Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels MAI FARAR ƘAFA (JAHILCI NE) NA MAMAN AFRAH FCW GAJERAN LABARI FREE BOOK🥳 Page 1️⃣➡️2️⃣ Zaune take a kan kujera mai zaman mutum biyu, ta yi nisa a cikin tunanin da ita kanta bata san lokacin da ta dulmiya ba bare har ta san lokacin da za ta dawo daga nisan kiwon saƙa da warwarar da zuciyarta take mata a kan al'amuran rayuwar aurenta. Fara ce amma ba sosai ba tana da matsakaicin tsayi sai dai ba za a kira ta da gajera ba, shekarunta ba za su haura ashirin da biyar ba. Safiyya kenan ƴa ga Malam Sadiq da Majida, abubuwan da suka taru suka cunkushe tare da cukurkuɗe tunaninta abu guda ɗaya ne wanda a kullum shi ne ginshiƙin da ya yi fice wajen daƙushewar duk wata walwala da farincikinta wannan abu ba komai bane fa ce jifanta da wasu mutanen suke da MAI FARAR ƘAFA. Wannan suna yana mata ɗaci a zuciyarta wanda wani s'in ta kan rasa a wane ma'auni za ta ajiye shi domin ita kanta bata san mafarin wannan al'amari ba bare har ta san ummul aba'isin samun sunan da har yau samuwarsa a gareta ba ƙaramin abu bane wanda take jin zai iya haifar da gagarumar matsala a rayuwarta matsawar dai mutane za su cigaba da mata kallon MAI FARAR ƘAFA. "Ni yanzu ya zan yi da rayuwata, shin ina zan saka kaina me ya sa mutane basa gane cewar ni ma mutum ce kamar kowa ni ma ina da galihu kamar kowace mace mai ya sa mutane ba za su fahimci ni ma ina da ƴancin da zan rayu a gidan aurena kamar yadda kowace mace take rayuwa ba, amma a iya ƙarancin shekaruna a ce wannan shi ne gidan aurena na uku kuma a kowane gida sai da na haihu amma zargi irin na jahilci ba ya bari na cigaba da kasanceqa da ƴaƴana a gidan ubansu sai dai kowane na fito na bar shi ba dan raina yana so ba sai dai babu wata mafita da ta fi hakan. " Safiyya ta kai ƙarshen zancen zucin nata da ɗan muskutawa ta gyara zamanta duk da har lokacin tana cikin kogin tunanin da ta dulmiya. "Kowace mace taa rayuwa a gidanta hankalinta kwance sai dai ɗan abin da ba a rasa ba amma ni a nawa gidan saɓanin haka ne, ni kullum cikin fargaba da zulumin wanzuwata a gidan auren ko akasin haka, kullum kunnuwana suna tsoron sauraran furucin saki sabo da na san mutane jahilcinsu ba zai bari su bar ni na rayu cikin farinciki ba. karkaceccen tunaninsu da ba shi da madogara ya hana su bar ni na rayu cikin kwanciyar hankali, tamkar dai ni ce kaɗai mace a doron ƙasa shikenan ni bani da kataɓus a gidan miji ko a unguwa, shin mutane mai ya sa ba za su gane komai Allah ne yake ƙaddarawa ba Allah kaɗai ne yake bayarwa kuma shi ke hanawa shi ke azurtawa kuma ya talauta, yana bayar da arziƙin ga wanda ya so a kuma lokacin da ya so sannan ya kan ƙwace a lokacin da ya so ba tare da sanin wani ɗan adam ba bate har a ce shi ne silar damuwa ko salwantar wani abu!" Ta kai ƙarshen maganar lokacin da hannunta ke kan tirtsetsan cikin da haihuwarsa ko yau ko gobe. Ba komai yake saka ta a damuwa ba a halin yanzu sai ganin samun mijinta Rabi'u ya ragu kuma ta ji yana ta faɗar maganganu irin wanda mutane ke jifanta da su, maganganu irin wanda su ne silar fitowarta daga gidan mijinta Sani da kuma gidan mijinta na biyu Salisu. Wanda lokacin da shi Rabi'un zai aure ta ya yi watsi da maganganun yana ikirarin jahilcin mutane ne amma yanzu ana wayar gari ya fara hasashe tare da fara gaskata maganganun mutane, wanda hakan ba ƙaramar barazana bace ga aurenta domin kuwa ta san hakan yana dai dai da mutuwa, sutura tare da binne aurenta, ita yanzu a tsorace take da lamarin Rabi'u ta san a ko da yaushe zai iya sakinta shikenan ita kuma haka za ta ƙare rayuwarta kullum cikin aure-aure? Auren da ba ya ɗaukan wani dogon lokaci yake mutuwa, da yarintarta amma ake mata auri saki ba tare da wani laifin komai ba. "Safiyya, Safiyya, Safiyya" Kiran da mijin nata Rabi'u kr faman zabga mata shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da bata san iya tsawon lokacin da ta ɗauka a ciki ba. A zabure ta fara ƙoƙarin tashi sabo da nauyi da jikinta ya mata, a gefe guda kuma zuciyarta na ata wani irin zillo wanda yake haɗe da faɗuwar gaban da ta ziyarce ta babu gaira babu dalili wani mugun tsoro yana yi wa gangar jikinta sallama a haka ta yunƙuro ta taso tana jin tsoron na ƙara kai mata ziyara dan daga jin kiran nan ta san akwai wata a ƙasa tabbas tana zargin akwai abin da ya faru ko kuma yake shirin faruwa. Da sauri -sauri ta taso ta fito daga ɗakin dan har ta manta da tirtsetsen cikinta da ke cikin wata na tara, sabo da tsabar kiɗimar da take ciki. A dai dai bakin ƙofar shiga falonsa suka yi kiciɓis yana ƙoƙarin fitowa. Tun da suka ci karon jikinta ya fara mata wata irin ƙyarma wanda ganin biro da takardar da ke hannunsa su ne suka haddasa mata hakan. Ko ta kanta bai bi tamkar ba shi ne ya ƙwala mata wannan kiran ba sai ma farar kujerar plastic da ya nufa ya fara. ɗora takardar hannunsa wacce shigowarsa yanzu ya shiga falonsa ya ɗakko, a lokacin da yake ƙwalawa Safiyya kiran. A hankali Safiyya ta fara ja da baya har sai sa ta ji ta jingina bayanta sa bango sannan a saka hannayenta ta daddafe, a lokaci guda kuma wasu hawaye masu zafi suka shiga wanke mata fuska wanda ba komai ya kawo hakan ba sai sanin da ta yi cewa zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi. "Oh ya Allah, ka zama gata kuma bangona abin jingina Allah ka bani ikon cinye duk jarabawar da ka jarabceni da ita da ma wacce za ka jarabce ni a nan gaba" Ta faɗa a zuciyarta idanunta kafe a kafin Rabi'u da ya sunkuya ya daddage yana rubutu a takarda. "Ungo nan kije na sake ki saki uku!" Maganarsa ta katse mata tunaninta. Kallon takardar da yake miƙo mata kawai take amma ta rasa ƙarfin gwiwar da za ta saka hannu ta karɓa. Jikinta kuwa sai rawa yake tamkar mazari gabanta banda dukan uku-uku babu abin da take. "Ki fice mini daga gida ga takardarki na sake ki saki biyu" Maganar sani ta faɗo mata a ranar da ya sake ta. "Kar in dawo in tarar da ke a cikin gidana ki fice mini daga gida na yanke igiyoyin da ke tsakani na da ke" Ta ƙara tuno maganar da Salisu ya faɗa mata ranar da zai sake ta sannan yanzu ma ga Rabi'u yana furta mata kalma mafi muni da rashin daɗin sauraro. "Babu yadda za a yi in cigaba da zama da matar da za ta kassara mini rayuwa, tun daga lokacin da na aure ki komai nawa ya tsaya cak, komai nawa ya canja daga fari zuwa baƙi ba na banbance duhu da haske ina dalili alheri sai ya zama mugunta na taimake ki na aureki amma kina neman ki daka na yi mutuwar tsaye komai nawa babu cigaba sai ci baya, a kullum al'amura daƙile mini suke kasuwa babu ciniki sai kwantan kaya, babu riba sai faɗuwa yanzu ina zuwa kasuwa na samu gobara ta kama shagon mu duk kaya sun ƙone mun yu mummunar asara duk da an kashe wutar amma ba ƙaramar asara muka yi ba, mai ya sa duk guntun shaguna basu kama da wuta ba sai nawa? Mai ya sa shagona da na maƙocina ne kawai giobarar ta yi wa dirar mikiya, sabo da shi ma ya raɓu da ni mijin MAI FARAR ƘAFA shi ya sa hakan ta same shi, kowane shago ana ciniki mutane suna ta tururuwar zuwa amma ni dai dai in gani daga nesa babu mai zuwa sai ƙalilan daga ƙarshe da aka ce kayana ne da tsada duk na karyar da su dan kawai na damu ciniki amma a banza shiru kake ji wai malam ya ci shirwa.To a yau na kai bango na kai maƙura na kai ƙarshe ya zama dole na jefar da ƙwallon mangwaro ko na huta da ƙuda kamar yadda sauran mazan da kika aura a baya suka jefar da ƙwallon mangwaron kuma suka huta da ƙudan ni ma yanzu na bi sahu sai a bi wani sarkin amma ba Rabi'u ba dan ni ko maƙiyina ne na ga zai auri mace MAI FARAR ƘAFA to wallahi zan ajiye ƙiyayyar da ke tsalaninmu in yada makaman yaƙina in yi ruww in yi tsaki dan ganin bai auri mace MAI FARAR ƘAFA ba" Rabi'u ya kai ƙarshen maganar yana mai ɗaga muryarsa tamkar wanda yake magana da wanda yake suke da muguwar razara a tsakaninsu bayan kuwa ga shi ga Safiyya wacce hawaye ke ta faman malala tamkar an buɗe famfo bakinta yana ta karkarwa tana ta so ta yi magana amma ta kasa tsabar kaɗuwa da maganganun Rabi'u duk da cewa ba wannan ne karo na farko da ta ji su ba , ta sha jin su daga bakuna mabanbanta, amma yau sai ta ji maganganun sun yi wa majiyar sautin ta shiga irin shigar karan tsaye wanda hakan ya ke ƙoƙarin yin barazana ga daƙushewar sauran jinta. "Wai ba magana nake miki ba kin tsaya sai zubar hawaye kike tamkar dai an saar da ke mutuwar wani shaƙiƙin ki?" "Dan Allah ka yi haƙuri wallahi duk abubuwan nan da kake faɗarsu ba laifina bane, ba ni ce ummul aba'isin faruwar hakan ba komai da kake gani muƙaddari ne daga ubangiji babu wani mahluƙi cikin bil adama da ya isa ya yi wa wani ɗan adam mummunan abu face komai yana faruwa ne da sanin da kuma izinin ubangiji komai sai Allah ya so yake faruwa duk abin da ya faru Allah ne ƙaddara kuma yana ji yana gani zai kawo maka mafita matsawar dai ka dogara da shi kuma ka yi imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau ka ɗauki komai a matsayin jarabawarka idan ka yi hakan Allah zai baka damar cinye jarabawar k... "Ke dalla malama dakata!!! Duk waɗannan abubuwan waye ya tambayeki? Shin kafirtani kike so ki yi? Ko an faɗa miki ban yi imani da Allah da ranar lahira ba hatta ƙaddarar na yi omani da ita dan kuwa yana daga cikin ƙaddarta aurenki tabbas ni na san auren MAI FARAR ƘAFA Allah ne ya ƙaddara mini amma babu yadda za a yi mutum yana ji yana gani ya je ya afka cikin wuta ya ƙone ƙurmus, dan haka ni yanzu babu komai a tsakanina da ke saki ne na sake ki gabaɗaya igiyar auren na yanke bare ki yi kwaɗayin in mayar da ke, ciki ne ki je gidanku ki haife zan masa yanka duk ranar da kika buƙaci bani ɗana to ƙofa a buɗe take za ki iya aiko mini da shi ko da kuwa a ranar da kika yaye shi ne kika cire shi a nono, yanzu ki karɓi takardar nan ki kama gabanki tun kan lokaci ya ƙure miki dan ni zamanki cikin gidan nan ma tamkar annoba haka na ɗauka" Ta kasa furta komai hannunta da ke karkarwa ta miƙa masa ya dangwara mata takardar, wani yawu ta haɗiye mai ɗaci tana jin tamkar wanda ya damƙa mata garwashin wuta a tafin hannunta, ba kowa take tunawa ba sai mahaifiyarta tabbas sai ta fi kowa shiga damuwa. MAI FARAR ƘAFA (JAHILCI NE) NA MAMAN AFRAH FCW GAJERAN LABARI FREE BOOK🥳 Page 3️⃣➡️4️⃣ A hankali ta fara jan ƙafafunta wanda suka mata ɗauyi hanyar ɗakita ta nufa duk da tana ganin wani dishi-dishi ga duhun ruwan hawayen da yake mata shamaki da ganin gabanta a haka ta tafi da tsohon cikin nan, bedroom ɗinta ta nufa ta ɗakko akwatinta ƴar tsakiya ta buɗe dama babu komai a ciki ta buɗe wardrobe ta shiga ɗaukan kayanta tana zubawa ita kanta bata san wane kaya babe take zuba wa shin hijabai ne ko mayafai ne ko less ko kuwa atamfofi abu ɗaya ta sani shi ne kayanta ne take zubawa. Bata ankara ba sai ganin ta yi idan ta zuba kayan suna zubewa a ƙasa sai a lokacin ta lura cewar akwatin ta daɗe da cika da kayan har ta kai matakin da murfin ma ba zai rufu ba bare a yi zancen zige zip. Hannu ta kai ta kwashi wasu kayan ta mayar ba tare da ra lura da yawan wanɗan da suka rage a akwatin ba ta zige zip ɗin ta ɗauki hijabin da take sallah wanda yake linke haɗe da sallayarta ta saka ta ɗauki akwatin har ta fara tafiya ra tuna da takardar sakin da aka bata yanzu wacce tun shigowarta da za ta ɗakko akwati ta ajiye a kan gado. Hannu ta sanya ta ɗakko takardar ta haɗo fa ƙaramar jakarta pos, tare da janyo akwatin ta fito falo wayarta ta ɗauka ta saka a cikin jakar tare da takardar ta fito daga falon janye da akwatin. Kallo ɗaya ta yi wa Rabi'u da ke tsaye a tsakar gidan ya kama tsantsa tamkar wanda yake jiran a ce masa kulle ya ce cass. Juyawa ta yi ta kama hanya za ta fice "Idan an tashi zuwa ɗaukan kaya ki yi wa iyayenki karnki biyo masu ɗaukan kayan, dan ba na son ki ƙara tako ƙafarki cikin gidan nan" Ta ji amon muryarsa ya ratsa dodon kunnenta ba tare da ta juyo ba ra cigaba da tafiya dan bata da wasu kalamai da za ta iya furta masa su. Tana fitowa ta tare ɗan sahu ta shiga tare da faɗa masa inda zai kaita, shi ya karɓi akwatin ya taimaka mata wajen shigar da ita cikin adaidaita sahun sabo da ganin yadda take jan akwatin dakyar sannan ga kuka wanda bai san dalilin zubar da hawayen nata ba. Haka ya shiga ya tada suka ɗau hanya. Safiyya kuwa tun da ya fara tafiya babu abin da take sai zubar da hawaye, ta wajen gidan Kakarta suka wuce gidan rufe yake da mukulli domin kuwa Kakar tata ta daɗe da rasuwa ta so a ce Kakar tata tana raye da a can za ta yi zamanta babu takura babu tsangwama saɓanin cikin gidan mahaifinta da ya zame mata kamar magarƙama sabo da rashin jin daɗin zama da kuma takurawa wanda take fuskanta a wajen kishiyar mahaifiyarta a duk lokacin da aurenta ya mutu tamkar a kanta aka fara mutuwar aure ta yi ta jifanta da mafanganu mararsa kai da ƙafa. Tana zancen zucin tana ta sharar hawaye bata ankara ba sai ta ji yo sautin muruar ɗan adaidaitan yana tambayarta. "Baiwar Allah a dai dai ina zan ajiyeki" Ya tambaya ganin sun shigo unguwar da ta ce ya kaita. Sai da ta sauke wata nannnauyar ɓoyayyar ajiyar zuciya sannan ta buɗe baki dakyar kamar mai ciwon baki ta ce "Wannan kwanar za ka shiga gida na biyu" Karya kwanar layin ya yi yana zuwa ya tsaya a ƙofar gida na biyun kamar yadda ta faɗa. Jim ta yi kamar ba za ta fito ba sai kuma ta sako ƙafafunta ya fito cikin sanyin jiki. Da kanta ta fito da akwatin nata ta buɗe pos ɗin ta bashi kuɗinsa kamar yadda ya faɗa yana karɓa ya ja ɗan sahunsa ya bar wajen. Yana ta tunanin kukan da Safiyyar ke ta yi bata ma tunanin ana kallonta tana kuka a titi sai dai tunawa da ya yi cewar akwai wasu damuwoyi da dama wanda mutum zai ji ya kasa riƙe zubar hawayensa ko da kuwa a ina yake kuma ko da a gaban waye. A hankali ta ja akwarin idanunta da ke cike taf da hawaye suna kafe a kan ƙofar gidan mahaifin nata ba komai take tunawa ba sai yadda mahaifiyarta za ta ji idan ta ji cewar aurenta ya ƙara mutuwa a karo na uku kuma ba tare da ta yi wa gabaɗaya mazajen da suka saketan wani laifi ba. Tafe yake a cikin motarsa, sanye yake da baƙin jeans da farar riga sai kuma baƙin takalmi da yake sanye cikin fararen ƙafafunsa. A hankali yake tuƙin idanunsa kafe a kan ƙofar gidan da yake hango wata a tsaye riƙe da akwati, amma shi wacce yake son yin tozali da ita ba ya tunanin a yau ma zai sake sakata a idanunsa domin kuwa ya ɗauki tsawon lokaci yana zuwa domin ya ganta ko da wulgawarta ne amma abin ya fassakara. "Kina ina ne sarkin kuka, shin mene ne damuwarki? Mai kike so waye ya taɓa ki kin barni a damuwa ina ta tunanin damuwarki duk da cewar baki san da zamana ba bare har ki san na damu da damuwarki, sai dai abin da ya bani ƙarfin gwiwar ci gaba da jiranki sji ne na san ba matar aure bace tun da gidan ya mini kama da gidanku ne ba wai gidan aurenki ba zan cigaba da jiranki har ranar da Allah zai ƙara haɗa ni da ke wanda hakan zai sanya na rufe duka babin damuwar da ke cikin zuciyata" Cewar Annur da ke zancen zuci yana tuƙi. A dai dai lokacin da ya ƙaraso ƙofar gidan da yake son ganin wacce yake fata da burin sanyata a idaniyarsa a kullum. Tun da yake a rayuwarsa sai biyu ya taɓa ganinta kuma a ƙofar gidan da take tsaye tana zubar da hawaye. "Allah ka karɓi addu'ata ka ƙara haɗa ni da ita ba tare da na bi ta hanyar wani ba" Ya faɗa a dai dai lokacin da zuciyarsa ta buga da uban ƙarfi sanadin idanunsa da ya sauke a kan kyakkyawar fuskarta wacce take zubar da hawaye kamar yadda ya taɓa gani sau biyu yau ma hakan ce ta faru sai yanzu ya tuna cewar gabaɗaya ganin da ya mata sau biyu lokacin ma tana riƙe da akwati a hannunta sai dai gabaɗaya akwatinan mabanbanta ne kamar yadda ya lura domin kuwa babu wani abu duk ƙanƙantarsa da zai manta a game da ita. Da sauri ya take birki wanda ƙaran ya sanya Safiyya da ke tsaye har lokacin bata shiga gidan ba ta juyo da sauri domin ƙaran motar ya dawo da ita daga tunanin da take na yadda za ta shiga gidan nasu da kuma abin da zai faru. Hannu ya sanya ya shafe fuskarsa tare da murza idanunsa domin tabbatar da abin da idanunsa ke masa tozali da shi, domin yana son bambance tsakanin aya da tsakuwa yana son tabbatarwa cewar ba ƙarya idanunsa ke masa ba, kuma ba gizo bane sannan ba mafarki bane kamar yadda yake yi a kullum ita ɗin ce a zahiri, sabo da tsabar farincikin da ya samu kansa ciki ko lura bai yi da tirtsetsen cikin jikinta ba. Safiyya kuwa dawowarta cikin hayyacinta daga tunani sai ta yanke shawarar shigewa cikin gidan. Annur kuwa da mugun sauri ya buɗe motarsa dan yana so ya cim mata amma yana sako ƙafarsa hakan ya yi dai dai da jan akwatin da Safiyya ta yi ta shige cikin gidan. Ko ƙofar bai tsaya rufewa ba dan so yake ya mata magana cikin gudu-gudu sauri-sauri ya tunkaro wurin sai dai cikin rashin sa'a Safiyya har ta shige dan ita bayan motar babu wani da ta gani dan gilashin motar yana da yalwar baƙi baka ganin na ciki bare ma tana cikin yanayin da ba za ta iya lura da ko waye a motar ba dan dama yana daga cikin halinta ƙin shiga sabgar mutane da shiga abin da babu ruwanta. A dai dai ƙofar ya tsaya daga ɗan baya-baya idanunsa kafe a jikin ƙofar zuciyarsa tana ta zillo tana kaiwa da komowa dan ganin wacce duk bugun da zuciyar za ta yi tare da ita yake bugawa duk da bai san sunanta ba. Hannayensa duka biyu ya saka a cikin kwantacciyar sumar kansa yana murzawa tare da yamutsawa idanunsa na kawo ƙwallar da bai san dalili ba sai dai hakan ya san ba ya rasa nasaba da halin da ya ga wacce yake muradin gani cikin halin damuwa na zubar da hawaye. Ya fi minti uku tsaye a wurin yana kallon ƙofar daga bisani ya juya cikin rashin ƙarfin jiki ya nufi motar tasa. Shiga motar ya yi ya zauna jiki babu ƙwari, goshinsa ya ɗora a kan sitiyarin motar yana jin wani abu na ratsa dukkanin ƙofofin jikinsa ya daɗe yana so ya ganta ko da daga nesa ne tsawon lokaci bai ganta ba amma kuma yau ya samu ganinta sai ya ji yana so ya mata magana, so yake ga ganshi tare da ita ya tambayeta damuwarta ta faɗa masa domin yana so duk runtsi ya yi maganin damuwar tata dan ba ya ƙaunar ganinta cikin ƙunci ya fi so ya ga murmushi shimfiɗe a kan fuskarta duk da bai taɓa ganin murmushin nata ba amma dai zai fi kyau a ce murmushin ne ya maye gurbin kukan dan ya san dai babu yadda za a yi kuka ya fi yi wa mutum kyau sama da dariya. Sai dai kash! Hakan bai samu ba. Ya jima zaune a cikin motar amma bai ga ta fito ba kuma bai ga wani ya shiga gidan ba duk da ya ɗaukawa kansa alƙwarin ba zai taɓa neman wani ya haɗa shi da ita ba ya fi so shi sa kansa ya samu wannan damar. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗagowa daga kan sitiyarin ya sanya hannu ya rufo ƙofar yana jin babu daɗi a ransa dan har wani ciwo-ciwo ya ji kansa yana yi masa. Motar ya kunna ya bar wajen yana rayawa a ransa cewar zai dawo ko Allah zai sa ya ƙara ganinta. Safiyya kuwa shigarta cikin gidan muryarta har rawa take yi wajen yin sallama, Mama Majida da fitowarta daga kicin riƙe da kofi ta ji sautin yin sallama amma muryar mai sallamar ta mata kama da ta wacce ta sha kuka ta ƙoshi dan haka wajen hanyar ƙofar ta kalla aikuwa idanunta suka sauka a kan Safiyya da ke ƙara yin sallama a karo na biyu da ƙarfi gaban Mama Majida ya bada wani sautin rass sabo da tsabar kaɗuwar da ta ziyarce ta a lokacin da idanunta suka sauka a kan akwatin ƴar tata. "Innalillahi wa inna ialaihir raji'un" Shi ne abin da take ra maimaitawa a zuciyarta. Duk da ta san aure rai ne da shi kuma babu wanda ya isa ya canja ƙaddarar ubangiji, sannan ba wai ta gaji da kasancewar ƴar tata ɗaya tilo bane da ba za ta so dawowarta gida ba duk da buri kowane iyaye a kan ƴaƴansu bai wuce su gansu zaune ɗakin mijinsu suna zaune lafiya da kuma kwanciyar hankali ba, babu wasu iyaye da za su so mutuwar auren ƴaƴansu sai dai idan haka Allah ya ƙaddaro sai dai ta san muddin auren Safiyya ya mutu to wani sabon tashin hankalin ne domin kuwa abokiyar zamanta da kuma sauran mutane ba za su bar ta ta rayu cikin farinciki ba sun ringa jifanta da maganganu da kuma kiranta da MAI FARAR ƘAFA. Ganin Safiyyar ta tsaya riƙe da akwatin ta kasa gaba ta kasa baya sai Mamar ta sunkuya ta ajiye kofin hannunta cikih sauri ta nufi wajen ƴartata zuciyarta na mata wani irin rauni da bashi da misali ko kwatankwaci tana zuwa suka rungume juna domin Mama ba sai an mata bayani ba yanayin da ta ga Safiyya a ciki yanayi ne da take ganinta a ciki a koyaushe idan rabuwar aure ta gifta mata, bare kuma akwatin fa ta gani shi zai ƙara tabbatar mata da hakan. Tun da suka rumgumi juna Mamar ke ta faman bubbuga mata bayanta alamar lallashi sabo da Mamar ta kasa furta komai harshe da laɓɓanta sun mata nauyi. "To fa! Na dawo in ji ɗan yawon duniya, baƙon jiya ne ya ƙara dawowa? Allah suturu buƙwi in ji kishiyar mai doro, taɓɗi! Ai dama banza ba ta kai zomo kasuwa tun da abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma dukansa ake. Ai sai ko dangana dan babu mai iya zama da ƴarki MAI FARAR ƘAFA! Haka kawai talauci ya baibaiye shi bai ji ba bai gani ba wannan shi ne aure na uku da ƙananan shekarunta kowane gidan biyu ta haihu wannan na ukun kuma an ƙoro miki ita da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe kai a yanzu ma naƙuda za ta iya tashi mata, ai abin da ya dace kawai ku samu dajin Allah ta'ala ku kafa bukka ku zauna ku rungumi ƙaddararku, kun ga kun keɓe kan ku daga jama'a babu wanda wata masifa za ta samu tun da kun nisanta da mutane dan kin san dai ko gidan nan ta zauna samun Malam raguwa yake a toh gwara ta fidda rai daga zaman aure dan ko aure ɗari Safiyya za ta yi sai an sako ta!" Muryar Umma Asiya ta karaɗe kunnuwan Mama da Safiya da ke rungume da juna sun yi mutuwar tsaye duk da sun saba jin maganganu sama da haka ma amma na yau sai suka fi na kullum zafi wai su koma daji su gina bukka su zauna su kaɗai wato ma sun zama annoba, har da faɗar ko aure ɗari ta yi sai an sake ta. MAI FARAR ƘAFA (JAHILCI NE ) NA MAMAN AFRAH FCW GAJERAN LABARI FREE BOOK🥳 Page 5️⃣➡️6️⃣ Cikin rashin kuzari Mama ta saki Safiyya daga rungumar da ta mata ta juyo tana kallon Umma Asiya da ke tsaye ƙofar ɗakinta tana wani hura hanci da ɗaga kai. "Wai hayaniyar mai nake ji ne? " Cewar Malam da ya fito daga ɗakinsa yana wani baza babbar riga. "A'a Malam gani ai ya kori ji, gata nan dai wannan mai ƙashin tsiyar ce wacce bata da ƙashin arziƙi mijin nata ya ga ba haza ya mata abin da ta saba ji da gani wato ya warware igiyar aurensa daga kanta, domin ya ga ba zai iya fuskantar raɗaɗin babun talauci ba shi ne nake cewa tun da ta ƙara kaso auren nata ta taho gida bayan ƙannenta duk suna gidan aurensu amma ita ta gwammace ta zo take haɗa kafaɗa da mu duk da dama kuma auren nata ma kasada ce yo kasada mana auren da baka da tabbas ɗin zamansa kullum kana jiran tsammani" Ta faɗa tana wani taɓa hannuwa tare da maida ɗaya hannun haɓarta. Mama kuwa kawai kallonta take idanunta cike da ƙwalla dan ta san makirci irin na sobar zaman nata shi kuwa Malam Sadiq dama duk abin da ta faɗa masa tamkar ta yi zane ne a kan dutse dan ba ya ji ba kuma ya gani. "Ke! Safiyya wato dai auren naki ne kika ƙara kashewa a karo na uku? To tun da ke bakya son zaman aure sai dai zawarci to ki san da saninki cewar na gama ɗaukan ɗawainiyarki dan yanzu kin kai munzalin da za a ce mijinki ne zai ɗauki ɗawainiyarki to tun da bakya son zaman aure ni babu akuyar da zan siyar ta dawo tana ci mini danga, dan haka ki kwana da sanin ke ce ci da shanki da kuma suturarki a cikin gidan nan. Tun da babu Allah a ranku daga ke har uwarki kullum aikin ku biye-biyen Malamai kuna tsotsewa mazan da suka aure ki samun su da kuma arziƙin da suka mallaka" Cewar Malam yana aikawa Mama da Safiyya wata uwar harara mai tattare sa tsabagen jin haushinsu. "Malam ko da bin Malamai sauran abin fa a jikinta yake baka ga ƴaƴana da suke da ƙashin arziƙi ba su suna can lafiya limi a ɗakin mazansu ba kullum arziƙin mazansu yana haɓɓaka ba, ai kawai in ka ga ba za ka iya ba ka hankaɗa keyarta daga gidanka ta nemi ko gidan haya ne ta tare dan ba zai iyu ake zaginka a gari ana cewa ka hana ƴarka zaman AURE ba basu san FARAR ƘAFARTA bace silar komai tun da dai ka san mu ma idan ta zauna a gidan nan ba tundun tsira muka hau ba samunka raguwa yake abinci ma yana neman gagararka samu" Umma ta faɗa cikin wat murya mai ɗauke da amon kissa da kisisina, har da wani karkata kai gefe dan maganganunta su ratsa majiyar sautin Malam ɗin da kyau kar fa a samu tangarɗa duk da ta san hakan mai wahala ne a samu. "Safiyya ki je ki kama hayar gidan da za ki zauna dan ni ba zan cigaba da zama da ke ba tun da kin ƙi zama a ɗakin miji, tun da ƙaddararki ce zama ba aure sai ki ware daga mutane dan kar FARAR ƘAFAR da kike da ita yake shafar jama'a" Sautin muryar Malam ya karaɗe majiyar sautin Safiyya wacce dama ta kwana da sanin faruwar haka sai dai bata yu zaton abun har zai yi tsamari haka ba. Wani duhu ta fara gani yana mamaye ma'adanar ganinta domin maganganun Malam da na Umma har wani amsa kuwwa suke mata musamman wurin da Malam ya ce wai ta nemi gidan haya ta zauna kenan abin har ya kai mahaifin da ya haifeta ya koreta daga gidansa, shin idan har wani ya mata abu za ta ji haushi ko ciwon hakan bayan wanda shi ne silar wanzuwarta a duniya ya ƙyamaci ta raɓe shi. "Gaskiya ka faɗa ai gwara ka faɗi gaskiya kar ka ƙwari kan ka, tun da ka dai gani duk auren da ta yi sai ta yi kashi kamar fara" Cewar Umma tana kallon Malam. "Bangane sai ta yi kashi ba?" Ya tambaya da alamar tambaya a fuskarsa. "Yo duk auren da ta yi sai ta haihu mana haihuwa kamar kaza shikenan ita haka za ta yi ta barbaɗen ƴaƴa ta haihu a can ta tafi can ta haihu" "To ai yanzu komai ya zo ƙarshe tun da ni dai na faɗa mata ta kama haya kin ga ko nan gaba ta samu mai kwasarta (Mai aurenta) Ta san idan ta ƙunso cikinta ma ta fito daga gidan mijin ita za ta ɗau ɗawainiyar yaron to za ta hankalta ta zauna a gidan aurenta" Cewar Malam yana gyara zaman hularsa a kansa. "Haba Malam Safiyya fa ƴarka ce ko wani ya faɗi magana a kanta ko ya gujeta bai kamata a ce kai ka kasance cikin masu aibatata da kuma gudun taɓarta ba ko kuma ƙin ɗaukan ɗawainiyarta ai ita macece da idan aka koreta daga gida aka ce ta ɗauki ɗawainiyar kanta tamkar an bata lasisin shiga gurɓatacciyar rayuwa ce ta karuwanci ko wani abu makamancin haka bai... "Majida ya isheki wato har rainin ya kai ban isa in yanke hukunci ba sai kin tsaya gatse-gatse a gabana kina min bita da ƙulli dukan kabarin kishiya, wato ni ban san abin da ya dace da wanda ya kamata ba sai ke, to ki sani ni dai na ce ta je ta nemi wajen zama in ta ga za ta kyautata rayuwarta wannan ruwanta, in kuma za ta munana ta shiga wata bauɗaɗɗiyar hanya shi ma duk ɗaya wai an ce da karuwa hayo gado, idan kuma kin ga za ki bita to hanya a buɗe take amma ki sani zan daddatse igiyar aurena daga kanki" Wannan furucib na Malam shi ne ya sanya Safiyya jin wani irin hautsinawa mararta ta yi tare da wani murɗawa mata a take ta fara jin gabaɗaya duniyar na juya mata, hannu ta sanya ta dafe mararta.Mama da ta lura da halin da ɗiƴar tata take ciki a hanzarce ta yi saurin riƙo ta tana cewa "Safiyya mene ne?" Safiyya kuwa ta kasa furta wa mahaifiyarta komai, ganin da Mama ta yi naƙuda ce ta taho gadan-gadan sai kawai ta fara tunanin abin yi dan bata son ƴarta ta haihu a gida sabo da gudun matsala. Safiyya kuwa duk da babu wani sauran kuzari a tattare da ita haka ta yi dibarar janye jikinta daga jikin mahaifiyarta ta juya riƙe da pos ɗinta ɗaya hannun kuma ta saki marar tata ta dafe bango, juya wa ta yi ta ɗaga ƙafarta da niyyar barin gidan nasu dan ta ji dai mahaifinta ya ce ba za ta zauna masa a gida ba sannan kuma ya ce matsawar Mama ta bi ta to zai yanke igiyar aurensu wannan dalilin ne ya sanya ta janye jikinta daga mahaifiyarta domin ta tafi ita kaɗai ta gwammace komai ma ya same ta idan ta tafi ko da kuwa a ce mota ce za ta yi ɗiban karan mahaukaciya da ita a hanyar to tana ganin za ta fi samun sauƙin idan ta koma ga ubangijinta domin tana ɗauke da tsohon ciki a kuma halin naƙuda dan haka zai kasance ta yi mutuwar shahada a kan abubuwan da take fuskanta na daga ƙaddarorin da suke afka mata wanda mutane suka yi wa hakan babbbar fassara ta jahilci suka danganta komai a gareta. Tafiya ta fara yi tana ɗaga ƙafafunta da take jin tamkar wani gagarumin dutse aka ɗora wa ƙafafun nata a haka ta tunkari ƙofar gidan gadan-gadan. Mama kuwa yadda take jin zuciyarta ta gwammace auren nata ya mutu auren da bashi da wani alfanu a tare da ita bayan cizgunawa da bautar da ita sa ake yi a gidan Malam ba ya jin maganar kowa sai ta Umma ko ƙarya ko gaskiya shi dai duk wani abu da xa ta faɗa ko ta aikata shi ne dai dai duk da cewar ana zargin kamar akwai sammu a al'amarin amma abin ya yi yawa tamkar ba Mama ce uwar gidansa ba. "Majida tun da kin zaɓi bin ɗiyarki ki j na sawwaqe miki na yanke igiyar aurena guda ɗaya a kan ki" Mama ta jiyo maganar Malam a kunnuwanta, maganar da ta ƙara tsanantawa Safiyya ciwon naƙudar da take ji, domin har lokacin jan ƙafa take bata fita daga gidan ba kuma tana iya jiyo duk maganganun da suke wanzuwa suna wakana a cikin gidan. "A hayye ayyiriri yiriiiiiiii" Umma ta rangaɗa wata uwar guɗa da sautin ta ya zama tamkar ana bugawa Safiyya guduma a kunne. "Allah sa haka ahi ne mafi alkairi" Shi ne kaɗai abin da Mama ta iya faɗa ta juya. "Hehehehe ba haka aka so ba dai ƙanin miji ya fi miji kyau, to Umma ta gaishe da Aisha, Malam dai ya jefar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda" Cewar Umma wani farinciki yana mamaye zuciyarta. Mama dai bata ƙara ko da waiwayensu ba ta bi bayan ƴarta. A dai dai bakin ƙofar fita ta cim mata, tana dafa bango tana tafiya dan lokacin ma kamar haihuwar ta zo dab. *ANNUR* Tun da ya baro ƙofar gidan su Safiyya ya kama hanya amma jinsa yake tamkar ba shi ba gani yake kamar idan ya tafi ba zai sake ganinta ba saƙe-saƙen da yake ta faman yi wanda ya sanya kwanyarsa ke barazanar tashowa jin ya rasa makamar lamarin sai kawai zuciyarsa ta yanke masa cewar ya dawo ya samu inuwa ya faka motar daga nan zuwa dare ba zai fidda ran ganinta ba dan haka a take ya juyo da kan motar ya dawo dan yana ganin wannan ce kaɗai hanya mafi sauƙin da zai sake ganinta a yau dan idan ya tafi ba ya fidda tsammanin wataƙila ya ɗauki dogon zango kafin idanunsa su sake yin tozali da ita. Yana shawo kwanar idanunsa suka sauka a kan wacce ya dawo domin ya ganta sai dai duk da cewa daga ɗan nesa ya hango ta hakan bai hana shi ganin wata riƙe da ita ba. "Ikon Allah mai kuma ya same ta, ko dama bata da lafiya? To ko dai kukan da nake ganin tana yi dama bata da lafiya, ko dai tana da matsala a ƙwaƙwalwarta? Shin ina za a kaita? Mene ne dalilin da ya sa ba za ta yi tafiya ita kaɗai ba sai an riƙe ta?" Zuciyarsa da ke ta faman bugawa da ƙarfi take masa saƙe-saƙen tambayoyin da shi a karan kansa bashi da amsar su. A sukwane ya ƙaraso ƙofar gidan sai da ya ɗan gota ƙofar sannan ya tsaya, a ɗan tsorace ya kafe su da ido yana son gano ainihin amsar tambayarsa. Aikuwa ya samu amsar domin idanunsa ne suka sauka a kan tirtsetsen cikinta wanda ɗazu so ya masa shamaki da ganinsa. Gabansa ne ya bada wani saurin duuuuum har wani zaro idanu ya yi sai kace wanda aka ce idan ya ƙifta idanun zai ga abin da bai yi zato ba. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, kenan dama matar aure ce?" Wani sashin na zuciyarsa ya jefa masa tambayar. "Ko dai cikin shege ne ta yi shi ya sa kullum take kuka?" Wani sashen zuciyarsa ya wurga masa tambayar da ta kusa barazanar tarwatsa masa tunninsa a lokaci guda kansa ya ɗauki wani ciwo. "Ƙarya neeeeee ba cikin shege bane" Ya faɗa a fili yana dafe kansa da hannu biyu yana jin wani tashin hankali marar misaltuwa yana mamaye dukkan ilahirin zuciyarsa. MAI FARAR ƘAFA (JAHILCI NE) NA MAMAN AFRAH FCW GAJERAN LABARI FREE BOOK🥳 Page 7️⃣➡️8️⃣ Wani sarawa kan nasa ke masa wanda yake jin tamkar ana soka masa kibiya a tsakiyar kan, har lokacin yana dafe da kan nasa sai ambaton Allah da yake jerowa a cikin zuciyarsa yana son ya samu sassauci game da sabon yanayin da ya far masa lokaci guda. Mama kuwa riƙe da Safiyya suka zo suka gota motar da yake ciki suna takawa a hankali dan dakyar Safiyyar ke iya tafiya Mama kuwa ganin halin da ƴarta ke ciki ya mantar da ita wanzuwar kowace damuwa da ke cikin zuciyarta yanzu burinta bai wuce a ce Safiyya ta haihu lafiya ba domin ta san duk wata mace da take cikin halin naƙuda to kuwa ba a ƙaramin siraɗi take ba siraɗi ne da yake kan rayuwa ko mutuwa. "Sannu Safiyya Allah ya raba ku lafiya kin ji bari mu damu abin hawa mu je asibitin" Cewar Mama tana jin tausayin halin da ƴar tata ke ciki. Safiyya babu abin da ta iya furtawa mahaifiyarta, dan yanzu haƙoranta na sama ta saka ta danne leɓenta na ƙasa sabo da tsananin azaba da take ji na ciwon naƙudar tana raya wa a ranta cewa ita dai haihuwa har kullum sabuwa take dal a leda ba a sabo da ita bare mutum ya ce ya yi ya sake. "Ba dan babu kyau mutum ya toƙarwa kansa mutuwa ba da na roƙi na ar duniya a cikin wannan yanayin sai dai sabo da jarabawar ƙaddarorin da Allah ke jarabta ta da su ba zan biye wa faɗar mutane ba zan yi a addu'ar Allah ya kawo mini mafita domin yana ji yana kuma gani" Cewar Safiyya a zuciyarta. "Ya Allah ka bamu ikon cin jarabawar da kake mana ni da mahaifiyata, ka fitar da ni daga cikin ƙangin jifan da mutane suke mini a kan cewa ni MAI FARAR ƘAFA ce ni nake talautar da mutane daga arziƙin da ka musu bayan babu mai talautarwa sai kai babu mai bayarwa sai kai tabbas suna magana da JAHILCI amma ni bani da yadda zan yi na fahimtar da su ya rabbi kana amsar addu'ar mai naƙuda a lokacin da take naƙuda, Allah ka amshi addu'ata ka kawo mini ƙarshen ƙunci da nake ciki ka bani miji wanda zai zauna da ni ba tare da zargin duk abin da ya rasa ni ce sila ba" "Wayyo kin ga wannan ɗan sahun ma mutane ne a ciki Allah ka kawo mana ɗauki kar yarinyar nan ta haihu a titi" Ta jiyo muryar Mama na katse mata zancen zucin da take. *Annur* Idanunsa da suka masa nauyi wanda har yake wani ƙaƙance su sabo da yadda ya ji suna neman gagararsa ya yi kallon da su, a hankali ya juya ƙofar gidan da ya gan su a tsaye sai dai wayam ya hangi wurin, aikuwa da sauri ya saka hannu ya mari gefen fuskarsa dan duk tunaninsa mafarki ne ko kuma kawai ganinsu ya yi a idon zuciyarsa ba a zahiri bane ya yi hakan yana fatan Allah sa dai mafarkin yake dan ba ya son ko kaɗan yarinyar sa yake kwana da ita yake tashi da ita a cikin zuciyarsa yake tsara komai na rayuwarsa tare da ita ba ya taɓa yin mintina ba tare da ya tuna da ita ba ta zama wani ɓangare a zuciyarsa amma a wayi gari cewar ita ɗin mallakin wani ce tabbas ya san ba ƙaramin ƙunci da tashin hankali zai shiga ba. Sai dai yana maida kallonsa gaban inda hancin motarsa yake kallon tarrr ma'adanar ganinsa suka sauka a kan su, kamar yadda ya gansu ɗazu a ƙofar gidan ana riƙe da ita yanzun ma hakan ne sai dai wacce ke riƙe da ita yanzu ta shiga tsakanin kafaɗarsa saɓanin ɗazu da take riƙe da ƙugu da hannunta. "A gaske ne Annur ba mafarki kake ba ita ce dai ɗauke da cikin haihuwa" Ya ji wani sashe na zuciyarsa ya kai masa amsar tambayarsa ta ɗazu. Idanunsa ya kafe a kansu yana jin bugun zuciyarsa na tsananta a yadda yake ji yanzu ya kasa gane haushinta yake ji ko tausayin halin da take ciki. Laimar da ya ji ta sauka a kan fuskarsa ita ya tilasta shi ɗakko hannayensa da ke dafe da kansa ya shafa fuskar da su aikuwa ya tabbatar da danshin hawayen da ke waricinsu a kan kumatunsa. Da sauri ya sanya hannayen ya share hawayen yana saka haƙoransa ya danne laɓɓansa da su idanun ya runtse da ƙarfi domin yana so ya aro jarumta domin ya samu ƙarfin gwiwar tunkararsu domin ya taimaka musu dan ya ga suna da buƙatar taimakon. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ni'imal maula wa ni'imal nasir, ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagis, aslihli sha'ani kullahu wala takilni ila nafsi ɗarfata ayn" Ya faɗa a fili yana buɗe idanunsa da ya runtse a hankali ya ji nutsuwa na ziyarta ruhi da gaɓoɓin jikinsa wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke key ya yi wa motar ya fara tuƙa wa cikin nutsuwa da ƙwarewa ya nufi wurinsu a lokacin da yake hango wacce ke riƙe da ita ɗin tana ta ɗaga wa wani ɗan sahu hannu wanda ya wuce bai tsaya ba. Sai da ya ɗan gota su kaɗan ya tsaya sannan ya iyo baya kaɗan har sai da ya zo saitinsu, cikin sauri ya fito ya gewaya sashen da suke tsaye da yake ba daga ɓangaren ƙofar da ya fito suke ba, a kan kyakkyawar fuskarta ya sauke idanunsa wanda ganin fuskar a saka shi jin wani maganaɗisu ya masa dirar mikiya dan bai taɓa yin kusanci da fuskarta haka ba yana hangota ne a kullun daga nesa, kafin ya sauke idanun nasa kan haƙoranta da ta danne laɓɓanta da su wanda ke jere rerasa tamkar masara a jikin sosuwarta. Da sauri ya ɗauke idanunsa daga kanta wanda duka wannan kallon ya yi sa ne a tsakanin sakanni, ya mayar da kallons kan matar da take riƙe da ita da yake yanzu a tsaye suke ba tafiya suke ba ya lura kamar dai ta kasa cigaba da tafiya ne shi ne suka ɗan dakata ta huta. Yana sauke idanunsa a kan matar ya mayar da su kan ƴar mamaki yake kamanninsu ɗaya sak banbanci kawai ita wacce ta riƙe ta, ta manyanta saɓanin wacce aka riƙe da yarintarta, a take ƙwaƙwalwarsa ta shaida masa cewa mahaifiyarta ce. "Dan Allah idan ba damuwa ku shiga na kai ku inda za ku je" Ya faɗa da ɗan sauri tamkar wanda yake da in'inna. Mama da dama take neman abin hawa kamar ruwa a jallo jin zai taimaka musu babu wani tunanin komai ta ce "To babu damuwa mun gode" Ta faɗa duk da muryarta akwai ɓurɓushin damuwa amma kallo ɗaya za ka mata ka san ta ji daɗin furucinsa, dan dama ta matsu ta gansu a asibiti ko dan ƴarta ta haihu a hannun likitoci ba a wannan tangararan titin ba dan bata san iya lokacin da za su ɗauka suna neman abin hawa ba da yake unguwar tasu tana a can cikin lungu ne. Kuma yau ko dan tana cikin halin son samun abin hawan ne duk sai ta ga babu abin hawan. Ita kam Safiyya ko a bata ce ba sabo da ita yadda take ji yanzu za ta iya hawa ko da amalanken shanu ne dan ya rage mata wannan tafiyar da take yi tana jin tamkar ciwon ake ƙara mata. Annur kuwa da sauri ya buɗe ƙofar bayan yana riƙe da murfin har mahaifiyarta ta saka ta ciki da sauri ta koma ɗaya ɓangaren ta shiga domin ita ƴar da ta zauna ta kasa matsawa sabo da tsananin ciwo, Annur ɗin ne ya rufe ƙofar ɓangaren Safiyyar yana jin wani tausayinta na mamaye masa zuciya ganin ta kifa kanta a jikin kujera tana ta faman ambaton "Wash Allah na, Alhumma ajirni fi musibati waklifni kairan minha" Duk da yana hana zuciyarsa ganin ita ɗin mallakin wani ce amma sai da ya ji tamkar ya je yake lallashinta. Cikin hanzari ya buɗe mazaunin direba ya shiga ya tada motar ya haura titi. Yana tuƙi yana ta saƙar jaki. "Ashe fa bata sanni ba, yadda nake jin ta a zuciyata duk zatona ita ma hakan ne, duk a tunanina ita ma zuciyarta ta san da zaman tawa zuciyar, mafarkinta da nake a kowane bacci da zai ziyarci maganaina ashe ita abin ba haka bane" Har ya karya kwanar da za ta sada shi da wata unguwa mai suna GUSAU. "Bawan Allah General hospital fa za ka kai mu"Muryar Mama ta katse masa tunaninsa. "Gwara dai a je privet hospital" Ya ba wa Mama amsa hankalinsa na kan tuƙin da yake. "Ka dai kai mu na gwabnati ba asibitin kuɗi ba wannan asibitin ba ƙaramin kuɗi za a kashe ba idan za a haihu a cikinsa" "Babu damuwa zan biya mata komai" Ya faɗa cikin sanyin murya yana jin ko wani ne zai iya kashe ko nawa ne a kansa indai a kan lafiya ne ko taimako bare wacce yake ji dalilint ma zai iya bada abin da ya mallaka bare kuma ita da kanta. "Matar aure ce" Wani sashen na zuciyarsa ya katse shi. "Allah da iko yake, kai amma mun gode Allah saka da alkairi" Cewar Mama tana jinjina abin alkairin a ranta ɗazun nan suke neman abin hawa da kuɗinsu suka rasa amma ga shi zai kai su kyauta ba tare da su suka nemi taimakon ya kai su ba sannan ma wai asibitin kuɗi kuma zai ɗauki ɗawainiyar lallai hanyar Allah yawa gareta. Mama da ke ta jinjina alkairin da zai musu a ranta take faɗa. "Amin ya hayyu ya qayyum" Haka kawai ya faɗa. Safiyya kuwa tana jin duk abin da suke cewa sai dai ciwo ya hana ta magana. A dai dai get ɗin asibitin mai suna FHARAHA ya tsaya, yana tsayawa Mama ta buɗe ƙofar ta fito ta gewaya ta buɗe wa Safiyya. "Sannu Safiyya, Allah raba ku lafiya" "Safiyya kenan sunanta Safiyya" Annur da fitowarsa kenan sunan Safiyya da Mama ta ambata ya yi wa majiyar sautinsa dirar mikiya. Yana ta maimaita sunan a zuciyarsa ya ga Mama ta fito da ita ƙarasa wa ya yi ya mayar da ƙofar ya rufe. "Mama ba zan iya hawa ba benen ba" Muryar Safiyya da ke cikin tsananin ciwo ta furta a hankali, Annur da ji ya yi tamkar ta masa busa da sarewa a kunne sautin muryarta tamkar wanda aka zuba wa zuma kan daɗi wai a hakan ma tana cikin halin rashin lafiya ne ina ga tana da lafiya ga muryar a hankali. "Matar aure ce" Wani ɓangaren na zuciyarsa ya katse shi lokacin da suka shiga get ɗin yana biye da su, kuma da yake gabaɗaya asibitin a saman bene yake dan ƙasan shaguna ne a wurin. "Ki daure ki hau kin ji" Annur da bai san da zaman fitowar maganar ba sai jin ta ya yi ta kufce masa ta fito ba tare da ya shirya ba. "Eh haka za ki daure ki hau" Muryar Mama ma ta ƙara da faɗin hakan. A hankali a hankali suke tafiya har suka hau saman Annur yana biye da su. Bayanan faɗa masa duka kuɗin ya biya ita kuma nurses sun shiga da ita labour room Mama tana nan tsaye ta kasa zama kana ganita ka san tana cikin damuwa. "Innalillahi wa inna ialaihir raji'u, La'ilaha ilallahu muhammadur rasulullahi S.A.W" Muryar Amminsa ta dawo masa a lokacin da take halin naƙuda tana ɗakin haihuwa ita ce magana ta ƙarshe da ta zauna daram a kunnensa maganar da ita ce maganarta ta ƙarshe a duniya haka ta tafi da cikin jikinta bata haihu ba. Wannan tunanin da ya faɗo masa wanda lokacin da abin ya faru suna tsaye a dai dai windown ɗakin haihuwar da mahaifiyarsa take ciki a wani asibiti na kuɗi yanzu kimanin shekara biyu kenan. Da sauri ya juya ya sakko daga saman benan jin hawaye suna neman zubo masa yana zuwa ya buɗe ƙofar motar ya shiga ya zauna ya rufe ya kifa kansa a sitiyarin yana jin ƙunci da damuwa suna yi wa zuciyarsa ƙawanya. "Shin ita ma kar dai ta je ta mutu" To ina zan sanya rayuwa ta, ko bata mutu ba ta haramta a gareka matar wani ce fa. Ina mijin nata yake mahaifiyarta ce kaɗai za ta kawo ta asibiti haihuwa shi wanda ya mata cikin ina yake ko ba ya muradi da murnar haihuwar da za a masa kamar yadda wasu mazan JAHILCI ke yi wa katutu a kan ba sa son haihuwa? Ko dai ba ɗan sunna bane ɗan gaba da fatiha ne?" "Noooooooo" Ya faɗa a fili yana ɗago kansa daga kan sitiyarin. Neman agajin da waya take yi shi ya dakatar da shi yana mamakin ina aka samu waya a mota dan ya san tashi tana aljihunsa. Cigaba da ƙaran wayar a motar ne ya so ya addabi majiyar sautinsa kuma ƙaran yana ƙara masa damuwa da ɓacin ran da yake ciki. A fusace ya juya yana kallon bayan motar aikuwa idanunsa suka sauka a kan wata ƙaramar pos da ke kujerar da Safiyya ta zauna. Ƙaran dai yana katsewa wani kiran ke shigowa, da sauri ua miƙa hannu bayan ya ɗakko wayar lokacin kiran ya ƙara katsewa wani ya shigo. "Kai ina dalili wannan mai kiran da naci yake ni yanzu su da suke cikin halin nan ma na nufe su da waya?" Cewar wani ɓangare na zuciyarsa. Kawai ka kashe wayar dan mai kiran ba zai daina kira ba in ya so daga baya ka sanar da su" Wani sashen na zuciyar tasa ya ƙara raya masa hakan. A ɗan fusace ya kai hannu ya zige zip ɗin, yana zigewa wata takarda ta faɗo wacce ba a linke take ba. "Na sake ta saki uku" Shi ne abin da idanun Annur suka sauka a ka. Cikin sauri ya ajiye jakar dai ko wayar da ke faman ruri bai fiddo ba, hannunsa har karkarwa yake wajen miƙar da takardar gabansa na bugawa da mugun ƙarfi dan tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin takardar saki ba. *Ni Rabi'u na saki Safiyya saki uku, ba dan ta min laifin komai ba sai dan tana ɗauke da FARAR ƘAFA da kuma ƙashin tsiya a tattare da ita kullum samuna raguwa yake ba ya ƙaruwa* Shi ne abin da ke ƙunshe a jikin takardar. "Safiyya, saki uku" Su ne kalam da suka fara kai kawo suna safa da marwa a ƙwaƙwalwar Annur. MAMAN AFREH 09030283375 MAI FARAR ƘAFA (JAHILCI NE) NA MAMAN AFRAH FCW FREE BOOK🥳 Page 9️⃣➡️1️⃣0️⃣ "Mene ne kuma MAI FARAR ƘAFA? Tana da ƙashin tsiya shin mai waɗannan kalamai ke nufi, amma ai ya ce bata masa komai ba" Cewar wani sashe na zuciyar Annur har lokacin idanunsa kafe a kan takardar kamar wanda aka ce zai gano asalin tambayar fa yake jefawa kansa domin shi bai san ma'anar kalmar FARAR ƘAFA ba bare mai ƙashin tsiya. "Shin dama kuka take mijinta ya sake ta? Kenan son sa take bata son ya rabu da ita shi ya sa har take yin kuka... Tun kan ya kai ƙarshen maganar zucin ya ji kishi ya turnuƙe shi, gabaɗaya ransa ya ɓaci tuna wa fa ya yi tana ƙaunar mijinta ashe ma ba shi bane a zuciyarta shi kaɗai yake kiɗansa yake rawarsa. "Ka manta bata sanka ba, ka manta bata sa ma kana sonta ba, to ma wai ko da ta sanka kana da tabbacin za ta soka, an sha samun namiji yana ƙaunar mace amma ita bata ƙaunarsa ko a samu mace na ƙaunar namiji amma shi ba ya ƙaunarta. "Ɗif bugun zuciyarsa da ke faman yi da sauri da sauri ya tsaya cikin ƴan sakanni kafin ya cigaba da bugawa da ƙarfi. "To kenan duk ganin da nake mata da akwati sakinta yake shi sa take kuka, to amma wannan ne karo na uku da nake ganinta a irin halin kuma dai yanzu saki uku na ga ya ce, ko dai sauran yaji ne take tahowa wannan karon ne ya sake ta?" Takardar ya tuƙunƙune ya ɗauki jakar ya tura a ciki haɗe da wayar ya ja zip ɗin jakar tamkar zai tsinke shi, jakar ya ɗaga ya jefa kan kujerar da ya ɗauka yana jin wani abu a ransa da ya kasa gane mene ne. Kansa ya mayar kan sitiyarin ya kifa tare da mayar da idanunsa ya lumshe. Gabaɗaya ya rasa wane kalar tunani zai yi ƙunci damuwa duk sun taru sun masa katutu a ƙahon zuciya, na rashin takamaiman abin da zai yi a gefe ɗaya kuma halin da take ciki na naƙuda yana karyar masa da zuciya. Sai dai wani tunani da ya masa dirar mikiya yanzu a ciki sakkani shi ne abin da ya sanya shi ɗago da kan nasa daga sitiyarin. "Tana haihuwa fa ta gama idda" Shi ne abin da zuciyarsa ta raya masa wanda hakan ya sanya shj ɗago da idanunsa wanda suka masa jawur ya sauke a kan saman benen asibitin tamkar dai wanda aka ce Safiyyar ce a wajen. Wani murmushi ne ya saɓuce masa yana jin wani yanayin mai daɗi na ziyartarsa har wani nishaɗi-nishaɗi yake ji saboda tunowa da ya yi cewar idan Safiyya ta haihu ta gama idda kenan za ta iya zama mallakinsa. Da sauri ya buɗe ƙofar ya fito cikin asibitin ya koma yana hawa matakalar da bibbiyu tamkar dai wanda aka sanar da shi Safiyyar ta masa alƙawari za ta aure shi, dan yana raya wa a ransa cewar zuwa yanzu ta haihu dan ya kwashe awa biyu a wajen. Yana hawa saman idanunsa suka sauka a kan Mama da ke ta safa sa marwa a santar wurin, idan ta je ta dawo sai ta ɗaga hannu sama alamar addu'a. Jikinsa ne ya yi sanyi daga ƙwarin gwiwar da ya shigo da shi a sanyaye ya nufi wajenta. Mama kuwa da juyowarta kenan ta sauke idanunta a kansa da sauri ta ɗan juyar da fuska gefe ta goge ƴar ƙwallar da suka taru a idanunta, a hankali ya ƙaraso wajenta yana jin tausayinta duk da bai santa ba a yau ya fara haɗuwa da ita sai ya ji tamkar mahaifiyarsa, ga shi ya lura mutuniyar kirki ce. "Ya jikin nata?" Ya jefa mata tambayar a ladabce lokacin da ya ƙaraso wajen. "Da sauƙi" "Bata sauka ba?" "Eh ana can ana fama, sun ce idan ta ƙara awa guda bata haihu ba tiyata za su mata sabo da sun lura ba za ta iya haihuwa da kanta ba" "Innalillahi wa inna ialahir raji'un" "Ina mijin nata ina son ganinsa a office" Likitan da ya fito daga ɗakin haihuwar wata nurse na biye da shi ya faɗa lokacin da ya zo wajen su Mama. Mama da tashin hankali ya bayyana ƙarara a fuskarta jin kalaman likitan ta buɗe baki da niyyar magana sai ta ji Annur ya ce "Ga ni, to bari na zo" Tsabar mamaki ma ya hana Mama magana dan ita tunaninta ma ta ce mijinta ba ya nan tun da dai ta san a halin yanzu babu wani miji da Safiyyar take da shi tun da ya sake ta duk da ɗansa ne za a haifa amma dai bata ga kyan wuri a kunnen jaka ba, dan ta san babu mutunci a al'amarin Rabi'u bare ta yi tunanin ma sanar da shi halin da ake ciki dan ta san neman da likita ke yi wa mijinta na sanya hannu ne a takardar da za a mata tiyatar da kuma biyan kuɗin aikin wanda ta san ko sama da ƙasa za ta haɗe Rabi'un ba zai taɓa biyan ki ƙwandala ba ko da bai sake ta bare kuma yanzu da ya san ya yanke alaƙar auratayya a tsakaninsu babu ruwansa ta yi rai ko ta mutu. Bare kuma mahaifinta wanda zai maye gurbinsa tun da duj inda aka nemi miji ya saka hannu in baya nan uba za a nema in ba ya nan wa ko ƙane ko wani shaƙiƙi wanda ta san basu da su gabaɗaga dan ita Mamar ita kaɗai iyayenta suka haifa kuma sun rasu sannan ita ma Safiyya ita kaɗai ta haifa sai ƴan uwanta mata wanda suke uba ɗaya wanda ko jituwa ma basa yi bare a yi zancen ƴan uwantaka dan duk sun ware Safiyya a cikin dangi a cewarsu annoba ce kar ta goga musu kashin kaji na FARAR ƘAFA. Kafin Mama ta ce wani abu sai kawai ta ga Annur ya bi bayab ɓɓn daktan da sauri. "Ah wannan yaro Allah maka albarka lallai mahaifiyarka ta baka tarbiya na taimako, kuma kana da zuciyar tausayi" Cewar Mama a zuciyarta tana kuma yi wa Allah godiya. Bayan an masa izini ya shiga office ɗin ɗauke da sallama. Amsa masa daktan ya yi ya masa nuna da wurin zama hannu ya bashi suka yi musabiha duk da shi Annur burinsa kawai ya ji mene ne dalilin kiran dan zuciyarsa cike take da tsabar fargaba dan tsoronsa ɗaya kar ma Safiyya mutuwa ta yi shi ne daktan zai faɗa masa. "Ina so ne ka saka hannu domin za mu yi wa matarka aiki mu ciro baby saboda babyn a kwanciyarsa ba a daidai take ba kuma mun yi ƙoƙarin mun juya shi sai dai abin ya faskara sai wahala take sha babyn ma na wahala amma haihuwar ta ƙi daɗi daga kan babyn ya taho sai ya koma dole sai an mata aikin dan ceton ranta da na abin da za ta haifa" Maganar dakta ta dakatar da Annur daga zancen zucin da yake. "Haba likita a kan me za ka kira mata mutuwa, bayan numfashi Allah ne kaɗai yake busawa kuma shi kaɗai ya san ranar mutuwar bawa ai kamata ya yi ka ƙarfafa gwiwa ba wai ka saka sarewa a zuciyar ɗan uwan marar lafiya ba" Annur da kalmar mutuwa ta daki zuciyarsa har ya fusata har ɓacin rai ya sanya shi faɗa wa likitan magana, kana kallon idanunsa ka san ransa a ɓace yake kuma yana cikin matsananciyar fargaba. "Ba haka nake nufi ba kuma ko ni ai ba zan so ta mutu ba kawai ina faɗa maka abin da zai faru ne idan aka ɗauki tsawon lokaci nan gaba ba tare da an cire babayn ba, tun da a halin yanzu an saka mata ruwan naƙuda ya ƙare duk wasu ƙwayoyin da za su taimaka mata wajen naƙudar an bata amma shiru duk ta bi ta galabaita dan haka yanzu ba surutanka nake buƙata ba ka yi saurin saka mini hannu ai ko ma me na faɗa a kan aikina nake" "Ko da shi aka haifeka" Annur ya faɗa yana jan takardar ya sanya hannu, wayarsa ya fito daga aljihu ya masa transper kuɗin da ake buƙata, shi dai likitan bai ƙara tanka masa ba dan ya san yana cikin damuwa ne kawai. Gaba ma ya iyo ya bar Annur ɗin a cikin office ɗin dan yana so a shiga da ita yanzu, shi ma Annur ɗin bayansa ya biyo yana jin dakyar yake iya ɗaga ƙafarsa saboda yadda jikinsa ya mutu. Yana fitowa ya ga Mama tsaye wacce ta rasa inda ma za ta sanya ranta, suna nan tsaye Annur ya jingina da jikin windown sai ga wata nurse ta kira Mama, haka Mama ta bi bayanta da sauri shi ma Annur bai san ma ya bi bayanta ba sai da ya ji wata nurse tana dakatar da shi a kan cewa maza ba sa shiga ɗakin haihuwa. Mama tana zuwa ta ga halin da Safiyya take ciki gabaɗaya ta galabaita ƙarfinta ya ƙare. "Mama ki yafe mini dan Allah" "Babu abin da kika mini Safiyya za ki samu sauƙi da yardar Allah za a yi aikin cikin nasara" Cewar Mama hannunta na cikin na Safiyya bayan nurse ta bata wata rigar yadi blue da huta mai raga-raga ta saka mata su ne uniform ɗin da ake saka wa wanda za a yi wa aiki. "Ni Mama kawai so nake a cire cikin in huta" Cewar Safiyya tana magana dakyar sai wani uban gumi ke tsatstsafo mata. Suna cikin wannan maganar likita ya dakatar da su ya sanya aka tura gadon Safiyya zuwa ɗakin tiyatar Mama tana biye da gadon idanunta kafe a kan ɗiyarta wani tausayinta na mamaye zuciyarta Alah sarki soyayyar uwa da ban ce babu wanda zai maka soyayya sama da ta mahaifiya shi ya sa ma Allah ya ambaci a yi wa mahaifiya biyayya mahaifiya sau uku sannan ya ambaci uba sau ɗaya. Annur da ke jingine a inda aka dakatar da shi ganin an garo Safiyya da ke kwance lifet a kan gadon sai ya ji hankalinsa ya yi bala'in tashi idanunsa a kanta ko ƙiftawa ba ya yi gani yake kamar kallon ƙarshe yake mata ganin Mama ta yi sauri ta riƙe hannunta sai shi ma ya nufi gadon idanunsa jawur ya ce "Sofy ki yi haƙuri kin ji yadda kika shiga lafiya za ki fito lafiya" Ya faɗa cikin sanyin murya da ido ta bi shi tana son karantar yanayin da ya mata magana duk da tana cikin wani hali amma kuma sai ta ji daɗin yadda ya mata magana da taushi da tausaya wa, hakan ya sanya ta ji wani sanyi a ranta dan ta san bayan mahaifiyarta bata da wani wanda yake mata magana mai daɗi cikin sanyin rai ta saba da jin baƙaƙen maganganganu mararsa daɗin saurare wanda basu da tushe daga bakin mutane mabanbanta. tabbas ta gane shi, shi ne ya kawo su asibiti a mota ya kuma biya mata komai tabbas da ganinsa mutumin kirki ne hakan ya sanya ta fara ƙoƙarin buɗe baki ta masa magana amma kuma wani uban koma wa da babyn cikinta ya yo gefe guda sai qata azaba ta ziyarceta wacce ta kasa tantance wa da sauri likitan ya bada umarnin a wuce da ita dama an dakata ne dan mijin nata ya mata sallama saboda kar ta Allah ta kasance. Hannunta ta ɗaga a hankali ta haɗe da ɗayan alamar godiya a haka aka shige ɗakin da ita Mama kuwa bata ma san mai ake ba dan ta juya tana ta faman share hawaye. Har sai da aka shige da ita ya daina hango ta sannan ya dawo hayyacinsa, jin wami danshi a fuskarsa ya yi saurin kai hannu wurin a take danshin ruwa hawaye ya yi wa hannunsa sallama. "Kuka?" Ya jefa wa kansa tambayar cike da mamaki. "Tabbas kuka kake, ai Safiyya ta wuce matsayin wasa a wurinka soyayya ce ta haƙiƙa kake mata in baka sani ba ma ka sani" Wani sashen na zuciyarsa ya bashi amsa. MAI FARAR ƘAFA (JAHILCI NE) NA MAMAN AFRAH FCW Page 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣ "Ya rabb ka dubi baiwar nan taka ka raba ta da abin da ke jikinta lafiyaka fito mini da ita cikin aminci ka raya abin da za ta haifa" Cewar Mama a fili tana tsaye a ƙofar ɗakin tiyatar, da yake akwai wani benci a wajen idan ta zauna sai ta tashi tsaye gabaɗaya ta rasa abin da za ta yi. Allah kaɗai ne ya san irin fargaba da tashin hankalin da take ciki domin bata son ta rasa Safiyya tana ƙaunar tilon 'yarta duk da kasancewar mutane na ƙyamatar ta ita kuma sai ta ji duk duniya bata da sanyin idaniyar da ya wuce Safiyya daa Bahaushe ya ce abincin wani gubar wani A hankali yake ɗaga ƙafafunsa da ya ji zuwa lokacin sun masa nauyi har suna barazanar kasa ɗaukan gangan jikinsa tabbas da a ce za a buɗe zuciyarsa babu yadda za a yi ba a ga an rubuta damuwa ba a nasa ganin kenan saboda irin ɗinbin damuwar da ta baibaiye masa ruhi ji yake kamar ya hankaɗa ƙofar ɗakin tiyatar ya shiga ya je ya ganta ko ya samu salama domin ya fi so ko mutuwa za ta yi ta mutu a kan idanunsa. Saboda a halin da yake ciki yanzu idanunsa ita kawai suke kallo gizo suke masa da ita ganinta yake lokacin da aka tura ta aka shige d ita tana haɗe masa hannayenta wanda ita ta yi ne a matsayin godiya shi kuma tasa zuciyar tana faɗa masa cewar sallama take masa tare da nuna masa ya yi haƙuri idan ta Allah ta kasance saboda yaudararsa da zuciyar tasa take tana nuna masa ta san yana ƙaunarta dan a yadda yake jinta a ransa gani yake zai yi wuya a ce bata san da zamansa a gogin zuciyarta ba. "Yanzu Annur idan ka ga sun fito da ita a mace ya za ka yi? Wane irin yanayi za ka shiga wani hali za ka kasance a ciki bayan barinta duniyar?" Wani sashi na zuciyarsa ya jefa masa tambaya dai dai da halin fargabar da yake ciki. "Ba za ta mutu ba, ba za ta mutu ba ba za ta mutu ba" Shi ne abin da yake maimaitawa a fili kamar wani zautacce. Mama da bata san ma yana wurin ba saboda ruɗanin da take ciki ita ta ɗauka ma yana wani wurin da ban ko ma ya yi tafiyarsa tun da ya musu mai wuyar amma jin kalaman da amon muryarsa ya isarwa majiyar sautinta shi ne abin da ya sanya ta juyo a firgice domin gane wa idanunta, shin waya yake yi shi ma wata yar uwarsa tana cikin wani hali dan da alama shi ma yana cikin irin halin da take ciki na fargabar mutuwa ko shi ma 'yar uwanrsa take cikin yanayi na halin rayuwa ko mutuwa kamar yadda ita ma take ciki. A kansa ta sauke idanunta ganin babu waya a kunnensa hakan ya dagula lissafinta, dan bata ga alamar ma ko wani yake faɗa wa maganar ba. Ƙafarsa ya tako ya nufo wajenta dama a can gefe yake yana zuwa ƙwallar da ke kwarmin idanunsa ta gangaro masa hawayensa suka riga furucinsa fitowa dan a lokacin yana cikin damuwar da yake son a lallashe sa, a faɗa mas kalma mai daɗi wacce za ta rage masa fargabar da yake ciki ko ma a maye masa gurbin damuwar gabaɗaya duk da ganin fitowar Safiyyar cikin ƙoshin lafiya shi ne ai haifar masa da hakan amma yana buƙatar ko yayana ne ya ɗan samu salama. "Ba na so ta mutu" Ya yi yaƙi fa bakinsa kafin ya samu damar fito da kalaman ya wannan da ya isar da su ga Mama wacce ke masa kallon rashin fahimta dan ita ta kasa gane mai yake faɗa a kan wa kuma yake furta maganar tasa domin kallo ɗaya ta masa ta ga damuwa ƙarara haɗe da tashin hankali marar misaltuwa kwance a kn dakalin fuskarsa. "Wacece???" Mama ta jefa masa tambayar a kiɗime dan tunaninta ya bata ko waya aka masa mahaifiyarsa ko wata 'yar uwarsa bata da lafiya shi ne ya shiga damuwa. Annur kuwa da ganin fuskar Mama da damshin hawaye sannan duk ta wani birkice kana ganinta za ka fahimci akwai matsala a tattare da ita, sai haka ya ƙara ɗugunzuma damuwar tasa. Dan sai yake kallon fuskar Mamar tamkar ta mahaifiyarsa dan ya san ita ce take lallashinsa duk lokacin da yake cikon damuwa bata taɓa bari ya shiga ƙunci duk runtse bata bari hawayensa ya zuba ɗan gata ne amma kuma bai rasa tarbiya da nagartattun halaye ba. Sai dai kashi mai raba wa ta raba, ƙasa ta rufe idanunta yadda ba zai sake ganinta ba ma bare ya tunkareta da damuwarsa har ta masa maganin matsalarsa tabbas uwa -uwa ce, kuma duk wanda bashi da ita ya yi kuka wanda yake da ita kuma ya kyautata mata ya ƙara yi wa Allah godiya saboda mahaifiya sanyin idaniya ce baka da kamarta baka da masoyi duk duniya saboda ita duk wanda zai nuna maka so ko ya baka kulawa to tabbas a bayanta yake. Tambayar da Mama ta jefa masa ita ce ta warto shi daga duniyar da ya lula a ciki sai lokacin ya ɗan dawo hayyacinsa, sai lokacin ya fahimci shi ke kiɗa da rawarsa babu wanda ya san abin da yake cikin zuciyarsa sai Allah. "Wacece ba za ta mutu ba, wata ce ba lafiya ne, kalli yadda kake kuka" Cewar Mama da tausayinsa ya baibayeta tana ganin shi ma ya yi ƙoƙari matuƙa wajen taimakonsu su ma ya kamata su tausaya masa tun da dai ta san ba ƙaramin abu bane zai sanya namiji kamar wannan zubar da hawaye. A take ita ma Mamar ta ji tata zuciyar ta ƙara shiga damuwa damuwar da take ciki ta ruɓanya kasancewarta mace kuma duk mace an santa da rauni. Annur kuwa hannu ya kai duka biyu ya yi saurin shafa wa aikuwa ya yi gam da katar na taɓo ruwan hawayensa da ke kwance yana gamgarowa a dakalin fuskarsa. Da sauri ya sanya tafukan hannun ya goge kamar mai gudun kar wani ya gani har sai da ya ji babu sauran hawayen a fuskar sai dai ya tabbatar ko babu kuka zahiri akwai na zuciya wanda ya fi na zahirin ciwo da kuma ƙuna a zuciyar mai yinsa. "Ba, ba, babu kowa" Ya ba wa Mama amsa har tana ɗan inda -inda tare da ƙoƙarin maye gurbin damuwar da murmushin yaƙe wanda ya yi ƙoƙarin hakan amma abin ya faskara. Mama kuwa da yake ba yarinya bace duk iya ƙoƙarinsa na ya ɓoye mata a matsayinta na mace mai yawan shekaru ta fahimci akwai gagarumar damuwa a tattarw da shi dan an ce labarin zuciya a tambayi fuska. Dan haka ko da ya yi ƙoƙarin yaƙi da fuskarsa wajen yin murmushin yaƙe bai samu zarafin yin hakan ba dan haka sai ya yi ƙoƙarin kawar da maganar da cewa. "Ba a fito da ita ba?" Ya tambaya dan ya nuna wa Mamar shi fa zuwansa wurin kenan.Ƙaran buɗe ƙofar ɗakin tiyatar shi ne ya dakatar da su daga maganar da suke a kiɗime su duka suka juya da sauri suka nufi wajen gadon Safiyyar da aka garo ta. Har rige-rige ake da Mama da Annur wajen zuwa wajen gadon da aka garo Safiyya da ke kwance lifet a kai. Daga Mama har Annur babu ma wanda tunanin ina babyn yake kawai hankalinsu gabaɗaya a kan Safiyya yake. Annur ne ma ana dab da shiga ɗakin hutun da za a kaita ya juyo zai yi wa likitan tambaya sai ya ga ashe saboda saurin da yake yana biye da gadon har ya ba wa likitan tazara, dan haka yana juyo wa ya sauke idanunsa a kan likitan da wacce take riƙe da babyn suna tahowa. Ganin zai ɓata wa kansa lokaci ma sai ya juya ya shige ɗakin dan dama so yake ya rage fargabar zuciyarsa dan tambayar likitan zai yi bata mutu ba? To kuma dai sai ya ga gwara ya bi su in ya so gani ga kori ji. Suna shiga aka kwantar da ita a kan gado, Mama da Annur idanunsu a kan cikinta suna ganin yadda cikin nata ke ɗaga wa alamar numfashi wanda hakan ke nuni da tana nan a raye bata mutu ba. Wata nannauyar ajiyar zuciya da Annur ya sauke wacce sai da kowa na wurin ya kalle shi aikuwa ya murtuke fuska yake muzurai. "Alhamdulillah!" Cewar Mama a zuciyarta tana ƙara gode wa Allah. Likitan da suka shigo ne, hankalin Mama ya koma kan babyn da ke hannun nurse ɗin wanda ke naɗe da ɗankwalin atamfar Mama da aka ce ta bada zanin da za a saka baby ganin basu zo da komai ba ya sanya ta ciro ɗankwalin ta bayar da yake ɗankwalin da girmansa kuma atamfar ma sabuwa ce wankinta ɗaya. Sai lokacin ma Mama ta tuna da ashe fa ɗa aka ciro dan ita gabaɗaya Safiyyar ce a ranta. "Ah ga babyn nan da ta haifa namiji ne, da kanta ma ta haihu dan ana shiga naƙudar ra zo gadan-gadan to da muka ga haka sai aka dakata ba a fara aikin ba, da yake Allah ya rubuta ba za a yanka ta ba sai ta haihu da kanta" Likitan ya kai ƙarshen maganar yana kallon Mama, sai kuma ya maida kallonsa kan Annur wanda fuskarsa take washe kamar auduga sai ka ce an masa albishir da gidan aljanna. "Za ka bini office ka bani acc no in maida maka kuɗin aikin da ka tura tun da ba a mata aikin ba" "Na bar maka" Annur ya faɗa cikin halin ko in kula. MMN AFRAH MAI FARAR ƘAFA (JAHILCI NE) NA MAMAN AFRAH FCW GAJERAN LABARI FREE BOOK🥳 Page 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣ "Ban gane ka bar mini ba, kuɗinka ne fa kuma na ce ba a kai ga mata aik... "Idan baka buƙata za ka iya ba wa wanda yake buƙata" Annur ya katse likitan cikin halin ko in kula hankalinsa ma na ga Safiyya da ke ta faman bacci. Daga Mama har likitan da kallon mamaki suka bi shi, amma shi ko a kwalar rigarsa. "Sai dai ina jimamin sanar da ku yaron bai zo da rai ba" Cewar likitan da ke kallon Mama tana karɓar babyn a hannun Nurse ɗin. "Allahu akbar kabiran " Cewar Mama da Annur da suka haɗa baki wajen faɗa. Cikin sanyin jiki Mama ta buɗe yaron da ke cikin ɗankwalin tana kallonsa kamar su ɗaya da mahaifinsa sai dai shi yaron ya ɗakko hasken Safiyya. "Allah sa mai ceto ne" Cewar Annur yana kallon Mama. "Amin ya Allah" Mama ta amsa cikin sanyin murya, ƙwalla na zubo mata ta saka hannu ta goge. "Allah sarki ta san ya mutu fa, babu rabon ta gan shi yana raye haka Allah dama yake yi wani mai gajeran lokaci ne sai dai Allah sa mai ceto ne" Cewar Nurse ɗin da ta miƙa wa Mama babyn. "Eh wallahi kuma kwa ga shi ta fi shan wahala a haihuwarsa"Cewar Mama tana kallon Safiyya da ta ɗan motsa. "Ta biyu ce haihuwar?" Nurse ɗin ta tambaya. Dudummm! Sautin ƙirjin Annur ya buga da mugun ƙarfi jin ana batun ba haihuwarta bace ta farko. "Kenan tana da wani ɗan? Za ta iya yin auren kisan wuta ta koma gidan mijinta dan saboda ɗanta ba la... " Wannan haihuwarta ta uku ce" "Uku?" Sautin maganar Annur ya daki majiyar sautin Mama kallonsa Mama ta yi ganin duk ya wani diririce sai ma ta rasa mene ne dalilinsa na yin wannan tambayar mai kama da titsiye?" "Allah sarki ni duk tunani na ma haihuwar fari ce" Ya wayance dan kar Mama ta fahimci inda ya dosa duk da yana ganin hakan da hawala amma kallo ɗaya za ka masa ka fahimci maganar ta buge shi. "A'a haihuwarta biyu wannan ce ta uku" Mama ta bashi amsa. Nurse ɗin kuwa bin su Annur take da kallon mamaki dan duk tunaninsu Annur mijinta ne amma kuma ga shi ta ji ya yi tambayar da ta fahimci ko yawan ƴaƴan mai haihuwar bai sani ba wanda a ƙiyasi ko da a ce ɗan uwa ne na kusa zai iya sanin yawan ƴaƴanta. "Allah raya" "Amin" "Ya kamata wannan a tafi da shi gida a masa sutura, ita ma idan ta falka muka ga babu abin da ke damunta za mu sallameta tun da lafiya ta haihu" Maganar likitan ta ratsa kunnuwan Safiyya da ke jin ta ita ba ido biyu ba ita ba mai bacci ba tana jin maganganun su Mama sama-sama. Jin wannan maganar sai ta buɗe idanunta dakyar dan ta san dai ita da Mama ne suka zo asibitin kuma su kaɗai suke da junansu idan Mama ta tafi da gawar ina za ta je a yi suturar tun da Baba ya kore su. Tana buɗe idanunta ta fara ƙarfin halin tashi zaune duk da ba wai gajiyar ta barta bane, dan bata gama jin ƙarfin jikinta ba amma ya zama tilas ta tashi dan idan an sallameta su tafi tare da Mama dan ta san yanzu za a fara cewa su kira ƴan uwansu. "Sannu" Cewar Annur da ke tsaye idanunsa ƙurrr a kanta. "Yawwa" Ta faɗa a hankali tana maida idanunta da suka mata nauyi ta lumshe saboda nauyin da suka mata tana buƙatar ta huta akwai bacci a idanunta sai dai damuwar da take ciki da kuma zuwan abin da ta haifa babu rai duk ya ɗauke baccin. "Sannu Safiyya" Cewar Mama tana matsawa ganin bayan ta rufe idanun ta sake buɗe su. Wannan lokacin bata amsa wa Mama sannun da baki ba, kanta kawai ta iya ɗaga mata tana kallon mahaifiyarta wacce tausayinta gabaɗaya yake mamaye zuciyarta ga shi a yau sanadinta mahaifinta ya sake ta duk da cewar dama ba wai tana jin daɗin zaman gidan bane amma dai ko yaya gidan aure rufin asirin mace ne kuma aure garkuwa ne ga kowacce mace. Duk da cewa wau matan na ganin wani auren ne ke amsa wannan sunan amma dai ko ma yaya ne aure ibadah ne. "Ku barta ta samu hutu domin ta wahala" Cewar likitan bayan ya duba wata marar lafiyar da kan wani gadon daga gefe ya saka kai ya fita. Mama kuwa da Annur kallonta suke da tausaya wa dan tuni bancin har ya ƙara kwasarta. Annur kuwa fita ya yi da takardar magungunan da likitan ya bashi wanda za a siya mata. Yana fita masallaci ya wuce ya gabatar da sallar la'asar dan dama lokaci da ya je ƙofar gidan su Safiyya daga masallaci yake wanda suke gabatar da sallar azahar sha biyu da rabi. Bayan ya yi sallar ya je ya siyo magungunan a parmacy na asibitin ya dawo da ledar maganin. Lokacin Safiyyar ta tashi ma tana zaune ta jingina da filo a kan gadon. Biyar da rabi likitan ya basu takardar sallama bayan ya tabbtar da babu wani abu da yake damunta. Da kanta a ta fito Mama tana riƙe da jaririn da har lokacin Annur cike yake da mamakin ganin babu wani nasu da suka kira kai ko da mahaifin yaron. Suna fitowa suka shiga motar Annur kuwa wani shago ya shiga jim kaɗan ya dawo niƙi-niƙi da ledoji. Ya buɗe gefen mai zaman banza ya saka ledojin ya shiga ya tada motar suka fara tafiya. Babu wanda ya ce komai sai Mama da ke ta saƙa da warwarar inda za su nufa a gefe ɗaya Safiyya tana jin nauyin ƙirjinta na ita ce silar damuwar mahaifiyarta. Tun da ya hau kan titi Mama take ta faman tunanin inda za ta ce ya ajiye su dan ta san shi a nashi tunanin gidan da ya ɗakko su zai mayar da su. "Bawan Allah ka gangara gefen titi mu sauka" Kalaman Mama suka sauka a majiyar sautin Annur. Safiyya kuwa bata yi mamakin furucin Mama ba, dan dama ta san an rina wai an saci zanen mahaukaciya. "A nan zan sauke ku kuma? Dama ba gida zan kai ku ba, ai ba damuwa indai dan ni ne zan kai ku har gida" Annur da tunaninsa ya basa cewa ko suna ganin da takura ne shi ya sa suka ce ya sauke su dan tunaninsa ko ɗan sahu za su hau. "Ba sai ka kaimu gidan ba, nan ma mun gode Allah saka da alkairi" Muryar Safiyya da ta fara keta hazon ta shiga gajimare har ta isa cikin kwararon kunnuwansa cikin sanyi da sanyaya wa. "Dan Allah ku barni in ƙarasa ladana mana ina ne gidan, ga shi ina buƙatar a sallaci gawar amma sai ku ce in ajiye ku a titi haba" Annur ya faɗa cikin sanyin murya idanunsa kafe a kan titi. "Kar ka damu ai ba gidan da ka ɗakko mu za mu je ba, kuma ma inda za mu je layin mota bata shiga" Mama ta faɗa tana kallonsa. Shiru ya ɗan yi yana nazarin magmar Mama amma kuma dai ko mota bata shiga layin ai dai ya rage musu hanya. "Ni ma ina son a yi wa yaron sutura tare da ni ga shi yanzu la'asar ta yi sosai ya kamata a je a sallace shi ko a miƙa shi makwancinsa" Ya faɗa yana waiwayo wa baya idanunsa kafe a kan jaririn da ke a naɗe yana hannun Mama. Safiyya ma kallon gawar yaron take idanunta cike taf da hawaye dan ita kukan zuci take wanda ya fi na zahiri ciwo, yaron da ko mahaifinsa bai san da zuwansa duniya ba ga shi yanzu ba komai take tunani ba sai waɗanda za su yi wa yaron sutura har su miƙa shi inda kowane ɗan adam yake dakon jiran ranar tafiya can. Dan wataƙila ma sai sun je sun nemi taimakon wanda zasu yi jana'izarsa. "Wace unguwa ce za a kai ku wane layi ne kuma" Muryar Annur ta katse shirun. "Haba Malam ba wai bamu ji daɗin taimakonka bane, tabbas mun ji daɗi kuma mun gode sannan ba za mu gushe ba muna maka fatan alkairi a kan alkairinka gare mu sai dai ba sai ka kai mu can ɗin ba a nan za mu sauka" Cewar Safiyya da zuwa lokacin abin ya fara ɓata mata rai domin ta fara ganin kafiyar mutumin hakan na neman nuna yana neman sanin sirrinsu da suke ɓoye wa babu wanda ya sani sai junansu. "Allah sarki ku yi haƙuri dan Allah ba wani abu nake nufi ba da ban" Annur ya faɗa kamar zai yi kuka dan yadda ya ga Safiyyar na maganar sai ya karanci akwai ɓacin rai a kwance a fuskarta shi kuma tausayinta ma duk ya bi ya addabi zuciyarsa ya lura da tana cikij dakuwa duk da bai san takamaimao damuwar ba sai dai ya san hakan ba ya rasa nasaba da sakin da mijinta ya mata har guda uku lokaci guda ga shi tana zuwa gida ba tare da ta huce daga ɓacin ran sakin ba naƙuda ta tashin mata wani ƙarin damuwar ɗan da ta sha wahalar haihuwarsa wada ya fi so da ƙaunarsa ya karɓi abinsa. "Bawan Allah gidan can da ka ɗakko mu haya muke kuma mai gidan ya sallame mu a kan bamu biya kuɗin hayar da yake binmu ba" Cewar Mama cikin hikima dan ta lura yana son taimaka musu bai kamata su watsa masa ƙasa a ido ba duk da cewar bata ƙaunar sanar da kowa cewar mahaifin Safiyyar ya kore ta daga gidan ita kuma ya sake ta duk da cewar zance ba ya ɓuya ko da kuwa rami aka haƙa aka saka shi sai an samu mai tono shi amma dai ita ba zaa ji mutuwar sarki a bakinta ba kuma ko dan a yi saurin yi wa yaron sutura ya kamata su sanar da shi cewa korarsu aka yi daha gidan haya a ƙalla dai ko ba komai ba zai ga laifinsu na ɓoye masa wani abu ba tun da dai zai fahimci basu da wurin zuwa bare ya takura sai ya kai su. Tun da Mama ta fara magana yake kallonta da tausaya wa, ashe dai basu da wurin zuwa shi ya sa suke ɓoye- ɓoye yake raya hakan a ransa. Safiyya kuwa tun da ta ji Mama ta fara magana sai ta sunkuyar fa kai dan ta ɗauka Mamar za ta sanar da shi asalon maganar a ganinta kuwa ai ba ƙaramin abin kunya bane a ce uba ya kori ƴarsa daga gidansa saboda wata manufa fa bata da madogara, kai ko da kuwa ƴar cikin shege ta yi gudun abin kunya ai uban ba ya koreta ba dan idan ya koreta bai san inda za ta je ba kuma bai san wace rayuwa za ta ƙara faɗa wa ba. Amma jin Mama ta yi hikima wajen faɗa masa sai ta ji zuciyarta ta yi sanyi ko ba komai maganar sirrinta ne. "Allah sarki ai da kin min bayani Mama da abin bai kai nan ba" Annur ya faɗa yana kiranta da Mama kamar yadda ya ji Safiyya tana kiranta. Mama na shirin magana sai ta ga ya ja motar ya hau kwalta a tunaninta ma ko gidan zai kai su ya ce zai biya kuɗin hayar hakan ya sa ya ji babu daɗi a ranta dan ta san zai ji ta masa ƙarya idan ya je zai biya kuɗin hayar aka tabbatar masa da cewa ba gidan haya bane ga shi kuma yana ganin girmanta hakan ya sanya ta ji duk ta shiga damuwa. Amma ganin ya ɗauki wata hanyar da ban sai suka shiga kallon kallo ita da Safiyya. Hanyar fada ya nufa sai da ya je wajen gidan sarki a karya kwanar da za ta sada shi da unguwar WAZIRAWA a dai dai ƙofar wani katafaren gida ya tsaya wanda gidan aka masa ado da dagi irin na sarauta. Ya shiga danna horn mai gadi ya buɗe musu get mamaki ne ya cika wa Mama zuciya ganin ya kawo su gidan Alhaji Anas Aliyu (SARKIN SHANUN GUMEL) Gidan hakimin da yake ji da tashen dukiya wanda kaf garin da wasu garuruwan da ma jihohi da dama sunansa ya shahara kasancewarsa mutum mai yawan alkairi da ƙaunar talakawa da kuma tausayin marayu. "Kar dai yaron nan ɗan gidan SARKIN SHANU ne?" Mama ta jefa wa kanta tambayar a zuciyarta kasancewar ta san alkairin mutumin a bakin jama'a daga shi har tilon matarsa wacce ta rasu kowa ya yi jimamin mutuwarta. Duk da bata taɓa shiga gidan ba amma tana ganin SARKIN SHANUN a kan doki idan ana hawan sallah dan in bata manta bama waccen sallar azumin shi ne ya lashe hawanda aka yi saboda tsaruwa da hawan masa ya yi ga dawakansa ƙosassu wanda aka ƙawatasu da kayan kwalliya na alfarma daga su har mahawan nasu. "Kenan shi ne ɗan gidan sarkin shanu ɗansa da ake faɗa tilo? Mama ta jefa wa kanta tambayar. "Dole ka yi tausayi, dole ka yi taimakon, dan ba a ƙasa ka ɗauka ba tabbas hali zane" Mama ta faɗa a z ranta idanunta taɓ da hawayen taimakon da Annur ɗin ya musu, ga kuma gawa a hannunta. Yana gama parking ya fito ya buɗe wa Mama ƙofar ta fito ita kuma Safiyya ta buɗe ɗayan ɓangaren ta fito tana ƙarewa gidan kallo sai lokacin ma ta lura da no motar Annur ɗin mai ɗauke da sunan SARKIN SHANU 3 a jiki. Mai gadin da wasu a wurin suka shiga masa barka da dawo wa da hannu ya musu alamar amsa wa ya buɗe ƙofar ya ɗauko ledojin da ya siyo wa Safiyya kayan shayi da abubuwan buƙata wanda ya yi niyyar basu idan ya sauke su a gidan dan da ya san ma gidansu zai taho da su ba sai ya tsaya ɓata lokacin siyan komai ba dan akwai komai da za su buƙata. Wani daga cikin mazan da ke zaune a get ɗin ya taso yana yi wa Annur ɗin kirari irin na saraita zai karɓi ledojin amma Annur ɗin ya dakatar da shi ya ɗauka a kansa dan yana ji a ransa cewar babu wanda ya dace ya ɗauki kayan Safiyya sama da shi. MAI FARAR ƘAFA (JAHILCI NE) NA MAMAN AFRAH FCW GAJERAN LABARI FREE BOOK Page1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣ Tafiya yake su Mama suna biye da shi a baya suka shiga cikin gidan tsaruwa da kyan cikin gidan har ya fi ƙofar gidan ma. Gida ne mai girman gaske ga kyau kamar ma ba a Nigeri'a ba. Can wani ɓangare ya nufa da su ya buɗe ɓangaren ya kai su wani babban falo ya ce su zauna zai je ya ce su shiga zai je ya sanar da Daddynsa, da to Mama kawai ta amsa suka shiga ɓangaren suna ta ƙarewa wajen kallo. Bayan sun zauna Mama ta kalli Safiyya da ta yi nisa cikin tunani pos ɗinta a kan cinyarta ta ce "Safiyya kar kike saka damuwa a ranki komai ya same ki a rayuwa ki zama mai fawwala wa ubangiji domin shi ne majiɓancin dukkanin al'amura. Yana sane da dukkan abubuwan da suke faruwa da ke dan haka ki ɗauki hakan a matsayin jarabawa sai dai ki yi fatan Allah ya baki ikon cinye wa. Shi kuma yaron nan dama Allah ne ya baki kuma yanzu ya karɓi kayansa, dan haka ki saka a ranki dama can Allah bai rubuta shi cikin wanda za su shaƙi iskar duniya ba , kuma ko da a a ce ya rayu tsawon lokaci yo akwai ranar fa ubangiji zai karɓi ransa domin alƙawarin Allah ne sai kowace rai ta ɗanɗani mutuwa kowa zaman jiranta yake wanda ya tafi bai yi gagggawa ba wanda ya yi jinkiri shi ma ranar ƙarewar kwanakinsa tana nan zuwa sai dai mu yi fatan cika wa da imani" Mama ta faɗa tana kallon Safiyya da zuwa lokacin hawaye ne suke ta zirya a fuskarta saboda sai ta ji tamkar Mama ta tsokano mata inda yake mata ƙaiƙayi. "Ba komai Mama dama bawa ba ya wuce ƙaddararsa, sai dai sakin da Baba ya miki ne a dalilina ban ji daɗi ba dom... "Haba Safiyya yanzu a ringa maimaita magana dai sakin nan fa ba wai laifinki bane kuma ki sani ba ke ce sila ba shi aure da kika ji da gani rai gareshi tamkar mutum shi ma akwai ranar da kwanakinsa za su ƙare dama can Allah ya rubuta cewa yau ne ranar da aurena da mahaifinki zai mutu kuma ko da a ce baki zo gidan ba tun da Allah ya ƙadarta zai sake ni a yau to dole sai ya sakie ni! Shi ya sa a rayuwa za ko ga ma'aurata suna zaune tsawon lokaci kuma suna samun saɓani wata rana ma saɓanin ya zama mai yawa kuma mai rikitarwa, wanda rikitarwasa da kuma ɓacin ran da aka fuskanta sai ki ɗauka a ranar auren nan zai mutu to amma kuma tun da Allah bai ƙaddara mutuwarsa a ranar ba sai ki ga duk girman laifin sun manta sun daidata sun cigaba da zama dama mata da miji sai Allah. Amma wani lokacin kuma sai ki ga wani abu ya gifta wanda bai taka kara ya karya ba, wanda bai kai ya kawo ba amma sai ki ga an kasa haƙuri an kasa jurewa sai ki ga abu ƙalilan ne ya kashe auren wanda an yi ta gumurzu a zaman sama da wanda ya yi sanadin mutuwar auren amma auren bai mutu ba sai a kan abu kalilan wanda za a yi ta cewa a kan abu kaza ya sake ta, to ba haka bane dama ranar Allah ya ƙaddara auren zai mutu dan haka ki daina ɗora wa kan ki laifin mutuwar aurena" Mama ta kai ƙarshen maganar idanunta kafe a kan ƴar tata ganin duk jikin Safiyyar ya yi sanyi. "Haka ne Mama ba zan ƙara tunanin hakan ba na yarda haka Allah ya ƙaddara" "Yawwa Safiyyata kar ki damu Allah zai baki miji na gari mai ƙaunarki wanda ba zai taɓa ƙyamatarki ba. Wanda zai yi sanadiyyar shigarki aljanna, saboda kullum na kai goshina ƙasa a matsayina na mahaifiyarki ba na ɗagowa har sai na roƙa miki miji na gari wanda zai riƙe ki amana wanda ba zai taɓa wulaƙanta ki ba tun kina ƙarama nake miki addu'a kuma kin san addu'ar mahaifiya tana da tasiri ƙwarai a kan ƴaƴanta bakin mahaifiya yana da kaifi shi ya sa ake so a koyaushe ya zamana abu mai kyau ne zai fito daga bakin mahaifiya ya zamana addu'ar alkairi ce ga ƴaƴanta ba wai sai a sallah uwa take yi wa ƴaƴanta addu'a ba ko aiki suka mata ko aikensu ta yi sai ta musu fatan alkairi ta musu addu'ar dacewa duniya da lahira. Ta nema musu tsari da mugayen abokai da mugayen ƙawaye ta musu fatan haɗuwa da mutanen kirki wanda za su zame musu farinciki ba wanda za su gurɓata musu tarbiya da rayuwarsu ba ta nema musu samun ilimi mai albarka ke hatta ƙoƙari uwa ce take yi wa ƴaƴanta addu'ar fin sauran ɗaliban ajinsu ƙoƙari da gane karatu hatta position uwa take yi wa ƴaƴanta addu'ar su zo su ne na ɗaya a cikin ajin islamiya da boko. Dan haka na jajirce wajen miki addu'a tun baki san inda yake miki ciwo ba ke tun kina ƙarama idan na ga kin zo ta biyu a ajinku to na kan ƙara zage dantse wajen dagewa da addu'a har sai na ga kin doke kowa kin zo ta ɗaya kina kawo kyaututtuka gida sannan hankalina yake kwanciya bare ɓangaren addu'ar samun abokin rayuwa na ƙwarai tun kina ƙaramarki mitsitsiya nake miki addu'ar hakan har girmanki dai dai da rana ɗaya ban taɓa fashin faɗa wa ubangiji hakan ba ke ko da ina al'ada (Fashin sallah) Nake to kuwa na kan yi alwala in hau sallaya in yi addu'o ina dan kar wannan rana ta wuce ban faɗa wa ubangiji buƙata ta ba. Ko aiki nake a zuciyata ina miki addu'a da kaina baki ɗaya dan haka ko da na ga kin yi auren farko baki dace ba kin fito ban damu ba haka aurenki na biyu ma, har kawo na uku duk na san jarabawa ce ko damuwar da nake shiga a sanadin mutuwar aurenki ina yi ne saboda damuwar da kike samun kan ki a ciki da kuma kalmar da mutane suke jifanki da ita ta MAI FARAR ƘAFA. Sai dai na san akwai lokaci, lokaci zai zo wanda komai zai zama tarihi lokaci zai zo wanda komai zai zama kamar ba a yi ba dan na san iya tsawon rayuwa na miki addu'a kuma na san Allah maji roƙon bayinsa ne sannan a duk lokacin da ɗan adam ya roƙi Allah wata buƙata to kuwa Allah ba ya maido wa bawansa addu'a face ya amsa masa ita ko dai ya samu jinkirin amsuwarta ko kuma addu'ar tashi ta tsaya a sama tana kokawa da wata musiba da za ta afka masa ma'ana addu'arsa tana tare wani abu marar kyau da zai same shi. Dan haka na san ko aure goma za ki yi to akwai wanda za ki aura wata wanda burina zai cika ki samu kwanciyar hankali dan haka ke ma ki kasance cikin yi wa ƴaƴanki addu'a da ke kan ki ma" Mama ta kai ƙarshen maganar tana kallon Safiyya. "In sha Allahu Mama na gode ƙwarai kuma ina alfahri da kasancewarki mahaifiya a gare ni, kuma uwa ta gari domin kowace uwa mahaifiya ce ce amma ba kowace uwa bace ta gari, uwa ta gari da ban take" Mama murmushi kawai ta yi sai ta ce "Ki kira Rabi'u a waya ki sanar masa cewa kin haihu amma ɗan bai zo da rai ba" "Mama ba lallai ya ɗauki wayata ba saboda da zan taho har gargaɗi ya mini cewar ko kaya za a je ɗauka kar na je masa gida... "To ai yanzu ba gidansa za ki je ba a waya za ki faɗa masa kin ga kar a binne ɗan bai sani ba kuma daga baya a zo ana A'i ina indo dan zai iya yin ƙaranki ma ya ce ki fito masa da ɗansa ko ya ce kashe masa ɗan kika yi da gangan" "Yo Mama ai ina da hujjar da zan kare kaina tun da ba a gida na haihu ba a asibiti na haihu ko masu asibitin za su shaideni" "Haka ne amma dai gwara ki kira shi yanzu maganin kar a yi kar a soma" "To" Cewar Safiyya tana fito da wayar daga pos ɗinta. *ANNUR* Tun da ya kai su Mama ya ajiye ledojin hannunsa ya fito part ɗin Daddy ya nufa yana jin wani nishaɗi a ransa ganin irin tarin baiwar da Allah ya masa a yau na kawo masoyiyarsa abar ƙaunarsa har cikij gidansu lallai yau rana ce da ba zai taɓa mantawa ba a cikin tarihin rayuwarsa domin ko a mafarki bai taɓa kawo hakan ba, kai bai ma taɓa tunanin a kwana kusa zai haɗu da ita ba amma sai gashi cikin hikimar ubangiji komai ya zo masa da sauƙi ko da ya same ta a matsayin matar aure sakakkiya sai ga shi cikin awanni ƙalilan idda ta fita daga kanta. "Assalamu alaikum" Ya faɗa yana daga bakin ƙofar falon mahaifin nasa yana jiran ya amsa masa kuma ya bashi damar shiga domin koyarwar mahaifiyarsa ce tun yana yaro ƙarami in zai shiga wuri sai ya yi sallama sannan idan aka amsa aka masa iso sai ya shiga. "Wa alaikumus salam wa rahmatullah, shigo" Ya tsinkayo muryar Daddy daga cikin falon. A hankali ya ɗaga labule ya kutsa kai cikin falon mahaifin nasa wanda ya ƙawatu ƙwarai da kayan alatu na more rayuwa. Ƙamshin freshner da sanyin AC ya haɗe falon. Zaune Daddyn yake a kan lallausan capet ya ringisa a kan tuntu sanye yake da yadin kufta wanda aka yi wa aikin hannu sai alkyabba marar nauyi wacce ta sha aiki na lafarma carbi ne ɗan dannawa (Counter) Maƙale a yatsan hannunsa na dama sai kuma hoton matarsa abin faharinsa a gefensa a jingine domin a duk lokacin da hoton yake kusa da shi ya kan ji tamkar ita ce a kusa da shi hakan yana rage masa kewar rashinta a tare da shi duk da ganin hoton ba ya rage masa raɗaɗin rashinta a zuciyarsa amma dai ya fi so hoton ya kasance a kusa da shi sai ya ringa jin tamkar dai ita ce domin a lokacin tana raye bata yin nesa da shi ta kan zauna su yi ta hira abinsu cikin so da ƙaunar juna tamkar sabbin amaren da suka tare a satin farko. Cikin nutsuwa ya ƙarasa wajen mahaifin nasa ya zauna tare da naɗe ƙafafunsa. "Daddy... "Annur wani irin abu ne ya faru da kai wanda ya sauya yanayinka gabaɗaya daga mai damuwa zuwa mai annushuwa tun a sallamarka na fahimci kana cikin farinciki a muryarka, yanayin tafiyarka da ka shigo yanzu fa ma zaman da ka yi duj cikin zumuɗi ne na ƙara fahimtar daɗin da ke lulluɓe ɓoye a cikin ranka ta yadda na ga walwala shinfiɗe a fuskarka ka sai wani walwali take tamkar sabon angon da ya dawo daga wajen ɗaurin aurensa" Daddy ya katse masa maganar cikin nuna tsantar farinciki yana son sanin mene ne ya canja shi lokaci guda Annur ɗin da har shi yake bashi umarnin ya fita ya zaga gari dan kawai ya rage damuwar ransa tun mutuwar mahaifiyarsa lokacin ya dawo daga ƙasar Ingila ya kammala karatunsa har yau bai ƙara ganin farinciki a tare da shi ba ya fahimci yana cikin damuwar da ba mutuwar mahaifiyarsa kaɗai bace damuwar tasa, ya fahimci akwai wani gagarumin abu da yake damunsa a zuciyarsa wanda ya ƙi sanar da shi sai dai a yadd ya fahimta ya yi ƙiyasin kamar dai soyayya ce yake fama da ita sai dai kasancewar Annur ɗin ba ma'abocin kula mata bane babu ruwansa da ƴan mata shi ya sa ya watsar da wannan tunanin a ransa amma kuma ya tabbata koma mene ne a yau ya samu warwarewarsa dan ba haka ya fita ba. "Daddy za mu yi maganar daga baya yanzu baƙi ne na kawo gidan nan wasu mutane ne masu kirki da karamci kuma suna buƙatar taimako na wurin zama shi ne na kawo su gidan nan" "Ma sha Allah, Annur hasken rai da zuciyata ai babu wani wanda za ka kawo gidan nan kai ko da a ce dabba ce bare kuma mutum ɗan adam mai cike da karamci da martaba da kuma daraja a ƙi karɓarsa dan haka ka kai su masauki ko da shekara nawa za su yi a gidan nan ba za a ƙyamace su ba kai ko da za su rayu a nan ne tsawon rayuwarsa babu wani abu da za su nema su rasa matsawar ina raye kuma kaima kan numfashi sai inda ƙarfinmu ya ƙare wajen taimakon bayin Allah" "Godiya nake Daddy" Annur ya faɗa farincikinsa ya kasa ɓoyuwa. "Babu godiya ai yi wa kai ne kuma aikin lada ne matsawar mutum na taimakon mutane masu buƙatar taimako to tabbas ba zai taɓe ba kuma arziƙinsa ba zai gushe yana ƙaruwa ba domin Allah na taimakon masu taimako" "Haka ne Daddy" "Maza ne ko mata, ko kuma maza da mata, sun kai kimanin nawa?" "Mata ne su biyu ne" "Ikon Allah mata, Allah sarki ashe ma masu rauni ne ka san mata suna da rauni, kuma ma a she su biyu ne basu da yawa ma Allah bamu ikon kyautata musu" "Amin ya rabb, amma Daddy uwa da ƴa ne kuma daga asibiti muke yanzu ƴar ce ta haihu dama a hanyarsu ta zuwa asibiti na haɗu da su ƴar tana naƙuda shi ne na kaisu asibiti to yanzu dai ɗan bai zo da rai ba shi ne nake so a masa sutura " "Allahu akbar kabiran ina alfahri da kai ƙwarai saboda taimakonka ga jama'a" "Daddy ai a wajenku na koya" "Mu je yanzu na gansu sai ka fita ka sanar da mutane a waje domin a sallace shi" "To Daddy" *SAFIYYA* Tun da ta fara kiran wayar Rabi'u yake katsewa har ta gaji ta ajiye sai Mama ta ce ta ƙara gwada wa ko Allah zai sa ya ɗauka dan Mama ta fi so a sanar da shi cewar ɗansa bai zo duniya da rai ba tun da dai har ya san ta taho da cikinsa to dole ya san halin da ake ciki. Haka Safiyya ta daure ta ƙara kiran nasa har ya katse bai ɗauka ba sai da ta yi sau huɗu a na biyar ɗin ya ɗaga da wata muguwar tdawa da ta sanya Safiyyar razana bata shirya ba kafin ta dawo daga razanar da ta yi ya kawo wata ashariya ya luƙa tamkar ɗan maguzawa. "Wai uban me zai miki da kika nace da kirana, bayan abin da ya haɗa mu da ke ya raba kuma ko cikin mafarkina bana fatan dake ko haɗa hanya da ke yanzu ma na ɗauka ne dan in miki kashedi a kan kirana da kike to ki sani ni dai na fi ƙarfinki a yanzu domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa kuma ina gama wayar nan da ke zan yi blocking ɗinki ke hatta wayar bayar da ita zan yi gudun kar muryarki ta sa wani abunki na FARAR ƘAFA ya shafe ni ko sim ɗin ma zan cigaba da amfani da shi ne saboda customer na da suke da number... "Ina son sanar da kai ne na haihu kuma ɗan bai zo da rai ba... Cewar Safiyya da ta katse shi daga munanan kalaman da yake faɗa mata domin zuciyarta zafi takw mata in banda ma Mama ta matsa da babu abin da zai sa ta kira wo shi, dai dai tun kan ta kai aya ya katse ta da faɗin. "Alhamdulillahi! Allah na gode maka da hakan ta faru shikenan ma na huta da baƙar jaraba don haɗa zuri'a da MAI FARAR ƘAFA ba ƙaramin jafa'i bane gwara ma da ɗan bai zo da rai ba shikenan a ja a je an hana tsohuwa shiga mota, ko suturarsa na yafe ba sai na zo ba ku binne shi Allah sa ya ceceni a lahira amma ba zan zo ba in raɓi inda ahalin masu FARAR ƘAFA suke" MAMAN AFRAH😍 MAI FARAR ƘAFA (JAHILCI NE) NA MAMAN AFRAH FCW GAJERAN LABARI FREE BOOK Page 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣ Gabaɗaya jikinta ne ya yi wani irin sanyi zuciyarta ta karaya ta shiga mata wani zugi na maganganun fa yake faɗa mata ta cikin wayar kafin ta samu ƙwarin gwiwar furta komai ya ja wani uban tsaki tare da yanke kiran. Hawaye ne suka shiga malalowa daga idanunta ko wayar ta kasa cire ta daga kunnen nata bare a yi zancen yin magana. Mama ce ta aro jarumta tare da ƙarfin gwiwa ta ce "Kar ki damu ai tun da kin faɗa masa kin fita haƙƙinsa, dama ni burina ya san da haihuwar da kuma komawar abin da aka haifar to tun da kin isar da saƙo baki da haƙƙinsa ko a wurin ubangiji kin fita" Cewar Mama tana dake muryarta dan bata so ƴar tata ta fahimci raunin da zuciyarta ta yi na sauraren maganar abin da aka mata ta waya dan akwai volume Mamar tana iya jiyo duk abin da Rabi'un ya ce "Danne zuciyarta ta yi tare da maida hawayen da ya yi wa idanunta tsinke, ta ce "Babu komai Mama" Saboda ta ji daɗin yadda mahaifiyarta take kwantar mata da hankali ko ba komai ai soyayya da kulawar mahaifiya sama take da kowa a cikin mutane. *BAYAN AWANNI BIYU* Mama, Safiyya, sai kuma Baba Dudu mai aikin gidan SARKIN SHANU su ne zaune a falon lokacin Safiyya har ta yi wanka da ruwan zafin da Baba Dudun ta haɗa mata tana zaune tana cin abincin da Baba Dudu da kuma Mama suka matsa mata. Dan ko Daddy da ya shigo sosai ya yi farinciki da ganinsu domin kana yin tozali da su za ka gane mutane ne masu karamci. Sannan shi ma Annur ya sake shigowa bayan sun dawo daga maƙabarta ya ƙara jajanta wa Mama tare da yi wa Safiyya sannu da jiki haka ta amsa tana jin kunya saboda kallon da ta lura yana jifanta da shi wanda ta kasa gane takamaiman dalilin yin kallon. *BAYAN SATI BIYU* Duk yadda Mama da Safiyya suka so su bar gidan amma Daddy ya hana su dan shi Annur ma daga Mama ta fara masa maganar barin gidan sai ya faɗa wa Daddy, haka Daddy zai yi ta musu nasiha yana jan hankalinsu a kan kar su damu ko su saka wani abu a ransu domin nan gidan babu wani abu da za a musu shamaki za su rayu ne a cikinsa tamkar dama a nan suke tun asali. Ganin hakan sai su Mama suka saki jiki suka zauna suke sabgoginsu ko rayuwarsu ta baya basa tunawa ga komai nan na buƙata babu abin da suka nema suja rasa dan ko aiyuka akwai masu yi da mai girki Baba Dudu dan ko Mama ta ce za ta tayata girkin bata yarda sai ta ce ta sha zamanta ta huta. Kwanci tashi asarar mai rai a haka har Safiyya ta zubar da wanka. Sun yi ƙiba abinsu sun yi kyau sosai jin daɗi da kwanciyar hankali ya bayyana a jikinsu. A haka har Mama ta kammala iddarta. Zaune yake a mota ya sako ƙafafunsa waje fa yake ƙofar a buɗe take. Ya yi nisa wajen kallon hoton Safiyya wanda ya ɗauketa ba tare da ta sani ba, suna zaune da Mama suna hira ya shiga gaishe da Mama bayan Safiyyar ta gaishe da shi ya amsa yana ɗan danna waya a haka ya saita fuskarta ya ɗauki hoton ba tare da Safiyyar da Mamar sun fahimci ya ɗauka ba. Ya kafe hoton da ido yana zooming kyakkyawar fuskarta ma'abociyar kyau wacce a koyaushe ba ya gajiya da kallonta har kullum ganin Safiyya yake tamkar sabuwar halitta a idanunsa duk da wani lokacin yana ta tunanin ina dangi da ƴan uwansu suke. Duk da cewar har yau Safiyyar bata wani saki jiki da shi ba iyakarsu gaisuwa ko zuwa ya yi ya tarar suna hira da Mama ko da Baba Dudu daga lokacin da ya shigo ɗakin za ta saka wa bakinta linzami ta rufe ruf tamkar ɗakin da aka kulle da ɗankwaɗo. Haka za ta yita sunkuyar da kai idan ma ta ga sun fiya haɗa ido da shi sai ta tashi ta shige ɗaki ta barshi da Mama a falon. "Ranka ya daɗe ga kukar kaɗin an samo kuma wallahi tana da kyau sosai" Cewar Ibra direban gidan su Annur. Ɗago kai ya yi daga kallon wayar da yake na ganin hoton Safiyya tare da sauke wata ajiyar zuciya ya kalli Ibra ya ce "Ka shiga da ita gida ka ce a mini ɗanwaken amma ka faɗa wa Baba Dudu Safiyya ce za ta mini ɗanwaken" Ya faɗa yana kallon Ibra da ya ɗan rissina cikin girmama wa dama ɗanwake ya ce a masa sai Baba Dudu ta ce babu kukar da za a yi shi ne ya aika direban ya siyo a kasuwa. "To ranka ya daɗe an gama" Cewar Ibra yana juya wa ya shige cikin gidan. Can kicin ya nufa inda ya san zai samu Baba Dudu. Zaune ya same su da wata wacce bai ga fuskarta ba dan ta bashi baya ne. "Hajiya Dudu an buga an barki" Dariya ta yi tana kallon Ibra ta ce "Aikuwa dai sai dai a barnin" "Ga wannan in ji yallaɓi ƙarami ya ce amma Safiyya ce za ta masa ɗanwaken" "To sannunka da ƙoƙari Safiyya lambarki ta fito" Cewar Baba tana dariya ta miƙa wa Safiyya ledar kukar da Ibra ya miƙo mata. Ita Safiyya rasa bakin magana ma ta yi sai kawai ta miƙa hannu biyu ta karɓa tana sakin murmushin yaƙe. Ibra da ke ta son ganin fuskar Safiyya sai kuwa aka yi sa'a ta ɗan juyo a nan ya yi gamdakatar na ganin fuskarta saboda bai san fa zamanta a gidan ba dan ya ɗan yi jinya ne ya daɗe ba ya zuwa aiki. "Safiyya!" Ya faɗa da mamaki. Juyo wa ta yi gabaɗaya sai ta sauke idanunta a kan fuskar Ibra. Cikin fargaba ta ce "Na, na, na'am" Har tana inda-inda dan ganin Ibra ya mugun tasar mata da hankali dan ta san shikenan yanzu sai ya yi sanadin barinsu gidan fa suke ganin sun samu kwanciyar hankali har suna mantawa ma da wani abu wai shi ɓacin rai ko baƙinciki na jifansu da magana da jama' a dan tun da suna samun komai na buƙata babu inda suke zuwa ko nan da can bare Safiyya dama bata da yawo ko da na gidan ƙawaye ne bare kuma da mutane suka canfa cewar ita MAI FARAR ƘAFA ce sai kowa yake gudunta ita ma kuwa sai ta daina zuwa wajen kowa bare ma har a wulaƙantata. "To iko sai lillahi! Wato dama a nan gidan kike ake ta raɗe-raɗin... "Ibra dakata dan Allah! Ni fa ban tambayeka koma mene ne ba dan haka duk wasu maganganunka ka riƙe kayanka" Safiyya ta faɗa tana ɗaukan ledar kukar ta tafi cikin kicin ɗin dan yin ɗan waken dan ta san Ibra tauraruwa mai wutsiya ne ganinsa ba alkairi bane. "Baba Dudu wai ko dalilinki ta zo gidan nan? Shin ta daɗe ne a nan gidan ko yanzu ta zo har na ji yallaɓi Annur na cewa a bata ta masa ɗanwake, ko dai ita ma aiki aka ɗauketa" Ya faɗa yana wani ɗaga wuya dan ya hango Safiyya da ta shige kicin yana wani waiwaye-waiwaye kamar marar gaskiya. "Ibra ka je ka tambayi masu gidan ni ma dai ai ka san aiki nake a gidan nan tun da kana buƙatar a maka ƙarin bayani sai ka tuntuɓi masu gida tun da dai ka san babu zai shiga gidan mutum ba tare da mai gidan ya sani ba" Baba ta faɗa tana ɗaure fuska dan dama ta san Ibra da shegen gulmar tsiya kuma tun da dai har ta ga Safiyya ta ɗaure fuska kuma ta nuna bata buƙatar yin magana da shi to tabbas akwai wata gulmar da yake son aiwatarwa duk da ita bata ga wani aibi a kan Safiyyar da mahaifiyarta ba , amma ɗan adam tara yake bai cika goma ba. Ganin Baba ta yi banza da shi ya juya yana waiwaye har yana yin tuntuɓen da ya nemi faɗuwa. *SAFIYYA* Tun da ta yi ido huɗu da Ibra gabanta yake faɗuwa dan ta san idan har Ibra ya yi wa masu gidan bayanin wacece ita to tabbas za a kore su daga gidan kuma bata san inda za su je ba. Dan Ibra unguwarsu ɗaya da shi babu abin da bai sani a kanta ba game da jifanta da ake na cewar ita MAI FARAR ƘAFA ce. A haka ta yi ɗanwaken cikin sanyin jiki fa saƙe-saƙe har ta gama ta sanya masa a foodflaks ta masa miyar jajjage dan da miya yake ci ba ya ci da yaji. A kicin ɗin ta bar masa dan ta san Baba za ta saka a kai masa part ɗinsa, fitowa ta yi daga kicin ɗin amma sai ta tarar Baba Dudu ta tashi daga wajen tunaninta ko ta tafi ɗakinta ne dan a gidan take kwacakam da zama tana aiki. Ɓangarensu ra nufa dama ta fito wajen Babar ne dan ta ɗan huta da zaman ɗakin sai ta bar Mama tana kallo. Da sallama ta shiga falon Mama ta amsa mata da kallo Mama ke binta ganin ta sauya jikinta sanyi ƙalaw ba kamar lokacin da ta fita ba. "Safiyya lafiya dai na ganki haka?" Mama ta jefa mata tambayar. Shiru ta ɗan yi da ba za ta faɗa wa Mama ba dan kar hankalinta ya tashi sai kuma ta yi tunanin gwara dai ta faɗa mata dan idan ta san da maganar ko da an kore su abin ba zai ɗaga hankalinta ba duk da ta san mahaifiyarta jarumar uwa ce tana tunkarar matsalar da ta tunkarota a koyaushe. "Ki faɗa mini mana kar ki manta baki da wacce ta fini a rayuwa ni ma kuma haka to mai za ki ɓoye mini Safiyya" "Mama Ibra ne ya ganni a gidan nan" "To sai aka yi yaya?" "Mama ina ga fa aiki yake a gidan nan kuma kin san shi da gulma saboda shi faɗi ba a tambayeka bane, yanzu na san dakyar ne in bai faɗa wa masu gidan cewar ni MAI FARAR ƘAFA bace" "To mene ne na damuwa? Kowane lamari fa Allah ake miƙa wa, kuma nan ɗin ma ba yin kanmu bane Allah ne ya sa masu gidan suka amincw da mu har suka yarda muka zauna musu a gida to haka in suka koremu Allah ba zai hana mu wani wajen da za mu zauna ba dan mutum komai yake ya saka Allah to kuwa Allah zai zame masa jagora!" "Haka ne Mama" "To ki kwantar da hankalinki komai muƙaddari ne daga Allah, ko yanzu aka zo aka ce mu tafi kar ko ɗaga hankalinki ai duniya da faɗi maye ba ya ci kansa ba" "To Allah iya mana" "Amin Safiyyata" Murmushi kawai Safiyyar ta yi. *IBRA* Ƙafafunsa har wani wani rawa-rawa suke tsabar sauri da yake yana son ya je ya barbaɗa wa Annur gulmar wacece Safiyya dan ya san duk wanda ya san cewa ita MAI FARAR ƘAFA ce ba zai bari ta raɓe shi ba. "Taɓ MAI FARAR ƘAFA a gidan SARKIN SHANU yo wannan kwana kaɗan ya rage duk wannan ɗinbin dukiyar da kuka tara sunanta ƘURMUS dan duk inda MAI FARAR ƘAFA ta raɓa sai komai ya lalace"Cewar Ibra a ransa bakinsa har wani mutsu-mutsu yake na son faɗin gulma da ɗumi-ɗumi. Yana fitowa sai ya ga Annur a kan mota a zaune amma lokacin ba wai waya yake latswa ba carbinsa na dannawa yake dannawa. "Ranka ya daɗe an isar da saƙon" Cewar Ibra yana ɗab rusunawa idanunsa kafe a kan fuskar Annur ɗin dan yana so ya ga fuskar da zai faɗa masa abin da ke ci masa tuwo a ƙwarya wanda ya gani yanzu, dan yana ganin idan har ya ɓoye kamar bai riƙe alƙawari ba ya ci amanar zaman tare. Ganin Annur ɗin ya tsare gida dan ko maganar ma bai amsa masa ba kawai hannu ya ɗaga masa. "To fa! Yallaɓai sarautar ta motsa ya wani haɗe rai gashi ni kuma ina son faɗa masa akwai MAI FARAR ƘAFA a cikin gidansu. "Am,um ranka ya daɗe dama akwai magana da nake son faɗa maka" Cewar Ibra a ɗan ɗarare yana kallonsa. "Ibra ba na son damu ka yi abin da ke gabanka ni ma ina da abin yi" "Yallaɓai wallahi tallahi maganar tana da matuƙar muhimmanci matuƙar ban faɗa maka ba hankalina ba zai kwanta ba gani nake kamar ma na ci amana ne f... "Ibra! Ka faɗi abin da ya kawo akwai abin da nake yi ne tun da har ka ji na bafa uzurina amma tun da har ka faɗi hakan ka gaggauta faɗa mini domin in cigaba da abin da ke gabana" Cewar Annur da bai so ya katse azkar ɗin da yake ba domin azkar ne da yake na neman Allah ya bashi ikon furta wa masoyiyarsa Safiyya kalmar so tare da dacewar ya samu ta amsa masa ta karɓi tayin da zuciyarsa za ta yi wa tata zuciyar dan ba ya fatan ta watsa masa ƙasa a ido ta hanyar ƙin karɓar kalmar so daga gare shi idan har haka ta kasance bai san makomar damuwarsa ba zai rayu ne cikin damuwa da ƙuncin zuciya saboda ya yi nisa ya yi nutso a cikin kogin sont d ƙaunarta wanda ba ya jin akwai wata mace da za ta samu kwatankwacin irin ƙaunar da yake yi wa Safiyya daga wani ɗa namijin dan shi ita kaɗai ce a zuciyarsa kuma da ita kaɗai yake fatan kasancewa har iya ƙarshen numfashinsa. "Ranka ya daɗe wata wuta na hango tana shirin kama wa a gidan nan wacce idan ta kama za ta haifar da gobara wacce ba ƙaramar ɓarna za ta yi ba don... "Ibra ka dai san ban cika son gutsiri tsoma ba, kuma ka san wannan doguwar Hausar da kake jerowa ba wai ina fahimta bane sanin kn ka ne ban zauna na yi rayuwa a ƙasar Hausa ba na tsawon lokacin da zan ke iya fahimtar wannan murɗaɗɗiyar Hausar gwara ka mini gwari-gwari yadda zan fahimta" "Ranka ya daɗe wata ƴar unguwarmu na gani a gidan nan mai suna Safiyya to cikin ikon Allah sai ma na ji ka ce ita ce za ta maka ɗanwaken" "To sai aka yi yaya? Mene ne matsalarka da hakan ni fa ba na son shishshigi in ma wa na ce ya girka mini kai mene ne naka a ciki" "Ranka ya daɗe ka gane mana, yarinyar nan aurenta uku, aurenta na farko ta auri wani Sani haihuwarta ɗaya suka rabu saboda gabaɗaya samunsa ya ragu sai uban talauci ya baibaye shi aikuwa suna gano FARAR ƘAFA gareta ya rattaba mata saki, ɗan ma mahaifiyarsa ya baiwa dan ba ya so FARAR ƘAFARTA ta shafe shi. Bayan ta fito ta auri wani Salisu shi ma dai hakan ce ta faru ɗan nasu yana wajensa ya ba wa sabuwar matar da ya aura. Ta zo ta auri wani Rabi'u shi ma dai auren bai je ko ina ba ya sako ta da tsohon ciki saboda karayar arziƙin da ya same shi talauci ko ta ina ya masa katutu ba komai bane sila kuma sai FARAR ƘAFAR Safiyya. Yanzu maganar da nake maka a ranar da ya sake ta ubanta mahaifi ya saki mahaifiyarta ya musu korar kare kuma ba a kan komai ba sai a kan FARAR ƘAFAR Safiyyar dan ba ya son komai nasa ta kassara masa shibya sa ya jefar da ƙallon mangwaro ya huta da ƙuda. Tun daga ranar ba a ƙara jin ɗuriyarsu ba aka rasa ma ta inda suka bar unguwar dan kowa sai ya ce bai gansu ba wannan ya sa mutanen unguwa suka yi ta murnar cewar annoba ta bar wajen su. To fa yanzu ina shiga gidan na yi arangama da tauraruwa mai wutsiya wacce ganinta ba alkairi bane wato Safiyya MAI FARAR ƘAFA. Shi ne na ce ba zan yi ƙasa a gwiwa ba dole in garzayo in faɗa maka domin a ɗauki mataki dan kar a sakankance sai dai ka ga komai na arziƙi yana ja baya komai yana lalacewa ya ɓalɓalce dan da zarar ta ɗauki kwanaki uku a gidan nan to kuwa abin ba zai yi kyan gani ba" Ibra ya kai ƙarshen magana yana kallon Annur da tun da ya fara magana yake kallonsa da baki a sake. "Allah mai hikima da baiwa, Allah mafi ji da gani Allah mai yadda ya so da bawansa. Wato ka ce ashe ƴar baiwa ce Safiyyar bamu sani ba" "Baiwa kuma Ranka ya daɗe, ana ga yaƙi kana ga ƙura, kaska raɓi mai jini ce fa ba wai baiwa gareta ba zama da ita jafa'i ne d... "Dakata Ibra!!! Ka san mai kake faɗa kuwa, Safiyyar kake jifa da munanan kalamai haka? Shin in banda JAHILCI da rashin imani da cewa Allah ke bayarwa kuma shi ke ƙwacewa a ce wai har ɗan adam yana iya hana alkairi ya samu mutum, ko kuma a ce yana sanya alkairin da mutum yake da shi ya rasa. Shin ina ilimin jama'a yake? Kenan idan har ɗan adam zai iya talauta wa to ina tauhidi yake? Shin ina imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau? Shin bayan faɗin ma'aikin Allah ne cewa mutum ya yi imani da Allah da mala'ikunsa da litattafansa da ranar lahira da kuma imani da ƙadddara, alkairinta da kuma sharrinta. To in har mutum ya yi imani da waɗannan abubuwan kenan ba zai zargi kowa a kan wani abu da ya same shi ba, duk abinda ya same shi zai fawwala shi ga Allah ne domin duk abinda Allah ya ba wa mutum to ko duniya za ta taru babu mai ƙwace masa haka idan Allah bai bashi ba ko duka duniya za ta taru ba za su bashi ba, saboda haka duk abinda Allah ya bayar shi ya ga dama ya bayar kuma a ko wane lokaci zai iya karɓa. Kuma da kke maganar idan ta yi kwana uku to a wata huɗu kaɗan ne babu a kwanakin da suka yi a gidan nan suna gidan nan daga ita har mahaifiyar tata kuma Alhamdulillahi arziƙinmu na ta haɓaka babu asara ko ta ƙwandala da ta same mu dan ko yanzu bayan shigarka cikin gidan nan an mini waya motocina da na yi odarsu suna nan zuwa na biliyoyi ma kuwa kuma sanin kan ka ne akwai kwangiloli da nake yi wanda kullum sai dai alkairi da samun nasara a cikinsu ba wai faɗuwa ba da a ce JAHILCIN da kuke jifan Safiyyar da shi na FARAR ƘAFA haka ne da tuni ai wata maganar ake ba wannan ba kuma ina so ka sani ko da a ce yau zamu wayi gari a gidan ƙasa da langa-langa wato mun talauce babu cin yau sai an nemo to wannan ba zai sa mu zargi Safiyya ko wani ɗan adam da haka ba dama Allah ne ya bamu kuma shi ya karɓa , dan ya bamu bai mana alkawarin za mu dawwama da arziƙin ba dan haka ka kiyaye idan ka ƙara wani furuci marar kyau a kan Safiyya wallahi!!! Sai ka gwammace kiɗa da karatu idan ku JAHILCI ya muku katutu to ni fa ilimina kuma Alhamdulillahi ina aiki da shi bar wurin nan" Annur ya kai ƙarshen maganar yana aika wa Ibra wata muguwar harara. "Haka ne, haka ne, haka ne" Shi ne kawai abinda Ibra ke maimaita wa yana tafiya cikin sanyin jiki kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki. MAMAN AFRAH😍 MAI FARAR ƘAFA (JAHILCI NE) NA MAMAN AFRAH FCW GAJERAN LABARI FREE BOOK 🔚🔚🔚 Page 1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣ Tun daga wannan dana Ibra bai ƙara gigin kai wa Annur gulmar Safiyya ba kai ko da ma abin da ya danganceta ne. Annur kuwa ya dage sosai wajen ƙoƙarin fahimtar da Safiyya soyayyar da yake mata tun tana jin kunyarsa har dai ta kai ta kawo ta fara sakin jiki da shi. Shi kuma bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen gina soyayyarsa mai tsafta haɗe da tsaya wa a rai da zuciya. Mama ta yi matuƙar yin farinciki da kasancewar Annur masoyi ga Safiyya saboda nagartarsa da kuma tsayar da ibada mutumin kirki ne da kowa yake yabonsa ko ita shaida ce a kan halaye na kirki masu nagarta da Annur ɗin yake da su mutum ne shi da kowace uwa za ta so ya kasance miji ga ɗiyarta kuma kowace mace za ta so ya kasance miji kuma uban ƴaƴa a gareta. A ɓangaren Safiyya ta yi murna sosai da bayyanar soyayyar Annur ɗin a gareta da yake nuna mata zallar ƙauna babu algus kuma ko a gaban waye. Da farko ta ji kamar bata cancanci kasancewa masoyiya a gareshi ba kasancewar bazawara wacce ta auri maza uku ta haifi ƴaƴa har uku amma kuma nuna ta isa tana da daraja da muhimmanci shi ne abu na farko da ya kawar mata fa duk wani tunani tare da rusar aƙidar da ta ɗauka na cewa ta daina yin soyayya bare har ta kai da yin aure saboda irin ƙalubalen da take fuskanta amma shigowar Annur rayuwar da kuma yadda ya nuna cewa ita ɗin daban take ita ɗin kamar kowa take ita ta musamman ce shi ne abin da ya sanya ta ji zuciyarta ta kwaɗaitu da kasancewa tare da shi bare uwa uba nasiha da jan hankali da Mama ke mata, ita da Baba Dudu hakan ya sanya ta jefar da duk makaman yaƙinta ta bada kai bori ya hau. Annur kuwa ji yake tamkar dai bai taɓa kasancewa a cikin farinciki ba sama da ranar da ya bayyana wa Safiyya soyayyarsa, rana ce da t kasance ta musamman a wajensa wacce ya saka a kuddin tarihin tayuwarsa da ba zai manta da ita ba ko da wasa. Domin rana ce da ya fitar da abinda je damun zuciyarsa tsawon lokaci wanda so ya masa kamun kazar kukun da bashi da wani buri da ya wuce ya bayyana wa abar son sa ƙaunar da yake mata bare kuma ranar da ta nuna ta amince da shi sai ya ji tamkar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha dan farinciki. Daddy kuwa sai ya ji kamar babu wanfa ya fishi jin daɗin hakan domin ya yaba da hankalin Safiyya kuma tun kan ya san Annur ɗin yana son Safiyyar ya masa sha'awar aurenta sai dai kasancewar ƴaƴan zamani kar ya masa tayin hakan ya watsa masa ƙasa a ido shi ya sa ya ƙyale shi yanzu kuma da ya bayyana sai ya ji ya yi frinciki kasancewar yana ganin nagartar Safiyya yayaba da hankali da tunaninta dan ba kamar sauran mata take ba gashi dai yarinya ce mai ƙananan shekaru amma kuma hankali da tunaninta na manya ne. *RABI'U* Tun bayan da ya saki Safiyya yake zaton zai samu hauhawar arziƙinsa da bunƙasar kasuwancinsa sai dai abin ya ci tura dan yana ganin kamar ya jefar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda ashe abin ba haka bane. Dan bayan rabuwarsu sai da komai nasa ya ƙare wasa-wasa sai ga shi hatta ƙananan abubuwa suna neman gaggararsa shi da yake da yara a shagonsa har ta kai ta kawo ya dawo shi ne yaron shagon, daga baya ma sai komai ya ɓalɓalce masa dan hatta kayan ɗakin Safiyya da yake ikirarin idan za a zo kwasar su kar a zo da ita sai gashi ko ɗaukan kayan babu wanda ya zo har ya siyar da kayan ɗakin da tufafinta ya ja jari da su dan ya samu labarin an ce tun daga ranar da ya sake ta ubanta ya koresu daga gidansa ita da uwarta. Hakan ya sanya ya ƙara ji a ransa dai dai ya yi da ya sake ta tun da ga shi uban da ya haifeta ma ya gujeta. Wani ɗan wuri ya samu ya haɗa rumfa a umguwarsu yana siyar d kayan miya su tumatur tattasai albasa da sauransu yana ji yana gani duniya ta juya masa baya lokaci ƙanƙani arziƙi ya koma talauci. Tun yana ganin sakin Safiyya mafita ce har ya dawo yana da na sanin sakinta dan wata bazawara da ya aura sai dai ya gwammace kiɗa d karatu ga rainuwar tsiya komai ya mata bata godewa saɓanin Safiyya mace mai haƙuri da kawar da kai, duk abin da kaa bata sai dai ta karɓa ta yi godiya da addu'ar samun buɗi kuma ba za ta taɓa cewa abin bai mata ba ko kuma ba zai ishe ta ba sai ga shi ya yi gamo da dai dai da shi wata rana ko magana yake idan tana masa jaraba kamar uwarsa ko ta ding nuna masa yatsa wataran har tsone masa ido take idan tana masa faɗa. Da na sani dai duj da ƙeya ce amma RABI'U ya yi ta tafi cikin carbi dan yana ganin samunsa da yake raguwa kamar daga gareta ne ai gashi Allah ya nuna masa ishara da bata nan ma talaucin ya fi baibayeshi har ta kai da zuwa kasuwa ya gagareshi ya dawo siyar da kayan miya. *MALAM SADIQ* Bayan korar su Mama daga gidansa ko sau ɗaya bai taɓa yin nadama ba, dan yana ganin abinda ya yi shi ne dai dai musamman ma da mutanen unguwa suke nuna masa ko waye ma hukuncin da zai yanke kenan har da masu cewa ai ita Mamar ita ta ga za ta iya tun da ta zaɓi bin ƴarta a kan zaman aure da yake ibada. Ko da wasa bai taɓa neman inda suke ba dan sai karensu suke ci ba babbaka shi da Umma. Kafin daga baya wata ƙaddara da suka rasa mafarinta ta fara afka musu dan duka ƴaƴan Umma mazajensu suka sake su suka dawo gidan banda bala,in faɗa babu abin da suke a tsakaninsu iyayen basu isa su tsawatar musu ba sai su dinga nuna wa kansu ɗaya da su, ga masifaffa yawon jaraba dan dama ba tarbiya ce da su ba ga babu ilimin addini abin sai ya taru ya musu yawa wai shege da hauka. Sanadin abubuwan da ƴaƴan Umma suke hawan jini ya fara yi wa Malam Sadiq dirar mikiya, jinya ba ya iya zuwa ko nan da can haka Umma ta barbaɗawa idanunta toka ta ringa gallaza masa ba sa taimakonsa daga ita har ɗiyant idan suka fice yawonsu suka kawo kuɗinsu sai su ba Umma su hana Baba abu ya tare masa goma da gomiya har ta kai ya dawo yana da na sani a kan abinda ya yi wa su Mama dan ya lura abinda ke faruwa da shi ba ya rasa nasaba da alhakinsu. Dan akwai wani lokaci yana kwance a ɗakinsa aka masa sallama ya bada izini ashe Salisu ne tsohon mijin Safiyya na biyu ya zo ya bashi haƙuri a kan ya aura masa Safiyya dan ya gane kurensa na JAHILTAR abubuwan da suke samunsa ya danganta su da ita sai yanzu ya gane gaskiya na Malam Sadiq ɗin ya fashe da kuka yana bashi labarin abinda ya faru ya faɗa masa a halin da ake ciki yanzu shi ma neman Safiyyar yake ruwa a jallo. Haka Salisu ya tafi cikin ƙunar rai yana jin son Safiyya na dawowa sabo dal a zuciyarsa yana ji da a ce yau zai ganta ya mayar da ita ɗakinsa to da ya fi kowane namiji sa'a a rayuwa. Bayan tafiyarsa da sati biyu Sani ma ya zo wajen Malam Sadiq bada haƙuri da neman bikon Safiyya dan ya samu labarin an ce aurenta ya mutu shi ma nan Malam Sadiq ɗin ya rattaba masa bayanin bai ma san inda Safiyyar take ba dan ya koreta a kan FARAR ƘAFAR d ake cewa tana da ita. Haka ya tafi yana addu'ar Allah ya bayyana Safiyyar ya mayar da ita ɗakinsa su yi zaman soyayya tare da rungumar ɗan da suka haifa wanda suka hana ta riƙe ɗan gudun kar ya raɓeta ya gogi annobar FARAR ƘAFA. *Mama* Abinda Daddy ya sanar da ita ne ya ɗaure mata kai, ta shiga tunani jin Daddy ya zo wajenta da ƙoƙon bararsa na soyayyarta tare da neman amincewarta a kan ta yarda ta aure shi. Ta yi mamaki tare da jin abin wani banbarakwai musamman da ya kasance Safiyya na soyayya da Annur har ana shirin yin aure. Safiyya kuwa murna take Mamarta ta samu nagartaccen miji wanda take ganin mahaifinta bai kai shi a komai ba, amma ba komai na dukiya ba ita tafi kwaɗayin halayyarsa dan dama maganar dukiya ma babu ita dan kuwa ba za ma a haɗa ba. *BAYAN WATA BIYU* A rana ɗaya aka ɗaura auren Mama da Dady Annur da Safiyya. Auren da ya zama sanadin wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan SARKIN SHANU auren da ya mantar da Daddy rashin mahaifiyar Annur da ke addabar zuciyarsa a kullum domin ya samu mace ta gari wacce take masa abu kwantankwacin wanda mahaifiyar Annur take masa wacce take bashi kulawa tamkar jaririn da aka haifa a daren yau! A gida ɗaya suke rayuwa kowa yana ɓangarensa da ban dan Daddy ya ce ba ya son su Annur su yi nisa da shi. Daddy Safiyya ce tashi Mama kuma Annur ne nata kowa da wanda ke masa ɓaci. A haka har aka wayi gari da ɓullewar ciki a jikin Safiyya wanda ta ga gata da kulawa daga wajen Daddy Annur kuwa tamkar ya goyata a haka ta haifi ɗiyarta mace wacce aka saka mata sunan Mahifiyar Annur Fatima suna kiranta da Timo. Wata rana Daddy da Annur suka ce Mama da Safiyya su shirya domin zuwa wani waje haka suka shirya Mama ta ɗauki Fatima suna baya ita da Daddy Annur da Safiyya a gaba Annur yana jan motar Safiyya sai murna take wata unguwa suka ga an nufa da su wani gida madaidaici a nan suka sauka suna shiga gidan suka tarar da Mahaifin Safiyya Malam Sadiq kwance ba lafiya yana ganinsu ya fara kuka yana neman yafiyarsu Mama da sanin babu abinda ya haɗa ta da shi tun da auren wani take yi yanzu dan haka ta ce dama bata riƙe shi ba Safiyya kuka take tana cewa ta yafe masa. Ashe Annur ne ya siya masa gidan da yake ciki ya ɗauki wani saurayi yake kula da shi dan Umma da ƴaƴanta sun guje shi dan Umma har sai da ta sanya ya sake ta ta bar shi da jinyar da suka yi silar samuwarta a jikinsa ita da ƴaƴanta. Tun daga wannan rana Safiyya kan zuwa ta gaishe da mahaifinta, ta kai masa abin arziƙi Daddy ya biya aka kai shi asibiti cikin ikon Allah ya samu lafiya yanzu bashi da wani abu da yake alfahri da shi sama da ƴarsa Safiyya wacce ya wulaƙanta a baya ya koreta gata yanzu ta zame masa sanyin idaniya. Malam Sadiq har malamin sunna ya sanya ya yi wa,azi a game da JAHILCIN da mutane suke na jifan wasu da masu FARAR ƘAFA Alhamdulillahi kuma saƙo ya je inda ake buƙatar zuwansa domin kuwa mutane sun falka daga duhun JAHILCIN da suka yi nutso a ciki sun gane cewar komai Allah ne yake bayarwa kuma shi yake ƙwacewa a duk lokacin da ya so babu wani ɗan adam da FARAR ƘAFAR sa za ta yi sanadiyyar rugujewar katangar samun mutum. Ibra yanzu an fahimta an daina gulma da tsegumin MAI FARAR ƘAFA dama komai ta yi farko yana da ƙarshe. Tafe suke a mota su biyu ne a ciki Annur yana gefe inda Safiyya take jan motar dan shi da kansa ya koya mata har ta iya ita kuma da ta iya in za su fita tare sai ta ce ita za ta tuƙa su. Duk da ita ma tana da mota yanzu ga kasuwanci da take wanda Annur ya bata jari mai kauri take yi. Daddy kuma ya biya musu aikin Hajj su duka suka je bayan ta yaye Fatima. Suna cikin tafiya ta ga wurin da suke siyar da goba (Guiva) Irin manyan nan. "Sweet hearta kanga irin gobar da na ce ja siyo min jiya amma ka siyo mini wannan nunanniyar ni na fi son wanda basu nuna ba"Ta ƙare maganar tana wani zumɓuro baki. "Takawarki lafiya Annurin zuciyata, yo ni in ma cewa kika yi in nemo bishiyar gobar ai sai inda ƙarfina ya ƙare, mu tsaya mu fita ki zaɓi irin wacce kike so da kan ki dan na fara fuskantar dab kije da yi wa Timo ƙani ko ƙanwa" Ya faɗa yana kanne mata ido ɗaya murmushi ta yi bata ce komai ba dan ita ma tana zargin ciki ne da ita. A dai dai wajen ta yi parking kafin ta buɗe ƙofar har ya fito daga cikin motar ya zagayo ya buɗe mata yana jiran fitowarta, kallonsa kawai ta yi tare da yin murmushi ta sako ƙafafunta ta fito suna yi wa juna murmushin so da ƙaunar juna. Rabi'u da ke zaune daga can gefen mai siyar da goba yana gyaran takalmi domin yanzu shoe shainer ne. Tun da motar ta tsaya ya ji tamkar dai akwai wani abu nasa a cikin motar hakan ya sanya ya dakata daga gyara takalminda yake yi wa wani saurayi d ya kaɗe mas hankali sai sanabe yake masa a kan irin gyara da wankin takalmin da yake so ya masa. Idanunsa suka sauka a kan Annur da ya fito ya kewaya yana shirin cigaba da gyaransa ya ga ya buɗewa wata mace kyakkyawa ƙofa wacce yanayin farin fatarta da irin hutun da jikinta ya nuna tana samu ya yi zaton ko balarabiya ce. Amma kuma ƙayataccen murmushin da ya ga tana jifan wanda ya buɗe mata motar shi ya ankarar d shi Safiyyarsa ce. Da hanzari ya yi jifa da takalmin hanunnsa ba shiri ya miƙe tsaye ya nufi wajensu hankali tashe dan har hawaye sun fara zarya a fuskarsa ganin yadda Safiyyar ta ɗaukaka shi kuma ya ƙasƙanta hakan ya nuna masa halih rayuwa da kuma fawwala komai ga Allah domin kuwa ga shi ya gujeta saboda gudun talauci amma kuma bai tsira ba saboda haka Allah yake son ganinsa kuma lokacin karayar arziƙinsa ya yi hakan ya sa bashi da tsumi bashi da dibarar tserewa ƙaddarar da ta tunkaro shi. Safiyya da suke tsaye gaban mai goba hannunsu cikin na juna kallo ɗaya za ka musu su baka sha'awa domin dacewar da suka yi da juna. Kawai sai ganin mutum suka yi a gabansu tamkar an jefo shi. "Safiyya dama kina raye? Ina ta fafutukar nemanki har gidanku na je amma mahaifinki ya sheda mini bai san inda kike ba dan Allah ki yi haƙuri ki dawo mu cigaba da rayuwarmu Safiyya na yi nadamar sakin ki yanzu ina matuƙar sonki da... "Dakata Malam! Ka adana kalamanka wataƙila idan ka je wani wajen za su maka amfani wannan matar aure ce tana tare da mijinta idan ka zauce ne ka dawo hankalinka" Cewar Annur yana mau shiga tsakanin Rabi'un da Safiyya dan gadan-gadan ya tunkareta. Baki sake Rabi'u ke kallonsa dan shi duk tunaninsa ma Safiyyar yawon banza take domin ganin yanayin shigarta ya nuna tana samun kuɗi hakan ya sanya ya ɗauka ko daduronta ne Annur ɗin dan bai taɓa tunanin ko a mafarki za ta samu miji kamar wannan ba bare har ta samu kulawa kamar wata sarauniya mijin ma wani yaro ɗanye sharaf da gani ya san saurayi ne duk da dai zai fi Safiyyar a haife. "Tabbas ni matar aure ce kuma da mijina nake tare, sannan idan maye ya ci ya manta uwar ɗa ba z ta manta ba, shin ka manta saki ɗai-ɗai har uku ka mini, babu kome tsakaninmu to wallahi ko da akwai kome kuma bani da aure ba zan koma gidanka ba, bare wani hanin ga Allah baiwa ne dan ni yanzu wallahi wutsiyar taƙumi ta yi nesa da ƙasa" Safiyya ta faɗa tana karɓar ledar gobar bayan Annur ya miƙa kuɗin ko canjin basu karɓa ba suka juya hannunsu cikin na juna dan Annur har da riƙo ƙugunta suka je ya buɗe mata ta shiga ya shiga tana shirin tada motar sai ga Rabi'u kamar an jefo shi ya zo yana kuka wiwi wai ta daure ta kashe auren ta dawo gidansa wani kallon raini ta watsa masa ta tada motar ta tada ƙura ta bar wajen a 360 Saurayin da Rabi'u je yi wa gyaran takalmi ne ya biyo shi yana cewa ya zo ya ƙarasa masa gyaran amma Rabi'u ko kallonsa bai yi ba ya juya ba tare da ya ɗau kayan gyaran takalmin ba ya nufi gida, yana jin ɗaci da kishin Annur a zuciyarsa ya gwammace ya je gida matarsa in tsikareshi ma za ta yi ta tsikareshi da bala'in da yake jinsa a ciki yana ta mamaki dan bai taɓa zaton akwai ranar da za ta zo ba shi da kansa ya nemi Safiyya ya rasa ba! Dama ai ɗan hakin da ka raina shi ke tsone maka ido. BAYAN SHEKARA BIYAR Yanzu Safiyya yaranta uku biyu mata ɗaya na miji, Fatima ce babba sai na miji Abubakar wanda ya ci sunan mahaifinta suna kiranshi da Sadiq sai kuma ƙaramar Munawwara. Soyayya suke nuna wa juna tamkar su haɗiye junansu basu da wata damuwa ko matsala sai dai wacce ba a rasa ba dama zaman aure ɗan haƙuri ne. Alhamdulillah a nan na kawo ƙarshen littafin MAI FARAR ƘAFA wanda na yi shi dan faɗakarwa da ake jifan wasu matan da masu FARAR ƘAFA ina fatan saƙon ya isa ga wanda suje aikata hakan ya kuma zama silar gyara halinsu ina roƙon Allah haɗa mu a ladan kuskuren cikinsa ya yafe mini👏🏻 Ina miƙa ɗimbin godiya ga masoyana a duk inda suke ina ƙaunarku irin sosai ɗin nan😍❤️🚶🏻‍♀ Sai kun sake jina a sabon littafina mai cike da barkwanci mai suna ƘARA'IN INNA DELU wanda zai nishaɗantar da ku kamar littafina YAR ZAMAN WANKA. NA GODE MAMAN AFRAH😍🚶🏻‍♀️ Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels