Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels 🌹GIDAN AUNTY 🌹 A heart touching love story Story & written By Aysha galadima ( mss Lee💕) https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 📚UK WRITERS (Unique kingdom writers)📚 Sabuwar marubuta masu tafiya da saban salo me kayatarwa. Littafina kirkirarran labarine banyi dan cin zarafin wani no ko wata ba, duk Wanda labarina ya zo daya da nashi yayi hakuri rashin sani ne. Yadda na fara littafinnnan a Sa’a Allah ya bani ikon kammalashi.. Bismillahir rahmanirrahim….. Paid book Book 1📕 Free page 1 TAHEE!!! TAHEE!!! “Naam oumma “ cewar wata yarinya wacce kallo daya zaka mata kasan bazata wuce 16 to 17 years ba, ta fito daga cikin wata kofa da kallo daya zaka mata kasan daga kitchen take, sabida flour da ya Dan bata mata jiki.” Har hanxu baki gama kwabin ba , kinsan abbanku ya kusan dawowa kuma kinsan inyazo ya taddaku haka ran mune zai baci duka ko!”kiyi hakuri oumma na kusa gamawa TAHEER nake jira ya taimakamun …”bata kammala magana ba sukaji anshigo falan ko sallama babu, Mai da hankalinsu sukayi kan kofa . Wata yarinyace itama da bazata wuce 15 to 16 ba a tsaye sai faman ya tsine take kamar wata babba, kura mata ido TAHEE tayi dan jiranjin mai zatace, dan tasan zuwan ameerah ba alkairi bane. Kamar kuwa ta shiga zuciyarta , “maryam dake da TAHEE wai Kuzo inji abba…, bata kammala maganar ta ba sabida saukar marukan da taji a waje maban banta. Kuka ta saki mai kara tana jiyowa. Karo taci da TAHEER da TAHEERA a tsaye sai faman huci suke saki, TAHEER ne ya soma magana “sau nawa zan fada miki duk lokacin da Kika kwaso rashin kuryarki ki dunga ajje ta a waje kafun ki tako mana daki, mahaifiyar Tamu kike dan baki da kunya “, kuka kawai ameerah take dan ba karamun zafin marin tajiba, dafe kuncinta tayi dagudu ta bar dakin . Kallansu oumma tayi cikin hade rai,”sau nawa zan ja muku kunne kudinga hakuri da mutanan gidan nan, ko so kuke kudinga ganin raina yana baci” , kamar hadin baki TAHEER da TAHEERA suka ruke kunnuwansu ,”oumma kiyi hakuri bazamu sake ba “, Daman ta San halinsu, dungure musu kai tayi, atare suka saki dariya dan dama sunsan ba fushi tayiba. Kamo hannayensu tayi tare da hadewa waje daya , TAHEE!! Naam oumma! TAHEERA ta amsa mata, maida kallanta tayi wajan taheer shima ta kira sunansa, amsa mata yayi shima yana kallanta. Numfashi oumma ta saki kafun ta soma magana cikin Sanyi , “ku kadai Allah ya bani, banaso kuna saurin fushinnan, inaso ko bayan raina kuzama masu kaunar juna kunji, ku zama masu hakuri da kawaici, Musamman Kai TAHEER , kafi saurin hawa”. Murmurmur taheer yayi tare da dan sosa keya, oumma kiyi hakuri, hararar wasa tasakar masa daman anan kafi kauri wajan bada hakuri. Kema taheera ki shiga taitayinki , hada ido Taheer da taheera sukai tare da hada baki , oumma kiyi hakuri bazamu sake ba . Girgiza kai oumma tayi kawai, basuyi wata wata ba suka rungumeta, hado kansu tayi su biyun ta rungume a jikinta. Suna cikin zamannan sukajiyo bugun kofa da karfin gaske , duk mimmikewa sukai tsaye, bakowa bane face abba sai faman huci yake bayansa kuma mamy ce hannunta rike dana Ameerah sai faman cika take . Baiyi wata wata ba ya tsinkawa oumma mari, Maryam sau nawa zan fada miki ki fita harkar yata,me yasa bakyajin magana, Tom bari kiji na fada miki na gaji da wannan halayen naki, ki tattara kayanki kije na SAKEKI. Kafun na dawo gidannan banaso naga fuskarki data yan iskan yayanki , sannan fuuu ya bar wajan. Shewa mamy ta saka toh maza maza azo abar mana gida tunda anzama bazawara, budar bakin ameerah sai cewa tayi da Yayan zawarawa sanin cewa ba mai tabata tunda uwarta na wajan , sai da mamy ta gama babatunta da zafesu tasss sannan takama hannun yarta sukabar wajan. Zubewa umma tayi a kasa zuciyarta na faman ta farfasa ga kuncin da zuciyarta ke mata, fashe wa kawai tayi da kuka, TAHEE ma zubewa tayi a kasa tana kuka sosai, TAHEER ne mai dauriyar cikinsu yake lallashinsu, abun yayi masa ciwo sosai, asaki mahaifiyarsu agaban idansu dan basu da gata. Abbu nayi kewarka , ALLAH YAJIKANKA ABBU!! Shima sai ya fashe da kuka , haka suka kwashi kusan minti 15 suna abu daya , ganin sunki daina kukan Yasa oumma tsayar da nata kukan, tashiga lallashinsu. Ganin sunyi shiru yasa ta mikewa, daki ta shiga ta tattaro musu Kayan sawarsu cikin jakunkunansu, sannan tasa taheer yasamo mata motar akurki dan kwashe mata kayansu, ba jimawa kuwa sai gasu, lokacin abba ya fita shiyasa mai akurkin ya shigo ya taimaka musu suka kwashe kayan.Mamy na labe ita da wata kawarta sai faman kwasan dariya suke , bayan sun gama kwashe komaine suka fito waje , oumma ta janyo kofar bangaransu Wanda ko cokali datasan natane bata bar musu shi ko daya ba. Awaje ta tarar da mamy ta fito sai habaici take tana kwasar dariya kawarta na tayata, sabida rashin tarbiyya har ameerah ce ke kiransu zawarawa da yayan zawara wa uwarta na biyemata. TAHEER da TAHEERA kuwa suna gefe sun cika bamm ji suke Idan suka kama ameerah ba abunda zai hanasu lallasata . Kamar oumma tasan abunda ke ransu takamo hannunsu suka fita , saida suka fita oumma ta fara tunanin ina zasu koma da zama. Ba yadda ta iya dole su koma BUNKURE da zama , Wanda ba tsoran komawa take ba , aah yadda rayuwar yayanta Zata koma , batasan abunda zai kuntata wa yayanta, ganin tsayuwar ba mai anfani bace yasata yiwa me motar magana , bawan Allah bunkure zaka Kai mu nawa zan baka, 7k zaki bayar. Haba bawan Allah kadan duba mana, shikenan ku kawo 6k , kallan TAHEE da TAHEERA tayi da su shiga , ko wannansu jiki a sanyaye yashiga inda abunda suka tsana shine zuwa bunkure yadda ake gallazamusu suda mahaifiyarsu, ba adau lokaci ba suka fara tafiya kowa yayi jigum ba meyiwa wani magana kowa da abunda Ke cin ransa. ASALINSU….. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ GARIN LAGOS Wasu dankara dan Karan Motocine kefaman zuga gudu akan titi, duk Wanda yazo wucewa sai ya tsaya motocinnan sun wuce tukunna sabida tanbarin da motocin ke Dauke dashi .Duk uban motocinnan basu tsaya a ko ina ba sai a NAHYAN HOSPITAL, one of the best hospital in Nigeria , ba karamun hospital bane da kallo daya zaka masa kasan ba karamun kudi aka kashewa asibitin ba , Kai tsaye wajan parking space suka nufa , cikin wani irin slow motocin suka tsaya , Wanda hakan ba karamun birge masu wucewa yayi ba . Bude motocin akai , wasu blacks American ne suka fito daga cikin motocin ko wannensu sanye da bakin suit da sunglasses,fuskarnan ba fara’a kwata kwata , yayin da hannunsu ke dauke da bindigogi. Daya daga cikinsu ,Wanda ya kasance kamar ogansu ne ya nufa wata black tinted Lamborghini sai faman sheki da daukar ido take.bude kofar motar yayi sai da aka dau kusan 40 seconds kafun ya zuro da kafarsa Guda daya , tubarkallah Masha Allah , wani irin takalmine a kafarsa kamar na sarauta, fatar kafarshi sai faman daukar ido take, wacce take fara kal cikin takalmin kafarsa, an dau kusan 2 minutes kafun mamallakin kafar fitowa. Oh my god , tubarkallah masha Allah , tabbas Allah madaukakin sarki yayi halitta anan, ba kowa bane face TAHNOON , one of the youngest billionaire kenan, daga tsohon president zayed Al_Nahyan, irin su ake kira one in thousand,dan guy din ya hadu tako ina ba Karya. Sanye yake cikin kuftan sai faman maiko da daukar ido take , wacce ta kasance blue colour , bakaramun kyau tayiwa surar jikin saba , wacce ta kasance kakkar fa, kallo daya zaka masa kasan yana motsajikin sa ,farine irin asalin fari mai shegen kyau da tsari, yana dauke da wasu irin sexy eyes fari tass dasu, kwayar idanshi ba Baka bace sannan ba brown bace ,wasu irin idanuwane dashi mai ladaftar da makaryaci, Wanda idanuwansa ba karamun tafiyar da yan mata yake ba, hancinshi dogone ba irin over dinnan ba, amma dogone da yayi matukar yiwa fuskarsa kyau , bakinshi dan madaidaicine Wanda ya kasance pink colour , yana da saje a fuskarsa wanda ya hade da gyaran fuskarsa. Kallo daya zaka masa kasan irin mutanan nanne da ake Kira half cast , ta ko ina gayen nan ya hadu, cikin taku da kasaita ya fara tafiya , Wanda da yawa mutane suke wa kallan girman kai, musamman in ya hadu da kasaitarsa da muskilanci , dan ba karamun miskili bane na bugawa a jarida, amma a hakan ba karamun tafiya yake da imanin mutane ba . Direct cikin premises din hospital ya nufa , duk inda ya wuce sai ma’aikata da majin yata sun gaishesa , daga musu hannu Kawai yake ,yayin da wadannan kattin ke binsu a baya , Daidai wata kofa naga sun nufa wacce ta kasance ta glass , kai tsaye wannan mutumin dazun ya bude masa kofa , lifter ce a wajan , shi kadai ya shiga wajen tare da wannan mutumin , yayin da Sauran suka tsaya . A flour 4 suka tsaya inda yakasance bakowa a wajan ( abun mamaki sai na tarar da wannan kartun sunja layi kamar masu jiran karban sadaqa😂), duk inda ya wuce sai sun Sara masa . Daidai wata kofa suka tsaya , anan ma wannan mutuminne ya bude masa kofa , tafiyar muntuna 2 biyune ya kaisu wata kofar , wata koface tsararriya a wajan me shegen kyau , direct cikin kofar suka shiga , babban office ne iya tsaruwa office dinnan ya tsaru, daga gefan hagunsa wasu dan ubansun cushion chairs ne masu shegen daukan ido ash colour , medium carpet din office din ma ash colour , daga gefan damansa kuma wani gadan duba marasa lapiya ne , daga inda kake kana iya hango table dinshi sai faman daukan ido yake ( irin na yan gayun nan😂), wajan sai faman daukar kamshi da sanyin freshener yake . Samun waje yayi kan daya daga cikin cushion chairs dinnan yayi tare da crossing legs, kallan mutuminnan yayi , cikin husky voice dinsa ya fara magana ,”zaki” shine Sunan da naji ya Kira mutuminnan Wanda in ba natsuwa kayi ba bazaka taba Jin mai have ba, “yes sir “Cewar zaki , “yaushene meeting dinnan”, “sauran few minutes sir “cewar zaki, jinjina masa kai kawai king Yayi tare da Mika masa wasu files karba zaki yayi tare da Sara masa tare da ficewa daga office din , duk wannan abun da yake fuskarshi kwata kwata ba annuri a ciki , ba a dau dogon lokaci ba daya daga cikin wayoyinsa ya fara ringing , sai da ta kusan katsewa sannan ya dauki wayar dake kusa dashi akan center table din gefenshi , UKTI shine sunan da ya bayyana akan screen din wayar , ajiyar nunfashi ya sauke ganin me kiran, dauka yayi cikin kamilalliyar muryarsa, “Assalamu alaikum”Shine abunda yace , ya dau sakanni kafun ya sake cewa komai, “masa’ul khair ukti( barka da Yamma yaya)”, bansan mai akace masaba amma ganin yadda ya natsu zai tabbatar maka da magana ce me mahimmanci suke tattaunawa,ya dau kusan 10 minutes yana wayar wacce ba abunda nakeji a ciki kasancewar cikin larabci yake maganar , baka Jin sautin muryarshi sai bakinsa dake motsawa, a haka zaki yazo ya tarar dashi , sannan suka dunguma zuwa inda aka kebanceshi dan yin meeting . Sun dau kusan 1 and half hours suna tattaunawa game da asibitin da kuma tsare tsaren da za a sake , basu sukabar NAHYAN HOSPITAL ba sai wajan karfe 5 na yamma, Kai tsaye NAHYAN ESTATE dake cikin BANANA ISLAND suka nufa . 🌹GIDAN AUNTY🌹 By mss Lee💕 👑 UK WRITERS 👑 https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 🫶 Dedicated dis page to my masoyiya ‘yar fillo ta zara’u our star lady ! I heart ❤️ you 🫶… PAID BOOK BOOK 1 📕 ……………..بسم اللهً الرحمنً الرحيم Free Page 2🦋 ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ WACECE TAHEERA TAHEERA yarinyace yar kimanin shekara 17 da dan biyunta TAHEER Wanda suke tsananin kama kasancewarsu yan biyu. Mahaifinsu Malam Mohammad nada wadatarsa kafun yasamu karayar arziki ,yarasu shekaru biyar baya , Wanda a kazo har gida akwai wa kisan gilla, kisan da haryanxu ba’a san ko suwanene ba , yana da mata guda daya me suna maryam wato oummansu taheera , haifaffiyar buzuwace fara tass da ita daga kasar Niger , anan suka hadu da mahaifin su taheera, Wanda yazo kasuwanci kasar. Mahaifiyarsu marainiyace wacce iyayenta suka rasu bata da kowa sai yayanta Wanda tun lokacin baya daya fita da daddare ba’a karajin labarinsaba . Bakaramun wahala da gwagwarmaya suka shaba arayuwarsu , tun bayan rasuwar mahaifinsu taheera , kasancewar dangin babansu basu so ya auretaba, sun so ya auri yar dangi amma malam Muhammad ya nuna baya Santa maryam yakeso . Bakaramun wuya maryam Tasha ba a hannun dangin mijinta, babu me kaunarta sai KILISHI, wacce ta nuna mata so, ta tallafi yayanta har bayan mutuwar yayanta. Kilishi kanwace ga Malam Mohammad wacce suka hada baba dashi kasancewar shi kadai mahaifiyarsa ta haifa sai yan uwa . Ba karamun rawar gani ta taka arayuwarsu ba sabida irin yadda take temaka musu.Itace mace kwallinkwal da take fadar magana aji atake a wajan dalilin Auran wani hamshakin me kudi da take a Garin Lagos , shiyasa duk dangi akejin maganarta.Bayan shekara biyu da rasuwar Malam Mohammed, Malam bashari yanuna Yanasan auran maryam amma kememe maryam ta nuna bazata iya aure ta bar ‘ya’yanta ba , ba irin magiyar da Malam bashari beyiba har maganar tazo kunnen hajiya kilishi, sanin cewa bazata iya yiwa hajiya kilishi musu ba yasa ta Amince amma da Sharadin tafiya da yayanta. Wannan abu beyiwa Malam bashari dad’i ba amma haka yabar abun azuciyarsa. Hajiya kilishi ita ta dauki nauyin kome da kome na bikin maryam, tundaga kan kayan daki da sauransu, shiyasa ba karamun ganin girman matar takeji ba. Shiganta gidan bashari ba karamun wahala Tasha ba ita da yaranta, sabida tsangwaman da ake nuna wa ‘ya’yanta hatta abinci baya bawa ‘ya’yan maryam , ko ta tanbayeshi dalili kaitsaye ze ce mata sabida bashine ubansu ba. Wahalar dasu d’in da yake ne yasa maganar har taje kunnen kilishi Wanda takirashi tayi masa tatas harda i’kirarin zata kulleshi sannan ya saduda. Malam bashari yana da matarsa daya kafun ya auro maryam, asabe kenan wacce suke kira da mamy, mamy wata irin muguwar matace da batasan zaman lapiya , duk wani kulli kulli da tashin hankalin dake faruwa a gidan harda sa hannunta, da farko taso kullum su dunga danbe amma ganin maryam bata biye mata yasa ta canza taku take biyowa ta bayan malam bashari.yar ta d’aya Ameerah , yarinyace fitinanniya bata jin magana , ga rashin kunya a cikinta , Ameerah ta tsani y’ay’an maryam kasancewarsu farare tass kamar ka taba namansu ya fashe wani irin kyaune da su da baki baze musaltaba musamman tahee da take da asalin gashin buzaye har kugu, kasan cewar mahaifiyar su buzuwa mahaifinsu kuma bafulatani . Dalilin da yasa mamy da yarta suka dauki Karan tsana suka dora musu, dan ko ita mamin tasan maryam ta wuceta akomai amma sabida harsada da kyashi taki barinta, a haka har suka kwashe tsawan shekaru uku kafin yanxu rabuwarsu da Malam bashari. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ BANANA ISLAND unguwace ta wane da wane da ta amsa sunanta, a jere motocin suke tafiya , tun kafin ayi horn sojojin dake gadin first gate suka wangale musu kofa, tare da Sara musu, wata iriyar koface a wajan kallo daya zaka mata kasan ba Karamun makudan kudi aka kashe akanta ba, cikin kwarewa motocin suke tafiya harsukazo gate 2, nan din ma wani abun kallo ne , karamun titi ne a wajan sai kananan shukokin dasukayiwa wajan kwawanya, wajan bakaramun haduwa yayi ba , minti uku kacal yakaisu main gate din gidan inda yafi ko ina tsare sabida sojojin da ke ke waye da wajan .sanin Wanda yake cikin motar yasa ba bata lokaci aka wangale musu gate , wow !! Wow !! Wow !! Shine abunda bakina ke furtawa tunkan na karasa shiga nasan bakaramun gida bane wannan, dan filine a wajan me dauke da korayen shukoki inda yayi wa wajan kwawanyaw, babban estate ne me dauke da part part na musamman, duk inda ka kalla zaka ga alamun hakan sabida giftawar da masu aiki keyi lokaci lokacin cikin shigar uniform Dinsu . Kai tsaye wani babban glass building motocin nan suka nufa Wanda yakasance daban cikin buildings din , Daidai parking lot din building din motocinnan suka tsaya , ba bata lokaci duk suka fito daga motar, yanxun ma zaki ne ya bude masa kofa, sea da ya dau tsawan lokaci kafun ya fito gaba daya daga cikin motar, Sara masa sukayi a tare , ba Wanda ya kalla a cikinsu sai ma kara tsuke fuskarsa da yayi , a hankali ya fara tafiya cikin takunsa kamar bayasan taka kasa direct main door ya nufa , still zaki na biye dashi har cikin farlon da ya gama haduwa , direct wata kofa ya nufa , shi kuma zaki files din hannunsa ya ajje tare da ficewa gaba daya daga cikin building din. WANENE TAHNOON TAHNOON Wanda ake wa lakabi da KING , shalele kuma mafi soyuwa a wajan mahaifinsa , saurayine Matashi dan kimanin shekara 33 a duniya . Mutumne me matukar dukiya , kasaita da kuma miskilanci , bayasan raini ko kadan,baya shish shigi da shiga sabgar kowa , King babban muskiline Wanda da yawan mutane ke yiwa kallan girmankai, dan da wuya kaji yayi dogon magana da mutum, yawancin maganarsa da idone,king ya kammala karatunsa na likitanci a kasar turkey, a yanxu haka doctor ne shi babba daya karanci bangarori na lafiya, mutum ne shi me temako da sanin darajar mutane , amma in ba zama kayi dashi ba bazaka taba sanin hakan ba. King na da babban asibiti mai suna NAHYAN HOSPITAL, asibitine da yake temakawa marasa karfi duk da kasancewarsa asibitin kudi.wannan dalili yasa mutane ke ganin girmansa da kimarsa.Wanda duk Garin Lagos da ke wayanta zaka samu talakawa nazuwa Neman temako, Hakan yasa talakawa ke mugun sonsa da kaunarsa. Ko guri zaibi zakaga manya da yara na daga masa hannu tare dayi masa kirari, hakan yasa yayi suna sosai a fadin Nigeria dan ba Garin Lagos kawai yake temakawa ba , shiyasa da yawa masu kudi basa sanshi. Mahaifinsa zayed-al-nahyan babban dan siyasane Wanda har mukamun shugaban kasa ya ruke , kuma hamshakin me kudine dayayi Fuce a kasar Nigeria gabaki daya da ke wayanta. Alhaji zayed mutumne adali me temakon jama’arsa,shiyasa ake matukar girmamashi, Adalin shugaban kasane Wanda har yanxu mutane suke kwadayin ya kara shugabantarsu.tsohon shugaban kasa yana da mata biyu, matarsa ta farko Itace hajiya suhaima, hajiya suhaima balarabiyar dubaice daga ita sai yayanta da kanwarta iyayenta suka haifa, macace me matukar miskilanci da kawaici, ga tarin dukiya da Allah ya bata , ga ilimin addini Dana zamani. Hajiya suhaima yayanta 4, Babban d’anta sunanshi mohammed amma Allah yayi mishi rasuwa shekarun baya da suka wuce sai ‘yarta ta biyu samreen suna kiranta UKTI , tayi aure yanxu tana saudiya ita da mijinta, sai king da autarsu zoya. Matarsa ta biyu Itace hajiya kilishi , kamilalliyar mata wacce tasan ya kamata , macece me matukar wasa da yara , baruwanta Sabida kyautatawar ta yasa yawancin yayan gidan suna part dinta. Yar ta d’aya zulaiha wacce ta rasu tun tana yarinya. Suna rayuwane da familyn su cikin da Kaunar juna, tare da kakarsu dasuke kira Dada. Dada masifaffiyar matace gata da rigima ta bugawa a jarida, amma hakan besa ta wulakanta kowa ba , mutumce me temako da san jama’a, duk cikin jikokinta tafisan king duk da yawancin lokuta cikin rikici suke da ita , sai uncles Dinsu guda biyu uncle musaddiq da uncle salim, suma ko wannansu na rayuwa agidan tare da iyalinsa. Uncle musaddiq na da mata biyu hauwau wacce suke kira da mamy tana da ‘ya’ya 3 , kabeer , ihsan, sumayya sai matarsa ta biyu kubra ana ce mata momy tana da ‘ya’ya 2, haroon , firdausi(feedy). Uncle salim kuma matarsa daya mai suna amina ana ce mata aunty , basu da ‘ya ko daya sai ‘yar rikonta mai suna amrah, sabida duk dan data haifa baya dadewa suke mutuwa sai kanwarsu zarmeen wacce take aure a abuja da danta sha’aban. Cigaban labari… ➰➰➰➰➰➰➰➰ Sai gabanin yamma suka karaso bunkure , lokacin ba karamun jigata sukayi ba, daidai babban gida na kasa daya kasance kamar family house suka tsaya , nan yara suka fara taruwa , ga yan birni , ga yan birni Wanda labari har ya fara karadewa . Nan mutanan gidan suka fara leke dan ganin ko suwanene, mutanan da suka ganine yasa su fara kuss kuss ana tuntsurar dariya , duk wannan abun da ake taheer and taheera na gefe, itama oumma duk jikinta a sanyaye yake harta kammala biyan mai mota kudinsa bayan ya temaka musu ya sauke musu kayansu . Tun a soran gidan suka fara cin karo da kwano, ga Shara a wajan. Oumma ce tayi sallama yayin da taheer da taheera ke bayanta,gaishe da su oumma da su tahee sukai ganin babu raya yanxu agidan ma duk an aurar dasu sai wa ‘inda ba a rasa ba, cikin izgili da wulakanci suka fara amsa musu gaisuwar tasu, tare da habaice habaice kowa na fadar albarkacin bakinsa . Wata tsohuwa ce ta fito daga wani daki gashin kanta duk yayi furfura da kar take iya tafiya,”wa nake gani kamar maryama da bankadaddun ‘ya’yanta, me ya dawo daku kuma , ko da yake daman kun saba zuwa ba nosis (notice).”to Nide wallahi babu ruwa na ga dakin kucan ba Wanda yake shigarmuku sabida hajiya kilishi ta Hana, amma wallahi bazaki takurani ba,”wai ma tsaya uban me ya kawo ku wannan karan kuma “, sun ku yar da Kai oumma tayi dan kwata kwata ta kasa magana ma, taheer da taheera kuwa ko wannansu hade rai yayi, in akwai abunda suka tsana a zagar musu mahaifiya. Tabe baki kaka ta bawa tayi” oh ni ‘yasu kujimun muna furci daga tanbaya sai ki wani fara sum sum da kai sai kace wata muna fuka”.tun tsirewa mutanan gidan sukayi da dariya, yayinda ko wa ke tofa albarkacin bakinsa. Ganin abun nasu ba me karewa bane yasa oumma mikewa tare da nufar dakinta Wanda ya kasance na hajiya kilishi ne mallaka musu,dakine a ciki da falo harda d’an kewaye da aka d’anyi mashi daga waje.Balefi kusan duk cikin gidan babu inda ya kai nasu kuma kilishi ta Hana kowa kwace musu acewarta wata rana in suka zo zasu dunga zama a ciki. Shigarsu cikin ‘bangaren sai da suka d’auki tsawan lokaci suna gyaranshi dan ba karamun daud’a yayi ba, suna gamawa duk sallah sukai suka mimmi’ke ga yunwa sunaji amma ba daman cin abinci sabida sunsan ko zasu mutu mutanan gidan bazasu basu ko ruwan shaba. Haka suka zauna oumma da tahee suna daki d’aya yayinda taheer kuma yake shinfida a falo dakin. Cab cikin dare lokacin da kowa ke hutawa wani ba’kin haya’kine ke tashi kad’an kad’an kafun daga baya wannan bakin ya bace batt…, can dakinsu taheera kuwa wani abune kamar silver yake faman she’ki a jikin taheera yayin da fatarta ke d’auke da wannan silver d’in kamar na maciji, kafun wani lokaci ta rikid’e tare da dawowa katuwar macijiya, ko munti 2 batai ba jikinta ya kuma dawowa Daidai, sai nan ta kara dawowa wannan macijiyar, daidai gabanin asuba jikinta ya dawo daidai, kwata kwata babu alamaun wannan macijiyar. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ Comment and share ✍️ GIDAN AUNTY ❤️ (A heart touching love story) By Aysha Galadima ( mss Lee) 💖The talent troupe🔥 PAID BOOK BOOK 1📕 Bismillahirrahmanir rahim….. Free page 3 🦋 ➰➰➰➰➰➰➰➰ Wani kayataccen daki yashiga babban gaske me shegen kyau da tsaruwa , duk da kasancewar komai na part din da glass akayishi hakan be hana tsantsan kyauwun dakin boyuwa ba sai ma kara futo da ainahin kyan da yayi.Direct inda wardrobe din dakin yake ya nufa, daga jikin wardrobe din ya danna wani abu me kamar design , take wardrobe din dakin ya rabe biyu wasu manyan elevator guda biyu ne suka bayyana,na farko yashiga inda ya danna 3, direct floor 3 ya kaishi, wani katafaran falo ne awajan komai na cikin falon white colour ne hatta da labulayen dakin, ga wasu dan ubansun 2 set sofa masu shegen kyau a wajan suma white colour , daga kasanshi kuma wani lallausan farin carpet ne me shegen laushi, daga gefe a kwai standard glass da komai na cikinsa kana iya gani, iya haduwa falon ya hadu , baka jin komai na tashi sai sanyin ac da kamshin turare , a hankalii yake taka kafarsa kamar bayasan takawa, kai tsaye center table din falon ya nufa , remotes din dake center din falon ya danna, a hankali gefe daya na labulen ya fara budewa, tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki, wani kayataccen daki ne ya bayyana komai na cikin dakin white colour din hatta furnitures din dakin , babban gado ne a dakin me girman gaske sai shimfidarsa da ya kasance white and black,, daga gefe daya wani chair ne a wajan me shegen kyau shima white colour , iya tsaruwa dakin ya tsaru, direct toilet ya nufa ya dau kusan 30 minutes aciki kafun ya fito da white din jallabiya fara kal da ita , gaban mudubin dakin ya nufa wanda yake shake da mayuka mabanbanta da turaruka masu shegen kamshi,imperial majesty kawai ya fesa a jikinsa , take dakin yacika da kamshin turarensa , ba’ajin kamshin komai sai na imperial majesty daya cika dakin. Rawanin da larabawa ke daurawa ya daura akansa,inda ya futo cak a balaraben sa,ba karamun kyau kayan sukayi wa fatar saba , iya haduwa ya hadu , daga gefan fuskar sa kwantaccen bakin kashin kansa ne ya fito sai faman kyalli yake, bakin sajan bakinsa me shegen kyau ya futo da ainahin pink lips dinsa,rawanin sai ya kara futo da kyawawan idanuwansa masu zara zaran eye lashes ,tare da bakar gashin girarsa,iya kyau yayi kyau ba karamun na wasa ba, duk wanda ya kallesa sai yaso yasake kallansa, fatabarakallahu ahsanil kalikin shine abunda nake fada kawai a raina. Yanxu ma be zauna ba, wayoyinsa kawai ya dauka tare da ficewa a dakin baki daya.direct down stairs ya nufa yanxu ma ta elevator ya nufa, a kasa ya tarar da zaki, zaki na ganinsa ya sara masa tare da saukar da idansa dan ba karamun kyau uban gidan nasa yayiba , “tabbas ubangidan sa na da kyau , kyau da ake kira kyau” duk cikin zuciyar sa yake magana , cikinsauri kuma ya bude wa king motar da ya dauko kirar mercedez benz ganin ya karaso inda yake ,basu tsaya a ko ina ba sai babban masallacin dake unguwarsu,bayan idar da sallar magriba din ma basu bar masallacin ba sai bayan sallar isha’i, duk kallan da ake masa yanaji amma ko dako wa yaga masu kallan nasa beyiba sai ma kara tsuke fuska da yayi, ana idar da sallah zaki yaja motar tare da barin unguwar baki daya. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰ Sallar asubane ya tayar da oumman nasu, tahee!! Tahee, “uhm” cewar tahee, oya a tashi lokacin sallah yayi, yanxu ma “uhm”ta karacewa kafun a hankali ta soma adduar tashi daga bacci,falo takoma tare da tashin taheer, ganin ya’ki motsawane yasa oumman mi’kewa “nasan sarai kana jina maxa ka tashi kafun ranka ya ‘baci”, murmushi yasaki tare dayin adduar tashi daga bacci, dama ya rigada ya tashi tun lokacin da oumma ta fara tashin taheera ya farka. mimmikewa sukai tare da dauro alwala kasancewar har gidan ana jin kiran sallah yasa su bin jam’i, bayan sun idarne ko wannan su yayi adduar safe da maraice kamar yadda suka saba a kullum,”oumma ina kwana”duk suka hada baki wajan gaishe da oumman tasu, murmushi oumma ta saki”fatan ‘yan biyu na sun tashi lapiya”, “lapiya lou” suka amsa mata.suna zaune sukaji sai faman buga musu kofa ake , tashi oumma tayi tare da bude kofar , ba kowa bace face kaka tabawa , daure da daurin kirji, gaishe da ita oumma tayi, tabe baki kaka tabawa tayi “ba gaisuwarkice ta kawoni ba, maza maza ki tashi kigyara tsakar gidan nan ga wanke wanke na jiranki, sannan kisaka tanbad’ad’d’un ‘ya’yanki su d’ebo mana ruwa,dan ba hutu kuka zoyiba”. “Insha Allahu zamuyi”cewar oumma, yanxun ma tabe baki kaka tabawa tayi”ke kika sani, kar Allah yasa kiyima”tana gama fada ta bar wajan , koma wa daki oumma tayi , yanda ta barsu a haka tazo ta samesu sabanin dazu yanxu ko wanne ya yi cidin cidin da fuska dan sarai sunji me kaka tabawa kecewa, murmushi oumma ta saki “kuyi hakuri yan biyun ummansu wata rana sai labari ai”,jikinsu ne yayi sanyi jin abinda oumma tace.kamo hannunta sukayi tare da sata a tsakiyarsu,”kiyi hakuri oumma ba wai fushi mukai ba , kawai bamasan abunda kaka tabawa da mutanan gidan nan suke miki”,shafa fuskar taheer dake magana oumma tayi,”bakomai taheer komai me wucewa ne bana so kuna sa abunda da suke mana a ranku, yanxu ku tashi kudebo musu ruwan da sukace kunji, ku kula sa hanya banda rigima”, “toh oumma “duk suka amsa mata , itama wajan ta biyosu tare da fara sharan tsakar gidan. Sun dau dogon lokaci suna d’ebo ruwan , lokacin har oumma ta kammala share tsakar gidan da ya dawo kamar bashine me tarkace ba. Tulun kayan wanke wanken suka hada ‘kuda sai faman bin kwanukan suke, sundau dogon lokaci suna wanke kwanukan , dadin su daya ma haduwa sukai su duka suka wanke dan ba karamun kwanuka aka bata ba ,gama wanke wankensu ba dadewa aka kawo markadan wake , zama tahee tayi ta buga wannan kullun, yayinda oumma ke hura jikakken ican da aka jika duk idanuwanta sunyi ja sabida yadda hayakin ya cika mata ido. Duk wannan abun da suke mutanan gidan sai faman kai kawo suke , ba wanda yace dasu ko sannu sai ma banzan kallan da ake binsu dashi da hantara.basu suka kammala ba sai wajan karfe shadaya,ragowar guntun dumamen tuwan jiya kaka ta bawa ta mikowa oumma,” kar alashemu ace bamu baku abinci ba ko akai mu duniya” cewar kaka tabawa ,kallan tuwan da baifi cin mutum daya ba oumma tayi, batace komai ba sai ma daki da ta nufa , anan ta samesu sai faman sauke nunfashin yunwa suke ,kwallace ta tarar mata , ganin suna kokarin mikewane yasata saurin goge idanuwanta kada suga rauninta, tuwan da ke hannunta ta ajje musu, cikin sauri suka mike tare da wanko hannayensu,har sun saka hannu zasu fara ci sai suka fasa tare da zubawa oumman tasu idanu,sarai ta fahimcesu amma ko motsawa batayi ba, langwabar da kai sukayi kamar wasu yara oumma suka kira sunanta , girgiza kai kawai oumma tayi tare da mikewa tare da zama a tsakiyarsu.taheer ne ya kutsuro tuwan tare da kallan oumman tasu “oumma haa” dariya duk suka saki ganin yadda ya bude bakin nasa , cikin kulawa yasa mata tuwan, itama taheera saka mata tayi a baki, hannu oumma ta saka itama ta fara basu a baki , duk da tuwan bashi da yawa amma haka ko wannansu yasamu yaci , cikin farin ciki da kaunar junansu. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ 10:20 pm motarsu ta danno kai cikin gidan , kamar ba dare ba har yanxu akwai hasken futullu da ya haska ko ina na gidan, daya daga cikin building din gidan zaki yayi parking , ya dau kusan 2 minutes zaune a cikin motar idanuwansa a lumshe kamar meyin bacci, a hankali ya zuro da kafarsa guda daya kafun a hankali ya juro da gaba dayar kafar tasa yana mikewa,cikin takunshi me kama da na izza ya fara tafiya tare da nufar kofar da zata sadashi da babban falon building din.Babban falo ne me kirgan gaske da ya cika da tsadaddun furnitures na alfarma , iya haduwa falon ya hadu ba abudna yake tashi sai daddadan kamshi da sanyin ac, ganin bata falon yasa ya juya da niyar komawa, foot steps dinta da ji ne yasashi tsayawa kafun ya juyo a hankali,murmushi ta sakar masa”son “ be amsa ba sai ma zuba mata kyawawan idanuwansa da yayi, sannu a hankali ta karaso wajan, sanye take cikin hijab hannunta dauke da tasbaha sai faman sakin murmushi take , sau da ta karaso inda yake kafun ya bude baki a hankali kamar wanda magana take wa wahala, cikin cool voice din shi me shegen dadi ya kira sunanta “Ammi,”hararar wasa ta jefa masa”sai yanxu ka tuna dani”lebensa ya motsa kamar me sanyin magana sai kuma ya fasa tare da dauke kansa, kamo hannunsa tayi tare da zaunar dashi kan daya daga cikin kujerun falon,”oya zauna ka ci abinci nasan yau kwata kwata ba abuncin kirki kaciba , na kusa yi maka aure kwanannan ko zaka shiga taitayinka”,bece komai sai hade fuska da yayi tare da kau da kansa, murmushi ta sakar masa “mai da wukar son wannan hade rai haka, nima wasa nake maka , ai samun wacce zata siyo zuciyar ka sai anshirya “a jiyar zuciyar da ko ammi dake kusa dashi bataji ba ya sauke tare da sassauto da fuskar tasa kadan . Abincin ta dakko masa da kanta tare da jerasu can center table din gabansa,zubawa tulun abincin data ajje a gabansa idanu yayi sai kace mutum goma zasu ci, bece komai ba sai idanuwansa da ya zuba mata ,sarai ta gane me yake nufi”duk suna part din dada tunda kai cin abinci cikin yan uwan naka ne bakaso”, lumshe fararan idanuwansa yayi, itama ammi bata kuma cewa komai ba sai abincin da ta zuba masa cikin hadaddan plate din da ta dakko, “oya haa” bude lumsassun idanuwansa yayi tare da kallanta, yanda tayinne yaso bashi dariya amma kwata kwata be yitanba, a hankali ya bude bakin nasa ta fara feeding din nasa , 7 spoon yayi tare da kawar da kansa,”son karkace mun kakoshi”lumshe mata ida nuwansa yayi, girgiza kai kawai ammi tayi tare da dakko masa hadaddan kunun ayar da tayi masa, sosai kuwa yasha kudin ayar bayan ya kammala shane ammi ta mike, “oya tuzuru aje a kwanta sea da safe”, bai ce mata komai ba sai mikewar da yayi , dariya amminta saki”bani na kar zoman ba rataya aka bani”inda sabo ta saba da halinsa na kinson yin magana tunda tasan halin kayanta,”Ammi sai da safe “ ya fada cikin husky voice dinsa, side hug tayi masa , Allah ya tashemu lapiya ka kwanta da wuri dan na san ka gaji, jinjina mata kai yayi alamar toh tare da ficewa. Har yanxu zaki na waje kikam kamar bushiya , inda ya barsa anan yazo ya samesa be ce masa komai ba , shima zakim bude masa kofar mota yayi, cikin takunsa na kullum ya nufi motar, haryasa kafa zai shiga sai kuma ya daga idanuwansa tare da kallan wani building sai kuma ya lunshesu tare da shiga cikin motar, daidai part dinshi zaki yayi parking yanxun ma shine ya bude masa kofa . “Sai da safe king”hannu king ya daga masa kabar bazai ce komai ba sai kuma ya bude baki a hankali “good night”. Murmushin jin dadi zaki ya saki be bar wajan ba har saida yaga shigewar king sannan shima ya barwajan. Direct yana shiga part din sama ya hau ta elevator , yana shiga dakin rawanin kasansa ya bayyana,kofar da zata sadashi da toilet ya nufa, ya dau mintuna a cikin toilet din kafun ya fito da wasu white pj mas masu laushi , imperial majesty ya fesa , dakin ya kara dauka da kamshin turaransa da ke kama daki,kan gadan sa ya nufa kai tsaye cikin luntsumeman gadansa, har ya kwanta sai kuma ya mike tare da dakko wasu magun guna .maganin hannunsa ya sha tare tare da bude bedside drawer. Har ya bude zai zubasu idanuwansa suka sauka kan wani hoto dan karami, daukan hotan yayi tare da zuba masa ido . Wasu matasan larabawane a jikin hoton sun rike hannun junansu, kana ganinsu kasan ba karamun kaunar junansu suke ba. Sauke ajiyar nunfashi yayi tare da mayar da magun gunan, shima hotan mayar dashi ma a daninsa yayi tare da danna wani remotes take futulun dakin suka dauke , wasu kaloli masu kyau da haske suka fara cika dakin me kama da dim lights , sannu a hankali bacci ya daukeshi. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ Comment and share 💖The talent troupe🔥 Writers of ….✍️ Duk karfin izzata Gidan Aunty Sarki sameer Jini daya Ya fita zakka….. 💖GIDAN AUNTY💖 ( A heart touching love story) By Aysha galadima ( mss Lee) 💖The talent troupe 🔥 PAID BOOK BOOK 1 📕 Bismillahirrahmanir rahim…… Free page 4 and 5🦋 Bugun kofar da akai da Karfine ya katsemusu hirarsu, TAHEER ne ya mike da Niyar bude kofar amma oumma ta tsayar dashi, “dawo taheer bari na bude” fita oummansu tayi suma mimmikewa sukai tare da bin bayanta. Yan gidan ne cike taf a wajan kowa sai faman zabga masu Harara suke , mazan gidan kuwa duk Wanda yaga taheera sai ya kara kallanta sai mafan satar kallanta suke sabamin matan dake harararta. “Munafukan Allah muna furcin me kuke kullawa, bayan kunsan akwai ayyuka a gabanku, shine dan muna furci da kinibibi kuka shige daki dake da ‘ya’yan ki masu kama da tattabaru” cewar wata da tafi kowa za’kewa a cikin su. Zuba wa sarautar Allah ido taheer da taheera sukai wai sune tattabaru hmm . Hakurin da suka ji oumma na bayarwa ne yasa suka maida hankalinsu kanta ,” kuyi hakuri Dije bansan akwai ragowar aiki ba shiyasa”. Matar da aka kira da dije ce ta Dallawa oumma harara “ kyaji da munafurcin ki, inba munafurciba ba me kuke kullawa a daki ko sallan karuwancin da kika saba kike koya musu” baki taheer ya bude daniyar yin magana amma kallan da yaga oumma tayi masane ya hanashi hakan , sun kuyar da kanshi yayi yana taunar lebensa. Wata daga cikin mutanan gidan ce ta soma magana itama “ kinsan dangin Matsiyata ba abunda suka iya sai tsiya in ba karuwanci take koya musu ba me suke yi a dakin”, nan da nan mutanan gidan suka fara musu gori da hantara , suna ci musu mutunci , kowa nagidan da abunda yake fada a kansu, kaka ta bawace kawai bata wajan . TAHEE da tunda aka fadi kalmar karuwanci idanuwanta Suka faru da ha waye ga wani irin ja da sukai, ba abunda ke mata yawa sai kalmar karuwanci ko magan ganun da mutanan gidan suke bata ji, wata gigitacciyar kara ta saki da ya firgita kowa dake wajan hatta taheer da ke kusa da ita, hannunta ya so kamawa amma ta hankadashi , daya bayan daya ta soma bin mutanan gidan da tun lokacin da ta saki ihu sukai shiru da kallo, ba Wanda ne tsure ba da irin kallan da take musu, ida nuwanta ne suka sauka a kan dije dake faman zare idanuwa , a guje tayi ganta , suna ganin hakan kowa na gidan ya Watse dan ba karamun firgitasu tayi ba daga mazan har matan. Wani murmushi taheer ya saki daman yasan za Arina, a zuciyarsa sai faman Allah shikara yake musu. Dije dake kokarin shiga daki tahee ta cafko, riko tayi mata ba na wasa ba , Innalillahi wa inna ilaihi rajiuna Dije take ta faman fadi , fuskar ta tuni ta jike da gumi sai faman zare ido take , jama’a ku kawo mun a gaji shikenan ni fatalwa ta kamani, kukai kawai Dije take majina duk ta bata mata fuska. Ita kanta oumma Dije ta bata dariya kuma ta bata tausayi dan Tasan kome zatayi yanxu TAHEE bazata hakura un tayi mata ta Karfi kuma rashin lapiyar tane zea tashi. Taheer ma dake gefe sai faman kunshe dariyarsa yayi ganin yadda Dije ke faman fadin fatalwa ta kamata. Kallan d tahee tayi mata ne ya sata kunshe bakinta “nayi shiru , Wlh nayi shiru” , tana gama fatar hakan ta rike bakinta gam hawaye na fita, Kwale idanuwan ta TAHEE tayi a kanta , take a wajan Dije ta saki futsari dariyar da taheer yake rikewane ta fito wajan dan ba karamun dariya ta basu ba. Baki TAHEE ta bude da nufin cizonta, lokaci daya kuma ta zube a wajan. Tana faduwa kuwa Dije ta arta a guje duk da kibarta a haka ta ke kudin tana tsine TAHEE a zuciyarta. Daukarta taheer yayi shi da oumma suka nufi daki da ita,” maza dakkomun maganinta “ cewar oumma , be dade ba ya fito dauke da roba a hannunta, ruwan adduar dake ciki oumma ta iba ta dan shash shafa mata a jikinta da fuskarta, nannauyar ajiyar zuciya ta saki , nun fashinanta na Daidai ta . Har yanxu akwai ragowar murmushi akan fuskar taheer , hararar sa oumma tayi” kasan Kai kadai ne zaka iya temakonta, me yasa baka temake taba kabarta a hannu tahee”, wani murmushin taheer ya saki” oumma kinsa konayi kokarin temakonta Nima hadawa zatai dani, ranta ya baci sosai ko nine naje wajan ba ragamun zatai ba “, jinjina Kai oumma tayi Alamar gamsuwa da maganarsa, wata ko daddiyar dari biyu ta dakko tare da mika masa” ungo maza jeka siyo mana kwaki da kyada nasan in ta tashi zata dan ji yunwa , nan yadda ka kalli kowa ba ko kace zaka musu wani abu nasan halin ka sarai, saura kace kaima zaka rama, in naji sabanin hakan ranka zai baci” jinjina mata kai yayi tare da amsa mata, dan tabbas ba hakura yayi ba amma yanxu ba yadda zeyi dadinshi daya tahee ta rama. Kasancewar basu da nida da me ka tin ba dadewa ya dawo , har lokacin tahee bata tashi daga baccin da take ba. Ajje Garin sukai sai da ta tashi sannan suka hada, har lokacin fuskarta a hade take , ba Wanda ya kulata a cikinsu har suka kammala cin abincin, maganin dazu oumma ta mikowa tahee , tana bata rai ta karbi maganin a haka ta shanyesa. Kiran sallar da ake ne ya sasu mikewa tare da dauro alwala, lokacin ta saki fuskarta kamar ba Itace tagama tsorata Dije ba, sallah suka kabbara tare da bin jam’i, bayan sun idan ne sukayi shafa’i da wuturi, sannan ko wannansu ya biya wa oumma haddar alqur’ani cikin natsuwa. Bayan sun kammala ne oumma ta kara musu arba’una Hadith da ahlari, sai da ta tabbatar sun gane sanna suka zauna suka fara hirarsu irin tasu sai faman tsokanar oumma suke kamar wata kakarsu. Ganin 11 tawuce ne yasa oumma ta umarcesu da suje su kwanta. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰ Karfe 2 ya farka daga baccin da ya daukesa, a hankali ya fara karanta adduar tashi daga bacci cikin daddadar muryasa, sanna ya mike kamar bayasan taka kafafuwansa. Toilet ya nufa be dade ba yafito kyakkyawar fuskarsa dauke da ruwa da Alama alwala yayi, duk da kasancewar dare ne hakan be Hana takunsa na mazantaka canzawa ba, inda shinfidaddiyar farar daddumar take ya nufa tare da kabbara sallah cikin nutsuwarsa,ya dade yana nafilfilu sannan ya fara karatun alqur’ani mai girma a hankali cikin daddadar muryarsa ne ratsa zuciya kamar karya dena .sai da ya kammala suratul bakara gaba dayanta , sannan ya fara adduoi cikin harshen larabcin da ya zauna a bakinsa, ko wace harafi na futo wa . 4:2 shine abunda agogon wayarsa ya nuna masa, lumshe fararan idanuwansa yayi da suka fara canza kala tare da mikewa, inda system dinshi yake ya nufa , ya dade yana operating a kanta , kiran da ake na sallar asuba ne ya katse masa aikin da ya fara a system din nashi, ajjeta yayi gaba daya tare da gyara zamanshi kamar Wanda bazai tashi ba sai kuma ya mike tare da nufar hangar da zata sadashi da bathroom dinsa. Be dade ba ya fito cikin wasu kananan kaya white colour masu shegen kyau, damtsen hannunsa ya fito sosai , yayinda budaddiyar rigarsa me shape din v ya futo da kirjinsa kadan , sosai kayan sukai masa kyau , yalwataccen gashin Kansa masu sheki da san tsi sun kwanta luff tare da harneda da sajan fuskarsa, sosai kayan sukai wa kakkarfar surarsa kyau , ba abunda yake tashi sai kamshim imperial majesty . Masallaci suka nufa shida zaki bayan An idarne kamar kullum ya umarci zaki ya bawa liman kudi yayi Sadaka,kamar yadda ya umarceshin haka yayi liman sai faman addua yake masa. Direct gida suka koma bayan an idar da sallah , part din dake tsakiya zaki yayi parking , king kuma ya shiga part din. Zaune yake cikin fararan kaya , dattijon arziki kenan, uban marayu, fari shima amma ba kamar king ba, kana ganinsa kaga bafullatani dattijo. Ciki ciki king yayi sallama tare da nufar inda mutumin yake , amsa sallamar mutumin yayi tare da zuba masa kyawawan idanuwansa irin na king, kawar da Kai king yayi tare da zama a kasa wajan kafafuwan mutumin . Ya dau kusan 5 minutes zaune a wajan bece komai ba shima mutumin bai tanka masa ba har ynxu kuma bai dena kallan nasa ba. Dakyar ya iya bude bakin sa cikin daddadar muryasa kamar Wanda aka sa dole,” ina kwana abeey, ya karfin jiki”, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da amsa masa , lapiya son , jikina kuma nayi sauki ai, am getting much better now “. Dago da kaifafan idanuwansa yayi yana kallan mahaifin nasa , kawar da Kai abey yayi daga kallan king ya maida kan jaridar dake hannunsa . Sallamar da akaine ya Hana king magana , akan kujeran falan suka zauna, daya daga cikin sune ya fara magana” yaya barka da Safiya”, murmushi Abeey ya sakar masa “ katashi lapiya musaddiq”, amsa wa yayi da “lapiya Lou “, shima na kusa dashi gaishe shi yayi abeey ya amsa cikin kulawa. Kamar be san da mutane a falan ba,ya dau kusan mintuna yana juya yadda zai fara , kafun ya soma magana ciki ciki” ina.. kwana uncles “ daga haka be kara cewa komai ba, duk cikin su babu Wanda be san halinsa shiyasa basu damu ba Suka amsa masa cikin kulawa . Mikewa yayi tare da kallan abeey” take care” , jinjina masa kai abeey yayi, yana gama fadar hakan ya juya tare da barin part din, da kallo duk suka bishi suna kara jinjina miskilanci irin na king . Yana komawa part dinsa , Wanka yayi cikin tsada sun suit dinsa black colour da suka fito da ainayin kalar fatar jikinsa , black hair din sa da ya hade da sajensa sai faman daukan sheki suke , hannunsa sanye yake cikin diamond watches , har yanxu fuskarsa a hade take karamun pink lips dinsa ya kara turuwa sosai , sosai kayan sukai masa kyau danshi din kyakkyawa ne da baki bazai iya fassara wa ba , yanxu ma ta elevator ya sakko kasa, ko kallan dining din da aka cika da kayan breakfast bayiba, zaki ne ya bude masa kofar falan shima fuskarsa a hade take sosai . Wasu irin tsadaddun motocine jere a wajan sai faman kyalli suke , wata farar Mercedes’ benz aka bude masa , basu tsaya ko ina ba sai wani babban part dake cikin gidan. Cikin daya daga cikin kayataccen chairs din falon ya zauna , daddadan kamshin turarensa ya mamaye ko wana turare dake falon bakajin kamshin komai sai kamshin imperial majesty. Sanye take cikin wasu cotton din kaya masu laushi da sanshi, idanta sanye da farin glass sai faman mita take ita kadai, ganin wanda ke falon ne yasata tabe baki, “ nifa Adena zuwa ana takuramin, ina dalili Ance kayi aure kaki sai kazo ka tare min a daki da sassafe fisabilillah “, kara tsuke fuskarsa king yayi cikin daddadar muryarsa ya gaisheta “ Dada ina kwana , ya karfin jiki”, sallallami wacce aka kira da dada tayi , “yanxu fisabilillahi saraki zautacciya kamayar dani da har kakemun ya jiki!”to wallahi bari kaji, lapiyar da nake da ita ko ubanka baba tunanin yana da ita , bai kula taba Samm , dada kuwa sai faman mita take yace mata ya jiki,mikewa tayi tare da shiga wata kofa bata dade ba ta fito dauke da wani glass cup , ajje sa tayi a gabansa “maza maza ka shanye furar da kazo ka ka tattara ka Barmin daki”, ko kallan furar da ta ajje beyi ba sai da ya Mula dan Kansa sannan ya fara sipping din furar a hankali, furar tayi masa dadi sosai amma a zahiri sai ka dauka dole akai masa yasha,ko rabin cup din be shaba ya ajjeta “pray for me” , inma zagina Kayi kai da Allah “purey (pray ) din kawai naji,”Allah ya tsare ka dan Jikalle , Allah ya kawo auranka jibi jibi” tsuke fuskar sa yayi jin adduar ta ta karshe , diamond watches dinsa ya kalla tare da nufar hanyar fita daga falan Daidai lokacin da abeey da uncles dinsa ke kokarin shigowa,cikin tsokana uncle salim ya soma magana “wato kazo kacinyewa yar tsohuwarmu abinci kabarmu da kanzo ko”, duk murmushi suka saki yayinda fuskarsa take a haden ta har ynxu , wani murmushin abeey ya saki dan Sarai ya gane be san surutun da uncles din ke masa, uncle musaddiq ma sai faman dariyarsa yake ,sallama yayi musu tare da nufar part din mahaifiyarsa, bakowa a kantameman falon , direct dakin da yasan zai sameta ya nufa, knocking din kofar yayi, shiru ba’a amsa ba na kusan sakanni kafun ta bada izinin shigowa, cikin nutsuwarsa ya tura kofar dakin tana zaune cikin shigarta ta kullum, garage kyakkyawa irin asali da kyawun larabawa, doguwar jallabiya ce a jikinta red colour me shegen kyau da tsada , stone din jikin rigar sai faman kyalkyali yake, wata farar yarinyace a jikinta fara sol me kama da king kamar an tsaga kara, sallama yayi tare da karasa shigowa dakin, dagowa yarinyar tayi da sauri tare da nufarsa “AKHI!! ANA FI AINTIZARIK MUNDH ALBARIHA(yaya!! Tun jiya nake jiranka) ta karasa fada kamar zata saka kuka, lumshe mata idanunsa yayi tare da shafa fuskarsa da kyar ya furta “ana asf habibaty ( am sorry sweetheart), “hasanan akhi’usamihuk( okay brother , I forgive you). Zoya !! Matar dake saune ta fada , cikin kinkina ta amsa mata “naam ummey”, ala yumkinuk an tahyiah lam ‘udadhirk min dhalik( bazaki gaishesaba , ban ja miki kunne ba) cewar ummey, kamar zatai kuka tace “ana asf ummey( kiyi hakuri ummey), sannan ta mayar da hankalin ta Kansa “ana asf akhi, sabah alkhaiyr( am sorry brother , ina kwana), girgiza Kai Kawai yayi dan har ta fara sa masa ciwon kai. Cikin Yaren larabci ya gaishe da ummey, ba yabo ba fallasa ta amsa masa, bayan gaisuwa ba wanda ya kara magana sai zoya dake faman yi masa surutu, mikewa yayi tare da yi mata sallama , bin bayansa tayi da kallo har ya bar part din ka fun sauke nannauyar ajiyar zuciya. Tun daga entrance din falan ya fara jiyo hayaniya na tashi sama sama , yana shiga ya tarar dasu zazzaune a falon sai faman kwasan dariya suke, ammi na zaune tana kurban tea . Sallamar da yayine yasa falon yin shiru, kamar ba kowa aciki sai faman zare idanu suke , ganin sunyi shirune yasa ammi dago da idanuwanta, wanda ta ganine yasa ta sakin murmushi ,daman nasan za arina ta fada a zuciyarta, dukansu sak kowa sukai daga kan kujerar da suke , sai faman muzurai suke , cikin hada baki yan matan saka gaishesa” yaya king .. ina kwana”, kallan da yayi musune yasa hantar cikinsu kadawa, be amsa musu ba sai ma tanbayar da ya jefo musu, cikin husky voice dinsa “me ya hanaku zuwa makaranta”, ko waccensu tsure wa tayi suna kallan ammi ta gefan ido ko zata sa baki,ammi kuwa sharesu tayi, fingers din hannunsa ya daga musu “10 minutes only”, a guje ko waccensu ta bar part din dan sunsan ammi ce ta cecesu da bata wajan da Sunansu sorry. Suna barin part din ammi ta kalleshi, kaji da di daka tarwatsamun yaya , be amsa mata ba sai gaisuwar da yayi mata, itama bea dade ba yabar part din. Cikin wasu irin slow motocinnan suka fara fita, duk inda ya wuce sai kaga ana saramasa, suna hawa kan titi motocin suka fara gudu, sir ina zamu cewar zaki, ya dau mintu biyu kamar bazai tankaba sai kuma ya bude bakinsa” company “. ➰➰➰➰➰➰➰➰ Manage please abubuwane suka dan shamun kai.. Comment and share ✍️🫶 💖the talent troupe 🔥 Writers of …… Duk karfin izzata Gidan Aunty Sarki sameer Jini daya Ya fita zakkshare 💖GIDAN AUNTY💖 By mss LEE 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 PAID BOOK BOOK 1📕 FREE PAGE 6 Yau ma da asuba suka tashi, bayan sun idar da sallah aikin gidan suka fara , TAHEER da TAHEERA suka debo ruwa kafin suyi wanke wanke, yau ko buga kofarsu da aka saba yi ba ayi ba, gidan tsit kamar ba kowa a ciki, suna kammala aikin nasu daki suka koma, wata tsohuwar 200 oumma ta basu “nasan kunajin yunwa, kuje Wajan abu me kosai kuce ta baku kosai”, Godiya sukai mata tare da nufar kofar da zata sadasu da waje , a hanya suka hadu da Dije zata shiga ban daki , tana ganin su tai saurin shigewa bayi tana tsine musu, basu bi ta kansu ba dan yunwa suke ji . Basu dadeba suka dawo, ganin oumma na karatun azkhar dinta yasa basu kuma cewa komai ba har saida ta kammala . Kosan tahee ta Mika mata tare da dakko musu wani plate din robber , juye kosan sukai a ciki tare da faracin abinsu, bayan sun kammala ruwa suka sha tare da yin hamdala, sai lokacin suka fara yar hirarsu, musamman taheer da taheera , oumma na sa baki lokaci zuwa lokaci. “Oumma” cewar tahee, amsa mata oumma tayi da “uhm” ko muma kosannan zamu kwadayi ko za a siya,Jim kadan oumma tayi kamar ne tunani abinda zatace sai kuma ta kalli tahee” banki ta taki ba auta, amma kinsani ko mun fara ba barinmu zasuyi muyi ba, kinmanta abunda ya faru kwanaki”, turo baki tahee tayi jin oumma tace mata auta” wai TAHEER ne fa auta amma kullum ni kike cewa auta”, kallan up and done TAHEER yayi mata “shikenan zo mu kwada tsaho , duk Wanda ya fi tsaho a cikin mu shine babba”, dariya duk suka saki dan sun sa da biyu ya fada mata wato dan ya fita tsaho. Daga waje suna jin yadda yan gidan ke musu habaici da zagin su musamman Dije da yarta. Da azahar ma haka suka sha kwaki da gyada cikin raha da kaunar junansu, bayan sallar isha’ine suka roki oumma zuwa dan dali, sai da oumma ta ja musu kunne sosai sannan ta barsu sukaje. Suna tafiya suna hirarsu Daidai sunxo shiga dandali tahee taji abu ya soketa, wajan ta taba Daidai inda shatin maciji ya fito a ciki dan kadan, TAHEER ne ya ankara da zanan macijin yayi sauri ya sa hannunsa a wajan, kamar kiftawar ido shatin ya bace bat. Hararar ta TAHEER yayi “me yasa ba kya kula , yanxu da wani ne yaga tanbarin macijin nan bani ba me kike tunani”, girgiza masa kai tahee tayi “bansan ya Akai ya fito ba sabida naji kamar wani abu ya tsirenii a wajan, ina tunanin akwia abunda yake faruwa a masarauta, dole muje mugani “daidai taheer ya bude baki da niyar yin magana yaji an bangajesu tahee har da faduwa kasa, kashi tayi a fusace da niyar bin bayansu amma TAHEER yayi azaman rike hannunta,” kasake ni, Raina ya baci”, kin sakinta taheer yayi sai ma wani abu me kama da na fito da ya dakko ya fara busawa , cikin kankanin lokaci tahee ta fara sauke ajiyar zuciya. “ ki dinga sassaita fushinki , banaso ranki yana baci , anjima zamuje daula”, gyada masa kai tahee tayi suka nufi wajan dandalin. Suna shiga aka fara gulmarsu ana zaginsu , iya kuluwa tahee ta kulu ganin yadda ake nunasu ana dariya, saurin damke mata hannu TAHEER yayi tare da girgiza mata kai suka kama hanyar komawa, jin muryar bintalo sukayi tana fadin “yanxu ma haka ana tunanin ba kawun mune ubansu ba , shiyasa ma ake nuna musu hantara ,kun manta uwarsu ba yar kasar nan bace kowa dai yasan halin buzaye da bun malamai “, saurin fusge hannunta tahee tayi, da nufar inda bintalo take , saukar marin da bintalo taji a fuskar tane yasa ta wuntsulo wa , tahee bata kyaletaba, ta kara tsinka mata wani marin, duk Wanda yayi kokarin binta sai tahee ta tsinka masa mari, taheer nagefe yana kallansu , sai faman sakin murmushin Mugunta yake, ganin tahee ta shako wuyan buntalo ne yasa shi nufar inda suke , yana zuwa da niyar rabasu shima ya samu nashi rabon dukan, kwata kwata tahee idanuwanta sun kulle, kara nufar su taheer yayi da niyar rabasu yanxun ma wani raban dukan ya samu, Daidai wajan kafadun ta ya samu ya daka da karfi, ko motsi bata karaba ta zube a kasa , bintalo ma sai faman zare ido take dan ba karamun shaka tahee tayi mata ba, duk kawayen ta da suka labe suka fito sai faman zugata suke akan abunda tahee tayi mata, ba Wanda ta kula a cikinsu sai kwallar bakin ciki da take, hanyar gida ta nufa kawayenta na taka mata baya , shima TAHEER kama tahee yayi suka nufi hanyar gidan. A soron gidan suka samu mutane shake a wajan, ga bintalo a gefe sai faman kuka take , kowa maida kallansa yayi kan su taheer dake shigowa, “muna fukan Allah har kun dawo,kenan toh wallahi bazata sabuba me yata tayimuku da zakuyi mata irin wannan bugun, ita uwar taku da yake tasan me kukai shiyasa ta makale a daki taki fitowa “cewar dije, kallanta TAHEER yayi kamar ma besan me ya faruba “aunty dije lapiya, ko Ance miki wani abune”, duk zuba masa ido suke bintalo kuwa tun bayan shigowarsu taji kamar abu ya shigar mata ido.hararar sa wata daga cikin kawayan Dije tayi” karya za ai maka kenan “, kallan ta TAHEER yayi sosai “ni bansan akan abinda kuke magana ba , in kuma akwai wani abun ai sai ta fada muji “,kallan bintalo dije tayi” maimaita abunda yayi miki ai ba karfin mu suka fi ba, ina daga masu kafane”,narnar bintalo tayi”inna daman ba abunda sukai mun, nice bansani ba na bangajesu suka fadi”, salati mutanan gidan suka fara , yayin da kawayen dijen suka fara binsu da kallo. Wani dan iskan murmushi TAHEER ya saki tare da nufar dakinsu da tahee duk wannan abun da ke faru oumma na daki na bacci batasan me ke faruwa va. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ Cikin wani hadaddan company motocinnan suka tsaya, daga saman company din ansa A_N_business enterprise’s, yanda aka rubuta sunan company din shi kansa abun kallo ne , komai na cikin company din da glass akayishi amma baka ganin komai da ke ciki saida su mutanan ciki su ganka. A Daidai wani parking space motocin sukai parking, zaki ne ya bode masa kofa, har yanxu lumshash shun idanuwansa a kulle suke, sai yanxu ne ya bude su a hankali, kafafuwansa ya fara zurowa kafun ya fito daga cikin motar gabaki d’aya,tunda ya shiga company’n ma’aikata ke ta faman miko gaisuwa,da hannu kawai ya ke amsawa bata re da yace komai ba Wanda sun Riga da sun saba da yanayin amsa gaisuwar sa . Daga inda zai hau lifter duk sauran bodyguard din suka tsaya ,shida zaki ne kawai a lifter din , Kai tsaye floor 4 dake last floor suka nufa,baka jin ko wace irin hayaniya a wajan komai tsit kakeji sai kamshin da sanyin ac dake tashi ta ko ina. Wata kofa zaki ya bude masa daga samanta an rubuta C.E.O TAHNOON cikin wani stylish way , ha daddan office ne ya bayyana me shegen kyau da tsaruwa iya kyau office din ya hadu kamar ba a shigarsa amma ko ina tsaf tsaf yake , daga cikin office din akwai wasu dan ubansu set din kujeru masu shegen kyau daga kan table din akwia wani dan karamin hotan samari su biyu masu dauke da harafin M&T,a kan daya daga cikin set din kujerun ya zauna, wasu briefcase zaki ya miko masa, be amsa ba illa “seat “ kawai daya ce cikin cool voice dinsa, cikin girmamawa zaki ya amsa da “ thank you boss” kafun ya samu waje ya zauna,rikitattun idanuwansa ya Dora kan zaki kafun a hankali ya furta “explain”. Gyara zaman shi sosai zaki yayi tare da soma bayani” boss duk wata sai an furar da makudan kudi daga a susun bankin company dinnan, batare da cikakken dalili ko sa hannu ba ,a cikin shekarar nan an rasa makudan kudade masu yawan gaske tacikin wani asusun banki da haryanxu ba a ganoshi ba”.sannan ya cigaba da yi Mishi bayanin abubuwan da ya shafi company din, kamar ba sai amsa ba tsahon munyi biyu kafin ya bude bakinsa” ina bukatar bayani game da futar kudinnan, sannan ta Wana bank ake fitar dasu”, jinjina masa kai zaki yayi “okay sir “ tare da nu far hanyar fita, “called zuhra” yaji saukar muryarsa, nan ma “okay “ kawai zaki yace masa. Dafe goshinsa yayi da ya fara sara masa sabida doguwar maganar da yayi, ko mintuna biyu cikakku ba ai ba akai knocking din kofar, shiru ba a amsa ba sanna ba a kara knocking ba kusan tsawan 3 minutes , kafun ya bude baki “come in”. Da Sauri aka bude kofar tare da shigowa ciki, tunda ta shigo ta zuba masa manyan ida nuwansa,be dago ba amma yaji yanda take binshi da kallo, ya tsani kallo amma duk da hakan be matsa daga inda yake ba , bata Ankara ba sai jin dakakkiyar muryarsa tayi “get out”, sosai jikin ta ya fara rawa sam hankali da nutsuwarta ya tafi akallon irin kyawun da yayi kamar kullum kara masa kyau ake , saukar marin da taji a fuskarta ne yasa ta shiga taitayin ta cikin rawar harshe ta furta “ am sorry boss” tare da nufar hanyar fita , sai faman tsine wa zuciyarta take akan gaggawanta dan ko zatai yawo tsirara king natane ( uhmm😟).ranshi ba karamun baci yayi ba amma a zahiri bazaka taba tantance Wana yanayi yake cigaba , system din gabansa ya dauka , ya dade yana anfani da ita ka fun ya ajje ta ya lumshe ido. Wutace keci sosai ta ko ina , da anyi kokarin kasheta karfin ta zai kara yawa, sosai wutar keci da wuta ga wasu bakin abubuwa dake yawa a wajan , gigitacciyar karar da aka sakine ya farkar Dashi daga baccin da ya fara . Launin idanuwansa harsun fara canzawa daga fari zuwa ja,gaba daya jijiyoyin wuyansa sun mike wata irin zufa ya fara , hannunsa na dama ya daga wani siririn diamond din abun hannune ya fito me dauke da harafin M&T, gaba daya zuciyarsa ba dadi, bazai taba mantawa da bakar ranar nan ba. Zaki ne yashigo office din ganin halin da king yake ciki ba karamun shiga tashin hankali yayi ba, wata drawer yayi saurin nufa cikin gaggawa ya dakko wata allura, da kyar ya samu yayi wa king a wuyansa,kafun a hankali nunfashin sa ya fara dawowa daidai, launin idan sa da ya kada ya fara dawowa Daidai. 5:30 sukabar company kai tsaye wani part yashiga acikin part dinsa, komai nacikin part din royals ne tunda ga kan kujerun falon da ya gaji da tsaruwa , be bata lokacin ba Kai tsaye bedroom din falon ya shin shima sosia dakin ya dahu iya haduwa. Ya dau kusan 10 minutes cikin toilet kafun ya fito sanye da white bathrobe kall dashi,jikakkiyar gashin kansa sai faman tsiyayar ruwa take. Wata kofa dake gefan Hagu ya shiga , ya dade a ciki kafin kamshin turaran sa ya kara de ko ina, a hankali yake fitowa daga cikin dakin , shigarsa ba karamin kyau tayi masa ba , yayi kyau sosai har ynxu fuskarsa a daure take . Masallaci suka dufa shi da zaki bayn an idarne suka dawo gida kai tsaye part din ammi ya nufa, ba kowa a part din,sai yalwataccen Hasken da ya cika falon, bin ko ina na falan yayi da rikitaccen idanuwansa, ringing din da wayarsa keyi ne ya katse masa, be dauki wayar ba har sai da ta kusa tsinkewa ,daga cikin wayar bata bari yace komai ba tace “part din granny now” , tana gama fadar hakan ta kashe wayanta. ******* Zazzaune ko wannansu yake a falon , ko wa ka gansa cikin farin ciki da annashuwa, daga gefe daya wasu yan matane su su hudu zAune a wajan sai faman hirarsu suke , daga Dayan side din ma wasu manyan mutane ne ke tattaunawa. A hankali kamshin turaransa Da baya boyuwa ya kara de ko ina na cikin falon, lokaci d’aya falan ya dauki shiru kowa hanyar shigowa ya zuba wa ido, a hankali yake taka kafarsa har ya shigo falon , fuskarsa kwata kwata ba alamun murmushi sai ma kara kadeta da yayi, sosai farin kayan jikinsa ya futo da tsantsan kyawunsa,motsa bakinsa yayi ciki ciki da yin sallama, a tare falon suka amsa dan ba wai sallamar sukaji ba ta motsin bakinsa suka gane. Zoyace ya taho da gudu da niyar rungumeshi, kallan da yayi matane yasata Jan burki “ana asf akhi( am sorry brother )kwalla harta fara tarar mata, lumshe idanuwansa yayi tare da bude mata hannusa guda daya , a guje ta karasa wajan sa tare da rike hannunsa” welcome back akhi , I missed you the whole day”, lumshe mata ida nuwansa yayi tare da budewa kasa kasa ya amsa mata “ me too”, direct inda mahaifinsa yake ya nufa, zazzaune ko wannansu yake cikin takaitaccen magana ya gaishesu, kowa amsa masa yayi sai faman binsa da kallo suke , abeey sai faman sakin murmushi yake . Hajiya Amina ( uwar gidan uncle musaddiq) wacce ake kira da mamy ce ta soma magana “ Kai dai king kayi wuyar gani, ba a ganinka Indai ba a part din dada ba ko na ammonia”, matar uncle Saleem ce ta Dora “ Aushe duk kanwar jace “. Murmushi ammi ta sakar musu “ Kude kawai kun fada ne”, mikewa king yayi tare da nufar wani sofa dake can gefe dasu, kallan dada zoya tayi, cikin tsokana ta kira sunan ta”dada”, harara dada ta wata a mata “kinibabbiya ba kiran Allah da annabi kikai mun ba, tunda kinga ubanki ai dole kikashen murya”,langwabar da Kai zoya tayi “Haba my dada nasan akhi na beci abinci ba , he need some coffee before eating”, tsaki dada taja “ ke kika sani kuma inma zagina kikai ba na hanaki yimun magana cikin yaran nasara ba, wani wai kamfin ( coffee)ke kika sanshi”,kowa na falon yadda dada ta kira coffee din sai da yaso basu dariya amma ba damar yi harta king maganar taso bashi dariya amma sai wani hade rai da ya kara.kallan akhi dake gefe zoya tayi, saurin daga mata hannu yayi alamun ba ruwansa ,maida kallan ta tayi kan ummey , itama dauke idanuwanta tayi daga kanta,mikewa ammi tayi nida ba a sako niba bari na bada coffee din, kulle idanuwanta zoya tayi tana dariya ,daya Daga cikin yan matan ne ta mike, kallanta ummey tayi amrah ina zuwa, cikin in ina wadda aka kira da amrah ta soma magana “dama zan taya ammi ne”jinjina mata kai ummey tayi , direct kitchen din dada ta nufa , basu dade ba suka fito daga kitchen din cikin yanga amrah ta ajje masa tray din abincin, “yaya king sannu da hutawa”, kamar wacce tayi magana da dutse yana zaune ko motsawa beyi ba ballantana tasa ran amsawa, zoya na gefensa a haka ammi ta fito da cup din coffee sai faman tiriri yake dayan kuma kayan tea ne a ciki da yaki bornviter , mika wa king coffee din tayi , lumshe mata ida nuwansa yayi , murmushi ta sakar masa kafun ta mikawa zoya tea dinta.beci abincin da aka kawo masa ba sai coffee dinsa da yake sipping a hankali yana gama sha ya mike tare da ce musu “good night “yana gama fada ya kama haryan fita . Cikin daga murya zoya ta soma magana “Laylat saeidat akhi, uhibuk( good night brother, love you)”,girgiza Kai kawai king yayi da barin part din. Sai a sannan yan matan suka tare da cigaba da hirarsu, dummy ce ta kalli amrah , Lalle amrah da raban kin kusa Shan Mari a wajan yaya king, Kinsan halinsa Sarai ba a burgeshi, cikin kasa kasa ihsan tace Garin masoya baya nisa kunsan yadda take mugun sonsa,murmushi amrah ta saki jin abinda ihsan tace “dadi na dake ihsan kin fisu fahimtar abu”ni kadai nasan yadda nake sanshi kumashidin mallakinane, dariyar mugunta firdausi ta saki , cikin kasa kasa da murya tace “mugani a kasa”, hararar ta amrah tayi dan Tasan itama san king take shiyasa basa shiri sosai , duk wannan magan ganun nasu cikin kasa kasa da murya sukai ba mejinsu, dago idanuwanta amrah tayi bata saukesu akan kowa ba sai nan auntyn ta , itama auntyn Tata daga mata hannu tayi alamun jinjina, firdausi ma maida hankalin tayi kan mahaifiyarta lokaci daya suka sakar wa juna murmushi duk wannan abun da suke ba Wanda ya lura dasu . (Uhmmmm 🤭😟) 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 Duk karfin izzata (star lady) Gidan aunty (mss Lee) Sarki sameer( xeemat love) Jini daya ( mss bbk) Ya fita zakka (maman sayyid) Comment and share 💖GIDAN AUNTY💖 ( A heart touching love story) By mss Lee 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 PAID BOOK BOOK 1 📕 Free page 7 🦋 Not edited Zaune Suke su biyu cikin wata katuwar masarauta me shegen kyau da daukan hankali, duk Wanda yazo wuce wa sai ya duka musu tare da gaishesu, TAHEER ne ya fito cikin wata kofa sanye da wasu kaya na alfarma masu tsananin kyau ba karamun kyau yayi a cikinsu ba , hannunsa dauke da wani siririn maciji fari tass dashi, Daidai inda tahee take ya nufa, zaune take cikin shigar alfarma na kayan sarauta , gefe da gefe masu yi mata fiffi tane ko wananne kawunanshi akasa, tanbarin macijin dake bayanta ya fito radau dashi, murmushi ta sakar masa ganin ya karaso inda take, shima murmushin ya sakar mata tare da Mika mata kyakkyawar farin macijin, mikewa tayi sosai tare da karban macijin, a daidai kan cinyarta ta dora macijin , shima macijin lumshe idanu yayi kamar mai jin bacci, kallan taheer tayi da mamaki dauke a fuskar ta,” kyauta ne na baki yau shekara 300 daidai da haihuwarki, zai debe miki kyewa “cewar taheer, tsananin farin cikine ya bayyana a kan fuskar tahee “ oh my god , nagode SIF” , jinjina mata kai kawai yayi , har ta bude baki zata sake magana sai wasu siraran hawaye suka zubomata”ka tuna lokacin da Nonna ta bani kyautar maciji kamar haka , amma sun kashe mun shi, sun kashe mun nonna , sun kashe mun susan”, shima girgiza mata kanshi ya shiga yi”Lola Raina yana baci duk lokacin da na turo wannan bakar ranar, kamar randa suka rabamu da nonna da susan Muma baza mu kyalesu ba,ga memaw nan ki rikeshi kamar yadda kika saba da susan, shima zaki soshi sosai”, yana gama fadar haka ya bar wajan , murmushin yake ta saki tana hadiye abunda ya tsaya mata a makogaro,kallan memaw din dake kan cin yarta tayi kafun ta kira sunan shi,”memaw”, bude idanuwansa yayi masu kalar baki tare da fara yawo a jikinta yana zagayeta , hakan ba karamin nishadi yasa taba, sai faman yawo suke , saida suka gaji dan kansu sannan suka tsaya har lokacin mucijin be dena yawo a jikinta ba.TAHEE!!TAHEE!!! A firgice ta farka daga baccin da take bakin ta dauke da adduar tashi daga bacci, kallan ta oumma tayi ganin yadda ta jike da zufa duk da kasan cewar akwai dan zafi zafin da ake ,”lapiyan ki kuwa”cewar oumma , saurin girgiza mata kai tahee tayi “ mafarki kawai nayi”, shafa kanta oumma tayi “ki kwantar da hankalinki mafarki ba gaskiya bane sannan ki dunga addua “nanma gyada mata kai kawai tayi,tunda umma ta fita a dakin kuma bata motsa ba mafarkin da tai na yi mata yawo aka“ NONNA,LOLA,SIF,SUSAN,MEMAW!? Sudin su wanene!? Maciji fa !?” Macijin da ta gani a mafarkine yashiga yawo a kwakwalwarta, amma sanin cewa mafarki ba gaskiya bane yasata share zancen tare da mikewa ganin oumma na kokarin shigowa dakin. Bayan sallar azahar kamar yadda suka saba bayan sun kammala ayyukansu, zama sukai suna hira , lokaci zuwa lokaci tahee sai ta dako ta kalli taheer har yanxu mafarkin da tayi yana mata yawo a ka , duk lokacin da tayi tunanin mafarkin sai taji wani abu kamar ya tabata, yanxu ma dago da fuskar ta tayi tana kallan taheer, hararar ta yayi ganin tun dazu sai faman binsa da kallo take kamar wata me aljanu “na canza miki ka manni ne kike faman bina da kallo fisabilillah”,cewar taheer yana hararar ta , murmushin da yafuto da dimples dinta ta saki”gani nai ka kara kyau kamar wani balarabe “ ta karasa maganar tare da kashe masa ido daya,yanxun ma wani hararar ya mata “dadin abun bake kadai ce me kyau ba, da nice mace ma kyan da zanyi sai nasaka maza kuka”, dariya duk suka saki, oumma ta girgiza kanta “Allah ya shiryeku “. ➰➰➰➰➰➰ A gajiye ya dawo gidan bayan mutane uku da yayi wa aiki a asibiti da kansa ,sai faman lumshe ido yake , amma a zahiri bazaka taba tunanin hakan ba , zaka dau ka yanayinsa ne haka , shaf shaf yayi wanka cikin armani white colour, sosai kayan sukai masa kyau , a maimakon gyara gashin da ya saba yan tajeshi kawai yayi ya zubo masa har bayansa, sosai yayi kyau a cikin shigarsa, wayoyinsa kawai ya dauka tare da nufar part din ammi, yau kwata kwata be sata a idanunsa ba amma a zahiri fuskarsa a hade take ba ko alamun yasan wani abu me kama da murmushi. Yana shiga part din ya tarar da su kowa da Riga da Wando sai faman rawa suke, amrah ce me koya musu yadda zasuyi step din rawar,kwata kwata basusan da shigowarsa ba , hatta kamshin turarensa da sukaji basu kawo komai a ransuba, dan kusan kullum da kamshin a cikin falon ammi. Folding din hannunsa yayi a kirji yana bin ko wannansu da kallo daya bayan daya ransa ba karamun baci yayi ba musamman irin shigarsu ko dan kwali babu, be tankamusu ba duk da yadda kan nasa ke Sara masa , sexy eyes dinsa dasuka fara canza kala daga launin fari zuwa ja ya zubamusu, ihsan ce ta fito sanye da hijab a jikinta hannunta dauke da cup sai faman tiriri yake, kallan su amrah tayi tare da girgiza kanta , “kunsan dai yaya king ya hana wannan raye rayen ko, Allah Inya dawo sai na fadamasa dan bazaku jajamun ba”, hararar ta summy tayi “ sannu kasa yanxun ma zaki iyazuwa, matsoraciyar banza kamar da gasken iya zuwa zakiyi”, girgiza kai firdausi tayi “Aah sumy Wana irin taje ta fada kinsan dai wallahi yaya king ya Kamamu ba karamun wuya zamusha ba musan man dressing dinmu, kuma kusan bama sawa sai in bayanan “, siririn tsaki amrah taja “matsalata da ku kun fiya tsoro wallahi, kafun ya dawo ba mun gama ba , ai baze san munyi ba , yanxu fa zamu gama step din rawar kafin ammi ta dawo”. Dukkansu yanajin abunda suke fadi , duk abunda suke yana ganinsu kwata kwata basu hankalta dashi ba, amrah ce ta kunna musu wata wakar, ta juya kenan a cikin salon rawar idanuwanta suka sauka a kanshi, sosai ta firgita , bakinta ne ya fara rawa kwata kwata ta rasa me zatace, kallanta summy tayi “ke kuma lapiya jikinki yake rawa”, girgiza mata kai kawai amrah take tama kasa magana ganin irin kallan tsanan da yake jifanta dashi “watan cin ubankune yayi”a zahiri kuwa yana yadda yake ko a fuskarsa bazaka gane yanayinsa ba duk da tsananin gajiyar dayayi. Ganin sai faman kallan waje taya amrah take jikinta na rasa yasa duk juyawa zuwa direction din,”Innalillahi wa’inna’ilaihi rajiun, shikenan mun kade har gay yan mu gashi ammi batanan “kowa da abunda yake sakawa a zuciyarsa , iya firgita sun firgita musamman ganin yadda launin idanunsa ya koma ,firdausi har da faduwa kasa tsabar rudewa,duk zubewa sukai akan gwiwowinsu ko waccen su sai matsar kwalla take,sosai suka rude musamman ganin irin kallan da yake bin kowannansu dashi, a hankali ya taka kafarsa tare da nufar sofa din dake left side dinsu , kwallar bakin ciki ihsan ta share dan duk su suka ja mata, ta ja musu Allah ya isa ba a dadi cikin zuciyarta, ba wacce ya kalla a cikin su sai ma wayar hannunsa da yake latsawa, cikin rawar murya me san sakin kuka ihsan tahe hannayanta “wallahi yaya zanyi bayani”, be Motsa da ga yanayin da yake ba balle su sa ran ze amsa mata, Kuka Kawai ihsan ta saki tana toshe bakinta karta kuma yin wani lefin, su amrah kuwa kowa sai faman zare ido yake fatansu Allah yasa be ji abunda suke tattaunawa. Kamar daga sama sukaji saukar maganarsa “ coffee “ da Sauri amrah ta tashi duk da acikin yanayin tsoran da take, dan iskan kallan da yayi mata ne yasa ba shiri ta koma tana zare idanu, ganin hakan yasa atsorace ihsan ta mike ganin be mata magana ba yasa ta nufar kitchen din cikin sauri, sai faman ajiyar zuciya take , duk tabi ta rikice ta rasa yadda zata hada masa coffee din , cikin sauri Sauri ta dakko wayanta dake aljihun Wandanta. Yanda ake yin coffee din tayi searching, cikin rudewa ta gama fito da abunda zata hada masa coffee din jikinta sai faman rawa yake . Cikin dan karamin tray ta fito da coffee din kusan na uku kenan tanayi kafun tayi wannan din, ganin su amrah na frog jump ne yasa kafarta rawa idanuwanta harsun cika da kwalla, coffee din ta ajiye masa tana komarin fara frog jump din ne abazata taji saukar muryarsa “ Leave” , nannauyar ajiyar zuciya ta dauke da harshi saida yajita “ nagode yaya king, na….” Hannunsa kawai ya daga mata ,cikin sauri ta bar wajan cikin gudu gudu, tunda Allah ya kubutar da ita. Sosai suke frog jump ko wacce fuskarta jaga jaga da majina , ga hawayen da suke yi, da zaran sunji kuka zai kwace musu zasuyi saurin toshe bakinsu gudun wani punishment’s din. Duk fadin falon ammi haka zuke zagayeshi ko wacce ta fita daga hayyacinta ba damar yin kuka a fili. Yana zaune sai faman operating wayar hannunsa yake se yanxune ya dauki coffe din da aka hada masa” kurba daya yayi amsa ya ajjesa. “Yaya dan girman Allah da manzan sa kayi hakuri”firdausi ce tayi maganar hawaye sai bin fuskarta yake, lumshe gajiyayyun idanuwansa yayi, tariga ta hadasa da abunda baze iya musu akai ba, “God save you”yafada cikin zuciyarsa “Leave “, baki summy ta bude Baki da niyar yin magana amma ya dakatar dasu ta hanyar dafe kansa , sun gane me yake nufi hakan yasa a guje ko waccen su ta bar part din Daidai lokacin da ammi ke shigowa, da kallo tabisu ganin babu Wanda ya kula da ita kafun ta karasa shiga falon. ➰➰➰➰➰➰ Karfe uku na dare ko ina yayi shiru kasan cewar ko wana bawa yana wutawa a irin wannan lokacin, wani macijine fari tas dashi ya fito cikin wani rani tare da kwanciya bayan tahee,cikin mafarkin da take tafara lalube lalube har hannun ta ya Kai…… Manage plx🥹 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 DUK KARFIN IZZATA (Star lady) GIDAN AUNTY( mss Lee) TAFITA ZAKKA ( maman sayyid ) JINI DAYA ( mrs bbk ) SARKI SAMEER (xeenat love ) 💖GIDAN AUNTY💖 ( A heart touching love story) By mss Lee 💖 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 PAID BOOK BOOK 1📕 Free page 8 🦋 Karfe uku na dare ko ina yayi shiru kasan cewar ko wana bawa yana wutawa a irin wannan lokacin , wani macijine tass dashi ya fito cikin wani rami tare da kwanciya a bayan tahee ,cikin mafarkin da take ta fara lalube lalube, har hannunta ya kai kan wannan siririn macijin, jin abu me laushi da san tsi besa ta bude idanuwan ba , sai faman shafashi ,a firgice ta farka daga baccin da take “mewam “ta furta cikin firgici, juyawar da zataine idanuwanta Suka sauka kan macijin , azabure ta Kwala ihu”oumma, oumma” ta fada a tsorace ganin duk ihun da tayi oumma bata motsaba, ja da baya ta fara ganin macijin na kokarin biyotan itama ,” Innalillahi me nayi maka kake biyoni, oumma ki temakamun”, duk ta firgice ganin macijin yayi Kuri da ido yana kallanta, ga oumma da ko motsawa batayi ba,kara nufota macijin yayi ta fara girgiza kai “ Dan Allah ba danni ba kayi hakuri , ni bansan me nayi maka kake bina ba, kayi hakuri dan Allah “ ta karasa fada tana fashewa da kuka, kamar daga sama taji saukar yar muryan dan yaro” ni ba abunda zan miki , kawai inaso na zauna wajanki “, waro manyan idanuwanta tayi kamar zasu fado kasa jin maciji na magana abunda bata taba jiba a rayuwarta,mintsinin kanta tayi dan tabbatarwa”kodai mafarki nake”, ta fara tanbayar zuciyarta,”Aah ba mafarki kikeba “ta kara jin saukan muryarsa , kara fashewa da kuka tayi fuskarta duk ta hada zufar wahala “ na rokeka koma wanene kai kayi hakuri ka kyaleni, ni ban muku komai ba”, be ce mata komai saima biyota da ya fara cikin tafiyar macijar, itama baya ta faraja tana girgiza masa , wani dan kwanan da ta gani tayi saurin dauka da niyar kwala masa , kamar wacce ta tuna wani abu sai ta tsaya tana kallansa”Mewam”a hankali ta fadi sunan, cikin sauri majicin ya karasa jikinta yana zagayeta , itama sai faman dariya take , duk wannan abun ba wanda ya farka daga baccinsa duk da tsananin ihun da ta kwala. Yau sun makara dukansu basu tashi sallar asuba da wuri ba, suna idar da sallah aikin gidan suka fara kafun mutanan gidan su fito,wanke wanke oumma ta fara su tahee na ebo mata ruwa , suna kammalawa tahee ta share tsakar gidan , sosia suka gyara gidan ganin yadda yayi Datti sosai kamar ba a gyarashi , Daidai lokacin da mutanan gidan ke futowa, daya daga cikin yayan gidan da suka zone tabi su da kallan kaskanci,”ke” ta fada tana nuna tahee , banza tahee tayi da ita kamar batasan da itaba,”bajini ina kirankiba ko sai na zageki zaki gane”, kallan tahee oumma tayi ba magana ake miki ba,dan karamun bakinta ta tura tana bin HAJJO da kallo, dan siririn tsaki hajjo ta saki”Aushe duk karyar banzace, ki jira ynxun ki mun wanki dan ba Hutu kuka zoyi mana gida ba”tana gama fadar hakan rai wuce warta, kande ma dake daki wuff ta fito”Nima yanxu zan gito miki da wankina “,da daidai da daidai mutanan gidan suka fara fitowa, kaka ta bawa da ke faman amma je ta karaso wajan , ke kuma uban me kike mana anan wajan ,muryar su hajjo taji”inna aiki muka sata , Kema in kina da wanki ki kawo tayi miki”,kaka ta bawace ta amsa mata “Aini baba rasa aikin sawa, yo inba aiki ba Menene anfanin katuwar budurwa haka har yanxu batai aureba”, da Sauri Dije ta fito hannun ta rike da mafici “ai inna kwara kiyi mata aure,ki duba ki gani ko bintalo da take 13 dududu saura mako uku bikinta”, dago da idanuwanta tahee tayi tana bin Dije da kallo sai kuma tayi saurin maidashi kan oumma da ta sun kuyar da Kai, zabura tayi da jin zancen inna” kuma kin kawo shawara me kyau dije, daman tanimu me guga ya dade yana santa,ubanta ne ya Hana yanxu kuma kin ga bayanan in yaso sai a hada Dana bintalo “, sosai mutanan gidan suka kwashe da dariya dan Sarai sunsan tahimu babban dan iskane a Garin ga shaye shaye da yake ,wuce wa oumma tayi daki batare da tace komai ba, taheer na tsaye duk ya hade ransa, dije kawai yake kalla yana girgiza kansa,kwallace ta tararwa tahee” ni zasuyiwa Auran dole , Auran ma da dan iska dan shaye shaye “ kawai sai ta fashe da kuka yan gidan kuwa sai faman shewa suke, tare da watsewa bayan uban tulun wankin da suka ajje mata, TAHEER ne yashiga lallashinta har tayi shiru sannan ya taimaka mata sukai wankin tare , duk jikinsu yayi sanyi musamman tahee dakanta ya fara ciwo. Suna gama wankin daki suka koma, oumma suka tarar tana gyara kayan sawansu”oumma “ tahee ta fada hawaye na kara zubomata, dakatar da ita oumma tayi tana daga mata hannu”bana san jin komai”tana gama fada ta dakko wa taheer ya mutsats tsiyar dariya biyar, ta lissa fa masa abunda zai siyo mata , karba yayi tare da fita daga dakin, itama tahee waje ta samu tare da juyawa tayi kwanciyarta, bunta da kallo oumma tayi tana kokarin share kwallar da take ta faman dannewa” ya Allah kai kadaine me iyawa ka kawo mana mafita “ ta fada a zuciyarta,itama taheen duk da yadda oumma ta share zancen tasan abun yana damun ta ne ba yadda zatayi ne , har taheer ya dawo daga aiken ko wannansu yayi jigum jigum, taliyar da oumma tasa ya siyo ma kasa cinta sukai saida oumma ta hade musu rai sannan suka tsast tsakura. ➰➰➰➰➰➰➰➰ Yau tun safe ba Wanda ya ganshi , hatta zaki bayan sun dawo daga masallaci be kara sanyashi acikin idanuwansa ba. Kwance yake kan kantamemen ‘kayataccen gadonsa, idanuwansa lumshe suke kamar mai yin bacci amma a zahiri ba baccin yake yiba, tsananin yanda kansa ke saramasa yasashi lumshe idanuwan, yunwa yake ji amma ba ze iya cewa a kawo masa a binci ba, a hankali ya bude kyawawan idanuwansa da sukayi matukar canza kala daga launin fari zuwa launin ja ja,idanuwansa ya maida kan agogon dakin kafun ya kara lumshe idanuwansa ya mike, sanye yake cikin wasu white kaya Riga da wando, wandon iya kwiwa , sosai kakkarfar jikinsa ya fito, inda coffee maker dinsa yake ya nufa, cikin kankanin lokaci ya hada coffee din , yana siffing a hankali bayan ya kammala Sha kai tsaye wani dan buttun ya dannan, take wata kofa dake jikin bango budewa da kanta, babban wajen Shaka tawa ne a wajan me girman gaske sosai , iya haduwa wajan ya haduwa , daga gefe daya wasu set din kujerane kawai a wajan sai wasu korayen flowers dasukayi wa wajan kawanya, sosai wajan ya hadu iya haduwa, inda take a cikin kejinta ya nufa,tana ganinsa ta fara bude fuka fikinta cikin muryan aku ta fara”gashinan yazo, gashinan yazo,king yajo “dan sakin fuskarsa da take a hade yayi tare da bude mata cage din , a guje kuwa ta fito tana zagayeshi kafun ta sauka a kan kafadunsa, shafa kanta yayi kadan kafun ya bude bakinsa” how’re you”, abun mamaki se ga tanan ta amsa masa, be kara cewa komai ba ya fito daga wajan .tabbas yasani a part from his family babu me damuwa dashi kamar zaki, wayar hannun sa ya dauka tare da danna wani number , seconds kadan aka amsa wayar sai da ya mula dan kansa sannan yasa wayan a kunnensa, sallamar zakice ta daki kunnensa, kamar baze ce komai sai kuma ya amsa, zaki zai kara magana yaji saukar muryar boss”am fine, you should rest too” yana gama fadar hakan ya kashe wayarsa. ***************************** ***************************** Zaune su amrah suke cikin wani kayataccen garden din da ya gaji da hanuwa, komai na wajan ya hadu sosai ba kadan ba ,ga sanyayyar iskar dake kadawa me shegen kamshi, sosai garden din ya hadu , amrah da ihsan suna zaune kan lilo be hade da flower gwanin ban sha’awa, sumayya da firdausi kuma suna zaune kan wasu kujeru, daga gefe daya yan aiki ne ke fan yi musu hidima, sosai suka cika gabansu da abubuwan ci kafun cikin isgilanci amrah tace musu subarwajan, suna barin wajan kuwa ihsan ta fara musu dariya, sosai take dariya musu tana binsu da kallo, dukan su sunsan dariyan me take shiysa suke binta da harara, sai data gama sannan ta kallesu “ wallahi yaya king halinsa saishi, ni Allah ne ya kubutar dani ,saura kadan na saki fitsari wallahi musamman yadda naga idanuwansa “, dukkansu dariya suka saki ,sumayyace ta kalleta “ Aini baku sani ba wallahi suma ne kawai banyi ba , dan ba karamun tsorata nayi da yanayinsa ba,zuciya tace kawai ke bum bum, amma duk da haka munci uban mu, Allah ne ya temakemu kuka tsaya a jan kunne be kada da tsitstsinka mana mariba”, yanxu ma duk dariya Suka saki tuno yadda yasasu tsallan kwani, ya tsine fuska Amrah tayi” ni kuma kunga ko a jikina dan my king ya samu wannan punishment din a Hakan ma ai na kalleshi da kyau “ dogon tsaki firdausi taja “shiyasa naga kin fi kowa rudewa ai , se shegen cika baki amma da kin gansa zaki fara ma kyarkyata” tana gama fadan haka ta tashi ta bar wajan, da harara Amrah ta bita" inma bakin cikin zan aura yaya king kike sai dai ki gama dan shi din nawa ne ni kadai”, babu Wanda ya Tanka mata tsakanin ihsan da sumayya sai binsu da kallo da sukai , inda sabo sun saba fada akan yaya king , kowa tace na tane sudai nasu ido kawai , daga nan suka canza hirar zuwa wata da ban suna yi suna dariya da Shan kayan da aka kawo musu har yamma suna wajan kafun su tashi kowa yayi part Dinsu. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ BUNKURE Dije ce rike da buta a hannu, yayinda take sanye da daurin kirji, daya daga cikin abubuwan da aka cika da ruwa ta nufa ganin ko wannansu cike taf da ruwa yasa cikin mugunta ta waiga ganin babu kowa a wajan duk sun shiga bacci yasa ta dauki a bu ta fasa daya daga cikin randar, take a Wajan ruwan ciki ya zube daman tafi ko wacce girma a ciki, d’ayar ta nufa da niyar fasa ta itama taji saukan Mari a fuskarta, ihu ta saka tare da sakin butar hannunta,wani kwakkwaran mari aka kuma yi mata , dafe kumatun nata tayi tana fashewa kuka, juya wa tayi dan ganin wanda ya marenta amma wayan bata ga kowa ba , a tsorace ta juya sai faman zare ido take , a hankali ta daga kafarta da niyar guduwa, sai Jinta tayi timmmmmmm a kasa ta fadi, wani a zababban kuka ta saki “ ku kuke ganin mu bamu muke ganinku ba , dan girman Allah kuyi hakuri”sai kawai ta kara fashe wa da kuka, jin shiru na wasu yan mintunan yasa ta mikewa da niyar guduwa , wasu kwararan maruka aka kara sakar maka , take a wajan ta suma fitsari na bi ta jikinta. ****** 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 DUK KARFIN IZZATA( star lady ) GIDAN AUNTY( mss Lee ) SARKI SAMEER( xeenat love) YA FITA ZAKKA (maman sayyid) JINI DAYA ( mss Bbk) ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 ( A heart touching love story) By mss Lee 💖 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 PAID BOOK MAI SON AI MAI TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581 BOOK 1 📕 Free page 9 🦋 ******** Suna zaune tun safe basu fito ba, oumma ta dafa musu ragowar taliyar jiya sukaji ana faman buga kofar da karfi kamar za a karya,” maryam bazaku fito bane kuna ji ina magana”, tsaya wa duk sukai daga cin abincin da suke jin muryar kaka tabawa, cikin damuwa oumma ta fito bayan ta yiwa su tahee kashedin karsu fito, a tsats tsaye tagansu ko wannan su , kaka ta bawa sai faman zaginsu take , “inna ina kwana”, bata bari ta karasa ba kaka ta bawa ta katseta“ban kwana ba , nace miki ban kwana ba , wallahi maryam kiji tsoran Allah , yanxu daman bakin cikin nace zan aurawa waccan yar taki me kama da aljanu tanimu shine zaku bi dare keda ban ka daddun ‘ya’yan ki ku fasa mun randa, kunsan tsawan shekarun randa ta da zaku tashi ku fasa mun” bata bari oumma tayi magana ba ta dora “ toh wallahi bari kiji,ko kina so ko ba kyaso aure kamar ya d’aurune dan ba fashi, itama munafukan da suka ‘ki futowa dani suke magana, ku fito ka aiki can kutashi kuyi, uban me ya hanaku yin aiki ma yau” sun kuyar da Kai oumma tayi kafun ta fara bata hakuri”kiyi hakuri inna, bamusan Wanda ya fasa miki randa ba” bata karasa ba Dije da bakin ta ya kun bura cikin haushi ta fara”toh karya za ai muku , in baku ba uwan wane ze fasa mata randa, yan bakinciki , shiyasa nace muku zuwan mutanen nan ba alkairi bane “ta kara sa da juyawa tana kallan mutanan gidan. “Hindu ce ta kalli inna ta bawa “ inna shiyasa ai jiya nace kawai kisa tanimu ya turo ba sai an jira bintalo ba, dan wannan bakin halin nasu ma waya sani ko sunbi wajan boka “ ta karasa tana hararar oumma da ta sun kuyar da Kai har ynxu fuskarta tana a yadda take. A daki kuwa jin yadda suke zagin oumman nasu yasa tahee fashe wa da kuka , sosai take kukan bakin ciki akan abunda suke musu, ita ba Auran ne ya dameta ba suje su aura mata duk Wanda suka ga dama amma bazata kuma lamunta da cin mutuncin da suke wa oumma ba, sosai shima taheer ransa ya baci. Kara fashewa da kuka tahee tayi jin kaka tabawa nacewa auwalu ya kirawo mata tanimu asa musu rana , sosai sukai musu tatas ko hakurin da oumma take bayarwa basu saurara ba suka bar wajan , Dije sai faman d’ingishi take dan tayi alwashin sai ta ruguza farin cikin su , dan tasan bokan da oumma ta ke bine yasa ayi mata haka (nace uhmmmmm Dije jikin ki be gaya miki ba kenan🤭). Farin macijin dake la’be tun dasu ya kurawa tahee ido ganin yadda take kuka shima sai launin idanuwansa suka canza daga baki zuwa ja ,sai ya silale ya fita baki d’aya daga dakin ganin oumma na kokarin shigowa. ➰➰➰➰➰➰➰➰ DADA zaune take cikin wasu lallausan kujera jikinta sanye da wasu fararan cotton din kaya , sosai kayan sukaiwa jikin tsufanta kyau,a center din gabanta wani dan madaidaicin glass jug ne cike da fura, sai faman tashi kamshin furar da yaji damu yake, kallan Aunty dake gefe a zauna tayi tare da gyara zamanta , inajinki Amina , cikin inda inda Hajiya Amina ta soma magana “ wai dada naga yan matan gidan duk sun tasa ne , shiyasa nake ganin me zai hana ayi Auran dangi, ko King ne a aura amsa amrah, naga kamar suna kyaunar junansu”, sosai dada ta zuba mata idanuwa kafun ta soma magana “amma dai haroon kike magana akai ko, ke yanxu Amina bazaki dena wannan halin naki ba , shi sadaukin Yaushe kike ganinsa har yace miki suna Kaunar juna”, kin kina ta soma tama kasa magana “ saurin da katar da ita dada tayi”bana san irin haka , inda shi sadaukin ne yace yanasan yar taki da babu abunda zai Hana Aki aura masa , amma tunda be fada ba kar nasake Jin wannan batu, zaki iya tafiya”, sosai ran hajiya Amina ya baci da magan maganun dada , dan tabbas tasan da hajiya kilishi ce ko uwar king din da babu abunda zai hana tayi naam da zancen, daman ta dad’e da sanin cewa dada ba kaunarsu take ba , amma fili sai ta saki murmushin nan nata “tuba nake dada , ban fada da wata manufa ba, na barki lapiya”, itama dadan jinjina mata kai tayi “akiyaye “,itama aunty mikewa tayi tana fadin “insha Allahu”, tare da kama hanyar fita daga falon, bin bayanta da kallo dada tayi kafun ta girgiza kanta tacigaba da sabgar gabanta. Kamshin da batayi tsammani bane ya cika mata hanci ,juyowa dada tayi domin tabbatarwa, shidin ne tsaye , fuskarsa kwata kwata ba annuri akai ,kallo daya dada tayi masa ta dauke kanta ,cikin kasan makoshi kamar bazai yi magana ba sai kuma ya bude bakinsa “Assalamu alaikum” dabadan hankalin ta na kansa ba da babu abunda zaisa taji sallamar tasa” Wa’alaykumussalm “ tabashi amsa itama ,ta kowa yayi ahankali tare da karaso wa inda take, a maimakon ya zauna a kujerar kusa da ita sai ya zauna akan kujerar da take , “barka da yamma dada”, ta bile baki dada tayi “sai yanxu ka bayyana kenan, Kai yanxu saraki da ban nemekaba da bazakazo ba kenan,kadai ji tsoran Allah “,amai makon ya bata amsa sai ya kwantar da kasan a kafadunta tare da dan kwa’be fuskarsa kadan,ture kafadarsa dada tayi tare da mikewa , cikin masifa ta soma magana “ kabari in kayi aure sai kawi wa matar ka haka , bani ba salan zawaran da sukeso su aureni su gudu sabida karyayyan kashi”,dan murmushi leben baki ya saki da ko dada dake kusa da shi bazata gane hakan ba, sosai yayi musamman da pink lips dinsa ya kara turuwa,harara dada ta sakar masa tare da ta’be baki “kajirani” tana gama fada ta mike da nufar kitchen dinta, bata dade ba ta fito dauke da wani dan karamun tray, cikin yanayinsa na rashin garaje ya mike tare da amsar dan karamin tray din da ta fito dashi, inda suke zaune suka koma sai a sannan dada ta karbi tray din, lafiyayyar tuwo ne da miyar kubewa d’anya da taji nama da Ganda , sai kifin da aka sa masa, sosai kamshin abincin yayi masa dadi amma sai ya dan kawar da kansa gefe, dungure masa kai dada tayi” toh d’an neman magana ni na yi da kaina”, sai a sannan ya jiyo fuska a sake amma kwata kwata babu murmushi akai,karban abinci yayi tare da fara ci bayan yayi Bismillah, sosai yaci tuwan dan ya dade beci abinci da yawa ba,tunda ya fara cin abincin dada take binsa da kallo, Itade tanasan jikan nan nata, maganar hajiya Amina ce ta fado mata arai, kamar zatai masa magana sai kuma ta fasa, tasan halinsa yanxu ze iya tsanar yarinyar ko yaje ya ‘bab’bala yar mutane. Ganin yadda take kallansa ne yasashi dage mata gira , waro idanuwanta dada tayi “yanxu ni sadauki kake dage wa gira daya , sai kace yar iska, toh maza maza tashi ka bar part dinnan, ga furar ka nan ma, ka ‘bacemun da gani” sallamar zoya ce ya katse dada , da sauri zoya ta karaso wajan king “akhi “,lumshe mata ido yayi tare da budewa”na’am ukhti”, dariya sosai ta saki jin ya kira ta da ukhti “akhii duk yau ban gankaba fa” ta fada tana marairaice fuska,kamar bashi ba , shima ya dan kwaikwayi muryarta “Nima duk yau ban ganki ba ukhti”, binsu da kallo kawai dada tayi tana tabe baki” da yake kin ga ubanki shine kika manta inda kikazo, toh ku tattara kubar min daki”marairaice fuska zoya tayi “Haba dadar mu”yanxun ma harararsu tayi “Oho dai “, king ne ce mata komai ba sai mikewa da sukai tare da daukan furarsu “sai mun kara dawowa dada”,ka tsesu dada tayi “bana bukata”, shima king din tabe baki kawai yayi suka bar part din, da kallo dada ta bisu tana sakin murmushi” kaidai ba me iya maka , zanga macen da zata iya hakuri da wannan baud’ad’d’an halin naka “. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ BUNKURE Kai tsaye macijin bai tsaya a ko ina ba sai cikin ban dakin gidan, Daidai kaka tabawa tana kama ruwa jitai kamar abu ya hau kanta, sai ta taba Wajan taji ba komai , sharewa tayi tare da cigaba da abunda take, dan karamin abu takumaji kamar yana yawo a jikinta, a sukwane tayi mike tana karka da jikinta, abun be dena yawo a jikinta ba sai ma kara yawa da yayi, ihu dada ta saki da nufar hanyar fita daga bayin, dan karamun halittar da ta ganin a kofar bayin yasata komawa ciki da sauri tana zare ido”nashiga uku” jitai wasu murya yan kanana suma suna cewa “na shiga uku”, amaimakon tayi salati sai ta fara “laha’ila, ni tabawa na shiga uku me nake gani” ta karasa maganar tana fashewa da kuka duk ta hada uban gumi, wata muryar daban sa’banin ta dazu itama” laha’ila ni tabawa na shiga uku ne nake gani” aka karasa maganar da fashewa da dariya, wani kukan kaka ta bawa tasaki ganin yadda halittar ta nufota Gadan gadan yasa kaka ta bawa sumewa take a wajan .macijin nanne ya bayyana tare da karasa wa inda take Daidai bakinta ya buga mata jelarsa, take a wajan bakin kaka tabawa ya kunbura, batt ya bace shima da barin ban dakin. Su tahee duk sun fito suna aikin su, yau kwata kwata ba annuri akan fuskokinsu, ruwa suka fara d’ebowa kafaun su fara aikin gidan , tana cikin aikin taji zuciyarta ta fara washewa daga cunkushewar da tayi a kirjinta, shima taheer hakan yaji, lokaci d’aya suka sake tare da cigaba da ayyukansu yadda suka saba, ganin haka yasa itama oumma zuciyarta yin sanyi ganin duk sun saki ransu, kusan awa daya suna aiki a tsakar gidan duk mutanan gidan sunshige ciki sabida ranar da ake me zafin gaske, ganin yadda ake kokarin bude bandaki yasa duk zubawa kofar ido, da kyar kaka ta bawa ta bude kofar sabida yadda bakinta ya kunbura sai faman din gishi take, binsu tayi da kallo ganin yadda suka tsare da idanuwa, bakin da ya kara kunbura ta bude daniyar zaginsu, zugin da taji ne yasa ra hadiye maganar tana matsar kwalla da bin gefensu ta wuce. Sosai dariya take so ta kwace musu ganin yadda ta wuce tana tsamin kashi, tana shigewa daki kuwa suka fara dariyarsu, TAHEER harda faduwa sabida dariya, itama oumman murmushi ta saki ganin yadda kaka ta bawa ta dawo kamar tsohuwar mahaukaciya, sosai suke dariyarsu, sai da suka gama dan kamsu sannan suka cigaba da aikinsu. **DIJE zaune take cikin dakinta da ya cika da uban shirgi ,sai faman tashin wari yake da d’oyi , ko ina na dakin yayi kaca kaca dashi ita kadai ce a dakin sai karamar nokia dinta dake hannunta , ta dad’e tana waya da kawarta jimmala kafun ta kashe tana dariyar mugunta, kamar jira ake kuwa tana kashe wayan aka tsinka mata mari, take a wajan tayi filinki sabida azabar marin da taji, bata dawo hayyacinta ba ta kara jin saukar wani marin a fuskar ta, kuka ta fashe da shi, sai faman waige waige take, ganin ba kowa a dakin yasa kudawa zuwan mata take a wajan, sosai ta kuma rud’ewa jin abu na yawo a jikinta,duk inda takai da tabawa sai taji ba awajan abun yake ba, sosai Dije ta rude sai faman marin kanta da take , tana marin tana kuka, ga majinan da ya cika fuskarta , sai faman tashin tsamin wari take… Comment and share 💖 THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA💖 👇 💖DUK KARFIN IZZATA (star lady)💖 💖GIDAN AUNTY (mss Lee )💖 💖JINI DAYA ( MRS bbk )💖 💖YA FITA ZAKKA(maman sayyid)💖 💖SARKI SAMEER (xeenat love)💖 Mss LEE💖✍️ ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 ( A heart touching love story) Story &written By Mss Lee💖 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 PAID BOOK MAISAN AYI MASA TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581 BOOK 1 📕 Free page 10 🦋 Shigowar bintalo dakin kamar wacce aka jefo ta ko sallama babu, yasa dije kamewa, komai sai ya tsaya mata, kallan kanta da dungayi ganin duk ta ya mutsa jikinta, kallan ta bintalo tayi rai a bace tana toshe hanci “Haba Dije , kazantar taki har takai kiyi kashi a jikinki, gaskiya kina bada ni , ji beki katuwar kawai sai wari kike faman yi , ga kashin ki me shegen d’oyi, ta karasa da hararanta. Dije ce ta soma magana “Haba bintalo , Kema kinsan haka kawai bazanyi kashi a jiki ba , lalurace ta sameni , ni kaina bansan ya akai hakan ta faru ba”, ta kare zance da zunbula hijabi, gudun kar yan gidan su ganta, tayi sauri tashige bayi bayan dan ruwan da ta dauka a buta. Su tahee ma ransu fess suka koma daki, bayan sun gama aikin su , haka suka yini a daki, lokaci zuwa lokacin tunanin dan iskan da akace za a aura mata yana fado mata arai. ******* A kwana a tashi ba wuya wajan Allah SWT, yau watan su tahee 1 da ‘yan kwanaki a bunkure, abubuwa da dama ya faru ciki harda maganar Auran tahee da tanimu da tayi mugun tsana. A yan kwanakinan ba karamun wuya suke shaba wajan mutanan gidan, musamman kaka tabawa da dije datayi mugun tsanar su, kullum da kalar ukubar da zasuyi musu, abu daya ne ke kwatarsu , duk lokacin da kaka ta bawa ta wahalar da su ranar bata iya baccin arziki sai safiya , a lokacin su tahee ke samun damar hutawa . Taheer ma yanxu ya koyi faci, Inya futa tun safe bashi ke dawowa ba sai 6 na yamma, a gida kuwa daga oumma sai tahee, yanxu ma kwance take kan cinyar oumma tana taje mata uban tilin gashin kanta da ya zubo har gadan bayanta da cikon da yake dashi, “oumma”cewar tahee,”naam aunty tahee”oumma ta amsa mata cikin zolaya , dariya tahee ta saka, “Allah oumma ni banasan wannan gashin kan nawa wani lokuta, kallifa ko tajeshi bana iyayi da kyau, “aikinsan hanyar iliya me aski, sai kije ya aske miki”, turo baki kawai tahee tayi dan tasan magana oumma ta fada mata. Suna zaune sukaji an banko kofar dakin , duk kallan kofar sukai lokaci daya , bintalo dake tsaye se faman cika take ta kalli tahee ba ko sallama , “toh matar mashayi sai kije angwan naki yazo”, tana gama fadar hakan ta banko musu kofa. Tsaki tahee taja tana kokarin kontawa oumma ta dakatar da ita “tashi kije”bata ce wa oumma komai ba ta zura hijabinta tare da ficewa waje. A tsaye ta ganshi cikin wasu yan iskan Riga da wando, sai faman tashin warin giya yake, saurin toshe hanci tahee tayi jin zata yi amai, ga bakikkirin bakar fuskarsa sai faman naso nake , cikin Maye ya zuba wa tahee jajan idanuwansa” ke dan uwarki , shine zan dunga kiranki kina kin zuwa, ke gaki yar iska ko” ya karasa yana tangal tangal kamar ze fado mata, matsala tahee tayi baya tana binsa n da kallan tsana “inka gama zan wuce dan banda lokacin dan iska”, wayo idanuwansa yayi cikin maye yana kifkifta kana nun inaduwansa” ke, ni kike cewa dan iska dan uwarki, toh bari na nuna miki iskanci, kafun na bada sadaki zan d’anaki nasan zakiyi ruwa” ya karasa tare da daga hannunsa zai tabata, saukar marin da yaji a fuskarsa ne yasa shi tangal tangal zai fadi, ganin yana ganin biyu biyu ne yasashi kara ware mummunar fuskarsa “ kutumar ubancan , ya na fara ganin garin yana juyawa ko an fara hazo ne “be kammala maganar tasaba tahee da idanuwanta suka juye ta kara tsinka masa mari” saurin dafe fuskar tasa yayi har yanxu bakin nashi be mutu ba” auzubillahi, ko an fara tafiya lahira ne ban sani ba” saukar marin da yaki a fuskarsa ne ya sashi zabura da fita “shikenan a fara sha hada , an fara mutuwa “, sai da ya bace wa ganin ta sannan idanuwan ta suka dawo Daidai ganin ba kowa a wajan yasata dage kafada da komawa cikin gida . Koda ta kowa cikin gidan oumma bata ce mata komai ma , itama tahee batace komai ba sai hirarsu da suka cigaba . ➰➰➰➰➰➰➰➰➰ LAGOS Tun d’azu ta kasa zama sai faman zirga zirga take , Aunty kawai take jira ta shigo, ta dade a tsaye kafun hajiya Amina ta shigo falon duk rai a bace , kallanta amrah tayi kafun ta sauke a jiyar zuciya, “Anda ce aunty!?” Ta tanbayeta da sigar tanbaya , bata kulataba sai da ta samu waje ta zauna “ amrah ban taba sanin matar nan makira bace sai yau, wai harni tsohuwar matar nan zata karya ta”, tass ta bawa amrah labarin abunda ya faru ta dora da cewa” wai ni amrah kina shafa kwallin tayar masa da sha’awan da Malam ya baki “ cikin kun burin fuska Amrah ta amsa mata “ ina shafawa aunty, gasky ya kamata a koma wajan Malamin dan bazan taba yadda wata ta same shi in ba ni ba, ni ko baze aureni ba inaso mujiyar da juna dan inasan na d’ad’and’ana zumarsa kona kashe sha’awar dake tasomun”jin jina mata kai kawai hajiya Amina tayi, itama amrah bata kuma cewa komai ba ta shige daki, da kallo aunty Amina ta bita “ ba ke ba ai amrah ko ninan da zan samu damar d’and’anasa so nake , musamman yadda yake da kakkarfar jikinta, ni kadai nasan dad’in da zansha “ duk cikin zuciyarta take wannan sa’ke sa’ken kafun ta nufi haryan dakin ta itama . *********** Ya dan Jima a hospital yau sabida wasu Mara lapiya a dake dake cikin wani mayuwacin hali, successfully kuwa akayi musu aiki, bayan ya dawo ne zaki ya kawo masa files din company, ba karamun barnan kudi akai ba, makudan millions sun ‘bata, batare da kwakkwaran daliliba,duk account din da kudin ke fita ta wajansu anne mesu anrasa, Wanda hakan ya bashi alamar tanbaya , tabbas ana fitar da kudi sannan dasa hannun wasu daga cikin companyn , amma tanbayar su wanene suke fitar dashi, daya daga cikin secret agent din companyn king yasa a nemo masa, tare da bashi Umarnin binciko masa komai daya danganci file din companyn,suna gama aikin da zasuyi sukai futar gaggawa shida zaki yau ko masu tsaro be fita dasu ba. ➰➰➰➰➰tunda ta tashi yau da fargaba ta tashi, ganin kullum mutanan gidan sai sunyi maganar aura mata dan iskan da suka ce, komai cikin sanyi take yinsa, “tahee”oumma ta kira sunanta “naam oumma”sosai oumma ke kallanta”meke damunkine yau”murmushin ya’ke tahee ta saki “babu komai oumma kawai yau da fargaba na tashi”, murmushin manya oumma ta saki” in Auran nan kikesa wa aranki kicireshi, ki dunga yawaita addua in alkairi ne, in kuma sharrine Allah ya nisan taki dashi”jin jina mata kai tahee tayi “insha Allahu oumma”. Bin bayan ta da kallo oumma tayi , abun na damunta sosai amma tana boye rauninta ne sabida kar tahee ta karaya, kullum adduar ta Allah ya zaba mata mafi alkairi. Shigowar tahee dakin ne yasa taheer sakin murmushi dan duk yaji zancensu,kara sakin wani murmushin yayi yana kamo hannun tahee din, be bari tayi magana ba ya dora da “nayi mafarki, nayi mafarki kinyi aure ,kin auri babban mutum da kowa yake san mallakarsa ba wancan dan iskanba, zakiyi rayuwa dasu sosai wasu zasu soki, wasu kuma zaki nuna miki ki”binsa da kallo kawai tayi duk da bata yadda da magan ganun saba amma hakan ya sanyaya mata zuciya . Karfe biyu na rana wasu manyan motocine suka shigo garin, kowa sai bin motar yake da kallo ana d’aga musu hannu, Daidai kofar gidansu tahee motocin nan sukai parking yara da manya kowa ya cika wajan , cikin gida kuwa har an kawo musu labari, da sauri kaka ta bawa ta shige daki tare da dakko wata farar Leda data cukurkude, bude ledar tayi tare da dakko tsinken turaran wuta, bayan ta kunna turaren wutarne ta koma ta dauko sabuwar tabarmarta ta shinfida a tsakar gidan , komai cikin sauri take yinsa . A hankali ta fito daga cikin bayan wata tinted prado,bayan uban damin kudin data bawa security su rabawa mutane , ba kowa bace face hajiya kilishi, a hankali cikin takun manyan mutane ta nufi cikin gidan fuskarta dauke da murmushi, yayinda biyu daga cikin security din suka fara fito da kayan motar suna shigar dasu cikin gidan . Tun daga kan matasan gidan har manya kowa tsugunnawa yake yana gaisheta, cikin sakin fuska take amsawa kowa harta karasa zama akan tabarmar da aka shinfida mata batare da ‘kyan ‘kyanin komai ba. Sosai sukai hirar Yaushe gamo ta bawa kowa tsarabarsa , duk wannan abun da ake su tahee basu sai me ke faruwa ba , sai hayaniyar da suke ji tana tashi sama sama,anan ne suke mata gulmar dawowar oumma da Sanar da tahee, sosai hajiya kilishi ranta ya baci akan rashin sanar da ita da basuyi ba , da Auran da suke san yiwa tahee, ranta ba karamun baci yayi har suka fara dana sanin fada mata , bata nuna musu komai ba sai fadan da tayi musu da Nasiha me ratsa jiki , sun dade suna tattaunawa kafin ta mike ta nufi dakin su tahee, kwankwasa kofa tayi , TAHEE dake tsaye rike da tsintsiya ta bude kofar , cikin waro ido da tsananin farin ciki ta furta “AUNTY” itama aunty tata murmushi ne kwance a fuskarta, budewa tahee hannuwa tayi da sauri kuwa tahee ta nufe ta , ta rungumeta sosai tayi farin ciki da ganin auntyn Tata har hakan ya kasa boyuwa, kallanta hajiya kilishi tayi ganin yadda ta kara ramewa ga bakin da tayi, batace mata komai ba sai girgiza kai kawai da tayi bayan tahee ta bata hanyar wucewa, sallar da hajiya kilishi tayi ne yasa ko wannansu kallan kofa, take ko wannansu ya saki murmushi, TAHEER ne ya tashi daga inda yake ya bawa aunty ta su waje , bayan sun gaisa sun dade suna hira kafun hajiya kilishi tayi wa oumma jajan abin da ya faru , kallan tahee hajiya kilishi tayi kafin ta kira sunanta” taheera “ tagowa tahee tayi tana amsa mata “na’am aunty” cikin dan hade rai hajiya kilishi ta soma magana” naji labarin kince kinaso kiyi aure har ankawo kudin ki , hakane “, fashewa da kuka tahee tayi tana girgiza kanta ni bana san shi aunty”ganin yadda take kuka ne yasa aunty tausaya mata itama tayi mata hakan ne sabida ta san asalin gaskiyar “shikenan share hawayen to” kamar yadda ta satan kuwa share hawayen tayi” yanxu zan baki za’bi zaki bini ko zaki auri tanimu” saurin dago da idanuwan ta tayi da zubawa auntyn tata, murmushi hajiya kilishi tayi tana mikewa “ kuyi shawara toh “, ganin yadda ta mike din zata basu waje oumma ta dakatar da ita “itama yar kice ai wata shawara zatayi , duk yadda kikayi ai Daidai ne”,Murmushin farin ciki hajiya kilishi tayi “nagode sosai yaya, Allah ya bar zumunci, nan da munti 30 zamu tafi “ tana gama fadar hakan ta bar dakin. Dan kallan oumma tahee tayi cikin damuwa tace “oumma kin yadda na tafi ya barku” yar harara oumma tayi mata kafun ta mike “ idan ba kyaso ki bita sai kitsaya ayi miki auren inyaso sai ki tare” tana gama fadar hakan ta shige dakin. Kallanta TAHEER yayi “ shawarar da oumma tayi miki shine alkairi a gareki dan mutanan nan bazasu kyaleki ba sai sun aura miki shegen mutumin can , me kama da biri “jinjina masa kai tayi cikin damuwar dake fuskar nan, ganin yadda ta damu yasashi fara janta da hira har ta sake. Suna zaune oumma tafi to tare da kallansu, sosai tayi wa tahee fada da nasiha akan ta rike mutuncin ta, ta zama me hakuri da kawaici a duk yadda ta sameta, sosai oumma tayi mata nasiha da nuna mata illar rashin yin azkar, har kuka tahee tayi ganin yadda oumma take Mata nasihan me ratsa jiki, ko wannansu dauriya yake, shima taheer ji yake kamar ya saki kuka amma ya dake tare da sakin murmushi, suna zaune a hakan hajiya kilishi ta dawo , kasan cewar tahee tayi wanka hijabinta kawai tasa tana sharar kwalla, TAHEER ya dauki jakar kayanta tare da fita dasu, oumma bata biyota rakiya ba gudun abinda ze je ya dawo . Cikin sanyin jiki tahee ta fito waje , tsatstsaye ta same mutanan yan gidan kowa sai faman harare Harare suke ba bakin magana , musamman Dije da har kwallar bakin ciki se datayi, bintalo ba sai faman zaginta take ganin ba a tafi da ita . Saida hajiya kilishi ta gama sallamarsu kafun ta kama hannun tahee ta shigar da ita mota, a haka motocin suka fara tafiya, tunda aka fara tafiya tahee tunani take , har aka karaso airport din bata sani ba sai da hajiya kilishi tayi mata magana , wata Hanya sukabi a cikin airport din da ya kaisu wani babban fili, wasu manyan jiragene awajan kusan guda uku, ko wanne da tanbarin AL_NAHYAN a jiki , daya daga cikin jiragen suka nufa jikin tahee sai faman rawa yake,Daidai bakin step din jirgin ta tsaya ta fara rarraba idanu, ruko hannunta hajiya kilishi tayi “karki damu ba abunda zai miki” saurin gyada mata kai tahee tayi zuciyarta sai faman bugawa take , ga hannun hajiya kilishi da ta rike gagam a haka suka shiga cikin jirgin, duk sauran bodyguard din Sara mata sukai tare da tsayawa a wajan jirgin…. Comment and share ✍️. 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 💖LITTAFAN SUNE KAMAR HAKA 💖 👇👇👇👇👇 💖DUK KARFIN IZZATA( star lady)💖 💖GIDAN AUNTY (mss Lee )💖 💖SARKI SAMEER (xeenat love )💖 💖YA FITA ZAKKA (maman sayyid)💖 💖JINI DAYA (mrs bbk)💖 Comment and share ✍️. Mss Lee 💖 ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 (A heart touching love story ) Story & written By Mss Lee 💖 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 PAID BOOK MAISO AYI MISHI TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581 BOOK 1📕 Free page 11 🦋 Karfe 9:10 na dare jirginsu ya sauka a murtala muhammad international Airport (MMIA) dake Garin lagos, wasu dankara dan karan motocine sukazo daukarsu,da kyar tahee take daga kafarta jin yadda kanta ke sara mata, mintuna 35 ne suka kaisu AL_NAHYAN EATATE dake banana island ,tundaga kan Layin gidan kan tahee ke matukar sarawa ga wani irin tsananin bugu da zuciyarta kema ta,ko ina da yalwataccen haske kamar ba dare ba , ta ko ina sojojine ke Sara musu, sosai tahee ta rike hannun hijabinta gagam ganin irin sojojin dake gidan , sabida ydda zuciyarta ke bugawa sosai ta kulle idanuwanta , direct motocin part din hajiya kilishi suka nufa,sau biyu hajiya kilishi na kiran tahee amma bata masa ba , ana ukunne ta tabata sosai tahee ta ware idanuwanta, kallan ta hajiya kilishi tayi na yan sakanni kafun ta soma magana “ lapiyan ki kuwa “ gyada mata kai taheera tayi sai kuma ta bude bakinta” Kai na ne ke dan ciwo aunty “, cikin damuwa hajiya kilishi ta kamo hannunta ta futo da ita daga cikin motar”sannu kinji, nasan gajiya ce muje ciki kisha magani sai ki kwanta”nan ma gyada kanta tahee tayi batare da cewa komai ba,kafarta ta taka da soma tayifa sosai wani azababban zafi ke ratsa kafarta , kamar wacce ta dora kafarta a garwashi, ko wacce addua tazo bakinta yi take , nan da nan taji zafin ya tafi, haka suka karasa ciki tana bun hajiya kilishi a baya, dakin dake gefen star case ammi ta bude , “Bismillah tahee”, shiga ciki tahee tayi bakin dauke da Bismillah kamar ydda hajiya kilishi ta umarceta,”ga ban daki nan , zansa a kawo miki abinci da magani sai kishi ki kwanta”cewar hajiya kilishi,”na gode sosai aunty ,Allah ya saka da Alkairi”bata bari ta karasa ba ta katseta”Godiyar ta isa haka kisa mu ki huta”tana gama fadar haka ta bar dakin.itama toilet ta nufa tare da kama ruwa sannan tayo Alwala , tana fitowa ta tarar da jakar kayanta, hijab ta dauka tare da nufar inda dadduma take shinfide,sallolin da ake binta ta rama tana cikin addua ne aka kwankwasa kofar, Tashi tayi tare da budewa , wata budurwace ta shigo sanye da blue din Riga da dark blue din skeat ,”good day ma”cewar ta, murmushi kawai tahee tayi batare da ta amsa ba, abincin dake hannunta ta ajiye cikin center table din dake kusa da ita , cikin gurbatacciyar hausarta tace” madam tace na kawo miki abinci sannan kisha magani ki kwanta,”toh na gode”, jinjina mata kai budurwar tayi tare da furo mata kofa , abincin da aka kawo mata ta bude lafiyayyan abincine me rai da lapiya a ciki,sai kunun aya da aka sa mata cikin wani mini glass jug, daga gefen tray din wasu Kayan mar marine aciki, kadan ta tsakuri abincin “da oumma da taheer sunanan tare za muci abincin , nasan yanxu Suna can su kadai”, cewar tahee harta kammala cin abincin, kuskure bakinta tayi tare da watsa ruwa , sannan ta hau kan lapiyayyan gadon dakin ,lilliba tayi jin sanyi na ratsata ta ko ina , bata dade da kwanciya ba bacci ya dauke ta . ➰➰➰➰ A gajiye ya dawo gidan bayan zaki ya ajjesa, ko part din ammi be Jeba, Wanka kawai yayi tare da nufar down stairs , Kai tsaye kitchen din dake falon ya nufa, banban kitchen ne da ya gaji da haduwa komai na anfanin kitchen akwai shi a ciki,kitchen din sai faman daukan kyalli yake, coffee ya hada cikin coffee maker din kitchen din, kan daya daga cikin kujerun dining din kitchen din ya zauna, a hankali yake sipping coffee din dake hannunsa,bayan ya shanyene ya kara hada wani tare da barin kitchen din, stair case ya dau tare da nufar kofar hagunsa, taku kadan ya kai shi wasu kofofi guda uku, kofar tsakiya ya shiga , ya dau dogon lokaci a ciki kafun ya fito, stair case din da zai kaishi second floor ya hau, a hankali yake taka stairs din har ya karasa hawa saman, kan daya daga cikin kujerun falon ya zauna tare da fara operating din system dinsa, ya dade yana anfani da ita kafun ya kashe ta gaba daya , toilet ya nufa be dade ba ya fito tare da nufar faffadan gadonshi, remotes din fitulun part din ya kashe kafun ya kwanta cikin lallausan gadonsa, be dade da kwanciya ba bacci ya daukesa. Wutace sosai take ci, da anzuba mata ruwa Sai ta kara tashi kamar wacce ake hurata , ga hayaki da ya gauraye ko ina, daga cikin wutar kuwa hannu ake miko masa cikin azaba “Akhee habeeby!!Akhee habeeby!!”hannunsa ya Mika da niyar ya kamo Wanda yake cikin wutar… farkawa king yayi sai faman hada gumi yake bayan sanyin Acn da ya cika dakin, adduoi ya fara karantawa a hankali wata nutsuwa tazo masa ,wayarsa dake side din gadan sa ya kunna,4:30shine abunda agogon ya nuna masa, mikewa yayi tare da nufar toilet, wanka ya fara yi kafun yayo Alwala, ya dade yana nafila kafun ai kirin sallah, direct kasa ya nufa bayan ya idar da sallahn , sanye yake cikin white jallabiya , sosai farar jallabiyar tayiwa surar jikinsa kyau,gashin kansa sanye yke cikin bakin rawanin larabawa, sosai kyawun fuskarsa ya fito, musamman idanuwansa da suka kara haske sai kyalli suke duk da kasancewar fuskarsa a hade yake,a hanyar zuwa Masallaci suka hadu da abeey shima zasu tafi masallacin,a haka motocin su suk fita , a dawo wa ma tare suka dawo gidan,Kai tsaye part din dada suka nufa dukansu, ganin babu kowa a falon yasa su samun waje ko wannan su ya zauna. Mintuna kadan sai gashi ta fita sanye da hijabi a jikinta , ko wannansu gaishe da ita yayi , yayinda take amsawa fuskarta washe da fara’a, kankance ido king yayi” dada yau naga sai fara a kike ko an miki albishir da zuwa umarace”a hankali yayi maganar amma duk da haka sai da ta jisa, hararar sa dada tayi”A’ah gorin daurin aurenka aka kawomun”kara hade fuska king yayi tare da dauke idanuwansa daga kanta,tabule baki dada tayi “Kai dai Kasani mutum kullum cikin daure fuska ,kamar audiga ina dalili”, be tanka mata ba sai ma lumshe ida nuwansa da yayi, abeey kam murmushi kawai yayi, hira suka dada ta fara tare da su uncle musaddiq , abeey na sa musu baki lokaci zuwa lokaci na yana kallan king, ganin hirar tasu bame karewa bace yayi musu sallama tare da nufar part dinsa. Gym room dinsa ya nufa , tare da sa kayn motsa jiki , ya dade yana motsa jiki kafun ya futo duk ya hada zufa ,kwantaccen gashin kansa ya zubo masa har wajan idanuwansa,Wanka yayi tare da shirya cikin wani hadadden suit red colour, daddadan kamshin turaransa ya cika ko ina , gashin kansa ya sha gyada yayin da gefe guda na fuskar sa gashin ya futo harwajan idanuwansa,pink lips dinsa ya turo sosai , yayinda fuskarsa take a daure,sosai yayi kyau cikin shigarsa , sai ta kara futo da ainahin kalarsa ta larabawa,cikin takun sa ya bar part din , direct part din ummey ya nufa, har lokacin zoya bacci take , be dad’e ba ya bar part din tare da nufar part din ammi. Yana shiga falan ya tarar da ba kowa a ciki sai yan aikin dake gyara dinning , suna ganinsa ko wanne jikinsa ya dau rawa, cikin rawar murya suka gaishe shi,da hannu kawai yayi musu alama , suna ganin haka sukai saurin barin wajan, kan daya daga cikin 2 sitter din kujerun ya zauna tare da crossing legs dinsa. Cikin shigar material ammi ta fito daga kitchen , hannunta dauke da tray din abinci, cikin na tsuwarsa ya mike tare da nufar inda take da nufin sauke mata tray din, girgiza masa kai tayi “no son,abincin daughter ne”, kallan ta yayi na yan sakanni kafun ya bude bakinsa” me ya kawo su part dinnan da sassafe”,hararar sa ammi tayi “Kai me ya kawo ka da sassafe, Kai tsaye ya bata amsa “to see my happiness “murmushi ammi ta sakar masa tana kara jin kaunarsa a ranta ,”ba abincin su amrah bane, wannan na sister dinka ce , you will see her soon”bai ce mata komai ba sai lumshe mata ido da yayi, itama Kai tsaye dakin da tahee take ciki ta nufa, akan dadduma ta tarar da ita , mikewa tayi tare da karban tray din hannun Amin ta ajje mata a gefe” ina kwana aunty”kallanta sosai Ammon tayi “from today ki kirani da ammi not aunty” jinjina mata kai tahee tayi sai kuma ta bude baki”insha Allah ammi” dariyar jin dadi ammi tayi “kin tashi lapiya, hope ciwan kan ya sauka”, “eh ya dena ammi”cewar tahee, “toh Allah ya kara sauki, ga breakfast nan in kin gama sai ki fito falo karkiyi ta zama a daki ke kadai”, jin jina mata kai tahee tayi “toh ammi na gode “, fita ammi tayi daga cikin dakin, TAHEE kuma waje ta Samu ta zauna “ya Allahu har na fara kewar ku oumma na da taheer dina “. A falo kuwa har yanxu king na zaune ya lumshe idanuwansa “if not for ammi, who dare to keep him waiting”,lips dinsa na kasa ya fara tsotsa kwata kwata bazaka gane yanayinsaba, shafa gefan fuskarsa da akaine yasashi bude idanuwansa,ammi ya tarar a tsaye sai faman murmushi take saki, dauke kansa yayi daga kallanta,”sorry my son”, dago da idanuwansa yayi tare da kallanta “it’s okay , ammi am hungry “,am coming” kawai tace tare da komawa kitchen , hadadden breakfast dinsa da tayi masa shida tahee takawo masa , tsabar sarauta a baki take bashi,kadan yaci tare da Shan kunun ayan da yake matukar kauna,bayan ya kammala cin abincinsa ammi ta kallesa “son Yaushe zaka dawo gida”Kai tsaye ya bata amsa” it can be possible da yamma , kina bukatar wani abune “girgiza masa kai tayi “no son na tanbaya ne kawai”,mikewa yayi tare da pecking din goshinta “am going now”, take care shine abunda ammi tace masa , jinjina mata kai yayi tare da barin part din. A daki Kuwa tahee wanka tayi bayan ta kammala cin abincin da ammi ta kawo mata, hijab dinta ta saka tare da kwashe kwanukan ta fito falo, Daidai lokacin da yan matan gidan ke shigowa, kallan tara saura kwata amrah ta bita dashi”ke kuma daga ina”,murmushin yake tahee ta saki”ina kwananku “wani hararan amrah ta bita dashi “bashi na tanbayeki ba”.ihsan ce ta katse mata zancen ta” easy amrah , ki bita a hankali mana”, kallanta ihsan tayi cikin sake fuska”yan mata ya sunan ki”, amsa mata tayi da “TAHEERA “tana sun kuyar dakai, lokaci d’aya zuciyar firdausi da amrah ya buga, “wow gaskiya kina da suna me dadi gaki kyakkyawa”,Shigowar ammi ne ya katse ihsan, “ah ah yan matana yana ganku a tsaye “, sumayyace tai saurin bata amsa “bakomai ammi mun shigone sai mukaga bakuwarki shine muke dan gaisawa”murmushi ammi tayi “kun kyauta kuwa , ku samu waje ku zazzauna , Kema tahee zo ki zauna”, kallan ammi tahee tayi “dama ina san wanke wadan nan kayan ne”girgiza mata kai ammi tayi “basai kin wahalar da kankiba”, wani dan button ta danna sai ga yan aiki guda biyu sun fito, kallan daya daga cikinsu ammi tayi “asabe ga kwanukwanan a hannun tahee su zaki kai kitchen”, toh hajiya cewar wadda aka kira da asabe,kwanukan hannun tahee asabe ta karba “nagode “murmushi asabe ta sakar mata ,”oya zo ki zauna “cewar ammi, waje ta samu daga kasa zata zauna ammi ta dakatar da ita, “ga waje zauna akan kujera”,batai musu ba ta hau daya daga cikin kujerun, “toh yan matana wannan sunan ta taheera ana ce mata tahee, Kema tahee wadaddan yayyunkine, wannan ta farkon ta nuna sumayya, sunanta sumayya,sai ihsan a kusa da ita , sai amrah da kuma firdausi”yawu firdausi ta hadiye”ammi ko itace wacce Kikace zaki kawo mana “, gyada mata kai ammi tayi, “tahee zata cigaba da zama tare damu, Inaso ku zauna kamar yadda nasan ku, hope zaku karbeta”, murmushin yake amrah ta saki “insha Allahu ammi”a haka suka dan taba hira kuwa da abunda yake sa’kawa a ransa, TAHEE ma duk a takure take ganin irin kallan da amrah take binta dashi,dama dama ihsan da ke janta da hira, sumayya da firdausi ko kallanta basa yi. Zuciyarta tafarfasa take ba abunda take nanatawa sai “bazai yuba, it’s impossible “ tare da mikewa ….. Comment and share 💖 Alkalamin Mss Lee ✍️ 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA 👇👇👇👇👇 DUK KARFIN IZZATA (star lady ) GIDAN AUNTY ( mss Lee) JINI DAYA ( mrs bbk) YA FITA ZAKKA( maman sayyid ) SARKI SAMEER( xeenat love) Alkalamin Mss LEE✍️✍️✍️✍️ Ina Godiya masu commenting , I heart you all💖💖. ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 (A heart touching love story) Story & written By Mss Lee 💖 PAID BOOK MAISAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581 BOOK 1 📕 Free page 12 🦋 Zuciyarta tafarfasa take babu abunda take nana tawa sai “bazai yiwu ba , it’s impossible “ tare da mikewa , kallanta ammi tayi “ah ah amrah ina zaki”cikin dan rawar murya ta amsa mata “dama ina da lectures naga lokaci yana tafiya inaso na shirya”jinjina kai ammi tayi alamar gamsuwa “All the best daughter”, murmushin yake amrah ta sakar mata “thank you ammi”, tana gama fadar hakan ta bar part din, cikin sauri ta nufi part din auntyn ta, cikin sauri take tafiya ko kula da auntyn ta dake falon batai tai shigewa dakinta, ganin hakan yasa hajiya ameena bin bayanta , a tsaye ta tarar da ita sai faman safa da marwa take , “lapiyar ki kuwa amrah kika shigo duk a rude ko har kingansa “, jijjiga mata kai amrah tayi sai faman zagaye take , kallanta hajiya amena tayi ,” kiyi mun ba yani mana”,aunty akwai matsala “ cewar amrah “kinsan jiya ammi tayi tafiya , yanxu baki gani ba da wata yarinya ta dawo , itama wai anan zata zauna “ta be baki hajiya Amina tayi “to sai me dan ta kawo wata yar kauye”girgiza mata kai amrah tayi “ah ah aunty bazaki gane bane , kinsan sharadin da boka ya sa mana , baki ga yarinyar bane , kyakkyawace sosai , gata a cike ta ko ina kamar wata babba, koni da na ganta sai da naji sha’awata ta motsa, balantana king da yake namiji, dole yaji wani abu aka ta, banasan kwata kwata king ya ganta , Kema kinsan dalilin da yasa nake zuwa part din ammi sabida kawai acan zan iya ganinsa” bata bari hajiya Amina tayi magana ba ta dora “ aunty ya kamata kiyi wani abu,dan wallahi duk Wanda yayi kokarin rabani dashi sai nayi azalinsa, hakuri ya fara kare wa duk lokacin da na gansa sai sha’awata ta motsa”, jin maganganun amrah ba karamun jijjiga hajiya Amina yayi ba “dole na kaiwa boka ziyara dan bazan taba bari dukiya ahalin nahyan ta su bucemun ba, yanxu ki kwantar da hankalin ki karyi abunda zai sa a zargeki, dan Nima ko zanyi yawo tsirara sai dukiyar nan ta dawo waje na “tana gama fadar hakan ta har dakin, waya amrah ta dakko tare da kiran wata number, ringing 2 aka daga wayar , bata jira cewarsava ta soma magana “ Ina bukatar ka kashe mun kishirwar data tasomun, zan fada maka inda zamu hadu”, tana gama fadar haka ta kashe wayarta, sai faman lumshe ido take tana Cizan yatsa. *****Apart din ammi duk yan matan sun koma part Dinsu, part din dada ammi ta nufa da tahee, sai faman bin ginin gidan take da kallo musamman wani dogon building din glass da ya burgeta , da wasu irin flowers me hade da pink colour , sosai flower din sukai mata kyau, falon dada suka shiga komai yana nan kamar yadda yake sai faman tashin kamshi yake kamar ba a amfani dashi,”Assalamu alaikum”cewar su ammi, itama dadan amsa wa tayi tana gyara farin glass din idanta, zama ammi tayi kan daya daga cikin kujerun falon, tahee kuwa samun waje tayi daga kasa kan carfet ta zauna, hakan da tayi ba karamun burge dada tayi ba amma bata ce komai ba. “Sannu da hutawa dada”, murmushi dada ta saki “Yauwa maman yara, a ina kika samo wannan kyakkyawar yarinyar”, murmushi ammi ta saki,”ina wuni “cewar tahee, amsawa dada tayi taba bin tahee da kallo, nutsuwar yarinyar ya birgeta,” dada wannan Itace yarinyar da nace miki inaso ta dawo waje na, na kawo miki itane ta gaisheki”,murmushin jin dadi dada ta saki “kin kyauta kuwa, yan mata ya sunanki” dada ta fada na mayar da hankali kan tahee, sun kuyar da Kai tahee tayi sunana Taheera , zaro ido dada tayi sai kuma ta tabe baki, yaran zamani kowa dai da irin nasa sunan , shi wancan bod’ararran ansa masa tahanuni (tahnoon), ke kuma ga naki salan sunan wai tahura (taheera), sun kuyar da Kai ammi tayi jin yadda ta kira sunan su, gashi ba halin dariya , dada kuwa bilhakki da gaske take ko dariya a fuskarta, kara kallan tahee tayi,”nikin ganni nan , wallahi iyayena sunan kwarai suka samun, ina dalili ai ku sunayan ku sai ku wallahi”,itama tahee dariya dada ta bata amma sai tai saurin gimshe kayarta amma murmushin yaki buya a fuskarta.”sannan ki saki jikinki nan ma gidan kune , ko me sikeso ki tanbaya za a miki kinji tahura “,sosai murmushin da take boyewa ya fito har dan gaf din hakorin ta fitowa “nagode sosai hajiya”dada bata bari ta karasa ba ta dakatar da ita”yau naji wani batu, dada zaki dunga cemun kamar sauran”,jinjina mata kai tahee tayi “nagode dada”sosai tayi wa dada adduar da har yar kwalla saida ta share “Allah yayi miki albarka “kasa kasa tahee ta amsa “ameen”ita de ammi sai binsu take da kallo tana sakin murmushi, kallanta dada tahee maman yara , gasky wannan ‘ya a kwai hankali, nasan a gajiye kuke , idan ta huta sai a gabatar mata da kowa na cikin a halin ta san yan uwanta, cikin girmamawa ammi ta amsa mata”mun gode sosai dada, Allah ya huta gajiya”, ameen aka wai dada tace mata kafin su kama hanyar fita da ga part din, bin bayansu da kallo dada tayi kafun ta saki wani murmushi akan fuskarta . ************ ILORIN babban waje ne katafaran gaske , me dauke da abubuwa mabanbanta a cikinsa , ba karamun makudan kudi aka kashe ba wajan gina falon, komai na cikin falon red colour ne tundaga kan carfet har zuwa kan labulayen dakin, hatta mutanan dake tsats tsaye ko wanne fuskarsa a rufe , matan sanye suke cikin jajayen kyalle iya gwiwa , yayinda mazan suka sanya dan karamun jan kyalle da ya bude al’aurarsu, magana suka fara cikin wani irin yare Mara dadin saturate, kasancewar falon babbane hakan yabasu daman Jan layi kowannansa dauke da glass cup ne Jan abu acikinsa, Yaren suka cigaba dayi , sunayi suna sunkiyar da kansu, wani hayakine ya cika falon , yayinda wata murya Mara dadin ji ta farara babbaka dariya, sannu a hankali ta koma ta jarirai, a haka karuwar muryar nan ta kuma karade ko ina da dariya , data gama sai kukan jarirai suma, an dau lokaci ana haka kafun hayakin ya dauke. Wata katuwar matace ta bayyana a falon , baka kirin da ita fuskarta dauke da wasu kananan kuraje ba kyan gani, durkusawa sukai baki dayansu tare da yi mata sujjada(wa’iyazubillah), sosai suka shiga yi mata kirari”shugaba me share mana hawayen mu, kece farin cikin kowa ne halitta , kece maganin kukanmu, kamar yadda kika saba share mana hawaye “, dariya Matar nan ta fara kafun lokaci daya ta hade ranta kamar ba yanxu ta gama dariya ba, cikin kakkausan murya ta soma magana “ lokaci yayi, lokaci yayi da zaku mallaki duniya, duniya takuce , mu kuma mune abun bautawanku, saura Kiris komai yazo karshe, tabbas aikin ku ya fara zuwa gangara “, kallan daya daga cikin mutanan falon tayi, “abar kauna”shine sunan da ta kira , wacce aka kira da abin kaunace ta fito tsakiya, “tuba nake me sharemun hawaye , tuba nake shugaban dudduniya”, shafa kanta wannan bakar matar tayi , “tabbas kaso mafi yawa na aikin nan yana hannunki,dole ki tabbatar jinin da kika dade kika kiwo ya kwaranya ga dodon tsafi , muna bukatar jinin kafun nan da mako biyu”kara sun kuyar da Kai Wadda aka kira da abar kauna tayi “Godiya muke abun bautarmu tabbas babu me share mana hawaye seke”kara hade fuskarta tayi tare da bin abar Kaunar ta da mayataccen kallo,Tashi tsaye abar kauna tayi , tare da rungumar bakar matar nan, matseta sosai matar tayi ajikinta tana shinshinar wuyan ta kafun lokaci daya su bace a falon ,sun kuyar dakai ragowar mutanan falon sukayi kafun ko wannansu ya buga cinyarsa sau uku,suna gama bugawa wani bakin hayaki ya cika falon, lokaci d’aya hayakin ya dauke, sabanin dazu, yanxu ba kowa a falon. ************* LAGOS zaune ammi take kan daya daga cikin sofa din falo, sosai taci ado cin ash din material sai faman walwali take , ga sanyanyan kamshi dake Tashi a jikinta, iya haduwa ammi ta hadu , har yanxu fuskarta dauke da murmushi akai kamar kullum, lokaci zuwa lokaci takan duba agogon wayarta , ganin 9:00 ta kusa yasa ta mike wa , hart fara taku zata bar Wanjan, daddadan kamshin turaran king ya cika falon, jiyowa tayi tana sakar masa murmushi, shima narkakkun ida nuwansa ya zuba mata yana binta da kallo, har ya karaso wajan, hannunsa guda daya yasa tare da kamo na ammi ya zaunar da ita, har lokacin be ce komai ba , kusan mintuna daya kafun ya ce mata”kinyi kyau” sosai hakwaranta ya fito waje jin abinda yace “kaima kayi kyau son , kamar Wanda ya dawo daga zance”, dan tabile bakinsa yayi tare da kawar da zancen,”coffee ammi” har ta bude baki da niyar bashi amsa wayar hannunta ta soma ringing, tana zaunan ta daga kusan mintuna biyu kafun ta kashe ,mikewa tayi tare da nufar kitchen , a tsaye ta tarar da tahee da asabe suna aiki, kallan asabe ammi tayi a hada coffee a kaiwa son , kinsan baya san jira , tana gama fadar hakan ta bar kitchen din, hannu asabe ta dora a ka “na shiga uku na lalace”sai kuma ta shafa kumatunta, tuni jikinta ya hau rawa, ita tahee dariya ma abun ya bata daga cewa takai coffee har da yar kwalla , bata ce Mata komai ba sai binta da kallo da take,girgiza kai kawai tayi atunanin tayi coffee din ne bata iya hadawa ba shiyasa duk ta zure haka “kawo kayan na hada miki”, sosai asabe ta shiga yi mata Godiya kamar zata zugunnata mata, kayan coffee din kuwa ta dakko mata , tare da nuna mata coffee maker din, bata san yadda ake anfani dashi ba, da temakon asabe ta hada coffee din da ko a ido sai ya burgeka, neman hanya guduwa asabe , tana ganin tahee ta kammala hadawa, tace mata bari taje ta dawo, TAHEE bata gane ba sai jinjina mata kai da tayi , kusan yan mintuna ganin coffee din na kokarin jin sanyi yasa ta dauka hankali kwance tare da nufar falon, agaban idan asabe dake bayan kofa sai faman hada zufa take, da sallamarta t shigo falon, Sam ta manta coffee ne a hannunta sabida dandanan kamshin da ya cika mata hanci, kanta a kasa sai faman murmushi take, jin tana kara kusanto kamshin da takejine yasata lumshe idanuwanta,sosai yanayin falon yayi mata dadi, da bugawa kadan kadan da zuciyarta ke mata, bata ankaraba taji ta taka abu, a firgice ta bude idanuwanta, tsabar firgita bata san lokacin da kofin coffee din ya subuce mata ba ,baya baya tayi zata fadi, sosai ta rintse idanuwanta dan ta sadakar faduwa zatai…. Comment and share 😎 Daga alkalamin Mss Lee 💖 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 💖DUK KARFIN IZZATA (star lady)💖 💖GIDAN AUNTY( mss Lee )💖 💖YA FITA ZAKKA( maman sayyid )💖 💖JINI DAYA (mrs bbk)💖 💖SARKI SAMEER( xeenat love )💖 ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖💖GIDAN AUNTY 💖💖💖 ( a heart touching love story ) Story &written By Mss Lee 💖 💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖 PAID BOOK Dedicated this page to masoyiya and the talent troupe writers, masoyiya I heart ❤️ you Lodi Lodi. Book 1 💖 Free page 13🦋 Sosai ta rintse idanuwanta , tsawan yan sakanni jin bata fadi kasa ba kamar yadda tayi tunani, hakan ya bata damar fara bude idanuwanta a hankali cikin fargaba, akan fuskarsa dake hade sosai idanuwanta suka sauka , ta manta a yadda take sabida shagala da tayi da kallan kyawun fuskarsa, tsawar daya daka mata a lokaci daya da sakin gefen rigarta ne ya firgitata, ga kafarta dake mata zugi kadan kadan adalilin sakin ta da yayi ta fadi, a hankali ta saki wata yar karamar kara tana rike kafartata “are you mad” taji kausashshiyar muryarsa cikin dodan kunnanta, girgiza masa kai tashiga yi , sosai ta tsorata da yanayinsa ko kallansa ta kasa,ba karamin baci ransa yayi ba ganin yadda ta basa amsa “are you mute” takarajin saukar muryarsa, nan ma kai tashiga kokarin girgiza masa,wata gigitacciyar tsawar data sata mikewa ya daka mata , bata san lokacin da ta fara “kayi hakuri dan Allah “, ta karasa a hankali tana sun kuyar da kanta kasa , dan siririn tsakin da ko ita bata jisa ba yasaki tare da komawa inda ya tashi ,”clean this mess, and bring my coffee”, ya fada a takaice har ynxu fuskarsa ba a kanta yake ba, da sauri ta jinjina masa kai sai kuma tayi saurin bude baki “toh” tana gama fada ta koma kitchen, cikin kankanin lokaci ta gama hada coffee din da sai faman kamshi yake , cikin wani dan cup me shegen kyau , a hankali tayi sallama cikin rawar murya, kamar ba zai amsa ba kuma sai ya bude bakinsa a hankali”Wa’alaykumussalm “, ko ita da ke shigowa falan bana tunanin taji , cikin rawar hannu ta karasa inda yake , duk kamshin turaran sa ya cika mata kunne , so take kawai taga ta kebance, kusan mintuna daya bece komai va kuma be amsa coffee dinva, saida ta gaji dan kanta kafun tace “gashi”kamar me kokarin sakin kuka , nan din ba bai amsa ba saida ya mula dan kansa sannan ya saka fararan hannunsa ya dauka a hankali, wani sanyayyar ajiyar zuciya tahee ta sauke ganin ya karba , sai ta koma kitchen ta dakko abunda zata gyara inda ta bata , a hankali take yin komai duk da yadda zuciya da jikinta ke rawa,cikin kankanin lokaci ta gama gyara komai ta mayar kitchen . Tana shiga bata tarar da asabe ba aciki, tunani ta fara ta tafi daki ko tajira ya tafi, dan harga Allah shakkar fita take, ta dau kusan mintuna ashirin a kitchen ganin lokaci yaja atunaninta ya tafi zuwa yanxu, Daidai ta kai tsakiya falon sabida yadda tasawa ranta ya tafi sai jin muryarsa kawai tayi a fiske “coffee” daga nan be kara cewa komai ba.”Innalillahi “ shine abunda tahee ta fada cikin zuciyarta kafun a hankali ta nufi kitchen kamar wata muna fuka , wani coffee din Ta hado masa, yanxu cikin rawar murya ta bashi, kamar dazu sai da ya gaji dan kansa sannan ya karba, ta juya da niyar komawa ta kara jin saukar muryarsa “wait”,ji tai kamar ta fasa ihu a wajan, gashi tana tsoran ta tsugunna kartaje tai wani laifin , tsawan mintuna goma tana tsaye bece da ita komai ba ,cikin dan guntun tunanin da ta fada ta kara jin saukar muryarsa “coffee”, kukane kawai tahee bata saka ba a haka ta koma ta kara hada wani coffee din ta na kawo masa bata jira cewarsa ba ta arta a guje sai cikin dakinta. A hankali ya dago da kyawawan idanuwansa “ is she mad “ ya tanbayi kansa sai kuma ya tabe baki tare da jan siririn tsaki a haka yaci gaba da sipping coffee dinshi a hankali,kusan 11 na dare yana falon kafun ya nufi nashi part din. A Daidai gaban dressing mirror din dakin ta tsaya sai faman haki take, ita kadai ta san karfin halin da tayi kafun ta rugo a guje , sosai zuciyarta take harbawa ga wani irin kasala da take ji, “amma kyakkyawa ne”ta fada a ranta sai kuma ta ja dan tsaki, tare da hade rai “coffee”,”coffee”,coffee”,ko wanne shi oho, bata gama tunaninta ba fuskarta ta hango mata yadda fuskarsa yake a hade, yawun bakinta ta hadiye”nide nashiga uku” sai kuma ta tsaya kamar me tunani “wata kila bakone shima , naga bayajin Hausa gashi dan balarabe dashi”da wannan tunanin ta kwantar da hankalinta, watsa ruwa tayi tare da kwantawa, lokaci zuwa lokaci tunanin mutumin na fado mata a rai musamman yadda dan karamin bakinsa ke cewa “coffee”. ******* WASHE GARI Tahee na zaune kan lallausan medium carfet din dakin tana karanta azkar din ta aka kwankwasa kofa , bada izinin shiga tayi, a hankali asabe ta turo kofar bakinta Dauke da sallama sai faman kawar da Kai take gefe , TAHEE na kula da yanayin ta amma batace mata komai tunda itama Allah ya tseratar da ita .gaishe da asabe tayi, duk sai asabe ta tsargu ta kasa cewa komai har tazo fita sai ta Waiwayo kanta a kasa,”uhm dama hajiya ce tace idan kin kammala cin abincin ki same ta a falo”, toh kawai tahee tace mata kafun asabe ta bar dakin. Tana kammala cin abincin da aka kawo mata kamar yadda ammi ta umarcetan falo ta nufa, anan ta tarar da ammi na kallo a tv, ammi na ganin ta tamike “Yawwa daman ke nake jira , nasan kowa yana falan dada”, da karfi zuciyar tahee ta buga , tuno fuskarsa da tayi “nashiga uku , yanxu ya zanyi idan naganshi acan”, ammi ce ta katse Mata tunanin da ta fara ,”muje ko”murmushin yake tahee ta saki har ynxu zuciyarta bata dena bugawa ba ,a haka suka nufi part din dada kasancewar hijabi ne a jikinta. Zazzaune suke a falon dada , sai faman hiransu suke gwanin burgewa , shigowar su ammi ne yasa ko wannansu maida hankali kan har yar shigowa, amrah na ganin tahee take a wajan wani tsanarta ya darsu a ranta, ji take da za ta kashe mutum babu wannan da zata kashe face wannan maiyar. Cikin sanyin jiki ta gaishe da kowa na falon , ganin irin kallan da kowannansu ke binta dashi, sabanin ummey da abeey da fuskarsu ne dauke da murmushi, sai kuma dada dake faman washe hakwaranta. “Zonan kizauna kusa dani”cewar dada , a hankali tahee ta koma kusa da ita , nuna abeey dada tayi “kinga wannan , toh shine babban dana , kuma shine baban yaran gidan, daga yanxu Kema zaki dinga kiransa da abeey kamar sauran”, sai musaddiq da uncle Saleem da ta nuna, “ wannan kuma Itace babbar maman ku, ana kiranta da ummey, ga kuma matan kawunki musaddiq , ana kiran wannan ta farko mamy sai kuma momy gatanan, sai kuma ta karshen su da ake kira da aunty , ita matar kawunci salim ce, ga yan matan gidan kuma ,duk da nasan zuwanki zaki iya saninsu tunda kullum suna wajan maman yara, bayansu akwai babbar yayarsu dake aure a saudiya sunanta samareena (samreen😂) ana ce mata ukuti( ukhti)zaki ganta wataran,akwai maza guda biyu suna karatu a turai, sai sadauki” tana ambatar kalmar sadauki gaban tahee ya fadi , jitai dada na cewa “ zaki ganshi shima wata ran amma kiyi taka tsantsan , ah too in fada miki gaskiya, ga autar gidan kuma can” ta nuna zoya dake kwance kan cinyar ammi tana bacci,kadan tahee ta dago ta kalleta “amma kyakkyawace sosai “ ta fada a zuciyarta”Nima akwai yar autata da ban fada miki ba sunanta “zarmeen sai danta kwallin kwal wato mijina sha’aban “.kallan abeey da ummeey tayi “nasan ku ai duk kunsan da zuwan ta ko” eh dada duk suka bata amsa , har yanxu da Sauran guntun murmushi akan kumatun ummey,” toh sunan ta tahura” yalwataccen murmushi abeey ya saki “taheera dai ko dada”, gyada masa kai dada tayi “ au kai da kasan da sunan ma amma sai ka wahalar dani”, wani murmushi abeey ya kara saki batare da ya ce komai ba , kallan ta hajiya ameena tayi cikin sakin fuska” gata kuwa kyakkyawa da ita kamar ka sace”, sosai ran amrah ya baci da Jin kalaman auntyn tata, ranta ya baci sosai da irin yadda kowa ke karbarta, “Shegiya in ma asiri kikai musu nice zan karyashi “ ta karasa tare da binta da kallan tsana bata re da kowa ya lura da ita ba . ********* ************** Zaune take kan daya daga cikin daddiyar kujerar falon mahaifiyarta, tunda suka dawo daga falon dada take zaune a wajan hannun ta dauke da juice yayin da Dayan hannun nata ke dauke da wayarta sai faman latsawa take , sam hankalinta na kan abunda take a wayarta, jin taku a falon yasa ta saurin fita daga abunda take tare da sassaita nutsuwarta, hajiya hauwace ta shigo falan, tun zuwansu falon dada sai yanxu ne take dawo wa , cikin izza take taku har ta karaso kan daya daga cikin kujerun dake fuskanta sumayya. Murmushi sumayya ta saki, mamy daman ke ce , “nice mana akwai Wanda kike jiran zuwan sane “, tabe baki sumayya tayi ,”toh mamy daga tanbaya, tun dazu nake jiranki fa , amma daga zuwanki kina so ki bata mun fai “, washe baki hajiya hauwa tayi “Haba summy ta ne yayi zafi kinsa Nima wasa nake miki”, jinjina kai sumayya tayi” mamy baki kula da yar iskar yarinyar da aka kawo gidan nan ba , ki duba ki gani fa yanda kowa ke kaffa kaffa da ita ko mu da muke jininsu ba ai mana wannan abun ma , musamman dada da ke faman nanike mata, wallahi in bamuyi wasa ba sai dai mu zama yan kallo a gidan nan , se abunda yar iskar yarinyarcan ta fada sannan za’ai , kina kallanta kinsan ba haka taxo ba , akwia wata kullalliya a kasa , ni tsorona kartaje ta asircemun king, sabida kinga yawanci king acan yake wuni kuma mu ba mu isa shigaba in yana nan, gaskiya mamy ya kamata ki dauki matakin gaggawa, bazan taba bari cikar burina ya tafi a banza ba , inaso nayi suna, inasan duniya ta san da za mana , inasan mallakar king ko ta halin yayane mamy”kin Hana na nuna alamun ina san sa a fili har waccan banzar take tunanin auransa, dole mamy na mallakesa sannan dukiyar gidan nan mu ya kamata muji dadin ta ba wasu ba”, ta karashe maganar tare da kurawa mahaifiyar tata idanu, sauke nunfashi hajiya hauwau tayi kafun ta soma magana “tabbas Kinyi gaskiya Nima na dade ina halkanta da hakan , a sannu zanyi maganin kowa dan bazan taba bari dukiyar da na kwallafawa Raina zubucewa ba , aure kuwa kamar anyi shine “. Sallamar ihsan ce ta katse musu zancensu , bin ko wannensu tayi da kallo tare da girgiza kai, tasan halinsu Sarai , fatan ta Allah ya shirya mata su, ganin yadda take bunsu da kallo ne yasa mamy mikewa tare da hararar ta sama sama ,bata jira cewar ihsan din ba tai wuce warts daki, itama sumayyan tashi tayi tare da nufar nata dakin,ganin duk sun watse ne yasata kiran number wayar da tayi saving da my yaya, bugu biyu ya dauka.. 🫧🫧🫧🫧🫧🫧 Tunda ta dawo daga part din dada take safa da marwa , ita kadai tasan radadin bakin cikin da takeji, ta tsani yarinyar tsana mafi muni, ko ita lokacin da tazo ba a nuna mata kauna haka ba kamar yadda aka nuna wa waccan , “tabbas sai na lahantaki, lahanin da ko kyawun da akace kina dashi ze gushe, da kanki zaki bar gidan nan”, duk wannan zan tuttukan ita kadai amrah take yinxu kamar wata zautacciya, tunani ta fara me zatayi mata da zai kunsasa mata , ta dade tana tsaye a falon kafun ta saki wani shu’umin murmushi, kitchen Dinsu ta nufa, ba a dau dogon lokaci ba ta fito sai faman sakin murmushi take , direct part din ammi ta nufa dan tasan har yanxu su ammi Suna part din dada, ilaikuwa tana shiga bata tarar da kowa ba sai kamshin turare da sanyin Ac dake tashi, jin motsi a kitchen yasa ta kara sakin wani shi’umin murmushin, ta dau kusan mintuna biyu tsaye a wajan, jin alamun taku kamar za a fito daga kitchen din yasata zuba mangyadan da debo a kan hanyar da ta san dole koma wanene ta nan zai wuce . Taheee ce ta fito daga kitchen din hannunta dauke da bottle water tana sha dan ishirwane ya kaita kitchen din, bata san da mutum a falon ba , sai ji tayi an tura ta da karfin gaske, kafarta ta sulleba a cikin man da amrah ta zube, sosai ta saki gigitacciyar kara tare da tafiya Gadan gadan zata fada , ta rotan da taji anyi , a lokaci daya da gigitacciyar marukan da aka suke akan fuskar wanda bata sani ba ya kara girgitata, lokaci d’aya nunfashin ta ya dauke alamun ta suma . Share ✍️ Littafin gidan aunty na kudine , akan 300 kacal , da zaran na gama free pages dina Wanda suka biya ne kawai zasu dinga samun update , mai don gidan aunty zai iya biyan kudin ta wannan account din 7041879581 opay, Ayshatou galadima sai a turo sheda ta wannan number 07041879581. 💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖 ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 (a heart touching love story) Story &written By Mss Lee💖 💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖 PAID BOOK Nakusa kammala free pages dina,littafina na kudine akan 300 kacal, VIP 500, special 1000 mai bukatar cigaba da karantawa zai biya 300 ta wannan account din 7041879581 OPAY, AYSHATOU GALADIMA, sai a turo shaidar biya ta wnn number 07041879581. Wanda suke da bukatar a tallata musu kasuwancin su kuma zasu iya yimun magana ta wannan number 07041879581. BOOK 1 📕 بسم الله الرحمن الرحيم 💖💖…… Free page 14 🦋 Wani gigitaccen marin ya kuma saukewa akan amrah da tayi mutuwar tsaye , sosai marin ya shigeta nan take ta fashe da kuka,a matukar firgice ta daga idanuwanta, Wanda taganine yasa zuciyarta bugawa da zauri , fitsarine ke kokarin kwace mata da bata shiryaba, batai tunanin samun sa anan ba ko waninsa , kallan dake firgita Mara gaskiya ya bita dashi kafun ya mayar da idanuwansa kan tahee da kallo daya yayi mata ya dauke kansa da jan tsaki , kan daya daga cikin 3sitter din kujerun falon ya kwantar da ita, wani siririn tsakin ya kuma saki ganin dan karamin abinnan ya sumarda ita, da baya wajan kenan mutuwa zatai, ya kara Jan wani Siririn tsaki “spoiled rat” ya fada a kasan zuciyarsa. “Water “ ya fada cikin da kakkiyar muryarsa, cikin zabura amrah da jikinta ke faman rawa ta nufi kitchen da sauri ta dakko, zuciyarta sai faman tsinewa tahee yake ”nashiga ukuna Shegiya yar yarinya daga zuwan ta tasa ya mareni, nashiga ukuna, Allah yasa bega man da na zuba ba”, sai kuma ta zabura cikin sauri ta fito daga kitchen tare da kai masa ruwan sai faman sauke kai take zuciyarta na tsananta bugu, bai kalletaba sai ruwan da ya bude ya yattafawa tahee, a firgice ta tashi zata kara sakin wani karan,” if you dare”taji saukar muryarsa , kara rintse idanuwanta tayi zuciyar ta na tsananta gudu, siririn tsaki ya saki tare da matsawa can gefe,amrah na tsaye sai faman gumi take hadawa, cikin kausasshiyar muryarsa yace “apologize “daga nan be kara cewa komai ba kamar bashine yayi maganar va, wani irin kuka ne yazo wa amrah amma ta rikeshi, sosai zuciyarta ta kara tsanar tahee,”are you mad” bata bari ya karasa ba ta ce “kiyi hakuri” ta karasa cikin rawar murya sosai takejin ba’kin ciki a cikin zuciyarta ,”kneel and apologize with sympathy “ba yanda ta iya haka ta tsugunna ta shiga bawa tahee hakuri , sai lokacin tahee ta bude idanuwanta, sosai kwayar idanuwanta suka canza kala musamman bakin idan nata da ya fara dan washe wa kadan, gaban amrah ne ya fadi da Sauri ta sun kuyar da kan ta, “bakomai ya wuce “ tahee ta fada, ganin king na falon tace “nagode “ duk da kwata kwata basu yake kalla ba. Sallamar ammi ce ta katse tunanin amrah , ganin ammin yasata mikewa , Binsu da kallo ammi tayi tare da nufar tahee “lapiyan ki kuwa” sai kuma ta maida kallanta kan amrah”amrah “ ta kira sunan ta , in ina amrah ta soma , ammi bata kulata ba ta kara maida kallanta kan king” son”, lumshe mata idanuwansa yayi tare da bude wa akanta ba yabo ba fallasa, “me yafaru “ ta kara tanbayarsu, dan tabile bakinsa yayi kamar bazai ce komai sai kuma yayi magana a fisge “ I just come in, but I will come back later “yana gama fadar hakan bai jira cewarta ba ya juya , duk da kallo suka bi bayansa “ ko shine babban yayan su “zuciyar tahee tabuga sosai , musamman da taji ammi na kiransa da “son”, katse mata tunani ammi tayi “ba magana nake muku ba” amrah ce tayi saurin bude baki”daman ammi santsine ya kwasheta, sai yaya king ya temaka mata” ta karasa maganar cikin Dacin rai.kallanta ammi tayi cikin damuwa”hope bakiji ciwo ba “ gyada mata kai tahee tayi, sai a sannan amrah tayi wa ammi sallama ta bar part din, tagefan ido tahee ta bita da kallo tana cije baki, sannu ammi tayi mata kafun ta nufi dakin ta, itama tahee mikewa tayi tare da nufar dakinta. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰ 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 BUNKURE Dije ce zaunce cikin wata bukka dake dauke da wasu irin tarkace , gefenta kuma bintalo ce sai faman bin wajan take da kallo duk da ba yau suka fara zuwa wajen ba, wani irin dariya aka brake dashi kafun wani hayaki ya cika wajan , kafun wani bakin mummunan mutumi ya bayyana a wajan, duk jikinsa tabo ne a jiki, ga wani irin wari dake tashi a jikinsa, kara bude bakinsa dake faman wari yayi yana faman sakin dariya , ko wannansu kasa sukai da Kai , duk da warin da yake , “Allah ya kara…. “ wata gigitacciyar tsawa ya daka mata, cikin wata murya Mara dadin sauraro ya soma magana “ hatta dai , kull din ki kisan yadda zaki dunga magana agaban shugaban ku “,sun kuyar da Kai Dije tayi” tuba muke boka , me biyawa kowa bukatunsa “, wata irin dariya ya barke da ita , kafun ya hade rai “ meke tafe da ku, ko da yake Munson me ke tafe daku, me kuke so ayi musu”, cikin jin dadi Dije tace so nake a batar dasu , itama wacca aka tafi da ita gidan daula a batar da ita ko a haukatata, sai yata bintalo takoma can da zama “, wata dariyar ya kuma yi kafun ya soma magana “bagamar a haukatar da yarinyarcan ba zaiyuba sai in har tana kusa daku, uwarta da dan uwanta kuma zaki iya kawar dasu cikin sauki idan kin bi sharadaina, a sannan ne kuma za a tura yar taki inda kikeso harta daukaka”, washe baki Dije da bintalo sukayi”Godiya muke boka” katseta yayi yana babbaka wannan mummunar dariyar tasa kafun wani dan karamun kulli ya fado a gabansu,” wannan zaki barbada musu a kofar dakinsu, da sun taka shikenan, amma kada ki kuskura wani ya taka basu ba , inba haka ba aikin ze ruguje, sharadi na biyu kuma dole ki bani yar taki na sadu da ita ,dan maniyinta kadai da aljani zai tabane zai zama cikar aikinkubayan hakan ba iya can din va, hatta maganarta sai andungaji akasin hakan kuwa rayuwarkuce zata kaskanta“, yana kammala maganar tasa ya babbake da dariya , tsuru Dije tayi tare da kallan bintalo dake faman zare ido”batare da wani dogon tunani va Dije tace “na amince”kara babbakewa yayi da dariya,cikin muryarshi da bashi da dadin sauraro yace” zaki iya tafiya, inna gama aikina sai ku tafi”, kallan Dije buntalo tayi kafun ta dauki maganin ya fita waje, yai saura daga bintalo sai wanan bokan da babu komai a jikinsa sai dan ganyen da ya rufe masa al’aurarsa. Cikin tsawa yace “mike” da sauri kuwa buntalo ta mike tana zare ido,”tube kayan ki , kizomun da baya da baya”, cikin sauri tsananin yadda ta tsorata da sauri ta cire kayanta , haihuwar uwarta, ta soma tahowa da baya da baya jikinta sai faman karkawa yake. Duwawunta ya zuba wa idanu sai faman hadiyar yawu yake yana sidar baki, cikin azama ya janyo hannunta ta fado kansa, wata kakkarfar ajiyar zuciya yasaki tare da sakin gurnani yana kara matseta a cikinsa, duk da warin da yake, ko motsi buntalo ta kasa sabida tsoran da taji, cikin azama ya juyar da ita ya Dane kanta, ba tare da wani abuba ya dage dan karamin ganyen jikinsa, take a Wajan bakakirin alaurarsa ta fito sai yawo take, bintalo kuwa harta fara hawaye, be tsaya wata jinkiriba ya shigeta da karfin gaske , tare da matseta a jikinsa yana sakin gurnani kamar wani mayun Wacin zaki……. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰ 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 Yana barin part din ammin nasa hadadden gym dinsa ya nufa cikin kayan motsa jiki, sosai ya motsa jikinsa, ya dau dogon lokaci yana motsa jiki da abubuwa mabanbanta , kafun ya koma dakin sa ya watsa ruwa cikin shigarsa da tayi matukar yi masa kyau ya fito , sanye da blue din t_shirt da white jeans , sosai kakkarfar damshen hannunsa ya fito, kayan ba karamin yi masa kyau yayi ma , gashinn kansa sai faman kyalli yake, duk inda ya wuce sai kamshin imperial ya cika wajan, bai dau dogon lokaci ba yashiga cikin farar Lamborghini din da sai faman kyalli take da dauka ido take, cikin lokaci kankani, jerin motocin nan suka fita daga cikin gidan, sojojin wajan sai faman sawara motocin suke. Karfe 8:30 na dare amrah ce sanye da dan karamin towel da ko kwiwa be kara sa mata va, sai uban gashin attachment din dake yawo a bayanta. Waka ta saka tana tikar rawar ta , saida ta gaji dan kanta sannan ta kashe tana sauke ajiyar zuciya. Toilet ta nufa da nufin watsa ruwa ko dan kwali babu ajikinta, ta karasa kenan zata kunna fanfo, abinda ta gani ne ya firgitata tare da sakin gigitacciyr kara….. Comment and share ✍️ ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** 💖💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖💖 Mss Lee 💖 Masu comment da masu yimun magana akan gidan aunty , ina matukar Godiya da jin dadi ✍️… ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA ‎ 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 ( a heart touching love story) Story &written By Mss Lee 💖 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖 PAID BOOK MAISAN GIDAN AUNTY DAGA FARKO HAR KARSHE YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581. MAI BUKATAR AYI MISHI TALLAH YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581 AKAN NAIRA 500 KACAL BOOK 1📕 بسم الله الرحمن الرحيم…….. Free page 15 🦋 Karfe 8:30 na dare, amrah ce sanye da d’an karamin towel da ko gwiwa bai karasa mata ba,sai uban gashin attachment din dake yawo a bayanta ,waka ta saka tana tikar rawarfa sai da ta gaji dan kanta sannan ta kashe tana sauke ajiyar zuciya. Toilet ta nufa da nufin watsa ruwa ko d’an kwali babu akanta, ta karasa kenan zata kunna fanfo, abinda ta ganine ya firgita ta tare da sakin gigitacciyar kara, a guje ta juya da niyar komawa , amma kafin ta karasa wajan komar wata irin mage ce ta fito ta wajan fara tass da ita, wata karan amrah ta saki, tuni ta fita a hayyacin ta sai faman ihun neman agaji take, dan karamun towel dinta ma tuni ya fadi a jikinta, saukar bulalar dataji a fatar jikintane yasata sakin razanannan kuka, sosai bulalar ta shigewa, bata gama shafa wajan ba ta karajin saukar wata bulalar, kuka kawai ta fashe da shi, ba tsaya ba aka dunga zulamata wannan bulalar, gadan gadan farar Magen nan tayo kanta, ganin haka yasa amrah sakin wani gigitaccen kara tana zube a kasa sumammiya. ******* Tana shiga daki ta fada kan gadanta sai faman murmushi take saki ita kadai, sosai take sakin murmushi idan ta tuno fuskarsa da irin yadda yake hade fuska, take fargaba da tsoransa ya kara shiga jikinta, musamman da taji ammi na kiransa da son.Lumshe idanuwanta tayi amma still shitake gani ,duk da tsananin tsoransa da ya dirar ma , amma sosai ya burgeta a iya ganin da tayi masa. Wanka ta tashi tayi kafun ta kwanta tana adduar bacci, mintuna kadan bacci ya dauketa. Sosai wasu irin halitta ke binta, yayinda tarike hannun wani da ba’a iya ganin fuskarsa, amma sai faman kareshi take daga cutar dashi dasuke kokarin yi, tun tu’ben da tayi ne yasa ta faduwa, shima Wanda tarikewa hannun ya tsaya har yanxu ba’a iya ganin fuskarsa, kafun suyi wani kwakkwaran motsi , wadannan halittun sun zagayesu sai tsalle suke saki , daya daga cikin sune yayi kanta yana zaro harshe , daidai yana kokarin cabkota wani irin girgiza ya karade ko ina, take a wajan wata katuwar farar macijiya ta bayyana a wajan, daga gefenta kuma wata farar kuliyace me shegen haske , sosai ta fito da farar farcinan, yayinda bakinta yake abune sai faman “meow meow “take cewa. Zabura wadannan halittun sukai kafun su fara Kai musu sara da faratansu, sosai macijin nan da Farar kuliya sukai musu jina jina lokaci daya suka bace batt ba aganinsu. A firgice tahee ta farka da ga mummunan mafarkin data fara duk jikinta yayi gumi sai faman zufa take hadawa, adduar neman tsari ta fara karantawa har taji nutsuwarta ta Daidai ta kafun ta mike tashiga bandaki, mintuna kadan tafito dauke da alwala, nafila tayi tare da adduoin da oumma ta koyasu hartaji ta kara samun nutsuwa kafun ta mike ta koma bacci. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 BUNKURE Duk da tsananin yadda bintalo ke ihun ta hakan be sa yaji tausayintaba sai ma kulle mata baki da yayi da kazamin bakinsa me shegen wari, sosai yake zuba muguntarsa akanta, tsabar wahala kusan sumanta uku , azaba na sawa ta farfado, iya rashin imani saida yayi mata yayi mata kaca kaca ko dan yatsanta bata iya motsawa, se hawayen azaba dake digo mata ta ido, azuciya kuwa ta tsinewa Dije yafi a irga duk da kasancewar ta mahaifiyarta. Saida ya gama lalatarsa sannan ya bawa Dije da ke rabe damar Shigowa ya tafi da ita cikin hade rai, duk jikinta yayi sanyi ganin irin aika aikan da yayi wa bintalo, amma ko saudaya batayi nadamar hakan ba tunda burinta zai ciki, cikin razananniyar muryarsa me tsoratarwa ya daka musu tsawa akan su bace da ganinsa, ganin yadda bintalo ta kasa ko motsine yasasa babbaka dariya” ku sawa ranku aikinku kamar ya tabbatune” sai ga wata kwarya nan ta fado kasa da dan karamun ruwa a ciki jaa da shi, ruwan yasa dije ta dauka ta kwarawa bintalo a gabanta, cikin Karkarwa ta dauka tare da kwara mata, wani irin gigitacciyar azabar kara bintalo ta saki da ya firgita Dije , kara babbakewa da dariya yayi tare da hade ransa , kusan mintuna uku bintalo na kukan azabar nan kafun ta sauke nannauyar nunfashi tare da mikewa da kanta, ganin hakan yasa dijen sakin ajiyar zuciya a haka suka ajiyewa boka kudin da suka zo masa dashi tare da fita da baya baya har suka bar wajan, sai lokacin bintalo ke taku da dingishi dukda azabar da take ji ta ragu babu ita,amma gudun kar a asirinsu ya tonu basu koma gida ba sai wajan shadayan dare lokacin babu wuta, sannan babu me gane halin da suke ciki, zuciyar dije sai faman zillo take akai ta aiwatar da kudurinta kan oumma da suka shige mata hanci , ga wani tsanar su da ke kara ruruwa a Zuciyar ta. ************ Tunda ya tashi yau be fita ko ina ba sai bayan karfe goma na safe bayan motsajikinsa da yayi, Hakanan yau besan jin kowa a kusa dashi ga yunwa yana jin amma ya kasa motsa koda dan yatsar sane, coffee yake San sha dan haka ya mike cikin takun kasaitarsa kamar kullum, a hankali yake taku sanye Yake cikin black trouser da black singlet , sosai kakkarfar surar jikinta ta bayyana , farar fatar jikinsa sai sheki yake dauka, a hankali ya karasa inda coffee maker din yake, cikin yan mintuna ya gama hada coffee dinsa , a nutse ya zauna kan daya daga cikin sofa din wajen , sipping daya yayi wa coffee din tare da ajjesa, wani irin daci yaji coffee din nayi masa kamar zaisa amai, a hankali ya kara lumshe idanuwansa ko me ya tuna oho, sai gashi ya mike tare da nufar wani daki, ko cikakken minti ashirin beyi ba wani daddadan kamshi ya karade ko ina , a hankali kamshi ya kara kusan towa kafun mamallakin kamshin ya bayyana , sosai shigarsa tayi masa kyau , sanye yake cikin black suit sosai bakin suit din cikinsa ya fito da ainahin kalar farar Tatar’s a da sai sheki take , bakin nan kullum sai kara turuwa yake kamar mai shafa abu wajan, har yanxu fuskarsa a hade take amma sosai yayi kyau , ga diamond watche dinsa sai faman kyalli yake, wayace kare a kunnansa sai faman motsa baki yake ko abunda yake cewa ba aji, be tsaya a ko ina ba sai part din amminsa . A zaune ya sameta cikin shigar manyan mutane da ta saba , sosai tayi kyau cikin shigarta, kujerar da take zaune ya nufa tare da langwabar da Kai kadan, kallansa tayi tare da dauke kanta, bai ce komai ba sai hannunta da ya kamo ya dora a fuskarsa , a fusge ya furta “sorry ammi”, ajiyar zuciya ta sauke daman ba fushin take dashi ba ganin yaki zuwa haryanxu kuma tayi kewarsa ne yasa ta yi masa haka, a hankali ya furta “ina kwana ammi na “, murmushinta da baya boyuwa ta saki “ ka tashi lapiya son” lumshe mata ido yayi kawai batare da yace komai ba , ganin hakan yasan ammi tasan yan miskilancin ne a kusa, kadan suka taba hira yana amsawa kadan kadan,shafa gefan fuskarsa tayi” da alama wannan son din nawa ne ci komai ba” kara lumshe mata ido yayi tare da bude wa alamun amsa . Mikewa tayi “bari na dafa maka abinci ko” riko hannunta yayi tare da kallanta “ coffee” shine kadai abunda yace mata , jinjina masa kai tayi tare da nufar kitchen din, a tsaye ta samu tahee da asabe na aiki a kitchen , sosai tahee take jin dadin hakan sabida tana Kaunar taga ta iya abinci hala hala , ba tare da ta kalla taheen ba ta soma magana, “tahee hadawa son coffee kafun na kammala dafa masa abinci”, suman tsaye tahee tayi , zuciyar ta sai bugawa take gashi bata da dalilin musawa, kamar wacce zata saki kuka haka ta hada coffee din tare da fita falo , ko ina na falon mayataccen kamshin turaran da ke mata dadi ne ya cika wajan, Zuciyarta sai faman zillo take sabida tsoro, a hankali ta karasa inda yake bayan tayi sallama , cikin in ina ta soma magana “ina.. kwana”, kamar wacce tai da gunki ko motsi beba sai ma sarrafa wayarsa da yake cikin nutsuwa , kamar wacce zata saka kuka ta kara cewa “ina.. kwana”, yanxu ma be motsaba balantana tasa ran amsawar, siraran hawayene suka dan zubo mata kadan tare da sun kuyar da kai, kamar daga sama tayi saukar muryarsa “ fine” , wani murmushi ne ya subuce mata, sosai taji dadin amsawar dayayi, a hankali ya sa fararan dogon yatsunsa tare da dauka cup din, a hankali ya fara sipping, zuyawa tahee tayi da niyar komawa tazo daf da kitchen din ta tsinkayi muryarsa “ who permit you to leave”, sun kuyar da kai tayi tare da dawo wa ciki “ bakowa “ ta bashi amsa , tsawan mintuna goma tana a tsayen , kofin hannunsa ya ajje tare da kyara zama, another cup,”Tom “kawai tace masa tare da nufar kitchen din, har lokacin ammi na tsaye tana masa abinci da kanta, kallanta ammi tayi sai yanxu, sauke ajiyar zuciya tayi “wani cup din yace na hada masa”kallanta ammi tayi sai dai bata ce mata komai ba sai jinjina mata kai da tayi, wani cup din ta kara hadawa tare da nufar inda yake har yanxu zuciyarta bata bar bugawa ba, sallama tayi a falan kamar bazai amsa ba , sai ya amsa a hankali, batare da wani dalili ba lokaci daya taji kanta ya sara mata Daidai lokacin da zata mika masa coffee din, a maimakon ya sauka a hannunsa sai ya subuce ya zube a jikin hadaddan suit dinsa ……. (😳😳Tahee )…… Manage plx …. Masu comment ina Godiya sosai da sosai MASU BUKATAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581 . MASU BUKATAR A TALLATA MUSU KASUWANCINSU SU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581 AKAN NAIRA 500 KACAL. 💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖 DUK KARFIN IZZATA ( star lady ) GIDAN AUNTY (mss Lee ) JINI DAYA (mrs bbk) YA FITA ZAKKA( maman sayyid) BABY (mhiz innocent) 💖💖💖💖💖Mss Lee ✍️. ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JyvVuOvzYyF19np8UmFKV4 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 (a heart touching love story) Story & written By Mss Lee 💖 PAID BOOK LITTAFIN GIDAN AUNTY NA KUDI NE AKAN NAIRA 300KACAL , MAI SAN CIGABA DA KARANTAWA HAR KARSHE ZAI BIYA KUDINSA TA WANNAN ASUSUN : 7041879581 OPAY AYSHATOU GALADIMA , sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581. BOOK 1 📕 بسم الله الرحمن الرحيم ❤️❤️… Free page 16 🦋 Sosai tazaro idanuwanta waje tana faman girgiza kai,bata san lokacin da ta karasa kusa dashi tana kokarin goge masa ba , gigitacciyar tsawar da ya daka mata a lokaci daya da lafiyayyen marin da ya sauke mata ne yasata kara firgita, ga kanta da yake tsananin sara mata, lokaci d’aya taji juwa na dibarta “Dan Allah kayi hakuri” shine abunda bakinta ya iya furtawa, be kuma cewa komai ba sai mikewa da yayi kwasan wayoyinsa,Daidai lokacin da tahee take kokarin fadawa kan wani designer dake gefenta , taku daya yayi ya riko damtsen hannunta tare da Jefata kan daya daga cikin kujerun tare da sakin siririn tsaki, cikin bacin rai ya bar part din azahiri Kuma fuskarsa tananan a yadda take, baka isa fassara yanayinsaba ” me ya Hana ban karyataba “ ya fada a cikin zuciyarsa ransa na kara baci , dogon tsaki yaja iya kasan makoshi, hatta zaki daya bude masa kofa yayi mamakin ganin sa haka amma bashi da hurumin magana a haka har suka koma part dinsa. Tunda ya jefata kan kujerar da ya tashi har yanxu bata bar wajan ba , sosai taji kanta na sara mata, ta dau kusan minti biyar zaune a wajan tana addua, kafin lokaci daya ta nemi ciwan kan ta rasa gabaki daya, ajiyar zuciya ta sauke sai a lokacin kumatunta ke mata zafin marin dayayi mata , dafe wajan tayi tana sosawa “Mugu kawai” ta fada a zuciyarta tana turo dan karamin bakinta, amaimakon ta koma kitchen kai tsaye dakin ta ta nufa tare da fadawa kan gado tana sauke a jiyar zuciya har yanxu hannunta na kan kuma tunta. *******Ta dade kwance a ban dakin a sume, bugun ban dakin da ake da karfine ya farfado da ita, tayi mamakin ganinta kwance a kasa ga tsami da jikinta ke mata,kara bugun kofar da akaine yasata mikewa cikin din gishi, towel dinta dake Yashe a kasa ta dauka tare da daurawa, da Kyar take taka kafarta dake mata tsami, sai bin ko ina da kallo take, da kyar ta karasa jikin kofar, a tsaye ta sami aunty duk ta rude, tana ganinta ta saki ajiyar zuciya” me kikeyi acikin ban daki tun dazu, kinsan irin neman ki da nayi”, batasan lokacin da bakinta ya furta “bacci ne ya daukeni “,kallan ta aunty tayi tana sakin baki “bacci fa Kikace amrah “, gyada mata kai amrah tayi tana turo bakinta tare da rabata tawuce , binta kawai aunty tayi da kallo batare da tace komai ba tabar dakin. Samun waje amrah tayi kan gadonta tare da dakko wayarta dake ajje saman gadan, dogon tsaki ta saki sai a lokacin take tuno abunda tahee tayi mata,azabure ta mike tsaye “ ni amrah , nice yau nake bawa wata yar iska hakuri, ni amrah hmmm” girgiza kai tashigayi “ yau nice na kaskantar dakai na bawa wata shegiya hakuri, wallahi ko zanyi yawo tsirara sai na wulakanta ta sai na musgunawa rayuwarta sai tasan dani take magana “ ta kare zancen tana sakin kwallar bakin ciki… ******* Director part dinsa ya nufa sai faman taunar lips dinsa yake, be bi steps ba ta elevator ya hau , a second floor dinshi ya tsaya ko ina sai faman tashin kamshi yake da sanyin Ac musamman kamshin turaransa da ya kama ko ina na part din, rigar jikinsa ya cire kai tsaye faffadan zurar jikinsa ta fita fari tass dashi,sosai muscles dinsa da 6 spacks dinsa ya fito kallo daya zaka masa kasan ba karamin motsa jiki yake ba,kofar da take facing dinsa ya nufa, ya dau kusan mintuna 30 aciki kafun daddadan kamshi ya karade ko ina , sosai yayi kyau , a maimakon suit yanxu kananan kayane a jikinsa ,tun daga kan bakar jigar jikinsa tare da bakin wanda jikinsa , sosai yayi kyau cikin kayan , sumammiyar gashin kansa ya fito sosai yau ma kadan daga cikin yalwataccen gashin kansa ya fito har wajan idanunsa, sabida tsananin bacin rai pink lips dinsa ba karamin turuwa yayi ba sai faman tsuke fuskar yake, cikin takunsa na kasaita ya hau elevator tare da nufar 3rd floor, a maimakon hanyar da ya saba bi yanxu wata daban yabi,babban waje ne nashakatawa gata iska me dadin gaske dake huro wajan,kayataccen wajan shakatawa ne a wajan sosai wajan ya hadu,ga gefe d’aya dayake abude ko ruwan sama akai yana dan shigowa kadan kadan , akan daya daga cikin kujerun shakatawan yazauna ne kama da sararin samaniya, sosai yanayin wajan yasakashi cikin nutsuwa sai faman lumshe ido yake, daga gefensa ma wani cup ne me shegen kyau cikin sa wani lemone kamana da sararin samaniya shima.sai faman lumshe idanuwansa yake yana budewa, wayarsa dake ringing a hankali ya dauka batare da bata lokaci ba, Ahankali yake magana ko nakusa dashi ba Lalle yaji me yake cewa ba,sai lumshe kyawawan idanuwansa da yake faman yi. 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 Futowar da ammi zatayi a kitchen ne taga babu king babu tahee, tsayawa bin falon tayi da kallo kamar anan ne zata gansu,a tunaninta tahee ta koma daki ne shiyasa bata bita ba ta dauki wayar ta da niyar kiran king, tana kara wayan a kunnenta ta haye stair case din din falon.. A dan kwanciyar da tayi batasan lokacin da bacci ya dauketaba, wasu matasan yara tagani da akalla befi su bata shekaru uku ba, kyawawa dasu sai faman kuka suke , daga gefensu wani farin macijine shima tass dashi, kallan tahee dake gefe sukai sai suka kara fashewa da kuka , suna kuka suna biyota , cikin tsorata tahee ta fara jan baya, girgiza mata kai suka shigayi, cikin daddadan muryarsu “sun kashe mana farin cikin mu , sun cutar damu, bamuyi musu komai ba, laifin me mukai musu, nace laifin me mukai musu” suka karasa cikin data tsawa , firgita tahee tayi da yanayinsu, ganin sun tsaye ne yasa itama tsayawa,cikin rawar murya tahee ta fara magana “su..suwane ku, me nayi muku”, dariya suka saki tare da kara sakin wani saban kukan, “SIF,LOLA,”sai kuma farar magan ciki ta shafa can macijin nan” SUSAN”, tana gama fadar haka suka kara sakin kuka tare da bace bat kamar basu taba wanzuwa ba. A firgice tahee ta farka daga baccin da ya dauketa bakin ta dauke da addua , shafa wuyanta da ya dan rike tayi” me yasa nake yawan mafarkin masu sunannan,su wanene su”ganin babu me bata amsa yasata mikewa , kayan jikinta ta cire tare da shiga wanka , mintuna kadan tafito daga nan dakin, daya daga cikin abayoyin da ammi ta bata ta saka , gaban mudubin dake shake da kaya ta nufa,kurawa fuskarta ido tayi ganin irin sahirtaccen kyan da tayi a cikin kwanaki uku da tayi a cikin gidan , sanye take cikin red Egyptian abaya sai faman walwali stone din jiki ke dauka,asalin farin fatarta ta buzaye ta fito tass a jikinta, yayinda cikakken yalwataccen gashin kanta ya sauko har wajan kugunta, sosai bakin kwantaccen gashin goshinta ya kara kwantawa tare da dogon siririn hancinta , ba make up ne a fuskarta ba amma fadin haduwarta bata lokaci ne musamman dan karamin lips dinta da ya fito tass dashi kamar wacce ta saka janbaki,bakin kwalli ta saka da ya fito da farin kyawawan idanuwanta, sosai kwallin ya fito da asalin kwayar idanunta,cikakkiyar gashin girarta da dogayen eye lashes din idanuwanta su suka kara fito da ainahin kyawun fuskarta , ba ma a bociyar lip gloss bace shiyasa tabar dan karamun lebenta a haka, ribbon dinta ta dauka shima red colour tana kichiniyar daurashi, sosai ta jigata kafun ta daureshi sabida cikowarsa,mayafin abayarta ta dauka tare da yafashi saman kanta, red din takalmin ta ta saka , gaban mudubin ta kara komawa tare da karewa kanta kallo , murmushi ta sakar wa kanta tare da rufe fuska , “ ke din me kyau ce “kalmar da kullum taheer ke fada mata, murmushi kawai ta kara saki , tayi kewarsu sosai, hanyar fita daga dakin ta nufa bayan ta gama feshe jikinta da turaruka, Daidai lokacin da yan matan ke shigowa part din,amrah sai faman dingishi take haryanxu jikinta be dena tsami ba, sakin baki tayi ganin irin kyawun da tahee tayi, bama ita kadai ba hatta su ihsan duk sakin baki sukai suna binta da kallo, gaishe da su tayi babu Wanda ya amsa mata sai ihsan dake faman sakin murmushi, “tubarkallah Masha Allah , gaskiya ke kyakkyawa ce tahee”,sun kuyar da kai kawai tahee tayi tana wasa da yan yatsun hannunta, binta da kallo su sumayya sukai kowa yana hadiye abunda ke ransa, dogon tsaki amrah taja tare da karasa kan daya daga cikin kujerun falon, sosai take bakinci, dama ace Itace take da wannan kyawun, wani dogon tsaki ta kuma ja tare da daukar wayarta suma duk yan matan waje suka samu tare da zama ,ihsan ce ke kokarin magana ,jin sallamar zoya ne ya katse mata zancenta, inda Ihsan take ta nufa “aunty ihsan” rungumeta ihsan tayi “na’am my baby”kallan yarinyar da aka kira da baby tahee tayi , Itace dai yarinyar da ta gani tana bacci,”aunty ihsan wai ina da wata aunty tana ina “murmushi ihsan ta saki, “toh daman bazuwan kowa kikai ba sai na auntyn taki ko”dariya zoya tayi tana rufe fuskarta , itama murmushi ihsan din ta saki “oya kinganta” juya wa zoya tayi tare da kallan Wanda aka nuna mata, zaro fararan idanuwanta irin na king tayi, “aunty ihsan tana kyau, harta fini ma, amma yaya king dina ya fita” dariya ihsan ta saki kawai , sai alokacin tahee taga tsananin kamanninta da Wanda yake zuwa part Dinsu,murmushi kawai tahee ta sakar mata, itama murmushi zoyan ta saki “Aunt ya sunanki” taheera shine kadai abinda tahee tace,kara zaro ido zoya tayi “sunanki me dadi , ni kuma zoya yanxu Kema kinzama aunt dina kinji”girgiza mata kai tahee tayi sosai yarinyar tashiga ranta, duk wannan abun su sumayya na zaune suna kallan ikon Allah musamman amrah dake jin kamar ta samu wuka ta caccakawa tahee..shigowar ammi ne ya katsemata tunanin da ta shiga,”yaude yan mata na sai yanxu nake ganinku” ko wannansu murmushi ya saki sabanin sumayya da amrah da suka saki na yake “Aah ammi kinsan akwai school shiyasa “gyada musu kai ammi alamun gamsuwa kafin ta mike ,”yanxu dai ku Tashi ku kaiwa son abinci sai a dawo a yi hirar”, cikin firgita kowannansu ya zaro idanuwansa tare da furta YAYA KING….. Comment and share . 💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖 Duk karfin izzata Gidan Aunty Ya fita zakka Jini daya Sarki sameer Baby . MSS LEE💖.. ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JyvVuOvzYyF19np8UmFKV4 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 (a heart touching love story) Story & written By Mss Lee 💖 PAID BOOK littafin gidan aunty na kudine akan 300 kacal ne so har karshe zai biya ta wannan bank din 7041879581 opay Ayshatou Galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581. Masu bukatar a tallata musu kasuwancin su , su tuntubeni cikin wannan number 07041879581. BOOK 1 📕 Free page 17🦋 Duk binsu da kallo ammi tayi ganin lokaci daya duk sun tsorata,suma duk sai sukai shiru ganin irin kallan da ammi ta bisu dashi, tahee da zoya ma duk tsayawa kallansu sukai, kamar daga sama cikin sauri amrah tace “zani ammi”jinjina mata kai ammi tayi tana sauke ajiyar zuciya, kafun ta karasa kitchen taji saukar muryar sumayya” Ammi nasan kayan sunyi yawa bari na temaka mata”ta karasa tare da dallawa amrah harara batare da ta bari ammi ta ganiba, ita tahee dariya suka bata ma, ko za a yankata aibazata je inda za a ballataba,jinjina mata kai ammi tayi tare da karasa shigewa cikin kitchen din, cikin sauri amrah ta jiyo tana kallanta,”mtswww na tsani shishshigi Wallahi “, kallan rainin wayo sumayya ta bita dashi, “zaki hanani taka ko ina na gidan mune”, dogon tsakin da firdausi taja ne ya katsesu “malamai kunbi kun ishemu inda gaske sansa kuke kuje kuce a aura muku shi mana kinbi kun cika mana kunne” tana gama fadar hakan ta mayar da headphone din kunnenta, ba Wanda ya kara cewa komai sai kallan banzan da suke bin junansu dashi , ihsan kam sharesu tayi tacigaba da game din da zoya ta sa musu , zuwa zaune kusan yan mintuna su asabe suka fito da kayan da za akai masa, har yan rigen rigen tashi ake tsakanin amrah da sumayya,amrah ce ta fara karasa tare da amsa kayan hannun asabe tana yatsina fuska,itama sumayya ragowar kayan ta dauka tana hararar amrah, Tashi tahee tayi da niyar komawa daki ammi ta tsayar da ita, “Kema daughter jirani na aikeki part din dada da na ummey”tana gama fadar hakan ta shige wani daki, mintuna kadan tafito dauke da wasu designers bag guda biyu, lokacin har su amrah sun bar part din, purple din ta nuna mata na dada ,red din kuma na ummey, mikewa zoya tayi “ammi zan bita”murmushi ammi ta sakar mata “toh daughter “kama hannun tahee zoya tayi, kowa na mamakin ganin lokaci daya ta sake da tahee, Kai tsaye part din dada suka fara zuwa Tun a hanya zoya Kezuba mata surutu falon yayi saura daga ihsan sai firdausi dake jin waka. Zaune dada take kasan lallausan carfet din falon ta, kamshin farfesun kayan cikin da akai mata sai faman tashin kamshi yake, cikin sallah tahee ta shigo falon tare da zoya,amsa sallamar dada tayi tana sakar masu murmushi” sai yanxu kika tuna dani tahura, ai nayi fushi “,sun kuyar da Kai tahee tayi cikin jin kunya” kiyi hakuri dada ba haka bane”, dan ta bile baki dada tayi “ gaskiya kam ki gyara, ko d’an hirar nan ki dunga zuwa kina tayani tunda su wadancan bankadaddun ba zuwa suke ba, sarakine kawai shima kullum cikin fada muke”, kallan ta zoya tayi”dada nifa , kinsan dai ina zuwa ko”,sakin baki dada tayi tana kallanta” kiji tsoran Allah, ni nayi mamakin ganin ki ma yau, ba dai kyau karya kinsani”, dariya zoya tayi tana rufe dan karamin bakinta, sakon da Ammi tabayar abata tahee ta mika mata “Allah sarki,kilishi ba dai mutunci ba ,duk gidan nan ita da hajiya suhaima ne masu kaunata sai sadauki”ta karasa zan Canta tana Shan farfesun ta, kallan tahee dake wasa da hannunta tayi”kinga zamu bata sai wani jin kunyata kike kamar wacce akace miki na zama sirikarki”, sosai dada da zoya suke janta hira tun bata sake ba har ta sake da su, sun dad’e suna hira kafin tahee tace zata kaiwa ummey sakonta,’kin barin ta dada tayi har saida taci farfesun da ta zuba musu zoya sai faman dariya take musu, da zata tafi ma sai da tayi wa dada alkawarin dawowa anjima sannan ta barta,tsakanin part din dada dana ummey ba nisa shiyasa basu dade ba suka karaso, sai bin ko ina tahee take da kallo ganin irin kyan da wajan yake dashi, zoya na gaba tahee na bayanta har suka shiga hadaddan kayataccen falon, sosai falon yake da girma da tsaruwa,ta ko ina kamshi ne ke tashi da sanyin Ac, ganin babu kowa a falon yasa tahee zama kan lallausan carfet din falon me shegen laushi da daukan ido, a guje zoya tashiga wata kofa kusan minti 5 sai gasu sunfi to ita da ummey dake sanye da black abaya sosai kyawun ta na larabawa ya bude shekarunta, wacce ta ganine yasata dan sakin murmushi, tare da zama kan daya daga cikin lallausan kujerun falon, gaishe da ita tahee tayi , yayinda ummey ta amsa mata cikin kulawa, haka kawai taji yarinyar ta kwanta mata arai sabida nutsuwarta, sakon ammi tahee na mika mata, wani murmushin ummey ta saki,”kice mata nagode sosai kuwa, bata gajiya “yadda ummey ta yabi ammin sai kaunar auntyn tata yakara shigarta sosai take santa,mikewa tayi daniyar tafiya ummey ta zaunar da ita “ ina kuma zaki, yanxu zamuyi lunch “ komawa tahee tayi ta zauna bazata iya yi Mata musuba sabida kunyarta da takeji, kallan ummey zoya tayi” ummey kingama a part din dada guduwa tasoyi “,girgiza mata kai ummey tayi cikin yaren larabci “bana hanaki surutu ba”, sun kuyar da Kai tayi”ana asf”ummey bata kulataba sai kallan tahee datayi “daughter taso muje muci abinci”ba yadda tahee ta iya dole ta mike ,tare suka nufa hadadden dining din dake falon,sosai wajan dinning ya hadu kasancewar wajanshi daban a cikin falon bayan antaka 3stairs, dakanta ummey tayi serving Dinsu , sosai kamshi girkin ya cika ko ina , nut spicy herb rice da Greek chicken kebab ummey ta zuba mata ,sai wani yan bowl masu shegen kyau da ta zuba mata salad da sauran dishes din, cikin glass cup kuwa strawberry milkshake ne aciki me shegen sanyi, sosai abincin ya birge tahee amma ta kasa moshi ,sai godiyar da tayi wa ummey kawai, itama ummey serving din su tayi ita da zoya, har sun fara cin abinci ganin sai wasa tahee take da spoon din hannunta ummey ta kalleta” daughter ya naga ba kyaci, ko abincin be miki bane”saurin girgiza mata kai tahee tayi “a’ah ummey yanxu zan faraci” ta fada tare da soma cin abincin a hankali , ummey batace komai dan Sarai ta gane kunyarta tahee takeji,suna cikin cin abincin kuwa daddad’an kamshin turaren da basuyi tsammani bane ya cika dodan hancinsu,da ma duk wani kamshi dake tashi a falon,kasa cigaba da cin abincin tahee tayi zuciyar ta sai faman bugu yake, naman da yake bakinta ma ta kasa taunawa sai faman tsotsanshin take, a hankali cikin daddadar muryashi yayi sallama , amsawa sukai baki daya banda tahee da ta kasa mosi, zoya sai kallansa take tanaso taje wajan sa amma ya Hana ta intanacin abinci,kan daya daga cikin kujerun falon ya zauna tare da crossing legs dinsa , binsa da Kallo ummey tayi , tayi kewarsa sosai da sosai amma a zahiri sai dauka hankalinta be kansa, cikin kasa kasa da murya zoya ta kalli ummey” ummey please ki cewa akhii yazo muci abinci , this once only please “kallan ta ummey tayi tare da dauke kanta,ganin hakan yasa zoya kara marairaicewa “please ummey”, girgiza Kai kawai ummey tayi har lokacin kuma tahee ta kasa ko kwakkwaran motsine, duk maganganin zoya yanajinta Sarai amma a zahiri sai ka dauka bayacikin falon,cikin larabci yaji saukar muryarta” taso muci abinci”,kamar bazai motsaba sai kuma ya tashi a hankali tare da nufar dining din ba tare da yace komai ba, Daidai inda yake shigowa tahee tana facing din sa, sarkewar da idanuwansu yayi te yasata shakewa da abincin da ke bakinta, sosai take tari dan ba hakaramun Shakewa tayi ba… *********Tun lokacin da suka baro part din ammi suke wa juna kallan kaskanci, daman ba shiri suke da junansu ba musamman da ya kasance suna san mutum d’aya , har suka karasa part dinsa ba Wanda yace wa kowa kala,duk da fargabar dake tattare dasu haka ko waccen su ta shiga falon dan bakantawa yar uwarta, bakowa a falon kasa ganin hakan yasa amrah nufar center kujerun tare da ajiye tray din hannunta, itama summy cikin gadara tanufi inda amrah ta ajje nata inama ta dora natan, ganin hakan yasa amrah saukar da na sumayya, itama sumayya sai abun ya bata haushi ta dan kwalar da na amrah, cikin kankanin lokacin suka fara ture turen abinci,a lokaci daya suka sa hannu tare da ture abinci junansu, take a wajan komai ya fadi kasa ya fashe Daidai lokacin da king ya fito daga wata kofa,bin ku waccen su yayi da rinannun idanuwansa , a part dinsa zasuyi masa wannan iskancin,kwata kwata basu ankara da shi a falon ba, amrah da tafi tsiwa ta tunkari sumayya , lokaci d’aya suka fara danbe da junansu, bece musu komai ba sai koma daki dayayi , cikin kankanin lokaci yafito hannunsa goye a bayansa sosai ransa ya baci, basu ankara ba sai saukar belt da sukaji, cikin bacin rai yake jibgarsu,”how dare you”, sosai suka firgita, sai faman hakuri suke bashi, sai da yasan sun daku sannan ya kyalesu, cikin nutsuwarsa ya zauna kan kujerar dake zaman mutum daya tare da crossing legs dinsa, ko wannansu zubewa yayi a kasa tare da yin kneeling, kowannansu na nadamar zuwa part din, kara had’e ransa yayi tare da kallan tulum abincin da suka bata,”it them all”, daga nan be kara cewa komai ba, sosai sumayya taji wani kukan na zuwan mata dan bata dade da cin abinci ba, amrah ma sai faman zare ido take hawaye na zubomata, belt din dake gefe ya dauka cikin sauri ko wannansu ya karasa inda suka zubar da amincin har da Wanda suka tattake, suna kuka suna tusa abiinci da suka zubar, ko wannansu ba yunwa sukejiba,sai tura tula abincin suke abaki,da Dinsu daya ko zuwa ne ya zube mutum zea iya tsugunnawa yasha sabida tsabtar wajan, saida suka cinye abincin tass ko wannansu na nishi sannan yasu suka gyara ko ina nafalon,yana zaune kan kujera saida ya tabbatar sun wahala sannan ya tashi ba tare da yace musu komai ba ya bar part din tare da nufar part din ummey. 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 BUNKURE Tun lokacin da suka dawo cikin dare Dije ke safa da marwa, sai tunanin yadda zata zuba wa su oumma magani abakin kofa take,ga bintalo dake kwance sai nishi take gabanta sai zafi yake mata,ta dade tsaye tana zagaye dakin kafun ta saki wani murmushin mugunta, samun waje tayi itama ta zauna ganin yadda bintalo ke ta faman nishi, ita kanta tasan da ita boka ya kusanta sai taji azaba balantana bintalo , amma duk da hakan bataji tayi danasanin yin hakan ba tunda Burinsu na daf da cika inyaso sai su koma wajan bokan ya basu abinda bintalo zayi anfani dashi takoma budurwarta.. Yau tunda sassafe Dije ta tashi ko alwala batayi ba bare tayi tunanin yin sallah , maganin da boka ya bata take faman jujjuyawa, kafin cikin sanda tafito daga cikin dakin su ta nufi nasu oumma , bakowa kuwa a wajan kasancewar Gari be dade da wayewa ba , kofar dakin su tahee tashiga bubbugawa sai da taji motsin an nufo kofar tayi saurin zuba maganin tare da komawa baya taheer ne ya bude kofar da niyar fitowa,jiyai an hankadashi ya koma baya ,ga wata yar iska da ta kara de wajan, ganin yana kokarin komawa Dije ta daka masa tsawa “ina kuke muna fukan Allah kufito”, ganin tana kokarin tara musu mutane ne yasasu fitowa taheer agaba oumma na biyedashi, ganin sun tsallaka garin maganin yasa dijen kyalkyalewa da dariya , binta sukai da kallo ganin irin dariyar da take kafun kuma ta yatsina fuska “inna tace ubanme kuke bakufito kunyi aikin da kuka saba ba, ga ruwa can babu kuje kudebo danshine aikinku”, tana gama maganar ta tabar Wajan sai faman sakin dariya take, duk binta da kallo sukai ganin irin dariyar da take kamar zautacciya, basu koma dakin ba suka fara ayyukansu cikin kankanin lokaci suka gama ,taheer ya tafi wajan garba mefaci da yake koyan gyara awajan sa , dakin yayi saura sai oumma ita kadai. 🦋🦋🦋🦋…… Ruwa oummey ta mika mata, ita da zoya sai faman sannu suke mata, amaimakon tarin ya lafa sai ya kara taso mata, tashi tayi cikin fitar hankali Sabida yadda ma’kogwaranta ya rike mata, a guje tayi hanyar barin wajan, kokarin dakatar da ita ummey tayi amma kwata kwata tafita hanyacinta, dausasan hannayensa yasa tare da janyota, kokarin fuskewa take haryanxu tarin yaki lafa mata , ganin hakan yasa oummey nufar daki da niyar dakko first aid box, hannu daya kawai yasa yana taffing din bayanta, yayinda yake hura mata iska a saman fuskarta, ya dau dogon lokaci yana hakan kafun ta fara sauke a jiyar zuciya nunfashin ta nadawo Daidai, ruwan da oummey tazuba mata ya nuna mata batare da ya kara kallan inda take ba, ruwan ta dauka tare da shanyewa tass tana sauke ajiyar zuciya Daidai lokacin da oummey ke dawowa wajan ganin tarin nata ya lafane yasata sauke ajiyar zuciya….,, Comment and share ✍️ LITTAFINA PAID BOOK NE AKAN 300 kacal , amma daga yau Tuesday zuwa ranar asabar duk Wanda zai biya 200 zai biya amaimakon 300 . Za’a biya kudin ta wannan asusun 7041879581 Opay, Ayshatou galadima sai a tura shaidar biya ta wannan number 07041879581. 💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖 _🦋Duk karfin izzata _🦋Gidan Aunty _🦋Sarki sameer _🦋Ya fita zakka _🦋Jini d’aya _🦋Baby MSS LEE💖💖✍️✍️ ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JyvVuOvzYyF19np8UmFKV4 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 (a heart touching love story) Story &written By Mss Lee 💖 PAID BOOK PLX WAYANDA ZASU BIYA KUDINSU DAN ALLAH KUYI HAKURI ANSAMU KUSKURE BA OPAY BANE PALMPAY NE YANZU ZAN KARA RUBUTA MUKU DETAILS DIN 7041879581 Ayshatou galadima , palmpay . GIDAN AUNTY NA KUDINE AKAN 300KACAL ,ME BUKATAR SAMUN CIGABA HAR KARSHE ZAI BIYA KUDINSA TA WANNAN ASUSUN 7041879581 PalmPay Ayshatou galadima sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581. MASU SAN A TALLATA MUSU HAJARSU SUYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMEBR 07041879581 BOOK 1 📕 Free page 18 🦋 Tunda yazauna akan daya daga cikin kujerun dining din bai kara motsawa ba har ummey tayi serving dinshi “thanks “ shine kadai abunda ya iya furtawa, ya dauka kusan mintuna 5 yana kallan abinci kafin ya dauki spoon din ya fara ci a hankali,tunda ya soma cin abincin tahee take satar kallansa ta kasan ido, duk abunda take yanaji aji kinsa ana kallansa,a bazata ya dago da kwayar idanunsa Daidai lokacin da tahee take dago da nata idanun, cikin sauri ta Dauke idanuwanta cikin yar yabar murya ta soma magana “Ummey nagode sosai,Allah ya kara arziki,bari na koma nasan ammi zata iya nemana” ta kare zancen nata tana sunkiyar dakai,”jinjina mata kai ummey tayi kafin ta mike “ am coming “kawai tace mata tare da barin wajan , har lokacin kan tahee na kasa ta kasa kwakkwaran motsi, ba’adau dogon lokaci ba ummey ta dawo da babbar Leda a hannunta, mikawa tahee ledar tayi” wannan naki ne daughter “,girgiza mata kai tahee tashiga yi, ta bude baki da niyar magana ummey ta dakatar da ita “I’m also your mom,karki karamin haka inna baki abu kinji”, cikin jin nauyinta tahee ta amsa mata tare da karbar ledar , sosai tayi wa ummey Godiya da addu’oi masu sanya zuciya tare da barin part din ,duk abun nan da suke king na zaune amma sam hankalinsa baya wajan sabida yadda yake jin wani irin turiri a jikinsa kamar ana hura masa huta,a hankali ya mike “I’m off “kawai yace batare da ya bari tace komai ba yabar part din, zoya sai faman tura karamin bakinta take yau be kulataba sosai , bin bayansa ummey tayi batare da tace komai ba, direct part dinsa ya koma cikin nutsuwarsa lokacin har an kara kyara wajan da su amrah suka bata,ko ina na falon sai tashin kamshi yake, cikin sassarfa ya shige wani daki, jijiyoyin kansa sun fito sunyi rudu rudu, sosai fuskarsa ta juye daga asalin farinta zuwa ja jawur, wani irin tururi ne yake taso masa kamar Wanda ake hurawa huta , gashin kansa da ya sha gyara ya fara batawa,tun yanayi a hankali har yazo ya fara fita hayyacinsa, gaban mudubin dakin ya karasa, a hankali ya fara fasa kayan gaban mudubin, duk abunda yaci kara dashi kawai ya ke dauka ya fasa , sosai ya farfasan kayan dakin, ganin hakan be masa ba yasashi dunkule hannunsa tare da bugashi da karfi akan madubin dakin, ji kake tasss madubin ya tarwatse gabaki Dayansa, kara yasaki tare da cigaba da buga hannunsa a jikin bango, sosai hannunsa ke Jini amma duk da hakan bai dena ba, wani show glass din da ya hango ya nufa Daidai lokacin da aka banko kofar da karfi, da sauri zaki ya karasa inda yake , hannunsa ya kai da niyar kama da king , be ankaraba yaji king yayi sama dashi tare da bugawa da kasa , sosai ya bugu a kafarsa amma duk da hakan bai hakura ba ganin inda yake nufane yasa zaki dakko wani allura a aljihunsa, a bazata ya tsirawa king a jijiyar hannunsa, juyo da rinannun idanunsa da suka matukar canza kala yayi tare da sauke su kan zaki, wata iriyar shaka yayi masa, sosai ya shakesa tare da bugasa da jikin bango, ko Karin kwacewa zaki yake daga Shakar da king yayi masa amma yakasa, ga idanuwansa da suka fara fito wa waje, cikin kankanin lokaci king ya fara sassauta rikon da yayi masa kafun a hankali ya fara lumshe idanuwansa da suka kada sukai ja sosai, ganin yana kokarin faduwa zaki yayi saurin taro hannunsa tare da kwantar dashi kan gadon, shafa wuyansa da king ya shake ya fara murzawa, saida nunfashin sa ya daidaita kafun ya fara gyara dakin , sosai ya gyara ko ina, wayanda suka faffashe ya waresu daban, ganin irin Jinin da king ke zubarwane yayi saurin futa daga dakin , cikin kankanin lokaci ya dawo dauke da first aid box a hannunsa, hannun king da ya ke futar da Jini yayi treating , yana matukar tausaya wa ogansa wannan yanayi da yake yawanshiga. *****A hankali tashiga falon dauke da sallama a bakinta, ammi dake zaune ne ta dago fuskarta da kyakkyawar murmushinta “daughter sai yanxu ake ganinki, karaso ciki mana kin tsaya kamar Mara gaskiya “karasa shigowa tahee tayi “ammi kiyi hakuri, su suka tsayar dani”, wani murmushin ta kara saki, “ai sunyi Daidai tunda bakya lekasu,nan gabama tattara miki kayanki zanyi ki koma can da kwata” ta karasa fada cikin zoyala, murmushi tahee ta saki da ya fito da ainahin gap teeth dinta dan siriri , ledar hannunta ta ajiyewa ammi, kallan ta ammi tayi tana san Karin bayani, cikin in ina ta fara magana “da..dama ummey ce ta bani banc….”katseta ammi tayi, shine kike dardar haka , “hope kin gode mata”jinjina mata kai tahee tayi, “good girl ,haka akeso anjima zan kara mata godiya , yanxu ki dauki kayan ki kaisu dakinki”dan murmushi tahee ta saki, “nagode sosai aunty” dan harara ammi kawai tayi mata ,harta juya zata tafi ammi ta tsayar da ita, tare da miko mata wayarta”nasan Kinyi kewar su yaya, gashinan ki kira ku gaisa “sosai farin cikin tahee ya kasa boyuwa har hakan yasa ammi farin ciki ganin ta cikin farin ciki, ta bude baki da niyar yi mata godiya ammi ta tsayar da ita”keje kiyi wayar ki, banasan wannan Yawan godiyar “tana gama fadar hakan ta nufi stair case , itama tahee murmushin jin dadi ta saki tare da nufar masaukinta da yanxu ya kasance kamar dakinta. 🫧🫧🫧🫧🫧 Tunda ta dawo daga bangaran king take kuka a daki, aunty sai faman lallashinta take akan ta fada mata abunda ke damun ta amma bata kulata ba sai faman kuka take, idanuwanta sunyi jajawur dasu, zabura tayi tare da mikewa , cikin kuna ta fara magana” Wallahi aunty na gaji, na gaji na fada miki hakurina ya kara gushewa , dole a auramun king ko yanaso ko bayaso, sannan a kawar mun da duk wanda yayi kokarin shiga gonata , bazan barsu ba, har ita yar iskar yarinyar can sai na kashe ta da hannuna, bama ita kadai ba , duk Wanda yayi kokarin kusantar inda yake bazan barsaba, aunty dole akoma Wayan boka , ko me za ai ma ayi inma dan dole zesa king yasoni yayi ni va damuwata bace”ta karasa maganar tare da sakin wani saban kukan,kallanta aunty tayi “ki kwantar da hankalinki yanxunnan zan kira yaya, aure kuwa kamar anyishine da kanki zaki dawo bawa mutanan gidan nan umarni bawaishi king kadai ba” ta na karasa zancenta ta bar dakin, wani lallausan murmushi amrah ta saki, “finally na zama mrs tahnoon, oh my god , bansan ya laushin faffadar kirjinka yake ba amma nasan ba karamun dadin kwanciya zanyi ba “ ta kare maganar tare da sakin dariya tana shiga bandaki…. 🫧🫧….. A bangaran sumayya kuwa bata shiga part din su direct ba sai da ta wanke fuskarta tare da sassaita fuskarta kamar ba abunda ya sameta, cikin takun yaukin ta , ta karasa shiga part Dinsu, kamar kuwa yadda tayi hasashe, ihsan da firdausi ne zaune a falo suka kallan wania series, kallansu sumayya tayi tana sakin murmushi da be kai zuciya ba, kallan ta firdausi tayi cikin tsokana “kaga matar yaya king bada kanki a sare, ina kika baro kishiyarki kuma yanxu “ jin maganarta ta karshene yasa sumayya Jan tsaki,”gatacan ta gudu sabida kar kuga shatin marukan fuskarta”ta karasa da sakin shegiyar dariya, binta sukai da kallo ganin irin shegiyar dariyar da take, ihsan dake kallanta ne ta dauke Kai tana sakin murmushi dan ta hango dan fashewar da bakinta yayi ga jikinta da ya dan ‘baci da abinci, basu kuma ce mata komai ba suka cigaba da kallan series dinsu hankali kwance. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰ BUNKURE Tun dazu take safa da marwa tare da zirga zirga a tsakar gidan ko zataga oumma ta fito a haukace, amma har yanxu shiru,ga oumma sai faman aikin ta take hankali kwance ita da taheer da ya dawo tun dazu, ganin hakan yasa ta yafa mayafi tare da nufar gidan boka, “gafaran ku de, boka me share mana hawaye , abun alfaharinmu”wata mummunar dariya aka saki cikin wata kausashshiyar magana aka soma magana” shigo da baya da baya” kamar yadda aka umarceta kuwa hakan tayi sai faman kirari da take masa, cikin bukkar dake shegen wari da zarni. Yana zaune a Inda ya saba cikin Kazan tarsa, yana ganinta ya fara sakin dariya “nasan me ya kawoki ba sai kin maimaitaba, tun ba a je ko ina ba kun fara lallata aikin ku, kije ki dawo da yarinyar da kuka zo da ita kwanaki in ba haka ba kuna cikin tsaka me wuya, rayuwarki da ta yarki Zata mu nana tasu kuma ta daukaka” yana gama fadin haka ya kara babbaka dariya “kije , kije ki taho da yarinyarnan In ba haka ba aikinku na gab da lallacewa”da sauri Dije ta fito sai faman buga sauri taje jin zantikan boka, tana fita kuwa bokan nan ya kara babbakewa da dariya tare da sidar baki…. Comment and share ✍️ Kudin littafin dari uku ne kacal 300 me bukata zai biya kudinsa ta wannan asusun 7041879581 palmpay Ayshatou galadima sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581. 💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖 Duk karfin izzata Gidan Aunty Ya fita zakka Jini daya Sarki sameer Baby . Mss Lee 💖✍️. ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 (a heart touching love story ) Story & written By Mss Lee 💖 PAID BOOK Duk me bukatar gidan aunty daga farko har karshe yamun magana ta wannan number 07041879581 ,bana da kira please . BOOK 1 بسم الله الرحمن الرحيم 💖💖……… Free Page 19 🦋 A hankali yake bude kyawawan idanuwansa da suka kada sukai ja, dafe goshinsa da ke tsananin sara masa yayi tare da mikewa zaune , bin dakin yake da kallo ta ko ina kafun ya dawo dashi kan hannunsa me ciwo, abubuwan da suka faru dazu ne suke dawo masa, sosai jijiyoyin kansa suka kara mikewa , ganin yana kokarin sawa kan sa wani ciwan kai ya mike tare da shiga toilet,ko kayan jikinsa be cire ba haka ya sakar wa kansu ruwan sanyi, sai faman sakin ajiyar zuciya yake, ya dade tsaye cikin ruwan kafun ya fito daga cikin toilet din , gashin kansa da ke faman d’igar da ruwa ya taba kafin yashiga wata door dake degensa , kusan awa daya da yan mintuna ya fito cikin sabuwar shigarsa, ash din Riga ce a jikinsa sai farin wandon da yasa, cikin sa sai faman tashin daddadan kamshin turaren sa yake, duk da yana yin da yake ciki ba karamin kyau yayi ba musamman gashin kansa da se faman kyalli yake , hatta ciwon hannunsa ya sake masa dressing kafin ya dauki wayoyinsa ya bar dakin , a kofar part din sa ya tarar da zaki sai faman kai kawo yake , Wanda ya ganine yasashi sakin ajiyar zuciya tun dazu yake tunanin ya koma ya duba sa amma yana shakkar shiga, ganin ya fito da kansa yasashi ajiyar zuciya , sau daya king ya kallesa tare da dauke kansa yana lumshe ido, wata hadaddiyar Ferrari la ferrari ya dakko sai faman kyalli take, ganin hakan yasa bodyguards dinsa matsowa, hannu daya kawai ya daga musu tare da nufar motar da zaki yayi Parking, cikin sauri daya daga cikin bodyguard dinnan ya bude masa kofar, bai ce komai ba sai shigewa dayayi, bayan ya kulle kofar sara masa sukai gabaki Dayan su kafun zaki ya tayar da motar tare da barin gidan gabaki daya , lokaci zuwa lokaci yakan dago idanuwansa ya kalli king da tun shigowarsa motar kansa yake a sunkuye kwata kwata ransa ba dadi , ya dago da niyar kara kallan sa yaci saukar muryarsa a bazata “ what happened “, ya gane me king ya ke nufi, be bata lokaci ba ya zayyane masa tun shigowarsa dakin har fitarsa saidai ya boye masa shakesan da yayi duk da yasan zai iya gane hakan.kara lumshe idanuwansa yayi sosai yake jin zuciyarsa wani irin amma a zahiri ko gezau bayayi har suka karasa katafaran asibitin Al_nahyan . ➰➰➰➰➰ Bata dau dogon lokaci ba , sai gata sun dawo ita da bintalo da sai faman ja mata Allah ya isa take a haka har suka kusa zuwa inda bukkar bokannan yake kafun tayi shiru, sai faman zare ido dake , dan ba karamun azaba Tasha ba a hannunsa, yana ganinsu ya fara babbaka dariya take da sudar baki kamar wani maye, jikinsa sai faman tashin wari yake .kara babbakewa da dariya yayi “kinsa mu duniya kamar yadda kuke so, burikanku zasu cika kamar yadda nayi muku alkawari, ayukanki da akai miki na baya bazasu taba fito wa fili ba hhhhhh” ya karasa tare da sakin sautin dariya Mara dadin ji,nannauyar ajiyar zuciya Dije ta sauke tana jin wani farincin na ratsata ta ko ina, bintalo na gefe jin ta take kowama zata iya takawa , sai faman washe baki take, kallansu bokan nan yayi tare da jefowa Dije wani magani, “ga wannan maganin kije ki zuba musu a duk inda kika san zasu taka, kada ki kuskura ki dawo nan wajen batare da kin cika aikin nan va,maza ki tafi”saurin daukar maganin Dije tayi sai faman Godiya take masa, tashi sukai da niyar tafiya ita da bintalo ya dakatar dasu”ke kadai zaki tafi, ita anan zaki barta sai kin dawo sai ku tafi a tare , Inba haka ba aikin da kuka fara zai karasa rugujewa da zarar kun isa wajan”, ko karin rike Mata hannu bintalo take bokannan ya daka masu tsawa” ku bace mun da gani “,hakuri Dije ta shiga bashi, bata tsaya sauraran bintalo ba tabar wajan ko tsoron halin da zata shiga batayi,tana fita bokan nan ya daka tsawa” zonan “ , jiki na rawa bintalo ta nufeshi, har kwalla ta fara tsoran ta karyace ze kuma tabata , bata karasa zancan nata ba taji razananniyar muryarsa” zauna anan “, inda ya nuna matane yasata sakin kuka , tsawar da ya daka matane yasa ba shiri ta zauna akan cinyarsa da ya bude,matseta yayi sosai a jikinsa yana shin shinarta, daga nan komai ya canza salo, sosai bintalo Tasha wuya a wajansa, ihu kawai take dan ji tayi azabar da taji yanxu yafi na wancan lokacin , kuka kawai take amma ko kezau bokannan beba sai da ya tabbatar ya biya bukatarsa sannan yayi jifa da ita har lokacin Dije bata dawo ba , ganin hakan yasa bintalo daukar hijabinta tare da rugawa a wuje sai a hanya tasaka hijabin sai faman tsine wa Dije take . 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 Zazzaune mutanan gida suke duka a falon dada , king ne kawai babu, zoya na gefan tahee yau sai faman hira take mata ita da ihsan , yan matan ma kowannansu na zazzaune a falon , amrah da sumayya sai faman harara juna suke batare da kowa ya hankalta dasu ba, musamman amrah da lokaci zuwa lokacin takan Kure tahee da kallo, ita kadai tasan abunda take rayawa akanta. Mikewa zoya tayi , aunty tahee please cakes dina zaki dakko mun kinji,jinjina mata kai tahee tayi tare da mikewa , kama hannunta zoya tayi suka soma tafiya, kallansu abeey yayi” yarana ina zuwa kuma “ sun kuyar da Kai tahee tayi “dama zoya tace zan dakko mata abune “, hararar zoya ummey tayi, kin kallanta zoya tayi tana buya bayan tahee, batace musu komai ba shima abeey da ammi murmushi kawai suke , su mamy kuwa kowannansu murmushin ya’ke yake saki, can dining su tahee suka nufa inda cakes din suke dayawa a ajje, kallanta tahee tayi “ wanne kikeso a ciki” wani me kalar chocolate ta nuna mata, daya daga cikin kankanin plate din tahee ta dauka tare da zuba mata chocolate cake din”, har tun juya da niyar komawa kuma sai tahee ta tsaya tare da komawa, cakes din ta zuba cikin kananun plates din tare da jerasu kan babban tray a haka harta karaso falon da suke zaune kowa sai binta yake da kallo, inda su dada suke zaune ta nufa tare da ajje musu tray din, babu Wanda be yi murmushi ba ganin abinda tayi, sosai ta burgesu musamman abeey da dada dake faman sakin murmushi, murmushin jin dadi uncel salim ya saki”mun gode sosai kuwa daughter , Allah yayi albarka “sosai kowa ya nuna jin dadin musamman dada da sai faman shi mata albarka take, abeey ne ya kalleta cikin zolaya yace “an kawo mana abun turawa daughter saura abunda sha”, murmushi ta saki tana sun kuyar da kanta , “tom bari na dakko muku” ta fada tana mikewa har lokacin zoya natare da ita kowa na mamakin sakewar da tayi da ita, murmushi amrah dake zaune tayi ganin ta kara komawa wajan dimming din, bata motsawa saida taga taheee ta futo da wani tray din cikin sa cups din glass ne sai juice din data dakko a kai tazo Daidai wjan da steps dinnan cikin Sauri amrah ta tashi da niyar wucewa sai ta bugar mata kafa batare da kowa ya lurasa sai aunty dake faman sakin murmushi ganin abinda amrah tayi,tray din hannun tahee ne ya fadi kafarsa sosai ta bugu jikin stairs din da kwalba ta fashe, mikewa kowa yayi ganin abinda ke faruwa, gadan Ganda kanta ya taho da niyar Dakar glass din, cikin sauri mutanan gidan suka nufeta , kara kawai tahee ta saki, Jin zata fada ga azaba da kafarta ke mata, ta sadakar faduwa kawai zatayi taji an riketa, sosai ta rike Wanda ya riketan, sai faman sakin kuka take, kafarta harta fara kumbura ga Jinin da yake fita a jikinta.. Ba yawa please . Comment and share. Mss Lee 💖✍️. ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 (a heart touching love story) Story & written By Mss Lee 💖 PAID BOOK BOOK 1 Free page 20🦋 Ganin wanda ya riketan yasa ko wannansu sakin ajiyar zuciya sabanin amrah da aunty ta da suka fara farin ciki, hatta sumayya sai da ta tausaya mata duk da ba kaunarta take ba, dada sai faman sallallami take ganin Jinin da yake fita a kafar tata, ganin ta kasa taka kafar ne yasa ta daukar ta gaba dayanta tare da nufar 3 sitter din kujerun, har yanxu fuskarsa a hade ba ko digon dariya ga kuncin da zuciyar sa take tun dazu, hannu yasa da niyar zare kwalbar ta saki karan azaba tare da sakin wani saban kukan, inda kwalbar tashige ya kurawa ido, tabbas yasan in yace zai cire da karfi zai kara raunana mata ne , inda ya kunbura ya kalla da lumshash shun idanuwansa, a hankali ya kai hannunsa wajan tare da Mara matsawa a hankali, kara goce kafarta tayi jin wani saban azaba da take ji,kowa na cikin falon hankalinsa a tashe yake musamman ganin yadda kafar ta kunbura,”son kodai asibiti zamu wuce”cewar uncle musaddiq , lumshe idanuwansa yayi ,bai san takura da zata kaishi da yin magana , shurun da yayi ne yasa abeey kallansa” baka ce komai ba , in baza aje hospital ba sai a tafi clinic room ai ko ”, a fiske ya furta “no need abeey” kafun ya ciro wayarsa, wasu numbers ya danna tare da kaiwa kunnansa , bai jira anyi magana ba ya furta “ large first aid box” yana gama fadar hakan ya kashe wayar, dan gajeran murmushi ya saki , yasan tabbas akwia abunda yake damun gudan jininsa tun ba yau ba amma da muwar da ya gani yanxu ta nunka wacce ya saba gani, fatansa ya samu wacce zata gyara masa wannan murd’ad’d’en halin nasa. Kukan tahee ne ya fargar dashi tunanin da ya fada , kanta na cinyar ummey sai faman sannu suke mata,dada ma ganin ciwon kafarta na kokarin tashi yasata yin shiru, kara rintse idanuwansa yayi ganin tana kokarin sa masa ciwon kai, dabadan su abeey ba da ba abunda zai Hana be faffalla mata mari ba, ko cikakken munti biyar ba ai ba sai ga zaki da wani dogon first aid Box a hannunsa, king ya ajiyewa kafun ya gaishe da mutanan gidan, a hankali yake motsa hannunsa kafun ya bude first aid box din, abunda zaiyi anfani dasu kawai ya dauka tare da nufar kafarta, sosai take hawaye duk da ba a jin sautin kukan nata,kwalbar data shige mata kafa yake kokarin cirewa sabida zafi batasan lokacin da ta kama hannunsa ba tana rintse idanuwanta,fuskarta duk ta baci da hawaye , cikin sauri ya dago da idanuwansa jin shock din da yaji lokacin da hannunta ya taba fatarta, Sau daya ya kalleta tare da dauke kansa, be wani sha wani dogon wahala ba ya cire mata doguwar kwalbar ,bin kafarta data kunbura yayi da kallo kafun yayi mata dressing dinta,har yanxu akwai ragowar hawayen a fuskarta, kowa na falan sai faman sannu yake mata,sabanin aunty dake mata dan dole, amrah kuwa sai faman danasanin turatan dayi take ganin king ya tabata,a fakaice take goge kwallar ba’kin ciki, yana gama dressing din be jira cewar kowa ba ya far part din fuskarsa a had’e har yanxu. 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 Tunda Dije ta koma gida neman hanyar da zata kuma sawa su oumma maganin nan tayi, ganin kowa hankalinsa ba ya kanta tashige nan garansu sai faman ya tsine take kuwa, taci sa’a kuwa tunda ta shiga bataji motsin kowa ba harta sa kafa zata shiga ciki jin motsin ana taba ban daki yasata barbada maganin nan cikin sauri tare da barin wajan , Daidai taheer na fitowa daga ban daki, bin kofar da aka ‘bane yayi da kallo a tunaninsa oumma ce ,ganin babu Wanda yake shigo musu ban gare sai neman Futuna, kofar dakin nasu ya nufa,kamar Wanda aka rufewa baki ko sallama beyi ba yashiga dakin, jiyai kansa ya sara masa, duk dakin ya canza masa, waje ya samu ya zauna kamar Wanda aka tsira kuma ya mike, sosai yaji dakin ya fita aransa bazai iya zama ba, har ya taka kafarsa da niyar shiga inda oumma take sai kuma yayi saurin ja da baya jin kamar ya taka kaya, sosai yaji jikinsa ya daukan zafi , da yayi baya baya kuma sai yaji zafin na raguwa, da sauri ya fita daga dakin jin zafin na raguwa ne yasasa rugawa da gudu da barin gidan baki daya duk akan idan Dije da ta la’be a kan soro ganin yadda taheer ya fitone yasata sakin dariya, a zuciyar ta sai gode wa boka take . A daki kuwa kusan awan oumma d’aya sai faman zagaye take ganin har yanxu taheer be shigo ba, kofar toilet din ta nufa tare da kwankwasawa”taheer !! Taheer!! Taheer!!’ Ganin ta kirasa har sau uku be amsa ba yasata bude ban dakin, babu kowa a ciki sai ruwan dake nuna anyi anfani dashi, batayi tunanin komai ba ta koma ta zauna kusan yan mintuna ganin be dawo ba har lokacin yasa hankalin oumma ya fara tashi, hijabinta ta dauka da niyar lekasa, a tsakar gidan ta samu wasu daga yan gidan zazzaune kamar yadda yazama al’adarsu, Dije dake zaune har lokacin ne Tasaka shewa” za a tafi yawan tazubar Din da aka saba cikin dare” oumma bata kulataba tayi ficewarta dan tasan kota musu bayani ba saurara zasuyi ba, ganin hakan yasa yan tsakar gidan fara kuskus. Duk inda tasan zai iya zuwa taje har wajan da yake koyan faci taje amma bata tarar dashi ba , sosai hankalinta ya kara Tashi sanin da tai masa ba ya dare haka ko zeyi ma zai fada mata kafin yayi, bata koma gida ba taci gaba da duba shi duk inda taje sai tayi musu kwatancan sa ko sun gansa amma babu Wanda yace ya gansa, hankalinta ba karamun tashi ya karayi ba ganin har karfe Tara da yan mintuna ba taheer ba alamunsa, sosai ta bazama nemansa har tayi nisa sosai da gida, kuka oumma kawai take fatanta Allah ya tsare mata d’anta, tunanin ko ya koma gida yana nemanta shima yasata juyowa daniyar komawa gida, Daidai zata tsallaka titi wata had’ad’d’iyar bakar prado tai bal da ita, birki me Motar yaja cikin sauri tare da fitowa, shima na bayan motar be jira an bude masa ba ya bude da kansa cikin takun dattako ya karaso wajan, ganin yadda take zubar da Jini ga bakowa a wajan yasa ya kalli babban dansa dake gefensa, “khaleed kamata a sata a mota”,ba bata lokaci kuwa khaleed din da aka kira ya sata a mota ganin Jinin har yanxu be tsayaba yasa ba bata lokaci suka tada motar tare da barin Wajan batare da sun damu da sanin daga ina take ba, a Tunaninsa in ta samu lapiya sai tayi musu kwatance su dawo da ita. **ganin har karfe goma ta wuce ba taheer ba oumma yasa dije kara sakin wata dariyar mugun ta , bintalo ma dake zaginta ganin har lokacin nan basu dawoba yasa ta dena zagin nata sai faman washe hakwara suke burin su ya cika , a yan gidan kuwa babu Wanda ya damu da dawowarsu balantana suyi tunanin ko wani abune ya samesu , hajiya kaka tabawa kuwa tun safe tana daki sabida cikon kafarta da ya sata a gaba , duk abun nan da yake faruwa batasani ba , babu Wanda yayi tunanin sanar da ita, a ganinsu in oumma ta dawo daga barikinta sai tayi musu bayani.. 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 Tun da ta tashi daga bacci taji zuciyarta na faman tsinkewa ,burinta yau taji muryar su oumma dan sosai tayi kewarsu, kafarta da ta kara kumbura ta kalla kafun ta mike a hankali dakyar take taku har ta karasa ban daki, ta dau dogon lokaci a cikin bayin sabida ciwonta kafun ta fito daure da towel , komai cikin karfin hali take yinsa , pant din ta kawai ta saka tare da doguwar Riga batare da tasa bra a ciki ba,kadan ta shafa turarenta tare da komawa kan gadon, sosai kafarta ta kara kunbura dan basosai take takataba, kwankwasa kofar da akai ne yasata dago da fuskarta, ammi ce ta shigo dakin bayanta kuma asabe ce dauke da babban tray a hannunta, ya jiki tayi mata tare da ajje mata tray din abincin, cikin tausayawa ammi ta kalleta, “sannu daughter, ko asibiti zamu tafi ne” saurin girgiza mata kai tahee tayi, “ah ah ammi ba sai munje asibiti ba zai warke ai”, sosai ammi ta kalleta “Anya kuwa daughter kalli yadda kafarki ya kunbura, gaskiya asibiti zamu tafi “ta karasa tare mikewa , saurin kamo hannunta tahee tayi kwalla harta soma taran mata” Allah aunty da gaske nake miki ya dena , saura kadan kuma shima ba sai munje asibiti ba”, ta karasa kwallar na sakko mata, girgiza kai ammi tayi daman Tasan halinta da mugun tsoran asibiti, shiyasa bata kuma cewa komai ba ta gyada mata kanta”shikenan ga abincin kinan Kici kafin na kawo miki magani”, katuwar ajiyar zuciya tahee ta sauke tare da sakin mata guntun murmushi “insha Allahu aunty”, bata kuma ce mata komai ba ta kama hanya tare da barin dakin, ganin ta fita ne yasata mikewa a hankali tare da dakko abincin da aka kawo mata , sosai taci abinda sabida yunwar da takeji, ta dade zaune a Wajan har ta fidda ran shigowar ammi sai taji an bude kofar dakin, ammin ce kuwa ta shigo,har ta bude baki da niyar yin magana ya shigo dakin fuskarsa a hade taka ina kamshin turarasan yacika wajan,saurin sunkuyar da kanta kasa tayi tana hadiye abunda ya tarar mata a makoshi, lokaci d’aya taji wasu hawaye na tarar mata, kallansa ammi tayi “son duba mata kafar naga har yanxu kunburun be sace ba”, be motsa daga jinginar dayayi ba har yanxu , har ammi ta bude baki da niyar sake magana ya bude lumsassun idanuwansa tare da zubasu a kanta a hankali ya soma tafiya kafun ya karaso gaban gadon, bin kunburarriyar kafar yayi da kallo ganin tafi kunbura fiye da jiya kafun ya dauke idanuwansa ya maida kan ammi,a fiske ya furta “man zafi” cikin sauri ammi ta karasa gaban mirror din tare da miko masa man da ya tanbaya, TAHEE sai faman zare ido take, akan kujerar dake gefen gadon ya zauna, hannun doguwar rigarsa ya fara nannad’ewa tare da tsuke fuskarsa, ganin hakan yasa ta fara sakin kuka kasa kasa,a hankali ya daura hannunsa kan kafar tasa, Baisan lokacin da yayi saurin daukewa ba sabida shock din da yaji , kusan sakanni ya dauka kafun ya mayar da hannun nasa kan farar kafarta da yayi jajur Sabida kunbura,kuka tahee ta saka jin azabar da taji be kulataba sai ma rike kafar da yayi gam yana kara hade fuskar tasa, ganin yadda tahee take kukane yasa ammi saurin barin dakin dan tasan in tazauna zata iya hanashi matsa kafar bayan ita ta kirashi da kanta. Tsurawa kafar ido yayi kafun yasaki iska kadan ta bakinsa, a hankali ya soma matsa wajan da ya kunbura cikin kwarewa, kara tahee ta saki tare da kankame hannunsa, kafarta take san kwacewa amma ta kasa sabida yadda ya rike kafartata, wani kukan ta kara saki gabaki daya tafita daga hayyacinsa, be kulata ba sai ma kara matsa kafar da yayi yana shafa mata maganin, Daidai inda yafi kumbura ya dora hannunsa , wata karar tahee ta saki da iya Karfiinta na karshe ta ture hannunsa da ya kara fama ciwon, a maimakon ya saki hannun sai kujerar da yake zaune tayi baya yayinda tahee ta fado ta gaba, gaba d’ayansu suka fadi kasan, shi yana kasa ita kuma ta fado kansa, saurin rintse idanuwansa yayi tare da fusgar nunfashin dake kokarin kwace masa, kara lumshe idanuwansa yayi lokaci d’aya kuma ya ware idanuwansa jin saukar lips dinta akan nasa tare da saukar tsayayyun breast dinta a jikin sa adaidai lokacin da ake turo kofar dakin ……… (Tofaa 😂)….. Comment and share….. 07041879581…. MSS LEE 💖.  ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 ( a heart touching love story) Story & written By Mss Lee 💖 PAID BOOK Littafin gidan aunty na kudine akan 300 kacal ,Sauran few pages na gama free pages dina , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 7041879581 palmpay Ayshatou galadima,sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581. Nagode … BOOK 1 Free page 21 🦋 Ba kowa bace ta shigo dakin face amrah dake a zabure idanuwanta duk sun kunbura, a yadda ta gansu ne yasata fashewa da kuka tare da barin dakin cikin sauri, da Sauri ya bangaje tahee da batasan meke faruwa ba sabida yadda kafarta ke mata ciwo a kasa , har ya daga hannu da niyar tsinka mata mari sai kuma ya dungule hannu tare da rintse idanuwansa da suka kada sukai ja, kallo daya kawai yayi mata tare da ficewa a dakin ransa a bace , ko da ya fito falon be tarar da ammi ba hakan ya bashi damar fita daga part din gaba daya, ko part din ummey be karasa ba ya bar gidan . ****Da gudu amrah ta karasa part din aunty, bakowa a falon tai saurin shigewa daki, kuka ta fashe dashi sosai , kome ta gani sai tayi bal dashi, a haukace take fasa abunda taci karo dashi,”taheera “shine sunan da take nanatawa tana hawaye “wallahi sai na kashe ki,sai naga bayanki, shegiya tsinanniya ,wacece ke da zaki rungumeshi har dayi mishi kiss, wallahi sai na la’antaki bazan kara fadawa kowa bama da kaina zan kashe ki har lahira sannan na kashe banza”, bata karasa zancan nata ba aka tsitstsinka mata mari dama da hagu, a tsorace ta dago da idanuwanta a tunaninta aunty ce ta mare ta ganin ba kowa a dakin ta fara zazzare idanuwa, mafarkan da ta dungayi jiya da daddare ne ya fado mata a zuciya ,da kyar take iya hadiye abunda ke makoshinta, taku ta fara a hankali da niyar barin dakin,talewar da kafarta tayi ne yasa ba shiri ta bige kafar take da sakin azababban kuka, wani saukan marin da ta kuma jine yasa ba shiri ta mike tsaye ga azaba da kafarta kemata kamar wacce tayi targade.”ke “ taji wata razananniyar murya ta kirata,cikin rawar murya ta soma amsawa “naa…am, dan.. Allah kuyi… hakuri innayi muku lefi…”bata karasa maganar taba taji saukar bulala a bayanta,ihu ta soma “nashiga ukuna na lalace,dan Allah kuyi hakuri na tuba bazan sake ba “, kamar wayanda ake zugawa haka suka shiga laftarta saida suka ga ta daku sannan aka daka mata tsawa cikin muryar mata ,”ke, mike tsaye”azabure amrah ta mike fuskarta duk ta baci da majina ga kukan da Tasha “rufe mana baki”aka kara daka mata tsawa, hannayenta biyu tai saurin daurawa abakin mata sai faman waige waige take ga hawayen da ke zuba a fuskarta,”rawa zaki mana yanxun nan , duk rawar da muka saki,kuka kuskura kika fadi zaki gane kuranki, kinajina”, da sauri ta shiga daga kai har ynxu hannunta na kulle a bakinta,dariya muryoyin mace da na mijin suka saka kafun lokaci daya wajan yayi shiru,”maza yi mana rawar dan biri”ana gama fada mata haka aka jefo mata ayaba kuda d’aya, da sauri ta dauki ayabar ta fara tsalle kamar yadda dan biri keyi, fuskarta duk ta baci da hawaye ga guntun gashin ta da ya barbaje sai ta dawo kamar dan birin kuwa, tanayi tana kwantawa alokaci daya kuma tana kuka, sosai taji muryoyin nan guda biyu suna dariya kafin ta karajin wani sautin,”yi mana yadda mage take kuka”, kara fashewa da kuka amrah tayi kafun ta fara “meowwww meowww meowwww moewwww” ta nayi tana share fuskarta da ta baci, sosai suka wahalar da ita, iya rawan dabbobin kam har Wanda bata sansuva tayi rawarsu,ga kafarta dake tsananin yi mata ciwo kamar wacce ta goce a kashi. ********** kwance take kan lafiyanyan gadon dakin nata, hannu daya wayane a ciki yayin da Dayan hannun take rike da apple, waya take sai faman murmushi take saki ita kadai, turo kofar dakin da akai ne yasata dagowa,wacce ta ganine yasata mikewa zaune tare da kashe wayar, Momy kice kuma yau adakina, karasa shigowa wacce aka kira da momy tayi kafun ta samu waje ta zauna daga bakin gadon, “ko na komane”ta fada tana zubawa firdausi idanuwa, dan jinjina mata kai firdausi tayi tare da dage kafadun ta kadan,”akan wana dalili zan hanaki shigowa momy, naga yanxu bakya shigowane tun bayan tafiyar yaya haroon,ta bile baki kawai momy tayi kafun su canza hirar tasu zuwa wata,kallan ta firdausi tayi “amma momy ba kya tunanin waccan yarinyar da Gangan ta bige dan taga mutanan gidan suka tarai rayarta, kalli fa wai yau yaya king ne ya taba wata, ni ko hannunsa aka ce ya dora akan wata ai bazan yadda ba balantana wayancan shashashan da suke wahalar dakansu”,murmushi kawai momyn ta saki ba tare da tace komai ba dan Akan idanta amrah ta tura taheen, ganin momyn tata bata biye mata ba yasa share zancen suka fara zancan dan uwanta. 💖💖💖💖💖 Tunda ya bar gidan a guje zaki ya fara tuka Motan ganin yadda lokaci daya king din ya canza masa kamar wani zaki,a dake ya furta “my house “ya karasa maganar tasa tare lumshe idanuwansa, tafiya akai sosai me dan ta Zara daga banana island kafun suzo kofar wani hadadden building me shegen kyau, tundaga wajan gidan da glass akayi shi komai na cikin sa glass ne , cikin sauri sojojin dake bakin gate din suka wangale baban gate ganin me gayyane da kanshi ya zo, a Daidai parking lot zaki yayi parking inda sauran manyan motocin suke, yau be jira an bude mishi kofarba, yana fito wa ciki ya shiga cikin sassarfa, kofar dake kasa kawai ya bude ya shiga, sosai dakin da yashiga ya hadu, kayataccen falo ne a wajan babban gaske da yafi Wanda yashigo haduwa, Komai na cikinsa whites ne tunda ga kan labulayen dakin har kan lallausan carfet din dake shinfide fari tass dashi, ko ina nawajan tashin kamshi yake kamar ana anfani da shi kullum, kan daya daga cikin white sofa din ya zauna ko takalman kafarsa be cire ba, idanuwansa ya lumshe a hankali ,jijiyoyin kansa ne suka mike sosai , kyakkyawar farar fuskarsa tayi ja sosai, kara rintse idanuwansa yayi da karfin gaske ganin har yanxu yanajin tsayayyun breast dinta a jikinsa, sosai gashin jikinsa ya mike ,a zamube ya fara bal da duk abunda yaci karo dashi, zafi yake ji sosai a cikin Jikinsa,sosai gashin jikinsa ya kara tashi ji yake kamar tana jikin sa haryanzu, adduar ya fara cikin zuciyarsa, tsawan lokaci kafun wata nutsuwa ta fara saukar masa, sosai ya ke ajiyar zuciya ganin lokaci daya azababban zafin dake ratsashi ya tafi sai ma sanyi da yake danji a haka wani daddadan bacci ya dauke sa. *****har yanxu tana zaune a kasa tun lokacin da ya tunku data, kafarta hannunta rike da kafar tata, shigowar da akai ne yasata saurin dago da kanta?ganin su dada ne yasata sakin ajiyar zuciya, da sauri dada ta karaso inda take “me nake gani haka , tahura ya naganki a kasa duk zafin ciwon ne”, rasa me zatace mata tayi kawai sai ta gyada mata kai alamar a’ah, murmushi ta sakar mata a hankali kafun ta gaishe ta “ina kwana dada” girgiza kai dada tashiga yi “Allah sarki tahura,lapiya ta Lou, jiya da kyar nayi bacci sabida halin da kika shiga “wani murmushin ta kara saki kafun ta gaishe dasu abeey, shima cikin kulawa ya amsa mata tare da tanbayarta ya jikinta, sosai ta dan saki dasu Bayan ta gaisa da su uncle musaddiq da suka shigo daga baya, ganin sauran yan gidan ma suna zuwa yasa duk suka koma falon ammi,sosai kafarta tayi sauki dan tana dan takawa kadan kadan , afalon suka cigaba da hira har ummey ta shigo part din yau batare da zoya Suke ba sabida makarantar da tafi,a haka kowa na gidan ya shigo sabanin amrah , wunin ranar a part din ammi sukayi shi sosai suka nuna mata kulawa musamman ummey dake gefenta. 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 BUNKURE Da sassafe kaka ta bawa ta tashi yau kai tsaye dakin su oumma ta nufa , bubbuga kofar dakin ta shiga yi, jin shiru ba abude ba yasata kara bubbugawa “maryama kina ji ina kiranki shine zakimun uwarshegu ko, zaki nunamun ba’kin halin naku kenan ko, bazaki fito bane kina jina”, ganin yadda take faman buga kofar dakin su oumma ne yasa mutanan gidan fara taruwa,Dije dake labe tun lokacin da kaka tabawa ta fito yasata karasowa wajan,kallan kaka tabawa tayi tana kumshe dariyar dake cint kafun ta soma magana”inna ai maryama yanxu ta zama abinda ta zama “kallanta kaka tabawa tayi kamar ya bangane ba,”oh ai inna komai a filine , jiya agaban idanunmu tafita daga gidan nan , har kokarin zagin mu tai da muka yi kokarin tsayar da ita” sosai kaka taba ta kalleta “kina nufin tana yawan dare kenan”, tabe baki Dije tayi”ai kowa nanan sheda ne inna ki tanbayesu”, nan da nan yan gidan kowa ya fara tashi gulmar,babu me fadar alkairi akan oumma su taheer ganin yadda tafita tun jiya bata dawo ba, girgiza kai kawai kaka tabawa tayi rai a bace ta bar wajan” za tazo ta sameni ne duk gidan karuwanci da take zuwa”, da dad d’aya kowa ya fara watse wa ganin hakan yasa cikin sauri Dije ta shige dakin harda taka rawa, kallan ta bintalo tayi,”ya naga sai faman washe baki kike kamar wata tababbiya”a maimakon ta tsawa tar mata akan kalaman ta sai ta kuma kyalkyalewa da dariya, nan da nan ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar wa bintalo, itama bintalon sosai tayi farinciki ganin burinta na Auran babban mutum zai cika ,wani shegen murmushi ta saki a zuciyar ta kuwa fadi take “lallai ma Dije baki da hankali,ai wallahi kafin nayi Auran nan sai na ci duniyata da tsinke yanda na fara jin dadin abinnan da boka Yayi mun ,wallahi yanxu na fara anjima ma sai na koma wajan sa dan ya mallake mun duk Wanda yace zai takuramun, ciki kuwa har dake dan ke kika koyamun”,duk wannan maganganun nata cikin zuciyar ta take kafun lokaci daya ta saki wata yar iskar dariya da ita kadai ta san ma’anarta. Comment and share LITTAFIN GIDAN AUNTY NA KUDINE AKAN 300 kacal zaku biya kudin ku ta wannan asusun 7041879581 palm pay ayshatou galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581. Saura few pages na gama sakin free pages dina . MASU COMMENT INA GODIYA SOSAI DA SOSAI , I HEART ❤️ YOU ALL ✍️. MSS LEE 💖✍️ ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 (a heart touching love story) Story & written By Mss Lee 💖 PAID BOOK NA KUSA KAMMALA FREE PAGES DINA Mesan KARANTA GIDAN AUNTY DAGA FARKO ZUWA KARSHE ZAI IYA BIYAN KUDINSA TA WANNAN ASUSUN 7041879581 palm pay ayshatou galadima sai a turo shaidar biya ta wanna number 07041879581 BOOK 1 Free page 22 and 23 🦋 A kwana a tashi ba wuya wajan Allah SWT, yau kusan sati biyu kenan da batan su oumma , Tsawan wannan lokaci babu Wanda ya damu da yasan inda suke ,hatta kaka ta bawa da ta share zancen, cikin wannan lokacin sosai bintalo ta fara bin maza ,ganin hankalin yan gidan su nasan komawa kanta ta koma wajan bokannan da mahaifiyarta Ke zuwa, gaba daya ta mallakesu ko dare zatayi babu me tanbayarta dalili, sosai ta baci da kazamin rayuwarnan, Dije kuwa kullum cikin farin ciki take idan bintalo ta Kawo mata kudi ko damuwa da inda ta ke samo kudin batayi,burinta ya cika tun lokacin da oumma tabar gidan,yanxu burinta ta kai bintalo can birni wajan da tahee take sannan itama tasa taheen ta shiga duniya. 🫧🫧🫧🫧🫧 A tsawan kwana kinnan sosai wata shakuwa me karfi tashiga tsakanin zoya da tahee, kullum in ta dawo daga makaranta zaki ganta wajan tahee tana fada mata abunda aka koya musu, yawancin lokuta suna part din ummey ko part din dada da yanxu take kulawa da ita sosai, ta bangaran yan gidan ma haka, momy tana sake mata sosai sabanin mamy da aunty,musamman aunty da ke nuna mata kyautata mata agaban yan gidan , abayansu kuma taita zaginta, ihsan da firdausi ma sosai suka sake mata a yan kwanakin nan, amrah da sumayya ne ko kallo basu isheta ba,ganin hakan yasa itama bata sake musu fuska. Cikin yan kwanakin nan sosai tayi kewar su oumma tanaso tacewa aunty ta kira mata su amma bata san ta yadda zata tanbaye taba. Yau ma tunda ta tashi da kewar su oumma ta tashi,so take kawai taji muryarsu sabida mummunan mafarkin da tayi a kansu, sai faman zagaye take a daki tana tunanin ta yadda zata tanbaye ammi , ganin bata da wata mafitane yasa ta mikewa tare da fitowa falo a hankali kamar Mara gaskiya, Daidai tana fito wa shi kuma yana shigowa ciki, kamewa tahee tayi wajan tare da rintse idanuwanta,yau sati biyu kenan rabanta da ta gansa, sosai ya kara yi mata kyau kamar kullum kara masa shi ake , a hankali tayi kokarin bude idanuwanta jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri ga kamshin turaransa da ya cika mata hanci, da gyar ta karasa bude idanuwannanta, Ganin baya wajan kamar yadda tayi tunani yasata sakin ajiyar zuciya, ta juya daniyar komawa kenan idanuwanta suka sauka a kansa, kyawawan fararan idanuwanta ta zuba masa duk da yadda zuciyarta ke faman bugawa, sosai shigarsa tayi mata kyau musamman gyaran gashinsa da ya tubke sai faman kyalli yake ,sak ya fito a balaraben sa dan Inba Hausa yayi baza ka taba tunanin yasan Menene kalmar ba, wayace a hannunsa sai faman dannawa yake cikin kwanciyar hankali,fuskarsa kwata kwata ba annuri kamar Wanda yayi rashin lapiya ga kafar sa da yayi crossing lokaci zuwa lokaci yana motsata, a hankali ya motsa pink lips dinsa kamar me sanyin magana sai kuma ya fasa tare da datse lips din nasa,tunda ta Kafe shi da ido ko motsi batayi sam ta manta ma agaban watake, a hankali ya dago da idanuwansa karaf suka hade da nata,bata janye idanuwan ba sai ma sarkewa da idanuwansu sukai cikin na junansu , bata farga da shirmen da take ba sai jin saukar tsawar sa tayi, sosai ta razana juyawa tayi daniyar guduwa ta ji saukar muryarsa “if you dare “ya karasa kamar be san yin magana , cak tahee ta Tsaya kamar me shirin sakin kuka , ahankali take juyo da fuskarta da ta dukar sosai take jin kunyar abunda tayi ,zuciyarta sai faman bugawa take da sauri da sauri kamar wacce tayi gudu. Lokaci zuwa lokaci take dago da idanta ganin hankalinsa baya kanta cikin rawar murya ta soma magana “ ina wu..ni”, be amsa mata ba haryanxu idanuwansa na kan wayarsa, kara dukar dakai tayi tana wasa da kasan hijabin jikinta,”ina wuni” ta kara gaishesa cikin rawar murya, yanxun ma be amsa mata , ganin hakan itama ta shareshi tana dan turo dan mitsitsin bakinta, dauke gansa yayi daka kallan dan mitsitsin bakin da ta motsa kafin cikin kasa kasa da murya ya furta “coffee”,kara turo dan mitsitsin bakin nata tayi gaba kafin ta nufi hanyar kitchen din , cikin kan kanin lokaci ta kammala hada coffee din azuciyarta sai faman mitar Shan coffee din nasa take ,”coffee ,coffee”, kafun kuma ta sassaita nutsuwarta ta fito falon, a yadda ta barsa a haka tazo ta samesan yana zaune da kafarsa da yayi crossing, duk da yadda zuciyarta ke rawa hakan be sa nutsuwarta fito wa ba” gashi” ta mika masa tana dan russunawa, be fi sakon biyu ba yasaka hannunsa kan dan karamin tray din da ta miko masa, sipping ya fara a hankali,ta kasan ido tahee take satar kallansa “shi wannan kullum cikin Shan coffee ko abincin arziki be ci,nan gaba inaji sai coffee dinnan ya fito masa a jiki”, ita kadai take hirar ta a zuciya,kamar yasan me take tattaunawa ya dago da idanuwansa ,saurin sunkuyar dakanta kasa tayi, dan ta bile bakinsa yayi kafin ya soma magana” get me something to eat “,da sauri ta dago idanuwanta jin abinda yace , bata ce komai ba sai kitchen da ta nufa, a ba’kin gas ta tsaya tana karewa kitchen din kallo,tu nani ta fara me zata dora masa Mara sauki , ganin tana bata lokaci ne yasa ta nufar babbar freezer din kitchen, manyan tilapia fish ta dakko guda biyu , cikin kwarewa ta gyara kifin kafun ta feraye Irish potatoes dinta, bata dau dogon lokaci ba ta kammala hada grilled fish dinta ,da yaji sauce din Dankali sai faman tashin kamshi yake, kunun ayan da ta ga ammi ta jera a fridge ta dakko tare da zubawa cikin madaidai cin jug, cikin lokaci kankanin ta kammala hada abincin , kafin ta fito falo zuciyarta sai bugawa take, hanyanxun yana zaune a falon sabanin dazu yanzu ya dan jingida da jikin kujeran, sunkuyar da Kai tayi kasa,”ga abincin”, be ce mata komai ma sai gyara zamansa da yayi kafun ya bude plate din, sosai yadda aka kawata abincin ya burgeshi amma a zahiri sai ma tabe bakinsa da yayi, be kulata ba ya faraci a hankali , 3 spoon yayi kawai tare da Shan kunun ayar Daidai lokacin da ake shigowa part din da sallama , ammi ce ta fara shigowa bayanta kuma su amrah ne , duk tsayawa sukai cirko cirko a tsaye kafun ammi ta karaso falon cikin mamaki,”son Yaushe ka shigo”kamar bazea ce komai ba sai kuma ya bude baki “am looking for u”, murmushi ta sakar masa “sorry son ina tare da su ummey ne”, lumshe mata idanuwansa yayi, cikin rawar murya su amrah suka bude baki tare da gaishesa, ba Wanda ya amsawa a cikin su saima cigaba da tsakurar abincin da yayi kamar Wanda aka saka dole , kallan tahee dake tsaye ammi tayi, “daughter yanaganki a tsaye ke kuma , kisa mu waje ki zauna mana “ dan dago da kanta tayi kadan tare da satar kallansa ,be dena abunda yake ba hakan yasata sauke a jiyar zuciya kadan ,cikin rarrabewar murya ta furta “daman ina gyara dakine “, jinjina mata kai ammi tayi ba tare da tace komai ba ganin hakan tai saurin nufar dakin ta, da kallo su amrah suka bita dashi ko wannansu na mamakin ganinta a falon. 🫧🫧🫧🫧 KANO UMC ZHAHIR HOSPITAL Wata kyakkyawar yarinyace me matsakaicin kyau zaune kan daya daga cikin kujerun da aka ajje a cikin dakin asibitin, sosai ta zubawa Wanda ke kwance akan gadon ido, kafun ta fara share hawa yan da suka tarar mata a ido, cikin sanyin murya ta soma magana “Allah sarki ummu na ,Allah ya jikanki da rahma”, bata kammala zancan nata ba ta fashe da kuma me cikin rai, tana cikin kukan ne tashi alamun taba kofa , cikin sauri ta goge hawayen da suke zubo mata kafun ta kakalo murmushi a fuskarta, sallama nurse din tayi mata kafin maza wani matashin saurayi ya shigo dakin bayan sa kuma wani kamilllan dattijo ne , drip din da ya kare nurse din ta cire ,cikin girmamawa ta kalli dattijon nan, “insha Allahu ta kusa farkawa a ko Wana irin lokaci “,jinjina mata kai dattijon yayi kafun matashin saurayin gefensa yayi mata godiya, murmushi ta sakar masa tare da barin dakin bayan ta kwashe abin drip din data cire, kujerar da budurwarnan take Kai ta mike tare da sakar wa dattijon nan murmushi “Daddy ga waje ka zauna”, binta yayi da kallo kafun ya sakar mata murmushi shima “nagode daughter” cikin takun dattakon ya karasa tare da zama kan kujerar, kallanta matashin saurayin nayi tare da hararar ta cikin tsokana yace “daman nasan yanxu ba kya sona , harda dauke kai kamar ma bakisan dani ba”dariya matashiyar yarinyar tayi “sorry yaya khaleed , kaima kasan inayinka over “, wani hararar ya je famata “daga baya kenan”, yana gama fadar Haka suka karasa gaban gadon ,cikin tausaya wa yarinyar ta kalli mahaifin nata” daddy Yaushe zata farka” wani murmushin dattijon ya saki, kafun ya bude bakinsa yayi magana hannun ta ya soma motsawa kadan kadan,kafin a hankali ta fara bude idanuwanta ganin hasken da ya haska mata ido sosai ne yasata rintse idanuwan kafun ta kuma budewa hawaye na bin fuskarta, duk zuba mata ido sukai suna kallanta,”taheer!!taheera”, shine sunan da kawai take nana tawa , kallan matashiyar budurwar mahaifinta yayi kafun ya kira sunanta “zahra” cikin Sauri ta amsa da “na’am dady” kallan matar yayi kafun ya kalleta, “tai maka mata”, yanxun ma cikin sauri ta amsa “toh dady”, karasawa inda take tayi ganin ta na kokarin tashi zauna ne yasa ta temaka mata,tunda ta zauna bata ce komai ba sai bin yan dakin da tayi da kallo,duk abunda ya farune ya shiga dawo mata kai cikin sauri ta zabura “taheer “ shine sunan da ta fada tana kokarin sakkowa kasa, kallan ta mutuminnan yayi kafun ya dauke idanuwansa,cikin sanyin murya ya furta “kiyi hakuri kici abinci tukunna inyaso sai muyi magana “katsetsi oumma tayi tana fashewa da kuka “bazan iya ba, ina taheer dina yake , inaso na san halin da yake ciki, su wanene ku, me nake yi a nan wajan”, kallanta mutumin yayi kafun ya soma magana cikin kamilalliyar muryarsa “ kiyi hakuri ,mune wayanda muka kadeki sati biyu da suka wuce , sannan muka kawo ki asibiti sai yanxu Allah yasa kika farka”, waro idanuwa oumma tayi “sati biyu” ta fada cikin rawar murya “kuna nufin satina biyu a asibitin “gyada mata kai mutumin kawai yayi, fashewa da kuka oumma tayi “shikenan na rasashi “, ta kara fashewa da wani saban kukan, kallan ta mutuminnan yayi idan bazaki damu ba zaki iya sanar damu wacece ke , me ya fito dake cikin dare ,naji kina maganar sunan wani da alama wani makusancinki kike Nema “, girgiza kai oumma tayi har yanxu hawayen basu dena zubaba,”zan baku labari na, sannan ina rokon ku da kumayar dani inda kuka dakko ni sabida na nemo yarona”, jinjina mata kai dattijon yayi, yayinda mace da namijin suka samu waje suka zauna suma suna binta da kallo ganin yadda take kuka ,” sunana maryam ni haifaffiyar buzuwace, ‘ya’yana biyu taheer da taheera,mijina Allah yayi masa rasuwa…………..” tundaga farkon labarin ta zuwa karshe sai da oumma ta basu tare da dalilinta na fitowa waje,sosai zahra take kuka shima saurayin da aka kira da khaleed shima sai da ya goge kwalla a idanuwansa , sosai suka tausaya mata, gyaran murya mutuminnan yayi “tabbas labarinki abin a tausaya miki ne, Insha Allahu shima yaron naki zamu binciko miki shi da yar dar Allah, amma kafin nan zansa a baki sallama sai muce gidana gabaki daya in kin yadda damu, ni sunana Alhaji kabeer mai zamani, ga babban d’ana sunansa khaleed , sai autata sunanta zahra, mahaifiyarsu kuma Allah yayi mata rasuwa, ina fatan zaki amince”, shiru oumma tayi kamar me tunani ganin bata da wani zabine yasa ta amince musu ko ba komai zuciyarta ta kwanta da su”, sosai zahra dake sharan kwalla yin farin ciki har hakan ya bawa mahaifinta mamaki, ba a dau dogon lokaci ba aka rubuta musu sallama ganin wanda ya bada umarnin sallamar, cikin kankanin lokaci suka kama hanyar nasarawa G.R.A dake Garin kano. 🫧🫧🫧🫧🫧 Sosai ya ci abincin yanaci yana babbata fuskarsa, yan matan falon sai faman satar kallansa suke ta kasn ido ganin ammi na zaune a falon , kallo daya yayi musu duk suka mike , kallansu ammi tayi, “sai ina kuma “ cikin sauri suka hada baki “ammi daman zamu je wajan abeey ne “ kallan ammi kawai tayi tare da girgiza kai , suna gita ta kallesa tare da hararansa “ka kyauta da ka koresu” bai ce komai ba lumshe mata idanuwa da yayi tare da mike wa cikin takunsa ya zauna akan kujerar da take ,kansa ya dora akan kafadunta yana lumshe idanuwa, murmushi tasaki tare da zura hannunta cikin lallausan gashin kansa tana masa tausa a hankali “ka rage hade fuskarta nan son , kullum inasan ganinka cikin farinciki kamar yadda nasan ka a baya banasan rashin fara’arka” ta karashe zance cikin karyewar murya , saurin mikewa yayi tare da kamo hannunta,”am sorry ammi na” daga nan bai kara cewa komai ba sai mama tsa mata hannun da yake a hankali, ganin bayasan hirarne yasa ta dakko wani zancen daban, sun dau dogon lokaci suna hirar duk da rabin hirar ammi ce keyi kafin yayi mata sallama, direct part din ummey ya nufa , be wani jima a ciki ba sabida be saba zama ba yana gaisheta ya fito daga part din tare da nufar part dinsa. 🫧🫧🫧🫧🫧 YOLA “Aikin ku na kan gangara, baku da dogon lokaci wajan cikar ragowar burinku, watanni biyu ne sukai muku saura ku tabbata kun kawo jininsa,karkuyi saken da Jini biyu zasu hadu waje daya, kuna gab da tafka babban kuskure musamman idan Jini biyun nan suka kasance a waje daya “, a fusace take musu magana cikin bacin rai kafin ta dora “kun tabka babban kuskure kuyi kaggawar gyara abinda kuke kokarin batawa, baku da dogon lokaci kamar yadda kuka kawar da dan uwansa, shima ya zama muku dole Inba haka ba za kuyi kuka da kanku”tana kammala zan centa ta bace bat kamar bata taba wanzuwa ba. Ba Wanda bai razana da maganganun ta ba duk da kasancewar fuskokinsu a rufe yake babu alamar da za a gane mu su wanene, wani mutumine ya soma magana “tabbas yanxu ne ya kamata mu fara aiwatar da shirin mu, duniya ta muce dole mu mulki mutanan duniyar, dukiyar NAHYAN mallakinmuce dole mu karar da tsantsan su”…… Comment and share Mss Lee 💖💖 Masu comment ina Godiya….. ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 ( a heart touching love story ) Story & written By Mss Lee 💖 PAID BOOK Mea bukatar complete din gidan aunty yayimun magana ta wannan number 07041879581 BOOK 1 Free page 24 and 25 🦋 “Tabbas yanxune ya kamata mu cika kudirin mu”,cewar d’aya daga cikin su me sanye da jajayan kaya a jikinta, gabaki d’ayan su maida hankalin su sukai kan daya daga cikinsu wacce take kishingide tun d’azu bata motsaba, tashi tsaye tayi tana kurban wani dan abu cikin wani Kofi me kayatarwa,duk da ba a iya ganin ko wacece cikin kausashshiyar murya ta soma magana rai a bace “bazan taba laminta ba , ginin da na soma tunda dad’ewa babu wani hamshakin daya isa ya rushe munshi”,duk hada baki suwai wajan cewa “tabbas maganar ki gaskiya ce abar kauna “,suka gamawa suka fara surutunsu cikin wani yare kafin su had’a kofunansu waje d’aya alamaun cheers . ****** KANO Kasantuwar akwai tazara tsakanin UMC da nasarawa hakan yasa saida suka danyi doguwar tafiya kafun su karaso Layin nasu, Kai tsaye daya daga cikin manyan gidajen dake Layin khaleed ya nufa,yayinda Alhaji kabeer yake zaune a dayan side din, zahra da oumma suna baya,tun bayan shigarta motar ta dukar dakanta kasa ,lokaci zuwa lokaci tana share hawayen da ke taran mata a ido, duk akan idon Alhaji kabeer da lokaci zuwa lokaci ya kan kalleta ta mudi bi, itama zahra nagefe ta zuba tagumi sosai take jin tausayin oumma da labarin ta, “ya kamannin taheer da taheeran suke “,tunda yan biyu ne zanzo naga kamanninsu nasan za’ayi kyawawa musamman yadda oummansu take da kyawu itama kamar wata balarabiya, tunanin da ke yi mata yawo akai kenan har su ka karaso gidan bata sani ba, horn khaleed yayi wani katan soja dake ganin gate din gidan ya bude tare da sara musu, babban gida ne Wanda ya hadu iya haduwa da kayan alatu komai na more rayuwa akwai a gidan, parking khaleed yayi a parking space,tare da futo wa ya bude wa mahaifinsa kofa,itama zahran futowa tayi har lokacin oumma kanta na sunkuye batasan an tsaya ba sai da zahra ta tabata,dago da kyawawan idanuwanta da suka sauya tayi tare da sakar wa zahra guntun murmushi,”nagode “,murmushi zahra tayi mata tare da bude mata kofar, fitowa oumma tayi tana bin katan gidan da kallo kafun ta sunkuyar da kanta ganin ta hada ido da Wanda yace mata sunansa Alhaji kabeer,murmushin manya Alhaji kabeer ya saki kafun yace “Bismillah “ya karasa da nufar inda zai sadashi da cikin gidan,”oumma Bismillah “ cewar khaleed da ke gefen ta ,saurin dago da idanuwanta tayi jin sunan da ya kirata da shi kafun ta soma tafiya cikin sanyin jiki zahra na binsu a baya, a cikin kyataccan falon gidan suka tsaya,sosai falon ya hadu iya haduwa, ba wani tarkacene aciki ba amma sosai ya hadu,kallan zahra Alhaji kabeer yayi “daughter kaita masauki ta dan huta” sosai zahra ta murmusa “to dady”kafun ta dauki magun mugun oumma ,kallan oumma tayi haryanxu da murmushin nan akan fuskarta” oumma bari na kaiki dakin da zaki hutu”,itama oumma dan murmushi ta sakarmata tana jinjina karamci irin na mutanan gidan duk da kallo daya zaka musu kasan masu arziki ne amma basu wulakanta taba. Wani dan corridor suka mi’ka kadan ya Kawosu wasu ‘kofofi dake kallan na junansu,kofar karshe zahra ta bude mata , babban d’a kine a wajan,gadone me fadi sai wardrobe ,komai na set d’in gado a kwai a dakin brown colour , murmushi zahra ta sakar mata “oumma Bismillah “ jinjina mata kai oumma tayi , a sanyaye ta furta “nagode”. 🫧🫧🫧🫧🫧🫧 Sanye take cikin maroon d’in abaya A shape,kayan sosai ya fito da shape din jikinta, cikakken gashin kanta ya fito sosai ta gefe gefen kanta da ya kwanta,kwance take kan 3 sitter din falon ammi tana bacci cikin kwanciyar hankali, zoya ce ta shigo falon itama cikin shigar ta sa’banin tahee ita kananan kayane a jikinta bink colour Riga da wando, kanta sanye da pink din hula itama gashin go shin ta sosai ya fito, gashin d’awisun da ta zo nunawa tahee take ta faman wasa dashi harta nufa hanyar dakin taheen sai kuma ta jiyo ganin ta kwance tana bacci, saurin rufe bakinta tayi tana dariya kasa kasa kafun ta salallabo a hankali ta nufi inda taheen take, gashin d’awisun ta dauka ta somayiwa tahee tafiyar tsutsa a tafin kafarta, motsa kafan kadan tahee tayi kafun ta gyara wanciyarta, kara sa mata gashin zoya tayi nan ma motsa kafar tata tayi a hankali tana ya mutsa fuska,ganin hakan yasa zoya cigaba da sa mata d’awisun, cikin sauri tahee ta farka har dan kwalinta na zamewa, sosai zoya ta fashe da dariya ganin yadda tahee ta ‘bata fuskarta, itama tahee ganin zoya yasa ta mike da niyar kamota,sauri kaucewa zoya tayi tana dariya, ganin hakan yasa tahee binta da sauri, gudu zoya ta sa tana dariya tare da komawa bayan kujera, ganin hakan yasa tahee binta da gudu har dankwalin kanta ya faduwa kasa, bata damu da faduwar da yayi ba ta cigaba da bin zoya da niyar kamota ,itama zoyan ta ki bari ta kamota sai zillewa take tana mata dariya, ganin hakan yasa tahee sakin duk karfin ta ta biyo zoya da ta nufi hanyar fita da gudu gashin kanta sai faman lilo yake a bayanta, karan da tayi da abune yasata yin baya baya kamar zata fadi , batasan lokacin da ta fado kansa ba,sai daddad’an kamshin da ya cika mata hanci , da sauri ta wayo idanuwanta waje “na shiga uku ni tahee, kullum sai kinyi lefi”, saurin sunkuyar da kanta kasa tayi tare da soma wasa da yan yatsunka, dai dai ta bude baki da niyar yin magana taji an capko dogon gashin kanta me shegen sanshi da daukar ido, tanbayar da ya jefo Matane yasata zare ido “ are you a non-Muslim da zakiyi Karin gashi a kanki” ya karasa zancen nasa da sauke idanuwanka kan gashin nata, sosai sukai masa dadin a tafin hannu musamman yadda suke kyalli amma a zahiri sai kara hade fuskarsa da yayi, “ni ban kara komai ba” ta fada muryarta na rawa rawa kamar me tsoran wani abu, kara damke kan nata yayi a hannunsa da karfi,sosai taji zafin yadda ya damki gashin nata ,bata san lokacin da dora hannunta kan nasa ba tana rintse idanuwanta, hawaye ne suka fara zubo mata cikin rawar murya ta soma magana “ka..kayi hakuri”, pink lips dinta dake motsawa a hankali ya zubawa idanuwa kusan minti daya ganin tana kokarin bude idanuwan yayi sauri hankad’a ta tafadi a kasa, amaimakon yashiga cikin falon sai ya bar falon gabaki daya, bin bayansa da kallo tahee tayi tana hararar iska ,”arrogant kawai “ta fada cikin sauri kafun ta toshe bakin ta gudun kar wani yaji, mikewa tayi a hankali “ke kuma zan kamakii, sabida kisan halin kayanki shiyasa kika gudu ni kuma aka Huce akai na thank god be ganki ba”ta karasa maganar tana sakin murmushi kasa kasa tare da shafa gashin kanta “wai gashin doki”wani murmushin ta saki tunano kalamansa, lokaci d’aya kuma duk fara’ar fuskarta ta dauke tuno oumma da taheer da tayi, yau kusan sati biyu basuyi waya ba, tunanin hakan yasa ta fara tunanin yadda zata yi Waja da su wajan ammi. 4:30 ammi ce ta shigo falon bakin ta dauke da sallama , har yanxu murmushin fuskarta be ‘boyuba, kallan tahee da ke zaune ita kadai tayi, “sorry daughter na barki ke kadai “, itama murmushi tahee ta sakar mata “sannu da zuwa ammi”saida ta zauna tukun na ta amsa mata, mikewa tahee tayi da nufar kitchen bata dade ba ta fito dauke da kara min tray, lemone a ciki masu sanyi gefe guda kuma kayan fruit ne cikin wa ni dan bwol, glass cup din dake kai tahee ta dauka da niyar zuba mata kunun ayar ammi tayi saurin Girgiza mata kai “no daughter ban dade da Shan ruwana ba , bani fruit din nasha “, bata ce komai ba ta ajje cup din tare da miko mata fruit din “nagode “shine abunda tace, murmushi tahee ta sakar mata batare da ta ce komai ba , kallan ta ammi tayi sau daya kafun ta dauki banana , sai da ta kammala cin bananar kafun ta dauki wayanta, dan danne danne tayi kafun ta dora wayan a kunne ,kusan sau uku tana hakan kafun ta kalli tahee, “yau 3 days ina gwada number yaya amma bata shiga, kiyi hakuri zan kara gwada zuwa anjima sai ku gaisa nasan kinyi kewarsu “sauke ajiyar zuciya tahee tayi lokaci daya jikinta yayi sanyi dan tunda tazo ammi take kyautata mata kamar yar cikin da ta haifa, kauda maganar tayi ta hanyar sa wata jiran, sun dade suna hiran su cikin raha lokaci zuwa lokaci ammi na kara wayarta a kunne , kiran sallahn magariba ne ya tayar dasu ,ita ta nufi sama tahee Kuma ta nufi dakin ta, tun jiya take jin wani iri kamar period dinta zaizo, koda tayo alwala sai da ta duba tukunna kafun ta fito, sallahr magariba tayi bata tashi a Wajan ba har saida tayi sallahr isha bayan karatun alkuranin datayi, yau akan daddumar bacci ya dauke ta lokacin da take karatun azkar dinta. Karfe 6:10am na safe tahee ta farka sabida ciwon maran da ta soma , sosai kafarta ta dama take mata ciwo, ban daki ta shiga domin gyara jikin ta ganin har yanxu period din be zo bane yasata yin sallah, kafarta sai faman ciwo take , asabe ce ta kwankwasa kofar daman shigo tahee ta bata sai faman yatsina fuska take, breakfast ta kawo mata yau ko hirar da suke batai ba bayan ta amsa tayi kwanciyar ta , fita asabe tayi bayan ta mata sallama tana mamakin ta, ganin ta fitane yasa tahee mikewa tare da nufar abincin, kadan tashi ta tashi aguje ta nufi ban daki, duk abunda taci saida ta amayo dashi, jikinta sosai yake mata ciwo, wanka tayi da kyar tare da saka dogon hijabi Sabida sanyin da ta keji,ko da ta fito falo bata tarar da kowa ba , ganin hakan yasa itama bata zauna ba ta nufi part din dada, tunda ta doshi hanyar zuciyar ta ke tsinkewa bata san dalilin hakan ba, ta dora kafar da niyar shiga kenan taji kukan ammi” BA’ASAN INDA SUKE BA ,DAGA ITA HAR TAHEER DIN ANNE MESU AN RASA ABUNKURE “ kalaman da suka shiga kunnanta kenan, bata san lokacin da ta kwalla kara da karfin gaske ba , kafarta da ke step na biyar ya gurde ta fado kasa Tim kanta ya bugu da jikin step din, sosai Jini ya barke mata akasan ta , kanta da ya buguma sosai yake zubar da jini , da gudun gaske sukayo kanta , tun lokacin da ta saki karar nan, ganin tahee Baje a kasan yasa hankulansu kara tashi kowa fatan da yake Allah yasa bataji me ake tattaunawa ba, wani saban kuka ammi ta saki, kaka ma ganin halin da tahee take yasata sakin nata kukan “shikenan ta faru ta kare”abunda dada ke fadan fada kenan , ummey da abeey sukai dauriyar dagowa, ganin yadda jikinta yasaki ne yasa dada sakin wani kukan” wai ina sadaukine ba bokan turai bane yazo ya dubamana amanar Allah”kallan abey dada tayi cikin fada fada ta soma magana me kuke jirane ku kira sadauki ya dubata duk kunbi kun tsare ta da itanuwa “ ta kara zancen nata da kallon su uncle salim da suka karaso suda iyalansu, sosai hankalin yan gidan ya tashi, “amma dada me zea hana a tafi asibiti kawai tunda nasan ba za a rasa king acan va” kwallar da ta zubo mata ta share maza zayed dauketa mu tafi asibitin kuma sai ku biyo bayan mu “da Sauri ammi ta mike ganin harsun nufi mota, baya ummey tashiga sai dada da tahee dake tsakiyarsu ba alamun rai , yayin da gaban motan kuma dr zayed ne da kansa zai tuka motar ammi na gefan sa, da gudun gaske suka bar gidan ganin haka yasa motoci biyu na sojoji bin bayansu, suma sauran yan gidan shiga mota sukai da bin bayansu sojoji ne take musu, aunty kawai aka bari datace ta zata taso amrah sai su taho tare, ba Wanda yace mata kala har suka taho asibitin. Koda su dada suka shigo asibitin da gudu sojojin nan suka zagayesu kowa duk Wanda yazo wucewa sai ya kallesu, kara dialing number king abey yayi akaro na ba adadi, yanxu ma kara kiran yayi not rechable Daidai lokacin da wasu manyan likitocin asibitin suka karaso da gadon daukar mara lapiya , inda take abeey ya nuna musu, daya daga cikin doctor dinne ya bude motar da niyar dakko ta, Daidai lokacin da motar king ta sharo da gudun gaske,Kai tsaye inda su abey suke zaki ya nufa, suna ganinsa suka sauke a jiyar zuciya yau da kanshi ya bude kofar ya fito tare da nufarsu,ganin su gabaki d’aya a wajan ne yasa ya maida hankali kan abeey” what happen “ ya fada a kasalance, kasa yi masa magana sukai sai bayan Botar da suke nuna masa , a hankali ya bude kofar wacce ya ganine yasa shi dan ja baya kafun cikin azama ya shige cikin kotar, ganin yadda jikinta ya baci da jinine yasashi rintse ido kafin ya dauke ka kamar yar baby a jikinsa , ko gadon da aka dakko be kalla ba ya nufa da ita ciki cikin sassafa, kowa na wajan binsa da kallo yayi amma ba bakin magana hatta ma’aikatan wajan kowa sai satar kallonsa suke, sau daya ya kalli doctor din gefansa , “doctor halima” yana gama fadar Hakan ya shige lifter tare da barin yan gidan , direct office dinsa ya nufa da ita duk jikinsa shima ya baci, cikin few minutes sai ga wata doctor mace tazo lokacin da yake mata dressing din ciwon kan nata, sau daya ya kalleta be ce mata komai ba ya dauki tahee yanxun ma cikin sassarfa ya nufi wani door da ita, itama ma doctor haliman cikin Sauri tabi bayansa bayan ta kirawo wasu nurse, duk ragowar likitoci tsayawa sukai suna tsoran shiga theatre din ganin be nemesu ba kowa ya koma gaban aikinshi, kusan hour daya da rabi ya fito daga cikin theater din, kallansa abeey yayi cikin damuwa “ yaya jikin nata “ duk zuba masa ido yan gidan sukai suna jiran amsarta sa “ sai ta farka tukunna” ya karashe zancan nasa da kallon ammi da yake jin kukanta har zuciya, muryar abeey ce ta Katse masa tunaninsa” zamu iya shiga” jin jina masa kai king Kawai yayi sabida ciwon kan da yake ji, wani baban daki aka kaisu inda aka kwantar da ita, sosai Wajan yake da girma kamar ba asibiti ba, kwance take kan gadon sanye da kayan marasa lapiya , kanta nannade da bandage sai drip din da aka sa mata, sosai fuskarta tayi fiyau da ita ga wani kyau data kara jikin ta kamar babu Jini a jiki, ko wannansu kallanta yake cikin tausaya wa hatta summy da bata santa saida ta zubar mata da hawaye, sun dade zaune a asibitin har wjan 2 na rana kafun abeey ya bada umarnin su koma gida yayi saura daga dada sai ummey saishi ,uncle Saleem da uncle musaddiq kuma suka tafi tare dasu, shima abeey office din king ya nufa cikin rashin sa’a ya tarar da office din a kulle, ganin ana kiraye Kirayen sallane Ysa abeey ya nufi masallaci koda aka idar da sallan be koma ciki ba sai da yayi la’asar. Koda ya koma cikin tashin hankali ya samesu ganin yadda tahee ta cire drip din hannunta sai kuka take , duk Wanda yayi yun kurin tabata sai ta buga masa wani abu, gabaki d’aya doctor din tsaya wa sukai suka su ammi kuka suka saka ganin halin da take ciki, zuyawa yayi da niyar kiran king sai gashi yashigo cikin wata shigar daban,bin dakin yayi da kallo ganin yadda ya baci, daya daga cikin nurse dince ta nufi tahee da niyar rigeta bayan ta ga Shigowar king , bata Ankara ba tahee ta buga mata abu ka , kara ta saki tana ja da baya , kuka tahee ta saka “karku tabani, su wanane ku, kumaini wajan dady na” sukenan kalaman da take, umarni king ya bawa doctors din su fice da ido kafun a hankali cikin takunsa ya nufi wajan gadon, cikin rufewar ido tahee ta dauki abu daniyar kwala masa sai kuma ta tsaya da kukan da take ta fara dariya kamar wata zautacciya, be ankara ba sai ji yayi ta rungumesa “daddy na “ shine kadai abunda tace tare da kudun dune king da ko motsi yakasa bayan rungumesan da tayi. Comment and share 😌✍️ Mss Lee 💖 ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 (a heart touching love story) Story & written By Mss Lee 💖 PAID BOOK MESAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581. BOOK 1 LAST FREE PAGE Free Page 26 and 27 🦋 “Dady na “ ta kara kira sunansa idanuwanta na zubar da hawaye, salati dada ta saki “ Innalillahi wa inna ilaihi raji’una, Allahumma a jirni fi musu bati , tahura wanene kuma dady”, dada ta fada da nufar inda tahee take , wani kukan tahee ta saka “karku tabani bana so, ku dena ta bani su wanene ku”, gabaki d’aya su abeey kasa motsi sukai sai Innalillahi da suke maimaitawa tun dasu , ammi ko tsayuwa ta kasa sai waje ta samu ta zauna ta cigaba da kukan da yazo mata.nunfashi king ya saki yana kara hade rai tare da kokarin banbareta daga jikinsa, kamar wacce ake karawa karfi haka ta kara kudun duneshi tana sakin kuka, nunfashi king ya saki me zafi , besan lokacin da ya data mata tsawa ba, sosai ta razana da tsawar da ya daka mata, hatta abeey sai da suka kallesa, kuka tahee ta fashe dashi, cikin futar hayyaci tayi kofa da niyar fita,ko karin riketa abeey yake ,wata karar tasaki “banaso banaso banaso, shima dady bayasona ,Nima banasan kowa” ta kara fashewa da kuka , cikin ta da ya murya ne yasata sakin kara tana durkushewa, a wajan tare da sakin wani saban marayan kuka tana dafe cikinta,taki bari kowa ya ta’bata sai kuka take, lumshe idanuwansa king yayi kafun a hankali ya tako inda take, jada baya ta soma tana girgiza masa kai tare da sakin wani saban kukan, be dena bin nata ba har ta jin gida da jikin bangon, tsayawa dada tayi zani a hannu tana kallan ikon Allah ,tun bayan kuka data sa mata ta buya bayan ummey dake tsaye itama , a hankali ya tsugunna a wajan kansa har ya fara sara masa, gefe tayi da kanta tana cigaba da kukanta ga ciwon cikin dake nukur kusarta sai faman rike ciki take, “kalle ni” ya furta a hankali yana binta da idanuwa,dan mitsitsin bakinta ta tabule kamar me shirin yin kuka “shhhhhh” yace mata , shirun kuwa tayi har yanxu taki dago da kanta sai hawayen dake biyo fuskarta,” me akai miki kike kuka “ ya furta a fusge kamar bashi ba, bakin ta bude daniyar kuka ya kara dakatar da ita “bana san kuka” kukai kuwa gaya dena “basu ne ba suna ta bani nace kuma sudena banaso, Kai ma bakasona ka koreni” ta karasa maganar tata tana turo dan karamin bakin ta kamar wata yar yarinya “ Wannan yarinyar Anya ba aljana bace “ ya fada a zuciyarsa, amma sabida buguwar datayi aka yasa bece mata komai ba, “toh shikenan mun dena , suma bazasu ta baki ba”, da sauri ta kallesa tana share hawayen fuskar tata, “dady da gaske kake”,girgiza mata kai yayi kawai ba tare da yace mata komai ba, da sauri ta fada jikinsa tana kara dukun kune shi” dady banasan su na tabani kaji”,be ce komai ba sai lips dinsa da ya datse “ dady ! You killed me “ ya fada a zuciyar sa , ganin ta fara kuka kasa kasa ne yasa ya kalleta, be auneba ta fashe masa da kuka, “dady cikina, cikina” ta fada tana rike cikin nata, kasan cewar yasan dalilin ciwon cikin nata yasa be ce komai ba , ya dauketa tare da barin dakin a hannunsa kamar wata yar baby, bin bayansu da kallo su dada sukai, kafun ta sauke a jiyar zuciya, kallan su ummey tayi” mude mun shiga uku, yanxu kenan sadauki yazama Baban ta, ku kalla fa , wai bata san muba “ babu Wanda ya kulata harta gama surutun ta kowa da abunda yake sa’kawa a ransa. 🫧🫧🫧🫧🫧 Tunda aunty ta koma part din ta tsabar murna bata bata sanar wa da amrah da bata falon komai va, yayarta da ta haifi amrah ta kirawo, “yar uwa rabun jiki, Al bishirinki “ banji amsar da aka bata ba sai dariyar da aunty ta saka “uhmmm tsinanniyar can ai ta mutu, yanxu aikin mu zaizo cikin sauki daman “ gabaki d’aya yadda ta ga taheen sai da ta sanar wa yar uwar tata suna yi suna dariyar farin ciki , tana gama wayar tata takirawo aminiyarta, bata jira komai ba ta nufi dakinta cikin kasa kasa da murya ta sanar da ita Abunda ke faruwa,banji me akace mata ba Amma sosai ta nutsu tana saurarar kawar tata , wata dariyar mugunta aunty ta Saki “ bar shashashu , a tunaninsa ina yin duk wannan abun sabida su, Kema kinsan wacece ni , ina gama an fani dasu zan zubar dasu”, kara kyalkyalewa tayi da dariya, sun dan jima suna wayan kafun ta kashe kiran. ******* wayace kare a kunnan amrah , sosai ta nutsu tana sauraran abunda ake ce mata, fuskarta dauke da yalwataccen murmushi, ta dauki dogon lokaci taba wayan kafun ta kashe , dariya ta saki sosai saida tayi me Isarta sannan ta tsaya “ Lalle yarinya da dani zakice zaki taka, cikin sauki na gama dake saura aunty inma in ta kammala mun aikin” ta karashe zan can nata tana sakin dariyar mugunta harda rike ciki, ta dade a hakan sai ga aunty ta shigo itama dakin, duk abunda ya farun saida auntyn ta sanar da ita, nunawa tayi kamar batasan anyi ba, ta kara shiga cikin murna dan tabbatar da zancan mahaifiyarta, tsabar murna har wata kwarya kwaryan liyafa suka hadawa kansu ko tunanin su duba a asibiti ba sayi , duk a tunaninsu ta mutu. 🫧🫧🫧🫧 Direct office dinsa ya nufa da ita sai faman kuka take masa, baice komai ba sai ajjeta da yayi cikin wani bedroom me kamar daki komai nacikin daki akwai a ciki ga wasu na urori dake dakin kamar ba cikin asibiti ba, murkususun ta cigaba dayi tana kiran “dady !! Dady”, kallanta yayi yana lumshe idanuwansa da suka fara gajiya sabida ciwon kan da yake ,kafun ya karaso a hankali inda take, wasu injection ya hada tare da nufar inda take, tana ganin injection dinnan ta kara sakin wani saban kukan, tana girgiza masa kai “banaso , banaso” be kulata ba har ya karaso wajan , a guje ta mike duk da ciwon dake cinta ta saka kafa zata gudu, taku daya yayi ya rike damtsen hannunta, kuka ta saka masa tana kokarin kwace hannunta da ya rike , ganin allurar hannunsa yasa taci gaba da kokarin guduwan, sosai tasaka iya karfinta tana san kwace wa , kwakkwaran riko daya yayi mata tare da zaunar da ita kan gadon har lokacin kuka take, alkuran ya ajje abayansa tare da kallonta “na fasa to, yimun shiru”, kallan hannunsa tayi ganin babu alluran yasa lokaci d’aya kukan nata ya tafi, jingina tayi da jikinsa tana dan turo baki , be ce mata komai ba har kusan minti daya tana wasa da abun rigarta, allurar da taji ya tsira matane yasata sakin kara da niyar mikewa, sosai ya riketa kwakkwaran motsi ta kasa harsaida ya kammala allurar tasa, hade rai yayi sosai kamar bashi ba , cikin kausashshiyar murya ya firta “yi mun shiru” tsit kuwa kukan nata ya dauke sai karamin lips dinta da take turo masa , tsawan lokaci suna a haka lokaci zuwa lokaci yakan dago da idanuwansa , jim kadan ya kara dago da idanuwan nasa yaga ta fara bacci, ajiyar zuciya ya sauke kadan” am dead “ ya furta kawai kafun ya dakko wasu na ura, sosai yayi bincike akan ta bayan Wanda yayi mata lokacin dressing , nunfashi ya fesar ganin kiran abeey, be dau dogon lokaci ba ya dauki kiran ,”kana ina “shine kadai abunda abeey yace masa, “office “ king ya furta tare da lumshe idanuwansa kamar abeey na kallonsa, ko minti biyar cikakkiya abeey beyi ba ya shigo office din, inda tahee take kwance ya kalla tare da girgiza kansa, “me ya sameta” ya kara tanbayar king din” she lost her memory abeey” da sauri abeey ya kallesa tare da furta Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ganin hakan yasa king ya mike daga inda yake tare da nufar abeey din,” please abeey karka tayar min da hankali , kasan ba lapiya Kake dashi ba please abeey “, zuciyarsa abeey ya dafa tare da dafe kan sa, rikosa sosai king yayi duk da yanayin tashin hankalin da ya shiga amma a fuska ba alamun hakan, dago da idanuwansa abeey yayi da suka fara jaa alamun ciwon sa zai tashi,”kayi mun alkawari guda daya” kallansa king yayi da lumsassun idanuwansa, sosai abeey ya kara dafe zuciyarsa “KAMUN ALKAWARI ZAKA AURETA YAU DINNAN “. Comment and share ✍️ Mss Lee 💖 Alhamdulillah yau na kawo karshen free pages dina , mea san cigaba da gidan aunty zai turo kudin sa fa wnn asusun 7041879581 palm pay Ayshatou galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581. Masu comment ina Godiya 💖🫶. 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 ( a heart touching love story) Story & written By Mss Lee 💖 PAID BOOK MAISAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581 BOOK 1 BONUS PAGE 28 and 29🦋 2 page ne na hade muku🫶. “IMPOSSIBLE “cewar king da idanuwansa suka fara canza launi,cikin bacin rai, be bari abeey ya kara magana ba cikin sarkewa,” how on earth abeey zakace na auri wannan yarinyar, as small as she is, yarinyar da in da Auran wuri nayi zan haifeta, please abeey mana I can’t marry her,never”, cikin sauri abeey ya kallesa ganin yadda idanuwansa suka fara canza kala ,yasan ransa ba karamun baci yayi ba Amma shima ba yadda zayyi tunda babu Wanda yake wucewa kaddarar sa,”bazaka iya aurantaba kake fadamun” abeey ya fada azafafe, “yes I can’t marry her ,and I will never “cikin bacin rai abeey ya mike tsaye, “shikenan kaje Kayi duk yadda kaga yayi maka tunda ban isa da Kai ba,yau ni ka kewa musu akan abunda na umarceka dashi, nagode sosai, Allah yajikan dan uwanka Muhammad nasan da yana raye da shine zaimun wannan alfarmar ya aureta”ya karasa a raunane , cikin sauri king ya dago da idanuwansa jin sunan da abeey yakira,”abeey” yakirawo sunansa a sanyaye, daga masa hannu abeey yayi “bana bukatar jin komai daga bakinka, kaje kayi duk yadda kakeso”, yana gama fadar hakan ya kama hanyar fita, jiri ne ya d’ebesa zai fadi cikin zafin nama king ya riko hannunsa tare da zaunar dashi, kara tashi abeey yayi wani jirin na kokarin ka yadda shi,”bana bukatar temakonka “, rintse idanuwansa king yayi, cikin sanyin murya ya furta “am sorry abeey, please ka zauna”be kulashiba sai ma kokarin tafiya da yayi “ Dan Allah “ king ya kara fada kamar Wanda nunfashinsa zai fita daga gangan jikinsa, kallansa abeey yayi duk da tsananin tausayinsa da yakeji a kasan zuciyarsa, azahiri kuwa hade ransa yayi shima, waje ya samu ya zauna , “am sorry abeey” king ya kara fada har yanxu idanuwansa na kasa,”ba fushi nake da kai ba,amma inaso ka tuna halin da amminka zata shiga, da me kake so taji da rashin ganeta da yarinyar bata yiba ko da rashin temakonta da zakayi,karka manta kai me temakon Al’umma ne, meyasa bazaka tausayawa rayuwar yarinyar nan ba ,sanadiyyar rashin mahaifiyarta da d’an uwanta tashiga wannan halin, kayi tunani inda nine..” be bari abeey ya karasa zancan nasa ba king ya soma magana” zan aureta amma da sharadi” da sauri abeey ya kallesa murmushi na kokarin su’buce masa,abunda bai taba tsanmanin jiba daga garesaba, bai kalli abeey ba yaci gaba”maganar yan uwanta zan sa a bincika,I will marry her just for her condition, idan memory dinta ya dawo zan saketa “ kallansa abeey yayi jin ya anbaci saki, amma be ce masa komai ba,yanxun ma be kalli abeey ba,”and it has to be a secret marriage,wannan ba aure bane temakone kawai data warke zan sauwake mata” yana gama fadar hakan ya kalli abeey, shima har yanxu abeey din shi yake kallo” na amince” abeey ya furta yana sauke ajiyar zuciya. Be kuma kallan abeey ba ya mike tare da shigewa toilet , da kallo abeey ya bishi yana girgixa kai, kafun ya mike tare da fita daga dakin, tunda ya shiga toilet ba abunda yayi sai jin gina kansa da yayi da kofar toilet din, sosai kansa yake sara masa,sink ya kunna,a hankali yake watsawa fuskarsa ruwa, ya dau godon lokaci a haka kafun ya fara sauke a jiyar zuciya, karar da ya Jine yasa shi bude idanuwansa da Sauri tare da barin toilet din, kwance take a inda ya barta , jikinta sai faman karkarwa yake, kara sakin wani karan tayi,”ze tura ta, ze turata “ shine abunda bakinta yake faman furtawa,a hankali ya karasa wajan tare da dora hannunsa kan goshinta, a matukar razane ta farka ,”Zee.. turata…. Zeee turata ,mugune shi” ta furta tana kokarin barin gadon, ganin yadda ta fita a hayyacin tane yasashi rike dan tsan hannunta, ture hannusan ta shiga kokarin yi, ganin ta kasa kwacewa ne yasata fashe cewa da kuka, “ze tureta “ ta kara furtawa, “shhhh” ya furta mata, bata kulawa ba sai kokarin kwacewa da take , tsawar da ya daka matane yasata hadiye kukan nata tana girgiza masa kai hawaye na futo wa daga idanuwanta,”zauna “ ya furta mata tare da sakinta, can nesa dashi ta zauna tana takurewa waje daya, yadda tayine yasa shi kallonta,”ya Allah “ ya furta kafun ya mike ahankali da nufar inda take, zama yayi daga gefen ta kadan , ganin tana kokarin ja da baya ne yasa shi kallanta “me ya faru”,lan gwabar masa da kai tayi tana turo baki, idanuwanta duk sun Tara kwalla, yadda tayi da fuskar ta tane yasa ya zuba mata idanuwa,kusan tsawan mintuna biyu yana kallan kyakkyawan fuskarta , ganin ta motsane ya sashi dauke idanuwansa,da sauri tahee ta kallesa “daddy na”ta karasa kwallar data tarar mata yana zubo mata, be ce Mata komai ba sai kallanta da yayi “mugune shi zai turata fa” zuwa lokacin harta fara shash sheka ,”it’s ok karkiyi kuka “ ya furta kamar wadda akasa dole , kara turo bakinta tayi gaba zata sake magana ya dakatar da ita,” yanxu zan tanbayeki, ki bani amsa kinji” gyada masa kai tayi kamar wata yarinyar, dafe goshinsa king yayi yana taunar le’be,” yaya sunan ki” ya furta a hankali,”shiru tayi kamar me tunani sai kuma ta washe fararan jerarrun hakoranta,”dady” ta furta tana tafa hannayenta, ya tsawa kallanta yayi “bani ba , sunanki na tanbayeki”, yanxun ma kara turo bakinta tayi,”sunana dady”,jinjina mata kai yayi batare da yace mata komai ba “dady”ya furta a kasan zuciyarsa,”I have a lot to do kafun na sake ki, I will try my best hankalinki ya dawo before I divorced you “, mikewa tsaye yayi ganin lokaci na tafiya, wasu magunguna ya dauka tare da allurai yasasu cikin wata bag kafun ya kalle ta,”Taso mu tafi” kamar jira take ,cikin sauri ta mike ta karaso inda yake , hannunsa ta rike gam kamar wacce za’a kwacewa ,be ce mata komai ba suka nufa barin office din, tunda taga sojojin dake ganin wajan jikinta ya fara rawa ta kara kankame hannunsa sai faman buya take a bayansa,zaki ne ya karaso wajan tare da sara masa, a guje ta juya daniyar guduwa cikin tsoro ganin kayan jikinsa,riko hannunta king yayi ganin ta tsorata da sojojin dake wajan, jakar hannunsa kawai ya mika wa zaki,kudun dune shi tayi tana kara buya a jikinsa,”Ya Allah” ya furta cikin zuciyarsa kafun ya fara tafiya da ita, dakin da su ammi suke ciki ya nufa, har yanxu suna a yadda ya barsu, kallo daya yayi musu tare da dauke kansa, ammin sa kawai take tunani ganin irin ramar da tayi lokaci d’aya,”tahura taho nan dada ce” dada ta fada tana miko mata hannu,kara boyewa tayi bayan king, matsowa dada tayi daniyar tabata, bata Ankara ba saiji tayi tahee ta fashe da kuka ,sallallami dada ta saka”Innalillahi wa inna ilaihi rajiun,ke yayi zafi “ dada ta fada tana sakin baki, duk kallanta su ummey sukai, itama ammin kokari take tayi magana amma ta kasa sabida yadda muryarta ta dushe, ummey ce tayi karfin halin magana”ya jikinta” kamar yadda ya fadawa abeey itama hakan ya fada mata “she lost her memory “ da sauri ta dago da idanuwanta tana fadan sunan Allah,kallanta dada tayi “yimun bayani naji yana mamori (memory)”, nunfashi ummey ta sauke kafun tayiwa dada bayani, itama dadan salati ta dauka , ammi ko jinsu batayi sai bin tahee da kallo da take, itama taheen tana bayan king tana binsu da ido ta rikesa gagam , shigowar abeey ne ya katse musu shirun su, da sallama ya shigo dakin fuskarsa dauke da yalwataccen murmushi, kallo daya yayi musu ya dauke kansa tare da kallan dada, “dada ya kamata mu goma gida ko, Inyaso sai a tattauna a can”, gyada masa kai dada tayi da Sauri”eh haka ya kamata,amma ita tahuran fa”, kallan king abeey yayi, shima king kallan yadda ta rike sa yayi kafun ya kallesu “zan taho muku da ita” abeey besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba ,be ce komai ba ya kalli dada” dada tunda zai taho da ita kinga sai mu jira su a gida “ yanxun ma kai dada ta daga masa ,dukansu mikewa sukai tare da barin dakin,har lokacin tahee na tare da king,yana ganin sun shiga lifter ya juya tare da koma wa office dinsa,suna sauka premises ba bata lokaci suka shiga motocin da aka fito dasu, manyan sojoji na biye dasu, Kai tsaye hanyar da zata sadasu da gida suka nufa. 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 KANO Tana zaune cikin dakin da zahra ta bude mata har yanxu ,so take ta rama sallolin da ke kanta amma batajin zata iyayi da kayan jikinta, tana cikin wannan tunanin taji an kwankwasa kofa,”shigo “ ta furta a sanyaye, zahra ce ta shigo cikin dakin bakinta dauke da sallama,bayanta ma khaleed ne da manyan ledoji, ledojin suka ajje mata,ko wanne fuskarsa dauke da murmushi, “oumma gashi dady yace akawo miki”kwalla ne oumma taji yana san taran mata,”nagode sosai “ ta furta musu, ganin yanayin da take cikine yasa ba Wanda yayi magana,har zahra zata bude baki khaleed yayi saurin rike hannunta” oumma bari mu baki waje ki shirya”jinjina masa kai tayi tana ajiyar zuciya, kama hannun zahra yayi tare da barin dakin,tsawan mintuna biyar tana zaune a inda suka barta ganin lokaci na tafiya ne yasa ta mike ,daya daga cikin ledojin ta bude, manshafawane da yawa a ciki da turaruka,dayan ledar kuma abayoyine da hijab a ciki, harta sa zata hannu zata bude ledar karshe sai ta fasa tare da shiga ban daki, tsawan lokaci kafun ta fito daya daga cikin abayoyin ta saka tare da kabbara sallah ganin alkibla, ta dade tana sallolinta ,har amrah ta dawo dauke da babban tray a hannunta, bata fita a dakin ba sai ma jera wa oumma kayan tayi a cikin kwabar dakin,ganin ta idarne yasa zahra dakko abinci da ta shigo dashi tare da ajje mata “oumma ga abinci , maganinki kuma suna wajan dady” dan murmushi oumma ta sakar mata,”Tom nagode da kulawa”sosai zahra ta washe hakwaranta kafun tayi wa oumma sallama , bin ta da kallo oumma tayi tana jinjina karanci irin da su a wannan zamanin, kallan abincin da aka kawo mata tayi ,kwallan da take kokarin boyewa suka sauko, saurin goge su tayi tana istigfari aranta “Allah na tuba , Kai ka dai ne abun bautawa,Allah kaine mahaliccinmu sannan kafi kowa son bawanka, Allah na rokeka ka karesa a duk inda yake” sosai tashiga yi masa addua tare da tahee tsawan lokaci ,kafun ta tsakuri abincin da aka kawo mata, ji take kamar tana cin magani ,a haka taci kadan tare da ajjewa….. 🫧🫧🫧🫧 Tunda suka dawo gida babu Wanda ya kara tada maganar, Kai tsaye part din dada suka nufa baki d’ayansu, waya abeey ya dauka tare da kiran mutanan gidan, gabaki d’aya ya umarce ganin manyan gidan,a karshe ya jaddada musu kar yaron da yazo wajan,kowannansu amsawa yayi cikin kan kanin lokaci suka halarci babban falon dada. Lokacin da uncle Salem ya kira aunty suna zaune ita da amrah , sun hada dan karamin kwarya kwayar walima,ko wannansu inka duba fuskarsa zaka ganta dauke da farin ciki,musamman amrah da ta fi kowa farin cikin jin labarin mutuwar tahee, suna cikin wannan yanayin ne uncle saleem ya kira aunty, cikin sauri ta dauki wayar tana kashe murya cikin damuwa,”Muna falon dada kizo ke kadai”yana cewa hakan ya katse wayar tasa, aunty har da mikewa dan murya kasan cewar a speaker ta saka wayar, kamar wasu kawaye haka suka tafa ita da Amrah, jin yadda uncle saleem yayi magana cikin sanyi yasa suka kara yadda da mutuwar taheen, mayafinta dake kan kujera aunty ta dauka tare da yafawa, kallan amrah tayi tare da kashe mata ido daya bayan ta marairaice fuskarta gwanin tausayi kafin su saki dariyar keta aunty ta nufi hanyar barin part din tare da nufar part din dada. A zazzaune ta tarar dasu kowa yayi jigum dashi,itama karasawa tayi fuskarta cikin sanyi kamar ba itaba, ganin yadda ko wannansu yayi jigum dashi yasa ta bude baki da niyar yi musu ta aziya,gyara zama tayi sosai tana saita muryarta “Aushe abunda ya faru kenan ,Allah ya jikan…” bata karasa ganin yadda ko wannansu ya zuba mata idanuwa suna jirin jin me zatace, dada ce ta katse su ta hanyar kallan abeey,”ka Tara kowa ,ka Hana yara zuwa ko zaka fada mana dalilinka na yin hakan”, gyada mata kai abeey yayi kafun ya gyara zamansa,”kamar yadda kuka sani , d’aya daga cikin ahalin gidan nan kaddara ta fada mata da Hakan yayi sanadiyyar samun babban rauni a gareta amma duk da hakan muna godewa Allah da takaita,sannan inaso ko wannanku yaci gaba da tayata da addua kasan tuwar ta manta tunaninta wato ta rasa memory dinta”, tunda abeey Ya fara magana aunty take kallansa, jira take taji ya ambaci mutuwar tahee, amma shiru ganin kamar bata mutum bane kamar yadda sukai tunani yasa zuciyar aunty tashi,tana cikin wannan tunanin ne kunnuwanta suka jiyo mata kallan data kwantar mata da hankali na memory din da tahee ta rasa,"wannan ma abun jin dadin mune tunda ta rasa tunaninta” aunty ta fada cikin zuciyar ta,”a karshe ina mai farin cikin sanar daku cewa ,a yau dinnan rana me kamar ta yau an daura Auran tahnoon zayed al-nahyan tare da amaryarsa taheera mohammed” a zabure mutanan falon suka kallesa, aunty har wani kwarewar azaba tayi a makoshinta, Sam ta manta a inda take azabure ta furta “aure fa kace,Sam bazai yuba”gabaki d’aya falon kallonta sukai cikin mamaki,shima abeey kara hade ransa yayi”kamar ya kenan “ ya furta yana kallanta, sai lokacin ta gane katobarar da tayi ,cikin in ina ta soma magana “daman inaso nace kamar hakan yayi wuri”dauke kansa abeey yayi tare da kallan dada datayi shiru,”dada da fatan hakan be bata miki rai ba” jimmm kadan dada tayi cikin dattako ta jinjina masa”tabbas ka cika uba na gari amma bani zaka tanbaya ba ,iyayensa yakamata ka tanbaya”ta karashe zancenta da kallon su ummey, itama ummey bata amsa ba sallan ammi da tayi, girgiza Kai ammi tayi cikin sanyin jiki,”gaskiya baza ayiwa don Auran dole ba inde ba da amincewarsaba “ ta furta muryarta a sanyaye case dan murmushi abeey ya saki,” ya amince “da sauri kowa ya kalli abeey cikin mamaki, ya bude baki daniyar sake magana kenan, daddadan kamshin turaransa ya cika ko ina na dakin,kowa maida hankalinsa yayi kan kofar shigowa , a hankali yake taku, bayansa tahee ce dake faman rakubewa a gefansa,har ynxu kanta da bandage din da aka nade mata ciwonta, be kalli kowa na falon ba yasamu waje ya zauna kan daya daga cikin kujerun falon, itama taheen zama tayi a gefensa tana rike masa rigar jikinsa ganin irin kallan da yan gidan ke binta dashi,gyaran murya abeey yayi yana kallan king da ya ki dago da idanuwansa, cikin dakewa abeey ya kalle sa “ nasan kun gaji, ya kamata ku huta” ya karashe zancen nasa yana kallan king har yanxu , kin dago da idanuwansa king yayi sai sallamar da yayi musu yana mikewa,da sauri tahee ta mike tana kokarin binsa, da mamaki yake kallanta yana mamakin inda zata,be ce komai ba ya juya daniyar tafiya, taku biyu yayi itama ta soma binsa, kara jiyowa yayi yana kallanta, a dake ya furta “ina zaki”, langwabar masa da kai tayi”dady”,muryar abeey da yajine yakatse shi daga yin magana”ku tafi tare”abeey ya kara fada, taune lips dinsa king yayi tare da soma magana, ganin hakan yasa cikin sauri tahee tabi bayansa, tsabar mugun ta yau be shiga motar ba,a kafa ya soma tafiya ,itama bata gaji ba a haka take binsan, ganin kamar tana kokarin faduwane yasa zaki ya karaso da motar inda suke, baya king ya shiga, TAHEE na biye da shi sabanin dazu yanxu ta rike masa Riga ganin zaki na wajan, a Daidai part dinsa zaki yayi parking,Kai tsaye ciki suka shiga, be kalli inda take ba ya nufa daya daga cikin kofofin kasan , Daidai ya soma balle rigar jikinsa itama ta shigo dakin, da mamaki dauke kan fuskarsa ya kalleta “me kika shigo yi anan” da Sauri ta furta “ni tsoro nake ji”tana turo dan karamun bakinta,kamar bazai kula ba ya kalleta”zauna”,cikin sauri kuwa ta zauna ,wata kofar ya nufa dake gefensa”karki kuskura ki biyoni”gyada masa kai tayi tana turo dan karamun bakinta, yana shiga ko munti uku beyi ba ta mike “Allah ni sai na bika dady” ta karasa zancan nata tana tun karar kofar dakin,bazato ba tsammani ya ji an shigo dakin, da sauri ya juyo dan ganin wanda yayi wannan gangancin, itama ihu ta saki tana kokarin juyawa, san shine ya kwaceta tayi baya zata fadi ,cikin azama ya riko ta towel din jikinsa na kokarin kwancewa,gaba dayansu baya sukai zasu fadi ,Allah yaso akwai sofa daya a wajan suka fada kanta dukansu,shi yana kan sofa din itama tana kansa,hannunta ne ya sauka kan towel dinsa, manyan idanuwansa ya zaro waje yana kokarin tureta, itama kuma sai faman taba towel din take kafun ta kalle sa”dady Menene wannan abun”…….. ALHAMDULILLAH…….. Mu hadu a next page ,ina Godiya sosai masu comment,masu yimun ya jiki kuma nagode sosai Allah ya bar zumunci, Aunty sadeeya (mrs bbk), masoyiya (star lady) da gabaki d’aya team din the talent troupe writers inayinku over ,Allah ya bar zumunci💔💖💖💖🫶. MSS LEE💖 💖💖💖 GIDAN AUNTY 💖💖💖 (a heart touching love story) Story & written By Mss Lee 💖💖 💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖 MAISAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER: 07041879581 Paid book Page 30 🦋 Zaro manyan idanuwansa king yayi,ganin tana kokarin zame masa towel din kugunsa,tsawa yake so ya daka mata amma bakinsa ya kasa motsi Daidai lokacin da hannunta ya sauka kan mararsa, da Sauri ya Bige mata hannu yana kokarin mikewa,turo baki tahee tayi har yanxu bata dena kici niyar taba towel din ba,”Allah niii.. dady sai naga menene,inaso na gani”,da Sauri ya kalle ta na yan second,har ya rike hannunta da niyar tureta kome ya tuna sai ya fasa tare da sakin guntun murmushi iya haba,kallan ta yayi sosai kafun ya soma magana kamar Wanda aka saka dole,” kinaso kigani”,saurin daga masa kai tayi tana turo baki,”me zakiyi inkin gani”ya kara tanbayarta,yanxun ma turo baki takarayiii “Nidea dady inaso naga Menene a wajan “,lumshe idanuwansa yayi,yana kokarin sake magana ta kwance towel din jikin nasa, gigitacciyar kara ta saki tana kokarin tashi daga kansa ,ganin hakan yasa ya rike ta sosai ko motsin kirki ta kasa sai rawa da jikinta ya somayi,kallan yadda jikinta yake rawa yai ga saitin zuciyar ta dake faman sama da kasa,sosai tsoro ya bayyana a fuskarta da ta kulle gam, kara kallan yadda ta kulle ido yayi har hawaye sun fara fito wa,”bude idanuwanki “ ya furta Daidai fuskarta,”dadyyy” ta fadi sunan nasa a rarrabe,be amsa mata ba sai ma kara maimaita maganar da yayi”bude su yanxu kafun ranki ya baci”, jin hakan yasa tayi saurin bude idanuwan kwallar data tarar mata suna zubowa, kallan yanda hawayenta suke zuba yayi kafin ya soma magana “me akaimiki “girgiza masa kai tayi da sauri tana hadiye kukan ,lokaci d’aya tsoransa yashigeta,”kin zama kurma”da sauri ta bude bakinta “babu komai daddy” ta furta tana san sakin kuka” ba kyajin magana ko, oya kalli abunda kikace kinaso ki gani”ya fada yana kara tsareta da idanuwansa ,baki ta bude da niyar sakin kukan,” kika kuskura kikai mun kuka sai ranki ya baci”hannayenta biyu tasa tare da goge hawayen nata,”oya kalla ,tunda ke kika bude”, girgiza masa kai tashiga yi da sauri tana fashe wa da kuka “dady kayi hakuri bazan sake ba”,be kulata ba har ynxu”kinsan menene shi”, yanxun ma girgiza masa kai ta shiga yi, lips dinsa ya taune kafun ya funciki hannunta ya dora kan marar tasa, gigitacciyar kara taheee ta saki tare da fadowa jikinsa alamar ta suma,nauyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idanuwansa,”you killed me,abeey duk kai ka jawomun” ya furta a hankali kafun ya nade towel din jikinsa, ya dau dogon lokaci zaune a inda yake ko motsin kirki yakasa kafun ya bude idanuwansa da suka gama rinewa,kallan inda take kwance yayi har yanxu tana suman, wata kofa yashiga a Wajan, cikin kankanin lokaci ya fito yana tsiyayar ruwa alamun Wanka yayi,kafun ya shirya a gaggauce,inda take ya nufa da hannu daya ya daga ta tare da sabawa kan kafadarsa,kofar ainahin bedroom din ya nufa tare da shinfideta akan lallausan gadon, bedside drowse din gadon ya bude tare da futo da wasu magunguna,guntun tsaki yaja kafun ya balli magungunan tare da balle murfin robar ruwan da ya dakko,bayan ya shanye maganin zama yayi Allan bed din yana rintse ido tsawan mintuna uku kafun ya bude, ruwan hannunsa ya zuba kadan a tafukan hannunsa kafun ya shafa mata shi a fuska,sau uku yana haka kafun taja wata doguwar ajiyar zuciya, ahankali ta fara bude idanuwanta kafun ta bud’esu gaba daya , azabure ta mike zaune idanuwanta ne suka sauka kan king dake zaune gefanta, Tara ta saki tana faman jada baya, sosai hawaye suka fara tarar mata, neman ta sauka take a kan gado tana girgiza masa kai,”dadyyy na dena kayi hakuri”tana gama fadar hakan ta sauka daga kan gadon zata gudu,taku daya yayi ya cafko hannunta,neman yi masa ihu take ya tsawatar mata ta hanyar cewa “yi mun shiru” shirun kuwa tayi tana sunkuyar da kai,kan gadon ya koma da ita kafun ya kalleta,”bakyajii ko” da Sauri ta girgiza masa kai “na dena dady” duk da tsananin tsoran da ya shige ta hakan be hana dan karamin bakinta turo kadan waje ba lokaci zuwa lokaci tana zabura gabanta na faduwa.cikin kakkausar murya ya soma magana “da yau idan aka hanakiii abu,kika kijiii ko ,kinsan me zan miki” girgiza masa kai tayi tana ware manyan idanuwanta,”ok zomuje wancan dakin se na nuna miki” da sauri ta langwabe kai “na dena kayi hakuri zan dunga jin magana”girgiza mata kai yayi”a’a zomuje na nuna miki” cikin tsoro ta kara kallansa “wallahi na dena”,uhmm kin kyauta, yana kammala maganar tasa ya nufi kofar fita, dan juyowa tare da d’age girarsa kadan,kika kuskura kika fito daga dakin nan hmmm… yana kammala magana ya fita daga dakin. ******* A firgice aunty ta koma part din ta , ko ganin hanya batayi sosai tana shiga falon ta tarar da ba amrah a falon, cikin sauri ta nufi dakin da amrah take ,tana shiga ta tarar da ita tana waya,ganin yadda aunty ta shigo cikin dakin ne yasa ta kashe wayar ,duk atunaninta mutuwar taheen ce ta komar da ita haka ,”aunty ya karin hakurin ku”, ta fada tana kyalkyalewa da dariya, cikin ba’kin ciki aunty ta kalleta “ubanki Kena ya karin hakurin “mikewa zaune amrah taji jin abunda aunty tace, waje ta samu ta zauna tare da fashe wa da kuka, tsaya kallanta amrah tayi,”wai ke aunty lapiya na ganki haka,mu da yau ta kasance ranar farin cikin mu”, bata kai karshen maganar ba ,aunty ta kudun Dino zagi ta dire mata,”ubanki ke da farincikin,dan ubanki da kinsan abun bakin cikin da naje na tarar bazaki mun wannan banxan zancen ba,toh bari na futo miki a mutun tunda bakya ganewa,ban taba sanin cewa sheguncan tsinannu bane se yn Andy, kamar ni zasu ha’inta”kamar ya aunty ban gane ba,cewar amrah ,wani dogon tsaki aunty ta karaja yanajin yadda zuciyar ta ke soyuwa da bakin ciki,”toh in baki sani ba yanxu ki sani,shegiyar yarinyarcan tana raye bayan tayi loosing memory dinta”,jin karshen zancan ta yasa amrah sakin ajiyar zuciya “aunty wannan me sauki ne tunda tayi loosing memory dinta ,kinga sai muyi anfani da wannan damar mu kasheta kawai”, a tsawa ce aunty ta tashi”ke dan ubanki me yasa kullum kwakwalwarki ta Kifi ce,to bari na fito miki dallah dallah, shegiyar yarinyarcan sun daura Mata aure da king, yanxu haka tana bangaransa “, kalmar an daura mata aure da king ne kawai ya shiga kunnanta, take a wajan ta yanke jiki ta fadi sumammiya, da sauri aunty ta nufi toilet,muntuna kadan tafito hannunta dauke da ruwa, watsawa amrah dake kwance tayi a wajan,tana farkawa tasaka kururuwa tana birgima kamar wacce aljanu suka shigeta,”bazata sa’buba wallahi bazan yadda ba , king nawane ni kadai ba wata shegiya da ta isa ta zama mallakinsa sai nii,wallahi sai naga bayanki, sai na kashe ki” itama aunty bata kulata ba sai ma barin dakin da tayi, sosai amrah ta haukace, sai faman fashe fashe take tana kururuwar bazata yadda ba ,tanayi tana kuka ,lokaci zuwa lokaci tana sakin dariya kamar me tabun hankali, da sauri ta nufi daya daga cikin a kwatunanta, tana budewa wasu magunguna ne a ciki, guda ukun cikinsu ta bude tare da kwankwadewa gabaki d’aya,lokaci d’aya ta bugu sai faman surutai take. ➰➰➰ A ‘ban garan mamy ma cikin futar hayyaci ta nufi ‘ban garanta,lokacin ihsan da sumayya suna zaune suna kallo, ganin yadda ta shigo ne yasa suka bita da kallo,”mamy lapiya naganki haka “cewar ihsan tana mikewa,bata kulataba sai ma zagaye falon da ta fara ,”shikenan aikin da muka dade munayi ya tashi a banza shegiyar yarinyar can na tsanekiii”, cikin hada baki suka kalleta”wace yarinya”yanxun ma bata kulasu ba, sumayya ce ta kulu cikin tabara tace”wai ke mamy ana ta miki magana sai wani faman ja mana rai kike”,girgiza kai mamy ta fara tana buga cinyarta, “shikenan ta faru ta kare, yanxu abunda zayed ya d’auke mu kenan,ya daurawa king aura ba tare da sanin muba” za bura sukai baki Dayan su musamman sumayya datafi kowa firgita,cikin rawar murya ta soma magana”wane..wane king din wai”dogon tsaki mamy taja,”Wana king kika sani, to bari na fada muku kuji ba sa kowa aka daura masa aure ba sai da wacce shegiyar taheera take kowa, ni zasu rai nawa hankali suce wai tayi loosing memory “,bushi bushi sumayya ta fara gani, take a wajan ta fada kan kujerar da ta tashi, d’age kafada ihsan tayi”toh mamy Menene aciki dan ya aureta inda da abincewarsa” bata karasa zancan taba taji saukan maruka dama da hagu” shegiya daman nasan ke ba Kaunar cigaban mu kike ba” ‘bace mun da gani,tana kammala zancanta ta kama hannun sumayya suka nufi up stairs,akabar ihsan da rike kumatu. 🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 KANO Knocking din kofar dakin akai, “shigo “oumma ta bada umarnin shigowa ,khaleed ne ya shigo dakin cike da sallama,”oumma barka da hutawa” ya furta yana sakin murmushi,itama murmushi ta sakar masa,”barka khaleed”ta fada da sigar tabbatar wa, sosai ya washe hakwaransa, baki manta sunana ba oumma,Kai naji dadi” itama oumma murmushi ta sakar masa,”oumma hira na zo na tayaki kar abar mun ke ,ke kadai “yanxun ma murmushi ta sakar masa, yana cikin maganar sane zahra ta shigo dakin itama “Laa,yanxu yaya khaleed ahaka Allah yace ,shine ka gudo kabarni ni kadai wajan dadi”dariya khaleed ya saki”nasan halinki ai shiyasa nazo bude fadata “, da sauri zahra ta shigo ta itama ta zauna kusa da oumma,”oho dai nide bazan yadda ba”, kallan oumma tayi ,”oumma Aini zaki fi so ko”gyada mata kai oumma tayi ,da sauri khaleed ya kalleta,ni bakya sona kenan ko, girgiza masa kai tayi “Aah Kai ma ina sanka”, kama hannunta yayi “toh oumma zaki dauke Muma kamar taheer da taheera “, ya fada a raunane tunowa da mahaifiyarsu da sukayi, itama zahra kwallace ta tarar mata ,ganin yanayinsu yasa oumma sakin guntun murmushi”sosai ma kai kamar taheer kake a waje na ,itama kamar taheera ta take”sosai farin ciki ya bayyana a fuskarsu,suna cikin zaman nan ne dady ya zo wajan,kallansu yayi tare da girgiza kai”me kuke anan ku taso kuzo ku kwanta kun cika ta da surutu”dan turo baki zahra tayi” to dadi zan kwana a…”bata karasa ba dady ya kalleta”Ah ah fa, ku tazo maza” tashi sukai tare da kallan oumma cikin hada baki,”oumma sai da safe”, Allah ya tashemu lapiya ,suna gama fadar hakan suka wuce,shima dady kallanta yayi”sai da safe” be jira amsarta ba ya bar wajan. 💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖💖 Mss Lee 💖 ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels