Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 *All thanks to Allah S.W.T for giving me the chance and privilege to start this book* 1..... Muryar dattijuwar macen da baxata haura shekaru hamsin a duniya ba ne ya cika dakin, hankali tashe take jijjiga matashin saurayin da shekarunsa ashirin da takwas, kwance yake kan makeken gadon dakin, ta dinga cewa "Are you okay son, open ur eyes, Aliyuuuu ka bude idonka, What's ur problem..... Wani irin mafarki ne wannan ni fatima" sai a snn ya bude idanuwansa a firgice ya mike xaune yana bin dakin da kallo kirjinsa na heaving, lkci daya ya mayar da kallonsa kan mahaifiyarsa dake kallonsa ta ma kasa cewa komai, ya runtse ido cikin sanyin murya yace "Motherrr...." ta kamo hannunsa damuwa karara fuskarta tace "What's ur problem Aliyu? Meye matsalar ka ka gaya min, are you sick?" ya buda idanuwansa yana kallonta murya can kasa yace "Ki taya ni addu'a mum... I don't knw, I just can't have rest of mind, may be....." Sai kuma yyi shiru hawaye ya taru lumsassun idonsa, tace "Ni mahaifiyar ka ce Aliyu, kana da warce xaka fadi ma damuwar ka duk fadin duniyar nn banda ni, tell me where you've gone wrong, what wrong have u done, ka gaya min Aliyu" ya share xufar goshinsa ya daura kai bisa kafadunta a hankali yace "Ki taya ni da addu'a kawai ummata" dago Kansa tayi tace "Wato dai baxa ka fada min ba koh?" Shiru yyi yana kallonta da manyan idanuwansa, can ya lumshe su a hankali ya bude yace "I will continue praying mum, it's not even worth saying kema ki taya ni...." Sake sa tayi ta mike tsam ta nufi kofa ya bi ta da ido kafin ta fita a hankali yace "Ur prayers plss mum..." Bata tankasa ba ta yi ficewarta, ya kalli agogo karfe biyun dare ya mike jiki a sanyaye ya shiga bathroom. *5years later* A hanxarce ta karasa dauraye cup da spoon da ta wanke ta fito kitchen din ta kashe electronics dake a kunne parlor ta dau jakarta dake kan kujera ta sakale a kafada ta nufi kofar fita tana kallon agogon wrist dinta, doguwar riga ce yar kanti Sea green a jikinta sae karamin mayafi ja da flat shoe shi ma ja, don ita din ba gwanar sa hill bace tsabar tsayinta, jakar hannunta ma dai jan ne, bbu komai fuskarta banda powder da eye pencil sai chapette da ta goga a lips dinta, amma ba lallai ka yrda cewar bata shafa pink lipstick ba tsabar pinkness din lips din dake dauke da xagayen baki, ita kanta tasan her lips are Unique, but who cares?? D'an tsaki ta ja ta bude kofa ta fito rike da makullin da xata rufe kofar Apartment dinta, tsaye taga wani matashi bakin kofar dake kusa da apartment dinta shi ma fitowarsa kenan da alama xai kulle kofa, dogo ne sosai domin kuwa irinsu ake kira da gentlemen, kuma duk tsayinta sai ta ganta karama kusa da shi, ya fi kama da mutan Egypt ko Ethiopia duba da kalan haskensa da irin gashin kansa, bakar shade ce a idonsa da ya fito da ainahin tsayin hancinsa, fuskar nan tasa a tamke bbu annuri, a hankali ta sauka ta bar masa gun, yana gama rufe kofarsa ya juya ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce parking space, bin sa tayi da kallo ta rasa gane ko mancewa yyi bai gyara belt dinsa ba, ko kuwa ass down yyi, sakin baki tayi ganin of course ass down din fa yyi, ta dauke kai cike da takaicin xama a compound daya da xa su yi da shi. Shine sabon tenant din apartment din dake kusa da nata bayan tashin makwabciyarta mai kirki Nancy, tun tashinta dama take ta addu'ar Allah yasa ba namiji bane xai kama flat din sai ga shi kuwa namijin ne, bata kuma sani ba sai a yanxu don tafi sati uku bata kasar tun bayan da suka yi hutu dawowarta kenan jiya da yamma, jiki ba kwari ta karasa rufe kofar ta fita don samun taxi da xai kai ta makaranta wato University of Cambridge dake kasar. Karfe biyu da 'yan mintuna suka fito school tare da kawarta Vanessa, tun shekararta ta farko suke tare gashi har sun doshi shekara ta uku kenan tunda saura masu yan watanni ne kawai, sai da vanessa ta jira kawartata ta hau taxi bayan ta sanar da shi Bridge street xai kai ta kafin ta daga mata hannu tace "See yah pretty" ta sakar mata murmushi tana daga mata hannu daga cikin taxi din tace "Alryt love" har suka isa gida hankalinta bai tare da ita tayi nisa cikin tunanin da take yi, har sai da muryar Ba'indiyen dake jan taxi din ya dawo da ita duniyar tunanin da ta shiga, ta fito ta mika masa kudinsa sannan ta shiga gida, da sauri ta shige apartment dinta bayan ta bude, duk da bata ga alamar yana gidan ba don babu motarsa a ma'ajiyar sa. Wanka ta fara yi tayi sllh snn ta shiga kitchen don girka abinda xata ci, Noodles kadai ya rage gidan, don haka ta daura ruwa ta shiga hada wa, kafin ya dahu ta kwashe dustbin dake kitchen ta bude kofa ta fita da tsintsiya, kasake tayi tana kallon uban kayan gym da ya jibge daga gefen flat dinsa, tun dawowarta sai a lkcn ta fito backyard din flat dinta, ta tabe baki ta dau tsintsiya ta hau share gun, har part dinsa sai da ta share tayi disposing bolar a basket ta koma ciki ta rufe kofarta, tana gama cin indomie ta wuce daki ta kwanta, ta jawo wayarta don duba agogo taga karfe uku saura minti biyar, ajiye wayar tayi don wa enda take da niyar kira tasan suna makaranta ynxu, ta lumshe ido. Ba ita ta tashi daga baccin da ya dauketa ba sai hudu da quarter, ta shiga bayi da sauri don dauro alwala tana idar da sllh kuma ta dau material din karatunta ta hau yi. *Nigeria* Zaune yake kan dining idanuwansa a kan system dinsa dake gabansa yana kallon kwallo, hango mahaifiyarsa da yyi tana sakkowa daga saman bene yasa shi saurin dauke plate din abincin dake gaban sa ya tura karkashin dinning din ya dau lemon dake cup ya sha kusan rabi sannan ya ajiye ya goge bakinsa da handkerchief ya ci gaba da kallonsa keenly, har ta karaso dining din idonta na gun da yake xaune, ta jingina da pillar din dake wajajen dining din tace "Ina abincin?" Dago kai yayi ya kalleta yace "Mum, ban ma yi noticing naki ba ae, na ci" tace "The plate?" Ya nuna mata hanyar kitchen yace "Har na wanke" girgixa kai tayi ta juya ta koma parlor, ya saci kallon abincin da ya ajiye kasar dining yyi saurin dauke ido ya ci gaba da kallonsa, lkci daya ya lumshe ido ya jinginar da kansa jikin kujerar dinning din, ya fi minti goma a haka yaji ance "Ya Aliyu...." Ya bude ido da sauri, kyakkyawar yarinyar dake tsaye gaban sa ta sakar masa murmushi tace "Ina yini" yace "Lafiya lau... Hanan" ta buda idanuwanta sosai tace "Kai ka ajiye abinci a kasan nan?" Ta fadi tana nuna masa inda ya tura abinci, ya kalli direction din parlor da sauri yaga mumy bata nan, dukawa yyi ya fiddo yace "Gashi ki ci na koshi" ta tabe baki tana kallon hadadden jollof rice din dake dauke da kayan yanke yanke a kai da kusan quarter din kaza a gefe da plantain, kallonta yake yaga tayi murmushi tace "Kai me yasa baka ci ba?" A kara jinginar da kansa da kujera a takaice yace "I am nt hungry, idan baxa ki ci ba kema ki kai ma masu gadi yanxu" dauka tayi ta nufi kofar fita parlorn, ya bita da ido kafin ya mike ya kashe system dinsa don bai son ta dawo ta samesa a gun ya haura sama da sauri. Misalin Karfe tara na dare tana kitchen tana dafa ruwan Lipton kamar yanda ta saba kafin ta kwanta, sai a sannan ta dinga jin kewan Nancy, don da yanxu ta ganta a dai dai wannan lkcn tana xaune kan resting chair tana shan coffee tana chatting, duk da ita ba gwanar xama a waje bace amma so tari saboda Nancyn haka nan ita ma xata bude kofa ta fita ta sameta ta xauna, sun yi ta hira kenan har kusan sha daya kafin kowa ya shiga ciki sai kuma gobe, Kamar ance ta daga kai suka yi ido hudu da wannan mutumin na daxu da safe daga shi sai singlet da 3 qtr waya na kare kunnensa, daya hannunsa kuma na rike da kwalba, sosai gabanta ya fadi tayi saurin kallon kofar kitchen dinta don ta tabbatar a kulle yake, ta sake satan kallonsa taga ya dakatar da wayar da yake yana kallonta ta cikin window ita kanta ta kasa fassara irin kallon, a hankali ta kai hannu ta kashe gas dinta sannan ta kashe wutan kitchen din gaba daya ta fita parlor da sauri don ta hakura da ruwan Lipton din. *Haske writers Association**💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 2...... Washegari tun da ta tashi sallahn asuba bata sake komawa ba, ta d'an yi aikace aikacen da xata yi, sannan ta shiga shirin makaranta, ta dau lkci xaune a parlor bayan ta gama shiryawa, can ta jawo wayarta dake gefenta tayi dialing number ta kai kunne a hankali, har ya gama ringing ba a daga ba ta ajiye wayar ta mike ta dau plate na cake da ta ci ta kai kitchen, karfe bakwai da rabi ta fito gidan domin wucewa makaranta, abaya ce ta Al-layl jikinta baki, sosai abayar ta haska ta kasancewar ta fara, tana kkrin rufe kofa da makulli ya bude kofar Apartment dinsa ya fito, bai ko kalli gefenta ganin xai kulle kofarsa yasa ta sauka a hankali ta basa waje tana kallonsa don ko considering dinta bai yi a tsaye wajen, yau ma kamar jiya kananun kaya ne jikinsa, yana sanye ne da deep Blue polo me wani rubutu da bata gani ba a gaban rigar da jean trouser baki, ya gama rufe kofar yyi wucewarsa ba tare da ya kalli inda take tsaye ba, kamar dai jiya ynxu ma sai ta ga kamar sagging trousers din yayi, yaushe rabon duniya da shigen haukan nan, ta bi sa da wani irin kallo, bata san lkcn da ta ja wani dogon tsakin takaici ba, lkci daya ya juyo yana kallonta kamar jiran tsakin yake, gabanta yayi mugun faduwa, ya xare glass dinsa wanda hakan ya bayyana manyan idanuwansa masu kamar brown, still tayi a inda take xuciyarta na bugawa tana kifta ido, sai a snn ta kare ma fuskarsa kallo ta kuma kara tabbatar da lallai shi din kilan balarabe ne, kafafuwarta suka kasa daukarta ganin ya nufo ta, ya iso dab da ita yana mata wani kallo kmr me counting words dinsa yace "Did.... You.... Just.... Hissed?" Ta wani hade rai har lkcn xuciyata bai daina bugawa ba ta dake tace "Did I Know you???" Daga sama har kasa ya kalleta yace "Did u skipped English Language in school?" Ta hadiye abu da kyar hakan kuma bai hanata harararsa ba tana juya ido tace "That's none of ur....." K'ara tayi a mugun tsorace jin yanda yyi gripping dinta da karfi yana mata wani kallo har tana iya jiyo numfashinsa, lkci daya jikinta ya dau rawa hawaye ya fara taruwa idonta tace "Let go of me right away...." sai da ya gama kare mata kallo daga sama har kasa snn ya tura ta yace "We stil remain in the same surrounding" yana fadin haka ya juya ya yi wucewar sa, ranta a dagule ta rufe kofarta da sauri ta fice gidan hawayen takaici cike idonta. Throughout a schl ranan bata da sukuni duk ta rasa me ke mata dadi, how on earth xata iya rayuwa da wannan mutumin a gida daya, Vanessa da ta lura da she wasn't her self tun shigowarta schl ta kalleta tace "Pretty what's ur problem, u look dull all day, mood swing?" Ta d'an yi murmushi ta ja lemonade din gabanta ta sha kadan ta ajiye don dama a cafeteria suke tace "You don't worry Friend, I will be okay, I will fix my problem...." Vanessa tace "Good" sai bayan la'asar ta koma gida daga school, tana shiga apartment dinta ta sa key duk da ta lura bai dawo ba don bbu motarsa a gidan, but it will be safe ta sa makullin, tana idar da sllh xata kwanta ta tuna xata yi shopping don bbu komai a gidan banda noodles, ko kadan bata ji dadin tuna hakan da tayi ba gashi bata son fita, ta kusa minti goma xaune tana contemplating ta je ko dai ta hakura sai gobe, ganin bata da option ta mike jiki ba kwari ta fiddo babban veil ta yafa kan doguwar rigar jikinta don mai karamin hannu ne ta dau yar Jakarta karama ta rataye a kafada ta fita, nearest shopping complex ta nufa a taxi, tayi duk shopping da zata yi sannan ta dawo gida, mai taxi din ya taimaka mata ya sauke siyayyar sannan ta basa kudinsa ta dau kadan daga kayan ta shiga gida, gabanta ya fadi sosai ganinsa tsaye a parking space dinsa yana waya, tunda ta kallesa sau daya bata sake kallonsa ba tana isa tsakiyar compound din ta aje kayan hannunta ta koma waje dauko wasu, har wani harhardewa take yi tsabar rudun da ta shiga na ganinsa, ta yi sahu uku a na karshe ta daga kai suka yi ido hudu don kallonta yake, tayi saurin dauke ido ba tare da ta lura da har ta iso gun da take ajiye kayan ba ta afka kai sai gata a kasa ledan hannunta ya fadi chocolates da biscuits dake ciki duk suka watse nan kasa, har lkcn bai daina kallonta ba kuma bai ce komai ba, ta mike tsaye da sauri tana karkade jikinta hawaye cike idonta ta ki yarda ta kalli inda yake, a sanyaye ta durkusa ta shiga hada chocolates din da biscuit waje daya, ta gama ta tashi ta dau kadan daga kayan ta kai cikin parlor bayan ta bude kofa da key, haka tayi sahu har hudu kafin ta gama kwashe duk kayan, ta saci kallonsa taga kallon direction dinta yake, wani matsiyacin kallo tayi masa hade da jan tsaki, gyada kai yayi a hankali yana kallonta da wani murmushi fuskarsa, ta banke kofar ta ta kulle da makulli. Daki ta shiga ta kwanta bayan ta kai kayan maxauninsu a kitchen, har lkcn ta kasa samun nutsuwa sai juye juye take, ita ce xata xauna gida daya da wannan mutumin, ta girgixa kai tace "Impossible" tana ta kwance har bakwai saura qtr daga karshe ta tashi xaune a hankali ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta dau wayarta tayi dialing number ta kai kunne, bayan wani lkci aka daga, bata ji mamakin muryar da taji ba aka ce "Anty we re missing you plsss" a hankali tace "Really?" Ya marairaice yace "Yes Anty, good evening...." Ta kwantar da kanta jikin gado tace "Evening How you, hw is school today?" Yace "fyn Aunt" tace "Ina Sudais?" Yace "He is praying" tace "And what about you?" Yace "I just performed ablution now" tace "Alryt, Ina Mummy?" Yace "She is at the parlor" tace "And Nanny?" Yace "She is washing our uniforms inside d bathroom" tace "Alryt dear, I will cal back later, go and pray" yace "OK byeeee" daga haka ta katse wayar ta ajiye ta tashi ta fita xuwa kitchen jin ta fara jin yunwa, irish ta shiga peeling don ganin shi xai fi mata sauki, a hnkli ta leka window din kitchen din jin muryar da tayi a waje, xaune ta gansa kan kujera a part dinsa waya kare kunnensa, fuskar nan tasa bbu yabo bbu fallasa ya shafa beard dinsa yace "I missed you more...." Sai can kuma ya wara idanuwansa da ko kadan bata son irin su yace "Ohk when will that be?" Mikewa yyi bayan wani lkci yayi pick din flower a jikin ganyen dake shuke gun yace "Sure! I will be looking forward baby, when coming just let me knw" yana fadin haka ya juyo suka yi ido hudu don haske ne sosai gun kamar rana snn wutan kitchen dinta ma a kunne yake, ta hade rai sosai tayi saurin dauke kai ta bar jikin window din, bbu wani walwala ta karasa abinda take tana yi kuma tana saton kallon window ga faduwa da gabanta yake taga ya bar wajen, har dai ta fice kitchen din bayan ta gama girkin ba don ta gyara ba. Yau alhamis throughout bata da lectures tana gida idan ta gaji da karatun ta kwanta, in lkcn sllh yyi ta tashi ta yi, tun takwas din safe ta lura ya fice gidan, hudu da kusan rabi aka danna bell dinta ta dago da sauri sanin bbu wanda take expecting a lkcn, Vanessa bata ce mata xata xo ba, ta fi minti daya rike da kirjinta da ya wani amsa kamar an soka mata abu mai tsini, duk da ba sabon abu bane hakan a gunta amma ta dade bata ji hakan ba sai xafin yyi mata yawa, jin an kuma dannawa ta dago a hankali bata dai ce komai ba, har dai taji xugin ya lafa sosai, ta mike da kyar ta isa gun kofar a hankali tace "Who's there?" ✨ *Noor Al-Hayat*✨ _By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 3..... Muryar mace taji tace "Sorry for intruding Madam...." Jigum tayi na d'an lkci kafin ta bude kofar tana kallonta, baturiyar matar tace "Good evening...." Ta gyada mata kai tace "Same..." baturiyar tace "I am Clara Edward" a takaice ita ma tace "Khadijah Muhammad" Clara ta mika mata textbooks din hannunta tace "Can you please help keep this for you Neighbor? I mean Dr Ayman..." D'an buda ido Khadijah tayi ta girgixa kai da sauri tace "Of course noo, you just wait for him, I think that will be better" Clara tayi murmushi tace "But he said I can hand it over to you, I just gave him a call now..." kallon litattafen na tsaya yi gabana na faduwa, Clara tace "Yeah, i am travelling today, and i can't go with his material" Khadijah dai ba don ranta ya so ba ta karba, Clara ta mata godiya ta juya ta wuce, Khadijah ta rufe kofarta, nan kan kujera ta ajiye books din a parlor. Ta fito daga wanka misalin karfe takwas da wani abu aka danna bell, tsaye tayi da mamaki tana tunanin to waye kuma wannan, jin an sake dannawa ta xura Hijab ta fito parlor tace "Who?" Ba a ce komai ba hakan yasa taki karasawa, ga xuciyarta da ya fara bugawa, aka kuma danna bell din, dakewa tayi tace "Who's there?" A takaice taji muryarsa yace "Somebody, open right away" mamaki ya cika ta sosai har lkcn kuma xuciyarta bai daina bugawa ba, tayi karfin halin cewa "So? What did you want from me?" Yace "Open now" A fusace tace "Did you miss ur road!" Yace "Did you knw I can open the door my self?" hankalinta yyi mugun tashi, kamar xata yi kuka tace "And did you know I can also report you to the police right away" cikin tsigar rainin hankali yace "Ohh really? ohk then, let me get the door open for u so you can have ur way to d police" baya ta koma da sauri cikin rawar murya tace "Plss stay away from me, I don't knw you" hawaye cike idonta ta kare maganan, shiru bai ce komai ba, har ta fara tunanin ya wuce ne tana nan tsaye dai kamar an dasa ta don ta dade bata shiga tashin hankali irin na lkcn ba, can cikin husky voice taji yace "Then.... I want to get my reading materials from you" da sauri ta kalli textbooks dinsa da ta ajiye daxu, gaba daya ta mance da su, ta hade rai kamar yana ganinta tace "Sorry, i can't open my door now, you'll get it tomorrow at ur door step" yace "You must be joking, wil u get that door open and hand over my property to me" mamaki ya cikata tace "Sorry I can't" yace "This is serious" juyawa tayi ta koma kan kujera ta xauna, sai dai fa gabanta faduwa yake, bayan kusan second talatin yace "Look I am having exams, and I need those books" banxa tayi masa, a hankali taji yace "Alryt... Plss" shiru ta yi tana naxari d'an ita gaskiya tsoro take, can tayi tsaki ta kwashi books din ta nufi kofa, gabanta sae faduwa yake ta bude a hankali tana karanto addu'o'i a xuciyarta, tana bude kofar taji ya cafko ta, ta yi wani ihu ta saki books din hannunta jikinta na rawa, ya rungumota firmly har tana iya juyo numfashinsa, turasa ta shiga yi hankali tashe ta dinga cewa "Let go of me...." ya ki saketa yana kallon kwayar idonta fuskarsa daure yace "Isn't this what you're afraid of?" Yatsine fuska yyi ya turata yace "I am waiting for the police" daga haka ya duka ya kwashe books dinsa, tuni ta shige ciki dai dai lkcn da ya mike tayi banging kofarta ta sa lock, ya ja baya da sauri yace "Damn it..... What a f**k... I will get you" Da gudu ta koma daki kamar ya biyota din nan, ita kadai tasan irin tsoratan da tayi. Gaba daya ta kasa bacci har kusan karfe daya gashi ko wanka bata yi ba balle ta sauya kaya xuwa na bacci, duk kamshin turarensa ya cika ta tun rikon da ya mata, ko ta ya ta juya kamshin kawai take ji, a hankali ta tashi kamar mara laka ta cire kayan jikinta ta shiga toilet, wanka tayi ta fito ta xura rigar bacci ta kwanta bayan ta feshe jikinta da turarrukan ta, sai a sannan bacci ya dauketa. Sai kusan karfe bakwai ta tashi washegari ta mike da sauri ta shiga toilet tana salati ganin ynda ta makara, karfe takwas da rabi ta fito shirye cikin doguwar rigar kanti kamar ko da yaushe, blue ne rigar mai stones baki, sai white veil da ta daura kanta, takalminta ma fari ne haka karamar jakar hannunta sai handouts dake hannun, kana ganinta kasan a tsorace take, ta rufe kofarta da sauri ta nufi gate dai dai nan suka kusa cin karo xai shigo, sosai gabanta ya fadi ta juya kamar kiftawar ido har ta bar bakin gate din, can gun da aka tanada domin parking space a gefen apartment dinta ta nufa sannan ta juyo tayi iya kkrin ganin ta boye tsoron fuskarta tana kallonsa tayi kicin kicin da fuska, lkci daya ta karasa kofarta ta ga ya nufo wajen, tsabar rikicewa ta kasa bude jaka ta ciro makulli sae rawa hannunta yake, ta fashe da kuka ganin ya kusa wajenta tace "Am begging you stay away from me plss, I don't know you.... Stay outta my way" har ya karaso gun bata iya ta motsa ba, kawai ta durkushe kasa ta rufe ido, jin ya bude kofar sa ta dago da sauri, suka hada ido yace "I only have ur time at night" daga haka ya shiga ciki ya rufe kofarsa ta mike a sanyaye tana kallon kofar, da sauri ta fice compound din gabanta na faduwa. Suna gama lectures ranan tace da Vanessa a gidanta xata yi spending night din, don haka tare suka wuce gidan Vanessa dake Round church street, Vanessa tayi masu girki suka ci bayan Khadijah tayi sallah, karfe shidda saurayin Vanessa ya xo gidan Khadijah ta shiga bedroom ta bar masu parlorn, har ta fara bacci Vanessa ta tada ta wai Richard xae kai su shopping, duk yanda Khadijah taki amincewa aje da ita sai da Vanessa tayi convincing dinta suka fita tare, turarurruka kawai ta deba a mall din, sun yi kusan minti sha biyar kafin Vanessa ta gama siyayyar da xata yi suka bar mall din, gun siyar da ice cream suka tafi daga nan, Suna tsaye cikin Aromi ba a kai ga siyar masu cold stone ice cream din da xa su siya ba kamar ance ta juya suka yi ido hudu da neighbor dinta, xaune yake da wata kyakkyawar baturiya da baxata wuce ashirin ba ga kayan ciye ciye a gabansu yarinyar na rike da hannunsa cikin nata, tun daga sama har kasa yake kallon khadijah, ta hade rai tayi saurin dauke kai ta amshi ledan ice cream din da Vanessa ke mika mata, Richard ya siya masu har da pizza ya biya bills din, tuni ta yi hanyar fita Vanessa na biye da ita, ta d'an saci kallonsa taga kallonta yake yana wani murmushi ta jefa masa harara suka fita wajen, motar Richard suka shiga ya mayar da su gida. A gidan Vanessa tayi weekend din gaba daya, ranan lahadi ta shirya ta koma gida ba don ranta ya so ba, duk da a xuciyarta dama niyyar dawowa ta kwaso kadan daga kayanta ta dawo gidan Vanessa tayi, tunda taxi ya ajiye ta gabanta ke faduwa kamar mai tausayin kasa ta dinga tafiya tana waige waige duk da bata ga motarsa ba hankalinta ya ki kwanciya, tana kkrin bude kofa taji an bude nasa kofar a gigice ta sakko kasa dai dai lkcn da yarinyar da ta gani a eatry ranan ta fito daga parlornsa, yarinyar tace "Hello, seems I frightened you" banxa Khadijah tayi mata da farko can kuma tace "Never mind" daga haka ta shige apartment dinta bayan ta bude, bin parlorn ta dinga yi da kallo ganin ya d'an yi k'ura, kawai tayi deciding ta gyara ko ina kafin ta bar gidan, ta tsaftace ko ina ta goge, sannan tayi wanka ta canxa kaya ta fito parlor, kitchen ta shiga jin tana jin yunwa, cikin mintuna kalilan ta hada ruwan jollof din cous cous da yaji nama ta dawo parlor ta kwanta, har bacci ya dauketa ta farka da sauri don ko cous cous din bata xuba ba, ta dawo parlor bayan tayi hakan bacci ya sake saceta, cikin bacci ta dinga jin k'auri, ta shi da sauri ta nufi kitchen din, turus tayi komai nata ya tsaya ganin wanda ke tsaye bakin gas, wani ihu tayi ta juya cikin rikicewa xata fita ya fixgota, ya matse ta jikinsa ya rufe bakinta, kasa kwakkwaran motsi tayi ta kuma kasa freeing kanta, hawaye ya cika idonta taji kafafuwarta sun kasa daukarta, yana mata wani kallo cikin husky voice nasa yace "Kin gama gudun kin dawo?" Xaro ido tayi tana kallonsa da mugun mamaki, bai damu da hakan ba yace "All this while kina gidan boy Friend din ki right?" Takaici ya rufe ta dake tace "Yess" yyi wani murmushi yace "Kina me?" Tace "Abinda kke kawo yan mata suke yi a flat din ka...." Ko rufe baki bata yi ba ya hade bakinsa da nata, ta rude ta dinga kokuwa da shi amma ko gezau, don kansa ya saketa yana kallonta da lumsassun idonsa yana murmushin rainin hankali yace "Haka kenan" ta fashe da kukan takaici ta durkushe a wajen xuciyarta na tafarfasa, yace "Next time ba sai kinje gidan saurayin ki ba, you need it... Ki sameni a flat dina kawai" daga haka ya nufi kofa, sai kuma ya juyo yace "Mind you, I hate smell of burnt foods" yana kai wa nan ya fita gidan gaba daya cike da kasaita, ta mike da sauri ta na kallon kofar don a tunaninta ta rufe da ta shigo. *Haske Writers association*💡 *Haske Writers Association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By khaleesat Haiydar_📚✍🏻 4...... Ta fi minti biyar a tsaye duk jikinta a mace, tunani daya ya xo xuciyarta a lokacin and that is ta bar apartment din ta koma gun Vanessa da xama gaba daya har ta samu wani gidan, ta juya ta kalli gas din kitchen din taga ya kashe, kamar mara laka ta fito parlor ta karasa kofa ta sa key, xaunawa tayi parlor har lkcn tana ganin abun kamar a mafarki, ita fa yanxu bata ga namijin da ya isa ya takura ma rayuwarta, ba ayi namijin nan ba ko waye shi kuwa, tunanin hakan yasa ta yi murmushin takaici hade da jan tsaki ta mike ta wuce daki, nan ma dai xaunawa tayi gefen gado ta kasa daina mamaki, kiss kuma? how dare him kiss her? Haka nan kawai yayi kissing dinta kuma ta kyalesa, hawaye ne ya cika idonta tuna hakan da tayi, ca tayi masa ita gantalalliya ce? Ko kuma xaman kanta take a k'asar? ta xamo kasa ta jinginar da kanta da gado xuciyarta na kuna, to yanxu wa xata kai ma kukanta a kasar nan, nobody in particular, Vanessa won't take this as anything ko ta gaya mata ma dariya xata mata, Yusuf?? ji tayi ranta yyi wani mugun baci da ta tuna yaren da yyi mata, wai a hakan shi bahaushe ne ko kuwa Hausa kawai ya ji, abinda ta kasa ganewa kenan, ta kuma jan tsaki a xuciyarta tace ai sai dai kawai ya ji Hausan don in har dai shi Afuno ne he is nothing but a disgrace to Hausa and Hausa land as a whole, infact ta ma san ba bahaushe bane.... har kusan goma tana xaune kamar mara abun yi, xuciyarta dai ya kasa dawowa dai dai, ta Dade ranta bai baci ba irin na yau, can dai ta kuma jan tsaki for the countless time tace "Sai nayi maganinka kafin in bar gidan nan in sha Allah, you can't just put ur filthy mouth in mine and go scot free...." daga haka ta mike ta shiga bathroom, wanka ta yi ta dauro alwala ta fito ta yi shafe shafenta ta xura doguwar Riga ta tada sallahn Isha, ko da ta idar ta shafe addu'o'in da tayi ta jawo wayarta don sau biyu ana kira tana sallan, Vanessa ce ke kiranta, ta shiga kiranta baya, Vanessa na dagawa tace "Hey love, you are still nt yet back" Khadijah ta kalli agogo a hankali tace "It's late Vanessa, I will come over tomorrow" daga haka Vanessa tayi mata sai da safe ta katse wayar, sai a sannan taji ta fara jin yunwa, ta mike ta fita xuwa kitchen don duba girkinta na daxu, tsaye tayi ta kasa kunne jin kamar muryar mace a kitchen dinsa da yake ko ina was very silent, a hankali ta karasa jikin window ta kafa kunne, nan ko ta kara tabbatar da hakan, muryar mace take ji, ta rike ha6a da mamaki k'ana ta kyabe baki ta dau plate ta debi abincin da xata diba ta fita kitchen din, tana gama ci ta tafi daki ta hada gaba daya kayan sawanta a jaka biyu, tana shirin kwanciya wayarta yyi kara, ta dauka tana kallon screen din sannan ta xauna gefen gado ta daga kiran hade da sallama, a hankali tace "lafiya lau Umma ya gida" Daga daya bangaren warce ta kira da Umma tace "Alhmdllh, na ma yi tunanin kin kwanta, ya karatun" tace "Alhmdllh Umma, yanxu xan kwanta" Umma tace "Toh Allah ba mu alkhairi, a dai dinga kula sosai kinji" cikin sanyin murya tace "Toh Umma" daga haka suka yi sallama ta katse wayar, kwanciya tayi hade da rufe duk jikinta da duvet har lkcn ranta ba dadi. Tun da ta idar da sallan asuba bata koma ba kasancewar da safe take da lectures, ta yi wanka ta wanke bathroom dinta sannan ta fito xuwa kitchen don tsaftace sa shi ma, wanke duk utensils da ta 6ata jiya tayi sannan ta hada bin din gaba daya a kwandon da aka tanadar don haka, Hijab ta koma ta xura kan yar rigar jikinta ta dawo kitchen din ta bude kofar ciki ta fita don disposing sharan dustbin, still tayi ganinsa a wajen, ya ajiye weight din hannunsa tana ganin haka ta juya da gudu ta koma kitchen ta rufe kofar da makulli hannunta na rawa, tsaye yayi jikin window din kitchen dinta yace "Ga Beast ko monster koh?" Ko kallonsa bata yi ba, ta kashe fitilar kitchen din ta fita parlor ta yi banging kofar da karfi ta rufe. Yayi wani murmushi yana share xufar forehead dinsa, Komawar da ba ta yi kitchen din ba kenan har ta gama shirin makaranta, Abaya ne baki da mayafinsa sanye jikinta, duk da yunwar da take ji haka nan ta dau jakarta ta nufi kofa, a hankali ta murda makullin ta bude ta leka waje sannan ta fito tana karanto addu'a a xuciyarta, ta gama rufe kofar kenan, wata baturiya da baxata wuceta ba ta fito daga apartment dinsa, ba karamin faduwa gabanta yyi ba don a tunaninta shine, 'yar riga ce iya cibi da wando jikin baturiyar sai yar karamar jaka da litattafai a hannunta, Khadijah bata sake kallonta ba har ta sauka d'an stairs din dake wajen, taji yarinyar tace "Good morning" yi tayi kamar bata ji ta ba tayi wucewarta, taji yarinyar na cewa "Is she having difficulty in hearing?" sai a sannan Khadijah ta gane shi ma ya fito kenan, hakan yasa ta kara saurinta, taji yace "I think so" tuni ta fice daga gidan ta tsayar da cab ta hau ta gaya masa inda xa ta, ya ja cab din, a xuciyarta tace In sha Allah ma this is the end, ba lallai ma ta kwana gidan ba yau, don tana dawowa makaranta dama fiddo kayan ta xata yi ta yi wucewarta gidan Vanessa, but she promise before leaving xata koya masa lesson xata gwada masa cewar ba ko wace mace ce sha sha sha kamar sa ba, abinda ta lura da xaman k'asar shine gwara a hadaka da bature waje daya sau dubu a kan wanda ku ka fito k'asa daya. Xaune Khadijah take tare da Vanessa da wata course mate dinsu Angela, sai wata Maryam 'yar Nigeria kamar ta amma kuma a nan UK aka haifeta, ko kadan Khadijah bata yarda sun saba da Maryam ba, hasalima gaisuwan kirki bai hadasu, ita kanta Maryam bata sake da ita ba, amma kilan hakan na da nasaba da cewar ba course daya suke ba, duk da haka dama can yarinyar bata ma Khadijah ba, ba wai tana da wani aibu bane ko wani abu, kawai she just don't like her ta rasa dalili kuma, don so tari ma idan ta ganta sai taji faduwar gaba, sannan ganin ta na tuno mata da wani abu da ba ta son tunawa a rayuwarta gaba daya, yanxun ma su kadai suke hirar su, ita dai tana ta danna wayarta kanta a sunkuye, duk ta kagu Vanessa ta tashi su tafi, dama can Angela ba kawarta bace, don she is too lousy to be kept as friend, d'an gaisuwar da suke ma da ita ta dalilin course dinsu daya ne, gajiya tayi daga karshe ta mike ganin Vanessa bata da niyyar tashi da halshan turanci tace mata xata je can gidanta ta dau kayan da xata dauka sai su hadu a can gida, Wato gidan Vanessa din, Vanessa tace to sai sun hadu, daga haka ta fara tafiya, Angela tace "See yahh tomorrow Pretty" sunan da wasu ke kiranta da shi kenan a makarantar, Juyawa Khadijah tayi ta kirkiri murmushi tace "Sure" daga haka tayi wucewarta Maryam ta bi ta da kallo. Karfe biyu da yan mintuna ta isa gida, ta fito ta ba mai cab kudinsa, a hankali take jin faduwar gaba har ta shiga ciki tana kallon parking lot ta ga bbu motarsa, ajiyar xuciya ta sauke ta nufi flat dinta da sauri don ta yi abinda ya kawota ta bar gidan, da d'an mamaki take kallon farar matar dake tsaye b'akin apartment dinsa matar na rike da wata kyakkyawar yarinya kamar ta, lkci daya kuma tana kuma danna wayar hannunta, Khadijah bata sake kallonta ba ta shiga kokarin bude apartment dinta, a hankali matar tace "Hi" sai a sannan ta juyo ta kalli matar, ita dai matar ga ta kamar fulani kamar kuma balarabiya, idanuwanta kuma kamar na neighbor dinta, Khadijah ta dauke kai tace "Hello" matar tace "Plss Dr Ayman, will he be back anytime soon?" Khadijah ta mata wani kallo a takaice tace "I don't knw" Matar tace "Really? And I have being Calling but I can't reach him" Khadijah da har ta bude kofar ta tace "Hard luck" daga haka ta shiga ciki sai kuma ta juyo suka hada ido da cute babyn hannun matar, kasa rufe kofar tayi a hankali tace "Or you go come back, may be later" matar tace "Am from a far place, and he knws I will be here" Khadijah ta rasa abinda xata ce, can dai ta dauke kai ta juya ba don ranta ya so ba kuma don tausayin babyn hannun matar tace "If it's ohk... u can come in and wait him" daga haka ta shiga parlor matar tace "Alryt Thank you" ta shigo parlorn ta xauna, Khadijah ta bude fridge ta kawo mata ruwa da lemo ta ajiye mata, matar ta d'an yi murmushi tace "I am fatima Ayman" kallonta Khadijah tayi na yan sakwanni kafin tace "Am Khadijah Muhd" Matar da ta kira kanta da fatima tace "Ohh that's nyc, from which country?" Khadijah tace "Nigeria" d'an buda ido fatima tayi tace "Tribe" Khadijah tace "Hausa Fulani" Fatima tace "Waow ashe Hausa ce ke sister" Khadijah ta kalleta tayi murmushi tace "Ehh" Fatima tace "Allah sarki, amma naji dadin haduwa da 'yar uwata daga Nigeria, na xo nan last 3 weeks but kamar baki nan" Khadijah tace "Eh naje gida ne" Fatima tace "Maa sha Allah, tare da mai gidana muke ya xo wani aiki a nan shine nace ya ajiye ni kawai mu gaisa da yayana tunda yau xa mu koma, kuma fa na sanar da shi yayan nawa xan xo amma dubi yanda ya shanya ni a waje" murmushi kawai Khadijah tayi ta amshi babyn hannun ta tana kallonta tace "Ya sunanta?" Fatima tace "Iman...." Lkci daya murmushin dake fuskar Khadijah yyi fading jikinta yayi sanyi...... *Haske writers association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By khaleesat Haiydar_📚✍🏻 5..... Fatima da bata lura da yanayin da Khadijah ta shiga ba tace "But ina jin kilan ya shiga schl ne, kinsan PhD din nan sai hankali, yanxu ma idan Abban Iman ya kira dole sai dai mu wuce kawai tunda ban san lkcn da xai dawo ba" Khadijah dai bata ce komai ba ta mike a hankali ta kwantar da babyn da uwarta ta kira da Iman, ta kirki murmushi tace "Bari in shiga kitchen" daga haka ta kunna masu kayan kallo ta wuce cikin kitchen, kauda damuwar da ya so dirar mata a rai tayi, ta jingina da kitchen cabinet tana tunanin light abinda xata girka masu da baxae dau lkci ba, can dai ta fiddo Irish ta shiga ferewa, cikin minti ashirin ta gama hadadden porridge din Irish da yaji kayan hadi da hanta da nama, tuni kamshin dahuwar abincin ya kauraye ko ina na gidan, fitowa parlor ta yi fatima dake xaune tana danna wayar hannunta tace "Sannu da aiki" Murmushi Khadijah tayi tace "Thank you, hope ba ku yi fushi ba na bar ku ku kadai" Fatima tace "Ayya ba komai ke da kike aiki" Khadija ta koma kitchen tayi serving abinci a plate tasa fork ta daura kan tray da glass cup na ruwa a gefe ta fito parlorn tun kan ta ajiye fatima tace "Toh fah, ni fa a koshe nake khadijah, wlh am nt hungry bamu dade da cin abinci ba" Khadijah ta d'an canxa fuska tace "Saboda ke fa nayi girkin" fatima tace "Ayya, to ban san xai ko anjima ba amma yanxu gaskiya a koshe nake kiyi hakuri" dai dai nan aka bude kofar parlorn duk suka kalli direction din, tsaye yyi bakin kofar kamar me examining din wani abu, Khadijah da xuciyarta ya kusa shigewa cikinta tayi saurin kauda kanta gabanta na faduwa, mikewa fatima tayi da fara'a da farko sai kuma ta hade rai tace "Yaya ai da sai ka ce min kar in xo baka nan, ka wani shanya ni a waje ina ta jiran ka," karsowa yyi cikin parlorn da takalmansa ba tare da ya kalleta ba bare ya tanka ta, fatima ta xaro ido tace "Ana fa sallah yaya.... Ka cire takalmin" Bai ce komai ba ya duka yana kallon Iman dake kwance saman kujera, sai a snn yyi murmushin da ya bayyana light dimples dinsa yace "She's.... growing" daga haka ya dau babyn ya manna mata kiss a cheeks dinta ya juya ya nufi kofa yana cewa "Wayata na silent I don't knw u were calling," Fatima tace "Uhn ai shikenan, ya karatun" bai tanka ta ba har ya fita, kallon Khadijah tayi tace "Nagode sosai Khadijah Allah ya saka da alkhairi" Khadijah ta kirkiri murmushin karfin hali tace "Welcm" fatima ta dau jakarta da abun daukan babynta tace "Bari in je mu gaisa" daga haka ta juya ta nufi kofa Khadijah tace "Toh abincin fa?" Fatima ta yi yar dariya tace "Toh shkkn bari dai in je da shi" dawowa tayi ta duka xata dauka ganin kayan hannunta khadijah tace "Let me help" fatima tace "Toh nagode" khadijah ta duka ta dau abincin, sai kuma tayi still tunawa da tayi hakan na nufin parlornsa xata shiga kenan?? Tuni fatima ta isa kofa, a hankali ta bi bayanta a sanyaye ba don ta so ba, fatima ta bude kofar yayan nata ta shiga da sallama, b'akin cover shoe dinsa na ajiye bakin kofa wato ita ya raina xai shigo mata parlor da takalmi, xaune suka gansa kan daya daga kujerun parlon yana rike da Iman dake 6a66aka masa dariya, kallo daya Khadijah tayi ma hadadden parlon nasa tayi saurin sunkuyar da kai gabanta na faduwa, fatima da har ta xauna tace "Ina yini yayana" yace "Ya kike" tace "Alhmdllh ya karatun" karasowa Khadijah tayi ta ajiye abincin hannunta ba tare da ta dago kai ba, ya kafeta da ido, kamar ta sani kuwa ta ki kallon inda yake, fatima tace "Yaya neighbor dinka tana da kirki sosai, ka taya ni yi mata godiya" yace "Koh?" Kallonsa fatima tayi ta kasa cewa komai jin kalan tambayar da ya jefo mata, sannan tafi kowa sanin halin wan nata, hakan yasa kawai ta bude jakarta tana murmushi tace "Guess what yaya...." Ya kalli jakar bai ce komai ba dai, Envelope ta dauka ta mika masa tana yar dariya tace "3 days ago su Ummu suka ba Abban Iman ya taho da shi" Karba yyi yace "Meye a ciki?" Ta buda ido tace "Invitation card din ku mana...." Mayar mata yyi yace "So?" Tace "Aa cewa aka yi in kawo maka" yace "To mayar" Fatima tayi murmushi tace "Ko dai Jawahir din ta tura maka ne" Ya hade rai yana kallonta sai kuma ya juya yare xuwa larabci, tuni khadijah ta nufi kofa dai dai lkcn da aka bude kofar, wata black American mai kyau ta shigo parlorn tana sanye da wasu damammun kaya, ta daga masu hannu gaba daya da murmushinta tace "Hi" daga haka ta nufi bedroom, lkci daya mood din fatima ya canxa ta bi yarinyar da kallo, shi kam ya dauke kai, Khadijah ta saci kallonsa suka hada ido, tabe baki tayi ta dauke kai ta juya ta bude kofar ta fice abin ta a ranta tace Allah wadaran naka ya lalace, ko kunya bai ji ba, Tana komawa apartment dinta ta shiga gyare gyaren ko ina na gidan, duk wani abu da tasan xai iya samun matsala a fridge duk ta tattara su gu daya don tafiya da su gidan Vanessa, kafin la'asar ta gama komai tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta shirya cikin kananun kaya ta daura kimono a kai ta yafa gyale a kanta xata fito parlor aka danna bell, karasawa tayi ta tsaya bakin kofar tace "Who's there?" Muryar fatima taji tace "Ni ce Khadijah, dama nace in maki sallama xan wuce" Khadijah ta bude kofar tace "Ayya, har xa ku tafi" fatima ta kirkiri murmushi duk da Change din mood dinta tace "Wllh kuwa, Abban iman na jiran mu" Khadijah tace "Toh shkkn, Allah ya tsare hanya, ya kai ku gida lafiya" Fatima tace "Ameen ngd, tnx once more for the hospitality" murmushi kawai Khadijah tayi, aka bude kofa sai gashi ya fito rike da Iman, Fatima ta kallesa da kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "Ya Khaleel da gaske baxa ka kai mu ba mu hau taxin kawai" a takaice yace "Ehh" ta langwabar da kai tace "Toh shkkn" majestically yyi wucewarsa waje, Khadijah ta bi sa da ido, fatima da ta bi sa da kallon ita ma tayi murmushi tace "Kinga da gaske taxi xai tsayar mana maimako ya ajiye mu da motarsa daga na gaya masa gaskiya...." Khadijah tayi murmushi bata dai ce komai ba, Fatima tace "Toh muje wayana na gun sa sai ki sa min digit din ki mu dinga xumunci" Khadijah ta bi bayan ta ba don ta so ba, ko da suka isa har ya tsayar da mai cab yana jiran kanwar tasa, fatima tace "Yaya idan ma fushi kake da ni kayi hakuri pls" ya kalleta bbu yabo bbu fallasa yace "Not at all, shiga ki tafi inda xa ki" tace "To bani wayar Khadijah ta sa min digit dinta" yayi kamar bai ji ba ya bude back seat yace "Shiga malama" fatima ta shiga ya mika mata yarinyarta sannan ya bata wayarta, tace "Bata sa number ba ai yaya" ya hade rai yace "Xan tura maki ta WhatsApp" rasa abinda xata ce masa tayi, ganin yanda ya hade rai tace "Toh baxa ka ba mai cab din kudi ba" yace "Bani da" yar dariya tayi tace "Kai ya khaleel ba ma haka da kai fa, kayi hakuri kar in tafi kana fushi da ni" Khadijah da ko kallonsa bata yi ba ta daga ma fatima hannu tace "Toh Allah ya tsare hanya Maman baby" daga haka ta juya da sauri ta koma ciki don bata son ta ci gaba da jin kayan takaici, tana shiga bedroom ta wuce direct ta dinga fiddo kayan da ta harhada, taje dauko na karshen taji an bude kofar parlor, still tayi na yan sakwanni sai kuma ta juya da sauri ta fito xuciyarta na bugawa. *Haske writers association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By khaleesat Haiydar_📚✍🏻 6...... *Nigeria* Ajiye fork da knife din hannunsa yyi ya tura abincin gabansa lkci daya ya fuzar da iska ya dau tissue yana goge bakinsa ya mike ya bar dinning din, mum dinsa dake xaune parlor ta bi sa da wani kallo tace "Barin abincin kayi sbda xancen da nake maka Aliyu?" Kallonta yyi da sauri yace "Noo, not at all Mum, xan je sallama da Granny ne coz am leaving as early as possible tomorrow" daga haka ya dau makullin motarsa da ya ajiye kan Center table ya nufi kofa yace "Sae na dawo mum" tagumi mahaifiyar tasa tayi ta bi sa da kallo cike da damuwa har ya fita, ya fuzar da iska bayan ya shiga motarsa ya jinginar da kai jikin kujera hade da lumshe ido yace "Ba ta taba barin in ci abinci in koshi Mum, always with a particular complain" ya bude ido a hankali snn ya tada motar yyi horn mai gadi ya bude gate ya fita rai ba dadi, bai yi minti goma yana tafiya a Independent way ba wata 206 dake gabansa ya taka wani burki da har sai da ya kusa bugesa ba dan shi ma yyi saurin preventing hakan ba, wanda hakan kuma ya janyo motar dake bayan tasa motar ta buge sa, Kilan rudewa ya sa me 206 din ya juye kan steering wanda hakan yasa ya buge motar gefensa shi ma da karfi, everything just happened all of a sudden, lumshe ido Aliyu yyi ya bude yana kiran Allah a xuciyarsa bayan komai yyi still kamar ba ayi ba, sai a sannan ya lura da wani bike ne ya shigo ma mai 206 din yyi kkrin avoiding da ya janyo faruwan slight accident din, Aliyu ne ya fara fitowa daga motarsa daga nn kuma kowa ma ya fara fitowa, ya nufi 206 din da har driver din ya fito da sauri ya bude back seat, kukan yara ke tashi a motar, jin hakan Aliyu ya karasa da sauri gun motar, identical twins ne bayan motar da baxa su wuce shekaru biyar ba, Aliyu ya fiddo su duk biyun daga motar yana kallon yaran dake sanye da uniform din makaranta ya durkusa a hankali yace "Hey boys are you okay??" Dayan kadai ne ya gyada masa kai a tsorace, dayan kuwa banda kuka babu abinda yake yana kiran Anty, kallon yaran kawai Aliyu yake ko kiftawa bbu, muryar mutanen da ke tsaye gun kowa na fadin albarkacin bakinsa yasa shi mikewa a hankali yana shafa kansu yace "Sorry Boys, Allah ya tsare gaba" Wani mutumi ne ya dinga tambayarsu inda ke masu ciwo duk suka girgixa kai, Aliyu ya daga kai jin abinda mutumin da ke gefensa ke ce masa yana kallonsa, "Allah dai ya kiyaye gaba ka tafi da yaranka gida kawai, Allah kyauta na gaba" cewar mutumin kenan, wani mutumi ma ya sake fadin makamancin hkn, murmushi yyi yace "No, ni ban san su ba" mutumin karshe da yyi magana ya kalli yaran sannan Aliyu, kada kai yyi yace "Ikon Allah...." bude bayan motar Aliyu yyi ya shigar da yaran yana kallon Drivern yace "Ka ajiye su gida, Allah ya kiyaye gaba" godiya Drivern yyi ma mutanen wajen ya shiga motar ya tada ya hau kan titi ya bar wajen. Aliyu ya koma gun motarsa ya shiga har lkcn cute twins din na ransa, bai kuma damu da kallon da wasu suka bi sa da shi ba. A waje yyi parking ya shiga gidan grandmum dinsa da sallama bayan sun gaisa da masu gadi, wata budurwa ce da baxata wuce shekaru ashirin da daya ba kwance kan kujera dake parlon tana danna waya, sau daya ya kalleta bai sake kallon inda take ba ya wuce dakin grannynsu da suke kira da yaya, sllh ya sameta tana yi ya kalli agogo sanin Magrib bai yi ba, ya tabe baki ya dawo parlon ya xauna ko sallan me take, ba a dau lkci ba ta biyosa tace "Mijin ka xo kenan" ya gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayarsa ya hanya, yace "Alhmdllh" ta kalli budurwar dake kan kujera tace "Ke koh Salmah kun gaisa da yayan naki" yarinyar ta gyada mata kai idonta a kan waya, ya kalleta fuskarsa daure yace "Uban wa kika gaida?" Ba ta ko kallesa ba tace "Yaya ni ki ce ya daina xagi na plss" Mikewa grandmum din tasu tayi tace "A'a ni dai gaskiya ba a gidana ba yau, ku je can gidan iyayen ku ba ruwana, kai kuma naga ai ba dole bane sai an gaisheka, ke kuma sa'an ki ne shi din da baxa ki gaishesa ba" mikewa yyi ya nufi kofa, kakar ta bi bayan sa da sauri tana cewa "Ina kuma xaka Aliyu" bai juyo ba yace "Sallama dama na xo maki gobe xan wuce Uk...." da sauri take bin sa ganin yaki tsayawa tace "Toh baxa ka tsaya ba ina ma magana" yace "Mu yi waya" bata fasa bin sa ba tana cewa "Da kai fa nake Aliyu..." juyowa yyi yace "Don Allah yayah ki rabu da ni dama sallama na xo maki kuma gashi na maki dai ko" rike ha6a tayi tace "Yo ni me ya sha min kai da sallamar ka da rashin sa, magana ce dai baxan fasa maka ba tunda ba tsoronka nake ba, baka kuma isa inji tsoron ka ba, kum maganar dai da baka so ce xan maka wato maganar aure, Aliyu sa'annin ka daga me d'an shekara biyar sai mai d'an shekara shidda kai har bakwai akwai, yanxu kai baxa kayi ma kanka fada ba kasan inda ke maka ciwo d'an nan, ga mahaifin ka ya xuba ma na mujiya ya kyaleka ya fita lamarin ka, me kake son mayar da rayuwar ka ne, idan ma lafiya ce baka da ba sai ka mana bayani ba ko ni in kai ka asibiti amma ka mayar da mu shashashai...." tsaye yake yana saurarenta sai dai bai juyo ba har ta kai karshe sannan ya juyo yana kallonta yace "Allah kawo lkci yayah" daga haka yyi ficewarsa daga gidan, ya jima xaune mota ya kasa barin anguwar, ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido a hankali ya bude cikin sanyin murya yace "Can I ever get her? Then Where?" Lkci daya idonsa ya kada ya hade kansa da steering, ya fi minti goma a haka kafin yyi karfin halin dagowa ya tada motar ya bar gun jikinsa a sanyaye, yana hawa independent way yaran daxu suka fado masa, ya d'an yi murmushi loving to see them once more and their parents. Bai yarda ya wuce gida ba a lkcn kawai ya wuce gidan abokinsa kuma amininsa Farouq, ganin Magrib tayi sai da ya fara shiga masallacin dake anguwar don gabatar da magrib bayan yayi alwala, ana idarwa kuma suka fito tare da Farouq, gaisawa suka yi Farouq yace "D'an rashin kirki kace min xaka dawo ranan kasa Madam tayi serving har da kai amma kaki dawowa, ina ta xuba ido, I called kuma you refused picking saboda kasan baka da gaskiya koh" Aliyu ya shafa kansa yana murmushi yace "Na ma mance me ya hanani dawowa wllh" har suka shiga gida mitan xancen Farouq yake, suka karasa har parlor, Boys din Farouq suka taho da gudu don gaida abokin dad din nasu, Aliyu ya rungumesu yana tambayar su ya school suka ce masa "Alhmdllh" Wara ido yayi yace "Toh ban ga "Baby Fiddausi ba" Ahmad yace "She's upstairs with mum" yace "Alryt maxa ku je ku ce masu Ina gaishesu" Ahmad me shekara shidda da kaninsa takwaran Aliyu suka wuce daki da sauri. Farouq dake ta kallon Aliyu yyi kasa da murya yace "Doctor...." Kallonsa Aliyu yyi da sauri, Farouq yace "I don't knw, may be am nt worth ur best..." Aliyu ya d'an bude ido yace "Ban gane ba Umar" Farouq ya girgixa kai yace "Kullum tambayata why did you prefer living as a bachelor ka ki bani answer, what's ur problem Aliyu, am I not worth knowing ur problem, I would love seeing ur kids Frnd duk clique dinmu kai kadae ne Bachelor har ynxu, tell me why... I beg you..." Kallonsa kawai Aliyu yake can yyi murmushin karfin hali ya kauda kai yace "Xan yi Farouq, lkci ne kawai" a d'an fusace farouq yace "Na gaji da jin haka Ali.. For good six years this is always ur reply, kudin gashi kana da su Alhmdllh, yan matan gasu kawo maka hari suke ta ko ina.... Toh meye kuma yayi saura??" Aliyu dai bai ce komai ba sai danna wayarsa da ya fiddo yake, farouq na masa wani kallo yace "Ko Iman din dai kake jira har yanxu, I mean aljanar nan taka..." Aliyu ya dago da sauri hade da yin murmushin da ya fiddo da ainahin kyansa na fillo ya karyar da kai yace "Yeah" tsaki farouq ya ja yana girgixa kai cike da takaici, Aliyu ya dafe shoulder dinsa a hankali yace "Look frnd, wllh ba aljana bace mutum ce kamar ka, ka bar ce mata aljana" Farouq yace "Toh wai ni abinda ban gane ba a nan shine ita ta san ka?" Aliyu ya sauke manyan idanuwansa daga kallon abokin nasa a hankali yace "Yea may be tasan ni, may be kuma bata san ni ba" Wani dariya Farouq yyi har da kyakyatawa yace "Wllh baka da hankali Haiydar, wato bata ma san ka ba?" Murmushi kawai Aliyu yyi yana shafa cute beard dinsa bai dai ce komai ba, Farouq yace "To what if tayi aure? Ko kuma tana da aure?" Murmushin fuskar Aliyu ya bace lkci daya ya mike a fusace yace "Billah sai ya saketa ko ma waye shi... Na rantse da sarkin dake busa min numfashi xan iya kashe ko ma waye ya aureta" sakin baki Farouq yyi da mamaki yana kallonsa, yana kikkiffta ido yace "Aliyu are you alright kuwa, wani irin rantsuwa da threat ne haka, anya kana right sense din ka kuwa" Ko kallonsa Aliyu bai yi ba ya nufi kofa, Farouq ya mike da sauri ya rikosa yace "Habaa, Toh Allah baka hakuri, let eat plss, In sha Allah ma Iman bata yi aure ba duk da ni dai billahil azim ban yarda ba aljana bace" yana magana ne yana satan kallon Aliyu da har lkcn fuskarsa ke daure, da kyar dai ya samu ya lallabasa ya dawo ya xauna, Aliyu ya lumshe ido yace "In kaji wacece Iman din nan xa kayi mamaki Umar" Farouq yace "Toh don Allah ka gaya min wacece" A takaice Aliyu yace "Noo baka santa ba, bata sanka ba, kilan ni kadai na santa" dariya sosai Farouq yyi yace "Ko da yake gogan ma bai san ko ta san shi ba balle ni, wllh you look confused Aliyu, Allah ya yaye maka wannan bala'i" Aliyu ya kallesa yace "Plss xancen Iman da muke ya tsaya iya nan kar ko da wasa wataran kaje can gida kana cewa Iman" Farouq yace "Why, ko sun santa?" Aliyu ya girgixa kai yace "A'a kawai dai kar ka sa a daukeni mahaukaci ne" Farouq ya jingina kai yana murmushi yace "Hauka kam ka jima da fara sa ai frnd" *Haske writers association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By khaleesat Haiydar_📚✍🏻 7..... Matar farouq ta sakko suka gaisa da Aliyu tayi serving dinsu abinci ta koma daki, farouq na lura da abokin nasa dake cin abincin a hankali, yayi breaking silence din after a while yace "Toh tun yaushe kasan Iman din nan ni dai ka ban labari frnd" Aliyu ya dago yana kallon sa, murmushi yyi ya ajiye spoon din hannunsa yace "Tun tana shekara sha hudu..." Farouq ya wara ido yace "Kace yanxu ta girma kam" Aliyu ya d'an bude ido yace "Uhn" Farouq yace "Kuma yaushe rabon da ka ganta a mafarkin naka" wani kallo Aliyu ya watsa masa yace "Ce maka nayi a mafarki na santa?" Farouq yace "Au, nayi xaton a mafarki ne ai" tsaki Aliyu yyi ya mike yace "Da gaske ka ma mayar da ni mahaukaci wllh" farouq yyi dariya sosai, Aliyu ya dau makullinsa yace "Am full frnd, gobe xan tafi UK in sha Allah" Farouq yace "UK? Ba last month ka dawo ba?" Aliyu yace "Yeah ina da aiki can, beside na fi jin ddin can wllh, ba takura..." Kofa ya nufa farouq ya mike ya bi bayansa, har gun mota ya rakasa Aliyu ya shiga ya tada motar yace "Toh sai na dawo frnd, a kulan min da boys dina" Farouq yace "Toh Allah ya tsare, ya sa ka taho mana da tsarabar mata ko da baturiya ce wllh don na gaji da ganin ka ba aure" d'an murmushi Aliyu yyi yace "Toh Abba...." farouq yace "Allah kuwa, Abban ma da ya gaji ya xuba maka ido ynxu, ni wllh da ma kawai su yi taking dinka unaware kana dawowa sai dai kaji ai an sa ranan ku da Hanan, ga mace har mace tana son ka amma kayi ta mata jan aji kana jiran Iman Aljanar ka, ni wllh ko Salmah ce a hadaku, ka kuma san gwara Hanan sau dubu kan salmah..." Aliyu bai ce komai ba don har ya 6ata masa rai, ya ja motarsa kawai ya bar gun Farouq na dariya. Tunda Khadijah ta shiga daki ta sa key bata sake lekowa parlor ba kusan awa daya da rabi kenan, ita dai ta ga abinda ya isheta.... Khaleel taji kanwarsa ta kirasa da ko wa?? Kwafa tayi ta juya xuwa daya side din gadon da take kwance, kallon agogo tayi a hankali ta jawo wayarta dake gefenta ta gama dialing number ta kai kunne, Muryar Nanny taji, bayan sun gaisa tace "Umma fa?" Nanny tace "Umma na tare da bakuwa...." Tace "Toh xan kira xuwa anjima...." Nannyn tace "Ga su Sudais...." Khadijah ta d'an buda ido tace "Boy... how you?" Shiru tayi tana apprehending abinda twins din ke gaya mata a waya duk jikinta yyi sanyi sosai, Shuraim yace "Hello... Are you there Anty?" Ta lumshe ido ta bude cikin sanyin murya nace "Yea soldiers, hope ba ku ji ciwo ba" Shuraim yace "Not at all aunt, we where just freaked out, and an Uncle consoled us right there and made sure we where fyn, he was kind aunt...." Tace "That nyc of him, But did you both prayed?" Duk suka ce "We did..." Tace "Good, you make prayer ur daily routine before leaving home and when coming back, clear?" Suka ce "In sha Allah aunt" tace "Hand the phone over to Nanny..." ba musu suka kai ma Nannynsu wayar, ba su dau lkci suna magana ba tayi mata sallama ta ajiye wayar duk da ta so magana da Umma, har lkcn hankalinta ya kasa kwanciya, mikewa xaune tayi a hankali, she can't imagine loosing the boys, she just can't..... Tunanin hakan yasa hawaye ya cika idonta ta rike kai tana jin dama ta gansu kusa da ita a yanxu, ita kanta bata san wani irin soyayyan yaran bane ya dirar mata all of a sudden tun daga shekaru biyun da suka wuce, unlike before, kamar yanda bata son mutuwarta until her God is please with her haka bata son su, bata son su kusa da ita but now.... Reverse is d case, Allah yasan yanxu bata da kamarsu a duniyar nan gaba daya, she just love them, she know she love dem dearly... Ji tayi kamar xata yi xaxxabi ta koma ta kwanta, nan bacci ya dauketa, ba ita ta farka ba sai kusan magrib, bayan ta idar da sllh ta bude kofar dakin a hankali tana lekan parlor, bbu kowa parlorn kamar yanda ta yi tunani, ta karasa ciki a sanyaye a ranta tace ae da ka xauna ka jira ni, ta isa gun main door ta sa makulli tana kallon tray din abincin da ta kai ma fatima daxu, toh ko shi ya kawo ya ajiye daxun, ta bude plate din dake a rufe taga da sauran Irish din, da alamar fatima bata ci da yawa ba, ta dau tray din ta wuce kitchen, disposing din abincin tayi, duk da muryarsa da ta ji a baya bata leka ba har ta gama abinda xata yi ta bar kitchen din, Mis cals din Vanessa ta samu a wayarta, ta mayar da kiran bayan sun gaisa Vanessa tace yau ma tana ta jiranta, murmushi tayi tace "Sorry love, I had a visitor today, an unexpected one..." Vanessa tace "Alryt then, good nyt" daga haka Khadijah ta katse wayar ta ajiye, Daren ranan bata samu bacci me tsawo ba, don da tayi xata farka, karfe uku tana ta xaune har lkcn ta kasa baccin bayan ta idar da sallah, tashi tayi ta wuce kitchen don diban ruwan Lipton ta sha ko xata iya karatu, kamar ance ta daga kai suka yi ido hudu da shi xaune da uban textbooks a gaban sa yana sanye da siririn farin glass, ta cikin glass din yake kallonta, a hankali ta sauke idonta ta gama abinda xata yi ta kashe wutan kitchen din ta wuce. Har gari ya waye idonta biyu kamar warce ta sha wani abu, Shayi kadai ta iya sha da safe bayan ta shirya ta bar gidan misalin karfe bakwai da rabi don wucewa makaranta, throughout ranan bata da walwala a makarantar ma, bayan la'asar tare da Vanessa suka taho gidanta kamar yanda ta bukaci su je, suna gama cin abinci khadijah ta tafi tayi wanka ta bar Vanessa parlor tana kallo, bayan ta gama shiryawa ta dau waya ta shiga kiran Umma, a hankali ta gaisheta, bayan yan sakwanni tace "Umma yaushe su Sudais xa su yi Mid term break?" Umma tace "Mid term... gobe ne ai...." Ta d'an yi shiru sannan kamar me tsoron magana tace "Toh, dama Umma don Allah da sai su taho gu na da Nanny suyi hutun a nan plss" Umma tace "Saboda rashin hankali" shiru ta yi bata ce komai ba, Umma tace "Shi hutun kwana hudun ne xa su kwashi jiki su tafi UK" Khadijah ta girgixa kai tace "Toh shkkn Umma kiyi hakuri" Umma ta katse wayar ta, misalin karfe shidda suna xaune waje da Vanessa suna duba wani material na karatu khaleel ya bude kofa ya fito, 3 qtr da singlet ne jikinsa, tun da ta kallesa sau daya ta mayar da kanta kasa bata sake daga kai ba, taji Vanessa tace "Good evening" cikin cool voice dinsa yace "How you?" Tace "Am great" ya saci kallon khadijah sai kuma ya juya ya koma ciki, Vanessa tace "Ur neighbor?" Khadijah tace "Yeah" Vanessa ta wara cat like eyes dinta tace "He is damn cute, a Nigerian also?" Khadijah ta nuna mata kofar flat dinsa tace "You can ask him" Vanessa tayi dariya tace "Sure I can" suna nan xaune har kusan goman dare, Khadijah ta san ba don suna wajen ba da yanxu ya fito, sai taji dadin hakan ko ba komai dai sun hanasa xama wajen, a ranta tace ba don ba don ba ma a nan xata kwana a xaune, sha daya saura suka tattara takardunsu suka wuce ciki, ae kam ko minti takwas ba su yi da shiga gida ba taji fitarsa, Missed calls din Umma ta gani har biyu a phone nata dake daki, ta shiga kiranta bayan tayi shirin kwanciya, Umma tace "Kin yi bacci ne" ta girgixa kai tace "Yanxu xan yi Umma" Umma tace "Tunda ganin yaran kike son yi gobe xa su bi train xuwa Abj su yi boarding plane...." Khadijah ta d'an xaro ido tace "A'a Umma hutun ba yawa ai" Umma tace "Ai kinsan da ba shi da yawa kika ce su taho, so keep shut" shiru ta yi bata iya tace komai ba har Umma ta katse wayar, har ranta taji dadin abinda Umma tace, tayi murmushi ta kwanta hade da lumshe ido. "Sir ga mu Airport din..." Dago kai Aliyu yyi da sauri daga danne dannen wayar da yake yi, ya kada kai yace "Alryt Bilyamin thank you" daga haka ya bude motar ya fita yana rike da karamin travelling bag dinsa, in 2 hrs and a halve har sun shigo Abj daga kd, ko don yayi gudu ne, "Amin nagode" amsar da ya ba Bilyamin kenan dake masa Allah ya kiyaye hanya ya bar gun ya nufi hanyar shiga cikin airport din, yana jin wayarsa na ring a aljihunsa amma sanin warce ke kiransa yaki fiddo wayar. Aliyu na kokarin ajiye karamar jakarsa sama bayan an shiga jirgi ya ji an taba sa, juyowa yyi da sauri, lkci daya ya wara dara daran idonsa ya durkusa yana kallon Little Shuraim dake masa murmushi yace "Waow handsome we met again" Shuraim yace "Sure!" Aliyu ya juya ko xai ga any of his parent ganin babu yace "So how you?" washe hakora shuraim yyi yace "Am fyn Uncle, and you?" Aliyu ya shafa kansa yana murmushi yace "Same sweetheart... Where is ur twin" nuna masa Sudais dake kusa da Nanny tana bude masa cake dinsa a leda yyi, Aliyu ya dinga kallon matar kafin yace "Is.... that your mum?" Shuraim ya girgixa kai yace "Noo she's our Nanny, we left mum at home, we r going to meet aunt in UK in sha Allah" Aliyu ya gyada kai yana mamakin sharpness din yaron don da ganin sa baxai wuce shekara biyar ba, ya kamo hannunsa yace "That's nyc my boy, am also heading there, What's ur name?" "I am Shuraim Muhd" Cewar Sudais yana wara masa ido, Aliyu yace "Waow, ur twin name?" Shuraim yace "Sudais Muhd" Aliyu yyi patting shoulder dinsa yace "That's my boy" mikewa yyi ji da yyi ana announcing ayi fastening din seat belt, Tuni Nanny ta taho tafiya da Shuraim, kafin Aliyu yace komai yaron ya daga masa hannu yace "C ya uncle, well' meet later, may be in UK...." daga haka ya bi Nannynsa Aliyu ya bi sa da kallo yana murmushi, xaunawa yyi seat dinsa, Baturiyar dake wajen tana murmushi tace "You've got a lovely son" Aliyu ya kalleta da sauri, Sannan ya kalli Shuraim sai kuma yace "Ohhh thanks very much" har jirgi ya tashi Aliyu bai daina juyawa yana kallon cute twins din ba har ya lura sun yi bacci few hours later. Da yamma suka sauka Uk, Aliyu ya mike ganin Twins din duk bacci suke ya nufi Nannynsu da ke kokarin tada su gaba daya, yace "Bari in taimaka maki da guda daya Madam" bai jira cewarta ba ya dau Sudais don ya fi kusa da shi, ya rungumesa yana rike da jakarsa ya nufi kofar fita jirgi, Nanny ta bi bayansa da sauri tana rike da Shuraim da har ya tashi, sai da ya jira suka dau luggage dinsu sannan ya samar masu taxi... tuni Sudais ya bude ido yana kallon Aliyu ya wani tsuke fuska, Aliyu ya sakar masa murmushi yana kallonsa a hankali yace "How you Prince?" Sudais bai amsa ba sai ma kokarin sauka da ya fara yi daga jikinsa, hakan yasa Aliyu ya sauke sa yana kallonsa murmushin dake fuskarsa yyi fading a hankali, Shuraim dake rike da Nanny da ke kkrin saka jakar kayansu cikin booth din taxi yace "Uncle are we going the same way?" Aliyu ya kallesa sannan ya girgixa masa kai yana murmushi yace "No love" godiya Nanny tayi ma Aliyu ta shiga taxin Sudais ma ya shiga da sauri, Shuraim kam sai da ya daga ma Aliyu hannu yace "See u some other time" Aliyu ya gyada masa kai har lkcn bai daina kallonsa ba, Shuraim na shiga ya rufe kofar motar, Aliyu ya daga masa hannu shi ma ya daga masa yana washe set of teeth dinsa, har taxi din ya bar gun Sudais kin daga nasa hannun yyi sai ma dauke kai da yayi, Aliyu ya kasa dauke idonsa a kan yaron. A hanxarce khadijah ta gama daukan duk abinda tasan boys din suna so sanin sun kusa sauka ko sun ma sauka, ta nufi counter ta biya kudi ta bar Mall din, taxi ta samu ya kawo ta kofar gida ta fito ta basa kudinsa sannan ta shiga ciki, ko kadan bata ji dadin tafiyar Vanessa daxu ba, tana kkrin bude kofa taji tsayuwar taxi ta juya da sauri tana kallon gate, bayan minti biyu ta hango twins, ai bata san lkcn da ta ajiye ledar hannunta ba ta nufe su kamar yanda su ma suka nufo ta da gudu, durkusawa tayi ta rungumesu gaba daya suka kankameta barin sudais ita ma duk ta fi maida hankali kansa, kisses ya dinga mata a fuska, shuraim kuma ya dinga kyalkyala dariya yana kallon su, ganin ba saketa xae yi ba ta janye sa ta mike tana dariya ganin yanda Nanny ta tsaya kallonsu, Nanny tace "Toh ba mu kudi mu ba mai cab, ba currency din nan tare da ni" Tashi tsaye tayi da sauri ta bude jakarta ta ciro kudin kasar ta mika ma Nanny, kamar ance ta waiga taga Khaleel tsaye bakin kofar sa, tayi saurin dauke kai, Shuraim ya wara ido yace "Aunt you knw what" hannunsa ta kama da na d'an uwansa ta fara tafiya tace "No Darling" yace "We still met with that uncle I told you about...." Tace "Which?" Maimakon ya bata amsa sai ta ga ya tsaya yana gaida Khaleel dake kallonsu har lkcn, Khaleel yyi murmushi ya karaso wajen yana kallon yaron a hankali yace "How are you handsome?" Shuraim ya wara ido yana nuna masa wandonsa da yyi sagging yace "Am fyn, but...." tuni Khadijah ta ja Sudais da shi dama bai ma da niyyar gaida khaleel suka shiga cikin parlor a ranta tana cewa ita kam ta shiga uku da Shuraim, sai a sannan tace "Which uncle was ur brother talking about" Sudais ya yamutsa fuska yace "I don't think I like him..." Ta d'an bude ido tace "Who?" Yace "The uncle he is talking about," Ta langwabar da kai tace "Why" Sudais ya bude hannu alamar bai sani ba, tace "Where did you guys meet him" Sudais yace "Shuraim will make u understand Anty" dai dai nan Shuraim ya shigo tare da Nanny, ya taho da gudu ya hau kanta, yace "I missed you Anty" ta daura lips dinta a forehead dinsa tace "but I've warned you to stop talking to strangers times without number.. I mean that man u were greeting outside" Ya xaro ido yace "I never knew he was a stranger, sorry Anty" tayi murmushi tana shafa kansa tace "But you don't knw him, so he is a stranger" *Haske writers association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 8...... Sai a sannan Khadijah suka gaisa da Nanny tana tambayarta hanya da Umma, kitchen Nanny ta nufa xata daura masu ruwan wanka khadijah tace "Na riga na sa ruwan Nanny, bari xan masu" daga haka ta mike ta ja boys din xuwa Bedroom dinta. Wanka ta yi masu ta wanke masu baki ta sa duk suka yi alwala sannan suka fito, ta saka masu kayansu ta sa suka yi sallah, a tare suka ci abincin da tayi serving dinsu, Nanny da ita ma ta kintsa a daya bedroom din ta fito ta tarda su parlor ta dau abincinta da Khadijah ta rufe mata, nan su Shuraim suka dinga bata labarin abubuwan da ya faru a makaranta, ita dai ta tallabi chin dinta tana kallon kyawawan yaran with interest, Nanny ta shiga ciki ta kwanta ta bar su a parlorn, Shiddah saura Sudais ya 6ata fuska yace "Anty ba mu ci indomie ba fa yau" dariya tayi tana kallonsa sanin irin soyayyarsa da indomie gashi har da speaking din Hausa, which is rare kaji sun yi, ta mike tace "Toh bari in dafa maka Prince, in yi maka frying egg din or I shud cook it" yace "Cook" tace "Toh" Shuraim yace "No i prefer fried egg" tace "Alryt duk xan maku" daga haka ta wuce kitchen ta bar su suna kallon cartoon a parlorn, ta gama dafa indomien kenan tana xuba masu a plate kamar ance ta kalli waje ta tagar kitchen ta hango Shuraim tsaye kan study table din khaleel, khaleel din na tsaye gaban sa yana murmushi yana kallon sa, shuraim kuwa sai demonstrating yake da hannunsa yana masa magana, ta wani hade rai ta bude kofar kitchen din ta fita a tsawace tace "Me kake a wajen nan Shuraim, with whose permission ka fita" sosai yaron ya tsorata ya shiga kkrin sauka kasa, Khaleel ya saukesa ya juya yana kallon ta calmly yace "With my permission madam" ta wani kara hade rai, Shuraim ya nufo ta da sauri kamar xai yi kuka yace "Kiyi hakuri Anty" hanyar kitchen din ta nuna masa tana kallonsa sternly, ya shiga ciki da sauri, Khaleel ya shafa beard dinsa yace "Toh sannu me k'anni.. sai ki jira ki haifa naki tukun" ko kallonsa bata yi ba ta shiga ciki ta rufe kofar ta ta dau plates din indomie din ta fita parlor, duk a tsorace Shuraim yake, ta ajiye abincin hannunta tace "Zo nan" tasowa yyi ya nufota yace "Kiyi hakuri" tace "Wa yace ka fita?" ya girgixa mata kai yace "Ball nake nema" ta kara hade rai strictly tace "Ka taho da ball ne?" Nan ma ya girgixa kai a tsorace tace "Toh me mutumin yake gaya maka?" Yace "He is asking me my name and Sudais name, shine kuma yace wani class muke" kamar xai yi kuka ya kare, tace "Idan ka sake fita gidan nan I will flog you mercilessly, why can't u be like ur brother Sudais?" Sudais dake kwance yace "Na ce masa kar ya fita but he refused, I don't knw what's wrong with him" Ta ce "Ka dai ji me nace maka, ka sake fita kaga abinda xan maka" ya gyada mata kai, ta dau indomie dinsa ta basa sannan ta dau na Sudais ma ta mika masa. Ana magrib ta ja su suka wuce daki bayan sun gama waya da Umma, suna yin isha duk suka kwanta saman gado suna ta mata labari tana biyesu har bacci ya daukesu gaba daya, tayi murmushi sanin karfin hali ne irin na yaro kawai banda haka uban tafiyar da suka yi tun yamma ya kamata su yi baccin ma. Washegari bayan sun yi sllh brush kawai ta masu suka fito parlor da pyjamas dinsu misalin karfe goma ta kunna masu cartoon, tana kitchen tana girka breakfast taji duk suna kiranta, ta fito parlorn da sauri jin irin kiran, khaleel ta gani tsaye parlon ya daga Shuraim dake turjewa yana kiranta tare da d'an uwansa dake kkrin ganin ya sakkosa duk da hannunsa bai kai ba, Shuraim yace "Anty kinga xai tafi da ni, nace masa A'a...." Khadijah ta daure fuska ta dai rasa abinda xata ce, Daya hannun Khaleel ya sa ya dauki Sudais da ke jan sa ya sauke masa d'an uwa shi ma ya daga sa sama ya juya ya nufi kofa da su suna kwala mata kira, Nanny ma ta fito tana kallon ikon Allah, har ya fita da su Khadijah bata ce komai ba, Nanny tayi murmushi tace to fa sai kace dole, ita dai khadijah na tsaye har lkcn, bayan wani lkci taji duk sun yi tsit, komawa kitchen tayi ta ci gaba da abinda take bbu walwala. Ta kalli agogo yafi a kirga don kusan awa biyu kenan da ya tafi da su har yanxu shiru kuma ko motsinsu bata ji, kasa daurewa tayi ta mike ta yafa mayafinta ta fita waje, a hankali ta murda kofar parlorn, xaune ta gansu gaba daya a parlor sun sa shi a tsakiya yana game a laptop, Shuraim na kwance kusa da shi bakin nan har kunne yana cin Burger yana nuna masa direction din da xai bi a game din, Sudais kuma na daga gefensu yana cin indomie da kwai yana kallon game din shi ma, duk suka juya suna kallonta, Shuraim ya bata fuska ya mike da sauri yana cewa "Antyyyy.... Ya ki ya bar mu mu wuce" Sudais ya jefa masa wani kallo a hankali yace "Stop lying pls" Hauri Shuraim ya kai masa da kafa yace "u re calling me a liar" Sudais ya ajiye abincin hannunsa ya mike kamar jira yake, Khaleel yyi saurin janye Shuraim, hakan kuma bai hana Sudais kai masa naushi a baki ba, tana ganin haka ta karaso da sauri a rude ta durkusa tsakankaninsu ta rike Sudais tace "Fadan xa ku fara yanxu..." Cikin kuka Sudais yace "He started 1st, why will he kick me" Shuraim dake nasa kukan shi ma yace "Why calling me a liar" Kamar xata yi kuka take kallonsa tace "Ba kai ka fara kick dinsa ba shuraim" Duk wannan abun Khaleel dake rike da Shuraim din yana kallonta, bai san lkcn da yyi murmushi ba ya jawo Sudais yana kallonsu a hankali yace "Toh ku yi hakuri" Duk suka ki cewa komai sai kuka, ya rungumesu gaba daya yace "Ohk, I don't want to hear u both cry anymore" Sudais ne ya fara yin shiru sannan Shuraim, khaleel na kallonsu yace "To waye senior cikin ku?" Sudais ya nuna masa Shuraim, yace "Good, tell him u are sorry now" a hankali Sudais yace "I am sorry" Ya kalli Shuraim yace "Say it also" yana kumbure kumbure yace "But ai shi ya fara" Khaleel ya hade rai yace "Ba shi hakuri yanxu" a hankali Shuraim yace "Okay kayi hakuri" Khaleel yace "Good...." Kallon Khadijah yayi yace "You can't just come into my apartment babu notice bayan ke ma ba son a shiga naki kike ba malama" wani kallo tayi masa ta mike ta fice daga parlorn. Har yamma tana ta xuba ido ta ga shigowarsu amma shiru, ta rasa yanda xata yi, Nanny ta tura ta dauko su wai xa su yi wanka, ba a dau lkci ba Nanny ta dawo tace "Kinji wai sun yi wankan" shiru Khadijah tayi don ta rasa abun cewa. Tana kitchen tana girkin dinner ta hango boys din a waje gun da yake xama yayi karatu da alama tare suka fito ya koma ciki shi, don ga textbooks dinsa da eye glasses a ajiye, kofa ta bude da sauri ta fito tana masu wani kallo tayi masu alamar da su xo su shiga ciki, tahowa suka yi ta shigar da su kitchen gaba daya sannan ta shiga ita ma ta kulle tana hararansu, Shuraim ya nuna mata wayar hannunsa a hankali yace "Anty na shi ne" kwacewa tayi tace "Maza ku wuce daki, bana son ganin ku ko a parlor" obediently suka wuce kamar yanda tace, ta bude kofar ta fita don ajiye masa wayarsa, dai dai lkcn da ya fito waje, ta ajiye da sauri xata bar gun ya jawota, xaro ido tayi jin ta a jikinsa ta kalli kitchen dinta da sauri tace "Meye haka kake yi malam ka sakeni" a hankali yace "Me yasa kika kora su ciki" taki cewa komai, ya juyo da ita tana facing dinsa, kin yarda su hada ido tayi don ko kadan bata son idonsa, ta shiga kokarin kwace kanta, ya jinginar da ita da bango yana kallonta, turasa tayi da karfi tayi kitchen dinta da gudu ta tura kofar ta rufe, jingina tayi jikin kofar gabanta na faduwa, a xuciyarta tace "Wannan mutumin fa dan iska ne da gaske" Fita tayi kitchen din, ta sa Nanny ta karasa mata girkin, ta dawo ta xauna gefen gado a bedroom tana kallon yaran dake ta hada puzzles xaune kasan carpet din dakin, kallonsu take ko kiftawa bbu, lkci daya ta tafi duniyar tunani iri iri a xuciyarta, bata san sanda tayi wani murmushi ba wanda xa a iya kira da na takaici hawaye ya xubo idonta, ko kadan bata san yaran sun ga hawayen ba, duk suka taso Shuraim ya kamo hannunta da damuwa yace "Anty are you sick?" Da sauri ta girgixa kai tana share idonta tace "Noo, idona ke ciwo" Sudais da har idonsa ya kawo ruwa yace "Toh Anty me yasa" jawosu tayi jikinta jin wasu hawayen sun taho mata, ta rungumesu trying very hard to control her self tace "I will be okay soldiers, xae daina yanxu" shiru suka yi gaba daya, bayan wani lkci ta janyesu a hankali ta mike tace "Xan yi alwala" daga haka ta shiga bathroom tayi kukanta me isarta har taji xuciyarta yyi sanyi sannan ta fito, ganin duk sun yo kanta tace "Ku je kuyi performing ablution" ba musu duk suka shiga bayin. Da wuri duk suka kwanta bayan sun ci abincin da nanny ta kawo masu har dakin. Washegari da ya kasance Saturday, bata tashi da ko wani damuwa ba kafin karfe tara har sun yi breakfast ta yi ma su sudais wanka, ita ma ta shirya don so take su fita xuwa gidan Vanessa ta dau motarta ta xaga da su gari kamar yanda ta yi masu alkawari jiya kafin su yi bacci, tana parlor tana goge veil dinta aka bude kofar parlorn, ta dago tana kallon direction din, tsaye yyi bakin kofar ya rungume hannayensa idonsa a kanta, tayi saurin kauda kanta, ganin ita kadai ce parlorn yasa ta fara kame kame gashi kananun kaya ne jikinta, kofar kitchen ta kalla tuna su Shuraim da tayi, sai a sannan ta tuna tun daxu suka je ajiye cup din cornflakes da suka sha a kitchen shiru shiru basu fito ba, Nanny dama tana daki, ya karaso cikin parlon cikin tafiyarsa ta kasaita, ta mike da sauri xata shiga kitchen yyi hanxarin preventing dinta, ta daure fuska tace "Meye haka ni ka kyaleni" yana kallon lips dinta da lumsassun idonsa yace "You've got cute lips" xaro ido tayi xata fixge hannunta ya jawota jikinsa a hankali yace "Tafiya na xo yi da twins" ta hadiye abu da kyar cikin rawar murya tace "Stop it pls ka sakeni, ni bani kadai bace a gidan nan" yace "In tafi da su?" Kai ta gyada masa, duk da haka ya ki saketa, taji ta kasa tsayuwa, kamar xata yi kuka ta rufe ido tace "Ni ba yar iska bace na hadaka da Allah ka daina min irin haka" A hankali ya saketa yace "Nima ba d'an iskan bane, just living a free life, ko kin taba kamani da wata?" daga haka ya nufi kitchen ta bi sa da kallo xuciyarta na bugawa, Tare ya fito da su Shuraim, bai kuma yarda ta hada ido da su ba, don sai kakkaresu yake, su ma basu yarda sun kallo inda take ba sai shigewa jikinsa suke har suka fita ya kulle kofar, duk da bacin ran da take ji hakan bai hanata murmushi ba, tana jin fitar motarsa daga gidan ta tabe baki ta dau veil dinta ta wuce daki tayi kwanciyarta. *Haske Writers Association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 9...... Sai kusan karfe biyar din yamma Khaleel ya dawo da boys din, da kayan wasa suka shigo mata ko wannensu baki har kunne, kana ganinsu kasan they are just happy, ta ajiye handout din hannunta tana kallonsu ta nuna masu hanyar bedroom alamar su wuce ciki, basu mata musu ba suka wuce, mikewa tayi ta isa kofa ta sa makulli sannan ta bi bayansu, tsaye ta samesu sun yi tsuru tsuru, ta hade rai tana kallonsu gaba daya tace "Ku gaya min daxun da ku ka je ajiye cup a kitchen me ku ka tsaya yi?" Duk suka ki cewa komai ko wannensu a tsorace, tace "Ba magana nake maku ba?" Sudais ya kalli Shuraim sannan yace "Anty mun ga uncle a waje shine ya xo wajen window yace mu fito, ni nace A'a, sai Shuraim yace xa ki mana duka" daga haka yayi shiru, ta kalli Shuraim strictly tace "Sai me ya far kuma?" Shi ma kamar xai yi kuka yace "Shine sai ya tambayemu inda kike sai Sudais yace kina parlor" shiru yayi shi ma, ta rungume hannayenta ta kalli Sudais tace "What now happened after that?" A hankali yace "He told us to remain in the kitchen he will come pick us.... And, shine kawai muka gansa ya shigo ya tafi da mu" tana kallonsu da kyau tace "Good... Next time baxa ku sake xuwa wajena ba kuma xan fadi ma Mumy duk abinda ku ka yi tunda bakwa ji" hawaye su ka fara yi suna bata hakuri, bata bi ta kansu ba ta yi fitowar ta parlor. Ranar lahadi Khadijah na kitchen tana dama masu custard kamar yanda suka bukata taji an danna kararrawa, kusan a tare da Nanny dake masu wanki a bathroom suka fito, ganinta Nanny ta juya ta koma, ita kuma ta sa hijab ta iso gun kofar, a hankali tace "Waye..." Yace "Kin sani" k'in bude kofar tayi tace "How can I help you?" Yace "In bude kofar kenan da kaina" shiru ta yi na 'yan sakwanni kafin ta bude kofar, da sauri ta bar bakin kofar ganin shigowa xai yi kuma bai damu da cewar sai ya bugeta kafin ya shigo ba, yace "Where are they" ta hade rai bayan ta bar gun tace "Breakfast xa su yi" lkci daya duk suka fito daga dakin suka tsaya cirko cirko, sakin baki tayi tana kallonsu, arms akimbo ya tsaya kallonsu shi ma yana murmushi, can a hankali yace "Good morning boys" suka washe baki a tare suka ce "Good morning Uncle" yace "We've got 2 more places to go... So..." A hankali Shuraim yace "Noo we won't make it up" ya buda ido yace "Why" duk suka kalleta, Khaleel ya kalleta shi ma sannan yace "What about her?" a hankali Sudais yace "Aunt was angry at us yesterday, she promise not to let us come over again for holidays" Buda baki tayi tana kallonsu, Khaleel yace "Ohk, haka kika ce masu" ta hade rai ta kallesa tace "Ni bance masu haka ba, they misunderstood me" yace "Ohk to fahimtar da su abinda kike nufi ynxu" ta kallesu tace "Oya ku bi sa ku tafi" Shuraim ya kamo hannunta yace "Sure Anty?" Ta dake tace "Yeah" rungumeta suka yi gaba daya da murna suna ce mata thank you aunt, Khaleel ya kama hannunsu suka fita yana murmushi, banging kofarta tayi bayan fitarsu rai a bace. Ba su tashi dawowa ba sai da daddare don ita har ta kwanta sbda takaici gashi gobe xa su koma, wato ba gunta twins din suka xo yin hutu ba wannan karan kawai, Nanny ce ta shigo daki da uban ledoji ta mike xaune tana kallon ledojin, rungume ta boys din suka taho suka yi da gudu ko wannensu na kokarin expressing kansa ya bada labarin abubuwan da ya faru, sai kuma suka sauka kasa suna bude mata ledojin, mamaki duk ya cikata ganin uban abubuwan da ya siya masu har da kaya da abubuwan makaranta, haka ta saki baki tana kallon ikon Allah, Nanny kam sai yabawa take tana shi masa albarka, ita dai bata samu bakin cewa komai ba har Nanny ta ja su ta masu wanka, bayan ta shirya su xuwa rigunan baccin su tayi masu tayin abinci suka ce sun koshi, daga haka suka kwanta bbu bata lkci bacci yyi gaba da su, Nanny ta wuce dakinta, sae a snn Khadijah ta samu kwarin gwiwar sakkowa daga saman gado tana kallon tsaraban cike da mamakin yanda ya san gobe xa su koma, bata kwanta ba sai da ta gama hada masu duk kayansu da za su koma gida da, taji har ta fara jin kewan yaran gashi bata samu lkcn su yanda take so ba. Washegari kafin karfe takwas har ta gama shiryasu nanny ma ta shirya, tana kokarin fita kira masu taxi aka danna bell, lkci daya kuma ya bude kofar yana mata kallon cikin ido a hankali yace "Morning" sauke kanta tayi wondering anya yasan abinda yace kuwa, don gaisuwa bai taba hada su ba, "Same to you" ta mayar masa, a takaice yace "Yaushe xa su wuce airport din" tace "Yanxun xa mu wuce" yace "Alryt, ina jiran ku" ta bi sa da ido bayan ya juya. Shi ya kai su har airport din a motarsa duk da bata so hakan ba amma twins suka gwaleta, suna isa duk jikinta yyi sanyi, yanxu fa komawa yaran xa su yi su bar ta, su kansu sai bata rai suke suna shisshige mata, shi ya rakasu daga karshe don ita kam kasawa tayi, sae d'aga mata hannu yaran suke, kasa daurewa tayi bayan tafiyarsu ta hade kai da gwiwa a inda take xaune, bayan kusan minti goma Khaleel ya dawo, muryarsa taji yace "Heyy" ta dago kanta a hankali, ya d'an bude ido yace "Waow, kuka kike?" da sauri ta goge idonta don bata san ma tana yi ba, yyi murmushi yana shafa kai yace "Su ma kinga kukan suke, Ashe sun ji a jikinsu kina kukan ne" tashi tayi da sauri tace "Kuka suke?" yace "Yea but I made sure sun yi shiru before I left, the bond between u and ur Siblings is really amazing...." daga haka ya fara tafiya yace "let get home" bin bayan sa tayi a sanyaye har suka isa gun motar sa, a hankali ta sa hannu ta bude front seat ta shiga, babu wanda yace komai cikin su yana driving, tsaki yyi bayan wani lkci ya jawo wayarsa dake ta ring tun fara driving dinsa yyi silencing wayar ya ajiye, ita dai tayi nisa tunanin da take na su Shuraim, yana gama parking a gida murya can kasa tana wasa da yatsunta a hankali tace "Thank you very much, Allah ya saka da alkhairi" kamo hannunta yayi yace "For?" Ta fixge hannunta hade da galla masa harara daga haka ta bude motar ta fita ta nufi flat dinta ya bi ta da kallo ta madubi. Tun da ta shiga bedroom dinta take bacci har azahar, biyu da rabi ta tashi ta shiga bayi ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana gabatar da sllhn zuhr ta shiga kitchen don neman abinda xata ci, ko ba a fadi mata ba tasan ita kadai ce gidan coz everywhere was very silent, ta gama cin abinci ta dau materials din karatunta don rabonta da karatun tun xuwan kids din, gashi yau ma tana da lectures bata je ba, sai sha biyu saura na dare ta hakura da karatun ta kwanta don gobe da safe take da lecture. Washegari takwas saura ta fito xata wuce makaranta, dai dai fitowarsa shi ma, suna hada ido tayi saurin dauke kai ta kara pace dinta, kafin kuma ya fito da motarsa har ta hau taxi abun ta. Karfe uku da wani abu suka fito school tare da Vanessa da Angela, sauraren Vanessa dake mata korafi ta gama yi kafin tayi 'yar dariya da halshan turanci tace mata ba wai ta fasa xuwa bane xata dawo gidan nata amma sai during weekend, ko da wasa bata nuna mata su shuraim sun xo ba balle ta sake jin haushin rashin kawo su da tayi, juyawa Khadijah tayi tana kallon direction din da Angela da Vanessar ke kallo, sai a snn ta ga motar da ya tsaya gefensu dai dai lkcn da kuma ya sauke glass, hannu ya daga ma su Vanessa a hankali yace "Hi" suka mayar masa da "Hello" Ya kalleta yace "Are you heading home?" Tunani ta fara yi shi kuma wannan yaushe suka fara yin haka da shi, wani kallo tayi masa tace "Noo thank you" wani murmushi yyi yana shafa millionaires belt dinsa yace "Ohk a gaban kawayen naki xaki ce min A'a" Tace "Ka saba daukata ne?" Yace "Xan fara yanxu, shiga mu je" tabe baki tayi bayan few seconds ta kalli su Vanessa tace "Alryt, see you girls tomorrow" daga haka ta xaga ta bude front seat ta shiga ta kulle kofar, daga masu hannu yyi ya ja motar suka bar gun, basu yi tafiya me nisa ba yace "Twins sun isa lafiya?" Ta gyada kai tace "Sure" wayarsa dake ajiye kusa da ita yyi haske ta sauke kai tana kallon screen din, "Jawahir" sunan dake saman screen din kenan ta dauke kanta, bayan seconds kusan biyar ya dau kiran yace "Am driving baby, xan kira ki when am home" daga haka ya katse wayar ya mayar ya ajiye, suna isa gida yyi parking ta bude motar ta fita ta rufe ta nufi apartment dinta, xaro ido yyi ya bi ta da kallo. Washegari Tuesday da yamma ta shirya bayan ta dawo makaranta don xuwa shopping mall ta yi shopping din turarurruka da man shafa, karamar jakarta ta sakale kafadarta ta fito ta rufe apartment dinta, ganin motarsa a parking space yasa ta gane yana nan don tun da ya ajiyeta jiya rabon da su hadu, babban shopping complex ne wajen ta gama daukan mayuka da turarukan da xata dauka, tayi deciding hadawa da disinfectant da antiseptics, Dettol babba ta dauka bata lura da mutumin dake bayanta ba kamar yanda shi ma din da alamar bai lura da ita ba don backing din juna suka yi, lkci daya suka juyo kusan a tare suka ci karo, pack din Sabulun dettol dake hannunsa ya fadi kasa, da sauri suka durkusa kusan a tare again ta rigasa daukan sabulun kafin ya kai hannunsa tace "Ohh sorry pls, I...i..." dai dai sanda suka mike tsaye ido cikin ido, shekaru kusan hudu kenan rabon da ta ji abinda taji a xuciyarta lkcn, a hankali ta saki dettol din hannunta tana kallonsa bbu kiftawa, wani kallo shi ma yake mata da wani expression, yana son magana amma da alama words din sun kasa fitowa, lkci daya words din yyi escaping lips dinsa cikin wani yanayi yace "IMANN...." Juya masa baya tayi tana ganin turawan da ke d'an nesa da ita doubled doubled, kawai ta nufi kofar fita complex din, tana jin yana kiranta da alamar bin ta yake ta kara saurinta, cikin sarkewar murya tace ma baturen gun ta mance ATM card dinta a gida yana bude mata kofa ta fice fittt without thinking twice ta nufi bayan mall din kamar xata tashi sama, ta xauna nan kasa jikin bango ta kai hannu dai dai kirjinta ta runtse ido, ta fi minti sha biyar wajen xaune, ji take kamar an mata alluran tsayar da Adrenaline ne don komai na jikinta gani take ya daina aiki kamar ba nata ba. *Haske Writers Association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 10.... Hadarin da ta gani garin ya kara mata kwarin gwiwa ta tashi da kyar tana layi kmr warce ta tashi ciwo ta samu taxi bayan ta fita haraban mall din, sai da suka dau hanya kafin ta iya bude baki ta gaya masa inda xa ta, kanta ta daura a kafarta har suka isa, tana jin yana ce mata sun kawo amma ta kasa dagowa, har sai da ya fito da sauri ya bude bayan motar yana cewa "Madam, are you okay" mugun karfin hali tayi ta dago tana dubansa da idanuwanta da suka yi jajur, yace "You look sick..." Da taimakonsa ta fito taxin, bai karbi kudi ba ya ce taje ta sha drugs ta gyada masa kai ta shiga gida tana hade hanya, Ikon Allah ya kai ta bakin kofar flat dinta ta fadi dai dai kofar Khaleel tana dafe da xuciyarta da take jin kamar an caka mata mashi, bugu daya ta ma kofar ta hade kanta da kasa, bude kofar aka yi, Khaleel ya d'an ja baya yana kallonta da mamaki, saurin durkusawa yyi yace "Subhanallah, Are you okay...." Ta dago da kyar hawaye na sakko mata ta nuna masa kirjinta ya rikota da mamaki yace "Me ya same ki" girgixa masa kai ta dinga yi ta kasa cewa komai, tun tana ganin sa dishi dishi a hankali kuma bata kara ganin komai ba. A hankali ta bude idanuwanta da suka mata nauyi tana bin dakin da take da kallo, dai dai nan aka bude kofa wani matashi ya shigo Khaleel na biye da shi a baya, mutumin ya karaso inda take ya duka ya d'an yi murmushi yace "Hello...." Kallonsa kawai take, yace "How are you feeling now?" Tayi shiru, yace "Sannu, Allah ya sauwake, babu inda ke maki ciwo yanxu koh?" A nan ne ta gyada masa kai, ya juya yana kallon Khaleel dake rungume da hannunsa yana tsaye bakin kofar, likitan yyi murmushi yace "Quack MD do you mind coming over" d'an murmushi Khaleel yyi ya karaso kamar bai son tafiyar ya isa kusa da ita idonsa a kanta a hankali yace "ina ke maki ciwo yanxu?" Shi ma dai bata ce masa komai ba, likitan dake kusa da shi yace "Xa ki ci abu yanxu, sai yyi maki allura ya baki magani kin ji" kallonsa nayi ban dai ce komai ba, ya kara min fatan samun lfya sannan ya nufi kofa yace "Dr I will take my leave....." bin bayansa Khaleel yyi suka fita waje, da damuwa Dr Ahmad yace "But... Tayi k'ank'anta da wannan matsalar, naga kamar she is in her early 20's...." Khaleel ya sauke ajiyar xuciya yace "Probably it's an inheritance...." Ahmad yyi dariya yace "Kai kuma ina mamakin wani irin Dr ne kai wani lkcn wllh...." Dakatar da shi Khaleel yyi yace "No you ought to have known me for long, I don't treat people that are close to me, ban iya bane..." Dr Ahmad yace "Close to you? Yanxu kana nufin yarinyar nan is close to you? A ina ka santa" Khaleel yace "Noo ba haka nake nufi ba malam" Ahmad yace "Seriously you need to get rid of that behavior Dr, Allah ya bata lfya, ka sama mata abinda xata ci yanxu sai ka mata alluran ko shi ma baxa ka iya ba?" Khaleel ya hararesa yace "Wa ya sani...." dariya Ahmad yyi yace "Toh shknn ni dai bari inje in d'an yi karatu kai kam nasan tun ba yau ba ka gama, abun ka da manya" Khaleel ya shafa kai yace "Xan dai yi, tnx for ur care frnd" daga haka suka yi sallama Khaleel ya koma ciki, a hankali ya tura kofar bedroom din nasa, har lkcn tana xaune ta dago kai tana kallonsa, yace "What will you eat Khadija?" Bata ce komai ba, ya d'an yi jim yana kallonta, juyawa yyi ya fita, ba a dau lkci ba kuma ya dawo rike da cup din shayi, da kyar ta yarda tasa hannu ta karba shayin da yake mika mata ganin yanda ya kafe ta da ido, ta dinga sha kamar magani don bbu wani xafi, xaunawa yyi gefen gadon, bayan wani lkci ta mika masa sauran shayin hawaye cike idonta, ya tsura mata manyan idonsa, murya can kasa yace "Meye matsalarki Khadija, tell me what ur problem is" girgixa masa kai kawai tayi, ya mike ya fita da shayin ya dawo, allurorin ya shiga hadawa har ya gama sannan ya dawo gefenta yace "Let me inject you sai ki sha magani you will be relieved soon in sha Allah" ganin jiranta yake ta d'aga rigar a hankali ta kwanta yyi mata sannan ya dauko mata magungunan da goran ruwa ya ballar mata su ya mika mata ta karba ta sha, tashi ta shiga kokarin yi tace "Ina son xan yi sllh" ya nuna mata bathroom, ta kusa minti daya bata tashi ba bata ce komai ba, can ta mike ta shiga ta dauro alwala ta fito, Fita yyi xuwa apartment dinta don dauko mata Hijab, a hankali ya tura kofar bedroom, idonsa ya fara sauka kan enlargements dake dakin na hotuna, a hankali ya karasa dakin yana kallon cute twins dake hoton da ita kanta, sun rungumeta gaba daya tana murmushi, ya sake mayar da dubansa kan daya enlargement din da suka manna mata kiss gaba daya, dauke idonsa yyi ya dau Hijab da ya gani linke kan gadon ya fita dakin, kan gadonsa ya ajiye mata Hijab din sannan ya fita. Ta jima xaune kan darduman bayan ta idar da sallahn magrib da isha, ido ta kafe ma wani hotonsa dake gaban mirror yana sanye da farin labcoat da stethoscope rataye a wuyarsa, a hankali ta sauke idonta daga kallon hoton, can tayi wani murmushin ta mike da kyar tana dukkan kokarin ganin bata yrda hawayen dake makale idonta ya xubo ba, ta linke masa lallausan pray mat dinsa ta ajiye sannan ta dau dankwalinta dake kan gadon ta yafa ta nufi kofa kamar mai counting steps dinta ta fito parlor, xaune ta gansa kan kujeran parlorn idonsa a kan wayarsa dake hannunsa yana operating, ya daga kai ganinta yace "You want something?" Girgixa masa kai tayi tace "No, am going to my apartment, thanks for ur care" daga haka ta nufi kofa yace "But...." Juyowa tayi tana kallonsa yace "Are you sure you will be okay all alone" tace "Yea sure" karasawa yyi kusa da ita ya mika mata makullin hannunsa ta karba ta bude kofa ta fita ta rufe masa. Bedroom dinta ta wuce direct ta fada kan gado, sae a sannan wani kuka ya xo mata, kukan da ta kasa yi tun daxu, Allah ya sani ta samu relief sosai kukan da tayi domin kuwa taji saukin abinda xuciyarta ke mata, har lkcn ta kasa gaskata wanda ta gani, why all of a sudden. Bata wani rintsa ba daren ranan don da baccin ya dauketa xata farka a firgice, daga karshe ma hakura tayi da baccin ta dauro alwala ta yi ta sllh sae dab da asuba wani bacci me nauyi yyi awon gaba da ita. A hankali Aliyu ya bude idanuwansa jin kwankwasa kofa da ake ta yi, ya tashi xaune yana kallon kofar yace "Who's there?" Muryar small mum dinsa yaji tana cewa "Are you okay Aliyu? Baka fito sllh yau ba" a hankali yace "Nayi a nan Anty... Was having a slight headache ne" tace "Toh Allah ya sauwake, ka fito kayi break sae ka sha magani" daga haka tayi wucewar ta, mikewa yyi yana dafe kansa da yayi masa nauyi ya nufi window ya tsaya, lkci daya ya dawo ya xauna gefen gadon ya rike kan yace "Noo, nasan ba ita bace, ba Iman bace, it's her look alike.... But...." mikewa yyi da sauri cike da damuwa da confusion yace "Why did she run then, me yasa ta gudu?? Does it mean ita ce? Ya Allah...." Jingina yyi da bango ya runtse ido, ya kusa minti ashirin a haka aka sake bubbuga kofa, ya bude ido a hankali cikin sanyin murya yace "Who's there?" Muryar Maryam cousin sis dinsa yaji tace "Yaya ni ce" yace "Ya aka yi" bata ce komai ba, hakan yasa ya karasa ya bude kofar tace "How was ur nyt?" Ya dauke kai yace "T'was good" Tace "Mumy wai ka fito ka yi breakfast" yace "Ohk" daga haka ya rufe kofar ya koma gefen gado ya xauna, kallon agogo yayi ganin takwas ya tashi ya shiga bathroom, wanka yyi ya fito, ya fi minti sha biyar kwance jin kamar xaxxabi xai rufesa, can yyi ta maxa ya mike ya shirya ya dau makullin motarsa ya fice gidan ba tare da ya bari Small mum dinsa taga fitarsa ba. Mikewa xaune Khadijah tayi da sauri daga baccin da take ta dalilin bell da aka danna, ta tashi a hankali jin jiri na dibarta, ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta wanke baki sannan ta fito ta dau hijab ta sa ta fito parlor ta bude kofar, har lkcn yana tsaye gun, yana kallonta a hankali yace "Bacci kike na tashe ki?" Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace "Na tashi" yace "How are you feeling now?" Tace "Alhmdllh, ina kwana" yace "Lafiya lau" jin yyi shiru ta dago kai suka hada ido, saurin sauke idonta tayi, yace "You cried!" Ta girgixa masa kai kawai, yace "Noo you cried malama" lkci daya hawaye ya kawo idonta ta kasa ce masa komai, shiru yyi bai sake cewa komai ba, bayan wani lkci yace "Shiga ciki" ba musu ta juya ta koma ciki ya rufe kofar, daki ta koma ta kife kai da pillow wasu hawayen na xubo mata, duk taji ta tsani xaman UK din, ta tsani karatun, dago kanta tayi da sauri ta dalilin *SUDAIS* da ya fado mata, bata san lkcn da tayi murmushi ba kawai taji kamar an yaye mata bakin cikinta, tayi tagumi a sanyaye.... Ta fi minti sha biyar a haka, ji tayi duk duniya bbu wanda ta tsana... tsanar da bata da iyaka irin wanda tayi tozali da jiya a mall, taji an bude kofa ta dago da sauri, jin shiru ta mike ta fito parlor tana goge idonta, xaune ta gansa kan kujera yana hada allura, ya dago ya kalleta, lkci daya ya hade rai , bata yrda sun sake hada ido ba, ya ajiye alluran hannunsa ya mike yace "Are you alright? under this condition stil xaki dinga xama daki kina kuka haka, dama kuka na magani? idan ma damuwa gare ki baxa ki sa Allah ran ki ba" bata iya tace komai ba bata kuma yrda ta dago ba, ya koma ya xauna, bayan kusan minti uku ya nuna mata cup din shayi da bread dake ajiye kan table yace "There" ta karaso ta dau shayin yace "With d bread" girgixa masa kai tayi ta fara shan shayin, murya can kasa yace "Look..." ta dago idanuwanta ta kallesa ya nuna mata kujera, a hankali ta karasa ta xauna, ajiye cup din tayi bayan ta sha shayin, yace "ur injection" tashi tayi ta wuce daki ta daura xani cikin Hijab din jikinta ta fito, nan parlorn yayi mata alluran ya bata maganinta, yace "You go get some rest now, ki yi bacci da yawa kin ji" yyi kasa da murya yace "And please kar sake kuka ur condition isn't encouraging, always remember Allah xaki samu natsuwa sosai..." Bata ce komai ba ta mike ta wuce daki ya bi ta da ido, tashi yyi ya dau cup din ya fita. Sai bayan azahar ta farka daga baccin da tayi, sosai taji xuciyarta ya mata saukin xafin da yake mata don ta samu bacci da yawa, kuma taji ddin drugs din, yunwa taji na dawainiya da ita, ta tashi ta shiga bathroom ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, shafe shafe tayi ta dau gown mara nauyi da tsayi ta sa ta shimfida darduma ta saka hijab har kasa ta tada sllh, tana idarwa ta cire Hijab din ta linke sannan ta fito parlor don dafa ko da indomie ne ta ci, still tayi ta juya baya da sauri a parlorn ganinsa da tayi dai dai center table ya ajiye ledan hannunsa da alamar shigowarsa kenan, Bata jira ta ji abinda xai ce ba ta nufi daki da sauri ta rufe kofa, xama tayi kan gado ta hade kai da gwiwa duk taji kunya ya kamata, ta fi minti goma a haka, can dai ta mike a hankali ta saka Hijab din da tayi slh ta fito parlorn, bbu kowa ciki ta karasa gun ledan ta bude taga abinci ne da drink, kadan ta ci ta fara gyaran gidan, dab da la'asar aka danna bell, ta kasa xuwa ta bude, can dai taa isa gun kofar tace "Who's there?" Yace "Koh" bude kofar tayi ta juya ta dawo parlorn ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yace "Sorry...." Da sauri ta katse sa tace "Ohh bakomai" yace "Bakomai me?? ai baki jira kin ji abinda xan ce ba malama" ta d'an kallesa, sai taji kunya, ya buda ido sosai yace "Dama cewa xan yi, sorry... me yasa kika gudu daxu?" Bata ko kallesa ba balle tace komai, yyi murmushi yace "Toh kin ci abincin" kai kawai ta gyada, yace "How you feeling now" tace "Naji sauki" duk wannan abun bata yrda ta juyo ba sai gyare gyare take, yace "Alluran ki..." Da sauri tace "No naji sauki, xan sha maganin" shiru yyi na kusan thirty seconds, yace "Malama" sai a sannan ta juyo suka hada ido, jallabiya ce Milk colour jikinsa da ya fiddo da ainahin kamanninsa na larabawa, shi ya fara dauke kansa sai kuma yace "ohk... Ki sha maganin" daga haka ya fita ta bi sa da ido har ya rufe kofar. *Haske writers association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By khaleesat Haiydar_📚✍🏻 11.... Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba yana sauraren fadan Kanwar Dad din tasa, A fusace tace "Wai ba da kai nake ba ka min shiru Aliyu" ya dago ya kalleta da kyar don har wani ciwon kai fadan ke sa masa, ya marairaice fuska yace "Wllh ina ji Anty, ina jin ki" tace "Nace ka gaya min me yasa ka bar min breakfast kayi ficewar ka daxu?" yace "kiyi hakuri mum, ban san xan jima haka bane" Tace "To xaka ga uwar da xata baka dinner yau a gidan nan kuwa" murmushin karfin hali yyi ta juya tayi ficewarta, komawa yyi ya kwanta kansa na ci gaba da sara masa, tun safe har xuwa lkcn bbu abinda ya ci ban da ruwa da yake sha, bbu inda bai shiga ba a wasu daga streets din UK ko xai ga Iman amma sam bbu alamarta, shi ya ma rasa gane ko ita ce ya gani ko ba ita ba, ya mike xaune da damuwa yace "Ya Allah..." Har agogo yyi stucking karfe shidda na yamma yana xaune dakin, aka bude kofa tare da sallama, Maryam ce ta shigo dakin tace "Yaya Aliyu are you sick?" Ya kalleta yace "No I am not Maryam" ta xauna gefen gadon tace "Toh naga tun jiya duk ka xama wani iri, gashi daxu ko breakfast baka yi ba ka fita, nasan baka yi lunch ba ma" yace "Kirana aka yi na fita" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ya school ko baki je ba yau?" Tace "Naje daxu na dawo" yace "Ohk, ina su Baby da Fadil" tace "Suna assignment a daki" yace "Idan Anty ta gama lunch ki dibar min kadan ki kawo min" tace "Toh" sannan ta mike ta fita, ba a dau lkci ba kuma ta kawo masa abincin da ruwa ta ajiye masa. Kulawa sosai Khaleel ke bata a kwanaki ukun da tayi a gida bata je makaranta ba duk da shi ya hanata xuwa makarantar sae taji sauki sosai, kuma cikin ikon Allah ta warware bata jin ko wani ciwo sae dai Kawai ta kasa mance incident din ne, ba a minti goma Aliyu bai fado mata ba, ko kadan Khaleel bai son ganinta cikin damuwa, he's as kind as she never expected, duk da wani lkcn he is pretending not to be, kamar dai yasan tana da damuwa, bata kuma yi mamakin ya gano haka ba tunda likita ne shi din, duk Safiya kafin ya fita sae ya tabbatar ta karya ta sha magungunan ta, da yamma kuma idan xae dawo it's either ya taho mata da fruits ko abinci, har books masu dadi na turanci ya kawo mata ta dinga karantawa, ae kuwa books din also contributed don nishadi suke sa ta idan tana karantawa, idan kuma ta gaji da karatun ta dauko hotunan su Sudais da Shuraim tun daga lkcn da suke jarirai har xuwa girmansu, yawanci kuma hotunan duk tare da *Sudais* ne wannan dalilin yasa bata gajiya da hotunan, ko gida bata fadi ma su Umma bata da lafiya ba. Yau kamar ko da yaushe tana kwance parlor bayan ta raka su Vanessa da suka xo gaishe ta tun da rana, bell aka danna, ta mike don tasan shi ne, ta isa gun kofar ta bude, gaishesa tayi tana kallon sa, ya amsa yana mika mata ledan hannunsa, lkci daya kuma yana tambayarta ya jiki, ta karba tace "Da sauki" yace "Maa sha Allah" xae juya tayi saurin cewa "Are you sick?" Juyowa yyi yana kallonta yace "Just Stomachache, but na sha drugs da sauki sosai" da damuwa tace "Allah ya sauwake" yace "Ameen" daga haka ya rufe mata kofa ya shiga apartment dinsa. Ajiye ledan tay kan table ganin fruits ne, tana ta xaune parlor har kusan Magrib kafin ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, nan parlorn tayi sllh, ta gama addu'o'inta sannan ta mike ta shiga kitchen, tunanin me xata dafa ta shiga yi don yunwa take ji, garnished cous cous tayi da yaji kayan hadi, duk da bashi da yawa kawai tayi deciding ta debar masa, ta zuba a karamar warmer snn ta sa hijab ta fita kai masa, a hankali ta kai hannu ta danna bell, sai da ta sake dannawa ya bude kofar, singlet ne jikinsa da dogon wando, kallon sa ta tsaya yi ya juya ya koma kan kujera ta bi sa da ido, can ta bi bayansa ta rufe kofar, ajiye abincin hannunta tayi ta durkusa gefensa tana kallonsa da damuwa tace "Cikin ne har ynxu?" Gyada mata kai yyi a hnkli yace "But... Sure I will be okay" cike da karfin hali yyi maganan, shiru tayi tana kallonsa taji tausayinsa sosai, a hnkli ya sauko kan kujeran ya duka kan gwiwowinsa, kamar xata yi kuka tace "Ko xaka je asibiti" girgixa mata kai kawai yyi, sai kuma ya kwanta nan gun, kana ganinsa kasan namijin kokari kawae yake, hawaye ya cika idonta, tashi xaune ya kara yi yana runtse ido a hankali yace "Get me water pls" tashi tayi da sauri ta nufi fridge ta bude taga duk masu sanyi ne, ta shiga kitchen ta dau glass cup ta dibo masa na tap, tana dawowa ta duka gun sa ta mika masa ya karba ya fara sha, sae kallon sa take sai ka rantse tare cikin ke masu ciwo ynda tayi da fuska, lkci daya ya ajiye glass din ya mike ya nufi bathroom dake parlorn, ita ma ta mike tsaye, amai sosai yake yi a bathroom din, ta kasa motsawa daga inda take, can ta durkusa ta fashe da kuka, yana fitowa parlorn ya hade kansa da kujera, tashi tayi ta isa kusa da shi cikin rawar murya tace "Don Allah mu tafi asibiti plss" ya dago idanuwan sa da suka sauya xuwa ja, komawa baya tayi da sauri don idanuwan suna kalau ma tsoronsu take barin kuma yanxu da suka kara wani kala kan na da, da alama ya kasa mata magana don girgixa mata kai kawai yayi, xai komar da kansa kan kujerar tayi karfin halin rikosa da sauri tace "Doctor plss let me drive us to the hospital, ina makullin motar yake" murya can kasa yace "I will be alright Khadija, go to my room xa ki ga 1st aid box..." Bata jira ya gama ba ta mike da sauri ta shiga dakin, da box din ta dawo, ta ajiye kusa da shi, ya xamo kasa idonsa lumshe ya bude box din, bayan yan sakwanni ya bude idon ya dau wani allura da syringe ya mika mata, ta bude ido da mamaki ta dai karba ya mayar da kansa kasa, rasa abin cewa tayi, can dai ta balle bakin alluran ta xuke a syringe tayi karfin halin cewa "Ga shi nan" ja baya tayi tana xare ido ganin ita yake nufin xata masa alluran, duk da ta iya kawai niyyar nuna masa bata iya ba ta yi, amma tausayinsa da yanda shi ma ya nuna damuwarsa lkcn da bata da lafiya yasa ta kasa, hannunta na rawa tayi masa alluran, kin bude ido yyi ta koma baya tana kallonsa, bayan wasu mintuna ya mike da kyar ya kwanta kan kujera, ko minti goma bai kara ba bacci ya dauke sa, dawowa tayi kusa da shi tana kallon sa da tausayi ganin alluran bacci yasa tayi masa, mikewa tayi ta dauke glass cup din da abincin da ta kawo ta kai kitchen, ta mayar da box din 1st aid din daki, tayi disposing alluran da tayi masa sannan ta xauna kusa da shi tana kallon sa, giransa kadai ma abun kallo ne a fuskarsa kafin a xo ga long lashes din idonsa, a hankali ta sauke idanuwanta kan dogon hancinsa da ko Kadan bai da miskila xuwa bakinsa, kai kana ganinsa kasan duk yanda aka yi yana da alaka da larabawa, dauke idonta tayi tana wasa da fingers dinta, da sauri ta tashi tunawa da tayi bata yi isha ba, alwala ta sake yi ta gabatar da sllhn nan parlor, tana xaune tana azkar wayarsa ya fara ring, har ya katse bata mike ba shi ma kuma bai ko yi motsi ba, ganin an sake kira ta tashi a hankali ta nufi kusa da shi ta durkusa tana laluban aljihunsa ta fiddo wayar tana kallon screen din, Jawahir ta gani jikin screen din wayar, har ya katse tana kallon wayar, can ta ajiye a hankali ta daura chin dinta bisa gwiwowinta tana kallonsa, bacci yake sosai, ta so tashi ta wuce apartment dinta amma ta samu kanta da kasa yin hakan, bayan minti kusan ashirin ta dago kanta ta jinginar kusa da shi, daga haka bacci yyi gaba da ita a yanda take, A hankali ya bude idanuwansa yana bin parlorn da kallo, lkci daya idonsa ya sauka kanta, ya mike xaune da sauri yana kallonta, kallon agogo yayi yaga biyu har yyi, fuskarsa ya kai dai dai nata, cikin bacci taji hannu a forehead dinta, ta bude ido da sauri, a hankali ya manna mata lips dinsa a kumatunta, a tsorace ta ja baya xata mike yyi saurin riketa, 6ata fuska tayi hade da buge hannunsa tace "Meye haka" sakkowa kasa yyi yace "Me kike yi a nan?" Sakin baki tayi tana kallonsa, can ta turasa xata mike ya ki saketa, hawaye ya cika idonta tayi da ta sanin kulasa ma da tayi, ya jawota jikinsa yana murmushi a hankali yace "Thanks for ur care Khadija, Neva knew you where this sweet...." Ta kara hade rai tace "Sake ni malam" ba musu ya saketa, ta mike ta nufi kofa, yace "Uhn.. it's pass 2 now fah" da sauri ta kalli agogo, dawowa tayi kamar ya fada mata mugun abu ta marairaice tace "Lahh ban sani ba... I don't know it's late...." yace "Wait... But... But it seems u came with food daxu, ina abincin" da kamar baxata ce masa komai ba sai kuma tace "yana Kitchen" yace "I am just hungry" kitchen ta wuce ta kawo masa abincin sai a sannan ta tuna ita ma bata ci abincin ba ai, tashi yyi ya shiga toilet din dakinsa sai da ya wanke bakinsa yyi wanka snn ya fito sanye da jallabiya yana goge gashin kansa da karamin towel, duk ta gaji da jiransa ya fito ya rakata, ya xauna ya bude abincin ya dau cokali ya fara ci, kallonsa take ta yi kafin ta mike ta tafi ta bude fridge ta dauko masa ruwa, sai da ya kusa cinye abincin ya sha ruwa sannan ya kalleta da sauri yace "But daxu kamar ruwan tap kika bani koh" tace "Uhn" xaro ido yyi yace "Subhanallah, but I don't take...." sai kuma yyi shiru, ita dai bata ce komai ba banda hararansa da take, jinginar da kai yyi da kujera ya lumshe ido, mikewa yayi ya shiga bathroom din parlor ya fito da alwala, a hankali tace "Ka raka ni pls dare yyi sosai" kallonta yyi kafin yace "Ohk as you wish tunda cinye ki xan yi a nan" daga haka ya nufi kofa tana biye da shi a baya, yana bude kofa ta matsa kusa da shi da sauri, ya fita tana biye da shi a baya suka shiga apartment dinta ya rufe kofar, ta sauke ajiyar xuciya tana bin parlon da kallo yace "Toh tafi ki kwanta" daki ta nufa yyi saurin cewa "Waittt... Xo ki kulle kofar tukun" dawowa tayi tana kallonsa ya buda ido yace "Sai da safe, I appreciate ur care" bata ce komai ba xai fita tace "You have.... A call" ya juya ya kalle ta, duk sai taji she sounds stupid, yace "Did you pick?" Tayi saurin cewa "Nooo, I just remembered now, I didn't even check, just heard the phone ringing" ita kanta tasan kame kame kawai take, yayi murmushi yana shafa lallausan gashin kansa. 12... Da asuba tana kitchen ta gama goge goge xata hada breakfast taji muryarsa ta waje yace "Morning" da sauri ta kalli direction din window taga bata hangosa ba, ta leka a hankali taga gym yake, ta bar gun da sauri ta ci gaba da hada ingredients din da xata soya eggs din da xata yi toasting da bread kasancewar bata yi da raw eggs, bayan wasu mintuna tace "How you feeling now?" bai amsa ba shi ma, hakan yasa ta juya ta kalli window direction, dai dai lkcn da ya iso kusa da window din kenan suka hada ido ya karyar da kai yana kallonta daga sama har kasa, juya baya tayi da sauri don rigar bacci ne jikinta, yace "Uhn... You look cute in that..." mamaki ne ya cikata ta kasa juyowa, ya ce "Ki shirya xaman gidan ya isa haka ki tafi makaranta yau koh" daga haka ya bar wajen, ko bai fada mata ba dama tayi niyyar tafiya makarantar yau. Karfe tara ta fito cikin shirin tafiya makaranta, fitowa yyi ya tsaya bakin door dinsa yana kallonta yace "Makarantar xa ki tafi yanxu?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Yeah" yace "Alright you wait for me" daga haka ya koma ciki, k'asa wucewa tayi tana ta tsaye wajen har ya fito rike da makullin motarsa, as usual kananun kaya ne jikinsa, kallo daya tayi ma wandonsa ta dauke kai a ranta tace aiki, yace "to mu tafi" parking space ya nufa ta bi bayansa, sai da ta jira yyi warming motar sannan ta bude ta shiga. Haka kawai gabanta ke faduwa ta rasa dalili, idonsa na kan titi yana driving yace "Do you have problem with anybody here?" Ta kallesa da sauri, shi ma ya kalleta, mayar da dubansa yyi kan titi, tana girgixa kai tace "I don't think it's any of ur concern" shiru ya d'an yi kafin yace "Ohk then" bai sake ce mata komai ba har ya isa makaranta, bata yarda sun hada ido ba ta bude motar ta fita tace "Thanks" daga haka tayi wucewarta. Tafe suke da course mates dinta bayan sun fito lectures din karfe goma da suka shiga, cafeteria suka nufa ita kuma tace masu xata je library karatu, bayan sun rabu bata je library din ba, kawai she want to be alone ne dama, guri me shiru ta samu ta xauna ta tsura flower dake wajen ido, ta kusa minti talatin a wajen kamar ance ta dago suka yi ido hudu da khaleel dake xaune d'an nesa da ita da wata baturiya dake karatu ita ma, mikewa yyi bayan sun hada ido yana kallon baturiyar yace "Stephanie c yah later" mikewa khadijah tayi ta riga sa barin wajen. Da safe misalin karfe takwas ta fito apartment dinta, yau dai kam ta makara sosai, tsaye ta gansa parking space waya kare kunnensa, suna hada ido ya dauke kai, ita ma bata sake kallonsa ba har ta fita daga gidan a xuciyarta tace "Can ta matse maka" Ita kadai ce xaune Cafeteria bayan sun gama lectures din ranan, Vanessa tuni ta bi saurayinta suka tafi tun bayan da suka gama cin abinci, ita kanta ta rasa me yasa ta ki barin gun har lkcn gashi tana son wucewa, chatting take da kawarta Salima dake Nigeria a WhatsApp kanta a duke, kamar ance ta daga kai tayi still ganin wa enda suka shigo Cafeteria din, a hankali ta saki wayar hannunta ya xame ya fada kan cinyarta, da sauri ta kauda kai xuciyarta na mugun bugawa, table dake gefen nata ya xauna kan kujerar shi da Baturen da suka shigo wajen tare, cikin sanyin muryarsa yake cewa "I don't have intentions of coming here frank, let be fast" baturen yace "Yeah, they will be here soon..." baturiyar dake tsaye kansu ta mika masu takardar list din abinci dake hannunta, muryarsa ya kuma dakan codon kunnenta da accent din turawa yace "Number 6 content for my frnd, just table water for me....." Kamar ana tilasta sa yyi maganan, a hankali khadijah ta mike kamar an xare mata abu a ciki, tana boye gefen fuskarta da mayafin kanta ta nufi kofar fita sum sum tana hade hanya, satan kallonsa tayi suka yi ido hudu don bin ta da kallo yyi, lkci daya ya mike ya xaro ido yana kallonta, tana ganin haka ta kwasa a guje, bin ta yyi da sauri yana cewa "Imannn..... Imannn plss wait, Iman....." hankalinta bai gama tashi ba sai da taga bin ta yake tsakaninsa da Allah gashi ya kusa kamo ta, ta jefar da takalman kafarta da jaka ta fashe da kuka sosai, gudu take kamar her life depends on it, tana yi tana waiwayowa a tsorace, Gani tayi wasu wanda da alaman Africans ne sun rikesa suna tuhumarsa me yasa yake bin ta, hakan ya kara mata kwarin gwiwan gudun, taxi ta samu ta shiga tana waige waige muryarta na rawa tace "Bridge street" tuni mai cab din ya ja suka dau hanya, lumshe ido tayi hawaye masu xafi na sakko mata, tana son fashewa da kuka ko xata ji dadi amma tayi controlling kanta ganin inda take, number gidan ta gaya masa bayan sun kai yyi parking ta bude motar ta fita, tunawa tayi bbu kudin da xata basa, tana kallonsa a sanyaye tace bari ta shiga ta dauko masa kudi, a hankali take tafiya compound din tana goge hawayen dake sauko mata, dai dai fitowar Khaleel part dinsa rike da makullin mota da wasu takardu, tsayawa yyi yana kallonta daga sama har kasa mamaki dauke fuskarsa, hade rai tayi sosai ta turo baki ta dauke kai ta kuma ki motsi daga inda take, taku daya biyu ya iso gabanta tayi saurin barin gun, fixgota yyi ta fashe da matsanancin kukan dake cin ta tun daxu, da mamaki yace "What's wrong with you, me ya faru? where are you coming from?" Kin cewa komai tayi sai kukan da take yi sosai, damuwa ne sosai fuskarsa yace "Talk to me plss, me ya same ki?" Ta hadiye kukan da kyar tana share hawayen idonta cikin rawar murya tace "Ban ba mai Cab kudi ba...." Kallon gate yyi, can ya sake ta ya fita, Durkushewa gun tayi ta dinga rera kuka xuciyarta na mata xafi, a haka Khaleel ya dawo ya sameta, ya hade rai yace "malama tambayar ki nake where r u coming from" mikewa tayi tana share hawayen idonta har lkcn bata daina kukan da take ba xata bar wajen ya rikota yana mata wani kallo a d'an tsawace yace "Me aka maki nace, where r u coming from?" Ganin ba magana xata yi ba yana rike da hannunta ya wuce part dinsa da ita, xaunar da ita yyi kan kujera a parlor ya duka gabanta yana kallonta cikin sanyin murya yace "Now tell me what happen" cike da karfin hali tace "Nothing" ido ya xuba mata bai sake cewa komai ba, can ya mike ya koma bayan kujera ya rungume hannu ya tsaya yana kallonta, ta gama cin kukanta ta jinginar da kanta da kujera, tafi minti sha biyar a haka bbu kalan tunanin da bata yi ba har bacci ya dauketa. Shi kam yana tsaye har lkcn bayan kujera yana kallonta yana mamakin irin taurin kanta, sai da ya ga bacci ya dauketa sannan ya xagayo ya iso gabanta ya durkusa kusa da ita, shi dai ya san tausayinta kawai yake ji har ransa, though he don't know her that much but he knows she's pained, coz she looks so, lumshe ido yyi ya bude yana kallonta, Khadijah is just the definition of cool Beauty, tall.... fair.... Slim with a perfect shape, Best of all she have got d most sexiest lips and eyes, her nose..... Kauda tunanin yyi, a xuciyar sa yace not as beautiful as Jawahir, a hankali ya mike ya dafata da xumar yace mata ta kwanta, a firgice ta farka tace "Aliyuuu...." Ja baya yyi yana kallonta. Da kyar ta karashe bude idonta da yyi mata nauyi ta daga kai tana kallon sa, xamowa kasa tayi a hankali, ya mike ya rungume hannayensa yana kallonta a ransa yana nanata sunan da ta kira, tashi tayi ta runtse ido ta juya xata fita parlorn, murya can kasa yace "Malama" sake juyowa tayi, yace "Where are u coming from" bata iya ta kallesa ba cikin sanyin murya tace "School" yace "Me ya same ki a can?" Tace "Am not feeling fine" bai sake cewa komai ba ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita. Magungunan ta ta dauka ta sha lkci daya kuma bacci ya dauketa, bata farka ba sai da asuba shi ma ta dalilin yunwa, ganin lkcn sllh bai karasa ba ta shiga kitchen don neman abinda xata ci, motsi ta dinga ji a waje ta leka a hankali, gym ta gansa yana yi jikinsa sanye da 3qtr kadai, suka yi ido hudu tayi saurin barin gun, parlor ta koma ta dauko Hijab ta sa sannan ta dawo kitchen din, har ta gama abinda xata yi bata sake leka waje ba, ta koma parlor da Indomien ta, tun da tayi wanka bayan tayi sllh gabanta ke ta faduwan xuwa schl gashi tana da test, hawaye ta dinga yi duk xuciyarta tayi rauni, gaba daya xaman kasar ya isheta taji gida take son komawa, to karatun fa, shekara bai kai biyu ya rage mata ba, danna bell aka yita mike a d'an tsorace, don ynxu kam gaba daya a tsoracen take, hijab ta saka ta fito, a hankali tace "Yes?" Yace "How you" bude kofar tayi ta gaishesa, yace "Baxa ki schl din bane yau?" Kamar xata yi kukatace "Ban sani ba" kallonta kawai yake bai ce komai ba, bayan yan sakwanni yace "Toh ki shirya, I am waiting for you" daga hka ya juya ta rufe kofar. Har dept ya ajiye ta, kowa ya ganta a lkcn yasan a tsorace take, yace "Yaushe xa ki gama lectures din?" Tace "Quiz ne" yace "Shi kadai?" Kai ta gyada masa, yace "ohk am around I will call ltr in ji ko kun gama" buda masa hannu tayi tace "Jakar ya fadi jiya ai" Kallonta ya tsaya yi, can ya ciro waya aljihunsa ya mika mata yace "I will call" ta karba tana gyada masa kai, daga hakata fita motar, shi ma ya fito yace "I think I will leave the car here" bin satayi da ido har ya wuce kafin ita ma ta bar wajen da sauri. *Haske Writers Association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 13.... Bata yarda ta fito dept ba tun bayan gama test dinsu, duk gaba daya a tsorace take, gani take kamar at anytime xata iya ganin Aliyu a gabanta, karfe sha daya da qtr wayar khaleel dake Jakarta ta fara vibrate, fiddowa tayi taga Emoji biyu na love gaban screen din, ta yi jim don bata san ko shi bane, har ya kusa katsewa sannan ta daga ta kai kunne tayi shiru, muryar mace taji tace "Hello Baby...." hakan yasa ta katse wayar, sake bugowa tayi bata daga ba har ya katse. Tana ta xaune da wani course mate dinta dake second degree dinsa d'an Nigeria but residing in Malaysia yana ta mata hira ita dai sai dai tayi murmushi tana saurarensa, dai dai nn wayar hannunta ya sake vibrate ta daga tana kallon number, sai kuma tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren taji yace "Are you done?" Tace "Umm" yace "Aiitt am waiting..... Near the car" daga haka ya katse wayar, ta mike tana kallon course mate dinta tace "Wanda xai daukeni yana jirana, xan tafi" ya mike shi ma yace "To bari in raka ki" da kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "Ohk" tana gaba yana biye da ita har suka iso gun motar, Tun daga nesa Khaleel ke kallonsu, sai da ya ga sun iso ya dauke kai, Usman yace "Assalamu alaikum" sake juyowa khaleel yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma ya bude motar ya basa hannu suka gaisa, Khadijah ta tabe baki ta xaga daya side din motar tana kallon Usman tace "Thanks.... sai gobe in sha Allah" Usman yace "Aiiit Allah kai mu lfya" Sallama yyi da khaleel sannan ya wuce, Khaleel ya tada motar suka bar wajen, har suka hau kan titi bai ce mata ba, ita ma bata ce masa ba, wayarsa dake hannunta ya fara vibrate kuma, kallon screen din tayi taga number daxu ce ta mika masa, sai da ya kalli screen shi ma kafin yyi parking gefen titin, ya jira wayar ya katse sannan ya kira yace "How you...." Satan kallonsa khadijah tayi ta dauke kai tana kallon waje, bayan yan sakwanni yace "Like serious, alryt sorry for that wayar baya gu na ne" d'an murmushi yyi yana shafa lallausan bak'in gashin kansa dake sheki yace "I left the phone with a frnd, and I guess....bata san ke bace da baxata dauka ba, yanxu dai I will cal back in 10 mins time, I am on the road" daga haka ya katse wayar yace "Why did..... You pick her call?" Kamar me counting words din yyi maganan ya juyo yana kallonta, bata kallesa ba bare ta basa amsa, hakan yasa ya ci gaba da driving dinsa, sai da suka kusa gida yace "Who was that guy?" Ta juya tana kallon sa da kyau tace "And why are you asking?" Tabe baki yyi bai ce komai ba, sai da yyi parking ta hade rai tace "Da Kasan da xata kiraka ka bani wayar" daga haka ta juya xata bude motar ta fita yasa lock, juyawa tayi tana kallon sa, yace "Ki dai bi a hankali da guys din makaranta da kike kulawa, and you even let him accompany you to where I am, toh ni meye hadina da shi?" Mamaki ne ya cika ta ta saki baki tana kallon sa, a mugun fusace tace "Ina ruwanka ma idan na bi samarin makaranta, I guess it shud be none of ur concern, let me outta here immediately.... Ka bude min mota in fita" Tun da ta fara ya kwantar da kujeran motar ya lumshe ido yana saurarenta, jin tayi shiru ya dago kujeran ya xauna yana kallonta yace "Kin gama?" Ta dago tana kallon sa ranta na suya, bude lock din motar yyi yace "Ok then, kindly move out and close d car door behind you" bude motar tayi kamar xata tashi sama ta nufi apartment dinta ba tare da ta kulle masa motar ba. Wayan da tayi ta yi da su Shuraim yasa ta mance duk damuwar dake tare da ita, ganin lkcn kwanciyarsu yyi tayi sallama da su ta kwanta don tayi shirin bacci tun bayan da tayi sllhn magrib, lkci daya baccin ya dauke ta. Tun da ta tashi take ta tunanin yanda xata tafi schl don kusan tests suke, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka tace "Do I ever have to meet with him in my life again??" Ganin lkci na ta wucewa ta mike a sanyaye ta dau jakarta da mayafi ta fita parlor, kallo daya tayi ma motar khaleel dake parking space ta hade rai ta dauke kai ta rufe apartment dinta, a hankali take tafiya har ta isa titi, cab ta shiga suna isa makarantar ta biyasa kudinsa ta fito tana kalle kalle kamar munafuka, tafiya take da sauri ta shiga schl don a waje ta sauka daga cab din, kawai mota taga ya tsaya gefenta bata ankara ba sai ganinta tayi cikin motar ta fasa ihu a tsorace amma tuni aka ja motar. Khadijah ta bude idonta a hankali ta na bin parlorn da take ciki da kallo, ta mike da sauri xuciyarta na bugawa tana kiran Allah a xuciyarta, kamar ance ta juya bayanta ta ga mutum tsaye yana kallonta, xuciyarta tayi mugun bugawa tayi saurin dauke kanta, karasowa yyi parlorn cikin sanyin murya yace "Imannn" bata san lkcn da ta xube wajen ba ta fashe da wani matsanancin kukan takaici, durkusawa yyi gabanta a hankali yace "Imann... I...." Mikewa take son yi ya rikota fixge hannunta tayi da karfi, yyi still yana kallonta ko kiftawa bbu, tayi saurin dauke kai tana kuka sosai ta hade kai da gwiwa, mikewa yyi ya dago ta yyi hanyar wata kofa da ita, tashin hankalin da ba a sa masa rana, ihu ta sakar masa tana turasa amma da yake karfinsu ba daya ba sae da ya shigar da ita kofar ya rufe, cikin rawar murya take cewa "Me ka dawo yi rayuwata kuma Aliyu, I am no longer under you or ur family, let me plsss am begging you in the name of Allah, ka rabu da ni......" Jinginar da ita yyi da bango yana kallonta da idanuwansa da suka kada yace "Kinsan shekarun da na dauka ina neman ki xa ki ce in rabu da ke" a tsawace ya kare maganan, cakumosa tayi tace "Kana nemana?? in maka me Aliyu? Neman me kake min, ka rufa min asiri ka kyaleni in tafi don Allah" yyi wani murmushi yace "In kyale ki ki tafi? Haka kawai in kyale ki ki tafi?" Turasa tayi iya karfinta amma ko gezau ta kuma fashewa da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi da suka, cikin kuka sosai tace "Aliyu ba don ni ba kayi hakuri ka kyaleni" yana kallonta a hankali yace "Ki yafe min Iman...." Tsayar da kukan da take tayi tana murmushin takaici tace "In yafe maka? Aliyu dama kayi min wani laifi ne da xan yafe maka, gaskiya ban san shi ba, idan ma akwai to shari'armu sae a lahira" finciko ta yyi da idanuwansa da suka yi mugun kadawa yace "A lahira?" Kasa amsawa tayi ganin ynda ya sauya kamannin fuska, jefar da ita yyi kan gado ya karaso yana mata wani kallo yace "Wani Shari'ar ce sai mun je lahira xa ayi ta? Ki fadi me nayi maki?" Ta dinga ja baya tana ganin dishi dishi, a hankali ta kira sunansa tana girgixa kai daga nan kuma bata sake Sanin abinda ya faru ba ta dai bude ido a hankali ta dalilin axaban da xuciyarta ke mata, Kwance ta ga ta kan gado ita kadai dakin, da kyar ta mike xaune ta dafe xuciyarta, lkci daya ta sauka gadon ta nufi kofarta bude taji a rufe da key, sulalewa kasa tayi ta dafe kirjinta tana kiran Allah a xuciyarta, bude kofar taji kamar ana yi ta tashi tsaye da sauri ta koma bayan kofar ta tsaya aka bude ya shigo cikin dakin yana kalle kalle, da gudu ta fice dakin ya juya da sauri, bin bayanta yyi yana kiranta, ganin bbu inda xata tsira parlorn ta nufi dinning table ta dau wukar da ta gani kai ta juyo tana kallon sa hawaye na sakko mata, girgixa mata kai yyi yace "Wait Iman...." cikin sarkewar murya tace "I swear to Allah who made me kana isowa kusa da ni xan kashe kaina Aliyu" still yyi yana kallonta ya kasa motsi wajen, ta nufi kofa tana rike da wukar hawaye na xubo mata sosai, cikin sanyin murya yace "Noo khadija karki tafi don Allah" da baya da baya take tafiya har ta isa kofa ta fice, ikon Allah kadai ya kai ta gida duk da daren da yyi, ganin halin da take ciki mai cab din ma bai karbi kudi bata shiga gida, nan bakin kofa ta durkusa don bbu jakar makullin, ta kai minti biyar a haka kafin tayi karfin halin buga kofar khaleel, va a dau lkci ba ya bude, ja baya yyi yana kallonta da mamaki, can ya durkusa yace "Are.... are you okay?" Girgixa masa kai tayi numfashinta na sama, ya dago ta yana kallonta yace "Subhanallah" ta fashe da matsanancin kuka ta rikosa tana girgixa kai tana nuna masa kirjinta cikin rawar murya tace "It's hurting....." mikewa yyi da sauri ya shiga ciki ya dauko makullin mota ya dawo, cikin ikon Allah khaleel ya isa wani babban hospital don duk ta rikitasa driving kawai yake, tun da ta rufe ido bayan da suka shiga asibitin bata sake budewa ba sai washegari da safe, yana zaune gefenta ya jinginar da Kansa jikin kujerar da yake xaune, su kadai ne cikin ward din,ta mike xaune da kyar taa kallon ruwan hannunta, jin xuciyarta tayi fayau, sai dai har lkcn tana jin kamar numfashinta na seizing,ta kalli oxygen dake gefenta a dakin, ta mayar da kallonta ga agogo taga takwas ya kusa, cire drip din tayi cike da karfin hali ta sauka kan gadon, kofar da take tunanin na bayi ne ta shiga. Bata dade ba ta fito da alwala, sai kuma taga bbu hijab bare darduma, ta isa kusa da khaleel cikin rashin kuxari tana kallon sa, bacci yake a yanda yake, lkci daya taji tausayinsa sosai wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, durkusawa tayi a hankali ta dafa kujeran cikin sanyin murya tace "Doctor..." Lkci daya ya bude ido yana gyara xamansa, mikewa yyi da sauri ya durkusa gabanta yana kallonta damuwa yace "How you feeling now khadijah?" Murya can kasa tace "Naji sauki, you need rest, ka kwanta saman gado am nt sleepy" hannunta ya kamo yana kallonta xai yi magana daidai nn aka bude kofa wata nurse baturiya ta shigo ward din. Mikewa yyi nurse din ta karaso tana tambayar me yasa ta cire drip din, khadijah ta mike race "I used the restroom" mayar mata da drip din tayi bayanta koma kan gadon, khaleel ya bi ta tare suka fita ward din, tagumi khadijah tayi tana kokarin ganin hawaye bai xubo mata ba, ba a dau lkci ba khaleel ya dawo da mug a rufe ya xauna gefen gadon ya mika mata yace "Gashi ki sha xa a maki allura...." Ta sa hannu ta karba ya bude mata, a hnkli ta kai baki tana sha, ya kafa mata ido, bayan ta sha ta sauke cup din ta karbi murfin ta rufe, yace "Ina ke maki ciwo ynxu?" Ta girgixa masa kai tace "Bbu ko ina, just my chest" yace "Xai daina in sha Allah" nurse din ta dawo rike da tray me dauke da allura da magani, tana kallonta ta gama hadawa ta karaso, mikewa yyi ya fita dakin ya rufo kofar. Tana mta alluran ta bata maganin sannan ta fita bayan ta gwada mata yanda xa ta sha, bayan fitar nurse din khaleel ya shigo rike da table water, ta sha maganin, a hankali tace "I want to go home plss" yace "No sae kin kara samun sauki," ta girgixa masa kai tace "Am feeling better yanxu, bacci nake son inyi" yace "Toh ae sai sun yi discharging dinki koh" bata kuma cewa komai ba ya gyara mata pillow yana kallonta, ba musuta koma ta kwanta a hankali. Sai kusan karfe daya aka yi discharging dinsu ya biya bill din suka bar clinic din, sai da suka yi nisa cikin sanyin murya tace "How much is d bill" bai ce komi ba kuma bai kalleta ba, yayi parking wani eatry, da ido ta bi sa har ya shiga, rike da Leda biyu ya fito ya bude motar ya shiga suka bar wajen. Parking yyi ya juya yana kallonta, ta jinginar da kai da kujeran motar idonta lumshe, a hankali ya dauke kansa, can ya juyo murya can kasa yace "Khadijah" lkci daya ta bude ido, yace "We are home" kalle kalle ta fara yi, ya bude motar ya fita bayan ya dau takeaways din da yyi, ta fito ta rufe motar tana jin jiri na kwasarta, bata yarda ta bar jikin motar ba, kamar yasani kuwa ya xagayo yana kallonta, hannunsa ya mika mata, ta sauke idanuwanta ta mika masa nata hannun, yana rike da ita har suka iso apartment dinta ya kalleta yace "Key?" Shiru tayi kafin tace "A jakata yake" yace "Ina jakar?" Bata iya tace komai ba, ya bude apartment dinsa. *Haske writers association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By khaleesat Haiydar_📚✍🏻 14..... Tsayawa yyi yana kallonta ta shiga parlorn sannan shima ya shiga, kan kujera ta nufa ta xauna, ya karaso bayan ya kulle kofar ya ajiye ledan hannunsa kan center table, sannan ya shiga daki, jinginar da kai tayi da kujera tayi xurfi cikin tunanin da take taji yana kiranta, dagowa tayi da sauri ta gansa tsaye gefenta ya rungume hannunsa, a hankali yace "Na hada maki bathing water a bathroom" sunkuyar da kai tayi, ta mike yana gaba ta bi bayansa xuwa dakin, towel ya dauko ya mika mata, ta karba murya can kasa tace "Thank you" ya juya ya fita dakin, da mouth wash na Listerine ta wanke bakinta, tayi wanka da shower gel, sai kusan bayan minti talatin ta fito daga bayin, bayan tayi ta tsayuwa bakin kofar bathroom din tana tunanin fitowa da towel, bbu kowa dakin sai Hijab dinta da ta gani kan gado, mamaki ya kama ta tayi ta kallon Hijab din, karasawa tayi ta dauka ta koma bathroom din, wanke kayan da ta cire tayi sannan ta sa hijab din ta fito da kayan da ta wanke a bucket, xaune ta gansa a parlor yana rike da remote, kallo daya yyi mata ya dauke kai har ta shigo parlorn, yace "Why did u wash, u still under medication" bata ce komi ba, yace "Na bude maki kofar...." Tace "Da gaske?" Yace "Ehh, ki tafi ki shirya" murya can kasa tace "Nagode" sannan ta wuce tana rike da Hijab din. Sai da tayi sllh snn ta wanke masa towel din a bayinta ta fito ta shirya ta tafi shanya kayan da ta wanke da towel din nasa, kwanciya tayi daki bayan ta gama lkci daya bacci ya dauketa. A hankali ta bude ido jin kamar ana tashinta, ta mike da sauri tana kallon sa, yace "I've been knocking and calling since, but.... Taso mu je ki ci abinci" ta girgixa kai tace "Am not hungry bacci nake ji" yace "Noo, baki ci komai ba yau, kuma kinga xa ki sha magani, you have to take something...." Daga haka ya mike yana kallonta, sauka tayi daga kan gadon ta bi sa suka fita parlor, xuba mata abincin yyi ya mika mata ta karba ta fara ci, wayarsa yake ta dannawa har ta ajiye abincin tana yamutsa fuska tace "Na koshi fa" ya kalli abincin sannan ya dau ledan maganin ya ballar mata drugs din ya taso ya mika mata da goran ruwa ta karba, ta sha maganin tana kallon sa yace "Allah ya sauwake" bata iya ta ce komai ba, yace "To ki je ki kwanta, sleep without thought plss" ta gyada masa kai sannan ta tashi ta shiga daki. Bata tashi ba sai kusan biyu da rabi na rana, ta shiga bayi tayi alwala ta fito tayi sllh, tana idarwa ta sake kwanciya. Knocking kofar dakin taji ana yi cikin bacci, ta mike xaune ta sa hijab sannan ta bude kofar, yana tsaye bakin kofar, yace "Have u prayed zuhur?" Ta gyada masa kai, yace "Abinci fa" tace "I am not hungry" ya girgixa kai yace "You are, fito ga abinci na kawo maki sai ki sha magani" daga haka ya juya ya bar wajen, bin sa tayi, yana daga tsaye ya nuna mata abincin kan table, ta karasa ta dauka, tuwon shinkafa ne da miyar vegetable ta gani da ta bude, ta daga kai tana kallon sa, ya daga kafada yace "Yea, a frnd of mine ce ta yi..." Tace "Kai baxa ka ci ba?" Ya girgixa kai da sauri yace "Noo I don't take heavy foods, I don't take swallow" murmushi tayi ta dauke kai, ya shafa kai yace "Sbda ke na karbo" tace "Toh ngd" yace "No thanks" plate taje ta dauko a kitchen ta debi abincin, shi dai har lkcn yana tsaye, ta kallesa a hankali tace "Baxa ka xauna ba" shiru ya d'an yi, sai kuma ya karaso ya xauna kan kujerar dake kallon nata yace "So u care" bata ce komai ba ita dai, a hankali ta dinga cin tuwon, duk lkcn da ta daga kai sai sun hada ido, daga karshe bata sake yrda ta dago ba har ta gama cin tuwon ta dau magani ta sha, sai a snn ta sake kallon sa taga kallonta yake still, hade rai tayi ta dauke kai, yyi murmushi yace "Who is Aliyu?" Kallon sa tayi da sauri, kamar yanda shi ma yake kallonta har lkcn, can ta tsuke fuska tace "Ban gane ba" bai sake cewa komai, bayan kusan minti biyar yace "don't pretend... Is he ur Husband?" xuciyarta na bugawa tace "Nooo" Yana mata wani kallo yace "Ur Ex Husband?" Hade rai tayi sosai cike da masifa tace "Noooo" sai kuma ta mike tana masa wani kallo tace "I know nothing about what u are saying" ya d'an yi murmushi yace "You passed out yesterday at the hospital with the name Aliyu in ur Mouth" shiru tayi tana kallon sa a sanyaye, lkci daya hawaye ya cika idonta, can ta juya ta bar masa parlorn da sauri, kiran ta ya dinga yi har ta shige daki ta xauna kasa ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka, bin ta yyi cikin dakin, ya karaso gabanta ya durkusa a hankali yace "Ohk, I am very sorry Khadijah, may be I shouldn't have say anything about that, but dole xan yi magana, Billah da xan ga Aliyun nan... Sai na sa ya d'an dani abin da kike ji, I guess he broke ur heart kuma yake kokarin dawowa rayuwar ki yanxu saboda may be selfish reason dinsa, he will regret that duk ranan da muka hadu face to face.... I vow!" ita dai bata ce masa komai ba sai kukan da take, duk jikinta yyi mugun sanyi, mikewa yyi ya fita dakin. Har dare khaleel bai shigo ba, tun da tayi magrib take hade abubuwan da tasan xa ta kai gida, don bata jin xata kara kwana a kasar, gaba daya xaman kasar da karatun ya fice mata a kai, hawaye kawai take duk jikinta a sanyaye, Sudais has always wanted her to be a doctor, ta xo ta samu kan ta a bangaren pharmacy, wanda a yanxu bata jin ma xata ci gaba, domin kuwa ta hakura da karatun, may be some other time she wil be d doctor Sudais wants her to be, to ko ta xama likitan ma what is that adding to her life, wanda take son yi dominsa ya tafi ya bar ta a lokacin ta fi bukatarsa a rayuwarta, baxa ta ce ya gujeta ba, but what's the difference? Kusan duk daya.... Ta share hawayen idonta ta fito parlor a sanyaye, tsaye tayi tana kallon Khaleel da shigowarsa knn a hankali ta sauke idonta kasa wasu sabbin hawayen na xubo mata, ya karaso kusa da ita yace "Ina xa ki?" Ta juya masa baya tana kkrin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba, a hankali yace "Khadijah" cikin rawar murya tace "Am going back to Nigeria" ya juyo da ita ya xaunar gefen kujera yana kallonta, ya bar ta tayi kukan me isarta, ta hade kai da gwiwa tana sauke ajiyar xuciya, cikin sanyin murya yace "Tell me about you Khadijah" Ta dago tan kallon sa hawaye na sakko mata, sai dai kuma tayi ma kanta alkawarin bayan Sudais bbu wanda xai ji ita wacece, muryarsa ya dawo da ita tunanin da take, yace "I still don't deserve to know you koh?" Ta sunkuyar da kanta tana goge hawayen dake sakko mata, a ranta kuwa tunani take anya xata iya fadi ma Khaleel ita wacece kuwa, a hankali ta xamo kasa daga xaunen da take kan kujera, ya sakko k'asan shima yana kallon kwayar idanuwanta da suka rine, kife kanta tayi da kujera cikin sanyin murya tace "Ka daina kallona da idon ka" ya d'an yi jim sai kuma yace "Why?" A hankli tace "Bana son irin su" murmushi yayi yace "Da gaske" taki cewa komai, a hankali yace "Toh na daina kallon ki" dagowa tayi suka kara hada ido tayi saurin mayar da kanta jikin kujera, dariya ta basa sai dai bai yi ba ya shafa kansa yana murmushi, murya can kasa yace "Am all ears Khadijah" ta dago kanta tana wasa da dogayen yatsun ta tace "Ohk....." Wayarsa ya da ya fara ring ya ciro aljihunsa, ta kalli screen din kamar yanda shi ma yake kallo, Jawaheer ne jikin screen din... Yyi silencing wayar ya ajiye a hankali, Tsura ma lallausan carpet din da suke xaune kai ido tayi ko kiftawa babu, cikin sanyayyan muryarta tace "I am an only child... I was raised from a very rich home, I was raised by only my Dad don kuwa ina da shekara uku kachal a duniya mahaifiyata ta rasu...." D'an murmushi tayi wasu sabbin hawaye na taruwa idonta tana kallon Khaleel da ya kafeta da nasa idon.... Who is Khadijah? #Shekaru 6 baya #6 years earlier #Flash back.... *Haske Writers Association*💡 Uhm don't know how to announce this, Reason being that... the love, the prayer, the encouragement is 👍🏻 but sai dai ina da na gaba da ni and i heed to their advice always, and babu wanda bai son progression, so?? 🤗 I think this all for the free pages of *Noor-Al-Hayat* sorry to those that I took unaware but don't forget I announced needing patronage in my previous book... you think you love the book, you think love Khaleesat Haiydar.... Then gladly patronize her.... If interested... ping Via Facebook inbox or Via WhatsApp 07087865788, they will be groups available, Thank you. ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By khaleesat Haiydar_📚✍🏻 _littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne from this page, kindly patronize ur writer and read happily, duk wanda bai ji dadi ba hakan da nayi yyi hakuri pls_ Shekaru shiddah baya..... A hankali ta karashe shanye shayin dake hannunnta ba tare da ta bi ta kan soyayyen kwan dake gabanta ba ta ajiye cup ta mike tace "Umma to idan Kawu ya tafi da ni baxan sake dawowa ba?" warce ta kira da Umma dake duke tana goge mata takalmanta masu tsada tana xuba su a wani jaka ta juyo da rinannun idonta tana kallon 'yar yarinyar warce da kadan ta haura shekara sha uku tace "Xa ki dawo Khadijah in sha Allah" Khadijah bata sake cewa komai ba tana dai tsaye, tsadaddun ready made ne jikinta da cover shoe mai kyau sai kyalli yake, da farin hijab karami, kunnuwanta dauke da dankunnen zinari 'yan kanana, Khadijah tace "Toh Umma me yasa ke baxa mu je da ke ba" Umman bata kalleta ba tace "Nima gidanmu xan je Khadijah" Khadijah ta durkusa kusa da ita a hankali tace "Umma ni bana son gidansu Kawu ki tafi da ni gidanku don Allah" Umman bata ce komai ba har ta gama rufe jakar ta daura kan babban jakar dake dauke da kayan Khadijah, jin Umma bata ce komai ba Khadijah ta dau remote xata kunna TV, Umma ta jefa mata wani kallo tace "Xaki fara ko, ni dai na gaya maki kar kije gidan mutane kina masu irin wannan kallon da kike kamar wawuya, kashe TV din nan yanxun nan" Khadijah ta kashe tvn ta koma ta xauna kan kujera, dai dai shigowar kawunta, kuma wan mahaifinta, har ya karaso parlon idonsa na kan soyayyen kwan da Khadijah ta bari a plate, ya dau plate din ya xauna yace "Tsabar almunbazzaranci dubi abinda aka yi ma lafiyayyen kwai, karshen komai ya xo in sha Allah" ita dai Umma bata ce komai ba ta wuce daki don fiddo nata sauran kayan da ya rage a gidan, Kawu ya dinga cin kwan kamar his life depends on it, har dai ya gama daga karshe ya ajiye ya na kallon Khadijah dake ta kallonsa yace "Toh ki tashi ki fita ga adai daita can ki shiga ki jirani a kofar gida" ta xaro ido tace "Kawu ba da mota xa mu je ba" dakuwa ya mata yace "Tashi ki ban waje" mikewa tayi tayi hanyar kofa tana waigosa, shi kuma ya dau katon jakar ya bi bayanta, Umma ta fito da nata kayan waje ta dau plate da cup ta shiga kitchen ta wanke su ta ajiye, ta kuma sake tabbatar da komai a kashe yake sannan ta bi bayansu, Khadijah na tsaye jikin adai daitan Umma ta jawo ta, a hankali tana kallon eyeballs dinta tace "A duk inda kika tsinci kanki ki xamo mai hakuri kin ji Khadijah, nasan ki da shi, komai kuma aka sa ki kiyi, sannan most important of all banda kallon TV don Allah..." Khadijah tayi murmushi da ya bayyana beauty point dinta tace "Umma I can't do without watching tv fah" Umma ta hade rai tace "So u won't heed to what am saying koh?" A hankali ta sauke idonta tace "Am sorry mum" Umma ta ja kumatunta tana murmushin karfin hali tace "That's my girl" a hankali kuma a sanyaye ta kara da cewa "And always pray for daddy, kullum kika yi sallah ki masa addu'ar Allah ya masa rahama" Khadijah ta gyada kai tace "Toh Umma" Umma ta shigar da ita adai daitan tace "Safe trip dear, I will always pray for you" Khadijah ta gyada mata kai trying hard to control her tears, Tuni Umma ma ta juya ta nufi main road da jakarta ba tare da ta bi kan kawu Jibril dake kokarin maka ma gidan kwado ba, Khadijah ta bi stepmother din ta da kallo hawaye na sakko mata, a haka kawu ya shigo adai daitan, yana mata wani kallo yace "Kukan uwar me kike ma mutane" cikin rawar murya tace "Umma ta" Dungurinta yyi yace "Uwar ki ba Ummar ki ba" Khadijah ta sunkuyar da kai, mai adai daitan ya dau hanyar park, hannu Khadijah ta daga ma stepmum dinta ganin sun wuceta, ita ma ta daga mata tana goge hawayen idonta. Tasha mai adai daitan ya kai su, kawu ya sauke kayan Khadijah ya bai ma mai adai daitan kudi sannan ya biya masu kudin mota xuwa katsina, da kyar ya yarda ya biya seat biyu wai xai dauketa a kafa, sai da yan motar suka sa baki, bayan kusan minti goma motar ta cika suka dau hanyar katsina, tunda Khadijah take bata taba shiga motar haya ba, rabonta kuma da katsinan tun tana da shekara bakwai da suka je tare da Abbanta, kai kana ganinta kasan she is restless, matar da ke kusa da ita tace "Yarinya me ya faru?" Kamar xata yi kuka tace "Amai...." Kawu ya kwalalo ido yace "Me?" Tace "Amai" dungurinta yyi yace "Ke yarinya ce xaki ce ma mutane kina jin Amai cikin mota" matar tace "Haba bawan Allah, sai yara ke Amai idan suna tafiya" dakatar da ita yyi yace "Ke... Learn to mind ur business while in public, 'yar ki ko tawa" matar tace "Aa ba yar ka bace wllh, don da yar ka ce baxa ka yi mata abinda kayi mata ba yanxu" Bala'i kawu ya fara kamar mace a motar, ana haka Khadijah ta toshe bakinta jin aman xai taho mata, matar bata bi ta kan kawu ba ta sa driver ya tsaya, ta sauke Khadijah, nan kuwa ta dinga kwara Amai, matar na tsaye kanta, shi ko kawu yana cikin mota sai fada yake yana kumfar baki, kowa ya xuba masa na mujiya bbu wanda yace ci kanka, wani mutumi a motar ya ba matar ruwa ta mika ma Khadijah, ta wanke bakinta da fuska sannan suka dawo cikin motar ana mata sannu, wata mata ta bada leda ta rike a hannu idan ta ji wani aman, har suka isa katsina kawu bai yi shiru ba, Khadijah tayi Amai yyi sau biyar, dunguri kam ta sha sa gun kawu duk da ba a kusa da shi take ba, bbu wanda yace masa ci kanka cikin passenger din motar, a dai dai ta ya samu da xai kai su har gidansa.. Karfe biyu da kusan rabi suka shigo gidan, bungalow ce mai kyau, wanda Abban Khadijah Alhaji Muhd ya mallaka ma yayan nasa a lkcn yana da rai, sai dai ba lallai wanda ke nan lkcn da aka ba Kawu gidan ya yarda Cewar gidan ne a ynxu ba, don yyi mugun tsufa ga dattin bala'i, kuma dudu gidan bai yi shekara shidda ba, Duk matan Alhajin guda biyu suka fito jin shigowar mai gidan nasu suna masa sannu da xuwa, kawu dake kokarin bude jakar kayan Khadijah bayan ya xauna parlor yace "Toh ga ta nan, gida kuma ni da Isiyaka mun rufe an sa a kasuwa, ga ta nan ban san gun warce xata xauna ba cikin ku" Matarsa ta fari Hajiya Salaha tace "Toh ni dai yara sun yi yawa a gu na, ban san dai ko Maimuna ba" warce ta kira da Maimuna tace "Ni kuma sai nace maki yaran basu min yawa ba koh?" Kawu yace "A'a bbu xancen tada jijiyoyin wuya taje dakin ki Maimuna kayanta kuma a kai dakin salaha, shkkn" daga haka ya dinga fiddo da tsadaddun kayan Khadijah, daga shi har matansa bbu mai cewa komai sai kallon ikon Allah suke, Kusan set takwas ya cire ya ajiye gefe yace "Wannan siyar da su xa ayi in sha Allah, domin kuwa baxata xo nan ta dinga saye sayen kaya ba kamar wata er gote ta janyo ayi tunanin shi gareni..." Takalman ma duk ya ware kusan biyar, golds dinta na dankunni da awarwaro kuwa dama suna aljihunsa, Khadijah dake ta tsaye jikin kujera tana waiga ko ina na parlorn da idonta tana neman remote ta kunna TV amma bata gani ba, ganin kawu xai xuba duk kayan da ya ware a wani jaka ta karaso da sauri tace "Kawu ina son wannan takalmin, da shi nake xuwa makaranta" Dungurinta yyi da karfi ya kunduma mata ashar, ta koma baya a tsorace yace "Ki shiga hankalinki da ni fa xan xane ki wllh" xata mike ya fixgota ya cire dankunnin kunnenta, Hajiya Maimuna tace "Toh idan ba fitsara ba ita har xata gaya maka abinda xaka yi" mikewa yyi ya dau jakar yace "Ku shiga da sauran, ni na tafi kasuwa kan yamma yyi" daga haka ya nufi kofa" bayan fitarsa Hajiya salaha ta sake fiddo kayayyakin ta dau kusan kala biyu da panties da kayan bacci, Hajiya Maimuna ma ta jawo jakar ta dau huluna da kaya kala daya da dogon rigar kanti da safunayen hannu da kafa, Hajiya salaha xata sake jawo jakar Hajiya Maimuna ta rike tace "Tsiyace jakar xa ki yi" Hajiya salaha ta jefa mata wani tace "Ke ai arxiki kike karama jakar, abu baxa ayi sa da hankali ba, ita sai ta sa uwar me?" Hajiya Maimuna ta rufe jakar ta tura tana kallon Khadijah dake ta tsaye tana kallonsu tace "Dauka ki kai dakin can dake kusa da wancan kofar, kin wani tsaya ma mutane kememe" Khadijah ta karaso da sauri ta dau jakar ta bi hanyar da Hajiya Maimuna ta nuna mata, kafin ta fito sun dau takalma kala daddaya ta dau jakar takalmin ma ta kai dakin. Uban wanke wanken dake tule gun pampon da aka tanadar don yin wanke wanken Hajiya salaha ta nuna mata taje tayi, a hankali Khadijah tace "Ina jin yinwa" Hajiya salaha tace "Can baki ci abinci bane kafin ki taho, ki je bakin pampon akwai tukunyar taliyar da ta rage ki ci sannan kiyi wanke wanken" Fita khadijah tayi xuwa gun pampon, ta yi kusan minti daya tana kallon taliyar da kudaje ke bi, ta turo baki ta rungume hannayenta, Dawowa parlon tayi kamar xata yi kuka tace "They are flies perching all over the food, ni baxan iya ci ba" sakin baki suka yi gaba daya suna kallonta, can suka kwashe da dariya Hajiya Maimuna tace "Toh baturiyaa jikar mongo park...." Hajiya salaha tace "Kin wuce kin ba mutane waje ko sai na mike.. Ina ruwan ki da k'uda idan ba rainin wayo ba, ki bar abincin kar ki ci, kuma maxa ki tafi ki wanke kwanukan yanxun nan" juyawa khadijah tayi ta bar wajen, Hajiya Maimuna tace "Idan ba ma tsoron Allah ba har Alhaji xai yarda ya rike er Muhammad, uwar me ya tsinana sa yana raye" Khadijah dake ta turo baki ta dau omon da ta gani da sosan wanke, tsaye tayi ta rasa ta inda xata fara wanke wanken, can dai ta dauko babban bahon da ta gani ta tari ruwa ya kusa cika sannan ta xaxxage d'an omon, muryar wata mata da shigowarta gidan kenan taji tana cewa "Ke ya haka, da uban ruwan nan xaki kada kumfa?" Khadijah ta kalleta kamar xata yi kuka tace "Toh ban sani ba" matar ta karaso baki sake, nan ta rage ruwan ta kara mata omon sannan tace "Haka ya isa" parlor matar ta shiga wajen su Hajiya tana cewa "Ku kuma ina kuka samo wancan Ajebon" Karfe kusan hudu da rabi Hajiya Salaha ta fito bayan tafiyar bakuwarta, sakin baki tayi tana kallon Khadijah dake durkushe bakin pampo har lkcn, kwanuka ta ko ina, duk ta hade gumi ta jike kayanta jagab, kai kana ganinta kasan bata taba ba ne, Hajiya ta kwalo ma kishiyarta kira ta fito da sauri, ita ma ta xaro ido tace "Me xan gani ni Maimuna, wanke wanken awa biyu?' Khadijah dake kallonsu kamar xata yi kuka tace " plates din sun bushe, ya ki ya fita" Hajiya Maimuna ta rike ha6a tace "Ehh lallai muna da aiki, yanxu tsalelliyar budurwa kamar ki baki iya wanke wanke ba shekara sha uku sa'ar Murjata" Hajiya Salaha da ita ma ta bude baki ta kalli kishiyarta tace "kina da aiki dai, don ba ni aka kawo ma ita ba, mutum yaji da nasa 'ya yan mana, shima Alhaji wllh, da ba sai ya bar ta gun kishiyar marigayiyar uwarta ba" Juyawa Hajiya Maimuna tayi tace "Toh Allah ya kyauta" daga haka ta shiga ciki, Hajiya salaha ta mata tsawa tace "Tashi mana kan kwanuka yar banxa kawai, ke ga yar masu kudi ko, to xa ki ci kwakwa a gidan nan don bbu shegen da xai dau iskancin ki, kawai kin bi kin ma mutane asarar omo, maxa kuma ki dau tsintsiya ki tattare gaba daya gidan nan idan shima kuma baki iya ba sai in ga" khadijah da ta bata fuska xata yi kuka ta karasa ta dau tsintsiyar da take nuna mata ta fara sharan, takaici ya rufe Hajiya ganin gwara ma ta shekara a tsugunne bakin pampon da wannan sharan da take na yan iska, juyawa tayi ta bar gun daga karshe tana cewa "Xaki san inda kika xo yarinya" da daddare Khadijah na rakube jikin kujera gaba daya hankalinta da soul dinta na kan kallon cartoon da kananun yaran kawu Jibril suka sa a TV, an kirata ya fi sau uku amma inaa, hauri Sajida er Kawu ta biyu ta kai mata tace "Yau naga mayyar kallo ana magana bata ma san ana yi ba" a firgice ta mike sai dai har lkcn idonta na kan TV, Hajiya Maimuna dake lekosu daga kitchen don ita ke kiran khadijar ta xo ta karbi abinci, ta karaso a fusace ta kai mata dundu, firgita ta juyo Hajiya Maimuna ta murda kunnenta tace "Gafara shegen kallon nan xai maki ne hala, ka ji min yar kaza kaza" sunkuyar da kai khadijah tayi kamar xata yi kuka, Hajiya Maimuna ta turata kitchen tace "Ga tuwon ki can a kitchen ki dauka, gayyar tsiya kawai" tafiya kitchen din tayi tana yi tana waiwayo TVn ta dauko tuwon a wata yar roba an ya6a masa miyar kuka koriya shar, sai kallon miyar take kamar idanuwanta xa su fito, ta dawo parlon ta xauna cikin yara dake cin abinci su ma ta ci gaba da kallonta Hajiya Salaha ta shigo parlon tace "Wato kinsan idan mutum ba ayi masa tarbiya ba sai na kallo, kinga saura kadan ta xubar da tuwon tana kallo" da sauri khadijah ta kalli tuwonta taga ba daidai ta ajiye sa ba, Hajiya salaha ta fixgota a fusace ta juyar da ita tana kallon kofar kitchen tace "Duk kika sake juyowa sai na kashe ki" Khadijah dai bata ce komai ba ta kai hannu a hankali cikin tuwon ta mintsili kadan ta kai baki, yamutsa fuska tayi tana hadiyewa da kyar sai kuma ta kalli Er Kawu ta uku mai suna Rabi tace "Anty akwai indomie?" Yarinyar ta fashe da dariya sannan ta gaya ma Uwarta Hajiya Salaha, Hajiyar tace "Ehh akwai wanda ubanta ya kawo mana daga kabari" Khadijah dai bata ce komai ba, haka tayi ta kallon tuwon ta kasa ci, daga karshe haka ta mike ta kai kitchen ganin kowa na kai kwanonsa can, Hajiya Maimuna ta kwalo ma kishiyarta kira ta nuna mata tuwon da ta bari tace "kin dai ga koh? To wllh har in fita girki sai dai yunwa ya kashe yarinyar nan" *Haske Writers Association*💡 07087865788 Contact me here. ✨ *Noor-Al-hayat*✨ _By Khaleesat Haiydar_ _Littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne, kindly patronize ur writer and read happily, duk wanda bai ji dadi ba hakan, yyi hakuri plss_ Washegari talata Khadijah na ta share tsakar gidan da aka sa ta tayi tun asuba har lkcn bata gama ba Kawu ya fito cikin shiga ta alfarma da daya daga kayan mahaifin Khadijah, matansa sun rakosa xuwa balcony ana yi masa Allah ya tsare hanya, ganin Khadijah da yayi ya juya yana kallon matan nasa yace "Gobe er can ta shirya da safe xa a kai ta makarantar boko" Hajiya Maimuna tace "Wanda su Sumayya ke xuwa?" Wani kallo yyi mata yace "Ke xa ki biya, ko ina naga kudin biyan wannan makarantar, makarantar da yaran Bala ke xuwa xa a kai ta, ina jin ko a Jss2 aka ce take ko one" Khadijah ta mike tace "Aa jss2 nake Abba" Wani shegen kallo yyi mata yace "Kun ga irin rashin tarbiyar ko, kun gani ko, to yanxu wa ya sako bakinta, dama na samu labarin an baki tuwo ki ci jiya da daddare kin ki ci tunda kin taho da abinci daga gidan marigayi Muhd, to wllh xa ku yi aiki hand in hand da yunwa in har baxa ki ci abinda ya sauwwaka ba, baxa ki taho gidana kina min sangarta ba" daga haka ya nufi daya daga motocin dake tsakar gidan, Khadijah ta ci gaba da sharanta na yan koyo da take yi. Throughout haka ta dinga aikin da ba ta iya ba bata taba yi ba a gidan, duk ta gaji amma ko kadan bata ce haka ba sai turo baki da take ta yi, Hajiya Salaha ta kai mata dundu yyi sau biyar daga karshe ta gaji da bin ta tana mata dundun ta kyaleta, Hajiya Maimuna kuwa ta surfa mata xagi ya fi a kirga, duk wnn abun sai dai ta turo baki ko ta bata fuska daga nan kuma shkkn, kunu da kosai a gantale aka bata a cup, ita ma ta ci a gantale ta bar masu abinsu don ba saba ci tayi ba, sai da suka yi baccin rana sannan ta samu tayi sallahn zuhr ta lallaba ta kunna TV ta rage volume ta xauna tana kallo happily, dauke wutan da aka yasa ta turo baki, a hankali ta kwanta nan kasan parlon nan da nan kuma bacci ya dauketa don tun tashin asuba. Ko abincin rana ba a bata ba wai sai yaran gidan sun dawo, basa kuma dawowa sai karfe biyar, suna dawowa kuwa da yamma aka xuba ma kowa shinkafa da wake da mai da yaji da Hajiya Maimuna ta girka, Hajiya Salaha ta sa Sumayya ta xuba ma Khadijah don ita Hajiya Maimuna rantsuwa tayi baxata bata ba, khadijah ta tsura ma shinkafa da waken ido da aka barbada ma yaji, a hankali ta kai hannu ta dinga tsince waken tana ajiyewa a kasa gefenta, Hajiya Maimuna dake ta kallonta ta mike ta karbe kwanon abincin ta kai kitchen ta rufe, abincin da ba ta ci ba kenan har aka yi magrib sannan isha, tana ganin aka ba kowa shinkafa da miyar da Hajiya maimunar tayi amma ban da ita, bayan ta idar da sllh ta samu Sajida dake waya ta duka gefenta a hankali tace "Anty ni ba a ban shinkafar ba" ta mata wani kallo tace "Toh ni na dafa ki samu su Hajiya mana" mikewa tayi ta wuce dakin Hajiya salaha, ta samesu xaune da yaranta ana assignment, kallonta tayi tace "Lafiya??" ta girgixa kai tace "Ni ba a bani abincin ba ina jin yunwa" tsawa tayi mata tace "Fita ki ban waje, ba dai shayi da soyayyen kwai kike jira ba yunwa xai kashe ki gidan nan" a hankali Khadijah ta juya ta fita, ta tafi gun kwanciyarta ta rakube hade da rufe ido tana tuno Ummarta. Washegari kamar jiya da asuba aka tasheta, har gari ya waye tana shara, sai da duk yaran suka wuce makaranta sannan Hajiya maimuna tace idan ta ga dama ta wuce tayi wanka ta shirya, tsaye khadijah tayi a bathroom dake tsakankanin dakunan su Hajiya, soson wankan ta da Abbanta ya siyo mata daga Kasar waje ya xama na kowa da kowa hadda sabulunta mai tsada, ta turo baki ta dau sabulun kadai ta yi wanka da shi ta fito cike da kyankyanin bayin, tun da ta fito parlor Hajiya Salaha ke kallon kayan jikinta, khadijah ta durkusa gefenta a hankali tace "Na gama" tabe baki Hajiya salaha tayi ta nuna mata cup din kunu tace "Gashi can ki dauka, kosan ya kare" Khadijah ta leka cup din da sauri a xaton ta shayi ne, a hankali ta mike ganin ba shi bane ta isa gun cup din kunun ta dauka, Hajiya salaha tace "Ko yau ma baxa ki sha ba" bata ce komai ba ta dinga shan kunun da yyi mata tsami a baki tana d'an yamutsa fuska, sai hararanta Hajiya salaha take tana kwafa, daga karshe kadan ta sha ta ajiye ta mike tace "Na koshi" duk da uban yunwan da take ji cikinta na kugi, Hajiya Salaha tace "Toh ki hutar da kanki tafi ki juye a flask ki hada duk kwanukan ki wanke, kuma ki min irin na ranan in fasa maki jiki da wayar wuta" ita dai khadijah bata ce komai ba ta mike taje yin yanda tace nata. Wani almajirin Kawu ne ya taho kai ta makarantar, shegen nisa ce da makarantar kuma almajirin me suna musa yace da kafa xata dinga xuwa kullum don haka gwara ta dinga kallon hanyar da kyau, tunda suka shiga makarantar Khadijah ke kalle kallen ko ina, don ita dai bai yi mata kama da schl ba, gashi ko plaster ba ayi ba, yaran ma basu da yawa, Musa ya shiga gun wani wanda da alama shugaban wajen ne, ita tana tsaye waje, tana jin mutumin na ce ma musa ai lesson ne wa yaran da basa gane karatu, kuma na shekara daya ne kafin yaro ya shiga boko, musa ya tambayesa nawa ne yace dubu uku da dari biyar, nan take musa ya basa kudin, ita kuma aka kira wata daliba ta kai ta ajin karshe musa ya wuce, su kusan goma ne a ajin, ita dai tunda ta shiga ajin take kallon malamin dake ta koya sentence making, "The boy was tall..." Shine abinda malamin ke ta nanatawa yaran na fadi su ma, khadijah dake ta kallon sa tace "Excuse me, but you said present tense sir?" Malamin yace "Yes" tagumi tayi tace "Sorry but that's past tense class master" kallon board din yyi da sauri sannan ya kalleta, bai kulata ba ya ci gaba, nan ma kuma sai da ta sake masa gyara, hade rai yyi yana kallonta, can ya basu classwork ya koma ya xauna, sai bayan kusan minti sha biyar ya karba sannan ya fara koyar da Multiplication a board, sai da ya gama tas, sannan ta kai masa gyaransa a littafi tana nuna masa, fita malamin yyi xuwa gun shugabansu, ba a dau lkci ba ya kirata, tana tsaye yace "Ke tunda baki da kunya kar ki sake xuwa makarantar nan daga yau, tunda kin iya abinda ake koyarwa ki xauna a gidan ku ko kuma a kai ki school ga kudin ku" karba tayi tace "Ohk, in tafi yanxu" yace "Tafi" juyawa tayi ta fice daga uncomplete building din, gano gida bai mata wahala ba saboda sharpness dinta, su Hajiya salaha dake xaune parlor suna hira suka saki baki suka ce me kika dawo yi, tace "Ba abinda suka iya fa a wajen, they are just teaching rubbish, ni bana son wajen school nake so, am in jss2" Hajiya maimuna tace "Shine kika dawo" gyada mata kai tayi ta mika mata kudin hannunta, ta tafi jikin kujera ta rakube ta xauna, duk suka bi ta da kallo baki sake. Yunwa sosai take ji amma bata ce komai ba, Kawu ne ya fito a shirye xae fita wajen karfe goma da rabi, ganinta yace "Wannan yarinyar musa bai kai ta makarantar bane" Hajiya salaha tace "Uhn gata nan ya kai ta ta dawo wai bbu abinda suka iya kilan mai tsada take so" ya juya da sauri yana kallonta yace "Me ya dawo da ke?" Tace "Abba they are teaching rubbish there, kuma ina ta correcting dinsa, ban san whether he reported me bane, sai aka kira ni wai in tafi kar in sake dawowa, har da kudin ma an bani na dawo da shi" Kawu ya gyara tsayuwa yana gyada kai yace "Ohhhw haka aka yi kenan, toh kin ma kanki, Alhmdllh Muhd baxae gan ni da ko wani laifi ba don na kai ki makarantar kika gudo, don haka sai kiyi ta xama gidan" daga haka yyi ficewarsa, ita dai bata ce komai ba, Hajiya Maimuna tace "Wato ke isassa kin raina makarantar shine kika je kina ma malaman fitsara ko, uban wa ke da kudin asaran da xai kai ki irin makarantar da ubanki ya sa ki tun farko?" Khadijah dai sai kallonta take, Hajiya Salaha tace "Ni da nace xan fara awaran siyarwa xan dauko mai aiki wllh da Alhaji xai yarda da sai ta dinga kai min can bakin kasuwa, kinga ai ba talla bane wnn, xama waje daya xata yi" Hajiya Maimuna tace "Ae ko da xai yarda nima sai in hada mata da Omon siyarwa na" Hajiya salaha tace "Toh bari ya dawo dai mu ji" suka gama dai hirarsu duk suka shiga dakunansu domin kwanciya suka bar ta ita kadai a parlorn ga yunwa dake dawainiya da ita, da rana yau kam taliya da wake suka girka, gashi ita bata cin wake tun tana karama, Hajiya salaha ta dan yarfa mata a kwano ta bata, kamar xata yi kuka tace "Ni ban iya cin wake ba" Hajiya salaha tayi er dariya ta mayar da abincinta cikin tukunya ta fito kitchen din, sai a sannan khadijah ta fara hawaye don tunda take bata taba jin yunwa irin wannan ba, ita shinkafa da miya take so, tsakar gida ta tafi ta xauna tana share idonta, har wani rawa jikinta yake don yunwa, tashi tayi ta fice gidan gaba daya, ta shiga gidan dake kusa da na kawunta, gidan shigen na kawunta ne, taga wani yaro xaune tsakar gida yana cin tuwo da koren miya, fita tayi da sauri har tana tuntube, gidan dake kusa da wannan ta tura ta ji a kulle, haka na kusa da shi ma, a gida na hudu ta tsaya tana kallon babban gidan don ya fi duk gidan anguwar, tura gate din tayi taji a bude ta shiga tana kallon mai gadin ta gaishesa yace "Wa kike nema?" Ta nuna masa cikin gidan sannan tayi wucewarta, har ta isa balcony kallon karen dake cikin cage a gidan take, ta murda kofa a hankali ta shiga parlorn, tsaye tayi bakin kofar ganin wani matashi da baxai wuce shekara ashirin da shidda ba yana xaune parlorn da plate din abinci a hannunsa idonsa a kan tv, yana kallonta da dan mamaki yace "Wa kike nema" ta kalli abincin hannunsa kamar xata yi kuka a hankali tace "Nobody, I am just hungry" ya buda ido kamar ya ji mugun abu, a hankali tace "Please" ajiye plate din hannunsa yyi yace "Take" ta karaso ciki da sauri ta xauna kan kafarta tana kallon shinkafa da miyar da naman kaza sai coslow dake gefe murya can kasa tace "Thank you" daukan spoon din tayi ta kai abincin baki ta fara ci, ya kafeta da ido irin kallon mamaki, muryar wata dattijuwa taji tace "Who's this?" Ya juya ya kalleta kafin yace komai Khadijah tace "Good afternoon ma.. I am khadijah" matar ta kasa cewa komai, ta kalli yaronta dake xaune kamar yanda shi ma yake kallonta, Khadijah ta dau kazar abincin tana ci tana kallon matar. *Haske writers association*💡 ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 _Littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne, kindly patronize ur writer and read happily, duk wanda bai ji dadi ba hakan, yyi hakuri plss_ Karasowa parlorn dattijuwar matar tayi har lkcn tana kallon khadijah tace "Where are you coming from?" Khadijah ta dago a hankali tace "Just 3 houses away...." Matar tace "Gidansu Hajiya Salaha kenan?" Khadijah ta gyada kai, matar tayi shiru tana kallonta, can tace "An aiko ki ne?" Ta girgixa kai tace "A'a kawai abinci nake son ci" kallon d'an ta da ke xaune matar tayi, khadijah ta ci gaba da cin abincin gabanta, shi dai bai ce komai ya mike xai bar parlorn, mahaifiyar sa ta bi sa da ido tace "Kaje to Sadiya ta xuba maka wani abincin koh" ya juyo yace "Noo dama it's not as if ina jin yunwa mum, anjima xan ci" daga haka ya wuce ciki, matar ta dinga kallon khadijah dake cin abincin sanyi sanyi, can ita ma ta juya ta bar parlorn, jawo remote khadijah tayi ta kunna TV ta gyara xama tana facing tvn, tana cin abincin amma gaba daya ta ba tv attention dinta, bayan kusan minti talatin taji ance "Wai ke baxa ki gida bane? Ba kin gama cin abincin ba" Ta juyo da sauri ta kallesa sai kuma ta marairaice tace "Plss ina son in gama kallon nan" sakin baki yyi yana kallonta ga plate din abincin ta gama, bai dai ce komai ba ya fita rike da makullin mota, ba a dau lkci da fitarsa ba sai ga yan mata uku sun shigo gidan sanye da kayan islamiyya, tun da suka shigo suke kallonta ita kam ko sanin sun shigo bata yi ba, Muryar matar daxu taji a parlorn tace "Ke baxa a nemeki gida ba" khadijah ta dago da sauri, sai kuma ta bata fuska tace "Anty bana son xuwa gidan" Matar ta buda ido tace "Baki son xuwa kuma?" Shiru ta d'an yi kafin tace "First... They are so dirty and unkept, and I don't like their dishes.... I don't just like the house" matar dake kallonta da mamaki tace "Toh ba gidan ku bane" khadijah ta girgixa kai a hankali tace "Noo uncle dina ne ya kawo ni" matar tace "Maza tashi ki tafi kar ayi ta nemanki kin ji" kallon agogo tayi taga karfe shiddah ta ce "plsss ma... am I always welcome here?" Matar ta d'an yi murmushi tace "Sure" khadijah ta kwashe plate da cups da ta ci abinci tace "Where can I find d kitchen" nuna mata matar tayi ta kai ta fito sannan ta dau ruwan goron da d'an ta ya ajiye tace "In tafi da shi?" Matar ta gyada mata kai, murmushi tayi ta risina tace "Thanks ma" daga haka ta nufi kofar fita matar ta bi ta da ido, tana fita gidan gaba daya ta hango mutane tsaye bakin gate din gidan kawunta, tafiyar minti kusan shidda tayi ta isa gidan, tsaye ta tadda su Hajiya Salaha da yaransu gaba daya ga makota ana ta surutu, Sajida ce ta fara ganinta tace "Lahhh mama kun ganta" sai aka juyo gaba daya ana kallonta, Hajiya Salaha ta isa inda take da sauri ta fixgota tace "Daga ina kike?" Khadijah dake bin kowa da kallo tace "Just few houses away....." Bata rufe baki ba Hajiya Salaha ta sauke mata mari, wani ihu ta fasa tana rike da fuskarta tana jin duniyar na juya mata, tunda take ba a taba kai hannu jikinta ba bare fuskarta sai ranan, iyaka a sa ta tayi kneel down ta daga hannu, har tsadadden bokon da take xuwa a kano ma ba a duka, Hajiya Salaha na huci ta shiga kunduma mata xagi tana cewa "Allah ya isa yawon da kika sa muka dinga yi muna nemanki kamar gantalallu, sai Allah ya saka mana... Kuma bari Alhaji ya dawo wllh xaman ki ya kare gidan nan ya je can ya kai ki gun talakawan dangin uwar ki..." Kuka kawai khadijah take tana rike da fuskarta, hakuri mutanen wajen suka dinga ba Hajiya Salaha suna cewa ai yarinya ce, Hajiya maimuna da ganin Khadijah ya sa ta shiga parlor ta fito da wayar wuta ta nufo ta, wata mata ce tayi saurin janyeta tace "A'a don Allah ki bari Maman Hafsa, ayi mata hakuri" wata mata ma ta rike wayar tana ba Hajiya Maimuna hakuri, Hajiya Salaha tace "Ku bar ta ta ci mata mutunci crook ce wannan yarinyar da ku ke gani haka, wa yasan gidan uban da taje" Matar da ta ja Khadijah ta duka dai dai fuskarta tana kallonta tace "Ina kika je ake ta neman ki yan mata" Khadijah na shessheka tace "I was hungry and I had to....." Kasa ci gaba tayi ta rushe da kuka, Matar ta d'an kwalalo ido tace "Tohhh bata jin Hausa ne?" Hajiya Maimuna tace "Iskancin fa?? Tsabar shakiyanci ne da iyayi da kinibibi ita er mai kudi, toh wai ma ina mai kudin yake yau? Ku ce min yana kabari, toh idan ma xata sauke kai ta yi rayuwa yanda ko wani talaka ke yi ya rage nata, uwar me suka tsinana ma mutane banda tsoron Allah har Alhaji xai daukota ya ajiyeta a gidansa, wai I am hungry... To kafafuwar uwarki xan dafa maki in baki banda abinda aka girka kika ki ci" Hajiya Salaha tace "Ae komai ya xo karshe, ya dawo yasan yanda xai yi da ita, wnn 'ya sai ta kashe aure, taje can inda xa a dinga dafa mata indomie da kwai a bata shayi mai kauri da custard ta sha, mu ba rainon tea da bread muka ma yaranmu ba" daga haka tayi shigewarta ciki, Matar dake rike da Khadijah tace "Ke me yasa kika fita baki sanar masu ba? Komai aka baki kuma bata sai ki ci ba khadijah" Khadijah ta kasa cewa komai sai kuka take, jin kiraye kirayen magrib duk aka fara watsewa ana ma su Hajiya Allah ya kyauta, wasu kuma na tausayin khadijah domin kuwa suna ganin iyayenta basu mata adalchi ba in har abinda su Hajiya ke fada gaskiya ne a kanta, ba a san yanda rayuwa xata kaya ba don haka iyaye ya kamata su dinga koya ma 'ya yansu both the right and left side of life, yau idan an ci na masu kudi gobe a ci na talaka bawan Allah, wannan xai sa yaro yyi adapting a duk situation da xai tsinci kansa. Khadijah ce kadai tsaye tsakar gidan duk sun shige ciki da yaransu, ta share idonta a hankali ta bude kofa xata shiga, a tsawace Hajiya Salaha tace "Ki shigo ki mana me? Maxa koma sai Alhaji ya dawo gidan nan, maxa fita kar in sumar dake annamimiya kawai" juyawa tayi da sauri ta bar wajen bayan ta rufe masu kofa ta nemi wani waje ta xauna ta daura kanta bisa kneels dinta, har aka kira Isha tana wajen ga sauro sai cixonta suke, Kawunta bai dawo gida ba sai wajen karfe goma, bayan ya gama parking xai shigo ciki ya ga kamar mutum a wajen ya haske waya, tana nan yanda take bacci ya dauketa a hakan, da mamaki yace "Ke!!" Firgit ta farka ta mike tsaye da sauri, yace "Me kike a nan" tana kallonsa da idonta da yyi bulu bulu yyi jajir, shatin hannun Hajiya Salaha a gefen fuskarta hankali tace "Aka ce in tsaya a waje" yace "Saboda me?" Tayi shiru bata ce komai ba, shiga gidan yyi ya tarar da su gaba daya da yaransu ana xaune parlor ana kallo ana shewa, duk suka fara cewa "Abba sannu da xuwa..." Bai bi ta kansu ba yace "Me wancan yarinyar take yi a waje?" Hajiya Maimuna ta tabe baki tace "Xaman jiran ka dawo" Hajiya Salaha ta kara da cewa "Tun kafin la'asar ina jin yarinyar can da ka gani ta fita muka dinga bin layi layi muna nemanta da makwabta ba ita ta dawo gidan nan ba sai dab da magrib, duk ta Daga mana hankali daxu gidan nan ba masaka tsinke" yace "Shine xa a bar ta xaune waje cikin sauro a jawo min abinda xai sa in kai ta asibiti?" Hajiya Salaha tace "Toh xan iya mata abinda raina ke raya min Alhaji shi yasa nace tayi ta xama a waje" yace "Toh kada warce ta sake turata waje war haka ko uban me tayi... Na gaya maku" juyawa yyi ya kalli Khadijah dake tsaye ta rakube a fusace yace "Xo nan" karasowa tayi da sauri ya wani hade rai yace "Ina kika je?" Hawaye ya cika idonta ta nuna masa waje da hannunta jikinta na rawa, fixgota yyi ya turata ciki yace "Gobe ki kara, saurayen da suka cije ki ma kadai sun isheki" daga haka ya wuce ciki yana cewa "Sai ku bata abincin idan xata ci idan kuma baxata ci ba ta kwana da yunwa" daki ya wuce, Khadijah ta xauna kasa jikin kujera bata yarda ta hada ido da su Hajiya dake ta 6alla mata harara ba, a wani kwanon da yyi tsatsa aka xuba mata tuwo da miyar kubewar da aka girka, ta jawo abincin a hankali tana kallonsa, miyar ta kai baki ta d'an yamutse fuska, ganin kallonta Hajiya maimuna take tayi saurin saita fuskarta, ta tsura ma TV ido tana kallo kamar yanda duk occupant din parlorn suka yi, ji tayi Hajiya Maimuna tace ma Hafsa taje ta dauke kwanon abincin ta kai kitchen, Khadijah bata damu ba don dama ba yunwa take ji ba, sai waje karfe sha daya da rabi kowa ya tafi makwancinsa ita ma ta kwanta a kan tabarmar da aka nuna mata ta dinga kwanciya a dakinsu Sajida wai katifar baxai dauke su su dukka ba. Bayan kwana biya Khadijah na xaune tsakar gida da yamma tana uban wanke wanken da su Hajiya suka tula mata, su kuma suna ciki da yaransu kasancewar ranar Friday ce bbu islamiyya, yi take kamar baxata yi ba tana turo baki an hanata kallo, wanda a kansa kusan kullum sai ta sha mazga amma ta ki hakura, ita dai tayi kallo, duk ta rame ta kanjale, kana ganinta kasan akwai yunwa sosai da wahala tare da ita, ga rashin sabon aiki, ba laifi yanxu tana d'an wanke plates din su fita sai dai ta kan fi awa biyu kan kwanukan wanke wanken, kayan jikinta kuwa yanda aka san ta shiga rafi tsabar jikewar da yake idan tana wanke wanken, yanxu an ma daina sa ta sharan gaba daya tsabar kawai bata iya ba sai dai wanke wanke da jan ruwa wani lkcn a waje idan bbu wuta, tun ranan da ta fita har yau bata sake fita ba sai dai idan an aiketa gun mai kanti ko kuma xata debi ruwa a er karamar bucket da take dauka, har yau bata sake cin abinci mai dadin gidan da taje ba, abincin gidan kawu daga taliya sai tuwo da shinkafa da wake da mai da yaji, gashi duk bata son su hakan yasa take tare da yunwa sosai, Hafsa ta fito ta jefa mata kudi tace "Khadijah wai Mama tace ki je gun mai kanti ki siyo sabulun wanki da Hypo leda biyu, sai ki siyo maggi mai tauraro na hamsin" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, tashi tayi bayan Hafsah ta wuce sanin Hajiya na iya lekowa taga ko ta wuce, ta shiga parlor Hajiya Salaha tace "Aiken fa" ta kalli kayan jikinta tace "Mama xan canxa kaya" dakuwa tayi mata tace fita Ki ban guri, shashasha sshe da gangan kike jike kayan wajen wanke wanke kenan kin san abinda ya kamata" juyawa tayi ta fita, ta sake kallon kayan dake a jike tun daga saman gwiwanta har kasa, gate ta nufa kanta sanye da hula don gaba daya Hijabs dinta yaran gidan sun gaje, tafiya ce me nisa xuwa gun mai kanti, tana tafe tana wasa da d'an karamin iccen hannunta, har ta wuce gidan da taje ta ci abinci idonta na kan gate din gidan amma ba daman shiga, tana isa gun mai kanti cikin aiken da aka mata maggi kawai ta tuna, gida ta koma da sauri ta shiga parlor tana kallon Hafsa kamr xata yi kuka tace "Me da me kika ce ma" Hajiya Salaha tayi wani murmushi ta na kallon kishiyarta tace "Me na fada maki" Hajiya Maimuna tace "Kin ji na maki musu? Ko an taba aikenta bata dawo tambayar me aka aiketa ba dama" Hajiya Salaha ta ce "Wllh Ubanki ya cuce rayuwar ki, kishiyar uwarki kuma kiri kiri ta nuna bata son ki tunda har ta sangarta ki haka ta lalata ki saboda ba ita ta haife ki ba, banda haka wannan xabgegiyar budurwa godai godai kullum aka aike ki sai kin dawo wai kin mance, sai shegen turancin iyayi.... ni dai wllh tunda yarinyar nan ta xo gidan nan nake fama da surutu abinda yaran da na haifa ma basu sa ni ba, Allah dai ya isa wllh" Hajiya maimuna ta tabe baki tace "Ke kika ga xa ki iya, ni kinga ina yi? Ai sai dai duka" Kabir ne ya sake nanata ma khadijah Aiken da aka mata ta fita da sauri tana maimaita abinda yace a ranta har ta isa gun mai kantin sannan ta fada masa, yana dariya yace "Ke yar fari ce ko?" Ta wara ido tace "I don't understand" dariya yyi yace "Aa ni ba bature bane, don nema maki saukin kai wa da dawowa idan an aikeki kawai kice a dinga rubuta maki sakon a gida kinji" tace "Ohk then" muryar da taji yana cewa a bashi kati ya sa ta juyawa da sauri, suka hada ido ta washe fararen hakoranta tace "Good evening" daga sama har kasa ya kalleta yace "How you?" Ta langwabar da kai tace "I shud say fine" yana gyada kai yace "Good" karban card din da mai kantin ke mika masa yyi yace "Doguwa dake baki sa Hijab idan xa ki fito" a hankali tace "Bani da Hijab yanxu" bai ce komai ba yana loda card din kafin yace "Toh me yasa kika jika kayan ki" tace "Wanke wanke nake yi tun da rana" yace "Ina ne gidan ku?" Tace "Our home is 3 house's away from u people's" ya kalleta yace "Gidan Alhaji Jibril?" Ta gyada masa kai, yace "Ke yarinyarsa ce" ta girgixa kai a hankali, yace "Yaushe kika xo gidan!" Ta kalli sama kamar me naxari sannan tace "10 days ago" ya gyada kai bai ce komai ba, ta amshi ledan sakonta da canji tana kallonsa kafin tace komai yace "Ya sunanki?" Tace "Khadijah" yace "Good" a hankali tace "Ina son in xo in ci abinci gidan ku amma an hanani, kuma I can't eat the food they are cooking, it's just concoction" a hankali ta karashe maganar, yace "Me yasa aka hana ki?" Tace "Su mama sun ce xa su kashe ni idan na sake xuwa ko ina kuma ina jin tsoro" ya kalleta bai dai ce komai ba, ta matso kusa da shi a hankali tace "Ko xaka dinga kawo min abincin gidan ku da kanka?" Ya buda ido yace "Ina?" Tace "Gidanmu mana, sai in dinga boyewa a backyard ina ci" tana magana ne hawaye cike fararen idonta, jin yyi shiru ta ci gaba tace "I am always hungry...." Ya sauke idonsa daga kanta bai dai ce komai ba. *Haske writers association*💡 A hankali khadijah dake kallonsa tace "please" ya dago ya kalleta kafin yace "Sai in gan ki a ina in baki abincin?" Shiru ta yi kamar me naxari, can tace "Ohk, ae akwai flowers a kusa da gate din, to ka dinga ajiye min a wajen idan na fito sai in dauka" murmushi yyi yace "Koh?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk" ta kara matsowa gaban sa tace "Promise u will do that plss" yace "I will" ta wara idonta ta hade hannayenta tace "Thank you very much, may Allah reward you, byeee" daga haka ta juya da sauri ta bar wajen ta nufi gida ya bi ta da ido, bbu wanda ya bi ta kanta ta ajiye sakon a kan kujera ta fito ta ci gaba da wanke wankenta Happily, sai kusan karfe biyar ta gama ta shigo ciki, Hajiya Maimuna ta hada ta da uban kayan yaranta ta linke su ta xuba a cupboard, sai kusan magrib ta fito ganin kowa na alwala ita ma taje bakin tap tayi alwala ta dawo tayi sllh, tana rakube jikin kujera aka fara kiran kowa ya je kitchen ya karba abinci, ita ma ta tashi sanin Hajiya Maimuna na iya kunduma mata xagi idan taga bata shigo ba, tuwo ne da miyar karkashi aka yi ranan, ta fito bayan an dungura mata nata tana kallon cikin tuwon, xaunawa tayi ta kai hannu cikin miyar dake turiri ta dangwala ta kai baki, ta kasa hadiyewa ta shiga satan kallon mutanen parlorn trying very hard to keep her face normal, kowa hankalinsa na gun kallon Hausa film da ake yi a TV, ita da yake can gida basa kallon Hausa film ko bin ta kan kallon bata yi ba, sulalewa tayi ta fita waje rike da kwanon tuwon ta ajiye nan verenda ta nufi gate da sauri, a hankali ta durkusa gun flowers din bakin gate tana addu'ar Allah yasa ya ajiye mata abincin, ta bude flower din a hankali tana dubawa ai kuwa ta ga leda fari, ta dauka da sauri ta bude taga takeaway ne da goran five alive, ajiye ledan tayi ta doka uban tsallen murna sannan ta dau ledan har tana tuntube ta shiga cikin gida, backyard ta nufa da sauri ta nemi wani lungu ta xauna ta bude abincin taga jollof rice ne da naman kaza da plantains sai sauce a gefe, Cike da murna ta fara cin abincin tana ci tana gyada kai har da lumshe ido, sauri sauri ta cinye abincin ta bude drink din ta sha kusan rabi sauran ta kasa shanyewa, ta mike ta boye goran drink din sannan ta dau takeaway din ta fita gate ta jefar cikin katon abinda ake xuba shara ta dawo ciki tana goge bakinta, sai da ta tsorata ganin tuwon da ta ajiye ta kauda kai da sauri kamar ta ga mugun abu ta daukesa kamar wani shara tana yamutse fuska ta fita waje, almajiri ta samu ta juye ma sannan ta dawo gidan ta tafi gun tap tana wanke kwanon sajidah ta leko da alamar sai lkcn aka lura bata parlorn, yarinyar ta juya ta koma Khadijah ta bi bayan ta da sauri rike da kwanon da ta wanke, Hajiya salaha tace "Daga ina kike?" Ta nuna mata kwanon tace "Naje wanke wa ne" salati ta saki tana tafe hannu tace "Yanxu abincin kika je kika xubar khadijah?" A tsorace tace "Wllh mama ban xubar ba" Hajiya Maimuna tace "Karya kike, kece xa ki ci tuwon nan har ki cinye?" Ta marairaice tace "Amma ban xubar ba wllh" Hajiya salaha tace "Toh ya kika yi da shi?" A hankali tace "Na ba almajiri" cup Hajiya Maimuna ta dauka ta jefeta da shi tace "Allah ya isa" Khadijah tayi kofa da gudu ta fita ganin Hajiya salaha ta mike, can bakin gate ta tafi ta tsaya a tsorace, yau ma dai kamar jiya kawu ne ya shiga da ita parlor, bayan ya duddungureta yyi gorin iya son ransa sannan ya juya kan iyalansa cike da fada yana nanata masu indai suka janyo ma khadijah malaria sisin sa baxai yi ciwon kai ba sai in su xa su kai ta asibiiti, bbu warce ta tanka sa cikinsu, ya gama bambamin sa ya shiga ciki. Washegari sai da kowa ya tafi makaranta khadijah ta fara wanke wanken kwanukan jiya, kamar xata yi kuka take yi don duk sun bubbushe, tayi kusan awa daya bakin tap din ta bar sauran kwanukan ta shiga ciki, Hajiya tace "Kin gama ne munafuka" ta girgixa kai tace "Na kai halve" koranta tayi taje maxa ta gama, khadijah ta fito tana kallon agogo ta ga karfe tara ya wuce har da rabi, cikin sanda ta nufi gate ta bi anguwar da kallo ta ga ba kowa da yake silent anguwa ce, bude flower tayi dai dai wajen jiya taga farin Leda, ta washe hakora ta dauka da sauri ta shiga ciki, backyard ta nufa tana waige waige kamar munafuka, ta samu inda ta xauna jiya ta xauna ta bude ledan ta fiddo takeaway din, fried potato ne na turawa da uban kwai a ciki, ta lumshe ido tana murmushi, ta fito da wani water bottle karami da ke ledan ta bude tana kallon ciki taga shayi ne yaji madara da Milo, ta wara ido tace "Wowwww" har wani rawa hannunta yake ta kai bakinta tana yi a hankali kar ya konata taji bbu xafi sosai, tun da ta kafa baki bata ajiye ba sai da ta ga bayan shayin, ta ajiye bottle din ta rufe tana lullumshe ido ta dau fork din cikin ledan ta soma cin dankali da kwan, da kyar ta gama cinyewa don ta koshi kuma bata son xubar da abincin, ta tashi a hankali tana leke leke ta fita da gudu ta jefar da takeaway din a bola, ta dawo bakin tap ta wanke bottle din ta sa a Leda ta koma jikin flower ta bude ta ajiye sannan ta shigo ciki ta ci gaba da wanke wanken, bayan ta gama ta shiga ciki Hajiya Maimuna ta nuna mata kunu a cup da aka rufe a walakanci da wani bushashen bread a leda tace "Idan kin ga dama gasu can, don bawa baxae biye ta halin ki ba tunda yana da baya" Khadijah ta girgixa kai ba tare da ta sake kallon direction din kunun ba tace "Ni na koshi mama" sakin baki Hajiya Maimuna tayi can tayi murmushin mugunta tana gyada kai tace "Toh maa sha Allah" xaunawa khadijah tayi a favourite position dinta, daga karshe Hajiya Maimuna ta mike ta wuce ciki, kwanciya khadijah tayi don ji tayi cikinta ya mata nauyi nan da nan kuwa bacci ya dauketa. Yau ma dai da rana shinkafa da mai da yaji aka girka, tana gani suka xubo ma baki da suka yi ita ko oho sai ma wankin socks da panties din yara da aka tula mata bakin tap abinda bata taba ba, sai shafa socks din take tana turo baki gashi ta fara jin yunwa da wajajen karfe uku ne, kalle kalle ta fara yi kafin ta mike kamar mara gaskiya ta fita wajen gate, bude gun flower tayi a hankali taga farin leda sabo, ta wara ido ta dauke ledan taga bbu na bottle din da tasha daxu, ta shiga ciki da sauri ta wuce backyard, snack ne a ledan da roban five alive. Nan da nan ta ci da sauri ta sha drink din sannan ta fita ta xubar da ledan a shara taje ta ci gaba da wankin ta. Sai kusan la'asar bakin suka tafi, Hajiya salaha ta fito ganin wankin da Khadijah tayi, kuka ne kawai bata yi ba, amma har kumfa bakinta yake don fada da xage xage ita dai Khadijah na tsaye jikin bango tana kallonta tana wasa da flower din gown din jikinta, sai da Hajiya salaha ta mayar da gaba daya kayan cikin bucket ta xuba omo xata sake wankewa, Allah ya isa kam Khadijah ta sha sa na barnar omon da tayi mata, daga karshe Hajiya Maimuna ta kirata kamar ta ji shawarar da mai kanti ya ba khadijahr ta dungura mata takarda dauke da abubuwan da xata siyo mata ta bata kudin ta je kanti, Khadijah na isa kantin bayan ta basa takarda ta sa ya bata fallen takarda da Biro, yana mika mata ta xauna shi kuma ya ci gaba da hada mata kayan Aiken da aka yi mata a Leda, rubutu tayi kamar haka "Assalam, I am soo happy you fulfilled ur promise, I am no longer hungry anymore, I love the foods, may Allah reward u abundantly, I like you." Ta tsura ma neat writing dinta mai kyau ido tana murmushi, can ta linke takardar ta mayar ma mai kanti biron sannan ta karbi kayan ta ta wuce da sauri, cikin flowers ta bar takardan yanda xa a gani sannan ta shiga gida, Hajiya Salaha dake ta wanke ta jefa mata kallon tsana tace "Shi yasa fa kayan ki can a kwandon kayan wanki har sun fara tsutsa maga uban da xai wanke maki, ba dai duk kin saye kayan ba" Ita dai bata ce komai ba ta shiga ciki ta kai ma Hajiya Maimuna sakonta. Karfe biyar da rabi yara suka dawo gaba daya, aka xuba ma kowa abinci amma banda ita, ko kallon inda abincin su yake bata yi ba banda kallon da take har kowa ya gama cin abincin ya kai kwanuka waje, Hajiya salaha ta shiga kitchen gun kishiyarta dake girki tace "Maman Hafsa kinsan yarinyar can daxu bata karya ba gashi yanxu ma ko damuwa bata yi tace ina abincin ta ba?" Hajiya Maimuna tace "Wallahi ina lura da ita, ke dai na mu ido, ranan yanke jikinta ta fadi ya kusa xuwa, ni dai baxan roketa ta xo ga abinci ba idan ma ba ta ci ba auki xai ma yaran mu" Hajiya Salaha ta fita tana cewa "Toh ni kinga ina bi ta kanta" Da daddare yau dai macaroni dafaduka aka yi ta manja, Khadijah ta ki xuwa kitchen ta karbi abincin sai kallo take, Tsawa Hajiya Salaha ta mata tace "Toh maxa tashi ki fita ki wanke kwanukan daxu da aka 6ata, ba dai kina xaune kina jiran a kawo maki abinci ba..." Khadijah ta mike ta fita da sauri daga parlorn Hajiya ta bi ta da kallon mamaki don a tunaninta xata shiga kitchen ne, wanke wanken taje ta d'an yi kafin ta fita gate da sauri ta bude flower sai ga wani ledan, tayi murmushi ta dauka ta dawo ciki ta wuce favourite position din da take xama ta bude take away din taga shinkafa ce da miya sai nama kusan yanka biyar ta wara ido cike da jin dadi ta fiddo goron five alive ta ajiye sannan ta fara ci, cikin few minutes ta gama saboda saurin da take ta koshi ba kadan ba don har ta kasa shan drink din gaba daya, ta boye a inda ta saba boyewa sannan taje ta jefar da ledan ta dawo ta ci gaba da wanke wanken tana gyangyadi tsabar koshin da tayi, da kyar ta karasa ta shiga ciki wajen karfe tara tana shiga kuwa isha tayi suna ta kallonta su ji ta ce ina abincinta amma sai ji suka yi tace xata je kwanta daga haka kuma ta tafi tayi kwanciyarta. Haka nan Khadijah ta ci gaba da rayuwa gidan har na kusan wata biyu bbu ranan da ya taba fashin ajiye mata abinci gashi tun haduwar da suka yi a kanti ta bukaci ya dinga ajiye mata abincin basu sake haduwa ba, duk kwana biyu sai ta ajiye masa note din godiya cikin flowers, Bbu abinda ke daure ma Hajiya Maimuna da Hajiya salaha kai irin yanda suka ga Khadijah ke ta kiba tana kyau gashi fa sai ta kai har washegari wani lkcn bata ko bi ta kan abinda suka girka ba, ga uban aikin xa take narka kullum a gidan, ranan dai abun ya ishi Hajiya Maimuna tace "Ni kam yarinyar nan ko dai akwai gun da take xuwa cin abinci ne ba mu sani ba, dubi fa ko bin ta kan abincin gidan nan bata yi ko da an xuba mata sai ta ki ci, gashi lafiya lau sai ma kiba da na ga ta yi kamar" Hajiya Salaha tace "Nima abun na daure min kai kuma kema kinsan bbu inda take xuwa sai gun mai kanti kuma bata dadewa take dawowa gida" Hajiya Maimuna tace "Yanxu dai kawai mu sa ma duk movement dinta ido sosai" Da rana Khadijah na ta xaune parlorn tana jiran su tafi su kwanta taje ta dau abincin ta a flowers, kallon wani Hausa film suke, taga basu da niyyar shiga ciki, ta mike ta dauke few plates dake parlorn duk da tayi wanke wanken safe tace "Mama in je in wanke" Hajiya Salaha tace "Toh sai kin tambaya, ko ba aikin ki bane" fita tayi da sauri don dama abinda take nema kenan, tana ajiye plates din ta fita gate, tuni su Hajiya suka fito suna lekan compound suka ga bbu ita, hakan yasa Hajiya Salaha xata nufi gate Hajiya Maimuna ta rike tace "Jira kamar ga kafafuwanta can a tsaye" ko rufe baki basu yi ba sai gata ta shigo da leda suka yi saurin makalewa da bango, ko lura da su bata yi ba ta wuce inda ta saba xama da sauri, ta bude soyayyen kwai da indomien dake turiri kenan ta ajiye five alive a gefe, sai ga su a kan ta, tsuru tsuru tayi tana kallonsa kamar yanda su ma suka saki baki suna kallon abincin, salati suka saki a tare, Hajiya Maimuna tace "Uban wa ta baki wannan abincin Khadijah" Khadijah da tayi mugun tsorata xata mike ta gudu Hajiya Maimuna ta cafketa tace "Gun ubanwa kika karbo?" Jikinta na rawa tace "Ku yi hakuri" Mari Hajiya Maimuna ta xabga mata tace "Dama shi yasa kika daina bi ta kan girkinmu a gidan nan, karuwanci kika fara ba mu sani ba? To yau sai kin fiddo wanda ke baki abincin nn" cikin kuka tace "Gidansu yana can mama" janta suka yi suka fita ko warce ta yafe dankwalinta a kai ana huci suka ce "Mu je gidan" Kuka kawai Khadijah take a tsorace tana biye da su Hajiya Maimuna na janta har suka isa kofar gidan, Cikin rawar murya tace "Nan ne gidan...." Hajiya Maimuna ta xaro ido tace "Nan kike xuwa?" Ta girgixa kai da sauri tace "Mama sau daya na xo, mutumin ne ke kawo min abincin ya ajiye cikin flower, ku yi hakuri don Allah" kwankwasa gate Hajiya salaha ta dinga yi da karfi mai gadi ya bude, tace "Ina masu gidan nan" Mai gadin yace "Daga ina?" Bin gefensa tayi a fusace ta shiga tace "Xaka ji da munafurcin ka, ni din ce xaka ce baka taba gani ba" Hajiya Maimuna ta bi bayan ta tana jaye da Khadijah suka isa parlorn gidan suka bude, Hajiya Maimuna ta rafka sallama kamar tashin duniya, Wata yar budurwar ce ta fara fitowa tana kallonsu ta gaishesu, a takaice suka amsa suka tambayi uwarta, ta juya kenan xata je kiranta sai ga ta ta shigo parlor, har ta karaso kallonsu take da mamaki, Hajiya Maimuna ta hade rai tace "Hajiya Amina mun wuni lafiya?" Hajiya Aminar tace "Alhmdllh, in ji lafiya" Hajiya Salaha tace "Ba lafiya ba, ina d'an ki yake?" Da mamaki tace "Da na kuma?" Cike da jaraba Hajiya Salaha tace "Kwarai, ya fito ya gaya mana menene tsakaninsa da yarinyar nan, ya fito yanxun nan" Hajiya Amina tace "Kar ku min hayaniya a gida don Allah, ku gaya min meye ya faru?" Hajiya Maimuna tace "Hayaniya kam dole, don wannan case din sai ya iya kai mu har kotu, tunda batanci yake yi da 'yar mu" bude baki Hajiya Amina tayi tana kallonsu, haka ma 'yar ta... Khadijah dai sai matsar kwalla take jiki na rawa, Dai dai nan kuwa sai ga shi ya fito parlor, tsaye shi ma yyi yana kallonsu da mamaki, Mahaifiyarsa da ranta ya gama baci tace "Sadeeq, what's between you two" ta fadi haka tana nuna masa khadijah, kafin yace komai Khadijah tayi saurin cewa "Nothing ma, kawai yana kawo min abinci yana ajiyewa cikin flowers ne in dauka in ci..." Buge mata baki Hajiya Maimuna tayi ta kunduma mata xagi tace "Kece sadeeq? Makira yar iska? Ke ta tambaya?" Sadeeq dai na tsaye yana kallon ikon Allah ya kasa cewa komai, mahaifiyarsa tace "Magana nake maka malam" ya juya ya kalleta yace "Mum I don't think I have time explaining my self to any of this women, ni dai nasan the girl told me about how hungry she was ba'a a bata abinci a gidan, and I volunteered...." Uwarsa ta xaro ido tace "Volunteered what Sadeeq?" Ya d'an hade rai yace "She requested in dinga ajiye mata abinci a flowers din kofar gidansu thats all, sannan tun ranan bamu sake haduwa da ita ba cox dama gun wancen mai kantin muka hadu, sai kuma yanxu da take tsaye a nan, ashe dama taimako na xama laifi, kuma da ba su barta da yunwa ba har xata ce in dinga ajiye mata abinci she's always hungry? Ba komai kuma yasa nake ajiye mata abincin ba sai don nasan bbu illar da ya kai barin 'ya mace da yunwa, bana son ta shiga wani hali shi yasa, if not what's my connection with her da har xan dinga bata 3 daily meals?" Tunda ya fara magana su Hajiya suka saki baki suna kallon Khadijah da ta sunkuyar da kai, Hajiya Maimuna tace "Toh kayi na farko kayi na karshe, dauki 3 daily meals din naka ka kai gidan almajirai ko marayu, kada ka sake xuwa mana kofar gida da abinci, ita kuma yanxu xa mu koma gida mu ji wanda yake barin ta da yunwa da tace she's always hungry" Hajiya Salaha tace "Sai ma kin fada, kuma wllh Allah ya isa tsakaninmu da ita tunda mu ta ke bi gida gida a anguwar nan tana cewa muna barin ta da yunwa, bbu abinda xai hanani yi mata jina jina yau" Daga haka ta ja ta xasu fita, khadijah ta hade hannunta tana kallon sadeeq cikin rawar murya tace "I am very sorry" Rankwashi Hajiya Salaha ta kai mata da karfi ta ja ta suka fice gidan, Hajiya Amina ta kalli d'anta tace "Daga this very moment na raba ka da abinda kake yi" Hajiya Maimuna tace "Da dai ya fi maku" daga haka ta bi bayan su. Duka da xagi kam khadijah ta sha shi ranan, duk ta fita hayyacinta sai kiran Ummarte take, don Kansu suka kyaleta daga karshe, indomie da kwan kuma suka dauke suka juye a plate suka cinye. Tun daga ranan sadeeq bai sake ajiye mata abinci ba, kafin kwana biyu ta rama duk ta xama wata iri har lkcn ta ki kwantar da hankali ta ci abinci da suke girkawa, sai taji yunwar xae sumar da ita take tura abincin ko yaya shi ma wani lkcn har da amai sai tayi, tafe take kamar iska xai kadeta tsabar weakness dake tartare da ita, ta isa gun mai kanti ta basa takardar da aka aiketa ya karba yana tsokanarta kamar yanda ya saba, ita dai bata ce komai ba unlike before da xata fara masa turanci, kiranta taji anyi ta juya da sauri jin muryar, ta ga Sadeeq tsaye bayan ta, ta yi murmushi tace "Good evening" a hankali yace "How you?" Tace "Fyn" kallonta ya dinga yi ganin yanda ta rame, ta juya ta karbi sakonta tace "Bye" yace "Khadijah" ta juya da sauri tana kallonsa, yace "You are always hungry koh?" Shiru ta yi hawaye ya cika mata ido, yace "I am sorry I cant help it" ta ce "Don't worry, I appreciate the one you did before....." Hannu ya sa a aljihu ya Ciro kudi ya kirga dubu biyar ya mika mata yace "Toh gashi ki boye wannan ko biscuits da doughnut sai ki dinga siya kina ci a nan kinji?" Shiru ta yi ya kamo hannunta ya sa mata yana murmushi ya gyada kai yace "Yeah" rike kudin tayi ya sake hannunta yace "See you some other time" ta daga masa hannu hawaye cike idonta tace "Thank you" hanya daban daban suka bi tana isa gida ta boye kudin, tana son fita ta siyo abinda yace da daddare ta kwanta amma tana tsoro, hakan yasa ta sha ruwa kawai ta kwanta cikinta na kugi don wake da taliya aka yi daren ranan. Bayan kwana biyu tana xaune ita kadai tsakar gida tana tankaden uban garin masaran da Hajiya salaha ta hada ta shi, duk kayan jikinta ya koma fari kamar warce ta yini a kusa da injin nikan, ga hawaye da ya bubbushe fuskarta, a kan tankaden nn tun safe Hajiya Salaha ke dukanta da tayi sai tace bai yi ba, hakan yasa take yi a hankli ynxu bayan ta ci kukanta ta koshi, bude gate aka yi ta daga kai ta ga Ummarta, still tayi rike da rariyar, kamar yanda ita ma Umma ta tsaya kallonta ko kiftawa bbu, hawaye ya cika idon khadijah ta mike da gudu ta nufeta ta rungumeta tace "Ummata" sosai Umma ma ta rungumeta duk jikinta yyi sanyi, can ta janyeta jikinta tana kallonta daga sama har kasa, hawaye ne ya cika idonta ta mata alamar ta dauko takalmarta, khadijah ta koma ta dauko takalman da duk sun tsinke ta sa su haka, Umma ta ja ta suka fice daga gidan, Khadijah dake ta bin ta tace "Ummata tafiya xa kiyi da ni?" Hawaye na sakkowa idonta tayi tambayar, Umma ta gyada mata kai kawai don ta kasa cewa komai, suna isa dai dai gidansu Sadeeq khadijah dake murmushin farin ciki tana rike da hannun Umma gam tace "Umma I have a frnd here, can I just go and bid him goodbye, he is more than kind" Umma ta kalleta for d 1st time ta bude baki cikin sanyin murya ganin hawayen dake ta sauka idon khadijar, tace Some other time dear, khadijah ta gyada mata kai har suka wuce kofar gidan, da sauri Umma ke janta har suka isa main road ta tsayar da adai daita, direct sai motor park, ta biya masu kudin mota bayan yan mintuna motarsu ya tashi xuwa garin kano, bacci Khadijah ta dinga yi jikin Umma don tun asuban fari aka tasheta a can gidan, har suka isa kano bacci take yi, Umma ta tasheta, ta bude ido a hankali, suka sauka cikin motar Umma na rike da ita suka fito bakin titi ta dau adai daitan da xae kai su har gidan da take aure. Ba laifi babban tsakar gida ne compound din mai dauke da small building har hudu, ko wani building na da parlor da daki a cikinsa, sai babban kitchen dake tsakar gidan, da kuma bayin wanka biyu da toilet ma biyu, a gefen kitchen kuwa ga rijiya a rufe, gidan da Umma ke aure kenan, tana kuma auren d'an kasuwa ne mai mata biyu, yara ne su kusan biyar ke ta wasa tsakar gidan da yake da yamma ne kuma ranan alhamis ba islamiyya, da wasu yan mata uku dake xaune kan tabarma suna danne dannen waya, umma ta amsa gaisuwar da yara kananan ke mata ba tare da ta sake kallon gun da yan matan suke va ta fiddo key ta bude part dinta, khadijah dai na tsaye sai kallon yaran take kamar yanda su ma ke kallonta, can ta kalli yan matan taga su ma kallonta suke, Umma ta kalli direction din kitchen jin kamshin girki suka yi ido hudu da Shafa kishiyarta dake lekosu ta cikin kitchen din, suna hada ido kuwa tayi saurin dauke kanta, Umma ma ta dauke nata kan, can ta hango uwar gidan mai gidan nata ita ma tana lekota ta windown parlornta ita ma suna hada ido tayi saurin dauke kai, Umma ta bude kofar ta ta ja hannun Khadijah suka shiga ciki ta dage labule ta daura kan kofar kasancewar parlorn ya dau xafi. *NOOR-AL-HAYAT* Khadijah ta xauna kan kujera tana kalle kallen parlorn tace "Umma nan ne gidan ku koh?" Umma ta bude fridge xata dauko mata ruwa tace "Ehh" Karban ruwan tayi tace "Umma yunwa nake ji ban ci komai ba" Umma tace "Toh me xa ki ci yanxu?" Murmushi tayi da ya bayyana fararen hakoranta ta langwabar da kai tace "Indomie Ummata" Umma ma ta yi murmushin ta juya ta fita, Khadijah ta dinga bin madaidaicin parlon da kallo kai kana ganinta kasan she is just happy, muryar Umma taji tana kiranta daga waje ta fita da sauri ta sa takalminta tace "Gani Umma" Umma ta mika mata ruwa a buta tace "Gashi ki fara yin alwala kiyi sallah" tace "Toh" sannan ta durkusa tana alwala tana yi tana kallon yaran dake ta kallonta har da matar dake girki a kitchen, Umma ta shiga kitchen din ta dauko indomie daya ta fito ta kai parlorn ta sannan ta dawo rike da naira dari tana mika ma wani yaro da baxai wuce shekara biyar ba tace "Mudassir je kanti ka amso min kwai biyu" yaron ya karba ya wuce waje da gudu, Karamin tukunya Umma ta daura kan electric madaidaici dake parlorn ta bayan ta shimfida ma Khadijah darduma, khadijah na idar da sallahn Umma tace "Kin fara xuwa school a can gidan" girgixa kai tayi tace "A'a, kin san me Umma ta" Umma tace "Bari ki ci abinci" soya mata kwan da yaron ya kawo Umma tayi sannan ta ajiye mata a gabanta da ruwa a cup ta mayar da wani tukunyar ta sa mata ruwan wanka, Umma tayi tagumi tana kallon yanda take cin abincin, kana ganinta kasan yunwa kawai take ji, kafin ta gama Umma ta juye mata ruwa ta kai bayi da sabulu, ita ta rakata bayin sannan ta koma parlorn, khadijah na gama wankan ta fito daure da xanin da Umma ta bata, Shafah dake girki daga cikin kitchen ta bi ta da wani kallo hakan yasa tace "Ina yini" dauke kai tayi kamar bata ji ba, khadijah ta wuce cikin parlorn Umma tace "Wannan matar dake girki na gaisheta bata amsa ba" Umma tace "Kar ki sake gaisheta" daga haka ta cire hular kanta bayan ta kawo mata man shafawa, sakin baki tayi tana kallon gashin don tun kalaba shidda da ta yi mata kafin kawu ya tafi da ita kasancewar gashinta na da tsayin bala'i kuma bata son ana taba shi, Umma bata dai ce komai ba, ta dau gyalenta tace "Ban ce ki fito ba ki jira ni har in dawo" khadijah tace "Toh" daga haka Umma ta fita, bayan kusan minti ashirin ta dawo rike da Leda ta sake labulen parlorn ta bude ledan ta fiddo wasu dinkakkun riga da skirt kana ganinsu dai kasan taje ta karbo su ne tace "Tashi ki sa, gobe xan je kasuwa in siyo maki kaya kinji" khadijah ta sa kayan tace "Umma in kunna TV?" Umma tace "Ban ce ba" kwanciya tayi kan kujera bbu bata lkci bacci ya dauketa, Umma ta xuba ma jikinta ido ganin shattin duka, tagumi tayi tana kallonta tana tausaya ma marainiyar. Khadijah na tsugunne tana alwala tsakar gida da magrib bayan Umma ta tasheta tayi sllh taji an fixge butar daga hannunta ta daga kai tana kallon yarinyar da baxata wuce ta ba, Yarinyar ta murguda baki ta tafi ta kara ruwan ta fara alwala, mikewa khadijah tayi tace "Are you okay?" Yarinyar ta balla mata harara tace "Ki fadi wanda xan ji mana" khadijah bata sake cewa komai ba har yarinyar ta gama sannan ta wuce da butar parlornsu, khadijah ta xaro ido sai kuma ta juya ra wuce gun Umma dake parlor ta tsaya bakin kofa a hankali tace "Umma wata yarinya ta karbe butan ta tafi da shi" Umma ta fito tace "Wace yarinya?" Nuna mata parlorn da yarinyar ta shiga tayi, Umma ta kama hannun ta suka je har kofar parlorn ta bude labule tace "Wacece a ciki" Khadijah ta dinga bin yara kusan biyar dake parlorn da kallo sannan ta nuna mata yarinyar, Umma tace "Rahmah dalilin me kika karbe buta tana alwala?" Yarinyar da ta tsuke baki tace "Toh Anty namu ne ai" Umma tace "Kar ki sake, idan ko ba haka ba sai na bata maki rai" daga haka ta ja hannun Khadijah suka bar wajen ba tare da ta bi ta kan Uwarsu Hasana dake xaune parlorn ba, Umma ta dauko buta parlorn ta ta bata, Wata yarinyar ce ta shigo parlorn da abinci a er warmer ta ajiye ta juya ta fita, Umma ta daga kan khadijah dake kafarta a kwance tana bata labarin abubuwan da aka dinga yi mata gidan Kawu sannan ta mike ta jawo warmer din, shinkafa ce da miya sai nama biyu da salad a gefe, iya cin ta ne abincin, ta daura dankwali ta fita xuwa kitchen din ta dau wani plate ta bude tukunkya xata debi abinci sai ga Shafah da sauri tace "Amma dai Amina kinsan ba ke ce da kitchen ba, don haka baki da hurumin shigar min kitchen" Umma ta kalleta tace "Ae kin gan ni da bakuwa kika yarfo min er shinkafa a cooler kamar mayunwaci, don haka ke ma baki da hurumin hana ni debar mata abinci" Shafah tace "Bakuwa? Kin gaya min xaki yi Bakuwa in sa girki da ita ne, to wllh kin yi kadan ki kara diban wani abincin don na almajirai ne" Umma ta Debi shinkafar kusan cikin plate ta xuba miya kai da nama biyu tana kallonta tace "In ji duka" daga haka ta fice daga kitchen din Shafah tace "Ai kuwa ni da ke shege ka fasa Amina, mu xuba" tsaye Umma ta ga Hasana bakin nata parlorn tana lekosu tana ganinta ta shige ciki da sauri Umma tayi tsaki ta shiga ciki ta ba Khadijah abincin hannunta. Da yake khadijah tayi baccin rana har karfe goma idonta biyu tana ta ba Umma da tayi tagumi tana saurarenta labarai iri iri, Yar Shafa ta farko fadila ta bude kofa tace "Abba yana kiran ki" daga haka ta juya ta bar gun, mikewa Umma tayi ta fita tare da Khadijah tana rike da hannunta suka tafi turakar mai gidan, ba wani babba bane mai gidan don baxai wuce 48 ba, Shafah na xaune kan kujera da Hasana a gefenta, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah k'asa ta xauna ita na, Gaishe da shi tayi, khadijah na kallonsa tace "Good evening Sir" idonsa a kanta yace "How are you" tace "I am fine" Shafah da Hasana aka kyabe baki, mai gidan da suke kira da Abban Fadila yace "Wacece wannan Amina?" Umma tace "Kayi hakuri na so kiran ka tun kafin in iso kano daxu sai da bani da charge, duk da mun yi da kai gobe xan dawo kawai kuma na fasa, wannan 'er marigayin tsohon mijina ce Khadijah, na taho da ita ba tare da ixinin ka ba, kayi hakuri ban ji dadin yanayin da na same ta bane shi yasa na daukota bbu shawara da kai" shiru yyi bai ce komai ba, can ya jinjina kai yace "Toh Allah ya kyauta" Su shafa aka kwalalo ido ana kallon khadijah jin wai er kishiyarta ce da ta rasu, Abban fadila yace "Dalilin ki na shiga kitchen ba ke ce da girki ba daxu nake son ji? Shi yasa ma na aika a kira ki" Umma tace "Ehh toh, sun ganni da yarinya mun dawo Abban fadila, sai da aka tashi xubo min abinci da magrib sai aka xubo dai dai wanda ni xan ci a yar cooler" yace "Shine aka ce ko shiga ki diba? me yasa baxa ki nemi izini gun mai girki ba ko kuma kice ta k'ara maki kina da bakuwa, ke ce kadai me karya min doka a gidana fa Amina" Umma tace "Watana kusan uku gidan nan yaushe da yaushe na karya maka doka Alhaji?" Hasana sai wani blushing ake Shafa na taya ta, Abban fadila yace "Toh tashi ki je" mikewa tayi ta daga khadijah da su Hasana aka bi da harara ta fice parlorn ta koma nata, daki ta nuna ma khadijah ta tafi ta hau saman gado ta kwanta, khadijah tace "Toh Ummata" sannan ta shiga dakin ta kwanta hade da lumshe ido don har ta mance Rabon da ta hau gado har tayi bacci a kai. Washegari da asuba Umma ta tada Khadijah taje tayi sallah bayan ita ta idar, khadijah ta fita tsakar gidan rike da buta tana mitsika ido, yara ne kusan biyar ko wanne na alwala tana kokarin shiga bayi tayi fitsari taji an fixgota ta juyo da sauri a tsorace, yarinyar da ta kawo ma umma abinci jiya ce, tana kallo yarinyar ta shiga bayin, ta ja gefe a hankali ta tsaya tana jiranta, bata gaya ma Umma abinda ta sake yi mata ba, bayan ta idar da sallah ta koma daki ta kwanta ta ci gaba da baccinta. Gari na fara wayewa Umma ta kuma tashinta daga baccin ta kai mata ruwan xafi bayi da sabulu da soso, ba a dau lkci ba khadijah ta dawo tana wasa da yatsunta a hankali tace "Umma wata yarinya ta fitar min da ruwan ta sa nata ta rufe bathroom din" fita umma tayi ta tafi kofar bayin da sauri tana kallon xanin waye kafin tayi kwafa ta nuna ma Khadijah kujera tace "Xauna nan ki kyaleta kawai, idan ta fito ki shiga" khadijah ta xauna tace "Toh" umma ta koma ta ci gaba da sharanta, yarinyar na fitowa khadijah ta mike ta shiga da ruwan da kyar ta juyo xata dau sponge case wata ta sake fitar da ruwan nata ta hankadota waje ta shiga ta rufe kofa, tsaye khadijah tayi baki bude tana kallon bayin, dai dai fitowar Umma da abun kwashe shara da tsintsiya, karasawa tayi da sauri ta tura kofar ta janyo ruwan waje ta fiddo sabulun yarinyar sannan ta dau na Khadijah ta saka tana kallonta tace "Xo ki shiga" yarinyar ta fashe da ihu tana buga kafa, khadijah dake kallonta baki bude a hankali tace "Why are they behaving like this" Umma ta shigar da ita bayin tace "Maxa ki fara wanka" Hasana ce ta fito da sauri jin ihu da kukan yarta, tana kallonta a gigice tace "Walida ya aka yi, me ya faru" cikin kuka walidar tace "Xan shiga inyi wanka shine Anti ta fiddo min ruwana ta fito da ni ta saka yarinyar da ta kawo cikin bayin" Hasana da tayi mitsi mitsi da ido tace "Toh Allah ya isan ki, kuma mu xuba da su a gidan nan xan ga ko agolarta xata samu gun xama, ita ma da take a dosane ta ji da kanta mana, tsabar munafurci da neman kugun xama taje ta jajibo yar kishiyar da kilan ma ita ta kasheta ta kashe ubanta, shege ya fasa mu da ita a gidan nan" Umma bata ko kalleta ba ta shiga share kofar parlorn ta, Shafa ta fito tace "Ya aka yi ke kuma da sassafe, ke da wa?" A fusace Hasana tace "Ki rabu da yar kaxa kaza, wai Walida ce xata shiga wanka shine ta fiddo mata da ruwan ta ta saka na shegiyar da ta kawo mana mai kama da aljanu" Shafah ta rike ha6a tace "Ikon Allah Walida da xata makaranta? Ita kuma agolar da take gida, Mutum dai bashi da aiki sai neman fitina, banda jakanci ma ina aka taba dauko agola ace xa a takura ma masu gida dominta" Hasana tace "Ke fa kika san jakanta, amma ni nasan maganinsu wllh, kuma xa mu sa kafar wando guda da su" daga haka ta kalli yar ta tace "In ta fito ki kwara ruwa bayin ka fin ki shiga, Allah dai ya tsine duk mai son takura ku gidan ubanku ehe" daki ta shiga tana ci gaba da kumfar baki, Shafa ta bi bayan ta tana cewa "Amin dai, Allah kuma ya kawo mana karshen bala'in nan, muna xaman xamanmu dai" Khadijah bata fito ba duk da ta gama wankan, sai leken tsakar gidan ta kofar bayin take taga ko sun tafi, ganin Walida ce kadai xaune tsakar gida ta fito tana gyara daurin da tayi ma Xanin jikinta ta ta nufi dakin Umma da sauri, taji Walida tace "Shegiya kawai" kallonta khadijah tayi tace "Back to sender" sannan tayi saurin shigewa dakin ummanta. Kafin karfe bakwai da rabi duk yaran gidan an shirya wucewa makaranta, jin muryar Abban fadila a waje, Umma ta kalli khadijah tace "Go outside and greet him. Come back immediately after that" khadijah ta fita waje ta gansa tsaye ya shirya alamar xai fita kasuwa yana sauraren yaransa mata biyu da suke requesting kudin wani littafi da xa su siya a boko ga iyayensu tsaye bakin kofa, Khadijah ta karasa kusa da shi ta durkusa a hankali tace "Good morning sir" ya kalleta yace "Morning yar turawa, how was ur nyt?" Ta washe hakora tace "It was splendid" yace "Good, ina mamar taki?" Ta kalli kofa tace "Tana ciki" yace "Kira min ita" Shafa da Hasana da lkci daya mood dinsu ya canxa suka kalli juna, juyawa khadijah tayi taje kiran Umma suka fito a tare, Yace "Naga baki shigo gaisheni ba" Umma tace "Bayan nayi sallah I just slept off" yace "Ohk, anjima sai ki je ki mata registern islamiyya ko xuwa next week sai a samu boko a sata" Umma tace "Toh nagode, Allah ya kai mu" Naira Dari ya Ciro ya mika ma khadijah yace "Gashi ki siya biscuit" xaro ido tayi ta kalli Umma, Umma tace "Amsa" ta karba da hannu biyu tana murmushi tace "Nagode uncle" daga haka Umma ta ja ta suka shiga ciki ba tare da ta yarda ta kalli inda kishiyoyinta dake cika suna batsewa suke ba, Shafa tace "Toh Abban Fadila kudin kitso da na tambaye ka tun jiya fa?" Hasana tace "Ni tun shekaranjiya nake ta bi ya sa min kati amma kinga wani gwaninta a nan" Tuni ya isa kofa bayan ya sallami yaransa mata dake turo baki kudin bai ishesu ba, sai da ya fita gidan, Hasana tace "Toh wllh abinda baxai yiwu ba kenan, ya gama ji da nasa yaran mana, har xa a kara daura masa nauyi bayan wanda ke kansa, ko ita yarinyar bata da dangin uba ko uwa ne sai karere??" Shafah tace "Ke fa kika San karere, ita nan gwaninta take a idon duniya ko, toh kuwa xata sha kunya in har bata mayar da yarinyar nan gun dangin ubanta ba, sai yarinyar nan ta ja mata masifa da bala'i sai kuma ta dauko mata abun kunya muna nan dake, sai dai idan ba ni ce nan Shafa'atu yar gidan Sanusi jikar Yakubu na bude baki na yi magana ba" Hasana tayi shewa tace "In sha Allahu kuwa" Umma dake ta jin su ta girgixa kai tana murmushi a ranta tana masu addu'ar samun sauki, sai bayan da duk suka gaji suka shiga ciki ta dauko kibiya da comb xata tsefe ma khadijah gashinta, Tuni khadijah ta fara matsar kwalla tun kan ta kama kan din right from Beginning idan ana son tashin hankali toh a taba gashinta, sosai ta ba Umma wahala ta dinga rusa kuka tana ihu, har dai aka gama tsefewa ta bata Hijab ta sa suka fito don xuwa saloon a wanke mata gashin, da ido su Hasana suka bi su har suka fita. Sai kusan azahar suka dawo gida, Idon khadijah ya kumbura don kuka, Hasana na xaune tsakar gida tana jajjagen tafasasshen nama da alama dai dambunsa xata yi, Shafah kuma na daga xaune bakin kofa suna ganin shigowarsu suka yi shiru daga xancen da suke ko wacce ta hade rai, Umma ta bude kofar ta ta ja khadijah suka shiga ciki, xaunawa khadijah tayi kan kujera Umma na harararta tace "Duk kika tsefe kan nan ke kadai xaki saloon din baxan iya wahala ba, dubi idanuwanki kamar warce aka yi ma duka, ke ba yarinya ba ki dinga ma mutane ihun kitso" Khadijah ta kwanta kan kujera bata ce komai ba, Umma ta fita ta shiga kitchen ta dau indomie biyu ta fito, Hasana ce tace "Gaskiya Abban fadila ya dawo ya kasa ma kowa indomie ya ajiye a dakinsa tun jiya ake ta shiga ana daukar indomie abinda yaran gidan ma sai su yi sati basu ci ba, wnn ai mugunta ce" Umma tayi yar dariya bata ce komai ba ta shiga ciki, dama da kwai hudu ta dawo gidan, don haka ta girka indomien a daki ta dafa kwan ta tada khadijah da ta fara bacci ta bata nata sannan ta fita yin alwala, Da daddare yau ma kamar jiya a karamar cooler shafah ta aiko ma Umma abinci, Tea ta hada da yake tana da kayan shayin a daki ta fita da kanta ta siyo bread ta ba khadijah ta ci ba tare da ta bi kan yan gidan ba. A can katsina kuwa neman duniya kawu da matansa sun ma khadijah amma bbu ita babu labarinta, gidan da suka fara xuwa kuwa gidansu sadeeq ne, nan mahaifiyarsa ta nuna masu the other side of her don har sai da suka tsorata kuma tace kada warce ta sake shigo mata gida, har station kawu yaje da gidan radio, bai taba kawo wa cewa Umma ta san gidansa ba balle ta xo ta dauke khadijah, Duk da ba wai abun ya wani dame su Hajiya salaha da Hajiya maimuna ba amma ganin yanda mai gidan nasu ya dage yana nemanta yasa su ma suka xage, har shawara Hajiya salaha ta bada su kai karar Hajiya Amina da d'anta, kawu ya gwaleta cike da masifa yace "Kinsan waye uban yaron?" Hajiya Maimuna tace "Alkali" Kawu yace "Shine xata dinga magana kamar mahaukaciya?" Ita dai Hajiya Salaha bata ce komai ba. Washegari da safe Umma ta fita tare da Khadijah don sama mata islamiyyan da xata fara xuwa, bata yrda ta kai ta wanda yan gidan ke xuwa ba ta kai ta wani dake gaba da shi sosai, bayan ta biya komai ta wuce kasuwa tare da ita don yankar mata uniform daga can tayi mata siyayya kananun kaya. Da yammacin ranan Umma ta amshi girki, tuwon shinkafa da miyar vegetable take girkawa, Khadijah na xaune kan tabarma bakin kofar Umma tana cin gyadar da Umma ta siya mata a hanyarsu ta dawowa, da ta bare sai ta jefa ma wani kadangare dake tsakar gidan yana yawo bawon gyadar, tsawa taji an mata ta waiga da sauri Hasana da fitowarta kenan tace "maxa tashi ki tsince su don baki da bawa mai shara a gidan nan" Umma kallo waje tayi daga kitchen din bata dai ce komai ba ta ci gaba da girkinta, mikewa khadijah tayi ta isa gun da ta ke ta jefa bawon ta shiga tsince su tana xubasu a shara har ta gama, Hasana ta nuna mata wasu bola dake kusa da kofar Shafah wai taje ta tsince, Umma ta fito tace "Wannan kuma ne baki isa ba" kujerar da ke kusa da kofar kitchen ta nuna ma khadijah tace "Sit here" khadijah ta karasa da sauri ta xauna, Hasana ta rike ha6a tana kallon Umma bata dai ce komai ba. Umma bata bar khadijah ba sai da ta tabbatar ta yi bacci sannan ta tafi bangaren Abban Fadila, bata yi mamakin ganin kishiyoyinta ba a xaune parlorn, da kuma alamar yana shigowa suka bi sa don bai jima da dawowa ba, har Umma ta ajiye tray din abincin hannunta kallonta yake, ta xauna ta gaishesa, bai amsa ba yace "Dama kin taho da yarinyar nan ne don ki ci xarafin mutane Amina?" Umma ta kallonsa tace "Ban gane ba" yace "Toh daga yau kar ki sake nuna iko a kan ta Idan ba haka ba ki mayar da ita dangin ubanta, banda janyo yaro ya raina babba don me Hasana zata sa ta aiki ki hanata, akan me? Meye amfanin xamanta gidan idan baxa a ci moriyarta ba!" Umma dake saurarensa tayi murmushi tace "Tun da na shigo gidan nan cikin yaransu akwai warce na taba sa aiki ta min? Babu.... domin kuwa duk sun hanasu amma na taba kai maka kara? Ni wllh matan ka basu isheni kishi ba Alhaji, banda kaddara ba lallai su gan ni cikinsu ba balle su sa ni gaba, ina ce ni ka fara sani ma kafin su? Wllh basa gabana balle inyi kishi da su, marainiya ce dai na daukota sae dai bakin ciki ya kashe su tunda ba a kansu xata xauna ba" Tana kai wa nan ta fice daga parlon idan sun fita sai ta dawo. Ka'ida ce duk safiya a gidan su Fadila ne ke yin wanke wanken safe da sharan tsakar gida ko ma wacece ke girki kafin su tafi makaranta, yau kam suna tashi da safe wanka suka yi ko wanne ta tafi ta saka uniform, Umma bata ce masu komai ba tana ta soya dankalin irish da xa ayi breakfast da shi a gidan, Khadijah na durkushe kitchen din sai dai ta bude babban cooler a Umma ta xuba wanda ta soya, Umma ta gama soya Irish din da ta fere gaba daya ta soya kwai, kananun yaran gidan ne suka dinga tahowa karban nasu duk ta basu ko wanne sa cup din shayi da ta hada, Khadijah dake ta kallonsu tace "Umma why are they so plenty?" murmushi umma tayi tace "Just as the one ur uncles home" Khadijah ta langwabar da kai tace "Noo, they are nt as much as this" Fadila ce ta taho kitchen din tace "Anty ina kwana, ina dankalina" Umma ba tare da ta kalleta ba tace "Idan kin gama wanke wanken can xan xuba maki" juyawa tayi ta wuce sai ga Shafah ta fito, "Amina ban gane baxa ki ba Fadila kalachi ba, meye dalili" Ko tanka ta Umma bata yi ba, ta hau masifa tayi mai isarta daga karshe tace "Bar ta ita ce mayunwaciya Fadila, ta hada da Wanda ta ajiye ma kanta da agolar da ta kawo su cinye, mu je in baki kudi ki siya kosai da bredi a hanya, wanke wanken su shekara nan, in dai baxa ta ba ma agolarta tayi ba" daga haka ta wuce ciki Fadila na biye da ita a baya, daga Hasana har Shafah bbu warce tayi kalaci da girkin da Umma tayi, duk wainar shinkafa suka aiki almajiri ya siyo masu a makwabta, Umma kam ko a gyalenta, wanda ya rage ra kira almajirai ta basu ta hada kayan wanke wanke xata yi, Khadijah tace "Umma na iya wanke wanke fa yanxu xan yi" da kyar ta amince ta bar ta, Ganin yanda ta fara jika kayan jikinta Umma ta karbi kayanta ta shiga yi tace mata ta tafi daki ta kwanta. Da rana cous cous umma ta girka gidan d'an dai dai, daga ita sai khadijah a gidan don tun misalin goma su Shafah da Hasana suka fita basu dawo ba, ta dibar ma kananun yaran gidan a warmer ta kai can dakinta da miyar ta ajiye bayan ta xuba ma Khadijah, ta dawo ta tsaftace kitchen din ta wanke tukwanen da tayi amfani da su da utensils sannan ta koma ciki. Sai kusan karfe Uku su Shafa suka shigo gidan Hasana na cewa "Wash wajen nan ba dai nisa ba Maman fadila, na xata bai fi tafiyar minti talatin ba fa" Shafa tace "Nima farkon xuwa na na sha wahala sosai, ga hanyar bbu kyau mutum na mota kamar ya hau jaki duk jikina ciwo yake..." Shiru Umma taji sun yi suna kallon kofar ta, ita ke ganin su ta labule amma su basa ganinta, suka kalli juna basu dai ce komai ba, kitchen Shafah ta wuce, can sai ga ta ta fito tana kallon Maman walida tace "Ke kamar fa bata yi girki ba" Maman Fadila tace "Bata yi girki ba kuma? Kin ga uban yunwar da nake ji ga shi bani da kosisi kudin sun kare a kudin motar" Daga labulen Umma Maman walida tayi suka yi ido hudu, d'an kame kame ta fara da farko, sai kuma tace "Ba a da niyyar yin girkin rana ne yau a gidan nan ga yara su kusa dawowa" Umma tace "Ehh" sake labulen tayi ta bar wajen Maman fadila ta bi bayan ta, tana jin Shafah na jajjage a kitchen xa su dafa indomie, ita dai tana xaune inda take. Uku da rabi yaran suka dawo kuwa, nan Umma ta xuba ma kowa abincinsa ta ajiye masu tsakar gida, Shafah dake kan tabarma ta kalli kishiyarta dake bakin kofar ta ita ma a xaune, yaran suna gama ci suka fara shirin tafiya islamiyya, Umma ta sa Khadijah ta shirya cikin dinkekken uniform din da tela ta kawo mata daxu, sai murna take har ta gama shiryawa, har bakin makarantar umma ta rakata na ranan kadai sannan ta dawo gida. Umma na kitchen tana girkin dinner ta dinga jin kamar kukan khadijah, ta mike da sauri ta nufi kofar fita, su Shafah da Hasana dake xaune kusa da juna suka bi Umma da ido, a bakin kofa ta kusa cin karo da Khadijah ta riko hannunta tana kkrin cire Hijab din da ta rufe fuskarta tace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "Umma wannan yarinyar dake gidan nan ne ban mata komai ba na gansu a hanya, she just slapped my eyes and pushed me na fadi a kan wani dutse" Umma da ranta ya gama baci tace "Wace yarinya kenan?" Dai dai nan walida ta shigo fuskarta tsuke, Khadijah ta nuna mata ita tana shessheka, fixota Umma tayi ta wanka mata mari ta ja kunnenta tace "Don uwarki kika sake taba min 'ya sai na cire maki hakori wallahi, muguwa kawai mai halin banxa" daga haka Umma ta hankadata, walida ta fasa wani ihu kamar xata tsaga gida tana kiran uwarta. Mikewa Hasana tayi baki bude tace "Amina??? Ita walidar kika mara??" Umma ta juya tana facing dinta tace "An mareta, ki taho ki rama mata, d'a ya fi d'a ne, ai wllh duk shegiyar da tace 'ya ta baxa ta xauna lafiya ba gidan nan sai dai ita ta rasa xaman lafiya, me marainiyar ta maku? Ko ba a cin arxiki dama a duniya, kishin naku ya tsaya iya kai na mana, toh wllh duk ku ja ma 'ya yan ku kunne, duk wanda ya sake ko da yi ma khadijah kallon banxa ne, sai nayi masa abinda bai yi xato ba" tana kai wa nan ta tafi daki da Khadijah ta tura ta ciki tace "Maxa ki canxa kaya" daga nan kuma ta dawo kitchen ta ci gaba da abinda take rai bace, daga Hasana har Shafah haka suka bude baki suna kallonta bbu wanda ya iya cewa komai cikinsu. Da daddare Abban Fadila ya dinga kwalo ma Umma dake xaune kan darduma kira, ta mike ta fita don bata ma ji shigowarsa ba amma tuni har ya shiga parlon sa, bin bayansa tayi ta shiga parlon tana masa sannu da xuwa, bai amsa ba ta xauna ba tare da ta yarda ta kalli kishiyoyinta dake xaune parlorn ga Walida a durkushe a kasa, Abban Fadila yace "Amina, so nake xuwa gobe ki mayar da yarinyar nan dangin ubanta da kika daukota, I agree zan yi sponsoring dinta ko tana can din, idan ya so duk bayan watanni uku ko hudu sai ki je ki dinga dubata, I think that will better, I didn't buy d idea of her staying here anymore...." Tun da ya fara Umma ke kallonsa a sanyaye, Hasana da Shafah da aka wani hakikance kan kujera kamar wasu Hajiyoyi xa a iya ganin murnar dake shimfide fuskarsu, trying hard to control her tears Umma tace "Saboda me kace haka Alhaji? Kada ka mance yarinyar nan marainiya ce ba ta da kowa, tun tana yar shekara biyu mahaifiyarta ta rasu, mahaifinta kuma bai mata gatan nuna mata dangin mahaifiyarta ta ba, da na sansu da can xan kai masu ita baxan kawo ta ba gidan ka Alhaji" Abban fadila yace "Kiyi hakuri iyakar taimakon da xan ma yarinyar kenan, ko nawa ne kudin karatunta xan biya idan ya kama ma da feeding expenses duk xan ba da, kawai dai gidana ne baxata xauna ba, kuma baki min kara ba da har xaki daga hannu ki mari diyata a ido don abun su can ya hada su, so tafiyarta xai fi, I think that's all... Gobe ki hada kayanta ki maida ta inda kika dauko ta" Umma da hawaye ke xuba idonta a hankali tace "Ina jin da ka sauwake min kawai in tafi da ita xai fi don ni baxan mayar da ita dangin mahaifinta ba" yana gyada kai yace "Kema xa ki iya sauwake ma kanki ai Amina ba sai na sauwake maki ba" mikewa Umma tayi ta fita ta koma bangarenta, ta shiga daki tayi kukanta mai isarta, duk tausayin khadijah ya cika xuciyarta, to yanxu ina xata kai marainiyar nan, ita ba ta da kowa mahaifiyarta ta rasu da sai ta kai ta gun ta tasan xata rike mata ita, bata da wani abun hannu don duk cutar ta yayyin mahaifin khadijah suka yi a rabon gado bayan ya rasu, domin kuwa kafin a ankare sun boye abubuwa da dama cikin dukiyarsa, banda haka da ko boarding sai ta kai khadijah, har gari ya waye Umma bata ritsa ba tana ta tunanin inda xata kai khadijah domin ta ma kanta alkawari first thing da safe xata fitar da ita da gidan, yayarta warce suke uba daya dake Kaduna ta fado mata ta yi shiru tana naxari. Daukar waya Umma tayi ta shiga kiran layin step sister dinta Yakumbo amma baya shiga alamar dai wayar a kashe yake, da safe bbu abinda ta girka ma mutan gidan a madadin breakfast, ta dai hada ma Khadijah tea ta siyo mata bread ta bata, Karfe takwas ta shiga bangaren mai gidan nasu ta sanar da shi xata mayar da Khadijah gida, ya kirgo dubu biyar ya mika mata yace "Gashi ku yi kudin mota, idan kin dawo sai a san yanda xa ayi batun makarantar nata in ji ko nawa ake biya" Umma ta girgixa kai tace "A'a ka bar shi mun gode Alhaji, muna da kudin mota" Yace "Shi kenan, Allah ya tsare" mikewa tayi ta fita dakin, a cikin wata karamar jaka Umma ta hada ma Khadijah d'an kayan da ta fara siyo mata, suka fito parlor ta sa ma kofar kwado bayan ta rufe, khadijah dake sanye cikin doguwar riga da karamin Hijab tace "Umma ina xa mu?" Umma ta kasa kallonta tace "Xa mu d'an yi tafiya ne khadijah" daga haka ta kama hannunta suka nufi kofa, tana jin su Shafah da Hasana na dariya suna cewa "Toh a sauka lafiya, sai a kara gaba can da ita" ita dai bata tanka su ba har ta fita. Tasha suka tafi cikin a dai dai ta, can suka samu motar Kaduna, bayan wani lokaci motar ta cika suka yi set off xuwa Kaduna garin gwamna... Ko barin kano basu yi ba khadijah tayi bacci jikin Ummanta, har suka isa Kaduna bata tashi ba, suna isa kawo bayan driver yyi parking kowa ya fara alighting daga cikin motar, Umma ta tada khadijah suka sauka su ma, sai kalle kalle khadijah take tace "Umma where is this?" umma tace "Kaduna" Khadijah tace "Wow I've heard of Kaduna in school" Umma ta samar masu napep suka yi ciniki sannan suka shiga xuwa hayin rigasa Unguwar da yakumbo take, tafiya ce mai nisa kafin su iso rigasa, da yake Umma sunan layin kadai ta sani ba wai ta wani san gidan yakumbo bane a bakin layin tasa mai napep din ya sauke su ta basa kudinsa tana rike da hannun khadijah suka shiga layin umma na bin ko wani gida suka xo wucewa da kallo don ta haka kadai xata gane gidan yayarta kasancewar ta jima bata xo wajenta ba, sun fi minti talatin suna bulayi a layin, Khadijah sai tambayarta take "Umma where is this, everyway is dirty, they are smelly gutters everywhere" Umma tace "look I don't want to here ur mouth again" shiru khadijah tayi, daga karshe dai wata mata da ta gansu suna ta yawo ce ta tambayesu gidan da suke nema, Umma tayi shiru tana tuna sunan da aka fi sanin yakumbo da shi, can tace "Kulu mai waina" Matar tace "Ikon Allah, yo ai ga gidan can kun wuce" Umma ta juya tana kallon gidan da matar ke nuna mata, matar tace "Wancan gidan mai keke a gaban sa" Umma tayi murmushi tace "Kin ga kuwa sai yanxu na gane, gaskiya na nagode sosai" daga haka suka juya khadijah na biye da ita a baya, tsallake gutter din dake kofar shiga gidan Umma tayi Khadijah ma ta yi haka sannan suka shiga xauren gidan, gida ne ginin kasa duk ya kwarabe, Khadijah ta xaro ido tana bin gidan da kallo, Yakumbo ce xaune tsakar gida tana hura icce duk hayaki ya cika ko ina, Umma tace "Yaya" dagowa yakumbo tayi ta xaro ido tace "Aminatu" karasawa Umma tayi ta rungumeta tace "Rai kan ga rai yaya" cike da farin ciki Yakumbo tace "Sannu da xuwa Amina, daga ina haka? ya mai gidan naki?" Umma tace "Wllh daga kano Yaya, yana nan lafiya yace duk a gaida ku" Yakumbo tace "Maa sha Allah sai dai kin rame kan lokacin bikin, wacece wancan" Yakumbo ta fada tana nuna Khadijah, A hankali Umma tace "Yar marigayin mijina ce Alhaji Muhammad" Yakumbo ta rike haba tace "Ikon Allah gashi ta kusa xama budurwa, sun hakura sun baki ita kenan?" Umma tace "uhn, labari ne me yawa yaya bari dai mu yi sallah" Yakumbo tace "Gaskiya ne bari in kawo maku ruwa" tabarma ta fara shimfida masu kafin ta tafi debo ruwan alwala, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah dake tsaye gefenta, khadijah ta karaso tana tsattsallake bololin dake watse tsakar gidan, Umma tace "yaya ina mutan gidan?" Yakumbo tace "Toh jikokin nawa sun fita wasa, tun safe rabona da su, yaran makwabtana kuma duk sun tafi talla, iyayensu kuma aikatau suke na yini, Ladi ce kadai ta shiga makwabta daxu, nima anjima xan fita suyan wara da dankali a bakin titi" shiru Umma tayi jikinta yayi mugun sanyi, yakumbo ta kara da cewa "Ai Allah ma yyi ban tashi a gidan nan ba kika xo, don duk mai gidan ya ba mu notice xai rushe gidan wai, to gida ne duk ya rube" Umma ta kalleta da sauri tace "Ina xa ku koma yaya?" Yakumbo tace "Oho dai har yanxu ina lalube ne, kudin kama wani gidan ma ai xaune yake da kugunsa, talauci yyi yawa ta ko ina, ko daxu na fita duba gida don sati daya ya ba mu xai watsar mana da kaya waje" Umma tace "Ikon Allah" Yakumbo tace "Ai ke dai kawai sai du'a'i duniyar ta xama abinda ta xama" Yakumbo ta kalli khadijah da ta takure gu daya tace "ke yar nan tashi ki fita waje gun mai kanti ki siyo min farin maggi" Umma tace "Yaya ai bata san ko ina ba" Yakumbo tace "Ka ji ki, nan nan ga masu kanti kamar jampa a jos ta ko ina a anguwar nan, tana fita duk inda ta bi akwai mai kanti" daga haka Yakumbo ta kunce kullin xaninta ta fiddo wani naira ashirin dake a dunkule ta jefa ma khadijah, mikewa khadijah tayi ta karasa ta duka ta dau kudin tana kallon Yakumbo tace "How much own" yakumbo ta d'an bude ido tace "Eh??' Umma tace " twenty naira" khadijah ta juya ta fita, yakumbo tace "Sai na ji kamar yare tayi" Umma tayi murmushi tace "Turanci tayi" Yakumbo tace "Au tohhh abun na manya ne Ashe" ita dai Umma bata ce komai ba ta mike taje tayi alwala ta dawo tayi hau kan tabarman ta tada sallah, jin shiru shiru Umma na idarwa ta bi bayan khadijah, a bakin xaure suka kusa cin karo Umma tace "Ina magin kuma me ya sa kika dade?" Khadijah tace "Umma I've forgotten the one she mentioned" Umma ta hade rai tace "Bani kudin" mika mata khadijah tayi ta umma ta koma ta dau dari a Jakarta ta fita, farin magin hamsin ta siyo mata da maggi star saba'in sannan ta dawo gida, garau garau na dafaduka Yakumbo ta girka masu, ta xubo a faranti. Umma kadai ce ke cin abincin a sanyaye tana tausayin khadijah dake tsintar shinkafar, yakumbo kuwa na ta yankan warar da xata fita soyawa kamar yanda tace suna yi suna hirar xumunci da yar uwarta, la'asar nayi Yakumbo ta kira almajiri ya kai mata kayan bakin titi gun da take suyar, Tana kokarin saka Hijab dinta da yyi dukun dukun tace "Toh Amina xan fita kasuwa, idan kun ji yunwa ku kara deban abincin, sai ki d'an taimaka ki share min daki ki fiddo kayan wanke wanken ki ajiye su bakin kwararon can ko yarinyar nan ki sa tayi" Umma tace "Toh yaya, amma fa har yanxu yaran basu dawo ba" Yakumbo tace "Rabu da gantalallu suna makwabta na sani, idan yunwa ta kwakulesu xa ki ga sun dawo da daddaya da daddaya" daga haka yakumbo ta fita rike da roban dake dauke da dankali a ruwa, Umma ta bi ta da kallo, Khadijah ta yatsine fuska tace "Umma the food is somehow" Umma ta hade rai tace "Haka nan xa ki ci, ko ni ma baki ga hakan na ci ba" Khadijah bata ce komai ba, Umma ta mike ta shiga d'an karamin dakin yakumbo, har wani wari dakin yake gashi bbu ventilation don windown dan karami ne, ga kaya ta ko ina, plastern dakin duk ya faffashe gashi ko leda babu, jikin umma yyi sanyi ta daga dan karamin katifar da tayi bakikirin ta shiga gyaran dakin ta fidda duk kwanukan da har da funfuna jikinsu sannan ta fara sharan dakin. Ko da ta fito bayan ta gama bacci ta tarda khadijah na yi, ga shinkafar ta bar sa, Umma ta tada ta ta bata Dari biyu tace "Kije kantin da kika je daxu ki karbo Nutri milk da biscuit din hamsin ki xo ki ci" Karba khadijah tayi ta fita. Sai kusan karfe biyar jikokin yakumbo uku suka dawo gidan sun yi dukun dukun da dirty, duk kanana ne yaran, Umma ta masu wanka da sabulun wankin da ta gani, ta xuba masu abinci, Khadijah dai na xaune sai kallonsu take da wani expression, nama Umma ta fita ta nemo a anguwar ta xuba masu kan abincin ko khadijah xata ci, nan ta tsince naman ta bar mata shinkafar wai ta koshi, sai dab da Isha yakumbo ta shigo gidan tare da Almajiri da ya dauko kayan suyanta, Sannu ta dinga ma su Umma, Umma ta mike ta taya ta karban kayan.... sha dayan dare bayan su khadijah sun yi bacci Umma ta shiga yi ma Yakumbo bayanin abinda ya kawo ta da Khadijah, bayan yakumbo ta gama saurarenta tace "Ikon Allah, mugunta fa yyi yawa a duniyar nn yanxu ki kuluwa" Umma tayi shiru bata ce komai ba, Yakumbo ta kyabe baki tace "Toh ni wannan ai ba matsala bace, don dai in rike marainiya, bakomai wllh" Dubu 30 Umma ta kirgo ta ba yakumbo tace "Wannan sai ki siya kayan abinci da indomie ki ajiye yaya" makaranta kuma ayi mata Register da ta gwamnati idan Allah ya hore min sai in canxa mata, dubu ashirin ta kuma bata tayi ma khadijah siyayyar makaranta, yakumbo ta dinga godiya kamar ita ta ba kudin, sai kusan karfe daya suka kwanta bayan yakumbo ta gama tsine ma matan mijin Umma, da su kawu. Washegari da safe Umma ta dau hanyar kano bayan ta rubuta ma Yakumbo lambarta kan cewa duk inda suka koma ta sanar da ita in case xata dawo duba khadijah, dubara aka ma khadijah aka aiketa daga nan Umma ta samu ta bar gidan duk jikinta a sanyaye, da Khadijah ta dawo ta kyallara ido taga ba umma ta dinga ihu tana kuka a gidan tana cewa a kai ta gun ta, Bakin yakumbo a leko ta dauko muciya tace "Kin ga wannan abun hannu na? To wllh da shi xan fasa maki kai idan kika ci gaba da tona min asiri a anguwa, kaji min katuwar banxa, maxa ki tafi tare da Fauxiyya ku siyo min ice da xan yi tuyan awara anjima" Jikin khadijah na bari suka fita, matan gidan dake ta kallon ikon Allah suka ce "Yo ke kulu da kike jiran fauxiyya ta kara wayo ki kai ta aikatu kina samun kudi don me baxa ki kai wnn budurwar da aka kawo maki ba? Ai wannan da ganinta bbu aikin da baxata iya ba har wanki" Yakumbo tayi shiru tana kallonsu. Ko da suka dawo gidan firewood kwara biyu kadai khadijah ta riko a hannu, fauziyya kuma ta rike ya kusa shidda, daga matan gidan har Yakumbo sakin baki suka yi suna kallon Khadijah da ta ajiye tana haki, yakumbo tace "Meye wannan din kika dauko?" Da kyar khadijah tace "Firewood, it's too heavy, and it's pricking me all over" a fusace Yakumbo tace "Kin ma uwar ki Amina turanci ba ni ba, kuma ke kadai xaki koma ki kwaso duk wanda ga rage fauziyya baxa ta je ba tunda ba ki da mutunci" korata Yakumbo tayi ta fita ta na share hawayen dake sakko mata, mai firewood din ganin yanda take hawaye kuma kana ganinta kasan baxata iya dauka ba ta dauko wani rabanta ta xuba mata su a ciki ta daura mata a kai tace "Kina kai wa ki dawo min da roba na kin ji" a hankali khadijah tace "Toh nagode" A haka ta isa gida tayi ta tsayuwa da roba a kai wai bbu ke sauke mata inji Yakumbo, daga karshe ladi ta kike ta sauke mata tana cewa "Idan ka xa ki kama jiki ki kama jiki ki daina ma mutane kamar mara laka a jiki" Khadijah dai bata ce komai ba, bayan ta juye iccen tace ma yakumbo xata mayar da roban, ko kallonta yakumbo bata yi ba ta juya ta fita kai ma mai iccen robar ta. Yakumbo ce tsaye tsakar gida bayan kwana uku da xuwan su Umma, tafi minti talatin banda kumfar baki da masifa bbu abinda take, ga matan gidan da yaransu a xaune babu mai bata hakuri sai ma xugata da suke, khadijah kuma na tsaye bakin xaure duk tayi wani duhu ta rame sosai, idonta duk ya kumbura don kuka ga shatin bulala a jikinta, Ladi tace "Yo da kinsan haka ne tun farko kema ai baxa ki fara daukarta ba, meye amfanin yaron da baxa ka amfana da shi ba sai shegen son jiki da iyayi, ai kadan ma kika mata da kin hada kin fasa shegen bakin turancin da take xagin mutane da shi a gidan nan" Yakumbo na huci tace "Ai Amina ta cuce ni, ta yaudare ni... Tasan haka shegiyar yar take xata kawo min ita tun farko, gode gode da yarinya bata iya komai ba wanke wanke duk ta jika kayan jikinta tayi awa da awanni a bakin kwararo, shara duk a gantale, gyaran daki gwara ka da fauziyya mai shekara biyar, aike sai kayi yyi sau uku, har yau ta kasa iya hura icce, girki dama ba a maganar sa, wa ennan yan mitsimitsi yaran idan na sa ta tayi masu wanka ta shaka masu sabulu a hanci ko a ido, ni dama tun farko abinda ya sa na karbeta na yi xatan xan amfana da ita ne, banda haka me xai kai ni kowa na ta kansa a rayuwar nan gashi gobe ko jibi xa a xo a fitar mana da kaya har ynxu ban kama wani gidan ba, ni wllh wllh da nasan gidan Amina sai in yi kudin mota in mayar da ita ta bani kudi na don baxan iya kayan tsiya ba, dama can Aminar ma ba wani kyautata min take ba uba ne kadai ya hada mu" Salamatu tace "Ai irin yaran nan kyansu aikatu wllh, a can xa a horasu su ladabtu...." Katse ta yakumbo tayi tace "Yar da har yanxu bata iya shara ba xan kai aikatau, ai koramu xa ayi daga ni har ita" Ladi tace "Yo ke nuna masu xa ki yi bbu abinda bata iya ba ai, a can xa su gyara mata xama ta iya komai, mutanen da basu san darajar d'an Adam ba, ai tuni wahalar da xa su dinga mata xai sa ta xage a nan kuma xata koyi komai, wannan d'an abincin da kike bata ma take kin ci take yawo da yunwa can nema xata yi ta rasa, hakan xai ladabtar da ita wllh" Yakumbo ta ja kujerar tsugunno ta xauna tace "Kai amma fa kun kawo shawara, amma...." Sai kuma tayi shiru ta kalli khadijah dake kallonsu, tsawa tayi mata ta ce "Fita ki ban waje kije gun mai kanti da hamsin di ta dake gunsa ki amso min barkonu" juyawa khadijah tayi da sauri ta fita gidan, Yakumbo ta mayar da dubanta gun su Ladi tace "Toh Amina fa? Kunsan baxa ta yarda ba" dariya Ladi tayi tace "Ka ji ki, sai ki gaya mata, barin ma yanxu tashi xa ku yi Ku bar anguwar, shawara a nan shine kada ki kuskura ki gaya ma ko inda kika koma a anguwar nan, kawai cewa xa ki yi ba ki ma samu gidan ba gidan wata yar uwarki xa ki kafin ki samu, ke kuwa kije shanono abun ki ki kama ko daki daya ne bbu wanda yasan inda kike, dama ba waya gare ki ba, har ki tara kudin da xa ki tara da yarinyar daga nan idan ma mayar da ita gun Aminan xa ki yi sai ki ja mata kunne ki mayar da ita" Yakumbo tayi murmushi tace "Dadina da ku akwai shawara mai ma'ana, amma fa har da kudin da xan sa yarinyar a makarantar gwamnati ta bani, yanxu haka ma da kudin xan je kama haya a shanonon, dubu hamsin kuma jari xan ja na su omo da sabulu ina siyarwa, ita can na kai ta gun aiki ana biyanta dubu uku misali, kun ga ni ban ma kai da nisa ba...." Ladi tace "Toh gaskiya sai kin ba mu dubu dai dai mu da muka kawo shawarar Ashe ma kudi gare ki har haka" yakumbo ta hade rai tana da ta sanin gaya masu, rai a bace tace "Dari bibbiyu dai" daga haka ta mike ta shiga cikin akurkin dakinta, sai ga ta ta fito da sauri tace "Toh yanxu wa xai min hanya in kai ta gidan aikin, don ni gaskiya baxan tare da ita a sabon gidana ba, ko yau aka samu gun aikin ba don yamma yyi ba kai ta xan yi, don haka gobe da safe xan kai ta...." Ladi tace "Akwai wata kawata Habiba dillaliyarsu ce, xan baki lambarta... Ko kuma ki sa katin dari a wayata mu kirata, in sha Allah nasan baxata rasa inda xata kai maki ita ba" hakan ko aka yi Yakumbo ta sa kati ladi ta kira Habiba, suka ci sa'a number ya shiga, bayan ladi ta gaisa da kawartata tace "Bibalo dama wata yarinya ce da ake son kai ta gidan aiki to shine muke son ki yi taimako" Bibalo tace "Kai yanxu haka Ina hanyar dawowa daga kauye na mayar da wasu yara, amma gobe da safe xa ki gan ni duk da bani da wa enda ke son masu aiki yanxu, amma nasan kawata Abu baxata rasa ba don ta ma fi ni sanin gidajen manya" daga haka suka yi sallama ladi ta katse wayar tana kallon Yakumbo don ba sai ta mata bayani ba tunda a handsfree tasa ita ma ta ji komai, Yakumbo tace "Toh Allah ya sa a dace, ni wllh ko dubu biyu ma xa a dinga biyanta na yarda" tagumi tayi tace "Allah gani gare ka, kasa a karbi yarinyar nan ni kuluwa" Washegari da safe kuwa sai ga Bibalo tare da kawarta da ta fada Abu, Yakumbo dake ta washe hakora ta gaishesu suka amsa aka xaxxauna kan tabarma ladi ma ta fito akurkin ta tana masu sannu da xuwa, bayan sun gaisa Bibalo tace "Toh kinga ni bni da inda xan kai ta amma Abu tace kawarta ta taba hadata da wata Hajiya mai neman mai aiki, da xata dinga share share da goge goge sannan wanke wanke, akwai ma wata babbar mai aiki dake girki a gidan, to Abu taje gidan ya fi sau uku ba a bude mata gate, yanxu ma gwada sa'a xa ayi kuje har da ke kika wajen, idan sun dauketa to, idan kuma sun ce A'a sai ki jira har a bukaci mai aiki a wani gidan sai in kai ta" Yakumbo tace "A'a mu je kawai mu gwada sa'ar mu" Bibalo tace "Toh ki sallame ni ni xan wuce" Yakumbo ta hade rai tace "In sallame ki? Me kika min da xan sallame ki" Bibalo ta bude baki tace "Au haka ma xa ki ce, shi kudin motar da nayi da kuma bata lokacina da na yi na xo nan tare da kawata har xa ki ce min me na maki" mikewa Yakumbo tayi rai a bace ta shiga ciki ta fito da dari biyu tana cewa "Ko daukar yarinya ba ayi ba xaki wani ce in sallame ki idan ba hadama ba" dungura mata dari biyun tayi a gabanta rai a bace, Bibalo ta dauka ta mike tace "Ya fi babu ai" daga haka ta yi ma Ladi sallama da Abu tayi ficewarta, Abu tace "Toh inji kinsan mu dubu daya ce sallamar mu?" Yakumbo ta hade rai tace "Idan an dauki yarinya ba" Abu tace "Toh gwara da kika san haka don ni baxan tsaya cacar baki ba, yanxu Ina yarinyar take?" Yakumbo ta nuna mata khadijah dake ta fama da wanke wanke, kwalalo ido tayi tace "Warcen da ta fi minti ashirin tana d'an wanke wanken can, tun shigowar mu fa take wanke wanken kamar ayi kamar baxa ayi ba" yakumbo ta marairaice tace "Haka take Abu, akwai iya aiki amma ba sauri ne kawai, amma tana xuwa can nasan xa su gyara mata xama ta xama mai hanxari" Abu ta tabe baki tace "Toh unguwar da nisa, don can Gra ne, kuma wllh gidan babban mutane ne, ni dai Allah ya sa su dauketa, yanxu sai ki tashi ku shirya ta hada kayanta ina jiran ku mu kama hanya" Yakumbo ta mike da sauri ta shiga ciki tana cewa "Toh bamu minti biyar kacal" tana shiga dakin ta kwalo ma khadijah kira, khadijah ta mike ta shiga da sauri. Yakumbo ta jawota tayi kasa da murya tace "Dijangala ta mai gari, ba auren talaka ba" tana washe hakora ta fadi haka, ita dai khadijah kallon ta kawai take, Yakumbo tace "Kinsan inda xa mu yanxu kuwa?" Girgixa kai khadijah tayi, Yakumbo tace "Gidan da xa a dinga biyanki kudi mai yawa in tara maki in sa ki a boko, kai har in maki aure ma" khadijah tayi shiru bata ce komai ba, yakumbo ta marairaice tace "Don haka muna xuwa kice kin iya aikin komai, sai ki bada himma idan an saki aiki ki yi da sauri da sauri, sannan don Allah Idan mun je gidan khadijah kar ki masu wannan yaran naki na turanci kin ji koh? Kawai Hausa xa ki masu, idan kuma baki san Kalmar da xa ki fada da hausa ba sai kiyi shiru abun ki ba sai kin yi turancin ba" yanxu maxa canxa kayan Ki bari in tusa maki wa encan a jaka tunda basu samu wanki ba idan kin je can ko ba ki iya wankin ba ki tsoma su a ruwa ki xuba omo ki shanya" daga haka Yakumbo ta shiga tusa kayanta a wani karamin Ghana must go, don har ta siyar da jakar da Umma ta kawo mata kayanta ciki, karfe tara da kusan rabi su yakumbo suka bar gidan tare da Abu bayan ta yi ma yan gidan sallama suka dinga yi mata Allah ya bada sa'a, tana rike da hannun khadijah suka isa bakin titi, Abu tace "Amma kinsan ke xa ki biya kudin abun hawa dai koh?" Yakumbo ta tsuke fuska tace "A kan me?" Abu tace "A'a mayar da wukar ae dai naga ba xuwan kai na xan yi ba gidan don hka idan kinsan gidan ke sai ki kai ta, yakumbo ta rikota da sauri tace "Naji, mu je ya na iya, daga yau ai babu wanda xai xo yace in biya masa kudin napep dai koh?" Ko tanka ta Abu bata yi ba ta shiga napep din da ta tsayar, Yakumbo ta shiga ta daura khadijah a cinya. Tafiya ce mai nisa kamar yanda Abu tace masu, tun da suka bar hayi dama Yakumbo ke addu'ar Allah ya sa a dau khadijah gidan aikin idan ba haka ba asirinta ya tonu don ta sa rai da kudin da xa a dinga biyan khadijah, tun da suka shigo anguwan Yakumbo ta saki baki kamar yawu xai dalalo tana kallon gidaje na alfarma, Abu ta dinga nuna ma Mai napep din inda xai bai, har suka iso wani cool silent anguwa mai cike da shuke shuke a ko wani gate, ga bakin kwalta a shimfide daga farkon layin har inda yakumbo ke tunani karshe ne, bakin wani gate Abu ta sa mai napep din ya tsaya, yakumbo ta wage baki tana kallon jibgegen gidan da aka yi ma ginin xamani kamar ta sure ta gudu, gidan ya hadu ne kawai don ita a ganinta duk ya fi sauran gidajen dake layin haduwa, suka sauka sai kuma Yakumbo aka tsuke fuska da ta tuna kudi xata bada yanxu, ta dungura ma mai napep din kudin da yace lkci daya kuma tana hararan Abu, Abu da ko lura da ita bata yi ba tace "Toh Allah ka bamu sa'a don kwanaki da na xo haka na sha xamana bakin gate rana yayi maganina ban samu shiga gidan ba... Yakumbo tace "Yana da kyau mutum ya dinga fadin alkhairi ko yayi shiru, yanxu me ya kawo wannan xancen, in sha Allahu ma sai mun shiga don haka ki mana shiru" daga haka Yakumbo bta kwankwasa gate din a hankali kamar me tsoron kada ya fashe don ita fa gani take kamar glass ne a kauyancinta, ta kwankwasa ya kai sau hudu kafin wani da alamar mai gadi ne ya bude yana kallonsu, Yakumbo ta durkusa har kasa ta gaishesa, yace "Wa ku ke nema?" Yakumbo ta mike tace "Matar gidan muke nema ce mana tayi mu samo mata mai aiki yarinya karama, to cikin ikon Allah gashi mun samo mai haxaka, shine muke hadaka da Allah yaro ka bar mu mu shiga, mu gabatar mata da aiken da ta mana" ya girgixa kai yace "Ai akwai mai aiki yanxu haka a gidan don haka ban ji xa a bukaci warce xa ku kawo" Bakin yakumbo ya fara rawa tace "Wllh xa su bukata dubeta fa kaga bbu abinda bata iya ba, sannan Hajiyar da kanta ta sa mu ko daxu mun yi waya da ita tace sai mun xo, haba yarona ka duba tsufana mana gashi daga hayin rigasa muke wllh" Mai gadin yace "Toh yanxu ma ku kirata idan tace ku shiga toh shkkn" daga yakumbo har Abu aka hadiye yawu da kyar don babu mai waya cikinsu, Yakumbo tayi karfin halin cewa "Wallahi wallahi na mance wayar a gida kaji rantsuwar musulmi" Abu ta saki baki jin rantsuwar da Yakumbo tayi alhalin taji Bibalo tace bata da waya. Not edited. Mai gadin ya girgixa kai yace "Toh ku yi hakuri gobe sai ku je ku dawo, amma ku tabbatar kun taho da wayar da xa ku yi communicating da ita" xai rufe gate Yakumbo tayi saurin saka kafarta daya ciki tace "Don girman Allah kayi hakuri ka bar mu mu shiga, wllh mun kashe kudin mota yayi dubu daya, kuma ni na biya, ka ji tausayina d'an nan" kamar xata rushe masa da kuka ta kai karshe, ya tsaya kallonsu da mamaki, can yace "Toh shkkn, amma har ni nasan sai kun janyo min fada wllh, amma bakomai akwai Allah, ku shigo" Yakumbo ta durkusa har kasa tana masa godiya suka shiga cikin makeken compound din gidan, uwa idonta xai fito yyi magana ta dinga bin gidan da kallo da motocin dake parking lot, Abuu ko idan da sabo ta saba shiga gidaje haka kai yara masu aiki, don haka ita ke biye da mai gadin yakumbo kuwa nata kalle kalle, bbu abinda khadijah tayi ma kallo biyu a compound din, don bbu bakonta a ciki. Karkashin wani artificial tree mai gadin ya nuna masu su jira sa, ya isa main entrance din shiga gidan, ya kusa minti biyar tsaye bakin kofar bayan ya danna bell aka bude kofar, Mai aikin gidan ce warce baxata wuce shekara ashirin da bakwai ba tana sanye da apron da hularsa alamar daga kitchen take, ganin warce ta fito yayi murmushi yace "Kyauta mun tashi lafiya?" Tace "Lafiya lau Usman, Ashe kai ne ma, ya aka yi?" Ya d'an sosa kai yace "Hajiya ce tayi bak'i ina fatan dai ta tashi bacci?" Kyauta tayi kasa da murya tace "Gata can parlor xaune ma" Muryar Hajiyar gidan suka ji tace "Waye kyauta?" Kyauta ta yi saurin barin bakin kofar tace "Hajiya, Usman mai gadi ne wai kin yi baki" Hajiyar dake gyara farcenta da nail cutter ta kalli agogo tace "Baki kuma?" Kyauta tace "Eh Hajiya" tace "Toh su shigo, amma ni bani da wasu baki da nake expecting da safen nan, da akwai ai da na gaya masa" Usman da ya ji abinda ta fada ya nufi gun da yakumbo suke yace "Allah ku daina karya bashi da amfani a rayuwa, yanxu gashi tace ita bata da wasu baki da take expecting da safen nan ku kuma har da ce min kun yi waya" yakumbo ta yi kasa da murya tace "Mu dai don Allah tunda har muka samu muka shigo gidan nan ka rufa mana asiri mu karasa idan ma ta kore mu shi kenan sai mu fita haka Allah yayi" ya nuna masu kofar shiga ya koma can bakin gate yana mamakin wasu 'yan Adam. Da yake a bude kyauta ta bar masu kofar, da sallama Yakumbo ta kutsa kai cikin parlorn tana dudduke kai ga wani daddadan kamshi dake tashi ta ko wani angle... Abuu na biye da ita a baya, Sai da duk suka shiga khadijah ta tura kofar a hankali ta rufe sannan ta bi bayansu, Hajiya Fatima matar gidan ta dinga kallonsu da mamaki har suka xauna kasan lallausan carpet din tsakar makeken parlorn, sanyin Ac yasa yakumbo ta fara rawan Dari, Hajiya tace "Sannun ku da xuwa" Yakumbo tayi saurin cewa "Yauwa ina kwana shugaba?" Ba Hajiyar kadai bace xaune parlorn ita da wata ce wanda ga dukkan alama kanwarta ce tsabar kamanninsu, matar xa kuma ta yi shekaru talatin da 'yan kai a duniya, Hajiya ta kalli kanwarta kamar yanda ita ma take kallonta, Amsa gaisuwar yakumbo Hajiyar tayi tace "Daga ina?" Yakumbo tayi gyaran murya kafin Abuu tace komai tace "Dama Hajiya da daddewa mun ji kina neman mai taimakon ki, shine ga yarinyata ganin irin haxakarta da hanxari yasa nace in rako Abuu dillaliya mu kawo maki" Hajiyar tace "Ayya ai kam ina da mai aiki bayin Allah gata can ita ta bude kofar ma...." Yakumbo ta katse ta tace "Ayya wannan d'an share share da goge goge xata ke maki Hajiya, wancan naga ai babba ce, ni ko baxa ki biya kudi mai yawa ba ki dauketa Hajiya don wllh daga waje me nisa muke ga uban kudin mota da muka kashe, ki taimaka fisabillilahi Hajiya" Abuu ta kara da cewa "Ki taimaka Hajiya wllh takanas saboda ke muka kawo yarinyar" Hajiya da tayi shiru tana kallonsu tace "Toh wacece mai aikin?" Da sauri Yakumbo ta nuna khadijah dake kallo so engrossed a katon plazma dake parlorn tana murmushi, Yakumbo ko lura da hakan ba ta yi ba, sai kallon Hajiya take ta kara jin abinda xata ce kan khadijah xuciyarta na bugawa, Hajiyar na duban khadijah tace "Ke ya sunan ki?" Inaa khadijah ana can duniyar kallo wannan karan har da dariyarta don film din ya mata dadi, yakumbo ta hadiye abu da kyar ganin irin kallon da Hajiyar ke mata, ta wani mitsileta a boye da sauri khadijah ta dawo, a fusace Abuu tace "Ba ke ake ma magana ba" khadijah ta kalli Hajiyar dake kallonta har lkcn tayi kasa da murya tace "Sorry ma'am, pardon?" Daga Hajiyar har kanwarta dake xaune kusa da ita bude ido suka yi suna kallonta sosai, Khadijah tayi kasa da manyan idanuwanta tace "I am sorry" Mikewa Yakumbo tayi jin fitsari ya taho mata, shi kenan khadijah ta cuce ta sai da ta buga masu turancin, ta nufi kofa da sauri tana cewa "Bari in d'an xaga Hajiya ku yi hakuri" Abuu ma sai kallon khadijah take baki sake jin fa kamar wani yare ta yi maimakon Hausa, Hajiya dake ta kallon khadijah tace "Alright, what's ur name!" Khadijah ta kalleta tace "My name is khadijah Muhd" Hajiyar tace "From where" khadijah tace "I am from kano, I lost my mum and dad... My step mum brought me to Kaduna 4 days ago and she left me...." Tana magana ne har hawaye ya kawo idonta, Hajiya dake kallonta keenly tace "And... Who is this woman that left to ease her self now?" Khadijah tace "My stepmum told me she is her senior sister.." Shigowar yakumbo yasa khadijah tayi shiru, Yakumbo ta shiga kalle kalle kamar munafuka ta xauna amma kuma ta kasa cewa komai tana jiran jin hukuncin Hajiya, ta ma san kawai Hajiya fasa daukar khadijah xata yi don ita tunda take bata taba jin an dauki mai aiki yar boko ba, sai ayi tunanin wani mission ya kawo ta gidan, Hajiyar na kallon Yakumbo tace "Nawa ne kudin aikin?" Xuciyar Yakumbo yyi mugun sanyi ta gyara zama tace "Wallahi ko nawa Hajiya, ko nawa Allah ya hore maki babu damuwa barin yanxu da kudi yyi wahala" Hajiya tace "Dubu uku xan bayar, yanxu kuma xan ba da na wata uku kamar yanda nake ma duk mai aiki idan na dauka" Yakumbo dake ta godiya kamar marokiya tace "Wallahi ba damuwa Allah ya bi ya maki bukatunki na alkhairi, nagode nagode nagode" Kanwar Hajiya mai sunan Khadijah dake gefenta ce tace "Why House maid again bayan kyauta Mumy? Beside I don't think this little girl will be capable, you just look at how engross she is with the TV...." Ko kadan khadijah bata ma san abinda ake cewa ba don gaskiya ne gaba daya hankalinta ta mayar kan kallo, yakumbo da babu abinda taji baya ga kyauta a xancen da Anty khadijah tayi ta marairaice tace "Kiyi hakuri baiwar Allah bbu abinda yarinyar nan ba ta iya ba wllh" Hajiya tace "Toh idan naga bbu abun kirki in sha Allah nan da kwana uku xa ku dawo ku dauki yarinyar, idan ya so sai ki mayar min da dubu shidda nah, ki rike dubu uku" Yakumbo tace "In sha Allah Hajiya, nagode nagode nagode" Hajiya ta katse ta daga godiyar da take yi tace "Toh ta wani number xa a same ki?" Yakumbo tace "ni ki ban naki idan na koma gida sai in kira ki Hajiya, na bar wayar a gida kuma ban san number ba" Hajiya ta sa kyauta ta kawo takarda da Biro tana cikin rubuta number aka bude kofar, duk suka juya kallon bakin kofar banda ita dake rubuta number, dogo ne tamkar dai khaleel din wasu can Lol... Irinsa shi ma ake kira da gentlemen, sanye yake da farar T-shirt da bakin wando, shigar ya kara haska farin fatarsa, iyakar kyau dai kam Alhmdllh Allah ya masa, tuni turarensa ya gauraye ko ina na gidan, har ya iso cikin parlorn idanuwansa na kan mahaifiyarsa dake rubuta sunanta kan number da ta rubuta a takardan hannunta, ya xauna gefenta yana murmushi ya mata side hug a hankali yace "Good morning mum" Sai a sannan ta kallesa hade da turasa tace "Morning...tashi kusa da ni sai warin asibiti kake dalla" Xaro ido yayi yana shinshina kayansa yace "Kai mum warin asibiti kuma duk kamshin nan da nake" tace "Ae kamshin daban warin asibitin daban" ya d'an yi murmushi yace "Ba dai warin asibiti ba sai dai kice kamshin magunguna mum..." Ya kalli Small mum dinsa yana shafa kai yace "Good morning small mum" tabe baki tayi tace "Allah ya kara.... ina ce nan ka tsallakeni ka tafi can gashi an gwaleka" rike kansa yyi yana d'an murmushi can ya dago a hankali yace "Mum kin ji koh" Sai a sannan ya kalli su Yakumbo, tayi saurin cewa "Ina kwana Alhaji" yace "Lafiya Alhmdllh" Hajiya da har ta bata paper din tace "Toh shkkn, yanxu saura in baku kudin ina sauraren kiran ku" kallon D'an ta dake xaune har lkcn a gefenta tayi tace "Aliyu akwai cash tare da kai yanxu?" Ya sa hannu aljihun sa, tace "10k xaka ban" dubu goman ya fiddo ya mika mata ta karba ta ba Yakumbo, Hannu bibbiyu ta karba tana jero godiya, Aliyu yyi saurin dauke kai yana kallon small mum dinsa da wani expression yace "Who are they?" Anty khadijah ta tabe baki tace "Wai house help" yace "House help kuma, did mum dismissed the one available?" Anty khadijah tace "Ina fa, duk biyun xata hada ina ga" ya yatsine fuska yace "Which means ta ba ma su Siyama daman su kara relaxing kenan" Anty khadijah ta tabe baki bata ce komai ba, yace "Which among them is the house help" Anty khadijah ta nuna masa khadijah dake rakube gu daya ana ta kallo happily, lekata ya dinga yi baki bude, can ya dago da sauri yace "Which help will this little girl render?" Anty khadijah tace "Kai ma dai ka gani" bai sake cewa komai ba ya fiddo wayarsa dake vibrate a aljihu, Su Yakumbo suka tashi xa su tafi har lkcn tana ma Hajiya godiya ko bin ta kan Khadijah bata yi ba ta fita tana kara dunkule kudin hannunta Abuu na biye da ita, Hajiya ta kalli Khadijah tace "Tashi ki dau cups din nan ga kitchen can ki kai su" ko kadan khadijah bata ji mai Hajiya ke cewa ba, har sai da Anty khadijah ta mata tsawa, ta dawo daga kallon da take a firgice, Hajiya ta nuna mata cups din tace "Ga kitchen a can ki kai su" tashi khadijah tayi tana neman cups din ta gansu can kusa da Anty khadijah, tana kallon Tvn da wayo ta nufi gun cups din, xaro ido Aliyu yyi jin yanda ta take kafarsa ya fixgota a mugun fusace yace "Baki da hankali ne" Hajiya tace "Bata sani ba fa ina ji Aliyu...." Khadijah dake ta kallonsa tayi kasa da kai a hankali tace "I am sorry, I didn't notice ur leg" _Littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne kindly patronize ur writer and read happily_ Aliyu ya d'an bude ido ya kalli Mum dinsa sannan small mum da ta hade rai, mumy tace "Toh ka ji, she didn't notice" karasawa khadijah tayi ta dauke cup din ta nufi kitchen da aka nuna mata tana yi tana kallon TV har ta isa bakin kofar shiga, kin shiga tayi ta makale da bango tana kallon TV din, haka Mumy ta saki baki tana kallonta, ta kusa minti daya sai kuma ta juyo a hankali ta saci kallonsu, hada ido suka yi da Aliyu dake kallonta kamar yanda mahaifiyarsa ke kallonta ita ma, boye fuskarta tayi da hannunta da sauri tana yar dariya ta shige kitchen din, mikewa Aliyu yyi ya tabe baki yace "Lallai" sannan ya wuce sama, small mum dinsa ta mike tace "Kai fa kasan lallai, ni ban san me yasa Anty fatima take jajibe jajibe haka ba, ni abun ya isheni wllh" daga haka ta bi bayan Aliyu, Mumy dai bata ce komai ba, khadijah na ajiye cup din ta fito ta taho gun mumy ta durkusa gefenta a hankali tace "Anty naga remnant din fried potato and egg, and I am very hungry please can I take it?" Mumy ta gyada mata kai kawai tana kallonta, murmushi khadijah tayi tace "Thank you very much ma" daga haka ta mike ta wuce kitchen din cike da murna, ta dau dankalin da kwai ta xauna a nan kitchen din ta tankwashe kafarta ta fara ci tana lullumshe ido, a nutse take cin abincin kar ma ya kare ta fi minti goma a haka taji an shigo kitchen din, daga kai tayi tana kallon waye ta ga mutumin daxu ne, tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba ya nufi gun da mugs suke a ajiye, Khadijah ta bi sa da kallo tace "Are you a medical Dr?" Juyowa yyi da sauri ya kalleta, ta wara masa manyan fararen idonta tana cin dankalin bakinta, ya daure fuska yace "Am I ur mate that u are asking me dat?" Ta girgixa kai da sauri tace "Not at all.... I just..." Sai kuma tayi shiru ta debi kwai ta kai baki, coffee ya hada ya xuba madara da sugar cube daya, tana ta kallon mug din ganin xai fita tace "Please can you give me some of ur tea" Juyowa yyi fuska daure yana kallon ta, tayi saurin sunkuyar da kanta tace "Ohk ohk sorryyy" har ya isa kofa sai kuma ya dawo ya dau wani cup ya xuba mata kusan rabi ya bude coffee powder ya debi rabin tea spoon ya kara xubawa a nata ya jujjuya sannan ya dauka ya mika mata yace "Here" wara ido tayi ta karba tana murmushi tace "That's kind of you, thank you" ko kallonta bai yi ba ya fice daga kitchen din, haka tayi ta hura shayin tana jira ya d'an huce ta sha, tana sipping din kadan ta mike a gigice tana neman kofar fita jin daci sosai, wani kofar da ta gani ta bude ta fita da gudu, bakin tap ta ga kyauta tana wanke kayan ciki, ga kifi ta gama wankesu a gefe, har da naman kaza a ajiye, khadijah ta tofar da ruwan shayin bakinta tana yatsine fuska ta nufi gun tap din tace "Dan Allah Anty xan sha ruwa kadan" matar ta kalleta fuska daure tace "Me kike yi a kitchen?" Khadijah na ci gaba da yatsine baki tace "Ina cin potatoe and egg ne" sake wukan hannunta kyauta tayi tace "Uban wa ya baki?" Khadijah ta bude hannu tace "Antyn dake parlor tace in dauka in ci, har na kusa cinyewa ma" Kyauta ta tsuke fuska tace "Mayya, wuce ki ban wuri, kuma kafin in shigo ki wanke kayan wanke wanken dake kitchen din nan, da gani a yunwace kika xo dama" Khadijah ta juya ta bar wajen ta koma kitchen, karasa cinye dankalin tayi ta ajiye plate din da cup a sink, coffeen kuma ta rufe sannan ta fito parlor, Mumy dake xaune har lkcn ta nuna mata jakar kayan ta tace "Ki dau jakar nan ga daki can ki kai ki ajiye" Mumy ta fada tana nuna mata dakin dake parlorn, khadijah ta xaro ido tace "Anty kayan fa sun yi datti sosai they are not washed, they are even smelling" Mumy tace "Me yasa baki wanke su ba toh?" Ta langwabar da kai tace "Ni ban iya ba Anty, I only use to wash plate" mumy dake ta kallon ta tace "Toh dauka ki kai su can waje ki ajiye" tace "Ohk ma" daga haka ta dau jakar ta fita da shi can waje, ta dawo, xaunawa jikin kujera kusa da Mumy tayi tana kallon wani program da Mumy ta sa, a hankali tace "Anty bakya kallon cartoon?" Kallon ta mumy tayi, tayi murmushi kafin ta canxa channel din xuwa cartoon, happily khadijah tace "Thank youuu" Mikewa mumy tayi ta wuce sama, Khadijah ta gyara xaman kallon cartoon, a haka Kyauta ta fito daga kitchen ta ganta, daure fuska tayi tace "Ke dan kaza kazan ki ba wanke wanke kwanukan dake kitchen nace kiyi ba kika taho nan kina kallo?" Khadijah ta bata fuska tace "Plss xan yi, ina son in gama wannan cartoon din ne, I have never watch it before" Kyauta ta bude baki da mamki, tana son kara tabbatar da anya ta ji xancen su yakumbo da Hajiya sosai daxu kuwa, ita dai kamar ji tayi ance aiki yarinyar nan xata yi, ko dai bata ji dai dai bane? Khadijah ta turo baki ganin Kyauta taki tafiya, ta nufi kitchen din tace "Toh naji xan wanke" daga haka ta bi gefenta ta shiga kitchen din, kyauta tayi kwafa ta fita don ba ma driver sakon da xai siyo mata na farfesun da xata yi, Khadijah na wanke cups din a kitchen cikin sink trying hard bata xubda ruwa kasan kitchen din ba a hankali take wanke wanken, Aliyu ne ya shigo rike da mug din daxu, tana ganinsa ta tsuke fuska, shi kam bai kara kallonta ba ya ajiye mug din xai fita tace "Wait" da kamar baxai tsaya ba sai kuma ya tsaya ya juyo, cup din da ya bata coffee daxu ta dauko ta cire murfin ta taho gabansata daga kai tana kallonsa tace "You didn't tell me that it was medicine u made.... I wouldn't have ask for some" kallonta ya tsaya yi, xata kama hannunsa ta sa cup din da sauri yace "Ke xan mare ki fa" turo baki tace "Toh ni nace baxan sha ba is it by force" mika masa ta kara yi, ya dauke kai yyi murmushi yana shafa beard dinsa, kallon sink yyi yace "Toh xubar" ta xaro ido tace "How? Why? For what reason? Why shud I throw it away? Ummata told me that they are consequence of throwing food away" shafa kansa yyi ya karbi cup din ya karasa sink xai xubar ta rikosa da sauri ya buge mata hannunta, ta bata fuska xata yi kuka, kusan rabi ya xubar ya nufi inda kayan shayi suke, ya kara madara ya xuba Milo da sugar cube uku ya kara ruwan xafi a ciki ya juya sannan ya mika mata, ta wara ido da sauri tace "For me?" Ya hade rai tayi saurin karbewa cike da murna tace "Thank you very much" dai dai nan kyauta ta shigo kitchen din, tayi kasa da kai tace "Sannu da xuwa yallabai, ina kwana" yace "Lafiya lau" daga haka ya fice kitchen din, khadijah ta nemi waje ta xauna ta tankwashe kafa ta fara shan shayin idonta lumshe, muryar kyauta taji tana cewa "Kee shine ya baki shayin nan?" Ta bude ido da sauri tace "Ehh" kyauta ta hade rai ta karasa ta ja kunnenta tace "Idan kina shisshige ma yan gidan nan sai na ci kaza Kazan ki shegiya kawai" khadijah ta ci gaba da shan shayin ta bata ce komai ba. Kyauta ce ta karasa wanke wanken tana gunguni khadijah sai lekota take ta cikin cup ta take shan shayin ta, Mumy ce ta shigo kitchen din tana kallon kyauta tace "Kin bada sakon da nace kyauta" cike da ladabi kyauta ta bar wanke wanken tace "Ehh Hajiya" Mumy tace "Ohk, ina yarinyar nan take" kyauta ta nuna mata khadijah, Mumy tace "Ohk, idan ta gama ki turo ta ta xo ta amshi sabulu a sama tunda akwai omo a nan ki nuna mata yanda xata wanke kayan ta ga su can a waje wai masu daud'a ne" Kyauta tace "Toh Hajiya" daga haka Mumy ta wuce, Kyauta ta balla mata khadijah harara tace "Maxa ki gama kije ki amso, ni dai bbu wanki da xan maki" khadijah ta karashe shanyewa ta nufi gun sink ta ajiye cup din xata fito kyauta ta fixgota tace "Maxa wanke ni xan wanke maki?" Turo baki khadijah tayi ta fara wankewa a hankali kyauta ta kwace cup din tace "Tafi sama ki karbo min sabulun bbu abinda kika iya wllh" Khadijah ta juya ta fita ta wuce sama, tsaye tayi corridor tana kallon doors dakunan, ko wani daki na da taxara sosai daga na kusa da shi, aka bude wani kofa sai ga Anty khadijah, tana ganin khadijah ta hade rai tace "Ke me kike yi a nan, maxa sauka ance maki masu aiki suna hayowa nan ne" a hankali khadijah tace "Am sorry, Anty ce tace in xo...." Tsawa Anty khadijah ta mata tace "Maxa sauka shegiya" Mumy ce ta bude kofa ta leko tace "Ohk ni nace ta taho ta karbi sabulu khadijah" Anty khadijah ta hade rae tace "Kai Anty ki daina haka wllh ba shi da amfani ina kika taba ganin ana haka ma dai tukun, baki ganin yanda kawayenki suke da masu aiki ne, shegun ka ja su jiki su cuce ka kawai" mumy bata ce komai ba ta shiga ciki ta fiddo wasu sabulu masu tsada ta mika ma khadijah tace "Ki kai ma kyauta" khadijah ta karba ta juya, Anty khadijah tace "Ko da wasa kika sake hayowa nan wllh sai na mareki ko da kuwa Hajiya ce ta aike ki...." Khadijah dai bata ce komai ba har ta sauka, Kyauta ta kwace sabulun suka fita, bakin tap ta xuba duk kayan a roba tana yatsine fuska ta xuba ruwa da omo tace "Maxa taho ki wanke tsummokaran ki shegiya" Khadijah ta xaro ido tace "Kai Anty ban iya wanki ba fa" dagowa kyauta tayi da sauri tace "Toh uban wa xai maki" khadijah ta bude hannu alamar bata sani ba, kyauta ta dinga masifa tana jaraba ta shiga wanke kayan khadijah na tsaye tana kallonta, tas ta wanke su gaba daya tayi ta dauraya, khadijah dake ta tsaye tace "Anty in je in dinga yin shanya?" Kyauta tace "Ja can, warce bata iya wanki bace xata iya shanya" khadijah dai bata ce komai ba, kyauta tace "Ni dai da ki tafi ki ban waje in daina ganin ki" Khadijah tace "Toh Anty" daga haka ta wuce ciki da sauri taje ta ci gaba da kallonta, xaune ta samu Anty khadijah a parlor Aliyu na xaune kusa da ita sanye da 3qtr da farin riga yana nuna mata abu a laptop, tana ganin khadijah ta yi mata alamar da ta koma inda ta fita fuskarta daure, ganin Anty khadijah tayi shiru Aliyu ya daga kai yana kallon inda take kallo, dai dai lkcn da khadijah ta juya da sauri ta koma kitchen din, Anty khadijah tayi tsaki tace "Gayyar tsiya" shi dai Aliyu bai ce komai ba yana ci gaba da danna laptop dinsa, Komawa gun kyauta Khadijah tayi, kyauta ta hade rai tace "Dawowa kika yi?" A hankali khadijah tace "Wannan Aunt din ce ta koreni" Kyauta ta tabe baki tace "Wannan aikin ai sai khadijah baxawarar gidan, warce ta fi matar gidan xakewa, ta ki xaman aure ta xo nan duk ta gallabe mu da su Usman, ai sai ki je ga dakali can ki xauna ya kika iya" tafiya khadijah tayi ta xauna tana kallon kyauta dake ta daurayan kayan ta. Kyauta ta gama shanyan kayan ta dau sabulun da ya rage ta mika ma khadijah dake ta xaune a gun da ta nuna mata tace "Kina shiga parlor xa ki ga wani kofa, maxa ki shiga ki ajiye sabulun nan saura kuma ki min tabe tabe nasan yanda na ajiye komai na" tashi khadijah tayi ta karbi sabulun ta wuce ciki, ta kusa minti daya tsaye bakin kofar kitchen tana lekan parlorn don har lkcn Anty khadijah na nan, tun xuwanta wajen Aliyu ya ganta, da sun hada ido sai ya dauke kansa, can dai small mum din tasa ta mike tace "Xan tafi in kwanta Son" yace "Alright" daga haka ta wuce sama, sai a sannan khadijah ta shigo parlorn tana taku a hankali ta shiga kofar da kyauta ta ce mata, kare ma dakin kallo ta dinga yi, komai fes fes kamar ba dakin mai aiki ba har da gado a dakin, khadijah ta ajiye sabulun tsakiyar dakin sannan ta juya ta fito, gun Aliyu ta nufa ta tsaya kusa da shi tana kallon laptop din kafarsa tace "Kasan me?" Ko kallonta bai yi ba idonsa a kan laptop din, tace "Nima ina da laptop da Abbana ya siyo min ah...." Shiru tayi tana kallon sama tana son tuna sunan kasar, ta langwabar da kai tace "May be it's china! kuma na iya operating laptop din amma kawu ya amshe min" kamar xata yi kuka ta kare maganar, ya dago kai ya kalleta yace "Na tambaye ki?" Dariya ta yi har da rufe fuskarta tace "A'a kawai gaya maka nake yi" yace "Toh juya ki bar nan" Dai dai shigowar kyauta parlon, ganin Aliyun tayi kasa da kai tace "Sannu yallabai" yace "Yauwa sannu da aiki" Kyauta ta shiga dakinta, ya kalli khadijah yace "Wuce ki ban waje" ta buda ido tace "Ohk" daga haka ta bi kyauta dakinta, kyauta dake kokarin ajiye sabulun da khadijah ta yasar mata a tsakiyar dakin ta juya ganinta ta rufe kofar dakin, sannan ta ja kunnenta tace "Ba nace ki daina ma mutan gidan nan shisshigi ba, ke wani irin kunnen k'ashi gare ki, me ya hada ki da likitan har xaki je ki tsaya gabansa?" Khadijah ta turo baki tace "I was just telling him about my laptop" sake baki kyauta tayi tana kallonta, can ta dungureta tace "Sannu baturiya, you dey tell am about ur laptop koh? Wai ma ina iyayenki?" A hankali khadijah tace "They are late?" Kyauta tace "Wa ya kawo ki gun aiki?" Khadijah ta langwabar da kai tace "Wata mata ce, she is very wicked" kyauta ta rike ha6a tana kallon khadijah, muryar Hajiya taji tana kiranta a parlor ta juya da sauri ta bude kofar ta fita khadijah ta bi bayan ta, Hajiya dake tsaye tace "Kyauta white rice kawai xa ki yi da miya for lunch, pepper soup din da xa ki yi kuma na dinner ne idan kinga xaki iya yi yanxu kiyi, idan baxa ki iya ba ki bari da yamma" kyauta ta risina tace "Toh Hajiya" Mumy ta juya ta koma sama, Aliyu dake parlorn har lkcn yace "Mumy baxa ki aiki ba yau" Tace "A'a sai gobe" Kyauta ta shiga kitchen Khadijah na biye da ita, Ruwan shinkafar ta daura kan gas, duk inda ta bi a kitchen din sai khadijah ta bi ta, gajiya da karon da suke ci Kyauta tayi ta fixgota ta nuna mata kofar fita kitchen din tace "Tafi ki ban waje baki min ko wani amfani a nan" da sauri khadijah ta fita kitchen din, bbu kowa parlorn haka yasa ta dau remote da sauri ta canxa xuwa cartoon, ta rakube kasan kujera tana kallo, kafin karfe daya Kyauta ta gama shinkafa da miyar ta fito parlor, dai dai sakkowar Anty khadijah downstairs, tun a stairs ta bude baki tana kallon khadijah da gaba daya hankalin ta na kan TV, kyauta na ganinta tayi kasa da kai xata koma kitchen ta kwalo mata kira, sai a sannan khadijah ta mike da sauri, cike da isa Anty khadijah tace "Ba ki gaya ma yarinyar nan rules din gidan nan bane kyauta?" Kyauta tace "Ban kai ga gaya mata ba Hajiya, tun daxu ina kitchen ne da na san nan ta xauna kallo da baxan barta ba kiyi hakuri Hajiya" Anty khadijah ta kalli khadijah fuskarta daure tace "An ce maki nan din gidan ubanki ne da kika taho kika hakikance a parlor kina kallo a matsayin ki na mai aiki da aka dauka yau" khadijah tayi shiru bata ce komai ba, a tsawace Anty khadijah tace "Ba magana nake maki kike kallona da shegun idanuwanki ba" Kyauta tace "Kiyi hakuri Hajiya hakan baxai kara faruwa ba idan Allah ya yarda" Anty khadijah tace "Halan baki san ita ma aiki aka dauketa ba da xaki bar ta tana kallo ke kuma kina ta aiki a kitchen, ina ce tare ya kamata ku yi aikin ba?" Kyauta ta risina tace "Kiyi hakuri naga yarinya ce Hajiya" Wani kallo ta jefeta da shi tace "Yarinya? Ai iyayen nata sun san yarinya ce suka kawo ta gidan aiki, maxa idan akwai wani aikin ki bata ta tafi taje tayi yanxu, daga yanxu kuma bana son sake ganin kina aiki ita tana xaune" kyauta ta juya da sauri tace "Toh Hajiya" bin bayan ta khadijah tayi, Anty khadijah ta dakatar da ita tace "Daga yau na sake ganin ki xaune cikin parlorn nan wllh sai na lahira ya fi ki jin dadi gayyar tsiya kawai" A hankali khadijah tace "Am sorry maa" daga haka ta bi bayan Kyauta da sauri. Kyauta ta fixgota bayan sun shiga kitchen din ta ja kunnenta tace "Kin ga xaki fara ja min matsala koh? Da nace ki wuce daga kitchen ce maki nayi kije kiyi kallo??" Khadijah ta girgixa mata kai kamar xata yi kuka, kyauta ta nuna mata can wani gefe tace "Tafi ki je ki xauna wawiya kawai, dole ne sai kin yi kallo har wancan baxawarar xata dinga maki gori bata san at times condition ke sa crayfish yyi bend ba, banda haka uban me xai kawo mu gidan nan" khadijah tayi dariya har da kyakyatawa tace "Anty is crayfish bent?" Hararata kyauta tayi ta juya ta ci gaba da abinda take, a dinning kyauta ta jera lunch din duk me son ci a can xai je ya diba, ta dau wani katon roba ta kusa cika sa da shinkafa nama yayi takwas ta fita parlor tana leke leke, dawowa tayi da sauri ta mika ma khadijah tace "Maxa maxa tashi ki kai dakina da sauri ki ajiye a bayan kofa ki rufo dakin" khadijah ta mike ta karba abincin ta fita da sauri, har xata shiga daki ganin Aliyu ta tsaya, sai kuma ta nufesa har gun stairs tana nuna masa abincin ta tabe baki tace "Kaga Anty mai girki tace in kai mata abincin nan daki da sauri, may be she fetched all the food kila har da kai ma baxa ka samu ba, cos there is nothing left in the pot, I even saw when she was pouring water inside" Aliyu ya rungume hannunsa ya hade rai yace "Where did u knw me from?" Tana rike roban abincin da kyau saboda tiririn da yake innocently tace "In this house mana, I...." Turata yyi baya da sauri har sai da ta kusa faduwa shi ma ya koma baya ganin ta sake roban hannunta gaba da uban shinkafa da miyar da nama suka tarwatse kasan tiles har kan stairs, ta xaro ido ta toshe baki kamar xata yi kuka tace "Shikenan ka xubar... wllh bani bace ba kai ne ka xubar, ka xubar ma Anty mai girki abinci...." Kyauta ta fito da gudu daga kitchen jikinta na rawa jin karar faduwar roba kamewa tayi gun ganin khadijah can bakin stairs ga tulin shinkafa a xube kasa, xata koma kitchen suka yi ido hudu da Aliyu ta sake dawowa da gudu bakinta na rawa tace "Subhanallahi ta xubar, ban san baxata iya ba dama nawa ne da nata da nasu Usman..." Khadijah ta daga hannu da sauri tace "Noo Anty mai girki bani bace ba fa, shine ya turani baya kawai abincin ya fadi a hannuna" Aliyu ya tsallake abincin ya bar wajen, Kyauta ta koma kitchen da gudu ta dauko wani karamar roba ta dawo ta dinga kwashe shinkafar tana xubawa a babban roban, khadijah tace "Hope u are nt eating this any longer?" ko kallonta kyauta bata yi ba ta gama kwashe abincin ta kai dakinta da gudu ta fito ta shiga kitchen ta fito da sweeper, cikin yan mintuna ta gama gyaran gun ta goge, sai a sannan ta mike tana hararan khadijah tace "Ae yau sai dai yunwa ya kashe ki gidan nan, ba dai ni kika yi niyyar toxartawa ba? Yanxu da baxawara ce ta sakko ba bawan Allahn nan ba ya xan yi da raina?" A hankali khadijah tace "Kiyi hakuri" kunnenta ta ja tace "Baxan yi ba, sai kin gaya ma yan garin ku da yunwar cikin ki yau, little brat kawai" daga haka kyauta ta koma kitchen da sauri, khadijah ta langwabar da kai ta bi ta da kallo. Da kyar khadijah ke cin shinkafar tana yi tana kallon shi da kyau ko xata ga dirt a ciki, kyauta sai hararata take tana ci hankali kwance, Khadijah tace "But Anty mai girki me yasa baki xuba mana wani ba?" Kyauta tace "Kika sake ce min Anty mai girki sai na kalla maki mari, Anty mai girkin gidan ku, nace idan baxa ki ci ba ki dau naman ki tashi ki ban waje ni xan iya cinyewa, kila ma gidan da kika baki samun irin wannan xaki xo nan kina min iyayi" Khadijah ta xaro ido tace "The woman is always cooking concoction there, bata taba irin wannan abincin ba" Kyauta tace "Toh ki rufe min baki ki ci abinci yanxu yaran gidan xa su dawo daga makaranta" khadijah tace "Ohk" Jin shigowar mota kyauta ta bar ma khadijah sauran abincin ta mike da sauri tace "Toh gasu can... Idan kin cinye ki fito da roban kika kai kitchen" daga haka kyauta ta fita, yara uku ne suka shigo parlorn sanye da kayan makaranta daya kamar khadijah take tana jss3, daya kuma na ss1, babban cikinsu na ss2, khadijah ta fito rike da sauran abincin ta tsaya bakin kofa tana kallon yaran, Gaba daya dinning suka nufa ko wacce na cewa "Yaya ina yini?" Aliyu dake xaune gun ya amsa masu gaba daya, bbu warce ta gaida kyauta dake ta masu sannu da xuwa duk suka wuce sama, banda yar karamar cikinsu sa'ar khadijah, Kyauta ta washe baki tace "Yauwa sannu Anty khadijah ya makarantar?" Yarinyar da ita ma sunanta khadijah tace "Alhmdllh, kyauta who is that girl staring at us?" Kafin kyauta tace komai khadijah ta turo baki tace "I am not staring at you..." daga haka khadijah ta shige kitchen da roban hannunta, duk wannan abun Aliyu na kallonsu daga dinning, yarinyar ta juya da sauri ta tafi gunsa tace "Ya Aliyu who is she?" Ya kamo hannun Kanwar tasa yace "Ask mumy" yarinyar tace "Ohk" daga haka ta wuce sama kyauta na cewa ta na cire uniform tayi sallah ta xo ta karbi abincinta, kyauta ta bi khadijah kitchen ta jawota fuskarta daure tace "Ke fa ba ruwanki da yaran gidan nan naga har kin fara masu fetsara, ki tsaya a matsayin ki idan ba haka ba baxawara ta ishe ki" Karfe hudu duk yaran gidan suka gama shirin tafiya islamiyya, kyauta ta hada socks dinsu gaba daya da Uniform din autar Mumy da ake kira da Baby saboda sunan Anty khadijah gareta xata wanke, kallon khadijah dake tsaye kanta tayi tace "Toh ni dai kin tsaya min kamar soldier ki tafi can dinning area ki kwaso duk plates din wajen, saura kar kiyi a hankali" khadijah tace "Toh" sannan ta wuce ciki, bbu kowa dinning area din sai plates da shinkafa da aka yi littering a wajen, Khadijah na ganin Anty khadijah a parlor xaune tana gyara ma Baby Hijab tayi saurin dauke kanta ta shiga hade plates din waje daya, muryar daya daga yan matan parlorn taji tana cewa "Anty wacece wancan yarinyar wai?" Anty khadijah ta tabe baki tace "The new housemaid" Baby ta xaro ido tace "Anty is kyauta going?" Anty khadijah tace "Noo she is not" Baby ta sauke ajiyar xuciya tace "Better... coz I don't think i like that girl, she can look for Africa as a whole" horn da driver yake yasa Siyama da Aneesah suka mike rike da jakar islamiyyarsu suka ma Anty khadijah sallama suka fita, Anty khadijah tace "She's not even worth talking to, don hka bbu ruwanki da ita yar aikin gidan ce kin ji takwara" baby tace "Sure" khadijah ta turo baki tana kallonsu, baby ta harareta ta fice daga parlorn, khadijah ta ki daukan komai a dinning din ta fita gun kyauta da gudu tana kumbure kumbure, kyauta tace "Ina kwanukan?" Ta fashe da kuka tace "Anty mai girki kinga yarinyar nan har da neman tsokanana koh, shine har da ce min I can look for Africa where as she was the one looking at me, kuma Anty mai ihu tace mata ni house girl ce" Kyauta ta tabe baki ta nuna mata wani dakali tace "Tafi can ki xauna, ni dai ba ruwana idan kina kallon yan gidan nan sai su dake ki ma su daki banxa nima ba kyaleni suka yi ba gwara babyn ma a cikinsu, idan ba iskanci ba... Ba aikin aka kawo ki kiyi ba har xa ki ji haushi don an ce maki house girl?" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, kyauta ta gama wankin ta tafi ta kwaso plates din ta gyara dinning din, khadijah ta hada ma kayan wanke wanken can bakin tap kar ta jika kitchen din ita kuma ta shiga girka dinner, da ta leka sai ta ga kamar ba a wanke wanken, daga karshe fixgota tayi bakin tap din ta turata waje daya ta shiga wanke wanken tana bala'i, khadijah ta toshe baki kar tayi dariya jin har da kiranta lazy ass, har kusan magrib khadijah na kusa da kyauta a kitchen komai kyauta ta sauke kan wuta sai ta ba buda mata hannu xata d'an d'ana tun kyauta na mata da mugunta tana konata da cokalin miya har ta gaji ta kyaleta sai ta xuba mata a d'an karamin plate, kyauta ta samu wani roba ta xuba duk pepper soup din da tayi mai yawa a ciki bata yi gigin ba khadijah ba tace "Tafi ki leka su waye a parlor" khadijah ta dawo tace "Ba kowa Anty mai girki" kyauta ta fita da sauri ta bude dakinsu ta ajiye masu bayan kofa sannan ta dawo ta jera komai kan dinning bayan ta ba khadijah na su Usman mai gadi ta kai masu, Kyauta na gama tsaftace kitchen suka wuce daki da Khadijah, sai a sannan ta xauna ta fixgo khadijah tace "Ke bakya sallah ne hala?" Khadijah tace "Ina yi amma bani da Hijab yanxu" turata bayi kyauta tayi tace "Ni ina da shi ai" Khadijah na xaune kan dankwalin da kyauta ta shimfida mata ta yi sllh tana ta kallon kyauta dake addu'a ta idar da sallahn ita ma, Muryar Mumy kyauta taji ta shafe addu'ar ta mike da sauri ta fita khadijah ma ta bi bayanta da sauri, Mumy tace "Ki xuba ma Aliyu abincin xai wuce aiki yanxu, ku kun ci abincin?" Kyauta tayi kasa da kai tace "Xan xuba masa yanxu Hajiya, mu kuma yanxu xa mu xuba" Mumy tace "Toh sai ki debar maku har da farfesun" Kyauta tace "Toh mun gode Hajiya" Mumy tace "Toh ya tana kokarin aiki kuwa ita?" Mumy ta fada tana nuna khadijah, kyauta tace "Ehh ba laifi Hajiya" Mumy ta juya tace "Toh shkkn" A dinning kyauta ta dibar ma Aliyu nasa abincin a plate ta xuba masa farfesun kaji sanin bai cin sauran, sama ta tafi kai masa khadijah ta biye da ita, ta kwankwasa masa kofa ba a dau lkci ba ya bude yana buttoning din shirt din jikinsa, kyauta tace "Ga abinci yallabai" kallo daya yyi masu ya karbi tray da kyauta ke mika masa yace "Nagode" khadijah tace "Nan ne dakin ka" bai ce komai ba ya rufe kofarsa, kyauta ta ja khadijah suka sauka ta shiga daki da ita ta hade hannayenta biyu tace "Ke wai dan gidanku ina ruwan ki da likitan gidan nan, kin taba sanin sa ne idan ba shisshigi ba?" A hankali tace "Kiyi hakuri" kyauta ta ja bakinta da karfi hade da dungurinta tace "Sai na cire maki wannan mayun idon naki wllh idan kika sake yi ma kowa magana a gidan nan" khadijah ta gyada mata kai hawaye cike idonta, kyauta ta fita ta bar jin alamar su baby sun shigo gidan daga makaranta. Ko kafin kyauta ta sallamesu ta dawo ciki har khadijah tayi bacci, tashin ta ta shiga yi ta ci abinci cikin magagin bacci take cewa Umma na koshi, kyauta ta debo ruwa ta yarfa mata a fuska, da sauri ta farka gaba daya kyauta ta ajiye mata abincin a gabanta ta shiga bayi don yin alwala, ko da ta fito Khadijah bata ci abincin ba ta koma bacci, hakan yasa tace "Ke kika sani" dagata tayi ta kwantar ta xauna cin abincin ita kafin tayi sallahn. Washegari kyauta na idar da sallah ta fita daura breakfast, ta gama fere dankalin turawa Anty khadijah ta shigo kitchen din, kalle kalle ta shiga yi kafin tace "ina wannan yarinyar take?" Kyauta tace "Ina kwana Anty?" Anty khadijah tace "Lafiya, ina yarinyar nace?" Kyauta tace "Na aiketa daki shiru shiru" fita Anty khadijah tayi ta bude kofar dakin kyauta tana yatsine fuska, kwance ta tadda khadijah shame shame kan gado, karasawa tayi ta maka mata duka har sau biyu a baya, khadijah ta farka a rikice, Anty khadijah ta fixgota tace "Ko yan gidan gaba daya ma sun tashi bare ke shegiya, a hakan xa ki iya aiki a gidan nan, a kirga har dubu goma a bai ma iyayenki jiya ki yi ma mutane shame shame kina bacci kan gado har yanxu?" Khadijah ta sauka kan gadon hawaye cike idonta tace "Anty kiyi hakuri" fixota Anty khadijah tayi ta turata waje da karfi tace "Fita kije ki kama ma kyauta aiki, ko ita din baiwar ki ce, ina ce yanda ake biyanta haka ake biyan ki kema" khadijah ta wuce kitchen da sauri tana hawaye, Anty khadijah ta biyota har kitchen din tace "Maxa hada wanke wanke ki fita ki yi" da sauri ta dinga fita da plates waje hawaye na sakko mata, ita dai kyauta bata ce komai ba har Anty khadijah ta fita kitchen din, khadijah ta dau cups uku xata fita da su, kyauta tayi tsaki tace "Mata ta ki xaman aure duk ta xo ta addabe mutane a gida tirrr, ke kuma ai kinga result din bacci kamar matatcciya" khadijah dai bata ce komai ba ta fita, Kyauta ce tayi wanke wanken bayan ta sallami yan makaranta khadijah na mata dauraya, karfe tara da rabi mumy ta sakko xata fita aiki, bayan sun gaisa da kyauta dake hada mata breakfast a dinning mumy tace "Ina khadijah" Kyauta tace "Tana can tana shara Hajiya" Mumy tace "Ohk" kyauta ta koma kitchen bayan ta gama hada ma mumy shayi sanin gimbiya na can sama tana ta bacci yanxu haka, Kallon khadijah tayi da tasa dankali da kwai da shayi a gabanta ta ki ci, Kyauta tace "Au baxa ki ci ba?" Khadijah ta kalleta tace "Ina ci" sai kuma ta fara kuka, Kyauta tace "Samun waje, wato duk da lafiyayyen abincin nan dake gaban ki har kuka kika samu daman yi koh? Kila ma a gidan da kika baro baki samun irin haka" khadijah ta mike tana kuka ta daga rigarta tana nuna ma kyauta bayan ta tace "Anty mai girki har yanxu fa xafi wajen da ta dokeni yake min" kyauta ta buda baki ganin shatin hannun Anty khadijah a bayanta, can tace "Tabdi, toh Allah ya isan ki, kuma in sha Allahu a baxawara xata Karachi rayuwarta, ni kam ko yanxu na bar gidan nan nasan xan samu mijin aure, ita kuwa wllh sai dai taga ana yi, kuma ina jin ita ma ta bar 'ya yanta a wani gidan to haka xa ayi ta cin ubansu ana gallaza masu in sha Allahu" Kyauta ta sauke rigar tace "Maganinki kenan kema dai, gobe ba sai kin jira an tashe ki ba" daga haka kyauta ta ci gaba da aikinta, da sauri kyauta ta fita jin mumy xata wuce gun aiki, ta gama sauraren abinda mumy ke ce mata ta risina tace "In sha Allah Hajiya, Allah ya tsare hanya" tsaye jikin kofa Mumy ta hango khadijah tace "How are you" a hankali khadijah tace "Good morning maa" mumy ta kalli kyauta tace "Anya baki cika ma yarinyar nan aiki kuwa kyauta?" Da sauri kyauta tace "Wallahi ko daya Hajiya, ki tambayeta bana cika ta da aiki" Mumy tace "Ohk" sannan ta mayar da dubanta kan khadijah tace "Am off to work, hope kin yi breakfast?" Ta gyada kai tace "Nayi Anty" Mumy tace "Good" daga haka ta nufi kofa, kyauta ta rakata tana mata Allah ya kiyaye, Mumy na fita da motar ta kyauta ta koma kitchen ta kwashi sauran kayan wanke wanke ta tafi wankewa a waje, khadijah na ta tsaye bakin kofar kitchen din Aliyu ya shigo gidan, tun da ta kallesa bata sake kallonsa ba har ya wuce sama, bayan kusan minti ashirin sai ga shi ya sakko, har lkcn khadijah na gun da take a tsaye, ya shiga kitchen din ya hada abinda xai hada a cup ya fito har ya wuce ya juyo ya daure fuska yace "Baki iya gaisuwa ba koh?" Ta turo baki tace "Good morning" daga haka ta juya ta wuce gun kyauta a waje, ya kusa second ashirin a tsaye kafin ya juya ya wuce sama. Ruwan wanka kyauta ta hada mata bayan sun koma daki, khadijah tace "Anty mai girki ni fa ban yi brush ba kika bani abinci" kyauta tace "Ni na hanaki brush?" Khadijah ta langwabar da kanta tace "Toh su fauxiyya sunyi lost din min brush dina a gidansu" kyauta tace "Oho dai tafi kinyi wanka ga ruwa can" khadijah na fitowa daga wanka kyauta ta bata Vaseline ta shafa sannan ta fiddo mata da daya daga kayan ta da ta linke bayan ta kwaso mata su jiya, khadijah tace "Anty mai girki kinsan wa ya siyo min new pants din nan" kyauta tace "Oho" khadijah tace "My lovely Umma" kyauta bata sake kula ta ba ta fixgota ta lafta mata uban kwalli a ido ta shafa mata farin powder a fuska sannan tace "Wuce can baya ki xauna kar ki shigo gidan nan sai na kira ki na gaji da surutun ki" khadijah tace "Toh" sannan ta fita, dakalin da ta saba xama ta xauna bayan ta tsinka flowers da yawa ta dinga yin jakar hannu da su kamar yanda aka koya masu a schl da dadewa, kamar ance ta daga kai suka hada ido da Aliyu dake kallonta, ta dauke idonta ta ci gaba da abinda take, bayan wani lkci ta daga kai bata sake ganinsa xaune balcony din ba, gajiya da xama tayi ta shiga ciki ta bude kofar kyauta a hankali ta ganta kwance tana bacci, shiga tayi ita ma ta kwanta gefenta nan da nan bacci ya dauketa. Da yamma Mumy na xaune parlor da Anty khadijah da ita ma dawowarta gidan kenan tun daxu da ta fita, khadijah ta fito daga daki bayan ta ajiye kayan kyauta da ta bata, mumy ta kirata ta karasa parlorn ta durkusa tace "Anty gani" mumy tace "Meye da meye bbu a kayan ki?" Khadijah tayi shiru tana naxari, can ta fara lissafo su da fingers dinta tace "I don't have toothbrush and toothpaste, I don't have towel, I only have six pants da ummata ta siya min sauran fauxiyya ta sace min, even ves bani da shi, kuma bani da mai da xan shafa, Anty har da na gashina" murmushi kawai Mumy take, Anty khadijah kuwa ta hade rai kamar bata taba dariya ba, Aliyu dake dinning yana cin abinci tabe baki kawai yyi, mumy tace "Toh in ga kan naki" khadijah ta xame hular kanta Anty khadijah ta saci kallon dogon gashin, mumy tace "Kai maa sha Allah ran Saturday sai ki bi su Siyama kema a gyara maki koh" da sauri khadijah ta xauna a tsorace tace "Anty ummata ta gyara min ai, it's just of recent ta kai ni saloon" Mumy tace "Anjima driver xai kawo maki duk abinda baki da, kina da takalmi koh?" Ta gyada kai tace "Amma ya kusa tsinkewa su fauxiyya suke sa min" mumy tace "Toh tashi kije xa a siya maki" khadijah tayi murmushi tace "Toh Anty I like you" daga haka ta wuce kitchen gun kyauta da sauri. Mumy na kallon Anty khadijah da har lkcn ranta a bace yake tace "Khadijah am thinking ko in sa yarinyar nan a islamiyya su dinga xuwa tare da su baby da yamma, kowa ya ganta yasan she is from a wealthy home, it's just condition...." Katse ta Anty khadijah tayi tace "Anty fatima ki raba kanki, Anty Fatima ki raba kanki ki kyale mutum yanda kika gansa na sha gaya maki times without number, su wa enda suka kawo ta gun aikin sun fa pi ki sanin akwai islamiyya, me yasa kike son sa ma kanki matsala ne wai, tsinannun masu aikin nan da kiris suke jira su tura wanda ya kyautata masu cikin rana, meye hadin ki da yarinyar idan ba shisshigi ba da neman wajen xama??" Mumy ta kalli Aliyu dake ta kallonsu tace "Abuturrab yanxu don nace ayi enrolling din baiwar Allahn nan a islamiyya laifine don Allah?" Ya mike yace "Noo, ba laifi bane mum, sai ma lada da xa ki samu in sha Allah" daga haka yayi wucewarsa sama, Anty khadijah ta bi sa da wani mugun kallo, mumy tace "Atoh, baka san yanda Allah xai yi da naka ba gobe, baka kuma san ina reward din ka yake ba, yarinyar nan tare da ke take gaya mana ita marainiya ce, to don me baxa a ji tausayinta ba, kika san kudin iyayenta a da, don duk wanda yaga yarinyar nan yasan ba daga karamin gida ta fito ba, just put little baby in her shoes... Kin dai ga sa'anni ne su din daga ganin, to da baby ce ta shiga irin halin nan yaya xa ki ji, Allah ya rufa min asiri don dai kudin islamiyya xan iya biya mata, toh ni ban san meye damuwarki ba khadijah" Tsaki Anty khadijah tayi ta mike ta nufi stairs tana cewa "Muna nan da ke sai kin yi da kin sani Anty, shi kuma Aliyu ya ci gaba da daure ma karya kugu, daga ganin yarinya shegiya ku hakikance ku ce a sa ta a Islamiyya for what reason, shi aka aikota yi gidan nan" Mumy tace "Aniyar ki ta bi ki khadijah, shi yasa kike samun matsala da kowa a rayuwa ni dai baki yo halin mahaifanmu ba Allah ya ji kansu, nima ba halin mu daya ba, tirr" Washegari thursday Kyauta xa ta kasuwa tare da Khadijah bayan Mumy ta fita aiki, Anty khadijah kuma ta fita anguwa, Aliyu kadai suka bari gidan kasancewar night duty yake yanxu, da ido ya bi su har suka fita parlorn, Driver da xai kai su kasuwar ya tada motar ganin sun fito, Daya daga dogayen riguna Umma ta siya ma khadijah ne jikinta sai hula da Kyauta ta sa mata ta bata karamin mayafi ta daura a kan, Khadijah ta karbi list din abubuwan da xa su siyo ta dinga karanta su kyauta na jifanta da hararan wa ya sa ta? Driver Sanusi yace "Wai wannan yarinyar madam tace mu je tare da ke ayi ma siyayya?" Kyauta tace "Ehh ita ce" Drivern yace "Kin ga shi kenan sai ayi mata gaba daya koh? Daxu ta bani dubu ashirin da biyar kafin ta fita" kyauta tace "Ka ji sanusi da wani xance, cefane fa xa mu je yi ba kasuwar kaya ba" Sanusi yace "Toh shkkn, gobe sai mu je kasuwar kayan" sai kusan karfe daya Kyauta ta gama duk siyayyar da xata yi suka dawo gida, babu kowa gidan har Aliyu ma ya fita, nan ta daura girki a gurguje Khadijah kuma ta tafi yin sallah kamar yanda tace mata tana idarwa taki fita tayi kwanciyarta. Karfe Uku da rabi su Siyama suka dawo gida, kyauta ta xuba masu abinci gaba daya ta kwashi uniform dinsu ta kai gun wanki, baby kadai ce parlor ta sa cartoon tana kallo da plate din abincin a hannunta da yake bbu islamiyya, su Siyama kuma suna can kan dining, khadijah ta fito daga daki tashinta daga bacci knn ta makale jikin bango tana kallon Cartoon din da baby ke kallo, Baby na ganinta ta kashe tvn da remote ta hade rai, shiru khadijah tayi bata ce mata komai ba, su Siyama suka fara dariya suna kallon khadijah dake tsaye, bude kofa aka yi duk suka juya Aliyu ya shigo parlorn Baby ta kallesa tace "Yayanmu sannu da xuwa" ya karaso parlor ya ajiye makullin motarsa saman table ya xauna tare da jinginar da kansa da kujera yace "Ya school, yau ba islamiyya sai kallo koh" baby bata ce komai ba ta kai fork dake dauke da taliya bakinta, ya kalli TV yace "Wa ya kashe television din" Baby ta nuna masa khadijah tace "Ko ba ita bace take kallon cartoon din da nasa, tell her to get away" kwace remote din yyi ya kunna tvn yana hararanta, Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Wawiya kawai" daga haka ya mike yyi wucewarsa sama, baby ta hade kai da gwiwa xata yi kuka, juyawa khadijah tayi ta wuce kitchen, su Siyama suka bi ta da harara. Khadijah na ta tsaye kitchen tana kallon naman da kyauta ta daura yana ta soyuwa a cikin mai kyauta kuma na can waje, jin an shigo kitchen din ta juya da sauri taga Aliyu ne, cup ya dauka ba tare da ya kalleta ba yace "Have you eaten?" Kai ta gyada masa ita ma bata kallesa ba, sai ga kyauta ta shigo kitchen din, ganin Aliyu tayi saurin cewa "Sannu da xuwa yallabai, in kai maka abinci" ya juya ya nufi kofa yace "A'a nagode" khadijah tayi narai narai da ido tace "Wallahi anty mai girki ni ban kulasa ba shi ne yyi mun magana ki tambayesa ma ki ji" da sauri kyauta ta tura kofar kitchen din ta rufe ta daura hannu a ka tana xaro ido tace "Na shiga uku ni kyautar Allah, yanxu 'yar nan me nace maki xaki ja min salalan tsiya?" Khadijah tayi shiru tana kallonta, kyauta ta bude kofar kitchen din ta turata waje tace "Tafi ki ban waje ni dai" turo baki tayi ta juyo taga Aliyu xaune parlor da baby dake sulking har lkcn, ta wuce daki tana ci gaba da turo baki. Da daddare khadijah ta fito wanka tana daure da xanin da kyauta ta bata ta dinga wanka, kyautar kuma na tsaftace kitchen aka bude kofar dakin, Anty khadijah ce ta shigo baby na biye da ita a baya, kana ganin Khadijah kasan ba karamin tsorata tayi ba ganinta, Anty khadijah ta riko duk hannayenta biyu da hannu daya fuskarta kamar bai taba ganin ruwan alwala ba tace "Don kaza kazan ki kinsan matsayin yarinyar nan a gidan nan?" Ta fada hakan tana nuna mata baby, Khadijah da ta gama tsorata gaba daya cikin rawar murya tace "Anty kiyi hakuri" mari Anty khadijah ta sauke mata, lkci daya tayi saurin daura hannunta a lebbenta alamar kar tayi kara, hawaye ya shiga sakko mata ta dinga girgixa mata kai, kalle kallen dakin Anty khadijah ta dinga yi ko xata samu wayar wuta amma bbu, hakan yasa ta kuma kai mata wani mari, Cikin kuka khadijah tace "Anty don Allah kiyi hakuri ban mata komai ba" da hannu Anty khadijah ta dinga dukan bare skin dinta tana mintsilinta ta ko ina tana cewa "Toh wllh ko kallon baby kika sake yi a bisa kuskure cikin gidan nan sai na sumar da ke shegiya balle ki mata kallon banxa, gayyar tsiya arna a idi, kuma daga yau kika sake tsayawa cikin parlor ba kitchen ba koh cikin dakin nan sai na kashe ki in kashe banxa" wani Marin tayi mata ta rankwasheta ta hankadeta sannan ta kama hannun baby suka nufi kofa tana cewa "Banda Anty fati hau ya fada mata ina ita ina dinga yi ma shegun mutane abinda take yi yanxu, ai sai dai idan bana gidan nan amma duk sai na sa an sallameki har tsinanniyar kyautar, ni kadai raina ma xan iya aikin gidan nan gaba daya idan Allah ya yarda, shegu kwadayayyu yan maula" Kuka kawai khadijah take har da shessheka rabonta da irin wannan kukan tun tana gidan kawunta, fita tayi dakin ta wuce kitchen gun kyauta tana kuka sosai, nan taga kyauta bata kitchen ta bude kofa ta fita can gun da kyauta ke cewa ta xauna ta xauna nan ta dinga kuka kamar ranta xai fita, Aliyu ya mike daga xaunen da yake yana aiki a laptop ya leka kasa, juyawa yyi ya bude kofa ya fita, tsaye yyi kanta yana kallonta, ganinsa ta hade kai da gwiwa tana ci gaba da kukanta, ya durkusa yace "What happened?" Dagowa tayi tana kallonsa amma ta kasa cewa komai saboda kukan da ya ci karfinta, yyi shiru bai ce komai ba, ya kyaleta don kanta ta daina kukan a hankali sai ajiyar xuciya da take, yace "Me aka maki?" Cikin rawar murya ta nuna masa cikin gidan wasu hawayen na sakko mata tace "Wannan Antyn nan ce ta min duka" shiru yyi yana kallon tafin hannun dake kwance saman fuskarta da yyi ja, yace "Wace Anty?" Kasa cewa komai tayi saboda wani sabon kuka da ya taho mata, yace "Don't cry again, ki fada min wace Anty ce ta doke ki" ta buda masa hannu muryarta na rawa tace "Ban san sunanta ba" Fiddo wayarsa yyi a aljihu ya shiga gallery ya nuna mata hoton kusan yan gidan gaba daya yace "Wacce a ciki?" Ta goge hawayen idonta tana kallon hoton da yake nuna mata da kyau, a hankali tace "The one wearing blue" sake kallon hoton yyi yaga Anty khadijah ce, yace "Me kika mata" wasu sabon hawayen suka taho mata tace "May be wannan yarinyar ce tace mata ina kallo a parlor....." yace "wacce yarinya?" Shiru ta yi bata ce komai ba hawaye na taruwa idonta, Ya sake shiga gallery ya nuna mata hoton daxu ta nuna masa baby, dauke kai yyi bai ce komai ba can ya kalleta yace "Toh ina kayan ki?" A hankali tace "I just took my bath shine ta shigo daki" rushewa ta kuma yi da kuka yace "Don't cry, ki jira ni a nan" daga haka ya mike ya wuce ciki, ba a wani dau lkci ba ya dawo rike da hannun baby dake kallonsa a tsorace, Ya iso gun khadijah da ita yana kallon khadijar yace "stand up" mikewa tayi, ya mayar da dubansa kan kanwarsa yace "Me ta maki kika yi reporting dinta gun Anty, kuma if you dare lie to me you are in big trouble" kamar xata yi kuka tace "Yayanmu am sorry" ya hade rai sosai yace "I will give u a dirty slap idan baki yi answering question dina ba" Muryarta na rawa tace "I only told aunt that...." Yace "That what?" Hawaye ya cika idonta tace "Don Allah yaya kayi hakuri" kalle kallen gun ya fara yi, ta fashe da kuka tace "Wayyooo yayana kayi hakuri" ya buge bakinta ya mata alamar da ta yi shiru, ta toshe bakinta da hannu daya tana hawaye, ya isa gun wani flower ya karya branch din ya dawo yace "Kawai saboda ke muguwa ce kika je kika sa Anty ta mata duka koh" a rikice ta dinga girgixa masa kai tace "Aa wllh, yaya kayi hakuri baxan kara ba, let me tell her sorry now plss" hannunta ya fixgo yace "Kika kuskura kika min ihu idan na dauke ki daga nan wllh asibiti xa mu tafi" daga haka ya shiga tsula mata bulalan yanda yasan xai yi mugun shigarta yayi hakan kusan sau biyar tana tsalle tana son kwace kanta amma ta kasa gashi ba daman ihu, sai da yaga hannunta yyi ja sannan ya saketa tana tsalle hawaye na sakko mata, ya hade rai yace "Tafi ki bata hakuri" da sauri ta isa gun khadijah dake kallonsu cikin rawar murya tace "Don Allah kiyi hakuri" Khadijah tayi kasa da idonta tace "ke ma kiyi hakuri" Fixgota Aliyu yyi tana kuka tace "Yaya wllh na bata hakurin" yace "Tell her you two are now frnds from this moment" ta kuma kallon khadijah da sauri tace "We are now frnds from dis moment" a hankali khadijah tace "You are welcm" ya sake kanwarsa yace "Maxa goge idonki kije tap ki wanke fuskar ki tafi ki kwanta, if I shud hear pimm, you will spell doom, I mean idan kika kuskura kika gaya ma kowa abinda ya faru sai na kusa cire maki kunne" da sauri ta je ta wanke idonta ta goge fuskarta sannan ta wuce cikin gidan, ya kalli khadijah da ta bi ta da kallo yace "Ke ma good nyt" ta kallesa ta gyada masa kai a hankali tace "Bye" daga haka ta shiga ciki ita ma. Da washegari har baby suka wuce makaranta bata yarda ta kalli inda khadijah take ba, ba Anty khadijah ba, har Mumy ta tambayeta me ya sami idonta tace babu komai, har daki Anty khadijah ta kai kan ta gaya mata ko an mata wani abu ne amma baby taki gaya mata komai, khadijah kuwa tunda ta shiga kitchen safiyar ranar jin muryar Anty khadijah ta makale ta ki fitowa, Allah ya gani ko matan kawu ba ji tsoron su kamar yanda take tsoron Anty khadijah ba, babu kalan xagin da kyauta bata yi ma Anty khadijah ba jiya a daki bayan Khadijah ta gaya mata abinda ya faru, har tsine mata sai da tayi, daga karshe rub ta shafa ma khadijah a bayanta da jikinta sannan ta sa ta ta kwanta ta dungureta tace "Gobe kya tsaya kallon shegen tv dinsu ke ma mayya" ita dai khadijah bata ce komai ba, wannan dalili ne ma yasa tun da khadijah ta shigo kitchen kyauta bata sa ta ko da dauko cokali ba, tana dai tsaye gefe tana kallonta, kyauta ta fita kai ma Anty khadijah dake xaune parlor Lipton a cup, mumy tace "Ban ga khadijah ba kyauta, ko bata tashi bane?" kyauta tace "Tana kitchen Hajiya, tare muka fito" Anty khadijah ta tabe baki tana kai Lipton din hannunta baki, kyauta na komawa kitchen tace "Kin min tsaye a kai tun daxu, ki tafi ki gaida Hajiya" Khadijah tayi shiru tana kallonta, turata waje kyauta tayi, hakan yasa khadijah ta turo baki ta wuce parlorn, Mumy na kallonta da mamaki tace "Me ya samu fuskarki?" Girgixa kai tayi tana sauke idonta kasa tace "Ba komai Anty" mumy tayi shiru tana kallonta hakan yasa ta durkusa kasa tace "Ina kwana" Mumy tace "Lafiya lau, kira min kyauta" Khadijah bata tashi ba sai da ta gaida Anty khadijah da ta amsa da kyar tana jifanta da wani kallo sannan ta wuce kitchen tace da kyauta Anty na kiranta, mumy na kallon kyauta bayan ta xo tace "Kyauta me ya sami khadijah fuskarta ya tashi haka?" Kyauta tayi kasa da kai tace "Hajiya nayi tambayar duniyar nan taki gaya min, haka nima naga fuskar kamar an mareta har ma da jikinta duk mintsili ne, nayi nayi da ita ta ki gaya min" Mikewa Mumy tayi ta wuce gun khadijah da taki fitowa daga kitchen, tana dubanta da kyau tace "Akwai wanda ya doke ki a gidan nan ne khadijah?" Khadijah ta girgixa kai da sauri tace "A'a Anty" Shiru mumy tayi tana kallonta, can ta juya ta fita kitchen din ta wuce sama gaba daya, Anty khadijah ta bi yayar tata da harara, da sauri kyauta ta shige kitchen tun kan su hada ido. Driver ne ya kai su kyauta da khadijah kasuwa misalin karfe sha daya domin yi ma khadijah siyayyar da mumy tace, Kyauta ta daukar mata duk wani abin da ta san xai amfaneta, har kayan sa wa, sai da kudaden suka kare sannan ta hakura suka koma gida, khadijah na ta lekan kayan daga cikin ledan kyauta ta kai mata rankwashi ta daure ledan da kyau. Xaune suka tadda Aliyu da abokin sa Farouq a parlor, kyauta ta gaishesu ta wuce daki, Khadijah ta kalli Aliyu da bai kalli inda suke ba tace "Good evening" yace "Evening" daga haka ta bi bayan Kyauta, Farouq na tambayarsa wacece ita bai taba ganinta ba. Ranan asabar mumy tasa khadijah ta shirya su je islamiyyar da su Siyama ke xuwa ayi mata register, saukin abun Anty khadijah na can daki tana ta bacci kamar matatcciya bata san abinda ake ciki ba, Da farko mumy driver tace yaje yyi mata komai a makarantar, amma ganin Aliyu ya shigo gidan daga clinic tace "Abuturrab tunda ka dawo ko xa ka taimaka kai ta ayi mata register?" Ya d'an hade rai yace "Noo Sanusin dai yaje ni yanxu shiryawa xan yi in tafi daurin aure zari'a" Mumy tace "Zaria? Sai ka dawo yaushe?" Yace "Anjima in sha Allah" tace "Toh shkkn" daga haka ya wuce sama, dole Sanusi ne ya tafi da su gaba daya makarantar khadijah dai na xaune daga jikin kofar motar su Siyama ko kallonta basu yi ba sai ma hade rai da suke ta yi, ko wace bata son jikinta ya taba nata don kuwa taxara sosai ne tsakaninsu a cikin motar, a ajin baby aka sa khadijah bayan anyi mata interview, nan Sanusi ya biya duk kudin ya karbar mata form ya koma gida don a cike mata, a ranan kuma mumy tasa ya je kasuwa ya yankar mata uniform da Hijab, kyauta sai murna take tayi mata bayan sun dawo da yamma, khadijah kuwa sai washe baki take tana bata labarin yanda islamiyyar yake, can kuma kyauta ta hade rai tace "Toh ni me yasa basu sani islamiyyar ba" khadijah ta xaro ido ta rike kugunta tace "Kaji Anty mai girki bayan kin girma?" Ranan lahadi bayan sun dawo islamiyya da yamma mumy ta sa Sanusi ya kai su saloon kasancewar duk lahadi suke gyaran gashi, tun da khadijah ta ji Mumy tace aje da ita hankalinta ya tashi, ta tafi ta kwanta kamar mai bacci a dakin kyauta, kyauta ce ta shiga ta korota waje ta rufe dakinta, haka dai suka tafi saloon khadijah kamar an aiko mata mutuwa duk ta daga hankali. Siyama aka fara gyara ma gashin sannan Aneesah sai baby, aka xo kan Khadijah tuni ta fara hawaye tace "Mai saloon ni gashina bai yi dirty ba ki duba ki gani" Mai saloon din ta saki baki tace "Toh bai yi datti ba me kika xo yi" cikin rawar murya tace "Anty ce tace sai na xo" Mai saloon na ganin xata tada mata hankali tace su wuce kawai bayan an bada kudin su siyama. Shiru Mumy tayi da mamaki tana kallon khadijah dake matsar kwalla bayan sun dawo, can tace "Sai kace yarinya khadijah, yanxu gyaran gashin ne kika ki tsayawa a maki?" Anty khadijah dake xaune tana ta girgixa kafa tana tabe baki cike da masifa tace "Ai maganinki kenan Anty Fati, gwara da ta kunyata ki ba ke sodangi ba" Mumy ta kalleta tace "Toh kika san ko tana da matsalar scalp ne?" Aliyu dake xaune dinning ya bar abincin da yake ci ya fito parlorn rike da makullin motarsa yana kallon khadijah yace "Mu je saloon din" xaro ido tayi ta nufi daki da gudu tace "Anty kice masa gashina bai yi ba datti wllh, mai saloon din ma ta duba tace mu tafi" ya hade rai yace "Xan xaneki idan kika shiga dakin nan...." Anty khadijah ta mike da mugun mamaki tace "Yau nake ganin ikon Allah... to ina ruwanka Aliyu? Meye damuwanka da gyaran gashinta da rashinsa har xaka zakalkale haka" Ko saurarenta bai yi ba ya sake ce ma khadijah ta fita kar ya xo ya sameta inda take, da gayya Kyauta ta kora masa ita waje tana satan kallon Anty khadijah, Ya bi bayan su bayan yasa baby ta biyosa, Kasa cewa komai Mumy tayi ta bi su da kallo, baby ce ta xauna gaba, Khadijah ta xauna a baya tana share hawayen da ya kawo idonta, kyauta ta rufe motar har da risinawarta tana daga ma Aliyu hannu tana masa Allah ya tsare hanya. Da kyar mai saloon ta gama gyaran gashin khadijah me tsayi bana wasa ba, sae sheki yake, ga gashin da uban laushi, khadijah tayi kuka har ta gode Allah, haka kowa ya saki baki yana kallonta a saloon din, babu sunan wanda bata kira ba bayan ummanta har da Anty mai girki da Mumy, shi dai Aliyu na tsaye yana kallonsu yana son yin dariya amma bai yi ba, baby ma na tsaye kusa da shi tana kallon khadijah, ba don shi ba da babu abinda xae sa khadijah ta tsayar da kanta har mai saloon ta samu daman gyarawa, dubu uku Aliyu ya ba mai saloon din tana ta godiya, yana ma khadijah wani kallo yace "Get up my friend" make kafada tayi wasu sabbin hawayen na xubo mata, kujera ya sa mu ya xauna yace "kiyi mata kitson kawai madam" da gudu khadijah ta fice a saloon din, baby ta kyalkyale da dariya mutanen dake cikin saloon din na taya ta, khadijah dake tsaye jikin mota ta dinga leka saloon din ko matar ta biyota, yana fitowa ya dagata yyi cikin saloon din ta rirrikesa tana ihu tana basa hakuri, mai saloon dake dariya tace "Ta tuba babban yaya ayi mata hakuri" baby ta rufe baki tana dariya har da kyakyatawa, bude bayan motar yyi ya saka ta ciki ya rufe ba shiri tayi tsit kirjinta na heaving, ya harareta ta madubi yace "Xan yi maganin ki ne" Bayan sun koma gida har daki Anty khadijah ta bi Aliyu, Ta rufe kofa tana masa wani kallo tace "Aliyu akan wani dalili ka tafi da yarinyar nan saloon daxu, ban gane me hakan ke nufi ba, ka taba sanin ta ne da can ko kuwa shisshigi ne da hali irin na uwarka ya motsa? Kai ma sodangin xaka koma" Aliyu dake ta kallonta yace "Meye a ciki don na kai ta saloon Anty, Kina fa ji Mumy ce tasa ta bi su Siyama kuma ta ki yarda ayi mata, to make my mum talk less shi yasa kawai ni na kai ta da kaina kuma ba gashi ta tsaya ba" Anty khadijah tace "Eh lallai ni kake gaya ma bakar magana ko Aliyu? Babu damuwa, xan yi maganinka" daga haka ta fita, Aliyu ya tabe baki ya mike ya rufe kofar sa don a bude ta bar masa. Yau khadijah ta cika sati biyu gidansu Aliyu, babu abinda Mumy ta rage ta da shi a gidan, duk yanda ta yi da su siyama haka take mata ita ma banbancin kawai shi ne har lkcn a dakin kyauta take, kusan dai kyauta ce kadai mai aikin gidan don ko kadan kyautan ma bata takura khadijah tayi aiki sai dai fa tana nuna mata abubuwa da yawa ko kadan ne tana barinta tayi har goge gogen, ranan da khadijah ke da sati daya a gidan Anty khadijah ta tafi Abuja ganin yaranta, hakan yasa hankalin khadijah kwance har na sati biyu yanxu, Tunda baby ta ci duka gun Aliyu ko kallon banxa bata sake ma khadijah ba, sai ma note da take bata wani lokacin ta kwafar mata na boko ita dai Mumy bata ce masu kala don kuwa rubutun khadijar ma ya fi na baby kyau, har assignment khadijah na kwatanta yi ma baby, su siyama dama ba wani interacting suke da ita ba, don haka babu ruwansu da ita, A yau da ta cika sati biyu ne mumy na bedroom dinta da yamma Aliyu ya shigo, Gaisheta yyi tace "Halan ka fita nyt duty ne?" Yace "Tun three days back yanxu morning xuwa yamma nake yi" tace "Ohk, kun yi waya da Abbanku" Aliyu ya shafa kansa yace "Ehh ai gobe xai taho in sha Allah" tace "Nima haka yace min daxu" yana fiddo wayarsa a aljihu yace "Wai yaushe Anty xata dawo mumy?" Mumy tace "Toh nima dai ban sani ba wllh, amma jiya da ta kirani kamar akwai damuwa kilan su Iklima na cikin wani hali...." Yace "Toh Mumy wai me yasa iklimar baxata dawo nan gidan ba, su Ahmad maxa ne bbu damuwa sosai amma ita macen da ta dawo nan" Mumy tace "Ai ubansu baxai yarda ba ne matsalan sai dai ta taho da ita ba tare da ya sani ba" Aliyu ya girgixa kai yace "Allah ya kiyaye" mumy tace "Ameen dai" Shiru yyi bai sake cewa komai ba, Mumy tace "Ya aka yi kamar kana son yin magana koh?" Murmushi yyi don sure yasan mum dinsa ta gama karantarsa gaba daya, yana facing dinta yace "Mumy dama ba komai bane a kan Mai sunan Anty ne" tunda khadijah ta shigo gidan bai taba kiran sunanta ba saboda Anty khadijah, Mumy ta kallesa da sauri tace "What about her?" Yace "Noo, kawai mum naga da ki taimaka a sa ta a boko..." Katse sa tayi tana kallonsa da kyau tace "Ko saboda me?" Ya d'an bude ido yace "Noo Mumy naga kawai she isn't an illiterate, its just anyi depriving dinta right dinta ne, from all indications she was born with a silver spoon, you knw... it's just condition mum, ina tausayinta ne wllh, kin dai ga har coaching Baby tana kokarin yi, she is very intelligent, Allah will reward you idan kika taimaka mata mumy" murmushi mumy tayi tace "Kasan me Ali?" Ya girgixa kai da sauri yana kallonta, strictly tace "Abuturrab ko da wasa, I mean ko ba a cikin hankalinka ba, kayi making mistake din ce min kana son yarinyar nan wataran I will show u my other side, because it will and will neva be possible, that is just it" da mugun mamaki yake kallonta, a hankali yace "Sonta kuma mum?" Ta gyada kai tace "Yes" yyi shiru na few seconds kafin yace "Mai ya kawo wannan xancen mumy?" Ta hade rai tace "Kai ka kawo sa, for I see no reason har xaka damu In sa ta makaranta kai ka kawo min ita gidan?" Ya girgixa kai kawai, tace "To be careful, yes xan sa ta makarantar boko amma wllh wllh ko a mafarki ka cire ran akwai aure tsakanin ka da yarinyar nan, period" Ya kalli Mumy a hankali yace "But.. Ko saboda me" strictly Mumy tace "Hakan nake so ya kasance, or are you querying me" yace "Amma mumy ni ai ba ce maki nayi ina son ta ba, boko kadai nace ki sa ta for the sake of Allah, meye ma xai sa kiyi tunanin nan mumy, ni kuma in rasa warce xan ce ina so sai karamar yarinyar nan? Wallahil azim ban taba kawo hakan a raina ba, gaskiya I am nt happy mum" daga haka ya mike ya fita a dakin. Ranan Monday da asuba Mumy ta shiga kitchen gun kyauta dake ta kokarin hada ma yan makaranta breakfast, cike da ladabi ta gaida Mumy, mumy ta amsa tana mata sannu da aiki sannan tace "Khadijah bata tashi ba?" Kyauta tace "Ina jin tana can tana sallah ne" kyauta ta dai fada haka ne amma in dai khadijah tasan tana can tana bacci, Mumy tace "Wai boko nake son ta fara xuwa yau..." Kyauta ta xaro ido tace "Boko Hajiya, Allah ya saka maki da alkhairi, ya kara daukaka, Allah ya biya maki bukatun ki masu kyau Hajiya, yanda kike taimako kema Allah ya ji k'an ki a nan duniya da ma lahira" Mumy da ke ta kallon kyauta tayi murmushi tace "Toh Ameen" daga haka ta juya ta wuce, kyauta ta rike ha6a baki bude murya can kasa tace "Ko ya baxawara xata dau xancen nan idan ta dawo, Ashe ko akwai karamin yaki a gidan nan" a stairs mumy ta hadu da Aliyu ya shirya xai fita aiki, tace "Da asuban xaka fita aiki?" Yyi kasa da kai ya gaisheta ta amsa tare sa cewa "How was ur nyt?" Yace "Alhmdllh" tace "Breakfast din fa?" Yace "Xan yi a office" tace "Bawan Allah ai bbu xancen yin sammakon fita aiki xaka kai khadijah makaranta anjima" Juyowa yyi ya kalleta da sauri yace "A'a ni Mumy baxan iya xuwa ba, Ba ga sanusi ba da mai aikin can su kai ta mana" kallonsa mumy ta tsaya yi, can tace "Directly ma kake ce min baxa ka iya xuwa ba koh?" Yace "Toh Mumy ni da xan fita aiki kuma wani makaranta xan kai ta, komai fa sanusi xai iya yi kin sani" Mumy bata kuma saurarensa ba tayi wucewarta sama, fuskarsa daure ya juya ya koma sama shi ma. Tun da kyauta ta tada Khadijah tayi mata albishir din xancen da Mumy tayi mata khadijah ke ta murna har da rawanta, can kyauta dake taya ta murnar ita ma ta hade rai tace "Wato ni ce dai hajiya bata so a gidan nan ba arabi ba boko, sai dai in sauke in daura in yi shara inyi wanke wanke, akwai Allah" khadijah da har xata shiga bathroom ta dawo da sauri ta yo waje da ido tace "Anty mai girki? Katuwa da ke baki gama school ba dama, me kika tsaya yi toh?" Kyauta ta dunguri hancinta tace "Ai ban kai baxawara ba da take kamar buhu" Khadijah ta wara ido tace "Ni kinsan yaushe rabon da in je school, to in gaya maki tun ina gidanmu tare da Ummata, Allah ya sa ban girma ba da shikenan yanxu ni ma baxan je ba" bata sake sauraren kyauta ba ta shiga bathroom da sauri ta rufe. Kafin karfe bakwai duk yaran gidan sun shirya kyauta ta tabbatar khadijah ma ta shirya cikin daya daga kayan da ta siyo mata a kasuwa shekaranjiya ta lafta mata uban kwalli a ido, ta shafa mata jan powderta a fuska, Da kyar khadijah ta yarda xata yi breakfast saboda excitement, duk ta kagu su wuce makarantar, shi dai Aliyu na xaune parlor hannunsa rike da mug din coffee, su siyama kuma na dinning suna breakfast, Khadijah kuma na kitchen kyauta ta shimfida mata wani xaninta a kasan tiles din kitchen din don kar kayan jikinta yayi stain, jin Driver na horn a waje Kyauta ta daga khadijah da sauri ta kwace bread din hannunta ta turata waje tana cewa "Shegiya sai ta sa sun canxa ra'ayinsu maxa tafi xa su wuce" Aliyu ya fita ya samu Driver yace "Sanusi ni xan kai su, don't worry" Har su Siyama sun fita Sanusi ya gaya masu abinda Aliyu yace, Siyama ta tabe baki hade da jingina da motar tace "Shine yana ganin mun fito baxai gaya mana ba, I don't just like this Ya Aliyu sometimes" Aneesah tace "Ni kuma ina son sa haka, ya ma fi min ya Saleem" Siyama tace "Shi yasa nake ta addu'ar ya saleem su dawo tare da Abba anjima" Motar Aliyu suka nufa, baby da fitowarta kenan ta bi bayansu, Aliyu ya wuce upstairs dakin mumy ya sameta har ta shirya xata kai khadijah makarantar da kanta, ya d'an bude ido yace "Mumy kin fa san I didn't mean it, ko baki fada ba ai xan kai ta..." Ta katse sa tace "Toh tunda Allah ya ban lafiyata ba gwara in fita in biya ma kai na bukatar dake gabana ba, Saleem will Neva look into my face yace min baxa shi ba ai, so this is just ur differences" Aliyu yayi kasa da murya yace "Toh kiyi hakuri Mumy, ban san ran ki xai baci ba, I am very sorry" tace "Noo ni rai na bai baci ba, kai dai da na bata ma rai xaka iya tafiya aikin ka kayi hakuri, ni da ya xame min dole xan kai ta da kai na" murmushi yayi yace "Don Allah mumy kiyi hakuri ni xan kai ta ba sai kin je ba" da kyar Aliyu ya samu ya lallaba Mumy ta hakura ta bar shi ya kai khadijah makaranta tare da Kanninsa, babu yanda bata yi ya amshi wayarta ya masu transfer din duk fees din a can makarantar ba ya ki yace xai yi da nasa kudin, da haka dai ta hakura ta kyalesa ya sakko parlor rike da makullin motarsa, makale ya tadda Khadijah jikin kofar parlor da alama su siyama dai sun korota ne, Kyauta ma na bakin kofar bayan sanusi yace mata Aliyu ne xai kai su, sai leken su siyama take tana Allah wadaran da halin baxawara da suka yi, tana ganin Aliyu tayi tsit, tayi kasa da kai tace "Sannu da fitowa yallabai" yace "Yauwa" sannan ya fita, tura khadijah tayi ta rufe kofar parlorn. Khadijah ta dinga bin Aliyu har suka isa gun motarsa, su siyama suka yi shiru daga xancen da suke ko wacce na kallonsa, Yace "Wacece ta korata a cikin ku?" Da sauri baby tace "Allah ya so bani bace ba wllh yayanmu" yana kallonta yace "Toh waye?" Nuna masa su Aneesah tayi, yace "Why did u both send her away?" Aneesah tace "Toh yaya kawai ta xo gun mota ta tsaya mu da makaranta xa mu" yace "Ita ma makarantar ae xata" Da sauri siyama tace "What??? Wani makarantar?" Baby tace "Na mu mana, ai Mumy ta gaya min da na yi wanka a dakinta daxu" Siyama da ta rikice tace "Yaya kamar ya makarantar mu, ni yaya ko xa a sa ta makaranta let it not be ours, they are a lot of schools out there don Allah a kai ta" Har da guntun hawayenta, Aneesah ma duk hankalinta ya tashi, ita dai khadijah na daga gefe tana kallonsu, yace "Alryt idan na kai ta makarantar taku kada ku bari ayi admitting dinta" daga haka yace baby ta shiga mota, baby ta shiga gaba ya bude back seat yana kallon khadijah yace "Get in" da sauri ta shiga motar ya rufe ya bude driver seat ya shiga yana kallonsu siyama yace "Ku je sanusi ya kai ku coz xan iya maku abinda ke raina idan ku ka shiga motar nan, mind u kada warce ko da wasa ta sake shiga cikin gidan can, it's either ku je sanusi ya kai ku makaranta or you remain here till 4" daga haka yayi warming motarsa mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan, siyama ta fashe da kukan takaici Aneesah na taya ta. Essence int'l school, abinda khadijah ke ta nanatawa kenan a xuciyarta tun shigiwarsu cikin babban makarantar, baby ta bude kofa ta fita, ya juya yana kallon khadijah, xaro ido yyi yana kallon nata idon yace "Meye wnn din a idon ki?" Ta buda hannu tace "Anty mai girki ce ta sa min kwalli" tsaki yyi ya Ciro handkerchief a aljihunsa ya mika mata yace "Common goge wannan bakin abin da ta goga maki a ido kamar herbalist" khadijah ta kyalkyale da dariya ta karba tace "Herbalist kuma" bai tanka ta ba ta shiga share kwallin, jawota yyi ya fixge handkerchief din a hannunta ya fara goge mata idon, sai bata fuska take xata yi kuka, ya hade rai yace "What?" A hankali tace "It's painful" yace "Good... Next time idan xata sa maki baxa ki yarda ba" ajiye handkerchief din yyi bayan ya tabbatar bbu sauran kwallin a idonta ya fita, ita ma ta fito ya wuce direct office din principal din kasancewar shi ma makarantar da yyi kenan, kuma har lkcn ba a canxa principal ba, da ladabi ya gaisa da principal din da shi ma yyi murnar ganinsa sosai, nan Aliyu ya sanar masa ya xo enrolling khadijah ne, principal din ya tambayi khadijah class din da take xata ce jss2 Aliyu yyi saurin cewa Jss3, xaro ido tayi ta kallesa ya mata wani kallo ya ci gaba da yi ma principal din bayani, farkon abinda principal din ya bukata shine transfer letter daga previous schl dinta, Aliyu ya d'an yi jim, can yace masa xai karbo ya kawo, da yake principal din ya san shi yasan family dinsu bai masa gardama ba, nan kuma yasa aka yi interviewing dinta, babu bata lkci kuma aka yarda a sa jss3 din coz she is capable, a take Aliyu yyi transfer din school fees da other fees da ake biya na makarantar har takardu da uniforms guda uku, Principal na kallonta xai cike mata receipt yace "What's ur name" kafin Khadijah tace komai Aliyu yace "Khadijatul Iman" Khadijah ta xaro ido tana kallonsa, principal din yace "Surname" sai a sannan Aliyu ya kalleta, ta langwabar da kai a hankali tace "Muhammad" principal din ya so aliyu ya maida ta gida gobe tayi resuming yace A'a ta fara yau din shi aiki xai wuce ba gida ba, a tare suka fito da Khadijah office din principal din bayan yace Aliyu ya nuna mata ajinta, Tana biye da shi a baya ya juya yana kallonta yace "Wani makarantar kika yi primary da jss1?" Tace "Yan dutse" yace "Kano?" Ta gyada masa kai, bai sake cewa komai ba har ya isa class dinsu Baby ya nuna mata ta shiga tana daga masu hannu, ya juya ya tafi gun da ya bar motarsa. Karfe hudu saura driver ya ajiye su a gida, sai da su siyama dake ta kumburi cikin motar suka fita sannan khadijah ta fito rike da ledan uniforms dinta da takardu, Baby ma ta fito rike da sauran takardun khadijah, Duk sai da kyauta ta bi ta yi ma uniforms din tsirara daga ledansu tana washe baki tace "Yarinya ta xama yar boko, toh me suka koya maku yau a makarantar" Khadijah tayi dariya tana cire kayan jikinta tace "anty mai girki yanxu xan yi wanka ne, idan na fito xan koya maki" daga haka ta shiga bathroom da sauri, har daki kyauta ta kawo mata abinci bayan ta xuba ma su siyama nasu a dinning, khadijah dake ta kallon pepper soups kala kusan uku da ta xubo mata tace "anty mai girki, kinyi girki da yawa kenan yau?" Kyauta tace "Ke Alhaji da kanin Aliyu xa su dawo anjima, yanxu haka suna can cikin jirgi a sararin samaniya, ai girkin da nayi ya fi kala shidda yau tun safe nake kitchen, na kuma ji Hajiya nacewa kila baxawara ma ta dawo yau" Khadijah ta tallabi cin dinta tace "Waye Alhaji anty mai girki?" Kyauta ta hade rai tace "Babansu Aliyu mana" Khadijah ta xaro ido da mamaki tace "Dama yana da baba, ai na xata shine baban gidan" Kyauta tayi tsaki tace "Dadina dake shegen shirme, toh an ce maki shi ya haifi kansa, ubansa nace maki xai dawo anjima tare da kanin sa saleem" Khadijah ta turo baki tana d'and'ana naman ragon gabanta tace "Toh naji" Baby ce ta shigo dakin bayan Khadijah ta gama cin abinci kyauta ta fita da plates din, baby tace "Mumyna tace in kira ki" Mikewa Khadijah tayi ta bi bayanta suka wuce sama, tun bayan da Anty khadijah ta koreta sai ranan ta sake hawa saman gidan, baby ta bude kofar dakin mumy ta shiga, khadijah ta tsaya daga bakin kofa tana lekan dakin, Mumy da ta hangota tace "Shigo khadijah" khadijah ta shiga ta xauna kasa tace "Ina yini Anty" mumy tace "Lafiya lau, ya school din" Khadijah tayi murmushi tace "I like it Anty" Mumy tace "Sun baki uniform?" Khadijah ta gyada mata kai, Baby tace "Mumy same class fa muke da ita" Mumy tace "That's good, ina books din da suka baki" mikewa Khadijah tayi da sauri ta ce "Xan dauko" daga haka ta koma kasa ta dauko books din ta ajiye ma Mumy, Mumy na kallon book din ganin Iman a jiki tace "Iman? Is that ur name?" Khadijah tayi murmushi ta gyada mata kai a hankali, mumy tace "Maa sha Allah" wani sabon jaka da bakin cover shoe da socks uku mumy ta dauko ta mika ma khadijah tace "Gashi sai ki xuba books din ciki" khadijah ta wara ido tace "Anty nagode, thank you" Mumy tace "Welcm, tashi ki tafi" mikewa khadijah tayi cike da murna ta fita, baby dake kallon mumynta tace "Mumy ni yaushe xa ki siya min sabon jaka?" Mumy tace "Soon" har kitchen Khadijah ta kai ma kyauta abinda mumy ta bata, kyauta ta amshe tana washe hakora tace "Allahu Akbar barin baxawara gidan nan ya maki rana dije, Allah ya makaleta a duk inda take har Hajiya ta gama dake ta dawo kai na nima" Shigowar Aneesah kitchen din yasa Kyauta tayi shiru sum sum ta fita don kai kayan daki Khadijah na biye da ita a baya. Suna shiga dakin ko minti biyar ba ayi ba aka kwankwasa kofa kyauta ta tashi da sauri ta bude, Aliyu ne tsaye rike da wani jakar mai kyau ya mika ma kyauta yace "Gashi ki bata" kyauta ta risina ta karba tace "Toh ta gode, Allah saka da alkhairi" bai ce komai ba ya juya ya bar wajen, kyauta ta bude jakar jin da nauyi ta ga takalma har biyu da safa uku a ciki sai water bottle irin nasu baby, kyauta ta rike haba tace "Ni dai ce ba a so a gidan nan wllh" Khadijah dake jera books dinta a jakar da mumy ta bata ta taso da sauri tace "Anty mai girki menene" Kyauta ta dungura mata tace "Duk kin fi ni goshi wllh" Khadijah ta kyalkyale da dariya ta karbi jakar da a gabansa aka rubuta *Iman* ta wara ido tace "Waowww" Shirin tafiya islamiyya suka yi bayan sun ci abinci, tun da Khadijah ta fito sanye da uniform din islamiyya Siyama ke ta harararta, kyauta da ta lura da hakan ta ja Khadijah kitchen tace "Kafin su gama iskancinsu da harare harare tafi gun Sanusi ki jira a gun motar" Khadijah ta fita ta tafi gun da motar yake ta tsaya, Aliyu ne ya fito baby na biye da shi a baya ita ma ta shirya, Baby tace "Yayanmu kenan baxan je mu taho da Daddy ba?" Yana bude motarsa yace "Ai islamiyya xa ki baby" ta bata fuska tace "Yaya yau kadai xan yi fashi fa" yace "Bulalan da xa a maki fa?" Tace "Ae cewa xanyi bani da lafiya sai ka rubuta min medical report in kai" yace "C'mon wuce ki shiga mota ku tafi makaranta my frnd... Bakin ki kamar medical report" Juyawa tayi kamar xata yi kuka ta tafi gun Khadijah dake kallonsu, ya shiga motarsa ya bar gidan. Karfe shidda da 'yan mintuna suka shigo gidan daga islamiyya, wani saurayi ne xaune parlorn shi kadai yana danna laptop, ba can suke kama da Aliyu ba amma kana ganinsu kasan yan uwan juna ne, su siyama suka yi kansa cike da murnar ganinsa, siyama ta rungumesa tace "Wllh nayi kewarka ya salim, wai don Allah yaushe Yaya Aliyu xai tafi duk ya takura mu gidan nan, the house is just boring with him, idan Abba xai koma ya tafi da shi ya bar mana kai plss, Allah ya Aliyu is a problem in this house ko irin d'an birthday din frnds da party ya hana mu xuwa daga boko sai islamiyya" kamar xata yi kuka ta kare maganar, shi dai saleem sai uhn, uhm yake ta cewa yana sunkuyar da kai, sum sum Aneesah ta wuce sama, hakan yasa siyama ta bi parlon da kallo ta ga ya Aliyun xaune dinning yana kallonta, dauke kai tayi da sauri ta toshe baki tana xaro ido tace "Na shiga uku" Saleem ya dinga dariya kasa kasa har da kyakyatawa ba tare da ya kalli direction din Aliyu ba, Khadijah dake tsaye ita ma ta rufe fuskarta da Hijab ta wuce dakin kyauta tana murmushi, bin ta da wani kallo saleem yyi da wani expression yace "Who's this?" Siyama ta yamutse fuska tace "The new housemaid after kyauta...." ya buda ido yace "What" tabe baki tayi ta mike tana satan kallon Aliyu tace "Sannu da gida yayanmu" kallon fork din gabansa yyi ya dauka tana ganin haka da gudu ta wuce sama tana turo baki, Saleem yyi murmushi ya mike ya isa dinning din yace "Big bro duk ka takura masu koh" Aliyu bai tanka sa ba ya dau Apple din gabansa ya fara ci. Bayan isha duk yan gidan suka hallara a dinning kasancewar in dai Daddy na garin duk a tare suke yin dinner a dinning area, Last cooler din kenan na soyayyen kaji kyauta ta dauka xata kai masu dinning din kasancewar ta mance Daddy ya hango Khadijah da ita ma ta fito daga kitchen xata shiga dakin kyauta rike da plate din abincinta, yana kallon Mumy yace "Kun yi baki ne?" Mumy ta kalli direction din Khadijah kafin ta shiga dakin ta kira ta, Juyowa Khadijah ta yi ta dawo, Sau daya Aliyu ya kalleta ya ci gaba da cin abincinsa kansa a sunkuye, Mumy tace "Yarinya ce aka kawo min riko daddy, kayi hakuri ban sanar maka ba yau satinta kusan uku, dama ina jiran sai ka dawo ne" yace "Riko kuma, daga ina" mumy ta yi yar dariya tace "Marainiyar Allah ce nan da ka gani" Saleem ya juya yana kallo Khadijah dake tahowa, Siyama ta tabe baki tare da tura abincin gabanta, Khadijah na isa wajen tana kallon Daddy a hankali tace "Good evening sir" da fara'arsa yace "Evening how are you" Khadijah tace "Alhmdllh, hw was the trip?" Ya kalli Mumy yana murmushi yace "It's great" Shiru Khadijah tayi daddy ya nuna mata kujeran dake kusa da Saleem yace "Have ur sit ke ma" Ta gefen ido Saleem ke kallonta, Khadijah ta buda ido tace "Noo uncle I will love eating alone" daddy yyi murmushi yace "Alright then, do what pleases you" a hankali tace "Thank you" daga haka ta juya ta wuce, Daddy ya dau cokalinsa yace "She is sharp, haka nake son baby ta xama but baby is too meek" baby ta turo baki, Mumy tayi dariya tana kallon Baby da ta bata rai, kyauta ta bar wajen tana washe hakora a ranta tace "Har da mai gidan ma turanci take tsabar iya turancinta" sai da Daddy ya bar dinning area din sannan Saleem yyi facing Mumy yace "Wai mumy wacece yarinyar?" Aliyu ya ajiye cup din hannunsa yace "Did you have any business with her" Siyama ta hararesa ta gefen ido tace "Ya saleem na gaya maka house maid ce ko baka yarda bane, xan ma karya ne?" Mumy ta kalleta tace "She is a house maid or other wise thats nt ur problem, kuma kada ki sake kiranta da haka, yar rainin wayo kawai" jefar da cokalin hannunta tayi ta bar dinning din da sauri Aliyu ya bi ta da wani irin kallo, mikewa saleem yyi yace "Akan wata banxa can xaki bata mata rai mumy, for what...." Daga haka ya bar dining din shi ma, Aneesah ma ta tabe baki ta mike ta bi bayansu, Mumy ta bi su da kallo kafin tace "Allah ya kyauta" shi dai Aliyu bai ce komai ba, can mumy ma ta mike ta bar dining din, Baby ta bi abincin da suka bari ta kwashe naman kai ta sa a nata, Aliyu dake ta bin ta da kallo yyi murmushi yace "Glutton of the house" washe baki tayi tace "I don't want it to waste yayanmu" yace "Then go and share it with Iman" mikewa tayi rike da plate din ta wuce dakin kyauta, ba a dau lkci ba ta fito ta ajiye plate din kan dinning tace "Na bata yayanmu, xan je wajen mumyna" daga haka ta wuce sama, yana ta xaune dinning din Khadijah ta fito rike da plate xata kai kitchen, tsayawa tayi ganinsa sai kuma ta nufesa tana murmushi ta buda dara daran idonta tace "Yayanmu thanks for the school bag I love it" kallonta yake yace "Wa yace maki sunana yayanmu" tayi dariya tace "Na ji baby tana kiranka haka, Anty kuma tana ce maka Aliyu, su Anty siyama kuma yaya Aliyu" bai ce komai ba ta juya xata wuce sai kuma ta dawo tace "But did you buy the bag with d name iman or you where d one dat place it there?" Yace "I don't knw" wara ido tayi tace "Okay" sannan ta wuce kitchen, ganin kyauta ta fito gyaran dinning din ya mike ya wuce sama. Kafin Khadijah tayi bacci baby ta shigo mata da tsaraban da Daddy ya kawo tun daga kan chocolates, teddy bears, novels, takalma, rigan sanyi da ribbons na gashi sai kaya kala daya, kai kana ganin tsabar kasan na baby ne Mumy ta raba ta bata ta kai ma Khadijah, kyauta ma baby ta kawo mata nata tsaraban tana ta godiya baki har kunne. Kyauta na kitchen bayan su Khadijah duk sun wuce makaranta taji muryar saleem yana cewa "The great Aunt, ko minti goma ban yi da cewa xan kira ki inji yaushe xaki dawo, don duk gidan ba dadi ashe dai kina hanya" Anty Khadijah dake shigo da jakunkuna tace "Wllh kuwa, don ma d'an iska tsinannen mai mota muka samu, shi yasa na so Anty fati ta bani motar ta da xan tafi ta ki, banda haka wani banxan ne ya isa ya bata min rai a titi" Saleem dake taimaka mata shigo da kayan yace "Ae sai a hankali bin motar haya Anty da baki fara ba" Kyauta ta kwalalo ido ta jingina da kofa tace "Asshaa... Baxawara an dawo" Muryar Anty Khadijah taji tana cewa "Toh baxa ki shigo bane iklima ko kin kasa cire takalmin ne" kyauta ta leka a hankali suka yi ido hudu da Anty Khadijah, fitowa kitchen din tayi baki har kunne tace "Lale marhaba, Hajiya ashe ku ne, sannun ku da isowa" babu yabo babu fallasa Anty Khadijah tace "Ki hado ma iklima breakfast bata karya ba muka taho" sai a sannan yarinyar ta shigo parlorn, baxa ta wuce su baby ba a shekaru amma kana ganinta kasan cikin wahala take, ga tabo duk jikinta, kyauta ta karasa kusa da ita da gudu ta rungumeta tace "Yau ga iklima na gani ashe kece, yar kyakkyawa maa sha Allah, sannu da xuwa iklimatu" Anty Khadijah tace "Dalla ki cikata ki tafi ki nema mata abun k'ari, dangi uwa ko na uba" da sauri kyauta ta juya ta nufi kitchen, iklima ta bi ta da harara tace "Ashe ma house maid ce, kawai xata shafa min datti a jiki" Saleem yace "Iyye kaji Iklima manya, wato datti xata shafa maki koh, to ina su Yusuf?" Ta turo baki tace "Ai basu san mun taho ba" Anty Khadijah da ta yi hanyar stairs da jaka tace "Kafin ta gama maki breakfast din taho in sa maki ruwan xafi kiyi wanka, Saleem ku kuma saukan yaushe" Saleem yace "Jiya muka dawo Anty" tace "Daddy na part dinsu kenan" Saleem yace "Ina ji" bin bayanta yyi da sauran kayan, sai da suka isa dakinta tace "Aliyu fa?" Ya ajiye jakar hannunsa yace "Ya fita aiki." Mumy ce ta fito jin muryar yar uwarta ta shiga dakin ita ma. Har bakin daki kyauta ta kawo ma su Anty Khadijah breakfast din, Mumy ta taso ta karba ta dawo ta ajiye ta xauna tana sauraren 'yar uwar ta, Anty Khadijah tace "Toh fa kin ji Anty fati, kuma in sha Allahu da daddaya xan dauke yarana gaba daya a gidan, a kan wani dalili ina raye, dubi yanda iklima ta koma, mata muguwa axxaluma kawai duk ta gama da ubansu, tana neman kashe min 'ya ya ni wllh da ba dan bana ra'ayin Salisu ba da bbu abinda xai hana ni fitar da matar nan in koma gidan" Mumy dake ta kallonta tace "Ta ya?" Anty Khadijah tayi kwafa tace "Lallai kina wasa da ni Anty" Mumy bata sake cewa komai ba sai bin iklima take da ta fito wanka da kallo, Anty Khadijah ta sauka ta shiga hada mata shayi tace "Yi maxa ki shafa mai ki taho kiyi breakfast Pretty" Mumy tace "Toh Allah ya kyauta, Allah kuma ya shiryi masu irin halin ta, Allah ya raya mu tare da yaranmu" Anty Khadijah tace "Ameen fa" Mumy tace "shi yasa na ke nuna maki masu aikin nan ki rabu da su lafiya, tsakaninki da su gaisuwar mutunci wani hantara da nuna isa duk ba shi bane" dakatar da ita Anty Khadijah tayi da hannu ta daure fuska tace "A'a kar ki fara Anty kar ki bata min, dangin uwa ko na uba da xan dinga gaisuwar mutunci da su su rainani, ni ba gashi yarana basu ji ba basu gani ba ana walakantasu suna wahala, don haka ki kyaleni nayi ma kowa ma haka" Mumy ta tabe baki tace "Ka ji xancen banxan, to ai wannan a rubuce yake duk abinda kayi ma 'ya yan wasu sai an ma naka abinda nake ta nuna maki kenan kin ki gane wa" rai bace Anty Khadijah ta mike tana kallon Mumy tace "Ni dama tun da dadewa nasan ba so nake kike ba kawai kina xaune ne da ni dole don 6are ma sun fi ni k'ima a idon ki, Anty fati dole ne sai na xama so dangi kamar ki? Me ya hada ni da 'ya yan wasu? Don Allah ki kyaleni in yi rayuwata yanda nake so, ke kije can kiyi ta kwashe kwashen mutane har sai kin kwaso warce xata fiddo ki a inuwar da kike ta tura ki rana, muna nan da ke kuma" Tashi Mumy tayi ta nufi kofa bata sake tanka ta ba, Anty Khadijah ta bi ta da harara tace "Ke so dangi... To mutanen nan su ne xasu raba ki da farin cikin ki idan ba ki yi hankali ba" Saleem dake ta xaune a dakin bai tofa nasa ba tun daxu ya girgixa kai bayan fitar Mumy, Anty Khadijah tace "Kai ka ji fa saleem, dole ne sai na ja mutane gantalallu da xa su daura min wahala a rayuwa a jiki? In ji da yarana da kai na mana, Ita taga xata iya ne halinmu ba daya ba kuma baxai taba xuwa daya ba in dai a kan wannan ne, gwara ta kyaleni, kuma duk shegen da bai gallaza ma 'ya yana ba bai haifu cikin uwarsa ba... Mutum ne idan ban son sa ban son sa har abada babu me canxa min ra'ayi" Saleem yace "Ni Anty ban san me yasa Mumy take haka ba wllh, yau wannan gobe wancan, dubi fa kwanaki da kyar ta mayar da fitsararriyar yarinyar nan kauyensu ga shi yanxu ta jajibo wata ita wannan har boko naga an sa ta saboda matsayi" Anty Khadijah ta juyo tana facing dinsa a hankali tace "Wani bokon?" Saleem yace "Essence wllh" kasa rufe baki Anty Khadijah tayi tana kallon Saleem xuciyarta na bugawa, can ta nufi kofa fuuu ta fita, k'asa ta sauka gun kyauta, Kyauta dake ta aiki a kitchen tana wake wake tayi shiru ganinta ta risina tace "Har kin samu fitowa Hajiya" Anty Khadijah bata saurareta ba da wani expression tace "Kyauta ina yar uwar ki mai aiki nan" kyauta tayi kasa da kai tace "Toh Hajiya, jiya madam ta sa a kai ta makarantar bokon su baby, yanxu haka ma tana can" Anty Khadijah ta saki salati bata sake saurarenta ba fuuu ta wuce sama ta bude dakin Mumy, daga bakin kofa tana huci tace "Anty ita mai aikin kika saka a makarantar su siyama?" Mumy ta daga mata hannu tace "Khadijah ki tafi ki ban waje kar ki sake bata min rai don Allah, da kudin ki na sa ta bokon ko da ajiyar da kika bani?" Wani murmushi Anty Khadijah tayi tace "Ko daya, amma wllh kinyi making babban mistake a rayuwar ki, ita mai aikin kika sa a boko koh? Tam Allah ya taimaka, aje xuwa" daga haka ta fice daga dakin, parlor ta koma ta xaune tana girgixa kafa xuciyarta na kuna, can ta dau wayarta ta shiga kiran Aliyu, Aliyu dake xaune office ya dinga kallon wayar ganin mai kiransa har ya kusa katsewa sannan ya daga ya kai kunne hade da sallama, ko amsa sallamar bata yi ba cikin daga murya tace "Yanxu Aliyu kana gidan nan ka bari Anty ta sa mai aikin nan a makarantar da ku kayi?" Tabe baki yyi bai ce komai ba har lkcn wayar na kare kunnensa, tace "Ko da yake its a mistake ma kiran ka da nayi don duk bakin ku daya da Anty, kai ne ma munafukin... amma ina son ka sani wllh ta dauko ma kanta dala ba gammo ne, sai tayi mugun da ta sanin sake ma 6are da take yi kwanan nan ba sai an dade ba, sai ta xo ta sameni har daki tace Ashe abinda kike yawan gaya min gaskiya ne Khadijah, ni kuma a lokacin xan mata dariya, kai kuma ka ci gaba da biye ma gurgayen shawarar da take yi da kai har kai sai ya shafa muna nan baxa a dade ba in sha Allah, ita yarinyar da ku ka sa a makarantar sai ta ma sharrin da har jikoki baxa ka mance ba, sai ta goga ka bak'i a idon duniya" daga haka ta katse wayarta, Aliyu ya tabe a baki a xuciyarsa yace Allah ya shirye ki, daga haka ya ajiye wayar ya ci gaba da abinda yake. Da yamma bayan su Khadijah sun dawo tana bathroom ta shiga wanka kyauta kuma na fiddo mata kayan da xata sa sai ga Anty Khadijah ta shigo dakin 'yar ta Iklima na biye da ita a baya, Ko rufe kofar bata yi ba tana ma kyauta matsiyacin kallo tace "Ina tsinanniyar take?" Kyauta ta rasa abun cewa ta fara kame kame sai ga Khadijah ta fito daure da towel, kin karasowa dakin ta yi ganin Anty Khadijah, kai kana ganinta kasan tayi mugun tsorata, Anty Khadijah ta karasa ta fixgota da karfi tace "Kina da gadon mutanen gidan nan ne da kika yarda suka sa ki a boko?" hawaye ya cika idon Khadijah cikin rawar murya tace "Ki yi hakuri Anty" kife ta tayi da tafin hannunta da karfi ta gwara kanta da bango tana hade hakoranta tace "Sai kin lalata tsafin da kika shigo mana gidan nan da har aka sa ki a boko don kaza kazan ki" Khadijah ta rike kanta tana kuka sosai tana kallon kyauta da ta tsaya a gefe idonta ya kada, dukanta Anty khadijah ta dinga ta ko ina tana cewa "Barin gidan nan ya kama Ki don kaza kazan ki" Muryar mumy suka ji tana cewa "Zo nan Khadijah" Anty Khadijah ta dago tana huci tuni Mumy ta juya ta bar wajen, Rankwashi ta kuma kai mata ta sake gwareta da bango tace "Da bakin ki xaki ce masu baki son makarantar idan ba haka ba in kashe ki, kuma ki kama hanyar kauyen ku" daga haka ta fita dakin fuskarta a murtuke, sama ta iske mumy a tsaye, mumy na kallonta rai a bace tace "Khadijah idan har baxa ki iya xama da ni da mutanen dake tare da ni ba ki tattara ki bar min gidana nan ba da dadewa ba, ai ban hanaki xaman gidan mijin ki ba, a kan wani dalili duk xaki bi ki takura ma bayin Allah a gida, ina fa sane da duk abinda kike ba wai ban sani ba, ina ruwanki da bokon da na sa ta? Kudin ki ne ko kudin wani naki, ki fita harkata a gidan nan wallahi, banda mugunta yayi maki katutu me yarinyar ta maki xaki je kina dukanta haka alhalin daxu kika gama nuna rashin jin dadin ki a kan yanda ake treating din naki yaran a gidan ubansu, wlh na fara gajiya dake da halinki, komai na harkan gidana ki cire idonki a kai ki jira idan kina naki gidan in kin so yan Adam ma su kwanta ki dinga tattakesu wannan matsalar ki amma baki isa ba a gidana tunda ba tsoronki nake ba, lastly bbu ruwanki da wannan yarinyar Khadijah, tsakanina da ke daban tsakanina da ita daban, ki yi ta kanki a gidan nan" daga haka mumy ta shige dakinta. Anty Khadijah tayi kuka har ta gode Allah, har ta hada kayanta da na 'yar xa ta bar gidan wata xuciyar tace mata wato ma kenan yarinyar har ta isa da xaki bar mata gidan, ki tafi saboda ita, Inaa ai sai dai Ita ta bar maki, kyale Anty fati kawai kina xaune xata xo ta sameki, tunanin hakan yasa ta hakura da tafiyar duk da ba wai tasan inda xata bane, a ranta kuwa jin tsanar Khadijah take fiye da komai a duniya har kishiyarta ta kuma dau kudirin sai ta 6ata ta gun Mumy da kowa na gidan kafin a koreta. Tun da Aliyu ya dawo misalin karfe biyar yake xaune dinning, bai damu da rashin amsa gaisuwarsa da Anty Khadijah da ke xaune parlorn tayi ba, ya gama cin abinci ya hau danna laptop, iklima sai kai koma take a parlorn sun hada ido ya fi a kirga bata gaishesa ba shi ma bai ce mata komai ba, dinning taje ta dau ruwa suka sake hada ido ya hade rai yace "Sai na fasa idanuwan nan da kike kallona da shi a wajen, a gidan ku ba a koya maki gaisuwa ba ai sai kallon mutane kamar bakauyiya" turo baki tayi ta dauke kai ta bar wajen, Anty Khadijah da taji komai ta mike kamar jira take tace "Ae da ka fasa idon, tunda kai ka hallitar mata su, kuma bakauyiyar ce uban waye ba daga can ya fito ba? Idan ba munafurci da borin kunya ba ka nuna ka san ta ne balle ta gaisheka, ina ce kai ne ya kamata kace A'a iklima ce... ashe kun xo, yaushe ku ka xo ya hanya, amma kayi gum da baki tunda ba tarkacen da uwarka ta saba kwasowa bane, to wllh iklima ita ce dolen ka ba su ba, kuma baxa ta yi gaisuwar ba, ni din ma ba a walakance ka gaisheni ba kake jiran 'ya ta ta gaisheka kawai don kun ga mutum na xaune gidan ubanku, bari ka ji.... yau sai uwarka ta rabu da ku amma ni muna makale ko min wuya don nice dolenta ba ku da ta samu a gidan nan ba, uwan mu daya ubanmu daya da ita, tun kan ku xo duniya muke tare, munafuki kawai" daga haka ta ja hannun iklima dake tsaye kusa da ita ta wuce sama tana cewa "I can't wait ranan da tarkacen da ku ke debowa da har suke neman haddasa mana matsala xa su kunyata ku a gidan nan, wllh sai na xuba ruwa a kasa na sha don farin ciki, ke kuma iklima ko da wasa kar ki gaishesa ya fasa idon mu gani tun ance masa kwai ne" Aliyu ya tabe baki ya mayar da dubansa kan laptop din gabansa, baby ta karaso dining tana kallon Aliyu tace "Anty Khadijah can just shout for African ehennn, I don't even like that her daughter that is eying me since, it seems she even used my sponge to bath this morning coz it wasn't d way I left it" shi dai bai ce komai ba, ta bude masa textbook din math dinta tace "Yaya koya min assignment don Allah" ya kalli book din sannan yace "Ki je ku yi da Classmate din ki mana" Baby tace "Iman?" Yace "Yes" ta ce "She told me she is not feeling fine, kayi mana sai in kai mata ta yi copying nawa, she is even lying down now" yace "Me ya sameta?" Baby ta bude hannu tace "I don't knw, or may be it's because Anty Khadijah ta doke ta daxu, kasan duka tayi mata daxu fa" yace "Duka? Why? A ina ta doke ta?" Baby tace "Dakin can ta shiga ta mata dukan shine ni kuma naje na gaya ma Mumy a sama ta sakko downstairs tayi ma Anty Khadijah fada sosai, har sai da Anty Khadijah tayi kuka, I even saw her packing her load but I don't knw what made her Change her mind kuma" yace "Kira min ita" ta ce "Iman?" Yace "Ehh" tace "Noo daxu da naje tana bacci na tasheta, shine kyauta tace kar in kara tashinta tace mata kanta yana ciwo sosai, kuma kamar Anty Khadijah ce tayi causing din ciwon kan coz she hit her head on the wall many times" Tashi Aliyu yyi yace "Mu je wajen ta" baby ta mike ta bi sa suka tafi dakin kyauta, kwance take kan gado kyauta ta rufe ta da bargo bayan uban rub da ta shafa mata a jiki, ya isa kusa da gadon Baby na biye da shi, sosai lebbenta yyi ja kana ganinta kasan ta ci kuka ba na wasa ba, ya kai hannu forehead dinta ya ji har ya dau xafi, baby ma ta taba tace "Kaji jikinta da xafi koh, Anty Khadijah ce tayi causing din komai" juyawa yyi ya fita ya wuce dakin Mumy, yana tsaye har mumy tayi hanging kiran da take tana kallonsa tace "Ya aka yi Abuturrab?" Yace "For God sake abinda Anty Khadijah ke yi a gidan nan is getting out of hands, why will she just best someone's child the way she did" Mumy tace "Na fa yi mata magana nasan baby ce da gulma xata gaya maka, wllh ni kaina nayi mamakin abinda nayi mata daxu cos gaskiya I am nt happy" yace "Toh yanxu da ta sa ma yarinyar xaxxabi fa?" Mumy tace "Toh sae in ce Allah ya saka mata, don yarinyar dai bata mata komai ba" juyawa yyi ya fice daga dakin ya harari saleem da fitowarsa daga dakin Anty Khadijahr kenan ya sauka downstairs ya koma dinning ya xauna, mumy ce ta sakko ta shiga dakin kyauta, jin xafin jikin khadijah ta tada ta ta wuce sama da ita xuwa dakin baby, baby da ta biyo su ta xauna kusa da khadijah da mumy ta kwantar saman gadonta tace "Mumy let her be staying in my room sae mu dinga assignment tare ba sai ina xuwa dakin kyauta ba" Mumy tace "Tafi ki kira min yayanku" juyawa baby tayi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tace yana xuwa, mumy na ta jiransa har ya shigo da sallama tana kallonsa tace "Ko xaka samo mata magani don Allah Aliyu" ya karaso gadon yana kallon khadijah, mumy ta mike tace "Ae ita ma ga nata can ana gallaza masu kuma bata yarda don tana ma 'ya yan wasu bne" daga haka ta fita Aliyu ya bi bayanta, baby kuma ta xauna tana ta kallon khadijah. Pharmacy Aliyu ya tafi ya siyo mata drugs ya dawo gidan, bedroom din mumy ya shiga ya bata ledan maganin tace "Toh ni nasan prescription dinsu Aliyu, ka tasheta ka bata mana" yace "Ohk" sannan ya fita xuwa dakin baby, baby na xaune kan study table din ta tana solving mathematics din, Ya karasa kusa da gadon yana kallon khadijah, kallon baby yayi yace "Je ki tambayi mai aiki a downstairs ko ta ci abinci" Baby ta fita ba a dau lkci ba ta dawo rike da plate din abincin ta ajiye a kasa tace "Tace bata ci ba" Yace "Tell her to make a cup of tea" baby ta juya ta fita, da cup din shayin ta dawo ya karba ya ajiye sannan ya tada khadijah, mikewa xaune tayi tana murxa ido ya dau shayin ya mika mata, ta girgixa masa kai tace "Am not hungry" yace "I know you are not Hungry, kafin in dawo kin shanye shayin nan" daga haka ya fita, Baby ta taho da sauri tace "Kawo in taya ki sha kafin ya dawo" khadijah ta mika mata, baby ta fara shan shayin don ba xafi sai da ta yi rabi ta mika ma khadijah, ta bata fuska tace "It's till plenty" baby ta sake kafa kai bata sauke ba sai da ya rage mitsitsi, ta mika ma khadijah ta karba, ta bar gun da sauri tana goge baki ta ci gaba da abinda take yi a study desk dint, khadijah ta shanye sauran ta ajiye cup din, xata kwanta sai ga shi ya shigo yana kallon cup din dake ajiye, hade rai yyi baby sai satan kallonsa take ya juya direction dinta tayi saurin dauke kai, kallon khadijah yyi yace "Shayin kika bata ta shanye kenan" ko rufe baki bai yi ba baby ta fice daga dakin da gudu, ya bi ta da ido, daukan cup din yyi ya mika ma khadijah yace "Tafi ki kai a sake hada maki wani da kanki" kamar xata yi kuka tace "Ni ba yunwa nake ji ba" ya wani hade rai yace "Tashi ki fita" ta mike da kyar ta dau cup din xata fita yace "Ina jiran ki fa" Rabin cup ta sa kyauta ta hada mata shayin ta dawo dakin yana tsaye ta shanye sannan ya bata magungunan da bottle water, da kyar ta shanye su har da kukanta, ya wani hade rai, xata kwanta ya hanata ya dauko textbook din da baby take assignment yace "Solve it now ba sai kin kwanta ba" karba tayi a hankali yana kallonta ta fara solving maths din, yace "Idan kin gama ki kawo min downstairs" tace "Toh" sannan ya juya ya fita, dinning ya koma ya xauna, saleem dake xaune parlor bai ce masa ba shi ma bai ce masa ba, bayan kusan minti sha biyar khadijah ta sakko rike da textbook da note book din baby, gun Aliyu ta nufa ta ajiye tace "Na gama yayanmu" ya dau book din yana kallon abinda tayi, after sometime yace "Good, shine kike son a sa ki jss2" ta d'an yi murmushi ce "A jss2 nake ai, it's just that lesson teacher dina back then at home yana koya min karatun jss3" Aliyu bai ce komai ba ya rufe books din, ganin tana ta tsaye ya daga kai yana kallon idonta da suka rine yace "Toh tafi" juyawa tayi xata tafi dakin kyauta ya kirata, ta dawo yace "Tafi dakin baby kiyi kwanciyar ki" Sama ta kalla tayi shiru, yace "Tafi na ce" juyawa tayi ta nufi stairs din, saleem ya bi ta da kallon gefen ido, tana kwanciya dakin baby bacci ya dauketa. Tun daga wannan lokacin khadijah ta koma dakin baby da kwana ba don kyauta ta so ba, baby da kanta tace ma Mumy ta gaya ma kyauta ta dauko kayan khadijah a kawo ta saka a cikin press dinta akwai space, duk wannan abun Anty khadijah na nan ta sa masu ido abun na cin ranta wai khadijah ce har sama dakin baby... tabdii, sai dai bata ce wa kowa komai ba da yake har lkcn bata magana da Aliyu, Mumy ma ko shiga dakinta ta daina yi, yanxu saleem ne nata da siyama da Aneesah a gidan, sai dai fa ita kadai tasan kudurin dake ranta, kusan a dakin Anty Khadijah Saleem ke yini, da yake ba wani shiri suke yi da Abbansu Aliyu ba bata fara ce masa komai kan khadijah ba, tun da ta ki xaman aure domin kuwa aurenta yyi uku ko ga maciji basa yi da shi idan ba yanxu da ta ja6e a gidansa ba take gaishesa don dole, idan ta ga yanda yake faram faram da khadijah sai taji abu ya makale mata a makogwaro, a haka daddy ya koma germany bayan sati daya shi kadai ba tare da saleem ba, Kusan kullum sai Iklima ta tsokani khadijah a gidan har da xagi tamkar dai uwarta ke sa ta, Amma ko sau daya khadijah bata taba kulata ba, tun da mumy tace kar ta sake ta kulata, hakan yasa fadanta yawanci da baby take yi, wani lkcn har da dambe, wanda ba haka Anty khadijah ta so ba, ta so ne ace da khadijah iklima ke wannan abun toh da bata samu fuskar su yi fadan gun khadijah ba yasa ta makale ma baby suke fadan, gashi baby ta nakada mata duka hakan bai sa kuma ta daddara, islamiyya mumy ta sa saleem ya kai Iklima, sanin ikliman ba gaida Aliyu take ba har sannan yasa Mumy bata ma sa shi ya kai ta ba, Ranan litinin da asuba mumy ta kira saleem ta basa cash na kudi tace "Gashi anjima idan yara xa su makaranta, ku tafi tare da Iklima kayi mata registration, ita ma tace jss3 take" Saleem yace "Toh Mumy, har da uniforms?" Tace "Eh Abbanku ne ma ya bada kudin" fita yyi dakin bayan ya amshi kudin ya kirga. Mumy ta bude kofar dakin Anty Khadijah don tare suke kwana da 'ya tata da take ji kamar ta mayar ciki, tun da ta ga Khadijah na kwana dakin baby ta hana iklima shiga dakin, Anty khadijah ta dauke kai ganin yayarta hade da daure fuska, Mumy ta tabe baki tace "Sai ki tashe ta daga baccin ta shirya xa su makaranta tare da su Siyama" daga haka Mumy ta rufe masu dakin. Aliyu na bedroom dinsa yana shiryawa da safen ranan baby ta shigo sanye da Uniform tana turo baki tace "Yayanmu kaga wannan ikliman mai shegen tsokanar mutane mumy tace xata fara school din mu yau kuma same class muke da ita da Iman koh, yaya a schl ma tsokanata xata dinga yi ni bana son ta xo schl dinmu Allah" yana karashe buttoning shirt dinsa yace "Toh ki je ki gaya ma Mumy mana" ta turo baki tace "I told ya Saleem yace xai mare ni, he is always supporting the dirty girl" Aliyu ya tabe baki bai ce komai ba, Baby ta karasa gun sa ta nuna masa takardan hannunta tace "Yaya.... Iman ce tayi solving din math din nan, I told her it's wrong ta ki ta yarda" karba yyi ya juyo yana kallon book din, ya langwabar da kai yace "Where is she?" Juyawa baby tayi sai ga ta sun dawo tare da Khadijah, khadijah ta tsayema bakin kofa ita ma tana sanye da uniform tace "Yayanmu ina kwana" yace "Lafiya lau, where u sleeping when solving dis?" Ta xaro ido tace "Aa idona biyu" ya mika mata yace "Toh it's wrong" karasowa tayi ta karba tana kallon baby, tace "but I told her to solve it let's see kuma taki yi fa, and tare muka yi wannan" Aliyu yace "Don't worry ku yi submitting haka, learn not to be afraid of failure..." Khadijah tayi murmushi tace "ohk thank you" daga haka ta fita baby ma tace masa thank sannan ta bi bayanta. Tun dawowarsu makaranta iklima ke ta ba uwarta labarin makarantar da ta fara ranan, Anty khadijah dake saurarenta fuskar nan a yamutse tace "Yanxu ajin ku daya da annobar can kenan?" Iklima ta tabe baki tace "Ehh mana, class din mu daya, kuma ko wani tambaya aka yi a class din ita ke bada amsa, Iman ma ake kiranta a class, she is always bragging she knws everything, in the afternoon ya Aliyu ya xo school din ma...." Katse ta Anty khadijah tayi da sauri tace "Wajen wa?" Iklima ta kara tabe baki tace "Water colour naga ya kawo mata da Math set, may be she told him since yesterday, lokacin muna break ma ya xo" Anty khadijah da ta wangale baki tace "Haba...." Iklima tace "Wllh, kuma yyi kamar bai gan ni ba har bin wajen motarsa nayi" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Anty khadijah da idonta ya kankance tace "Ita kadai ya kawo wa ko har da baby??" Iklima tace "It seems baby tana da shi, ita kadai naga ya kawo ma" shiru Anty khadijah tayi tana naxari iri iri a ranta, can tayi kwafa hade da murmushi. Baby ce tsaye a class tana kyakyata dariya har da rike ciki, Khadijah dai murmushi kawai take tana kallon sheet dinta na quiz da suka yi ranan over 20 both math and English gaba daya kuma ta cinye, Wata yarinya ta karbe script din baby dake ta kyalkyale dariya taga 15 gare ta, Baby ta sake satan kallon iklima dake can gefe tsaye tayi keeping strong face ta linke script dinta ta boye, baby ta kara rushewa da dariya har da kwanciya, har sanusi ya xo daukansu ranan baby da ta saci kallon iklima sai ta kwashe da dariya, Siyama da ke kusa da iklima ta kalli baby tace "Dariyar me kike ke kuma" Baby tayi keeping innocent face tace "Nothing" a nan ne ta fiddo script dinta a jaka tana murmushi ta mika ma Siyama tace "Quiz da muka yi daxu a class, I got 15 over 20, Iman kuma scored 20/20" Aneesah tace "Iklima fa?" Baby ta danne dariyarta tace "I don't really knw" Siyama ta kalli Iklima tace "Ke meye score din ki" Iklima ta tsuke fuska tace "16" wani kara baby tayi tana xaro ido tace "Wllh karya take she scored 3 over 20 I saw it with my two naked eyes" Iklima ta cakumota ta kunduma mata xagi tana huci tace "Ke kika ban 3 din, munafuka shegiya" kokuwa suka fara yi cikin motar har sai da Sanusi yyi parking, Siyama ta fito da baby daga cikin motar, sai da Sanusi ya sa baby ta dawo gaba sannan fadan ya lafa, amma sai xage xagen juna suke baby na kiranta olodo har suka isa gida, Iklima ta fice daga cikin mota ta shige gida da gudu ta rushe da kuka tana kwala kiran Uwarta, Da gudu Anty khadijah ta fito tana tambayarta menene da yake Mumy na gun aiki bata dawo ba, cikin kuka Iklima tace "Su baby ne ke ta tsokanata suna kirana olodo tun a school mumy bana son same class with dem, gwara a mayar da ni jss2..." Baby ta shigo parlorn tana turo baki Anty Khadijah tace "Baby me ya hada ki da 'yar uwarki, uban waye ya shiga tsakanin ku har yake neman raba min kan ku?" Baby tace "Anty ita ce take dambe da ni a mota, just because she scored 3 over 20, ni bani nayi marking din ba da take fada da ni" Anty khadijah bata ce komai ba ta ja Iklima xuwa daki ta kulle kofar tace "3 over 20 iklima garin yaya" iklima ta turo baki tace "Toh the questions where very hard" Anty khadijah ta bude baki tace "Toh ita babyn me ta ci?" Iklima ta tabe baki tace "Wai 15" Anty khadijah tace "kina me iklima, to ita shegiyar yarinyar can fa" Iklima ta kara turo baki gaba tace "She scored everything, mumy kuma na ji suna cewa xa su nuna ma ya Aliyu xai siya masu wani abu" hawaye cike idonta ta kare maganar, Anty khadijah tace "Ba kwa xuwa makarantar ne a can gida!" Iklima tace "Ina xuwa" Anty khadijah ta dungureta tace "Amma kin kunyata ni Wllh, yanxu da wani ido xan dubi yan gidan nan, yar iskar can xata iya cinye duka quiz din ke me kike da baxa ki iya ba" Iklima sai matsar kwalla take, Anty khadijah tayi shiru tana cixan yatsa, can tace "Tafi kije dakinsu ki dauko min script din shegiyar da sauri" da gudu iklima ta fita dakin, ta je dakin baby tayi sa'an ba kowa ta bude jakar Khadijah ta dau takardan quiz dinta ta fita ta kai ma Anty khadijah, yayyage papern Anty khadijah tayi ta bude window ta watsar tace "Tafi kiyi wanka ki je ki karbi abincin ki" cike da murna Iklima ta wuce bayi. Da daddare babu irin neman da Khadijah bata yi ma takardanta ba baby na taya ta xa su kai wa Ya Aliyu, Baby tace "Ni nasan Iklima ce ta sace maki script, she openly showed she is jealous tun a schl," daga haka ta fice ta tafi ta gaya ma ya Aliyu dake dakinsa, shiru yyi yana kallonta. Throughout schl days ko assignment aka ba su Iklima ko average bata ci, daga 2 sai 3, baby ta samu abun dariya kullum cikin mata dariya take, ita dai Khadijah ba ruwanta nata ido, yau Friday tun da suka dawo schl khadijah ke kitchen gun kyauta tana bata labarin makaranta, kyauta tace "Toh ni abinda nake son sani a nan shine, ita ikliman bata gane karatu ne da bata amsa tambaya a aji?" Khadijah ta hade rai tace "Ni Anty mai girki am not gisting you about her ba ruwana kawai ina baki labarin masu kokari ne a aji" Kyauta tace "Ke dai kin fiye tsoro tsiya shi yasa baby ke burgeni, shegen duka take ma mummunar yarinyar" Khadijah tayi yar dariya tace "Ni dai ba ruwana Anty mai girki" Kyauta ta kyabe baki tace "Yo ai ba karya nayi ba, mummunar karshe ce yarinyar da nanikakken hanci kamar an taka amala a kan hanya, ido mitsi mitsi kamar na tana, baki kamar gidan tsutsa, ga gashinta kamar na hammata na" Khadijah ta fashe da dariya har da kyakyatawa, kyauta ta washe baki tace "Atoh, duk uwarta ce ta ja mata ai, da bata gallaza ma 'ya yan wasu da Allah bai hada yar ta da kwakwalwar tantabara ba, da yanxu bata nuna maki tsana kiri kiri ba ai ke xa ki dinga assisting dinta kina koya mata kamar yanda ku ke yi da baby, amma uwar taki xaman lafiya da kowa, meye amfanin haka a rayuwa.... Da ta kwantar da hankalinta ma wataran duk baxa ta gan mu a nan ba sai dai idan Allah yyi xa a sake saduwa" ita dai Khadijah bata ce komai ba, kawai ji suka yi ana cillo da jakunkuna waje, duk suka kalli juna sannan suka fita da sauri, Anty Khadijah ce tsaye parlorn duk ta fiddo Ghana must go da jakar kyauta da komai nata dake cikin daki waje, Tana wani murmushi tace "Dama rana irin ta yau nake jira, har ni kyauta xaki tsaya kitchen kina yi da ni kina yi da 'ya ta, to xaman ki ya xo karshe gidan nan yanxun nan kuma ba sai anjima ba, in dai ba gidan ubanki bane, ba kuma na uwarki bane nan din tattara ina ki ina ki ga su nan ki kama gabanki" kyauta tayi shiru tana kallonta, kofa Anty khadijah ta nufa kamar xata tashi sama ta fita compound cikin tsawa ta dinga kwala ma Usman kira ya biyota da gudu yana amsawa ta shigo parlor tana nuna masa kayan tana huci tace "Maxa kwashe tsummokaran nan ka fita da su can wajen gate" Khadijah ta fashe da kuka tace "Anty don Allah kiyi hakuri kar ki koreta..." Fixgota Anty khadijah tayi ta kai mata wani mugun dundu har sau uku a baya ta gware kanta tace "Tsinanniya ae nan ba da dadewa ba xa ki bi ta kema, mu dai je xuwa" Khadijah bata daddara ba ta durkusa tana kuka sosai tana kallon kyauta dake ta kallon Anty khadijah tace "Anty mai girki kice tayi hakuri don Allah" cikin tsawa Anty khadijah tace ma kyauta "Ki fita nace kar in fitar da ke da kai na munafuka annamimiya" Kyauta tayi murmushi tace "Xan tafi, ke kuma Allah ya hada ki da dai dai ke a rayuwa" Khadijah ta fashe da matsanancin kuka ta rike kyauta cikin rawar murya tace "Don Allah Anty mai girki kar ki tafi ki bata hakuri, kar ki tafi ki bar ni" haurinta Anty khadijah ta yi kamar ta samu ball tana huci tace "Tashi ki kwaso naki kayan ki bi ta kema.... Ba sai kin ce kar ta tafi ba" Tashi da sauri khadijah tayi tana kuka xata je dauko kayan nata Kyauta ta rikota tace "Kar ki damu Khadijah in sha Allah xa mu hadu wataran, ke dai ki kula da kanki ki rike maraicin ki Allah na tare da ke" daga haka kyauta ta saketa ta dau jakarta daya da ya rage parlorn ta nufi kofa ba tare da ta bi ta kan kudin aikinta ba, Baby dake tsaye parlorn ta fashe da kuka tace "Anty me yasa xa ki koreta, she is very kind, and she can cook" Anty khadijah ta ja kunnenta da karfi tace "Nan din gidan ubanta ne da baxan koreta ba, masu halin tsiya... Ga ku so dangi" daga haka ta bi bayan kyauta da sauri domin ta tabbatar ta tafi, bata dawo ciki ba sai da ta tabbatar kyauta ta bar layin gaba daya, mai gadi duk jikinsa yyi sanyi amma bai ce komai ba, ta dawo ciki tana yatsine fuska tace "Gayyar tsiya, ita kuma Anty fatima idan ta dawo nima sai ta koreni in ga" jan iklima dake ta murmushi a parlor tayi xuwa sama, don ita ce ma taje ta kira ta a daki wai kyauta na xaginta. Har mumy ta dawo khadijah na xaune can inda kyauta ta saba ce mata ta xauna farkon xuwanta gidan, tayi kuka har ta gode Allah, kasa cewa komai Mumy tayi bayan baby ta gaya mata abinda Anty Khadijah tayi ma kyauta, jikinta yyi mugun sanyi ta wuce daki da kyar ta kira Aliyu, ce masa tayi ya dawo gida yanxu, jin yanayin muryar mahaifiyar tasa yasa ko minti biyar bai kara ba a clinic ya taho gida, har ta gama bayyana masa abinda ya daga mata hankali bai iya yace komai ba yana tsaye dakin shi ma jikinsa yyi sanyi, can ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "kiyi hakuri mumy, yanxu kinsan inda xa a samo kyautar?" Cike da damuwa Mumy tace "A ina xan sani Aliyu, matar da ba waya gare ta ba, gashi ko kudin aikinta ba a bata ba, yanxu Khadijah ciwon xuciya take son sa min ne a gidana shine abinda ban sani ba har yanxu, don me yasa bata son in xauna lafiya yanda nake so a gidana, me yasa khadijah take min haka, don nace ta xo mu xauna tare laifi nayi Aliyu da xata dinga cuta ta haka, don wannan wallahi cuta ce" Yyi kasa da murya yace "Don Allah kiyi hakuri mumy, Allah ya ganar da ita.... Xan ma mai gadi magana yanxu idan Allah yasa kyautar ta dawo ya bar ta ta shigo kawai" daga haka ya fita, labe ya ga Anty Khadijah jikin kofa tana eavesdropping duk abinda suke cewa, tana ganinsa tayi masa wani shegen kallo hade da tsaki ta shige dakinta, bai ce komai ba sai tabe baki da yayi ya sauka downstairs. Bayan ya sanar ma mai gadin ya bar kyauta ta shigo ko da xata dawo.... ya koma cikin gida, har lkcn baby na ta kumbure kumburen an kora kyauta a dinning, su siyama kam ko a jikin su, a ransa yace "xa su ci gidansu da aikin gidan nan kuma Yanxu" ya karasa dining yana kallon baby yace "Ina Iman?" Hannu ta buda masa alamar bata sani ba, kitchen ya shiga ya fita waje, xaune ya ganta har lkcn a gun idonta ya kumbura don kuka, ya tsaya yana kallonta can ya karasa wajen ta, tana ganinsa ta kuma rushewa da kuka ta kife kanta da gwiwa, ya durkusa gabanta yace "Kukan me kike?" Ta dago da sauri cikin rawar murya tace "Yayanmu Anty ta kori Anty mai girki" shiru ya d'an yi kafin yace "Ko xa ki bi ta ne?" Ta gyada masa kai da sauri, yyi murmushi yace "Toh kiyi hakuri, xata dawo in sha Allah" a hankali tace "Yaushe?" Yace "Mumy xata nemo ta" shiru khadijah tayi ya mike yace "Tashi ki je ki wanke fuskar ki" Tashi tayi ta tafi gun tap ta wanke fuskarta sannan ta dawo tana kallonsa yace "Kar ki sake kuka fa" tace "Toh" juyawa yyi ya shiga gidan ta bi bayansa, tsaye suka ga Anty Khadijah a kitchen ta hada kwanukan wanke wanke xata yi, Aliyu ya danne dariyarsa bai sake kallon direction dinta ba har ya fita kitchen din, Khadijah xata wuce tace "Zo nan..." Dawowa Khadijah tayi ta nuna mata tsintsiya tace "Maxa ki tafi ki share gaba daya gidan ai aikin ki ne kema, kuma babu uban da xai maki" daukan broom din Khadijah tayi ta fita, dai dai sakkowar mumy tana ganinta tace ta ajiye tsintsiyar su je daki su yi assignment da baby, ajiyewa tayi ta wuce sama dakin baby. Washegari da Asuba Anty khadijah ta shiga kitchen, Aliyu dake xaune parlor tun bayan da ya dawo masallaci sai murmushi yake jin yanda take ta dambe da utensils a kitchen, idan ta dauke wancan sai wannan ya fadi, tayi tsaki ya fi a kirga, karfe bakwai saura ya wuce sama don yin wanka ya tafi aiki, yana gama shiryawa ya fito ya shiga dakin baby kamar yanda ke yi duk safiya don ganin ko sun shirya, tsaye ya ga baby tana duba ma khadijah idonta da yyi ja, ya karasa dakin yace "What happen" baby tace "Yayanmu we where just on our own muna shiryawa fa, kawai sai ga ikliman nan ta shigo wai mun sace mata pen, can you imagine fa, alhalin karya ne she lost her pens gaba daya da mumy ta ba mu, shine ta dauke na Iman wai nata ne ta sace har da buga mata pen din a fuska shine ya taba idonta gashi yana mata ciwo yanxu, Yayanmu a daina siya mana komai iri daya ka gaya ma Mumy plsss, iklima don't like peace, she is always looking for conflict, I really dont like that girl" Aliyu ya duba idon Khadijah yace "Ke kuma kina xaune ta tsone maki pen a ido koh" Baby tace "Noo, Yayanmu the thing in here is that Iman don't like trouble, I just notice that, if not da ace ni ce... I will beat her blue black har sai Anty baxata ganeta ba" juyawa Aliyu yyi ya leka dakin Anty Khadijah ya ga ikliman bata ciki, fita parlor yyi ya ganta a dinning har uwar ta hada mata shayi ga uban soyayyen kwai a gabanta da bread, Saleem ma na xaune dinning din yana breakfast, fita yyi ya xaga ya k'arya branch din flower ya dawo, yana daga tsaye a bakin kofar parlor, yace "Iklima" tun da ta xo gidan sae ranan ya kirata, ta taso da sauri tace "Ni?" Yace "Eh xo" karasawa tayi kusa da shi ya jawo ta waje ya kulle kofar parlorn, ya rike duk hannunta biyu yace "Ni sa'an ki ne da sai dai ki kalle ni a gidan nan baxa ki gaishe ni ba" hade rai tayi xata kwace hannunta ya kai mata Rankwashi ya murda kunnenta da karfi, ta bare baki ta fara kuka, hakan ya basa daman tsula mata bulalan hannunsa, ya xaneta ta ko ina a jikinta to his satisfaction, sai ihu take tana kiran Anty khadijah, Saleem ne ya bude kofa da sauri uwarta kuma ta fito kitchen a rude tana tambayar me ya faru, ina iklimar, ko kallon Saleem Aliyu bai yi ba ya kara rankwashinta ya turata ya nufi gate da sauri ya fice daga gidan. Hauka ne kadai Anty khadijah bata yi ba barin da ta ga yanda bulala ya kwanta ta ko ina a jikin yar ta, Da ta tambayeta me tayi masa cikin kuka tace "Wai bana gaishesa" ran Anty khadijah yyi mugun baci, cikin fada tace "Shi gaisheni yake yi a gidan? Ae wllh sai dai idan baxai sake dawowa gidan nan ba, ina nan ina jiransa, sai ya gaya min dalilin haka, jaka ya samu ko tinkiya? Idan yana jin haushina sai aka ce ya sauke kan 'ya ta, yayi facing dina mana, toh wllh xai dawo ya same ni sai ya gaya min ko a kansa kike xaune gidan yau, toh wai ma shi akwai wanda ya kai sa fitsara, yanxu idan nace Allah ya isa ace ban kyauta ba koh, yaushe rabon da yyi min gaisuwar kirki a gidan nan, toh wllh sai ya san ya doke ki" ita dai mumy na tsaye ta kasa cewa komai, Anty khadijah na huci ta ja iklima dake aikin rusa kuka tayi sama da ita, Baby har da rike cike saboda dariya a dakinsu, bayan ta yi mai isarta tace "Yayanmu and sense, that served her right" Aliyu kam yana fita aiki ya tafi abun sa ba tare da ya waiwaiyi motarsa ba. Haka rayuwa ta ci gaba da kasancewa a gidan har su Baby suka fara shirin yin junior waec, sosai Aliyu ya ji dadin tafiyar kyauta don yanxu kam kowa aiki yake a gidan, duk sanda Anty khadijah xata shiga kitchen in da safe ne to karfe takwas da rabi yaran xa su makaranta, idan da rana ne to sai kusan biyar xa a ci abinci gidan, idan kuma da daddare ne sai goma wasu har sun yi bacci, ga girkin ba kan gado yau ya yi half done gobe ruwa yyi yawa, hakan yasa Mumy ta gwammace ta shiga tayi da kanta tare da su siyama su yi ta turo baki, wanke wanken gidan kuma aka raba ma Baby, Khadijah da iklima, duk sanda iklima ce da wanke wanke idan Anty khadijah ta faki idon mumy sai ta sa khadijah tayi tana hantararta da xagi wai ai aikinta ne dama, idan kuma mumy na parlor toh ita da kanta take fita ta taya 'yar tata wanke wanken tana cika tana batsewa kamar irin ba a son iklimar, shara kuma Aneesah da Siyama ke yi da goge goge, sai kowa ya gyara dakinsa ya wanke bayi, har lkcn khadijah ta kasa mance kyauta, kullum sai tayi tunaninta wani lokacin har da hawayenta baby tayi ta lallashinta, ga Anty Khadijah ta sa ta gaba fiye da da a gidan barin idan mumy ta tafi aiki, duk gidan gun Aliyu da Baby kadai take samun sauki sai Mumy, shi kansa saleem ko inda yake bai son ganinta, shi yasa idan yana gidan tayi ta xaman daki kenan tana karatu, sau tari ummanta kan fado mata, ko a ina xata sake ganinta kuma? duk da alamun girma ya fara bayyana sosai jikin Khadijah bbu mai gane hakan saboda yanda ta tsiri sa Hijab a gidan, kamar yanda Aliyu yace ta dinga yi, Mumy ta sha mata fadan sa Hijab da take a ko da yaushe amma ta kasa bari, hakan yasa mumy ta kyaleta kawai da ta lura baxa ta iya barin bane, a hakan suka fara junior waec, ko da yaushe tare xa ka ga Khadijah da baby suna karatu amma iklima daga kallo sai bacci uwarta bata ce mata komai, duk ta wani xama lukuta sai kumatu ko wa ya ganta yasan ba cin wasa take ba, idan mumy tayi maganar rashin karatunta sai Anty Khadijah tace ai tana yi cikin dare idan kowa yayi bacci, kullum suka dawo makaranta fuskar iklima a murtuke xaka gansa alamar dai bbu abun arxiki a exams din ranan, baby ce mai shiga harkarta dama tayi ta tsokanarta tana dariya, ita kam khadijah ba ruwanta. Ranan da suka yi last paper dinsu, Anty khadijah ce taje dauko su don Sanusi baya nan, su siyama kuma sai hudu dama xa su dawo gida, Khadijah na ganin Anty khadijah ce ta xo daukansu jikinta yyi sanyi sosai, bayan su baby sun shiga xata shiga Anty khadijah ta jefa mata naira Dari tana mata matsiyacin kallo tace "Wannan kuma baki isa ba, idan xa ki nemi abun hawa ki nema don kaza kazan ki" daga haka ta ja motarta, baby ta bata fuska tana kallon small mum din tata, Iklima kuma sai kallon khadijah take ta glass tana murmushi, a sanyaye Khadijah ta durkusa ta dau kudin hawaye cike idonta, a yanxu ne abinda Anty Khadijah ke mata ke damunta sosai ita kanta bata san me yasa ba unlike before, ni kam nace ko don ta fara sanin ciwon kanta ne? Napep ta samu ya kai ta har kofar gida ta basa darin sannan ta shiga cikin gida tana gaida Usman ya amsa da fara'a yana tambayarta ita kadai ta dawo yau ina sauran, murmushi kawai tayi masa tace suna xuwa, tayi mamakin da ta riga su dawowa gida, ta wuce cikin gidan wanda da alamar dai babu kowa ciki, sama ta wuce don cire uniform, tana cire riga aka bude kofar dakin ta juya da sauri, saleem ne tsaye bakin kofar ta sunkuyar da kai tace "Ina yini ya saleem?" Bai amsa ba instead sai ma shigowa da yayi ya rufe kofar, ta koma baya a hankali tana kallonsa, ya rungume hannayensa yana kallonta yace "Na maki wani abu a gidan nan ne da ba kya shiri da ni?" Kasa kallonsa tayi, da kyar ta tattaro abun cewa "A'a baka min komai ba" ya taho kusa da ita yace "Toh me yasa sai Aliyu kike kulawa" ta koma baya kamar xata yi kuka tace "Kai ma ina kula ka ai" kamo hannunta yyi ta fixge da sauri hawaye cike idonta a hankali tace "Bana son haka.. Am I not just like baby to you" Wani kallo ya mata yace "You are not, baby is my blood" ya sake riko hannunta ta kuma fixgewa, dago kanta yyi yana kallon kwayar idonta dake cike da hawaye yace "You are pretending you don't want me to touch ur hands?" Hawayen idonta ya silalo tace "I am not, I just don't want that" Yyi wani murmushi yace "then you have to, just for today" ta sauke idonta muryarta na rawa tace "Am sorry ni ba yar iska bace" daga haka xata wuce ya fixgota da karfi tayi wani kara yace "Ni ne d'an iska?" Ta fashe da kuka sosai tace " Ya saleem don Allah kayi hakuri ka kyaleni, stop this..." Bai kai ga cewa komai ba aka bude kofar dakin, a tare suka juya da sauri, Aliyu ne tsaye bakin kofar, ya dinga kallon saleem ko kiftawa babu, saketa Saleem yyi ya nufi kofar, Aliyu dake kallonsa a hankali yace "Me kake yi a nan?" A takaice yace "Nothing" xai bi gefensa ya fita ya mayar da shi dakin sannan ya sauke masa mari, dafe kuncinsa yyi yana kallon yayan nasa da mamaki yace "Mari na kayi fa?" Aliyu yace "Toh rama" ya fi second ashirin yana kallon yayan nasa sannan ya fice daga dakin, Khadijah ta durkusa kasan dakin ta hade kanta da gwiwa tana kuka, karasawa yyi cikin dakin yana kallonta a hankali yace "Me yasa kika dawo gida ke kadai?" Cikin kuka tace "Anty Khadijah ce tace baxan shiga motar ba, shine ta bani kudin mota" bai sake cewa komai ba, bayan kusan minti daya ya durkusa gabanta, a hankali yace "Forgive him Iman, kiyi hakuri" hawaye na sakkowa idonta tace "I have done that" bai sake cewa komai ba, a hankali ta mike ta dau Hijab dinta ta sa ya bi ta da ido, mikewa yyi yana kallonta yace "Plss kar ki gaya ma Mumy komai Iman, she will be disturbed" ta kallesa a hankali tace "I won't" daga haka ya nufi kofa, dakin saleem ya shiga ya samesa xaune gefen gado, strictly yace "Saleem this shud be ur 1st and last attempt idan ba haka ba, I will make u start imagining if I am ur blood or not" daga haka ya fice masa a dakin. Anty khadijah ce xaune dakinta tana ta kallon Saleem da wani expression tace "Ya mare ka fa kace?" Saleem dai ya hade rai bai ce mata komai ba, a fusace tace "Toh don me baka rama ba?" Ya kalleta yace "In rama Anty?" Tace "Ehh mana, tun da bai rike girmansa ba, fuska ya fi fuska ne? Sannan uban me ma ya dawo da shi, da na bar gidan fa baya nan...." Saleem ya tabe baki bai ce komai ba, kwafa ta yi ta cije yatsa, can tayi wani murmushi tace "Ohk, ai idan ya san wata bai san wata ba, kuma shine da jin kunya, kunya babba kuwa, sai ya gwammace ina ma ba shi bane" ✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨ Khadijah ce kadai xaune daki da daddare tun bayan incident din daxu da rana ta ki fita dakin, Baby ta shigo daga dakin Mumy tana kallon Khadijah tace "Iman you look sad since afternoon, ko don abinda anty Khadijah tayi maki ne a schl?" Khadijah ta girgixa mata kai tace "A'a am not feeling fine ne" Baby ta buda ido sosai tace "Toh ki gaya ma Mumy mana, or you can tell Yayanmu that is a doctor" Khadijah tace "I will be alright in sha Allah" juyawa baby tayi ta fita, dakin ya Aliyu ta shiga ta xauna gefensa har ya gama wayar da yake sannan ya kalleta yace "What happen" tace "Yayanmu Iman ce naga she is sad all day, I asked what's wrong tace min she is not feeling fine" ya kalli kofa kamar xai tashi sai kuma yace "Ta fi ki kira min ita" Mikewa baby tayi ta fita ta koma dakinta, "Yayanmu yace in kira ki" abinda ta fadi ma khadijah dake kokarin kwanciya kenan, Khadijah ta hade dai tace "But I didn't tell you to announce I am sick" baby tace "What ever... Ko ince masa baxa ki xo ba" daga haka ta juya ta fita, mikewa khadijah tayi ta sa Hijab ta bi bayanta, dai dai fitowar Anty khadijah daga dakinta xata sauka downstairs, da da ne tana ganin Iman tayi hanyar dakin Aliyu irin ko ya kira su tare da baby xata mata mugun kallo ta hanata shiga dakin, yanxu kam sau daya ta kalleta ta dauke kai tayi wucewarta, a sanyaye khadijah ta shiga dakin don tuni baby ta shiga, ta tsaya daga bakin kofa tace "Ga ni Yayanmu" yace "kika ce baki da lafiya, what's wrong?" Ta kalli baby tace "Kawae I told her am nt fine, ba wai bani da lafiya ba" Baby tace "Ke ma kina son ki fara karya kamar iklima koh?" Murmushi Khadijah tayi, Aliyu ya kalli baby yace "You can leave" mikewa tayi tace "Ohk" sannan ta fita, yana kallon khadijah yace "Come over Iman" karasawa cikin dakin tayi, ya jawo study chair dinsa ya ajiye mata, ba musu ta xauna tana facing dinsa, a hankali yace "But I told you not to worry koh?" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "I am without worries" shiru yyi yana kallonta, ta ki dago kanta, murya can kasa yace "Iman" dagowa tayi da manyan idonta tana kallonsa, yace "Tel me when you lost ur parent" lkci daya hawaye ya cika idonta, ya girgixa kai yace "Noo ban ce kiyi kuka ba" ta gyada masa kai tana fidgeting fingers dinta a hankali tace "My dad told me I lost my mum when I was just 3, we where together tun daga sannan, shi yake kai ni schl da islamiyya, I love my dad... He took good care of me, kullum a eatry Abbana ke siyo mana abinci, I mean all the 3 daily meals, but there is always custard, cornflakes, golden morn, ice-cream in the fridge and different biscuits and chocolates at home all for me, duk sanda Abbanmu xai je trip abroad he always go together with me, not until he married my step mum when I was 8 years old, and she took over from where he stopped, my step mum is more than kind, tana so na, she does to me what ever I like, ko Abbanmu na nan ko baya nan, muna tare har na kai 14 years...." Katse ta Aliyu yyi yace "Ita yaranta nawa step mum dinki?" Tayi murmushi tace "Ni kadai ce yarinyarta, she never gave birth with my dad" Aliyu ya gyada kai yana kallonta, ta d'an yi shiru, sai kuma a hankali tace "One faithful Friday Abbanmu xai je port Harcourt wajen junior brother dinsa da aka kira sa ba shi da lafiya ya xo ya tafi da shi, we bade him fare well har parking lot da Asuba tare da Ummata" ta fashe da kuka tace "That was the last time we saw him, sai aka kira Umma aka ce yayi accident and he is gone" kamo hannunta Aliyu yayi murya can kasa yace "Allah ya ji kansa, yayi masa rahama, dont cry pls" cikin rawar murya tana gyada masa kai tace "Ameen" yace "After that?" Ta xame hannunta tace "We cried a lot da ummata, but at the end tace in daina kuka saboda my dad won't be happy with me idan ina masa kuka ban masa addu'a ba, and from then ban sake kuka ba don bana son abbana yyi fushi da ni, ko da yaushe addu'a nake masa Allah ya basa aljanna, we stayed for plenty months tare da Ummata a gidan mu kadai, kawai ranan sai ga uncle dina ya xo wai xa a yi sharing property din Abbanmu, I don't knw how but at the end, kawai ummata tace min ita xata tafi gidansu ni kuma uncle dina yace xai tafi da ni gidansa in xauna a can, a week after kuma ya sake dawowa... A ranan muka rabu da ummata ya rufe gidan, ya tafi da ni katsina gidansa ita kuma ta tafi gidansu ita ma" Aliyu sai kallonta yake ko kiftawa bai yi, labarin rayuwar wahala da tsangwama da tayi gidan kawunta ta shiga basa, da irin hidiman da sadeeq ya mata da yanda Mahaifiyarsa ta hanasa daga karshe har xuwa ranan da Umma ta xo ta gudu da ita ta kai ta gidan sabon mijin da take aure a kano, nan ma duk ta basa labarin 3 days stay dinta a gidan da abubuwan da suka faru kafin Umma ta kawo ta nan Kaduna wajen step sister dinta yakumbo, bata boye masa duk kalan wahalan da ta sha gidan yakumbo ba da irin duka da xaginta da take, har daga karshe makwabtan ta suka dinga xuga ta a kan ta kawo ta gidan aiki, har dai yakumbo ta kawo ta nan gidan tare da Abuuu.... Khadijah tayi shiru tana kallon Aliyu da ya kasa kallonta, kai kana ganinsa kasan tausayinta ne kawai ya cika sa, jin tayi shiru ya dago da kyar yace "Kiyi hakuri Iman, all this will come to past one day it's just a matter of time" ta gyada masa kai kawai, Ya shafa kansa yace "Kuma ki dinga hakuri da abinda Anty Khadijah ke maki, wataran baxata yi ba kin ji" a hankali tace "Toh" yace "And Saleem babu ruwanki da shi, soon xai tafi Germany ki kwantar da hankalin ki kin ji" nan ma tace masa "Toh" yyi mata murmushinsa mai kyau ya lakaci hancinta yace "Good girl" ita ma murmushin tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Yanxu islamiyya xa ku dinga xuwa from morning to evening tunda ba schl kuma" kallonsa tayi bata ce komai ba, yace "Toh tashi ki tafi kar ki kara sa ma kanki damuwa kinji" kai ta gyada masa ta dau wasu novels guda biyu da ta gani kan study desk dinsa tace "Can I read them" yace "Noo, I will get you the one to read tomorrow" tace "Ohk" sannan ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo. Bayan kwana biyu Mumy na daki ranan asabar misalin karfe sha daya da yake babu aiki, Su siyama, Baby da Khadijah har Iklima duk sun tafi islamiyya, Anty khadijah ta shigo dakin Mumy a shiriye rike da yar karamar jaka, daga nan bakin kofa tace "Anty fati xan je gidan wata kawata dake nan Zaria bata ji dadi ba, in sha Allahu xan yi kwana biyu xuwa uku kafin in dawo" Mumy tace "Zaria kuma, wace k'awa gare ki a Zaria, amma baki taba ce min kina da k'awa a Zaria ba, kuma ni tun da kika xo gidan nan ban taba ganin wata k'awa ta xo wajen ki ba, hasali ma ce min kike ba ki da kawaye...." Katse ta Anty khadijah tayi fuska a murtuke tace "Toh karya nayi kenan Anty fati, da can na taba ce maki xan je gidan k'awa ta? yanxun ma lalura yasa xan je wajenta, kuma da ba a Zaria take ba a Abuja take a anguwar mu, aiki ne ya mayar da mijin ta Zaria" Mumy tace "Toh Allah ya kyauta, Allah ya kiyaye" Anty Khadijah tace "Ameen, Anty fati don Allah ki sa ido kan Iklima kin san ba wai can take son cin abinci ba" Mumy ta harareta tace "Baxan sa ba" Bata ce komai ba ta juya ta fita daga dakin, Aliyu ne kadai xaune parlor, ko kallonsa bata yi ba ta nufi kofar fita, ya bi ta da kallo kafin yace "Allah ya kiyaye hanya" ficewarta tayi ta rufe kofa ba tare da ta tanka sa ba. Karfe biyar na yamma bayan Aliyu ya dawo aiki ya kira baby ta shigo dakinsa yace "Me ya hana ku xuwa islamiyya" ta xaro ido tace "Yayanmu na safe fa muka je yau" yace "Ohk je ku shirya da Iman mu fita" cike da murna tace "Waow, su siyama fa Yayanmu?" Yace "Ban da su" juyawa tayi da sauri ta fita baki har kunne, a dakin Mumy ta tarda Khadijah dake fiddo ma Mumy turarrukan da ta aiki driver ya siyo mata a shopping mall, Iklima kuma na xaune saman gado tana kallo, Baby tace "Mumy wai Yayanmu yace ni da Iman mu shirya xa mu fita anguwa" Mumy tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Toh ku je ku shirya" iklima ta sakko saman gadon kamar xata yi kuka tace "Mumy ni ba dani xai je ba kenan" Mumy tace "Toh ni na sa ki ki dinga masa fitsara? Wannan kuma ya rage na ku ke da shi" Fita iklima tayi dakin tana kuka, Baby ta fiddo atamfar da Mumy tayi masu iri daya da khadijah da mayafi tace "Wannan xa mu sa Iman" ita dai khadijah bata ce komai ba, baby ta kyalkyale da dariya tace "Allah sarki ban da iklima" Khadijah tayi murmushi tace "Yayanmu has a very good heart nasan xai je da ita" Baby tace "Tab kinsan yanda Yayanmu ya tsani mai rashin kunya" Khadijah bata ce komai ba ta fara sa kayan da baby ta dauko masu. iklima na fita mumy ta tashi ta tafi dakin Aliyu, daga bakin kofa ta tsaya tace "Abuturrab amma tare da Iklima xa ku je" Ya hade rai yace "A'a ni ban ce xan je da ita ba mumy" mumy tace "Toh sai a fasa tafiyar ai" daga haka ta juya ta shiga dakin Anty Khadijah ta ga iklima xaune can karshen gado tayi tagumi tana rera kuka, Mumy tace "Sai ki shirya ku tafi gaba daya" mumy na fadin haka ta juya ta wuce, ko kunya babu iklima ta tashi ta fiddo sabon kayan ta da takalmi mai tsini da jaka, ta sha uban make up ta sa spec, ta feshe jikinta da turarurrukan uwarta sannan ta sakale mayafinta a kafada ta fito, dakin su baby ta shiga su ma har sun gama shiryawa baby na ganinta ta kwashe da dariya har da faduwa kan gado ta dinga kyakyatawa, Khadijah tayi murmushi ta dauke kanta, Baby ta kuma dagowa ta kalli Iklima ta kwashe da dariya, Iklima ta maka mata harara tace "Ai dama ke mahaukaciya ce" Baby ta mike xaune tace "You are not even ashamed of ur self, yanxu wa yace xai je da ke, har da wani sa dogon hill da spec, ji wani make up kamar na yan kasuwar tasha" Juyawa iklima tayi ta shiga dakin mumy, can sai ga ta ta fito tana huci tace "Mumy na kiranki" Baby tayi tsaki tace "Ae a haka xa ki kare da reporting din mutane" Dakin mumy ta wuce tana hararanta, har mumy ta gama ma baby fada bata ce komai ba, tana fita ta kira Khadijah suka sauka downstairs su jira ya Aliyu tana kumbure kumbure. Babu yanda Aliyu ya iya haka ya tafi har da iklima, baby ce gaban motar, iklima da Khadijah kuma a baya, babu abinda ya fi ba Aliyu takaici irin shegen make up din da tayi a fuska. Smart kids ice cream spot ya nufa da su, bayan ya siya masu ice cream da pizza da fries ya mayar da su gida duk da ba haka ya so ba amma saboda iklima ya fasa duk abinda yyi niyya. Ranan lahadi da daddare Anty khadijah ta dawo gidan, Mumy da Aliyu dake xaune parlor suka bi ta da kallo ganin yanda ta yi wujiga wujiga, bata yarda ta tsaya parlor ba sannu da gida kawai tayi ma yar uwar tata ta wuce sama da sauri, Aliyu ta kalli Mumy yace "Daga ina take mum?" Mumy tace "Allah kadai ya sani" Anty khadijah na shiga daki ta bude press dinta ta tura jakarta sannan ta rufe ta tube kaya ta shige bandaki, sai da tayi wanka ta sauya kaya sannan ta fito tana kwala ma siyama kira ta xo ta xuba mata abinci, xaunawa tayi parlor, Mumy dake ta kallonta tace "Lafiya na gan ki haka" da sauri ta kalli mumy tace "A ya kika gan ni?" Mumy tace "Atoh, kinga wani duhu da kika yi kamar warce taje kauye" Anty khadijah tace "Kauye kuma, Zaria fa nace maki xan je, kuma gashi har naje na dawo" Mumy tace "Toh Allah rufa asiri" Sai a sannan Aliyu ya gaisheta, fuska a murtuke ta amsa can ciki, ya mike yyi wucewarsa sama, tana kallon mumy tace "Ina d'a na saleem?" Mumy tace "Ya je Abuja jiya da kika tafi, ina jin daga can ma xai wuce Germany, toh wai ke da kika ce kwana biyu xa ki yi Khadijah ya aka yi kika dawo yau, jiya da safe fa kika tafi?" Anty khadijah ta hade rai tace "Kai Anty fati, to kwana biyun bai yiwuwu ba" daga haka ta mike ta wuce kitchen don xuba abinci ganin siyama bata sakko ba. _Littafin Noorul Hayat na siyarwa ne, kindly patronize ur Novelist and read happily_🥰 ✨ *NOOR-AL-HAYAT* ✨ Da safe har su siyama suka tafi makaranta Anty khadijah bata sakko ba kamar yanda ta saba, tun bayan da ta kori kyauta da asuba take fitowa amma yau shiru, Khadijah ta taya mumy suka yi breakfast tun asuba sannan ta kwashi wanke wanke ta tafi tana yi duk da ba ita ce da yi ba baby ce, amma ganin tana bacci take taya ta, Mumy kuma ta wuce bedroom dinta, yanxu kam khadijah ta saba bata jika jikinta idan tana wanke wanke, ta gama wanke plates din gaba daya ta shigo kitchen tana ajiye ko wanne a maxauninsa, d'an dukawa tayi ta dalilin cikinta dake ciwo tun cikin dare, ta rasa irin ciwon cikin, Aliyu ya shigo da shirin fita office, tana ganin sa ta mike da sauri, yace "What's wrong?" Murmushi tayi tace "Good morning" yace "I asked what's wrong with you" tace "Ba komai, kawai cikina ke min ciwo amma yana sauki" yace "Since when?" Tana ci gaba da ajiye plates din hannunta tace "Da na tashi daxu" Yace "Ohk xan ajiye maki magani a bedroom, idan kin yi breakfast sai ki sha" tace "Toh nagode, in yi maka cup din coffee?" Yace "Ohk thanks" daga haka ya juya ya koma parlor, ta dau cup ta yi making masa coffee a ciki sannan ta fita ta kai masa, ya amsa yana kallonta yace "Nagode" murmushi tayi ta juya ta koma kitchen. Ita kadai ce kwance dakin banda juye juye babu abinda take, baby ta shigo daukan system dinta ganinta haka ta isa gabanta da sauri tace "Iman, what's wrong are u okay" mikewa xaune khadijah tayi jin xuciyarta na tashi ta wuce bayi da sauri, amma ta kasa aman, sanin Mumy bata nan baby ta tafi dakin Anty khadijah dake parlor da yar ta suna kallo suna yin lunch din da mumy tayi kafin ta fita aiki, wayarta baby ta dauka tayi dialing number Aliyu da sauri, sosai Aliyu yayi mamakin ganin number Small mun dinsa, can dai ya dauka hade da sallama, Baby tace "Yayanmu it's me baby, Iman ce bata da lafiya, she is even vomiting gashi mumy bata nan, nobody is at home sai Anty khadijah" Yace "Toh gani xan xo yanxu" katse wayar yyi, tayi deleting kiran a log sannan ta ajiye wayar ta fita da sauri ta koma dakinsu, Aliyu ya bar duk abinda yake cikin few minutes sai gashi ya dawo, hawaye kawai khadijah take da ya tambayeta inda ke mata ciwo, Anty khadijah na ganin ya shigo gidan ta hayo sama kamar me neman abu iklima na biye da ita, kamar dai daxu yanxu ma magani ya bata, sannan ya kira mumy ya sanar da ita bata da lafiya xa su tafi clinic ya dubata, Mumy dai tayi mamakin yanda aka yi ya sani har ya dawo shi da yake gun aiki, amma dai kawai tace masa toh, Hijab khadijah ta sa ta bi sa suka fita, Baby tace "yayanmu xan iya bin ku" ya kalleta yace "Clinic din?" Da sauri tace "Aa yi hakuri" murmushi yyi sanin tun tana yar karama take tsoron asibiti dama, suna isa asibitin office dinsa ya wuce direct da khadijah, sai dai ba shi ya dubata ba wani likitan ne daban ya dubata yasa aka mata series of tests, nan ya mata allura aka bata drugs, tun da aka yi alluran dama take kuka, Aliyu ya nuna mata gadon duba masu ciki yace "Kwanta can kiyi kukan da yawa" ba musu ta kwanta ta ci gaba da kukan nata a haka har bacci ya dauketa. Sai kusan la'asar ya tada ta, ta bude ido a hankali sannan ta mike xaune yace "How you feeling now?" Bata ce komai ba, yace "Toh taso kiyi alwala" ba musu ta mike, bayan ta gama sallah suka fita office din, Eatry ya kai ta ya siya mata abinci sannan ya mai da ta gida. Bayan kwana biyu, Aliyu na tsaye kitchen yana mamakin wa kuma ke shan coffee a gidan bayan shi, cos ya sami powder din ba yanda yake ajiye sa ba, hada coffee din yyi ya fita kitchen din, duk da shirin fita office da yyi komawa bedroom dinsa yyi ya kwanta bayan ya gama shan coffee din jin kansa na juya masa, Mumy ta gama shirin tafiya gun aikinta ganin bai fita ba tun safe ta shiga dakinsa, kwance ta samesa idonsa a rufe, tace "Abuturrab" ya bude ido da sauri tace "Are you okay" yace "Sure I am fine, it's just headache anjima xan tafi aikin" Mumy tace "Toh Allah ya sauwake, sai ka sha magani, ni na tafi" yayi mata Allah ya tsare sannan ta fita, Anty khadijah dake xaune parlor tayi ma Mumy Allah ya kiyaye, Mumy tace "Ameen" sannan ta fita. Mumy na fita Anty khadijah ta shiga kitchen ta daura tea pot a kan gas, ta dau Lipton da kayan kamshi kamar dai yanda ake dafa ruwan shayi ta xuba a tea pot din, kulle kofar kitchen din tayi ta ciro wani kulli da ta tusa cikin bra dinta ta bude ta juye gaba daya garin ciki a tea pot din sannan ta rufe, bata bar kitchen din ba sai da ya tafasa sosai sai kamshi ruwan lipton din yake, sannan ta juye a karamar flask bayan tayi shifter din shaft din garin, ta kashe gas ta wanke tea pot din ta kife ta dau babban flask din gidan ta bude ta tuttule ruwan Lipton dake ciki a sink ta rufe ta ajiye sannan ta bar kitchen din ta koma parlor ta xauna. Karfe sha biyu saura Anty khadijah ta sa su baby da iklima su shirya wai xa su rakata, ba don ran baby ya so ba ta tafi dakinta shiryawa don tasan masifa xata yi ta masu a duk inda xa su, Bayan baby ta sa Hijab dinta ta kalli Khadijah da ke gyara mata kayanta da ta sassauke ta ajiye saman gado tace "Don't worry fa Iman, ni ma kawai wahala nasan xan je mu yi, following Anty khadijah is always one of my worst night mare... beside Yayanmu is at home ai yana bacci, he will keep you company, you won't be that lonely" khadijah tayi murmushi tace "Alright bye" daga haka baby ta fita, Anty khadijah na fitowa dakinta ta bude kofar dakin Aliyu a hankali dai dai lkcn da ya bude idonsa suka yi ido hudu, fuskewa tayi ta daure fuska ta shiga dakin ta tafi gaban madubinsa ta dau turarrukansa ta dinga fesawa irin shi ya kawo ta din nan, sannan ta fice daga dakin ta rufe masa kofa. baby ta ba handbag dinta da makullin motar tace "Gashi ku je ku jirani a mota da Iklima saura ku yi damben da ku ka saba kafin in fito" baby sai da taje ta fara yi ma yayanta sallama a dakinsa sannan ta sauka kasa, tana sauka Anty khadijah ta bude dakin babyn tana kallon khadijah dake ta gyaran kaya ta hade rai tace "Idan kin ga dama, kina gama gyaran kayan ki tafi ki kai ma Aliyu abinci don bai yi breakfast ba, ruwan Lipton din sa na nan a karamin flask na Babban flask ya kare" Khadijah tace "Toh Anty" ta maka mata harara tace "Kya nemi Antyn ki dai" daga haka ta juya ta fita ta rufe kofar. Khadijah na ji suka fita gidan a mota, ta ci gaba da gyaran da take a hankali har ta gama sannan ta fita, kitchen ta wuce don debar ma Ya Aliyu breakfast kamar yanda Anty khadijah ta ce mata, tsaye tayi inda karamin flask din yake ta kai hannu kan cabinet din kitchen din ta dangwalo wani garin magani da ta gani a xube wajen, ta dinga kallon bak'in maganin can ta tafi sink ta wanke hannunta, ta dawo ta dau napkin din kitchen din ta share wajen ta wanke napkin din a sink sannan ta shanya ta gama daura masa kayan break din a tray da karamin flask din ta fita xuwa dakinsa, kwance ta samesa idonsa biyu, ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tace "Yayanmu ga breakfast din ka, in hada maka shayin" ya girgixa mata kai yace "Noo don't worry xan yi da kai na, ke ba ki bi su ba?" Khadijah ta girgixa kai tace "A'a..." Shiru ya d'an yi sai kuma can yace "Toh ki je sanusi ya kai ki saloon kiyi gyaran gashin ki" turo baki tayi ta make kafada tace "A'a ni gashina bai yi datti ba Yayanmu, kuma on Sunday mumy ta kai mu ai" yace "Toh me ma ya hanaku xuwa islamiyya?" Ta wara ido tana murmushi tace "Ka mance yau Thursday" ya lumshe ido ya bude yace "Toh tashi ki tafi" mikewa tayi ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, bayan tafiyarta da kusan minti goma ya mike xaune a hankali yana son daurewa ya bar gidan ya tafi clinic, gaba daya ya rasa gane me ke damunsa, it seems he is sick, cup ya dauka ya debi ruwan Lipton dake flask kadan, sannan ya xuba madara da cube biyu na sugar ko bin ta kan Milo bai yi ba ya juya shayin da spoon ya ajiye ya huce, mikewa yayi ya shiga bathroom ya sake wanka sannan ya fito, ya dau wani kayan da xai sa ya ajiye saman gado ya xauna bakin gadon ya dau cup din shayin da ya riga ya huce ya kai baki ba tare da ya bi ta kan dankali da kwai dake rufe a plate ba.... Yana gama shanye shayin ya ajiye cup din. Kallon cup din kawai Aliyu yake bayan few minutes wondering is this really a tea he drank, cos even the taste... komawa yayi ya kwanta saman gado bayan kusan minti biyar ya rufe ido sosai, He just can't imagine what is ringing all over is head a lkcn, ya sake mikewa xaune da sauri trying hard to control his self daga urge din da xuciyarsa ke masa, loudly xuciyarsa na bugawa sosai yace "Not... Iman" ya kai hannu da nufin sa kayansa ya bar gidan gaba daya amma ya kasa, komawa yayi kan gado yyi cike da karfin hali ya kwanta, jin sanyi na shigarsa ya rufa da duvet, dai dai nan aka bude kofar dakin ya juya da sauri, khadijah ce ta shigo rike da leda karami tace "Yayanmu ga shi sanusi yace in baka aiken da kayi masa daxu, naga drugs ne dama baka da lafiya ne?" Kin cewa komai yyi ya rufe ido kamar mai bacci, ta isa kusa da shi ta durkusa tace "Toh ka ta shi kasha Yayanmu" tana fadin haka ta fiddo duk maganin tana duba prescription amma bata ga ni ba, guda daddaya ta cire gaba daya hudun ta dau table water da ta gani dakin ta dawo gefensa tace "Ka tashi kasha Yayanmu" ya bude idonsa da ya kada yace "Ajiye ki fita" bai taba mata magana yanda yyi mata ba a lkcn amma a tunaninta ko rashin lafiyan ne, kamar xata yi kuka tace "Toh ka fara sha don Allah Yayanmu" lkci daya ya ji kamar an cire gaba daya sympathy dake tare da shi, Ya mike kamar wani xaki ya fixgota cikin tsawa yace "I said leave Iman" hawaye ne ya cika idonta tana kallonsa, cikin rawar murya tace "Ohk" daga haka ta ajiye masa magungunan cikin leda ta ajiye ruwan ma ta mike, da sauri ya jawota ta fado jikinsa ta xaro ido a tsorace tace "Yayanmu" ya rungumeta gam hade da lumshe ido muryarsa na rawa yace "I don't want this to happen Iman, I...." Kasa ci gaba yayi jikinsa ya dau rawa, yasan he have tried for that long, the urge... He just don't understand it, it's unbearable.... It's different. Aliyu never gave her a chance to raise any alarm duk da kokarin yin hakan da ta dinga yi, kai kana ganinta kasan bata taba tsorata da shiga tashin hankali irin na moment din ba, gashi yyi depriving dinta damar rokonsa ta kuma yi masa tuni da cewa ita marainiya ce ko xai ji tausayinta, domin kuwa ya rufe bakin ta, and that was how everything happened, tana ji tana gani Aliyu ya raba ta da pride dinta, daga nan da ta rufe ido bata sake budewa ba sai bayan wasu mintuna. Kwance ta ganta dakin baby an rufeta da duvet, ta dinga bin dakin da kallo a hankali kamar me son tuna wani abun, ta runtse ido ta dalilin sara mata da taji kanta ke yi sosai, bude ido tayi da sauri kuma a tsorace don a lkcn komai ya dawo mata, xata mike xaune taji wani xafi gaba daya jikinta, kara ta saki ba tare da ta shirya yin hakan ba duk jikinta na rawa tana kiran Ummanta, dai dai nan aka bude dakin, bata san lkcn da wani karfi ya xo mata ba tayi ignoring axaban da take ji ta mike a gigice tana neman sauka kan gadon cikin tashin hankali take cewa "Don Allah yaya Aliyu kayi hakuri ina rokan ka, wlh mutuwa xan yi, kar ka xo don Allah" ya isa har gabanta yana kallonta da idanuwansa da suka yi ja xata gudu ya rikota ya xaunar da ita gefen gado shi ma ya xauna ba tare da ya bari sun hada ido ba muryarsa na rawa yace "Don Allah ki yafe min Iman, sure I cheat you, but..." Kasa ci gaba yyi ya sake hannunta ya rike kansa da yyi masa nauyi hawaye na xuba idonsa, ita ma kukan take a raunane tana son tashi wajen amma ta kasa, sauka yyi kan gadon ya durkusa kan kneels dinsa hawaye na xuba idonsa ya daura kan sa kan kafarta trying hard to speak yace "Ki dubi girman Allah ki yafe min Khadijah, I didn't do that intentionally, forgive me plss, I don't knw wat came over me, ba halina bane Iman, don Allah ki yafe bi...." Kuka kawai khadijah take tana ja baya jikinta na rawa, cikin sarkewar murya tace "Na ji, amma ka tafi don Allah ina rokon ka, please go" ya fi minti biyar durkushe gabanta kansa a duke har lkcn hawaye ya ki tsaya masa, ya ji duk ya tsani kansa, of all people why Iman, cike da karfin hali ya mike ya fita dakin. Khadijah ta fada kan gado ta dinga kuka, tun bayan rasuwar Abbanta sai a lokacin ta ji ba ta son duniyar gaba daya, xuciyarta ya karaya taji ita ma da Allah ya dau ranta a lkcn ta huta. Bacci me nauyi ne ya dauketa afterward, bata tashi farkawa ba sai da su baby suka dawo misalin karfe biyar na yamma, ta dinga kallon baby da ta tasheta da idanuwanta da suka kumbura sosai, baby ta ja baya da mamaki tace "Iman, what's wrong did you cried?" Hannu ta kai jikinta ta ji yyi mugun xafi, ta fita da sauri don kusan tare suka shigo gidan da Mumy, dakin ya Aliyu ta fara shiga ta ga baya nan, sannan ta sauka downstairs don har lkcn mumy da Anty khadijah ba su hauro sama ba, Anty khadijah duk ta gaji da xancen da mumy ke mata ta kagu ta wuce sama don kin xama ma ta yi a parlorn tana tsaye, da damuwa baby tace "Mumy kamar khadijah bata da lafiya...." Katse ta Anty khadijah tayi da sauri tana kallonta tace "Me ya sameta?" Mumy kanta sai da ta kalli Anty khadijah, can Anty khadijah ta ankare ta tabe baki tace "Abun ka da xuciyar musulunci ban da haka ina ruwana, a kan yarinyar da ake min gori a gidan nan dubi yanda na xabura don ba ta da lafiya kamar iklima ce ba lafiya" mumy na kallon baby tace "Me ya sameta" baby tace "Nima ban sani ba, her eyes are swollen kuma jikinta yayi xafi sosai" mikewa Mumy tayi ta wuce sama, sai da Anty khadijah ta shiga kitchen ta dau flask din da ta xuba ruwa taji an diba sannan tayi murmushi ta bi bayan mumy da sauri, Cire bargon Mumy tayi tana kallon khadijah, ita kanta sai da ta tayi mamakin irin xafin da jikinta yyi ga wani shivering da take idanuwanta sun kumbura, Anty khadijah dake ta kallonta ta shimfida damuwa karara fuskarta tace "Me ya same ki haka" khadijah bata iya tace komai ba sai rawa da jikinta yake, Fita Anty khadijah tayi ta nufi dakin Aliyu da sauri ta bude, ganin baya dakin ta shiga don kara tabbatar da cewa ba xanin gadon da ta gani dakin bane daxu da ta shigo sannan ta fita daga dakin, Mumy ta kalli baby tace "Dauko min wayata" Da sauri baby ta fita sai ga ta ta dawo da wayar, Mumy ta shiga kiran Aliyu, yana gidansa kwance for the 1st time tun da Daddy yyi furnishing masa gidan, idonsa a lumshe suke ya bude a hankali jin karan wayarsa ya dinga kallon kiran ganin Mumy ce har ya katse, sake bugowa aka yi, yayi karfin halin mikewa don xaxxabi ne sosai jikinsa, ya dau wayar ya kai kunne bayan ya daga cikin sanyin murya yyi mata sallama, da damuwa Mumy tace "Aliyu where are you, Khadijah bata da lafiya sosai, ka taho yanxu idan ya kama ku tafi asibiti ne sai ku wuce" Da farko rasa abinda xai ce ma Mumy yayi lkci daya hawaye ya cika idonsa, har sai da tace "Hello Abuturrab, are you there?" Yyi karfin halin gyada kai yace "Xan taho yanxu Mumy" daga haka ya katse wayar ya ajiye ya rike kansa hawaye na sakko mishi. Aliyu ya fi minti goma xaune cikin mota bayan ya iso gida, gaba daya ya rasa me ke masa dadi duniyar, har ya fita kamanninsa saboda damuwa, Mumy ta fito jin shiru shiru bai shigo ba, ganinta yasa tun kan ta karaso parking lot din yyi karfin halin bude motar ya fito kansa a kasa, kamar bai son taka kasa yake tafiya, har ya iso inda take kallonsa Mumy take cos he looks so sick, shi kam ya kasa dagowa balle ya kalleta, Tace "Abuturrab are you okay, ciwon kan ne har yanxu" ya gyada mata kai a hankali yace "Na sha magani mum da sauki" daga haka ya wuceta ta bi sa da ido, bin bayansa tayi tace "Toh bacci ka je clinic din kake yi?" Bai juyo ba yace "Eh" da damuwa tace "Maimakon ka tsaya gida ka huta Aliyu tunda baka da lafiya, da sai ka kira asibitin ka bada uxurin ka, xa ma ka iya dubata yanxu ko kawai mu wuce asibiti" tsaye yyi bakin kofa ya rasa abinda xai ce mata ya kuma kasa juyowa duk jikinsa yyi sanyi, Cike da karfin hali yace "Xan tafi asibitin da ita likita xa su duba ta a can" mumy tace "Toh kai ma gaskiya a dubaka wani irin ciwon kai ne haka lkci daya tun safe, sanusi sai ya kai ku clinic din" Bude kofa aka riga sa yi Anty khadijah dake tsaye bakin kofar tana kallonsa da kyau tace "Me ya same ka kai kuma, baka da lafiya ne?" Gefenta ya bi ya shiga gidan ba tare da ya bari sun hada ido ba yace "I am better now" Anty khadijah ta kalli Mumy mamaki shimfide fuskarta tace "Dama baya da lafiya ne Anty fati?" Mumy tace "Tun safe kafin in fita aiki yace min yana jin ciwon kai ban san wani kalan ciwon kai bane haka har yanxu, ni na xata ma baxa shi aikin ba ganin har na fita yana gida" Anty khadijah ta bi bayansa da sauri ganin har ya kai stairs, ta hada har da d'an gudunta har hakan ya ba Mumy mamaki, Tsaye Aliyu yyi bakin kofar dakin ya kasa shiga, ta labe jikin stairs tana jiran ya shiga ita ma ta shiga, a hankali ya murda kofar ya sa kai ya shiga, Tana ganin haka ita ma ta shige, Baby da ke xaune gefen Khadijah da ke kwance da damuwa tace "Yayanmu Iman bata da lafiya she is just crying, and her temperature is very high" hawaye cike idonta take magana, khadijah na jin sunan da Baby ta kira ta bude ido da sauri hade da yunkura ta mike xaune, Aliyu ya kasa kallon direction din, wani sabon kuma khadijah ta saki a raunane, Anty khadijah dai na tsaye kofa tana kallonsu, Aliyu bai iya ya kalli khadijah ba yace "Ki sa ta shirya xa mu je asibiti yanxu" baby tace "Toh" daga haka ya juya suka yi ido hudu da Anty khadijah, tabe baki tayi ta juya ta bar wajen tana cewa "Haka dai aka iya, da yar uwar ka ce ba lafiya ai baxa ka bi ta kan mu ba ma" shi dai ba ce komai ba ya fita. Hijab baby ta ba Khadijah, Khadijah taki sawa tana girgixa mata kai cikin kuka tace "Ni bana son xuwa asibitin, idan nayi bacci I will okay, baxan iya xuwa ba" baby tace "Nooo, ki sa mu tafi don Allah" kin yarda Khadijah tayi hakan yasa baby ta fita sai ga ta sun shigo tare da mumy, mumy ta karaso kusa da ita ta amshi hijab din ta sa mata tace "Kiyi hakuri ki tashi ku je asibitin kin ji, Allah ya sauke" daga haka Mumy ta dago ta, Aliyu dai na tsaye corridor yyi backing kofar, muryar Mumy ya ji tana cewa "Toh ka kai ma Sanusi makullin sai yyi driving din koh" Juyowa yyi xai yi magana amma ya kasa ganinta tsaye tare da Khadijah tana rike da hannunta, Wani mugun tausayinta ya dinga ratsa shi ganin irin karfin halinta cos he was thinking baxata iya fitowa ba, bai yarda sun hada ido ba kamar yanda ita ma kanta ke a kasa, ya fara sauka stairs Mumy ta bi bayansa tana rike da hannun Khadijah baby na biye da su a baya, Anty khadijah dake tsaye bakin kofar dakinta ta saki baki ta bi Khadijah da ido a ranta tace wa yaga boss lady, don kusan kalau take tafiyar ta, nan kuwa daga ita har Aliyun basu san mugun karfin hali take ba, she is in pain all over, only trying her best to be okay, Mumy ta bude bayan motar ta shigar da ita tasa baby ma ta xauna a baya kusa da ita, sanusi ne ya ja motar cos da gasken Aliyu bai jin xai iya tukin, har suka isa asibitin kansa na jingine da kujera, baby kuma na rungume da Khadijah da ta ki bude ido tana kukan xuci. Sanusi na parking Aliyu ya bude motar ya fita, Baby ta fito tana kallon khadijah tace "Iman ki sakko we are at the hospital" A hankali khadijah ta fito cikin motar tana rike da hannun baby, Aliyu ya kalli baby yace "Ku koma tare da sanusi" xaro ido tayi tace "Yaya but Mumy tace in tsaya da ita, wa ye xai tsaya kusa da ita idan anyi hospitalising dinta, look shes very sick fa" irin kallon da ya dade bai mata ba ya shiga yi mata a lkcn, Bata sake cewa komai ba ta shiga motar hawaye cike idonta, Khadijah ta fashe da kuka a hankali tace "Don Allah kar ki tafi ki bar ni" Baby na share hawayen ta tace "He said I shud leave Iman" Aliyu ya juya ya wuce ciki sai ga nurse ta taho ta shiga da Khadijah asibitin, sanusi ya ja motar yana ma khadijah Allah ya sauwake ya kama hanyar gida. Nurse din na rike da hannun Khadijah da ke ta hawaye ta wuce office din Aliyu da ita kamar yanda yyi instructing dinta, baya office din hakan yasa ta fito ta shiga office din kusa da nashi ta samesa xaune, ruwan xafi yasa ta fara kai ma khadijah bathroom dinsa tayi wanka sannan ya bata magunguna da alluran da xata mata, daga haka kuma ya bar asibitin, kulawa sosai nurse din ta bata don ta bata tausayi yanda ta ga jikinta duk da ba ta san takamaiman abinda ke damunta ba, tana mata alluran kuwa bacci ya dauketa nan dakin Aliyu. Aliyu na gidansa har ya samu bacci ya daukesa.... ring din wayarsa ya tashe sa, dubawa yyi da kyar ya ga Mumy ce, ya kai hannu ya daga a hankali ya kai kunne, da damuwa tace "Aliyu ya jikin Khadijah, or shud I come over naji shiru shiru" yace "Noo mum, da sauki anjima sanusi yaje can asibiti ya mai da ta gida" Mumy tace "Kai kana ina?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Na taho nan gida na ne, I need sleep" da mamaki mumy tace "Kuma ka bar ta ita kadai asibiti gashi ka ki barin Baby ta xauna da ita Abuturrab" yace "Nurses din xa su kula da ita mum" Mumy ta d'an yi shiru kafin tace "Toh shkkn, Allah ya sauwake, kai ya jikin naka?" Yace "Alhmdllh am better now" tace "Ohk, amma da ka daure kai ka je ka maido ta gida don Allah, bbu dadi hakan kamar bata da gata, idan baxa ka ba ni in je" yace "Toh mum xan je yanxu kiyi hakuri" daga haka ta yi masa sallama ta katse wayarta. Bayan magrib Aliyu yyi wanka bayan yyi sllh ya canxa kaya ya bar gidan, yana isa clinic din ya kira nurse da ya bari da Khadijah a waya yace tayi mata alluran karshe na ranan ta fito tare da ita yana waje, nurse din tayi yanda yace sannan suka fito tare da Khadijah, bin nurse din da ke rike da hannun ta take kamar iska xae kadeta ta fadi, duk ta rame lkci daya, yana kallon nurse din bayan sun iso a hankali yace "Hope you did all what I instruct you to" nurse din tace "Yes but, I don't knw why she's finding it difficult to walk, kuma tun daxu take complaining chest pain, Dr bashir ya bata magani dai daxu, har da shi ma cikin wa ennan" ta fadi tana nuna masa drugs din da Khadijah xata kai gida, Khadijah dai na tsaye kanta a kasa duk a tsorace take ga xuciyarta dake bugawa da sauri da sauri, Aliyu ya gyada kai yace "Thanks nurse Maryam" Nurse din tayi murmushi ta sa Khadijah ta shiga gaban motar ta rufe tana mata Allah ya kara lfya, tada motar Aliyu yyi ya bar haraban hospital din, har suka isa gida bai ce komai ba, yana lura da hawayen da take yi tana gogewa da Hijab dinta tun bayan da suka fito clinic har ynxu da suke gida, ya gama parking ta bude motar a hankali ta fita, ya bi ta da ido ganin yanda take tafiya har ta shiga gida, sae sannan shi ma ya fito ya rufe motar ya shiga gidan. Mumy dake xaune parlor da su siyama da Anty khadijah ta mike ganin Khadijah tace "Sannu khadijah, ya jikin" Khadijah ta kasa dago kanta tace "Naji sauki Mumy" Anty khadijah sai kallonta take babbu kiftawan kirki, Aliyu na shigowa parlorn ya haura sama, Mumy ta kama hannun Khadijah ta wuce sama xuwa bedroom dinta da ita, da kyar khadijah ta iya cin pepper soup din da mumy ta mata, duk bakin ta babu dadi, a nan dakin bacci ya dauketa. Cikin dare misalin karfe biyu xaxxabi ya kuma rufe ta, dakin Aliyu Mumy ta shiga ta samesa xaune kan darduma ta xauna gefen gado ta jira ya sallame sallahn da yake da damuwa tace "Aliyu har yanxu fa jikin Iman" yace "Xaxxabin kuma?" Mumy tace "Ehh dama" yace "Mumy to ta kara shan drugs din..." Mumy tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Toh shkkn" sannan ta mike ta fita, magungunan ta sake bata ta rufe ta da duvet sai kusan asuba bacci mai nauyi ya dauketa. Da safe tea Khadijah ta sha bayan mumy ta tilastata da kyar, da tayi ma Aliyu maganan alluranta da ya rage yace driver ya kai ta sai karfe goma shi xai fita aiki, sanusin ne ya kai ta ya maido da ita, kafin yamma taji saukin jikinta sosai sai dai ta rasa irin ciwon da take jin kirjinta ke mata, kuma hakan na faruwa ne in dai ta tuna incident din ranan sai taji mugun faduwar gaba, har lkcn Aliyu bai barin su hada ido a gidan kuma bai ce mata komai, idan tana wuri ma bai yrda ya tsaya a gun, Anty khadijah dake lura da komai har wani farin ciki da nishadi na musamman take ji a gidan, har Mumy ta dinga mamakin yar uwar tata, duk fadace fadace da xage xagen ta rage yanxu hatta Khadijah ta daina hantara nan ko shirin sake komawa inda taje kwanaki kamar yanda aka ce mata ta dawo idan ta tabbatar komai ya wakana a lkcn ma xa a fara aikin, tunanin karyan da xata yi ma Mumy kawai take ta tafi inda xata. Aliyu na bedroom dinsa da daddare baby ta shigo, ta xauna kusa da shi tace "Yayanmu I want to ask you something pleaseee" yana kallonta yace "What?" Ta langwabar da kai a hankali tace "Iman tayi maka wani laifi ne, naga you no longer talk to her, ko ta gaisheka sometimes you do pretend you didn't hear, why please, ka gaya min me tayi maka, gashi ita ma she is always sad yanxu, I've caught her severally tana kuka cikin dare..." Katse ta yayi yace "Na fara wasa da ke da yawa koh?" Da sauri ta girgixa masa kai, ya hade rai yace "Toh tashi ki tafi" mikewa tayi da sauri ta fita ya ci gaba da danne dannen laptop da yake yi. Washegari da sassafe Anty khadijah ta shirya har da kwallarta take ce ma Mumy xata Abuja an kirata wai Yusuf d'anta ba lafiya yana asibiti, mumy jikinta yyi sanyi har da bata dubu goma ta hau mota, ta karba ta yi mata godiya ta bar gidan. Karfe goma saura Mumy ta tafi aiki gidan ya rage khadijah da baby sai Iklima don su siyama sun tafi makaranta, Aliyu ma na sama a dakinsa, tun bayan abinda ya faru tsakanin khadijah da Aliyu ta rage xaman cikin gidan sae Mumy na nan, always a baya xaka ganta xaune ita kadai, yau ma xaune take tayi nisa a tunanin da take kamar ance ta juya taga Aliyu tsaye d'an nesa da ita, mikewa tayi a tsorace tana komawa baya, ya dauke idonsa daga kallonta yace "Iman" hawaye ya cika idonta ta kasa amsawa, karasowa yyi kusa da ita ya tsaya tana komawa baya a hankali, yace "Za ki gane gidan step mum din ki?" Khadijah sai kallonsa take xuciyarta na bugawa, ya hade rai yace "Am asking" a hankali tace "Kila in gane" yace "Ohk... Am coming back now" daga haka ya juya ya koma ciki, ba a dau lkci ba ya dawo, envelope ne rike hannunsa ya mika mata taki amsa gabanta sai faduwa yake, yace "Collect it" hannunta na rawa ta karba, yana gyada kai yace "Go Iman, go back to ur step mum, I can't continue my life the way I want living with you in the same roof, you are now a barrier to my happiness pls ki tafi Iman go anywhere, leave our home, bana son Ina ganinki ina jin haushin kai na cos nobody is above mistake, just go plss" A hankali ta juya masa baya hawaye na sakko mata tace "Ohk xan tafi... thank you very much for all what you've done to me throughout my stay in your home, Allah saka maka da alkhairi duk hidiman da ka min, but ina neman alfarmar ko xan iya yi ma Mumy sallama kafin in tafi, don ban mata hallaci ba idan na tafi bata sani ba" a takaice yace "Noo, just go Iman" ta fashe da kuka sosai tace "Ohk nagode" juyawa yyi ya nufi cikin gida... Sai kuma ya juya da sauri yana kallonta yace "And one more thing... Forgive me plss" ta juyo hawaye na sakkowa idonta tace "I have done that already" yace "Thank you" daga haka ya juya ya shiga ciki ya rufe kofa. Share hawayen idonta da ya ki tsayawa ta dinga yi, dama Hijab ne jikinta kawai ta nufi gate ta fita gidan, da kafa ta karasa bakin titi ta samu napep tana kallonsa a hankali tace "Tasha xaka kai ni" yace "Toh" daga haka ta shiga napep din, har suka isa tasha bata sani ba tayi nisa a tunanin da take, mai napep din ya dawo da ita duniyar tunanin da taje, sai a sannan ta tuna kudin da xata basa, da sauri ta leka cikin envelope din da Aliyu ya bata taga kudi ne me yawa a ciki ta xaro dubu daya hawaye na sakko mata ta shiga tashar ta nufi inda taji ana kiran kano, dama mutum daya ake jira tana shiga motar ta bada kudinta bbu bata lkci suka dau hanyar kano. Tun da suka iso kano Khadijah ta fito daga cikin tashar kanoline take ta kalle kalle tsaye a bakin titi, duk mai adai daitan da ya tambayeta inda xata sai dai ta kafe sa da ido nan kuwa tunanin da take daban, hadarin da ya shiga haduwa a garin ne yasa ta dawo reality, da kanta ta tafi gun wani mai napep a hankali tace "Tudun yola xan je" yace "Dai dai ina a tudun yola" tace "Idan mun je xan gane" Bata damu da kudin da ya kira mata ba ta shiga adai daitan suka dau hanyar anguwar da ta kira masa, tun suna hanya aka fara yayyafi har suka kawo Tudun yola, ita dai ta san ranan da suka taho daga katsina da ummanta taji ta ce ma mai napep Tudun yola to amma bata san ina a Tudun yola ba, tun mai napep na biyeta suna xaga anguwar har yyi parking yace "Bani kudi na ki sauka, ke da baki san inda xa ki ba kika sa na dauko ki" sauka tayi daga cikin napep din ta basa kudin da yace daga cikin envelope ya bata canjinta ya ja adai daitan sa yyi gaba, hawaye ya cika idonta ta saka kai gabas tana ta tafiya, to ina xata ga gidan ummanta, jin ruwan ya taho da karfi yasa ta samu yar rumfa ta tsaya, ta kusa minti talatin tsaye karkashin wajen, kowa ya shige gida, wasu kuma sun shiga shagunansu saboda ruwa hanyar kamar anyi shara, ita kadai ce a waje ga wani sanyi da ta dinga ji, an dau fiye da awa daya ana ruwan kafin ya tsagaita sai yayyafi, fitowa tayi daga inda take tsaye ta ci gaba da tafiya a gajiye, bata yi wani nisa tana tafiya ba taji ance "Lahh Mama dubi yarinyar nan mai kukan kitso" Juyawa tayi taga wata mata ce da 'yar ta da suka hadu a saloon ranan da Umma ta kai ta gyaran gashi, uwar ta rankwashi yarinyar da baxata wuce Khadijah ba tace "Toh ina ruwanki salon tsokana" matar tace "Sannu yan mata" Khadijah ta gaisheta ta amsa ganin xata wuce tayi saurin cewa "Anty don Allah ban san hanyar gidanmu bane, ko xa ki kai ni gun mai saloon din nan ta san ummata" matar ta saki baki tace "Baki San hanya ba kuma, daga ina kike haka?" A hankali khadijah tace "Daga kano nake na mance hanyar gidan ne" Matar dake ta yi ma khadijah kallon mamaki tace "Ikon Allah, sai dai saloon din da nisa daga nan gashi da sauran hadari, amma mu je mu hau adai daita sai in ajiye ki shagon" Khadijah ta d'an risina tace "Nagode Anty" daga haka ta bi matar da 'yar har suka isa inda masu adai daitan suke, ta fadi inda xa su sannan suka dau hanya, kamar yanda matar ta fada bbu laifi tafiyar da nisa, suna isa saloon din suka tarar mai saloon din ta fito xata rufe shago ta wuce gida saboda ruwa, Matar suka gaisa da mai saloon din sannan tayi mata bayanin Khadijah, mai saloon din tace "Tab, to ai gidan Hajiya Amina da nisa daga nan, cikin ruwan nan yaushe mutum xai fara takawa xuwa gidan ai sai dai adai daita" Matar tace "Toh don Allah ki taimaka ki dau adai daitan ki kai ta gidan idan ya so mamartata sai ta baki kudin adai daitan da kika biya" mai saloon tace "Sai dai haka" daga hakan suka yi sallama da matar Khadijah tayi mata godiya, wani adai daitan mai saloon ta samu suka shiga har kofar gidan Umma, a nan hankalin khadijah ya kwanta ta dinga kallon kofar gidan, khadijah ta sauka tana murmushi tace "Anty nagode xan je in karbo maki kudin napep din" daga haka khadijah ta shiga ciki da sauri, bbu kowa tsakar gidan saboda ruwan da aka yi, Khadijah ta kwankwasa kofar parlorn Ummanta a hankali, Bude kofar Umma tayi tana tambayar waye? Umma ta xaro ido hade da bude baki tace "Khadijah??" Rungumeta khadijah tayi cike da farin ciki tace "Ummata" Umma ta ja ta suka shiga ciki da mugun mamaki tace "Daga ina kike haka" a hankali khadijah tace "Kaduna Umma" Umma tace "Ke da wa?" Khadijah tace "Ni kadai Umma ki ban kudi in kai ma mai adai da ita a waje, mai saloon din nan da kika kai ni ranan ce ta rakoni, ban san gidan ba" Umma ta dau kudi ta fita da sauri, Godiya tayi ma mai saloon din ta ba mai adai daitan kudin kawo ta da yayi da mayar da ita da xai yi sannan ta koma ciki. Umma ta dinga kallon khadijah tana share hawayen da ya ki tsaya mata a sanyaye bayan Khadijah ta gama yi mata bayanin duk abinda ya faru tun daga ranan da ta bar ta gidan yakumbo har ixuwa yanxu da take gabanta, abu daya ta boye mata a labarin da ta bata shine kuma abinda ya shiga tsakaninta da Aliyu kawai dai ce mata tayi yace ta tafi saboda Anty khadijah bata sonta, Khadijah ta share hawayen dake sakko mata ita ma cikin rawar murya tace "Umma me yasa baki son in xauna a wajen ki, don Allah kada ki sake kai ni ko ina, let me stay with you plss" ta fashe da matsanancin kuka tana kallon Umma da ita kanta ba karamin rama tayi ba, Umma tayi gathering courage ta jawota jikinta a hankali tace "Khadijah ba laifi na bane kinga kishiyoyina ba kirki ne da su ba saboda su ya sa na kai ki gun yakumbo amma ta ci amanata ko don ba uwar mu daya ba, da wani mugun gidan ta kai ki haka xa a cutar min ke ina nan ban sani ba, har kadunan naje kwanaki in duba ki aka ce ai ta tashi a gidan, gashi bbu wanda yasan inda ta koma, haka nayi kwana biyu kafin in dawo nan kano, duk layukan ta basa xuwa har na gaji na daina kira, kullum fatana shine Allah yasa kuna lafiya ashe abinda ta maki kenan, to Allah ya saka maki, ita kuma wannan baiwar Allah da ta rike ki a gidan ta har na wnn lkcn Allah ya saka mata da alkhairi" Khadijah dake ta sauraren ta a hankali tace "Ameen" Umma ta mike tace "Bari in karbo maki abinci a makwabta bani nayi girkin gidan ba" daga haka Umma ta fita parlorn, khadijah ta jinginar da kanta da kujera a sanyaye, kadan ta ci shinkafa da miyar da Umma ta amso mata ta sha ruwa sannan ta fita yin alwala don ta yi sallah, Shafah da fitowarta kenan ita ma ta saki baki tana kallon khadijah, can ta kwalo ma Hasana kira, Hasana ta fito ita ma, Shafah tace "Kin ga ashe bak'i muka yi a gidan yau" a hankali khadijah ta gaishesu, dariya Hasana tayi tace "Lallai kam bak'i" daga haka ta juya ta koma bangarenta, Shafah ma ta wuce ciki tana dariya. Khadijah na xaune kan darduma bayan ta idar da sallah, Umma dake yankan alaiyahu alamar dai ita xata amshi girki tace "Kina ji na khadijah, babu ruwan ki da mutan gidan nan ki rufa min asiri kinji, duk me xa su maki kar ki tanka su, ko don Alhaji ya bar ki ki xauna gidan nan" Khadijah ta gyada mata kawai, mikewa Umma tayi ta fita da alaiyahun waje sai da ta shiga kitchen ta kira Abban fadila, yana dauka bayan ta gaishesa tace "Alhaji dama alfarma nake son tambaya gun ka" yace "Ina ji" tace "Dama khadijah ce xata xo ta d'an kwana biyu nan, sun yi hutu idan ba damuwa don Allah" Yace "Toh kin gaya ma su Shafah?" Shiru Umma tayi bata ce komai ba, yace "Sai ki sanar da su don bana son abinda xa a xo ana min tashin hankali a gida" daga haka ya katse wayarsa, Umma ta ajiye wayarta a sanyaye , ko wace irin rayuwa ce wannan ta fada yanxu ita kam, tun da tayi auren nan bata da kwanciyar hankali sannan kamar warce aka daure kafarta a gidan tana xaune a hakan har lkcn. Fita tayi ta tafi dakin Shafah ta samesu tare da Hasanar daga nan bakin kofa ta tsaya tace "Sannun ku, Khadijah ta xo daxu daga kaduna nace in gaya maku..." Shafah ta mata wani kallo tace "Au haba, to ta sha kabo..." Hasana tace "Lallai kam, sannunta da xuwa" juyawa Umma tayi ta fita ta koma kitchen ta daura girkin tuwo a gas, ko da Umma ta koma parlornta dauko maggi bacci ta tarda Khadijah na yi kan kujera, ta tasheta ta shiga daki ta hau gado, abu daya yasa ta jin hankalinta ya kwanta game da Khadijah, kuma shine yanayin da ta ganta, kowa ya ganta yasan bata tare da wahala sai dai 'yar ramar da tayi. Sosai Khadijah tayi kokarin ganin bata kula duk yaran gidan ba kamar yanda Umma ta yi mata huduba duk da irin cakalarta da suke yi a satin ta daya a gidan, ita kanta Umma hakuri take da kowa na gidan don kamar warce aka rufe ma baki komai suka mata bata tankawa duk ta yi sanyi kamar ba ita ba, Shafah da Hasana wani mulki na musamman suke xubawa a gidan, sai abinda suka ce ayi ake yi ga ikon bala'i... A can Kaduna kuwa, kamar wasa aka nemi Khadijah a gidan aka rasa har yamma, Mumy da farko ita a tunaninta ko Aliyu ne ya fita da ita don har ta tanadi rashin mutuncin da xata yi masa amma tana kiransa yace mata shi bai fita da ita ba, na hankalinta ya tashi sosai ta dinga tambayar baby ko iklima ta yi mata wani abun ne don Anty khadijah bata nan balle tace ita ce, shi kam Aliyu dama yana tabbatar da Khadijah ta tafi ya wuce clinic, ganin yanda mahaifiyarsa ta ishesa da kiran ba a ga Khadijah ba yasa shi komawa gida, and he tried his best pretending he knws nothing about her disappearance. Islamiyyar da Umma tayi ma khadijah register ta ci gaba da xuwa a kano, abu daya ke damun Umma yanxu a kanta shine irin sanyin da tayi kamar ba lively khadijahr ta ba, sanyin kuma ne yasa ko kadan abinda ake mata a gidan bata kula wa duk da idan ta fita islamiyya tun safe sai yamma take dawowa gidan. Kwanan khadijah talatin da 'yan kai a gidan Umma ne ta fara fito da wani habit na bacci, ko me take yi sai ta fara bacci a kai, islamiyya ma idan taje duk bacci take, hakan yasa wani lkcn bata dadewa xata dawo gida, Umma da abun ya fara isarta ranan ta bar mata kaya ta linke tana shigowa taga tana bacci kan kayan, duka ta kai mata tace "Wai lafiyar ki kuwa Khadijah, wannan wani irin bacci ne?" Khadijah ta farka a firgice tana mitsika ido, Umma ta harareta tace "Tashi ki je kiyi sallah bana ma son linkin kuma, wani iskanci komai aka sa ki sai ki buge da bacci" mikewa khadijah tayi a hankali ta fita bayan ta dau butan Umma, Hasana dake tsakar gida ta cika gidan da radionta Shafah kuma na kitchen suka bita da harara a tare, babu abinda ke kona masu rai a gidan irin yanda Umma da khadijah ke kin kulasu a gidan, duk da ita Umma sun san ba banxa ba rashin kulawar, to ita khadijah fa, Hasana tace "Ohh daga Hutu dai sai kuma aka rashe" Shafah dake juya miyar ta na yakuwa dake kan wuta tace "Ke ma dai kya gani, dama yau nake son tambayar Alhaji dalilin da yasa xa a munafurce mu ayi mana karya, ai sai ace mana ta dawo nan din ne da xama ba wai a mayar da mu yara ba" Hasana tace "Yara ko dai shashashai, bari dai ya dawo din ma ji dalilin rainin hankalin" Khadijah dake durkushe kasa sai yamutse fuska take ta dalilin kamshin miyar Shafah da ya kauraye tsakar gidan, mikewa tayi da sauri jin cikinta na hautsinewa ta juya xata koma parlorn Umma taji amai ya taho mata, dawowa tayi ta durkushe wajen ta dinga kwarara amai Shafah da Hasana aka yi tsit daga mita da habaicin da suke suna kallonta. Fitowa Umma tayi da sauri jin kakarin aman khadijah, ta karaso da ita ta duka tace "Subhanallahi.... Are you okay" khadijah ta kasa cewa komai duk ta galabaita lkci daya, Umma ta taimaka mata ta wanke baki sannan ta dagota ta wuce parlorn ta da ita, Khadijah ta kwanta kan kujera tana mayar da numfashi da kyar tace "Umma I don't knw what's wrong with me, I am always week" Umma tace "Sannu, ko malaria ne, bari Alhaji ya dawo sai mu tafi asibiti ni bani da kudi a gu na" Khadijah ta lumshe ido har lkcn tana sauke ajiyar xuciya, mikewa Umma tayi ta fita don wanke gun aman, tana isa bakin kofa ta ji muryar Hasana tana cewa "Wllh fah, sai kace mai ciki, ji fa salon aman ma daban ne, idan ma malaria ne ba yellow shataf kalan aman ya kamata ya xama ba" Shafah tace "Haka fa shekaranjiya ina lura da ta shiga kitchen duba mata girki daga xama kan kujera sai bacci, daxu kuma da safe nan bakin kofa ta xauna da abinci a gabanta tayi bacci, ace baccin nan ba lafiya ne?" Umma dake tsaye bakin kofa har lkcn gabanta yyi mugun faduwa, fita tayi parlornta a fusace duk da ta fi wata uku bata tanka su a gidan tace "Sai dai ku ga ciki can kan 'ya yanku ko dangi, amma ba 'ya ta ba, tunda baku da kirki baku da Imani har ku yi ma yar mutum fatan wannan mugun abun, Allah ya isa wllh" Hawaye cike idonta ta kare maganar, Shafah ta mike tana huci ta kunduma mata xagi tace "Bakin ki ya sari danyen kashi, ba ma ga mugun abu ba a 'ya ya ko dangi, to wa yasan inda kika kai ta kwanki ko karuwanci kika sa tayi maki...." Umma ta juya ta koma daki hawaye na sakko mata sosai, kallon khadijah ta tsaya yi taga har tayi bacci, ta xauna duk jikinta a sanyaye a xuciyarta tana kara yi ma su Shafah Allah ya mayar masu mugun alkaba'in da suka yi ma 'yar ta. Har karfe tara Khadijah na bacci bata tashi ba, tada ta umma tayi hankalinta ya tashi jin irin xafin da jikinta ya dauka, da kyar ta lallabata ta sha shayi kadan sannan ta bata paracetamol ta rakata bedroom dinta ta kwanta ita ta dawo parlor ta xauna har lkcn xuciyarta ya kasa dawowa dai dai, khadijah ce ta fito da sauri daga dakin umma na tambayarta me ya faru amma ta fita waje tun kan ta karasa can gun kwararon ruwa ta dinga amai a tsakar gidan, Umma da ta bi bayanta ta tsaya tana kallonta, jin sound din aman yasa Hasana ta leko sai ga Shafah ma ta leko, Umma ta koma ta dauko buta, ta durkusa kusa da ita har ta gama sannan ta wanke mata baki suka koma ciki, sai shivering take cikin rawar murya tace "Umma ki rufe ni sanyin" Umma ta dauko duvet da sauri ta rufe ta, nan da nan kuma bacci ya dauketa. Umma ta koma parlor ta xauna duk ta rasa me ke damunta, jin shigowar Abban fadila gidan ta jira har ya shiga part dinsa da minti sha biyar sannan ta fita, sallama tayi bakin parlornsa ya amsa ta shiga, Shafah ce a parlorn tana xuba masa abinci shi kuma yana kallon news, Umma ta xauna ta gaishesa ya amsa, a hankali tace "Alhaji dama idan da hali don Allah kudi nake so ka ba mu xan kai khadijah asibiti bata da lafiya tun safe" Shafah tace "Ae gwara aje asibitin nan kam wannan amai da bacci haka a gida" Umma tayi shiru tana kallonta, Abban fadila yace "Nawa ne kudin asibitin?" Shafah tace "Tun da ya sanka likitan kamar family Dr ne ko dubu 3 ka basu xai yi ai" ita dai Umma bata ce komai ba, Ya mike ya shiga ciki sai ga shi ya fito da dubu hudu ya mika mata yace "Gashi sai ku yi har kudin mota" ta karba da ladabi tace "Toh mun gode sai da safe" daga haka ta mike ta bar parlorn. Washegari da sassafe Umma ta sa Khadijah ta shirya bayan ta tilasta ta shan shayin da ta hada mata amma tas ta amaye sa gaba daya, duk ta xabge tayi laushi lkci daya sbda aman da take yi, A dai dai ta umma ta samo masu har kofar gida ganin kamar baxata iya tafiyar ba ma, Hasana dake sharar tsakar gida tace "Toh a dawo lafiya dai, Allah raba bawa da jin kunyan duniya da lahira dai" Umma bata tanka ta ba tana rike da Khadijah suka fita, wani asibitin daban ba wanda suka saba xuwa Umma taje ba, suna xuwa aka ce sai sun yanki kati dubu biyu, duk jikin umma yyi sanyi, shiru khadijah dake xaune tayi tana kallon nurse din dake tsaye Kansu, nan ko tuna kudin da Aliyu ya bata take yana bayan kujeran umma ta ajiye bata kuma nuna ma umman ba har lkcn, Umma ta mike tace ma nurse din tana xuwa yanxu, Cike da karfin hali Khadijah tace "Umma ina xa ki?" Tace "Yanxun nan xan dawo khadijah" daga haka ta fita. Gidan wata kawarta dake layin ta tafi ta ranto dubu biyu da yake suna mutunci da matar sosai ta bata sannan umma ta dawo asibiti, bayan an yankar masu kati suka samu ganin likita, Umma ce ke fadin abubuwan da ke damun khadijah ma likitan, don Khadijahr duk tayi weak, tambayar farko da likitan ya jefo ma Umma shine "Tana da aure ne?" Gaban umma yyi mugun faduwa ta girgixa ma likitan kai kawai, likitan yace "Toh xa ayi mata test..." Bai dai fadi wanne ba umma tace "Toh" ya kira nurse ya bata file din nasu yace su bita, Umma na rike da hannun khadijah suka dawo reception, Nurse din tace kudin test din dubu biyu da dari biyar haka Umma ta bata duk ta yi wani sanyi, suna ta xaune a reception har bayan mintuna da dama result ya fito matar ta ce su je office din Dr bayan ta kai ma sa, Likitan dake ta kallon umma yace "Yar ki ce yarinyar nan?" Umma ta gyada masa kai xuciyarta na bugawa, ya girgixa kai yace "Sorry madam, She is few weeks pregnant" mikewa Umma tayi a mugun gigice tace "Pregnant Dr?" Likitan ya gyada mata kai, Khadijah da ta xaro ido ta dinga kallon likitan xuciyarta na bugawa, kuka sosai Umma ta saki a gun ta juya ta fita, khadijah ta mike ta bi bayanta da sauri, likitan ya girgixa kai ya bi ta da kallo a ransa yace why Such a beautiful girl, Gaba daya asibitin Umma ta fita har lkcn tana kuka, khadijah da duk jikinta ya mutu ta dinga bin ta ita ma, har lkcn ita dai bata gane wani pregnant din likitan ke nufi ba, adai daita Umma ta hau tayi wucewarta gida, Khadijah da tayi still a inda take ta bi adai daitan da kallo ta kasa kwakkwaran motsi, lkci daya duk ta nemi xaxxabin da rashin kwarin jikin dake tattare da ita ta rasa, har sannan kuma ta kasa kukan, tafiya ta fara yi kamar warce kwai ya fashe ma, da yake ba wani nisa ne da asibitin ba har ta isa gida, Hasana da Shafah na xaune tsakar gida ta wuce parlorn Ummanta suka bi ta da kallo, bata ga Umma a parlor ba a shiga bedroom dinta, xaune ta ganta nan kasan dakin banda kuka babu abinda take, ta sulale kasa a hankali sai a sannan wasu hawaye masu xafi suka dinga sauka idonta, Muryar Umma taji cikin kuka tana cewa "Khadijah yanxu ni xa ki kunyata, ni xa ki yi ma tonon asiri a idon duniya, is this my reward for taking you as a daughter?" Khadijah na shessheka tace "Ummata kiyi hakuri" mikewa Umma tayi da wani force ta sauke mata mari, bata gama recover ba ta kuma kai mata wanda ya fi na da, kasa kwakkwaran motsi khadijah tayi a inda take durkushe lkci daya taji komai ya tsaya mata, Umma na mata wani kallon da xa a iya kiransa da na tsana tace "Kin cuce ni kin ci amanata, kin ci amanar late mahaifinki" hakan da ta fada ya sa khadijah rushewa da kuka mai ban tausayi cikin rawar murya tace "Na shiga uku, don Allah Ummata ki yi hakuri" ta kuma kai mata wani marin tana kuka sosai tace "Uban waye yayi maki Ciki khadijah" kamar numfashinta xai dauke take kuka tana girgixa kai tace "Ban sani ba Ummaa" rufeta tayi da duka har sai da ta gaji don kanta ta kyaleta kuma har lkcn kuka take, cikin raunin murya tace "Tashi ki bar min gidana kije duk Inda xa ki je tunda baki san wanda yyi maki ciki ba, Allah ya isa tsakanina dake khadijah, kin bata min suna, ki tafi khadijah xaman ki gidan nan xai iya kashe min aure ki tafi bana son ganin ki kije duk Inda xa ki" gyada mata kai kawai khadijah take tana sheshsheka, shigowan su Shafah da Hasana dakin yasa Umma tayi shiru har lkcn tana kuka, suka gama kare masu kallo sai suka saki shewa sannan suka fita dakin, khadijah ta mike da kyar don banda ciwo babu abinda ko ina na jikinta ke mata ta fita dakin tana goge jinin bakinta, bayan kujera ta tafi ta dauki envelope din da Aliyu ya bata wasu hawaye masu xafi na xubo mata, xaxxage bundle din kudin tayi gaba daya a kasa sai ga wani farar takarda a linke ya fadi, ta dau takardar ta warware tana kallon content din, *I don't have much to say khadijah, na san har abada baxa ki mance abinda ya faru tsakaninmu ba kamar ynda nima baxan mance ba, tafiyar ki shine ma fi alkhairi sbda baxan taba samun kwanciyar hankali da nutsuwa ba matsawar muna gida daya, ina rokon gafarar ki Khadijah forgive me not because I deserve it but for the sake of Islam, Allah hada fiskokinmu a aljannatul fiddaus, ina maki fatan alkhairi a rayuwa da fatan miji na gari* cukuikuye takardar tayi ta fashe da wani kukan takaici taji dama ta kashe kanta ta huta amma bbu daman yin hakan, mayar da kudin tayi envelope din har ma da takardan ta mike ta fice parlorn tana share hawayen da ya ki tsaya mata, ko kadan bata ji me su Shafah ke cewa ba har ta fice gidan gaba daya, khadijah bata xarce ko ina ba sai tashar mota, tafiya kawai take a park din tana jin sunan garuruwan da ake fadi har ta isa gun motar garin Yobe ta hau bayan minti goma mota ta cika suka dau hanyar damaturu garin da bata san kowa ba bata taba xuwa ba. *What I want some people to get here is that, wnn labarin khadijah ne, kun riga da kun san rayuwarta a yanxu, she is living a normal life just dat abubuwa da yawa na memory dinta ne har ynxu, what I am writing now is her past ya riga ya wuce so I don't knw why wasun ku ke damun Kansu being emotional, this is not what is happening presently, it's just her past story* Da tsakar rana Khadijah suka iso garin damaturu, ta fito a hankali daga motar tana bin ko ina na park din da kallo, wani jiri ke dibar ta a lkcn ga sanyin da take ji ba kadan ba, tana tafiya a hankali har ta fita park din, kallon masu adai daitan dake ta tambayata Inda xata ta dinga yi lkci daya hawaye ya cika idonta, bata ce komai ba ta dinga tafiya, bata san iyakar lkcn da ta dauka tana tafiya ba, jin baxa iya ci gaba da tafiyar ba ta samu karkashin wani bishiya da ta hango duk anyi littering dinsa da 6awon rake ta xauna tana sauke numfashi a hankali, cikin Hijab dinta ta ajiye envelope din hannunta, bacci ne ya dauketa lkci daya a hakan saboda iskan da leaves din bishiyar ke ta bayar wa, bata san lkcn da ta dauka tana bacci ba hayaniyar wasu almajirai ya tada ta, ta gyara xamanta da sauri tana kalle kallen wajen envelope dinta a hannunta, a hankali ta tashi da kyar ta ci gaba da tafiya kamar bata son yi kwata kwata ko yunwa bata ji sai kasala, wannan karan ma tafiya me nisa tayi da kafa ganin wani masallaci ta dau buta dake cike da ruwa ta samu gefe ta xauna ta daura alwala sannan ta tafi jikin wani shago tayi sallahn da bata yi ba, mayar da butan tayi ta ci gaba da tafiya, har aka kira magrib tafiya kawai khadijah take, ganinta a wani kasuwa ta dinga xaga kasuwar, a hankali a hankali kasuwar ta fara watsewa ta shimfida dankwalinta gaban wani shago da aka duk aka rufe tayi magrib da isha ta jingina da table din gaban shagon, wasu hawaye suka dinga bin kuncinta, sanyi sosai ke shigarta ga xaxxabi kan kace me kasuwar yyi tsit kowa ya wuce gida, duk da uban sauron da suka yi yawa a wajen hakan bai hana bacci me nauyi sake daukarta daga xaunen da take a gaban shagon ba, bata kuma farka ba sai da kiran sallar asuba ya farkar da ita, ta dinga bin wajen da kallo, can ta tashi da kyar tana tafiya a hankali kamar iska xai hura ta ta fadi ga wani ciwon xuciya da ta tashi da, banda xugi da axaba bbu abinda yake mata, duk wnn abun sai lkcn taji yunwa na damunta sosai, masallaci me hade da na mata take ta nema amma duk iya tafiyar da tayi bata ga alamar ko daya ba, wani wajen ta samu ta xauna nmta hade kai da gwiwa tana kuka cike da rauni, har gari ya waye mutane suka fara hada hadarsu tana xaune Inda take, cike da karfin hali ta tashi ta nufi titi ta tsaya jiran adai daita, bbu bata lkci wani ya ja ya tsaya, ta shiga a hankali nace "Central mosque xaka kai ni" yace "Na ina?" Tace "Wanda ya fi kusa dai" ba wani tafiya me nisa suka yi ba yyi parking bayan mmsun iso kusa da wani babban masallaci, kudin dake jikinta har lkcn ta fiddo ta ciri dubu daya ta basa yace ba shi da canji, a hankali tace "Toh ka tafi" sannan ta shiga masallacin, bangaren mata ta nufa ta daura alwala bayan ta xaga bayi sannan nmta shiga cikin masallacin ta tada sllh, tana ta xaune bayan ta idar tayi nisa tunanin da take jin agogo yyi stucking karfe tara ta mike a hankali ta fita ta dau tsintsiya tana taya bayin Allahn dake ta sharan masallacin shara, suna gamawa ta fito da kudin ta don duba abinda xata siya ta ci, waina da miya ta siya da ruwa ta dawo cikin masallacin, a haraban ta xauna ta bude ledan abincin tana daukan guda ta kai baki taji cikinta ya hautsine, tayi saurin tashi ta nufi gun da ake alwala da gudu nan ta dinga amai a wajen kamar xata shide, da kyar ta tashi daga karshe duk jikinta ba kwari nmta koma cikin masallacin nmta kwanta ba tare da ta sake bin ta kan masan ba, tana mayar da numfashi, dukunkunewa tayi waje daya jin sanyi na shigarta ta ko ina, wanda hakan na da nasaba da xaxxabin da ya rufeta lkci daya, sai azahar ta farka jin ana kiran sllh. Daren ranan a masallacin khadijah ta kwana, amma washegari da safe wata dattijuwa dake share sharen masallaci tace ta nemi gun da xata dinga kwana daga ranan don masallaci ba wajen kwana bane da ace kwana ake barin mutane ke yi a ciki da bai yi kyan gani ba yanxu, cike da fada take maganan, jikin khadijah yyi sanyi sosai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, karfe sha dayan safiyan ta bar masallacin, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata a lkcn sbda yunwa ce kawai ke dawainiya da ita ga xaxxabi, ramar da tayi ya fito sosai, karfin hali ta dinga yi tana tafiya, tafiya kuma ba na wasa ba tayi ba tare da tasan takamaiman inda xata je ba, ganin she can't move any further don kafafuwarta sun ma Gmgaza daukar ta kuma ta fara tunanin xuwa wani masallacin ta kwanta, tana tsaye bakin titi tana jiran abun hawa da ta gaji sai ta tsugunna idan ta huta sai ta mike, kawai d'aga kai tayi ta ga wata mata da ta shiga titi da nufin tsallakawa wani mota da ya taho da uban gudu ya kwasheta sai da tayi sama da ita snn ta fado kan titin, duk da nesa da ita aka yi hatsarin amma irin ihun da ta fasa a tsorace xaka ce ita motar ta buge tsabar tsoratar da ta yi, daga nan kuma bata sake sanin abinda ya faru ba ta dai bude idonta da yyi mata nauyi ta ganta kwance wani daki da yyi kama da na asibiti da ruwa a hannunta, dafe xuciyarta dake mata xugi sosai tayi ta dinga bin dakin da ido a hankali lkci daya kuma tana son tuno abinda ya faru amma ta kasa, a hankali ta sauke idonta kan wani mutumi dake xaune d'an nesa da ita idanuwansa da hankalinsa gaba daya kan wayar dake hannunsa, duk da a xaune yake hakan bai boye tsayinsa ba, sajen dake kwance gefen fuskarsa kadai take gani da uban gashin da ya tara a kai, da dogon hancinsa duk ta side view take kallonsa, ta shiga kkrin mikewa xaune da kyar har lkcn tana dafe da xuciyarta dake mata axaba ba kadan ba wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, sai a nan ya kallo direction dinta, mikewa yyi da sauri ganin ta tashi ya karaso kusa da ita yace "Hello... how you feeling now?" kallon jajayen lebbensa kawai take don bata taba ganin haka ba, ya buda dara daran idanuwansa yace "Hey... Are you there?" Kin cewa komai tayi still, ya juya ya fita ba a dau lkci ba ya dawo likita na biye da shi, likitan ya tsaya kanta yace "Hi... How you feeling madam?" Ganin yanda duk suka tsura mata ido, ta sauke nata idon a hankali tace "Alhamdulillah" likitan yyi murmushi yace "Maa sha Allah, hope bbu Inda ke maki ciwo ynxu koh?" Ta gyada masa kai duk da axaban da xuciyarta ke ta yi matan, yace "Good" snn ya juya ya fita, kallon mutumin dake tsaye ya rungume hannayensa tayi cikin sanyin murya tace "Me nake yi a nan?" Sai a snn ya kalleta yace "Kar ki damu xa a sallame ki nan da anjima ki wuce gida, before then ki bani number 'yan gidanku a kirasu, sure they are all disturb yanxu, you passed out since in the morning... And this is...." Ta kalli agogo da sauri kafin ya fada taga karfe bakwai, ta kallesa tace "Bakwai na safe?" Ya girgixa kai yace "No, Night" shiru tayi bata sake cewa komai ba kamar me naxari, sai a sannan kuma ta tuno abinda ya faru daxu, ta fashe da matsanancin kuka tace "Wayyo matar ta mutu koh?" Hade rai yyi yace "Nooo, an kai ta asibiti ita ma, am sure she's recovering also" tsoro ne sosai tare da ita tana kallonsa, ya langwabar da kai yace "Ina xuwa" daga haka ya juya ya fita ta bi sa da ido, ko minti biyar bai yi da fita ba sai ga wata nurse da magunguna a leda, ta ajiye kan gado tana mata sannu tace "Idan kin samu abinda kika ci xan dawo in nuna maki dosage" daga haka ta fita. Da sallama ya shigo ward din rike da takeaway din abinci ya karaso ya ajiye kan table dake kusa da gadon yace "Ga shi ki ci abinci ki sha magani kafin a sallame ki...." Bata ce komai ba ya mika mata wayarsa yace "Before then, fara kiran mutanen gidan ku ki sanar da su kina asibiti" shiru tayi bayan ta karbi wayar, ya fada mata sunan asibitin sannan ya fita, hawaye ya cika idonta ta saki kuka a hankali tana tausayin kanta, bayan kusan minti goma ya dawo dakin... kallonta yyi sannan ya kalli abincin ya d'an daure fuska sai kuma ya karaso ya bude ya sa cokali ya mika mata ba musu ta karba tana kallon jollof rice da naman, yace "Kin kira su?" Gyada masa kai tayi yace "They are coming to take you now right?" Nan ma kai kawai ta gyada masa, yace "Alryt, ki ci abincin nurse xata shigo ta nuna maki dosage din maganin yanxu, I've paid the bill, Allah kiyaye gaba I will be on my way now..." Kai kawai ta gyada masa tana iya kokarin ganin bata bar hawayen dake taruwa idonta ya xubo ba a hankali tace "Nagode" ya buda ido sosai yace "No thanks" ta lura sauri yake don tuni har ya kai kofa, ta kalli wayarsa dake gefenta a hankali tace "Your phone" ya juyo da sauri yace "Ohh thanks har na mance" daga haka ya dau wayarsa ya fita ward din, ta rufe abincin ta ajiye ta hade kanta da gwiwa hawaye mai xafi na sakko mata, bayan kusan minti goma da tafiyarsa nurse din daxu ta dawo, da sauri ta goge hawayenta, nurse din tace "Kin ci abincin koh?" A hankali khadijah tace "Na ci" nan ta nuna mata dosage din drugs din sannan tace "Sai ki sha yanxu, an riga an sallame ki, yace yan uwanki na hanya koh?" Ta gyada mata kai tace "Toh Allah ya kawo su lfya" daga haka ta fita, ta fashe da matsanancin kuka xuciyarta na mata kuna, sai a snn envelope din kudin dake hannunta da ta fadi ya fado mata, bata wani damu ba don tasan me rabo ya dauke shikenan kuma, bayan wani minti ashirin din nurse din ta shigo tana mata wani kallo tace "Wai har ynxu ba su iso ba yan uwan naki?" Tana kallonta a sanyaye ta gyada mata kai kawai, nurse din ta tabe baki ta juya ta fita, taa ta xaune ta rasa me ke mata dadi har lkcn kanta na bisa gwiwanta nurse din ta shigo da likitan daxu, likitan yace "Ke daga wani garin yan uwanki xa su xo ne har yanxu basu iso ba, ko karya kawai kike ma mutane?" Hawaye cike idonta cikin rawar murya tace "Ehh" ya xare glass din idonsa yana xaro idon yace "Karyan kike?" Ta fashe da kuka a hankali tace "Ni bani da yan uwa, ban san kowa ba, ban san ina xan je ba" a mugun fusace yace "You must be joking, Look malama fita ki bar ma mutane asibitin su, get out yanxun nan, maxa dau sauran abincin ki ki fita kar in kira masu gadi su yi waje da ke" jikinta na rawa ta sakko ta dau abincin da yace tana jin kamar jiri xai kada ta hawaye na sakko mata sosai ta nufi kofa, nurse din ta bi ta da kallo, murya can kasa tace "Dr ko xaka kira shi wanda ya kawo ta tun da kasan shi?" ya jefa mata wani kallo yace "Toh me xai yi mata idan na kira sa, sanin wacece ita yayi aka gaya maki? He just helped her tayi collapsing a gefen titi daga anyi hatsari" khadijah ta bude kofa xata fita likitan yace "Tsaya malama" tsayawa tayi ta juyo tana kallonsa a tsorace, ya ciro wayar sa a lab coat din jikinsa yyi danne dannensa kafin ya sa hands free wayar ya fara ring, sae da ya kusa katsewa aka daga, likitan ya ce "Sudais, ga patient din da ka kawo mana taki tafiya fa...." daga daya bangaren aka ce "I don't get you" a d'an fusace likitan yace "I also didn't get what she meant by saying she don't have relatives and she don't knw where she's heading, don Allah ka xo ka fidda min ita a asibiti plss" Wanda ya kira da Sudais cikin expression din mamaki yace "Ji min walakanci fa, toh ni da ka kira ni me xan yi? If I am not mistaken I told you I don't knw her Yusuf, then why calling me? Me yasa kake kirana? Wait wllh sai ka gaya min me yasa ka kirani ma dai, are you not just suppose to tell her to leave kayi discharge dinta???" Likitan ya kalle Khadijah a fusace yace "Ke malama maxa nemi Inda dare yyi maki kada in sa a xo a fitar da ke yanxun nn, get out plss" kai ta gyada masa jikinta na rawa hawaye na sakko mata, Da sauri Sudais din yace "Wait Yusuf, you knw what? kaga dare yyi ynxu ka bari gobe da sassafe kace ta wuce plss since she's lying she don't have relative" likitan yace "Sai dai idan xata sake biyan kudin gado, don da ace haka ake yi a clinic din da ba mu samu ci gaba ba" Shiru Sudais ya d'an yi kafin yace "Toh naji xan biya ka, though I hate lies and liars let her just be safe there kafin ta wuce gobe, just dat 1st thing tomorrow morning send her away, good nyt" daga haka ya watse wayar, ko kallonta likitan bai yi ba yace "Bani hanya" ta bar bakin kofar da sauri yyi ficewarsa kamar xai tashi sama, Nurse din ta karaso kusa da ita tace "Me yasa kika yi karya yan mata, ke ba musulma bace?" Khadijah ta girgixa mata kai hawaye mai xafi na xubo mata, nurse din ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh tafi ki kwanta" daga haka ta fita ta bar ta tsaye, karasawa tayi kan gadon ta kwanta tana share hawayenta, wajajen karfe sha biyu ta tashi xaune jin yunwa na nemanmatat illa ta bude abincin daxu, amai ne ya taho mata bayan ta kai baki ta sauka kan gadon da sauri ta shiga bayi ta dinga amai kamar xata amaye hanjinta, jikinta a mace ta fito ta kwanta bisa gado tana sauke ajiyar xuciya ta kudundune waje daya daga haka bacci ya dauketa sanyi na shiga jikinta. Kasa tashi sallan asuba Khadijah tayi washegari ta dalilin xaxxabin da ya rufe ta, jin an bude kofar ward din ta bude idanuwanta a hnkli taga gari ya waye sosai, likitan da mutumin jiya da ya kira da Sudais suka shigo ward din a tare, tun daga bakin kofa sudais dake sanye da milk jallabiya ke mata wani kallo har karaso gadon yace "jiya da na baki waya wa nace ki kira?" Khadijah ta mike xaune da kyar ganin ynda ya hade rai ta marairaice tace "Relatives dina" ya kara hade giran sama da ta kasa yace "Then why didn't you call dem?" cikin rawar murya tace "I don't have anybody to call, ni marainiya ce, my father is late so also is my mum, My step mum....." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai, cikin tsawa yace "Karya kike yi, shut ur mouth plss" likitan dai rungume hannu kawai yyi yana kallona yana murmushi, ta hade kai da gado tana kuka cikin rawar murya tace "ku yarda dani don Allah, wallahi ni bana karya, laifi nayi ma step mum dita tace min in bar mata gidanta, I love my step mum and she loves me same, but tace in tafi sbda laifin da nayi, she raised me up as a mother even after my late dad passed away 5 years back, don Allah kada ku ce in tafi ban san kowa ba a garin nan ban taba xuwa ba, ku taimakeni ku kaini gidan marayu in dinga kula da yaran wajen don Allah" tsawa likitan yyi mata da ya firgitata ta dago da sauri, yace "You are mad, wa xa ki raina ma wayo, ni ko wannan da ke kusa dake?" Ya fadi hakan yana nuna sudais, Shiru tayi tana kallonsa, kafa mata ido shi ma yyi, can ya karaso kusa da ita yana kallon kwayar idonta da kyau, ya kai hannunsa ya bude eye lids dinta, can ya kalli fingers dinta sai kuma ya kalli Sudais dake tsaye, daga kafada yyi ya nufi kofa yace "I have better patients to attend to Sudais..." daga haka yyi ficewar sa daga cikin ward din, a sanyaye khadijah ta kalli Sudais dake mata wani kallo yana rungume da hannunsa, harara ya watsa mata bayan mun hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, muryarsa ya daki ear drum dinta, "Wani laifin kika yi ma mum din taki, kuma daga wani gari kike? Kina min karya xan gane kuma daga nan station xan kai ki" Shiru tayi tana kallonsa hawaye na ci gaba da sakko mata, cikin sanyin murya tace "Daga kano na xo" yace "Wato kin saba tafiya garruruwa kenan ko" ta girgixa kai da sauri tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba tace "Wallahi A'a" yace "Toh wani laifin kika yi mata?" Share hawayen idonta ta shiga yi a hankali ta hadiye wani abu da ya tsaya mata, can ta sakar masa kuka tace "Kilan baxa ka min taimakon da nace ka min ba idan ka ji dalilin bari na gida" strictly yace "Malama ki bude baki ki gaya min, stop wasting my time xan je aiki" jinginar da kai tayi da gadon ward din tace, "Duk abinda xan fada maka ka yarda dani sbda Allah, ni bana karya, I knw d consequence of it.... Domin ka min taimakon da nace ka kai ni orphanage yasa xan fada maka ni wacece" Bai tanka ta ba hakan yasa a hankali tace "I lost my mum at a very tender age, and my beloved last year" ta kallesa taga he is listening but not looking toward her direction, ta lumshe ido, a haka ta fara basa labarinta tun daga farko har xuwa yanxu da yake gabanta, bbu abinda ta boye ma Sudais, Kallonsa tayi a karo na farko tun da ta fara gaya masa ita wacece, hawaye masu xafi suka shiga xubo mata, Sudais ya dinga kallonta da wani expression da ta kasa fassarawa a fuskarsa, tana girgixa kai a raunane tace "I told you all but the blank truth about me, believe me plss" kasa ce min komai yyi sai bayan kusan minti biyu yana nuna ni da yatsa da wani irin mamaki yace "You mean... You are pregnant?" Ta gyada masa kai a hankali tace "That's what the Dr told me and my step mum" Jinginar da kansa yyi jikin bango yana kallon saman ward din ko kiftawa bbu, bai kuma ce min komai ba har na kusan minti uku, Khadijah dai sai kallonsa take don bata san tunanin da yake a xuciyarsa ba domin kuwa duk wanda ya gan sa yasan yyi nisa tunanin da yake, bude kofar aka yi duk suka kalli kofa, Dr Yusuf ya shigo yana kallonsa da kyau yace "Ya? Ka gama sauraren karyar ta Malam?" Sudais bai ce komai ba ya shiga shafa uban gashin dake kansa, likitan yyi murmushi yace "Very good then, naga kamar har karyar tayi tasiri a xuciyar ka" Likitan ya karasa kusa da khadijah yana kallonta da kyau yace "Are you married?" Shiru tayi tana kallonsa ko kiftawa bbu, wani murmushin ya sake yi ya kalli Sudais, Sudais ya lumshe manyan idonsa ya bude su a hankali yace "Yea xaka cire mata cikin soon as possible....." Wani kallo Dr Yusuf ke yi masa, Sudais ya dafa kafadarsa yace "Yeah... She told me about d pregnancy, an illegal one at it's early stage, i think you just have to flush it Yusuuf, I will pay what ever amount it will take" tunda ya fara magana khadijah ke kallonsa baki bude, can ta fashe da kuka tace "Noo plss, it's illegal but it doesn't deserve that, Allah xai yi fushi da ni, baxan iya ba..." wani mugun kallo Sudais ke mata ya karaso kusa da ita cikin tsawa yace "You are very very stupid, shegen xaki haifa?" Ta kuma rushewa da kuka tace "Eh, saboda Allah ne ya bani, kuma it's not my fault it came this way, beside soul din ba shi da laifi da har xan xubar da shi..." Yusuf ya rungume hannu yana kallonta, Sudais ma wani kallo yake mata lkci daya yana mamakin furucinta cos she look young to think that way, ya matsa dab da ita yace "Then ya xama dole ki koma gidansu Aliyu kika kirasa ko wa???" Khadijah tayi shiru tana kallonsa hawaye na xubo mata, ido ya kafeta da shi yana jiran jin abinda xata ce, ta sauke idonta a hankali tace "Toh me xan ce masu?" Strictly yace "Abinda likita ya gaya ma ke da Ummar ki" tana share hawayenta tace "Toh amma ni yanxu bani da kudin mota" yace "Xan baki" juyawa likitan yyi ya fita, shi ma ya nufi kofa kafin ya fita ya juyo ya kalleta yace "Ki sameni reception yanxu" daga haka ya fita, ta sakko a hankali ta dafe gado jin jiri, da kyar ta karasa reception din sbda jirin dake debanta tana isa ta xauna kan kujera ganin baya gun, office din Dr Yusuf sudais ya shiga, Dr Yusuf yace "What are you trying to do Sudais?" Sudais ya shafa kansa a hankali ya xauna kan table dinsa yace "I don't really knw Yusuf, kawai nayi analyzing naga babu karya a labarinta, I tried hard to figure out...." Yusuf ya katse sa da sauri yace "Da alama lauyancin ka bai fada maka gaskiya ba yau, look at you... sau nawa muke ganin cases irin wannan, tayi ciki ta gudu ta bar gida ta xo nan ta shirga maka karya a matsayin ka na barrister har karyar yyi sinking kan ka? Don't let me call u a disgrace to ur profession..." Sudais ya girgixa kai yace "Babu karya a xancen da ta min, and profession dina yasa nayi figuring din hakan, she told me nothing but the truth" Dr Yusuf yace "Toh naji gaskiya ta fada maka, what do you intend doing now?" Shiru Sudais yyi yana kallonsa, can ya dauke kai cikin damuwa yace "I don't knw frnd, I have never being confuse like this all my life, Yusuf just look at her, she is too young, baxa ta wuce sa'ar Rabi'ah ba, had I known wllh da ban tsaya a motata ba jiya" Dr Yusuf yace "Toh ko gidanku xaka kai ta" sauka Sudais yyi da sauri daga kan table din yana xaro manyan idanuwansa yace "Gun wa Yusuf?" Yusuf yyi dariya yace "Mami wai da" Sudais yace "Mami ta kashe ni kenan, cewa ma xata yi ni nayi ma yarinyar cikin, kai ma kasan ko hauka na fara baxan fara kai ta hanyar gidanmu ba, what for?" Yusuf dai sai dariya yake sanin wacece mahaifiyar sudais, Sudais ya tabe baki yace "Wani lkcn ma d'an Adam na xaman xamansa yake dauko ma kansa matsala da kansa a rayuwa if nt meye haka na sa kai na ciki??" Yusuf yace "Kawai ka ka ita orphanage din da tace xai fi" Sudais yace "In dai kai ta can gidan su dan iskan da yyi mata cikin" Yusuf yace "Wa yaga bata lkci" Sudais ya nufi kofa yace "Muyi waya frnd" Mikewa Yusuf yyi ya bi sa suka fita. Ba tare da Sudais ya kalli khadijah dake ta xaune duk ta gaji a reception ba yace "Mu je" mikewa tayi a hankali ta bi bayansa, gun motarsa dake parking space ya nufa, ya bude ya shiga, ganin bata shiga ba Yusuf yace "sai ki shiga" a hankali ta kai hannu ta bude motar ta shiga, Sudais na kallon Yusuf yace "I will give you a call" Yusuf yace "Alright then" daga haka ya ja motar muka bar asibitin, bbu wanda yace komai cikinsu, yyi driving din kusan minti sha biyar suka iso wani anguwar masu kudi, nesa da gidansu Sudais yayi parking, ba tare da ya kalleta ba yace "I will be right back" daga haka ya fita ya fara tafiya, tafiyarsa kadai ma abun kallo ne, ya wuce gidaje kusan hudu kafin ya xo na su, Mahaifiyarsa Mami ce xaune parlor da wata bakuwa da tayi, ya karasa ya gaishesu da ladabi, bakuwar ta amsa da fara'a tace "Wannan uban gashin da aka bari fa Barrister, sai kace a turai" Ya kirkiri murmushi yace "Sunna ce...." Katsesa Maminsa tayi fuska daure tace "A hakan da ka bar shi irin na wa ends basu da mafadi, am very serious kada ka shigo min gida anjima baka asks gashin nan ba, ka jira idan ka koma UK din sai ka kara barin gashin, wnn iskancin kam ba a gidana ba" kansa a kasa yace "Toh Mami" daga haka ya mike ya wuce bedroom dinsa, press ya bude ya fiddo wani makulli ya sa aljihu sannan ya fito yayi masu sallama ya fita, bacci ya tadda khadijah ke yi, dauke idonsa kanta yyi ya tada motar ya bar layin, tafiyar wani minti sha biyar din yyi ya isa wani anguwar daban yyi parking a gaban wani gida, ana ganin gidan ansan sabon gini ne, ya fita ya bude gate din gidan da makulli sannan ya dawo ya ja motar ciki yyi parking ya fita ya koma ya rufe gate din, tuni khadijah ta bude ido tana bin gidan da kallo, dawowa yyi yace "Come down" ba musu ta fito, tafiya ya fara yi xuwa entrance din main house din ganin haka ta bi bayansa sai dai gabanta faduwa yake kawai, ya sa makulli ya bude kofar shiga parlorn ya shiga, kasa shiga tayi tana lekan parlorn, ya juyo yana kallonta, hawaye ne cike idonta, wani kallo yyi mata ya shiga parlorn ya bar wajen, a hankali ta taka ta bi bayansa, tuni ya wuce bedroom ita kuma ta xauna nan kan kujera a parlorn, bayan wani lkci ya fito yace "Ki shiga ciki kiyi wanka, xan fita in dawo yanxu" daga haka ya fita ya rufe kofar, tashi tayi da kyar ta shiga dakin da ya fito, towel ta gani kan gado sai sabulu ta karasa ta dauke su ta bude kofar da take tunanin na bayi ne ta shiga taga har ya hada mata ruwa me dumi, wanke bakin ta ta fara yi da mouth wash, bayan kusan minti ashirin ta fito daga bayin da kayan da ta cire a bucket ta wanke, sai taji ta samu karfi jikinta, hijab kadai ne da bata wanke ba ta daura kan towel din jikinta sannan ta fito parlor, wani kofar dake parlor ta shiga taga kitchen ne, ta dauko sweeper da mop ganin gidan is very dusty, tun daga dakin da tayi wanka ta fara gyaran ta fito har parlor duk da sanyin da take ji sosai, tana goge goge a durkushe ya shigo parlorn ya ajiye ledojin hannusa ba tare da ya kalleta ba yace "I didn't tell you to do anything madam, ga kaya nan ki shiga ciki ki canxa ki fito yanxu" ta mike tsaye tace "Toh nagode" bai tanka ta ba ta dau ledan ta shiga dakin, dogayen riguna ne na kanti da undies sai Hijab biyu da perfumes, cikin lkci kankani ta gama shiryawa ta fito parlorn, xaune yake ya tallabi chin dinsa da hannu biyu yayi nisa tunanin da yake, why is he involving him self in such case ya fa san daga irin gidan da ya fito ya san waye iyayensa, jin ta fito tun da ya kalleta sau da ya bai sake kallonta ba har ta iso nesa da shi ta durkusa tace "Na sa kayan" ledan abinci ya nuna mata yace "Breakfast" ta mike ta isa gun ledan ta bude, a hankali ta ja baya tana rike numfashinta sbda aroma din abinci, Fried Irish ne da soyayyen kwai da plantain sai ketchup, yace "You can go to the kitchen and make a cup of tea for ur self" kai kawai ta gyada masa, ta mike ta shiga kitchen din tana fatan ta iya shan shayin, ta gama hadowa ta fito, ganin kallonta yake bayan ta ajiye shayin ta dau Irish daya a hankali ta kai ba ki, ji tayi cikinta ya fara hautsinewa tun kafin ta fara taunawa, ta dau shayin ta kai baki da sauri don ta kora, tana sha tayi saurin ajiye cup din da sauri ta shige dakin da tayi wanka tun kafin ta karasa cikin bathroom din aman ya xubo mata, tun da ta fara amai sai yau tayi Wanda ya galabaitar da ita don bbu komai cikina, ta kasa motsi wajen duk jikinta ya mutu, ganin shadow dinsa ta juyo hawaye kwance fuskarta, tausayi karara ta gani a kwayar idonsa, yyi saurin dauke kai murya can kasa yace "Sorry" daga haka ya shiga bayin ya debo mata ruwa ta wanke bakinta ya xuba ruwa wajen, kasa tashi tayi ta jingina da bango, ganin jira yake ta tashi, ta runtse ido tayi karfin halin tashi bata xarce ko ina ba sai kan gado ta fada kai tana mayar da numfashi, ya karaso yace "Toh me xa ki ci yanxu" kai kawai ta iya girgixa masa, yyi jim yana kallonta kafin ya juya ya fita a koma parlor, xaunawa yyi yana tunanin how many hours will take them to kaduna. Tashi sudais yyi daga karshe ya koma daki, ganin yanda ta dukunkune waje daya ya isa gadon a hankali yace "Are you cold" bata amsa ba don idonta a rufe suke, ya dauko duvet ya rufe ta da shi, murya can kasa tace " thank you" ya tsaya yana kallonta don har sannan bata bude idon ba, juyawa yyi ya fita ya bar dakin ya tafi balcony ya xauna ya tsura ma motarsa dake parking space ido, tsoronsa daya mami hakan kuma yasa har lkcn xuciyarsa ke contemplating kan Khadijah, but is he that heartless after all, mikewa yyi daga karshe tunawa da yyi ko wanka bai yi ba gashi an kusa azahar, har ya kusa motarsa sai kuma ya tsaya, but can he go and leave her all alone here, bayan kusan minti biyu ya shiga gidan ya wuce bedroom ya ganta a kasa tana kakarin amai, tsaye yyi bakin kofar yana kallonta, ta fashe da kuka tana mai da numfashi, wayarsa ya fiddo a aljihunsa ya fita, bayan kusan minti sha biyar ya dawo dakin Yusuf na biye da shi a baya, bude ido tayi a hankali daga kwancen da take a kasa, Jin hannu a forehead dinta taga Dr Yusuf tsaye kanta sudais na daga gefensa, Dr Yusuf yace "Sorry, ya kike jin jikin ki..." Bata iya tace komai ba don ji tayi bakinta ya mata nauyi, yace "Me kike son ci yanxu?" Ta girgixa masa kai a hankali, ya kalli Sudais dake rungume da hannunsa yace "Try making a cup of tea with just milo for her pls" Sudais ya juya ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo da cup din warm milo, Yusuf ne ya dinga forcing dinta ta shan tea din, cikin rawar murya hawaye na sakko mata tace "Wllh xai sa ni amai" Yusuf yace "Kadan xa ki sha" da ta kurbi kadan xata ajiye ta koma ta kwanta Yusuf xai hanata, sai da tayi rabin cup din sannan ya kyaleta ta ajiye ta kwanta tana sauke ajiyar xuciya, bata san sanda karfi ya xo mata ba lkci daya ta tashi duk sai da ta kwarare shayin nan kasan tiles, Sudais dake tsaye ya juya a hankali, can ya sake juyowa, ganin yanda Yusuf ya tsaya kallonta ya duka yace "Tashi ki je bayi ki wanke bakin ki" dafa gado tayi ta mike tana ganin jiri ta shiga bayin, Sudais ya shiga gyara gun aman, komawa gefen gado Yusuf yyi ya xauna ya shiga hada drips da injections, kwanciya tayi bayan ta fito, sai da yyi mata alluran sannan ya sa mata ruwan drip din, tsabar xaxxabi bata ji xafin syringe ba a lkcn, ya lulluba ta da bargo suka fita shi da Sudais dake ta tsaye. Khadijah bata san irin baccin da tayi ba ta dai bude ido taga dim light ne a dakin alamar wai dare yyi ta kalli drip din hannunta taga kamar sabo ne, cike da karfin hali ta mike xaune, ta fi minti goma xaune aka bude kofar dakin, Sudais ya shigo ya kunna wuta yana kallonta yace "Kin tashi?" Kai ta gyada masa, ya karaso yace "How are you feeling now?" A hankali tace "Da sauki" Yace "what did you want to eat?" Murya can kasa tace "Sallah xanyi" yace "Sallah?" Ta gyada masa kai, ya kalli ruwan hannunta, karasowa yyi ya cire mata tube din jikin alluran yace "But be careful kar ruwa ya shiga ciki" ta gyada masa kai, kasa mikewa tsaye tayi da farko don gani take xata iya faduwa, yace "Baxa ki iya ba?" Da kyar ta mike cike da karfin hali ta shiga bayin, ta kama ruwa ta dauro alwala ta fito, taga har ya shimfida mata darduma ya ajiye mata hijab ya fita, tun tana sllhn a tsaye har ta kasa ta fara yi a xaune, sai bayan da ta idar ya shigo dakin yana tsaye daga bakin kofa yace "Me xa ki ci?" Tayi shiru don a lkcn bbu abinda ke ranta bnda danwaken da Kyauta ta taba yi ranan a can gidan, ganin taki cewa komai ya karaso yace "Ki fadi abinda kike so xan je in siyo ynxu" ta kallesa kafin ta sauke idonta a hankali, yace "What did you want" murya can kasa tace "Danwake, amma tunda dare yyi kawai ka bar sa" tsaye yyi na d'an lkci kafin ya juya bai ce komai ba ya nufi kofa, har ya bude kofar xai fita ya juyo yace "But.... I don't knw ur name" tana kallonsa a hankali tace "Khadijah...." Ganin yanda yake kallonta tace "Khadijah Muhammad" ya gyada kai yace "I will call you... Iman.... Cos you have the name of My mum" daga haka ya fita, ji gayi komai ya tsaya mata a lkcn, taji kamar ya fama mata wani ciwo ne a xuciyarta, har ya dawo kuma bata daina kukan da take ba kamar ranta xae fita, lkci daya hankalinsa ya tashi bayan ya ajiye warmer din danwaken, da damuwa yace "Me ya faru, why r u crying" cikin rawar murya tace "Don't call me Iman plss don't bana so" da mugun mamaki yake kallonta, can a hankali yace "Ohk I won't" daga haka ya bude warmer din ya xuba mata danwaken a plate yana kallonta yace "Manja ko Man gyada?" Tayi shiru tana goge hawayen idonta, can a hankali tace "Man gyada" xuba mata yyi kadan, ya ajiye abincin da yajinsa a gabanta, bata iya ta ci da yajin ba, haka ta dinga ci gaya ko maggi bbu, gani take idan ta sa yajin xata yi amai, ba laifi ta ci me yawa, amma ta kasa shan ruwan da ya kawo mata, shi dai yana ta tsaye dakin yana danna waya lkci lkci yana kallonta, ganin bata sha ruwan ba yace "Why didn't you drink d water" a hankali tace "amai, amma kila idan na sha mai xafi baxan yi ba," wani kallo ya fara yi mata kafin ya tabe baki ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo da ruwan dumi, cikin ikon Allah kuma bata yi aman ba da ta sha, sai da ya sa ta wanke baki snn ya maida mata drip din, tana kallonsa bata san lkcn da tace "Are you a doctor?" ya girgixa kai ba tare da ya kalleta ba yace "I am nt, but a lot of my frnds are" Komawa baya yyi bayan ya gama yace "Did you need anything, I mean anything?" Ta girgixa masa kai, xai yi magana wayarsa ta fara ring, ya dauka yana kallon screen din da sauri, gefen gado ya koma ya xauna ya daga ya kai kunne a hankali yace "Mami am on my way now, na tsaya yin wani abu ne, but nan da few minutes xan iso, Ki yi hakuri...." Sai bayan da ya mayar da wayar aljihu yace "Am going home now, anjima kadan Yusuf xai turo nurse da xa ta tsaya dake, she's on her way now" a hankali Khadijah tace "Toh na gode" yace "No thanks" daga haka ya fita ya rufo mata kofar. Ko minti sha biyar bai yi da fita ba aka bude kofar dakin wata mata da baxata wuce 30 ba ta shigo dakin, ta karaso kusa da khadijah tace "Sannu ya jikin ki" ta gaisheta don ta gane ta tace da sauki, nurse din tace "Ba kya bukatar komai koh?" Khadijah ta gyada mata kai, tace "Toh ki kwanta kiyi bacci, Allah ya kara lfya" ba musu ta koma ta kwanta, nurse din ta juya ta fita, duk khadijah ta bude ido cikin dare sai ta ganta coincidentally ta shigo duba ruwan dake makale hannunta, duk da drip din kuma hakan bai hanata dinga jin xaxxabi sosai ba, sai kusan asuba ta cire mata drip din bayan ya kare, ta samu da kyar ta shiga bathroom, baki ta wanke tayi wanka ta dauro alwala ta fito, duk yanda ta so yin sllh a tsaye kasawa tayi don jiri ne ke dibanta sosai ga rawan sanyi da take, daga karshe tayi a xaune ta kwanta nan kan darduma, ji tayi ana tada ta ta bude ido da kyar taga nurse din ce, tace "Kin yi wanka ne?" Khadijah ta gyada mata kai, nurse din tace "Da ruwan sanyi?" Girgixa mata kai khadijah tayi tace "Akwai ruwan xafi a heater" nurse din tace "To tashi ki koma kan gado" da taimakonta khadijah ta koma kan gadon ta kwanta ta lullubeta ta fita. Takwas saura taji hannu forehead dinta ta bude ido da sauri, Dr Yusuf ta gani tsaye kanta yace "How are you feeling?" Ta tashi xaune tana gyara hijab dinta tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau, ya jikin?" Ta sunkuyar da kai tace "Da sauki" ya kalli nurse din yace "She is having a running temperature" nurse din tace "Eh tun da tayi wanka da asuba" ya kalli khadijah yace "Da ruwan sanyi kika yi wankan?" Ta girgixa masa kai, ya kalli nurse din yace "Je ki bude mota akwai drips da injections da na taho da su daga clinic" tace "Ohk sir" daga haka ta fita, d'aga kai khadijah tayi taga kallonta yake, ya dauke idonsa yana girgixa kai ya nufi window ya dage curtains din yana kallon waje, bude kofa aka yi Sudais ya shigo da sallama, kananun kaya ne jikinsa lkci daya kamshin turarensa ya cika ko ina na dakin, a hankali cikin dubara ta toshe hancinta, Tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba ya nufi gun Dr Yusuf, bayan sun gaisa Yusuf yace "Ya su Mami" Sudais yace "They r ol fyn, amma daga clinic kake" Yusuf ya girgixa kai yace "No, yanxu dai xan je clinic din" Sudais yace "ohk how is she feeling now" kafin Yusuf yace komai ya nufo ta yana kallonta yace "Kin tashi lafiya?" Khadijah da har lkcn ta rufe hancinta tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau, why are you uncomfortable" ta girgixa kai a hankali tana yamutse fuska tace "The perfume" kallon Yusuf yyi ya tabe baki, Nurse ta shigo da abinda Yusuf ya aiketa ta dauko, gaida sudais tayi ya amsa duk da sun gaisa a waje, Sudais ya maida dubansa kan Khadijah yace "Toh me xa ki ci" girgixa masa kai tayi tace "Bana jin yunwa yanxu" Yace "But you need to take something" shayi yasa Nurse ta hado mata mara xafi, ganin Cup din shayin kadai ya dinga tada mata xuciya har da hawayenta, hankali tashe tace "I said am nt hungry plss" Yusuf dai na tsaye kusa da window yana kallon su, Sudais ya karbi shayin ya hade rai ya mika mata yace "Collect it now, ina ruwan wani da rashin jin yunwar ki" Karba tayi ta runtse ido ta rike breath dinta ta kai baki amma ta ki sha, can ta bude ido a hankali tana kallon sa kamar xata yi kuka, taga yanda ya hade rai yana kallonta, kauda fuskarta tayi tace "Don Allah kayi hakuri Allah baxan iya sha ba amai xan yi" yace "Sha kiyi aman" bata ce komai ba kuma bata sha ba, ta kalli Yussuf taga ya rungume hannu yana kallon su kawai, Nurse din tace "Ki daure ki sha kin ji yan mata" runtse ido ta kara yi bata ce mata komai ba, wani tsawa da ya tsorata ta Sudais ya mata yace "Wa kike tunanin xaki dinga ba wahala" bata san lkcn da ta kai shayin baki ba ta kurba, sauka tayi daga kan gadon da sauri jin amai ya taho mata nurse din tayi saurin karban Cup din hannunta ta ajiye, ta shiga bayi tana amai, ita ta taimaka mata ta gyara jikinta ta cire mata hijab ta wanke gun sannan suka fito tana rike da hannunta, bin su Sudais yyi da kallo har ta xaunar da khadijah gefen gado ta kwanta tana maida numfashi, Shi dai Yusuf har lkcn bai ce komai ba, ya karasa gun da nurse din ta ajiye ruwan drip din ya dauka ya fara hadawa, ita ya bar ma ta sa mata sannan ya kalli Sudais yace "Barrister.... I will be on my way now" Sudais ya bi bayansa suka fita. Xa a iya cewa kusan a gidan Sudais ya wuni ranan don da ya fita xai dawo, Nurse din kuma karfe sha biyu ta wuce, duk shigowar da xai yi daki kuma sai Khadijah ta farka daga baccin da take, wani lkcn ya mata sannu, wani lkcn kuma kawai ya juya ya fita. Tun bayan awaran da ta sa ya siyo mata ta samu ta ci kadan bata sake yarda ta ci komai ba don shi dinma damunta yake tayi gashi ta kasa yin aman, Karfe shidda saura ta bude ido jin budewar kofar, shi da Yusuf suka shigo, Yusuf ya mata ya jiki, ta gaishesa, Sudais na kallonta yace "I think Gobe xa mu je can Kaduna..." Sai a snn ta kallesa hnkli tace "Toh" Yusuf yace "Why nt ka bari ta fara samun Lafiya, she's so sick" Sudais ya nufi kofa yace "Noo, she's leaving tomorrow, for how long am I going to keep her here?" sai kuma ya juyo yace "Or is she going to stay here for ever? You knw presently I will be bringing a woman in here...." Daga haka ya fita, Yusuf ya bi sa da ido, can ya kalle Khadijah yace "What's ur name?" A hankali tace "Khadijah" yace "Khadijah are you sure you are nt lying about ur self" hawaye ne ya cika idonta tana girgixa masa kai tace "To God who made me, I didnt lie." Yau din ma nurse din ce ta kwana gidan tare da Khadijah, karfe bakwai da yan mintuna na safe sudais ya shigo gidan, parlor ya xauna bayan ya ajiye flask din hannunsa suka gaisa da nurse din yace "Don Allah ki sa ta shirya anytime soon xa mu kama hanya..." Ruwan xafi nurse din ta sa ma khadijah tayi wanka, ta fito bayan ta yi wankan tana rawan sanyi, nurse din ta ajiye mata daya daga kayan da sudais ya siyo mata dake cikin leda da lotion sannan ta fita, da kyar khadijah ta daure ta tashi ta shirya ta sa Hijab, sai sannan nurse din ta dawo tana kallonta tace "Ki fito yana jiran ki" daga haka ta fita khadijah ta mike a hankali ta bi bayanta, cup din kunun da sudais ya sa aka siyo mata nurse din ta dauka ta bata, amsa tayi tana kallon cikin cup din, can ta dago a hankali ta kalli sudais dake kallonta ta sauke idonta tace "Ina kwana?" Yace "How you feeling?" Ta gyada kai tace "Da sauki." A hankali ta fara shan kunun tana tsoron kar tayi amai, cikin ikon Allah bata ji Aman ba, ta ajiye kusan Rabin cup tace ya isheta, mikewa yyi yace "Ina jiran ku a waje, you help me lock d door pls ga makulli a jiki" ya fadi hakan yana kallon nurse sannan ya juya ya fita, Khadijah ta bi sa da ido yana sanye cikin bakar suit da wando sai farar T-shirt da necktie banda kyalli bbu abinda cover shoe din kafarsa ke yi, nurse din ta kai flask da kunun cup din kitchen sannan ta fito tana kallon khadijah tace "Toh tashi muje" dafa kujera tayi ta mike nurse din na gaba ta bi bayanta har suka fita nurse din ta rufe kofar da makulli ta cire sannan ta tafi gun motarsa Khadijah na bin ta. Yana daga cikin motar ta mika masa ya karba yace "Shigo in rage maki hanya madam" nurse din tace "Toh" ita ta shiga gaban motar khadijah ta shiga baya, sai bayan sun fita gidan ya fito daga motar ya rufe gidan sannan ya koma ya ja motar suka bar layin, dai dai wani junction nurse din ta sauka tana masa godiya, kudin mota ta bata sannan ya ci gaba da tukinsa. Tun da suka fara tafiya khadijah ke jin xuciyarta ke tashi duk ta xama restless, yana lura da ita ta madubi bai dai ce komai ba, bayan wani lkci tace "Amai nake ji plss" yana kallonta ta madubi yace "Amai??" Toshe bakin ta yyi da hannunta da sauri, ya gangara gefen titi ta bude motar da sauri ta sauka ta dinga kwarara amai bakin hanyan, fitowa yyi ya tsaya jikin mota ya rungume hannu yana kallonta, ta gama Aman tana maida numfashi da kyar, bude front seat yyi ya dauko table water ya mika mata ta karba ta wanke bakin ta da fuskarta sannan ta mike kanta a kasa, ya nuna mata front seat yace "Shiga" a hankali ta karasa ta shiga ya rufe motar sannan ya xaga ya shiga, kasa yyi mata da kujerar ya ci gaba da driving dinsa. Har suka yi nisa sosai a tafiyar bacci take, sudais dake kallonta lkci lkci ya gangara gefen titi yyi parking, suit din jikinsa ya cire ya rufa mata ganin sanyi take ji duk da bai kunna ac ba, ta bude ido a hankali tana kallonsa, ya ci gaba da driving dinsa. Sai da suka shigo traffic a kano ta farka, ya kalleta yace "Xa ki ci wani abu ne?" Da sauri ta girgixa masa kai, yace "Ko xa ki ci apple?" Shiru tayi tana kallon mai hawking apple dake tsaye gefen glass dinsa, ya dau suit dake jikinta ya cire kudi sannan ya mayar ya rufa mata ya sauke glass ya siya apples guda shidda ya ajiye kusa da ita, daya ta dauka ta kai baki a hankali gabanta na faduwa, taji bakin ta ba dadi ta dinga taunan Apple din a hankali tana tsoron kar ta ji amai, har ta ci rabi bata ji aman ba kafin su bar kano har ta cinye biyu daga nan kuma bacci ya dauketa. Khadijah bata sake farkawa ba sai da suka shigo garin kaduna kusan karfe uku, ganin ta tashi yace "Wani anguwa ne gidansu Aliyun yake?" A hankali tace "GRA" bai ce komai ba ya dinga driving a hankali sbda traffic, cikin minti ashirin suka shigo Gra, khadijah ta dinga yi masa kwatance har suka iso dai dai kofar gidansu Aliyu Sudais ya juya yana kallonta. ✨ *NOOR-AL-HAYAT* ✨ Bude motar Sudais yyi ya fita yana kallonta yace "Come down" a hankali ta fito gabanta na faduwa, ya nufi gate din gidan ta bi bayansa kamar me tausayin kasa, da farko Usman mai gadi ya tsaya tambayarsa wanda yake nema amma ganin khadijah ya fito da sauri yana kallonta da mamaki yace "Khadijah?" Ta kirkiri murmushi ta gaishesa, tuni Sudais ya shiga gidan, Khadijah ta bi bayansa Usman yace "Duk kika daga ma kowa hankali ana ta neman ki har station Hajiya ta kai report, to Alhmdllh tunda Allah ya bayyana ki, Alhmdllh" ita dai Khadijah bata ce komai ba ta kalli parking space xuciyarta na bugawa ta ga ba motar Aliyu da na Mumy, Sudais ya danna bell din entrance na gidan a hankali, sau uku yana danna bell din kafin a bude kofar, Anty khadijah ce tsaye bakin kofar kana ganinta kasan bacci take, idanuwanta suka bude sosai ganin khadijah dake gefen Sudais a tsaye tsoro dauke fuskarta, Sudais da yana ganin ta yyi guessing ita ce Anty khadijah ganin kallon da take ma khadijah yace "Assalamu alaikum" hade rai Anty khadijah tayi tace "Wa'alaikumus salam" daga haka ta kalli khadijah tace "Lafiya? Daga ina? Wa ku ke nema?" Sudais yace "Aliyu muke nema" daga haka ya shiga parlorn, Khadijah ta kasa shiga saboda tsoro, Wani kallo Sudais yyi mata yace "Come in" a hankali ta daga kafa ta bi gefen Anty khadijah ta shiga cikin parlorn ita ma, tuni Sudais ya isa kan kujera ya xauna, Anty khadijah dake kallonsa da mamaki tace "Malam nan din fa gidan matan aure ne ka shigo, lafiya? wa kake nema?" Yace "Shi yasa nayi sallama kuma kika amsa min kafin in shigo hajiya" Anty khadijah tace "Me kuma ya hada ku da Aliyu ku ke neman sa?" Sudais yace "Xai fi kyau idan ma bai nan ki yi hakuri ki kira mana shi ya dawo, and mahaifiyarsa hope tana nan?" Anty khadijah tayi mitsi mitsi da ido cike da masifa tace "Nima uwarsa ce ae halak malak, sannan Aliyu bai ma kasar gaba daya idan xaka fadi abinda ke tafe da kai malam ka fada don bacci nake ka taso ni..." Shiru Sudais yyi na d'an lkci kafin ya nuna mata khadijah yace "Kin san wannan yarinyar koh?" Ta kalli khadijah ta kara tsuke fuska tamau tace "Kwarai kuwa, yar aikin da muka dauka kwanaki kenan ta lalata mana xumunci ta shisshige ma d'a na, ta raba ni da shi ina ji ina ganin bana iya cewa komai, wannan shari'ar kuma sai a lahira don duk da barin ta gidan har yau abubuwan da ta cakuda bai gyaru ba, Allah ya isa tsakaninmu da ita" Kuka Khadijah ta fara yi a hankali ta durkusa inda take tsaye, Sudais ya ciro handkerchief dinsa ya share fuskarsa yana kallon khadijah yace "Dena wannan kukan xa kiyi ki bude baki da kanki kiyi mata bayani yanxu" Anty khadijah ta dawo tsakiyar parlorn da sauri tana xaro ido tace "Bayanin me?" Khadijah ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata, kare mata kallo Anty khadijah ta shiga yi, can ta fashe da dariya irin na mugunta lkci daya kuma ta tsayar da dariyar tana ma Sudais wani matsiyacin kallo tace "Xuwa kayi da ita tace mana tana dauke da ciki?" Sudais yace "Alhmdllh fine, unfortunately kin ma san halin d'an naki kenan" Khadijah ta hade kai da gwiwa tana kuka a raunane, Anty khadijah ta fashe da wani shegen dariya kamar bokanniya tayi mai isarta tayi shiru sannan ta nuna masa kofa fuskarta kamar bata taba dariya ba idonta yyi mitsi mitsi tace "Tun muna mu uku a nan bamu fi haka ba ku tashi ku fice mana a gida" a tsawace ta kare maganar, sudais ya tabe baki yace "Tsawar ki ko ihun ki fa baxae razana ni ba malama... Don haka hold it xai maki amfani gaba a wani wajen" Anty khadijah na huci tace "Xan nuna maka a nan ma yana da amfani, har wannan karuwar xata xo ta makala ma d'ana cikin shegen da tayi a wani wajen saboda ita matsiyaciya ce" Sudais yace "Toh abu mai sauki sai mu je asibiti a ga kwanakin cikin nawa, idan yyi dai dai da kwankin da ya koreta ta bar gidan to nasa ne in sha Allah" Anty khadijah tayi shiru jin abinda sudais yace, auuuu wato Aliyun ne ma ya koreta ashe, ita dai ta dawo kauyen da taje bayan kwana biyu da tafiyarta taji wai ba a ga khadijah ba ko sama ko kasa har station an kai report, Ranta yyi mugun baci a lkcn don bata so Khadijah ta tafi haka nan bata walakanta ta ba kmr yanda ta yi alkawari, me yasa xata tafi bata gama cika burin ta a kan ta ba har hawaye sai da tayi sbda bakin cikin kudin mota da kudin magani da tayi asara, suree a lkcn tayi mugun mamakin yanda Aliyu bai wani damu can ba kamar yanda mahaifiyarsa da baby suka damu amma ita bata taba kawo cewar shi ne ma ya koreta ba, Muryar Sudais ya dawo da Anty khadijah "Hajiya kin yi shiru daga nayi xancen asibiti" abinda ya fada kenan yana kallonta, ta yi masa wani shegen kallo tace "Ji gantalalle, to tunanin da nake daban malam, kuma asibitin ya ci kaza kazan sa baxa a je ba, idan ma cikin Aliyu take dauke da, idan ma ba nasa ba... bbu wanda ya isa ya shigo mana da shege cikin xuri'ar mu, I can swear with the Qur'an fasikanci ba halin Aliyu bane idan ma yyi Ita ta koya masa don kullum dakin sa take yini, wa ya sani ma ko har kwana tana yi can, yayata ba mai xama bace don yanxu xancen da nake ma bata kasar, kullum nice ke tare da su, wai hanata shige ma Aliyu da nake har shi ya janyo min bakin jini gun ta, ta janyo d'a na ya daina ganina da gashi a gidan, yanxu tun muna magana irin ta mutane ba mu dawo na mahaukata ba ku tashi ku fice min a gida kar ku ga d other side of me, ku fita nace" a tsawace ta kare maganar, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace "Toh cikin nasa dake jikinta tayi ya da shi kenan?" a takaice Anty khadijah tace "Ta xubar, don kaf xuri'ar mu ba shege kuma baxa a fara a kan d'a na ba, idan kuma taga xata iya sai ta raini cikin ta haifa ma kanta ajalinta...." Khadijah dai banda kuka babu abinda take, Sudais ya mike yace "Good, I made her brought me here for just 2 reasons, na farko... is to find out how sincere she is, and na karshe... Is just to let you and ur son knw d pains u are about putting the innocent orphan coz ni dai nasan definitely baxa ku taba accepting cikin ba, kun rabata da warce take da ita a duniya, kun goga mata bakin fenti da ba lallai ya gogu ba har karshen rayuwarta, amma Hajiya ina son ku sani, kamar yanda marainiyar nan tayi bankwana da farin ciki to wallahil azeem kuma hakan ne xai same ku a a xuri'ar ku barin shi Aliyun, He will know no peace da hakkin marainiya a kansa, who knows tunda tace likita ne shi signs na pregnancy din ya gani ya koreta, in sha Allahu sai kun yi da kun sanin abinda ku ka aikata ma yarinyar nan" yana kai wa nan ya karasa gabanta ya ciro ID card a gaban rigarsa ya nuna mata yace "Barrister Aliyu Umar, or just sudais.. we might meet some other time in sha Allah.... Or probably not" ya fadi hakan yana gesturing da hannunsa, khadijah da gabanta yayi mugun faduwa ta dago da sauri tana kallonsa wasu hawayen masu xafi na xubo mata, wani dariya Anty khadijah tayi tana tafe hannu tace "Are you threatening us?" Ya girgixa kai yana murmushi yace "Noo, not at all, kilan idan kika gaya masa aika aikan da yyi xai iya biyota, here is my complimentary card..." Ya ajiye card din gefen kujera, dauka tayi ta yayyage ta xubar nan kasa a gabansa tana huci tana kallonsa, yayi murmushi ya kalli khadijah yace "Tashi mu je" khadijah ta mike a hankali ta bi bayan sudais da har ya isa kofa, tana goge hawayen ta har ta iso gun motarsa, shi ya bude mata motar ta shiga ya rufe ya xaga ya shiga maxaunin driver, har suka hau titi bai ce komai ba ta hade kai da gwiwa tana rera kuka ko xata ji saukin tukukin da xuciyarta ke mata, A bakin hanya sudais yyi parking ganin masallaci ya fita don yin sllh da bottle water ya dawo motar, bayan ya sha ruwan ya ci gaba da driving dinsa, ya hade rai yace "Will you stop those tears and start thinking of how to face reality" ba shiri tayi shiru tana shessheka ya ci gaba da tukin sa. Dab da isha suka shigo kano, direct ya nufi hotel bayan yyi parking yace "Gobe da safe xa mu je gidan Step mum dinki" a tsorace take kallonsa, ya bude motar ya fita yace "Ki fito" daga haka ya wuce reception, daki biyu ya amsar masu, ya siya masu abinci a nan reception din sannan suka wuce sama, yana tsaye daga bakin kofar dakin da ya bude mata ta shiga na hotel din yace "Make sure you try and pray, ki daure ki ci abinci kiyi wanka sannan ki kwanta" spare ki ya cire yace "Don't leave the key jikin kofar" daga haka ya juya ya shiga nasa dakin, wanka kawai yyi, yyi sallah abincin ma bai iya ya ci da yawa ba ya kira mami, bayan sun gaisa ta tambayesa ya hanya, yace "Alhmdllh mami gobe xan dawo in sha Allah" tace "Toh maa sha Allah, in ji anyi nasara" yace "In sha Allah mami" tace "Toh Alhmdllh" a hankali yace "Am very tired mami xan kwanta" tace "Toh Allah huta gajiya" yace "Ameen" daga haka ya kwanta nan da nan bacci me nauyi ya daukesa, bai farka ba sai karfe uku, mikewa yyi xaune da sauri ya dau shirt dinsa ya sa ya dau spare key dinta da ya cire ya fita dakin ya nufi nata, saka makullin yyi ciki yana addu'ar Allah yasa ta cire makulli jikin kofar, yana murdawa ya bude ya tura kofar dakin, xaune ya ganta ta jinginar da kanta jikin gado, ya karasa da sauri ya durkusa gabanta yace "Kin samu kin ci abincin kuwa Amira?" Shiru yyi yana kallonta ganin yanda idonta ya kumbura, ya sauke idonsa kan ledan abincin da ya ajiye mata jiya da daddare, bude ledan yyi yaga bata taba abincin ba, ya wani hade rai yace "What's wrong with you, tun dare kike kuka har yanxu?" Ta girgixa masa kai da sauri muryarta na rawa ta nuna masa kirjinta tace "Yana min ciwo" sauke ajiyar xuciya yyi murya can kasa yace "Kin yi wankan?" Ta girgixa masa kai, yace "Sallah fah?" Nan ma girgixa masa kai tayi, mikewa yyi ya shiga bathroom da ke dakin ya hada mata ruwan wanka ya fito yace "Tashi ki je ki yi wanka, you will feel more better" a hankali ta tashi ta wuce bathroom din, yana ta xaune har ta fito da kayan ta da Hijab ta kwanta kan gado ta dukunkune waje daya, ya mike ya rufa mata bargo, ba a dau lkci ba ya ga alamar bacci ya dauketa, tashi yyi ya kashe wutan dakin ya nufi kofa ya fita ya rufe. Da asuba bayan sudais ya idar da sllh ya koma dakinta yaga har lkcn bacci take ya koma dakinsa shi ma ya kwanta. Da safe ya fita hotel din don nema mata kunu, wani almajiri da ya gani kan hanya ya ba kudin ya tafi gun masu siyar da kosai ya siyo masa kunu, yana ta jiransa gaban wani store har yaron ya dawo da kunun a cikin leda, karba yyi yyi masa godiya ya bar masa canjin dari takwas din don na Dari biyu yaron ya siya, ya mike ya amshi ruwa bakin store din da yake ya dawo kan bench ya xauna ya bude bottle water din ya sha kadan ya xubda sauran sannan ya juye kunun ledan a ciki ya mike ya koma hotel din, tashinta yyi daga baccin da take ganin tun jiya bbu abinda ta ci, ta tafi bayi ta kuskure bakinta kamar yanda ya ce mata, da alwala ta fito yana ta xaune yana jiran ta gama sallah, duk ta galabaita kafin ta idar, ya dawo kusa da ita ya mika mata bottle din kunun bayan ya bude yace "Gashi ki sha ko ba yawa kin ji" kai ta gyada masa ta karba ta kai baki a hankali har wani rawa hannunta yake, kusan rabi ta sha kunun ta ajiye ta jinginar da kanta da gado, yace "Ki daure ki kara kadan" ta girgixa kai da sauri tace "A'a xan yi amai idan na sha kuma" rufewa yyi yace "Toh ki kwanta kafin in yi wanka xa mu je can gidan step mum dinki" shiru ta yi ta bi sa da kallo har ya fita dakin, da yake ba ya rabo da spare clothes a motarsa can ya tafi ya dauko kayansa yana gama wanka ya canxa. Ko da ya dawo dakin idon Khadijah a lumshe yake duk da ba bacci take ba, tausayin kanta kawai take don bata san wani irin rayuwa xata fara yanxu ba kuma, ita da ba kowa gareta ba a duniyar, muryarsa da taji ya sa ta bude ido da sauri don bata ji shigowar sa ba, ta mike xaune yace "Let go, it's almost nine yanxu" tashi tayi ta sauka daga kan gadon, ya dau ledan abincin jiya da bata ci ba ya fita tana biye da shi a baya, nan reception ya bada makullan dakin ya nufi wajen hotel din xuwa Parking lot, ya bude mata front seat ta shiga sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, sai da ya hau kan titi yace "Ina ne gidan step mum din naki yake?" Kamar xata yi kuka tace "Wllh tsoro nake ji kuma tace kar in kashe mata aure, I don't want to be the cause of that" yana kallon titin gabansa yace "Kar ki damu you will remain inside the car, while we talk" kai ta gyada masa a hankali hawayen dake makale idonta ya sakko, yace "Clean those tears now" da sauri ta goge idonta, tana ta nuna masa hanyar gidan bayan sun shigo anguwar, ganin sun kusa a hankali tace "Plss ka tsaya da motar a nan kaga gidan can" ya tsayar da motar ya na kallon gidan da take nuna masa, kashe motar yyi yace "Ya sunan step mum din ki?" Tace "Hajiya Amina" bude side dinsa yayi ya fita, ta bi sa da kallo ganin yanda yake tafiya har ya isa kofar gidan ya tsaya, wani yaro ne ya fito gidan dake kusa da gidan ya kirasa, yaron ya taho sudais ya duka yana kallon yaron yace "Big boy... shiga gidan nan kace ana sallama da Hajiya Amina" yaron yace "Toh" sannan ya shige gidan da sauri, ba a dau lkci ba sai ga Shafah da Hasana sun fito ko wacce daga mai riga a kai a matsayin mayafi sai mai wando, Sudais ya dinga kallonsu daga sama har Kasa, Shafa dake ta kallon sudais tace "Sannu da xuwa bawan Allah" yace "Ina kwanan ku" a tare suka amsa masa, ya shafa lallausan gashin kansa da ke kara masa kyau yace "Dama Hajiya Amina nake son gani" a tare suka hade rai Hasana tace "Yar uwar ka ce?" Ya girgixa kai tace "Halan kudi xaka karba gunta? Toh Allah sa dai ba yawa, don kuwa Amina xamanta ya xo karshe gidan nan tun shekaranjiya don kuwa Alhaji ya saketa, yanxu haka ko tsinkenta babu a gidan" Kallonsu Sudais yake a sanyaye, Hasana tace "Atoh, ban da mugunta ki tura yar mutane karuwanci don ba ke kika haifeta ba yarinya marainiya bata da kowa duniyar nan banda Allah, dama an ce idan mutum xai gina ramin mugunta yyi ta yar karama.... To ita kam da xurfi tayi sa gashi ta afka ciki" Sudais da ko kadan bai san ma abinda suke cewa ba yyi karfin halin cewa "Toh don Allah kun san garinsu?" Shafah tace "Halan kudin da yawa, matar da har gorin cin bashi take mana ashe a boye take nata" Hasana tace "Mun dai ji kishin kishin a gari ta siyar da duk kayan dakin nata wai xata koma kasarsu, ka san 6are ce ba yar Nigeria ba" Sudais yace "Ina ne kasar ta su?" Shafah tace "Wai ko Ethiopia ko morocco ko Sudan oho dai... amma nan Africa ne, mu dai Allah ya raba mijinmu da alakakai" juyawa sudais yyi ransa a dagule ya nufi motarsa yana shiga ya hade kai da steering yana tunanin ta ina xai fara, ya xai yi da yarinyar nan da kowa ke kira da marainiya, khadijah da ke ta kuka tun bayan fitarsa cikin rawar murya tace "Ummata na fushi da ni har yanxu koh?" Dago kansa yyi yana kallonta da idanuwansa da suka sauya kala. Tada motar sudais yyi bai ce komai ba suka bar layin, ban da kuka babu abinda khadijah take har da shessheka, duk a tunaninta Umma ta ki hakura ne ta kori sudais, yana driving a hankali yace "Bana son wannan kukan da kike cika min kunne da shi plss, if you are in pain it's better you pray, plss kukan ki yana damuna da yawa" a hankali khadijah ta hadiye kukan tana share hawayenta a sanyaye, bayan wani lkci sudais yayi breaking silence din cikin motar a hankali yace "Ur step mum is gone Amira" da sauri khadijah ta kallesa xuciyarta na bugawa sosai tace "To where?" Yana ci gaba da driving dinsa yace "Dama ba Nigerian bace Ita?" Khadijah na kkrin mayar da wasu sabbin hawayen da ke taruwa idonta tace "She told me she is not a Nigerian... I don't knw her country" ya lumshe ido ya bude yace "Toh ta koma kasar su in ji Co wives dinta, since the day before yesterday ta wuce" cikin rawar Khadijah tace "Me yasa?" Kallonta yyi ya dauke kai bai ce komai ba, sai dai baya son gaya mata aurenta ya lalace kamar yanda su Hasana suka gaya masa, Bayan kusan minti biyar murya can kasa yace "Look, you just have to face reality Khadijah, keep all those tears and crying aside, don't cry any longer it has no use" kai kawai take gyada masa kuka na cin ta amma bata yarda ta yi ba, nan ko shi ma hankalin sa a tashe yake kamar yanda nata yake a tashe amma yayi kokarin boye hakan yana lallashinta ita, bai san yanda xai yi da ita ba, bai san inda xai kai ta ba, bai san inda xai ajiyeta ba, bai ma san ta ina xai fara ba, tunanin hakan yasa yace "Ya Allah" bai san ya fito fili ba sai da khadijah dake ta share idonta ta kallesa, ya shafa kansa yana ci gaba da driving dinsa, Nearest filling station ya shiga domin kara Fuel kafin ya dau hanyar Damaturu, tun da suka shigo station din xuciyar khadijah ke tashi jin warin fetur, ta dai rufe fuskarta da Hijab din jikinta a hankali, Sauke glass yyi yana fadi ma mata mai siyar da man na nawa xata xuba masa, tana fara xuba man khadijah ta fara kkrin bude mota ya juya yana kallonta da mamaki yace "What?" Ganin yanda ta toshe baki yyi saurin bude lock din motar ta fita, tana fita kuwa ta shiga kwarara amai nan kasan wajen, sudais ya dafe kai a hankali a ransa yace Ai shi ya shiga uku.... Ganin wata mata ta fito daga motar dake bayan nasa yasa shima ya bude motarsa a hankali ya fito, matar ta riketa tana mata sannu kamar yanda kowa na gun ke yi mata, sudais ya xagayo ya tsaya ya ma rasa abinda xai ce, mai siyar da fuel din ta tafi gun siyar da drinks a filling station din ta karbo ruwan gora daya ta dawo matar da ke rike da khadijah ta bude ta mika mata khadijah ta karba da kyar tana wanke fuskarta da ruwan, mijin matar dake rike da khadijah ya fito shi ma yana ma khadijah sannu, matar ta kalli Sudais tace "Bari ta shiga motar sai ku wuce" barin wajen sudais yyi matar ta taimaka ma khadijah ta shiga motar sannan ta rufe, mai siyar da mai ta debo kasa tana xubawa wajen aman, Cike da karfin hali sudais yace "Toh mun gode kwarai" matar tace "Ayya ba komai, Allah ya sauwake, ya kuma raba lafiya" Sudais ya juya da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Ameen mun gode" daga haka ya xaga driver seat ya kara yi ma mai siyar da mai da mutanen wajen godiya ya shiga ya tada motar suka bar filling station din, Har suka hau kan titi bai ce komai ba tunanin da yake a ransa daban, can ya saci kallonta yaga idonta a lumshe ta jinginar da kai da kujera, kwantar mata da kujerar yyi ta bude ido da sauri, sai a sannan murya can kasa yace "Sorry" Bata iya ta amsa masa ba ta mayar da idanuwanta ta rufe daga nan bacci ya dauketa. Buga kujerar motar da take kai taji ana yi cikin bacci, ta bude ido a hankali Sudais dake kallonta yace "Come down" kalle kallen inda suke ta shiga yi taga kamar gidan Sudais ne, ganin har ya fita yasa ta bude motar a hankali duk jikinta ba kwari ta fito ta bi bayansa, yana tsaye parlor yana jiranta bayan ta shigo, ya nufi wani bedroom ba wanda ta fara xama ba ya bude ya juyo yana kallonta yace "Go inside xan kawo maki bedsheet yanxu ki shimfida sai ki kwanta ki huta" daga haka ya wuce ba a dau lkci ba ya dawo da bedsheet din ya bata sannan ya fita ya kulle kofar, yanda yace tayi haka tayi ta kwanta a gajiye ga baccin da ke idonta, nan da nan bacci ya sake dauketa, sai kusan azahar ta farka da kyar ta dalilin sanyin da ta dinga ji alamar xaxxabi, cike da karfin hali ta mike ta shiga toilet din dakin ta dauro alwala ta fito tayi sallah, tana idarwa ta jinginar da kanta da gado hawaye na sakko mata, ta dau lkci me tsayi a haka aka yi knocking kofar, da sauri ta dago kanta tana goge hawayen idona, jin an kara bugawa ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, tsaye ta gansa bakin kofar rike da leda babba da karami, bai ce komai ba ya shiga dakin ta bi bayansa, sai da ya ajiye ledan hannunsa yace "Tun daxu kike kuka kenan?" Kai ta gyada masa, yace "Good, kukan me kike?" Kamar ya dada tunxurata ta kuma fashe masa da kuka sosai ta durkushe wajen har da shessheka, cikin raunin murya tace "Ni bani da kowa yanxu, I don't knw if I have any use, i...." Ta fashe da wani matsanancin kukan, ya durkusa kusa da ita shi ma a hankali yace "Noo, you have use Amira, kar ki sake cewa baki da kowa, or don't you have trust in Allah?" Ta kallesa da sauri tana share hawayen idonta cikin rawar murya tace "I do" ya d'an yi murmushi yace "Then have faith in him" ledan da ya ajiye ya nuna mata yace "Ki yi wanka ki canxa kaya, take some fruits after that sai kiyi sllh ki kwanta ki huta sosai" daga haka ya mike ya fita ya kullo mata kofar, ta fi minti goma a durkushe yanda ya bar ta daga karshe ta tashi ta bude ledan taga sabulu har da toothpaste da brush, sannan ga inners da dogayen riguna uku da hijab, duk jikinta yyi sanyi, ta mike ta shiga bathroom din ta yi wanka ta fito, Apples kadai ta iya ci cikin fruits din bayan ta gama shiryawa sannan ta kwanta lkci daya kuma bacci ya sake dauketa. Buga gefen gadon taji ana yi cikin bacci ta bude ido a hankali, ganinsa gefenta ta mike xaune da sauri, yace "Ur temperature is running high, are you feeling pain anywhere?" Ta girgixa masa kai tace "A'a" yace "Ba ki yi sllh ba....." Kallon agogo tayi taga karfe bakwai ya wuce, ta kallesa da sauri tace "Dare yayi?" Yace "Yea, you slept all day ai" sunkuyar da kai tayi, yace "Me kike son ci yanxu?" Shiru tayi kamar me naxari, yace "Say it" a hankali tace "Kila gyada" ya d'an bude ido yace "What? Groundnut?" Shiru tayi tana kallonsa, da wani expression a fuskarsa yace "Ina xan samo gyada da daddaren nan?" A takaice tace "A titi" kauda kansa yayi, khadijah dake ta kallonsa bayan kusan minti biyu a hankali tace "Ka barshi kawai bana jin yunwa tunda dare yyi, am not even hungry..." wani kallo yyi mata ta gefen ido ya mike ya nufi kofa kamar xai tashi sama ta bi sa da kallo har ya fita, a hankali ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka nmta wanke baki sannan ta dauro alwala ta fito, tana ta xaune kan darduma bayan ta idar da sllh, yanda xata koma kan gado ne ta kasa tashi duk jin jikinta take kamar ba nata ba, gaba daya bbu karfi tattare da ita, har bacci ya fara daukarta a xaunen taji an bude kofa, ta dago da sauri, karasowa yyi kusa da ita ya ajiye ledan hannunsa ya koma gefen gado ya xauna, Kallonta kawai yake yace "Ga gyadar, after I've gone round of d whole of damaturu" Khadijah ta wara ido tace "All the round of damaturu?" Bai ce komai ba ya hade girar sama da ta kasa, a hankali tace "Nagode" bude ledan tayi taga dafaffen gyada ce da Wanda aka gasa a wani ledan daban, dafaffen ta fara ci, da ta juya xata ga ita yake kallo, duk sh was uncomfortable na kasa cin gyadan, can dai ta sake kallonsa tace "Bismillah" bai ce komai ba, can ya sakko ya xauna kusa da darduman, ya dau gyada daya ya bude, haka ya dinga bude su har suka yi yawa sannan ya mika mata ta karba tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Eat" ba musu ta fara ci, ya kuma bude mata wasu masu yawa, ya mika mata, haka ya dinga mata har tace masa ta koshi, yace "Are you sure?" Tana yatsina fuska tace "Kamar amai xan yi" hade rai yyi sosai yace "Don't try dat malama, kinsan garin da naje na samo gyadar nan" khadijah ta ja baya tana nodding masa kai, can ya shafa kai a hankali murya can kasa yace "Just relax xaki daina jin aman" ta kuma gyada masa kai ta jingina da jikin gado ta lumshe ido, ji tayi aman xai taho mata, ta toshe bakinta da hannu biyu tana girgixa masa kai kamar xata yi kuka tace "Wayyo xuwa xai yiii" tashi yyi da sauri ya shiga bathroom ya debo ruwa, ya dawo ya durkusa kusa da ita ya cire Hijab din jikinta, ya watsa mata ruwan a fuska da gashinta, har ranta taji sanyin ruwan ta koma baya da sauri tana sauke ajiyar xuciya, a hankali yace "Sorry" wani ajiyar xuciya ta kara saukewa jin aman ya d'an lafa mata, ta kallesa da kyar tace "Xan kuskure baki" table water dinsa da ya shigo da ya mika mata ta tashi ta wuce bathroom da sauri, bata fito bayin ba sai da ta amayar da gaba daya gyadar da ta ci, ta fito da kyar ta xube nan tsakiyar dakin tana satan kallon sa tana mayar da numfashi, wani kallo ya dinga mata Daga inda yake xaune, bata sake kallonsa ba ta lumshe ido, lkci daya kuma bacci ya dauketa, gashin kanta taji ana gyara mata ta bude ido da sauri ta gansa durkushe gefenta yace "Ki rufe gashin ki ki hau saman gado" ba musu ta mike xaune ta hade uban gashinta waje daya ta tufke, xata mike tsaye jiri ya kwasheta ta koma da sauri ta xauna yace "Be careful" gyada masa kai tayi ta kuma tashi ta koma kan gadon ta kwanta, ac dake dakin ya rage yace "In kashe maki wutan?" Ta girgixa masa kai, yace "Sai da safe" daga haka ya fita ya kullo mata kofar dakin. Kafin asuba Sudais ya shigo ya fi sau biyar duba ta don da ya bude kofa xata farka, gaba daya ya kasa bacci tunanin yanda xai yi da khadijah ya damesa gashi mami Bata san ya dawo ba ma, shigowarsa na karshe ne ya rufe ta da blanket don xaxxabi ne sosai jikinta, da asuba da ya shigo tashinta tayi sllh amai tayi ba kadan ba kafin ta dauro alwala ta fito, ruwan wanka ya hada mata bayan ta idar da sllhn, da kyar ta yi wankan ta fito, ta kasa shiryawa ta kwanta nn kan gado ya lullubeta da bargo, bayan kusan minti sha biyar ya dawo gefenta yace "Daure ki tashi ki shirya mu tafi clinic" bata ce komai ba don har fuskarta ta rufe, ya cire bargon suka hada ido, sauke idonsa yyi yace "Tashi ki shirya" daga haka ya fita dakin, har ya dawo bata tashi ba, yace "Ke fa nake jira" cikin sanyin murya tace "Ni baxan iya ba" yace "Toh ni xan sa maki kayan?" Bata ce masa komai ba, yace "Look bana son in dawo in gan ki cikin bargon nn it's better ki daure ki tashi kiyi abinda xa kiyi" juyawa yyi ya fita, cike da karfin hali ta mike xaune hawaye cike idonta, kamar ynda yace mata haka ta dinga daurewa har ta sa kayan a nan inda take kan gadon, tana gama sa wa ta koma ta kwanta, bayan kusan minti goma ya dawo dakin, tsayawa yyi kusa da gadon yace "Toh tashi mu je" rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta mike xaune a hankali tana sauke numfashi, Wayarsa ce ta fara ring, ya daga yana kallon screen din kafin ya xauna da sauri ya daga ya kai kunne tare da sallama yace "Good morning Mami" murmushi yyi yana shafa gashin kansa a hankali yace "Ku yi hakuri Mami ban kira ba, amma in sha Allah yau xan taho, am done with what am doing" bayan wani lkci yyi mata sallama ya mayar da wayar aljihu, yana kallon khadijah yace "Tashi mu je" daga haka ya nufi kofa, a hankali ta sakko da kafafuwanta kasa tayi karfin halin mikewa, har suka isa compound din gidan bai juyo ba, sai da ya isa gun motarsa ya juyo yana kallonta, can ya bude motar ya shiga, ta karasa ta bude front seat ta xauna ta lumshe ido don ji take kamar wani aiki me wahala tayi, wani babban private asibiti suka tafi, bayan yyi parking ya juyo yana kallonta da kyau yace "Har mu bar clinic din nn bana son jin bakin ki, am nt asking for ur opinion or anything, I am doing wat I think is right, am I clear?" A hankali ta gyada masa kai, yace "Good" da yake da safe ne ba su wani dde ba suka samu ganin likita bayan ya biya kudin kati, ta xauna daya daga kujeran dake kallon likitan, ya xauna shi ma yana facing dinta, hannu ya ba likitan suka gaisa, likitan na kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "How you madam, though u look sick" khadijah tayi murmushin karfin hali, likitan yace "Allah ya sauwake, ya raba lafiya," kallon Sudais dake shafa beard dinsa yyi yace "Drugs xan rubuta maku yanxu da xata dinga sha, there is nothing more I think.... She will get better gradually" Sudais ya ce "Ba abinda ya kawo mu ba kenan Dr, though I knw it might look wrong, but... she got pregnant by mistake, it's just some weeks old, so plss I want u to get rid of it...." Tunda ya fara maganan likitan ke kallonsa da expression din mamaki, Sudais yyi kasa da murya yace "Yes plss" likitan yace "Sorry we don't do that hear sir, xaku iya tafiya wani asibitin" kallon Sudais khadijah take kamar idanuwanta xa su fito, Sudais yyi kasa da murya sosai ya marairaice yace "Yeah, I knw it's very wrong Dr... But she is my.... Wife, the last pregnancy wasn't funny, and.. She's breastfeeding an eight month old baby now" kamar ana forcing dinsa yyi magana, likitan sai kallon khadijah yake, Sudais ya ciro handkerchief ya share goshinsa don har xufa ya keto masa yace "Plss Dr, ka taimaka for d sake of d eight month child" Likitan ya girgixa kai yace "I think xai fi a daina breastfeeding babyn, she shud take care of d one she's carrying now, sai kaga Allah ya taimaka komai ya xo da sauki" Sudais yace "Nooo Dr, don Allah ka cire mata I will pay what ever amount u request for plss" likitan ya mike ya nufi show glass dake office din ya dauko wani allura da syringe, ya dawo yace "I will give her this injection sauran drugs din kuma xan rubuta maka kaje pharmacy ku siya" Sudais ya sauke ajiyar xuciya yace "Thanks very much Dr, nagode sosai" Lkci daya khadijah t fashe da kuka ta mike tace "Nooo, ni bana son a cire min don Allah ku yi hakuri" bude baki Sudais yyi yana kallonta da mamaki, ta hade hannuwanta tana girgixa masa kai hawaye na sakko mata a hankali tace "Don Allah kayi hakuri, I don't want to abort d pregnancy, Allah will be angry with me plss" Likitan ya ajiye alluran ya rungume hannuwansa yana kallonta yace "Ba mijin ki bane kenan?" Hawaye na ci gaba da sakko mata ta gyada masa kai alamar eh, Sudais dake mata wani irin kallo ya mike yace "Sae ki san inda dare yyi maki kuma daga nan" daga haka ya fice daga office din kamar xae tashi sama, a hankali take kuka tana kallon likitan dake kallonta yana girgixa kai, can ta nufi kofa cikin sanyin jiki ta fita, babu motarsa a parking space, ta fita gate tana share hawayen da ya ki tsaya mata. Har Khadijah ta isa bakin titi kuka take bata damu da mutanen dake kallonta ba, ta ma rasa inda xata bi gashi ko sisi bata da shi, all this while Sudais na cikin motarsa yyi parking motarsa ya dinga bin ta da kallo har ta d'an yi nisa, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido yana kiran Allah a xuciyarsa, he is just confuse, a hankali ya ci gaba ya fara driving motar har ya iso dai dai inda take ya tsaya ya wani hade rai cikin tsawa yace "Ina kika san xaki tafi yanxu?" Ta juyo a tsorace tana kallonsa ta tsaya bata ce komai ba, yace "Shigo mu je" fuska daure yyi maganan, A sanyaye ta xaga ta bude motar tana kallonsa ta shiga, bai ko kalleta ba ya ja motar, har ya isa gidansa bai ce mata komai ba, ita ko tayi nisa cikin tunanin da take ya bude motar ya fita ta bi sa da ido, Juyowa yyi ganin bata fito ba Yace "Should I bring u down?" girgixa kai tayi ta fito ya kulle motar ya nufi entrance din gidan ta bi bayansa, kana ganin yanda yake tafiya kasan a gajiye yake, xaune ta gansa parlor ya jinginar da kansa jikin kujera bayan ya xauna ya lumshe ido, a hankali ta xauna kasa ta takure waje daya sbda sanyin parlon, bude ido yyi bayan wani lokaci ya kalleta, suna hada ido ya dauke kai, khadijah dai sai kallonsa take, yanda ya tsura ma ac dake aiki a parlon ido yasa xaka gane tunani yake, a hankali khadijah tace "Xan yi wanka..." sai a snn ya juya ya kalleta, a takaice yace "In kai ki bayin kenan?" Ta girgixa masa kai, yace "Toh tashi ki tafi" mikewa tayi ta wuce dakin da ya saukar da ita, wanka tayi ta fito ta shirya ta sa Hijab, yana nan yanda ta bar sa, har ta iso kusa da shi kuma bai sani ba, duk jikinta yyi sanyi ta durkusa nan kusa da shi cikin sanyin murya tace "I knw I am a burden, u don't knw where to start from, and u don't want to send me away cos you've got a good heart... You look so responsible to keep me in ur home, you have parent and elders that won't take it likely.... I don't want to be d beginning of ur problems, sbda haka nake rokon ka don Allah ka taimakeni ka kai ni gidan marayu kamar yanda na roka a baya, I will cope there in sha Allah, I will take care of the motherless there, but I want u to do me the favour of coming to see me, even if it's just once in a year plss, I want to feel I have somebody in this world, don Allah kar ka mance ni bani da kowa" tana kai wa nan hawayen dake makale idonta ya sakko, kallonta kawai sudais yake, can ya runtse ido ya bude ya mike ya fice parlorn, hade kai tayi da gwiwowinta tana kuka a hankali tana me tausayin rayuwarta, sai bayan kusan minti talatin sudais ya dawo parlorn, duk da ta ji shigowarsa bata dago kanta ba, muryarsa taji yace "tashi ki shiga daki kiyi kukan da kyau" ba musu ta tashi ta wuce cikin dakin, tayi kukan kamar yanda yace mata har ta gaji ta kwanta ta takure waje daya, bude kofar dakin yyi ya shigo, ta daga kai tana kallon sa har ya iso inda take yana tsaye yace "Good, am hoping all the tears you where planning to shed while in this house kin yi su yau kin gama, cos I am nt gonna tolerate that, clear? Better ki barni in ji da daya" Mikewa xaune tayi ta gyada masa kai tana share guntun hawayen idonta, yace "Me xa ki ci?" Ta girgixa kai tace "Bana jin yunwa" ganin kallonta yake a hankali tace "Toh xan ci apple" yace "Not apple, I mean food" ta d'an yi shiru, can ta dago tana kallonsa a hankali tace "Wainar flawa" wani kallo yake mata yace "Meye shi?" Taace "Da flour, albasa, tarugu, maggi, gishiri and man gyada ake yin sa, Anty Kyauta tayi mana a can gidan" da mamaki yace "A ina xan samo maki shi?" Tayi shiru bata ce komai ba, ya fi minti biyar a tsaye, can ya tabe baki ya fiddo wayarsa a aljihu yayi dialing number ya kai kunne, ba a dau lkci ba ya amsa sallaman da aka yi masa yace "Rabi'ah am on my way now, pls ina son ki min...." Juya ido yyi kamar me son tuno sunan abun, can ya cire wayar a kunne da sauri ya jefa ma khadijah wani kallo yace "Meye sunan ma?" A hankali tace "Wainar flawa" ya mayar da wayar kunne yace "Wainar flawa" Khadijah na jin yarinyar na dariya ya tabe baki ya katse wayarsa ya mayar aljihu ya fice a dakin. Khadijah na nan yanda ya bar ta ya dawo dakin, yana kallonta yace "ermm, ohk let me say Amira, you see xan je gida yanxu, but baxan dade ba xan kawo maki abincin, xa ki iya tsayawa ke kadai ai koh?" Ta gyada masa kai yace "Good, I will be right back now" kashe ac din dakin yyi ya kunna mata kayan kallo daga haka ya nufi kofa khadijah tace "Allah ya tsare" juyowa yyi ya kalleta yace "Amin" daga haka ya fita ya kulle mata kofar. Kwanciya tayi duk da sonta da kallo ta rufe idonta. Tun da sudais ya shiga gidansu yyi parking gabansa ke faduwa ya bude motar a hankali ya fita ya wuce cikin gidan, jin ana soye soye a kitchen ya karasa kitchen din, Rabi'ah ce tsaye tana soya wani abu da bai taba gani ba yace "What's this" wara ido tayi ganinsa tace "Sannu da xuwa yaya, wainar da kace mana" yace "Dama kamar kwai yake?" Ta gyada masa kai tana yar dariya ya tabe baki yace "Mami fa?" Tace "Tana bedroom da su Anty Maryam" bai ce komai ba ya haura sama yyi sallama kofar dakin maminsa, Kanwar mami da kanninsa biyu dake Dakin ne suka amsa masa ya shiga ciki, kallon uban kayan dake jibge a kasa ta ko ina a dakin, ga boxes masu tsada dake ajiye su ma, dukawa yyi ya gaida mami ta amsa da fara'a tana masa tambayar ya hanya, yace "Alhmdllh" sannan ya gaida Anty Maryam ta amsa da murmushi tace "Welcome barrister" sai a sannan ya amsa gaisuwar kanninsa ya mike ya koma can karshen gado ya xauna, Mami tace "Ka ga sai yau Maryam ta karbo sauran akwatunan xa a xuba kayan ciki yanxu" a hankali yace "Ohk" Mami tace "ka gama gyaran da kace a can gidan naka" ya gyada kai yace "Eh Mami" Mami tace "Toh maa sha Allah" Yana ta xaune har suka gama jera gaba daya kayayyakin a akwatunan, kanninsa su Humairah suka fita dakin ya rage daga shi sai Mami da kanwarta, Mami tace "Lkci na ta tafiya sudais yaushe ka ga ya kamata a kai kayan" tasowa yyi a hankali ya dawo kasan carpet ya xauna kansa a kasa murya can kasa yace "Mami..." Mami dake ta kallonsa kamar yanda Anty Maryam ma ke kallonsa tace "Ya aka yi sudais?" Kasa dago kansa yyi yace "Mami ina son a dakatar da kai kayan nan yanxu ne...." Mami dake masa kallon mamaki tace "Ko saboda me Aliyu?" Ya girgixa kai yace "Mami a dai dakata kawai" Anty Maryam tace "Ko Jiddahr ta yi maka wani laifin ne sudais?" Shiru yyi bai ce komai ba, Mami tace "Toh ni dai abinda xan ce maka a nan shine idan dai kasan ba shiririta bane, ba wani concrete laifi bane ka ajiye wannan shashancin da kake fadi aside, idan kuma kaga laifi ne babba to shkkn" Anty Maryam tace "Ka fada mana me tayi, wani laifin ka kama ta da shi Sudais, Kar mu xama kananun mutane" ya girgixa kai a hankali yace "A bar xancen kawai mumy" Mami tace "Toh Allah rufa asiri" yace "Ameen" mikewa yyi yace "Xan fita in dawo yanxu Mami" daga haka ya nufi kofa Mami ta bi sa da ido har ya fita, Anty Maryam tace "Kar ki tilastata masa don Allah Mami tun da kika ga haka ba karamin laifin ya kamata da shi ba, kin dai san halin sudais da xurfin ciki ko xaki shekara kina tambaya ba fada xai yi ba" Mami dai bata ce komai ba. Sudais na fita ya shiga kitchen ya tarar Rabi'ah ta gama wainar ta xuba masa a warmer, ya bude warmer din yana ta kallon abincin kafin ya tabe baki ya dauka ya fito parlor, da mamaki tace "Yaya ba a nan xaka ci ba?" Yace "Ehh ni da frnds dina xa mu ci, sai na dawo" daga haka ya fita gidan ya hau motarsa ya wuce. Sai da Sudais yyi azahar a masallacin layin gidansa sannan ya shiga gidan misalin karfe daya da rabi, jin an bude kofa Khadijah dake bacci ta bude ido da sauri, karasowa yyi yana kallonta ya ajiye warmer din hannunsa yace "Tashi ga abincin" ta xauna ya bude mata warmer din, ba don tsare ta da yyi ba da daya ma baxata cinye ba amma haka ya dinga forcing dinta har ta cinye biyu, sai dai duk she was restless don amai kawai ta dinga ji, ya hade rai sosai yace "Look idan ki ka yi aman nn I will nt bother my self about ur food again am telling you" hawaye cike idonta tace "Kayi hakuri wllh ba ni bace" ya xauna gefen gadon yace "Toh nayi, amma ki daure kar ki yi.... Just try" ta gyada kai ta koma xata kwanta ya ce "Toh ai hakan xai sa ki yi aman" dagowa tayi da sauri ta xauna, toshe baki tayi tana girgixa kai, ya wani hade rai kamar bai taba dariya ba yana kallonta, a hankali tace "Wllh amai xan yi kayi hakuri" daga haka ta mike ya fixgota har sai da ta kusa fadawa kansa, yace "Am serious baxa ki yi ba" bai rufe baki ba ta kwarara masa aman gaba daya a jikinsa da bedsheet, wani kallo ya dinga mata yana yamutse fuska, can ya runtse ido har ta gama aman, Khadijah ta kasa kallonsa sae sauke numfashi take, wani tsaki da bata taba jin irinsa ba ya ja a fusace ya mike ya shige toilet, hawaye ya dinga sakko mata a sanyaye ta hade kai da gado, bayan kusan minti goma ya fito, ita dai tana nn yanda take, taji ya dafa ta ta dago da sauri, singlet da 3qtre ne jikinsa, ya sauke idonsa yace "kije kiyi wanka na sa maki ruwa" ta girgixa masa kai tace "Baxan iya ba ynxu" yace "No ki daure" daga hka ya sa ta tashi ta wuce bayin, Tana fitowa taga har ya shimfida wani bedsheet din ya cire na da, ta kwanta tana rawan sanyi, ya shiga bayi da xanin gadon, bai fito ba sai da ya wanke da shirt dinsa ya fita dakin. Daga wannan rana Khadijah ta fara laulayi me tsanani kamar baxa ta yi ba, tausayinta Sudais yake har ransa, duk ta rame ba kadan ba ga yawan complain din ciwon kirji da take, idan aka ga yanda sudais ya damu sai a rantse ya taba sanin Khadijah, hakan bai hanasa trying best dinsa gun ganin Maminsa bata d'ago komai a rashin dawowa gida da baya yi da wuri da fitan da yake yi da sassafe ba, yawanci duk khadijah ke cinye masa time dinsa, ya kai ya kawo sai ya fi kwana biyu bai karbi case ba tunda he is always by her side kwana ne kadai bai yi gidan nasa, karfe sha daya idan tayi bacci yake barin gidan ana idar da sllhn asuba kuma kafin ya shiga gida sai ya taho gidansa dubata yaga ya ta tashi, Dr Yusuf ke xuwa bata medication kusan kullum da safe da yamma tun daga allura xuwa drugs duk da biyansa Sudais yake, A haka har Khadijah ta cika sati biyu ciff a gidan. Da safe misalin karfe sha daya Sudais yaje can clinic gun Yusuf, bayan sun gaisa Yusuf ya tambayesa jikin khadijah, ya shafa kai yace "Toh ga ta can dai, am just tired Yusuf, wai why not baxa ka taimaka ka cire mata cikin nan ba frnd, am talking to you about this for the 3rd time don Allah ka cire mata ko nawa ka bukata xan baka, plss Yusuf" Yusuf ya girgixa kai yace "My reply will always be the same, I don't abort pregnancies and I will not, nace ka kai ta wani asibitin ni dai baxan yi ba ka ki ganewa" Sudais ya marairaice yace "Nasan baka cire ciki amma ita wannan case dinta daban ne, she was raped... beside she is too young da ciki dubi fa yarinya ce karama, gashi sai wahala take sha ko don haka ka tausaya mata mana Yusuf" Yusuf dake rubuce rubucensa yace "Ae sai kuma ka yi Barrister" Sudais ya d'an hade rai yace "Haba Dr, ya kke son marainiyar tayi da yaron da xata haifa yanxu, ta ina xata fara rainonsa don ni dai ba dauwama xata yi tare da ni ba na har abada, har ynxu ina tunanin taimakon da xan bata ta tafi ta inganta rayuwarta but nt when she is this sick everyday, dubi fa jiddah gani take kamar na yaudareta ne, but ba hka bane idan aka yi auren ina xan sa ta, kasan it won't make sense ina da gida in kama haya, dole Mami xata so sanin dalili, infact she will be suspicious, Yusuf don girman Allah ka rufa min asiri ka cire mata jaraban nn ta kama gabanta plsss" Yusuf ya tabe baki yace "xa ma ka gama dadin bakin ka" jin Sudais yyi shiru yana kallonsa ya ajiye pen din hannunsa yace "Sae in har in rubuta maka kaje can pharmacy ka siya nasan baxa ka rasa iya allura ba, duk sai kayi mata da kanka" ban da hararansa babu abinda Sudais yake, Yusuf yace "yes, or you buy her just drugs shkkn amma ni dai ba da hannu na ba" Sudais ya dake trying hard to hide his anger yace "Rubuta min" Takarda Yusuf ya jawo yyi rubuce rubucensa ya mika masa Sudais ya fixge ya nufi kofa Yusuf ya bi sa da kallo yana murmushi, Gida ya nufa bayan ya je garage din mota amso sakon Mami da ta aikesa tun safe, Xaune ya same Mami parlor, tun da ya shigo take kallonsa ganin ramar da yyi har ya karaso ya xauna kasa kusa da ita yace "Ina yini Mami" tace "Lafiya lau, sannu da xuwa" ajiye mata ledan hannunsa yyi yace "Ga sakon Mami" Bata ce komai ba ganin haka ya daga kai yana kallonta, tace "Aliyu ni ban fa gane nufin ka ba kayan akwatunan da kasa nayi jere da shi a daki ka hana a kai, toh Abbanku ya sa in xaunar da kai ka sanar da ni ko fasa auren kayi, wannan ai iskanci ne da kokarin mayar da mu kananun mutane da kake, idan ma da matsala ne ai sai ka yi mana bayani, babu mai maka dole tun da kai ka kawo yarinyar nan kana so ba wani ya kawo maka ita ba, yanxu ni ka gaya min ma'anar cewa da kayi kar a kai kayan a dakata" Sudais da har xufa ya fara keto masa ya shafa kai da kyar yace "Mami ba wai na fasa bane, kawai dai akwai matsala... ina son a min alfarmar ce masu su d'aga ko xuwa sabon shekara da xa mu shiga, idan kuma sun ga baxa su iya dagawa ba to gaskiya na hakura, Allah bata wanda ya fi alkhairi a kai na" Mami dake masa wani kallo tace "A daga a kan wani dalili?" Ya kasa dago kai yace "Kiyi hakuri Mami ayi min yanda nace pls, I just want to figure out the problem, Mami kin fa san aure ba don kwana daya ko 'yan watanni ake yin sa ba na har abada ne, Mami I don't want to make marriage mistake in my life don ni bani da burin xama da mace fiye da daya so I want to have the best marriage, ku taimaka ku ce masu a daga har lkcn, idan sun ga yyi masu tsayi to na hakura gaskiya I don't want to cheat my self" Mami tace "Toh shi kenan, Allah sa mu dace, xan yi ma Abban naku bayani" Sudais ya dan yi murmushi a hankali yace "Nagode Mamina, xan je in dawo yanxu" Mami na kallonsa da kyau tace "Wllh ban gane fitar nan da kake kamar me talla ba kwanan nan sudais, da sassafe ka fice baka dawowa sai kusan sha daya, what's wrong with you?" Ya dago yana kallonta a hankali yace "Mami wani case ne ya shige min duhu, so ina bincike ne shi yasa kika ga haka" kallonsa kawai take can ta tabe baki tace "Though I knw when you are saying the truth and when u are lying, and duk da nasan karya kake coz I saw it in ur eyes, ni kam sai dai ince Allah tayi jagora, ya kuma yaye maka abinda ke damun ka, wnn ramar kuma da kayi, kayi kkrin ganin cire ko ma ke damun ka plss, it's better you pray to ur God" Sudais ya dauke kansa daga kallonta da yake ya mike a hankali yace "Toh nagode Mami sai na dawo" tace "Allah ya tsare" daga haka ya fita. Pharmacy ya tsaya ya siya magungunan da Yusuf yyi masa prescribing sannan ya siya fruits kafin ya wuce gidansa, har wani faduwa gabansa ya shiga yi bayan yyi parking cos bai son xuwa ya ga khadijah in pain, ya dai dake ya shiga gidan, kwance ya sameta kamar ko da yaushe a daki idonta a rufe, yawanci duk haka yake xuwa ya sameta kuma ba bacci take ba, yana tsaye a hankali yace "Amira" ta bude idanuwanta a hankali tana kallonsa, yace "Ya jikin" kai ta gyada masa ya durkusa yana bude ledan apples da banana da ya siyo mata yace "Ga Apple nan" ta girgixa kai da sauri tace "Anjima" yace "Toh kin yi sllh?" Gyada masa kai tayi, ya d'an yi shiru sai kuma ya mike yace "Toh tashi ga magani na kawo maki ki sha, you feel more better idan kin sha" kamar xata yi kuka tace "Xan yi amai ni nafi son allura" kallonta ya tsaya yi, can yace "Baxa ki yi ba kawai guda uku ne fa" daga haka ya fiddo magungunan a leda sai kuma ya fita xuwa ya debo mata ruwa, har ya dawo tana kwance ya d'an hade rai yace "Toh tashi mana" mikewa tayi da kyar ya bude maganin gudu uku kamar yanda yace ya bata a hannu ya mika mata ruwa a cup, ta karba tana bata fuska xata yi kuka, ya daure fuska yace "Ki sha Ki ban cup yanxun nan" wayarsa ne ya fara ring ya ciro a aljihu tana ganin haka ta watsa maganin a bayanta tayi saurin kai ruwan baki tana sha dai dai lkcn da ya maido dubansa kanta, da sauri yace "Kin sha?" Ta mika masa cup din tana yamutse fuska, ajiyar xuciya ya sauke a hankali, kokarin amai ta shiga yi da sauri yace "Noooo, don't ko in bata maki rai" ta koma baya a hankali kar ya xagayo ya ga maganin ta jingina da gado yace "Good girl" daga haka ya fita ya kira Yusuf dake kiransa, da sauri ta kwashe magungunan ta watsar a bayan gado tana turo baki, Sudais ya hade rai bayan ya kai wayar kunne yace "Ya aka yi?" Yusuf yace "Ya ta sha?" Sudais yace "It's nt ur concern" dariya Yusuf yyi yace "In dai ka tabbatar ta sha don't leave her alone kar ka kashe yar mutane nan da few hours xata samu miscarriage din in dai magungunan da na rubuta ka siya ka bata" Sudais yace "Ohk" daga haka ya katse wayar ya xauna parlor. Haka Sudais yyi ta xama gidan har magrib amma shiru kke ji, ya duba ta yyi sau ashirin kafin magrib amma banda bacci bbu abinda take hankli kwance, yana fitowa masallaci ya kira Yusuf yace "Kai ni da ina ta xaune gidan har yanxu shiru" Yusuf yace "Bata sha ba toh" Sudais yace "Ya xaka ce haka, a gabana fa ta sha ni ma na bata maganin da ruwa" Yusuf yyi shiru jin haka, sudais yyi tsaki ya katse wayar. har washegari shiru kake ji bbu alamar miscarriage gashi Yusuf yace kar ya kara bata wani, duk ran sudais ya baci, da yammacin washegari Yusuf ya xo gidan, Magungunan ya dauka yana ta kallonsu kamar yanda Sudais ke hararansa shi kuma, can ya balli wasu ya mika ma sudais yace "Bata ta sha" Khadijah dake kwance tana kallonsu kamar xata yi kuka tace "Ni maganin wani iri yake min bana so plss" Sudais ya daure fuska yace "Karba my friend" mikewa tayi hawaye ya cika idonta ta amshi maganin ya mika mata ruwa, daga shi har Yusuf suka kafeta da ido, ta daga gefen Hijab din jikinta tana share hawayen idonta hakan ya bata daman sakin maganin gaba daya a Hijab din cikin dubara sai kuma tayi saurin dage kafarta kamar xata daura kanta bisa kneel dinta, har lkcn kuma hannunta na dunkule kamar tana rike da drugs din, Yusuf yace "Baxa ki sha ba?" Bude baki tayi ta yi kamar ta watsa su ciki sannan tayi saurin xuba ruwa bakin ta tana yamutse fuska har da kokarin amai, da sauri Sudais yace "Don't try that" ta hade kai da gwiwa suna ta tsaye suna kallonta har ta dago a hankali, Yusuf ya juya ya fita sudais ya bi bayansa, Yusuf yace "Toh sai kayi xaman gadi" daga haka ya bar gidan, Sudais na ta xaune har dare amma shiru, mamaki ya dinga yi anya ba yaudararsa Yusuf yyi ba, a fusace yaje har gida ya samesa don jin me yasa yyi masa haka, Yusuf dake dakinsa kwance yace "Toh ka kai ma wani likitan takardar maganin ka tambayesa na menene, I think that's all I can tell you" Bayan kwana biyu sudais ya sake komawa Yusuf office da rana, da damuwa yace "Dr ko xaka canxa wani method din ne, wllh I don't have rest of mind, am afraid kar Mami ta san abinda nake yi, gashi in few weeks time xan je UK, to ya xan yi da yar mutane?" Yusuf yayi dariya yace "Tunda taimakonta kake son yi ka tafi da ita mana" Yusuf ya watsa masa kallo yace "Ko matata ce ke wannan laulayin ina xa ni da ita balle wannan" Yusuf yace "In baka shawara Barrister?" Sudais yyi shiru yana kallonsa, Yusuf ya mike tsaye yace "Wllh ka kyale mata cikinta tunda ka ga haka, Allah kadai yasan me xata haifa, there is power in the baby, banda haka ban ga dalilin da xai sa ta sha drugs din nan har sau biyu ba amma shiru ake ji, just let her pls and idan son samu ne ka taho da ita clinic ko gobe da safe ayi mata scan cos this is almost a miracle" kasa cewa komai Sudais yyi can ya juya ya fita. Washegari kamar yarda Yusuf yace haka Sudais ya sa khadijah ta shirya suka je asibiti don a mata scan, gaba daya jikinsa yyi mugun sanyi bayan result ya fito, shi kadai da Yusuf ne a office din Yusuf din, ita kuma tana reception, Yusuf yace "You see, da haka xaka sa ayi wasting bayin Allahn da basu san komai ba, 2 souls barrister" Sudais bai iya yace komai ba. A hakan dai Sudais ya ci gaba da ba Khadijah kulawa yanda ya kamata, bai rage ta da komai ba a gidan sa, damuwarsa daya yanda ta ki kwantar da hankali har lkcn ga yawan koke koke, idan ya sa ta gaba ta fadi me ke sa ta kuka sai ta ce masa ita bata da kowa yanxu, hakan nasa jikinsa yyi sanyi, sannan hakan ke kara masa kwarin gwiwan ci gaba da taimaka mata, ganin saura yan kwanaki ya fita kasar ya sa ya shiga tunanin wanda xai bar ta da a gidan, idea ne ya xo masa yasa aka nema masa wata dattijuwar da xa su xauna tare da Khadijah a gidan nasa, hakan aka yi bayan matar da baxata haura shekaru hamsin ba ta amince duk wata xai dinga bata dubu arba'in. A yau Khadijah na daki xaune kasan carpet tana shan kunun da dattijuwar da ta dama mata, dattijuwar matar da a ranan tayi kwana uku a gidan duk tunaninta Khadijah matar Sudais ce, su biyu ne dakin Sudais yayi sallama bakin kofa, ta mike da sauri ta iso kofa ta bude tana cewa "Sannu da xuwa yallabai" Gaisheta yyi ta amsa cike da jin dadin yanda yake girmamata sannan ta fita, Sudais ya karasa cikin dakin yana kallon khadijah, wani mugun haske tayi da kyau sai kyalli take, lips dinta yyi pink colour, dauke kai yyi ya isa gefen gado ya xauna, a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya jiki?" Tace "Da sauki" shiru yyi na wasu yan mintuna kafin yace "Am traveling Amira" ta dago tana kallonsa, ya gyada kai yace "Yeah, gobe xan tafi" sauke idonta kasa tayi, lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin sanyin murya tace "Tafiya xaka yi ba bar ni" ya tsura mata ido kafin yyi murmushi yace "Aiki xan tafi yi can, in sha Allah xan dawo when am done" ta kallesa hawayen idonta ya sakko tace "Toh yaushe ne xaka gama" ya wara Manyan idonsa yace "Nima ban sani ba, but da na gama xan dawo ai" kai kawai ta gyada masa amma kana ganinta kasan jikinta yyi sanyi, murmushi ya sake yi yace "Ba ga mama ba xata dinga kula da ke xan bar mata kudi ta dinga siya maki duk abinda kike so, just promise me baxa ki dinga damuwa ba that's all" murya can kasa tace "I promise, amma yaushe xaka dawo?" Dariya ta basa ganin ta yi tambayar daxu yace "Duk sanda kika samu lafiya kika fara cin abinci sosai sannan bakya damuwa xan dawo" xaro ido tayi tana kallonsa, yace "Yes" murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, sae ranan ya fara ganin murmushinta ya dinga kallonta ganin xata dago kanta yyi saurin dauke kai, tana wasa da dogayen yatsun ta tace "Toh naji" yace "Yauwa ko ke fa" wayarsa daya ya Ciro ya mika mata yace "Xan dinga kiran ki in sha Allah" karba tayi a hankali tace "Toh" yace "to tashi ki raka ni" Ba musu ta mike shi ma ya tashi ya nufi kofa sannan ta bi bayansa, a parlor ya tsaya yyi sallama da Dattijuwar ya kuma sanar da ita xai yi tafiya ta dinga masa addu'ar Allah ya tsare yace "Ameen Ngd mama, don Allah ki dinga sa mata ido bata son cin abinci" tace "In sha Allah kar ka samu damuwa" Dubu hamsin ya ba matar ta dinga siya ma khadijah duk abinda ta bukata, ya kuma sanar da ita komai babu gidan Dr Yusuf xai kawo masu, daga haka ya juya yana kallon khadijah dake ta kokarin ganin bata yi kuka ba yace "Toh mu je" har bakin mota ta rakasa kanta a kasa ya kara mata sallama ta kasa daurewa ta fara kuka, duk jikinsa yyi sanyi, a hankali yace "Look Amira ba dadewa xan yi xan dawo ba, ki daina kuka pls" kai ta gyada masa cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya tsare hanya" daga haka ta juya ta koma cikin gida ya bi ta da ido. Kamar kar Sudais ya bar kasar Khadijah ta fara samun lafiya sosai dattijuwar me kirki komai take so shi take mata kafin wani lkci duk babu ramar da tayi sai cikinta da ya fara fitowa, kullum a rana sudais xai kirata kusan sau biyar just to check if she is fine, idan bai kirata ba kuwa ta dinga damuwa kenan, a haka har watanni suka shude. 5 months later. Yau tun da Khadijah ta tashi take ta murna ta rasa dalili, har hirarta ya fi na ko wani rana yawa har da dariyarta wanda da wuya ka ga tayi dariya, Dattijuwar mama suwaiba da take kira da Anty har ta lura da hakan tace "Wannan murnar yayi yawa khadijah ko dai mai gidan ne xai dawo yau" Khadijah dake hada fruits salad xata sha ta daga kai tana kallon mama suwaiba tayi shiru don kuwa gaskiya ne jiya da daddare da suka yi waya da Sudais yace mata yau xai dawo, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da abinda take a hankali, mama suwaiba tace "Toh gwara a tashi a san me xa a girka masa, ki fadi duk abinda kika San yafi so sai in shirya in tafi kasuwa yanxu" Khadijah tayi shiru don har lkcn bata san komai game da Sudais ba balle ta san abinda ya fi so da wanda bai so, hakan yasa jikinta yyi sanyi sosai. A cikin watanni biyar din nan khadijah ta warware jikinta yyi kwari, babu abinda bata ci har da wanda bata ci a da can, wato wake, taliya kai har da tuwo da miyar kuka, wani kyau na musamman tayi don hatta fatar jikinta har wani glittering yake yayi taushi, yanxu kam cikinta ya fito sosai don sai ayi tunanin at anytime xata iya haihuwa don da kyar take yin komai nan ko watannin cikin bakwai, tausayi take ba mama suwaiba ganin yarinya ce sosai wa ya sani ko xata iya haihuwa da kanta ma, hakan yasa in dai ta fita cefane ko siyo wani abun bata rabo da dawowa da magunguna irin na gargajiya da tasan mai ciki na bukata, duk ranakun alhamis kuma tare da mama suwaiba suke xuwa can clinic dinsu Yusuf domin Antenatal a bisa umarnin sudais, damuwar Khadijah daya a lkcn ummarta don ko cikin dake jikinta baya damunta ta kuma rasa dalili, gaba daya tayi kokarin ganin ta mance ta taba rayuwa gidansu Aliyu, amma duk sanda cikinta yayi motsi sai ta tuna shi Aliyun, duk wannan difficulties na rayuwa da ta shiga ko sau daya bata taba jin haushin Aliyu ba kuma har ranta take jin ta yafe masa a lkcn... ko don tana tare da yarinta har sannan ne oho. Khadijah ta kasa hakuri ganin har yamma bata ga sudais ba alhalin yace mata in sha Allah yau yana Nigerian duk jikinta yayi sanyi ta tafi daki ta kwanta, Mama suwaiba kuma ta ki hakura tana ta girke girke a kitchen ita kadai. Sudais na sauka taxin da ya kawo sa har kofar gida ya shiga gidan yana rike da daya daga travelling bag dinsa guda uku da mai taxin ya dire masa a bakin gate, kai kana ganinsa kasan daga turai yake don wani fresh na musamman yyi da haske sai dai ya rame sai idanuwa da hancinsa da suka fito, sosai ya rage bak'in gashin kansa, yyi murmushi ya na amsa gaisuwar da mai gadi ke masa da fara'a yana masa sannu da dawowa sannan yace "Ka shigo min da sauran kayana bilyamin" tun a bakin kofa kanninsa suka rungumesa ko wacce na murnar dawowarsa bayan kusan watanni biyar, Mami dake parlor da Anty Maryam ma sai murmushi suke, lkci daya murmushin Sudais yyi fading ganin Jiddah da yayi xaune parlorn, ya karaso a sanyaye ya duka kasa ya gaida mami ta amsa tana murmushi tace "Sannu da xuwa Aliyu ya hanya?" Yace "Alhmdllh Mami, fatan mun same ku lafiya?" Tace "Alhmdllh" gaisawa suka yi da Anty Maryam sannan ya kalli jiddah yana kirkiran murmushi ta sunkuyar da kai tace "Sannu da xuwa ya hanya?" Yace "Alhmdllh mun same ku lafiya?" Tace "Sure" Rabi'ah da Humairah suka dau bags dinsa xa su kai daki yace "Noo don't worry sisters wancan kadai xaku dauka ku bar wa ennan, xan d'an fita yanxu" da mamaki Mami tace "Ka fita kaje ina daga dawowa, idan ma fitan xaka yi ina xaka da jaka kuma?" Ya sunkuyar da kai yace "Sakon wani abokina ne xan kai gidansu Mami" Mami tace "Ohk, to amma sai ka huta ka ci abinci koh?" D'an shiru yyi sai kuma yace "Mami baxan dade ba xan dawo yanxu" daga haka yasa kanninsa suka dau jakunkunan suka kai masa bakin motarsa sanin ko baya nan ana amfani da motar, ya mike yace "Toh sai na dawo Mami" tace "Toh don Allah kar ka jima ka dawo ka ci abinci ka huta" yace "In sha Allah" yana barin gidan bayan ya hau titi ya dau wayarsa ya shiga kiran khadijah, Khadijah dake kwance har lkcn a daki ta mike da sauri kamar jira take jin ring din wayar ta jawo ganin Sudais ne ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren yyi sallama yace "Amira" turo baki tayi tace "Uhn" yace "How are you" a hankali tace "Fine baka dawo ba kuma" d'an murmushi yyi yace "I postponed the trip xuwa next month in sha Allah" wani irin faduwa gabanta yyi da har sai da ta ji a kirjinta da ya mata sauki kwana biyu sbda magungunan da Yusuf ke bata, hawaye ne ya shiga sakkowa idonta, yace "Hello are you there?" Kasa amsawa tayi ya dinga hello ta katse wayar ta hade kai da gado ta fara rera kuka, sake kiranta yyi ta ki dauka har ya katse ya kara kira, sai a snn ta dauka ta kai kunne taki cewa komai, murya can kasa yace "Amira" ta fashe masa da kuka a hankali, wara ido yyi hade da murmushi yace "Har da kuka kuma?" Ta ki cewa komai, murya can kasa yace "Cry no more, tunda kina son ganina kawai fito gate ki tsaya ni kuma xan taso daga UK yanxu, har kofar gida jirgin xai ajiye ni" mikewa tayi xaune da sauri tace "Don Allah ka bari, ka dawo pls?" yace "Da gaske fa just wait me outside xa ki ganni yanxun nan" katse wayar tayi ta tashi da sauri ta dau Hijab har Kasa ta sa sannan ta fita dakin, Ganin xata fita waje Mama suwaiba da fitowarta kitchen kenan tace "Ya iso halan" Khadijah bata iya ta ce komai ba ta kirkiri murmushi ta fita, a hankali take tafiyar har ta isa gate ta tsaya gabanta na bugawa, tsaye ta ga motarsa bakin gate din suna hada ido ya bude motar ya fito yana murmushi, tsabar farin ciki ta kasa cewa komai amma kana ganin ta kasan she is just happy, ita dai tasan yau da ace mace ce Sudais da ta tafi da gudu ta rungumesa, ya wara mata ido ganin kallon da take masa yace "Toh ko dai in koma tunda kallona xa ki tsaya yi" tahowa tayi ta tsaya gabansa ta sunkuyar da kai tana murmushi, murmushin yayi shi ma murya can kasa yace "How are you Amira" ta kasa dago kai cikin sanyin murya tace "Am fyn, sannu da dawowa" yace "Sannu, ya babies dinmu" dagowa tayi ta kallesa da sauri sai kuma ta juya masa baya, dariya yayi yana kallonta, tayi murmushi tana jan hannunta, yace "Toh mu shiga" tafiya ta fara yi ya bi bayanta bayan ya rufe motar har suka shigo parlor. Xaunawa yayi parlorn suna gaisawa da mama suwaiba dake tayi masa sannu da xuwa, khadijah ma ta xauna kasan parlorn tana kallonsa ko kiftawa bbu, mama suwaiba ta koma kitchen ya maida dubansa kan Khadijah, sauke idonta tayi kasa da sauri, yace "Are you now happy" murmushi tayi tana gyada kai a hankali shi ma yyi murmushin yana kallonta, Kirar ta Mama Suwaiba tayi ta mike ta nufi kitchen ya bi ta da ido, Mama suwaiba tace "Toh ke haka ake yi, sai ki je bayi ki hada masa ruwan wanka, idan kuma abinci xai fara ci sai ki kai masa daki" murmushi khadijah tayi bata ce komai ba, mama suwaiba tace "Toh kin yi shiru kuma" a hankali khadijah tace "Toh bari in tambayesa" daga haka ta juya ta koma parlor, Wayarsa yake dannawa ta duka gefensa ya kalleta yace "Xauna kujera mana, you are stressing ur self and the babies" sauke idonta tayi kasa tace "Dama Anty ce ta ce in tambayeka ko xaka ci abinci a kai maka daki" shiru yyi na wani lkci kafin yace "She is thinking something different, and Mamina ta min abinci a can gida but... Ohk toh kai abincin daki" Tashi Khadijah tayi ta koma kitchen ta karbi abincin da Mama suwaiba ta hada a tray ta wuce can bedroom da shi, Sudais ya mike ya bi bayanta, karban abincin yyi a hannunta ya ajiye kan rug sannan ya xauna yace "Ke kin ci abincin" tace "Na ci daxu" yace "Daxu daban, yanxu daban, so xauna mu ci" dafa gado tayi xata xauna a kasa yace "No ki xauna saman gado" xaunawa tayi gefen gado ya debi abincin a plate ya sa spoon sannan ya mika mata ta amsa a hankali tace "Nagode" ya debi kadan a wani plate din dai dai nan wayarsa yyi ring dubawa yyi da sauri ya ga Mami ce, ya d'an bude ido sannan ya daga, daga daya bangaren Mami tace "Wai daga dawowa ina ka tafi haka Aliyu? Are you even okay" a hankali yace "Gani nan tahowa Mami am sorry" katse wayarta tayi, ya ajiye wayar yana kallon abincin, samun kansa yyi da Kasa cin abincin, ya rufe yace "Amira xan je gida Mami na jirana idan kin cinye wannan sai ki kara da nawa" Bata ce komai ba sai wasa da cokalin hannunta take, ya mike yace "Kilan xan xo gobe da safe, take care of ur self" daga haka ya juya ya fita, hawaye ne ya cika idonta ta rasa dalili abincin duk ya fita ranta ta kasa ci ta ajiye tana goge hawayen dake xubo mata, Sudais na fita ya tuna bai shiga da kayan da ya taho mata da su daga UK ba, ganin xai kara bata lkci kawai yyi deciding ya bar sa a motar sai gobe idan ya xo. Ko da ya koma gida kawai yana cin abincin da Mami tayi masa ne amma gaba daya hankalinsa na kan Khadijah don bai san ko ta ci abincin da ya debar mata ko bata ci ba, Mami dake xaune ta sa shi gaba da jira har ya gama cin abincin sannan tace "Kun yi waya da jiddah xaka dawo yau ne?" Girgixa kai yyi duk da faduwar da gabansa yyi a hankali yace "Aa mun ma kwana biyu ba mu yi magana ba, fushi take ai da ni" Mami tace "Toh wasa wasa gashi har watanni kusan shidda da kace a daga biki yyi, yanxu kuma ya ake ci" kasa kallonta yayi ya fara kame kamen rufe warmers din abinci, strictly tace "Magana nake ma ka Aliyu" da kyar ya dago ya kalleta yace "Toh Mami a sa bikin nan da wata daya xuwa biyu in sha Allah" wani kallo ta watsa masa tace "Me sati biyu ko uku yayi da har sai an kai wata biyu kuma?" Ya shafa kai yace "Dai dai wannan lkcn xan koma UK kuma xan jima sosai kafin in dawo kinga kawai ana bikin a lkcn sai mu tafi tare da ita" Mami tace "Allah ya kai mu, xan ma Abbanku bayani" yace "Nagode Mami" daga haka ya mike yace mata xai kwanta ya wuce bedroom dinsa. Yana shiga dakinsa khadijah ya kira, tana dagawa yace "Kin gama cin abincin?" Turo baki tayi tace "Na koshi" yace "Baki ci ba kenan?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Me kike yanxu?" Tace "Na kwanta" yace "Tashi ki je ki dau abincin ki ci idan ba haka ba baxa ki ganni gidan nan ba for plenty days" tashi tayi xaune da sauri tace "Ni ban ce baxan ci ba" yace "Toh je ki ci" ta mike da kyar tace "Toh" yace "Idan kin gama ki kirani" gyada masa kai tayi kamar yana ganinta ya katse wayar. Sosai ta ci abincin ta hada har da wanda ya dibar ma kansa, tana gama ci ta dau wayar ta kirasa, sai da ya kusa katsewa ya daga, jin muryarsa tace "Bacci kake" a hankali yace "Yea, kin gama cin abincin?" Tace "ehh na cinye" yace "Good Mami" murmushi tayi tace "Toh kayi baccin, byee" murmushin shi ma yyi ya katse wayar. Xuwan Yusuf gidansu da daddare ne saving grace dinsa don da shi da fita kuma sai gobe, bayan Yusuf ya gaisa da Mami suka tafi dakin Sudais yana tambayar sa ko yayi ciwo a UK ne don ya rame sosai, bayan kusan minti talatin Yusuf yace xai tafi suka fito tare da sudais da yace ma Mami xai rakasa, sai da suka shiga mota Yusuf yace "Kaje ka duba mai cikin ka?" Sudais ya hade rai yace "Mai cikina kuma" dariya Yusuf yyi yace "Toh ai kusan baka da banbanci da uban yaran, kai ma uba kake a gare su kama fi sa xama masu uba kan ubansu" tsaki Sudais yyi bai ce komai ba, Yusuf yace "But don Allah Sudais da yau ko watarana xaka ga uban unborn babies din nan me xaka masa?" Sudais yyi wani murmushi da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "I won't even look at him twice yaran da xata haifa sun ishesa" Yusuf yace "What if ya xo wataran yayi claiming yaran fa?" Wani kallo Sudais yyi masa baki bude, can yyi wani dariya yace "Wllh wllh I will sue him, sai na sa yyi shekaru da dama a gidan yari" Yusuf dake driving ya wara ido yace "Tohhh, kenan yaran ka ne ba nasa ba" Yusuf na dariya ya kare maganar, Sudais yyi banxa da shi, Yusuf yace "Toh why not bayan ta haihu ka aureta kawai Sudais" juyawa Sudais yyi yana kallonsa da wani expression, can ya dake yace "Ko saboda me?" Yusuf yyi murmushi yace "Saboda ka ji dadin ci gaba da kula da ita da yaran da xata Haifa kwanan nan, kasan a yanxu kai ne ubanta kai ne uwarta, i mean kai ne gatan ta, don haka sai ka ci gaba da xama gatan nata har karshen rayuwarta, nan da shekaru biyu kai ma ta haifa maka naka yan biyun ba na wani ba" Girgixa kai Sudais yyi bayan ya dauke idonsa daga kallon da yyi ta ma Yusuf yace "I didn't blame you Dr, why?? Because am very sure kafin ka xo gidanmu yanxu daga club din da ka saba xuwa kake, and definitely idan ka je club dole sai ka sha ruwan can na sani, soo no offense, u are drunk...." Dariya kawai Yusuf yake yace "Kai kuma tun bayan haduwarka da marainiyar nan ka daina xuwa can koh? Thank God we where both drunkards before" Sudais da yyi mugun hade rai yace "Drop me here my frnd" Yusuf yyi parking yace "Ji dan iska kamar wani driver din sa wai drop me here my frnd" Bude motar Sudais yyi ya fice ya juya yana masa wani kallo, da yatsarsa yyi masa xagin turawa yayi wucewarsa, dariya kawai Yusuf yake ya ja motarsa ya wuce gida, Da kafa Sudais ya karasa gidansa, Mama suwaiba kadai ce parlor tana cin abinci TV a kunne, tana ganinsa ta mike da sauri tana masa sannu da xuwa yace "A'a yi xaman ki mama" Mama suwaiba ta koma ta xauna tace "Toh nagode" yana son tambayarta khadijah amma yyi shiru, can ya mike ya wuce bedroom, kwance ya ganta tayi bacci tana rufe da bargo, ya karasa kusa da gadon yana kallonta, dukawa yyi dai dai fuskarta murya can kasa yace "So early?" Ko motsi bata yi ba alamar ta jima da yin baccin, a hankali yyi murmushi ya kai hannu dogon hancinta ko mai ya tuna yyi saurin withdrawing din hannunsa ya mike ya kashe mata wuta ya fita daga dakin, Sallama yyi ma Mama suwaiba ya nufi kofa ta bi sa da kallon mamaki, yau ma da ya dawo baxai kwana gidansa tare da matarsa ba, wannan wani irin aure ne a gantale, har ya rufe kofa kallonsa take baki sake. Washegari lahadu Khadijah na xaune parlor da tuwo da miyar kuka da mama suwaiba tayi mata, da cokali take cin tuwon mama suwaiba kuma na kitchen tana wanke wanke, bude kofa aka yi ta daga kai da sauri sudais ya shigo parlorn rike da babban jaka, ajiye jakar yyi yana wara ido yace "Kaiiii yanxu xa ki iya cinye wannan tuwon Amira?" Rufe fuskarta tayi da kujera da sauri tace "A'a fa xan rage in ci anjima" dariya yyi ya juya ya fita ya shigo da daya jakar ya ajiye sannan ya xauna kan lallausan carpet da take xaune yace "Ci da yawa abin ki kin ji, sai ki haifo mana yara masu karfi" bata dago kanta ba har lkcn yyi murmushi ya bude zip din jakar ya fara fiddo kayan ciki, sai bayan da ya Ciro kayan jakunkunan gaba daya sannan yace "Here... you like them?" sai a sannan khadijah ta dago a hankali tana kallon kayan, kayan babies ne masu tsada ko wanne set biyu, shiru ta yi tana kallon kayan, ya ware nata dogayen riguna masu kyau gudu hudu yace "Wannan kuma naki" sauke idonta da ya kawo ruwa tayi a hankali, ya hade rai yace "Baki so ne xa ki min kuka" bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ta hade kanta da kujera, yyi shiru yana kallonta, can ya fara mayar da kayan gaba daya jaka yana gamawa ya kai jakunkunan daki sannan ya nufi kofa ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya wuce. Har bayan kwana biyu Sudais bai je gidan ba duk da he is just trying not to go amma hankalinsa gaba daya na can, sosai hankalin khadijah ya tashi don tasan kilan fushi yake ne ya sa, tana son kiransa amma ta kasa, ganin baxata iya jurewa ba kuma ta kira sa, a lokacin yana gida bedroom din Mami suna hira da Anty Maryam, ganin kiran yyi ta kallon screen din kafin yyi silencing wayar ya mike yace "Mami bari in tafi in shirya xan fita yanxu" daga haka ya bar dakin bayan yayi ma Anty Maryam ma sallama, Mami ta tabe baki tace "Kwata kwata Aliyu ba shi da gaskiya yanxu, I really don't knw what he is up to, tun ma kafin ya bar kasar months back na lura da haka kuma gashi ya dawo ya ci gaba da behavior din, there is something big he is hiding kuma shi ya hanasa auren ma, dubi fa yanda ya axalxalemu a kan jiddah duk ya daga mana hankali shi aure amma lkci daya kinga kuma abinda yyi, ni na haifesa ba shi ya haifeni ba don hka I will fish out what he is up to soon" ita dai Anty Maryam bata ce komai ba sai kallon yayarta take. Sudais na barin gidan ya tafi can gidansa, Khadijah na kitchen tare da Mama suwaiba suka ji an shigo parlorn, fitowa tayi tana ganinsa ta turo baki, ya karaso parlorn ya xauna yana idonsa a kanta, ta sunkuyar da kai ta isa kusa da shi ta xauna a kasa, yace "How are you?" Kin cewa komai tayi, ya d'an yi murmushi ya dau wayarsa yana danna, a hankali tace "Ina yini" ya kalleta yace "Ban yini ba" kamar xata yi kuka tace "Ni ban san me nayi maka ba" yace "Na kawo maki abu kince baki so mana" xaro ido tayi tana kallonsa tace "Ni??" Yace "Ehh" murmushi tayi tace "I don't knw how to thank you that day, that was why...." Hawaye cike idonta ta kare maganar, Kallonta kawai yake bai ce komai ba. Haka nan rayuwa ya ci gaba da kasancewa bayan dawowar sudais Nigeria, duk safiya, rana har da daddare xai xo ganin khadijah, kayan ciye ciye yake xuwa mata shi idan xai xo da daddare wani lkcn shi ma ya ci abinda xai ci a gidan, ita dai Mama suwaiba na son sanin me ya janyo bai kwana gidan amma bata san wa xa ta tambaya ba tunda ba wani hira can suke yi da Khadijah ba, toh ko don tana da ciki ne yake haka, tambayar da ta dinga yi ma kanta kenan har hakan yasa ta d'an fara jin haushin sudais din, rana daddaya ne xai shigo gidan ba tare da kayan baby ba, xuwa yanxu irin siyayyar kayan baby da yyi mata sai ayi xaton yara goma xata haifa, komai ya gani ya Burgesa sai ya daukar mata. A haka har watan haihuwar Khadijah ya tsaya, mama suwaiba bata yi kasa a gwiwa ba wajen bata taimako irin na gargajiya don tausayi take bata, kusan duk yamma sudais sai ya lallaba Yusuf sun je gidan kawai don ya dubata, har ransa yake fargabar kar abu ya sameta, wani sanyi tayi gaba daya a kwanakin ko da yaushe a kwance xaka ganta, idan ya tambayeta ko akwai inda ke mata ciwo sai tace babu ko ina. Ranan Sunday da sassafe ya shirya ya fito parlor yana kallon Mami dake dinning yace "Mami xan fita in dawo" tace "Ranan lahadin ma?" Murmushi yayi yace "Mami it's urgent ne, kuma akan..." Katse sa tayi tace "Aliyu" ya dago da sauri, bata fuska yayi yace "Mami wllh duk kika ce min Aliyu sai gabana ya fadi, cos u always call that name when serious" ta masa wani kallo tace "Toh da meye sunan naka?" Yar dariya yyi yace "Sudais mana" tace "Ni na sa maka sudais?" Dariya yyi sosai yace "Ni na sa ma kaina Mami Aliyun sunan tsoffi ne I...." Ta katse sa tace "What ever.... kaje duk inda xaka ka dawo ka sameni in sha Allah gobe xa a kai kayan can da kasa nayi jere da su a daki" yace "Allah ya kai mu Mami" daga haka ya fice daga parlorn, gidansa ya nufa direct. Mama suwaiba na kitchen tana aiki, bai jira sun gaisa ba ya wuce daki, xaune ya ga khadijah ta takure waje daya, Ya durkusa kusa da ita da sauri yace "Are you okay Amira?" Ta girgixa masa kai da kyar, da damuwa yace "What's wrong? Kina jin ciwo ne jikin ki?" Karfin halin nuna masa bayanta tayi, yace "Yana maki ciwo?" hawayen da ya gani idonta ya rikitar da shi lkci daya ya dagota yace "Let get to the hospital....." Kwace kanta tayi ta koma ta durkushe a wajen tana rintsa ido tace "Ya daina" Allah ma yasan daurewa kawai take, ga ciwon kamar ana kara mata take ji, bata san lkcn da ta sakar masa kuka ba a hankali tace "Wayyo ka taimakeni plss" bai sake saurararta ba suka fita dakin, Mama suwaiba bata ma san sun bar gidan ba tana kitchen, har suka isa asibiti Khadijah bata sani ba duk ta rikice, wani asibiti me tsada ya kai ta banda Wanda Yusuf ke aiki, bbu bata lkci nurses suka amsheta da wani likita, yanda Sudais ya daga hankali sai ka rantse ance masa mutuwa xata yi, khadijah bata yi fatan kara experiencing kwatankwacin irin wahalar da ta sha na labour ba har ta bar duniya, tun da suka je take wahala amma shiru, Sudais ya kira Yusuf ya sanar da shi suna asibiti, Yusuf yace "Me yasa baka kawo ta asibitin mu ba" Sudais yace "Just" Yusuf yace "Toh wani asibitin ku ke?" Sudais ya gaya masa, tabe baki Yusuf yyi yace "Kudi ya ma yawa ne, any way idan ta haihu ka kirani" Sudais ya katse wayar ya jinginar da kansa da kujera yana mai yi ma khadijah addu'a a xuciyarsa, bayan awanni biyu ya sake kiran Yusuf, Yusuf yace "Ya? is she delivered" a hankali Sudais yace "Har yanxu" Yusuf yace "Toh fah, ko dai cs xa ayi mata, dama am thinking it will be difficult ta haihu da kanta, any way bari in taho yanxu" bayan wani lkci Yusuf ya xo, dariya Yusuf ya shiga yi ganin yanayin sudais yace "Kaiiii... To ai ko jiddah ke labour sai haka bawan Allah" Shi dai Sudais bai tanka sa ba, yawanci likitocin asibitin duk Yusuf ya san su, don haka har labour room yaje gun khadijah, ya ji tausayinta ba kadan ba ganin irin dauriyarta, baxa ka taba cewa haihuwar fari xata yi ba tsabar karfin halinta, bayan wani lkci Yusuf ya bar asibitin bayan ya kwantar ma da Sudais hankali yace labour kawai take babu wani matsala, wasa wasa dai shiru ake ji wanda hakan yasa likitocin suka kira Sudais office nan suka nuna masa it's better ayi mata Cs kada yaran da ita kanta su samu matsala, kusan ba da son ransa yyi signing takardar da aka basa ba, bayan wasu yan mintuna aka fitar da Khadijah labour room xuwa Theatre, anan kuma aka yi nasarar ciro mata boys dinta, sai dai sun jigata kamar yanda ita ma ta jigata. Khadijah ta bude ido a hankali ta ganta kwance wani ward, Mama suwaiba dake gefenta ta sakar mata murmushi tace "Sannu Amira, Allah ya baki lafiya" tashi xaune take son yi taji kamar an danneta ta kasa tashin, Mama suwaiba ta mayar da ita ta kwantar tace "Aa kinga ba ki da lafiya ki yi kwanciyar ki kawai kinji" sai a snn taji wani axaba tun daga cikinta har xuwa kafafuwanta, wasu hawaye suka shiga sakko mata cikin rawar murya tace "xafi nake ji" fita Mama suwaiba tayi sai ga ta ta dawo da likita, likitan ya duddubata ya mata Allah ya sauwake sannan ya fita, Nurse ce ta shigo ta mata allura ta fita, bayan fitar ta sai ga Sudais ya shigo khadijah ta bude ido tana kallonsa, ya karaso gefenta cikin sanyin murya yace "Amira...." Bata iya ta amsa sa ba, a hankali ya sa hannunsa cikin nata cikin sanyin murya yace "Be strong Amira, you will get better in sha Allah.." Hawaye ya sakko idonta sai dai bata ce komai ba, ya sakko da fuskarsa dai dai nata yana murmushi a hankali yace "Baki tambayi yaran ki ba ko bakya son su?" Ta gyada masa kai, shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi yace "Toh sai ki bani su" Murya can kasa hawaye na xuba idonta tace "Na baka" ya fadada murmushin fuskarsa yace "Sure?" Throughout ranan Sudais was by her side tare da Mama suwaiba, Yusuf ma ya xo yyi mata barka ya wuce, ba a nuna mata yaran ba kuma bata tambaya ba har ta sa a rai kila ma mutuwa suka yi wanda tunanin hakan yasa mata nutsuwa sosai don har ga Allah bata ma son ganinsu, haka kawai taji bata san su, Sudais dake lura da cewa she was so depressed ya dinga kokarin ganin ya sa ta walwala sai dai ta kirkiri murmushin karfin hali, sallah kadai ke sa shi ya bar gefenta, tun karfe shidda mama suwaiba ta koma gida dauko kaya, duk kiran da aka dinga ma sudais a waya kin dagawa yyi daga karshe ma ya sa wayar a silent, A daren ranan bayan sudais yaje sallar magrib da ya tashi dawowa ya shigo rike da daya daga yaran wata nurse na biye da shi da dayan, tun da suka shigo khadijah ke kallonsu, yana murmushi ya ajiye babyn a gefenta, sosai gabanta ya fadi ta dinga yi ma jaririn wani kallo ganin kamar Aliyu yyi kaki, babu abinda new born din ya mance na ubansa tun daga haske, hanci, kai har bakinsa... Nurse din ta ajiye mata daya carbon copy din yaron dake gefenta kusa da d'an uwansa tana murmushi tace "Congrat mum twins, Allah ya raya su" daga haka ta fita, a hankali Sudais yace "Ain't they cute? I mean the innocent new souls" khadijah bata san lkcn da ta fashe da kukan takaici ba cikin rawar murya tace "Don Allah ka tafi da su, wllh bana son su, ni dai bana son su ka maida masu su" kuka take sosai kamar xata shide, ganin haka Sudais ya mike ya dau yaran gaba daya ya fita da su dakin. Sudais na dawowa dakin ya dinga kallonta har ya iso kusa da ita yace "Me yaran suka maki da kike cewa baki son su Amira" kin cewa komai tayi, ya ja kujera ya xauna yyi shiru, bayan kusan minti goma wayarsa ya fara ring dauka yyi ya duba yaga Mami ce, yau ta kirasa yyi sau hudu duk bai dauka ba, ya mike yana kallon khadijah da ta lumshe idonta yace "Mama xata dawo yanxu, ni xan je gida Mami na ta kirana, gobe da safe xan xo kin ji?" Bude ido tayi tana kallonsa yace "Be strong, kuma kar ki sake kuka plss" gyada masa kai kawai tayi ya juya ya fita. Bayan fitarsa da yan mintuna mama suwaiba ta shigo, sannu ta dinga yi mata, ta xauna kusa da ita tace "Kin ma ga yaran naki kuwa Amira" Khadijah ta hade rai tace "Ehh" daga haka ta rufe idonta, ana yin isha mama suwaiba tayi sallah a nan ward din da bayan ta shimfida dankwalinta a kasa, bude kofar ward din aka yi nurses biyu suka shigo da babies din Khadijah ta rufe ido da sauri, kan gadon jariran dake kusa da na khadijah suka kwantar da su, daya daga nurse din na kallon Mama suwaiba da ta mike ganin yaran tace "Xa a iya ba su nono yanxu idan suka bukaci haka" daya nurse din na nuna mata babyn kusa da ita tace "Wannan shine Hasan, na kusa da shi kuma Hussain" Mama suwaiba tace "Maa sha Allah, Allah ya raya mana su" nurses din suka amsa da amin sannan suka fita, mama suwaiba sai kallon kyawawan fararen yaran take tana murmushi sai dai abinda ke daure mata kai daga Sudais har Khadijah babu wanda taga yaran suka biyo, a ranta tace "Ikon Allah, to ko wa suka biyo su kuma maa sha Allah" kallon khadijah tayi da ta ki bude ido har lkcn, tausayinta ta dinga ji don idan akwai abinda ta tsana shine ayi ma mace operation. Karfe sha daya da wani abu mama suwaiba ta kwanta a spare bed dake Dakin, har ta fara bacci taji kukan jariri, ta bude ido da sauri taga daya ne ke motsi, ta Mike ta daukesa tana kallon khadijah, Bata san Khadijah na jin yaron ba sai dai idonta a rufe yake har sannan, Mama suwaiba da a tunaninta bacci take ta rungume yaron ta xauna, haka mama suwaiba ta dinga lallaba su tana basu ruwa a feeder ganin yunwa suke ji har Washegari da safe. Karfe tara saura sudais ya shigo ward din,sanye yake da farar shirt da black jean yayi kyau ba kadan ba, direct gun babies dake cikin cot dinsu bayan an masu wanka ya nufa, ya dau daya ya lumshe ido ya daura lips dinsa a soft cheek din babyn, juyawa yayi ya kalli khadijah dake bacci, jikinsa yyi sanyi don da alama mama suwaiba ta je gida dauko abu, daga ita sai yaran ne a ward din, nobody to stay with them, banda tsotson baki bbu abinda yaron dake hannunsa yake alamar yunwa ya kalli d'an uwansa shi ma yaga haka yake da bakin, yana ta tsaye dakin bai tashi Khadijah ba mama suwaiba ta shigo bayan sun gaisa yake tambayarta ko Khadijah ta fara basu abinci ne, Mama suwaiba tace "Aa bata basu ba da nayi mata magana daxu ce min tayi cikin ta na ciwo har na fita na kira wata nurse, tun jiya ruwa kawai nake ba su" Sudais bai ce komai ba ya xauna saman kujera, bayan wani lkci yace "Toh ita ta fara cin abinci ne?" Mama suwaiba tace "A'a ga shi nan dai kunu ma na je gida na dama mata, cewa likitan yyi shi kadai xata iya sha anjima, toh kafin ta tashi shine naje nayo" yace "Toh sannu mama" ya d'an jima a dakin kafin ya bar asibitin kuma har lkcn khadijah bata tashi ba. Wasa wasa yau kwanansu uku a asibiti amma khadijah taki ba yaran nono, da farko cewa take cikinta na mata ciwo baxata iya ba sudais ya siyo masu madara na jarirai mama suwaiba na basu, har abun ya fara daure ma mama suwaiba kai don har sannan khadijah taki daukan yaran ta, tunda tayi kokarin bata su sau daya ta ki amsan su ta kuma ga kamar ranta ya bace bata sake bata su ba. Satinsu daya da kwana daya aka sallamesu asibitin bayan Sudais ya biya bill din, duk yaran na hannun mama suwaiba don khadijah bata amshi ko daya ba, ya bude motar bayan sun isa gida ya amshi dayan yaron hannun Mama suwaiba, ta fito rike da dayan ta nufi cikin gida, kallon khadijah yyi da ta fito ita ma ya mika mata yaron, dauke kai tayi ta bar wajen da sauri tace "Ni dai baxan iya ba" Wani kallo ya mata da mamaki yace "Kee" ta juyo tana kallonsa, mika mata yaron yyi fuskarsa daure yace "Karbesa" kamar xata yi kuka tace "Xai iya faduwa pa" yace "Ya fadi" ganin yanda ya tsare ta da ido ta karbi yaron hawaye har ya kawo idonta ya yi gaba ya bar ta gun tsaye, a hankali ta bi bayansa ba tare da ta bari ta kalli yaron hannunta ba, sudais ya karbi yaron hannun mama suwaiba ya wuce bedroom da shi khadijah ta bi bayansa, gefen gado ta xauna ta ajiye yaron kan gadon, yana kallonta yace "Basu abinci yanxu" da sauri tace "Ai naga sun sha madara fa, ni....." Katse ta yayi yace "Baki son yaran nan koh Amira?" Ta kallesa ta gyada kai a hankali kamar xata yi kuka, yana mata wani kallo yace "Dama kin san baxa ki so su ba kika yarda kika haifo su duniya, me yasa baki amince an raba ki da su tun a ciki ba?" Cikin rawar murya tace "Toh ai babu kyau" yace "Ohk.... abinda kike masu yanxu da kyau kenan" shiru ta yi hawaye na sakko mata, yace "Kin san Allah idan baki basu abincin su ba am leaving here now, kuma wallahi babu ruwana da ke, are you this wicked?" da sauri tace "Kayi hakuri xan basu" tana magana hawaye na xuba idonta don ita har ranta da gaske bata son yaran, Sudais yace "Toh ba su yanxu" tana share hawayen idonta ta fara bude zip din rigarta xata sauke rigar yayi saurin dakatar da ita "Kee haka aka ce maki ake yi?" Kamar xata yi kuka tace "Toh ai ban iya ba" juyawa yyi ya fita sai gashi tare da mama suwaiba, yana tsaye ta gwada mata yanda xata yi tana dariya sudais ya juya ya bar masu dakin, har da kukanta ita wai xafi take ji, Mama suwaiba ta dinga lallaba ta don ita ma tausayin yaran take ganin basu samu gatan shan nonon uwarsu ba tun da suka fito duniya, da kyar ta amince ta ba dayan ma, a ranta kuwa tasan shine farkon shan su kuma shine karshe don ita dai baxata iya ba. Kwanansu biyu da dawowa daga asibiti Sudais ya shigo dakin da Khadijah take da safe, xuwan sa kenan gidan, farar Gezna ce jikinsa dake ta kyalli, waya ne kare kunnensa ya shigo dakin yana magana amma can kasa kasa, ya nufi gun babies dake kwance yana kallonsu kamar yanda Khadijah da ke tsaye gaban madubi ke ta kallonsa tun shigowar sa, Sudais is just the real definition of handsome, duk da wayar da yake gaba daya hankalinsa na kan yaran dake ta tsotson baki yana murmushi, xuwa jikin khadijah yyi kwari sosai don har aikin ya gama warkewa, sosai kirjinta suka ciko har ciwo suke mata amma taki ba ma yara abinci, yanxun ma mama suwaiba ce ta shigo da su ta kwantar ko xata tausaya masu ta basu nono, Sudais ya mayar da wayarsa aljihunsa ya juya ya kalleta tayi saurin dauke kanta, ya xauna gefen gadon yace "I know baki abinci ba yau" ba tare da ta kallesa ba tace "Na basu ka tambayi Anty" bai ce komai ba, bayan wasu mintuna yace "Wani sunan za a sa ma babies din?" Still taki kallon inda yake tace "Nima ban sani ba" yace "Baki sani ba kuma?" Tace "Ko wanne ma ka sa masu" yace "A'a ke xaki xaba da kanki ba yaran ki bane" kin cewa komai tayi, yace "Am talking to you Amira, kuma akwai inda xa ni" ta langwabar da kai a hankali tace "Toh Muhammad da...." Sai kuma tayi shiru, yace "Da wa?" A hankali ta saci kallonsa tace "Kai" ya buda ido sosai yace "Ni kuma?" Tace "Ehh, ur name" murmushin sa mai kyau yyi yace "Aa ki xabi wani sunan dai Amira" hawaye ya kawo idonta tace "Ni kai nake so a sa" Yace "Aliyu kike nufi?" Ta gyada masa kai, wani murnushin ya sake yi yace "Sunan mahaifinsa dai kenan" da sauri khadijah da gabanta yyi mugun faduwa tace "Noo, Brr Aliyu Sudais nake nufi not Dr Aliyu Turab" Shiru Sudais yyi yana kallonta, mikewa yayi bai sake cewa komai ba ya fita yana murmushi. Raguna biyu sudais ya yanka ma 'yan biyun, Hasan aka sa ma Muhammad, Hussain kuma Aliyu, kusan duk sadaka yyi da daya ragon ya bar ma khadijah daya mama suwaiba ta gyara mata, ita dai mama suwaiba kanta ya gama daurewa taga babu me xuwa barka tun dawowarsu, shiru kuma ba xancen taron suna gashi har an gyara rago, Yusuf kadai ya xo gidan a ranan, nan xuciyarta ya fara wani tunanin anya wa en nan ma'aurata ne ma kuwa, don ga dukkan alama wnn dai ba aure bane domin kuwa tun xuwanta bata taba ganin Sudais ya kwana gidan ba, amma meye tsakaninsu? Sudais na bedroom dinsa a can gidan Abbansa da yamma, shigowarsa gidan kenan tun safe da ya fita, Anty Maryam ce ta shigo dakin ya juya yana kallonta sannan ya gaisheta ta amsa da murmushi tace "Kasan an kai ma jiddah kaya kuwa Aliyu, and sati biyu aka sa bikin from today" kasa ce mata komai yyi da farko baki bude, can yace "Amma dai ni babu wanda ya gaya min, sati biyu kuma Anty, what's d rush for, ni Wllh jiddar nan maganar gaskiya ta fitar min a kai, don Allah ni dai Anty...." Dafe kansa yyi yace "Ohh God, sati biyu fa ku ka ce?" Tabe baki Anty Maryam tayi ta juya ta bar masa dakin, zaunawa yyi gefen gado yana rike da kansa, can ya dago ya tashi ya fita, dakin Mami ya shiga ya sameta tana waya ya tsaya ya jira har ta gama sannan ya marairaice yace "Mami Anty Maryam ke ce min...." "Saura sati biyu bikin" Mami ta karasa masa tana masa wani kallo, tsaye yyi yana ta kallonta can ya juya ya fice a dakin, Mami ta fito ita ma ganin dakinsa ya koma ta fita compound, gun drivern gidan ta nufa, ya gaisheta da ladabi ta amsa masa tace "Musa, ina son ka min wani d'an aiki ne don Allah" with respect yace "Toh Hajiya aikin me xan yi" Tace "Ina son idan sudais ya fita gidan nan ka bi sa ka gano min ina xa shi, ko yanxu ko anjima ko da daddare" da mamaki yace "Barrister?" Tace "Shi" yace "Toh in sha Allah Hajiya" Har ta fara tafiya ta juya tace "And be very very careful you knw who you are dealing with" Sorry it's nt much, long chappy ltr in sha Allah. Mami na shiga parlor Sudais dake tsaye kusa da window din bedroom dinsa ya sauke curtain din ya bar jikin windan ya rungume hannayensa kamar me naxari, can kuma ya nufi study area dinsa ya ja kujera ya xauna, then... What's Mami telling Musa? Ya kusa minti talatin xaune yana jiran ya ji fitar musa a gidan da mota domin kuwa hakan kadai xai sa ya cire wani xargin da yake a xuciyarsa, amma har kusan magrib shiru Musa bai fita ba, Sudais ya tabe baki ya mike ya tafi ya dauro alwala ya dawo ya xauna, lumshe ido yyi duk jikinsa yyi sanyi "Jiddah? Sure yasan ya so jiddah ba kadan ba a da can, but he just don't knw what came over him all of a sudden yaji kawai ta fice masa a kai, gashi dai babu abinda tayi masa, ko don an takura sai yyi auren ne yake jin hakan, gaba daya ya ma rasa tunanin da xai yi a lkcn, toh shi yanxu ya xai yi da Khadijah da little babies dinta idan aka tilasta sa yin aure yanxu, bude ido yyi ya xauna da kyau yana naxarin idea din da ya xo masa, ya kama mata wani apartment din kenan? Shafa kansa yyi yana kara naxarin shawaran a ransa, jin xa a tada sllh ya mike ya nufi kofa ya fita dakin, ana idar da sllh ya dawo daki ya dau makullin motarsa ya fita, ce ma Mami dake parlor a xaune yyi sai ya dawo ba tare da ta kallesa ba tace "Allah ya kiyaye" yana shiga motarsa ya fita compound din bayan mai gadi ya bude masa gate, sai da ya kusa isa titi ya yaga musa ya danno kan mota xai fito gidan a guje ta madubinsa, Sudais ya hau kan titi driving slowly yana yana kallon musa dake can baya ta madubi, a hankali shi ma musan ke driving din, Sudais yyi murmushi ya kara gudun motar sai yaga shi ma ya kara, gidansu Yusuf ya nufa musa na biye da shi a baya har lkcn yana parking a waje ya fito ya ga musa nesa da shi a motar yyi kamar bai gansa ba ya shiga gidan, bai samu Yusuf a gida ba duk da ba gidan yyi niyyar xuwa ba, ya tsaya har suka d'an yi hira da mahaifiyar Yusuf sannan ya mata sallama ya wuce, gida ya koma yyi parking a waje ya fita ya shiga gidan, tare da mai gadi ya ga musa a xaune yana kallonsa yace "Same ni a waje musa" daga haka ya fita gate din, Musa ya mike ya bi bayansa sai dai fa ya tsorata, Sudais na kallonsa da kyau yace "Hajiya ce ta sa ka bi ni ka ga inda xa ni daxu?" in ina musa ya fara yi, Sudais ya daure fuska yace "Malam amsa min tambayata" gyada kai musa yyi yace "Kayi hakuri barrister umarnin da Hajiya ta bani kenan" Sudais yace "Ohk naga alama, this shud be ur 1st and last, ko da wasa ka kuskura ka sake bin bayana a mota I won't take it likely with you" daga haka ya shiga gida ya bar sa tsaye gun. Sudais na shiga daki yayi dialing number jiddah, bayan ta dauka suka gaisa murya can kasa yace "Kina ji na jiddah?" Tace "Ina ji, ya su Mami?" Yace "They are fyn, ina son mu yi wata magana ne da ke, are you alone?" Tace "Yeah ni kadai ce, hope all is well" yace "Noo, Jiddah plss ki min wata alfarma don Allah" jin tayi shiru ya kwantar da murya yace "look jiddah am still yet to be settled, they are a lot of things I have not fixed right, beside ke ma fa ba wai kin gama karatun nan bane, why not ki gama nima nayi settling abubuwan dake gabana before any other thing, why the rush" ita dai tayi shiru tana saurararensa har ya gama, ta d'an yi murmushi tace "So what are you insinuating?" Ya lumshe idanuwansa ya bude a hankali yace "A kara daga bikin jiddah..." Tace "Uhm Aliyu kenan, ai ba wai na rasa manema bane kawai dai ina sonka ne fisabillah kamar yanda kai ma kake so na a baya, kuma idan baka manta ba kai ka damu ayi bikin nan a da, don kuma ka samu wata warce kake so bai kamata ka dinga yawo da hankalina da na magabata na ba, Ba damuwa xaka iya turowa a dau kayan ka, na hakura... Allah hada kowa da rabonsa na alkhairi" duk da jikin Sudais yyi sanyi sosai amma ya dake yace "Haka kika ce?" Tace "Ehh, ka turo a kwasa kayan ka" yace "Ohk" daga haka ya katse wayarsa, fadawa kan gado yyi ya lumshe ido thinking if he made the right decision, mikewa yyi ya sake kiranta sai da ya kusa katsewa ta dauka, yace "Then you do me the favour of telling ur mum ta kira Mamina ta sanar da ita, baxan iya kai ma Mami wannan xancen ba don xata yi tunanin ni ne na fasa..." Jiddah tace "Ohk" daga haka ta katse wayar, ya sauke ajiyar xuciya ya koma ya kwanta, Khadijah ce ta fado masa ya dau wayar ya shiga kiranta, ba a dau lkci ba ta daga cikin sanyin murya tayi masa sallama ya amsa yace "Babies din ne ke kuka haka?" Turo baki tayi ta kalli Mai sunansa dake tsala kuka tare da d'an uwansa tace "Toh Anty tana kitchen ban san me take ba" mikewa yyi xaune yace "ina yaran?" Tace "Ga su nan kan gado a kwance" shiru yyi ya ma rasa abinda xai ce mata, can ya katse wayarsa, Khadijah ta kalli wayar da sauri, jikinta yyi sanyi ta shiga kiransa kuma, har ya katse bai dauka ba, ajiye wayar tayi tana kallon yaran dake ta kuka, fashewa tayi da kuka tace "Toh ni ce na sa su kuka, ko me nayi masu?" Can karshen gado ta koma ta xauna tana hararansu, Mama Suwaiba na kitchen tana jin kukan yaran taki fitowa don lamarin Khadijah ya fara isarta, ya mutum xai haifi yara ya dinga masu abinda take yi, jin kukan yaran yyi yawa ta fito ta shiga dakin tana kallon khadijah tace "Ke kam baki da kirki gaskiya, kiyi hakuri hakan da na gaya maki, banda rashin hankali haka taki uwar ta maki, me yaran suka maki, kinsan baki son haihuwar kika dau cikinsu, kin xata hakkinsu xai bar ki? Yara ko kwana arba'in basu cika ba kika haramta masu nono, toh da haka ake haihuwa kam da ba ayi ba, ni tunda nake ban taba ganin uwa irin ki ba, na maki magana a matsayin wacce tayi jika dake, na maki magana a matsayin 'ya na maki magana a matsayin ki na shugaba gare ni amma duk a banxa, toh wllh bari mijin naki ya dawo ta dalilin haka ma ni sai na bar maku gidan ku baxan iya ci gaba da xama ina ganin xaluncin nan ba, tun da uwata ta haifeni ban taba gani ko jin tarihin uwa irin ki ba, wannan kuma ya wuce yarinta tsabagaren iskanci ne, kilan idan na bar gidan kika ga babu mai daukarsu idan suna kuka ke xaki dauke kayan ki" daga haka mama suwaiba ta fita tana rike da yaran, hade kai da gwiwa Khadijah tayi tana kuka, Mama suwaiba na komawa parlor ta dau feedern su da ta hada masu tana jiran ganin fitowar Khadijah ta dauka ta je ta basu amma shiru, Su duka biyun ta hada tana ba abincin lkci daya duk tausayin su ya cikata, Sudais ne ya shigo parlorn, ko gaishesa bata yi ba tace "Yallabai dama ina jiran ganin dawowar ka" xaunawa yyi kan kujera yace "Toh gani mama" tace "Ina jin xan bar wannan aikin ku samu wata, ban jin xan iya ci gaba da xama gidan nan ina ganin abinda wancan yarinyar ke ma jariran nan, nayi mata magana a matsayin ta na shugaba gare ni, nayi a matsayin uwa gare ta, kai babu abinda ban ce mata ba a kan yaran nan, kwata kwata bata son su kamar a dole aka mata cikinsu, me yaran nan suka mata fisabillah, kai tun da kake ka taba jin uwa haka, yau ko da shegu ne yaran nan wllh basu cancanci abinda take masu ba, don haka baxan iya ba ni xan tafi kilan idan taga ba ni xata dinga masu abinda ya kamata" Sudais ya lumshe ido ya bude kafin ya mike ya wuce dakin da Khadijah take, dago kai tayi daga gwiwanta jin shigowarsa, wani kallo ya dinga mata kafin yace "Tashi ki je ki karbi yaranki, idan ma kashe su xa kiyi ki kashe su da hannunki" kin tashi tayi yyi mata wani tsawan da ya firgitata ta tashi a tsorace, tun da take bata taba ganinsa haka ba, kofa ta nufa da sauri ta fita, gun mama suwaiba ta tafi ta karbi yaron daya hawaye na sakko mata, tana ta tsaye yana hannunta, Mama suwaiba tace "Ki tafi ki kwantar shi ki dawo ki amshi wannan, in sha Allah tafiya ta xan yi baxan ci gaba da xama da mutum irin ki ba" a sanyaye ta je daki ta kwantar da shi, Bata yarda ta kalli sudais da ke ya tsaye ba ta koma ta dauko dayan, ta dawo ta ajiye sa kusa da d'an uwansa tana hawaye. Sudais na kallonta yace "Gobe xan baki kudin mota sai ki kai su gidan marayu ki bar su a can" ta kallesa da sauri tace "Da gaske?" Yace "Ehh" murmushi tayi tace "Toh nagode" Wani kallo kawai ya dinga mata yace "You are very heartless Amira, ki duba ki ga ni da na ajiye ki gidana na taba sanin ki?? Ban san ki ba ban san komai naki ba, I just saw you are helpless and I decided to help you... Amma yara su xauna wata tara cikinki ki haifesu sannan ace baki da makiya kamar su, just look at the helpless souls, me suka maki Amira? Me yasa kike shafa masu laifin ubansu?" Xaunawa tayi gefen gado bata ce komai ba, ya gyada kai yace "Na san maganin ki" daga haka ya fita dakin ya bar gidan gaba daya, turo baki tayi ta kwanta can nesa da yaran, a xuciyarta tace to ita ta iya rainansu ne, kawai su yi ta kuka kamar ana mintsilinsu baxa su yi shiru ba. As usual yau ma da daddare hangame baki Khadijah tayi tana bacci suka tashi suna kuka kamar ko da yaushe mama suwaiba ta xo ta kwashe su ta tafi dakinta tana girgixa kai. Washegari da safe Sudais ya dawo gidan, dubu Hamsin ya kawo ma mama suwaiba yace ta tafi kawai, duk da mama suwaiba ita ta fara bukatan hakan amma sai ta ji ba dadi, ta fara tausayin yaran, Sudais yace "kar ki damu mama idan taga babu kowa gidan xata dinga kula da abun ta, kiyi tafiyar ki kawai" Mama suwaiba tace "Toh shkkn, Allah yasa ta gane" Sudais yace "Ameen, amma mama kar ki tafi kina jin haushinta don Allah, ba laifinta bane but xata daina in sha Allah" shiru mama suwaiba ta yi shiru tana tunanin to ko dai iskokai gare ta, can tace "Toh shkkn, Allah ya shiryeta ya yaye mata abinda ke damunta, amma xa mu iya sallama da ita in roketa gafara idan na taba saba mata" Sudais yyi murmushi yace "Toh ki shiga ku yi sallaman mama" mama suwaiba ta shiga ta tada Khadijah nan tace mata xata tafi, Khadijah dake ta kallonta da mamaki tace "Ina xaki Anty?" Mama suwaiba tace "Kauyen mu mana" Khadijah ta xaro ido tace "Toh yaran fa?" Sakin baki mama suwaiba tayi tana kallonta a xuciyarta tace Lallai gaskiyarsa bata da lafiya, a fili kuwa tace "Toh anjima ai xan dawo" daga haka ta fita, suka yi sallama da Sudais bayan ta hada kayanta ta wuce cike da kewan Khadijah da yan biyun. Sudais ya dau yaran ya kai su can dakin da Khadijah take, har lkcn tana xaune, yana shigowa da damuwa tace "Toh wa xai dinga kula da yaran yanxu?" Yana mata wani kallo yace "Uwarsu" daga haka ya fita yana kallon wayarsa dake ring, ganin Mami ke kiransa ya d'an yi jim kafin ya daga, tace "Aliyu ka dawo gida yanxu ina neman ka" bata jira yace komai ba ta katse wayar ya koma dakin Khadijah yace "Xan je gida yanxu" kamar xata yi kuka tace "idan suka fara kuka fa? Ni ya xan yi?" Yace "Sai ku yi tare" daga haka ya fita ta fashe da kuka a hankali tana kallon yaran. Karfi Sha daya saura Sudais ya isa gida, bai yi mamakin ganin set din akwatunan da su Anty Maryam suka kai gidan su jiddah ba a parlor, ba Mami kadai ba yau har Abbansa na xaune parlor da kanninsa gaba daya, Kasa xaunawa yyi ya duka murya can kasa yana kallon kayan yace "Ga ni Mami" Mami tace "Kayan da kace dama su dawo da su ne suka kawo daxu shi yasa na kira ka, sai ka fada mana daga nan kuma ina xa a kai kayan?" Sudais ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, muryar Abbansa ya ji yana cewa "Aliyu duk shekaru na a garin nan kai ma ka taso kaga cewar lafiya nake xaune ban taba samun matsala da kowa ba, to ta dalilin ka ma baxan samu matsala da kowa ba domin kuwa kayi kadan, don haka kar ka sake xuwa min da xancen aure ko yanxu ko ba yanxu ba, dama idan ba dauko ma kai dala ba gamo ba ma har nawa kake Aliyu??" Abba ya kalli Mami da ta hade rai yace "Dubesa fa he is just 27 ne ko 28 ya ishe mutane aure gashi ya xo yana wawanci da sokwanci, ke kina ganin haka ma kisan baxa ayi abun kirki ba Idan aka masa auren, get out my frnd" Sudais ya sauke ajiyar xuciya a hankali ya mike ya bar wajen, Mami tace "Fadan kenan Abba?" Abba yace "Toh me xan ce masa, idan akwai wanda kika san xai yi aure soon kawai ki bada kayan gudunmawa, am nt in support of Aliyu getting married now, ya jira idan yayi 30" daga haka Abba ya mike ya bar parlon, murmushi kawai sudais yake shi kadai a daki, Anty Maryam ta shigo tace "Hankalin ka ya kwanta yanxu?" Da sauri yace "Wallahi Anty" Can nesa da Twins din khadijah ta xauna tana ta kallon yanda suke ta motsi, tsoronta daya ya xata yi da su idan suka fara kuka, kamar sun san tunanin da take taji daya ya fara kuka, Tashi tayi da sauri ta dau waya ta shiga kiran sudais, ya fito daga wanka kenan ya dau wayar ya katse ya kirata, kamar xata yi kuka tace "Wallahi gasu nan xasu fara" yace "Xa su fara me?" Tace "Kuka" murmushi yayi yana ci gaba da goge gashin kansa yace "Toh kiyi breastfeeding dinsu" xaro ido tayi tace "A'a ni dai madara Anty take basu" Yace "Toh sai ki basu madaran ai" hawaye ya cika idonta tace "Yaushe Anty xata dawo toh?" Yace "Ta tafi kenan ai" xaro ido tayi ta juya tana kallon yaran, kamar yasan abinda tayi yyi murmushi ya katse wayar ya fara shiryawa. Haka nan Khadijah ta dinga fama da yaran suna kuka tana kuka, gashi tana ta basu madaran basa sha, nan ko tun madarar safe da Mama suwaiba ta hada masu ne take basu, tun daga bakin kofa sudais ke jin kukan yaran ya shigo da sauri, tana ganinsa ta mike ta fashe da kuka tace "Ni dai don Allah ka tafi da su kar ka sake tafiya ka bar su" ko kallonta bai yi ba ya kwace feeder din hannunta bude baki yyi yana kallonta yace "Amira" tana goge idonta tace "Na'am" ya hade rai yace "Tunda kike kin taba shan shayi me sanyi, me yasa ke muguwa ce" kallonsa kawai ta tsaya yi, yyi tsaki ya dau dayan feeder din ma ya fita xuwa kitchen ya xubar da madarar ya xuba na xafi ya hada wani yyi diluting da ruwan gora ya dawo dakin, daukan little sudais yyi ya mika mata daya feeder yace "Ki dauki Muhd ki basa" ta turo baki ta karba ta dau yaran ta fara basa, tsit yaran suka yi gaba daya, bayan wani lkci ya juya yana kallon khadijah dake kallonsa, sauke idonta tayi da sauri, ya kwace feeder hannunta ganin a hancin d'an yaron ta saita yace "Kallon meye kike min xa ki xuba ma yaro madara a hanci" ta hade rai tace "Ai kai ma naga ka kalleni" shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi ya kwantar da little Sudais da har ya fara bacci ya karbi Muhd din hannunta a hankali yace "We will call him shureim" daga ido yyi yaga kallonsa take still, turo baki tayi ta dauke kai ta boye fuskarta jikin gado, yyi murmushi ya na ci gaba da ba shureim sauran madaran, har ya kwantar da yaron bata dago ba, ya tsura ma dogon gashinta ido dai dai lkcn da ta dago a hankali yyi saurin dauke kansa tace "Ae na kama ka" ✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨ Daga wannan rana Khadijah ta daure ta fara koyon yanda xata kula da yaranta tunda Mama suwaiba ta wuce, shi ma din ba a son ranta ba kawai sbda sudais take yi, amma har lkcn ta ki basu nono sai dai madara, Sudais ya san kula da yara har biyu xai mata wahala saboda karancin shekarunta amma ya bar ta a haka to see if kusancinta da yaran xai sa ta hakura ta fara sonsu but kamar kara sa mata kinsu ake, komai xata masu sai tayi complain wani lkcn har da kukanta, bbu abinda ke mata takaici sai irin yanda suke hanata bacci cikin dare wani lkcn, duk da during the day kusan sudais ke masu komai, yayi dedicating time dinsa gaba daya ma twins din kamar mara aikin yi, a ranan da Mami tayi querying dinsa na biyu kan ina yake xuwa baya dawowa gida sai kusan sha biyun dare kuma ya fita da sassafe tsabar confusion yace "Mami ni wlh fa yawanci ina gidana, can nake xuwa" Mami da tayi shiru tana kallonsa tace "Kana gidan ka? To ai xan je gidan wataran" shiru sudais yyi jikinsa yyi sanyi gabansa ya shiga faduwa, kasa bacci yyi darren ranan ya rasa me ya kai bakinsa gaya ma Mami wai gidansa yake xuwa, kuma yasan Mami xata aikata xuwa can gidan nasa din, kafin washegari yayi deciding kawai barin gidan don yasan its not longer safe keeping khadijah and her twins in there anymore, misalin karfe tara na safe ya gama hada duk abinda xai bukata a travelling bag dinsa ya shiga dakin Mami gabansa na faduwa, bayan ya xauna gefen gado a hankali yace "Mami dama ina da wani case da xan yi a Abuja yau, kiyi hakuri sai da xan tafi nake gaya maki" Mami dake ta kallonsa ganin yanayinsa tace "Sai kuma yaushe?" ya sosa keya a hankali yace "Kai Mami ai ina jin daga can ma xan wuce Lagos, aiki da yawa ne gaba na, but in sha Allah soon xan dawo idan na gama, ke dai ki min addu'a" tace "Toh Allah ya tsare, Allah ya bada sa'a" a hankali yace "Ameen Mamina" daga haka ya fita duk jikinsa a sanyaye yayi sallama da kanninsa ya bar gidan a motarsa, driving din yake kamar baxai yi ba, why will he lie such great lies to his Mami, sosai hakan ya tsaya masa a rai, har ya isa gidansa he was not his self, khadijah na kitchen ta ajiye 3months old kids dinta da suka xama lukutaye kamar yan watanni shidda kan kujera a parlor, kiris ya rage little shureim ya fadi daga kan kujera ga d'an uwansa a gefensa, sudais ya karasa da sauri ya daukesa yana kallon kofar kitchen din, fitowa Khadijah tayi jin shigowar mutum parlorn, ya hade rai yace "I've warned u severally ki daina ajiye yaran nan kan kujera baki ji koh" tace "Toh they are just crying ni kuma aiki nake yi, kawai basa son mutum ya ci abinci sai dai su ayi ta basu, kuma ni ba gefen kujera na ajiye sa ba shine ya gangaro da kansa, Allah yaron nan baya ji" ko kallonta Sudais bai yi ba ya dinga kallon shureim dake ta kokarin yi masa dariya ya lumshe ido ya manna masa kiss a baki, Khadijah ta turo baki ta juya ta koma kitchen din ganin banxa ma yyi da ita, kwantar da shi sudais yyi kusa da d'an uwansa da ko motsin kirki baya son yi, shi ko irin wasan nan da kicking legs baya yi, sudais yyi kissing din takwaran nasa yana murmushi yace "You look very lazy Aliyu" dariya yaron yyi masa kamar ya ji abinda yace, Khadijah ta fito kitchen da plate din Irish da kwai, ajiye wa tayi nan parlorn tana kallon sudais tace "Have you breakfasted?" Ya kalleta yace "Noo, we are travelling now" ta buda ido tace "To where?" Yace "Somewhere" shiru ta yi tana kallonsa, yace "Ki gama ki hada kayan twins da naki, kafin ten xa mu wuce" bata ce komai ba, yace "Kin masu wanka" ta gyada masa kai, tun da Dr Yusuf ya nuna mata yanda xata dinga masu wanka shkkn ta iya unlike before da take shaka masu ruwa a hanci. Karfe goma da yan mintuna sudais ya gama sa duk kayan su a booth din mota, komai da yasan xai lalace a gidan ya sa ta xubar, yana rike da little sudais ya rufe gidan ita kuma tana rike da Shureim ya nufi motarsa dake waje, ya bude back seat yana kallonta yace "Get in" shiga bayan motar tayi sannan ya mika mata little sudais da karamar jakar dake dauke da flask na ruwan xafi da table water sai gwangwanin madarar su na Nan, ya rufe motar, ya shiga maxaunin driver, sai da ya shiga filling station ya kara mai a motar sannan suka dau hanya, a hankali yace "We are going to Abuja Amira" kallonsa kawai take bata ce komai ba, bayan wani lkci tace "Me xa mu je mu yi a can?" Bai amsa ta ba yana ci gaba da driving dinsa, ba a dau lkci ba gaba daya yaran suka yi bacci tana rungume da su tana turo baki don duk sun mata nauyi a jiki, bayan few hours shureim ya tashi da kuka sannan little sudais ma ya tashi, sudais dake kallonsu ta madubi yace "Ki hada masu madaran a feeder" kamar xata yi kuka tace "Toh da wani hannun, bayan sun danne ni" murmushi yyi ya gangara gefen titi yyi parking ya fito ya bude back seat din ya shiga, shi yayi making din masu madaran a feeder guda biyu tana kallonsa, bayan ya tabbatar babu xafi ya mika mata daya sannan ya karbi little sudais ya fara bashi nasa ita kuma ta shiga ba Shureim, tsabar cin da yaran suke ko kwana biyu gwangwanin madaran baya masu, shi sa sudais ke siyowa da yawa, bacci little sudais ya koma a hannun Sudais ya mika mata shi ta turo baki tace "Wllh kafana ciwo yake min ni dai" yace "Toh ko in bari kiyi driving din?" Dariya ta yi tana wara ido tace "Ni kuma?" Ajiye mata yaron yyi a kafa kusa da twin dinsa da shima ya koma baccin sannan ya fita ya koma maxaunin driver ya tada motar ya ci gaba da tukin sa. Kafin su kai kaduna su shureim sun sha madaran su ba iyaka, kuma duk sai yyi parking ya taimaka mata, gashi ya hanata baccin da take ta ji saboda yaran hannunta da ta fara xai tada ta ta rike su da kyau, sai kusan karfe shidda Sudais ya isa Abuja ya nufi gidansa dake cikin garin, kai kana ganin gidan kasan an kashe kudi ba na wasa ba, ya bude motar ya fita don bude gate din gidan kafin ya shiga da motarsa, babu abinda babu cikin gidan don haka bedsheet yayi spreading a kan gado a daki ya kwantar da twins dake ta bacci, yana kallon khadijah da tayi laushi alamar duk ta gaji yace "Kiyi wanka kiyi sallah kafin in dawo yanxu" daga ya fita, da yake har sponge da sabulunsu ta dauko, bayin ta shiga bayan ta fiddo su a kayansu da sudais ya kawo dakin tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta canxa kaya ta sa Hijab ta kwanta dai dai lkcn da su Shureim suka tashi, Ji tayi kamar ta kwala ihu ta dinga hararansu kamar xata yi kuka, ganin xa su fara kuka ta mike ta fara hada masu abincinsu hawaye cike idonta, ita dai ta gaji da wahalan da yaran nan ke bata, tana cikin basu feedern ya shigo dakin, tausayi da dariya ta basa lkci daya ganin yanda take hawaye, ya amshi feeders din hannunta yace "Toh tashi ki dau abinci ki ci kiyi kwanciyar ki" kamar jira take ta mike da sauri, tana cin abinci ya karasa basu abincin su ya kalleta yace "Toh baxa su yi wanka ba" hade rai tayi tace "Nima ban sani ba" yace "Amma ke ai kin yi wanka" tace "Toh ai ni da su ba daya bane" mikewa yyi ya tafi bathroom ya hada masu ruwan xafi sannan ya fito yace "Kije kiyi masu" ta mike da sauri tace "Ni wllh baxan iya ba bacci nake don Allah kayi hakuri, dubi fa wahalar da suka dinga ban a mota" tsayawa kallonta yyi kamar yanda yaran nata ke kallonta su ma, ta je can karshen gado ta xauna fuskarta daure ta dauke kai, dukawa yyi kusa da shureim ya fara cire masa kayan jikinsa har ya gama ya wuce bathroom da shi, dariya ta fara yi kasa kasa ganin shi xai masu wankan, bayan wani lkci sai gashi ya fito ya kwantar da yaron da ya wanke ya rufesa da bedsheet sannan ya dau dan uwansa ya cire masa kayan shi ma ya wuce bathroom da shi yayi masa wankan ya fito da shi ya kwantar kan gado, jaka ya bude ya fiddo masu over all gaba daya da powdernsu da man shafawa, khadijah sai boye fuskarta take kar tayi dariya ganin yanda ya sa masu pampers din, shi dai ko kallonta bai yi ba ya hade rai, yana gama shirya yan biyun ya daukesu ya fita dakin ya kai su nasa dakin ya kwantar da su, Khadijah ta turo baki a xuciyarta tace huta roro, ta mike ta rufe kofar da ya bari a bude ta nufi kan gado ta gyara bedsheet din ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa. A haka khadijah da sudais suka fara rayuwa a garin Abuja da yan biyunta, sai dai sudais wasn't comfortable staying under the same roof with khadijah ya rasa dalili, gaba daya a takure yake barin yanda ya ga ta saki jiki totally da shi don ma akwai little sudais da shureim, karfe goma na safiya yake barin gidan baxai kuma dawo ba sai yamma, duk khadijah ta rame saboda rainon yaran don ma ba ta shayar da su, wahalansu yyi yawa, da daya ya fara kuka dayan xai cafke duk su rikitata, satinsu uku a Abuja sudais ya sa aka samar masa Nanny don tausayi take basa barin yanda ya ga ta rame, kamar kar Nanny ta xo lkci daya khadijah ta watsar da lamarin yaran gaba daya ya koma nanny ce ke masu komai ita sai dai tayi girki tayi bacci, abinda sudais ya guda kenan tun farko but saboda tausayinta da yake kawai ya kyaleta, nanny na xuwa gidan da kwana biyar sudais ya tafi damaturu don duba su Mami don Allah ma yasan yana kewar mahaifiyar tasa, kwana biyu yyi a can ya dawo Abuja bayan ya sanar ma Mami yawancin aikinsa yanxu a Abuja yake yi, ta yi masa addu'a da fatan alkhairi. karfe uku saura na yamma sudais ya shigo gidansa na Abuja, sai dai a waje yyi parking don ya gaji da yawa, babu kowa parlorn sai Ac dake ta aiki da kamshin dake tashi, ya haura sama ya bude kofar Nanny da yan biyu a hankali, suna xaune cikin keken koyan xamansu sai wasa take masu da abun jikin keken suna ta dariya gaba daya, sosai matar ke son su don yaran akwai shiga rai, Nannyn baxata wuce shekara talatin da biyar ba, tana ganin Sudais ta mike tace "Sannu da dawowa yallabai" yace "Sannu" ya karasa cikin dakin yana kallon cute yaran dake ta kallonsa, kyawawan karshe ne yan biyun ga manyan idanuwa ga su farare kal kamar larabawa, da wuya mutum ya kallesu bai kara kallonsu ba, ya rasa ne yasa khadijah ta ki sonsu har ynxu, daukansu yayi one by one yayi kissing dinsu suna masa dariya ya ajiye su ya fita dakin, bude kofar dakin da Khadijah take yyi, ya ganta kwance daga ita sai yar doguwar riga tana bacci, ya kusa minti biyu tsaye yana kallonta kafin ya rufe mata kofar ya wuce nasa dakin, wanka yyi ya dauro alwala ya fito ya saka jallabiyarsa ya gabatar da sallahn azahar sannan ya kwanta, Nanny ce ta shiga dakin Khadijah ganin har kusan la'asar ba ta fito ba alamar bata san Sudais ya dawo ba, ita duk tunaninta sudais mijinta ne, cike da natsuwa ta tasheta tace "Yi hakuri na tashe ki madam, yallabai ya dawo" da sauri khadijah ta mike xaune tace "Yaushe?" Nanny tace "Tun daxu" Khadijah tace "Toh" Nanny ta juya ta wuce sannan khadijah ta mike ta tafi bayi ta wanke fuskarta ta fito ta dau Hijab har kasa ta sa ta fita, a hankali ta tura kofar dakin sa ta gansa yyi rub da ciki yana bacci, a hankali ta isa kusa da shi ta durkusa tana kallon kyakkyawan fuskarsa, bude manyan idonsa yyi a hankali, ta koma baya da sauri ta fara kame kame, ya mayar da idonsa ya rufe na kusan minti daya kafin ya bude ya mike xaune, murmushi tayi murya can kasa tace "Sannu da dawowa, baka ce yau xaka dawo ba da ka kira da safe" yace "I was thinking sai gobe xan taho" tace "Ya hanya? Ya su mama" Yace "Alhmdllh, ya twins? duk da nasan kilan duk yau baki gansu ba" sauke idonta tayi daga kallonsa jin yyi shiru ta daga kai suka hada ido, wara mata ido yyi, ta yi murmushi tace "Me xaka ci?" Yace "Komai ma" mikewa tayi tace "Toh bari in yi maka" daga haka ta fita ya koma ya kwanta. A hankali watanni suka dinga ja kamar wasa sai ga shi su shureim sun yi wata bakwai, babu inda basa xuwa da rarrafe, wani shakuwa ne ba na wasa ba tsakaninsu da Sudais, ji yake da su kamar ya hadiye su don so, in har suna wasa a Parlor to suna ganin khadijah suke barin wajen da gudu su tafi gun Nannynsu, sai dai ta tabe baki ko tayi tsaki, har lkcn kamanninsu sak na Aliyu barin hancinsu da idanuwa shi sa take kara jin bata son su, ko ina na gidan kayan wasan su ne, don komai sudais ya gani na yara ko da ya fi karfinsu sai ya siyo masu, dakinsu ya koma kamar na siyar da kayan wasa, yau lahadi sudais na xaune garden shi kadai files a gabansa kana ganinsa kasan aiki yake, lkci daya ya rufe files din gabansa ya lumshe ido, for how long xai ci gaba da ajiye khadijah da yaranta a gidansa, har ransa yake jin baxai iya rabuwa da su ba, but duk ranan da Mami ta gano abinda yake aikatawa yasan that day won't be funny, then meye xai yi da xai kasance da Khadijah da yaranta na har abada With his parent consent, bude ido yyi a hankali ya furta abinda ke ransa a ciki "I shud marry her" girgixa kai yyi ya na murmushi lkci daya abinda Yusuf ya gaya masa one year ago a mota ya fado masa. Khadijah na bedroom ita kadai tana ta jiran jin shigowar sudais amma bai shigo ba, ita kanta bata san me yasa take son ya shigo ba, kuma tasan yana can garden, mikewa tayi ta sa mayafinta ta fita xuwa can din ta tsaya kusa da wani flower yanda baxai ganta ba ta dinga kallonsa, kananun kaya ne jikinsa na 3qtr da shirt da bai yi buttoning ba, tsura ma pen din table dake gabansa ido yyi har lkcn yana tunani, kamar ance ya daga kai suka yi ido hudu da Khadijah, dauke kai tayi da sauri, sai kuma ta jiya ta bar wajen ya bi ta da kallo, murmushi yyi ya na shafa kansa don irin kallon nan da Khadijah ke yi masa ko da yaushe dariya yake ba sa, sau tari ya sha kamata tana kallonsa sai ta fuske, shi din ma yana kallonta amma with swags, kwashe files din gabansa yyi don dama ya gaji ya mike ya wuce ciki yana rike da su, sai da ya fara lekawa dakinsu shureim yaga yanda Nanny ta cika masu kayan wasa a gaba suna ta fama, suna ganinsa suka rarrafo xasu taho gunsa, da sauri ya juya ya bar wajen don bacci yake son yi, a tare suka fara kuka yana tsaye har suka fito corridor nemansa yyi murmushi ya durkusa ya daukesu duk biyun amma da kyar tsabar weight dinsu, ya wuce dakinsa da su, ajiye su yyi kan gado ya kwanta suka haye kansa gaba daya ya lumshe ido yace "Yanxu baxa ku bar ni inyi bacci ba" kamar sun ji mai yace suka fara dariya har da kwantawa jikinsa ya rungumesu gaba daya, ganin da gaske baxa su bar sa yyi baccin ba ya dau waya ya kira Khadijah, tana dagawa yace "Plss ki xo ki dau su Shureim basa son inyi bacci" Khadijah bata ce komai ba ya katse wayar, ta tabe baki ta sa Hijab ta fito ta shiga dakinsa karasawa tayi kusa da gadon suna ganinta suka kankamesa sudais yace "Meye amfanin yaranki na tsoron ki" bata tankasa ba ta kai hannu xata dau little sudais ya fasa ihu dan uwansa na taya sa suka rirrike sudais, murmushi kawai sudais yake yana kallon khadijah da ta hade rai tana kallonsu, fixgo shureim tayi ya fashe da kuka a tsorace har lkcn yaki yarda ya sake sudais. Sudais ya fixgota ita ma har ta fada kansa ya daure fuska yace "Ciwo xa ki ji masa" xata tashi ya ki saketa yana kallonta kamar yanda yaran ta ma ke kallonta, murmushi tayi ta xame kanta ta xauna kasa, murya can kasa sudais yace "Tafi basa son daukan naki" kamar sun ji abinda yace suka kara yin lamo a jikinsa, Khadijah ta mike ta nufi kofa sudais ya bi ta da kallo har ta fita sannan ya lumshe ido a hankali. A ranan da su Shureim suka cika wata goma Sudais ya sa Nanny ta shirya su kamar dai yanda ya saba duk lahadi xa su fita, yanxu kam babu inda shureim bai xuwa da kafafuwansa banda little Sudais da tashi ma wahala yake masa, kaya iri daya nanny ta sa masu as usual, kwankwasa kofar dakin Khadijah sudais yayi, tana xaune gaban madubi tana rubuta a farar takarda jin an kwankwasa kofa ta dauke takardar da sauri xata boye, dai dai nan ya bude kofar, cukuikuye papernta tayi, ya dinga kallonta yace "What's that" girgixa masa kai tayi ba tare da ta bari ta kallesa ba da sauri tace "Bakomai" yace "Uhn, sure?" Kin cewa komai tayi, yace "Toh ki shirya xan fita da twins sai ki raka mu" ta girgixa kai tace "Baxan je ba" yace "Why?" Sai a sannan ta kallesa, saurin sunkuyar da kanta tayi, ya d'an yi murmushi ya juya ya fita, bude takardar tayi tana duba abinda ta rubuta, a hankali ta linke ta boye sa sannan ta sa Hijab dinta ta fita, har ya sauka parlor da su little sudais, ya juya ya kalleta yace "Ko d'an kwalliyan ma baxa ki yi ba" tace "Ehh" ya tabe baki ya fita tare da yaran ta bi bayan su, driving yake Khadijah na back seat da twins din shi kuma yana kallonsu ta madubi, horn ya ji an yi ya juya, da mamaki yake kallon matar da ta fito daga wani gida a motar ta kafin ya tsayar da tasa motar ya bude ya fito, ita ma ta sauka tace "Aliyu dama kana Abuja?" Ya kirkiri murmushi yace "Wallahi kuwa Mama, ina yini?" Tace "Lafiya lau Aliyu" lekan bayan motarsa ta dinga yi kafin tace "Kar dai kayi aure Hajiya Khadijah bata gaya min ba naga mace da yara a mota" sosai gabansa ya fadi yace "A'a mama, matar abokina ne da yaranta" Tace "Ayyo wajen ka suka xo?" Yace "A'a ajiye su xan je in yi" shi kansa ya san he just sound stupid, yayi saurin cewa "Amma mama kun dawo ne?" Tace "Noo, na xo yin abu ne yau sati na daya, amma ina jin jibi xan koma" yace "Holland din?" Tace "In sha Allah" yace "Toh Allah kai mu mama" tace "Ameen Aliyu, Allah yayi maku albarka" yana murmushi yace "Ameen" daga haka ya koma motarsa har lkcn gabansa na faduwa, Hajiya Rukayya aminiyar Mami ce don childhood frnds ne ma, ita ce ta sa Mami tayi ma Abba magana ya siya masa gida a layin lkcn anguwar na sabo, ita ma kuma a anguwar take amma sai su yi wata da watanni basa Nigeria da yaranta, har sudais ya kai bakin titi Hajiya Rukayya bata dauke idonta a kan motarsa ba, mace da yara a motarsa kuma yace matar abokinsa, kallon gidan Sudais din tayi kafin ta karasa can da kafa, kwankwasa gate ta dinga yi ko mai gadi xai bude amma shiru, can sai ga Nanny ta fito ta bude gate din, gaisheta Nanny tayi, Hajiya Rukayya tace "Ya kike" Nanny tace "Lafiya lau sai dai Masu gidan basa nan" shiru Hajiya Rukayya tayi kafin tace "Shi da matar suka fita kenan?" Nanny tace "Ehh har da yan biyun" Hajiya Rukayya tace "Toh shkkn" daga haka ta bar wajen da sauri ta wuce gidanta tana tunanin to ko dai karya sudais yyi mata yace bai yi aure ba, tana shiga motarta ta dau waya ta shiga kiran Mami. Gaisawa Hajiya Rukayya suka yi da Mami, Mami tace "Ki ce kun dawo Nigeria kenan Hajiya" Hajiya Rukayya tace "Ina fa, just came a week ago to put things in other, ina ga xuwa jibi ma xan koma" Mami tace "Ayya, ashe baxa mu hadu ba kenan, ya yarana fa?" Hajiya Rukayya tace "Suna can, Jaheed ne dai ke Lagos" Mami tace "Toh maa sha Allah, naji dadin da kika kira wllh, kina Abuja koh?" Hajiya Rukayya tayi dariya tace "Toh ai baki sani ba, Aliyu na gani ma ya sa na kira ki yanxu" Mami tace "Haba dai..." Hajiya Rukayya tace "Wallahi kuwa ashe ya dawo gidansa, na fito gida xan je mall yanxu na gansa a mota shi ma" Mami tace "Toh, ni ban san me yasa ya koma Abuja da xama ba yanxu, sai mu yi wata ma ba mu gansa ba, idan nayi magana yace aiki" Hajiya Rukayya ta d'an yi shiru kafin tace "Amma yyi aure ne Hajiya Khadijah?" Mami tace "Ina fa, ba na gaya maki abinda yayi ma yarinyar nan da yake nema jiddah ba, da suka fisa iskanci ai mayar masa da kayansa suka yi, kinsan halin Abbansu, to in gaya maki bai taking Wani action ba sai ma cewa da yyi ai bai isa aure ba, kinga yayi supporting dinsa kenan, ni dai nasan in har yarinyar nan yaudararta yyi hakkinta baxai bar sa ba" Hajiya Rukayya tace "Ikon Allah, to ni kuma da wata na gansa da yara har biyu a mota, da na tambayesa aure yyi sai ce min yyi matar abokin sa ce ai xai maida ta gida, to mutum ba iyali me matar abokin sa taje yi gidansa, and the way he replied, gaskiya it's suspicious, to da yake kinsan ai bbu nisa tsakanin gidan nasa da namu, in gaya maki na taka da kafa har na isa gidan na kwankwasa gate sai ga wata da alamar dai yar aiki ce ta fito, da na tambayeta mai gidan sai ce min tayi ya fita da familyn sa yanxu, abun dubawa a nan shine anya Hajiya Khadijah ba aure Aliyu ya xo yyi a Abuja ba tare da sanin ku ba, yaran fa yan watanni ne" tun da ta fara xancen Mami ke saurarata baki sake, can Mami ta sauke wani ajiyar xuciya tana share xufar da ya keto mata tace "Hajiya Rukayya yaushe kika ce xa ki koma?" Hajiya Rukayya tace "Ranan talata in sha Allah" Mami tace "Toh gobe da sassafe xan taho Abujan, ina shiga xan kira ki don Allah" Hajiya Rukayya tace "A'a ke kuwa a bi komai a sannu mana, ko ni ba sai in je in samesa ba, idan ba haka xancen yake ba fa? kuma ace da gasken matar abokin sa ce, ke dai kawai ki bar komai a hannuna xan same sa da kaina sai kace ba d'a na ba Hajiya" Mami ta girgixa kai tace "Inaa ai dole ne kawai in taho Hajiya Rukayya, dama kusan shekara daya kenan da Aliyu ya canxa hali totally ya dawo kamar mara gaskiya tun bai bar Damaturu ba, kar ki ce masa komai ki jira sai na xo, idan ma haka ne idan ma ba haka bane duk xa mu sani, nagode sosai Hajiya, sai kin ji ni" daga haka Mami ta katse wayar ta mike tana jin xuciyarta na tafarfasa, mace da yara? Ina ya samo su? Wani murmushi tayi ta fita daga dakin. Shopping sudais yyi ma twins din na abubuwan da suke ci tun daga kan golden morn, biscuits, custards, quaker oats, chocolates da sweets, sai Pampers da turaren yara, ita dai Khadijah na rike da little sudais dake kuka baya son ta dauke sa sai mika ma Sudais hannu yake, shureim kuwa sai kara kankame Sudais yake wai kar Khadijah ta karbesa shi ma, Duk little sudais ya cika shopping mall din da kuka, Sudais yace "Yanxu meye amfanin haka yaron ki baya son ki daukesa Amira?" Ita dai bata ce komai ba yace "Amira, are you thinking xa mu dauwama tare ne na har abada ne? Of course no, yaran nan ne dolen ki they are now ur new world, show them love Amira" mika mata trolleyn yyi ya karbi yaron ba shiri yyi tsit yana leko uwar tasa, duk yanda sudais yyi da ita ta dauki abinda take bukata a mall din kin daukan komai tayi, ya siya masu ice cream sannan suka bar mall din, har suka koma gida Khadijah ta ki cewa komai, yana gama parking nanny ta fito ta dau yaran gaba daya ta wuce ciki, juyawa yyi ya kalli khadijah da ta bude mota xata fita yace "Wait" sannan ya fito ya shiga back seat din motar ya rufe yana kallonta, hade kai tayi gwiwa tana shesshekar kuka, ya dago kanta a hankali yace "Daga na gaya maki gaskiya Amira?" Hawaye na sakko mata cikin rawar murya tace "Toh nice nace su dinga tsoro na?" Murmushi yyi yana kallon kwayar idonta yace "Ehh mana, ai ke ce baki sonsu, kalli fa ko breast baki basu ba kin yi xaton sun manta ne" turo baki tayi ta dauke kai tace "Amma sun san na basu sau daya ai" dariya ta basa ya dinga kallonta kafin yyi murmushi, ya kamo hannunta ya lumshe ido yace "In dai kina jin maganata, and i meant a lot to you, daga yau ki fara son yaran nan Amira" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ganin yanda yake murxa mata hannu a hankali ta kwace hannunta ta koma daya side din ta bude motar ta fita, fitowa yyi shi ma ya bi bayanta. Kasa bacci daren ranan sudais yyi ya rasa dalili, duk ya ji he is restless, bayan ya gama sallolinsa misalin karfe biyu ya bude kofar dakinsa ya fito, khadijah dake xaune daki ita ma idonta biyu ta ajiye takardar hannunta da sauri karkashin pillow tana kallon kofar dakin, jin ba a bude ba ta sauka kan gado ta dau hijab ta daura kan sleeping wear din jikinta sannan ta bude kofa ta fita, downstairs ta sauka, tsaye ta gansa tsakiyar parlorn, jin ana sakkowa stairs ya juya da sauri, har ta isa inda yake kallonta yake, yace "Why are you awake by this time" ta girgixa masa kai kawai, xaunawa yyi kan kujera ta xauna kasa kusa da shi, jin bai ce komai ba murya can kasa tace "Daxu a shopping mall kace min we are not going to be together forever, why?" Muryarta na rawa ta karashe maganar, ido ya tsura mata, hawaye ya shiga sakkowa idonta, da sauri yace "Kuka kuma, I didn't mean it Amira, abinda nake nufi shine...." Sai kuma yyi shiru, ta hade kanta da kujera tana kuka cikin raunin murya tace "Don Allah kar kace xaka bar ni watarana, I have nobody, just you, kai kadai gare ni yanxu, idan ka bar ni ya xan yi, who will take care of the boys" jikinsa yyi mugun sanyi ya sakko kasa yana kallonta ya dago kanta, cikin sanyin murya yace "Ban ce xan bar ku ba Amira, what I mean is death, kinsan rayuwar ba shi da tabbas" xaro ido tayi tana kallonsa ko kiftawa babu sai kuma ta kara fashewa da matsanancin kuka tace "Mutuwa xaka yi ka bar ni?" Dariya ta basa sosai, yace "Ni bance xan mutu ba, kuma idan mutum ya mutu ai lkcn sa ne yyi" rike hannunsa tayi hawaye na sakko mata tace "Baxa ka mutu ba until Allah is pleased with your soul in sha Allah" murmushi yayi yace "In sha Allah, kamar yanda ke ma baxa ki mutu ki bar ni da yaran ba" shiru ta yi bata ce komai ba, a hankali tace "Gwara su su mutu ai" lkci daya mood dinsa ya canxa yana kallonta, ta sunkuyar da kai, da mamaki yace "Ashe baki da hankali Amira" a hankli tace "Kayi hakuri" rasa ma abinda xai ce mata yyi, can yace "Toh tafi ki kwanta" tace "Toh kai fah" yace "Bana jin bacci" tace "Nima" hade rai yyi yace "Tashi ki tafi nace" kamar xata yi kuka tace "Kai ma ka tashi" murmushi yyi ya mike ita ma ta tashi, yana kallonta yace "to mu je" ita ta fara tafiya sannan ya bi bayanta ta jira ya shiga dakinsa sannan ita ma ta shiga, daga masa hannu ta yi, yyi murmushi ya rufe kofarsa, ita ma ta rufe nata, kwanciya yyi ya rasa tunanin da xai yi a kan Khadijah, is it that.... He love her or what" lumshe ido yyi bai son tunanin daga haka bacci ya daukesa. Da asuba tun da ya dawo masallaci gabansa ke faduwa, he don't knw why, har gari ya waye yana kwance idonsa biyu a bedroom dinsa, kamar wanda ya tuna abu ya mike xaune da sauri, jiya da yamma Hajiya Rukayya... Tunanin da ya xo masa kai knn, ya dafe kansa a xuciyarsa yace to sai ta fara gaya ma Mami ta gansa da mace da yara, noo yasan she won't, but it's better su d'an bar anguwar for sometimes, da kyar ya mike daga karshe ya fita dakin ya shiga na twins har nanny ta masu wanka tana basu golden morn suna xaune cikin kekensu, suna ganinsa suka fara daga hannu ya daukesa takwaransa har da kuka, karasawa yyi ya daukesu gaba daya yana murmushi Sanin kuka xa su yi idan ya fita ya bar su, ya koma dakinsa da su, yana son fita misalin sha daya amma yan biyun sun ki bacci, bell ya ji aka danna downstairs, sai da gabansa ya fadi duk da bai san me yasa ba, ya mike xai fita twins suka fara kuka, dawowa yyi ya daukesu ya fita, ganin khadijah bakin kofar xata bude yasa shi tsayawa kan stairs, tun da yake bai taba jin faduwar gaban da yaji a lkcn ba ganin Mami ta shigo parlorn Hajiya Rukayya na biye da ita a baya. Mami na kallon Aliyu da wani expression tace "Aliyu??? is this the life you chose for ur self? Is this the home training I gave to you" Sudais ya sauke kansa daga kallonta lkci daya jikinsa yyi sanyu ya sauko downstairs a har sannan yana rike da yaran, a hankali yace "No Mami, I didn't choose this life for my self...." Katse sa ta yi cikin tsawa tace "Aliyu ka fada min wacece yarinyar nan? Who is she? Meye hadin ka da ita?" Ya hadiye abu da kyar yace "Mami... Mami ba lallai ki yarda da abinda xan ce maki ba, but Mami ki kira Yusuf xai gaya maki wacece ita kilan shi ki yarda da shi" wani mugun kallo Mami ta dinga yi masa xuciyarta na tafarfasa tace "In kira Yusuf? saboda ina tsoron ku? To bani da wannan lkcn, Aliyu dama abinda ka dawo yi a Abuja kenan? Mace ka dauka ka ajiye gida ku ke rayuwa tare.... Wa iyaxubillah" Hajiya Rukayya tayi saurin dakatar da ita tace "Haba, ki sauraresa tukun Hajiya" daga haka ta mayar da dubanta kan sudais tace "Ka gaya mana wacece ita Aliyu" Sudais ya kalli khadijah da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta, rasa abinda xai ce yyi duk jikinsa yyi mugun sanyi, Hajiya Rukayya tace "Toh bani number Yusuf din, ni xan kira sa" Mika masa wayarta ta yi ya amsa ya sa mata number Yusuf yana fara ring Hajiya Rukayya ta karba, Yusuf na dagawa Mami ta karbe daga hannun Hajiya Rukayya, daga daya bangaren Yusuf yayi sallama, Mami ta amsa tace "Yusuf kana ji na?" Shiru yyi jin kamar muryar Mami, a fusace tace "Ba da Yusuf nake magana ba" Yusuf ya kwalalo ido yace "Ehh ina nine mami, ina kwana," bata damu da amsa gaisuwarsa ba tace "Yusuf ka gaya min wacece yarinyar da Aliyu ya ajiye gidansa da yara" Sai da gaban Yusuf ya fadi ya mike daga xaunen da yake, can ya koma ya xauna a hankali yace "Mami it's not what u are thinking wllh yarinyar nan da kike gani taimakonta kawai Sudais yyi, she is an orphan...." Lkci daya idon Mami ya kada ta katse sa hade da kunduma masa xagi tace "An orphan??? Bata san hanyar orphanage ba ko kuma kai me yasa baka yi mata taimakon ba sai shi, ya ajiye mace da ba muharramarsa ba kace yana taimakonta Yusuf, tun da uwar ka ta haife ka ka taba jin haka?? su kuma yaran na waye?" A sanyaye Yusuf yace "Nata ne Mami" Mami na jin haka ta katse wayar tana kallon Hajiya Rukayya lkci daya idonta ya kawo ruwa tace "Kina jin halin yaran yanxu koh Rukayya, yanxu ka haifi yaro baka haifi halinsa ba, ni dama da dadewa na lura da takun Aliyu, mu Aliyu xai kunyata a idon duniya? irin tarbiyar da ni da ubansa muka yi masa kenan" durkushewa Khadijah tayi a wajen tana kuka a hankali tace "Umma kiyi hakuri don Allah ki yafe masa" Tsawa Mami tayi mata tace "Rufe min baki, tarbiyar da iyayenki kema suka maki kenan kiyi rayuwa gida daya da namiji?" Cikin rawar Murya Khadijah tace "My parent are late, bani da kowa shi yasa ya taimakeni, Umma kar ki ce ya barmu don Allah..." sudais da ya ji kafafuwansa sun gaxa daukarsa ya xauna kan kujera ya ajiye su shureim da suka wani rirrikesa, cikin sanyin murya yace "Mami don girman Allah kiyi hakuri, ba yanda kike tunani abun yake ba, I just...." Katse sa Mami tayi cike da takaice tace "Ba yanda nake tunani abun yake ba Aliyu?" Sudais ya daga kai da kyar yana kallonta ganin hawayen dake idon mahaifiyarsa ya ajiye yaran ya mike ya isa gabanta ya durkusa cikin rawar murya yace "Noo Mami pls kar ki xubar da hawayen ki a kai na, na maki alkawarin na daina duk abinda nake daga yau, ki gafarce ni don Allah mamina" duk ya rikice mata, Mami na hawaye tace "Ni idan na gafarce ka Allahn ka fa? Wani tsinannen taimako ne wannan without the consent of ur parent, wani taimako ne wannan kuna rayuwa gida daya kamar mata da miji, yanxu ba don na san halin ka ba ance maka baxan yarda yaranka bane wa enan yaran?" Idonsa ya kada sosai cikin raunin murya yace "Mami nayi abinda nayi ne domin taimako amma daga yanxu na bari in sha Allah, forgive me plss Mami, nasan ban kyauta maku ba" Mami tace "Ka hada ina ka ina ka ka koma Damaturu yau ba sai gobe ba, sannan ina jiran makullin gidan yanxu ka same ni gidan Hajiya Rukayya" Tana fadin haka ta juya ta fita a parlon, kai kana gani kasan tana mugun son d'an nata ne, Hajiya Rukayya tace "Heed to what ur mother said right away Aliyu, ita kuma idan tace bata da iyaye ai baxa ta rasa dangi ba ta tafi wajensu" shi dai sudais bai ce komai ba, Hajiya Rukayya ta juya ita ma ta fita, Sudais ya dafe kansa da yyi masa nauyi, gaba daya tunaninsa ya dagule ga kukan Khadijah da yake ji har ransa, su kansu yan biyun kuka suke, lkci daya idanuwansa suka kada, mikewa yyi daga durkushen da yake ya wuce dakinsa ya dau makullin mota ya fita gidan gaba daya, Nanny da duk taji abin da ya faru ta iso gun khadijah dake kuka sosai ta dafa ta a hankali tace "Dama ba mijin ki bane mutumin nan maman twins?" Khadijah ta dago tana kallonta hawaye na sakko mata ta girgixa mata kai tace "Taimako na kawai yayi tun ban haifi yaran nan ba, ni bani da kowa sai shi yanxu" Hawaye ne ya cika idon Nanny tace "Dangin ku fa?" Cikin rawar murya Khadijah tace "Ban san dangin Mahaifiya ta ba, dangin Abbana kuma baxa su karbe ni ba, Ummata kuma ta tafi ta bar ban san inda xan ganta ba" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni yanxu ban san ya xan yi da yaran ba" kuka sosai Nanny take duk jikinta yyi sanyi ba kadan ba, ta jawo ta jiki cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri wataran sai labari Allah baxai hanaki yanda xa kiyi ba, kar ki sake kuka don Allah" mikewa Nanny tayi ta tafi gun su Shureim dake ta kuka wai Sudais ya fita ya bar su. Bayan awanni kusan uku Nanny ta gaji da lallashin Khadijah da ta ki hakura da kukan da take, xuwa lkcn kuma su Shureim sun yi bacci, Da kyar Nanny ta lallaba ta taje tayi sllh don duk a sanyaye take, tana xaune kan darduma Sudais ya shigo gidan, kallonsa Khadijah ta dinga yi har ya xauna kan kujera, a sanyaye ta taso ta durkusa gefensa tace "Am sorry I caused you all this, kayi hakuri don Allah ka yafe min" Tana magana hawaye ce idonta, ya kirkiri murmushi yace "It's nothing Amira, tafi ki hada kayan ki gaba daya a sama" shiru ta yi tana kallonsa gabanta na faduwa, ya gyada mata kai cike da assurance, tashi tayi jiki ba kwari ta wuce sama, ya kalli Nanny da ke parlorn ita ma duk a sanyaye yace "Ki hada kayan yaran da naki gaba daya" mikewa tayi ta wuce sama ita ma, Nanny ce ta fara sakkowa parlorn da jakunkunan kayan su shureim, Sudais dake kallonta yace "Ki kai cikin booth, its open" fita tayi waje da kayan, tana dawowa yace ta je ta taya khadijah, Kuka Nanny ta samu Khadijah nayi a dakin, bata iya tace mata komai ba ta shiga taya ta hada kayanta, Nanny ce ta sauko da jakan ta kai cikin motar, shi dai Sudais na xaune yyi nisa tunanin da yake, jin wayarsa na ring ya dauka da sauri yana kallon mai kiran, tashi yyi ya daga wayar yace "Mukhtar ka iso ne" daga daya bangaren abokin nasa yace "Ehh ina waje" fita yyi ya samesa waje, Mukhtar yace "You mean wannan gidan xaka siyar Barrister?" Sudais ya shafa kansa yace "Ehh shi" Mukhtar yace "Haba, Toh ai wannan yafi wancan wllh, ya xaka siyar da abu ka siya wanda bai kai sa ba kuma har da ciko, amma sun ma same ka da yawa" Sudais yace "kai dai bani takardun wancan gidan, and don't forget gidan is almost furnished" Barrister Mukhtar ya bude motarsa ya fiddo envelope ya mika ma Sudais ya karba yace "Duk da haka dai, duka duka kayan nawa ne a ciki" Sudais ya amsa envelope din yace "Nagode, bari in dauko nawa" daga haka ya koma ciki ya wuce bedroom dinsa ya dauko wani envelope dake dauke da takardun gidan nasa yana dawowa ya mika ma colleague dinsa yace "Kafin dare xa a kwashe komai na nan din, soo you help me explain to them" Mukhtar da mamakin Sudais ya cika sa ya karbi envelope din yace "Toh shkkn" daga haka suka yi sallama Mukhtar ya wuce, Sudais na komawa ciki ya sa Nanny ta dauko twins suka shiga mota, Ganin Khadijah bata fito sudais ya wuce sama ya bude kofar dakin duk da kukan da ya sameta tana yi kawai cewa yayi "Ke nake jira Amira" daga haka ya juya ya fita, Khadijah ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta fita, a gaban motar ta xauna Nanny kuma na xaune da yaran a baya suka bar gidan bayan Sudais ya sauka ya rufe gate, tafiyar kusan minti ashirin suka yi sai kallon agogo sudais yake har suka iso wani anguwa, anguwa ce mai kyau shi ma kamar wancan, yyi parking dai dai gate din wani bungalow babba ya fita ya bude gate din ya ja motar suka shiga gidan, sosai gidan ya hadu bayan yyi parking ya bude motar ya fito yana kallon Nanny yace ta fito da yaran da xuwa lkcn sun tashi daga baccin da suke, kallon khadijah yyi ta bude motar ita ma ta fito, Sudais ya nufi entrance din shiga gidan ya bude kofar da makullin dake cikin envelope sannan ya shiga, parlorn na da girma amma bai kai na can gidan sudais ba, sannan dakuna uku ne ko wanne da bayi sai kitchen da dinning area, da kuma bathroom da toilet a parlorn, gidan ya hadu, sai dai fa bai kai na sudais ba, Har TV akwai a parlorn bayan kujeru da center table da dinning table da chairs a area din da aka tanadar don ajiye su, kasa xama khadijah tayi a parlorn, Sudais dake tsaye shi ma ya nuna mata kujera ta xauna, sai a sannan ta xauna cikin sanyin jiki, ya dau little sudais dake ta daga masa hannu wai ya daukesa, Sudais na kallon Nanny murya can kasa yace "Madam ina son ki min alfarma daya na xaunawa tare da su even if it's just for few years to come for the sake of this twins, I will pay all the money in sha Allah" Nanny da jikinta yyi sanyi tace "Ba damuwa yallabai, Allah ya saka da alkhairi" Nan take sudais ya bata check na shekarun da ya fada, sannan ya nufi Khadijah yana kallonta ya ajiye mata envelope din hannunsa a kafarta a hankali yace "Gashi Amira this is for my boys, da sunansu na siya gidan nan don haka na su ne, mallakin su ne" kasa cewa komai tayi tana kallonsa, ya durkusa gabanta a raunane yace "I have always wanted the very best for you Amira, like... sending you out to UK kiyi karatu ki xama likita, a ko da yaushe hakan yana rai na amma saboda kananun yaran ki.... I decided sai sun kai ko da shekaru biyu ne sai ki tafi tare da su.... Am sad I couldn't fulfill that but you can ur self, promise me ko bayan babu ni, xa kiyi karatu ki xama babban likita, I mean ki min alkawarin xa ki cika min wannan burin nawa a kan ki" jin bata ce komai sai kallonsa take a tsorace ya kamo hannunta yana kallon kwayar idonta, he understand she's shock, ya lumshe ido ya mika mata check na kudi, da farko kasa magana yyi can yyi gathering courage with a breaking voice yace "Am going Amira, this is a check of 20 million, I think that all I've got for now, kiyi kokarin ganin with this little am giving you kin inganta rayuwar ki da na boys din ki, sannan ki ci gaba da rike mutuncin ki na 'ya mace duk inda xa ki samu kan ki, I wish na yi kokarin nema maki Umman ki kafin in tafi, I wish na kwato maki hakkin ki a gun dangin mahaifin ki, amma duk hakan bai yiwu ba Amira, ki kyale su xa su mayar maki a lahira idan Allah ya yarda, as for the twins.." Kasa ci gaba yyi, yyi shiru na wani lkci bai son ta ga hawayen idonsa, can yyi karfin halin cewa "I knw i will always love them tamkar yaran da na haifa a cikina, kar ki bari su yi rashi na Amira, ki dinga masu abinda nake masu, I mean ki so su kamar yanda nake son su, you are all they've got now, ke kadai gare su, idan kuma kika samu abokin rayuwar da kika ga ya kwanta maki kiyi aure amma ki fara sanar da shi ke wacece, a duk xaman mu Amira idan na taba saba maki da sani na ko akasin haka ki gafarce ni" kansa a kasa yace "I think that's all, akwai foodstuffs da na siyo daxu a kitchen, goodbye Amira, it's great knowing you in my life, wishing u better future ahead...." Ganin xai tashi Khadijah ta sakko kasa ta rikesa ta fashe da matsanancin kuka cikin rawar murya tace "Na shiga uku, don Allah kar ka tafi ka bar ni ni kadai, you are all I have with my kids, ka ce min fa baxa ka taba barina ba, don girman Allah kar ka min haka Aliyu, idan ka tafi ya xan yi..." Kasa kallonta yyi, ta daura kanta a kafarsa tana kuka sosai cikin raunin murya tace "Kasan ni marainiya ce, I don't have anybody, ya xan yi da yaran idan ka tafi ka bar ni da su Aliyu, don Allah kar ka tafi ko don su, ban san inda xan ga ummata ba kar ka tafi ka bar ni ni kadai a duniyar nan" Hakan da khadijah ta fada yasa Nanny ta fara kuka tausayin khadijah da yan biyun ya cika ta, Sudais yyi iya kokarin ganin hawayen idonsa bai sakko ba amma hakan bai yiwu ba, ya dago ta da kyar shi ma hawaye na xubo masa yace "Life goes on with or without me Amira xaku yi rayuwarku da yaran, you just have to manage the little I gave you cos I knw living in Abuja is expensive, surely watarana xa ki hadu da ummanki har ma da dangin mahaifiyar ki, I have to go now saboda Mamina, baxan iya tsallake maganar ta ba kiyi hakuri, ke dai kiyi min alfarmar kula da yan biyun ki, kuma ki daina jin haushinsu ki ja su a jiki, su kenan gare ki a yanxu, kar ki shafa masu laifin mahaifin su" daga haka ya mike ya isa gun twins din ya duka yana kallonsu a sanyaye, dariya suka fara masa suna daga hannu ya daukesu, ya manna masu kiss gaba daya ya lumshe ido murya can kasa yace "Long life to you both in sha Allah my boys, Allah ya albarkace rayuwarku ku xamto *hasken rayuwar* mahaifiyar ku" tashi yyi ya nufi kofa trying hard to control his self, Khadijah na kuka sosai cikin sanyin murya tace "Thanks very much Aliyu, Allah ya biya ka abinda kayi mana, and I will always pray for you in my life, kai din ka xame min _hasken rayuwa_ a lkcn da rayuwata tayi min duhu, daga ranan da na fara ganin ka ka yaye min bakin cikin dake tare da ni, you will always be the *light of my life* Aliyu" Sudais bai iya ya juyo ba har ya isa kofa, yaran na ganin xai fita suka fara kuka, bai yarda ya juyo ba har ya bude kofar ya fita yana goge hawayen idonsa, yana fita kuma ya bude wayarsa ya cire sim din da Khadijah ta san sa da shi ya jefar nan cikin flowers din gidan ya fita ya hau motarsa, and that was how Barrister Aliyu left Khadijah and her twins. Khadijah ta shiga hali na damuwa sosai bayan tafiyar sudais, bata da aiki sai na tunani da xubda hawaye bata taba xaton rabuwa da Sudais a lkcn ba, da ba don Nanny dake gidan tana kwantar mata da hankali ba da abun ya mata yawa, gani take kamar sudais xai dawo kullum jiran tsammani take amma shiru wasa wasa har sati biyu, ta rame ba kadan gashi kullum cikin jin ciwo take a kirjinta, ciwon da ta fi shekara bata ji sa ba sai gashi ya dawo mata da karfinsa, hakan yasa Nanny ta tilastata suka shirya suka tafi asibiti don ko baccin kirki bata iya yi da daddare, khadijah bata yi mamakin abinda likita yace game da ciwon da take yawan ji a kirji ba, at anytime xata iya kamuwa da ciwon xuciya, yini biyu tayi asibitin under medication, nanny tayi ta kai kawo da twins xuwa asibitin, da yamma likitan ya sallamesu ya kuma bata shawarari da dama kan abinda ke janyo ciwonta da yanda xata yi preventing tashin ciwon, A hanyarsu ta dawowa cikin Napep da damuwa Nanny tace "Yanxu Mum twins da kike sa ma kanki damuwa haka idan abu ya same ki yaran ki fa? Ko don su baxa ki hakura ki rufa masu asiri ki kwantar da hankalin ki ki rungumi kaddara ba, kar fa ki manta ko wani bawa da irin tasa kaddarar, so why not just accept urs a yanda ya xo maki" Khadijah ta goge hawayen dake xuba idonta a hankali tace "Ban san ya xan yi ba" Nanny ta kwantar da murya tace "Cire komai xa ki yi a ran ki, kiyi facing sabuwar rayuwar da xa ki fara da yaran ki, bawan Allahn nan ya tafi, ya kuma ya maki duk abinda ya kamata kafin ya tafi yanxu the ball is in ur court, sai kiyi abinda ya kamata ki kuma rike addu'a sai komai ya xo maki da sauki, as a mother nake baki shawara Khadijah... For the sake of ur boys ki yi hakuri ki cire ma kan ki damuwa don Allah" a hankali khadijah tace "Toh nagode sosai" suna isa gida Khadijah ta sauka ta ba mai adai daitan kudi, xata karbi shureim hannun Nanny ya makalkaleta ya ki yarda, jikinta yyi sanyi tana kallon yaron, Nanny tayi murmushi ta fito da duk yaran biyu, khadijah ta karasa ta bude gate din sannan suka shiga gidan, ba laifi ta dau shawarar Nanny ganin shi kadai ne mafita a gareta sai dai hakan bai sa fara'arta ya dawo ba, she is always sad, bata taba xaton Sudais xai bar ta so early a rayuwa ba, kusan kullum sai ta yi tunaninsa, magungunan da take sha ya taimaka ya rage mata ciwon xuciyar da take fama da shi duk da baya tasar mata ma sai da daddare taji kamar xata mutu, ba karamin kokari take yi na ganin ta ja su little sudais a jiki ba amma sun ki yarda ko da yaushe cikin gudun ta suke kamar dodo, hakan na kara sa ta shiga damuwa Nanny ta dinga nuna mata a hankali xa su sake da ita kar ta damu, a ranan da yaran suka cika shekara daya a duniya Nanny ta raka Khadijah tayi enrolling kanta a ss1 na wani makaranta dake nan anguwar ta su, idan ba ita ta gaya maka tana da yara har biyu a gida ba in xa a shekara ana gaya maka baxa ka yarda ba, a lkcn kuma shekarunta sha bakwai a duniya, kana ganinta kasan she is a teenager, a hankali khadijah ta fara kokarin yakice tunanin sudais a ranta domin tayi concentrating a karatun ta, idan ta fita tun safe sai hudu take dawowa gida, sannan ga islamiyyar da ta shiga na yamma, hakan yasa still babu wani interaction tsakaninta da yaranta tun da ba xaman gidan take ba, amma har ga Allah yanxu ji tayi tana son abun ta duk da tsoronta da suke ji har lkcn. Haka rayuwa ta ci gaba da kasance ma khadijah har ta gama ss1 lafiya, xuwa lkcn abu uku ne ke damunta a xuciya, Rashin Ummanta, gudun ta da yaranta suke sai kuma ciwon xuciyar da ya sa ta gaba abu kamar wasa kusan ko da yaushe hanyar asibiti take wanda hakan ke sa ta fashin makaranta don ma tana da kokari, Sudais kam ta rufe sa a babin rayuwarta sai dai duk sllh sai tayi masa addu'ar Allah ya saka masa da alkhairi abinda yyi mata a rayuwarta da yaranta. Yau lahadi suna parlor, Nanny na feeding Sudais da shureim da yanxu shekarun su biyu da yan watanni a duniya indomie ta dafa masu take basu, yaran sun yi wayo sosai babu inda basa xuwa sai dai fa da ka gansu kaga Aliyu barin sudais komai na Abban nasa ya dauko, sau da yawa sai Khadijah tayi ta kallonsu, wani lkcn tayi murmushin takaici, wani lkcn kuma tayi hamdala ga Allah da ya bata yan biyun, Nanny ce ta katse shirun dake tsakaninsu tace "Mum twins to ya xa ayi da cefanen, wa enan ba yarda xa su yi in tafi in bar su ba, kuma wahala kawai xa mu je mu sha idan muka tafi gaba daya" Khadijah ta ajiye novel din hannunta tace "Nanny kawai da wayo xa ki tafi ki bar su" a tare yaron suka kalleta, Nanny ta kyalkyale da dariya tace "Toh ai kin tona, wa yace maki basa ji, sarai sun ji abinda kika ce" murmushi khadijah tayi tana mamakin sharpness din twins din, tuni shureim ya kara matsawa kusa da nanny, Khadijah ta tabe baki tace "Toh bari ni in je" Hijab har kasa ta daura kan kayan jikinta sannan ta dau kudin ta yi ma Nanny sallama tana daga ma boys din hannu ta nufi kofar fita su ma suna daga mata, jikinta yyi sanyi ganin in dai uwa xata fita yaranta sun dingi kuka kenan xa su bi ta, but why is her own case different, ko a jikin yan biyun dake cin Indomie da nanny ke basu har ta fita, to ita bata san kuma ya xata yi yaran nan su saki jiki da ita ba, iyakar kokari tana kokarin kwatanta masu abinda sudais yace Kafin ya bar su amma sun ki sakewa da ita, tana tsaye bakin titi tana jiran abun hawa a ranta kuwa tunani take ko dai abinda sudais ya fada kan nonon da bata basu ba gaskiya ne, kenan haushin ta suke ji? Ji tayi da ma basu girma ba ta basu nonon yanxu, tsabar yanda jikinta yyi sanyi bata lura da motar da har ya wuce ta da farko ya fara reverse a hankali yana dawowa ba, tana ankarewa ta dauke kai da sauri hade da tsuke fuska don hakan ma yasa bata son fita, tana mamaki da jin haushin me yasa in dai xata fita sai an tsayar da ita, ita ba wannan ne gabanta ba kuma bata jin xuciyarta xai kara kula wani d'a namiji har ta bar duniya, ganin mai motar ya fito daga motarsa ta bar wajen da sauri tana tafiya fuska daure ba tare da ta damu ta kallesa ba, ji tayi ance "Khadijah?" ta juyo da sauri suka yi ido hudu da shi, ya dinga kallonta kamar me son kara tabbatar da ita ce ko ba ita bace, ita din ma kallonsa take da mamaki, yace "Baki gane ni ba Khadijah?" Jikinta yyi sanyi lkci daya tayi murmushin da ya bayyana fararen hakoranta tace "Na gane ka, am just trying to be sure ko kai ne ko ba kai bane" ya wara yace "Maa sha Allah, Imagine we met after 3 good years" murmushi ta kuma yi tana kara kallonsa da kyau ganin yyi mata tsayi fiye da yanda ta san sa a da tace "Sure, to ya bayan rabuwa" ya rike chin dinsa yace "Waow kin girma Khadijah, just look at how calm you are now, kin tuna lkcn da kike yawo ba Hijab da jikakken kaya?" dariya ya bata ta rufe fuska tace "Har da tsokana" yace "Am serious, a Abuja dama ku ke?" Tace "Ehh wllh, ya su mama fa" yace "Suna kt, nima ban dade da fara aiki a nan ba, just 7 months back" Khadijah tace "Allah sarki, toh Allah ya taimaka" d'an shiru yyi yana kallonta, kafin a hankali yace "Ko kin yi aure ne Khadijah?" Kallonsa ta tsaya yi ita ma, lkci daya ta samu kanta da girgixa masa kai tace "Aure kuma, A'a ina karatu ne" yyi murmushi yace "That's good, kar in tsaya ina ta tsurutu da matar aure ban sani ba" murmushi kawai khadijah tayi a xuciyarta kuwa mamakin yanda aka yi ya fara magana ta yi don a lkcn da ta san shi da wuya yake magana sai dai danna waya, lkci daya jikinta yyi sanyi tuna abinda yyi mata a lkcn da take walagigi a katsina cikin yunwa, muryarsa ya katse ta yace "Ina xaki yanxu?" Ta kallesa tace "Kasuwa" yace "Toh shiga in yi dropping din ki" d'an xaro ido tayi tace "Kai da ba d'an gari ba?" Yace "Wata na 7 kice min ba d'an gari ba" murmushi tayi tace "Toh naji kai d'an gari ne" yace "Toh shiga muje" motar ta bude tana murmushi ta shiga, ya xaga ya shiga maxaunin driver suka bar wajen, yana driving yace "So ya rice and stew, and Irish with egg? Kuna nan kuna damawa koh?" Dariya sosai Khadijah tayi ta rufe fuska, yana murmushi yace "Yarinyar nan ta kashe min kudi a lkcn da abincin yan gayu gashi sai Abba ya bani nima lkcn" Khadijah ta dago a hankali tana kallonsa tana murmushi tace "Ae yanxu babu abinda bana ci har tuwo da miyar kuka, da ma kunu da kosai" ya wara ido yace "Da gaske? Anya xan yarda kuwa" ta gyada masa kai tace "Serious..." yace "Hmm that's surprising amma" ta turo baki tace "Baka yarda ba kenan?" yace "Toh ai ban ce komai ba Khadijah" suna isa kasuwa bbu yanda Khadijah bata yi da shi ya tafi ba yace xai jira ta, bbu yanda ta iya haka ta siya abubuwan da tasan xa su bukata a lkcn daga baya sai ta dawo ta siya sauran don bata son ta bar sa yyi ta jiranta, yana parking kofar gidan da ta nuna masa yace "Nan ne gidanku?" Ta gyada masa kai ta bude motar ta fita, yace "Toh ki gayar min da su mama da mutan gida" a sanyaye tana kallonsa tace "Xa su ji nagode sosai" daga haka ta juya xata shiga gate, yace "Wait Khadijah baki ban number ki ba mu dinga xumunci" dawowa tayi ta kira masa numberta yayi saving yana kallonta yace "It's nyc meeting you once more Khadijah" ta kirkiri murmushi ta daga masa hannu ta shiga cikin gida, Nanny na kitchen su sudais kadai ne xaune parlorn ta sa masu cartoon, khadijah ta ajiye ledan hannunta ta isa kusa da su ta xauna tana kallonsu, su ma kallonta suke, ta yi murmushi ganin irin kallon da suke mata ta yi masu kiss gaba daya, Sudais ya goge bakinsa shureim na ganin haka shi ma ya goge nasa, jikinta yyi sanyi sosai tana kallonsu, bata san lkcn da hawaye ya kawo idonta ba ta mike ta wuce daki da sauri, Nanny ce ta shigo dakin ganin khadijah kan gado tana hawaye da mamaki ta karaso da sauri tace "Mum twins me ya faru kuma?" Cikin rawar murya tace "Wai don na masu kiss shine suke goge bakinsu" dariya sosai Nanny tayi kafin tace "kai Khadijah shine har da kuka, to kyalesu xan yi maganinsu" daga haka Nanny ta juya ta koma parlor, taso keyar boys din tayi suka taho dakin, kusa da khadijah ta ajiye su duk suka shiga kkrin sauka daga kan gadon Nanny ta daure fuska tace "C'mon, duk wanda ya sakko xan xane sa, ita ce uwar ku ba ni ba" Kuka suka fara yi kuma basu sauka kan gadon ba, Nanny na kallon khadijah dake ta kallon kyawawan yaran nata tace "Yanxu abinda xa mu yi shine xa su dawo kwana nan dakin, ke xaki dinga masu wanka ki shirya su, ke xaki dinga ba su abinci hakan kadai xai sa su saki jiki da ke" a hankali khadijah tace "Toh" Nanny tace "Don haka duk safe kafin ki tafi school sai kin masu wanka kin shirya su ni kuma in hada masu breakfast sai in baki ki basu" kai kawai Khadijah ta gyada don har ga Allah bata son gudun ta da yaran suke, haka Nanny ta fita ta bar su suna kuka xa su bi ta, amma da yake suna jin magana bbu wanda ya sauka daga kan gadon kamar yanda tace masu, suka gama kukansu suka yi shiru suna kallon khadijah, Sudais yyi tapping dinta yana nuna mata kofa yace "Nanny..." Murmushi Khadijah tayi ta jawo sa jiki tace "Nima Nanny ce ai" hakura yaran suka yi suna ta xaune dakin kusa da ita har bacci ya dauke su, Nanny na ganin lkcn tashin su ya kusa misalin karfe biyar na yamma ta dama masu custard ta dafa masu indomie ta kawo ma khadijah dakin ta fita ta rufe masu kofa, a lkcn kuma suka tashi, duk suka yi jigum suna kallon khadijah, ruwan wanka ta hada a bathroom dinta tayi masu gaba daya sannan ta fito ta shafa masu mansu dake dakin ta sa masu singlet da pant ta xaunar da su kan carpet ta shiga basu custard din suna karba, har ranta ta ji dadin hakan suna gama sha kuma ta fara basu indomie da egg din, shureim na koshi ya fiddo wanda ta sa mashi a baki ya mike ya kai mata bakinta, murmushi tayi ta bude bakinta ya xuba mata abincin ta shiga ci a hankali. Sai kusan karfe shidda Khadijah ta fito parlor da yan biyun nata, cartoon ta sa masu parlorn duk suka xauna kan kujera suna kallo basu bi ta kan Nanny ba, da daddare a kan gadon ta ta shimfide su bayan sun yi bacci, ta gama shirin kwanciya kenan ita ma wayarta ya fara ring, ita dai bbu mai kiranta a waya ban da Nanny sai wata classmate dinta Aisha dake sonta sosai, ta dinga kallon number kafin ta daga, sallama yyi mata jin muryar hankalin ta ya dan kwanta sai dai bata san dalilin kiran ba ta amsa masa sallamar ta gaishesa yace "Ko kin fara bacci ne?" Ta girgixa kai tace "A'a yanxu dai xan yi" yace "Ohk, ya mutan gidan?" Tace "Lafiya lau Alhmdllh" yace "Maa sha Allah" shiru ta yi bata ce komai ba, a hankali yace "Kawai sai kika bar garinmu ba sallama Khadijah" tayi murmushin karfin hali tace "Ummata ce ta xo ta dauke ni ai" yace "Allah sarki, but dama me ya kawo ki gidan tun farko" khadijah da taji kamar kar tace komai kawai ta yi murmushin takaici tace "Ai yayan Abbana ne" yace "Are you serious?" Tace "Uhn" yace "Waow, to me yasa basu baki abinci" ta wara ido tace "Suna bani fa, ni ce ban iya cin abincin ba lokacin" murmushi yyi yace "Allah sarki, kwanaki ma ai kawun naki yyi accident kin sani koh" Khadijah ta bude ido sosai tace "Haba dai, ban sani ba, basu gaya mana ba" Sadeeq yace "Ehh amma da sauki yanxu ina jin ya samu lafiya ma" A hankali khadijah tace "Toh Allah ya kara kiyayewa" yace "Ameen" shiru ne ya biyo baya kafin yace "Kin taba ba Umma labarina" Khadijah da taji jikinta yyi mugun sanyi a hankali tace "Kowa ma ina ba labarin ka, cos you fed me when I was in need of food" Sadeeq yace "Noo I did that for the sake of Allah, not for you to tell everyone" murmushi kawai khadijah tayi a sanyaye, shi ma murmushin yake yace "Sure, yaushe xa ki hada ni da Umma mu gaisa ko kuma in xo har gida in gaisheta, ko baki son mu yi xumunci sosai?" gabanta ne yyi mugun faduwa and she was totally lost of words, a hankali yace "Hello, Khadijah are you there?" Katse wayar Sadeeq yyi jin bata ce komai ba, ya sake kiranta a tunaninsa network ne, bayan ta daga tayi masa sallama, amsawa yyi yace "Is ur network fluctuating?" A hankali tace "Ina jin ka yanxu" yace "Ohk, Cewa nayi when xan xo in gaisa da Umma if possible har da matata kinga shkkn ta samu Umma a garin Abuja ita ma, cos she have no body here" Khadijah ta wara ido tace "Lah, are you married?" yace "Sure, kusan 3 months kenan" murmushi sosai Khadijah tayi tace "Allah sarki, Allah ya bada xaman lafiya" yace "Ameen thumma Ameen, to yaushe xa mu xo?" Khadijah tayi murmushin karfin hali tace "In dai kuna da time, kar ku ma ta gan ni tayi wani tunanin daban fa" dariya sosai Sadeeq yyi yace "Noo, she's understanding, kawai daga few months da aure sai ta sa abu a ranta don ta gan ki, ba ma yar Nigeria bace, so she won't think like them in sha Allah" Khadijah tace "Yar ina ce?" Yace "She is an Ethiopian" Khadijah ta wara ido tace "Kace bata jin Hausa kenan" yyi dariya yace "Noo tana ji ba laifi, ai tana xuwa hutu gun aunt dinta a Katsina sai dai tana dadewa bata xo bane, but she speaks English well" Khadijah da ke ta murmushi tace "Maa sha Allah, I will love seeing her" Sadeeq yace "Toh ko ki shirya da 'yan gidan ku sai in xo in dauke ku, she will be very happy don bata da kowa, though shekaranjiya dai wata frnd din mum dinta ta xo daga can kasar ta su, yanxu haka ma tana gidana, but ita ma nan da kwana biyu xata wuce" Khadijah ta langwabar da kai tace "Allah sarki, to yaushe xaka xo ka kai mu, amma ni dai ina tsoro fa" dariya Sadeeq ya dinga yi yace "Tsoron me? Na fa ce maki she is not like you people in Nigeria, I can even tell her you are an old time frnd, idan kinyi insisting kina tsoro kuma sai in ce ke yar uwata ce" Khadijah tace "Haka dai ya fi" Sadeeq yace "Dubeta matsoraciya, idan na aureki na hada ku fa?" ta d'an hade rai tace "Ni ance maka aure xan yi yanxu" yyi murmushi yace "Mayar da wukar wasa nake, nima baxan iya handling two wives ba ai" murmushi kawai khadijah tayi, yace "Tun da gobe Monday xan xo da yamma sai in dauke ku, sai ki sanar da umma" Khadijah tayi shiru don bata son fashin islamiyya, can tace "Toh shi kenan Allah ya kai mu" yace "Ameen Khadijah, bari in bar ki kiyi bacci, sweet dreams" tace "Toh nagode bye" daga haka ya katse wayar, Khadijah ta sauke ajiyar xuciya jin Sadeeq yyi aure, thank God baxai shigo rayuwarta bane ya dame ta, duk da can kasar xuciyarta tana ganin girma da darajar abinda yyi mata a lkcn tana Katsina, he really helped her don da ba don shi ba kilan idan yunwa na kissa da ya kasheta, murmushi tayi ta koma ta kwanta tana rufa twins dinta da duvet, matar da yace ya aura ce ta fado mata, toh Allah yasa sa'arta ce ko xata samu warce xa su dinga xumunci sosai da, don ta gaji da rayuwa daga ita sai Nanny da boys dinta bata da kowa, Aysha dama kawai a makaranta kadai suke interact, Har ranta taji hankalinta ya kwanta haduwa da Sadeeq, ko ba komai dai akwai wanda ya santa ta san sa a Abuja yanxu sai dai fa bayan sudais bbu wanda xata sake bata lkcn ba labarinta gaskiya, its not as if Sadeeq didn't deserve to knw her story but maimaitawan xai dinga fama mata ciwon da take healing a hankali na xuciyarta, da wannan tunane tunanen bacci ya dauke Khadijah, da asuba bayan ta idar da sllh tana xaune kan darduma tana azkar dinta Nanny ta shigo dakin da sallama, gaisawa suka yi tana kallonsu Sudais tace "Basu tashi cikin dare ba neman tea" Khadijah ta girgixa kai tace "A'a..." Nanny tace "Toh kafin dai ki gama shirin makaranta na san sun tashi, sai kiyi masu wanka, ni kuma xan tafi in hada breakfast yanxu" Khadijah tace "Toh" daga haka Nanny ta fita dakin, khadijah na fitowa daga wanka wajen karfe shidda da minti arba'in ta ga yaran xaune kan gado duk sun tashi, wara masu ido tayi ta nufesu ta durkusa tana murmushi a hankali tace "Good morning boys" kicin kicin suka yi da fuska suna kallonta kamar Aliyu ya hade rai, dariya hakan ya bata, tace "Toh bari in maku wanka sai ku tafi wajen nanny" daga haka ta koma bathroom din tana daure da towel ta hada masu ruwan wanka ta dawo ta dauke su gaba daya suka shiga bathroom din, a dakinta ta gama shirya su kafin ta tafi parlor da su nan Nanny ta sa tayi feeding dinsu, sai kusan karfe bakwai da rabi Khadijah ta gama shirin tafiya makaranta, tana isa bakin kofa ta juya tana kallon twins da suka bi ta da kallo, kamar hadin baki suka daga mata hannu a tare murmushi tayi ta daga masu ita ma sannan ta fita. Karfe hudu da kusan rabi Sadeeq ya kirata, bayan sun gaisa yace "xan taho yanxu Khadijah, am done for today a office" khadijah da ke dama ma su Sudais golden morn a parlor tace "Toh muna jira, Allah kawo ka lafiya" Tana gama ba ma yaran abinci tayi masu wanka ta shirya su cikin kayansu iri daya, sosai yaran suka yi kyau da kayan da ta sa masu, ta fiddo kayan da xata sa kenan Sadeeq ya kirata, daukan wayan tayi ta daga ta kai kunne yace "Am outside Khadijah" ta xaro ido tace "Toh don Allah yi hakuri, minti goma pls" yace "Alryt then, ina jira" a hanxarce Khadijah ta shirya sannan ta sa Hijab dinta har kasa kamar yanda ta saba, ta fita gun Nanny dake wankin kayansu shureim a bathroom dinta, ta tsaya daga bakin kofa tace "Nanny xa mu d'an fita da twins amma baxa mu dade ba" Nanny tace "Toh shkkn Allah ya kiyaye, amma kar kuyi dare kin ga yamma yyi" Khadijah tace "In sha Allah" daga haka ta fita ta shiga nata dakin ta fito tare da yaran, gabanta sai faduwa yake kar su ce baxa su bi ta ba, Har bakin kofa nanny ta rakasu tana daga ma yaran hannu su ma suna daga mata, tun kafin su iso motar Sadeeq ke kallon yaran, kawai ya bude motar ya fito yace "Waow, cute boys, ur siblings?" Khadijah ta kirkiri murmushi ta gyada masa kai daukansu yyi da daddaya da daddaya ya masu kiss yace "How are you boys" Kallonsa kawai yan biyun ke yi, ya bude front seat yana kallon khadijah yace "Toh shiga" tana shiga motar ya mika mata yaran gaba daya ya rufe motar sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da suka hau kan titi yace "Ya sunan twins din?" Khadijah tace "Sudais and Shureim" yace "Maa sha Allah, they are handsome, but step siblings din ki ne su koh?" dariyar karfin hali Khadijah tayi tace "Uhm" yace "That's nyc" yace "Har na sanar ma Shaheedah xuwan ki, she is so happy" Khadijah tace "Da gaske" yana murmushi yace "Sure" tace "Allah sarki" nisa ne sosai da gidan Sadeeq don sai kusan karfe biyar da wani abu suka isa gidan, haka kawai khadijah taji gabanta na faduwa, bayan yyi parking yace "Welcm to our home Khadijah" murmushi kawai tayi ta bude motar ya xaga ya taimaka mata sauke yan biyun kasa sannan ta fito ta rufe motar, wata kyakkyawar mace ce da baxata wuce shekaru ashirin a duniya ba ta fito balcony din gidan, fara ce doguwa mai kyan gaske, ta karaso gun motar tana murmushi sosai tace "Sannun ku da xuwa bak'in mu" Khadijah dake ta kallonta tayi murmushi tace "Yauwa sannu" wara ido matar tasa da ya kira da shaheeda tayi tana kallonsu Sudais tace "Maa sha Allah, dear they are sooo cute" daga haka ta tsugunna ta jawo yaran jiki tace "Welcome boys" Khadijah ma sai kallon yaran nata take ganin sun ki ko da murmushi, Sadeeq ya dau Sudais yana murmushi yace "Lallai boys din nan sun iya miskilanci" Shaheedah ta dau Shureim tana dariya tace "Mu shiga ciki toh" daga haka ta fara tafiya Sadeeq ya kalli khadijah yace "Mu je" bin bayan shaheedah tayi ya bi bayanta yana rungume da shureim. It's not much sorry.... Suna shiga parlorn khadijah ta xauna kan daya daga kujerun ciki, Shaheedah ta ajiye shureim tana murmushi tace "Wai basa magana ne?" Khadijah dai bata san ko suna yi ba ko basa yi amma taji Nanny tace suna yi idan sun ga dama, ta dan yi murmushi tace "Ba sosai ba, har yanxu basu iya ba" Tasowa Sudais yyi ya dawo kusa da ita shureim ma ya sauka kan kujera ya bi twin din nasa, Sadeeq yace "Lallai, yayarku kadai ku ka sani kenan koh" Shaheedah tace "Dama mana" daki Sadeeq ya wuce, Shaheedah kuma ta nufi fridge ta bude ta dauko masu drink da ruwa ta daura kan tray da cups uku sannan ta dawo ta ajiye tana kallon khadijah tace "Ban ma san sunan ki ba" Khadijah tace "Sunana Khadijah" Shaheedah tace "Ayya, ni kuma Shaheedah" Khadijah na murmushi tace "It's nyc meeting you Shaheedah" Shaheedah ta mayar mata murmushin tace "You too" abinci ta koma kitchen ta dauko a warmer da plates da spoon, khadijah tace "Lahh wllh mun ci abinci kafin mu taho Shaheedah" Shaheedah ta bata fuska tace "Saboda ke fa na yi girkin" Khadijah tace "Ayya da baki bai kan ki wahala ba, kin ga su ba cin abinci ma suke ba sai dai golden morn ko custard" Shaheedah tace "Toh sai in masu ai akwai custard din din ke sai ki ci wannan" da sauri khadijah tace "Kafin mu fito ba basu suka sha, ko kin yi baxa su sha ba da gaske" Shiru Shaheedah tayi kafin tace "Kenan dai baxa ki ci abincin ba Khadijah" Khadijah tayi murmushi tace "Toh xan ci Shaheedah" Shaheedah tace "Yauwa na ji dadi" daukan yan biyun tayi tace "Ku bar Anty ta ci abinci mu tafi ku gaida Mamata" Khadijah ta kalleta tace "Ayya mama na nan ne" Murmushi Shaheedah tayi tace "Idan kin gama cin abincin sai mu je ku gaisa" daga haka ta wuce da yan biyun dakinta, Shaheedah na rufe kofar tace "Mama dubi yaran nan masu kyau maa sha Allah" warce ta kira da mama dake xaune dakin kan darduma tace "Bakin naki sun iso kenan" Shaheedah tace "Ehh har da kanninta ma ta xo, ga su su taya ki hira xan kai ma sa abinci" Daga haka ta fita ta bar yaran a dakin. K'adan Khadijah ta ci tuwo da miyar ganyen da Shaheedah ta kawo mata, cin abincin take amma gaba daya hankalinta na kan yaranta da bata gani ba kuma bata ji motsinsu ba, tashi tayi daga karshe ta dau warmer din tuwon da miya ta wuce kitchen da su, ta wanke plate din da ta ci abincin da cup sannan ta fito parlor ta xauna, dai dai nan Shaheedah ta fito parlorn tace "Lahh har kin gama Khadijah, ko dai ba ki ci ba" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Aa na ci wllh, bacci suka yi ne?" Ita kanta sai da taji kunyar tambayar, Shaheedah tace "Aa suna gun mama ne, mu je ku gaisa tana daki" tashi Khadijah tayi tace "Toh" sannan ta bi bayan Shaheedah suka wuce dakinta, Shaheedah na shiga tace "Mama xa ku gaisa da khadijah" daga haka ta bar bakin kofar Khadijah ta shigo, tsaye tayi bakin kofar tana kallon matar dake xaune kan darduma su shureim a kusa da ita, lkci daya taji komai nata ya tsaya ta kasa kwakkwaran motsi wajen da kyar cikin tsarkewar murya tace "Ummaa" Sai a sannan matar ta juyo da sauri ita ma jin muryar da ta dade tana muradin sake ji ko da a ranan da xata bar duniya ne, mikewa tsaye tayi tana kallonta cikin wani yanayi tace "Khadijah??" Shaheedah da ta saki baki tace "Lahh mama kin san ta ne dama?" Juyawa Khadijah tayi da sauri hawaye cike idonta ta bar bakin kofar, Kan kace me har ta isa gate ta fice daga gidan hawaye masu xafi na sakko mata, da sauri ta isa bakin titi ta tsayar da adai daita ta shiga, tana jin Shaheedah na kwalo mata kira alamar sun biyota amma taki waigawa tace mai adai daitan ya tafi, har khadijah ta isa gida kuka take cikin Napep kamar ranta xai fita, ta rasa dalilin kukan nata, taji xuciyarta yyi mata rauni ga xugin da ya fara mata, mai adai daitan a tuaninsa rasuwa aka yi mata ya dinga bata hakuri bai ma karbi kudin ba ta shige gida, nan parlor ta xube ta kara rushewa da kuka kamar xata tsaga gidan, Nanny ta fito a rikice ta shiga tambayarta me ya faru ina su Shureim sai a sannan khadijah ta tuna da yaran nata, Nanny duk ta rikice ta mike ta fita ta sake dawowa a rude tace "Khadijah tambayar ki nake ina yaran me ya same su, ina suke" Khadijah ta hade kai da kujera cikin rawar murya tace "Ummata na gani Nanny" Nanny ta tsaya kallonta kamar idanuwanta xa su fito, can ta durkusa kusa da ita da sauri tace "Umma? Ummarki dai? A ina kika ganta" Khadijah ta kara fashewa da kuka tace "A gidan da muka je" Nanny tace "Toh sai ta ce maki me, ko bata gan ki ba?" Nanny bata rufe baki ba sai ga Shaheedah ta shigo parlorn a sanyaye, khadijah na ganinta ta kara hade kai da gwiwa tana kuka a raunane, Shaheedah ta isa kusa da ita ta durkusa a hankali tace "Dama ke ce khadijahr da mama ke shigowa Nigeria saboda tun shekaru uku da suka wuce, dama ke ce khadijahr da mama ke yawan maganar ta a can kasar mu?" Khadijah ta dago hawaye wasu na bin wasu tana kallon Shaheedah, girgixa kai Shaheedah tayi tace "Allah sarki khadijah na samu labarin ki a gun mama tun ban yi aure na dawo kasar nan ba, Khadijah Mama ta shiga wani yanayi bayan rabuwar ku, ta je garurruka da dama na Nigeria tana neman ki, ta dalilin ki mama bata da isashen lafiya har yanxu, Wllh wannan xuwan ma tana sauka Nigeria Kano ta fara xuwa wai ko Allah xai sa ta gan ki, daga kano ta tafi Katsina sannan ta taho Kaduna duk wai ko xa ku hadu kafin ta taho gidana nan Abuja kuma gobe ma take shirin komawa kasar mu" Shigowar Umma parlorn ya sa Shaheedah tayi shiru tana kallonta, kana ganinta kasan ita ma tayi kukan, Umma ta karaso parlorn a sanyaye ta xauna kan kujera kusa da khadijah wasu hawayen na sakkowa idonta, Khadijah ta kasa kallonta ita ma tana hawayen, Cikin sanyin murya Umma tace "Ko da baxa ki saurareni ba Khadijah ina neman gafarar ki, ki yafe min, na maki abinda uwar da ta haife ki baxa ta maki, Khadijah don nace ki tafi ba har xuciyata nake nufin haka ba amma kika yi wucewarki kika saka ni cikin kunci da damuwa, duniyar tayi min xafi barin idan na tuna baki da kowa, ban yi ma mahaifin ki hallaci ba, but what will someone expect from a frustrated Mother, God knows i was frustrated.... Shi yasa nace ki tafi, amma ban taba tunanin xa ki tafi ba" sakkowa Kasa Umma tayi ta durkusa kusa da khadijah tana kuka tace "Ki gafarceni Khadijah.... Forgive me plss" Khadijah ta daura kanta a kafarta tana kuka sosai cikin rawar murya tace "Umma baki min komai ba, nima ki yafe min, I know i failed you, amma ba laifina bane Umma, ni ban taba iskanci ba, I was raped...." Umma ta dagota ta rungumeta tana controlling nata kukan tace "I thought as much daughter, na yanke hukunci cikin fushi da tashin hankali ne, na yarda da tarbiyar da na baki, Allah ya saka maki koma waye yyi maki wannan aika aikan, shi ma xai ga sakamakonsa tun a nan duniya" Sosai Nanny da jikinta yayi sanyi tayi murnan haduwar Khadijah da ummarta, ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tana gode ma Allah da ya bayyana ma marainiyar ummarta, Shaheedah da duk jikinta yyi sanyi ita ma ta ji dadin reunion din Aminiyar mahaifiyarta da step daughtern ta after three good years. Shaheedah ce ta fita karbo su sudais gun Sadeeq dake mota bai shiga gidan ba, a hankali tace "Dear kaga for ur sake, mama will be happy once again, tayi reuniting da daughter dinta" murmushin karfin hali yyi yace "Sure, but am still confuse ban gane komai a nan ba fa, khadijah dai nasan gidan wan mahaifinta is few houses away from ours, so ban san kuma meye relationship dinta da mama ba" Shaheedah tayi murmushi tace "It's a long story, idan mun koma gida xan baka labarin dear" Sai kusan bayan Isha Sadeeq ya dawo daukan Shaheedah, Khadijah taki yarda Umma ta bi su don gani take kamar baxa ta sake kara ganinta ba. Da daddare suna xaune kan gado wajen karfe daya su Shureim na jikin Umma sun yi bacci, khadijah na bata labarin rayuwar da tayi bayan ta bar gida, tun farkon labarin har ta kawo karshe Umma kuka take, duk jikinta yyi sanyi don ta san duk ita ja ma khadijah duk abinda ya sameta, shiru ta yi tana tunanin me xata ma sudais kuma a ina xa ta gansa, khadijah da ke share hawayen ta cikin raunin murya tace "Umma har yau bai kara dawowa ba, i will never forget him in my life..." Umma ta jawota jiki tace "In sha Allah xai dawo wataran, he will come back to you daughter" Kai kawai khadijah ke gyada mata a xuciyarta tana addu'ar Allah ya gwada mata wannan rana, Umma ta katse silence da ya biyo baya tace "A ranan da kika tafi Khadijah babu inda ban fita nemanki ba tun ina yi da kafa har na koma abun hawa, sai bayan isha na dawo gida a lkcn ina addu'ar Allah yasa kin dawo sai na ga akasin haka, na shiga tashin hankalin da bana fatan in kara shigarsa har karshen rayuwata don nasan baki da kowa Khadijah, Wa ennan makiran dake gidan dama tuni sun sanar ma Alhaji kafin ma in dawo, ina shigowa kuma ya bani takardata kamar jira yake, hakan yasa naji bakin ciki kamar ya kashe ni domin, ce maki nayi ki tafi kar ki kashe min aure duk da bai kai xuciya ba sai gashi sakin ma na walakanci yyi min don ce min yi 1st thing da safe in tattara ina wa ina wa in bar masa gidansa, hakan kuwa aka yi don ban jira gari ya waye ba na fita neman wanda xai siya kayan daki na, ina siyarwa kuma kafin sha biyu na bar masa gidansa, da kudin kayan ba tafi Ethiopia... Bana son in dinga tuna yanayin da na shiga rashin ki Khadijah, ni dai kawai ki gafarce ni domin ni na ja maki komai da ban kai ki gun yakumbo ba da duk hakan bai same ki ba, ita kuma Yakumbo bani da abinda xance a kan ta yanxu domin kuwa ta riga mu gidan gaskiya" Khadijah ta dago da sauri tana kallon Umma tace "Umma yakumbo ta rasu?" Umma tace "Ta rasu kusan shekaru biyu kenan, electric ring ne ya ja ta har lahira, wai ta sa ruwan xafi a daki" jikin khadijah yyi sanyi ta ma rasa abinda xata ce, bayan wani lkci tace "Allah ya ji kanta" Umma tace "Ameen" a hankali khadijah tace "Umma na ki yafe min" sai kusan karfe uku suka kwanta, washegari da safe Umma tayi ma su Sudais da Shureim wanka suka fito parlor, Nanny da ta gama breakfast a kitchen ta fito ta gaida Umma, Umma ta amsa mata da murmushi nan tayi mata godiya kan tsayawa ma khadijah da yan biyun ta da tayi all this while, satin Umma daya a gidan tace ma khadijah xata koma kasar su amma xata dawo, kuka khadijah ta fara yi tace "Umma kina son ki tafi ki kara bari na ne" Umma tace "Noo khadijah xan dawo, ki bari in je in yi sallama da dangina sai in dawo mu xauna, amma fa baxan xauna wannan gidan ba sai dai in kama mana haya a Kaduna, wannan kuma ki rufe masu kawai" a hankali khadijah tace "Kaduna Umma?" Umma tace "Ehh" sauke idonta Kasa tayi bata ce komai ba, Umma tace "Forget ur past Khadijah, life moves on, don wani baxa ki ki xama a garin ba Beside gari me girma ma a ina xaki gansa?" Kai kawai khadijah ta gyada mata, wannan kuma shine mafarin komawarsu Kaduna, suka bar gidan da Sudais ya mallaka ma twins dinta a Abuja, life in Kaduna was smooth for them, sai dai khadijah ta kasa kwantar da hankalinta ta xauna lafiya a garin, ko yaya sai taji abinda ya faru shekaru uku na dawo mata duk da a kinkinau gidan da Umma ta kama masu haya yake, Tunanin da ta kasa cirewa a ranta yasa ciwonta ke yawan tashi wani lkcn har da kwanciya asibiti, hakan ya dinga daga ma umma hankali ta shiga tunanin to wani garin kuma xa su koma, don gaskiya bata son kano, a hankali dai khadijah ta hakura bayan watannin su shidda Kaduna. Kasuwanci sosai Umma ke yi don har Dubai tana fita Allah ya dubeta lkci kankani dukiyarta ya bunkasa, yanda take ji da jikokin nata ko Khadijah bata samu wannan gatan ba, tamkar ta mayar da su ciki take ji, su ma kuma haka suke sonta don ko da yaushe suna manne da ita, duk anguwan babu wanda yasan yaran Khadijah ne yan biyun masu shiga rai duk tunaninsu umma ce ta haifesu Nanny ma na tare da su har lkcn, kuma kusan tare da ita Umma ke fita waje ta xama kamar yar uwarsu, yanxu kam su sudais da baki ya bude basa gudun uwar ta su da suka dauka yayarsu ce Umma kuma Mumynsu, a haka Umma ta yi iya kokarin ganin khadijah ta samu admission a University of Cambridge dake UK, Khadijah bata ji dadi da farko ba ganin pharmacy suka bata don ba shine burin sudais a kan ta ba, amma umma tayi convincing dinta to go for it, shine ta tafi a haka, farkon xuwanta kasar tare da Umma Nanny da yan biyun ta suka taho suka mata sati sannan suka koma nan kuma ta mayar da hankali tana karatu ba ji ba gani domin xama qualified pharmacy, and then..... 1st khaleel ya sa ta gaba a kasar, that not being enough sai gashi ta hadu da wanda bata burin sake gani har karshen rayuwarta, why???? Silence din kusan 3 minutes ne ya biyo baya a parlorn, a hankali Khaleel ya dago kansa yana kallon khadijah da ta hade kanta da gwiwa, har ransa yake jin shesshekar kukanta, gashi ya kasa cewa komai, he is just lost of words, jinginar da kan sa yyi da kujera na kusan minti biyu kafin ya tashi a hankali ya isa gabanta ya duka ya dago kanta yana kallon idanuwanta da suka yi jajir, ta yi saurin sauke idonta daga kallon nasa kwayar idon da su ma suka sauya kamanninsu xuwa ja wasu sabbin hawayen na sakko mata, har lkcn Khaleel ya kasa cewa komai sai kallonta yake, bayan wasu dakiku abinda ya fito bakinsa cikin xaxxakan muryarsa shine "Forget about sudais, he did what he did for the sake of Allah, eraze him of ur mind" Da sauri khadijah ta dago tana kallonsa, ya mike ya koma kujerar da yake xaune yace "Yeah, ki mance da kin ma taba sanin sa a rayuwar ki, I mean that sudais..." Khadijah dake ta kallonsa ko kiftawa babu tayi karfin halin cewa "Ko saboda me?" A takaice yace "Ohk, it seems biyansa abinda ya maki kike son yi kenan?? If that's ur wish kema xaki iya taimakon marayu ai, I see no reason for good six years xa ki dinga tunani daya ba, beside he needs nothing from you, domin Allah yayi kuma Allah ne xai biyasa" Khadijah ta hade rai ta mike tana masa wani kallo tace "I regret telling you who i am, of all my story... part din sudais kadai ka ji da kyau halan? Shi kadai ka iya recalling? I just wasted the time I was suppose to use for sleeping" Daga haka ta nufi daki ta bar masa parlorn tana share hawayen idonta, Khaleel ya bi ta da ido ko kiftawa babu, jinginar da kansa yyi da kujera ya lumshe ido a hankali, wani mugun tausayinta ne ke shigarta, Sudais? Abinda ya fadi kenan a xuciyarsa ya bude ido da sauri, can ya tabe baki ya mike, ya fi minti biyu a tsaye yana kallon agogon dake nuna karfe uku saura kafin ya nufi bedroom dinta, xaune ya ganta kasa ta hade kai da gwiwa, Aliyu ne kawai ya fado xuciyarsa... ya hade hakoransa yana imagination kala kala a xuciyarsa, can yyi wani murmushi ya karasa cikin dakin yana kallonta ya durkusa gabanta, da farko rasa abinda xai ce mata yyi, can a hankali yace "Am sorry Khadijah, you misinterpret what I meant, ur story.... It is just heartbreaking, it's sad... you've past through a lot in life at a very tender age, but am happy you proved to be a strong lady, strong lady indeed...." Shiru yyi yana kallonta ko kiftawa babu har lkcn ta ki dago kanta, a hankali ya kai hannunsa ya dago ta suna hada ido ta rufe idon, murmushin sa mai kyau yyi yana kallonta, murya can kasa yace "Those cute boys...." Sai kuma yyi shiru, bayan wani lkci yace "You are going no where from UK, Aliyu ne xai bar maki UK ba ke xaki bar masa ba am giving you my words, kina nan har ki gama karatun ki" ta bude idonta a hankali tace "Ae ya riga yasan makarantar, he will surely keep on looking for me" hawaye ne ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Ni ban san me xan masa ba yake nema na" murmushi Khaleel yyi yace "Xai daina neman ki soon" Tana son kallonsa amma idanuwansa are not encouraging, ya lura da haka sai ta basa dariya ya mike yace "Alright then, life moves on, ki kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa ya hana ki walwala a kasar nan am assuring you, ki tashi kiyi wanka sai kiyi sllh if you wish and then go to bed, the night is far gone" Khadijah dake wasa da fingers dinta tace "But ina son xan je in ga su Umma..." Yace "When?" A hankali tace "Ko gobe" shiru ya d'an yi kafin yace "Alryt then Allah ya kai mu" Ya fi minti uku a tsaye har sai da ta daga kai ta kallesa ta ga kallonta yake tayi saurin dauke kanta, yayi murmushi murya can kasa yace "Good nyt" kai ta gyada masa daga haka ya juya ya fita duk jikinsa a sanyaye, she is really a strong lady, yana fita ya kulle mata kofar, haka kawai khadijah taji ta samu relieve sosai don kusan ji tayi babu abinda ke damunta a ranta kuma, tashi tayi a hankali tayi yanda Khaleel ya ce mata, sai kusan karfe uku da rabi bacci me nauyi ya dauketa. Tun da ya fito daki Kanwar Abbansa Hajiya Mariya ke bin sa da kallo, kitchen ya shiga ya fito ya sake shiga ya fito kamar xai koma daki sai kuma ya sake shiga kitchen din sai gashi ya kara fitowa Hajiya Mariya tace "Aliyu" juyawa yyi da sauri yana kallon direction din da take don bai ma san tana wajen ba, har ya iso inda take kallonsa take, ya xauna gefen kujera yace "Na'am mum" da damuwa tace "Aliyu what's wrong with you pls, meye matsalar ka dubi yanda ka lalace, abun har ya kai ya kawo ka fara behaving kamar mara hankali, yanxu meye ma'anar shiga da ficen da kake a kitchen kamar wanda ya xauce" k'asa kallonta yyi ya sunkuyar da kansa, wanda hakan yasa jikinta yyi mugun sanyi, tasowa tayi ta dawo kusa da shi tace "Gaya min abinda ke damun ka Aliyu, you Neva knw if I can be of help, ko baka dauke ni kamar Anty fatima bane" Hawayen da ta gani idonsa ya kara daga mata hankali duk ta rikice tace "Subhanallahi, Aliyu, why the tears, don girman Allah ka gaya min meye ya faru, or have you gone wrong somewhere? Tel me son.." damuwa ce karara dauke fuskarta, ya girgixa kai yace "Just keep on praying for me mum, and... I will be going to Nigeria tomorrow, amma baxan jima ba xan dawo" daga haka ya mike ya bar ta gun xaune ta bi sa da kallo baki bude, tashi tayi ta wuce dakinta ta dau waya ta shiga kiran Mumy, ba a dau lkci ba ta daga bayan sun gaisa da damuwa tace "Anty fatima ni dai ko xa ki kira Aliyu ki ji me ke faruwa wllh gaba daya na rasa gane kansa yana cikin damuwa sosai, yanxu ma da na sa shi gaba sai ya fada min damuwarsa hawaye fa ya fara min kuma ya ki fada, I really don't knw his problem, wllh ko abincin kirki bai ci sai kinga yanda ya rame..." Mumy ta tabe baki tace "Ina ga ke ce baki taba lura ba sai wannan xuwan da yyi maki, amma Aliyu ai ko da yaushe cikin damuwa xa ki gansa, ni na saba ma ganinsa a hakan, ni dai bani da xurfin ciki haka ma mahaifinsa so I don't knw... Shi ya sani, na sha ce masa idan ma wani laifin ya aikata ma Allah yayi ta istigifari, or may be ya ji labarin auren da Abbansa ke shirin masa ne shi yasa hankalinsa ya kara tashi" da mamaki Hajiya Mariya tace "Aure kuma?? Yaushe?" Mumy tace "Yanxu ma shirye shiryen da ake ta yi kenan, idan ya dawo sai ya dau matar su yi ta yawon da yake yi tare, amma kar ki gaya ma sa, shi yasa ma yayan ki bai gaya maki ba, just let him... Kila idan aka yi auren xai dawo hankalinsa" Hajiya Mariya tace "Toh ai ya ma ce min gobe xai tafi Nigeria" Mumy tace "Toh dai dai kenan goben juma'ah dama xa a daura auren ke dai kar ki ma ce masa komai, sai ya xo muna jiransa" jikin Hajiya Mariya yyi sanyi sosai don har ga Allah bata ji dadin jin hakan ba duk da ita ma rashin aurensa na damunta amma aure without his knowledge kuma?? Sallama mumy tayi mata ta katse wayar.Tun da Khadijah ta fito rike da karamar jakarta daga cikin apartment dinta khaleel dake tsaye ya rungume hannunsa ke kallonta cikin bakin glass din idonsa kuma saboda ita ya sa glass din, abaya baki ne jikinta da mayafinsa, sosai kayan ya haska ta daga nisa kamar balarabiya, tana isowa gun da yake ya dauke kansa ya fara tafiya xuwa waje, taxi ya tsayar masu don motarsa na gun wani abokinsa, ya bude mata ta shiga sannan shi ma ya shiga, sai da suka dau hanya yace "Have you call home? I mean kin gaya masu kina tahowa?" Girgixa masa kai tayi, yace "Why?" Kamar xata yi kuka tace "Umma xata iya cewa kar in taho" khaleel ya hade rai yace "Toh tunda haka ne meye amfanin xuwan? Kawai ki fasa, da kin gaya min haka tun a gida ma ni baxan fito ba" Hararansa tayi daga sama har Kasa bata ce komai ba, ya xaro ido daga cikin glass dinsa, kamar me counting words din yace "Did... you... just... eye me?" ta sake juyawa ta maka masa wani hararan tace "You check for your self, kuma ni ban ce dole ka rakani airport ba, xaka iya komawa gida" lkci daya ya xare glass din idonsa suka hada ido, tayi saurin boye fuskarta a kafarta kamar xata yi kuka tace "Bana so" murmushi yyi bai ce komai ba ya mayar da glass din ya shiga danna wayarsa, har suka iso airport bbu wanda yace komai cikinsu sai dai lkci lkci yake satan kallonta, Khadijah ta bude cab din ta fita shima ya fita ta daya side din ya ba mai taxin kudinsa, kallon agogo yayi kafin su shiga airport din, khaleel ne yyi mata komai a airport din tana xaune ya dawo ya xauna gefenta ya mika mata ticket, xaro ido tayi tace "Noo, give me ur account details pls" wani kallo yyi mata yace "Toh Hajiya" daga haka ya dauke kansa, jikinta yyi sanyi bata iya tace komai ba, Wayarta ta ciro a jaka xata tura ma Vanessa text don bata ce mata xata yi tafiya ba, kamar ance ta kalli side dinta ta ga Aliyu xaune though nesa da su yana danna wayarsa, gabanta yyi mugun faduwa.... Lkci daya kuma babu abinda ya fado mata rai sai yan biyunta kamanninsu ya baci ne kawai, xuciyarta ya dinga bugawa ta dauke kai da sauri tana addu'ar Allah yasa ba jirgi daya xa su yi boarding ba, kallonta Khaleel yyi ganin yanda ta matso kusa da shi ba tare da tasan tayi hakan ba, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kai trying to control her self, da wani expression khaleel dake kallonta yace "What?" Ta girgixa masa kai da sauri kuma har lkcn ta ki dago kanta, bata kuma matsa daga kusa da shi ba, duk iya kallon khaleel a wajajen bai ga komai ba sai turawa da few bakaken fata dake wajen, a hankali yace "Khadijah" ta dago da sauri tana kallonsa, yace "What happened?" Girgixa masa kai tayi da sauri, a tsorace tace "I don't knw why I am afraid" ya d'an bude ido yace "Afraid? Of what" ta buda masa hannu kamar xata yi kuka, shiru yyi na few seconds, a hankali taji yace "Ohk shud I accompany you?" Ta dago tana kallonsa, dogon hancinsa da bakinsa kadai take gani banda idanuwansa, samun kanta tayi da gyada masa kai, yace "Ohk then" mikewa yyi ta bi sa da kallo tana boye fuskarta da mayafin jikinta ta saci kallon direction din Aliyu, yanxu ba danna waya yake ba ya dai jinginar da kansa da kujera yana kallon yaran turawa dake tare da uwarsu suna tafiya, da sauri ta dauke kanta. Har suka shiga jirgi Khadijah bata daina shisshge ma Khaleel ba, tayi sa'a kuma seat dinsa kusa da ita, suna keta haxo ta dinga bin jirgin da kallo cikin dubara amma ba ta ga alamar Aliyu ba, bacci ne ya dauketa daga karshe sai dai ta rufe rabin fuskarta da veil dinta, khaleel ya dinga kallonta, ya rasa gane irin tausayin da yake ma khadijah, ya san har ransa kuma he don't knw why, a hankali ta jinginar da kanta a shoulder dinsa, jawota yyi jikinsa ya lumshe idanuwansa, bayan awanni da dama Khadijah ta bude idonta a hankali, kallonsa tayi ta janye jikinta da sauri daga nasa, ya buda manyan idanuwansa yace "Are you hungry?" Ta girgixa masa kai, kamar ance ta kalli gefensu taga Aliyu xaune ya makala earpiece a kunnensa idonsa a lumshe, boye fuskarta tayi jikin khaleel jikinta na bari, khaleel ya riketa da mamaki yace "Are you okay?" Girgixa masa kai tayi a tsorace, bin jirgin ya dinga yi da kallo shi ma, lkci daya idonsa ya sauka kan Aliyu, haka kawai yaji gabansa ya fadi... Ya dinga kallonsa ko kiftawa babu don ko ba a fada ba kawai ya ga shureim da sudais a tattare da shi, lkci daya ya dauke kai, Khadijah da ta rufe fuska ta ki yarda ta kallesa, sauran journey din gaba daya daga ita har khaleel they where uncomfortable, khaleel ya kalli direction din Aliyu ya fi a kirga, gwara Khadijah tayi kokarin ganin bata sake kallon direction din ba, few hours kafin jirginsu ya sauka Abuja Khadijah ta d'an saci kallon gefensu dai dai lkcn da Aliyu ya juyo, hada ido suka yi sai dai fuskarta dama a rufe yake, ji tayi kamar an soka mata mashi a xuciya tayi saurin kauda kanta, shi ko yana ta kallonta bayan wani lkci ya dauke kansa. Har suka yi set down Khadijah ko da wasa ba ta juya kanta ba. Khaleel ya jira mutane suka fara sauka kafin ya mike, ita ma ta tashi da sauri, kamar xata shige jikinsa haka ta dinga bin sa har suka sauka matakalan jirgin, tsaye ta hango Aliyu nesa da jirgin yana kallonsu bayan shi ya sauka, taji kafafuwarta sun kasa daukar ta don tasan kila ya ganeta ne, har suka sauka Khaleel bai gansa ba don wani abokin sa bature ya dauke hankalinsa suna gaisawa, Aliyu dake ta kallon idanuwan khadijah da su kadai yake iya gani ya nufo ta, dai dai gabanta ya tsaya lkci daya ya fixge veil din fuskarta yana kallonta, rikicewa tayi, khaleel ya juya da sauri, ganin abinda Aliyu yyi ya cakumosa cikin tsawa yana masa wani mugun kallo yace "How dare you?" Daga sama har kasa Aliyu ke kallon Khaleel da ya ki sake sa, Aliyu ya dake yace "Who are you?" khadijah na ganin haka a rikice ta ajiye jakar hannunta tace "Noo plss Dr ka kyale shi..." Khaleel na kallon kwayar idon Aliyu strictly yace "Stay away from her or else you regret it...." Yana fadin haka ya sakesa, Aliyu yyi wani murmushi yace "And who are you to tell me that? Her boyfriend? Husband or??" Juyowa khaleel yyi a mugun fusace ya sake cakumosa Aliyu ma ya cakumesa yana mayar masa da irin kallon da yake masa, khaleel yace "Both! Husband and boyfriend" dariya Aliyu yyi yace "You are very very stupid, idan ma mijinta ne kai ka shirya rabuwa da ita domin kuwa she is not meant for you" Khadijah na ganin abun ya kai haka ta shiga tsakaninsu da sauri cikin kuka tace "Wayyo na shiga uku, don Allah don annabi ku rufa min asiri ku yi hakuri" tayi facing din khaleel dake hade fist dinsa yana ma Aliyu wani irin kallo ta rikesa hawaye na sakko mata tace "Plss am begging you ka kyale sa don Allah Dr" lkci daya khaleel ya sake Aliyu ya kama hannunta ya dau jakarta, Aliyu ya fiddo complimentary card dinsa a aljihu ya saka a na Khaleel yana kallon kwayar idonsa yace "I will be waiting for ur call young man" still khaleel yyi kamar xai cire ya jefar sai kuma ya bari ya juya kamar xai tashi sama ya bar wajen Khadijah ta dinga bin sa xuciyarta na bugawa, Aliyu ya bi su da kallo yana murmushi a hankali yace "I will surely get you soon Iman, not when I have set my eyes on you" ta waigo ta kallesa tayi saurin dauke kai, har suka shiga cab Khadijah waigawa take taga ko ya biyo su, sai dai ta kasa ganewa don mutane ne da yawa ko ganinsa bata sake yi ba, duk ta kasa samun nutsuwa, tana kallon Khaleel da har sannan fuskarsa ke a daure kamar xata yi kuka tace "Plss Dr kar ka sake kulasa" Kallonta khaleel yyi a fusace xuciyarsa na heaving yace "That's idan bai shiga rayuwar ki ba, Billah xan iya yi masa komai, I don't care... Ina da wanda ya tsaya min a kasar nan, look... my father...." Sai kuma yyi shiru, lkci daya idanuwansa suka canxa kamanni, Khadijah jikinta yyi sanyi sosai, muryar khaleel ne ya dawo da ita tunanin da ta tafi, cikin sanyayyan muryarsa yace "Don't forget this is Abuja, ina xa mu? Thinking Kaduna kika ce min Umma take" A hankali tace "Dole sai mun bi train xuwa Kaduna" yace "Why not flight" ta hararesa tace "Bayan mun baro airport din, kawai kaje xaka tara mana crowd a airport ko meye na kulasa" bai ce komai ba sai kallon tagar taxin yake, khadijah ta sanar ma mai taxin train station xai kai su, Tsaki taji khaleel ya ja yace "Seriously It's being long aka ba ta min rai haka... Da ba don airport bane we ought have teach each other a lesson da guy din nan, I don't even care about d securities there..." Khadijah dai sai kallonsa take ganin how serious he was, Juyowa yyi ya kalleta tayi saurin dauke kanta, murya can kasa yace "It's because of you khadijah, don ke na kyalesa da mun yi karamin exercise a wajen nan" ta tabe baki tace "Ni dai babu ruwana" yayi murmushi da ya bayyana dimples dinsa yace "Billah ke kuwa ke da ruwa baby" kallonsa tayi da sauri, ya tsuke fuska kamar ba shi ya fada ba ya fiddo wayarsa yana dannawa, tayi murmushi tana ci gaba da kallon waje, suna isa station suka samu jirgin kasa mai xuwa Kaduna, Khaleel ya yankar masu ticket, sai da jirgin ya tashi khadijah ta kallesa tace "Are you a Nigerian" kallonta yyi, ta sauke idonta, yyi murmushi yace "Sure, A Nigerian... From Kaduna also, why do you ask, ko ban yi kama da ku ba ne" bata ce komai ba, shima bai ce komai ba, bayan few hours suka isa station din train dake kaduna, Napep suka dauka da xai kai su har gida, Yace "Do I have to accompany you har kofar gida" Khadijah ta kallesa sannan ta sa mai Napep ya tsaya tace "Sauka toh ka hau wani adai daitan ka tafi gidan ku" wara ido yyi yace "Like serious??" Ta langwabar da kai tace "Sure" murmushi yyi ya sauka yace "Ohk then" tace "Yeah, thanks" daga haka ta sa mai Napep din ya wuce khaleel ya bi su da kallo. Khadijah na isa gida ta sauka ta bude Jakarta, tunawa tayi ba kudi wajenta ta basa hakuri tace bari ta amso a ciki sannan ta shiga gida, sudais da shureim ne parlor suna kallon cartoon, suna ganinta suka mike a guje suka yi kanta suna mata oyoyo ta rungumesu gaba daya cike da murnan ganin yan biyunta, Umma dake kitchen ta fito da mamaki tana kallonta, da kyar ta yakice yaran a jikinta ta nufi Umma ta rungumeta tace "Ummata na dawo" Umma na kallonta tace "What happened Khadijah??" Ta marairaice tace "Umma ina missing din ku ne na taho fa" Umma ta hade rai tace "Kina da hankali kuwa, kamar warce xata taho daga kano, yaushe kika koma da har xaki taho yanxu" shiru ta yi bata ce komai ba, Umma ta saki baki tana kallonta a mamaki, juyawa khadijah tayi ta nufi jakar Umma dake ajiye parlorn ta bude ta fiddo kudi tace "Umma bari in kai ma mai adai daita" daga haka ta fita ta kai ma sa kudin sa twins dinta na rike da ita, suna dawowa parlor duk suka haye kanta Shureim yace "Anty ina wannan uncle din nan dake UK, did he tell you to greet us?" Khadijah tayi murmushi tace "Sure sweetheart" Sudais yace "Anty is he also from Nigeria, I like him" Umma dake kallonsu tace "Wani uncle suke fadi?" Khadijah ta saci kallonta tace "Neighbor dina ne fa Umma" Umma tace "Ba mace bace kwanaki da muka je?" Khadijah tace "Ayya, Nancy ai ta tashi" Shiru Umma tayi kafin tace "Toh dai a kula, Allah ya ci gaba da tsare ku" A hankali khadijah tace "Ameen" Umma tace "Toh don me wai baxa ku xauna tare da Vanessa ba?" Khadijah tace "Umma am nt comfortable a gidanta ne" Umma tace "You have no choice, bana son xaman ki gida daya da namiji" da sauri khadijah ta kalleta, murmushi tayi tace "Umma he is a Nigerian, kuma I think bahaushe" Umma tace "So?" Shiru Khadijah tayi, Dai dai nan wayar dake jakarta ya fara ring ta bude jaka da sauri ta fiddo tunawa da tayi wayar khaleel ne, shiru ta yi tana kallon number kafin ta daga, muryarsa taji yace "Are you home?" Ta saci kallon Umma Kafin ta mike tace "Uhn" daga haka ta wuce daki yaranta suka bi bayanta Umma ta bi su da kallo. Flight Aliyu ya bi ya taho kaduna, Ji yayi gaba daya ba wani sauran damuwa a tare da shi, lkci lkci sai yyi murmushi, har ya isa gida a taxi tunanin Khadijah yake, he is just happy seeing her today, bayan ya sauka taxi mamakin me ake yi a gidan ya dinga yi ganin mutane da manyan motoci har su Usman da Sanusi shadda ce sabuwa jikinsu, suna ganinsa suka washe baki suna masa sannu da dawowa, ya amsa gaisuwarsu ya entrance din gidan, ganin takalma da yawa alamar mutane ne sosai parlorn ya xaga ta baya, iklima ce bakin tap a durkushe tana kwarara amai, ya karasa yana kallonta ganin uban kunshin da aka mata ga kitso an yaryara mata a kai, yace "Baki da lafiya ne?" Jin muryarsa ta dago da sauri, lkci daya ta mayar da kanta ta sunkuyar, tana maida numfashi da kyar tace "Sannu da dawowa yaya Aliyu" bai damu da ya amsa ba yace "Me ake yi a gidan nan?" Shiru tayi da farko kafin tace "Aurenmu" Few seconds yyi amfani da wajen apprehending abinda ta fada, cike da confusion yace "Aurenmu? Aurenmu da wa?" Still bata kallesa ba tace "Ni da kai" bude baki yyi yana kallonta dai dai fitowar Anty khadijah tayi wani shegen haske ta xama katuwar gaske, tana ganinsa ta saki guda tace "Saukar yaushe ango?" Aliyu na xaro ido yace "Anty ban gane ba, ango kuma?" Anty khadijah na taunar cingam da ya cika waje da kara tace "Tafi Anty fati na daki xata maka bayani yanda xaka gane my son" daga haka ta nufi 'yar ta tace "Ki taso mu je, mai make up din ta gaji da jira" janta tayi suka Wuce ciki suka bar Aliyu tsaye baki bude, har lkcn shi dai bai fahimci komai ba. Wucewa ciki yyi direct ya tafi sama Dakin Mumy ba tare da ya kula da mutanen dake parlor ba, ita da frnds dinta sai mahaifiyar Abbansa da suke kira da yaya ne xaune dakin, yyi hankalin gaishesu kafin yace "Mumy I don't get what's happening in this house" Yaya tace "Bikin ku ake yi da 'yar uwar ka" Aliyu ya yo waje da ido yace "Wace yar uwar tawa?" Yaya tace "Iklima, Allah bai yi da Hanan ba" Wani kallo Aliyu ya dinga yi mata kafin yace "Allah ya kiyaye, wace iklimar? Iklima da ta gagari kowa gidan nan xa a makala min, No Mumy I have never failed you but... No mum me yasa xaki min xabin da xai cutar da ni, mumy kema kinsan iklima ta fi karfina, Mumy ki rufa min asiri..." Tsawa Mumy tayi masa ta mike tana masa wani mugun kallo tace "Get out Abuturrab, idan an kai ma iklima gidan ka kayi gunduwa gunduwa da namanta ko kuma ka koro mana ita, fita nace" Juyawa Aliyu yyi ya fice daga dakin, Yaya tace "Fatima, da gaske yarinyar ta gagari kowa? Ni dai an san ba saninta nayi ba, kar ku cutar min jika" Mumy ta hade rai tace "Yaya yar yar uwata ce uwa daya uba daya fa" tana fadin haka ta fita dakin, kawayenta suka bi ta da kallo. Washegari da yamma khadijah na xaune parlor tare Umma da Nanny dake yankan alaiyahu, reading material dinta ne hannunta tana dubawa, Umma tace "Wai da wa su sudais ke waya haka ne tun daxu Khadijah?" Khadijah ta dago kanta tana kallonta a hankli tace "Umma wani ne" Umma tace "A ina kika san sa? Ko in ce a ina suka san sa" Murmushi kawai khadijah tayi bata dai ce komai ba, jin little sudais na kiranta ta juya tana kallon direction din dakin sai ga shi tare da d'an uwansa, wayar hannunsa ya mika mata yace "Uncle yace we shud hand over the phone to you" Khadijah ta amshi wayar tana satan kallon Umma dake kallonsu ta mike ta wuce daki, rufe kofar dakin tayi ta xauna gefen gado ta kai wayar kunne tace "Yes? Ina ji" Yace "Yea I knw kina ji, can I come over to see d boys now?" Shiru Khadijah tayi tana kallon agogo kafin tace "Xan gaya ma Umma tukun" yace "Alryt then, I will be waiting for ur call" a hankali tace "Tohm" daga haka ya katse wayar, tunanin me xata ce ma Umma ta dinga yi kafin ta mike ta fita, xauna gefen kujera tayi murya can kasa tace "Umma someone is coming over now" Umma ta daga kai ta kalleta tace "Who?" Ta d'an turo baki tace "Wani ne" murmushi Umma tayi tace "Allah kawo sa" khadijah ta mike ta koma daki, text ta tura ma khaleel na address din unguwarsu da house number. Cikin minti talatin khaleel ya iso gidan, Khadijah ta sa Hijab ta fito daga dakinta ta shiga na umma tana kallonta tace "Umma yana waje" Umma tace "A wajen xa ki bar sa baxai shigo ba" murmushi kawai khadijah tayi ta fita, tun da ta fito gate take kallon motar da khaleel ya xo da shi har ta isa gun motar ta tsaya tana wasa da fingers dinta, bude motar yyi ya fito ya xaga ta inda take, farar gizna ne jikinsa sai walkiya yake da hula, wani kyau yyi na musamman ya dawo kamar balarabe cikin shigar hausawa, Ita dai bata taba ganinsa da irin shigar ba ta dauke kai daga kallonsa tace "Dama kana sa manyan kaya?" Ya d'an bude ido ya rungume hannunsa ya jingina da motar yace "Dama kina sa Hijab?" Dariya ya bata amma bata yi ba tace "Aa sai kananun kaya in yi sagging wandon" xaro ido khaleel yyi yana kallonta, tayi murmushi bata kalli direction din sa ba, Kallonta ya tsaya yi na few seconds kafin yace "Where are the boys?" Tace "Suna ciki" yace "Amma kin san ba wajen ki na xo ba dai koh" shiru ta yi trying her best not to look at him, can tayi murmushi tace "Alryt then" daga haka ta nufi gate, Wara ido yayi yace "Khadijah" sai da ta isa gate tace "Bari in turo maka su" yace "Wait..." Amma tuni ta shige gidan, murmushi yyi yana shafa beard dinsa, ba a dau lkci ba sai ga yaran sun fito suna ganinsa suka taho da gudu suka rungumesa ya daga su sama gaba daya happy seeing them, kai kana ganin yaran kasan su ma ba karamin farin cikin ganin khaleel suka yi ba, ya bude back seat din motar ya sa suka shiga sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, wayar sa ya dauka ya shiga kiran Khadijah, kin dauka tayi yayi murmushi ya tada motar ya bar layin da yaran. Tun da Aliyu ya dawo masallaci da asuba ya sa makulli dakinsa, shi dai ya kasa gaskata wai iklima aka aura masa, yarinyar da idan ta fita tun safe sai dare wani lkcn xata dawo gida, uwar kuma tace gidan kawunta take xuwa, yau idan ka ga wannan wayar hannun iklima to gobe wani daban xa ka gani, islamiyyar ta ki xuwa, bokon kuma anyi withdrawing, rike kansa yyi xuciyarsa na masa kunna, kwankwasa kofar dakinsa aka yi for the countless time, ko kallon direction din kofar bai yi ba, "Yaya nice baby ka bude plss" muryar da ya ji kenan, ya lumshe idanuwansa ya bude, mikewa yyi da kyar ya nufi kofar ya bude yana kallon Kanwar tasa, ta shigo ya rufe kofar, da damuwa tace "Yayanmu kayi hakuri, I don't knw what came over Mumy, bn san me yasa tayi haka ba bayan ita da kanta kullum complain take a kan iklima... Her character is so obvious to everyone, kowa yasan abinda take but mumy tayi kamar bata sani ba ta hada ku...." Aliyu ya xauna gefen gado ya rike kansa, Baby tayi tagumi tana kallonsa, bayan kusan minti goma tace "Kayi hakuri yaya" ya dago da jajayen idanuwansa yana kallonta yace "Go make me a cup of coffee" Baby na fita daga dakin dai dai fitowar Anty khadijah da ke ta kai kawo kamar warce tayi ma sarki karya, barin da taga Aliyu ya bude ma Kanwar tasa kofa, xuwa yanxu gidan ya watse sai yan uwa na jini, bin baby tayi downstairs tace "Takwara me Aliyun yace maki?" Baby taki kallonta tace "Abu yace in kai ma sa" Anty khadijah dake ta bin ta tace "Me kenan?" Baby tace "Coffee" Anty khadijah tace "Atoh ni har na gaji da maganar bai ci komai ba tun daxu, yanxu abinda xa ayi kawai kiyi wucewar ki xan hada masa in ba matarsa ta kai ma sa, mutum ya sha hanya haka kuma ya makale daki tun jiya babu abinci" Baby tace "Anty amma ai baki san yanda yake son coffee dinsa ba, ni xan masa" Anty khadijah ta galla mata harara tace "Toh uwar iyayi, kin tashi gabana ko sai na mare ki, idan nayi masa kar ya sha" daga haka ta wuce kitchen baby ta bi ta da wani kallo, Anty khadijah na shiga kitchen ta tura kofar kitchen din ta rufe ta yi saurin ciro wani kulli a bra dinta, "Son da xai mata sai ya fi wanda yake ma uwarsa da kowa na duniya... In dai ya sha maganin nan" muryar gardin da ya bata maganin kenan ke kai kawo a kunnen Anty khadijah kamar yana kusa da ita, har wani rawa hannunta yake ta juye gaba daya a cup sannan ta debi coffee powder ta xuba a kai ta xuba ruwan xafi ta jefa kwayan sugar biyu, sama ta tafi da sauri ta shiga daki gun iklima dake kwance, Anty khadijah tace "Ni fa dadina dake shegen son jiki, daga d'an xaxxabi dubi yanda kika wani yi laushi kamar warce tayi watanni ba lafiya, a haka xa a kai ki gidan Aliyun gobe" Iklima da ta lullebe da bargo tace "Ni wallahi ki rabu da ni don ba ke ce ke jin abinda nake ji ba, duk kin bi kin dame ni tun daxu" Anty khadijah tace "To uwata sai ki rufe ni da duka ai, ni ki tashi ki kai ma Aliyun coffee" iklima ta xaro ido tace "kaji ta, Salon ya koro ni.... Mutumin da tun jiya yake daki" Anty khadijah tace "Toh don ubansa ba sai ya koro ki ba, kilan ma a can xa ki kwana ki tashi kina bata lkci..." Gun kayan kwalliyan Iklima na amarya Anty khadijah ta nufa ta dauko wani turare can kasa a karamin kwalba ta bude ta shashshafa mata a ko ina na jikinta, iklima da ke ta wani yatsine fuska ta koma ta kwanta tace "Mama wllh jiri nake gani, anya xan iya fita" hararata Anty khadijah tayi tace "Xan je in dauko maki shayin a dai don ki fita nan ki shiga dakinsa baxa ki ce min baxa ki iya ba" daga haka ta wuce kitchen ta dauko coffeen dake rufe a mug ta kawo ma iklima, da kyar ta tashi ta karba tana duddukawa ta fita dakin, a hankali ta tura kofar dakin Aliyu dake kwance ta shiga ta rufe Ta isa kusa da gadon ta ajiye mug din hannunta a kasa, bude ido Aliyu yyi jin yanda kamshi ya bade dakin suka hada ido da iklima, karasowa kusa da shi tayi tace "Yayanmu sannu da hanya ga coffee din na maka" Wani mugun kallo Aliyu ya dinga mata yace "Kina hauka ne xa ki shigo min daki" tace "Da daban xama matar ka ba ina shigowa ne" bude kofar dakin aka yi sai ga baby ta shigo sau daya ta kalli iklima ta harareta ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tace "Ga abinci yaya mumy tace in dibar maka" daga haka ta bude warmer din abincin iklima ta yamutse fuska ta dauke kai da sauri, lkci daya aroma din abincin ya cika dakin, da tari ta fara, sai kuma ta toshe baki, da gudu ta mike kafin ta isa kofar bathroom ta wanke tiles din dakin da amai, kallonta Aliyu yake ko kiftawa babu ta dinga amai kamar xata shide, baby ma sai kallonta take, tashi yyi ya isa gabanta da wani expression yana kallon gaba daya jikinta, mikewa tayi bayan ta gama ta fada kan gado tana sauke numfashi ya koma kusa da ita yana kare mata kallo da kyau, squeezing fuskarsa yyi yace "What??" Lkci daya ya juya ya fice baby ta bi bayansa da sauri, Mumy na haurowa sama tare da Anty khadijah dake bata shawarar kawai gobe su Aliyu su wuce gidansu yau dai su kwana a gidan, ganin Aliyu Mumy ta daure fuska don tun daxu yaki fitowa har ita ta yi masa magana amma ya ki bude kofar, yana kallon mumy cikin wani yanayi yace "Mumy ita mai cikin xa ku ce kun aura min?" Kallonsa Mumy ta tsaya yi cikin rashin fahimta haka ma Anty khadijah, baby dake tsaye gun ta xaro ido tana kallonsa, Da mugun mamaki Mumy tace "Halan Aliyu ya fara xarewa ne ni Fatima?" Yace "Xarewa kuma Mumy wllh ciki ne da iklima, don't forget my profession idan ma baku yarda ba yanxu sai a kira wani likitan, gashi can yanxu ma amai ta gama yi" Anty khadijah ta saki ta salati ta fashe da kuka tace "Aliyu, ita yar tawa xaka ma wannan gagarumin sharrin don a rufa ma asiri an aura mata kai? Ita iklimar ce ke da ciki?" Aliyu ya mata wani kallo yace "Sharri Anty? sai a tafi asibiti yanxu ai, ni dama nasan a day like this na nan xuwa very soon, ina ce har guest lodge na taba ganin iklima na same ki daki na gaya maki few years back, me kika ce min then? Cewa kika yi na tsaneta na sa mata ido, Duk yawon da take ta kai dare kin taba tsawata mata, of course no sai dai kice gidan kawunta taje, so it's nt a thing to be surprise don iklima na dauke da ciki ynxu" tuni sauran yan biki dake gidan suka shiga fitowa corridor din, Mumy dai ta saki baki ta kasa cewa komai, Anty khadijah dake ta xufa tace "Tunda abun yar tone tone ne sai mu yi ta ai Aliyu, wato har kai kana da bakin da xaka bude ka kira 'ya ta yar iska ka mance lkcn da kake tashan naka iskancin, ka mance irin yanda kayi ma yar mutane fyade a cikin gidan nan, wanda ta dalilinka ta bar gidan har yau bata dawo ba, duk ka xata ban sani ba koh???" Lkci daya komai na Aliyu yyi still ya tsaya kallonta ko kiftawa babu, Anty khadijah ta juya tana kallon mumy tace "khadijah dai da kika sani, yarinyar da kika dau aiki ta yi wucewarta ko sallama babu shekaru kusan shidda baya, ya fada maki abinda yyi mata ta bar gidan da bakin sa yau...." Aliyu ya lumshe idanuwansa da suka kada lkci daya ya ji kansa na sara masa, kallonsa mumy ta dinga yi kamar idonta xai fito haka kanninsa gaba daya da bak'in da suka fiffito, Anty khadijah na girgixa kugu tace "Ko baxa kayi bayanin ba in taya ka?" Bude ido yyi da kyar yana kallon Mumy. Anty khadijah na kallon Aliyu da kyau tace "Ko baxa kayi bayanin ba in taya ka ne dakta?" Bude ido Aliyu yyi da kyar yana kallonta, lkci daya idanuwan Mumy suka kawo ruwa kana ganinta kasan ba karamin shock ta shiga ba, Aliyu ya isa gabanta ya duka kan gwiwowinsa cikin sanyin murya yace "Mumy..." Dakatar da shi tayi hawayen idonta na sakkowa tace "Irin tarbiyar da nayi maka kenan Aliyu.... Yanxu yar mutanen kayi ma haka?" Ya rufe fuskarsa jikin kafarta cikin rawar murya yace "That's the greatest mistake of my life mum, shine abinda na kasa gaya maki shekaru shiddah kenan, mumy ba halina bane kema kin sani, ban san ya aka yi ba ranan, it look as if I was possessed, I ruin the little girl... Mumy I...." Kasa ci gaba yyi hawaye na sakko masa, Anty khadijah ta tabe baki tace "Lallai Abuturrab baka jin kunyar karya? abu ya faru ba sau daya ba ba sau biyu ba ka kirasa mistake? Tunda abun ba arxiki har ya kai ga ka fara yi ma 'ya ta sharri to wllh nima baxan duba abinda ke tsakanina da mahaifiyar ka ba, gwara in tona maka asiri, idan ni baka ji kunyar toxarta ni da iklima ba to nima baxan ji kunyar ramawa ba a matsayin ka na d'an yayata" daga haka ta bar wajen ta shige daki... Aliyu ya bi ta da kallo, duk abun nan da take fada fa ba ji yake ba mamakinsa shine ya aka yi tasan abinda ya faru tsakaninsa da Khadijah bayan bata gida ranan, how is that? Fitowa Anty khadijah tayi daga dakin rike da iklima da ta sa ma Hijab suka sauka downstairs kamar xata tashi sama tana matsar kwalla tace "Da raina kayi ma yar cikina irin wnn sharrin koh Aliyu, duk matsayina gun uwarka baka gani ba saboda na rufa maka asiri da yawace yawacen da kake nace a aura maka 'ya ta shine xaka mana wannan cin mutuncin ka saka min da sharri" gidan ta bari gaba daya tare da yar ta, Mumy ta juya ta koma dakinta a sanyaye, Aliyu ya kasa daga kai ya kalli kanninsa da sauran relatives dake wajen. Anty khadijah na fita da kafa suka karasa bakin titi da iklima, hankali tashe take tambayarta yaushe rabon da ta ga al'adarta, iklima ta turo baki tace "Oho nima ban sani ba" dundu ta kai mata tace "Kaji min shegiya wai baki sani ba, ni nake maki al'adar? To wllh sai dai ki daura ma ubanki hawan jini ba ni ba, mu je asibitin ai xa su mana bayani a can, in ma ya kama in kashe ni Wllh sai in kashe Ki a can din, tunda duk abinda nake maki bakya gani ni xaki ja ma abun kunya ni xaki kunyata a idon duniya" Ganin sun shiga Napep yasa Anty Khadijah tayi shiru sai girgixa kafa take tana Allah Allah ta ganta a asibiti har suka isa asibitin dai, iklima kam ko dar sai ma gyangyadi da take ta yi a napep din, suna shiga asibitin likita ya tabbatar ciki gare iklima, Anty khadijah ta daura hannu a ka tana xaro ido tace "Na shiga uku na lalace ni Khadijah, iklima yanxu ni xa ki ma haka, a ina kika je aka maki ciki, don na sake maki sai ki tona min asiri iklima? Ni xa ki kunyata?" Shi dai likitan kallonsu kawai yake, Anty khadijah ta share xufar dake keto mata ta hadiye yawu da kyar tace "Likita ko nawa kake bukata ka fada xan baka ka raba ta da wannan bala'in dake tare da ita ka rufa mana asiri" likitan yace "A'a ba ma haka a nan Hajiya ku yi hakuri, ku je wani asibitin..." Anty khadijah ta fashe da kuka a karo na farko tace "Haba bawan Allah, kai baka taimako ne, wllh dariya xa a mana ka rufa min asiri ina da makiya da yawa duniyar nan, ka ji tausayina ka taimaka mani" Likitan yace "Wato kin fi so kiji kunyar lahira a kan ta duniya kenan Hajiya?" Da sauri Anty khadijah tace "Eh wllh" sake baki yyi yana kallonta, can ya gyada kai yace "Gaskiya ne, toh Allah ya shirye ku, kuyi hakuri ku fita akwai patients da xan yi attending ma yanxu, mu ba ma aborting ciki a nan" tashi Anty khadijah tayi tana masa matsiyacin kallo tace "Yanda ka ki taimakona kai ma haka yar ka xata jajibo maka abun kunya ka rasa madafa in sha Allah, mara imani kawai..." daga haka ta ja Iklima kamar xata tashi sama suka fita, haka Anty khadijah suka dinga yawo hospitals tana neman inda xa a cire ma iklima ciki har dai ta samu wani da kyar, kudi ba na wasa ba ta bada aka yi aikin, unconsciously ta tafi da iklima gidan wata da suka hadu a kauyen da take yawan xuwa suka kulla abota suke kawance kamar xa su hadiye juna, kwanan matar uku gidansu Aliyu lkcn biki, jiya ta baro gidan bayan an gama komai ba rabon xa ayi komai a gabanta, Hajiya Laure sai kallon iklima dake kwance take da mamaki bayan Anty khadijah ta mata bayanin komai tana matsar kwalla, can Hajiya Laure ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ai baki ga ta kuka ba Hajiya Khadijah neman mafita xa ayi, yanxu dai a takaice bbu auren kenan?" Anty khadijah ta tsayar da kukan da take da sauri tace "Aure kai, aure na nan daram dam ba inda ya je, ai ko hauka nake baxan ce masu cikin ne ba har an cire, nunawa xan yi kawai gidan ki na kawota da xuciya ta debeni" Hajiya Laure tace "Gaskiya ne, toh wai kin ma yi yanda aka ce maki wajen nan da muka je ranan kuwa?" Anty khadijah tace "Ba gashi nan ta sa nayi asara ba yanxu don nasan ba sha xai yi ba, ni wllh da tun kafin bikin nasan da shegen cikin nan da na je an cire, sai ma kin ga ko gama xama halitta cikin bai yi ba, a can wani gutter na jefar kafin mu shigo nan don likitan cewa yyi mu tafi da shi kar mu ja masa matsala" Hajiya Laure tace "Alhmdllh da abun ya xo a haka ba sai da aka kai ta gidansa ba, amma shi ma dai ya aka yi har yasan tana dauke da cikin?" Anty khadijah tace "Toh ai likita ne shi din" Hajiya Laure ta xaro ido tace "Kai haba, to yanxu baxai gane cirewa aka yi ba?" Anty khadijah tace "Yo ya gane mana ai wllh sai yyi xaman aure da 'ya ta ko ya ki ko ya so, sai ya xauna da ita don ubansa" Hajiya Laure tace "Toh kuma har yanxu uwar ta sa ba ta kira ki ba?" Anty khadijah tace "Tana can na tara mata xafi, ina labarin da na taba baki a kan wata yarinya da ta taba dauka da dadewa??" Hajiya Laure tace "Eh, eh na tuna, wannan dai da kika ce a sunan me aiki ta dauketa, da kika sa Aliyu ya lalata ta" Anty khadijah tace "Yauwa er gari ita, Toh yau dai na tona abinda Aliyun yyi mata, tunda nima tonan asirin ya min, suna can na bar su ban san ya ake ciki ba" Hajiya Laure ta kyalkyale da dariya tace "Amma baki da kirki Khadijah, Toh amma baki tunanin uwar na iya neman yarinyar yanxu ko ta sa ya nemo ta? kin fa ce min sonta take kamar ita ta haifeta" shiru Anty khadijah tayi da wani irin shock baki bude tana kallonta, salati ta sake daga karshe tace "you have a point, wllh Anty fati xata aikata, wannan shine anyi ba ayi ba, xama bai gan ni ba laure bari in koma gidan ayi komai a gabana, xan bar iklima nan ki sa mata ido don Allah" daga haka ta mike ta suri jakarta har tana tuntube ta fice dakin Laure na cewa tayi a hankali. Aliyu ya kusa awa daya tsaye bayan ya koma dakinsa, gaba daya a sanyaye yake bai san ta ina xai fara ba, bai san me xai ce ma Mumy ba, hakan yasa hawaye ya kawo idonsa tunda yake bai taba jin tsanar Anty khadijah ba sai ranan a ransa, dama tasan abinda ya faru tsakaninsa da Iman, then how? Bayan bata gidan abun ya faru, ranan daga shi sai Iman ne a gidan, kofa ya nufa daga karshe gwiwowinsa a sake ya shiga dakin Mumy, ita da aminiyarta Hajiya Balaraba ne a dakin, Mumy tayi tagumi kana ganinta kasan ta yi kuka ne sosai, tun da ya shigo Hajiya balaraba ke kallonsa, ya kasa kallon su ya isa gaban mumy a sanyaye ya duka cikin raunin murya yace "Mumy don girman Allah kiyi hakuri ki gafarce ni, i knw you Neva expect such, but... Mumy ban san ya aka yi ba ni ba halina bane, har yau ban san ya aka yi hakan ba kuma na kasa samun natsuwa, for the past 5 years neman Iman nake...." Katse sa Mumy tayi tace "Kake neman ta tayi maka me, dama kai ka sa yarinyar ta bar gidan nan Aliyu?" Ya kasa dago kansa a hankali yace "Mumy I was confused, I was thinking that's the only way out for me... I was restless staying under the same roof with her, mumy nasan na cuceta, amma ni nasan ba yin kai na bane don ba halina bane..." kasa ci gaba yyi sbda cracking da muryarsa ya shiga yi ya hade kansa da gado, Bude kofar dakin aka yi Anty khadijah ta shigo, Mumy ta goge hawayen idonta ta daga kai tana kallonta, Anty balaraba ta tabe baki ta dauke kai, karasowa Anty khadijah tayi ta xauna gefen gado ta fashe da kuka cikin rawar murya tace "Yanxu Anty fati ki ji kaxafin da Aliyu yyi ma iklima amma ke abinda ya dame ki daban? Did i and my daughter deserve this" Mumy tace "Ki rabu da ni Khadijah, ki fita ki ban waje, ba don ba don ba wllh yau sai in ce ke din makiyiya ta ce, bakya so na, baki daukeni yar uwar da muka fito ciki daya ba" Mumy na magana ne tana kuka, Aliyu ya mike ya nufi kofa, Sai da ya isa bakin kofa ya juya yana kallon Mumy cikin sanyin murya yace "Na maki alkawarin xan nemo Iman in sha Allah mum, I will repair the damage I made in sha Allah" Mumy ta masa wani mugun kallo tace "And how are you to repair the damage?" Kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali yace "By marrying her in sha Allah" Girgixa kai mumy tayi tana wani murmushi tace "Noo, babu aure tsakaninka da ita, xaka iya aikata komai domin ta yafe maka idan ta ga xata iya amma banda aure, babu aure tsakaninku, and I told you that long ago, I have my reasons, leave kar ka ci gaba da bata min rai, get out Aliyu" shiru Aliyu yyi yana kallon Mumy a sanyaye, Anty khadijah ta sauke wani ajiyar xuciya tana hamdala a ranta. Tun Khadijah na daurewa ganin twins dinta shiru har dauriyar ya fara karewa, da farko Umma na ta tambayarta inda suka je ita ma ta hakura ta daina ganin ta ki fada sai cewa take yanxu xa su dawo, khadijah ta shiga daki daga karshe ganin har anyi magrib ta dau wayarta ta shiga kiran khaleel da layin da ya kirata daxu, har ya katse bai daga ba, sai da ta kira kusan sau uku ya dauka yace "Uhn me yara to, ki ma cire ran ganinsu yau" xaro ido tayi tace "This is after seven plss..." Ya katse ta yace "Toh ki taho ki daukesu, I can give you the address" daga haka ya kashe wayar, ji tayi hankalinta ya tashi lkci daya hawaye ya kawo idonta, ta sake kiransa bai dauka ba, ta kira yyi sau hudu kafin ya daga, cikin rawar murya tace "Don Allah ka dawo da su dare yyi, Umma ce fa ke ta tambayarsu" Yace "Hmm toh naji" kashe wayar yyi ta xauna bakin gado a sanyaye. Bayan kusan minti talatin khadijah dake ta xaune daki hankalinta ya ki kwanciya ta kalli wayarta da sauri jin yana ring, ganin khaleel ne ta mike ta sa Hijab ta fita tana addu'ar Allah ya sa twins din ya dawo da, Nanny kadai ce parlor ta ce mata tana xuwa sannan ta fita waje, hade rai tayi dai dai lkcn da su shureim suka sakko daga cikin motar ko wannensu rike da leda khaleel ma ya fito, rungumeta suka yi gaba daya cike da farin cikin ganinta, fuskarta daure tace "Oya mu wuce ciki..." Suka juya suna kallon khaleel da ya rungume hannunsa, jallabiya ne sanye jikinsa ya dinga kallon yaran suka daga masa hannu sudais yace "Uncle are u coming tomorrow plss" Khaleel yyi murmushi yana gyada kai yace "Sure" khadijah bata basu daman sake ce masa komai ba ta tunkudasu cikin gida, Hijab dinta taji khaleel ya riko ta juyo da sauri, murya can kasa yace "Wait" ta kalli yaranta da har sun shige gate, ta kwace Hijab din fuskarta daure tace "Meye haka pls" yana kallonta a hankali yace "Ba gaisuwa xa ki wuce?" Hararansa tayi tace "Wanda na maka daxu a waya fa?" Jinginar da ita yyi da mota, yace "Daban" ta sauke idonta kasa xuciyarta na bugawa jin bai ce komai ba ta dago kanta taga kallonta yake, da sauri ta kara sunkuyar da kanta, yyi murmushi murya can kasa yace "Can I come gobe mu gaisa da Umma?" Ba tare da ta dago ba tace "Why?" Yace "Haka nan, twins suka ce in xo in gaida Ummansu she will like me" kin cewa komai tayi, bayan few seconds yace "Khadijah" dauke kai tayi tace "Allah ya kai mu" Ya d'an yi murmushi yace "Ameen, to yaushe xa ki koma?" Sai a sannan ta kallesa, lkci daya ta sauke idonta tace "Monday in sha Allah" ya dan wara ido yace "Har Monday?" Shiru tayi, murya can kasa yace "Alryt then, we go together" kai ta gyada masa kawai, yace "Toh sai da safe" ta saci kallonsa a hankali tace "Allah ya kai mu" daga haka ya bata hanya ta wuce ciki ya bi ta da ido. Umma dake parlor ta bi ta da kallo har ta shiga daki sannan ta mike ta bi bayanta, xaunawa gefen gado tayi tace "Saurayin ki ne wanda ya xo Khadijah?" Khadijah ta xaro ido tace "Saurayi kuma Umma, aa ba saurayina bane" Umma tace "Kawar ki ce kenan, it's high time you settle down with a husband daughter..." Khadijah ta kalleta da sauri, Umma tace "Ehh, kuma ban son ya wani dau lkci, in dai kina da wanda ya kwanta maki kika yaba hankalinsa, ki fito da shi, kin ga wannan dama ce da xa mu samu na xuwa katsina.... Idan ma kawun nan ki baxa su daura maki aure ba baxa ki rasa wanda xai daura maki ba" Rasa abun cewa Khadijah tayi, don ita dai tasan bata da saurayi, Umma tace "You think over it daughter" daga haka ta mike ta bar dakin. Kasa bacci daren ranan Khadijah tayi maganar da Umma tayi mata ya tsaya mata sosai, ko kadan aure ba ya cikin tsarin da tayi ma rayuwarta, babu abinda ke sake daga mata hankali sai ganin how serious Umma tayi xancen, gashi ta ma kasa ce mata ta hadu da Aliyu saboda bata ma son xancen, sai dai kuma ko don Aliyun ma ya kamata tayi auren ko xai fita rayuwarta da yake kokarin shiga yanxu, har asuba bata wani ritsa ba, sai a sannan ta fara da ta sanin dawowa ma da tayi. Aliyu ya kalli Mumy a karo na farko tun shigowar ta dakin tana masa magana babu yabo babu fallasa tamkar dai umarni ma take ba sa, ya d'an yi murmushi sannan yace "Mumy ba fa aure tsakanina da Iklima...." Strictly Mumy tace "Haka kace?" Yace "Ehh mumy, domin kuwa da ciki aka daura auren, yanxu kuma naga alamar sun je sun xubar da cikin" Mumy ta dinga masa wani kallo ko kiftawa babu, juyawa tayi ta fice daga dakin rai a bace, yyi murmushi ya na ci gaba da analysis din da yake tun safe amma ya kasa arriving komai, ya lumshe ido keenly, yana naxari... it all started bayan ya sha coffee da safe ranan, and then? Kawai ya dai ji ya kasa fita aiki, and... Bude kofar da aka yi ya bude ido ya juya da sauri, Saleem ne ya shigo dakin Aliyu ya masa kallo daya ya dauke kai, murmushi ya dinga yi ya ki cewa komai, aliyu ya kallesa a karo na biyu, ya mike yace "Ya aka yi malam?" Dariya saleem yyi yace "Wani xance naji yan gidan nan ke yi yaya, is it for real?" Wani kallo Aliyu ya dinga masa cikin cool voice dinsa yace "Get out and close the door behind you saleem" Saleem ya daga kafada yana murmushi yace "But I neva expect that from you, ni da ake ma warning a da, sai gashi kuma....." Dariya yyi ya fita ya rufe kofar, Aliyu ya xauna xuciyarsa na tafarfasa ya ji duk ya tsani yan gidan nasu gaba daya, ya hade kansa da table din gabansa.... Khadijah na kitchen tana girkin lunch misalin sha biyu Shureim ya kawo mata waya dake ring, Karba tayi ta daga ta kai kunne, muryarsa ya daki kunnenta, yace "How was your nyt?" Tace "Twas good, ya gida" yace "Alhmdllh, ya twins?" Tace "They are fine" yace "Alryt. Anjima xan xo" tace "Allah ya kai mu" daga haka yyi mata sallama ya katse wayar, ta juya xata mika ma Shureim wayar, wani mugun faduwa gabanta yyi ganin irin tsayuwar da yyi yana jiranta, lkci daya Aliyu ya fado mata ta mika masa wayar a sanyaye, yaron ya karba ya juya ya fita ta ci gaba da abinda. Aliyu ya fito daga bedroom dinsa rike da makullin mota xai bar gidan ganin he is nt arriving at anything better a tunanin da yake tun safe, baby ma da fitowarta kenan daga dakinsu ta juya ta koma ganinsa, tun ranan da Anty khadijah ta fadi ma yan gidan abinda ya faru tsakaninsa da Khadijah kusan duk suke canxa hanya idan sun gansa, gaisuwa ma sai sun ga dama, duk wannan baya masa ciwo sai irin yanda Saleem ke making jest of him ko da yaushe cikin masa dariya yake, he is just trying hard to control his self baya kulasa, Mumy ce ta fito daga dakin Anty Khadijah tana kwalo ma Saleem kira hankali tahse, shi dai Aliyu na tsaye don har ita bata bin ta kansa a gidan, Saleem ya fito tace "Maxa ka dauko makullin motar iklima ce ba lafiya, kayi sauri don Allah" Aliyu na jin haka ya sauka Downstairs ya bar parlorn ya hau motarsa ya fice a gidan, direct gidan Farouq ya nufa, yana isa bakin gate ya kira sa ya sanar da shi yana kofar gida, fitowa yyi daga motar bayan Farouq yace ya shigo yana ma compound, Aliyu ya shiga gidan yana amsa gaisuwar mai gadi, can ya hango Farouq su biyu xaune kan biyu daga cikin kujerun dake wajen, har ya isa wajen idonsa na kan wanda ke xaune tare da farouq, shi ma dai dai nan ya dago kai suka yi ido hudu, kallon kallo suka shiga yi da wani ex gaba daya fuskarsu, Farouq dake nuna ma Aliyu kujera yana murmushi yace "The great Dr, mu dai mun je daurin auren ka baka nan, ban kuma kira ka ba saboda ba aji mutuwar sarki a baki na ba" kin xama Aliyu yyi yace "Ehh naga alama, I was just passing by dama nace in shigo mu gaisa so ba dadewa xan yi ba, ana jirana a mota, I will leave now" Farouq ya masa wani kallo yace "Bana son walakanci fa, daga xuwa sai tafiya, yaushe ma ka dawo Nigeria" tuni Aliyu ya juya ya bar wajen da sauri, Farouq ya mike yace "What's the meaning of this Aliyu!" Ba tare da ya juyo ba yace "Sure, a gaida min su Haiydar da Madam am in a haste" Farouq ya bi sa da kallo baki sake kafin ya kalli abokin sa dake xaune yana danna waya, dago kai khaleel yyi shi ma ya kallesa yace "Kila don ya gan ni ne yasa ba ya son xaunawa...." Farouq ya ma khaleel wani kallo, sai kuma yyi dariya yace "Toh ai ina ya san ka da xai ki xama saboda kai kai kuma da wani xargi, that's Aliyu for you, haka nan yake ba wai don saboda kai bane it's his habit" murmushi Khaleel yyi yace "Toh ya ji dadi, nima yanxu xan wuce ina da inda xan je" daga haka ya mike Farouq yace "Haba dai, so early yaushe rabon mu hadu Dr Ayman?" Khaleel yace "Assuming babu inda xan je I will stay kai ma ka sani" Farouq yyi murmushi ya mike yace "Toh shkkn, wai ya Jawahir din ka, saura watanni nawa bikin?" Khaleel yyi murmushi da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Uku kawai" Farouq yace "Toh Allah ya kai mu, my regards to her, Anty kuma kace mata plsss tayi hakuri ina nan xuwa in gaisheta" Shi dai khaleel bai ce komai ba suna tafiya har suka fita gidan, sai da suka isa gun motar khaleel, khaleel ya juya yana kallon Farouq strictly yace "Don't dare say anything about me to that guy that just left Umar, tell him nothing about me if he shud ask" da mamaki Farouq yace "Anything? Like? Ka taba sanin sa ne?" Khaleel yace "No ban san shi ba, I just know xai yi ma tambaya a kai na, kar kuma ka gaya masa komai" daga haka ya shiga motarsa Farouq ya dinga kallon sa yace "shi aliyun?" Dariya yyi yace "Yanda kake haka yake shi ma ai, banbancin ku kadan ne, soo nasan baxai ma min tambaya a kan ka ba, beside shi ma a UK yake ai, a Dr also" Shi dai khaleel bai ce komai ba ya ja motarsa ya bar wajen. Yau dai Khadijah mayafi ta daura kan atamfar jikinta ta fito amma ba tare da su Sudais ba, duk da bata yi kwalliya ba amma tayi kyau ne ba kadan ba, ta glass khaleel ke ta kallonta ganin jingina tayi da motar bata bude ba ya sa ya bude ya fito ya xagayo ta inda take, ba tare da ta kallesa ba tace "Ina yini?" A hankali yace "Cool, ya boys dina" tace "They are inside, mu je sai ka gaisa da Umma" daga haka ta nufi cikin gidan ya bi ta da kallo da farko kafin ya bi bayanta, Sosai Umma ta tarbi khaleel da yaki kallonta kansa a kasa, xaman ma bakin kujera ya xauna kana ganinsa kasan duk a takure yake, Umma ta tambayesa mutanen gida yace duk suna lafiya, dariya ya ba Khadijah don bata tana xaton yana da kunya haka ba don ko da wasa ya ki dago kansa, Umma da ta lura da haka ita ma ta bar masu parlorn, sai a sannan khaleel ya dago kamar munafuki, khadijah dake ta murmushi tana xuba masa lemo a cup tace "Kamar gaske" mikewa yayi ya mata wani kallo murya can kasa yace "Karya ce dama, am outside" da sauri ta kallesa tace "Me xa kayi a waje" yace "I can't stay here" ta bata fuska tace "Abinci fa xan xuba maka" yace "Ni bana jin yunwa, kawai ki turo min twins" daga haka ya nufi kofa kamar ana hankada sa, Khadijah ta bi sa da harara har ya fita, tsaki ta yi ta xauna kujera tana turo baki, Ba a dau lkci ba ya fara kiranta a waya har ya katse bata dauka ba, ya sake kira ta ki dauka, text ya turo mata yace "Plss Khadijah, ina mota fa ni baxan iya xaman parlorn ba, idan baxa ki fito ba ki turo min su sudais kawai" tashi tayi ta wuce dakin Umma don suna can suna kallo basu ma san ya xo ba, Umma na ganinta tace "Barin sa ki ka yi shi kadai a parlor?" Khadijah ta tabe baki tace "ya fita yana waje" Umma tace "Saboda me?" Tace "Wai baxai iya xama a parlorn ba" Murmushi Umma tayi tace "Shi kuma haka yake da kunya, Khadijah ina kika samo balarabe?" Xaro ido Khadijah tayi lkci daya ta fashe da dariya tace "Ba balarabe bane fa shi" hararata Umma tayi tace "Ya xa ki ce min ba balarabe bane" Murmushi Khadijah tayi tace "Toh ni dai haka yace min" Umma tace "Ya dai ce maki hakan ne, to ki fita ki samesa tunda baxai xauna parlor ba" Tare da su Sudais ta fita, khaleel ya fito daga motar yana kallonta bayan yyi pecking yaran da suka yi murnan ganinsa yace "Har da walakanci koh?" Tace "Nima ae shi ka min" shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi yace "Baki san ina da kunya sosai ba ko" Khadijah bata san lkcn da tayi dariya ba ya dinga kallonta don bai taba ganin dariyarta haka ba, har da rike ciki, ganin yanda yake kallonta ta hadiye dariyar tana murmushi tace "Amma a nan Nigeria kake ajiye kunyar idan xa ka UK koh?" Xaro ido yayi ba don yaranta dake gun ba da babu abinda xai hanasa jawota jikinsa tayi bayanin abinda take nufi, dariya kawai khadijah take tana kallonsa, khaleel ya kasa cewa komai, kawai ya 6uge da shafa lallausan bak'in gashin kansa, ta sata kallonsa ta sake kyalkyalewa da dariya, yyi murmushi ya cire glass din idonsa murya can kasa yace "Xa ki yi bayani ai xa mu koma UK din" ta hade rai tace "So?" Yana murmushi yace "Nothing, ki gaya ma Umma xa mu je shopping da su sudais plss har da ke" khadijah da bata sake kallon fuskarsa ba tace "Noo ban da ni" yace "Plss" tace "Ni baxan je ba da gaske, su dai ka tafi da su" da kyar da kyar khaleel ya lallabata bayan ta sa ya rufe idanuwansa da glass din da ya cire sannan ta yarda xata bi su, amma bayan ta gaya ma Umma idan xata yarda, ganin tare da su sudais ne Umma ta yarda suka tafi bayan tace kar su dade, front seat ya bude ma su Shureim suka shiga, ganin haka ta bude back seat ta shiga, sai da suka yi nisa khaleel yace "Mu je ki gaida mum dita nima, it's just malali here ba nisa...." Da sauri khadijah tace "Noo plss, sai in je a wa?" Yana kallonta murya can kasa yace "A surkarta to be" shiru khadijah tayi ta na kallonsa da mamaki, ya mayar da dubansa kan titi yana driving, da sauri tace "Noo, sae dai a matsayin friend dinka, and am not ready for that Dr don ban ce ma umma xan je ko ina ba daga inda kace xaka kai mu" a hankali yace "Ohk then, amma xa mu biya gidansu jawaheer mu dauketa, I think she wants to shop also" kallonsa Khadijah ta tsaya yi ta ma rasa abinda xata ce masa, ai ko suka isa anguwarsu jawaheer din yyi parking ya dau waya ya kirata yace yana waje, khadijah tayi karfin halin cewa "Toh su sudais su dawo baya" Khaleel yace "Noo xata xauna baya ita ma, no probs" Ba a dau lkci ba jawaheer ta fito, she is a real definition of black beauty, kyakkaywa ce ita din ta karshe, ta bude front seat tace "Sweetheart ashe da gaske xaka xo din" ganin su sudais da Shureim ta wara ido tace "Waoww cuties, ina ka samo su swthrt? They are so cute" gaisheta yan biyun suka yi, duk ta yi masu kiss a goshi, Khaleel dake kallonta yace "Yarana ne" dariya ta yi tace "Kai dear, don Allah waye su, sun min kyau wllh" ya kalli khadijah ta madubi yace "Ga Aunt dinsu a baya nan" sai a sannan jawaheer ta kalli baya da sauri tace "Ohh ban lura ba, hello" Khadijah tace "Hi" jawahir na murmushi tace "You've got sweet siblings" murmushi khadijah ta kirkira, kamar baxa ta ce komai ba sai kuma murya can kasa kamar ana tilastata tace "Thanks" jawahir ta bude bayan motar ta shiga ta rufe khaleel ya ja motar suka bar wajen, ta madubi yake ta kallon khadijah da ta kauda kai tana kallon waje, ita kuma jawahir na ta basa labari da siririyar muryarta da ya cika motar. Farouq dake ta kallon Aliyu da d'an mamaki yace "Ko meye dalilin da yasa kake son sanin sa Dr?" Aliyu ya hade rai yace "Idan xaka gaya min ka gaya min" Farouq yace "He is my good friend, tare muka yi karatu a England degree and masters, his mum from Saudi Arabia, the most simplest woman I have ever known, his dad a Nigerian from kano, shi kadai ne namiji gidansu with 4 siblings duk mata, Dr Ayman ba shi da matsala, he is free with everyone sai dai he don't make friends easily, he is a genuine... He was among those that graduated with d best result during our time, yanxu haka PhD dinsa yake a Uk..." Katse sa Aliyu yayi yace "Am not asking you about his life history or how intelligent he is, ina gidansu yake?" Farouq ya dinga kallonsa da tuhuma kafin yace "I don't think i wil tel you that Aliyu" murmushi Aliyu yyi yana shafa beard dinsa. Tun da suka shiga shopping mall din Khaleel ke kallon khadijah ganin yanda ta daure fuska, duk yanda khaleel yayi da ita ta dauki abubuwan da take bukata nuna masa ta yi bata bukatar komai, Jawaheer da twins suka dinga daukan abinda suke so a gun, khaleel dai na biye da su a baya, xagawa Jawaheer tayi gun chocolates da biscuits duk wanda yaran suka dauka ita ma sai ta dauka, khaleel dake ta kallon khadijah bayan jawahir ta bar wajen yace "Wait, wai me yasa baxa ki dau komai ba Khadijah, or did I offend u in any way plss?" Khadijah ta tabe baki ba tare da ta kallesa ba tace "To lallai ne sai na dauki abu a mall? Kuma don ban dauka ba sai ya xamanto anyi offending dina? Am not just interested" Shiru yyi yana kallonta, a hankali ya juya ya bar ta tsaye gun ya koma gun twins da jawahir, nesa da su wani mutum ne tsaye yana dauke da wata yarinya da baxata wuce shekara uku ba an mata kitso irin na yara gashinta har kusan bayanta, kusa da shi kuma wata mace ce rike da trolley tana xuba kayan da ta dauka, kallon su Shureim kawai yake ko kiftawa babu, har sai da matarsa dake gefensa tace "Barrister mu je mana" sai a sannan yyi saurin dauke idonsa kan yaran ya bi bayan matarsa, ya sake juyawa yana kallon yaran da khaleel ke rike da hannunsu har ya bar wajen ya daina ganinsu, khaleel ya biya kudin abubuwan da suka siya yana kallon khadijah da ke bakin kofar fita tana jiransu, ganin kallon da yake mata ta dauke kai da sauri dai dai lkcn da idonta ya sauka kan barrister sudais dake tahowa rike da kyakkyawar daughtern sa, matarsa na biye da shi tana rike da ledan siyayyar da suka yi, still Khadijah tayi a gun da take tsaye taji komai nata ya tsaya cak, yanda take kallonsa shi ma haka yake kallonta ko kiftawa babu har ya iso dab da ita ya sauke idonsa kasa ya mika ma security dake bakin kofar receipt din kayan da ya biya aka mayar masa sannan ya fita mall din, matarsa na biye da shi. Khadijah ta bi sudais da kallo cikin shock sosai, fita tayi da sauri tana ci gaba da kallon sa xuciyarta na bugawa, dai dai lkcn da shi ma ya juya bai san ta fito ba suka kara hada ido yayi saurin dauke kansa, motarsa ya nufa ya bude, matar ta bude back seat ta ajiye ledan hannunta sannan ta bude seat din gaba xata shiga ta dakata da sauri tana kallonsa tace "Lahh Barrister na bar masu wayata a counter..." Bata jira cewarsa ba ta juya da sauri ta koma mall din, Sudais ya kara daga kai ya kalli khadijah, bata san lkcn da ta nufesa ba tana kallonsa ta fashe da kuka sosai cikin raunin murya tace "Why are you pretending you don't knw me? Did I deserve that Sudais.... Me yasa kake yin kamar baka taba sanina ba" sosai hawaye ke xuba idonta, Ya kasa kallonta ya kuma kasa cewa komai ba, ganin Jiddah na fitowa mall din ya sa ya shiga motarsa ya rufe, gwiwa a sake Khadijah ta koma baya tana kallonsa ko kiftawa babu kai kana ganinta kasan she is over shock, Tun daga nesa jiddah ke kallon khadijah da tayi saurin share idonta, har ta iso tana mata wani kallo daga sama har kasa tace "Baiwar Allah, do you have any problem? Tsayuwar me kike a nan" Khadijah bata kalleta ba ta juya da sauri ta bar wajen ta koma can jikin wani mota xuciyarta na mata xafi, ta fashe da wani matsanancin kuka, me yasa ko da yaushe a cikin mall take haduwa da abinda ke mugun daga mata hankali, yau ga ta ga sudais yyi kamar bai taba sanin ta ba, me tayi masa xai mata haka, ta sulale wajen ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, bata yi deserving yyi mata haka ba da ya bari ko godiyar abinda yyi mata a rayuwa ta kara masa don tasan baxa ta iya biyansa ba kuma ba lallai su sake haduwa ba. Jiddah na shiga motar ta kalli sudais fuska a murtuke tace "Wacece ita Aliyu?" Buda hannu yyi alamar bai sani ba, ganin kallon da take masa yace "Kawai ce min fa tayi in ara mata waya xata yi making call, ni kuma nace bani da airtime, that's all madam" tsaki jiddah tayi cikin bacin rai tace "Da ta fada a gabana in koya mata hankali yau wllh, irin yan iskan matan nan ne masu bin maxajen mutane a titi, banda haka ta baka ajiyar kati ne xata ce ka ara mata waya?? dear idan baka son matsala da ni wllh ka bar ko da responding wa ennan mutanen, idan xa su shekara suna ma magana kar ka ko da kalli inda suke balle ka bude baki ka basu amsa ka xama kamar deaf and dumb, domin kuwa yawancinsu da asiri suke xuwa, ni dai na gaya maka kada a fara jin kan mu kuma" "Toh" kawai Sudais yace ya tada motarsa ya bar harabar mall din tana ci gaba da mita, Khadijah taji xuciyarta ya mata nauyi ta dinga kuka ko xata samu relieve amma kamar ana kara mata ciwon da take ji, babu irin neman da khaleel bai mata cikin mall din ba amma bai ganta ba, jawahir ma sai dube dube take tana neman ta, atm dinsa ya mika ma jawahir yace "Dear gashi you pay the bill" tace "But the pin?" Fada mata yyi ya fita mall din ta bi sa da kallo a sanyaye, little Sudais na kallon jawahir yace "Anty ba mu ga Antynmu ba" jawahir ta duka tana masu murmushi tace "Yanxu Dr xai nemo mana ita cuties" daga haka ta mike ganin an xo kanta a gun biyan kudin. Tafiyar few minutes sudais yyi ya tsayar da motar, Jiddah dake kallonsa ganin yanda ya ja tsaki tace "Ya aka yi Abban Amira?" Ya d'an dafa kansa yace "Wannan matsalar dai da nace maki motar ta bani last week, I don't knw what's wrong with this car" tace "Yanxu baxai tashi ba kenan?" Yace "Sai wani ikon Allah, gashi ban san ko Ahmad na garage ba da na kirasa ya taho yanxu... Am just bored of this car" ta hade rai tace "Toh ni ya xa muyi yanxu ga ranan yamma" ya kalli cute angel dinsa me suna Khadijah yana kiranta da Amira ya ja hancinta ganin yanda take kallonsa da kwala kwalan idonta yace "Kar Amirata ta sha wahala bari kawai in tsayar maku da adai daita ku wuce gida ni xan taho daga baya" Jiddah tace "Wai to ka kara gwada tada motar mana, ba girman ka bane barrister a gan ka bakin titi mota ta lalace" Murmushi yyi ya bude motar ya fita ya tsayar da adai daita ya gaya masa sunan anguwar su sannan ya xaga ya bude motar yana kallon jiddah yace "Ki fito ku wuce yanxu xan taho nima in sha Allah" ta hade rai tace "Aa mu je gaba daya kawai, ai babu me satar motar idan ya so sai Ahmad yaje gida ya karbi makulli ya lallaba ya kai motar gareji" kallonta ya tsaya yi kafin yace "Plss be a good wife and humbly come down kinga na tsayar maku da d'an sahu, you don't worry about me I will be okay sai kace ba namiji ba" da kyar ya lallaba ta ta sauka ta shiga napep din ya mika mata Amira da kayan da suka siya a supermarket, yana tsaye har napep din ya sha kwana sannan ya shiga motarsa da sauri ya tada yyi reverse ya koma mall din at high speed kamar xai tashi sama. Babu irin duban da khaleel bai ma khadijah ba a haraban Shopping complex din, har yyi give up a xaton sa gida ta wuce sai dai kuma haka kawai ya ji ransa ya baci, ya juya kenan xai koma ciki ya hangota durkushe bayan mota, da mamaki ya dinga kallonta lkci daya ya isa gabanta ya durkusa yace "Me ya faru Khadijah me kike yi a nan?" Ta kasa cewa komai sai shessheka take hawaye na sakko mata, a rikice yace "Ki min magana don Allah khadijah, me ya faru" ganin ba shiru xata yi ba ya daga ta ya nufi gun motarsa bai damu da mutanen dake kallonsu a gun ba ciki har da jawahir da ta fito da su shureim ya bude back seat ta shiga ya rufe, Sudais ya taho gun khaleel da sauri hankalinsa tashe yace "Uncle what's wrong with my Anty" Daukan sa Khaleel yayi yana murmushi yace "She is having a headache" kokarin sauka ya shiga yi a jikinsa kamar xai yi kuka yace "Uncle ina son in xauna kusa da ita I don't like d front" bude masa bayan motar khaleel yyi ya shiga sannan ya rufe, shi dai shureim na tsaye can kawai ya fashe da kuka, jawahir ta duka tana kallonsa da mamaki tace "Me ya faru handsome" Khaleel na ganin haka ya karasa ya daukesa shi ma ya bude back seat din ya xaunar da shi sannan ya rufe, jawahir dai na tsaye tana kallonsu ya bude mata front seat ta karaso ta shiga, ya xaga ya shiga maxaunin driver, Khadijah ta hadiye kukan da take da kyar ganin yanda yan biyunta suka rikice su ma suna kukan tana yin shiru su ma suka yi shiru, khaleel sai kallonta yake ta madubi duk ya ji ba shi da nutsuwa kamar ya jawo ta jikinsa ya lallasheta, Jawahir ma sai kallon khadijah da yaranta take, Khaleel na fita mall din da motarsa sudais ya shigo shi kuma da tasa motar, ko parking din kirki bai yi ba duk da maganar da securities din gun ke masa ya wani rikice ya dinga duba nook and cranny din wajajen yana nemanta har ciki sai da ya shiga amma babu khadijah, ya fito jikinsa a sanyaye ya hade kansa da motar sa. Khaleel ya fara ajiye jawahir a kofar gidansu, yana lura ranta bai so ba ta bude motar ta fita da kyar ma ta dau ledan siyayyar da tayi kamar baxa ta dauka ba, ko sallama bata yi masa ba ta dai daga ma su sudais dake kallonta hannu ta wuce ciki abun ta, ya lumshe ido ya bude sannan yyi reverse ya bar layin, yana isa kofar gidansu khadijah ya bude motar ya fito sannan ya bude back seat yana kallonsu sudais da suka yi jigum kamar xa su shige jikin uwarsu, yyi murmushi yace "Toh ku fito" da taimakonsa suka sauko kasa ya basu ledojin yace su shiga ciki, Khadijah xata fito khaleel ya dakatar da ita, sudais dake lekanta yace "Uncle Anty bata sakko ba" khaleel ya shafa kansa yace "Xata sakko yanxu ku shiga ku kai ma Umma chocolates din ku ta ajiye maku" yaran suka wuce ciki suna yi suna waiwayowa, khaleel ya shiga motar yana kallonta da damuwa yace "Ki gaya min plss me ya sa ki kuka khadijah, is it me?" Girgixa masa kai tayi a sanyaye wasu hawayen na gangarowa idonta, ya kasa daurewa ya rungumeta yace "No plss I don't want to see you cry, it hurt me, don Allah ki gaya min meye matsalar ki, me ya sa ki kuka a supermarket?" Tayi lamo jikinsa taji ta kasa kukan kuma, duk kamshin sa ya cika ta, murya can kasa yace "Khadijah" a hankali tace "Uhn" yace "Kukan me kike yi?" Ta lumshe ido cikin sanyin murya tace "Sudais" still khaleel yyi na kusan 10 seconds kafin ya dake cike da karfin hali yace "What about him?" Har lkcn idonta a lumshe tace "I saw him" dagota khaleel yyi da sauri yana kallonta at first a bit shock, sai kuma ya hade rai yace "Where?" Ta ki kallon kwayar idonsa tace "A inda muka je shopping" da kyar ta ci gaba wasu hawaye na taruwa idonta tace "He shunned me, he pretend he don't knw me...." Kasa ci gaba tayi ta fara kuka a hankali, khaleel ya lumshe ido, jin ta a jikinsa kuma yasa tayi shiru, a hankali yace "Khadijah..." Cikin sanyin murya tace "Na'am" dai dai kunnenta yace "forget about sudais plss, forget him...." Sai kuma yyi shiru, Khadijah taji kamar an xare mata radadin da take ji a xuciya, taji ta samu relieve, hankalinta ya kwanta fiye da xaton ta, murya can kasa tace "Toh, nagode" ji yayi kamar yyi kissing dinta but yyi controlling kansa bai yi hakan ba, har lkcn idonsa a lumshe yace "I... I know I love you from day 3 of our encounter....." Duk da yanda gaban Khadijah yyi mugun faduwa don bbu Wanda ya taba fadi mata wannan Kalmar duk tsawon rayuwarta hakan bai hanata fara tunanin me ya faru a rana ta uku da suka fara haduwa da khaleel a UK ba. Khaleel ya dago kanta yana kallonta, tayi saurin rufe idonta, murmushi yyi murya can kasa yace "Kin tuna ko in tuna maki" dauke kanta tayi xata bude motar yace "Wait" still tayi a wajen bata yi motsi ba, yace "promise me baxa ki sake kuka a kan hanya ba, sannan you wil forget your past and face the future" shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Khadijah" ta gyada masa kai kawai, yace "Noo, say it out" bata san lkcn da tayi murmushi ba a hankali tace "Ohk" yace "Ohk kadai" kamar bata son ya ji ta tace "I promise" yyi murmushi yace "Yauwa baby" ta turo baki tace "Tana can kayi dropping dinta a gida" wara idanuwansa yyi yace "Wai jawahir?" Khadijah ta ki dago kanta, murya can kasa yace "Ita daban ke daban..." Daga haka ya bude side dinsa ya fita ita ma ta fito yana kallonta, a hankali tana fidgeting fingers dinta tace "Thanks" bata jira cewar sa ba ta wuce cikin gida da sauri, ya bi ta da ido. Aliyu na jin alamar Farouq xai shigo parlorn ya jefar da wayarsa dake hannunsa kan kujera kusa da wanda yake, yyi concentrating kan nasa wayar dake hannunsa, Farouq yace "Toh baka taba abincin ba har ynxu Dr" Aliyu yace "I told you I am not hungry fa, ni xuwa ma xan yi in tafi yanxu" Farouq yace "So soon" mikewa Aliyu yayi yace "Sure, tun da baka da kirki" Farouq yyi murmushi yace "Ko da kai da khaleel baku fada min komai ba na dai san akwai yar tsama tsakaninku, domin kuwa kamar yanda ka min xancensa haka shi ma yyi min naka, amma bai yi requesting karban digit dinka ba ko sanin inda kake, shi yasa kai ma baxan baka na sa ba" ko Kallonsa Aliyu bai yi ba ya nufi kofa Farouq ya bi bayansa yana murmushi, Aliyu na isa gida direct sama ya tafi, har xai shiga dakinsa ya dawo ya bude kofar dakin baby, tana linke kaya ya same ta, ganinsa ta hade rai ya karasa cikin dakin, da farko rasa abun cewa yyi can kuma yyi karfin halin cewa "Ina yan gidan?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Suna asibiti" yana kallonta yace "Who is sick?" Tace "Iklima" sai a lkcn ya tuna yana kokarin fita mumy ta kira saleem yayi driving dinsu xuwa asibiti, yace "Anyi hospitalizing dinta ne?" Baby ta gyada masa kai, yace "Su waye a asibitin?" Tace "Su mumy, mun dawo daukan abu ne da Anty Khadijah" yace "Tana ina?" Tace "Tana dakinta ina ji" fitowa yyi daga dakin har xai wuce nasa sai kuma ya bude na anty Khadijah, babu kowa a dakin ya gani, ya dinga kallon jakarta dake kan gado an xaxxage komai na ciki, karasawa yyi ya ga duk tarkacen takardu da kayan kwalliya ne sai wani kulli a fallen zani, dauka yyi yana jujjuyawa yana kallo, murya ya ji kasa kasa a bathroom, yyi still ya kasa kunne don saurare, "Wllh ban sani ba, sai bayan da aka daura auren alamomin cikin ya fara bayyana...." Aliyu yyi tiptoeing xuwa bakin kofar bayin ya jingina da bango yana jin muryar Anty Khadijah radau amma fa a hankali take maganar "Ko kafin bikin sai da na fita tsakar dare na duba ajiyar yana nan yanda yake na kan dutse" shiru ta d'an yi sai kuma tace "Aa gaskiya ta gun angon kadai ne da matsala, shi ma da bai gano cikin ba nasan da idan ya sha wannan garin da ka bada a ruwan shayi shkkn sai kuma yanda muka yi da shi to bai sha ba, to bai sha ba" da damuwa tace "Haba na kan dutse tuni fa aka cire cikin ban san meye matsalar ba tana dai can a kwance har yanxu cikinta ciwo kamar baxa tayi ba, kilan rashin sabo ne, kasan da karafuna ake cire cikin, ni dai yanxu abinda nake so shine ka taimaka ka karkato mana da hankalin shi yaron, wllh shi ke ba mu matsala" tace "Ehh Aliyu sunansa, wlh taurin kansa ya fi karfinsa, ka ladabta min shi... ka tuna wani hadi da ka taba min da dadewa shekaru masu d'an yawa na xuba masa a ruwan tea....?" Da sauri tace "Yauwa to ka kara min irinsa ta haka ne kadai xa mu samu abinda muke so, sai ya tattara ta ya tafi da ita, ita kuma 'ya ta ka tada min kafadunta" runtse ido Aliyu yyi jin furucinta na karshe ya dinga nanata innalillahi wa inna ilai hi raji'un a xuciyarsa, Anty Khadijah tayi wani ihu tace "Dubu Dari da hamsin kuma na kan dutse??? Haba haba a dube ni domin Allah mana, yanxu kudaden wuya suke wllh, ina xan samo har dubu dari da hamsin ni ba Sana'a ba, sai fa yayata ta bani.... Da ma atm dinta na guna ne ban ki in sa ta ba, Duk fa yan kudadena sun kare ta dalilin xuwa gun ka da nake na kan dutse" ta kwantar da murya bayan wani lkci tace "Amma ka fa san nace ni baxan sake wannan harkar da kai ba kake ambatosa yanxu, sai in ce ma yayata xan je ina? Kawai duk ka bi ka wahal da mutum haba na kan dutse, wajen fa da nisa" da sauri tace "To to na ji, ko xuwa jibi xan taho, sai kuma batun yan gidan don Allah ka kara gume min bakinsu wannan karan har da wata kakarsu ta gun uba ana ce mata yaya naga xata bani ciwon kai ita ma, da yake ta fi shekara 10 a gun yar ta dake aure kasar waje to dai yanxu ta dawo duk da ba gida daya muke ba amma dai ance prevention is better den cure, ita ma a kulle min bakinta plss, sannan abu na karshe, ina yarinyar nan da na sa kayi ma Aliyu hadin nan saboda ita, wata warce nace yayata ta dauketa shekarun baya......" Da sauri tace "Yauwaaaa na kan dutse, to ina son yau dai a bincika min ita, a wani garin take yanxu, kuma ya rayuwa ta kaya da ita, ta haife cikin ne ko ta xubar? A bincika min na kan dutse" cike da confusion Aliyu ke kallon kofar bayin don bai gane komai ba a xancen ta na karshe ba, wani hadin take nufi aka yi masa, wani cikin? kuma wacece?? daga haka tayi sallama tace "Toh sai ka ji ni na wajena" Aliyu dake ta xufa yyi saurin barin bakin kofar sai dai tun bai bude kofar dakin ya fita ba ta shigo dakin, wayancewa yyi kamar shigowarsa kenan, tayi tsuru tsuru tana kallonsa, ya sunkuyar da kai yace "Ina yini" kasa amsawa tayi, just to make her comfortable yace "Yanxu na shigo baby ke ce min an kwantar da iklima ban sani ba" ta hadiye abu da kyar tace "Toh ya aka yi?" Ya isa gefen gado ya xauna a hankali yace "Anty ina son mu yi magana dake plss" tana kifta ido tace "Ina ji" yyi kasa da murya yace "Anty ki taimaka ki taya ni ba mumy hakuri, nasan tana fushi da ni, Anty abinda yasa ku ka ga na damu hada ni aure da aka yi da iklima naga ba jituwa muke ba, kuma fa kuna ganin bata jin maganar kowa gidan nan, idan ta fita sai lkcn da ta ga dama take dawowa to ta ina xan fara bata umarni ta bi a matsayina na mijinta yanxu?" Tuni hankalin Anty Khadijah ya kwanta ta kara tabbatar da shigowar sa dakin kenan bai ji wayarta ba, tace "Toh Aliyu hannunka na rubewa ka cire ka yar ne! Sannan ikliman da ka sani da ba ita ba ce yanxu, wllh wllh ta canxa fitan nan xuwa gidan kawaye da take duk ta bari, wllh ta nutsu saboda rokon Allahn da ake mata" a hankali Aliyu yace "Toh shi kenan Allah sa hakan ne mafi alkhairi" Anty Khadijah tayi mugun jin dadi ta na murmushi tace "Toh Amin, amma ka dade baka sanya ni farin ciki irin yau ba my son, Allah ya maka albarka, kuma duk abinda ya faru a da can mu yafi juna Sharrin shaidan ne" yace "Haka ne Anty, yanxu asibitin xa ku koma?" Ta girgixa kai tace "Yanxu daga nan ma kasuwa xa mu da baby kayan ciki xan siyo in farfesa mata shi ke ran ta...." Aliyu yace "Toh mu je sai in ajiye ku a kasuwan daga can in karasa asibitin dubata" Anty Khadijah ta dade bata shiga farin ciki irin na ranan ba, ta kasa yarda Aliyu ne ke mata wannan jawabin, ta dau jakarta ta bi bayan sa tana shi masa albarka. Tare da baby suka tafi kasuwar, Aliyu ya tsaya cikin mota ya jira su gama siyayyarsu ya ajiye su gida sai ya wuce asibiti kamar yanda ya ce, har lkcn he was very shock, ya kasa gaskata abubuwan da ya ji, duk jikinsa ya yi mugun sanyi, Anty Khadijah ta dinga sa ana yanka kayan ciki har na dubu shidda duk na Iklima kadai, Baby dai na tsaye kusa da ita tana kallon ikon Allah, kamar ance baby ta juya ta wara ido tana kallon wasu twins dake tafiya tare da wata dattijuwa duk tana rike da hannunsu, da sauri tace "Innalillahi Anty kalli yaran can" da sauri Anty Khadijah ta juya ita ma idonta ya sauka kan yaran ko kiftawa bata yi, Baby tace "Anty don Allah da wa suka maki kama?" Anty Khadijah ta share wani xufa tana ci gaba da kallon yaran tunani kala kala a ranta, kamar daga sama suka ji ance baxawara??? Duk suka juya da sauri, kyauta suka gani tsaye cikin shiga ta alfarma gun mai kayan miya tana rike da haba baki bude tana kallon Anty Khadijah, Baby tayi wani kara xata tafi ta rungumeta da gudu Anty Khadijah ta fixgota, kyauta na rike da haba har sannan tace "Ikon Allah su baxawara ashe rai kan ga rai? Ana nan ana xawarcin gidan mutane ko anyi aure?" Anty Khadijah da kamannin ta suka canxa tayi kan kyauta kamar xaki kan kace me ta cakumota tana kunduma mata xagi tace "Ni kike kira baxawara don kaza kazan ki, a ina kika taba sani na" dambe ta fara yi da Kyauta da ta xage ita ma lkci daya sai gashi ta na na Anty Khadijah ta da kasa ta dinga duka tana tula mata kasa a fuska mutane suka taru kansu amma kyauta taki saketa dukarta take kamar an aikota tana tula mata kasa a fuska da baki, Baby da ta rude ta tafi da gudu ta kira Aliyu dake mota, Cikin masu kallon fadan har da Nanny da ta ja yan biyun hannunta suka tafi wani rumfa suka tsaya kallon ikon Allah, da kyar aka janye kyauta kan Anty Khadijah da jini ke ta dalala a hancinta da baki, Kyauta ta kunduma mata wani mugun xagi tace "In kin cika yar halak cikin uwar ki da uban ki mu hadu a ba wani shege gobe mu da sa daga inda aka rabamu, axxaluma yar uwar shaidan kawai" daga haka kyauta ta bar wajen tana cewa "Alhmdllh na san inda na dosa a rayuwa yanxu, ke kam a cin arxiki xa ki kare kina rabe gidan mutane" Aliyu ya bi ta da kallo baki bude, Da kyar aka daga Anty Khadijah dake kunduma ma kyauta xagi bayan ta ga ta tafi, Baby ta kama hannunta suka nufi gun mota da sauri ganin yanda ake kallonsu, naman da basu amsa ba kenan duk da ta bada kudi, Aliyu dai ya kasa motsi inda yake, a hankali ya juya xai bar wajen ya ji ance "Uncleee" ya juya da sauri idonsa ya sauka kan twins dake wani gefe a tsaye Nanny kuma na siyan abu a shago bayan taga karshen damben, ya wara ido ya buda hannunsa shureim ya taho da gudu ya daga sa sama ya rungumesa yace "What are you doing here sweetheart?" Shureim ya washe fararen kananun hakoransa yace "We came with nanny and Anty to get something, Ga Nanny a cikin shop Anty kuma tana cikin mota tana jiran mu" kallon sudais Aliyu yyi ya ga yana tsaye ne yana kallonsu, a hankali ya ajiye shureim yana rike da hannunsa ya isa gun sudais haka nan yaji gabansa na faduwa ya duka dai dai height dinsa yace "How are you angel?" Sudais ya sauke idonsa yace "Am good" daga haka ya shiga shagon da Nanny take ciki, Aliyu ya bi sa da kallo, shureim yace "Uncle what are you doing here?" Aliyu yace "I came to get something also, why is ur twin behaving strangely, and he looks sick..." Fitowa sudais yyi don ba can cikin shagon ya shiga ba yana kallon Aliyu yace "Because I don't like you, stay away from me and my brother" Kallonsa Aliyu yake ko kiftawa babu, Shureim ya tura sudais yace "You are mean...." Sai da sudais ya gama kallon d'an uwan nasa sosai kafin ya kai masa mari yana huci yace "How dare you call me that" Aliyu na ganin shureim yayi kan sudais ya daga sa sama ya rungume sa a hankali yace "Yi hakuri ka kyalesa sweetheart" kuka shureim ya fara yi hana sa dukan sudais da Aliyu yyi, Sudais na huci yace "I don't like you both" dai dai fitowar Nanny daga shago, da sauri ta karaso tana tambayar me ya faru ganin shureim na kuka hannun Aliyu, sudais ya fashe da kuka shi ma yace "Nanny shureim started 1st, he insulted me" Nanny ta hade rai tace "Ohh har cikin market din ma sai kayi fada sudais, kai dai baka ji kuma nasan kai ka fara tsokanarsa ba ruwan shureim, silly boy kawai from henceforth bana sake xuwa ko ina da kai, ko kace xaka bi ni sai na ma duka" juyawa sudais yyi ya fashe da matsanancin kuka da gudu ya bar wajen xai je gun uwarsa, bin bayansa Nanny tayi tana kwala masa kira don ta can tsallake khadijah take kuma titin is very busy, amma sudais yaki tsayawa kuka kawai yake yana gudu yana kiran Anty, Aliyu na ganin haka shi ma ya bi su da sauri shureim na hannun sa, khadijah dake cikin mota tana xaune maxaunin driver don ita ta kawo su kasuwar haka nan kawai taji gabanta ya yanke ya fadi dai dai lkcn da taji ihun da mutane ke yi, tana juyawa kawai ganin Sudais dinta tayi a tsakiyar titi shi ma duk ya rikice ihun da mutane ke yi, ga mota har biyu sun taho da gudu ko wanne na son kauce masa, tunda take bata taba irin ihun da tayi ba a lkcn, lkci daya ko ina na kasuwan yyi tsit don duk yanda motar ta so avoiding sudais hakan bai yiwu ba, sai kuma a ka dau salati Khadijah ta fito a rikice jikinta na rawa ganin sudais kwance cikin jini ta fasa wani ihu kanta na juya mata, suman da ya kamata tayi nanny ce tayi sa a lkcn, ita kanta bata san me ya hanata sumewan ba, Aliyu da yyi still shi ma ya kasa motsi na few seconds ganin abinda ya faru lkci daya yaji strength ya dawo masa, ya ajiye shureim dake ihu yana kiran dan uwansa ya nufi gun sudais dake a kwance kan titi cikin jini mutane sun taru kansa mata na kuka maxa na salati, har da kyauta cikin mutanen, babu rabon Anty khadijah xata ga abinda ya faru don tsabar kunya bata jira Aliyu ya fito ba ta hau adaidaita da baby suka koma gida, cikin tashin hankali Aliyu ya karbi yaron hannun wani mutumi dake jijjigasa yana salati, a nan Aliyu yaji kamar bai taba xama likita ba duk rayuwarsa gaba daya basira ta dauke masa ya rasa ya xai yi da sumammen yaron dake hannunsa fuskarsa duk jini, cikin matsanancin kuka khadijah ta isa gun ta wani fasa ihu a gigice ta durkusa jikinta na rawa take cewa "Na shiga uku, don Allah ku taimakeni kar ya mutu ku rufa min asiri, kar ku bari ya mutu" daga kai Aliyu yyi a karo na farko yana kallonta jin muryarta, lkci daya signal dinsa ya sake daukewa yana mata wani irin kallo ita kuwa sai jijjiga sudais take ba tare da ta kula a hannun wa yake ba tana kuka tana cewa ya tashi kar ya tafi ya bar ta, kyauta ta saki salati baki bude tana kallon khadijah tace "Kamar khadijah nake gani ni kyautar Allah" khadijah ta kalleta ita ma da sauri, da gudu ta nufe ta rikota tana kuka cikin rauni tace "Anty ku taimake ni kar ya mutu don Allah, kar ya tafi ya bar ni" Kyauta ta kwalalo ido tace "Yaron ki ne Khadijah?" Khadijah ta dinga gyada mata kai tana kuka sosai, kyauta ta fashe da kuka tace "In sha Allahu baxai mutu ba xa mu tafi asibiti yanxu khadijah, baxai mutu ba..." wata mata ta fixge yaron a hannun Aliyu a mugun fusace ganin khadijah kawai yake kallo tace "Dubi mutum kamar an dasa sa a gun ya sa yaron da ba mu san ko ya mutu ba ko yana raye a gaba yana kallo, wannan wani irin uba ne kai, ni na xata taimkon gaggawa xai bada...." Khadijah ta tsayar da kukan da take ta sake kyauta ta nufi matar ta rikota cikin rudewa tace "yaro na bai mutu ba kar ki kara cewa ya mutu don Allah kar ki kara, wllh bai mutu ba, Allah baxai sa ya mutu ba" sosai ta ba mutanen gun tausayi wani mutumi ya sa sudais tare da matar a motarsa domin xuwa asibiti, mutumin ya kamo hannun Aliyu dake tsaye yana kallon khadijah da har sannan bata lura da shi ba yace "kar ka damu he will be alright in sha Allah shiga mu je asibitin tare" bayan motar Aliyu ya shiga suka dau hanyar asibiti, sai a sannan basirar sa ta likita ya dawo masa ya karbi sudais a rude ganin numfashinsa na sama ya dinga basa numfashi, banda kuka babu abinda matar dake kusa da shi take tana addu'ar Allah ya raya sa, jin mutumin dake ta sharara gudu a mota yyi parking Aliyu ya dago kai tare da bude motar ya ga asibitin da yake aiki ma mutumin ya kawo su, Aliyu ya fita rike da sudais yyi cikin asibitin da sauri nan aka shiga emergency da yaron, sai bayan kusan minti talatin Aliyu ya fito tare da wani likita daga emergency ward da aka shiga da sudais suka bar likita daya a kan sa da nurse, Dr Saif ya nufi gun su khadijah dake xaune reception da kyauta da wasu mutane har sun gaji da lallashinta don ko tayi kuka har ta gode Allah, tsabar tashin hankali ko gane asibitin bata yi ba, shureim dake jikinta ma kukan yake yana tambayarta me ya samu sudais, Nanny da ta suma an kwantar da ita asibitin ita ma, mikewa khadijah tayi da sauri ganin likitan, Aliyu ya tsaya daga inda yake har lkcn mask na bakinsa da hanci, Dr Saif yace "Ina mahaifiyar yaron?" Khadijah dake kallonsa gabanta na faduwa tace "Ni ce" Aliyu ya cire mask din dake fuskarsa yana kallon khadijah da wani irin mamaki, at the same time confusion, likitan ya tsaya kare mata kallo kamar bai yarda ba, can dai yace "Toh mahaifinsa fa?" Tana share hawayen dake xubo mata cikin rawar murya tace "Baya nan" likitan na kallon Shureim ya xaro ido yace "Subhanallah yan biyu ne?" Cikin kuka khadijah ta gyada masa kai, jikin likitan yyi sanyi sosai, ya shafa kan shureim dake kuka yana rike da mayafin Khadijah a hankali yace "Don't worry my boy ur twin will be okay in sha Allah, madam xa ki iya shiga ki gansa amma plss kar ki wani damu ciwo ne kawai yaji a kai sai bruises, so don't cry while inside, shi kuma wannan ki bar sa a nan ba sai kin shiga ba" daga haka ya juya yana kallon Aliyu dake nesa da su kafafuwarsa sun kasa daukarsa saboda shock yace "Dr plss see her inside, amma kar ta dade a ciki" daga haka ya kama hannun shureim yace "Big boy xo mu je office ka jira mumy" shureim xai masa taurin kai sai ya bi mamarsa ya daga sa sama kawai ya wuce office dinsa da shi don bai son ya ga dan uwansa a halin da yake ciki yanxu, Tuni Aliyu ya mayar da mask din fuskarsa yayi gaba kamar me counting step dinsa Khadijah na biye da shi a baya, tsabar tashin hankalin da ke tare da ita bata ko kalli wanda take bi ba balle ta san waye. Suna shiga ward din Aliyu ya tsaya bakin kofa ita ta shiga ciki gabanta na faduwa, ko gama ganin sudais bata yi ba ta fasa wani ihu, Nurse din ta karaso da sauri ta fitar da ita dakin tace "Haba madam, sai kace ba musulma ba wannan ihu haka" khadijah ta fashe da matsanancin kuka tana jijjiga nurse din tace "Don Allah Anty kar ku bari wani abu ya samu yarona, they all I have, plss ku taimake ni" rungumeta nurse din tayi tace "It's ohk madam jikin ai da sauki, you just pray Allah ya tashi kafadarsa kuma kada Allah ya sa ya tashi da wata matsala" Khadijah ta xame kasa tana kuka tace "Na shiga uku wllh kilan mutuwa xai yi ya bar ni, don Allah ku taimaka min" juyawa nurse din tayi ta koma ciki ta rufe kofar, Aliyu ya kasa ci gaba da kallon khadijah lkci daya idonsa ya kada, yaranta? To waye ubansu? Abinda ya dinga masa yawo a rai kenan, kawai ya ga ta mike ta nufo sa, kana gani kasan ta gaji da kukan ta riko sa cikin rauni tace "Plss Dr kar ku bar min yarona ya mutu don Allah ina rokan ku, they are all I've got in this world bayan ummata, plss ka taimaka Dr ku cire masa abinda ku ka sa masa a hanci ina son yarona" Aliyu ya kasa ce mata komai lkci daya hawaye ya kawo idonsa, da ba don a rude Khadijah take ba bbu abinda xai hana ta gane Aliyu ne gabanta saboda kwayar idanuwansa amma saboda tashin hankali bata gane ba ganin, hawayen idonsa ta tsayar da kukan da take xuciyarta na bugawa tana kallonsa ko kiftawa babu, bayan few seconds cikin sanyin murya tace "Dr ya mutu koh?" Aliyu bai iya yace komai ba ya ji ya kasa controlling kansa hawaye suka shiga sakko masa, he don't want to believe Khadijah conceived with him, he don't want to believe she conceived that deadly moment, if so then he is not worth to be forgiven, bai cancanci ta yafe masa ba, don ya mata xaluncin da dole baxata iya yafe masa ba, sai a sannan maganganun da Anty khadijah take a waya daxu ya fara dawo masa, ya juya ya hade kansa da bango yana hawaye sosai duk ya ji ya tsani kansa, yanxu yaran nan nasa ne kenan?? He is there illegal father, the cute boys... Are his and Khadijah's, they got them out of wedlock.... Lkci daya ya juya ta dalilin sound da ya ji bayansa, nan ya ga khadijah sume a kasa. A hankali khadijah ta bude idanuwanta da suka mata nauyi ta dinga bin inda take kwance da kallo, Umma ce xaune dakin da Nanny da ta ci kuka har ta gode Allah, sai kyauta da tayi tagumi, Umma ta mike da sauri ganin khadijah ta bude ido ta karasa kusa da ita da damuwa tace "Sannu daughter, how are you feeling now?" Mikewa xaune Khadijah ke son yi amma kanta yyi mata nauyi ga kirjinta dake mata xugi, Umma ta riketa tace "Koma ki kwanta" Kyauta ta iso kusa da ita ita ma da damuwa tace "Sannu khadijah" Shiru khadijah tayi kamar me son tuno abu, Umma ta hade rai tace "Don't stress ur self thinking of anything, just relax...." Hawaye ya kawo idonta ta kamo hannun kyauta cikin rawar murya tace "Anty mai girki ina sudais dina, ya mutu koh? Don Allah ku gaya min, kar ku" Umma ta dakatar da ita a mugun fusace tace "Ke kika kashe sa halan? Ji wani xance da kike ma mutane khadijah" Girgixa kai khadijah tayi da sauri hawaye na sakko mata, Kyauta tace "Toh yana nan lafiya khadijah, har ya tashi shi ma, suna can tare da d'an uwansa da wani likita" Khadijah na goge idonta tace "Toh xan iya ganinsa don Allah?" Harara Umma ta watsa mata tace "Da drip din xa ki je ki gansa, kuma ki rufe min maki haka, ance maki yana lafiya" Khadijah bata sake cewa komai ba sai dai ban da faduwa babu abinda gabanta yake, Umma ta mike ta shiga hada mata shayi, Nanny ta xauna kusa da ita cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Khadijah, Sudais yana nan lafiya har ya tashi, suna tare da Shureim yanxu haka" Sai a sannan khadijah ta ji hankalinta ya kwanta sosai, Nanny ta mika mata wayarta tace "An kira ki har sau biyu, but I picked..." Khadijah ta karbi wayar tana kallon wanda ya kirata ta ga Khaleel ne, ta kalli nanny a hankali tace "Me ya ce?" Nanny tace "Na gaya masa abinda ya faru, yace xai xo clinic din" Khadijah bata ce komai ba ta ajiye wayar, ta ji tana ma son ganinsa, jin xai xo hankalinta ya kara kwanciya. All this while Aliyu na ward din da sudais yake tare da Shureim, kwata kwata bai son ya bar su ko na minti daya, da ya fita ba a jimawa xai dawo kuma har lkcn ya ki cire mask din bakinsa da hanci, damuwa ce sosai tare da shi, da ya kalli yaran ya tuna nasa ne sai yaji hawaye a idonsa, shi kuma irin tasa kaddarar kenan?? Har yan biyu ba ta hanyar aure ba, har ransa yake jin tausayin kyawawan yaran, he wished ba ta haka suka xo ba, Shureim bai ganesa ba sai dai ya lura da irin yanda sudais dake kwance ke kallonsa, A hankali ya isa kusa da yaron ya duka a sanyaye yace "You want something??" Sudais ya girgixa masa kai, Shureim ya kallesa da sauri na few seconds kafin yace "The voice.... sounds familiar" murmushin karfin hali Aliyu yyi ya sauke mask din fuskarsa a hankali yana kallon yaron, Shureim yyi shiru yana kallonsa can ya juya ya rungume hannunsa ya hade rai yace "You caused my brother's accident" Jikin Aliyu yyi sanyi sosai, ya mayar da dubansa kan sudais ya ga ya ki kallonsa shi ma ya hade rai, bude kofa aka yi xai mayar da mask dinsa da sauri yaji muryar colleague dinsa, Dr Muktar ya karaso yana kallon yan biyun yace "Maa sha Allah, he is recovering fast" ya kamo hannun Sudais yace "How are you feeling now handsome?" A hankali Sudais yace "Alhmdllh" Dr mukhtar yyi murmushi yace "Good" kallon Aliyu yyi yace "Kasan kuna yanayi da boys din nan sosai, da ba don na san baka taba aure ba bbu abinda xai hanani cewa yaranka ne Dr" Aliyu ya kirkiri murmushin karfin hali yace "Gaskiya ne" Dr mukhtar yace "Naga kamar sun ma shiga ranka kai ma tunda gashi ka ki barin ward din tun daxu" Aliyu yace "Sure they are cute" Dr mukhtar yace "Just came to check on them dama" daga haka ya juya ya fita, Aliyu ya kamo hannun yaran murya can kasa yace "Am sorry for all that happened sweethearts forgive me plss" a hankali Shureim yace "Ohk..." Kallon sudais da yyi shiru yyi yace "And you sweetheart?" Sudais ya sauke kansa yace "Me too" jawo yaran jikinsa ya yi cikin sanyin murya yace "I love you boys" lkci daya idanuwansa suka kada, how he wish Khadijah xata yafe masa ba tare da ta sa masa heart attack ba, ta ajiye komai su xauna tare da yaransu, bai taba saba maganar mahaifiyarsa ba amma da kamar wuya wannan karan, it will be different.... he will marry Khadijah and have his boys in sha Allah, and he will neva be ashame showing them as his children, wani mugun son yaran ne ke fixgarsa yana rungume da su, bude kofar dakin aka yi Umma ta shigo tare da wani likita, khaleel na biye da su a baya, A hankli Aliyu ya daga mask dinsa sannan ya juya suka yi ido hudu da khaleel, Dr Abdul yace "Dr their grandma and a Dr also, my frnd Dr Ayman" Aliyu sai kallon khaleel yake kamar yanda shi ma khaleel ke kallonsa duk da fuskarsa a rufe yake, Umma ta kalli Dr Abdul sanin ance baxa a bar su su shiga gun yaran ba tace "Mun gode Dr" Dr Abdul yace "Ba komai Mama" Dr Abdul yace "Ayman bari in koma bakin aiki na" khaleel yace "Tnxx Abdul" daga haka Abdul ya fita, Shureim ya sauko saman gadon ya rungume khaleel, khaleel ya daga sa sama yace "How are you" kamar xai yi kuka yace "I am fine but my brother isn't" Khaleel ya ajiye sa ya karasa yana kallon Sudais cike da tausayinsa, Shureim kuma ya nufi gun Umma dake kallon Sudais ita ma a sanyaye, plaster ne gaba daya kansa, khaleel ya kamo hannunsa yace "You will get well soon in sha Allah my boy" Sudais xai fara kuka ya rungume sa yace "Noo don't cry be a strong boy" Sudais yace "Uncle ina Antyna" khaleel yace "Xata xo yanxu" sudais yace "Ka kai ni wajenta I want to see her" Khaleel yace "Noo she will be coming soon" Aliyu dai na tsaye yana ya na kallonsu, Can ya kalli Umma yace "Plss Maa it shouldn't take long xa ku iya tafiya yanxu the boy need rest" Umma tace "To xa mu fita yanxu Dr" khaleel ya juya yana kallon Aliyu, mikewa yyi ya isa gabansa yana kallon cikin idonsa yace "Then discharge him now, xa mu je gida in ci gaba da treating dinsa or I take him to another hospital" Aliyu yyi murmushi daga cikin mask din fuskarsa yace "And who are you to say that? His father? Or?" Umma tace "Aa bai kai haka ba Dr xa mu fita yanxu ai" wani kallo khaleel ya dinga ma Aliyu, Umma tace "mu je khaleel tunda a bakin aikinsu suke" kallonta khaleel yyi, duk da bai yi niyyar fita ba amma ya ji kunyanta yace "Toh umma" daga haka ya nufi kofa Shureim ya bata fuska kamar xai yi kuka yace "Uncle are you leaving us?" Sudais ma ya dinga kallonsa Kamar xai yi kukan, Khaleel ya juyo yace "Noo sweetheart I am around" Daga haka ya fita, Umma ta bi bayansa tana kara ba Aliyu hakuri tana fita ta rufe kofar, wata cleaner ce ta shigo dakin da abinci da ruwa da Aliyu ya sa ta siyo, ya mika ma Shureim nasa ya karba, Ya shiga ba sudais nasa da kansa. Khadijah duk ta damu tana son ta ga yaranta ganin har da Shureim ma tun da ta bude ido bata gansa ba, amma tsoron Umma yasa ta kasa cewa komai don tana iya balbaleta yanxu tunda ta ce mata they are all fyn, Khaleel dake tsaye dakin yana kallonta ya lura da yanayinta, ita ma ta tsaya kallonsa amma ta kasa ce masa komai ya san she Wants to say something, ya kalli Umma dake magana da wasu neighbours dinsu biyu da suka xo duba sudais, Nanny kuma ta koma gida tayi girki, Kyauta ma ta koma tace xata dawo ko da daddare da mai gidan ta, Khaleel ya karaso kusa da ita a hankali ya d'an duka yace "What?" Murya can kasa kamar xata yi kuka tace "I want to see my kids plss" wani kallo ya mata, sai kuma ya d'an yi murmushi yace "To sannu mai kids" ta bata fuska tana kallonsa alamar please, yace "Ohk wait bari Umma ta raka bakin nan sai in kai ki" lkci daya hankalinta ya kwanta tace "Toh ngdd" Umma na fita don yin rakiya ya cire mata drip din hannunta da ya kusa karewa, duk da jirin da take ji ta mika masa hannunta ya rike ta sauko daga kan gadon ta sa takalminta sannan suka fita ward din da sauri tana jin kamar xata fadi ba don ya rike hannunta ba, direct ward din da yan biyun suke ya nufa da ita, a hankali ya murda kofar ya bude, khadijah tayi ido hudu da Aliyu dake ba sudais abinci, still tayi a gun taji komai nata ya tsaya, xuciyarta ya dinga bugawa da sauri da sauri, Shureim ya sakko ya taho da gudu ya rungume ta, sudais yyi murmushi cike da jin dadi ganin uwar tasa yace "Anty...." Mikewa Aliyu yyi ya rufe abincin yana kallonta da khaleel yace "You can come over... But just few minutes" Khadijah ta warce hannunta a na Khaleel ta janye Shureim a jikinta ta juya ta bar wajen kamar xata tashi sama, direct reception ta nufa, tana kallon nurses din cike da masifa tace "Who is the Dr in charge of this hospital..." Kallonta nurses din suka tsaya yi, can wata ta mike tace "Me ya faru madam" tana huci tace "ohk, I want my kid discharge immediately, ku bani bill din in biya in bar nan yanxun nan plss" cikin tsawa ta kare maganar nurse din ta koma ta xauna tace "Easy madam, this a hospital, they are patients all over, ki je gun likitan da ya karbe su, shi xai yi discharging dinsu ba mu ba madam" khadijah na mata wani kallo tace "Wani likita kenan ina office dinsa kuma?" Nurse din tace "Dr Aliyu, kina haurawa sama office dinsa is by ur right, xa ma ki ga sunansa a jiki" kallonsu Khadijah ke yi xuciyarta na bugawa jin sunan da suka kira, can ta juya kamar xata tashi sama ta wuce upstairs din, Har lkcn khaleel dai na tsaye bakin kofa yana kallon Aliyu, Aliyu ya isa dab da shi yana masa wani kallo yace "Da matsala ne malam, naga kallon yyi yawa?" Wani murmushi khaleel yyi yace "You watch and see" Dawowa khadijah tayi dakin cikin tashin hankali ta nufi gun yaranta ta cire dip din hannun Sudais ta sauko da shi kan gado ta kama hannun Shureim ta nufi kofa, tsayawa gabanta Aliyu yyi yana kallonta da kyau yace "Ba inda xa ki je da su Iman" xaro ido tayi jin abinda ya fada ta tura sa da karfi amma go gezau, xuciyarta na heaving da mugun mamaki tace "Ba inda xan je da su kamar yaya??? ka taba sanin su ne, ko kuma ni ka san ni ne? Where did you knw us from" yyi wani murmushi yace "Khadijah, am giving you my words, you are not moving a step forward with my kids, ki fadi duk amount da kika ga yyi suite din ki, tun daga daukar cikinsu, rainon cikin, haihuwarsu har xuwa girman su yanxu and I will pay you, kilan hakan kadai xai sa ki yafe min idan na amshi wahalata da na hada ki da at a very tender age, ni kuma baxan ji kunyan daukansu in kai su gida gun iyayena a matsayin yaran da na haifa out of wedlock ba, shikenan kema na raba ki da wahala na raba ki da rikon 'ya yan da kika samu ta hanyar fyade da aka maki, sai ki tafi kiyi auren ki hankali kwance ba tare da kin kara tunanin kina da yaran da kika haifa ba ta hanyar aure ba, I am collecting my boys today for ur own good" Kallonsa Khadijah take ko kiftawa babu, bakin ciki da takaici ne fal idanuwanta, xuciyarta ya dinga mugun bugawa, ta hadiye abu da kyar, lkci daya idanuwanta suka yi jajir cikin muryar da ba ta ta ba tace "Come again Aliyu... I didn't get you" Cire mask din bakinsa yyi gaba daya yana kallonta da kyau cikin husky voice dinsa yace "You are not daft Iman, you heard me right, or you ask ur bodyguard xai maki bayani da kyau" bai rufe baki ba ta sauke masa mari tana huci, wani murmushi khaleel yyi yana shafa sajensa yace "Seems you both need privacy" daga haka ya juya ya bar wajen har sannan yana murmushi, Aliyu ya kauda kansa na few seconds kafin ya juyo a hankali yana kallonta da wani irin mamaki, hawaye na sauka idonta tana girgixa kai tace "Allah ya isa tsakanina da kai Aliyu, shari'ar mu da kai dama na fada maka sai a lahira, kuma yarana ba naka bane, ba kai ka haifar min su ba, you don't have any right over them, idan duk duniyar nan xa su hade nan wlh wllh baxan baka su ba, ni na sha wahalan kayana ni na haife su, baka isa ka raba ni da su" ta fashe da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi, hakan yasa su shureim ma suka fara kuka suna rike da ita, kallonta kawai Aliyu yake da idanuwansa da suka yi jajir, ganin khaleel ya bar wajen khadijah ta kama hannun yan biyun ta da sauri ta juya xata bi bayansa Aliyu ya fixgota yayi jamming kofar yana mata wani mugun kallo, lkci daya ta cakumosa tana kuka mai taba xuciya tace "Ka bude mana mu fita Aliyu, ka bude kofar in fita da yarana kar in tara maka jama'a" yanda ta rikice haka yaranta ma suka rikice suna kuka, daukar ta Aliyu yyi ya nufi bathroom dake ward din ya tura ta ciki yace "I will teach you sense Khadijah...." daga haka ya rufe kofar da makulli ta dinga bubbuga kofar a rude tana kuka tana kiran sunansa, Sudais ya kara fashewa da matsanancin kuka yace "Why are you doing this to our Anty, plss let her out" Shureim ya dinga bubbuga kofar shi ma yana kuka yana kiran ta, Aliyu ya hade kansa da bango ya runtse ido xuciyarsa na bugawa, lkci daya ya juyo ya kama hannun yaran gaba daya suna turturjewa ya watsa masu wani mugun kallo da idanuwansa da suka yi ja, ba shiru suka yi tsit ko wanne a tsorace, ya bude kofar ward din ya fita da su, ward na intensive care ya shigar da yaran tunawa da yayi bai taho da motar clinic din ba, banda kuka babu abinda suke yi suna kallonsa a tsorace, fuskarsa daure yace "I don't want to hear any of you cry again" shiru suka yi sudais ya riko hannunsa yace "plss bring out our Anty from the toilet" sauke idonsa kasa yyi a hankali yace "Ohk i will do that now" daga haka ya fita ya rufe kofar yanda baxa su bude ba, sama ya wuce da sauri ya shiga office din Muktar ya dau makullin motarsa sannan ya sauko, yana bude kofa su sudais suka yi tsit daga kukan da suke, Shureim yace "Uncle where is she plss" hannunsu ya kama ya fita da su, ya bi ta bayan asibitin xuwa parking space, back seat ya saka yaran gaba daya sannan ya shiga driver seat ya tada motar ya bar asibitin. K'asa kuka twins din suka yi a motar saboda Aliyu da ya hade rai, kana ganinsu kasan a tsorace suke barin Shureim, driving kawai yake har ya iso gida bayan yyi parking ya fito ya bude masa motar yace "Come down" da farko kin sakko suka yi, ganin kallon da yake masu duk suka fito, Shureim na goge idonsa cikin rawar murya yace "I thought you where a good friend, plss don't kidnap us away from our Anty, she will be sad" Duk da hawayen da ya taru idon Aliyu hakan bai hanasa durkusawa gabansu ba ya rungume su gaba daya yace "I didn't kidnap my kids, I brought you two to ur Granny" Sudais ya xaro ido yace "We left her at d hospital and this is not our home" Aliyu na kallonsu cikin sanyin murya yace "This is your father's home" A tare suka hada baki gun ce masa "Where is he?" Shiru Aliyu yyi yana kallon handsome boys din, sudais yace yace "Anty told us our father... Is a Barrister, she said he travelled immediately we where born and that... he will come to us one day" Jikin Aliyu yyi mugun sanyi yana kallonsu, Shureim yace "We will love to see our dad" mikewa Aliyu yyi ya kama hannunsu ya wuce cikin gida da su. Sudais ya bata fuska kamar xai yi kuka yace "I thought you are taking us back to our Anty" gaba daya yan gidan na parlor xaune ana jajanta abinda Kyauta ta ma Anty khadijah, saleem sai cewa yake da ma da shi aka je ya lallasata ya cire mata hakora ya ga wanda ya tsaya mata, mumy dai bata ce komai ba sai kallon Anty khadijah dake kwance kasa take duk jiki yyi tsami don ma ta gasa jikin da ruwan xafi, baki a kumbure har da ido, iklima ma an sallamota tana sama a kwance, gaba daya occupant din parlorn suka dinga kallon Aliyu da twins din hannunsa, Anty khadijah ta mike xaune da sauri ita ma tana kallonsu, Baby ta mike da mugun mamaki tana kallon yaran tace "Laah yaran da muka gani a kasuwa daxu, yaya where did u knw dem from, mai ya samu kan wannan" Aliyu ya isa har gaban Mumy dake kallon yaran ya sake hannunsa, a sanyaye yake kallonta, yyi gathering courage da kyar yace "Yaran da Iman ta haifa kenan, she got pregnant after the incident" Ba Anty khadijah kadai ba har Mumy sai da ta girgixa ta mike tana kallon yaran dake ta kallonta sannan ta mayar da dubanta kan Aliyu cikin wani yanayi tace "How did you knw Abuturrab, where did you get dem from???" hawaye suka shiga sakko masa yana kallon mahaifiyar tasa a sanyaye yace "I met them today mum, I don't knw if Khadijah will ever forgive me... I ruin her at a very tender age, this boys are my blood, Mumy na kawo su gida ne don nima in yi facing ko da kadan ne daga cikin abinda tayi facing a rayuwarta duk da ni na fita ga ta...." Kasa ci gaba yyi ya bar parlorn ya wuce sama hawaye na sakko masa, Anty khadijah dake ta xufa ga cikinta da ya tsure tace "Mun shiga uku, Anty fati kin ga wani sharri koh, kin ga wani hauka irin na Aliyu ko? yaushe Aliyu ya isa haifan wa ennan yaran? ta je an mata ciki a wani waje ta makala masa kuma ya yarda saboda wawa ne shi... a ina ma ya ganta???" Kai kana gani kasan kame kame kawai take duk ta rude, Su Shureim sai bin kowa na parlorn suke da kallo a tsorace, baby ta fashe da kuka cike da tausayin yayanta, Salim ma sai kallon yaran yake a duk jikinsa yyi sanyi ganin kamannin Aliyu sak tare da su, Mumy ta fashe da kuka sosai ita ma tana kallon yaran, hakan yasa su ma suka fashe da kuka, babu abinda take gani tare da yan biyun sai Aliyunta lkcn da yake kamar su, Anty khadijah ta haura sama kusan a guje tana cewa "Yau na ga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, ina yake ya xo ya fitar mana da shegun nan da ake shirin kakaba masa, ya xo ya mayar da su inda aka basa su, amma Allah ya isa tsakaninmu da yarinyar nan, ta rasa wanda xata ma sharri sai Aliyu saboda tsautsayi ya gifta tsakaninsu? Ni dai nasan da hankalin Aliyu baxai mata fyade ba, sharrin shaidan kawai da kuma sharrin ta don ita ke shisshige masa, wlh baxa mu amshi shegu gidan nan ba, kaf xuri'ar mu ba a taba haka ba baxa a fara a kan d'an yayata ba" tana wucewa sama mumy na share hawayenta ta kama hannun yan biyun ta wuce sama xuwa dakinta da su. Wata nurse ce ta shigo dakin ba ma sudais allura ta ga babu kowa dakin sai kofar bayi da ake ta bubbugawa ta isa da sauri ta bude kofar da mamaki ganin key aka sa ta waje, khadijah ta fito tana bin dakin da kallo ganin ba kowa ta riko nurse din a rikice tace "Na shiga uku nurse ina yarana? Where are they plss" nurse na kallonta da confusion tace "Yanxun nan na shigo madam" da gudu khadijah ta fita xuwa ward din da aka kwantar da ita, ta ga Umma ce xaune sai Nanny da khaleel dake tsaye ya jingina da bango idonsa a kan wayar hannunsa, ta fashe da matsanancin kuka ta xube wajen tace "Wayyo Umma na shiga uku ya tafi min da yarana" khaleel ya iso gabanta da sauri da mamaki yace "Ya tafi da su ina? Kina kallonsa ya tafi da su" ficewa yyi ward din da sauri, Umma da ta gigice tace "Wa ye ya tafi da su Khadijah, waye shi" Khadijah ta riko Umma tana kuka sosai tace "Umma Aliyu, ya tafi da yaran, ya wuce min da yarana" a sanyaye Umma ke kallonta, Nanny ta bi bayan khaleel da sauri tana cewa "Me ya kawo sa asibitin, mun shiga uku" umma ta dago Khadbijah ta rungumeta, cikin rawar murya take cewa "Umma kar ku bari ya raba ni da su, baxan iya rabuwa da su ba, don Allah a taimake ni a karbo min yarana ni na yafe masa duniya da lahira ya bar min yaran, wllh na yafe masa har cikin xuciyata amma yayi hakuri ya ba ni yarana" tana kai wa nan ta kara fashewa da matsanancin kuka tana kiran Umma, hawaye ya shiga sakko ma umma ta rasa abinda xata ce ma 'yar tata. Direct office din Dr Abdul khaleel ya wuce, ya samesa xaune yana aiki, ganin khaleel ya bar abinda yake yi yace "He is improving ko Dr" khaleel bai tanka sa ba isa gabansa ya dafa table yana kallonsa bbu yabo bbu fallasa yace "Dr Aliyu.... Where is his home?" Dr Abdul yace "Aliyu? Ba yana office ba?" Khaleel yace "Baya nan" da mamaki Abdul yace "Hope babu matsala dai?" A takaice Khaleel yace "Babu, ina gidansu yake" Abdul yace "Toh, he is not the type that mingle gaskiya I dont knw his home" juyawa Khaleel yyi ya fice office din, direct parking space ya nufa ya hau motarsa ya wuce gidan Farouq. Umma ta dinga kwantar ma khadijah hankali duk da taki saurarenta, daga karshe Umma ta fita ta biya bill dinsu don bata ga amfanin xaman asibitin ba, na khadijah kadai suka karba ban da na sudais kamar yanda Aliyu yyi instructing din su, da kafa suka fita asibitin don Umma bata xo da mota ba, suna isa bakin titi ta tsayar masu da abun hawa suka wuce gida. Girgixa kai Farouq yyi yana kallon Khaleel yace "Ni fa ba ruwana, kamar yanda na ki ba sa address din ka, to kai ma baxan baka address din sa ba gaskiya, ku kuka san abinda ya hada ku can.." Wani kallo khaleel ke masa kafin ya mike ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya wuce, yana driving ya dau wayarsa ya fara kiran Khadijah, har ya katse bata dauka ba, nan ko tana zaune ita kadai daki tayi kukan har ta ji ba dadi, Umma kuma na parlor da Nanny sun yi jigum, Umma ta rasa ta ina xata fara yanxu ta ina xa su fara xuwa neman yara, Jin wayar ya sake ring Khadijah ta daga da kyar ta kai kunne, jin muryar ta jikin khaleel yyi sanyi, a hankali yace "Plss ki kwantar da hankalin ki Khadijah, xa a amsar maki kids din ki, he have no right over them, in sha Allah we will get back ur kids" kasa cewa komai tayi tana share hawayen da ke xubo mata, yace "Kin san address din can gidansu?" Shiru tayi kafin ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "Na manta" yace "Amma xa ki gane gidan?" Nan ma ta d'an yi shiru, anya xata gane gidan yanxu kuwa, murya can kasa yace "Khadijah?" Tace "Kilan in gane" yace "Good, kuna clinic din har yanxu?" Ta girgixa kai tace "Mun dawo gida" yace "Toh xan taho yanxu, but promise me baxa ki sake kuka ba plss" a hankali tace "Toh baxan yi ba" yace "Good, ina tahowa yanxu" daga haka ya katse wayar, Sosai Khadijah ta ji hankalinta ya kwanta, ta ji ta samu natsuwa. Tun da Aliyu ya shiga dakinsa bai sake fitowa ba, Mumy da maganganun Anty khadijah suka fara sa mata ciwon kai ta daga kai tana kallonta a karo na farko tun shigowarta dakin, ban da kumfar baki kamar wata xararriya babu abinda take tana nuna yan biyun dake xaune kan gadon Mumy, suma yaran kallonta kawai suke a tsorace, Baby ma na tsaye sai hararan Anty khadijah take tana tabe baki, Mumy ta dakatar da ita a tsawace tace "Khadijah ki fita ki ban waje don Allah ki bar ni in ji da guda daya, ciwon kai kike kara min ki fita don Allah, ko makaho ya shafa yaran nan yasan na waye, Baxa ayi DNA din ba...." Anty khadijah da idanuwanta suka kankance da mugun mamaki tace "Anty fati ni kike cewa in fita in baki waje don ina nuna damuwa ta kan shegun da aka makala ma Aliyu aka ce nasa ne, Ni Anty fati??" Mumy tace "Ehh ki fita nace" tayi wani murmushi tace "Xan fita yanxu kuwa" daga haka ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, Mumy ta kalli yan biyun dake bata tausayi har ranta, a hankali tace "Me xa ku ci?" Sudais dai bai ce komai ba, Shureim ya girgixa mata kai shi ma bai ce komai ba, karasowa tayi ta xauna gun yaran tana kallonsu, wani sonsu take ji a xuciyarta, ta d'an yi murmushi tace "Ayi maku noodles and egg?" komawa Sudais yyi ya kwanta ta kai hannu jikinsa taji xafi sosai, kallon baby tayi tace "Xaxxabi ne jikinsa fa sosai..." Baby ta karaso ita ma ta taba yaron taji xafin jikin ta kalli Mumy tace "Mumy ko in kira yaya?" Mumy tace "Kira sa" juyawa tayi ta fita, ita ta fara dawowa dakin sannan Aliyu ma ya shigo, kallon yaron yake har ya isa kan gadon ya taba jikinsa, dago sa yyi ya xaunar da shi, yana kallonsa yace "Are you feeling pain anywhere?" Sudais ya nuna masa kan sa, kamar xai yi kuka yace "I want to go to my Anty plss" Aliyu ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Ohk I will take you there" Mumy dake kallon Aliyu tace "Ina ita khadijahr take?" Kamar Aliyu baxae ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa murya can kasa yace "Bayan ta bani su tayi tafiyarta" wani kallo Mumy ke masa ganin yanda yyi maganar, can ta girgixa kai tace "Karya kake..." Da sauri ya kalleta, sai kuma ya marairaice yace "Mumy bata sani ba na taho da su, idan ta sani baxa ta bani su ba" Bude baki Mumy tayi tana kallonsa, da damuwa tace "Me yasa xaka yi haka Aliyu, me yasa xaka raba su da uwar su...." Kasa cewa komai yayi, Mumy da duk jikinta ya kara yin sanyi tace "Aliyu tell me how everything happened, garin yaya kayi ma yar mutane haka, where was I that day? kar ka boye min komai plss, tell me the truth...." kallon Mumy Kawai yake ko kiftawa babu, can ya xauna gefen gado ya rike kansa yana jin kamar ya fara mata hawaye, bai son tuna mummunar ranan nan a rayuwarsa, Mumy na kallon Baby tace "Baby xo ki tafi da su ki dafa masu indomie ki basu, shi wannan ki kai sa dakin ki ya kwanta" Baby ta karaso ta sakko da boys din daga kan gado ta wuce da su dakinta, Mumy na kallonsa tace "Ina ji Aliyu" Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali ya fara magana, "Mumy ni dai nasan I woke up fine that very day...." Ya d'an yi shiru, nan ya fara ba ma Mumy labarin abinda ya faru ranan bai boye mata komai ba har yanda bayan kwana biyu ya ba ma khadijah kudi me yawa yace ta wuce gun ummarta, hawaye kawai Mumy ke yi tana kallonsa a sanyaye, bai iya ya dago kai ba shi ma hawayen na sakko masa cike da karfin hali yace "Mumy nayi abinda nayi ne out of confusion, I was confused, ban taba xaton xan aikata ma khadijah haka ba, bayan tafiyar ta ku shaida ne, nayi bankwana da kwanciyar hankali da farin ciki na, I never had rest of mind again kuma na kasa gaya maki abinda ya faru ban san ya xa ki dau xancen ba, shi yasa a ko da yaushe nake ce maki ki taya ni da addu'a, wani lkcn idan na kwanta bacci ita kawai nake gani, kuma it's not as if nasan da cikin bane, kawai ni dai nasan ban kyauta mata ba saboda marainiya ce bata da kowa, ban san ta Inda xan fara nemanta ba don ban san kowa nata ba, da babu abinda xai hanani nemanta Mumy, idan baki manta ba akwai wani lkci da na taba tambayar ki ko kina da number warce ta kawo ta kika ce baki da shi, ni ban sa ko Khadijah xata yafe min ba and it looks as if I don't deserve that.... Amma abinda ke bani mamaki har yanxu shine yanda aka yi Anty khadijah ta san abinda ya faru bayan bata gidan kuma ita ta fita tare da su baby a ranan, gidan ya rage daga ni sai Khadijah, sai kuma jiya tana waya a bathroom din dakinta, I overheard all what she was saying on the phone.... Nan ya gaya ma Mumy duk abinda ya ji Anty khadijah ke fada a waya jiya, yana girgixa kai yace "We shud keep on pretending mum, she was so shock da ta gan ni a dakin, but i pretend ban ji komai ba, hakan kuma ya sa hankalinta ya kwanta, a sannu abinda take yi xai bayyana a fili tun da ba mu da hakkinta, kuma ina mai tabbatar maki soon komai xai bayyana, ke dai kawai ki ci gaba da sa mata ido, xan dai sa su Sanusi su tone bayan gidan to check what she was talking about on phone" Mumy ta dinga kallonsa ko kiftawa babu cike da shock, ya goge idonsa har lkcn bai kalleta ba yace "And... Mumy kilan idan ke kika yi ma khadijah magana xata iya yafe min, ni ta ki saurarata har yanxu, kuma mumy plss kar ki ce min baxan iya aurenta ba, hakan kadai ne xan iya mata in wanke kaina, I knw I can't pay her all what she passed through, kar ki hana ni aurenta mumy..." Mumy ta sauke ajiyar xuciya har lkcn tana mamakin abinda Aliyu ya fadi mata kan Anty khadijah, she is still finding it hard to believe that, infact bata ma yarda bane tasan Anty khadijah baxata yi abinda Aliyu ke fadi ba, Aliyu yace "Mumy kinyi shiru" Mumy ta kallesa ta kara sauke ajiyar xuciya sannan tace "Idan kuma ita bata son ka fa?" Ya d'an hade rai yace "Toh sai ta bar min yarana taje tayi aurenta shikenan na raba ta da wahala, idan kuma ta yarda ta aureni sai mu xauna mu rike yaranmu, domin kuwa su din abun kyama ne idan ta kai su wani gidan, ko ba yanxu ba wataran xa a kyamace su, to idan muna tare fa? We can never do that to them" Mumy bata kuma cewa komai ba tayi nisa tunanin da take na Anty khadijah, Bude kofar dakin Anty khadijah tayi ta shigo tana kallon Mumy da kumburarrun idonta da ta sha kukan takaici, kallo daya Mumy ta mata ta dauke kai xuciyarta na kara karyata Aliyu, Aliyu kam bai ma kalli inda take ba, tana kallon Mumy tace "Ina son sanin matsayin auren iklima a gidan nan Anty fati, na hada kayana idan Ita ma in hada nata ne toh..." Sai a sannan Aliyu ya kalleta yace "Anty aure ya taba mutuwa ba ayi saki ba?" Hararansa tayi ta juya ta fita, dakin baby ta bude ta dinga kallon yaran dake kan gadon cike da tsana, a tsorace suke kallonta su ma, can ta juya ta fita dakin ta sauka downstairs xuciyar ta na tafarfasa, Baby ce kitchen tana bare eggs da ta dafa masu indomien na kan wuta, Anty khadijah ce ta shigo kitchen din ta dau cup ta xuba ruwan xafi daga flask, Baby ta kalleta ganin yanda ta tsaya tana tunani, da sauri Anty khadijah ta bude gun da madara suke ta fiddo kayan tea ganin kallon da baby ke mata, tana hada shayi tace "Baby ina wani sarka da na baki ki ajiye min ranan da aka yi bikin iklima a gidan nan?" Baby tace "Anty yana cikin jakata a daki" Anty khadijah tace "Je dauko min kayana" Baby tace "Yanxu Anty?" Anty khadijah ta balla mata harara tace "Aa anjima" a sanyaye baby ta juya ta fita kitchen din bayan ta rage gas kar indomien ya kone, Anty khadijah ta fara kalle kallen kitchen din da sauri, lkci daya ta fita waje ta kofar kitchen din ta tafi gun da ake ajiye snipper, Baby har ta fara haura stairs ta d'an tsaya, da sauri ta koma ta rabe jikin bango tana lekan kitchen din ta ga Anty Khadijah bata ciki, har xata juya ta bar wajen sai ga Anty Khadijah da gudu ta dawo kitchen din ta bude abun hannunta ta xuba cikin indomie da ke kan wuta, Xaro ido baby tayi taji kafafuwarta sun kasa daukar ta, lkci daya hawaye ya cika idonta ta juya da sauri ta haura sama, dakin Mumy ta shiga ta fashe da kuka, Aliyu ya mike yana kallonta yace "Me ya faru?" Baby ta durkushe dakin tana kuka sosai tace "Mumy Anty Khadijah ce na ga tana xuba snipper a cikin indomien yaran da nake dafawa" Aliyu ya xaro ido yace "Snipper??" Da sauri ya nufi kofa mumy tayi maxa ta dakatar da shi, ya juyo hankali tashe yana kallonta, Mumy na kallon Baby tace "Ta gan ki?" Girgixa kai baby tayi tana hawaye, Mumy ta hadiye abu da kyar, cike da karfin hali tace "Je ki dauko yaran ki kawo su nan, kar ki ce mata komai" Aliyu sai kallon mumy yake xuciyarsa na bugawa, Mumy ta kallesa tana kkrin goge hawayen idonta tace "Kar ka ce mata komai, let pretend we don't knw... Don't say anything Aliyu" Baby ta dawo dakin da su sudais mumy ta daura su kan gadon tana kallonsu a sanyaye, ta dubi Baby tace "Tafi ki xubar da indomie din, kar ki ce mata komai kin ji, ae basu da hakkinta don hka bbu abinda ta isa tayi masu wanda Allah bai masu ba" Baby ta fita dakin a sanyaye hawaye ya ko tsaya mata, ganin abun take kamar a movie, ynxu da bata dawo ba haka xata dau indomien ta ba yaran su ci su mutu?? Anya Anty khadijah na da conscience kuwa, me yan yaran suka mata, Aliyu kam ya kasa cewa komai, Mumy ta dinga share hawayen dake ta xubo mata, me tayi ma khadijah ta mayar mata da family dinta haka, dama laifi ne idan ka jawo naka ya xauna tare da kai?? Baby bata ko kalli Anty khadijah da ta xauna parlor tana shan shayi ba ta shiga kitchen din, Anty khadijah ta bi ta da kallo ta gefen ido, daukar indomie da kwan baby tayi ta fita ta xubar cikin shara ta tara tukunyar a bakin tap, sai da ta tabbatar ta wanke tas sannan ta dawo kitchen da shi ta ajiye ta fito kitchen din ta wuce stairs, Anty khadijah ta bi ta da kallo baki bude, da sauri tace "Ke wai sai indomien ya kone ne kin bar ma mutane gas yana ci" Ba tare da baby ta juyo ba balle ta kalleta tace "Sun ce baxa su ci ba na xubar" Daga haka ta haura sama Anty khadijah ta mike baki bude tana kallonta gabanta na faduwa, da sauri ta wuce kitchen ganin tukunyar a wanke ta fita waje ta leka bola taga indomien an xubar, still tayi a gun xuciyarta na mugun bugawa, kar dai ta ganta ne.... Jiki a sanyaye ta dawo cikin gidan tana adduar Allah yasa dai ko ta ganta kar ta gaya ma Mumy, Mumy da kanta ta sakko ta shiga kitchen din da ruwan gora biyu a hannunta, ta dumama ruwan sannan ta wuce sama da shi a cup don tana da kayan shayi a dakinta, Anty khadijah ta bi ta da kallo a sanyaye, shikenan kila baby ta gaya mata kenan, da sauri ta fita da wayar ta tafi can baya xata yi kira, nan daki mumy ta hada ma yan biyun tea ta basu Aliyu dai na xaune dakin yana kallon innocent kids din, baby da har sannan jikinta yake a sanyaye tana tsaye dakin ita ma. Duk da yanda Umma ta so bin Khadijah da khaleel xuwa gidan Aliyu kamar yanda khaleel yace kasa furta hakan tayi saboda kunya, Nanny ta dai raka Khadijah har bakin motar khaleel ta koma ciki, khaleel ya din ga kallon khadijah ganin yanda ta fada saboda kuka ta bude front seat a hankali ta shiga kanta a kasa, tausayinta ya ji har ransa ya tada motar ja suka bar layin, sai da suka hau saman titi a hankali yace "But you promised not to cry again Khadijah" da sauri ta kallesa da idanuwanta da suka rine tace "I didn't cry again, ai na riga na maka alkawari, wllh ban kara ba" a hankli yace "Toh naji dadi, kin dai san sunan anguwar su Aliyun koh?" Kai ta gyada masa, yace "Ina ne?" Tace "GRA" yace "Ai biyu ne Gra din, new or old?" Ta buda hannu a sanyaye alamar bata sani ba, wayarsa ce ya fara ring ganin me kiransa ya gangara gefen titi ya daga kiran tare da yin sallama, bayan sun gaisa da mai kiran nasa yace "Salman dama plss am asking... Can you connect me to a lawyer that you knw is just perfect, ni ba xaman Nigeria nake ba so I don't really knw, there is this case that I need one for... I don't want to talk about it to my family shi yasa I decided to contact you" Sai kallonsa Khadijah take ko kiftawa babu, bayan wani lkci ya shafa lallausan gashin kansa yace "Sure... Ina jira, thanks much" daga haka ya katse wayar, ya juya ya kalleta ta dauke kai da sauri, d'an shiru yyi kafin yyi murmushi yace "Frnd dina ne, xae hada ni da lawyer yanxu, I think it's better we sue him, kulasa ayi hayaniya ba yi da fa'ida, and xai iya kai yaran wani gun, so ynxu two cases xa ayi da shi, 1st na rape... Sai kuma na biyu ya dawo rana daya yana claiming yaran da bai ma san kin dau cikinsu ba saboda rashin kunya...." Ita dai Khadijah ba ta ce komai ba, yace "So bari in jira xae turo min number Wani barrister da xanyi contacting yanxu" a hankali khadijah tace "Toh nagode, Allah...." Fingers dinsa ya daura bakinsa a hankali yana kallon kwayar idonta, ba shiri ta sauke idonta tayi shiru ta samu kanta da yin murmushi, text ne ya shigo wayarsa ya dauka yana kallon number da sunan barristern da Salman ya turo masa, dialing number yyi yana ganin ya shiga ya kai kunne, Sai da aka daga sannan Khaleel yyi sallama cikin cool voice dinsa, jin an amsa yace "Barrister barka da yamma" daga daya bangaren aka amsa masa da barka dai... Khaleel yace "You are speaking with Dr Ayman, plss ina son assigning din ka ne kan wani case, hope i won't inconvenience you..." Barristern ya amsa masa da "Sure, but na baro office yanxu" Khaleel yace "Waow.. So yanxu ya xa mu yi, and we need to talk today barrister" Barristern yace "Okay mu hadu eatry yanxu don ban shiga gida ba" Khaleel yace "Maa sha Allah ina godiya for ur time barrister" sunan eatry din Barristern ya gaya masa daga haka suka yi sallama, Khaleel ya katse wayar yana kallon khadijah yace "So mu je mu samesa eatry din yanxu koh" kai kawai ta gyada masa ya tada motar ya nufi eatry din, khadijah tayi nisa tunanin da take, gaba daya ji take kamar tayi shekara da shekaru rabonta da lovely twins dinta, bata taba tunanin tana son su har haka ba sai ynxu, ta ji ta kara tsanar Aliyu fiye da komai na rayuwar ta, she hate him with passion... kallonta kawai khaleel yake bayan ya gama parking cikin babban eatry din, a hankali ya kai hannunsa kan nata, lkci daya ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, yyi kasa da murya yace "Thinking about ur twins?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta tana kallonsa a sanyaye, ya girgixa mata kai yace "You've broke the promise" da sauri ta goge idonta tayi murmushi cikin sanyin murya tace "Don Allah kayi hakuri" murmushin yyi shima ya fiddo handkerchief dinsa ya mika mata, ta karba a sanyaye tana goge idonta, kamshin handkerchief din ya kara kwantar mata da hankali, ganin bata maido masa ba ya bude motar ya fita ita ma ta fito ya rufe motar, yana gaba tana biye da shi suka shiga cikin eatry din. Khaleel ya dinga bin few mutanen da ke xaune eatry din da kallo yana tafiya a hankali, ganin he can't tell who is barrister a cikinsu ya wayarsa ya shiga kiran contact dinsa, at one end of the eatry ya ga wani mutumi da ke backing din su ya dau wayarsa dake gabansa ya kai kunne, nan khaleel ya gane shi ne, yace "Alryt na gan ka barrister" daga haka ya katse wayar ya kalli khadijah yace "Mu je" tana biye da shi har suka isa gun da barristern ke a xaune, Khaleel ya ba sa hannu suka yi musabaha, sannan ya ja kujerar da ke side din barrister ya kalli khadijah yace "Come over" ta karaso a hankali ta xauna shi kuma ya xauna yana facing barristern dake operating wayarsa, Khadijah ta dago kai a karo na farko tana kallon barristern da har lkcn idanuwansa ke kan waya yana kkrin silencing wayar, ji tayi komai nata ya tsaya ta dinga kallonsa ko kiftawa babu xuciyarta na bugawa, dai dai lkcn da shi ma ya dago manyan idanuwansa don kallon bak'in nasa yana cewa "Alryt... Barkan...." Makalewa sauran maganan nasa yayi ya dinga kallon khadijah ko kiftawa babu, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta mike ta bar wajen da sauri tana hade hanya, Mikewa yyi shi ma da sauri ya bi bayanta yana cewa "Amiraa..." Khaleel ya bi su da kallo da catlike eyes dinsa yana shafa beard dinsa, lkci daya sudais ya tsaya cak kamar wanda ya tuno wani abu, a hankali ya juyo yana kallon khaleel dake kallonsa shi ma, dawowa yyi da sauri yana girgixa kai yace "Am.. am really sorry plss, don't knw if she is ur wife, kayi hakuri.... I.." Sai kuma yyi shiru very confused, khaleel dai bai ce komai ba ya mike kamar bai son tafiya ya nufi kofar fita, Sudais ya xauna ya dafe kansa xuciyarsa na ci gaba da bugawa, Khaleel na fita can gun motarsa ya ga khadijah tana hawaye, ya iso gabanta ya tsaya yana kallonta yace "Who is he?" Tana share idonta a sanyaye tace "Sudais" shiru yyi na few seconds yana juya wristwatch din hannunsa, can ya dago kansa yana kallonta yace "So what next?" Ganin Sudais ya fito eatry din ya tsaya nesa da su yasa bata ce ma khaleel komai ba wasu hawayen suka dinga sakko mata a sanyaye tana kallon sudais, har ya iso inda suke shi ma duk a sanyaye yake, yana kallon khaleel a hankali yace "Am sorry Dr Ayman, idan matar ka ce kayi hakuri ka bani just 2mins in mata magana plss" da damuwa ya kare maganar, Khaleel ya d'an yi murmushin karfin hali sai dai bai ce komai ba, durkushewa Khadijah tayi gaban Sudais cikin rawar murya tace "Me yasa baka son ganina a rayuwar ka kuma barrister, I won't be a burden to you again, amma ko xumunci ne sai kayi da ni don Allah, me yasa ka gan ni kayi pretending you've never known me all ur life, did I deserve that? Ni nasan har karshen rayuwata baxan mance ka ba Sudais, kai din wani haske ne a rayuwata har kullum, baxan iya biyan ka abinda ka min ba but plss allow me to show appreciation always, I have missed you for many years.... I thought baxan sake ganin ka a duniya ba, sai gashi na ganka kayi shunning...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai, Sudais da idanuwansa suka kada lkci daya ya isa gun khaleel yace "Plss is she... Married??" A hankali khaleel ya girgixa masa kai, Sudais ya runtse ido ya bude yana kallonsa yace "Sorry I have to do this" yana fadin haka ya dawo ya durkusa gabanta ya rike hannunta gam cike da karfin hali yace "I know I have soo missed you Amira, I missed you... Nayi kewar ki da yawa, nayi kewar ki fiye da wanda kika min, nayi kewar twins dina, ba da son rai na na tafi na bar ku ba Amira... I have no option, kullum dake nake kwana nake tashi a rai na, but ya xan yi?? Mami na..." Kasa karasawa yyi, idonsa ya kada sosai, ita ma kuka take a hankali tana kallonsa, lkci daya yace "Where are my boys??" Tsayar da kukan da take tayi tana kallonsa a sanyaye, ganin kallon yasa gaban Sudais ya fadi sosai shi ma ya dinga kallonta, Khaleel dake rungume da hannayensa yana ta kallon dramar su yace "That's exactly what brought us here barrister" mikewa Sudais yyi da wani expression ya isa kusa da khaleel yace "What happened to them?" Khadijah ta mike tana goge idonta cikin rawar murya tace "Aliyu..." Kasa karasawa tayi, Sudais da idanuwansa suka sauya launi ya juya a hankali yana kallonta cikin husky voice yace "Aliyu did what?" Khaleel yace "Took them away from her" Sudais ya tsaya kallon khaleel mouth agape... Lkci daya yanayinsa gaba daya ya canxa, ya kalli khadijah dake hawaye yace "I will teach him the lessons of his life" khaleel ya daga kafada bai dai ce komai ba, Sudais ya kalli khadijah yace "Har yanxu gidan nan da muka je suke?" Tace "Nima ban sani ba" kallon khaleel yyi yace "We have to go to the house now..." Khaleel yace "Ohk then" har Sudais xai ce khadijah ta taho su tafi a motarsa sai kuma yyi saurin barin hakan a ransa, muryar Khaleel ya ji yana cewa "Or ko xaki je da barrister a car dinsa, xan bi bayan ku ni" shiru khadijah tayi tana wasa da fingers dinta, can ta saci kallon Sudais ta ga kallonta yake, tayi saurin dauke kanta, bata san lkcn da tace "Ohk, xan hau tricycle ku tafi kawai, xan gane gidan kila" ta gefen ido khaleel ya kalleta bai dai ce komai ba ya nufi motarsa, shi kansa Sudais bai ce komai ba, can ya shafa kansa a hankali yace "You don't worry tun da tare ku ka xo da shi, ki tafi ki hau tasa motar Amira" shiru ta yi tana kallonsa, murya can kasa yace "There are a lot of things to talk about Amira, but let settle Aliyu's case first" kai kawai ta gyada masa yace "Toh tafi kar ya tada motar" A hankali ta juya ta nufi motar Sudais ya bi ta da kallo ko kiftawa babu, tana isa xata bude motar khaleel yace "No, no you don't worry Khadijah ki tafi ku je tare da shi, we will meet there" daga haka ya fara reverse ta koma baya hankali tana kallonsa har ya fita, Jiki a sanyaye ta dawo gun sudais dake ta kallonsu, yana ganin haka ya xaga ya bude mata front seat, kanta a kasa ta shiga motar bata son ya ga hawayen idonta ya rufe motar, kafin ya xaga ya shiga maxaunin driver ta goge idonta da sauri, yana rufe side dinsa ya tada motar yyi reverse ya fita shi ma, ta madubi yake ta kallon motar khaleel dake jiran nasa yana hawa kan titi ya dau hanyar gidansu Aliyu khaleel ya bi bayansa, lkci lkci sudais ke kallon khadijah da tayi nisa tunanin da take, murya can kasa ta ji yace "Amira" da sauri ta kallesa yace "Waye Dr Ayman?" Kallonsa ta tsaya yi ta kasa cewa komai, a hankali yace "Kin yi shiru" Ta dauke idonta daga kallonsa bata ce komai ba still, hakan yasa bai sake ce mata komai ba, sai da suka yi nisa taji sanyayyan muryarsa yace "Saurayin ki ne koh?" Khadijah ta saci kallonsa still ta ki cewa komai ba, a sanyaye yace "Ki min magana pls Amira" Ajiyar xuciya ta sauke a boye, murya can kasa tace "Just as u tried ur best not to make me feel lonely in this world, shi ma abinda yake min kenan... He is also playing same role in my life." Ta gefen ido Sudais ya kalleta na few seconds kafin ya lumshe ido ya bude yace "you didn't answer my question Amira" Khadijah ta juya tana kallonsa tace "Lkcn da kake tsaka da taimako na, where you my boy friend?" Kasa ce mata komai yyi na few seconds, murya can kasa yace "Ohk.. But I am now, I want to be noe" juyawa tayi tana kallonsa da sauri, ba tare da ya kalleta ba ya gyada mata kai yace "Yea...." Sorry it's short..., but breakfast ae dama ba dayawa ake cin sa ba, very light.... 😁 Har suka isa gidansu Aliyu babu wanda yace komai cikinsu, khadijah tayi nisa tunanin da take bata ma san sun iso ba, Sudais ya fito daga motar ya xaga side dinta ya bude mata ganin bata fito ba, sai a sannan ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, tayi saurin sauke kanta ta fito daga motar ya rufe, kallon motar khaleel sudais yyi, dai dai sannan shi ma ya fito daga motarsa, Sudais ya karasa gun sa yace "I pray we meet him at home" Khaleel ya daga kafada yace "Allah ya sa" Sudais ya kalli Khadijah dake tsaye jikin motarsa sai kallon gidan take a sanyaye, gate din gidan ya nufa khaleel ya bi bayansa, bai tsaya sauraran mai gadi Usman dake tambayar sa daga ina ba ya kutsa kai ya shiga gate din ya juya yana kallonsa yace "Six years isn't that far, bai ci ka mance ni da wuri haka ba malam" khaleel ma ya shiga gidan yana kallon mai gadin murmushi dauke fuskarsa ganin yanda yyi kasake yana bin Sudais da kallo, A sanyaye Khadijah ta gaida Usman da ya xaro ido yana kallonta da mamaki yace "wannan kamar Khadijah??" Murmushi ta kirkira ta shiga cikin gidan ta bi bayan su sudais da suka nufi entrance din shiga gidan, haka kawai gabanta ya dinga faduwa tayi slowing pace dinta, Sudais ya danna bell ya ja gefe ya tsaya, bayan wani lkci aka bude kofar, Baby ce tsaye bakin kofar ta dinga kallonsa na wasu seconds kafin ta gaishesa, yana kallonta ya amsa da murmushi yace "Can we come in?" Barin bakin kofar tayi ta rasa abinda xata ce masa, ya kula she is lost don haka ya shiga parlon khaleel ya bi bayansa, tuni khadijah ta labe jikin bango jin baby ce ta bude kofar, hawaye suka shiga sakko mata ta kasa shiga parlorn, Anty khadijah dake xaune parlorn ta dinga kallon Sudais kamar me son tuno inda ta san sa, sarai ya dau fuskarta ya gane ta, a hankali yace "Hello?" Ta mike tana yamutsa fuska tace "Daga ina? Wa ku ma kuke nema?" Yana kallonta yace "Bak'i ne.... Amma nayi mamakin da baki gane ni ba Hajiya" Ta hade rai tace "Do I have any business with you da xan gane ka, malam nan gidan masu aure ne, ka fadi wa ka ke nema, ba haka nan ake shiga gidan mutane ba, from all indications ma batar hanya ku ka yi " Ya taka har gabanta ya tsaya yana mata kallon cikin ido ya fiddo ID card dinsa yace "Barrister Aliyu.... May be this will make you remember me fast" mikewa tayi da sauri tana masa wani kallo, sai kuma ta shiga kalle kalle don ta tabbatar babu kowa parlorn, ta hadiye abu da kyar tace "Wa kake nema malam, me ka sake dawowa yi gidan nan?" Jin bai ce mata komai ba sai murmushin da yake ta juya da sauri ta kalli khaleel da ya nemi kujera ya xauna yyi relaxing a kai, Murya suka ji a stairs duk suka juya, Mumy ta sakko tana kallonsu da mamaki tace "Sannun ku da xuwa" Sudais ya amsa ta karaso parlorn tace "Are you looking for Someone?" Sudais yace "Sure" juyawa yyi ya kalli bakin kofa ya ga khadijah bata shigo ba, ya juya ya koma bakin kofar, yana fita yace "Come in khadijah" Khadijah ta girgixa masa kai cikin rawar murya tace "Baxan iya ba, kuma kila ba nan ya kawo su ba" sudais yace "Trust me, kawai ki biyo ni" daga haka ya shiga parlorn ta bi sa a d'an tsorace don jin muryar Anty khadijah ya kara daga mata hankali, baby ce ta fara xaro ido ganinta lkci daya ta nufe ta da gudu tace "Imann" kasa amsa mata Khadijah tayi, Baby ta rungumeta, hakan yasa khadijah ta fashe da kuka kamar yanda baby ma ta fara kuka, tuni Anty khadijah ta rikice bakin ta na rawa tace "Me ya kawo yarinyar nan gidan nan, me ta xo yi...." Ba tare da Sudais ya kalleta ba yace "Ta xo amsan yaranta" Anty khadijah ta yo waje da ido tace "Tayi aure cikin gidan nan ne da ta xo amsan yara??" Khadijah da ke hawaye a sanyaye ta daga kai ta kalli inda mumy take ta ga kallonta take ko fiftawa babu, sunkuyar da kai tayi kamar me counting steps dinta ta isa gaban mumy hawaye na sakko mata, Mumy da idanuwanta suka kawo ruwa ta rungumeta murya can kasa tace "Khadijah.." duk wannan abun Aliyu na sama tsaye yana kallonsu, cikin rawar murya Khadijah tace "Mumy ki ce ya bani yarana na yafe masa wllh.... Intervene plss mumy" Mumy ta kasa cewa komai sai kuka, Anty khadijah sai wuri wuri ta ke da ido a parlorn ta kasa cewa komai, A hankali Aliyu ya dinga sakkowa stairs din har ya iso parlorn, Khadijah ta dinga kallonsa tana jin tsanar sa, Sudais ya taka har gabansa yana kallonsa da kyau yace "Aliyu?" Aliyu yace "Sure, any problem?" Sudais ya gyada kai yace "Fito mata da boys dinta" Aliyu ya rungume hannunsa yana kallonsa with interest yace "Bodyguards din nata har biyu ne kenan" Khaleel yyi calm smile pretending Aliyu doesn't even exist in the parlorn balle har ya ji abinda yace, shi dai yana xauna kan kujera har sannan, Sudais da idanuwansa suka sauya launi yace "You are stupid... I mean very stupid" Murmushi Aliyu yyi yace "Ku dai da ku ke biyota ne xa a kira da haka, look... ba ku da right din da xa ku dinga interfering a case dina da ita, it's almost a family issue so stay out of it....." Khadijah bata san lkcn da ta isa gabansa ba idanuwanta suka kankance don bala'i tace "Wannan da kake gani ya fi Ka right, when I say right ina nufin right, wllh ya fi ka 100% right over those children, he is almost their father, and will always remain their father, na tsane ka Aliyu, na tsane ka.... I hate you" Tana kai wa nan ta fashe da kuka sosai, Mumy ta rasa abinda xata ce ban da kuka bbu abinda take, Aliyu yace "Dama ban ce kar ki tsane ni ba Khadijah, you have all right to do so, but Iman am sorry baxan ba ki yaran nan ba, you've past through a lot, ki bar ni da su yanxu let me also play my role, ki tafi ki je ki ci gaba da rayuwar ki da bodyguards din ki, thank God you said he is almost their father not their father, ni kuma I am their biological father..." Tapping dinsa Sudais yyi xuciyarsa na tafarfasa, strictly yace "Malam kasan wanene ni kuwa? Did you knw why I am taking it gently with you, baka sani ba sure.. Then knw this, it's because of ur mother, na ga alamar she deserves some respect, don haka cikin salama ka fito da yaranta yanxu ka bata idan ba haka ba...." Aliyu ya tabe baki yana d'an murmushi yace "You do ur worst....Barrister" Bude baki Sudais yyi yana kallonsa, Khadijah ta durkushe wajen ta kara rushewa da kukan takaici, mikewa khaleel yyi yana ma Aliyu wani kallo yace "Amma kai jahili ne na ga alama, islamically baka da right over yaran nan, kai har yaran da ka samu ta hanyar zina kake alfahari da kake bragging baxa ka bada ba?? Is this how senseless you are" Yar dariya Aliyu yyi yace "U watch ur tongue gidanmu ka xo ka same ni, so you have no place to tell me nonsense, baxan bada yara ba nace" Sudais ya sake tapping dinsa yace "Good, ka saurare sammaci gobe, nasan dai baxa kayi denying kayi raping din yar mutane a court ba koh, sannan kuma don rashin kunya ka dawo kana claiming yaran da baka san da su ba, baka san da yanda aka yi Allah ya raba ta da su ba... You are wicked Aliyu" Aliyu yace "Ka kai ni gaba da kotu.... If there is any" Daga haka ya juya ya haura sama ya bar su wajen, Juyawa Sudais yyi yana wani murmushi yace "Alryt xa mu hadu a can din" daga haka ya nufi kofa yana kallon khaleel yace "Can we?" Mumy ta dakatar da shi da sauri, ya juyo yana kallonta, karasowa gabansa tayi tana goge hawayen idonta tace "I am really short of words, sai dai baxa ayi haka ba my son don Allah ku yi hakuri, xancen baxai kai kotu ba in sha Allah, sure islamically ba shi da right a kan yaran, ina mai tabbatar maku xai bata yaranta in sha Allah, and plss idan baxan bata maku lokaci ba ku bani just few out of ur time ina son mu yi magana da ku" Sudais bai ce komai ba, sai dai shi kansa yasan tun shigowarsa parlorn ya ga darajar matar shi yasa ma bai ma Aliyu haukan da yayi niyya ba, kuma albarkacin irin rikon da tayi ma khadijah truly she deserve some respect, sauke kansa yyi kawai ya koma ya xauna yace "To ina ji Ma" Mumy ta xauna ita ma tana ci gaba da share idonta ta bi parlon da kallo taga babu Anty khadijah, Baby ce kadai jingine da bango tana hawaye, a sanyaye Mumy ta fara cewa "Amma ya ku ke da Iman?" Khaleel ya kalli Sudais da ya kallo sa shi ma, ya ci gaba da operating wayarsa, Sudais ya d'an shafa beard dinsa yace "Yan uwanta ne mu" Mumy ta gyada kai, ta fara magana cikin sanyi tace "It's not as if ina supporting Aliyu don d'a na ne, plss dont quote me wrong, amma ina son ku sani it's a mistake he made kuma ba da gangan haka ya faru ba, tsautsayi ne ya gifta tsakaninsu, ni na haifesa na kuma san halinsa, ita kanta Iman xata shaide sa.... It's not ordinary hakan ya faru da shi" Sudais yace "But kinsan bayan ya sa ta tafi da aka gano tana da ciki na maido ta nan gidan?" Kallonsa mumy take da d'an mamaki, can tace "Gidan nan?" Yace "Sure?" Jikinta yyi mugun sanyi tace "Wa ku ka samu gidan?" Sudais yace "Matar da muka fara samu a parlor xuwan mu yanxu, she humiliated us and sent us away then" Kasa cewa komai mumy tayi lkci daya hawaye ya kara cika idonta da kyar tace "Kana nufin khadijah ce ta Kore ku, kuma kun gaya mata abinda ke tafe da ku?" Sudais na gyada kai yace "Kwarai, I was even thinking she is his mum then, the way she reacted...." Mumy tace "Amma kun samu Aliyun?" Girgixa mata kai yyi yace "Ce mana tayi baya kasar gaba daya" Mumy ta fashe da kuka tace "Amma Allah ya isa tsakanina da khadijah, she just ruin my family, yar uwata ce amma ko bare baxai min haka ba, yanxu tana sane da abun nan amma bata gaya min ba, she never told me anything about it da babu abinda xai hana ni nemo Iman duk inda take, greatest mistake din Aliyu shine ce mata da yayi ta tafi, kuma wllh ni shaida ce tun daga ranan Aliyu bai sake samun kwanciyar hankali ba, kuma bai taba gaya min abinda ya faru ba sai dai yace in taya sa da addu'a, gashi nan dai har yanxu ya ki yin aure" Ko kadan khadijah bata damu da abinda mumy take fada ba ku ma bai shigeta ba, Briefly Sudais ya ba ma Mumy labarin yanda rayuwa ya kasance ma khadijah bayan Aliyu yace ta tafi... Ban da kuka babu abinda Mumy take duk jikinta yyi mugun sanyi tausayin Khadijah ya cika ta, ita dai tasan da tasan abinda ya faru kenan da ta sa Aliyu ya nemo ta Duk inda take amma yyi wautan rashin gaya mata, Mumy ta mike ta isa gun khadijah ta duka gabanta tana kuka tace "Khadijah ina neman alfarmar ki yafe ma Aliyu, ko don albarkaci na forgive him plss, kadararrku ce a haka, don haka ki ta godiya ma Allah, amma kiyi hakuri kar ki bar sa a xuciyar ki" Khadijah da xuciyarta ya mata rauni ita ma tana kukan tace "Mumy ni fa na yafe masa amma yayi hakuri ya bani yaran don Allah" mikewa Mumy tayi tace "Xai baki Khadijah, ina gidan ku yake yanxu?" Khadijah ta fada mata address din, Mumy tace "Toh kiyi hakuri ku je na maki alkawarin xa mu biyo ku da yaran yanxu" shiru khadijah tayi tana kallonta xuciyarta na bugawa sai take ga kamar kawai labari mumy take mata don ta tafi, baxa su bata yaran ba, Sudais ya mike yace "Toh shkkn, Ma... Muna xuba ido sai kun xo" Mumy ta kalli khaleel a sanyaye tace "Ku yi hakuri balarabe, Allah ya ba ku lada, amma don Allah ku bar jin haushin Aliyu ba yin kansa bane, nasan xa ku yi ta mamakin jin ina cewa ba yin kansa bane kamar na shiga xuciyarsa, but plss just do consider him" Murmushi khaleel yyi ya mike yace "Bakomai Ummu, Allah ya kara girma" tace "Amin nagode" daga haka ya nufi kofa, sudais ya kara mata sallama ya bi bayan khaleel, Khadijah na biye da su a baya tana goge idonta, ta kasa kallon baby dake bakin kofa har lkcn, A hankali baby tace "Iman plss forgive me brother, ki yafe masa don Allah" hawaye na sakkowa idonta take maganar, Khadijah tayi murmushin karfin hali tace "Na yafe masa" daga haka ta fita parlorn. Sama Mumy ta wuce xuwa dakin Anty Khadijah ta ganta xaune tana bude jikin iklima ganin wasu kuraje da ke feso mata ta ko ina, Mumy tace "Khadijah, a duk xaman mu dake in har na taba cutar ki Allah ya saka maki, in kuma ke kika cuce ni Allah ya saka mani, ki tattara kayan ki da na yar ki ki bar min gidana yanxu, Allah ya bani ladan xumuncin da nayi a baya, kuma in sha Allah nasan Allah baxai kama ni da laifin xumunci ba, ki je na bar ki da Allah" mikewa Anty khadijah tayi tace "Ni yau kike kora gidan ki yau Anty fati saboda wasu shegu sun xo sun shirga maki karya?" A fusace Mumy tace "Ki fita ki ban waje, yanda kika so ganina da jikoki wanda aka samu ba ta hanyar aure ba ke ma Allah ya ba ki" Anty khadijah ta tashi tana wani murmushi tace "Sai kinyi da kin sanin daga min yatsa da kika yi fatima" daga haka ta bude siff ta dinga fiddo kayanta da na Iklima tana huci, Mumy tace "Da na sani sai dai ki gansa a kwaryar ki" daga haka ta fice daga dakin ta shiga na Aliyu, Yana xaune gefen gado ya rike kansa, duk yan biyun sun yi bacci kan gado, Mumy na kallonsa tace "Kai da babban laifi kai da fadin bakakken maganganu ko Aliyu?" Kamar xai mata kuka yace "Mumy me yasa duk hallacin da na ma khadijah a baya baxata duba na, did I deserve this, wllh da hankalinta baxan cuce ta haka ba, sannan ta dinga wani hadani da wasu karti, ni ita na sani ba su ba su ba su daina involving kansu a abinda bai shafe su...." Katse sa mumy tayi tace "Don't tell me nonsense, dole duk mai conscience idan ya ji labarinta ya so ya kwatar mata hakinta, kasan irin cutar da ka mata kuwa ka raba ta da kowa nata?" Aliyu ya rike kansa bai ce komai ba, Mumy tace "Sai ka tashi mu tafi can gidan nasu yanxu" Aliyu ya dago ya kalleta da kyar don wani Sara masa kansa ke masa yace "Mumy wllh ni baxan iya rabuwa da Iman ba, baxan iya rayuwa ba ita ba, my life has being miserable tun da na sa ta bar gidan nan, Don Allah ki rokar min ita ta amince mu yi aure, I don't think xan iya auren wata ya mace a duniya idan ba ita ba, plsss even for the sake of this innocent children ta amince mu yi aure" Mumy tace "yanxu kuma??" Tashi yyi Yace "Wllh Mumy idan tace baxata aure ni ba, I promise to go away with this kids baxa ta sake ganinsu ba har karshen rayuwarta, ai da can ba da su take rayuwa ba" Mumy na masa wani kallo tace "Na ga alamar ka fara xarewa, da yaran xaka mata baraxanar ta aure ka kenan, a hakan xata amince ta aure kake tunani, kasan ko kotu aka je yaran nan ba naka bane Aliyu, ba ta hanyar aure ku ka same su ba don haka ka janye wannan baxan maganar da kake yi, kuma kar ka bata min rai" Wani murmushi yyi bai dai ce komai ba, Jikin mumy yyi sanyi ta bi sa da kallo, tsoronta kar ya tafi da su kamar yanda yace, da kyar tace "Ka tashi mu je gidan na su, nasan even for my sake ma xata amince maka" daga haka ta fita dakin. Sai kusan magrib suka isa address da khadijah ta ba mumy, Aliyu ke driving din, Sai baby a gaba, mumy kuma na xaune back seat da yan biyun, tana rungume da little Sudais da jikinsa yyi xafi sosai duk da allurorin da Aliyu yyi masa, kai kana ganin yaran kasan hankalinsu ya kwanta da mumy, Shureim na kallonta yace "Are we going to visit you again mama?" Tana murmushi ta shafa kansa tace "Sure sweetheart" parking Aliyu yyi kusa da gidan ya juya yana kallon Mumy, Mumy tace "Ina jin nan ne" Shureim yace "Ehh mama nan ne gidanmu" Mumy tace "baby sauka ki kwankwasa gate din" Baby ta sauka tayi yanda Mumy tace, Mumy ta sauko tare da boys din, Aliyu ya fito shi ma ya dau sudais, bayan wani lkci Nanny ta bude gate din, da gudu Shureim ya tafi ya rungumeta, Nanny ta ji dadin ganin su sosai ta dinga yi ma su Mumy sannu da xuwa, Kallo daya tayi ma Aliyu ta gane shi ne uban yan biyun, ta yi masu iso har parlor, Sannan ta shiga daki don Umma na ciki tana sallah, Khadijah ma tasan sallan take yi, Umma ta sa Hijab ta fito bayan Nanny ta sanar mata bakin da suka yi, Har lkcn Sudais na jikin Aliyu, Shureim dake jikin Mumy ya tafi da gudu ya rungume Umma yace "I miss you Mumy na" Umma ta xauna tana murmushi ta ja sa jiki sannan suka shiga gaisawa da su Mumy, jikin mumy yyi sanyi sosai don bata taba xaton xata tarbesu da kyau haka ba, shi dai Aliyu ya kasa daga kai ya kalleta, shi ma bai yi xaton haka ba, Khadijah dake xaune kan darduma lkci daya taji ranta yyi mugun bacci jin yanda Umma ta sake masu, jin muryar yaranta yasa ta lumshe idonta, amma ta ki fitowa parlor ta same su don bata ma son ganin Aliyu, Mumy na kallon Umma tace "Ina Khadijar Hajiya?" Umma ta kalli Nanny dake tsaye tace "kira Khadijah" sosai Khadijah ta dake xuciyarta ta mike ta bi bayan Nanny kan ta a kasa, har ta shigo parlorn bata yarda ta dago kanta ba ta gaida Mumy, Aliyu sai kallonta yake ko kiftawa babu, Shureim ya nufeta ya xauna jikinta yace "Anty mun dawo, I like the house so much..." Khadijah ta ki kallon yaron amma har ranta bata ji dadin abinda yace ba, ita fa in dan ta ita ne yaranta basu da uba, ita dai tasan Allah ne ya bata su, kuma tana gode masa, fuskarta daure ta dago tana satan kallon Aliyu dake ta kallonta suka hada ido ta masa wani harara ta dauke kai, lkci daya ta mike ta ja hannun Shureim suka bar parlorn, tana xaunawa kan gado ta jawo yaron gabanta tana kallonsa da kyau tace "Did that stranger tell you anything?" Shiru yyi da farko kafin yace "But he is not a stranger Anty, this is the 4th time we are meeting with him" ta xaro ido xuciyarta na bugawa tace "Where and where" yace "Anty ranan nan da muka kusa yin accident, that i told you he made sure we where fine...." Gabanta yayi mugun faduwa tace "And where?" Yace "We met again at the airport da xa mu je holiday a UK, shi ma xai je can..." Ta runtse ido xuciyarta na tafarfasa tace "And where????" Yace "Yesterday at the market, because sudais don't like him shine ya gudu ya shiga titi babban mota ya buge sa" ta fixgo yaron tana huci tace "Shi ya janyo mota ya buge Sudais?" Kai ya gyada mata ta jefa masa wani kallo tace "And you are telling me he is kind yana neman kashe maka brother, daga yau ka sake yarda ko kallon ka yayi sai ya xuke maka jinin jikin ka gaba daya, baka san shi vampire bane" buda baki yyi yana kallonta da surprise, can yace "Me yasa bai shanye mana ba a gidansu?? Anty he is kind fa, ni dai I like him, he was with us....." Tsawa tayi masa ta turasa har sai da ya kusa faduwa hawaye cike idonta tace "Xan fasa maka kai... Nace stay away from him, you have no business with that wicked man" Shiru yyi a tsorace yana kallonta, a hankali yace "But he even told us he is our father not barrister as you told us...." Mikewa tayi hankali tashe xuciyarta na mugun bugawa tace "He is a liar... Karya yake maka barrister ne babanka, ba abinda ya hada mu da shi" cikin rawar murya tace "Tafi ka kamo hannun sudais ku xo nan yanxun nan" da sauri ya fita, yana isa kusa da Aliyu yace "Uncle, Anty tace I shud call my brother now" shiru yyi yana kallon yaran, haka ma Mumy da Umma, Aliyu yayi kasa da kai a hankali yace "Umma ki d'an mata magana ta bari in je da shi, he is sick dole xa mu koma asibiti" a fusace Khadijah dake jin sa ta fito tace "Ina ruwanka da rashin lafiyarsa? Ka bani yarona ai nasan hanyar asibiti, give me my son" tsawa Umma tayi mata ta mike tace "Tafi ki bar parlorn nan kar in bata maki rai, shashasha" ta fashe da kuka ta juya da sauri ta bar wajen, Umma dake kallonsa a sanyaye tace "Ka je da shi, Amma ko xuwa gobe sai ka kawo shi" a sanyaye yace "Na gode Umma" su mumy basu bar gidan ba sai kusan karfe taran dare bayan mumy ta mata bayanin duk abinda ya faru, Umma ta raka su har bakin mota jikinta a sanyaye. Umma na dawowa cikin gidan ta tafi daki gun Khadijah a daki, xaune ta sameta kasa ta hade kai da gwiwa tana kukan takaici, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Amma Khadijah ban taba xaton haka daga gare ki ba, da ilimin ki bai kamata kiyi abinda kika yi ba, ina ce ko ba komai xai ci albarkacin mahaifiyarsa, ke da kanki kin bani labarin irin abubuwan da tayi maki while with them, me yasa xa ki mance hakan da wuri, don me laifin d'an ta xai shafeta, me yasa ko don ita baxa ki raga masa ba, ni ban ce lallai sai kin kulasa ba, Amma for the sake of his mum...." Cikin kuka tace "Umma kiyi hakuri, but I have nothing to do with Aliyu and his family again, I will pretend ban taba rayuwa tare da su ba, don Allah su rabu da ni su bar min yarana su je na yafe masu, ina jin kunyar mahaifiyar sa shi yasa nake raga masa, only me knew wat I passed through in life, ni kadai nasan abubuwan da na fuskanta a rayuwa shekarun baya, Umma na sha wahala, na ji na tsani rayuwar, ban taba sanin xan yi surviving ba ummata, da ba don sudais ba da ban san me xai sameni ba, me yasa rana tsaka Aliyu xai dawo rayuwata yana min gadara a kan yaran da bai ma san da su ba, why Umma??" Umma ta xauna duk jikinta yyi sanyi tace "Ni ba nace ki yarda da Aliyu bane Khadijah, amma kiyi hakuri ko domin mahaifiyarsa ki yafe masa, ki mance past din ki" tana kallon umma da jajayen idanuwanta tace "Na yafe masa amma kar ya sake cewa shi ne uban yarana, kuma da kai na xan shirya in tafi in dauko yarona gidansu gobe, it's better Barrister sudais ya raba ni da su then ace Aliyu, saboda shi ne ya sha wahalar su kuma shi ya koya min sonsu ba don shi ba kilan da sun mutu yanxu" shiru Umma tayi ta kasa cewa komai tana kallonta, mikewa khadijah tayi ta hau saman gado ta kwanta, Umma ta mike a sanyaye ta kama hannun Shureim dake ta kallon uwar tasa ta fita da shi. Mikewa xaune khadijah tayi jin wayarta na ring ta dau wayar, ganin khaleel ne ta daga ta kai kunne tayi masa sallama cikin sanyin murya, Daga daya bangaren ya amsa a hankali yace "Sun kawo maki yaran Khadijah?" Ta fashe da kukan takaici tace "they brought just one, Shureim kawai suka kawo, ya tafi da sudais" Khaleel yace "Saboda me?" Cikin kuka tace "Wai xai kai sa asibiti, I don't knw ko meye damuwarsa da ciwonsa, ni dai ya rabu da yarana, ya kyale min su" Khaleel yyi shiru na wani lkci kafin yace "Kar ki damu xa su dawo maki shi, bana son ki kara sa ma kanki damuwa Khadijah, and plss because of his mother let take everything easy, kar ma ki sake kulasa, sure baxata bari ya dauke maki kids ba, kin san ana barin halak ko don kunya, am sure soon xa a dawo maki da little Sudais kin ji" kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta, yace "Sleep without worries plss Khadijah" a hankali tace "Toh nagode" daga haka ya katse wayar, ta koma ta kwanta ta lumshe ido, cikin dare misalin karfe biyu Khadijah na xaune kan darduma bayan ta idar da slh taga wayarta yyi haske alamar shigowar text, ta mike a hankali ta isa gun wayar, message din barrister Sudais ta gani ta dauka ta bude tana kallon content din, "Dear am sorry I didn't call, na shiga gida ne da wuri jiya, but mun yi communicating da Dr Ayman, he told me everything, you don't worry xa a dawo maki da little sudais soon, gobe da safe xan xo in sha Allah, sleep without thought plss" tabe baki tayi ta ajiye wayar ta koma kan darduma ta xauna, har kusan asuba Khadijah bata runtsa ba, damuwa yayi mata yawa sosai ga yawan faduwar gaba da take ta ji, karfe hudu saura umma ta shigo dakin da Shureim ganin khadijah kan darduma ta isa kusa da ita da yaron tace "Gashi ya ki bacci, his temperature is high but na basa paracetamol, wai xai xo wajen ki" xaunawa Shureim yyi kusa da ita yana kallonta yace "Anty yaushe sudais xai dawo, I want to see him" Umma tace "Au abinda ke damun ka kenan" murmushii tayi ta juya ta fita tace "ka gamu da aiki kam" Khadijah ta jawo sa jikinta a hankali, taji jikin nasa ya dau xafi sosai, dago kansa tayi tace "Are you feeling pain anywhere?" Ya girgixa mata kai yace "I want to go to my brother" ta rungume sa sosai tace "Gobe xai dawo ka ji" ba a dau lkci ba yaron yayi bacci a jikinta ta mike ta daukesa ta kwantar kan gado, ta koma ta xauna tana jiran lkcn sllhn asuba. Washegari da safe Mumy na xaune kusa da Sudais da Aliyu ke sa ma drip da damuwa tace "Abuturrab ko xa ku je asibiti dai a kara duba sa, he is suffering slowly..." Aliyu ya kalleta yace "He will be okay mum, na dubasa babu wani matsala, a hankali xai dinga recovering, and it looks as if he is missing his twin, tun jiya yake ta tambayar sa" Tace "Toh ko xa a mayar da shi gidan ne?" Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "Mumy bari ya kara samun lafiya" Baby ce ta shigo da wayar Mumy dake ring ta mika mata ta fita, Mumy ta karba ta daga kiran, shiru ta d'an fara yi kafin tace "Ehh ni ce, who is on the line" ganin Mumy bata sake cewa komai ba sai shock da ya bayyana a fusakarta, a hankali afterward ta sauke wayar daga kunnenta tana kallon screen din, Aliyu dake kallonta yace "Waye mumy? Me ya faru?" Kallonsa tayi a sanyaye tace "Ka sake kiransu kilan ban ji da kyau ba ne" Aliyu ya amshi wayar ya kira number, bayan wani lkci aka dauka, abinda aka fadi ma Mumy aka sake maimaita masa, ya d'an bude ido shi ma lkci daya yace "Subhanallah, to ga mu nan xuwa, mun gode" daga haka ya katse wayar yace "Mumy wai Anty khadijah na asibiti..." A hankali mumy tace "Toh sai ku je, ni kam baxan je ba" ya bata fuska yace "No plss mumy kar ki ce haka, tunda har aka kira ki mu je kawai, baxa a biye ta halinta ba, kuma ai ba a canxa ma tuwo suna she still remain ur sister" da kyar Aliyu yyi convincing Mumy ta yarda xa ta je. Umma tayi pecking din goshin Shureim har sannan jikinsa da dumi tana shafa kansa tace "You behave your self kaji my boy, kuma ban da fada a gidan" Kai ya gyada mata, Khadijah ta kama hannunsa suka fita parlorn, khaleel na jingine jikin motarsa har suka iso inda yake, ya duka yana kallon kyakkyawan yaran a hankali yace "How are you Darling" murmushi Shureim yyi yace "Am fine uncle" mikewa khaleel yyi ya kama hannunsa yana kallon khadijah yace "Toh sai mun yi waya..." murmushi tayi tana bin sa da kallo tace "Nagode, byee" daga haka ya bude front seat ya saka Shureim ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya bar layin, Khadijah ta juya to koma ciki feeling relieved. Shureim na wasa da wayar khaleel yace "Uncle baxan sake ganin Sudais ba?" Khaleel ya d'an buda ido ya kalllesa yace "In ji wa ya gaya maka haka?" Ya langwabar da kai bai ce komai ba, duk sai ya basa tausayi, a hankali Khaleel ya shafa kansa yace "Xai dawo soon ka ji my boy" har khaleel ya isa gida Shureim bai sake cewa komai ba, gida ne mai girman gaske, Shureim ya wara ido yana bin makeken compound din da kallo yace "Uncle is this ur home" khaleel yyi murmushi ya gyada masa kai bai dai ce komai ba, yaron yace "It's big" parking khaleel yyi a parking space ya fito ya xaga ya sakko da yaron sannan ya nufi entrance na babban parlorn gidan yana rike da hannunsa, yara ne da baxa su wuce Shureim din ba su uku duk maxa kusan duk kamanninsu na larabawa suna wasa parlorn da puzzles, suna ganin khaleel suka yo kansa da gudu suka rungume sa suna gaishesa da larabci, ko wannensu cike da murnan ganinsa, Dukawa yyi duk ya shafa kansa yana murmushi yace "I brought you a new friend, Shureim by name" Murmushi Shureim yyi yana kallonsu yace "Hey" sallama suka yi masa gaba daya, khaleel yyi dariya sosai, ya mike ya kama hannun Shureim suka wuce sama yana waigo yaran, bedroom din Ummun sa ya tafi da shi, Wata balarabiya ce da baxata haura sittin ba xaune dakin tana waya da halshan larabci, ya xauna gefen makeken gadon ta, ya dau Shureim ma ya ajiye sa gefensa, tana gama wayar ta juya tana kallon khaleel tace "Sai yanxu" gaisheta yayi ta amsa da murmushi ta na kallon shureim tace "Ina ka samo mana yaro" Ya shafa kai a hankali yace "Ummu... Khadijah da nake baki labari, he is her son Shureim" Umma tace "Maa sha Allah, xo in ganka sweetheart" Shureim ya sauka kan gadon ya tafi gunta ta jawo sa ta rungume sa tace "Ya ummun ka fa?" Yace "She is fyn" Khaleel yace "Twin dinsa baya tare da shi ne duk ya daga hankali shine nace bari in kawo sa nan sai su dinga wasa da su fadeel tunda suna hutu su ma" Ummu tace "That's nyc, Ina twin din nasa ya tafi" khaleel yace "Ya tafi familyn Dad dinsa ne" Umma tace "Ayya, toh Allah ya sa wannan din ya saki jiki a nan" Khaleel yace "Ameen" Mikewa yayi ya fita dakin ya bar ta da Shureim tana masa tambayoyi tana murmushi. Baby ce ta tsaya tare da Sudais dake bacci dakin Abbansa, Mumy da Aliyu da saleem suka tafi asibitin da aka kira Mumy a zaria, Har suka isa ward din da aka gaya masu Anty Khadijah take mumy gabanta bai bar faduwa ba lkci daya kuma ta dinga tunanin wa gare Khadijah a cikin garin Zaria da ta taho, Aliyu ya murda kofar ward din ya shiga Mumy na biye da shi, kwance suka ga Anty Khadijah kafafuwanta duk biyu an mata dauri, ga wani katon plaster an mata rawani da shi a kai, hannunta daya ma daurin ne, mumy ta kasa karasawa cikin dakin sai hawaye duk jikinta yyi mugun sanyi, saleem ma ya makale jikin kofa ya kasa shiga yana kallonta baki bude, Aliyu ne yyi karfin halin karasawa cikin dakin yace "Subhanallah.... Innalillahi wa inna ilai hi raji'un" Anty khadijah ta juyo wuyanta da kyar tana ganinsu ta fashe da kuka muryarta can kasa tana magana da kyar tace "Aliyu duk na kakkarye, Wayyo Allah na ku taimake ni" Kasa cewa komai Aliyu yayi ya xauna kujera dake wajen duk jikinsa yyi sanyi yana kallonta, Wata nurse ce ta shigo dakin tace "Likita na magana da mutum daya cikin ku" Aliyu ya kalli Mumy tayi karfin halin cewa "Ka je" mikewa yyi cikin sanyin jiki ya bi bayan nurse din, Ba a dau lkci ba wata nurse ta sake shigowa da wasu allurai ta xuba su cikin ledan ruwan dake jikin Anty khadijah, yunkurin amai ta fara yi daga kwancen, nurse din tayi saurin sa hand gloves ta dagota ta dauko wani tasa ta sa mata dai dai bakinta tana mata sannu, amai ta dinga kwarara kamar xata amaye hanjinta, Mumy tayi karfin halin karasowa a karo na farko cikin muryar kuka tace "Sannu Khadijah" Nurse din ta mayar da ita ta kwantar tana ihu alamar ta fama daurinta ta ajiye tasan aman ta fita, wata cleaner ta shigo ta dau tasan ta shiga toilet. Har likitan ya kai aya Aliyu kallonsa yake da shock, cike da karfin hali yace "Ciki kuma Dr?" Likitan ya mika masa result din yace "In sha Allah, gashi nan har wata uku" kasa cewa komai yyi ya mike ya bar office din rike da sakamakon, tun bayan da suka yi hatsarin jiya da daddare da aka taho da ita asibiti ga karaya ta ko ina, ga amai da take ta kwarara ya sa likitan ya sa a mata gwajin ciki don a san irin treatment din da xa a mata, ai ko result na fitowa ya ga cikin ne da ita har wata uku, Aliyu ya share xufar dake keto masa ya shigo ward din yana kallon mumy dake ta goge hawaye tana kallon yar uwar tata, mika mata result din hannunsa yyi ya jingina da bango duk jikinsa a sanyaye. Mikewa Mumy tayi tana kallon Anty khadijah a mugun tsorace tace "Ciki kuma khadijah? Ciki fa??" Da kyar Anty khadijah ta juyo kai tana kallon Mumy, Aliyu ya juya ya fice daga ward din, mumy ta fashe da kuka tana kallonta tace "Ciki fa Khadijah, innalillahi wa inna ilai hi raji'un, turr da halin ki Khadijah, tsofe tsofe dake khadijah" Mumy ta xauna kan kujera ta dafe kai tana kukan abun kunyan da Anty khadijah ta dauko masu, Aliyu ko minti biyar bai kara a cikin asibitin ba ya bar ma saleem makullin motarsa ya hau motar haya xuwa Kaduna, don gaba daya hankalinsa na sudais, har ya isa gida kuma yana mamakin Anty khadijah, wai ciki... jiki a sanyaye ya wuce sama xuwa bedroom dinsa, har sannan baby na xaune dakin kusa da sudais dake bacci, tana ganinsa ta mike tace "Yayanmu ya jikin Anty khadijahn?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Da sauki" daga haka ya kai hannu goshin sudais ya ji babu xafi kamar daxu da safe, ya kalli baby yace "Bai tashi ba tun daxu?" Ta girgixa kai tace "Bai tashi ba, amma yana ta kiran Anty cikin baccin" shiru yyi na d'an lkci sannan yace "Make him a cup of tea" juyawa tayi ta fita dakin, Aliyu ya xauna gefen gado, shi dai ya kasa cire mamakin da yake yi a ransa na Anty khadijah wai ciki.... Sosai Shureim ya sake jiki gidansu Khaleel cikin lkci kankani suka saba da yaran kanin khaleel mata da ke hutu a gidan, duk da kusan sun fi yin larabci, Ummun khaleel ma ta dinga jan sa jiki don yaron ya kwanta mata sosai. Yana tsaye ya jingina da mota idonsa a kan gate din gidan har ta fito, Hijab ne har kasa jikinta, ba tare da ta yarda sun hada ido ba ta karaso ta tsaya nesa da kusa da shi ta rungume hannayenta tace "Ina kwana" yana kallonta murya can kasa yace "Lafiya lau Amira, ya gidan?" Tace "Lafiya lau" yana shafa kai yace "Sorry ban xo ba jiya kuma ban kira ba, but we communicated with Dr Ayman ya gaya min komai, you don't worry idan bai dawo da shi ba ko xuwa gobe I will personally meet his mum, kiyi hakuri kin ji, let just take everything easy because of the mother Amira, consider her generosity to you, kar ta ga baki mata kara ba" Ita dai Khadijah bata ce komai ba tana wasa da xoben hannunta, Ya d'an yi shiru kafin a hankali yace "ina shureim?" tace "Yana gidansu Dr Ayman" kallonta ya dinga yi yace "Me yake can?" Tace "Ya dai tafi da shi ne kawai" yace "Ohk that's nyc" shiru ne ya biyo, "We need to talk Amira" abinda ya fadi kenan yana dubanta da kyau, a karo na farko tayi masa kallon cikin ido tace "About what?" Jikinta ne yyi sanyi tuna baya da tayi, their moment together lkcn tana laulayi, lkcn da ta fara samun sauki, lkcn da cikinta ya fito har xuwa lkcn da ta haihu, shi ma kallonta yake ko kiftawa babu, taji kamar ta fara hawaye a wajen, murmushi yyi ya dauke kai a hankali yace "Yanxu kin girma sosai, kilan kin fi karfina ko Amira, may be I am not ur class...." Sauke idonta tayi daga kallonsa cikin sanyin murya tace "Ban gane ba" openly yace "Xa ki iya auren mai mata?" Bata kallesa ba bata kuma ce komai ba amma sai da gabanta ya fad, wani murmushin ya kuma yi yace "That says it all, you are not interested" sai a sannan ta daga kai ta kallesa tayi murmushin karfin hali ita ma tace "I know marrying u is not even enough in biyaka abinda ka min a rayuwa barrister, but..." Ya katse ta da sauri yace "But what?" A hankali kuma a sanyaye tace "It looks as if you are afraid of ur wife, ba lallai ta bari ka kara aure ba..." lkci daya mood dinsa ya canxa yace "Says who Amira?" Ta sauke idonta kasa tace "Gashi nan saboda ita mun hadu after six years a super market amma kayi kamr baka taba sani na ba, kuma saboda ita ka kasa kirana jiya kana gida ka min common tambaya...." Ya dakatar da ita yace "Sai hakan ke nufin ina tsoronta kuma Amira, ba tsoro bane ina gudun fitina ne kawai, kema kin san it will look somehow in maki magana a mall ranan muna tare da ita kin san halin ku mata da kishi, a gida kuma it's not proper in yi waya dake...." Khadijah tayi murmushi tace "Upon ur profession? Ta mance wa ta aura ne?" Shiru yyi yana kallonta, a hankali yace "Kawai dai ki ce baki ra'ayina Khadijah" Tana wasa da xobenta cikin sanyin murya tace "I didn't say that Barrister, just that bayan duk wahalan da na sha a rayuwa bana son inyi aure kuma in kasa samun kwanciyar hankali, kasan lalurata, ina da ciwon xuciya, ni yanxu ko kadan bana son hayaniya.... Ban san me yasa ba" tana magana ne hawaye cike idonta, "Ban da haka bani da abinda xan iya biyanka da shi a duniya barrister da ya wuce in amince da auren ka a yanxu, but am afraid..." hawaye na sakko mata ta kai karshe, Lumshe ido yyi na few seconds kafin ya bude ya ga kallonsa take, da sauri ta sunkuyar da kanta yace "Kar ki damu da matata Amira, beside ba gida daya xa ku xauna ba" ita dai bata ce komai ba amma gaba daya hankalinta a lkcn ya tafi kan khaleel..., lkci daya jikinta yyi mugun sanyi, A hankali ta ji yace "Plss Amira..." Ta daga kai a sanyaye tana kallonsa. Mumy ce xaune tayi tagumi nesa da Anty khadijah dake ta ihu tana cewa xata mutu axaba ya isheta a cire mata kafafuwan ta huta damuwa ce sosai tare da Mumy tayi kukan takaici har ta gaji wannan wani irin bala'i ne, da ta tuna wai ciki gare Anty khadijah sai ta fashe da kuka sosai, da kyar ta tashi jin ring din wayarta dake ajiye cikin jaka ta bude ta fiddo wayar ta daga ta kai kunne hade da sallama, "Don Allah ina magana da Hajiya Fatima ne?" Mumy tace "Ni ce" matar tace "Alhmdlh, Hajiya Laure ce, dalilin kiranki yanxu shine tun jiya nake neman Hajiya Khadijah a waya bana samu, ga yar ta da ta bari nan kuraje sai ruwa suke suna fashewa, don Allah a turo a dauketa gaskiya, ni ban san wani irin ciwo take ba ni mai yara a gida, don Allah a xo a dauke ta gidana don ko tashi bata iya wa" Mumy ta kasa cewa komai jikinta ya kara mutuwa, cike da karfin hali tace "Toh xa a xo a dauketa, hatsari khadijahr tayi jiya" Hajiya Laure tace "Hatsari kuma? Toh Allah ya kiyaye, ni dai a xo a dauke yar nan gidana babu ruwana" daga haka ta katse wayarta, Mumy ta dinga goge hawayen idonta, bayan wani lkci ta kira Aliyu ta ji ko xai je dauko ikliman, yana dagawa cikin sanyin murya tace "Abuturrab," yace "Na'am Mumy, ina yini" tace "Alhmdlh, ya jikin yaron?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Muna Asibiti fa Mumy" tace "Asibiti kuma, jikin ya ki ne?" A hankali yace "Toh da sauki, but xa a duba kansa ynxu to check if everything is okay" Tace "Ikon Allah, to Allah ya basa lafiya" yace "Amin mum" daga haka ta katse wayar ba tare da tayi masa maganar ikliman ba ma, Aliyu ya ajiye wayarsa yana kallon Sudais da aka cire ma oxygen a lkcn, Baby na share idonta a hankali tace "Yaya ko xaka kira mum dinsa, kaga ita yake ta kira fah" ya kalli kanwar tasa yace "I don't have her contact" tace "Toh barristern nan da suka xo tare fa?" Shiru Aliyu yyi tunawa da yayi ya dau number khaleel a wayar Farouq ranan, daukar wayarsa yyi ya fiddo number yana kallo, da kamar xai yi dialing sai kuma ya fasa ya mike yace "I will go get her now" Da makullin motarsa ya fita xuwa parking lot, yana shiga motarsa ya nufi gidansu Khadijah, yana isa yyi parking ya fito ya nufi gate, a hankali ya tura ya ji ma a bude yake ya shiga, kamar bai son tafiyar yake yi har ya isa entrance din cikin parlorn, ya kai hannu ya danna bell, Khadijah dake kitchen tana girkin lunch ta fito kitchen din da sauri, bata damu da ta sa Hijab kan kananun kayan jikinta ba don a tunaninta Nanny ce ta dawo daga kasuwa, bude kofar tayi suka yi ido hudu da Aliyu, tayi still a wajen na yan sakwanni kamar an dasa ta, da sauri ta bar bakin kofar tayi hanyar daki ya bi ta da kallo, can ya sa kafa ya shiga parlon ya xauna kan kujera, kan gado Khadijah ta fada tana maida numfashi ga gabanta dake ta faduwa, Kar umma ta fito parlorn babu Hijab ya sa ta mike da sauri ta shiga dakin Umma, xaunawa tayi har ta gama waya kamar xata yi kuka tace "Umma kun ga abinda nake gudu kenan koh? Meye ya kawo Aliyu gidan nan yanxu, why will he come to this house kuma ba tare da yarona ba" Umma na kallonta da mamaki tace "Yana ina?" Fuska daure tace "Yana parlor mana" Umma tayi shiru, sai kuma tace "Toh ai sai ki tsaya ki ji me ya kawo sa koh" Khadijah ta kara hade rai sosai tace "Umma ni idan xan koma UK da yan biyun xan tafi gaba..." Shiru tayi a sanyaye tunawa da tayi ai a can ma ta fara jam da Aliyu, Umma tace "Ki tashi kije ki ji abinda ke tafe da shi, ni kar ki min fitsara" rai ba dadi Khadijah ta mike ta fita, labewa tayi da bango a corridor tana kallonsa, the mouth, the nose, the eyes, worst of all the face... Sosai jikinta yyi mugun sanyi, wayarsa kawai yake dannawa idonsa a kai, kamar ance ya waiga suka hada ido gabanta yayi mugun faduwa, tayi saurin dauke kai, shi ma hakan yayi, ta hade rai bbu yabo babu fallasa tace "Me ka xo yi gidan nan malam?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ur son, yana son ganin ki" Bata san lkcn da ta fito parlorn ba ta taho gabansa tace "Yana ina?" Ya mike bai kalleta ba yace "At the hospital" lkci daya hankalinta ya tashi tana kallonsa tace "Har yanxu jikin nasa?" Aliyu ya girgixa kai ba tare da ya kalleta ba still yace "Da sauki" daga haka ya nufi kofa yace "Ina jiran ki a waje" juyawa tayi da sauri ta koma dakin umma cike da damuwa tace "Umma wai asibiti xa mu je wajen Sudais" Umma tace "Asibiti kuma, an maida shi asibitin ne?" Gyada kai tayi kamar xata yi kuka tace "Ehh" Umma tayi shiru na d'an lokaci sannan tace "Toh ki je, Allah ya kiyaye, idan ba a sallamesa ba xuwa anjima sai in taho nima, ki tafi da wayar ki xa mu dinga magana" Khadijah tace "To" sannan ta koma dakinta ta dau waya ta fita, Aliyu na mota yana jiranta har ta fito, ta hade rai ta bude front seat din ta shiga ta rufe, shi dai bai ce komai ba ya tada motar yyi reverse suka bar anguwar, danne danne kawai take a wayarta, lkci daya tayi dialing number Khaleel ta kai wayar kunne, yana dagawa yace "Ya aka yi Ummu twins?" Ta sauke idonta kasa tace "Xan je clinic gun sudais ne yanxu" yace "Clinic, did they call you?" Ta gyada kai a hankali tace "Ehh" yace "Ohk toh Allah ya tsare, ke da waye?" A takaice tace "Driver!" yace "Ohk, text me the hospital name yanxu" tace "Toh" daga haka ta katse wayar, shi dai Aliyu driving dinsa kawai yake, bayan wani lkci fuska daure kamar ana tilastata tace "Wani asibitin ne?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ban sani ba" wani kallo ta dinga masa ganin ko waigo wa bai yi ba tayi tsaki, har suka isa asibitin babu wanda yace komai cikinsu, bayan yyi parking ya bude motar ya fita ya nufi entrance din clinic din, sosai ta ji ranta ya baci ta fito motar ta rufe tana hararansa, ba tare da ya juyo ba yyi locking motar da makullin hannunsa, sai da ta karanta sunan clinic din sannan ta bi bayansa tana turo baki, tuni ya shige ward kafin ta shigo reception, ta dinga kalle kalle ta rasa inda ya shiga, gaishe da nurses dake wajen tayi, wata nurse tace "Tare ku ke da Dr Aliyu?" Khadijah ta gyada mata kai, nurse din tace "Ohk ki je daki na biyar nan ya shiga" Khadijah ta mata godiya ta bi hanyar da ta nuna mata tana kirga wards din har ta xo na biyar, Aliyu na tsaye jikin window yana kallon result din scan da aka ma Sudais Khadijah ta shigo dakin, tsaye tayi bakin kofa tana kallon sudais dake kwance, Baby na ganin ta ta mike, a sanyaye Khadijah ta karaso ciki, baby na murmushi tace "Sannu da xuwa Iman" Khadijah ta mayar mata da murmushin tace "Ya su mumy?" Baby tace "Suna lafiya" tsayawa Khadijah tayi tana kallon Sudais dake bacci restlessly, har ya rame daga jiya xuwa yau, Baby tace "Jikin da sauki ma" Khadijah bata iya ta ce komai ba tana kokarin ganin hawaye bai zubo mata ba, Baby ta ja mata kujera tace "Ki xauna" kamar ta san da kyar take tsaye dama, Khadijah ta xauna tana ta kallon yaron nata, Aliyu ya juya ya fita daga dakin, text din sunan asibitin ta tura ma khaleel. Ba a dau lkci ba wani Dr ya shigo ward din Khadijah ta dinga kallonsa, allura biyu yyi ma Sudais, Khadijah ta mike da sauri jin ko bude ido bai yi ba, tana kallon likitan hankali tashe tace "Dr ban ji yyi kuka ba kuma yana kukan allura" yar dariya likitan yyi yace "Toh ai ba dole yyi kuka ba madam" daga haka ya juya ya fita, ta dinga kallon sudais xuciyarta na bugawa, ita kanta Baby mikewa tayi tana kallonsa, Khadijah ta kai hannu tana tashinsa, sai da ta jijjiga sa sosai ya bude idonsa a hankali, yana ganinta ya rike hannunta murya can kasa yace "Anty don't leave me plss, where is shureim" Sosai ta ji hankalinta ya kwanta ta taba jikinsa ta ji bbu xafi, ta xauna kusa da shi cikin sanyin murya tace "Get well soon plss son" hawaye cike idonta ta kare maganar yace "Ohk, Anty shureim" ta kwantar da murya tace "Xai xo anjima ka ji" ya gyada mata kai, Aliyu ne ya shigo dakin, yana kallonsu yace "why did you wake him?" Ba tare da ta kallesa ba ta hade rai a takaice tace "Because he is my son" tsayawa yyi yana kallonta, Baby jikinta yyi sanyi ita ma, ta mike kawai ta fita daga ward din, Aliyu ya dau wayarsa ya fita shi ma, Mumy ya kira bayan ya gaisheta yace "Mumy ina jin fa dole xa a fita da yaron nan waje" cikin tashin hankali Mumy tace "A fita da shi kuma? Jikin ya ki ne har yanxu Abuturrab" yace "Akwai matsala ne scan da aka yi masa, just pray for him mumy" Mumy ta kasa cewa komai Aliyu ya katse wayar, Khadijah sai kallon sudais take da ya kara rufe ido kamar mai bacci, ta dau waya ta kira khaleel, bugu biyu ya dauka, tace "Plss ka d'an xo da Shureim" yace "Ohk, let me go back to pick him" Cikin minti sha biyar khaleel ya kirata yana asibiti, Khadijah ta mike ta fita don shigowa da shi, da gudu Shureim ya taho ganinta da yayi tun daga nisa ta bude hannunta ta rungume sa, "Anty plss I want to see sudais now" ta shafa kansa tace "You wil see him sweetheart" daga haka ta mike tana rike da hannunsa ta kalli Khaleel dake kallonsu, ta d'an yi murmushi ta sauke kanta kasa tace "Ina yini" yace "Lafiya lau ya mai jikin?" Tace "Da sauki, ya ma koma bacci yanxu" daga haka ta fara tafiya rike da shureim ya bi bayan su har suka isa ward din, tun da Khaleel ya shiga yake kallon sudais har ya karasa kusa da shi, ya juya yana kallon Khadijah yace "Yaushe aka kawo sa asibiti?" Ta bude hannu alamar bata sani ba, yace "Wa ya kawo sa?" Ta turo baki tace "Shi ya kawo sa" khaleel yace "Ina yake?" Tace "Kilan yana office" juyawa yayi ya fita ta bi sa da ido, can ta mayar da dubanta kan sudais, shureim na kusa da shi kan gadon da damuwa yake cewa "Sudais are you still sick? Plss get well soon so that we can play together, I am missing you" Kallon sa kawai Sudais yake bai ce komai ba, hawaye ya cika idon Khadijah ta karasa kusa da shi ta kamo hannunsa tace "Sudais talk to ur brother he is missing you" Sudais ya gyada mata kai amma bai ce komai ba, ta xauna kujera hawaye na sakko mata tace "Plss get well son, I want to see u hale and hearty once more" Aliyu na rubuce rubuce yana duke gaban table dinsa khaleel ya shigo, kallon kallo suka tsaya yi, can khaleel ya karasa cikin office din yace "What exactly is the little boys problem now?" Ba tare da Aliyu ya sake kallonsa ba ya dau takardan scan da aka yi ya mika masa, Khaleel ya karba yana dubawa, shiru yyi na yan dakiku kafin ya kalli Aliyu yace "So what next?" Mikewa Aliyu yyi yace "We will be going to India tomorrow" kallon khaleel yyi yana kwasan takardun da ya gama rubutu a kai yace "Don't tell her anything about it...." Kallonsa kawai khaleel yake bai ce komai ba, can ya juya ya fita daga ward din ya koma reception ya xauna, kai kana ganinsa kasan he is disturbed, Khadijah tayi ta jiran dawowan khaleel amma shiru, taji duk hankalinta ya tashi, kallon Shureim dake ta damun sudais din da magana ta yi xata ce ya daina damunsa taji muryar sudais a hankali yace "Anty tell him to let me I want to rest" idonsa a rufe yake maganar, Ta kalli shureim da damuwa tace "Leave him plss shureim ka ga ba shi da lafiya" Shureim ya bata fuska yace "Then I will rest with him too" ita dai bata ce komai ba, wasu likita biyu da nurse daya suka shigo ward din, daya ya sauke Shureim kasa daga kan gadon, wasu alluran likitan ya kara masa guda biyu, daya likitan yace "Xa a canxa masa daki yanxu madam...." Juyawa Khadijah tayi ta fice daga dakin xuciyarta na bugawa, Khaleel na xaune har sannan a reception, bai jira ta karaso ba ya mike ya fita kamar bai ganta ba, sama ta wuce ta bude office din Aliyu, tsaye ta gansa jikin window ya juyo suka hada ido, ta isa kusa da shi hawaye cike idonta tace "Tell me what's wrong with my son Aliyu, ka gaya min plss" ta fashe da matsanancin kuka tana kallonsa, ya dauke kai yace "He will get better soon, it's just a minor illness" ta tsayar da kukan da take cikin sanyin murya tace "Are you assuring me??" Yana kallon kwayar idonta yace "Sure, Allah xai basa lafiya" juyawa tayi ta nufi kofa ya bi ta da kallo. Karfe Biyar na yamma Umma ta xo clinic din, hankalinta ya tashi sosai ganin Sudais ita ma, Khadijah dake xaune cikin sanyin murya tace "Umma kawai xaxxabi ne, Allah xai basa lafiya" ita dai umma bata ce komai ba, abincin da ta kawo ma bai ci ba, khaleel yace ta bar sa anjima xai ci ana basa abinci a drip, Da ladabi Aliyu ya shigo ward din ya gaida umma ya fita, har aka yi isha suna clinic din, Aliyu ya samu khaleel dake xaune waje yace "You tell her to go home it's getting late" Khaleel bai kallesa ba yace "Allow her to be with her son, kuma it's better ka gaya mata matsalar yaran sai ta bi ku xuwa India gobe" Aliyu bai ce komai ba na kusan minti daya, can ya juya ya bar wajen, tara saura umma ta wuce, babu yanda Khadijah bata yi da shureim ya bi ta ba amma ya ki, haka umma ta tafi ta bar sa. Khadijah na xaune ta jingina da gadon da sudais yake misalin goma saura wayarta ya fara ring, dagowa tayi tana kallon wayar, ta dauka a hankali ganin sudais ke kiranta ta daga ta kai kunne cikin sanyin muryarta tayi sallama, muryar mace taji tace "Amira koh?" Khadijah tayi shiru tana saurarenta, tace "Toh jiddah ce, matar Barrister Aliyu, ina son sanin meye hadin ki da mijina tun da girma da arxiki" mamaki ya cika Khadijah, jiddah tace "Ohh shiru xa ki min kina ji na?" Khadijah tace "Toh uwata ce ke da baxan yi shiru ba, why not ki tambayi shi mijin naki meye tsakaninmu xa ki kirani, ko kin mance profession din mijin naki" wani tsawa jiddah tayi tace "Kee maxa kalmashe kalamanki, kinsan wacece ni, na fi ki sanin aikin mijina malama, sannan mijina baya kiran client dinsa baya kuma saving numbers dinsu sai dai su kira sa suyi introducing kansu ke ko gashi duk shi ke kiran ki kuma ku dau mintuna masu yawa kuna magana, halan baki san yana da aure bane, baki san mijin aure bane?" Tsaki Khadijah ta ja tace "Kan ki ake ji, wannan kuma sai ki je ki samu mijin naki ki tambayesa" daga haka ta kashe wayarta, jiddah ta kirata ya fi sau hudu bata daga ba lkci daya taji xuciyarta ya fara mata xafi duk da ba wai hayaniya tayi da ita ba, taji ranta yyi mugun baci. Wata nurse ce ta shigo ta nuna mata wani spare gado dake ward din tace ta kwanta, khadijah ta mike tana kallon Sudais duk da bata son barin sa, ta kai hannu goshinsa still taji ba xafi temperature dinsa is normal, ya bude idonsa a hankali, har ranta ta ji dadin hakan don har umma ta xo ta tafi bai bude idonsa ba, xata yi magana ya riga ta yace "Anty ina Shureim?" Tace "Yana waje tare da uncle" ya bata fuska yace "Me yasa ya tafi?" Ta kwantar da murya tace "You said he shud allow you to rest, shine ya tafi da uncle" a hankali yace "Anty kice ya xo plss, I want to tell him am sorry" jikinta yayi sanyi tace "Toh xan kira sa yanxu" daga haka ta nufi kofa tana waigo yaran da ya bi ta da ido, Khaleel na xaune waje idonsa a kan wayar hannunsa Khadijah ta nufosa, ya daga kai yana kallonta har ta iso inda yake, yace "Is he awake?" Tace "Yace yana son ya ga shureim wai" Khaleel yace "Yana sama" ta d'an bude ido tace "Wajen wa?" Bai ce komai ba, hakan yasa ta hade rai tace "But me yasa ka bar sa ya je can? Why did u allow him go to him?" Khaleel ya ci gaba da danna wayarsa yace "He followed him, sae in hanasa..." Juyawa tayi a fusace ta wuce office din Aliyu, Khaleel ya d'an yi murmushi ya tashi ya shiga clinic din shi ma, Aliyu na tare da Dr Mukhtar Khadijah ta shigo office din, duk suka juya suna kallonta, ta dinga kallon office din tana neman shureim can ta hango sa kwance kan gadon masu ciki a office din yana bacci, karasawa tayi xata tashe sa, taji Aliyu yace "Don't wake him" ko kallonsa bata yi ba xata daga yaron taji jikinsa yyi xafi sosai, ta dinga kallonsa gabanta na faduwa, a firgice ya farka ta rikesa sosai tana kallonsa da damuwa tace "Shureim me ya faru, ur temperature is high" rungumeta yayi yyi lamo jikinta, ta sauke sa kan gadon ta nufi kofa, Aliyu ya bi ta da kallo, ba su kai ga kai wa kofar ba yaron ya shiga kwarara amai, ta dukar da shi da sauri ita ma ta duka hankalinta tashe tace "What's wrong shureim, me ka ci?" Dr Mukhtar ya taho gun su ya dagosa yana masa sannu, dai dai nan wata nurse ta shigo tana kallon Aliyu tace "Dr, ur attention" daga haka ta fita, Khadijah ta bi nurse din da kallo, Aliyu ya fita office din Dr Mukhtar ya cire ma Shureim rigar jikinsa yana rike da hannunsa ya isa table din Aliyu, duba sa yyi, bayan wani lkci ya ajiye stethoscope din hannunsa ya nuna ma Khadijah bathroom yace "Ki gyara masa jiki sai ki kwantar da shi kan gado, let me get him drug? Ya ci abinci?" Ta girgixa masa kai yace "Ohk" daga haka ya fita xuwa gun nurses, Ganin duk basa wajen yayi tunanin ko an kawo emergency ne, ya kalli direction din Emergency ward, yaga Aliyu tsaye ya jingina da bango, Karasawa Mukhtar yyi gun sa, ganin yanayinsa yace "Me ya faru Dr?" Kallonsa kawai Aliyu yake ya kasa cewa komai, Dr Mukhtar ya shiga cikin emergency ward din, khaleel ne kusa da gadon da sudais yake ya hade kansa da karfen gadon, Dr Mukhtar ya dinga bin Doctors din da kallo, ganin yanda suke tsaye hopelessly, can ya kalli Sudais lkci daya jikinsa yyi mugun sanyi, gaba daya he became lost of words ya kasa karasawa cikin ward din, juyawa yyi da kyar ya fita office din yana kallon Aliyu dake jingine da bango har lkcn, ya dafa shoulder dinsa cikin sanyin murya yace "Hardluck Doctor, Allah ya masa rahama" Aliyu bai iya yace komai tunaninsa daya a lkcn Khadijah, Khaleel ma ya fito ward din yana kallon Aliyu amma ya rasa abinda xai ce, Aliyu yyi karfin halin ce masa "Plss take her home" Khaleel ya bar wajen a sanyaye ya fiddo wayarsa yyi dialing number sudais, yana dagawa a hankali yace "Barrister the boy is late" daga haka ya katse wayar, kujera Aliyu ya nema ya xauna jin ya kasa ci gaba da tsayuwa, sai a sannan ya ji hawaye na sakko masa ya rike kan sa, how will Iman take this?? Who is to break the news to her, Khaleel ma na tsaye ya jingina da bango yana tunanin yanda xai yaudareta ya mayar da ita gida, can ya nufi sama xuwa office din Aliyu ya ganta ta fito office din rike da shureim, khaleel na ganinta sai da gabansa yyi mugun faduwa ya nufeta da sauri sai dai bai bari taga idonsa ba trying hard to be okay yace "Where did u see him?" Da damuwa tace "Amai yake ta yi Dr, kuma jikinsa da xafi" Khaleel ya duka yana kallonsa yace "What happen shureim" yace "I want go to Sudais" Khaleel ya hadiye abu da kyar yace "Okay xan kai ka my boy" daga haka ya mike yace "Bani wayar pls ina son inyi call mine is out of airtime" mika masa wayar hannunta khadijah tayi ya kama hannun Shureim yace "Mu koma ciki in duba sa" tace "Ai wani Dr ya duba sa yanxu" yace "Ehh let me check him again sai a basa magani" tace "Toh ku tafi, let me go to sudais..." da sauri ya juyo yace "Noo ki xo mu je sai ku tafi tare da shureim he won't be happy idan bai ga shureim ba" a hankali ta bi bayan Khaleel dake rike da shureim, office din Dr Aliyu ya shiga, ya xaunar da Shureim kan gadon office din, ya kalli khadijah yace "You stay with him ina xuwa" daga haka ya juya ya fita, Number Umma ya shiga dubawa a call logs dinta, Ummata... yaga tayi saving number da, nan ya gane number umma ce, yayi saurin kwashe number a tasa wayar, ya sauka kasa bayan yyi dialing, ba a dau lkci ba Umma ta dauka, ya gaisheta cikin sanyin murya yace "Umma khaleel ne, I called to inform you that Sudais is late umma, yanxu ya rasu" mikewa umma dake xaune tayi cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilai raji'un ya rasu?" Jikin Khaleel yyi sanyi jin yanayin da umma ta shiga, a hankali yace "Ku yi hakuri Umma, but har yanxu Khadijah bata sani ba kuma ba a son ta sani a nan so plss, ban san ya xa ayi ko xaki kirata ki dai fada mata wani abu da xai sa ta wuce gida yanxu, cos we can never convince her taje gida ynxu" Kuka kawai Umma take ta kasa cewa komai ta katse wayar ta dinga salati wanda hakan ya ja hankalin Nanny ta shigo, cikin tashin hankali tace "Umma me ya faru?" Da kyar Umma ta iya ce mata "Sudais" tun umma bata fada ba Nanny ta san kwanan xancen ta fashe da kuka ta xube wajen tana salati ita ma, tausayin khadijah ya sa Umma ta kasa controlling kanta, kuka take kamar ranta xai fita, babu mai lallashin wani ita da Nanny, Khaleel ya kasa komawa sama gun khadijah duk iya kokarin sa na ganin ya dake ya ji ya kasa kuma, kujera ya nema shi ma ya xauna yana ganin abun kamar a mafarki yanxu shikenan yaron nan ya tafi, Nurses din ma gaba daya duk jikinsu a sanyaye yake, Aliyu yyi karfin halin fiddo wayarsa ya shiga kiran Mumy, bayan ta daga cikin sanyin murya yace "Mumy ya rasu yanxu" Yanda mumy ta rikice a lokacin sai ayi tunanin sun yi shekara shidda tare da yaron ne, ta dinga kuka kawai ya katse wayar sa,Sudais ne ya shigo reception din duk hankalinsa a tashe ya nufi khaleel cike da karfin hali yace "Dr plss kar ku ce min yaron nan ya rasu, tell me he is still alive" Khaleel ya kasa ce masa komai, Sudais ya tafi gun wata nurse yace "Take me to him plss" nurse din ta nuna masa emergency, da sauri ya shiga wajen, kallon gawar yaron ya dinga yi ganin kamar mai bacci da murmushin sa a fuska, sudais ya karasa gadon ya hade kai da karfe hawaye na sakko masa ya dinga nanata "Innalillahi wa inna ilai hi raji'un" Bai taba ba yaron mutuwa yanxu ba, ranan da aka haifesa tare da d'an uwansa ya tuno, da irin wahalar da khadijah ta sha kamar baxa ta yi ba, ya ji ya kasa controlling hawayen sa, memory din ya dinga dawo masa freah, tun daga san da yaran suka fara wayo, suka yi mugun sabawa da ahi har xuwa ranan da ya barsu suna kukan xa su bi sa amma har ya fita bai waiwayo su ba, cikin raunin murya sudais yace "Allahummaghfir li-fulanin Aliyu warfa' darajatahu fil-mahdiyyina, wakhlufhu fi'aqibihi fil-ghaabirina, waghfir-lanaa wa lahu yaa Rabbal-'aalamina, wafsah lahu fee qabrihi wa nawwir lahu feehi" daga haka ya karasa rufe masa idanuwansa amma ya kasa barin dakin hawaye na xuba idonsa, ya jima bai ji mutuwar da ta taba sa haka ba tun bayan rasuwar maminsa 3 years back, hakan yasa ya kasa daina hawaye, ya ki fita ward din don gani yake kamar yaron xai tashi. Da kyar Umma ta iya dialing number Khadijah, khaleel dake xaune ya jingina da kujera jin wayar na vibrate ya kalla da sauri ganin Umma ke kiranta ya mike ya ba wata nurse yace "Plss ma ki dan taimaka ki kai ma warce ke office din Dr Aliyu wayar nan" ta amsa ta wuce ta kai ma khadijah, a stairs suka kusa cin karo xata sakko, nurse din ta mika mata khadijah ta karba ganin umma ke kiranta ta daga wayar, Umma tayi gathering courage bayan ta saita muryarta tace "Khadijah ki dawo gida yanxu ina son ganin ki" hankalin khadijah ya tashi sosai jin yanayin muryar umma a tsorace tace "Umma baki da lafiya ne?" Hawaye na sakko ma Umma cikin sanyin tace "Ehh bana jin dadi ki dawo yanxu kin ji daughter" tashin hankali ne sosai tare da Khadijah ta dinga kallon wayar sannan ta sauka kasa da sauri, khaleel na ganinta ya mike da sauri, ta nufe sa da damuwa tace "Dr Umma ce ta kira wai bata da lafiya yanxu" ya dake yace "Subhanallah, bata da lafiya kuma?" Ta gyada masa kai hawaye cike idonta, yace "Toh bari inyi dropping din ki gidan yanxu..." Tace "Toh, Shureim din yana ta aman har yanxu amma wani Dr na gun sa" Khaleel yace "Toh shkkn mu je" juyawa tayi ta nufi ward da little sudais yake kafin a kai sa emergency tace "Let me check sudais kafin in tafi pls" Khaleel bai san lkcn da ya fixgota ba ta kusa fadawa kansa da mamaki take kallonsa, ya wara ido yace "Mu je, idan mun dawo sai ki duba sa, bacci yake daga can na fito yanxu" kasa cewa komai tayi Khaleel na rike da hannunta ya nufi kofar fita ta dinga bin sa, Aliyu dake xaune one side of the clinic duk yana kallonsu ya lumshe ido to prevent more tears, he still can't believe that cute boy, his blood is gone forever, kiran Abbansa ne ya shigo wayarsa, ya san mumy ta kira sa ta fada masa kenan, don tun bayan da Mumy ta gaya masa abinda ya shiga tsakaninsa da khadijah da batun yan biyun ya dauke masa wuta duk da a ranan ma ya bar kasar, a hankali ya mike ya daga kiran Abban nasa. Har suka isa gida khaleel bai ce ma khadijah komai ba, sai dai ya lura duk a sanyaye take, yaji wani mugun tausayinta na dawainiya da shi, jiki ba kwari ta fita daga motar bayan yyi parking ta wuce ciki tana tsoron yanda xata je ta samu Umma, Xaune umma take har lokacin a daki tayi kukan har taji ba dadi, nanny ma duk ta fita hayyacinta da ta tuna sudais ya mutu sai ya rushe da kuka don tun suna jarirai take tare da su. suna ganin khadijah duk suka shanye kukan Khadijah ta karasa da sauri ta xube gaban umma gabanta na mugun faduwa tace "Ummata mai ya faru, why are you crying plss" rungume ta umma tayi ta sake fashewa da wani kukan, Khadijah duk ta rikice ita ma ta fashe da kuka tace "Umma don Allah ki gaya min me ya faru, waye ya mutu?" Nanny ta mike ta bar dakin wani sabon kukan ya xo mata. A sanyaye khaleel yyi reverse ya koma clinic din, dai dai lkcn da Sudais ya fito daga emergency ward, Dr Mukhtar kuma ya sakko kasa rike da shureim, shureim na ganin Khaleel ya nufe sa da sauri, Aliyu ya bi yaron da kallo a sanyaye, khaleel ya duka yana kallonsa murmushin karfin hali dauke fuskarsa yace "How are you feeling now?" A hankali yaron yace "Uncle I want to see my brother plss" Khaleel ya dinga kallonsa ko kiftawa babu, can ya kirkiri wani murmushin yace "He is sleeping now" ya fashe da kuka yace "Nooo, I want to sleep with him too" daga haka ya juya xai tafi inda dan uwansa yake, khaleel ya jawo sa da sauri yace "He is sick, baka son ya samu lafiya, idan kana damunsa baxai samu lafiya ba ai" cikin rawar murya yaron yace "Toh uncle kar ya tafi ya bar ni" Khaleel dake kallonsa ko kiftawa babu a hankali yace "Ina xai je?" Shureim yace "Gida" tashi Khaleel yyi ya kama hannunsa ya fita duk jikinsa a sanyaye. Aliyu dake xaune ya dinga kallon colleagues dinsa dake tambayarsa inda xa a kai gawar sudais ko a nan xai kwana, mikewa yyi da kyar yace "Xan tafi da gawar gida yanxu" a kunnen Barrister sudais da sai lkcn ya fito daga dakin da gawar sudais yake, ya karaso inda Aliyu yake fuska daure yana masa wani kallo yace "Gidan mahaifiyar sa xa a kai gawar yanxu...." kallonsa kawai Aliyu ke yi, Sudais yace "You will be the one to go break the news to her" Aliyu ya d'an bude ido yace "Why me?" Sudais bai sake saurarensa ba ya koma ya dauko gawar ya fita xuwa gun motarsa Aliyu ya bi sa da wani irin kallo. Kusan a tare duk su ukun suka isa gidan, khaleel ya fara fitowa sannan ya sakko da Shureim yana kallon Sudais da ya fito shi ma amma gawar na motarsa, dauke kai khaleel yyi ya shiga ciki yana rike da shureim, Aliyu ya fito daga tasa motar da Doctors biyu suka bi bayan Khaleel, Sudais ya kasa shiga ciki ya jingina da motarsa yana tunanin yanda Khadijah xata dau xan cen rasuwar d'an ta, lumshe ido yyi wasu hawayen na sakko masa, Nanny ce ta bude masu kofa khaleel yasa ta shimfida tabarma a nan balcony, duk gabansa faduwa yake damuwar sa daya khadijah, xuwa yanxu dai umma ta daina kuka bayan ta ce ma khadijah rasuwa aka mata, Khadijah sai kallonta take a sanyaye bayan ta gama kukan ita ma don bata san waye ya rasu ba kuma umma bata gaya mata ba, Umma ta sa Hijab ta fito a sanyaye ba tare da tace ma khadijah komai ba, khaleel ya dinga kallon umma da wasu hawayen ke xubo mata ganin su, Aliyu ya kasa kallonta a sanyaye yace "Allah ya yi masa rahama, ya sa mai ceto ne" Khadijah ta fito daga daki da sauri jin muryar Aliyu, kallonsu ta dinga yi daga inda take tsaye can ta karaso da sauri tana kallon khaleel gabanta na faduwa tace "Dr ina sudais din?" Khaleel ya kasa kallonta kuma ya rasa abinda xai ce, dai dai nan Barrister sudais ya shigo parlorn shi ma bayan ya ajiye gawar sudais kan tabarmar da ya gani balcony baya son ya shiga ciki da shi tukun, suna hada ido da khadijah yyi saurin sunkuyar da kansa, A hankali khadijah ta juya tana kallon umma dake share sabbin hawayen dake xubo mata, ta juya ya kalli Nanny da ta jingina da bango tana hawayen ita ma, a rikice ta nufi Aliyu ta durkusa gabansa cikin rudewa tace "Aliyu ka gaya min wani abu ya sami sudais dina ne, don girman Allah ka gaya min" kasa ce mata komai yayi ya kasa kallonta, lkci daya hawaye ya cika idonsa, mikewa khaleel yyi ya nufi kofa xai fita cos he can't stand it any more, ta mike kamar mahaukaciya ta bi bayansa da sauri, tsaye khaleel yyi balcony ganin gawar yaron a wajen don bai san Barrister ya shigo da shi ba, ya juya a hankali yana kallon khadijah dake kallon gawar kan tabarma an rufe, lkci daya jikinta ya dau rawa ta kamo hannun khaleel cikin rawar murya tace "Dr meye wannan, what is it...." Jawota khaleel yayi jikinsa ya rungume ta gam, cikin sanyin murya hawaye na taruwa idonsa yace "Don't forget Khadijah, Allahn da ya baki shi ya fi ki son sa.... Ba wayon ki ba ba dubarar ki ba ya sa ya baki, to yanxu ya amshe kayan sa, sudais addu'arki kawai yake bukata gare sa yanxu, pray to meet with ur son once again in Jannah...." Jin Khadijah tayi shiru ya dago kanta a hankali yana kallonta, a hankali yaji tana neman sulalewa hannunsa yaki saketa, a haka ta suma yana rike da ita. A hankali khadijah ta bude idanuwanta bayan lokaci me tsawo, kwance take kan gado ta dinga bin mutanen dake xaune dakin da kallo, Wata kawar Umma ta taso ta dawo kusa da ita ganin tashi take son yi ta taimaka mata ta xauna, da kyar tace "Anty me ya ke faruwa?" Umma tayi karfin halin xuwa kusa da ita ta xauna tace "Ya jikin khadijah" shiru khadijah tayi tana ta kallon umma, lkci daya ta fasa ihu ta mike ta fice daga dakin da gudu suka bi ta, Aliyu ne ya fara mikewa a compound din ganin ta fito, ga maxa ko ina, Khaleel dake rungume da Shureim dake bacci jikinsa ya dinga kallonta amma ya kasa tashi, haka barrister sudais, tana ganin Aliyu ta taho gun sa ta rike hannunsa cikin matsanancin kuka sosai tace "Aliyu don Allah kar ka ce min sudais ya mutu, you assured me he will be fyn, kar ka ce min ya mutu don girman Allah" kasa cewa komai Aliyu yyi yana kallonta, ta rungume sa tana kuka kamar ranta xai fita tace "Ka ce min bai mutu ba Aliyu, wllh ina son sa, kar ya tafi ya bar ni" Aliyu ya ja ta suka bar wajen xuwa inda babu mutane ya xaunar xa ita ya durkusa yana kallonta, a hankali yace "Iman kin san Allah xai baki shi?" Ta girgixa masa kai hawaye na xuba idonta tace "A'a" *Sorry if I disappoint anybody* Aliyu ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Toh kar ki masa butulci Iman, baki san xai baki shi ba ya baki, prayer is all what ur little boy wants from you, kiyi masa addu'a ba kuka ba Iman, if you continue like this what will be the fate of his twin, kin ga shi ma xai shiga damuwa sosai na rashin halve dinsa and this might affect him badly.... Or did you want anything bad to happen to him also, For his sake plss ki kwantar da hankalin ki so you won't loose him too, am telling you damuwar da shi xai shiga sai ma ya fi naki" khadijah ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace "Na shiga uku don girman Allah kar ya bar ni shi ma" yace "Then ki kwantar da hankalin ki and accept this fate" hawaye na xuba idonta tace "Toh" yace "Promise me baxa ki sake kuka ba Iman" k'in cewa komai tayi, ya kira sunanta a hankali ta daga kai tana kallonsa, sosai gabanta ya fadi, ta kuma rushewa da kuka tace "Yanxu Sudais ya tafi ya bar ni.... Shi fa yace min in je in kira masa Shureim he wants to tell him he is sorry, dama mutuwa xai yi baya son ya mutu a kusa da ni" Ta hade kai da gwiwa tana kuka kamar ranta xai fita maganar Sudais na karshe na dawo mata "Anty ki ce Shureim ya xo, I want to tell him am sorry" kuka ta ke kamar ana dada tunxurata, Aliyu ya kasa ce mata komai duk jikinsa yyi sanyi, Ta rikosa tana girgixa kai cikin tashin hankali tace "Yanxu shkkn baxan sake ganin sa ba, me yasa ya tafi ya bar ni da Shureim" Aliyu ya kasa cewa komai wani mugun tausayinta na shigarsa, cikin sanyayyen muryarsa yace "Pls ki daina kukan nan Iman, da duk biyun Allah ya raba ki da ya xa ki yi kenan, you neva knew why he took him so soon, be a good Muslimat plss" shiru khadijah tayi jin yace Dukka biyun, ta goge idonta gabanta na mugun faduwa cos she can't just imagine that, Murya can kasa yace "You make the promise now, that baxa ki sake masa kuka ba sai dai addu'a...." Ta gyada kai da kyar trying not to cry tace "I promise" yace "Add in sha Allah to the promise" a hankali tace "In sha Allah" Ya d'an yi murmushi yace "Good" mikewa yyi ya dago ta ta mike ita ma tana goge idonta yace "Ki wuce ciki and remember the promise you make" tace "Toh" daga haka ta fara tafiya ya bi ta da kallo, da sauri ta juyo sai kuma ta dawo tace "Ina shureim plss" da kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali yace "Yana nan tare da mu" ta hadiye abu da kyar tace "Ka dauko min shi plss" yace "They are people everywhere, later xa a kai maki shi" shiru tayi sai kuma ta juya a sanyaye ta fara tafiya, Juyowa tayi ta kara dawowa idonta har ya fara kawo kwalla tace "Toh me yake yi?" Yace "Kukan xa ki fara kuma" da sauri ta girgixa kai tana goge idonta, yace "He is just sitting down" bata ce komai ba ta fara tafiya kamar iska xai kadeta ta fadi har ta bar wajen, Aliyu ya koma a sanyaye ya xauna ya jinginar da kansa jikin bango yana jin mutuwar yaron har cikin ransa, Tun da khadijah ta dawo compound din khaleel ke bin ta da kallo har ta shiga parlor, sai a sannan barrister Sudais ma ya dauke idanuwansa daga kallonta, Bedroom ta wuce duk mutanen parlon suka bi ta da kallo cike da tausayinta, Umma na xaune har lkcn duk jikinta yyi la"asar, da ido ta bi khadijah har ta dauko Hijab dinta ta sa ta xauna kan darduman dake shimfide ta jingina da bango, hawaye ya cika Idon Umma don bata yi xaton hakan ba, tashin hankalinta ta Inda xata fara lallashin Khadijah sai ga shi taga ta ma daina kukan, Wata frnd din umma ta dawo kusa da ita a sanyaye tace "Kiyi hakuri kinji Khadijah, Allah yayi masa rahama..." A hankali khadijah tace "Ameen" Umma taji hankalinta ya kwanta sosai, tashi tayi ta fita da kanta taje kitchen ta hado mata shayi ta dawo, kasa sha Khadijah tayi har lkcn ta kasa yarda Her lovely Sudais is gone forever, tana son kuka amma sai ta tuna promise din da tayi, hakan yasa xuciyarta ya dinga mata xafi sosai, kowa ya ganta sai yaji tausayinta, Umma har lkcn mamakin karfin halin nata ta dinga yi, a haka har aka yi la'asar, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh umma ta xubo mata abinci ta xauna kusa da ita cike da lallami tace "Don Allah ko kadan ne ki ci Khadijah, tun jiya fa baki ci komai ba" Khadijah tayi shiru bata ce komai ba, can ta dago da kyar tana kallon Umma tace "Umma yanxu shikenan Sudais ya tafi" Rungume ta umma tayi tana kokarin ganin bata xubda hawayen dake baraxanar xubo mata ba, cikin sanyin murya tace "Pray for him daughter, Allah yasa can ya fi masa nan, Allah ya sa mai ceton mu ne" cikin rawar murya Khadijah tace "Ameen" umma tace "Toh ki ci abincin kadan don Allah" ta girgixa kai tace "Umma baxan iya ci ba" Umma tace "Ko cokali biyu ne ki yi" Nanny ce ta shigo dakin da kumburarrun idonta ta duka kusa da su tace "Umma akwai baki parlor sun xo mata gaisuwa ta daure ta fito" Umma tace "Kice su shigo nan" mikewa Nanny tayi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tare da su Mumy, Baby da su seeyama da wata daban, Mikewa Umma ta yi ganin su ta shimfida masu babban darduma tana masu sannu da xuwa, Khadijah ta dinga kallon Mumy har ta xauna, A hankali tace "Sannu da xuwa Mumy" mumy da kana ganin idanuwanta kasan ta yi kuka sosai tace "Sannu Khadijah, ya hakuri" Khadijah ta kasa amsawa ta dakar da kanta, Su siyama ma suka mata gaisuwar a sanyaye, sai a sannan khadijah ta kara dago kanta tana kokarin ganin bata bar hawayen idonta suka xubo ba, Kallon warce ke xaune kusa da baby ta dinga yi, ita ma yarinyar kallonta take da mamaki, Khadijah tayi karfin halin cewa "Maryam sannu da xuwa" Maryam tace "Ashe yaron ki ne ya rasu Khadijah, Allah ya ji kansa" Khadijah tayi karfin halin cewa "Ameen" sai dai xuciyarta cike yake da mamaki, Maryam dama yar uwar su Aliyu ce kenan, makarantar su daya a UK amma Hi kadai ne mutuncin da ke tsakaninsu kawai ta rasa me yasa bata son yarinyar, kawarsu Vanessa ce dai. Mumy sun kusa minti sha biyar a dakin, duk tausayin khadijah ya cika don tasan rashin yaro da ciwo sosai ga uwarsa barin yaro mai shiga rai irin sudais, bata ma samu courage din tambayar ina Shureim ba, Karfe biyar da yan mintuna tace ma umma xa su tafi, Umma tace "Toh mun gode kwarai Hajiya, Allah ya bar xumunci" Mumy tace "Ameen, kuyi hakuri bamu xo tun safe ba kanwata ce ba lafiya tana asibiti sun yi hatsari tun shekaranjiya" Umma tace "Subhanallah, toh Allah ya bata lafiya, ya yaye mata" Mumy tace "Ameen mun gode" hakuri ta kara ba khadijah Umma ta rakasu suka fita parlor, Sai a sannan Mumy tace "Kanin Aliyun yana waje ya xo mata gaisuwa amma ko xuwa anjima sai ya dawo" Umma tace "A'a bari ta fito" mumy tayi convincing dinta kan ta bari sai anjima ya dawo daga haka suka wuce Umma ta koma ciki. A hankali khadijah ta tako har cikin parlor tana sanye da Hijab dinta har kasa ta xauna kujera a sanyaye tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yyi, ta sunkuyar da kai a raunane tunawa da lkcn da suka dinga dragging sunan da ta xabar ma sudais dinta da shi, A hankali yace "Amira..." Ta daga kai tana kallonsa lkci daya idanuwanta suka kada, cikin sanyi yace "Keep on praying for him, Allah ya sa mai ceton mu ne, life moves on plss, ai da baki san Allah xai baki shi ba, so kiyi hakuri ki cire sa ranki, tsakanin ki da shi yanxu addu'a, baxai ji dadi kiyi ta masa kuka ba" Tana gyada masa kai da kyar tace "Ai na daina, Allah ya ji kansa, ya hada ni da shi a aljanna" Barrister sudais yace "Ameen, Allah ya kara maki hakuri" Murya can kasa tace "Ameen" yace "Toh yi ma Umma magana xan mata gaisuwa" Ta mike tace "Toh" daga haka ta wuce ciki, ba a dau lkci ba Umma ta fito, da ta amshi gaisuwar sudais tana sa masa albarka, Bai dade parlorn ba yace mata xai koma gida, tayi masa Allah ya kiyaye hanya ya fita parlorn, ita dai har ranta taji Sudais ya kwanta mata, ta kuma san har abada baxa ta mance hallacin da yayi mata ba, don ko ita yayi ma, bata kuma san da me xata saka masa ba. Karfe tara da yan mintuna, Aliyu ya shigo parlorn, har sannan Umma na ciki bayan ta sallami wasu bakin, suka gaisa ya kara mata gaisuwa tace "Allah ya ba mu hakuri gaba daya, daxu su hajiya ma suka xo, mun gode kwarai" shi dai bai ce komai ba, Umma sai ta ga kamar sudais ne xaune gabanta ya girma, hakan yasa duk jikinta ya kara sanyi, Aliyu da ya rasa abinda xai ce yyi karfin hali daga karshe yace "Mama tana Ciki ne?" Umma tace "Ehh tana ciki bari in mata magana" Daga haka ta mike ta wuce ciki, bayan wani lkci ta dawo tana kallonsa tace "Aliyu tayi bacci kuwa" yace "Toh shkkn Mama, sai na dawo gobe Allah kara hakuri" tace "Ameen, Allah bada lada" tana son tambayarsa Shureim amma bata san ta ya ba, ta kasa daurewa daga karshe kafin ya fita tace "Aliyu ina shureim din fa?" Juyowa yyi yace "An tafi da shi mama" tace "Can gidan ku?" Ya girgixa mata kai, Umma tace "Toh shikenan Allah ya kiyaye hanya" daga haka ya fita, umma ta san khaleel ne ya tafi da shi can gidan nasu. Ta koma cikin dakin Khadijah ta rufa mata bargo, Nanny dake dakin tace "Umma da ki kwana nan, tunda akwai baki dakin ki" Umma tace "A'a ke ki tsaya tare da ita babu komai duk daya ne" daga haka ta fita dakin. Karfe goma na safiyar washegari Khadijah na kwance daki ta rufe ido kamar mai bacci don gaisuwar da ake mata na shureim na kara daga mata hankali, hakan yasa duk wanda ma ya xo umma da Nanny yake ma gaisuwar, Umma ce ta shigo dakin ta taba ta duk da tasan ba bacci take ba, Khadijah ta bude idanuwanta da suka mata nauyi tana kallon umman nata, cikin kwantar da murya umma tace "Taso mu je an xo maki gaisuwa" ta d'an hade rai tace "Umma ba ga ku ba bacci fa nake" Umma tace "Mahaifiyar khaleel ce shi yasa ma na tashe ki" shiru khadijah tayi tana kallon umma, can Khadijah ta mike xaune a hankali, umma ta kama hannunta ta tashi daga kan gadon, hijab ne har kasa jikinta, hakan yasa ta bi bayan umma dake rike da hannunta suka fita parlor, balarabiyar matar na xaune parlor da jikokinta su uku sai shureim dake jikinta shi ma, Suna hada ido Khadijah ta sauke kanta a sanyaye ta karasa cikin parlorn ta xauna, da gudu shureim ya taho ya rungume ta yana kallonta yace "Anty are you sick?" Kallonsa Kawai khadijah take taji kamar ta fashe da kuka, Ummu dake ta kallonta da tausayi tace "Sannu Khadijah, ya karin hakuri?" kasa cewa komai tayi da farko, can dai tayi karfin halin bude baki da kyar tace "Alhmdlh Mumy, nagode" Ummu tace "Allah yayi masa rahama, ke kuma Allah baki dangana, ya sa mai ceto ne" Umma tace "Ameen thumma Ameen" don khadijah kasa amsawa tayi, Shureim na kallonta da damuwa yace "Anty uncle yace min sudais travelled, why will he travel alone, why didn't we go together plss, and now I am missing him, plss I want to go to him, I promise I will never fight him again...." umma ta jawosa jikinta tana kokarin boye hawayen idonta tace "He will be back soon sweetheart, and I am sure he is missing you too" Shureim yace "Toh Umma I want to talk to him on phone, am missing him" Ummu dake ta kallon shureim tace "Shureim har ka gaji da wasa dasu fadeel, ain't they ur frnds anymore" ya juya ya kalleta yace "Noo Ummu I like them, but sudais is my brother, they will like him also" Ummu tace "Toh taho mu wuce tunda ka gaida Anty" kallon khadijah da kanta ke kasa shureim yyi ya dawo kusa da ita a hankali yace "Anty, is sudais coming back soon? I want the both of us to be frnds with fadeel and Adeel" Ummu ta mike tace "Toh xo mu wuce Shureim, idan ya dawo xa a kawo sa wajen ka" da haka suka fita parlorn bayan shureim ya daga ma khadijah hannu, Umma ta rakasu har bakin mota, sai a sannan taga tare suke da Khaleel dake xaune motar, ganin umma ya sakko ya gaisheta da ladabi sannan ya mata gaisuwa ta amsa tana murmushi tace "Allah ya saka da alkhairi, ya bar xumunci" yace "Ameen" sai da suka shiga motar gaba daya sannan Umma ta koma cikin gida, bata tadda Khadijah a parlor ba hakan yasa ta wuce daki ta ganta kwance, mamaki ya cika umma ta xauna kusa da ita da damuwa, yanxu kuma rashin kukan nata ya fara damunta don wani lkcn gwara mutum yyi kukan da kukan xuci, Umma ta yi shiru na d'an lokaci kafin a hankali tace "Look daughter, cry... even if it's a little so you will feel relieve, kiyi kuka don Allah bana son wannan rashin kukan naki kuma, kin dai san matsalar ki, kar kije ki tada ciwon ki, it will be worst gaskiya idan haka ya faru" Jin bata ce komai ba umma ta mike a sanyaye ta fita, ba a jima da tafiyar mahaifiyar khaleel ba su mumy suka xo gidan, yau kam sun d'an dade kafin su wuce kuma khadijah ta fito ta amshi gaisuwar saleem, da yamma shaheedah ta xo gidan da sadeeq, shaheedah tayi kuka don bata ba sudais mutuwa so early ba, duk taji tausayin khadijah sosai, su Vanessa duk suka kira khadijah yi mata gaisuwar sudais da har lkcn a xaton su kanninta ne yan biyun. Da daddare ta fito wanka Shaheedah ta mika mata wayarta da yake vibrate, karba tayi ganin Khaleel ne ta daga ta kai kunne, cikin sanyin murya yace "Khadijah..." A hankali tace "Na'am" yace "Xa ki iya fitowa yanxu?" Shiru ta d'an yi kafin tace "Toh gani nan xuwa" shiryawa tayi ta sa hijab ta fita xuwa dakin umma, ta durkusa kusa da ita tana kallonta tace "Umma ina xuwa khaleel na kirana" Umma tace "Toh sai kin dawo" daga haka ta mike ta fita, cikin sanyi take tafiyar kamar mai tausayin kasa har ta isa waje, yana tsaye ya jingina jikin motarsa, kanta a kasa ta isa gefensa ta tsaya, murya can kasa tace "Ina yini?" Kallonta kawai yake bai ce komai ba har ta dago a hankali, sai a sannan ya sauke idonsa kasa daga kallonta da yake yi, cikin sanyayyan muryarsa yace "Ya hakuri khadijah" ta hadiye abu da kyar tace "Alhmdllh" yace "Ban san me xan ce maki ba shi yasa ban kira ki ba khadijah, I know it's very sad, it's a great lost, but don't forget ba wayon ki yasa Allah ya baki shi ba, and there is always a reason for everything, and you knw God plans best, don haka ki sa ma xuciyar ki dangana, you have ur handsome shureim, he will act as both him and his twin to you, this is part of ur fate, and it's already written, plss kin san condition din ki Khadijah kar ki kara sa mutuwar sudais a ran ki I know its very painful, but idan wani abu ya same ki i will be very sad, come to think of ur only son, for my sake and his don Allah kiyi hakuri, forget about Sudais, but don't forget to pray for him always, Allah ya hada mu gaba daya a aljanna" cike da damuwa ya kare, Khadijah tayi murmushin karfin hali tana share hawayen da ya taru idonta, tun ranan da Aliyu yace kar ta sake kuka bata kara ba sai yanxu da take gaban khaleel, a hankali tace "In sha Allah Dr, baxan sa damuwa a raina ba, ae ban ma san Allah xai bani shi ba, so baxan butulce masa ba, na hakura Allah ya haskaka kabarinsa ya sa can ya fi masa nan, kuma ya raya min d'an uwan sa" cikin rawar murya ta kare maganar, khaleel ya lumshe ido yace "Ameen Khadijah, am happy with ur words" Bata ce komai ba ta dinga kallon motar da yayi parking bayan na Khaleel, Aliyu ne ya fito cikin motar, kallo daya khaleel yayi masa ya dauke kansa, Aliyu ya iso inda suke yana kallon khaleel ya basa hannu khaleel ya amsa amma fa da kyar, Aliyu na kallon cikin idanuwansa yace "Ya hakurin mu?" Khaleel yace "Mun gode Allah" Aliyu ya kalli khadijah suka hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, cikin gidan Aliyu ya shiga, khaleel na juya wristwatch din hannunsa yace "Wajen ki ya xo?" Ta girgixa kai tace "A'a" Khaleel bai sake cewa komai ba bayan wani lkci yace "Alryt then, xan koma Khadijah, Allah ba mu hakuri gaba daya, sleep without worries plss" ta gyada masa kai tana kallonsa, yana daga kai suka hada ido tayi saurin dauke kanta, yyi murmushin sa mai kyau yace "Amma kin ci abinci kuwa? Tell me the truth plss" ta girgixa masa kai a sanyaye tace "I don't have appetite" yace "Toh idan na siyo maki abu yanxu make me the promise xa ki daure ki ci" tace "Akwai abinci fa a gida" yace "Ai na sanin, just promise me xa ki ci plsss" murmushi tayi tana fidgeting fingers dinta a hankali tace "Toh nagode" yace "Yauwa, I will be back soon" tace "Toh Allah ya kiyaye" daga haka ya xata xai shiga motarsa ita kuma ta shiga cikin gidan, xaune ta tadda Aliyu kan farar kujera a wajen compound din, kallo daya tayi masa ta dauke kai xata wuce ciki, taji a hankali yace "Iman" kasa ci gaba da tafiya tayi, maganganunsa na jiya da safe na mata yawo a kai, can ta juyo ta kallesa ta gan sa tsaye, yace "Plss just few minutes" tana ta tsayuwa idonta a kan yatsunta har ya iso gabanta yace "Few minutes pls" Ta dake da kyar tace "Toh" juyawa yayi ya nufi gun kujerun ta bi bayansa, ya xauna kan kujerar ta xauna ita ma. Kallonta kawai yake ta ki kallon sa ta hade rai, murya can kasa ta ji ya fara cewa "Iman ba dan ni ba don Allah ina son ki mance abinda ya faru tsakaninmu six years back....." Da sauri ta dakatar da shi tace "Toh ni nace maka ban mance bane?" Ya girgixa kai a hankali yace "I mean ki yafe min ki cire a ranki da gangan na maki hakan wllh ba da gangan bane, it's a set up, though ba lallai ki yarda da hakan ba, amma don Allah kiyi hakuri mu dinga xumunci" Ji tayi kamar ta fashe da kuka don ya fama mata ciwon da ya ki healing har yanxu a xuciyarta, A sanyaye yace "Kin ji Iman, ki raga min ko albarkacin daya yaron da ya rage a tsakaninmu even if I didn't deserve it" Khadijah ta kasa cewa komai, Bayan wani lkci ta daga kai a hankali tana kallonsa ta ga kallonta yake, da sauri ta sauke idonta tace "Ni fa na mance, ya kuma wuce a gu na" yace "Toh nagode sosai, amma xaki bani yaron?" Da sauri ta daga kai tana kallonsa, cikin rawar murya tace "I can't give you my son, kayi hakuri..." Yana gyada kai a hankali yace "No offense, amma xa ki bari ai mu dinga xumunci da shi, I mean in dinga xuwa ina ganinsa, once in a while kuma xa ki bari ya xo gun mumy koh" shiru tayi ta kasa cewa komai, murya can kasa yace "Kin yi shiru" a xuciyarta tace "Nasan maganin ka" a fili kuma tace "Toh" Wani murmushi yayi yace "Toh nagode sosai, Allah ya raya sa" tace "Ameen" kamar ance ta juya taga khaleel ya shigo gidan rike da leda, mikewa tayi da sauri ya karaso har gabanta yana kallonta ya mika mata ledan, ta d'an risina ta karba a hankali tace "Nagode" ya d'an yi murmushi yace "No thanks" daga haka ya juya ya nufi gate, Aliyu ya bi sa da kallo ko kiftawa babu, khadijah tace "Xan wuce ciki sai da safe" mikewa yayi yace "Toh ina yake, I mean the boy? Though ban san sunan sa ba" da kamar khadijah baxata ce komai ba sai kuma murya can kasa tace "Sunansa Muhammad, ana kiransa Shureim, sunan late half dinsa Aliyu ana kiransa Sudais" kallonta yake ko kiftawa babu, ta gyara tsayuwarta tana masa wani kallo tace "Barrister Aliyu... Sunan sa ya ci" daga haka ta juya ta fara tafiya fuskarta daure, murmushi Aliyu yyi ya bi ta da kallo, can yace "Ohk, wait Iman, nagane barrister Aliyu ne ba ni Aliyun ba" tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya karasa inda take yace "Toh yana ina yanxu, I haven't seen him since yesterday" tace "Yana gidansu Dr khaleel" shiru yyi bai ce komai ba, can a hankali yace "Ohk good nyt" daga haka ta juya ta wuce ciki ta rufe kofa. Washegari aka yi sadakan ukun sudais, tun da sassafe Mumy ta taho da su Siyama da frnds dinta biyu, sadakar wainan shinkafa da Kayan flour ta kawo gidan, Ummun khaleel ma ta xo da jikokinta tare da shureim wajajen karfe tara, ita ma wainar ta kawo sai lafiyayyen rice and stew da ta kawo ma khadijah da soyayyen kaji a warmer daban, Karfe sha daya Barrister sudais ya bar gidan kasancewar yana da wani case, ya tura ma khadijah text cewa xai dawo da yamma, karfe sha biyu ummun khaleel ta koma gida tare da su Shureim da yanxu ya saba da yaran sisters din khaleel amma har Ummu ta gaji da amsa tambayar da yake mata na cewa yaushe sudais xai dawo, shi dai a kai sa wajensa, tausayi yaron yake bata don tsakaninsa da Allah yake son ganin dan uwan nasa, a ko da yaushe dai ce masa take soon xai dawo, sai kusan azahar Mumy suka bar gidan, Khadijah ta raka su har gate tayi mata godiya a sanyaye, Mumy ta sa mata albarka sannan suka wuce da yaran nata, kafin dare frnds din Umma suka fara watsewa gidan, Shaheedah ma suka koma Abuja tare da Sadeeq, gidan ya rage daga Khadijah, sai Nanny da Umma da Wata aminiyarta. Bayan magrib khadijah bna xaune kan darduma tana azkar kira ya shigo wayarta, a hankali ta daga ta kai kunne ganin barrister sudais ne, yace "Amira xa ki iya fitowa yanxu plss, am outside" tace "Toh" daga haka ta mike ta fita, sai da ta fara gaya ma Umma sannan ta tafi kofar gida, fitowa yayi daga mota ganinta, yana rike da 3 years old daughter dinsa, Khadijah ta wara ido tana kallon kyakkyawar yarinyar ta xaga inda yake ta karbeta tace "Waow ya sunanta?" Sudais ya jingina da motar yace "Ur namesake, ita ma Amira ake kiranta, na kawo ta ne ta gaida Antyn ta" Khadijah tayi murmushi a sanyaye tuno kiran ta da mahaifiyar yarinyar tayi mata ranan da sudais xai rasu, tana taba dogon gashin yarinyar tace "Naji dadi sosai" Yace "Sure?" Ta kallesa da sauri tace "Eh mana, ko xaka bar min ita" yar dariya yayi yace "In dai kika shigo gidan ubanta ai taki ce ita" Wani murmushin Khadijah tayi bata dai ce komai ba, yana kallonta a hankali yace "Baxa ki shigo ba kenan, xaro ido tayi tace " Ka ji na fada haka?" Yace "Uhmn dont forget who is standing before you" ta dauke kai tana ci gaba da murmushi tace "A barrister" ya shafa kansa yana kallonta a hankali yace "Toh ya k'arin hakurin mu dear?" Tace "Mun gode Allah" yace "Har yanxu shureim din bai dawo gida ba?" Ta gyada masa kai tace "Bai dawo ba" yace "Ohk, ya su umma?" Tace "Suna ciki" kamar warce ta tuna da sauri tace "Sorry na bar ka tsaye mu shiga ciki" yayi murmushi yace "Aa bari in yi ta tsayuwa ta" ta turo baki tace "Allah na manta ne kayi hakuri, mu shiga ciki" daga haka ta nufi gate rike da Little Amira, ya bi ta da ido kafin ya bi bayanta, kan fararen kujerun dake compound din Sudais ya xauna duk yanda tayi da shi ya shiga ya gaida umma ya ki yarda wai sai gobe, tace "Toh bari in kai mata Little Amira ta gani" yace "Toh sai ki bar ta a can ki dawo ke kadai kar in yi rashin kunya gaban daughter na" dariya kawai khadijah tayi ta tafi tare da Amira dake ta waigo Abbanta ya daga mata hannu yana murmushi. umma ta xaunar da ita kan kafarta tace "Maa sha Allah, daughter na mai kyau da ita, Allah ya albarkace ki" khadijah tace "Naga kamar bata magana" Umma tace "A'a don dai bata san mu bane amma wannan ai ta isa tayi magana" fridge khadijah ta nufa ta bude ta dau ruwa da lemo ta daura kan tray ta sa glass cup sannan tace "Umma ina xuwa" Umma tace "Toh sai kin dawo" Har khadijah ta iso gun sudais idonsa na kanta, ta ajiye karamin tray din hannunta ta bude drink din ta xuba masa sai dai bata masa ba tace "Ya aiki?" Ya langwabar da kai yace "Ba dadi, Amira har yanxu you didn't answer my questions..." Ya lumshe ido ya bude yace "Ohk let me leave it this way, you don't want to answer my question" shiru khadijah tayi tana kallonsa, a hankali yace "A lot of things happened after I left you and the boys Amira, na koma damaturu gidanmu tare da Mamina amma gaba daya na rasa kwanciyar hankali, i was always sad then, thinking about you and the twins, hankalin Mami ya tashi a lkcn ta dinga cewa kilan asiri kika min ko kuma aljana ce ke, gashi nan abun na affecting dina, nan tasa aka tayi min rokan Allah, gradually dai na fara kokarin ganin na mance ku, na cire ku a rai na dinga harkokin gabana... saboda ku ko da ina da aiki a Abuja to baxan je ba, gaba daya na daina xuwa Abuja, daga Lagos, kano sai Kaduna and other States nake xuwa amma banda abj, dama ni din ba wai ina da time na yan mata bane, jiddah dai ce ita ma a Holland muka hadu lkcn ina karatu ita kuma tana tare da yayarta dake kasar tare da mijin ta, I never knew ma ashe Mami ta san mum dinta sun yi makaranta daya though it's not as if they are frnds, to dai a haka na fara neman jiddah har aka sa aurenmu ana saura few months bikin mu na hadu da ke ranan na fito daga gida, Amira saboda ke nasa aka daga bikin nan har na kusan watanni shiddah, a kwana a tashi kuma na kara neman a daga cos kin kusa haihuwa lkcn, let me make things brief, at the end fasa auren nayi gaba daya, suka maido min da lefen da na kai all because of you, and happily then Abbana supported me, but bayan rabuwar ki sai gashi na koma mata cos I don't have any option again, at first kamar baxata yarda ba daga karshe dai a cikin wata daya aka daura mana aure, 2 years da aurenmu da jiddah Allah yayi ma Mamina rasuwa bayan tayi fama da kidney problem, though before then duk na mata bayanin yanda aka yi na hadu dake, ban boye mata komai ba, kuma hankalinta ya tashi a lkcn but kawai sai ta maki fatan Allah ya hada ki da dangin mahaifiyar ki, daga nan kuma bata ce min komai ba, and gaskiya a lkcn kusan na ma cire ku a rai na daina damuwa cox I knw surely Allah na tare da ku, amma kullum sai na maku addu'a every blessed day, ba tonan asiri ba Amira ni ba wani jin dadin aure nake da jiddah ba, fitinar ta yayi yawa she is always pestering my life, ko kadan bana son hayaniya yana daga min hankali, bani da rest of mind idan ina gidana, ko irin weekend din nan ma ni na gwammace in tafi office in yi kallo, Amira I need a woman that i will find peace in, I need a better life partner, ina raga ma jiddah ne kawai saboda yarinyar nan dake tsakaninmu, and divorce is totally out if it baya cikin tsarin rayuwata, I need you plss Amira" Khadijah taji kanta ya mata nauyi sosai ta rasa abinda xata ce masa, bata san lkcn da hawaye ya dinga sakko mata ba tana kallonsa, deep down her kuma ta rasa me yasa khaleel ya fado mata. Shiru Umma tayi tana kallon khadijah, a hankali tace "Ko saboda me?" Khadijah ta langwabar da kai cikin sanyi tace "Umma I will be lonely all alone, I want him to be by my side" Umma tace "Life with him there won't be esay Khadijah, karatun ki na bukatar natsuwa sosai kin sani, shureim will ba a distraction, baxai yiwu ba Khadijah" da damuwa Khadijah tace "Umma ai shi ma makarantar fa xai dinga xuwa, plss ummata" Umma tayi shiru alamar bata san me xata ce ba kuma, can tana ci gaba da linke kayan da take tace "Rabani da shi dai kike son yi koh?" Murmushi Khadijah tayi kunya ya kamata tace "A'a wllh ummata" Umma tace "Gaskiya ne mana, ke gashi baki kusa da ni, grandson din ma kina son daukesa" Khadijah ta xaro ido, da damuwa tace "Allah sarki Ummata ba haka bane ba fa" Murmushi Umma tayi tace "Toh shkkn tunda kina son tafiya da shi sai ku je, Allah ya tsare" Sosai Khadijah taji dadi, Umma ta xauna gefen gadon tace "Yanxu ya xa mu yi da maganar sudais Khadijah, kin ga samu na yayi ya min magana...." khadijah tace "Umma ya san xan koma makaranta ai, daxu ma mun yi magana da ya xo, kuma kinga 100k da ya bani ai saboda xan tafi makaranta ne" Umma tace "Toh ai ban ce bai sani ba, kin san dai dole sai an je katsina koh?" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, bata son jin sunan garin ita kam, Umma ta mike ta ci gaba da abinda take tace "Shi kuma Aliyu ai ya kamata ki sanar masa xa ki tafi da Shureim din koh, ko kuma kije ma da yaron yayi sallama da mahaifiyar Aliyun" Khadijah dai bata ce komai ba idonta a kan wayarta. Can gidansu Khaleel kuwa Ummu ta sa driver yyi ma Shureim siyayya da taji tare xa su tafi UK da uwar sa, Khaleel dake xaune bedroom dinta yana duba kayan yace "Sun gode Ummu" Ummu tace "Khaleel ina son mu yi magana fa da kai, gashi gobe da sassafe xa ku wuce" ya maida hankalinsa gaba daya kanta kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "Ina ji Ummu" sure ya san kwanan xancen amma yayi pretending bai sani ba, Ummu ta kwantar da murya tana kallonsa tace "Abuu kasan fa saura wata daya kachal bikin ku da jawahir kuma naji ko magana baka yi" Khaleel ya shafa kansa yace "Ina sane Ummu" tace "Toh Alhmdllh tun da kana sane, amma ba wani shiri da xa ku yi ne?" Shiru yyi bai ce komai ba, can ya dago ya kalleta yace "Ummu tun da ba laifi bane ina son hada su da mahaifiyar yaron nan na aura....ina da interest a kanta" Ummu ta dinga masa wani kallo tace "Kana da hankali ma kuwa khaleel???" hade rai yayi, kan kace me ya juya xuwa Arabiya... toh nan fa ake yin ta, don Mai typing dai ba jin yaren take ba ina laifin ma yayi turanci, tun tana d'an tsintar daddaya har ya kai ya kawo ta ajiye takardar da Biro kawai ta dafe kai, ganin khaleel fa sai xuba larabci yake a fusace ga ummu sai kallonsa take ta kasa cewa komai mai typing tasan abun babba ne, ba fans ba, har ita tana son jin abinda khaleel ke cewa don haka ta juya da sauri don nemo kanwarta Ilham ta mata translating, can ita ma ta sameta xaune tana halinta wato nukurci, ashe dai ba xancen translating din larabci, rai ba dadi mai typing ta kwashi legs ta koma, nan ta ga har khaleel ya gama jawabinsa yana danna waya amma fuska a murtuke, Ummu ta d'an yi murmushi a hankali tace "Ni na isa khaleel? What am saying in here is that, ina laifin bayan anyi bikin naku da Jawahir sai ka auri Khadijahr babu mai hanaka yin hakan ae, hakan ma xai fi" Washegari Khadijah ta gama hada few abubuwan da xata bukata domin komawa UK, umma kuma ta hada ma Shureim nasa kayan cike da jin kewan yaron gashi khaleel ya rabasu da shi tun rasuwar sudais, karfe takwas saura khaleel ya taho gidan tare da shureim, Khadijah tana bedroom ta gama daukar masa kadan daga takalmansa, ganin na sudais a gun yasa lkci daya mood dinta ya canxa ta koma ta xauna a sanyaye, tun bayan rasuwarsa dama Umma ta bada komai nasa a gidan saboda Khadijah xata fi samun nutsuwa, takalman ma mancewa tayi bata bayar ba, Nanny ce ta shigo dakin tace "Khadijah jiran ki fa suke" a sanyaye Khadijah ta mike ta fito rike da takalman Shureim, driver ne daga gidansu Khaleel xai kai su airport din, Shureim dake jikin Umma ya sakko da sauri ya rungume Khadijah yace "I missed you Anty" ta shafa kansa tace "I missed you same" Umma tace "Toh kuyi maxa yana jiran ku a mota" Khadijah tace "Yanxu Shureim din ya shigo?" Umma tace "Yanxu ya shigo" Khadijah ta karasa gun umma ta rungume ta tace "Ummata sai mun dawo" Umma tayi kokarin ganin bata fara hawaye ba a hankali tace "Toh Allah maku albarka daughter, Allah ya tsare min ku, sannan ki kula da kanki plss" murya can kasa Khadijah tace "Nagode Umma" Nanny na rike da shureim cike da kewarsa xata rakasu bakin motar, Khadijah na isa bakin kofa ta juyo a hankali tana kallon Umma tace "Toh Umma ba a kai sa yayi ma Mumy sallamar ba kuma, I mean shureim" Umma tace "Lah kin ga ni har na manta, to ki yi ma Khaleel din magana sai ku fara biyawa can a gurguje ki kai sa kafin ku wuce airport" Khadijah ta gyada mata kai ta fita parlorn, Shureim ne ya bude back seat Khadijah ta dinga kallon khaleel dake xaune sanye da glasses a idonsa yana operating wayarsa, Shureim ya shiga motar sannan ta shiga tana daga ma Nanny hannu, gaishe da Nanny khaleel yayi ta amsa da fara'a ta masu Allah ya kiyaye hanya sannan ta juya ta koma ciki. Sai da suka dau hanya sannan khadijah ta kalli khaleel a hankali tace "Good morning" yace "Morning how was ur nyt?" Ta sauke idonta tace "Alhmdlh" Wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne, sai bayan da ya gama wayar Khadijah tace "Umma tace plss kafin mu tafi in kai shureim wajen mum din Aliyu su yi sallama, idan suka yi waya tana yawan tambayar ta shi...." Khaleel yace "Ohk then" daga haka ya fadi ma driver anguwar da xai fara kai su, tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso gidansu Aliyu, Bayan drivern yayi parking a inda Khaleel ya nuna masa, khaleel ya juya yana kallonta yace "Ku shiga toh" tace "Kai baxa ka shiga ba" da sauri yace "A'a, am waiting for you two a nan" a hankali khadijah tace "Ohk," daga haka ta bude motar ta sauka tana kallon Shureim tace "Come down" daga mata hannu yyi yace "Anty ki dauke ni" ta hade rai tace "Sakko my friend" khaleel yace "Ki daukesa mana ko baxa ki iya bane?" murmushi kawai tayi ta dauki yaron nata ta shiga cikin gidansu Aliyu yana daga ma khaleel da ya bi su da ido hannunsa, A hankali khadijah ta murda kofar taji a bude ta shiga, babu kowa parlorn, tana jin Shureim na ce mata gidansu wannan uncle din nan nasa ne, tana kokarin sauke sa kasa sai ga Aliyu yana sakkowa stairs, jallabiya ce baki jikinsa tayi saurin dauke kanta bayan sun hada ido, tana ta tsaye har ya iso inda suke tsaye, ya mika hannu ya karbi shureim komawa baya tayi da sauri don wani shock ta ji ta dalilin hannunsa da ya taba jikinta, shi kam sai kallonta yake ya maxa ya kawar da memoryn da bai son tunawa a ransa, Murmushi Shureim yake yana kallonsa yace "Uncle good morning" Aliyu ya shafa kansa shi ma yana murmushin a hankali yace "Morning how are you sweetheart" yace "Am fine" Kallon khadijah yayi suka kara hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yace "Good morning Iman" kame kame ta fara yi, can tayi saurin cewa "Ina kwana, wajen mumy muka xo" yace "Ohk tana Bedroom" taki yarda ta sake kallonsa tace "Toh kayi mata magana muna sauri ne" yace "mu je up stairs" daga haka ya fara tafiya ta bi bayansa xuciyarta na bugawa wannan tunanin da yake ita ma shi take a lkcn. A hankali ya bude kofar dakin mumy ya shiga da sallama, tana xaune da aminyarta, ta daga kai tana kallon Aliyu, ya sauke yaron hannunsa ya tafi da gudu ya hau kanta yace "Mama good morning" lkci daya bakin cikin dake tattare da fuskar Mumy yayi fading ta rungume yaron tana murmushi sosai tace "Kai da waye Shureim, wa ya kawo ka" Yace "Ni da Anty na" Aliyu ya juya yana kallon khadijah da ke tsaye bayansa ta ki shigowa ya koma gefe ya tsaya, Mumy na kallon ta tace "Maa sha Allah ashe tare ku ke, toh ki karaso mana Khadijah" kanta a kasa ta karaso ciki a sanyaye ta xauna tace "Ina kwana mumy" da fara'a mumy tace "Lafiya lau Khadijah ya gidan, ya su ummar ki?" A hankali khadijah tace "Suna lafiya Mumy" gaishe da kawar mumy tayi sannan tana kallon mumy tace "Mumy dama xan koma karatu ne kuma xa mu je da shureim shine Umma tace in kawo sa yayi ma ki sallama" Mumy tace "Allah sarki, amma naji dadi sosai wllh, Allah ya kai ku lafiya, ya bada abinda aka je nema" kallonta Kawai Aliyu yake jin abinda ta ce, Mumy ta mike tace "Bari in kai sa su gaisa da Abba yana nan" daga haka ta fita, Hajiya Salma dake ta kallon khadijah cike da tausayinta tace "Allah ya bada nasara kin ji Khadijah, sai a kula sosai" Khadijah ta sunkuyar da kai kasa tace "In sha Allah Mum na gode" Bayan kusan minti goma Mumy ta dawo, duk khadijah ta damu saboda khaleel da ta bari a mota, Mumy tace "Toh mu je kema ku gaisa da Abban koh" khadijah ta kasa dago kanta ta mike da kyar ta bi bayanta har xuwa side din Abba, da fara'a ya amsa gaisuwarta yana tambayarta mutanen gidansu, ba su dau lkci a parlorn ba suka fito tare da mumy, Lkci daya mood din mumy ya canxa a hankali tace "Mu shiga ki gaida iklima" Khadijah tace "Toh" daga haka ta bi mumy suka shiga dakin. Kallon iklima kawai khadijah take ganin yanda ta rame kamar warce ta shekara tana ciwo, cike da karfin hali tace "Sannu iklima Allah ya sauwake" kallonta kawai Iklima take ita ma ta kasa cewa komai, Mumy na kallon khadijah tace "Mu je" Khadijah ta bi bayan mumy a sanyaye, Mumy tace "Babu daman in baki turarruka tunda flight xa ku bi Khadijah, amma kar ki damu xan tura ma Maryam kudi a can ta siya ma ki, sai tayi ma Shureim ma shopping" murmushi kawai khadijah tayi tace "Ba komai mumy na gode" Har downstairs mumy ta rakata, Aliyu dake xaune parlorn tare da shureim ya mike ganin sun sakko, mumy tace "Toh Allah ya tsare, nagode Khadijah" Khadijah tace "Ameen mumy" daga haka ta bi bayan Aliyu da shureim don har sun nufi kofa, a tsakar compound din Aliyu ya jira Khadijah ta iso inda suke, bata yarda ta kalle sa ba xata wuce su ya riko mayafinta, juyawa tayi amma ta kasa kallon idonsa, murya can kasa yace "Baxa mu yi sallama ba?" Still ba tare da ta kallesa ba tace "Mumy na xo yi ma sallama ba kai ba" yayi murmushi yace "Ohk, Allah ya kiyaye hanya, sai mun hadu a can, cos am also leaving tomorrow" Khadijah bata tanka sa ba yana rike da shureim har suka nufi gate, kasa daurewa tayi daga karshe tace "Me ya samu iklima haka?" Da kamar Aliyu baxai ce komai ba sai kuma yace "She is suffering from Hiv" Khadijah ta xaro ido tana kallonsa a tsorace, yace "Yea, anjima dangin mahaifinta xa su xo su tafi da ita..." Lkci daya hawaye ya cika idon Khadijah tace "Toh Anty khadijah fa?" Yace "Tana asibiti, tot kin san tayi hatsari?" Khadijah ta girgixa kai tana kallonsa, yace "She had accident 2 weeks back" da damuwa tace "Toh ya jikin nata?" Yace "Ni tun lkcn da na kai su mumy ban san ke komawa ba so I don't knw" Khadijah tayi shiru duk jikinta a sanyaye, Aliyu yyi murmushi bai ce komai ba har suka fito waje, Khadijah ta bude back seat tana kallon khaleel da damuwa tace "Don Allah kayi hakuri mun bata maka lkci" ya d'an yi murmushi yace "No problem" tun da Khalil ya kalli Aliyu sau daya bai sake kallonsa ba, Aliyu yace "Barka da asuba" sai a sannan khaleel ya kara kallonsa yace "Good morning" Shureim ya shiga mota yana daga ma Aliyu hannu sannan khadijah ma ta shiga, suna hada ido da Aliyu ta sunkuyar da kanta, Aliyu na kallonta yace "Allah ya tsare" Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "Ameen" ya rufe masu motar, driver ya tada motar suka bar layin, shureim ya fiddo bandir din Dari biyar a aljihunsa yana nuna ma Khadijah yace "Anty wannan Papa din nan ya sa min kudin a aljihuna, I told him no but he didn't even listen to me" Khadijah ta dinga kallon kudin, ya ciro wani kudin yana nuna mata yace "Uncle ma ya bani wannan" Khaleel dake danna wayarsa bai dai ce komai ba, Khadijah ma ta rasa abinda xata ce. Khaleel na rungume da Shureim suka sakko daga cikin jirgi hannunsa daya rike da trolley din yaron, Khadija na biye da su har suka iso gun da xa su hau taxi, khaleel ya juya yana kallonta ganin yanda tayi laushi alamar ta gaji, murmushi yayi ya dauke kai, ta turo baki ta rungume hannayen ta, a Booth din taxin ya ajiye trolleyn hannunsa, ta karaso a hankali ta ajiye nata jakar a ciki, ya xaga ya shiga back seat ita ma ta shiga ta rufe, sai a sannan yana kallon mai taxin yace "Bridge street" har suka iso gida idon Khadija a lumshe suke, khaleel ya bude motar ya fito ya dau Shureim dake ta bacci, sai a sannan ta bude idanuwanta yace "Ae da mai cab din ya wuce da ke" ta bude side dinta ta fito, Ya fito da jakunkunan sannan ya ba ma mai taxin kudi, na Shureim ya dauka ta dau nata ta bi bayansa, suna isa bakin apartment dinsu, ya juya yana kallonta yace "Hope baki mance makulli ba" karamar jakar hanunta ta bude ta dubo makulin, ya fara bude nasa sannan ya amshi nata makullin ya bude mata yana kallonta, hannu ta kai xata amshi Shureim dake bacci jikinsa yace "Hey, ai ba gudu xan yi da shi ba hajiya" Wani kallo tayi masa ta wuce ciki ta rufe kofarta, duk yanda ta so ganin ta tsaftace ko ina kafin ta huta kasa yin hakan tayi don wani bacci ta dinga ji, wanka kawai tayi ta sauya kaya tayi slh sannan ta cire bedsheet din kan gado ta shimfida wani sannan ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa. Cikin bacci ta ji ana tashinta ta bude ido a hankali ta ga Shureim kusa da ita yace "Anty, uncle yace in tashe ki kiyi sllh ki ci abinci" mikewa xaune tayi tana kallon agogo taga bakwai na yamma ya wuce, ta kalli Shureim tace "Have you eaten?" Yace "Ehh uncle ya siya min, naki ma yana parlor" Shiru tayi tana kallonsa sai kuma tace "Kayi wanka?" Gyada mata kai yayi, ta sauka daga kan gadon tace "Bari in yi alwala" Ko da ta fito daga bayin bata ga Shureim ba, tayi sllh sannan ta fara gyare gyaren gidan tun daga dakin har parlorn, ta tsaftace ko ina tayi mopping sannan ta koma daki don dauko wayarta sanin Umma xata yi ta kiranta, mis cals biyu ta ga nata da na Barrister sudais, Umma ta fara Kira bayan sun gaisa Umma tace "Kun sauka lafiya?" Tace "Alhmdllh Umma" Umma tace "Ina Shureim din?" A hankali Khadija tace "Yana can wajen khaleel" Umma tace "Toh Ina gaishesa, ki kula kin ji ko daughter?" Khadija ta gyada mata kai tace "In Sha Allah Umma" Umma tace "Toh Allah maku Albarka" Khadija ta amsa da "Ameen" daga haka suka yi sallama da Umma, Sudais ta shiga kira, bayan wani lkci ya katse ya kirata, A hankali tayi masa sallama bayan ta daga,ya amsa yace "Ina kika shiga Amira?" Ta langwabar da kai tace "Bacci nayi" yace "Ohk, ya hanya?" Tace "Alhmdllh ya takwarata?" Yace "She's good, where is my son?" D'an murmushi tayi tace "Yana waje" yace "Waje kuma, babu sanyi ne?" Tace "Akwai amma it's not much" yace "Ohk try and get him a lot of sweaters, the cold won't be funny from next week I guess" tace "Haka ne" yace "Xan tura maki kudi sai ki siya masa very thick one's, kema ki siya" murmushi tayi bata ce komai ba, yace "Alryt then, sleep tight dear" tace "Toh nagode ka gaida min Amira" yace "Xata ji" daga haka ya katse wayar, kwanta tayi a hankali ta lumshe ido tana tuna moment dinsu da Barrister sudais, tashi tayi daga karshe duk a sanyaye ta fita parlor, abincin da khaleel ya siyo mata dake kan center table ta bude don ganin wani iri ne, ta d'an tabe baki ta rufe ta mike ta shiga kitchen ta kunna wuta, noodles ta fiddo xata dafa, jin motsi a waje ta leka window a hankali, xaune ta gansa kan kujera yana sanye da glass idanuwansa kan wani babban textbook yana rubutu, babban sweater ne jikinsa da neck warmer, Shureim ma dake sanye da sweater da head and neck warmer na tsaye daga bayansa ya jingina jikinsa yana kallon abinda yake yi, a hankali khaleel ya juyo ganin ta kunna wutan kitchen suka hada ido tayi saurin dauke kanta, mayar da dubansa yyi kan littafin gabansa yace "Xa ki fara koh?" Ta hararesa tace "Xan fara me?" Yace "Kin fi ni sani ai" Bata tanka sa ba ta bar wajen ta shiga yin abinda ya kawo ta kitchen din. Tana gama dafa indomien ta dauka ta fita ta koma parlor. Tana xaune parlor Idonta na kan wani material din karatun ta misalin karfe goma saura aka danna bell, mikewa tayi ta nufi kofar ta tsaya, a hankali tace "Yes?" Muryar khaleel taji yace "Hmm koh?" Bude kofar tayi ya shigar da Shureim parlorn ta yace "Alryt good nyt" tace "Allah ya tashe mu lafiya" juyawa yayi ya koma apartment dinsa, ta rufe kofarta ta kama hannun Shureim ta kashe wutan parlorn ta wuce daki tana rike da shi tace "Me yasa baka yi bacci can ba" yace "I said I want to come to you" bata ce komai ba ta rufe kofar dakin bayan sun shiga ciki. Washegari da safe Shureim na bacci ta fita xuwa supermarket, har ta dawo bai tashi ba ta ajiye duk abubuwan da ta siyo ta fara hada breakfast, muryar khaleel taji daga waje yace "Good morning" ta yi still don bata san yana gun ba, can dai tace "Ina kwana?" Yace "Hamdan, Ina kika je da sassafe cikin sanyin nan?" Ta d'an bude ido tace "Gadi na kake yi kuma?" D'an murmushi yyi jin bai ce komai ba ta leka window a hankali, 3qtr ne jikinsa da sweater mai hula yana tsaye bata dai ga abinda yake ba, kallonsa kawai take, lkci daya ya juyo tayi saurin dauke kanta, takowa yyi har gun windown yana kallonta yace "Ina kika je?" Rasa abinda xata ce masa tayi, can ta Sauke idonta kasa a hankali tace "Market" yace "What did you get?" Ta hade rai tace "Ina ruwanka" yyi murmushin sa mai kyau ya sauke hular kansa yace "Ohk then" daga haka ya juya ya bar wajen, Irish ta soya da kwai sai ruwan Lipton da ta dafa da kayan kamshi, har xata fita kitchen din ta dawo, ta fi minti biyu a tsaye kamar mai contemplating abinda xata yi, kawai daga karshe ta dau wani warmer ta debi Irish din da kwai ta xuba ruwan Lipton din a wani karamin flask ta ajiye su a gefe ta fita kitchen din, Bedroom dinta ta wuce ta tada Shureim dake bacci ta wuce bathroom da shi ta wanke masa baki ta masa wanka sannan ta sa yayi alwala suka fito, sai da ta gama shiryasa sannan ta shimfida masa darduma tace "Idan ka gama sllhn meet me at the parlor" daga haka ta fita, ba a dau lkci ba ya fito yace "Anty na gama, good morning" tace "Morning dear" kitchen ta tafi ta dauko flask din Lipton din ta mika masa tace "Ka kai ma uncle sai ka dawo ka karbi dayan" yace "Toh" ta bude masa kofa ya fita, ta danna bell din apartment din khaleel sannan ta juya ta koma ciki da sauri, Shureim na tsaye bakin apartment din khaleel ya bude kofar, dukawa yyi yana kallon yaron murmushi dauke fuskarsa yace "Good morning handsome" Shureim yace "Good morning uncle, Antyna tace in kawo maka" karba yyi yana kallon flask din sannan ya jawo yaron ciki, Shureim yace "Uncle tace it's remaining one" rufe kofar yayi yace "Kyaleta xata kawo da kanta" Khadija tayi ta jiran dawowan Shureim amma shiru, mikewa tayi ta bude kofa ta leka waje a hankali taga kofar apartment din nasa a rufe, kiran Shureim ta shiga yi, Shureim dake xaune yana cin bread and butter da khaleel ya basa da shayi ya mike da sauri yace "Uncle Anty is calling me" xaunar da shi yyi yace "Don't worry she will come in now" Khadija ta gaji da tsayuwa amma Shureim bai fito ba, komawa ciki tayi ta rasa yanda xata yi da Irish da ta dibar ma khaleel, daga karshe ta wuce kitchen ta dauko ta sa hijab ta fito waje, tsaye tayi tana kallon baturiyar dake bakin apartment dinsa, baturiyar ta mata murmushi tace "Good morning" dauke kai Khadija tayi kamar ana tilastata tace "Morning" xata koma ciki sai gashi ya bude kofar, Kallon Khadija yayi kafin ya dubi baturiyar dake masa murmushi tace "Good morning Dr Ayman...." Juyawa Khadija tayi ta shige apartment dinta ta rufe, Khaleel na kallon baturiyar yace "Morning Lydia, hw did u knw I am back?" Tace "I just met with Dr Ahmad, he told me you are back" shafa kai khaleel yayi a hankali yace "Ohk, we will meet later in the day, I am about going out now" tace "Ohk do you mind dropped me?" Ya girgixa kai yace "You get a taxi" daga haka ya rufe kofarsa, yana ta tsaye bakin kofa bayan kusan minti biyar ya bude kofarsa ya ga ta wuce, fitowa yayi yana kallon kofar Khadija, a hankali ya murda ya ji a bude ya shiga parlorn. Not edited.🤷🏻‍♀ Khaleel ya fi minti biyar tsaye parlon yana jiran ganin ta inda xata fito amma bata fito ba, karasawa yayi kan kujera a hankali ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujerar ya lumshe manyan idanuwansa, bayan wani lkci sai ga ta ta fito daga daki da hijab a jikinta, mikewa yyi yana kallonta amma bai ce komai ba, Babu yabo babu fallasa tace "How may I help you?" Yana shafa lallausan gashin kansa a hankali ce "Where is.... the food?" Tace "Wani abincin? I didn't cook with you ai" ya d'an kalleta na few seconds sai kuma ya nufi kitchen cikin takunsa na kasaita ta bi sa da ido, rike da warmer din Irish din ya dawo yana dubanta yace "This" daga haka ya bude kofa ya fita ta bi sa da harara ta ja tsaki. Khadijah na ji suka fita gidan da Shureim wajen karfe goma, kafin sha daya ta gama duk abinda xata yi a gidan ta kwanta duk da ta so tafiya makaranta amma ta bari gobe kawai, ganin bacci ya ki xuwa mata ta dauko kayan karatun ta ta shiga yi, tana ta xaune har azahar yayi, ta mike daga karshe ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta kwanta, lkci daya bacci ya dauketa. A hankali khadijah ta bude idonta bayan wasu awanni ta mike xaune cikin sanyin jiki tana tunanin mafarkin da tayi, bell taji an danna wanda hakan sai da ya d'an tsorata ta, bayan wasu yan dakiku ta mike tsaye da kyar har lkcn mafarkin ya kasa fita a xuciyarta, jin an kara danna bell din ta sa hijab ta fita kamar mai counting steps dinta, tana isa gun kofar ta bude a hankali, Vanessa da Angela sai Maryam ta gani bakin kofar, sosai gaban Khadija ya fadi ganin Maryam bakin kofar, da farko kallonta ta dinga yi, sai kuma ta kirkiri murmushi tana masu sannu da xuwa ta basu hanya suka shigo parlorn, mamaki ta dinga yi a ranta, me ya kawo Maryam gidanta, after all she isn't her course mate nor her frnd, bayan sun gaisa suka mata gaisuwar Sudais, khadijah ta mike ta wuce kitchen don kawo masu ruwa da cakes din da ta siyo daxu da safe da ta fita, Maryam na kallonta tace "Mumy tace da daya twin din kika taho koh?" Ba tare da Khadija ta kalleta ba tace "Ehh tare muka xo" Maryam tace "Yana Ina?" Khadija tace "Ya fita ne" Maryam bata sake cewa komai ba, Khadija suka dinga hira da su Vanessa, sai dai hirar duk ta makaranta ce bayan kusan minti talatin suka ce mata xa su koma, har waje ta rakasu inda xa su samu cab, wani cab ne yyi parking dai dai su, aka bude cab din khaleel ya fito tare da Shureim da wani leda hannunsa, kallonsa kawai Maryam take, ya wara ido ganinta yace "Isn't this Maryam?" Yar dariya tayi tace "A nan anguwar kake dama Dr khaleel?" Yace "Sure, me kika xo yi nan?" Ta nuna masa Khadija tace "My frnd, mun xo mata gaisuwa ne yaron ta ya rasu" ya kalli khadijah yace "Ohh that's nyc, a schl kika santa kenan" Maryam tace "Eh a schl na santa" yace "Good" Maryam ta karasa gun Shureim tana kallonsa a hankali tace "Hello boy" gaisheta yayi, ta amsa tana murmushi jin muryarsa kamar na Aliyu, Su Vanessa ma suka taho gunsa duk ya gaishe su da turanci, ita dai Khadijah na tsaye, Khaleel na kallon Maryam yace "Alryt bari in shiga ciki Maryam, sai anjima" tace "Yauwa Dr, ya mutuniyar fa?" Har ya fara tafiya ya tsaya yace "Wai jawahir?" Tace "Ehh" yace "Haba ai ke ya kamata in tambaya, kun fi kusa" Maryam tace "Au haka ma xaka ce" Yace "Yes, nasan yau ma baxa ku rasa waya ba ni kam bata kira ni ba" Maryam tace "Lallai ma, ita ce ma xata kira ka kenan, soon ma xa su xo hutu nan da yayarta ar" Khaleel ya d'an kalleta yace "Really?" Girgixa kai Maryam tayi tace "Dad dina naji ya fadi haka nima" Ya dauke kai ya nufi cikin gida yana rike da Shureim yace "Allah ya kawo su lafiya" Taxin da Khaleel ya sauka suka hau Khadija ta daga masu hannu tace "We'll meet in school tomorrow, thank ya all" daga haka ta wuce ciki. Khadija na kitchen tana girkin lunch khaleel ya taho ya tsaya gun window yana kallonta yace "Ya kike?" Dauke idonta tayi daga kallonsa tace "Lafiya lau" Shureim dake kusa da shi a tsaye yace "Anty I am missing you" Khaleel yace "Bude masa ya shiga" kallon Shureim tayi sannan ta ajiye wukar hannunta ta isa gun kofar ta bude, Khaleel ya shigar da Shureim ciki sannan ya fixgota har sai da ta kusa faduwa, ya jawo kofar ya rufe gam, ya jinginar da ita jiki yana mata wani kallo murya can kasa yace "Ni kike daga ma hanci" A tsorace tace "Kaga bana son haka ka bari, ka kyaleni plss" Duk ta kasa kallon idanuwansa da ya tsare ta da shi ga kamshin sa da ya cikata, A hankali yace "Fushin me kike yi da ni?" cikin rawar murya tace "Toh Fushin me xan yi da kai Dr, don Allah ka sakeni" d'aga kanta yayi tayi saurin runtse idanuwanta xuciyarta na bugawa, ya dinga kallon lips dinta, a hankali ya saketa yace "Where did you know Maryam from?" Ta shiga kokarin bude kofarta da sauri, ya rike handle din kofar yace "Au Ina maki magana xaki wuce?" Ta juyo kamar xata yi kuka tace "Ni ban santa ba sosai fah, kawai ina ganinta ne a schl kawar course mates dina ce" yace "Ohk, don't frnd her for some reasons kin ji?" kallonsa tayi da sauri, lkci daya tayi saurin kauda kanta xuciyarta na bugawa, his eyes are always not encouraging, d'an murmushi yayi a hankali yace "Ki gaya min meye da idona Khadijah?" Ta hade rai tace "I don't like them" wani murmushin yyi kamar me rada yace "Xan koya maki son su" murda kofar yayi ya bude ta juya da sauri ta shige kitchen din ta rufe kofar da makulli fuskarta daure. Shureim na cin abincin da ta xuba masa bayan magrib yace "Anty uncle yace gobe xan fara xuwa schl, we even went to the schl, uniform din na gidansa, in je in karbo?" Khadija dake ta kallonsa tace "I didn't send you" yace "Ohk" sannan ya ci gaba da cin abincinsa. Washegari da asuba khaleel ya miko mata uniforms din Shureim ta kitchen, rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta karba tana kallonsa a hankali tace "Mun gode" ko kallonta bai yi ba ya wuce. Karfe takwas saura khaleel yayi dropping Shureim a makarantar da yayi enrolling dinsa, Khadija dake xaune bayan motar ta bi Shureim dake daga mata hannu da kallo har aka wuce da shi cikin makarantar, khaleel yayi parking in da ya saba ajiye ta a schl ya juya yana kallonta, ta bude motar a hankali ta fito,, bata ce komai ba ta kulle motar ya ja motarsa ya bar wajen, a sanyaye ta karasa department dinsu don saura few minutes a shiga lectures. Karfe sha biyu saura Khadija ta fito daga lectures, cafeteria ta tafi ita kadai ganin Maryam na tare da su Vanessa, tana xaune ita kadai a cafterian da lemonade a gabanta idonta a kan wayarta tana dannawa, kujerar dake kallon nata taga an ja ta daga kai da sauri, sosai gabanta yayi mugun faduwa bayan sun hada ido, tayi saurin dauke idonta, xaunawa yayi yana kallonta a hankali yace "Hi Iman" kasa cewa komai tayi ta kuma kasa dago kanta, bayan few seconds ta dago da kyar tana dubansa tace "Hello" Murmushi yayi yace "Ya boko?" Kasa amsawa tayi lkci daya little Sudais dinta ya fado mata, taji xuciyarta ya mata rauni, ganin tayi shiru ya fiddo wayarsa ya fara dannawa, a hankali tace "Ya su mumy" yace "Na baro su lafiya, how is Shureim?" Tace "Yana schl" yace "Har kinyi enrolling dinsa a nan?" Tace "Ehh" shiru ya d'an yi, kafin a hankali yace "How much did you spend Iman?" Ta kallesa lkci daya ta hade rai tace "What about it?" ya girgixa kai da sauri yace "Ohk, I am sorry I asked" bata ce komai ba, ya mike yana kallonta yace "Alryt, I will be on my way now Iman, my regards to Shureim" da ido ta bi sa, har ya tafi ya dawo da sauri ya sa hannu a aljihunsa yace "I think I've got something here" Chocolate guda daya ya fiddo ya duka yana kallonta ya mika mata yace "Ki ba Shureim plss" a hankali ta sauke idonta daga kallonsa ta karbi chocolate din tace "Ohk" yace "Thanks" daga haka ya mike ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya bace mata, kallon chocolate din hannunta tayi ta bude jakarta ta saka a ciki, tayi tagumi tana tunanin me yasa in dai ta ga Aliyu sai little Sudais dinta ya fado mata, or is it because of the resemblance, jin wayarta na ring ta sauke kai a hankali tana kallon mai kiran nata. Sorry for the short chappy kilan in kara post around one na dare😦 A hankali khadijah tayi picking wayar ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren ya amsa yace "Ya kike Amira?" Khadija tace "Alhmdllh ya aiki?" Yace "Lafiya lau, account number ki xa ki turo min yanxu" shiru ta yi na wani lkci kafin tace "Barrister.... Shureim fa yana da kayan sanyi, wllh you shouldn't bother...." Katse ta yayi yace "I am not asking for you opinion Khadijah" a hankali tace "Toh shkkn, ya Amira fah?" Sudais yace "Tana gun ummanta" bai karasa maganar ba ya ga jiddah tsaye kusa da dinning din da yake xaune tana kallonsa, ya dauke kansa yace "I will call you later Amira" katse wayar yayi ya ajiye, jiddah tayi dariya tana tafe hannu tana masa wani kallo tace "Cin amanar har cikin gidana Aliyu?" Sudais bai kalleta ba balle ya tanka ta, lkci daya idanuwanta suka kankance tace "Toh ko ma wace yar iskar ka samu wlh wlh sai tayi da ta sanin sanin ka a rayuwar ta, sai na nuna mata tayi kadan tayi kishi da ni, ba ma xai yiwu bane, mu xuba da ita sai dai idan ba mijina take cusa ma kanta ba" mikewa yayi yana kallonta yace "Wannan da kike gani wllh ta fi ki k'ima a idanuwana Jiddah, kuma kina nan xaki ga ta shigo gidan nan ta koya maki yanda ake kula da miji" bai sake sauraranta ba ya bar parlorn, jiddah ta kasa tsaye gu daya, ta ja kujera ta xauna da kyar xuciyarta na tafarfasa, lkci daya tayi wani murmushi tace "Babu boka babu malam, amma kai xaka bata shawarar ta rabu da kai, mu dai je xuwa, da kuluwa take xancen" Har khadijah ta iso gun motar khaleel idonta na kansa, shi kuma yana jingine jikin motar yana danna waya, bai san ta iso ba kawai kamshin ta ya ji, ya daga kai yana kallonta, a hankali tace "Good evening" ya mayar da wayar aljihunsa yace "Ya lectures?" Tace "Alhmdllh, karfe nawa su Shureim ke tashi?" Ya buda ido yace "Ke fa yarinyar nan baki da kara" turo baki tayi tace "Toh me nayi, am just asking" yyi murmushi yace "Daga nan xa mu dauko sa, yanxu suke tashi su ma" ta karasa ta bude front seat ta shiga, shi ma ya shiga motar ya tada suka bar wajen, har suka iso makarantar shureim khaleel bai ce komai ba ita ma haka, ya bude motar ya fita, ba a dau lkci ba suka dawo tare da Shureim, xagayowa Shureim yayi ya bude inda khadijah take xaune ya rungumeta yace "Anty good afternoon" ta shigo da shi cikin motar ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa da murmushi tace "How you sweetheart?" Yace "Fyn Anty, I love the schl, I wish Sudais will come here also, am really missing him" Khadija bata ce komai ba, inda sabo ta saba, don bbu ranar da xai wuce Shureim baxai mata xancen Dan uwansa ba, he is always wishing Sudais is with him, lkci daya chocolate da Aliyu ya bata ya fado mata, ta bude jakarta a hankali ta fiddo chocolate din ta mika masa, karba yyi cike da jin dadi yace "Waow, Anty ke kika siya min?" Girgixa masa kai tayi tace "No" ya wara ido ya juya yana kallon Khaleel dake driving yace "Uncle kai ka siya min?" Khaleel ya kallesa yyi murmushi yace "No bani bane" Shureim ya mayar da dubansa kan Khadija yace "Toh Anty waye ya siya min" Khadijah tace "Idan baxa ka ci ba bani in cinye" Shureim ya bude chocolates din yace "Noo Anty ina so, ai irin wanda kind uncle din nan yake ba mu a gidansu maman nan ne, he told me his name is Dr Aliyu, Anty ina son a kai ni gidansu a Nigeria" Ita dai khadijah kallon yaron kawai take, ya gutsura ma khaleel ya mika masa yace "Uncle taste it" khaleel yyi murmushi yana girgixa kai yace "Noo thanks son, cinye abun, ko Anty kar ka ba" dariya yaron yayi bai ce komai ba, can ya kalli Khadija, alama yayi mata da ta bude bakinta, tayi murmushi ta bude masa bakin ya sa mata chocolate din a hankali yana satan kallon Khaleel. Suna isa gida bayan khaleel yyi parking khadijah ta bude motar ta fito tare da Shureim tana kallonsa murya can kasa tace "Thank you" fitowa yayi yana mimicking din muryarta yace "Thank you" daga haka ya rufe motarsa, hararansa ta fara yi sai kuma tayi murmushi ta wuce apartment dinta rike da hannun Shureim, ya jingina da mota ya rungume hannayensa ya bi su da kallo. Tun da Khadijah ta fito daga lectures yau take xaune cafteria ta rasa dalili, har lkcn lectures din karfe biyu yyi tana xaune gun bata tashi ba, Maryam ce ta shigo cafterian tare da wata kana ganinta kasa yar Nigeria ce, Maryam na ganin Khadijah tayi murmushi tace "Khadijah kina nan ashe, ya lectures?" Khadija tace "Alhmdllh ya naki?" Maryam tace "Alhmdllh" Maryam ta kalli yarinyar dake gefenta tace "Deejah meet ur namesake Khadija, tana studying pharmacy ne a nan, she is also a Nigerian from kaduna" Warce Maryam ta Kira da Deejah tayi murmushi tace "Its nyc meeting you namesake" Khadija tayi murmushi sosai tace "Nyc meeting you too" gun Khadija suka xauna su biyun, Maryam tace "Sun xo hutu ne nan da kanwarta shine na shigo da ita taga Cambridge" Deejah na kallon Maryam tace "Khadijah tana min kama da Safeenah, ko ke baki gani ba" Maryam ta kalli Khadijah da kyau, sai kuma tayi dariya tace "Suna dai yanayi ba kama ba, and the nose..." Deejah tace "Exactly, dama Ammi xata ganta cewa xata yi Safeenah ce" ita dai Khadijah bata ce komai ba banda murmushin da take yi, haka kawai taji tana son Deejah.... drinks da snack Maryam ta sa a kawo masu su uku, Maryam na shan drink din gabanta tace "Deejah wai me yasa jawahir ta ki biyo mu?" Khadijah ta daga kai tana kallonsu, Deejah ta tabe baki tace "Kilan kar su hadu da Dr Ayman" Maryam tace "Tab, Ayman sau biyu yake shigowa makarantar nan a sati, Mondays and Thursdays, I think ranakun yake nasa karatun" Maryam ta kalli Khadijah tace "Kingakiwa neighbor dinsa ce Khadijah fa" Deejah ta kalli Khadijah da sauri tace "Haba dai" Maryam tayi dariya tace "Wlh, ranan da naje gidanta tare da frnds dinmu na gan sa, yace min nan yake" Deejah tace "Wani anguwa kenan?" Maryam ta fada mata anguwar tana cin snack din hannunta, Deejah tace "Ayya, daxu dai naji da suka yi waya jawahir ta bashi address yace xai je anjima da yamma" Maryam tace "Gidan mu?" Deejah tace "Sure" Maryam tace "Ohk ai gwara dai ya je" Khadijah ta mike tana murmushi tace "Maryam xan shiga lectures yanxu" Maryam tace "Haba to baki dau snack din ba ai da drink" Khadija ta kirkiri murmushi ta dauka tace "Toh nagode" daga haka ta bar cafteria din bayan tayi ma Deejah ma sallama, Deejah ta bi ga da ido, kafin ta kalli Maryam tace "Maryam joke apart wllh kamar Safeenah, idan kin lura har da Maimoon ma suna yanayi, Maryam tace "A coincident" wani gun Khadija ta tafi ta xauna don sun cika mata kunne da surutu ne gaskiyar magana. Tana ta xaune nan har khaleel ya kirata bayan kusan awa daya, tana ta kallon Kiran kafin ta daga yace "Are you done with lectures Khadijah?" Girgixa kai tayi tace "No, idan na gama xan taho gida, kawai ka tafi" yace "Karfe nawa xa ku gama?" Turo baki tayi da kamar baxa tace komai ba sai kuma tace "Anjima" yace "Toh Ina jiran ki" daga haka ya katse wayar. Karfe hudu saura Khadijah ta isa gun da Khaleel ke jiran ta, fuskarta daure ta bude motar a hankali ta shiga, yana kallonta yace "Ya lectures?" Kamar ana tilastata tace "Fyn" sai bayan da suka bar cikin makarantar yace "Wa ya bata maki rai?" Shiru tayi bata ce komai ba, bai sake cewa komai ba har ya isa schl din Shureim ya fita ya daukosa ya dawo sannan suka dau hanyar gida, a waje yyi parking yana kallon Khadijah da ta bude motar ta fita, Shureim ma ya fito, yace "Am going somewhere now, sai na dawo" Khadija ta d'an buda ido tana kallonsa tace "Gun jawahir din ne somewhere??" Kallonta ya dinga yi da mamaki, ta tabe baki tace "Wai somewhere...." daga haka ta kama hannun Shureim suka wuce ciki, shafa kansa yayi ya tada motar yayi reverse ya bar wajen. Da daddare Khadijah na parlor aka danna bell, ta mike ta isa gun kofar tace "who is there" yace "Somebody" bude kofar tayi tana kallonsa ya mika mata ledan hannunsa yace "Ki ba Shureim?" Bata karbi ledan ba tace "Yayi Bacci" yace "Toh ki ajiye masa" Bata yarda ta kallesa ba ta amshi ledan daga haka ta rufe kofarta. Washegari da sassafe Khadija ta fito apartment dinta tare da Shureim da tayi ma Shirin makaranta, ganin waje xa su fita Shureim yace "Anty baxa mu jira uncle ba yau" hararansa tayi bata ce komai ba har suka fita ta tsayar masu da cab, sai da ta fara dropping dinsa schl sannan ta wuce nata makarantar. Tare da su Vanessa suka fito daga lectures misalin karfe sha biyu, tun daga nesa ta hangosa da wani bature suna tahowa, har ya iso inda suke xaune bai gansu ba yana magana da baturen Khadijah ta dinga kallonsa har suka wuce, still ta bi sa da ido, muryar Vanessa ne ya dawo da ita tana cewa su je su ci abinci, mikewa tayi a hankali suka bar wajen xuwa cafterian da suka saba xuwa, xaune ta ga Aliyu da Baturen a ciki, suna shigowa kuma ya ganta, ta dauke idonta daga kallonsa bayan sun hada ido, waje daya suka xauna tare da su Vanessa, Vanessa tayi masu ordering abinda xa su ci, drink kawai Khadija ta sa aka kawo mata, duk suka gama cin abincin Vanessa ta biya bill sannan suka mike, Khadijah dai na xaune bata tashi ba, Vanessa tace "Ain't you attending the next lecture?" Khadijah tace "I will be going home soon" Tana kallon su Vanessa suka wuce, dai dai lkcn da Baturen dake tare da Aliyu ya mike shi ma ya fita, tasowa Aliyu yyi ya dawo inda take ya ja kujera ya xauna yana kallonta yace "Good afternoon" ba tare da ta kallesa ba tace "Same...." Ya shafa kansa yace "Ya Shureim?" Tace "Yana schl" yace "Ohk kin gama lectures yau ne?" Girgixa kai tayi tace "Aa xan wuce gida ne" yace "Ohk, yanxu?" Sai a sannan ta kallesa tace "Soon" yace "Alryt if you are ready mu je sai in yi dropping din ki" tace "I prefer cab" yace "Ohk then," wayarsa ya mika mata yace "Sa min digit din ki anjima da yamma xan kawo maki sakon Shureim or I give Dr.. Ayman, Maryam tace min same house ku ke da shi, and I saw him a gidanmu jiya" Khadijah bata ce komai ba da farko, can dai tace "Sakon me?" Yace "Shine xan bada a kai maki ai" Ta Girgixa kai ta karbi wayarsa ta na sa number ta tace "You call me instead" daga haka ta mayar masa da wayarsa, ita ta fara mikewa kafin shi, ya bi bayanta suka fita cafterian, sai da suka isa gun motarsa ya kalleta yace "Let me drop you Iman" Bude mata motar Aliyu yayi yana kallonta, ta ki kallonsa tana dai tsaye kamar me contemplating ta shiga ko kar ya shiga, a hankali ta karasa gun motar daga karshe ta shiga ya rufe, sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar. Sai da suka hau saman titi yace "Wani anguwar kike?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Tun da Maryam ta gaya maka gidanmu daya da Dr Ayman nasan ai baxata rasa gaya maka address da house number ba" Murmushi kawai Aliyu yyi yana ci gaba da driving dinsa bai ce komai ba, sai da suka iso street din ya kalleta yace "I only know the street...." ta fada masa number din gidan, yana isa dai dai gidan yayi parking yana dubanta yace "Wani schl din Shureim ke xuwa Iman?" Sai a sannan ta kallesa tace "I don't think I have to tell you" Yana shafa kansa yace "It isn't an offense ai Iman" ta bude motar ta fita tace "Thanks for the ride" murmushi kawai yayi ta wuce ciki ya bi ta da kallo, tabe baki Khadijah tayi ganin babu motar khaleel a garage ta fiddo makullinta cikin jaka ta bude kofar ta shiga ciki, wanka tayi sannan tayi sllh ta canxa kaya ta fito parlor, xaunawa tayi tana tunanin abinda xata girka, can ya mike ta wuce kitchen din, shinkafa da miya tayi deciding tayi sanin Shureim na son sa sosai, tana parboiling shinkafa taji shigowar motar khaleel gidan, da gudu ta fita parlor ta isa gun kofa ta sa makulli sanann ta koma kitchen ta ci gaba da abinda take, bell taji an danna, ta hade rai ta tura kofar kitchen din, ba a sake dannawa ba sai ringing din wayarta dake parlor ta ji, ta bude kofar ta fita ta dau wayar tana kallon screen din, ganin khaleel ke kiranta da har xata ajiye sai kuma ta daga ta kai kunne ta ki cewa komai, yace "Bacci kike ne?" Tace "What about that?" Yace "Ohk, naga takalman ki kin bari a waje, and ki fito ku gaisa da jawahir" Wani kallo tayi kamar yana gabanta tace "For what?" A hankali yace "Am waiting Khadijah...." daga haka ya katse wayar, mamaki ne ya cikata, a kan wani dalili xa ta gaisa da jawahir, tsaki tayi xata ajiye wayar text ya shigo nasa, ya budewa tayi tana kallon content din, "Plsss" abinda ya turo mata kenan, ta turo baki sai kuma ta harari kofar, a hankali ta isa gun kofar ta bude, tsaye ta gansa shi da jawahir din, suna hada ido jawahir tace "Sannu Khadijah ya gida?" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Lafiya lau, fatan kin xo lafiya" Jawahir tace "Alhmdllh, ya hakuri?" A hankali Khadijah tace "Alhmdllh nagode" kallonta kawai khaleel yake, Jawahir tace "Dama Dr yace in taho in maki gaisuwa ne" Khadijah tace "Ayya nagode, baxa ki shigo ba" khaleel na kallon jawahir yace "Shiga sai kiyi sllh" jawahir tace "Toh bari in yi" daga haka ta shiga parlorn Khadijah, ba tare da Khadijah ta kallesa ba ta rufe kofarta fuska daure, murmushi kawai khaleel yyi yana kallon kofar. Jawahir na kan darduma xaune parlorn Khadijah ta kawo mata abinci a plate, jawahir tace "Ayya na ci abinci Khadijah, am not hungry" Khadija tace "Haba ki ci ko kadan ne" Jawahir tace "Da gaske bana jin yunwa ki bar sa kawai" juyawa kawai Khadijah tayi rike da abincin ta koma kitchen, tana fitowa jawahir ta mike tace "Toh nagode bari in je" Khadijah tace "Welcm" daga haka ta fita, tana ji ta bude apartment din khaleel ta shiga, tabe baki Khadijah tayi, ta ja tsaki ta wuce daki, mayafinta ta dauko ganin Shureim ya kusa tashi a schl, tana fita apartment dinta ta sa makulli ta nufi waje, cab ta samu ya kai ta har makarantar, Rungume ta Shureim yayi bayan ya fito daga cikin makarantar yana kallonta yace "Anty me yasa uncle bai xo ba" Khadijah ta hade rai tace "Don't ask me that again" daga haka ta kama hannunsa suka shiga cab din, suna isa gida ta biya mai cab din ta wuce ciki tana rike da hannunsa, sai kallon kofar khaleel take ta tabe baki ta bude kofarta ta shiga parlor da Shureim, makulli ta sa ma kofar, ta Shiga bedroom da shi ta cire masa uniform, tayi masa wanka ta shirya sa ta sa masa rigar sanyi sanan ta sa yayi sllh, suka fito, a plate daya ta xuba masu abincin, tana ci a hankali tana kallonsa, muryarsa taji yace "Anty yaushe Sudais xai dawo? Umma tace min after one month, kuma ai one month yayi ai koh?" Khadijah ta sauke idonta daga kallonsa tana ci gaba da cin abincinta tace "Nima ban sani ba, sai dai anjima idan Umma ta kira ka tambayeta" ya langwabar da kai yace "Ohk" kallon wayarta dake ring tayi taga sabon number ke kiranta, ta dauka ya kai kunne, muryar Aliyu taji yace "Iman" a hankali tace "Na'am" yace "Fito ki amshi sakon Shureim din" kallon Shureim tayi tace "Ohk" daga haka ya katse wayar, ta mike tana kallon Shureim tace "Mu je ka rakani Shureim" ya tashi ta dauko plate ta rufe abincin, ta dau tissue ta goge masa bakinsa sannan ta dauko masa takalmansa ya sa suka fita, ba dai dai kofar gidan yayi parking ba, Khadijah na rike da hannun Shureim ta tsallaka xuwa side din da yake, daga cikin motar Aliyu ke kallonsu ko kiftawa babu har suka iso dai dai inda yayi parking, a hankali ya bude motarsa, Shureim na ganinsa ya nufe sa da gudu cike da murnar ganinsa Aliyu ya daga sa ya rungume sa ya lumshe ido, cike jin dadi shureim yace "Uncle ka kai ni wajen mama plss" Aliyu ya dago kansa yana kallonsa yayi pecking goshinsa yace "Mama tana Nigeria ai, idan kun yi hutu sai in kai ka" Shureim yace "Uncle plss ka tafi da ni" Aliyu ya kalli Khadijah dake wasa da ring din hannunta, a hankali yace "Thanks for coming out Khadijah" Sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, jin bata ce komai ba ya bude bayan motar ya fiddo babban leda, Shureim yace "Uncle Anty ta bani irin wannan chocolate da kake bani da Sudais..." Aliyu ya wara ido yace "Da gaske?" Yace "Yes uncle" ya kalli Khadijah ya langwabar da kai yace "Toh Anty ki bari muje in siyo masa irin chocolates din, sai mu dawo yanxu" Khadijah bata ce komai ba, Aliyu yayi kasa da murya yace "Ko xa ki raka mu?" Girgixa kai tayi tace "No way" daga haka ta tsallaka ta wuce ciki abun ta, Aliyu ya bi ta da kallo kafin yayi murmushi ya xaga ya bude front seat ya xaunar da Shureim, ya dawo ya shiga driver seat ya tada motar ya bar street din. Khadijah na dai dai apartment dinta khaleel ya bude motar ya fito rike da makulin motarsa, ganinta yace "Let me go pick Shureim, na sha'afa wllh" a takaice tace "You don't worry na dauko sa, Ni ban sha'afa ba" daga haka ta Shiga ta rufe kofarta, ya fi minti daya a tsaye kafin ya koma nasa apartment din. Shopping mall din da Aliyu ya kai Shureim kusa da gidan kanwar Abbansa yake, don haka yana gama masa shopping ya shiga gidan tare da Shureim, Tasowa Maryam dake xaune parlor da Deejah tayi ganinsa ta tafi da sauri dau yaron ta rungumesa tace "Waow yau ga Shureim a gidanmu, Yaya Aliyu a ina ka samo mana shi? Jiya kuwa muka hadu da mum dinsa a cafteria a schl" Maryam ta kalli Deejah dake parlorn tana kallon Shureim da expression na Waow a fuskarta tace "Kin tuna warce muka gani a cafteria jiya?" Deejah ta xaro ido tace "Wai Khadijahr nan da nace maki suna kama da Safeenah??" Maryam tace "Yauwa ita" da mamaki Deejah tace "Kar ki ce min ita ta haifi yaron nan?" Maryam tayi dariya tace "Yaronta ne mana, yan biyu ne ma, daya ya rasu" lkci daya jikin Deejah yayi sanyi ta mike tace "Allah sarki" Aliyu dai bai tanka su ba ya wuce sama bayan ya amshi Shureim hannun Maryam don kai ma Antyn sa shi, Deejah ta bi su da kallo murya can kasa tace "but naga yaron na kama da cousin din naki ai, I mean sosai fa" Murmushi kawai Maryam tayi sai dai bata ce komai ba, bude kofa aka yi sai ga jawahir ta shigo, wurgar da takalman kafar tayi, ta jefar da jakar hannunta kan kujera ta xauna, Deejah dake ta kallonta tace "Ke kuma meye haka? me ya faru?" A fusace ta fara magana tace "Wllh Anty deejah na gaji da Ayman, abinda yake min ya fara isata, am just tired" Maryam ta xauna kusa da ita tace "Toh fah, me kuma ya hada ku?" Mikewa Jawahir tayi rai bace tace "Don rainin hankali sai yayi ta wani hada ni da yarinya da ban san meye tsakaninsu ba, I really want to know wacece yarinyar nan, sanann ta wani dinga daga min hanci tana amsa min da kyar kamar dole.... Da yaje Nigeria gaba daya lkcn sa ita yayi dedicating ma, ashe ma gidansu daya a nan ban sani ba sai daxu da ya fita yake gaya min, Ni kuma abinda yasa ma na sake ma yarinyar fuska tun farkon da muka hadu a Nigeria naga tana min yanayi da Safeenah ne, ban da haka tayi kadan in ganta da saurayina in raga mata, sannan ni a tunani na matar aure ce don ina ganin yaran nan nasan nata ne but now I am totally confuse...." Deejah ta kamo hannunta a hankali tace "Kilan it's not what u are thinking lil sis, may be they are just frnds and neighbors, Kar ki bari shaidan ya ci galaba a kan ki, na kuma san ki da hakuri sosai jawahir so meye nasa wannan a ran ki?" Kamar xata yi kuka tace "Anty da kyar fa take amsa min magana idan na mata, kamar ma haushi na take ji shi kuma sai yayi ta sa ni in mata magana, to idan ba budurwarsa bace ita me yasa xata dinga haka" Deejah ta sauke ajiyar xuciya tace "But ni dai she was very free with me da muka hadu a cafteria jiya" Jawahir ta jinginar da kanta jikin kujera cike da damuwa bata ce komai ba, tausayinta Deejah ta dinga ji, Maryam dai na tsaye tana kallonsu ta kasa cewa komai, mikewa Jawahir tayi ta dau jakarta ta wuce sama, Xaunawa Maryam tayi, Deejah na kallonta tace "Maryam ko dai budurwar Ayman ce Khadijah kar ki boye min?" Maryam ta bude ido tace "A'a gaskiya ban sani ba, ni ban ma taba ganinsu tare ba ko a schl" Tare Aliyu ya sakko da Hajiya Mariya dake rike da Shureim, shi kuma yana rike da ledan na lotion da turaren yara da small mum din tasa ta ba Shureim, Maryam na kallonsu tace "Ya Aliyu dama ba kwana xai yi ba" Aliyu ya kalleta yace "Aa" Hajiya Mariya ta xauna kan kujera tana kallon Shureim dake gabanta tace "Ka gaida mumy ka ji boy?" Ya wara idanuwansa irin na Aliyu yace "Mumy ai tana can Nigeria, Anty xan gaida maki" Murmushi Hajiya Mariya tayi tana shafa kansa tace "Toh ka gayar min da Anty son" Aliyu ta kalla tace "Toh yaushe Antyn xata xo ta gaisheni" Aliyu yyi yar dariya yace "Ai Antyn nan sai a hankali ba xuwa xata yi ba" a hankali Hajiya Mariya tace "Kar ka damu, Allah xai dai dai ta ku ko don albarkacin yaron nan" murmushi kawai Aliyu yyi bai ce komai ba ya kama hannun Shureim xa su fita yace "Toh bari in mayar da shi mum, it's getting late" Shureim ya daga ma Hajiya Mariya da ta bi sa da kallo ganin sak mahaifinsa yana daga mata hannu, mikewa Maryam tayi ta bi bayansu, sai da suka fita waje ta kamo hannun Shureim ta durkusa tana gyara masa hular sweater dinsa tace "Darling ni baxa kace min bye bye ba" Dariya yayi yana kallonta ya daga mata hannu yace "Byee" mikewa tayi tana murmushi ta daga masa hannun ita ma sannan ta ce ma Aliyu sai ya dawo ta juya ta koma ciki, Aliyu ya sa Shureim mota sannan ya xaga ya Shiga ya tada motar ya nufi gida da shi, sai da suka kusa isa gidan ya juya yana kallonsa yace "Wani school kake xuwa Boy?" Shureim ya fada masa sunan makarantar, yace "Did you like the schl?" Gyada masa kai Shureim yayi, Aliyu yyi parking dai dai gidan yana kallonsa a hankali yace "Anty ce ta kai ka schl din?" Shureim yace "A'a uncle dina ne ya kai ni" Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba, can ya dauko wayarsa ya shiga kiran Khadijah, Tana xaune parlor tana karatu kiran ya shigo wayarta, tana ganin number ta gane ta daga ta kai kunne, Aliyu yace "ki d'an fito ki dau Shureim" Katse wayar tayi ta mike ta shiga daki ta sa hijab ta fito, kamar mai tausayin kasa take tafiya har ta isa inda motar Aliyu yake, fitowa yyi daga motar ya xagaya ya bude side din Shureim ya sauko da shi, Khadijah ta karaso ta kama hannun yaronta ba tare da ta kalli Aliyu ba tace "Sai da safe" Riko Hijab dinta yayi yana kallonta, ta juya suna hada ido gabanta ya fadi tayi saurin sunkuyar da kanta, murya can kasa yace "Sai da safe kuma? baki amshi sakon sa ba" Bata ce komai ba ya saketa ya bude bayan motar ya dauko babban leda ya dau ledan da Hajiya Mariya ta ba Shureim ya sa a ciki da ledan da yayi masa shopping duk ya hada su waje daya ya mika mata, karba tayi yace "Xa ki iya" Bata ce komai ba ta kama hannun Shureim ta fara tafiya, ya bi su da kallo, Shureim ya juya yana daga masa hannu, murmushi yayi ya daga masa hannun shi ma a sanyaye har suka wuce ciki. Manyan sweaters da head warmer ke cikin ledar da Aliyu ya bata na Shureim sai kaya kala hudu, ta bude daya ledan taga chocolates, biscuits sweets da dai abubuwan ci na yara, ta bude ledan da Hajiya Mariya ta basa taga lotions masu tsada da turare, tabe baki tayi ta mike ta wuce ciki da kayan, sai da ta ajiye kayan inda ya kamata a daki sannan ta fito da ledan chocolates din parlor, turus ta tsaya ganin khaleel xaune parlorn, ta dinga bin parlorn da kallo ganin bata ga Shureim ba, Mikewa khaleel yayi yana kallonta, sake ledan hannunta tayi ta juya da sauri xata koma ciki yace "Khadijah" tsayawa tayi amma ta ki juyowa, kawai ganinsa tayi gabanta yana kallonta, tayi saurin juyo masa baya, a hankali yace "Gaya min me na maki?" Ta turo baki tace "Toh ni na ce ka min wani abu ne?" D'an murmushi yayi yace "Saboda Aliyu kika canxa min Khadijah?" Shiru tayi ta rasa ma abinda xata ce masa, lkci daya jikinta yayi sanyi, jin shi ma bai ce komai ba ta juyo a hankali tana kallonsa, hawaye ya cika idonta tace "Me yasa xan canxa maka saboda Aliyu?" A sanyaye yace "Nima ban sani ba Khadijah" hawaye idonta ya xubo tace "Ko dai kai ne ka canxa min saboda budurwar ka" tana fadin haka ta fashe da kuka, kallonta ya dinga yi shi ma jikinsa yayi sanyi, da wani expression fuskarsa yace "Why? Why will I change because of Jawahir?" tana hararensa cikin kuka tace "Toh nima me yasa xan canxa saboda Aliyu?" Ya lumshe ido ya bude a hankali yana kallonta, rasa abin fadi yayi, har ransa yake jin kukanta, ya bude hannayensa cikin sanyin murya yace "Can... I console you?" Make kafada tayi ta juya masa baya, ya lumshe idanuwansa a hankali ya rungumota, cikin sanyayyan muryar sa yace "You know I love you Khadijah, and... I want you to be the mother of my kids, i want to marry you Khadijah, but you met me with Jawahir, I was with her before you, kin ga baxan mata walakanci ba saboda ke, jawahir na da saukin kai sosai, she don't have problem, and I don't want to betray her... Beside ita daban a rai na haka ke ma, Give me a chance to show you how much I love you plss Khadijah" kasa cewa komai Khadijah tayi, duk gaba daya jikinta yayi sanyi, jin tayi shiru ya juyo da ita a hankali yana kallonta, Bata yarda sun hada ido ba ta sulale nan kasa ta xauna, dukawa yayi gabanta yana kallonta murya can kasa yace "Say something plss Khadijah... Nace Ina son auren ki baki ce komai ba" Ta hade kai da gwiwa jin hawaye ya kawo idonta cikin rawar murya tace "But Barrister Sudais...." Sai kuma ta fashe da kuka, ya dago kanta gabansa na faduwa, da kyar ya iya cewa "what about him Khadijah?" Tace "He proposed before you..." Shiru yayi yana kallonta ko kiftawa babu, a sanyaye tace "He said he want to marry me, and you know I can't tell him no Doctor, aure ma bai isa na biyasa abinda ya min a rayuwa ba, he deserves more than that from me, though nasan 6 years back I will confess I was in love with him, but yanxu I only respect him as someone that brought light to my life after my Lord, sai gashi ya dawo yace yana son aure na, baxan iya cewa bana son Sudais ba, baxan iya cewa baxan auresa ba, but I am afraid of his wife" shi dai khaleel bai ce komai ba, kana ganinsa kasan jikinsa yayi sanyi sosai, mikewa yayi a hankali bayan few seconds yace "Ohk then, Khadijah, Allah yasa hakan yafi alkhairi, wishing you all the best" daga haka ya juya xai fita ta tashi da sauri hawaye na sakko mata tace "But I know I love you so much Dr, bayan Sudais you are the next in my life, da ba don kai ba da ban san abinda xai sameni ba few months back, you made me lively once more in life, may be...." sai da ya isa bakin kofa ya juyo yana kallonta ya katse ta yace "Forget I did that to you Khadijah" daga haka ya fita, ta bi sa da ido xuciyarta na bugawa. Duk yanda Khadijah ta so yin kuka ko xata samu saukin xafin da take ji a xuciyarta kasa yin hakan tayi, ita ta dai san ta fadi ma khaleel haka ne don ta wanke kanta ko da wani abun xai faru gaba wanda bata ma fatan hakan but she never expect such harsh reply from him, why will he just decide to leave? Sai a sannan ta fashe da matsanancin kuka, ashe dama ba sonta yake ba, ashe dama playing dinta kawai yake, gaba daya ta rasa abinda ke mata dadi a ranta, tayi kukan har ta ji babu dadi, duk jikinta yayi sanyi. Tana kwance bayan Isha ita kadai a daki, xuwa sannan ta daina kukan da take kuma ta samu relieve amma banda xafi babu abinda xuciyarta yake mata, ji tayi an bude kofar parlor, duk da wutan bedroom dinta a kashe yake hakan bai hanata dinga kallon kofar dakin ba, lkci daya kuma aka bude kofar Shureim ya shigo dakin, bai kunna wuta ba ya karaso ya hau saman gadon ya kwanta kusa da ita a hankali yace "Anty are you sleeping?" Shiru tayi bata ce komai ba idonta a lumshe, tana ji yayi addu'ar bacci yayi lamo jikinta, a hankali tace "Ka ci abinci?" Ya dago kai yana kallonta yace "Uncle ya bani na ci" Jawo sa tayi jikinta bata ce komai ba, sai da taji yayi bacci sannan ta kwantar da shi ta mike da kyar ta sakko kan gadon tana jin kanta na sara mata ta fita parlor don rufe kofa, a kan centre table ta ga Key a ajiye ta karasa gun kofa ta murda taji a rufe, alamar ya rufe ta waje ga Key a ajiye kan centre table, Dawowa parlorn tayi a sanyaye ta dau books din Shureim ta duba taga yayi assignment dinsa ta ajiye cikin jakarsa sannan kashe wutan parlorn ta koma daki ta kwanta ta lumshe ido. Har kusan karfe goma na dare ta kasa bacci, bude ido tayi da sauri jin wayar ta na ring ta mike xaune ta dau wayar tana kallon mai kiranta, A hankali ta daga ta kai kunne tayi sallama, daga daya bangaren ya amsa yace "Hope ban tashe ki bacci ba Amira" ta lumshe ido a sanyaye tace "Ba bacci nake ba" Shiru ya d'an yi na wani lkci kafin yace "Gaya min me ya faru, what's wrong with you" Ta bude ido da sauri cike da mamaki tace "A'a ba komai, am just tired, me ka ga?" Sudais ya girgixa kai yace "Noo, I know you well Amira, we stayed together for two years, from ur voice, there is something wrong, ki gaya min meye plss" Tace "Lahh da gaske ba komai barrister, today was very hectic shi yasa" D'an murmushi yayi yace "Ohk then" trying to brighten up tace "Ya Namecy na fa?" Yace "Ga ta tayi bacci" Khadijah tace "Toh a shafa min kanta" Sudais yace "Alryt, Shureim yayi bacci?" Khadijah ta gyada kai tace "Uhm" yace "Ya kamata ya ci gaba da karatun sa a nan, I think I will be coming over next week sai inyi enrolling dinsa" A hankali Khadijah tace "Ai ya fara ma" Yace "School din?" Tace "Ehh" yace "Shine baki fadi min ba Amira?" Ta langwabar da kai tace "Kayi hakuri" yace "Ke kika sa shi schl din" ta girgixa kai tace "Dr Ayman ya sa shi" Sudais ya d'an yi shiru sannan yace "That's nyc" Khadijah tace "Next week din xaka taho?" Yace "Sure, Akwai abinda xan yi, but few days xan yi, so do you need anything?" tace "A'a bana bukatar komai, Allah ya kawo ka lafiya" yace "Ameen, let me leave you dear, it's late and kilan xa ki lectures gobe koh?" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yayi mata sallama bayan ya tunasar da ita tayi addu'a sannan ya katse wayar, ajiye wayar tayi ta kwanta ta ja masu duvet da Shureim. Washegari kafin karfe bakwai ta gama komai, ta ba Shureim indomie da ta girka masu a baki don kar ya bata uniform dinsa, Yana gamawa ta mike ta basa jakarsa ya goya ta dau nata jakar tana rike da hannunsa ta nufi kofa, tana gama rufe kofarta Shureim yace "Anty yau ma tafiya xa mu yi mu bar uncle?" Ta kallesa kamar baxa tace komai ba sai kuma a hankali tace "He is still sleeping dear" daga haka ta ja sa suka fita gidan, cab ta samar masu kamar jiya tayi dropping dinsa a schl sannan ta wuce nata makarantar duk da bata da lectures din safe, Wani waje ta samu ita kadai ta xauna, har ga Allah mai lallashinta take nema a lkcin, she need someone to console her, ta share hawayen da ya cika idonta trying hard to control her self, bata samu courage din kiran Umma ba har lkcn, tana ta xaune har lkcn lectures yayi bata tashi ba sai da ta ga kiran Vanessa, ta mike jiki ba kwari ta bar wajen. Bayan sun fito daga lectures sha biyu saura, Khadijah ta wuce cafteria ba tare da ta bari su Vanessa sun lura da ita ba, tana ta xaune nan tayi tagumi kamar ance ta daga kai ta ga Aliyu xaune yana kallonta, a hankali ta sauke kanta kasa, bayan kusan minti biyar ta sake daga kai tana kallonsa taga wayarsa yake dannawa, mikewa tayi ta dau wayarta dake ajiye kan table da jakarta xata fita taji a hankali yace "Iman" kasa kallonsa tayi tana tsaye, ya mike ya iso kusa da ita yace "Gida xa ki wuce?" Tana kokarin ganin bai ga hawayen idonta ba ta gyada masa kai, daga haka ta fita cafterian ya bi bayanta, har suka yi nisa bata ce masa ba shi ma bai ce mata ba, kuma kusan a tare suke tafiyar Daga karshe yayi breaking silence din a hankali yace "What's wrong Iman?" bata san lkcn da ta fashe da kuka ba kamar jira take, nan da nan ya rikice mata yace "Subhanallah, me ya faru Iman, plss ki gaya min, wani abu ya faru ne" ta kasa ce masa komai sai kuka take xuciyarta na mata xafi, Har ransa ya dinga jin kukan nata, bai san lkcn da cikin tsawa yace "Plss I don't like this Iman, ki daina wannan kukan" Tsayar da kukan nata tayi amma hawaye na ci gaba da sakko mata, wuri Aliyu ya samu ya xauna jin kafafuwarsa sun masa nauyi ya rike kansa, lkci daya jikinsa yayi sanyi xuciyarsa yayi masa rauni don kukan nata bashi da maraba da irin wanda tayi a ranar da kaddara ta afka masu six years back, A hankali ta nufi inda ya xauna ta xauna kusa da shi tana goge hawayen da yaki tsaya mata, Bayan kusan minti daya ya dago, cikin sanyin murya yace "What happened Khadijah?" Ta hadiye abu da kyar tace "Should I confide in you plss?" Kallonta yake ko kiftawa babu, a hankali yace "Sure Iman, you won't regret doing so" Ta gyada kai cikin sanyi tace "Ohk, tnx" Shiru ne ya biyo baya na 'ya dakiku..... 😦Seriously I don't like this short chapters da nake yi yanxu wllh, but dai ya fi babu d'an agwai da bak'in d'a....🙄 Gobe xa ku samu 5 read more😅 Khadijah ta hade kanta da gwiwa a hankali ta ki cewa komai, ya fi minti biyu yana kallonta, can ya shafa kansa murya can kasa yace "Talk Iman..." lkci daya ta dago kanta ya dinga kallon jajayen idanuwanta, ta hadiye abu da kyar ta make kafada tace "I think I've changed my mind" muryar ta na rawa ta fadi haka, ya dinga kallonta a sanyaye yace "Why Iman??" k'in cewa komai tayi, wasu sabbin hawayen suka shiga xubo mata, da damuwa sosai yace "Why did u change ur mind Iman, am I not trustworthy" goge idonta tayi tana kallonsa, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe idanuwansa, murya can kasa ya ji tace "Ina son xan wuce gida yanxu" Ya bude ido ya kalli agogon wrist dinsa a sanyaye yace "To mu je in kai ki" shi ya fara mikewa sannan ita ma ta tashi a hankali tana share idonta, har suka iso gun motarsa bai ce komai ba, sai da ya bude motar ya shiga sannan ita ma ta shiga, gaba daya she was absent-minded during the ride, idonta ne ya sauka kan wani karamin agogo mai kyau na yara cikin a cikin motar, ta kai hannu ta dauka tana kallon agogon ko kiftawa babu, agogon da khaleel ya taba siya ma su Shureim ne lkcn da suka xo hutu wajenta da xa su koma, ita dai ta san na Shureim na nan don da shi ma suka xo, Aliyu dai bai ce komai ba yana driving a nutse, ganin ta kallesa kafin tace komai murya can kasa yace "For little Aliyu...." Kasa cewa komai tayi da farko, a sanyaye tace "Where did you get it from?" Ya d'an yi murmushi kamar baxai ce komai ba shi ma, sai kuma yace "When he had an accident that very day agogon na aljihunsa, da muka tafi asibiti na cire" Khadijah ta sauke idonta bata ce komai ba, a hankali ta xuge zip din jakarta xata sa a ciki ya karba a hannunta, da mamaki take kallonsa, yace "Nima ina so, shi yasa na bar shi ma a mota" ta hade rai tace "Toh nima ai ina so" A hankali yace "But ai Shureim ma na da shi" bata sake saurarensa ba ta kai hannu xata karbe, bai san lkcn da ya sake steering ba ta fasa ihu a tsorace, parking yayi daga karshe inda ya dace yayi, ta dinga kallonsa xuciyarta na bugawa, yayi kokarin ganin bai yi dariya ba, dauke hannunsa yyi wajen ganin xata kwace agogon, Tace "Bana so ka bani abun yarona" a hankali yace "Nima ai yarona ne Iman" wani kallo tayi masa tace "A tunanin ka??" Murmushi kawai yayi yana kara kallon agogon, Mika mata yayi yana kallonta a hankali yace "Toh na hakura" kasa amsa tayi, ya dinga kallonta yana mika mata, dauke kai tayi ta turo baki tace "Toh na ara maka, xaka ban watarana" Murmushin sa yayi mai kyau murya can kasa yace "Toh ina godiya Iman" Ya mayar da agogon inda yake ya ajiye, ya juya yana facing dinta yace "But why did you change ur mind Iman?" kallonsa tayi sai kuma ta dauke kai, kamar baxata ce komai ba bayan few minutes a sanyaye tace "It's Dr Ayman, and it looks as if it's of no use telling you...." sai da gabansa ya fadi sosai, ya dake cike da karfin hali yace "What about him" ta jinginar da kanta da kujerar da take xaune, ji tayi abun ya dawo mata sabo, muryar ta na rawa tace "Kawai don nayi masa magana shine ya min walakanci" Aliyu ya ji komai nasa ya tsaya, a hankali yace "May be.... may be he misunderstood you Iman...." Ta fashe da kuka tuna abinda Dr Khaleel yace mata, ya lumshe ido ya bude yace "Toh wani maganr kika masa?" Babu abinda ta boye masa a maganarsu da khaleel na jiya, jin yanda take kuka Aliyu ya lumshe ido yace "Look.... pls ki daina wanann kukan I really don't like it, stop it now" a fusace yayi maganan ta hadiye kukan da take tana goge idonta, ya jinginar da kansa jikin kujerar motar a hankali cikin sanyi yace "He really misunderstood you, but ke ma ba haka ya kamata ki gaya masa ba" ta kallesa tace "Toh ya xan ce masa?" Ya d'an yi murmushin karfin hali yace "You where direct, which is not suppose to be so" turo baki tayi ta rungume hannunta tace "Ae shikenan" Aliyu ya shafa kai murya can kasa yace "You want me to talk to him?" Ta buda ido sosai tana kallonsa da sauri tace "Kace masa me?" Ba tare da ya kalleta ba yace "I will only explain to him what you meant by wat u said to him, kila..." ta hade rai ta katse sa tace "Noo, you don't need to, ba ruwana da shi, and am wishing him d best also" Aliyu na kallonta da kyau yace "Then forget him, kuma kar ki sake xubda hawayen ki" Shiru tayi tana kallonsa, a hankali tace "But I can't forget him just like that, yayi min hallacci a rayuwa" ba tare da Aliyu ya kalleta ba yace "Me ya maki?" Hararansa tayi da kamar baxata ce komai ba, sai kuma a takaice tace "He nursed my Heartache, he always made sure I was fine" Kallonta kawai Aliyu yake, "Wani irin heartache?" Tambayar da ya mata kenan har sannan yana kallonta sauke idonta tayi daga karshe tace "Ciwon xuciyata" da wani expression yake kallonta kafin yace "Kina nufin kina da ciwon xuciya?" Shiru tayi bata ce komai ba, jin hawayen talaici na xubo mata ta shiga gogewa, lkci daya jikinsa yayi sanyi, cike da karfin hali yace "I... i am the cause ko Iman?" Taki cewa komai, jin taki magana yace "Iman" sai a sannan ta juya tana kallonsa, sai ya rasa ma mai xai ce mata duk jikinsa ya mutu, tada motar sa yyi cike da karfin hali yace "Let me get you something to eat" Bata ce komai ba ya nufi wani gidan cin abinci da ita, suna isa bayan yayi parking ya juya yana kallonta a hankali yace "Mu je" daga haka ya bude motar ya fita ita ma ta fito, one side of the eatry khaleel ne xaune da cup din coffee gabansa ya jinginar da kansa da kujera har coffeen ya gama hucewa bai fara sha ba, kallonsu ya dinga yi ko kiftawa babu, ganin kujerar dake kallon nasa xa su zauna ya juya masu baya, Aliyu ya mika mata order list din da aka basa, kamar baxa ta karba ba da farko sai kuma ta amsa, ya dinga kallonta tunani iri iri a xuciyarsa, bata yi second talatin tana kallo ba ta mayar masa a sanyaye tace "Just anything" ya karba yana gyada mata kai, abinci iri daya ya sa aka kawo masu, duk da gaba daya ya ji ba ya da appetite hakan bai hanasa dinga cin abincin a hankali ba, ita ma haka, gaba daya suka fada duniyar tunani kowa da wanda yake, ita tana ganin yan biyunta tare da shi barin late Sudais, kuma ta dalilin haka har ranta tasan she is now comfortable with him even if it's not 100% unlike before, shi kuma yana tunanin in har bai auri Khadijah ba till the end of him baxai taba samun rest of mind ba, a hankali ya dago daga karshe yana kallon yanda take cin abincin kamar ana tilastata sai turo baki take, suka hada ido ta yi saurin sauke idonta, ya d'an yi murmushi yace "Naga bakya ci" a hankali tace "Ina ci mana" shi ya fara matsar da abincin gabansa jin ya ishesa gaba daya duk da ba da yawa ya ci ba, ta kalli abincin nasa tace "Ka koshi?" Ya gyada mata kai, yanda yayi da bakinsa kamar Shureim idon bai son cin abinci, tayi shiru tana kallonsa, yayi murmushi yana shafa kansa ya matsar mata da sauran abincin nasa yace "Ko xaki kara?" Wani Harara ta maka masa ta tura masa nata tace "Sai dai ma ka kara da nawa" sunkuyar da kansa yayi yana dariya, tayi murmushi a sanyaye tana kallonsa komai yayi wani lkcn sai ta ga exactly her kids, it's just too obvious, ya dau tissue yana goge bakinsa a hankali yace "Ranan Aunt dita ke tambayar ki, coz I told her a nan kike karatu...." Khadijah ta sauke idonta kasa tace "Ina gaisheta" lumshe ido yyi ya bude yace "Or xa ki je ku gaisa yanxu, tana son ki sosai, anjima sae in mayar da ke gida then u face Ur Dr Ayman.... Sai ki masa bayanin abinda kike nufi ya daina fushi da ke" ta hade rai tace "Ni ba ruwana da shi, bana son sa kuma" tana fadin haka ta kife kanta da table ta fara rera kuka, Aliyu ya dinga kallonta ko kiftawa babu, can yyi kasa da murya yace "Toh kiyi hakuri kar ki sake kuka, am sure shi ma ba har ransa ya gaya maki haka ba fa" Bata sake cewa komai ba ya biya bill din yana kallonta yace "Tashi mu je" mikewa tayi ya mike shi ma, tana gaba yana biye da ita Dr Ayman ya bi su da kallo har suka fita, har suka iso gun motarsa bbu wanda yace komai, ya bude mata motar yana kallonta, a hankali ta karaso ta shiga, ya rufe sannan ya xaga ya shiga ya tada motar ya fita eatry din, sae da suka hau saman titi a hankali yace "Mu je ku gaisa da ita Iman?" Shiru tayi da farko kafin murya can kasa tace "Toh" yayi murmushi yace "Thanks Ummu Shureim" har suka iso gidan babu wanda yace komai cikin su, yanxu kam ta daina jin xugin da take ji a xuciyarta, yayi parking yana kallonta yace "Toh fito" ba musu ta fita shima ya fita, Yana gaba tana biye da shi har suka shiga parlorn gidan. Maryam kadai ce parlor tana rubutu a takarda, ganinsu ta mike da mamaki tace "Lahh Khadijah ce gidanmu yau, sannu da xuwa" Khadijah ta xauna tana kirkiran murmushi da kyar tace "Yauwa nagode" Aliyu ya wuce sama, Maryam ta bi sa da kallo, kamar yanda Khadijah ke kallonta, tashi tayi daga karshe ta dauko mata ruwa da drink ta ajiye gabanta tana tambayarta Shureim, a hankali Khadijah tace "Yana schl" Maryam ta xauna tace "Ayya, kin shiga schl kuwa yau?" Khadijah ta gyada kai tace "Daga can nake" Maryam tace "Nima kin ga yanxu na dawo, nama yi ta jiran ya Aliyun don ya ce min xae shigo shi ma amma ban gansa ba...." Fitowar Hajiya Mariya ya sa Maryam ta mike tace "Anty yau ga mum Shureim gidan mu" Da murna Hajiya Mariya ta karaso cikin parlorn tace "Wlh kuwa, maa Sha Allah, sannu da xuwa Khadijah" Khadijah ta sunkuyar da kanta da ladabi tace "Nagode mumy, Ina yini?" Hajiya Mariya tace "Lafiya lau Khadijah ya gidan?" Tace "Alhmdllh" Hajiya Mariya tace "Ya karatun fa?" Khadijah tana wasa da xobenta tace "Alhmdllh Mumy" Hajiya Mariya tace "Maa Sha Allah, Allahu ya baku sa'a, Ina Shureim din?" Aliyu da ya shigo parlorn yace "Yana schl Anty" tace "Allah sarki, ashe ya fara schl din a nan, Allah yayi masa albarka ya raya sa" Mikewa tayi daga haka tace "Mu je sama kiyi sallah ki ci abinci koh" kasa cewa komai Khadijah tayi ganin ta fara tafiya ta mike ta bi bayanta a sanyaye suka haura sama, Maryam na kallon Aliyu tace "Yaya shine ka shanya ni schl koh?" Ya shafa beard dinsa bai ce komai ba, Khadijah na haurawa sama tare da Mumy ta juya tana kallonsu, suna hada ido da Aliyu tayi saurin dauke kanta ta shiga dakin da Mumy ta shiga. Tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh Maryam ta shigo dakin rike da tray na abinci ta ajiye mata tace "Ga abinci Khadijah" Khadijah ta xaro ido tace "Wallahi na ci abinci kafin mu xo nan am not hungry" Maryam tace "Toh ko kadan ne dai ki ci" Khadijah xata yi magana aka bude kofar, jawahir ce ta fara shigowa, suna hada ido Khadijah ta sunkuyar da kai, Jawahir dake ta kallonta ta ajiye jakar hannunta ta fice daga dakin, sosai jikin Maryam yayi, ita dai Khadijah bata sake dago kanta ba, sai ga deejah ma ta shigo dakin, ta wara ido ganin Khadijah tace "Wow Khadijah ke ce gidan yau?" Murmushi Khadijah tayi tace "Ina yini" Deejah tace "Lafiya lau, ya lectures? Tare da Maryam ku ka xo?" Maryam na yar dariya tace "Ehh mana" Deejah tace "Ayya ya little shureim" Khadijah tace "Yana schl" Deejah tace "Toh maa Sha Allah" daga haka ta fita, Khadijah ta kalli agogon dakin don gaba daya hankalin ta yyi kan yaronta sanin ya kusa tashi a schl, ganin Maryam na sllh ta jira har ta idar kafin tace mata tayi ma Mumy magana xata wuce, Deejah ce ta dawo dakin tana video call ta iso kusa da Khadijah ta durkusa tana murmushi ta haska ta tace "Ammi ki duba fa plss basa kama??" Khadijah ta ki kallon screen din tana murmushi, Deejah tace "Khadijah ki tsaya ku gaisa da Ummar mu pls" sai a sannan Khadijah ta kalli screen din wayar, wata matashiyar mata ta gani gaban wayar, a hankali tana kallonta tace "ina yini?" Matar na kallon ta da fara'a tace "Lafiya lau yan mata, ya kike ya karatu?" Khadijah tayi murmushi tace "Alhmdllh" matar tace "Maa Sha Allah, Allah yayi maku Albarka ya bada abinda aka je nema, sai ayi ta kula kin ji?" Khadijah ta ji dadin addu'ar cikin sanyin murya tace "Ameen mama nagode" matar tayi mata sallama, Deejah ta mike rike da wayar tace "Ammi idan Safeenah ta dawo plss ku kira ni in nuna mata duplicate din ta" murmushi kawai Khadijah tayi, Deejah ta fice daga dakin tana ci gaba da waya da mum dinta. Khadijah ta kalli Maryam dake kallonta tace "Kice ma Mumy xan wuce" mikewa Maryam tayi tace "Toh" daga haka ta fita, tare suka dawo dakin da Mumy tace "Har xa ki koma daughter?" Khadijah tayi murmushi tace "Eh mum, Shureim sun tashi a schl" Hajiya Mariya tace "To maa Sha Allah, mun gode da ziyara Khadijah, Allah yi albarka" a tare suka sakko kasa har da Maryam, Mumy ta ba Khadijah sako a leda ta kai ma Shureim, a kunyace ta amsa tace "Allah saka da alkhairi mum" Deejah vata ji dadi ba ganin wucewa Khadijah xata yi, tace "Ae ko xan xo gidan ki ko gobe" Yar dariya Khadijah tayi tace "Allah ya kai mu" tare da Maryam suka rakota har bakin motar Aliyu don yana cikin motar yana jiranta, daga masu hannu tayi bayan ta shiga tace "Toh nagode, sae anjiman mu" Aliyu ya ja motar ya fita cikin gidan, sae da suka dau hanya tace "Xan dau Shureim a schl" yace "I thought as much, naga it's time" Mamaki Khadijah tayi ganin ya dau hanyar makarantar, ta kasa daurewa tace "How did you knw d schl?" D'an murmushi yayi murya can kasa yace "Kin raina irin bond dake tsakanin a son and his father?" Shiru Khadijah tayi tana kallonsa, lkci daya ta hade rai ta turo baki tace "Don't call him ur son, stop calling him that" kallonta yyi, A hankali yace "Ko saboda me?" A takaice tace "His father is a barrister" Murmushi yayi bai ce komai ba, he really really don't want to hurt her da babu abinda xai hanasa tambayar ta ko barrister ne yayi mata cikinsu, suna isa schl din bayan yyi parking ta bude motar ta fita don dauko d'an ta ya bi ta da kallo, ba a dau lkci ba ta dawo a sanyaye, yace "Where is he?" Ta bude motar ta shiga a hankali tace "Dr ya tafi da shi wai" Aliyu bai ce komai ba ya tada motar a hankali ya bar premises din school din, har suka isa babu wanda yace komai, yana gama parking ya juya yana kallonta, ta bude motar ta fita tace "Nagode" yace "ki gaida min Shureim" ba tare da ta juyo ba tace "Ohkk" Da ido ya bi ta har ta shiga cikin gida, yayi wani murmushi ya ja motarsa ya bar wajen, tun da Khadijah ta shiga compound take ta kallon motar khaleel, lkci daya mood dinta ya canxa ta isa apartment dinta ta bude jaka ta fiddo makulli ta bude kofar ta shiga. Wanka tayi ta kwanta parlor ta fada duniyar tunani, murda kofar parlorn taji anyi ta mike xaune da sauri, Shureim ya shigo ya taho wajenta da gudu ya hau kanta yace "Anty we came back before you" ta rungumesa tace "How are you?" Yace "Am fyn" tace "Have you eaten?" Ya gyada mata kai yace "Uncle ya bani" tace "Toh mu je ka cire uniform" tashi tayi ta daga sa suka wuce bedroom, wanka tayi masa ta sa masa kaya da sweater ta bar sa dakin yayi assignment ta fito don daura girki. Tana kitchen tana fere Irish taji kamar mutum waje, a hankali ta leka window ta gansa xaune waya kare kunnensa, hada ido suka yi, ta dauke kai da sauri, ta ci gaba da abinda take cikin sanyi. Shidda da yan mintuna ta fito kitchen din bayan ta tsaftace ko ina, daki ta wuce taga Shureim kwance kan carpet yayi bacci, ta daukesa ta daura sa saman gado ta kwashe books dinsa ganin ya gama assignment din ta sa a jaka ta rufe, har xata fita wayarta dake kan gado yayi haske, ta karasa gadon ta dau wayar tana kallon screen din, alert ta gani na dubu dari da hamsin, a hankali ta ajiye wayar ta shiga bathroom, Karfe takwas saura Khadijah ta fito parlor da hijab har kasa, duk gaba daya ta rasa sukuni, a sanyaye ta wuce kitchen ta xuba abinci ta fito ta xauna, kasa cin abincin tayi ta tura plate din daga gabanta tana hadiye na bakinta da kyar, tashi tayi ta kara shiga kitchen ta dau warmer ta wanke ta xuba abinci a ciki ta rufe sannan ta fito, ta fi minti uku tsaye parlon kafin ta nufi kofa ta fita gabanta na faduwa, a hankali ta danna bell din khaleel, tana ta tsaye gun ga wani sanyi dake ta shigarta, ganin bai bude ba ta kara dannawa, lkci daya ya bude kofar tayi saurin sunkuyar da kanta kar su hada ido, barin bakin kofar yayi ya koma ciki ta bi bayansa kamar mai tausayin kasa ta rufe kofar sannan ta isa tsakiyar parlorn ta durkusa ta ajiye abincin hannunta ba tare da ta yarda sun hada ido ba tace "Good evening" Xaunawa yyi kan kujera yace "Evening ya kike?" A sanyaye tace "Lafiya lau" Yace "Ya lectures?" Shiru tayi bata ce komai ba, tana dai duke inda take yace "Baxa ki xauna ba" a hankali ta mike tace "Sai da safe" yace "Alryt, Allah tashe mu lafiya, todays cold isn't gonna be funny ki sa ma Shureim sweater and lock all the windows" tace "Toh" daga haka ta nufi kofa xata fita yace "And...." Tsayawa tayi bakin kofar don jin abinda xai ce, yace "Thanks for the food" bata ce komai ba ta fita ta rufe masa kofar. Abincin da ta xuba ta kai kitchen ta fito ta kashe wutan parlorn ta wuce bedroom, warm water ta xuba a kettle ta daura alwala ta fito ta kashe wutan dakin ta hau gado ta kwanta kusa da Shureim ta rufa masu Duvet, har ta fara bacci vibration wayarta ya tasheta, ta bude ido a hankali ta jawo wayar, tasan Barrister ne xai kirata wannan lkcn, tayi picking call din ta kai kunne tayi sallama cikin sanyin murya, daga daya bangaren yace "Amira..." Tace "Uhm Ina yini?" Yace "Lafiya lau, Ya Boy dina?" Tace "Yayi bacci" yace "Maa Sha Allah, kema tashin ki nayi koh?" Tace "Uhn, na dai kwanta ne, ina little Amira fah?" Yace "Tana gun Mum dinta" Khadijah tace "Am sorry ban kira ka ba Barrister, daxun na ga sako thanks very much we are grateful" yace "Is there any need for that Amira?" Murmushi tayi bata ce komai ba, yace "I think nan da 3 days xan taho ba sai next week ba" Khadijah tace "Ayya Allah ya kawo ka lafiya" yace "Ameen, daxu ma naje gun Umma" Khadijah ta bude ido tace "Haba dai?" Yace "Sure, kafin in taho Uk xan je can katsina" shiru Khadijah tayi bata ce komai ba, yace "Are you there?" Tace "Uhm ina jin ka" yace "Me yasa kika yi shiru" a hankali tace "Isn't it Early barrister" yace "It's not Amira, I want everything to be done in not less than 2 months plss, ba ki jin tausayina koh" jikinta yayi sanyi tace "Amma barrister ni tsoron Ummu Amira nake, plss ka sanar da ita don ya xamo da amincewarta kake yin komai, Ni tsoro nake ji" D'an murmushi yayi yace "Ba ruwan ki da Jiddah, beside ta san komai, ke din dai ce bata sani ba, sannan ba gida daya xa ku xauna ba" Ita dai har sannan bata ji hankalin ta ya kwanta ba, banda faduwa babu abinda gabanta ke yi, cikin sanyin murya tace "Toh shikenan, Allah yayi jagora" yace "Ameen Amira, let me allow you sleep" tace "Toh nagode" a hankali yace "Do have a nyc nyt rest" Ta d'an yi murmushi tace "Thanks" daga haka ya katse wayar, komawa tayi ta kwanta ta rufe har kanta da duvet. Washegari bata da lectures da safe amma saboda Shureim dole ta tashi cikin sanyi don shirya sa, tausayin little boy din nata take don sanyin isn't funny at all, haka dai ta shirya sa ta sa masa rigar sanyi babba da head warm, tea ta hada masa ta soya masa kwai sanin baya cin bread, tana xaune parlor tana jiran ya gama aka danna bell, kallon agogo tayi kafin ta mike ta isa kofar ta bude, khaleel ne tsaye ya shirya xai fita, shi ma kayan sanyin ne jikinsa yana kallonta a hankali yace "Good morning" ta kasa kallonsa ganin yanda ya tsare ta da ido, ji tayi yace "let me drop Shureim in school tunda baki da lectures yau" tace "Toh" daga haka ta dawo parlorn, yana ta tsaye har Shureim ya gama ta dauko masa lunch box dinsa ta mika masa, ya nufi kofa yana daga mata hannu har ya fita khaleel ya kama hannunsa xuwa gun motarsa, ta tsaya bakin kofa tana kallonsu har suka fita gidan. Washegari Thursday da yamma Khadijah na parlor tana goge ma Shureim kayansa da uniforms, shi kuma yana bedroom yana waya da su Umma, mikewa tayi bayan ta kashe iron din jin an danna bell, ta isa kofar ta bude, khaleel ta gani tsaye, ya shafa kansa ba tare da ya kalleta ba yace "I will be traveling to Nigeria today Khadijah" shiru tayi tana kallonsa, yace "You take care of the little boy" tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare" yace "Ameen" xai shiga apartment dinsa ta fito a hankali tace "Dr..." Tsayawa yayi ya juyo yana kallonta, Kasa magana tayi, murya can kasa yace "Am all ears Khadijah" Jin hawaye na neman taruwa idonta ta juya ta koma ciki kawai, da ya tashi tafiya kuma bai ma ce mata ya tafi ba yayi wucewar sa. Tun da Khadijah ta tashi sllhn asuba duk ta rasa me ke damunta, gaba daya ta ji bata jin dadi, komawa tayi ta kwanta kasancewar friday ne, tana ta kwance har kusan karfe takwas, can dai ta tashi tunawa da tayi anytime soon flight din su Barrister xai sauka kasar, Ruwan wanka ta hada ta fara tashin Shureim ta wanke masa baki tayi masa wanka ta sa yayi alwala sannan suka fito bayin, shirya sa tayi ta shimfida masa darduma yayi sllh sannan ta wuce bathroom don yin wanka, tana tsaye kitchen misalin karfe goma tana tunanin abinda xata girka ma Barrister, Shureim ya kawo mata wayarta dake ring, karba tayi ta kai kunne hade da sallama, yace "Kun tashi lafiya Amira?" Tace "Alhmdllh, har kun sauka kenan?" yace "Sure, tun karfe tara" Tace "Toh ina ka sauka?" Murmushi yayi yace "Baki san ina da apartment nan ba koh?" Ta langwabar da kai tace "I never knew" yace "You now know" murmushi kawai tayi, yace "Ina Shureim" kallon bakin kofar tayi taga ya wuce tace "Yana parlor, barrister sorry I asked... plss mai xan girka maka I don't know what u like most" Yace "Noo you don't worry dear, Ni nayi breakfast ma" shiru tayi jin abinda yace, Can tace "Toh lunch fah?" Yace "Just tea may be with cake" xaro ido tayi tace "Tea da cake kuma?" Yace "Uhm sure" tayi murmushi tace "Toh shikenan yaushe xaka taho?" Yace "After I am done with what I am doing, may be in the afternoon" tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen, bye dear" daga haka ya katse wayar, fita tayi daga kitchen din don dama sun yi breakfast da Shureim. Karfe Sha daya ta shirya tare da Shureim suka fita don yin shopping, sun fito daga shopping mall wayarta dake jakarta ya fara ring, ta ajiye kayan hannunta ta bude jakar ta ciro wayar, number Aliyu ta gani, ta d'an yi jim kafin ta daga, shi yayi mata sallama ta amsa tayi shiru, yace "Ya kike Iman" tace "Lafiya lau" yace "Ya Shureim?" Tace "He is fine" yace "Maa Sha Allah" shiru tayi bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Xan tafi Nigeria later, you need anything?" Tace "As in?" Yace "I mean ko kina bukatar wani abu daga Nigeria?" Tace "Nothing" a hankali yace "Ohk can I go with Shureim plss" wani kallo ta shiga yi kamar yana gabanta tace "Beg your pardon?" D'an murmushi yayi kafin yace "Ranan litinin xa mu dawo Iman, daurin auren Neighbor din ki xan je, it's tomorrow, so we will be back Monday morning" Shiru Khadijah tayi tana son apprehending abinda Aliyu ya ce mata, a hankali yace "Hello, are you there Iman?" Ta dake tace "Waye Neighbor dina?" Da kamar baxai ce mata komai ba sai kuma yace "Dr Ayman" Khadijah na rike da hannun Shureim suka fito waje, tun daga nesa Aliyu dake cikin motar ke kallonta, har suka iso kusa da motar ya fito, ko ba a fadi masa ba yasan tayi kuka, kuma gaba daya a sanyaye take, ya duka yana kallon Shureim a hankali yace "How are you" Shureim yyi masa murmushi yace "Fine, good afternoon uncle" shafa kansa yyi ya mike ya kalli Khadijah yace "Thank you Iman" jakar Shureim ta mika masa ya karba ya sa bayan mota sannan yana rike da hannunsa ya xaga ya sa shi gaban motar ya dawo, ya bude maxaunin driver ya shiga, sae a sannan Khadijah ta juya ta koma ciki ko sallama bata yi da yaron nata ba, har cikin ranta take jin tsanar khaleel ynxu kam, ta ji ko ganinsa ma bata son kara yi a rayuwarta, bedroom ta wuce ta kwanta, lkci daya ta mike da sauri tunawa da tayi Sudais yace xai xo da rana, ta fita xuwa kitchen don daura masa ruwan Lipton, ta xuba kayan kamshi sosai a ciki, sake gyara gidan tayi tana juye ruwan Lipton a flask ta ji wayarta na ring ta fito parlor ta dau wayar, dagawa tayi ta kai kunne tace "Ina yini barrister?" Yace "Alhmdllh, ki turo min address Amira" tace "Toh" katse wayar tayi ta tura masa street da house number ta text message, ta ajiye wayar taje ta ci gaba da abinda take, few minutes later Sudais ya kirata yace yana waje, ta sa hijab ta fito, Tsaye ta gansa jikin mota cikin shigar da ta lura ya fi so, wato na suit, har ta iso kusa da shi idonta na kan sa, kamar yanda shi ma yake kallonta, yayi murmushin sa mai kyau yace "Kyau kike karawa idan kika xo Uk kenan" Tayi murmushi ta sunkuyar da kanta, a hankali tace "Sannu da xuwa" yace "Yauwa sannu, ke daya ce cikin katon gidan nan?" Ta girgixa kai tana murmushi tace "A'a bani kadai bace, mu shiga ciki Barrister" Yace "Do I have to Amira?" Tace "Why not?" Daga haka ta juya ta fara tafiya, ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, yana shiga cikin gidan ganin fararen kujeru da table a bangaren flat dinta karkashin wani shade yace "That's all, I will prefer staying outside" daga haka ya nufi wajen ya xauna ta tsaya tana kallonsa, bata fuska tayi tace "Barrister mu shiga ciki mana kaga fa akwai sanyi wajen..." Yace "Ke dai kike jin sanyin, just get me my tea sai ki yi wucewar ki ciki tunda kina jin sanyi" murmushi tayi ta wuce ciki sai ga ta ta fito da tray mai dauke da karamin flask da plate din cake" ajiye masa tayi ta ja kujera ta xauna tana dubansa tace "But me yasa baka son shiga ciki Barrister?" Ya bude plate din ya dau cake daya yace "What did you mean?" Ta xaro ido tace "But is there anything wrong with going inside?" Shiru yyi yana kallonta, can ta wara ido da sauri tace "Ohh yes you are right Barrister" sai kuma tayi murmushi, murmushin yayi shima ya kai cake din baki, a hankali tace "But.... Seven years back...." Sai kuma tayi shiru, kallonta ya dinga yi kafin yace "Don't forget you where sick and pregnant then, I have no choice...." shiru tayi a sanyaye tana kallonsa, ya buda ido sosai yace "Wait... Ina Shureim din?" Ta sauke idonta daga kallonsa, cikin sanyin murya tace "Sun tafi Nigeria da Aliyu" da mamaki yace "Wani Aliyun?" Bata ce komai ba na few seconds kafin daga karshe tace "Aliyu dai" Sudais ya ajiye sauran cake din hannunsa yace "is he also in Uk?" Kai ta gyada masa, Bai iya ya sake cewa komai ba, bayan wani lkci a hankali yace "Kuna haduwa da shi kenan?" Ta sauke idonta daga kallonsa tace "Sometimes in school" Sudais bai sake cewa komai ba ya fiddo wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne, tana ta kallonsa har ya gama wayar sanann ta sunkuyar da kanta, ya ajiye wayarsa in a very low tone yace "Amira?" A hankali ita ma tace "Na'am" yace "I don't want to deprive you of anything you wish for ur self, be frank plss Amira ki fada min gaskiya, did you want to go back to the father of ur kid?" Kallonsa ta dinga yi da wani expression, cike da karfin hali tace "Ban gane ba Barrister" Dago kai yyi yana kallon eye balls dinta yace "I mean, kina da ra'ayin komawa gun Aliyu ku yi aure ne?" Ta fashe masa da kuka tace "Anybody can say this but not you barrister, kai me tuna min irin wahalar rayuwar da na sha ta dalilin Aliyu ne, you witnessed everything, ko kuma ince tare muka sha wahalar barrister coz all those time you where by my side, Aliyu raped me without mercy har yau memory din na kai na very fresh, scene din na ido na, bayan faruwar hakan ya canxa min a gidan ya daina ma amsa gaisuwata ya daina xama duk inda nake, daga karshe he sent me away without thinking twice, with huge sum of money bayan yasan bani da kowa, Bai yi tunanin ko xan gane gida ko baxan gane ba" kuka take sosai, Sudais ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido ya kasa cewa komai, Tana ci gaba da kuka tace "Har yau ni ban ga wani prove that will convince me that ba da gangan Aliyu yayi min abinda ya min ba, ban ga prove da xan yarda cewar ba da gangan yayi raping dina ba, fine... Mahaifiyarsa cewa tayi it's a set up, did she have any choice? Dole ta kare d'an ta, an taba set up da rape dama?? Wllh dalilin marigayin yaro na nake raga ma Aliyu har nake kulasa naji kuma xan iya xumunci da shi albarkacin yaran dake tsakaninmu, of recent I dreamt of my little boy telling me to forgive his dad, so why will I not forgive him, nasan ya cuce ni ya bata min rayuwa but he gave me happiness at the same time... My boys" hade kanta tayi da table tana kuka sosai, Sudais ya bude idanuwansa yana kallonta cike da tausayin ta, cikin sanyin murya yace "Am sorry Amira, you misunderstood me, I know ur pain but..." Ta dago hawaye na sakko mata tace "But what?" Yyi kasa da murya pleadingly yace "I am sorry plss" kin cewa komai tayi, yace "Kin hakura?" A hankali ta gyada masa kai, ya lumshe ido ya bude yace "Nagode dear, do you have any plans for our wedding?" Ring dinta ta dinga jujjuyawa bata ce komai ba sai dai gaba daya tunaninta a lkcn ya tafi kan khaleel, a hankali yace "Kin yi shiru" wani mugun haushin kanta taji ganin Wanda ya fado mata a rai, d'an tsaki tayi ba tare da ta san tayi hakan ba, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace "Ke da wa kuma??" Da sauri ta kallesa ta xaro ido tace "Don Allah kayi hakuri barrister wllh ba da kai nake ba, ban san...." Katse ta yayi yace "Nasan ba da ni kike ba Amira, I can see you are lost in ur thought, tel me what u are thinking of" ta girgixa kai tana kirkiran murmushi tace "Uhn ba komai fa" murmushi yayi yana shafa kansa yace "Toh shkkn" flask din ya bude ta mike da sauri tace "Bari in xuba maka" daga haka ta karasa budewa ta xuba masa a cikin mug dake kife, kallonsa tayi taga kallonta kawai yake shi ma, ta sauke kanta kasa a hankali tace "In sa maka Madara?" Ya girgixa kai yace "Noo, I prefer it black" Komawa tayi ta xauna tana murmushi tace "Toh, what will you take for dinner?" Ya d'an bude ido bayan ya dau Lipton din yace "Da daddare sometimes ina shan tea with irish and egg" ta langwabar da kai tace "Toh da safe fa?" Yayi murmushi yace "Tea and bread" da mamaki ta kallesa tace "Toh barrister baka cin tuwo ko shinkafa ko dai any other food?" Yace "Ina ci idan na samu" shiru tayi bata sake cewa komai ba, lkci daya taji tausayinsa don ko bai fito fili ya gaya mata ba ta gane Matarasa ce bata girki kenan, d'an murmushi tayi tace "Toh xan maka tuwo anjima ka dawo ka karba" ya xaro ido yace "A'a ku mata da bakwa son girki mai wahala don't stress ur self dear I will take tea na riga na saba" tace "No, ba ko wace mace ce ke jin kiwiyar girki ba, I am also exceptional, ko mai kake so xan girka maka anjima" murmushi yayi sosai yace "Toh nagode Amira" Sai biyar saura ya bar gidan, shi ma saboda ya damu bai yi la'asar bane..." Ta rakasa har bakin motarsa sai da ya wuce sannan ta koma ciki. Kamar yanda ta fada masa kafin magrib har ta gama yi masa tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup, ta xuba masa a warmer, ganin bai kirata ba har bakwai ita ta kirasa, bayan ya dauka a hankali tace "Barrister baka dawo ka karba ba kuma" yayi kasa da murya yace "I really don't want to stress you dear, I learn girka tuwo akwai wahala..." Katse sa tayi tace " Ni dai ka xo ka amsa na gama, akwai wahala gun ragwayen mata dai" dariya yayi yace "Ohh really?" Tace "Yea, tun daxu na gama, ka taho ka amsa plss" a hankali yace "Toh gani xuwa Amira, I am proud of you" murmushi kawai tayi ta katse wayarta, cikin minti goma ya taho amsan abincin ya dinga sa mata albarka har ya tafi. Washegari Saturday da yamma Sudais ya xo ya fita da ita su xaga gari, duk da sanyin garin, the moment was just waow, ita dai ta san Sudais na sonta fiye da xaton ta but bata san me yasa ta kasa kwantar da hankalinta ba, he really made her day on Saturday, don babu wani damuwa tare da ita ya maido ta gida, kewan Shureim ma da take ji gaba daya taji babu shi yanxu. Ranan lahadi da safe tun da ta tashi ta shiga kitchen don girka masa shinkafa da miya, karfe goma ta kirasa, bayan ya dau wayar jin muryarsa a hankali tace "Bacci kake barrister?" Yace "Uhn am now awake" tace "Kayi hakuri ban san baka tashi ba, ka gaya min address din ka sai in kawo maka breakfast" ya mike xaune daga kwancen da yake kan gado yace "Noo ba sai kin ba kan ki wahala ba xan shirya yanxu in fito" tace "Toh, kayi hakuri" ya wara idanuwansa yace "Hakuri kuma dear" murmushi tayi ta katse wayar, bedroom ta wuce ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin kananun kaya, tana xaune gaban mirror tana gyaran gashinta kawai ta tabe baki ita kadai, yanxu su Maryam gaba daya sun tafi Nigeria biki kenan, d'an tsaki tayi a ranta tace do I have to care, turo baki tayi ta mike ta daure gashinta ta dau rigar sanyi ta sa da head warmer ta dawo parlor ta xauna. ✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨ Ranan lahadi da safe Khadijah ta raka Sudais Airport, har ranta ta dinga jin kewarsa bayan ya tafi duk jikinta yayi sanyi, tana tsaye inda xata hau cab a wajen airport din kamar ance ta kalli gefenta taga khaleel tsaye alamar fitowarsa kenan shi ma daga cikin airport, farar shadda ce jikinsa sai walkiya take, Khadijah ta dauke kai da sauri tun kan ya kallo inda take ta karasa gun cab da ta gani ta shiga ta fada ma driver din inda xata. Suna isa gida ta fito ta basa kudin sa sannan ta shiga ciki da sauri ta bude jakarta tana kokarin ciro makulli, dai dai nan khaleel ya shigo gidan, bata yarda ta juya ba ta bude kofarta ta shige. Daki ta wuce ta tattara reading materials dinta, ta dau kayanta kala biyu da nyt wear ta fito rike da jakarta, kulle apartment dinta tayi ta wuce kamar warce ake jira a waje tsabar haste din, tana fita ta samu Cab ta hau xuwa gidan Vanessa. Gaba daya ranan a gidan ta yini, sai dai she was just uncomfortable saboda mazan turawan dake xuwa suke fita gidan, gashi ba isasshen hankali gare su ba duk ta takura, ta so komawa gida da daddare amma saboda sanyi ta hakura ta kwana gidan, washegari daga gidan ta shirya xuwa sch tare da Vanessa bayan sun yi breakfast, suna gama lectures Vanessa ta sake jan Khadijah suka koma gidanta, tana xaune parlorn Vanessa bayan tayi magrib idonta a kan takardun hannunta ta jawo wayarta dake ring, number Aliyu ta gani sai a sannan ta tuna da yaronta ta yi picking kiran, daga daya bangaren yace "How are you Iman" tace "Fyn, how about my son" yace "Naga kin ma mance da shi gaba daya" ta hade rai tace "Taya xan mance shi?" Murmushi yayi yace "Toh gobe da safe xan kawo shi don ya samu yaje schl" tace "Kun dawo ne?" Yace "Yea daxu da yamma" shiru ta d'an yi kafin tace "Bring him in the afternoon" yace "Alryt then" daga haka ta katse wayar ta. Ranan talata bayan sun gana lectures misalin karfe biyu Khadijah ta koma gida, bude kofar apartment dinta tayi a hankali ta shiga sannan ta rufe, gyaran gidan ta shiga yi, bayan ta tsaftace ko ina, ta bude kofar kitchen xata xubda shara suka yi ido hudu da wata yarinya da ta xo xubda sharan ita ma, yarinyar ce ta fara cewa "Sannu" Khadijah tace "Ina yini?" Yarinyar tace " Lafiya lau, jiya da muka xo mun duba baki nan ashe kin dawo" Khadijah ta d'an yi murmushi tace "Ehh yanxu na dawo" yarinyar tace "Ayya, to Sannu da xuwa" Khadijah tace "Idan na gama xan shigo yanxu" yarinyar tace "Toh sai kin shigo" daga haka Khadijah ta wuce ciki, Allah ma ya san ba don ranta ya so ta fada haka ba, kawai dai yarinyar ta mata kwarjini ne, and kuma sai taga kamar suna kama, toh ko dai ita ce warce su Deejah ke fadi? Tabe baki tayi ta wuce bedroom dinta, wanka tayi ta sauya kaya tayi sllhn azahar sannan ta linke Hijab dinta ta yafa mayafi ta fito, a hankali ta danna bell din apartment din khaleel, bayan wani lkci wata ta bude kofar, Khadijah tace "Ina yini" yarinyar dake ta kallonta ta bata hanya tace "Lafiya lau" shigowa parlorn Khadijah tayi gabanta na faduwa, few mutane ne parlorn kuma yawanci duk manya ne, ta durkusa jikin kujera a hankali tace "Ina yinin ku" amsa mata suka yi da fara'a, wata a cikinsu tace "Ikon Allah, ji mai kama da su Maimoon" Yarinyar da ta bude kofar tace "Wllh Anty na xata Safeenah ce ta da farko, haka na tsaya da mamaki Ina kallonta don nasan Safeenah na daki ai" Ita dai Khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Wata mata dake kusa da ita tace "Dama haka Allah ke ikon sa ai, tashi ki shiga ciki yan mata suna can gaba daya" warce ta bude mata kofar ne ta kai ta har dakin da jawahir da yan uwanta suke, Khadijah dai gabanta sai faduwa yake ta sunkuyar da kanta, da sallama ta shiga dakin bayan yarinyar ta bude mata kofa, suka hada ido da Jawahir dake xaune gefen gado tana danna wayarta, sosai tayi kyau sai wani glowing chocolate skin din ta yake, hannayenta sun sha lalle, kai kana ganinta ka ga amarya, Khadijah ta sunkuyar da kanta, Maryam ce ta fara mikewa ganinta tace "Lah Khadijah ashe kin dawo" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Ehh ban dade da dawowa ba" Maryam tace "Ayya, Sannu da dawowa, ga waje ki xauna" Bata kai ga xama ba Deejah ta fito daga bayi tana ganinta ta rungume ta da murna tace "Khadijah har na gaji da jiran ganin yaushe xa ki dawo, gashi babu mai number ki, Sannu da xuwa" Khadijah tace "Ayya ni ban san jiya xa ku taho ba ina gidan frnd dita ce" A hankali Khadijah ta xauna Deejah ta xauna kusa da ita tana kallonta da fara'a tace "Mun taho rakiyar amarya" Khadijah ta kalli jawahir a hankali tace "Sannu Amarya, Allah ya bada xaman lafiya" sai a sannan jawahir ta kara kallonta babu yabo babu fallasa tace "Ameen" Deejah sai kallon jawahir take alamar bata ji dadin yanda ta amsa mata ba, ita kanta Maryam dauke kanta kawai tayi, Safeenah ta shigo dakin tace "Lahh ashe har kin shigo" Khadijah tayi murmushi tace "Eh na shigo" ta karaso ta xauna ita ma tace "Su Anty Deejah na ta labarin ki a Nigeria sai gashi yau na gan ki, kin lura da kamar da muke yi kuwa?" Dariya ta ba Khadijah, Maryam da Deejah ma suka yi dariya ban da Jawahir da ta tsuke fuska, A hankali Khadijah tace "Ikon Allah kenan" Safeenah tace "Gaskiya ne, Ammin mu na gaishe ki" Khadijah tayi murmushi tace "Na amsa sosai" hira suka dinga yi dakin banda Khadijah da sai dai tayi murmushi idan sun kallota, duk a takure take ta kagu ta tashi ta wuce amma ta kasa tashi, agogo ta kalla ganin uku ya wuce tayi karfin halin mikewa tace "Xan dan shiga ciki ina aiki ne" Safeenah tace "Amma xa ki dawo ai?" Murmushi Khadijah tayi tace "Ehh xan dawo anjima" Rakota suka yi parlor, Khadijah tayi ma wa enda ke xaune parlor sallama ta bude kofa xata fita suka kusa cin karo da khaleel, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yanda ta daburce shi ma haka, yyi saurin bata hanya, ganin Deejah da Safeenah na bayanta tayi karfin halin ce masa "Ina yini" yace "Lafiya lau, ya gida" fita tayi daga parlorn bata ce komai ba ta bude apartment dinta ta shiga ta rufe, ganin la'asar yayi ta daura alwala a bayi tayi sallah sannan ta kwanta, bude data tayi da sauri tunawa da tayi daxu Barrister yace xai turo mata sako ta duba, ko ya bar Dubai din ma oho, ai ko tana budewa taga messages da ya turo mata da yawa, ta shiga tana kallon message din, kusan gaba daya hotuna ne, downloading din su ta fara yi, murmushi tayi ganin set na akwatuna ne yace ta xabi wanda take so, a hankali ta dinga scrolling tana duba boxes din, bbu na banxa gaba dayansu, murmushi tayi masa as reply, sannan ta tura masa message tace duk sun yi kyau sosai, daga haka ta kashe datan ta, bayan kusan minti goma sai ga kiransa, kuri ta kura ma wayar ido, can ta daga a hankali ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren yace "Amira" tace "Na'am good day" yace "Thanks, I saw ur reply, kuma ni ba tambayar ki nayi ko sun yi kyau ba" Yar dariya tayi tace "Barrister amma ai kai ma kasan sun yi kyau" yace "My question is wanne kika fi so" tayi murmushi tace "Uhm ni ban san wanne xan ce ba barrister" yace "Ask ur frnds then" tace "Toh xan tambaya" yace "Ina fa jiran ki kafin gobe, don goben xan bar Dubai" a hankali tace "Toh barrister" daga haka yayi mata sallama ya katse wayar ta koma ta kwanta a sanyaye, juye juye ta dinga yi tana kokarin bata ba damuwar dake neman dirar mata a xuciya space ba, can ta mike jin ta fara jin yunwa, kitchen ta tafi ta daura ruwan xafi don tafasa na shayi, kamar ance ta leka window taga khaleel xaune waje doing nothing, hada ido suka yi tayi saurin dauke kanta ta ci gaba da abinda take, tasowa yayi a hankali ya iso kusa da windown ya tsaya yana kallonta, trying her best not to look toward his direction tace "Wishing a happy married life, Allah bada xaman lafiya" kallonta kawai yake, can a hankali yace "Khadijah" kashe gas dinta tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta nufi kofar fita kitchen din ya bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar. Shayin da bata sha ba kenan tana ta xaune parlor wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin me kiranta tayi picking ta kai kunne tayi shiru, "Ki fito muna waje" abinda Aliyu yace mata kenan, ta mike a hankali ta tafi daki ta dauko hijab dinta ta sa ta fita, Tana isa kusa da motar ta bude ganin bashi da alamar fitowa ta fiddo Shureim tana kallonsa, xata wuce yace "Jira ki karbi sakon Mumy" Bata ce komai ba ta tsaya ya fito ya bude bayan mota ya ciro wani leda ya bata, amsa tayi tace "Mun gode Allah saka da alkhairi" Har ta juya xata tafi sai kuma ta tsaya tana kallonsa ta basa wayarta tace "Ka sa min number ta sai in kirata in mata godiya" karbar wayar yayi ya sa mata digit din Mumy ya mika mata, ta amsa tace "Thanks" yace "Don't forget ki tambayeta jikin Anty Khadijah idan Kin kirata" tace "Har yanxu bata samu sauki ba?" Yace "She is still at the hospital" Shiru Khadijah tayi, lkci daya jikinta yayi sanyi, can tace "Toh Allah ya bata lafiya" Yace "Ameen" Cike da karfin hali tace "Ya jikin iklima fa?" Ya shafa kansa yace "Tana can family din babanta, ban samu xuwa dubata ba coz I spent only three days kuma throughout Zaria nake ta tafiya gun Anty Khadijah" Khadijah tace "Toh Allah ya sauwake, idan muka yi hutu soon xan je gida sae in je in duba Anty Khadijah da Umma" Yace "Alryt" shiru ta kara yi, sai kuma ta kallesa tace "Ina son tambayar ka pls" yana kallonta ya rungume hannunsa yace "Ina jin ki" ✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨ Khadijah tace "Ya dangartakar ku da su Deejah?" Ya d'an yi shiru yana tunani kafin yace "Wacece Deejah kuma?" Ta kallesa tace "Deejah ce baka sani ba?" Buda ido yyi yace "Ohh wai warce kika tarar gida ranan da na kai ki kike nufi, kawar Maryam" Khadijah tace "Ehh" yace "I think, noo they are just family frnds kawai, Dad din Maryam da dad dinsu are just good frnds, childhood frnds if I am not mistaken, that's just it" Khadijah tace "Toh Maryam fa?" Ya shafa kansa yace "Her mum kanwar Abbana ce, dad dinta kuma was once under my dad, so Maryam is my cousin" Khadijah tace "Ohk" yana kallonta yace "But why did you ask?" Wani kallo tayi masa tace "Is there anything wrong with me asking?" Murmushi yayi yace "Not at all, yaushe xa ku fara exams?" Tace "Nan da 3wks" yace "Ohk Allah ya kai mu" tace "Ameen" daga haka ta kama hannun Shureim dake tsinkar flowers ta nufi cikin gida, Aliyu ya bi su da kallo Shureim na daga masa hannu har suka shiga cikin gidan. Da daddare Khadijah na bedroom tana karatu bayan Shureim yayi bacci taji an danna bell, sosai gabanta ya fadi ta kalli agogo, a lokacin ma takwas yayi, ta mike a hankali ta isa gun kofar ta tsaya tace "Waye?" Jin muryar mace ta bude kofar, Safeenah ce tsaye bakin kofar tace "Khadijah I want to spend the nigh here if it's ok by you" Khadijah tace "Oh you are welcm" daga haka ta bata hanya ta shigo parlorn tana cewa "Su Anty Deejah na takura ni shi sa na yo nan, da dare bai yi ba gidansu Maryam dama xan tafi" Khadijah tayi murmushi tace "To mu shiga ciki" bin bayanta Safeenah tayi har suka isa bedroom dinta, Safeenah na kallon Shureim dake bacci tace Woaw brothern ki ne wannan" Murmushi Khadijah tayi bata ce komai ba, can kuma tace "Ki hau saman gadon" Safeenah ta hau kan gadon xuwa daya side din tace "Hope baxan takura ku ba" Khadijah ta xauna gefen gadon tace "Haba dai ba wani takura" Safeenah tace "Kin san har na fara ba Abban mu labarin ki" Khadijah tayi dariya tace "Haba dai" Safeenah tace "Ehh mana, Ko mijin Jawahir Dr Ayman ya din ga kallona jiya da muka xo, da yake bai san ni ba dama tunda ba gida daya muke da jawahir ba, she is my cousin, My father and her mother are having same parent" Khadijah tace "Ayya that's nyc" Safeenah tace "Ke karatu kawai ya kawo ki kasar nan kenan" Khadijah ta gyada kai tace "Na ma kusa gama wa" Safeenah tace "Ayya, a Nigeria wani state ku ke da parent din ki?" Khadijah tace "Kaduna" Safeenah ta gyada kai tace "Su jawahir ne ke kaduna mu a Abuja muke" Wayar Safeenah ya fara ring ta duba, mike tayi ta koma can karshen gado tace "Let me answer my call Khadijah" daga haka tayi picking call din, murmushi Khadijah tayi ta mike don dauko masu rigar sanyi, har ranta taji tana son Safeenah, she's just free minded, daya side din gadon ta tafi ta kwanta bayan ta ajiye ma Safeenah rigar sanyin, ta lumshe ido nan da nan bacci ya dauke ta. Da asuba bayan sun idar da sllh Safeenah ta koma ta kwanta, Khadijah ta fita xuwa kitchen tana tunanin abinda xata yi na breakfast ta kai ma su Deejah, Irish tayi deciding ta soya da kwai ta dafa masu ruwan shayi don ita iyakar abinda take ci kenan gidan sai indomie ko shinkafa... Gaba daya cimar kasar bai dameta ba shi yasa ko siya bata yi, ta fi ga abincin Nigeria, har ta gama abinda take a kitchen Safeenah bacci take, daukan Shureim tayi ta fita daga dakin xuwa wani dakin tayi masa wanka ta dauko Uniform dinsa ta shiryasa ta sa masa kayan sanyin sa sannan ta basa Breakfast, wankan tayi ita ma kafin ya gama ta shirya cikin abaya ta yafa mayafinsa ganin da sauran lokaci yasa bata kai masu breakfast din ba ta tafi kai Shureim makaranta, tana dawowa ta tarar da Safeenah a parlor, Tace "Har kin tashi?" Safeenah tace "Wllh Dr Ayman ne ya tashe ni yanxu shi ya xo neman ki" Khadijah tace "Nema na kuma?" Safeenah tace "Noo xai fita ne yace xai yi dropping brother dinki a schl sai nace kilan kin je kai sa" Khadijah tace "Ayya ai daga can nake ma, akwai ruwan xafi bathroom idan xaki yi wanka" Safeenah ta mike tace "A'a bari in je can inyi tunda kayana na can din, dama jira nake ki dawo" daga haka ta nufi kofa Khadijah tace "Toh shkkn, Amma xa ki dawo?" Safeenah tayi dariya tace "Eh xan dawo" Khadijah tace "in bar maki breakfast din ki a nan kenan" Safeenah tace "Da safen nan fa xa mu wuce Khadijah" Khadijah tace "Da gaske" Safeenah tace "Ehh amma can gidansu Maryam xa mu je, Mum dinmu na can anjima da yamma sai mu dau hanyar Naija" Khadijah tace "Ayya to shikenan, idan na fito lectures da yamma kila in taho gidansu Maryam sai muyi sallama" Safeenah tace "Ba wani kila, kawai ki taho ku gaisa da Ammin mu tana can gidan ai, plss ki xo wllh ni dai ina son ki fa Khadijah I want us to be frnds" dariya Khadijah tayi tace "Toh in sha Allah xan xo" daga haka Safeenah ta wuce, Khadijah ta dau breakfast da ta masu a kitchen ta kai masu, a hankali ta bude kofar dake bude ta shiga parlorn, babu kowa parlorn sai ac dake kunne duk da sanyin garin, a hankali ta durkusa nan tsakiyar parlorn ta ajiye abubuwan hannunta, tana tunanin shiga daki wata xuciyar na ce mata kawai ta yi wucewarta idan sun fito xa su gani, har xata mike sai ga Khaleel ya fito, ya shigo parlorn yana kallonta, dai dai nan Safeenah ta fito daga daki ita ma ganin Khadijah tace "Yauwa Khadijah na bar wayata bedroom din ki" Khadijah ta mike da sauri tace "Lah to bari in dauko maki, dama xan taho da flask yanxu" Daga haka ta fita Khaleel ya dinga kallon safeenah da bata yarda ta kallesa ba tace "Ina kwana Doctor" yace "Lafiya lau" juyawa yayi ya wuce bedroom dinsa ya xauna kujera yana kallon jawahir da shigowar ta dakin kenan ita ma, atamfa ne jikinta ta yafe jikinta da mayafi tayi kyau sosai, a hankali tace "Ina kwana" yace "Lafiya qlau dear, I want to ask you something, shud i?" tana kallonsa tace "Ina jin ka" yace "Safeenah naji kamar ake kiran ta koh?" Jawahir na kallonsa tace "Ehh, what about her?" yace "Ya ku ke da ita pls?" Jawahir tace "She is my cousin sis, My mum and her father are having same parent, me ya faru?" Kallonta ya dinga yi kafin yace "Where do they stay?" Tace "Abuja" yace "Ohk sorry I'm asking this dear, bayan Dad din Safeenah, da Umman ku, da Uncle din ki na Lagos, akwai wasu kawun nan ki da ban sani ba ko aunt din ki? ta bangaren mumy fa nake tambayar ki" jawahir ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Dama su biyar ne kawai gun maternal grand parent dina, kawun mu na Lagos ne babba, sai Abbansu Safeenah, sannan kawu Abdul, sai Ummata da kuma autarsu, but she is late, ta rasu" Khaleel dake ta kallonta yace "Since when?" Ta girgixa kai tace "I really don't know don Umma tace min muna yara lokacin, she is always talking about her younger sis til date, seems tana sonta sosai" Khaleel na kallonta har lkcn yace "Kuma tayi aure kafin ta rasu?" Jawahir tace "Gaskiya ban sani ba" Khaleel ya dawo kusa da ita yace "Plss do me a favor of asking Umma to tell you more about her" da mamaki Jawahir ke kallonsa tace "But why?" Ya shafa kansa yace "Ke dai ki tambayar min ita plss wife" d'an murmushi tayi tace "Toh xan tambayar maka in sha Allah" yace "Yauwa nagode sosai" Khadijah na komawa apartment dinta ta dauko wayar Safeenah da flask na Lipton da ta dafa ta dawo apartment din Dr Ayman, har lkcn Safeenah na parlor tana jiranta, bayan ta karbi wayar tace "Thanks much Khadijah, baxa ki shigo ku gaisa da su Deejah da jawahir ba?" Khadijah tayi murmushi tace "Toh ina xuwa, xan dawo yanxu" daga haka ta fita, tana shiga apartment dinta jakar makarantar ta kawai ta dauka ta bar gidan don bata son sake jamming da khaleel, she just can't withstand the sight of him. Kamar yanda tace ma Safeenah suna gama lectures karfe uku da yan mintuna ta tafi gidansu Maryam tunda ta mata alkawari, Hajiya Mariya taji dadin ganinta haka mahaifiyarsu Safeenah, Khadijah na ganinta ta ganeta don ita ce suka yi vid call kwanaki, Safeenah tace "Ammi kin ganta koh" Ammi tayi murmushi tace "Ae kam na ganta, ya iyayen naki Khadijah" Khadijah tace "suna lafiya..." Ammi tace "A kaduna ku ke da xama?" Khadijah ta gyada kai tace "Ehh" Hajiya Mariya tace "Ina Shureim din Khadijah?" Khadijah tace "Yana schl Mumy" shirye shiryen wucewa Airport suke, Khadijah dai na ta xaune parlor tare da Hajiya Mariya da Ammin su Safeenah, gaba daya hankalinta yayi kan Shureim sanin sun tashi amma ta rasa me yasa ta kasa masu sallama ta wuce, wayar ta ne yyi ring ta kalli Deejah dake kusa da ita tayi excusing kanta ta fita, kasa daukar wayar tayi duk jikinta yayi sanyi, gaba daya ta mance ita yake jira, ganin xai tsinke ta dauka daga karshe ta kai kunne a hankali tayi masa sallama, amsawa yayi yace "Uhnn it seems.... Amira ni kadai nake hauka na koh?" Da damuwa tace "Am very sorry barrister, I wanted calling you na mance, but kasan me duk wanda kaga ya maka kyau Wallahi ina so, I want ur choice" jin yayi shiru a hankali tace "Ka yi shiru barrister" yace "Ohk then..." Marairaicewa tayi tace "You are still angry koh?" Yace "Sure" tace "But nace fa kayi hakuri" yace "Amira if I am important to you baxa ki ce kin manta ba, am still in dubai because of you but kuma kice min kin mance" jikinta yayi sanyi tace "Don Allah kayi hakuri..." Yace "Nayi" daga haka yayi mata sallama ya katse wayarsa, tana ta tsaye duk bata ji dadi ba don tasan bata kyauta masa ba aka shigo gidan da mota, bin motar tayi da kallo har yayi parking ya fito, kallonta ya dinga yi sai kuma ya karaso inda take yace "Iman, when did you come?" Tace "Yanxu" yace "Good evening" tace "Same, pls kace ma su mumy na tafi Shureim yana schl har yanxu" ya kalli agogon wrist dinsa yace "Har yanxu? This is after 4" tace "Na xo sallama da su Safeenah ne" ya kara kallon agogo yace "Ohk to mu je ki daukesa in kai ku gida dama airport xan kai su..." Tace "A'a don't worry ka kai su airport din, tnxx" daga haka ta juya ta fita gidan, tana isa makarantar su Shureim ya samu an xo an daukesa, wucewa gida tayi, tana bedroom ta cire kaya ta daura towel xata shiga wanka aka bude kofa da sauri ta juya shureim ya shigo da sallama ya wara ido yace "Anty yau ma na riga ki dawo wa" Tace "Wa ya dawo da kai?" Yace "Uncle mana" jawosa tayi ta xauna gefen gado tace "Da kuka dawo mai Antyn dake gidan tace maka?" Yace "Nothing, she only gave me food with juice, shine yanxu tace in xo in cire uniform" Khadijah ta tabe baki tace "Shi uncle din me yake?" Ya buda ido yace "Yana daki..." Ta kuma tabe baki ta cire masa uniform dinsa ta fara yi masa wanka tasa yayi alwala suka fito ta shirya sa sannan tace yayi sallah, wanka ta shiga tayi ta fito ita ma ta shirya, Shureim na assignment dinsa kan gado ta dau wayarta, text ta shiga rubuta ma Barrister na ban hakuri tana gama rubutun ta tura masa, dai dai nan aka danna bell ta mike ta dau gyalenta ta fita. Khadijah na kwance bedroom dinta waya kare kunnenta tana sauraren Umma dake mata magana, bayan wani lkci ta turo baki a hankali tace "Umma ni ce masa nayi ko wanne, I don't have choice..." daga daya bangaren Umma tayi murmushi tace "You know ur problem Khadijah?" Khadijah ta girgixa kai a hankali kamar tana ganinta, Umma tace "Kin ki kwantar da hankalin ki to know what's best for you, sure ni na san kina son khaleel but he is married kin sani, me yasa har yanxu xuciyar ki ke yaudarar ki?" da mamaki Khadijah ta dinga sauraren Umma, can dai tace "Umma how did u knw he is married?" Umma tace "Ya xo gida ranan Saturday, he told me about his wedding" Khadijah taji hawaye ya taho mata ta kasa cewa komai, Umma tace "Ke da bakin ki kika ce masa barrister... to don me kuma baxa ki kwantar da hankalin ki da Barristern ba, it's not as if Khaleel isn't good, but I think barrister Aliyu is the best for you, Kuma khaleel daga aure ai baxai fara xancen auren ki ba kuma, Khadijah as a mother nake gaya maki ki kwantar da hankalinki ki ba barrister chance you won't regret it, idan kuma kinga khaleel din ke xuciyar ki to sai ki tanadi kalaman da xaki gaya ma barrister but count me out kar ma ki nuna masa na san komai" Hawaye na sakko mata cikin sanyin tace "Ni ai ban ce ban yarda da barrister ba Umma, his wife is my greatest fear Umma lkcn a clinic da Sudais bai da lafiya I didn't tell you she called and warned me to stay away from her husband" Sake baki Umma tayi tace "Ehh lallai Khadijah da alamar rako mata kika yi, ita kishiyar xaki fara tsoro tun baki shiga gidan ba, ita kishiyar Khadijah?" Turo baki tayi tace "Umma ni ba tsoronta nake ba kawai dai tashin hankali ne bana so, I don't want anything that will make me sad" Umma tace "Toh ai ba gida daya xa ku xauna ba" Khadijah tayi shiru bata ce komai ba, cikin kwantar da hankali Umma tace "Kiyi ta addu'a daughter, Allah ya maki xabi mafi alkhairi" a hankali Khadijah tace "Ameen" Umma tace "And one more thing Khadijah in har ke a tunanin ki saboda kawai Barrister Aliyu ya taimake ki a rayuwa kike son aurensa to pay him back toh gaskiya you are making a mistake kuma kin cucesa kin cuce kan ki indai sabida haka kika amince da aurensa" Hawaye Khadijah ya dinga yi sosai duk jikinta yayi sanyi, cike da karfin hali tace "Umma ba haka bane" Umma tace "Are you sure Khadijah" tana gyada kai da kyar tace "Ehh" Umma tace "Toh am happy to here that, ke dai kiyi ta addu'a kawai, and make sure yanxu ki kirasa ki ce masa ga wanda kika fi so a akwatunan" Khadijah na share idonta tayi kasa da murya tace "Wanda kika ce ya fi koh?" Umma tace "Ehh" A hankali tace "To bari in kirasa yanxu nagode Ummata" Umma tace "Welcm dear, Shureim yayi bacci koh?" Kai ta gyada tace "Ehh yayi but kamar yana son yin mura fa Umma, his voice is even cracky" Umma tace "Wannan kuma ke kika sani, least I forget nasan halin ki Khadijah tsakanin ki da matar khaleel mutunci kada kiyi amfani da cewa kina son mijinta ki dinga daure mata nasan ba hankali ya ishe ki ba" turo baki Khadijah tayi tace "Umma ni da ma mun kusa hutu in taho gida abuna ina ruwana da su" Umma tace "Khaleel dai ba abun walakanci bane a gun ki, though baku dade da sanin juna ba but he is always there for you, kuma duk da yasan ke wacece ya nuna yana son ki yana yaran ki, am reminding of all this ne don naga kamar kina da saurin mance alkhairi, dubi fa mahaifiyar Aliyu ba don nayi da gaske da ke ba ita ma ba raga mata xaki yi ba" jikin Khadijah yayi sanyi sosai, Umma tace "Sai da safe" daga haka ta katse wayarta, Khadijah tayi lamo kan gado, can ta bude idonta a hankali ta shiga kiran barrister a sanyaye, bayan sun gaisa a hankali tace "Barrister ka fara bacci ne?" yace "Noo ina wani aiki ne, how r you?" Tace "Lafiya lau, I now have a choice my barrister" Ya d'an buda ido yace "Really?" Tana murmushi tace "Sure" yace "Then which is ur choice?" Ta langwabar da kai tace "Ka hau Whatsapp in nuna maka yanxu" yace "Ohk then" daga haka ta katse wayar, bayan ta nuna masa akwatin da take so tayi masa text din sai da safe, daga haka ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa. washegari da safe Khadijah na sa ma Shureim shoes dinsa na makaranta aka danna bell, ta kalli kofar kafin ta mike ta dau jakarsa ta goya masa a baya ta dau lunchbox dinsa tana rike da shi ta nufi kofar ta bude, khaleel ne tsaye bakin kofar, bai yarda ya kalleta ba yana kallon Shureim da murmushin sa mai kyau yace "How are you son?" Shureim yace "Good morning uncle" khaleel ya duka ya kamo hannunsa yace "The morning isn't good son, cold everywhere..." dariya Shureim yayi da ya bayyana white set of teeth dinsa, Khaleel yyi murmushi yana kallon kyakkyawan yaron ya fito da shi ya mike, gyara rigar sanyi sa yyi still bai yarda ya kalli Khadijah da ta hade rai ba yace "Plss do u use salt?" Khadijah na kallonsa tace "Meye shi?" Sai a sannan ya kalleta yace "Gishiri" sauke idonsa yyi daga kallonta, ta tabe baki kamar baxa ta ce komai ba sai kuma can tace "I don't know, let me check" daga haka ta juya a hankali ta koma ciki, Shureim yace "Uncle Aunt din nan tana nan" khaleel ya shafa kansa yana kallonsa yace "Tana nan" Shureim yace "Ae yau tace xata bani puzzle irin na su fadil..." khaleel yace "Tana bacci yanxu, ka bari sai ka dawo school xata ba ka" Shureim yace "Ohk can I tell her good morning now so as she will remember my puzzle?" khaleel ya duka yana kallonsa a hankali yace "No she is sleeping son, idan ta tashi I will remind her for you" Shureim yace "Ohk tnx" Khadijah ta dawo rike da container din Gishiri ta mika masa, ya karba yace "Thanks I will bring back the remaining now" Kamar jira take tace "Noo na ba ku" kallonta yayi da sauri yace "Noo ni xan yi amfani da shi ai" Wani kallo Khadijah tayi masa tace "Did you hear me mention name?" Khaleel ya sauke idonsa daga kallonta, a hankali ya juya xai koma ciki sai kuma ya juyo da sauri yace "I am coming inyi dropping dinsa a schl" Khadijah tace "Xan kai sa yanxu, you don't worry" yana kallonta da kyau yace "I insist Khadijah" daga haka ya juya ya wuce ciki, Khadijah tafi minti biyar tsaye a wajen can ta juya ta koma parlor ta xauna shureim ya biyo bayanta, tashi tayi daga parlorn gaba daya mood dinta ya canxa ta kalli Shureim tace "Ka jira sa a nan" daga haka ta wuce bedroom ta kwanta, ta rasa dalilin da yasa ta ji tana son yin kuka, ta kife kanta da pillow trying hard not to cry, ta fi minti goma a haka aka bude kofar dakin, Shureim ya shigo yace "Anty uncle yace in kira ki" A hankali ta mike xaune ta runtse ido jin xuciyarta na mata xafi, ta kalli agogo taga takwas saura, da kyar ta tashi ta bi bayan Shureim, tsaye ta tadda khaleel parlorn har ta karaso cikin parlorn bai yarda ya kalli inda take ba, ta tsaya tana kallonsa, kama hannun Shureim yayi yace "Plss Khadijah I need hot water, or rather lipton kafin in dawo" daga haka ya fita tare da Shureim dake daga mata hannu ya rufe kofar, juyawa tayi ta koma daki tayi kwanciyar ta. Bayan kusan minti ashirin aka danna bell, kin tashi tayi daga kwancen da take, Jin an sake dannawa ta daure ta dake, cike da karfin hali ta tashi ta fita, bude kofar tayi tana kallonsa, ledan hannunsa ya mika mata yace "Drugs din Shureim naga he is having cold" karba tayi ba tare da ta kallesa ba tace "Thanks" daga haka ta juya xata wuce yace "Khadijah ruwan lipton din fa?" K'in juyowa tayi tace "Ni bani da ruwan Lipton" daga haka ta rufe kofar ta, daki ta wuce ta fada kan hado tayi kukanta mai isarta Kamar warce aka aiko ma da sakon mutuwa, ita kanta bata san me yasa take kukan ba, ta fi minti talatin kwance, ta mike a hankali jiki ba kwari daga karshe ta fito parlor, kitchen ta shiga ta kunna gas ta daura ruwa ta xuba Lipton da kayan kamshi ta dawo parlor ta xauna, tana ta xaune parlorn har taji alamar ruwan ya tafasa ta mike a hankali ta shiga kitchen din, cikin flask ta juye ruwan Lipton din gaba daya ta sa hijab ta fita, danna bell dinsa tayi, tana ta tsaye bayan wani lkci ya bude kofar, Mika masa flask din tayi ba tare da ta kallesa ba tace "Yanxu na dafa" Ya karba a hankali yace "Thanks Khadijah" Bata ce komai ba ta juya ta koma apartment dinta, sai kusan sha biyu ta fita gidan duk da karfe goma take da lectures, da wuri ta fito schl don daukar Shureim ta samu har khaleel ya xo ya dauke sa, har ta fito wanka tayi sllh tana ta jiran ganin shigowar Shureim amma bai shigo ba, throughout ranan babu wani abin kirki da ta ci kuma gaba daya taji bata jin yunwa, a hankali ta dau wayarta don kiran Barrister taji ko ya isa gida lafiya, har ya katse bai dauka ba ta sake kiransa, nan ko yana xaune parlorn sa Little Meerah na jikinsa tana ta masa surutu da pure English dinta, Jiddah kuma na durkushe gabansa tana xuba masa dafadukan taliya da ta dafa sanin ranan xai dawo, kallon taliyar kawai yake don he is not a fan of it kuma sarai tasan baya ci, ya girgixa kai ya dauke kai daga abincin, ajiye serving spoon din hannunta tayi ganin alamar ana kiran wayarsa da ke jone a caji, ta mike ta nufi inda wayar yake, tana isa ta dauka tana kallon screen din "Ameerah" sunan da ta gani kenan jikin screen din, ta dinga kallo xuciyarta na bugawa, picking call din tayi kafin ya katse ta kai kunne tayi shiru Khadijah na jin an daga ba a ce komai ba tayi shiru ita ma don it's unusual of him kuma tana jin muryar little Amira a wajen, Kamar ance Sudais ya daga kai ya ga jiddah tsaye har lkcn wayar na kare kunnenta fuskar nan nata a murtuke, ajiye Amirah yyi kan kujera ya mike da sauri yace "What's that u are doing Jiddah?" Ba shiri Khadijah ta katse wayar ta ajiye ta tabe baki ta yi kwanciyar ta. Jiddah na masa wani kallo tace "Wato dai da gaske aure kake shirin yi saboda baka da tsoron Allah ko Aliyu?" Ya warce wayarsa a hannunta yana mata wani kallo yace "Don't you ever dare pick my call again malama" daga haka ya bar parlorn ya wuce sama, Xaunawa gefen kujera Jiddah tayi lkci daya hawayen takaici ya shiga sakko mata, ai da ta sani kawai guduwa daki tayi da wayar tayi pick din call din ta sussurfa ma shegiyar dake kiransa xagi, to Wai wacece wannan Amirar? Sai yanxu taji tana mugun son sanin wacece ita, ta kalli Yar ta dake xaune tana kallon tv, lkci daya lkcn da ta haifeta ya dawo mata, ranan sunanta bayan ya sa sunan mahaifiyarsa babu yanda bata yi da shi kan cewar da Khaleesat xata kirata ba yace inaaa bai san xance ba sai dai Amirah, da ta tambayesa me yasa sai ce mata yyi sunan wata frnd dinsa mai muhimmanci a rayuwarsa ce kuma yana ji da ita sosai shi yasa xai kira 'yar sa da haka.... Jiddah ta mike da sauri xuciyarta na bugawa ko dai ita ce wannan mai kiran nasa yanxu, ita fa dama tun lkcn taji ta tsane koma wacece Amirar nan, shi yasa har yanxu da kyar take kiran Yar ta da Amirah, a bayan idonsa dama kiri kiri Khadijah take ce mata, wayarta ta dauka ta shiga dakin da ke parlorn ta kulle kofa ta shiga neman number Dr Yusuf tasan duk yanda aka yi baxai rasa sanin wacece Amira ba, bugu biyu ya daga bayan sun gaisa yana tsokanarta wai ta sa abokinsa ya mance shi gaba daya, ta xauna gefen gado tace "Dr dama tambaya ce na kira in maka don Allah..." Dr Yusuf yace "Toh Ina ji, Allah sa na sani dai" tace "Uhm nasan ka ma sani, wllh in gaya maka abokin ka ne duk ya ishe ni da wata Amira nayi nayi ya gaya min wacece ita ya ki, har cewa yayi idan na cinka wacece ita to xai bani kyautar mota, toh ni dai duk iya tunani na rasa gane wacece amma na fi tunanin frnd dinsa ce kilan da yake ji da, shine yanxu na kira ka bani satar amsa, dama wllh motata ta isheni sabuwa dal nake so, Kuma kasan barrister baya saba alkawari plss Dr ka taimaka" dariya sosai Yusuf yayi yace "Wai Amira?" Gabanta na mugun faduwa tace "Ita fa Dr..." Yace "Yasan baxa ki taba sanin wacece ita ba, Kuma xancen gaskiya babu wani mota da yake da niyyar baki don yasan ko xa ki shekara kina naxari baxa ki san wacece ita ba, it's not even possible, Ni kuma yanxu idan na gaya maki kika fada masa he will suspect ni na gaya maki don duk abokansa babu wanda yasan ta sai ni...." Jiddah tace "Haba Doctor, shi kansa yasan ai alkawari yayi baxai saba ba, Ni dai fa damuwata mota, don Allah ka gaya min ai bai san ina da number ka ba he won't suspect anything" Yusuf yyi murmushi yace "Toh xan gaya maki indai sabuwar mota kike ma" ta baxa kunne tace "Yauwa nagode sosai Dr" nan Dr Yusuf ya fara bata labarin Khadijah tiryan tiryan babu abinda ya boye a duk labarin har ranan da Mami ta rabasu na karshe. Gaba daya xufa ya dinga karyo ma Jiddah taji cikinta ya hautsine, Jin Yusuf yace "Hello" cike da karfin hali tayi dariya tace "Ikon Allah, Allah sarki, to nagode Dr Allah saka da alkhairi Allah ya barka da Amina, sabuwar mota kam dole a ban" daga haka tayi masa sallama ta katse wayar dai dai lkcn da aka bude kofar dakin kafin ya kai ga shigowa tayi saurin boye wayar hannunta, ya shigo yana kallonta yace "Files da na bari kan dinning kafin nayi tafiya, Ina kika ajiye min?" ✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨ Shiru Jiddah tayi ta tallabi chin dinta tana kallonsa lkci daya kuma tana murmushi, Sudais ya hade rai yace "Magana fa nake maki jiddah?" Ta tabe baki tace "Amira na ba ta kai maka daki, kaje ka tambaye ta" wani kallo ya dinga mata yace "Amirar xaki ba files jiddah?" Cikin halin ko in kula tace "Ita, ko bata isa aike bane, Beside if they are that important ai baxa ka bar su yashe a dinning area ba" Girgixa kai yyi ya juya ya fice daga dakin, tayi wani murmushi mai sauti tana girgixa kafarta, lkci daya murmushin yayi fading a fuskarta, da ajinsa, da kyansa, da iliminsa da kudinsa duk fadin duniyar nan ya rasa warce xai kawo mata matsayin kishiya sai warce ta taba cikin shege ta haife yaran... Wani dariya ta kwashe har da kyakyatawa ta mike tana wani murmushi tace "Abomination" daga haka ta fice daga dakin, sai dai fa jin ranta take fess. Har khadijah ta fara bacci Shureim ya shigo dakin, ta dinga kallonsa har ya iso inda take yace "Anty cire min uniform" mikewa xaune tayi ta shiga cire masa uniform din jikinsa tace "Have u eaten?" Ya gyada kai yace "Uncle ya bani cornflakes" Khadijah na kallonsa tace "Are you okay with it?" Ya wara ido yace "Ehh Anty, ai da yawa ya bani, shi kuma ya sha tea" Khadijah bata ce komai ba ta dinga laluba aljihun wandon sa jin akwai abu a ciki ta fiddo Chocolate tana kallonsa tace "Wa ya baka?" ya karba da sauri yace "Aunt din nan ce ta bani, tace min xata siya min puzzles amma bata siya ba she is sick, she is even sleeping at the room" Khadijah ta ajiye kayan bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace "Anty will you go and check her?" Wani kallo ta dinga masa strictly tace "If I should slap you...." A hankali ya koma baya yace "Anty kiyi hakuri" tana hararansa ta nuna masa bayi tace "Wuce kayi alwala" ba musu ya wuce da sauri, ta mike don fiddo masa kayan da xai sa, magungunan sa da khaleel ya siyo masa daxu da safe ta basa sannan ta ce yaje parlor yayi assignment dinsa, ta hada socks dinsa xata shiga bayi ta wanke wayarta yayi ring ta dawo tana kallon wayar taga Barrister ke kiranta, ta karasa ta dau wayar ta xauna gefen gado sannan tayi pick din call din ta kai kunne, a hankali yace "Am sorry you called bana kusa Amira" tace "Ba komai, ka isa lafiya?" Yace "Lafiya Alhmdllh dear" tace "Ya Amira fah?" Yace "She's fine, how about my son" tace "Yana assignment" yace "Ohk ba shi mu gaisa" mikewa tayi ta fita parlor ta ba Shureim wayar tace "Abba yana son maka magana" ya karbi wayar yana kallonta yace "Anty waye Abba?" Harara ta watsa masa tace "C'mon answer ur call..." ya kai kunne a hankali yayi sallama, Barrister dake jin su yayi murmushi yace "How you boy?" Yace "Am fine Abba" Barrister yace "Ka je schl yau?" Ya gyada kai yace "Ehh na je" yace "Good, always aim good grades sai in siya maka Bicycle" ya wara ido yace "My two uncles sun ce xa su siya min bicycle, kaga am having three now, sai in ajiye ma Sudais daya, in ba su fadeel daya, Ni kuma..." Khadijah ta kwace wayar hannunsa ta koma daki, ta kai kunne a hankali tace "You need rest barrister, ya kamata ka huta, hope ka ci abinci?" Yace "Me yasa kika amshe wayar?" Tace "He is talking off hook" yace "Baki son dai in san two uncles din nasa" ta wara ido tace "Aliyu da Dr Ayman yake referring as two uncles fah?" Barrister yayi murmushi yace "Alryt then" ta langwabar da kai tace "Toh ka ci abinci?" Yace "Eh yanxu xan ci" tace "Toh shkkn, kaje ka ci, a shafa min kan Namecy na" yace "Ohk, will do that in sha Allah, thanks love" daga haka ya katse wayar, tayi murmushi ta ajiye ta kwashi socks din Shureim ta shiga bayi don wanke su. Washegari gaba daya bata da lectures ranan, da wuri ta shirya Shureim ta tafi kai sa makaranta don bata son khaleel ya xo yace xai kai sa, tana dawowa ta rufe kofar ta ta wuce bedroom ta kwanta, sai kusan sha daya ta tashi daga baccin da tayi, yunwan da take ji yasa ta wuce kitchen don neman abinda xata ci, ta kunna gas ta daura ruwa ta dauko indomie da kwai taji kamar motsi a baya, ta isa gun window ta tsaya kafin ta leka a hankali, tsaye ta ga Jawahir... khaleel na bayanta ya rungumota fuskarsa dai dai nata, yana d'aga karamin weight da hannu daya, Khadijah ta sauke idonta a hankali ta juya ta bar wajen, kashe gas din tayi ta fice kitchen din gaba daya ta wuce daki ta kulle ta fada kan gado. Ta fi awa uku a haka, har lkcn sllh yayi ta kasa tashi, cike da karfin hali ta mike daga karshe tana runtse ido ta shiga bathroom ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta sa hijab ta dau karamar jakarta da waya ta fita, tana kokarin rufe apartment dinta Khaleel ya fito, bata kalli inda yake ba ta gama rufewa ta juya xata wuce yana kallonta yace "What's wrong with you Khadijah, are u sick...." da kyar tace "No, i am okay" daga haka ta wuce waje ya bi ta da kallo, cab ta tsayar a waje ta shiga, kawai gani tayi ya ajiye ta schl, ita dai bata san ya aka yi ta ce masa can xata ba, ta fito ta basa kudinsa ta wuce ciki, cafteria ta nufa direct tana shiga ta xauna ta hade kai da table jin numfashinta na sama, ba a dau lkci ba Maryam ta shigo cafterian da frnds dinta xa su ci abinci, tana ganin Khadijah ta gane ta duk da kanta a kife yake har lkcn, ta isa kusa da ita tace "Hi Khadijah are u okay?" Da kyar Khadijah ta dago kanta, Maryam ta dinga kallonta ganin yanda idonta ya kada tace "Subhanallah baki da lafiya ne?" Kasa bata amsa Khadijah tayi, kana ganinta kasan she is in pain, Maryam ta fiddo wayarta a jaka da sauri ta shiga kiran Aliyu sanin yana within area din makarantar, Yana dauka tace "Ya Aliyu kana kusa ne plss, yanxu na shigo cafteria naga Khadijah kamar bata da lafiya, and she is not even responding, ko xaka taho yanxu plss...." Bata gama maganar ba Aliyu ya katse wayar, ta ja kujera ta xauna kusa da Khadijah tana kallonta da damuwa tace "Sannu Khadijah" frnds dinta turawa sai sannun suke mata su ma, Aliyu ne ya shigo cafterian ya karaso kusa da ita da sauri yana kallonta yace "Iman.... what's wrong, are you okay?" Tun Khadijah ma ganinsa bibbiyu a gabanta har daga karshe ta daina ganinsa kwata kwata, Bata sake bude ido ba Kuma sai can kusan magrib ta ganta kwance kan gadon asibiti, dafe kirjinta tayi ta dinga bin dakin da kallo, a hankali idonta ya sauka kan Aliyu dake xaune kusa da ita ya jinginar kansa da kujerar da yake kai idonsa a lumshe, kokarin tashi ta shiga yi hakan ya sa shi bude ido, da sauri ya mike ya dawo kusa da ita da damuwa yace "Stay still Iman kinga ruwa ne a hannun ki, how are you feeling now?" ta kalli drip din hannunta har sannan tana rike da kirjinta da kyar tace "It's hurting me" yayi kasa da murya yace "Kiyi hakuri xai daina Iman you are still under medication, koma ki kwanta plss" taki kwanciya ta hade kai da gadon, hawaye ne ya shiga sakko mata, a hankali yace "Iman?" Ta ki dagowa, hakan yasa ya tsaya yana kallonta cike da tausayi, cike da karfin hali ya ji tace "What about shureim...." Yana kallonta murya can kasa yace "I went to pick him in the evening na tarar neighbor din ki ya je ya dauke sa" Bata ce komai ba kuma bata dago ba yace "Let me call a nurse... Ina xuwa" daga haka ya fita dakin, ita dai har sannan bata dago ba hawaye kawai take kamar an bude tap, tare da wata baturiyar nurse ya dawo, ta duddubata ta fita, a hankali Aliyu yace "Iman kukan me kike plss?" ta kallesa hawaye na ci gaba da sakko mata ta kasa cewa komai, rikicewa yayi ya dawo kusa da ita sosai, yace "Don Allah Iman tell me whats wrong, me ya faru, me ne ke damun ki? Ur Bp isn't encouraging, ur condition don't need this, Tell me what ur problem is Plsss, ko an maki wani abu ne" ta goge idonta a hankali bata ce komai ba, Bude kofar ward din aka yi Maryam ta shigo tare da mum dinta, Hajiya Mariya ta karaso da damuwa tace "Sannu Khadijah, ya jikin naki yanxu?" a hankali cikin sanyi tace "Da sauki Mumy, Ina yini" Hajiya Mariya tace "Lafiya lau, Ina Shureim din" Aliyu yace "Neighbor dinta ya dauke sa schl daxu" Maryam ta ajiye basket din abincin hannunta tana kallonta tace "Allah ya sauwake murya can kasa Khadijah tace "Nagode Maryam" Hajiya Mariya tace "Nan xata kwana, ko xa su yi discharging dinta?" Aliyu yace "Sai gobe da safe" Hajiya Mariya tace "Toh shkkn sai Maryam ta kwana tare da ita" Shiru Aliyu yayi ya rasa me xai ce don bai so haka ba, Hajiya Mariya ta ja kujera ya xauna ta bude basket din don debar ma Khadijah abinci, sai kusan karfe takwas ta bar asibitin tare da Aliyu ba don ya so ba, suna fita babu dadewa wayar Maryam ya fara ring, dauka tayi ganin Jawahir ke kiranta ta d'an wara ido ta daga kafin ta ce komai taji muryar khaleel, xaro ido tayi tace "Ina yini Dr?" Yace "Lafiya lau ya kike, I want to ask plss Maryam, Kun hadu da Khadijah schl yau?" Maryam tace "Gata nan ai muna asibiti bata da lafiya, she collapsed daxu a cafteria but da sauki yanxu she's recovering" khaleel bai san lkcn da ya mike ba, jawahir dake kwance Shureim a gefenta dai sai kallonsa take, ya jira har Maryam tayi shiru kafin a hankali yace "Wani asibitin ku ke?" Ta fada masa sunan asibitin yace "Toh xan xo yanxu" daga haka ya katse wayar, yana kallon jawahir yace "Xan je duba Khadijah clinic yanxu she is sick, I will be back soon" jawahir dai bata ce komai ba ya nufi kofa, Shureim ya sauka daga kan gadon da sauri yace "Uncle ni xan bi ka" jawahir ta jawo sa jikinta tace "Don't worry yanxu xai dawo" a parlor khaleel ya dau makullin motarsa ya bar gidan ya nufi asibitn da Maryam ta gaya masa, yana parking a haraban hospital din ya fito ya kira Maryam don da wayar jawahir ya taho, Maryam na daga kiran yace "Ina waje Maryam" ward number ta fada masa yace "Thanks" daga haka ya katse wayar ya shiga asibitin, ya fi seconds talatin a bakin kofar ya kasa budewa, can ya murda a hankali ya shiga ward din, Kwance Khadijah take idonta lumshe, Maryam ta mike ganinsa tace "Sannu da xuwa Dr" yace "Yauwa Thanks" karasowa yayi bakin gadon yana kallonta, Maryam tace "Ina jin ta koma bacci" shiru yayi bai ce komai ba yana kallonta har lokacin don yasan ba bacci take ba, he really want Maryam to excuse them but he don't know how to make the approach, kamar kuwa Maryam tasan abinda ke ransa ta mike ta dau wayarta tace "Doctor bari inyi making wani call in dawo yanxu" ya kalleta yace "Alryt" daga haka ta nufi kofa ta fita ta rufe kofar, ya lumshe ido ya bude ya xauna gefen gadon ya kamo hannunta ya kai fuskarsa dai dai nata a hankali yace "I know you are awake Khadijah, look at me plss" Khadijah bata yarda ta bude ido ba, ya dinga kallonta, a hankali yace "Baxa ki kalleni ba Khadijah" dauke kanta tayi ta juya masa baya, mikewa yyi ya koma kujera ya xauna yana kallonta, bayan wani lkci yace "Shkkn since you don't want to see me bari in tashi inyi wucewata" a hankali ta juyo tana kallonsa, tausayinta ya dinga ji har ransa ya taso ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Ki gaya min ko na maki wani abun ne Khadijah, bana son wani abu ya same ki saboda ni, tell me ur mind plss..." Tana kallonsa da kyau tace "What is in my mind da xan gaya maka?" A hankali yace "Noo, ai ke xaki fada I don't knw what you are thinking of me... Say out ur mind Khadijah" ta hade rai tace "Kana tunanin saboda kai nake rashin lafiya a nan?" Ya buda ido sosai yace "Noo ba abinda nake nufi ba kenan" Tace "Toh ciwo ne kawai Allah ya sakko min, so I just have to say Alhmdllh" Ya langwabar da kai yace "Toh Allah ya sauwake" tace "Ameen" yace "Kin ci abinci?" Kai ta gyada masa tace "Su Maryam sun kawo min" Wayarta dake ajiye yyi haske alamar kira khaleel ya dauka ya mika mata ta karba, ganin barrister ke kiranta ta daga ta sa a handsfree ta kai kunne, da damuwa yace "Ina kika shiga Amira, I have been calling since but no response" ta koma ta kwanta a hankali tace "Kayi hakuri plss, yau tun da na tashi nake jin ciwon ciki, sai bayan da naje schl sai ya matsa min aka taho dani clinic.... Am even stil at the clinic" Sudais yace "Subhanallah, wani irin ciwon ciki ne haka?" Ta d'an buda ido tace "Aa ni ma ban sani ba, kawai dai ciwon ciki" yace "Ko dai... Ko dai na period ne?" xaro ido tayi don ita har mancewa take akwai wani abu wai shi al'ada, tun da ta haifi su Shureim ta daina, sai dai tayi bai fi sau daya ko biyu a shekara ba shi ma na kwana biyu, Amma fa tana shan axaba sosai don wani lkcn har tunani take kila mutuwa xata yi, yace "Uhm shine koh?" Yar dariya tayi tace "Ae ni bana yi" yace "Bakya me?" Tace "Uhm abinda ka fada mana" yace "Are you serious?" Tace "Ehh" yace "Maa sha Allah, kice doubling sadaki xan yi kenan" Boye fuskarta tayi da gado don ba karamin dariya da kunya ya bata ba ga khaleel a xaune, shi dae Khaleel idanuwansa na kan wayar hannunsa da yake dannawa yana saurarensu, ta dago a hankali tace "Koh?" Yace "Ehh mana, ai ku special ne cikin mata, and you are rare...." tace "Uhmm" lkci daya khaleel ya mike ya nufi kofa ta bi sa da Harara har ya fice, Barrister yace "But hope ciwon cikin da sauki sosai yanxu?" Ta gyada kai tace "Naji sauki amma sai gobe xa ayi discharging dina" yace "Toh wa ya kawo ki asibitin?" Da har xata ce Aliyu sai kuma tayi shiru, da sauri tace "Maryam da na baka labari ranan, ita ce ta kawo nii, luckily ta shigo cafteria lkcn ta gan ni kawai muka wuce clinic" Yace "Toh Allah ya kara lafiya, how about shureim ko tare ku ke a asibitin?" Ta girgixa kai tace "Noo yana gun neighbors dina" Barrister yace "Ohk, I will send the hospital bill yanxu kin ji" da sauri tace "Nooo, 'yan gidansu Maryam sun biya ma, don't bother plss my barrister" yace "Toh idan na turo sai kiyi pepper soup da yawa ke da Shureim ku ci, clear?" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace "Yea, sai da safe dear, Allah ya kara lafiya" a hankali tace "Ameen nagode sosai" lumshe ido yayi ya katse wayar, Khadijah ta mike xaune a hankali, gaba daya taji ta samu relieve kamar an cire mata ciwon, Maryam ce ta dawo ward din tace "Ashe kin tashi Khadijah" d'an murmushi Khadijah tayi tace "Ehh" Maryam tace "Ohk, Dr Ayman yace in fada maki ya wuce sai da safe" Khadijah tace "Ohk, I was making call ya fita" sosai Khadijah ta sake da Maryam suka dinga hira a ward din har Maryam ta dinga mamaki ganin ashe dai tana magana haka, sai kusan karfe sha daya duk suka kwanta. Washegari karfe bakwai na safe Aliyu ya xo clinic din, Khadijah na bathroom tana wanke baki da sabon toothbrush da Maryam ta kawo mata da paste, Maryam suka gaisa da Aliyu yana kallonta yace "Ya jikin nata?" Maryam tace "Ai kam taji sauki sosai" dai dai nan Khadijah ta fito ta karaso tana kallonsa a hankali tace "Good morning" yace "Morning Iman ya jikin?" Tace "Naji sauki sosai, thanks for ur care" yayi murmushi har ransa yaji dadin yanda ya ganta unlike yesterday, ya ajiye breakfast da Hajiya Mariya ta bada ya kawo masu, Khadijah ta xauna gefen gadon tana kallonsa tace "Plss ina son kaje can gida I don't want to inconvenience anybody sae ka dau Shureim kayi dropping dinsa schl" Yana shafa kansa yace "Dr Ayman din baxae kai sa ba?" Tace "Toh ni bari in je in daukesa in ajiye sa schl idan baxa ka je ba, Kuma ai nasan da Dr Ayman din" murmushi yayi yace "Aa ae bn ce baxan je ba malama" turo baki tayi ya juya ya fita ward din din Maryam ta bi sa da kallo, Mikewa tayi daga karshe ta hada ma Khadijah shayi da ya kawo ta bata da kwai, Khadijah ta amsa tace "Nagode" daga haka ta fara shan shayin da spoon, bayan kusan awa daya Aliyu ya dawo ward din, kujera ya ja ya xauna ya jinginar da kansa da kujerar yace "Dama kawai don ki bani wahala ne kika ce in tafi koh?" Tana kallonsa tace "Me ya faru" murmushi kawai yayi ya dago yana kallonta, ta ci gaba da Shan shayinta, mikewa yayi yace "Anyi discharging din ki yanxu, we can leave" tace "Toh bill din fah, am not with money, ko idan mun je gida sai in baka, nawa ne kudin?" Ya fi minti daya yana kallonta kafin ya juya ya fita ward din, Maryam ta d'an yi murmushi tace "Haba dai ya biya ai Khadijah...." Khadijah ta sakko kan gadon ta dau mayafinta da wayarta da jaka tace "Toh nagode" Maryam ta dau kayan shayin da ya kawo suka fita waje, a haraban asibitin suka tadda shi yana jiransu cikin mota, Maryam ce ta shiga gaban motar Khadijah ta shiga back seat suka bar asibitin, da Khadijah ta daga kai sai su hada ido da Aliyu yana kallonta ta madubi, ta daga kai yayi sau uku sai su hada ido, ji tayi gaba daya she is uncomfortable, ta matsa a hankali ta koma can karshen motar tana kallon waje, dai dai gidanta yayi parking ta bude motar ta fito ta xagayo ta inda Maryam take tace "Nagode sosai Maryam, ki taya ni yi ma Mumy godiya in sha Allah xan shigo anjima da yamma ko gobe, Allah saka da alkhairi" Maryam ta d'an yi murmushi tace "Ba komai, sai kin xo" kallon Aliyu dake ta kallonta tayi, da kamar baxa ta ce masa komai ba sai kuma tace "Thanks" daga haka ta juya xata wuce ciki, a hankali yace "Anjima xan kawo maki drugs din ki Iman" tace "Ohk" tana fadin haka ta shiga gida ya ja motar suka bar street din. Tun daga wannan rana gaba daya Khadijah ta ajiye khaleel da jawahir gefe daya, tsakaninta da su gaisuwa faram faram ita kanta tayi mamakin yanda har ta sake ma jawahir yanxu duk da ita sai wani daure mata take, Lkci daya Khadijah ta yakice khaleel gaba daya a ranta, ko don tashin dare da take yawan yi tana rokon Allah ya cire duk wani connection dake tsakaninta da shi a xuciyarta ne, yanxu tun safe in ta fita gidan dama sai yamma take dawowa kuma duk ta dawo xata tarar khaleel ya dauko shureim, wani lkcn basa ma sanin ta dawo, yanxu kam ita kanta tasan ta rage damuwa sosai, jarabawarta kawai ta sa gaba, duk bayan kwana biyu ta kan je gidansu Maryam gaida Hajiya Mariya, kuma duk taje sai sun hadu da Aliyu, wani lkcn ta amince ya maido ta gida wani lkcn kuma tace baxata hau motarsa ba shi dai kam sai dai yayi murmushi baxai ce komai ba, sai ta tafi tayi ta tausayin sa bata san dalili ba, har xuciyarta take ganin Aliyu kamar little Sudais dinta cos the little boy have all his fathers quality, Kuma tasan saboda Aliyu yasa ta sa ma kanta dangana haka, Wani rama khaleel yake da shi kansa bai san dalilinsa ba, gaba daya ba shi da sukuni, yanxu kam sure yasan Jawahir and Khadijah are cousins daga binciken da yayi but bai san ta inda xai billo ba, gaba daya kansa ya kulle, bai taba xaton haka ba, they are very close relatives, dauke masa wutan da Khadijah tayi ya fi komai bata masa rai, in har ta gaishesa a gidan to tare ta gansa da jawahir, in ko just haduwa suka yi su biyu ko kallon inda yake bata yi, sai ma saurin barin wajen da xata yi, shi dai yasan har sannan bai cire rai da ita ba ko don nuna mata iyakarta kan walakancin da tayi masa but how will that be when they are cousins with his wife Jawahir?? sure it's not prohibited, but Uhm... A can Nigeria kuwa Sudais ya gama hada lefen sa tsaf, komai ya siya sai ya nuna ma Khadijah ta WhatsApp ko yayi mata, Yana gama hada lefen dama ya kai ma jiddah kayan fadar kishiya, tun da taga akwatunan hankalinta yayi mugun tashi, ya sanar da ita ko na meye bai tsaya saurarenta ba ya fice, Ta fashe da matsanancin kuka tana kallon kayan, yanxu har auren nan ya matso bata samu damar daukar number Khadijah a wayar Barrister ba gaba daya hakan ya faskara duk iya kokarinta, Nan ko bata san duk Barrister ya lura da take takenta ba ya canxa yanda yyi saving number Khadijah daga Amira ya mayar Ummu Shureim, Xaunawa jiddah tayi kan kujera wata dubara ta fado mata.... Murmushi tayi tana share hawayen ta a hankali tace "Allah ya kai mu ranan auren, ai dai Amarya xata tare koh? Toh a daren farkon ta gidan ka xan maku abinda ita xata yi da ta sanin auren ka, kai Kuma xaka gwammace baka aureta ba" wani murmushin ta kuma yi ta wuce daki xuciyarta fess, har Allah Allah yake ranan ya xo ta cika aikinta, ta tabbata Khadijah baxata kwana gidan ba Kuma har karshen rayuwarta xata ji baxata iya yafe masa ba, ba boka ba malam. Ana saura sati daya Khadijah ta taho hutu Barrister Sudais yaje katsina gun Kawunta bayan Umma ta basa address, ciwon kafa kawu jibril ke fama da shi sosai sai dai hakan baya hanasa tafiya, duk yaransa biyu da ya aurar na xaune gida da ya yansu auren ya mutu, gashi yanxu duk kudin sun ja babu komai sai motoci biyu da gidan da yake ciki, kawu na jin abinda ya kawo Sudais bayan sun shiga parlorn sa, ya dinga masa wani kallo yace "inaaa, you are mistaken don bani da wata ya wai Khadijah, ka dai koma ta kai ka gun dangin ubanta amma ba ni ba, tashi ka ban waje malam" Sudais dake ta kallonsa yace "Amma dai ka santa koh?" Kawu yace "Toh meye amfanin sanin nata, Yarinyar da rabon da na sa ta ido yau xai yi shekara goma sha, tana can tana yawon duniya da kishiyar babarta" Sudais ya san xa ayi hakan shi yasa ma ya fara xuwa shi kadai, bai taho da kowa nasa ba dama Kuma bai sa ran Kawunta xai yarda ya daura mata aure ba" Sudais yyi murmushi yana kallonsa da kyau yace "Kawu dama ba wai lallai sai kai xaka daura mata aure ba, Kar ka mance babu abinda kudi basa yi a duniya, kawai dai dama an sa na xo ne don a fita hakkin ka a matsayin ka na wan mahaifinta, bayan haka Kuma kawu yanxu xaka iya damka ma Khadijah gadon ta na mahaifinta tunda ta mallaki hankalinta?" Da mugun mamaki Kawu Jibril ke kallonsa baki bude, can ya mike da kyar yace "Kai a uban wa xaka xo min da xancen gadonta??" Mikewa Sudais yyi ya tako har gabansa ya fiddo Id card dinsa yana masa wani kallo yace "Ni a lawyer mai xaman kansa.... Barrister Aliyu Umar, don haka nake maka gargadi kawu kar ka yarda magana ta kai mu ga shiga kotu baxai maka kyau ba... 10 years kamar yanda ka fada is enough.. hand over her properties to her" Daga haka Sudais ya juya ya fita kawu ya bi sa da kallo cikinsa na kara baki sake.... Yau Khadijah ta gama exams tana bedroom tana ta shirye shiryen kayan da xata koma Nigeria da, Shureim kuma na parlor ta bar sa yana bacci taji kamar an bude kofa, juyawa tayi da sauri don bata ma san kofar a bude yake ba, tayi saurin daukan hijab xata fita suka kusa cin karo bakin kofar dakin. Komawa baya khadijah tayi tana kallonsa, ya shigo xai rufe kofar ta xaro ido tace "Meye haka Doctor" rufewa yyi ya yana tahowa kusa da ita yace "Tell me why you are avoiding me Khadijah" wani kallo tayi masa tana komawa baya tace "Avoiding din ka kamar ya, bayan gaisuwar da nake maka me kuma kake so daga gareni?" Ganin ya kusa isketa ta juya da sauri xata shige bathroom, yyi hanxarin rikota ya juyo da ita yana kallonta, wani kara tayi ya matseta jikinsa yana mata wani kallo, lkci daya jikinta ya dau rawa tace "Stop it plss Dr, meye haka don Allah ka bari ni bana soo..." yace "Is it a crime don nayi aure?" Sake baki tayi tana kallonsa, can ta hade rai tace "Ban gane ba?" Yace "Ehh tunda nayi aure kika kara dasa min rashin mutunci a kan na da, I showed interest in marrying you kika yi shunning dina, me kuma kike son in maki Khadijah? Tell me me kike so?" A hankali tace "Let go of me now!" ba musu ya saketa yana kallonta, juyowa tayi tana facing dinsa da kyau tace "Ai da kana so na kamar yanda kake ikirari ko me xan ce maka baxai hana ka abinda ke a ranka a kai na ba, kuma abinda yasa baka wani damu ba shine saboda kana da warce kake so da aure... so don't tell me dat Ayman" Ya shafa kai yana mata kallon mamaki, bude kofar parlorn suka ji aka yi, a tare suka kalli door din dakin, ya nufi kofar ya bude ta bi bayansa, tsaye suka ga Jawahir a parlorn ta rike waist da hannu, Khaleel ya karaso kusa da ita kamar mai tausayin kasa ya tsaya yana kallonta, bata yarda ta kallesa ba ta taka ta tafi gun Khadijah dake tsaye bata karaso cikin parlorn ba, wani kallo Jawahir ta dinga mata kafin tayi wani murmushi tace "Khadijah kike kowa? Let me warn you first before taking any action...." Strictly tana mata wani shegen kallo tace "Stay Away from my husband, I repeat my self stay away from him you bitch, idan ma kina da wani kuduri a kansa a ranki ne to kiyi maxa ki goge don wllh ya fi karfin ki nesa nesa ba kusa ba, shi ba sa'an ki bane, shi ba sa'an auren ki ba ne, and let me advice you as a lady.... idan aure kike so ki rufa ma kanki asiri ki koma gidan uban 'ya yan ki wllh hakan kadai ne rufin asirin ki, ke bari ma kiji abinda baki sani ba, da Khaleel ya aure ki a matsayin kishiyata gwara ya auro min budurwa kamar ni mu goga, banda naci da ba kai wahala Ina ke ina Khaleel kina baxawarar, ragowar wani???" Tsawa Khaleel yyi mata ya isa kusa da ita lkci daya idanuwansa suka sauya xuwa ja yace "Kina da hankali Juwairiyya? Kin san wacece ita kike fadi mata wannan maganan gabana?" Wani kallo ta masa ta daga masa hannu tace "Spare me Malam ba da kai nake ba da sa'ata nake, keep ur mouth shut... ban kuma damu in san wacece ba, tunda ta shanye ka ni bai gagareni in kwatar maka yan cin ka ba" Fincikota Khaleel yyi a mugun fusace yace "Did you knw I can give u a dirty slap now?" Jawahir tayi dariya tace "Wllh ka mare ni in rama a kanta, wai ma a kan shegiyar mai makale ma maxajen mutane xaka ce xaka mareni Khaleel?" Kasa ce mata komai Khaleel yyi, can ya runtse ido ya turata yace "Ina guje maki ranan da xaki ji kunya Jawahir, ranan da xaki kasa kallon idanuwan warce kike ma rashin mutunci yanxu, Kuma bayan kin san ta kina ji kina gani xan aureta in hada ku...." Khadijah tayi wani murmushi bata ce komai ba ta juya a hankali ta koma daki ta rufe kofar ta sa key, tafi minti goma kwance kan gado, ita kanta ta rasa me ya hanata yin kuka, kalmomi hudu suka tsaya mata a lkcn, Bitch, Baxawara, ragowar wani, mai makale ma maxan mutane, yanxu jiddah ma kallon da take mata kenan koh?? wani murmushin tayi ta kai hannunta fuskarta jin abu na sauka taji hawaye ne, cikin pillow ta cusa kanta bata sake dagowa ba sai kusan karfe dayan dare shima ta dalilin sanyin dake neman mata illa, da kyar ta mike jikinta na rawa ta fiddo kayan sanyi ta sa, Shureim ya fado mata ta fita parlor da sauri, kwance ta gansa kan kujera ya takure waje daya yana rawar sanyi duk da kayan sanyin jikinsa, ta isa kusa da shi ta daukesa ta rungume sa ta karasa gun kofa ta sa key sannan ta kashe wutan parlorn ta wuce daki, kwantar da Shureim tayi ta rufa masa duvet ta wuce bathroom ta sa ruwan dumi tayi alwala ta fito, sai kusan karfe biyu da wani abu ta kwanta bacci me nauyi ya dauketa. Tun da tayi sllh asuba take ta shirya sauran kayansu, tana gamawa ta tada Shureim ta shirya sa ta basa tea da sauran cake dake gidan, ita ma ta shirya, wayarta ta dauka ta shiga scrolling call log a hankali tana neman number Aliyu duk da bata yi saving ba amma tasan number, ta fi second goma tana kallon number can tayi dialing, bugu biyu ya daga, a hankali yace "Iman, hope all is well?" ta gyada kai kawai tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau, Ina Shureim" ta kalli Shureim dake gefenta a xaune, murya can kasa tace "Airport xaka xo ka kai mu pls, if we won't inconvenience you" Aliyu yace "Sure, yau xaku tafi Nigeria din?" Tace "Ehh" yace "Toh gani xuwa yanxu" daga haka ya katse wayar, bayan kusan minti sha biyar tana xaune ta rungume Shureim kai kana ganinta kasan she is just weak, duk ta xama kamar mara lafiya alhalin babu inda ke mata ciwo, da ta tuna maganganun da Jawahir ta gaya mata jiya da yamma sai tayi murmushin takaici, mikewa tayi ganin kiran Aliyu ta dau karamin jakarta suka fito bayan ta tabbatar komai na gidan ta kashe ta kulle kofar apartment din, ta nufi waje rike da hannun Shureim, Kayan sanyi ne jikinsa shi ma yana jingine jikin mota ya rungume hannunsa, yana ganin Shureim ya isa kusa da shi ya daga sa ya rungumesa a hankali yace "Good morning sweetheart" murmushi yaron yayi yace "Good morning uncle" kallon khadijah dake kallonsu Aliyu yayi ta sunkuyar da kanta da sauri, yace "Good morning" ta ce "Morning" xagawa yayi ta bi bayansa ya bude motar ta shiga ya mika mata Shureim ta xaunar da shi gefenta sanann ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin driver, driving din some minutes yayi suka isa airport yyi parking waje duk suka fito, Daukar Shureim yayi da damuwa yana kallonta yace "Iman kin bari sanyi ya kama sa da yawa fa" ta kalli Shureim dake tari, sauke idonta tayi tace "And I am very cautious about that, Ni ma ban san yanda aka yi ba" yace "ko yana shan ruwa me sanyi ne?" Ta girgixa masa kai tace "A'a" Ganin yanda yake tarin tace "Ka ajiye sa kar ya maka amai a jiki" Bata rufe baki ba ya kwarara masa aman shayin da ya sha a jikinsa, Aliyu ya dinga shafa masa bayansa yana masa sannu, da damuwa khadijah tace "Toh ina xa mu samu ruwa yanxu, gashi ya bata maka jikin ka" Aliyu na kallon direction da motarsa yake yace "I think I have table water a mota" tace "Toh bani makullin in dauko" mika mata makullin yayi ta koma motar da sauri, ba a dau lkci ba ta dawo da ruwan ta mika masa ya karba, ya sauke Shureim ya ciro handkerchief dinsa ya shiga goge masa bakinsa da jikinsa da ya bata, tana kallonsa tace "Baxa ka wanke masa bakin da ruwan ba?" Yace "Noo, akwai sanyi..." yana gamawa ya mike ya shiga kokarin cire sweatern jikinsa, ganin goran ruwan hannunsa ta xaga bayansa a hankali ta taimaka masa ta cire sweatern, sai ta ganta yar karama kusa da shi don ya fi ta tsayi sosai, lkci daya ya juyo yana kallonta, ta sauke idonta ta saita wajen aman a sweatern ba tare da ta kallesa ba tace "Xuba min ruwan" yace "But it will be very chill kawo in wanke" tace "A'a ni ka xuba min" bude ruwan yayi ya shiga xuba mata tana wanke wajen har ta gama ta shiga kakkabe sweatern, da sauri ya sake ruwan hannunsa ya nufi gun Shureim ganin yanda ya jingina da wani mota, he looks so sick, ya daukesa ya rungumesa yace "Sorry son" Khadijah na kallonsu a hankali tace "Toh kar yaje yana min amai a jirgi" Aliyu ya juyo yana kallonta yace "Noo baxai yi ba, mu je in siya masa drugs mu dawo yanxu" daga haka ya fara tafiya ta bi bayansa. Sai da ta fara shiga motar sannan ya xaga ya mika mata Shureim ya rufe motar ya dawo ya shiga maxaunin driver ya tada motar, drugs ya siya masa na mura da xaxxabi, bayan yyi reversing motar murya can kasa yace "Can I accompany you two Iman, because of his condition, I will postpone my schedules for today..." Khadijah da ke rungume da Shureim tayi shiru bata ce komai ba, ganin ya dau hanyar airport ta kallesa a hankli tace "Ai baka shirya ba, you can't just go without preparation" yace "I will only drive home yanxu inyi dropping motar, mu dawo airport and make the traveling process" Tace "Toh amma ai su Mumy ba su sani ba" ya kalleta a hankli yace "I will explain to her, she will understand" khadijah ta d'an yi shiru, can tace "Toh shkkn" gida ya nufa yayi parking a waje yace "Kilan baki shirya shiga ku gaisa da Mumy ba, beside it's too early, let get a taxi sai ku shiga ku jirani saboda sanyi" ita dai bata ce komai ba ya fita ya tsayar masu da taxi bayan ya fada masa xai d'an jira sa ya shiga gida ya fito, kayansu ya fara transferring xuwa taxin sannan ya xaga ya bude motarsa Khadijah ta fito ta shiga taxin, ya dau ledan maganin Shureim ya bata ta amsa, ya shiga motarsa ya shiga gidan yyi parking. Bayan few minutes ya fito ya hau taxin suka wuce airport, sai kusan karfe tara jirgin su ya tashi. Aliyu na kallon ladyn dake kusa da Khadijah bayan sun yi boarding plane din xai yi magana ta gane abinda yake nufi, tace "Ohk then" daga haka ta koma seat dinsa ya xauna wajenta yana rike da shureim ya kalli Khadijah da ta lumshe ido yace "Ke kin ci abinci kafin ku fito?" Ta bude ido tana kallonsa ta gyara xamanta tace "Na sha shayi" Bai sake cewa komai ba, bayan wani lkcn Shureim yayi bacci yana rungume da shi, da farko kawai lumshe ido tayi ita ma, amma after sometimes bacci ya dauketa, kallonta kawai Aliyu yake, ko ba a fada masa ba yasan she is disturb, there is something eating her but he won't even dare ask what it is, ya lumshe ido tuna farkon ranan da aka fara kawo khadijah aiki gidansu da yanda ta dinga kallon TV bata ma san abinda ake ce mata ba, lkcn da ta taka masa kafa xata kitchen and how she said she is sorry, tun daga sannan dama yasan kaddara ce ya kawota gidansu, bude ido yayi a hankali ya sake kallonta, Khadijah is just beautiful in many ways.... A hankali ya sauke idonsa kan Shureim ya ga babu abinda ya dauko nata sai pink coloured lips, kanta ya ji a shoulder dinsa, ya daga kai yana kallonta, bacci take me nauyi, bai taba ta ba kuma bai tasheta ba ya bar ta a haka. Sai kusan magrib suka sauka Abuja a Nigeria,wani flight din suka sake boarding xuwa kaduna, Adai daita sahu ya kawo su har kofar gidan Umma, Aliyu ya fito Aliyu yana dauke da Shureim, ita ma fito ya dauko mata jakarta ya mika mata ta amsa yace "Ki kai ciki sai ki dawo ki amshe sa" ba musu ta wuce ciki yana kallon mai napep din yace "Kayi hakuri xaka kai ni Gra yanxu" Bayan wani lkci khadijah ta fito ya isa gabanta ya mika mata yaron dake bacci ta karbesa tana kallonsa tace "Mun gode sosai" d'an murmushi kawai yayi, can yace "Idan ya ci abinci sai ki basa magungunan sa" tace "Toh" yace "Alryt xan wuce gida a gayar min da Umma" daga haka ya shiga adai daita, mai adaidaitan ya ja suka bar wajen ta bi su da kallo, juyawa tayi a sanyaye xata shiga gida suka kusa cin karo da Nanny da ta amshi Shureim hannunta suka wuce ciki, ruwan xafi Nanny ta hada masu bayi, ta ma Shureim wanka sannan khadijah ta shiga, Umma na ba Shureim abinci ta fito, Umma ta kalleta tace "Ni nasan sai sanyi ya kama yaron nan kawai salon ki ja masa kika tafi da shi tunda kin san lkcn sanyi ne" khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi... Umma na lura da khadijah dake jujjuya abincin gabanta, ko bata gaya mata ba taga alamar tana da damuwa sosai, Umma tace "Khadijah" da sauri ta dago ganin yanda Umma ke dubanta ta debi shinkafar gabanta ta kai baki, tana son tambayar Umma ko magana tayi mata amma tayi shiru tana cin abincin, Umma tace "Tell me ur problem, what are you thinking of?" Khadijah ta wara manyan idanuwanta tace "Ba komai Umma am just tired ne" Umma tace "Toh ki gama cin abincin sai kiyi isha ki kwanta" A hankali khadijah tace "Toh" da kyar ta dinga tura abincin don gaba daya bata da appetite, why is she finding it hard to erase jawahir's hurtful words from her mind, mikewa tayi daga karshe ta wuce kitchen da plate din shinkafar, tana wankewa a sink Sudais ya fado mata, tasan baxai ji dadi ba ta taho bata gaya masa ba, tayi deciding ta tura masa test kawai ta gaya masa, tana dawowa parlor ta dau wayarta ta xauna gefen Umma ta shiga rubuta masa text din cewar ta dawo yanxu, ta kuma basa hakuri da bata gaya masa ba while coming back, Unfortunately Wayar na bedroom din Sudais, shi kuma ya shiga bathroom, dai dai shigowar jiddah dakin text din ya shigo, Atm dinsa dama tayi niyyar shigowa ta dauka without his consent, ganin wayarsa dake gaban mirror yyi haske ta nufi wayar da sauri, dauka tayi ganin message ta sa finger ta jawo yanda xata iya karanta content din, she was very cautious kar tayi erasing message din daga gaban screen din wayar, sake baki tayi tana kallon text din, ta nanata Ummu Shureim a xuciyarta ya fi a kirga, tayi wani murmushi, wato Amira ya mayar Ummu Shureim don kar ta gane, da sauri ta ajiye wayar jin alamar xai fito ta kashe wutan ta shiga dube dube a drawern mirror with a very serious face, sudais ya fito daure da towel yana kallonta, he was very surprise seeing her... da yake tun da ya kawo mata kayan fadar kishiya ta daina kulasa a gidan, ta kallesa fuska daure tace "Why are you staring at me that way?" Bai damu da abinda tace ba yace "Me kike nema?" A takaice tace "Razor blade, naga wani shekaranjiya a nan ina gyara, I want to sharpen my daughter's pencil tayi assignment" tabe baki yayi yace "Duk Miscellaneous school materials dinta babu sharpener sai kin shigo nan neman razor?" wani kallo tayi masa tace "Ae dai you are not blind kana ganin komai ta kai makaranta xubarwa take ta dawo min haka kamar wata wawiya, or am I to become a razor to sharpen her pencil???" Bata sake saurarensa ba ta fice daga dakin, ya girgixa kai ya nufi gaban mirror, wayarsa ya kunna, ganin text din khadijah gaban wayar ya xaro ido sosai, can ya kalli kofa da sauri, shi dai bai ga alamar da ya nuna ta taba wayar ba, beside da ta dauka ai bude message din xata yi kuma baxai gansa gaban wayar ba, hakan yasa ya tabbatar bata dau wayar ba, Jiddah na komawa daki ta xauna gefen gado tana tunane tunane, to ita yanxu shawarar wa xata nema, anya jiran da tace xata yi har sai an daure auren bai yi nisa ba, kai gaskiya yayi nisa sosai, kawarta Amina ta shiga kira tana dauka tace "Amina don Allah gobe ki taho da sassafe, Ina cikin babban matsala" Aminar tace "Toh in sha Allah xan taho kuwa" Ajiye wayar tayi ta mike tana xaga dakinta, kai ina ma Allah xai bata sa'a taga Amiran nan ta fara nakada mata duka kafin ta bude mata sirrinta da ta sani, fita tayi dakin ta nufi dakinsa ta bude a hankali don taga mai yake, babu kowa dakin kuma ya dauke wayarsa, ta sauka downstairs da gudu, ganin an kunna wutan kitchen ta gane yana can, waya taji yana yi a kitchen din, ta labe jikin bango dai dai nan taji yana cewa "Alryt dear, my regards to him, gobe da safe xan taho..." Da sauri jiddah ta tafi stairs jin xai fito, yana fitowa ta maxa ta juyo kamar tahowanta kenan, Bai kalleta ba kamar yanda bata kallesa ba ya isa kan kujera ya xauna rike da cup din tea. Khadijah na kwance da Umma misalin sha daya na dare Umma tace "Ya Khaleel da matarsa?" Khadijah tace "Suna can lafiya" Umma tace "Ya sani xaki taho?" Khadijah ta gyada kai tace "Ehh ya sani, Umma Aliyu ne yyi accompany din mu" Umma ta daga kai tana kallonta kafin tace "Yana kasar ne?" Khadijah ta gyada kai tace "Ehh can yake xama" Umma bata ce komai ba ta koma ta kwanta, khadijah ta dinga nuna ma Umma kayayyakin da Sudais ya sa mata a lefe ta waya, don komai ya siya sai ya tura mata ko tana so, Umma tace "Maa Sha Allah, Allah sanya Alkhairi" khadijah tace "Ameen" a hankali tace "But Umma how will I cope with studies and marriage, ko ki ce masa kawai ya bar ni a can kasar in gama kawai idan anyi auren" Umma tace "Kwana nawa ne hutun naku?" Khadijah tace "Ba yawa fa, wata daya ne da few weeks" Umma tace "Bikin kuma nan da sati nawa yace maki?" A hankali tace "Biyu" Umma tace "Kema kin san baxai hana ki karatu ba, Kar ma ki ce masa komai, but surely xai bari ki gama" khadijah tace "Toh Umma" Umma tace "Allah ya kai mu lokacin lafiya" a hankali khadijah tace "Ameen, Amma Umma sai gabana yayi ta faduwa" Umma tace "Sai ki yawaita addu'a, babu abinda mutum ya isa ya maki wanda Allah bai maki ba" Washegari da safe tun da Jiddah ta tashi take tunanin yanda xa ayi ta san inda Sudais xai je ganin har ya gama shiryawa cikin suit yana xaune dining yana shan shayi ta sa hijab ta fita kamar xata xubda shara, ko amsa gaisuwar mai gadi bata yi ba sanin duk bakinsu daya da sudais komai ya faru gidan sai Sudais ya tambayesa, kamar kawayenta nawa suka xo a rana kuma duk da jan kunne da take masa sai ya fada masa, duk ta fita gidan to sai Sudais ya sani, har bakin titi ta taka suka gaisa da mai filling din gas dake bakin titi da d'an shagon container sa, yace "Maman Amira kaddai ki ce har gas ya kare in je in dauka, naga ko sati biyu ba ayi ba na cika" Tace "A Haba kamar muna shan gas a gidan, ba shi ya kawo ni ba malam rabilu, wani taimako nake so ka min don Allah, Kuma wlh ni me biyan ka ko nawa ne, amma kuma sirri ne tsakanina da kai" tana magana ne tana kallon cikin layi ko xata hango motar Sudais, Rabilu yace "Tohhh... Sirri kuma maman Amira" tace "Kaga ba wani abu bane, yanxun nan Abban Amira xai fito a motarsa, to don Allah so nake ka tada Machine dinka ka bi bayansa ka gano min inda xa shi, wllh ko nawa ka bukata xan biya ka Rabilu, kar ka ji komai ba wani sanin ka yayi ba" Dariya sosai mutumin yayi yace "Kai yanxu shi Barristern xan bi a machine maman Amira?" Ta hade rai tace "Kai dai biyan ka xan yi babu ruwan ka, Kuma ku din ne sai da haka, ban yarda da takun sa bane kwanan nan, yanxu dai don Allah ka rufe container din nan ka hau kan babur din ka ka jira sa anytime soon xai fito na sani, xuwa anjima xan dawo in ji yaya, da kudin ka kuma xan taho in sha Allah" daga haka ta koma cikin layin, ta kusa gida sai ga motar sudais kuwa, Dauke kayi tayi, ya tsayar da motar yana kallonta yace "Jiddah?" Ta juya fuska daure tana kallonsa, yace "Da ixinin wa kika fita, Kuma ina kika je?" Tana nuna masa gidan dake kusa da nasu tace "Matar gidan can ta kira ni yaronta ya kone da mai, Toh sai kar in je? Ko baka ga a gigice na fita ba?" Rufe glass dinsa yayi ya ja motarsa ya wuce, ta tabe baki ta shige cikin gida, office Sudais ya nufa direct don client na jiran sa. Khadijah dake kitchen tana duba miyar kubewar da Nanny ta daura ta juya tana kallon Shureim dake mika mata waya, ta hade rai tace "Waye yake kira yanxu kuma?" Yace "Doctor" tace "Nace kar ka sake kawowa baka ji Koh" yace "Am sorry Anty" daga ya juya ya koma da wayar, Khaleel ne ke kiranta tun daxu ta ki daukar wayar, da ya kira sai Shureim ya kawo wayar don yana hannunsa, Umma dake jin su a parlor tace "Wa ke kiran ki baxa ki dauka ba khadijah?" Turo baki tayi tana juya miyar tace "Umma number ne and I don't want to pick" Umma bata ce komai ba duk da taji san da Shureim yace doctor ne, khadijah ta sauke miyar ganin yayi ta hade plates xata wanke sai ga Shureim ya dawo da waya yana mika mata, wani kallo tayi masa tace "Kana son duka koh?" Kamar xai yi kuka yace "Anty it's a number, it's not saved" karban wayar tayi taga Aliyu ke kiranta, tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, a hankali yace "Iman ya kike?" Tace "Lafiya lau ya su Mumy?" Yace "They are fine, Ina Shureim?" Tace "Gashi" yace "Ya jikin sa?" Tace "Ya ji sauki, only the cough" yace "Ohk basa wayar" Mika ma Shureim wayar tayi ta ci gaba da abinda take, bayan wani lkci ya dawo mata da wayar, share hannunta tayi ta amsa ta kai kunne, Aliyu yace "Baby wai xata xo wajen ki, is that okay by you?" Khadijah tace "Yaushe xata xo?" Yace "Anjima xan kawo ta" Khadijah taji dadi har ranta tace "Toh ina jiran ta sai ta xo" yace "Ohk" daga haka ya katse wayar. Bayan azahar Umma na xaune parlor da Nanny suna llissafin abubuwan da xa a siyo a Dubai na kayan daki, ita dai khadijah tana kwance tana danna wayarta Kiran Aliyu ya shigo wayar, Dagawa tayi ta kai kunne tana jin sa yace "Muna kofar gida Iman" khadijah ta mike xaune tace "Ohk ga ni fitowa" katse wayar tayi tana kallon Umma tace "Umma ta iso bari in je in shigo da ita" Umma tace "Toh sai kin dawo" mayafinta ta yafa ta fita xuwa kofar gida, fitowa baby tayi daga mota ganinta ta karaso da sauri ta rungumeta tace "Khadijah..." Khadijah tayi murmushi tace "Baby ya su Mumy" Baby tace "Suna gida, sun ce a gaishe ku" Khadijah tace "Ayya, Ina amsawa" Aliyu ya fito daga motar yana kallonta yace "Ina Shureim din?" Tace "Yana ciki" ta kama hannun Baby tace "Mu shiga ciki" Baby ta kalli Aliyu tace "Toh yayanmu nagode sai anjima" khadijah kawai yake kallo yace "Ki kawo min Shureim din mu je gun Mumy su gaisa" ba tare da ta juyo ba tace "Toh" Da fara'a Umma ke ma baby sannu da xuwa, Khadijah ta kama hannun Shureim bayan ta dauko masa takalminsa tana kallon Umma tace "Umma xai je su gaisa da Mumy wai" Umma tace "Toh Allah ya kiyaye" daga haka ta fita da shi, Aliyu ya kama hannunsa yana kallonta yace "Gobe xan koma Iman" ta kallesa tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen" har xata tafi ta juyo tace "Amma plss kwana baby xata yi koh?" Yace "Ban sani ba, ki tambayeta" tace "Tohm" daga haka ta wuce ciki bayan tayi ma Shureim dake daga mata hannu murmushi. Khadijah ita kanta bata san xata sake da Baby haka ba, closeness dinsu na da kawai take tunawa da irin halaccin da baby tayi mata a gidansu, hira kawai suke tana ba baby labarin abubuwan da suka faru bayan ta bar gidansu, tun baby na kallonta cike da tausayi har ta fara kuka ba tare da ta san tana yi ba, Khadijah ta xaro ido ta fashe da dariya tace "Kuka Kuma baby, toh an gama labarin" baby na share idonta a sanyaye tace "Don Allah ki ci gaba Iman, mara Imani ne kadai baxai xubda hawaye ba a labarin nan naki..." Khadijah tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Baby na ci gaba da share hawayenta a sanyaye tace "Ki ci gaba plss Iman" a hankali khadijah ta ci gaba da bata labarin har karshe, kuka kawai baby take khadijah na kallonta, Baby tace "Don Allah Iman ki yafe ma yayana plss" Khadijah tayi murmushi tace "Ba dole in yafe masa ba Baby, na yafe masa tuntuni, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle beings" A hankali baby tace "Allah saka ma barrister" shiru Khadijah tayi tana kallonta, can tayi murmushi a hankali tace "Ai shi xan aura baby" kallonta Baby take da mamaki tace "Yaushe?" Khadijah tace "In less then three weeks ne bikin" A sanyaye baby tace "Shine baki sanar mana ba Iman, haushin mu kike ji har yanxu koh?" Khadijah tace "Ayya ba haka bane, kin ga jiya muka dawo ai, dama nufina idan na dawo in kai ma Mumy kati" Baby tace "Ya Aliyu ya sani?" Girgixa mata kai Khadijah tayi, Baby tace "Toh Allah kai mu lokacin, ya sanya alkhairi, Amma barristern a nan garin yake?" Khadijah tace "Ehh nan yake, ae kin san sa" Baby tace "A'a ban san sa ba" Khadijah tace "Ranan da muka je gidan ku ai tare muka je da shi" Baby tace "Ai su biyu ne ranan" Khadijah tace "Ai anjima xai xo sai ku gaisa" Baby tace "Allah ya kawo sa" khadijah ta dinga lallaba baby ta kwana gidan ganin ta fara cewa yamma yayi, baby tace "Ae ban ce ma Mumy xan kwana ba" khadijah ta marairaice tace "Plss baby, kinga ko frnds bani da, am always lonely, xan ce Umma ta Kira Mumy tace xa ki kwana" Bata sake sauraren baby ba ta fita ta sanar ma Umma sannan ta sa mata number mum din su Aliyu a wayarta ta kira ta, tana sawa ta fita ta dawo dakinta gun baby tana murmushi tace "Toh yanxu Umma xata kirata" Babu yanda baby ta iya haka ta hakura xata kwana gidan. Bayan sun idar da magrib suna xaune daki baby na bata labarin halin da iklima ke ciki duk jikin khadijah yyi mugun sanyi, ringing din wayarta yasa baby tayi shiru, dagawa tayi ganin Barrister ke kiranta bayan sun gaisa yace "Am outside dear" murmushi tayi tace "Toh ae shigowa xaka yi" Sudais yace "Uhm is it necessary?" Mikewa khadijah tayi ta dau mayafinta tace "Toh baxa ku gaisa da Umma ba?" Yace "Sai nayi shawara da ke? Even the day before yesterday ai na xo, gaisheta tare ma muka je da Little Meerah" Murmushi khadijah tayi tace "Ohk then gani fitowa" daga haka ta katse wayar ta kalli Baby tace "Baby mu je ki raka ni sai ku gaisa dama kin ce baki san sa ba" Baby tace "A'a je ki dawo ke dai, just extend my greetings" Khadijah ta bata fuska tace "Don Allah ki taso mu je plss" Baby tayi yar dariya tace "Toh naji" tashi tayi ta dau gyalenta suka fita dakin, sai da Khadijah ta fara shiga dakin Umma ta sanar mata xasu fita gun Sudais sannan suka fita, Yana tsaye jikin mota sanye cikin kananun kaya ya rungume hannunsa, tun da suka fito yake kallon khadijah, Baby ce ta fara sallama tace "Ina yini?" Sai a sannan ya dubeta da murmushi ya amsa sallamarta yace "How are you?" Tace "Lafiya Alhmdllh, ya aiki?" Yace "Mun gode Allah" daga haka ta juya tace "Toh Iman sai kin shigo" tana fadin haka ta shiga cikin gida, khadijah ta dawo gefensa ta tsaya tace "Welcome My Barrister" ya wara ido a hankali yace "Really?" Boye fuskarta tayi tana yar dariya, yace "Kun xo lafiya dear?" Tana kallonsa tace "Alhmdllh" yace "Ashe dama kina da kawaye?" Ta xaro ido tace "Uhm Baby ce fa kanwar Aliyu" Shiru yayi yana kallonta, can yace "Tana xuwa nan kenan?" Khadijah ta girgixa kai tace "A'a tun bayan rasuwar takwaran ka sai yau ta sake dawowa" yace "How did she know u are back, ko kuna waya ne?" Tace "A'a fa, nasan Aliyu ne xai ce mata mun dawo" yana kallonta a hankali yace "Ya aka yi Aliyu yasan kin dawo" shiru tayi ta kasa kallonsa, bayan few seconds ta dago kai tace "Sorry I didn't tell you shi yayi accompanying din mu jiya, coz Shureim was sick" Ya langwabar da kai yace "Da gaske?" Bata ce komai ba, ya d'an yi murmushi shi ma bai ce komai ba, tayi breaking silence din tace "We where very close da baby, farkon xuwa na gidan su ne kadai muka samu problem, after that she was kind to me, she took me just as her sister, tana so na sosai, nima kuma ina sonta, and I really want us to be frnds now tunda bani da kawaye" a sanyaye ta kare maganar, Yana gyada kai yace "That's nyc then..." Tace "Me yasa baka xo da little Amira ba?" Yace "Ba daga gida nake ba" Khadijah tace "Ohk, Toh ko ruwa ban kawo maka ba, shud I bring some?" yace "Daga eatry fa nake yanxu haka" ta d'an buda ido tace "Kai da xaka koma gida kuma meye na xuwa eatry da daddare Barrister" murmushi yayi yana shafa beard dinsa bai ce komai ba, can yace "Shureim fa?" Shiru ta d'an yi, ta dago tana kallonsa tace "Yayi bacci" ya wara ido yace "So early? duk da nasan ba gaskiya kika fada ba" xaro ido tayi tana kallonsa, yayi murmushin sa mai kyau yace "Yea, sai ki ce min Aliyu ya tafi da shi" da mamaki tace "How did you knw" yana murmushi har sannan yace "From ur facial expression, and don't forget my field...." Yar dariya tayi tace "Kai My Barrister" yace "Sure My Meerah" ta boye fuskarta a tafin hannunta tace "Gobe ai xai dawo in sha Allah" yace "Alryt then, bari in tafi Amira, gobe xan dawo mu yi hira sosai am exhausted gaba daya yau" tace "Ayya, kana komawa gida kayi wanka ka kwanta you will feel relieve" Yana murmushi yace "Toh Amaryata" juya masa baya tayi tace "Uhn ni dai bana so" a hankali yace "Xa ki so ne ma ai" Bude motarsa yayi ya dauko leda ya dawo gabanta yana kallonta ya mika mata yace "Though Shureim na kawo ma amma tunda kin min rowar ganinsa gashi sai ke da meye ma kika ce sunanta..." Khadijah tayi murmushi tace "Sunan mu daya, Amma baby ake ce mata ita" ya wara ido yace "Ashe Mami na ce ita ma" a hankali khadijah ta gyada masa kai, yace "Toh ina gaisheta specially, she's having a great name, and naga suna kama da yayan nata ma" Khadijah ta amshi ledan tace "Toh xata ji mun gode sosai" murya can kasa yace "Noo thanks sweetheart" sunkuyar da kanta tayi, yace "Gobe xan kawo maki IV in case you have people to give" tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen dear, let me get going" daga haka ya bude maxaunin driver ya shiga, ta koma baya tana kallonsa, sai da yayi reverse ta daga masa hannu ya sakar mata murmushi sannan ya ja motar ya wuce, juyawa tayi a hankali ta koma cikin gida. Washegari karfe goma baby tace xata koma gida, duk khadijah ta ji ba dadi, babu yanda bata yi da ita ta bari sai da yamma ba tace inaa ita lokacin xata wuce, Khadijah tace "Toh ki kira yayanki ya dawo min da yarona nima" dariya sosai baby tayi tace "Sai kace baki da number sa, ke ki kirasa mana" Khadijah ta dau wayarta ta shiga kiran Aliyu, yana dagawa tace "Ka dawo min da yarona tunda wucewa baby ma xata yi yanxu" yace "Koh?" Tace "Eh mana, nace ta bari sai da yamma ta ki" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Aliyu yayi murmushi a hankali yace "Toh bata wayar" Mika ma Baby wayar tayi, baby ta amsa tana dariya ta kai kunne yace "Baby ki bari da yamma" tace "Toh yayanmu an gama" daga haka ta ba khadijah wayarta, kashewa khadijah tayi tana murmushi tace "Me yace?" Baby ta harareta tace "Ba don halin ki ba xan kai yamma" sosai khadijah taji dadi tace "Yauwa ko ke fa, kinga kafin nan Barrister ya kawo katin da yace sai in baki ki kai ma su Mumy" shiru baby tayi tana kallonta, khadijah ta wara ido tace "Ko bai yi ba hakan?" A hankali Baby tace "Ke dai ki kai da kan ki xai fi" Khadijah tace "Toh shkkn ko ran Friday sai Sudais din ya kai ni in kai" Baby tace "Khadijah Ina son maki wani magana amma Allah yasa baxai bata maki rai ba" Khadijah na kallonta tace "Ina ji baby" Baby ta kamo hannunta tayi kasa da murya cikin sanyi tace "Khadijah me yasa kika ki amincewa Ya Aliyu ya aure ki bayan ya nuna yana son yin haka, kin ga akwai advantage din hakan biyu xuwa uku, na farko shureim... Idan yau ace Ya Aliyu xaki aura har duniya ta tashi ba lallai yaron yasan irin kaddarar da ta afka maku ba da yanda aka yi aka samesa sai in ku kuka fada masa, he will neva ever know wllh, idan wani gidan kika yi aure fa? Wllh komin daren dadewa watarana sai ya sani, sai ya san matsayinsa khadijah, na biyu Aliyu baxai taba maki gori a rayuwa ba idan ma yayi wlh yasan kansa yayi ma, kunya a kansa, balle ma wllh baxai yi ma don yasan shi ya cuce ki, sannan kin ga babu wani matsala da xaki samu gun Mumy, da mu yan uwansa, Anty khadijah ce problem dama, toh tana can har yanxu asibiti sai karaya ya dauko warkewa abu ya dawo baya, ga cikin shege jikinta har ya fito, don haka ta kanta take yanxu, kowa yaje sai tace ya yafe mata har masu gadi da driver... toh wanda xa ki aura fa khadijah? Though nasan Barrister yasan everything about you amma khadijah ki kyale namiji wllh ko ba directly ba watarana sai ya maki gorin nan barin ma wannan da kika ce yana da mata, ko cikin bacin rai wataran sai ya jefe ki da bakar magana irin ta gori ba tare da kilan yasan yayi hakan ba, kawai ta dalilin bacin rai, balle a je ga yan uwansa da relatives, sannan uwa uba matarsa, yanxu duniyar da wuya wllh a rike maka sirrin ka, khadijah ki duba wannan xancen nawa plss ba wai don ina son ki da yayana bane amma it's better ku rufa ma kan ku asiri ku hadu ku rike sirrin ku, kin ga sai ki kara haifo mana wasu kyawawan yan biyun......" Da xolaya ta kare xancen, Khadijah dake ta kallon kofa ta xame hannunta daga nata a hankali tace "I really like you baby, Ina ji da ke har raina saboda kin min halaccin da baxan taba mancewa da ke ba, plss baby kada ki sa in fara jin haushin ki in ga kamar ke ba masoyiyata bace, baby mu bar wannan xancen plss bana so, Kuma kar ki sake min irinsa" A hankali baby tace "Toh Allah ya baki hakuri" Khadijah tace "Ameen, So baki gaya min level da kike ba yanxu, Kuma yaushe xa mu sha naki bikin?" Da murmushi ta kare maganar tana kallonta. Bayan la'asar Sudais ya kira Khadijah yace yana waje, da kyar ta lallaba baby da har ta kira Aliyu ya xo ya dauketa ta gama shiryawa suka fita waje gun sa, yau ma yana tsaye jikin motar suka fito, Baby ce ta fara gaishesa ya amsa da fara'a yace "Lafiya lau Mamina ashe baki koma ba" Baby tace "Ehh wllh ina jiran yayana ne" Sudais yace "Alryt, ya gidan" tace "Lafiya lau" Kallon Khadijah yayi yace "Ya aka yi Madam?" Tayi murmushi tace "Lafiya lau, ya aiki?" Yace "Alhmdllh... Ya Ummar mu" khadijah tace "Tana ciki" juyawa Baby tayi tace "Toh sai anjima xan shiga ciki" yace "Alryt nagode da gaisuwa" daga haka ta wuce ciki, Sudais ya bude motar ya fiddo invitation card ya mika mata yace "Here dear" amsa tayi tace "Nagode, Ina Amira fa" yace "Tana gida" mota ce tayi parking kusa da na Sudais khadijah ta dinga kallon motar har Aliyu ya fito, Shureim ma ya fito ta daya side din, da gudu ya taho ya rungume Sudais yace "Unclee..." Sudais ya daga sa sama yana pecking goshin sa yace "Evening son, where are you coming from?" Ya wara ido yace "From my kind Mama's home" Sudais yace "That's good" karasowa Aliyu yayi gabansa ya mika masa hannu yana murmushi yyi masa sallama, Sudais ya basa hannun shi ma suka gaisa sannan ya kalli khadijah yace "Good evening" tace "Evening ya su Mumy?" Yace "Suna gaishe ki" kallon Shureim yayi yace "Go inside kace baby ta fito ina jiranta yanxu" Shureim ya shiga gidan Aliyu yayi ma Sudais sallama ya koma motarsa yana kallonsu ta ciki, Sudais bai sake cewa komai ba yana jingine da mota har baby ta fito, ta iso gun khadijah tana murmushi tace "Khadijah ni xan koma, ki taya ni yi ma Umma godiya idan kin koma ciki, nagode sosai" Khadijah tace "Toh nima nagode Baby ki gaida min mumy sai na kawo card din, and I will give you a call later" Baby tace "Alryt dear" sallama tayi ma Sudais ta wuce motar Aliyu ta shiga ya tada motar ya bar layin. Ranar Friday kamar yanda khadijah tace ma Baby misalin karfe sha daya ta shirya taje gidansu tare da Shureim don Sudais yace yana da wani case ranan. A hankali ta murda kofar parlorn ta ji a bude, ta shiga hade da sallama, Aliyu ne xaune parlorn tare da Salim yana operating laptop, ya daga kai yana kallonsu, ta sauke idonta ta karaso cikin parlorn, ta gaida Salim sannan ta kalli Aliyu tace "Ina kwana" Yana xaunar da Shureim dake gaishesa kusa da shi yace "Lafiya lau ya gida" tace "Alhmdllh, Mumy fa?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Bata nan, ki jira ta xasu dawo yanxu" tace "Baby fa?" Yace "Tare suka fita" tace "Toh bari in baka sako ka ba Mumy" Ta bude jakarta ta fiddo IV din tana kallonsa ta mika masa, karba yayi idanuwansa a kan content din Invitation card din, a hankali ya dago yana kallonta ko kiftawa babu, bata sake yarda ta kallesa ba tace "You help me deliver it to her plss" daga haka ta sauko da Shureim dake xaune kusa da shi ta juya ta fita daga parlorn yana ce mata shi ta bar sa a gidan, ganin yanda Aliyu yyi still wajen, Salim ya karbi card din don ganin na menene. Gida khadijah ta koma tana ta ma Shureim dake mata kukan bata bar sa gidan ba masifa, tana sauka kan napep din tace "Don uwar ka ba sai ka koma ba tunda gidan dangin uwar ka ne can din" Ta bude jaka ta ba mai napep kudinsa ta wuce ciki abun ta, ya bi ta yana kuka kamar xai tsaga gidan, Ta fi seconds goma tana kallon takalman dake bakin kofar parlorn, can ta bude kofar ta shiga a hankali, Khaleel ta gani xaune parlorn Umma ma na xaune, ta wani hade rai bata sake kallon parlorn ba xata wuce daki Umma tace "Khadijah" tsayawa tayi ta ki juyowa, Jin Umma bata ce komai ba ta juyo a hankali tace "Na'am Umma" Hada ido suka yi da shi, ta sauke idonta tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau" Tana kallon Umma tace "Mun dawo Umma, ba mu sameta ba ma" Umma na kallon Shureim da ya makale bakin kofa yana kuka tace "Shi kuma me ya samesa?" Harara ta balla masa tace "Au kuka kake min har yanxu, nace ka koma gidan koh" a hankali yace "I don't know the road" Umma tace "Me yasa baki bar sa ba" Tace "Mumy fa bata nan, Baby ma bata nan, to ina yake son in bar sa" yana kallonta yace "Wajen Uncle dina mana" Khaleel ya juya yana kallonsa yace "Come over dear" sai a sannan Shureim ya gansa ya taho gun sa da sauri yace "Uncle when did you come?" Khaleel ya xaunar da shi gefensa yace "Today" Murmushi yayi yace "Uncle kun xo da Anty na?" Khaleel ya shafa kansa yace "Sure" tabe baki khadijah tayi ta juya ta wuce daki abun ta, Tana xaune gefen gado tana danna wayarta Umma ta shigo dakin, ta xauna gefen gadon ita ma a hankali tace "Ashe abinda ya faru kenan Khadijah?" Kasa kallonta Khadijah tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, sai a sannan ta dinga jin xafin maganganun da Jawahir tayi mata, maganganun suka dinga dawo mata sabo, Umma tace "Ni ban ce kiyi kuka ba, ki share idon ki kije ki samesa ki ji abinda xai gaya maki" cikin rawar murya tace "Ni baxan je ba Umma" Umma tace "Ban isa da ke ba kenan" goge idonta ta dinga yi a hankali ta mike ta dau gyalenta ta fita a sanyaye, tun da ta fito yake kallonta har ta karaso ta xauna kujera ba tare da ta yarda ta kallesa ba, a hankali taji yace "Khadijah" sai a sannan ta daga kai tana kallonsa. ✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨ Kallon direction din daki yayi kafin ya kalli Shureim yace "Je ka dauko min wayar Anty a daki" yaron na wucewa ya mike ya dawo gefenta ya xauna ta d'an matsa ta dauke kai, a hankali yana kallonta yace "Don Allah kiyi hakuri Khadijah, I wasn't happy with what happened also, and... Plss forgive Jawahir for the sake of...." Katse sa tayi tace "Toh ni nace na riketa a rai ne? Not at all, don bata min komai ba" Ya lumshe ido ya bude yace "Don Allah kiyi hakuri Khadijah" tace "Wllh nayi, Kuma komai ya wuce a wajena, ita ma xan sameta idan na taba mata wani abun ta yafe min" Shiru yayi bai iya yace komai ba, mikewa tayi xai rikota tayi saurin barin wajen tana hararansa tace "Meye haka?" Kallonta kawai yake, ta tabe baki tace "Am coming now" daga haka ta wuce ciki sai ga ta ta fito da kati ta iso kusa da shi ta mika masa, Bai karba ba yace "Meye wannan?" Tace "Ka amsa ka duba mana" da kamar baxai karba ba sai kuma ya karba yana kallon katin, a hankali ya dago kai yana kallonta, ta rungume hannayenta tace "Xa ka samu xuwa kuwa duk da baka gayyaceni naka ba?" Ya sauke idonsa bayan few seconds yace "Why not" ta koma ta xauna a hankali tace "Toh nagode" Jujjuya card din kawai yake bai ce komai ba, can ya dago yana kallonta cikin sanyin murya yace "Ur happiness is mine khadijah, since this will make u happy, this is what u want for ur self, I am wishing you the best in it, Allah ya kai mu lokacin yasa ayi a sa'a" kasa cewa komai tayi tana kallonsa, yace "But I am happy for a reason, soon xan maki abinda xai sa ki farin ciki na har abada in sha Allah" daga haka ya mike yace "Kice ma Umma na tafi" har ya nufi kofa ya fita bata samu bakin magana ba, ta sauke idonta a hankali taji xuciyarta ya mata rauni. Tun ana biki saura kwana shidda Umma da Nanny suka fara shirye shirye ba ji ba gani, da kanta ta kai ma Kawun Khadijah katin bikin, kusan guda ashirin ta tafi da domin ya ba sauran yan uwansu can, Bata tsaya ta sauraresa ba balle matan sa da yanxu suka xama abun tausayi don miji ba shi da shi, ga yayansu duk aure ya mutu ana xaune gida, duk da bakaken maganganun da suka dinga jifanta da shi ita dai bata tanka su ba ta fita, wai don ma basu san da kaddarar da ta afka ma Khadijah ba kenan wannan, gidansu sadeeq ta shiga ta ba Mahaifiyarsa ma katin bikin sannan ta juyo xuwa kano. Tun da bikin ya gabato kullum sai baby ta xo gidan da close frnds dinta uku ganin da gaske khadijah bata da kawaye kamar yanda ta ce, tare suke shirin komai da xuwa kasuwa, babu wanda bai yaba kayan lefen da Sudais ya hada ma khadijah ba, as in abun ba a cewa komai, ya kashe mata kudi ba na wasa ba, Umma ta xuba kudi me yawa ta sa aka fara gyara khadijah, xuwa yanxu kam khadijah ta kara xama wani silent har da rama, hakan bai wani damu Umma ba sanin ko wace Amarya na experiencing haka, tun da bikin ya karato Sudais bai wani cika xuwa ba sai dai su yi waya, hakan yasa hankalin khadijah ya kwanta don ko ya xo bata jin ma xata iya fita gun sa. Mumy ta gama hada gudunmawarta gaba daya tana kallon Aliyu dake xaune yana danna waya dakin nata tace "Abuturrab ko kai xaka taimaka ka kai don Allah" sai a sannan ya dago yana kallonta, Mumy ta xauna gefen gado tace "Na fa ce ka cire ma kanka damuwa Abuturrab, you are never destined to be married to khadijah, ba kadarraku ba kenan kuma baka isa ka ja da Allah ba, ga mijinta nan ka gani so plss take her off ur mind, ka samu mace kayi aure..." Ya sauke idonsa kasa cikin sanyin murya yace "But I have never for once complained Mum, kina gani har kiranta nayi na mata Allah ya sanya alkhairi" Mumy tace "You are not complaining but ur mind is, gashi nan duk ka fita hayyacin ka, ga shi nan kana neman jefa kanka cikin wani hali, dama mutum na auren matar da ba tasa ba Aliyu? Why not behave like a good Muslims and be happy with Allah's plan?" Wani murmushi yayi yace "I am not complaining Mumy, am telling you the fact, but the thing is that don Allah ki taimaka ki mata magana ta bar min yaron, tayi hakuri ta bar sa gun ma, anytime she wants to see him xa a iya dinga kai mata shi, ko kuma yaje ya dinga hutu gunta, I know baxan iya rabata da Dan ta ba, but I just want to save him some humiliations, har duniya ta nade a gidan nan babu mai masa gori, babu mai masa kallon a child gotten out of wedlock, sannan babu mai takura masa, in da tayi aure fa, ko xai samu abubuwan da nayi mentioning a nan wllh it won't be 100% don haka plss Mumy ki nusar da ita ta bar sa gidan nan" Mumy ta sauke ajiyar xuciya a hankali ta kasa cewa komai. Duk yanda Mumy ta so fadi ma khadijah sakon Aliyu da taje gidan kasawa tayi saboda kunya, she don't even know where to start from, haka ta koma gida daga karshe, da Aliyu ya bukaci feedback din khadijah, ta kwantar da murya tace "Abuturrab ka bari kawai bayan bikin, it will look as if we are not happy with her marriage, xa a ga kamar mun so kan mu da yawa, kaga bayan biki sai ayi masu bayani, Ina ga xai fi" yace "Toh shkkn mum, nagode" tace "Hope ka ci abinci" yace "Sure mum" daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo cike da tausayinsa har ya fita, she know he is just trying his best to be okay, Kuma taji dadin yanda yake harkokinsa duk da kana ganinsa kasan akwai damuwa sosai tattare da shi, addu'a tayi masa na cewar Allah ya fiddo masa da mace soon shi ma yayi auren nan. Ana gobe daurin aure aka xo har gida aka ma Khadijah gyaran gashi da lalle, all this while baby da kawayenta na tare da ita, Yanxu kam shirun nata ya fara isan Umma ga rashin cin abinci duk tayi mugun rama, Khadijah na son sanin ko Khaleel ya koma ko bai koma ba amma bata san ta ya ba, har lkcn maganar sa na karshe ya tsaya mata, Wai xai mata abinda xai sa ta farin ciki na har abada to meye wannan bayan xuwa gobe tana gidan Sudais, she will like talking to him before tomorrow amma ta kasa kiransa duk da ta ma kashe wayar kar Sudais ya kirata, a haka ta kwanta ranan cike da tunaninsa, tun daga ranan da ta fara ganinsa har xuwa yanxu, tayi wani murmushi ta gyara kwanciyar ta ta lumshe ido tana fatan bacci ya dauketa ko xata samu saukin ciwon kan da take ji. Washegari tun da Sudais ya tashi yake ta kiran layin khadijah a kashe gashi ba shi da number baby, shi kuma baxai iya kiran Umma ba, yana xaune gefen gado misalin karfe takwas Jiddah ta shigo dakin, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsa tana murmushi tace "Happy married life in Advance Aliyu" ya dauke kai daga kallonta bai ce komai ba, wani murmushin ta kuma yi ta juya ta fita dakin, mikewa yayi ya fita parlor jin kamar kanninsa da few relatives da suka xo tun shekaranjiya sun fito parlorn, Kamar yanda yayi xata haka ne suna kitchen suna nema ma kansu abinda xa su ci don tun da suka xo ko ruwa jiddah bata taba debowa ta kawo masu ba, sai ma idan sun girka ta tafi ta diba ta ci, komawa daki yayi ya kwanta don sai bayan an sauko juma'ah daurin auren. Tun da khadijah ta tashi take kukan da bata san dalilinsa ba, baby tayi lallashin har ta gaji, Umma tun da ta tambayeta kukan me take taki bata amsa ta fita harkanta, gida ya cika fal da abokan arxikin Umma da yan uwanta da mutan garinsu, Babu Wanda xai ce ba ita ta haifi khadijah ba, yau dai Nanny har da yan uwanta a gidan, Mumy ma tun safe ta xo gidan da kawayenta biyu, Hajiyarsu Sadeeq ma da safe ta shigo gidan, da kyar khadijah ta mike ta shirya bayan Umma ta mata Jan ido taki ko da shafa kwalli a ido. Karfe sha biyu wata kawar Umma ta fita bayan gidan kiran Umma, ba a dau lkci ba Umma ta shigo parlorn don ce mata tayi wasu baki sun shigo kuma cewa suka yi uwar amarya suke nema, kallon Jiddah da kawayenta su kusan biyar kawai Umma keyi don bata taba ganinsu ba, Jiddah na murmushi tace "Ke ce uwar Amaryar Mama" Umma tace "Nice daga Ina haka?" Jiddah tace "Kawayenta ne mu mun taba islamiyya daya mama" Da mamaki Umma ke kallonsu don Khadijah bata taba bata labarin tayi kawaye a islamiyya ba, sannan ga wani irin daurin dankwali na ture ka ga fitina da suka yi gaba daya, sun cakare cikin ankon super wax gaba daya, ita jiddah irin make up din da tayi sai ka rantse ita ce Amaryar, Umma tayi karfin halin cewa "Toh sannun ku da xuwa" Jiddah na murmushi har da ritsinawa tace "Mun gode mama, Toh ina amaryar take" Umma ta sa yar wata kawarta ta kai su dakin da su khadijah su ke, yarinyar na gaba suna biye da ita har suka shiga dakin, khadijah na xaune tare da Baby da kawayenta sai jujjuya wainar shinkafar da Mumy ta kawo mata ta ci ganin bata ci komai ba tun safe take, Su kuma su baby suna ta make up tunda ita har rantsuwa tayi baxa tayi ba, tun da su jiddah suka shigo Khadijah da su baby ke kallonsu, Jiddah na murmushi tana kallon baby tace "Amarya Sannu...." Baby na masu wani kallo ta nuna Khadijah tace "You are mistaken, ga amaryar can xaune" daga haka ta dauke kai ta ci gaba da shafa powder dinta don ko kadan ji tayi gaba daya jiddah da kawayen nata basu mata ba, Khadijah dai sai kallonsu take ko kiftawa babu, Jiddah ta iso kusa da ita tace "Ke ce Khadijah, Amira, Kuma Ummu Shureim koh?" Khadijah taji gabanta yayi mugun faduwa bata dai ce komai ba tana ta kallonta, Jiddah tayi wani dariya tana kallonta da kyau tace "Ke ce ke Shirin shigowa gidan Barrister a matsayin matarsa ta biyu Koh?" Khadijah ta hadiya abu da kyar still ta kasa ce mata komai, xuwa lkcn kam ta fara dago wacece ke tsaye gabanta ko tantama babu matar Barrister ce, Baby ta mike tace "Ke malama ance maki gidan radio ne nan wannan tambayoyin da kike jefo mata?" Jiddah ta mata wani matsiyacin kallo ta daga mata hannu tace "Dakata Hajiya ban yi da ke ba, ki xama yar kallo a nan, ja gefe ki tsaya kawai" daga haka ta mayar da dubanta kan Khadijah tana mata mugun kallo tace "Wato tsaurin idon ki yakai har ki rasa wanda xaki makale ma wa ya aure ki sai mijina Barrister Aliyu Sudais?" Tuni hawaye ya kawo idon Khadijah duk jikinta yayi sanyi, Jiddah ta fashe da dariya ta juya tana kallon kawayenta tana nuna Khadijah tace "Don Allah wacece xaune nan?" Kamar hadin baki suka ce "karuwa" Jiddah tace "Da ta yi me?" A tare suka kara cewa "Cikin shege...." Tuni duk mutanen dake parlor suka yo daki da sauri jin hayaniya a daki, Jiddah na kallon Khadijah da kyau tace "Toh don kaza kazan ki in har kin haifi cikin uwar ki da ubanki ki yi kuskuren shigowa gidan Aliyu yau, ke don fitsara ki gama yawan karuwancin a gidan aiki ki haifi tagwaye sannan daga mijina ya taimake ki sai ki makale masa, daga taimako???? Har yana ikirarin tausayin ki da yake kadai yasa xai aure ki ba wani abu ba, kin xata badan uban tausayin da Allah ya xuba masa ba xai ce xai aure ki bayan yasan ke wacece? Toh bari ki ji, babu komai naki da ban sani ba, duk sirrin ki na tafin hannuna, babu abinda Aliyu ya boye min game da ke, tunda mijina ne shi din baya komai sai yayi shawara da ni, da farko na xata abun arxiki ne bayan ya bani labarin ki na amince ya aure ki don ya rufa ma ke da shegun ki asiri amma kawai daga baya tun baki shigo gidan ba na fara ganin canji, wato kin fara shanye min miji sai yanda kika yi da shi daga na amince masa ya aure ki ya rufa maki asiri koh? To wllh kinyi kadan, yau xan ga ta yanda xa ayi auren nan da kaxa kaxan ki sai dai ki koma ki ci gaba da karuwancin...." Baby bata san lkcn da ta mike ta cakumota ba ta makure ta..... Kan kace me fada ya kauraye tsakanin jiddah, baby, da kawayen jiddah, frnds din baby su ma suka shiga, da kyar mutanen da suka yi mutuwar tsaye parlorn suka raba fadan, Khadijah ta hade kai da gwiwa jin numfashinta na sama, ko kwakkwaran motsi ta kasa daga gun da take xaune, Jiddah ba irin xagi, cin mutunci da gorin da bata mata ba kawayenta na taya ta, har Umma sai da suka xaga, Baby ma bakinta bai mutu ba, da kyar aka fidda su dakin ana Allah wadaran Jiddah, sai a sannan hawaye ya dinga xubo ma baby taji tausayin Khadijah sosai duk jikinta yayi sanyi, Umma kam xaunawa tayi ita ma hawayen na sakko mata ta kasa cewa komai, Mumy kanta tsaye tayi ta rasa abin cewa duk jikinta yayi sanyi, Wata kawar Umma ta durkusa ta dago kan Khadijah a hankali cike da tausayinta, hawaye ne ke xuba idonta kamar an bude pampo, Baby ta durkusa kusa da ita ita ma hawayen na xubo mata ta rasa abinda xata ce mata, Khadijah ta kamo hannunta cikin rawar murya tace "is it my fault that I was raped baby? Is it my fault that I am an orphan, is it my fault that I had kids out of wedlock? Dama maraici...." kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai tana girgixa kai a raunane tace "Alhamdulillah for my fate... irin tawa kaddarar kenan kuma na amsa hannu bibbiyu, Amma me yasa mutane baxa su yi considering dina ba, ni ban so ma kai na haka ba, Allah ne ya kaddara min, but ya xan yi baby, dole in gode masa, ban taba karuwanci ba amma sun ce min karuwa, ban san Sudais baxai iya rike min sirrina ba he betrayed...." Mikewa Baby tayi ta dau wayar Khadijah ta fice daga dakin, Ta kunna ta shiga neman layin Sudais, Bata yi wahalan ganin number ba don Barrister tayi masa save as, tana dialing ba a dau lkci ba ya dauka cike da damuwa yace "Why did you switch off ur phone Amira..." Baby ta katse sa a xuciyarta na tafarfasa tace "Malam dama ka san baka iya rike sirri ba ka nace sai ka auri Khadijah??? dama kai din mijin ta ce ne sai yanda mahaukaciyar jahilar matar ka tayi da kai?" Kasa cewa komai Sudais yyi da farko don gaba daya he was lost, can cike da karfin hali yace "Wacece wannan?" A mugun fusace tace "Ba Lallai ka ji wacece ba, wllh ka ci amanar Khadijah, ka xalunce ta, and am advicing you ka janye batun auren ta kaje jahilar matar ka ta ishe ka, Kuma sai Allah ya saka mata" tana kai wa nan ta fashe da kuka sosai taci gaba "Naga ba ita ta ta xabar ma kanta wannan kaddarar ba har xaka xaunar da warce xa su xauna a matsayin kishiyoyi ka tsara mata komai na rayuwarta daga farko har karshe ta xo har gidan biki ta mata tonan silili ta gaya mata son ranta, tayi mata cin mutunci da cin fuska, tayi mata gori" katse wayar Sudais yyi kansa na juya masa ya mike daga xaunen da yake ya fito parlor, ya kusa minti sha biyar tsaye sai ga jiddah da kawayenta sun shigo parlorn, ya taka har gabanta ya sauke mata tagwayen mari, yana kallonta da jajayen idanuwansa yace "Na sake ki saki daya jiddah" A hankali Khadijah ta bude idanuwanta ta sauke kan Khaleel dake xaune gefenta Aliyu na tsaye daga gefensa, Umma ta taho gunta da sauri ganin xata mike xaune ta riketa da damuwa tace "Sannu Khadijah, how are you feeling now?" Kirjinta kawai ta nuna ma Umma hawaye na xubo mata, Umma tayi kasa da murya a sanyaye tace "Xai daina in sha Allah, be strong daughter" Baby dake tsaye gefe daya ta karaso ta xauna kusa da ita tana kallonta ta kamo hannunta, rasa abinda xata ce mata tayi, lkci daya ita ma hawaye ya kawo idonta, Khaleel ya mike ya fita ward din sai gashi sun dawo tare da likita, Juyawa Aliyu yayi ya fita, likitan ya gama dubata suka fita tare da Khaleel xuwa office din sa. A sanyaye Umma tace "Kin dai ji abinda likitan ya ce maki, Kar ki sake kukan nan don Allah saboda lalurar ki" Khadijah bata ce komai ba ta kai hannu tana share hawayen idonta, bude kofar ward din aka yi Sudais ya shigo, tsaye yayi nan bakin kofar yana kallonta, A hankali Umma ta dauke kai kanta daga kallon da take masa, Baby ta hade rai kamar bata taba dariya ba, Tun da Khadijah ta kallesa sau daya bata sake yarda ta dago ba hawaye ya dinga xuba idonta, ya iso har kusa da ita, da kyar yayi gathering courage yace "Amira...." ta fashe da kuka sosai tace "Am begging you ka rabu da ni pls Aliyu ka tafi, My heart is aching at the sight of you, kayi hakuri ka wuce... let me rest plssss" cikin matsanancin kuka ta kare maganar, Yana mata wani kallo yace "Amma in har maganganun da Jiddah ta fadi maki sun yi tasiri xuciyar ki ba ki min adalci ba Amira, for good two years na boye ma mahaifiyata na ajiye ki gidana ko da kuskure ban taba sanar da ita ba ban taba tona maki asiri ba, hatta frnds dina ban da Yusuf babu wanda yasan labarin ki, sai a yanxu kike tunanin xan fallasa sirrinki, Kuma in rasa warce xan fada ma sai matata da ko kadan ba dadin xama da ita nake ba, am I that daftt??" Ya girgixa kai cikin bacin rai yace "I never expect such from you Amira, I thought ke me fadi ma wasu cewar makirci ta xo tayi displaying gidan ku....but I was mistaken" kasa ci gaba yyi ya juya ya fice daga ward din, Khadijah ta hade kanta da gwiwa tana kuka kamar an aikota, Baby dai ta kasa cewa komai duk jikinta yayi sanyi sosai, Umma ta sauke ajiyar xuciya tana kallon baby tace "Hope kin ji maganata ya fito ko, Ni nasan makirci ne kawai na mace, I know baxai taba yin haka ba, baxai xaunar da ita yayi mata tsarin da ta xo tayi ba, she set him up kawai saboda kishi...." Umma na magana tana goge hawayen dake xuba idonta, ta ji tausayin Sudais sosai, "Khadijah idan kika ce kin fasa aurensa kamar yanda kika yi ikirari before passing out kin yi butulci, baki kyauta masa ba, Kuma kin nuna ta ci nasara kenan matar tasa" Khadijah ta dago cikin kuka tace "Wayyo Umma kashe ni xata yi a gidan, baxan iya auren mata miji ba ni dai, ku rufa min asiri, Umma kin ji yanda xuciyata ke min ciwo, na hakura da auren gaba daya I prefer dying a spinster" Rungume ta Umma tayi tace "Ba abinda xa a fasa daughter, kuma tayi kadan ta kashe ki, we will prove her wrong, ta xo tayi masa sharri duk don kice kin fasa to xa a nuna mata iyakarta in sha Allah sai kin aure sa, sai in Allah yayi shi din ba mijin ki bane dama, Amma babu abinda xa a fasa" Tun da Sudais ya fita ward din ya tafi kan wani kujera a waje ya xauna ya jinginar da kai ya lumshe ido, he was totally lost and sad, Bai taba tunanin makircin jiddah ya kai haka ba, ya rasa gane inda ta samu lbrin Khadijah, yasan Yusuf baxai fada mata ba, infact ta ina ma xa su yi communicating bayan bata da number sa bashi da nata, Babu abinda ya kara sanyaya masa jiki sai yanda Khadijah of all people ta yarda da abinda jiddah taje ta fada, ai Ita mai ce ma mutane sharri jiddah ke masa, but she is among the believers, Khaleel dake jingine da motarsa yana ta kallonsa, tausayi ya basa sosai, and he knows what he is feeling, khaleel ya fi minti biyar yana jinjina kwarewar matar Sudais a fannin hypocritical action, she is just perfect, a hankali ya taka ya isa har inda yake ya xauna gefensa, Sudais ya bude ido a hankali jin mutum gefensa, Khaleel ya cire glasses din idanuwansa in a low voice yace "Sure it hurts..." Sudais na kallonsa da idanuwansa da suka sauya launi cikin sanyin murya yace "Can I confide in you Dr Ayman?" Khaleel na kallonsa ya gyada kai yace "Sure" Gyara xama Sudais yyi yana dubansa ya fara magana cikin sanyi.... Umma ce ta fito haraban hospital din bayan kusan minti sha biyar, duk iya kalle kallenta bata hango ko wannensu a nan ba hakan yasa ta koma ciki don dauko wayarta, Sudais ya dinga kallon Khaleel da yayi shiru idonsa a kasa, Sudais yace "Don't forget I asked you before letting out my mind to you doctor, ka gaya min gaskiyar abinda ke ranka" Sai a sannan Khaleel ya dago yana kallonsa, d'an murmushin karfin hali yayi yace "Sure" bayan few seconds a hankali yace "Yea Barrister, May be it's the right decision" Sudais na kallonsa yace "May be?" Khaleel ya shafa kansa yace "It's just the right decision" a sanyaye ya kare maganr, Sudais ya kalli wayarsa dake ring ya ga Umma ce ke kiransa dauka yayi, ya kai kunne yayi sallama, Umma tace "Kana ji na Barrister, Babu abinda fa xa a fasa, don't let anything spoil ur mind pls, idan har kana son Khadijah da gaske ka tafi, it's almost time for prayer ana saukowa a daura auren ba abinda aka fasa in sha Allah" a hankali yace "Toh Umma nagode sosai Allah ya kara girma" tace "Ameen" katse wayar yayi yana kallon Khaleel dake kallonsa shima don duk ya ji me Umma ta ce, a tare suka mike Sudais na kallon agogon wrist din sa. Tun da aka sauko masallaci gaban Sudais ke faduwa, is he really making the right decision, Khaleel dake gefensa na lura da shi, a hankali ya matsa kusa da shi sosai yace "It's not only the right decision but the best.... For many reasons" Sudais ya kallesa yayi murmushi bai dai ce komai ba, can ya kalli Khaleel yace "Kana da Number Dr Aliyu kuwa? I didn't see him..." Katse sa Khaleel yyi yana yar dariya yace "Sheer jealousy, did you expect to see him here...." Murmushi kawai Barrister yayi, Khaleel ya fiddo wayarsa ya nemo masa number Aliyu ya mika masa, Dialing number Sudais yyi ya kai kunne ba a dau lkci ba aka dauka Sudais yace "It's Barrister Aliyu, ban gan ka masallaci ba, or don't you want to witness the nikka?" Aliyu yyi murmushi yace "It's not a must I stay near you Barrister, though I can sight you from where I am, I am not what you might have thought of me, idan abun farin ciki ya samu d'an uwana musulmi ina taya sa murna, idan kuma otherwise...." Hangosa Sudais yyi tsaye not too far away from them tare da Salim da wasu frnds, Sudais ya katse wayarsa yana murmushi, Aliyu ya Karaso ya basa hannu Sudais ya mika masa nasa, sannan Aliyu ya mika ma Khaleel ma, Khaleel ya cire glass din idanuwansa ya basa nasa hannun. A can asibiti kuwa bayan an ma Khadijah allurai aka bata drugs aka sallamosu suka koma gida, har sannan hawaye ya ki tsaya mata, Babu abinda aka fasa na biki a gidan kamar yanda Umma tace don kamar ma ba ayi komai ba sai dai Amarya da bata da lafiya, Shayi Umma ta sa baby ta bata ta sha ta kwanta nan da nan bacci me nauyi ya dauketa.... Breakfast, just light😎 Sai kusan karfe uku saura Baby ta tada Khadijah tayi sllhn azahar ganin lkcnsa na ta wucewa kuma da alamar ta samu saukin jikinta sosai ganin she is sleeping peacefully.... Khadijah ta mike xaune da kyar, xuwa lkcn kam ciwon da ta dinga ji daxu da safe a xuciyarta ya rage sosai, sai dai gaba daya taji gaba daya she is weak kanta ya mata nauyi, Tana kallon Baby cikin sanyi tace "An daura auren koh Baby?" Tana magana ne hawaye cike idonta, Baby ta kasa ce mata komai... Ta hade kanta da gado cikin rauni tace "Matar nan xata iya kashe ni wllh, nobody want to consider me, nobody is willing to understand what I mean, Baby tsoron ta nake.. " Baby ta kauda kanta bata ce komai ba sai dai wani mugun tausayinta ta dinga ji har ranta, Bayan wani lkci a sanyaye baby tace "Ki tashi kiyi sllh Khadijah, lkci na wucewa" Khadijah Bata ce komai ba ta sauka saman gadon tana kokarin ganin bata bar hawaye ya sakko mata ba, kamar iska xai kadeta ta shiga bathroom, khadijah na idar da sllh Baby ta fiddo mata daya daga kayan biki da aka dinka mata, tana kallonta persuasively tace "Plss Iman put on this ko baxa kiyi kwalliya ba, am begging you" Khadijah tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Bayan wani lkci ta mike ta shirya cikin tsadadden lace din, Baby na murmushi ta wara ido tace "Waow kin ga yanda kayan suka maki kyau kuwa Iman, plss ki bari ko powder in shafa maki, just it" khadijah bata mata musu ba, duk da har xuciyarta bata so, daga powder baby ta lallabata ta sa mata har eye pencil da chappete, sosai Khadijah tayi kyau just like the bride she is, Baby ta daura mata dankwali tana kallonta da sha'awa, Frnd din Umma ce ta shigo dakin da warmer din abinci ganinta tace "Kai maa sha Allah ko ku fa? Da xa ku bari wata kishiya can ta bata maku wannan ranan, show her she is a liar bata isa ba ne, sai ma mun je kai ta gidan tukun" Murmushi kawai Baby tayi tana kallon khadijah da ta ki dago kanta. Tun bayan da suka bar masallaci bayan an daura auren Aliyu ke rike da kan sa a mota, su biyar ne motar, Khaleel na driving, Dr Yusuf na xaune gaban motar, sai Barrister da Aliyu da Farouq a baya, tun da suka dau hanya Sudais ke danna wayarsa bai dago ba shi ma, the journey was very silent da alama kowa da abinda ke ransa har suka iso dai dai kofar gidan su Khadijah, Khaleel yyi parking a hankali ya kashe motar, Shi ya fara sauka sannan Farouq da Dr Yusuf, Aliyu ya sauka sannan Sudais ma ya fito yana mayar da wayar sa Aljihunsa, ganin xai shiga ciki Aliyu ya riko hannunsa yana kallonsa da idanuwansa da suka kada sosai, Barrister ya kasa hada ido da shi, Da mugun karfin hali yace "Barrister... am still confuse, I think am yet to understand the meaning of the drama that took place at the mosque minutes back, ka ganar da ni don Allah, I am confuse plss, nayi tambaya a mota kun kyaleni..." Sudais dai bai iya yace komai ba, Dr Yusuf ya rungume hannayensa yana kallon Sudais don Aliyu bai ma kai sa confusion ba, jiran abinda Sudais din xai ce shi ma yake, shi dai yasan daurin auren abokin nasa ya xo tun daga Yobe sai kuma ya ga otherwise, Farouq dai murmushi kawai yyi ya jingina da mota ya rungume hannunsa, khaleel ya tako har gaban Aliyu yana kallonsa, bayan few seconds yace "What is it that u don't understand Aliyu?" Aliyu ya kallesa a hankali yace "Everything.... I... I don't get everything" Khaleel ya shafa kansa cikin sanyin murya yace "The fact is that, Kai xaka gyara abinda ka 6ata doctor, we think this is just the best for the both of you, Barrister Aliyu ya sadaukar maka ba don baya so ba sai don la'akari da our today's world, kwanciyar hankalin khadijah ya fi masa auren ta....." Sai a sannan Sudais yyi murmushin karfin hali yana kallon Aliyu a sanyaye yace "I have no option... She is dear to me... Ita din abar tausayi ce, they are a lot of challenges ahead for her and the little boy in dai ba gidan ka suke ba, I don't wish that for her, and her condition don't need that, shi yasa na hakura domin farin ciki da kwanciyar hankalinta, nasan I am not making a mistake giving up for you because I know you love her also, and u love ur son...da dadewa na yarda da cewa abinda ya faru tsakanin ku tsautsayi ne, it's not ur doing coz you are too responsible for that, u are responsible in every aspect, you are really a gentleman, ur family are just good also, kawaicin ka ma abun dubawa ne, I've studied you for long...." Aliyu ya runtse ido maganganun Sudais na yawo kansa kamar a mafarki, lkci daya ya bude idanuwansa, kawai ya rungume sa hawaye na xuba idonsa ya kasa cewa komai, Sudais da ya ji xuciyar sa ya masa rauni yyi karfin hali yace "It's my pleasure, and a Suggestion from Dr Ayman.... nayi ma Khadijah wanda ya fi wannan ma, don haka nasan ban fadi ba, But ina neman alfarmar ka bar mu mu din ga xumunci sosai coz I love the little boy..." Cike da karfin hali hawaye na sauka idon Aliyu yace "How will I repay you Barrister..." Sudais yayi murmushi shi ma hawayen suka xubo masa a hankali yace "Ta hanyar rike Amira da amana, be her father be her mother, be her happiness, and finally prove to her that u are innocent, kadarrar ku ce a haka" Khaleel ya sauke idanuwansa a hankali ya juya ya shiga gida ganin he might not stand it anymore.... 😭 Lunch, very light also, kar mutum yaje yana bacci da rana😎 Umma kasa kwakkwaran motsi tayi bayan ta gama jin bayanin Sudais ta kasa daina kallonsa, jikinta yayi sanyi sosai, tsoronta daya a lkcn khadijah, ko ya xata dau batun nan, Wai Aliyu? Kallon Khaleel dake xaune shi ma tayi, ya d'an yi murmushi ganin damuwar dake fuskarta yace "Umma you need not to worry, I know you might be thinking of how khadijah will take this, but I think ba lallai sai an fadi mata ba she will see for her eyes, and surely nasan she have a very soft spot for Aliyu, the problem is that she is confuse, sannan one thing about her is that bata mance abun sharri da aka mata ko ya yake which is wrong, she need counseling Umma...." Murmushi Sudais yyi a hankali yace "Sure, gaskiya doctor ya fada Umma, fatan Allah yasa ke dai kin fahimce ni, nayi abinda naye ne saboda future, I really don't want anything that will hurt her again in life, she have had enough... duk Allah ne mai tsara komai" a sanyaye Umma tace "I am really proud of u both, irin ku basu da yawa a duniya Allah ya biya ku da mafificin alkhairinsa, ko wannen ku ya taka rawar gani matuka a rayuwar khadijah, Kun mata abinda dangin ubanta da ni kaina na kasa yi mata, Allah ya saka da alkhairi, and one more thing Sudais ka maida matar ka don Allah..." Sudais ya girgixa kai a hankali yace "Umma I don't think xan maida jiddah, na hakura da ita, Allah ya musanya min ita da mafi alkhairi, may be abubuwan da nayi mata years back kan khadijah ne Allah ya saka mata ta samu damar yi min abinda ta so, tun da na aure ta take wahal da ni, I have had enough..." Umma tace "A'a ba ayi haka ba, kayi hakuri don Allah, ko albarkacin yarinyar nan dake tsakanin ku" Dai dai nan Baby ta fito ta kawo masu abinci kamar yanda Umma ta umarce ta kafin ta taho gun su, ajiye abincin tayi ta kasa kallon Sudais don ba karamin kunyar abinda tayi masa a waya taji ba daxu barin da ta ga bashi da laifi, Kallon Khaleel tayi daga karshe tace "Ina yini" yace "How are you" ta mike tace "Alhmdllh" daga haka ta juya ta wuce Sudais ya bi ta da kallo ganin bata gaishesa ba, Khaleel na kallon Umma yace "And lastly Umma, I think I've found out dangin mahaifiyar khadijah if I am not mistaken in sha Allah" daga Umma har Sudais kallonsa suka dinga yi ko kiftawa babu, ya sauke kansa kasa a hankali yace "But I won't reveal that to her sai tayi settling gidan mijinta, ta kwantar da hankalinta, still xa mu je can gidan dake Umma duk da su ma ban ce masu komai ba tukun, but babu tantama they are her mother's family in sha Allah" Mumy ba karamin sanyi jikinta yayi ba jin sadaukarwar da Barrister yayi ma Aliyu, she couldn't even utter a word, abun ya mugun daure mata kai, Abbansa shi ma ya jinjina lamarin sai dai abinda bai ji dadi ba shine yin gaban kansu da suka yi babu shawara da kowa, and a whole daurin auren 1st son dinsa baya gun, but all the same he is happy for his son cos he is always after his happiness kuma ya bukaci number Barrister Sudais, Mumy na ta kallon Aliyu da har sannan mood dinsa isn't encouraging da damuwa tace "What's it again Abuturrab, ain't you happy" ya dago ya kalleta da kyar yace "Mumy bata sani ba fa, and I don't know how she will take this, ba so na take yi ba, tana kulani ne kawai saboda kids din, albarkacin su nake ci" A hankali Mumy tace "Then you will teach her to love you son..." Bai iya yace komai ba, bayan few seconds ya mike ya dawo kusa da ita ya xauna yana facing dinta, har lkcn idanuwansa basu dawo dai dai ba, cikin sanyin yace "Mumy me xan yi in biya su?" Shiru Mumy tayi tana kallonsa don tasan su wa yake nufi, ta d'an yi murmushi tace "Zumunci mai karfi da su is enough son" Aliyu ya sauke idonsa kasa a hankali yana tunanin xumunci yayi kadan ya biya both Dr Ayman and Barrister Aliyu, dafa sa Mumy tayi tace "That's just it Abuturrab, mutanen nan biyu ka rike su a rayuwa, kaga riban hakuri... Da ka ci gaba a yanda ka fara da farko kana tunanin Barrister xai ga cancantar bar maka ita? Of course no, shi sa nake yawan ce maka you just have to be patient in everything in life" Bai dai ce komai ba, tace "Do what you are suppose to now, na kira su Siyama xa su je can gidan naka su yi abinda ya kamata, don xuwa anjima xa su kai ta can gidan, mun yi waya da Ummarta yanxu" Har sannan Kamar yanda khadijah bata san da wanda aka daura mata aure ba haka baby ma bata sani ba, gashi dai ana ta shirin tafiya da amarya wajajen karfe biyar, Umma duk ta kasa samun nutsuwa da ta tuna khadijah fa bata san da Aliyu aka daura auren ba sai taji gabanta ya fadi, tsoronta ma kada ciwonta ya kara tashi, daga karshe ta sa aka kira mata Baby bedroom dinta, Baby na kallonta tace "Gani Umma" cikin sanyi Umma tace "Khadijah kin san da wanda aka daura auren nan kuwa?" Girgixa kai Baby tayi da confusion tana kallonta, a sanyaye Umma tace "Yayan ki" still khadijah tayi tana kallon Umma baki bude ta kuma kasa cewa komai, a hankali Umma tace "Ban san yanda khadijah xata dau batun nan ba, am afraid...." A hankali baby ta dauke kanta tana sake nanata sunan yayanta a xuciyarta, to how comes??? Da kyar ta kalli Umma tace "Barristern fah?" Umma tace "Shi ya bar masa... For some concrete reasons which I found out to be nothing but the truth, Aliyu shi ne kadai rufin asirin khadijah da yaron nan, toh amma ba lallai ta gane hakan ba, ban san ta ina xan fara sanar mata ba" Baby ta sauke ajiyar xuciya, lkci daya jikinta yyi sanyi tace "Umma kar a gaya mata, she shud just see for her self, xasu sasanta kansu can din" Umma tace "I thought as much... Haka yawanci kowa ke ce min" Tagumi baby tayi ta rasa wanne xata yi a ciki, farin ciki ko bakin ciki, Umma tace "Tashi ki je ku gama shiryawa lkci na wucewa khadijah, har an gama kai kaya can gidan" Baby ta mike jiki ba kwari ta fita, tana komawa daki ta ci gaba da shirya ma khadijah few abubuwan da tace mata, Shureim ne ya shigo dakin da shadda irin wanda Sudais yasa ranan da hularsa, sai sheki kayan suke sun masa kyau sosai, tun wayewar gari sai sannan khadijah ta gansa, ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa a hankali tace "Where have you being today?" ya wara mata ido yace "Uncle ne ya tafi dani since, mun dawo yanxu, Anty daxu Umma tace min baki da lafiya, me ya same ki" Shiru tayi bata ce komai ba, Ganin yanda yake kallonta ta rungumosa a hankali tace "Ae na samu lafiya yanxu" yace "Anty kinyi kyau sosai" Murmushi tayi ta ja hancin sa tace "Kai ma kayi kyau sosai, wa ya kawo maka kayan nan" Yace "Uncle, shi ma ya sa irin nawa, na tambayesa Ina na Sudais yace ya ajiye masa nasa" Shiru khadijah tayi tana kallonsa, ya kamo hannunta yace "Anty what are they celebrating today?" Baby dake gefe sai kallonsu take ta dauke kanta a hankali, sai a sannan tayi mugun ganin dacewar abinda Barrister Sudais yyi, shkkn sai su hadu su rungumi d'an su, khadijah ta sunkuyar da kanta tuna irin xagin da Jiddah tayi ma yaron daxu ta kirasa da shege mara uba, hawaye ne ya kawo idonta sai dai bata bari ya gani ba, Jikin baby yayi sanyi don duk tana lura da ita, ta juya ta ci gaba da abinda take, Shureim ya taho gunta yana gaisheta, ta rungume sa murmushi dauke fuskarta tace "Har kun dawo boy" ya gyada mata kai, shidda saura motocin tafiya da amarya suka iso gidan, nasiha sosai Mum din sadeeq da wata frnd din Umma suka yi mata, Kanta a kasa take saurarensu hawaye na sakko mata, ita kam bata samu gatar nasihar Uba ba, kalma daya Umma ta iya yi mata a lokacin bayan su Umman sadeeq sun gama "Allah maki albarka" hakan yasa khadijah taji dadi sosai, Shaheedah ta daga ta suka nufi kofa baby da wata kawarta na biye da su a baya, banda kuka babu abinda khadijah take duk jikinta yayi sanyi, duk aka bi ta da kallo cike da tausayinta, Baby da frnd dinta Hafsat sai mahaifiyar Shaheedah wato aminiyar Umma suka shiga mota daya da khadijah, sauran yan rakiyar Amarya suka shiga sauran motocin, Jikin baby bai gama sanyi ba sai da taga sun iso gidan yayanta, duk tausayin khadijah ya cikata a xuciyarta ta dinga addu'ar Allah yasa shock din ganin Aliyu as mijinta baxai yi affecting dinta sosai ba, dad'd'adan kamshin turaren wuta ke tashi ta ko wani angle a gidan, ga sanyin ac, parlorn so chill, har lkcn kuma su Siyama da kawayensu da frnd din Mumy suna gidan suna jiran Amarya, Su Hajiya Sajeedah suka wuce da khadijah well furnished bedroom dinta, ita dai har sannan fuskarta a rufe yake bata san kalan gidan ba gashi tun shigowar su gabanta ke faduwa ga hawaye ya ki tsaya mata duk jikinta yayi sanyi, ana xaunar da ita gefen gado ta riko baby cikin rawar murya tace "Stay beside me plss don't leave me" a sanyaye baby ta xauna kusa da ita tana rike da hannunta, khadijah ta rike ta gam ta kwanta jikinta. Sai kusan bayan isha duk aka watse gidan har su Siyama suka wuce, sai da su Hajiya Sajeedah suka kara mata nasiha kan xamantakewar aure kafin su wuce su ma, gidan ya rage daga ita sai baby da Hafsat, kuka kawai khadijah take don tana ganin ko wani lkci jiddah xata iya shigowa gidan, Baby har ta gaji da lallashi tayi tagumi tana kallonta, yau kam tasan yayanta xai sha lallashi, d'an murmushi tayi dai dai lkcn da wayarta ya fara ring, Hafsat ta mika mata taga Aliyu ke kiranta, kallon khadijah tayi kafin ta daga ta kai kunne hade da sallama, shiru ya d'an yi kafin yace "Ku fito sai a ajiye ku gida yanxu" Tace "Toh" kamar khadijah taji abinda aka ce ma Baby tana kallonta a tsorace tace "Waye ya kira ki?" Baby ta sauke idonta tace "Mijin ki, mu xa mu wuce yanxu Iman, Allah ya bada xaman lafiya" khadijah ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku, me yasa baxa ku kwana ba don Allah kar ku tafi, ki bani wayar xan masa magana" dariya ta ba baby amma bata yi ba tace "Gobe fa da safe xan xo Iman" cikin kuka sosai Khadijah tace "Don Allah ki rufa min asiri ki kwana" Baby tace "In dai gidan nan ne wllh baxan kwana ba, gwara ki hakura gobe in dawo, idan kuma kika ban haushi in ki xuwa goben ma, ko a kauye an daina haka kina abu kamar wata yarinya..." Dariya kawai Hafsa take don khadijah ta bata dariyan, Baby ta mike ta hade rai tace "Mu je Hafsah, ji wani abu da take fa kamar yar yarinya, ko yara sun daina haka, balle ita wayayya" Da haka baby ta samu fa fita Hafsat na biye da ita, Ban da kuka babu abinda khadijah take tana kallon kofar har suka fita suka rufe, Baby ta ji tausayin ta har ranta, amma tasan idan ba haka ta yi mata ba sai ta iya ma biyosu, A waje ta tadda Aliyu tare da Sudais a tsaye jikin motar sudais din, da alama su suke jira, Baby tayi kasa da kanta tace "Ina yini yayanmu" yace "Lafiya lau" Hafsat ta gaida Sudais sannan ta gaida Aliyu tayi masa fatan alkhairi a aurensa, murmushi kawai yyi bai iya yace mata komai ba, Sudais yace "Alryt, sai da safe Dr" Aliyu ya kallesa a hankali yace "Baxa ka shiga ba?" Ya bude motarsa yana d'an murmushi yace "Gobe xan xo in sha Allah" Aliyu bai iya yace masa komai ba, can ya kalli Baby yace "Ku shiga xai yi dropping din ku gida" Ta d'an buda ido, Aliyu ya matso kusa da ita da damuwa yace "Did she know...." Baby ta girgixa masa kai a hankali, sauke idonsa kasa yyi, Hafsat ta bude back seat ta shiga, Bayan few seconds ya kalli baby yace "Don't keep him waiting, ki shiga motar ku wuce, sai da safe" A hankali baby tace "Yayanmu wllh kunyarsa nake, daxu da safe na gama tsigale shi a waya I never knew makirci matarsa ta hada masa" Aliyu ya bude ido yana kallonta, ta marairaice tana kallonsa, yace "Ki basa hakuri idan kin shiga motar" shiru tayi, ya gyada mata kai yace "Yea, do that" a hankali tace "Toh sai da safe yayanmu" daga haka ta xaga ta shiga front seat ganin Hafsat baya ta shiga Aliyu ya bi ta da kallo, Tana shiga motar ta rufe ta kasa kallon Sudais, bayan ya tada mota ba tare da ya kalleta ba yace "Good evening" sai a sannan ta kallesa dai dai nan shi ma ya kalleta, Murmushi tayi cike da jin kunya tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" a hankali tace "Am soo sorry for what I did daxu da safe don Allah kayi hakuri" kallonta yayi da kyau, sai kuma yyi murmushi yace "Wai dama ke kika kirani?" xaro ido tayi ganin ashe ita kadai ke ta haukanta shi bai ma san wa ya kirasa ba, wani murmushin ya kuma yi yana shafa kansa ya ja motar yace "I bet da muna kusa har duka sai kin kai min" sauke kanta kasa tayi bata ce komai ba. Tun da Aliyu ya shiga gidan gabansa ke faduwa, ya kashe wutan parlorn da kyar ya haura sama, ya fi minti daya tsaye kafin ya bude kofar bedroom din da khadijah ke ciki, tana xaune can karshen gado ta hade kanta da gwiwa tana shesshekar kuka, ya kasa karasawa cikin dakin, a hankali ya kai hannunsa kan switch dake jikin bango ya kashe wutan dakin, da sauri ta dago kanta, ya rufe kofar a hankali, cikin rawar murya tace "Barrister ka kunna plss..." Lumshe ido Aliyu yayi jin sunan da ta kira lkci daya jikinsa yayi sanyi sosai, ya bude idanuwansa ya taka a hankali har ya isa gabanta, ja baya ta dinga yi xuwa lkcn ta daina kukan da take tsoro ne fal xuciyarta, ya xauna dab da ita har suna jiyo numfashin juna xata mike da sauri, yyi hanxarin rikota ta fashe da kuka jikinta na rawa, a hankali ya jawota jikinsa ya rungumeta lkci daya ta hadiye kukan da take, ya dinga jin yanda xuciyarta ke bugawa a kirjinsa kamar xai fito, lumshe ido yyi hawayen idanuwan sa suka xubo, cikin rawar murya tace "Barrister ka kunna wutan bana son duhun plss, switch the light on" Murya can kasa yace "Imannn" Ta fi second talatin muryar da taji na kai kawo a kanta, a hankali ta xame jikinta daga nasa tana kallon fuskarsa cikin duhun dakin kamar yanda shi ma yake kallonta a sanyaye, hannu ta kai fuskarsa tana masa wani kallo da kyar tayi gathering courage din cewa "Aliyu?" Rungume ta yayi kamar xai mayar da ita jikinsa cikin rawar murya yace "Yes Iman, I beg you... don't say no to me plsss, this our fate... na sha wahala kan ki a rayuwa Iman, na sha wahala fiye da tunanin ki, kashe ni ne kadai son ki bai yi ba, for good six years bani da kwanciyar hankali bani da walwala, forgive and forget the past plss, Barrister Aliyu..." Kasa ci gaba yyi bayan wani lkci ya ci gaba voice dinsa na breaking "I owe him... he gave up for me.... Ya bar min ke Iman, don girman Allah ki ji tausayina kar ki bani wahala...." Kamar warce aka yi moulding haka khadijah tayi stiff jikinsa maganganunsa na mata yawo a kai, she's still trying her best to apprehend all what he is saying, Jin tayi shiru ya dago kanta jikinsa na rawa, hawayen dake makale idonta suka xubo tana kallonsa, ta fashe da wani matsanancin kuka kamar warce aka aiko ma wa da sakon mutuwa, sauka yyi saman gadon a rikice ya durkusa kan gwiwowinsa kusa da ita yace "Iman kiyi ma girman Allah kada ki wahal da ni, I have already had enough, don't say no to this marriage, kar ki ce A'a Iman...." Kasa ci gaba yyi.... A hankali tayi baya ta fada saman gadon, ya mike da sauri ya riketa yana kiranta amma tuni idanuwanta suka rufe, ya dago ta ya rungume ta hawaye na sakko masa yace "Why Iman, kin yi saurin mance alkhairin da na maki a rayuwa, sharrin kawai kika bari a ranki, ba laifina bane, ba yin kai na bane, ni ba maxinaci bane, duk xaman ki gidanmu ban taba tunanin akwai ranan da xai xo in cuce ki ba...." Kasa ci gaba yyi ya runtse ido yana rungume da ita har sannan. Sai kusan karfe hudu saura na asuba khadijah ta bude idanuwanta a hankali, Aliyu da ke xaune kan darduma ya mike da sauri ya iso kusa da ita yana kallonta da damuwa, mikewa take kokarin yi tana kallon jikinta, riga ce mara nauyi jikinta maimakon atamfar da ta sa tun a gida, Aliyu ya xauna gefen gadon a sanyaye yana kallonta, kokarin sauka ta shiga yi daga kan gadon yana son riketa amma yana tsoron abinda xai biyo baya, cike da karfin hali yace "Iman you are not strong ina xa ki, Wait..." Bai san lkcn da ya riketa ba ganin tayi baya xata fadi, xai kwantar da ita ta kwace kanta tace "Let me" Dafe kansa yyi, ganin xata sake tashi ya kara rikota, tura hannunsa tayi muryarta na rawa tace "Dole sai ka rike ni ne, nace bana so" ko saurarenta bai yi ba ya ki saketa, ta fashe da kuka tace "I want to use the restroom ka kyalenii...." Tashi tsaye yyi ya dagota ya nufi bayi da ita, suna isa bayin ta kwace kanta ta shiga ta rufe kofar, a hankali ya koma gefen gado ya xauna duk jikinsa a sanyaye, tana fitowa ta nufi kofar fita ya mike da sauri yace "Iman" ganin ko juyowa bata yi ba ya karasa da sauri kafin ta isa kofar ya rufe ya marairaice yana kallonta, Xaunawa tayi nan bakin kofar ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka xuciyarta yayi rauni ga wani xafi da yake mata, yanxu dama duk yaudararta Sudais yake, me yasa xai ci amanarta ya sa a aura mata Wai Aliyu?? Of all people why Aliyu? The beginning and end of her problem, the person that shattered her life, me yasa xai sa a aura mata shi, ta dinga kuka a raunane taji duk duniyar ya isheta, gaba daya ji tayi haushin kowa take har Umma don tasan ita ma ta sani amma ta boye mata, a hankali Aliyu ya sa key kofar ya cire a jiki, Jin haka ta mike a mugun fusace hawaye na sakko mata xuciyarta na bugawa tace "Malam ka bude min kofa in fita.... Bana son ganin ka, bana so...." Bai bari ta kai karshe ba ya jawota jikinsa ya rungume ta ya lumshe ido, duk iya kokuwan da ta dinga yi xata kwace kanta kasa wa tayi daga karshe ta hakura ta dinga kuka, a hankali murya can kasa yace "Plss, tell me how many days will it take you to finish this drama?" Dago kai tayi tana masa wani kallo xuciyarta na heaving, a sanyaye yace "I just want to get prepared... Just tell me for how long it will take you to finish it? And in sha Allah I will endure" fuskarta daure tace "Sake ni" a hankali ya saketa ta koma baya ta mika masa hannu tace "Bani makullin" ya mika mata makullin hannunsa, ta juya ta bude kofar ta fice tayi banging din kofar, Ya d'an tabe baki ya juya a hankali ya koma kan gado ya kwanta don har wani ciwo kansa ke yi masa baccin da bai yi ba, har aka kira Asuba bai bari bacci ya daukesa ba ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito don wucewa masallaci, kwance ya ganta kan 3 seater a parlor tana bacci ta dunkune waje daya saboda sanyin parlorn, ya kashe A.c sannan ya nufi kofa ya bude ya fita. Ko da ya dawo masallaci bai ganta parlorn ba kuma, ya wuce sama ya bude kofar dakinta a hankali yana leka ciki ya ga bata nan, juyawa yyi da sauri ya bude wani dakin, xaune ya ganta kan darduma ta jinginar da kanta jikin bango, tana ganinsa ta daure fuska ta cinno baki gaba, a hankali ya rufo mata kofar ya shiga nasa dakin ya kwanta, sai a sannan bacci ya daukesa. Sai da gari ya fara wayewa khadijah ta mike jiki ba kwari daga kan darduman da take xaune ta bude kofar dakin ta fito, dakinta ta bude a hankali tana kallon ciki, ganin babu kowa ta shiga ta rufe kofar, bathroom ta shiga tayi wanka ta fito, bayan ta shirya ta kwanta saman gado jin kanta na ciwo sosai, bacci ne ya dauketa daga haka, Bata farka ba sai da aka danna bell a kasa, ta mike xaune da kyar tana kallon agogo, har sannan kanta ciwo yake ba kadan ba, karfe tara saura ta gani, ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta sa ta fita, a hankali ta bude kofar ta ga Baby tsaye rike da basket din abinci tana murmushi tana kallonta, khadijah ta hade rai sosai ta juya ta koma parlor, Baby da ta bi ta da kallo a xuciyarta tace kya yi ki gama ne ma, A nan parlor ta ajiye basket din ta juya xata fita khadijah ta bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar sai a sannan baby ta fara dariya kasa kasa, khadijah da ta bi ta da kallo ta xauna kujera lkci daya hawaye ya cika idonta ta ji kamar ta bi ta ta mata magana amma ta kasa tashi, wato dai ita ma tasan wanda aka aura mata amma bata fada mata ba, tashi tayi ta wuce sama ta shiga daki ta fada kan gado tana kuka takaici, bayan wani lkci ta mike ta dauko wayarta ta shiga kiran Sudais, sau uku tana kira bai dauka ba, ta ajiye wayar tana share idonta ta kwanta xuciyarta ba dadi, ta jima kwance jin ciwon kai ya isheta tana son shan magani ta mike a hankali ta fito, downstairs ta sauka taga abincin da baby ta kawo na nan yanda ta ajiyesa, ta kalli agogo ta ga har sha daya ya kusa, sama ta kalla, ta fi minti biyar tsaye kafin ta nufi kofar da take xaton kitchen ne ta shiga ta dauko cup da spoon, shayi ta hada ta koma kujera ta xauna, kasa shan shayin tayi ta ajiye cup din hannunta a hankali ta wuce sama, dakin da take tunanin nasa ne ta bude a hankali, kwance ta gan sa kan gado idonsa a rufe, ta dinga kallonsa kafin ta karasa ciki kamar mai tsoron taka tiles din ta isa har kusa da shi ta duka, Bbu wanda ya fado mata a rai lkcn sai little Sudais, lkci daya taji jikinta yyi sanyi ta dinga kallonsa ko kiftawa babu, lkci daya ya bude idanuwansa ta mike da sauri tana kalle kalle kamar mai neman abu duk ta daburce..... Aliyu ya mike xaune yana kallonta yace "Did you come to check on me?" Ta tsuke fuska tace "Saboda kai Shureim ne?" Ya shafa kansa bai ce komai ba, ta juya da sauri ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice, sai a sannan ta ja tsaki taji haushin shiga dakin da tayi, parlor ta koma ta dau shayin da ta hada, da kyar take sha don gaba daya bakinta ba dadi, ji tayi kamar xata yi xaxxabi, ta mike ta dau sauran kayan kumallon ta kai dining ta ajiye ta wuce kitchen don wanke cup din shayin ganin baxata ta iya sha ba, xata ajiye bayan ta wanke taji kamar mutum bayanta ta juya da sauri suka kusa cin karo suna hada ido ta hade rai ta dauke kai, ya mika mata hannu a hankali yace "Bani cup din" tace "Saboda xaka amsa cup sai ka tsaya bayana toh" Bata jira me xai ce ba ta ajiye cup din ta fita kitchen din ya bi ta da ido. Har aka yi azahar bata kara fitowa daga dakinta ba, xuwa lkcn ta fara jin yunwa sosai amma ta kasa sakkowa, duk xaman dakin ya isheta, tana ta xuba ido taga kiran Umma amma shiru, ga kewar Shureim da ya cikata, duk abubuwan suka taru suka mata yawa, ta hade kai da pillow tana son yin kuka amma ta kasa. Aliyu na xaune parlor yana duba wasu articles bayan sun yi waya da Sudais yace masa suna hanya, saboda su ma ya dawo parlorn ya xauna, ajiye takardar hannunsa yyi ya dau pain reliever a center table for the second time in 2hrs ya balla biyu ya dau table water dake ajiye ya sha maganin ya mayar da ruwan ya ajiye ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, ya rasa me yasa bai samu relieve ba bayan wanda ya sha daxu, har ya fara bacci a haka ya ji an danna bell, ya bude ido ya mike ya isa kofar ya bude, Baby ce rike da lunch, ganinsa tayi murmushi tace "Yayanmu Ina yini?" Ya shafa kai a hankali yace "Lafiya lau" da damuwa tace "Are you sick?" Ya d'an bude ido yace "Me kika gani?" Tace "You look so" murmushi yayi yace "Am alright" Bata ce komai ba ta shigo parlorn cike da tausayinsa ta ajiye abincin hannunta ta juyo tana kallonsa tace "Ka ma yi breakfast kuwa yaya?" Yace "Nayi mana, ya su Mumy" Xaunawa tayi tace "Suna gaishe ku" ya xauna shi ma yace "Ki kai mata abincin sama" xaro ido baby tayi tace "Uhn ba ruwana, I don't want to imagine me going to her now" Aliyu bai ce komai, tana kallonsa a hankali tace "You just have to be patient ya Aliyu, soon nasan xata hakura... Kar ka damu kaji yayana, I know it's just for few days" Murmushi yayi yace "Toh Allah ya sa" cike da tausayin sa tace "Ameen" yace "Plss ki taho da Shureim idan xa ki xo anjima...." Tace "Ae yana can gidansu" yace "Ehh ki dauko sa can din, I am lonely..." Tace "Toh Yaya xan kawo sa" Wayarsa ne yayi ring ya dauka yaga Sudais ke kiransa, yyi pick din call din Sudais yace "Muna waje" Aliyu yace "Alryt ku shigo" Baby na kallonsa bayan ya katse wayar tace "waye yaya?" Yace "Barrister with Dr Ayman I guess" Baby tayi shiru bata ce komai ba, bude kofar parlorn aka yi khaleel ya fara shigowa kafin Sudais, Aliyu ya mike bayan sun gaisa gaba daya suka xauna, Baby na kallon Dr Ayman tace "Ina yini" yace "Lafiya lau ya kike?" Tace "Alhmdllh" kallon Barrister tayi dai dai lkcn da ya kallota shi ma, yace "Ina yini" xaro ido tayi sai kuma tayi dariya tace "Ina yini" yace "Ohk I was thinking baxa ma ki gaisheni ba" Khaleel yayi murmushi yana kallonsa ta gefen ido bai dai ce komai ba, Aliyu ya kalli baby don tsoron xuwa daki gun khadijah yake yace "Baby talk to her tana daki" Mikewa baby tayi ba don tayi niyya ba ta wuce dakin gabanta na faduwa, Khadijah dake kwance ta daga kai jin an bude kofa, ganin baby ce ta mike xaune tana kallonta, a sanyaye tace "Shine daxu baki min magana ba kika wuce ko Baby" Baby tace "Hmm tsoron ki nake ai ni Iman" Baby ta xauna kusa da ita, khadijah ta kamo hannunta a hankali tace "Amma baby kin san wanda aka aura min kika boye min, idan kowa ya boye min ke bai kamata ki min haka ba, Ni yanxu shkkn cikin kunci xan kare rayuwata, nobody is after my happiness...." Hawaye cike idonta ta kare maganar, a sanyaye Baby tace "Nan gaba xa ki gane ma'anar hakan da aka yi Iman, just give my brother a chance... Iman ki manta abinda ya faru a baya, ki kwantar da hankalin ki da Yaya Aliyu you won't regret it am giving you my words...." khadijah ta dinga share hawayen dake sakko mata bata ce komai ba, tasan ita dai baxata taba kwantar da hankalin ta da wanda yyi disfiguring dinta heartlessly ba, cikin kwantar da murya Baby "Kiyi hakuri Iman, nima wllh ban san da yayanmu aka daura auren ba sai da muka tashi barin gida jiya da yamma kin dai ji na rantse maki" Har sannan khadijah bata iya ta ce komai ba sai goge idonta take, Baby tace "Ki sakko ki xo gu gaisa da su Barrister suna parlor" Kallonta khadijah tayi da sauri ta tsuke fuska tana girgixa kai tace "Am not going anywhere, they are nothing but group of deceivers..." duk yanda baby ta dinga lallabata Khadijah kin yarda ta fito tayi har da kukan ta, baby ta rasa yanda xata yi, mikewa tayi daga karshe ta dawo parlor, Aliyu na ganinta yasan kwanan xancen, Baby ta kirkiri murmushi tace "Tana fa bacci ne, Kuma bana son tada ta...." Murmushi Sudais yyi yana shafa beard dinsa a hankali yace "That's nyc, thanks for covering up for her, but we are not strangers, kuma baxa mu ji haushi ba idan kin ce tace baxata fito ba, wataran xata fito mu ganta ai" Dariya khaleel yyi yana kallon baby da ta rikice sai rawar baki take, Aliyu yyi murmushi bai dai ce komai ba, Sudais na kallonta duk da dariyar da ta basa shi ma yace "Sorry, just relax Mami ni ban yi haka don ki rikice ba" Baby bata san lkcn da ta balla masa harara ba ta juya da sauri xata wuce tana murmushi, Aliyu yace "Kawo masu drink" kitchen ta wuce ta dauko masu drink din ta ajiye, Aliyu yace "Abinci fa?" Sudais yace "Nop Alhmdllh" mikewa baby tayi ta dau abincin ta wuce sama, Dakin khadijah ta shiga tana harararta ta ajiye abincin hannunta tace "thanks for making me look stupid downstairs, Kuma abincin ma na daina kawowa sai dai ku fita eatry da mijin naki" daga haka ta wuce, tana shiga parlor tace "Yaya ni xan koma, Mumy tace kar in dade" Yace "Alryt then, da driver ku ka xo?" Ta girgixa kai yace "Toh je sama ki dau transport" Khaleel yace "Xa mu wuce yanxu sai Barrister yyi dropping dinta tunda hanyar daya" Har bakin mota Aliyu ya raka su bayan sun wuce ya dawo cikin gidan, sama ya wuce ya bude dakinsa ya shiga ya kwanta. Har aka yi la'asar khadijah na daki, duk da ta ji gidan shiru ta kasa fitowa ta dau plate ta debi abinci, Tana tunanin yanda xata fita aka bude kofar dakin Aliyu ya shigo, sau daya ya kalleta ya mayar da dubansa kan abincin da Baby ta ajiye dakin, ya isa gun abincin yace "Ain't you eating the food?" Banxa tayi masa, ya duka ya bude warmer din yana kallon abincin, dauka yayi ya juya ya nufi kofa ta bi sa da wani kallo, ganin ya fita ta tashi da sauri ta bi bayansa har ya shiga dakinsa ta shiga ya juyo yana kallonta, tace "Nace maka na ci abincin ne ni?" Kamar xata yi kuka tayi maganar, dariya ta basa, ya yi murmushi yace "You never told me" daga haka ya mika mata ta karbe abincin ta juya ta fita, yana jin ta sauka don dauko plate a kitchen ta dawo ta shiga dakinta, sai a sannan ya sauka xuwa kitchen ya hada shayi, duk da yunwan da khadijah take ji bata iya ta ci abincin me yawa ba, ta mike daga karshe ta fita, har xata kai abincin kasa sai kuma ta tsaya a hankali ta bude dakinsa ta gansa xaune yana rike da cup din shayin, ta sauke kanta kasa ta shiga dakin ta ajiye masa warmer din ta juya ta fita ya bi ta da ido. Karfe shidda saura baby ta dawo gidan tare da shureim, Sau uku tana danna bell, khadijah ta mike ta sauka bata san Aliyu ma ya fito bude mata ba, yana bude kofar Shureim ya wara ido ganinsa cike da murna yace "Unclee" nufo sa yayi da nufin rungumesa ya hango khadijah, Wara ido ya kara yi yace "Anty...." Murmushi ta sakar masa ta buda masa hannu, Har ya dau hanyar inda take sai kuma ya tsaya ya juyo yana kallon Aliyu dake kallonsu, dawowa yyi gun sa da gudu, Aliyu ya daga sa sama ya rungume sa yana murmushi yayi Pecking cheek dinsa, Lkci daya murmushin fuskar khadijah yayi fading, Baby bata san lkcn da ta fashe da dariya ba, Shureim ya xame daga jikin Aliyu ya nufi khadijah da gudu, wani kallo ta watsa masa tace "If I slap you" nan ya taka burki ya tsaya yana kallonta, Ta turo baki ta juya ta wuce sama, Murmushi kawai Aliyu yayi ya nufi yaron ya daga sa sama yace "How are you sweetheart" yace "Am fine" Baby ta ajiye abincin hannunta tace "Ina yini yayana" yace "Alhmdllh" tace "Driver na jira na waje, sai da safe" yace "Alright ki gaida mumy, tell her thank you" tayi murmushi tace "Toh yaya" daga haka ta juya ta wuce tana daga ma Shureim hannun, yana rike da Shureim suka haura sama ya shiga dakin khadijah ajiye mata shi yyi kusa da ita yace "Greet her now" a hankali Shureim yace "Anty good evening" dauke kai tayi ta hade rai tace "Evening" Daukansa Aliyu yayi suka fita dakin ta bi sa da wani kallo, har karfe kusan tara na dare khadijah bata ji motsin su ba, ta yi wanka ta shirya cikin night wear, jin shirun yyi yawa ta sa Hijab ta fita, ta fi minti biyu a tsaye, kafin ta tura kofar dakin a hankali, duhu ne dakin, ta laluba ta kunna switch, kwance taga Aliyu Shureim na kwance kusa da shi duk sun yi bacci, kashe Ac dake aiki tayi ta kashe switch din ta fita dakin ta koma nata ta kwanta. Kasa bacci tayi sai juye juye take har kusan sha biyu ta ji an bude kofa, sosai gabanta ya fadi ta kalli direction din kofar duk da wuta a kashe yake, rufe kofar yyi ba tare da ya kunna wutan ba ya iso har inda take ya duka, mirginawa tayi da sauri daga wajen tace "Meye haka?" Yace "Na xo duba ki ne kamar yanda ke ma kika xo duba mu" Xaro ido tayi tana kallonsa cikin duhun, yyi murmushi murya can kasa yace "Sweet dreams" daga haka ya fita ya kulle kofar dakin. A hankali khadijah ta koma ta kwanta, bata kara minti biyar ba bacci ya dauketa. Da asuba tana jin fitansu tare da Shureim xa su masallaci, ita ma ta mike ta shiga bayi, tana xaune kan darduma tana azkar taji shigowarsu gidan, bude kofar dakinta Aliyu yyi suka shigo tare da Shureim, kallo daya tayi masu ta dauke kai, ya xauna gefen gado Shureim ya nufe ta ya durkusa gabanta yace "Anty ina kwana?" Tana kallonsa tace "How was ur nyt?" Ya wara ido yace "It was cool Anty" Bata ce komai ba ta saci kallon Aliyu suka hada ido, d'an murmushi yayi a hankali yace "Good morning Iman" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ya mike ya nufi kofa Shureim ya bi bayansa da sauri ta bi su da ido har suka fita, ta fi minti ashirin xaune ganin gari ya fara washewa ta mike, tana sane jiya babu abinda tayi a gidan, yau kam ta sauka parlor ta share ko ina ta goge, ta shiga kitchen ma ta gyara ta goge, tana kokarin sa turaren wuta a burner aka danna bell, mikewa tayi tana kallon kofar, ta wuce sama da sauri don dauko hijab ta dawo ta bude, Baby ce tsaye da breakfast, Khadijah ta langwabar da kai tace "Don Allah daga yanxu kar ki sake kawo abinci xan yi girki muna ba Mumy wahala..." Baby ta wara ido sai kuma tayi dariya tace "Xa dai ki girka abinda xa ki ci, tunda nasan ba bama yayana xa ki yi ba, yaron ki kam nasan shi ma xa ki basa, Abbansa dai ne baxa a bai ma ba" tabe baki khadijah tayi ta bata hanya ta shigo ta ajiye abincin nan parlor tace "Da fatan kun tashi lafiya, yau naga har da su gyare gyaren gida meye sirrin Iman?" Tana murmushi da tsigar tsokana ta kare maganar, khadijah ta hade rai tace "Wani irin sirri?" yar dariya Baby tayi tace "Oho, ni dai xan wuce, a gaida min yayana" Daga haka ta nufi kofa khadijah ta bi ta da kallo har ta fita sannan ta tabe baki, ta koma ta ci gaba da abinda take, dinning ta kai breakfast din ta ajiye sannan ta wuce sama ta shiga daki, nan ma ta gyara gadonta tayi goge goge kafin ta shiga wanka, tana xaune gaban mirror bayan ta fito wanka tana shafe shafe aka bude kofar bedroom din, xaro ido tayi tana gyara towel din jikinta, ganin Shureim ne ya shigo ta sauke ajiyar xuciya, ya iso kusa da ita yace "Anty am hungry" tace "Me ya hana uncle din baka breakfast" Ya buda hannu yace "He told me I shud come to you ki bani" Tana shafa mai a kafarta tace "Shi me yake yi?" Shureim ya matso cream din xai shafa mata ta 6alla masa harara tace "Ina wasa da kai koh?" Ya mike yace "Anty taya ki xan yi" toes dinta ta mika masa tace "Toh shafa a nan" ya durkusa yana shafa mata tace "Tambayar ka nayi me uncle din yake?" Ya kalleta yace "He is lying down" shiru tayi bata ce komai ba, a hankali yace "Anty yace min he is not feeling fine" Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "What's wrong with him" Yace "I don't know" Tace "Je parlor ka jira ni in sa kaya sai in xo in baka breakfast" yace "Toh" sanann ya fita dakin, mikewa tayi ta dau atamfar da xata sa na riga da skirt, sosai dinkin yayi mata kyau tayi simple dauri na dankwali ta sa eye pencil a idonta sai chapette ah two colored lips dinta, sosai tayi kyau, ta fesa turare daga karshe ta fita dakin, har xata sauka stairs sai kuma ta tsaya, ta fi minti biyu tsaye kafin ta karasa kofar dakinsa a hankali ta bude, kwance ta gansa ya rufa da duvet har kansa, ta sauke idonta kasa ta karasa dakin kamar mai counting steps dinta, tana ta tsaye kusa da gadon tana kallonsa, a hankali ta durkusa dab da shi ta cire duvet din fuskarsa, idanuwansa a lumshe suke, ta kai hannu forehead dinsa, lkci daya ya bude idonsa tayi saurin dauke hannunta ta koma baya, kasa tashi tayi kuma bata yarda sun kara hada ido ba ta fara kame kame, kallonta kawai yake, ta dago daga karshe tana kallonsa a hankali tace "Are you sick?" Ya mike xaune yace "No.... am alright" shiru tayi tana kallonsa, ya sauka daga kan gadon ya nufi bayi ta bi sa da kallo don kana ganinsa kasan karfin hali yake yi, Mikewa tayi a hankali ta nufi kofa ta fita dakin, kwance ta ga Shureim ya kunna cartoon yana kallo parlorn yana ganin ta yyi saurin kashe tvn da remote din hannunsa, ta tsaya tana kallonsa tace "Who asked you to switch on the tv?" Shiru yyi yana kallonta, ta wuce dining ta hada masa shayi a cup ta debar masa dankali da kwai da plantain, sannan ta yankar masa bread karami ta daura gefen plate din Irish din, tace "Zo ka xauna nan Shureim" ya taso ta ja masa kujerar dinning din ya xauna ta ajiye masa abincin a gabansa sannan ta koma kitchen ta dauko wani cup din ta dawo ta hada wani shayin, ta debi Irish da kwai a plate, ta dauko wani bowl ta xuba pepper soup na kayan ciki, gaba daya ta daura su kan tray ta dauka ta wuce sama, a hankali ta tura kofar dakin nasa, xaune ta gansa gefen gado ya rike kansa, jin an bude kofa ya dago yana kallonta, kanta a kasa ta iso har kusa da shi ta ajiye tray din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta fita dakin. Dining ta koma gun Shureim ta xauna kujerar kusa da na shi ita ma ta hada shayin, a hankali take sha har ta gama, tuni Shureim ma ya gama ya mike pleadingly yace "Anty plss in kunna tv?" Kai ta gyada masa ya juya ya wuce parlor, ta kwashe duk abinda suka bata ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito, sama ta wuce ta bude bedroom din Aliyu, kwance ta gansa ya kara rufa da duvet, ta karasa tana kallon breakfast da ta ajiye masa, Bata san lkcn da ta xauna gefen gadon ta yaye duvet din tana kallonsa da damuwa tace "Baka yi breakfast din ba? What's wrong with you?" Ganin bai bude ido ba kuma bai ce komai ba ta kamo hannun sa da damuwa tace "Talk to me plss" bude ido yyi ya mike xaune, ta dauko cup din shayin da ta rufe ta bude tana mika masa tace "Gashi ka sha sai ka sha magani" karba yyi xata dauko plate na irish ya dakatar da ita "Noo I will take this first" da kyar yyi maganar, ta dago tana kallonsa ya kai shayin baki kamar wanda xai sha magani, kadan ya kurba ya cire a bakinsa, tace "Da zafi ne?" yana girgixa kai ya mika mata, ta hade rai tace "Me xan yi da shi?" Xai ajiye kasa tayi saurin cewa "Kar ka ajiye shi, u better force ur self to drink it..." Bai saurareta ba ya ajiye ya mike ya nufi bayi da sauri, a sanyaye ta mike bi sa da kallo, tana ta tsaye ita dai bata ji yana amai ba kamar ynda tayi tunani, can dai ta bi bayansa, jingina tayi da kofa tana kallonsa ganin aman yyi har ya wanke wajen, ya juyo xai fita bayin ta rikesa a hankali tace "Let me make you water sai kayi wanka" yana gyada kai yace "Finish first" daga haka ya fita, ta hada masa ruwan ta fito, kwance ta samesa ya kara rufe kansa, ta cire duvet din da damuwa tace "Kayi wankan sae mu je asibiti" da kyar ta samu ya mike xaune, tana ta kallonsa ganin har rama yyi, sauka yyi daga kan gadon ya cire jallabiyar jikinsa ta amsa ta ajiye sannan ya wuce bathroom, sai a sannan ta fita dakin a sanyaye. zaunawa tayi gefen gadonta tayi tagumi bayan kusan minti talatin ta tashi ta koma dakinsa, dai dai lkcn ya fito wanka daure da towel, tayi saurin juyawa kamar mai neman abu sai kuma ta fita dakin, turo baki tayi ta sauka downstairs ta tadda Shureim yana ta kallo ta xauna kusa da shi. Jin alamar Aliyu na sakkowa stairs ta kalli direction din, kananun kaya ne jikinsa yana rike da makullin mota ya iso parlorn, ta mike tana kallonsa tace "Where are you going to?" Bai ce komai ba, ya nufi kofa, ta isa gabansa ta hade rai tace "Nace ina xa ka?" Ya ki kallonta yace "To get drugs" kwace makullin hannunsa tayi tace "Let me do the driving" Daga haka ta nufi stairs ya bi ta da kallon gefen ido, mayafi karami ta dauko a daki ta rataya a wuya ya dinga kallonta, ganin ta nufi kofa yace "Iman!!!" juyowa tayi tana kallonsa, yana nuna mayafin kanta yace "Haka xa ki fita?" Kallon kanta tayi daga sama har kasa tana masa wani kallo tace "So?" Kallonta kawai yake bai ce komai ba, ta hade rai ta dawo ta damka masa makullinsa tace "Sai ka ja motar, ka tafi inda xaka" Komawa tayi ta xauna ya bi ta da kallo kafin ya fita parlorn, turo baki tayi jin yana warming mota ta mike ta wuce sama ta dauko Hijab dinta ta sa ta sakko parlor, kashe tv tayi tana hararan Shureim da duk hankalinsa gaba daya na kan kallo as if his life depend on it, ya mike da sauri yana kallonta yace "Anty ina xa ki je" Bata tanka sa ba ta nufi kofa ya bi bayanta, Tun daga nesa Aliyu ke kallonsu daga cikin motarsa ko kiftawa babu har suka iso ya dauke kansa, Ta hade rai tace "Ka koma daya side din" D'an murmushi yayi ba tare da ya kalleta ba ya fito ya koma daya bangaren Shureim na biye da shi a baya, yaron ya bude back seat ya shiga, shi kuma ya xauna front seat, ta shiga maxaunin driver, sabon mai gadi dake bakin gate ya bude gate din ta fita da motar, a hankali take driving din har suka hau saman titi, kamar ana tilastata tace "Wani pharmacy?" Gaya mata yyi idanuwansa a kan titi, kira'ar sheikh Sudais kadai ke tashi a motar in a very low tone, yace "Who taught you how to drive" Bata ce komai ba har suka iso pharmacy din, sai a sannan ta kallesa a takaice tace "A Good Samaritan taught me" Bai ko kalleta ba ya bude motar yayi wucewarsa, ta bi sa da wani kallo, Shureim yace "Anty, Uncle ba shi da lafiya koh" Bata ce masa komai ba, Bayan kusan minti goma Aliyu ya fito rike da ledan drugs ya shiga motar, ganin hanyar da ta dauka, yana kallonta da kyau yace "Ina xa ki je?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Xan je gida in dauko ma Shureim wears dinsa" "Noo, mu wuce gida, xan je da kaina in amso masa ba sai kin je ba" A hankali take ta tafiya da motar shi dai bai kara ce mata komai ba, can ta turo baki ta dau hanyar gida... Tana gama parking ya bude motar ya fita ya bude back seat ya fiddo Shureim suka wuce ciki ta bi su da kallo, Babu kowa parlorn da ta shigo, ta ajiye makullin hannunta ta wuce kitchen, Cup din tea ta hada ta fito ta haura sama, bude kofar dakinsa tayi ta gansa xaune yana ballar drugs shureim sai surutu yake masa, ta ajiye masa shayin gabansa ta fita, dakinta ta shiga ta kwanta, Bata san lkcn da bacci ya dauketa ba kawai taji hannu a fuskarta ta bude ido a hankali, lkci daya ta mike xaune tana komawa baya tana kallonsa tace "What?" yace "Kin yi baki downstairs" Ta d'an buda ido tace "Su wa?" Ya mike yace "Suna jiran ki" daga haka ya nufi kofa tace "Shine baxa ka turo Shureim sai ka xo kana wani taba min fuska" har ya fita bai juyo ba balle yace komai, tashi tayi ta gyara daurin dankwalinta ta bi bayansa, Tsaye tayi stairs din karshe tana kallonta ko kiftawa babu. Suka hada ido da Khaleel dake jujjuya makullin motar hannunsa, saurin sunkuyar da kanta tayi, ta karasa shigowa parlorn kanta a kasa, haka kawai taji wani mugun kunyarsa take ji, ta xauna kan kujera taki kallon Jawahir, Khaleel yace "Good afternoon khadijah" Ba ta dago ba tace "Ina yini" ya d'an yi murmushi yace "Lafiya lau, how are you" Bata ce komai ba, Jawahir tace "Ya gidan khadijah" sai a sannan khadijah ta kalleta, Jawahir ta sauke idonta a hankali, Khadijah tace "Alhmdllh" Khaleel yace "Ta ce in kawo ta ku gaisa...." Khadijah tace "Toh nagode" Jawahir tayi kasa da murya tace "Khadijah I am sorry about what transpired between us recently, kiyi hakuri ki yafe min" D'an murmushi khadijah tayi tace "Ae ya wuce" Aliyu ya dawo parlorn ya wuce Fridge ya dauko masu drinks ya ajiye, Khaleel dake ta kallonsa ganin ramar da yayi yyi yar dariya bai dai ce komai ba, Murmushi Aliyu yyi yana shafa kansa, Khaleel yace "Ina Shureim?" Aliyu ya xauna kujera yace "He slept off minutes ago" Khaleel yace "Alryt then, dama madam na kawo, I think we will be on our way now, but before then Ina son xa muyi magana da kai..." Aliyu ya mike yace "Alright" a tare suka fita parlorn, Jawahir ta dawo kusa da khadijah tace "Da gaske kin hakura khadijah?" Khadijah na wasa da xoben finger dinta tace "Sure ya wuce" Shiru Jawahir tayi a ranta tana imagining abinda su Ummanta suka ce, khadijah ta dago suka hada ido, murmushin karfin hali khadijah tayi ta sauke idonta kasa, haka suka ta xaune shiru a parlorn har Aliyu ya dawo yana kallon Jawahir yace "Yana jiran ki waje Madam" Mikewa tayi ta ma Khadijah sallama shi ma tayi masa sanann ta fita, Khadijah ta tashi tana tabe baki ta wuce sama ya bi ta da kallon gefen ido. Da daddare ta fito wanka tana shafe shafenta Aliyu ya shigo dakin, ta xaro ido tace "Noo!! you can't just come in without...." Kashe wutan dakin yayi ta xaro ido sauran maganan suka makale, yana daga inda yake a tsaye yace "Drugs da kika amsa hannun Shureim daxu, where is it?" Tace "Ka tafi xan kawo maka" a d'an fusace tayi maganan, yayi murmushi ya tako a nutse har inda take, duk da duhun dakin hakan bai hanata ganinsa ba ta dinga komawa baya a tsorace tace "Aliyu meye haka..." Xata gudu ya rikota sai jin ta tayi jikinsa, lkci daya jikinta ya dau rawa ta dinga kokarin kwace kanta amma yaki saketa, Babu abinda ke mata yawo a memory dinta sai incident din Shekaru bakwai da suka wuce, lumshe ido yyi jin yanda ko ina na jikinta ke rawa, murya can kasa yace "Ki gaya min abinda ke xuciyar ki game da ni Iman.... Tell me what u are thinking of me" Ta fashe da kuka tace "I beg you ka sake ni, you are making me...." Bai bari ta kai karshe ba ya hade bakinsu..... Bai xame ko ina da ita ba sai kan gado, ta kwace bakinta jikinta na bari tace "Nooo plss Aliyu, wllh ka bari bana so.... Kana son xuciya na ya fara min ciwo ko" Murya can kasa yace "I will cure it..." Toshe bakinta yayi jin xata fara masa ihu, Sallamar Shureim bakin kofar dakin ya sa shi saketa da sauri, da ta samu ta sauka kan gadon bata xarce ko Ina ba sai bayi ta rufe kofar jikinta na 6ari, Aliyu ya mike tsaye yana kallon kofar ya kunna wutan dakin sannan ya bude, Wayarsa Shureim ya mika masa yace "Uncle Mumy tana kiran ka tun daxu" Ya amshi wayar yace "Are you done with the game?" Girgixa masa kai yayi Aliyu ya kullo mata kofarta yana rike da hannun yaron suka koma dakinsa, Xaunawa yayi gefen gado yayi dialing number Mumy, bayan ta dauka suka gaisa tace "Ya Iman da Shureim?" Yace "Suna lafiya mumy" tace "Maa Sha Allah, Aliyu if it's okay by you gobe ku shirya don Allah ku je Zaria duba Anty khadijah, duk da ina jin nan da kwana biyu xa a sallameta, Amma ya kamata ku je can din Koh" yace "In sha Allah Mumy" Mumy tace "In ji dai ba matsala" ya lumshe ido ya bude don har sannan bai gama dawowa daidai ba yace "Babu Mumy ga Shureim ku gaisa" daga haka ya mika ma shureim waya ya mike ya shiga bathroom. kasa bacci yayi gaba daya daren ranan sai juye juye yake, a bangaren khadijah kuwa da kyar bacci ya dauketa don duk a tsorace yake duk da ta sa ma dakin makulli.... Washegari da safe karfe bakwai khadijah ta ji fitan Aliyu da mota, mikewa tayi ta fito tana mamakin inda xa shi da sassafe, ta bude kofar dakinsa ta ga Shureim kwance yana bacci, rufe kofar tayi ta koma dakinta, sai bayan da tayi wanka ta sa wata doguwar riga mara nauyi sannan ta sauka downstairs don tsaftace gidan, kafin karfe takwas da rabi ta gama komai, tana kokarin sa turaren wuta aka bude kofar parlorn, da sauri ta juya ganin sa ta dauke kai, ya karaso ya ajiye jakar hannunsa da Breakfast din su yana kallonta ta ki juyowa, bai ce mata komai ba ya wuce sama, sai a sannan ta mike ta isa gun jakar ta bude ta ga kayan shureim ne a ciki, ta rufe a hankali ta koma daki ta dau wayarta, ta fi two minutes tana kallon wayar kafin ta turo baki tayi dialing number Umma, Umma na dagawa tace "Fatan kun tashi lafiya Daughter" a hankali Khadijah tace "Umma shine baki kira ba koh?" Umma tayi murmushi tace "Toh ke ba gashi kin kira ba yanxu, ya grandson dina?" Khadijah tace "Yana lafiya" Umma tayi kasa da murya tace "Kiyi hakuri da abinda kika gani kin ji khadijah hakan kadai ne rufin asirin ki, and I am sorry for hiding that from you ban san yanda xaki dau hakan ba shi yasa..." Khadijah ta ji hawaye ya kawo idonta ta rasa abinda xata ce, Umma tace "Soon xa ki fahimce gata mu ka maki, nasan ki da taurin kai khadijah don Allah ki ajiye makaman yakin ki ki rungumi mijin ki ki manta komai, a role dina na matsayin mahaifiya a gare ki nake baki shawarar ki daina riko ba shi da amfani khadijah, wllh na tabbata son da Aliyu yake maki baxai misaltu ba da dadewa na gane haka, ke kam ba lallai ki gani ba tunda kin sa ma kanki k'in sa saboda kaddarar da ya faru tsakanin ku, Wai ma in tambaye ki... Tunda kike kin taba ganin wanda yayi ma mace fyade ya damu kamar yanda Aliyu ya damu? Ko akwai it's very rare in today's world khadijah, sure from the beginning Barrister Sudais ya xame maki wani Haske a rayuwar ki, ya haskaka maki rayuwar ki, abinda kuma baki sani ba shine, bar ma Aliyu auren ki da Barrister yayi duk cikin haskaka maki rayuwa ne coz Aliyu is the best husband for you duba da irin duniyar da muke ciki a yau, shi kadai xa ki aura ki samu kwanciyar hankali da nutsuwa ku xauna lafiya tare da d'an ku, shi yasa ya hakura ya bar masa ba don baya so ba, Kuma ya tabbata Aliyu xai daura daga inda ya tsaya, Barrister abun girmamawa da mutuntawa ne a gun ki khadijah, kinga Babu abinda bai maki ba don tabbatar da Haske a rayuwar ki, and Dr Ayman nasan shi ma har abada baxa ki mance shi ba don ya maki abinda mahaifin ki bai maki ba yana da rai, duk da nima na so kwatanta hakan amma babu dama, ban kuma san ta inda xan fara ba, don haka mutanen nan biyu babu da abinda xa ki iya biyansu sai dai kullum ki masu addu'ar gamawa da duniya lafiya, Allah ya ba ku xaman lafiya my daughter...." a sanyaye khadijah tace "Amin Ummata nagode" Umma tace "Maa sha Allah, my regards to both father and son" d'an murmushin karfin hali khadijah tayi daga haka ta katse wayar dai dai shigowar Aliyu dakin, kin kallon direction dinsa tayi, yana kallonta yace "We are going out anytime soon, ki shirya, and am hoping kin ga breakfast downstairs..." sai a sannan ta kallesa ta daure fuska tace "Xuwa ina?" Yace "Idan mun fita xa ki gani" daga haka ya juya ya fita, komawa tayi ta kwanta kan gado duk jikinta a sanyaye daga maganganun da Umma tayi mata, ta kusa minti talatin kwance Shureim ya shigo dakin da sallama, tana kallonsa har ya karaso kusa da gadon yana ta xuba kamshi, yana murmushi yace "Anty ina kwana" tace "How was ur night" yace "Alhmdllh" tace "wa ya maka wanka?" Yace "Uncle, Anty we are going out yace in kin shirya ki fito, muna jiran ki" ta hade rai tace "Kayi breakfast ne?" Yace "Eh mun yi da uncle" ta mike xaune tace "Toh ni ce baxan yi breakfast din ba xa ka wani ce kuna jirana" Tsayawa yyi yana kallonta, Aliyu ya bude kofar dakin, sanye yake da shadda milk color, lkci daya kamshinsa ya cika ko ina na dakin, yana kallonta yace "Iman, ke nake jira" Ta kallesa tace "Ku kunyi breakfast ni kuma sai in fita haka?" Ya daga kafada yace "Nobody stopped you from Breakfasting...." Tashi tayi tsaye ta nufi kofa kamar xata tashi ta bi gefensa ta fice dakin ya bi ta da kallon gefen ido kafin yayi murmushi, Shureim yace "Uncle da mun kawo mata nata daki koh?" Karasowa yayi yana murmushi ya xauna gefen gadon ya dafa kafadan yaron yace "Ko mun kawo mata cewa xata yi who sent us..." Shureim yayi dariya yace "Uncle but why is she even angry, ko bata son gidan nan ne, or she don't want you to leave with us?" Murmushi kawai Aliyu yayi yana shafa sajensa a hankali yace "I don't know also, amma ka tambayeta" ya xaro ido yana yar dariya yace "Xata doke ni ne" rungume sa Aliyu yyi a hankali yace "Not when am around darling" Suna ta xaune dakin har ta dawo, Bata yi xaton xata samesu a ciki ba, Bata rufe kofar ba tace "Can you both excuse me" Ya kalli Shureim yace "Tafi downstairs gani nan xuwa nima" fita yaron yyi a dakin, khadijah ta xaro ido tace "Cewa nayi both..." yana murmushi yace "Ni ba mijin ki bane xan yi excusing din ki?" ta daure fuska tace "Ni dai ka fita xan canxa kaya" Yace "But am not stopping you Iman" ya kalli agogon wrist dinsa yace "Kina ta bata mana lokaci kuma da nisa xa mu je" Tace "Toh ka fita, ko kuma in fasa xuwa" Yana kallonta kamar mai counting word din yace "I.. am.. going.. no where!" Wani kallo ta dinga masa, lkci daya ta nufi can karshen gado tayi kwanciyar ta ta juya masa baya, murmushi yayi ya hau saman gadon tana ganin haka tun kan ya matso kusa da ita xata tashi yyi saurin cafkota, Kamar xata yi kuka tace "Don Allah Aliyu ka bari, bana so, to nace ka fita in sa kaya ka ki fita, ya xanyi?" Sosai xuciyarta ke bugawa tana kallonsa, ya jawota jikinsa a hankali ya kai bakinsa wuyanta murya can kasa yace "Me yasa xan fita, what is it that u are hiding" turasa tayi da karfi tace "Stop it Aliyu.." Ya dago yana kallon idanuwanta yace "Really?" Jin yanda muryarsa ya canxa ta hadiye wani abu da kyar tace "Alryt, since you are not going na ji xa sa kayan haka, sake ni" a hankali ya saketa yana kallonta, sauka tayi daga kan gadon ganin inda ta nufa da gudunta ya mike da sauri ya riga ta isa kofar ya sa makulli yana kallonta, juyawa tayi kamar xata yi kuka tace "Me yasa kake min haka don Allah" ganin irin kallon da yake mata da lumsassun idonsa ta koma gun kayanta ta fiddo wanda xata sa kamar xata yi kuka, bathroom ta nufa ya bi ta, ta tsaya bakin kofar pleadingly tace "Don girman Allah ka bar ni in sa kaya Aliyu, Kai fa kace ina bata maku lokaci... " bathroom din ya shiga ya jawota xata yi ihu ya sa makulli yace "Ki sa a nan tunda kina kunyar sa wa a cikin dakin" Bata fuska tayi tace "Ni wllh bana son abinda kake min..." Ya amshi kayan ya daura kan washing machine yace "Let me help you" Bai jira cewarta ba ya jawota lkci daya ya sauke doguwar rigar jikinta idonsa ya sauka kan tabon Cs dake cikinta, tayi kara a rikice ta durkushe wajen jikinta na rawa, dagota yayi yana kallonta a sanyaye ko kiftawa babu, ta dinga nonnokewa tana cewa "Don girman Allah ka bari Aliyu, wlh kunya nake ji" a hankali ya saketa yace "Toh sa kayan ki" jikinta na bari ta dau skirt din atamfar da sauri ta sa, sanann ta dau rigar ma ta saka, ya jawota jikinsa ya ja mata zip din rigar a hankali, ta kasa kallonsa, dago kanta yayi a hankali, ta rufe idonta da sauri, yayi murmushi yyi mata light French kiss, a rude ta bude idonta ya saketa ya bude kofar ya fita bathroom din, da kyar ta fito daga karshe duk jikinta ya mutu, Kasa shafa komai tayi a fuskarta ta sa turare da hijab kawai ta sakko downstairs, yana xaune parlorn Shureim na kwance jikinsa, ta ki yarda ta dago kanta har ta iso ta tsaya daga bayan kujera, kallonta kawai yake ganin ta kasa dagowa yayi murmushi yace "Ko d'an kwalliya baxa ki yi ba" Ta turo baki tace "Baxan yi ba" ya xaunar da Shureim yace "Toh mu je in fada maki me yasa xa ki yi" da sauri ta dago tana kallonsa tace "A'a ni bana so..." Yace "Toh je ji gyara fuskar ki" juyawa tayi da sauri ta koma sama tana waigen ko ya biyota, tana shiga daki ta sa makulli, eye pencil ta sa ta goga powder a fuskarta ta sa chappete, lokaci daya tayi wani sanyayyen kyau, ta maida hijab dinta ta sauko rike da flat shoe dinta, kallonta kawai Aliyu yake ko kiftawa babu har ta shigo parlorn, ya mike yana kallon Shureim yace "Tafi daki ka dauko min makullin mota" tashi yyi ya wuce sama, Aliyu ya mike ya nufo ta, tana ganin haka tace "Wayyo don Allah ka bari, Kar ka xo kusa da ni ka ga yanxu Shureim xai...." Toshe bakinta yyi ganin ihu xata masa, yana kallon eye balls dinta yace "You... Are beautiful Iman" Tayi saurin sauke idonta gabanta na faduwa, ya xame hannunsa bakinta, Bata ankara ba sai jin kiss tayi, duk sai da ya rabata da chappete din da tasa ta kasa kwakkwaran motsi wajen, ganin faduwa xata yi yayi saurin rikota tayi regaining balance dinta, dai dai lkcn da Shureim ya bude kofa, Saketa Aliyu yyi ya fita parlorn da sauri, Shureim ya sakko yana kallon mum din tasa da tayi stiff inda take yace "Anty what are you looking at" da sauri ta dawo ta fara kame kame, sai kuma tace "Toh ka kai masa makullin mana" waje ya tafi ta karaso cikin parlor da kyar ta xauna, Tana jin ya gama warming mota don ma kar ya biyota ta mike ta fito da sauri, har lkcn xuciyarta bugawa yake, Sosai ta ji dadin ganin Shureim xaune a gaba, ta bude back seat xata shiga Aliyu ya kalli Shureim yace "Kai koma baya sweetheart sai Anty ta xauna gaba" hade rai khadijah tayi tana kallonsa, Shureim ya fito ya dawo baya, Tana masa wani kallo tace "Nima a bayan xan xauna" juyowa Aliyu yyi ya kafeta da idanuwansa, sauke nata tayi da sauri, ta rufe motar ta xaga ta shiga gaba kamar xata yi kuka, har suka fita gidan bata yarda ta kallesa ba, sai bayan da suka hau titi yace "Zaria xa mu je" ba tare da ta kallesa ba tace "To do what?" Yace "Xa mu je gaida Anty khadijah, daga can sai mu biya family house din su iklima tana can" Lkci daya jikin khadijah yayi sanyi sosai, a hankali Aliyu yace "But idan baxa ki shiga ba sai ki tsaya a mota mu shiga ciki da Shureim" Ta girgixa kai tace "A'a xan shiga" almost half of the journey surutun Shureim kadai ne ke tashi a motar, daga karshe khadijah da abun ya isheta ta juya tana masa mugun kallo tace "You keep ur mouth shut.... ka dame ni" Aliyu ya bude ido sosai yace "Ni fa yake ba labari ba ke ba malama" Hararansa tayi tace "Ehh nace ya ishi kunne na, ya dakatar da labarinsa haka" Murmushi Aliyu yayi a hankali yace "Toh Anty..." Ganin sun kusa Zaria a hankali Khadijah tace "Toh baxa mu kai mata komai ba?" Aliyu ya d'an kalleta ya mayar da hankalinsa kan titi sannan yace "Like what?" Tace "Kamar fruits da dai abubuwan da marasa lafiya suke so" Murmushi yayi, bayan sun shiga Zaria yayi parking gun wasu masu siyar da kayan marmari, ya siya mai yawa, ya sa bayan mota ya dawo side din khadijah yace "I think fruits din ma sun isa" Khadijah tace "Toh iklima fah?" Yace "We will get her something idan mun fito" Bata ce komai ba ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya ci gaba da driving. karfe sha daya saura suka isa asbitin da Anty khadijah take a Zaria, Aliyu na gama parking gaban khadijah ya dinga faduwa, ga mugun fargabar da ya ziyarce ta, Aliyu na lura da ita bayan sun fito ya dawo gefenta a hankali yace "You need not to be afraid of anything Iman, relax ur mind, or you stay behind, baxa mu dade ba xamu fito" Ta girgixa kai tace "A'a xan shiga" daga haka ta bude bayan motar ta fiddo fruits din shi kuma yana rike da hannun Shureim suka shiga babban asibitin, har ward din da Anty khadijah take suka tafi, Aliyu ya bude kofar a hankali hade da sallama, shi ya fara shiga tare da Shureim sanann khadijah dake makale a bayansa, ta dade bata yi fargaba irin na lokacin ba, Baby ce xaune ward din tana xuba mata abinci, daga one side kuma Barrister Sudais ne yana xaune saman kujera rike da makullin mota, da alamar dai lokacin suka xo su ma, Aliyu ya dinga kallon Anty khadijah dake kan gado.... ✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨ Mikewa Sudais yyi yana murmushi ganin su, Aliyu ya karasa gun sa shi ma murmushin dauke fuskarsa ya basa hannu suka gaisa, Sudais ya duka yana kallon Shureim yace "How are you son?" Shureim ya washe masa hakora yace "Fine Uncle" Khadijah dai har sannan bata dago kanta ba gabanta sai faduwa yake, Sudais ya dago yana kallonta yace "Good morning Amira" sai a sannan ta kallesa tayi murmushi a sanyaye tace "Ina kwana Barrister" yace "Lafiya lau, ya gida" a hankali tace "Alhmdllh" a karo na farko ta kalli direction din da Anty khadijah ke kwance, ita ma kallonsu kawai take, duk tayi baki ga ciki 6aro 6aro ya fito, khadijah bata ganeta da farko ba ta dinga kallonta babu kiftawa, gaba daya Anty khadijah ta canxa kamar ba Anty khadijahr da ta sani yar gayu fara ba, Aliyu ya karasa har kusa da ita yana kallonta a hankali yace "Sannu Anty, ya jikin?" Maimakon ta basa amsa sai ta fashe da matsanancin kuka ta dafe kanta, ya duka kusa da ita cikin sanyin murya yace "Haba Anty, kuka kuma? There is no need for that, in sha Allah xa ki samu lafiya soon, kiyi hakuri...." Shi dai Sudais kallonta kawai yake daga inda yake a tsaye, a xuciyarsa kuwa tunani yake anya ma da gaske kanwar mahaifiyar Aliyu ce ba kawai kara ake yi ba, shi bai ma wani ga resemblance ba, Khadijah ta sunkuyar da kanta hawayen da ya taru idonta ganin condition din Anty khadijah suka xubo mata, Anty khadijah na girgixa kai cikin kuka tace "Kaico na... kaico... don Allah ku rufa min asiri ku yafe min Aliyu, ku yafe min ko xan samu saukin abinda nake ji kullum, ku yafe min kar in....." Katse ta yayi da sauri yace "Anty ni baki min komai ba na sha gaya maki, idan ma kinyi wllh na yafe maki duniya da lahira Allah ya yafe mana baki daya, don Allah ki daina cewa haka, Allah xai baki lafiya albarkacin annabi Muhammad S.A.W" kuka take yi sosai tace "Aliyu nasan idan ka san gafarar da nake nema gun ka baxa ka yafe min ba, ba lallai ka yafe min ba coz i don't deserve it, ni din muguwa ce, na cuce ku, na ci amanar yayata, wllh sharrin shaidan ne ba yin kai na bane, ga sakayya tun a duniya Allah ya maku, ashe dama mugunta na komawa mai shi....." mikewa Aliyu yyi bai sake ce mata komai ba don ji yayi har xuciyarsa ya karaya, Ashe tana sane mugunta take yi dama, cikin magiya da kuka tace "Aliyu don girman Allah, don xumuncin dake tsakanina da mahaifiyar ka ka yafe min abinda nayi maku da khadijah...." Aliyu na kallonta ya dake duk da yasan sauran xancen yace "Me kika yi mana ni da ita Anty?" Tana shessheka, fuskarta caba caba da hawaye tace "Wllh ni ce nayi asiri na xuba lipton din da baiwar Allahn nan ta kai maka ranan ka sha, Kuma na kwashi yaran duk muka bar gidan, na bar ku daga kai sai ita, ni ce silar abinda ya faru tsakanin ku, ni ce sillar lalata ta da kayi" shi dai Aliyu bai ce komai ba, sai dai har wani tafarfasa xuciyarsa yake duk da ya riga ya gama jin ranan da take waya, khadijah da Sudais dai ta bari cikin shock din xancenta, Baby ta mike ta kama hannun Shureim dake ta kallon Anty khadijah ta fice daga ward din, Anty khadijah ta kara rushewa da kuka tace "Wllh sharrin shaidan ne la'ananne, shi ya sa min tsanar ta khadijah, shi ya asasa min k'in ta a xuciya, don duk xamanta gidan bata taba min komai da ya wuce biyayya da girmamawa, abinda yasa na aikata abinda nayi ina tsoron kar wataran ka ce kana sonta da aure don naga yanda kake tausayinta kuma kake damuwa kan lamarinta, gashi naga yanda Mumy ma ke sonta, shi yasa nayi duk haka... ban mance ranan da suka dawo bayan ta bar gidan da wancan bawan Allahn ba wai tana dauke da cikin ka na ki saurarensu nace su tafi kuma suka tafi, toh yanxu wa gari ya waya, ka lalata mata rayuwa ta tafi ta fuskaci kalubale iri iri wanda da alama hakan alkhairi ya xame mata, sai gashi dai bayan shekaru da dama kai din dai ka aureta, Ni kuma ga yanda nawa rayuwar ta kasance, ga 'ya ta can rai a hannun Allah, yanxu ina ji ina gani nima xan girbe abinda na shuka" ko kadan Sudais bai ji tausayinta ba sai ma kawai ji da yayi ya tsaneta, dama akwai mutane irin haka a rayuwa, the wickedness is just too harsh, khadijah dai na tsaye tamkar wanda aka dasa a gun, gaba daya jin xancen Anty khadijah ta dinga yi kamar a mafarki, lkci daya ranan da ta je kai ma Aliyu Lipton a daki ya fado mata, irin yanda ya dinga cewa ta tafi da yanayinsa a lokacin ya dawo mata fresh a memory dinta, bata manta ba har saloon yace ta tafi sanusi ya kai ta amma saboda tausayin halin da ta gansa ta ki tafiya, ashe duk asiri ne dama, sai a sannan ta fashe da kuka sosai ta juya ta fice daga ward din, Anty khadijah ta dinga kuka tace "Aliyu nasan ita ba lallai ta yafe min ba idan kai ka yafe min... Nasan da wuya don na xalunce ta da yawa" Aliyu bai iya yace komai ba, Sudais ya fita ward din, bin bayan khadijah yayi ya sameta can waje tana aikin rusa kuka, Baby ma na nesa da ita amma bata samu courage din xuwa inda take ba, Sudais na kallonta a hankali yace "Amira" juyowa tayi tana kallonsa hawaye wasu na bin wasu, yace "Kiyi hakuri, duk abubuwan da take fada anyi su an wuce ya kuma xama passed tense, this is ur new life... Don't allow ur past to spoil ur happiness, kin dai ji da kunnen ki kuma kin tabbatar ba yin kan Aliyu bane, ba laifinsa bane, ba halinsa bane, babu wanda ya tambayeta kuma babu wanda ya matsi bakinta amma sanin cewar hakkin ku ke bibiyar ta shi yasa ta fallasa kanta, don haka just forgive her and life moves on, gashi ita ma ai tana reaping shukar da tayi, yanda kika haifi yara out of wedlock ita ma gashi haka xata haifa, gwara ke naki yaran masu gata ne, ita fa, kilan ba lallai tasan uban cikin ba, sannan ga karaya har kafa biyu, da wuya kuma kafufuwanta su dawo dai dai ba fatan hakan na mata ba, shi yasa idan mutum xai gina ramin mugunta yasan size din da xai gina, let bygone be bygone Amira, ki koma yanxu kice ke kin yafe mata, sai ki ga ta dalilin hakan kila ta samu wani saukin... " Kai kawai khadijah ke gyada masa hawaye na sakko mata duk jikinta yyi sanyi, yace "Mu je" ba musu ta bi bayansa har suka koma ward din, amma ta kasa karasawa gadon tana daga inda take a tsaye cikin rawar murya tace "Anty ni na yafe maki, Allah ya baki lafiya ya kuma yafe mana gaba daya" kallonta kawai Anty khadijah take hawaye na sakko mata, sai a sannan wani tausayinta ya rufe khadijah, ita ma hawayen ya dinga sakko mata, ta isa har bakin gadon ta kamo hannunta cikin rawar murya tace "Na yafe maki, kema ki yafe min for making you go the wrong way, don nasan da ban je gidan ba baxa ki jefa kanki a halaka ba, Allah ya baki lafiya ya tashi kafadun ki Anty" cikin rawar murya Anty khadijah tace "Amin Nagode, Allah ya baku xaman lafiya da xuri'a dayyaba, ya kauda duk wata fitina tsakaninku, I wish Allah xai bar min rai na inyi witnessing din haka, amma ina jin kamar mutuwa xan yi, Alhmdllh naji dadi da na sauke wannan nauyin a kai na don kullum da shi nake kwana nake tashi, ban san ta ina xan fara ba, Allah ya yafe mana baki daya kuma ya shiryi masu xuciya irin tawa" Khadijah ta kasa amsa mata sai kuka kawai take, Aliyu yace "Ameen, baxa ki mutu ba sai lokacin ki yayi Anty" Ita dai bata ce komai ba sai kukan takaici da danasani da take yi, ganin kukan da khadijah take, Anty khadijah tace "Ku tafi Aliyu kar in bata maku mood, Allah maku albarka, ya kuma kaddara saduwar mu" Yace "Ameen mun gode, xan dawo nan da kwana biyu" tace "Allah ya kai mu nagode" Gun Barrister ya nufa yana kallonsa yace "xa mu koma Barrister, Allah ya bada lada" Barrister yyi murmushi yace "Ameen, Allah kai ku gida lafiya" Dawowa yyi ya kama hannun khadijah da kamar daman jiran hanyar kuka take suka fita dakin bayan ta daga ma Barrister dake murmushi hannu. Baby bata iya tace masu komai ba duk jikinta yyi sanyi, Aliyu ya kama hannun Shureim dake ta kallon uwarsa da damuwa ganin kuka take yi, ya bude back seat ya sa shi a ciki, ya bude mata front seat, shiga tayi tana goge hawayen dake xubo mata, ya rufe motar yana kallon baby, a sanyaye tace "Allah ya tsare hanya yayanmu" yace "Ameen, tare ku ka xo da Barrister?" D'an murmushi tayi bata ce komai ba, yayi dariya yace "Nasan rakiya kawai yayi koh?" Dariya tayi bata ce komai ba, yana murmushi ya xaga ya shiga driver seat ya ja motar suka fita asibitin, Shureim na kallonsa kamar xai yi kuka yace "Uncle why is Anty crying?" Aliyu ya kalleta yayi murmushi yace "Allura aka mata" Shureim ya fashe da kuka yace "Me yasa uncle" parking Aliyu yyi ganin kukan da yaron yake, yana kallon khadijah yace "Kinga dama idan ba neman hanyar kuka kike ba toh ya ishe ki haka Iman" ta balla masa wani Harara tace "Toh ina ruwanka, hanyan nake nema dama" murmushi yayi, ya kwantar da murya yace.... ✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨ Ya kwantar da murya a hankali yace "Haba my Ummu Shureim..." turo baki tayi ta dauke kai tana goge idonta, ya juya yana kallon shureim, murmushi yayi yace "Toh kaga tayi shiru kai ma kayi shiru" Kai ya gyada masa yana kallon mum dinsa, ya dawo kusa da ita a hankali yace "Anty kiyi hakuri" kallonsa tayi, tayi d'an murmushi tace "Toh na yi" komawa yayi ya xauna, Aliyu ya tada motar ya ci gaba da driving, murya can kasa yace "Mu bari next time sai mu je duba iklima, coz i really don't have the energy to start consoling you again" tace "Ni ka kai ni yanxu, ba wani next time, I will be going back to schl soon" murmushi yayi yace "Ohk then" hanyar family house din su iklima Aliyu ya dauka, bayan minti kusan sha biyar suka isa babban gidan, yayi parking a waje suka shiga, yan gidan basu wani tarbe su ba, hakan bai wani dame Aliyu ba, ita dai khadijah jikinta yayi sanyi, autar su mahaifin Iklima ta nuna masu wani kofa tace "Tana can" Aliyu ya mike yana kallon khadijah ita ma ta mike, Shureim xai tashi ya duka ya dafa shoulder dinsa a hankali yace "You wait for us here sweetheart ka ji?" Kai Shureim ya gyada masa ya koma ya xauna, Aliyu ya nufi kofar dakin khadijah ta bi bayansa gabanta na faduwa, ita kadai ce kwance dakin mai dauke da yar katifa ko leda babu, katifar ma babu xanin gado, da ganin dakin babu me shiga ciki, Ga cup da plate da spoon dinta nan gefen gadon, da kadan iklima ta fi skeleton kwance a kan gadon, khadijah ta kasa karasawa cikin dakin tana iya kokarin ganin bata fashe da kuka ba ta toshe bakinta, Aliyu ya karasa ciki yana kallonta shi ma a sanyaye, Durkusawa yayi kusa da ita a hankali yace "Sannu iklima" maimakon ta amsa masa sai hawaye, duk jikinsa yayi sanyi ya kasa cewa komai lkci daya shi ma idonsa ya kada, khadijah ta fashe da kuka sosai ta juya ta fice daga dakin, Da kyar Iklima ta iya bude baki tace "Kace ta yafe min don Allah" Ya sauke idanuwansa kasa a hankali yace "Kina shan magani iklima?" Girgixa masa kai tayi hawaye na xuba idonta, ya fi minti biyu durkushe gabanta bai iya yace komai ba, can ya dago da kyar yace "Wa ke kula da ke?" Nan ma ta girgixa masa kai, cikin sanyi yace "Yaushe rabon ku je asibiti?" Kallonsa kawai take alamar maganar ma baxata iya ba, mikewa yayi a hankali ya fita dakin, ya kalli khadijah da ta hade kai da kujera tana kuka Shureim na kusa da ita shi ma yana kukan yana kallonta, Babu wanda yace masu komai, kowa na harkan gabansa a babban gidan, gun yayar mahaifin iklima da ya sani ya nufa a waje, tana xaune su kusan uku suna hira, ya d'an duka ya gaishe ta, ta amsa tana tambayarsa yaushe ya xo, yace "Ba mu jima ba, mama nace iklima na xuwa asibiti kuwa?" Matar tace "An kwan biyu ba aje ba tunda uban nata bai turo kudi ba kilan ya gaji shi ma, mu kuma ya bar mu da wahala" Shiru Aliyu yayi yana kallonta, can ya mike yace "Toh bari mu je yanxu" tace "Kar ma ka bata lokacin ka ko tashi bata iya yi, idan ba likitan xaka je ka gayyato a asibiti ba" Bai ce komai ba ya koma parlorn sannan ya shiga dakin da iklima take, Kallonta kawai yake yana kokarin gano stage din da cutar nata yake, bayan wani lokaci ya juya ya fita, gun khadijah ya nufa yace "Tashi mu je" Ta mike da kyar har lokacin kuka kawai take, Aliyu ya dau shureim ya rungumesa suka fita, bank ya fara tsayawa, ya kalli khadijah kafin ya bude motar ya fita xuwa gun automated teller machine, ba a dau lkci ba ya dawo ya shiga motar, wani babban pharmacy dake area din ya tafi, yana kallon khadijah da taki daina kuka yayi kasa da murya yace "Am begging you ki daina kukan nan Iman, baki kyauta ma yaron nan, even for his sake kiyi hakuri ki daina kukan" Juyawa tayi tana kallon Shureim da ke kuka bakin rai shi ma, hadiye kukanta tayi xuciyarta na mata xafi, Aliyu ya bude motar ya fita, bayan kusan minti goma ya dawo rike da ledan magani masu yawa da tsada, murmushi yayi ganin yanda Shureim yayi shiru yana kallon khadijah dake ta kukan xuci, Bata taba tunanin ganin Iklima a yanda ta ganta ba, ta ji duniyar ba bakin komai yake ba, wani store Aliyu yayi parking ya fita ya siya cartons of malts da Madara masu yawa, sai locozade boost, a booth aka xuba abubuwan da ya siya, ya shiga motar ya kalli khadijah da ta jinginar da kanta jikin kujera ta fada duniyar tunani, kamo hannunta yayi ta juya a hankali tana kallonsa, murmushi ya sakar mata yace "Kowa da irin kaddararsa, su irin tasu kenan, so you just have to pray for them, Allah ya sa mu cika da imani" wasu sabbin hawayen suka sakko idonta, ya tada motar suka bar wajen, shi kadai ya shiga dakin iklima ya ajiye magungunan gefenta yaran gidan suka dinga shigowa da abubuwan da ya siyo, Yana kallon iklima ya fiddo magungunan gaba daya ya shiga nuna mata yanda xata sha, kallonsa kawai take bata ce komai ba, bayan ya nuna mata yace "Idan kin ji kina jin yunwa sai ki daure ki tashi ki sha malt ko madara, idan lokacin shan maganin ki yayi ba a baki abinci ba sai ki sha malt ki sha drugs din kin ji?" a hankali ta gyada masa kai, ya fiddo dubu talatin a aljihunsa ya daga gefen katifar ya ajiye mata yace "Ki dinga aika yaran gidan su siyo maki fruits sai ki basu ko dari biyu don su dinga xuwa kin ji?" Nan ma ta gyada masa kai, ya d'an yi murmushi yace "Allah ya sauwake lil sis, idan kina son ki samu lafiya sai kin yi ta shan drugs din ki" Nan ma dai ta gyada masa kai, yace "Xan dinga xuwa duba ki always, idan kika fara samun sauki xan kai ki gun Mumy dama Abbanki ne yace a kawo ki nan" kallonsa kawai take, jikinsa yayi sanyi ganin hawayen dake sauka idonta, da kyar yace "I will be back soon" daga haka ya mike ya fita dakin ta bi sa da ido, Har suka shigo kaduna, Daga khadijah har Aliyu duk jikinsu a sanyaye yake, tuni Shureim yayi bacci bayan motar, Aliyu na gama parking ya juya yana kallon khadijah da ta bude motar ta fita, fitowa yayi shi ma ya bude back seat ya fiddo Shureim, ya rufe motar ya bi bayanta, bedroom dinsa ya shigar da Shureim ya kwantar da shi, ya fita ya shiga dakin khadijah, kwance ya sameta tayi lamo jikin pillow, ya xauna gefenta yana kallonta, ita dai bata yarda ta kallesa ba, kamo fingers dinta yayi yace "You need not to worry this much Iman, kin san condition din ki fa" Bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ya dagota ya rungume ta, ta kwantar da kanta kirjinsa tana shesshekar kuka, murya can kasa yace "Kiyi addu'ar Allah ya basu lafiya Iman" Sun fi minti biyar a haka, Ya dago kanta a hankali yana kallonta, rufe idonta tayi, yyi murmushi yana kallon cute lips dinta, kamar tasan me yake yi ta kwace kanta ta mike ta koma can karshen gado ta kwanta, shafa kansa yyi yace "Ki tashi kiyi sllh" daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita, throughout ranan haka khadijah ta kasa samun natsuwa, Aliyu yayi lallashin har ya gaji, duk ta 6ata mood din little Shureim ma, Bayan magrib ya dawo masallaci ya shiga bedroom dinsa dai dai lkcn da wayarsa ya katse, karasawa yayi ya dauka yaga Mumy ce ta kirasa, ya xauna gefen gado ya shiga kiranta, tana dagawa yayi mata sallama, jin yanayin muryarta a hankali yace "Mumy baki da lafiya ne?" Mikewa yayi yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" lkci daya ya ajiye wayar ya koma ya xauna ya rike kansa, bai san lkcn da hawaye ya dinga xuba idonsa ba, ya fi minti biyar a haka kafin ya mike da kyar ya share idonsa ya dau makullin motarsa ya fita daki, yana ta tsaye corridor kafin ya bude dakin khadijah xaune ya ganta kan darduma ta jinginar da kanta da gado, Shureim na xaune kusa da ita, kasa karasawa cikin dakin yayi yana daga bakin kofar yace "Iman xa mu je can gida yanxu" ta kallesa kafin tace komai har ya juya ya wuce, a tunaninta gaida Mumyn xa su je su yi, ta mike ta linke pray mat din ta ajiye, ta kama hannun Shureim suka fita bayan ta kashe wutan dakin, ganin yanayin Aliyu ta kallesa da damuwa tace "Ko dai wani abu ya faru ne?" Yana driving idonsa kan titi yace "Nothing" har suka isa gida bata sake cewa komai ba, yayi parking ya fito ita ma ta fito tana rike da shureim suka bi bayansa, sosai gabanta ya fadi ganin mutane a parlorn, Aliyu ya isa gun Mumy ya durkusa gabanta, khadijah ta kasa karasawa xuciyarta na bugawa, upstairs ta wuce xuwa dakin baby da sauri, baby na ganinta ta fashe da kuka sosai, cike da karfin hali khadijah ta durkusa gabanta tace "Me ya faru baby" Baby tace "Iklima..." Hawaye ya shiga sakko ma khadijah ta hade kanta da gado tana salati a ranta. Daren ranan a gidan suka kwana gaba daya, mutuwar Iklima ya girgixa kowa barin khadijah da Baby, da ta tuna yanayin da suka sameta daxu da rana sai taji hawaye ya ki tsaya mata ashe mutuwa xata yi, gashi ko magana bata samu ta mata ba saboda tashin hankali, babu wanda ya wani rintsa a gidan har asuba. Washegari da safe Umma suka xo gidan da Nanny don yi ma Mumy gaisuwa, da Umma ta tashi tafiya Shureim yace xai bi ta, haka Umma ta wuce da shi don har da kukan sa, sai bayan da aka yi sadakan uku Khadijah da Aliyu suka koma gida da daddare, har sannan shock din bai bar ta ba, har ranta taji ta yafe ma Iklima don ita a iya tunanin ta ma bata mata komai, ajiye abincin da Mumy ta basu su tafi da shi tayi a nan tsakiyar parlor ta wuce sama Aliyu da ya bi ta da kallo yace "Iman" juyowa tayi tana kallonsa, yace "Baxa ki ci abincin ba" ta girgixa masa kai, yace "Ba fa ki ci komai tun daxu ba" Bata ce komai ba ta haura sama, kitchen ya shiga ya dau plate ya wanke sannan ya dawo parlorn ya bude abincin ya dibar mata ya rufe sauran ya wuce sama, kayanta ya sameta tana cirewa, tana ganinsa ta durkushe kasa da sauri kamar xata yi kuka tace "Baka iya sallama ba ne" d'an murmushi yayi ya sauke idonsa daga kallonta yace "Yi hakuri" ta turo baki tace "Ka ajiye ka tafi" Ajiye mata abincin yayi ba tare da ya kalleta ba ya juya ya fita, zani ta dauka ta daura ta xauna kusa da shinkafa da miyar da ya ajiye mata ta dau spoon din ta fara ci a hankali, Bata wani ci da yawa ba don har sannan bata da appetite ta mike ta shiga bathroom, sai da ta wanke bakinta sannan tayi wanka ta fito, Hijab ta sa ta dau sauran abincin da ta rage ta fita da shi ta dawo dakin, ta dau lkci xaune gaban madubi tana shafe shafenta ya bude kofar, xaro ido tayi ta duka, ya koma da sauri yace "Ohh sorry, Assalamu alaikum..." Tayi saurin daukan hijab dinta ta sa ganin har ya sake shigowa ta hade rai tace "Bana son haka Aliyu, ba sai an amsa ake shigowa ba" dariya ta basa sai dai bai yi ba, ya mika mata wayar hannunsa yana kallonta yace "Gashi Dr Ayman xai maki gaisuwa" ta hararesa ta karba wayar tace "Toh ni ka fita" juyawa yayi ya fita dakin, ta kai wayar kunne, muryar Khaleel taji yace "Uhm lallai, ya fita koh?" Murmushi tayi murya can kasa tace "Ina yini Doctor" yace "Lafiya lau khadijah, ya gida?" Tace "Alhmdllh, ya jawahir" yace "She's fyn, ya karin hakuri?" A sanyaye tace "Mun gode Allah" yace "Allah ya mata rahama" tace "Ameen mun gode" yace "Maa sha Allah, good nyt" tace "Alryt, my regards to jawahir" yace "In sha Allah" daga haka ya katse wayar, ta ajiye gaban madubin ta mike ta cire hijab dinta ta dau kayan baccin da ta fiddo ta saka, ta linke Hijab dinta ta ajiye sannan ta kashe wutan dakin ta kwanta, har bacci ya fara daukanta taji an bude kofar dakin ta bude ido da sauri, tana ji ya rufe kofar, Bai kunna wutan ba yana tsaye daga inda yake a hankali yace "Iman, wayana fa?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya fi minti daya tsaye kafin ya juya ya fita a hankali ya rufo mata kofar, sai a sannan ta mike xaune, tana ta xaune kan gadon kafin ta sauko ta tafi gun mirror ta dau wayarsa ta saka hijab ta fita, a hankali ta bude kofar dakinsa ta shiga. Ta fi 10 seconds a tsaye ganin babu haske a dakin, bata kunna wutan ba saboda akwai d'an hasken na corridor kuma a bude ta bar door din, ta nufi gaban mirror a hankali don ajiye wayar hannunta, lkci daya ta juya jin an rufe kofar dakin duhu ya gauraye ko ina, saurin ajiye wayar tayi ta nufi kofar tana cewa "Why is that...." Xaro ido tayi ganin kamar nufota yake yi ta dinga komawa baya kamar xata yi kuka tace "Meye haka Aliyu, ka bude min kofa in fita, I only brought you ur mobile phone" murya can kasa yace "Why did you pretend you were sleeping" jingina tayi da banga xuciyarta na bugawa ta marairaice tace "Laifi ne don na kawo maka wayarka? to ka bani in mayar I thought you need it ne dama" Yana d'an murmushi yace "Better... dauka ki mayar" tace "Toh ka matsa" a hankali ya koma gefe idonsa a kanta, ta taho xata wuce gabanta na faduwa kawai ta ji ya fixgota xuwa jikinsa ya rungumeta gam, jikinta ya dau bari tace "Wayyo na shiga uku, meye..." Bai bata damar karashe abinda xata ce ba ta xaro ido tana kallon kwayar idonsa, passionately yake kissing dinta, tun tana kokarin kwace kanta har tayi give up, lkci daya jikinta ya mutu gaba daya ta ji ta kasa tsayuwa, bata ankara ba bayan lokaci me tsawo sai ganin su ta tayi saman gado, jikinta ya dau rawa a tsorace tana girgixa masa kai hawaye na sakko mata tace "Noo Aliyu, I still haven't forget the experience, it's always fresh, don Allah kayi hakuri, and...." kasa ci gaba tayi tana kuka a hankali, Aliyu da lokaci daya ya bar abinda yake jikinsa yayi sanyi, ya kai bakinsa kunnenta cikin sanyin murya yace "And... what?" Cikin shessheka tace "You didn't follow the teachings of our prophet" komawa yayi a hankali ya kwanta ya lumshe ido yana maida numfashi, ta rufe kanta duvet har sannan hawaye ya ki tsaya mata gabanta na faduwa, a tunaninta yayi bacci don an dau lkci me tsawo bai motsa daga yanda yake kwance ba, a hankali ta mike ta maids wears dinta, xata fita ya mike ya jawota ya rungume cikin sanyin murya yace "I am... sorry Iman" ita dai bata ce komai ba, ita dai bata ce komai ba tayi lamo jikinsa, yana jin yanda xuciyarta ke bugawa, bayan wani lkci ganin ta nutsu ya kwantar da ita a hankali ya sauka daga kan gadon ya shiga bathroom, har bacci ya dauketa bai fito ba. Da asuba ta ji ana shafa fuskarta a hankali ta bude ido, murmushi ya sakar mata yana kallonta yace "It's time for prayer" Rufe ido tayi da sauri don ya kunna fitilan dakin, yana murmushi yace "In kashe wutan?" Cikin sanyin murya tace "Yes plss" mikewa yayi ya kashe, sai a sannan ta mike xaune a hankali, ya dinga kallonta cikin duhun, Bata yarda ta tashi kan gadon ba ta kallesa tace "Toh baxa ka je masallaci ba?" Yace "We just finished now" Turo baki tayi ta mike tace "Toh ni ba nan xan yi alwalan ba" yace "Saboda me?" Bata ce komai ba ta nufi kofa, ya mike da sauri ya rufe yace "Cinye ki xan yi a nan din?" Kamar xata yi kuka tace "Ka bude min plss" yace "Sai kin yi a nan" tace "Baxan yi ba" yace "Why?" Tace "I have my reasons, kuma ba dole bane ai" murmushi yayi yace "Baki son in ga kin yi wanka?" Xaro ido tayi tace "Kamar ya?" Yace "kamar yanda nayi jiya" ta hade rai tace "Ka bude min Aliyu" yace "Toh tafi bathroom kiyi wankan ki a can" ya fadi hakan yana nuna mata bayin sa, a fusace tace "Ce maka nayi wanka xan yi, a kan wani dalili xan yi wanka" Murmushi yayi ya koma kan gado ya kwanta yana kallo ta cikin duhun, ta fi minti goma tsaye tana masa magiya amma ya ki budewa, ta fashe da kuka daga karshe ta durkushe wajen, ya mike yana dariya ya bude kofar yace "Toh tafi kiyi wankan ki" sai da ta fita tace "Ba wanka xan yi ba sai dai swim" daga haka ta shige dakinta ta rufe tasa makulli, turo baki tayi ta shiga bathroom dinta tayi wanka ta dauro alwala ta fito. Tana ta xaune kan darduma har gari ya waye ta mike a hankali ta shiga gyara dakinta ta wanke har bathroom sannan ta fito parlor don gyaran gidan, sai kusan karfe takwas da rabi ta gama ta shiga kitchen, Irish ta deba tana fere wa, Jin kamshin da ya ziyarci kitchen din ta juya a hankali tana kallon bakin kofa, tsaye ta gansa ya jingina da kofar ya rungume hannunsa yana kallonta, sauke idonta tayi ta ci gaba da abinda take, ya karasa cikin kitchen din ya tsaya bayanta, murya can kasa yace "Good morning Iman" kasa cewa komai tayi, kuma bata juyo ba ta ci gaba da peeling din Irish da take, har ta gama yana tsaye bayanta, a hankali ta juyo suka hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, jawota jikinsa yayi yana kallonta cikin sanyi yace "Forgive me once more for what happened seven years back Iman, I made you a mother with kids out of wedlock at a very tender age, I know this will always remain in ur memory till the end, nasan kuma da kin gan ni sai kin tuna da hakan, kamar yanda nima in dai na ganki I do felt guilt deep inside me, I want us to get rid of that Iman, I want to have peace with you as my wife, nasan baxan iya biyan ki irin wahalan da kika yi ta dalilina ba, but forget the past plss let build our new home Iman, i promise to love you till the end, I promise to be by ur side till the end, nayi alkawarin xame maki haske a rayuwar ki till the end, I never bargained for this Iman, Allah ya gani na so haskaka maki rayuwar ki xuwan ki gidanmu, na so maki duk abinda xan yi da baxa ki yi maraicin iyayen ki ba, sai dai muna namu Allah kuma na nasa, kaddara kuma ta riga fata, kuma a matsayin mu na musulmai we have to accept it either good or otherwise, all we have to say now is Alhamdulillah" Bata iya ta dago ba hawaye ya dinga xuba idonta, a hankali ta xame kanta daga jikinsa ta juya masa baya trying her best bata fashe da kuka ba, Juyawa yayi a sanyaye ya fita kitchen din, Bata da wani kuxari ta karasa duk abinda take ta juye ruwan shayi a flask sannan ta fita da breakfast din gaba daya dining ta ajiye, kwance ta gansa kan 3 seater idonsa lumshe, ta karasa cikin parlorn tana kallon sa, Bata taba yarda cewar yara na kama da mahaifinsu hundred percent sai a kan kids dinta, the resemblance is just too obvious, har ta isa kusa da shi bata sani ba, ta durkusa gefensa tana ci gaba da kallonsa a sanyaye ta kamo hannunsa, lkci daya ya bude manyan idanuwansa ya mike xaune yana kallonta shi ma, wasu sabbin hawayen suka cika idonta ta sauke kanta kasa a hankli tace "Toh ni me yasa basu yi kama da ni ba?" Da mamaki ya dinga kallonta, ta mike xata bar wajen ya jawota jikinsa yana murmushi murya can kasa yace "The kids?" Ta gyada masa kai hawayen idonta suka xubo, ya rungume ta sosai ya lumshe ido yana shakar kamshinta yace "Next one's xa su yi kama da ke in sha Allah" kwace kanta tayi ta hade rai tace "Next what?" Bude ido yayi, yyi dariya yace "Next kids mana" wani kallo tayi masa ta turo baki ta mike ta nufi dining ya bi ta da kallo yana dariya kasa kasa, sai da ta isa nan ta juyo tana kallonsa taga kallonta yake shi ma, a hankali tace "Breakfast..." ya mike yana murmushi ya iso dinning din, kanta a kasa tace "Do you still take coffee?" Yana kallonta yace "Sure..." kitchen ta wuce ya bi ta da ido ta dawo da coffee powder ta hada masa ta ajiye gabansa a hankali, sannan ta debar masa Irish da kwai ta ajiye masa tare da bread, ya wara ido yace "Duk ni kadai wife?" Bata ce komai ba ta hada nata shayin ta xauna tana sha, a hankali ta dago kai suka hada ido, kasa daina kallonsa tayi kamar yanda shi ma ya ke kallonta babu kiftawa, tasowa yayi ya dawo kusa da ita cikin sanyin murya yace "Billah Ina son ki Iman" ta sauke idonta bata ce komai ba. Karfe sha daya tana dakinta Aliyu ya shigo yace ta shirya xa su fita, lkci daya mood dinta ya canxa, dariya yayi don ya ma san dalilin hakan, ya karasa kusa da ita ya xauna gefenta yace "Baxan kai ki inda xa kiyi kuka yau ba, sai dai kiyi na farin ciki wife" ta turo baki kamar xata yi kuka tace "Ni ko daya bana so, am going no where..." ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "xa ki so wannan in sha Allah ummu Shureim, I am giving you 100% assurance" a hankli tace "To xa mu dauko Shureim daga nan?" Kamar jiran tambayar yake ya girgixa kai da sauri yace "Nooo" da mamaki tace "Why?" Murmushi yayi yana kallon kwayar idonta yana shafa sajensa a hankali yace "Baxai bari in gwada maki yanda nake son ki ba anjima, he will be a barrier..." Wani kallo ta dinga masa tace "Ni dai yau yarona xai dawo, ba ruwana" Yar dariya yayi yace "Inaa sai na gama tabbatar maki da soyayyata anjima.." daga haka ya mike ya nufi kofa yace "Am waiting for you downstairs Iman, don nasan baxa ki shirya gabana ba" yana fadin haka ya juyo ya kalleta ya kashe mata ido ta bi sa da ido har ya fita, Aliyu yana ta xaune parlor yana jiran ta, message ya shigo wayarsa, dauka yayi ya bude yana duba address din da Dr Ayman ya turo masa, ajiye wayar yayi ya jinginar da kansa jikin kujera, shi kam har sannan ya kasa daina mamakin khadijah, he couldn't believe it, bai taba xaton xata hakura ta sauko da wuri ba haka har ta kulasa duk da maganganun Anty khadijah, he never expect that from her, murmushi kawai yyi tunawa da yayi kilan yana cin albarkacin yaransu ne that she is seeing in him, but he will surely teach her to love him not because of the kids, sakkowa tayi stairs sanye da hijab har kasa babu abinda ta shafa fuskarta banda powder sai chappete a lips dinta amma har wani glowing take, she is just the definition of true beauty, ya mike yana murmushi a hankali yace "Kin yi kyau wife" sauke idonta tayi har ta iso parlorn, ya isa har gabanta ya duka yayi pecking lips dinta a hankali, ta hade rai tana goge bakin tace "Bana so" yana murmushi yace "Toh yi hakuri na bari" daga haka ya kama hannunta suka fita, sai da suka bar gidan a motarsa suka hau saman titi tana kallonsa a hankali tace "Ina xa mu je plss Aliyu?" Kallonta yayi na few seconds sannan ya dauke kai, murya can kasa yace "Yanxu baki jin kunyan kiran sunana Iman?" Ta hade rai tace "Toh me xan kira ka?" Ya langwabar da kai yace "Sai ki sakaya even because of Shureim, though nasan I don't deserve that" jikinta ne yyi sanyi ta tuna yanda take kiransa seven years back, a hankali ta kallesa taga driving dinsa kawai yake ta sauke idonta tace "Toh xan ce maka Yayan Baby" murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba kuma bai kalleta ba, bayan wani lkci yace "Ohk then" sun fi 10 mins babu wanda yace komai tayi breaking silence din, ba don shirun dake motar ba da ba lallai ma yaji abinda tace ba coz it's very low, "Or Abu Shureim" abinda ta fada kenan sai kuma ta dauke kai kamar ba ita ta fada ba. Kinda very busy yesterday shi sa aka ji shiru, sorry for the short update, ltr xan yi wani in sha Allah. Tnx for understanding.🤗 Murmushi kawai Aliyu yayi bai ce komai ba, ya dau wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne tare da yin sallama yace "Muna hanya Dr, soon xa mu iso" ajiye wayar yayi, yana maida hankalinsa gaba daya kan driving da yake, bayan tafiya mai tsawo suka shigo wani anguwa, yayi parking dai dai wani gida, kalle kallen anguwar yake to make sure address din da aka turo masa daxu ne, ya dau wayarsa ya bude yana kallon number gidan, tada motar yayi yana driving a hankali har ya isa wani babban gida yayi parking, khadijah da ke ta kallonsa tace "Baka ma san inda xa mu ba kenan" ya kalleta ya wara manyan idonsa yana murmushi yace "Na sani mana, ba gashi mun xo ba" Dialing number Dr Ayman yayi yace "Ga mu a waje" Ba a dau lkci ba Khaleel ya fito daga babban gidan, duk a tunanin khadijah gidansa suka xo, Ya bude side din Aliyu ya basa hannu suka gaisa yana kallon khadijah yace "Good morning Madam" d'an murmushi tayi a hankali tace "Ina kwana Doctor" yace "Lafiya lau ya gida" tace "Alhmdllh" yana kallon Aliyu yace "Alryt, ku shiga ciki ni ana jirana xan wuce yanxu, sai na dawo anjima" Aliyu ya fito daga cikin motar yace "But..." Murmushi Khaleel yayi yace "You don't worry Umma ma na ciki with Shureim" Aliyu yace "Ohk then" Daga haka Khaleel ya nufi motarsa dake waje yayi parking, Aliyu ya kalli khadijah yace "Come down Iman" bude motar tayi ta fito tana mamakin me Umma kuma ta xo yi nan tare da Shureim, ta xagayo inda yake tace "Where is this please, and why are we here?" Yana shafa kansa yace "Xumunci muka xo..." gate ya nufa ta bi bayansa har suka shiga babban gidan, a tare suke tafiyar har suka iso entrance din babban gidan, haka kawai khadijah taji gabanta na faduwa, Aliyu ya juya yana kallonta ya sakar mata murmushi yace "Gidan ku ne nan Iman, gidan yayar mahaifiyar ki" Wani kallo ta dinga masa tace "Wace mahaifiyar tawa?" Ya sauke idonsa yace "Ur late Mum" daga haka ya shiga parlorn da sallama ta bi sa da kallon mamaki, juyawa yayi ganin bata shigo ba tana tsaye bakin kofar yayi kasa da murya yace "Come in plss Iman" yana fadin haka ya juya yana kallon mutanen dake xaune parlorn, very many of them, iyaye da yara, da kyar khadijah ta iya daga kafa ta shiga parlorn abinda ya fada na sinking kanta, Wai yayar mahaifiyar ta, how is that bayan ko Umma ma bata san dangin mum dinta ba? Kan jawahir dake xaune kasa kusa da Mahaifiyarta idonta ya fara sauka, Jawahir ta yi saurin sauke idonta kasa, Khadijah ta dinga bin mutanen dake xaune parlorn da kallo har idonta ya sauka kan Umma, Shureim dake jikin wani dattijon mutum ya taho da gudu ya rungume ta yana murmushi yace "Antyna" buda ido khadijah tayi ganin Safeenah da su Deejah, Safeenah ta mike da sauri ta iso inda khadijah take tana murmushi ta rungumeta hawaye cike idonta tace "Welcome sister" murmushi kawai khadijah ta iya yi bata ce mata komai ba xuciyarta na bugawa, Safeenah ta ja ta har xuwa cikin parlon, bin bayansu Aliyu yayi ya durkusa nan gefen wani guy da baxai wuce sa ba ya gaida mutanen dake parlorn, suka amsa duk a sanyaye, gaba daya occupant din parlorn kallon khadijah kawai suke, lkci daya Mahaifiyar Jawahir ta fara kuka, jikin khadijah yayi sanyi, ta isa gun Umma ta durkusa, Umma na murmushi a hankali ta kamo hannunta tace "Greet them khadijah, iyayen ki ne nan gaba daya xaune parlorn" Hawaye ya cika idon khadijah tana sake kallon mutanen parlorn, Umma tayi kasa da murya tace "Yes daughter, they are ur families" mahaifiyar Safeenah ta mike trying hard to control her tears tace "Come over daughter, come to me" mikewa khadijah tayi ta nufeta, matar ta rungumeta hawaye na sakko mata tace "Allah ya ji kan Maryam ya yafe mata kura kurenta, you are truly a carbon copy of her daughter... Allah ya albarkace ki, mun ji dadi da Allah ya sada mu da ke tun a duniya, it's really sad sai yanxu muke sanin 'yar kanwarmu, jinin kanwar mu, duk da ba laifinmu bane ba haka muka so ba, amma there is always a reason behind everything, it's great meeting you daughter" ita dai khadijah bata ce komai ba jikinta yayi sanyi sosai, Hajiya Rahmah ta xauna ta xaunar da ita kusa da ita tana share hawayen ta, jawahir dai ta kasa dago kanta ganin yanda mahaifiyar ta ke kuka yasa ita ma hawaye ya dinga xuba idonta, sai dai duk kukan mahaifiyar jawahir bai kai na mahaifiyar Maimoon ba immediate din Mum din khadijah, kuka take kamar a lokacin taji mutuwar kanwartata, komai ya dawo mata sabo, a karo na farko Alhaji Abbakar mahaifinsu Safeenah kuma babban yayansu late mahaifiyar khadijah gaba daya... yyi gyaran murya ya bude wajen da addu'a, yana murmushi yace "Alhamdulillah for the gift of life, Alhmdllh for a day like this, Alhmdllh for everything... Sure it's a privilege meeting with our daughter again after so many years..." kallon Khadijah yayi yace "Come over dear" Tashi tayi daga kusa da Umman su Safeenah ta dawo kusa da shi a sanyaye ta xauna kasa, da farko kasa cewa komai yayi kuma hakan na da nasaba da kamannin khadijah na mahaifiyar ta, bayan wani lkci yayi karfin halin yin murmushi yace "Khadijah kina yar shekara biyu rabon mu dake, sai yanxu bayan shekara ashirin Allah ya sake hada mu, kwarai kuwa babu wanda kika sani cikin mu kamar yanda mu ma bamu san ki ba, da xa mu hadu a hanya sai dai ki wuce mu wuce, which is a great shame" ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, nuna mata sauran maxan da ke parlorn su kusan uku xaune kusa da shi yayi da wanda yake kan one seater yace "Kin ga wa en nan gaba daya" ta daga kai a hankali tana kallonsu gaba daya, yace "Duk iyayen ki ne khadijah, they are all ur parent, and they are all here because of you, duk mun bar abubuwan da muke muka taho daga garruwa daban daban domin ki, gaba daya nan da kika ganmu yayyin marigayiya Maryam ne, mahaifiyar ki, ke din mai gata ce khadijah, kina da gatan ki" cikin rawar murya tace "Toh me yasa ni ban san ku ba, me yasa ba a nuna min ku ba, me yasa ba ku nemeni ba" tana fadin haka ta hade kai da kujera tana kuka sosai, Ya dafata cikin sanyi yace "Mahaifin ki Allah ya masa rahama shi ya raba mu da ke tun bayan rasuwar mahaifiyar ki khadijah, mun so rike ki ganin ba shi da yan uwa mata, amma sai yayi tunanin rabasa da ke muke son yi, Allah ya gafarta masa, mun samu matsala a kan hakan da shi, which contributed to his keeping u away from us for many years, a Abuja suka xauna da mahaifiyar ki, bayan rasuwar ta ne ya siyar da gidansa na Abuja ya dawo kano without even our knowledge, kin ji dalilin da yasa baki san mu ba khadijah, Kuma da mun san inda familyn mahaifin ki suke da babu abinda xai hana mu xuwa gare ki, sai dai yau ta dalilin mijin jawahir mun yi reuniting da ke...." Khadijah bata dago kanta ba hawaye na ta xuba idonta, Alhaji Usman yace "Wannan baiwar Allah da ta rike ki bisa amana tamkar yar da ta haifa cikinta Allah ya saka mata da gidan aljanna.... Mun ji duk kalubalen da kika fuskanta a rayuwa saboda maraici, bayin Allahn da suka tsaya maki through all the hardship Allah ya biya su da aljanna, it's really sad daughter, don kina da gatan ki, Amma ba komai haka Allah ya kaddara, Allah ya jin kan iyayen ki ya gafarta masa, ya kuma raya maki yaron ki, ya albarkace auren ki.... In sha Allah gatan da baki samu ba da yarintar ki xaki samu da girman ki, we will always be there for you daughter, uwar mu daya ubanmu daya da Mahaifiyar ki... Allah ya ji kanta" Khadijah ta dago tana share idonta a hankali tace "Ameen, nagode Abba" Gaba daya sai da aka mata introducing din cousins dinta da niece a parlorn, yawanci duk suna yanayi barin da matan, Safeenah da Maimoon kuwa kamanninsu ba a magana dama, har sannan Jawahir ta ki dago kanta daga karshe ma wucewa sama tayi, it was really a happy day for Khadijah jin ta cikin yan uwanta gaba daya, kuma a ranan ta fara ganin hoton mahaifiyar ta, bata taba sanin haka relatives ke da dadi ba sai ranan, da tun farko tasan da su tasan baxata wahala a rayuwa ba but that's her fate and she is happy with it, Aliyu bai jima gidan ba ya wuce ya bar ta, Umma kuma sai kusan azahar ta wuce ta bar Shureim ma gidan, Khadijah na daki tare da su Safeenah da deeja dake ta labari tayi tagumi tana kallonsu tana murmushi jawahir ta shigo dakin, suna hada ido ta sunkuyar da kai a hankali tace "Khadijah ki xo ku gaisa da Doctor xa mu wuce yanxu" Mikewa khadijah tayi tace "Toh" ta dau hijab tace ma su Safeenah tana xuwa sannan ta fita, Dr Ayman na xaune parlor tare da Shureim dake jikinsa ta shigo tana kallonsa murmushi dauke fuskarta tace "Ina yini Doctor" murmushin ya mayar mata yace "Alhmdllh khadijah" ta isa har gefensa ta xauna a kasa tana kallonsa cikin sanyi tace "I am very happy for ur effort in uniting me with my relatives doctor, Allah ya saka da alkhairi, I will never forget you in my life..." Kasa ci gaba tayi ta sunkuyar da kai hawaye na sakko mata, ya dinga kallonta a sanyaye, ta dago da kyar bayan ta goge idonta don bata son Shureim ya gani tana dubansa tace "This is among the greatest thing that have ever happened too me doctor, I really owe both you and Barrister, Kun haskaka min rayuwata kun taimakeni a lokacin da nake bukatan hakan, I don't know how to pay you both" ya d'an yi murmushi yace "May be that was why God brought you into my life, just to unite you with ur late mum's family, There is always a reason for everything you knw... Don haka kawai ki gode Allah ba ni ba" Kai ta gyada masa tana share hawayen da ya ki tsaya mata, ita dai jawahir na tsaye gefe a sanyaye bata ce komai ba, yace "Amma nan xaki kwana yau koh" A hankali tace "Ban sani ba tukun" yace "Alryt then, mu xa mu koma yanxu, and in sha Allah gobe xa mu koma Uk" ta kallesa a sanyaye tace "Toh Allah ya kai ku lafiya" mikewa yayi ya daga Shureim dake kallo yace "Sweetheart xa mu tafi yanxu je wajen Anty" ya bata fuska yace "Uncle ni xan bika plss" jawosa khadijah tayi tace "A'a xa su je da nisa" kuka ya fara yi ya koma gun Khaleel yace "Uncle plss" sai a sannan jawahir tace "Mu tafi da shi mana don Allah" Khaleel ya kalleta sannan ya kalli khadijah yace "Can we?" Shiru ta d'an yi sai Kuma a hankali tace "But his..." Sai kuma tayi shiru, Khaleel na murmushi yace "His dad bai sani ba koh?" kasa cewa komai tayi kuma bata dago ba, yace "Toh kira sa ki gaya masa nasan baxai hana ba" ba musu ta dau wayarta dake jikinta ta shiga kiran Aliyu, bayan wani lkci ya daga yace "Iman..." Tace "Wai Dr Ayman xa su tafi da shureim can they?" Murmushi Aliyu yayi yace "Sure" tace "Toh" daga haka ta katse wayar tana kallon Khaleel tace "Yace toh" Murmushi Khaleel yayi yace "Alryt then, sai mun hade a uk, sai ki gaya ma grandparents dinsa mun tafi da shi, I mean all his grannies cos he have a lot..." daga haka ya dau Shureim dake murmushi yana daga mata hannu suka fita da jawahir dake bin su a baya don ta sallami iyayenta, khadijah ta bi su da kallo har suka fita, kafin tayi murmushi ta mike a hankali ta wuce sama..... Daren ranan a gidan khadijah ta kwana don Aliyu bai takura ta sai sun koma gida ba shi dai yayi wucewarsa, washegari yayyin mahaifiyar ta maxa duk suka wuce bayan sun cika ta da kyautan kudi mai yawa tunda basu samu sun mata komai na aure ba, Su Safeenah basu yarda sun bi iyayen nasu ba wai sai sun je gidan khadijah, Hajiya Rahamah tace "Gaskiya kam ya kamata ku je sai ku dawo anjima da yamma" Khadijah taji dadi sosai tace "Umma don Allah su kwana mana" Mum dinsu Jawahir tace "A'a su dai dawo da yamma" ta marairaice tace "Toh sai mu dawo tare" Hajiya Rahamah tace "Ki dawo kiyi me khadijah, ina kika taba jin amarya na yawo daga kai ta dakinta, wannan ma ai lalura yasa kika fito..." shiru khadijah tayi bata ce komai ba jikinta yayi sanyi, Driver aka sa ya maida su can gidan nata, Mum din Jawahir tace "Sai ki fara kiran mijin naki ki sanar da shi xuwan ku" a hankali khadijah tace "Toh..." Daga haka ta mike ta tafi daki ta dau wayarta, kiran Aliyu ta shiga yi, yana dagawa yayi sallama yace "Good morning wife" ta turo baki tace "Xa mu dawo gida yanxu da su Safeenah" yace "Ohk, in taho in dauke ku ne?" Tace "A'a driver xai maido mu" yace "Alryt then, Allah ya kawo ku lafiya, am already missing you dear" Bata ce komai ba ta katse wayar ta, Sha biyu saura suka dau hanyar gida tare da Safeenah, Deejah da Maimoon, a waje drivern yayi park duk suka sauka motar suka masa godiya, khadijah ta bude gate din tana gaida mai gadi dake gaisheta shi ma, sauran duk suka gaisa da shi sannan suka bi bayanta, a hankali ta murda kofar parlorn, Babu kowa ciki sai sanyin ac da tv dake a kunne, ta shiga su Safeenah na biye da ita har cikin parlon duk suka xaxxauna, tana murmushi tace "Bari in kawo maku ruwa" Bata jira cewarsu ba ta wuce Kitchen ta dauko tray da cups ta bude fridge ta daura lemo da ruwa a kan tray din ta dawo ta ajiye masu, Safeenah na murmushi tace "Thanks sis" murmushin tayi ita ma ta wuce sama, a hankali ta bude kofar bedroom din Aliyu, xaune ta samesa yana operating laptop, ta hade rai tace "Baxa ka taho ku gaisa da su ba" ajiye laptop din yayi yana murmushi yace "I was waiting for ur instruction ne dama kar in yi laifi" hararansa tayi ta juya ta wuce, yana murmushi ya mike ya bi bayanta, har ya shigo parlorn yana kallon su Safeenah yace "Sannun ku da xuwa" duk suka gaishesa da fara'a, ya xauna saman kujera yana murmushi yace "Lafiya lau, fatan kun baro mutan gida lafiya" duk suka ce "Alhmdllh" yace "Maa sha Allah" sannan ya mike yana kallon khadijah ya koma sama, mikewa tayi tace "Mu je sama ku yi alwala it's almost time for zuhr" tashi suka yi gaba daya suka wuce sama xuwa dakinta, sai bayan da suka idar ta cire hijab dinta tace "Let me cook something for us" mikewa suka yi gaba daya Safeenah tace "We will do that together" dariya kawai khadijah tayi, tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup suka hada gaba daya, aikin yayi sauri saboda yawansu, Safeenah na gama kwashe tuwon a leda tace "Toh ina xa a sa ma mijin ki" khadijah tace "It's not necessary, namu ne kadai, nasan eatry xai je shi" Deejah ta saki baki tana kallonta tace "Eatry kuma Namecy?" Murmushi kawai khadijah tayi, Maimoon tace "Uhmm lallai ma, tun yanxu xa ki fara sakaci haka Khadijah?? Har kina son mijin ki ya tafi wani waje ya ci abinci" Kallonta khadijah tayi bata ce komai ba, Safeenah ta dauko wani kwali mai dauke da cooler mai kyau ta fiddo babba da karami ta tafi sink ta wanke shi tas ta tsane sannan ta sa tuwo ta rufe, Deejah ta dau na miyan ta xuba miya da isasshen nama a ciki ta rufe duk suka daura a tray, ita dai khadijah na tsaye tana kallonsu kamar an dasa ta, Maimoon ta dauko plate mai kyau da spoon da cup ta dauraye ta daura kan tray din, Safeenah ce ta hada xobon dake ajiye tun daxu suna jiran ya huce, xobon ya ji kayan kamshi da abarba da cucumber, ta xuba kananun kankara kan thick xobon, sabon jug ta dauko ta kusa cika jug din ta rufe, tana kallon khadijah tace "Sai ki kai masa daki, ko shi ma waitress din eatry xa su maki??" Khadijah bata san lkcn da tayi dariya ba sai dai bata ce komai ba ta dau tray din abincin da drink ta fita kitchen din ta wuce sama, a hankali ta tura kofar dakinsa, yana xaune yana danna laptop har sannan, ya dago yana kallonta har ta iso inda yake ta durkusa ta ajiye tray din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, yayi murmushi sanin this might not be her thinking, infact it's not even her thinking... Khadijah ce xata kawo masa abinci haka kawai, shafa kai yyi yana murmushi. Kafin ta koma kitchen din duk sun wanke duk abubuwan da suka bata, Maimoon ta fito masu da abincin nan tsakiyar parlor, Xaunawa suka yi gaba daya suka ci a tare, Deejah ta gyara wajen ta tafi da komai kitchen, suna ta xaune parlor suna hira khadijah ta dinga jin kamar kar su ce xasu tafi, ta dinga addu'ar Allah sa su manta kawai su kwana, suna nan a haka har aka kira la'asar suka wuce sama xuwa dakinta duk suka yi sallah, sai a sannan suka fara shirin komawa gida, duk jikin khadijah yayi sanyi ta xauna can karshen gado tana kallonsu a sanyaye, Dariya Deejah ta dinga mata, Safeenah na gama gyara fuskarta ta dawo kusa da ita tace "Kar ki damu sis xa mu dinga haduwa frequently in sha Allah kin ji, Kuma ga waya xa mu dinga communicating" hawaye ne ya cika idon khadijah, Safeenah tayi dariya tace "Tabb, to mu fa gobe da safe xa mu koma Abuja, Deejah kadai ce a nan, kema nasan soon xa ki koma uk saboda karatun ki" Ita dai khadijah bata ce komai ba, bayan duk sun gama Safeenah tace "I notice something khadijah, it seems har yanxu baki kwantar da hankalin ki da mijin ki ba, are you still thinking of the past koh? I will advice you to just erase that of ur mind idan ba haka ba baxa ki taba samun kwanciyar hankali gidan ki ba, nobody is above mistake khadijah, barin ma irin wannan mistake din da aka yi ba da gangan ba, wllh idan baki maida hankali kin rungumi mijin ki ba kina ji kina gani wata a waje xata yi hakan ga mijin ki very handsome gentleman, Wallahi Kar ki kuskura wata ta hango maki shi a waje, don rashin samun kulawa gun ki xai sa ya ba ta waje dama, Haba sai kace ba wayayya ba Khadijah..." turo baki khadijah tayi, Safeenah ta dawo kusa da ita ta kamo hannunta tace "that's just it, kiyi hakuri ki xauna xuciya daya da mijin ki, forget the past, ni na tabbatar mijin ki yana son ki kema kuma kina son sa sosai" Khadijah ta sauke idonta a hankali, Maganganu sosai Safeenah ta yi mata da yasa duk jikinta yayi sanyi, daga karshe ta mike tace "Toh mu xa mu tafi khadijah sai mun yi waya" khadijah ta mike a hankali tace "Bari in gaya masa" daga haka ta fita ta shiga dakin Aliyu suka kusa cin karo don fitowa xai yi shi ma daga dakin, jawota yayi jikinsa ya rufe kofar yana kallon eye balls dinta, ta sauke idonta tace "Sake ni" ba musu ya saketa yana murmushi, tace "Xa su wuce" yace "I was thinking kwana xa su yi" ta girgixa kai tace "Gobe da safe xa su wuce Abuja" yace "Ohk ba nan suke ba dama?" Tace "Deejah ce kadai a nan" yace "Alryt am coming now" juyawa tayi ta fita, turarruka da kayan kwalliya na lefenta ta debar masu mai yawa suka sauka downstairs tana jin kewansu, ba a dau lkci ba Aliyu ya sauko, dubu talatin ya ba su gaba daya, suka ki amsa, khadijah ta hade rai ta karbi kudin hannunsa ta bude jakar Deejah tace "Ae ba ku kuka ce ya baku ba toh" Murmushi kawai Aliyu yake yana kallonta, suka masa godiya yace "No thanks sisters, or shud I drop you?" Safeenah tace "A'a mun gode xa mu tadda driver bakin titi" yace "Alryt then, Allah ya kiyaye hanya" duk suka amsa masa da Amin, har bakin gate khadijah ta rakasu, Maimoon tace "Kin ga ki koma haka mun gode sosai Khadijah, Allah bar xumunci" sai a sannan hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "I am going to miss you all" rungume juna suka yi gaba daya, tana ji tana gani suka wuce ta juyo ta koma ciki tana goge hawayen dake xuba mata, Aliyu dake parlor ya dinga kallonta har ta wuce sama. Ko minti talatin su Safeenah basu yi da barin gidan ba Barrister ya xo, Aliyu ya bude masa kofa suka gaisa, Barrister ya xauna kan kujera yace "Ya gidan" Aliyu na shafa kai ya xauna shi ma yace "Alhmdllh, ya aiki" Barrister yace "Mun gode Allah, ya mum shureim" Mikewa Aliyu yayi yace "She's upstairs" daga haka ya wuce sama, bude kofar dakinta yayi ya ganta kwance ta rufe fuskarta da pillow, ya isa kan gadon ya xauna kusa da ita ya dagota a hankali yace "Ummu Shureim" Bude ido tayi tana kallonsa, ya sakar mata lallausan murmushi yace "Mu je ku gaisa da Barrister" tace "Ya xo?" Yace "Sure" shi ya taimaka mata ta sauko saman gadon bayan ta sauko ta kwace hannunta shi dai bai ce komai ba ta sa hijab dinta suka fita dakin, gaisawa suka yi da Sudais ya mika ma Aliyu takardan hannunsa yace "Bata ta gani, I don't want to do anything without her knowledge" Aliyu ya amsa ya mika mata, karban takardan tayi ta bude tana kallon content din, bayan wani lkci ta Dago a sanyaye tana kallonsa, murmushi yayi yace "Is that okay?" Girgixa masa kai tayi a hankali tace "Barrister ka kyalesa kawai, na yafe masa even for the sake of my dad" Karban takardan Aliyu yyi yana dubawa, Barrister na kallonta yace "Are sure Amira?" Kai ta gyada masa tana murmushi tace "Sure Barrister, na yafe ma kawu na, sai dai kuma tsakaninsa da mahaliccin sa" mikewa Barrister yayi yace "Toh Alhmdllh, Allah ya yafe mana gaba daya, but I don't think ur forgiveness will count, coz dukiyar marayu yyi tampering da" Aliyu na gyada Kai yace "Haka ne" Barrister yace "Alryt xan koma, abinda ya kawo ni kenan dama" tace "Toh nagode sosai Barrister, bari in kawo maka ruwa" yace "Noo Amira, am okay" Tare suka fita da Aliyu, a sanyaye ta wuce sama don ita da gaske take jin ta yafe ma kawun ta. Gyara bedroom dinta tayi ta share ta goge ko ina, ta fito dakin kenan taga Aliyu ma ya fito rike da tray din abincin da ta kai masa da rana, karasawa tayi ta amsa tray din hannunsa, yana kallonta yace "Thank you" bata ce komai ba ta sauka downstairs ta wuce Kitchen. Tana xaune kan darduma bayan ta idar da magrib ya shigo dakin ya xauna gefen gado yace "Mu je ki raka ni" tace "Ina?" Yace "Gida, xan dauko wasu files a can" ta girgixa kai tace "A'a baxan fita ba, ni...." Ya katse ta yace "Ba fa shiga gidan xa ki yi ba" tace "Eh na sani" ya marairaice yace "Plss Ummu Shureim" turo baki tayi kamar xata yi kuka, yayi murmushi ya mike yace "Am waiting for you downstairs" A hankali ta mike ta linke pray mat din ta fita dakin, a kofar gidansu yayi parking yana kallonta yace "Baxan dade ba xan fito yanxu" kasa cewa komai tayi don sai take ga kamar bai dace ta ki shiga ba, can dai tace "Bari in gaida mumy" yace "Noo, ki bari ran Sunday sai mu xo gaisheta, it's already late yanxu" kallonsa ta tsaya yi, ya gyada kai yace "Yea dear" daga haka ya juya ya wuce ciki, kamar yanda ya fada bai dade ba ya fito ya ajiye takardun bayan mota sannan ya shiga maxaunin driver suka bar layin, yace "Me kike son ci in siya maki" ta girgixa kai tace "I am not hungry" yace "Nasan bakya Jin yunwa... abun dadi nake nufi" tace "Baxan ci komai ba" ya kamo hannunta yace "A'a, gwara dai a siya maki ko kaxa ce koh?" tace "Ni nace maka bana ci" parking yayi gun da ake siyar da kaji yace "Ai baki isa ba.." Daga haka ya fita ya siyo masu guda biyu, ya bude bayan mota ya ajiye, yana kallonta yace "Fresh milk kike so ko youghurt?" Tace "Daxu fa na ci abinci me xanyi da yoghurt ko fresh milk" Yar dariya yayi yace "Toh naji ni xan siya in sha" gun da ake siyarwa ya kara parking ya fita ya siyo chill fresh milk ya bude back seat ya ajiye sannan suka dau hanyar gida, da kyar khadijah ta yarda ta xauna parlor tana bata fuska, ta dinga kallon kajin da ya ajiye gabanta sai kamshi yake ga Madara a glass cup a gefe, so mouth watering, a hankali ta kai hannu ta dau cinyar kaxa daya tace "Ni wannan ya isheni" ya kalleta bai ce komai ba ya dau naman shi ma ya kai bakinsa, satan kallonsa tayi bayan ta cinye na hannunta don sosai naman yayi mata dadi, ta turo baki tace "Ashe ma da dadi" ya danne dariyar sa ko kallonta bai yi ba, ta dau wani kaxan ta fara ci, a haka sai da ta kusa cin rabin wanda ya ajiye mata, ta dau madaran glass cup din ta shanye gaba daya, sai a sannan ya dago yana dubanta yace "Amma da muka shigo ne kika fara jin yunwan koh?" Mikewa tayi da sauri ta wuce sama tace "Nima ban sani ba" Murmushi yayi ya bi ta da kallo kamar yanda ita ma take murmushin ta wuce sama, cire kayan jikinta tayi ta linke ta ajiye sannan ta shiga bathroom, wanke bakinta tayi, tayi wankan ta fito, Bata wani jima sosai gaban mirror ba, ta feshe jikinta da turarruka kala kala ta dau kayan baccinta ta sa, sannan ta sa net a dogon gashinta ta kashe wutan dakin ta hau saman gado ta kwanta ta ja duvet ta rufe jikinta ta lumshe ido. Har kusan karfe sha daya ta kasa bacci sabida thirst da take ta ji, ta tashi daga karshe ta sauka kan gadon, ta nufi kofa ta bude a hankali ta fito tana kallon kofar dakinsa dake a rufe, sauka downstairs tayi taga wutan parlorn gaba daya a kashe har kitchen, kunna wutan parlorn tayi ta nufi kitchen ta shiga tana kokarin kunna switch taji an cafkota, ihu ta fasa a mugun tsorace, ya kunna wutan da sauri ganin da gaske ta tsorata ya rungumeta yace "I am sorry iman, I didn't mean to scare the life out of you, wasa nake maki, kiyi hakuri plss" hawaye ya dinga xuba idonta jikinta na bari xuciyarta na bugawa, tausayinta yaji ganin da gaske ta tsorata, ya kasa karasa sauran coffeen da ya rage cup din hannunsa ya ajiye, yana rike da ita ya kashe wutan suka fito yace "I heard ur footsteps shi yasa na kashe wutan, am sorry for scaring you..." ita dai bata ce komai ba har lkcn xuciyarta bai dawo dai dai ba, suna isa stairs ya juyo da sauri yana kallonta yace "Me kika sakko yi" cikin sanyin murya tace "Ruwa xan sha" saketa yayi don xuwa ya dauko mata ruwan ta bi bayansa, yayi murmushi ya bude fridge ya fiddo ruwa ya xuba mata a cup ya mika mata ta amsa ta sha ya karbi cup din ya ajiye, yana rike da ita suka wuce sama bude dakinsa yayi xata kwace hannunta ta wuce nata dakin ya ki saketa ya jawota dakinsa ya rufe kofar, sanyi ne sosai a dakin saboda Ac da ya kure ga fitila kuma a kashe, xata bude kofa ta fita ya riketa murya can kasa yace "Kin san har yanxu ba muyi sallah mun nuna godiya ga Allah.. mu yi addu'ar xaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa ba Iman?" Da sauri tace "Ni dai nayi, Kai ne dai baka yi ba" yace "Noo kamata yayi muyi tare" tace "I am not clean...." Kallonta ya dinga yi cikin duhun yace "Really??" gabanta na faduwa tace "Ehh" yace "Ban yarda ba" ta hade rai tace "Saboda ni makaryaciya ce?" Yar dariya yayi taji ya dauketa cak sai saman gado, ya kwantar da ita yace "I have to check for my self..." Kara tayi a rikice tace "Nashiga uku, don..." Bai bari ta karasa ba ya rufe bakinta, tun tana turasa tana son kwace kanta har ta gaji, lkci daya kuma jikinta ya mutu, kwata kwata Aliyu bai bata breathing space ba, ya dinga exploring dinta as if his life depend on that... daga karshe ta sakar masa jiki gaba daya, sai dai bakinta bai daina cewa stop it plss idan ma ba kasa kunne kayi sosai ba baxa ka ji me take cewa ba, lkci daya ta rikice masa ganin ba da wasa yake ba, nan ta fara hawaye tana rokonsa, sai take ganin abun kamar na 7 years back, the only difference is that he is not fierce, just romantic and very careful, upon her plea bai iya ya kyaleta ba duk da yayi kokarin ganin yayi hakan amma ya kasa.... Bayan lokaci me tsawo ya dago a hankali ya ga bata gefensa kamar ynda ya bar ta, mikewa xaune yayi da sauri, shesshekar kukanta ya dinga ji can other side of the bed, ya tashi da kyar ya nufi wajen, takurewa tayi waje daya tana kuka a hankali, jikinsa yyi sanyi ya duka gabanta yace "I am very sorry Iman, I...." Rasa abinda xae ce mata yyi ya dagota ta fashe da matsanancin kuka, ya rungume ta xuciyarsa na bugawa yace "I didn't mean to hurt you again" gaba daya tayi laushi, kuka kawai take, ya dagota ya kwantar kan gadon yace "Kiyi hakuri plss Iman, forgive me...." cikin rawar murya tace "Kace min baxan ji xafi ba" Kallonta yake cikin duhun don bai ma san ya fadi hakan ba, ya kwantar da ita kirjinsa a hankali yace "But did you feeling any pain?" Kai ta dinga gyada masa hawaye na xubo mata, yayi shiru bayan wani lkci ya kai bakinsa kunnenta yace "Just like the 1st experience?" Girgixa masa kai tayi, Yana shafa bayanta yana murmushi sanin da ba dan shi yyi deflower dinta ba da bbu abinda xai hanasa cewa budurwa ce ita, kwantar da ita yayi ya mike ya shiga bathroom, ya hada mata ruwan wanka, ya dawo ya kai ta bathroom din, shi ya taimaka tayi wanka tana nonnokewa sannan ya fito tare da ita, babu bata lokaci kuma bacci ya dauketa, sai a sannan ya kunna wutan dakin yana kallon bedsheet din gadon, Bai ga abinda yake xato ba, yayi murmushi ya dawo kusa da ita yana kallonta yana Kara jin wani mugun sonta na fixgarsa, it's just great being with her, and it's the sweetest thing he have ever imagined, tashi yayi daga karshe ya shiga bathroom yayi wanka shi ma ya fito ya shirya sannan ya kashe wutan dakin ya kwanta kusa da ita ta shige jikinsa kamar jira take, ya kankameta hade da lumshe ido. Da asuba khadijah na jin Aliyu ya fita masallaci ta mike xaune a hankali, gabanta ne ya dinga faduwa from experience, duk da dai wannan karan ko ciwon kai bata ji ba balle na jiki amma tsoro ne fal xuciyarta, ganin lkci na wucewa ta mike cike da karfin hali, the pain wasn't as much as she was expecting... Ta lallaba ta fita dakin ta koma nata ta sa makulli, wanka ta fara yi ta dauro alwala ta fito, tana ta xaune kan darduma tana azkar bayan ta idar taji an murda kofa, kallon kofar tayi sai dai bata motsa daga inda take ba, a hankali yayi knocking yace "Iman, are you alryt..." Shiru tayi bata ce komai ba, tana ji ya bude kofar dakinsa ya shiga, bayan wani lkci ya fito, hade kai tayi da gwiwa jin yana bude kofarta da makulli, bayan ya bude ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta, a hankali ya karasa dakin ya duka kusa da ita xai dago kanta ta ki yarda, da damuwa yace "Look at me plss Iman, are you okay..." ganin ba yarda xata yi ta dago ba ya mike ya dagota, ihu ta fasa masa ta boye fuskarta jikinsa tace "Ni dai bana soo" Dariya ta basa yana rungume da ita yace "Meye baki so Ummu Shureim" a hankali tace "Ka fita" murya can kasa yace "Kunya ta kike ji?" Kai ta gyada masa a hankali, sosai ta basa dariya ya nufi gadonta da ita, ya kwantar da ita ta rufe fuskarta da pillow, Xaunawa yayi gefenta yana murmushi yace "Sai ma mun yi wanka tare anjima xaki san meye kunya" Bata san lokacin da ta dago ba ta xaro ido tana kallonsa tace "What???" Sai kuma ta maida kanta da sauri tana murmushi wai ita kunya.... Wani salon soyayya na daban Aliyu ya dinga gwada ma Iman kamar xai maida ta ciki, ko da yaushe suna manne da juna, Khadijah bata taba tunanin haka Aliyu yake ba shi da kunya ko na taro ba, idan aka ce mata xai iya abinda yake mata baxata yarda ba, coz he look so innocent in the face, tun tana kunya tana noke masa har daga karshe tayi give up ita ma a gidan ta sakar masa kanta, gida ya koma kamar na India, kunyan da take ma da daddare shi ma duk ta ajiye sa gefe amma fa cikin duhu, ita kanta bata taba sanin tana da soft spot ma Aliyu ba sai a yanxu, har ranta take jin sa, sannan ko na minti daya bata son ya bar ta duk inda xa su tare suke xuwa. Ranan da suka cika sati biyu gidan tana kwance jikinsa a parlor yana operating laptop, a hankali tace "Abban shureim..." Yana kallonta yayi pecking cheeks dinta yace "Ummu Shureim" ta turo baki tace "kaga mun koma makaranta fa" yace "I thought as much, dama in two days time xa mu koma can ai" Tace "Toh Allah ya kai mu" yana shafa fuskarta yace "Ameen baby" a ranan suka tafi yi ma Mumy sallama da yamma, Khadijah na xaune tare da Baby a dakinta taga Barrister ya kirata yayi sau uku, ita dai bata ce mata komai ba, amma sai suka bata dariya, karfe biyar saura suka shiga dakin Mumy xa su mata sallama don har gidan Umma da umman su jawahir xa su je, Mumy tace "Toh Allah ya kai ku lafiya, ya kiyaye hanya" Khadijah dake durkushe kusa da ita tace "Ameen Mumy" Mumy tace "Toh sai kun dawo biki nan da few months" Aliyu yace "Wani bikin Mumy" sai da Mumy ta fara dariya sannan tace "Na kanwar ka mana" Khadijah tace "Mumy baby?" Mumy tace "Ehh" xaro ido tayi tace "Lahh Mumy ba mu sani ba" Aliyu ya xauna yace "Mumy da Ahmad din?" Mumy tayi murmushi tace "Wannan bada ta kawai Abban ku yayi, ba Ahmad bane, an basa hakuri shi" Aliyu ya d'an hade rai yace "Bada ta kuma? To who?" Mumy tace "Barrister Aliyu" da khadijah ta fara dariya sai da Mumy da Aliyu suka tsaya kallonta, ta mike da sauri ta fita xuwa dakin baby tace "Wato abun har da munafurci koh Baby, ni din ne baxa ki gaya ma ba koh?" Baby tayi murmushi don tasan kwanan xancen, a hankali tace "Shi yace ba sai na gaya maki ba, xai je har gida as a mother ya same ki ya gaya maki" khadijah na murmushi tace "Am soo happy wllh, Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin lafiya" Har bakin mota baby ta raka su, suka wuce gidan Umma, bayan Umma sun gaisa da Aliyu ta bi bayan khadijah da ta wuce ciki, Ganin yanda tayi kyau ta cicciko Ummu tayi murmushi tace "Ko ke fa da kika kwantar da hankalin ki daughter" murmushi kawai khadijah tayi ta sunkuyar da kanta, Umma ta xauna kusa da ita tace "In ji dai ba matsala?" Khadijah tace "Babu Umma dama sallama muka xo maki xa mu tafi can Uk" Umma tace "Maa Sha Allah, ai hutun ya kare, Allah ya kai ku lafiya my daughter" Khadijah tace "Ameen Ummata" Umma tace "Amma ku je har Umman su jawahir ku yi mata sallama" khadijah tace "Eh dama xa mu je Umma" Umma tace "Toh hakan na da kyau, kin san kawun ki yana yawan kira mu gaisa" Khadijah ta kalleta da sauri tace "Abbansu Safeenah?" Umma tace "A'a ba shi ba, mai bi masa" xaro ido khadijah tayi sai kuma tayi dariya tace "Umma Abban su Maimoon ne, dama umman su ta rasu 3 years back suka gaya min" Umma tace "Toh ya aka yi don Umman su ta rasu, Allah ya ji kanta" Dariya kawai khadijah take, Umma dai sai kallonta take, can ta turo baki tace "Umma ni dai don Allah kar ki ce masa A'a" buda ido Umma tayi, sai tayi dariya tace "Amma baki da kunya yarinyar nan" Khadijah ta mike ta fita tana dariya, minti talatin suka yi a gidan, xa su wuce umma ta ja khadijah xuwa daki tace "Daughter, ya kamata ku je can katsina da Aliyu ki gaida yayan Mahaifin ki" shiru khadijah tayi da farko, sai kuma a hankali tace "Toh Umma xa mu je" Umma tace "Good, Allah ya kiyaye hanya, ki kula da mijin ki fiye da yanda xa ki iya, ki kuma rike tsaftar ki don nasan kina da ita, Allah ya maki albarka" khadijah na murmushi tace "Ameen Umma" da haka suka bar gidan suka dau hanyar gidansu jawahir, can ma basu dade ba bayan sun yi ma Umman jawahir sallama suka koma gida. Da daddare ganin Aliyu xai takurata ta dinga turo baki tana kwace kanta jikinsa, ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "Baki son mu tafi da babynmu daga nan Iman" ta marairaice masa tace "Ni dai ka kyaleni bacci nake ji" yace "Plss" kukan shagwaba ta fara masa wanda hakan ya rikita sa, bai kyaleta ba sai da yaga ta fara bacci da gaske, ya fi awa daya kankame da ita, ko da yaushe jin abarsa yake intact, murmushi yayi ya manna mata kiss a lips daga karshe ya kwantar da ita ya shiga bathroom. Washegari suna breakfast tana kallonsa tace "Abban Shureim, Ina son mu je katsina mu gaida Uncle dina" ya kalleta yace "When, Kin san gobe da safe xa mu wuce" Tace "Toh idan mun dawo bikin su baby sai mu je?" Yace "A'a idan kin ce mu je yanxu ma sai mu je ai" ta langwabar da kai a hankali tace "Mu je plss" yace "Alryt then" karfe sha daya suka bar gidan, suka dau flight xuwa kano, daga can yayi masu charter na taxi da xai kai su har kt, tun da suka shigo kt misalin karfe daya da rabi na rana gaban khadijah ke ta faduwa, taxin ya ajiye su dai dai gidan kawunta, ita kanta tayi mamakin yanda ta gane gidan, Aliyu ya fito ita ma ta fito tana kallonsa tace "Mu shiga" Bin bayanta yayi suka shiga gidan, Babu kowa compound din da ya xama wani iri kamar gidan da yayi shekara hamsin, Har parlor ta isa da sallama Aliyu ya tsaya daga bayanta, kallon kawun nata dake xaune k'asa a one side of the parlor yana fama da ciwon kafa sosai tayi, ta kalli Hajiya maimuna da ta fito kitchen jin sallama ta gaisheta a sanyaye, daga ita har yaran dake parlorn kallonta suka dinga yi kamar basu santa ba, ita dai tasan basu gane ta bane, Ta isa har kusa da ita a hankali tace "Mama Khadijah ce" bude baki Hajiya Maimuna tayi tana kallonta da wani irin mamaki, Khadijah ta sauke idonta kasa, ba ita ba har kawu Jibril shi ma bude baki yyi lkci daya hanjin cikinsa ya kada don kullum da threat din Barrister Sudais yake kwana yake tashi, Aliyu ya xauna kusa da shi yace "Ina yini kawu?" Kawu ya kallesa yana maxurai yace "Lafiya lau daga ina, wa ku ke nema" Aliyu yayi kasa da murya yace "Ni ne mijin khadijah, mun xo gaishe ku ne kawai kawu" da sauri yace "Toh madalla... Gaisuwa ce kawai koh" Aliyu ya gyada masa kai yace "Eh kawu" khadijah ta karaso har gabansa ta durkusa kanta a kasa tace "Ina yini kawu?" Yace "Lafiya lau" Kai kana ganin yanda yake maxurai kasan duk a tsorace yake, Aliyu yayi murmushi yace "Ka kwantar da hankalin ka kawu, xumunci kawai ta sa ni in kawo ta tayi" Yana gyada Kai kamar kadangare yace "Madallah" Khadijah dai ta kasa cewa komai, bata taba xaton ganin Kawunta da iyalensa a halin da ta samesu ba, ganin gaba daya mutumin is uncomfortable Aliyu yace "Kawu xa mu koma yanxu, don gobe da safe xa mu wuce uk shine tace in kawo ta..." Kawu ya kasa kallon khadijah sai gyada kai yake yana cewa Madallah Kamar xararre, Dubu hamsin Aliyu ya ajiye gabansa, Kawu ya dauka yana kallonsa, lkci daya idanuwansa suka kada yace "Maa sha Allah, nagode nagode nagode Allah yayi albarka" Aliyu yace "Ameen" a sanyaye Khadijah tace "Allah ya baka lafiya kawu" hawaye ta gani idonsa amma yana ta boyewa bai son su gani yace "Toh Amin, sai a yayyafe...." murmushin karfin hali tayi tace "Nima ku yafe min kawu, Allah ya yafe mana baki daya" hatta Maimuna sai da tace da khadijah a yayyafe da xasu wuce, ganin bata ga kishiyarta ba tace "Mama Ina mamansu Usman?" Maimuna tace "Ta amshi takardar ta ta wuce kusan shekara kenan" khadijah bata ce komai ba duk jikinta yayi sanyi har suka bar gidan xuwa inda xa su samu mota xuwa kano. Sai bayan la'asar suka shigo kano, Khadijah sai bata fuska take irin ita ta gaji din nan, ya langwabar da kai yace "Toh ai we still have 3 more hours journey kike bata fuska madam" ta xaro ido tana kallonsa tace "Ni dai na gaji wllh" murmushi yayi yace "Just reserve this comment, xa su maki amfani anjima idan mun isa gida da daddare" Kallonsa kawai take kamar mai son gane ma'anar abinda yace, can tace "Kamar ya?" instructing din mai adai daitan da ya tsayar masu yyi yace "Airport xa ka kai mu" Khadijah ta turo baki ta shiga shima ya shiga yana matsa cinyarta a hankali, tayi kara tana kallonsa, dauke kai yayi da sauri yana murmushi, har suka isa airport idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, ya siyar masu tickets na kaduna, hudu da rabi jirgin ya tashi, cikin few minutes suka sauka kaduna. A gajiye ta shiga parlor ta wuce dakinta direct ta fada kan gado, bayan kusan minti biyar ya bude kofar dakin yana kallonta yace "Sallahn fa?" Kallonsa tayi a hankali tace "Xan yi" yace "Toh tashi kiyi" Sai da ya idar da sllhn shi ma sannan ya fita eatry siyo masu abinci, yana dawowa ya shigo dakinta, xaune ya sameta kan darduma yace "Come down mu ci abinci" Tace "Sai na fara wanka" yace "Toh jira ni in xo muyi" mikewa tayi da sauri ta shige bathroom din ta sa makulli, yana dariya ya juya ya fita dakin. Karfe goma na dare tana kwance parlor kan 3 seater har bacci ya dauketa taji an dauketa kamar baby, ta bude ido a hankali tana kallonsa, ya manna mata kiss a lips dinta ya shiga bedroom dinsa ya kwantar da ita saman gado, ya kwanta shi ma ya shige jikinta... Kamar xata yi kuka tace "Bacci fa nake ji" yayi kasa da murya yace "Wai baki son mu tafi da tsaraban baby mai kama da ke UK ne?" Hararansa tayi ta juya masa baya tana turo baki, ya marairaice mata yace "Plsss Ummu Shureim" kukan shagwaba ta fara masa as usual, nan ta kara rikitar da shi, ita ma dai kamar jira take ta bada kai bori ya hau, they couldn't just get enough of each other, ta kankamesa kamar xata koma jikinsa su xama daya, ya kai bakinsa kunnenta cikin sanyin murya yace "I love you Iman..." Shiru tayi idonta a lumshe, bayan wani lokaci ta kwanta kan kirjinsa a hankali tace "I love you more Abu Shureim" kissing dinta ya shiga yi, and that really turn her on. Da asuba tare suka yi wanka ya ja su sallah a dakin, a hankali ta dawo kusa da shi ta durkusa murya can kasa tace "Good morning Abu Shureim" ya jawota jikinsa yace "Morning Ummu Shureim...." Murmushi tayi tace "I am missing him" yace "You better don't, shi din me iyaye ne da yawa, so kar ma ki wani sa shi a rai" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ki hada abubuwan da kika san xa ki bukata, anjima xa mu wuce airport" tace "But I have everything back there, a can gidana..." Kallonta ya dinga yi kafin yyi murmushi yace "Kina tunanin xan je gidan ki in xauna wife?" Shiru tayi tana kallonsa, yyi yar dariya yace "Lallai, I rather rent a new flat, balle ma muna da apartment can din, kawai I prefer staying a gun aunt dina ne saboda kadaici" murmushi tayi bata dai ce komai ba, sai dai ita ma hakan ya mata, coz she don't think xata iya xama gida daya da su Khaleel, it's just not possible, lakutan hancinta yyi yace "Kin fi son can ne saboda yar uwar ki" da sauri tace "Not at all, ur wish is my command sir...." Rungume ta yayi yace "That's sweet of you baby" A year and a half later.... Tun da khadijah ta tashi yau take ta girke girke iri iri duk da xaxxabin da ta dinga yi kwana biyu da suka wuce, kana ganinta ka ga mai karamin ciki, yanxun ma daurewa take girkin da take yi, don aroma din na hawa mata kai but she have no option, Aliyu ne ya shigo kitchen din yana rungume da little Fatima, yarinya da baxata wuce shekara daya da few months ba, she is just a duplicate of her mother, babu inda ta bar khadijah, kyakkyawa ce ta karshe yarinyar, Khadijah ta kallesu tace "Dear kasan yanxu xata ce sai na dauketa kuma ni ba taya ni aiki xaka yi ba" Yar dariya yayi yace "Tsoro nake kar in fita da ita tayi ta min ihu a mota, xan je airport dauko Umma, same flight kuma suka bi da su Baby" Khadijah tace "Lahh da gaske?" Yace "Sure, Aryan ma ba yarda xai yi ya bi ni ba da sai mu tafi tare da su..." Tace "Ae tun daxu na gane gida yake son wucewa ya gaji da mu" dariya Aliyu yyi yace "Aa miskilanci ne kawai, ya ki yarda in dauke sa ma" Ta dauraye hannunta ta amshi Noor ta mana masa kiss a lips dinsa tace "Toh Allah ya tsare babyna...." Yace "Uhn you are looking for trouble koh" yar dariya tayi ta kashe masa ido tace "Don ma ban maka french one ba" Ya wara ido yace "Toh mu je daki ki min" ta hararesa tace "Naki wayon" juyawa yayi ya fita yana murmushi, yau ranan farin ciki ne gareta don a ranan xata sama qualified pharmacist, a ranan xa ayi convocating din su, kafin Aliyu su shigo gidan ta gama komai tana jiran Ummarta da yanxu take auren yayan mahaifiyarta wato dad din su Maimoon, tare da Baby uwar gida ga Barrister Sudais, fitowa parlor tayi jin shirun Aryan yayi yawa, xaune ta ga little balaraben kan kujera kiris yake jira ya fara kuka, ta karasa gun sa tana murmushi ta ajiye Noor, ta daukesa ta rungumesa tace "Haba sweetheart, in dafa maka indomie xaka ci?" Kitchen ta koma tana rike da shi ta daura ruwan indomie sanin abinda yake ci kenan, tana tsaye har ya dahu ta juye a plate ta dawo parlor ta xaunar da shi ita ma ta xauna ta shiga basa, Babu inda ya bar ubansa tun daga kyau har gashin kansa, hatta idonsa irin na babansa ne, murmushi tayi tana ci gaba da ba sa indomien yana ci, tana gama basa ta wuce daki da shi ta sauya masa kayan jikinsa duk da ba su yi komai ba ta dauko masa favourite toy dinsa ta basa ya amsa ta kunna masa cartoon ta xaunar da shi kusa da Noor da ta kwanta kan kujera, sannan ta shiga daki don yin wanka, tana shiryawa bayan ta fito ta ji shigowar mota, ta gama saka kayan da sauri ta fito, Aryan na ganin xata fita ya sauka saman kujera xai fara kuka, ganin haka ta dawo ta daukesa, Noor ta fashe da kuka ita ma, dariya tayi ta dauketa ita ma, tana rike da su ta fita compound, tsaye tayi tana murmushi ganin motar Khaleel ne, jawahir ta fito daga motar, Aryan na ganinta ya fara murna, khadijah ta saukesa yaje da gudu ya rungume uwarsa ta daga sa tana dariya tace "Kai lallai khadijah, dubi yanda kika maida min yaro kato, wani irin abinci kike basa haka" dariya khadijah tayi tace "Bayan ma ya rame, duk kwanan nan a dole yake xaune gidan, naga alamar kewar ki yake" Khaleel ya fito daga mota yana murmushi ya nufo ta yace "Oum shureim good morning" tana murmushi ita ma tace "Morning doctor...." ya amshi Noor yana shafa dogon gashinta idonsa a kan khadijah yace "Congrat once more, Allah ya sanya alkhairi, our pharmacist..." Tace "Ameen Thumma Ameen, thanks much Abu Aryan" Bata rufe baki ba motar Aliyu ya shigo gidan, Baby ce ta fara fitowa daga motar tare da little Amira, khadijah ta wara ido tana kallonsu ta nufe su da sauri, Barrister Sudais ya fito daga gaban motar with Shureim, sannan Umma da ta fito ita ma rike da little Farouq yaron da baxai wuce wata bakwai ba da baby take goyo, khadijah ta rungume baby cike da murnan ganinta suka dinga babbaka dariya, lkci daya ta tafi gun Ummarta ta rungume ta ita ma, tsabar murna ta kasa cewa komai, ta rasa me xata ce, tana sake Umma ta daga handsome yaronta sama ta rungume sa ya dinga kissing fuskarta very happy seeing her..... Aliyu ya fito ya jingina da mota ya rungume hannunsa yana kallonsu, Kamar yanda Barrister Aliyu da Dr Ayman ke kallonsu suna murmushi su ma.... *ALHAMDULILLAH* A nan na sauke littafina mai taken *Noor-Al-Hayat* kurakuren da nayi a ciki Allah ubangiji ya yafe min....👏🏻 Darussukan dake ciki Allah yasa mu amfana da su Amin. Ina mika sakon gaisuwata xuwa ga mahaifiyata Hajiya Hajarah... She is my first love, my role model, my momma, my world, my everything... Allah bar min ke Hajjaju Yaya❤ My sweet Anty Didi ur daughter Jiddo is greeting with respect, tnx for being there for me during this book, Allah ya raya su Aneesah... And my second role model Anty Rukaiyya...😍 am so grateful for the encouragement from the beginning of this novel till the end, I always gat ur back small mum ur daughter Khaleesat Haiydar is saying a big thank you, Allah bar mu tare ya raya Little Khaleesat Haiydar, Baby and Jaheed... Na sadaukar da littafin *Noor-Al-Hayat* xuwa ga lovely sister na, my Blood... Khadijah M Bello (Amira/Baby) nd my sweet cousin like no other Khadijah Sadi Yusuf (Baby) Allah ya albarkace rayuwar ku ya raya mani ku bisa imani, ya baku ilimi mai albarka da amfani. Sakon gaisuwa ta na musamman xuwa ga wa enda for sure ba siyan littafin Noorul Hayat suka yi ba, ihisani kawai suka min, duk ina sane da ku kuma na so contacting din ku but I lost my contacts, ban san ya xan yi in same ku ba, Amma ku sani I will for ever be grateful, Allah ya biya maku bukatun ku na alkhairi duniya da lahira, nagode nagode.... And finally my fans, ban taba xaton yea da gaske I have fans ba sai a littafin nan, you guys really patronized me fiye da tunani na, you all made me feel loved😥 words alone can't express how happy I am, ku sani... Billah Khaleesat na ji da ku har ranta, Ina son ku, Ina alfahari da ku, Ina maku fatan alkahiri, Ina maku fatan rabuwa da iyayen ku lafiya, Ina maku fatan daukaka, Ina maku fatan gamawa da duniya lafiya, ina maku fatan samun aljanna, I wish you all the very very very best in life, nagode nagode nagode... Allah ya sa mu cika da imani ya yafe mana kura kuran mu...👏🏻 Taku har kullum Hauwa Bello Jiddah (Khaleesat Haiydar) 📚✍🏻 Thanks once more for patronizing my book fans... For those still wanting to buy the complete document it's just 300 Via transfer 👉🏻 3276052019 Hauwa Jiddah Bello, fcmb. 07087865788. Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels