Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels  🌹🌹*ASHE ZAMUGA JUNA*🌹🌹 *_ story $ written _* By * _ MRS 🌹 ISHAM 🌹_* *The writer of* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* *YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT* *Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.* Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰. Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃. Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖 Kuma akwai naku .🤩🤩 1,. Snow Whitening Soap 2,. Snow Whitening Oil 3,. Glowing Oil 4,.Whitening Face cream 5. Pure whitening scrubs 6,. Lightening Dilka Soap 7,. Anti-dandruff Hair Oil 8,. Shampoo Deep Comfortable Deep Cleaning 9,. Maganin infection da na Sanyi 10,. Ruwan matsi 11,. Gunmban Dabino da Madara, Gunmban Kwakwa da Madara 12,. Tabajen Zo Mubaje 13,. Tsumin Tabani ka Ji Ruwa 14,. Sweetener powder 15,. Kamshi Khumar 16,. Kamshi Oils 17,. Pure Shea Butter and pure Alaidi Oil And More Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯. *YAR GIDAN TAFIDA* Tana da alaidi Akwai pure man kadai Akwai gumba ta madara da kwakwa Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍. *Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects. Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯 *Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum masoyana, masoyan NIDA PATIENT DINA Allah yabani ikon sake rubuto sabon littafina , ya Allah ina rokonka yanda kabani damar farawa lafiya kabani damar gamawa da lafiya* *Ina fatan kamar yanda kuka bani hadin kai a NIDA PATIENT DINA fatan zaku bani hadin kai a wannan sabon book din domin comments dinku shine babban karfin guiwa na , Allah yabar zumunci ,inayinku over 😘* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ____~THE BEGINNING~_____ Page__01 BORNO MAIDUGURI. *Damboa road* Babban anguwa ne acikin Maiduguri inda yatara manyan gidajen hamshaƙan masu kuɗi da kuma yan siyasa, daga kanuri,shuwa,da kuma hausa fulani , da turawa , duk suna rayuwarsu acikin anguwar, kasancewar babbar anguwa ne yasa yake da manyan gate din rufewa ga kuma masu gadi da jami'an tsaro tundaga farkon anguwar har izuwa karshe saboda tsaro banda tsoro ba, wani hadadden gidane mai matukar girman gaske wanda kaff cikin anguwar nan babu gidan da yakaishi kyau da girma hade da tsaruwa tundaga mansion din ma abin kallo balle ace mutum ya shiga cikin gidan ,awajen gidan akwai manya_manyan sojoji dakuma polisawa suna tsaron gidan da ko a kasar waje se shahararrun masu kuɗi ne da masu muƙami zasu iya mallakar gidan nan , abakin gate din akwai katon sign bod na karfe an rubuta *BISHARA's FAMILY* duk wanda yaji wannan sunan to yasan sunan shuwa arab ne ______acikin bishara's house kuwa kyawawan yara ne mata suna wasa,gabaki dayansu sunada matukar kyau kuma suna shigen kama da junansu haka yasake tabbatarwa da duk yan ahali dayane, wasan boji_boji sukeyi yara matan du ka bazasu wuce shekara biyar zuwa shidda ba , se ƴayyun su maza da suke yan matasa manyan cikinsu sukuma suna suna buga table tennis sauran kuma wa'yanda suka girmesu suna can gefe suna zaune suna kallonsu suna wasa, wasa sukeyi a babban wajan spot dake gidan sauran kuma wa'yanda suka ɗarasu girma kuma suna zaune agefe jikinsu sanye da jessi alamun ball suka gama suna zaune suna kallon yan kannen nasu suna wasa. _____ Abbas ne ya kai kallonshi bakin kofar wajan spot din tsaye yaganta tana kallonsu hannunta rike da teddy pink color, fuskanta ashagwabe se karewa yan uwanta kallo take kamar akwai wanda take nema , farace sol skin dinta har wani glowing yakeyi tsabar hutu kanta nadauke da yalwataccen gashi baki wuluƙ an mata kitso kwalli daya se shining yakeyi ga kwantaccen sajen dake kwance agaban goshinta ya kwanta luf_luf , fuskanta na dauke da manyan idanu farare sol cikinsu kuwa tabb yake da ruwan hawaye amma fa ba hawaye bane se wanda yalura dakyau zegane hakan irinsu ne ake ce musu masu oily eyes, hancinta dogo bakinta dan karami pink dashi tanada dimple aduka kumatun nata jikinta nasanye da riga da ya tsaya mata adede guiwanta ƙafarta sanye da takalmi me matukar kyau yarinya ce karama yar shekara shidda, kyakkyawa ce kyanta yawuce misali , tana tsaye abakin wajan se wur_wurga manyan oily eyes dinta takeyi ko zata ganshi amma kaff wajan babu shi babu alamar shi. Yar murmushi Abbas yayi yataba sauran yan uwanshi yana musu alama da ido suma maida kallonsu kanta sukayi wani kyakkyawan saurayine acikinsu wanda kansu daya da Abbas din kuma suna mugun kama ya ce " Abbas amma kai aganinka wa take nema haka" Abbas ya ce " Ahmed wa kuwa take nema da yawuce TAJUDDIN, inkaga ASRAH ta sake tana wasa da yan uwanta to TAJUDDIN yana wajen " dariya sukayi Ahmed ya ce" gaskiya ASRAH akwai rigima, ga shi wai yar karama da ita ta iya rashin kunya da neman tsokana ko dayake ba'a Nigeria aka haifeta ba kuma tunda aka haifetan basu dawo Nigeria ba se sati biyu nan da suka wuce duk yarinyar an sangartata zamansu uncle hameed da anty amarya a California yanzu yafi shekara bakwai fa tun kafin a samu cikinta " " ni kuma kunsan meyake bani mamaki kuwa ? Wallahi yanda TAJUDDIN yake matukar santa ne abin yake ban mamaki yaron da mugun miskilanci yamishi ƙatutu dashi da kurma basu da maraba ga uban zafin zuciya da girman kai tun yana karami dashi duka_duka fa TAJUDDIN baze wuce shekara sha bakwai ba amma baya kallon kowa da gashi ko mu nan bamu isheshi kallo ba balle sauran yan uwanshi mata amma duk inda ka ji muryan Taj yana magana tofa shida Asrah ne duk gidan nan ita kadai yakeyiwa magana na tsawon wasu mintuna tsabar son da yake mata " cewar Haris da shima duk sa'an su Abbas da Ahmad din ne , cire rigar jessi jikinshi Abbas yayi yana cewa " karkayi mamaki Haris karku manta fa tunda anty amarya tasamu cikin Asrah duk sanda ammi ko hajjatiye inzasu je California tare suke zuwa, Taj yana matukar son cikin anty amarya yana kula da ita, kullum maganar shi daya shine inde mace ta haifa shize aureta, shisa duk zafin kanshi da miskilanci tofa bayayiwa Asrah haka itama duk rashin kunyarta batayi mishi, Allah de yakaimu lokacin da zasuyi aure bakaramin murna zanyi ba " haka suka dinga hira kafin Haris yatashi yaje gaban Asrah ya ce" Asrah wakike nema kuma gacan su Umaisha suna wasa bakije kunyi tare ba " cuno baƙi tayi da muryanta siriri wanda Hausa be ishesa ba ta ce" ya Haris ina tajujuna? i couldn't find him " dariya Haris yasa jin yanda take kiran sunan Tajuddin din wai tajuju tsagaitawa yayi ya ce " kishigo ki zauna tajujun ki na zuwa maybe yana wani abu ne " maƙe kafada tayi ta ce " bazaje din ba se yazo tukun " lallaminta yayi yasamu ta biyoshi suka shiga ciki zama tayi akujeran kusa dasu kafin ta kalli Abbas ta ce " yaya did you perhaps saw my tajuju?" yana kunshe dariyar da yakeson kuɓuce mishi ya ce" noo i didn't " tundaga nan fuskanta yasake komawa irin na tausayi. Sauran matan dake wasan boji_boji suna ganinta suka rugo da gudu wajan da take zaune su biyar suna haki dayar ta ce" Asrah let's go and play " " no Umaisha am not going anywhere until tajuju come " cewar Asrah, rike hannunta Iklas tayi ta ce" zezo ai to muje muyi wasa Please Asrah " dukkansu haka suka dinga roƙonta shuru Asrah tayi musu tana rungume da teddy dinta ,sude su Abbas zuba musu ido sukayi dan sunsan Asrah akwai taurin kai inta nace akan abu tofa zeyi wahala tacanza. Saghar dake nesa dasu suna buga table tennis shida su salim da Sahil ya hangi abinda yake faruwa tsuke fuska yayi shidama rashin kunyar da Asrah takeyi agidan ya isheshi har wani tsayawa sukayi suna roƙonta suzo suyi wasa amma tana ja musu rai karasowa yayi wajen nasu afusace daka mata tsawa yayi ya ce " nikam Asrah ke wani irin shegen taurin kai ne dake har sister's dinki zasu zo suna roƙonki amma kinƙi tashi kuje kuyi wasa ! get up idiot tashi ki wuce kije kuyi wasa " yafada yana rike hannunta Abbas ne ya ce " haba saghar kadena mata shouting kabita a hankali yarinya ce fa" ko gama rufe baƙi Abbas beyi ba sukaji Asrah ta bude baki ta fashe da wani gigitaccen kuka kamar wacce akayiwa mugun duka duk tsayawa sukayi suna kallonta cike da mamaki tsabar yanda take kuka har jikinta rawa yakeyi , da karfi tana kuka tana " my tajuju kazo suna dukana " kama baƙi sukayi jin sharrin datayi musu wanda yamata tsawa daban kuma bama dukanta yayi ba he just yelled at her. Daga bayansu sukaji daddadar muryanshi yana fadin " come here my Asrah waye ya taɓamunke?" duk juyawa sukayi suna kallonshi , dan matashin saurayi kyakyawa ajin farko fuskanshi a turnuke daga gani ranshi amatukar ɓace yake yana sanye da wandon sojaji three quarter se baƙar riga kanshi na sanye da facing cap . Asrah najin muryanshi taraba ta tsakiyarsu taje da gudu ta rungumeshi tana sheshekar kuka. gaba dayansu seda sukasha jinin jikinsu banda Abbas da Ahmad da Haris ,amma daga kan su Umaisha,Iklas, zoya ,parsa,rameesa, saghar,salim,Sahil,sudais , kallonsu yayi da rikitattun idanunshi murya adaƙile yana shafa bayan ya ce " Asrah waya taɓaki acikinsu " yayi maganar yana dagota ajikinshi kallonsu itama tayi kafin tafara nunasu da ɗan yatsanta ta ce " all of them dukansu sun zageni kuma sun dakeni" a kausashe ya ce " na rantse da Allah duk wanda ya sake sa hannunshi ajikinta da sunan duka kokuma yi mata tsawa ko faɗa ze hadu da fushi na " yana gama fadin haka yadauketa yadaurata akan wuyanshi suka bar wajan spot din, sude da kallon mamaki kawai sukabi bayansu saghar kamar zeyi kuka ya ce " Allah sena kama Asrah nayi mata ɗan banzan duka sede Tajuddin ya kasheni " ya karishe maganar hawaye Tabb a idonshi, girgiza kai Haris yayi ya ce" karufawa kanka asiri dan kasan halin Taj zakajane yamaka duka inde akan Asrah ne , sede kuyita hakuri da ita harta saba da halin nan tunda kunga ai ba anan ta tashi ba kuma karamace " kwafa saghar yayi yabar wajan sudais yabi bayanshi duk watsewa sukayi suka shiga cikin mansion din. Yana dauke da ita akan wuyanshi tanata dariya suka shiga cikin tamtsamemen mansion ne na gani na faɗa komai na ciki anzuba dukiya kamar ba'a so , tundaga kan kayan furniture har izuwa kayan alatun dasuke falon duk yan kasar waje ne saboda irin kyaun su da tsarin su kai daga gani ma base an fada ba kasan cewa wannan babban gidan alfarma ne ganin yanda dukiya ke kuka , ga manyan kujeru masu numfashi da ɗaukan hankali. Cikin ƙatuwar haɗeɗɗiyar falon na dauke da stairs matakalar bene kusan fiye da goma inda duk wanda kahau ze sada ka da part din wani ,shi kanshi matakalar benen abin kallo ne saboda yanayin design dinshi, in har nace zan tsaya fada muku irin kyan da gidan yake dashi tofa ko one page baze dauka ba kude ku ƙiyasta kawai . Kamar bega kowa a falon ba yanufi part dinshi shida Asrah duk maida kallonsu sukayi kansu. Uncle Hameed ne ya ce " Taj ba magana ne ?" Kallonsu Taj yayi batare da yace komai ba yahaura upstairs yanufi part dishi kamar bega Abbu da Abbie da kuma uncle Hameed dasuke zaune afalon suna mishi magana ba. Girgiza kai Abbie yayi ya ce " Hameed bansan yazanyi da Tajuddin ba gabaki daya shi fa rayuwarshi a murde yake yaro tun be tafasa ba haryafara konewa ? ni agaskiya nafara canza shawara akan samo mishi addimission a U.S military academy at west ,saboda Tajuddin be zama soja bama ya muka ƙare dashi balle kuma idan yazama sojan ƙasa da ƙasa bana tunanin wannan shawara ce me kyau " Abbie ya ya karishe maganarsa da damuwa akan fuskarshi. Abbu da uncle Hameed sukansu lamarin Tajuddin na damunsu domin Taj mutum ne da inzaku zauna tsawon shekara ɗari tofa seyayi ra'ayin maka magana kafin yayi ,ba koda yaushe bane yake magana ba. Abbu ya fuskanci ya'yan nashi wato Abbie ya ce " ya Mubarak ni aganina canza shawara akan makarantar dazeje bashida fa'ida tunda ka san wannan shine babban burinshi yanason yazama soja wannan shine mafarkinshi kuma dukkanmu munsani , to ruguza mishi mafarkinshi kuma dede yake da ruguza mishi rayuwarshi , muda muke neman hanyar da zamu dinga faranta mishi ko Allah zesa yadawo mutum kamar kowa yadinga walwala wallahi tun marigayi baba Allah yajikanshi ,nadade banga mutum irin Tajuddin ba amma gado yayi agun baba" Yawwa muddin kunaso muci gaba da tafiya yanda Yakamata shine nadinga ganin comments dinku hakan ne ze tabbatar min da kuna biye dani 😒😒😒😒. 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ Page 02 _______ " abinda kafada hakane kam ya Ismail saboda hanashi yin abinda yakeso zesa murɗeɗen halinshi sake ninkuwa fiye dana da,kaga garin neman gira kuma an rasa ido "cewar uncle Hameed jinjina kai Abbie ya yi dan ya gamsu da maganan ƙannen nashi , amma shi a har kullum burinshi yaga ɗan shi yadawo kamar kowa , but lamarin Taj kullum gaba_gaba yakeyi du ka nawa yake amma tun bekai haka ba shi kadai yatara zafin zuciya, miskilanci,rashin damuwa da damuwar kowa, karfi ga kuma tsastsauran ra'ayi da murdeden hali , kamar ba'a gidan yake rayuwa ba. Haka suka dinga tattaunawa akan Taj da bemasan sunayi ba yana can a part dinshi shida Asrah suna painting room domin kuwa Tajuddin da Asrah Allah ya yi musu baiwar drawing wato (zane) duk sanda suka shigo painting room shida Asrah tofa kafin su fita Asrah seta zana hotonshi fiye da goma. __________ yanzu ma kamar yanda ta saba tana zaune agaban painting board hannunta rike da pencil ta tsurawa Tajuddin ido tana kallonshi tana zana shi , shikuwa yana drawing din ɗawisu duk kallonshi da takeyi yana sane da ita kuma yasan shi take zana wa ɗan inde yashigo da ita nan tofa shine abin zanawarta setayi fiye da goma. Gama zanen ta yi, ta dauko papper da ta yi ta nufeshi tace " tajujuna kalla kagani yayi kyau?" sa hannu yayi yakarba yaci karo da kyakkyawar fuskarshi ga facing cap din dake kanshi ya ce " ehhh not bad yayi kyau" murna tafara yi harda tsalle leƙa kanta tayi tana son ganin meyake zanawa , ganin ta zuro kanta ne yasa ya juyar da kanshi gefe da kuma paint board din yaci gaba da zanenshi zama tayi akan kujera tana kallon nata drawing din,bayan wasu mintuna yazaro papper batare da yace mata komai ba ya miƙa mata, sa hannu tayi ta karba ta kalli zanen dakyau ita ce ya zana tana zaune acikin garden ga ɗawisu zagaye da ita hannunta kuma na rike da dan karamin yaron zomo, da iya karfinta ta saka ihu me karfin gaske wanda seda yasa part din nashi dauka, du ka hannunshi biyu yasa ya toshe kunnuwanshi yana runtse idanunshi domin ihun datayi seda yaji gaba daya ilahirin kanshi yadauka nan take yaji ciwon kai , itakuwa Asrah duk farin ciki ne yasata haka ganin irin kyaun din datayi gata ga dan jaririn zomonta datake mugun so shisa ta daukoshi tundaga California. baƙinta dake dauke da kananan hakwara da wasu sunfita tafara fanfara ta budesu se dariya takeyi tana tsalle sannan ta rungumeshi daga kanta tayi ta kalleshi ta ce " my tajuju what's that me ?" ka sa ce mata komai yayi ɗan har lokacin kanshin na damunshi girgiza mata kai kawai yayi . Bude kofar bedroom din Tajuddin tayi ta shigo hankalinta atashe gaba da ta firgice,kai kallo daya zaka mata kasan eh tabbas ita ce ta haifi Asrah saboda suna kama sosai, ga wata hamshakiyar mata kyakyawa abayanta fuskanta manne da medicated glass fari , matar na kama sosai da ita mahaifiyar Asrah sede ta girmeta , ganin Asrah da Tajuddin din basa bedroom dasauri suka nufi painting room din Taj , tana bude kofar painting room din hankalin Asrah dake rungume ajikin Taj yadawo kansu taje wajansu ɗan nuna musu zanen da Taj yamata ɗagata sama anty amarya tayi tana kallonta ganin babu abinda yasameta hasalima farin ciki takeyi hankalinta akwance.mamaki ne yakama anty amarya da Ammi ganin babu abinda ya sami Asrah din sauketa ƙasa anty amarya ta yi ta durgusa agabanta ta ce " my baby girl meyasameki mukaji ihunki " da fa anty amarya Asrah tayi tace " mom there's nothing wrong with me my tajuju ne yayi drawing dina am so happy and excited" tafada cike da yarinta tana nuna musu zanen ,dafe goshi Ammi tayi anty amarya kuma tasaki baƙi tana kallon yar tata, duk sun ƙasa magana jin abinda Asrah ta faɗa musu wai saboda kawai anyi drawing dinta ne yasata wannan ihun da ya matukar daga musu hankali duk sunyi zaton mugun abune yasameta shisa cikin gaggawa suka nufo part din Taj din amma with their surprise babu abinda yasameta sema samunta dasukayi tana farin ciki da nishadi , sake jinjina ƙiriniya dakuma sangarcewar Asrah sukayi , girgiza kai kawai sukayi Ammi dakyar tasamu bakin cewa " Asrah you're unbelievable yanzu just because akan zane yasa kike wannan ihun " ta tambayeta tana karasowa kusa dasu gyada mata kai Asrah tayi ta ce " yes Ammi my tajuju made it for me" satan kallon Tajuddin Ammi tayi ta kasan ido dake zaune abakin gado yana danna wayarsa kamar besan da ruwan alamarsu a dakin ba ɗan ko kallon inda sukema beyi ba tun shigowarsu, yar murmushi anty amarya ta yi ta ce " Allah ya shirya min ke " kafin tasa hannu ta dauketa taname mayarda kallonta kan Tajuddin " Taj ina cikin yi maka favorite dinka kawai naji ihun wannan sarkin rigimar zakazo kaci ne ko in kawo maka shi!? koɗe in bawa Ammin ka zakazo kaci a part dinta ?" ta fadi hakan tanameson jin abinda zece zuciyarta a karye , Ammi ka war da kanta gefe tayi kamar batasan akanme suke magana ba . Dakatawa da danna wayar da Tajuddin yakeyi ya yi ya dago ahankali da shanyayyun idanunshi da se yanzu ne cikinsu suka samu damar fitowa saboda maida facing cap din kanshi baya dayayi manyan idanunshi da eyeballs din suka kasance golden color ne yasaukesu akan anty amarya yafi tsawon minti biyu yana kallonta batare da yace wani abu ba sema lumshe idon da ya yi kafin da narƙekkiyar muryanshi ya ce " anty amarya koda danni kika dafa bazanci ba ki dauka kibawa yar uwarki kawai , and please zaki iya ce mata tafita min a part dina" wannan kalmar da Tajuddin yayi bakaramin girgiza zuciyar anty amarya yayi ba jin yanda Tajuddin yake furta magana kamar Ammi ba ita ce ta haifeshi ba , dukda ba wannan ce rana ta farko ba kuma irin wa'yannan kalaman sun saba dajinsa abakin Tajuddin amma hakan be mata dadi ba, ammi kam dakyar ta iya danne kuncin zuciyarta tafice tabar musu part din bin bayanta Asrah tayi tana " Ammi ki daukeni " tsayawa tayi ta dauki Asrah din suka fice a part din nashi . Zama kusa dashi anty amarya tayi kamar yanda ta saba ta kalleshi dakyau ta bude baki zatayi magana kenan ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yana " Please anty amarya not again na gaji da jin wa'yannan kalaman naki akan yar uwarki bana bukatar ji " ajiyar zuciya anty amarya tasauke sannan tace " Taj dole sena fada maka gaskiya abinda kakeyi sam be dace ba duk abinda yahaɗaka da Ammi karka manta fa ita ce ta haife ka ko bakomai taci darajan mahaifiya domin ita ce sanadiyyar zuwanka duniya! wallahi Ammi na sanka dan Allah kamanta da komai kadena daurawa kanka damuwa tun kana ɗan karamin ka dakai Please my Taj " tunda tafara magana yake gyada kai kamar wanda yayi na'am da maganar nata jin tayi shuru ne yasa ya ce " kaina ciwo yakeyi i need to rest " yana gama fadar haka kuwa ya kwanta abinshi yabarta a zaune tana binshi da ido, mikewa ta yi ta fita adakin ɗan ta lura bayason ana dauko mishi maganar Ammi kwata_kwata amma itade bazata taba hakura ba seta shirya tsakanin yar uwarta da ɗanta. Seda ya tabbatar da tafice a part din gaba daya sannan ya mike zaune yana jingina jikinshi a makeken gadonshi , shi da zasu gane da sun dena shiga harkanshi ɗan ba son magana yake yi dasu ba, shisa yake son yasamu addimission din nan yafito yatafi yayi nesa dasu ko zesamu nutsuwa baya kaunar yanda suke dauko mishi maganar Ammi , yafison yanda yadauko rayuwar shi yakare ta ahaka. haka yadinga tunani iri_iri dayan zuciyarshi ta ce mishi to inka tafi ya kake tunanin Asrah zataji ? ahankali yafurta ko ɗan ita zandawo bayan shekara goma zandawo in aureta sannan indauketa muje muyi rayuwar batare da sun addabi rayuwata . Ammi dakyar ta iya kawo kanta babban falo ta zauna zuciyar ta na radadi hade da ɗaci ,danasani fal acikin zuciyarta abinda yafaru shekaru sha bakwai ne yafara dawo mata ƙwaƙwalwarta datasan hakan ze dawo mata babban firgice da ta rungumi ƙaddararta da tasan zata haifi abin cikin nata kuma tazo tana mugun kaunarsa dabatayi wannan kuskuren ba. tunani tafara tayanda zata shawo kan Tajuddin ya yafe mata se wata zuciyar ta ce mata karfa ki manta bawai laifi daya ne kikayiwa Tajuddin ba ,manyan laifi guda biyu kikayi mishi ta ina za ki fara neman afuwarsa? Sosai jikin Ammi yayi sanyi se saƙa da warwara takeyi , shigowa falon Hajiya badiyya tayi tundaga nesa data hangi Ammi tasan akwai abinda ke damunta zama tayi kusa da ita,tsabar yanda Ammi tayi nisa cikin tunani batasan ta shigo falon ba, taɓata Hajiya badiyya tayi ta ce " Hajiya hamdiyya lafiya naganki cikin damuwa? ko dayake nasan be wuce tsakanin ki da Tajuddin ba " kallonta Ammi tayi ta ce " Hajiya babba wallahi bansan yazanyi in shawo kan Tajuddin ba, abu ne me matukar wuya " ta kare maganar tana zare medicated glass din idonta tana fuskantar kishiyarta ta, ɗan nisawa Hajiya badiyya tayi ta ce " kuskure an rigada anyishi amma duk da hakan kema danaki laifin duk wani ɗa yana bukatar mahaifiyar shi ta jawoshi ajikinta amma Tajuddin be samu haka daga gareki ba ga laifin da kikaso tabkawa tun kafin yazo duniya bayan wannan kinsake yin wani laifin da haryanzu Taj dashi yake kallon ki. Hajiya hamdiyya ke Mahaifiyarsa ce haryanzu kinada damar da zakije ki neme afuwarshi nasan Taj yanada zuciya me kyau idan kikayi mishi bayanin komai dakuma dalilin haka nasan ze fahimceki , kiduba kiga yaron nan tunyanzu yanaso yarikoɗe yakoma boss wannan dalilin ne yasa Abbie dinsu yake tsoron zuwanshi makarantar sojoji domin a yanzu ma ya'ya? Ya muka ƙare da Taj inaga yatafi yaje yayi shekara goma yana daukan horon sojoji. tun kafin yasa ƙafa yabar kasar nan Yakamata muyi kokarin sassauto mishi da zuciyar shi yayi sanyi yasan kedin uwarshi ce bawai maƙiyarshi bace domin khareema tarigada data gama poisoning zuciyarshi da tsanarmu , har kullum cigaba da cusa mishi ƙiyayyar yan uwanshi da iyayenshi takeyi " tunda Hajiya badiyya tafara magana Ammi ta mayar da hankalinta gaba daya kanta domin maganar ta hakane dolene tasan hanyar da zata ƙwato ɗanta daga sharrin Hajiya khareema domin tanason juyawa Taj ne tunaninshi akansu bude baki tayi zatayi magana sega Hajiya khareema tafito tana nufo inda suke, tsayawa tayi akansu ta riƙe kugu ta ce " naji kamar gulmata kukeyi to adeji tsoron Allah adena gulma da munafurci in an girma asan an girma , duk wani kulle_kullen dakuke kullawa agidan nan ina sane daku yanzu muka fara muzuba mugani kaff senayi maganin ku" tana magana tana kallon Asrah dake wasa acan gefen su mugun kallo ta watsa mata cike da tsananin tsana , Hajiya babba da Ammi de acikinsu babu wanda ya kulata balle tacigaba dayi musu rashin kunya hakan yasa taja doguwar tsaki tayi gaba tana kokarin shiga part din Taj. Girgiza kai kawai Ammi da Hajiya babba sukayi kafin sukaci gaba da tattaunawar dasukeyi. Tana daf da zata shiga part din Taj ta hango anty amarya tafito malalacin murmushi ta sake da ita kadai tasan ma'anarshi , ka war da kai anty amarya tayi kamar bata gantaba , bangaje anty amarya Hajiya khareema tayi dayasa saura kadan ta fadi , sannan tayi gaba abinta kamar babu abinda tayi . afusace anty amarya tabi bayanta tasa hannu ta jawo hannun rigarta ta dawo baya sannan itama ta hankaɗeta ta fadi ƙasa warwas kafin ta nunata da yatsa " wallahi khareema ki shiga taitayinki dani acikin gidan nan karki ga idan kinayiwa su yaya suna ƙyaleki ni to bazanyi shuru kice za ki takani ba , ah ah baki isa ba munafukar banza munafukar hofi" yanda anty amarya take magana ranta amatukar ɓace ya isa yanuna kancewa tabbas akwai babbar yar tsama a tsakaninsu.dafa kujeran dake kusa da ita tayi ta mike ta ce.... Comments, like and share for more... *🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹* *_Story & written_* By *MRS🌹ISHAM🌹* ( Yar lelen Jarumai) *THE WRITER OF 🖋️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️ Page 03 Da fa kujerar dake gefenta ta yi ta mike ta ce " Abida kenan , duk wani kule_kulen munafurcin da kuke yi dake da wancan munafukar ya'yar ta ki Hajiya hamdiyya dakuma ɗayar munafukar taku Hajiya badeeya ina sane daku kuma nafi karfinku , karkuyi tunanin zan zuba muku ido , ina nan ina bin duk wani takun ku !" Magana takeyiwa anty amarya hade da makirar murmushi dauke akan fuskarta,anty amarya kuwa binta kawai takeyi da kallon tsana saboda duk duniya babu irin mutumin da ta tsana sama da munafiki kuma makiri. Batare da anty amarya ta ce mata komai ba ta juya tana kokarin barin wurin riko hannunta Hajiya khareema tayi tazo dede kunnenta tafurta mata " hankalina baze taba kwanciya ba sena raba ku da Tajuddeen sannan kuma in mai dashi karkashin ikona se yanda nayi dashi bayan hakan ya faru kuma zan raba shi da farin cikin rayuwa . wannan alkawari ne dani Hajiya khareema na daukawa kaina " tana gama fadin hakan tasaki hannun anty amarya ta wuce tabarta awajan ta shige part din Tajuddeen, kamar wacce aka shuka awajen anty amarya ta ka sa koda kwakkwaran motsi kirjinta se bugawa yakeyi da karfi domin kuwa ba ta raba dayan biyu tasan abinda Hajiya khareema ta faɗa tabbas zata aikata, saboda tun farko ita ce ainihin musabbabin cusa ƙiyayyar kowa acikin zuciyar Tajuddeen aciki kuwa harda Ammi. "Ya Allah ka shiga tsakaninmu da wannan makirar baiwar ta ka da ta shigo rayuwarmu da muguwar nufi , Allah karka ba ta Sa'a akanmu ." Anty amarya ta yi maganar azuciyarta jiki asanyaye. ji ta yi an rike hannunta tasan ba kowa bace fa ce Asrah , kai dubanta ta yi zuwa kanta , ƙakulo murmushin dole ta yi ta sawa fuskanta ta tsuguna agaban Asrah ta ce " Asrah din mommynta ya akayi har kingama wasan naki ne ?" Ganin ta tsuguna ne yasa Asrah zagayawa ta hau bayan anty amarya, ta ce" mommyna ki goyeni muje gun daddy " tashi anty amarya ta yi da Asrah din dauke a gadon bayanta suka isa falo anan ta iske Ammi ( Hajiya hamdiyya ) da kuma Hajiya babba ( Hajiya badeeya ) suna tattaunawa. Tun kafin anty amarya ta karaso Hajiya babba take watsawa Asrah dake goye abaya hararan wasa tana fadin " gaskiya Asrah kinji kunya, shame on you ahakan kikeso in aura miki ɗana Tajuddeen? Kin girma bakinsan kin girma ba no!no bazeyu ba , jibeki katuwa dake abayan mamanki gaskiya bazaki auri Tajuddeen ba" dariya Ammi da anty amarya sukayi banda Hajiya babba da ta danne nata dariyar ta koma serious face dan tasan yanzu zasu ɗibi adashen tsiya ita da Asrah. Kokarin sauka tafarayi abayan anty amarya ta name kwabe fuska jin abinda Hajiya babba ta faɗa, sauketa ƙasa anty amarya tayi . Wajan Hajiya babba Asrah taje ta tsaya ajikin kujerar datake zaune, ido tabb da hawaye ta ce " adiya babba dan auri tajuju ko " girgiza mata kai ta yi ta ce" no bazaki aureshi ba ,cos he don't loves you" da karfi ta ce" he loves me " ta faɗa tana goge guntun hawayen idonta sannan ta ƙara da fadin " kuma ! Kuma seya aureni din " ta karishe maganar tana murguda dan karamin bakinta , tabe baki Hajiya babba ta yi ta ce" to ai se ya aurekin mugani " anty amarya de da Ammi yan kallo suka zama domin kuwa sun san mudin Asrah ta shaqa tofa gidan nan yau ba zaman lafiya dan rigimarta ma kadai seya hanasu bacci , saboda tasan me ake nufi da kalmar love duk da kananun shekarunta , tunda tashin turai ce. yara tun suna ƙanana zakaga wai sun san meye soyayya,shisaka duk ranar da akace Tajuddeen baya sonta ko kuma baze aureta ba tofa ranar akwai chakwakiya agidan. Kuka tafarayi a hankali tana " tajuju loves me and we will get married tomorrow" bakaramin dariya Maganar ta yabasu ba hakan yasa suka sa dariya dukkan su harda Hajiya babba dake tsokanar nata , dariyar da taga sukeyi mata ne yasa ta sake hassala ta fashe da kuka da karfi . Tun bayan rabuwar ta da anty amarya ta shiga part din Tajuddeen bude kofar bedroom din ta yi ta zuba mishi ido , yana kwance yabawa kofar baya. idanunshi a rufe amma jikinshi yabashi ana kallon shi , murmushin mugunta Hajiya khareema ta yi aranta ta ce " Tajuddeen Mubarak Bishara kaida samun farin ciki arayuwarka sede bayan na mutu amma mudin ina raye , sena rabaka da kowa " cikin kissa da kisisina ta shigo bedroom din ta zauna a bakin gadon shi tasa hannu ta yaye bargon dayake rufe dashi " my son bacci kakeji ne ? gaskiya bazan barka ka kwanta haka ba, tashi ka zauna bari in sa akawo maka abinci ka ji?" tana magana hade da kallon fuskarshi da babu walwala a cikinta ,mikewa ya yi ya zauna yana facing dinta, riko hannunta ya yi murya akarye ya ce " Ammuh duk faɗin gidan nan ke kadaice kika damu dani kuma kika damu da damuwata, duk da ci miki mutunci da ake yi akaina amma hakan besa kindena sona ba" yana magana yana sauke ajiyar zuciya saboda be saba magana me tsayi ba , murmushin samun nasara ta yi kafin ta koma kalar tausayi kamar wata mutumiyar kirki ta ce" ɗana Tajuddeen, banida burin da yawuce inga yan uwanka da iyayenka sun fara sonka narasa wace iriyar tsana sukayi maka , karkaga laifina idan nace hakan yasamo asali ne daga wajan Amminka , ɗan da ace ta nuna maka soyayya dakuma janka ajikinta tofa da kowa ze so ka, amma ah ah ta fifita sauran yan uwanka akanka , kullum kokarina shine inga na nunawa Hajiya hamdiyya abinda takeyi bata kyautawa ita da Hajiya babba amma daga nafara faɗa musu gaskiya sesu fara zagina da cin mutuncin hade da faɗin ina ruwana dakai , nikuma wallahi Tajuddeen bazan iya juya baya akan rayuwarka ba. Allah ya samun sanka tun daga ranar da kazo duniya na mayar dakai ɗana" ta karishe magana tana hawayen munafurci tasaka gefen gyallenta ta goge hawayen, kallonta yakeyi cike da tausayawa saboda Tajuddeen shi gani yakeyi ita kadaice masoyiyarshi acikin gidan daga ita se anty amarya se kuma Asrah da ya mayar da ita wani bangare na rayuwarshi. Ci gaba ta yi da magana tana nuna mishi hannunta da ya gurje lokacin da anty amarya ta hankaɗata ta fa di ƙasa ashe ta gurje a hannu , yana fitar da jini kadan_kadan dake farar macece se wajan yayi jawur " kaduba ka ga abinda Amminka dakuma Abida suka aikata agareni" rai abace ya ce " Ammi ce tayi miki haka ita da anty amarya?" Cikin salon makirci ta ce" su sukamin haka Tajuddeen saboda naje nasamesu inayi musu magana akanka ,shine sukamin koran kare danaƙi tafiya kuma shine su biyun suka tureni nafadi aƙasa. Amma bawai na faɗa maka hakan ɗan in tayar maka da hankali bane kokuma in shiga tsakaninka dasu ba kayi hakuri karka musu magana ,in sha Allah wata rana se labari komai ze wuce ." Tana magana ne hade da satan kallonshi ta ƙasan ido . Tunda ta fara magana yake kallonta jikinshi duk ya yi sanyi jin wai ta dalilinshi akayi mata hakan lumshe idanunshi yayi ya makasa cewa komai saboda shi ba ma'abocin so da kuma yin dogon magana bane,shisa yarasa wata kalma zeyi amfani wajan bata hakuri akan abinda Ammi da anty amarya suka mata , kamar yanda ta faɗa . Mikewa ya yi slowly yanufi toilet ze dauko first aidbox domin yayi mata treatment din ciwon da taji . Ya riko first aidbox Yana kokarin fitowa yaji kamar kukan Asrah dinshi, ka sa kunne ya yi dan ya tabbatar shin dagaske ita ce din take kuka ko kuwa, sake ji yayi hakan ya tabbatar mishi da antabo mishi Asrah fitowa yayi daga toilet din da sauri batare da ya dauko first aidbox din ba ɗan hankalinshi ya koma kan Asrah da take kuka , be ko kalli inda Hajiya khareema ke zaune ba yanufi hanyar barin bedroom din. da mamaki take binshi da kallo ganin irin saurin da ya keyi kamar wanda ze tashi sama ,yana daff da barin bedroom din ya tsinkayo muryanta ,tana fadin " son saurin me kake yi haka " amsa yabata da" kukan Asrah naji shine zanje in daukota " beko jira abinda zata faɗi ba ya fice , afusace ta ce " bazeyuba dole in fara ka war da Asrah domin ita ce zata hanani cika burina akan wannan yaro saboda ba karamin so yake mata ba ,in banyi wasa bama zata iya wargaza min aikina danayi shekara da shekaru inayi . Dole indau mataki akanta" ta faɗa tana huci. Comments, share and like 🥰🥰 Share fisabilillahi 🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹 *Story & written* By MRS🌹ISHAM🌹 ( Yar lelen Jarumai) *THE WRITER OF 🖋️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ 🌹*ASHE ZAMUGA JUNA*🌹 📚📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚📚🖋️ Page 04 " Se tajuju ya aureni ! se munyi aure ! and we love each other" kalmomin da tadinga faɗa kenan tana kuka , tun suna mata dariya har suka koma lallashinta ƙin sauraransu ta yi , ta ci gaba da kukanta jikinta har rawa yakeyi lokaci daya ta haɗa zufa saboda kuka , daukanta Hajiya babba ta yi ta daurata akan cinyarta tana lallashinta amma sam taki shiru. Abbie, Abbu , uncle Hameed suna zaune suna tattaunawa suka ji ihun kukan Asrah dafe goshi uncle Hameed ya yi. murmushi Abbie ya yi ya ce" to yanzu kuma wa ya taɓo wannan rigimammiyar " ya faɗa yana mikewa yar dariya sukayi su ma suname bin bayanshi , su iklas dasu Abbas duk suna part din Hajiya babba gaba dayansu , yaran matan sun duƙufa suna homework Hafiz na gyara musu in basuyi dede ba , saghar tun da suka shigo be kula kowa ba ɗan har iya zuwa lokacin fushi yakeyi ,yakoma gefe aranshi kuwa yana aiyana irin mugun dukan dazewa Asrah aduk lokacin da Tajuddeen yatafi U.S.A , idan ya tuna Tajuddeen zeyi nesa dasu ne yake jin ranshi nayi mishi sanyi ɗan hakan ne ze bashi damar cin zalin Asrah yanda yaga dama. Kukan Asrah suka faraji da rigimarta kallon juna Abbas da Ahmad sukayi sukasa dariya , Ahmad ya ce" tabb dijam ! Yau anya zamu yi bacci kuwa? gaskiya Asrah akwai shegen rigima " " ni wallahi kukan yara dagamin hankali yakeyi , Allah de yasa Tajuddeen na gida , ɗan kuwa inde baya nan banajin akwai wanda zesa yarinyar nan ta yi shuru" cewar Abbas . Dogon tsaki saghar yaja ahassale ya ce " wannan iskancin da yarinyar nan takeyi guri ta samu ,aikin banza " ya mike yabar musu part din,girgiza kai kawai Hafiz ya yi bece komai ba. " zoya,parsa,umaisha,rameesa kuzo muje gurin Asrah kunji tana kuka ko " cewar iklas da ta mike tana jiran sauran yan uwan nata su tashi suje, mikewa sukayi su ma suna kokarin tafiya, daka musu tsawa sahil ya yi ya ce" common ku zauna babu inda zakuje, ta yi kukan jini ma ina ruwanku " duk tsilli_tsilli sukayi da ido kamar wasu marasa gaskiya, basu zauna ba kuma basu tafi ba . sake daka musu tsawa ya yi yana kokarin mikewa suka zura aguje sukayi part din Tajuddeen ɗan saboda suna kyautata zaton Asrah na can. Kwafa sahil ya yi ya ce" zamu haɗu ai duk senayi maganin ku " Abbas, Ahmad,Hafiz de basu ce musu komai ba karshema tashi sukayi suka bi bayansu parsa zuwa part din Tajuddeen din. " Ohhh no! wa ya taba Asrah ne haka, meyafaru yar lelen Abbie" Abbie ne ya yi magana a yayinda yake sa hannu yadauketa akan cinyar Hajiya babba suka zauna akan manyan kujerun da ke zagaye a falon. Rarrashin ta Abbie yakeyi ko zasu samu ta yi shuru amma ina ,kamar ana zugata ga har kanta yafara daukan zafi , uncle Hameed ne ya kalli anty amarya ya ce " nikam Abida wa ya taɓo wannan rigimammiyar" dariya anty amarya ta yi ta ce" ita da Hajiya babba ne , ce mata ta yi bazata aura mata Tajuddeen ba shine ta ke wannan kukan " dukkansu dariya sukayi harda su Abbas da su ma suka shigo, ga su parsa atsaye sunyi carko_carko duk jikinsu ya yi sanyi sosai ganin irin kukan da yar uwarsu Asrah keyi , ɗan kuwa ba karamin so sukeyi mata ba shisa kullum se sunje wajanta duk da ita bata wani shaƙu dasu ba ,saboda ba kasafe take zama a cikinsu ba. " Haba Hajiya babba ! kinsan halinta inde akan Tajuddeen ne tofa seta hanamu bacci agidan nan " cewar Abbu fuskarshi dauke da murmushi . Shigowa cikin falon ya yi idonshi akan Asrah da ke zaune akan cinyar Abbie tana kukanta , sake tsuke kyakkyawar fuskarshi ya yi babu annuri a fuskar, ko kallonsu beyi ba yakarasa tsakiyar falon ya tsaya , tunda ya fito , cak kukan nata ya tsaya kamar anyi ruwa an dauke tafara dariya kamar ba ita ce take wannan kukan ba da kururuwa , hannu ya mika mata ya ce" let's go Asrah" cikin hanzari ta sauƙo akan cinyar Abbie ta riƙo hannun nashi hade da rungume shi, duk zuba musu ido sukayi babu wanda ya ce mishi uffan , ɗan sun san wani inya mishi magana acikinsu ze iya basu amsar da bazeyi musu daɗi ba , domin Tajuddeen inda kunya yabi ma be biba , riko hannunta ya yi yajata zuwa part din shi suka barsu afalon. Ajiyar zuciya Ammi ta yi kawai taname bin bayan Tajuddeen da Asrah da kallo, kallon Abbie ta yi taga shima ita yake kallo, alama yamata da ido ,ta kwantar da hankalinta, gyada mishi kai ta yi sannan ta mike ta bar falon ta nufi nata part din ,hadaddiyar bedroom dinta tashiga na alfarma dayasha dukiya, zama ta yi akan gado. wasu abubuwan da suka faru shekaru sha takwas abaya ne yake dawo mata acikin kwakwalwar ta , bedside table takai idonta ,yar karamar hoton enlargement ne me kyau ita ce acikin hoton da wani kyakkyawan yaro ajikin hoton sa hannu ta yi ta dauki hoton , shafawa ta yi hawaye na fita a idonta " am sorry my Tajuddeen, ɗana ka yafemin ninasan me laifi ce agareka amma ban cancanci haka daga gunka ba, wallahi bantaba jin bana sonka ba kawai ,abinda ya faru sharrin shaidan ne " ta faɗa tana kuka ta rungume hoton a kirjinta , haka ta kwanta da hoton rike ahannunta , shigowa bedroom din Abbie ya yi yabiyo bayanta domin yasan inde tashiga daki setayi kuka hakan ya rigada ya zame ma ta jiki, tana jin motsi , da sauri tasa hannu ta goge hawayen fuskanta, zama Abbie ya yi a kusa da ita yasa hannu ya ɗagota ta zauna , ganin idonta ya yi ja ne yasa ya ce " sarauniyata kuka kika yi ?" girgiza mishi kai ta yi" ah ah kuka kika yi mana ga idonki ya yi ja ! nasan abinda yake damunki nikaina abun na damuna, wallahi nafara zargin kode sihiri akayi wa wannan yaron , da nayiwa malam baba gana magana ya ce babu sihiri ajikinshi . bansan meye matsalar shi ba " Kwantar da kanta Ammi ta yi akan kafaɗar Abbie ta yi shuru tana sauraranshi. Cikin tsigar lallashi ya ce" sarauniya ta , ki kwantar da hankalinki in sha Allah zanyi iya kokarina inga Tajuddeen yadawo kamar kowa " bata fuska ta yi domin ji ta yi ranta yafara ɓaci ta ɗago ta kalleshi ta ce " ka fa riga da kasan matsalar kasan wacece ta shiga tsakanina da ɗana, amma narasa wani daliline ya hanaka yarda da hakan" murmushi Abbie ya yi ya cire glass din idonshi sannan ya ce" bansan meye matsalarku da Hajiya khareema ba , ko da yaushe ita kuke kallo amatsayin me laifi , bayan ita tsakani da Allah take son Tajuddeen. babu mugun nufi aranta amma kun ka sa fahimtar hakan ! to gaskiya banason irin haka " yagama maganar shi yana me janyeta daga jikinshi sannan yafita yabar dakin nata babu walwala atare dashi . Ammi kam bakin ciki da bacin rai ne ya hanata magana se ma bin bayanshi da takeyi da kallo harya bacewa ganinta .ta rasa dalilin da yasa Abbie kwata_kwata ya tsani akawo mishi aibin Hajiya khareema, kallon mutumiyar arziki yakeyi mata ,domin duk inda makira algunguma take tofa inde akasamu Hajiya khareema magana ya ƙare. Kwafa Ammi ta yi azuciyarta tafurta " ina sha Allah sena kwato ɗana da mijina daga sharrinki khareema". Shigowa bedroom dinshi sukayi yana rike da yan dugui_dugui din hannunta, yanda yafita yabar Hajiya khareema ahaka yadawo yasameta sede wannan karon yanayinta babu yabo babu fallasa, zaunar da ita ya yi akan gadon ,tun kafin yakai da zama akan gadon,zazzakar Muryar Asrah kamar wanda aka barbaɗawa suga ya dira musu akunne tana faɗin" my tajuju ai zamuyi aure ko" bece mata kala ba face gyada mata kai da ya yi, dan tun ahanya ta cikashi da surutu hade da bashi labarin abinda yahadata da Hajiya babba cike da yarinta gwarancinta. nan ne ya gane asalin musabbabin kukan nata da yajiyo , har cikin ranshi yaji dadin yanda Asrah take matukar kaunar shi da har yakai in ance bazata aureshi ba kokuma baya sonta take kuka kamar wacce taci duka , duk dakuma kananun shekarunta, shisaka yake jin duk fa ɗin duniyar nan bashi da mata sama da Asrah domin son dayake mata tun tana cikin mahaifiyarta yakamu da sonta , hakan yasa yasanyawa ranshi duk dadi duk wuya yana tare da ita baze taba barinta ba . muguwar kallo Hajiya khareema take bin Asrah dashi domin yanda ta tsani yarinyar ma aranta to bazata iya faɗa ba domin tsanan yawuce misali , duk wata hanya dazatabi wajan ganin ta ka war da Asrah tagama shirya komai kawai lokaci take jira tarusa farin cikin anty amarya da uncle Hameed da sauran mutanen cikin gidan.mikewa ta yi ta ce" my son nafarajin bacci bari inje in kwanta sannan zanbawa parsa abincinka ta kawo maka " lumshe mata idanunshi dasuka kasance masu daukar hankali ya yi. kan nan tafice a part din nashi tana tafiya tana sake_sake na ganin bayan Asrah in bahaka ba kuwa zata bata mata aikinta ne. Dawo da kallonshi ya yi kanta yaga ta dauki headphone dinshi tasa akunne , kokari takeyi wajan ganin ta kunna ƙida amma takasa , girgiza kai ya yi dan yasan yanzu zatace seya kunna mata ,aikuwa hakan ce ta kasance datayi iya yinta ta ka sa budewa ta miko mishi " tajuju play a song for me" karba ya yi ya ajiyeshi ya ce" not now , ke bakyajin bacci ne karfe 9 fah " turbune fuska ta yi zata mishi kuka ya ce" karma ki fara ɗan drygon zan kira miki " nan take tayi shuru kamar ba ita ba ,saboda tana matukar tsoron wannan karen nashi da yasa mishi suna drygon hakan yasa cikin tsoro_tsoro ta ce" tajuju ka kaini wajan mommyna zanyi bacci" ta yi maganar tana hawa bayanshi . har part din su yakaita abakin bedroom din anty amarya ya ajiye ta da gudu ta shige ciki ɗan gani takeyi kamar ze iya kiran karen. Washe gari 6:00am Yawan comments dinku yawan read more din da zan muku ah to. Se mun haɗu gobe in Allah yakai da rai da lafiya. Comments,share and like 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 Page 05 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ Page 05 Duk yaran gidan sun tashi daga bacci tunda sukayi sallah asuba basu koma bacci ba , iyayensu sun koma bacci amma su basu koma ba , kaltume tana shiryasu dan ganin kar suyi letting a makaranta, amma gaba daya sun ƙi natsuwa se raba mata hankali gida biyu sukeyi musamman ma umaisha tafisu rashin ji , dakyar da suɗin goshi ta samu ta kammala shiryasu ta kwashe su dukkansu biyar din suka wuce dinning table. Kitchen kaltume ta shiga ta Samu me girkin gidan fatime ta gama shirya musu breakfast dinsu , gaisawa sukayi cikin mutunta juna kafin suka fito atare rike da food flask din abinci suka jera a dinning . Kallon fatime kaltume ta yi ta ce" fatime naga yan mazan basu fito ba ko za ki je ki taso su karsuyi letting" ba don ran fatime yaso ba ta gyada mata kai, ta nufi part din yaran mazan tana tunani iri_iri aranta, domin tasan halinsu wasu daga cikinsu ma dakyar insun tashi daga baccin, part din twins tafara shiga ta yi Knocking daga ciki aka amsa da" Yes come in " turo kofar ta yi ta tsaya daga bakin kofa. Dukkansu biyu sun shirya sahil ya kammala necktie yake sawa. shikuma salim takalmin makaranta yake sawa batare da sun ɗaga kai sun kalleta ba suka hada baki wajan faɗin" fatime ya akayi ?" Mamaki ne yau yakamata ganin yau sune akazo aka samu sun shirya suda kullum se sunyi letting kafin su tashi jinjina kai ta yi aranta ta ce" ahh lallai yau sahil da salim sunyi abin kai " afili kuwa ta ce" dama nazo in tasheku ne ,kuzo kuyi breakfast". " okay" salim ya furta suka ci gaba da shirin da sukeyi . Fita tayi anasu part din ta shiga na Saghar , Jawan da Sudais , su kam ma a falo ta samesu sunfito hannunsu rike da school bag gaisheta sukayi ,ta amsa tarike haɓa kafin ta ce " dama ku zanje in taso kuzo kuyi breakfast saboda karkuyi letting " murmushi kawai suka mata , suka wuce ta . Daga karshe part din Tajuddeen ta nufa tana tunani yau kuma wani irin wulakanci zeyi mata , sadaƙarwa ta yi kawai ta shiga part din kai tsaye ta wuce bedroom dinshi knocking ta yi taji ji shuru babu amsa , hakan yasa ta sake gwadawa duk da tasan abune mawuyaci Tajuddeen yabude. haka tai ta gwadawa kusan mintin ta goma a tsaye awajan cire rai ta yi da ze bude ta juya tafara tafiya ta ji , yabude kofar dawuwa ta yi ta tsaya kanta akasa domin kuwa dukda Tajuddeen beda wasu Shekaru bata iya kallon fuskarshi tunda tazo gidan saboda yana da matukar gwarjini ga wannan golding eyes din nashi da in ya tsare mutum dasu tofa se ka sha jinin jikinka. Yana sanye da kayan bacci fuskar nan yaci murr ga idonshi da har lokacin akwai alamun bacci acikinta yawatsa mata harara dashi, cikin daga murya da rashin nuna ko In kula ya ce" meyafaru kikazo kina dokamin kofa da wannan safiyar ?" Hadiye wani yawu ta yi muryanta yafara rawa dakyar ta iya furta dama nazo in tasheka ne ! ka shirya zuwa makaranta kuma angama breakfast kai kadai suke jira " wani banza kallo yabita dashi ranshi yayi matukar ɓaci " daga yau se yau karda ki kuskura insake ganinki a part dina da sunan kinzo tashi na daga bacci , sannan wa'yanda suka turoki ki tasheni din kije kice musu bazanje makarantar ba" ya yi mata maganar cike da gargadi da izza da rashin kunya sannan yana kammala faɗa mata abinda ze faɗa ya rufe kofar da karfi kamar ze ɓalle ta , ya koma ciki yana tsaki yana rike kanshi dan ji ya yi kamar ze faɗi , ɗan duk sanda a ka tashe shi daga bacci tofa se ciwon kai ya ziyarce shi. Jikin fatime a sanyaye takoma falo taje ta samesu duk suna zaune a dinning table suna zaman jiran Tajuddeen dukda sun san mawuyacin abune yafito tunda yariga da ya yi pepper tare da yan ss3 ya dena zuwa makarantar, jiran admission dinshi kawai yakeyi , dukda sun san ba lallai yafito ba amma basu da ikon cin abinci harse ance baze fito ba , domin wannan shine dokar gidan basa cin abinci a ware , Jawan ne ya ce " fatime yaya Tajuddeen din ya ce baze je ba ko ?" gyada mishi kai ta yi , tun daga nan be sake cewa komai ba ya ja plate din omelette din gabanshi yafara ci. Salim ne ya ce " hmm dama ai bro Tajuddeen ba lallai ya fito ba tunda shi yanzu ya rena kowa agidan " dakatawa da cin omelette din dayakeyi Jawan ya yi ya kalli salim ya ce" babu ruwanka da rayuwar dan uwana ka ji da abinda yake gabanka, banason reni yaya Tajuddeen ba sa'anka bane " tsaki salim ya yi be kula Jawan ba , sudais ne ya kalli salim ya ce" salim karka sake irin haka , wannan rashin kunya ne " tunda akayi haka babu wanda sake cewa komai harsuka karisa cin abinci , fita sukayi izuwa packing space , motaci uku suka shiga se escort din da suka bi bayansu zuwa makarantar. Tajuddeen ba shi ya tashi daga bacci ba har 10:00am toilet yafada ya yi wanka yafito ya shirya cikin ƙananan kaya riga da wando saman rigar yadaura rigar sanyi me hula, hular yarufe mishi rabin fuskar shi, sannan ya yadauki headphone dinshi ya toshe kunnenshi dashi . Kafin yafito kai tsaye dinning ya wuce. duk a dinning din yasamesu wasu sun gama cin abinci wasu kuma suna kan ci , se hira sukeyi gwanin burgewa ,Hajiya khareema na sashinta bata fito ba. Jan kujera ya yi ya zauna batare da ya kallesu ba balle su sa ran ze gaishesu, kallon fatime dake tsaye akanshi ya yi murya kamar wanda aka tilastawa dole ya yi magana, ya ce " in banida rabon abinci ne yau kifadamin in tashi in tafi " ya faɗa yana me tsareta da wa'yannan mayun golding eyes din nashi da se ƙyalli sukeyi kamar wa'yanda aka kunna kwan fitila, hannun fatime na rawa tafara bubbude food flask din da suke wajan domin ya zaba wanda zeci , gama bude gaba daya food flask din dake kan dinning ta yi tana jiran yazaba wanda ze ci ,dan gudun kartasa mishi wanda ba shi yake da niyyar ci ba ta yi laifi . ganin ta budesu bata zuba mishi bane yasa yagane me take nufi slide murmushi ya yi ya ce " karki damu kisamin ko wanne in bawai akwai poison aciki bane " dukkansu da kallo suka bishi domin sun san da biyu ya yi maganar, girgiza kai Abbie ya yi kawai bece komai ba, Ammi da tasan da ita yakeyi ka sa hakuri ta yi ta ce" Taj waye kake tunanin zasu sa maka poison din ?" Shuru ya mata be kula ta ba , kamar ma besan da shi takeyi ba , nunawa fatime food flask din da ke dauke da sinasir ya yi da sauri tazuba mishi da miyar taushe da ya ji kayan hadi . Anty amarya ce ta taɓa hannunshi ta ce" Tajuddeen Amminka na maka magana " ɗago kai ya yi ya kalli Ammi da itama shi ta tsurawa ido tana kallonshi , sunkuyar da kai ƙasa ya yi ya ce " mutane da yawa mana , wa'yanda suke son ganin na mutu ". Ran Abbu ne ya ɓaci dan yasan Tajuddeen da Ammi yakeyi " yanzu kai Tajuddeen ɗan bakada hankali mahaifiyartaka kake cewa tana son taga ka mutu anya Kanada cikekken hankali kuwa ?" Cikin natsuwa ya ke cin sinasir dinshi kamar be san Abbu na mishi magana ba , Abbas ne ya ce" dan Allah kuyi hakuri ku mishi uzuri in sha Allah zedena wa'yannan abubuwan da yakeyi " " hmmmm! Abbas kenan ai dama kai da Ahmad da sameera bakwa taɓa ganin laifinshi kullum cikin daure mishi gindi kuke " cewar Abbu ɗan har lokacin be sauko ba saboda ba karamin bata mishi rai maganar da Tajuddeen yafaɗa ya yi ba . Ammi mikewa ta yi tabar musu dinning table din dan dama ta gama cin abincinta hiran da akeyi ne ya tsayar da ita , Abbie, da Hajiya babba basu sa musu baki ba a maganar su kawai mafita suke nema ta yanda , zasu ga Tajuddeen ya komar da rayuwarshi irin na kowa . Mikewa ya yi ya yagi tissue ya goge hannunshi ya juya ze tafi dan surutun da suke mishi ya ishe shi , ta kasan ido ya kalli anty amarya murya a dakile ya ce" anty amarya ina Asrah ?" Fushi takeyi dashi hakan yasa batako kalleshi ba ta ci gaba da shan kakƙaurar tea dinta da fatime ta haɗa mata, se uncle Hameed ne ya amsa mishi da" tana bacci ". Harya soma tafiya Abbie ya kira sunan shi " Tajuddeen" cak ya dakata kafin yajuyo batare da yakarisa inda suke ba , hannu Abbie ya mikawa uncle Hameed,. Ya miko mishi da wata envelope me girma , tashi Abbie ya yi ya isa inda Tajuddeen din yake tsaye ya mika mishi " ga shi addmission dinkane na U.S millitary academy at West , nan da two weeks zaka tafi ka zama cikin shiri . Allah yabada Sa'a" har ranshi ya ji dadin wannan addmission din nashi da ya fito ,domin wannan shine burinshi kuma ga shi ya samu,beyi tsammanin yanda Abbie ba ya son shi ba ze cika mishi burinshi ba ( shifa Tajuddeen gani yakeyi duk gidan babu wanda suke sonshi,domin akan hakan Hajiya khareema ta daurashi kullum cikin zigashi takeyi da hure mishi kunne ). Duk da basason yatafi yabarsu amma sun taya shi murna , sunyi tsammanin yau kam rana daya da yasamu abinda yake so zasuga farin ciki a tattare dashi ,amma se sukaga sabanin hakan , komawa Abbie ya yi kan kujeran da ya tashi babu wanda ya yi tsammani kawai suka ji Tajuddeen ya furta " thanks" sannan ya haura upstairs part din anty amarya da uncle Hameed. Hajiya babba de in banda gyada kai babu abinda takeyi " anya bamuyi ganganci ba kuwa , muda muke neman sassauci akan halin yaron nan shine zamu turashi yaje yasamu horon soja harna tsawon shekaru goma , soja fa ze dawo yakuke tunanin ze koma " shuru suka yi suna nazarin maganar ta, tabbas suma sunyi tunanin haka amma mudin sukaki cika mishi burinshi tofa zasu hadune da fushin Hajjatiye , dan takan Tajuddeen zata tayar musu da hankali su rasa ina zasu sa kansu , amma banda Hajjatiye da bazasu turashi ba se sun ga yafara dawuwa kan hanya aiba tsoron shi sukeji ba , " Hajiya babba kinsan rikicin tsufan Hajjatiye fa tam " cewar Abbas da yake dariya yabar dinning din , bin bayanshi Hafiz ya yi , Ahmad de har lokacin be gama breakfast din ba jin an kira sunan hajjatiye ne yasa shi dariya ba ƙaƙƙautawa har kamar ze gware, watsa mishi harara Abbie ya yi sannan ya ce "wato uwar ta muce abin dariyarka ko, Ahmad ka tashi ka bar gurin nan kafin in dau spoon din nan in dake ka dashi"Abbie ya karasa maganarsa yana kokarin daukan cokali acikin spoon set,da sauri Ahmad ya mike ya dauki plate din abincin shi ya bar dinning din yana dariya,su kansu seda suka murmusa ganin har lokacin da Ahmad yabar wajan dariyar yake yi kuma sun san dalilin da yasa yake wannan dariyar duk be wuce irin rabuwar da sukayi da hajjatiye ba. Ci gaba da maganar su da suke yi sukayi " Ya Mubarak hakan da mukayi shine mafita , Allah ya sanya mishi albarka a karatunshi da aikinshi" uncle Hameed yafada jinjina kai Abbie ya yi ya ce" Abida kije ki sameshi dan Allah ki tausasashi ko ze saurareki, tunda kaff gidan nan yafi sauraran Hajiya khareema da kuma ke " cikin girmamawa anty amarya ta ce" in sha Allah zan sameshi ya ya " Maida hankali kan Abbu Abbie ya yi ya ce " nikam yau me ya hana Hajiya hurairah fitowa cin abinci ne?"fuska da ɗan damuwa Abbu ya bashi amsa da"ba ta gida"ko kadan basuyi mamakin jin wai Hajiya hurairah bata gida ba saboda inda sabo sun saba da shegen yawonta. haka kowa ya watse a dinning din . Tun bayan shigowar shi dakin anty amarya ya iske Asrah nata sharara baccinta hankali akwance , tana rufe acikin bargo iya fuskanta ne awaje ta turo wannan ɗan karamin bakin nata , yanayin fuskanta kuwa kamar wacce take murmushi , murmushin gefen baki ya yi can kasan makoshinsa ya ce" sleeping beauty and also sarauniyar rashin ji" zama ya yi akan daya daga cikin lumtsattsun kujerun dake dakin . Bude envelope din ya yi yafara yaga addmission dinshi da su password dinshi da komai dayake bukata takardun duk suna ciki ajiyar zuciya ya yi ya kalli inda Asrah dake bacci yana tuna yazasu ƙa re da rigimarta inya tafi. Yana zaune yana wannan tunanin anty amarya tashigo ta sameshi zama ta yi akusa dashi ta ce" bata tashi ba ko? " Gyada kai ya yi " Tajuddeen yanaga kamar bakayi farin ciki da addmission din naka ba ne " ka war da kanshi gefe ya yi kafin ya ce" me mika gani " " Tajuddeen gani mukayi fuskanka babu alamun farin ciki ! Shisa ka na tambayeka ai " kwantar da kanshi ya yi ajikin kujeran ya ce" dan ina farin ciki ai ba se na nuna kowa ya sani ba " " tofa wata sabuwa , shikenan to tunda ka yi farin ciki da hakan ,nidama ajikina nasan zakayi murna" ta faɗa tana murmushi " to yanzu_yanzu faɗamin in ka tafi zaka dinga zuwa hutu de ko?" da mamaki dauke akan fuskarshi ya kalli anty amarya yama rasa me ze ce mata jin tambayar da ta mishi na kancewar ze dinga zuwa hutu ,ganin irin kallo da yake mata ne itama yabata mamaki domin bata ga aibin abinda ta faɗa ba balle ya tsaya yana mata wannan kallon . " Meye kakemin irin wannan kallon??" girgiza kai ya yi ya ce" bakomai ,ke yanzu tunanin ki ya ba ki inna tafi zandawo hutu ?"batare da yabata amsar da ta tambayeshi ba shima yasake jefa mata tambaya. Sake baki anty amarya ta yi tana ƙa re mishi kallo , bazatace Tajuddeen wasa yakeyi ba saboda basa irin wannan wasan da ita bama ya yi da kowa inya faɗi magana tofa har ranshi yafada kuma ba ya shakka ,duk yanda zata maka daci arai shi baze dameshi ba , tunda ta ji ya faɗi haka tasan daga cikin zuciyarshi maganar nan yafito. Ƙaƙulo yaken dole ta yi ,ta ce " to ita Asrah din taka fa" maida kallon shi ya yi kan makeken gadon da take kwance ya yi , tana kwance tafara mutsu_mutsu tanason ta tashi . Ya ce" Asrah zamu dinga video call da ita " anty amarya de rike habarta ta yi tana mamakin irin wannan hali irin na Tajuddeen. Yaye bargon da take lullube dashi ta yi ta tashi ta zauna a tsakiyar gadon , tana hamma. Se mun haɗu gobe in mai duka ya kaimu da rai da lafiya. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 Page 06 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ Page 06 Bata lura da akwai mutane a dakin ba tunaninta ita dayace yasa ta ɓare baki zata fara kuka , " shiiiiii karki yarda ki so ma " tajiyo muryan Tajuddeen na ma ta gargadi. kallon inda maganar yafito ta yi taga mommynta ne da tajuju zaune , saukowa ta yi akan gadon jikinta nasanye da kayan bacci na yara , wajansu taje ta zauna a tsakiyar su ,shafa gashinta Tajuddeen ya yi yana kallonta , ya mutsa fuska Asrah ta yi ta ce" mommy am feeling hungry" ta yi maganar tana daura hannunta akan cikinta, daukarta anty amarya ta yi suka shiga toilet ta yi mata brush da wanka ta naɗeta a towel tafito da ita , mayuka masu tsada ta dauko akan mirror ta fara shafa mata , mikewa Tajuddeen ya yi" anty amarya inta gama ina painting room" abinda ya faɗa kenan kawai ya fita , Asrah da ba ita ya yi wa magana ba da karfi ta yi magana yanda ze ji ta ta ce" toooooooo! Tajuju ina juwa " lumshe idanunshi ya yi bayan yaji abinda ta faɗa,anty amarya dariya ta yi kawai taci gaba da shiryata ,sannan ta haɗa mata breakfast dan dama ita kadaice batayi karin kumallo ba agidan. Fitowa ta yi zataje part din Tajuddeen ta yi kyau sosai dan karamin bakin nan anty amarya ta sa mishi jan janbaki, tana sanye da yar karamar riga se wandon legis da take sanye dashi , har ta kusa isa part din Tajuddeen sekuma ta yi wani tunani, fasa zuwa part din ta yi ta juya zuwa part din yan aikin gidan mata , sanda_sanda take tafiya kamar mara gaskiya,dakin kaltume ta leƙa ta ganta tana kwance tana bacci dake dakin abude yake hakan yabata damar kallonta ,wuce dakin ta yi ta nufi dakin fatime , ganin dakin nata yana rufe babu ta yanda zatayi ta leƙa yasa ta kwanta akasa tana leka ta, fatime na zaune a ƙasa hannun ta rike da wani abu kamar aska kamar karfe yanada kaifi , irin zanen da yan da sukeyi ahannunsu wasu zakuga sunyi zanen kaɗangare wasu kuma zanen kalangu kowa da irin nashi wanda yanzu da zamani yacanza aka maida shi tattoo , sosai zanen fulawan da fatime takeyi ahannunta yaja hankalin Asrah dukda hannun nafito da jini. Cike da yarinta ta tashi tana murmushi domin tasawa ranta se fatime ta yi mata , knocking kofar ta yi jin an bubbuga kofa ne yasa fatime ajiye abin hannunta , tazo ta bude kofar bataga kowa ba , saboda bata kalli ƙasa ba balle taga Asrah maida kofar take kokarin yi tarufe . Asrah ta ce" fatime ni ne fa" kallon ƙasa fatime ta yi da sauri dan batayi tsammanin yara bane dariya tayi ganin Asrah ce yar duƙul da ita agabanta matsa mata ta yi tabata hanya ta shigo sannan tarufe . Zama ta yi akan gadon dakin tana kallon fatime da taci gaba da zanenta tana runtse ido saboda zafin da takeji. Kiran sunanta Asrah ta yi" fatime!" "na'am Asrah ya akayi?" saukowa kasa Asrah ta yi, ta yi zaman dirshen agabanta kamar me neman gafara " fatime nima kimin irin wannan zanen inaso " zaro ido waje fatime ta yi" ke rufamin asiri karkisa akoreni dan Allah" girgiza kai Asrah ta yi ta ce" noo ai mommy ce ta ce inzo kimin dazun taga kinayi" ko ajikinta ta shararawa fatime karya, kallonta Fatime ta yi cike da tuhuma domin takasa yarda da maganar Asrah din taya anty amarya zatace wai ayiwa Asrah wannan zanen tana yar karama da ita.fahimtar da ta yi fatime bata yarda da ita bane yasa ta mike tsaye da niyyar tafiya dan Asrah akwai shegen wayo ta ce " shikenan bari inje incewa mommy kince wai bazakiyi ba " dasauri fatime tajawo hannunta har hantan cikinta yakaɗa ,saboda ita kaffa_kaffa takeyi bakaramin so takeyiwa aikinta ba kuma ta lura mutanen gidan nada kirki , insuka koreta batasan aina zata samu irin wannan gidan ba . " Haba Asrah meyasa zakimin haka bakince mommyn kice ta ce ayi miki ba.. to zo ki zauna " maƙe kafada Asrah ta yi " no zancewa mommy kince bazakiyi ba" jawota ta yi ta zaunar da ita akasa ta ce" ah ah zan miki mana wani kallan zane zan miki " murmushi Asrah ta yi cikin murna da farin ciki ta ce " tajuju zakimin " tana magana tana cire rigarta ta ajiye akan gadon fatimen, juya mata baya ta yi , itade fatime yau tana ganin ikon Allah babu yanda ta iya haka tabude jakarta ,tafito da sabon karfen zanen tasa laita takona bakin karfen seda yahuce sannan ta daurashi abayan Asrah fargaba fal cike a ran fatime amma inta tuna kancewa anty amarya ce tace ayiwa Asrah se taji nutsuwa ya ziyarceta. Gefen bayanta na hagu fatime tasaka karfen gabanta na faduwa tafara rubuta Tajuddeen, runtse ido Asrah ta yi da karfi jin azaban zafin da ya ziyarceta nan take ruwan hawaye yafara zarya afuskarta , dake ita tasa kanta yasa ta danne kukan ya ƙi fitowa dan tasan sarai ta fara wannan kukan fatime zatace bazata mata ba . Haka fatime tagama mata zanen sunan Tajuddeen abayanta da manyan harufa gakuma dan karamin fulawa da tayi akasan sunan , se tsatsafo da jini wajan yakeyi ya yi jaa sosai ya ɗan kumbura abinka da farar fata , yar towel fatime tasaka da warm water ta goge mata bayan nata ,tadan gasa mata shi sannan tasa mata toka , zagayowa ta yi ta gaban Asrah taga yanda idonta ya yi jaga_jaga da hawaye hancinta shima ya yi ja ga majina , sa towel din ta yi ta goge mata fuskanta tanayi mata sannu. Tashi ta yi tabawa fatime rigarta tasaka mata sannan tafita jiki ba kwari dake ita ce ta ce tanaso mit ko tari batayi ba balle ajita , ahankali_hankali take tafiya ta nufi part din Tajuddeen abude tasamu kofar falon,tashiga wucewa direct bedroom dinshi ta yi ,azaune ta sameshi yana game a tv tsayawa ta yi daga bakin kofar tana hawaye ,ɗago kai ya yi yakai kallonshi inda ta ke tsaye ganin yanda jikinta duk asanyaye ga fuskarta da ya yi ja tsabar kuka , kashe Tv ya yi. Inda take tsaye ya isa yadauke ta suka koma kan kujera yana tambayar meya sameta amma ta yi mishi shuru taƙiyin magana harya gaji da magana, shi zaton shi ma ita da yan gidan ne , cikin rashin sani yakai hannunshi bayanta yana shafawa hade da rarashinta , taɓo inda aka mata zanen ya yi batare da ya sani ba wani gigitaten kara tasaka da seda ilahirin part din nashi yadauka, kafeta ya yi da ido yana nazarin ta na wasu sakonni , juyar da ita ya yi ya sa hannu ya cire mata rigar jikinta , sauƙe idonshi ya yi akan sunanshi dake rubuce agadon bayanta ga wajan ya yi ja sosai ,runtse idanunshi ya yi yana ji tamkar ajikinshi ne, bakaramin ɓaci ran Tajuddeen ya yi ba ,daka mata tsawa ya yi ya ce" uban waye ya miki wannan zanen abayanki ?" cak lokaci daya kukan da takeyi ya tsaya tafara tsilli_tsilli da dara_daran idanunta, tsoronshi ne Yakamata saboda bata taɓa ganinshi a irin wannan yanayin ba. Sake daka mata wani tsawan ya yi,murya na rawa ta ce" Ni ne nacewa fatime tamin sunanka" watsa mata harara ya yi,kafin yadauketa akafadarshi suka fito tsakiyar main falon gidan . Murya da karfi yafara kwala kiran sunan " fatime!fatime!fatime" kowa dake cikin gidan seda sukaji shi , babu shiri duk suka fito , baiwar Allah fatime jiki na kyarma hantar cikinta se kaɗawa yakeyi haka tafito ta tsaya a gefe hankali atashe , Abbu ne ya ce" meyafaru Tajuddeen?" be furta mishi komai ba yana tsaye yana watsawa fatime mugun kallo , Abbie ne ya ce" meyake faruwa ne kake wannan kwala mata kira duk ka tayar mana da hankali " " saboda nishadi na yi , ita nakira ai bance kowa yafito ba " ya yi maganar shi kai tsaye batare da wani shakka ko wani abu ba be kuma kalli inda suke ba . " Ke zo nan " jiki anarke fatime ta karaso kusa dashi ta tsaya . Zura hannayenshi ya yi a aljihu ya ce" uban waye yabaki damar yiwa wannan yarinyar zane da karfe?" kulululu haka ta ji cikinta yabada ƙara, Hajiya khareema na upstairs tana tsaye tana kallon abinda yake faruwa se tabe baki takeyi . Mamaki sukayi jin abinda Tajuddeen yafaɗa ga kuma fatime takasa cewa komai se ma rawa da jikinta yakeyi da hawaye ,da sauri Hajiya babba ta karasa gaban Asrah dudduba jikinta ta yi bata ga komai ba hakan yasa ta cire mata rigar jikinta ta juya bayanta , sosai ranta ya sosu saboda jikin Asrah danyen jikine da ita kuma yarinya , jikinta yasaba da hutu bazata iya jure zafin da ze mata ba kafin ya warke,itama kanta ranta yabaci , duk kallon bayan Asrah din sukayi duk basu ji dadi ba runtse idanu anty amarya ta yi dan bazata juri kallon bayan ƴarta a haka ba. amma bazasu yanke hukunci ba se sunji ta bakin ita fatime din hakan shine adalci. Hajiya babba ce ta soma magana " fatime meye yasa za ki mata wannan zanen bakiga itadin yarinya bace , da hankalinki da tunaninki" goge hawayen da takeyi ta yi sannan ta kwashe duk yanda sukayi da Asrah ta faɗa musu ta kara da" wallahi ina tsoron rasa aikina shisa na mata gudun kar anty amarya ta ce , banbi umarnin ta ba akoreni " dukkansu sallallami sukayi da rike baki tabbas sun sani Asrah batajin magana ga kuma karambani zatayi fiye da haka duk kallonta sukayi sun ƙasa ce mata komai, ita kuma Asrah se wuri_wuri take yi da ido kamar wacce ta yi sata wa sarki,Abbie ne yacewa fatime ta koma dakinta tare da mata gargadi karta sake maimaita irin wannan kuskuren, godiya ta yi musu hade da basu hakuri ta wuce dakinta kaltume ma tabi bayanta. Tajuddeen kam tsaban takaici ma kasa magana ya yi,ya ja doguwar tsaki yajuya ze wuce part din shi , Asrah ta fara binshi ,juyawa ya yi ya kalleta " karki yarda inganki a part dina yau tunda bakyajin magana " fashewa ta yi da kuka ta zauna zaman dirshen akasa tana kuka , part dinshi yashiga yasa key yazauna yaname tausaya mata ,kara jinjina rashin ji da karambanin Asrah ya yi. Daukanta Ammi ta yi ta wuce da ita part dinta ta mata wanka ta shafa mata magani awajen sannan tabata pain reliever, ta samu ta yi bacci . Anty amarya,Abbu,Abbie ,Hajiya babba su kadai suka rage afalon suna jinjina lamarin Asrah. Haka tasha baccinta har yamma ya yi su iklas suka dawo makaranta . " Dad ! Meyasa yafini komai duk abinda ya nema yana samu , kuma familyn su yafi namu karfin suna , babanshi shine tsohon governor Maiduguri , dayan ƙanin babanshi babban alƙali ne a court of appeal , dayan kawunshi kuma babban doctor ne da kowa yasanshi a fadin duniya . wallahi dad na tsani Tajuddeen Mubarak Bishara! natsane shi!" ya ƙarishe maganar da karfi yana dukan glass table din dake kusa dashi seda ya fashe, matashin yarone wanda kusan zasu iya jerawa a shekaru da Tajuddeen , kyakkyawane shima fari , yanda yake magana zallar wutar ƙiyayyar Tajuddeen ne a cikin kwayar idonshi . Wani babban mutum ne a gefenshi wanda daga gani mahaifin shi ne , da fa kafarɗar shi ya yi ya soma Magana" Fu'ad kenan duk yanda ka kai da tsanar su baka kaini ba , musamman inna tuna lokacin da nake neman kujeran governor ,saboda Mubarak Bishara na rasa kujeran nan daga karshe shine ya mulki Maiduguri,kuma ni zan tsaya maka se kafishi komai baze taba nasara akanka ba ,se ka nuna mishi kaidin jinina ne , Fu'ad Abubakar daula " Murmushi ya yi ya ce" Dad sekayi alfahari dani amatsayin ɗanka domin ni din nan dakake gani nafika rashin imani!se na zamewa Tajuddeen babban matsala a rayuwarsa bama shi kadai ba gaba daya mutane se na zame musu bazana" kecewa sukayi da dariya harda tafawa kamar wasu abokai. Damaturu " Wallahi yau se kin barmin gidana ke da wannan shegiyar ƴar taki ,domin wannan ba ƴata bace , ko kuma in kasheku na kashe banza " yana magana yana dukan matarshi dake kwance akasa tana kuka ga kuma wata yarinya yar karama kyakkyawa bazata wuce shekara shida zuwa bakwai ba tana rike da kafar mutumin tana kuka , sa kafa ya yi ya hambareta ta fa di ta fasa hancinta da bakinta , rarrafawa matar ta yi taje ta dauki ƴarta ta rungumeta suna kuka tare ,yarda belt din hannunshi ya yi ya tsaya gantsan_tsan akansu yanuna su da yatsa " wallahi Maryam karki yarda in dawo insamu wannan yar shegiyar a gidan nan in ba haka ba kuwa ƙonata zanyi da ranta sannan in haɗa dake , jaka mara mutunci kawai har ni za ki kalla kice wannan yarinyar yata ce bayan kuma duk cikin ahalina babu farin fata kinje kinyi zinan ki , kinsamu cikinta za ki ƙaƙabamin ita to tun wuri kinje ki fadawa kwarton naki bazan karbi shegiya ba " fuuuu yafice agidan kamar ze tashi sama ,Maryam na kuka tana gogewa yarta jinin dake zuba a hancinta da bakinta ta ce" Allah shine shedana wallahi ni ba mazinaciya bace , wannan yar takace kuma jinin ka, in sha Allah, Allah ze saka mana" kallon mamar nata ta yi ta ce" mama mu gudu kar baba yadawo yasamemu , banaso yadinga dukanki" wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata tasa hannu ta share ta face majina ta ce" karki damu Asmita in sha Allah babu abinda ze mana tashi inyi miki wanka se in miki kwaɗon ƙanzo da kuli_kuli kici kijin ko" haka ta dauki yarta ta yi mata wanka da klin dan ko sabulun wanka babu agidan kuma bawai dan bashi da halin siya bane muguntace kawai irin na malam Mamman. Gyara mata kwanciya tayi akan yamutsatsiyar katifar dake dakinta ta yi ta dauko fallen zanin daurawarta ta shifida mata , datse kofar dakin ta yi da sakata ta yanda koda malam Mamman yadawo baze shiga dakin ba . Suna cikin bacci sukaji yafara doka kofar dakin kamar ze ballashi , afirgice suka tashi ,rungume Asmita Maryam ta yi ƙam ajikinta muryan malam Mamman sukaji yana " wato ni zakiyiwa wayo ko Maryam to gwarama kitashi ki bude in kuma ba haka ba a dakin zan ƙonaku dukkan ku biyu" . " wallahi Mamman seda ka ƙona mu amma bazan taɓa bude maka kofar dakin nan ba ,tunda kai babu Allah azuciyarka mara imani kawai . Kuma ko mutuwa ka yi wallahi Asmita nada gadonka domin ƴar kace ta halak" Ta bashi amsa tana kuka kamar ranta zefita , har lokacin tana rungume da Asmita datake a tsorace gani takeyi kamar baban nata konasu zeyi , babu wanda Asmita take tsoro aduniyar nan sama da malam Mamman domin yatsaneta kullum cikin dukanta yakeyi da aibatata ,kuma yaro yana sake jikine da wa'yanda yake sonshi , ga shi agabanta kullum se ya da ki mamanta. Kokarin fasa kofar yakeyi amma yakasa saboda kofar karfece, makobtanshi ne suka shigo suna hanashi abinda yake da niyyar yi , komawa kansu ya yi ya karta musu rashin mutunci daga karshe yakoresu ya ce musu kar ya sake ganin ko wani munafikin a gidanshi. Haka Maryam da Asmita suke rayuwar wahala agidan ko kadan basa samun farin ciki , farin ciki yakauracewa Maryam tundaga sa'in da ta haifi Asmita , jaririyar tana da hasken fata malam Mamman ya ƙyankyashe ƙasa ya ce shi wannan ba yar sa ba ce seda ko maryam na da kwarton da yake amfani da ita. F and share 🖋️🖋️ 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 Page 07 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ Page 07 Yau sati daya kenan , zanen Asrah harya warke dake bata da ƙyan jiki kuma tana samun kulawa sosai ,wajan yabushe ya yi baƙi ga sunan Tajuddeen baro_baro abayanta kullum in za'a mata wanka seta tsaya a gaban mudubi ta karkace gefe ta kalli sunan hakan ba karamin nishadi yake sataba, shikanshi Tajuddeen inya gani yanajin sanyi aranshi . Kamar kullum tana painting room din Tajuddeen tana zaune Kamar wata uwar mata ta maida hankalinta tana zanen Tajuddeen , shikuma baya nan yana garden yana zaune , dan bazaka taba ganinshi acikin yan uwanshi yana hira ko wani abu da su ba . Zanenta takeyi cikin kwanciyar hankali batasan su parsa sun shigo painting room din ba , kasancewar yau Friday da wuri suka tashi daga school . Yanda tamaida hankali akan zanen ma batama san da shigowar su Zoya,umaisha,iklas,parsa,Rameesa ba ,tafiya suke yi sanɗa_sanɗa basa son tasan sun shigo dan so suke yi su dauke drawing din da take yi umaisha ce take directing dinsu yanda zasu yi ita ce boss. A hankali umaisha tasa hannu tadauki zanen da Asrah takeyi suka gudu daga part din suna ihun" yeeeeeeeh mun dauke_mundauke" bin bayansu ta yi itama da gudu dan bataso su yaga mata zanen ta, ɓace mata sukayi da gani bata gansu ba, dubasu ta yi ako ina bata gansu alamar ma kamar ba sa cikin mansion din , fitowa ta yi cikin compound din nan ma bata gansu ba , kuka tafarayi tana bubbuga kafa ,ga shi bata haduda yan gidan ba se masu aikine da masu tsaron gidan ne suke ta fita da shiga . Garden ta nufa tana kukan ɗauke mata zanenta da sukayi kuma bata san inda suka yi ba,volume din kukan nata sake ƙaruwa ya yi lokacin da ta hangi Tajuddeen na zaune acikin garden din ,wajan ta nufa tana isa ta kwanta abayanshi,sa hannu ya yi ya jawota ta dawo gabanshi goge mata hawayen fuskar ta ya yi " hey! Why are you crying?" " to basu zoya bane ba! suka daukemin drawing dina ba suka gudu " yanda take maganar tana turo baki ya bashi dariya amma beyi ba kawai murmusawa ya yi ," Okay kyalesu zasu dawo kinji?" " Tom" Sake kallonta ya yi ɗakyau ,dama so yake yafaɗa mata nan da kwana biyar ze tafi amma ba ya tunanin tanada wayon da zata fahimta . Magana yafara yana kallon shuke_shuken dake garden din " Asrah zanyi tafiya ,zan jima amma ba sosai ba .I want you to take good care of yourself " narai_narai ta yi da ido ,se kwabula fuska takeyi tana shirin yi mishi kuka , " wai ke bakida aikinyi se kuka?" Girgiza mishi kai ta yi sannan ta ce" to bakai ne kace zaka tafi kabarni ba, nide se na bika" nan nauyar ajiyar zuciya Tajuddeen yasauke " Asrah sanda zamu tafi inda nake rayuwa daga ni seke na zuwa,za ki bini batare da izinin kowa ba " Itade jin shi kawai takeyi bawai dan ta fahimci inda maganar ta shi yadosa ba . Cikin aljihun rigar shi yasa hannu yafito da wani box me matukar kyau , budeshi ya yi yafito da wasu abin hannu masu matukar kyau da tsada me daukar hankali, guda biyu na diamond silver color, yanayin design din ma kawai abin kallo ne ya hadu sosai,abin hannun yana da adjust za'a iya ragewa kuma za'a iya ƙarawa saman shi kuma anyi rubuta " T&A" wato Tajuddeen da Asrah kenan . Kamo hannunta ya yi na dama yasaka matashi ya ragesa yakoma dede hannunta yanda nan gaba inta ƙara girma ita da kanta zata iya ƙara shi , " woww, tajuju ya yi kyau sosai! I love it " ta faɗa tana shafa abin hannun se santin kyau din abin hannun takeyi , saka nashi shima ya yi a hannunshi bakaramin kyau ya mishi ba , ɗago kai ya yi on a serious face ya kalleta ya ce " ko da wasa karki yarda ki rabu da wannan abin hannun kinji ko" gyada mishi kai ta yi tana murmushin farin ciki , mika mata tafin hannunshi ya yi " Promise me bazaki taba rabuwa dashi ba ko da bama tare. " Daura hannunta ta yi akan nashi ta ce " I promise you tajuju , I am going to keep it safe " Tana gama faɗar haka ta sauko daga kan kujeran ta ruga aguje , da kallo yabi bayanta . Aranshi ya ce " Nasan zuwa nan da 10 years za kiyi hankali sosai, za ki zama budurwan da babu wanda ze yi gigin neman soyayyarki domin kuwa kedin matar Tajuddeen Mubarak Bishara ce " Kokarin shiga mansion din ta keyi taci karo da Saghar da Hafiz suna kokarin fitowa , ja baya ta yi sanin Saghar ze iya maketa , watsa mata harara ya yi ganin yana hararanta ne yasa ta murguɗa mishi baki amma shi be ma lura ba Hafiz ne kawai ya gani. yasa kai ya yi gaba yabar Hafiz a tsaye awajan ta . Kallon ta ya yi yaga se washe baki takeyi kamar gonar auduga ,shi dariya ma ta bashi ya ce " Asrah wannan murnan da akeyi haka na meye ne ?" Batare da tabashi amsar da ya tambayeta ba ta nuna mishi hannunta dake dauke da abin hannun da Tajuddeen yasa mata, riko hannun ya yi yana " wowwww, gaskiya ya yi kyau sosai wallahi inyaaa Asrah din Tajuddeen dinta " shi kanshi bakaramin kyau abin hannun ya mishi ba yanayin design din so simple ga shi na diamond ne silver color ga shi first alphabet din sunansu ne ajiki T&A ,se yabawa yaketa yi , " To kar fa ki yarda shi a garin ƙiriniya kinji ko?" Gyada mishi kai ta yi kafin ta sa ke rugawa aguje cikin gida abinta duk wanda ta hadu dashi se ta tsaya ta nuna mishi abin hannun da Tajuddeen yabata . karo ta ci dasu umaisha suna neman ta ga zanen a hannun Zoya sun raba shi gida biyu"Asrah kinga parsa ta yaga miki drawing din ki ko?"cewar umaisha tana nunawa Asrah zanen dake hannun Zoya yana a yage,turo bakinta Asrah ta yi ta ce"i don't have your time!look at my banglesssssss" ta yi maganar tana jujjuya musu hannunta matsowa duka suka yi suna so su kalla ta ruga aguje ta barsu a wajan. Part din su ta shiga da gudu , akwance ta samu anty amarya tana bacci dan ciwon kai ne yake damunta tashigo saboda ta kwanta , hawa kan gadon ta yi , shigewa jikin anty amarya ta yi tana ta mutsu_mutsu kamar bera , bude ido ta yi tana hararanta dakyar ta iya cewa " Asrah kinsan Allah zan dakeki , bakisan banida lafiya bane kinzo za ki dameni tashi ki tafi gun Ammi" Sadaf_sadaf ta mike saboda tasan halin mommynta sosai dukda yanda take matukar sonta tofa Hakan baya hana in ta yi laifi ta mata duka domin anty amarya no nonsense ne bata daukan reni tana da zafi in aka kureta . Part din Ammi ta shiga bata samu Ammi a dakin ba hakan yasa ta ɗale kan gado ta rufe kanta acikin bargo inba mutum ya lura ba ,bazesan akwai mutum akai ba. Shigowa bedroom din Ammi ta yi tana manne da waya akunnenta tana waya da Hajjatiye se buhun masifa take zazzaga mata , Ammi de kunshe dariyarta takeyi tana bata hakuri . Zama Ammi ta yi akan gadonta , Asrah jin an zauneta ne yasa ta fasa kara tana kokarin tashi . A razane Ammi ta tashi akan gadon kirjinta nadukan tara tara se "innalillahi wa'innailaihi rajuun" takeyi ko kadan batayi tunanin mutum bane awajen , tsorata iya tsorata ta yi saboda lokacin da take da cikin Tajuddeen haka yataba faruwa da ita, shine yasa hankalinta ya tashi . Asrah jin an ɗaga ta ne yasa ta ya'ye bargon ta fito kallon_kallo suka tsaya yi ita da Ammi, tafa hannu Ammi ta yi tana sallallami " ungo naki Asrah ja'ira kawai " ta faɗa tana mata daƙuwa , ita de ba ta ce komai ba se fiki_fiki takeyi da dara_daran idanunta " Kai yarinyar nan kin tsoratar dani wallahi Allah yashiryeki ! Yaushe kika shigo bansaniba?" Kwabe fuska ta yi tana kwanciya akan gadon , ta ce " ai mommy ne ta koreni " kamar zatayi kuka ta yi maganar , murmushi Ammi ta yi dama tunda ta ganta tana kumbure_kumbure tasan akwai wani zama ta yi akan gadon itama cikin kwantar da murya ta ce " Ba koranki mommynki ta yi ba , bata da lafiya ne shisaka . Idan mommynki ta yi miki faɗa kidena bata rai babu kyau kinji ko?" Gyada kai Asrah ta yi , rungume Ammi ta yi tana gyara kwanciyarta ajikinta , kallonta Ammi ta yi cike da son yar kanwar nata sauke idonta ta yi akan hannun Asrah dake dauke da abin hannun da Tajuddeen yabata , rike hannun ta yi tana ƙare mishi kallo nan ta fahimci ta inda Asrah ta samu , ajiyar zuciya ta yi aranta tana " ya Allah kai kadai kasan karatun kurma , Allah ka tabbatar da alkhari dake tsakanin Tajuddeen da kuma Asrah " Kallon fuskar Asrah ta yi taga har ta yi baccinta , ahankali ta kwantar da ita akan gadon ta rufe ta da bedsheet , ta mike ta nufi part din anty amarya . " Abida anya kinsha magani kuwa ? nasanki sarai da ƙin shan magani tashi kisha " cewar Ammi da bata dade da shigowa bedroom din ba . Mikewa zaune anty amarya ta yi tana dafe kanta ta zuro ƙafafunta ƙasa. Magani Ammi ta dauko da ruwa a glass cup ta bata,babu musu tasa hannu ta karba tasha sannan ta jinginu ajikin , makeken gadon ta na alfarma. Sosai Ammi ta kare mata kallo kafin ta girgiza kai " Abida meyesa kike saka damuwa aranki yakamata ki fawwalawa Allah komai " Wasu hawaye masu zafi ne suka gangaro mata " Anty hamdiyya dole in damu , musamman inna tuna kan cewa bazan sake haihuwa ba , karki manta fa ancire min mahaifa , har abada bazan sake haihuwa ba. Asrah ita kadai Allah ya bamu wallahi anty hamdiyya bazan boye miki ba Abdulhameed yana matukar kaunar yara nina sani komin daren dadewa ze ƙara aure saboda yasamu yara shima kuma ni bazan taɓa shiga hakkin shi ba , bazeyu ni bana haihuwa kuma in hanashi aure ba " Sosai tabawa Ammi tausayi jikinta ne taji ya yi matukar sanyi , riko hannunta ta yi ta ce " Ya isa shikenan kidena kuka , kamata ma ya yi kidinga godewa Allah , wasu fa neman ko da guda dayan sukeyi su samu amma ina Allah yasa babu haihuwa a ƙaddarar rayuwar su ,amma kefa kinga jininki aduniya , se bayan kin haife Asrah fa aka cire miki mahaifa , aduk san da kika kalleta ki dinga godewa Allah wasu neman guda daya ma sukeyi sun rasa , maganar Abdulhameed ze ƙara aure kuma ki kwantar da hankalinki ko da ze Ƙara aure wallahi bazeyi ɗan yaci mutuncinki ba, ɗan saboda yana matukar sanki, kuma namiji mijin mata hudu ne karma ki ce za ki sa wannan aranki . Ni yar uwarki ce ciki daya uwa daya uba daya nasan irin raɗaɗin da kikeji , Allah yana sane dake" Murmushi ta yi ta kwantar da kanta akan kafaɗar Ammi " Nagodewa Allah dayasa nayi aure akusa da yar uwata , aduk sanda nake cikin damuwa ke kike kwantar min da hankali ina matukar alfahari dake anty hamdiyya" Shafa kanta Ammi ta yi tana murmushi,son kanwar nata nasake ratsa ta. Uncle Hameed da tun lokacin da suka fara magana ya shigo bedroom din yake tsaye abakin kofa yana harde da hannu a kirji , dukkansu biyun babu wanda ya san da yana dakin , karasawa cikin bedroom din ya yi se sannan ne suka ganshi saboda hankalinsu ya yi nisa cikin maganar da suke tattaunawa. Durƙusawa Uncle Hameed ya yi agaban anty amarya ya rike kafaɗunta da dukkan hannayenshi biyu yasa idonshi cikin nata " Abida wallahi babu irin wannan tunanin araina , eh tabbas inason yara inason inga yarana na shawagi atare dani amma ki yarda dani bantaba sha'awar haihuwa da wata mace ba in bake ba . Kuma godewa Allah zamuyi tunda seda muka haife Asrah kafin hakan yafaru ,kinga ai muna ganin gudan jininmu tana a tare damu me ze sanyamu bakin ciki? Kuma sannan koda ace bamu haife ta ba aka cire miki mahaifa wallahi bazan taɓa auro wata matar ba ,dan saboda ta haifa min yara ba ,babu wannan burin araina dake nafara rayuwata kuma dake zan gama duk runtsi duk dadi muna atare da junanmu , fatan da zamuyi shine muyi addu'a Allah ya raya mana Asrah dinmu muga lokacin aurenta da Tajuddeen " Uncle Hameed ya ƙarishe maganar sa yana dan jan hancin anty amarya ,duk murmushi sukayi musamman ma maganar shi ta karshe da ya yi akan Asrah da kuma Tajuddeen. Ammi ranta fal da farin ciki ganin kanwar nata ta ɗan saki ranta ,sake godewa Allah ta yi da yasa kanwarta ta auri namiji da yasan yakamata arayuwarshi me kuma sonta, saboda uncle Hameed yana da saukin kai sosai kuma an hadu andace ne shida anty amarya,sede ita tana da zafi bata daukan reni amma kam tana da kirki sosai kusan halinsu daya ne ita da Ammi . Juyowa uncle Hameed ya yi ya kalli Ammi ya ce " ina matukar godiya anty da yasa ko yaushe kina me nuna mata hanya da kuma faɗa mata gaskiya " Murmushi Ammi ta yi ta ce" Allah yabarku tare bari in koma part dina na bar wancan rigimammiyar tana bacci " Mikewa ta yi ta musu sallama tafice. Gangarowa downstairs Ammi ta yi with full surprise taga yaran gidan gaba daya a hade awaje daya kusa da Abbie da alamar abu suke kallo ko kuma video call suke yi wani tunani ne ya faɗo mata a rai " to kodai da mom Rumanatu suke wayane?" ta ƙarishe maganar taname ci gaba da saukowa main part din. ( mom Rumanatu Bishara ƙanwa ce agun Abbie da kuma Abbu se kuma ita last born kuma shine uncle Hameed su hudu ne agun iyayensu. Mom Rumanatu tana aure a Katsina tare da ƴaƴanta hudu da kuma mijinta) Zama Ammi ta yi tana kallon yaran nasu yanda suke ta shan waya da mom Rumanatu gwanin sha'awa hakan kadai ze nuna maka akwai kauna me tsanani a tsakanin su ta cikin laptop din ta ji muryan mom Rumanatu na tambayar ina Tajuddeen da Asrah suke Abbas yabata amsa da "Taj yana part din shi ita kuma Asrah ni yau tunda nadawo gidan nan ma ban ganta ba"Zoya ce ta ce "dazun munga tashi ga part din Ammi" haka suka dinga hira daga karshe yaran suka watse suna mata sallama. Abbu ne ya shiga part din su saghar ya samesu suna zaune suna searching a goggle tsikayan muryanshi sukayi yana tambayar su"ina mamanku?"kallon_kallo saghar da sudais suka tsaya yi kafin Sudais ya ce"Abbu ni Wallahi bansan ina Ummah take zuwa ba kullum bata gida" girgiza kai Abbu ya yi jin abinda yaran nasu suke faɗa wato su ma gantalin da uwarsu take yi yana damunsu. Cikin kwantar da murya Abbu ya ce "karku damu in sha Allah everything will be history, in ta dawo ku ce mata Ina da Shari'a gobe zan shiga kotu da wuri" "to Abbu Allah ya taimaka" saghar da sudais suka faɗa,amsawa ya yi sannan ya juya ya fice. Se mun haɗu Monday in Allah yakaimu da rai da lafiya. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 Page 08 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ Page 08 Washe gari Abbu da wuri ya shirya dan zuwa court misalin 9:00am tunani ya fara yi na ko Hajiya hurairah ta na nan ko ta yi ficewarta dan jiya bayan ya shigo yaji shigowar ta bata nemi tazo taji ko yana lafiya ba ko akasin haka ba taje ta yi uzurin ta,shisa shima daya gama shirya wa ya fito be ko kalli inda dakinta yake ba yabar part din. me aiki ya gani tana kokarin shiga ta yi musu gyare_gyare nan ne ya tambaye ta ko taga Hajiya hurairah ta amsa mishi da"yau Hajiya da wuri ta fita tun asuba naga fitar ta"gyada mata kai kawai ya yi yasa kai ya wuce yana hasaso irin kwakkwaran matakin da ze dauka akan Hajiya hurairah domin abin nata yafara wuce gona da iri. BORNO STATE HIGH COURT " Ya me girma me Shari'a wanda nake karewa malam isah gwani ya kama abokinshi wato labaran sha'ibu yana kokarin yin lalata da matarsa Hajara , yana kokarin keta mata haddinta amatsayinta ta matar aure kuma mace , malam isah gwani yasan wannan kotu me adalci ne za'a bi musu hakkin shi ,shida matarsa Hajara shisa yakawo wannan ƙaran nan . ya me girma me Shari'a da wannan nake rokon kotu tabi musu hakkinsu , kuma labaran sha'ibu yakarbi hukunci dede da abinda ya shuka Nagode" Lauyan na gama fadin haka cikin girmamawa dakuma sanin aikinshi yasamu guri ya zauna. Yar rubuce rubuce alƙali Isma'il Bishara ( Abbu) ya yi idonshi manne da farin glass. Karewa kotun kallo nayi nan na sake fahimtar babban kotu ne ga al'umma a cike maƙil da kotun kowa ya yi shuru ya ka sa kunne ana sauraran wannan shari'ar , dakuma son jin hukuncin da alƙali ze yankewa mai laifin duk sun matsu suji . Ɗago kai alƙali ya yi bayan yagama rubuce rubuce ya ce " Kotu ta yankewa labaran sha'ibu hukuncin bulala 100 abisa kokarin yin zina da matar aure tare da cin taransa na dubu ɗari sannan kuma ze bawa malam isah gwani da matarsa hakuri." Yana kammala fadin haka ya buga guduma Aka amsa da " kotuuuuuuuuu" Mikewa ya yi polisawa da lawyer's suka bi bayanashi domin takewa babban alƙali baya har packing space din kotun bude mishi motar jami'an tsaron sukayi ya shiga , motoci goma ne suka fita a kotun don zuwa gidan Bishara . Kowa dake cikin kotun se alhamdulillah sukeyi da hukuncin da aka yankewa labaran saboda irinsu ne maciya amana da koda anbasu amana zasuci tunda ga shi yaje yana kokarin keta haddin matar abokinsa , hakan ya zama izina ga yan baya.wa'yannan sune mutanen da zaka nemi Allah yarabaka dasu domin ba abokan zama bane . BISHARA'S FAMILY Motacin da suka rako alƙali suna gama shigowa motar Hajiya hurairah yashigo Packing ta yi ta fito tunda tafito Abbu yake kallonta ranshi na ƙuna saboda tafita batare da izininshi ba duk da ba yau ta fara ba , ganin yana jefa mata harara yasa ta dauke kanta kamar bata ganshi ba ta wuce ta gabansu kanta asama , mansion din ta shiga ta ƙare mishi kallo ajiyar zuciya ta sauke ganin yaranta suna zaune suna kallon Tv a main part din dan rabonta dasu tun asubahi data fita agidan part dinsu ta nufa hankalinta kwance bata damu da tambayoyin da Abbu ze mata ba domin kuwa tana dede dashi har ta yi nisa a haura steps taji an dafa kafaɗarta juyawa ta yi dan ganin waye haka . Murmushi suka sakarwa juna lokaci da ta juyo jan hannunta Hajiya hurairah ta yi zuwa part din. Tana shiga suka tafa hade da yin shewa zama sukayi abakin gado . Hajiya khareema ta ce " aminiyata faɗamin ya ake ciki ya kukayi da boka mauzau , shafamin inji nakosa " Dariya Hajiya hurairah ta yi ta bude hadadden handbag dinta tafara fito da kayan tsubbun da boka mauzau yabatasu masu yawa sosai daga kan layoyi dakuma wasu abubuwa akulle a ledoji. Wata bak'ar leda ta dauko yana ƙunshe da wani maganin tsubbun aciki. ta kalli Hajiya khareema ta kashe mata ido ta ce " Yau din nan jinakeyi nafi kowa farin ciki , kinga nan da gobe zuwa jibi ? to labarin yarinyar da take kokarin bata miki aiki yakare batt zasu nemeta su rasa na tsawon har abada" " Heeeee kai kawata inaji dake wallahi shisa nadauki ragamar wannan aikin nabaki shi a hannun ki kafin a zo mataki na biyu" cewar Hajiya khareema tana bata hannu suka tafa , ci gaba da magana Hajiya hurairah ta yi. " Wannan maganin da kike gani acikin bakin ledar nan shine za ki san hanyar da za'ayi asashi a abincin gidan nan gabaki daya kowa yaci harta masu aiki, jami'ai, masu gadi da kuma mutanen gidan! daga zaran sunci abincin nan dake dauke da wannan maganin tofa sufa labarin su yakai monday domin bacci zasuyi sosai yanda har a shigo adauke Asrah aje akasheta ma bazasu taba sani ba se safiyar washe gari . Maganin zesasu ne suyi dogon bacci me nauyin gaske , rikeshi a hannunki" Ta faɗa tana miƙa mata sa hannu Hajiya khareema ta yi ta karbe shi tana jinjina kai cike da farin ciki. " sekuma wannan layar kinganshi nan ? acikin gidan nan za ki binne shi , tayanda ze hanasu yunkurin neman yarinyar sannan kuma zasu manta da ita na har abada ke in taƙaice miki ma babu wanda ze sake koda ambatan sunan Asrah " Jinjina mata ta yi da babban yatsar hannunta kafin Hajiya khareema ta ce.. " gaskiya hurairah kedin fa bata wasa bace , shin boka mauzau yabaki wanda yarinyar zata manta komai nata harta sunanta ?" " Eh yabani ga shi nan ma " tafada tana fito dashi acikin jaka, kamar ruwan turare yake ɗan kaɗan a kwalba gyara zama Hajiya hurairah ta yi ta soma magana " kinga wannan kuma kadan za'a saka acikin hanky se a shaƙa mata a hancinta daga zaran ta shakeshi tofa ko kanta bazata sake tunawa ba daga nan ma mutuwa zatayi saboda duk wanda ya shaƙi wannan turaren shida sake rayuwa kuma se wani ikon Allah" Ajiyar zuciya Hajiya khareema ta sauke sannan ta sa hannu ta kwashi kayan tsubbun nasu ta saka acikin yar handbag dinta ta kalli Hajiya hurairah ɗakyau ta ce" kinyi mini kokari sosai kawata , kuma in sha Allah zan cika miki burinki na mallakar dukiyar wannan ahalin gaba daya , yanzu bari in wuce in tafi in samu in adana wa'yannan kayan kar mijinki Abbu ya shigo yasamemu " tana magana tana tafiya da sauri_sauri dan batason su hadu da Abbu a hanya saboda ta lura kamar yafara zarginsu , bin bayanta ta yi saboda tarakata , sosai suke murna yau ce rana ta farko da zasu fara cin nasara akan wannan family din. Bata koma ciki ba har se da taga Hajiya khareema ta bace mata da kallo kokarin komawa takeyi idonta yasauka akan Abbu da yake daff da shigowa daure fuska ta yi itama sannan takoma ciki ta tsaya , yana shigowa babu abinda ya ce mata fa ce zaman da ya yi akan manya_manyan kujerun da suka zagaye falon nasu , ganin bece mata komai bane yasa ta shiga kitchen ta dauko mishi ruwa me sanyi ta kawo mishi sannan ta tsiyaya a glass cup. Abbu de da ido kawai yake binta takaicinta ma ya hanashi magana saboda Hajiya hurairah kamar ba zaman aure sukeyi dashi ba duk sanda ta yi niyar fita ,fita takeyi abinta ako wani irin lokaci kuma tadawo aduk sanda ta yi niya abin na matukar kona mishi rai , aduk sanda ta fita se ya mata faɗa daga karshe yakara mata da nasiha kullum cikin cewa take bazata karaba. Daukan glass cup din ruwan Abbu ya yi yasha ya ajiye duk tana zaune a kujera me zaman banza tana kallonshi. Rike haɓa Abbu ya yi ya ce" Hurairah Ina kikaje yau tunda asuba kika fita ?" Ɗan nisawa ta yi tana tuno me za ta faɗa mishi can wani tunani ya faɗo mata a rai . " Abbu ina wannan ƙawar tawa rukayya? to ita ce mamar ta ba lafiya shine ta ƙirani mukaita asibiti" girgiza kai Abbu ya yi saboda ko kaɗan be yarda da wannan maganar na taba ,dama ita inde tafita bata rasa abin faɗa uzuri kala_kala kullum da irin karyar da take mishi , mikewa ya yi yana cire babbar rigar jikinshi yarike a hannu ya ce " nasha faɗa miki na tsani irin wannan fitan hurairah ko kadan banaso amma , bazakisan banaso ba sena dau mataki akai " yawuce yabarta awajen zaune. tabe baki ta yi sannan ta fito daga part din nasu zuwa can main part din gidan ta nufa saboda kiran yaranta Sudais da Saghar da kuma yara matan ta. (wlh mata da yawa ba su dauki irin wannan fitan abakin komai ba zakaga mace ta fita aduk lokacin da take so batare da izinin mijinta ba.wata kam ma jira take yi yasa ƙafa ya fita yana sa kafa ya fita itama zata bazama nata wajen,bayan kuma hakan da mata keyi kwasarwa kanmu zunubi mukeyi duk taku daya da za ki taka Mala'ikun Allah na tsinuwa ne gareki.shin menene ribar haka kina saɓawa mahaliccinki, babban abinda yake kashe aure kenan saboda babu abinda maza suka tsana sama da irin haka musamman ma su dawo gida suna tsammanin zasu tarar da matan su agida amma ah ah bakya nan kuma fitan naki bawai da izinin shi ba hakan ne ze tunzurshi yasa ku fara samun saɓani,ba ma wannan ba wasu matan basa tunanin tsautsayi kin fita batare da sanin mijinki ba ƙila ma yace miki karki fita kika ƙi jin maganar shi wani tsautsayin ya rifta wa gari ya waya?Allah yasa mu dace ya bamu ikon gyarawa Allah yasa a fahimci wannan kuskure ne.) Ammi,Hajiya babba,Anty amarya duk suna zaune a main part suna hira gwanin burgewa,anty amarya ta warware taji sauki dama damuwar da tasawa ranta ne yake damunta haryaso ya kwantar da ita . Shigowa falon Hajiya hurairah ta yi bakinta dauke da sallama atare suka kai idonsu kanta sannan suka amsa zama ta yi akan daya daga cikin kujerun aka ci gaba da hiran da ita, daga zaran sun haɗa ido da anty amarya se ta sake mata wani munafukin murmushi da ita kadai tasan ma'anarshi ranta fes , anty amarya ta rasa gane wannan murmushin da Hajiya hurairah takeyi ma ta na menene hakan yasa ta tsame bakinta daga hiransu ta yi shuru kamar bata wajan saboda dama bawani yi sukeyi da Hajiya hurairah ba musamman da taga sun shaƙu sosai ita da Hajiya khareema. Kallonta Ammi ta yi kawai ta girgiza kai tasan sarai saboda Hajiya hurairah anty amarya ta yi shuru , Hajiya Babba ta ce" Abida ya kikayi shuru kuma?"yaƙe anty amarya ta yi ta ce " ah ah bakomai Hajiya babba" bata yarda da abinda ta faɗa tasan dalilin Hajiya hurairah ta yi wannan shurun. " yauwa dazun Abbie dinsu naji yana faɗin Asrah itama gobe za'a mata registration a makarantar su iklas tunda yanzu kundawo Nigeria da zama " anty amarya na kokarin bawa Hajiya babba amsa karaf Hajiya hurairah ta riga ta cikin suɓutar baki da ita kanta batayi tsammanin bakinta ze furta haka ba ta ce " ai karma ku wahalar da kanku kan makarantar Asrah bayida amfani" se da ta tuna abinda ta yi kuma ta datse harshen ta cike da da nasanin abinda ta faɗa, duk zuba mata ido sukayi jin maganar da ta yi wai saka Asrah a makarantar bayida amfani hakan yasa suke kallonta cike da son jin ƙarin bayanin dalilin da yasa ta fadi haka,me take nufi kenan. Yar dariyar borin kunya ta yi saboda batason suyi zargin wani abu dangane da abinda ta faɗa yasa ta ce" eh mana nide aganina bayi da amfani su Abbie ko Abdulhameed su kaita tunda kinga duk suna da wajan zuwa ni zan kaita da kaina shisa nace babu amfani " jinta kawai sukayi , tsaki anty amarya ta yi ciki_ciki ta ce " bana bukata ko ni zan kai ƴata makaranta base kin kaita ba " ta yi maganar tana gyara dankwalin kanta sannan tabar part din fuuuuu kamar zata tashi sama. kunya ne sosai yarufe Hajiya hurairah saboda yanda anty amarya ta sace mata guiwa murmushi ta yi ta ce" Allah sarki Abida kamar ranta yabaci , bari zanje in bata hakuri " kallon juna Ammi da Hajiya babba sukayi suka tabe baki , Ammi ta ce" karki damu ba se kinje ba zan mata magana " haka ta mike ta basu guri. " Allah yakyauta to" cewar Hajiya babba Ammi ta ce" ameen ameen". 5:00pm na yamma dukkansu amma fa babu Tajuddeen aciki , sun hallara a spot area Babban wajen dake cikin gidan wanda yafi girman part biyu ko uku , duk wasu kayan nau'in game babu wanda babu awajen ko ina da shi harda bangaren gym , su Jawan suna buga ball , manyan cikinsu su Abbas kuma basa ma gida sunje gidan ya'yunsu da yau wata biyu kenan da yin aurensu Sakeena da Sameera sun kai musu ziyara gidan Sakeena suka fara zuwa daga nan suka wuce gidan Sameera. Umaisha, Asrah, Rameesa,Parsa,Zoya, Iklas boji_boji sukeyi se dariya da tsalle_tsalle sukeyi cike da farin ciki , Rameesa da idonta ke adaure da ƙyelle tanata lalubawa acikin filin ko zata gansu amma ta ka sa kama ko mutum daya dakyar tasamu ta cafke Asrah, Parsa ce ta kulle mata idanunta su kuma suka boye haka suka ta wasansu har kusan mangrib suka koma ciki saboda suyi sallah . DAMATURU malam Mamman ne ya shigo gidanshi bakinshi a washe kamar ba shi ba hannunsa na rike da ledoji niƙi_niƙi ,abakin murhu yasamu Maryam tana durƙushe se hura wuta takeyi tun dazun amma yaƙi kamawa batamasan ya shigo ba , gyaran murya ya yi ,agigice ta juyo ta kalleshi. mamakine ya bayyana ƙarara akan fuskarta da ya haɗa zufa ga idonta ya yi ja saboda hayakin murhun da take kunnawa. sakaka Maryam ta yi da baki tana kallon fuskar malam Mamman da har izuwa lokacin bakin shi yaƙi rufuwa se murmushi yake . Mikewa tsaye ta yi ta gyara kodedden zaninta da take daure dashi miko mata ledar ya yi yana faɗin" Maryam matar Mamman kinsan yanda nake sonki kawai de saboda wannan yarinyar ce yasa nake jin haushinki amma yanzu dukkan ku inasonku sosai wallahi" ita de ta kasa janye idonta akanshi tsaban ruwan mamakin da yabata domin duk abinda yake faɗa ita de bawai ta gasgata bane . lura da ya yi taƙi sakin jiki dashi ne yasa ya ajiye ledojin hannunshi,yaje can bakin dakinshi ya dauko tabarma yazo ya shimfida , ya jawo hannunta ya zaunar da ita ,buɗe manyan ledojin ya yi yafito da dangwala_dangwalan kaji da suka sha ga'shi se maiƙo sukeyi ga yajin kajin daure agefe , kamshim namar kazar ne ya da ki hancin Maryam, hadiye wani yawu ta yi da se da maƙoshinta ya ce "kwatt" , nan take yawunta ya tsinke. Maryam baiwar Allah rabonta da taga irin wannan tun lokacin da suke shan soyayya da malam Mamman kafin ta haifi Asmita. Duk da yanda ranta yabiya da namar kazar amma taƙi saka hannunta aciki , malam Mamman ya ce" Maryamata kici mana saboda ke da yarmu Asmita na siyo wa'yannan kayan daɗin amma kin ƙi ci. Sa ke kallon shi ta yi murya asanyaye ta ce " dagaske Malam ka karbi Asmita amatsayin yarka ?" Jiki na rawa ya ce " kwarai ma kuwa nakarbeta kuma nagane kuskurena! Tunda na dawo ma banganta ba ina take " ya yi magana yana kalle_kalle agidan kwala kiranta ya yi" yar baba Asmita kizoki " Fitowa Asmita ta yi tana rakube_rakube saboda tsananin tsoronshi da takeji mikewa ya yi ya daukota ya zaunar da ita akan tabarman. Daga Maryam har Asmita jin lamarin sukayi bankwarakwai , cinyar kaza ya dauka ya bawa Asmita " maza ci yata , ci nama" da sauri Asmita ta karba tafara ci ,haka suka za ge suka ci kaji dakuma su kayan kwalba da malam Mamman yakawo ranar de sunci dadi sosai, da dare ma yasake kawo musu kayan daɗin suka ci suka kwanta , Maryam tana ta murna mijinta yadawo kan hanya. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ 🌹🌹*ASHE ZAMUGA JUNA*🌹🌹 Page 09 *_ story $ written _* By * _ MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️ Page 09 Washe gari As usual kamar yanda suka saba duk sun shirya cikin shiga ta uniform dinsu da ya kasance fari da maron , riga da skirt ɗan guntu se legis fari da suke sanye dashi a ta ciki, se fararen sandals da safa a ƙafafunsu ga baby hijab dinsu suna sanye dashi sunyi kyau sosai sede fah yanda suke tafiya matan su biyar yau ansamu ƙarin mutum daya wato Asrah sun zama su shida yanzu , anyi mata komai da komai zata fara zuwa yau , se murna takeyi itama yau zata cigaba da zuwa makaranta , rabonta da makaranta tunda suka baro California shisa she's very excited yau , duk sun gama breakfast , su sahil suna waje sunyi gaba. Abbu ne yafito hannunshi riƙe da car key ya ce" kuzo in kaiku " dukkansu ihu suka yi suna " yeeeeh yau Abbu ne ze kaimu school" dariya Abbu ya yi ya girgiza kai ya yi gaba suka biyo shi a baya. Dropping dinsu ya yi acikin school din yana kallonsu seda ya tabbatar sun shiga class sannan ya tafi . Shiga sukayi class din suka samu seniors din su sun shigo yan SS2 ,kallonsu sukayi sukaga babu yayyunsu maza aciki su Saghar,jawan a SS1 suke. Sudais da Salim,Sahil, sune suke aji daya da su Tajuddeen wato SS2 sede shi ya rubuta paper tare da yan SS3 shisa ya dena zuwa makarantar. Wuce seniors din sukayi suna gaishesu cikin harshen turanci. Asrah dake bayansu tazo ta wuce bata ko kallesu ba daya daga cikinsu ne ya ce " hey you come here " juyowa ta yi ta kafesu da wa'yannan mayun oiling eyes dinta tana kwabe fuska , sosai Asrah ta tafi da imanin Fu'ad Abubakar Daula ji ya yi be taba kallon yarinya me irin kyau din Asrah ba hakan yasa ya ji yana sonta , magana friends dinshi suke mishi amma shi gaba daya akalar hankalinshi yanaga Asrah. Matsowa kusa da ita ya yi ya ce " what is your name?" " am Asrah Abdulhameed Bishara by name "ta bashi amsa murmushi ya sa'ke jin yar gidansu Tajuddeen ce ya ce" good go and sit down" wucewa ta yi taje ta zauna a kusa da Zoya . Bacci yakeyi amma ji ya yi kamar ana kallonshi hakan yasa ya tashi yana Dan mutsuke ido , sauke idon ya yi akan Ammi dake zaune a gefen gadonshi ta zuba mishi idanu kamar zata cinye kauda kanshi gefe ya yi ya tashi akan gadon ya nufi toilet ya yi brush ya wanke fuskanshi ya fito ya zauna akan gadon batare da ya ɗago kai sun hada ido ba . Ammi girgiza kai ta yi dan tasan inzasu shekara a haka Tajuddeen bazece mata komai ba ta ce " ina kwana Tajuddeen?" tunda yake be taba jin kunya ba irin na yau saboda shi babu agender kunya ma arayuwarshi amma yau se yaji ya kunyata a gaban Ammi, na gaidashi da ta yi hakan yasa ya ji kamar be kyauta ba , kamar yadda yake kuma nature shi yake kullum babu walwala atattare dashi murya ciki_ciki ya ce " ina kwananki " da sauri Ammi ta kalleshi tana tantaman shin maganar nan da gaske daga bakin shi ya fito ko kuma kunnenta ne ya mata gizon jin da ta yi saboda a iya sanin ta bata taɓa jin Tajuddeen ya gaisar da kowa ba saboda hatta a makaranta an sha yin wannan case din ɗan kuwa ko mutuwa malami zeyi Tajuddeen baze taɓa gaisheshi ba,har gwara malamin da yakoyar da su a gida dake wannan ya shafi addini yana iya kokarin shi wajan cewa ya uztaz din "barka da zuwa ya hanya"shikenan iya maganar kenan har malamin ya gama koyar da su ya tafi. Bata gama wannan tunanin ba ta sake tsinkayan muryanshi yana gaisheta. Muryanta na fita da sauri_sauri ta ce" lafiya lau Taj " tundaga nan kuma shuru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa komai , matsowa kusa dashi Ammi ta yi gabaki ɗaya yanayin ta ya sauya kallo ɗaya za'a mata a fuskanci tana tattare da damuwa. " Tajuddeen jibi ne tafiyanka banason ka tafi da fushin Amminka aranka , shisa nazo na roki yafiyarka daka yafemin akan abinda na maka , kayi hakuri karka tafi dani aranka wallahi ina azabtuwa da yanda kake kin kulani da kuma sauran yan uwanka nayi maka imani da Allah babu wanda yataba sa'ka tsanarka aranshi duk muna sonka ,kaine kawai ka cire kanka daga cikinmu ban taba jin inason wani abu arayuwata ba irin kai ɗana dan Allah dan Annabi ka yafemin wallahi abinda yafaru awannan lokacin sharrin shaidan ne " folding din hannunta ta yi tana ba shi hakuri ga idonta da ke tsiyayo da ruwan hawaye , be taba tunani akwai ranar da arayuwarsa ze zo ya tsaya ya saurari Ammi ba saboda kullum laifinta yake gani ,ita ya yi holding responsible na rushewar farin cikinsa amma da yake tsakanin ɗa da uwa se Allah yasa ya ji , baze jure shareta ba har iya rayuwarsa dukda kuwa girman laifukan da ta mishi , (duk wani ɗan arziki kuma ɗan halak baze taba kaunar ganin hawayen Mahaifiyarsa ba sede kuma in wannan ɗan bayida albarka saboda duk duniya babu abinda zaka gani ka ji ko kuma ka tuna kana da ita ka ji dadi kamar mahaifiya , sune jigon rayuwarmu sunyi mana komai alokacin da bamuda komai muna naɗe acikin tsumma ta kula da mu ta yi mana duk abinda ze samu farin ciki. ta sadaukar da nata farin cikin aduk saboda inganta rayuwarmu kuma har izuwa girman mu , wallahi duk wanda yakeson gamawa da duniya lafiya to yabi Allah da manzonshi Annabi Muhammad saw sannan kuma yabi mahaifiyarsa sau da kafa domin in karasa ta bazaka taba samun wata kamarta ba har duniya yanaɗe, Allah kabamu ikon ci-gaba da yiwa iyayenmu biyayya , ya Allah kamar yanda suka faranta mana Allah kabamu ikon faranta musu Duniya da lahira .) Juyawa ya yi rungumeta ya kwantar da kanshi akan kafadarta yana sauke ajiyar zuciya , a iya saninshi tunda yasan kanshi be taɓa jin shi ajikin mahaifiyarsa ba se yau hakan yasa ya ji shi gaba daya wani farin ciki ya mamaye shi gaba dayanshi kamar ba shi ba, Ammi kam se godewa Allah takeyi da ya nuna mata wannan rana da ta kasance tare da ɗanta mafi soyuwa a gareta shafa kanshi ta yi ahankali ta furta " Ubangiji Allah ya yi maka albarka yabaka Sa'a aduk abunda kasaka agabanka ya karemin kai aduk inda zakaje ka " " ameen " kawai ya ce raba jikinsu ta yi ta ce ta ce " tashi muje dinning muyi breakfast na fara jin yunwa " har cikin zuciyar shi baya son zuwa amma bayajin ze iya ja da maganarta ayanzu , mikewa ta yi ta riko hannunshi suka fito . Duk suna zaune a dinning table anyi saving dinsu breakfast amma babu wanda yaci suna jiran fitowar Ammi ne sufara cin abinci, Hajiya khareema dama ita ba wani hulɗa takeyi da su ba yasa bata fito ba tana part dinta in takaice muku ma ba ta fiya cin abinci tare da su ba. Ammi suka hango tana saukowa daga stairs hannunta rike da na Tajuddeen ware idanunsu sukayi sosai dan son tabbatarwa shin dagaske Tajuddeen suke gani da Ammi ko de basu gani da kyau ba.idan kuwa dagaske suɗin ne ta yau ranar Sa'a ce agaresu shine abinda suka daɗe suna jiran su ga ranar da zasuga haka yau Allah yanuna musu . Har su Ammi da Tajuddeen suka iso dinning table din basu sani ba suna ta al'ajabi hade da farin ciki zama Ammi da Tajuddeen sukayi Ammi da kanta ta yi saving din Tajuddeen breakfast yafaraci batare da ya kula kowa dake wajen ba , Ammi ta ɗan kalleshi tana ɗan taɓa hannunshi ɗago kai ya yi ya kalleta yanda babu wanda zejita ta yi mishi rada a kunne " baka gaishe da Abbie din ku ba da sauran " shuru ya yi be yi yanda ta ce din ba yaci gaba da cin abincinshi ,sude duk ido suka zuba mishi Abbas, Hafiz, Ahmed se murmushi sukeyi sukansu sunyi farin cikin haka da yafaru saboda duk acikin kannensu sunfi kaunar Tajuddeen kullum basu da burin da yawuce suga suna tare dashi suna hira na farin ciki da annashuwa amma hakan beyuba . Seda ya kusa cinye breakfast din shi tukun kanshi na akasan be ɗago ba ya ce " ina kwana" gaisuwar ya yi be kira sunan kowa ba murmushi kawai sukayi suka amsa atare , haka sukayi breakfast dinsu yau na musamman duk da Tajuddeen tunda ya yi wannan gaisuwar be sake ce musu komai ba har ya gama ya mike ya yi part din anty amarya dan duba Asrah shi duk a tunaninshi tana can tana bacci bayida masaniya akan yau ta shiga school , yana daff da fara haura upstairs Hafiz ya ce " Asrah fa sun tafi makaranta itama yau ta jonasu" kallon Hafiz ya yi ya ce" okay " yawuce part din shi . Abbie ne ya kalli Ammi ya ce " alhamdulillah hamdiyya gwara da kika je kika samu kukayi magana dashi naga yafara saukowa yanzu , Allah ya sassauto mana da irin wannan zuciyar ta shi " dukkansu da ameen suka amsa amma banda Hajiya Hurairah da ranta ko kadan be so haka ba Allah_Allah takeyi a watse ta je ta samu Hajiya khareema ta shafa mata labarin abinda yake faruwa , domin hakan barazana ne ga kudirin su . Tun daga safe har yanzu da ya kasance karfe biyar saura sun kusa tashi , Fu'ad Abubakar daula ya shiga ajinsu Asrah yafi aƙirga dan kawai ya kalleta , su kam sunata murna ankusa tashi su dawo gida . Lokaci nayi aka buga kararrawar tashi driver's din sune suka zo suka daukesu zuwa gida . Misalin ƙarfe 5:30pm na yamma malam Mamman yashigo gidanshi hannunsa rike da wata atamfa me saukin kudi dakin Maryam yashiga yasameta suna zaune suna shan shayi da biredi ita da Asmita zama ya yi fuska asake ya ce " yar baba gama kizo muje mukai ɗinkin kayan kin nan dana siya miki " cike da yarinta Asmita ta ce" to baba" kallonshi Maryam ta yi ta ce" malam senaga kamar yamma ta yi da kun bari ko go...... "be bari ta karasa faɗan abinda takenso faɗa ba ya yi saurin ta ran numfashinta ta hanyar faɗin" ah ah Maryamata yau zamu kai dinki dan gobe mukayi da telan ze gama mata kayan " sam hankalinta yaki yarda da fitan da zasuyi amma gudun bacin ranshi yasa ta yi shuru , zuciyarta se sake_sake yake mata ga zuciyarta dake bugawa sosai , ka sa ci gaba da shan shayin ta yi ji tayima ba ya mata dadi ko kadan , Asmita na kammalawa ta ce" baba na gama " " yar baba tashi muje " saka mata hijabi ya yi ya dauketa suka fito har bakin kofar gidan Maryam ta rakosu se bye-bye Asmita take mata da murmushi me ƙayatarwa akan fuskanta har suka bacewa ganinta sannan ta koma cikin gida , ji ta yi abu me sanyi ya sauko mata akan kumatunta da sauri tasa hannu dan jin menene wannan ruwan hawaye ta gani aranta ta ce" to menene yasa idona yake zubar da ruwa ?Allah kadawomin dasu lafiya " ta shiga daki ta zauna. Napep malam Mamman ya tara suka shiga ciki ya fadmɗawa me napep inda ze kaisu , tafiya suka yi me matukar nisa da seda yasa Asmita ta gaji ta kwanta ajikinshi har bacci ya fara daukanta taji napep din ya tsaya fitowa ya yi da ita ya sallami dan adedeta sahun ya yi tafiyarsa , wata dankareriyar bakar jeep yanufa yana rike da hannun Asmita lokacin da ya iso motar kwankwasa gilashin ya yi aka sauke wasu murɗa_murɗan maza nagani zaune aciki fuskar su babu alamar imani , malam Mamman jiki na rawa ya ce" yawwa ga yarinyar na kawo muku ita seku ban sauran cikon kudin nata " fitowa daya daga cikinsu ya yi. ya karbi Asmita a hannun malam Mamman tirjewa tafarayi tana kallon babanta agaban idonta aka fito da kudin da suka kai kimanin naira dubu dari biyar aka ba shi, wanda yake zaune acikin motar ya ce" da farko mun baka dubu ɗari biyu yanzu ga cikon saura nan du ka yakama ka siyar mana da yarinyar dubu ɗari bakwai kenan " hannu na ɓari yakarbi kudin yana " eh hakane ranka ya dade Nagode sosai" sa Asmita sukayi a motar suka zuge gilas din motar tana kuka kamar ranta se fita ko ajikinsu suka ja motar suka tafi , se da sukayi nisa da suka ga kukan nata ze damesu suka shaka mata wani abu a hanci nan take bacci ya kwashe ta. ( kai rayuwa abin tsoro ne Allah karabamu da sharrin zuciya. ) Hankali kwance malam Mamman ya koma gida seda yakusan isa gidan tukun ya zuba kasa a jikinshi ya yi futu_futu yakoma kalar tausayi ya shiga gida abakin kofa yasamu Maryam ta doka uban tagumi tana jiransu ganin ya shigo shi kadai ne yasa ta mike tsaye dasauri ta ce" malam har kundawo ? yana ganka kai ɗaya ina Asmita?" Goge guntun hawaye ya yi ya ce" Maryamata munje munkai dinki mun fito zamu dawo taga yar baby ta ce ina siya mata acikin rububin mutane na nemi Asmita na rasa neman duniyar nan na mata amma ban gantaba" kukan kura Maryam ta yi ta cukumi wuyan malam Mamman" karya kakeyi dan iska munafuki mara tsoron Allah wallahi seka fito min da ƴata dama tunda naga ka fara son yarinyar nan zuciya ta ya rayamin wani abu mugu azzalumi kaje ka salwantar min da rayuwar yarinya " duk wannan maganar da takeyi da karfi takeyi tana kuka kuma tana damke da wuyan malam Mamman da iya karfinta, makobtansu jin hayaniya ya yi yawa yasa suka shigo , matan ne sukaje suka samu suka raba Maryam ajikin malam Mamman faduwa kasa ta yi tana kuka da birgima abin tausayi wannan zafin uwa ce kadai zatasan zafinshi in aka rabata da ɗanta . Ɗagata sukayi suka kaita ɗaki suna tambayar ta abinda yafaru dakyar ta isa sanar musu su kansu hankalinsu yatashi nan take aka bazu aka fara neman Asmita hade da yin shela acikin garin damaturu. *MAIDUGURI* Suna dawuwa gida ko part dinsu bataje ba ta nufi part din Tajuddeen , ya fito daga painting room kenan ya ji an rungumeshi durƙusawa ya yi ya iso tsayinta yana ƙare mata kallo sosai ta yi kyau da uniform din slice smile ya yi ya ce" kinyi kyau" fari ta yi da ido ta rike kugu ta ce " tajujuna let's go and play on the field" be bata amsa ba yaje jikin bedside locker ya ɗauko wata hadaddiyar camera hoto yake so ya yi mata saboda uniform din sunyi matukar yi mata kyau sosai ɗaukanta a hoto yafara se iyayi take zuba mishi shi kuma yana snapping dinta se da ya gaji dan kanshi kafin ya ce" okay go and take up your uniform" tanajin haka ta fita da gudu zuwa part dinsu. uncle Hameed na kokarin fita yaci karo da ita " Asrah har kun dawo ?" Gyada mishi kai ta yi sannan ta ce" Daddy ka ciremin uniform dina zamuyi wasa da tajujuna " janta ya yi bakin kujera ya zauna ya ajiye wayoyin hannunshi ya cire mata uniform din sannan ya dauketa yaje ya mata wanka yasa mata kaya marasa nauyi ya ce " to adawo lafiya" tun be karasa cewa komai ba tafita da gudu tana mishi bye-bye murmushi ya yi sannan ya koma ya canza kayanshi dan ruwa yaɗan taɓa shi da ya mata wanka. Wasa sukeyi a field din dagashi se ita yana koya mata gudu tun tana iya yi harta gaji tana zauna a tsakiyar filin tana turbune fuskanta daukar ta ya yi yasata awuyanshi suka koma ciki . Kowa ya gama cin abinci sun gama abinda zasuyi har sun shiga ciki an kwanta se kuma asuba ta gari . ( *BISHARA'S FAMILY MEMBERS*) *KAƊAN DAGA CIKIN TARIHIN AHALIN BISHARA* Mubarak Yousuf Bishara shine babban ɗa awajan Yousuf Bishara, Mubarak Bishara shine tsohon gwamnan jihar Borno yanada mata uku,matar shi ta farko ita ce Hajiya Badeeya sunyi auren soyayya da ita duk da lokacin mata biyu ze aura saboda yana soyayya da Hajiya hamdiyya to se aka fara auren shi da Hajiya Badeeya bayan kamar wata uku Kuma ya auro Hajiya hamdiyya tsakanin Hajiya Badeeya(Hajiya babba) da Hajiya hamdiyya (Ammi) akwai kyakkyawar fahimta suna zaman lafiya sosai kusan a tare suka samu ciki sede Hajiya babba ce ta fara haihuwa ta haifi ƴarta mace aka sa mata suna Sakeena bayan wata ɗaya Ammi ta haifi ƴarta itama mace taci suna Sameera tare suka taso yaran suna son junansu sosai saboda ganin yanda iyayen su suke zaman lafiya bayan shekara uku Hajiya babba ta sake samun ciki ta haifi na miji Aka sa mishi suna Abbas tana cikin renon Abbas ciki ya bullo tanaji tana gani tayi ciki da goyo wata tara ta sake haihuwa ta haifi na miji shima aka sa mishi suna Ahmed ,tsakanin Abbas da Ahmed be wuce shekara ba. ana haka Abbie ya sake aure ya auri Hajiya khareema tundaga nan ne kuma zaman lafiyan gidan yafara ƙaranci saboda Hajiya khareema ta tsani a zauna lafiya kuma ahakan ma Ammi da Hajiya babba basa biye mata, Hajiya khareema itama ta haife ɗanta na miji aka sa mishi suna Hafiz shekara daya da rabine tsakanin su da Abbas da Ahmed. har izuwa wannnan lokacin Ammi bata sake samun wani cikin ba saboda dama planning takeyi domin karatun da takeyi bata so ta samu ciki ya ka tse mata karatu. Su Abbas nada shekaru huɗu kwatsam se ga ciki ya bayyana ajikin Ammi tunda ta fahimci tana da ciki ta fara kokarin ganin ta zubar dashi batare da kowa yasan akwai wannan ciki din ba,duk wani nau'in maganin zubar da ciki Ammi seda tayi amfani dashi amma ciki yaƙi fita yana zaune daram dam_dam hakan yasa ta tsani cikin kamar ranar mutuwarta,yanke shawara ta yi domin zuwa asibiti a yi flushing din cikin kawai nan ne doctor da taje wajen shi ta faɗa mishi abinda za'a mata shi kuma ya kira Abbie ya sanar dashi abinda take shirin aikatawa sosai ran Abbie ya ɓaci yazo asibitin ya sameta ya dauketa suka koma gida nasiha ya yi mata akan abinda takeson yi amma ta rufe ido ta nuna mishi ita batasan wannan ciki saboda karatunta yafiye mata shi.hatta Hajiya babba babu irin shawaran da bata bawa Ammi ba amma haka taƙi sauraran su hakan kuwa ya jawo musu babban saɓani ita da Abbie.wanda har ya kusa jawo sanadin aurenta wanda se da yakai manya sun shiga cikin lamarin acikin wannan matakin da ake ciki Isma'il Yousuf Bishara (Abbu)wato ƙani agun Abbie ya yi aure ya auri Hajiya hurairah. Ammi babu yanda ta iya domin manya sunyi magana badan ta so ba haka ta reni wannan cikin amma inta kalle shi kamar ta sa wuka ta tsaga cikin ta fito dashi yabar jikinta takeji.ranar da ta haifeshi juyin duniya anyi amma taƙi ta bawa wannan jaririn nata nononta ɓacin rai da takaici ne yasa Abbie ya saki Ammi saki daya,hakan ne yasa ta nutsu bata tafi ko ina ba tana gidan saboda jegon da takeyi Hajiya babba ce tasamu ta shawo kanta da kyar ta fara shayar da shi ranar suna yaro yaci suna *TAJUDDEEN* nan ma da kyar aka samu Ammi ta yi hoto dashi a ranar sunan.haka Ammi ta dinga nunawa yaron nan tsana da kuma halin ko in kula in yana kuka ko kadan bata damu da daukan shi ba.Tajuddeen nada wata uku Hajiya khareema ta sake haihuwa ta haifi yara yan biyu maza wato Salim da Sahil bata jima da haihuwar su ba Hajiya hurairah ta haifi na miji itama aka sa mishi suna Sudais duk babu rata a tsakanin su. Hajiya khareema ganin Ammi bata wani damuwa da Tajuddeen yasa ta daukeshi taci gaba da renon su tare shida su Salim da Sahil nan ne tasamu daman cusawa yaron ƙiyayya,tun yana karami kullum se ta faɗa mishi yanda aka sha fama da Ammi kafin ta yarda ta haifeshi har ya zama wa Tajuddeen kamar karatu kullum se ta maimaita mishi domin so takeyi maganar ya samu guri ya zauna dam acikin zuciyarsa.aikuwa haka akayi yaro yafara girma da wasu irin murɗaɗɗun hali da shegen taurin kai wanda ko ita kanta uwar riƙon nashi bayayi mata magana sosai ita dasu Abbie se suka fara tunanin ko de bebe ne baya magana.domin har ya kai shekara hudu baya wani magana kuma lafiyarsa kalau.daga wa'yannan shekarun ne fa Ammi ta fara kokarin jawo shi ajikinta domin farat daya taji son ɗan nata ya shiga xuciyarta lokacin tana da cikin jawan sede time is too late Hajiya khareema ta riga da taci nasara akanta domin ta juyawa Tajuddeen tunani ta hanyar makircinta ko da Ammi ta kira shi ba ya zuwa ko kusa da inda take hakan yasa hankalin Ammi yafara tashi danasani yafara ɗawainiya da ita. Kusan tare suka sake haihuwa Hajiya hurairah ta sake haihuwan namiji me suna Saghar,Ammi kuma ta haifi santalelen yaronta me kama da Tajuddeen wato Jawan. Haka rayuwa yaci gaba da tafiya.bayan wasu shekaru uncle Hameed ɗan karamin ƙanin su Abbie ya yi aure ya auri kanwar Ammi wato Abida bayan anyi aurensu ta samu ciki kusan sau uku amma suna zubewa sakamakon matsala da take dashi a mahaifarta.daga karshe de itama atare duk su hudun suka samu ciki abun burgewa kamar wa'yanda suka haɗa baki.yaran mata dukkansu suka haifa,hajiya babba ta haifi Rameesa,Ammi kuma ta haifi Umaisha,Hajiya khareema kuma ta haifi Iklas, Abida da suke kira da anty amarya kuma ta haifi kyakkyawar ƴarta aka sa mata suna *ASRAH* amma sede ba a Nigeria ta haife ta ba saboda bayan aurensu basu jima ba suka koma California da zama saboda aikin uncle Hameed.Hajiya hurairah ta haifi Zoya haka suka reni ya'yansu cike da so da kauna bayan shekara ɗaya Hajiya hurairah ta sake haihuwar ya mace me suna Parsa. *WANNAN SHINE KAƊAN DAGA CIKIN TARIHIN AHALIN BISHARA SE NAN GABA ZAN KAWO MUKU SAURAN TARIHIN NASU NAN NE ZAKUJI LAIFI NA BIYU DA AMMI TA SAKEYIWA TAJUDDEEN DA YASA HAR YA ƘULLA CE TA* Mubarak Bishara tsohon gwamnan jihar Borno yanada mata uku ... Matarshi ta farko ita ce Hajiya badeeya tana da yara kamar haka Sakeena ita ce babba se Abbas se Ahmad, Rameesa. Se matarshi ta biyu ita ce ta Hajiya hamdiyya tanada yara hudu sune... Sameera se Tajuddeen , se kuma jawan se yar autarta Umaisha. Se matarshi ta uku ita ce Hajiya khareema yaranta sune Hafiz , se twins Sahil da Salim sekuma Iklas. Alƙali Isma'il Bishara matarshi guda ɗaya ce Ita ce Hajiya Hurairah tanada yara hudu sune .. Sudais, Saghar,Zoya ,parsa Doctor Abdulhameed Bishara matarshi daya tal tilo ita ce Abida suna da yarinya sunanta Asrah. *Karku manta da hakan* Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 Page 10 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ Page 10 Yau babu inda sukaje ana hutun public holiday ba makaranta suna gida se rashin ji da suka ishi mutane dashi ga ɓarna kala da iri da sukeyi suna ɓatawa fatime da kaltume suna gyarawa , Ammi , Hajiya babba da anty amarya kuma basa gida sunje gaishe da kanwar Hajiya babba tayi rashin lafiya kwananta biyu a asibiti shine sukaje gaida ita Abbie kuma ya tafi meeting da ministan tsaro Abbu na kotu haka uncle Hameed ma yatafi hospital daga Hajiya khareema ( Ammuh sunan da suke kiranta kenan ) se Hajiya Hurairah (ummah suke ce mata ) su kadai agida se yaran Abbas hayaniyarsu ya dameshi hakan yasa ya musu magana amma sun ƙi de nawa da ya gaji kawai ya kwanta akan kujera ya zuba musu ido , musamman Asrah da Zoya da Umaisha,parsa sunfi kowa ƙin ji , Hafiz da Ahmad kam ma sun gagara ce musu komai. Shigowa falon ya yi yaga yanda suka hau kan kujeru suna ihu suna tsalle " dalla kuma mutane shuru "ya daka musu tsawa suna ganin shine kuwa duk suka zazzauna akan kujeran sukayi mukui kamar basa gidan duk sun shiga rigar nutsuwa ɗan suna matukar tsoron Tajuddeen saboda ba shiga harkansu yakeyi ba , Hafiz ne ya yi dariya ya ce " yan renin hankali wato mu kuka rena da kunci gaba ai " nan ma shuru sukayi . Karasowa falon ya yi ya zauna yaja hular riganshi ya rufe mishi fuska sannan ya maƙala heaadphone a kunnenshi , se yanzu su Abbas sukaji gidan yadawo dede dasu Asrah suka nutsu suma suka fara hiran makaranta domin Abbas da Ahmad,Hafiz suna University . _____" duk abinda ze faru gwara yafaru yau kawai ayi awuce wajan muje next step ayau ba se gobe ba yarinyar nan zata bar gidan nan " cewar Hajiya khareema dake zaune akan lallausan Chinese carpet me laushin gaske a gerden suna zaune ita da Hajiya Hurairah sunata kulle_kullensu sun gama tsayar da mafita kan cewa yau zasu sa a dauke Asrah komai sun tsara shi yanda yakamata jira sukeyi a daura abincin dare. 6:50pm Su Hajiya babba basu suka dawo ba har se bayan mangrib sun dawo sun samu angama komai na abincin dare an jera akan dinning ma'aikatan gidan duk an kaiwa kowa abincinsa wanka sukayi suka fito dinning . Duk sun hallara a kan kujeran cin abincin ansawa kowa nashi , Abbie ne ya kalli fatime ya ce" ina Hurairah da khareema?" ta bashi amsa da" sun ci nasu kafin ku dawo " gyada kai ya yi sannan kowa yafaracin abinci ,babu abinda kakeji se karan cokula kowa ya nutsu ana cin abinci ,suna gama ci suka farajin idanunwasu yafara musu biji_biji alamun bacci haka sukayi sallama kowa ya wuce bangarenshi , suna shiga ko minti biyu basu ƙara ba wani irin nannauyan bacci ya daukesu , daga yara manya masu aiki kowa seda ya yi wannan doguwar baccin . Ammuh da umma ne idonsu biyu . Fitowa sukayi sadaf_sadaf suka fara bincika gidan ɗan tabbatar da kowa ya yi bacci aikuwa kamar yadda boka mauzau ya faɗa musu hakanne ya kasance , komawa ciki sukayi suna dariyar mugunta daukan waya Umma ta yi ta kira number wani me suna Black yana dagawa ta ce " ku karaso duk sunyi bacci " banji me aka faɗa mata ba ta dayan bangarenta kawai naga ta ajiye waya tana murmushi tafawa sukayi ita da Ammuh. Karfe 10:00pm dede na dare wata bakar mota ta shigo gidan wasu masu bakaken kaya fuskokinsu duk rufe da mask suka fito suka shiga cikin mansion din da bindigu a hannunsu kai tsaye wajan Umma da Ammuh suka nufa su suka kaisu har part din anty amarya bude bedroom din sukayi uncle Hameed da anty amarya suna kwance sun sa Asrah a tsakiyar su , dariya umma da Ammuh sukayi kafin umma tasa hannu ta dauko Asrah ta mikawa daya daga cikin yan kidnappers din da suka dauko ya karbeta yana kallonta mika mishi wannan kwalban turaren ta yi suka fito daga part din zuwa downstairs hankalinsu kwance bayanin yanda zeyi amfani da shi ta yi masa sannan ta sake faɗa musu da su tabbatar da sun kasheta karsu yarda su barta da rai suka amsa da to suka sa ta a motar suka ja suka tafi da Asrah dake baccinta peacefully. Komawa ciki sukayi suna sauke ajiyar zuciya abinsu sukaje suka kwanta kamar basu san komai ba. Tafiya sukayi me nisa sosai suka iso gurin wani daji kafin suka faka motar su, ogansu ne yafito da wata karamar wuƙa se sheki yakeyi ya seta dede wuyan Asrah ze yankata dasauri daya daga cikin yaranshi ya rike hannunsa " no boss karka kasheta yanzu fa samun wannan yarinyar da mukayi fa shima wani ƙarin samun kudine agurinmu " duk zuba mishi ido sukayi ogan ya ce " kamarya kenan ? ta ya zata zama ƙarin samun kudin mu?" " Boss kar mu kashe yarinyar nan kaga su fah 4million suka bamu akan mu sace ta mu kasheta . kasan Mark yana safaran yara mata zuwa Lagos a gidan karuwai kawai muje mu siyar mishi da ita se mu mishi bayani daga gidan da take saboda ya gudu da ita adaren yau domin in suka kai gobe a Maiduguri za'a iya kamashi" jinjina kai boss din ya yi dan gaba dayansu sun gamsu da maganar shi ya kalli Asrah kafin ya maida kallonshi kan yaron nashi " ya ce bawai naki ta naka ba kasheta fa sukace muyi kar kuma ta tona mana asiri " fito da kwalban da Umma ta bashi ya yi ya ce" ai inde da wannan magana ya ƙare " yafaɗa yana nuna musu kwalban dukkansu dariya sukayi suna jinjina basira irin nashi fito da hanky ya yi ya ɗiga turaren ajiki sannan ya shaƙawa Asrah abun wani irin miƙa ta yi da seda ta sandare idanunta suka firfito waje bakinta yafara fitar da kumfa , tsorata sukayi hankalinsu ya tashi gani suka yi kamar guba suka bata tana kokarin mutuwa goge mata bakin sukayi sannan suka tsura mata ido , ahankali_ahankali ta fara komawa normal kafin daga baya taci gaba da baccinta . Jan motar sukayi izuwa can bayan gari inda zasu samu Mark din nan sukayi cinikin Asrah yabasu 1million suka tafi suka bar mishi Asrah. Kallon Asrah mark ya yi sannan ya maida kallon shi kan Asmita da itama take kwance agefe tana bacci ga wasu kananan yara da su ma sun kai rai goma suna kwance Suna bacci nan yafara shirin barin garin cikin gaggawa. Asuba ta gari . Tashi uncle Hameed ya yi yaga babu Asrah a tsakiyar su amma hakan be dameshi ba saboda yasanta wata rana inta riga su tashi tana zuwa part din Ammi ko Hajiya babba , tashin anty amarya ya yi akan taje ta yi sallah shi ze tafi masallaci saboda sun kusan makara ma , mikewa ta yi tana sallati lokacin da taga Asrah bata bed din girgiza kai ta yi kawai ta mike tashiga toilet ta dauro alwala uncle Hameed kuma yafice yasan su Abbie suna jiran shi suje masallaci duk suna main falon gaba dayansu su ka wuce masallaci . Bayan sun dawo ma sukaci gaba da barci se 10:00am sukayi wanka suka fito saboda ayi breakfast, duk suna kan dinning gaba daya ahalin gidan banda mutum biyu Asrah da Tajuddeen,shima be jima ba yafito yazo ya zauna ,yau tsaban ruwan munafurci umma khareema da bata cin abinci a dinning dan taga reaction din anty amarya yasa ta fito ita kadai se murmushi take . Ba su fara cin abinci ba anty amarya ta zuba ido tana jiran taga fitowar Asrah amma shiru bama ita kadai ba duk wani dake gurin ita suke jira Abbu ne ya ce " nikam Abida Asrah bata farka bane " murmushi anty amarya ta yi ta ce" ai tama rigamu farkawa tana part din Ammi ne " ɗago kai dasauri Ammi ta yi ta ce" gaskiya yau banga idon Asrah ba kwata_kwata batazo min ba sede ko In ta kaiwa Hajiya babba ziyara " yar dariya sukayi . Kallonsu gabaki daya Hajiya babba ta yi ta ce" no rabona da Asrah tun daren jiya da muka rabu a dinning batazo part dina ba " cak lokaci daya murmushin dake kwance akan fuskar anty amarya ya dauke ta ce " gaba dayanku kunce Asrah batazo wajanku ba to ina take kenan " ganin tana kokarin ta da hankalinta ne yasa Abbie ya ce" kwantar da hankalinki Abida kinsan Asrah fa yanzu haka tana wani gurin ! Abbas,Hafiz , Ahmed ku je ku dubomin Asrah" cike da bin umarni suka mike suka rabu suka fara dubata a cikin gidan . Su Kuma suna dinning sunyi shuru suna jiran dawuwan su Ahmad da haryanzu basu dawo ba ,anty amarya de hankalinta ya kasa kwanciya kawai so takeyi taji ance mata anga Asrah, haka Tajuddeen ma yarasa gane wa kanshi tunda yatashi yakejin zuciyarshi na yawan tsinkewa . Bayan kamar 30mint suka dawo suna haki domin zagaye Bishara house kadai in akace kayi an haɗaka da babban aiki Hafiz ne ya ce" Abbie ko Ina mun duba acikin gidan nan lungu da saƙo amma bamu ga Asrah ba hatta masu aiki mun tambaya sunce basu ganta ba suma" Duk tashi tsaye sukayi a matukar tashin hankali jin abinda Hafiz ya faɗa , daura hannu aka anty amarya ta yi ta ce" nashiga uku na, ina Asrah tashiga? " jawota Hajiya babba ta yi ta riketa tana " karki damu za'a ganta kinsan gidan nan da girman gaske duk yanda akayi tana ta wani gurin " ba shiri daga manya har yaran suka watsu aka fara neman Asrah , babu irin nemanta da ba'a yi ba amma shuru babu ko alamar ta acikin gidan kusan awa daya ana nemanta . Dawuwa falo duk sukayi akayi cirko_cirko kiran jami'an tsaron gidan Abbu ya yi ya ce musu ko sunga wani bakon fuska, suka ce mishi sude karfe uku na dare suka tashi kuma basuga wata alamar kan cewa an shigo gidan ba . Ana cikin haka kenan wata me aiki da ita take shara agidan ta shigo da gudu har kamar zata faɗi murya na rawa ta ce" ranka ya dade naga wani takun sawu da ban yarda dashi ba " tashi sukayi gaba daya suka bita tundaga bakin ainihin main part din gidan har zuwa cikin compound akwai sawun tafiya kusan na mutane hudu kuma sawun takalmin ranbut ne da alama akwai inda suka taka laka basu sani ba hakan yasa shatin takalminsu ya bayyana hakan ne ya tabbatar musu da har cikin gida aka shigo aka dauke Asrah amma babban abinda yafi daure musu kai shine wani irin bacci sukayi haka da har aka shigo aka dauke Asrah babu wanda yasani. Duk suna cikin tashin hankali da baze iya faɗuwa a baki ba musamman ma anty amarya da takejin jikinta ya yi mata nauyi sosai ga kuma zuciyarta da se tafarfasa yakeyi kamar ana watsa mata garwashin wuta akai daurewa kawai takeyi amma harta su ɗin ganin su takeyi bibbiyu. Few hours latter Manya_manyan jami'an tsaro masu mukami gaba da an hallara a Bishara house se bincike akeyi lokaci daya cikin Umma da Ammuh yafara kaɗa ƙugi ,alama ummah tayiwa Ammuh akan taje ta samu ta binne wannan layan da boka mauzau ya bayar saboda dakatar da binciken. part dinta tashiga ta bude locker data ajiye layar aciki kamar wasa taga wayam bakomai aciki nemanshi tashiga yi sama ko ƙasa amma babu shi babu dalilinshi hankalinta ya tashi tarasa ina ta boye zaman yan bori ta yi akasa tama ka sa fita daga dakin .(abinda ya faru shine bayan gari ya waye duk suna dinning zasu yi breakfast kaltume ta shigo part din Ammuh saboda ta yi aikinta na yau da kullum da ta saba tana cikin yin shara kawai idonta ya sauka akan laya yashe a ƙasa kwata_kwata ranta be yarda dashi domin tasan mugun halin Ammuh tana tsoron karta cutar da bayin Allah hakan ne yasa ta daukeshi da sauri tasaka a hularta ta fita a part din ta shiga kitchen ta dauki kalanzir da ashana ta fito backyard ta duba lungu da saƙo taga babu kowa.ta fito da layar ta ƙona shi ƙumurus bata bar wajan ba se da ta tabbatar da wutar ya mutu ta share wajan gudun kar ayi zargin wani abu, se a sannan ne hankalinta ya samu kwanciya.) Bayan anty amarya Tajuddeen yafi kowa shiga tsantsan madarar tashin hankali gaba daya ya fita a hayyacinsa idon nan ya yi ja sosai hatta eyeballs din shi da suka kasance golding in color seda suka canza kala.domin duk duniya in aka cire Allah da Manzonsa tofa Asrah ce mutum ta farko da yake matuƙar haukar so,yafi sonta sama da son da yake yiwa kanshi. ji ya yi gaba daya komai baya mishi dadi zufa ne yake zubo mishi ta ko ina ya ma rasa ina ze tsoma ranshi har yanzu yama ka sa yarda da wai ansace Asrah bata gidan daga zaran yarufe idonshi ganinta yakeyi ta nayi mishi gizo runtse idon ya yi kawai. Yau Bishara house ba lafiya su Zoya suna part din ya Abbas suna kuka , su Abbas din kuma suna main part inda ake ta bincike, Hajiya babba da Ammi suna part din anty amarya suna lallashinta da bata baki kancewa in Sha Allah za'a ga Asrah. Itade jin su kawai takeyi amma tunaninta yatafi wata duniya. dede da hawaye babu a idonta dama in tashin hankali yakai tashin hankali hawaye ma kanshi nemanshi zakayi karasa inbanda girgiza kai babu abinda anty amarya takeyi se kukan zuci da takeyi ta ciki. Abinka da masu hannu da shuni akasar Nigeria nan take duk wani hanyar shiga da fita dake cikin Maiduguri anrufe. babu me shiga babu me fita nan take aka fara yaɗa hotunan Asrah a kafafen sada zumunta ana cikiyarta da alkawarin duk wanda ya samota za'a bashi kyautar naira millon goma . Kamar wasa tun safe ake neman Asrah har karfe sha daya na dare shuru babu ita babu alamarta gaba dayansu babu wanda ya iya sawa cikin shi wani abu duk basa cikin nutsuwar su. Washe gari ma akayi neman duniyar nan anyi kuma har lokacin ba'a bude Maiduguri ba , gaba daya kasar Nigeriya ansa tsaro ana nemanta amma shuru ba'a yi nasara ba , acan kuwa gida yanda suka ga rana haka sukaga dare kananan yaran ne kawai sukayi bacci se wa'yanda sukasa aka dauketa din. Duk suna zaune afalo sunyi tagumi sunyi jugum_jugum har yar rama seda sukayi hankalinsu atashe anty amarya kam rabonta da magana tun jiya sede ta yi ta binsu da ido. Abbie ne yacewa uncle Hameed yakaita daki ta kwanta inta ci abinci. Riko hannunta ya yi yadagata suka fara tafiya ji ya yi ta tsaya kallonta ya yi yaga tazuba mishi ido ga jinin dake fita a hancinta sekuma tasa hannu a setin zuciyarta idanunta yafara rufewa da sauri uncle Hameed ya rungumota jikinshi ya yi dede da daukewar da numfashinta ya yi cak rai ya yi halinsa . Innalillahi wa'innailaihi rajuun 🥺🥺🥺 Se mun haɗu gobe in mai duka ya kaimu da rai da lafiya. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ Share , comment and like https://chat.whatsapp.com/DuXNzdLkDfm1U0dZg9YE73 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 Page 11 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ Page 11 Cikin kiɗima da tashin hankali duk suka rufu akanta suna kiran sunanta "Abida! Abida! Abida" amma ina ta yi nisan da bazataji kira ba domin kuwa babu alamar rai ajikinta, Hajiya babba ce ta sunkuya agabanta ta daura kanta asetin zuciyar anty amarya bugawa da karfi ta ji yake yi da sauri ta kalli uncle Hameed ta ce"ayi gaggawan kaita asibi......"kafin ma ta iddasa maganar ta uncle Hameed ya suri anty amarya ya yi waje da ita a hannu , driver's kusan hudu ne suka rufa mishi baya daga cikinsu ne yabude mishi back set ya sakata aciki driver yaja motar suka wuce asibiti, su Abbie dasu Ammi duk bin bayansu sukayi hankalin Ammi ya yi kololuwar tashi ganin halin da kanwarta take ciki wanda ita kadaice tarage mata afadin duniya. After one hour Doctor ne yafito daga dakin da akayi admitting din anty amarya ya ce" she's out of danger now sede kubita a hankali kar adinga bata mata rai , ta kamu da ciwon zuciya na farat daya , zuciyarta ze iya bugawa idan har yaci gaba da fuskantar kunci da tashin hankali kuma dole ku dinga kasancewa tare da ita gudun kar a barta ita daya ta faɗa tunani . Kudinga tayata hira domin dauke mata kewa Allah yabata lafiya" duk jikinsu ya mutu jin anty amarya ta kamu da ciwon zuciya dama tana cikin damuwar rashin haihuwa ga kuma yarta daya tilo data mallaka aduniya ansace ta. Dakyar suka iya amsawa doctor da ameen sannan suka shiga ciki tana kwance tana baccin wahala gaba daya ta tane sosai ta yi fayau kamar ba jini ajikinta bacci takeyi amma hawaye ne yake fitowa daga idanunta zama kusa da ita uncle Hameed ya yi hawaye na zubowa daga idonshi tausayin kansu ne ya kamashi da kuma tausayin matar shi na irin halin da take ciki sun yi rashin babban farin cikinsu da in sun kalleta suke jin sanyi da kwanciyar hankali a tare dasu.ita kadai suka mallaka a duniyar nan ga shi to mara imani sun dauketa. Abbie ne ya tsaya kusa da uncle Hameed ya dafa kafardar shi cikin sassauto da murya ya ce "in sha Allah za'a ganta" kiran waya ne yashigo wayar Abbu dubawa ya yi yaga DPO ne da sauri ya yi picking , a dayan bangaren aka fara magana"ranka shi dade !a iya binciken mu mungano bawai aikin enemies bane , daga shekaran jiya zuwa jiya ansace yara ƙanana mata sama da goma , daya a Damaturu uku a pataskum , uku a biu sekuma hudu a nan Maiduguri harda yar gidanka itace cikon na goma din kuma binciken mu ya nuna mana yaran nan da masu garkuwar basa cikin garin Maiduguri amma duk inda suka shiga zamu nemosu in Allah ya yarda"Abbu dake tsaye ne yasamu guri ya zauna zufa na tsatsafo mishi be iya cewa DPO komai ba kawai ya kashe wayar kallon shi Abbie da uncle Hameed sukayi dasu Hajiya babba ganin reaction dinshi tambayanshi suka shigayi , "babu komai" ya ce musu jan hannunshi Abbie ya yi sukayi waje nan Abbu ya kwashe duk yanda sukayi da DPO yafaɗa mishi.shi kanshi Abbie jin yara har goma aka sace hankalinshi yatashi sosai , waya yadaga ya kira gomna sukayi magana sosai sannan ya kashe. Yau kwanan anty amarya biyu a asibiti , kuma har izuwa yanzu ana binciken neman yara mata goma da aka sace amma shuru babu su babu alamar su kamar ba sacesu akayi ba makwamusan sunada matukar basira sosai basu bar alama ko sheda ƙwalli daya ba wanda za'a kamasu ,har suka isa inda zasu isa cike da basira babu wanda yaci nasarar kamasu saboda ba haka suka zauna ba harda tsafi a lamarin kwamushen su shisa ba'a taba kamasu. Bayan an sallame su sun dawo gida ana kulawa sosai da anty amarya kullum Tajuddeen na tare da ita duk da rashin son yin magananshi ga kuma abinda ya hadu mishi na rashin Asrah hakan ne yasa ya dauwa kanshi alkawarin cewa inya zama babban soja shida kanshi ze nemo Asrah aduk duniyar da take sannan ya kashe duk wanda yake da sa hannu a saceta ,gaba daya ya zama kamar wanda beda lafiya ji ya yi ma zama acikin gidan batare da itaba ya ishe shi hakan yasa ya gama shiryawa gobe ze bar kasar kuma ya fadawa Ammi akan ta faɗa wa Abbie , yanzu ma yazo wajen anty amarya ne yana tayata zama dukda akwai mutane atare da ita saboda inba bacci ba ba'a barinta ita kadai tadena magana sosai tadena shiga cikin mutane komai dinta ya canza , su Saghar duk suna tare da ita haka anty Sameera da anty Sakeena suma kusan kullum se sunzo gidan . Haka de gidan yakoma kamar gidan zaman makoki. Washe gari misalin ƙarfe goma na safe Tajuddeen ya gama duk wani shirin da zeyi na tafiya kowa an hallara a falo saboda rakashi airport ,fitowa ya yi sanye da wandon sojoji da bakar riga me hula ya rufe fuskarshi dashi falon ya shiga ya zauna kusa da Hajiya khareema (Ammuh) nan suka fara mishi addu'ar samun nasara akan karatunshi, tashi ya yi yaje gaban anty amarya ya tsuguna ya rike hannunta yana kallon cikin idonta ya ce"Anty amarya nayi miki alkawari da hannuna zan dawo da Asrah cikin wannan gida,ko min daren dadewa ina me tabbatar miki da zamuga juna , ki yarda dani " shafa kanshi anty amarya ta yi tana yar murmushi ta ce "na yarda dakai Tajuddeen nasan duk inda Asrah din ka take zaka dawo mana da ita in Sha Allah , zan zuba idanu domin inga wannan rana idan har Allah ya aramin tsawon kwana , Allah yabaka Sa'a akan karatunka" murmushi kawai ya yi ya mike ,Abbie ya zubawa Tajuddeen ido yanaso yaga ko ze mishi magana ko bazeyi ba , kallon Abbie Tajuddeen ya yi ya taka zuwa inda suke tsaya batare da ya ce musu komai ba da fa kafaɗar shi Abbie ya yi yana murmushi ya ce" nasan zaka sani alfahari arayuwata da kowa in ya ganka zece wannan ɗan Mubarak Bishara ne I have trust in you" murmushi kawai ya yi. Ammi na zaune ta yi shuru ji tayi dama ace kar ya tafi."Ammi" ya kira sunanta murya akarye dagowa ta yi ta kalleshi mika mata hannu ya yi, ta rike ya dagota tsaye sannan suka rungume juna kusan minti biyu , addu'a sosai Ammi ta yi mishi saketa ya yi yaje ya rungumi Hajiya khareema se goge hawaye takeyi " son zanyi kewarka sosai" " me too Ammuh na "murmushi Hajiya khareema ta yi ta ce"ka kulamin da kanka sosai domin na damu da kai da kuma rayuwarka!"gyada mata kai ya yi. Hajiya babba ma sosai ta yi mishi addu'ar samun nasara arayuwa ya amsa mata. Fitowa sukayi su Abbas ne dasu Abbie ne suka rakashi airport, fita ya yi a motar yana kokarin nufan wajen jirgi, bin bayanshi Abbas da su Hafiz sukayi riko riganshi Abbas ya yi, juyowa Tajuddeen ya yi ya fuskance su " Tajuddeen mudinma fushin da kakeyi damu na ba gaira ba dalili dashi zaka tafi azuciyarka ba zaka rungumi yan uwanka ka musu bankwana ba?"buɗe musu hannu ya yi dukkansu suka rungumeshi can ƙasan makoshinsa ya ce"zanyi missing naku" suma suka ce "muma haka amma duk end of month zamu dinga kawo maka visit in Sha Allah" haka suka rabu akan idonsu ya shiga cikin jirgi after few minutes jirgin yatashi. Ajiyar zuciya sukayi suka koma motar yau zasu ji gidan wani iri ba Asrah ba Tajuddeen. Haka rayuwar gidan yaci gaba da kasance babu wani walwala sosai atare dasu, yau sati biyu kenan da dauke Asrah kuma haryanzu anata bincike amma shuru sede muyi addu'a muce Allah ya bayyana su. Lokacin da Fu'ad Abubakar Daula ya samu labarin an sace Asrah kamar zeyi hauka, bori da faɗe_faɗe babu irin wadan beyiwa mahaifin shi ba Abubakar Daula kan cewa lallai se yasa an samo mishi Asrah din shi ko kuma shi ya bazama duniya ya nemota dakyar Abubakar Daula ya shawo kan Fu'ad ya nutsu gaba daya ya tarwatsa bedroom din shi ya jijjima kanshi ciwo Abubakar Daula ne ya ce "Fu'ad karka damu zan sa a nemo maka Asrah amma ba yanzu ba, se bayan komai ya lafa tukun dan banaso ayi tunanin akwai hannunmu acikin saceta da akayi saboda kowa yasan irin gaban dake tsakanin mu da su just calm down"ya faɗa yana dafa shi,zubewa akan guiwowin shi Fu'ad ya yi rai a matukar ɓaci batare da ya ɗago kai ya kalli Abubakar Daula ba ya ce"dad leave my room bana san ganinka just leave me alone" "Fu'ad I promi....."kafin ya karasa maganar shi afusace Fu'ad ya waigo ya kalleshi ya ce"get the hell out of my room I said I don't wanna see you kafice min da gani kawai"Abubakar Daula sanin halin ɗan nashi ne in be samu abinda yakeso ba yanzu se ya kusan tayar mishi da karamin haukanshi hakan yasa ya fice simi_simi a dakin. Bin bayan shi da mugun kallo Fu'ad ya yi kafin ya daga kai ya kalli celling din dakinshi da karfi ya ce"shin kina ina neeeeeeeeeee Asrah? aina zan ganki?waye ya sace mini future wife dina Wallahi koma waye se ya yi da nasani arayuwarshi domin ni Fu'ad Abubakar Daula bazan taba kyale shi ba" Kamar wani zararre haka yake magana kamar da wani a dakin, juyawa ya yi ya kalli yamma da kudu sannan ya ce "noooooooo! bazeyu ba ni Fu'ad Abubakar Daula nayiwa kaina alkawarin ni zan fara ganin Asrah komin daren daɗewa se munga juna,bazan taɓa bawa Tajuddeen damar samunta kafin ni ba,dole nine zan fara nemo Asrah sannan in aureta.tabbas hakan ne ze faru hhhhhhhhhhhhhhhhh"ya gama maganar yana kecewa da wata mahaukaciyar dariya.tabbas Fu'ad yana da matsala a kwakwalwar shi wanda shisaka komai ya yi yake ganin a dede yake. Tofa ana wata ga wata dukkanin su biyu sun daukarwa kansu alkawari me girman gaske wanda ..... Fu'ad Abubakar Daula ya yi wa kanshi alkawarin shi ze fara samo Asrah,shi ze fara haɗuwa da ita komin daren daɗewa. A yayinda Tajuddeen Mubarak Bishara ya dau wa kanshi alkawarin shi ne ze dawo da Asrah cikin rayuwar gidansu shine nan ze kawota gida komin daren daɗewa. Shin waye ne ze fara haɗuwa da Asrah a rayuwa?shin Asrah zata rayu?shin su Hajiya hurairah da Hajiya khareema zasu cimma burinsu?. Ku biyoni domin jin yanda zata ka ya. *LAGOS* A FAFA Anguwar afafa, Babban anguwane da ya amsa sunansa acikin Lagos inde harkan karuwanci ne tofa babu inda yakai afafa babu irin tsiyar da ba'a tsulawa awannan wajen daga karuwanci,damfara,sata,yan rawa,shaye_shaye safaran mata ,renon kananan yara su girma suma ajefasu a harkan karuwancin manya_manyan jiga jigan karuwai ne a wajan,duk wanda yashigo wannan anguwar tofa yasan babu mutanen kirki aciki sede ko shima holewa yazo ayi dashi,gidajen karuwai ne birjik da gidajen gala komai anayi a Afafa,duk inda zaka wuce sekaga mata atsaye ko azaune dukkansu babu me kayan arziki ajikinsu ga masu shaye shaye agefe wasu kam ma a kan hanya suke baɗalarsu gurine na yar iska da dan iska , wucesu nayi na nufi inda naga yafi kyau awajen shiga nayi nafara tafiya ina kalle_kalle har idona yasauka akan wata ƙatuwar kofa me labulaye kamar makaroni ga hayaki dake fitowa awajen , ciki na nufa ina lekawa wasu yan mata nagani cike a babban falon dukkansu baza su wuce irin shekara sha sha takwas ko sha tara wasu na shan shisha gamasu shan w'iwi ga wasu can agefe suna can suna biyawa kansu bukata lesbian wa'iyazubilllahi abun ba kyaun gani . magana na faraji da ɗan karfi hakan ya nuna me maganar nan tabbas tana da babban murya, hankalina ne ya rayamin da inje inga wacece haka ,dakin na shiga na leka kaina.wata rusheshiyar mata nagani katuwa ce tana da jiki sosai ga kuma tsayi gata munmuna baƙa tana hakimce akan kujera ga wani namiji na tsaye akusa da ita suna magana da alamun masifa take surfa mishi , sake zura kaina nayi aciki wasu yara ƙanana nagani wasu na zaune wasu kuma suna kwance masu kuka nayi yarane da akalla sun kai goma, ji nayi tana faɗin" Mark dama kai bagidaje ne bansaniba tunda nake dakai ka taba jin na siya yarinya da kudin da yakai duba dari bakwai ? amma dake bakasan muhimmancin kuɗi ba shine zaka batamin kudedena kasiyo yara masu mugun tsada har guda biyu ko? to acikin sallamarka, nunamin wacce ka siya dubu dari bakwai din inganta" shide duk masifar da take mishi yana tsaye kanshi a ƙasa saboda itace shugaba acikin Afafa magajiyar karuwai kenan sunanta boss lady ko kadan bata wasa inde ta kan kudine bata da tausayi ko kadan, sa hannu ya yi ya jawo mata Asmita da tashinta daga bacci kenan ta cigaba da kuka, kaita gabanta ya yi ya ajiyeta kare mata kallo ta yi ɗakyau daga sama har kasa, sosai taga Asmita tayi mata kyau, kallonshi ta yi ta ce"Allah yataimakeka da ace ba kyakkyawa bace wallahi da se kaga yanda zanyi dakai !fito min da wacce kasiya har million daya inganta" murmushi Mark ya yi jin uwar dakin nashi ta yaba mishi da taga Asmita yasan muddin ya nuna mata Asrah tofa zaucewa za tayi har ta ƙara mishi kudi, wajan Asrah dake kwance tana bacci bata farka ba yanufa yasa hannu ya ɗagota yakaita gaban boss lady. Boss lady na kyallara idonta Akan Asrah seda yasa ta mike zaune daga kishingiden da take , a iya tarihin Rayuwar ta na karuwanci dakuma safaran yara ba'a taba kawo me kyau din Asrah ba sede masu madedecin kyau amma Asrah makurace , sa hannu tayi ta shafa fuskarta tana "wowwww! Mark aina ka samu wannan zazzafar yarinyar?" Bayanin komai ya yi mata kamar yanda su black suka faɗa mishi kuma ya faɗa mata kancewa yar Bishara family ne tsohon gwamnan jihar Borno, sannan ya sanar da ita koda ta tashi bazata iya tuna komai na rayuwarta ba , duk abinda aka faɗa mata dashi zatayi amfani , boss lady bata tabajin dadin aiki da Mark ba irin yau domin wannan yarinya mudin ta girma tasan zata samu maƙudan kuɗaɗe da ita. Karawa Mark kudi ta yi sannan ta sallame shi ya tafi, har lokacin tagagara dena kallon Asrah, da muryanta me kama da anbuga ganga ta kwala musu kira " Teema baby da Rash baby duk kuzo nan "tana gama rufe bakinta wasu yan mata suka shigo dagasu se pant da breziya ƙafafunsu na sanye da sarka. Teema baby da Rash baby su kansu seda Asrah ta tafi da imaninsu ga kuma Asmita itama kyakkyawa da ita. "Kunga wa'yannan yara guda biyun?so nake tauraronsu ya daukaku sosai a idon duniya, musamman wannan kyakkyawar.duk wani salon karuwanci da damfara,sata,salon duk wani makirci da kuma salon yaudara kuyi musu training na musamman ku koya musu rawa kuma ku kula dasu domin da kudi masu yawa na siyesu, so nake su taso da farin jini na daban acikin duk wasu karuwan dake gidan nan, Teema zoki tasheta har yanzu tana bacci"tashinta Teema ta yi , tashi Asrah ta yi ta zauna tana mutsutsuke idonta alamar baccin be ishe ta ba , turo bakinta ta yi gaba fara ƙarewa dakin kallo ta yi kafin tafara kallonsu ,kallon_kallo aka tsaya yi tsakanin ta dasu, tana kallonsu kamar idonta ze faɗo ƙasa so takeyi ta tuna aina tasansu amma tagagara tuna komai , shafa mata kumatu Teema ta yi" tace yanmata meye sunanki ?" Kallonta Asrah ta yi tanason tuna sunan nata amma ta gagara hakan yasa ta ce" bansaniba" murmushi boss lady ta yi ta ce"ɗakyau Teema samo suna me dadi ki saka matashi" nisawa sukayi kafin Rash baby ta ce" asa mata Sunaya ,yayi ?"girgiza kai boss lady ta yi alamar ko kadan sunan be mata dadi ba , ganin hakane Teema baby ta ce" to adinga kiranta da *SABRIYAH* sunan ya yi ko boss lady?" murmushi boss lady ta yi ta ce"sosaima kuwa ya yi dadi" kafin ta kalli Asrah da itade kawai da ido take binsu ta ce" daga yau sunanki shine *SABRIYAH* ,faɗa inji" gyada mata kai Asrah ta yi ta ce" daga yau sunana *SABRIYAH*" murmushi boss lady ta yi da su Teema, sannan ta maida kallonta kan Asmita da tazuba musu ido tana kallonsu , boss lady ta ce "ke kuma menene sunanki"a dan tsorace Asmita ta ce" sunana Asmita" "Ku daukesu kuje dasu sashinku ku basu daki daya su biyu,ku musu wanka ku basu abinci zan turo da kayan su, sauran yaran kuma su ma za'a zo a kwashesu" cewar boss lady , riƙe hannun SABRIYAH Teema baby ta yi ita kuma Rash ta riƙe hannun Asmita suka nufi sashin su. Wanka suka musu sannan suka basu abinci me kyau suka faraci , tana cikin cin abincin ta shaƙe tafara tari kamar zata mutu dakyar ta iya furta"wayyo Tajujuna zan mutu" ruwa suka bata tasha Teema tana shafa bayanta seda ta gama tarin kafin , Teema ta ce"Sabriyah waye kuma Tajuju ?"shuru ta yi tanason tuna me sunan amma ta manta amma daga zaran ta rufe idonta kanta take gani da wani saurayi kyakkyawa suna zane dasauri ta bude idonta ta ce "nima bansan waye ba" abincin da bata karasa ci ba kenan ta tashi tahau gado ta kwanta, ficewa adakin sukayi dan su barsu su huta, kuka Asmita tafarayi tanajin tsanan mahaifinta na shiga cikin zuciyarta, jin kukanta ne yasa Sabriyah ta ɗago kai ta kalleta saukowa ta yi akan gadon ta zauna akusa da ita ta ce"meyasa kike kuka?" Kallonta Asmita ta yi ta ce"babana ne ya siyar dani awajensu yarabani da mamana" " to kidena kuka wata rana zakije gurinsu " gyada mata kai Asmita ta yi ta ce"kema ai siyar dake akayi"girgiza mata kai ta yi tace "to aini banida kowa, Tajuju kadai nake iya gani a idona"ta yi maganar cike da yarinta kamar zatayi kuka.sannan tana me rufe idanun nata sosai rayuwarta da Tajuddeen ya dinga mata flash a ido musamman lokacin da suke zane tana hango kanta tana zanen hoton Tajuddeen komai na rayuwarta dashi tana ganin shi afuskarta da kuma shi din bayanshi kuma bata ganin kowa a ahalinta .kallon abin hannunta ta yi ta kafeshi da ido tana kallo sannan ta yi murmushi ta ce" nasan wata rana zakazo gareni tajuju" rike hannunta Asmita ta yi ta ce"to daga yanzu munzama kawaye sosai ko"Sabriyah ta ce"eh"."to Kinga basa nan kizo mu gudu kinji"Asmita ta yi maganar tana riko hannun Sabriyah ta fara janta saboda Asmita ta tsani wajan fitowa sukayi daga dakin basu haɗu da kowa ba lokacin har duhu ya fara yi.lungu_lungu suka fara bi domin guduwa har sun kai bakin gate se suka ga an rigada an datse kofar fita din ga shi sunyi nisa da inda suka baro ga garin hadari ne ya kankama sosai nan take iska yafara tashi aka fara yayyafi suna damƙe da hannun juna tsoro ya gama kamasu ganin yanda ruwa lokaci daya ya fara sauka kamar da bakin kwarya basu da wani option da ya wuce su koma.haka suke tafiya a yayinda ruwa ke yi musu mugun duka nan take jikin su ya soma rawan sanyi musamman ma Sabriyah hatta harshenta karkarwa yakeyi domin ita yar hutu ce bata saba da irin wannan rayuwar ba tafi sabawa da rayuwar ac da air conditioner.a hanyar su ta komawa sashin da suka baro suka mance daga ina suke suka dinga dabur_dabur ga ruwan na dukansu kuma har izuwa lokacin basu samu wajen fakewa ba zubewa akasa Asrah ta yi ga ruwa dake wucewa akasan kamar karamin kogi dungulewa ta yi waje daya tana kuka da iya karfinta har muryanta ya koma dishi_dishi Asmita zama ta yi kusa da ita itama suka hadu suna kuka har na kusan minti biyar kafin daga bisani ta ji Asrah ta yi shuru . matso da fuskanta dede da nata ta yi taga idonta arufe ga shi bata motsi dake yarinya ce se ta yi tunanin Sabriyah din bacci ta yi.haka suka kasance a wajen su biyunsu babu kowa. Teema baby da Rash ne suka shigo dakin nasu domin dubasu ko akwai abinda suke bukata amma da mamaki se suka ga babu su a dakin hakan yasa suka dauki lema da torchlight suka fito suna dudduba su har suka hangosu da sauri suka isa inda suke bakaramin tashi hankalinsu ya yi ba ganin halin da suke ciki ba ga Sabriyah dake sume a ƙasa cikin ruwa cikin rudewa Teema baby ta ce "Asmita meya fito da ku awannan ruwan?me ya sami Sabriyah?"ta jero mata maganar a yayinda ta sa hannu ta dauki Sabriyah din ta saɓata a kafardata, Asmita dake rawan sanyi kuwa bata samu damar bata amsa ba haka suka koma sashin su kwantar da Sabriyah Teema baby ta yi akan gado ta cire mata kaya da sauri haka Rash ma ta canzawa Asmita kaya har lokacin Sabriyah bata farfaɗo ba hakan yasa Teema baby ta dauki lema ta nufi bangaren boss lady domin sanar da ita halin da ake ciki.sosai ran boss lady ya ɓaci wato yaran so suke yi su gudu ta yi asarar kuɗinta kenan jinjina kai ta yi a ranta ta ce"zan yi maganinku" kafin ta daga waya ta kira wani doctor ta sanar dashi akwai mara lafiya in ruwa ya dauke yazo ya dubata kafin ta kashe wayar ta juya kan Teema baby ta ce "ku kuna ina lokacin da su ke kokarin guduwa?nace kuna ina ?ko ba cewa nayi ku kula dasu ba kuɗi da yawa nasa na siye su da ace kudi kaɗan ne ko mutuwa sukayi Ni bazan damu ba amma bazeyu inyi asarar wa'yannan yaran ba,amma dake ku din ballagazazzu ne ga shi kun barsu suna shirin guduwa to wlh duk sanda yaran nan suka sake kokarin guduwa Teema abinda zan aikata agareki se kinyi da nasanin rayuwarki.banza kawai ɓace mini da gani ko na dauke ki da mari wa'yanda basu san darajan kuɗi ba" sosai idanun Teema baby ya cicciko da ruwa ta bar sashen boss lady da sauri tana me tausayin rayuwarta da kuma sauran da suka tsinta kansu acikin wannan halin nan ne ta sake jin kaunar Sabriyah aranta sosai domin yaran tunda ta gansu dazun taji tana mugun tausayinsu kuma ta yi alkawarin zata kula dasu sosai. Wannan kenan,bayan ruwa ya dauke likitan da boss lady ta kira yazo ya duba Sabriyah kuma ya gano ta kamo da (pneumonia) nimoniya hakan yasa ya rubuta mata magani sannan Asmita ma ya rubuta maganin mura sannan ya kara musu da kar a dinga barin Sabriyah tana mu'amala da ruwa sosai musamman ma me sanyi Sannan ya tafi abinshi. Washe gari se karfe goma Sabriyah ta farka daga bacci Teema baby ne a dakin se Asmita ruwan wanka ta daura ta mata wanka da ruwan zafi ta haɗa mata shayi da biredi yanda Asmita ta karya. Bayan ta gama ne tabata magani ta sha haka Teema baby ta dinga kulawa da Sabriyah hatta warware. Bayan sati daya su Asmita, Sabriyah sun shaƙu sosai da Teema baby da Rash kamar da can sun san juna haka suka koma kiran su da anty Teema da anty Rash,dake sun samu masu ɗebe musu kewa har sun fara sabawa da wajan kuma har zuwa lokacin boss lady ba ta zo ba. Yau ma suna zaune Sabriyah na gaban anty Teema tana yi mata kitso amma dake gashinta yanada tsantsin gaske se yaƙi kitsuwa haka ta gyara mata gashin,agefe daya kuwa anty Rash ne da Asmita suna kwance suna baccin rana akan katifa,basuyi tsammanin zuwan boss lady ba kawai ganinta sukayi akan su"ke Teema baby tashe min Rash da wancan yarinyar"tashi anty Teema ta yi taje ta tashi Anty Rash mikewa sukayi suna gaisheta ta amma sannan ta maida kallon ta kan Sabriyah da Asmita ta ce"wato naji kuna kokarin guduwa ko? warning nazo muku duk sanda kuka sake yunkurin gudu karnuka zan sa su biku su cije ku,su cinye naman ku har se kun mutu.kun ga wannan gidan duk wanda ya shigo gidan nan baya fita har abada sede ko in mutuwa ya yi,to nan gaba in kuka sake yunkurin guduwa mutuwa zakuyi kunde jini ina?."cike da tsoro sukace mata to sannan ta ce wa Anty Rash"kizo ina neman ki." Bayan fitan su ne Anty Teema ta sake musu faɗa ta ce kar su sake kokarin guduwa. Haka su Sabriyah da Asmita suka ci gaba da rayuwa a gidan karuwai tare da yaran da aka kawo su tare har an fara musu duk wasu training din da boss lady ta ce ayi musu salo kala _kala ana koya musu tun suna ganin abun wani iri har ya bi jikinsu. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ https://chat.whatsapp.com/DuXNzdLkDfm1U0dZg9YE73 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 Page 12 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ Page 12 *This is just the beginning* AFTER TEN YEARS OF LIFE (bayan shekaru goma na rayuwa) Gidan rawan cike yake da mutane maza da mata ga manyan mutane masu zuwa daukan yanmata suje su kwana dasu,in banda filin da za'ayi rawan babu wani space aciki ko ina damke yake da mutane kowa so yakeyi yaganta yakuma ga rawanta na musamman da takeyi me daukan hankali,shisa duk karshen sati suke biyan kudi suzo su ga rawanta,kamar yadda aka saba yauma karshen sati ne ranar Lahadi kenan karfe 8 nadare, duk sun zauna ita kawai ake jira ta karaso. Kunna wata wakar India akayi wanda nora fatehi tayishi me suna kusu_kusu. Cike da yanga take tafiya jikinta se juyawa yakeyi kamar wata macijiya,tundaga tafin kafarta nafara ƙare mata kallo har sama. Kalar fatarta fara ce irin farin nan mai kyau da tafiya da hankali babu mis ko ta ina fari sumul ga jikinta da se sheki yakeyi , doguwa ce amma ba can sosai ba matsagaiciya ,Siririya bata da jiki sede akwai shape sosai tana da hips ga kirjinta dake cike taf da tula_tulan dukiyar fulani suna atsaye se daukan ido suke ,cikinta a shamule yake sosai kamar wacce batacin abinci, komar da kallona nayi izuwa fuskanta, innalillahi wa'innailaihi rajuun tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, kyakkyawa ce ta ajin farko tana da ɗan dogon fuska me dauke da dogon hanci kamar anzana pencil,kumatunta kuwa na dauke da dimple aduka biyu bangaren, wanda ko murmushi tayi se sun lotsa balle ace ta yi dariya ko kuma ta yi magana,tana da manya_manyan idanu masu jan hankali cikin idon din nata na dauke da oiling eyeballs ga dogayen gashin idonta dasuke ajere reras kamar wacce tasaka eyelashes sunyi gazar_gazar, bakinta dan karamine sosai pink color yanayin suffan bakinta kamar heart aka zana mata,gaban goshinta na dauke da lallausan saje dake kwance luf_luf gashin kanta ya zubo tundaga kanta har izuwa kusa da kugunta yanada tsayi da kuma cika sosai ,duk inda za'a sako kyakkyawa tofa wannan ita ce zatazo a farko domin makura ce wajan kyau, jikinta na sanye da wasu tsinannun kaya wanda dasu da babu duk daya , irin kayan da nora fatehi tasaka a wakar kusu_kusu , irin kayan nan na yan rawa da India ko larabawa ke sawa , dogon skirt ne wanda ya kasance a rabe biyu gefe da gefe ga ya matseta sosai hips dinta sun fito kayan se daukan ido yakeyi yana walwali rigan skirt din kuma bashi da maraba da breziya sede yadan fi breziya girma kadan tula_tulanta duk suna waje kadan ne acikin rigar , tsayin rigar ko cibiya be kaiba se wasu chain ne da aka musu kwalliya dashi ,hannunta na dauke da abun hannu kalan kayanta baƙi se kuma wani abun hannun da ya kasance silver color me kyau da design din suna ajiki yazauna dass a hannun, yarinya ce yar shekara goma sha bakwai. Tunda ta shiga cikin filin nan aka fara kururuwa ana kiran sunanta , rawa tafarayi tana lankwasa kugunta kamar babu ƙashi ajikinta , ga kuma kirjinta da take jujjuyawa kamar wata yar India haka take rawa duk wani bangare na jikin na juyawa kamar ba mutum ba ,haka ta dinga rawa baji ba gani cike da kwarewa tanayi tana tauna chew gum din dake bakinta su kuwa mutanen da suke wajan se ihu suke mata ana watsa mata kudi ana kiran sunanta"*SABRIYAH*!*SABRIYAH*!*SABRIYAH*". Se karfe goma dede ta gama show din rawan. nan take akafara zafga mata tafi raf!raf!raf jama'ar gurin se yabonta sukeyi da kuma zuzuta kyawun da Allah yamata sukeyi,tana kokarin barin filin wani saurayi yazo yasameta"Sabriyah wani ne ya ce yana son magana dake"zuba mishi idanunta masu daukar hankali ta yi cike da tsiwa ta ce" cele kaje kace mishi bazanzo ba" "Sabriyah karki yi haka babban mutum ne kuma daga gani za'a samu kuɗaɗe a hannunshi ki biyoni kawai idan be miki ba sekiyi tafiyarki"ganin inbatayi yanda yaceba ze bata ma ta lokaci kuma akwai wanda tabari yana jiranta sunyi dashi akan zasu hadu. Bin bayanshi ta yi suka kutsa cikin mutane ko ajikinta,abakin wata mayyar motar kirar corolla s black color ya tsaya , juyawa ya yi yabarta atsaye awajen ,yar tsaki ta yi kadan kafin ta kwankwasa glass window din budewa ya yi hamshaqin attajirin me kudi ne zaune acikin motar murmushi ya yi mata ya ce "shigo mana hot girl" batare da ta bashi amsar tambayar da ya mata ba ta rankwafo ajikin motar kirjinta da fuskanta na ta cikin motar tana tauna cingum ta ce" ya! Lafiya ka sa akirani?"murmushi kawai ya yi dan ya lura yarinyar akwai zafin kai da tsiwa hade da rashin kunya ya kwantar da kai ya ce "ni baƙo ne a garin nan na kama hotel zan kwana biyu kafin in tafi !to sede bana iya kwana batare da na ji ni akusa da mace ba , shisa nakeso muje ki tayani kwana ko nawa kikeso zan sallame ki dashi"dariyar renin hankali ta yi ta ce"sede kuma kayi rashin Sa'a akwai wanda nayiwa alkawari zamu kwana , ga shawara akwai wasu matan anan kaduba su kawai se anjuma"ta faɗa tana juyawa ta tafi bin bayanta ya yi da kallo yanda shape din kugunta yake juyawa nan ne yaji ranshi ya sake biyawa da ita harta ɓule mishi sannan yaja motarshi. Duk inda ta wuce setaga mace da na miji sunata alfasha ko kuma mace da mace ko kallonsu ba tayi ba ta ci gaba da tafiyarta hankali kwance har takai bakin kofar da zata shiga ta hango rabin ranta na tsaye jikinta da wata yalolon riga yar karama, hannunta rike da kwalban piscup tana sha kadan_kadan rai abace Sabriyah ta nufeta , tana isowa wajan tasa hannu ta fisge kwalban totoline din a hannunta tayi wurgi dashi, ɗago kai Asmita ta yi ta kalli Sabriyah ta dan sosa gashinta ta ce" kiyi hakuri my Tom bazan sa ke shan wani abu ba"watsa mata harara Sabriyah ta yi ta ja hannunta sukayi kofar da tazo zata shiga ta ganta , tana mata masifa"wlh my Jerry zan fara ja miki Allah ya isa in kika sake bari naganki da kayan maye,ke bakisan illar shi bane . kinaso ki mayar da shaye_shaye abin ado awajanki to zamu samu matsala ta kan haka"murguda mata baki Asmita ta yi"nifa karki takuramin maganar illa kam ai rayuwata yadade da samun illa tun lokacin da ubana ya siyar dani akan dubu dari bakwai,ga shi yanzu na zama karuwa karfi da yaji , kidena min yawan wannan fadan naki banijin dadi.so nakeyi in tara kudi sosai ta yanda wata rana in na hadu da mahaifina zan wasa masa su afuska kuma in dauki mahaifiyata in siya mata gida da duk wani kayan more rayuwa"dakatawa da da jan hannunta da takeyi Sabriyah ta yi suka tsaya kallon fuskan Asmita tayi taga kuka takeyi hakan yasa ta rungumeta tana faɗin"ki godewa Allah ke kin ma san iyayen ki nifa bansan kowa ba bana tuna komai na yarintata kawai mutum daya nake iya tunawa Tajujuna shi kadai nake iya zana hotonshi kuma in inya tuna fuskarshi, yanzu mu bar wannan maganar zo ki rakani akwai wanda ya ce zan tayashi kwana yana ciki" goge hawayenta Asmita ta yi ta yi dariya jin abinda Sabriyah tafada wai akwai wanda zasu taya kwana. Cikin dakin su ka shiga suka sameshi yana kwance daga shi se gajeren wando ya zubawa kofa ido da alamu ita yake jira.suna shigowa ya mike ya zauna yana murmushi , kallon tumbin shi Sabriyah ta yi tana yamutsa fuska" yan mata kindawo kenan ai tundazun ke nake jira zo mufara,nakosa in farajin dadinki" matsowa kusa dashi Sabriyah tayi ta ce "gaskiya ni bazan kwana dakai ba"dasauri ya ce"haba hot girl karki min haka wallahi ke kadai nake da bukata ko nawa zan baki ko 30mint muyi"girgiza kai ta yi "ni kudinka be dameni ba kawai de saboda wannan abun naka ne yasa bazan yarda kayi komai dani ba maganar gaskiya kenan"ta yi maganar tana tuttura baki Asmita dake gefe kam babu abinda takeyi da ya wuce aikin dariya dama wallahi tasan za'a rina kadan daga iya shegen Sabriyah kenan, ƙare wa kanshi kallo ya yi yana neman abinda take magana akai ,"hot girl saboda me kike magana akai ?"da kyawawan hannunta ta nuna mishi tumbinsa ,ɓata rai ya yi ya ce"ke banason iskanci saboda tumbina ne zakice bazaki yarda ba? ke da kike karuwa har sekin zabi da wanda za ki yi mu'amala?"gyara tsayuwarta tayi ajikin bangon dakin tana girgiza kai kamar wata me jin waƙa ta ce"eh naji ni karuwace ka faɗa da karfi ka ƙara da ihu kuma karuwar ma me lasisi, amma bazan bar me shegen tumbi kamar wanda ya haɗiyi tukunyan giya ya kwanta ajikina ba atoo kaje ka rage wannan cikin naka wasu insun ganka ma zasuyi tunanin cikin wata tara ne dakai"tunda yake ba'a taɓa ci mishi fuska da mutunci ba irin yau ba a harzuke ya kai hannu ze cakumeta ta gauce ta bude kofa ta fice a ɗari Asmita dake dariyar mugunta itama tabita abaya suna gudu suna dariya hade da tafawa "wallahi my Tom bakida kirki bawan Allah ya gama saka rai zaku kwana shine zakici mishi mutunci"far_far da idonta ta yi ta ce"to ai ina zan tsaya ma wannan katon mutumin" "to inya kai ƙaran ki gurin boss lady fah?"kwashe gashinta ta yi ta dauresu da daya daga cikin abun hannunta ga kayan jikinta ma sun fara takura mata "oho ina ruwana seta san yanda zatayi dashi"haka suka koma sashinsu suna tafe suna hira.suna shiga suka hangi anty Teema na zaune ga kwalin sigari agabanta da laita sede bata kunna ba alama ta tafi duniyar tunani ne domin ko shigowar su ma ba ta ji ba. Zama sukayi Asmita ta ce"anty Teema mun dawo"se a lokacin ne ta fahimci cewa su Asmita su shigo girgiza kai ta yi murya a sanyaye ta ce"dama yanzu nakeson zuwa in kira ku na ji ku shuru kuma nasan in kunyi wasa bakwa daɗe wa" Sabriyah de tunda suka shigo ba ta ce komai ba se nazartan antyn sun takeyi"anty Teema dan Allah meyake damunki ne gaba daya kin canza ba kamar yanda muka sanki ba tun bayan mutuwar anty Rash gaba daya kin koma wata kala Wallahi ni gaskiya banajin dadin ganin ki ahaka"murmushin takaici anty Teema ta yi ta ce"ku haryanzu yarane amma abun da kullum nake faɗa muku shine karku yarda boss lady ta turaku wajan da za'a kwanta da ku domin daga za ran kun shiga wannan harka na karuwanci da take saka yara Wallahi rayuwarku ya lalace kamar yanda nawa rayuwar ya lalace nasan kusan abinda ya kashe Rash ciwon ƙanjamau ne ya yi ajalinta nima kuma ina dauke da wannan cutar.kullum cikin nadaman wannan rayuwar nake ina so inga iyayena bansan ko suna raye ko sun mutu ba, guduwa nayi daga gida saboda za'a min auren dole ashe a hannun boss lady zan faɗa na bijirewa iyayena nazo na shiga duniya.inde da raina da numfashina bazan taba barin boss lady ta mayar da ku karuwai ba yanda take buri duk da ta yi rabin hakan duk wanda ze ganku se ya kira ku da Wannan suna na karuwa se de ko in ba'a garin nan ba.rawa,damfara,shaye_shaye domin Asmita ke naga kin fara mayar da kanki yar shaye_shaye to dan Allah ki raba kanki da kayan maye domin ni nasan illar su.duk kun rigada kun faɗa wannan harkan yanzu jira takeyi nan da kwana biyar akwai manya_manyan masu kuɗi da zasu zo diban wa'yanda zasu kwana da su daga nan ne kuma zata fara safaran ku"tabe baki Sabriyah ta yi ko ajikinta ta ce"nifa anty Teema haryanzu ban ma ga na mijin da zan iya bashi jikina ba sede ko boss lady kasheni zatayi amma Wallahi bazeyu tasani inje wajan wani banza ba, wasar rawar da nakeyi ma kadai ya isheni shi dinma dan kawai innayi inajin nishadi ne amma badan haka ba babu abinda ze sani inyi yawwa"duk zuba mata ido kawai suka yi saboda sun san halin Sabriyah sarai akwai taurin kai bana wasa ba in ta faɗa magana tofa ko me ze faru ba zanjawa takeyi ba in ma zata canza se ankai ruwa rana. "Ni barin ma inje in canza wannan kayan sun dameni"ta yi maganar tana mikewa sannan ta sa hannu ta kwashe duka kwalin sigarin dake gaban anty Teema. Riko hannunta Asmita ta yi idonta sunyi ja sosai ta ce"Sabriyah wai ke bakya tunanin gida ne,bakya son barin nan?"dawuwa ta yi ta zauna ta fuskanci Asmita ta ce "to yazanyi?koma ina son komawa gida su waye iyayena?bansan su ba ku kadai nasani se kuma tajuju na kullum shine yake zuwa mini a mafarkina,ku kadai nake dashi shisa ma ni ban taba kwadayin barin wannan gida ba domin inna barshi ma bansan ina zani ba.kefa kina son barin nan?"ta gama maganar tana jefawa Asmita tambaya gyada mata kai Asmita ta yi"tabbas ina son zuwa gida ina son gani n mamata in jini acikin jikinta sannan in tara kudin da yakai yawan million dayan inje in samu fuskan babana in watsa mishi su wannan shine burina"sosai Asmita tabawa Sabriyah da anty Teema tausayi domin daga yanayin muryanta kadai ma in ka ji kasan deep down her heart akwai babban ciwo arayuwarta domin kullum se ta yi mafarkin lokacin da malam Mamman ya rabata da gida ya je ya siyar. da wannan dalilin ne yasa ta faɗa harka shaye_shaye ko hakan ze taimaka mata ta manta da komai amma hakan be samu ba,shafa fuskanta Sabriyah ta yi ta ce"za ki je gida wata rana tashi muje mu kwanta mubar anty Teema ta huta"mikewa sukayi suka mata sallama suka shiga nasu dakin bin bayansu da kallo kawai anty Teema ta yi tana rayawa aranta ina ma ace tana da damar kubutar da wa'yannan yara guda biyun. Dakin nasu balaifi ɗan matsakaici akwai katifa ga gefe kuma wadrobe na sa kayan su se risho da wasu tukuye da kwanukan da basu fi biyar ba. Suna shigowa Sabriyah toilet ta shiga bayan ta watsa sigarin da ta dauka a gaban Anty Teema a cikin dustbin,ta cire kayan jikinta ta yi wanka ta daura zani a kirjinta ta fito ta zauna abakin katifa tana duba basilin dinsu ganinshi ta yi ta dauka ta fara shafawa Asmita ma wanka tashi ga bayan ta fito ne ta dauko musu wani yalolon riguna masu dogon hannu suka saka suka kwanta dan yau a gajiye suke sosai musamman Sabriyah da tayi rawa. Washe gari basu suka tashi ba se misalin ƙarfe goma dukkansu brush sukayi suka yi wanka suka zo suka zauna a dakin nasu Asmita ta ce"my Tom nikam bazamu karya bane kin wani kwanta"mikewa ta yi ta ce "naga ai bakice kinajin yunwa ba nadauka se anjuma ne ai"tsaki Asmita ta yi ta ce "Wallahi kina da matsala kinsan karfe nawa ne yanzu? nikam in akwai kudi a hannun ki bani inje in nemo mana abinda zamu karya dashi"kasan filo Sabriyah ta daga mata kudin da ta damfari mutumin jiya ne naira dubu goma ne ta dauko dubu biyu ta ce"ya yi ko in ƙara?kar mu cinye kudin kuma muzo muna muzurai tunda Kinga kowa a gidan nan shi yake ciyar da kanshi" " gaskiyan ki ne hakan ma ya isa tashi muje mu dawo se mu daura nasan anty Teema ma ta farka."mikewa sukayi suka fice dukkansu babu wanda yasa gyalle balle hula duk gashin su a fake kamar wasu arna Asmita na sanye da riga me guntun hannu red color da wando trequater grey color,Sabriyah kuma riga ce ajikinta yar guntuwa ya tsaya mata a guiwa duk da rigar play ce amma seda tudun hips dinta suka fito hankali kwance suke tafiyan su har sunyi nisa suka jiyo murya a bayansu tana"ku jirani dan Allah" dakatawa sukayi suna jiran nata Asmita ne ta ce "Nabiha kuma ina zataje take wannan saurin" "wa ya san mata ne"cewar Sabriyah.iso wajen su tayi ba laifi itama tana da ɗan kyau black beauty ce daga ita se wata guntuwar mini skirt da karamar riga kanta yasha kitson attachment ta ɗan yi kwalliya a fuskarta. "Ina zakuje"Sabriyah ce ta bata amsa da"bakin titi zamuje siyan kayan karyawa! kefa ina zuwa?"murmushi ta yi ta ce"wani sabon kamun kifi nayi yace inzo da safen nan shine na fito" "okay to munje in yaso ke kya tsaya abakin shagon nasan za ki samu abun hawa"cewar Asmita tafiya sukeyi suna hira har suka iso shagon da zasu shiga din nan suka rabu da Nabiha ita kuma ta hau mashin ta tafi. "Me shago kabamu idomie da kayan shayi da biredi" Asmita ta faɗa ko ajikinta duk da ta kalli layi ake bi a shagon juyowa mutanen sukayi suna watsa musu harara wata krista ce ta ce"uban wa kuka fi gadara anan da zaku zo kuga layi bazaku bi ba sede ku wani ce abaku kaya"ke Sabriyah da bada ke akeyi ba yar ta ran aradu da ka a harzuke ta ce "ubanki mukafi gadara shisa mukace abamu" "kan uban can ubana kika zaga?" "Iyi shi na zaga ko akwai matakin da za ki dauka ne"ganin su Sabriyah sun fita budewar ido yasa ta yi tsaki ta ce "aikin banza zakisan kin zageni" me shagon ganin zasu tayar mishi da faɗa a shago ne ya ce "me za'a baku?"sake faɗa mishi Asmita ta yi aikuwa da sauri ya haɗa musu ya mika musu suka bashi kudinsa suka tafi, akan hanya suna kan dawowa Sabriyah ta ja dogon tsaki kallon ta Asmita ta yi ta ce "me kikewa tsaki haka"da ido ta nuna mata gabansu wata farar jeep ce a fake mutumin ciki ya zubawa Sabriyah ido kamar wani tsohon maye kasa_kasa da murya Asmita ta ce"my Tom kin san shine naga yana miki irin wannan kallon kwarillan?" bata rai Sabriyah ta yi ta ce"ehh nasanshi jiya bayan na gama show cele yazo yasameni wai mutumin na kira na,ni Wallahi be burgeni" "ohhh nagane amma Wallahi karki kuskura mutumin nan ya tafi be baki wani abu ba ahh! kinsan de kayan abincinmu yakare "yanda Asmita take mata magana cike da umarni ne abin yabata dariya. Isowa sukayi kusa dashi basu ce mishi komai ba ya ce "ku shigo mana in sauke ku?"girgiza kai Sabriyah ta yi ta ce"ba bukata ya akayi?me ya kawo ka?" Kare mata kallo ya yi ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce"yau de ina neman alfarma kizo ki tayani kwana" cike da gadara ta ce"okay naji"murmushi ya yi"yawwa hot girl ga shi bari in baki transport ga kuma address dina"ya yi magana yana fito da band din dubu daddaya guda biyu daga cikin aljihun shi ya mika mata wanda a ƙala ze kai dubu ɗari.karba ta yi ta ce"okay "sannan suka wuce shi se da suka tabbatar da ya tayar da motarshi sannan suka fito da kudin suka kirga dubu ɗari ne cas tafawa sukayi Sabriyah ta yaga address din nashi da yabata ta ce"bari anjuma cele yazo zan bashi yaje ya siyo mana kayan abinci". Bayan sun koma ne sukayi abin karyawa sukaci dama sun rigada sun kaiwa anty Teema nata duk suna baranda suna hira su uku boss lady ta shigo tafiya ma dakyar take iya yi saboda kiba da ya mata yawa ita da wani dan daudu suka shigo dauko mata kujera anty Teema ta yi fuska ba yabo ba fallasa boss lady ta ce" ba zama ne ya kawo ni ba wajan wa'yannan marasa jin maganan yaran naki nazo yiwa kashedi"gaban Asmita ne ya yanke ya fadi domin ita tana matuƙar tsoron boss lady, Sabriyah de da ido take binta kawai kallon Sabriyah ta yi ta ce"iskanci n da kike yi hot girl ya fara isa na a gidan nan maza goma suna kawo mini ƙaranki akan abinda kike musu to ki bude kunne kiji in faɗa miki wannan iya shegen naki ya fara isana in kinsan bazaki je mutum ya biya bukatarsa dake ba kar ki ƙara karban kudin wani"turo baki Sabriyah ta yi ta ce"boss lady nifa haryanzu banga namijin da zan bata lokacina akanshi ba sannan kuma maganar karban kudi kuma ke kika koya mana. in bamu karba kudi ba dame kike so muci abinci kowa ciyar da kanshi yakeyi a gidan nan,ko da munyi show na rawa kudin gaba daya kikeso a kwashe miki dame zamu yi rayu....."bata gama maganar taba boss lady ta sharara mata maruka masu zafi a kumatu. "Ke har za ki tsaya ina magana kina bani amsa ko kin manta a karkashin ikona kuke nice nan gatan ku duk duniya baku da wacce tafini shashasha wacce bata san inda yake mata ciwo ba ko an gaya muku na siye kune dan inzuba muku ido"hawaye ne suka zubowa Sabriyah tana riƙe da kuncinta ta kafe boss lady din da ido Asmita na rungume da ita,anty Teema ne ta ce"dan Allah boss lady kiyi hakuri ita din yarinya ce bazata sake mayar miki da magana,ke Sabriyah bata hakuri"sanyi_sanyi anty Teema take magana, sunfi minti biyu suna jiran Sabriyah tabawa boss lady hakuri amma taƙi.anty Teema ce ta ce "dan Allah Sabriyah" ganin antynta na haɗata da Allah ne yasa murya ciki_ciki ta ce "kiyi hakuri boss"hararanta ta yi ta ce "Sabriyah ki ka sa kunne kijini da kyau jibi za ki iya yin baƙo kuma ko mutuwa zakiyi se ya more ki domin tun kafin yazo ma ya turo mini da dubu dari uku babban mutum ne naɗe faɗa miki ga wannan kije ki siya abinda baku dashi". Boss lady ta yi maganar tana cilla mata kudin da yakai Naira dubu dari da hamsin,kuma ta bata kudin ne saboda shi bakon yace mata yana son yarinya yar gayu shisa yabada kudi akan bawa Sabriyah ta je ta yi shopping. Boss lady na gama magana tafice a sashin duk jugum_jugum sukayi Asmita tana rungume da Sabriyah har lokacin anty Teema jikinta ya yi sanyi sosai saboda ita tasan halin boss lady fiye da wasu,sa hannu Sabriyah ta yi ta dauki kudin ta ce"my Jerry dena daga hankalin ki akan maganar ta yau Allah ne ya kashe yabamu bazama mu jira cele ba tashi muje babban kasuwa.yanda take magana ranta fes kamar babu abinda yake damunta. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ Page 13 Se yamma liris tukun suka shirya dan zuwa kasuwan suna kokarin fitowa cele ya shigo kai tsaye dakin nasu ya shigo"mutumiyar yau fa ban ganku ba kwata_kwata"kwasan kudin Sabriyah ta yi tasa acikin jaka sannan ta ce "iyi yau ka yi nisan kiwo naga alama"yar dariya ya yi ya kalli Asmita dake zaune tana bin su da ido"Asmita yau ba magana ne?"tsaki ta yi ta kau da kanta gefe"ai ni Wallahi cele kabani mamaki har in ce ka kawo min abu ka ƙi"se da ya kalli Sabriyah kafin ya ce "nifa karki ga laifina hot girl ce ta ce kar ta sake kallon a na kawo miki kayan more wa"Sabriyah najin su amma ko kallonsu ba ta yi ba ta ce"ku tashi mu tafi in kunyi niya"ta yi gaba abunta bin bayanta sukayi har suka cimma ta. "Wai kunji labarin jibi manyan alhazawa zasu zo ko?" "Ehh haka mukaji"cewar Asmita murmushi Sabriyah ta yi ta ce"ai za'a ci uwar sabada Wallahi ko a wasan rawa ma nasan zan samu kudi sosai ɓalle kuma ace na nuna musu na yarda da bukatar su, nifa kun san abinda yake burgeni kuwa?kawai in ga ina wasa da hankalin namiji shine kawai ya ke burgeni kuma in ci kudin su son raina saboda wannan karon lokacin samun kudin mu ne so nake in haɗa kudaden in bawa my Jerry ta je garin su"duk sake baki suka yi suna kallon ta Asmita ne ta ce"ke a tunanin ki zan bar gidan nan ba tare da ke bane?ai ƙafana ƙafarki yawwa" dariya cele da Sabriyah suka yi harda tafawa Sabriyah ta ce"ke waya faɗa miki zan taɓa barin gidan nan tabb ai ina nan daram dam_dam se munga abinda ya turewa buzu naɗi. burina kawai shine in ga rayuwarki ya yi kyau Asmita." "uhmmm"kawai Asmita ta iya cewa dan bataso su ja maganar ya yi tsayi ranta ze iya ɓaci saboda ta lura Sabriyah dagaske take bazata bar gidan ba tarasa me yasa Sabriyah batason barin wannan gida da ba komai take amfanuwa dashi ba. Bayan sun gama siyayyan kayan abinci ne suka koma cikin kasuwa saboda siyan kaya, Asmita kiran me siyar da karas ta yi yazo saboda tanaso sosai. mutumin ɗan dattijo dashi ta ce ya bata na dari uku har ya zuba mata ze tafi se ya kuma tsaya ya kalli Sabriyah daga sama har ƙasa sannan ya ce "ƴata amma ke musulma ce kuwa?" kallon tara saura ta mishi batace mishi komai ba taci gaba da abinda takeyi shi kuma ganin hakane yasa ya ce "karku ga kamar na yi muku katsalandan amma be kamata ba kuna yaran musulmai kuna wannan shigar, duk suran jikin ku awaje dan Allah ku gyara"duk zuba mishi ido sukayi suna ganin wani karfin hali irin nashi Sabriyah ta ce"ka ga malam babu abinda ya shafe ka damu je ka ci gaba da siyar da karas dinka bawai shiga rayuwar mutane ba,haba wannan ai gulma ne"girgiza kai ya yi kawai ya ce"to Allah shi kyauta"ya fece dan ya lura yaran ba kunya ne dasu ba, za ma su iya zagin shi in beyi wasa ba. A gajiye suka koma gida Lokacin har 7:50pm ya yi Asmita ce ta musu shinkafa da mai da yaji su uku harda cele sun kusa cinye wa Nabiha ta shigo jiki a sanyaye alamar ma kuka ta yi idonta ya ɗan kumbura dakatawa sukayi suna tambayar ta"Nabiha lafiya meyafaru ne?"zama ta yi akan bakin katifarsu kusa da cele da shi ma ya cire hannu acikin abincin da suke ci. "Boss lady ce ta ce a kira mata duk wata matashiyar yarinya a gidan nan an sace mata sarkan gold dinta"gaban Asmita ne ya faɗi jin abinda Nabiha ta faɗa ita de Allah ya zuba mata tsoron boss lady kamar dodo yanzu tsoronta bata san wani irin hukunci boss lady zata yi musu ba. Jin sharrin sata ne jikin su ya yi sanyi sosai saboda sude sun san basu dauka ba kuma bama shiga wajan boss lady din sukeyi ba se in ance ana bukatar su,ganin yanda Nabiha har lokacin take hawaye ne hankalin Cele yaɗan tashi saboda yana matukar sonta amma babu wanda ya taɓa faɗawa hakan har ita kanta Nabihan bata sani ba. "Tunda kude kun san baku dauka ba ku kwantar da hankalinku babu yanda boss lady ta iya daku ku tashi kuje kar aga kun daɗe a yi tunanin ko wani abun kukeyi"cewar cele ya faɗa yana mikewa,jikinsu a sanyaye su ma suka mike suka fita abincin da basu karasa ci ba kenan. cele ya tafi dan zuwa gidansu saboda shi bayi da nisa da afafa saboda shakuwar da ya yi da su Sabriyah ne yasa ya koma abokin su kullum suna tare ko da safe ko da dare.sashin Boss lady suka nufa tun shigowar su suka ga yan matan dake cike duk sunyi carko_carko ga magajiya boss lady na hakimce a zaune a tsakiyar gidan se hura hanci takeyi suma tsayawa sukayi a layi kamar yanda suka ga sauran sunyi boss lady ta fara magana. "Wato ku yanzu satan naku ya komo kai'na kenan ko? a cikin ku wace tsinanniya ce ta shiga ta ɗaukar mini sarkan gold ɗita?, wanda aƙalla yakai darajan Naira miliyan daya da rabi!?"ta yi maganar tana zare musu ido. duk rantse mata suka fara yi ko wacce da abinda take faɗi, daga me cewa "Wallahi boss lady bani bace"se me cewa"na rantse da Allah boss lady ban masan wani kala bane ban taɓa kallo ba"haka suka dinga rantse mata.afusace ta mike tsaye ga ɗan daudun dake take mata baya a gefenta se wani yauki da yanga ya keyi kamar mace ta ce"kenan sarkan ya yi ƙafa ya gudu ko?haka kuke nufi ko!?"shuru sukayi kansu a ƙasa, Asmita, Nabiha da Sabriyah su de babu wanda ya yi magana acikin su. "Kai caje mini su daga pant din su har breziya ko wacce a cikinsu maza_maza"ta yi maganar tana kallon dan daudun.fara cajesu ya yi daya bayan daya har yazo kan Nabiha ko ajikinta tabar shi ya cajeta hannu yakai kan Asmita yana kokarin sa mata acikin riga da sunan cajewa ta ja gefe tana watsa mishi harara"kai meye haka ƙaton gardi dakai zaka wani yi kokarin sa mini hannu a nono"Asmita ta yi maganar tana ci gaba da zabga mishi harara Sabriyah murmushi ta yi kawai saboda dama jira take yi kawai dan daudun yazo kan Asmita tasan za'a dibi yan kallo.kowa zubawa Asmita ido sukayi suna ganin ikon Allah har wasu ma sun fara tunanin ko de ita ce ta sace sarkan gold din,boss lady daka mata tsawa ta yi "ki barshi ya caje ki kar ki bari Wallahi in iso wajan nan Asmita"duk da yanda Asmita take matukar tsoron boss lady amma ja baya ta yi murya kasa_kasa ta ce"nide boss lady ki sa wata macen ta cajeni amma banda wannan ƙaton ƙazamin"iya ɓaci ran Boss lady ya ɓaci ganin Asmita na kokarin yi mata rashin kunya ɗauketa ta yi da wasu gigitattun maruka har guda biyu runtse idanu Sabriyah ta yi saboda ita taji zafin nan take idonta ya cicciko da ruwa,dafe kuncinta Asmita ta yi tana hawaye damƙar gashinta boss lady ta yi ta ce"mutumiyar banza wato har kin yi girman da za ki dinga maida mini magana!ko kin manta nice uwarki nice ubanki gabaki ɗayan ku baku da kowa sama dani tunda na riga da nayi muku lasisi to nayi muku komai a duniyar nan. shegiyar yarinya tsinanniya wato ke ce barauniyar da kika sace mini gold dina kenan!?shisa kika ƙi yarda a caje ki to fito dashi ko kuma na lahira yafiki jin dadi"kuka Asmita ta fashe dashi saboda yanda boss lady ta rike mata gashin kanta azaba kawai take ji,a tsorace Sabriyah ta fito ta zube akasa ta rike ƙafar boss lady saboda tasan yau Asmita tunda ta shiga hannun boss lady kasheta ne kawai bazata yi ba.cikin rawan murya Sabriyah ta soma magana"dan Allah boss lady kiyi hakuri Wallahi Asmita ba ta daukar miki sarka ba yau tun safe muna tare ki rabu da ita niiii....zan caje miki ita yanzu ma kuwa"haka ta dinga bawa boss lady hakuri amma daga karshe saboda rashin imani irin na boss lady hannu tasa ta dago sabriyan ta gashin kanta itama dukan su rike gashin kansu ta yi ta ce"baƙaƙen munafukai ku fito mini da sarka na ko kuma dukkan ku in kai ku dakin horo Wallahi se kunyi sati daya aciki"duk yan matan dake wajan sunyi matukar tausayawa Asmita da Sabriyah domin kuwa yau sun faɗa tarkon boss lady. Duk kuka suke yi musamman ma Asmita"boss lady dan Allah ki rabu da Asmita batasan komai ba, nice na ɗauke sarkan gold din"Sabriyah ta faɗi haka saboda ta kwaci Asmita a hannun boss lady in yaso ita se amata hukuncin,duk da irin zafin da Asmita take ji amma hakan be hanata faɗar"boss lady karya Sabriyah takeyi!! ta faɗi hakane saboda ki kyaleni amma ni na dau sarkan gold din"hararanta sabriyah ta yi ta ce "Asmita meyasa kikeyin haka dan ki ceceni, bazan taɓa barin ayi miki hukuncin da nice da laifi ba boss lady karki yarda da ita nice nan na sace!". fara birkitawa boss lady lissafi suka fara yi ta rasa waye me faɗar gaskiya da kuma waye me faɗan karya acikinsu, Asmita ce ta sake cewa"Wallahi karya ne nice na dau.........."boss lady bata bawa Asmita damar karasa maganar da take kokarin yi ba ta daka musu tsawa da wannan ƙatuwar muryan nata"ya ishe ku haka!ku fadamin waye ainihin wanda ya sace ko kuma dukkan ku biyu ku fuskanci hukuncin saboda kuna kokarin yin wasa da hankalina."Asmita na kokarin yin magana Sabriyah ta tari numfashinta ta hanyar faɗin"boss lady ki yarda dani nice nan na sace miki sarka da safe na shigo na samu kina bacci shine na ɗauke."wurgi da Asmita ƙasa boss lady ta yi ta ce "Allah ya taimakeki bake kika dauka ba"rike kanta Asmita ta yi da duka hannunta saboda azaban raɗaɗin da yake mata ga bakin cikin karbar laifin da Sabriyah ta yi bayan dukkansu biyu babu wanda ya dauka.maida kallonta Boss lady ta yi kan sabriyah dake rike da hannunta da ta rike mata gashi"boss lady akwai zafi gashina ze fita"saketa boss lady ta yi taje ta zauna akan kujera ita kuma Sabriyah ta zube akasa rarrafowa Asmita ta yi kasa_kasa ta ce"my Tom meyasa zakiyi haka duk da bamu muka dauka ba da kin bari ta hukunta ni" "bazan iya gani tana miki azaba ba karki damu,duk abinda zatamin inde akan ki ne bazan ji zafi ba" Girgiza kai Asmita ta yi" my Tom karki yi haka kinsan halin boss lady ni banaso ta cutar mini dake" "Ubanme kuke faɗa ne ku ka wani haɗe kai ke hot girl zo nan"boss lady ta tambaye su tana kiran Sabriyah da hannu mikewa ta yi ta je gabanta ta tsaya tana me jin kamar ta shaƙe boss lady ta mutu har lahira. "Kowa ya watse anan bana san kallon ku sannan duk wacce ta je ta kwana ta tabbatar da takawo mini balance dinta in ga cinikin da ta yi,maza_maza je ku samo kudi yara kuyi manyan kamu, saura kuma inji labarin kun bawa matsiyaci ya ci yabaku dariya biyar ko dubu daya ku ɓace mini da gani". watsewa sukayi gaba dayan su ya yi saura Nabiha da Asmita kallon Asmita boss lady ta yi ta ce"ke kuma karki kuskura in ga ƙafarki a nan se nan da sati daya kizo ki karbeta yanzu za'a kaita dakin horo anan zatayi sati daya.muddin naga idonki kuwa kema za ki ganki acikin dakin horo"sosai Asmita take kuka jin an rabata da rabin ranta harna tsawon sati daya kuma tunda suka taso kullum tare suke bacci,hira,cin abinci,yawo,komai na rayuwarsu tare suke yi amma yau akan laifin da ba su suka aikata ba za'a azabtar da Sabriyah hankalinta ya tashi matuƙa. Ɗagata Nabiha ta yi muryanta a sanyaye ta ce "mu tafi Asmita zan dinga ta ya ki kwana"haka Nabiha tabar wajan da Asmita bin bayansu da kallo Sabriyah ta yi tana ajiyar zuciya,se sannan ne hankalinta ya tashi da ta tuna ina ne dakin horo. Dakin horo wani keɓebben wajene acikin gidan karuwan babban ɗaki ne da bashi da ko da window ɓalle haske ya shigo iya kofa ne kawai a dakin ko tafin hannu mutum baze iya gani ba,anan ne boss lady take hukunta duk wata karuwar da ta yi laifi ko kuma ta karya doka,mata da yawa sun mutu acikin dakin horo saboda tsananin zafi,duhu,rashin samu a shaƙi iska ga tsananin yunwa saboda sau daya kawai ake kawo wa mutum abinci wannan dalilin yasa duk wacce ta shiga dakin horo basa fitowa da rai. Hankalin Sabriyah be sake tashi ba seda taga wannan ɗan daudun ya nufota jan hannunta ya yi tana tirjewa tana kuka haka ya kaita dakin duhu ya wurgata a ciki yasa sakata ya rufe. Wani irin haukaciyar tsoro ne ya kamata nan take jikinta yafara rawa musamman ma da ta ga ko tafin hannunta bata iya gani ga shi ji takeyi kamar motsi takeji aciki, haɗe kanta da guiwa ta yi tana ci gaba da kuka. *LAGOS ORIENTAL HOTEL* Kwance yake a hadadden dakin hotel din, side din da yake vip ne,ya yi rub da ciki da alama ya tafi duniyar tunani. kira ne ya shigo wayarshi dake kan Centre table din dakin seda ya kusa katsewa tukun ya mike zaune tsaki ya yi kafin ya tashi tsaye,masha Allah kyakkyawa ne.fari dogo yana da tsayi sosai amma be da wani jiki sosai yana da kyawun fuska dede gwargwado very handsome kanshi babu wani gashi sosai an mishi aski lowcut yana sanye da jallabiya baƙi . Ɗaga kiran ya yi yasa akunne"hello ina wani abu zan kira ki anjuma"be bari ta bashi amsa ba ya katse kiran yana me jan doguwar tsaki ya koma ya zauna hannu yasa ya da ki jikin gadon ya rasa ya zeyi da ranshi kwankwasa kofar dakin nashi akayi ya bada umarnin a shigo namiji ne ya shigo irin masu share_share yazo ya duba ko akwai abinda yake bukata. "Sir do you need anything?"kallon shi ya yi ya ce"nope am okay"juyawa ɗan saurayin ya yi ze fita a dakin,tunani ya yi se kuma ya sake kiran shi"come here"dawuwa yaron ya yi ya tsaya yana jiran yaji me ze ce. Karewa saurayin kallo ya yi yaga eh tabbas ya yi kallan gari dan ɗan gaye ne kam. Ya ce"ya sunanka?"saurayin ya bashi amsa da"umar" Jinjina kai ya yi kafin ya ce " okay Umar!I need your help,shin akwai in da zan samu a rage mini gajiyata ne anan kusa ?"murmushi Umar ya yi ya ce"haba ranka shi daɗe kode ka manta a garin da kake ne Lagos ne fa! in mata ashirin kake so tofa zaka samu"gyada kai ya yi ya ce"akwai wacce kasani kyakkyawa,me shape wanda ze dau hankali kuma wacce ta iya tsabta?" "Ehh sede ka duba akwai hotunan su da kuma videos a wayata se in nuna maka su kazaba,kasan kaff garin nan babu kn da yakai afafa yawan ashawo."yana maganar yana laluba wayarsa acikin aljihun wandonshi ji ya yi wayam nan ya tuna ya baro wayar a reception ya ce"give me some minutes bari in dauko a reception"gyada mishi kai kawai ya yi. Bayan kamar minti goma umar ya dawo hannunshi rike da wayar tashi shiga cikin gallary ya yi, ya mika mishi yana kallon hotunan duk yan matan babu wacce ta yi mishi acikinsu miƙa masa wayar ya yi ya ce"banga wacce ta min ba"da sauri ya karbi wayar ya lalubo mishi video wata tana rawa "ga wannan ka kalla na tabbatar da se ta burgeka"karba ya yi ya fara kallo. Dirin jikinta da skin dinta haɗe da tsawon gashinta ne ya tafi da gaba daya ilahirin imaninshi be san lokacin da murmushi ya subuce mishi ba ya ce "tabbas wannan ta yi sede nafi son virgin wacce ni zanyi disvirgin dinta da kaina" "a afafa take Wallahi dan ma bakaga fuskanta bane kyakkyawa ce ta ajin farko kaff cikin afafa babu wacce ta kaita kyau" daga filo ya yi kuɗaɗe ne zube akan gadon bandir biyu ya lalubo ya ce"okay ga shi karike wannan"hannu na rawa Umar ya karbi kudin a iya rayuwarsa be taɓa riƙe irin wannan kudin ba wanda a ƙalla sun kai dubu ɗari biyu se jujjuya su yakeyi"Nagode!nagode sosai ranka ya daɗe"murmushi ya yi ya ce "karka damu gobe ka shirya se ka rakani can din in je in daukota. saboda bana iya yin bacci se na ji ni ajikin mace,zaka iya tafiya."cike da farin ciki ya bar dakin yana sake gode mishi domin kuwa shi yau ya haɗu da babban rabo. Washe gari da wuri ya shirya yazo dakin nashi. bayan ya bashi izinin shigowa,zaune ya sameshi daga shi se singlet da guntun wando ga laptops a gabanshi jere akan gadon sun kai biyar mamaki ne ya kama umar aranshi ya ce"mutumin nan meyakeyi da wa'yannan laptops din?an ya ba ɗan yahoo bane kuwa?"shi kadai yake magana kuma yake tambayar kansa sanin babu wanda ze bashi amsar ne yasa ya gaisheshi ya ce"sir na shirya zamu iya tafiya?"kallon agogon hannunshi ya yi yaga almost 10:00am ya ce "eh bari in shirya se muje ka jira ni awaje inna gama zan sameka." "To shikenan"murda handle din kofar dakin ya yi ze fita ya ji yana waya abinda yaji ya futar shine..."wa ya gaya musu zasu iya dani?mutum nake me kama da aljan.just becarefull domin naji an ce shi aka bawa case din kuma yana da matukar hatsari ni na sanshi ku bi umarnina ku cece rayuwark...."be karasa maganar shi ba sakamakon ganin Umar da ya yi a tsaye a bakin kofar be fice ba.daga kai ya yi yaga suka haɗa ido da Umar din yana tsaye be tafi ba duk da yabude kofar watsa mishi harara ya yi ya ce "akwai wani abinda kake jira ne?"da sauri ya fice daga dakin zuciyarsa ya fara zargin shi,"shin wanene shi din?"tambayar da yake tayiwa kanshi kenan duk da a ido beyi kala da mutanen banza ba very gentle man. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ *🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹* Page 14 *_Story & written_* By *MRS🌹ISHAM🌹* ( Yar lelen Jarumai) *THE WRITER OF 🖋️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️ Page 14 Shiryawa ya yi cikin kananun kaya ya fito hannunshi rike da car keys a reception ya sameshi suka fito suka shiga mota umar ne ya dinga mishi kwatance har suka shiga cikin afafa, packing ya yi a bakin gate din gidan karuwan suka fito hannunshi na cikin aljihun shi se ƙarewa wajan kallo ya keyi ga yan mata se shige da ficen su sukeyi ko wacce babu isasshen sutura ajikinta,wata ce tazo wucewa Umar ya tsayar da ita ya tambayeta inda zasu samu boss lady,ita ta musu jagora har wajan boss lady kamar ko yaushe tana hakimce akan kujera dan daudun nan na yi mata yankan farce. Shigowa sukayi su ka samu waje suka zauna boss lady na kallon shi tasan eh za'a samu kudi awajan shi nan take ta fara washe baki nan ya faɗa mata bukatarsa "ai inde wannan ne karka damu akwai tsala_tsalan yan mata agidan se wacce ka zaba"wani munafukin murmushi ya yi ya gyara zama ya ce"nooo!akwai wacce aka nuna mini kuma saboda ita kadai nazo nan but zan fi jin dadi idan ita din virgin ce" nuna mata video suka yi murmushin dake kan fuskan boss lady ne lokaci daya ya dauke ta haɗa rai ta ce "ka zaɓi duk wacce kake so acikin gidan nan amma banda Sabriyah"da mamaki su ke kallonta jin abinda ta faɗa.umar ne ya ce"amma meyasa banda ita?"boss lady ta ce "saboda ta yi laifi tana dakin horo se nan da sati daya za'a fito da ita sede in zaku dawo bayan sati daya"girgiza kai ya yi, ya ce"bazan kai sati daya a kasar nan ba!laifin me ta aikata haka ina da matukar bukatar ta"tabe baki ta yi ta ce "sarka na da yakai darajan Naira miliyan daya da rabi ta sace"murmushi ya yi ya ce "ki fito da ita zan baƙi million uku"zaro ido waje boss lady ta yi tana sake kallon shi ɗan son tabbatar da abinda ya faɗa bama ita kadai ba dukkansu mamakin shine ya kamasu gyada mata kai ya yi alamar tabbatarwa jiki na rawa ta cewa dan daudun "jeka fito da hot girl"da hanzari yabar wajan yana tafiya yana rangwada. Bayan mintuna ya dawo yana gaba Sabriyah na binshi abaya gaba daya ta galabaita ga idonta ya kumbura sakamakon kukan da ta yi se ya mutsa fuska takeyi tsayawa ta yi agabansu. ɗan daudun ya ce"boss lady ga ta nan"jin an ce ga tanan da akayi ne yasa ya ɗago kai ya zuba mata ido,kasa janye idonshi ya yi akanta kyawunta ne ya fisgeshi da be san lokacin da ya mike tsaye ya nufi inda take tsaye ba kanta a ƙasa hannu yasa ya ɗago habarta suka zubawa junansu ido, watsa mishi harara ta yi da idanunta da suke a kumbure cikin tsiwa ta ce" meye hakan dalla sakeni"ƙayitatciyar murmushi ya yi, ya ce "I like that ina son yarinya me tsiwa da rashin kunya irinki, so sexy"bata fahimci me ya ce ba saboda sauran maganar da ya yi din da turanci ya yi shi tsaki ta yi ta ja baya tana ci gaba da hararanshi. Boss lady ta ce "ki dena mishi wannan shegiyar rashin kunyar taki saboda shine nan ya fanshe ki! ɗa yanxu kina can cikin dakin horo,ɗan haka binshi zakiyi har se ranan da ze koma idan ya tafi se ki dawo"wani irin bakin cikine ya tokarewa Sabriyah maƙoshi jin abinda boss lady ta faɗa satan kallon shi ta yi taga ita yake kallo yana mata murmushi se sannan ne ta kare mishi kallo balaifi ya burgeta. Ciki_ciki ta ce"to barin inje inyi wanka"bata sauraresu ba ta bar sashen ta nufi nasu abakin kofa ta tarda Asmita zaune gaba daya bata cikin walwalar ta tafi duniyar tunani Nabiha na ciki ta daura musu abinci. har Sabriyah ta shigo Asmita bata sani ba ji kawai ta yi an rungumeta dagowa ta yi dan taga waye.ganin sabriyah ne yasa ta yi ihu ta rungumeta itama suna dariya "my Tom ya akayi tabarki kika fito?"Asmita ta tambayeta. nan Sabriyah ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar da ita,Nabiha dake gefen su ta ce "gaskiya wannan gayen ya kyauta kawai ki bishi ki bashi kaya"hararan wasa Sabriyah ta mata ta ce "duniya da ƴaƴanta za bashi ba kaya ba"dariya sukayi dukkansu Sabriyah ta ce "my Jerry tashi mu shirya dan ƙafata, ƙafarki tare zamu je in ya so yamma se mu dawo amma nikam bazan kwana a wajan shi ba". MAIDUGURI Kyawawan yan matan Bishara's ne zaune a falo su hudu babu mutum daya ko wacce da abinda ta keyi daga me danna waya, se me cin snacks,sauran biyun kuma suna ludo. "Zoya miƙo mini laptop ɗin ki zanyi downloading,nawa na barshi a balcony"Umaisha ce ke yi wa Zoya magana tana kwance ko juyowa batayi ba balle ta bata laptop din nata tana kwance akan kujera tana chatting. "Dama dena bata baƙin ki kikayi, kinsan iskaci irin na Zoya ai,shisa na tsani Wallahi magana ya hadani da ita shegen girman kai da renin wayo"Parsa ta faɗa tana watsawa zoyan harara saboda ta tsani halin Zoya tana da mugun shariya duk da uwa daya uba daya suke amma hali be zo daya ba,jin abinda Parsa ta faɗa ne yasa Zoya ta mike zaune kanta babu hula gashinta bashi da tsayi sosai a kafardata ya tsaya tana sanye da riga bubu na atamfa ta ce "nikam Parsa ina wasa dake ne!? ko kuma reni ne da har kike kokarin zagina?"tsaki Parsa ta yi suka ci gaba da ludo da sukeyi ita da iklas. A harzuke Zoya ta yi kan Parsa zata kai mata duka saboda tsakin da ta mata ya bata mata rai sosai,hannu Umaisha ta sa ta jawo rigar Zoya "meye haka!? dan kawai ta faɗa miki gaskiya shine za ki daketa? Wallahi Zoya ki canza hali" "ina ruwanki kanwar ki ce ko kanwata?" Saketa Umaisha ta yi ta ce "to Wallahi ko ke kika haife ta bazan bari ki dake ta ba se kace wani girmanta sosai kikayi tsakanin ki da ita shekara daya ne amma se shegen son girma kamar gembo"duk wannan rikicin da Zoya da Umaisha sukeyi su iklas da Parsa basu kula su ba saboda dama sun saba kullum cikin faɗa suke,ke Zoya shariya ko zaka shekara kana mata magana bazata kulaka ba amma duk wannan abun nata batayiwa sauran brothers din su dan tasan duka zatasha iya kaci su Iklas din takeyi wa se kuma wanda be santa ba,ga bak'ar magana. ita kuma Umaisha tsokana da shiga abinda ba'a sa da ita ɓa.babu ruwanta kowa natane tana da saurin sabo bata da girman kai komai dinta simple ne a kwai barkwanci tana kuma son yan uwanta musamman ya'yanta Tajuddeen. Tattausan murmushi Parsa ta yi nan ainihin kyawunta ya sake fitowa saboda dariya da murmushi dabi'ar ta ne shisa idan ta bata rai har kamar kamanin ta sauya wa yake hakan ya rigada yabi jininta abu mawuyacine Parsa ta bata rai sosai akai,bata iya dogon fushi da mutum ko da kuwa mutum ne ya bata mata rai to ita zata bishi ta bashi hakuri, dan su ci gaba da magana,ko da wani abu kayi ko ka faɗa dan yabatawa Parsa rai tofa kayi abanza saboda ita babu ɓacin rai a cikin rayuwarta komai dinta murmushi ne haka zalika tana son yan uwanta sosai,shisa take jin haushi duk sanda taga abinda Zoya takeyi wa mutane. Murmushi ta yi ta ce "haba ku kuwa maganar ma nadauka ya wuce,Zoya kiyi hakuri baxan ƙara ba kinji!?kema Umaisha kiyi hakuri Zoya ba zata sake yunkurin dukana ba.kun ji masoyana ina sanku sosai"ajiyar zuciya Zoya da Umaisha suka sauke kusan a tare, murmushi Zoya ta yi ta ce "shikenan masoyiya bazamu sake ba,yanzu ku tashi muje muyi sallah kunga an idar da la'asar a masallaci kar su ya Sudais su zo su ga ba muyi sallah ba." Rike haɓa Umaisha ta yi cike da neman tsokana ta ce"Allahu Akbar!! yau wa ze mutu Zoya na yiwa mutane wa'azi!! gaskiya Allah ya miki albarka masoyiya, kullum ki dinga mata kafin ku fito da safe ko......"bata karasa maganar ta ba taji an wurgo mata filo tasan aikin Zoya ne dariya sukayi harda iklas da ta yi tagumi tana kallon su tana dariya,guje_guje Zoya da Umaisha suka fara yi a falon suna dariya Zoya ta nace se ta kama Umaisha. Murmushi da baya daukewa akan fuskar Parsa ba tare da dalili ba yana nan azuciyarta ta ce"duk wani farin cikina ze biyo baya ne,bayan naku ina matukar kaunar ku family na". Nufan hanyan fita falon Umaisha ta yi tana kallon bayanta bata san akwai mutum a gabanta ba kawai taji ta buge mutum,ja da baya tayi ta dago kai ta kalleshi mugun kallo da yake mata ne yasa taji gabanta ya faɗi lokaci daya ta shiga rigar nutsuwarta. Zoya dake Binta a baya ma tunda taga waye ne yasa simi_simi ta gudu sama, haka iklas da Parsa duk guduwa sukayi. A kausashe ya ce "bana hanaku wasan banza ba!?ko har yanzu ku yara ne!?"ya tambaye ta yana kallon fuskar ta da ta sunkuyar dashi ƙasa, girgiza mishi kai ta yi dan tama ka sa magana.rankwashi ya mata a kai wanda se da yasata ta yi ƙara ta daura hannu awajan tana shafawa. "Ina dankwalin ki yake!?yaran nan yanzu ba a isa a faɗa muku magana ku ji ba kenan ko!?" Gudun kar ya sake ka fa mata wani rankwshin ne ya sa ta ce "dan Allah ya Sudais ka yi hakuri Wallahi baxan sake fitowa ba hula ba!" Kallon gashin nata da yake kwance a gadon bayanta ya yi ya ce"in na sa ke ganin ki ba hula ki sa aranki ranan kwanan wannan gashin naki ya ƙa re.matsa kiban guri ko in yi ball dake."da sauri ta matsa tabashi hanya ya wuce ta bishi da kallo,fari ne dogo kyakkyawa yana da ginan nen jiki yana sanye da farin uniform na custom da hula komai dinshi fari alama daga office yake.murguda mishi baki ta yi kafin itama ta sa kai ta wuce ciki. Duk dramar da akeyi Rameesa na daga saman upstairs tana kallon su tunda ga lokacin da Zoya da Umaisha suka fara faɗa har zuwa lokacin da suke guje_guje da kuma shigowar Sudais din.banda dariyar mugunta babu abinda takeyi tana"Umaisha Wallahi in bakiyi wasa ba wata rana sede kiji ya Sudais yasa almakashi ya gimtse miki wannan gashin naki"ita kadai take magana tana dariya. "Ke kuma ke dawa kike wannan dariyar kamar wata kun kuncecciya!?"cewar Ammi da fitowar ta kenan daga part din Hajiya babba ta hangi Rameesa se dariya takeyi rungume Ammi Rameesa ta yi kafin ta tsagaita da dariyar nata ta ce"Ammi Wallahi su Umaisha basu jin magana wata rana se sun wayi gari sunga anyi musu malu,sun san sarai su ya Sudais,ya saghar,ya Jawan,ya Salim,ya Sahil, se sun musu magana akan saka hula ko dankwali amma su basu ji"dariya Ammi ta yi, ta mata marin wasa ta ce"ja'ira ke dinma yaushe kika fara saka dankwalin ina se da Jawan ya dake ki kafin kikayi hankali?"turo baƙi Rameesa ta yi"ni Ammi dena tuna min."dariya sosai Ammi ta yi kafin ta ce "nikam ɗaga ni,in yi gaba"dagata tayi tana dariya ta yi part din su da gudu.girgiza kai Ammi ta yi aranta ta ce "yaran nan kude bazaku taɓa girma ba". Duk suna zaune a part din su, Umaisha na zaune har lokacin hannunta na bisa kanta tana shafawa,Zoya ta ce "Allah ya taimakeni da ya Sudais ya ganni Wallahi nasan yau jikina se ya faɗamin saboda yau da safe kafin ya fita aiki seda ya mini rankwashi" "ke nifa tunda ya Jawan ya taba lafiyar jikina nadena yawo ba hula,ku ai bakwajin magana kun san sun tsani suga mutum ba hula akanshi"cewar Rameesa dake zaune kusa da Parsa,gyara zama Parsa ta yi ta ce "bama maganar basa so ba babu kyau ne yawo gashi awaje kuma duk mun sani yakamata mu gyara saboda shedanu"haka suka dinga hiransu Umaisha de batace musu komai ba,dan har lokacin kan nata na mata zugi. "Anty amaryanmu me kike dafa mana ne naji irin wannan kamshi me dadi haka!?"juyowa ta yi ta ɗan yi murmushi ta ce"abincin dare ne Saghar !me kake so a yi maka?"ta yi maganar tana kallon shi. "Ni banason komai na fi son abu liquid haka ko romon farfesu kawai amma kar asamin nama kawai romon nakeso." Rike baƙi Anty amarya ta yi ta ce "ku fa likitocin nan kunfi kowa kinibibi,da kai da uncle din ku kuna bani mamaki wai kuce ku bazakuci abinci da daddare ba sede kawai abu ruwa_ruwa.muda mukeci de ga shi bawai lafiya kuka fi mu ba."dariya Saghar ya yi "Anty amarya bazaku gane bane,da kun san illan cin abinci me nauyi da daddare tofa da kun dena domin ze sa muku upset stomach" "dallah yi mini shuru jeka zan biyoka da romon"sa kai ya yi ya fice yana dariya yabar Anty amarya ma tana darawa. Bayan sun yi sallar isha kowa yadawo sun hadu a dinning table banda Abbu da Abbie da ba sa ƙasan. Serving din kowa abincin da ranshi yake so fatime da kaltume suka yi,a tsanake suke cin abincin Ummah ta kalli Saghar ta ce "yau da ka dawo me ya hanaka zuwa ka gaishe ni Saghar?!" Ajiye spoon din hannunshi ya yi ya zuba mata ido domin ta taɓo mishi inda yake mai kaikayi Ammi ce ta daura hannunta akan nashi alamar kar ya ce komai,amma ya gagara shuru"kin zauna agidan ne ɓalle mu ganki mu gaisheki!? kullum kina hanya baƙi da lokacin Abbu ɓalle mu yaranki to aina nasan zan sameki har in ce zan gaida ke ummah!?" "Saghar ya isa haka"cewar Hajiya babba,spoon din ya dauka ya cigaba da shan romonshi ,mikewa ummah ta yi tabar dinning din. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ *🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹* Page 15 *_Story & written_* By *MRS🌹ISHAM🌹* ( Yar lelen Jarumai) *THE WRITER OF 🖋️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️ Page 15 Haka suka gama cin abinci kowa ka kalla zakaga fuskar shi da alamar damuwa, uncle Hameed ne ya kalli Saghar da Sudais ya ce"ina son magana daku biyun"mikewa su Zoya sukayi suka bar dinning din Jawan da Sahil,Salim suma suka tashi sukayi.saura daga uncle Hameed din se Hajiya babba, Ammi,Anty amarya se su wa'yanda akace su tsayan wato Saghar da Sudais. Maida hankalinshi uncle Hameed ya yi kansu sannan ya fara magana"meyasa kuke haka Saghar, yanzu ga shi tabar dinning din batare da ta kammala cin abinci ba!, ka bata mata rai. ba ko da yaushe zaku dinga titsiyeta akan yawan fitan da takeyi ba kamata ya yi kuje ku sameta cikin lallama da kuma daɗin baƙi ku nuna mata yawan fitan da takeyin nan ba kwa so tun kuna yara ake abu daya ga shi har kun girma kun mallaki hankalin kanku you're all matured enough.kai doctor ne shi kuma Sudais custom,babu wanda yakamata yasan matsalar mahaifiyar ku sama da ku din nan kunga de Zoya da Parsa bawani girma sukayi ba,ni se nake gani kamar akwai wani abinda yake damunta wanda bataso kowa ya sani tabbas tana cikin damuwa,kallon mintuna biyu nayi mata na nazarci hakan a tattare da ita,so please take good care of your mother mahaƙurci,mawadaci". Sun matuƙar gamsu da maganar uncle Hameed dama su abinda yake bata musu rai shine yawan fitan da takeyin ne,kuma har yau babu wanda ya san ina take zuwa. Sudais ya ce"in sha Allah zamuyi yanda kace uncle Hameed duk da bamu san menene matsalar ba,ni bawai yini nakeyi a gida ba in na fita 10:00am na safe bana dawuwa se yamma kuma duk da hakan bazan samu ummah a gida ba abin na sosa mini rai matuka." Haka Hajiya babba da su Ammi suka sake musu nasiha akan kulawa da mahaifiya,kafin daga bisani suka watse sudais ne kaɗai ya yi saura akan dinning din yana zaune yana danna wayarsa, buɗe sakonnin da suke shigowa ya keyi.kusan awan shi ɗaya a wajan masu aiki suka gama kwashe komai aka gyara duk yana zaune. Fitowa Umaisha ta yi daga ita se riga da wando na bacci masu kauri black color kanta babu dankwali bare hula. saboda batayi tunanin zata hadu da kowa a ko ina ba shisa ta fito haka kanta tsaye ko ajikinta. Saukowa ta yi dinning ba ta ga kowa ba sakamakon kashe wutan da Sudais ya cewa fatime ta yi hakan yasa bata ga mutum awajan ba ta shiga kitchen dan daukan ruwa da snacks dama abinda ya fito da ita kenan,tun shigowar ta ya hangota girgiza kai ya yi a hankali ya furta "yaran nan ba sa jin magana" gently ya mike ya nufi kitchen din ya tsaya a kofar ya harde hannunshi a kirjinsa yana kallonta rai abace.daukan abinda zata ɗauka ta yi ta juya domin barin kitchen din haɗa ido sukayi nan take tsoro ya kamata batasan lokacin da ta zubar da abubuwan hannun nata ba saboda tasan yau bazata kwana da gashinta ba tunda har ya yi mata warning akan hakan tasan yau shikenan malu Sudais ze yi mata. Daura hannu aka ta yi ta fara w'iwi da hawaye ta riƙe gashin nata ta soma magana kamar wata zararra"ya Sudais ka yiwa Allah ka yi hakuri bazan sake ba, karka rabani da gashina, wayyo Allah shikenan gashina.ya Sudais daga yau inka sake ganina ba hula kamin duk hukuncin da zakamin, amma dan Allah karka rabani da gashina kaga kowa na dashi su Rameesa zasu mini dariya "tana magana tana yarfa hannunta.tama ƙasa nutsuwa ta yi magana,matsowa kusa da ita ya yi ya sa hannunshi daya ya cire hannun da ta rike gashinta da shi,da hannu daya ya haɗe hannayenta duka biyu ya riƙe su gam.sannan yasa hannu a bayan aljihun shi ya fito da wuka yar karama se sheki yakeyi kamar ba'a taɓa amfani da ita ba ya kalli fuskar Umaisha yaga yanda ta zaro manyan idonta waje ga hawayen da takeyi har lokacin,a tsorace ta ce"innalillahi wainna'ilaihi rajuun!ya Sudais dan Allah kayi hakuri ka rufamin asiri kaga ni yarinya ce dan Allah karka rabani da gashina Wallahi bazan sake yawo ba hula ba, i promise you.in kaaaaaaaaa...aske mini gashi na miji zan koma me malu dan Allah ka yi hakuri". Ko kallonta be yi ba yasa hannu ya haɗe gashin waje daya ya ce"da na ke ce miki banason ku dinga yawo haka kam ba kun renawa mutane wayo ba!? kullum sekinyi alkawari bazaki sa'ke fitowa ba hula ba yau kam dole fa sena aske gashin nan sede in mutuwa zakiyi amma for sure zan aske".ga nin tabbas dagaske ya keyi askin ze mata yasa ta faɗa jikinshi sannan ta rike hannayenshi da ke rike da wukar tana kuka"ya Sudais bazan sake ba ka ji!?kayi hakuri". Da sauri ya rabata da jikinshi yana watsa mata harara ya ce"munafuka duk senayi maganin ku daya bayan daya tunda kunce ku bakwa jin magana da ƙaton kanki kamar randa, ki wuce ki bani wa..."be ma kammala magana ba ta sa gudu. taku biyu me kyau ya yi, ya riko hannunta ya ce"wa kika barwa kayan nan da kika zubar a ƙasa?!" Jiki na rawa ta fara kwashewa Allah _Allah takeyi tabar wajan gudun kar ya canza ra'ayi,maida snacks din ta yi ta ajiye ta ɗauki iya ruwan kawai ta fice da gudu, murmushi ya yi yabi bayanta da kallo koma wa dinning table din ya yi yadau wayarsa ya koma part din shi. Rameesa da iklas sune suka rage idon su biyu sauran kam duk sun yi bacci a dakin nasu dama haka sukeyi zasu zo dakin Rameesa da iklas su yi hira. suma su koma dakin su duk da a haɗe yake kofa ce kawai ya raba su,yaran matan part din su daban. babban falo ne da two bedrooms komai na jin dadi akwai aciki duk inda suka gadama suna kwana kuma kowa ni bedroom akwai manya_manyan gadaje har guda uku.some times a daki ɗaya suke kwana dukkansu.yau ma haka bayan sun baro dinning suka shigo dakin su Rameesa suna cikin hira umaisha ta ce zataje ta dauko musu ruwa da snacks, kafin ta dawo ne Parsa da Zoya suka yi bacci ya rage saura Rameesa da iklas ne idon su biyu. Shigowa ta yi tana kuka harda shesheka tasowa sukayi suka je suka rike hannunta suka zauna abakin gado suna tambayar ta me ya faru dakyar ta iya faɗa musu abinda ya faru tsakaninta da Sudais,jikin su ne ya yi sanyi jin saura kadan yau Sudais yayiwa umaisha aski da wuka,sosai suka dinga bata hakuri har ta yi shuru sannan suka kwanta bacci. A bangaren Sudais kuwa yana shiga part din shi ya tarar da Jawan da Saghar aciki da mamaki yake kallon su kafin ya shigo ya zauna yana faɗin "wai ku bakwajin bacci ne?"kallon shi sukayi a tare Jawan ya ce"ya Sudais wannan ɗan renin hankalin na biyo ya faɗa mini yaushe ze dauki hutu muje wajan hajjatiye, dan Wallahi muka bari tazo mu ba muje ba mun shiga uku tunda abbu da Abbie ma kafin suyi tafiya seda suka ƙara jaddada mana akan zuwan namu amma Saghar kam ya yi burus da zancen"rufe laptop din gabanshi Saghar ya yi ya ce"ya Sudais shi baze gane bane aiki ya mini yawa amma nan da next week se mu shirya mu tafi"shi de Sudais bece musu komai ba se binsu da ido da yake yi, saboda yasan sarai su Abbie suka dawo suka ji basu je ba ransu ne ze ɓaci,yana kokarin musu magana kira ya shigo wayarsa picking ya yi yasa a kunne. Wata tausassan murya me zakin gaske da kuma amo yana da kauri irin muryan jaruman maza da suke cike da izza,isa,gadara,haɗe da kuma umarni ne ya sauka a kunnen Sudais,ya ce "sa wayar a handsfree "yanayin yanda ya yi maganar kadai ma ya isa ya kwadaitawa mutum yaso ganin wanene mamallakin wannan murya,domin yanda ya ke fitar da maganar ma kadai abin burgewa ne. Kamar yanda ya faɗa haka kuwa Sudais ya yi yana murmushin mugunta ya saka wayar a handsfree din,kallon Sudais suke yi suna jira suji waye ze yi magana har kusan minti biyar kafin ya futar"ku shirya gobe ku tafi"iya abinda ya furta kenan 'kitt' ya kashe wayar dariya Sudais ya yi dan yasan yanzu kam tunda ya basu umarni yasan dole su je kuma a gobe_goben domin basa jayayya da maganar shi kallon Sudais Saghar ya yi ya ce"ya Sudais meyasa kafadawa LTG.Taj maganar tafiyan!?" dariya me yar sauti Sudais ya yi ya ce "ko kadan Ni banyi wannan maganar dashi ba,duk wani motsin ku yana kallon kowa, kaff gidan nan akwai cameran tsaro, part biyar ne kawai babu daga part din Ammi, Ammuh, Hajiya babba,Anty amarya,ummah.nan ne kawai babu a part din iyayenmu mata ne kawai babu CCTV camera" dariya Jawan da Saghar sukayi. "Yanzu de zuwa Sudan ya kamamu gobe wajan hajjatiye,amma su ya Sahil sun sani kuwa!?"cewar Saghar "malam kowa fa yasani kude kuyi booking tickets kawai"Sudais ya faɗa yana nufan bedroom din shi.hira sukaci gaba da yi se around 12:00 na dare kafin kowa ya nufi inda yake kwana. LAGOS ORIENTAL HOTEL Bayan sun iso hotel din da yake suna ciki an kawo musu lafiyayyun abinci sukaci,nan ya zauna yana jan su dan hira saboda su sa'ke dashi, aikuwa hakane yafaru domin yanda yake musu kamar ya daɗe da sanin su,lokaci daya suka saba dashi,duk wani motsin Sabriyah yana kan idonshi ji ya yi yafasa abinda ya yi niyar aikatawa da ita saboda kallon mata a gareshi ya fara mata duk wani abinda tayi burgeshi takeyi baya gajiyawa da kallonta, Asmita ce ta mike zata fita Sabriyah ta ce "my Jerry ina zakije!?"se da ta bude kofar kafin ta ce "zan leka cikin hotel din ne in dawo!"ta fice, dawuwa kusa da Sabriyah ya yi ya zauna cikin nutsuwa yafara mata magana. "Sabriyah nasan kinsan dalilin da yasa na dauko ki!?nayi ne saboda in samu wacce zata biya mini bukatata, but bansan meyasa ba tunda na daura idona akan ki se naji bana bukatar yin mu'amalar banza dake,ni bazan boye miki ba kullum sena kwanta da mace amma yanzu da ina tare dake se naji bana bukatar hakan! lokaci daya soyayyar ki ya kama zuciyata yanda bakya tunani.bansan ta ya'ya zan miki bayani yanda za ki fahimta ba,ji nakeyi akwai wata alaƙa me karfi tsakanina dake tunda jimawa wani irin lamari me karfi nakeji a tattare da ke Sabriyah. ki bani damar nuna miki soyayya ta har ki zamo mallaki na."kamar wani mutum mutumi haka Sabriyah ke kallon shi ko kyafta ido batayi ji tayi maganar nashi wani bankwarakwai ta ma rasa wani irin amsa zata bashi saboda ta fahimci he's a good guy amma bazata iya bashi damar soyayya ba saboda akwai sarkinta acikin zuciyarta duk da bata sa rai akan zata ganshi a rayuwarta ba amma ji takeyi intayi soyayya da wani ɗa namiji kamar taci amanar tajuju ne. "Meyasa kakeson yin soyayya dani?shin babu wata mace a rayuwarka ne!?"ta yi mishi wa'yannan tambayoyin tana kallon cikin ƙwayar idon shi, murmushi ya yi se da ya yi jim kaɗan kafin ya ce"akwai wata acikin rayuwata wacce a ko da yaushe nemana akanta yake, nemanta nakeyi acikin wannan duniyar ba dare ba rana.zan iyayin komai domin in samota zan ka war da duk wanda ya zaɓi ya shiga tsakanina da ita,ban taɓa tunanin zan so wata ya mace bayan ita ba se kuma ga shi bayan ganin ki da nayi se zuciyata ta kamu da sonki,kin san ance zuciya batada ƙa shi,zan aure ki duk sanda na sameta sannan itama in aureta." Ƙayitatciyar dariya Sabriyah ta yi wanda se da ya yi sanadiyar lotsewar kumatunta da suke dauke da dimple kyawunta ya sake fitowa, kallonta yakeyi kamar wani tsohon maye duk abinda tayi burgeshi takeyi, yarinyar she's so simple and dam beautiful. Dakyar ta iya dakatawa da dariyar renin hankalin da takeyi ta ce "ya ma sunanka dan Allah!?"ya ce "FU'AD na ke" "yawwa Fu'ad Wallahi kabani dariya dakace wai zaka auremu mu biyun,ni ina da wanda nake matukar kauna a rayuwata duk da bansan aina ne zan sameshi ba. amma, ina fatan haɗuwa dashi ko da ranata na ƙarshe a duniya ne ruhina ze samu sallama a duk sanda na hadu dashi."duk da ta faɗa mishi wannan maganar amma har lokacin murmushin kan fuskar shi be kau ba se ma ƙa ru wa da ya yi,ya ce" amma ya sunan shi saurayin da kikeso din!?"langwabe kanta gefe ta yi ta lumshe idanunta ta ce"sunanshi ta..."ba ta karasa ba a sakamakon kiran waya da ya shigo wayar Fu'ad ya ce mata "bani minti biyu bari inyi picking call"gyada mishi kai ta yi,fita a dakin gaba daya ya yi yana waya.dawo da kallonta kan kujerar dake dakin ta yi taga tarkacen laptops kusan biyar ga wayoyi da suka kai goma zuciyarta ne ya biya mata da son kallon abubuwan da suke ciki,mikewa ta yi ta isa har gaban kujerar tana kallonsu mamaki ne Yakamata tafara tambayan kanta to me Fu'ad yakeyi da wayan nan wayoyi da laptops masu yawa haka?, wani kofi ta gani na glass sims ne aciki masu yawan gaske wanda zasu iya kaiwa ɗari,sun cika kofin ga wani farar leda cike da cocaine wato fodar ibilis,duk da shi cocaine din bata san menene ba sa hannu ta yi ta dauki leda daya tana jujjuyawa,cike da karambani irin na Sabriyah yasa takai shi dede hancin ta tana kokarin shaƙa saboda tasan meye aciki,daga bayanta taji ya daka mata tsawa "Sabriyah"da sauri ta ajiye ta juyo tana kallon shi karasowa wajanta ya yi ya ce "me kikeyi anan!?"kallon su laptop din da suke jibge akan kujerar ta yi babu ko shakka ta ce "Fu'ad meye kakeyi da laptops masu yawa ga wayoyi ma,kalli sims masu uban yawa har cika kofi sukayi ,sannan kuma meye wannan a farar ledar nan!?"ta yi maganar tana nuna mishi su ɗaya bayan ɗaya. Shafa gashin kanshi ya yi,ya yi mata wani irin kallo ta kasan ido sannan ya riƙo hannunta suka koma kan gado suka zauna ya ce "babu kyau taɓa abinda ba'a baka izini ba akai, sannan kuma babu kyau dogon bincike!nidin me siyar da kayan wayoyine dasu laptops ina da babban shaguna a Maiduguri Sannan kuma ina gyaran su. wa'yannan mutane da yawa ne suka bani domin inyi musu gyara sims din kuma in na cire acikine nake ajiye musu."gyada kai ta yi alamar ta yarda da abinda ya faɗa mata ta ce" okay nagane!to shi kuma wancan farin garin fa me kama da foda "kallon cocaine din ya yi ya ce "wannan kuma abin wanke toilet ne" "okay"ta faɗa ta kwanta akan gadon,ta kasan ido yake kallonta yana kokarin danne fushinsa domin yau badan Sabriyah ɓace ta yi mishi wannan abun to da ya daɗe da kashe mutum amma da yake ita yana santa hakan yasa ya shanye mikewa ya yi, toilet ya shiga ya kunna shower, batare da ya cire kayan jikinshi ba ya sakarwa kanshi ruwa yana jiƙa shi hannu yasa yana dukan gefen kanshi da karfi kamar wani mahaukaci yana cikin dukan kan nashi kuma se ya dakata ya kalli yamma da kudu sannan yasa hannu a cikin aljihu ya fito da wata ledar cocaine ya zuba a bayan hannunshi sannan ya ka fa kanshi akan hannun ya shaƙa da karfi,ɗago kan ya yi ya jijiga shi sosai sannan ya samu ya dawo dede. Tana kwance tana tunanin ina kuma Asmita ta tafi da haryanzu bata dawo ta ji ya bude kofar toilet din ya fito ya canza kayan jikinshi da ya jika zuwa brown color din jallabiya kamar ba shine ya gama hauka acikin toilet ba se sakar mata murmushi ya keyi itama ta mayar mishi da martani ta ce "Fu'ad nikam bari in duba my Jerry a waje har yanzu bata dawo ba!" gaban mirror ya je ya tsaya ya ce "karki damu yanzu zata zo ba ta yi nisa ba"suna cikin maganar ta ta shigo,a rude jikinta har rawa yakeyi tazo ta rungume Sabriyah tana sauke ajiyar zuciya,ganin yanda ta shigo ne bata cikin nutsuwarta yasa Sabriyah ta ce "my Jerry meyafaru na ganki haka!?"numfashinta na fita dakyar ta iya cewa "my Tommmmmm,ina wannan din nannnnnn!?"magana take son faɗa mata amma tashin hankali da kiɗimewa ya hanata se jan maganar takeyi numfashinta na kokarin yanke. Tunda Sabriyah taga haka tasan tofa abinda Asmita ta gani babban abu ne hakan yasa tasake rungumeta tana shafa bayanta duk dan tasamu nutsuwa. Duk abinda suke yi yana kallonsu ta cikin mirror be ko waigo ba balle yace musu komai. Dakyar nutsuwar Asmita ya dawo ta tashi ajikin Sabriyah ta ce "my Tom yau naga abinda ya tayar mini da hankali,ina wannan Umar din nan da suka je afafa shi da wannan!?"ta faɗa tana nuna Fu'ad dake zaune a gaban mirror.gyada mata kai Sabriyah ta yi alamar ta ci gaba da maganar. Ta ce "yanzu aka fito da gawar shi acikin dustbin din hotel din anyi mishi kisan gilla seda aka sassara shi sannan aka jefa shi cikin dustbin."zaro ido waje Sabriyah ta yi tana me tuna lokacin da aka fito da ita daga dakin horo tare ta gansu shida Fu'ad a zaune. "Allah sarki bawan Allah ko waye ya mishi wannan kisan gillan oho, gaskiya yanzu duniya abin tsoro ne"ta cikin mudubi yake kallonsu yana sakin murmushin da shi kadai yasan ma'anarta a ranshi ya ce "shi ya jawa kanshi mutuwa,babu wanda yake Sanin abu akaina kuma in barshi yaci gaba da rayuwa"yana maganar yana murmushi tsinkayar muryar Sabriyah ya yi tana cewa "Fu'ad Allah sarki wanda kukazo afafa dashi yaron hotel din nan de an kashe shi."nan take ya sauya fuska zuwa na mutanen kirki me cike da jimami ya juyo da sauri ya ce"innalillahi wainna'ilaihi rajuun Umar din!?"ya faɗa da alamun tashin hankali a tattare dashi ya mike da sauri yabar dakin jikinshi na rawa. Bin bayanshi sukayi da kallo cike da jimami Asmita ta ce "Allah sarki ji yanda hankalin Fu'ad ya tashi" Sabriyah ta ce "eh ai dole hankalinshi ya tashi,kinsan Umar din yaron shine!shi yake mishi hidima a hotel din nan" haka suka dinga jimanta mutuwar Umar din. Ba'a yi wani dogon bincike dangane da mutuwar Umar ba saboda Lagos oriental hotel,babban hotel ne a Lagos yana daya daga cikin hotel din da ake ji dashi.idan aka fara bincike kuma ze jawo hankalin al'umma hakan yasa aka kashe maganar kawai dama bashi da wani gata yaron. Bayan sati daya shakuwa sosai ya shiga tsakanin Fu'ad da Sabriyah and Asmita saboda yanda yake kulawa dasu komai yi musu ya keyi kamar wani ɗan uwansu,ya hana su komawa afafa ya ce su bari in ya tashi tafiya shi da kanshi ze kai su, a yayinda yake kwana a falo Sabriyah da Asmita kuma suna kwana a bedroom,har zuwa wannan lokacin be nemi Sabriyah da wata mu'amala ta banza ba, saboda kamar yadda ya faɗa mata son tsakani da Allah yake mata. Asmita ta yi wani saurayi acikin hotel din ya dawo daga Indonesiya ya sauka a hotel din a ranar ya hadu da Asmita sosai suke soyayya har waya ya siya ya bata,hakan yasa Fu'ad ma ya siyawa Sabriyah waya Samsung Galaxy S20. Sabriyah da Fu'ad se Asmita ne zaune a falon hotel din Sabriyah ta ce "nikam Fu'ad ba kace nan da sati daya zaka tafi bane!?,ni Wallahi na gaji da zama a hotel din nan kawani killace mutane haba."dariya shi da Asmita sukayi ya ce"kai Sabriyah kina da matsala yanzu ke hakan be fi miki ba?,akan gantalin da kukeyi afafa!?"harara ta watsa mishi cikin ɓacin rai ta ce "ba gantali mukeyi ba,a haka muka taso kuma ni bani da wajan da yafi mini wannan gidan"tana gama maganar tabar falon domin maganar da Fu'ad ya faɗa ya bata mata rai,kallon juna Asmita da Fu'ad suka yi cike da mamaki domin sude acikin wannan maganar ba su ga abin ɓacin rai ba,bin bayan sukayi domin ba ta hakuri. THE UNITED STATE OF AMERICA MILITARY HEADQUARTER. Manya_manyan sojoji ne masu muƙami a zaune acikin wani keɓebben dakin bincike su biyar kuma dukkanninsu turawa ne daga General, brigadier general,major general, surgeon general, colonel general duk suna zaune da alama akwai wanda suke jira domin su ci gaba da tattaunawar da zasu yi ɗago kai general ya yi cikin harshen turanci ya ce"anya lieutenant general ze samu zuwa kuwa!?"colonel general yana duba wasu files da sukayi ƙura ya ce "tabbas lieutenant general ze zo saboda,burinshi shine criminals su shiga hannunshi su sha azaba,ba ya wasa da abinda ya kasan ce me mahimmanci,kar ku manta shifa sojan ƙasa da ƙasa ne dole ne ma yazo saboda rayuwanka al'ummar ko wata ƙasa yanada alhakin kare su"jinjina kai sauran sojojin sukayi. bude kofa wata kyakkyawar baturiya ta yi jikinta sanye da kakin uniform din sojaji ga bindiga a gefen kugunta, tana shigowa ta ƙame sannan ta sara musu. shigowa dakin binciken ya yi cike da jarumta irin na manya_manyan sojoji,yana sanye da army trouser wato wandon sojoji,yayinda yake sanye da riga armless na sojaji yaɗan matse shi,ya nada wata irin sura me matukar razanarwa, rikitarwa da kuma jan hankali haɗe da ƙayatarwa, saboda a halitta dogo ne me farfadar kirji a bude yake,ga six packs din shi baro_baro ya cika vest din kana ganin zanen kirjinsa ya fito a ta cikin vest din da ya sa'ka,idan ka kalli damtsen hannunshi kuwa se ka tsorata,kana gani kasan yanada matukar karfin gaske kamar dan wrestling haka surarsa take mutum ne me ji da karfi. Idan muka je wajan cikin sa kuwa a shafe yake babu alamar yana cin abinci saboda yanda wajen ya yi flat. Launin fatarsa kuwa fari ne sol irin wannan farin larabawa saboda shidin jinin shuwa Arab ne bugu da ƙari kakar mahaifiyarsa ta kasance baturiya. A wajan kyau kuwa sede muce tubarakallah Masha Allah domin Allah ya yi masa baiwar kyau me matukar razanarwa da kuma kayatarwa,ko na miji da suke jinsi daya se ya zuzutawa kyawunsa ɓalle mace. bugu da ƙari dogo ne ga murɗaɗɗen,ƙarfaffa duk abinda mace za ta bukata a jikin namiji Allah ya wadatasa da shi.sumar kansa kuwa yana ɗauke da wata irin aski me suna faded hair cut gefe da gefen kan an rage wannan ƙayitatciyar sumar, se ya zamana tsakiyar kan ne ke dauke da suma me matuƙar yawa da tafiya da hankali, sumar baƙine sosai yana kwance se sheki da daukan ido da yake yi,irin gashin larabawa. askin kanshi ma kadai abin kallo ne,hatta gaban goshinsa akwai suma a kwance,gashin jagirarsa kuwa tamkar an zanasa yana cike har suna kokarin hadewa waje daya,idan muka koma kan idanunsa kuwa sun kasance manya masu daukan hankali yana dauke da dogayen eyelashes, Allah ya ba shi kyawawan idanu masu girma da ga su so sexy da kuma tsoratarwa,farare tass da su me dauke da kwayar ido golding color masu shining kamar an kunna haske da kuma daukan ido.yana da dogon hanci me kyau da tsayi kamar pencil ga red libs din shi da suka kasance dan karami kamar ya shafa jan baki.fuskar shi na kewaye da wani irin kwantatciyar saje, da ya yi wa fuskarsa ado. Hannunsa na hagu na sanye da wrist watch kirar Breguet wanda kudinsa yakai kimanin N=950000 dubu ɗari tara da hamsin.yayinda hannun dama shi ke dauke da wani bangule fashion designer ne silver color ya yi masa kyau sosai. Zama ya yi akan daya daga cikin kujerun ya miƙa musu hannu suka gaisa ba tare da ya yi musu magana ba,nan suka fara tattaunawa akan abinda ya tara su a wajen. "The Italian Mafia gangs sune abinda muka maida hankali akai suna da matukar hatsari, musamman boss din su da bamu san ya kamanin shi yake ba hatta su yan kungiyar ba su san wanene shugaban su, saboda ya kasance me wayo,basira da kuma basaja shisa har yau ba'a yi nasarar kama shi ba,su din yan ta'adda ne masu matukar hatsari.amma daga zaran an kama shugaban nasu to game din su yazo karshe,se wasa yakeyi da hankali hukuma domin yasan neman shi mukeyi ruwa a jallo!"duk wannan jawabin general din su ne yake yin su,su kuma sun kasa kunne suna saurarar shi. Ci gaba da magana ya yi cikin harshen turanci"a cikin kwanakin nan mun samu update kan cewa yana Cameron so ya kamata kafin ya yi wani kokarin cutar da mutane ya kamata ya shigo hannun mu." "No!he is not in Cameron"ya yi maganar calmly yana kallon gefe duk zuba mishi ido sukayi,major general ne ya ce "how do you know that?"basarwa ya yi kamar ba shi ya yi maganar ba. General ne ya ce"*LIEUTENANT GENERAL TAJUDDEEN* ka sanar da mu yanda akayi kasan baya Cameron"juyawa ya yi ya kalli major marry Johnson ta hannun damarshi ita ce duk inda zeje take tsaron shi wato sakatariyar shi kenan,cikin zafin nama tafito da wani ɗan karamin converter a aljihunta ta miƙa mishi sannan taje ta haɗa slide show ta koma ta tsaya. Mikewa ya yi, ya taka izuwa inda slide show din ya ke yayi connecting din sa da converter nan take bangaren da yake ya koma kamar akwai tv awajan hoton katoton map ne ya bayyana. Facing din su ya yi ya soma magana kamar ba yaso"last week anyi updating dina kan cewa shugaban Italian Mafia yana Cameron but dana sake bincike se na fahimci ya yi hakan ne ɗan ya juyar da tunanin mu akan inda ze je"jinjina kai sukayi sannan colonel general ya ce"to inde ba ya Cameron to yana ina!?" "He is in Nigeria!yaje Nigeria ne ɗan akwai wani mission din shi da yakeso ya yi accomplish amma bazan taɓa bashi wannan damar ba ni da kaina zan kamo shi in mishi hukunci mafi girma da azaba"tafa mishi sukayi suna yabawa kaifin basirarsa da kuma naciya akan aikinsa bugu da ƙari yana da ƙwaƙwalwa wacce take da kusan karfin computer yana da saurin nazartan abu da kuma hasasowa, gaskiya Allah ya yi wa lieutenant general Tajuddeen baiwa. "LTG.Taj wannan case din yana hannunka ko ta wani hali muna bukatar shugaban Italian Mafia ko a ma ce ko a raye,all the best."cewar general,gyada musu kai ya yi sannan ya karbi sun glass din shi a hannun major Marry ya saka fita ya yi daga dakin binciken, major Marry na biye dashi abaya,sojoji birjik na gani ko ta ina duk inda ya wuce se an sara mishi sannan kuma su biyoshi a baya nan na fahimci nan din HEADQUARTER sojoji ne wa'yanda suke biyosu kuma duk sojojin sa ne,bude mishi motar akayi ya shiga sannan major Marry ma ta shiga. motocin da suka kai guda goma ne suka fita a cikin headquarter din domin zuwa gidan LTG.Taj. Yana cikin mota kira ya shigo wayarsa dake rike a hannun major Marry dubawa ta yi cikin harshen turanci ta ce "Ammi is calling you LTG."miƙa mata hannu ya yi ya karbi wayarsa kirar iphone 15 pro max wanda kudinsa yakai 2.5million, ganin video call Ammi ke kiransa yasa ya yi picking. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ 🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹 Page 16 *Story & written* By MRS🌹ISHAM🌹 ( Yar lelen Jarumai) *THE WRITER OF 🖋️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ 🌹*ASHE ZAMUGA JUNA*🌹 📚📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚📚🖋️ Page 16 Cire sun glass din idonsa ya yi ya zubawa kyakkyawar fuskar Ammi ido, murmushi ta yi ganin shi acikin motar ne ya tabbatar da baya gida. Slowly ya ce "Ammi kuna lafiya?" "Lafiya klau Taj,yaushe zaka shigo Nigeria ne kam nagaji da zuwa ganinka,rabonka da gida yau shekaru goma kenan ka ƙi dawuwa!"ta yi maganar tana tsare shi da idanu. Ba ze iya faɗa mata kan cewa yanzu haka ma yana shirin shigowa Nigeria ba ,saboda in suka san da zuwansa to zasu dame sa bazasu barshi ya yi abinda ya kawo shi ba.hakan yasa ya ce mata "Very soon Ammi"sun danyi hira balaifi daga bisani suka yi sallama,ya yi dede da isowar su makeken gidansa dake cikin babban birnin Green bye Wisconsin. Wa'yannan manyan samudawan ne suka bude mishi motar, major Marry ce ta fito ta tsaya, seda ya kusa mintuna uku sannan ya fito duk sara mishi sukayi. be bi takansu ba yawuce direct cikin haɗeɗen gidansa. Babban gida ne me kyau da tsari komai na jikin gidan glass ne kama daga windows,kofofi,da kuma wasu bangaren jikin gidan glass ne,daga ta waje painting gidan light brown ne amma daga zaran mutum ya shiga cikin gidan , nan ne ze san anyi wasa da kuɗaɗe acikin wannan gida kamar ba'a so, painting ciki White color ne,falo yana da girman gaske ga manyan kujerun da suke ciki suma farare hatta carpet, chandelier light se kawo wuta kala_kala sukeyi,ga makeken tv dake manne a jikin ginin kamar tare aka gina gidan dashi,gefe daya na kuma wani wajene da aka tanadeshi dan shan dumi, idan ana sanyi wajan duk gilashi ne amma shi da kanshi ze kunna wuta ya bawa falon warm weather,iya haɗuwa falon ya haɗu,ga matattakalar bene dake falon wanda in mutum ya hau ze sadashi izuwa wajan lifter. anan zaka samu damar zuwa bangarori da suke dauke da wasu ɓangaren daban acikin gidan,suma wannan bangaren sun gaji da haɗuwa dan zan iya cewa ya mafi downstairs tsaruwa da hafewa.gidan LTG.Taj ya hadu ta ko ina innace zan tsaya zayyane muku irin kyawun gidan to fa ko page daya be ze ishemu ba. Ya na shigowa falo ya cire armless vest din dake jikinsa ya rike a hannunsa ya haura stairs domin ya sada shi da lifter da ze kai shi part din shi.bayan lifter ya tsaya bedroom din shi ya shiga ajiye vest din ya yi akan gado sannan ya nufi toilet ya yi wanka ya fito daure da guntuwar towel daure a kugunsa nan ne nasake ganin ainihin zubin halittar jikinsa, farfadar kirjisa na dauke da wasu kwancecciyar suma mai laushin gaske sun yi luf_luf akan fatar kirjinsa haka daga abinda ya yi cinyar sa har izuwa ƙafafuwan sa akwai wayan nan kananun sumar nasu jan hankali, remote control ya dauka ya ɗanna nan take wani bangare daga cikin dakin ya bude ko ta ina gilashi ne ,a wajan shiga ciki ya yi,dakin kayan sawan sa ne kawai aciki komai wani irin nau'in kaya bangaren sa daban haka zalika bangaren uniform din shi ma daban,three quarter na company Dior designer black color yasa ka,ba tare da yasa riga ba ya fito daga dakin ya dawo bedroom din shi ya kwanta akan gadonsa. Nigeria Sauri_sauri ya ke tafiya saboda baze iya gudu ba, sakamakon raunin da ke ƙafar sa,burinsa shine ya samu wanda ze yarda dashi ya dauki wannan ma'adar memory card din,yabasa da yake tare da shi.waigowan da zeyi se yaga sun kusa cin masa acikin bakar motar hakan yasa ya faɗa cikin wani restaurant (cin abinci)da ba kowa aciki alamar sun tashi a aiki,ya buya a kasan table,haka wa'yanda suke binshi a motar suka shigo cikin wajan suka neme shi amma basu gan shi ba,fita sukayi a wajan cin abincin suka ci gaba da neman shi,nauyayyan a jiyar zuciya ya sauke ya fito daga kasan table din yana goge zufan da ke kan fuskarsa.fito da memory card din ya yi yana tunanin waye ze bawa wannan memory, saboda duk mugun shirin su ya rigada ya yi recording a ciki.kallon ƙafarsa ya yi da yake daure da rigarsa gudun kar jini ya dinga zuba saboda harbin bindigan da suka mishi, amma da yake gudun ceton ranshi ya keyi hakan yana mishi jin raɗaɗin da karfasa yakeyi. Motsi yaji a bayan shi hakan ne yasa ya juya, daya daga cikin ma'aikatan restaurant din ne, kallon tuhuma take bin shi dashi kafin ta ce "Malam daga ina!?kuma ne kake yi a ciki nan a irin wannan lokacin!?" "Ki taimake ni in kwana anan,wasu ne suka biyo ni zasu kashe ni."cikin tsoro ta ce "what!!su waye su din kuma meye alaƙar ka da su!?"be iya ce mata komai ba se ma runtse idanunshi da ya yi ganin hakane yasa ta rike hannunsa ta taimaka mishi suka shiga can ciki wani dakin dake cin restaurant din ta taimaka mishi ya kwanta, warware rigarsa daya daure ƙafar dashi ta yi,ganin harbin bindiga ne yasa duk ta rikice ga shi ita ba doctor ɓace ɓalle ta cire mishi harsashin. Shi ya dinga faɗa mata yanda zata yi har ta cire harsashin yana ƙaran azaba itama tana kuka saboda ba aikin ta bane,bayan haka kuma mata suna da matuƙar rauni. Wayewar garin yau ne Fu'ad ya fara shirin tafiya ji yakeyi kamar kar ya tafi saboda har ya fara kewar su Sabriyah da Asmita duk da ya musu alkawarin ba ze daɗe ba ze dawo, sannan babu yanda be yi da Sabriyah kan ze siya musu gida su bar afafa ba, amma fir ta ƙi ta ce ita babu in da yafi mata can dinm hakan yasa babu yanda ya iya ya kyaleta ya dauki makudan kuɗaɗe ya basu. Fitowa ya yi da trolley din kayansa ya samesu a falo suna zaune, mikewa sukayi da suka ga yafito su ma da nasu trolley din su a hannu.karewa Sabriyah kallo ya yi daga sama har ƙasa tana sanye da wandon jeans crazy blue color,se riga me daguwar hannu me high neck white color gashin kanta ta sa'ke su a bayanta murmushi ya yi ya ce "Sabriyah kinyi kyau sosai"ba ta bashi amsa ba illa murmushi kawai da ta mishi .duk babu dadi takeji domin sabo turkin wawa ne.fitowa sukayi daga hotel suka shiga motar shi yakai su har afafa,fitowa sukayi daga motar suna wa juna bye_bye,se da ya tabbatar sun shiga cikin gidan sannan ya wuce, komawa hotel din da ya baro ya yi, ya canza daki daban ya kama wani.wasu mutane ne sukayi knocking ya je ya buɗe musu kofar, wasu zabga_zabgan matasa ne su bakwai suka shigo dakin ko ina na jikinsu a murde yake wani irin alama sukayi da hannunsa alamar girmamawa gyada musu kai kawai ya yi,kallon su ya yi cikin harshen yaren French ya ce "kun kama shi ne!?"dayan su ne ya ce "ah ah ya ɓace mana amma ko ta halin ƙa'ƙa se mun kama shi domin inde wannan daukan ya fita shirin mu ya tashi a banza!" "To ku gaggauta yin hakan, in kuma ba haka ba ku fuskanci hukunci,domin ya riga da ya kwashi duk wani sirrin mu a cikin wannan daukan da ya yi.gobe zan bar Nigeria ku tabbatar kafin in tafi kuzo mini da albishirin kun kasheshi."ya gama maganar idon shi na kansu. Sa'ke yin wannan alamar sukayi kafin dukkansu suka haɗa baki wajan faɗin "we are the mafias!, blood shed blood!,we stand with our words!,the world is ours!,we choose who to live, and we choose who to die!, mafias are the most strongest union."suna gama fadin hakan suka fita acikin dakin hotel din suka tafi. A bangaren su Sabriyah kuwa ko da suka shiga ciki basu samu Anty Teema ba,zama sukayi acikin dakin suna ta hiran irin kyautatawar da Fu'ad ya musu.wayar Asmita ne ya yi ƙara dubawa ta yi taga saurayinta Taheer ne hakan yasa ta dauka tasa a kunne hira sukayi sosai har take sanar dashi sun dawo afafa. Se karfe biyu na rana Anty Teema ta dawo jin kamar motsin sune yasa ta leka dakin nasu tun daga bakin kofar dakin ta fara magana "in ya!!, yara kun zama ajeboters se yau Allah ya yi kuka dawo kenan?",tayi maganar tana karasowa cikin dakin nasu ,da gudu suka je suka rungumeta sun yi kewarta sosai,shafa kansu ta yi tana dariya ta ce"har wani fresh kukayi abunku!"dariya su din ma sukayi suka zauna akan katifa, nan fa hira ya barke tsakanin su sunata bata labarin rayuwar da suka yi a oriental hotel,da kuma yanda Fu'ad ya dinga kulawa da su,nan Anty Teema ta ce "ai Wallahi Sabriyah gwara da kika ce mishi ku nan zaku dawo in bahaka ba, boss lady har can oriental hotel din zata tura a dauko mata ku,ɓalle ma ke yanda ta mayar dake ATM din ta, yanzu haka ina shigowa naga gidan rawa ana gyara shi alamar yau za'a yi show shine na fara tunanin cewa de ku bakwa nan,ashe ku har kun dawo ma abunku."kallon juna Sabriyah da Asmita sukayi cike da mamaki domin kuwa yau ai ba lahadi bane ɓalle ace suna da show din rawa yau Alhamis ,ta ya hakan ze kasance. Mikewa Sabriyah ta yi ta ce "bari in je wajan boss lady din in gaisheta in ji yau nice zan yi show din ko wata ce!"ta yi maganar tana saka takalmi a ƙafar ta,ba ta saurari Anty Teema dake mata magana ba ta yi gaba.a hanyar zuwanta wajan boss lady ta hadu da ƙawar Nabiha suka gaisa ta tambayeta ina Nabiha nan ta ce mata sun fita dazun ita da Cele. "Okay in ta dawo kice mata mun dawo dazun" sannan ta wuce. ta shiga wajan Boss lady.a kwance ta sameta ga dan daudun nan yana daddanna mata kafofunta ita kuma tana daga kwance tana shan w'iwi,zama a kusa da ita Sabriyah ta yi ta gaisheta, murmushi Boss lady ta yi ta ce"hot girl manya,yanzu kam nasan zaman da kikayi a wajanshi ya mayar dake cikakkiyar mace,shisa naga ko ina na jikinki ya ciko,ai hannun namiji iri ne."murmushi kawai Sabriyah ta yi dan batasan me za ta cewa boss lady ba hakan yasa ta canza maganar ta hanyar faɗin "boss lady naga anata shirya gidan rawa!,akwai wacce za ta yi wasa ne!?" "Ehh ke da Asmita ne zakuyi wasa saboda muna da manyan ba ƙi,ga kayan nan ki tafi dasu"ta ƙarishe maganar tana daukan ledar sabbin kayan rawan ta miƙa mata,kar ɓan su Sabriyah ta yi cike da nishadi ta tashi ta yi mata se anjuma ta koma sashin su.yanda ta tafi tabar anty Teema da Asmita haka ta same su nan ta faɗa musu yadda sukayi ita da boss lady.ita de Asmita wannan rawan bawani son yi takeyi ba,kawai tanayi ne dan babu yanda ta iya tunda de bata Isa ta ce bazata yi ba.ita kuma Sabriyah babu abinda idan ta yi take samun nishadi irin wasan rawar hakan na kwantar mata da hankali,shisa duk sanda ya kasance ranar zatayi wasa to fa za'a ganta cikin walwala,haka suka ci gaba da hira har lokacin da Cele ya shigo yana ganin su yabasu hannu suka tafa nan fa sabon hira ya barke a tsakaninsu kamar wa'yanda sukayi shekara basu haɗu ba.fita a dakin Cele ya yi ya je ya siyo musu nama da drinks.ya dawo aka daura hira daga inda a ka tsaya. 8:00pm na dare Sabriyah da Asmita anyi musu kwalliya ga kayan da suka saka ya ainihin fito musu da shape din su,har sun zo fita Sabriyah ta lura abin hannunta ba ya tare da ita nan ta fara dubawa,ko ta yarda shi ne a dakin. Asmita da ta lura da kamar abu ta ke nema ne ya sa ta ce. "My Tom me kike nema ne haka!?" batayi wata_wata ba ta bata amsa,jim kaɗan ta yi ta ce "to ai tun kafin mu bar gidan nan babu shi a hannunki". Arazane Sabriyah ta kalli Asmita cike da tarin tambaya "bangane ba,me kike nufi da baya hannuna!?".hannu Asmita ta sa ka a saman window dakin nasu ta dauko mata shi ,ta ce "kina bacci ne ya fita a hannunki shine na adana miki, anan kan cewa washe gari in ba ki to kuma se na manta har muka tafi ban ba ki ba ."ajiyar zuciya Sabriyah ta yi har idonta ya cika da hawaye ta ce "Nagode sosai my Jerry,da ace wannan abun ya bata da bansan wani irin hali zan shiga ba,domin wannan din alkawarine tsakanina da Tajuju na,in na batar dashi kamar na batar da soyayyar da nake mishi ne."gaba daya jikinta ya yi sanyi ji ta yi kamar bata kyauta ba da har tabar abin hannun ya fita a hannunta,dafa kafardata Asmita ta yi ta ce"kar kuma jikin ki ya mutu mana,ko kin manta yau ranar nishadin ki ne!?"murmushi ta yi suka rungume junansu kafin suka fita a dakin,suka nufi gidan rawan da ya cika makil su kadai kawai ake jira. Suna shiga aka hau musu tafi da watsin kudi,nan suka fara gabatar da wasan rawar nasu cikin kwarewa. Se kusan karfe goma suka kammala wasan nasu, sun sha ruwan kudi na fitan hankali,manyan baƙin da boss lady ta yi se turawa sukeyi a kira musu Sabriyah da Asmita,amma fir sunki zuwa daga karshe ma barin wajan suka yi saboda tsananin gajiyan da sukayi,dakin su Nabiha suka wuce nan suka sameta tana gyara kayanta da ta wanke, zama sukayi gefenta ,kallon su Nabihan ta yi ta ce "gaskiya yau na yi missing banga wasa ba" "uhmmm kin kyauta ai,Cele ya ce mana zakizo se bamu ganki ba"in ji Asmita,ajiye kayan da take ninkewan ta yi,ta ce"ke Wallahi Asmita ba ki iyawa mutum uzuri ba,sugar daddy na ne ya ce in shirya gobe zamuyi tafiya shisa ban samu fitowa ba." Sabriyah kam zani ta dauka ta daura a kirji sannan ta kwanta ta basu baya tana jin su se hiran su sukeyi,anan wajan suka raba dare har wajan karfe sha biyu sannan suka koma na su bangaren. Suna isa Sabriyah ta ji wayarta na kara dubawa ta yi taga Fu'ad ne ya mata kusan 10 missed calls,kiransa ta yi suka sha waya sannan ya ce tabawa Asmita wayar su gaisa hakan akayi kuwa nan ma sun bata tsawon lokaci suna hira da Asmita kafin nan sukayi sallama. Kwanciya suka yi da niyar yin bacci,har bacci ya fara daukan su Sabriyah ta farka, soma yi wa Asmita dake bacci magana ta yi. "My Jerry kin san abinda ya kamata muyi kuwa gobe!?" Asmita da idonta duk bacci ga Sabriyah ta tasheta ta ja tsaki ta ce "meye ne ɗan Allah,baccin ma ba za ki bar mutum ya yi ba haba!" Dariya ne yaso kufcewa Sabriyah ta danne ta ce "gobe ya kamata mu shiga kasuwa tunda kin ga akwai kudaden da Fu'ad ya bamu,mu yi siyayya mu gyara dakin mun nan Wallahi,mu sa mishi komai sabo!" Wani irin kututun bakin ciki da takaicin Sabriyah ne ya tsaya mata a rai,ta kalli Sabriyah,rai abace ta ce "yanzu saboda wannan banzar maganar kika tasheni Sabriyah!?nikam wai meye nufin kine?kina tunanin zamu tabbata a cikin wannan ƙaddararren gidan ne?,ke shikenan ko da yaushe magana daya biyu baya wuce akan gidan nan,to nikan nagaji Wallahi ko kina so ko bakya do Sabriyah se mun bar gidan nan gaba."yanda Asmita take magana kadai ya isa ya nuna kan cewa ranta ya yi mugun ɓaci, saboda ita ta rasa menene abinda Sabriyah ta gani a cikin gidan da kullum in an tashi magana se ta ce bata da wajan da zataje yafi mata wannan gidan,a duk lokacin da ta yi wannan maganar ran Asmita bakaramin ɓaci yakeyi ba. Lura da ta yi ranta ya ɓaci ne yasa ta mayar da maganar wasa amma ita kam har ranta tana son zaman gidan saboda muddin tabar gidan batasan ina kuma rayuwarta ze ƙare ba tunda ba iyayene da ita ba ,ɓalle ta ce tasan wata rana zata hadu dasu,bata da kowa,shisa duk irin ɓacin ran da take fuskanta a gidan be sa tayi tunanin barin gidan ba. "Ke dallah karki mini masifa wasa nake miki,amma de kinga ledar dakin mu ya mutu, se muje mu siya wani goben!". Watsa mata harara ta yi ta ce"ki fadawa wanda be sanki ba,nayi miki sanin da ko kaina banyiwa ba,kamar yanda kika mini farin sani haka nima nayi miki,dole duk maganar da kikayi in san da gaske kike ko kuma wasa.amma wannan maganar ta ki kam nasan har cikin ranki kika faɗe ta saboda ba tun yau kika saba faɗa ba." Tsaki Sabriyah ta yi ta juya mata baya ta ce"se kuma kiyi ai kanki ake ji." Baccin da basu yi da wuri ba kenan saboda cacan bakin da suka tsaya yi daga karshe ma Sabriyah juya mata baya ta yi ta kyaleta,haka Asmita ta yi ta masifa kamar zata aro bakin wani ta ci gaba, babban abinda ya bata mata rai ma shine shareta da Sabriyah ta yi taƙi biye mata su ci gaba da faɗan,hakan yasa ta zuba mata dundu a tsakiyar bayanta. Sosai dukan da ta mata ya yi mata zafi amma ɗan neman magana kawai se tafara munshari irin bacci ya yi nisa da ita, tana dariya kasa_kasa,haka Asmita ta gaji da masifar ta kwanta ta yi bacci. Tunda garin Allah ya waye babu wanda ya kula wani acikinsu kowa harkan gabansa yakeyi, Kamar kullum Asmita ce ta musu abin karyawa ta zuba musu a plate sukaci, Sabriyah ce ta fara yin wanka sannan Asmita ta shiga. Shiryawa Sabriyah ta yi cikin doguwar riga mara nauyi ya dangale mata pink color,yana da open shoulder rigar kafadarta awaje da kuma bayanta ga sunan Tajuddeen baro _baro da yafito abayanta ,gashin kanta kuma ta daure su waje daya da ribbom ta saka hula shima pink.kallon Asmita dake kwance ta yi ta ce "ki tashi muje mu siyo ledar dakin!" ɗa kamar bazata je ba se kuma ta mike ta dau wayar ta,ta ce" muje" Ledar dakin suka siya sannan suka fara kokarin koma wa gidan hango wata yaloluwar riga Asmita ta yi ta cewa Sabriyah "barin in je in siya ina zuwa". Tsayawa a wajen Sabriyah ta yi rike da ledar tana jiran Asmita da taje siyan riga. Shuru_shuru Asmita daga siyar riga daya se ta ɓige da duba wasu kayan. Tsaki Sabriyah ta yi aranta ta ce bari in je in samu wani wajan in zauna in jirata . Daukan ledar dakin ta yi ta soma tafiya waigawa bayanta ta yi saboda taga ko Asmita ta fito daga shagon. Gif!taji ta buge abu kamar gini da sauri ta juya dan taga menene mutum tagani a gabanta sanye da kananan kaya fuskar shi da facemask da kuma hular facing cap idon shi kawai da ke binta mugun kallo ta iya gani me kama dana zakin zakuna wanda yafito farauta,kayan hannunta ne ya zube akasa da kuma wayarsa a tare suka sunkuya domin daukan kayansu,tsaban tsaurin ido irin na Sabriyah duk da yanda ta ganshi a murde amma tsaban yanda take fama da rashin kunya ta ja tsaki ta ce "kai makaho ne ko kuma gani ne bakayi zaka wani buge mutane!?" ,a tare suka sake mikewa, kallonta ya keyi da mamaki yarinya karama da ita har tana da karfin halin mishi rashin kunya se kuma ya tuna location din da yake ance duk karuwai ne suka fi yawa a wajen nan take yaji wani tsanar ta me karfi ya kamashi ya fara binta da kallon tsana hannun shi ɗaya yasa ya hankaɗe ta ta faɗi akasa har seda hannunta ya gurje wajen ya yi ja ko juyawa be sake yi ba ya yi tafiyar sa. Bin bayanshi ta yi da kallo ta daga murya tace "Allah ya isa mugu kawai, azzalumi macuci ma yaudari,ma ha'inci!" Haka ta dinga faɗa da karfi tana hararan bayanshi tana kuma shafa hannunta da ya yi ja,tana tura baki,duk maganar da take yi akan kunnenshi danne fushinsa ya yi domin kuwa yasan muddin ya koma wajanta tofa se ya kasheta,shisa kawai ya yi tafiyar sa ,nan take kuma ya tsaya sakamakon wani irin luguden duka me karfin gaske da yaji zuciyarsa tana yi kamar ze fito waje,duk jarumta irin nashi ya kasa ci gaba da tafiya saboda yanda yaji zuciyarsa take bugawa,ji ya yi kamar akwai abinda ya jefar atare dashi da yakamata ace ya tsaya ya nema ko kuma ya yi mantuwar wani abu. "Hello LTG. we have found them"muryan major Marry ya ji ta cikin Bluetooth din dake manne a kunnen shi, nan ya dawo cikin hankalinsa sannan ya cigaba da tafiya. Fitowa Asmita ta yi daga shagon ta hango Sabriyah a ƙasa har lokacin bata tashi ba tsabagen takaici kuma bata bar zage_zagen da takeyi ba kamar zata ci babu.da gudu ta iso wajanta ta dagata ta ce "garin ya ya kika faɗi my Jerry!?"cikin ƙuluwa ta ce "uban waye ne ya ce miki faduwa na yi!?wani mugu mara tausayine ya tureni na fadi." Sannu Asmita ta yi mata ta dinga dannata ta yi shuru amma ta ki yi se ci gaba da magana takeyi kamar wanda ya tureta din yana gabanta. Napep suka shiga suka fara tafiya har sunyi nisa kwatsam from nowhere mutum ya faɗo musu cikin napep, jikin shi da raunin se haki yake ta yi damƙar hannun Asmita ya yi numfashinsa na fisga da kyar ya iya furta. "Na ji ajikina ke din nan za ki taimaki al'umma, dan Allah ko ta wani hali ki tabbatar da kin kai memory card din da zan baƙi wajan hukuma domin al'umma suna cikin hatsari ,saboda yan ta'adda masu hatsarin gaske sun shigo cikin Nigeria"daga Asmita har Sabriyah gaba dayansu tsananin tsorone yasa ko da yawu sun gagara haɗiyewa,yanda yake a firgice yana musu magana haka suma suke a firgice hatta me napep din da ya dauko su shima a tsorace ya ke. Dakyar Asmita ta iya haɗiye wahalallen yawu da ya wuce dakyar se da yabada sauti 'kwatt' ta ce"tooooo....meneneeee... sunanka!?" Yanda take jan magana ma kadai ya isa ya nuna zallan tsoron da take dauke da shi. "Sunana Barrister Lameer,ni lauya ne, ina dauke da wani babban sirrin wasu yan ta'adda wanda hakan yasa suke son kasheni,nasan bazan yi tsawon rai ba!dan Allah ku tabbatar da kun damƙa wannan memory wajan hukuma.!"ya yi maganar yana damƙa wa Asmita memory card din gam a hannunta,duk da yanda yake cikin firgici da tashin hankali amma hakan be hanashi ganin digon tawadar Allah guda uku da suke gefen yatsunta ba,da sauri ya ɗago yana faɗin. "Asmitaaaaaaa......"yana faɗar sunanta wa'yanda suke binsu abaya suka sa hannu suka jawo shi acikin napep din sukayi wurgi dashi akan titi motar ya bi ta kanshi. Razanannen ƙara Asmita da Sabriyah suka saka,tunda suka zo duniya basu taɓa ganin irin wannan tashin hankalin ba se yau, karan bindiga ne ya din ga tashi ana binsu a baya kankame junansu sukayi suna kuka,me napep se gudu ya keyi,karan bindigan ne ya fara lafawa,leka kanshi me napep din ya yi sannan ya ce "yanzu babu wa'yanda suke binmu a baya" sude hankalinsu be kwanta ba,burinsu kawai su gansu a afafa. Sauke su ya yi yaja napep din shi ya yi gaba yana me da_nasanin fara sana'ar napep a rayuwarshi. Tsayawa sukayi a bakin gate din su basu shiga ba,har lokacin rawa jikinsu yakeyi riko hannun Sabriyah Asmita ta yi ta ce"my Tom ki rike wannan memory card din a wajan ki saboda kece me yawan saka breziya masu zip a ta ciki"ta yi maganar tana damƙa mata a hannunta,jiki na rawa Sabriyah ta karba ta jefa memory card din cikin breziyar ta. Jiki a sanyaye suka shiga cikin dakin su. suka zauna ko wacce da abinda take ai yanawa aranta can Asmita ta ce "my Tom amma ta ya Barrister Lameer yasan sunana " Kan sabriyah a ƙasa ta ce "nima abinda nake ta nazari kenan aina ya sanki to!?". Babu wanda ze basu amsar wannan tambayar hakan yasa suka yi shuru har zuwa lokacin kirjinsu na bugawa. haka suka yini a ranar kamar zakaran da ruwa ya yi wa duka, babu wani kuzari a tattare dasu. Lagos oriental hotel "LTG. Wannan sune ɗaukan CCTV cameran wannan hotel din."cewar security hotel din,matsowa LTG.Taj ya yi ya fara duba daukan Cameran,shige da ficen Asmita da Sabriyah ne yafara gani lokacin da suke hotel room din da Fu'ad yakama,ga Fu'ad din a tare dasu,se de kwata_kwata fuskar Fu'ad be bayyana ba. Kallon security din hotel din LTG.Taj ya yi ya ce "meye alaƙarsa da wa'yannan yan matan!?". Nuna Sabriyah security ya yi ya ce "wannan din ƙaruwar sa ce saboda kwanan su goma acikin wannan hotel din ,dayar kuma ƙawarta ce.". Zooming din fuskan su LTG.Taj ya yi,nan take fuskar Sabriyah ya bayyana me kyau ajikin screen din.kallo daya ya mata ya tuna haɗuwar su a cikin kasuwa,kallon major Marry ya yi ya ce"with less than 5 minutes, I need more information about her, saboda dole tasan inda shi saurayin nata yake!?. Ɗaukan hoton major Marry ta yi ta maida shi wani na'urar tonon asiri wanda iya jami'an tsoro ne na kasar waje suke iya amfani dashi. Nan take suna da komai da komai na Sabriyah ya fito ajikin na'urar,saboda tanada lasisin karuwancin da akayi mata shisa komai nata ya bayyana cikin sauki. "LTG.the girl is a prostitute,and she lives in afafa the most popular place for the criminals and prostitute's!". Fita ya yi awajen batare da ya yi musu magana ba,bin bayanshi major Marry ta yi, dukkansu biyu daga ita har shi LGT.Taj suna cikin shiga na farin kaya babu wanda ze gansu ya yi tunanin sojoji ne. Haka suka kwana basu saka komai a cikinsu ba,Anty Teema ta musu tambaya har ta gaji amma sunki faɗa mata abinda ke faruwa. Tana toilet tana wanka soso ya rike abin hannunta, ta yi iya yinta amma ya ki fita ajikin soson hakan yasa ta cire shi a hannunta.se sannan ne ta samu ya fita ajikin soson ajiyeshi ta yi a gefe ta gama wankan ta,bayan ta kammala ta daukeshi ta fito miƙawa Asmita ta yi ta ce "rike mini bari in sa kaya" karba Asmita ta yi tasa shi a hannunta. Bayan ta gama sa kayan kuma ta manta bata karba ba. Gari na wayewa suka farka duk da hakan ba ɗabi'ar su ɓace, amma yau haka kawai suka tashi da wuri,baranda suka fito suka zauna suna kallon masu wucewa suna hira sama_sama har Anty Teema ta fito ta samesu a wajan,komawa cikin dakinta ta yi ta dauko musu kankana ta basu karba sukayi suna gaisheta. Hira sukayi sosai duk da firgicin abinda ya faru jiya be fita a ransu ba har yanzu suna kallon yanda wa'yannan azzaluman suka kashe Barrister Lameer yanda suka jefashi kan titi mota ya takeshi. Har kusan karfe sha ɗaya duk suna zaune awajen anan sukayi karin safiyar su. Taheer ne ya kira Asmita a waya,ya faɗa mata yana baƙin gate din gidan,kallon Sabriyah ta yi ta ce "my Jerry muji waje Taheer yazo." Barin Anty Teema sukayi a wajan suka ce mata bari su je wajen Taheer. Fitowa sukayi suka sameshi a bakin gate a cikin motar shi tun kafin su iso ya keyi wa Asmita murmushi shiga cikin motar su kayi suna hira se jan su da zolaya yakeyi,be fi minti talatin ba ya ce musu ze tafi Saboda yanxu haka ma airport zeje Ya ce bari yazo ya ga Asmita. bankwana sukayi dashi yaja motar ya tafi tsayawa sukayi suna bin bayan motarsa da kallo. wata ƙatuwar bak'ar jeep ya tsaya agabansu,kafin suyi wata_wata wani namiji ya fito ya sa hannu ya janyo hannun Asmita dake riƙe dana Sabriyah cikin motar,raba hannun nasu ya yi ya rufe kofar motar ya ja suka tafi. Sabriyah dake tsaye a wajan kamar gunki,daura hannu akai ta yi tasa ihu me matuƙar ƙaran gaske Wanda yayi sanadiyar jawo hankalin al'umman Wajan kanta da gudu tabi bayan motar amma ina sunyi mata nisan gaske zubewa ta yi akasa lokacin da ta dena hango su tasa Marayan kuka kamar ranta ze fita,ji ta yi ansa hannu an ɗago ta sama kallon wanda ya ɗagonta ta yi taga mutumin jiya da suka haɗu a kasuwane har ya wurgata kasa ne.bude baki ta yi zata yi magana yasa hannu a aljihun jacket din shi ya fito da hanky ya shaƙa mata a hanci nan take ta sume ta faɗo jikinshi. Hannu ɗaya LTG.Taj ya saka ya dauketa kamar yar tsana ya nufi mota da ita da sauri major Marry ta bude mishi motar ya shiga driver yaja suka tafi. Tafiya me nisa sukayi kafin suka tsaya a wani katafaren filin da babu gida ko daya a wajen se private jet din LTG.Taj ne kaɗai a wajen fitowa ya yi,ya shige cikin jirgin, major Marry ce ta dauko Sabriyah a kafadarta suka shiga jirjin,nan take ya tashi a cikin sararin samaniya. MAIDUGURI STATE Karfe biyu na dare su ka shigo Maiduguri saboda sun tsaya a headquarter Damaturu,kowa ya yi bacci a gidan Masu tsaron gidan ne da kuma sojojin da suka zo daga gari mabanbanta domin kulawa da lafiyar LTG.Taj, ne kaɗai idon su biyu packing motar driver ya yi acikin gidan,fitowa ya yi yana me karewa gidan kallo, saboda ganin gidan ya keyi kamar sabon waje a wajensa domin an sabunta komai a cikin gidan,shekaru goma ya diba be waiwayi wannan gidan ba. Daukar ta ya yi ya nufi cikin Mansion din da ita yana isa ya jefata akan 3 seater na main part din gidan ya haura upstairs din da ze sada shi da part din shi,kallon Sabriyah major Marry ta yi se taji,be kamata abarta ta kwana a wajen ba amma babu yanda ta iya haka ta haura upstairs din itama ta bi bayan shi,be juyo ya kalleta ba ,da hannu ya nuna mata wani bedroom da yake upstairs alamar anan ne zata sauka shiga ciki ta yi taga komai akwai acikin bedroom din nan take ta shiga ta yi wanka saboda sun kwaso gajiya. A bangaren LTG. Taj ma haka wanka ya yi,sannan ya yi wasu bincike kafin nan ya tada sallar nafila. Asuba na gari, mazan gidan kowa ya tashi saboda zuwa Masallaci duk babu wanda yasan da zuwan Tajuddeen, sede kawai sojojin sa da suka gani acikin gidan,da mamaki suka je sukayi sallah suka dawo kowa ya koma domin ci gaba da bacci. 8:30am A hankali tafara bude manyan idanunta da suke a kumbure saboda kuka da kuma baccin da ta yi tun jiya,ji ta yi sun yi mana nauyi sosai, mikewa ta yi ta zauna tana riƙe da kanta,da shima ya mata nauyi,se a sannan ne idonta ya samu damar budewa gaba daya,da mamaki taƙe ƙarewa falon da take ciki kallo,da hanzari ta mike tsaye tana kallon ko ina na cikin falon.nan take ta tuna abinda ya faru jiya.aranta ta ce "wato ji mini ciwon da ya yi ne be isheshi ba shine ya sato ni,to Wallahi ni be isa ya sato ni ba" Dawuwa tsakiyar falon ta yi ta rike kugunta cikin daga murya ta ce"uban wayeeeeeee. Ne ya kawo ni gidan nan!?in ka isa ka fito ka mayar dani in da ka sato ni!". Da iya karfinta take magana,tana jiran ya fito,ganin babu wanda ya fito yasa ta ci gaba da magana da karfi wanda hakan ya yi sanadiyar tashin mutanen gidan daga bacci duk suka fito falon maza da mata,amma banda anty amarya,suna kallon Sabriyah acikin falon suka fara tambayar junansu ita kuma wannan wacece?. Saghar ne ya ce"ke kuma daga ina zakizo kina yi wa mutane ihun hauka!?,wait! in the first place uban waye yabaki izinin shigowa cikin gidan nan!?" Kowa dake cikin falon se kallon Sabriyah sukeyi suna mamakin me take yi a cikin gidan. Watsawa Saghar harara ta yi,cikin tsiwa da daga murya ta ce "na fiku rashin mutunci ni za'a gwada wa duniya da bariki nida na fito daga cikinta,a sato ni sannan a zo ana tambayata me nake yi anan.ka da ka kuskura ka zageni yauwa." Tashin hankali su Zoya kam da ido kawai suke bin Sabriyah suna jinjina rashin Kunyar ta ganin yanda ko tsoron Saghar bataji ba,ta tsaya tana gaya mishi maganar da ranta ya so. Sahil ne da yaga in sukace ta haka zasu biyo mata tofa bazasu ji abinda suke son ji a wajanta ba,hakan yasa cikin ruwan sanyi ya ce"baiwar Allah daga ina me kike bukata?" Juyawa ta yi taga me maganar ta ce"ai ku zan tambaya,meye dalilin ku na sato ni?". Kallon juna suka fara yi. Ammi ce ta matso kusa da ita ta ce"yan mata ki nutsu ki faɗa mana menene ya kawo ki". calmly Ammi ta ke mata magana wanda hakan yasa taji Ammi ta yi mata matukar gwarjinin da bazata iya bata wani amsar da bashi bane. "Wanine ya sace ni,shine yanzu ina farkawa na gan ni a nan".jinjina kai Ammi ta yi ta ce "daga wani gari kenan!?",amsa Sabriyah ta bata" daga Lagos afafa " dukkanin su zaro ido waje sukayi se sannan ne ma suka sa'ke kare mata kallo sukaga irin shigar dake jikinta. Tsaki Ammuh ta yi ta ce "to wani shegen ne ya kawo mana karuwa kuma cikin gidanmu,na halak!?" Muryansa da basu yi tsammani ba suka ji ya ce. "Ni na kawo ta" Gaba dayan su a tare suka maida kallonsu da kuma hankalinsu upstairs,cike da al'ajabi suke kallonsa babu ko kyaftawa. Cikin isa da takama yake saukowa daga stairs din kamar bayaso,yana sanye da gajeren wando da kuma rigar t-shirt gaba daya farfadar kirjinsa a bude saboda botile din rigar biyu kawai yasa, damtsen hannunsa duk yana waje rigar me guntuwar hannu ne. Karasa saukowa ya yi falon idonshi akan Ammi da take sakar mishi murmushi. Se mun haɗu Monday in me duka yakaimu da rai da lafiya. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ *🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹* Page 17 *_Story & written_* By *MRS🌹ISHAM🌹* ( Yar lelen Jarumai) *THE WRITER OF 🖋️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️ Page 17 Karasowa cikin falon ya yi da mamaki suke kallonsa,suna al'ajabi yaushe ya zo,cike da kissa Ammuh ta zo ta rungumesa ga murmushi a fuskarta tana"oyoyo!oyoyo! oyoyo!ɗana sannu da zuwa, gaskiya na yi kewarka sosai"hugging dinta back shima ya yi,duk da bayason yawan magana amma hakan be hanashi cewa Ammuh "missed you too Ammuh dina"saketa ya yi,ya je wajan Ammi ya rungumeta yana me sauke ajiyar zuciya,hakan da ya yi bakaramin bata ran Ammuh ya yi ba,nan take taji ranta be so hakan ba,aranta kuwa se kulle_kulle takeyi tana son ta sake taso da tsohuwar ƙiyayyar da Tajuddeen yakeyiwa kowa. A tare samarin gidan suma suka rungume shi suna mishi sannu da zuwa,su Zoya kam kwakkwaran motsi sun gagara yi ɓalle su mishi sannu da zuwa, Parsa dake dauke da wannan ƙayata zaciyar murmushin nata ne tazo ta rungume shi tana. "Welcome back ya Taj we have missed you alot". Shafa bayanta ya yi be ce komai ba,kaff gidan kowa yana son yarinyar saboda ko kadan bata da damuwa, she's very unique,kusan ma za'a iya cewa ita ce logon su,weak point din su,ji sukeyi da ita kamar yanda ake ji da kwai.wannan dalilin yasa kowa na gidan yake son ta hatta shi kanshi LTG yana ji da ita. Kowa dake falon seda suka mishi sannu da zuwa duk da bawani amsawa ya keyi ba. A bangaren Sabriyah kuwa tunda LTG ya sauka take kallonsa musamman damtsen hannunsa da kuma farfadar kirjinsa, tunda take bata taɓa ganin mutum me irin zubin halittar jikinsa ba,hakan yasa ya koma tv awajanta.can kuma ta tuna da sace ta da ya yi, ga kuma mutanen gidan sun wani tsaya se wani sannu da zuwa suke mishi sun manta da sabgarta hakan ne yasa,ta matso kusa da shi. Ta ce "wato raunin da ka ji mini a kasuwa be isheka shine ka sato ni,to baka isa ba kawai in kanason kwanciyar hankali da kai da mutanen gidan nan ka maidani gidanmu!"ta karasa maganar tana wani girgiza kai kamar dukan shi zata iya yi ,ga ta yar karama a gabanshi se ta daga kanta tukun take kallonsa duk da itama tana da tsayi dede gwargwado. Ko kallon in da take tsaye be yi ba bare ta sa ran ze amsa mata,se ma juyawan da ya yi ze koma part din shi.da sauri ta bisa a baya tana"kazo ka mayar dani dan Allah,akwai yar uwa ta da aka sace zan nemo". Su de su Ammi da kallo kawai suke binsu,domin kuwa sun rasa dalilin da yasa LTG ya daukota ya kawota gidan. Haurawa ya yi ko juyowa be yi ba,ganin ya haura ne yasa ya tsuguna agun ta fashe da wani sabon kuka, babban damuwarta ita ce Asmita,bata san wani hali take ciki ba, batasan su waye suka sace ta ba.burinta kawai taga ta samo Asmita,gaba daya abubuwa sun haɗe mata kai ta rasa da wanne zata fara guda daya. Ganin ta tsuguna tana kuka ne a matattakalar benen yasa Ammi ta haura ta ɗaukota suka dawo kasa,zaunar da ita ta yi, akan kujera.hajiya babba ce ta matso ta zauna kusa da Sabriyah ta ce "yarinya ya sunanki!?",se da ta goge hawayen fuskarta tukun ta iya cewa" sunana Sabriyah". "Meyasa kike kuka kuma meye ya haɗa ki da Tajuddeen!?", Hajiya babba ta sake je fo mata tambayar,tsaki Ammuh ta yi ta ce "gaskiya mutanen gidan nan akwai ku da son yin gwaninta!,karuwar ce ku ka tsaya kuna wani lallabata!?"ta faɗa tana harare_harare kafin ta sa'ke jan wani tsakin ta wuce part dinta,ummah part dinta itama ta wuce dama ita tunda ta fito batace komai ba.sude su Sudais da su Zoya duk suna tsaye a falon sun zubawa Sabriyah ido,gani sukayi tana kusan yanayi dasu,ga kuma kyawunta me jan hankali kukan da takeyi ma ƙara mata kyau ya yi, girgiza kai Hajiya babba ta yi kawai sannan ta ce "kar abinda ta faɗa ya dameki faɗa mini inajinki",kwashe gashinta da ya zuba ta gefen wuyanta tayi ta maida shi baya kafin ta ce"ah ah maganar ta be ɓata mini rai ba,kuma ai gaskiya ta faɗa!,na haɗu da wannan mugun ne a kasuwa ban taba ganinsa ba amma ranar da muka haɗu dan kawai munci karo da juna shine ya yi wurgi da ni,na faɗi se da naji ciwo a hannuna,ranar da wasu wa'yanda bamu san ko su waye ba suka sace mini yar uwa ta,aranar shima ya sace ni ya kawo ni nan."jinjina kai sukayi bayan sun gama jin abinda ta faɗi su de har yanzu basu ga wani dalilin da har ze sa, LTG ya sace yar mutane ba,abin ya daure musu kai,duk shuru sukayi basu ce komai ba, kowa da abinda yake saƙawa a ransa,ɗago kai Sabriyah ta yi ta kalli Ammi ta ce"ki yiwa wannan mugun magana ya mayar dani inda ya dauko ni,in je in nemo yar uwa ta".murmushi Ammi ta yi jin yanda Sabriyah ta ke kiran LTG da mugu duk da har ranta bataji dadin kalmar ba amma yanda Sabriyah ta yi mata magana cikin shagwaba ya bata dariya hakan yasa ta ce"shikenan ki kwantar da hankalinki zanyi mishi magana kuma ze mayar dake nice mahaifiyar sa,in Allah ya yarda za ki koma garin ku."gyada kai Sabriyah ta yi,kallon su Umaisha Ammi ta yi ta ce Umaisha zo ki dauketa kuje part dinku ku zauna tare. "Okay Ammi"umaisha ta faɗa tana yiwa Sabriyah murmushi,yatsina fuska Zoya ta yi,cikin mamaki ta ce"like serious Ammi!?, gaskiya wannan karuwar bazata je mana part din mu ba,najasa ce f......"wani irin tsawa Sudais ya daka mata wanda ya hanata karasa maganar da zata faɗa."will you be quiet,you idiot!in na sa'ke jin muryarki se na ci ubanki a gidan nan mahaukaci kawai."nan take ta nutsu ta sun kuyar da kanta dan tasan karamin aikin Sudais ne yanzu yamata ɗan banzan duka. Hajiya babba ta ce "Zoya wannan banzar halin naki ki gaggauta barinsa nade gaya miki yarinya kenan se bakin hali"haka Hajiya babba ta dinga surfa mata masifa.duk cikinsu babu wanda ya ji dadin maganar da Zoya ta faɗa,saboda duk yanda mutum yake baze ji dadi ba in aka kirasa da wannan abun. Rike hannun Sabriyah Umaisha ta yi ta ce "sis ta shi muje part din mu"fisge hannunta Sabriyah ta yi,ta ce "babu inda zani fa,bazan taɓa motsa wa anan ba se wancan mugun ya fito ya maida ni"ikon Allah yau ake yin ta,yau Allah ya hadasu da me taurin kai da naci,ga ta daga ido de ba za'ayi tunanin za ta yi taurin kai ba, se de duk wanda ya mata kallo ɗaya yasan za ta yi masifa da tsiwa da kuma rashin kunya amma alamar taurin kai be nuna a tattare da ita ba. Kallon Zoya Sabriyah ta yi ta galla mata harara ta ce "ke kuma dakikiyar banza da kike cewa karuwa bazata shiga muku waje ba ,to ni me ma ze kaini ko an gaya miki ina son in ƙara ko da second daya a gidan nan ne!?,ki shiga taitayinki nafiki hauka tam.karki ga ke yar masu kuɗi ce, ki ce zakimin tijara.sauya miki kamanni zanyi babu abinda yashamin kai".yanda Sabriyah take magana da masifa_masifa kamar zata je ta da ki Zoya ne ya bawa Sahil,Salim,Jawan dariya ganin sun samu wata comedian a gida. "Yi hakuri Sabriyah,tashi ki bi umaisha kuje ku ciki, lokacin breakfast ma ya wuce kuyi sauri, Umaisha ki nuna mata komai tayi wanka,ki bata kaya tasa"Hajiya babba ta yi magana tana kallon umaisha sannan ta kalli kayan dake jikin Sabriyah ta girgiza kai aranta tana tambayar kanta ko yarinyar nan musulma ce.domin kuwa shigar jikinta kwata_kwata beyi tsari ba. Rike hannun Sabriyah Umaisha ta sakeyi a karo na biyu,bin bayanta Sabriyah ta yi badan taso ba,bataso ta tsaya musu da su Hajiya babba da Ammi ne. saboda duk fitsaranta bazata iya musu ba.har sun haura upstairs Ammi ta kira sunan Umaisha juyawa ta yi,Ammi ta ce "Umaisha give a decent dress please" "okay" sannan sukaci gaba da tafiya,Zoya de tunda Sabriyah ta zazzage mata salon nata rashin kunyar da tsiwa ta yi shuru bakinta ya mutu murus,part din Ummah ta yi fuuuu,kamar zata fire sama.bin bayanta sukayi da kallo,Jawan cikin daga murya da tsokana ya ce"gaba ma da gabanta aljani ya taka wuta,kin haɗu da wacce ta fiki rashin ji ai"ko waigowa Zoya bata yi ba se ma kara saurin da ta yi,dariya duk sukayi, Parsa ta ce "Rameesa, Sabriyah kyakkyawa ce ta burgeni sosai "dariya Rameesa da iklas sukayi.iklas ta ce "honestly she's very gorgeous" "to yanzu de kuzo muje muyi wanka se mu fito a yi breakfast"cewar Rameesa da ta fara tafiya bin bayanta sukayi su dema. Zama Saghar da Jawan sukayi kasa_kasa da murya Saghar ya ce "amma Jawan kai a naka tunanin me zesa LTG guda ya sato mace!?",shima Jawan kasa da murya ya yi,ya ce"that's what am still wondering!me ze sa ya Taj ya sato wannan zankaɗeɗiyar budurwan batare da dalili ba!?".haka suka dinga magana kamar wasu munafukai,babban abinda basu sani ba shine su Sudais Sahil, Salim, Ammi,Hajiya babba duk sunji abinda suka faɗa.tafa hannu Hajiya babba ta yi "la'ilahaillahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallama,yanzu dama maganar da ake faɗa a gari cewa gulma ya tashi daga kan mata ya koma kan maza ashe da gaske ne!ikon Allah wato Saghar da Jawan kude bazaku dena wannan iya shegen naku ba.tabb dijam ahhh lallai lamarin ku ya girmama,ku de bari Tajuddeen ya ji ku". tunda Hajiya babba ta fara magana suke dariya har su masu gulman saboda su kwata_kwata basu yi tunanin ana jinsu ba.tsagaitawa da dariyar Salim ya yi ya ce"ai Hajiya babba kaff gidan nan babu irin Saghar da Jawan a wajen fannin sa ido da gulma ne"tabe baki Hajiya babba ta yi sannan ta ce"yooo ai naga alama,bari ma in shige ciki."haurawa part dinta ta yi tana tafiya tana tafa hannu irin abin ya bata mamaki.(hhhhhhh, Hajiya babba kema akwai abin dariya ba laifi,to ai gulma ya daɗe da koma kan maza mutanen mu). Ammi de se murmushi take musu maida hankali ta yi kan Sudais ta ce "rabu da wa'yannan naga yau su basu da niyar yin breakfast din ɓalle suje wajen aiki".kallonta sukayi atare su biyun suka haɗa baki wajan faɗar "Ammi abin kuma wariyar launin fata ne!?"Saghar da Jawan suka faɗa,marairace fuska twins Sahil, Salim sukayi sukace"ayyah Ammi muma fa yan gaban goshin ki ne,shine za ki cewa Sudais shi kadai ya ke da niyar zuwa gun aiki!", kwaikwayon yanda sukayi maganar Sudais ya yi yana"yen!yen!yen!ƙatti da ku agaban ƙannenku kuna wani shiririta shame on you guys" Ammi de ce musu ta yi"ku de ba'a iya muku,se anjumanku mu haɗu a dinning kawai".ta faɗa tana barin falon. Duk watsewa suka yi a falon kowa yaje dan ya shirya . Part din su suka shiga,cike da walwala Umaisha ta ce "muje ki sauka a dakin mu !"burki Sabriyah taja ta haɗa fuska ta ce "ke banason iyayi fa, na ce bazan sauka a wajanku ba dole ne!".zaro ido waje Umaisha ta yi tana mamakin hali irin na Sabriyah aranta ta ce "wai nikan wannan ba'a mata gwaninta ne?ohhh wato kowa da irin halinsa"karewa part din nasu kallo Umaisha ta yi,idonta ne ya sauka akan wani daki madaidaici wanda ya kasance extra room din dake part dinsu,bayan daki guda biyun dake cikin part dinsu din akwai daki madaidaici. Gaba Umaisha ta yi ta ce "to muje dakin nan,ke kadai anan din,tunda kin fison zama ke daya,ai kadaici kadai ma se ya isheki.nifa inni ce wallahi bana iya zama Ni daya kamar mayya,ko yaushe nafison injini cikin mutane ai yafi dad'i, mutane rahama ne!,ke nifa bama wannan ba,abinda yasa bana zama ni kadai ina da matukar tsoro,se in ga kamar dodo ze kamani.yanzu ke haka kika zabawa kanki zama ke daya!?,haba Sabriyah ke haka za ki zauna Kamar wata mayya!?,"bin bayanta Sabriyah ta yi tana mamakin surutu irin na Umaisha tafiya takeyi amma se zuba takeyi kamar kurna, bata ko haɗiye yawu,jera magana takeyi ko gajiya batayi ba.sabriyah takasa dena kallonta,ita de tana fama da abinda yake damunta na sace Asmita ga kuma kawota nan da LTG ya yi ga kuma Umaisha da tasata a gaba da magana kamar wata yar jarida. Dakin suka shiga, ya hadu komai akwai aciki. Nuna mata yanda zata yi amfani da toilet din da kuma sauran abubuwan ta yi,kafin ta ce"kiyi wanka bari in kawo miki kayan sawa".ba tace mata komai ba toilet ta shiga,ita kuma Umaisha ta fita a dakin da hanzari,wanka Sabriyah ta yi ta ta wanke gashinta, daura towel din da ta gani ta yi. fito gashinta na diga da ruwa,tsane jikinta tayi ta goge dogon baƙin gashinta,tana zaune a gaban mirror ta shafa mai din da ta ganim ta taje gashinta ga handryer a kan mirror amma bata san meye amfanin shi ba kuma bata san ya akeyi dashi,ta cikin madubi ta hango kayan da Umaisha ta kawo mata,mikewa ta isa gaban gadon ta dauki kayan,warwaresa ta yi,abaya ce dark brown color har ƙasa yasha stones ta ko ina se kuma wando jeans black color wanda za'a sa ta ciki,tsaki ta yi a yayinda take wurgi da rigar akan gado ta ce "Tabb dijam waye ze saka wannan ƙatuwar rigar lallai kam ai dole in nemi wata rigar da zansa da wandon nan,ita kadai take magana ta nufi hanyar barin dakin daga ita se towel a daure a kirjinta ga rabin fararen tula_tulanta awaje,dakin da ta gani kusa da inda ta sauka ta shiga ta tsaya daga bakin kofa,ta ce "abani riga t-shirt!"Parsa da ita kadai ne tayi saura a dakin ne,ta ɗago kai ta kalleta ta yi murmushi ta ce"okay bari in kawo miki"da sauri ta mike ta nufi dressing room din su ta dauko mata sabuwar riga acikin ledarta ta fito ta bata,karba Sabriyah ta yi a wajen ta saka ta dawo da towel din kugunta sannan ta bar bakin kofar ta koma nata masaukin. Shiryawa ta yi tsab cikin riga da wandon ta zauna a dakin tana tunani ina zata samo Asmita,wani hanya ya kamata tabi ta samo Asmita, Rameesa ta shigo ta ce "hi yan mata!ance ki zo muci abinci." "nakoshi"cewar Sabriyah,barin dakin Rameesa ta yi bata sa'ke magana ba. Kowa ya hallara a dinning table hatta LTG da major Marry duk suna zaune kowa ya fara cin abinci Rameesa ta dawo ta ce "Ammi wai ta ce ta koshi"gyada kai Ammi ta yi ta kalli fatime ta ce "ki shiryawa bakuwarmu abincinta,ki kai mata". "to Ammi" shiryawa Sabriyah abinci fatime ta yi,ta nufi upstairs. Kallon Ammi anty amarya ta yi ta ce "Ammi yaushe akayi bakuwa!?, wacece haka!?"ta jerowa Ammi tambayoyi tana son jin amsarta,kafin Ammi ta yi magana Ammuh ta rigata cewa"wata karuwa ce Taj ya kawo"da mamaki anty amarya ta ce "karuwa kuma!?, kamarya karuwa!?"LTG de abincinsa kawai yake ci kamar be ji me suke faɗi ba.major Marry kuwa se kallon bakinsu takeyi yana magana amma bata iya gane ko da kalma daya da suke faɗa tunda ba Hausar take ji ba. "Tajuddeen ne ya kawo ta duk da be faɗa mana dalilin da yasa ya kawo ta ba". Ammi ta gayawa anty amarya jinjina kai ta yi taci gaba da cin abincinta. Uncle Hameed ya ce"LTG meyasa ka daukota, kuma naji Ammuh dinku na cewa wai karuwa ce?". Sipping din black tea din dake hannunsa ya yi ba tare da ya ɗago ba ya ce"bincike ne ya biyo ta kanta"daga haka be sa'ke ko da tari ba,su ma kuma basu sa'ke yunkurin sa'ke yi masa wata tambayar ba. "Rameesa bakuwar na part din ku ne?" "Eh anty amarya tana can"Rameesa ta bata amsa tana kai soyayyen kwai bakinta. Anty amarya ta ce"to mu gama,muje in ganta". Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 Page 18 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ Page 18 zaune take a cikin dakin, fatime ta shigo hannunta da tray din abincim da ta shirya, harda mini flask din tea. "Barka da safiya ga breakfast din ki" "yawwa", ficewa ta yi bayan ta ajiye mata. Bude kulolun ta yi taga sinasir ne da miya yasha kayan hadi ga nama acikin kamar zasu yi magana,dayan kulan kuma farfesun kifi ne a ciki,daukan plate ta yi ta zuba ta fara ci.bayan ta gama,ta haɗa tea ganin arhan madara da milo yasa se da tea din nata ya koma kamar wani kunu tana sha ta rube ido,ji ta yi koshi har wuya sannan ta kwashe plate da cup din ta sa acikin tray. ɗaukar tray ta ajiye akan mirror ta dawo ta zauna. Shigowa dakin anty amarya da Rameesa sukayi, ɗago kai Sabriyah ta yi suka haɗa ido,a tare sukaji zuciyoyinsu ya buga kamar an buga ganga.mikewe Sabriyah ta yi,har lokacin idonsu na cikin na juna,wani irin alaƙa ta jini ne yake fisgan anty amarya harta isowa ga Sabriyah da take kallonta kamar wata bakuwar halitta daga wata duniyar,sa hannu ta yi ta shafa fuskar Sabriyah da ta zuba mata manyan idanunta, lokaci daya anty amarya ta kusan burkicewa jikinta yana bata akwai wani babban alaƙar jini a tsakaninta da yarinyar amma ta rasa wani irin alaƙa ce wannan,kuma har wannan lokacin zuciyoyinsu be dena bugawar da yake yi da karfi ba. Da kyar anty amarya ta tattara nutsuwarta waje guda,under her breath ta ce,"ya sunanki?" Muryar Sabriyah na rawa ta amsa mata,"Sabriyah" "Ke din yar wata gari ce!?kuma sannan meye abinda ya kawo ki gidan nan!?" "Ni yar Lagos ce a afafa,kuma wani mugu ne, ya kawo ni gidan nan, ga shi an sace mini yar uwata'. Iska anty amarya ta furzar daga bakinta me zafi ta ce"Allah ya bayyana ta,bari in je se anjuma". Rameesa suman tsaye ta yi a wajen ganin yanda anty amarya da Sabriyah suke tsananin kama,amma se wanda ya zuba musu ido sosai ze fahimci hakan,duk da tunaninta be kawo mata kan cewar akwai wata alaƙa ba,amma ta yi matukar mamakin yanda suke kama fiye da tunanin me tunani. Da sauri anty amarya ta juya ta fice daga dakin ta nufi part dinta,bin bayanta Rameesa ta yi.ba ta cimmata s hanya ba.daki anty amarya ta faɗa, zubewa akan gado ta yi, numfashinta na fita dakyar,jawo maganinta ta yi tasha,nan ne taji nutsuwa ya fara shigar ta, cikin tsantsan damuwa ta shiga magana"ƴata Asrah kina ina ne?,ganin wannan yarinyar da nayi de naji tamkar kece a gabana,jikina yana bani kina raye.ya Allah na rokeka da sunanka tsarkaka ka bayyana mini ƴata cikin aminci".kwararo addu'o i sosai ta shiga yi. Jiki a sanyaye Sabriyah ta zauna a bakin gado tanajin wani irin kadaicin da tunda take bata taɓa jinsa ba, fashewa ta yi da kuka me cin rai da ta rasa dalilin wannan kukan da takeyi, haɗe kanta da guiwa ta yi tana kuka me sauti haɗe da shesheka, zuciyarta ce ta tambayeta. "To kukan me kike yi haka?" Ɗago kanta Sabriyah ta yi,a fili ta furta "Nima bansan kukan me nakeyi ba" "To ai ba'a kuka dole seda dalili" "Kila kewar Asmita ne ya dameni" Ita kadai ta dinga magana da zuciyarta,in ta yi maganar ta gaji kuma seta saka kuka,nan take idanunta ya yi ja. Durkusawa ta yi a ƙa san tiles din, ta zauna ta ci-gaba da kukan. A wannan halin major Marry ta sameta, cikin hanzari ta iso wajan ta tsuguna tana tambayarta abinda ya sameta cikin harshen turanci. "Beautiful girl!why are you crying like this!?,did someone said something bad to you!?". Ko daya daga cikin kalmomin da major Marry ta faɗa Sabriyah bata gane ba, ɓalle ta bata amsa goge fuskarta ta yi,ba ta cewa major Marry komai ba,tunda de ba gane maganar juna zasu yi ba. Ganin Sabriyah ta ƙi kulatane yasa ta ce"okay dear sorry for bothering you, LTG wants to talk to you! let's go". Major Marry ta yi maganar tana ɗago Sabriyah. Rike hannunta ta yi suka fice a part din. Su parsa suna zaune a cikin falo,suka ga fitowar major Marry rike da hannun Sabriyah, Umaisha ce ta fara magana "Sabriyah in zo in raka ku ne!?". Kallonta Sabriyah ta yi fuska ba yabo ba fallasa ta ce"ah ah ba se kinzo ba". Dariya sukayi banda Zoya da ko kallonta batayi ba, hasalima haushi ta ji da taga yanda Umaisha suke janta da zolaya. Parsa ne ta miƙe ta bisu a baya ta ce"nide Wallahi sena biku". kallonta kawai Sabriyah ta yi taga tana mata murmushi, itama murmushin ta mayar mata. Sannan suka fice garden suka nufa tun daga nesa suka hango LTG zaune akan kujerun da suke cikin garden din yana sanye da army trouser se rigar t-shirt me budeden gaba, sojoji kuma na zagaye dashi ta ko ina,ga wasu maza guda biyu da aka musu daurin huhun goro da igiya zaune akasa. Karasowa wajan sukayi major Marry ta jawa Sabriyah kujera ta zauna. "Ya Taj ashe kana nan dazun muka ta neman ka bamu ganka ba"ta yi maganar tana shagwabe fuska. Wayarsa yake dannawa cikin kwanciyar hankali tunda suka iso wajen be ko daga kai ba. With his sexy voice ya ce"yeap am here do you need anything?" Cikin jin dadi Parsa ta ce "yes!Muna son muje mu siya ice cream, chocolate and some yogurt". Yanda take lissafin ne ya bawa major Marry dariya...ita de Sabriyah da ido kawai take binsu. "Give her the ATM"cewar LTG,fito da ATM da suka kusa takwas major Marry ta yi ta mikawa Parsa guda daya. Tsalle ta yi tana"thank you sweet bro".da gudu tabar garden din,dan taje ta bawa su Umaisha labari.yau ai tunda ATM ya shiga hannunsu se abinda hali ya yi. Ajiye wayar hannunsa ya yi,ya ɗan kalli wa'yannan mazan da suke daure da igiya, "kun san wannan!?"ya faɗa yana nuna musu Sabriyah da ido,a galabaice daya daga cikinsu ya ce "ah ah Wallahi bamu santa ba". Gyada kai ya yi "ke kin san su?"harara ta watsu musu ta ce "Ni ban san su ba." "Shikenan!amma shi ogansu ai kin sanshi tunda har kukayi kwanaki goma a hotel,yanzu ina so ki sanar dani aina zan sameshi!?"tunda ta ji ya ambaci tayi kwanaki goma a Hotel da wani ta gane magana yake yi akan Fu'ad. baƙi ta buɗe da niyar zata yi magana ta ji ana mata rada a kunne,kuma ba muryar kowa bane, fa ce na Fu'ad"my Sabriyah dan Allah karki nuna musu kan cewa kin san ni,nemana suke yi,ruwa a jallo,saboda su kasheni,babu abinda na musu kawai zalunci ne irin na soja.ki taimaki rayuwata dan Allah Sabriyah" Shuru ne ya biyo baya hankalinta ya yi gaba wajen sauraran abinda Fu'ad yake ce mata,a dayan bangaren kuwa tana mamakin taya hakan ya kasance amma wannan ba shi bane damuwarta,abinda yafi damunta jin wai nemansa suke yi su kasheshi,hakan ne ya tayar mata da hankali, tambayar kanta takeyi,shin menene abinda Fu'ad ya musu,bawan Allah da Babu ruwansa,kamilin mutum me kyautatawa mutane. Wannan dalilin ne yasa tasa aranta ko da kasheta zasu yi ba zasu taɓa jin wani abu dangane da Fu'ad a bakinta ba. Ganin ta yi shuru ta faɗa duniyar tunani ne yasa LTG ya da ki table din gabansun da karfi,har seda ta firgita tana kokarin mikewa. "Zauna" Ya yi maganar fuskarsa kamar hadari. "Inajinki" Cikin inda_inda ta soma magana"ni ban san akan waye kake wa'yannan maganganun ba,ka kyaleni in je in nemo yar uwata'".ta karisa maganar idonta na ciki da hawaye. LTG dama yasan za'a rina saboda shugaban kungiyar Italian Mafia ba karamin shu'umin mutum bane zeyi fiye da haka ma.yasan ko shekara daya zasu yi yana tambayarta game da shi bazata taɓa faɗa masa komai akan sa ba,kamar yadda shugaban Italian Mafia ya yi blackmailing din ta shima dole ne ya yi blackmailing dinta saboda ta wannan hanyar ne kawai ze samu ta yi magana, saboda shugaban Italian Mafia yana kokarin juya mata tunaninta ne da karfin sihirinsa.. Kallon major Marry ya yi ya mata alamar da ta komar da ita ciki. "Okay" marairace fuska Sabriyah ta yi "dan Allah ka taimakeni ka mayar dani inda ka dauko ni,sun sace mini yar uwata' akan wani abun da baya wajen ta yana wajena,sun saceta bansan a wani hali take ba".tana magana hawaye na zubowa daga idanunta. maida kallonsa kanta yayi,jin abinda ta faɗa. yana me son gasgatar da hasashen da ya keyi game da abinda Sabriyah ta ke magana yana wajenta,fatan shi ɗaya shine Allah yasa wannan ma'adanar memory card din ne a wajenta. "Akan me kike magana meye a wajen naki!?"ya faɗa yana tsare ta da mayun idanunsa,ka war da kanta gefe tayi saboda bazata iya kallon cikin kwayar idanunsa ba,ji ta keyi kamar akwai guba me zautar da mutum acikin idanun nasa.wannan dalilin yasa ko da yaushe take avoiding din haɗa ido dashi. "Am......amm......dama wani Barrister Lameer ne ya bawa Asmita ma'adanar memory kan cewa ko ta wani hali mu tabbatar da mun miƙa wannan abun wajen hukuma,ita kuma ta bani.shine suka kashe Barrister Lameer din,suka biyo mu har gida aka sace Asmita". Zuba mata ido kawai ya yi,yana sauraranta,lumshe kyawawan idonsa ya yi ganin ya samo abinda suke nema har gida,domin lokacin da suka jefo da Barrister Lameer kan titi yayi dede da i sowarsu wajan nan suka fara ɓarin wuta har suka samu suka kashe wasun su wasu kuma suka kama su,anan ne Barrister Lameer ya sanar dashi kan cewa ya bawa wasu yan mata ajiyar memory din.kiran ambulance sukayi aka dauki Barrister Lameer zuwa asibiti domin a bashi taimakon gaggawa. Ashe wa'yanda yake nema tana tare dasu. Idonsa a lumshe kamar me bacci ya furta, "bani memory card din!" Mikewa Sabriyah ta yi, "ban yarda dakai ba,babu dalilin da zesa in baka wannan memory ko da kuwa kasheni zakayi"tana gama maganar ta fara tafiya,zata bar garden din.cizan libs din sa na kasa ya yi,ya ce "in dan kika bani,nikuma na yi miki alkawarin nemo miki yar uwarki a duk duniyar da take". Cak ta dakata da tafiyar da takeyi jin ya ambaci ze nemo mata Asmita,da sauri ta juyo ta dawo inda yake zaune ta ce "ni kuma muddin ka nemo mini ita zan baka wannan memory card din".tana ga fadin hakan ta sa kanta ta wuce cikin gidan,ta barsa zaune a wajen murmushi ya yi. kawai yana binta ne cikin ruwan sanyi ta ba shi,amma in ya gadama a yanzu ze ƙarbi memory a wajanta,domin duk wani motsin mutanen gidan nan yana sane dashi,amma ze barta ya ga iya gudun ruwanta. "Find the other girl,and kill this bastards"abinda ya ce kenan sannan ya mike,a tare sojojin dake wajen suka sara mishi.barin garden din ya yi wasu daga cikin sojojin suka bi bayan sa. Kallon wani soja major Marry ta yi, ta ce "Khalifa! hand me the gun"miko mata bindiga ya yi,.nan take tsoro ya dira akan fuskokin wa'yanda za'a kashen suka fara neman afuwa. Ko ajikinta ta seta kansu ta ɗa na kunamar bindigar sannan ta sake shi akan goshin na farko nan take ya fadi awajen matacce,haka dayan ma ta harbeshi a goshi. Bindigar da ta yi amfani dashi,bayi da ƙara hakan yasa mutanen gidan basu ji kar'ar ba, ficewa ta yi itama taname basu umarnin su kwashe gawan nasu a wajen. Birkita dakin ta yi kamar wata mahaukaciya tana neman breziyar ta,amma bata gani ba hakan ya daga mata hankali sosai,wanda yasa ta fara zargin ko wani ya shigo ya dauke ne musamman inta tuna da yanda sukayi da LTG,leƙawa kasan gado ta yi nan ta gansa yashe awajen. ashe da ta fito daga wanka ne ta yi wurgi dashi kan gado se ya faɗa bayan gadon. Da hanzari ta shige kasar gadon kamar wata bera,daukowa ta yi ya,ta na kokarin fitowa ta ji muryoyinsu a dakin suna "to ina kuma taje?" Fitowa ta yi hannunta riƙe da breziyar nata ta gansu dan tsuke fuska ta yi,bata ce musu komai ba. Kallonta sukayi suna mamakin ita kuma me yasa ta shiga ƙasan gado.Rameesa ta ce"Sabriyah me kikeyi a kasan gado kuma". Ajiyar zuciya ta yi "breziya ta na dauko" "okay!dama zamuje shan ice cream ne mukace bari muzo muce ki shirya muje". Yatsina fuska ta yi ta ce"ku je kawai bazan samu zuwa ba". "Sabriyah kin ka sa sakin jikin ki damu,kingan mu nan ko kadan bamu da matsala Please ki saki jiki,mu zama Kamar yan uwa"Umaisha ta gama magana tana riƙe hannun Sabriyah, kamar zatayi kuka ta ce"kaina ciwo ya ke,bazan iya fita ba" "Ayyah sorry my dear Allah ya ƙara sauki bari inje part din ya Saghar in dubo miki medicine"Iklas ta faɗa tana fita daga dakin dan zuwa part din Saghar dubo mata maganin. Zama sukayi tare da ita suna dan magana sama_sama,ba su san hakan damun Sabriyah yake yi ba,bazasu taɓa gane halin da take ciki ba ,gani take su basu da wata matsalar komai din su yana tafiya dede a rayuwarsu,amma ita daga lokacin da tasan kanta ta fara gwagwarmayar rayuwa komai sede ta yiwa kanta,da Asmita harta rawan da takeyi tana yine dan su dinga samun abinda zasu ci,da kuma abinda zasu sawa jikinsu, lokacin da Anty Teema ta fara jinyan cutar ƙanjamau nan ne nauyin ya sake ninkuwa mata, maganin Anty Teema duk yana kanta,haka take damfaran maza domin ta biya musu bukatunsu na yau da kullum,domin Asmita rawa kawai take yi wani lokacin ma bayi takeyi ba,saboda bataso .sede Sabriyah ta wakilce ta. Musamman Asmita da take da babban ciwo a rayuwarta wanda inde bata cika wannan buri nata ba na watsawa Mamman kudin da kullum shine maganarta, har ya zamana wannan shine mafarkin da in ta kwanta barci se ta yisa,ga kuma shaye_shaye da take son mayar dashi jiki a wajenta. Gaba daya bata san jin dadi ba daga wannan se wannan ga shi ita kanta ba isheshen lafiya ne da ita ba,ciwon nimoniya dinta in ya tashi kamar zata mutu. Tagumi ta yi kawai ta zuba musu ido bawai dan tana fahimtar su ba, ankara da ita Rameesa ta yi "yan mata ya da tagumi". "Hmmm!bazaku gane bane,babu bukatar sanar da ku". Sabriyah ta bata amsa tana cire tagumin. "Sede in ba ki faɗa mana ba amma zamu gane..."cewar Iklas da ta shigo hannunta riƙe da sudrex da kuma glass of water. Karba Sabriyah ta yi badan taso ba tasha ta kwanta ta juya musu baya kamar bacci zatayi saboda tana so su dan ba ta guri,ga breziyar a hannunta taki ajiye wa. "To iyayen shegen surutu let's leave her alone to rest"cewar umaisha,gyada kai suka yi sannan suka fice. Se da ta tabbatar da sun fice sannan ta mike ta garkame kofar da key ta dawo ta zauna tana buɗe zip din breziyar nata,sannan ta fito da memory card din ,ganin yana nan ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tana "yauwwa,yana nan".mayar dashi cikin breziyar, ta wurga breziyar kasan gadon domin gani take yi se yafi samun tsaro a wajen.kwanciya ta yi tana jin ranta duk babu dad'i,mutane uku ne suka tsaya mata arai da bata san halin da suke ciki ba,mutum na farko farin cikin ranta wato Asmita na biyu kuma anty Teema,mutum na uku kuwa shine Fu'ad tana son sanin yana ina kuma meyasa wa'yannan mutane suke farautar rayuwarsa.aranta ta ce"Allah sarki Fu'ad kai din mutumin kirki ne Allah ya tsare ka da sharrin wannan mugun". Haka ta dinga saka da warwara tana kwance,har bacci barawo ya yi awon gaba da ita. Duk wani abinda takeyi,yana zaune ya yi relex a cikin dakin binciken dake cikin part dinsa yana kallon ta yana shan coffee cikin kasaita, murmushi ne ya subuce akan kyawawan libs din shi.ganin in da ta wurga breziyar na ta, kwantar da kansa akan kujerar da yake zaune ya fara juyawa dashi ahankali_hankali. wato shi wannan yarinyar zata gwadawa wayo,shi da ya dauki tsawon shekaru goma yana karatun bincike da kuma karantar mutane da sauran abubuwa shine zata gwada masa tana da wayo.shafa lallausar sumar kanshi da ke da yawa ya yi,sumar ne ya shige cikin ɗan karamin ɓulin dake cikin abin hannunsa,da dabara ya shiresa, ya dawo da hannun fuskarsa yana kallon abin hannun nasa,kasa janye idanunsa yai akan abin hannun,ya daura hannun akan kirjinsa yana lumshe sexy golding eyes dinsa yana jin wani nutsuwa na shigarsa ta ko ina. A lokacin da yake USA ko da yaushe cikin binciken Asrah yake ba ji ba gani ta dalilin nan ne ma yasa ya gagara dawuwa Nigeria,seda binciken nan ya dawo hannunsa ya dawo. Amma a yan kwanakin nan yana mamakin kansa da ya dena neman inda Asrah take ,domin yana jin kusancinsa tare da ita,ji yake yi kamar yana a tare da ita,tunda ya shigo Nigeria yakejin wani kwanciyar hankali da nutsuwa. Ajiyar zuciya ya yi wanda ya fito da sunanta"Asrahhhhh...". Tunaninta ya fara lokacin da take yar karama da ita,wani wurin in ya tuna ya ɗan girgiza kai wani wurin kuma ya ɗan sa'ki yar karamar murmushi. "My little stubborn girl!am feeling your presence in everywhere". Yana gama faɗar haka ya mike cike da jarumta ya fice daga dakin binciken ya koma bedroom dinsa,ko minti biyar be kai da zama ba kira ya shigo cikin wayarsa be yi picking ba,seda wani kiran ya sa'ke shigowa, mika daguwar kyakkyawar hannunsa kan filo ya ɗauki wayar. se da ya kusa katsewa kafin ya daga yasa a handsfree"assalamualaikum! Tajuddeen fatan kuna lafiya!?". "Alhamdulillah! Abbu ya aiki?" A bangaren Abbu dake kusa da Abbie shima wayar a handsfree yake,"Alhamdulillah mun gama duk wani abinda yakaimu, we're expecting to be back within next week in sha Allah". "That's good,ina Abbie my regards to him, tell him I missed his jokes and ......"kasa karasa maganar ya yi sakamakon jin bakinsa ya gaji da maganar saboda ta yi tsayi sosai bayan haka kuma yau ya yi magana me ɗan yawa.... Daga can bangaren su jin ya carke yasa suka fahimci cewa ya gagara karasawa ne,saboda da gajiyar da ya yi. Abbie ne ya karbi wayar"Son don't stress your self!you need to rest,inna dawo zan koya maka doguwar magana okay?". "Uhmmmm"kawai LTG ya ce sannan ya hanging phone din. "Kaga wani ikon Allah ko Isma'il!?,yanzu har Tajuddeen ne ze iya wannan maganar lallai nasha mamaki'.cewar Abbie,yana faɗawa Abbu. "In sha Allah addu'ar mu na tare dashi babu wani mugun mutum ko aljani da zeyi nasara wajen ruguza rayuwarsa, ba ma shi kadai ba duka yaran namu". "In sha Allahu!da yardar Ubangiji", Abbie ya yi maganar yana kiran number Ammi. Ammi dake zaune akan gadon ta tana gyaran farcenta ne taga kiran Abbie ya shigo da sauri ta daga tana murmushi. "Sarauniyata fatan kina cikin koshin lafiya!?". dariya Ammi ta yi tana jin farin ciki na mamaye ta har cikin ranta, duk da yanzu sun manyanta amma hakan be hana Abbie kiranta da sunaye masu dad'i ba sede in suna gaban ƴaƴansu ne. "Lafiya klau alhmdllh,ya aiki ya abbu duk kuna lafiya?".gaisawa sukayi da juna kafin ta bashi labarin yarinyar da LTG ya ɗauko,shima Abbie ya yi mamaki duk da,basu san meye dalilin sa ba, amma yana addu'ar Allah yasa alkairi ne. Sosai suka sha hira kafin ya sanar da ita sun kusa dawuwa.a haka sukayi sallama. "Hajiya khareema!ina so ki faɗa mini meye kike nufi dani tunda burukan ki suka fara cika,kika yasar dani agefe wato amfani na ya ƙare ko!?,na gama miki amfani shine za ki cire ni daga lamarin ki.bari kiji in faɗa miki Wallahi muddin kikayi tunanin yi mini butulci tofa zan tona mana asiri kowa ma yasan abinda ya faru tunda kince ke butulu ce"cike da ɓacin rai ummah ta ke faɗawa Ammuh maganganu,ita kuma zaune take tana kallon ta hankalinta kwance. "Am sorry Hajiya hurairah,bawai na cireki a kan wannan shirin bane,ko dan saboda kin gama mini amfani, ah ah!na ɗan janye jiki dake ne saboda na lura Abida tafara zargin akwai wani abu tsakaninmu ko kuma muna da wani manufa.to wannan ne yasa nafara nunawa kamar bama shiri sosai, amma ke kin sani,kinsan yanda nakeji dake,kece ginshikin wannan aikin namu.kiyi hakuri kin ji?".se a sannan ne ta ji hankalinta ya kwanta,yanda Ammuh ta cireta a plans din ne yasa ta fara shirya yanda zata tona musu a siri. "Se yanzu naji hankalina ya kwanta, yanzu aina muka kwana". "Ko kefa Hajiya Huraira abinda nakeson ji kenan,yanzu shirina na gaba shine dawo da Tajuddeen karkashin ikona,zan haɗa shi aure da yar autarmu,Naziya, Wannan shine shirin gaba". Murmushi ummah ta yi"kina ganin Naziya zata iya janyo hankalin Tajuddeen!?".wani shegen murmushi Ammuh ta yi"Naziya is a very innocent and kindhearted girl,da ita zanyi amfani ". Suna tsaka da tattaunawa Tajuddeen ya shigo part din,shuru sukayi suna tunanin kode ya ji tattaunawar da suke yi,tsayawa ya yi a kusa da Ammuh"Ammuh! i need fryed egg" "To ɗana bari in soya maka"ta faɗa tana mikewa ta nufi kitchen ummah kuma ta fice daga part din. Zaune take a kan kujerar karfe, an haɗe hannunta da ƙafafunta an daure a jikin kujerar ga bakinta manne da gam,gashin kanta duk ya hautsine kallo ɗaya zaka mata kasan cewa bata cikin hayyacinta musamman yanda idanunta suka gagara tsayawa guri daya bata iya rufesu haka kuma bata iya buɗesu. Cikin wani ɗan karamin daki madaidaici babu komai acikin dakin se kayan karafuna,ko fulasta babu acikin daki ɓalle kuma fenti. Wasu ƙartan maza ne masu ji da karfi suka shigo dakin kallonta sukayi suka ga haryanzu bata dawo hayyacinta ba. "Yarinyar nan fah ta ƙi faɗan inda ta ajiye memory nan,dole mu sa'ke shaƙa mata cocaine din nan ko zata yi magana". Cikin takaici dayan ya mishi kallon banza"Samuel kai wani irin mugu ne kam,ita din fa macece ba wai na miji ba,yau kwana biyu kenan safe da yamma kullum se an shaƙa mata haba abin ya yi yawa ze iya mayar da ita mahaukaciya". "Yeeeeeeeh!tahhh shut up you dey craze? kana son mu a kashe mu kenan?, wannan yarinyar dole ta yi magana in ta ƙi kuma tabar duniya". Shide be ce mishi komai ba yasa hannu ya ɓare mata gam din bakinta. Kamar me koyan magana tana hado kalmomi dakyar ta iya furta"sab......ri..........yah......" Oho sude basu fahimci me take cewa ba,suka sake rufe mata baki suka barta. Fita sukayi a wajen,aka barta ita daya a dakin. After one week Tunda ga wannan ranar da Anty amarya ta sa Sabriyah a ido ta ji son ta ya shiga zuciyarta,haka uncle Hameed ma.Sabriyah bata fitowa cikinsu amma,anty amarya zata zo su zauna suyi hira ta yi ta zolayar ta kafin a ankara shakuwa me karfi ya shiga tsakanin Sabriyah da anty amarya, Ammi, Hajiya babba, Umaisha, Parsa, Rameesa, iklas.shirinta da Zoya ne har yanzu jininsu be haɗu ba,haka Ammuh ta rasa dalilin da yasa ta tsani Sabriyah kuma duk sa'in da suka haɗu se ta jefeta da mummunar kalma ta na hantarar ta,dake Sabriyah dinma fitsararriya ce bata raga mata bata shakkar fadawa Ammuh duk maganar da yazo bakinta, ummah kam dama tun lokacin da aka kawo Sabriyah gidan magana ko wani kallon banza be taɓa haɗa su ba. Duk kayan da aka kawo mata haka ta zauna ta dinga reɗesu da almakashi tana rage musu tsayi, saboda bata saba sa kaya masu tsayi ba,in ta sakama takura mata yake yi. A bangaren LTG Taj kuwa tun ranar da yasa major Marry ta fito da ita ya fara mata bincike,har yau bata sake sakashi a idonta ba, sede yasa major Marry ta ci-gaba da bincikar ta amma basa fahimtar juna ko kadan domin Sabriyah batajin turanci ita kuma major Marry batajin Hausa, wannan dalilin yasa Khalifa ya dawo shine me mata binciken, duk sanda aka tambayeta meye alaƙarta da Fu'ad amsar ta daya ne shine batasan akan wa suke magana ba.har izuwa yanzu kuma basu fasa binciken ba kuma itama bata canza amsar ta ba. Washe gari around 12:00pm Cikin shigar suit da ya ƙarbesa ya mishi kyau ya zo fita a falon,duk suna zaune sun maida hankalinsu kan cartoon din da suke kallo a system din Zoya,basu lura dashi ba har ya kusan fita ya tsinkayo muryan Parsa "ya Sahil in zaka dawo a siyo mini Teddy"hararanta ya yi "masoyiya yaushe na zama ɗan aikenki?"dariya Parsa ta yi,ta mike ta nufo inda yake tsaye,a jikin kofar ta tsaya ta rike handle din tana murdawa, kunyar haɗa ido ta keyi dashi a duk sanda take mishi magana. "Kin yi shuru kuma wannan bakin ya nuna da akwai alamar magana a cikinsa!"ya yi maganar yana zura hannayensa cikin aljihun wandon suit din,ya zuba mata ido,jin idonshi ta yi yana yawo a jikinta daburcewa ta yi tama rasa meyasa ta taso daga inda take. "Uhmmm.....ya Sahil teddy please,wanda ka siya min last time ya tsufa,and....and i want a new one"yanda take magana a shagwabe tana jan maganar hade da inda_inda da takeyi ne yabawa Sahil dariya,kallon Rolex wrist watch dinsa ya yi "masoyiya am getting late,bazan miki alkawarin zan siya miki ba,sede zan bawa security kudin ya siyo miki,is that fine for you!?". Sosa wuya ta yi kafin ta gyada kai,"good girl "ya faɗa yana jan kumatunta sannan ya fita.ka sa komawa wajensu ta yi ta tsaya tana bin bayansa da kallo. Ita kadai kuma ta rufe fuskarta da hannayenta tana dariya,kowa dake cikin gidan yawancin lokuta da masoyiya suke kiranta amma idan Sahil ya kirata da sunan masoyiya,har ranta take jin dadin sunan,, se taji babu wanda yakai shi iya kiran sunan nata. Tana tsaye awajen bata san da isowar Salim ba kawai dafata taji anyi kallonsa ta yi tana murmushi,kallon inda ta ke kallo shima ya yi. murmushi ne ya subuce masa lokacin da ya hango bayan Sahil. Ya riƙe kugu kamar wani mace"to in kina yiwa Sahil irin wannan kallon ai se ki sa ya yita tuntube,a dinga yin kallon kadan_kadan mana masoyiya". Rufe fuska ta yi tana"ya Salim kabari banaso,zan haɗaka da Ammi"dariya kawai ya yi. "Bye masoyiya take care"ya barta tsaye a wajen. Bin bayansa ta yi tana murmushi,komai dinsu iri daya kamanin su ɗaya ainihin identical twins ne,ko kaya kala daya suke sawa sede color ya bambanta,yanzu ma haka Sahil yana sanye cikin Black suit a ya yinda Salim ke sanye cikin white color suit. Su biyu din sana'ar su iri daya,yan kasuwa ne,matasan yan kasuwan da suke ji da kuɗi,da kuma kyau. 5:00pm dirin motocin LTG da tawagar sa suka diro cikin gidan,fitowa sukayi suka tsaya,bude mishi kofa Khalifa ya yi,yana fitowa suka sara mishi.woww Masha Allah yana sanye cikin full dress uniform,ya fito a ainihin Lieutenant general Tajuddeen Bishara,bakaramin kyau ya yi ba fuskarsa nan me razana marasa gaskiya yana nan a murtuke babu ko da ɗigon murmushi. Kai tsaye cikin gida ya nufa. Tunda ya shigo bedroom dinsa ya gane an shigo masa part.bayan shigarsa ciki kuma ya sa'ke tabbatar wanda ya shigon har yanzu yana ciki, be damu da ko waye a ciki ba ya cire uniform din jikinsa ya rage daga shi se short. "Da alama na samu baƙon gawa"daukar bindiga ya yi,ya seta yana kara'kat!kat!kat'. Fara bin ko wani dungu na dakin ya yi ,yana nuna bindigar kamar ze harba. Sabriyah dake cikin labule tana kallon duk abinda yake yi,in hankalinta yakai million tofa se da ya tashi,ita kam ta gama sadakarwa yau mutuwa zatayi,nan take taji wani zawo yana kokarin zuba mata ga zufan dake yanko mata kamar an watsa mata ruwa,aranta kuwa se tsinewa umaisha da Rameesa takeyi buhu_buhu,domin ba dan su ba da babu abinda ze kawo ta part din wannan mugun. duk Wannan gurguwar shawaran su ne,inta tuna dalilin zuwan nata part din nasa ma se ta sa'ke tsine musu cikin kwando_kwando.wai suna son ganin yanda bindigar gaske yake su sede kullum su ta gani agurin Sudais ko kuma Jawan,se kuma major Marry ,suna haka shine Umaisha ta ce me ze hana suje part din LTG suyi video ainihin bindigar su dinga kallo,nan de suka yanke cewa Sabriyah ce zataje ta musu biyon,da farko ta ƙi amincewa amma dake sun fita yawa babu yanda ta iya haka ta amince,Zoya dariyar mugunta ta yi ta ce "Allah yasa LTG ya kamata a part dinshi kasheta ze yi da bindiga"haka suka rakata part din, su kuma suka dawo. Yanzu de ga shi sun ja mata,karkarwa jikinta yake yi kamar mazari, musamman da taga ya dunfaro ta da bindiga. Nan take hawaye ya fara wanke mata fuska tasan yau itakam se buzunta...... Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ 🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹 Page 19 & 20 *_ story & written_* By *_MRS 🌹 ISHAM 🌹_* (Yar lelen Jarumai) *The writer of ✍️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️ *Kamar yanda kuka sani wannan littafin paid book ne,yanzu saura pages kadan free book ya ƙare,ya kamata tun yanzu ku fara biya kafin lokacin ya yi dan banason bata lokaci ina gama book one za'a daura da book two* *Ga duk me son biya, littafin ASHE ZAMUGA JUNA naira ₦300 ne only ga mutane 20 da zasu fara biya yanzu. Za'a biya via opay account 8166018849 Aisha Abbas bidami opay account,idan mutum ya tura da kudin se ya yi screenshot ya turo mini da evidence of payment ta whatsspp number ta 09024503194 Mrs isham.* Ga wa'yanda basa iya tura kudi ta opay account,zasu iya sawa ta wannan account din 2309617787 Fatima Abbas UBA BANK.duk wanda ya tura ya yi screenshot na evidence of payment ya tura min. Page 19 & 20 Nan take hawaye ya fara wanke mata fuska tasan yau kam se buzunta,bata san wani tsautsayin bane yasa ta biyewa haukar su Umaisha. Dunfaro inda take boye cikin labulen kamar wata mage,se mutsu_mutsu take yi,ta ka sa tsayawa waje daya,kwashe labulen ya yi, ya maida su gefe yana rike dashi a hannunsa. Runtse idonta da har lokacin hawaye ne yake faman Zarya kamar an kunna gamfo,jin ya bude labulen da ta boye aciki.tsoronta daya kar ya fasa mata kai da bindiga. Haɗe hannayenta waje guda ya yi, ya janyo ta tsakiyar dakin. "Me ya kawo ki bedroom nawa!?"ya tambayeta calmly,yana kallon fuskarta. Ido a rufe bakinta ya fara motsi,ta ma rasa menene abinda zata faɗa mishi ta wanke kanta, ko giyan wake tasha bata isa ta ce mishi bindigar sa ne tazo yiwa video ba. Cikin sarkewan magana,irin na marasa gaskiya ta furta"dama banida lafiya ne,shine nake neman magani na ɗauka nan sashen ya Saghar ne". Duk wani alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita,hakan yasa kalma daya da ta faɗa be yarda dashi ba. "Ayya!ka barni in fita ka ji!?" Bindiga ya daura mata a kai, kamar ze harbeta ta kwala ihu. "Wayyo na shiga uku na,dan Allah karka kasheni!, banason mutuwa yanzu,bazan ƙara shigo maka sashen ka ba"da iya karfinta take magana tana kuka jikinta gaba daya ya jike da zufa,ga cikinta se ƙa ra yake yi. "Shut up "tsawan da ya daka mata wanda seda yan hanjinta suka ƙara tsurewa. A bangaren su Rameesa kuwa tunda suka ji diran motocin LTG suka shiga tashin hankali sun san yanzu haka Sabriyah ta shiga hannu, duk jugum_jugum suka yi abin duniya ya damesu ga da_nasanin turata,jiki a sanyaye Parsa ta ce "ga shi kun ja mata,ni tun farko ban yarda da wannan shawarar ta ku ba,kunsan ya Taj no nonsense ne,yanzu ga shi abinda ya biyo baya". Su de shuru suka mata dan basu da bakin magana. Zoya ranta fes ko ajikinta se ma nishadin da take ciki na ganin LTG ya kama Sabriyah a part dinsa. "Ni Wallahi hakan ya min dede, Allah yasa ya kakkaryata kowa ma ya huta, kunga gobe babu wacce zata sake yin gigin zuwa part dinsa in baya nan!, gaskiya na dade ban shiga farin ciki irin na yau ba". Takaicin maganganun da Zoya ke faɗi ne yasa duk suka watsa mata harara. "Ai ke kinyi a sara Zoya,yar uwarki mace na cikin wani hali shine ki ke farin ciki,meye ribarki in ya Taj ya mata wani abu!?,ke wannan mugun halin naki ne yake haɗa ni dake,yar iska kawai"cewar umaisha da ranta ya kai kololuwa wajen ɓaci. Rameesa da se yanzu ne ta samu bakin magana"kyaleta de mugun bakinki se ya dawo kanki". "Can muku de yanzu kam "Zoya ta fada tana danna wayarta bata biye musu ba. Tagumi Iklas ta yi ta ce"kun san me mu gwada kiranta a waya muji ko ta buya a wani wurin".duk sun yarda da shawarar ta hakan yasa suka kira wayar dake hannun Sabriyah. Bindiga na a tsakiyar goshinta, kwakkwaran motsi bata iya yi ji takeyi in ta motsa LTG ze tarwatsa kanta da bindigar. Wayar dake hannunta ne kira ya shigo,wayar na vibration, idonsa ne ya sauka akan wayar hannun nata karba ya yi, ya saka a kunne,muryar Umaisha ce ya ji tana magana cikin raɗa."Sabriyah fatan de ya Taj be ganki ba ko!?,kar ki fito daga inda kika buya zamuzo mu fitar dake". "Naganta kuma ku dinma yanzun nan kafin in bude idona inasan ganin gaba dayanku a nan".yana sanar da ita haka ya kashe kiran. A zuciyar Sabriyah ta ce"shikenan kuma kun shiga hannu,gwara kuzo ya harbemu tare din,shegu tunda ku kuka ja mini". Sauke bindigar ya yi ya barta a wajen ya koma kan gado ya zauna,yana duba wasu files da major Marry ta ajiye masa. Duk wannan budurin da ake yi Sabriyah bata bude ido ba se da taji ya cire bindigar akanta,kallon inda yake zaune ta yi,ta gan sa daga shi se short,zare idonu waje ta yi tana bin halittar jikinsa da kallo,sosai take ƙare masa kallo kamar zata haɗiye sa. Unexpected ta ji muryarsa yana mata magana "banason irin wannan kallon yana fusata ni"da sauri ta ka war da kanta gefe dan batayi tsammanin yasan tana kallon sa ba. Ba tare da ya dago ya kalleta ba ya ce"kneel down"gabanta ne ya faɗi jin abinda ya faɗa domin tasan ma'anar kneel down saboda,time din da suke yara inde sukayi laifi haka boss lady zata sa su yi,se sun kusan yin awa takwas a haka. Hannu yasa yana kokarin daukar bindigar,a tsorace ta zube akan guiwowinta, ta yi kneel down din,ta daga hannayenta sama. A cikin wannan yanayin su biyar din jere reras suka tsaya acikin kofar bedroom dinshi ko wacce jiki a mace.ganin yana kokarin ɗago kanshi ne suka shigo da gudu suka tsatstsaya,se zazzare ido suke kamar magen da ya yiwa kare sata. Shuru sukayi suna jiran su ji abinda LTG ze ce. "Be on your knees"abinda kawai ya faɗa kenan. Kamar zasu sa ihu, haka suna ji suna gani sukayi kneel down suma a kusa da Sabriyah. Tana fama da zafin da guiwowinta suke mata ga kuma hannunta dake sanƙare,amma tsabar mugunta itama tana under punishment amma hakan be hanata kwashewa da dariyar da batasan ta yi ba.ga shi tana son dakatawa amma ta gagara se kyakyatawa da dariya take. Kallonta sukayi da mamaki ganin basu kadai aka sa punishment din ba harda ita. amma tsaban iya shege irin na Sabriyah dariya take musu,ita kuma babban abinda yasata dariyar shine,ganin tana kokarin rufa musu asiri a wajen LTG amma tsabar iyayi irin nasu suka wani kirata a waya ga shi suma sun jawa kansu kamar yanda suka ja mata, musamman ma inta haɗa ido da Zoya nan take wani sabon dariyar ya ke kamata,domin Zoya ce duk ta mata wannan mugun bakin harda cewa Allah yasa LTG ya kamata ya kasheta da bindiga yanzu ga shi dukkansu sun shiga hannu. Hararanta Rameesa ta yi, ga shi babu halin yi mata magana gudun kar LTG ya kara musu wani sabon punishment din. Slowly ya kalli inda take tsugune ta yi kneel down din har lokacin fuskarta na dauke da sauran dariyar da ta gagara shanyewa. Mamaki ne ya kamashi ya fara tunanin meye yasata dariya kode punishment din da ya bata ne ta rena?. Pointing dinta da yatsa ya yi,"come here".kamar anyi ruwa an dauke dariyar da takeyi ya dauke ta shiga firi_firi da ido,mantawa da LTG na wajen yasa take wannan dariya yanzu kam da ta ji husky voice din shi, ta shiga cikin rigar nutsuwa. Ƙa sa da murya iklas ta ce"kiranki fa yake yi ,ki rufa mana asiri kije". Simi_simi taje gabansa ta tsaya kamar bishiya. Kusan mintunta biyar a tsaye be ce mata komai ba yana duba file din gabanshi. Ranta ne ya soma baci cikin gunguni yanda baze ji ba ta yi magana"Ni fa ba kayan wanke bace da za'a shanya". Cak ya dakata da bude pages din da yakeyi , maganar da tayi duk a kunne sa yajita,da hannunsa na hagu ya yi amfani wajen ɗauketa da marin da batayi tsammani ba se kawai jin saukar sa ta yi,komai ɗauke mata wuta ya yi na wasa sakonni ta fara ganin stars yana wucewa ta gabanta.dafe in da ya mare tan ta yi,tana jin wani abu na sukan zuciyarta kamar ana daɓa mata mashi.kukan da takeson yi ma ya ƙasa fitowa fili, haka ta haɗiye, tuna afafa ta yi yanda take yin yanda ta gadama in banda boss lady babu me sa hannu ya daketa,ko waye shi seta ga ta mishi rashin mutuncin da beyi tunani ba.zaman da takeyi a gidan nan a takure take jinta kawai de in da abin yake zuwa da sauki akwai masu ɗebe mata kewa badan haka ba da ko ta wani hali se ta bar gidan nan.tafi samun freedom din da take bukata acan gidan karuwan. Sabriyah aka mara amma su Umaisha su sukaji zafin,,,tausayi tabasu ga tarin danasanin abinda suka aikata ta dalilin su ne zata fuskanci hukuncin da bata da sa hannu. yanzu ma ta dalilin su LTG ya mata wannan marin duk su suka ja mata,jikin su ya yi weak sosai, Parsa iyayen tausayi da son jama'a tun sanda LTG ya mari Sabriyah ta fara hawaye tana jin kamar ta jawo Sabriyah jikinta ta bata hakuri,amma tasan duk yanda LTG yake sonta yake ji da ita baze juri renin hankali ba. "Bana son rashin kunya kuma bana son me yin sa,be very careful around me, Kiyi kneel down anan" ya yi maganar yana ajiye file din ya tashi ya shiga toilet yabarsu a wajen,yana barin gurin Sabriyah ta yi kneel down din da ya bata umarni akai. Cikin rada Rameesa ta mata magana"we're sorry darling,kiyi hakuri kinji bazamu sake irin wannan wasar ba"murmushi ta mata like nothing happened."Mtsssw!ai ni kam kun cuceni, I won't forgive any one of you, kun haɗa abunku kunja ya Taj ya haɗa dani acikin punishment".duk suna jinta babu wanda ya kulata suna durkushe kamar basu jita ba,haka Zoya ta yi shuru dan kanta. Se da ya ɓata 20 minute yana wanka sannan ya fito sanye da jallabiya ash color ya yi fitting dinsa sosai,kyawunsa ya sake fitowa,ta kasan ido dukkanin su suke kallonsa saboda tsoron kar ya kamasu suna satan kallonsa,shi mutum ne da ya tsani yawan kallo,ya tsani a zura mishi ido ana kallonsa,kamar yanda ya sanarwar Sabriyah yawan kallo na tunzurashi,amma duk da haka seda ya kamasu suna kallon shi cikin tsawa wanda ke haɗe da ɓacin rai "what are you looking at!?,ko kunga dodo a jikina ne!?"ya faɗa rai a ɓace,kallon ƙa sa suka koma yi a tsorace. Kwafa ya yi kafin yaje gaban mirror ya gyara gashinsa da hair brush,, falo ya fita ya barsu a bedroom din ya zauna ya yi saving din kanshi abinci,fried spaghetti da akayi da chicken.be wani ci sosai ba even though favorite dinsa ne. General ne ya kirasa suka fara waya akan binciken da yake yi,ba wani jimawa suka yi suna magana ba, email ya shiga yaga anturo mishi da wani short video da wani unknown email account, playing video ya yi yaga macece daure a jikin kujera se shaƙa mata cocaine ake yi,a ƙa san video anyi Caption da "ka rabu da Sabriyah nikuma se in saki wannan yarinyar".shuru ya yi na Wasu sakonni. nan ya fahimci wannan ita ce yarinyar da Sabriyah ta damu da zataje nemanta. Cizan red libs dinsa na ƙasa ya yi kafin ya kira major Marry a waya. Be bata damar yin magana ba ya ce "find that girl in any cost, don't waste my time"."okay LTG "cewar major Marry, sannan hanging call din. Yasan dole in de yasa aka kwato Asmita to Sabriyah cikin ruwan sanyi zata ba shi memory card din babu jayayya, bayason ya shiga hakkin su ne na nuna mata karfi tunda tun farko, su alhakin wannan memory yake wajen su, shisa baze takura ba yafi son tabashi cikin salama. Duba time ya yi, yaga lokacin dawuwan Sudais ya yi,ya fita daga part din,palour ya samesu su uku suna zaune, Sudais,Sahil da Salim,kusa da kujerar da Sudais ke zaune ya zauna shima.hira suke yi shide ba wani sa baki yake yi a hirar ba se jifa_jifa. "Nikam ya Hafiz ya dawo ne?"kallon Salim da ya yi tambayar Sudais ya yi, ya ce "dama baya nan ne?,dazun naga missed call din sa ina aiki , kuma yanzu ma na manta ban kirashi ba ". "Ehh sunyi tafiya da matarsa da yaronsu,amma kamar gobe zasu dawo nake tunani,ko kuma in su Abbie suka dawo". Haka suka dinga hiransu seda aka fara kiraye_kirayen sallah mangrib ne, LTG ya mike"lokacin sallah ya yi". Yana sanar dasu haka ya fita bin bayan sa suka yi. Bayan sun dawo daga masallaci ne,ya nufi part din shi,biyosa suka yi suma. Juyowa ya yi ya kallesu ya tsare su da ido"maye kuma kuke bina!?"kunshe dariyar dake son kufce musu sukayi kafin Sahil ya basa amsa"yau a wajen ka zamu tare,tunda ka dawo bamu samu lokacin taɗa rayuwar duniya ba".jin abinda Sahil din ya faɗa bankwarakwai wai taɗa rayuwar duniya se kace wasu mata. Tsaki ya ja"Nifa banison surutu bazaku addabeni ba kusa yaran nan suna dawuwa daga wajen aiki su biyo ku "(yana magana ne akan Saghar da Jawan)dariya sukayi Sahil da Salim cikin shakiyanci suka ce "Yes sir" a tare suka shigo part din nashi,shi yama manta da yabar wasu aciki. Zama a palour su kayi suka fara hirar wajan aikin su nan ne de LTG ya saka baƙi,kasa_kasa suka fara jin sheshekar kuka Kuma bana mutum ɗaya ba,ka sa kunnawan su sukayi suna son gasgata abinda kunnesu yakeji, tabbas kuka ne yake fitowa daga dakin LTG amma to su waye ne a ciki,cikin tuhuma suke kallonsa. Sudais ne ya tambayeshi"LTG Taj!su waye suke kuka a bedroom dinka!?",seda Sudais ya tambayesa tukun ya tuna da su Sabriyah da ya bari a ciki,kusan awowinsu uku kenan suna ciki ya ma manta da al amarinsu ashe suna ciki.ko a jikinsa babu alamar ya damu ya furta"yaran nan ne suka zo mini bincike nasa su kneel down"ya yi maganar can cikin makoshi badan suna kusa dashi ba to da bazasu taɓa jin abinda ya faɗa ba. Da sauri Sahil ya mike yana"masoyiya"yana kiran parsa yana shiga cikin dakin LTG, dukkansu suna tsugunne kamar yanda ya barsu,sun ci kuka harsun gaji,sun galabaita fuskar nan da ido ya yi ja sosai kallo ɗaya zaka musu su baka tausayi. Da sauri Sahil ya isa gaban Parsa yasa hannu yana kokarin mikar da ita tsaye,karan azaba tasaka ko wani ga ɓa na jikinta ya rike ya yi tsami ga kuma ciwon da suke yi, kuka take yi sosai ganin bazata iya tashi da kanta bane yasa ya zaunar da ita. "Sannu masoyiya!ku ma bakwa jin magana me ze haɗa ku da part din LTG ba ya nan".kallon su ɗaya bayan ɗaya ya yi sun bashi tausayi,idon sa ne ya sauka akan Sabriyah da ke kneel down din rakube ajikin bangon dakin,ita kam tsabar wahala ko idonta bata iya budewa. Lamarin LTG ya bashi mamaki yanzu har da wacce yake bincike akanta din ya saka kneel down din bayan su Umaisha ne suka mishi laifi(Ni Ko araina na ce ai kai Sahil kawai kayi shuru ba kasan komai ba,ita Sabriyah ce ya fara kamawa!hhhhhhh). Shigowa sukayi dakin banda LTG dake zaune abin sa a palour. Rike kugu Sudais ya yi duk da baya wani wasa da su sosai saboda a cewarsa basa jin magana.kwashewa da dariyar mugunta ya yi yana binsu da kallo musamman da idonsa ya sauka akan Umaisha da ta marairace fuska tana kallonsa, maimakon ta bashi tausayi amma se ma sake basa dariya ta yi. "Ba kun ce bakwa jin magana ba!ai ko nine na kuskura naji ko da labarine kunje part dina bincike to abinda LTG ya muku kadan ne". hararansa Sahil ya yi "yanzu Sudais dan Allah basu baka tausaya ba?, shine zaka wani tsaya kana dariya jibi yanda suka galabaita"dage kafadunsa ya yi alamar i don't care. "Ka duba har da Sabriyah fa da ba wani biye musu takeyi ba"Sahil ya sa'ke magana yana musu nuni da Sabriyah dake gefen su. A tare Salim da Sudais suka kalli inda Sabriyah take,zaro manyan idanunsu waje suka yi cike da mamaki Salim ya ce "yanzu tsabar iskanci irin naku se da kuka jawa yarinyar nan!?,nasan de Wallahi babu ruwanta". Zoya dake fama da kanta tana kuka ta ce"ya Salim ita ce fa,ya samu tana mishi bincike"mugun kallo ya watsa mata saboda be yarda da abinda ta faɗa ba. "Karya kikeyi Zoya da bansan rashin jin ku bane!". Kamar zata yi kuka ta ce "shikenan ai" Wajenta yaje ya taimaka mata ta zauna. duk zaunar da su sukayi. Rameesa da Umaisha ko magana basa iyayi sede binsu da kallo da suke yi ,yau LTG yabasu a jikinsu. "To yanzu ke Umaisha tashi ki wuce part din ku"Sudais ya yi maganar fuska babu alamun wasa. Marairaicewa ta yi kamar zata yi kuka"ya Sudais Wallahi ƙafata sun yi tsami,bazan iya tafiya ba"kamar zata yi kuka ta ƙarishe maganar. Hararanta ya yi ya ce"to ina ruwana?,ku de ba rashin ji ba?". Shigowa dakin ya yi, ya tsaya daga jikin kofar ya harde hannunsa a kirji. Salim ne ya kallesa "LTG a yi musu afuwa bazasu karaba" "Su bar mini part kafin in canza ra'ayi" Dariya sukayi dukkansu mazan banda shi LTG din. Sahil ne yasa hannu ya daga Parsa,dakyar ta iya mikewa ta rike shi gam tana cize libs dinta saboda azaba. Taimaka mata ya yi,ya kaita har part dinsu ya ajiye ta akan gado sannan ya koma. Mikawa Sabriyah hannu Salim ya yi yanaso ya taimaka mata. "Ban gama da ita ba ku barta anan ita". Kallonsa sukayi jin abinda ya faɗa. "Haba LTG wannan fa bakuwarmu ce,dan Allah kabarta haka".Sudais ya yi maganar yana kallon shi. kamar wanda yake magana da gini haka LTG ya sharesa be kulasa ba,ganin haka da Sudais ya yi yasan baze bar Sabriyah din ba. Wajen Zoya Salim ya je yana hararanta ya dauketa can kuma ya fashe da dariya"ƙaramar mara kunya,yau kinci Sa'a ba dan tausayin da kika bani ba ko kallon ki bazanyi ba". Ita de batace komai ba Allah _allah takeyi ya fitar da ita daga part din,suna kokarin fita Sahil ya shigo. Ɗaukan Rameesa ya yi da se" wayyo Allah! Abbie ƙafafuna sundena aiki" "za ki mini shuru ne ko se na sauke ki!?"shuru ta yi dan tasan karamin aikin Sahil ne yabarta agurin. Kwashe su sukayi a wajen ya yi saura daga Sabriyah se Umaisha, Sudais kam ma waje ya samu ya zauna suna magana da LTG. Gasu Sahil da Salim tunda suka dauki Rameesa, Iklas, Parsa, Zoya bazasu ƙara dawowa ba. Tagumi Umaisha ta yi tana hawaye zaman da tayi dinma kwata_kwata be mata dadi ba rabin hips dinta ya gaji,kallon Sabriyah da ta jingina kanta da jikin gini idanunta a rufe kamar me bacci,ta yi sannan ta maida kallonta kan LTG da Sudais da suke magana. Fashewa ta yi da kukan takaici ganin sauran yan uwanta duk an kwashe su saura ita,tunda Sabriyah LTG kam ya ce be sallame ta ba. Ta kasan ido Sudais ya kalleta yaga yanda take kuka bil haƙƙi, murmushi ya yi. "Kukan me kike wa mutane"ya tambaye ta yana tsare ta da ido. Tsinkayar Muryar sa da tayi yasa ta dago suka haɗa ido,irin kallon da taga yana mata ne yasa ta sunkuyar da kai,ta riga da tasan inde Sudais ne ze dauketa to zatayi shekara a haka. Ji ta yi an dagata sama a tsorace take kokarin sa ihu ta ji,muryarsa"shiiiiii!be quiet"tunda take bata taɓa kawowa a ranta yau ya Sudais ze taimaka mata ba, saboda yadda yake cin zalinta da kuma mata faɗa, babban abinda ya fara haɗa su shine rashin saka dan kwali. Zubawa kyakkyawar fuskarsa ido Umaisha ta yi tana kallonsa. Har ya kaita part din su bata dena kallon da take mai ba,kallon cikin nata idon ya yi kafin yaci gaba da tafiya. bedroom dinsu ya shiga, duk sun baze akan gado suna kwance ko wacce se ya mutsa fuska suke yi masoyiya Parsa kam tana toilet ta yi wanka ta tsaya danna ƙafafunta da ruwan zafi. Sauketa akan gadon ya yi,shi bayan dariyar da suka bashi har da haushi. Kallonsu daya bayan daya ya yi,"meyasa kuka ja punishment din ya shafi Sabriyah,ku bakwa martaba bako ne?". Rameesa mikewa zaune ta yi, ta ce"ya Sudais Wallahi Sabriyah bata da laifi duk mu muka ja mata"nan ta fara bashi labarin abinda ya faru. Girgiza kai Sudais ya yi"Allah ya shirye ku to, in kuma ba zaku shiryu ba jikin ku ze dinga faɗa muku"ya fice a dakin . Fitowa daga wanka Parsa ta yi taji dadin jikinta ba kamar dazun ba da komai wahala yake mata. "Da wannan kwanciyar da kukayi da wanka kuka rufawa kanku asiri ku kayi se kun fi samun salama" "Shawara me kyau masoyiya bari in yi kawai"Rameesa tana magana ta yi shigewarta toilet. Daga shi se ita ne a bedroom din nasa tana a yanda take , jingine da bango idanunta har time bata bude su ba. "Ka sato ni ka kawo ni gidan ku da sunan bincike,na nuna maka bansan akan abinda kuke tuhuma na dashi ba,shin menene kake so wanda zan maka ka mayar dani in da nake in nemo yar uwata!?, Asmita ita ce farin cikin rayuwata bana iya komai seda ita haka itama nice komai dinta,ka faɗamin meyeeeeee..... Kake bukata a wajena nagaji da rayuwa awannan kurkukun"ta gama maganar da karfi Muryarta cike da kunci da damuwa. "Memory card din wajanki za ki ban daga nan kuma zan kyaleki ki tafi duk inda kika gadama".ya faɗa yana danna wayarsa. Rarrafowa gabanshi ta yi,da alamar tambaya ta soma cewa"shin in na baka memory card din zaka kyaleni!?,kuma zaka tabbatar da ka cika burin Barrister Lameer kamar yanda ya buƙata!?"ta yi masa tambayoyi biyu a lokaci daya tana kallon cute face dinsa. Gyada mata kai ya yi "kwarai kuwa". Da sauri tasa hannu a cikin rigar roba body hood dake jikinta ta ja zip din breziyar ta fito da memory. Zuba mata ido ya yi ganin tasa hannu acikin kirjinta,be sa'ke mamaki ba se da yaga ta fito da memory a ciki. Mika mishi ta yi,ya tsina fuska ya yi kamar wanda yaga kashi ya ce"baki da hankali! ki fito da abu a brest dinki sannan kice in karba?,wait!meye ma zesa kisaka shi a cikin nan!?",ya tambayeta yana nuna dede kan tula_tulanta. Yau badan bata cikin mood din masifa ba,yau da se yasha maganganu masu zafi a wajenta saboda abinda ya yi ya bata mata rai,ita da ko wani na miji yake mararin jikinta,kowa yana mararin taba wa'yannan tsayayyun tula_tular amma shi yanda yake nuni dasu kamar wanda yaga wani abun ƙyamar. Amma duk da hakan se da tabashi amsa da"nono na ne zan iya ajiye duk wani abinda na gadama akai ga memory din in ka gadama ka karba". Sosai ya girgiza jin yanda ta kira sunan brest ba tare da kunya ko kuma kawaici ba,hakan ya sa'ke tabbatar mishi da yarinyar nan cikekkiyar yar hau ce.be yi kasa a guiwa ba wajen cewa"ko kadan banyi mamakin jin haka daga gare ki ba domin karuwai basa da kunya da kamun kai". Ko a jikinta da maganar da ya faɗa,ko mutum ze shekara yana kiranta da karuwa tofa hakan baya damunta tunda tasan eh ita karuwar ce,kuma wacce take da cikakken lasisi. Hanky chef ya dauka yasa a hannunsa, kafin ya iya karbar memory card din. "Za ki iya tafiya" Bata tanka masa ba ta mike tana cizan libs dinta ta fice masa a part. Kai kanta toilet ta yi,ta gasa jikinta da ruwan zafi nan taji dadi.ko lotion bata shafa ba ta saka wata karamar riga ta kwanta. Shigowa dakin Rameesa ta yi tazo dubawa ko Sabriyah din ta dawo,ko kuwa LTG har yanzu yana rike da ita.nan ta sameta baje akan gado. "Sabriyah yana ganki a kwance!?"ta yi mata tambaya tana shigowa dakin,dago kai tayi ta je fa mata uwar harara kafin ta bata amsa "da a tsaye kikeso ki gan ni!?"ta tambaye ta tana maida kanta ta kwanta. Dama Rameesa dan neman magana ne yasa ta yi mata wannan tambayar,tana sanye da hijabin da ta idar da sallah isha ta zauna a gefenta. "Tashi muje dakinmu yau a can zamu ci abinci"cewar Rameesa,tabe fuska ta yi kamar zata sa ihu ta ce"Rameesa dan Allah ki barni in huta bana jin yunwa,haba tun shigowar ki kika dameni da magana bana ciki da tambaɗa", "hhhhhhhh! Allah yabaki hakuri sarkin yaƙi" Tana gama gaya mata haka ta fice. Suna zaune a dinning kowa anyi saving dinsa abinci mazan sun fara ci Ammi ta ce"wai nikam ina yan mata na ne!?" "Nima abinda nake son na tambaya kenan yau tunda na dawo aiki banji ɗu riyar su ba"Saghar ya faɗa yana ajiye spoon din hannunshi. Sahil ya ce"yau ɓarna suka je yi wa LTG shikuma ya sa su punishment,yanzu de suna part dinsu ko wacce na jinyar jikinta",anty amarya, Ammi, Hajiya babba,ummah kallon Sahil dake basu labari suke yi dan su da suke cikin gidan ma basu san anyi haka ba. Mikewa uncle Hameed ya yi yana magana"yanzu shalelen yan matan namu LTG ka galabaitar wayyo,ko wani hali Madam Zoya take cike oho!?"dariya suka kwashe dashi harda shi uncle Hameed din da ya yi maganar sannan ya nufi part dinsa,shide LTG ko ta kansu be bi ba cikin nutsuwa yake cin abincisa. Sahil ya sake cewa"kuma babban abin tausayin shine harda wannan Sabriyah din da ya kawo gidan nan ya saka punishment din"zaro ido waje Ammi da anty amarya sukayi sannan suka maida kallonsu kan LTG. "Yanzu Tajuddeen har da bakuwar mun ma baka bari ba!?,ni Wallahi har kunyarta ya kamani,ka sato ta sannan kazo kana haɗa ta da kannnenka kana musu Punishment!?"ta tambayesa tana riƙe habarta. Ɗaukar wayarsa ya yi, ya bar musu dinning table din,ya nufi part din Abbie da baya nan. Anty amarya da Ammi ne suka shiga part din dubasu.ga kuma fatime da ta shirya musu nasu abincin ta kai musu. Sosai Ammi ta musu faɗa akan shiga masa part binciken da sukayi domin koda basu ɗauki komai ba ze ce sun mishi ɓarna,ga shi yanzu a banza ya sa su punishment. Haka suka je wajen Sabriyah ma nan kam sannu sukayi mata sannan anty amarya ta zauna da ita tana bata abinci abaki tun bata karba hatta soma karba,bata barta ba se da ta tabbatar da ta koshi.lokacin har karfe 9:00 saura nan ta yi mata se da safe ta fita.kwanciya Sabriyah ta yi dan bacci takeji sosai sannan ta kwanta da ya ƙinin gobe LTG ze mayar da ita Lagos. Sergent Khalifa ne da suke cikin dajin Kano sun yi ɗauki ba da ɗi da yan ta'addan da LTG ya tura su wajensu kuma sunyi nasara,nan ya samu ya kira LTG din a waya. Yana dakin bincike da layin wayarsu yake bibiyar yan ta'addan da kuma su major Marry,shi yake basu direction akan inda zasu je da kuma yanda zasu yi yana daga zaune akan kujera ga hot black tea a kusa dashi. "Hello LTG, Alhamdulillah mun gama dasu sede an harbi major Marry a hannunta na dama, sannan munyi losing din sojan mu daya!". "Na sani na turo muku helicopter,ku dawo yanzu.and what about the girl fatan basu kasheta ba!?". LTG ya jefawa Khalifa tambaya. "Mun samota sede bata cikin hankalinta ina tunanin ma zeye wuya in bata haukace ba sakamakon bakar fodar ibilis din da suka dinga shaƙa mata" Jinjina kai kawai ya yi,ya kashe wayarsa. Bari mu leka bangaren magajiya boss lady. Tun ranar da aka sace Sabriyah da Asmita boss lady ta tayar da hankalinta,ko ina a cikin Lagos tasa a nemo mata su tunda har ita zasu iya yaudara su gudu daga gidan ba tare da ta yanta su ba amma ba'a samesu ba, domin ita gani take yi Sabriyah da Asmita guduwa sukayi daga gidan, wa'yanda akayi abun a gabansu sun yi mata bayani dallah_dallah kan cewa sace su akayi ,amma fir boss lady ta ƙi yarda da hakan, ta kudiri niyar duk sanda ta yi tozali dasu ko kuma tasa aka kamo mata su seta sa sun dandana guɗarsu. Cele kullum se ya shigo afafa da sa ran ko ze ga Sabriyah da Asmita sun dawo,amma haka ze jisu shuru,ga anty Teema da ciwonta yanzu ya fara tashi gadan_gadan babu wanda yake zuwa dubata da taimaka mata se Nabiha da Cele,su suke kawo mata abinci da kuma magani. Katsina state Gidan mom Rumanatu Bishara yau zamu leka. Babban gida ne kerarren gida wanda ya gaji da haɗuwa wato gidan minister Abu Sufyan Ubaid. Abu Sufyan ministan harkokin jiga da ficen kuɗaɗe ne,suna rayuwar farin ciki shida matarsa ɗaya se ya'yan su hudu biyu maza biyu mata. Babban dan su shine Ashman da ya kasance babban manager a company babanshi Abu Sufyan,se Dawood shi kuma engineer ne. Se ƙannen su mata,wanda suke saƙo da saƙo, Iftisan ce babba se yar autar su Jaleelah me shekara sha shida. Tunda na shigo gidan na soma jin hayaniya kamar ana dambe a falo,leka kaina ciki nayi na hango wasu kyawawan yan mata guda biyu wanda kan su ɗaya kayan jikinsu kuwa dayar na sanye da jeans din wando baƙi da riga,dayar kuma doguwar riga take sanye dashi. Dambe suke yi kamar zasu kashe junansu kuma badan komai ba se akan remote,da gudu na hango mom Rumanatu ta sauka daga downstairs tana ihun. "Iftisan da Jaleelah bazaku bar wannan faɗan ba ko!?"karasowa cikin falon ta yi ta samu ta shiga tsakanin su ta raba faɗan, dukkansu biyu se haki suke yi suna hararan junansu. "Mommy kin ga yanda Jaleelah take hararata ko!?, gaba-daya ta gama rena ni"Iftisan ta yi maganar tana nuna Jaleelah da yar yatsa. "Yanzu wannan damben da ku ka za ge Kunayi kamar wasu makiyan juna duk akan menene!?"mom Rumanatu ta tambayesu tana bin ko wacce da kallo. Cikin shagwaba Jaleelah ta ce "mommy ina zaune ne fa ina kallon cartoon shine Iftisan tazo wai sede in bata remote ta kamo mbc Bollywood shine na ƙi bata remote din,shine fa...shine fa ta fara dukana". Kallon Iftisan din mom Rumanatu ta yi"yanzu akan wannan abin kuka tsaya faɗa,ina ce ta kan hakane ko waccen ku aka sa mata Tv a bedroom dinta!?,amma hakan be muku ba se kunzo falon downstairs kun yi mini faɗa ko!?,to bari yayanku ya dawo sena saka ya muku dan banzan duka.kuma daga yau kar wacce na sa'ke kallo a falo, da sunan tazo kallo tunda ku kamar wasu mayu kullum kuna cikin faɗa,jini daya uwarku daya ubanku ɗaya amma ko da yaushe kuna cikin faɗa kamar wasu ka ji". "Mommy kiyi hakuri bazamu sa'ke ba!,and kiyiwa wannan fitsararriya magana ta dena mini rashin kunya na girmeta da shekara daya so am not her mate". Iftisan ta yi magana tana zazzagawa Jaleelah buhun harara kai kace idanunta zasu faɗo kasa. Girgiza kai mom Rumanatu ta yi dan ita rikicin Iftisan da Jaleelah ya fara isarta,jira take yi Ashman ko Dawood wani ya dawo tasa su zane mata su. Ta ce"ku bani guri ko in gwara kanku da kujerar nan"turo baki Jaleelah ta yi ido cike da hawaye ta ce"sorry mom! please karki faɗawa su ya Ashman". hararanta mom Rumanatu ta yi, sannan ta sake daka musu tsawa da gudu ko wacce ta nufi bedroom dinta. Zama ta yi a palour tana girgiza kanta,kallon agogon dake manne a falon ta yi taga 9:50pm na dare ga shi basu dawo ba,jiransu takeyi dan tasan daga su har daddyn nasu suna tare. Da sauri me aikinta ta shigo falon riƙe da wayar mom Rumanatu da ta barshi a bedroom dinta. "Anty! Hajjatiye ce ke kiranki"ta faɗa tana me miƙa mata wayar,da sauri mom Rumanatu ta karba jin an ce mahaifiyar su ce kiranta. Tana sa wayar a kunne ta ji Hajjatiye ta fashe da kuka. Gabanta ne ya faɗi aranta ta ce "yau kuma laifin me nayiwa Hajjatiye ni Rumanatu". Murya a sanyaye ta yi magana"assalamualaikum! Hajjatiye na Barka da wannan lokacin". A bangaren Hajjatiye kuwa jan majina ta yi,ta ce "munafukar banza da wofi babu tsiyar tsinantakar da gaisuwar ki zata mini!ku kasheni kawai ku huta,nagaji da tsiyar tsinantakar ku bazan iya ba,baze yu ba". Daura hannu aka mom Rumanatu ta yi jin yanda Hajjatiye ke surfa mata ruwan masifa. Ta ce"haba Hajjatiye na, faɗamin laifin me mukayi nida su ya Mubarak din!?". Cikin masifa Hajjatiye ta sa'ke hayayyaƙowa mom Rumanatu"bansaniba!, ni zaku mayar tsohuwar banza ko,ku ce zaku turo anlikonta ya ɗauke ni inzo Nijeriya shine zaku watsa mini ƙasa a ido ko!to duk sena yi maganin tsinantakar dake damunku!su kam ma da suka saka yaransu da matan su suka rena ni ina zasu ga girmana kowa yana tsula tsiyar da yake so,to bazaku kasheni ba se lokacin mutuwata ya yi ".magana take yi amma mom Rumanatu tana jiyo hucin da takeyi ta waya. Dariya ne yaso kufcewa mom Rumanatu jin yanda Hajjatiye ta kira helicopter da anlikonta,ga kuma maganar dawuwarta da takeyi wai anki turawa a ɗaukota.bayan yau da safe aka gama waya da ita ana sanar mata kan cewa gobe jirgi zezo ya dauketa.duk yanda su Ammi suke mata ladabi da biyayya amma yanzu rikicin tsufa yasa tana cewa wai duk sun renata basa ganin girmanta. Gyaran murya mom Rumanatu ta yi cikin kwantar da murya da ya,lallashi haɗe da girmamawa ta fara bawa Hajjatiye hakuri da kuma rarrashinta har ta samu ta shawo kanta.da kuma yi mata alkawarin gobe za'a zo a dauketa. Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba. Comment,like and share 🖋️🖋️ *🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹* Page 21&22 *_Story & written_* By *MRS🌹ISHAM🌹* ( Yar lelen Jarumai) *THE WRITER OF 🖋️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️ *Kamar yanda kuka sani wannan littafin paid book ne,yanzu saura pages kadan free book ya ƙare,ya kamata tun yanzu ku fara biya kafin lokacin ya yi dan banason bata lokaci ina gama book one za'a daura da book two* *Ga duk me son biya, littafin ASHE ZAMUGA JUNA naira ₦300 ne only ga mutane 20 da zasu fara biya yanzu. Za'a biya via opay account 8166018849 Aisha Abbas bidami opay account,idan mutum ya tura da kudin se ya yi screenshot ya turo mini da evidence of payment ta whatsspp number ta 09024503194 Mrs isham.* _______________________________ Page 21&22 Ga wa'yanda basa iya tura kudi ta opay account,zasu iya sawa ta wannan account din 2309617787 Fatima Abbas UBA BANK.duk wanda ya tura ya yi screenshot na evidence of payment ya tura min. Ba ta daɗe da gama waya da Hajjatiye ba, su Ashman suka shigo da daddyn su,bata rai mom Rumanatu ta yi.ba tason daren da suke yi a waje. Ta ce "yau kuma aina kuka tsaya!?"murmushi abu Sufyan ya yi,ya ce "amana afuwa mun tsaya wani meeting shisa mukayi dare". "Shikenan abincinku na kan dinning"wucewa dinning din Ashman da Dawood sukayi dama a gajiye suke ga kuma yunwan da suke ji, mommyn su ta hana su cin abincin da bana gida ba. Serving din su ta yi,itama ta zauna suna hira nan take cewa Ashman tana suyiwa Jaleelah da Iftisan dukan tsiya. Kallonta Abu Sufyan ya yi "yanzu,yaran nan duka nawa suke da zakice wai a dake su!?,ni fa banason lamari da duka da faɗa". Tabe baki mom Rumanatu ta yi domin ko baya nan se tasa an zanesu, wannan alkawarine,saboda rashin jinsu ya ishe ta. Ashman deke cin abinci ne ya dakata ya soma faɗin"daddy gaskiyar magana,kai ka sangarta Iftisan da Jaleelah,gaba daya yara a ce ko laifi sukayi baza a musu faɗa ba" "ehh!na ce ba'a dake su din ba,ko kana da ja ne!?"shuru suka yi dan yanzu inde akan Iftisan da Jaleelah ne,se ku kusan yin faɗa da Abu Sufyan. Canza hira mom Rumanatu ta yi,nan tabasu labarin yanda sukayi da Hajjatiye sun sha dariya kam, Abu Sufyan cikin dariya ya ce "Allah sarki Hajjatiye namu,Allah yakara miki lafiya da nisan kwana!"duk suka amsa da Ameen sannan ya sa'ke cewa"in ta shigo Katsina gobe,mu kuma se mu tafi Maiduguri jibi".haka suka ci ga hirar su suna taɓa abincin gabansu din. Kammala cin abinci suka yi kowa ya wuce part dinsa,Abu Sufyan bedroom din Iftisan ya shiga ya sameta ta yi bacci,rufa mata blanket ya yi ya kashe wutan dakin ya shiga bedroom din Jaleelah zaune ya sameta rike da teddy tana kuka,da sauri ya karaso kan gadon ya zauna tana ganin shine ta rungume shi tana"daddy!". Shafa bayan yar autar nashi ya yi yana tambayarta "meyafaru leelah! waya taɓo mini ke!?". Sauke ajiyar zuciya ta yi "daddy kaga kullum se Iftisan ta dukeni, and se tasa mommy ta yi mana faɗa" "shikenan kiyi shiru bazata sake ba,nayi miki order favorite teddy din ki ke da Parsa in zakuje Maiduguri se ku tafi mata dashi". Dariya ta soma yi jin an siya musu teddy . Be bar bedroom din nataba se da ya tabbatar da ta kwanta sannan ya fita. Washe gari 8:00am na safe,kowa na bacci su Khalifa suka dawo,da majinyata biyu da major Marry da kuma Asmita. Khalifa ne ya shiga part din LTG ya sanar masa da sun dawo. Fitowa daga part suka yi tare ya shiga na Saghar ya tashe shi daga bacci ya ce akwai patient din da ze duba,da ke suna da clinic a cikin gidan. Kai major Marry da Asmita aka yi,da dukkansu suna sume,cire mata bullet din hannunta ya yi,ya kara mata ruwa,bayan ya gama treating din major Marry ne ya koma kan Asmita dake kwance kamar gawa,sosai ya dubata nan ya gane brain dinta ya ɗan tabu, sanadiyyar cocaine din aka dinga dirka mata ba dare ba rana, namiji ma me karfin ƙwaƙwalwa,in ana masa wannan shaƙar dole yamu matsala ɓalle ita mace me karamar ƙwaƙwalwa. Duk wani abinda ze mata ta farfaɗo ya mata a haka suka fita daga clinic din suka koma cikin falo,nan Saghar ya ke sake faɗa masa binciken da ya yi game da brain din Asmita. Gamsuwa da bayanan nashi ya yi,ya ce "is okay dama muna da bukatar sanin duk wani plan dinsu, yarinyar can ta bayar da memory card din, binciken ze zo da sauki,yanzu anjuma ka sanarwar da Jawan da Sudais ina son ganin su". "Okay LTG, yarinyar nan tana buƙatar brain surgery,in kuma ba surgery ba she needs best medication and caring"cewar Saghar,haka suka dinga magana har suka isa part din LTG,a bedroom din Saghar ya koma bacci. Kamar yadda suka saba yau ma haka karfe goma kowa ya fito saboda ya yi breakfast,anty amarya dake kusa da uncle Hameed, ƙa sa da murya ta yi mishi magana "daddyn Asrah dama tun jiya akwai abinda nake so in sanar maka to kuma se nayi bacci da wuri"murmushi uncle Hameed ya yi,ya ce "inajinki" "yanzu de ka bari se mun koma part din mu".ya gyada mata kai. Uncle Hameed ya yi tambayar"ina Sabriyah!?", Rameesa iyayen surutu ta yi saurin faɗin "tana bedroom din ta, uncle ka san ita bata son cin abinci a dinning"girgiza kai uncle Hameed ya yi "wannan ba hujja bane"ya kalli fatime ya ce "je kice mata ina kiranta" "to" ta haura upstairs. LTG shi ya rasa meye matsalarsu da yarinyar kowa maganar ta,shi ba wani son kallon fuskarta yake son yi ba.amma su daga sun zauna se sunyi maganar ta. Saukowa dinning fatime ta yi ga Sabriyah dake bayanta sanye da wando jeans da riga ta yi donot da gashinta a tsakiya, Tsayawa ta yi ta ce "ina kwanan ku"amsawa sukayi.ban da shi da ko ɗago kai be yi ba. Uncle Hameed ya mata nuni da kujera dake gefen anty amarya "daga yau har sanda za ki tafi ki dinga fitowa Muna yin breakfast tare kin ji ko!?",gyada mishi kai ta yi sannan ta zauna, murmushi anty amarya ta mata. Hajiya babba ta ce "yanzu ke ce kika zama cikiton yan matan suka zama guda shida,har na tuna da Asrah da tana nan nasan da yanzu ta damu kowa da surutu", murmushi uncle Hameed ya yi yana tuna irin rigimar da Asrah take yi. "Da yanzu ta na nan nasan da tana gefen LTG ta dameshi da surutu,ko kuma wajen Ammi". Duk murmushi sukayi hatta shi LTG din jin an fara hirar farin cikin rayuwarsa,hakan yasa shi murmusawa. Anty amarya ta maida hawayen da taji yana son fitowa daga idonta,ta ce"nasan da Asrah na nan, da ta ce mommy ki goyani,hhhhhh!ko da yake ma nasan inta girma bazata yi ba,sede shagwabar da ya riga da yabi jikinta daga anyi mata faɗa zata fara kuka tana neman Tajuddeen dinta",duk jikin su ne ya yi sanyi sosai jin yanda muryar anty amarya yake fita. Cikin zolaya dan ya kawar da damuwar kan fuskar anty amarya Saghar ya ce"Abokiyar faɗa ta ba, kullum se munyi faɗa, ga kuma LTG dake shiga mata faɗa, lokacin da LTG ya samu addimission,na yi farin ciki sosai saboda na sa araina in ya tafi zanci zalinta sosai"dariya sukayi gaba dayansu hatta LTG se da ya murmusa.amma babu wanda ya lura da hakan Saboda kansa dake ƙasa yana danna waya. "Yanzu da zan samu ganin yar kanwar tawa zan jata a jiki sosai bazan taɓa barin muyi faɗa ba, ko da kuwa rashin jinta ya zarce na Umaisha da Rameesa"nan ma murmushi suka yi,yau de gaba daya hirar su akan Asrah ne,babu wanda ya saka abinci a bakin shi se hiran da suke yi,duk suna cikin nishadi da kuma kewarta sosai,a duk sanda aka fara hirar Asrah a gidan tofa se sun dau lokaci me tsayi sunayi domin tunawa da ita. Murmushi Zoya ta yi, ta ce "bana manta lokacin da muna yara haka zamuje wajenta dan muyi wasa amma haka zataki binmu se munyi dakyar kafin nan zata yarda". "To kin manta lokacin da mukaje painting room muka dauke zanen da take yi muka gudu a hanya muka yagashi!"cewar umaisha. Ammi ne ta yi dariya"ai yanzu da tana nan kaf dinku da mun aurar da ku "rufe fuska Parsa ta yi tana dariya. Ummah dake gefe ta ce"wato anyi maganar aure kin rufe fuska"dariya sukayi,ganin tana ta dariya. Tun lokacin da suka fara hirar su suna ambaton sunan Asrah ta farajin kanta na wani irin juyawa,a duk lokacin da aka ambaci sunan se taji tsigar jikinta ya tashi ta rasa meyasa hakan,kuma ita tunda tazo gidan bata ga Asrah din da suke magana akai ba 'shin tana ina ne to?' ta jefawa kanta tambaya. Dakyar ta kauda damuwar kan fuskarta ta ce "Ammi to ina Asrah din yanzu take!?". Anty amarya dake gefenta ne ta bata amsa da "Asrah bata a tare damu,bamu san duniyar da take ba ko tana raye ko tana mace!,amma ni a har kullum ina da yakinin tana raye kuma ina jin kusancinta, ina rokon Allah yasa koda a ranar da zan bar duniya ne inga ƴata". tausayi sosai anty amarya ta basu,sun san tana cikin damuwar da ita kadai tasan zafin da take ji. Shuru Sabriyah ta yi jikinta a mace.ashe kowa yana shiga irin wannan damuwar idan ya rasa farin cikin sa,ta dauka ita kadai ce takejin zafin rabuwa da Asmita. Murya a karye ta furta"Nima na shiga irin wannan matsanancin damuwar da tashin hankali a lokacin dana rasa Asmita,kowa yana jin ba daɗi a duk sanda ya rasa wani bari na rayuwarsa". Duk kallonta suka yi cikin jimami,Ammi ta ce"in sha Allah, Allah ze bayyana mana su". Murmushi me ciwo anty amarya ta yi bata iya cewa komai ba. Mikewa LTG ya yi a dinning din ya fice daga Mansion din gaba daya. Bin bayansa da kallo sukayi sun san an fama mishi inda ke mishi ciwo ne yasa ya tashi ba tare da ya yi breakfast din ba. Serving din kowa abinci Fatime ta yi.suks fara breakfast. Tashi ta yi ta zauna a tsakiyar gadon da aka kwantar da ita. ƙarewa wajen kallo ta yi sannan tasa hannu ta fincike ruwan hannunta,tsoro ne yakamata ganin ita daya ce a dakin yasa ta fashe da kuka,kamar karamar yarinya. Fitowa ta yi acikin dakin tana tafiya tana kuka harta iso cikin main part falo,bata dena kukan ba. Cikin yarinta ta soma kiran sunan Sabriyah,tana tura baki . Tana kokarin kai bread bakinta taji kamar murya Asmita ce ke kiranta hakan yasa ta kasa kunne ko zata sake ji, amma shuru hakan yasa tayi tunanin ko imagination da ta saba yi ne,dan haka kullum se ta ji kamar Asmita na kiranta. Ci gaba da breakfast dinta ta yi,da ɗan karfi taji an sa'ke cewa "Sab.....ri....yah". A zabure ta mike tsaye wanda yasa duk seda suka kalleta, tambayar ta Sudais ya yi "Sabriyah lafiya!?". Cikin rawar murya kamar me shirin yin kuka ta ce, "ba kuji kamar ana kirar sunana ba!?,muryar Asmita nakeji"da mamaki suke kallonta amma ɗan son tabbatarwa se suka kasa kunnesu suma,nan sukaji "Sab..ri....yah" tabbas su ma sun ji an kira sunanta,da gudu ta bar dinning din suma miƙewa sukayi suka rufa mata baya. Tana shigowa tsakiyar falon taga Asmita a tsaye se waige_waige take yi da alamar ita take nema,farar fatarta ya yi duhu ga gashin kanta daya hargitse kayan jikinta kansa ya yi datti. Kamar a mafarki take kallon Asmita murya na rawa ta ce"My Jerry"da sauri ta juyo jin muryar Sabriyah,da gudu suka rungume junansu suka fashe da kuka me ban tausayi,sunkuyawa ƙasa sukayi har lokacin suna rungume da juna,shafa bayan Asmita Sabriyah takeyi tana kuka dan tayi matukar kewarta kukan farin ciki, da kuma na kewarta takeyi ga kuma ganin yanda duk ta lalace kamar ba Asmita ba. Dakyar ta dakata da kukan ta ce "my Jerry su waye suka sace ki,ya akayi kika zo nan"a maimakon ta bata amsa se turo baki ta yi "my Tom ba kece kika gudu kika barni ba!,tom muje mu hau lilo kinji"zaro duk idanunta waje ta yi kamar zasu fadi ka sa domin tunda Asmita ta bude baki ta fara magana ta fahimci ba a hankalinta take ba ga yanda take magana kamar wata karamar yarinya me kananun shekaru. Tallafo fuskarta ta yi da duka hannunta biyu ,"my Jerry meyasa kike magana kamar yarinya karama Meye abinda wayan'can mugayen suka Miki!?"oho ita de bata fahimci inda zancen ta ya dosa ba.hakan yasa ta zuba mata ido kafin kuma lokaci daya idanunta ya rufe ta kwanta ajikinta, jijigata Sabriyah ta yi taga bata motsi. Suna tsaye a falon suna kallon su tausayinsu ya cika su,ganin irin shakuwar da ke tsakanin su,dole ne in babu ɗaya,dayan su ya shiga damuwa,ga kuma mamakin abinda ya faru da Asmita suke yi. Kusa dasu Saghar yazo ya tsaya yaga yanda ta daga hankalinta. "Sabriyah ki kwantar da hankalinki!jiya LTG Taj yasa aka kwato ta daga wajen yan ta'adda,ta samu matsalar ƙwaƙwalwa ne ta sanadiyyar shaƙa mata fodar ibilis din da suka dinga yi hakan ne yasa ta samu matsala ,in sha Allah zata warke". " Wani shock Sabriyah taji tunda ga tafin ƙafanta har zuwa tsakiyar kanta,wai Asmita ta samu matsala a kwakwalwarta. Kamar wata wawiya ta ce "matsala a kwakwalwa kuma ya Saghar!?",gyada mata kai ya yi,kuka tasaka tana kallon kyakkyawar fuskar Asmita da ya yi fayau. "Kiyi hakuri Sabriyah wannan kukan bashi da amfani ki mata addu'a kawai tunda Allah yasa Tajuddeen ya sa an kwato ta,ku taimaka mata,a kai Asmita daki"cewar Ammi. Su Umaisha ne suka taimaka mata wajen ɗaukan daukan Asmita suka tafi part dinsu. Zama sukayi a falon uncle Hameed ya ce "gaskiya na tausayawa rayuwar yaran nan duk da bamu san labarin su ba" "ni kaina rayuwar su tausayi yake bani,musamman da Sabriyah ta faɗa mini daga garin da suke". "Tun jiya nakeson sanar da ku abinda ke zuciyata kuma nasan zaku bani goyon baya akan hakan".cewar Anty amarya,maida hankalinsu kanta sukayi domin jin menene take son sanar dasu.iya kan su ne a falon se su Sudais,su Umaisha kuma basa nan. Ci gaba da magana anty amarya ta yi "na yanke shawarar zan yi adopting din Sabriyah in mayar da ita ƴata banason tabar wannan gidan,nayi rashin ƴata Asrah wacce ita ce farin cikina banida damar iya haihuwar wata yar,tunda banida mahaifan daukan wani cikin,tun ranar dana fara ganin Sabriyah naji ta shiga raina, Allah ya daura mini son yarinyar,jinta nakeyi kamar jinina!,kamar ni na tsuguna na haife ta haka nake ji.zan maye gurbinta da Asrah kafin Allah ya bayyana mini ita in rikesu su biyun.zan zame mata uwa da ba ta dashi,zan zame mata duk wani gatan da ta rasa,zan mata komai, makaranta boko da islamiyya". Shuru ne ya biyo bayan,duk sun yi shuru suna nazari akan maganar da ta faɗa,sun san inde ta ɗauki Sabriyah din hakan ze rage mata raɗaɗin da takeji na batan Asrah,kuma inta yi haka zata samu lada. "Mun ji bayanin ki kuma ni kaina,na gamsu da hakan sede ki bari su Abbie su dawo,se mu ji ta bakinsu tunda Kinga sune manya"cewar Hajiya babba,sun gamsu da zancen ta,tunda yaran nan in an barsu sun tafi ruwa zasu sake komawa. "Ohhhhh!wato Abida ta nan ta bullo kenan,dole in samu Hajiya khareema in bata wannan sabon labarin"duk wannan zancen da Ummah take yi a zuciyarta take yinsa. Suna a falon ne nurses guda biyu suka shiga sanye da uniform, Saghar ne ya kira su domin kula da Asmita shi bayi da wani isheshen lokaci. Kallon kaltume Saghar ya yi ya ce"please kaltume dan rakasu dakin Sabriyah mana". Bismillah ta musu ta yi gaba su kuma suka biyo ta abaya.dakin suka shiga nan suka samu Asmita dake a sume,ga Sabriyah a gefenta ta zuba mata idanu tana kallon ta ga tausayinta fal ranta,tama rasa ya zatayi,ji takeyi dama matsalar ƙwaƙwalwar ya dawo kanta. Gabatar mata da kansu sukayi ,su ka sheda mata sune masu bawa Asmita kulawa,ta yi murna sosai duk dama ita dayanta za ta iya kulawa da Jerry dinta.a zuciyarta kam mamaki ya kasa dena mata,a ce LTG ne ya ceto Asmita,batasan da wani irin baki zatayi amfani wajen gode masa ba. Dan Allah ki dan bamu waje zamu dubata ba dan ranta yaso ba haka ta fita ta basu guri. Ruwan Allura dayar nurse din ta ja a syringe,ta je gaban Asmita ta tsaya tana jan hannun rigarta kasa zata mata,kamar wacce tasan allura za'a mata ta mike da sauri ta ɓige hannunta,ta koma can kuriyar gado ta manne tana kuka,duk iya kokarin su na ganin sun rike Asmita su mata allurar amma abin ya ci tura,saukowa ta yi da gudu zata bar dakin taga Mutum a tsaye a bakin kofar, faɗawa jikinsa ta yi ta rungume shi gam kamar zata koma Cikinsa. "Banaso!banso!banaso!,ka ce musu kar su mini banason allurar can".,a hankali yake kokarin rabata da jikinsa amma ta ƙi sake shi ga kukan da takeyi,dama ya yi tunanin hakan ze iya faruwa shisa ya biyo bayansu.dede kunnanta ya ce"kyalesu duk se na musu duka, ni da kaina zan yi miki allurar kinji,daga nan se in daukeki ke da Sabriyah muje wajen lilo,da kuma shan ice cream bayan nan se in siya miki biscuits da minti ko".cikin ƙaguwa ta ce "yeeeeeeeh!kuma ma kaima ai zaka hau lilo din ko!?",ta tambaye shi tana kyalkyalewa da dariyar murna, gyada mata kai ya yi,bata ga hakan ba domin tana rungume a jikinshi,kuka ta sa'ke sawa tana bubbuga ƙafafunta,dafe kai ya yi yau yaga ta kanshi,cikin nutsuwa da magana me dad'i wa patient ya ce "Meye kuma Asmee?", "To ai ba kace zaka hau lilo din ba!",ba shi ba hatta nurses dake kallonsu seda su kayi dariya jin maganarta. "Eh mana ni zan kai ku,dukkanmu zamu hau lilo kowa ma ze hau, shikenan!?"raba jikinta da nashi ta yi tana kallon shi, ta tafa hannu ta fara tsalle_tsalle,juyawa wajen su nurses din ta kallesu tana musu gwalo,ta ce"bazaku hau lilo baaaaaaaa!"dariya kawai suka yi mata,rike hannunta ya yi ya kaita bakin gadon ya zaunar da ita. "Doctor Saghar!ta ƙi yarda muyi mata allurar". "Karku damu zan mata da kaina"Saghar ya faɗa yana sunkuyawa a gabanta,hannu yasa cikin aljihun wandon sa ya fito da chocolate diary milk,ya mika mata,karba ta yi tana washe baki, ba tare da bata lokaci ba ta bare ledar chocolate din ta fara sha tana lumlumshe ido,cikin dabara ya karbi allurar a hannun dayar nurse din,ya ɗan zagaya ta bayanta ya mata shi,tana shan chocolate dinta ta yi dama_dama da bakinta da chocolate batama san ya mata allurar ba. Doctor Saghar na matukar burgesu ya kware sosai akan aikinsa, kwararren doctor ne da ake ji dashi,in yana gaban patient dinsa zakayi tunanin ko a gaban kanwarsa yake,yanda yake maida kansa kamar karamin yaro, musamman in yaje duba patient din da suka kasance yara ko kuma masu matsala irinta Asmita, ya nada saukin kai da kuma zolaya,amma wani lokacin bayason magana. Miƙewa ya yi ze bar dakin da sauri ta riƙo bayan rigarsa ta shagwaba fuska, kallonta ya yi yaga yanda ta yi da fuska. "Dan bika ka ji?" "Ah ah ki bari yanzu zakiyi wanka ki sa kaya masu kyau se ki bini kinji!?, Kinga kayan jikinki sun yi datti"kallon kayan jikintan ta yi taga sunyi dattin,turo baki ta yi "to karka gudu"gyada kai ya yi sannan ya fice a dakin,dede ze bar part din nasu ya hadu da Sabriyah dake shigowa. "Ya Saghar yana ganka anan?" "Asmee taki yarda nurse din su mata allurar shine na yi mata da kaina"murmushi ta yi "okay nagane"har ta juya zata shiga,ya kira sunanta dawuwa ta yi ta tsaya tana kallonsa. "Ki bi ta aduk yanda tazo tunda Kinga ba'a hankalinta take ba, kwakwalwarta ya koma na yarinya me shekara takwas a duniya,ki bita a hakan se mun fi samun saukin komai,karki yi kokarin tuna mata abubuwan da suka faru, hakan ze sa ta fara ganin flash wanda hakan zesa ta koma wata matsalar kuma daban.shi wannan matsalar nata baya bukatar gaggawa,kulawa da kuma magani masu kyau da manyan allurai take bukata.zan turo mata da chocolate anjuma". "Shikenan ya Saghar zan kiyaye"a haka suka rabu shi ya fice ita kuma ta shiga bedroom din,samun Asmita ta yi zaune a tsakiyar gado daga ita se towel a daure. Tsayawa kawai ta yi,tana kallonta har yanzu mamaki be fita a ranta ba,wai yau Asmita ce, a haka kai gaskiya rayuwa abar tsoro ne. "My Jerry waya baki chocolate!?"ta mata tambaya tana zama a gefenta. Washe baki Asmita ta yi seda ta ɗan yi jim kamar wata me tunani can kuma ta ce "me kyau ne yabani"dariya ta yi wato Saghar din ne me kyau,hmm lallai kam gaskiya ta faɗa domin gaba daya mazajen gidan suna da matukar kyau me tafiya da hankali uwa uba suna shigen kama da juna,haka yan matan ma. Surutu Asmita take ta mata,ita a hakan wai labari take bayarwa,wani maganar dakyar Sabriyah take ganewa. Wanka masu kula da ita suka mata,suka shiryata cikin dogon riga na material ɗinkin play,ta yi kyau sosai duk da akwai rama a tare da ita, dankwali za'a daura mata,ta da ka tsalle tace bata san zancen ba,ita sede a raba gashinta gida biyu a mata fakin haka kuwa sukayi mata da dogon gashinta. Su Rameesa ne suka shigo dakin su hudu,banda Zoya dake part din Ammuh.iklas hannunta na dauke da abincin da Ammi ta turo ma Asmitan. "Hi! Asmita yakike?"su ka faɗa tare, tana kwance ta yi filo da cinyar Sabriyah,dago kai ta yi tana kallon su,ta kuma ƙi musu magana,"my Tom inyi musu magana!?"ta tambayi Sabriyah,gyada mata kai ta yi. "Ku ma zakuje lilo din ne!?,ni an min wanka an yi mini kwalliya ma na shirya me kyau nake jira" "eh mana duk zamuje, yanzu ki fara cin abinci tukun nan"Iklas ta yi magana tana buɗe mata plat din abincin,chips ne da miyar hanta se soyayyen kwai. Maƙe kafaƙa ta yi alamar bazata ci ba,rike hannunta Sabriyah ta yi tana shagwabe fuska itama"to shikenan karki ci din,ni kuma bazan je lilo din ba tunda abin hakane"da sauri ta jawo plat gabanta dan bataso Sabriyah ta ce bazata je ba,"yauwwa ko kefa"ta faɗa tana fara bata abincin abaki,su Umaisha bakaramin burgesu sukayi ba,duk da ya kasance Asmita bata cikin hankalinta amma kaunar dake tsakanin su be gushe a wajenta ba,tana bata abinci abaki tana yi mata hira,suna dariya. Tayasu hira sukayi har lokacin sallah Azhar ya yi suka tashi suje suyi. Ya yi saura su biyu a dakin nurses dinma sun fita, Asmita bacci ya dauke ta,in ta ga Asmita sanyi takeji a ranta,yanzu mutane biyu ne ya yi saura ta ji halin da suke ciki, kwana biyun nan tana yawan mafarkin anty Teema tana ce mata yaushe zata dawo se in tana kokarin bata amsa se ta farka. Se kuma Fu'ad da batama san ta ina zata fara binciko shi ba,fatan ta ɗaya shine Allah yasa yana cikin koshin lafiya.wayarta yana a dakin su na afafa,lokacin da suka fito ita da Asmita zuwa wajen Taheer, basu fito da wayoyinsu ba,ga shi bata rike number Fu'ad akanta ba ɓalle ta kirashi. Kano state Falo ne me girma,me kyawun tsari gwanin burgewa, mutane uku ne a ciki biyu mata se na miji guda daya, dayar macen Mahaifiyar namijin da macen ne saboda kamar da sukeyi. Fuskanta dauke da tarin damuwowi dan banace damuwa daya ba,ta kalli na mijin gabanta ta ce "Taheer har yanzu shuru babu labarin ya'yanku Lameer, shikenan ya bata kenan?, shikenan yanzu a kasar nan daga ka zama me gaskiya da riko da amana se anyi kokari an ga bayan ka?,sun salwantar da rayuwar Lameer". Taheer shuru ya yi yana sauraran hajiyar ta su,tun lokacin da babban ya'yansu Barrister Lameer ya bata suke cikin wani hali na rashinsa,sun neme shi har sun gaji amma shuru babu labarin sa. "Hajiya ni abun daure mini kai yake yi,su waye suke neman kashe ya Lameer,meye abinda suke bukata a tare dashi, gaskiya duniya yanzu babu gaskiya.ranar da mukayi waya dashi na ƙarshe shine ranar da ya ce min yana Lagos na yi farin ciki sosai da jin haka nan nima nake sanar dashi ina Lagos, se ya ce mu haɗu a wani restaurant akwai abinda yake so mu tattauna.mun gama waya dashi se nazo wajen yarinyar danake baku labarin inason in aureta, Asmita,ban bata lokaci a gun nata ba, na koma a hanyata na ta kiran wayarsa baya shiga har izuwa rana me kama ta yau babu labarin ya Lameer". Yana magana ne cikin muryar me ban tausayi,domin shi da dan uwansa akwai shakuwa me karfin gaske,wasu ma har tunanin yan biyu ne su,komai din su tare aikine kawai kowa da irin nasa, Lameer lawya ne,shi kuma Taheer pilot ne,matukin jirgin sama. Yar karamar kanwarsu me suna yusra, kyakyawa da ita daga ganin ta bazata wuce 17 yrs ba, ta yi tagumi tana kallon Hajiyar tasu da ya'yanta,dama tun can ita ba gwanar magana bace,da wannan abun ya sake faruwa kuma se ta sake zama shuru_shuru. Hajiya ta ce"ya lamarin Asmitar da kake magana an sameta ne!?" "Ah ah Hajiya itama shuru"girgiza kai ta yi,jim kaɗan kuma ta furta"Sunan budurwar kan nan in naji se na tuna da kanwarka" "Nima haka Hajiya". Katsina state Yau de Allah ya yi wa Hajjatiye ikon zuwa Nigeria,tana gidan mom Rumanatu,tunda ta zo ta sasu agaba se de su wuce Maiduguri ita ba zata iya zama anan ba, Abu Sufyan ne ya samu ya shawo kanta ta yarda kan cewa gobe da safe zasu tafi dama jiran su Abbie suke yi su dawo kuma su din ma yau da rana Flight din su ze yi landing. Iftisan ba wani shiri suke yi da Hajjatiye ba,ba ta ma zama kusa da ita,domin inta zauna kusa da Hajjatiye tas take kare mata zagi bata rage mata, Jaleelah ce yar gaban goshinta. Saukowa Ashman ya yi cikin shirin zuwa wajen aiki ya tadda su zaune a falo,gaida su ya yi yasa kai yafita,rike haɓa Hajjatiye ta yi ta kalli mom Rumanatu,"nikam Rumanatu wa'yannan sabga_sabgan balagaggun kam me kuke nufi da har yanzu baku musu aure ba!?,ki duba yaron nan da ya kamata ace yanzu yana da mata biyu yara takwas amma ace yana nan yana yawo fikau fiyau ba mata!"gyara zama mom Rumanatu ta yi ta soma magana"to Hajjatiye ya za muyi dasu yaran nan sunki maganar aure kwata_kwata,ko jiya seda mukayi wannan maganar nida ya'ya Isma'il,haka su Tajuddeen din ma shuru babu wacce yake da budurwa balle a yi maganar su dedeta maganar aure". Gyara daurin dankwalin kanta da ta tokaro shi gaba ta yi, ta ce"ai duk ku kuka sangarta su, haba wannan abun kunya ne yara daga masu shekara ashirin da bakwai se zuwa da takwas amma a ce ba sa maganar auren to kode basu da lafiya ne!?,in yaso ni da kaina zan samo musu maganin karfin mazantaka ne!?,yoooo ina dalili,ga yaran matan ma duk sun balaga kalli kirjin yaran nan naki duk ya gama cika da kirgen dangi,har ya fara kwanciya basuyi aure ba". Hajjatiye ce ke magana amma mom Rumanatu ce take jin kunya dama Hajjatiye ita babu ruwanta ko a gaban waye duk maganar da yazo bakinta se ta fadeta sede ta barka da jin kunya,dan ma Allah yasa su Jaleelah duk suna bedroom din su. "Shikenan Hajjatiye gobe de in mun je Maiduguri se a yi maganar". Haka ta tashi ta shiga kitchen ta yi mata abincin da takeso da kanta. "Kasan yanda rayuwar su yake da mahimmanci a wajena kuwa!?,kasan yanda nakeson su ne?, dalilin son da nakeyiwa Sabriyah yasa na fara kaunar Asmita jinta nakeyi kamar kanwata,da nace ku sace ta,ta baku memory in kuma baya wajanta ku sa ta ta faɗa muku a inda yake, bawai ku kusan kasheta da cocaine ba,common yanda zaku yi aikin kuma baku sani ba,bayan kunyi laifin nan kuka bari har sojojin Tajuddeen suka gano inda kuke suka kai muku hari, kun cancanci tukuici daga wajena saboda babu wanda yake wargaza mini shirina ban bashi tukuici ba"Fu'ad ne agaban Samuel da kuma dayan da suka kamo Asmita su kadai ne suka tsira daga farmakin da su major Marry suka kai musu,nan take suka zo wajen Fu'ad din. Magana yake musu yana nuna su da bindiga daga ganinsa kasan ranshi ya yi muguwar ɓaci,har kamanin sa ya sauya ya koma boss,bazaka ce shi ne wannan Fu'ad da Asmita da Sabriyah suke yabo ba,wannan kamilin Fu'ad,bawan Allah da babu ruwansa. A kirji ya harbi dukkansu biyu suka fadi a mace.durkusawa ya yi, ya dangwali jinin Samuel da hannu ya shinshina a hancin sa,wani irin nannauyan ajiyar zuciya ya sauke,yana jijiga kansa cikin nishadi miƙewa ya yi, ya fara rawa a wajen kamar mazari lokaci daya kuma ya dakata ya nutsu,ya sauya fuska izuwa abin tausayi kamar mutumin kirki, Sunkuyar da kanshi ƙasa ya yi "yanzu shikenan kun mutu!?,bazaku taɓa dawuwa ba,ahhhhhh! babu abinda yakai jini kamshi,inajin dadi da tsintar kaina a farin ciki a duk lokacin da naga ina kashe mutane kururuwar neman taimako da kuma ganin zallan tsoro a cikin ƙwayar idon su yana ƙarfafa mini guiwa"ya yi maganar yana wani juyi. Ya sa'ke cewa"my Sabriyah karki damu ina nan zuwa gareki,ke din tawa ce,zanyi faɗa da kowa domin ganin na kwato ki,my Sabriyah da taimakon ki zan ga bayan lieutenant general Tajuddeen Bishara"ya gama maganar yana kecewa da mahaukaciyar dariya. Tabbas Fu'ad cikekken hatsabibin mutum ne da gane inda ya dosa se Allah da kuma mutum wanda ya fisa kaifin basira,ya wuce duk tunanin me tunani, yana da fuskokin da bazakayi tunanin ze iya yin muguwar muguntar da yake aikatawa ba,in ya juya mutumin kirki zakayi tunanin wani malami ne wanda yasan Allah yasan addini,amma in ya koma hatsabibinsa to ko shedan haka ya ganshi ya barsa,duk wanda ya shiga tarkon Fu'ad tofa sede ya yi addu'ar Allah ya kwacesa daga sharrinsa shine kawai. Barin dajin ya yi ya fito bakin titi nan ya samu napep ya tara. Shirye_shirye da girke_girke ake yi sosai na tarban su Abbie, family kowa yazo an hallara. Anty sakeena da anty Sameera sun zo da yaran su,haka ya Abbas,ya Hafiz,ya Ahmad duk sun zo da familynsu gwanin ban sha'awa.kowa yana gida mazan ne suka tafi airport dauko su. Umaisha ce ta sauko tana neman Jawan Ammie ta sa ta kira mata shi zata bashi sako,duddubawa ta yi bata ganshi ba ta tambayi matar Ya Abbas ina yake,nan take ce mata ai duk sun tafi dauko Abbie,"okay"ta ce mata sannan da sauri ta nufi part din LTG. Seda ta shiga sannan ta yi sallama knocking ta yi a bedroom dinsa.izinin shigowa ya bata,da sauri ta shigo ta matso kusa da shi,"ya Taj Ammi ce ta ce in kiraka" "okay ina zuwa"ficewa ta yi ta barsa,bin bayanta ya yi kusan a tare suka shiga part din Ammi ,samunta sukayi ta gama shiryawa cikin dakakkiyar less,ta yi kyau sosai tsantsan kamaninta ya sake fitowa da LTG da Jawan da kuma Umaisha,anty Sameera ta fi kama da Abbie sosai.murmushi ya sakar mata ta yi masa kyau sosai da yasa ya gagara boye farin cikinsa. "Tajuddeen,dama tambayarka zanyi ko Sabriyah ta baka labarinta!?".nan take mood din fuskarsa ya sauya jin sunan da ta ambato mishi. da yasan akan wannan abun take neman sa,da babu abinda ze kawo shi,shi meye hadin shi da ita da zeji wani banzan labarinta da babu komai a ciki se karuwanci da fitsara,ko da kusa dashi bayason yaganta,shi mutum ne da ya tsani yaga karuwai na shawagi hakan yasa a USA kaff seda ya rufe gidan karuwan da suke can ya tsani abinda suke aikatawa hasalima shi kyamar su yake yi. Cike da bakin ciki yake kallo Ammi ya ma rasa ya zeyi can de ya ce"please Ammi karki sake mini magana akanta"yana gama fadin hakan ya juya ya bar part din nata, yana tafiya shi kadai se tsaki yake yi kamar tsaka,dole ne ma daga zaran an gamawa dayar treatment dinta ta warke ze koresu su bar gidan,baze iya jure ganin shige da ficen ta a gidan ba. Tana sauri batasan waye agabanta ba ta ji ta buge shi,ja baya ta yi tana kallon sa, haɗe fuska ta yi tana kokarin wucewa hannu yasa ya jawota da karfi seda ta ji kamar hannunta ze fice daga jikinta. Hannu ya sa ya damki gashinta, ƙara tasa"ka sa'ke ni,akwai zafi!mugu kawai azzalumi kai baka da wani aiki se mugunta"tunzurashi kalmar mugu da ta kirasa dashi ya yi,runtse idonsa da ya yi ja lokaci daya.ya dunkule hannunsa,jijiyar hannunsa ya fito rudu_rudu,da wannan hannun nasa in yakai mata naushi to sede a haifi wata amma ita kam bazata rayu ba,duk namijin da ya yiwa naushi da wannan hannun nasa, tofa sede gawa,wurgi ya yi da ita ta faɗa hannun uncle Hameed da tun haurowan shi ya ga abinda yake faruwa gudun kar a yi bacecciya ne yasa da hanzari ya iso upstairs din,kuma ya yi dede da wurga Sabriyah da LTG ya yi, Allah ya bashi ikon rikota ta faɗo hannunsa,sannu ya yi mata yana duba ko ta ji ciwo ajikinta. Bin bayan LTG da tun lokacin da ya wurgata ko juyowa beyi ba, balle yasan wani hali take,ya yi tafiyar sa, girgiza kai kawai uncle Hameed ya yi,ya dagata ta mike. "Sannu kinji!?"gyada masa kai ta yi tana riƙe kanta da taji yafara mata ciwo, saboda damƙar da ya yi wa gashin bana wasa bane ko lokacin da boss lady take damƙar mata gashinta bata jin wannan azaban domin ya ninka na boss lady sau dubu. Fahimtar da kanta yana mata ciwo ne yasa uncle Hameed jan hannunta zuwa kan kujerar ya zaunar da ita sannan ya kama kan nata yana mata addu'a. Sa'ke kan ya yi ya ce "yanzu ya kike ji!?" "Da sauki uncle" "ki dena shiga lamarin Tajuddeen kin gan sa baya wasa da yara ko kadan,zan iya cewa tunda nasan shi da yarinya daya nasan ya yi rayuwa me tsayi yana wasa da ita harda dariya,kuma in kinji yana dogon magana to da ita ne.shi mutum ne me murɗaɗɗen hali,a hakan ma yanzu mun samu ya sauko,se de addu'a"ya karasa maganar yana yar dariya. Tunda ya fara magana take kallon shi haɗa ido sukayi,ta yi saurin sunkuyar da idonta. Camly cikin wani irin yanayin son jin wata yarinya ce LTG yake so haka da yiwa magana da wasa ta ce"amma uncle wata yarinya ce haka!?",ya ce "Asrah!ita ce farin cikin Tajuddeen yana sonta sosai yarinyar da yake da burin aure in ta girma,so ne me karfin gaske a tsakanin su".jikinta ne yafara rawa ta rasa dalilin da yasa duk sanda aka ambaci sunan Asrah se taji tsigar jikinta ya tashi,Wannan shine karo na biyu da taji wanann sunan a yau yanzu jikinta rawa yake yi.da mamaki uncle Hameed ya kalleta ya ce"Sabriyah lafiya ko de baki da lafiya ne!?"yana taɓa wuyanta ya ji ko zazzaɓi ne amma jikin babu alamar zazzaɓi.rasa amsar da zata bashi ne yasa kawai ta ce"babu komai uncle". "Kin tabbata?"ya tambayeta yana kallon ta,gyada masa kai ta yi. "Ya jikin yar uwar taki ta samu bacci ko?",nan ma gyada masa kai ta yi, murmushi kawai uncle Hameed yake aikinyi,be san meyasa inde yarinyar tana a tare dashi se yaji kamar yana tare da yarsa ta cikinsa wacce ya haifa,se yaji yana sha'awar ya ta janta da hira. Bude baki ya yi da niyar yin wata maganar ya ji horns din motoci sun shigo gidan, murmushi ya yi,ya ce "madallah sun dawo kenan,tashi muje ki rakani tarbo baƙi"bata iya masa musu haka ta mike yana rike da hannunta suka sauko main part,da mamaki matan su ya Abbas suke kallon uncle Hameed da yarinyar da yake tare da ita suna tambayar kansu wannan kuma wacece kuma daga ina?,maye hadin ta da uncle Hameed da har yake rike mata hannu baya tsoron matarsa ta gansu?,Ammuh da mugun kallo ta bisu har suka fice, tana me aiyana abubuwa aranta kallo ɗaya tayiwa Sabriyah tun zuwanta gidan ta ji ta washi yarinyar ta tsaneta,se kuma labarin da ummah ta kai mata wai anty amarya tana son adopting dinta ta zama yarinyarta,dole ne ma tasan yanda zata yi ta kora Sabriyah ta bar gidan. Fitowa waje sukayi shi da ita suka tsaya suna jiran su abbu su fito daga motar.bubbude musu akayi suka fito,sauka idon Abbie da abbu ya yi akan uncle Hameed dake tsaye riƙe da hannun Sabriyah,basu yi mamaki ba saboda duk tunanin bakuwarsu ce,kila acikin surkansu ne wata tazo da ita. su ya Ahmad suma suna mamakin wannan bakuwar fuskar da suka gani, cike da farin ciki suka rungume juna uncle Hameed na musu sannu da zuwa,raba jikinsu Abbie ya yi yana kallon Sabriyah dake tsaye a gefen su sanye da riga da wandon jeans babu ko dankwali a kanta. Kallonta ya yi sannan ya kalli uncle Hameed "Hameed Wannan yarinyar fa?,yar waye!?"abinda Abbu yake shirin tambayarsa kenan se Abbie ya rigasa.shima uncle Hameed din kallonta ya yi cikin zolaya ya ce "ƴata ce"da alamar tambaya suke kallon shi cikin tuhuma.dariya uncle Hameed ya yi ganin irin kallon da suke binsa dashi ya ce"just kidding!, bakuwarmu ce, shikenan?",dariya suma sukayi. "Yarinya ya sunanki!?"Abbie ya tambayeta" "Sabriyah"ta basa amsa cike da kunyar da bata san tana dashi ba. Murmushi Abbie da abbu sukayi. Kafin ya sake cewa"to Sabriyah ina dankwalin ki!?ba ki san babu kyau yawo babu dankwali ba!?"girgiza mishi kai ta yi alamar bata sani ba,kallon juna abbu da Abbie sukayi,katse zancen Saghar ya yi,ta hanyar faɗin"Abbie mu karasa ciki".shiga ciki sukayi ,kafin su zauna su Rameesa suka zo dukkansu suna musu oyoyo,yanda su duka suka kam kame abbu da Abbie ne yabawa mutanen falon dariya. Abbie ya shafa kansu"oyoyo!yan matan Abbie"cikin shagwaba Parsa ta ce "munyi missing din ku sosai kunje kun daɗe" "we missed you too masoyiya,yanzu kam ai mun dawo". Zama sukayi gaba dayansu,ana faman gaishe da su Abbie da kuma yi musu sannu da hanya,ganin sun shiga rububi ne yasa Sabriyah ta fece zuwa dakinsu.ita bata cusa kanta cikin abun familyn duk da familyn na burgeta sosai yanda suke da son junansu da girmamawa. Shigowa dakin ta yi ta ga wayam babu Asmita da tabarta akan gado tana bacci dubata ta yi a toilet nan ma wayam bata nan shiga dakunansu Umaisha ta yi nan ma bata ganta ba.hankalinta ya tashi tafara tunanin ina Asmita kuma ta shiga daga ɗan fitan ta da ta yi din nan. Book one ya kusa karewa remain some few pages,na yi wa mutane 20 na farko discount din 200,zasu biya 300 kenan.idan mutum ashirin na farko suka gama biya ze koma 500 domin wannan shine standard price dinshi.luckiest 20 people ku hanzarta biyan naku.😍😍😍😍😍💝 Comment,share and like. *🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹* Page 23&24 *_Story & written_* By *MRS🌹ISHAM🌹* ( Yar lelen Jarumai) *THE WRITER OF 🖋️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️ Page 23&24 Da gudu_gudu ta fito daga part din tsaban ta rude ma bata san wani part ta shiga ba, ita de tasan neman Asmita take yi,a tsawace ta ce "ke meya kawo ki nan!?,za kizo ki shafa min najasa ko to fice tun kafin na lahira yafiki jin dadi"mugun kallo ta watsawa Ammuh,"Mtsssw!ni in banda tsautsayi meze kawani wajen ki,je kiji da matsalar dake gabanki tsohuwar banza kawai"a harzuke ta kai hannu zata mare ta, tayi gaggawar rike hannunta ta ce "Wallahi ko a mafarki ki ka ga kin mareni to kiyi gaggawan tashi daga wannan mafarki domin murde hannunki zan yi ya koma baya,babu ruwana da girmanki,ki kalli cikin kwayar idon nan tawa in kinga kunya a ciki, to ki dau mataki akaina,yanda kika tsane ni ,haka na tsaneki kuma ina da tabbacin nawa ya ninka naki"ta sake mata hannu ta fice dan neman Asmita ne a gabanta bata da lokacin ɓatawa. Suman tsaye Ammuh ta yi tana ta nanata maganar da Sabriyah ta gaya mata,ji take kamar an watsa mata garwashi a kirji,lallai dole ne ta dau mataki akanta saboda taga alama yarinya nan in ta samu guri zatayi abinda yafi haka.kwafa ta yi "za ki shiga hannu". Ta duddubata a bangaren sama bata ganta ba hakan yasa bata da wani zabi da yawuce ta dawo downstairs. Kusan yawanci ma basa nan,matar ya Hafiz ce a falon se Zoya da kuma yara. Bata tambayi ko daya daga cikinsu ba. da taga de bata falon kawai ta fita,a waje ne ta tambayi securities ko sunganta,dayan su ne ya sanar da ita tana garden ,yana gama faɗa mata ta nufi garden din da sauri,tun kafin ta iso ta hangota zaune akan lilo dake cikin wajen.girgiza kai ta yi, ta karasa wajenta ta baya batare da tasani ba ta rike lilo ya tsaya ,juyawa ta yi tana ɓata fuska "my Tom ki bar mini lilo na" "Asmita meyasa kika baro can ki ka barni ina ta nemanki gaba daya hankalina ya tashi,banason sa'ke rasaki a karo na biyu". Tasan abu ne ma wuyaci ta fahimci me take nufi.hakan ya sa ta ci gaba da turata a lilon,ita kuma tana dariyar farin ciki,haka suka kwashe mintuna Ashirin a haka. Dakatawa Sabriyah ta yi,gaba daya ta gaji tana riƙe ciki ta ce"My Jerry zo mu tafi se anjuma mu dawo ko?",gyada mata kai ta yi ta sauko akan lilon.ta rike hannunta suka bar garden din suka koma ciki. Muryar Ammi sukaji tana musu magana ."Sabriyah kuzo ku nan dama ku nake nema"karasawa wajenta sukayi ,kallon Asmita Ammi ta yi kafin ta maida kallon ta kan Sabriyah "tun dazun!,su Rameesa suke neman ku,Abbie yabada naku tsaraban abaku,ki dena yawo da wannan kayan sun matse miki jiki sosai Zoya ta faɗa mini cewa duk kayan da aka kai miki rage su kikeyi.nasan baki saba sa irin wa'yannan kayan ba amma ki daure ki dinga sawa ke macece,mace kuma an santa da kamun kai da kunya ,suturta jikinta"shuru Sabriyah ta yi,jikinta ya yi sanyi ba'a taba tsayar da ita an faɗa mata haka ba. Murmushi karfin hali ta yi wanda kana gani kasan cewa be kai zuciya ba"Ammi!,na taso ne a inda babu me ce mini dede nakeyi ko kuma akasin haka, wa'yannan kaya masu nauyi kuma ban saba da su ba bana iya samun nutsuwa a cikinsu.Ammi yanda nake rayuwata bazance inajin dad'i ba kuma ba zance banajin dad'i ba".sosai Ammi take kallon idon Sabriyah domin iya gaskiyar ta take gani, tabbas an yiwa rayuwar yaran nan illa me muni ma kuwa. "Bakomai Nasan in kina tare damu duk za ki saɓa da hakan"gyada kai kawai ta yi,ta ja hannun Asmita dake wasa da flowers din kan table.da tun tsayawar da Sabriyah ta yi wajen Ammi ita kuma ta tsuguna ta fara wasanta. Suna haurawa stairs Asmita ta ce "my Tom" "uhmm" "Ni banga me kyau ba ina yaje,nayi lilo shi be yi ba"bata amsa mata ba, suna ci gaba da tafiya ne ta ce"yau yana aiyuka sosai,ba zaki samu ganinsa ba"bata rai ta yi da alamu bata ji dadin maganar Sabriyah ba,ita tana son ganin me kyau suje su yi lilo kuma ya bata chocolate. Har suka shiga daki bata sake magana ba se da Sabriyah ta ce "my Jerry ki dena fita batare da nasani ba,kina tsorata ni in naga bakya nan,kinji ko"gyada mata kai ta yi alamar "to". Wanka ta shiga tayi yau duk bata samu ta sake yin wani wankan ba,tun na safe da ta yi ga shi yanzu har yamma ya yi. Bayan ta fito daga wanka ta bude wardrobe din kayan kallon kayan da aka saka musu, ita da Asmita zuba musu ido ta yi tana tunanin wanne zata ɗauka,ga maganar Ammi da taji yana mata yawo a tsakar ka. Runtse ido ta yi tasa hannu ta dauko wando falazo da riga.sakawa ta yi ta gyara gashinta kawai ko mai bata shafa ba. Hawa gadon ta yi wajen Asmita da ta kwanta kamar me bacci amma idon ta biyu ta zubawa bango ido. "My Jerry tashi kiyi wanka"maƙe kafada ta yi,"yi hakuri shalelena tashi kiyi wanka kinga dare ya kusan yi, sa'ke make kafadar ta yi. Dafa goshi ta yi"haba my Tom ki tashi mana meyasa kike da taurin kai ne ?,"da karfi ta ce"banason wankan banaso "ta yi maganar tana bubbuga ƙafafunta akan gado,tuna maganar da Saghar ya gaya mata yasa ta kyaleta domin ya ce bata da buƙatar a dinga takura mata, lallabata yakamata a dinga yi. Ya Abbas suna falon Abbie ana hira, matansu kuma suna wajen su Ammi suma. "Tajuddeen be san mun dawo bane?"Abbie ya tambayi Sudais dake zaune kusa dashi. "Ehh gaskiya ba lallai ne yasan kun dawo ba"ya basa amsa. "Shikenan ni zanje ai in same shi". Se da aka kira sunan Tajuddeen ne ma Saghar ya tuna da ya sanar dashi cewa yana son ganin sa da, Sudais da kuma Jawan. Taɓa Jawan ya yi "kaga na manta ko, LTG ya ce yana son magana da mu, da ya Sudais". "Shikenan se dare se muje "cewar Sudais. Abbie yana matukar son ganin Tajuddeen se zuba ido yake yi ko ze zo amma shuru babu ko alamar sa,ana hirar ma shuru kawai ya yi burinsa kawai yaga Tajuddeen yazo masa sannu da zuwa ya rungumesa,amma tunda yaga har zuwa yanzu be zo ba tofa baze zo din ba. "Yawwa nikam Hameed yarinyar waye naganku tare dazun!?"Abbu da ya kasa hakuri ya sa'ke tambayar uncle Hameed. "Ita ce wannan yarinyar da Tajuddeen ya kawota gidan nan yana bincike akanta". "Ikon Allah, lokacin da kuka tsaya tare se tayi kamar ƴarka"abbu sake faɗa domin shi yaga kamar Sabriyah da uncle Hameed. Dariya kawai suka yi. Saghar da ya manta da allurar Asmita da zeje ya mata, seda a ka kira sunan Sabriyah ne ya tuna da ze mata allura. Gyaran murya Abbie ya yi sannan ya soma magana "gobe Hajjatiye zata zo,kun san Allah wanin ku ya kuskura ya ɓatawa uwarmu rai tofa ba babu ruwana da girman da kukayi jikin ku ze baku labarin shekaru sha daya da yawuce tam"yar darawa sukayi, Ahmed ya ce"duk sanda Hajjatiye zata zo se anyi mana warning yanzu fa mun girma yakamata a dena maimaita mana Abbie ". Cikin harshen shuwa abbu yace"da yafi muku". Yaron ya Hafiz ne ya shigo dan shekara biyar hannunsa rike da bindigar wasa,ya zauna a kusa da Abbie"ah ah Ameer kar de mu za'a harbe da bindigar nan"Abbie ya tambaye sa cikin wasa, maganar cike da gwaranci irin na yara ya ce "nooo!terrost za'a halbe ko kaka"dukkansu dariya sukayi,"naga alama babanninka Tajuddeen ko Sudais ko kuma Jawan zaka ga'do "uncle Hameed ya faɗa yana shafo kan Ameer dake wasa shi da bindiga. Sosai suka sha hira,ganin har lokacin LTG be shigo bane yasa Sudais ya kirasa,3missed calls ya mishi amma beyi picking ba daga karshe ya turo mishi da text,bude sakon da LTG ya turo masa ya yi. "Bro!call you back,am in important meeting right now can't talk". Murmushi Sudais ya yi,shi dama yasan zeyi wuya in LTG na gidan. Shima ya rubuta mishi message kamar haka. "Okay,Kayi sauri ka dawo Abbie is eager to see you". Har bayan 5mint bayi mishi reply,yasan yaga message din. "Abbie LTG baya gida yana meeting shisa ka ji shi shuru"Sudais ya faɗa masa,se yanxu yaji sanyi a ranshi,domin tunda suka dawo yakeson ganin sa it has been a while rabon da ya gansa. "Ammi Tajuddeen fa tunda nazo ban ganshi ba"Anty Sameera ta tambaya,anty sakeena dake sawa karamin ɗanta pampas ta ce"Nima abinda nakeson tambaya kenan,ko baya nan ne" "ehh ya fita,nikam bazaku koma gidajenku bane dare fa yanayi"Ammi ta tambayesu ,tana bin ko wacce su da kallo dariya Anty amarya ta yi "haba Ammi yakike korasu ne"hararanta ta yi ta ce "to ai naga dare ya fara ne ai,kuma banga alamar zasu tafi ba, ko kuna nufin haka zaku bar mazajen naku su kadai a gida!?", marairace mata suka yi "ayyah Ammi dan Allah ki bar mu mu kwana, Wallahi seda muka sanar musu zamu kwana kafin muka taho kuma sun yarda"cewar anty sakeena. "Se kuma kuyi ai,yanzu nan ko wacce ta shirya ta wuce gidanta,babu wacce zata kwana",Hajiya babba tana zaune tana jinsu bata sa musu baki ba. "Ammi kiyi hakuri ki barsu tunda sun tambayi mazajen nasu,kuma kinga Hajjatiye da Rumanatu duk gobe zasu zo,su Abbas ma duk anan zasu kwana"anty amarya ta roki alfarma.. "Shikenan Allah yakaimu "suka amsa da Amin. Yau su Umaisha ana wajen Abbie da Abbu,a wajensu suka tare se surutu suke musu,rabonsu da part dinsu tun karfe biyu basu sake komawa ba. Sabriyah bata sake jin d'uriyarsu ba,kuma hakan be dame ta ba,tana tare da Asmita suna ta shirmensu, knocking aka yi ta ce "a shigo". Saghar ne ya shigo hannunsa rike da kwalin chocolate din da yace ze bada a kawowa Asmita ya manta. Tana jin muryar sa ta mike ta tsaya akan gadon tana ihun"me kyau!me kyau!me kyau"murmushi ya mata,tana daga kan katifa ta rungumoshi a jikinta kamar wani ɗanta,wani shock ya ji tundaga tafin ƙafar sa har cikin kwakwalwarsa da sauri ya raba jikinsa da nata beyi taba kawo tsammanin zata rungumesa ba. Tura masa baki ta yi"me kyau na hau lilo babu kai"se ta nutsuwarsa ya yi kafin ya ja hannunta ya kaita gaban mirror ta zauna Sabriyah na zaune tana kallonsu,komawa ya yi wajen da ya ajiye kwalin ya bude ya fito mata da chocolate ya kawo. Buɗe mata chocolate din ya yi,yabata raba chocolate din gida biyu ta yi tabashi rabin girgiza mata kai ya yi alamar bazesha ba. Fara sha ta yi idonta akanshi,kawar da kansa ya yi, ya haɗa allurar ya mata cikin dabara,se da ya gama ze tafi tukun ta ce baze tafi ba se yasha chocolate din,karba ya yi gudun kar tayi kuka,yasha ya ce "shikenan!?", "Ehh". Sabriyah ta ce "my Jerry ni baza'a ban chocolate din ba?",sake raba chocolate din ta yi tasa mata abaki. Fita Saghar ya yi adakin yana dariya.abincin darensu Fatime ta kawo musu fuska a sa'ke suka gaisa. Bude kofar bedroom din ya yi yaje ya zauna akan gadon Abbie yana jiransa,daga wanka ya fito beyi tunanin zega mutum a ciki ba,da mamaki yake kallon LTG dake zaune akan gadonsa. Miƙewa ya yi yaje ya rungume Abbie yana faɗin "i missed you so much Abbie" "nayi missing dinka nima sojana "zama sukayi akan gado. "Nayi tunanin bazaka zo ka ga Abbie dinka ba"LTG ya ce"nope ina meeting ne sorry for the delay". "Is okay ya aiki,banyi zanton dawuwanka nan kusa ba se gashi ka dawo, amma Jawan ya sanar min bincike ne ya dawo dakai", gyadawa Abbie kai ya yi. Sun bata kusan two hours tare suna hira,kafin ya yiwa Abbie se da safe. Yana shiga part din sa ya tarar da Jawan, Saghar, Sudais suna jiransa. "Very good guys,na ɗauka baku zo ba ai"ya faɗa yana wucewa dakin binciken,bin bayansa sukayi ciki suna shiga kofar ya rufe. Suna zaune suna kallonsa ya fito da memory card din ya jona a babban system, connecting ya yi sannan ya dawo ya zauna suka fara kallo. Fuska Barrister Lameer ne ya fara bayyana ajikin video din.yana magana murya kasa_kasa da alamu yana tsoron kar wani ya ji shine. "Sunana Barrister Lameer muktar.ni mazaunin garin Kano ne,na samu sakon sirrine kan cewa wasu mugaye kuma hatsabibai yan ta'adda sun shigo kasar Nigeriya,wanda kasashen waje ma basu iya kawo karshen ta'adda cin su ba.sun shigo Nigeria ne da nufin kashe rayuwaka masu dimbin yawa. Wannan dalilin yasa nasa rayuwata a cikin hatsari domin haɗa bayanai akansu nasan ba lallai in rayu ba,rayuwata dakyar ne in zan iya fita daga sharrinsu amma Allah ya fisu". Yana gama wannan jawabin duhu ya bayyana akan screen din,duk shuru sukayi hankalinsu yana kan screen din, musamman LTG yana son yaga abinda suke shiryawa. Mutane ne kusan su goma sha biyar zazzaune akan kujera ga tarin makamai,da bindigu,a gaban su ba iya bakaken fata bane harda turawa a cikin su. Ogan dake zaune akan kujerar tsakiya fuskansa na sanye da mask baki irin wanda barayi suke sawa,in zasu je fashi. Magana ya fara da turanci"babban abinda nake muradi shine zubar jini,ko da wasa wani acikin ku ya bata mana aikin da mukayi watanni goma muna shiryawa to dashi da familynsa makomarsu lahira ne,asibitoci guda ashirin ne acikin Nigeria wanda zamu dasawa boma_bomai,da Masallatai,da kuma churchs, kasuwanni,makarantu,ko ina za'a dasa bom,bayan nan kuma zamu kwashe samari mu karasu akan dakarun mu,zamu yaƙi sansanin sojaji da yan sanda,babu wa'yanda zamu kyale da rai.yan mata ɗari da daya zamuyi garkuwa dasu duk wanda yazo kawo fansar su a kasheshi,yara matan kuma zamu maida su namu,ta border za'a shigo mana da manyan makamai,da kuma sauran mutanen mu duk ta jirgin ruwa zasu zo".cikin jinjina wa da girmamawa suka fara zuba mishi tafi,hannu ya daga musu ɗan su dakata.cak suka tsaya. "Ku tabbatar da a cikin ku duk wanda ya bata mana aiki komin muƙaminsa a cikin Italian Mafia dole ze mutu,mutuwa kuma mara dadi". A tare suka mike tsaye sunawa kansu kirarin ƙungiya su. "we are the mafias!, blood shed blood!,we stand with our words!,the world is ours!,we choose who to live, and we choose who to die!, mafias are the most strongest union".suna gama anthem dinsu suka fara shan giya ana shagali. Barrister Lameer ya ce"innalillahi wainna'ilaihi rajuun,to kunji abinda wa'yannan azzaluman suke shiryawa.sunan location din da suke shine,okir......."buge wani karfen ya yi ya fadi a ƙasa yabada sauti da seda suka ji. Da karfi" sukace waye a wajen" ku duba ko waye sannan ku kashe shi,nan take Barrister Lameer ya fara salati domin yasan tunda suka ganshi kam na shi yazo karshe.fita a inda ya buya ya yi ya fara gudu yana son barin wajen,yana cikin gudun ya cire memory cikin wayar ya jefasa cikin bakinsa.nan ne video din ya dauke gaba daya. Ransu ya matukar ɓaci lokaci daya kuma ya tashi,suna son kashe rayuwakan al'umma da basu ji ba ,basu gani ba. Da Karfi LTG ya daki table din gabanshi da karfi ,idon sa ya yi jajir. Furzar da iska me zafin gaske ya yi daga bakinsa. Sudais shafa gashin kansa ya ce"wa'yannan sun riga da sun gama shirin su,babban abin takaici shine bamu san ya kamanin sabon shugaban nasu yake ba, yana da wayo yaƙi yarda a san fuskar sa,ba musan a wani lokaci ne zasu tayar da bom din ba yakamata mu dakatar da su". "Duk wayon sa baze taɓa kaucewa tarkona ba,koma wanene shi se na kamosa na mishi hukunci dede da Abinda yake aikatawa"LTG ya faɗa yana miƙewa tsaye.yana kallonsu"Sudais dakai zan fara, suna kokarin shigo da mutanen su da mugayen mukamai ta border,you're comptroller General,nauyin dakatar dasu ya rataya a wuyanka kabada umarni duk wani abinda za'a tsallakar dashi border daga yanzu zuwa end of this month, ka sa a rufe border babu abinda za'a shigo dashi har se da sa hannunka,saboda you're comptroller General Sudais"jinjina kai Sudais ya yi. Maida kallonsa kan Jawan ya yi "kai mataimakin commissioner of police ne,ka zuba jami'o'i ta ko ina bama iya garin nan ba da duk sauran state. communicate with your co assistant commissioner of police". Gyada masa kai Jawan ya yi.pointing din Saghar da hannu ya yi"Saghar make sure ku ankara a hospital daga zarran kaga wa'yanda baka yarda dasu ba don't hesitate to inform me". Yaci gaba da magana"bana son kowa yasan da shirin da muke yi so becarefull". "In sha Allah LTG,zamuyi nasara akan su" "very good,nasanku bakwa wasa da aikin ku, rayuwakan al'umma shine muka shiga wannan aikin akai with any cost we have to save their life's"ya ƙarishe maganar yana rike kansa dake sara mishi.yana jin kan ya fara ciwo,amma bayanin da zeyi yana da matukar muhimmanci hakan yasa yaci gaba da maganar ba tare da ya dakata ba,amma shi kadai yasan yanda yake ji,abun a jininsa yake rashin dogon magana in ba ya zama dole ba,baya dogon magana. Kallo ɗaya suka mishi suka fahimci kansa ya fara mishi ciwo.hannu Saghar ya sa a aljihunsa ya fito da maganin ciwon kai ya basa karba ya yi ya jefa abaki ya haɗiye. "LTG!,make sure you drink water saboda maganin ya yi melting "hararansa ya yi"ba zan sha din ba,kufa doctor's din nan ko..."ya yi shuru yana zama,dariya sukayi Jawan da Saghar suka tafa. "Ku de anyi yan air,yanzu de kunji maganar da LTG ya yi so concentrate" "In sha Allah ". karfe goma na dare kafin suka bar part din nasa cike da tunanin yanda zasu kawo karshen Italian Mafia. Se 11:00pm suka baro wajen abbu nan ma seda Hajiya babba ta korasu,kafin suka tafi. Basu shiga bedrooms din su ba suka shigo nasu Sabriyah suna kwance suna bacci. "Ayyah yau nasan sun yi missing din mu"gobe se mu haɗu. Suka faɗa yana barin dakin, Parsa kashe musu wuta ta yi kafin ta bi bayan yan uwanta. Washe gari bayan sun karya babu wanda ya fita aiki saboda su mom Rumanatu ana hanya sun kusan sauka. Duk wani abinda ya dace da za'a karbesu an yi sa. Karfe sha biyu na rana suka shigo gidan,bayan yan gaisa ne suka wuce masaukinsu, Ashman da Dawood a part din Sudais suka sauka.jaleelah da Iftisan part din su parsa suka sauka. Sauka sukayi sukayi sallah sannan suka huta,bayan sun gama cin abinci ne aka dawo falo ana hira. Hajjatiye da a jirgi tazo ba'a motar ba amma se bala'in ta gaji takeyi,su Hajiya babba suna mata sannu,Ammuh dake hakimce akan kujera tunda suka zo sannu da zuwa ta yi musu ba ta sake ce musu komai. "Bak'ar annamimiya,dama nasan tsinannen bakin halinki be ze bari kice mini sannu,yau da zan faɗi in mutu da kin fi kowa murna,ke kam khareema kin yi asarar rayuwa.babu yanda kika iya dani nan gidan ƴa'ƴa nane se in sa ya sake ki inga tsiyar tsinantakar da ze faru,ni maye ma haka yaganni ya barni,bare kuma ke yar adama,mara mutunci kawai". shuru wajen ya yi babu wanda ya isa yace ta yi hakuri ta hakura, mutum na sa baki zata dawo kansa. Su Ammi de ido suka zuba musu,tun lokacin da Abbie ya auro Hajiya khareema haka kurum basa shiri saboda girman kan Hajiya khareema.shisa Hajjatiye bata santa. "Hajjatiye wai Ni kadai kika tsana a gidan nan ne!?,duk lokacin da kika zo se kin kwashemin albarka meye na miki da zafi haka ga su hamdiyya da Badeeya,ga Abida su baƙi tsane su ba se ni!?", Bude baƙi Hajjatiye ta yi alamar mamaki"lahaula wala quwata illabilah!, khareema yanzu zagina kike yi saboda ni ba uwarki bace shine zaki za ge kina zagina ko, tabbas Mubarak yau ni matarka take zagi saboda lalacewa yakai lalacewa"ta fashe da kuka,abinda suke gudu kenan da ace Ammuh ta yi shuru batace mata komai ba da Hajjatiye shuru zatayi in ta gaji dan kanta. Dawuwa kujerar da take zaune Abbie ya yi ya hau bata hakuri,mom Rumanatu da abbu, uncle Hameed suka sa baƙi suka bata hakuri, dakyar ta yi shuru. Ta goge fuskarta da gefen gyallenta ta ce "nadawo kanku,yanzu meye abinda kuka ribantu dashi da kuka bar yaran nan zabga_zabga dasu babu aure cikin su babu wanda baze iya yiwa matarsa ciki ba, ɓalle a ce basu kai aure ba,dubi yan matan. duk kun haɗa yara kun barsu a gantale se anyi magana a ce wannan soja ne, wannan likita,wannan kustam,wannan police, wannan yan kasuwa,yara duk sun kosa amma kunki aurar dasu se an kawo muku jarirai daga waje a ce wani ya dirkawa wata ciki ko"duk se da sukaji kamar su nitse kasa tsabar kunya, miƙewa da sauri Hajiya babba da Ammi sukayi. "To Ku kuma ina zakuje,anyi maganar ku aurar da yara kun wani miƙe zaku gudu,wato kun fi so ku gansu jere da ku a rasa waye uwar waye yar,to dawo ku zauna "simi_simi suka dawo suka zauna,babu yanda suka iya amma kunya kam sun sha shi. Masifar Hajjatiye kam sun sha,ta yi hatta gaji ta yi shiru,se kuma aka dawo hirar Sudan da ita kamar ba ita ce ta gama Masifa ba. Saghar ya ce"Hajjatiye ni fa da kince zaki samo mini mata a Sudan yanzu ya ake ciki"washe baki ta yi "yaron kirki ai matan aure kam akwai su zan sa akawo maka guda uku se dirje ka zaɓi daya a cikinsu musha biki"dariya ya yi"to ai kuwa hakan za'a yi". Bude baki Hafiz ya yi ze yi magana abbu ya galla masa harara yasan be wuce tsokana bace zeyi. Ba shiri ya yi shuru. "Nikam ina katon Gwauron gidan nan ne ko be da wo ba ne haryanzu!?",Ammi ta ce"ya dawo bari a kirasa"tafa hannu Hajjatiye ta yi,ta ce"lallai hamdiyya wuyarki ya yi kauri,yanzu jikan nawa in banda baƙin hali irin naki se na tambayi ina yake kafin za ki sa a kirawo sa,tabb dijam"cikin girmamawa Ammi ta bata hakuri. Dawood ne yaje ya kira LTG da be ma san da zuwansu ba. Shigowa falon ya yi yana taku na kasaita jikinsa na sanye da dogon wando da rigar me doguwar hannu. Hajjatiye na ganinsa ta fara sakin murmushi. "Kun ga na miji sojan yaƙi,me firgita abokan hamayya,daya tamkar da dubu, Allah de ya biya na mijin duniya". murmushin da beyi niyya bane ya subuce masa duk da se wanda ya kula sosai ze gani.zama ya yi a kusa da ita yana rike hannunta. Farin cikin Hajjatiye yakasa boyuwa, LTG yana daya daga jikin wanda ta fi kauna acikin jikokinta daga shi kuma se Asrah,kwata_kwata bata ganin laifin sa duk abinda ze yi bata masa faɗa,bazaka tabajin Hajjatiye tana yiwa LTG Masifa ba. Kunnesa ta kama ta yi masa magana wai batasan munafukai su ji me ta faɗa mishi,shima da ya tashi bata amsa a kunne ya sanar mata. Kallon su kawai sukeyi,ga shi suna son yin dariya amma wanda ya kuskura ya yi ma yasan ya jawo wa kansa hakan yasa duk suka zuba musu ido kawai. Hajiya babba ta ce "Abbie dama akwai maganar da nakeso muyi dangane da yarinyar da Tajuddeen yakawo,amma zan so mu fara jin tarihin su tukun,saboda Abida ta nuna tana ra'ayin adopting din dayar yarinyar" "to tana ina ne yarinyar!?",Abbie ya tambayeta. Kallon Zoya Hajiya babba ta yi ta ce "je ki kira mini Sabriyah"ranta be so ba haka ta mike ta nufi part din su. kallon anty amarya da aka ce zata zatayi adopting din Sabriyah LTG ya yi,be iya cewa komai ba se kwantar da kansa akan kujerar da yake zaune ya lumshe idanunsa. Dawuwa falon Zoya ta yi Sabriyah na biye da ita a bayanta,tana riƙe da hannun Asmita. Ganin yanda suke da yawa a falon, suna shigowa ciki ido ya dawo kansu nan tajita a takure saboda idonsu. Zama Zoya ta yi ta barsu a tsaye, Abbie ya ce mata "zo ku zauna"in da su Parsa suke zaune a kan lallausan carpet su ka zauna.zaman su beda wuya Asmita ga Saghar. Da sauri ta tashi taje wajensa ta riko hannayensa biyu"me kyau ka zo muje mu hau lilo"da mamaki suke bin Saghar da Asmita da kallo musamman wa'yanda basu san condition din da take ciki ba,dan in ba tayi magana ba babu wanda ze ce tana da Matsala,kallon su Abbu ya yi yaga yanda idanunsu yake akanshi. "Asmee je ki zauna wajan Sabriyah anjuma kadan zamu je lilo"sa'ke sa ta yi tafara kirge da hannunta,kamar me lissafi can kuma ta sa'ke cewa"tom shikenan ai jiya da yanzu zamu tafi ko"gyada mata kai ya yi saboda ya samu yaje ta zauna. Komawa wajen Sabriyah ta yi,cikin rada ta ce"my Jerry in kika sake tashi a wajen nan to zanyi kuka"kwabe fuska ta yi "tom ba zan kara ba". Gyaran murya Abbie ya yi,ya soma magana"Sabriyah wannan din meye din ki ce!?",a hankali ta ce"yar uwata' ce kuma ƙawata". Jinjina kai ya yi ya sa'ke furta"ina son ki bamu tarihin rayuwar ku". har lokacin LTG yana a yanda yake be bude idonsa ba duk abinda ake faɗa yana jinsu. Dogon numfashi ta ja,ta soma magana"sunana Sabriyah wannan kuma sunanta Asmita,mun taso a gidan karuwai ne wanda ni da ita anan muka taso tun muna yara kananu,bata san kowa ba haka nima babu wanda nasani, wannan dalilin yasa muka yiwa kanmu,alkawarin zamawa junanmu uwa,uba,yar uwa,kawa, magajiyar da ta siye mu ta gana mana azaba wanda se da mukaji dama bamu zo duniya,tun muna yara take aka koya mana abubuwan da zamu dinga kawo mata kudi, karuwanci,sata,damfara,rawa.dukka babu abinda bama aikatawa.tun ban kai haka ba nafara rawa a cikin gidan wasa,ban wani saba ba,in mun kayi ranar haka zamu kwana da ciwon jiki babu me bamu maganin ciwon kai,kudin da aka samu da mu a wajen rawa ko ruwa ba'a siya mana dashi,abinci ma sau daya ake turo mana dashi arana, se de wacce ta rene mu ita ce in ta fita nata wajen take samo mana abinda zamu ci,har yakai ga karfinta ya ƙare takamu da ciwo,ya zamana babu me taimakonmu wannan dalilin yasa na busar da zuciyata,na fara yin rawa,domin in samo mana abinda zamu dinga ciyar damu,domin tunda muka kai shekaru goma sha uku boss lady ta cire hannunta akan mu abinci sau daya da ake turo mana ma tadena haka zamu sha wahala muyi rawa amma kudin gaba daya zatasa a kwashe mata,ko biyar bama ci aciki. Samarin da na fara yi ne suka fara bani kudi,nan na samu nafara biya mana buƙatar mu,nice nake ciyar damu,suturarmu duk yana kaina, in wani babu lafiya a cikinmu nice nake siya mana magani,maganin antynmu da ta rene mu nice nan nake samowa.daga zaran muyi mata laifi ko min kankantar laifi,zata haɗa mu ta mana muguwar duka,duk abinda ze same mu ita be dame ta ba,inde zamu kawo mata kuɗi to magana ya ƙare.bamu da yanci a wannan gidan,in kanason ka samu yanci shine se an maka lasisi,kafin ayi mana lasisi munsha bakar wahala, tasan sarai inada ciwo amma daga zaran na mata laifi haka zata barni a cikin ruwan sama ya mini dukkan da se ciwo na ya tashi ko kuma ta sa in yi kneel down haka zata sa a dinga diban ruwa ana shekamin. Tunda nayi baki har na fara iya mayar mata da martani,sun riga da sun bude mini ido bana shakkan kowa,duk wanda yace ze takani to Ni se na ta kashi.daga ni har Asmita se da ta tabbatar da ta mayar damu karuwan suka fi kawo mata kudi kafin nan hankalinta ya kwanta daga nan ne ta yi mana lasisin karuwancin. A da banijin dadin rayuwar can amma nazo na saba da komai in su naji banida in da yafi mini can,domin duk inda naje jina nakeyi kamar akan kaya nake bana samun nutsuwa se in na koma can, kullum maganar Asmita shine yaushe zamu bar wannan gida,ta tsani gidan fiye da mutuwarta. Ita babanta ne ya siyar da ita a wajen boss lady saboda son abin duniya.da wannan abun Asmita ta taso shine a mafarkinta ta kasance cikin kunci da raɗaɗin abinda mahaifin da ya haifeta ya aikata a gare ta, kullum in tayi bacci se ta yi mafarkin lokacin da babanta ya siyar da ita,ta wannan dalilin ne yasa ta fara shaye_shaye ko zata ji saukin raɗaɗin da takeji, kullum cikin yi mata faɗa nakeyi akan shan kayan mayen da takeyi, amma ko a boye se ta sha. A haka na haɗu da wannan a kasuwa daga nan ne rayuwar mu ya shiga cikin babban matsala,mun haɗu da wani ya bawa Asmita memory card, daga nan ita kuma ta bani shi na boye,a washe garin suka saceta sun yi zaton memory yana wajenta nikuma wancan ya sato ni, wannan shine kadan daga cikin tarihin rayuwarmu". Sunyi matukar tausayawa yara batare da sun san komai ba aka jefa rayuwar su cikin garari,aka yi musu muguwar illa,sun yi rayuwa batare da sun san dadin ta ba,babu boko ba bu arabic,ba sallah ɓalle salati. Babu abinda yakai wannan cutarwa ce babu wani kyakyawar alaƙa tsakanin ka da mahaliccinka,baka ma san meye dede maye ba dede ba,hakkin su yana rataye ne akan wuyan wa'yanda sukayi sanadiyyar shigar su cikin wannan muguwar rayuwa. Ammi,Hajiya babba,Anty amarya,mom Rumanatu hawaye ne kawai yake zuba daga idanunsu suma iyayene yau ya zasu ji idan ace ya'yansu akayi wa haka.ya zasu ji idan a ce yau ƴaƴansu aka mayar karuwai amma ance ko wani bawa da kalar tasa ƙaddara,su tasu kaddarar a haka yazo. Yan matan kansu kuka suke yi da sukaji labarin Asmita da Sabriyah hatta Zoya se da tayi kuka ta yi danasanin abinda ta aikatawa Sabriyah. Hajjatiye tsabar tausayinsu seda ta yi kuka itama tana tsinewa wa'yanda suka musu haka. Su Saghar idanunsu ya yi ja sosai ran maza ya ɓaci sun dau alwashi yanda boss lady take wargaza rayuwar yara mata ita ma se sun wargaza nata rayuwar. Me gayya me aiki kuwa yanda yake zaune kuwa ji yake yi kamar ya je gidan karuwan ya kashe boss lady y kuma kona gidan,ya tausaya musu da halin da suka tsinci kansu,be taɓa kawo tunanin cewa wannan ne dalilin da yasa suka tsinci rayuwarsu a haka ba,domin akwai ballagazazzu matan da suka watsar da kansu babu wanda ya musu dole,su suke mayar da kansu karuwai.wasu su gudu su shiga duniya suna sheka ayarsu,ga wa'yanda kwadayin abin duniya yake jawo su bariki.wasu kuma matsalolin rayuwa ce.amma koma wani matsala ne be kamata bawa ya jefa kansa cikin saɓon Allah ba. Hakan ne yasa ya mata kallon ɗaya daga cikinsu ashe ba haka bane.ya kudurta a ransa ze dau mummunan mataki akan boss lady. Ammuh da Ummah ko kadan basu,basu tausayi ba tabe baki sukayi suna watsa musu harara. Su Abbie sun jinjina lamarin kuma sun tausaya musu sosai,ganin da cewa su din yara ne da kansu daya da ya'yansu. Jikin abbie ya yi sanyi sosai da dakyar ya iya cewa"munji labarin ku Sabriyah, tabbas labarin ku akwai darasi a ciki,an cuce ku an cuci rayuwarku,ko kadan baku da hakki wa'yanda suka aikata hakan sune alhaki yake wuyansu, Allah zeyi muku sakayya,in sha Allah daga yanzu duk wani wahalar ku yazo karshe,babu wani wanda ze iya cutar da rayuwarku.kun zama ya'ya a wajen mu.ki saki jikinki da kowa, Asmita kuma Allah ze bata lafiya". Kowa ya masa da 'in sha Allah". "kin ga wannan"ya faɗa yana,nuna mata anty amarya da har lokacin hawaye takeyi tana tuna to ita yanzu wani hali nata yar take ciki,a wani duniya take. Gyada masa kai ta yi alamar ta ganta. Abbie ya sa'ke cewa"daga yau ita ce mahaifiyarki,ki maida ita mamarki,tana son ki zama yarta,yanda zakiyi wa mahaifiyar ki biyayya haka zaki mata,shi kuma wannan shine mahaifin ki"ya sa'ke nuna mata uncle Hameed"sune iyayenki kinji ko?,gyada masa kai ta yi. Kallon gaba daya wa'yanda suke cikin falon ya ce "daga rana irin ta yau, Sabriyah da Asmita suma ya'ya ne a gidan nan,yanda kuke da yanci a gidan nan suma daga yau haka suke dashi, ya'ya ne a wajena,wajen Isma'il,wajen Abdul Hameed,kuma yaya a wajen iyayenku mata.ku duakesu kamar yanda kuka dauki yan uwanku,ku daukesu kamar yanda kuka dauki ƙannen ku,kar inji kar in gani banason nuna bambanci duk da nasan yarana ba haka suke ba,kuna da ilimin da bazaku taɓa wulakanta dan adam ba,kunde ji abinda na faɗa ina!?",ya tambayesu yana kallon ko wanensu, suka amsa mishi da eh. Murmushi ya yi"very good yanzu ku,nuna mini me zakuyiwa kannen naku da zasu ji dadi!?",Abbas ne ya fara ajiye ATM dinsa ya ce"ga shi a cire duk adadin kuɗin da akeso ayi musu abinda yakamata "Ahmad ma ya ajiye na shi ATM din"ga shi duk kudin dake ciki a yi musu amfani dashi"haka Hafiz shima ya ajiye nashi, Sudais ya ajiye nasa ya ce"na bawa ƙannena ATM din nan a musu duk abinda suke so da kudin ciki nasu ne hallaka malak",Sahil da Salim ma suka ajiye nasu, Saghar na murmushi ya ajiye nasa ya ce"nima ga nawa nan ayi sister's dina abinda ya dace,sannan duk sanda ake da bukatar a yi musu allura in basu da lafiya,dan Allah a sanar mini"dariya sukayi gaba dayansu,Jawan ma ya ajiye nashi "ya ce tom dama ance yan mata se da ado ga shi a siya wa ƙannena kayan make up da duk abinda ya dace".Abbie ya ji dadin yanda suka nuna soyayyarsu akan su,duk abinda suke so cikin mintuna ƙalilan zesa akawo musu amma dake yanason yaga yanayin yanda suka karbesu ne shisa ya yi haka. Hannunsa yasa acikin wallet dinsa ya fito da ATM guda biyu ya ajiye ba tare da ya yi magana ba ya mike,da kallo suka bishi suna murmushi dan sun san dama, rashin damuwarsa da damuwar mutane be kai har nan ba yana da tausayi sosai,kawai mutum ne in be san shi ba ze mishi kallon mugu. Haurawa part din sa LTG ya yi.. Dawood da Ashman suma sun ajiye nasu ATM.. Anty Sameera ce ta matso kusa da ATMs masu yawan dake zube a inda suka ajiye su,ta ce"gaskiya Sabriyah yayyunku suna matuƙar sanku wannan ruwan ATM haka bari mu kirga mugani".kirgawa ta yi tana jinjina kai "inyaaaah!,guda goma sha daya,se san barka"murmushi sukayi. Tunda take a rayuwarta bata taɓa tunanin wannan ranar yana zuwa a cikin rayuwar su ba,bata taɓa tunanin wasu zasu maida su ya'yan su ba, musamman ma yanda wasu suke kyamarta su suna kiran su da karuwai.wai yau sune aka wayi gari kowa yana yin abinda ze sasu farin ciki,yau jinta tayi duk wani gurbin kadaici da take tare dashi ya cike jinta take yi,kamar yanda masu iyaye suke ji. Batasan da wani baƙi zata gode musu ba . Kukan farin ciki ta fashe da shi wanda bata taɓa tunanin zata yi sa ba. Folding din dukka hannayenta ta yi tana kuka ta soma magana. "Mungode! mungode! mungode,ban san da wani baƙi zanyi amfani wajen gode muku ba ,ku din mutanen kwarai ne,ban taba tunanin rana irin na yau zezo a cikin rayuwarmu ba,kowa kyama yake nuna mana,amma yanzu kun zame mana ahali,uwa,uba,yan uwa duk kun bamu,ko da yaushe inuwar kadaici je bibiye dani kullum cikin kadaici nake jina amma yanzu na ji ni kamar kowa,nima yanzu naji rayuwata tana da amfani,a ko da yaushe Asmita tana cewa my Tom duk sanda muka bar gidan boss lady to wajen mamana zamu koma,se inji jikina ya yi sanyi inna tuna Ni banida kowa,banda wanda zan kira nawa a wannan duniya se Asmita kadai.amma yau nasamu a halin da suka amshe mu hannu biyu cike da kauna.ya saka muku,yanda kuka taimakawa rayuwarmu,kuma Allah ya taimaka muku a lamurran ku."ta gama maganar tana fashewa da sabon kuka me taɓa zuciya. Tashi yan matan sukayi gabaki ɗayansu harda Jaleelah da Iftisan suka zo suka rungume su,suma suna hawaye suna jin kaunar su na shiga zuciyar su musamman Sabriyah. "Am sorry Sabriyah!,kiyi hakuri ki yafewa yar uwarki"cewar Zoya dake rungume da ita. "Nima kiyi hakuri"Sabriyah ta faɗa. Kukan Asmita sukaji,tana kuka sosai itama idanunta ya yi jajir,da sauri Sabriyah ta rikota ta yi tunanin ko akwai abinda take bukata ne yasa take wannan kukan. Muryar ta sukaji tana cewa"my Tom bana faɗa miki ba,akwai lokacin da ƙaddara ze fitar damu daga wannan gidan!?,mun gode muku sosai ku din mutanen kirki ne"mamaki iya mamaki sun sha shi domin ba suyi tsammanin zata dawo hayyacinta a yanzu ba amma sun yi murna da haka,banda mutane biyu da uncle Hameed da Saghar domin su kadai suka san meye matsalar da hakan ze jawo domin ta dawo hayyacinta ne ta karfin tsiya,kuma mantawa sukayi da baza su bari Sabriyah ta fadi tarihin rayuwarsu a gabanta ba. Abinda ya faru shine tun sanda Sabriyah ta fara bada labarin su ta fara jin kanta na juyawa,nan take ta fara ganin flash din hotuna a idonta,a haka ta dawo hayyacinta, batare da kowa ya sani ba,taci gaba da sauraran abubuwan da suke faruwa. Tallafo fuskarta Sabriyah ta yi tana hawaye ta ce"my Jerry na godewa Allah da kika dawo hayyacinki" "nayi kewarki my Tom, wayan'can mutanen sun wahalar dani sosai"ta faɗa ta hawaye.share mata hawayen fuskarta ta yi. Abbu ya dora daga in da Abbie ya tsaya"to Alhamdulillah, Allah shine abin godiya,da ikon sa ga shi kin samu lafiya kin dawo cikin hankalinki.kamar yanda muka dauke ku kamar ya'yan mu kuma ku sa'ke jiki,kunji!?,kuma nan gidan ku ne,Umaisha yanzu tunda kun kara yawa zaku koma babban part din kusa daku be three bedrooms a ciki da extra room se kunfi sakewa a can". A tare suka ce"to Abbu". Wani farin abu ne kamar kunu yanada dan kaurin fari tas ya fara zubowa daga hancin Asmita hannu tasa ta lakuto shi ihu ta yi ganin abun dake fitowa daga hancin ta. Lura da abinda yake fitowa daga hancin ta yasa suka rufu akanta,dama uncle Hameed da Saghar sun san za'a rina. Rike kanta ya fara yi,anky chef Saghar yasa yana goge mata hancinta rike hannunsa ta yi kam tana kuka.kallonta ya yi kafin ya ce "shiiii!,ki yi shuru ki sa idonki cikin nawa"hakan ta yi,idonsu na cikin na juna.yasa hanky chef din yafara jawo farin abun dake fitowa din,sosai ya fito dasu, ƙasa jure kallon cikin kwayar idonshi ta yi se kawai ta rufe,se da ya fito da su tas kafin ya sake kanta.kallon Fatime ya yi "please a gyara wajen nan"fita tayi domin kawo abubuwan da zata kwashe su dashi. Kallo abun suke kafin Abbie ya ce "to shi wannan din meye!?", Saghar ya ce"cocaine din da suka dinga dirka mata ne ya taro a waje daya,kuma ya taɓa mata kwakwalwarta,dawowa hayyacinta da tayi cikin karfi,ze iya jawo mata babban matsalar da yafi na farko,abinda za'a yi cikin gaggawa shine a yi mata brain surgery shine kawai solution in kuma ba haka ba,zata faɗa faint condition,ze zama a ko da yaushe zata dinga suma ne,duk bayan awa daya."be gama rufe bakinsa ba ta sume a jikin Sabriyah da Zoya. Abbie ya ce "ayi gaggawar yi mata aiki". Hajjatiye ta ce "yaran nan kuma ganin rayuwa Allah sarki Allah de ya saka muku". Se mun haɗu Monday in me duka yakaimu da rai da lafiya. Book one ya kusa karewa remain some few pages,na yi wa mutane 20 na farko discount din 200,zasu biya 300 kenan.idan mutum ashirin na farko suka gama biya ze koma 500 domin wannan shine standard price dinshi.luckiest 20 people ku hanzarta biyan naku.😍😍😍😍😍💝 Comment,share and like. *🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹* Page 25&26 *_Story & written_* By *MRS🌹ISHAM🌹* ( Yar lelen Jarumai) *THE WRITER OF 🖋️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️ __________________________________ Page 25&26 "Saghar kai ta part dina,kafin a gama shirin yi mata aikin"dagata ya yi cak i zuwa part Hajiya babba din,bin bayansu Sabriyah take kokarin yi,ta ji muryan Ammi na cewa"karki damu ze dubata"ba don ta so ba haka ta tsaya,murna ya koma ciki,da ta ga Asmita ta farfaɗo ta yi tunanin matsalar su yazo karshe,yanzu ga maganar aikin da za'a mata. Rike hannunta anty amarya ta yi suka tafi part dinta. Kiran asibitin ya yi ya sanar dasu da komai ya zama cikin shiri zasu zo dan gabatar da aiki. Dawuwa falon Saghar ya yi bayan ya kai ta part din Hajiya babba kamar yanda ta umarce shi da ya yi. "Uncle yau ne za'a mata aikin!?"cewar Dawood,"eh yau ne yanzu ma kuwa,ku fara yin gaba da ita banason Sabriyah ta fito ta samu baku tafi ba,dan zata ce dole se ta bi mu,so you have to hurry"a tausashe Dawood ya sa'ke cewa" Saghar ku tashi muje" "Ammi ba se kunzo ku ba, duk ku zauna a gida daga zaran aiki ya yi kyau an kammala lafiya se mu sanar daku,ku zo ku duba ta,in ba haka ba in Sabriyah ta fito taga bakwa nan zata fara zargin wani abu dan yanzu haka ma jikinta ya yi sanyi"uncle Hameed ya yi maganar yana miƙewa,ya fice a cikin Mansion. Wannan karon Hajiya babba da Ammi ne suka fito da Asmita a ka sa ta a motar.su kuma suka wuce asibiti.koma wa ciki sukayi suna addu'a Allah yasa aiki ya yi kyau. Yana part dinsa,system ne a gaban shi yana video call da general cikin turancin da ya zauna a bakin shi kamar yarensa,ya ke sanar da general ya samu memory sede ba ya son kowa ya ji abinda ake ciki har se an kammala operation din da suke yi na kama Italian Mafia,domin ya gano kan cewa akwai munafiki a cikin su yana sanar da shugaban Italian Mafia duk wani motsin su.jinjina masa general ya yi ya kuma dau masa alkawarin baze sanar da kowa abinda ya ke faruwa ba. Shigowa major Marry ta yi ta zauna a kan kujerar dake facing dinsa hannunta sanye cikin jakan da ake sa hannu in an samu wani rauni, sosai ta samu lafiya hannun ne kawai ya rage ta yi recovery. "LTG i heard that, you have the memory with you!?" .. "Yes!how are you feeling now?",ya tambayeta yana rufe system din. "Am quite well buh I have important information to share with you"kallon ta ya yi alamar go ahead. "i already sent it to you through your email" Duba wayarsa ya yi kafin ya ɗago ya kalle ta. "Are you sure this information isn't wrong!?" "Am hundred percent sure LTG" Umarnin tafiya ya bata, sannan ya tashi ya yi wanka, ya sa uniform. yana saka takalmin sa ne Khalifa ya shigo,nan LTG ya sanar dashi da su shirya zasu shiga daji operation,sara mishi ya yi kafin ya fita da sauri nan take ya sanar wa sojojin dake gidan,shiryawa sukayi cikin ka'kin uniform din sojoji,ko wanne ka gani da bindiga a jikinsa,ga motocin da ke fake yana jiransu dan fita daji. Suna shiga part din, anty amarya tasa ta ta yi wanka a toilet dinta,ta fito mata da riga da skirt na Atamfa super wax ya sha dinki ya yi kyau sosai, tunda telan ta ya kawo mata su ta fahimci kayan baze shigeta ba yasa bata sake bi ta kansu ba se yau din nan.ajiye su ta yi akan gado. Fitowa ta yi daga wankan sanye da dogon hijab din da anty amarya ta bata ta saka, towel na daure a ta ciki.bakaramin kyau hajab din ya mata ba, kyakyawar fuskarta ya fito ya yi kyau. "Anty amarya na fito ina mai in shafa"ɓata fuska anty amarya ta yi, daga gani bata ji dadin sunan da Sabriyah ta kira ta dashi ba hakan ya sa ta, cewa "Sabriyah ba ki dauke ni a matsayin uwa bane yasa ba ki kirani da mommy ko mama ba!?"cikin jin kunya ta ce "kiyi hakuri mommy bazan ƙara ba" "yawwa daughter na!,hijab din nan ya Miki kyau sosai"murmushi kawai ta yi,ita saukin kan anty amarya da rahanta yana burgeta har cikin rai takejinta kamar ita ce mahaifiyarta saboda yanda take nuna mata soyayya. Zaunar da ita ta yi akan kujera gaban mirror ta shafa mai kafin anty amarya ta mata light make up ,ta bata kayan ta ce ta je ta saka a cikin dress room. Kallon kayan ta yi tana tunanin ta ina zata fara sakawa,ita sam ba ta taɓa saka irin wannan kayan ba,daga riga da wando se riga,sune kadai iya kayan da take sawa,yanke shawara ta yi ta dauki skirt ta fara sawa,kayan tab ya kamata Kamar telan da ya dinka ya gwada ta, ta sa rigar.masha Allah ita kanta seda ta ji sauyi a jikinta,gaban madubin da ke cikin dressing room din taje ta tsaya tana kallon kanta,seda ta ja baya tana mamakin kanta,gani take yi kamar ba ita ba gaba daya kayan sauya mata kamani ya yi, tsananin kyaun da kayan ya mata ya sa ta fara juyawa tana karewa kanta kallo kamar ba ita ba,gashinta dake zube a bayanta ta fara kokarin daure su waje daya,dakyar ta iya daurewa,ta dau dankwalin kayan ta fito,tun da anty amarya ta daura idonta akan Sabriyah ta gagara daukewa kallon fuskar yar karamar ƴarta da ta rabu da ita take yi a fuskarta, fuskar Asrah take gani lokacin da tana karama a fuskarta,ta kasa janye idonta akanta bata ma san ta iso kusa da ita ba tana mata magana amma ina hankalinta ya yi nisa. "Mommy ki daura mini dankwalin ban iya ba"shiru anty amarya ta yi tana kallonta, taɓa hannunta ta yi tana sa'ke cewa"mommy ki daura min"se sannan ne ta dawo tunaninta,da sauri ta ce"sure kawo in daura miki "miƙa mata ta yi batare da ta yi tunanin komai a ranta ba. Daurin dankwali me kyau ta mata ta saka mata sarka da ɗan kunnen gold me kyau simple design,ji ta yi kayan yana muskulinta tasa hannu zata dan ja zip kasa kadan,rike hannunta ta yi tana tambayarta "meye zakiyi haka"shagwabe fuska ta yi da iya gaskiyarta ta ce "mommy Wallahi muskulina yakeyi"dama ta yi tunanin za'a yi haka duba da babu irin wannan kayan a rayuwarsu bama su taba sawa ba. "Karki cire ki daure kidinga sakawa a s haka zaki saɓa,ke bakiga yanda kika yi kyau a cikin kayan bane,kamar wata amarya"tsadadden murmushinta dake ƙara mata kyau ta sakarwa anty amarya"mommy dagaske na yi kyau sosai!?"ta tambayeta with excited face,kai ta gyada mata alamar ta yi kyau sosai,itama da murmushi akan fuskarta nan ne dimples dinta suka bayyana,dan yatsa ta saka a ciki ta taɓa kamar wata karamar yarinya ta langwabar da kanta gefe tana kallon kyakyawar fuskarta anty amarya da za'a iya cewa photo copy dinta ce. "Laaah mommy kema kina da dimple guda biyu iri daya da nawa,kuma ma a waje daya suke"hararan wasa ta mata"ke dama baki taɓa gani bane se yau". "Allah ban taba lura ba,se yau.mommy kin san meye!?"girgiza kai ta yi kawai ba ta ce komai ba. "Mommy ke kyakyawa ce sosai ko fa murmushi kikayi se kin ƙara kyau,kalli idanunki Wallahi kamar akwai wani abu kamar man gyada_man gyada a cikin su"rike haba ta yi tana kallon Sabriyah da mamakin ta,kenan itama surutacciya ce rashin sabo da kuma rashin wanda zaka zauna ka sa'ke dashi har ka ta yi masa surutun ne ta rasa shisa a ke mata kallon bata wani magana sosai. Yanzu da ta samu anty amarya kuma ta dauketa tamkar uwa shisa take ta mata surutu.kuma ita ta ji dadin hakan sosai yanda ta ji free da ita babu wani shuru_shuru ko kuma wani kunya,ta fito tana ta mata surutu da shagwaba hankalinta kwance. Tunawa ta yi da Asrah,duk lokacin da ta yi kwalliya se ta shafa fuskarta ta ce "mommy kinyi kyau sosai, you're so beautiful mom". Ruko hannun Sabriyah ta yi "Tom Nagode babyn mommy, yanzu kije palour,in kije ki gaishesu daya bayan daya bawai yanda kika saba yi ba"gyada kai ta yi ta mike da niyar tafiya. "Sabriyah zo nan"dawuwa ta yi,ta tsaya,dauko gyalen shantali ta yi ta yafa ma,akai. Fita ta yi a part din ta nufo main part da tabar su. A hankali take taka stairs da takalmi me madaidaicin tudu,kamar wata hawainiya take tafiya kai kace tsoron taka kasan takeyi,ita kuma ji takeyi in ta yi tafiya da sauri to skirt dinta ze rabe gida biyu duk da kamatan da ya yi ba sosai bane kawai rashin sabo da irin kayan ne yasa takejin wannan sabon a al'amarin. Jin ƙaran takun takalmi ne yasa suka maida idon su wajen dan ganin waye haka. In badan sun santa ba to babu abinda ze hanasu cewa wata shuwa arab mix with Hausa ce,yanda ta atamfar ya yi fitting din jikinta se ya zamana kamar tun asali shine suturanta. Saukowa downstairs ta yi idanunsu duk a kanta musamman su Umaisha da su Ashman,kallonta suke yi babu ko kyaftawa. Yanda anty amarya ta sanar ita hakan ta yi wajen Abbie ta fara zuwa ta gaisheshi. "Abbie ina wuni!?". "Lafiya klau Sabriyah,ya mommy ki!?". A hankali ta ce "Mommy na lafiya" Ta je wajen Abbu shima ta gaisheshi. "Abbu in wuni!?". "Lafiya klau alhmdllh yarinyar kirki" A marairace Jaleelah ta ce "Abbu mu ba yaran kirki bane!?". Gwalo Sabriyah ta musu "Eh din,kun ji haushi ne?" Hararan wasa Rameesa ta mata ta mike ta dawo wajen abbu ta zauna cikin shagwaba ta ce "Abbu mu ma ai yaran kirki ne ai ko?". Dariya abin na su yaba kowa wai kishi suke yi,gyada kai Abbu ya yi kafin ya samu damar cewa "Dukkan ku yaran kirki dan Allah ku barni haka"sa'ke kwashewa da dariya sukayi harda Sabriyah dake tsaye kusa da Ammi. Seda ta gaisar da duk wa'yanda suka girmeta a falon,kafin ta lura akwai wa'yanda basa nan. Hajjatiye ma ba ta nan, uncle Hameed, saghar, Dawood,sun tafi da Asmita asibiti.se kuma LTG da tun lokacin da ya tashi be sa'ke dawuwa ba. Jan hannun Parsa ta yi tana"masoyiya zo muje ki rakani part din Hajiya babba in ga my Jerry"ta kira Parsa da masoyiya kamar yanda ta ji kowa na gidan yana kiranta. Kame_kame suka fara mata sun rasa ta wani hanya ne zasu hanata zuwa part din Hajiya babba. Abbie ya ce "Sabriyah bari in ta tashi daga bacci se kije gudun kar ki tasheta" Murmushi ta yi,cikin farin cikin da bata taba tsintar kanta a ciki ba ta ce "Abbie ka yarda dani,ko motsi na bazata ji, kallonta kawai zan yi in fito". Ta faɗa tana kuma jan hannun Parsa din. "Sabriyah bazaki samu ganinta yanzu ba"Sahil ya faɗa yana kallon su. Kallon tuhuma ta fara binsu dashi jikinta ne ya fara bata akwai wani abu da suke boye mata. Slowly ta ce "meyasa ka faɗi haka ya Sahil akwai abinda kuke boye mini ne!?"ta tambayashi tana kallon su gaba daya. Daga bayanta ta ji muryarsa yana faɗin. "Bazaki samu ganinta yanzu ba kamar yanda Sahil ya faɗa miki saboda yanzu keda su anty Sameera zaku fita siyayya ita kuma Asmita,ba ta tashi ba tukun nan bana son musu"ta kasan ido take watsa mishi harara,yana sanye cikin ka'kin uniform dinsa da ya sake fito zallan madaran kyawunsa. Sarai ya ga hararan da ta yi mishi amma dake yana da important issues da yakamata ya yi clearing dinsu ya sa be bi ta kanta ba,saboda yasan tunda ya ce bazata shiga ba to,babu yanda za'a yi ta shiga sede in taurin kan nata yana kusa.komawa sukayi daga ita har Parsa suka zauna.shi ma zaman ya yi akan kujerar dake facing na Abbie. Ganin shi cikin uniform ne yasa Hajiya babba cewa"Tajuddeen ina zuwa haka". "Zamu je wani dan karamin aiki ne". Ta ce "Allah ya taimaka"ya amsa mata da"Ameen". Kallon Ammi ya yi yaga idonta na kansa. "Ammi zan fita". "Allah ya taimaka yabaka nasara". Har cikin ransa ya ji dadin wannan addu'ar da Ammin sa ta mishi,.ya amsa da"Ameen". Kallon yan matan anty Sameera ta yi ta ce" to maza duk ku tashi muje a yi shopping,Sahil da Sudais ku tashi muje ku zaku kaimu". Hajjatiye da fitowarta kenan ta ji tattaunawar da suke yi ta ce"kayya! dan Allah kwashesu kaf ki tafi dasu ni dama sun isheni,gwara su je su dede ta kansu a yi tuwona mai na". Yar dariya kowa ya yi, Sahil ya ce"Tabb waya gaya miki Hajjatiye ni zan yi auren gida!?,ai ina da budurwata a kano to kuma me ze sanya ni in yi auren gida ". "Ah ah babu kam se ka kawo mana ita ai mu ganta"cewar Hajiya babba tana dariya domin duk sun fahimci ya yi hakan ne dan raha. Tunda ya furta wannan maganar murmushi da walwalar dake kan fuskar Parsa ya dauke cak, idanunta suka cika da hawaye,zufa ya fara tsatssafowa wuyanta da goshinta, sunkuyar da kanta kasa ta yi bata san kowa ya fahimci halin da take ciki.ji tayi komai ya dena mata dad'i,kenan dama duk dakon soyayyan ya'yan nata da ta jima tana yi yana da budurwa ba ta sani ba?,duk da tasan ita kadai take san shi,be ma san tana yi ba shi kallon kanwa ya keyi mata,kuma babu wanda ya fahimci hakan a gaba daya ilahirin gidan se Salim,shine ya fahimci ta fadawa soyayyan dan uwanshi amma ko da ya fahimci hakan be sa ya nuna mata kan cewa yasan wani abu ba. A duk lokacin da ta yanke shawarar taje ta samesa ta sanar dashi irin son da take mishi ko da Allah ze sa ta samu waje a cikin zuciyarsa,amma kunya da gwarjinin da yake mata se ya hanata tabuka komai.ga shi yau kunnenta ya jiyo mata abinda bata taɓa tunanin jin sa ba a wajensa,ashe ita haukanta kawai take yi.(hmmmm,ni ko nace matsalar soyayyar bari daya kenan ". Salim da ya lura da yanda mood dinta ya sauya ne yasa ya ji wani iri a ransa, yarinyar da babu wanda ze ce ya taba ganinta a cikin wannan ɓacin ran,ko da yaushe murmushi dauke akan fuskarta se gashi yau ta kan abinda ya kasance ba gaskiya ba,ta shiga wani yanayi,yanke shawara ya yi ze samu Sahil din ya sanar da shi Parsa na matukar kaunar domin shi yafi kowa sanin babu wata mace a cikin rayuwa Sahil kawai yanxu ma ya faɗa ne saboda rashin sani da kuma raha. LTG dake jin hiran na su ne ya ɗan yi tsaki,shi gani yake yi ja musu reni za'a a wajen wa'yannan kananun yaran. "Ku tashi mu tafi ko,kar yamma ya yi, Sakeena zakije ne!?"ta tambayi anty sakeena dake magana da Hajjatiye,se kus_kus suke yi. "No sekun dawo kawai" Ta faɗa mata haka sannan suka ci gaba da maganar su. "To Allah ya tsare ya kuma kare ku da karewarsa"can kasan makoshi ya amsa addu'ar da Abbie ya musu sannan ya mike ya fice,yana fitowa yaga rundunar sojojin sa shi kadai suke jira,duk a tare suka sara masa gyada musu kai ya yi Khalifa ya buɗe mishi ya shiga yana kokarin rufe motar major Marry ta fito ita ma cikin shirinta tana sanye da uniform. Dasauri ta iso tana kokarin shiga. Kallon ta ya yi irin kallon me kike kokarin yi din nan. Ta fahimci abinda yake nufi hakan yasa ta ce "Please LTG I want go along with you". Cikin harshen turanci ya ce mata bazata je ko ina ba,se jikinta ya gama yin sauki. Babu yanda ta iya tunda bazata tsaya jayayya da lieutenant general ba uban gidanta. Ta na ganin su suka fita a gidan ko kadan ba ta ji dadi ba,raunin hannunta nan ne ya kwafsa mata saboda tana son ta ganta a bottle field ana fafatawa da ita. Komawa ciki ta yi babu yanda ta iya haka take ta kwanta. Fitowa packing space sukayi, Jawan, Sudais, Sahil suka fito da motocin su dan kai su kasuwa. Jaleelah ce ta yi hanzarin zama a gaban motar tana murguɗawa Iftisan baƙi. Kallonta Jawan ya yi,ya kuma ga hararan da Iftisan take yi mata. "In kin gama neman tsokanar seki fito min a motar"tura baƙi ta yi can kasa _kasa ta ce "baza'a fito din ba". "Rike kugu Jawan ya yi yana mamaki wato wannan rashin kunyan da ya sansu da shi musamman ma ita Jaleelah da tafi Iftisan sangarcewa yana nan. Hannu yasa ya buge bakinta.kuka tasa ka tana kama bakinta, karasowa bakin motar anty Sameera ta yi jin kukan Jaleelah,kallon Jawan da kukan nata ko ajikinshi ta yi ta ce "meye kayi mata Jawan!?". "Zagina ta yi shine na buge bakin"ya bata amsa yana yiwa Umaisha alamar ta zo da hannu. Cikin kuka ta ce "Wallahi anty Sameera ni ban zage shi ba sharri ya min"hannu yasa ze sa'ke buge bakin anty Sameera ta yi saurin rikesa. "Yi hakuri,kidena kukan.kai kuma Jawan ka kyaleta please". Bude murfin motar ta yi ta ce "kuma,ma na fasa tafiyan". Galla mata harara ya yi,ta shige da gudu tana kuka. Dariya Iftisan ta yi taji dadin yanda Jawan ya yiwa bakin rashin kunyar Jaleelah. Sabriyah motar Jawan ta shiga ita da anty Sameera da kuma Iftisan din. Yayinda Umaisha,Zoya, Rameesa suka shiga motar Sudais. Baya Iklas ta shiga,Parsa dake tsaye a bakin motar bata ma da niyar shiga,fuska a ɗan haɗe. Kallonta Sahil ya yi "masoyiya zo shigo Mu tafi". Maƙe kafada ta yi, ta ce "Iklas ki dawo gaba ni abaya zan zauna"with full surprise a fuskarsa yake kallonta,gani ya yi Kamar ba Masoyiya Parsa ba,da duk lokacin da zasu fita inde har dashi tofa tana gaban motar amma yau ita ce take yin tayin zaman gaban motar. "Yau kuma!,nikam get in don't waste my time"sa'ke maƙe masa kafada ta yi a karo na biyu. Da ya fuskanci dagaske ta ke ne yasa ya haɗa rai ya daka mata tsawa da yasa ta shige babu shiri. "Za ki wuce ki shigo ne ko sena shigo dake da kaina!"zama ta yi fuskarta babu walwala,shima da yaga yanda ta yi kicin_kicin da rai ne yasa shima be bi ta kanta ba,duk da yana mamakin meye haka ya samu Parsa da yau ya ganta a haka. Shi da Iklas ne suke ta hiransu,ita kam ko tari bata yi ba tunda ta shiga motar. A motar Sudais ma su na nan suna ta surutu gaba daya sun cika wa Sudais kunne, musamman Umaisha an fi jin muryarta. Juyowa da kansa ya yi ya watsa musu harara,ai babu shiri duk sukayi shuru. Har aka isa shopping mall din babu wanda ya sake cewa komai. Ciki suka shiga suka bar mazan suna waje suna jiran su. Sosai sukayi wa Sabriyah da Asmita shopping kaya na ban mamaki masu yawan gaske da kuma tsada,kama daga kan kayan sawa,kayan make up, perfumes, shoes, bags,hijabs,gyale, jewelrys,sari(lufaya), shower items, lotions,duk wani abinda aka san mace zata yi amfani dashi seda aka siya musu,wajen pad suka je,anty Sameera ta fara ɗiba musu tana sawa a basket,daukan guda daya Sabriyah ta yi ta matsa kadan taji da laushi. "Anty Sameera meye wannan din?, amfani me ake yi dashi?"anty Sameera ta ce mata "wannan din pad ne ,ana amfani dashi ne lokacin period". Sa'ke je fa mata wata tambayar ta yi domin bata fahimci abinda take nufi da period da kuma pad ba. "Anty Sameera su din meye su to"se yanzu ne anty Sameera ta kalleta da mamaki,dazun da ta mata tambayar menene pad ko kadan bata yi mamaki ba saboda wasu basa amfani dashi,da tsuma suke amfani shisa bata kawo komai a ranta ba. Danne mamakinta ta yi,ta ce "idan kina al'ada da me kuke amfani ke da Asmita"nisawa ta yi kadan domin anty Sameera ta sa ta a duhu bata fahimci abinda ta ke nufi ba. "Ban san me kike nufi ba anty Sameera"kallon yan matan ta yi taga babu wacce hankalinta yake kansu kowa tana ɗaukan abinda take so ne. Ta jawota gefe kadan ta ce "Sabriyah idan karshen wata yazo,in kuna jinin al'ada da me kuke amfani!?", girgiza mata kai ta yi,kamar wata wawiya ta ce"jini?, karshe wata? ni haryanzu bangane ba jini aina!?",ta jefa mata tambayoyi uku at one time. Jinjina kai anty Sameera ta yi wato de in ta fahimta Sabriyah na nufin ta ce mata,daga ita har Asmita babu wacce ta taɓa yin period a cikinsu,tunda ga shi bata ma san ni ba,ta yi mamaki sosai.ta ce zasu karasa maganar a gida. Bangaren wayoyi suka je,nan Anty Sameera ta dauka musu waya iphone 12 normal su biyu ita da Asmita,irin na hannun su Umaisha. Layi me register suka karba guda biyu.komai sun gama siya,an je wajen bill anty Sameera ta bayarda ATM guda daya. Duk hankalinsu nakan wajen bill suna hira. Ji ta yi an rike hannunta an cusa mata takarda a hannu da sauri ta juya dan ganin waye haka, bata iya ganin fuskarsa ba se bayansa yana tafiya harya yi nisa. Kallon takardar ta yi kafin ta bude,suna ne a jiki da kuma number waya.suna an rubuta Fu'ad. Amma bata iya karatu ba ɓalle ta fahimci sunan. Chukuikuye takardar ta yi da niyar ya sarwa,se zuciyarta ta raya mata da ta kira number ta ji waye.sake kankame takardar a hannu ta yi tana mamakin to waye haka,kuma aina ya santa. Yaran shopping mall din ne suka kwashi kayan suka kai musu zuwa motar. yanda suka zo haka suka koma, yanzu kamar dazun har suka dawo gida Parsa batayi magana ba.ita kanta Iklas seda ta yi mamaki kowa yasan ba halinta bane wannan amma ta yi shuru kamar me tunani. Fita a motar Iklas ta yi ta barsu su biyu.kokarin bude motar ta yi taji taki budewa ta fahimci sarai Sahil ya saka lock ne a motar. "Masoyiya meya sameki gaba daya kika sauya kamar ba ke ba!?"ya tambayeta yana tsareta da idon sa da takejin kunyar kallo. "Bakomai"ta ba sa amsa a hankali. "Karya kike, kowa yasan ba haka kike ba so tell me is something wrong?"girgiza mishi kai ta yi. Haɗe fuska ya yi "kalli idona da kyau"ka sa dagowa ta yi. Ya sake maimaita mata a karo na biyu. "Kalli idona Parsa". Dakyar ta iya masa kallon da be fi na second biyu ba. "Tom sanar da ni meke faruwa". Hawaye ne ya gangaro daga fuskarta,ya ɗigo akan hannunta. Da mamaki ya sa'ke kallonta. "Bazakiyi magana ba!?". Tana sheshekar kuka ta ce "to ai ya Sahil kai ne". "Ni ne meye Parsa" Share fuskarta ta yi ta ce "to ba kai bane kace kana da budurwa a kano ba,kuma shine baka sanar damu kana da budurwa ba, ko a waya fa baka taɓa haɗa mu da ita ba ɓalle mu san antyn na mu,for God sake hakan ya yi ya Sahil.kasan yanda muke so a sha biki a gidanmu kuwa musamman na aurenka se yafi na kowa dadi,se munyi event goma a matsayin mu na ƙannen ango". lokaci daya ta canza magana domin bata da karfin guiwar da zata iya faɗa masa tana san shi, wannan dalilin yasata sauya maganar kawai. Tunda ta fara magana yake kallonta,be yarda da Abinda ta faɗa ba,kawai ya ji ta ne, murmushi ya yi ya bude mata kofa yana murmushi. Ya ce"shikenan yau din nan zan haɗa ku waya da ita". Yaƙe ta yi ta fice a motar. Bin bayanta ya yi da kallo har ta shige ciki. Ajiyar zuciya ya yi, ya ce "nasan abinda yake cikin ranki masoyiya". Yana fitowa daga motar yaga su Abbu sun fito duk sunyi alwala zasu je masallaci binsu ya yi. "Saghar sun dawo ne,ya aikin nata?" Ya tambayi Ashman. "Alhamdulillah an yi aiki successful.se gobe za'a fara ganinta". Shima "Alhamdulillah"ya faɗa. Suna shigowa Sabriyah ta nufi part din Hajiya babba ta ga ko Asmita ta farka daga bacci,sannan ta yi mata albishiri da an siya musu sabbin wayoyi.ga kuma takardar da har lokacin yana rike kam a hannunta. Haɗuwa da Hajiya babba ta yi a mahayan ƙarshe,ta ce"har kun dawo kenan?!", "Eh mun dawo Hajiya babba zan je in duba Asmita ne "riƙo hannunta ta yi ta ce"ya'yan ku Tajuddeen yace kar abar kowa ta shiga part din se bayan ya dawo". Ba dan ranta yaso ba haka suka dawo main part da Hajiya babba, Anty sakeena ta ce "ku je kuyi sallah"miƙewa sukayi banda Sabriyah dake zaune ta saba duk sanda zasu je yin Sallah tana zaune abunta. Kallon ta anty sakeena ta yi. "Sabriyah tashi muje muyi sallah" "to" ta bi bayanta. Ta ce mata ta shiga ta yi tsarki.bayan ta yi ne,ta koya mata yanda zata yi alwala.itama ta dauro nata alwala. Sannan ta ce mata duk yanda ta yi a sallah itama ta yi. Haka sukayi sallah tare suka idar. Uncle Hameed ya dawo gida.ya sanar da mom Rumanatu da Abbie,an yi nasara a aikin da aka mata,ba za'a jima ba zata farfaɗo shisa Saghar be dawo ba yana can. Lokacin dinner ma gaba dayansu sun hallara,a dinning an yi saving din kowa abincin da yake so, Ammuh de bata fito ba dama can ita bata cin abincin su akan dinning se lokaci zuwa lokaci da Abbie yaga bata so se be ce lallai dole se tazo ba,haka ummah ma duk da ita tana fitowa amma bako da yaushe ba. Fatime na gama serving din su takaiwa Ammuh da Ummah nasu part din su. Ita de Sabriyah ta gama fahimtar akwai wani abu da ake boye mata,ba sa son ta sani,amma tunda LTG ya ce se ya dawo zataga Asmita to ita kuma ko karfe ɗari na dare ze dawo seta jirasa. Bata wani ci abincin sosai ba,ta cire hannunta ba wani yunwa take ji ba. "Ya kika cire hannunki"cewar Parsa. "Masoyiya na koshi Wallahi". Anty amarya dake gefenta bata ce mata komai ba, tasan dalilin ta be wuce rashin ganin Asmita bane. Dawood ne ya miko mata wayarta. "Yawwa ga shi na seta miki komai,daga icloud har updating din wayar na miki. Wayarki za ki iya fara amfani da ita.akwai kati a ciki sannan data kuma daga zaran kin kunna WiFi shikenan,bakya bukatar data gidan nan kowa WiFi dinsa yake budewa". "To na gode ya Dawood". "Don't mention ". Kallon wayar ta yi.tana Allah_ Allah su watse anan taje ta dauko takardan da ta boye,ta kira taji waye ne. Hira sukayi kafin Hajjatiye ta ce ita fa surutun ya ishe ta,ta barsu a falo taje ta kwanta. 9:00pm na dare ta fara motsawa alamar zata farka.dakyar ta samu ta daga hannunta da ya yi mata nauyi ta ɗan da fa kanta,ji tayi kan akwai bandeji gaba daya an zagaye sa dashi,ga wani uban ciwo da kan yake mata. Runtse idonta ta yi,tanaso ta tashi amma jiri ya hanata. Ta riga da tasan a inda take,domin lokacin da suka iso asibiti ta farfaɗo nan uncle Hameed ya sanar da ita yanzu za'a shiga da ita operation,allura akayi mata na bacci fuskar Saghar shine fuskan wanda ta gani kafin ta faɗa bacci. Hakan yasa a hankali muryanta baya fita sosai ta soma kiran sunan sa. "Me kyau!me kyau!me kyau"yana bakin kofa suna magana shida wani doctor ya ji kamar ana magana a cikin dakin. Shigowa ya yi ya sameta tana kwance idonta abude. Murmushi ya yi ganin ta farka. "Sannu ko,yanzu ina ne yake miki ciwo". Bata ba shi amsar tambayar da ya mata ba ta ce"Sabriyah ta zo ne!?". girgiza kai ya yi. Murya a hankali ta kuma cewa"meyasa batazo ba to me kyau !?",jin sunan da ta kirasa dashi ne yasa ya kalleta da kyau,wato wancan memoryn yarintar da ta shiga ba duka bane ya gushe ba,tunda ga shi still bayan ta dawo hayyacinta tana kiransa da me kyau. Ya ce"bata ma san an yi miki aiki ba saboda zata iya tayar da hankalinta amma gobe duk zasu zo dubasu da jiki"gyada masa kai ta yi. "Kai na!,na mini ciwo sosai kuma ina ganin jiri"zama ya yi a gefen gadon ya ce "ehh wannan normal ne,nan da wasu kwanaki za ki dena jin haka". Shuru ne ya biyo baya daga ita har shi babu wanda ya sa'ke cewa komai. "Me kyau ban san sunanka ba"batare da ya kalleta ba,ya amsa mata da "Saghar". Nan ma shuru ne ya sa'ke ratsawa, miƙewa ya yi ze fice,dan ya rasa meyasa duk lokacin da yake tare da ita se ya ji wani iri. "Ya Saghar tafiya zakayi ka barni ni ɗaya!?"ya tsinkayi muryarta tana tambayarsa. juyowa ya yi idonshi ya sauka cikin nata narkakkun idanun ta kafesa dashi tana kallonsa. Komawa ya yi,ya zauna yana kallonta. "Asmee dama kema matsoraciya ce!?". "Ah ah naga zaka tafi ne ai to" "Ke kuma bakya son in tafi?",sun kuyar da kanta ƙasa ta yi. "Kina bukatar hutu ne za'a miki allura,za ki yi bacci ba'a son ki dinga magana sosai"gyada masa kai ta yi. Yanda suke yiwa juna magana duk wanda ya kallesu ze yi tunanin sun daɗe da sanin juna,ko kuma akwai shakuwa sosai. Se karfe goma ya bar dakin nata se da ya tabbatar da ta yi bacci kafin ya fito.yana kashe mata light. Tana part din anty amarya idonta biyu ba tayi bacci ba tana jiran dawuwar LTG. Anty amarya ma idanunta biyu,ita kanta jiran LTG takeyi ya dawo, saboda duk sanda ya fita ya yi dare ita da Ammi in ba sunji dawuwar sa ba tofa basa iya bacci. Suna zaune tana ta koya mata wasu abubuwa.idanunsu biyu har sha biyu ya gota,nan ma shuru be dawo ba. Wayarta ta dauka ta kira layinsa sede switch off.hakan yasa anty amarya ta dinga addu'a Allah de yasa lafiya. Karfe 1:00 na dare motocin suka diro cikin gidan,anty amarya da Ammi da Abbie da suka kasance idon su biyu suna jiran dawuwar su sukayi hamdala. Dama ya saba duk sanda ya yi dare ita yake kira a kawo masa coffee. Suna zaune kira ya shigo wayarta ganin shine yasa ta daga. "Anty amarya coffee please"haka kawai ya ce ya kashe wayar. Miƙewa ta yi ta shiga kitchen din part dinta,cikin mintuna ƙalilan ta haɗa masa coffee, tunani ta fara zuwa ta tashi fatime ko kaltume,se kuma taga in ta yi haka kamar bata kyauta ba,duba da yanda suke yini suna aiki,dare ne kawai lokacin hutun su. Kallon Sabriyah dake ɗale akan gado ta yi ta ce"sa hijabi ki zo ki nan"dogon hijab din da ta cire akan gadon ta dauka tasaka har ƙasa yazo mata. Ba ta tray din coffee din ta yi,"ki kaiwa ya'yan ku Tajuddeen". "To"har ta kai bakin kofa anty amarya ta ce"karki kuskura ki kirasa da wannan mugun da naji kike kiransa,ya Taj haka su Umaisha suke kiransa"gyada kai ta yi ta fita. Knocking ta yi,ta ji shuru kusan five minutes tana tsaye can ta yanke shawarar shiga ciki kawai. Ba kowa a bedroom din da alama yana wanka. Ajiye coffee din ta yi akan Centre table.ta tsaya tana jiransa dan ta kudurci niyar tambayarsa ganin Asmita. Idonta ne ya sauka akan wani ƙaramin hotonsa da Asrah a jiye akan bedside locker. Nufan wajen ta yi tasa hannu ta dauki hoton kenan ta ji alamar mutum daf da ita.a tsorace ta juya,yana tsaye daf da ita distance din dake tsakanin su be fi taku biyu ba kwakkwaran motsi in ta yi jikinsu ze iya haɗuwa,ja da baya ta yi ta manne a jikin bango. Dan ta tsorata da ganin yanayinsa na yau fuskarsa kamar wanda aka yiwa mutuwa,hannu na rawa ta ajiye hoton a inda ta dauka. Yana sanye da rigar towel da ya rufe masa jiki kafafunsa ne kawai a waje. Kallon hoton da ta ajiye ya yi kafin ya kalleta. "Meye kike yi da wannan hoton!?"ya tambayeta yana matsowa kusa da ita. "Ya Taj kawai na ji ina son gani ne" Banzan kallo ya watsa mata kamar ze daketa. "Fita ki bani guri". Da sauri ta ce"to!to,ya Taj dan Allah inje in ga Asmita!?". "Fita ki bani guri"ya sa'ke maimaita mata. A maimakon ta fita din kamar yanda ya buƙata se ƙara tambayarsa da ta yi akan Asmita. "Gobe za ki ganta" Jiki a sanyaye ta ce "to". "Kina da tabbacin za ki kai goben ne?"cikin rashin fahimta ta ce "bangane ba". "Da kika ce to kawai,kina da tabbacin za ki kai gobene!?, Allah yakaimu ya kamata ki faɗa". "Allah ya kaimu". Ta juya da niyar fita a dakin hannunta ya rike. Ya ja ta zuwa gaban mirror wani magani me kama da makilin na kashe raɗaɗi, ya bata,ya sa'ke jawo ta zuwa kan gado. Umarni ya bata da ta hau ta zauna. Tana dar_dar ta hau jikinta na ɗan rawa,yana ankare da ita,tsaki taja. "Ubanme kike tunanin zan yi miki,da jikinki yake rawa haka".. Ita de bata ce mishi komai ba. Zama ya yi a gabanta ya juya mata baya. Ita de ta rasa gane me yake kokarin aikatawa,zame rigar towel din jikinsa ya yi. Zaro manyan idanunta waje ta yi gani ciwuka a bayan sa har waje biyu da alama da wuka aka ji masa su. Jin bata fara masa komai bane ya ce"ki shafa min mana". Hannunta na rawa ta matsa ta fara shafa masa kamar me tafiyan tsutsa,ita tsoro take ji karta fame mishi ciwo. Tana tunanin to aina ya ji wannan ciwo haka. Yau sun kama kuma sun kashe yan kungiyar Italian Mafia kusan mutane talatin a daji sun yi garkuwa da mutane rai bakwai se yan matan da suka kama,sun kai ashirin,da niyar yi musu fyade da kisan gilla su aikawa iyayensu. Nan ne major Marry ta samu information akan inda suke shine ta turawa LTG,shine fitan da sukayi shida sojojin sa. Sun kubutar da mutanen da yan kungiyar Italian Mafia suka kama gaba daya se yarinya daya da already sun yi mata fyade ta mutu. Bayan sun kashe na kashewa ne sun kama na kamawa sun sa a mota,wani daga cikinsu batare da sun san dashi ba yazo da wuka ta baya da niyar ya kashe LTG, Allah be basa Sa'a ba,ya yanke sa s waje biyu. Juyowa LTG ya yi ya damkesa,kamar wuyan kaza haka ya murde wuyan sa. Hankalinta ya yi gaba wajen tunanin ta yanda ya ji ciwo ta taɓa wajen ciwon. Sautin "ashhh" ya fitar saboda zafin da ya ji. "Dan Allah ka yi hakuri Wallahi ba da gangan bane". "Ki kashe ni kawai ki huta!,common shafa abu ne ba ki iya ba se wani shafe ni kike yi kamar wacce ta samu bayan kuliya". Ya faɗa a faɗace. Miƙewa ta yi,seda ta zo dede bakin kofa ta ce"tom sannu dama mutane irin ku ba'a musu gwaninta,gobe ko zakuna ne suka ji maka ciwo bazan taimaka maka ba".yi ya yi kamar ze miƙe ai kuwa ah million ta fice a part din. Kwafa ya yi yaba bayanta da kallo "matsoraciya kawai". Komawa part din anty amarya ta yi,ta samu ita take jira.bata tambayeta me ya rike taba. "Kije ki kwanta dare ya yi". "Seda safe mommy"ta faɗa tana daukar wayarta ta shiga daki na kusa dana anty amarya.key ta murza ta je kasan katifa da ta boye takardar tafito dashi. Loda number jikin ta yi a wayarta,cikin uku ya yi aka dauka. "Hello waye ne". Muryar mutumin daya fara taimakon rayuwarsu ta ji ya sauka a kunnenta,da alamun kuka yake yi. "My Sabriyah na yi kewarki sosai"hawaye ne ta ji ya taru a idonta. Under her breath ta iya furta. "Fu'ad!, da gaske kaine?". "Ni ne my Sabriyah,ashe zan sake jin muryarki kafin in mutu na dauka se a lahira zamu haɗu,ina Asmita, na yi matukar kewarku"ya faɗa yana kuka. Ita ma yanda taji yana kuka ne yasa ta fashe da kuka. "Fu'ad kana ina ne,meye abinda ya faru dakai bayan rabuwar mu,"sune tambayoyin da ta masa. Sa'ke fashewa da kuka ya yi "my Sabriyah, rayuwata tana cikin halin ha'ulayi.ina cikin masifa.wannan sojan da ya ɗauke ki ne ya kamani ya daureni kullum se an min azaba daban daban,abinda baki sani ba shine yasa aka dauke Asmita saboda yana son wannan memory nan a wajenta.ni kuma ya kashe min mamana da babana dan kawai ya nemi in faɗa masa in da ze same ku ni kuma naki.wannan dalilin yasa ya kashe min kowa nawa ni kuma ya min azaba wanda se da na rokesa da ya kasheni kawai". Komai ji ta yi ya tsaya mata cak gumi ya fara yanko mata, al'ajabi ya hanata magana,taya hakan ze faru ashe duk tashin hankalin da ta shiga akan Asmita da Fu'ad dama LTG ne ya sace su?,dama abinda yake kullawa kenan,. wannan tambayoyin ta dinga yiwa kanta. Nan take taji wani irin zazzafar ƙiyayyar lieutenant general Tajuddeen ya mamaye cikin zuciyarta,inda za'a bata wuka ko bindiga a ce ta kashe mutumin da ta tsana yanzu to shine wanda zata aika lahira. Ganin ta yi shuru ne yasa ya fahimci cewa,ta faɗa tarkonsa,domin ya yi imani da taimakon Sabriyah ze samu damar kashe LTG, muddin in bega bayansa ba tofa babu yanda za'a yi shirin su ya yu, saboda barnan da ya masa yau bana wasa bane,ya kashe masa mutane sosai. Cikin sheshekar kuka ya ce "my Sabriyah kina jina kuwa?". "Ina jinka Fu'ad, kawai na ka sa yardan wai ya Taj ze iya aikata hakan ne". "Sabriyah karki manta mugu bashi da kama,ze iya canza fuska duk yanda ya gadama". "Hakane kam, Wallahi natsane shi,ban taɓa kawo ze aikata min haka ba". Murmushi ya yi"yanzu kinsan taimakon da nakeso kimin". Kamar yana gabanta ta girgiza mishi kai. "Da taimakon ki zamu ka re mutane da yawa daga muguntarsa.dole ne mun yi hanyar da za'a kamashi yaje ya girbi abinda ya shuka.duk wani motsinsa ina so ki dinga sanar da ni,ki shiga jikinsa sosai ta yanda zamu dau fansar mu akansa.bincike za ki mana sosai akansa Kinga ke ce kuke gida daya,duk wani shirinsa daga zaran kin gano ki sanar dani". With full confidence ta ce"na maka alkawarin aiwatar da hakan Fu'ad".ji ta yi kamar motsi yasa ta kashe wayar.ta ajiye agefe. Jin bata sake jin motsin bane ya sa ta,kwanta tunani fal ranta, gaskiya ne maganar da Fu'ad ya faɗa mata shi mugu bashi da kama. Se juyi takeyi amma bacci ya gagara daukar ta har karfe hudu na dare idonta biyu. Yawancin ku baku san two pages nake haɗa muku ba, wanda hakan na nufin in an yi update yau, baza'a yi gobe ba se jibi. *🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹* Page 27 *_Story & written_* By *MRS🌹ISHAM🌹* ( Yar lelen Jarumai) *THE WRITER OF 🖋️* *NIDA PATIENT DINA* ~And now~ *🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹* 📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️ ____________________________ Page 27 Se da aka fara kiraye _kirayen sallah asuba ne bacci ya ɗauke ta.tasha kukanta san ranta hatta gaji. Anty amarya ta tasheta ta hanyar kwankwasa kofar dakin da take kwance,tashi ta yi ta bude mata. "Sabriyah lokacin ya yi" to "ta ce ta dauko hijab tabi anty amarya zuwa bedroom nata. Bayan sun idar da Sallah nan ne anty amarya take sanar da ita yau malamin islamiyya ze zo yake koyar da su, boko ma gobe zasu fara zuwa. Godiya ta yi mata Sannan ta hau kan gado ta kwanta dan kuwa ba ta gaji da yin bacci ba.ita ma kwanciya ta yi kusa da ita tana kallon yanda take bacci. Karfe tara suka farka bacci,wanka sukayi suka shirya zuwa dinning ita de Sabriyah hijab ta saka dan yanzu dadinsa takeji. Bedroom din uncle Hameed anty amarya ta nuna mata kafin su fita. Shiga ta yi ta sameshi yana zaune akan sallaya da alamu tunda suka dawo daga masallaci be koma bacci ba. Zama ta yi a kasan carpet tana gaisheshi. "Ina kwana daddy" Sunan da ta kirasa dashi, ya ji dadi sosai,tun bayan ɓatar Asrah ba'a sake kiransa da daddy ba. "Lafiya klau sab,ya mommy ki!?" "Tana Lfy lau, lokacin karyawa ya yi"murmushi ya yi, ya ce "to muje ko!?" Ya mike suka fito a tare suka samu anty amarya tana tsaye inda ta barta. Dinning suka shigo suka samu an gama serving din breakfast,kowa na wajen da murmushi suke kallonsu sun yi kyau gwanin sha'awa family. Zama suka yi,ana cikin cin abinci Hajjatiye ta soma magana. "Nikam meye ya hana, khareema da Huraira zuwa cin abinci cikin mutane sun maƙale a part din su kamar wasu munafukai,ko har yanzu khareema na nan da ba ƙin halinta nakin zuwa a ci abinci da ita"ta yi maganar tana tsare Abbie da ido. Abbie bawan Allah gaba daya ya ma rasa ta ina ze fara sanarwar Hajjatiye da Ammuh bata cin abinci kwata_kwata da kowa,ba dan ya so ba ya mata karya ta hanyar faɗin. "Hajjatiye!, khareema yau da ciwon kai ta tashi" Dogon tsaki Hajjatiye taja ta ce. "To waye ya damu da tsiyar tsinantakar ciwon kanta,mu din aka ce mata,wani lafiyar ne garemu ai sede kawai a ce Alhamdulillah,to Wallahi kar ta kuskura a sa'ke zuwa cin abinci ba ta nan ran kowa ze ɓaci". "In sha Allahu, hakan baze sa'ke faruwa ba".cewar Abbie,dan ya lura Ammuh na son ja mishi magana ne a wajen Hajjatiye.dole ya taka wa rashin fitowarta burki. Ta maida kallonta kan Abbu,kafin ma ta yi magana ya ce. "Hurairah bansan me ya hana ta zuwa cin abinci ba". Tabe baki ta yi, "To ai dama iyayin su daya,ita da khareemar". Su de sauran cin abincinsu suke yi suna saurarar abinda ke faruwa. "Kuna gama cin abinci duk za mu tafi asibiti,bana son African time"Hajiya babba ta faɗa tana rufe plate din gabanta, alamar ta kammala cin nata. Shurun da taga kowa ya yi basu tambayi waye a asibiti ba,yasa ta fara tunanin to waye ba lafiya. Se kuma ta yi tunanin ko LTG aka kai asibiti tunda jiya bashi da lafiya. Tabe bakinta ta yi, acikin zuciyarta ta yi maganar amma bata san cewa ya fito fili ba. "Allah yasa ma shine"kallonta aka yi nan ta fahimci an ji abinda ta faɗa sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tana wasa da spoon. Hajjatiye ta ce "sanariya ke da waye haka". innalillahi ga dariya ga kuma basu isa su yi shi ba yanzu se ran kowa ya kusan ɓaci a wajen,wai sanariya, Sabriyah din ne bata iya faɗa ba take cewa sanariya. Salim duk yanda ya so rike dariyar sa,abin ya gagara se fa da ya kwashe da wani dan banzan dariya kai kace wani zararre ne. Cikin basaja ya soma faɗin. "Haba Fatime taya za ki sakamin ruwan tea da yawa duba kiga duk na shanye,ashe zan iya" maganar yake yi amma dariya ya ci karfinsa. Kowa na wajen ya gano sa.banda Hajjatiye. Watsa mishi harara Abbie ya yi,irin zamu haɗu din nan. Dakyar ya tsagaita da dariyar. Hajjatiye ta ce"amma yaron nan an yi ja'iri, saboda kawai ruwan shayi ya yi yawa ka shanye ne yasa ka wannan dariyar,to zakaci kwal ubanka dakai da tsiyar tsinantakar ruwan shayin". Tashi kawai ya yi yabar wajen dan ya lura inde Hajjatiye tana magana tofa baze fasa dariyar ba,har ta gano ita yake yi wa dariya,ga kuma kallon da yaga Abbie na yi masa. Kammala breakfast din aka yi suka dawo falo suka zauna,anty Sameera na rike da baby a hannunta. Ta cewa su Zoya. "Ku din kun shirya ne" "eh a shirye muke"duk suna sanye da hijabs. Sabriyah de yau ba wani son yin magana take yi ba domin abinda ta ji, jiya dashi ta kwana a ranta,duk tunaninta yanzu ya koma ne ta kan ta ya zata fara sanin menene abinda LTG yake shiryawa.shin taya zata shiga jikinsa yanda zata dinga sanin duk wani abinda yake shirin yi. "Sanariya!,zo ki kira LTG kice mishi,zamu je asibiti"Sudais ya faɗa,yana tsokanar ta.murmushi ta yi dan ta gane tsokanar ce,wato Hajjatiye de ta sa mata wani suna daban. Ba dan ranta yaso ba ta mike tana tambayar kanta "dama ba ya Taj bane a asibitin ba!?,to waye ba lafiya haka!?",da wannan tunanin ta shiga part din nashi ,ko sallama ba tayi ba ta kutsa cikin bedroom dinsa. Baccinsa yakeyi gently,his innocent face looks so cute. Yana cikin bargo ya rufe ko ina a jikinsa, fuskarsa ne kawai a waje. "Mtsssw!a kwai kyaun fuska kam,amma babu na zuci.mugu kawai".ta faɗa a ranta. Karasawa jikin gadon ta yi da niyar tashinsa a bacci da yake yi.wani tunani ta yi. "Uhmm,yanzu ina tashinsa ze hau ni da faɗa kamar wani ubana,gwara in je in samu ya Sudais in ce masa,ya ce bazeje ba kawai "ta faɗa a hankali. Tana gama faɗar maganar,ta ji an ja hijab din ta,a tsorace ta kai idonta kan fuskarsa domin ita ta ɗauka ya farka ne ya rike mata hijab,ashe cikin bacci ne ya juya ya daura kansa akan hijab dinta,da bata san ya aka yi ta daurasa kan gado ba. A hankali ta sa hannuta ta fara kokarin jan hijab din nata yanda baze tashi ba.tana kallon kyakyawar fuskarsa,a lokaci daya kuma tana jan hijab din ta. A cikin bacci yasa hannu ya riƙo hijab din nata gam a hannunsa ya cigaba da bacci. Zaro ido ta yi ta bude baki ta ce"na shiga ukuna,yau in ya Taj tashi se ya kasheni"ta yi maganar idonta ya fara raina fata. Wani irin juyi ya yi da,wanda kafin ta ankara taji ta gaba daya ta faɗo jikinsa. Ji ta yi kamar zata yi fitsari a wando.ta rasa wata kalma zata yi amfani dashi wajen ceton kanta in LTG ya farka ya gansu a haka. Jin mutum ya faɗo kansa ne,yasa ya bude manyan rikitattun idanunsa da sukayi ɗan yi ja saboda baccin da be samu a wadace ba, hatta golding eye balls din seda suka ɗan canza kala. Idanunsu ne ya sarke cikin na juna.bakaramin tsorata ta yi ba da ganin idonsa ga kuma irin kallon da yake mata,babu abinda take tunawa irin rabuwar da sukayi daren jiya ga shi yanzu ta kawo kanta da kanta. Shi kuma kallon da yake mata,kallon me yakawo ki dakina har kan gado na. Hannunsa yasa ka ya rike ta gam yanda bazata samu damar guduwa ba,tana kwance akan kirjinsa, fuskarsu na fuskantar na juna. Bude baki ya yi ze yi magana,tsoron jin abinda ze furta mata ne yasa da sauri,tasa yatsan ta,guda daya ta daura akan libs din sa.tana kallon cikin idanunsa,saukar da idonsa ya yi ya kalli hannunta da ta daura masa akan libs,watsa mata harara ya yi,duk da hakan bata cire ba. "Ya Taj,an ce ne in zo in tasheka zamu je asibi.....". Wani mugun kallo ya watsa mata da ya sa ta gagara karasa maganar da take masa. Hannu yasa ya janye yatsan nata ya maida shi baya ya matse, ƙara ta sa sakamakon zafin da taji ya ziyarci hannunta. "Kirana kika zo yi shine se kin hau har kan gado na!?"ya tambaye ta murya a narke ba kamar yanda ya saba yin magana ba. "To ai na baka hakuri"ta faɗa tana murguɗa masa baƙi,tsurawa dan karamin baƙin nata da take murguɗawa ido ya yi,yana jin kamar yasa almakashi ya gimtse sa. "Tashi a jikina,wato kinga farar fata, mekyau yana shining, shine za ki kwanta akai,yafi na wa'yannan nan kazaman yan iskan samarin naki".tura baƙi ta yi jin abinda ya faɗa. "Bazaki tashi min a jiki bane,ko se na yi wurgi dake tukun nan!?"ya faɗa yana jefa mata harara. Kamar zata fashe da kuka dan takaici,ta ce"to ka sa'ke ni mana". Kura mata ido ya yi,yaga yanda ta ke mutsu_mutsun kwatar kanta.da hannunsa guda daya ya rike ta amma ta gagara kwacewa. "Meye kike shiryawa!?"kamar saukar aradu haka taji tambayar ya sauka a kunnenta,dago idonta ta yi,cikin tashin hankali,murya na rawa ta ce"bangane abinda kake nufi ba". Murmushin gefen baki ya yi irin na bakida hankali, ya ce"ina saurayin naki yake!?,ina guje miki yin aikin danasani saboda rashin sanar da ni inda yake dede yake da jefa rayuwar ki, cikin hatsari,ni rayuwata,na ƙasa ta ce,in na mutu nayi shahada,amma ke in mutum daya ya mutu ta dalilin ki,to se Allah yabiwa wannan bawan nasa hakkinsa,je kiyi tunani akai".gaba daya ya kashe mata jiki da maganganunsa,kenan hakan yana nufin ya san tayi waya da Fu'ad kenan?,taya akayi ya san abinda suke shiryawa. Meye hakan yake nufi to, Fu'ad ya sanar da ita cewa LTG shine yake kokarin zaluntar al'umma,shi kuma LTG ya ce mata,in mutum daya ya mutu ta dalilinta se Allah yabiwa wannan bawan nasa hakkinsa. Har ya sa'ke ta bata ma sani ba,ta faɗa duniyar tunani. Ɗagata ya yi a jikinsa ya tashi zaune ya barta akan gadon,miƙewa tsaye ta yi,jiki a mace. "Kai ma ai zaluntar al'umma ka ke kokarin yi,ka kuma cutar da ni,da yar uwata". Be kalli inda take tsaye ba ya bata amsa da. "Ke ba ki kai matsayin da zan tsaya ina miki bayani ba,je ki yi duk yanda kika gadama". Da gudu ta fice a dakin,tana gudu numfashinta na sauka da sauri sauri,kirjinta ya rike,sun sa ta a tsaka me wuya,yanzu da maganar waye a cikin su tasan zata yi amfani?. Bayan balcony ta je in da babu wanda ze ganta,ta zube akan guiwowinta tana maida numfarfashi. Se da ta kusa 20minute a haka kafin ta samu nutsuwa. "Ko ma me ze faru sede ya faru amma bazan taɓa juyawa Fu'ad baya ba, wannan alfarma ne da ya nema a wajena taya zan watsa mishi kasa a ido in ƙi cika masa burinsa na son ganin al'umma tasamu zaman lafiya". Ita kadai take magana kamar wata zautacciya. Se da ta gama samun nutsuwa kafin ta mike ta koma main part Sudais, yana ganinta ya ce"Sabriyah ai na kika tsaya ne!?,ina LTG?"jiki ba kuzari ta ce "ya ce wai baze je ba". Gyada mata kai ya yi. Shiga motar sukayi suka wuce asibitin. shigowar su dakin da aka kwantar da Asmita sun samu ta na jingine da filo.Saghar na gefenta ga kuma fruit agabanta,tasha kadan ta bari,jin sallamar su ne yasa suka maida idonsu baƙin kofar. Mamaki da al'ajabi lokaci daya ya kama Sabriyah ganin Asmita kwance akan gado ga kanta dake nade da bandage,da gudu ta shigo dakin,ta zauna akan gado, bata gajiya da kallon Asmita da itama din ita take kallo.wato wayo sukayi mata,su ka dinga ce mata Asmita na hutawa,ashe basa son tasan an yi aikin ne. "My Jerry yaushe akayi miki aikin?,yanzu ya kike jin ki!?,me yake miki ciwo yanzu!?, sannu kinji".ta watso mata tambayoyi ba tare da ta bata damar amsa mata ko daya ba ta sa'ke cewa. "My Jerry,kanki ba ya Miki ciwo ko!?"murmushi kaɗan Asmita ta yi. Murya na fita a hankali ta bata amsa da. "My Tom ina lafiya". Zata sake yin wata maganar Saghar ya dakatar da ita ta hanyar faɗin. "Ba'a son ta dinga magana sosai". Gyada masa kai ta yi tana riƙe hannun Asmita. Sannu su kayi mata da jiki kafin suka zauna suna. Har karfe hudu na yamma suna tare a asibiti mazan kuma sun tafi wajen aikinsu. Kullum se sunje asibiti duba jikin Asmita, Alhamdulillah jikinta yana sauki sosai, Sabriyah ta fara zuwa school an sa ta a jss 2,an samo malamin da yake koya mata karatun addini a gida,kuma ba laifi tana ganewa sosai da sosai.in ta dawo gida kuma su Parsa haka suke haɗuwa su sa'ke koya mata duk wani abinda bata gane ba,sune malaman lessions din ta. Bayan wata daya, abubuwa da dama sun faru,mom Rumanatu ita da yaranta sun koma katsina.an sallamo Asmita daga asibiti jikinta ya yi sauki,har ta fara maida kibanta,sunci gaba da zuwa makaranta tare da Sabriyah sun yi kyau sosai sunyi fresh sun zama yan gida su ma,duk abinda za'a yiwa su Rameesa tare ake yi musu.kullum se ta yi waya da Fu'ad idan ta tabbatar da kowa ya yi bacci,duk da ta rage alwashin da ta dauka akan LTG domin taga duk tunaninta, LTG ya take ta ya shanye,ita yanzu tsoro ma yake bata,wani abun kamar akan idonshi takeyi hakan yasa ta watsar da mukaman ta,duk da haka Fu'ad be dena in gizata ba.duk da yaga yanzu ita ta karaya.wannan dalilin yasa ya sake sabon mugun shiri. Daga LTG, Sudais, ACP Jawan duk busy ya musu yawa kullum karfe shida na safiya suke fita,su dawo tara ko goma LTG kam yana kaiwa har karfe daya wata rana ma baya kwana a gidan.aiki ya sha musu kai suna nan suna dakon shugaban kungiyar Italian Mafia,domin any moment ze iya yin abinda yace ze aikata. Wannan dalilin ne yasa rabon da Sabriyah tasa LTG a idonta hatta manta domin yakai kusan sati biyu rabon da taga ko da gilmawarsa,sede tana yawan ganin major Marry. Yau Friday tun 12:00 aka tashe su daga makaranta driver yazo ya maida su gida.suna shiga suka ga samarin gidan gaba daya cikin fararen shadda ɗinkin half jumfa bakaramin kyau sukayi ba,sun shirya zuwa masallaci tare da su Abbie da Abbu, uncle Hameed,suna zaune da alama akwai wanda suke jira ya fito. Tunda suka shigo cikin falon Saghar da Asmita suke satan kallon junansu.uniform din jikinta da ta saka ne yau yasa ya ji kishi yakamasa ransa ya ɓaci ya rasa dalilin da yasa ranshi yabaci dan yaga Asmita da uniform din bayan kuma Sabriyah ma shine a jikinta amma be ji hakan ba,kuma su Rameesa ma makarantar sukayi amma be taɓa jin akwai wani abu dangane da uniform din ba se yau da ya gani a jikin Asmita. Riga da wandon spot Wear ne wandon yana da fa ɗi,haka rigar ma yana da girma kadan da kauri,irin kayan yan kwallo,sun saka baby hijab.ga school back din su dake rataye a kafadarsu. Kauda idonsa ya yi daga kanta ya fuske kamar be ganta ba. Shigowa sukayi wajen su, suka gaishe su cikin girmamawa. Murmushi Abbie ya yi "sannunku da dawuwa yan boko,kun sha gajiya kam"su ma murmushin suka yi, Asmita ta ce "Abbie ai ba wahala,kawai de zama"dariya sukayi. ACP Jawan ya ce "to ai babu maraban dambe da faɗa" "tom wannan waya gaya maka Hausa ya ishe ta ɓalle ta san me kake nufi"cikin zolaya Sudais ya faɗi haka. Shagwabe fuska ta yi "Abbie ka ga ya Sudais ko!?" "Kyaleshi kishi yake yi dan kina zuwa makaranta shi baya zuwa".dariya Sabriyah ta yi jin shirmen Asmita.ga Abbie ma da ya biye mata. Duk yanda tasan zata yi Saghar ya kalleta ko za ta samu nutsuwa amma abun ya ƙi,tunda ya sunkuyar da kansa kasa yafara danna wayarsa be sa'ke dagowa ba. Fitowa ya yi falon yana sanye cikin farar danyen shadda half jumfa ,me tsadar gaske,an yi mishi aiki na alfarma,yana sanye da bak'ar takalmi,ga Rolex wrist watch daure a hannunsa.kan sa babu hula se gyararren bakin sumar kanshi da yasha gyara yana sheki da daukar ido.ga baƙin tsadadden sun glass manne a fuskarsa,ya ƙara ƙawatar da fuskar. Ya yi kyau sosai me matukar nutsuwa da daukan hankali,duk yanda ka kai ga kamewa,idan ka masa kallo ɗaya se ka ji sha'awar sa'ke daura ido a kan sa,ga daddadar Kamshin turaren dake tashi a jikinsa. Tunda ya shigo falon Sabriyah ta kasa dauke ido akansa,bata taɓa ganin sa da manyan kaya ba se yau,se ta ga manyan kayan ma sunfi mishi kyau da karban sa. "Tajuddeen manyan kaya suna maka kyau sede bakason sawa"Abbie ya faɗa yana dafa shi. Kallon Abbie ya yi be ce komai. Haɗa ido ya yi da Sabriyah dake satan kallon sa, harara ya watsa mata. Tabe baki ta yi,magana kawai ta yi.ba tare da kowa ya ji ba iya labban bakinta ne yake motsawa yanda iya LTG ne ze ganta ta ce. "Ko kyau bakayi ba,ka dena wani yanga,kanajin kanka na wani girma". Hannunsa yasaka a wuyansa ya mata alamar se na yanka ki. Dariya ma yabata.yanda ya mata alama da ze yankata ne abin yasata dariya. Tana dariya ta ce"to se kun dawo Allah ya kiyaye hanya, Abbie, Abbu, daddy,amana addu'a " "in sha Allah "suna bata amsa ta haura part din su Asmita ma tabi bayan ta. Abbie da Sudais su kadai ne suka lura da abinda LTG da Sabriyah sukayi,su kansu abin nasu ma dariya ya basu, wato tsakanin LTG da Sabriyah babu shiri. Ko wannensu motarsa ya shiga driver yaja su , sojoji da kuma da polisawa da securities ne suka musu taki har masallacin. Suna shiga dakinsu suka tarar da su parsa a ciki,suna taɗi, hiran wani saurayin da Zoya ta yi jiya sukeyi,suna dariya. Ɗago kai sukayi dukkansu, dama zaman jiran dawuwar su, sukeyi su basu labari. Cikin dariyar mugunta Rameesa ta soma cewa "gwara da Allah yasa kuka dawo yanzu" cire hijab din kanta Sabriyah ta yi,dama bata saka hula ta ciki ba gashin kanta baki wuluk na daure da ribbom babba ja. Ta ce"ai ke Rameesa in an ga kina irin wannan yar iskar dariyar taki tofa abun mugunta ne ya samu"sa'ke tuntsirewa ta yi da dariya. "Dadina da ke Sabriyah akwai ki da gane abu.kinsan jiya Zoya da iklas sun je gidan ya Abbas,to wai su iyayen kinibibi suka fita siyan abu waje,a hanyar dawuwar su ne suka haɗu da wani wai yana son Zoya.nan ya fara cika su da surutu kamar wani aku.Sau uku suna ce mishi zasu tafi amma yana dakatar dasu,har ya kure hakurin Zoya,kin san mutumiyar taki,nan fa ta mishi tas bata raga masa ba!"dariya Asmita da Sabriyah suka kwashe harda tafawa. Asmita dake cire safar ƙafarta ta ce"haba ke kuwa Zoya,kin yi saurayi amma shine zaki kora shi da masifarki".galla mata harara ta yi,"ku fa baku da hankali. dan de baku gansa bane Wallahi kamar wani ɗan shaye_shaye". Haka suka ta hirarsu,suna shan dariya, Zoya har kwatanta musu yanda saurayin yake magana yana wani buɗe ƙafadata kamar wani boss take yi,su kuma suna kallonta kamar sun samu Tv suna dariya. Daga masallaci ACP Jawan station ya wuce saboda kiran da DPO yake masa ya wuce misali.jikinsa ne ya bashi akwai abinda yake faruwa,shisa ana idar da sallah ya wuce direct station. Yana shiga yaga yan sanda se shige da fice suke yi. Yana shigowa suka sara mishi. Office dinsa ya wuce ya samu waje ya zauna.shigowa DPO ya yi da tarin files a hannunsa da a ƙalla zasu kai guda goma zuwa sha wani abu. Sara mishi DPO ya yi kafin ya fara magana "ACP!yau tunda garin Allah ya waye muke ta karban cases din kidnapping,i zuwa yanzu an yi kidnapping mutane sama da goma.shisa nake ta kiran ka,this is getting out of hand ACP".Shuru Jawan ya yi yana wani tunani,inde tunanin sa ya bashi dede to wannan aikin Italian Mafia ne. Kallon DPO,ACP Jawan ya yi kafin ya ce"have a sit"zama ya yi yana"thank you sir ". Danna kira ACP Jawan ya yi ya kira, commissioner a waya suka yi magana ya sanar dashi halin da ake ciki. Suna cikin yin magana,wata mata ta shigo station din tana kuka haɗe da kururuwa.ta cika station din da kuka. Tambayarta kurtun yan sandan sukayi nan take sanar musu da yaranta mata guda biyu da ta mallaka a duniya an yi garkuwa dasu. Da sauri wani dan sanda ya shigo office din ya sanar dasu. Fitowa suka yi ACP Jawan ya taimakawa yar dattijuwar ta mike ya zaunar da ita akan kujera yana lallashinta,da bata karfin guiwar cewa da yardar Ubangiji za'a ga yaranta. *🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹* Page 28,29,&30 *_Story & written_* By *MRS🌹ISHAM🌹* ( Yar lelen Jarumai) 📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️ Three in one Page 28,29&30 Rubuta report matar ta yi sannan ACP Jawan ya bada umarni aka mayar da ita har gidan ta. Da haka shima ya koma gida bayan yasa yan sanda sun fara binciken yaran da aka sace. Karfe 5:00 dede ya iso gida polisawa suka bude masa kofa,yana fitowa suka sara mishi fara tafiya ya yi suka yi kokarin mara masa baya hannu kawai ya daga musu, dakatawa sukayi suna "Yes sir". Ko part din sa be shiga ba ya wuce na LTG nan ya samu baya nan,ga shi tun yana office ya ke kiransa be yi picking ba,dama LTG haka yake in ba wai shi ya kiraka ba tofa in ka kirasa ma,abanza domin baya daga kira se in ya zama urgent and important. Koma wa nashi part din ya yi,wanka ya fara yi sannan ya sauya zuwa ƙananan kaya. ACP Jawan da LTG suna tsananin kama da juna sede abinda ya bambanta su shine, kwayar idonsu ya sha bambam dana juna LTG nasa golding eye balls wato Hazel eye balls,which is the combination of green, brown,gold.yake dashi wanda ya gado a wajen kakar su Ammi da anty amarya,hatta farinsa ma irin na turawa ne da kuma sumar kanshi,while ACP Jawan nashi kwarya idon sa brown ne shida Umaisha. "Me yasa ke dakikiya ce kam Naziya!?,ke kullum a ce bazaki nutsu ki san ciwon kan ki ba!?,to ko mutuwa zakiyi se kinzo Maiduguri kuma bazan taɓa canza abinda na yi niya ba,gwara ma ki rufawa kan ki asiri ki zo ki dangwali arziki ki barsa a inda yake,in kika auri Tajuddeen ai ba ma mu kadai ba,gaba daya danginmu sun warke,amma tsabar doloncin da ke damun ki,kin ƙi nutsuwa ki bani haɗin kai.to na riga da na gama magana ta gobe_goben nan za ki ta ho.saura kuma ki zo ki dinga nunawa mutane wannan shegen sanyin halin naki"ita de tunda antyn nata ta fara magana kawai jinta take yi amma ita ko kadan bata son zuwa musamman ma da tasan manufar da ake son amfani da zuwan nata.ita ta riga da tasani ko mutuwa zatayi tasan bata ishi LTG kallo ba ɓalle har ya ce ze aure ta shisa ta ke ajiye kan ta inda Allah ya ajiye ta,ko zuwa Maiduguri ma sau biyu kawai ta taba zuwa. Cikin sanyi murya irin na ta,ta soma magana. "Anty khareema da kinyi hakuri da wannan burin na ki,ni takura min kikeyi,tun ba yau ba,kinsha min wannan maganar amma na nuna miki banida wannan ra'ayin.mijin da zan aura har gida ze zo ya sameni in sha Allah,amma kin dauki buri da son abin duniya kin daurawa kan ki.ki ji tsoron Allah anty khareema.ni de bazan zo abanza ki dinga ja min wulakanci ba". Cike da Masifa da ya rufe mata ido ta ce"kam uban can dan uwarki Naziya Ni ki ke cewa in ji tsoron Allah?,in ban ji tsoron Allah ba tsoron ki zanji,yar iska bagidajiya,kar ki ga dan kina kanwata kice zaki faɗa min maganar banza in kyale ki,yar karamar ƴata ita ce sa'ar ki!,amma saboda reni ya shiga tsakanina dake har ina magana kina bani amsa ko Naziya???".ya mutsa fuska ta yi kamar tana gaban Ammuh din. A hankali ta ce"ai dama ita gaskiya ɗaci gareta,to nide banaso babu yanda za'a yi in yarda kiyi mini dole akan wanda baya sona baya ra'ayina, shine kawai anty khareema". Ummah dake gefen Ammuh suna saurarar abinda ta ke faɗa, domin wayar na a handsfree. Ta mata alama da ta danne fushinta, ta lallaba Naziya din wuyarta tazo ne ai. "Shikenan yar kanwata yanzu de mu bar maganar Tajuddeen ki shirya gobe ki zo ki kawo min ziyara". "Ni fa anty khareema na san halinki kawai de wayo kike son ki min, Wallahi in na zo bazan wuce sati daya ba zan dawo,taraba!". Haɗiye bakin cikin da ya tokare mata wuya ta yi, saboda inde ta ce zata tsaya suna sa'insa da Naziya tasan ba zuwa zatayi ba. "Shikenan na amince yanzu zan tura miki 100k a account din ki,ki biya kudin motar". Tabe baki ta yi ta ce"to Allah yakaimu goben da rai da lafiya ". Ko amsa mata ammuh ba tayi ba ta kashe wayar dan haushin Naziya take ji,ita halin ta daban, se ka ce ba ciki daya suka fito ba.komai se ta dinga nuna tsoron Allah da kuma tausayi se kace tafi kowa,ga shi ita kuma ta kwallafa rai akan se ta haɗa LTG da Naziya aure,ita kuma Naziya na kokarin ba ta matsala.. Dafa ta ummah ta yi"haba Hajiya khareema,ke yanzu a ganinki in kina binta a haka kina tunanin zata yarda ta zo ne?,lallabata yakamata kiyi,kin tsaya kina mata tsawa da Masifa, ba kin san yaran yanzu ganin kansu suke yi dede da na kowa ba . abu me wuyar shine ta zo gidan nan, muddin ta riga da taxo tofa magana ya ƙare,duk da naga ita ma Naziya akwai taurin kai in ba haka ba,ana nuna miki hanyar arziki amma kina kaucewa tsaban yarinta da hauka". Ajiyar zuciya ammuh ta yi,ita da ace tana da wata karamar ƙanwa tofa babu abinda ze sa ta tsaya bata lokacinta akan Naziya.tun ba yau ba suke kai ruwa rana da ita akan cewa tana son ta auri LTG amma ta nuna sam ita bazata auri wanda baya son ta ba. "Ke de bari kawai Hajiya hurairah na daɗe banga jakar yarinya mahaukaciya ba irin Naziya. wai ni ina dubawa kanwata yanda rayuwarta ze yi kyau, amma wannan yar iskar yarinyar tana kokarin watsa min kasa a ido.ni banida matsala da Tajuddeen tunda da boka mauzau zamu haɗa sa Kinga kuwa ai soyayya shi da ita dole". Ta yi shiru tana girgiza ƙafarta dake daure akan daya. "Yanzu de bari ta zo din se mu ga ya abin ze kasance".cewar ummah. Suna tsaka da magana masoyiya Parsa ta shigo dakin da wannan murmushin nata kwance akan fuskarta ta zauna tana me kwantar da kanta ajikin Ammuh.dakatawa da maganar sukayi saboda shigowar ta. "Parsa daga ina haka"kallon ammuh ta yi ta ce "Ammuh ina falone, dama ina so in gayawa ummah gobe zamu je gidan anty Sameera ne nidasu Umaisha"haɗe fuska Ammuh da Ummah sukayi jin sunan da ta kira"meye zakuje yi gidan Sameera?",da mamaki ta kalli Ammuh kafin ta kalli ummah. "Ziyara zamu kai mata tunda gobe weekend ne so i thought that was a good idea". "To naji amma bazaku je gobe ba se next week,yanzu kije ki huta". Murmushi ta yi ta ce"to ummah"ta shiga bedroom din Ummah ta kwanta. Bin bayanta sukayi da kallo, Ammuh ta ce"Hajiya hurairah kinsan me nagani kuwa!?"girgiza mata kai ummah ta yi. Ammuh ta sa'ke cewa"me ze hana mu haɗa Parsa da Salim aure,ni a ganina sun yi matukar dacewa".jimantawa ummah ta yi kafin ta ce"to ai ba mu san ko suna ra'ayin juna ba,sede mu tuntube su". "Eh hakane kam in sha Allah zan yi wa,Salim din magana ke ma se kiyiwa Parsa din "cewar Ammuh. A haka suka bar maganar tasu.(lallai kam, sunan wani abu wai kwamachala.parsa na son Sahil,nan kuma Ammuh da Ummah suna shirin haɗa ta da Salim). Zaune suke a falon su,sun nutsu suna yiwa Asmita da Sabriyah lessions. Kusan tsawon awa daya suka kwashe kafin nan suka gama,kai school bags din su bedroom sukayi suka dawo. Asmita da take fama da ciwon kai ne,ta zauna tana daura kanta akan kafadar Sabriyah. tunda ta ga haka ta san akwai abinda yake damunta. Shafa kanta ta yi "my Jerry meyafaru ne naganki haka!?". "Kai na ke min ciwo sannan kuma se in dinga ganin jiri na son kwashe ni". Rameesa da hankalinta ya tafi gaba daya wajen ganin wani memes na abun dariya a facebook ta ce "kinsan dama you're still under medication dole wata rana kiji irin haka,in ya tashi miki Kisha maganinki se ki samu ki kwanta ki huta". Miƙewa Sabriyah ta yi,da niyar ɗauko mata maganinta tasha,ta rike hannunta. "Maganin wajena ya ƙare,sede bansan ko akwai a wajen ya Saghar ba". "Eh shikam baze rasa ba"Zoya ta faɗa tana tapping bayanta. Maida kanta kan cinyar Zoya Sabriyah ta yi,ta fice a falon ta nufi part din Saghar sallama ta yi hatta gaji amma bata ji alamar mutum ba,hakan yasa ta nufi downstairs, Hajjatiye kawai ta samu anan. "Barka da hutawa Hajjatiye ". "Yauwa sanariya,wa kike nema haka!?". Yar guntun murmushi ta yi sannan ta ce"ya Saghar nake nema zan ƙarɓawa Asmita maganinta ne". Kamar wani abun tashin hankali ne ya faru Hajjatiye ta soma salati tana riƙe haba. "Yanzu abinda Saghar din yake aikatawa har ya kai haka,ohh ni hajja yau ni naga bak'ar mugunta, yarinya ba lafiya amma ya bata magani ma abu ya faskara ". Baki a bude take kallon Hajjatiye jin yanda ta juya fahimtar maganar daban ita da ta ce tana neman sa ta ƙarɓawa Asmita magani,amma Hajjatiye tana wani magana daban yanzu wani in ya ji ai se a yi wani tunani daban. Saukowa downstairs ummah ta yi ta ji abinda Hajjatiye take faɗa ga Sabriyah a gabanta nan take ta ji ranta ya ɓaci. "Yanzu har kin samu damar da zaki iya kawo kar'ar ɗana dan kawai be bawa wancan kazamar magani ba,saboda yana taimakon ku yana dubata.shine har zaki samu kwarin guiwar kawo kar'ar ɗana?,da ma ɗan Adam butulu ne ba'a iya masa,duk yanda za'a yi wajen kyautatawa mage tofa bazata gani ba".tun da kika zo gidan nan dama naga kanki na wani fisga yana hayaki, wannan dalilin yasa, na ke kauci rashin kunyar ki,amma yanzu dole in taka miki burki tunda har yakai ki fara kawo kar'ar ɗan masu gida shida gidan ya kasance na ubansa ne. ku kuma fa taimakon ku akayi a ka bar ku anan amma yanzu dole zaman ku ya ƙare anan". Jikin Sabriyah ne ya yi sanyi dama ita tasan in ba wai mutum me fahimta ba,ze yi wuya duk wanda yaji yanda Hajjatiye take mayar da magana ya fahimci kan zancen,dole za'a ga kamar kar'ar Saghar din ta kawo wajen Hajjatiye. "Ummah kiyi hakuri ki fahimce ni bawai kar'ar ya Saghar na kawo ba. kawai ina neman sa ne in ƙarɓawa Asmita magani"daga mata hannu ummah ta yi alamar ta dakata bata son jin komai. "Rufe mini baki bak'ar munafuka ke yanzu ki dubi kan ki, yanzu da kuma yanda kukazo gidan nan a tsiyace a wulakance wanne ku kafi kyau?,yau har kin yi gogewar da za ki iya taka ɗan masu gida!?,kina karuwa dake dube ki fa,mara asali, wacce ta gama rabarwa mazan titi kanta,da ke da wancan mahaukaciyar yarinyar yau din nan zaku bar gidan nan tunda ba gidan uban ku bane". Jin yanda take goranta musu da aibata su ne yasa Sabriyah ta fara kuka, maganganun ummah ya so sa mata rai ta ci mutuncin su ta tozarta su. "Yi mini shuru mara mutunci yanzu Huraira ko kunyar idona bakiji ba kika tsaya kina gorantawa yarinyar nan,anya kina da hankali kuwa?,". murmushin takaici ummah ta yi"Hajjatiye kenan dama ai bayansu zaki bi yaran da suka fito daga gidan karuwai ai babu abinda bazasu iya ba dan ganin sun siye zuciyar kowa amma banda nawa, kuma bazan taɓa lamuntar reni daga wajensu ba wa ni ko wa ya'yana". "Ina magana kina bani amsa ko,eh lallai nuna min irin ta ki fitsaran da khareemar ta koya miki". Damko hannun Sabriyah dake kuka kamar ranta ze fita ga zagin cin mutuncin da ummah ta musu ga kuma faɗar da yake kokarin afkuwa tsakanin ita da Hajjatiye kuma duk ta dalilin su. Jan hannunta ummah ta yi da karfi kamar zata ƙaryata,ta fara janta da niyar fitar da ita daga cikin Mansion din, tirjewa Sabriyah ta fara yi tana bata hakuri tana kuka. "Dan Allah ummah kiyi hakuri Wallahi abinda kike tunani ba haka bane". Ummah na janta tana cewa "yau ai ko gidan nan gidan uban ku ne se kun barshi dama haushin ganin ku nakeyi a gidan". Zubewa a ƙasa ta yi amma hakan be sa ummah ta dena jan nata ba,Fatime da kaltume ne da suke kitchen suka jiyo hayaniyar dake tashi suka shigo da gudu fatime ta haura part din Hajiya babba domin sanar da ita tasan Ammi,da anty amarya suna can.kaltume kuma ta nufi part din Abbie domin sanar dashi. Riko dayan hannun Sabriyah Hajjatiye ta yi ranta a matukar ɓace ta ce"ki sa'ke ta nace Huraira Wallahi zanyi mummunar ɓata miki rai,kar ki bari in miki rashin mutuncin da kowa se ya yi dana sani". Idon ummah ya riga da ya rufe in bawai fitar da Sabriyah ta yi daga cikin gidan ba hankalinta ba ze taɓa kwanciya ba.tana haki ta ce"Wallahi ko da zakisa Isma'il ya sakeni ne yau tofa wa'yannan tsinanun annoban se sun bar gidan nan ko kuma ni in bar musu gidan"kamar za su raba Sabriyah gida biyu haka suke janta,Ummah na ja Hajjatiye na ja,wani irin wawan fisga ummah ta mata a hannun Hajjatiye da yasa seda ta buge kanta da glass din flower dake falon nan take gefen kanta ya fara zufar da jini domin glass din irin me karfin nan ne,duk da buguwa da ta yi dashi amma hakan be sa ya fashe ba. Azaban da ya ziyarceta ne yasa ta kwala razananniyar ƙara da seda illahirin gidan ya amsa. Tana riƙe da wajen da ya fashe tana kuka. Abbie da Abbu kaltume ta samesu ta sanar dasu abinda yake faruwa,da hanzari suka baro part din nashi a hanya kuma suka ki kar'ar da Sabriyah ta yi hakan yasa suka sa'ke sauri gudun kar a yi barna. Haka su Ammi ma Fatime cikin tashin hankali ta sanar dasu abinda ya faru,suma babu shiri suka fito a hanyarsu ta zuwa downstairs ne suka jiyo ihun Sabriyah. Rameesa da tun dazun suna jiran dawuwar Sabriyah ne suka ki wannan gigitancen kar'ar da tayi ne yasa suma suka fito da gudu har da Asmita. Sahil da Salim da yanzu shigowar su gidan suma suka ji ihun ne hankalinsu ya tashi.suka shigo da gudu. Suna zaune a dakin bincike su hudu suna meeting akan kidnapping din da aka fara yi ne, LTG jikinsa ya bashi kamar akwai wani abu da yake faruwa hakan yasa ya Kunno CCTV din falo nan take ya hango yanda ummah ke dragging din Sabriyah da ke durkushe a ƙasa tana tirjewa ga kanta dake zubar da jini. "Ohh shit"LTG ya faɗa yana miƙewa da sauri ya fice a dakin binciken,kallon system sukayi suka ga abinda yake faruwa suma da sauri suka rufawa LTG baya da ya riga da ya ma bar part din. su Ammi ne suka riga kowa shigowa falon se su Abbie da gudu Hajiya babba ta je tasa iya karfinta ta fincike Sabriyah dake kuka abin tausayi a hannun ummah. Boyeta a bayanta Hajiya babba ta yi "hurairah an ya akwai sauran hankali a tattare dake kuwa?, wannan wani irin mugunta ce dan fisabilillahi?". Watsawa Hajiya babba banzan kallo ummah ta yi "dan Allah dakata Hajiya babba ke kinsan abinda yarinyar nan ta aikata min kuwa?". Anty amarya da tana karasowa wajen Sabriyah ta rungumota a jiki,tana sa gyalenta ta goge mata jinin dake zuba a kanta. Bude baki ta yi zata yi magana, Abbu ya daka mata tsawa ranshi a ɓace. Su Asmita da shigowar su falon kenan suka ga abinda yake faruwa ta je ta rungume Sabriyah itama ta fashe da kuka duk da basu san abinda ya faru ba. "Lallai Isma'il yau matar ka ta nuna fin ni bani na haifeta ba,tunda har ina hana Huraira aikata abinda take yi amma ta ƙi saurara na". Su gaba daya their confused basu san abinda ya ke faruwa ga kuma Sabriyah da kanta ya fashe. Kukan Sabriyah da Asmita ke tashi a falon.ganin Asmita ne yasa ummah dasauri tasa hannu ta cafkota,ta fara janta. Hannun ummah anty amarya ta rike,ranta a ɓace ta ce"Huraira ki sa'ke yarinyar nan kar daga ni har ke, ran mu ya yi mummunar ɓaci kinji na faɗa miki ". Dariyar renin hankali ummah ta yi"ai yau Wallahi yaran nan ba zasu ƙara ko awa daya a gidan nan ba barima ki gani"ta na gama fadin haka ta ture anty amarya da sauri Ammi ta riƙota. Ji ta yi an riƙe hannun ta kallon wanda ya riken ta yi ta ga Saghar ne"Saghar ka sa'ke min hannu ko in saɓa maka". Saghar da yanzu shigowar su falon suka tarar da abinda yake faruwa ne ya yi hanzarin rike hannun ummah. Gently ya ce"ummah please ki sa'ke ta". "To sannu ubana!na ce sannu ubana,to bazan sa'ke ta ba yau wa'yannan tsinannun yaran se sun bar mana gida nagaji da kallon su". Ammi da ba ko da yaushe take saka baƙi a al'amarin gidan ba musanman ma abinda ya shafi Ammuh ko ummah ba. Amma yau ummah ta kawo ta makura ganin abinda takeyi wa yaran . "Babu wacce zata bar gidan nan Huraira wannan wani irin rashin imani ne haka,meye yaran nan suka tare miki,to na rantse da wanda ya halicce ni bazasu fita a gidan nan ba a yau,sede kiyi duk abinda zakiyi". Dogon tsaki ta ja sannan ta fincike hannun Saghar da ya rike mata nata hannun. Ransa ya ɓaci iya baci daga shi har Sudais da Abbu ganin abin kunyar da Ummah take aikatawa. Idonsa a rufe ya ce "Ummah ki sa'ke ta nace". "Huraira ki sa'ke yarinyar nan,kar ki bari in sa'ke miki magana"cewar Abbu da ransa ya gama ɓaci domin ya gaji da halin Ummah yau kuma ga abinda ta bijiro dashi. Hajjatiye na zaune akan kujera tana kukan cin mutuncin da ummah ta mata Hajiya babba na rarrashinta,Abbie ma yana tsaye ya zuba ido ya rasa menene abinda ze cewa ummah, LTG yana tsaye shima ya zuba musu ido shima be san mezece ba,ga Sabriyah da ya gani durkushe a ƙasa tana kuka.ga Asmita a hannun ummah taki sa'ke ta, Sudais in rasa ya yi dubu to seda ya ɓaci,ganin abinda ummah take yi. Yan matan ma suna tsaye ganin tashin hankalin da aka tashi dashi yau a gidan nasu,suna tsaye suna hawaye,ga shi yanda ummah ta tsaya tana cin zarafin su Sabriyah abin be musu dadi ba ga faɗar da iyayen su suke yi. Ammuh tana tsaye a gefe tana murmushin jin dadi, ummah bata taɓa burgeta ba irin yau da ta fita musu a giya. Rike kugu ummah ta yi tana kallon cikin idon Abbu "ko zaka rabu dani ne ta dalilin wannan yaran?,se ka zaba ko ni Ko su". Fisgo Asmita ya yi a hannun ummah ta faɗo jikinsa, jikinta har ya dau zafi ga rawan da yake abinda yake faruwa ya daga mata hankali dama ba wani isheshen lafiya ne da ita ba,yanzu kuma ga rashin mutuncin da ummah take musu. Taɓa jikinta ya yi yaji yanda ya dau zafi rau. "Saghar ka rabu da yarinyar nan,ko kuma...." Abbu ya ce "ko kuma me?,na ce ko kuma me ". Tana huce da hura hanci ta ce "hmmmm.waya'nnan karuwan de se sun bar gidan nan su je can su ci gaba da rabawa yan titi,Yan iska marasa asali,yau yanda suka gama gantalewa a titi wani dan iskan ne ze aure su". Jikin Saghar har tsuma yaƙe yi yarasa ya zeyi da maman tasu. "Ina santa!ni nan zan aure ta"gaba daya kallon su ne ya koma kanshi jin abinda ya faɗi. Kallon sa Asmita ta yi,maganar da yi ya da ki zuciyarta,ta rasa wani irin yanayi ta ji farin ciki ne ko kuma akasin haka. Kamar wata mahaukaciya sabuwar kamu ta daka tsalle ta zo gabanshi ta ce"maimaita abinda kafada Saghar in ji,menene ka faɗa yanz_yanzun nan dan ubanka meye abinda kunnuwana suka ji mini, Allah yasa ba da gaske ba, ɗana da karuwa har abada baze yu ba". Da karfi yanda kowa ze ji ya sa'ke furta "zan auretaaaaaaaa.....,ni ina son Asmee zan aure ta"kukan kura ummah ta yi ta chukumo wuyan Saghar kamar wacce ta samo tabin hankali ta soma magana"baka isa ba, baka isa ka zubar min da mutunci ba a dinga nuna ni ana cewa yarona ya auri karuwa,ina! karya kake yi,ko ubanka be isa ya sa ka aureta ba ɓalle kai". Murmushin jin dadi da takaici Abbu da su Hajiya babba sukayi. Abbu ya ce"dagaske Saghar kana son Asmita!?"gyada masa kai ya yi ko shakkan ummah dake rike da wuyan rigarsa be ji ba. "To shikenan kasa a ranka kamar ka auri Asmita,baka da matar da ta wuce ta in sha Allah". Yau in hauka ne yaci a ce ummah ta yi shi ganin abinda Saghar da Abbu suke da niyar haukata ta. Kamar zata yi kuka ta ce "Isma'il ni zaka tozarta?to Wallahi tallahi ko zan yi yawo tsirara se na hana wannan cin mutuncin da kuke kokarin yi min, da rai na da lafiya ta bazan taɓa barin ɗana na cikina ya auro karuwa ba sauran da wani ya ci ya rage, budurwa sabuwa fil a leda zan aura masa yanda shine nan ze bude ta da kansa". Runtse ido Sabriyah ta yi jin mummunar kalmar da ta jefesu dashi wai sauran da wasu suka ci suka rage,ina bazeyu ba,dole ne ma su bar gidan nan yau an musu irin wannan tereren tambadar basu san gobe wani kala za'a zo musu dashi ba. Hajjatiye dake zaune akan kujera tana yar kuka ne ta rangwada gu ɗa"aiyiriyiri!, Ubangiji Allah ya maka albarka Isma'il na yafe maka duniya da lahira,gwara da ka gwadawa wannan mara mutuncin matar ta ka kai ka isa da ya'yanka.kuma inde da ranmu da lafiyar mu se an yi auren Asmita da Saghar sede in mutuwa za kiyi ki mutu.saghar Allah ya sanya alkairi ya nuna mana ranar auren naku mu yi rawa har da karya kwankwaso". Ba Hajjatiye ba kowa dake falon wannan abin ya musu dadi jin Saghar ya ce yana son Asmita,su ga iya gudun ruwan ummah din. Mutsu_mutsu take yi a jikinsa tana so ya sa'ke ta,kowa dake falon yana kallon su. Can ciki ta yi magana. "Ya Saghar ka sa'ke ni". "Bazan sake ki din ba"shima ya mata rada a kunne. Taga tabbas da gaske yake yi ,ba sa'ke ta din ze yi ba hakan yasa ta cize shi a damtsen hannunsa, sa'ke ta ya yi yana kallon idonta da har yanzu be dena zubar da hawaye ba,wajen da Sabriyah ke durkushe ga anty amarya na shafa kanta ta nufa ta zauna a ƙasa tana kwantar da kanta a kafadarta suna kuka a tare. Folding din hannunta waje daya ta yi alamar roko. "Ummah kiyi hakuri ba abinda kike tunani bane,ki yarda dani,baki san ainihin abinda muke tattaunawa da Hajjatiye ba,kin zagemu kin kiramu da suna ye kala_kala,tabbas mu bamu da asali bamu da ahali,amma ba laifi muna jin dadin rayuwar mu a inda muka baro din,bamu taɓa kwadayin shiga wajen da Allah be kaimu ba,duk irin azabtar da mu da ake yi amma bamu yi kwadayin shiga cikin wasu ba.gudun gori da wulakanci duk da mu din wulakantattun ne kamar yanda kika ce,amma bama yarda a tozarta mu,muna iya kokarin mu wajen kare mutuncin kan mu. Ba ma son zaman silar haddasa faɗa ko tashin hankali a cikin wannan gida na ku,domin kun dauke mu Kamar yaranku,kun nuna mana so da kauna har abada baza mu taba mantawa da haka ba, kuma zamu ci gaba da muku addu'a har iya rayuwarmu da gode muku.kun taka muhimmiyar rawa a Rayuwar mu,kun nuna mana hanyar dede,mun san mu su waye ne a yanzu.mun gane addininmu duk ta dalilin ku bamu da bakin da zamu gode muku. Amma yanzu lokaci ya yi da zamu bar wannan gida bawai dan kun gazaba,sedan kar mu haddasa muku fitina,kafin muzo hakan baya faruwa amma daga zuwan mu ta dalilinmu kun fara samun saɓani.ku yafe mana mun gode sosai ". Jikinsu ya yi sanyi sosai ganin yadda suke kuka tana magana. Anty amarya ma sosai take kuka ga idonta ya yi ja. In su Sabriyah suka bar gidan nan ba kowa aka yi wa ba sama da ita,domin yanzu jin kanta takeyi a matsayin uwa,taya zata juri rasa wata ƴar idan kuwa suka tafi bazata taɓa yafewa ummah da ta zama silar haka ba. Muryarsa sukaji daga bayansu yana faɗin "Babu wacce za ta bar gidan nan"kallon shi Sabriyah ta yi idonta na zubar da hawaye ta ce "ya Taj,dole zamu tafi domin kuma ku samu kwanciyar hankali". Kafeta da ido ya yi,yana kallonta ya dede da yin observing din Sabriyah tana da matukar taurin kai,in ta kafe akan magana to bata taɓa sauya wa musamman ma in ranta na a ɓace. Be sa'ke cewa komai ba domin tunda ya ji ta ce se sun bar gidan yasan ko da ba'a sani ba zasu iya bari din. Gyaran murya Abbie ya yi da gaba daya he's out of words, takaici ya gama dabaibaye shi. "Tashi kuzo nan Sabriyah da Asmita". Miƙewa sukayi jikinsu a sanyaye suka je wajen Abbie din shafa kansu ya yi kafin ya rike hannunsu ya zaunar da su akan kujera kallon Saghar dake tsaye kamar dutse ya yi,"zo ka mata dressing din kanta nan da ya fashe". Ba ce komai ba ya nufi clinic ya dauko first aid box. Ya fara wanke wa Sabriyah ciwon kanta, runtse ido ta yi lokacin da ya fara goge mata da hydrogen har cikin ranta take jin zafin kawai daurewa takeyi,gaba daya ta kosa a gama su tafi. Bayan ya gama ne,ya bawa Asmita maganinta tasha. "Kuyi hakuri da abinda ya faru yau din nan tabbas an ci mutuncin ku,wanda gaba dayanmu ba mu ji dadin hakan ba,umman ku ba ta kyauta ba, ɗa na kowa ne amma ku yafe mata in sha Allah bazata sake ba,kun ji ko". Gyada masa kai sukayi. Ya ci gaba da magana"yanzu kuna da damar da za ku zaɓi a duk in da kuke son kasancewa,kuna son komawa afafa ne"ya tambaye su yana kallon ko wacce,da sauri Asmita da Sabriyah suka gyada masa kai tabbacin suna son komawa. Murmushi irin tasu ta manya ya yi ya ce"shikenan zaku koma,kun ji ko, tunda gobe da jibi babu makaranta se ku je ko".da zallan mamaki dauke akan fuskan ko wanensu suke kallon Abbie jin abinda ya faɗa,domin kuwa babu wanda ya yi tsammanin abinda ze faɗa kenan,to menene yasa Abbie ze ce za su koma afafa.me yake shiryawa dan haka kawai bazece zasu je su afafa ba.to kode ya faɗa hakane dan ya kwantar musu da hankali. Murmushin gefen baki LTG ya yi domin yasan abinda Abbie yake da niyar yi,kuma tunanin su yazo daya. Ammi ta ce"amma Abbie ta ya kuma za'a mayar dasu can din?,ko ka manta wata irin rayuwa sukayi abaaya?",daga mata hannu ya yi,shuru ta yi bata sa'ke cewa komai ba. Duk masu son yi magana da su ka ga yanda Ammi sukayi da Abbie se suka ja bakin su sukayi shuru suna son ganin iKon Allah. "Yawwa gwara de su tattara su bar gidan nan in ana so a samu zaman lafiya dani"cike da takaici Abbu ya juya ya kalli Hajjatiye ya ce "Hajjatiye kwanaki ba kin yi mini tayin auren Hajiya lubabatu ba?,to na amince zan aure ta ko zan samu salama da irin bakin cikin da Huraira ta ke cusa min". Hajiya Hajjatiye abin nema fa ya samu dama tun shekaru uku da suka wuce take mishi maganar wata Hajiya bazawara da mijinta ya rasu tana da yaronta na miji guda daya tal,kuma matar na da kirki sosai ga hankali da sanin yakamata shisa ta yi wa Abbu kwadayin aurenta amma da ta masa magana se cewa ya yi shi yanzu baze iya yin wani aure ba matar sa da yaranshi zasu ga kamar ya yi hakan ne dan cin mutumci,amma yau shi da kansa ya ce yana bukatar aurenta.hakan yasa ta sa'ke rangwada gu ɗa. "Se yau na san yarana jinina da halina suka dauko yau Isma'il ka nuna min ka haifu a cikina,ba a cikin ko wacce shegiya ba.uba da ɗa sun kusan angwancewa".ta yi maganar tana gyara daurin zanin ta. Saghar da Sudais, Parsa ko a jikinsu da suka ji Abbu ya ce ze ƙara aure domin kuwa ummah ita ta jawa kanta da batayi haka ba babu abinda ze sa Abbu yin wannan maganar,yau ta kuresa ne,mutum me hakuri dama in aka kai sa bango to babu dadi. Hajiya babba kam aranta ta ce "gwara a yi mata hakan ai ko zata yi hankali". Ummah daura hannu akai ta yi tana"Isma'il ka yi kadan da ka wulakanta ni a gaban yarana,ba de aure ba to daga kai har Saghar din sede in bayan rai na ne zakuyi auren,a yi mugani in tusa zata wura wuta"ganin ta fara faɗe_faɗe ne Ammuh ta zo ta ja ta dakyar zuwa part din ta. Parsa da idonta ya yi ja tsaban kukan da tasha ne,ta je wajen su Asmita tana basu hakuri. "Dan Allah kuyi hakuri da abinda umman mu ta yi muku,.. tabbas bata kyauta ba,ku yi hakuri Allah yana son me yafiya,Dan Allah karku tafi please,mun riga da mun zama yan uwan juna baza mu ji dadi ba in kuka tafi kuka bar mu". Murmushi yaƙe Sabriyah ta yi"bakomai masoyiya ummah ai kamar uwa take a wajen mu komai ta yi mana bazamu rike ta a zuciya ba,amma kam zamu tafi afafa". Shuru ta yi tarasa me zatace musu ganin takeyi kamar laifin da umman su ta yi ne ya shafe su dayasa Asmita da Sabriyah suka dage se sun bar gidan. Haurawa Anty amarya part din ta,ta yi tana hawaye saboda Abbie ya riga da ya gama magana,babu wanda ze sa shi ya canza se Hajjatiye ka dai,bin bayanta Ammi ta yi da sauri. Sahil da Salim dake tsaye su basu da bakin yin wata maganar ma. "Kuje part din ku lokacin sallah ya yi"part din su suka wuce su bakwai din. A dakin su Sabriyah suka yada zango,kamar sune suka aikata abinda ummah ta yi haka suka hadu suna ba su hakuri more especially Zoya da Parsa. Umaisha da ta yi tagumi kamar wata marainiya"Sabriyah tunda kin nace se kun tafi nide duk weekend se na kawo muku ziyara, Wallahi abinda ya faru yau din nan kamar a mafarki,babu wanda ya yi tsammanin haka zata faru". "Karki damu ai komai ya wuce"cewar Asmita. A Falo kuwa Abbie ne yake magana da Sudais da Saghar. "Kun ji abinda Abbu din ku ya faɗa ko,ze ƙara aure fatan baku da matsala da hakan"Saghar ne ya fara magana saying. "Allah yabasu zaman lafiya nide banda matsala"murmushi Sudais ya yi"Nima haka". "Shikenan zaku iya tafiya, Tajuddeen ka tsaya kai". Barin falon sukayi ya rage daga Abbie, Abbu, Hajiya babba, Hajjatiye, LTG. Dama uncle Hameed ba ya gida duk wainar da aka soya baya nan be san abinda ke wakana ba. "Tajuddeen nasan ka fahimci dalilin da yasa nace yaran nan zasu koma afafa gobe?"gyada kai ya yi without saying anything. "Good,ka sanar wa Khalifa shi ze kai su a private jet din ka,daga nan kuma se ku yi abinda ya kamata". "To shikenan Abbie dama na daɗe da son yin haka kawai wani aikin ne nakeson kammalawa amma tunda bukatar hakan ya taso za'ayi". Abbu dasu Hajiya babba de basu fahimci inda zancen Abbie da LTG ya nufa ba shisa kawai suke kallon su. Barin falon ya yi domin dauro alwalar sallar mangrib. Se da suka tabbatar da babu sauran yaran da suka rage a downstairs din kafin. Abbu ya rarrafo akan guiwowinsa yazo gaban Hajjatiye ya daura kansa akan cinyarta murya a sanyaye with full of regret ya soma magana. "Ina me baki hakuri a madadin Huraira,naji takaicin wai yau matata ce ta tsaya tana yiwa mahaifiyata rashin kunya,dan Allah ki yafe min,in sha Allah se na dau mataki akan abinda ta aikata yau din nan". Shafa kansa Hajjatiye ta yi ta ce "ban amince ka ce zaka dau mataki akanta ba,ni a wajena komai ya riga da ya wuce,ka dena damun kanka". Murmushi Hajiya babba ta yi wannan dalilin ne suke sa'ke son surkar tasu,ko min irin masifar da zaka ga tana yi tofa bazata yarda wani abun ya ruguza ahalinta ba,wanda be san ta bane kawai zece tana da faɗa. Magana sukayi sosai kafin Hajjatiye da Hajiya babba suka haura upstairs jin an kira sallah. Su kuma suna jiran su LTG su fito su tafi masallaci. A part din Ammuh kuwa,ummah se faman Safa da marwa takeyi tunda suka shigo ta kasa tsaye ta kuma kasa zaune. Ita kan ta Ammuh lamarin ya girgiza ta, "Hajiya Huraira dan Allah ki nutsu mu san mafita, wannan Safa da marwa da kike yi babu inda ze kai mu". Zama ummah ta yi"kamar ni Isma'il ze tozarta a gaban yara da kuma kishiyoyin balbali na?". "Calm down first wannan fa ba wani babban matsala ba ce amma duk kin bi kin tayarwa da kanki hankali,ko kin manta abinda zamu iya aikatawa ne". "Hajiya khareema ina sane amma dole raina ya ɓaci kishiya fa?,tun da be min kishiya ba se yanzu da na girma ga yara na sun gama girma shine ze min kishiya". Matsowa kusa da ita Ammuh ta yi dan ta lura har yanzu Ummah bata dawo dede ba. "Ki shirya ranar Lahadi muje wajen boka mauzau,daga auren shi Abbu din harna Saghar din se mun watsar dashi". Se sannan ne taji hankalinta ya kwanta ruwa me sanyi ta bata tasha. Bayan sallar isha uncle Hameed ya dawo kai tsaye part dinsu ya nufa. Tsaye a jikin window ya iske Anty amarya, kallo ɗaya ta mishi ta kauda idonta,tunda yaga haka yasan cewa akwai wani abinda ya faru ga idonta da ya kumbura tasha kukanta hatta koshi. Wajen ta yi nufa. "Amaryata me yake faruwa na ganki haka"murya na rawa ta sanar masa da duk abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa,kafin ya shigo din nan Hajiya babba da Ammi suka fita a part dinta bayan sun gama rarrashinta. Jawota jikinsa ya yi yana bata hakuri shi kanshi be ji daɗin abinda ya faru ba, yasan Abbie baze taɓa yanke wannan hukuncin ba,batare da kwakkwaran dalili ba. "Kiyi hakuri in sha Allah a wannan karon bazamu rasa yarmu ta biyu ba Sabriyah, Allah yana sane da mu,kuma ya Mubarak nasan akwai dalilin da yasa ya yanke wannan hukuncin ". Ba ta ce mishi komai ba. 8:00pm dede lokacin cin abinci as usual ummah da Ammuh basu fito ba,haka LTG shima yana part din sa, uncle Hameed ya yi iya yin sa amma Anty amarya taki fitowa itama. A bangaren su Umaisha ma dakyar suka sha kansu Sabriyah suka je dinning. Kowa ka gani fuskar sa babu walwala da annuri,kawai de ana cin abincin ne,bawai dan yana shiga yanda ya kamata ba. Kallon Asmita dake tsakuran abinci Saghar ya yi yana ajiye spoon din hannunsa,jikinta ne yabata ana kallonta haka yasa babu shiri ta dago suka haɗa ido,hararanta ya yi,dan haushi ta bashi da Abbie ya tambaye su ko suna son komawa afafa har da cewa eh. Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi taci gaba da tsakuran abincin. Bayan sun gama ne.zasu koma ciki Abbie. Ya ce "Tafiyar ku da safe ne so be ready,kuma karku dau kaya da yawa saboda Monday akwai school kunji ko". Ido kawai suka zubawa Abbie dukkansu suna tambayar kansu to me yake nufi?,kenan in suka tafi zasu dawo kenan,tunda ga shi har cewa musu yake Monday akwai school. Ta rasa me zata ce kawai ta ce"thank you Abbie"kafin ta ja hannun Asmita suka wuce part din su,binsu a baya su Umaisha sukayi,kowa de ya rasa gane inda lamarin Abbie ya dosa. Saghar da ya ƙasa hakuri ne ya ce"Abbie kenan zasu je su dawo ne?,Ni ban fahimta ba". Fuskar Abbie ba yabo ba fallasa ya ce"ga shi nan de!"ya yi maganar yana fuskewa. Be sa'ke cewa komai ba,ya miƙe yabar wajen. Kamar yanda Abbie ya bukace su da suyi haka kuwa suka yi yar karamar trolley ta dauka ta saka musu kala biyu a ciki se dogayen hijabs. Lieutenant general Tajuddeen Yana nan a dakin bincike yana aiki,yaran da aka sace yau binciken sa ya tabbatar masa da Mafias ne suka sace su shisa ka ya maida hankali akan neman in da aka kai yaran,in har hasashen sa yabashi dede yaran da kuma masu kidnapping din Suna cikin garin Maiduguri kuma baze taɓa barin su bar garin nan ba se ya kwato yaran,karfe sha biyu ya kira Khalifa a waya ya sanar masa da ze kai Sabriyah Lagos gobe. Tunda sukayi sallah asuba sukayi wanka suka shirya cikin dogayen rigunan abaya,daukan trolley din Rameesa ta yi sukayi fito falo. Gaida kowa da suka samu afalon sukayi.dubawa ta yi taga anty amarya bata fakon hakan yasa ta haura part din ta sallama ta yi tana daga tsaye a bakin kofar,amsawa anty amarya ta yi. "Mommy ina kwana?". "Lafiya klau mommy's angel,how are you?". "Am fine mommy"murmushi ta yi jin ta amsa mata da turanci,wato suna fahimtar karatu kenan duk da ma wa'yannan ƙananan words din bame wahalar wa bane. "Mommy zamu tafi shine nazo miki sallama ki yafe min"shafa fuskarta ta yi,tana danne abinda yake yunkuro mata na baƙin ciki. Ta ce"baki taɓa min laifi ba daughter, and in sha Allah za ki dawo wannan gidan da izinin Allah ta Allah". Hawaye ne ta ji ya cika mata ido, hakan yasa ta rungume anty amaryan,. Sun kusa minti uku a haka kafin ta zame jikinta ta ce"ko ma me ze faru kiyi min alkawarin bazaki taɓa komawa rayuwarki na ɗa ba?". "Na yi miki wannan alkawarin mommy,". Dawuwa falon tare sukayi.kowa ya hallara a falon ummah da Ammuh suna upstairs suna kallon duk wani abinda yake faruwa suna murmushi Finally burinsu de ya cika Sabriyah da Asmita sun bar gidan. A babban filin farfajiyar gidan private jet na wajen, Khalifa su yake jira su fito,rako su har wajen sukayi suka shiga ciki. Suna musu bye_bye a haka jet din ya tashi sama.sun tafi. Lagos Bayan sun isa Lagos ne motar ya zo ya dauke su ya ajiye su har cikin afafa a bakin gate din gidan karuwan da suka baro. Duk wacce su ka haɗu a hanya se ta kallesu suna mamakin sauyawan da sukayi da kyaun da suka ƙara. Sashen su na gidan suka nufa,suna shiga suka iske,anty Teema ita kadai tana zaune ta rame sosai ta yi baƙi ta kode kamar ba ita ba,tana daure da fallen zani. Cikin tsoro suke kallonta a tare suka haɗa baki wajen cewa. "Anty Teema". Ta jima da cire tsammanin sa'ke jin muryoyin su a rayuwarta,bude idonta da bacci ya fara saceta ta yi taga dagaske yaran nata ne. "Hot girl!, Asmita da gaske kune?,kun ga ni yanda na koma ko?, kullum addu'a ta shine, Allah yasa in gan ku kafin in mutu ashe de da rabon za mu ga juna?". Gyara mata zama Sabriyah ta yi, tana me jin tausayin Antyn nasu,ganin yanda gaba daya ta canza ta kare. Asmita kam ta ma gagara magana. "Anty Teema meyake faruwa ne,,shin maganin ki ne ya ƙare?". "Ai komai ma ya ƙare Sabriyah rayuwar bariki be yi ba ko kadan,yanzu abincin da zan sa abakina ma babu rabona da abinci tun jiya da rana.mutane biyu ne kawai suke taimaka min daga Cele se Nabiha suma tun shekaran jiya basu zo ba". Ta yi shiru,can kuma ta sa'ke magana. "Ku da Allah yasa kuka bar nan wani ƙaddarar ce ya dawo daku gidan nan?, kullum inna tuna bakwa s wannan gida ina jin dadi a raina domin jikina yabani kuna a hannu na gari,dubi yanda kuka yi kyau kuka canza kamar ba ku ba,cikin shiga na mutunci". Yanda take magana ma dakyar take iya bude bakinta,se sukaji kamar basu kyauta ba na barin antyn nasu har tsawon Wannan lokaci basu san halin da take ciki ba. Gyara mata dakin nata suka yi kafin suka dauki kuɗin da Abbie ya basu koda suna bukatar wani abu. Suka fice, babban pharmacy suka je suka siya mata magungunanta, sannan suka tsaya a shagon trader suka siya kayan abinci. Suna a hanya suna tafiya ne, suka hango cele na nufo su, da alamar ya ji labarin dawuwar su ne. Yana isowa ya ƙare musu kallo sama da kasa kafin ya basu hannu suka tafa,su kansu sun yi tsananin kewar abokin nasu biye da yanda ba'a magana,sun yi farin ciki sosai da ganinsa haka shima bakinsa ya kasa rufuwa se yabon kyau da kibar da sukayi yake yi.nan ya taya su daukan kaya suka koma gida. Asmita me girkin su ita ce yauma ta musu jallof din macaroni.ta zubawa anty Teema da yawa ta kai mata ta kai mata harda ruwa. Kiran Nabiha a waya Cele ya yi ya shaida mata,su Sabriyah sun dawo. Dama tana dakin su bata je ko ina ba,ai kuwa da gudu ta nufo sashen nasu. Tana zuwa suka rungume juna cike da kewa. Nan fa aka fara hirar yaushe gamo,suna hira a na cin abinci. Ko da suka gama cin abincin ma baranda suka dawo suka zauna suna hira harda anty Teema,da ta ɗan warware dama har da yunwa a abinda yake damunta. Labarin dawuwar Sabriyah da Asmita ya gama kararide gidan,tun shigowarsu dan daudu ya gansu da gudu ya je ya sanarwa boss lady cewa sun dawo, dariyar mugunta ta yi,domin dama ta dau alwashin in de suka dawo se ta yi musu abinda basu taɓa tunani ba. Lokacin Sallah na yi suka tashi suka yi. Bayan sun idar ne, Nabiha take basu labarin abubuwan da suka faru bayan barun su gidan,ta ƙara da. "Amma meyasa kuka dawo?,ni de Wallahi banji dadin dawuwar ku ba,domin ko nice na samu wannan damar baza'a sa'ke kallon ko da inuwata ba, ɓalle kuma ni". Murmushi kawai suka mata,suka ka war da maganar. Se karfe biyar Cele ya tafi Nabiha kam ta ce yanda ta yi kewar su dole tare zasu kwana duk da katifarsu baze ishesu ba. "My Jerry nasan wannan abin hannun nawa yana a dakin nan namu,shisa ban taɓa tambayarki ba,dubomin a inda kika a jiye min". "Ah ah baya a dakin nan ai ranar da kika bani ban cire ba,har lokacin da wayan'can mugayen suka sace ni yana hannuna bansan ya akai ya ɓata ba". Jiki a mace ta ce"Tom shikenan bakomai yanzu de abin Tajuju na ya ɓata,amma kinfi min abun hannun daraja". Nabiha tana zaune tana kallonsu tsananin kaunar dake tsakanin su ne yake burgeta, bata gajiya da son kasancewa a cikinsu. Saura jallof din su ne suka cinye, se da suka tabbatar da anty Teema tasha magungunan ta kafin suka baro wajen ta. Sukayi sallah isha sannan suka kwanta,nan ma ba bacci sukayi ba su ukun hira kawai suke yi kamar wa'yanda suka yi shekara uku ba su haɗu ba.se da bacci barawo yazo ya sace su. Har karfe 8:00am na safe basu tashi ba saboda babu masallaci a kusa da ze kira sallah ɓalle su ji kiran sallah su tashi. Suna cikin bacci suka ji saukar ruwa me sanyin gaske a jikinsu.a zabure suka tashi suna rawar sanyi, musamman Sabriyah jikin ta ne ya kama rawa bata shiri da ruwan sanyi shisa take kiyaye kanta da kuma lafiyarta domin ciwon nimoniya dake tare da ita. Boss lady ne suka gani tsaye da babban bokiti tana tsaye akan su ga kuma bulala a dayar hannun nata. Kafin su gama dawuwa dede ta fara shiga jikinsu da bulala,duka ko ta ina, dakyar suka samu suka kwace kansu suka fito a cikin sashen nasu suna kuka. Ga kayan jikinsu dake ɗiga da ruwa Nabiha kam guduwa dakinsu ta yi. Suna tsakar gidan suna kuka,sanyin dake kaɗa kayan jikinsu ne ya sa'ke tsananta rawar da jikinta yake yi. Lallabawa anty Teema ta yi ta fito ta fara bawa boss lady hakuri, amma ko saurarar ta bata yi ba. Karuwan dake gidan gaba daya taruwa suka yi suna kallon abinda yake faruwa. "Kun gama yawon duniyar taku da kuma guje_gujen kun dawo kenan,ai ni banso ku dawo yanzu ba,yanda kuka sani a sarar kudina da kuma bata lokaci wajen neman ku yau se kun yabawa aya zakinta". Bata hakuri suka shiga yi, tana matsowa suna matsawa baya,har suka fita gidan a bakin gate,zagi iri da kala babu wanda boss lady bata musu ba, Cele da ya hango dandazon mutane ne yasa ya iso wajen da gudun gaske nan fa ya tarar da abinda yake faruwa bashida ikon kwatarsu a hannun boss lady hakan yasa ya koma gefe yana bata hakuri. Ga mutane da suka yi cincirindo suna kallonsu kowa na tofa albarkacin bakinsa. Sanyi ya gama ratsa ko wani lungu da saƙo na jikinta har wani tsuma takeyi idonta ya fara kakkafewa.. Lura da ciwonta ya tashi ne yasa Asmita ta rungumeta gam a jikinta tana kuka. Ko damuwa da halin da Sabriyah ta ke ciki boss lady ba ta yi ba,ta daga doguwar bulalar injin da iya karfin ta, zata zafga mata,ta ji an rike bulalar ta baya, ja ta yi amma kamar ma bata motsa ba,da sauri ta juya dan ganin waye ne. Bata iya ganin fuskarsa ba saboda face mask dake manne a fuskar tasa,hannu yasa ya dauke ta da lafiyayyun maruka guda biyu,ihu boss lady ta sa,dan tunda take bata taɓa jin marin da ya ratsata irin wannan ba,se da taji kunnenta da dayan idonta lokaci daya sun dena aiki. Kafin ta gama dawuwa hayyacinta, yasa ƙafa ya kwasheta ta zube kasa warwas, ƙafa yasa ya take hannun nata daa take rike da bulalar da takalminsa,da ƙafarsa ya dinga dukanta kamar ya samu wani katon dabban jaki. Ɗaukan bulalar ya yi,ya ci gaba da dukanta dashi ihu da kururuwa boss lady take yi na neman a gaji amma babu wanda ya yi gigin kusanto su domin wanda yake dukan nata majiyin karfi ne, kar ya hada dasu, se ma ƙara ja baya da suka yi,da yawansu suna hamdala da godewa Allah da ganin irin wannan rana. Kallo ɗaya Asmita ta masa ta gane shi. A hankali ta furta"ya Taj???" Seda ya yiwa boss lady dukan mutuwa yaga numfashinta na kokarin daukewa ne ya kyaleta.ya yi dede da isowar manya_manyan motoci guda bakwai wajen.tika_tikan sojojine suka fiffito a ciki kafin. Sudais ya fara fitowa,se Sahil da Salim, Saghar, ACP Jawan. Tun kafin su iso wajen suke bin boss lady dake kwance a ƙasa da kallon tsana,su Abinda LTG ya mata ma kwata_kwata be ishesu ba. Da sauri suka karaso wajen Asmita dake rungume da Sabriyah tana a sume kuma har yanzu jikinta be bar tsuma da rawa ba,daukan ta sukayi suka sa ta a motar Salim da ACP Jawan suka wuce da ita asibiti.domin halin da take ciki. Ɗagota Saghar ya yi daga ƙasan, kayan jikinta danye, cire jacket din cikinsa ya yi ya rufa mata.kafin ya ja hannunta izuwa cikin motar. Kallon fuskarta ya yi "Asmee ta daƙe ku ne"gyada masa kai ta yi alamar eh. Komawa ya yi inda yabar su boss lady ya karbi bulalar hannun LTG ya ci gaba da dukan boss lady kamar Allah ne ya aikoshi. Haɗe fuska Sudais ya yi,ya rike sa "meye haka Saghar baka da hankali ne?,ko so kake yi ta mutu ba tare da na samu damar yi mata nawa dukan ba?, dallah malam bani bulalar". Ya kwace bulalar a hannunsa shima ya je ya yiwa boss lady nashi dukan kamar baze barta ba,ko ina na jikinta se da suka fasa shi. "Ah ah lallai kun ban mamaki,yanzu meye nufin ku kenan?,so kukeyi ku ce ni bazan daketa ba?,bayan kuma seda na daukarwa Parsa alkawarin yi mata dukan tsiya".Sahil ya faɗa shima yana karbar bulalar a hannun Sudais. Kallon dan daudun dake tsaye a gefe yana yarfe hannu ya yi nan take ya tuna da labarin da Sabriyah ta basu,wato de wannan shine wannan dan iskan dan daudun?. Shako wuyarsa ya yi ya fara jifgarsa,seda ya mishi lilis kafin ya barsa ya sa'ke dukan boss lady. Sude yau mutanen afafa sun ga tashin hankali,dama kowa haushin boss lady suke ji,yau ga shi Allah ya haɗata da dede da ita,ko motsi ta gagara yi tana yashe a ƙasa a wulakance. Asmita na daga motar se ihun dad'i takeyi taso ace Sabriyah taga irin dukan da aka yiwa boss lady,yau Allah ya rama musu abinda take musu. Wasu manyan katafila ne suka shigo wajen masu rusau. Sudais ne ya dauki loud speaker ya dawo tsakiyar filin ya ce"an yanta kowa,duk wacce take son kanta da lafiya ta bar gidan nan,domin yanzun nan za'a rusa gidan nan, kowa za'a bata kudin da zata gyara rayuwarta kuma ku koma gaban iyayenta,in kuma ba haka ba.... shikenan de".kafin kace kwabo sun fara tattara abubuwansu,sauke glass din motar Asmita ta yi ta kwalawa Cele kira,da sauri yazo inda take. "Cele akwai wayoyin mu a dakin mu taimako ka dauko mana"cikin gidan ya shiga ya dubo musu wayar su da trolley din da suka zo dashi. Tunda ta kira Cele Saghar yake kallon su, yana tambayar kanshi meye kuma hadinta da wannan zuciyarsa ce take son cusa mishi wani tunani da sauri ya ka war yana"astagfirullah"gudun kar shedan ya yi nasara akansa. Kauda idonsa akan su ya yi. Kawo mata su ya yi ta karba tana mishi godiya. ,suna gamawa aka fara rusa gidan,motar polisawa ne suka iso wajen nan LTG yabasu umarni aka sawa boss lady ankwa suka jefata a bayan motar kamar wata trash. Gaba daya gidan seda aka rusa shi kaf wajen ya koma farfajiyar fili. Ko wacce dake cikin gidan se da aka bata 300k(dubu ɗari uku ta nemi sana'a sannan ta koma gaban iyayensu. Asmita ce ta gabatar musu da anty Teema da ta rene su. Shiga motar sukayi harda Cele da anty Teema, Nabiha suka tafi asibitin da aka kwantar da Sabriyah. Alhamdulillah har ta farfaɗo tana zaune Jawan da Salim se janta da hira suke yi tana dariya. Shigowa dakin suka yi,ko ya jiki LTG be mata ba,sama fitar da ya yi, yana "karku bata min lokaci,ina jiran ku kuzo mu wuce"daga haka ya fice be ko juyo ba, murmushi Sabriyah ta yi tana bin bayansa da kallo tana tuna,lokacin da take kokarin suma shine mutum na karshe da tayi tozali dashi,duk da yana sanye da face mask amma seda ta gane shi. Kallon anty Teema Sudais ya yi ya ce "duk kan ku zaku koma Maiduguri tare da mu". Cikin farin ciki suka ce sun amince. Bayan awa daya suka kimtsa private jet guda uku suka yi amfani shi ya kwashe su zuwa Maiduguri. Karfe 8:00 suka iso Maiduguri motoci na fake yana jiransu. Shiga,ciki suka yi suka dauki hanyar gida. Su Umaisha na jin dirar motoci suka sa ihu da tsalle suna "Su Sabriyah sun dawo". Dariya Ammi ta yi,anty amarya ihun su da ta ji ne yasa ta sauko downstairs din. Tun kafin motar ya gama fakin Sabriyah da Asmita suka bude domin sun hango su Umaisha gaba daya sun nufo motar da suke da gudu,suma da gudu suka fito suna rungume juna. Ciki suka shiga gaba dayansu.rungume su anty amarya ta yi tana murmushi. Kowa ya yi murna da damuwar su, su Ammuh de basa gida,tun safiya suka nufi wajen boka mauzau. Naziya ta zo tun ranar asabar wato ranar da su Sabriyah suka bar gidan kenan. Bayan wasu yan gaishe_gaishe da akayi ne, suka yi wanka. abinci a ka kai musu,har lokacin bawai jikin Sabriyah ya gama warwarewa bane kawai tana karfin hali ne. Yanda suka karbi su Asmita haka suka karbi Nabiha ita ma cikin sakin fuska. Kiran wayar Sabriyah anty amarya ta yi ta ce mata ta zo su kwana a part dinta haka kuwa a kayi itama dama ta yi kewar mommyn nata. Washe gari Monday tun kafin su Nabiha su tashi daga bacci har sun gama shiryawa cikin uniform driver yakai su school. Haka suka ci gaba da rayuwar su kamar babu abinda ya faru ko da su ummah suka gansu a gidan basu ce komai ba. Bayan zuwan su da kwana uku ne aka samarwa Cele aiki.anty Teema kuma aka bata gidan dake cikin gidan,da masu yi mata hidima. Har yanzu ana kan sace yara da ake yi daya bayan daya,... Wata ranar talata Umaisha da Iklas sun fita shopping a hanyar su ta dawuwa aka tare su sannan aka kashe driver da ya dauko su,aka ɗauke su. Shuru_shuru ana jiran dawuwar su,amma Shuru har yamma ya yi nan fa aka fara neman su.motar da ya daukesu aka gani bakowa a ciki se gawar driver dake yashe a ƙasa. Hakan yasa suka fahimci an yi garkuwa dasu ne. Lokacin da suka ji wannan labarin hankalin kowa ya tashi.an yi binciken amma Shuru bayan su an sake sace yara yan mata goma. Har karfe sha biyu suna zaune a Falo sun yi carko_carko,kowa ka gani kasan yana cikin matsananciyar damuwa. Su Sabriyah sun yi kuka yar sun gaji suna zaune a Falo. Kiran waya ne ya shigo wayar LTG,kin dagawa ya yi domin a halin da yake ciki bayajin ze iya yin magana da kowa,kira ne kan kira yake shigowa,kallonsa Abbie ya yi "Tajuddeen waye haka yake kiran ka Kaduba ka gani". Kallon screen din ya yi yaga unknown number. Picking ya yasa a handsfree,dariya ne suka fara ji yana tashi irin na mugunta din nan,duk ƙasa kunne sukayi su ji kowa waye wannan. A bangaren wanda ya kira din kuwa ya fara magana cike da izza"Tajuddeen Mubarak Bishara, babban sojan ƙasa da ƙasa,wanda ko ina ake ji dashi.na musamman da babu kamar sa, jami'i me kwazo.wayyo meyasa nake cika ka da wannan dogon surutun yanzu de bari in gabatar maka da kaina. Ni ne nan shugaban Italian Mafia da ka dade kana nema ruwa a jallo,nasan kasan yan mata talatin suna hannuna idan aka haɗa da ƙannnenka kuma sun zama talatin da biyu, ya ka ji lissafin?"ya tambaya yana kecewa da mahaukaciyar dariya. Runtse ido LTG ya yi yana jin tsokan namar jikinsa na rawa.wato ɗan ta'adda har yana da gards din da ze kira wayarsa. "Tun kafin ka fusata ni in yi farautar ka da kaina ka sa'ke yan matan da suke wajen ka sannan kuma ka miƙa wuya". LTG ya faɗa. "Hhhhhhhhhhhh!,soja ya harzuka.. kana ganin barazanar ka zata yi aiki a kaina ne?,in har kana son in rabu dasu to gobe ka kawo mini kan ka da kanka rayuwar ka shine ze fanshi rayuwarsu,idan kuma ka yi gangancin yin wani dabara irin naku na jami'ai to na rantse maka sena kashe su gaba dayansu,rami me zurfi zan sa a ha ƙa in kunna wuta a ciki,haka zan dinga jefasu daya bayan daya a ciki,nikuma ina dariya domin jin kuka da kururuwansu yana sanya ni nishadi da jin dadi". Hannu Ammi ta sa ta rufe bakinta ta fashe da kuka"innalillahi wainna'ilaihi rajuun, shikenan ze kashe mana yaran mu!".dafata Hajiya babba ta yi ita kan ta ji take yi kamar ta yi kuka,karfin hali kawai take yi in su suna kuka to waye ne ze rarrashi su Sabriyah dake kuka. "MRS Bishara ki dena wannan kukan abun me sauki ne, kawai kiyi shahada ki turomin ɗan ki ,se in sa'ke gaba daya wa'yanda suke waje na".ya mata magana cikin shakiyanci. A fusace Sudais ya ce"ka dena yiwa mahaifiyar mu magana damu zakayi ita din ba Sa'ar ka bace.idona idonka se na yi gunduwaduwa da namar ka". Sudais ya yi maganar jikinsa har rawa yake yi. Dariya ya yi "ka sassauta Muryar ka,Ko kamanta da Umaisha ne kam?, wannan din nan kanwar taku me shegen surutu babu karya yarinyar ta ji kyau akwai diri da shape ko ina dinta a cike yake,idan ka sa'ke daga min murya to da ita zan huta a wannan daren bayan na more kuma kasheta in ga yanda danayi". Innalillahi wainna'ilaihi rajuun tabbas ba yi da imani tunda ya iya sace yara masu yawa haka to kashesu ko kuma aikata abinda ya faɗa baze mishi wahala ba. Abbie ji ya yi jiri na kokarin kwashe sa duk da yana zaune amma ji ya yi kamar ze fadi, Hajiya babba can't hold her tears nan take ta fara hawaye itama,anty amarya kam kukan da take yi baze misaltu ba.jikin Ammuh ya gama yin sanyi. Sabriyah da Asmita daskarewa suka yi a inda suke zaune jin muryar wanda ko a mafarki suka ji se sun gane waye ne. A hankali Sabriyah ta furta"Fu'ad?"tunani ta fara yi dama wannan shine true color din Fu'ad?, mutumin da suka dauka a matsayin dan uwa, shine na farko da yabawa rayuwarsu muhimmanci,a she wannan shine asalin sa, gaskiya Allah na son ta daɓe sa ta faɗa tarkon da yaso cilla ta ba. "Na amince zan sadaukar da kaina a madadin su". LTG ya faɗa a dake domin yasan kamar yanda ya faɗa in bawai zuwa din ya yi ba baze taɓa sa'ke su ba. "Da kyau soja!, warning na gaba da zan maka shine ko da wasa karka yi gigin zuwa da sojoji ko wasu jami'ai.kasani kasan abinda zan aikata. Kai sheda ne,ni na kona babban asibitin Turkish dake dauke da mutanen sama da dari tara,Bama se na tsaya ina tuna maka abubuwan da suka faruwa shekara hudu baya ba nasan ka tuna ko?". "Zan yi yanda ka ce,kar ka yi musu komai". Cike da nishadi Fu'ad ya ce"Nagodeeeeee, soja". Ya kashe wayar. Su de yau suna cikin tashin hankali taya za'a yi su yarda LTG ya tafi wajen mutum me matukar hatsari irin wannan batare da jami'an tsaro ba ko kuma makami ba. Kallonsu major Marry ya yi"do not make any move,am going there alone" "Ya Taj babu yanda za'a yi mu Barka ka tafi wajen wannan hatsabibin mutumin kai kadai"cewar ACP Jawan. Abbie ma ya ce"haka ne Jawan dole a san yanda za'a yi amma kam baze je shi kadai ba". "Abbie ni kadai zan tafi,ku baku san hatsarin wannan mutumin bane duk abinda ya ce ze aikata to fa se ya yi din".. Ammi dake kuka ta ce "baze yu ba,ni de bazan yarda kaje ba,ka rufamin asiri ka zauna bana son rasaka". Murya a tausashe Sudais ya ce"Ammi dole LTG ne ze je amma ba shi kadai ba,dole zamu bishi da kuma sojoji se mu labe daga baya" Duk sun amince da shawarar da Sudais ya bayar amma shide LTG kawai ya jisu ne, yasan abune ma wuyaci. Suna nan zaune a falon har kusan karfe uku na dare babu wanda ya runtsa. Miƙewa Sabriyah ta yi ta faki idon kowa ta shiga dakinsu number Fu'ad ta kira. Yana dagawa tafara zazzaga mishi ruwan Masifa. "Calm down my Sabriyah, kin san bazan taɓa cutar da rayuwarku ba,kawai ni Tajuddeen din nake buƙata in kuma be zo ba Wallahi sena kashe su". A firgice ta ce"dan Allah Fu'ad kar ka yi haka menene Abinda suka aikata maka in ma gaban ka kakeyi ai da ya Taj ne ba wai da su Umaisha ba". "To in har kina so in rabu dasu dukkansu dole se kin sanar dani duk wani abinda suka shirya nasan sun yi planing din yi min ha'inci". Tana share hawayenta ta ce"na yi alkawari zan faɗa maka komai amma dan Allah karka cutar da Umaisha da Iklas". "Karki damu my Sabriyah, muddin kika min yanda na ce nima na miki alkawari bazan musu komai ba". Kashe waya ta yi dan ta rasa takaicin waye zataji na Fu'ad din ne ko kuma na kanta da ta kasance wawiya ta yarda dashi. Komawa falo ta yi ta zauna,tana jin duk tattaunawar da ake yi,amma duk wanda ya mayar da hankalinsa akan ta ze gane ba'a cikin nutsuwarta ta ke ba. Kiraye_kirayen sallah asuba ne yasa su tashi suka je suka gabatar da sallah. Bayan sun dawo daga masallaci ne, sojoji da yan sanda suka kimtsa kansu domin tafiya hatta su ACP Jawan da Sudais sun shirya. Fitowa LTG ya yi cikin shirinsa na uniform din sojoji fuskar nan dama ba annuri ne akai ba yanzu yafi ko yaushe ban tsoro. Addu'a sosai su Ammi suka musu.na samun nasara. Kirane ya shigo wayar Sabriyah ta inda Allah ya taimaketa wayar na vibration. Fakan idon su ta yi ta shiga kitchen da babu kowa a ciki daga waya kafin ya ce komai ta sanar dashi shirin da sukayi sannan ta kashe wayar ta,ko muryarsa bata son ji. Kira ne ya shigo wayar LTG ɗagawa ya yi yasa akunne,bayan ya gama saurarar Abinda aka faɗa ne ya kashe wayar idonsa yana ƙara rinewa yana ja. Kallonsu ya yi."kowa ya samu guri ya zauna ni kadai zan tafi". A rude suka kalli shi"meyasa haka LTG?". Sudais ya tambaye shi. "Dan Allah karku hana ni,ya riga da yaisamu labarin shirin da ku ka yi,yanzu haka ya kashe yarinya ɗaya, bana son a sa'ke kashe wata,kar ku hanani,kuma kar wanda ya biyo ni".yana gama fadar haka ya fice a falon dan bayason ganin fuskar Ammin sa dake kuka". Suna kiran sunanshi amma ko juyawa be yi ba,ya shiga motar ya fisgeshi yabar gidan. Fashewa ta yi da kuka musamman idan ta tuna cewa Fu'ad kashe LTG ze yi kuma ita ce ta bada,taimakonta.da gudu ta bar falon tana kuka, direct part din LTG ta nufa ta tsaya tana kuka. Ji ta yi tana sha'awar duba part din nashi. Bedroom dinsa ta shiga wannan hoton da ranar ya hanata gani shi ta dauka tana kallo,zaro manyan idanunta ta yi kamar zasu faɗo ƙasa ganin wacce take jikin hoton. Duk da bata da hoton kanta a yanzu Lokacin da take yarinya karama amma tana ganin wannan hoton ta gane cewa ita ce a jiki,ƙaryata kanta ta yi ta bude locker din nan taci karo da folder din hotuna fito dasu ta yi, ta fara gani hotuna ne gaba daya a jiki,da wanda aka yi drawing da kuma wanda aka dauka a camera,bata sake shiga firgice da rudani ba se da ta buɗe wani shafin da taga hotonta da wannan saurayin da take yawan gani a mafarkinta,yana rungumeta da ita aka musu hoton,a ƙasa an rubuta "Asrah din Tajuju"sa'ke folder hoton ta yi ya fadi a ƙasa.jikinta ne ya dau rawa kamar mazari,gani take yi kamar a mafarki taya hakan ze yu, ta ya za'a yi ya kasance ita ce wannan Asrah din da wannan ahalin basu da magana da ya wuce nata.wani irin Flash ta fara ganin a idonta,tana jin muryoyi ana magana.rufe idonta ta yi ta sa hannu ta toshe kunnenta,a cikin idonta ta hango wannan yarinyar da ta gani ajikin album din da anty amarya a filin garden suna wasa,anty amarya na binta a baya ita kuma tana guda tana yiwa anty amarya dariya. Kokarin faɗuwa yarinyar ta yi,anty amarya ta ce "Asrah becarefull"riƙe yarinyar wani kyakyawan saurayi ya yi yana dagata ya daura a wuya. "My Tajuju". Da sauri Sabriyah ta bude idonta waral kamar fitila,nan take numfashinta ya fara fita da sauri sauri. "Kenan ni ce Asrah?,ni ce Asrah din da suke nema?,taya hakan ze kasance?"faɗuwa ta yi akasa ta na me yin ihu"bani baceeeee"domin har yanzu ta gagara gaskata ita ce Asrah. Da sauri kuma ta sa hannu ta bude shafi na ƙarshe a folder din hoton Asrah ne tana tsaye ba riga a jikinta,rubutun sunan Tajuddeen baro_baro ya fito a bayanta. A tsorace kamar wacce taga fatalwa ta yarda folder din a karo na biyu. Hannu tasa taja zip din rigarta ƙasa ta je gaban mirror dakin nashi ta juya bayanta kadan nan take sunan ya bayyana. "Innalillahi wainna'ilaihi rajuun shikenan ni da kaina na tura muradin rayuwata wajen da za'a kashe shi,na tura tajujuuuuu na wajen da za'a kashe sa, muddin wani abu ya samu Tajuju to bazan taɓa yafewa kaina ba". Kamar mahaukaciyar da ta gudo daga gidan asibiti take magana tana kuka kamar ranta ze fice daga jikinta. Da gudu ta baro part din nashi tana sambatu,kowa na zaune a falo ana jimamin halin da suke ciki ta fito da muguwar gudu zata wuce su,ga kururuwar kukanta da ya cika gidan. Da gudu Sudais ya yo kanta ya damki hannunta kamar wata me aljanu ta fara fisge_fisge tana "dan Allah ya Sudais kabarni, Wallahi ze kashe shi,ze kashe min shi!,na shiga uku na ze kashe min farin cikin rayuwata". Ganin yanda take magana ne yasa suka yi tunanin ko aljanu ne suka shigeta, zaunar da ita Sudais ya yi amma ta sake yunkurin miƙewa. Maida ita uncle Hameed ya yi ta zauna,wasiwasin abinda ya sameta suka shiga yi. Abbie ne ya ce "Sabriyah menene abinda ya sameki,kuma waye kike cewa za su kace miki?"duk zuba mata ido sukayi suna son jin amsar da zata bayar. Da karfi ta ce "Tajujunaaaaaaaaaaa" Sa'ke zuba mata ido sukayi ɗan son tabbatar da abinda ta faɗa. Anty amarya murya na rawa ta ce "Sabriyah bamu fahimci abinda kike son cewa ba". Tana kuka ta ce "Fu'ad ze kashe min Tajuju na,nice!nice!nice"ganin yanda take jin kamar ana rike mata wuya ne yasa ta juya musu baya ta ja zip din rigarta kasa nan take sunan Tajuddeen ya bayyana a gadon bayanta. Tirka_tirka,wani irin shock ne ya kamasu,basu taɓa shiga cikin matsananciyar al'ajabi ba irin wannan. Kusan a tare gaba dayansu suka furta. "Asrahhhhhhhhhh?". Gyada musu kai ta yi tana kuka. "Wallahi Fu'ad bashida imani ze kashe min Tajuju na,kuma muddin ya mutu Wallahi nima mutuwa zan yi in bar Duniyar nan". Don't forget to comment, share and like. Anan na kawo karshen book one, Book two din na kuɗi ne ga duk me bukata ya min magana ta whatsspp number ta 09024503194. Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels