko kadan a halin yanzu. Allah ka yi mana da kyau A yanzu zainab da Mahmud ranar biki kawai ake jira , domin tuni an yi shiri tsaf dukkan family suna ta murna da wannan had'i . Haka farin ciki a gurin su baba anje , komai ya komai daidai ba su da wata damuwa , Umar yana tare dasu ga dukkan abin da ya taso musu , domin ya sadaukar da rayuwarshi ga Kalisa , sai dai muce Allah ya jikan wanda suka rasu , muma kuma Allah ya.... Matukar ciwo Harun yake ciki, yana tabbatar wa kanshi wannan yanayi da ya tsinta kanshi sa'bon Allah ne da ya ringa aikatawa, sai dai a halin yanzu Harun ya matukar shan jiki Wannan ciwon kunne , matukar wari, ruwa kuwa ba dare ba rana , sai ya tafi ya fara jin sauki sai komai ya sake lalacewa, ya ringa sunbatu ke nan har yake sanar da iyayensa irin abin da ya aikata a kano , ya ce musu alhaki ne ke bibiyarshi, su dena nemar masa magani . Sun matukar koka sosai dajin halin yaron nasu , sai dai dukkan inda aka ji mai magani ana nemawa Harun , amma har yau ba a dace ba , ko da ya tafi sai ciwon ya dawo , har da kanshi ya gane mutane gudunshi suke saboda wannan wari da yake cutar dasu. Babban abin da ya sake girgiza shi yadda doctor Sa'id ya tabbatar masa da mutuwar wulakancin da Uncle Yahaya ya yi abin ya sake d'aga masa hankali da jin tsoron duniya. Wata mata ce dumur mur da ita zaune a falo tana wasa da 'yarta wacce bata wuce shekara biyu ba Matar tana jin an kwankwaso kofar falon ta tashi ta bude Mijinta ne ya dawo daga wajen aiki , nan ta tarbeshi ya karaso ciki yana d'aukar 'yar tashi yana mata wasa Matar tashi ya kallah yana cewa, "Faiza wannan babyn tamu fa ta yi wayo , a gaskiya ya kamata a yi maka 'kani." Ohhhh ni ko na ce ashe faiza ce da mijinta , iko sai Allah Cikin wata kissa ta kalleshi tana amsar babyn ta aje ta gefe , kana ta rungumo mijin nata tana cewa, "Ai ni kai nake jira , duk sanda ka shirya." Yadda yaji yanayin ya masa dadi ya sa ya fara sunbatar Fa'iza , ita ko ta sake kankameshi tana....... Ooooooohh nan mata da miji ne , kowa ya basu guri , daman Fa'iza yaya a baya , bare yanzu me dalili . Ni ko na ce Alhamdulillah ala kulli halin , anan na kawo karshen wannan kaggagen labari mai suna GUBAR RAYUWATA⚡🎈 Abin da mukai daidai Allah ya amfana Abin da ya faru sakamakon karancin ilmi ina fatan Allah ya haskakan anan gaba Ni Fatima Abdallah kano (Autar marubuta) Ina mika godiya ga masoyana masu comments, like da kuma sharing Allah ya saka muku ya cika muradan ku. A kan haka nake muku albishir da sabon labari mai suna FATIMA DA ZARAH. Wanda ya samu tsarawa da shiryawa daga gareni . Anan zan barku tare da dukkan wani fatan alheri 🙏🙏🙏 07040805269 Autar marubuta Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels