Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 🔥💔𝑨 𝒕𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝒉𝒆𝒂𝒓𝒕𝒔 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒔𝒕𝒐𝒓𝒚, 𝒅𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚 𝒐𝒃𝒔𝒕𝒂𝒄𝒍𝒆, 𝒂𝒏𝒅 𝒓𝒐𝒎𝒂𝒏𝒄𝒆💔🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 *Gargaɗi! Gargaɗi!! Gargaɗi!!! Ban yardaba! ban Amince ba! ban lamunceba! A juya mun labarin LITTAFINA tako wacce sigar, bana so, ban bada damaba, idan kana buƙata akwai numberta a jiki ki\ka nemi izinina, ban yarda a karanta mun shi a youTube ba, ko a haɗa mun Document, a kiyaye domin zama lafiya yafi zama ɗan sarki! In kunne yaji gaggan jiki ya tsira. Wannan littafin RAWANIN ZALINCI haƙin mallakarsa nawane FATEEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA)!.* *Ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon fara wannan littafi lafiya, Allah ya bani ikon kamala shi lafiya.* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM. mun fara da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, da shi muka dogara kuma a gare shi kawai muke neman taimako.🥰 Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Rahma ɗan gata a wajen Allah, kuma fiyayyen halitta wato Annabi MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA🤍* ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 28/6/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 ❤️𝑬𝑷𝑰𝑺𝑶𝑫𝑬__________1🔥 Iska mai matukar ƙarfin gaske ne yake kaɗa dogayen bishiyoyin dake a kewaye da wannan ƙungurmin dajin! Tamkar za'ayi ruwan sama, garin ya haɗe ya yi duhu bakin kirin da hadari, sararin samaniya ya bada wasu launuka, ja, sky blue, navy blue, da kuma dark ash masu matuƙar ɗaukar hankalin, saboda hadirin!. Daga gabas ta tsakiya wani tapkeken bakar gizo ne wato Rainbow ya fito a sararin samaniyar. Sannu a hankali walkiya ya fara wanzuwa a sararin samaniyar, haka zalika tsawa ta fara bayyana, alama ce ta ruwan saman ya gabato. Iskar kara tsananta take yi sosai, while shima hadarin kara baki yake yi sosai, yana mamaye ko'ina a faɗin garin, gabaɗaya korayen ganyayyaki da dogayen ciyayin dake cike a wajen, sai wani irin kaɗawa suke yi har suna kwanciya, tamkar za su tsigo daga jikin tushensu, da alama dai wannan ruwa ne mai karfin gaske yake zuwa, da iska da tsawa!. Daji ne mai cike da yalwar itatuwa, dogaye, manya manya masu kauri, akwai yalwar ƴaƴan itatuwa kala kala sosai a cike a cikinta, akwai ƴelwar abubuwa masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, irinsu koramai dake zubar da ruwa mai ban sha'awa, duwatsu manya manya masu ɗaukar hankali, koguna wato kogon dutse manya da kanana, tsaunika masu tsawo, rafuna masu cike tab da ruwa mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, a saman mafiya yawan tsaunikan dake a cikin wannan dajin da akwai jiga jigan kogunan duwatsu a wajen, ga kuma bishiyoyi masu ɗaukar hankali, da dai sauransu. Sai dai da alama akwai haɗari matuƙa a cikin wannan daji, domin kuwa ba za'a rasa muggayen namun dawa masu haɗari irinsu Zaki, Damusa, Kura, Giwa, Sloot, dabba mai nawa da saiɓi, Puma Tiger, Guanaco, dabba mai kama da raƙumi, Vampire Spader, masu kashe sauro, Honey vaja, Dage, Damusar chiter, Dila, Dilar Jakal, Birrai, Gorillas, Tsuntsaye, Macizan kubras, Hayanas da dai sauran mugayen namomin daji. Wani irin sauti ne yake tasowa tamkar na sahun gudun ɗan adam, sautin yana fitowa ne daga bayan wasu dogayen bishiyoyi na zaitin dake fuskantar gabas ta tsakiya, bishiyoyin suna a cunkushe ne waje guda, sai wajen ya bada duhu tamkar maraice ne a lokacin. Da kaɗan da kaɗan sautin nan ke tahowa, har ya fara karaɗe kewayen wajen. Bayan wani ɗan lokaci wannan sauti ya kara matsowa kusa sosai, kasan cewar gari ne na damuna, ta ko'ina akwai ruwa wanda ya kasance ya yi ramuka kanana, sannan wasu gurare daga cikin wannan katafaren dajin sun kasance da akwai taɓo, wasu kuma farin kasa yashi ne tas, kamar dai sauran manya manyan dajuka da kuka sani. Wannan ramuka kanana masu ruwan, duk in aka takasu sai ruwan ya yi kara palcam, hakan yasa sautin gudun ya kara fitowa ɓaro ɓaro sosai da ya karaɗe yankin wajen!. Jim kaɗan ta bayyana a tsakiyar dogayen bishiyoyin nan. Mace ce fara tas tamkar balarabiya, a kallon farko idan ka yi mata sai ka yi wani irin razana, saboda tsannin kyau da kuma yanayin da ta bayyana a wajen, tamkar wata rafaniya ko ace irin kyawawan aljanun nan masu kamar su suka yi kansu dan kyau. Launin hasken fatartata gwanin ban sha'awa, luwai luwai, jajir da ita a cikin korayen ganyayyaki, ya kuke tunanin bayyanarta zai kasance a idanun ɗan adam?, dole duk wanda ya ganta a wajen sai hantar cikinsa ta kaɗa ya tsorata aihun, dan kyau na ɗiga. Da kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci cewa daga gidan hutu ta fito! Dan jiki duk madara da ice cream ce! Kyakkyawar gaske ce, gata da tsawo, doguwa da ita, a shekaru ba zata wuci 22 to 23 years a duniya ba. Sanye take da kaya masu bala'in kyau da tsada, kaya ne irin na hamshaƙan gimbiyoyi, ire iren waɗan nan dogayen riguna ne da ƴaƴan manya manyan jiga jigan sarakuna suke sanyawa, rigar kawai abar kallo ce, dan ta tsaru iya tsaruwa, ta sha kwalliya da wasu shegun duwatsu masu bala'in haske har suna wani ɗaukar idanu. Daga kanta har ƙasa wani dankarere kuma haɗaɗe tsadadden alkyabba ce mai hula, launin Golden color, while shi kuma doguwar rigar jikin nata launun ligh ash ne, sai launin alkyabban ya hau da rigar sosai. Kunnenta hannunta zuwa wuyarta, shake suke da dankara dankaran kayan ado na gold masu bala'in tsada, shi sarkar wuyarta ma yana da tsawo har saman breast nata, ga shi da faɗi, na zallar madarar gold ne babu sirki. Takalmar dake kafafunta ma kawai abin kallo ne, irin takalmar nan ne da manyan gimbiyoyi da ake ji dasu a duniya suke amfani da su, takalma ne masu matukar tsada wanda kwalliyar jikinsu ma da gold aka yi su, sai wani ɗaukar idanu suke yi. A takaice dai jikin wannan mata daga sama har kasa narkakkun makudan dukiya ne ba na wasa ba aka kashe, bakina ni dai PRINCESS TEEMA ya yi kaɗan ya zayyana maku irin kuɗin da aka narka a kwalliyar dake jikinta. Daga cikin hular alkyabbar jikin nata, kana iya hango wani kwantatcen bakin gashi siɗif da ya zubo mata ta saman shoulders ɗinta har izuwa kirjinta ta gefen dama. Tana da dara daran idanu sosai, launin kwayar idanunta ash color ne, irin light ash ɗin nan da zaku kalli kamar basu iya ganin mutane, saboda kyallin idanuwan nasu, dan ya yi light, sai ya yi kamar yana. Tana da dogon fuska, amma ba sosai ba, sannan ba laifi tana da ɗan cikar fuskar, haka zalika tana da innocent face sosai, da kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci she is so silent, bata da hayaniya, bata da ƙiba sosai, ƴar caras cas da ita. Karshen haɗuwa ce ita ɗin!! Kamar ba mutun ba dan kyau!. Daga saman kanta har izuwa fararen lausasan kafafunta, gabaɗaya gumi ne ya jiketa sharkaf, daga gefe da gefen face nata, wasu zufa ne suke kara tsastsafo mata kamar ruwa, fuskarta gabaɗaya ya jike sharkaf da gumi, tamkar wadda aka watsawa ruwa a face ɗin tata, wani irin uban haki take fitarwa sama sama, idanuwanta har wani irin juyewa sama suke yi, saboda wahalar gudun nan da ta sha, gabaɗaya a tsananin razane take, wannan innocent face ɗin tata ta koma a wani irin razane gwanin ban tausayi. Daga gani kasan gudun cetan rai take yi, ga tsohon cikin a jikinta, wanda a kalla ya kai watanni haihuwa, kuma da alama ma ta fara naƙuda, ko kuma wahalar gudun ne ya bayyana a jikinta tamkar mai naƙuda. Amma a haka take wannan uban gudun, daga ganin kasan bala'in da ya korota ta shigo cikin wannan bakin daji ba ƙaramin abu ba ne. Duk da wannan tsohon cikin nata, haka ta jure take tika uban guda, ta gaji iya gajiya, amma bata tsaya ba, ta yi wani wiki wiki da ita gwanin ban tausayi, duk ta fita daga cikin hayyacinta. Gudu take yi bata san ina ta dosa ba! Duk wanda ya kalleta a cikin wannan hali da take a ciki, sai ya matsa mata kwallah, babban abin tausayin ma shi ne wannan tsohon cikin nan da yake jikinta. Kutsawa ta sake yi ta cikin wasu bishiyoyin mangoro dake ɗan nesa daga in da ta fito, sai wani irin haki take yi mai matukar razanarwa, sama sama take fidda numfashi mai sauti, da sauri sauri tamkar wadda aka shake na tsawon lokaci bata sami iska ba, daga baya aka saketa, haka take fitar da numfashi, da alama ma faɗa take yi da numfashin nata, domin ta dai'dai ta shi ya dawo dai'dai, wani irin razanannen tashin hankali ne bayyane a saman fuskarta. Tabbas wannan mata tana cikin bakin bala'in tsaka mai wuya!!. Wani uban sautin gudun lafiyayyun dawakai ne yake tasowa daga ta hanyar da ta fito ɗan nesa kaɗan, da karfi-karfi dawakan nan suke gudu, kai daga ji kasan suma suna gudune domin cinma wani abin da idan ba su cin mishi ba, suna iya rasa rayukansu, ma'ana suma dai gudun cetan nasu rayukan suke yi kenan. A lokacin already matar ta kutsa ta cikin bishiyoyin dake fuskantar yamma kenan. Da karfi karfi gudun waɗan nan dawakai ke kara dimfarowa kusa, sai wani irin uban haniniya dawakan suke yi, da alama waƴan da suke a kan dawakan, a ƙage suke da su je in da suke da buƙatar zuwa, suna ba wa dawakan wuta sosai ne, ma'ana suna sanya dawakan gudun wuce ka'idar dabbobi. Jim kaɗan!. Duk wani mutun mai rai matuƙar yana wannan waje, to sai ya yi mahaukacin razana a lokacin da waƴan nan dawakan suka bayyana a tsakiyar filin bishiyoyin nan. Wasu irin mahaukatan manya manyan dawakai ne, masu tsantsar lafiya tare da ƙoshi! Da alama sun kiwatu fiye da tunanin mai tunani, dama can kun san doki da shegen karfin tsiya, bare ace ya samu kiwo mai kyau, ai abin sai wanda ya gani kawai. Wasu irin shirga shirgan jiga jigan manya manyan sadaukan yaki ne a saman waƴan nan ƙosassun dawakan, wanda ganinsu kawai sai ya razana duk wata halittar ɗan adam mai rai. Gabaɗayansu sanye suke cikin kayan yaki a jikkunansu, kayan yaki kuma irin wanda ake yin su da dafaffen karfe, wadda bullet ko kifiya or takobi bata huda su, daga ganinsu kasan daga wani katafaren Kingdom (Masarauta) suka fito, fuskokinsu gabaɗayansu a rufe da irin waɗannan hular kayan yakin nasu da suke sawa, kayin hular nasu yana da kaho guda biyu kamar na ɓauna, baka iya ganin fuskokinsu, sai ido, hanci da kuma tsagen baki, dan hular nasu tamkar mask haka yake, dan ya tare musu kansu idan ana yaki, kun dai gane hular mayaka dai ko? To su dai. Daga bayansu kuma manya manyan lafiyayyun kwari da kifiyoyi ne tsakale a bayan nasu, wanda ba sa saɓa saiti, shi suka ratayo a bayan nasu, dai'dai kugunsu kuma, wasu irin mahaukatan zaratan takuban nan ne, masu kaifin bala'i, wanda kaifin su zai iya fille wuyar mutun nan take, kafafunsu na sanye cikin irin waƴan nan takalmar nasu na mayaka, masu kama da waterproof shoe, sai dai nasu yana da igiya wanda aka ɗaure har saman kaurin damatsan kafafunsu. Ko baka ga fuskokinsu ba, kasan waƴan nan basu da imani ko miskala zarratin a ransu, saboda mawuyacin abu ne mai imani ya biyo mace mai tsohon ciki tana naƙuda a irin wannan dokar bakar daji haka, babu tausayi ba imani su biyota da dawakai suna neman hallaka ta, innalillahi wa inna ilaihir rajiun........😭 Dawakai shidda ne, haka zalika Warriors (mayaka) shidda ne a kansu, sun horu a fagen yaki sun ƙoshi, kamar wasu bujuman mayunwatan zakuna haka suke. Tamkar sun san hanyar da ta bi, suma nan suka nufa da wani mahaukacin gudu. A ɓangaren wannan mata kuwa, tun da ta kutsa ta cikin waɗan nan bishiyoyin, wani azababben kuma balaƴaƴƴen ciwon ciki ne ya turnuketa lokaci guda, wani irin kullewa mararta ta yi, ta riƙe gam tana yi mata bala'in ciwo na gasken gaske kuwa. (ALLAH SARKI KO DAN JIJJIGA CIKI NATA DA TA YI NA WANNAN UBAN GUDU DA TA SHA, DOLE NEMA CIKIN NATA YA YI CIWO......😭) Da kyar take jawo wani wahalallen yawu tana haɗiyewa, saboda bala'in kishin ruwa da take ji, maƙoshinta ya bushe sosai. Ƙasa cigaba da guduwa ta yi, wanda hakan yasa ta zube kasa a saman gwiwowinta gaban wasu bishiyoyin kashu, tana mai fafutukar jawo numfashinta, ta daidai ta shi dan ta ceci rayuwarta da na abin da yake a cikinta. Baiwar Allah da hannu bibbiyu ta tallaɓo katon cikin nan nata ta kasa, ji take yi tamkar cikin nata zai faɗi kasa ne, dan tsabar bakar wahala har ji ta yi cikin nata ya rabu da mahaɗar haƙarƙarinta ya yi kasa,.............. Wayyo Allah, ya ilahi ya lillahi. Zufar azaba da wahale ne yake cigaba da tsantsafo mata daga gefe da gefen kunnenta, fuskarta kuwa tuni ya kara jikewa sharkaf da gumi, tamkar wanda aka watsawa ruwa, wani irin wahalallen marayar kuka ta saki, wanda kuma muryarta kwata kwata bata fita, babu sauti a tattare da ita, wahala ta yi wahala, ta ma nemi hawayen a jikinta ta rasa, yau hawayen kukan ma babu shi, dama kuma duk wahalar da ake yi wa hawaye, to bata kai wahala ba, muddin ta kai wahala, da kanka zaka nemi hawayen ka rasa shi. Tana a tsaka da wannan hali, kunnuwanta suka fara tsinkayo mata sautin gudun tare da haniniyar waƴan nan dawakan daga can nesa da ita a karo na biyu!. Jin sautin na kara dinfarota gadan gadan ne yasa ta ji wani irin mahaukacin karfi ya zo mata, a wahale ta daure tare da ciza laɓɓanta da karfi tamkar zata fasasu, da iya karfin da ya rage mata baiwar Allah ta miƙe dan ta cigaba da gudu ko zata tsira da ranta. Bata san ina ta nufa ba, bata san ina take takawa ba, haka ta cigaba da gudu, ta cigaba da tsaga tsakanin manya manyan dogayen bishiyoyi tana wucewa!. Wannan Baiwar Allah dai ta ci bakar wahalar da ko makiyinka ba zaka yi mashi fatar faɗa wa makamancin wannan wahala da bala'i ba, sai nishi take yi sama sama, da alama tana da yakinin da kuma burin cigaba da rayuwa, alamu sun nuna akwai tsantsar burin son ta cigaba da rayuwa a tattare da ita, kuma daga kwayar idanunta zaka fahimci akwai wani babbar Al'amari da take buri da kuma fatan cinma shi a rayuwarta, daga yanayin yanda take gudun take ƙoƙarin ganin ta rayu duk da mawuyacin abu ne ta zullewa waƴan nan mayun azzaluman dakarun yakin, sai dai wani ikon Allah, amma dai bata sare ba, kuma bata yanke kauna ba, haka zalika bata cire rai daga samun Rahmar Ubangiji ba. BABBAR MAGANA KO YA YA WANNAN AL'AMARI ZATA KASANCE? FARKO KENAN DAGA CIKIN LITTAFIN RAWANIN ZALINCI, (🤍 PRINCESS TEEMA CE 🔥💘 HAR WA YAU.) Bata yi nisa a gudun nata ba ta isko karshen hanyar, wanda kuma ya kasance wani katon dutse ne da baka ganin iyakarsa a faɗi, ƙasan dutsen kuwa, katafaren teku ne mai girman gaske, tekun cike yake maƙil da farin ruwa tas, har wani ɗaukar kalar sararin samaniya ruwan nan yake yi, saboda haskensa! Sai dai kuma tsakanin tekun da wannan dutse da take a kai, akwai nisa sosai, sannan kuma, akwai dogayen bishiyoyi ta gefe gefe ruwan, bayan haka akwai abubuwa da dama dai irin na ko wace babbar daji da ta amsa sunanta daji. Dakatawa ta yi daga gudun da take yi tana mai kallon wannan tapkeken tekun, tana sakin wahalallen nishi. Wannan shi ne gaba babu hanya baya ma babu hanya, gaba teku baya warriors! Ya kenan?. A hankali tamkar mai tsoron juyowa ta juyo dan ta kalli waɗan nan masu bin nata, wanda suma a daidai lokacin suka cin mata, har lokacin tana cije da laɓɓanta bata saki ba, hakan zai fahimtar da kai tana cikin azaba. Juyowarta ya yi daidai da ɗaya daga cikin warriors ɗin ya ciro kwari da baka daga bayansa, ya ɗana kifiyarta tare da ja da karfi, ya saitata, kai tsaye ya harbeta sai saman katon cikin nan nata ta gefen hagu. Wani irin jini jajazir ne ya fallatsa ya fito daga jikinta, da alama jinin nata ma, ya jijjiga sosai, dan kuwa yanda ya fallatsar nan tamkar jira yake yi a huda mishi hanya ya fito. (*PRINCESS TEEMA CE....✍️🔥💘* ) Saboda gajiya da kuma bakar azabar wahalar da ta sha, muryarta baya fita sosai, wani irin wahalallen ihu ta saki wanda sautinsa bai fita ba, cikin bakin azaba da wahala ta sanya hannunta bibbiyu ta dafe cikin nata tare da riƙo kifiyar da suka harbeta da shi ɗin gam tana nishi, lokaci guda fuskarta ta sauya, har wani kumburi ta yi cikin ƙanƙanin lokaci, dama kuma ga na ciki a gefe, sai abin ya haɗu ya yi mata yawa, duk wanda ya kalleta a halin da take a ciki, komai rashin imaninsa matuƙar musulmi ne yasan kalmar shahada, kai ko ba musulmi ba sai ya matsa mata kwallah ba kaɗan ba, domin tana cikin wani irin bakin mawuyacin hali wanda baki ma ba zai iya misilta shi ba. Su kuwa waƴan nan shaiɗanun azzaluman, ko a jikinsu, tamkar ba mutane bane, tamkar babu zuciya a kirazansu, tamkar wasu dafaffun karafuna ne ko ace duwatsu ne a matsayin zukatansu ba zuciya ba, saboda tsantsar zallar madarar rashin Imani dake tattare da su, sai ma ƙoƙarin ciro wani kifiya ɗaya daga cikinsu ya yi domin ya kara sake mata a cikin nata, duk da halin da take ciki basu da niyar raga mata ko su tausaya mata. Cikin fitar hayyaci ta saki wani marayar wahalallen kuka tare da yin baya baya ta faɗa kasan wannan katafaren kogi ko ace teku, dan ko rani ya yi damina ya ɗauke, wannan tekun bata ƙafewa, shi kuma kogi yana iya kafewa a lokacin da ba damuna bane. Faɗawarta kasar wannan dutsen ya yi dai'dai da kecewar ruwan sama kamar da bakin kwarya, ga tsawa da walkiya mai karfin gaske. Tsakanin wannan dutse da kuma ruwan dake a ƙasansa, zai iya kai a kallah 3.6 meter, amma haka ta faɗa kasan, hakan kuma zai kara tabbatar muku da cewa tabbas bata son mutuwa a hannun waƴan nan azzaluman, tabbas tana da bukatar cigaba da rayuwa. Ganin ta faɗa kasan ne yasa suka ƙariso waje ba tare da sun sauƙa daga kan dawakansu ba, babu alamar tsoro, tausayi, imani a tattare dasu, sai ma alamar jarumta tare da taurin zuciya. Ruwan saman na dukansu, haka suka tsaya a cikinsa dan cimma burinsu, sai wani irin numfashi mara daɗin ji dawakan nasu suke fitarwa, su kansu warriors dake a saman dawakan, sai wani numfashin suke yi alamar sun wahala a gudun da suka sha. Suna ƙarisowa ɗaya daga cikinsu ya sauƙa daga saman dokin nasa yana wani irin taku wanda yake nuna cikakken warriors ne, wato (Mayaki) lafiyayye mai jini a jika, duk in ya taka kasa, sai wajen ya amsa, yana da tsawo ga faɗin kirji sosai, sannan ga cikar halittar namiji, wanda yake nuna maka cewa cikakken gwarzon mayaki ne, ya horu ainun. Kasan dutse ya zo ya leƙa a yayin da su kuma sauran suke a saman dawakansu suna jiran su ji me ake ciki. Ko alamarta bai ga ni ba, da ya leƙa, alamu sun nuna ruwa ya tafi da ita, a nasa tunanin, katafaren teku ne wanda ya kai har mararrabar Masarautar su da kuma ƙasar dake makwabtaka da su, ma'ana wannan tekun ya zama kamar itace bordersu kenan. Juyowa ya yi ya nufi bujumin dokinsa yana girgiza masu kai, alamar su je kawai babu wata matsala. Juya kan dawakan nasu suka yi, a guje suka bar wajen suka nufi hanyar da suka fito. Sun ɗan yi gudu mai nisan kafin su zagayo ta kasan dutsen, wajen ruwan kenan, dan su duba ko za su iya ganin wannan matar. Duk da idanunsu ya gane masu faɗawarta kasar tekun, ba gaya masu aka yi ba, gani suka yi, amma basu yarda da cewa ruwa ya tafi da ita ko makamancin haka ba, shi ne yasa suka zagayo dubawa. Warriors (Mayaƙa) guda biyu ne suka sauƙa daga saman dawakansu, suka nufi bakin ruwan dan su duba da kyau da kyau. Kash ko alamar wannan mata babu a wajen, da alama ruwa ya tafi da ita da gaske ne, ga kuma baiwar Allah tana nakuda, ga kifiya a cikinta, ya ilahi ya lalliahi.......😭 Juyawa ɗaya daga cikinsu ya yi ya dubi waƴan da suke akan dawakan. "Da alama fa ruwa ya tafi da ita, ku muje kawai, domin ina da tabbacin ba zata taɓa rayuwa ba, ba'a taɓa wanda ya shiga cikin wannan ruwan ya fita da rai ba! Ko da kifiyar da muka harbeta da shi bai kasheta ba, mugayen dabbobin cikin ruwan nan za su hallakata!". Ya yi maganar cike da nuna jarumta da izza, kalaman nasa akwai kaushi, kuma suna nuni da cewa ya jima a sadaukan yaki, domin kuwa babu tsoro ko ɗar ɗar a tattare da shi, ko ace da su bakiɗaya, babu wani shayi a maganarsa. Ɗaya daga cikin waƴan da suke a kan dawakan ne ya girgiza kai yana faɗin "No, ya zama dole mu nemota, mu fasa cikinta mu ciro abin da yake ciki mu koma da shi masarauta, idan dai muna son rayukanmu da lafiyarmu!!". Kenan hakan yana nufin abin da yake cikin cikin nata suke da buƙata?.........🤔...... Kenan ba niyar kashe abin da yake cikin nata suka yi ba? To in dai haka ne meyasa zata gudun masu? Meyasa ba zata tsaya ta haifa ta basu ba tun da ba kashewa zasu yi ba? Su meyasa suke son karɓar babyn dake a cikin natan? Me zasu yi da shi? Waye ne ma mamallakin cikin nata? Ma'ana uban cikin?. Tab akwai cakwakiya ba kaɗan na. PRINCESS TEEMA ce taku ta amana🤍 Da alama wanda ya yi magana yanzu shi ne babbansu, dan tun da ya fara magana suka wani sunkiyar da kai, suka kara nutsuwa tamkar masu karɓar umarni. Jinjina kai suka yi suna mai nuna alamar sun ji maganarsa sun kuma gamsu. A tare dukkansu suka diro ƙasa daga saman dawakan nasu, ji kake yi dip, dip, dirowar manya. Fara kewaye wajen suka yi, dan su ga ko zasu yi nasarar samun wata makama, dukkansu basu da wani burin da ya wuce ace sun ga wannan matar, kowannansu burinsa ace shi ne ya yi nasarar ganinta ya kuma ciro babyn dake cikin cikin nata ya mayar da shi masarauta, da alama ba karamar kyauta aka sakawa duk wanda ya kawo babyn dake a cikin wannan matar ba, saboda yadda suka zage da iya karfinsu tare da kwarin gwiwa suna aikin nemanta. Amma duk da hakan kuma sun kasa yin gigin yunkurin shiga cikin ruwan, dan sun san zurfin ruwan nan ya wuci tunanin mai tunani. Sun jima suna kewaye a wajen, amma babu komai a cikin ruwan sai manya da kananun jiragen ruwa dake shawagi a can nesa da in da suke, ta tsakiyar ruwan. Daga karshe dai suka hakura ba dan sun so ba, suka haye saman dawakansu, suka kutsa ta cikin wasu dogayen bishiyoyi dake a wajen, suka tafi. *TO FAH, FARKO KENAN DAGA CIKIN LITTAFIN RAWANIN ZALINCIN, KU DAI KASANCE DA ALKALAMIN PRINCESS TEEMA DAN JIN YANDA ZATA KASANCE, KUN DAI JI TA YADDA LABARIN NAMU YA SOMA, NA SAN ZAKU SO JIN AINAHIN KAN LABARI, WACECE WANNAN MATA? MEYASA SUKA KASHETA? SU WAYE SU? MEYASA SUKE SON ABIN DA YAKE A CIKIN CIKINTA? ME ZASU YI DA SHI? ITA MEYASA TA ZAƁI MUTUWA A KAN TA BADA ABIN DA YAKE A CIKIN CIKIN NATA? SHIKENAN YANZU RUWA YA TAFI DA ITA? TA MUTU DA GASKE? GA KIFIYA A CIKINTA SUN HARBETA DA SHI? GA SHI TANA NAKUDA BAIWAR ALLAH. TO DAI MU KASANCE A TARE DAN WARWARE WANNAN SARKAKIYA A TARE, KADA FA KU YI WANI TUNANI TUKUN NAN,🥱 MASU YI MUN PREDICTION ME ZAI FARU A GABA NA LITATTAFINA SAY HII😂 KAMAR YANDA TRIPLETS YA RIKITA MAKU TUNANI, KUKA KASA HASASHEN GABA, TO WANNAN KO FARA HASASHENSA BA ZAKU YI BA, DAN KUWA SALONSA DABAN NE!🔥 AKWAI RIKITA KWAKWALE, MU JE DAI ZUWA, NAYI GABA SAI KUN ZO!!.* *PRINCESS FATEEMAH, PRINCESS TEEMA DUKKA SUNANA NE, DAN NAJI WASU SUNA TAMBAYA💫❤️* To!! To!! To!! Ina masoyana? kai harma da makiyana, ina kuke? Ina masoyan littafin TRIPLETS? Ina masoyan Noorish and Meesha? Ina masoyan babyn baby and his baby? Ina masoyan Heartbeat and Heartbeat? Ina masoyan Sudais and Anaya? Ina masoyan Uncle T and Aafia? Ina masoyan sir Arvin and Maryam?, Ina masoyan Alex and Adiva?, ina masoyan Imran and jelly, Akila and Umaisha, Irfan and Pinky, masoyan Hjy gwaggo mai zamani, duk dai Ku matso da sauri, dan a yau PRINCESS TEEMA ta sake dawo maku da wata zazzafar littafin mai tashin kai, shi wannan ba zazzafa bane ba, tafasa yake yi yana bada tiriri, salonsa daban ne, ina mai tabbatar maku salonsa daban ne, ku my peoples kun sani already ba sai na sake faɗa ba, PRINCESS TEEMA taku mai abin ban mamaki ce, kun san zaku sha mamaki a wannan karon ma, kun san idan nace salonsa daban ne, to fa daban ɗin ne, trust me ya sha banban da sauran labaran da kuka sani, dan fa a shiryena na taho In Sha Allah,🤍 zan tashi kanku in sanya maku hayakin kwakwalwa my peoples, yanzu dai ba QUADRUPLE bane fa😂 kada ku yi mani irin ruɗewar da kuka yi a TRIPLET'S🥺 wannan ina kara gaya maku yasha banban da kowani irin littafi, dan haka kada ki yarda ki bari a baki labari, da a baki ai gara ki bayar, gani ya kori ji, dan haka ki hanzarta maza ki kasance a cikin tafiyata, dan ki gani ba ki ji labari ba👌 ina kara jaddada maku wlh ba zaku taɓa yin danasanin bibiyar wannan littafi mai suna RAWANIN ZALINCI ba In Sha Allah, tabbas zaku yi alfahari da ni fiye da tunaninku, kun sani Alkalamin PRINCESS TEEMA alkalamina mai ilmantarwa, fadakarwa, wa'azantarwa, tare da nishaɗantarwa ne, na san kun san da hakan, dan kune ma kuka shaideni da hakan, bani na faɗa da bakina ba, shaidarku ce wannan, kun shaidani bana rubuta shirme da abubuwan banza a labarina, bana rubuta abin da hankali ba zai ɗauka ba! Bana rubutu kamar tatsuniya! Ina rubutu ne kamar gaske, abin da yake kewaye damu!! Kada dai na cikaku da surutu, mu haɗe daku a cikin littafin RAWANIN ZALINCI page 2 kawai.🔥🌹 Ku daga jin sunan RAWANIN ZALINCI kun san da akwai abubuwa ba kaɗan ba wadda baki ya yi kaɗan ya kwatantasu. *Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 🔥💔𝑨 𝒕𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝒉𝒆𝒂𝒓𝒕𝒔 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒔𝒕𝒐𝒓𝒚, 𝒅𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚 𝒐𝒃𝒔𝒕𝒂𝒄𝒍𝒆, 𝒂𝒏𝒅 𝒓𝒐𝒎𝒂𝒏𝒄𝒆💔🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 29/6/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________2🔥 Baƴan lokaci mai tsawo da tafiyar waƴan nan jiga jigan worries ɗin, har lokacin ruwan sama na cigaba da zuba tamkar da bakin kwarya, ga garin sai kara wani uban duhu na hadari yake yi, tamkar yanzu za'a fara ruwan ma, wani irin walkiya mai matuƙar haske ne yake ta famar walwali a sararin samaniyar, ga wani irin uban rugugin tsawa mai sanya hanjin cikin duk wata halitta razana, sai ka rantse da Allah tsawar nan zata faɗo kasa ne. Da kaɗan da kaɗan haki da nishi yake tasowa daga ɗan nesa da bakin wannan teku, da sauri da sauri nishin yake fita tamkar idan mutun ya rike numfashinsa na ɗan lokacin daga baya ya saki, to a wannan lokaci numfashin zata fita da sauri sauri kuma da karfi karfi, dan hanya da ta samu, haka wannan numfashi da hakin yake tashi!. Kara yawaita wannan numfashin yake yi, daga can nesa da wannan tekun. Wasu ramuka ne masu ɗan zurfi kamar rijiya a ɗan nesa da bakin ruwan, mafiya yawan manyan dajuka irin hakan ana samun irin waɗan nan ramuka sosai, wasu ramukan zaka tarar irin bishiyoyi masu fitowa a kwancen nan suna rufe kofar shigarsu, wasu kuma ganyayyaki da dogayen ciyayine ke cika rakukan, bare yanzu da ya kasance gari na damuna, akwai yelwar ganyayyaki koraye shar a ko'ina a dajin, hakan yasa baka iya ganin wasu ramuka ma sosai. Kwance take a cikin wani katafaren rami mai kama da rijiya, ramin yana da ɗan zurfi kuma yana da faɗi, haka zalika akwai yelwar dogayen ciyayi a cike a ciki wanda suka rufe har baki, muddin mutun yana ciki ba zaka iya ganin shi ba har sai idan shi ya yaye waɗan nan ganyayyaki ya leko kansa waje, sannan ne zaka gan shi. Abin da ya faru shi ne, a lokacin da ta faɗa kasan dutsen ne iska ya kwasheta zuwa cikin ramin, dama kunsan idan kazo faɗawa waje irin wannan akwai igiyar iska mai karfi tamkar ta ruwa da take fisgar mutun, bugu da kari ga iskar ruwan sama mai karfin gaske, Allah ya taimaketa ya kuma ceceta ta yi sa'a a in da ta faɗa cikin ciyayin ba tare da ta ji ciwo ba, ta kuma faɗa ta baya baya ne ba ta gaba ba, Allah ya kare mata cikin nata, ikon Allah kuma bata ji wani jiri ko wani abu makamancin shi ba, sai dai suma da ta yi saboda razana na irin tsayin wajen da ta faɗo ɗin, dama kunsan irin wannan akwai razana zuciya. (Sai dai ni Princess Teema ban yarda da cewa ita ta shiga cikin ramin nan ko iska ya kai ta ba, dan dole akwai ayar tambaya, amma dai bari mu cigaba da bibiyarta mu gani!) Bayan faɗawarta da ɗan tsawon lokaci ne ta farfaɗo daga sumar da ta yi saboda ruwan sama dake zuba yana taɓata, har a lokacin babu alamar hawaye a idanunta ko kaɗan, idanunta suna bushe, da alama ta saba da wahala sosai, zuciyarta ta bushe sosai, dan duk wannan abin da ya faru bata sare ba, bata karaya ba, muradin cigaba da rayuwa ne ziryan a cikin kwayar idanunta, da alama jaruma ce ta gasken gaske! Dan kuwa ko da ta faɗa cikin ramin babu alama na wahala ko nuna gajiya a tattare da ita, tana da taurin zuciya da taurin rai, da alama an gwabza abubuwa da ita ba kaɗan ba, an kara da ita ba kaɗan ba a baya, ga dukkan alamu ba karamar yaki aka buga da ita ba kafin a iya kaita ƙasa ko in ce a iya samun nasarar jefata cikin wannan hali da take a ciki!. Jini ne yake zuba sosai daga cikin nata, sai dai da ikon Allah ta iya cire kifiyar da suka harbeta da shi, kuma ta yi sa'a kifiyar bata soketa sosai ba, da alama wanda ya harbeta da kifiyar duk yadda aka yi akwai wani abin a ƙasa tsakaninta da shi, domin kuwa bai harbeta a in da zata raunata sosai ba, bai harbeta a in da zata mutu ko kifiyar ta yi mata illah ba, kuma da alama kwararren maharbine, yasan kwari da baka sosai, yana da saiti, domin kuwa yadda ya harbeta a gefe guda babu saɓa saiti ko kwana kwana, alamu sun nuna yana sane ya kaucewa harbinta a in da zata iya mutuwa ko ta cutu, wata kila da wata manufa ya aikata hakan, amma lokaci ne zai nuna mana komai. Tattare iya karfinta ta yi tare da miƙewa zaune ta cire alkhabbar jikinta, sai haki take yi sosai, dan a lokaci da ta farfaɗo ta fahimci waɗan nan azzaluman mayakan sun nufo in da take suna nemanta, hakan ne yasa ta rike numfashinta ta hanyar toshe hanci da bakinta da gefen alkyabbar tata, shi ne yasa yanzu take numfashi sama sama, dan sai da ta ji motsin barinsu wajen, sannan ta saki numfashinta, kunga kuwa dole ta yi haki sosai, dan rike numfashi ba wasa ba. Da kyar ta iya zare alkyabbar daga jikinta, a in da ta ɗaure gefen cikin nata da yake zubar da jini da shi, sai buɗe baki take yi alamar kishin ruwa kamar zata mutu. Idan ya jima ya jima sai ta ɗaga kanta sama tare da buɗe baki tana tarar ruwan sama dan ta samu ruwan ya shiga bakinta ta ɗan sha, so abin ku da ruwa idan ba'a indararo yake ba, sam baya zuba sosai duk karfin gudun ruwan sama, amma Alhadulillah ta ɗan sha sosai har ta ji duniya ya ɗan saki mata ta dawo cikin hayyacinta. Ƙoƙarin miƙewa ta yi dan ta fita daga cikin ramin, lokacin ta ji ta ɗan sami sauki bayan wasu mintuna kenan, amma ina ta kasa miƙewa, koda kuwa ta miƙe ba zata iya fita daga cikin ramin ba, saboda yafi tsawonta sosai zurfi, da wannan katon cikin nata kuma ba zata iya buɗe kafafunta ta taka gefe da gefensa dan ta fita ba. Komawa ta yi ta zauna sai a lokacin ta lura da ta kukkuje a hannunta, jajir kuma lallausan fatarta na singalalin hannu zuwa yatsunta duk sai jini yake yi, dama ga fatar luwai luwai da shi, zai yi saurin jin ciwo, ba iya hannu ne kawai ta kukkuje ba, har da kafafunta da sauran sassa na jikinta. Har lokacin bata iya wani numfashin kirki, runtse idanuwanta ta yi a inda ta fara karanto addua'o'i kala kala dan neman taimakon mahaliccinmu, domin kuwa idan ba Allah ba, babu wanda ya isa ya ceceta daga cikin wannan hali da take a ciki. A hankali ruwan sama ya fara cika wannan rami, da yake a gangaren tekun ramin yake, sai ruwan gudu ya fara shigowa. Jin hakan na ruwa na shigowa ne yasa ta yi yunkurin ta sake gwada miƙewa a karo na biyu, amma ina, ko motsin kirki ta kasa yi. Hasbunallahu wani'imal wakil shi ne abin da take ta maimaitawa a cikin zuciyarta. Wani irin azababben murɗa da cikinta ya yi ne yasa bata san lokacin da ta kwallah kara wanda har sai da muryarta ta fita duk dashewa da ta yi ba, da yake ta sha ruwa ne sai muryar tata ta ɗan saki har sauti yana fita. Dafe cikin nata ta yi tana mai cigaba da furta sunan Allah a ranta. Da kaɗan da kaɗan ciwon cikin nata yake karuwa yayinda mararta ya kulle gam yana yi mata wani irin azababben ciwo. Nan take idanuwanta suka kara raina fata a in da a wannan karon suka yi jajir kamar wuta, saboda azaba. Cigaba da murkusoso tayi a wajen tana damke ganyayyakin dake kusa da ita, ta ciza laɓɓa gam da kyawawan fararen hakwaranta tas kamar audiga, tamkar zata fasa laɓɓan nata da hakwaran, idan cikin nata ya murɗa sai ta kara ciza laɓɓanta da karfi, Baiwar Allah, kamar laɓɓan ne suke yi mata laifi. Haka ta yi ta fama na tsawon mintocin da a kallah zai kai arba'in zuwa hamsin, duk ta galabaita ta fita a hayyacinta, duk wasu sauran albarkatun karfi da suka rage mata sun kare, harta ciyayin da take rikewa ma yanzu ta kasa rikewa, saboda babu wani karfi da ya rage a tattare da ita, sunan Allah ma yanzu a iya zuciya kawai take iya furtawa, bakinta banda kerma tamkar wanda ciwon sanyi ya kama babu abin da yake yi, ruwan sama na cigaba da gangarowa izuwa cikin ramin, a yanzu haka yanda take zaune ruwan ya kai mata har zuwa kugunta daga zaunen. Nakuda gadan gadan take yi, da kyar ta samu ta iya cire kayan jikinta, bata rage komai a jikin nata ba, duk ta kwaɓe komai saboda azabar wahala, Baiwar Allah sai take ganin kamar kayan ne suke kara mata zafin da wahala, duk wasu gwala-gwalai tayi wurgi da su gefe guda, ta yi ƙoƙarin ta yaga rigarta ko alkyabbar ta dan ta ɗaure cikin nata in da suka harbeta da kifiyar da kyau, amma ina ta kasa, bata da karfin iya yaga komai, haka ta daure ta hakura tare da dafe wajen kawai. Ganin cewa kamar lokacin mutuwar tane ya yi saboda azaba yasa ta daure cikin wani irin mawuyacin hali ta fara faɗin. "Ya Ubangiji na, kai kaɗai zaka taimaka mun a cikin wannan bakin azabar da nake a ciki, ya Allah dan karfin ikonka ka kawo mun ɗauki cikin gaggawa, ka saukakamun wannan nakuda cikin gaggawa, ya Allah kada ka bari na mutu ba tare da na kalli abin da zan haifa ba, ya Allah ko bayan raina kasa abin da na haifa ya zamana shi ne sanadiyar rugujewar RAWANIN ZALINCI ya tayar da RAWANIN ADALCI da aka kwantar, ya Ubangiji ko na mutu ko ban mutu ba na baka amanar abin da zan haifa, Allah ka kula mun da shi, ka raya mun shi, ya Allah ka bashi basira da kaifin kwakwalwa da tunanin da zai iya tunkarar waɗan nan azzaluman da suka zaɓi ɗaura RAWANIN ZALINCI a kansu, ya Allah ka bashi iko cika mun burina, ya Allah ka sanya mashi tsoronka da kuma aiki da abin da kace, kasa ya zamana Zaki a cikin zakuna mai ruguje ZALINCI ya kafa ADALCI tamkar jinin ABDUL MUTALLAF na hakika, ya Allah kada ka bar mahaifinsa........." Bata kai karshen addu'ar tata ba wani irin azababben nishi ya kwace mata wanda ya sanyata dakatawa daga addu'ar nan take. Babu wani sauran karfi da ya rage mata, dan haka nishin ma bata iya yin shi sosai ba, amma a haka take ta ƙoƙari tana fama, abin gwanin ban tausayi. Sai dai kuma abin mamaki a nan shi ne yadda take faman tana son ganin ta haihu tamkar wadda ta taɓa haihuwa, kamar ta san komai dangane da haihuwa, ga dukkan alamu wannan ba shi ne haihuwarta ta farko ba, idan ma shi ne to tabbas tana da sani sosai a wannan ɓangare, ko kuma likita ce ma. Jim kaɗan ta saki wani nishi wanda ya zo mata da karfinsa, nan take baby ya faɗo cikin wannan ruwa, ya kuma faɗo duniya da kukansa na nuna alamar lafiyayyene. Cikin sauri ta sanya hannu ta ɗauke shi, dan saboda kada ruwan ya kashe mata shi. A saman kirjinta ta manna shi sai kuka yake yi, ita ma sai a lokacin ta sami damar yin kuka sosai. Jim kaɗan bayan faɗowar baby kamar da minti ɗaya wani sabon nakuda ya taso mata gadan gadan, kankame babyn nata ta yi a saman kirjinta tana salati a cikin zuciyarta tare da ciza laɓɓa, murkusoso ta fara yi, tana wani irin numfashi mai matuƙar ban tausayi. (Kai ko ni Princess Teema ina son sanin labarin wannan mata, kuma ina yi mata fatar Allah ya amsa mata addu'arta ta samu mai kwata mata ƴanci kamar yadda ta buƙata😭 irin wannan azabar zalunci haka?😭) Duk kuma wannan wahala da take ciki taki sakin babyn da yake hannunta, haka ta kankame abinta gam. UWA KENAN BA WANDA ZAI IYA YIN HAKAN SAI ITA!. A nakuda na biyu bata wani wahala sosai ba, ba ta ɗauki lokaci ba shi ma sai ga nishi ya zo mata da karfi, nan take baby na biyu ma ya sake faɗowa, ga na farkon sai kuka yake yi mata, da faɗuwar baby kamar da minti ɗaya sai ga mahaifa ya biyo baya. Mahaifa na faɗowa kuma ta nemi duk wani ciwon kaf ta rasa, Allah ya sawwaka mata. A hanzarce ta ɗauko ɗayan babynma ta haɗe su a saman kirjinta, sai dai baby na biyun sam bai yi kuka ba, bai kuma yi motsi ba, tamkar babu rai a jikinsa, bata damu ba, kuma bata ma lura da babayn bai yi kuka ba, saboda kukan na farkon ya toshe mata kunne kuma ya ɗaga mata hankali, dan tana tsoron kada ace waƴan nan dakarun yaki da suka biyota ɗin suna kusa su jiyo kukan jariri su zo su hallakata su karɓe mata baby's su rabasu, saukin abin ma ɗaya da akwai karan zubar ruwan sama na tashi kuma suna cikin rami, so kukan baya tashi zuwa waje sosai. Kasancewar har lokacin ruwan gudu nan na gangarowa cikin ramin ne yasa ruwan ya kai mata har izuwa saman cikinta a yanzu. Ganin hakan ne yasa ta yi yunkurin miƙewa tare da baby's ɗin suna manne a kirjinta. Amma ina sam ta kasa tashi, wani irin kuka ne ta ji ya zo mata, yanzu idan wannan ruwa ya cika ramin ya zasu yi? Ƴaƴanta mutuwa fa zasu yi, abin ku da jarirai mutuwarsu ba zai yi wahala ba. Tuna cewa idan ruwan nan ya cika ramin nan baby's ɗinta mutuwa zasu yi ne yasa ta sake yin yunkurin tashi, amma ina ta kasa, kara ƙanƙame ƴaƴan nata tayi tana ambaton sunan Allah da ya kawo mata ɗauki, ruwa kuma yana ta kara cika rami, ga ruwan sama sai kara karfin zuba yake yi, walkiya da kuma tsawa ya yawaita a sararin samaniya, duniyar ta yi duhu sosai tamkar dare ne. TO KO TA YA YA WANNAN MATA ZATA FITA DA ƳAƳAN NAN NATA⁉️ A hankali ta dawo da kallonta a kan wannan baby daketa zuba kuka tamkar makoshinsa zai ɓalle. Wasu zafafan hawayene ta ji sun fara zubo mata a saman kuncinta gwanin ban tausayi, yanzu shikenan tana ji tana gani baby's nata zasu mutu a hannunta? Ita sam bata damu da kanta ba, burinta kawai ƴaƴanta su rayu, koda kuwa ita zata mutu, dan tana da yakini da kuma sa ran Allah zai amsa mata addu'arta. Ga baby's ɗin kuwa, jajir da su, haskensu ma irin hasken Koreans ne, dukkanninsu idanunsu a rufe gam, kyawawan gaske ne na wuce misali, dogon hancin nan sak irin na mahaifiyar tasu, wannan mai ihun ɗan bakinsa ɗan karamin, bata duba me ta haifa ba, mata ne ko maza or mace da namiji, sai hankali a kwance ake wannan, ita dai ta rungume kayanta, amma fa ba karya kyawawa gaske ne baby's ɗin, bare ma wannan mai tsallah ihun, ɗan bakinsa jajir sosai, da yake yanayin fatarsu kalar madara kalar Koreans, sai jan lips ɗin ta kara bayyana over. Ɗayan baby dai shiru har yanzu bai motsa ba, da alama dai kamar babu rai a jikinsa, shi kuma lips nasa dark purple ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Wannan baby da bai motsa ba gashin kansa launi ne mafi tsada a duniya, wato launin white color, ba irin normal white da kuka sani ba ne, a'a na babyn ya yi wani irin gold white ne a kwance yana ɗaukar idanu, mai azababben kyau da shi, ba kasafai aka cika samun masu irin gashin a duniya ba, sai ɗaiɗaiku, ɗaiɗaikun ma sai ta can ƙasashen AREWACIN DUNIYA, ta yanki Asia ta Arewa kenan, kuma a bincike ya nuna mafiya yawan masu gold white hair nan, ba karamar baiwa da basira ke garesu ba, amma sai dai kash baby baya motsi, yaki ya motsa, babu rai a jikinsa. Ɗayan baby dake ta tsallah kukan kuwa, gashin kansa bakinkirin ne mai bala'in tsantsin gaske, ya yi tamkar an kifa mishi hula ne a kan nasa, tsabar bakin gashin nasa har ya yi tamkar dark blue, yana wani irin kyalli na daban, ga gashin nasu yar'yar sai tsawo ba cika, kana iya ganin farin fatar kansu, saboda rashin cikar gashin, tsawo kuma ya sauko musu har gaban goshinsu, ya kusa rufe masu idanu. A takaice dai dukkansu biyu suna da tsananin kyau na wuce misali. A hankali hankali fa ruwan nan sai haurowa sama yake yi, yanzu ya fara taɓa mata baby's ɗin nata. Kara haurar da su saman wajen shoulders ɗinta ta yi, tana mai cigaba da kuka tare da ambato sunan Allah da ya kawo mata ɗauki. Bata gaji ba, haka take ta kokarin miƙewa dan ta ceci ƴaƴanta, amma duk wasu gaɓoɓi na jikinta sunki yarda su bata haɗin kai wajen ta iya miƙewa, kada ku manta tana da ciwo a cikinta na kifiya da aka harbeta, ga kuma haihuwa, ai ta auna babban arziki ma da har yanzu take cikin hayyacinta, har yanzu tana karkashin kariyar Ubangiji dan shi kawai take ambata a baki da zucinta, idan kuma ka riki Allah to wlh wani abin idan Ubangiji ya hukunta a kanka, sai mutane su rinƙa kallon kamar tsafi ko asiri, saboda irin baiwar da kuma iko na mahaliccinmu, babu abin da ya fi karfin Allah a duniyar nan. WANNAN ABIN DA SANYA MUTUN CIKIN TASHIN HANKALI YAKE... *Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 🔥💔𝑨 𝒕𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝒉𝒆𝒂𝒓𝒕𝒔 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒔𝒕𝒐𝒓𝒚, 𝒅𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚 𝒐𝒃𝒔𝒕𝒂𝒄𝒍𝒆, 𝒂𝒏𝒅 𝒓𝒐𝒎𝒂𝒏𝒄𝒆💔🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 30/6/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ *Ga waɗan da basu sani ba, ni ina da tsayayyen lokaci na yin posting nawa, 5:30 dai'dai nake yin posting na littafina, duk wanda yake a grp nawa lokacin TRIPLETS ya sani, sai dai idan matsalar network aka samu, amma 5:30 na yamma dai'dai nake update 💘* E____________3🔥 Tana a cikin wannan hali Allah ya aiko mata wani bawan Allah, da alama maharbine, matashin saurayi ne mai jini a jika, yana da tsawo sosai, ga faffaɗar kirjinsa kamar wani zaki, jajir da shi kamar tsada, a shekaru ba zai wuce 15 years ba, dakakken namiji ne, dan daga ganin irin yanayin tsayuwar da ya yi a bakin ramin, alamu sun nuna ba rago bane, namiji ne sosai, ko da yake dama rago ba zai iya kasancewa a cikin irin wannan daji ba, duk wanda ka gani a cikinta to jarumta ta ratsa jinin jikinsa sosai!. Yana sanye da irin takalmar nan na maharba mai kama da waterproof shoe a kafafunsa, irin kayan nan da ake saƙawa da zare da audiga ne a jikinsa, wandoce mai matuƙar kyau da aka saƙata da audiga, sakar hannu ce mai kyau, ta saƙu sosai, wandon launin brown color ce, ta sama riga ce mai karamar hannu launin white color, ita ma ta sakar ce, yana sanye da hular sanyi ta saka a kansa, hular ta kasance brown color kalar wandonsa, daga kugunsa ya ɗaura wata kyakkyawar belt launin white color kalar rigarsa, ita ma ta sakar ce. Kayan sun yi matuƙar yi mashi kyau sosai da sosai, ga su tsab tsab, babu datti ko kaɗan, tamkar yanzu ya sakosu, kamar ba maharbi bane ba, da alama yana da matuƙar tsabta sosai, dan babu alamar kazanta, datti a jikinsa. Kyakyawan gaske ne wannan matashi, kamar ba mutun ba kuma, jajir da shi, kalar fatarsa tamkar madara, tamkar bai taɓa fita rana ba, skin nasa har wani kyalli take yi, tamkar wadda ya girma a cikin A.c da kuma rayuwa a manya manyan jiga jigan gidajen manyan muryoyi a duniya, sam bai yi kalar wannan dajin ba ko miskala zarratin. Yana da doguwar hanci mai matuƙar kyau, hancin nasa bata yi irin doguwa zud ɗin nan ba, ɗan dai'dai mai matuƙar ɗaukar hankali, kasancewarsa fari kal da shi, sai yasa pink lips nasa suka kara bayyana sosai, tamkar lips ɗin mace, har wani kyalli suke yi, saboda ruwan sama da ya jiƙasu, bakin nasa ɗan karami, yana da dara daran idanu farare kal kal kamar audiga, bakin cikin kwayar idanun nasa kuwa, ya yi bakin kirin da shi, irin bakin nan da zaku ga har wani kyalli yake yi, saboda ya yi baki siɗif, sexy eyes ke gare shi, yana da gashin gera mai yawa sosai, a cike suke, sai dai suna kwance luf, saboda tsantsi, ga wani bakinkirin ɗin saje ɗan dai'dai a face ɗin nasa kamar babban mutun, face ɗinsa ya kasance kamar egg face, wato fuska mai ɗan tsawo ba cancan ba, face ɗin nasa kuma tana da cika, ba'a rame yake ba, alamar ya ci ya ƙoshi, sam babu alamar yunwa a tattare da shi, daga yanayin zubin halittarsa ma sam bai yi kala da wannan dajin ba, yafi kama ne da ƴaƴan manya manyan mutane waɗan da maƙudan dukiya suke yi masu mubaya'a, hakika wannan matashin kyakkyawan gaske ne, kuma babu tsoro ko miskala zarratin a cikin waɗan nan dara daran idanuwan nasa, dan a bushe suke, zara zaran eyeslashes nasa nan a tsai tsaye suke, alamar babu tsoron da yake ji. Yana rike da wata iriyar lema wadda babu irinta a yankin nan, ƙasashen Arewacin duniya ne suke amfani da irinta, lema ce wadda aka kerata da itace, abin gwanin ban mamaki sosai, komai na jikinsa ba irin na yau da kullum bane, sabbin kere kere ne a zamanin nan. Yana wucewa ne yaji kukan jariri a wajen wannan ramin, shi ne ya ƙariso wajen dan ya duba, yana leƙa ramin ya gansu. A hanzarce ya kara waro dara daran idanuwansa yana kallonta, kamar mai tsoron juyawa ya juyo a hankali yana kallon gabas da yamma gudu da arewa, abin ya bashi mamaki ne, mace da yara a cikin wannan daji kuma cikin ramin nan haka, dole ya yi waige waige ko zai ga wani abin, fuskarsa a cike fal da mamakin ganinsu. Ko da ya jujjuya bai ga alamar mutun ko wani abin mai rai a wajen ba, hakan yasa ya dawo da kallonsa a kanta. Duƙawa a saman gwiwowinsa ya yi tare da miƙa mata hannunsa a kan ta miƙo mashi baby's ɗin, ga ruwan sama na zuba mashi a kansa sosai, dan ganinsu yasa ya saki lemar hannun nasa ya faɗi kasa ba tare da ya lura bama, sun bashi tausayi ne ainun ga mamaki da al'ajabin abin. Da farko taki yarda ta miƙa mashi baby's ɗin, sai da ta kalli da gaske ruwa zai cika ramin, dan izuwa yanzu ruwan ya hauro mata har izuwa kirjinta ta sama, sam ba'a iya ganin breast nata, ruwa ya rufe, hakan ne yasa ta yi hanzarin miƙa mashi wannan mai tsallara ihun. Karɓa ya yi tare da ɗan ɗago jikinsa daga kan ramin kaɗan. Sam bai iya rike jariri ba, ga kuma cibiya a jikin babyn ba'a yanke ba. Haka ya ɗan kwantar da shi a gefe, sannan ya cire rigar jikinsa ya nannaɗo babyn a ciki, duk da rigar tasa ita ma a jike take, amma tafi babu gaskiya. Kwantar da babyn a gefe ya yi tare da komawa ya kifa jikinsa a bakin ramin, dan ya karɓi ɗayan babyn. Yana miƙa mata hannu ta yi maza ta miƙa mashi babyn, karɓa ya yi tare da ɗago da jikinsa, ya haɗe baby's ɗin duk ya kudundunesu a cikin rigar tasa, sannan ya mike da su tsaye daga wajen, ya rungumosu sosai a jikinsa. Ƙasan wata katuwar bishiyar mangoro ya je ya kwantar da baby's ɗin, Allah sarki wannan baby mai tsallara ihun shi ma ya yi shiru a yanzu, da alama dama sanyin ruwan saman nan ne tasa yake wannan uban kuka haka, shi kuma ɗayan dai shiru bai motsa ba har wa yau. Ganyen bishiyar manya manyan ya karyo tare da shunfuɗawa a ƙasa kamar katifa, sannan ya ɗaura baby's ɗin a kai, ya kuma karyo wasu ganye ya rufa masu a saman kayan nasa da ya kudundunesu. Da sauri ya juya ya koma wajen ramin, a lokacin ita kuma matar ta yi iya ka bakin ƙoƙarinta ta maida kayanta jikinta da ta cire, ta duka tamkar mai yin ruku'e daga zaune tana ƙoƙarin laluɓar sarkokinta da sauran abubuwanta a cikin ruwan, da alama abubuwan suna da matuƙar muhimmanci sosai kasancewarsu a tattare da ita, shiyasa take ta ƙoƙarin laluɓarsu a cikin ruwan. Yana zuwa ya yi mata magana a kan ta kawo hannunta bari ya fito da ita, ya yi maganar ce da wata harshe na daban, hakan yana nufin yana da yare a bakinsa kenan. Ɗagowa ta yi daga sunkuyen da take, sam bata san me ya faɗa ba, saboda bata jin yarensa, kura mashi idanu kawai ta yi tana kallonsa, sai da ta ga ya miƙo mata hannunsa ne yasa ta gane abin da yake nufi kenan. Kin miƙa mashi hannunta ta yi, saboda wani dalili nata da bata bayyana ba. Sake yi mata magana ya yi a kan ta kawo hannunta ruwan nan yana karuwa ne. Nan ma bin shi da idanu kawai ta yi, dan bata gane ko kalma ɗaya da ya faɗa ba. Da yaga hakan, sai ya miƙe ya nufi wajen manyan itatuwa dake wajen, zabgegiyar itaciya ɗanya shakaf ya karyo, sannan ya dawo bakin ramin. Zura mata itaciyar ya yi a cikin ramin. Ba musu ta kama itaciyar shi kuma ya ja, da kyar ya iya fitar da ita, alamu sun nuna hannunta ne bata son ya taɓa, kome dalili? Mu je dai zuwa, koma menene zamu ji. A bakin ramin ta zauna tare da dafe cikinta tana numfashi da kyar da kyar kamar zata mutu. Tsugunnawa a kusa da ita ta gabanta ya yi yana tambayarta meyake damunta?. Sam bata jin yaren da yake yi mata, bata gane komai ba. Ganin bata bashi amsa bane yasa ya fahimci bata jin yarensa ne, dan haka sai ya ce mata "Are you hearing English?". Ya yi maganar a hankali, yana da sayayyar murya sosai. Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar tana ji, tana ciza laɓɓanta saboda azabar da take ji. "Okey what i said here is what's wrong with you? Is there any problem?". Ya yi maganar cikin sanyin murya sosai, kuma daga yanayinsa ya nuna shi mutun ne da sam sam bai da yawan magana, so silent yake, face nasa ta nuna ba mutun ne mai son hayaniya ba. Da hannu ta nuna mashi cikinta dake ta faman zubar da jini. Kai kallonsa wajen da take nuna mashi ɗin ya yi. A dubu ya zaro waɗan nan dara daran fararen idanuwan nasa yana kallon yadda kifiyar ta soketa, sam bai lura ba time da ya jawota ta fito daga cikin ramin. Hannu ya kai zai taɓa wajen, cikin sauri ta ɗan ja baya, hakan yasa ya ce mata to ta lallaɓa su je wajen da ya kwantar mata da yaranta, bari ya ciro ganye ya yi mata rumfa da shi, sannan sai ya kawo mata maganin kifiya. Kasa tashi ta yi, duk wasu gaɓɓai a jikinta sunki bata haɗin kai wajen ta ɗan miƙe, duk sun galabaita, hakan yasa ta fara ja a kasan kawai. Da kyar da suɗin goshi suka isa wajen. Tana zuwa wajen ta kwanta tare da sake dukkanin ilahirin jikinta ta bi lafiyar kasa tana mai da numfashi. Kamar yanda ya faɗa, ganyayyaki dayawa haɗe da itacuwa ya karyo, ya zo ya yi masu rumfa kamar ɗakin bukka, da alama ya jima a wannan dajin, dan ga dukkan alamu yasan duk wasu dabaru na zaman daji ta yadda wata dabba bazata cutar da mazaunan wajen ba. Yana ƙoƙarin yi mata magana kamar saukar aradu wata zazzaƙar murya mai sautin amo mai matuƙar daɗi ta karaɗe kewayen wajen da faɗin "KAMRAN! KAMRAN where are you". Muryar ta kasance muryar mace ce mai zaƙi. Da sauri ya wuce yana mai buɗe muryarsa shi ma da karfi yana faɗin "Here I am, one minute am coming". Daga haka ba'a sake yin magana ba, shi ma bai sake yin magana ba ya yi maza ya kutsa ta cikin wasu dogayen bishiyoyin ɓaure dake fuskantar gabas. Ita kuwa wannan mata tun da ta kwanta ta lumshe idanu, bata sake motsawa ba, suma baby's ɗin nata basu sake motsawa ba, shi ma mai tsallara kuka ɗazun ya yi shiru, da alama ya yi barci ne, ko kuma dai wani abin, amma fa ɗayan babyn nan sam bai motsa ba, da alama dai babu rai ɗin ne da gaske a tattare da shi. Haka har ruwan saman nan ya ɗauke, gari ta washe, ta yi shar shar, amma har yanzu daga baby's har maman baby's babu wanda ya sake motsawa a cikinsu, shi kuma wadda ya taimaka masu, wato wadda aka kira da KAMRAN, har yanzu bai sake dawowa wajen ba, tun da ya tafi shiru kake ji. After some hours. A hankali maman baby's ɗin ta fara motsawa, gabaɗaya jikinta ya yi mata wani irin muguwar nauyi, da kyar ta iya waro idanuwanta da suke kunbure sun yi luhu luhu, saboda azaba da ta sha. Tana waro idanuwanta kai tsaye sai a saman ganyayyakin da KAMRAN ya yi masu rumfa kamar bukka, a lokacin ruwan sama ta ɗauke cak, gari har ta ɗan fara yin haske. A hankali tamkar mai jin tsoron wani abin ta kai hannunta ɗaya a saman cikinta in da kifiyar nan ta caketa, ga mamakinta sai ta ji wajen a ɗaure, tamkar an sanya abune an ɗaure mata, kara waro idanuwanta sosai waje ta yi, dan ta tabbatar wa da kanta ba mafarki take yi ba. Tabbas ba mafarki bane, magani aka sanya mata a wajen, sannan aka ɗaure mata wajen da wata farar kyakkyawar kyalle mai matukar kyan gaske, shi ma kyallen ta sakar audiga ce, kuma sakar hannu ce, kamar dai kayan jikin KAMRAN. Da yake akwai sauran jini dake fitowa kaɗan kaɗan a wajen, sai ta ɓata wannan farar kyalle da aka sanya mata, kyallen ta yi ja ta ɓaci da jinin. Yunƙurawa ta yi domin ta mike, sai dai ina, ko motsawa ba zata iya yi ba, gabaɗaya gaɓɓan jikinta sun yi la'asar over, sun yi laushi, ga wani irin azababben ciwo da take ji a ko'ina a jikinta, mararta ma ciwo yake yi mata. Ganin ba zata iya miƙewa bane yasa ta hakura ta kwanta shiru tare da ɗan juyo da kanta gefen da yaranta suke kwance, dan ta kalli shin a ina suke ne?. Sun kasance ne a cikin wani ɗaki kamar bukka wanda aka saƙa shi da ganye and itace, kamar dai bukkar rugar Fulani, sai dai wannan ya sha banban da bukkar ruga, domin sakar ma ba iri ɗaya bace, wannan daban take, kwararrun masu fikira ne suka saƙa shi. Ga wasu kwarya masu kyau da ɗaukar hankali a kusa da ita, anyiwa kwaryar zanen kwalliya mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, baby's nata suna kudundune a cikin wani kyakkyawan towels farare kal kal da aka saƙa da audiga, ga kuma wani katon kasko irin na taɓo da ake yin nan, an cika kaskon da garwashin wuta a cikinsa, wutar ta yi jajir, hakan yasa gabaɗaya wajen ya ɗauki ɗimi, kamar ba yanzu aka gama sharara ruwan sama mai uban sanyi ba, da alama suma baby's ɗin wannan ɗimin yasa suka yi shiru suna barci, dama shi ɗayan baby already kunsan bai motsa ba tun da aka haifesu. Daga gefen baby's ɗin kuma wasu kyawawan towels na sakar ce guda biyu da aka ajiye masu bacin wanda aka lulluɓesu da shi, sannan da alama an yi wa baby's ɗin wanka ko kuma dai an goge masu jiki, kuma an yanke masu cibiya. To fa waye kuma ya yi masu dukka wannan hidimar?. Da kyar ta iya motsa hannunta ta ɗan buɗe baby guda ɗaya. Kara waro idanuwanta waje sosai ta yi, mamaki ne ya lulluɓeta na ganin anyankewa babyn cibiya, ga jikinsu babu datti ko kaɗan, duk da cewa dama already ruwan sama ya taɓasu. Zuba masu idanu ta yi da mamaki fal a cike a cikin ranta, da alama ba ita kaɗai aka yi wa magani ba, har da baby's ɗin aka yi wa magani, dan kuwa ga jikinsu nan duk an murje masu ganye, sun yi kore shar, ganyen magani kuma irin na cikin wannan kwarya da yake a kusa da ita ɗin ne. Jin yanda wajen yake da ɗimi duk da ruwan saman da aka yi ne yasa ta fara jujjuya idanuwanta tana bin ko'ina da kallo daga kwance, ta yi mamakin jin wannan daddaɗar ɗimin a wajen, sai dai bata iya hango kaskon wutar, saboda yana ta wajajen kafafunta ta kofar bukkar ne, kallonta ba zai iya kaiwa can ba daga kwance, sai ta miƙe. A hankali ta lumshe idanuwanta tana mai tsananta godiyarta ga Allah a cikin zuciyarta, yau Allah ya ceceta ita da baby's ɗinta, koma waye ya yi mata wannan hidima ta sanya wa ranta cewa bawan Allah ne from nowhere Allah ya aiko masu. To bari mu kutsa cikin dajin, dan muga menene a cikinta, wata kila kafin mu dawo Maman ƴan biyu ta kara samun sauki. Kamar dai yadda kuka sani ne, daji ne mai matuƙar girman gaske wanda kallon iyakarsa ma ba abu bane mai yiwu wa sam sam, sannan akwai haɗari sosai a cikinsa, sai dai haɗarin ta wasu ɓangarori daga cikin dajin ne yake, ba dukka ko'ina bane, muggan namun dawan ba'a ko'ina suke zama ba, suna da ɓangarorin da suke zama a cikin dajin, already kunsa kowani dabba da irin wajen da yake yin rayuwa, ko a daji ba'a ko'ina suke zama ba, sai wajen da ya yi dai'dai da rayuwarsu. Saman wani katafaren tsauni, a hankali wani hayaki yake tashi daga wajen, da alama akwai mutane a wajen, saboda su dai namun dawa basu shiri da wuta bare hayaki, sam basu so, basu zama ma a wajen da aka kunna wuta, sai dai idan ɗauresu a wajen aka yi babu yadda zasu yi, amma basu son wuta ko ya take. Sannu a hankali wannan yanaki yake fitowa, kuma bashi da yawa, sannan hayaki ne mai haske ba irin bakin hayakin nan ba, wannan tsauni yana nesa daga in da maman waɗan nan ƴan biyun take, sai dai idan ka tsaya a samanta ka yi magana da karfi, to duk wanda yake kewayen wannan yanki zai jika, saboda dajin tana amsakuwa. Dai'dai tsakiyar saman wannan tsauni ta gabas ta sakiya, wani jibgegen dutse ne a wajen, yana da girma da kuma faɗi, sannan yana nan tamkar kogo, dan yana da zurfi da faɗi cikinsa, daga ta cikinsa wannan hayaki yake fitowa, kofar shiga cikinsa kuwa, ɗan ƙaramin ne wanda babban abu ba zai iya shiga ba, idan ɗan Adam ya cika ƙiba sosai, to ba zai iya wucewa ta kofar ba, dan bata da girma, sannan akwai wata ƙaramar dutse mai kauri da ake rufe ɗan bakin kogon da shi, alama dai ya nuna wannan ƙaramin dutsen shi ne kofar kogon. Tamkar gida haka cikin wannan kogon yake, an yi ciki da parlour da wani ɗaki na daban, duk kuma jinin anyisu ne da taɓo, ma'ana an gine cikin kogon, kasancewar yana da girma sosai cikin kogon, sai ya bada abin da ake so, ginin nasu kuma ya fita sosai, duk da cewa da taɓo suka yi shi, ga kuma itatuwan bambu da suka yi amfani da su wajen kawata kujerun zama na saka, tamkar gado haka suka yi kujerun zamar, ma'ana babu Head na kujerun, iya wajen zama ne kawai, haka zalika beds dake a cikin bedrooms guda biyun, dukka da itacen bambu da kuma ganyen ciyawa mai kyau aka yi su, shi ainahin gadon anyi shi da itacen, katifa kuma da ciyawan harawa, sai dai ya saƙu da kyau da kyau ba karya, ya yi matuƙar kyau kuma, an shinfiɗe bed's ɗin da bedsheet na sakar audiga ta hannu, kunsan sakar hannu da masifar kyau, ga shi bedsheet ɗin an yi mai two color, sai abin ya kawata idanuwar mai kallo sosai, ga ɗaukar hankali, wasu kyawawan smalls pillows ne jere a saman beds ɗin dukka ɗakuna biyun, suma pillows ɗin suna sanye ne a cikin rigarsu irin kalar bedsheet ɗin, sun kara kawata beds ɗin sosai. Komai da yake a cikin wannan kogo da itacen bambu da kuma taɓo aka kyara su, tukunyaye da kaskon wuta duk na taɓo ne, da alama makyarin waɗan nan abubuwa mutun ne mai kaifin basira da ƙwaƙwalwa sosai, dan harda kwanon cin abinci da aka yi da itace, ga su cups, tamkar kowani gida dai, haka suke, harda yi wa kwanikan nasu design kala kala da wani jar kala, sun kuma yi bala'in kyau ba kaɗan ba. Ƙasar wannan kogon kuwa ya kasance itacen bambu ne suka yi shi kamar tiles, ya kawata wajen sosai, abin da zai kara burgeku da wannan gida nasu shi ne, yadda ya kasance kowane kofar ɗaki da labulen da aka saka da audiga, very talented people's ne suke zaune a wannan waje, dan komai dake wajen basira ce ziryan ta yi aiki a kansa ba kaɗan ba, da akwai ramuka da suka ɗan huhhuda, saboda samun haske da kuma iska a cikin ƙogan, ramukan suna da yawa, amma basu da girma, kanana aka hudasu, kuma haske da iska suna shiga sosai, dan kunsan shi iska baya rena hanyar wucewa, abin kara ɗaukar hankali ma cikin wannan gida shi ne, harda dining table suke da shi a parlourn nasu, dining ɗin shi ma da itacen bambu suka yi shi, ya saku sosai, ya yi matuƙar kawata wajen sosai da sosai. Ko'ina tsab yake tamkar babu kowa da yake amfani da wajen, sai kamshin kayan itatuwa da yake tashi a wajen. Kwance a saman ƴar kyakkyawar bed nasa KAMRAN yake, a nasa bedroom ɗin kenan, hannunsa na rike da wani littafi mai matuƙar kyau yana karantawa, da alama littafin tarihi ne, sam ba kayan ɗazun bane a jikinsa, ya canza izuwa wasu masu kyau, suma dukka na tsakar audigan ne, still da akwai hular sanyi a kansa, kyakyawar fuskar nan tasa sai glowing take yi, tamkar ya shafa baby oil, sai ya kara wani irin kyau abinsa. A zahiri idan ka kalle shi karatun littafin yake yi, amma kuma baɗininsa ba ita yake yi ba, ya rike littafin ne kawai, hankalinsa yana can wani wajen. "Kamran the food is ready, am waiting for you". Wannan zazzaƙar murya ta ɗazun da ta kira shi ne time da yake wajen maman ƴan biyu, ita ce ta sake yin wannan magana a yanzu. "Mamma am okey, I can't eat anything today". Ya faɗa yana ɗaure fuska, tamkar Mamman tasa tana a gabansa. A hanzarce aka yaye labulen dake kofar bedroom ɗin nasa aka shigo. Kyakkyawar mace ce kyakkyawar gaske, doguwa sosai, gata ƴar caras cas, fara kal da ita kamar madara, launin fatarta ya banbanta da tasa sosai, saboda ta fishi haske nesa ba kusa ba, ga hanci har baka, da gani ba tambaya kasan mahaifiyarsa ce, saboda tsananin kamanceceniya da take a saman fuskokinsu, itama idanuwanta dara dara farare kal da su, sai dai ita kwayar idanuwanta ba baki irin nasa bane ba, ya ɗan yi brown mai haske, sai ya yi kamar foreign tiger eyes, tana da tsananin kyau da abin da ake cewa farin jini, da ganinta ba tambaya kasan jarumace sosai, dan kuwa waɗan nan idanuwan nata babu alamar tsoro ko miskala zarratin a tattare da ita, macece mai kamar maza, jarumar gaske, da alama a wajenta ya gaji jarumta. Ita ma tana sanye da doguwar riga ta saka launin white color mai matuƙar kyau. "Kamran what are you saying? You can't eat anything today? why?". Ta faɗa a ruɗe, tana magana dimple nata suna lotsawa, ga dimple ɗin nata gwanin ban sha'awa, dan bai yi irin zurfin nan sosai ba, ɗan daidai mai ɗaukar hankali. Tana da sayayyar murya irin tasa, da ga ji maganarta kasan a wajenta ya gado cool voice. "Mamma yes i can't eat anything today until you tell me the reason why you don't like people? Why you don't want me to go out? Everyday you're try to hidden our life, ni gaskiya am tied, kuma ni ina son in taimaki mutane, meyasa ke baki so? Haka last time wancan mutumin da Tiger can ta cinye, kika ki yarda mu taimaka mashi, muna ji muna gani wannan bakar damusa ta hallaka shi har lahira, why?". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa zaune yana mai rufe littafin da yake a hannunsa, ya ajiye a saman waɗan nan kananan pillows ɗin. Ƙarisowa cikin ɗakin ta yi, jiki a sanyaye ta zauna a saman bed ɗin, hannu ta kai ta fara shafa lallausan kumatunsa da yake kamar ta jarirai saboda laushi. A nutse ta fara magana. "Kamran you know that i can't do something to hot you or na takurawa rayuwarka ko? Duk abin da zan yi i can do it because of your happiness ne my son, mutane ba abin yarda bane, don't trust anyone in your life, just trust yourself only". "Amma kuma Mamma wasu mutanen ai ba mugaye bane ba, wannan mata da na gaya maki fa wlh she's...........". Katse mashi maganar tasa ta yi ta hanyar ɗaga mashi hannu. "Kamran! Kowani mutun da kake gani a rayuwar nan to wlh ba abin yarda bane, suffar tausayi ita ce suffa mafi haɗari a duniya, wanda kuma ni ba zan taɓa yarda da ita ba, duk wanda zai zo mun da fuskar tausayi dan na tausaya mashi, ba zan taɓa yarda da hakan ba". "Mamma koda kuwa da gaske yake yi yana da bukatar taimakon ki?". Ɗaure fuska sosai ta yi kafin ta ce. "Yes Kamran, ina son ka sani shi fa mugu bashi da kama, mugu yana yin galaba a kan mutun ne ta hanyar suffar tausayi, tabbas akwai masu bukatar a tausaya masu ɗin, amma kuma wake ɗaya yake ɓata gari, tabbas na tsani na ga mutun ya zo mun da suffar ban tausayi, dan haka na yanke hukunci, mu ba zamu taɓa taimakon kowa ba a rayuwarmu, mu kaɗai zamu zauna, ko da kuwa me zai faru!!". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa da nufin ta fice daga cikin ɗakin, da alama ranta ya ɓaci sosai, dan kuwa gabaɗaya yanayin face nata ya sauya. Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa. "Mamma but why? Ki gaya mun dalilinki na ji, if the reason is so......". Katse shi ta yi ta hanyar cewa. "Kamran ni ce nan na haifeka ba kai ka haifeni ba, babu wani dalili, bani da wata dalilin da zan ce maka ga shi da yasa bana son kowa ya raɓemu, kada ka sake jefo mun wata tambayar kuma!!". Tana kai karshen maganar ta fice daga cikin ɗakin da sauri. Idan ransa ya yi dubu, to ya ɓaci, meyasa Mammansa take yin hakan ne? Furzar da iska mai zafi daga bakinsa ya yi yana wani huci. Wani irin dunƙule hannunsa ya yi tare da kaiwa jikin bangon kogon dutsen wani irin naushi. Nan take hannun nasa ta fashe sosai, saboda dutsen yana da masifar karfi. Sake kaiwa dutsen naushi a karo na biyu ya yi, kuma dukka da wannan hannu da ta fashe a karon farko, ga jini har ya fara malala, jajir jinin nasa, tamkar ba jikinsa bane ba, tamkar baya jin zafi haka ya sake kaiwa dutsen naushi a karo na uku, yana yi yana huci kamar wani kububuwa. Da gudu Mamma ta dawo cikin ɗakin, a ruɗe take faɗin. "Kamran ka fara halin nan naka ko? Ka bari mana". Sake dunƙule hannun nasa ya yi a karo na ukun zai kai naushi wa bangon. A dubu ɗari ta rike hannun nasa tana faɗin. "Ya isa haka mana". Ƙoƙarin kwace hannun nasa ya fara yi, sai dai ina ya kasa kwacewa. Da hannu ɗaya ta rike shi, amma ya kasa kwacewa, dan Mamma fa jarumar macece ba raguwa ba, akwaita da karfi sosai. Ganin ba zai iya kwace hannun nasa bane yasa ya yi ƙoƙarin miƙewa ya fice mata daga cikin ɗakin. Riƙo shi ta yi da kyau tana faɗin. "Haba my son, what's all this meaning for?". Ta yi maganar cikin sanyin murya. Sai huci yake yi yaki ya yi magana, ga hannunsa dake ta famar malalar da jini, yatsarsa ta tsakiyar nan ma kamar ta karye ne ko dai ta samu targaɗe, domin kuwa gata ta kumbura suntum. Rungumarsa Mamman ta yi tana ɗan bubbuga bayansa alamar rarrashi, kamar zata yi kuka take faɗin. "Kamran wai sai yaushe zaka dai'na wannan halin naka ne? Meyasa kake son ganina a cikin ɓacin rai ne? Meyasa kake damuwa da al'umma? Meyasa kullum akan jama'a muke samun saɓani da kai? Baka taɓa ɓata mun ba, baka taɓa kin bin maganata ba, baka yi mun musu, baka ce mun a'a, komai nace to kawai kake cewa, but why a wannan karon ma a kan jama'a ba zaka ce mun to ba? Why?". Har wa lokacin bai iya ce mata ko uppan ba, bayan wannan huci da yake yi babu wani abin kuma da yake fitowa daga garesa, ya dai kwantar da kansa shiru a saman shoulder ɗinta, ya lumshe idanuwansa kamar mai jin barci, zuciyarsa ce take tafasa mashi tamkar an ɗaura dalma a wuta, hakan ce ma ta hana shi iya buɗe baki ya yi magana, wannan abin yana mugun damunsa, yana kuma taɓa mashi zuciya, meyasa Mammarsa bata son ya yi taimako? Ga shi dai tana da kyakkyawar zuciya a gare shi, amma kuma ko mutuwa a gabanta wani bare yake yi ba zata taimaka mashi ba, kuma ba zata taɓa bari shi ya taimaka mashi ba, to meyasa? Ga shi shi kuma Allah ya yi shi mutun ne mai bala'in son taimako, baya burin yaga wani bawa a cikin damuwa bai taimaka mashi ba, amma Mamma sam bata son hakan, ko zai yi taimako sai dai y yi a ɓoye kada ta sani, idan ta sani sai sun samu saɓani sosai. Nasan zaku so jin wanenen KAMRAN, to ku kasa kunne kuji ɗan kaɗan daga cikin labarin wanene shi. Su dai mazauna wannan dajin ne na tsawon shekaru, kusan ma za'a ce a nan aka haifi Kamran ɗin, su biyu kawai suke yin rayuwarsu, daga shi sai Mamma, suna rayuwa ne cike da so da kaunar juna, Mamma tana bala'in kaunar ɗan nata, Mamma mace ce jaruma mai tafasasshiyar jini, bata da tsoro ko kaɗan, a shekarun baya lokacin da Kamran yake ƙarami har faɗa da damusa ta taɓa yi, Allah ya bata nasara kuma ta kashe damusar, sam bata san menene tsoro ba, bugu da kari mace ce mai magana guda ɗaya, tana da tsayawa a kan maganarta kuma, duk wuya duk daɗi baya sa Mamma ta juya baya a kan abin da ta yi niyya, abin ban mamaki tare da ban sha'awa a rayuwar tasu kuma shi ne, Mamma mace ce mai bala'in ilimi ga tarin baiwa da Allah ya yi mata, duk wasu abubuwan da yake a cikin gidan ita ta kera kayanta, a matakin karatu ko mai degree ba zai nuna mata komai ba, tana karanta da Kamran sosai, a yanzu yana matakin Ss 2 a makarantar tata da dake karantar da shi, yana da ilimi na wuce misali, ga baiwa da ya gada daga wajen Mammar tasa, sai dai kuma yafi Mamma zuciya, duk da take mace jaruma mai zuciya, to wlh ya ninkata, dan idan ransa ya ɓaci kamar yadda kuka ga ya yi yanzu, ya rinƙa buga hannunsa da jikin dutse har ya ji ciwo, to haka yake yi idan ransa ya ɓaci. Dole ce tasa yake yin hakan, domin ba yadda zai yi da Mamma, mahaifiyarsa ce, ko murya bai isa ya ɗaga mata ba, so dole idan ransa ya ɓaci ya nemi mafita, kada ya je ya haɗiyi zuciya ya mutu a banza, ga shi shi mutun ne da bai iya danne zuciyarsa ba, hakan tasa yake yin irin wannan abin na buga hannunsa da dutse ya jiwa kansa ciwo dan ya samu zuciyarsa ta yi sanyi. (Ba wani a kusa bare ya sauke ɓacin ran a kansa😅 Mamma dai ita kaɗai ce😅 dole nan gani nan bari😅 ba yadda zai yi da ita) A kowace safiya Mamma da Kamran suna gabatar da training na motsa jiki, a tare suke yin komai, ita ce malamarsa mai koya mashi faɗa, duk wasu dabarun yaki da salon faɗa ta koya mashi, ga shi daman kakkarfar mutun ne shi, sabon jini mai tafasa, hakan yasa Mamma take matuƙar Alfahari da shi. Wannan shi ne kaɗan daga cikin tarihin Mamma da kuma Kamran. Nasan kuna da tambayoyi da dama a kansu, ni kai'na ina da waɗan nan tambayoyin, dan dole ne rayuwarsu akwai tambayoyi! Amma koma me, lokaci ne zai nuna mana!. Ta jima a rungume da shi tana jiran zuciyar tasa ta ɗan yi sanyi. Ba ita ta sake shi ba har sai da ta ji ya dai'na wannan hucin, sannan ta sake shi tare da miƙewa ta nufi waje. Jingina bayansa da jikin ƙogon dutsen ya yi yana sauke numfashi a hankali hankali. Jim kaɗan Mamma ta dawo hannunta a ɗauke da wani kwando irin na itacen ayaba da ake sakawar nan, kwando ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ƙasashen Arewacin duniya sun fi yawan amfani da ita wajen zuba kayan miya ko kuma fruits. A in da ta tashi ta koma ta zauna tare da riƙo hannun nasa. Wani farin audiga mai ɗan girma ta fitar daga cikin kwandon, fari tas da shi. Jinin hannun nasa ta fara goge mashi tana yi mashi sannu. Lumshe idanuwansa ya yi kamar bai ji me ta ce ba. Bayan ta goge jinin ne ta ɗauko wani purple abu a cikin wani ɗan ƙaramin mazubi wanda ta kyara kayanta da itace, ta yi kamar kwanon sha da marfin, gwanin birgewa, da alama Mamma likita ce. Wani audiga ta gutsuro tare da ɗan dangwalo wannan purple abin, sannan ta fara goga mashi a wajajen da hannun nasa ta farfashe. Sai sannu take ce mashi, saboda tasan abin akwai bala'in zafi sosai, amma shi kuwa yadda yake zaune tun farko, ko motsawa bai yi ba, kuma bai nuna wata alama da zata nuna cewa ya ji zafin abin ba, ya dai ɗaure fuska tamau kamar hadari. Bayan ta gama saka mashi wannan abin ne ta mayar da abin cikin kwandon, sannan ta ɗauko wani ɗan ƙaramin audiga tare da wani ganye da ta kwaɓa da wani magani, shima yana cikin wani ɗan mazubi ne wadda ta kyara kayanta. A gefe guda kusa da ita ta ajiyesu kafin ta riko yatsar nasa da ta kunburar. Duba yatsar ta fara yi dan ta gani karayace ko gocewar ƙashi. Ta ɗan ɗauki lokaci da a kallah zai kai 5 mins tana ɗan jujjuya yatsar kafin ta saki hannun nasa, sannan ta miƙe ta nufi waje. Duk abin da take yi mashi yana ji har cikin ransa, amma saboda dakiya da jarumta sam bai nuna alamar kamar yasan tana taɓa shi bama. Hannunta ɗauke da wani kyakkyawan mazubin ruwa da ta kyara da itace ta dawo cikin ɗakin. Ruwa mai zafi ta ɗebo a cikin wannan mazubin, sai tashin tiririn hayaki ruwan yake yi. A kusa da shi ta zo ta ajiye ruwan kafin ta wuce wajen ajiye kayansa. Wani ɗan karamin towel na sakar zare ta ɗauko, fari kal towel ɗin. A in da ta tashi ta koma ta zauna tare da sake riƙo hannun nasa, sai kara kumbura hannun nasa yake yi sosai da sosai, ba karya ya bugu kam. Ɗan dai'dai tsakiyar yatsar ta riƙo ta fara ɗan jujjuyata daga kasa kafin ta ja da karfi. Har lokacin bai nuna wani alama ta yana jin abin da take yi ba, saboda tsabar jarumta da juriya, ya dake tamkar bai san ta rike hannun ba. Bayan ta ja sai ta ɗauki wannan ɗan ƙaramin towel ɗin ta saka shi a cikin ruwan zafi, sai da ya ɗauki zafi sosai, ta sa hannu babu ko tsoro ta ciro towel ɗin, da zafinsa yana tiririn hayaki ta matse ruwan jikin, ko kaɗan ita ma babu alamar tsoro ko jin wani yanayi mara kyau a tattare da ita. A saman hannun nasa ta kai towel ɗin ta fara ɗabba mashi wajen. Haka ta cigaba da yi har sai da wannan ruwan zafin ya yi sanyi. Abinku da fararen fata jikin madara, nan take daga ita mai rike towel ɗin da hannunta har shi da ake ɗabbawa hannu dukkansu hannayensu ya yi jajir tamkar ya tara jini ne a wajen, sai dai duk da haka babu alamar kamar sun ji zafi ko wani raɗaɗi a saman face nasu. Wani irin mai mai sanyaya ciwo ta shafa mashi. Har cikin ransa ya ji sanyi sosai, bandeji ta ɗauko ta ɗaure mashi hannun nasa. Har lokacin kuma bai buɗe idanuwansa ba, yana dai ji ta gama mashi komai tsab, sannan ta miƙe tare da ɗaukar kayayyakin da ta shigo dasu dukka ta fitar da su. Tana fita ya gyara ya kwanta a saman bed ɗin nasa tare da ɗaura hannunsa guda a saman face nasa yana tunanin maman twins ɗin nan, shi dai har ga Allah matar ta shiga ransa, kuma ya kuduri niyar koda Mamma bata so sai ya rinƙa taimakawa matar a ɓoye, dan shi yana da tausayi sosai, yana da zafin zuciya da kuma faɗa sosai kamar Mamma ɗin tasa, sai dai kuma akwai shi da tausayi da son taimakawa jama'a. *Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 🔥💔𝑨 𝒕𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝒉𝒆𝒂𝒓𝒕𝒔 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒔𝒕𝒐𝒓𝒚, 𝒅𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚 𝒐𝒃𝒔𝒕𝒂𝒄𝒍𝒆, 𝒂𝒏𝒅 𝒓𝒐𝒎𝒂𝒏𝒄𝒆💔🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 1/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________4🔥 *DOMIN NEMAN KARIN BAYANI KU NEMENI TA WANNAN NUMBER 08161390581* Jim kaɗan Mamma ta dawo cikin ɗakin hannunta ɗauke da wani kyakkywar mazubi da suke zuba abinci, tamkar plastic plat haka ta kera kayanta, Mamma ba dai basira ba, daga kanta an rufe kofa, jajirtattiyar mace ce, hazika mai kaifin basira da ƙwaƙwalwa, ga tafasasshen jini na jarumta tamkar wata ƴar commander mayaka. Sai tashin tiriri abincin nata yake yi, ya sha kayan kamshi na ganyayyaki masu inganci da karawa jiki lafiya, komai nasu fresh ne, dan komai na cikin wannan daji babu busasshen, ɗanyu ne, su corry leaf, carrots, green beans, peas, eggplant, spinach, cabbage, cucumber, tamator da dai sauransu, komai nasu fresh ne, hakan yasa abincinsu yana da matuƙar kyan gani a idanu ga kuma ɗanɗano mai daɗi a baki, akwai wani ɓangare daga cikin dajin in da Kamran ɗin yake ɗebo masu gishiri, basu da maggi, saboda kowa yasan a wannan dajin dai babu in da zasu samo maggi, amma kuma a cikin gayyayyakin da suke amfani dasu da akwai waɗan da suka fi maggi ɗanɗano mai daɗi, hakan yasa abincinsu yake da ɗanɗano na musamman, sannan dama already su basu san menene maggi ba, dan kunga a wannan daji suka taso, so ɗanɗanon da suka saba da shi tun farko, basu da wani sama da shi. A saman katakon ta ɗaura plate na abincin, da akwai wani kyakkyawar cup mai ɗauke da wani irin red tea, shayi ne da ya ji gayyayyaki masu kara lafiya da inganci, ganyen shayin nasu ne yake red color tamkar ganyen shayin da jama'ar Arewacin duniya suke amfani da su. Ga wani gasasshen nama da yake ta tashin tiriri da kamshi, namar nan ta gasu sosai, dan sai da ta sanya yawuna ya tsinke. Suna da wadatatcen nama sosai a gidan nasu, domin Kamran jarumin namiji ne sadauki kuma mafarauci, shi yake farauto masu nama duk bayan kwana biyu, sai mamma ta dafa ta kuma soya da man namar, idan tana so kuma tana iya ajiye ɗanyen ta hanyar saƙala shi a jikin wasu itatuwa wadda ta dasasu a cikin madafinta, wato in da take girki kenan, kasancewar a koda yaushe tana cikin yin girki yasa wannan nama da take ajiyewa baya yin komai, sai dai baya wuce kwana ɗaya suke yin amfani da shi, dan in ya wuce haka zai lalace. Haƙiƙa rayuwarsu gwanin birgewa ne, musamman yadda suke da kayayyakin ci na morewa, ga fresh fruits ɗin nan kala kala, wata fruit ɗin ma sai dai ka ganta amma baka san suna ba, saboda ba a ko'ina aka cika samunta ba, mafita yawancin abubuwan da suke cikin wannan dajin, abubuwa ne da yafi yawaita ta ɓangaren Arewacin duniya, so ba'a ko'ina ake samunsu ba. Wannan cima mai kyau da suke samu ne yasa jikinsu yake da bala'in kyau, sai ka gansu kamar waɗan da suke rayuwa a wani hamshakin Daula mai cike da kayan more rayuwa, ka gansu wasu luwai luwai da su gwanin ban sha'awa. A kusa da shi ta zo ta ajiye wannan kayan abinci da ta ɗebo kafin ta zauna a gefensa. Cikin wannan sanyayyar muryar tasu ta fara ambatar sunansa a hankali hankali. Kasa kasa kamar mai ciwon baki ya amsa mata ba tare da ya buɗe idanuwansa ko kuma ya ɗago kai ba. "Stand up and eat your food". Ta faɗa tana ƙoƙarin cire mashi kyakkyawar hular sakar da yake a kansa, dan ta kallah yana haɗa zufa, da alama hannun nasa ne ta fara jiƙa yasa yake wannan uban zufar, kowa dai yasan yadda gocewar ƙashi take, koba ki taɓa yi ba nasan kin taɓa jin labari, zafin bala'i ke gare shi, kawai dauriyar bala'i da taurin zuciya ce gare shi yasa bai nuna alamar kamar yana jin wani abu da ya danganci zafi ko ciwo ba. "Mamma i can't eat anything now, i want to sleep, because am feeling sleeping". Ya bata amsa can kasan maƙoshinsa. Nisawa ta yi tare da miƙewa ta fice daga cikin ɗakin ba tare da ta ɗauki kayan abincin ba, ta bar mashi su a wajen, da alama kuma ranta ya ɓaci. Fita daga cikin kogon mai gabaɗaya ta yi, a saman tsaunin ta zauna saman wata dutse tare da buga uban tagumi tamkar mai tunanin wani abin. Daga yanayinta alamu sun nuna tana a cikin damuwa, dan face nata gabaɗaya ya canza, jikinta ya yi sanyi, tamkar ba ita ba, da alamu Kamran ya taɓo mata wani part da bata da buƙata ne a rayuwarta. Ta yi nisa cikin duniyar tunanin data lula, tamkar daga sama ta ji an kwanto a saman bayanta, ya kuma zuro kyawawan fararen hannayen nan nasa ta saman wuyarta yana sauke numfashi a hankali hankali. Shiru ta yi bata motsa ba kuma bata ce mashi ko uppan ba. "Am so so sorry Mamma". Ya faɗa in a low voice. "Sorry for what Kamran?". Ta yi maganar tare da kai hannunta tana shafa hannayen nasa da ya zuro mata ta saman wuyar tata. "I knew kin ji babu daɗi, kiyi hakuri my Mamma". Juyowa ta yi ta rungumesa tana faɗin. "Is okey my son, ni ban ji babu daɗi ba, kuma bana fatan wata rana ta zo wanda zaka sa naji babu daɗi, kai ɗin ɗan albarka ne, a ko'ina kake kana tare da albarkata, yanzu je ka ɗauko abinci kazo mu ci". Manna mata sumbata a lallausan kumatunta ya yi kafin ya miƙe ya nufi cikin gidan nasu, dan gidansu za'a ce tun da a nan suke rayuwarsu, kuma rayuwa ce kamar kowa suke yinta, sun fi wasu masu rayuwa a cikin gari ma jin daɗi da ƴanci, dan su babu ruwansu da hayaniya da matsalolin rayuwa na yau da kullum, kullum a cikin farinciki suke, su bama su san da akwai wasu mutane da suke rayuwa a wajen dajin ba, bare har su san da wasu matsalolin. Ajiyar zuciya Mamma ta sauke tare da yin hamdala ga Allah subhanahu wata'ala da ya bata yaro mai biyayya irin Kamran, yana da bala'in zuciya na wuce misali, ga saurin fushi, sai dai kuma duk fushin da yake a ciki da zarar yaga Mamma a cikin ɓacin rai shi zai danne nasa fushi ya kwantar da kai da murya dan ya ganta a cikin farinciki, shi ɗin mutun ne mai tsananin son mahaifiyar tasa, bashi da burin da ya wuce ya ganta a cikin farinciki, ita ce komai nasa, ita ce duniyarsa, ta sha ɗawainiya da shi, ta sha fama da shi, ta wahala wajen renonsa, ta tsaya sayin daka tare da jajircewa wajen ganin ya samu komai na rayuwa kamar kowani yaro, ta mai da shi jarumin sadaukin, ta gina mashi rayuwarsa a kan jarumta da rashin tsoro, bai san wani abu wai shi tsoro ba kamar dai ita ma Mamma, rayuwarsu gwanin ban sha'awa abin koyi ga al'umma. Fitowa ya sake yi hannunsa ɗaya mai lafiyar na rike da kayan abinci. A kusa da ita ya zo ya zauna tare da ajiye mata abincin a gabanta yana kallon fuskarta, while ita ma shi take kallo, kamar nace zan rabasu. Wani irin gurnanin Tiger ne ya fara tashi daga bayan kogon nasu. Ko a jikinsu tamkar basu san da cewa Damusa ce take kuka ba, abincin kawai Mamma ta fara bawa Kamran ɗin a baki kamar wani ƙaramin yaro. A wani irin mahaukacin gudu wani shirgegen damusa ya hauro saman dutsen, yana da girma sosai ga cikar razanarwa a tattare da shi, ƙosasshe ne mai lafiya, ganinsa kawai ya isa ya sanya bawa haɗiyar zuciya ya mutu, dan ba ƙaramin Tiger bane ba, sai wani girgiza yake yi yana jijjiga jikinsa, tamkar wanda ya taso daga barci, kunsan haka Tigers suke yi idan suka taso daga barci ko kuma suka ci suka ƙoshi, to haka suke yi. Kai tsaye wajen Kamran ɗin ya nufa, yana zuwa ya kwanta a kusa da shi yana wani zuro da harshe waje, da alamu sun saba sosai. Hannunsa guda ɗaya Kamran ɗin ya ɗaura a saman Tiger yana faɗin. "Mamma kin ga Rocky tun jiya da ya yi fushi da ni sai yau ya dawo ko?". Tana ɗebo mashi wani abincin ta bashi amsa da cewa. "Kai ne baka kyautawa Rocky, shiyasa yake yawan yin fushi da kai". Buɗe baki ya yi ta zuba mashi abincin da ta ɗebo ɗin, a hankali ya cigaba da tauna yana faɗin. "Amma kuma Mamma ai ba zai iya fushi dani mai gabaɗaya ya tafi ya barni ba, dole idan ya yi fushin ma sai ya sake dawowa, yanzu ma ba ga shi nan ya dawo ba, ni ai bani na je na nemosa ba, idan ya isa ya tafi mai gabaɗaya ya barni mana". Girgiza kai kawai ta yi, dan tasan komai wuya komai daɗi Rocky ba zai taɓa rabuwa ba Kamran ba, saboda wani lokaci dabbobi sun fi mutane amana, yau tsawon shekaru goma shabiyar kenan tun ranar da aka haifi Kamran ɗin suke tare da Rocky, a tare suka yi wasa a wannan dajin, so tasan kome Kamran ɗin zai yi mashi ba zai taɓa rabuwa da su ba, sai dai wani ikon Allah, idan Kamran ya yi mashi ba dai'dai ba, sai ya yi fushi ya tafi, amma anjuma kaɗan zai sake dawowa abinsa, kullum suna a tare. Kun san Damusa da Zaki daban daban suke, ita Damusa tana iya haura sama da shekaru ashirin tana rayuwa a duniya, ita kuma Zaki bata kaiwa sai wani ikon Allah, wannan zafin zuciyar nasu da wannan kukan da suke yi shi ne yake yawan kashe Zakunar, so su basu rayuwa mai tsawo sosai kamar Damusa, kun san sunfi kowace dabba zafin zuciya, to shi ne yake hallakasu basu jimawa a duniya, fatan kun gane?. Abincin ta cigaba da bashi yana ci yana shafa jikin Rocky ɗin, shi ma yana tsananin kaunar Damusan, dan yana da amana ga kuma taimakonsu da yake yi, baya barin sauran muggan namun dawa su cutar da su. Bayan ya kammala cin abincin ya ƙoshi ne ya miƙe tsaye yana faɗin. "Mamma am coming, I want to go to somewhere, is very close". One thing about KAMRAN yaruka biyu kawai yake ji a rayuwarsa, daga yaren da ya yi wa maman ƴan biyun nan magana da farko, sai kuma English, yarika biyun nan kawai ya iya. "Kamran kada ka yi nisa fa, sannan ka dawo da wuri, dan anjuma kaɗan kai da Rocky zaku je ku farauto mana nama, bamu da ɗanyar mama, kuma ina son gasa mana da daddare". Jinjina mata kai kawai ya yi tare da sa kai ya wuce. Da ɗan gudu Rocky ya rufa mashi baya. Da kallo Mamma ta bisu, tana tsananin kaunar ɗan nata, shi ne duniyarta, abin da yasa bata hana shi fita ba shi ne, tasan cewa kullum suna zuwa yawace yawacensu shi da Rocky, sai dai basu taɓa yin nisa da ita, da ta kwala mashi kira zai amsa, kun dai ga ɗazun da yake wajen Maman twins ta kira kuma ya amsa, to haka suke, baya taɓa yin nisa da ita, dan yasan bata son hakan, bata son yin nisa da shi. Ta ɗan jima a wajen tana zaune kafin ta miƙe ta nufi cikin ƙogon nasu, dan ta je ta cigaba da yin ƴan aikace aikacenta. Shi kuwa Kamran, kai tsaye wajen mum twins ya nufa abinsa, dan matar ta tsaya mashi a ransa, yana son ya koma ya sake dubata ita da ƴaƴan nata. Sai binsa da takun ƙatsaita Rocky yake yi, yana wani irin jijjiga jiki, irin shi ne shugaban nan. Turus Kamran ya ja birki a lokacin da suka isa wajen da mum twins ɗin take. Zallar madarar mamakice ziryar ta bayyana mashi a saman face nata, ɗan zaro idanuwansa waje ya yi yana kallon wajen da kyau, gani yake kamar ba wajen bane ba. Mamaki ya lulluɓe shi ya ƙasa gaba ya ƙasa baya, while shi kuma Rocky ya yi gaba abinsa yana son wucewa ya je ya shiga cikin bukkar. Ganin Rockyn zai shiga ciki ne yasa shi ya ɗan farfaɗo daga sumar mamakin da ya afka. Da sauri ya ƙarisa ciki dan ya kara tabbatarwa da kansa abin da yake gani. Tabbas ba gizo bane, kamar yadda mum twins ta sha madarar mamakin ganin an taimaka masu an gyara masu komai, haka shi ma ya sha wannan madarar mamakin. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanuwansa suka sauka a kan mum twins da babynta, da farko ya ɗauka basu nan ne, ganin suna nan yasa ya ji wani sanyi ta ratsa shi. Da sauri ya ƙarisa kusa da mum twins ɗin yana mai gayawa Rocky kada ya ce zai shigo cikin ɗakin nan ya ɓallah masu abubuwa, dan kofar shiga ma ta yi mashi kaɗan, idan ya ce zai shiga kaf zai karya itatuwan da aka kafa a bakin kofar, dan haka ya tsaya a waje. Wani irin gurnani ya yi alamar bai ji daɗi ba, Kamran ya hana shi shigowa yaga ne a ciki. (Ga ji mun Rocky da gulma😒 wato suma sun san gulma fa😅) Jin motsin mutun a kanta ne yasa ta yi saurin waro fararen idanuwanta waje, dan taga wanene. Duk da cewa ɗazun da ya taimaka mata ita da baby's nata suka fita daga cikin ramin nan bata a cikin hayyacinta, amma hakan bai sa ta ji tsoron ganinsa ko makamancin haka ba, sam bata iya gane face nasa a ɗazun ba, tana cikin wani hali, bata san wanene a kanta ba lokacin. Ganin shi cikin nutsuwa da kamala sosai a tattare da shi ne yasa ta kura mashi idanu tana mai binsa da kallo. Tsugunnawa a gabanta ya yi, cikin sanyin murya ya tambayeta wanene ya yi mata dukka wannan abin? Ko dai ita da kanta ne ta yi?. Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a ba ita ce ta yi ba, amma bata iya buɗe baki ta yi mashi magana ba. Sake shiga cikin kogin madarar mamaki ya yi, amma sai ya daure ya kawar da mamakin nasa tare da ce mata. "Zaki iya tashi zaune?". Nan ma girgiza mashi kai ta yi alamar. "In ɗaga ki?". Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a bata buƙatar ya ɗaga ta. Zai sake yin magana ɗaya daga cikin baby's ɗin nan ya fara motsi haɗe da kuka kaɗan kaɗan. Kusan a tare ita da shi ɗin suka kai kallonsu a kan yaran. Wannan mai black cuiry hairn ne dai yake motsi tare da kukan. Da sauri Kamran ɗin ya kai hannunsa ya ɗan ja towel da aka lulluɓesu zuwa kasa kaɗan, ɗan girgiza babyn ya fara yi. Ai kuwa yana taɓa babyn kamar ya ce ya kara ihu, wage baki ya yi ya fara zunduma ihun da gasken gaske, dama already kun ga da kuka ya zo, sarki ne wajen zuba kuka, dan haka kuwa sai ya cika masu kunne da ihu. Runtse idanuwanta gam maman nasu ta yi, har can cikin ranta take jin wannan kukan nasa, wani irin zafi zuciyarta take yi mata. Hannu biyu Kamran yasa zai ɗauki babyn, ai kuwa bai kai ga ɗauka ba ɗayan baby mai golden white hair ya fara ihu shi ma. Kasancewar daga Kamran har maman tasu basu san cewa tun da aka haife shi bai yi kuka ba, sai kukan nasa bai basu mamaki ba, sai ma rikita Kamran ɗin da suka yi, ya rasa me zai yi masu, ya kuma rasa wanne zai ɗauka daga cikinsu. Allah sarki uwa da ƴaƴan, jin kukansu su dukkansu biyu yasa ta ji ba zata iya jurewa ba, ciza laɓɓanta da karfi ta yi tare da yunƙurawa dan ta miƙe zaune. Da sauri Kamran ya juyo da kallonsa a kanta. Wani irin wahalallen kara ta saki tare da dafa kasa da iya karfinta tana son tashi, nan take har wani irin zufar wahala ya fara tsastsafo mata, daga gani kasan tana jin azaba ba kaɗan ba, dama kuma ai dole ta ji azaba, suka da kifiya a ciki ai ba wasa ba, dan ma ta auna arziki ne ba kaɗan ba, ba dan haka ba ai da ta jima da mutuwa, kuma kunga wanda ya harbeta da kifiyar bai harbeta a in da zata cutu sosai ba, ya mata da sauki. Kamran sarkin tausayi, duk zafin zuciyarsa akwai tausayi sosai, har cikinsa yake jin wani irin matuƙar tausayinta ya lulluɓe shi, ji yake yi kamar yasa hannu ya ɗagata, amma sam bata son ya taɓata, sanin tana gudun ya taɓata ne yasa ya hakura ya jure yana ganinta cikin wannan hali bai yi yunƙurin taimaka mata ba, ya bita da kallon cike da tausayawa fal a face nasa. Bai kuma hanata miƙewa ɗin ba, duk da yasan tana da ciwo a cikinta, kasancewar yaga anyi mata aiki sosai a kan ciwon ne yasa sai bai hanata ba, amma kuma duk da wannan magani sosai da aka zuba mata, yana da kyau ta sami kamar kwana uku bata motsawa sosai, dan wajen ya ciko da wuri, sai dai ina, hakan sam ba zai yiwu ba, saboda yaran nan nata, da alama rigimammune number ɗaya, dan sarakan kuka ne, ita kuma ba zata iya jure jin kukan nasu ba, hakan yasa zata miƙe zaune dan ta san ta yadda za'ayi ta basu nono. To ya Ubangiji ka sakawa iyayenmu da gidan Aljanna, ya Allah kamar yadda suke sadaukar da abubuwansu da dama masu matuƙar mahimmanci wani lokaci ma har da rayukansu a kanmu, ya Allah kasa su zamana daga cikin al'ummar da annabi zai fara ceta a ranar gobe kiyama, ka bamu ikon yi masu biyayya sau da kafa a kan dai'dai. Da kyar da suɗin goshi ta iya tashi zaune, ta jingina bayanta da jikin itatuwan da aka haɗa masu ɗakin, tsabar azaba har wani irin jajir idanuwanta suka yi, tamkar wadda ta sha kuka na tsawon lokaci ta ƙoshi, zufa cigaba da tsastsafo mata yake yi a gefe da gefen face nata, fuskar nan tata tamkar wadda aka watsawa ruwa. Ta datse lausasan laɓɓan bakinta gam da hakwaranta, ta kuma datse idanuwanta gam tana girgiza kai alamar azaba take ji sosai. A hankali take sauke numfashin da yake fito mata tamkar wadda ta sha uban gudu ta ƙoshi, sai a lokacin kuma ta ji nauyin kayan jikinta ya ragu, alamar an rage mata kayan jikin nata. Tana son buɗe idanuwanta ta bi jikin nata da kallo, amma ta kasa iya buɗesu, saboda azaba, ji take yi kamar idan ta buɗe kara karuwa raɗaɗin ciwon zai yi mata. Sosai Kamran ya yi matuƙar jinjina mata, dan kuwa ta yi namijin ƙoƙarin na wuce misali, ba kowa ne irin abu haka zai faru da shi kuma ya iya miƙe zaune a yau ba, sai wanda yake da matuƙar jarumta, da alama jaruma ce sosai ita ma, dama idan baku manta ba a baya na gaya maku da alama jarumace, da alama an sha fama da ita sosai kafin a iya kaita ƙasa. Duk jarumta irin na Mammansa yau dai Kamran ya jinjinawa maman twins ma, bai taɓa tunanin aduniya za'a sami jaruma mai tafasasshen jini irin Mammansa ba, sai ga shi yau ya ganta duk da bata kai Mamma ba, dan ita Mamma karshe ce, jarumtarta tamkar wani sadaukin yaki haka take, macen da zata yi faɗa da Damusa ai kunga ba ta wasa bace ba!. Su dai baby's da yake basu san halin da ake ciki ba, sai tsallara ihu suke yi abinsu, ko a jikinsu, duk sun sa Kamran ya shiga ɗimuwa, ya rasa waye za rarrasa, sun rikita bawan Allah, duk da dama can ba iya rarrashin ya yi ba, yana dai kwatantawa ne, kunga shi kaɗai ne a wajen Mamma, bai da kani ko kanwa bare ace yana ganin yadda Mamma take renonsu shi ma ya koya. Da hannunta ɗaya ta dafe wajen ciwon nata, ɗayar hannun nata kuma idanuwanta a datse gam ta fara yi wa Kamran ɗin nuni da ya bata baby's ɗin, ba halin yin magana, baki na datse gam. A hanzarce ya ɗauko wannan mai bakin curly hair ya miƙa mata, dan yafi tsala ihu, babyn nan tamkar maƙoshinsa zai fashe, saboda iya kuka. A karkace Kamran ya ɗauko shi ya ɗaura mata a saman cinyarta. Jin babyn a jikinta yasa ta sauke wani irin wahalallen nauyayyar ajiyar zuciya, alamar ta ji sanyi ya ratsa cikin zuciyarta. Da kyar ta iya tallabo babyn ta fara kiciniyar bashi nono duk da bata da tabbacin tsabtar jikinta, ita dai burinta kawai ta shayar da su su daina wannan ihu, dan a tunaninta yunwa suke ji sosai ne yasa suke irin wannan uban ihu haka. Shi dai Kamran yana son taimaka mata, sai dai babu hali, dan kuwa bazata taɓa yarda ya taɓa jikinta ba, sanin hakan yasa ya kawar da kansa daga kallonta ya cigaba da girgiza ɗayan babyn dan su sami saukin wannan ihun da yaran suke rera masu. Shi kuwa Rocky ya yi kwanciyarsa a bakin kofar shigowa, sam ba haka ya so ba, ba yadda ya iya ne kawai, yana jin maganar Kamran sosai. (Hmmm Damusa dai ki sabo ne! Duk da akwai masu amana kamar yanda yake a ko'ina akwai masu amana dana banza, Allah dai ya tsare mana su Kamran, kada wata rana Rocky ya rasa abinci ya yi ram da su😅.) Da kyar ta iya fitar da nonon ta sakawa babyn abaki. Ai kuwa kamar jira yake yi ya fara sha babu kakkautawa, Allah sarki ashe da gaskiyarta, ashe tasan me suke yi wa kuka, uwa kenan! Babu biyunta a duniya!. Mamaki ne ya kama Kamran sosai na ganin yadda wannan babyn ya yi shiru yana shan nono, sai a lokacin ya lura da babu wannan alkyabba ta jikin Maman twins ɗin wanda kuma yasan dai ya fitar da ita daga cikin ramin nan da wannan alkyabbar a jikinta, to ko waye ya cire mata shi?. Ya tambayi kansa da kansa. Ƴar waige waige ya fara yi ko zai ga ta in da aka ajiye mata alkyabbar tata, sai dai ina, bata babu labarinta. Shiru ya nutsa cikin tunaninsa yana tunano a ina alkyabbar to? Waye kuma ya ɗauketa?. Sai a lokacin ya tuna da cewa ba iya alkyabbar bace kawai, akwai sarka, abin hannu, da kuma ɗankunnenta na zallar madarar gold, suma ina suke? Dukka babu ko zobbe a wajen, bayan kuma shi yasan da hannunsa ya kwaso mata su daga bakin ramin ya biyota da su zuwa wannan wajen time ɗin da take ja a kasa da zasu zo wajen. Da hannunsa ya ajiye mata su a kusa da ita a lokacin yana yi mata sannu, to ina suke yanzu kuma? Abin da ban mamaki sosai gaskiya, kuma ga dukkan alamu ba wai satarsu aka yi ba, babu ma ɓarawo a wannan daji, tsawon shekaru 15 ɗin nan daga shi sai Mammansa ya sani suke rayuwa a cikin wannan dajin, sai baƙin maharba idan sun zo wucewa, sai kuma idan hanya ta kubcewa mutun ya faɗo cikin dajin, ko su maharba ba kasafai suka cika shigowa cikin wannan dajin ba, dan akwai manyan namun dawa a cikinta, idan suka yi wasa su da suka zo farauta to za'a faraucesu kamar kuda da bujumin sa, hakan yasa sam basu gigin zuwa dajin farauta, sai time to time. Wannan dalilin yasa abin ya ɗaurewa Kamran kai ya kuma bashi mamaki, to wani ɗan albarkan ne kuma ya kwashi kayan maman twins? Allah masanin gaibu. Sai da ta ji alamar barcin babyn dake a hannunta ne ta kara sauke nauyayyar ajiyar zuciya, ya sha ya ƙoshi sai barci. A hankali ta waro idanuwanta waje, sun yi jajir da su kamar wuta, baiwar Allah fuskarta duk a kumbure kamar ba ita ba. Zubawa babyn idanu ta yi tana mai karewa ɗan kyakkyawar face nasa kallo, ga dukkan alamu wannan baby mai golden white hair yana da matuƙar hakuri sosai, domin kuwa wannan jijjiga shi da Kamran yake yi yana ɗan bubbuga shi a hankali hankali yasa ya hakura ya yi shiru kamar babu shi a wajen, saɓanin mai black hair nan, ai shi ko jijjigawar ma baya jin ana yi, ihu kawai abinsa, da alama acici ne, sarkin cin abinci ne ba wasa!. Hannu ta kai ta ɗan buɗe towel ɗin jikin babyn da kyar da makyarkyata, domin ta duba shin wai me ta haifa ne?. Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ta kalli cewa macece wannan babyn dake a hannunta, wani irin daɗi da sanyi ta ji yana ratsata, wanda ita kaɗai ta san dalilin. Ni kuma dai na saka mata ayar tambaya? domin kuwa dole akwai wata a kasa da yasa zata ji daɗi tare da murnar haifar mace da ta yi, ita da take son su ɗauka mata fansa? Mata dai ba iya ɗaukar fansa zasu yi ba, to ko me dalilinta na murnar samu ɗiya mace? Ina da tambaya, amma lokaci ne zai amsa mana waɗan nan tambayoyin. Ganin tana murna da samun ɗiya macece yasa shi ma Kamran ɗin ya ce bari ya duba babyn dake a wajensa ya gani. Yana dubawa sai yaga ita ɗin ma macen ce, ajiyar zuciya ya sauke tare da dawo da kallonsa a kan mamar tasu yana mamakin irin uban annuri da farinciki da ya bayyana a saman fuskartar daga ganin ta haifi mace ko ace mata, duk sai kansa ta kulle bawa Allah. A dai'dai wannan gaɓar ni PRINCESS TEEMA nasan na jijjige teburin dayawa daga cikin makaranta wannan littafin mai albarka, some that are sayin this twin's it's all boy's how far?. And also some that are saying it's boy and girl greeting from this side..........🥳😅🥱 Dawo da kallonta a kan Kamran ɗin ta yi, tana son ta ce mashi ya ɗauke mata wannan babyn tun da ta yi barci ya bata ɗayar ta shayar da ita, amma ta kasa iya yi mashi magana, domin juriya ce kawai irin tata yasa ta iya miƙewa ma. Ganin tana ta kallon shi babu ko kyafta idanu ne yasa ya fahimci lallai da akwai abin da take son gaya mashi, kada ku manta yana da kaifin ƙwaƙwalwa kamar Mammansa. Ɗan zuba mata idanu shi ma ya yi, a nan ne ya fahimci ga abin da take da buƙata wadda ta kasa gaya mashi ya yi mata. Hakan yasa ya kai hannu cikin nutsuwa ya ɗauki babyn yana bin fuskar yarinyar da kallo, kyakkyawar gaske ce kamar ita ta yi kanta. A in da ya ɗaukota da farko ya mayar da ita ya kwantar kafin ya ɗauko baiwar Allah sarkin hakurin nan ya ɗaurawa maman ita a saman cinyarta, sai kallon fuskar yaran yake yi, dukkansu idanuwansu a rufe, ita ma mai black hair har ta gama zuba ihunta bata buɗe idanu ba, suna a rufe take wannan zunduma ihun, har ta sha nono ta ƙoshi ta yi barci da haka. Bawan Allah Kamran, shi ma sai zogi hannunsa da ya ji ciwon nan yake yi mashi, amma haka ya daure ya jure. Ita ma wannan baby ana bata nonon ta yi maza ta capke ta fara sha kamar ba gobe, bayin Allah yunwa ce ta yi masu yawa. Ɗago kai maman twins ɗin ta yi tare da dawo da kallonta a kan Kamran ɗin, tana son ta tambaye shi waye shi? Me yakawo shi nan?, amma ba halin iya buɗe baki ta yi magana, dan wani irin azababben nauyi ma harshenta ya yi mata, ko motsa shi bata iya yi bare ta yi magana. Shi ma Kamran ɗin a nasa bangaren yana son ya tambayeta wacece ita? Me kuma ya kawota wannan bakin daji mai haɗarin? Amma ina, shima sai ya ji harshensa ta yi mashi nauyin da ya kasa iya tambayarta, sai dai ya bisu da kallo kawai. Kukan da Rocky ya yi mai ɗan sauti ne yasa dukkansu suka mayar da kallonsu izuwa bakin kofar shigowa. A takaice Kamran ya ce da Rocky ka gama kukanka dai ba zanzo ba, yau ba wani yawon da zamu je, muna tashi daga nan gida zan koma. Ya yi maganar ne da wannan yaren nasa, da alama yafi yawan magana da wannan yaren, domin tafi zama sosai a bakinsa. Sam Maman twins bata ji me ya faɗawa Damusar ba, dan bata jin wannan yaren, sai dai jin ya yi magana da wannan yaren ne yasa tunanin abin da ya faru ɗazun a baya ya faɗo mata. Shiru ta yi tana tunanin tabbas ta ji irin wannan yaren ɗazun ya daki dodan kunnenta, amma bata iya tuna wanenen ya yi magana da yaren kuma a ina aka yi maganar ba, ta dai san ta ji wannan yaren ɗazun. Ganin yadda ta lula duniyar tunani ne yasa Kamran ya fara bubbuɗe kwaryayyakin da suke a rufe a gefenta, dan yaga menene a ciki, da farko duk a zatonsa abinci ne a ciki, sai da ya buɗe yaga ashe magungunar gargajiya ne a cike a ciki. Mamaki ne ya kama shi, wanene ya kawo waɗan nan magunguna? Ya dai san wannan ba na Mammansa bace, domin haɗin maganin Mammansa ba irin wannan bane, kuma yasan ita Mamma wlh ba zata zo nan ba, ita fa a gaban idanunta bakar Damusa ta hallaka wani bawan Allah da hanya ta kwace mashi ya shigo cikin dajin, Kamran ɗin yana kuka yana su taimaki mutumin, amma Mamma taki yarda su taimaka mashi, a gaban idanunta ya mutu ko a jikinta, so ita ba zata taɓa yin taimako ba a cewarta, sam ba ita ta kawo waɗan nan abubuwa ba, bama su yi kama da nata ba, to waye ya kawosu?. Dole Kamran ya tambayi kansa dan dai yasan su kaɗai ne a cikin wannan daji. Ni ma dai dole na shiga ruɗani kuma na tambayi kai'na, waye ya yi wannan aikin dukkan?. To koma wani ɗan albarka ne ko wace ƴar albarka ce lokaci zai nuna mana ita ko shi. Ganin lodin magunguna ne a ciki yasa Kamran ɗin ya miƙe tsaye dan ya je ya samowa maman twins ɗin abin da zata ci, saboda ko ba'a gaya mashi ba yasan tana jin yunwa sosai. *Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ *Labarin RAWANIN ZALINCI labari ne a kan sarauta dake tafe da Zalinci, cin amana, tauye hakki, walaƙanci, zanba cikin aminci, ku dama daga jin sunan RAWANIN ZALINCI kun san batu ake a kan sarauta mai tsuma zuciya da gabaɗaya ilahirin gangan jiki, soyayya mai cike da bahagon kuma makauniyar kalubale tattare da kaddarori, fata na dai kada ku yi sauri, ku daure ku bi komai sannu a hankali har mu kai in da kuke da buƙata, duk wanda yake da wata tambaya ko wata magana dangane da littafina RAWANIN ZALINCI, to kai tsaye ya mun magana, 08161390581 my contact, ni ce mai littafi, a wajena zaku sami duk wasu amsoshinku da kuke da buƙata. And lastly duk wanda labarin RAWANIN ZALINCI ta taɓo yarensu, al'adarsu, da sauransu, to ya mun afuwa, akasi ne* E____________5🔥 Ganin lodin magunguna ne a ciki yasa Kamran ɗin ya miƙe tsaye dan ya je ya samowa maman twins ɗin abin da zata ci, saboda ko ba'a gaya mashi ba yasan tana jin yunwa sosai. Waje ya nufa. Da kallo ta bishi, tana son ta yi mashi magana, amma ba hali, dan bata da bakin iya yin magana, sai kawai ta bishi da idanu har ya kurewa ganinta. Ajiyar zuciya ta sauke kafin nan ta dawo da kallonta a kan baby's ɗin nata, har cikin ranta take jin tsananin kaunar yaran nan, tana kuma godewa Allah dayasa ƴaƴa mata ta haifa, da alama ta fi buƙatar mata sosai. Shi kuwa Kamran, yana fita gida ya koma, ya yi sa'a Mamma tana wanka, a hankali ya lallaɓa ya shiga cikin wajen da take girki, shi kuma Rocky yana tsaye a waje yana jiransa, dan ba zai iya shiga cikin ƙogon ba, kofar ta yi mashi kaɗan, idan baku manta ba dama na gaya maku kofar karama ce sosai, bazaku haɗa jikin mutun da Damusa ba, shi Kamran zai iya shiga, amma Rocky ba zai iya ba. Kayan cima da mamma ta girma lodi ya ɗebo a cikin kwaninan cin abincin nasu, ya haɗa duk abin da yake ganin ya dace mashi, cikin sauri ya ɗauka ya nufi waje. Kai tsaye wajen maman twins ya koma. Mamma kuwa, tana fitowa daga wanka ta fahimci ya shigo cikin ƙogon, sahun kafarsa ta gani, kada ku manta gari ne na damina. Shiru ta yi tana mamakin yadda aka yi yau Kamran ya shigo cikin sanɗa ya kuma sake fita, abin ya bata mamaki, tunani take yi a kan anya kuwa ba zata bi bayansa dan taga me yake yi ba?. Tunawa da abin da ya faru a tsakaninsu ɗazun na ya ce mata ta taimaki wata mata ta ce ahir ba zata taimaka ba, tuna hakan yasa ta girgiza kai tana mai ciza laɓɓanta, alamar abin bai yi mata daɗi ba. Hakiƙa Mamma tana da wata ɓoyayyiyar baiwa, domin rashin tsoron nan nata da wannan uban jarumtar tata dole akwai ayar tambaya, tabbas ana samun mata marasa tsoro, amma kamar Mamma haka dole a dasa mata ayar tambaya, ita ɗin ba mace bace kamar sauran mata, akwai dai wata a ƙasa, lokaci shi ne alkalin komai. Cikin ɗakin maman twins ya sake komawa, a kusa da ita ya zauna tare da ajiye mata kayan abincin. Buɗe kwano ɗaya ya yi, wani irin gasasshen nama ne mai matukar kyau a ido, ga kamshi da yake tashi, namar shaniyar daji ce, da alama Mamma bata jima da gama kasawa ba, dan akwai ɗumi a jikinta sosai, ta sha kayan kamshi irinsu curry leaf da sauransu, duk wanda ya ga namar nan sai yawunsa ta tsinke. Ita kanta maman twins sai da ta ji yawunta ya tsinke da ganin namar, sai dai bata jin kamar zata iya cin wani abin, bakin ta babu ɗanɗano ko kaɗan. Cikin harshen turanci ya sanar da ita cewa ga abinci ya kawo mata ta ci mana. Da kallo kawai ta bishi shi da abincin nasa ba tare da ta motsa koda laɓɓan bakinta ba. Ganin sai kallonsa take yi taki ta yi magana ne yasa ya miƙe tsaye yana gaya mata zai tafi, amma zai dawo anjuma da yamma can. Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar to ta ji. Daga haka bai sake yin magana ba yasa kai ya fice abinsa. Yana fita Rocky ya rufa mashi baya, gida suka nufa, dan ya san in dai Mamma ta fito daga wanka sai ta fahimci ya shigo cikin wannan ƙogon, zata gane sarai, hakan yasa ya yi saurin komawa, saboda kada ta biyo bayansa, ƙarami ne daga cikin aikinta ta biyo shi ta ce bari ta je taga me yake yi, ba yau bane farau wajen biyo bayansa da take yi idan ya fita, in kuma ta zo ta tarar da ga abin da yake yi na taimako, to wlh suna ina samun gagarumin matsala a tsakaninsu, kamar yadda ta tsani ranar mutuwarta, haka ta tsani ta ga Kamran ya raɓi wasu, ko kuma wasu sun raɓesu, shiyasa bata son ya fita, bata kauna ko kaɗan, ita ko maharban da suke wucewa time to time ma sam bata son Kamran ɗin ya ce masu ko sannu. To fah, Mamman akwai matsala babba in kuwa haka ne, da alama dai akwai wani gagarumin al'amari dan gane dake a ƙasa. Ni kam ina da tambaya sosai a kan Mamma gaskiya, lamarinta akwai ban mamaki, nasan kuma my people kuna da tambayoyi a kanta dayawa, to ku adana tambayoyinku, lokaci zai bamu amsoshinmu. Yana komawa ya wuce cikin ɗakinsa ya kwanta, zuciyarsa cike fal da tunani iri iri a kan maman twins, yana son sanin wacece ita? Me ya kawota wannan waje?. Da wannan tunani a ran nasa barci ya yi awon gaba da shi. Mamma ta jima a tsaya tana kare mashi kallo ba tare da ya sani ba, tun shigowarsa cikin ɗakin ta biyo bayansa, sai dai bata shigo ciki sosai ba, ta tsaya ta bakin kofa ne tare da zuba mashi idanu babu ko kyaftawa, da alamar tarin tambayoyi da take son yi mashi sosai a saman fuskarta, amma ko da sunan wasa bata furta ko kalma ɗaya ko ta yi wani motsi da zai sa ya ga tana kallon shi ba, tana gani har ya yi barci. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙarisowa cikin ɗakin. A gaban ƴar bed ɗin nasa ta tsaya, sosai ta kura mashi idanu babu ko kyaftawa, sai kallon face nasa take yi kamar wadda taga bako daga wani duniya mai wata halitta na daban ba irin na mutane ba, da alama dai akwai wata a ƙasa, wannan kallo bana banza ba, gata da sexy eyes da idan idanun mutun biyu ta tsare shi da kallo to sai ya shiga ruɗu. Ta ɗauki a kallah good 30 mins tana kallonsa from head to toe kafin ta sa kai ta fice daga cikin ɗakin bayan ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya kenan. Nata ɗakin ta koma ta zauna a saman bakin bed tare da buga uban tagumi ta afka cikin kogin tunani, sai Allah kaɗai yasan tunanin me take yi. Shi kuwa Rocky yana kwance a wajen ta bakin ƙogon dutsen abinsa, dama kullum haka suke yi, kamar wani shi ne mai gadinsu, Allah sarki ya yi girman da baya iya shiga cikin ƙogon, hakan tasa sai ya yi zamansa a bakin kofar yana ta kalle kalle, wani lokaci har barci ta ɗauke shi. To mu dai bari mu kutsa cikin labarin mu duba wani part dan mu ga me ake ciki, wata kila kafin mu dawo wasu abubuwa sun ɗan daidaita ko sun bayyana mana a wannan dajin, dan gaskiya muna da buƙatar bayyanar abubuwa dayawa. Wasu kyawawan ƴan matasan ƴan'mata ne su biyu suke tafiya, jikinsu na sanye da uniform na islamiyya launin sky blue, wando ce doguwa da riga zuwa gwiwa, sai farar hijabi har ƙasa. Babbar ba zata wuce 7 years ba, karamar kuma 5 years, kamanninsu kusan ɗaya, sai dai karamar fara ce sosai, babbar kuma ta ɗan yi duhu, ma'ana wankar tarwaɗa, amma da kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci iyayensu guda ne, dan fa ga kamar jinin karara a saman fuskokinsu. Daga islamiya suke, suna tafiya cikin nutsuwa sosai saɓanin sauran yaran da zaka gansu idan an taso daga islamiya ko makarantar boko suna tafiya a kan hanya suna wasa, wasu ma ka gansu suna guje guje a kan hanya. Su waɗan nan a nutse sosai suke tafiya, bare ma ƴar babban cikin nasu, tana da nutsuwa sosai, da alama sun fito ne daga gidan tarbiya. Suna rike da wata ƴar ƙaramar jaka na zuba litattafai, jaka ce dai ta ƴaƴan dai'dai mai rufin asiri, uniform ɗin jikinsu ya sha guga sosai, har wani kyalli yake yi, ga karin gugur nan ta zauna sosai a jikin uniform ɗin, da alama mahaifiyarsu jajirtatciya ce wajen iya wanki da guga wa yaran nata, da alama suna samun kulawa sosai, dan daga jikin yara ake gane tsabtar uwa, to gaskiya ita dai wannan uwar ba karya, akwai tsabtar. Karamar ce ta rike masu jakar, da alama jakar babban ce, karamar ta yi karama da abata Alqur'ani mai girma da sauran litattafan addini, bata da wayo sosai. Ita kuma babbar hannunta na rike da wata bakar leda, da alama aika ne a ciki. Sai magana ƴan yaran cikin unguwar suke yi wa karamar, amma bata kula kowa ba, ko ɗaga idanu bata yi ta kalli in da suke ba, kasancewar yanzu aka taso daga islamiyar, yaran dayawa ne suke shawagi a sararin unguwar, kowa yana ƙoƙarin nufar gidansu, saboda mangariba ta kawo kai. Wani ɗan madaidaicin gida waɗan nan matasan ƴan'mata suka shiga, gida ne dai'dai na masu rufin asiri, daga kan kofar gidan har izuwa fentin gidan dukka sun nuna alamun mai gidan mutun ne mai zuciyar yi, kun san ba neman kuɗin ba, zuciyar yi ita ce, akwai masu kuɗin da kuɗinsu bata ciwuwa, akwai kuma wadda zaku gani talaka ne, amma mai zuciyar yi, baya samu sosai kamar sauran mutane, amma da yake akwai zuciyar yi ɗin, sai ku ga ƴaƴansa da gidansa duk kusan dai'dai da na wani mai kuɗin, komai mai kyau zaku ga ya sayawa ƴaƴansa da matarsa gwanin birgewa. Ko'ina na cikin wannan gida siminti ne, babu kasa, an wanke ko'ina fes babu alamar datti ko kaɗan, kana sako kafarka a cikin gidan ma wani daddaɗar kamshin turaren wuta ne zai daki kofofin hancinka, gwanin burgewa gidan. Babbar parlour ce a tsakiya mai ɗauke da ɗakuna uku a cikinta, kowace ɗaki da toilet a cikinta, sai wata ɗaki irin ta matasan nan ta wajen tsakar gidan, filin tsakar gidan tana da girma ba laifi, akwai kitchen a tsakar harabar gidan sai toilet ɗaya da ake yi a ta karshen ginin ɗakuna haka. Wannan mai gida yana da ƙoƙari sosai, har da bohol suke da shi a cikin gidan nasu, suna da ruwa available, ruwa abokin aiki kenan. Parlourn nasu tamkar sauran kowani parlourn na masu rufin asiri ne, kujeru ne set ɗaya manya manya masu laushi, launin ash da baki, sai ƴar madaidaiciyar TV plasmarsu 32 inches, akwai ƴar karamar freezer a ciki ta kusa da TV, sai wasu kyawawan jeren flowers da aka kawata parlourn da su, fanka ke garesu ba A.c ba, haka zalika ceiling garesu ba P.O.P ba, sai dai kasan parlourn nasu fa tiles ne mai kyau da zanen flowers a jikinsa, launin sky blue, ya sha mopping sosai, sam babu alamar datti, ga karamar welcome carpet a bakin kofa, abin dai gwanin birgewa da ban sha'awa, sai tashin kamshi wannan parlourn yake yi, ko'ina tsab kamar ba'a amfani da abubuwan ciki. Tsabta akwai daɗi, kai da kanka idan ka tsabtace waje sai kaga ya yi wani irin masifar kyan gani, komai talaucin mutun idan yana da tsabta yana da sha'awar kallo a ido wlh. Bakinsu ɗauke da cikakkiyar sallama irin ta addinin Musulunci waɗan nan yara suka shigo cikin gidan nasu. Dayawan mutane ba kowa ne yake yin cikakkiyar sallama ko ya amsa sallamar a cikenta ba, dayawa mutane suna yanketa wanda hakan kuma ba dai'dai bane, domin kamar yadda kuka yanketa haka ma'anarta ta yanke. Dayawan mutane zaka ji suna cewa Salamu alaikum, masu amsata kuma suna cewa Alaikumussalam, wanda hakan sam ba dai'dai bane, nasan dayawanku baku san kuskure kuke yi ba, to tabbas kuskure ne yanke sallama da kuke yi, kuna yanke ma'anarta. Masu shigowa zasu ce Assalamu alaikum, Mala'ikun Rahma suna amsata da Amin wa'alailumussalam, idan ku dayawa ne kuka shi go kenan, idan kai ɗaya ne, Amin wa'alaikassalam, shi ne cikakkiyar sallama ta addinin musulunci, Allah ka yafe mana kura kuranmu. Masu cewa in rinƙa rubuta addu'a ko wata tunatarwa kamar dai sallama dana gyara maku yanzu, masu cewa na rinƙa rubutawa da hausa ba da larabci ba, dan basu iya karantawa ba, zan yi ƙoƙarin yin hakan In Sha Allah, amma wani lokaci dole ne na rubuta da larabcin kun gane ai?. Daga cikin ɗaki aka amsa masu cikakkiyar sallamar tasu tare da cewa. "Ƴan mata na an dawo?". Babban cikinsu ne ta amsa da. "E mama mun dawo". Tana magana tana cire hijabin jikinta, sannan ta ajiye wannan ledar dake a hannun nata a tsakar gidan, kafin ta wuce izuwa cikin parlourn. Ita kam karamar dama tun shigowarsu ta sanya kai izuwa cikin parlourn da sauri abinta tana faɗin. "Mama baba ya aiko mun da lemun?.......". Turus ta ja birki a tsakiyar parlourn lokacin da idanuwanta suka sauka a kan maman nata tare da wata bakuwar mata suna zaune a saman sofa suna hira. Mama ta sha kwalliya cikin wani haɗaɗɗen lace mai tsada da ya sha ɗinkin doguwar riga, ta yi kyau sosai, launin black color ne lace ɗin da ratsin milk, hakan ya kara mata kyau sosai kasancewarta farar fata, ta sha ɗaurin ɗan'kwalinta ɗas da shi. Ita kuma wannan bakuwa tana sanye da abaya launin ash color, ta yafa mayafin abayar a kanta. Nan take yarinyar ta ɗaure fuska sosai kamar ba ita ba, duk da cewa dama can fuskar tata ba wani murmushi ne a samansa ba, daga ita har babban yayar tata babu alamar murmushi a saman fuskarsu, da alama basu da yawan fara'a, shi ne ma yasa da suna dawowa daga islamiya sai magana yara sa'anninsu suke yi masu, amma sun ki kula kowa. "Zinarun babanta ya kika tsaya haka? Ki ƙariso ciki mana". Cewar matar dake hira da mamar tasu. Kara ɗaure fuska sosai Zainab ta yi, da alama bata kaunar matar ko kaɗan. Daidai lokacin ita ma babbar ta shigo cikin parlourn tana faɗin. "Mama ga can kayan miyar nan na kawo maki, amma mama wai fa babu attarugun ɗari biyu, shi ne na saya maki ta ɗari biyar kawai, shi ma baki gansa ba ɗan kaɗan da shi........" Bata kai karshen maganar ba ita ma idanuwanta suka sauka a kan wannan matar, ɗaure fuska sosai ita ma ta yi tare da wucewa zata nufi ɗaya daga cikin ɗakunan dake a cikin parlourn. "Khadija baku ga Auntynku bane? Aunty Hauwa ce fa, ba zaku gaisheta bane". Cewar maman tasu. Wucewa Zainab ma ta yi ta rufawa Khadijah ɗin baya, dan su shiga cikin ɗakinsu. "Sannunki da zuwa Aunty Hauwa". Cewar Khadijah, ta yi maganar tana wani irin kunbura kumatu, alamar sam bata ji daɗin sakata gaisheta da aka yi ba. Washe baki Aunty Hauwar ta yi tana faɗin. "Hadiza bage maganin maza, wai ni kam duk masu suna Khadijah haka suke ko? Haka kanwata ma take sam bata son baki". Wata uwar harara Zainab ta wurga mata ba tare da sun lura ba, cikin ɗaki ta wuce abinta, har ga Allah ta tsani wannan Aunty Hauwa ɗin, ko me dalili?. Turɓune fuska Khadijah ɗin ma ta yi kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwa, yara kanana da su sun san kin abu, kome dalilinsu oho. Uniform ɗin jikinsu suka cire, suka sanya kayan gida, wasu dogayen riguna bakake, iri ɗaya kayan, sai dai na Khadijah mai kwalliyar flowers ja ne, na Zainab kuma mai kwalliya pink color, shi ne kawai banbancin kayan nasu. Fitowa suka yi suka sake wuce maman tasu da Aunty Hauwa, waje suka nufa, a lokacin sai kiraye kirayen sallar mangariba ake yi. Famfo tsakar gidan suka je suka kunnna, Khadijah ce ta fara gabatar da alwala kafin ta bawa Zainab waje ita ma ta ɗauro nata alwalar, da alama mamansu ta saba masu da yin komai cikin tsari, dan daga yanayin yanda suka shigo suka je suna cire uniform suka fito suka ɗauro alwalar nan, alama ya nuna cewa tabbas an sabar masu da hakan ne. Ciki suka koma, dai'dai lokacin aka kawo wutar nepa, sallah suka je cikin bedroom nasu da yake tsab tsab suka gabatar, ita kuma mamar tasu tana zaune ta biyewa Aunty Hauwa sai zuba hira suke yi har yaran suka idar da sallarsu. Abin mamaki cikin nutsuwa suke gabatar da sallar nan tasu tamkar wasu manya. Bayan sun idar ne suka fito parlourn, a yadda suka bar mamarsu haka suka fito suka sameta. Khadijah ce ta ce. "Mama yau kin manta baki yi sallah da wuri ba". "Ban manta ba Khadijah, ai ba'a mantuwa da ibada, yanzu nake son tashi na yi". Da gudu Zainab ta nufi kofar fita daga parlourn jin an taɓa kofar gida, faɗi take yi oyoyo baba oyoyo Yah Haidar. Da sauri Khadijah ma ta rufa mata baya, tamkar basu ne masu ɗaure fuska yanzun nan ba, a take suka fara zuba murmushi na ganin mahaifin nasu da kuma yayansu, ashe dai suna dariya, amma da alama ƴan gidansu kawai suke yi wa dariyar. Yah Haidar ɗin nasu yana rike da kaji na hausa guda biyu a hannunsa, zakara da kuma mace, sai kuma wani katuwar bakar leda a ɗayar hannun nasa, shi kuma baban nasu yana rike da wata leda irin mai zane a jikin tan nan, kayan fruit ne a cike a cikin ledar. Khadijah tana zuwa ta fara kiciniyar karɓawa baban nasu ledar hannun nasa, ita kam Zainab tuni ta yi tsalle ta ɗale jikinsa tana dariya har da kyakyatawa, kamar ba ita ce yanzun nan ta gama hararar Aunty Hauwa tare da turɓune fuska ba, dama fa masu suna Zainab da Khadijah wlh sai a hakankali, kusan kaso tamanin cikin ɗarinsu haka suke, akwai shegen tsare gida, sai dai suna yi wa wanda suka ga dama fara'a, kamar dai yadda kuke ganin waɗan nan yaran baban nasu. "Zeezeena kun yi sallah?". Shi ne tambaya ta farko da wannan uban na garin ya fara yi masu, ya yi maganar kuma yana sakewa Khadijah ledar fruit dake a hannunsa, yaran kirki, yana da kyau duk wata uwa ta koyawa ƴarta karɓar abin da mahaifinsu ya shigo da shi, hakan shi ne tarbiya. Khadijah ce ta bashi amsa da. "Mun yi baba, amma mama bata yi ba, tana can suna hira da wannan Aunty Hauwar ta gidansu Khadijan nan na islamiyyarmu". Dariya kaɗan Haidar ya yi yana faɗin. "Ke yanzu Khadijah waye ya tambayeki mama ta yi sallah ko bata yi ba? Ba dai ke kin yi ba? To Allah ya karɓa, ni bana hanaku faɗi ba'a tambayekun nan bane wai?". Ɗaure fuska Khadijah ɗin ta yi tare da wucewa ta nufi cikin parlourn tana turo baki, ita a dole Yah Haidar ya shiga maganarta ba da shi take yi ba, ranta ya ɓaci. Wucewa wajen ɗan madaidaicin kitchen ɗin nasu Haidar ɗin ya yi, a ciki ya ajiye kajin tare da ledar cefenen da yake a hannunsa, sannan ya fito ya nufi wannan ɗakin samarin da yake a harabar gidan. Ita kuwa Zainab baba ya ɗagata sama suka nufi cikin parlourn. Bakinsa ɗauke da cikakkiyar sallama ya shigo cikin parlourn. A tare Aunty Hauwa da maman nasu suka amsa mashi sallamar. Ƙarisowa ciki ya yi tare da wucewa ya nufi ɗaya daga cikin ɗakunan dake a cikin parlourn, har cikin ransa yake jin daɗin shakar wannan daddaɗar kamshin turaren wutar da yake tashi a cikin parlourn, bai ce da Aunty Hauwa ko sannu ba, da alama irin mazan nan ne da idan bakin matansu sun zo gida ba su kulasu, in dai ba su ne suka ɗaga masu gaisuwa ba, to ko sannu ba zasu ce masu ba, ko kallon in da suke ma ba zasu yi ba, dan haka shi ma dai ko kallon Aunty Hauwa ɗin bai yi ba, ya sa kai zai wuce abinsa, yana ɗauke da Zainab a saman kafaɗarsa. Cikin sauri Aunty Hauwa ɗin ta ɗaga mashi gaisuwa tana wani kara faɗaɗa murmushin da yake a saman fuskarta. A takaice ya amsa mata da amsa ɗaya wato lafiya, ya amsa kuma ba tare da ya kalli in da take ba, daga haka kuma yasa kai sai cikin bedroom nasa abinsa. Ajiye ladar da ta karɓo daga hannun baban nata Khadijah ta yi a tsakiyar parlourn, sannan ta yi sauri ta bi bayansa izuwa cikin ɗakin nasa. Miƙewa Aunty Hauwa ta yi tana faɗin. "Babansu Zainab ya dawo, bari na je gobe zan dawo mu karisa maganarmu". Da sauri maman tasu ta ce. "A'a tsaya ki sha fruits mana". Ba kunya ta ce to a bata, ita kuma maman cike da zumuɗi ta buɗe ledar ta fara haɗo mata komai ɗaɗɗaya kamar ita ta kawo ta ajiye. Kuskure ne idan mijinki ya sayo abu ki ɗauka ki yi kyauta da shi ba tare da saninsa ba, ansan cewa duk abin da zai sayo ku ya sayowa, amma kuskure ne ki kyautar baki tambaye shi ba, koda ƴan uwanki zaki bawa, yin hakan wlh sam bai dace ba, kina zubar da kima da kuma darajarki ne a gabansa, kuma hakan yanasawa namiji ya ji ya daina sha'awar saya maku abu idan ya fita, dan zai ga kamar baku ɗauki abin da mutunci da daraja ba, tabbas idan kin tambaye shi zaki yi kyauta da shi zai yi wuya ya hanaki, wannan tambayarsa da zaki yi ɗin zai kara maki kima da daraja, zai kuma sa mijin naki ya ji cewa yana da kima a idanunki da har zaki tambaye shi kafin ki yi kyauta da abin da ya saya maku, koda bai nuna maki ya ji daɗin tambayarsa da kika yi ɗin ba, wlh ina mai tabbatar maki ba ƙaramin daɗi suke ji ba, dan haka koma me ya kawo koda kannenki zaki bawa, ki tambaye shi cewa zaki bawa su wane kaza abu kaza, musamman ma idan a lokacin ya kawo abin, yasan adadin yawansa da in kin kyautar zai gane, wasu mazan in kin tambayesu zasu ce maki to ki bayar mana ba ke suka kawowa ba? Kada ki damu wlh suna jin daɗin tambayar, kuma kada amsarsu yasa gobe ki fasa tambayarsu, ki tambaya ɗin zai fi. Ai kuwa ita dai maman su Zainab duk ta haɗawa Aunty Hauwa fruits ɗin nan komai ɗaɗɗaya, ta ɗauko wani leda daga cikin kitchen ta sanya mata a ciki, sannan ta rakota har kofar gida, sai zuba godiya Aunty Hauwa ake yi kamar me. Naira dubu ɗaya mamansu Zainab ɗin ta bata a kan ta hau abin hawa zuwa gida. Sai murmushi take yi tasa hannu ta karɓa, tana ta zuba godiya ta tafi. Ita kuma Maman Zainab ta juya ta dawo cikin gida. A parlourn ta isko su Zainab suna zaune, bata ce da su ko sannu ba ta yi saurin wucewa cikin ɗakin baban nasu, dan ko ba'a gaya mata ba tasan ya fito daga wanka ne ya ce su Zainab su je parlourn bari ya sanya kaya, dama haka yake yi da su. A hanzarce ta faɗa cikin ɗakin baki ɗauke da sallama, daidai lokacin yana ƙoƙarin zura jallabiya a jikinsa. Ƙarisowa kusa da shi ta yi tana faɗin. "Ka yi hakuri baban Zainab, yau Hauwace ta tsayar da ni ban zo na fitar maka da kayan sakawa ba". Fuskarsa a ɗauke da ƙayatattcen murmushi ya bata amsa da. "Kada ki damu, ai kullum kina fitar mun, dan yau kawai baki yi ba ai ba komai, muje bari maje masallaci lokacin sallar issha ta gabato". Dayawan maza suna bawa mata irin wannan masa da baban Zainab ya bata a yanzu, wanda kuma magana ta gaskiya wlh ba har cikin zuciyarsu wannan amsa take ba, suna dai faɗa ne kawai, dan haka mata sai ku kiyaye, kada ki bari ya maimaita maki irin wannan amsa sau biyu zuwa uku, daga haka za'a fara samun matsala, wani ma idan ya cigaba da maimaita maki sai ki ji ya bushe idanu wata rana yana ce maki ai bama ki taɓa fitar mashi da kayan sawa ko makamancin hakan ba, duk kuma ke kika fara jawowa kanki, kada ki bari dan kin yi bakuwa tasa ki fasa yi wa mijinki abin da kika saba yi mashi, idan bakuwar ba zata jiraki ki yi attending nasa na ɗan lokaci ba, to gara maki ta tafi zai fi, dan haka sai a kula sosai. Murmushi ta yi ita ma tana mai kara bashi hakuri, cigaba da gaya mata babu komai ya yi kafin ya ɗauko perfume nasa mai daɗin kamshi da nufin ya feshe jikinsa da shi. Hannu ta kai ta karɓi perfume ɗin ta fara fesa mashi tana mai yabawa kyan da ya yi. Ba karya fa babansu Zainab kyakkyawa ne sosai, sai dai chocolate color ne, ya fi mamar tasu kyau sosai, ita kuma ta fishi hasken fata, farace sosai, su Zainab duk shi suka ɗauko a kyau, sai dai ita Zainab ta ɗauko hasken mamanta, kyan babanta, ita kuma Khadija komai na baban ne harta launin fata. Bayan ta gama fesa mashi perfume ɗin ne ta ɗauko mashi wayarsa babba da karamar da suke a saman shinfiɗaɗiyar bed nasu 6/7, gadon ya sha gyara kam, ba karya maman Zainab akwai ƙoƙari wajen sake jiki ta yi aikin gidanta da kyau da kyau, yanzu haka wannan jallabiya na jikin baban Zainab ita ce nan ta wanke ta zuba mata guga, sai kyalli take yi, ta sha iron, ita fa maman Zainab da alama gugan kaya baya yi mata wahala, dan harta bedsheet dake a shunfuɗe a saman bed ɗin nan ya sha guga sosai, da yake ma sun saba shan guga sai ka gansu da karin gugan ya fito ɓaro ɓaro, ya riga ya kama kayan, to abu ne da ake yi ba jiya ba ba shekaran jiya ba, an jima, dole kunga su kama karin guga. Parlourn suka fito, a nan ya isko sanyin idaniyarsa wato ƴaƴan nasa, Zainab tana kallon Tv, ita kuma Khadija tana rike da wayar mamanta tana buga game. "Zeezeena zan je masallaci amin addu'a". Ya faɗa yana nufar kofar fita daga cikin parlourn. Har suna rige rige ita da Khadijah wajen zuba mashi addu'ar adawo lafiya Allah ya tsare ya kiyaye hanya. Da amin ya amsa masu kafin ya fice. Har harabar gidan maman nasu ta rako shi kafin ta dawo wajen famfo dake harabar gidan ta ɗauro alwala, a lokacin aka fara kiraye kirayen sallar issha. Fitowa daga nasa ɗakin Haidar ya yi, cikin sauri ya kariso wajen famfon dan shi ma ya ɗauro alwala. Sannu ya yi wa maman Zainab ɗin tare da tsayawa a gefe guda yana jiranta ta gama. Amsa mashi sannun nasa ta yi tare da tambayarsa ya kasuwa. Alhdulillah ya amsa mata da shi, sannan ya ɗaura mata da cewa. "Sadiq dai yaki dawowa yau ɗin ko?". Ɗagowa ta yi daga wajen fanfom tare da kasheta tana faɗin. "Ba yadda ban yi da shi ba a kan ya dawo, ya ce mun sam shi bai kalli mama sosai ba, wai sai jibi zai dawo". Ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi hanyar komawa cikin parlourn. "Gaskiya Sadiq bai kyauta mun ba, sam goben nan ban so fita kasuwa ba, dan ina da wanki da ɗan aikace aikace da zan yi a ɗakinmu, amma shi ne yaki dawowa, next time ba zan barshi ya yi tafiyar nan ba". Murmushi kaɗan ta yi tana faɗin. "Ai kun fi kusa". Daga haka ta wuce ciki abinta. A parlourn ta isko su Zainab ɗin a saman dadduma, sallah suke yi, wucewa nata bedroom ɗin ta yi, dan ta biya sallar mangariba kafin ta ɗaura da issha. Bayan sun idar da sallar, zama suka yi a saman dadduma Khadija tana karawa Zainab karatun malumat da Nahhu, a haka babansu ya dawo daga masallaci ya samesu, a lokacin kuma mamansu ta idar da nata sallar har ta zo ta ɗauki fruit ɗin da ya kawo ta wankesu tsab, ta zuba masu su a cikin plate tare da sanya masu wuƙa a saman plate ɗin wanda zasu yanka fruit ɗin, ta ajiye a tsakiyar parlourn haɗe da abincin darensu, akwaita da ƙoƙarin aiki kam, bata da son jiki, bayan ta yi dukka wannan ma kitchen ta wuce ta hau shirya kayan cefanen da Haidar ya shigar dasu ciki, su curry ne dasu maggi, kayan kamshi da dai sauran kayan girki, su tattasai da attarugu ne kawai babu a ciki, baban Zainab akwai shi da iya sayan kayan kamshin girki, ya iya cefene sosai kamar wata mace, idan ya yi cefenensa ma yafi wata macen. Bayan ta shiryasu cikin robobin kayan miyarta ne ta dawo ta ɗauki kayan miyar da Khadijah ta ajiye mata a tsakar harabar gidan, tomatoes ne da su attarugu, dama su babansu bai cika sayo irinsu a cikin cefenensa ba, da yake cefenen sati sati yake yi, su kuɗi yake bawa maman nasu ta saya. Kitchen ta kai kayan miyar ta shiryasu yadda ya dace, dan na miyar gobe da safe ne, dama haka suke yi kullum, tun da yamma a hanyar islamiya Khadijah take yo masu cefanen su tomatoes na miyan washegari, dan su ajiye komai ready, saboda kada su Khadijah su yi lattin zuwa makarantar boko a dalilin jiran girki ya nuna. A parlourn ta isko baban nasu tare da Haidar sun dawo daga masallaci, a kusa da baban ta zauna tare da fara ƙoƙarin zuba masu abinci, dan duk zaman cin abinci suka yi, da alama da yunwa suka dawo daga kasuwar nan. Jawo plate na kayan fruits ɗin nan baban nasu ya yi, fuskarsa ɗauke da ƙayatattcen murmushi ya fara faɗin. "Zeezeena zo ki sha lemun da kika yi ta tuna mun a waya na saya, sarkin son lemu". Khadijah ce ta ce. "Baba ni kuma ina inabi na?". "Mamana na sayo maki kema ai, ban manta ba, duk kuzo ku sha". Ya yi maganar yana yankawa Zainab lemun zakin da ya ɗauko. Yana yanka lemun yana kallon cikin plate na fruits ɗin, idanuwansa kamar suna yi mashi gizo ne, dan bai ga inabin Khadijah a ciki ba, kuma itace ɗaya ya sayo inabin dama, wa ita kaɗai, ita kaɗai ya sayawa, dan ita kaɗai take shan inabi a gidan, Zainab lemu take so, ita kuma mamansu Apple, kowa da abin da ya fi so, shiyasa idan ya tashi saya yake sayowa kowa nasa, baya manta na kowa, shi kuma kankana yake sha shi da Haidar, sun fi sonta. "Maman Zainab kin rage wasu fruits kin saka a cikin fridge ne?". Ya yi maganar yana miƙawa Zainab lemu. Tana kan zuba masu white rice and beans ɗin a cikin plate ta bashi amsa da. "A'a ban rage komai ba, dukka fruits ɗin ne kenan". Dawo da kallonsa a kan Haidar ya yi kafin ya ce. "Haidar malam Sani bai saka mana inabin Khadijah da kuma abarba ba". "Any kuwa? Kamar fa ya saka a ciki, naga lokacin da ya ɗauko ya saka". Haidar ya bashi amsa. "To amma ya babu a ciki?". Baban ya sake jefa masu tambaya fuskarsa da alamar damuwa, dan shi mutun ne da baya son ko da sunan wasa ƴaƴansa su ji cewa kamar yana yi masu banbanci a tsakaninsu, da yasan babu inabi da ba zai bawa Zainab lemun nan ba har sai ya sake fita ya sayowa Khadijah nata, sai ya dawo ya basu a tare, dan komai a tare yake yi masu, yana nuna masu cewa dukkansu ɗaya. Shiru maman Zainab ɗin ta ɗan yi na ƴan sakani kafin ta ce "E akwai inabi fa, dan na ɗauki itace ɗaya ma na haɗawa Hauwa a cikin fruit dana ɗeba mata". Da sauri ya ɗago kai tare da watsa mata wani irin kallo mai nuni dacewa meyasa zata yi hakan?, domin kuwa inabi guda ɗaya ya sayawa Khadijah ita kaɗai. Amma duba da yaran suna nan sai bai yi magana ba, ya yi shiru, har cikin ransa sam bai ji daɗim hakan ba, sai ma ya ji duk abincin ta fita mashi a ransa, ya ji babu daɗi sosai, ya sayowa ƴaƴansa abu ta wani ɗauka ta kyautar kamar ya aiketa, in da ma kankanarsa ta kyautar ba zai damu ba, amma na Khadija takwarar mamansa guda, gaskiya bata kyauta mashi ba. "Kiyi hakuri mamana, bari Yah Haidar ya je ya sayo maki wani yanzu nan, jeki ɗaki ki ɗauko kuɗi a wajen drawer ta ki kawo mun". Ya faɗa cikin sanyin murya, daga jin yanayin maganarsa kasan sam bai ji daɗin abin da maman nasu ta yi ba, ita ma kuma ta lura da bai ji daɗin ba, duk sai ta ji babu daɗi ita ɗin ma. "A'a ta bar kuɗin da akwai kuɗi a jikina bari na sayo mata da shi". Cewar Haidar. Taɓe baki maman Zainab ɗin ta yi tana mamaki, yau Haidar da kyauta, sam baya taɓa masu kyautar ko Naira biyar ɗunsa, idan kaga ya bawa su Khadijah kyautar wani abin ci ma ba kuɗi ba to wlh sai idan babansu yana nan, eyes service gare shi, in babansu baya nan ko tsinkensa basu ci. Allah mai iko, kaga dayawa idan kana raye. Miƙewa ya yi ya fice daga parlourn, sai hakuri baban nasu yake ta bawa Khadijah, ta dai ce mashi to, amma ji take kamar zata fashe dan haushi, sai ta ji ta kara tsanar wannan Aunty Hauwar. (Masu suna Khadijah idan suka tsaneka ka shiga uku😅 kome zaka musu ba zasu ga farinka ba😅 in sun riga sun saneka fa to sai dai ka yi hakuri ka rungumi sorry ka kyalesu😅 ina ga dalilin cinye masu abubuwa da Aunty Hauwa take yi yasa suka tsaneta😅) Abincin suka fara ci cikin nutsuwa, maman Zainab ba dai iya girki ba, ta kware sosai, idan kana cin girkinta idan ka yi wasa sai ka fara zuba santi ba tare da ka sani ba, saboda daɗi da iya tsara girkin. A wannan hali Haidar ya dawo ya samesu, bai samu inabi ba, masu fruits na unguwar tasu duk basu kawo inabi, kun san yana da tsada, ba kowa yake sayansa ba, hakan yasa ba kowani mai sai da fruits yake kawo shi ba, sai manya masu sayarwa. Jin cewa ba'a sami inabin ba yasa Khadijah ta fashe da kuka tare da miƙewa ta bar abincin nata, fuuu ta nufi cikin ɗaki. Kallon maman baban nasu ya yi, irin kallon nan na ke kika jamun, ita ma shi take kallo, irin kallon nan na kayi hakuri. Bai ce da ita ko uppan ba ya miƙe ya bi bayan ƴar tasa dan ya rarrasheta, ga shi kuma dare ne, idan ya ce zai je neman inabi a yanzu sai ya hau mashi ya fita cikin gari ta wajajen kasuwar tasu, zuwa wajen kawai ma 500 naira ne kuɗin mashi, dawowa ma haka, bare kuma daren nan kunsan kara kuɗin mashi suke yi, gaskiya maman Zainab dai bata kyauta mashi ba, kuma idan bai nemo wannan inabi ba Khadijah dai ƙaramin aikinta ne ta yi mafarki, shi ma dai ba zai iya yin barci cikin daɗin rai ba, dan yasan waye Khadijah bagensa, sarkin zuciya da rigima, dole dai anemo inabi, kuma tsautsayi ne tasa yau ya sayi inabin guda ɗaya, sau da dama biyu ko ukku yake saya, zaka gansu a jikin itacensu ba'a cire ba an sako mashi guda uku, to yau sai malam Sani ya saka masu guda ɗaya tak, Mama ta bawa Aunty Hauwa, aiki babba kenan, akwai rigima. Nikuma dole na dakata da rubutu a nan, Maman Zainab baki kyauta mana ba, shiyasa ake son a rinƙa tambayar mutun abu idan ya kawo, ba wai ayi gaban kai ba.....….😌😒 *Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 3/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________6🔥 Kwance ya isko Khadijah kadina kadin Allah a saman ƴar madaidaiciyar bed nasu 6 by 6. Gadon a shunfuɗe yake da zanin gado mai kyau lunin pink color da ratsin baki, tsab da shi, sai kamshi ɗakin nasu ma yake yi, ga drawer kayansu mai ɗan girma a gefe guda, sai drawer bed ɗin da suke jera kayan kwalliyarsu da kuma mayukan shafawarsu. Sai wani irin kuka take yi, irin kukan nan da idan mutun zuciyarsa ta hasala sosai, sai ka ji yana wani irin kuka kamar mai sifirin..........😅 To haka Khadijah take wanan kuka. A bakin bed ɗin ya zauna tare da sanya hannu ya ɗagota yana mai bata hakuri. Cigaba da kuka ta yi abinta, tana yi tana wani irin jan numfashi alamar fa ta kai kololuwa wajen jin haushi. "Mamana ta shi ki je ki ɗauko hijabinki mu je bakin kasuwa a tare mu sayo wani inabin kin ji?". Ya faɗa cikin sigar rarrashi. Maƙe mashi kafaɗa ta yi, da kyar ta iya cewa. "Ni baba ka bari sai gobe, kada ka fita da daddaren nan, kaga ranar ma da ka fita sayowa Zainab magani masu kwacen waya sun tareka a hanya ko? Tom ka bari sai gobe kawai ka dawo mun da shi daga kasuwa". Tana magana wasu hawaye suna gangaro mata, kai daga jin maganar tata kasan ba daga cikin zuciyarta ya fito ba, ta faɗa mashi hakan ne kawai dan son da take yi mashi, bata son waɗan nan gurɓatattun mutane masu kwacen wayar su yi mashi illah, dan a wancan karon da suka tare shi har sun buge shi da sanda a hannu, sannan suka kwace mashi waya, haka hannun nasa ta kumbura tsawon sati biyu baya zuwa kasuwa, baya fita ko'ina, da kyar ya samu hannun ta yi sauki, shi ne yasa yanzu da sun yi sallar issha dai sun shiga kenan, zasu rufe gidan abinsu, a lokacin da abin ya faru Khadijah ta sha kuka kamar ba gobe, dan tana tsananin son baban nata, yana kyautata masu over. "Amma mamana ki bari naje a sayo maki, dan nasan kina so, ga shi ma kin kasa dai'na yin kuka, kawai ki barshi bari na je na saya maki". Cikin sauri ta kai hannunta a saman face nata ta fara goge hawayen nata tana faɗin. "Baba ga shi nan ai na dai'na yin kukan, ni dai ka bari sai gobe ka sayo mun". Ƙaƙalo murmushin dole ya yi tare da sanya nashi hannun ya fara tayata goge hawayen yana faɗin. "Tom shikenan, gobe idan Allah ya kaimu guda biyu zan sayo maki, yanzu tashi muje mu ci abinci ko?". "Baba Allah bana son wannan Aunty Hauwar, haushi take bani, kullum idan ta zo gidan nan sai mama ta bata abubuwanmu ta tafi da shi gidanta". Ƴar murmushi ya yi kafin ya fara bata amsa da cewa. "Haba mamana, kada ki zama mai rowa mana, menene dan mamanki ta bawa wata kyautar abu? Ai lada zamu samu, kin ga wannan Aunty Hauwar taku? Mamanku bata da kawa biyunta, tare suka taso unguwa guda, a tare suka yi wasan kasa, a tare suka yi karatu, Allah da ikonsa kuma sai ya kawosu aure gari guda, kin dai san mamanki bata da kowa a nan ko? Iya ƴan uwana kawai ke gareta, nata ƴan uwan babu ko mutun ɗaya a nan, to haka ita ma wannan Aunty Hauwar, bata da kowa sai ƴan uwan mijinta sai kuma mamanku, kinga dole zasu kaunaci juna su kuma haɗa kai da juna dan su ɗebewa junansu kewar iyayensu da ƴan uwa, dan haka ki dai'na cewa kin tsaneta kin ji ko? A matsayin ƴar uwar mamanku take, ku ɗauketa tamkar kawu Sadiq naku, ba kuna son Kawu Sadiq ba?". Da suri ta gyaɗa mashi kai tare da faɗin. "E baba muna son kawu Sadiq sosai, kullum baya taɓa dawowa gidan nan ba tare da ya kawo mana abin kwalama ba, amma shi Yah Haidar sam baya bamu komai, sai shegen masifa ya iya, shiyasa ni nafi son kawu Sadiq nawa". Shiru baban nata ya yi, har cikin ransa bai ji daɗin maganarta ba, ransa ya sosu, amma ya zai yi? Gaskiya take faɗa, dan Khadijah bata karya, Haidar ɗin shi ya jawa kansa. Nasan zaku so sanin wanene Haidar a gare su, wanene kuma Sadiq, to Haidar dai ɗane ga babbar ƴar babansu, wanda tun yana ƙarami baban nasu ya rike shi, a tare suke zuwa kasuwa, yana taya shi sayar da kaya, mutun ne shi mai irin halin mata, akwai shi da gulma, ga shegen iya eyes service, idan babansu yana nan zai kulasu, a bayan idanun babansu kuma sai hantararsu ya iya yi da zagi, baya wani kulasu, maman nasu ma ba wani ɗaukarta da daraja ya yi ba, ta rike shi tun yana ɗan shekara 8, yanzu har ya kai 18 years a duniya, amma hakan bata hana idan ta yi mashi ba dai'dai ba ya yi mata rashin mutunci, ga shehen kai gulma cikin dangi, ya ja ayi ta zagin Mamansu Zainab ɗin a kan ta mallake babansu, abu dai babu daɗi, yanzu duk ƴan uwan mijinta basu sonta, kuma duk wannan Haidar ɗin shi ne sila, ya je yana kwasan duk sirrin gidan yana kaiwa dangi, har da karawa da karyarsa son ransa. Shi kuma Sadiq kani ne ga maman nasu, yaron kirki, ko da yake dama dole ya zamana yana kaunarsu Zainab ɗin sosai, saboda ƴar uwarsa, tun da aka aurota tana amarya ta taho da shi, dan bata da kanwa mace, sai shi kaɗai, shi ne ta roki babanta lokacin tun yana da rai, ta roƙe shi ya bata Sadiq ɗin, da kyar aka yarda aka bata shi, a lokacin yana da shekaru 7 a duniya, ta rike shi har yanzu ya kai yana da 17 years, yaron kirki mai yin komai tsakaninsa da Allah, yana kaunar su Khadijah ɗin sosai, ko fita ya yi waje zai sayi abu, to ba zai dawo cikin gidan ba sai da sweet ko biscuits, ya kawo masu, su yi ta murya, yana kyautata masu sosai, duk abu mai kyau idan ya gani zai saya masu ya kawo masu, ko kaya ya gani a kasuwa an kawo sabbi masu kyau, da kuɗinsa yake cirewa ya saya masu, wani lokaci har faɗa yake yi da Haidar ɗin akan hantararsu Khadijah ɗin da yake yi idan babansu baya nan, kullum kuma idan suka yi faɗa sai Haidar ɗin ya yi mashi gorin cewa wai iyayensa basu da karfin rikesa ne yasa suka haɗawa kawunsa wato banansu Zainab ɗin kenan nauyi, wai yazo yana cinye masu arziki shi da ƴarsa, wani lokaci har ikirarin cewa sai ya yi sanadiyar barinsu gidan daga shi har ƴaƴar tasa Haidar ɗin yake yi, shi ala dole ana cinyewa kawunsa kuɗi, saboda jahilci, bai san me ake nufi da mata ba!. Wani lokaci har kuka Sadiq ɗin yake yi ya ce ba zai zauna a gidan ba zai koma garinsu, dan yana da zuciya, Mamansu Zainab ɗin ce take bashi hakuri ta yi ta lallaɓa shi, ta ce mashi idan ya koma ya barta ita da waye zata zauna? Waye zata gani ta ji daɗin rayuwa? Ya sani ƴan uwan mijinta duk basu sonta, idan ya tafi ya zata yi da rayuwarta?. Da haka take lallaɓa shi ya yi hakuri ya zauna. Shi Sadiq ya yi karatu, yanzu haka yana Ss3, shi kuwa Haidar tun daga primary 4 ya fasawa malamin English nasu kai dan bai yi class work da aka basu ba malamin ya zane shi, shi ne ya fasa mashi kai da katako ya gudu ya bar makarantar, tun daga lokacin ya ce ya ajiye karatu, ba yadda ba'ayi da shi ba ya koma makaranta, amma fir yaki yarda, har canza mashi makaranta banansu Zainab ya sake yi, amma sam yaron nan yaki, ya ce shi neman kuɗi zai yi, ga jahinci a cike da kai, shiyasa yake gulmace gulmace da tsugudidi tare da kananan maganganu, da ace yana da ilimi ya yi karatu, da sam ba zai yi wannan shirme ba, yanzu yana nan babu boko babu Arabic, shiyasa a haukarsa yake ganin cewa wai Mamansu Zainab tana cinyewa kawunsa kuɗi ne ita da kaninta Sadiq, to bai ma san me ake nufi da mata ba, ba ilimi, matar ma wadda ta haifawa kawun nasa ƴaƴa har guda biyu, ai ta wuce wasa. Allah ya gani baban Zainab yana iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya kyautata masu, daga Haidar ɗin har sauran ƴan uwansa, shi yake ciyar da Mamansu Haidar ɗin, dan mijinta dai sai a hankali, bashi da ko sisi ba aikin yi, hakan tasa baban Zainab ɗin yake ɗawainiya dasu, amma duk basu gani, sai suce Maman Zainab tana hana shi ya taimaka masu, ta kanainaiye komai ita da ƴan uwanta. A kasuwa duk wani harkar kuɗi da lissafi da Sadiq baban Zainab yake yi, dan Haidar kam kan fanko ce, bai san komai ba, hakan ne ma yasa ƴan uwan baban Zainab ɗin suka dage a kan lallai maman Zainab asiri ta yi wa ɗan uwansu, wai tun da harta harkar kuɗi a kasuwa da Sadiq kaninta ake yi, Haidar ya zama bare saniyar ware ɗan kallo, ita dai maman Zainab sai dai ta toshe kunne kawai baiwar Allah, shi ma Sadiq ɗin yanzu dan dolensa ya ko yi toshe kunnensa, baya kula kowa, idan maman Haidar ta isko shi a kasuwa, zagi da cin mutuncin kala kala take yi mashi, idan ta gama sai ya ce Allah ya bata hakuri kawai, dan bai san me zai cigaba da ce mata ba kuma. Wannan shi ne kaɗan daga cikin tarihin Sadiq da Haidar, to mu je dai zuwa. "Baba ya ka yi shiru?". Cewar Khadijah. Doguwar numfashi ya ja tare da saukewa a hankali. "Babu komai mamana, muje parlourn ki ci abinci ko?". Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar to suje. Miƙewa ya yi tare da riƙo hannunta ya sauketa kasa, sannan suka nufi parlourn. A yadda suka bar Zainab da Maman Zainab haka suka dawo suka samesu, kasancewar baban nasu yana nan ne yasa Haidar ya ce. "Khadijah uwar rigima, daga cewa ba'a sami inabin ba har kin fara kuka". Cewar Haidar sarkin eyes service. Wata uwar harara ta wurga mashi ba tare da ta amsa mashi ba, yanzu haushin kowa take ji, har maman nata da ta bawa Aunty Hauwa wannan inabin, ita ma duk haushinta take ji. A baki baban nasu ya rinƙa bata abinci yana rarrashinta, yau an yi sa'a ƴan mutunci suna gaba goshi, dan haka sai ta hakura ta ci abincin, ba musu. Bayan sun kammala ne suka zauna yin kallo kaɗan, ita kuma Maman Zainab ta hau tattare kayan abinci. A cikin wannan daren ta yi wanke wankenta, ita bata barin kayan abincin da aka yi anfani da su da daddare su kai wayewan garin gobe, a daren take wanke su tsab, haka kayan wanki, waɗan da aka cire a ranar bata taɓa bari ya kai gobe ma bare har ya taru mata sosai, a ranar take wanke su abinta, so haka ta wanke kayan abincin nan fes tare da dawowa ta sake yin mopping na parlourn sosai, sannan ta kunna buner ta zuba turaren wuta mai daɗin kamshi kafin ta haye saman sofa kusa da baban nasu ta zauna. Wani American film suke kallah a MBC, sun nutsu tsit kamar babu kowa, ita kuma Khadijah kaf hankalinta baya a kan Tv, sai tunanin islamiya take yi, dan an kara masu karatu yau, kuma da daddare ne kawai take samun damar yin karatun, da safe zasu tafi makarantar boko, ba zasu dawo ba sai karfe uku, idan suka dawo kafin su ci abinci su yi wanka haɗe da shirin islamiyar, karfe huɗu ta yi, dole islamiyar zasu wuce a dai'dai wannan lokacin, so babu time, yanzu haka Khadijah tana primary 2 a makarantar boko, ita kuma Zainab primary one zata shiga yanzu, suna da ƙoƙari sosai, saboda kula da suke samu daga wajen iyayensu, babansu ba wai ɗan kasuwa bane kawai, degree gare shi a fannin electric engr, kuma ya fito ne da first class, kawai yanayin kasar ce tasa ya zama ɗan kasuwa mai sayar da atamfofi, lace, shadda, da dai sauransu, babu aikin yi, ya gama karatu bai sami aiki ba, shi ne ya zaɓi ya fara kasuwancinsa kawai, ya tattara result na makarantar ya ajiye a gefe guda. Mammansu kuwa ta gama secondary school nata, tana da ilimi dai'dai gwargwado, sannan macece mai ilimin addini, ga saukin kai da tausayi tare da fawwalawa Allah komai nata, so a takaice dukkansu daga maman har baban duk ba jahilai bane ba, suna da ilimi, shi ne yasa suke kula da karatun su Khadijah sosai da sosai. Sai misalin ƙarfe 9:30 su Khadijah suka miƙe suna yi wa iyayen nasu sai da safe, dama already sun rigada sun sani, karfe 9:30 suke shiga su kwanta, saboda tashi zuwa makaranta, tun suna yara mamansu ta tsara masu tsari mai kyau na rayuwa, wani abin ba sai ance su yi ba, sun riga da sun saba yi. "Mamana kada ku manta ku yi addu'ar kwanciya, nima zanzo in yi maku nawa idan zamu shiga". Cewar babansu. Da to suka amsa mashi tare da wucewa cikin ɗakin nasu. Wata riga da wando mai laushi sosai Khadija ta ɗauko masu daga cikin drawer saka kayansu, iri ɗaya ne kayan launin navy blue. Miƙawa Zainab nata ta yi, karɓa ta yi suka hau canza kayan ba ɓata lokaci, kayan barcinsu ne. Bayan sun canza Zainab ta haye saman gado, ita kuma Khadijah ta ɗauko takardun islamiyarsu tare da ɗauko littafinta na Nahhu ta buɗe shafin filul mahdi dan ta kara duba karin karatun da aka yi masu. Ta ɗauki a kallah minti goma tana ta karanta wannan filul mahdi'n kafin ta rufe takardar ta mayar cikin jaka, sannan ta mayar da jakar mazauninta, a lokacin har Zainab ta fara zuba barcinta abinta. Zama ta yi a tsakiyar gadon ta fara karanta kulhuwallahu kafa uku, falaki da nasi suma kafa uku uku, sai ayatul kursiyu kafa ɗaya, sannan amanar rasulu shi ma kafa ɗaya, ta tofa a hannunta kafin ta shafa a jikinta gabaɗaya, ta juya ta shafawa Zainab ma, kamar wata babban mace, bayan ta shafa mata ne ta jawo masu bargo, dan garin akwai sanyi sosai, gari ne na damina, Khadijah tana tsananin son Zainab over to over wlh, ita kaɗai ce ke gareta. Su kuma iyayen nasu, sai da suka kai har karfe 11 suna kallo, sai da suka ƙarisa kallon wannan film ɗin, shi ma Haidar saboda tsabar gulma yaki wucewa ɗakinsu, yana nan a tare suka ƙarisa kallon, sannan ya miƙe ya nufi ɗakin nasu yana yi masu sai da safe. Mamance kawai ta amsa, baba bai amsa ba, dan shi har ga Allah baya son wannan hali na Haidar, kawai ba yadda zai yi ne, ya yi iyaka bakin ƙoƙarinsa a kan yaron nan ya canza hali, ya koma makaranta lokaci bata kure mashi ba, amma sam yaki yarda, ya zauna sai shirmen banza da wofi yake yi, yana mayar da kansa irin local matan nan masu shegen tsugudidi. Ga shi babu halin baban Zainab ɗin ya kore shi daga gidan, dama yaya lafiyar kura bare ace ta yi zawo? Yanzu ma ana cewa maman Zainab ta yi mashi asiri ta mallake shi, to ina ga kuma idan ya kori Haidar? Ai shikenan abu ya sake kwaɓewa, sai aje ayi ɓatattciya da dangi, zaman lafiyarsa kawai ya cigaba da bin Haidar ɗin da idanu har lokacin da zai girma hankalin manyantaka ta shigesa, wata kila a lokacin zai iya gane dai'dai da ba dai'dai ba. Miƙewa baban Zainab ya yi ya je ya rufo masu kofar parlourn bayan tafiyar Haidar ɗin kenan, dama already ya rufe masu kofar gida kam tun tuni, suna dawowa daga sallar issha suke garƙame kofar gidansu, saboda tsaro, akwai gurɓatattun matasa ɓata gari a unguwar tasu sosai, shi ne yasa basu wasa da rufe kofar gida. Kowannensu ɗakinsa daban, baban nasa daban, ita ma Maman nata daban, amma dayawa lokuta a ɗaki ɗaya suke kwana, inma na maman or na baban, a dai ɗaki ɗaya suke kwana, yau ma ɗakin baban suka wuce a tare bayan sun kashe kayan kallon nasu tare da wutar parlourn haɗe da tattare komai nasu, suka shiga wajensu Zainab suka yi masu addu'a, sannan ne suka nufi ɗakin barcinsu. A suba ta gari............ ♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥♥︎♥︎♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥ 🏞️Forest🏞️ Tun da Kamran ya yi wannn barci bai farka ba har washegari da safe, abin abin ban mamaki mai rikitarwa, ko da ya farka kuma ya jima sosai idanuwansa biyu ya kasa motsawa, jikinsa duk wani irin azabbabben ciwo yake yi mashi, duk ya ji wani irin tamkar ba shi ba, kamar wanda ya sha kayan maye overdose suka sanya shi barci, jin jikinsa yake yi tamkar ba shi ba, kamar an canza shi, da kyar ya iya samun dama ma ya waro idanuwansa waje, wani irin nauyi idanun nasa suka yi mashi, da farko ma ji ya yi tamkar an manne mashi su da super glue, sai da ya yi da gaske ne ya iya buɗesu. A hankali hankali ya fara kallon wani irin jiri jiri tana ɗebarsa daga kwance, saman ɗakin nasa ne ya fara juya mashi kamar fanka. To me ya sami Kamran ɗin mu?. Dishi dishi idanuwansa suka fara ganin masa, like idan mutun yana ƙoƙarin sumewa, haka zai fara gani dishi dishi, yunƙurin miƙewa ya fara yi domin ya lura abin tana so ta fi karfinsa, sai dai ina, bai iya ko motsin kirki ba, tamkar an sanya igiya ne aka ɗaure shi ɗaurin goro, ƙoƙarin buɗe bakinsa ya yi domin ya kira Mamma, nan ma ina ya kasa, dan kuwa ji ya yi tamkar an ɗaure harshen nasa ne kam, ya kasa. Sanya dukka ilahirin karfinsa ya yi da nufin ya miƙe da karfin gaske, duk da haka a banza man kare, ko motsawa bai iya yi ba, ya juyar da idanuwansa ya kalli gefe guda ma ya kasa, iya saman ɗakin nasa kawai yake iya kallah, duk wata jijiya a jikinsa sai da ta tsaya sak da aiki! Jinin jikinsa duk ya dai'na gudu, nan take idanuwansa suka kara firfitowa waje sosai tamkar zasu faɗi ƙasa, tamkar wadda aka matse sosai, sai ƙoƙarin ya yi magana yake yi, yana son ya kira Mamma ta kawo mashi agaji, amma ina ya kasa, harshensa ma a ɗaure take gam. Dai'dai lokacin Mammar ta faɗo cikin ɗakin tana faɗin. "Tun jiya barci yaki karewa kamar ba lafiya ba, maza ka tashi lokacin motsa jiki ya yi, ka kama ka tafi yawonka ba dole ka gaji ka yi ta barci ba, kafa baya zama waje ɗaya, baka bawa jikinka hakkinsa na hutawa!". Jin motsin shigowar Mamma tana waɗan nan surutan ne yasa gabaɗaya ya ji jikin nasa ta sake, nan take ya ji ya koma normal kamar ba shi ba, abin da ɗaure kai da kuma mamaki. Waro idanuwnsa da suke jajir saboda barci ya yi a kan Maman tasa dake tsaye a kusa da bed ɗin nasa tana faɗin ya tashi su tafi, ya zo sai wani zuba barci yake yi tun jiya da yamma, da daddare ta tashe shi har ta godewa Allah yaki ya tashi, har ruwa ta shafa mashi a fuska, amma yaki tashi, sai dai ya ɗan motsa kaɗan ya sake cigaba da barcin abinsa, da farko abin har ya fara bata tsoro, sai daga baya kuma ta kyale shi kawai ta je ta ci abincinta ta kwanta, to shi ne fa bai iya farkawa ba sai yanzu, e gaskiya kam abin da abin mamaki sosai Wlh, akwai kuma ɗaure kai!. Kada ku manta daga cikin littafin RAWANIN ZALINCI wanda alkalamina ni PRINCESS TEEMA ya rubuta maku kuke karanta wannan daddaɗar labari mai cike da ruɗu da ɗaure kai, to yanzu muka fara, bamu ma fara kutsawa cikin labarin ba tukun nan, bamu ma yi komai ba, ku dai ku kasance dani, na tabbata In Sha Allah ba zaku taɓa yin danasanin karatan wannan littafin ba!. Har yanzu lokacin harshensa ta yi mashi nauyi wajen magana, da kyar ya iya furta. "Mamma ya naji kina cewa tun jiya nake barci sai yau na tashi? Kina nufin kwana ɗaya ta wuce kenan?". "E mana Kamran, kwana ɗaya ta wuce, wai me kasha jiya ne? Ka je ka sha ƴaƴan wata itaciyar mai bugar da mutun ko? Ina ta tashinka daga barci kaki ka tashi" . Zaro idanuwansa ya yi tare da furta what?! Da ɗan karfin, kwana ɗaya ta wuce kuma? Ya sake tambayar kansa. Ganin haka yasa Maman ta ce. "Kamran anya are you okey kuwa? Menene kuma ya faru?". Ɗago dara daran idanuwan nan nasa ya yi a in da ya sauke su a saman fuskarta, shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Mamma yau ba zan motsa jiki ba, ina zuwa, bari na je nan baya yanzun nan na dawo, sai na zo na yi wanka......." Wani irin kallo da ta wurga mashi da waɗan nan sexy eyes ɗin nata ne yasa bai san lokacin da ya haɗiye sauran maganar tasa bai ƙarisar ba. "Wuce muje ka fara aikin motsa jiki, idan ka gama ka yi wanka ka ci abinci sai ka tafi in da zaka je, dama zaka je kawo mana nama ai, babu abin da zai hanaka yin training, wai shin ni ina ma ka je jiya da ka dawo mun kamar a buge ne?". Da kyar ya iya miƙewa zaune yana turɓune fuska tare da ɓata rai. "Mamma ni ina kuma zanje da ya wuce in da muka saba ni da Rocky, wai Mamma please yau ki kyaleni da zancen motsa jikin nan mana". Shiru ta yi mashi bata sake ce mashi ko uppan ba. Yasan fassarar shirunta, hakan yana nufin dole sai ya motsa jikin nan ko yana so ko baya so, ga kuma ciwo a yatsarsa. Dole tasa ya miƙe jiki duk ciwo take mashi, gaɓɓansa duk suna yi mashi zafi, haka ya wuce gaba yana kara turɓu ne fuska. Rufa mashi baya ta yi, a saman tsaunin ta bayan kogon nasu suka tsaya, ga wasu manya da kananan duwatsu a wajen, a nan suka tsaya ya fara aikin training da waɗan nan duwatsu, ita kuma Mamma ta wani tsaya kamar jarumar sadaukiyar yaki, yacce kuka san wata commender masu bawa mayaka horo, haka ta wani tsaya tana aikin kirga sau nawa ya ɗaga wata katuwar dutse. Sai da ya ɗaga sau hamsin cif tana kirgawa, sannan ta ce ya fara press up, haka ya fara yi kamar zai yi kuka, yau duk jikinsa ciwo take yi mashi, ga shi Mamma ta zo tana kara mashi azaba a kan azaba, haka dai ba yadda ya iya, dole ne ya yi idan yana son zaman lafiya. Da Mamma ta lura fa baya yi da sauri zai ɓata mata lokaci, sai ta koma cikin ƙogon nasu. Tana tafiya ya yi zamansa yana tunanin maman twins, sai wani mai da numfashi yake yi da sauri da sauri, irin ya sha aiki ya ƙoshin nan. A hanzarce ya tashi ya cigaba da yi jin alamar takun dawowar Mamma wajen, ba shiri ya ɗaura daga in da ya tsaya. Kusa da shi ta zo ta tsugunna hannunta na rike da wata iriyar doguwar takobi na mayaƙa, sai dai takobin tana a cikin gidanta, bata fito da ita ba, da ƙotar gabaɗaya ta ɗauko. Ɗaga takobin ta yi ta fara kai mashi wajajen hannunsa, hakan yasa ya fara yi da sauri, dan idan ya bari takobin ta taɓa hannunsa zata ji mashi ciwo, dama ga ciwo a yatsar hannunsa tana yi mashi zogi, dan ma dai da diddigen tafin hannu ya dafa ƙasan ne, bai isa ya tsunsa sun taɓa kasa ba, saboda ciwon yatsar nan. Mamma ta wata fuska idan ka gani sai kaga kamar bata son ɗan nata, amma kuma ita ce ainahin mai sonsa da gaske, yanzu duk in da ya shiga zai iya kare kansa ba sai ya jira wani ya zo ya kare shi ba, sai dai ni PRINCESS TEEMA ina ganin akwai wani dalilin da yasa Mamma ta zaɓi Kamran ya zama jarumi sosai har take bashi irin horo haka mai haɗari, hannunsa yana ciwo ma ba zata kyale shi ba, sai ta sanya shi yin wannan abin, haba mana Mamma..........💔😭 Yau sai da ya kusa saka mata kuka, sannan ne ta rabu da shi tare da kama ƴatsar tasa dan ta cire wannan bandejin nasa ta kara yi mashi dressing na wajen. Shi dai burinsa ɗaya kawai, shi ne ta barshi ya je ya ga maman twins, ko yunwa ma baya ji, yana son ya koma ya sake ganin yaran ne, amma bai isa ya tirjewa Mamma ba, dole ya bita a yadda take so dan kada ta yi zargin yana aikata wani abin a ɓoye, dan haka sai ya hakura ta sake yi mashi dressing na wajen ciwon nasa, ta gasa wajen sosai da ruwan ɗumi, sannan ta ce ya je ya yi wanka ya zo su yi breakfast. Ba musu ya je ya aiwatar da duk abin da ta ce cikin zafin nama, dan ya yi sauri ya gama ya laƙa mum twins. Zama suka yi suka ci abincinsu kamar yadda suka saba, sannan Mamma ta ce mashi ya je gonarsu ya kawo masu masara ɗanya, ya duba ƙosassu ya ciro, sai ya haɗo masu da nama, daga karshe ta yi mashi kashedi a kan ya kula da yatsar nan tasa sosai, dan yatsar kamar tana son samun matsala. Okey kawai ya amsa mata da shi kafin ya miƙe ya koma cikin ɗakinsa, kwari da bakarsa masu lafiya ya ɗauko domin farautar nama, sai wata ƴar wuka mai kaifin gaske da ya ɗauka dan tsaro, a kugunsa ya sanya ƴar wukar, ita kuma kwari da bakar ya ratayota a bayansa, sannan ya sanya takalmarsa mai kama da waterproof shoe, a hanzarce yake yin komai, duk dan ya yi sauri ya fita. A wajen madafa ya isko Mamma, kwandon da suke ciro tomatoes a ciki ya ɗauka dan zubo mata masarar da ta ce ya ciro masu a gonarsu, sannan ya ɗauki wata karamar kwando ma wanda zai zubo masu fruits, dukka kwandunar da itace aka saƙasu, sai dai sun saƙu da kyau. Sallama ya yi wa Mamma tare da nufo kofar fita. Sosai ta sake yi mashi kashedi a kan kada ya yi wasa da hannun nan nasa fa, ya kula sosai. Okey ya amsa mata da shi tare da ficewa, yau ya fito sak maharbi. Wajen wata bishiyar lemu ya tsaya ya fara ciro lemun da suka nuna, yana cirowa cikin nutsuwa. Ɗan dai'dai ya ciro kafin ya je wajen bishiyar gwaiva, ita ma ba dayawa ya cire ba, sai mangoro da ita ma bata fi biyar ya tsinko ba, dukka nunannu yake bi yana cirowa, haka ya tara fruits ɗin dayawa, sannan ya nufi hanyar wajen mum twins dan ya je ya kai mata fruits ɗin, ita ya cirowa wannan, na Mammansa sai yana dawowa zai ciro mata, yaron kirki...........😅 Tafiya yake yi cike da jarumta, yana wani bubbuɗe kirji kamar wani mayunwacin zaki, ko alamar tsoron wannan daji babu a idanunsa, tsuntsaye sai shawagi suke yi abinsu, shi ma sai tafiya yake yi abinsa. Wani irin mahaukacin birki ya ja lokacin da ya isa wajen da mum twins ɗin take, sam bai san lokacin da ya saki kwandon fruits na hannunsa ta faɗi ƙasa ta tarwatse ba, fruits ɗin duk suka watse a wajen. Wani irin kara zaro idanuwansa waje ya yi, nan take fuskarsa ta bayyanar da alamar zallar madarar mamaki, cikin hanzari da zafin nama ya kara matsowa wajen dan ya tabbatar da gaske ne abin da yake gani. Tabbas gaskiya ce, babu mum twins kuma babu twins, ɗakin bukkar da aka yi masu ma duk an kakkarya shi, an karya itatuwar gabaɗaya, tamkar waɗan da suka yi faɗa da Damusa ko kuma Damusa ya faraucesu, duk komai a kakkarye, ga kwaryar magangunanta a wajen duk a farfashe, an fasasu, ga kuma towel ɗin da aka rufe baby's ɗin duk suna nan, babu abin da aka ɗauka a wajen face baby's ɗin da Mamansu. Tamkar a mafarki haka Kamran yake ganin wannan al'amari, tambayar kansa yake yi to ko Damusa ce ta shigo wannan yankin ta cinyesu? Kasancewar shi bai san da cewa biyo maman nasu aka yi daga masarauta za'a kwacewa mata baby's ba, sai bai yi tunanin ko mutanen masarautar tasu ne suka zo suka ɗauketa ba, shi dai tunaninsa wata dabbace a cikin wannan daji ta hallakasu ta kuma ɗaukesu suka tafi cikin dabbobi ƴan uwanta suka cinyesu. To waye ya ɗauki mum twins? Shin da gaske wata dabbace ta cinyesu ko kuma dai waɗan nan warriors na masarautar tasu ne suka dawo suka ɗauketa? Allah mai iko, Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana❤️ Wani irin bakin ɓacin rai ne ya bayyana a saman fuskar Kamran, tamkar ya saba da su, tamkar ƴan uwansa haka yake jin mum twins ɗin nan, kawai daga jiya da la'asar zuwa yau ace bata nan? Ina take?. Idanuwansa ne suka kaɗa suka yi ja sosai saboda tsananin ɓacin rai, har wani huci ya fara fitarwa. Cikin matsananciyar damuwa ya fara kewaye wajen yana nemansu, a cewarsa idan ma damusa ce ta faraucesu zai ga ragowar kasusuwansu, shi ne ya bazama ya fara nema, duk wasu lunguna da saƙuna, bayan bishiyoyi da bayan duwatsun, ƙoguna da ramukan itace dake arear wajen, ko'ina shiga yake yi yana leƙawa, nemansu a haukace kawai yake yi, duk yana kiɗi me, baya damuwa da in da yake shiga, ba ya damuwa ko akwai maciji ko wata muguwar dabba da zata cutar da shi, shi dai kutsa kai a ko'ina kawai yake yi yana nemansu, har cikin ramuƙan dake arear wajen irin ramin da ta faɗa ciki ta haifi twins ɗin, har ciki duk sai da ya bi ya rinƙa leƙawa, amma ko alamarsu babu a wannan arear, tamkar ma ba'a taɓa yin wasu halittu irinsu a wajen ba. To fa babbar magana, tashin hankali da ba'a saka mashi rana, my people ina mum twins?. *Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 4/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ *My people's duk abin da kuka ga na rubuta a cikin wannan littafi na RAWANIN ZALINCI ba sai kun tambayeni a kan meyasa aka yi kaza ba, idan kuka nutsu za'a warware maku komai, ita labari ai ba lokaci guda ake warware komai ba, ku da kanku ba zaku so labarin da komai nata yake a wangale ba, duk abin da marubuciya zata rubuta maku a cikin storynta, ku sani tana sane da wannan abin da ta rubuta, kuma idan kuka yi hakuri zata zo da kanta ta warware maku komai a nutse ba sai kun yi ta tambaya ba, fatan kun gane?. And lastly littafin RAWANIN ZALINCI babu complete nasa, masu tambayata complete babu, yanzu nake rubuta shi!!* E____________7🔥 Sosai Kamran ya bazama ciki dajin nan yana nemansu, duk ya shiga damuwa bawan Allah. A takaice dai ya kwashe shekaru yana neman mum twins, kullum da su yake kwana yake kuma yashi a ransa, sun zo lokaci guda sun shiga mashi cikin tunaninsa da kuma rayuwarsa, lokaci guda kuma sun tafi sun bar shi, kamar ba'a taɓa yinsu a wannan daji ba, a cikin waɗan nan shekaru da suka suɗe babu wata rana da zata zo ta wuce Kamran bai yi tunaninsu ba, duk idan suka fita farautar nama shi da Rocky, to sai sun yi ta kewaye a cikin dajin ta arearsu ko Allah zai sa ya ga koda tsinke ne daga cikin kayansu ko wani abin nasu. Amma ina, bai ga komai ba sam, kuma tsabar ƙoƙari irin nasa bai taɓa cire tsammani tare da sa ran ganinsu ba, yana ji tamkar ko ba jima ko ba daɗe zai gansu, dan yana ji a jikinsa basu mutu ba suna raye, to Allah dai shi ne masa. And One think about KAMRAN and MAMMA, both of them are not Muslim, ba musulmai bane ba su ɗin, basu da addini dukkansu biyu, Mamma bata yarda da kowace addini ba a rayuwarta, a kan haka ta reni Kamran, sai dai Allah da ikonsa shi Kamran zuciyar musulunci ke gare shi, dan tsantsar son taimakawa na ƙasa da shi yake da, ga son ganin mutane cikin farinciki, wasu abubuwan nasa idan yana yi kamar cikakken musulmi. Kullum ya zauna sai ya bawa Mamma labarin mum twins, tun Mamma bata kula shi har kunnunwanta suka saba da jin labarin, sai dai bata taɓa bashi goyan baya a kan ya shiga sauram yankunar dake a cikin dajin ya dubasu ba, hasalima ɓacin ranta ne yake bayyana a duk lokacin da Kamran ɗin ya yi zancen wasu bama mum twins kawai ba, sam bata son jin yana magana na ko da maharba ne, amma ba yadda ta iya, mum twins ta riga da ta shiga cikin tunanin ɗan nata, ya rigada ya sanyasu a ransa, ko Mamma bata so dole dole sai ya bata labari, dan dole take saurara. Mum twins dai shiru, ba ita babu labarinta, babu wanda yasan in da ta yi tsawon shekaru, ko ina suke? Allah masani. To bari dai mu ɗan kutsa ta wani ɓangare na cikin wannan littafi na RAWANIN ZALINCI ko zamu sami wani ɗan haske a kan abubuwan da suka faru a baya, ko kuma dai har yanzu lokaci bai bamu dama ba, bari dai mu gani. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ KINGDOM OF POWER💪👊🔥 Masarauta ce da babu biyunta a tarihi, ku daga jin sunan POWER kun san me sunan yake nufi, kalmar POWER ta tattara karfi! Isa! Izza, taƙama dukka!. Masarauta ce mai cike da karfin da jin sunansu kawai ya kan sanya duk girman Daula ta girgiza, suna da horarrun jaruman sadaukai yaki sama da dubu uku, mayakansu mayaka ne da ba su sarewa a pagen yaki, matuƙar sun fara yaki, to fa komai wuya komai daɗi ba su juya baya har sai sun cimma abin da suka je nema, mayakansu ne ake yi wa lakabi da Dangerous warriors, wato mayaka masu haɗarin gaske, jin sunan mayaƙansu kawai ya kan sanya hantar manya manyan masarautu su kaɗa, basu da tausayi ko kaɗan, aiki ziryan suka iya. Commander ZAFAR shi ne commander na mayaƙansu bakiɗaya, dattijo ne wadda a kallah zai kai shekaru 50 zuwa 55 a duniya, amma da yake dakakken horarran mayaki ne, ya sha training ya ƙoshi, jikinsa duk ta murɗe sosai, idan ka gan shi, sai ka rantse da Allah ba zai wuce ɗan 35 years ba, saboda kyan jikinsa, ya murɗe sosai, damatsan hannun nan nasa tamkar za su fashe, yau sama da shekara 30 yana training tare da bawa mayaƙa horo da dabarun yaki, ai kunga dole jikinsa ya murɗe sosai. Commander ZAFAR yana da wani dakakken horarran jarumin yaro ɗaya tamkar da dubu mai suna HOORAIN, HOORAIN dakakken namiji ne, tsayyayye, kuma shi ne mataimakin mahaifin nasa, wato assistant commander na mayaƙan KINGDOM OF POWER a yanzu, matashi ne mai jini a jika, shekarunsa 28 a duniya, tun yana ɗan yaro Commander ZAFAR yake koyar da shi yaki, shiyasa ya taso a sadauki kuma cikakken jarumin namiji da KINGDOM OF POWER take alfahari da shi, bashi da mahaifiya, kuma bashi da kani or kanwa, shi kaɗai Commander ZAFAR ya haifa. KINGDOM OF POWER dai Shinfiɗaɗɗiyar masarauta ce wanda ta kasance na cikakkun jarumai da suka tsaya tsayin daka wajen ganin sun tsayar da masarautarsu ta yarda babu wani mahaluƙi a duniyar nan da ya isa ya nuna su da hannu, koda gate na farko na shiga wannan masarauta ka nuna da hannu, to wannan hannun naka sai ta tashi a aiki, dan sai an sareta daga diddiginta. A bakin gate na farko na shigowa cikin wannan katafaren Masarauta dai gumakan zakuna ne guda biyu waɗan da aka sassaƙasu, suna daga zaune sun buɗe baki ga waɗan nan gabza gabzan hakwaran nasu, an yi fentinsu da fenti launin gold color, daga bayan zakunan kuwa gunkin mutun mutumin wata jarumar macece wadda aka sassaƙata tana a zaune saman dokinta rike da takobi cikin shiga ta doguwar riga. A takaice KINGDOM OF POWER katafaren masarauta ne wanda yake da gate ɗin shiga ɗai, ɗai, ɗai har guda 5, girman masarautar ta wuci tunanin mai tunani, fadoji har guda uku ne a cikin wannan katafaren masarauta, ko wani fada ya haɗu haɗuwa ta wuce misali, ya kawatu da kayan kwalliya na alfatma irin na sarakuna, masarautu manya manyan guda goma ne a karkashin KINGDOM OF POWER, ga su da tarin uban dukiya na wuce misali tare da maadanan cikin ƙasa. Babbar fada wanda sarki ya fi yawan zama a cikinta, girmanta ya wuci misali, an zuba kayan iya kayan more rayuwa wadda suka amsa sunansu, komai na cikinta Golden color ne, hakan tasa suke wani irin kyalli tamkar gold, suna ɗaukar ido, akwai wasu kwalliya na jikin kujerar sarki waɗan da aka yi su ne da zallar madarar gold, shinfiɗun alfarma dake a tsakiyar fadar nan kuwa kawai abin kallo ne, bare azo kan irin kwalliyar da aka kawata gabaɗaya cikin fadar har izuwa jikin bangon, abin sai dai baki ya furta masha Allah kawai, su kansu luntsuma luntsumar sofa sets dake a cikin wannan fada kyansu ya sha gaban tunani, komai na cikin wannan fadan daga ƙasar Dubai yake. BARDE KING ZUHAIR ABDUL MALIK, shi ne sarkin KINGDOM OF POWER daya karɓi mulki daga hannun marigayi King ABDUL MALIK BADEEN, wato mahaifinsa kenan. KING ZUHAIR ABDUL MALIK jarumin ubane jajirtatcen sarki ne wanda ya tsaya tsayin daka akan ƴaƴansa da kuma al'ummar kasarsa bakiɗaya, yana da adalci fiye da tunanin mai tunani, shi ma kafin ya karɓi mulki wajen mahaifinsa, jarumin sadaukin yaƙi ne, ya taɓa zama commander warriors nasu a lokacin da babansa ABDUL MALIK BADEEN yake a kan karagar mulki, yana matashi lokacin, sai dai bai ruke muƙamin commander sosai ba, kasancewarsa ɗan sarki ne, dama kuma su ƴaƴan sarakuna suna karɓar horon yaki ne domin kawai su kare kansu ba dan su yi mu'amala da mayakan dake a cikin masarauta ba, sai dai idan suna ra'ayi, za su iya shiga yaki idan za'a je, wannan ra'ayin kansu ne, amma banda haka sunfi karfin wani mayaki ma ya kalli in da suke, to dai shi ma King ZUHAIR ABDUL MALIK jarumin sadaukin yaƙi ne, hakan kuma yasa ma ake ce mashi BARDEN namiji, domin kuwa BARDEN ne da gaske, ba wasa, jininsa a tafashe yake, bugu da ƙari KING ZUHAIR ABDUL MALIK bamodare ne, nasan dayawanku baku san su waye modarawa ba, modarawa larabawa ne wanda tun zamanin kakanni sun yi suna wajen jarumta da ba'a barin ko ta kwana, da ka taɓa bamodaren balarabe gwara maka ka kwana da yunwa, tun zamanin da can kowa yasan modarawa basu yafe laifi idan aka yi masu, komai ƙanƙantar laifi idan ka yi masu sai sun rama, ga zuciyar bala'i, jininsu a tafashe yake, ga su da shegen haɗin kan bala'i, idan ka taɓa bamodaren balarabe guda ɗaya wlh sai goma sun hayayyaƙo maka, to haka suke, jarumai ne da suka shiga kundin tarihin duniya. So haka BARDE KING yake, tsayayyen namiji ne mai cikar zarra da halitta. Ƴarsa ta farko shararriyar sadaukiyar yaki ce kafin ta yi aure, jaruma ce a cikin jarumai, ta iya takobi fiye da tunaninku, jininta a tafashe yake tamkar na mahaifinta, bata da wasa kuma bata ɗaukar wasa, har gunkin mutun mutuminta aka gina a bakin gate na farko na shigowa cikin KINGDOM OF POWER, an ginata tana a zaune saman dokinta rike da takobi, ta fi iya takobi sama da komai, tsayawa zayyana maku jaruntar gimbiya Miemie ma ɓata lokaci ne, dan baki ba zai iya faɗen shi ba, duk da ta yi aure, amma tana a cikin KINGDOM OF POWER da mijinta har yanzu, saboda ɗa ga abokin mahaifinta ta aura, wanda shi ma a cikin KINGDOM ɗin yake, jarumine na gaske, kuma su a al'adarsu ce hakan, su zauna inuwa ɗaya, wato family su haɗu su cure waje guda, har gobe Gimbiya Miemie tana wasa da tokobi tamkar mai wasa da ƴar baby, shekarunta 37 kacal a duniya, saboda auren da yake a kanta ne yasa ta dai'na duk wani abin da ya shafi yaki da sauransu, sai dai ta koyar da kananan yara mata masu tasowa ruke tokobi da kuma amfani da ita, wato ta bawa mata horan yaki, amma fa duk wani yaki da za'a tafi, sai mahaifinta ya nemi jin ta bakinta, dan ita ɗin mace ce mai kaifin fikira da basira tare da sanin dabarun yaki, to haka dukka ƴaƴansa suke, jarumai ne na kin karawa, a tsarin KINGDOM OF POWER basu tunkarar waje da yaki kuma su juya, basu ja da baya a yaki, idan fa suka dumfari waje, to komai girman Daular sai sun jijjigeta sun jefar da ita, idan suka ja wa masarauta kunne taki ji, to sai sun rugujeta sun shafe babinta a doran duniya, basu shiri da rashin adalci, duk in da ake yin zalunci, to zasu daka masu warning, idan suka ki ji, to za su shafe babinsu, jininsu a tsananin rafashe yake, baki ba zai iya gaya maku jarumtarsu ba. King ZUHAIR ABDUL MALIK su huɗu ne a wajen mahaifinsu wato Sarki ABDUL MALIK BADEEN kenan, mahaifiyarsu kuma sunanta Gimbiya JALILA, ƴa ce ga sarkin Dubai, balarabiya ce, kyakkyawar gaske, hakan yasa su King ZUHAIR duk suke kyawawan gaske, King ABDUL MALIK BADEEN mahaifiyarsa ainahinta Sarauniyar Saudi Arabia ce, shi ne ya auri Gimbiya JALILA ƴar sarkin Dubai, ita ce kaɗai matarsa, dukkaninsu tushen iyayensu mata larabawa ne modarawa, shi ne yasa suke da tsananin kyau, ga su jajir kamar ka taɓa jini ya zuba, fararen tattabaru ne da babu ɗigon baki a jikinsu. Gabaɗaya ƴaƴan King ZUHAIR ABDUL MALIK haka suke, kamar ka taɓasu jini ya zuba, saboda haske da tsantsar kyau, sai ka rantse da Allah basu taɓa taka kasa ba, kamar basu taɓa fita rana ba, saboda tsantsar kyau da haske ga kyan fata luwai luwai. King ZUHAIR ABDUL MALIK shi ne babba, yana da mata uku, kunsan sarki dama baya yin mace guda ɗaya sai dole, matarsa ta fari ma a rana ɗaya aka ɗaura auransu su biyu da ta biyu kenan, da Gimbiya Umaima, wadda ta kasance ƴa ce ga Aminin mahaifin King ZUHAIR ɗin, so ita ba wata ƴar manya ba ce cancan, ita ce kuma uwargida, suna kiranta da Mummy, sai Gimbiya Aleezarh da ta kasance ƴa ce ga prime Minister of Saudi Arabia, suna ce mata mama, so a rana ɗaya King ZUHAIR ya aurensu, daga baya ya auro ƴa ga sarkin Dubai na yanzu, Gimbiya RAHILARH, wato ƴa ga uncle nasa yayan Mahaifiyarsa Gimbiya JALILA kenan, suna kiranta da Momma. So Mummy wato uwar gida yaranta uku, Jaruma Gimbiya MIEMIE ƴar ta ce, kuma ita ce ƴar farin King ZUHAIR ABDUL MALIK. A takaice kenan na fayyace maku wannan Masarauta, sauran bayanai zai biyo daga baya!. Part na family'n king, wata shirgegiyar benece mai hawa huɗu, ga wata haɗaɗɗiyar elevator da take kai komo tana ɗaukar mutane izuwa sama or ƙasa, ba sai na faɗa ba kun sani gini ne da aka kerashi da tiles and glass, kasancewar KING ZUHAIR architecture ne, shi ya fitar da zanen tsarin gidansa ta yadda ya ja hankulan dubbanin jama'a, dan kuwa wani irin tsari ya zubawa ginin nan nasa wanda ko a ƙasashen turawa da wuya a samu mai irin tsarinsa, tsarin ta fita ne iya fita, dan idan aka bar mutun da kallon wannan tampatsetsen gidan ma kawai sai ya wuni ya kwana yana kallon iya waje kawai. Ƴaƴan KING kowa da bedroom nasa na daban, kowa kuma bedroom nasa aljannar duniya ce, musamman auta da ta kasance sanyin idaniyar babanta, kuma jika ga sarkin Dubai wato kakanta wanda ya haifi mamanta, kuma ta kasance jika da kakan nata ya fi kauna, ita na ta ɗakin ma idan ka shiga sai ka yi tunanin ba a duniya kake ba, saboda tsantsan tsaruwa da kawatuwa, KING ya zuba mata makudan kuɗaɗe a ɗakin nata, haka zalika kakanta, daga Dubai aka kawo komai na cikin ɗakin. Sanan ko wace mace fa wato su mummy kenan, ko wace Part nata daban ita da ƴaƴanta, sai dai part ɗin daddy wato KING yana a tsakiya ne, hakan yasa aka yi kofofi da zata sada ko wani part da part ɗin na daddyn a hawa na uku kenan, a nan suke haɗuwa su yi hira, su ci abinci a babban parlourn KING. Wannan a takaice kenan tsarin KINGDOM OF POWER. Cikin wani katafaren garden mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, garden ɗin ya ji komai na more rayuwa, luntsuma luntsumar sofas dake ciki farare kal da su gwanin ban sha'awa, sai tashin wani daddaɗar kamshin flowers garden ɗin yake yi. Daga can gefe guda wajen wani kyakkyawar tsadadden grass carpet, wasu kyawawan ƴan mata farare tas da su kamar wasu tattabaru ne suke zaune a wajen, saman grass carpet ɗin dai'dai in da suke a zaune shinfiɗe yake da wani irin Turkey carpet mai matuƙar laushi, ga wasu manya manya throw pillows dake a saman carpet ɗin masu matuƙar kyau. Waɗan nan ƴan mata su huɗu ne, kyawawan gaske ne, farare tas dasu, tamkar ka taɓa jini ya zuba. Sun kasance kamanninsu ɗaya ne sak, da gani ba tambaya kasan jini guda ne, dukkansu babu wacce zata kai shakaru 17 a cikinsu, ƴan mata ne caras cas da su. Sanye suke cikin shiga ta ƴaƴan sarakuna, shiga ce mai matuƙar ɗaukar hankali, doguwar riga ce fara kal wadda ta sha kwalliyar duwatsu golden color masu bala'in ɗaukar idanu. Daga samar rigar tayi masu cif a jikinsu, daga ta wajen plat tummynsu rigar ta yi wani uban buɗewa tamkar umbrella har kasa, dukkansu rigar tasu tana ja har kasa. A saman rigar tasu kuma sun ɗaura wani dankareriyar shegiyar alkyabba mai bala'in kyau da tsada, launin golden color mai haske. Uku daga cikinsu waɗan da suka fi manyata suna sanye da hular alkyabbar a kansu, ɗaya kuma dake zaune a ɗan gefe saman throw pillow, ita sam bata sanya hular alkyabbar a kanta ba, ta bar kanta babu ɗan'kwali, ga gashin kan nata gwanin ban sha'awa, bakinkirin da shi, ya zubo mata har gadon bayanta, sai kyalli yake yi, duk cikinsu ita ce ƙarama, kuma ta fi su kyau nesa ba kusa ba, dan ma dai jini ba wasa bane yasa kamannin jini ya bayyana a tsakaninta da su, bacin haka ita ɗin daban take a cikinsu, harta yanayin hasken fatarta ba irin nasu bane, ita ɗin fatarta tamkar madara haka yake, su kuma jajir suke kamar tsada. Dukkansu suna da dogayen hanci masu matukar kyau da ɗaukar hankali, sannan waɗan nan ukkun dukkansu lips nasu ya kasnace pink color ne, da yake suna da hasken fata, sai kalar lips ɗin nasu ta bayyana sosai tamkar sun saka lips stick, ita kuma karamar cikin nasu lips nata red color ne mai bala'in kyau, ya yi red sosai gwanin burgewa, har wani shining yake yi. Duba da dara daran idanu farare kal kal tamkar audiga, kwayar idanunsu bakin kirin har yana wani walwali, eyelashes nasu zara zara sosai like gashin doki. Ita kuma ƙaramar cikin nasu kwayar idanunta ba baki bane, hazel eyes ke gareta, kasancewar idanun nata fari ne tas, hakan ya bawa launin kwayar idanun nata damar kara fitowa sosai. Wasu shirga shirgan dakarun yaki masu ji da lafiya da karfi ne a tsaye a ɗan nesa kaɗan da waɗan nan ƴan'matan, da alama bodyguards nasu ne, dan kamar yadda suke su huɗu a wajen, dakarun yakin kuma su uku ne a wajen, da alama kowacce jarumin sadaukin dakare ɗaya ne yake gadinta duk in da zata je, saboda yanayin yadda dakarun suka tsaya tamkar wasu saƙaguna, kowannensu yana fuskantar mace ɗaya, hakan ce zai baka tabbacin cewa kowanne da wadda yake gadi, sai ita kuma karamar cikinsu babu wani dakare da ya fuskanceta a wajen, da alama nata dakaren baya wajen ko kuma wani abin makamancin haka. Sai hira ƴan mata ukun nan suke yi cikin harshen larabci, ita kuma ƙaramar tana zaune rike da wani hoto a hannunta tana kallo, ta ƙurawa hoton idanu sosai, kome take kallo a ciki?. Daga karshe ma sai ta sauka daga saman throw pillow da take zaune, ta koma saman carpet ɗin ta zauna, tare da kishingiɗa a jikin pillown tana mai cigaba da kallon hoton. Wani cikakken gwarzon namiji ne ya shigo cikin wajen, sanye yake a cikin kayan yakinsa shi ma, baka iya ganin face nasa saboda hular kayan yakin nasa dake a kansa, yana tafiya ne irin na cikakkun gwarazan maza, ga tafiyar tasa cikin wata iriyar nutsuwa da kamala, sam babu hayaniya a tattare da shi, sai wani irin dake a tare tattare da shi, yana buƙe kamar wani zaki. Hannunsa na rike da wata kyakkyawar kwando mai ɗauke da fruits a cike a cikinta, fresh fruits ne mai matuƙar kyan gani a idanun. A gaban ƙaramar cikin nasu ya zo ya tsungunna tare da ajiye mata kwandon fruits ɗin a gabanta, cikin girmamawa ya ce. "Ranki ya daɗe ga shi nan". Ƴar yarinya da bata wuce 11 to 12 years ba, kanta ta ɗago daga kallon hoton da take yi tare da sauke dara daran Hazel eyes nata a kansa. Cikin sauri ya kara risinar da kansa ƙasa alamar girmamawa. "Banace maka ka daina ce mun ranki ya daɗe ba? Ka kira su Aunty MieMie da ranki ya daɗe, ka kira su Aunty chuchu da ranku ya daɗe, nima da nake ƴar yarinya sai ka wani ce mun ranki ya daɗe? To ni bana so, kawai kace mun auta ta ko kuma ka kirani da baby kamar yadda uncle Taheer yake ce mun". Ta yi maganar cikin kwararriyar laraɓcinta, ga ta da zaƙin murya sosai, voice nata gwanin daɗin saurara. "Kiyi hakuri ranki ya daɗe, zan gyara". Ya bata amsa da yaren da ta yi mashi magana, ya yi maganar a sanyaye cikin nutsuwa. "Ba zaka gyara bakam, ga shi yanzu ma ka sake ce mun ranki ya daɗe, to shikenan tun da ba zaka canza hali ba". Ta kai karshen maganar tare da ɗaukar ƴar wukar da yake a cikin kwandon fruits ɗin da kuma Apple guda ɗaya da nufin ta fara yankawa ta ci. Waɗan nan ƴan mata guda ukun da suke wajen har suna rige rigen karɓar wukar daga hannunta tare da Apple ɗin, shi ma wannan dakaren nata ya yunkura zai karɓi wukar ne sai ya ga ƴan uwanta sun riga shi, hakan tasa sai ya koma ya nutsu. "Ke auta so kike yi ki yanke hannunki uncle Taheer da daddy su bamu hukunci ko?". Cewar ƴan matan, sun yi maganar har suna haɗa baki. "Kai Aunty Chuchu ni fa yanzu na iya yanka fruits, baki ji uncle Taheer ya ce yakamata nima na fara koyan takobi bane? Ya ce na girma yanzu". Miƙewa tsaye dakaren nata ya yi tare da tsayawa a ɗan gefenta kaɗan, kamar wani mutun mutumi, kun san haka dakarun yaki suke tsayuwa dama, cike da jarumta sosai, musamman idan aka basu kula da mutun mai mahimmanci, ai sam basu zama, Auta tana da matuƙar mahimmanci sosai ga kowa da yake gidan, ƴa ce ga Gimbiya Rahilarh, wato amaryar King Zuhair kenan, ƴar ta ce, shi ne yasa ma ta fisu kyau, dan ita gaba da baya dukkan jinin larabawa ne babu mix, kada ku manta mamanta ƴa ce ka sarkin Dubai, King Zuhair ma nasan baku manta tushensa ba, so ita auta bata da mix ko kaɗan, suna ji da ita, suna sonta sosai, shi ne ma yasa King Zuhair ya wakilta assistant commander mayakansu wato HOORAIN da ya kula da ita, ya zama shi ne mai bata tsaro, tsabar son da yake yi mata ne ya yi mata wannan gata, duk sauran ƴaƴansa normal mayaka ne suke tsaronsu, amma banda ita auta, ita assistant commander da kansa ne yake tsaronta, da da dama ma da commander za'a sanya ya yi tsaronta, duk wani motsin da zata yi ya kula da ita sosai, idan ta yi koda tuntunɓe ne zai sha hukunci. (Kai irin wannan soyayya haka, to Allah muma ka yi mana arzikin da zamu yi wa ƴaƴanmu fin haka ma🤲) "Ba wani girman da kika yi, ki bari mu yanka maki ko a kira kuyangu su yanka maki ki sha". Cewar ɗaya daga cikin ƴan'matan, wadda aka kira da Aunty Chuchu kenan. Ɗan turo baki ta ɗan yi kafin ta ce. "Amma Aunty Chuchu kin san ni bana son na kuyangu ko?" Gyaɗa mata kai Aunty Chuchu ɗin ta yi alamar e ta sani "Tom shikenan, ni bari ma na je wajen daddy a faɗa kafin ku gama yankawa, dama nace mashi zan je hutu wajen Mai rankarfe, this time Dubai zan tafi, bari na je na tuna mashi da batun hutu nawa, dan gobe nake son a kai'na". Still cikin harshen larabci ta yi maganar tata, da voice nata na yara mai shegen daɗi. Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye, tana da tsawo dai'dai gwargwado, ba gajera bace ba, kafarta na sanye da cover mai bala'in kyau launin gold color miƙewarta tsaye yasa tsananin kyanta ya kara bayyana sosai, kyakkyawa ce ajin farko. Wucewa gaba ta yi HOORAIN ya rufa mata baya, yana taku na kikakkun jarumai waɗan da jininsu yake a tsananin tafashe, Hoorain baya magana, tamkar wani kurma haka yake, sai iya cika aiki cikin zafin nama. Da kallo su Chuchu suka bita da shi har ta fice daga cikin wajen. Duk in da ta zo wucewa sai manya manyan dakarun yaki sun sunkuyar da kansu ƙasa alamar girmamawa a gareta, idan kuma bayi ne sai sun zube gwiwowinsu a ƙasa haɗe da sunkuyar da kai dan girmamawa, ba zasu ɗago kansu ba har sai ta wuce, gata wata ƴar firitu a wajen, amma haka ake bata wannan girma dan dole, kun san yadda gidan sarauta take, musamman sarauta mai cike da girma irin haka, girmama ɗan sarki dole ne ga bayi, koda kuwa jariri ne. Tafiya take cikin nutsuwa har izuwa kofar tampatsetsen babban fadar mahaifin nata, wasu jiga jigan zataran matasan dakarun yaki ne suke gadin kofar shiga fadar, suna shirye cikin kayan yakinsu, tsayawa zayyana maku haɗuwa da kyan kofar shiga cikinta kawai ma ɓata baki ne, dan ba zata faɗu a baki ba. Fada ce irin na hamshaƙan sarakuna masu faɗa aji a duniyar mulki, sai dai kuma wannan fada ta fita daban a duk cikin fadojin da kuka sani a duniya, saboda fada ce ta manya. Tun da auta ta saƙo kafarta, da Sallama ta fara cin karo, Sallama wani bawan sarki ne wanda kamar matsayin PA yake, duk wani mai son ganin sarki in ma a cikin gida ko kuma a waje or a fada to dole sai ya bi ta hannun Sallama, idan ba haka ba ba zai sami damar ganin sarki ba, kun dai san yadda matsayin PA yake ko?, To haka matsayin Sallama a cikin fadar sarki yake. Ganin Gimbiya auta ce tasa Sallama ya fara washe baki tare da fara zuba mata kirari. "Takawarki lafiya ƴar sarki jikan sarki, mace mai farar aniya tare da farar zuciya, farar mace alkyabbar mata, tauraruwa a cikin taurari, ƴar gata kuma ƴar lelen kowa dake a cikin masarautar nan, Queen Zunaira taka a sannu masu kasar Dubai da kewaye". Yana zuba mata kirarin ne tare da ɗaga hannunsa ɗaya sama alamar jinjina, ya kuma sunkuyar da kansa kasa alamar girmamawa. Duk wanda yake son zaman lafiya a cikin KINGDOM OF POWER to ba shakka dole ya kaunaci Gimbiya Zunaira, dan King Zuhair ya fi kaunarta sama da yadda yake son kansa, hakan tasa sallama ya zage yake ta zuba mata kirari babu kakkautawa, dan ya faranta ran sarki. Da yake kamar yadda Sallaman ya faɗa, ita ɗin macece mai farar zuciya, ga kyauta kamar babanta, ga san jama'a da saukin kai, duk ƴaƴan KING ZUHAIR suna da masifar jiji da kai haɗe da izza ta gidan sarauta, kunsan yadda jikin sarauta suke, iya fadanci, nuna tsantsar isa da takama, izza da nuna fifiko, to duk haka ƴaƴansa suke except auta, ita kaɗai ce mai saukin kai tare da ɗaukar mutane da daraja a cikinsu, sai kuma Gimbiya Chuchu wadda ita sam bata da wata matsala, bata da jiji da kai, bata ma da yawan magana, in kaga tana magana to da su Gimbiya Zunaira ɗin ne, ban da haka ita bata kallon mutane ma bare ta yi masu walaƙanci, ita kuma auta tana tsayawa ta saurari mutane ɗaya bayan ɗaya, yanzu ma tsayuwa ta yi tare da kai kallonta cikin ainahin fadan, sannan ta furta cewa a bawa Sallama kyautar kujerar Makka, daga haka ta wuce ciki abinta, da sauran ƴan uwanta ne ko kallon arziki sallama ba zai samu ba bare har su yi mashi magana, akwaisu da izzar bala'i, musamman ma wata yar autar mai suna Gimbiya SAREENA, ta fi kowa iya jiji da kai tare da nuna izzar sarauta, isa da taƙama, kamar ba zata mutu ba Kai tsaye saman stage da mahaifinta yake auta ta nufa, sai faman duƙar da kai ƙasa duk wasu mayakan dake a matsayin bodyguards a cikin fadar suke yi, alamace ta suna girmamata. A saman wajen stage da sarki yake daga ta bayansa akwai wasu dakarun mayaka guda biyu wanda ake kiransu da sunan sarakan Figini, su ne masu yi wa sarki firfita da maficin gashin jimina, sai fifita suke yi mashi da wasu tampatsetsa tampatsetsan maficin gashin jimina. Daga ta can gefen kujerar sarki da iyalansa kuwa, wasu hamshaƙan sofa sets ne a wajen, su kuma kujerune waɗan da aka ware na zaman malam liman, wato limamin Fada, sai Galadima, yana cikin majalisar sarki, Madaki, Yana daga cikin ƴan majalisar sarki shi ma, sai Sarkin Dawakin tsakar Gida, ko ban faɗa ba kun san shi ne mai jagorantar masu kula da dawakan gidan sarki. Daga kasar stage ɗin ma akwai wasu sofa sets tantsama tantsama, wasu daga cikin manyan fada ne suke zama a kai, irinsu sarkin gida, mai jagorantar masu shige da fice na cikin gidan sarki kenan, sai sarkin hatsi, mai kula da wajen ajiye kayan abinci, shi ne kuma mai fitar da zakkar sarki idan lokaci ya yi, duk wata sadakar kayan abinci da za'ayi dole sai da saninsa, komai dai da ya danganci abinci shi ne mai kula da shi, ko in ce jagoran ma'aikatan da suke kula da su, akwai ɗan iya, mai rerawa sarki waƙa kenan, yana da zazzaƙar murya, dan mai murya sosai ake nemowa, mai kuma ilimi sosai, sannan akwai sarkin bayi, ko ban faɗa ba kun san shi ne mai kula da duk wasu bayi da suke a cikin wannan Masarauta, sai Kasheka, wanda shi ne yake kasancewa a tare da sarki kullum, duk in da sarki zai je dole Kasheka ya kasance a tare da shi, sai amintattcen sarki, wanda wannan muƙami ne da ake bawa wanda sarki ya aminta da shi sosai, still akwai kilishi, kilishi wani bawan sarki ne wanda alhakin yi wa sarki shimfiɗa ya hau wuyansa. A duk gurin da sarki zai zauna, to kilishi ne yake yi masa shimfiɗa, imma a cikin Masarauta ko a wajenta, sai sarkin mayaƙa wato commander ZAFAR, shi ma a cikin fada ya fiya yawan zama, domin idan za'a fita yaki ko wani abin ya sani. Akwai dai muƙa mai da dama a cikin fadar sarki, amma waɗan nan sune manyan muƙaman, na kawo maku su ne kuma dama dan ana karatun littafi ne domin a samu karuwar ilimi, so ko baki taɓa shiga fadar sarki ba idan kika karanta littafin nan zaki san abubuwa da dama da suka danganci sarauta, shi ne amfani karatun dama, shi ne kuma yasa nake ƙoƙarin ganin na faɗaɗa maku komai dan ku sani ku sami karuwar ilimi. Kasancewar wajen zaman sarki waje ne da kowa ya sani na daban ne, tampatsetsan kujera ne na alfarma mai zaman mutun biyu, sai kuma na iyalansa dake a gefe da gefen nasa, wanda idan sun zo cikin fada zasu zauna a kai, babu wanda ya taɓa zama a saman kujerar sarki sai sarkin, koda kuwa matansa ne basu zama, shi kaɗai yake zama abinsa, amma saboda son da yake yi wa Auta, idan ta shigo a gefensa take zama, saman kujerar tasa. Yanzu ma da ta shigo a gabansa ta zo ta tsugunna, cikin girmamawa tare da ladabi da biyayya ta sunkuyar da kanta ƙasa, cikin sanyin murya ta yi mashi barka da hutawa, while shi kuma Hoorain yana waje bakin kofar fadar yana jiran fitowarta, dama baya binta ciki idan suka zo, a waje yake tsayawa abinsa. King Zuhair duk da yana jikin naɗin farar RAWANIN sarautarsa, ya sha alkyabbarsa mai bala'in tsada, hakan ba zai hana ka ga madarar kyau ba, kyakkyawar gaske ne shi ɗin, namiji mai cikar haiba da kamala, ya hakince a saman kujerar nan tasa yana gudanar da mulki bisa gaskiya da amana tare da adalci. Ƙasa ƙasa ya yi magana ta yadda ko masu yi mashi fifita na bayansa ma basu ji me ya ce ba, duk da cewa yana cikin naɗin RAWANIN mai kamar nikaf. Auta dake a gabansa ne kawai ta iya jin abin da ya faɗa, dan haka sai ta miƙe cikin nutsuwa ta koma kusa da shi ta zauna tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya. "Me yake tafe dake Mamana?". Ya sake yin magana ƙasa ƙasa cikin nutsuwa, harshensa akwai kaifi sosai, maganarsa tana da kaifin da idan ta ratsa dodan kunne sai ganganjiki ta amsa, dama akwai masu irin wannan murya a cikin jama'a, sai dai ba kasafai aka cika samunsu ba, mutun ne da zaku ji muryarsa mai kaifi, idan ya yi magana koda cikin nutsuwa ne sai masu sauraronsa sun shiga taitayinsu, koda kuwa raha yake yi da su, saboda kaifin harshensa sai kaga suna tsoron yin magana da shi, ko da ba mafaɗaci bane, bare kuma shi King Zuhair da ya kasance jinin Modarawa, ai kunsan faɗa dole, zafin rai dole, dan a jinin Modarawa dai babu rago mara zuciya, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa KING baya magana da ɗaga murya, dan tsaro, shi kansa yasan yana da kaifin harshe, so ɗaga muryarsa ga al'umma haɗari ne babba, zata iya sa wani da bai ji ba bai gani ba ya mutu saboda tsoro. "Daddy dama na zo ne na gaisheka". Ta faɗa a nutse. Ba tare da ya kalli in da take ba, dan suna jere ne wajen guda, cikin sanyin murya ya amsa mata da. "Anya kuwa autana gaisuwace ta kawo ki?". Ɗan guntun murmushi ta yi wadda sai da dimple nata suka lotsa, fararen hakwarantan nan suka bayyana, ga wani ɗan siriri wushirya a tsakanin hakwaran nata, kyau iya kyau ya kara bayyana dalilin wannan murmushin. "Kai daddy shi na zo yi mana". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe. "Ai nasan halinki ne, haka kawai rana tsaka baki zuwa wajena, keda wani lokaci ma sai na sanya an nemo min ke, to yanzu dai gaya mun kawai me kike so kika zo a dai'dai wannan lokacin?". Ɗan kwanto da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi tana mai cigaba da murmushi, daddyn ya gama ganota 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI. 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 6/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________8🔥 Ɗan kwanto da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi tana mai cigaba da murmushi, daddyn ya gama ganota. "Daddy dama batun zuwana wajensu mai rankarfe ne fa". Ta yi maganar kamar wata mai in'ina. "This time kuma can kike son zuwa?". Ya faɗa yana fitar da hannunsa ɗaya dake a cikin alkyabbar tasa, lallauran kumatunta ya fara shafawa. "Daddy ba Mummy ta ce Yah Omar zai kammala secondary school ɗinsa this time ba? Kuma ta ce yanzu zai dawo nan da zama idan ya kammala, shi ne zan je mu dawo a tare da shi ai". "Ya kammala dai ba zai kammala ba mamana, shirye shiyen dawowa ma yake yi, sai dai ki je ki tarosa ku dawo a tare". Shiru ta ɗan yi kafin ta sake cewa. "To daddy yanzu a nan zai cigaba da karatu ko?". Jinjina mata kai ya yi alamar e, da alama bai cika son yawan magana sosai ba, dan daga yanayin amsa mata ɗin da yake yi zai nuna maka cewa sam baya son motsa bakinsa, dan ma ita ce, ba dan haka ba da ba amsawa zai yi ba. Wani dakakken jarumin mayaki ne ya shigo cikin fadan, cikin girmamawa ya duƙa dan gaisuwa ga sallama, sannan ya sanar da shi cewa Sarkin yammaci yana son ganin sarki. Cikin hanzari sallama ɗin ya ƙariso gaban stage da King yake a kai, a nutse ya haura sama, a daf gabansa ya zo ya zube gwiwowinsa a ƙasa, cikin girmamawa tare da zubawa King kirari kafin nan ya sanar da shi cewa Sarkin yammaci yana neman iso a gare shi. Shiru na ƴan mintocin da akallah zasu kai uku King ya yi, da alama fa King jinin mulkin nan ta ratsa shi sosai, dan izzar bala'i ke gare shi, magana cike da class, maganar mai sifirin ce, ana yi kamar ba'a son yi, ana yi kuma ana hutawa. "Daddy in tafi ko?". Cewar auta, dan ita sam bata son hayaniya, yanzu ta san idan sarkin yammacin nan ya shigo sai an yi ta zuba mashi kirari, kuma sarkin yammacin matsayin wa yake ga marigayi King ABDUL MALIK BADEEN, dan dai a tsarin mulki idan mutun ya fika matsayin kujera to ya fika ne, ba dan haka ba ai da King Zuhair ɗin ne ma ya dace da ya je ganin Sarkin yammaci ba wai shi ya zo ba, idan kuka yi duba da kasancewar Sarkin yammaci a uncle na King Zuhair ɗin kenan, amma da yake kujerar yammaci tana a ƙarƙashin mulkin king Zuhair ne, dole sarkin yammaci ya zo da kansa idan yana da buƙatar ganin King. "Kin gaji da zama ne?". Har lokacin kallonsa yana fuskantar cikin tsakiyar fadar, bai juyo gareta ba. "Daddy ai naga kaka zai shi go ne, shi ne yasa zan tafi, sai can yamma ai zan dawo". Jinjina mata kai kawai ya yi, ba dan yana son ta bar kusa da shi ba, sai dan kawai zai so ya gana da uncle ɗin nasa ne cikin nutsuwa da mutunta juna ya kuma bashi hankalinsa waje guda. Har lokacin Sallama yana duƙe a saman gwiwowinsa yana jiran amsar da king zai basa, dama a tsarin KINGDOM OF POWER wlh babu wanda ya isa ya shigo fada ta kofar can taba family ba ba tare da izini ba sai, mulki mai karfi ke garesu, kuma suna gudanar da mulkin nasu ne bisa ga bin dokokin da suka tsarawa masarautar, idan kun san abin da ake cewa ba sani ba sabo, to shi ne yake aiki a cikin dokokin wannan masarauta, babu sani kuma babu sabo, duk wanda ya yi ba daidai ba hukunci kawai ake yanke mashi, koma waye shi, hakan kuma ita ce adalci, ita ce dai'dai, wannan dalilin ne kuma yasa masarautar ta tara ɗinbin makiya na kin karawa, ba'a taɓa masarauta wadda ta tara maki a tarihi ba irin wannan masarauta, dama kun san idan mutun ya ce zai yi aiki bisa gaskiya da amana, zai yi mulki kamar yadda ta zo a Shari'ance, to ba shakka zai tara makiyan da shi kansa sai ya ji ya tsani duniyar ma gabaɗaya, dan duk in da ya juya makiya ne ta ko'ina, burin kowa kawai ya kaisa ƙasa, saboda kawai wannan gaskiya tasa, zata zamana harta makusantarsa ma basu barshi ba, wata kila ya taɓa hukuntasu dan sun yi laifi, suma sai su shiga sahun makiyansa, to a takaice dai haka King Zuhair yake da waɗan nan tarin uban makiyan ta ko'ina, sai dai shi mutum ne da ya riki Allah hannu biyu, sannan kuma mulki yake gudanarwa dai'dai da koyarwar addini, baya damuwa da kowa da komai, koda ɗansa ne ya yi laifi sai ya hukunta shi, adalci kawai ya sani, kuma duk wanda yasan tarihin modarawa dama yasansu da wannan ɗabi'ar, suna da adalci, basu taɓa mutum haka kawai sai in har shi ya taɓosu, idan kuwa ya yi gigin taɓosu fa sai dai mu ce sunansa sorry, dan gangan ma sai ta fishi dakuwa, gari sai ta fishi niƙuwa, MODARAWA No be wasa Wlh!!. Miƙewa auta ta yi tare da cewa sallama ya sanar da Hoorain ita zata bi ta kofar nan da zai sadata da part nasu, ba zata fita ta kofar da kowa yake shigowa ba, wato kofar da ta shigo kenan, da yake kunsan da akwai kofar da zai iya sadaka da part na King a cikin fadar, dayawan lokuta ta nan ma family suke shigowa cikin fadar. Kun san dai yadda tsarin mulki take, kuma ku daga gani kunsan madarar mulki ziryar ake bugawa a cikin wannan masarauta babu wasa. Dan haka ƙasa auta ta duƙa dan yi wa mahaifin nata sallama, wannan ma ɗaya ce daga cikin dokokin masarautu, ko da mahaifinka ne a kan mulki dole ka bashi girma fiye da tunaninku, kamar dai yanzu ita auta da ta zube gwiwowinta a ƙasa, ƴa ce mafi soyuwa a wajen babanta, amma dole ta bi dokar masarauta, shiyasa na ce maku king Zuhair harta ƴaƴansa idan suka yi laifi yana hukunta su, ba sani ne kuma babu sabo. Sai da King ya bata izinin tafiya, sannan ta miƙe tsaye, cikin tsantsar so da kauna ta manna mashi kiss a kumatu kafin ta juya ta nufi step na sauka ta bayan King ɗin, dan kofar tana ta baya ne ba ta gaba ba. Dawo da kallonsa a kan sallama dake tsugunne ya yi, cikin sanyin murya tare da magana ɗaya ya furta an bashi izini, daga haka ya mayar da hannunsa da ya fitar daga cikin alkyabbarsa dan shafa kumatun Auta, sannan ya mayar da kallonsa a kan tsakiyar fadar. Kirari sosai Sallama ya fara zuba mashi tare da ɗaga hannu sama ya dunƙuleta yana aikin zuba mashi jinjin da kuma faɗar kyawawan fararen halayensa. Yana dake a saman kujerar nan bai ko motsa ba, ya hakince abinsa. Almost 2 mins Sallama ya ɗauka yana zuba wannan kirari kafin ya miƙe ya nufi kofar fadar dan ya isar wa da sarkin yammacin saƙon King. A bangaren ita kuma Auta, tana fita cikin ainahin part nasu ta koma, ta baro su Chuchu a garden suna aikin yanka mata fruits. Akwai bayi sosai da suke ta faman safa da marwa a part ɗin nasu, kowace baiwa da aikin da take yi, duk idan auta ta zo wucesu sai sun tsugunna mata ƙasa alamar girmamawa. Kai tsaye wani babban part ta shiga, tun daga kan yanayin tsarin wajen kasan wajene na mutane na musamman a cikin masarautar, saboda tsari ne mai matuƙar kyau da aka tsara shi, harta kwalliyar jikin bangon ginin wannan part ɗin kwalliya ne na musamman. Ciki ta shige abinta, a babbar parlourn ƙasa ta tsaya, parlourn ya tsaru iya tsaru, dukiya ta yi kuka a wannan waje, komai na cikin parlourn launin dark blue and gold ne, kalar kuma ta yi matuƙar bada abin da ake so, dan ta kara bayyanar da cewa lallai nan gidan sarauta ne. Kuyangu ne suke ta faman aikace-aikace na gyara a cikin parlourn, ƴan mata ne su huɗu, kowacce da abin da take yi, daga mai gyara shinfiɗun alfarma dake saman kujeru, sai mai shirya pillows, ɗayar goge wajen Tv take, ɗayar kuma goge katafaren parlourn take ta faman yi. Suna ganin auta suka zube gwiwowinsu a ƙasa tare da sunkuyar da kai ƙasa. "Inan Akka?". Shi ne tambayar da autar ta jefa masu. Cikin girmamawa har suna haɗa baki wajen cewa. "Akka tana sama". Da sauri ta haye saman ba tare da ta sake bi ta kansu ba, wajen kyakkyawar elevator ta nufa, sama ta haye, sai faman farinciki take yi kamar wadda aka yi wa wani kyauta mai girma, daɗi take ji yayanta ya kammala secondary school zai dawo. A hawa na ukku ta tsaya, sauka ta yi ta nufi cikin katafaren parlourn saman, cikin wani katafaren bedroom mai girman gaske ta shiga. Wani shinfiɗaɗɗen king bed na alfarma ne a cikin wannan ɗaki, bed ɗin yana da girma sosai, kayin wannan King bed ɗin ya kai kusan taɓa sama, dan ya fi rabin bango, kuma iya wannan bed ɗin ne kawai a cikin wannan katafaren bedroom ɗin, sai wasu gajerun luntsuma luntsumar Dubai carpet dake shunfuɗe a kasar floor na ɗakin, tiles na cikin ɗakin gabaɗaya launin sky blue ne, sun sha gyara, sai ka ce kafa bai taɓa bi ta kansu ba, saboda tsafta, ga wasu triplets door masu kyau a jere ta ɓangaren dama a cikin ɗakin, ɗaya door ɗin toilet ne, ɗayan kuma na balcony, ɗayan kuma dressing room ne. Akwai kuyangu guda biyu a cikin ɗakin da suke yi wa mamallakin wannan ɗakin hidima, ƴan mata ne kuyangun masu jini a jika. Wata kyakkyawar farar balarabiyar dattijuwa ce ke kwance a saman wannan katafaren bed ɗin, kuyanga ɗaya tana aikin matsa mata fararen kafafun nata, abinku da jiki na tsufa, ɗayar kuyangar kuma tana matsa mata hannunta, ita kuma tana kwance shiru abinta. Hayewa saman bed ɗin auta ta yi bayan ta gabatar da sallama kenan. "Akka, Akka tashi ki ji wani labari". Shi ne abin da autar take ta faɗa. Buɗe idanuwanta wannan dattijuwa ta yi, kwayar idanunta sak irin na autar, duk da take tsohuwa kyakkyawar gaske ce. "Wani labari ne wannan haka Auta?". Ta yi maganar tana ƙoƙarin miƙewa zaune. Cikin hanzari kuyangun nan nata suka ja da baya kaɗan tare da cire hannayensu daga tausan da suke yi mata. "Akka Yah Omar ya kammala secondary school, kuma daddy ya ce zai dawo nan" Akka zata yi magana sallamar Gimbiya Chuchu ya katse ta. "Wato ke auta a nan kika zo kika yi zamanki kin barmu muna ta jiranki a garden ko? To ga can Aunty Fanan tana jiranki da fruits a hannu, ni ba zan iya ba na taho na yi wanka". Cewar Gimbiya Chuchu kenan. "Aunty Chuchu ni fa na fasa shan fruits ɗin, kuma ba yanzu zan koma garden ba, yanzu ina nan tukun nan". Ta kai karshen maganar tare da kwanciya a saman bed ɗin ta tada kai da cinyar Akka. Juyawa Gimbiya Chuchu ta yi ta nufi waje tana faɗin. "Ke dai kika sani, ni kinga wucewata, bari naje bedroom ɗin can na yi wanka hai". Ta kai karshen maganar tata ma a kofar waje, dan tana tafiya ne tana maganar. Bedroom na kusa da na Akka ɗin ta shige, tana shiga kuma ta hau cire kayan jikinta kamar wadda take sanye da ƙaya dama. Toilet ta nufa dan yin wanka, kasancewar wannan part ɗin na kakansu ce, Akka ita ce ta haifi King Zuhair, so kowa daga cikinsu yana da damar shigowa cikin wannan part ɗin ya yi abin da yake so, babu wanda zai yi mashi wata shamaki. Ita kuwa auta, ta yi kwanciyar suka cigaba da hira a tare da Akka, shi kuwa Hoorain ya koma cikin mayaƙa ƴan uwansa, dama sai ta fito yake kula da ita, idan ta koma ciki shi ma komawa wajen ƴan uwansa mayaka yake yi. Shi kuma King Zuhair suna can suna tattaunawa da Sarkin yammaci a kan yanayin halin rayuwa da al'umma suke a ciki, suna ta faman neman mafita, dan samawa mutanensu saukin wahalar rayuwa da ake ciki. Idan muka waiwaya gidansu Zainab kuwa, and kafin mu waiwaya let me tell you one think about me and my story, ina son ku sani kowace marubuciya a duniyar nan da yanayin tsarin salon rubutunta wadda ta tsarawa kanta, kowacce da abin da ta fi karkata a kai, to abin da nake son ku sani a kai'na shi ne, ni salon rubutuna yana tafiya ne a kan part, part! Wato labaraina suna da ɓangarori da dama, nasan da dama daga cikin waɗan da suka karanta littafin TRIPLETS sun san yana da parts parts daban daban, a fita wannan a shiga wannan, idan ban yi karya ba a kallah akwai parts mabanbantan sama da guda 13 a cikin littafin TRIPLETS, parts nasu Abba ne, nasu Abbi daban daddyn jelly da dai sauransu, kuma kowani part kun sani da nashi roll ɗin da yake playing a cikin littafin, ba'a banza nake sako parts da dama ba, so ni haka salon nawa rubutun yake, kowacce writer da nata salon, ina maku albashir da cewa shi ma littafin RAWANIN ZALINCI tafe yake da parts mabanbanta da zasu ƙayatar da ku matuƙa, duk da cewa ba lallai ya kai yawan parts na TRIPLETS ba, sannan kowani parts da nasa cakwakiyar, kuma duk wanda kuka ga sako a cikin labarina da rawar da zai taka, ba haka kawai nake sakosu dan jin daɗin kai'na ba, fatan kun gane?. ❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥ GIDANSU KHADIJAH🧡 A yanzu Khadija an zama ƴan'mata, kyau ya kara bayyana, ga surar jiki komai masha Allah, su Zainab iyayen san kyalliya ma an zama ƴan'mata, mamansu tana matuƙar kula da su, kamar yadda kuka sani ne babansu yana kula da su sosai, kuma tun daga kan Zainab mamansu bata sake haihuwa ba har yau, dangin miji sun sakota a gaba a kan cewa shiru shiru bata sake haihuwa ba, dama su jama'a ba'a iya masu, ka haifi dayawa ace ka cika haihuwa, idan kuma Allah ya dakatar maka da haihuwar, nan ma su isheka da shirun ya yi yawa yakamata ka kara, sai kace akwai wanda yake bada haihuwa ne a duniya, wlh jama'a muji tsoron Allah, ban cire kowa ba muji tsoron Allah! Mu dai'na takurawa waɗan da basu haihuwa da wuri ba ko kuma waɗan da basu samu haihuwa ba kwata kwata, domin kowa yasani cewa babu wanda ya isa ya bada haihuwa sai Allah mahalicci mai kowa mai komai, amma saboda son zuciya sai a murje idanu ayi ta takurawa baiwar Allah wai har yanzu bata haihuwa ba, to kada dai a manta mai bada haihuwar yana sama yana jin duk abin da ake yi kuma yana gani, ku ta cin zarafin yarinya idan bata haihu da wuri ba, a dai rinƙa jin tsoron Allah, wata ma idan ta haifi maza ace ta cika haifar maza, ta cikawa mutane gida da maza, idan kuma mata ne nan ma ace ta cika gida da ƴaƴa mata kamar dai Maman Zainab a yanzu, su maman Haidar sun sakota a gaba wai ta tara ƴaƴa mata kuma daga su ta lafe shiru ba kari, to gaskiya su shirun ya yi masu yawa, ko ta kara haifar wasu ko kuma baban Zainab ya karo aure daga cikin family, abin mamakin kuma duk wannan bala'i da maman Haidar ɗin take yi fa ita ma ƴaƴanta biyu rak, amma saboda son zuciya bata duba nata ba ta sakawa wata ido, da yake dama ba kaunar maman Zainab ɗin suke yi ba, dama ance laifi tudu, ka taka naka ka hango na wani, wannan matsala ta haihuwa ko rashinsa yana ɗawainiya da mata dayawa, to wlh mu ji tsoron Allah, mu sani Allah shi ne mai iko da komai, shi haihuwa idan Allah ya tsara ga lokacin da zai zo to fa babu uban da ya isa ya hana shi zuwa, ko uban magani kike sha dan hana ɗaukar ciki, wlh idan lokacin da Allah ya rubuta zaki haifi ɗan ya zo duniya, to fa ba makawa sai kin haife shi a lokacin, and lastly su ƴaƴa ai ba'a ƙayyadewa kai ga iya adadin da ake so, sai dai bawa ya faɗa kawai dan jin daɗin bakinsa, amma Ubangiji ya riga ya tsara maki ƴaƴa nawa zaki haifa a rayuwarki, dan haka ba sai kin wahalar da kanki ko kin wahalar da ƴar wasu a kan zancen bata haihuwa ba! Ki sani kema watara zaki iya haifar ɗiya mace, nasan babu wadda zata ji daɗi a sako ƴarta a gaba da cin mutunci a kan rashin haihuwa, to ki sani alkawari ne duk abin da kika yi wa ƴar wani sai anyi wa taki. Ita dai Maman Zainab kome za'a faɗa sai dai ta kawar da kai tamkar bata san suna yi ba, dan ba yadda za ta yi da su, yayyun mijinta ne, dama kannensa ne to da sai ta iya saka baki, amma yayyunsa ne da mahaifiyarsa, dole ta ja bakinta ta yi shiru. Wani babban abin bakin cikin kuma a nan shi ne, wai Haidar yana son Khadija, mamarsa kuma ta dage sai shi za'a bawa ita, kwata kwata yanzu fa shekarun Khadijan 17 years, shi kuma Haidar a yanzu yana da 27 years, amma haka yaron nan ya kafe wai sai ita yake so, yaga ta zama ƴan'mata yanzu, komai zam zam, gata da tsafta da son kwalliya, dan tun suna yara mamansu ta saba masu da kwalliya idan baku manta ba, so yanzu abin ya bi jikinsu, tsaf tsaf da su. Khadijah sam bata son shi, dan idan baku manta ba a baya tun suna yara yake kyararsu, baya kyautata masu, kun san yaro kuma da iya rike abu, to Khadijah dai bata manta da irin harara, mari tare da zagin da ya rinƙa yi masu tun shekaru goma zuwa shaɗaya a baya ba, dan haka sai ta tsane shi sosai. Bugu da ƙari Khadijah bata son shi ne saboda rashin iliminsa, kunga dama shi bai yi karatu ba, to yanzu ita kuma tana Ss2, ganin wani iri wawa ma take yi mashi, dan ko sunaye bai iya rubutawa ba, idan an kira shi a waya sai ya tambayi Sadiq wanene mai kiran nasa, Sadiq ɗin ne yake gaya mashi sunan mai kiran nasa, ko saving number mutane a kasuwa Sadiq ɗin ne yake tallafa mashi ya rufa mashi asiri ya yi masa, babu abin da ya sani, shiyasa Khadijah ta yi mugun rai'na mashi wayo take ganinsa a very local, ga shi kuma kakanta wadda ta haifi babanta da kuma maman Haidar ɗin sun zage a kan tabbas shi zata aura tun da ya nuna yana sonta ai ba zasu bawa bare ba. Tirƙashi!! Yau ake yinta. Kullum cikin kuka take yi baiwar Allah, har abin ya fara shafan karatunta, da babanta ya fahimci haka shi ne ya ce ta yi hakuri In Sha Allah ba zata auri Haidar ba, zai yi magana da mamar tasa, wato kakansu kenan, sannan ta rage zuwa gidan kakan nasu dan ta ɗan huta da zancen Haidar ɗin da ake yi mata, ita kuma kakan ta rike wuta a kan lallai Khadijah ɗin tana gama Ss 3 sai aure kawai. Babbar magana, ko yaya wannan aure zai kasance? To mu dai namu ido. Zainab dai sai dai ta bisu da ido abinta, babu ruwanta da su, a maimakon Haidar ɗin ya ce Zainab yake so tun da ita ce kara ma kuma ta fi Khadijah kyau, sai ya nace ya khafe lallai shi Khadija yake so, kuma ba komai ne yasa ya kafe sai ita yake so ba face surar jikinta, Zainab yanzu take girma, halittar jikinta bai bayyana sosai ba, su tula tula duk basu ciko sosai kamar yadda yake so ba, ita kuma Khadijah sai dai muce Masha Allah, komai ya ciko, abinku da jahili mara ilimi, tula tulanta da shape nata ne kawai suke ɗauke mashi hankali, sune a gabansa, dan ko wayarsa ka karɓa banda hotunan mata masu tula tulanta breast manya manya babu abin da zaka gani, yana sha'awar hakan sosai, ita kuma Khadijah akwaisu sosai, shi ne yasa ya nace dole sai ita yake so, kayan takaici! Dama ace son Allah da annabi yake yi mata ne, da sai ace to da sauki, amma saboda surar jikinta yake sonta kuwa kunga akwai babbar matsala, yana iya mayar da ita karamar bazawara, dan ba hankali ke gare shi ba, mutumin da ko karatun sallah bai gana iyawa ba, sai dai ba bi jam'i a masallaci, ai kunga babu abin da ba zai iya aikatawa ba, dama kuma ba ganin Mahaifiyarta da mutunci yake yi ba, abin dai sai dai mu saka Khadijah a addu'a. ❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥ Zaune suke a parlourn, Maman Zainab kamar kullum ta gama shirya masu abincin darensu a tsakiyar parlourn, sun yi sallar issha suna zaune suna jiran Baban Zainab. Yanzu an kara gyara parlourn sosai, arziki ya ci uban na da, dan baban Zainab mutun ne mai taimako, hakan tasa arzikinsa yake kara bunƙasa sosai. Zainab tana kallon labarai a kan KINGDOM OF POWER a news, a duniya yarinyar nan tana son wannan masarautar sosai, musamman idan ana magana a kan KING ZUHAIR ABDUL MALIK da ƴaƴansa, abin yana ƙayatar da ita. Ita kuma Khadijah ta buga uban tagumi tana tunanin maganar da suka yi da Haidar ɗazun a kan cewa wai yanzu yakamata ta rinƙa kai mashi abinci ɗaki ne, bai kamata ya rinƙa zuwa da kansa yana ɗauka ba, dan saura ƴan watannin da basu fi 8 ba su rubuta waec and neco, suna rubutawa kuma sai aurensu, irin shi ya fara jin kansa a angon nan. To kawai ta amsa mashi da shi, domin idan ta tsaya yin dogon magana da shi ma ko kuma ta ce zata yi mashi gardama, ƙaramin aikinsa ne ya mareta, Mamansu kuma bata da bakin magana, idan ta yi magana to ta jira isowar maman Haidar ɗin da tawagarsu gidan, tsabar bakin ciki wani lokaci ma ji Maman Zainab ɗin take yi kamar ta haɗa kayanta kawai ta bar gidan, amma idan ta tuna cewa idan ta bar gidan dole zata bar su Khadijah ɗin a gidan, ta gudu kenan bata tsira ba, ai gara mata ma ta zauna da su, dan kada ta tafi wani abin ya haɗo Haidar da Khadijah ya zo ya yi masu ba dai'dai ba, dan ba hankali ke gare shi ba. Wannan dalilin kawai yasa take hakuri ta cigaba da zama cikin takurar wannan balaƴaƴƴar wato Maman Haidar, shi ma baban Zainab sam baya jin daɗin abin, amma yana can yana ta faman neman mafita ta yadda zai lallaɓa mahaifiyarsa ta hakura da zancen auren, su bar Khadija ta kawo mijinta wanda take so, kullum suna cikin zuba addu'a sosai. Sallamar Aunty Hauwa ce ta katse masu abin da suke yi a in da dukkansu suka kai kallonsu kofar shigowa, amma ban da Khadija da kanta yake kallon ƙasa ta buga uban tagumi, da alama ma bata ji sallamar Aunty Hauwa ɗin ba. Hannunta ɗauke da manya manyan ledoji ta shigo cikin parlourn. Da murna Maman Zainab ta tarbeta tana faɗin "Daga ina kuma Hauwa da wannan uban kayan?". Da yake yanzu Aunty Hauwa fa ta zama dillaliya, saye da sayarwa take yi, har gida mata suke kawo mata kaya irin kamar mace ta yi suna an tara mata atamfofi tana son ta sayar, sai ta kaiwa Aunty Hauwa ta saya da sauki ta bata kuɗin, sannan ta fitar ita kuma ta sayar a sabo, ba abin da bata saya ta kuma sayar, har da su gadaje second hand, su kujeru dukka. A tsakiyar parlourn ta shirge niki nikin kayan tare da zama a saman sofa tana mayar da numfashi, tamkar ba matar aure ba ta wani yafo ɗan mayafin da ko kafaɗunta basu gama rufewa ba. "Wlh daga gidan wata dillaliya nake, na je ne nan na kwaso wasu manya manyan zannuwar gado, shi ne na ce bari na kawo maki ko zaki saya". Cewar Aunty Hauwar kenan. "Kai Hauwa akwai ki da neman magana, ai kin san ni komai baban Zainab ne yake saya mun, kin taɓa ganin na sayi wani abin da kuɗi na ne?". Girgiza mata kai Aunty Hauwar ta yi alamar a'a bata taɓa gani ba. "To kin gani, shi ne nan mai sayan komai, zannuwar gado duk bayan wata biyu yana zuwa mana da sabbi daga kasuwa". Ɗan taɓe baki Aunty Hauwar ta yi kafin ta furta kun ji daɗinku ai. Murmushi maman Zainab ta yi tare da faɗin. "Gaskiya kam mun ji daɗi, kema ai kina jin daɗi, sai kasuwancinki kike yi kina tare kuɗaɗe". "Hmmm kasuwanci ko wahala? Yanzu duba fa sai da na fita na je na kwaso kayan nan da kai'na, ke kuma fa? Kina zaune a gida babu in da kike zuwa, baki shan wahalar nema, baki shan rana, sai dai duk abin da kike so ayi maki, ai kinga ni dake akwai banbanci, ku ne masu jin daɗi, Allah dai yasa mu adanshinku". Kara faɗaɗa murmushinta Maman Zainab ta yi. "Zainab ba zaku gaishe da Aunty Hauwa ba ne? Ki kawo mata ruwan sanyi ta sha". Ɗan turo baki gaba Zainab ɗin ta yi tare da miƙewa ta nufi wajen fridge, tana yi wa Aunty Hauwar sannu da zuwa. Ruwa mai sanyi roba ɗaya ta ɗauko mata tare da wani kyakkyawar plastic cup. A gabanta ta zo ta ajiye mata, sannan ta juya ta nufi cikin ɗakinsu. Miƙewa ita ma Khadijah ta yi, ba tare da ta kalli in da Aunty Hauwa ɗin take ba ta yi mata sannu da zuwa kafin ta sa kai ta wuce ɗakinsu. "Maman Zainab wai menene yake damun Khadijah ne? Yau na ganta wata iriya da ita, sam bata da walwala". Cewar Aunty Hauwar, ta yi maganar kuma tana zuba ruwan da Zainab ta kawo mata a cikin cup dan ta sha. "Hauwa kenan ke da kin san komai, maganar nan ne dai na aurenta da Haidar, wai ina kika baro su Khalid ne Hauwa?". Sai da ta sha ruwan da ta zuba a cup ɗin, sannan ta amsa mata da cewa. "Su Khalid suna gidan kakarsu, amma kema maman Zainab wlh da laifinki, yaushe zaki tsaya suna yi maki irin wannan cin kashin? Sai na yi maki magana sai ki ce ai yayyunsa ne ba kannensa ba, to su yayyun nasa idan suka yi ba dai'dai ba ba'a gyara masu zama ne? A ina kika taɓa jin irin wannan? Ki zauna ki yi shiru kina ji kina gani za'a lalata maki rayuwar yarinya, kefa haka kike, tun muna makaranta ma ni nake tare maki faɗa, sai ki yi shiru ki bari kowani kare da doki yana takaki son ransa, ni wlh ba zan ɗauki wannan iskanci ba, shiyasa ma nake kara godewa Allah da ya bani yara dukka maza babu mace a ciki, dan na huta da waɗan na rigingimun". Ta kai karshen maganar alamar ranta ya ɓaci. "Hauwa ke ba zaki gane bane, wlh ni ba zan iya fito na fito da mahaifiyarsa ba, saboda kinga babban Zainab bai cancanci na yi koda musu ne da mahaifiyarsa ba, shi zaki duba, yana yi mana komai dan ya sanya mu cikin farinciki, a gaskiya ko ba dan ma haka ba ni ba zan iya tsayawa ina fito na fito da mahaifiyarsa ba ko na yi mata rashin kunya, ba zan iya ba, dan uwa uwace ko mai lalacewarta". Girgiza kai Aunty Hauwar ta yi. "Ai nima ban ce ki yi fito na fito da mahaifiyarsa ba, ita wannan Maman Haidar ɗin zaki gyarawa zama, ita zaki takawa birki, cin kashi ya yi yawa, suna zaginki a kan kin tara masu ƴaƴa mata a goda, ga shi har Yanzu shiru baki sake haihuwa ba sai dai ki ci ki kwanta sai kiɓa kike yi, sannan kuma saboda basu da kunya sai su dawo suna neman auren ƴar taki da kika tara masu a gida wa ɗansu? Kuma duk da suna neman auren ƴar taki ma basu dai'na ci maki mutunci ba? A haka kuma kike tunanin zaki zuba masu ido? Ai wlh basu isa ba, bari zaki yi rana ɗaya idan Maman Haidar ɗin ta zo ta nemi kawo maki rai'nin wayo, a nan ne zaki taka mata birki, ki karta mata jar warning mai zaman kanta, hakan zai sanya ki ɗan huta, haba abin ya yi yawa mana". Tana magana tana wani kara ɓata rai. "Hauwa ba zaki gane bane, misali yanzu idan na yi wa maman Haidar magana cikin ɗaga murya ma, wlh to ki jirayi zuwan kakansu, dan sai ta je ta kwashi karya da gaskiya ta gayawa mahaifiyar tasu, ita kuma zata sako hijabi ta zo nan ta ci mutunci na fes, kullum sai ta ce zata sanya baban Zainab ya sake ni, ni kuma a yadda su Zainab suka taso yanzu suke ƙoƙarin zama ƴan'matan nan zamana dasu shi ne mafi a'ala a gareni, a yanzu nisa da su babbar haɗari ne a gareni, kinga yanzu suke tashen girma, yanzu ne suke buƙatar kulawata sosai, dan haka gara na jure na cigaba da hakuri na zauna da babansu har izuwa lokacin da zan kaisu ɗakin mazajensu lafiya, daga nan sai na san abin yi". Ta kai karshen maganar tamkar zata yi kuka, idanuwanta sun ciko tab da kwallah, abin gwanin ban tausayi, takura sam bashi da daɗi a rayuwar nan. Aunty Hauwa na ƙoƙarin yin magana suka tsinkayo sallamar baban Zainab ɗin a bakin kofar shigowa parlourn, sun dawo ne daga masallacin sallar issha. Jin sallamarsa yasa Aunty Hauwar ta miƙe tsaye tana faɗin. "Zamu karisa maganar idan kin zo gida ko kuma idan na sake zuwa, yanzu dai bari na wuce dare ya yi, kuma kinga unguwar nan taku sai a hankali, kada wani ya bugeni ya kwashe mun kaya". Tana magana tana tattare kayan nata, haka ta jidesu ta nufi waje. Dai'dai lokacin kuma Baban Zainab ya shigo cikin parlourn. Kamar yadda kuka sani ne, ko sannu bai ce wa Aunty Hauwar ba, yasa kai zai wuce, dan haka yake. Cikin sauri ta ɗaga mashi gaisuwa, ya sha dakakkiyar shaddarsa ɗinkin mutunci, yanzu kuɗi sun fara zama mashi zamzam, wani katafaren gini ma yake ta faman gina masu, hawa ɗaya ce gidan, idan ya kammala zasu koma can abinsu, sai dai kash dangi sun sako shi a gaba a kan ya kara aure tun da Maman Zainab taki ta sake haihuwa, Maman Haidar har da wani cewa sun gaji suna son sake ganin yara ƴan dogwai dogwai a gidan. Ɗan adam kenan, ba'a iya mashi. A takaice ya amsa mata gaisuwar tata tare da sanya kai ya wuce ciki abinsa. Har bakin kofar gida Maman Zainab ɗin ta rako Aunty Hauwar, yau ma kamar kullum sai da ta bata dubu ɗaya wai ta hau mashi. Karɓa ta yi tare da zuba mata godiya. Daga haka suka yi sallama, Maman Zainab ta wuce ciki, ita kuma Aunty Hauwar ta nufi waje. Tana fita Sadiq bawan Allah ya fito daga cikin ɗakinsu ya zo ya rufe kofar gidan tare da kalewa da sakata, sannan ya koma cikin ɗakin nasu. Haidar sai faman sanya kaya yake yi shi a dole zai fito tsakar gida su yi hira da Khadijah, ita kuma sam bata son yin hira da shi da daddare, dan kullum sai ya rinƙa ƙoƙarin taɓa jikinta, tsabar jahilci sai ya ce ai ita ƙanwarsa ce kuma aurensu ya kusa. A kule take ce mashi ya bari sai anyi auren tukun nan, haka dai take fama da shi, baiwar Allah, ga shi ta kasa iya gayawa babanta abin da yake yi mata su ɗauki mataki, ta rasa ina zata saka kanta, mamanta ta yi so silent over. Shiyasa wani lokaci shiru shiru ma bashi da daɗi sam. Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI. 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 8/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________9🔥 A saman sofa baban Zainab ya zauna yana jiran shigowar maman daga rakiyar Aunty Hauwa da ta yi. Bawan Allah tunaninsa duk yana wajen yadda zai yi da mahaifiyarsa, ga jikin tsufa, idan ka fara yi mata magana duk sai ta bi ta rikice ta ce wai an zageta, haka take yi, ta tsufa sosai, dan a ƴaƴanta Baban Zainab shi ne wajen na shidda, and dukka mata ne ƴaƴan nata shi ne kawai namiji, uku daga ciki sun rasu sun bar mata jikoki tana tare da su, wani lokaci ƴaƴan suna wajen kakarsu ta wajen ubansu kenan, wani lokaci kuma suna wajenta, yanzu daga maman Haidar, sai wata mai bin Maman Haidar ɗin takwarar Zainab, sai babansu Zainab, sune manyan da suka rage, sai kanana mata guda biyu da duk suma sun yi aure suna ɗakin mazajensu, so a takaice dai tsohuwa ce sosai kakar tasu, shi ne yasa take a birkice sosai. Baki a ɗauke da sallama Maman Zainab ta dawo cikin ɗakin, kusa da shi ta zo ta zauna tana yi mashi sannu da dawowa daga masallaci. Ƙaƙalo murmushin dole ya yi kafin ya ce. "Ina su Khadijah? And ina kayan da na dawo da shi daga kasuwa?". "Suna ciki, kayan ma na kai ɗaki". Ta bashi amsa tana miƙewa tsaye, ɗakinsu Khadijah ɗin ta nufa domin ta kirasu su zo su ci abincin dare. Da fitowarsu kallo ɗaya baban ya yi wa Khadijah ɗin ya kawar da kallonsa, har ƴar rama ta yi. A in da suka saba zama a nan suka zauna. "Khadijah ɗauki abincin su kawu Sadiq ki kai masu". Cewar mamanta, da yake bata san abin da yake faruwa ba, bata san cewa Haidar ɗin yana son keɓewa da Khadijar dan ya rinƙa taɓa mata jiki ba. Cikin sanyin murya a takaice ta ce. "Zainab ta kai masu pls Mama". Babansu ne ya amsa da cewa. "Yeah nima abin da zance kenan, Khadija ba zata sake kai masu abinci ba, ita ma Zainab ɗin daga yau idan ta kai masu shikenan, su zo su rinƙa ɗauka da kansu!". Ya yi maganar ne cikin umarni, babu wasa a tattare da shi, hakan yasa Maman Zainab ɗin ta amsa mashi da to In Sha Allah hakan za'ayi. Turo baki Zainab ta yi kamar zata sa ihu, dan ita fa a duniya ta tsani zuwa koda kofar ɗakinsu ne, bare ma idan kawu Sadiq baya nan, sai ta ji kamar ta yi ta zunduma ihu idan aka aiketa koda ɗaukar abu ne a cikin ɗakin, bata son ganin Haidar, amma ya zata yi? Dole ta miƙe ta zuro hijabi kafin ta ɗauki ƙatuwar kular abincin tare da plates ta nufi waje da shi. A bakin kofar ta tsaya ta kaiwa kofar ɗakin kauri da kafa kamar shi ne ya yi mata laifi, yadda kuka san kofar ne ya sakata dole ta kawo abinci. Daga ta cikin ɗaki Sadiq bawan Allah ya ce. "Zainab ba? Ai nasan sai ke ce zaki buga mana kofa irin haka, to sannu da ƙoƙari ƴar neman rigima......" Bai gama rufe baki ba Haidar da yake tsaye wajen mirror ya karɓi zancen cikin faɗa da cewa. "Ai wlh Zainab sai na koya maki hankali a gidan nan, ba ke baki da hankali ba? Yanzu mu sa'anninki ne da zaki zo ba sallama ki hau dukan mana kofa? Bari na same ki a waje sai na sharara maki Marika". On a serious note ya yi maganar. Murguɗa mashi baki ta yi dan tasan baya ganinta, sannan ta ce. "Kawu Sadiq ga abincinku nan in ji mama". Har suna haɗa baki shi da Haidar wajen magana, shi Sadiq ya ce ta ajiye a waje bari ya zo ya ɗauka, shi kuma Haidar ya ce to uban waye take so ya zo ya karɓa? Waye sa'anta? Ta kawo ciki ta ajiye. Banza ta yi da Haidar ɗin kamar bata ji me ya ce ba, dan dama ita Zainab haka take, yadda kuka san me za'a ce ne, ta iya mannin hauka ta mayar da mutane ƴan iska, idan ka yi mata maganar da bai yi mata daɗi ba kuma kana da matsayin da ba zata iya ramawa ba kamar dai yayan nasu, sai ta mayar da kai ɗan iska, ta yi kamar ma bata ji me ka ce ba, kamar ma bata san kana yi ba, idan kuma tasan tana da halin ramawa, to wlh bata barin kota kwana, tsab zata solleka soso da sabulu. Yanzu ma abin da ta yi kenan, ta ajiye abincin a kofar ɗakin tare da murguɗa baki kamar Haidar ɗin yana ganinta, sannan ta watsa masu daƙuwa da yatsunta biyar yadda kuka san suna ganinta, kofar ɗakin ma fa a rufe yake, amma haka ta tsaya tana huce haushinta a waje, abin gwanin ban dariya. Bayan ta watsa masu dakuwar ma bai yi mata ba, sai da ta dunƙule hannu ta yi alamar zata kai haushi tana wani watso harara da waɗan nan fararen idanuwan nata kamar na mage. Muryar Haidar ne ya katseta da cewa. "Ke ba zaki kawo mana abincin bane kina tsaye a waje?". Kara murguɗa baki ta yi kasa kasa ta ce. "Mahaukacin banza ba za'a kawo ɗin ba". Ta yi maganar ta yadda ita kanta bata wani ji sautin muryarta ta fita sosai ba, sannan tsabar faɗa irin nata da rigimar tsiya har da murguɗa mazaunanta kafin ta sa kai ta wuce parlournsu ba tare da ta sake kula Haidar ɗin ko ta ce masu ga abincin a kofar ɗaki ba, ta mayar da Haidar ɗan iska, ta barshi yana ta zuba masifa a kan ta kawo abinci cikin ɗaki, irin shi yaya babban nan, Zainab kam dai'dai take da shi yarinyar nan, ita ce nan tasan maganinsa, idan yana mata magana ma wata sain wlh sai ta toshe kunne, ko kuma ta kara gaba ta bar shi a gantale. Shiru shiru Haidar ya ji Zainab dai bata amsa ba kuma bata shigo da abincin ba, a kule ya nufo kofar ɗakin da nufin yana buɗewa sai ya zabga mata mari. Sai dai kash, yana buɗewa bai ga ko mai kama da ita ba, tuni ta ajiye masu abincin a bakin kofa ta yi gaba abinta. Ransa idan ya yi dubu ya ƙara ɓaci sosai, amma ba yadda zai yi, dan babansu yana nan, bai isa ya je ya kamata ya daka ba, hakan tasa ya hakura ya koma cikin ɗakin kawai, tsabar shegen son girma sai bai ɗauki kular abincin ba, ya koma cikin ɗakin ya ce Sadiq ya je ya shigo da abinci. Sadiq kuwa bawan Allah ɗan ba ruwana, miƙewa ya yi ya ɗauko abincin ya shigo masu da shi ciki, sai wani cika Haidar yake yi yana batsewa, shi a dole an ɓata mashi rai. A can cikin parlourn kuwa, Khadija cikin hanzari ta ci abincin darenta, a daddafe ma ta tura abincin, ba wani ɗanɗano da take ji, ci kawai take yi. Suna kammalawa ta miƙe sauri sauri ta wuce cikin bedroom nasu, da kallo iyayen nata suka bita da shi, dukkansu ba karamin tausaya mata suke yi ba, babanta ya so ya tsayar da ita dan taga kayayyakin da ya sayo masu daga kasuwa, ya so su buɗe kayan a daren nan ya bawa kowa nasa, amma ganin bata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yasa ya kyaleta zuwa da safe. Ita kuwa Zainab sai da ta ɗan jima a parlourn tana hira da babanta bayan sun gama cin abincin kenan, sai ƙarfe 9 dai'dai ta miƙe tare da yi masu sallama ta wuce ciki. Kwance ta isko Khadijah a saman bed, sai dai da alama bata yi barci ba. Wanka Zainab ɗin ta yi tare da fitowa ta yi shirin kwanciya, sannan ta haye saman bed ɗin tana kallon ƴar uwar tata. "Baki kashe wutar ɗakin ba ai Malama". Cewar Khadijah. "Aunty khadina ki bar wutar a kunne mana tun da dukka labulayenmu a sake". Shiru Khadija ɗin ta yi mata, bata sake yin magana ba. Zainab bata shiri da duhu ne, bata barci cikin duhu, idan kunga sun kashe wutar ɗakin nan nasu to sai dai idan Zainab ta yi barci ne, sai Khadijan ta kashe, wani lokaci dukkansu suna yin barci su barshi a kunne, sai iyayensu sun shigo yi masu addu'a, sannan ne suke kashe masu wutar ɗakin. Kwanciya Zainab ɗin ta yi tana tunani rayuwar yayar tata. A hankali Khadijar ta ambaci sunanta Zainab. Juyawa gareta Zainab ɗin ta yi suna fuskantar juna. "Lafiya Aunty Khadina?". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Babu komai, amma anjuma idan kin tashi yin sallar dare ki sakani a cikin addu'a sosai, dan ni yanzu na shiga lokacin rashin sallah tun bayan sallar issha da na yi, dan haka kada ki tasheni yau". Shiru ta ɗan yi kafin ta bata amsa da cewa. "Aunty khadina ai kinsan kullum ina yi maki addu'a, da izinin Allah ba zaki auri Yah Haidar ɗin nan ba, Allah ni kakan nan ma wani lokaci idan tana masifar nan tata kamar na kifeta da mari nake ji". Harara Khadija ɗin ta wurga mata kafin ta ce. "Ki mareta ta mutu ki shiga uku, wannan tsohuwa baki mareta ba ma tana rangaji ita kaɗai a saman iska, ai kina yin kuskure ko kaɗan ne kika bugeta wlh ranga ranga za'a kwasheta, kin ga daga nan ke kuma sai koma". Guntun tsaki Zee ɗin ta ja tare da juyawa ta bawa Khadijahr baya tana wani ƙara haɗe rai. Da alama fa da Zainab aka ce za'ayi wa wannan aure to ba shakka zata yi fito na fito da su, sam lamarinta babu sauki, da wuya su Maman Haidar su sha a hannunta, dan da alama zasu gasu sosai, yanzu ma dan mamanta na taka mata birki ne, ba dan haka ba, da ba abin da zai hanata yi wa Maman Haidar ɗin tas idan ta zo gidan tana zuba masifa, amma Mamansu da yake macece mai tarbiya tana tsawatar masu sosai, tana gaya masu maman Haidar dai ɗaya take da babansu, so idan har Zainab zata yi mata rashin kunya, to kenan zata iya yi wa babanta, dan haka babu ruwansu, idan ma sun ga Maman Haidar ɗin ta zo maza su wuce cikin ɗaki, kada ma su kawo kunnuwansu a kan abubuwan da zata yi ta faɗa, su kyaleta watarana sai labari. A can parlourn kuwa, Haidar ya zo da nufin su yi hira da Khadijah, babanta ya ce mashi ta yi barci, tsabar bashi da kunya wai a tasan mashi ita akwai abin da zai gaya mata ne. Da farko Maman Zainab zata je ta tasheta, sai baban ya ce a'a a barta ta yi barci sai da safe ko idan sun dawo daga makaranta sai ya gaya mata koma me zai gaya mata, yanzu dai tun da ta rigada ta yi barci ya kyaleta. Da farko kamar ba zai tafi ba, dan ba hakan ya so ba, ransa ta ɓaci, ya so ne su yi hira da ita, amma da yake kawun nasa ne ya yi magana dole ya hakura, da ace Maman Zainab ita kaɗai ce a gidan da ba abin da zai hana shi shiga cikin ɗakinsu ya tasheta ta fito ayi hiran dole, dan ba kunya ne ke gare shi ba, ga rashin hankali cikakke, kuma kun san ba ganin mutuncin Mamansu yake yi ba, tsab zai iya cewa zai shiga ya tasota da ace baban baya nan. Amma fa duk rashin kunyar Haidar yana tsoron kawun nasa, dan fa baban Zainab shi ma mutun ne mai zafi sosai, kawai sai anyi mashi ba dai'dai ba ɗayar halin nasa ta zafin rai take bayyana, Haidar ɗin ya ci duka a hannunsa lokacin da yake kin zuwa makaranta, ya sha punishment, sai da kakansu wato maman baban Zainab ɗin ta ce bata so kada ya sake dukan Haidar, ya kyale shi mana tun da ba za'a ci karatu ba, har da cewa wai shi ma baban Zainab ɗin da ya yi karatun ai ga shi nan result ɗin bata amfane shi ba, ya ajiyeta a cikin akwati kawai yana kallo, to dan haka ya rabu da Haidar ɗin, kun san kaka dama yawanci haka suke, sai su hana a ladabtar da jikokinsu. Haidar dai kamar zai yi kuka ya wuce ya koma cikin ɗakinsu, a lokacin shi kuma Sadiq yana zaune ya zuba abinci a cikin plate dan ya ci abinsa, shi ko zancen auren ma baya yi, yanzu haka master nasa yake haɗawa a ɓangaren computer engineering, ya gama degree nasa bawan Allah, akwai shi da ƙoƙari sosai, so baya batun aure ma, mata ma yanzu ba su ne a gabansa ba, ilimi da kuɗi kawai yake nema, mamansa ta ce ya nemi kuɗi da ilimi mata zasu biyo shi har in da yake ba sai ya wahalar da kansa ba wajen bin matan ba, ya bi kuɗi da ilimi a guje su kuma mata zasu biyo shi a guje, uwa ta gari kenan, saɓanin uwar Haidar da take cewa ilimi bashi da wata amfani. Washegari da safe kamar yadda suka saba, tun karfe biyar na asuba bayan sun yi sallar asuba Maman Zainab ta wuce cikin kitchen, abinci mai rai da lafiya ta girka masu a matsayin breakfast, a tare da Khadijah suka yi aikin komai, ita kuma Zainab ta gyare masu gidan ko'ina tsab, ta zuba turaren wuta mai rai da lafiya kamar dai yadda suka saba, yanzu Maman Zainab ƴan'matanta sun girma, aiki ya ragun mata sosai, idan Khadija tana kitchen, ita kuma Zainab zata hau gyaran gida, komai a tare suke yi su ukun kamar wasu kawaye, haihuwan ƴaƴa mata akwai daɗi kuma akwai falala da rahama sosai, ƴa macece kawai Allah ya ce a ranar gobe kiyama zata kai iyayenta aljanna, manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce duk iyaye da suka haifi ƴaƴa mata guda uku, suka tarbiyantaddasu har suka aurar da su ba tare da waɗan nan ƴaƴa sun taɓa yin zina ba, to ba shakka sanadiyar haka Allah ya bawa waɗan nan iyaye aljanna, ƴan macece kawai take da wannan falala, amma a duniyarmu ta yau dayawan iyaye maza basu son a haifa masu ƴaƴa mata, ɗa namiji baya kai iyayensa aljanna kai tsaye, mace kawai Allah ya bawa wannan falala, ai ko dan kwaɗayin aljanna dole muso ƴa ƴa mata, idan ka duba sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, irin shekarun da suka shafe suna aikata aikin Allah ba dare ba rana kafin su sami aljanna, wasu daga cikinsu ma kashesu aka yi, wasu daga cikinsu kafurai sun azabtar dasu azaba mafi muni, idan ka dube su ka dubi ɗan aikin da kake yi, sai ka ji aljanna fa ba abar wasa bace, ba'a samunta a sauki, Allah dai ya bamu ita ba dan halayenmu ba, sai dai mu roki cin albarkacin fiyayyen halitta. Karfe 6 dai'dai suka kammala girki, ita kuma Zainab ta kammala gyaran gida har ta yi wanka ta shiryo cikin white uniform ɗinta, kal kal da shi, ya sha guga malam, ta fito fes, Zainab sarkin farin jini, kowa ya ganta sai ya ce yana sonta, sai dai akwai ta da mugun hali in ji matasa da suke biyota bata kulasu, suka ce mugun hali ke gareta......... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce tsare mutunci da tsare kai dai, ba wani mugun hali munafukai, dan basu sami abin da suke so ba, bata kula kowa, ga shegen kyau jajir da ita, nan gani nan bari munafukai kawai.........😂😅 A parlourn suka zauna dan yin breakfast kamar yadda suka saba, Khadija ta wuce cikin bedroom nasu dan ta yi wanka ta shirya cikin uniform nata, ita kuma Maman Zainab ta wuce nasu bedroom ɗin dan ta taso baban Zainab ya yi wanka ya zo su yi breakfast, sai ya ɗauki su Zainab a kan mashin nasa zuwa makaranta, dama shi yake kaisu, lokacin tashi kuma sai ya bawa Sadiq key ɗin mashin ɗin daga kasuwa ya zo ya ɗauko su ya mayar da su gida sai ya dawo, islamiya kuma a kusa da gidansu yake, ba nisa sosai, so da kafa suke zuwa. After some minutes Gabaɗayansu sun haɗu a parlourn, baban Zainab ma ya yi wanka ya yi shirin zuwa kasuwa. "Zainab ɗauki abincin su Sadiq ki kai masu". Cewar mamansu. Babansu ne ya ce. "Ba na ce su zo su rinƙa ɗauka da kansu ba?". "Yi hakuri na manta ne ban sanar da su su zo su rinƙa ɗauka ba, amma idan sun fito zan gaya masu, yanzu dai ta ɗauka ta kai masu". Shiru ya yi bai sake magana ba. Ita kuwa Zainab tamkar zata zunduma ihu dan bakin ciki, ga shi jiya ta yi wa Haidar rashin kunya ta gudu, yanzu in ta je idan ta yi knocking na kofar, in dai Haidar ɗin ne ya fito tasan confirm sai ya rankwasheta a kai ko kuma ya mareta, da dai Sadiq ne ya fito lafiya lou zai karɓi abincin ya koma ciki. Rai a matuƙar ɓace tana hura hanci ta ɗauki kular abincin tare da plates ɗin ta fito. Ta kuwa yi sa'a tana fitowa ta ci karo da Sadiq wanda ya fito a lokacin shi ma, ya fito zai fitarwa da babansu mashin nasa ne, yana shirye cikin white shaddarsa mai shegen kyau, ɗinki half jompa, ya sha hularsa, sai ya fito a babban mutun mai kima da mutunci, yanzu yana da 28 years, sai ya fito a cikakken matashi mai cike da nutsuwa da kamala. "Kawu Sadiq ina zaka je?". Cewar Zainab ɗin. "Babu gaisuwa sai tambayar ina zan je ko?". Ƴar murmushi kaɗan ta yi, Zainab baka taɓa ganin fara'arta sai idan da Sadiq ko iyayenta or Khadijah suke tare, nan ne zaka ga tana murmushi. "Ai mantawa na yi, naga kayi kyau sosai ne yau shiyasa na manta da gaisuwar, to ina kwana". Ta kai karshen maganar tare da ƙarisowa gabansa. Hannu yasa ya karɓi kayan abincin yana amsa mata gaisuwar kafin ya ce mata. "Ina da class 7:30 dai'dai ne, yau ba kasuwa zan wuce kai tsaye ba, shiyasa na yi kyau haka, ko baki son na yi kyau ne?". Girgiza mashi kai ta yi tana faɗin. "Kawu Sadiq ai dama kai kana da kyau, ranar ba na gaya maka kafi mamanmu kyau ba? Baba ya ce mama dan ita fara ce kawai, da ita baka ce mummuna ce, wai ka fita kyau baba ma ya ce, so ko baka yi kwalliya ba dama kana da kyau sosai, yau ɗin ne naga kyanka ya karu sosai". Cool murmushi ya sakar mata kafin ya ce. "Bari maman ta jiki kin ce na fita kyau, idan ta rikeki ba mai karɓarki a gidan nan, kin san ko lokacin da muke gida kafin ta yi aure bata taɓa yarda ace na fita kyau, Allah ki bari ta jiki zaki yi bayani ne ba ruwana, yadda take jin ita kyakkyawa ce ɗin nan". Dariya sosai ta yi har sai da wishiryar dake tsakanin fararen hakwarantan ya bayyana. "Allah kawu Sadiq ka fi mama kyau sosai, amma na san mama da Oumma take kama shiyasa, kai kuma da Abba kake kama" Abba shi ne mahaifinsu Sadiq ɗin, kakansu namiji kenan, Abba suke ce mashi, kakansu mace kuma Oumma. "Kai, kai, kai, lallai Zainab yanzu kam ni ne zan zaneki, Oummar tamu ce kenan mummuna ko? Shiyasa da mamarki ta yi kama da ita ita ma ta yi muni ko? To baki isa ba wannan kuma, Allah duka zaki sha, ni Oummarta kyakkyawar gaske ce da babu biyunta a duniya, mamarki dai sai Allah kaɗai yasan da waye take kama". Ya kai karshen maganar yana fitar da wallet nasa daga aljihunsa. Sai dariya take yi tana kara gaya mashi Allah kakarsu mace mummuna ce, shiyasa mamarsu bata da kyau sosai sai hasken fata. Kuɗi 1k ya ciro ya bata, sannan ya juya ya nufi cikin ɗakinsu yana faɗa mata su yi breakfast da 1k ɗin idan sun je makaranta, dan yasan ƴan makaranta ba'a rabasu da saye saye na kwalama. Sosai ta yi mashi godiya sannan ta wuce izuwa cikin parlourn ita ma. A gaggauce suka karya, dan lokaci karfe 7 ta yi, kuma 7:30 dai'dai suke shiga cikin school kullum, babansu baya yarda su yi latti, yana kula da karatun nan nasu fiye da tunaninku. Bayan sun kammala sai suka fito harabar gidan da nufin tafiya, su Zainab kowacce ta goyo jakarta a baya, Mamansu ta rakosu harabar gida kamar yadda suka saba. Jin fitowarsu harabar gidan yasa Sadiq ya fito domin ya fitarwa da Baban Zainab ɗin mashin ɗinsa daga cikin kitchen ya kai mashi waje, haka suke yi kullum, shi kuma Haidar sarkin son girma yana ciki. Kun san jahilci tana tare da girman kai, girman kai kuma yana tare da shegen son girma kamar me, mutun mai ilimi wanda yasan abin da yake yi ba zai yi girman kai ba wlh, wannan sai jahili, to dai haka Haidar yake da bala'in son girma kamar menene, ga shegen girman kai rawanin tsiya. Ya fito da mashin ɗin harabar gidan kenan da nufin ya fitar waje, shi kuma Haidar yana ciki yana aikin zuba barci, dan shi kasuwar ma sai sanda ya tashi barcinsa yake zuwa, wani lokaci sai 11 na rana yake zuwa, shegen barcin safe ke gare shi. Murmushi ne a saman fuskar kowannensu, musamman baban Zainab, sai tsokanar Sadiq yake yi a kan ya yi kyau sosai yau dan ba Kasuwa zai je ba, wato zai je school akwai ƴan'mata a can shi ne ya tsara kwalliya ko?. Sai murmushi Sadiq ɗin ma yake yi yana cewa da ai shi babu ruwansa da mata. Maman Zainab kuwa ta ce ba wani nan idan ba dan ƴan'mata ba ai ba zai yi irin wannan shiga a kullum idan zai tafi makarantar ba, meyasa baya yi irin shigar idan zai je kasuwa? Sai dai ya ɗauki wasu tsofaffin kaya ya sa ya tafi kasuwar, makaranta kuma a tsantsara kwalliya. Zainab sai dariya take yi mashi tana faɗin Allah ya kama kawu Sadiq, yau asirinsa ya tonu. Khadija kam fuska kamar ko yaushe, sam bata a cikin walwala baiwar Allah. Sadiq bai kai ga fitar da mashin ɗin ba suka ga an banko kofar gidan an faɗo masu cikin gida. Zainab sarkin tsoro har ta juya zata zunduma cikin ɗaki da gudu, ita kuma Khadija da yake dama hankalinta baya a tattare da ita, sai bata wani tsorata sosai ba, Maman Zainab ma saura kaɗan ta zunduma da gudu izuwa cikin parlourn. Baban Zainab da Sadiq ne kawai basu tsorata ba, suna tsaye a yadda suke. Tun daga kofar gida ake surfa uban masifa, ba kowa bace face Maman Haidar, kakansu da kuma ɗayar ƴar babansu Zainab ɗin mai suna Zainab. Tun daga bakin kofar gida suke surfa uban masifa tamkar zasu tashi garin. Da sauri Mamansu Zainab ta juya da nufin ta wuce cikin parlourn abinta, dan ba zata iya masu ba. Sirikar tata ce ta daka mata tsawa a kan ta zo nan munafuka, ai wajenta suka zo, zata wani sa kai kamar wata tsohuwar munafuka zata wuce. Cikin girmamawa ta ɗagawa surukar tata gaisuwa da "Ina kwana". Cikin faɗa surukar tata ta ce. "Da ban kwana ba zaki ganni ne? Wato dama baki so na kwana a duniya ko? To na kwana na tashi, kuma ni dai nan gani nan bari, baku isa ku mallakeni ba, nafi karfinku". Shiru Khadija ta yi tana sauraron kakar tata, idan kakan nan nasu tana magana sai ka rasa ina ma ta dosa, sam maganarta babu kan gado, idan ba rashin kan gado ba yanzu me ya kawo wani zancen mallaka da kuma zancen wai Mamansu bata son kakar tasu ta kwana a duniya, daga cewa ina kwana? Abin ma abin dariya, ko me haɗin ina kwana da kuma ba'a son mutun ya kwana a duniya? Kawai jaraba ce da dole sai anyi faɗa. "Mama wai me yake faruw ne?". Cewar baban Zainab ɗin, ya yi maganar a nutse. "Rufe mun baki hai, ai yau wlh kome wannan matar taka ta yi maka ta mallakeka sai ta karya shi". "Sadiq ku je ka kai su Khadija makaranta daga nan ka ajiye mun mashin ɗin a kasuwa zan hau mashin ɗin kasuwa na je kasuwar". Cewar baban Zainab ɗin. A hanzarce Sadiq ya amsa tare da jan mashin ɗin ya fitar da ita waje, su Zainab suka rufa mashi baya da sauri. Ran Zainab kamar bakar leda saboda bakin ciki, zuciyarta sai tafasa take yi, kamar ta tsinke kakan nata da mari take ji, mata ce sai jarabar bala'i, sai ka rasa me matar nan take so a duniyar nan, kamar wadda ake sakawa battery, idan ta fara zuba bala'i ita da kanta bata sanin me take faɗa. "Mama mu je cikin parlourn koma menene sai mu tattauna a cikin nutsuwa ko?". Cewar baban Zainab ɗin dai. Ita dai maman Zainab bata da bakin magana. Cikin faɗa mamar tasa ta ce. "Kai har kana da ɗakin da zan shiga in zauna ne? Babu in da zan shiga sai wannan bakar munafukar matar taka ta gaya mun uban me ta yi maka ka lalace ka dawo mata soko sai abin da ta ce kake yi". Shi dai baban Zainab har yanzu bai gane a kan me mamar tasa take surfa wannan bala'in ba. "Maman Haidar wai me yake faruwa ne? Waye ya taɓo mama yau kuma?". Cewar baban Zainab, ya yi maganar kuma yana kallon Maman Haidar dake tsaye tana wani cika tana batsewa. "Ba gaka ga mamar ba, ai ita zaka tambaya, ni ka rai'na zaka tambaya ko?". Maman Haidar ɗin ta bashi amsa tana wani watsa mashi harara. Nisawa ya yi kafin ya mai do da kallonsa a kan ɗayar yayar tasa dake tsaye shiru tana binsu da ido. "Maman Hanif ke ki gaya mun wai meyake faruwa ne? Me aka yi wa mama? Ko me aka ce nayi?". Nisawa ita ma ta yi tare da fara magana a nutse. "Wata ce nan ta je ta gaya masu cewa wai jiya ka sayawa matarka tsadaddun lace da shaddoji da sauran kaya namu na mata, ta dai ce makwabciyarku ce ita, wai maman Zainab ta mayar da kai wani soko, kai ne kake yin sharar gida da komai da komai, maganganu dai dayawa ta gayawa mama, ni ina waje sama sama najiyosu suna tattaunawa da mama......". Katseta mamar tasu ta yi da cewa. "To karya aka yi mashi ne? Ai idan da baya yi makotansu ma ba zasu sani ba, abin da kika ga har makota sun sani ai kinsan ba karamar abu bace ba, abin ya yi yawa kenan". Dafe kansa ya yi, dan shi yasan ba wata matar da ta gaya masu, karya ne, Haidar ne ya kai masu wannan magana, dan shi ne mai kwasan duk abin da yake faruwa a cikin gidan yana gaya masu, kuma duk abin da Haidar yake yi mamarsa ta koya mashi, dan ita ce tun yana ƙaramin yaro idan ya je wajenta sai ta rinƙa tambayarsa me aka yi a gidansu Zainab ɗin, me yake faruwa a gidan, shiyasa babban kuskure ne idan yaronka ya je waje ya dawo ka rinƙa tambayarsa me aka yi a wannan gidan, ko me suka dafa da ya je, hakan ba ƙaramin mummunar dabi'a bace kake koyawa yaro. Ni kuma PRINCESS TEEMA shawarar da zan bawa mata a nan shi ne, kuskure ne ki bari wani daga cikin familyn mijinki da kike rikonsa ya rinƙa sanin halin da kuke ciki ke da mijinki, ke ko ɗan miji kike riko, kada ki yarda ki bari su rinƙa sanin me yake faruwa a gidan, ko kuma ya tukunyarki take, ace komai mijinki zai saya maki sai sun sani, ko cefenen gida sai sun san komai da yadda aka yi. Kun dai san abin da yake faruwa a gidansu Zainab ɗin nan kaf abu ne da yake faruwa sosai a cikin al'umma, amma dayawa daga cikin mata basu san daga ina matsalar take samo asali ba, na tabbata mata dayawan zasu gyara wasu abubuwa nasu a dalilin karanta labarin gidansu Zainab, dan labari ne mai cike da darusa sosai, ko ya kike da mutu kada ki bari ya san abin da mijinki yake yi maki na kyautatawa, kome zai saya maki ya zama sirrin ke da shi, kada ki nunawa kowa sai iyayenki da kannenki idan kina da su, domin duniyar yanzu wlh ta wuce tunaninki, ke zaki gayawa mutun abin alkhari da mijin yake yi maki dan ya tayaki murna da farinciki kin yi dace, baki san shi haushin ki yake ji kin sami abin da shi bai samu ba, hakan zai sa ya yi duk yadda zai yi ya shirya maki mugunta, dan tsabar bakin ciki da hasada, dan haka mata sai ku kula, maman Zainab tun farko ita ta yi kuskure, ita ta yi ganganci da ta sakewa Haidar fuska, ta kyale shi yana shigo masu har cikin ɗaki, duk abin da Baban Zainab zai yi ma matarsa da ƴaƴansa sai ya sani, kome suke ciki yana sane, a lokacin maman Zainab tana ɗaukarsa yaro, a duniyar yau wlh yara sunfi manya iya gulma da munafurci, ta yi sake ga shi yanzu abin ya kwaɓe mata ba yadda ta iya, abu ya fi karfinta, Allah dai ya kyauta ya kawo mata mafita. "Maman Hanif zaki iya gane fuskar matar?". Cewar baban Zainab ɗin, duk da zuciyarsa tana gaya mashi Haidar ne ya je ya kai masu rahoton ko ya kirasu a waya ya gaya masu cewa babansu Zainab ɗin ya dawo dasu laces and atamfofi a leda, sai dai bai isa ya nuna cewa yasan Haidar ɗin bane, dan idan ya ce shi ne to ba makawa wata ruwan bala'in ce zata sauko mashi, dan yanzu Maman Haidar ɗin zata yi tsalle ta dire ta ce ai ya zagan mata yaro, ita ma kakan ta hau kai ta zauna. Amsa maman Hanif ta bashi da cewa. "Matar sanye take da nikaf a fuskarta, ban ga face nata ba". Shiru ya sake yi yana tunanin irin wannan rayuwa, tabbas bai yarda da zancen Maman Hanif ɗin bama, ba wani bata gane wacece bace, gaya mashi gaskiyar cewa Haidar ne ya yi hakan ne ba zata yi ba, domin Haidar ɗin ne ya san cewa ya ɗauko atamfofi daga kasuwa, shi ne kuma yasan cewa ya sayo masu abubuwa na mata daga kasuwa, so dole shi ne ya kai rahoto. Kakar tasu ce ta katse mashi tunanin da yake yi cikin faɗa da cewa wlh dukka kayan nan da ya kawo ya yi maza ya kwasosu ya kawo mata dukka. Da yake zaman lafiya yake nema, sai ya ce da maman Zainab ta je ta ɗauko masu kayan, ya kudurci niyar zai kawo masu wani ba tare da sanin kowa ba, ko Sadiq ba zai bari ya sani ba bare Haidar. Da sauri Maman Zainab ta wuce cikin parlourn, sai kuka take yi hawaye bibbiyu, wannan jarabar bala'i dame ta yi kama? Kamar yadda ya kawo masu kayan a leda haka ta ɗauko ta fito masu da shi, dama can bata wani cire kayan daga ledojinsu ba, dama sun bari sai da safe ne su buɗe suga irin kayan da ya kawo masu. Tana zuwa ta duka ƙasa ta miƙawa sirikar tata. Cikin faɗa tasa hannu ta karɓa tare da cewa su Maman Haidar su wuce su tafi, sannan ta dubi baban Zainab ɗin cikin fushi ta ce maza ya sameta a gida, daga haka suka wuce fuuuu kamar wasu kumfaye suka nufi waje. Suna fita Maman Zainab ta saki wani marayar kuka tare da juyawa da sauri ta koma cikin parlourn. Bayanta baban Zainab ɗin ya bi, hakuri ya je ya rinƙa bata tare da yi mata alkawarin anjuma da rana zai kawo mata wasu kayan waɗan da suka fi wannan kyau. Cikin kuka ta ce ita ba kayan ne ya dameta ba, meyasa zasu rinƙa zaginta haka? Su zageta su zage iyayenta, laifin me ta yi masu?. Hakuri dai ya cigaba da bata, ba shi ya tafi kasuwa ba har sai da ya san ya sanyata murmushi ta cire damuwar a ranta, sannan ya fito ya nufi kasuwa, shi kuma Haidar sai zuba barci yake kamar wani gawa, duk wannan rigima da aka yi a cikin gidan sam bai sani ba, nauyin barci ke gare shi, idan ya yi barci kamar wanda ya mutu. Baban Zainab na tafiya ta rufe kofar parlourn da key ta wuce cikin bedroom nata ta haye gado domin ta ɗan yi barci, dama haka take yi, zata tashi tun asuba ta yi aiki, idan ta sallamesu suka fita sai ta kwanta ta yi barci zuwa 11, sannan ta tashi ta hau aikin girkin rana, dan karfe 2 dai'dai Sadiq zai zo ya ɗaukawa baban Zainab abinci rana zuwa kasuwa, su Khadijah kuma karfe 3 suke tashi makaranta. To bari mu waiwaya bangaren su KAMRAN, wato daji kuma muga me ake ciki tun da Maman Zainab ta yi barci. 🏞️FOREST🏞️ Tafiya Kamran yake yi cikin wannan shiga tasa dai da kuka sani, ya ratayo kwari da baka a bayansa, da alama farautar nama zai je yi, yanzu ya zama matashi, kyau da cikar haiba tare da kamala sun kara bayyana a tattare da shi, yanzu yana da 25 years, dan rabonsa da su twins yanzu shekaru 10 kenan, kirarsa na jaruman maza ya kara bayyana, Mamma ta iya reno sosai kam, cikakken jarumi ne mara tsoro, haka yake kutsa cikin wannan ƙungurmin dajin babu ko ɗar ɗar a tattare da shi. Sai tafiya yake yi Rocky yana gefensa, yanzu Rocky ma ya tsufa, ya zama wani bujumi da shi, ya kara girma sosai............. Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI. 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________10🔥 Sai tafiya yake yi Rocky yana gefensa, yanzu Rocky ma ya tsufa, ya zama wani bujumi da shi, ya kara girma sosai. Sai kutsawa cikin dajin sosai suke yi, da yake basu saba zuwa wannan yankin ba a cikin dajin, sai Rocky ya fara yi mashi alamar sun wuce dai'dai in da suke tsayawa fa, sun fara shiga wani yanki na daban, sai alama yake yi mashi ta hanyar tsayawa yaki tafiya. Sarai Kamran ɗin yasan me Rockyn yake nufi da shi, amma sai yaki kula shi, domin yau yana da burin ya tsalleke yankinsu ya shiga wani, dan shi ma dai ya kalli wannan dajin da kyau da kyau. Da dai Rocky yaga da gangan Kamran ɗin yaki kula shi, sai ya sha gabansa tare da ɗaga kai sama zai zuba wannan kukan nasu mai rikita dabbobin dake yankin. Hannu Kamran ɗin ya ɗaura mashi a saman kansa, still da wannan yare nasa dai ya yi mashi magana a kan cewa ya bari suje wasu yankuna koda guda biyu ne a cikin dajin dan suga abubuwa, wata kila akwai abin da akwai a sauran yankunan babu a nasu part ɗin, sai su ɗebo su kawowa Mamma. Girgiza jiki Rocky ya yi kafin ya wuce gaba, da sauri Kamran ɗin ya ce lallai ya dawo baya ko kuma ya dawo su jera a tare kamar yadda suka saba tafiya. Kin dawowa ya yi, sai ma cigaba da tafiya da ya yi. Shi kuwa Kamran kamar ya kifa mashi mari dan haushi, sai dai koya mare shi ma shi ne zai ji zafin hannunsa, Rocky kam babu abin da zai ji. Kamran yana matuƙar jin haushi idan suna tafiya Rocky ya wuce gaba, abin yana baƙanta mashi rai sosai, ya fi son shi ya yi gaba, a cewarsa idan Rocky ya yi gaba kenan tsaro Rockyn yake yi, shi kuma wai baya son ace ga wani yana bashi tsaro, yana ji da jarumta sosai, ya fiso ace shi ne a gaba shi ne jarumi. Cak suka tsaya a wani wani mai cike da dogayen itatuwa masu yelwar cikar ganyayyaki korayen shar, kasancewar itatuwar suna da tsawo sosai, sai cikar ganyayyakin jikinsu bai sa wajen ta yi duhu ba, sai ma hasken rana da ya bayyana ta tsakiyarsu, abin ya kawatar da mai kallo matuka, kasan wajen ya kasance farin yashi ne tamkar yashin bakin manya manyan tekuna na ruwa. Bin wajen da kallo Kamran ya fara yi, hakiƙa wajen ya yi matuƙar burgesa sosai, ga yanayin weather wajen is very very so nice, akwai yelwar ɗumi a wajen, tamkar ba a cikin dajin wajen yake ba, da yake dama dajin Allah mai girma haka ai sai abin da ka gani kawai, Allah ya yi ikonsa kala kala a ciki, duk abin da ka gani kawai ka gara jinjinawa iko da kudura ta Ubangiji. Shi kansa Rocky da yake yawace yawacensa son ransa, babu inda baya shi ga, tabbas wannan waje ta bashi mamaki kuma ta yi matuƙar burgesa. Shi dai Kamran yana zuwa bakin teku ya ɗebi wasu abubuwa daga cikin albarkatun cikin ruwa, amma bai taɓa ganin farin yashi (ƙasa) tas irin na wannan waje ba, dan wannan ya fi ƙasar bakin teku haske sosai, idan hasken rana ta haska yashin ma har wani kyalli sosai yake yi. Gabaɗaya ma yanayin tsarin wajen idan ka gani sai ka ji imaninka ya karu, domin babu ɗan adam da ya isa ya yi wannan halitta, yadda kasan a manyan wajajen buɗe idanu na duniya suke, tamkar ba'a cikin dajin ba. Duk da cewa Kamran bai san Allah ba, bai ma taɓa jin sunan Allah ba, bai san a akwai Allah ba, bai san akwai wanda yake halittar abubuwa ba, amma da ya zo wannan waje ya ji a jikinsa yana son sanin wadda yake halittar waɗan nan itatuwa da sauransu, saboda itatuwa ne irin masu bala'in tsawon nan, bai taɓa ganin irinsu a cikin wannan dajin ba, dan suna da tsawo sosai gaskiya, shi ne yasa ya ji cewa gaskiya yana son yaga waye ne yake gyara itatuwar nan haka? Waye mamallakin wannan dajin? Ya kuma kudurci niyar idan ya koma gida sai ya tambayi mamarsa, sai ya tambayeta ta gaya mashi wanene mamallakin wannan dajin? Dan a ilimin da yake da shi dai yasan abu bata kyara kanta, dole duk abin da ka gani akwai makerinta, musamman idan ya waiwaya ya dubi yadda Mammansa take kyara tukanen dafa abinci da taɓon da yake ɗebo mata, sannan ta kyara kwanikan cin abinci da katakon itatuwa da yake saro mata, hakan ce ta kara tabbatar mashi da cewa lallai komai da ka gani akwai wanda ya yi shi......... Toh fa, Kamran ya ɗauko babbar magana, kuma ya fara tunanin ta gaskiya, domin komai da ka gani a duniyar nan baya taɓa kyara kansa, masu cewa babu Allah kowaye ya halicce su?🤔 A barka da iya dutse ma kawai ka gaya mana waye ya yi ta?🤔 Ko kuma ka kawo wani ya yi ta mu gani, an dai ba zata kyara kanta ba kam, idan ka kai dubanka izuwa kan motoci da abubuwan hawa, dukkansu akwai waɗan da suka kyarasu, to sai halittun Ubangiji ne za'a ce babu wanda ya haliccesu dan kin gaskiya da son dole sai an shiga wutar jahannama?.🤔 To Allah ya kyauta ya kuma yafe mana zunubanmu ya kara ɗauramu bisa tafarkin koyarwan fiyayyen halitta. A hankali hankali kunnuwansa suka fara tsinkayo mashi sautin zubar ruwa sha tamkar ruwan sama. Dawo da kallonsa ya yi daga kallon wajen izuwa kan Rocky. Kasa kunne shiru suka yi dan su ji menene yake wannan shahhhh kamar zubar ruwan?. Karar tana ɗan nesa daga in da suke, hakan yasa Kamran ɗin ya kara gaba domin ya ga menene? Kai tsaye babu tsoro ko shakka ya nufi ta hanyar da yake jiyo wannan kara. Da sauri Rocky ya rufa mashi baya, haka suka cigaba da tafiya, sai dai a wannan karon tafiyarsu ta sauya daga ta jarumta izuwa ta mutumin daji, wato tafiyar sanɗo kenan, tamkar wadda yaga wata nama zai farauceta, saboda basu san me yake wannan kara ba, gada ya zamana sun dimfari abin gadan gadan kuma ya fi karfinsu, gara koma menene su yi mashi tafiyar mage mai kwanciyar ɗaukar rai, idan yaso in sun ga menene, sai su san abin yi. Kara matsowarsu ta in da wannan kara yake tashi ne ya bawa Kamran ɗin damar fahimtar cewa lallai ruwa ne yake zuwa daga ƙoramar dutse, duk da cewa babu irin wannan ƙoramar dutse dake zubar da ruwa a yankinsu, amma Kamran ɗin yasan da akwaita a cikin wannan dajin sosai, dan idan ya tsaya a saman ɗaya daga cikin tsaunikan dake ta kusa da su yana iya hango koraman dake kusa da yankinsu, waɗan da suke zubar da ruwa, sai dai kanana ne waɗan da suke kusa da su, ba katafare tamkar wannan da yake karan bane, su waɗan can ma ba zaka ji karar ruwan sosai ba, amma shi wannan karar ruwan tun daga nesa kunga suka fara jiyo shi, alamu sun nuna katafaren ƙorama ne sosai. Jin cewa sautin zubar ruwan korama ne yasa Kamran ɗin nufar wajen cikin takun jarumta tare da isa da ƙasaita, akwai dogayen ciyayi a gabansu waɗanda suka kare masu hangen ƙoramar daga nesa, kai tsaye ya nufi wajen ciyayin. Shi kuma Rocky wata hanya daban ya bi, dan yana jin wata iriyar kamshi a wajen wadda sam bai yarda da ita ba, kunsan su dabbobi da kamshi ko wari suke iya tantance abu yana waje ko akasin haka, musamman ma ɗan adam, da kamshin mutun suke iya fahimtar lallai akwai ɗan adam a wannan waje, so shi Rocky ya ji kamshi ne ya tafi duba menene? ROCKY BA DAI GULMA BA, WAI YA JE DUBA MENENE KAI JAMA'A 😅 Shi kuwa Kamran yana zuwa ya sa hannu ya ya ye waɗan nan dogayen ciyayi dake a wajen, nan take katafaren ƙoramar ta bayyana a idanuwnsa. Zaro dara daran idanuwan nan nasa ya yi yana mai kallon ƙoramar, katuwa ce sosai, ruwan da yake taruwa a ƙasarta ma teku ne guda, ruwan yana ganganrawa ne har izuwa cikin tapkeken tekun dake gaba da ƙoramar, sam Kamran duk yawonsa a cikin wannan daji bai taɓa sanin cewa akwai wannan tapkeken tekun ba, haka zalika bai taɓa sanin da akwai wannan tapkeken ƙoramar ba. A zahirin gaskiya kowa ya kalli Kamran a wannan hali da yake ciki da kuma irin wannan tsayuwa da ya yi zai ce wannan ƙoramar yake kallah, amma kuma sam ba ita yake kallah ba, shi kwata kwata idanuwansa ma basu sauka a kan ƙoramar ba, yana yaye ciyayyin idanuwansa suka yi wani irin kyakkyawar gani wanda bai taɓa yin irinsa ba, hakan tasa bai ma bi ta kan ƙoramar ba, kawai ya tsaya cak yana ta kare mata kallo. Macece ƴar yarinyar da bata wuce shekaru goma ba a duniya, kyakkyawar gaske ce sosai, a kallon farko ma idan ka kalleta sai ka rantse da Allah aljanace ta rikiɗe izuwa siffa mafi kyau a duniya, sanye take da kaya masu bala'in kyau sosai, ba irin kayan dajin bane, hakan yasa ta sake yin kama da aljana, domin kuwa kayan jikin nata ba kaya ne kamar sauran kayayyakin da kuka saba gani yau da kullum ba. Wata iriyar skit ce wadda daga kugunta zuwa mazaunanta ya yi mata daidai cif cif, daga dai'dai matsayar hips nata zuwa ƙasa ya yi wani irin bala'in buɗewa sosai, sai ƴar farar vest ta sama wadda ta tsaya mata a iya cibiyarta, launin skit ɗin pink color ne, yana da kyalliya sosai a jikinsa wanda kwalliyar ta mamaye ko'ina a jikin kayan, baka iya tantance ainahin yadin da aka yi amfani da shi wajen yin wannan sket ɗin, saboda yawan kwalliyar jikinta, ga kuma duwatsu masu haske da aka kawata ta da shi. Zaune take a saman wani dutse mai ɗan girma da yake a kusa da ƙoramar, ta zura kyawawan fararen kafafunta a cikin ruwan dake a gaban ƙaramar, ruwan da yake gudu izuwa cikin tekun nan kenan, ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana da wani irin bakin gashi, ya yi baki sosai har ya yi kamar dark navy blue, sai wani irin sheki yake yi, an ɗaure mata gashin kan nata ɗauri biyu, gefe da gefe, jelar gashin nata ya sauko mata har bayanta, kasancewar kanta na sunkuye sai jekar gashin ya sauko mata ta gabanta har izuwa saman kirjinta, hannunta na rike da wani sanda ɗan ƙarami tana kaɗawa, ta yi shiru kamar mai tunanin wani abin, duk da bata ɗago kanta ba, a iya fatar jikinta zaka tabbatar da kyakkyawar gaske ce, fara tas da ita, ga jikin nata mai bala'in kyau, da alama girman kayan marmari ce, kun san kayan fruits da balai'n gyarawa ɗan adam fatar jikinsa yake, daga gaban koshinta wasu kyawawan sidif ɗin kashi ne dake kwance a wajen, tana da gashi ɗan dai'dai a gefe da gefen fuskarta, gashin yana kwance luf, farar fata ga bakin gashi kwance a wajen, ya kuke ganin kyan zai kasance? Abin ba'a magana. Ga ta ƴar caras cas, babu ƙiba, jikinta mai kyau ne sosai, ƴar ɓul ɓul da ita, alamar ta ci ta ƙoshi dai amma ba ƙiba. Kamran dai ya zaro idanu yana kallon wannan kyakkyawar halittar, ya ƙasa motsawa daga in da yake, da alama ya afka wata duniyar ne, bai taɓa kallon kyakkyawar halitta irin wannan ba, Mammansa kyakkyawar mace ce sosai, amma gaskiya bata kai rabin wannan yarinyar a kyau ba, shi kansa Kamran ɗin kyakkyawa ne sosai, amma ina, wannan yarinyar kyanta na daban ne, hasken fatarta har ma ta fi Mamman Kamran ɗin haske, kun san dama Mamma ta fi Kamran haske sosai, to wannan yarinyar dai ta fi Mamman ma haske, in dai mutun ba jarumi ba, kai ko jarumi ne idan ba ya dake sosai ba idan ya yi ido biyu da wannan kyakkyawar halitta a kallon farko sai ya tsorata, bare ma ace yasan babu mutane a dajin, wlh tsab kyanta zai tsorata shi ya ce aljana ce. Amma shi Kamran ya dake sosai, dan shi fa tun da ya taso bai san menene ma tsoro ba a rayuwarsa, kuma kunsan mutun ya girma a irin wannan dajin ai dole ba zai san menene tsoro ba, this Forest no be small thing ooooo. Ya yi nisa a kallonta da yake yi bai ankara ba sai ganin Rocky ya yi a bayanta, dama idan baku manta ba shi Rocky ya yi wata hanya daban, dan ya ji kamshi ɗan adam a wajen, shi ne ya je dubawa, to yanzu ya ganta. Da gudu ya hauro saman dutsen, kuma ya hauro ne da nufin ya far mata, saboda shi Rocky idan ba Mamma da Kamran ba to baya ragawa kowa, wlh ko maharbi ya gani idan yana jin yunwa cinyewa yake yi fes abinsa, kuma dai kunsan damusa ki sabo ce, da alama zamansa da su Mamma ma ba haka kawai bane ba, amma koma dai me lokaci ne zai nuna mana. Jin diran abu a kusa da ita yasa ta ɗago kai a tsananin raza ne, ɗago kai da zata yi kuma kai tsaye kallonta sai cikin idanuwan Kamran da yake tsaye ya tsareta da idanu, dan suna saiti da juna ne. Wannan ɗagowa da ta yi yasa ta kara jefa mana Kamran namu cikin wata iriyar ruɗu tare da afkawa wani irin kogon yanayin da baki ba zai iya fassarawa ba, dan yadda kasan ita ta halicci kanta, face nata ɗan dai'dai, hancinta dai'dai da face nata, bai yi irin mummunar tsawon nan ba, ɗan dai'dai, sai olive dara daran eyes nata, farin idanun nata kuwa, fari ne tas, sai ka rantse da Allah tasa kwalli a ido, saboda yadda idanun nata suka kara fitowa sosai kamar tasa kwalli, olive green eyes ɗin nata ya fito sosai da sosai, lips nata jajir da shi, ga bakin nata ɗan karami da shi, kumatunta ɓul ɓul. Har cikin ido take kallon Kamran, ta kasa iya juyawa ta kalli damusar dake kusa da ita, da alama mayyar tsoro ce sosai yarinyar, dan daga jin numfashi Rocky dake futa da wani irin gurnani yasa har jikinta ya fara kerma sosai, nan take wani irin tsoro na wuce misali ya bayyana a saman wannan kyakkyawar fuskar tata, tsuke ɗan bakin nan nata ta yi tana mai cigaba da kallon Kamran ɗin, sai dai da alama kallon Mamaki take yi wa Kamran ɗin, da alama bata taɓa yin tunanin zata yi tozali da wata halitta ta ɗan adam irin tata a cikin wannan dajin ba, shiyasa take yi mashi kallon mamaki har haka. Wani irin numfashi mai karfi da Rocky ya saki ne yasa bata san lokacin da ta kara tsuke fuska ba, balai'n tsoron juyawa take yi su yi ido biyu da Damusa. (Amma na ce ba My people's idan kune a cikin irin wannan hali anya zaku iya juyawa ku yi ido huɗu da Rocky kuwa?😅 Ni dai zan iya amma idan na furta kalmar shahada na gama😅 dan ko ya haɗiyeni ma burina ya cika na karisawa da kalmar shahada 😅) Shi kuwa Kamran ya zubawa waɗan nan olive eyes ɗin nata idanu kawai yana ta kallo, da yake shi ya saba da Rocky, sai sam abin bai dame shi ba, a tunaninsa Rockyn ba zai yi mata komai ba, shiyasa ya kyaleta da shi, shi kuwa Rocky har ga Allah cinyeta ya yi niyar yi, dan dama yana ɗan jin yunwa. Kafin Damusa ta ci mutun, kai ba ma mutun ba, Damusa tana da wata dabi'a guda ɗaya, kafin ta ci abu sai ta waje baki tare da ɗaga kai sama, wani lokaci idan suka daga kan nasu suna yin wani irin kuka, wani lokaci kuma basu yi, amma confirm ainahin Damusa baya cin abu sai ya yi wannan abin, ɗabi'ar su ce, so shi ma Rocky hakan ya yi, ya wani wage bakin nasa gari guda, dai'dai lokacin kuma yarinyar ta yi namijin ƙoƙari wajen iya juyowa a hankali hakwaranta na garuwa da juna, saboda tsananin tsoro. Tana juyowa kuma ta yi ido biyu da garma garman hakwaran Rocky da ya buɗe baki, ga hakwaran waɗan nan biyu na sama da biyu na kasan kamar wasu kifiyoyi, suna da tsini sosai, su Damusa take kafawa a jikin wuyar dabba ko mutun, idan ta cakasu suka shi cikin namar mutun, sai su tsinka mashi jijiyar wuya da ita, haka ma idan dabba zasu kashe, shiyasa idan suna farauta zaku gansu wuya kawai suke kamawa, saboda su tsinka agarar wuyar, kunga kuwa suna tsinke agarar wuyar shikenan abu ya zama gawa. Wani irin ihu ta saki mai razana ƙwaƙwalwa, kan kace me tuni ta yanke jiki ta faɗa cikin wannan uban ruwan. Shi kuma Kamran ganin Rockyn ya buɗe bakin yasa bai san lokacin da ya nufesu da sauri yana ƙoƙarin yiwa Rockyn magana ba, sai dai bai kai ga yin magana bane yarinyar ta juya taga hakwaran Damusan, daga haka kuma sai suma. Kunsan ita fa Damusa wlh ko bata buɗe baki ba ka ganta sai zuciyarka ta tsinke, idan kana da zuciya a kusa ma sai suma ko mutuwa, saboda tsananin kwarjininsu, dole ake jin tsoronsu ko ba'a so. And one thing about Damusa, basu shiga cikin ruwa, akwai waɗan da suke shiga cikin ruwan, sai dai masu shiga cikin ruwan basu da yawa, normal Tiger daji kamar sauran dajuka basu shiga cikin ruwa, bawai ba zasu iya shiga bane, no zasu iya, kawai basu shiga ne, dan idan ruwa ta yi yawa tana tafiya dasu. A dubu ɗari Kamran ya ƙariso wajen, da gudu Rocky ya nufesa, wani irin harara ya wurgawa Rockyn kafin ya yi tsalle ya faɗa cikin ruwan shima, Rocky ya bashi haushi ba kaɗan ba. Tsayuwa a wajen Rockyn ya yi yana wani girgiza, shi a dole ransa ya ɓaci bai ci nama ba, sam bai damu da harararsa da Kamran ɗin ya yi ba, shi dai nama kawai yake tunani........😅 Da kyar da suɗin goshi Kamran ya iya ceto yarinyar nan daga cikin ruwan, amma ta sha ruwa sosai kam, Allah ma yasa bata ƙarisa faɗawa cikin ainahin tekun ba ya kamata, da ta faɗa sai wani labarin ba dai nata ba, kasancewar ruwar tana ganganrawa ne yasa Kamran ya sha bakar wahala wajen iya fitowa daga wajen, da ace ruwan yana tsaye ne to da sauki, amma tana gudu kuma ganganra, kuma kunsan ba dan ya saba da shiga cikin ruwa ya kuma iya ruwa sosai ba, ai da daga shi har ita sai sun faɗa cikin tekun nan, kuma suna faɗawa shikenan, sai dai Mamma ta rungumi sorry ta kurɓi ruwan ganye shayi, dan Kamran kam da ya tafi kenan, dan ma Allah yasa duwatsu ne a wajen sosai, ya yi ƙoƙari wajen kakkamasu har ya samu ya hauro sama daga gangarar ruwan, kuma ya yi sa'a yarinyar karama ce, bata da wani nauyi, hakan tasa ya ɗauketa a saman shoulder ɗinsa kamar ƴar baby. A bakin ƙoramar ya kwantar da ita, da gudu Rocky ya ƙariso wajen yana wani numfashi mara daɗin ji, alamar huci yake fitarwa na ransa ya ɓaci. Shinshinar yarinyar ya fara yi kamar wani tsohon maye, cikin wannan yaren nasu Kamran ɗin ya ce mashi. "Rocky ka kyaleta mana, ka sa ta faɗa cikin ruwa ma bai isheka ba sai ka zo kana wani shinshinata ko? To cinyeta zaka yi ne?". Yana magana yana ƙoƙarin haɗa hannayensa dukka biyu waje guda, dan ya danna mata cikinta ta amayar da ruwan da ta sha. Cigaba da shinshinata Rocky ɗin ya yi, ya yi kamar bai ji me Kamran ɗin ya ce ba, kunsan dama dabbobi irin wannan haka suke yi wa mutun, sai su yi ta wani shinshinasa kamar wasu mayu. Sai da Kamran ɗin ya sake yi mashi magana ne, sannan ya koma gefe guda ya kwanta yana wani zuro harshe waje yana lashe bakinsa. (Tab da Kamran bayana nan fa da yanzu Rocky ya cinye mana wannan kyakkyawar halitta...💔😭 Amma da mun yi asara😅) Daddana mata cikinta a hankali hankali ya fara yi, nan take ta fara amayar da ruwan da ta sha. Cigaba da danna mata ya yi har sai da ya tabbatar ta amayar da ruwan da ta sha tas, sannan ya zame hannunsa daga saman lallausan fatar cikin nata yana mai cigaba da kallon face nata. Shiru shiru bata farka ba, ga dai ruwan ta amayar da shi, amma bata farfaɗo ba. Ganin hakan yasa ya matso kusa da ita sosai tare da matso da kansa izuwa saitin kirjinta, kunnuwansa ya kai saitin kirjin nata, dan ya ji shin kirjinta yana harbawa ne ko dai ta mutu?. Ba shakka kirjinta yana harbawa fat, fat, fat, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ji daɗi sosai da ya ji tana raye. Zuba mata idanu kawai ya yi yana ta kallonta, ta jima sosai a haka kafin ta fara motsawa, duk kuma wannan jimawa da ta yi Kamran na tsare da kallonta, kamar zai cinyeta da ido. Kyawawan fararen kafafunta ta fara motsawa, kun san dama idan mutun ya tsorata ta dalilin haka har ya suma, to farfaɗowarsa akwai wuya, bare kuma ita da ta faɗa cikin ruwa, tana faɗawa kuma ta farfaɗo saboda ruwan da ya taɓata, ta sha ruwa ta sake suma, ai tama yi ƙoƙari da ta iya farfaɗowa a yanzu. A wani irin razane tana kurma ihu ta farfaɗo, a zabure ta miƙe zaune tana ƙoƙarin tashi ta gudu, da alama ba'a cikin hayyacinta ta farfaɗo ba, ta tsorata ne ainun. Da sauri Kamran ɗin ya rikota, dan idan ya barta zata je ta afka wani wajen ta cutu ba tare da ta sani ba, dan bata a cikin hayyacinta. Ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi, idanuwanta a rufe ruf, burinta kawai ta gudu, a tunaninta ma damusar ce ta riketa, hakan yasa ta sake zunduma ihu mai sauti, sai ƙoƙarin fusgewa take yi. Da hannu ɗaya Kamran ɗin ya riketa, amma ta kasa iya kwace kanta, ga shi taki buɗe idanun taga a hannun waye take. Cikin yaren nan nasa dai ya yi mata magana a kan ta nutsu. Sai dai ina, sam bata ji me ya ce ba, sai cigaba ma da ƙoƙarin kwatar kanta da ta yi dan ta gudu. Ganin haka yasa tunanin Mum twins ya faɗo mashi a cikin ransa, ya tuna ranar da ya fara yi wa mum twins magana da yarensa, sam bata ji, sai turanci kawai take ji, hakan yasa sai ya yi wa yarinyar ma magana da turanci a kan ta yi shiru ba Tiger bane, shi ne nan ya riketa. Jin sautin muryarsa yasa ta ɗan nutsu, sai dai ta kasa iya buɗe idanuwanta, dan tana ganin kamar idan ta buɗe idanu fa waɗan nan garma garman hakwaran Rockyn zata sake gani, hakan yasa taki yarda ta buɗe idanuwanta. Shiru Kamran ɗin ya zuba mata idanu yana ta kallonta, shi dai a duniya bai taɓa ganin kyakkyawa haka ba, bare ma fatar jikinta, a hankali ya mayar da kallonsa izuwa saman wuyarta, tana da abin da ake cewa gurun wuya, ga shi gurun wuyar tata mai balai'n kyau, bai yi irin cika sosai ɗin nan ba, ya yi dai'dai da jikinta, namar wajen ya ciko dai'dai, hakan ba kamamin kyau ya yi mata ba. Jin shirun ya yi yawa ne yasa ta fara motsa idanuwanta a hankali tana son buɗesu. Sai dai kash, tana buɗe idanun nata ta yi rashin sa'a a in da ta sake yin ido biyu da Rocky da ya iso wajen yanzu, dan ya kalli Kamran ɗin ya sankare waje guda yana ta kallon face nata ne yasa Rockyn ya kariso wajen shi ma yaga me yake kallo haka. Wani irin mahaukacin ihu ta sake zundumawa tare da fara ƙoƙarin kwace kanta daga hannunsa ta gudu. Ganin hakan yasa ya yi saurin juyar da kansa dan ya ga me ta gani daga buɗe idanuwanta ta sake ruɗe mashi haka. Gamin Rocky ne yasa ya yi ƙoƙarin gaya mata cewa ta nutsu Rocky babu abin da zai yi mata, idan ta gudu ne ma zai bita, dan zai yi tunanin ta yi wa Kamran ɗin wani abin ne ta gudu, so zai bita ya kamata ya dawo da ita wajen Kamran ɗin, rufin asirinta kawai ta nutsu. Amma ina ita ai ta kasa yarda ta nutsu, gani take tsab Rocky zai cinyeta idan ta tsaya. Da iya karfinta take ƙoƙarin kwace kanta. Ganin da gaske take yi zata kwace kanta ta gudu ne yasa Kamran ɗin ya jawota jikinsa sosai, ya riketa da kyau yana mai cigaba da ce mata ta nutsu babu abin da Rocky zai yi mata. Kankame shi ta yi tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tun da take bata taɓa kallo Tiger a wajen ba, da alama babu Damusa ko kaɗan a yankin nan nasu, kuma da alama basu shigowa wajen, dalili kuwa shi ne yashi (kasa) ta yi yawa sosai a wajen, sannan kuma akwai teku a wajen, Damusa kuma bata son waje irin haka sam, shiyasa ma basu leƙowa arear wajen, dan tekun da yake wajen ma ba irin kogin da namun dawa suke zuwa shan ruwa bane, babban teku ne wanda suke tsoron zuwa wajen, dan kar ruwa ya tafi da su. Wani irin kuka take yi wadda duk wanda ya ji sautin sai ya ji ta ratsa mashi zuciya sosai. Haka shi ma Kamran ya ji sautin wannan kukan nata tana ratsa mashi zuciya, hakan yasa ya kara rungume sosai yana mai cigaba da gaya mata ta yi shiru babu abin da Rocky zai yi mata, har da gaya mata ya yi cewa Rocky fa abokinsa ne, dan haka ta kwantar da hankalinta. Ina ta jima tana wannan kukan zuci a kusan kafin Kamran ya samu ta yi shirun da kyar, sai sauke ajiyar zuciya take yi. Sun ɗan jima a haka kafin ta ɗan ɗago kanta daga saman kirjin nasa, cikin tsananin tsoro ta ɗan ɗago idanunta tana leƙo da kai tana leƙen Rockyn, shi dai yana tsaye yana ta kallon ikon Allah. Ganin sai kallonsu Rockyn yake yi ne yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai yanzu ta yarda da zancen Kamran ɗin na cewa babu abin da Rocky zai yi mata, yanzu kam ta yarda, tun da ga shi yana tsaye shiru yana kallonsu bai cinye su ba, hakan yasa ta yi ƙoƙarin barin jikin Kamran ɗin, tana cigaba da sauke nannauyar ajiyar zuciya. Bai hanata barin jikin nasa ba, sai ma binta da kallo da ya yi, sai a yanzu da ta nutsu sosai ne kamanninta ya kara bayyana, kuma a yanzu kusa da kusa yake ganinta. Ɗan kara zaro idanuwan nasa ya yi yana kallonta sosai, ko mutuwa ya yi ya dawo ba zai taɓa mantawa da kamanin mum twins ba, domin lokaci guda matar ta yi wani irin shiga mashi cikin ransa sosai, bayan Mammarsa da kuma Rocky bai taɓa kaunar wani abin a duniya ba kamar yadda ya kaunaci mum twins da twins nata, kullum suna cikin tunaninsa. Ganin ya kara zaro mata waɗan nan fararen idanuwan nasa yana kallonta ne yasa ta ɗan tsorata, nan take tsoro ya bayyana a saman fuskarta, hakan kuma sai ya kara bayyanar mashi da kamanninta da mum twins, dan rana ta farko da ya fara kallon mum twins fuskarta a cike yake tab da tsoro, duk a firgice take, so ba zai taɓa mantawa da wannan yanayi da ya fara ganinta a ciki ba. Da sauri ta raba jikinta da nasa, a tsorace ta fara yunƙurin barin wajen. A hanzarce ya riko hannunta, da harshen turanci ya tambayeta ina mamanta da ƴar uwarta?. Ɗan zaro idanunwanta ita ma ta yi tana tunanin a ina ya san tana da mama da ƴar uwa? Waye shi ma tukun nan. Bata bashi amsa ba, sai ta yi ƙoƙarin gudu ta bar wajen, sake ta ya yi tare da miƙewa tsaye, nan take yanayin face nasa ta sauya, kome yasa hakan oho? Yana saketa ta miƙe da gudu ta nufi ta gefen ƙoramar. Da gudu Rocky ya yi yunƙurin bin bayanta, da sauri Kamran ɗin ya dakatar da shi, dama yasan in dai ta gudu Rocky zai bi bayanta ya kamota ya dawo da ita. A hanzarce Kamran ɗin ya rufa mata baya, dan yaga ina ta nufa, ita kuwa tana barin wajen nasu sai ta daina guduwar, ta fara tafiya da sauri sauri, dan kafarta babu takalma, idan ta ce zata yi gudu to tana iya taka wani abin ya ji mata ciwo, so dole ta kula sosai, ta tafi cikin nutsuwa, ta kuma lura da in da zata taka. Bata san Kamran ɗin ya biyo bayanta ba, dan a sese ya biyo ta, baya son ta gansa, yana so ne kawai yaga shin suna a tare da mamarsu ce ko dai bata a tare da su. Meyasa yake tunanin bata tare da su kuma? Hakan na nufi akwai wata a kasa kenan? Ko kuma akwai wani abin da ya sani? To mu dai namu ido kawai. Ta yi tafiya mai ɗan nisa kafin ta isa wani wajen da gabaɗaya farin yashi ne a wajen, babu ciyayi, sai bishiyoyi dake ɗan gefe gefe. Cigaba da tafiya a cikin yashin ta yi har sai da ta isa karshen yashin, ta fara shiga cikin ciyayi, sannan ta tsugunna a wajen tare da sa hannunta a cikin ciyayin ta buɗe wani waje kamar kofa da aka yi da itace, tana buɗewa ta shiga cikin wajen tare da zuro hannunta ta ja marfin ta rufe, wajen ya koma kamar ba'a taɓa buɗe shi ba. Mamaki kaɗan ne ya ɗan kama Kamran ɗin, a jikinsa yana jin duk yadda aka yi wannan ƴar mum twins ce, koma yaya ita ce ɗaya daga cikin twins, dan ga kamannin mamarsu a saman fuskarta, duk da ba wani kama sosai suke yi ba, amma tabbas wannan ƴaƴanta ne, dan jini ba wasa ba. Nan take kuma fuskarsa ta sake sauyawa, alamar damuwa da ɓacin rai ta bayyana a saman fuskar nasa, a take jikinsa kuma ta saki kamar wadda aka zarewa laka, tunanin mum twins yana jefa shi cikin mawuyacin hali, ko me dalili oho?. Ya jima a tsaye a wajen kamar wadda aka zarewa laka, jikinsa duk ya yi la'asar, da kyar ya iya motsawa daga in da yake tsaye ya nufi wajen da ta shiga ɗin, dan ya duba ita da waye a cikin?. kafin ya ƙarisa wajen bari mu leƙa KINGDOM OF POWER mu dawo. 🔥✨KINGDOM OF POWER💪👊 Zaune Gimbiya Zunaira take a saman wani haɗaɗen shinfiɗi na alfarma, tana zaune ne a wani irin waje da aka kawata shi da.......... Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581. 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI. 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 10/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________11🔥 🔥✨KINGDOM OF POWER💪👊 Zaune Gimbiya Zunaira take a saman wani haɗaɗen shinfiɗi na alfarma, tana zaune ne a wani irin waje da aka kawata shi da kyawawan kwalliya na gidan sarauta, da alama wajen hutawa ne, wajen hutawar ma da alama na wani babba daga cikin ƴan gidan ne, babba kuma wanda ake ji da shi, domin yanayin wajen sam bai yi kama da na ƙananan kwari ba, na manyan kai ne. Tulin tuffa ne a cike a cikin gwando a gabanta, kuyanga ce ta kawo mata tuffar, yau dai Hoorain baya a tare da ita, da alama yana ta wani wajen, tana nan dai cikin wannan shiga tasu ta ƴaƴan manyan sarakuna da ake ji da su, shigar yana yi mata mugun kyau sosai, kowa dai yasan kayan yara ya fi na manya kyau, to haka idan ta sa kaya sai ya fi kyau a jikinta sama da su Gimbiya Chuchu. Har wa yau dai bata sanya hular alkyabbar a kanta ba, sai dai a yau ta sanya wani kyakkyawar hula mai matukar kyan gaske a kan nata, ta rufe gashinta, ba kasafai ta cika yawan sanya ɗankwali ba, dayawan lokuta zaka ganta babu ɗankwali a kai, ta fi son shan iska ta ko'ina. A nutse ta kai hannu ta ɗauki apple guda ɗaya daga cikin kwandon Apple dake a gabanta, ta kai saitin ɗan bakinta zata gutsira. Bata ji motsin mutun ba, bata ji komai ba sai gani ta yi an kwace apple ɗin daga hannunta, bata ƙarisa kai shi bakin taba. Cikin sauri ta ɗago kanta tare da ɗago da idanunwanta sama, dan taga wanene da wannan ɗanyen aikin?. Tsaye yake a gabanta, cikin kayansu na jarumai kuma jajirtattun mayaka, kamar kullum wannan hula tasu mai kan zaki tana a kansa, tsayuwar jaruman mazan nan nasa masu jini a jikan nan dai ita yake yi a kullum, kai daga ganinsa ma bakaga wajen wasa ba, baya ɗaukar wargi. Zuba mashi ido ta yi bata ce da shi ko uppan ba, yau karo na farko da ta ji tana son kallon fuskar wannan dakaren nata. Ɗan dukar da kansa ƙasa ya yi, cikin girmamawa ya ce. "Afuwa ranki shi daɗe, ina neman izinin yin magana". Yau ya yi maganar da ɗan sauti, sau da dama idan ya yi magana na kusa da shi ma basu jin me ya faɗa, saboda a hankali yake magana, baya fitar da sauti, baya ɗaga murya. Gera ɗaya ta ɗaga mashi alamar go ahead ya yi maganarsa ba tare da ta yi magana ba. Sake ɗan risinar da kansa ƙasa ya yi alamar ya karɓi umarnin kuma ya gode. Cikin natsuwa ya fara magana words ɗinsa na fita ɗaya bayan ɗaya babu hayaniya. "Afuwa ranki shi daɗe, ban binciki tuffar bace shiyasa ban bari kin kaita bakin ki ba, Gimbiya Sarina ce ta aike ni, shiyasa ban samu damar bincikar tuffa ɗin ba har aka kawo maki". Tun da ya fara magana ta zuba mashi wayan nan dara daran idanun nata, ta kasa koda kyaftawa, yau shine rana ta farko da ta fara jin muryarsa da sauti, idan yana magana kasa kasa sosai yake yi, kullum tana tare da shi, amma bata taɓa ganin ya yi magana da kowa ba, sannan bata taɓa ganin fuskarsa ba, sakamakon wannan hular tasu ta mayaka dake rufe musu ko'ina a fuskarsu, baka ganin komai sai ido da tsagen ɗan baki, sai kofofin hanci, suma kaɗan kaɗan ne, bayan haka baka samun damar ganin komai na fuskarsu, ga kayan yakin nasu kuma da karfe aka yi shi, kunsan dai yadda kayan shahrarrun mayaka suke ai?, Amma duk cikin dakarun dake Masarautar ya fi su natsuwa, yana da hankali sosai, yana bata kulawa, gabaɗaya masu kula da su shi yafi bata kariya yadda ya dace, ko motsi ta yi sai ya matso kusa da ita dan ya ga menene, tana da tabbacin ko barci dare baya samun dama ya yi sosai, saboda ita, baya taɓa rabuwa da bakin kofar shiga arear part na King Zuhair. Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce mashi. "Ai babu komai a cikin Apple ɗin, daga ɓangaren Momma aka ɗauko mun fa, kuma Aunty Chuchu da kanta ita ta haɗa mun su a kwando, amma nagode da kulawarka a gareni". Ita ma cikin nutsuwa take magana, da alama yarinya ce mai hankalin manya. Jinjina mata kai ya yi tare da risinar da kai ya sake ɗagowa, sannan ya tsugunna a gaban kwandon Apple ɗin, dan ya duba ya tabbatar da ingancinsu, saboda ya tabbatar da aikinsa, ya tabbatar ya bata tsaro yadda ya dace. Da ido kawai ta bishi da kallo, bata ce da shi komai ba, shi ma bai sake yin magana ba har ya kammala bincikensa a kansu, sannan ya miƙe tsaye tare da komawa ɗan gefenta kaɗan ya tsaya. Ƙasa ƙasa kamar dai kullum ya ce mata zata iya cin Apple ɗin yanzu, babu wata matsala. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da dawo da kallonta a kan gwadon Apple ɗin, a kullum idan zata ci abu in dai a waje ne ba'a cikin ɗakinsu ba, to sai Hoorain ya binciki wannan abin tsab, sai ya tabbatar da ingancin wannan abin, sannan yake barinta ta ci, hakan yasa take jin daɗin kasancewa a tare da shi, yana da kula sosai, ga shi babu ruwansa da kowa da komai, in da ya sa kansa kawai yake kallah, baya ɗaga kai ya kalli wasu ma abinsa, ga namijin jarumta da kuma nutsuwa.......... Ɗa ɗaya tilo ga commander ZAFAR kenan.💪 Baki a ɗauke da sallama wata kuyanga ta shigo cikin wajen, hannunta na rike da wani kyakkyawar kuma tsadadden Apple laptop, sabuwa gal da ita. A gaban Gimbiya Zunaira ta zo ta tsugunna, cikin girmamawa ta nemi izinin yin magana. Yadda kuka san mutun mutumi haka Hoorain yake tsaye, ko kallon in da suke bai yi ba, yana tsaye kamar saƙago yana fuskantar kofar shigowa abinsa. "Mama Haulat menene yake tafe dake?". Cewar Gimbiya Zunaira ɗin. Kuyangar ta kasance babbar macece, dan zata iya kai 35 to 40 years a duniya, hakan yasa Gimbiya Zunaira take girmamata take ce mata Mama, duk cikin ƴaƴan KING ZUHAIR babu wanda yake girmamata yake ce mata mama sai Zunaira, dama na gaya maku ita tana da saukin kai da kuma girmama na gaba da ita, sam bata ɗauki duniya da zafi ba, kuma ita wannan Mama Haulat ɗin ita ce kuyanga mafi matsayi a cikin kuyangun dake yi wa Momma wato mahaifiyar Zunaira ɗin hidima, so a part ɗin su Zunaira ɗin take. "Dama ranki ya daɗe Gimbiya Momma ce ta ce na kawo maki wannan abin Yah Omar yana son ya yi magana dake". Ta kai karshen maganar tana miƙo mata laptop ɗin. Kyawawan hannayenta dukka biyu tasa ta karɓi laptop ɗin, sannan ta juyo da screen ɗinta a dai'dai saitin fuskarta. Wani kyakkyawan matashi ne yake a zaune a saman ɗaya daga cikin wasu shegun luntsuma luntsumar sofas masu bala'in kyau, zaune yake a cikin wata katafaren parlourn mafi haɗuwa da ƙawatuwa, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, kyawawan fararen halayensa ɗaya na rike da cup mai bala'in kyau, ɗayan hannun kuma yana rike da pen, sai tiriri ne yake tashi daga cikin cup ɗin, da alama abu mai zafi yake sha. Kyakkyawa ne sosai, da ka gansa babu tambaya kasan yayan Zunairar ce, dan suna kama duk da ba sosai can can ba, fari tas da shi shi ma, gashin kansa baki siɗif, ga gashin nasa ya sauko mashi har gaban goshi, da alama kuma shi yake yanke baki bakin gashin yana dai'dai tasu, shiyasa suka yi mashi kamar wadda ya kifa hula a kan nasa, yana da dara daran idanuwa kamar na King Zuhair, farin idanun nasa ya yi tas da shi, kwayar idanun nasa kuma bai yi baki sosai ba, idan ka gansa ma zata zaci brown ne ba baki ba. A shekaru ba zai wuce 15 to 16 years ba, sanye yake da puma rigar da wandon dukka farare tas, bai sanya hular kayar a kansa ba. "Yah Omar me kake yi ne?". Ta faɗa tana kallon pen ɗin hannunsa, ta yi maganar kuma cikin Dubai Arabic nata. "Koyar da gaisuwa nake yi". Ya baya amsa calmly, kamar mai ciwon baki, voice nasa yana kama da nata, ance blood is thicker than water!. "Kash na manta ne ina wuni tom?". Ta yi maganar a shagwaɓe. Cup dake hannunsa ya kai saitin bakinsa ya ɗan kurɓi abin da yake ciki kafin ya amsa mata gaisuwar tata, sannan ya ce mata. "Ina Akka?". "Tana part nata". Ta bashi amsa tana mai cigaba da kallonsa. "Ai na ɗauka kina wajenta ne". "A'a tun ɗazun na baro wajenta, amma zan je anjuma kaɗan, yawwa Yah Omar kada ka dawo fa ka jirani sai na zo mu taho a tare". Shiru ya ɗan yi mata kafin ya ce. "Kin gayawa daddy aikar da na yi maki ne?". "Laaaa wlh na manta, amma zan je na gaya mashi". Guntun hararar wasa ya wurga mata kafin ya ce. "Tun jiya fa na aikeki, Ina Omaid da Obaid?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Kila suna part ɗin Mommy, kasan yanzu basu cika zuwa part ɗin Mama ba ai". Kasancewar yasan matsalar gidan nasu sai bai tambayeta dalilin da yasa su Obaid basu zuwa part na Mama ba, sai ma ya kawar da zancen da cewa. "Yah Jawad ya tafi office ne?". "Ni ban sani ba, rabona da shi tun da safe". "Tom ki je ki gayawa daddy saƙona kin ji ko?". "To amma Yah Omar gaskiya sai anjuma zan je, yanzu fada tana da baki sosai, dan na kalli motocin dayawa sun zo". Ta yi maganar tana ɗago da kallonta izuwa kan Hoorain dake tsaye tamkar saƙago. "Ba wasu baki, uncle Abbas ne ya zo wajen daddy, ai Momma ta gaya mun, dan haka ki je ki gayawa daddy abin da na ce". Miƙewa ta yi tsaye, cikin murna tare da bayyanar ƙayatattcen murmushi a saman fuskarta ta ce. "Yah Omar da gaske uncle Abbas ne ya zo?". Jinjina mata kai ya yi alamar e. "Wayyo daɗi, yau su Aunty Sarina zasu ga daddynsu, ni ma bari na je na gansa". "Bafa ganinsa na ce ki je ki yi ba, ki je kawai ki gayawa daddy saƙona, idan kin faɗa in ya so sai ki tsaya a wajen uncle Abbas ɗin". Da okey ta amsa mashi tare da miƙewa wannan kuyangar wato mama Haulat laptop ɗin, cikin hanzari ta nufi hanyar fita daga wajen. Cikin zafin nama da taku irin na jaruman maza Hoorain ya rufa mata baya, sai murna take yi a kan zata je ta ga uncle Abbas wanda ya kasance kani ne ga mahaifinta, shi ne yake bin King Zuhair a wajen haihuwa, cikakken ɗan siyasa ne mai faɗa aji a faɗin ƙasar, yana da aure, matarsa ɗaya da ƴaƴansa huɗu, maza biyu mata biyu, familynsa suna cikin KINGDOM ɗin, shi ne dai ba mazauni ba, time to time yake zuwa, mutun ne mai kirki da son ƴan uwansa, yana matuƙar kaunar King Zuhair da ƴaƴansa, sai dai ita kuma matarsa tana so ne yazama shi ne sarki ba King Zuhair ba, shi kuma sarauta ba ita ce a gabansa ba, siyasa yake da ra'ayi, ita kuma a haukarta cewa take yi kujerar siyasa ba'a gadarta, idan ya gama wa'adin mulkinsa sauka zai yi wani ya hau, amma ta sarauta kuma fa? Ba zai sauka ba sai lokacin da ya tsufa, sannan kuma ɗansa ne zai gaji kujerar idan ya sauƙa, wannan shi ne dalilin dayasa tafi son ya mulki KINGDOM OF POWER ba wai siyasa ba. Akwai case fa my people. A can cikin gida kuwa, labari ya gama shiga ko'ina cewa uncle Abbas ya zo, sai murna kowa yake yi, dan har ga Allah gabaɗaya ƴaƴan KING ZUHAIR suna matuƙar kaunar uncle ɗin nasu, kun san kowace zuciya tana son mai kyautata mata, to shi gaskiya mutun ne mai faram faram ga jan ƴaƴan nasa a jiki, hakan yasa idan ya kawo masu ziyara sai ka ɗauka wani hamshakin biki ake yi, su yi ta murna suna farinciki. Sai shirin zuwa wajensa gabaɗaya ƴaƴan king Zuhair suke yi, Gimbiya Chuchu da ta fi kowa zaƙuwa ta gansa sai ƙoƙarin shiri take yi, yanzu ta fito daga wanka, ɗaure take da ɗankaramin towel da bai gana rufe mata cinyoyinta ba, tana rike da haɗaɗɗiyar wayarta kirar iphone 15 pro max, sai ɗaukar hoton face nata take yi. A duniya Chuchu tana kaunar hoto, ko barci ta tashi sai ta ɗauki kanta a hoto, ita bata da wata matsala a rayuwarta, bata bi da kan kowa, gata da shegen son gayu, ga bala'in son jiki, kamar mage haka take, komai da kuka sani kuyankunta suke yi mata, wanka da saka kaya ne take yi da kanta, sai sallah da cin abinci, banda haka tsabar son jikinta bata son ɗaga koda tsinke, sai dai ta cancaɗa kwalliya ta haye saman bed abinta, gimbiya Chuchu ƴa ce ga Mummy, wato uwar gida kenan, kanwar Jaruma Gimbiya Raseesa ce, sai dai ita Chuchu bata da jarumtar, sai lalaci da son jiki, bata gado ƴaƴarta da mahaifinta king Zuhair ba, raguwa ce mayyar son jiki. Sai kashewa kanta hoto take yi abinta, a ɓangaren Akka take, dan ta fi yawan zama a wajen, part na mamanta ma idan kun ganta a wajen to wani abin ta je ɗauka, kullum tana part na kakarta abinta. Hakan yasa kayayyakinta da sauran abubuwanta suka yawaita a part na kakar tata. Sai da ta ɗauki hotunanta kala kala wajen kala goma, a haka ma wai tana sauri zata je wajen uncle Abbas ne, badan haka ba da dani da ku ba zamu iya kirga hoton da ƴar tahaliƙarnan zata ɗauka ba, dan mayyar hoto ce. Wasu irin shegun tsadaddun lotions ta shafa a jikinta, tana shafawa tamkar bata son taɓa skin ɗin nata, saboda shegen son jiki, bata son wahala yarinyar nan sam, bata son abin da zai taɓa wannan kyakkyawar jikin nata. Wasu tsala tsala kaya ta ɗauko, doguwar riga ce wadda ta sha kwalliya na wuce misali, kasancewar ba wata babba bace sai bata sa breaziya ba, dan bata wuce 14 years ba a yanzu, bata saka bra, haka take tsara kwalliyarta abinta, sai dai fa da yake akwai ta da halittar jiki mai kyau, idan ka kalleta sai ka yi tsammanin 16 years take da shi, tula tulanta suna cike fam da su, ga shape sosai tana da shi. Tana ƙoƙarin zura rigar a jikinta bayan ta zuge zip ɗin kasa ne karfen bayan wuyar rigar ya maƙale mata a gashin kanta, da yake babu ɗankwali a kan nata, ta tara wannan gashin nasu na larabawar ta ɗaure a tsakiya, ta zuba jelar a bayanta, hakan yasa karfen rigar ta iya kama gashin nata. Ƙoƙarin cirewa ta fara yi, amma ina ta kasa, ga rigar ta rufe mata fuska. Sunan Gimbiya Zunaira ta fara kira, dan tasan ita ce kawai za'a samu a part na Akkar by this time around. Tana ta ƙoƙarin cire karfen tana kuma kiran sunan Zunaira. Shiru Auta bata amsa mata ba, bata ma san cewa auta kam tana fada a halin yanzu ba, tana can ta haye jikin uncle Abbas tana zuba shagwaɓa abinta. Ƙoƙarin jan rigar ta yi ta cire shi daga saka shi da ta fara yi, a tunaninta idan ta cire rigar zata iya cire karfen daga gashin kanta. Bata kai ga cire rigar ba ta ji an sanya hannu ana ƙoƙarin cire mata karfen da ya kama gashin nata, rigar ta rufe mata idanu, bata iya ganin wanene?. "Auta tun ɗazun ina ta kiran sunanki sai yanzu zaki zo ba? Da na faɗi fa? Kina ganin sai da na fara zura rigar a jikina karfen ta saƙalomin gashina, rigar ta ki wucewa ta karisa shiga jikina, ta tsaya ni baga saka riga ba ba kuma ga iya cireta ba, idan nace zan tafi izuwa wajen Akka kuma faɗuwa zan yi". Tana maganar ne ba tare da ta san wanene a wajen ba, a duk tunainta auta ce. Cire mata karfen rigar ya yi tare da karisa saukar mata da rigar a jikinta, sannan ya sanya kyawawan hannayensa yana mai ja mata zip ɗin rigar sama kafin ya kama wannan ɗan karfen da ya saƙalo mata gashin kan nata ya haɗa shi da ɗan uwansa ya mannesu, dama kamar botir suke. Da sauri ta juyo dan jin kamshin perfume nasa bai yi kama dana auta ba, bugu da kari kuma ba a amsa mata maganar da ta yi ba, da auta ce to tabbas zata amsa mata maganar tata. Tana juyowa suka yi ido huɗu da Jawad, tsayayyen namiji mai jini a jika, matashi mai 25 years a duniya, ɗa ne ga uncle Abbas, shi ne second born nasa, kyakkyawa ne sosai, ba sai na sake gaya maku ba, gabaɗaya ƴaƴan Akka wato mahaifiyar king Zuhair, ƴaƴanta kyawawane, haka zalika ma jikokinta, cikakkun larabawane jinin Modarawa, hakan yasa suke da kyau sosai kamar su suka yi kansu, sai dai wannan yafi wannan kyau, wannan kuma ya fi wannan haske, haka suke!. Ɗan kasa kaɗan ta yi da kanta tana ƴan kame kame, dan duk a tunaninta auta ce, da ta san shi ne ba zata yarda ya saka mata kayan ba, wani tunani ne ya faɗo mata cikin ranta, yanzu shikenan Yah Jawad ya kalleta daga ita sai towel? Waye ma yasan tun yaushe yake wajen? Kila tun da karfen ya riƙe mata gashi yake kalleta. Shiru ya tsaya yana kallonta ba tare da ya yi magana ba, sai ma zura hannayensa da ya yi a cikin aljihun wandon suit dake a jikinsa, da alama daga office ya fito, dan shigar zuwa wajen aiki ne a jikinsa, white suit ce mai bala'in kyau, sai white cover shoe masu bala'in tsada a kafafunsa, daga ta ciki kuma safa ce baka, kyakkyawar bakin gashin kansan nan a kwance luf, ta gaba har gaban goshinsa, ta baya kuma har bayan wuyarsa, sai sheki gashin yake yi, ha sha gyara, ga wani daddaɗar kamshin da yake zubawa. Daga Akka har marigayi King ABDUL MALIK duk suna da tsawo sosai, hakan yasa daga ƴaƴansu har jikokinsu suke da tsawo sosai, so haka shi ma Jawad yake da tsawo, ga cikar kirar karfi na lafiyayyun maza. "Yah Jawad ina wuni?". Ta faɗa murya na kerma, dan ita tsoronsa ma take ji, saboda bashi da wasa da yara, kuma bashi da yawan magana, haka zalika sam bashi da fara'a ko kaɗan, wannan dalilin yasa suke jin tsoronsa. Nisawa ya yi ba tare da ya amsa mata gaisuwar tata ba, sai cewa ya ya yi. "Meyasa baki rufe kofar ɗakin ba?". Kasa kasa ya yi maganar. Cigaba da muzurai ta yi tana wani ƴan kame kame, sam bata san lokacin da ta fara murza ƴan yatsun hannunta ba, dan bata da abin yin da ya wuce haka. "Am.... In... Dama na manta ne.... Kuma dama muna tare da auta ce, ta ce mun tana zuwa ne ta fita, shiyasa ban rufe kofar ba, dan ina tunanin zata dawo". Yadda take magana muryarta na rawa, words ɗinta suna rarrabewa, hakan zai kara tabbatar maka da ba ƙaramin tsoronsa suke ji ba, dan fa da gaske ne bashi da wasa kuma baya ɗaukar wasa. "Lafiyarki kam ko?". Ya tambaya yana mai cigaba da kallonta, ya ji ne sai famar in'ina take yi mashi a magana, sai ka ce ya ce zai zaneta ko wani abin, duk ta bi ta ruɗe mashi. "Lafiya lou". Ta bashi amsa still voice nata na kerma. "Ina zaki je haka? And ina Akka? Dan na shiga ɗakinta bata nan?". Sai a lokacin ta ɗan ɗago da dara daran idanuwanta a hankali dan ta saci kallonsa, jin bai yi mata tsawa ba, ya yi magana cikin sanyi murya, kuma bai ce ta yi laifi ba, sai hakan yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Ajiyar zuciyar da ta sauke sai da yasa shi ya ɗan kara kwanto da kansa kaɗan yana kallon face nata, ya fita tsawo sosai, so a yadda ya tsaya a gabanta ɗin baya samun damar ganin face nata da kyau, sai dai tsakiyar kyakkyawar bakin gashinta yake kallo. "Akka ni ban san in da ta yi ba, ɗazun dai na barta a cikin bedroom nata". Ta bashi amsa tana lallaɓawa a hankali tana ɗago idanunta dan ta saci kallonsa, tana son ganin yanayin face nasa. "Ke kuma nace ina zaki je haka?". Ya yi maganar yana ɗan ja baya daga kusa da ita, saboda ya sami damar ganin face nata da kyau. "Part na Mammie zan je, uncle Abbas zan je gani". Ta bashi amsa dai'dai lokacin da take ɗago idanu zata saci kallonsa. Kash bata san cewa kallon face nata shi ma yake yi ba, hakan yasa tana ɗago kai suka yi ido huɗu da shi, karaf suka kalli juna cikin ido. Da sauri ita ta yi ƙasa da nata idanun, shi kuma still dai yana kallonta bai cire idonsa ba, ga idanun nasa kamar na Akka, manya manya kamar ball. "Bani wayarki". Ya faɗa tare da ciro hannunsa guda ɗaya daga cikin aljihun wandon nasa. A hanzarce ta miƙo mashi wayar, dama tana rike da wayar idan baku manta ba. A hankali ya dawo da kallonsa a kan wayar da ta miƙo mashi. Ganin yadda hannun nata yake kerma ne yasa ya mayar da kallonsa a saman fuskarta. "Lafiya kike kuwa?". Da mamaki ɗauke a saman fuskarsa ya wurga mata wannan tambayar, dan yaga yadda hannun nata yake ta famar kerma. "Lafiya lou nake wlh Yah Jawad". Shiru bai sake magana ba, ya kai hannu ya karɓi wayar tata tare da juyawa cikin nutsuwa ya nufi waje da wayar. Yana fita ta faɗa saman katafaren bed ɗin dake a ɗakin tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, hannunta dukka biyu tasa ta dafe kirjinta dake ta faman harba mata fat, fat, fat, saboda tsoro, sai ajiyar zuciya take saukewa, tamkar wadda ta sha gudu ta ƙoshi. Ta ɗan jima a haka kafin ta furta. "Ko me kuma zaka yi da wayata Yah Jawad?". Auta ce ta shigo cikin ɗakin bakinta a ɗauke da sallama. Da sauri ta kariso ciki tare da hayewa saman bed ɗin tana faɗin. "Aunty Chuchu tashi kiji me daddy da uncle Abbas suka ce". Miƙewa zaune ta yi tana faɗin. "Rabu dani auta, kada ma ki gaya mun abin da suka ce, dan yanzu ma zuciyata a kusa take, kina gaya mun wani abin na tsoro suma zan yi, yanzun nan Yah Jawad ya fita daga cikin ɗakin nan, ba jiya Aunty Sarina ta ce ya kwace mata waya ba? To nima yau ya kwace mun tawa, sai dai ni bai mun faɗa ba, ita kuma Aunty Sarina kin ji ta ce ya yi mata faɗa sosai a kan wayar". Cikin halin nuna ko in kula Autar ta bata amsa da cewa. "To shi Yah Jawad me zai yi da wayoyinku da ya kwace?". "To ko zaki je ki tambayo mana shi ne me zai yi dasu?". Ta faɗa tana zuro kyawawan kafafunta kasan gadon, dan ta miƙe ta karisa shirinta na zuwa wajen uncle Abbas. "Kai Aunty Chuchu rufa mun asiri, ni na isa in je in ce mashi me zai yi da wayarku ne? Dama dai uncle Taheer ne ko kuma su Yah Obaid". "Saboda kin rai'na su Obaid ɗin ba?". Ƴar murmushi ta yi kafin ta ce. "Yah Obaid fa Momma ta ce shekaru biyun da suka bani ma bai cika biyu dai'dai ba, shekara ɗaya ne da wata takwas suka bani, yanzu su basu cika 13 years ba ai, ni kuma na cika 11 years". Cigaba da yin shirinta ta yi tana faɗin. "E lallai auta kin girma, wato ji kike yi kusan ɗaya kike da su ko? Wlh bari Omaid ya jiki, kin san halinsa da shegen son girma, ranar har da cewa ya yi wai ya girme ni". Dariya sosai autar ta yi, Obaid and Omaid akwai shegen son girma kamar me, sai dai kuma kash sun yi rashin sa'a sune kanana, auta kawai suka fi shekaru a gidan, amma sai su dage su ce sun fi su Chuchu shekaru. Ƙarisa shirinta tsab ta yi, sai ta fito a cikakkiyar jinin sarauta, ta ɗauko wani dankareran alkyabbarta fara tas ta ɗaura a saman doguwar rigar tata, ga rigar launinta baki ne, sai alkyabbar ta zauna sosai, ta yi kyau sosai da sosai. Feshe jikinta da daddaɗar Dubai perfume nata ta yi kafin ta fito da wani kyakkyawar tsadadden cover shoe na ƴaƴan sarakuna ta sanya a fararen kafafunta, cover shoe ɗin launin white color ne kamar alkyabbar jikinta. Hular alkyabbar ta sanya a kanta kafin ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin tana cewa auta ta zo su yafi wajen uncle Abbas. Da saurin autar ta miƙe ta rufa mata baya. Elevator suka hau zuwa kasa. Suna sauka kasa suka nufi part na uncle Abbas ɗin, part ɗin yana ɗan gefe da nasu ne. Ƴan'sanda da sojoji ne cike ta ko'ina a arear part ɗin, dan fa uncle Abbas babban ɗan siyasa ne wanda yake a matsayin vice president mai ci a yanzu, mulki a hannunsu take, kasancewar KINGDOM OF POWER tana da manyan ƙusoshin gwamnati da suka fito daga cikinta ne yasa masarautar ta kara karfin iko tare da karfin faɗa aji a duniya, dan babu wani gwamnatin da zai kawo masu wargi, dama can shi King Zuhair gwammati bata ishe shi kallo ba. Duk in da suka zo wucewa sai sojoji da ƴan'sandan sun sara masu, saboda kowa yasan su waye ne su ɗin. Kai tsaye cikin part ɗin suka nufa, kowani kofa suka je sai ɗan'sanda ya buɗe masu kofar, a haka har suka isa wajen elevator, nan ma wani ɗan'sanda ne tsaye a wajen. Shiga ciki suka yi tare da nufar hawa ta biyu abinsu, sai hira suke yi tamkar wasu taurari, ba zaka taɓa cewa ƴaƴan kishiyoyi bane su ɗin, sun haɗa kansu sosai, da yake ma dukkansu basu da matsala, basu ɗauki duniya a bakin komai ba, ba ruwansu da wani zancen ai su ƴaƴan kishiyoyi ne, iya abin da suka sani kawai shi ne ubansu ɗaya, kuma suna girmama mahaifiyar kowa daga cikinsu tamkar ita ta haifesu, su biyun nan na ce maku sun fita zakka a cikin ƴaƴan king Zuhair, suna da banbanci dasu Fanan, Sarina and bloody sosai, bama su haɗa hanya ba. Kai tsaye babbar parlourn uncle Abbas suka nufa, bai jima da dawowa daga fada ba, yana zaune a tare da Jawad suna hira, da alama saboda zuwan nasa ne ma yasa Jawad ɗin ha dawo daga office, ya zo su gaisa da mahaifin nasa su ɗan yi hira. Ita kuma Mammie wato mahaifiyarsu Jawad ɗin bata wajen, da alama tana cikin part nata. A kasa saman wata lallausan Turkey carpet suka zauna, carpet nan ta amsa sunanta, ga laushi ga kyau da tsada, naunin ash color mai duhu kalar luntsuma luntsumar sofas dake a cikin parlourn, parlourn dai ba sai na gaya maku ba, kunsan ya haɗu over, ya ji komai na more rayuwa. Jawad yana zaune a saman sofa mai zaman mutun biyu, shi kuma uncle Abbas yana zaune a saman sofa mai zaman mutun uku, babu maraba a tsakanin fuskar Jawad da ta mahaifinsa, suna kama sosai, sai dai Jawad da yake sabon jini ne ya fi uncle Abbas kyau sosai, kyansa ya fi fitowa sosai. One think about familyn marigayi King ABDUL MALIK, kusan gabaɗayansu idanuwansa mai design na kifi ne, irin idanun nan ne da zaka gansu tamkar zanen ice fish mara bindi, ga idanun nasu dara dara kuma farare tas, duk sun gado marigayi. Cikin girmamawa gimbiya Chuchu ta ɗagawa uncle Abbas gaisuwa. Wani irin fara'a ce ta bayyana mashi a saman fuskarsa. "Ku tashi ku zauna a saman sofa, a saman sofa ma ku dawo kusa da ni". Shi ne abin da ya ce dasu, mutumin kirki, su kuma yaran kirki, sun sami tarbiya sosai. Ba musu suka koma saman sofar da yake zaune a kai suka zauna. Cikin girma da arziki suka gaisa da shi, sai murmushi yake yi ya jawo auta jikinsa. Ko kallon in da suke Jawad bai yi ba, sai ma fitar da wayarsa da ya yi ya fara aikin latsawa. "Yah Jawad ina wuni." Cewar Auta. Ba tare da ya ɗago da kallonsa daga kan wayar ba ya amsa mata a takaice da lafiya. Shiru Chuchu ta ɗan yi tana tunanin ta gaishe shi ne ko dai ta yi shiru tun da yanzu ba jimawa suka gaisa. Ganin cewa auta ta gaishe shi yasa ita ma ta ce. "Yah Jawad ina wuni?". Ita ma ba tare da ya ɗago da kallonsa ba ya amsa mata da lafiya a taƙaice. Sai satar kallonsa Chuchun take yi, tana son ganin a ina ya ajiye mata wayarta ne? Me kuma zai yi da ita? And ina wayar Aunty Sarina ma da ya karɓa jiya?. Uncle Abbas ɗin ne ya katse mata tunanin da take yi ta hanyar tambayarsu ya school. Da murna suka amsa mashi da school Alhdulillah. Daga haka ya shiga tambayarsu yasu Momma da sauran abubuwa, suka kama hira dai a kan gidan da kuma familyn. Miƙewa Jawad ya yi ya fice daga cikin ɗakin ya basu waje abinsa. Nima na haɗa kayana zuwa wajen KAMRAN, wata kila kafin mu dawo sun gama hirar gari sun shiga wani sabgar. 🏞️FOREST🏞️ A hanzarce Kamran ya ƙarisa wajen da wannan yarinyar ta shiga. Da sauri Rocky ya rufa mashi baya. Yana zuwa bai yi wata wata ba ya sa hannu kamar yadda yaga ta yi shi ma ya buɗe wajen. Wayam cikin babu kowa kuma babu komai sai wani tsani mai ɗan tsawo da aka kyara shi da itace da yake a bakin ramin, shi ake takawa a sauka ciki. Babu tsoro babu komai Kamran ya afka ciki ramin abinsa, dan shi burinsa kawai ya kalli Mum twins, bai san ya yanayin wajen yake ba, bai san menene a cikin wajen ba, shi dai kawai ya afka, wannan shi ne komai ta fanjama fanjam............. 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 11/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________12🔥 Babu tsoro babu komai Kamran ya afka ciki ramin abinsa, dan shi burinsa kawai ya kalli Mum twins, bai san ya yanayin wajen yake ba, bai san menene a cikin wajen ba, shi dai kawai ya afka, wannan shi ne komai ta fanjama fanjam. Rocky ya yi ƙoƙarin shiga cikin wajen ya bisa, sai dai ina, ba zai iya wucewa ba, jikinsa ta yi girma sosai. Wani irin kuka mai haɗe da wannan irin gurnani na Tiger ba Lion ba ya saki, da alama ya ji babu daɗi ne, dan ba zai so Kamran ya shiga wani wajen da bai sani ba a cikin dajin nan, kada wani abin ya same shi, hakan yasa sai bai ji daɗi ba sam da jikinsa ta kasa wucewa. Kun san ita dabba fa a yadda kika reneta a haka zata taso maki, yanayin training ɗin da kika bata tun tana karama a haka zata kasance, to shi Kamran a gaskiya duk inda zai shiga a cikin wannan daji a tare suke shiga da Rocky, cikin kogonsu ne kawai Rocky baya iya shiga, shi ma ai kunga saboda girman jikinsa ne, so tun da suka taso haka suke da Kamran ɗin, hakan yasa a yanzu idan Kamran ya je wani wajen da shi ba zai iya shiga wajen ba, sai ya yi ta kururuwa yana kuka, ko gida ya je bai sami Kamran ɗin ba irin ya fita cirowa Mamma wani abin, to ba shakka Rockyn sai ya nemosa sun dawo a tare, kamar wasu abokai. A bakin ramin ya tsungunna tare da sa kansa a wajen ramin yana bibiyar numfashi da kuma yanayin kamshin dake wajen, ɗaya daga cikin baiwar Damusa kenan, ba dai iya tantance abu da kamshi ba kam, yanzu zata gane menene. Shi kuwa Kamran tafiya mai ɗan zurfi ya yi a cikin wannan rami, a nan ne ya fahimci e lallai hanya ce wajen, bama gida bane tukun nan, hanya ce wadda jiga jigan mutane madaka katti suka haɗa su, tun da yake a wannan daji bai taɓa ganin irin wannan hanya ba, hakan ya bashi tabbacin cewa lallai wannan hanyar hannu ne ya kyarata. To waye kenan?. Mu je dai zuwa, in dai ana tafiya komai nisan waje ai za'a cin mata, lokacin ne zai yi mana alkalanci. Cak ya ja ya tsaya a lokacin da idanuwansa suka sauka mashi a saman ginin da yake a cikin wajen bayan tafiya mai ɗan nisa da ya yi a tsakaninsa da bakin kofar shigowa ramin. Da farko idan ka shigo cikin ramin ma wlh zaka yi zaton rami ne kawai wadda ƙasa ta burma, sai ka lura da kyau zaka ga wata ƴar siririyar hanya ta wucewar mutun ɗaya a wajen, da alama koma wanene ya yi wannan gini mutun ne mai matuƙar basira, domin ya yi ginin ne ta yadda komai nacinka ba zaka taɓa sanin akwai mutane dake rayuwa a cikin wajen ba, shi ma Kamran ɗin ba dan ya riga da ya ga shigarta wajen ba, da ba zai taɓa yarda cewa da akwai mutane a cikin wajen ba, da farko ma har yaso ya koma da ya ga cikin ramin babu komai, sai daga baya ya lura da wannan ƴar hanyar da take wajen, wadda take manne da jikin gini baka iya ganinta cikin sauki, sai mai kaifin basira. Tun da yake bai taɓa ganin gini da ɗaki irin wannan ba, akwai komai a wajen, tamkar ɗakin gaske, komai da suke amfani da shi a wajen ya sha bamban dana Mamman Kamran ɗin, and then suna da ventilation sosai a wajen, wadda aka yi su tamkar da pipe na ruwa, ginin dai ya tsaru matuƙa. Zuba ma yarinyar da ta gudu ta shigo cikin wajen idanu ya yi yana kallonta, canza kayan jikinta take yi kasancewar sun jike da ruwa, ga wata kyakkyawar yarinya mai kama da ita sak kwance a saman bed, sai dai ita gashin kanta golding white ne. Abin mamaki tana kwance a saman wannan gado nasu mai kyau ba irin na Mamma ba, idanuwanta a buɗe tana fuskantar Kamran ɗin, amma kuma bata yi magana ba, ga idanuwan nata dara dara kamar na wancan yarinyar, ga su farare tas da su, kwayar idanunta kuma sak na wancan yarinyar wato olive. Ganin sai kallonsa take yi babu ko kyafta ido kuma bata yi magana ba yasa Kamran ɗin ya ɗaga mata gera guda, alamar ya aka yi ne?. Ita kuma ɗayar yarinyar sam bata san da ya shigo cikin wajen bama, sai ƙoƙarin cire kayanta take yi. Ta cire sket da rigar, ya rage daga ita sai pant, tana ƙoƙarin ciro wasu kayar daga wani waje mai kamar da wardrobe da aka yi shi da katako. Sai dube dube Kamran yake yi a cikin wajen ko zai ga mum ɗinsu, amma ina babu ko mai kama da ita a wajen. Ciro wata doguwar riga mai bala'in kyau ta yi, Kamran bai taɓa ganin kayayyakin sakawa irin haka ba, shi dai na saka kawai ya sani wadda Mammansa take saƙawa, hakan yasa ya kara kurawa kayan hannun nata idanu sosai. Ba abin da ya bashi mamaki ma face irin yadda aka kyara saman ɗakin, ta yadda ya zauna zam zam, da alama ba ƙaramin aiki aka sha ba wajen haɗa wannan waje, koma suwaye suka yi shi sun sha aiki kam babu karya, kuma sun yi namijin ƙoƙari. Zura doguwar rigar ta yi a jikinta tana faɗin. "Sweetie bari in zo ki ja mun zip na rigar nan". Ta yi maganar ne cikin harshen turanci, to su da suke daji kuma a ina suka koyo turanci? Da alama dai Mum ɗinsu ba ta a tare dasu bare ace ita ta koya masu kamar yadda Mamman Kamran ta koya mashi. Tana ƙoƙarin juyawa sai ji ta yi mutun ya ja mata zip ɗin rigar. A razane ta juyo, duk da cewa tasan ba ita kaɗai bace a cikin ɗakin amma ta razana, dalili kuwa shi ne ita sweetie bata gani, ga idanuwanta a buɗe dara dara farare tas, amma sam bata iya ganin komai, makauniya ce, kunga kuwa dole ta tsorata da jin an ja mata zip ɗin. Tana juyowa taga mutun a tsaye a bayanta, tsoro ne ainun ya bayyana a saman fuskarta, hannayenta har sun fara kerma, da alama mayyar tsoro ce sosai. "Where's your mum?". Shi ne tambayar da Kamran ɗin ya jefa mata bayan ya kammala ja mata zip ɗin rigar sama. "We don't know where she is". Ta bashi amsa muryarta a matuƙar tsorace, sai ma rawa muryar tata take yi. Hakiƙa ta kasance tana da zaƙin murya mai bala'in daɗi sosai. Sweetie dake kwance a saman bed ɗin ne ta ce. "Pretty you and who, who are you talking with?". Sweetie tana da sanyi murya mai daɗi sosai ita kuma, Pretty zaƙin murya Sweetie sanyin murya. Cike da tsoro ta kawar da kallonta daga kansa izuwa kan sweetie dake shirin ta yunƙura a yanzu zata miƙe zaune, dan ta ji ƴar uwar tata tana magana, kuma ta ji wata murya ta daban da bata taɓa ji ba ya yi magana, shi ne abin ya ɗaga mata hankali, dan ita dai tasan su biyu ne kawai a cikin wannan waje, to da waye pretty take magana? Ta tambayi kanta. Cikin hanzari ta raɓa ta gefen Kamran ɗin ta wuce izuwa kusa da sweetien tana mai gaya mata. "I don't know him, kawai nima ganinsa na yi". Ta bata amsa tare da matsowa kusa da ita sosai. Shi ma juyowa ya yi ya biyota izuwa in da suke zaune ɗin, a gefe ya zauna yana mai cigaba da tambayarsu ina Mamarsu. Sweetie ce ta ce mashi. "Who are you? And what do you want from our mum? Why are you asking where's she?". Ita ma muryarta na rawa ta yi maganar. Kankameta Pretty ta yi kamar Kamran ɗin ya ce zai rabasu ne, suka wani rungume juna. Nisawa ya yi kafin ya bata amsa da cewa. "Please tell me where's she?, I want to talk to her". Pretty ne ta karɓi zancen da cewa. "Mum isn't around, we don't know where's she, since last year ago we're looking for her, but we didn't see her". Tana magana tana kara ƙanƙame sweetie sosai. Shiru ya ɗan yi yana tunanin maganganunsu, kenan sun girma a tare da mahaifiyarsu? Last year ne suka rabu da ita? To ina take? Ya aka yi suka rabu da ita bayan kasancewarsu tsawon shekaru tara a tare?. "Who are you?". Sweetie ne ta jefa mashi wannan tambayar, wadda hakan yasa ya dawo daga cikin duniyar tunanin da ya afka. "Am Kamran, ku ba zaku sanni ba, but your mum know me well, zaku iya gaya mun ya aka yi kuka rabu da mum ɗin taku?". Da alama sweetie ita ce babba a kan pretty, domin yanayin maganarsu ne ya nuna haka, and da alama sweetien ta fi nutsuwa da sanin yakamata, gata so silent bata da hayani, Allah sarki ga laluran rashin gani. "Fita waje ta yi zata je ciro mana kayan marmari da sauran abubuwan da muke amfani da su a gidan nan yau da kullum, shi ne bata sake dawowa ba, mun nemeta har mun gaji bamu ganta ba". Cewar sweetie. Ta kuma kai karshen maganar idanuwanta a cike tab da kwallah. Da sauri Pretty ta ɗago tare da ɗan raba jikinsu daga ƙanƙame juna da suka yi, murya cike da damuwa ta ce "Sweetie don't cry please, kin san mum ta hanaki kuka ko? Idan kika yi kuka idanunki ba zasu taɓa warkewa ki fara gani ba". Ta yi maganar kamar zata yi kukan ita na. Da mamaki ɗauke a saman fuskarsa yake kallon su, ya kasa gane me suke faɗa ma, dan duk hankalinsa ya karkata ya koma tunanin mum ɗin tasu, ina ta je tsawon shekara ɗaya haka ta barsu? Duk soyayyar uwa da ƴaƴan tan nan dai ta tafi ta barsu? Abin da mamaki. Pretty ne ta katse mashi tunanin da yake yi da cewa. "Mum ɗin mu ta ce akwai wani da ya taɓa taimaka mata a lokacin da ta haifemu a cikin wannan dajin, mun sha nemansa sosai bamu gansa ba, ko zaka taya mu nemansa? Dan mum ta ce mu nemesa ko bayan babu ita". Ƙasa da kansa kaɗan ya yi yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, koba komai ya ji daɗi da ya kasance mamansu bata manta da shi ba, har ma ta gayawa ƴaƴanta su neme shi, ya ji daɗin hakan sosai. "Kin san kamanin wanda ya taimaketa ɗin ne?". Ya tambaya yana ɗago da kallonsa a kanta. Da sauri ta girgiza mashi kanta alamar a'a bata sani ba, har yanzu gashin kanta akwai danshin ruwa sosai, hakan yasa ya mammanemata a wuyarta har izuwa bayanta, dan bai bushe ba. "Tom shikenan zamu nemo mutumin kin ji? Amma yanzu faɗa mun me ya sami Sweetie a ido da yasa bata gani?". "Wani itaciya mai guba ta je ta taɓa a lokacin tun muna da 7 years a duniya, da ta taɓa kuma sai furen itaciyar ya zuba mata a cikin idanunta, hakan shi ne yasa ta dai'na gani, mum tasha kuka sosai a lokacin da ta dai'na ganin". Nisawa ya yi, ko ba'a gaya mashi wace itaciya bace yasan wacce ce, muguwar guba ne da itaciyar, har kurumta mutun tana yi, tana kisa sosai, dan yadda kuka san poison haka take, ba'a cika samunta a kananan dajuka ba, sai a manya manyan irin wannan dajin, bata da yawa sosai itaciyar, tana nan tamkar itaciyar dalbejiya, sai dai jikinta ma yana yin wani irin farin abu kamar kumfa, gabaɗaya jikin itace a mamaye yake da wannan abu kamar kumfar fari kal, a yankin Arewacin duniya suna kiranta silent killer, anfi samunta ta gefensu kuma, irinsu wani ɓangare daga cikin Asiya, irinsu noth korea duk sun shiga ciki, north Korea dama kunsan yana ta East asia ne, da irinsu Canada, Greenland, Mexico, Central America, Bahamas da dai sauransu, anfi samun irin itaciyar ta wajajen. Shiru dukkansu suka yi, kowannensu da abin da yake tunani, can Kamran ya katse masu shirun da cewa. "Wanenen ya gyara maku wannan ɗakin?". Sweetie ce ta amsa mashi da cewa. "We don't know them, mum ɗinmu ce kawai ta sansu, da ita kawai suke yin magana idan suka zo, and suna zuwa su kawo mana abubuwa irinsu kayan sakawa da kuma abinci da sauransu, su ne suka gyara mana ɗaki, amma tun da mum ta tafi suma basu sake zuwa ba, so only me and pretty ne kawai muke rayuwarmu a yanzu". Shiru ya ɗan yi yana tunanin ranar da ya fitar da mum ɗin tasu daga cikin wannan ramin, da Mamma ta kira sa ya je, kafin ya dawo ya samu an gyara yaran da Mamar tasu, abin ya bashi mamaki, ashe ga wani abin mamakin ma a nan, to wanenen wannan da yake taimaka masu ɗin kuma? Su waye suma tukun nan?. Ganin ya yi shiru ya lula duniyar tunani ne yasa pretty ta ce."Zamu je mu nemo mutumin ne yanzu? Dan mum ta ce lallai mu nemo shi ko da bata nan, wai da shi kaɗai ta yarda a dajin nan". Zuba nata idanu ya yi yana kallon ɗan bakin nan nata, ba abin da ya faɗo mashi a cikin ransa face ranar da aka haifesu da ta rinƙa kuka kamar wadda ake zanewa, bai san lokacin da gajeran murmushi ta bayyana a saman fuskarsa ba, yanzu ta girma an dai'na kuka. "Sai gobe zanzo muje neman mutumin a cikin daji, yanzu dai zan je gida, idan shirun ya yi yawa Mamma zata nemeni, amma anjuma zan dawo na sake duba ku?". Da alama baya son gaya masu shi ne wanda suke nema, kome dalilinsa oho, suma kuma ko me dalilinsu na nemansa oho. "To zamu jiraka, amma dai ita Sweetie bata fita waje fa, dan kaga bata gani, kada ta je ta ji ciwo, so ita a nan zamu barta". Cewar pretty kenan, ta bashi amsa. Girgiza kai ya yi yana faɗin. "A'a dole yanzu zata rinƙa fita waje, saboda idan bata fita tana ganin hasken rana da sauransu, to idanun nata kara lalacewa zasu yi". Jinjina kai dukkansu biyu suka yi, alamar sun yarda da zancensa, sun yarda Sweetie zata rinƙa fita waje ita ma, ba kullum ta yi ta zama waje ɗaya ba. Miƙewa tsaye Kamran ɗin ya yi, jikinsa duk a mace, duk ya yi sanyi, kamar an zare mashi laka, sai dai a cikin ransa ya kudurci niyar kula da twins ɗin nan tamkar yadda zai kula da kansa, kuma ya kudurci niyar neman mum ɗin ta su ko tana a cikin wannan dajin ne, ko wani dabba ne ya cinye ta? Yara bayin Allah gwanin ban tausayi. Nufar hanyar fita daga wajen ya yi. Da ido Pretty ta bishi da kallo. Sai da ya tafi ya ɗan yi nisa, sannan ya ɗan juyo da kallonsa a kansu, har lokacin ita ma Pretty shi take kallah. Sai da ya ji tsikar jikinta ta tashi wannan haɗa idon da suka yi, shi idanun nata ma suna sanya shi faduwar gaba, idanun ne kamar ta sanya masu kwalli, ga su dara dara farare tas, olive ɗin kuma ya fito kalarsa sosai, sai hakan yana sanya ya rinƙa jin faɗuwar gaba, bare ma idan ta kafe shi da su, duk sai ya nemi nutsuwarsa ya rasa, sai ya fara wasu ƴan kame kame kamar wani mara gaskiya, sai ka ce ba jarumi Kamran ba, kaifi ne da idanun nata da idan ta tsare mutun da shi sai jikinsa ta amsa. Ganin sai kallonsa take yi babu ko kyaftawa ne yasa ya ce mata lafiya?. Girgiza mashi kai ta yi alamar babu komai. Shiru ya ɗan yi yana jin kamar kada ya tafi ya barsu a wajen, sai dai kuma babu yadda ya iya, ko zai mutu Mamma ba zata karɓesu ba, ai da ba abin da zai hana bai ɗaukesu daga wajen nan ba, har cikin ransa yake matuƙar kaunarsu kun sani, sai dai hakuri kawai zai yi, dan ba yadda ya iya da Mamma, bawan Allah baruwansa da hayaniya. Mamma kuma babu sauki lamarinta. "Pretty why are looking at me like that?". Ya faɗa shi ma yana cigaba da kallon face nata, sai dai ya kawar da kallonsa daga ganin cikin kwayar idanunta, dan shi dai har ga Allah idanun nata suna rikita shi bawan Allah, shi ne yasa baya iya kallonsu sosai, ga su kuma da shegen kyau, duk wanda ya kallesu zai so ya sake kallah, amma shi Kamran ina, yana son kallo amma rashin kallonsu ɗin ya fi mashi alkhari. Babu komai ta bashi amsa, sannan ta ɗan kawar da kallonta daga kansa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da tafiya yana aikin tunani a kan wanda yake zuwa taimaka masu a lokacin da mum ɗin take nan, to meyasa yanzu da mum ɗinsu bata nan ya dai'na kawo masu agaji? Ai a yanzu ne ma ya kamata koma wanenen ya rinƙa kawowa yaran ɗauki, yanzu ne suke da buƙatar taimako tun da mum ɗinsu bata nan, amma kuma sai a ɗauke masu tallafi, kenan dan mum ɗinsu dama ake yin hakan? To wai ina mum ɗin? And meyasa daga ɓatarta masu taimaka masun ma suka ɓata? Wannan abin da ɗaure kai yake, su dai warriors da suka biyota a farko alamu sun nuna ba ita suke da buƙata ba, abin da yake cikin cikinta suke da buƙata, hakan yana nufin twin's ɗin zasu ɗauka idan ma ɗauka ne ba mum ɗinsu ba, wai me yake faruwa ne?!!!!. Yana juyawa ya cigaba da tafiya ita kuma ta dawo da kallonta a kansa, cigaba da kallonsa ta yi har ya kai dai'dai kwanar da zai ɓacewa ganinsu, hakan yasa shi ma ya sake juyowa a karo na biyu domin ya yi masu kallon bye bye. Ganin ya juyo yasa ta kawar da kallonta daga kansa, ta sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da ƴan ƴatsun hannunta. Ita dai Sweetie da yake bata iya ganin komai, sai ta yi shiru abinta babu ruwanta. Ya ɗauki a kallah two mins yana kallonta kafin ya sa kai ya wuce. Kafin ta ɗago kai ta yi mashi kallon karshe har ya wuce ya bar wajen. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta dawo da kallonta a kan Sweetie dake fuskantar hanyar shigowa, sai dai baiwar Allah bata iya ganin komai, abin gwanin ban tausayi. "Sweetie ki koma ki yi kwanciyarki, mutumin ya tafi ai, ni kuma bari na yayyaka mana irin gayyakin da mum take yanka mana ɗin nan". Ta yi maganar tana mai taimaka wa ƴar uwar tata dan ta kwanta. Duk wani abin da yake cikin ɗakin nan nasu daga cikin gari aka kawo masu shi, waɗan nan masu taimaka masun ne suka kawo komai, amma sun kasa iya ɗaukarsu su fitar da su daga cikin wannan dokar dajin, sai dai su kawo masu taimako a cikinta su kuma tafi su barsu a cikinta, abin da abin mamaki da kuma ɗaure kai!. Kamran kuwa, yana fitowa Rocky ya yi maza ya miƙe yana shinshinarsa, wucewa gaba ya yi ba tare da ya bi ta kan Rockyn ba, dan yanzu baya a cikin natsuwarsa sosai, ƙwaƙwalwarsa cike take tab da tarin tambayoyi game da tunani, ya saka wancan ya kwance wancan, ya rasa amsar da zata gamsar da shi, ya rasa amsar da zata sanya mashi nutsuwa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga ruɗani sosai a kan al'amarin twins ɗin nan da mum ɗinsu. Da kyar ya iya farautowa Mamma namar da ta aike shi, jikinsa duk babu kwari, a mace yake. Yau nama ɗaya ma ya kama, kuma akuyar daji ce ya kama, a saman bayan Rocky ya ɗaurata, dan shi yau baya da kuzarin iya ɗaukar abu mai nauyi. A haka suka isa wajen tsauninsu, Rocky ne ya fara hayewa dan ya je ya sauke wannan akuyar dajin dake a saman bayarsa. Shi kuma Kamran ɗin yana ƙoƙarin hawa ya ji alamar motsi ta bayan tsaunin nasu. Shiru ya kasa kunne yana son ya ji motsin menene?. Tabbas akwai motsin dake fita da sauti kaɗan kaɗan, sai dai bai iya tantace motsin menene bane, hakan yasa ya fasa hawrawa saman tsaunin, sai ya nufi wajen da yake ɗan jiyo motsin dan ya duba. Kai tsaye ya nufi wajen, bai yi tunanin komai ba, dan a cewarsa ai motsin babu sauti sosai, dan haka koma menene a wajen ƙaramin alhaki ne. Sai dai kash ya yi tunani mara kyau a wanna gaɓar, dan kuma yana dimfarar wajen wasu jiga jigan zataran warriors ne guda huɗu a wajen, suna tsastsaye kamar wasu zakuna, duk sun sauƙa daga saman dawakansu, ɗaya daga cikinsu yana gyara wukar takobin dake a ƙugunsa, ɗaya daga cikinsu kuma yana ɗaure takalmar dake a kafafunsa da kyau da kyau, biyun kuma suna tsaye suna bin dajin da kallo, sun rike linzaman dawakan nasu. Ba halin Kamran ya koma da baya, dan ya riga da ya dimfarosu gadan gadan, bai yi tunanin mutane bane a wajen, sun kuma rigada sun gan shi, ba halin ja da baya. Hakan yasa ya tsaya cak a in da yake ɗin yana binsu da kallo. Cikin zafin nama biyu daga cikin warriors ɗin suka nufesa tare da zare takubansu, kamar waɗan da suke jiran shi dama, yadda kuka san dama suna jiran kiris ne su farwa duk wanda suka samu. Shi kuwa Kamran ko alamar tsoronsu babu a idanuwansa, ganin kananan kwari ma yake yi masu, kada ku manta renon Mamma ne shi ɗin. Suna zuwa basu yi wata wata ba suka yi yunkurin sare mashi wuya dan zalunci, sai kace ya yi masu wani laifi. Ai kuwa shi ma bai yi kasa a gwiwa ba wajen ƙoƙarin kare kansa, nan take faɗa ya kaure a tsakaninsu mai munin gaske, dan ƙoƙarin kashe shi suka so yi, shi ma ya fito da nasa wukar dake a ƙugunsa ya fara ƙoƙarin kare kansa da ita. Da yake shi ma ya san dabarun faɗa, yasan cewa faɗa ba karfi ake sakawa ba a cinma nasara, dabara ce kawai da zaka yi wajen ganin ka kai abokin faɗan naka ƙasa, sai Allah ya taimakesa ya kashe ɗaya daga cikinsu da wannan ƴar karamar wuƙa da take a kugun nasa, saboda shi ma yasan dabarun yaki ba kaɗan ba. Amma fa duk da haka yasha wahala kafin ya kashe ɗayan nasu, domin kuwa suma ba ƙananan kwari kamar yadda yake tunani bane, suna da karfi, kuma a matsayinsu na warriors kuma kunsan ai dole su san dabarun yaki, dan tsayayyen namiji ne shi ɗin yasa ma ya iya samun damar kashe ɗayansu, bugu da kari kuma bai tsokane su ba, bai shiga hanyarsu ba, kawai su suka kawo mashi farmaki, shiyasa Allah ya taimakesa a faɗar. Kashe ɗayansu da ya yi ne ya kara harzuwaƙasu, gadan gadan suka nufe shi gabaɗayansu, bawan Allah bai yi masu komai ba saboda shegen zalunci sun farmakesa, a wajen kare kansa ya kashe ɗaya kuma sun sake harzuƙa sun yi kansa da nufin kashesa, a cewarsu wannan ƙaramin kwaron har ya isa ya yi wani yunkuri a gabansu, basu san cewa giwa yake mai tafiyar ƙasaita ba, basu san cewa shi ne king of this Forest ba, basu san cewa shi ɗin gayyace mai zaman kansa ba, guru ne renon zakanya Mammarsa!!. Faɗa suka fara yi cikin tsantsar kwarewa da nuna fifiko a tsakaninsu, su uku bawan Allah shi kaɗai. Cikin ikon Allah, Allah ya bashi iko ya sake kashe mutun ɗaya daga cikinsu, hakan yasa suka fusata sosai, a harzuƙe suka yi kansa a in da suka damƙe shi, ɗaya daga cikinsu ne ya damƙe shi tare da yin baya da hannayensa, suka murɗe mashi hannayensa dukka biyu baya, hakan yasa dole ya nutsu, amma sai tafasa zuciyarsa take yi mashi, kunsan dama Kamran ba dai zuciya ba, akwai ta kam na kin karawa. Ɗayan ne ya matso kusa da su tare da ɗaga takobinsa zai cirewa Kamran ɗin wuya, shi kuma ɗayan yana rike da shi gam ya murɗe mashi hannu ta baya, sai haki suke ta yi tamkar waɗan da suka sha gudu suka ƙoshi, ba karamar wahala suka sha ba wajen samun damar kama shi, dan Kamran fa ba baya ba wajen faɗa, idan ka taɓo shi tab kafin a iya kwantar da tarzomar faɗarsa sai an shirya. Wani irin haniniya da dawakansu suka fara yi suna ƙoƙarin guduwa ne yasa warrior da ya ɗaga wuƙa zai cirewa Kamran ɗin wuya ya dakata, a dubu suka juyo da kallonsu izuwa kan dawakan nasu, domin suga menene yasasu irin wannan haniniya suna ƙoƙarin watsewa su bar wajen?. Wayam basu ga komai ba, sai dai basu ankaraba kuma suka ga gabaɗaya dawakan su watse da gudu kowanne ya yi ta kansa. A zabure warriors ɗin suka fara waige waige suna neman menene dawakan nasu suka gani da yasa su suka yi irin wannan watsewa haka? Ko dai maciji suka gani ne? Kunsan doki bata shiri da maciji ko kaɗan, basu haɗa hanya. Suna tsaka da wannan waige waige nasu basu ankara ba kamar daga sama Rocky ya faɗo gabansu yana wani irin numfashi mai rikitarwa. Ai wannan warrior da ya rike Kamran ɗin bai san lokacin da ya sake shi a dubu ɗari ba, shi ma wanda ya zaro takobi zai cire mashi wuya bai san lokacin da ya yi wata uwar ja da baya ba. Damuwa akwai kwarjinin bala'i, komai jarumtarka idan ka ganta sai ka ji fitsari na ƙoƙarin zubo maka, yo ka yi haɗuwar mutunci da damusa ma ya ka kare da bugawar zuciya da sauri da sauri, bare kuma ace ka yi haɗuwar rashin mutunci da ita? Ai shikenan faɗuwar gaba da bugawar zuciya ce ma kawai zata kasheka har lahira, kun san Damusa ta fi Zaki faɗa sosai, shi Zaki yana da hakuri, ba kasafai ya cika faɗa ba, sai zuciyar bala'i ke gare shi, amma ita Damusa, habawa ai koba tsokaneta ba wlh ta ganka sai ta farma, zaka iya tsokanar Zaki ya hakura kamar bai ganka ba, amma Damusa tab hmmmm ba'a magana. Wani irin tsalle Rocky ya daka kan kace me ya kafawa ɗaya daga cikin mayakan waɗan nan garma garman hakwaran nasa a wuya, sai jini, tuni ya tsinke agarar wuyar. Ai a dubu ɗari ɗayan ya fasa cikin dajin da masifar gudu yana kurma ihu. Gudu biyu Rocky ya yi ya capkosa, dama ina za'a haɗa gudun mai kafa biyu da kuma mai kafa huɗu? Ai ba zasu haɗu ba sam. Nan take Rocky ya kashesu dukkansu biyu, ya samu nama, ya maye gurbin namar Pretty da Kamran ya hana shi ci. Duk wannan faɗar da suke yi fa Mamma tana tsaye a sama nauninsu tana kallonsu, sam abin bai yi mata daɗi ba, bata so Rockyn ya kwaci Kamran ɗin daga hannunsu ba, tafi son Kamran ɗin ya kwaci kansa gabaɗaya, dan a tunaninta irin horon da ta bashi ya ci ace zai iya kashe warriors ire iren waɗan nan har guda 20 ba tare da ya gaji ko ya nuna sarewa ba, a tunaninta a irin horon da ta bashi waɗan nan mayaƙa kananan kwari ne a gabansa, sai kuma ta ga kash da sauran aiki a gabanta, ba yadda take tunani bane, dole sai ta sake ɗaura ɗamara sosai in har tana son Kamran ya kai matsayin da take kai shi ɗin nan. MAMMA LAMARINKI BABU SAUKI🤦 LAMARINKI ABIN DUBAWA NE, YANZU INA LAIFI A NAN? AI YA KWACI KAN NASA KO? YA KASHE ZARATAR MAYAƘA DA AKA SHA DAMAWA DA SU A FAGEN YAKI YA KASHE HAR MUTUN BIYU AMMA A HAKA KICE BAI YI ƘOƘARI BA?🤔 YA MAMMA TAKE SON KAMRAN YA KASANCE KENAN?🤔 Nufar saman tsaunin Kamran ɗin ya yi yana mayar da numfashi, ya baro Rocky yana cin nama, yau dai sallar Rocky, namomi baja baja abinsa, yo me yafi ransa? Ai yau shar zuciyarsa, Rockyn mu na amana.........😅 Dawakan warriors ɗin kuma sun watse sun bazama cikin daji, sun yi ta kansu kenan. Ganin Mammarsa tana tsaye tana kallonsu ne yasa ya bita da kallon mamaki. "Mamma what are you doing here?". Ya faɗa yana mai cigaba da mayar da numfashi. "Yanzu Kamran waɗan nan ƙananan kwarin ne ba zaka iya kashesu ba har sai da Rocky ya taimaka maka?". Yadda ta yi maganar zaka fahimci tabbas ranta ya sosu sosai da rashin kashesu gabaɗaya da Kamran ɗin ya yi. "Mamma me zai hanani iya kashesu? Ai goma irinsu ma zan iya faɗa da su, kina tunanin zan bari su kashe ni ne? Ai ba zan tsaya ba, kawai dai shi Rocky shi ya yi shigar faɗar shigar sauri, kuma kinsan ba wanda ya isa ya hana shi shigar mun faɗa ko? Ba dan haka ba da kai'na zan gama da su". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi wajen da Rockyn ya yardar mashi da akuyar dajin da ya kamo. Juyawa Mamma ta yi ta nufi cikin ƙogon nasu, tabbas ta yarda da zancen ɗan nata da yake cewa zai iya kashesu, dan ita tasan ba horon wasa ta bashi ba, tun yana ɗan shekara uku a duniya ta fara koya mashi faɗa, tana da burin taga ya zama shahararren guru, bujumin Zaki, Barde tsayayyen jan wuya wanda jarumtarsa zata gigita duk wani halitta mai rai, wannan dalili yasa ta tsaya tsayin daga a kansa babu wasa. Aikin gyarawa Mammar tasa namar ya fara yi, yana feɗe fatar akuyar kamar yadda ya saba yi mata idan ya kawo namar, shi yake gyarawa ya yanka gunduwa gunduwa, sannan ya kai mata wajen madafanta ta ƙarisa sauran aikin. Sai dai yana yin aiki zuciyarsa gabaɗaya yana wajen tunanin su pretty, burinsa kawai yanzu ya gama taya Mamma iya abubuwan da zai tayata, ya yi wanka ya je wajensu, shi ko tunanin cin abinci ma bayayi, so bai sanya abinci a lissafinsa ba, shi dai ya gamawa Mamma aiki ya yi wanka ya nufi wajensu kawai. Bawan Allah ba, baruwansa da rigingimun duniya, kamar wani Musulmin kwarai. Ni kuma kafin nan bari na leƙa gidansu Khadija, kafin mu dawo kila Kamran ya gama gyaran nama ya yi wanka, sai mu bishi wajensu pretty a karo na biyu mu ga me ake ciki.🤨🧐 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 🔥GIDANSU KHADIJAH💔🥲 Misalin karfe biyuna rana dai'dai baban Zainab ya dawo gidan, kamar yadda ya yi mata alkawarin kawo mata wasu kayan haka ya dawo mata da su, sai dai kuma da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan cewa yana cikin tsananin damuwa da tashin hankali, da alama haɗuwarsa da mahaifiyar tasa sam bata yi mashi daɗi ba. Ganinsa a haka yasa Maman Zainab tasha jinin jikinta, dan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayi ba......... 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 12/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ For information 0816139058 Whatsapp me only!!. E____________13🔥 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 🔥GIDANSU KHADIJAH💔🥲 Ganinsa a haka yasa Maman Zainab tasha jinin jikinta, dan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayi ba. Kamar ko yaushe sannu da dawowa ta yi mashi kafin ta karɓi kayan hannunsa, bata jima da kammala girki ba, fitowarta daga wanka kenan, ko kaya bata sanya ba, towel ne a jikinta sai ta sanya hijabi jin cewa ana buga kofar gida, sai ta je ta buɗe kofar. A parlourn ya zauna yana mayar da numfashi, kamar wanda ya yi gudu, duk ransa a matuƙar jagule yake. "Ina Haidar yake maman Zainab?". Shi ne tambayar da ya fara jefa mata. Shiru ta ɗan yi tana mamaki, domin ita ko in da Haidar ɗin yake ma bata sani ba, time da ya bar gidan tana barci, a tunaninta ai baya zuwa ko'ina sai kasuwa ko wajen mamansa, bata san Haidar kam kasuwar ma sai ya yi ra'ayi yake zuwa ba. "Haidar ya fita, kuma ina barci time da ya fita, so na ɗauka ai yana kasuwa". Shiru ya ɗan yi mata na a kallah tsawon good 5 mins, sannan ya nisa kafin ya ce. "Jeki gama shirinki kizo mu yi magana kafin su Khadija su dawo daga school, dan naga lokacin dawowarsu ya kusa, yanzu ba jimawa Sadiq zai je ɗauko su". Cikin nutsuwa ta amsa mashi da to, sannan ta miƙe ta nufi cikin bedroom tare da kayan da ya shigo da su, shi kuma ya kishingiɗa a saman sofa tare da miƙe ƙafafunsa ya ɗaura hannu guda a saman idanuwansa kafin ya lumshesu. Cikin ƙanƙanin lokaci Maman Zainab ta kammala shirinta, yau ko make up bata tsaya yi ba, saboda saurin da take yi ta ƙariso wajensa, dan ya ce magana zasu yi, so bata wani ɓata lokaci ba ta shirya ta fito. A saman kujerar dake kusa da wanda yake kwance ta zauna, cikin nutsuwa dai ta ce mashi gata nan ta fito. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe zaune daga kishingiɗar da ya yi tare da gyara zamansa da kyau da kyau ta yadda yana fuskantarta. "Fitana daga gidan nan da safe wajen Mama naje kafin na wuce kasuwa kamar yadda ta buƙata kafin ta bar gidan nan da safen". Kara nutsuwa Maman Zainab ɗin ta yi tare da tattara mashi dukkannin hankalinta a waje guda, dan ta saurare shi da kyau ta kuma fahimce shi. Cigaba da yin maganarsa ya yi shima cikin nutsuwa tare da tattara mata hankalinsa a waje guda. "Na je mun yi magana da ita ko kuma nace maki tayi maganarta bisa bani umarni da zaɓi guda biyu, a ciki dole na zaɓi guda ɗaya...." Cikin zaƙuwa ta katse shi da tambayar wacce irin zaɓi ne ta bashi umarni a kai haka?. Ɗan nisawa ya yi kafin ya ce. "Na farko ta ce mun ko na sake ki na auro wadda take kaunarsu, ko waye ya ce masu ke baki kaunarsu? Na yi ƙoƙarin gaya mata duk wadda zan auro ba zata taɓa kaunarsu kamar yadda ke kike kaunarsu ba, amma bata saurareni ba, kuma kema kin san dama ba zata saurareni ba, and zaɓi na biyu kuma shi ne, idan bana son rabuwa dake ba zata takura mana ba, amma nan da one month na zaɓi yarinya a cikin family na aura, a tunanin mama aure a cikin family shi ne zai sa na auri mai kaunarsu kamar yadda suke faɗa ɗin, na yi ƙoƙarin gaya mata ni bana da buƙatar mata biyu, dan ina da abin da nake son ginawa familyna wanda ko yau na mutu ba zasu wahala ba kuma ba zasu walaƙanta ba, amma ta zage sam sai na kara auren ko naki ko na so, and lastly ta ce a tare za mu koma sabon gidanmu da ita, sannan da amarya!". Babbar magana!!. Ya kai karshen maganar yana kawar da kallonsa daga saman fuskarta, saboda baya ma son yaga halin da zata shiga, ya sani idan akwai abin da maman Zainab ta yi wa muguwar tsana a duniya to bai kai tsanar kishi da ta yi ba, sam bata son jin batun kishiya, saboda gani take yi kamar kishiyar zata rabata da mijinta da ƴaƴansu, hakan yasa ta tsani jin koda sunanta. A ɓangaren shi kuma baban Zainab saboda kyautatawa da take yi mashi yasa ya sanya a ransa ba zai taɓa yi mata kishi ba, saboda ita ɗin macece mai kirki da shi da kansa yana jin kunyar ya yi mata abin da bata so, idan kaga ta yi mashi abin da ya ɓata mashi rai to wlh babban akasi aka samu, banda haka kullum tana ƙoƙarin ganin ta kiyaye bata yi abin da baya so ba, shiyasa shi ma duk abin da bata so yake ƙoƙarin kiyayewa, mutun ne shi mai ilimi, yasan da cewa a duniyar yanzu idan mutun ya faɗi ya mutu idan ba yana da makudan kuɗaɗe ba to babu wanda zai kula ƴaƴansa da matarsa ma bare har ya yi ƙoƙarin tallafa masu, mutun yana raye bai mutu ba ma idan bashi da dukiya babu mai kula shi ba mai zuwa gidansa bare kuma idan ya mutu, in kaga family suna rige rigen ɗaukar yara idan mahaifinsu ya mutu to wlh ya mutu ya bar masu dukiya mai yawa ne, nan ne zakuji har faɗa ake yi a kan ɗaukarsu, da zarar kuma ancinye dukiyar gadon shikenan za'a fara yi wa ƴaƴan riƙon sakainar kashi, a barsu suyi ta gantali a bakin layi, mai ƙoƙari ne ma zai sanyasu a islamiya, wannan mai mutunci sosai daga cikin ƴan uwa kenan, mara mutunci ma ai sai dai ya turasu wajen uwarsu idan ya kammala cinye dukiyar, ta je can ita ta karita da su, idan ma zasu mutu su mutu!. So shi baban Zainab yana da dogon tunani, hakan tasa ya yi wa kansa plan tun yana da rai, plan da zata inganta mashi rayuwar ƴaƴansa da matar tasa ko bayan babu shi, wannan dalilin yasa baya da sha'awar tara ƴaƴa da mata, rashin haihuwar maman Zainab ɗin ba daga ita bace, daga shi ne wanda ya dakatar masu da shi ita ma ba tare da saninta ba, sam bata sani ba, ta dai ga haihuwarta ya dakata, da yake tana da tawakkali kuma sai bata buƙaci jin ba'asi ko kuma ta tuhumi wani ba, sai ta ɗauka a matsayin Allah ne ya dakatar mata da shi, dan tasan babu wanda ya isa ya dakatar da haihuwa har sai idan Allah ya rigada ya rubuta su ɗin kenan zata samu. Babban burin baban Zainab shi ne, idan ya kammala masu ginin nan nasu suka koma, the second abin da zai yi shi ne ya sanya Maman Zainab ɗin a harkar kasuwanci sosai da sosai, this is the best way na farko da zai fara gina rayuwar iyalansa, abin da yasa ya yi plan ɗin hakan kuma shi ne, ya san cewa a duniya idan kowa zai guji rike mashi ƴaƴa saboda talauci to banda mahaifiyarsu, ita ce duk wuya duk daɗi zata zauna da su, zata iya yin kwana biyu tana kwana da yunwa in dai ƴaƴanta zasu ci abinci, zata iya kwana a waje bakin kofa ƴaƴanta suna cikin ɗaki idan ɗakin ya yi masu kaɗan, zata iya zama a cikin ruwan sama, rana, da kuma iska su kuma ta ajiyesu a inuwa idan filin ba zai ishesu ba, uwa ita kaɗai ce ba zata taɓa bari rayuwar ƴaƴan da ta sha wahala ta haifosu ta renesu ya tagayyara ba, sai dai idan babu yadda ta iya ne, amma ba zai taɓa yiwuwa ta barsu a gantale ba. Wannan dalilin yasa baban Zainab ɗin yake planing ɗin ita ce ya dace da ya fara ingantawa tun yana raye, ita ce ya dace da ya fara ginawa a kan komai nasa, ya koya mata kasuwanci tun yana raye, ya kuma bata makudan kuɗaɗe na jari, tun yana da rai ta ginu ta tsaya da kafafunta, hakan zai sa ko bayan ya mutu, idan ma ƴan uwansa sun cinye gadon yaran, to uwassu tana da abin yi, kuma nata dukiyar dai babu wani daga cikin ɗan uwansa da ya isa ya zo ya kwace mata shi da sunan gadon yara, yasan wacece maman Zainab sarai, shi ne yasa baya da wata damuwa zai ninke makudan kuɗaɗe ya bata jari tare da nuna nata yadda zata yi. A tsarinsa ba wai ita ce zata fita ta yi business ɗin ba, a'a amintattun daga cikin ƴan uwanta ko kannenta zata ɗauko ta ɗaura a kan kasuwancin nata, kowani sati ta rinƙa yin lissafi da su tana cire ribar tana zubawa a cikin account nata, idan ta ga dama ta kara bunƙasa kasuwancin da ribar, shi dai a matsayinsa na cikakken ɗan kasuwa zai yi ƙoƙarin ya bata shawarar da ta dace game da kasuwanci a koda yaushe, sannan kuma zai sanar da ƴan uwansa cewa wannan dukiyarta ne da aka bata na gadon mahaifinta da ya rasu ta fara kasuwanci da shi, zai yi hakan ne kuma gudun fitina, kada azo idan ya mutu ace wannan dukiya da take juyawa ma nashi ne a kwace, yasan halin mutane, to wannan shi ne plant ɗinsa ta farko kenan game da familynsa, shiyasa baya son aurar wata mata, dan baya son bayansa su walaƙanta. Bawan Allah shi da yake da tunani kenan, da ya yi ta aure yana haifar ƴaƴa gara mashi ya inganta rayuwar waɗan da yake da su a gida ta yadda ko bayan ya mutu ba zasu sha wahalar rayuwa ba, amma a duniyarmu ta yau magidanci ya bawa matarsa jari a cikin gida ta yi sa'anaa ma gani yake asarace, kuma idan ta tambaye shi buƙatunta ba biya mata yake yi ba, idan ta nemo jari ta fara kasuwancin ma wani mijin saboda mugunta sai ya san yadda ya yi ya cinye mata jari, wani ma sai ya rinƙa hanata isashen kuɗin cefane yana cewa ta cika zai biya ko makamancin haka, da haka jarin nata yake karewa, sun gwammaci su je su yi ta karo aure kamar wasu bunsuraye, sun gwammaci su yi ta tara yara dayawa su kasa riƙewa, yara su zama ba boko ba Arabic, su saki ƴaƴa a layi babu ɗaya kanin biyu, yara duk su girma ba ilimi bare sanin yakamata, mahaifiyarsu baiwar Allah tana can ta kashe kanta a neman masu abin da zasu ci bata wani zama ta basu tarbiya sosai, duk su taso babu tarbiya su zama ƴan iska, wasu ma ƴan shaye shaye, wasu daga haka suke ɗaukar makamai su fara sace sace suna addabar al'umma, wlh da kowanu uba tun farko yana kula da ƴaƴansa ya sakasu makarata ya basu ilimin addini dana boko, to wlh da yau babu ɗan iska ko guda ɗaya a duniya, duk ƴan iskan nan jahilai ne, ba Arabic bare boko, wani ko karatun fathiha bai iya ba, kuma ya girma ya zama matashi an fara rubuta mashi zunubi, ba gasu nan zube a layi ba, sai anyi magana kuce annabi ya ce a hayayyafa dayawa dan ya yi alfahari da al'ummarsa ranar gobe kiya ma, tambayata a nan shi ne da ƴan iskan annabi zai yi alfahari ne? Ai wlh ka haifo ƴan iska sai dai ka je cikin kabari kana kwance kana fama da azaba su kuma suna duniya suna kara labto maka wata azabar, wlh kasani in dai baka bawa ƴaƴanka tarbiya ba, to duk abin da zasu aikata kana da kaso a ciki, kana kabari kana karɓar azabar da suke aikatawa a duniya, ka je lahira Allah ya ce maka ya ka yi da amanar da ya baka? Nan idan baka bada amsar da ake buƙata ba ka sake karɓar wani sabon gashi na musamman, annabi bai ce kowa ya haifi ƴaƴan da ba zai iya kula da tarbiyarsu ba, ko shin kansa karin aure annabi ya ce in kasan ba zaka yi adalci ba ka tsaya a kan guda ɗaya, domin kuwa in dai ka yi rashin adalci aranar gobe kiyama a mai shanyayyen ɓari guda na jikinka zaka taso, amma sai kaga wasu shaiɗanun mazan da sun kara aure uwar gidansu da suka sha gwagwarmaya a tare ta zama bola kayan banza, su rabu da ita tana gantali tsakanin layi da gidajen maƙota dan neman abin da zata ci ita da yara, su watsar da yara su gasu bunsuraye iyayen son mata, wlh ku ji tsoron Allah, abu guda ɗaya Ubangiji ba zai manta ba sai ya tambayeku, idan ku kun manta shi Ubangiji ba zai manta ba, duk sai ya bi ɗaya bayan ɗaya ya tambayeku, Allah dai kasa mu dace. (Yau dai za'a ga rubutun alƙalamin nawa ta yi zafi, abin ne yana bakanta mun rai in ga yadda maza suke walaƙanta mata a kan karin aure, wannan abin da ciwo yake wlh🥲 Allah dai ka haɗamu da abokan zama na gari masu ƙoƙarin bin tarihin manzon Allah kuma suna koyi da shi tare da litattafan musulci haɗi da Alqur'ani mai girma.) Mu koma kan labarinmu. Idan ran maman Zainab ya yi dubu to fa ya ɓaci a wannan lokaci, wani irin tukukin bakinciki ne ya taso mata daga ciki ya tsaya mata a wuya, zuciyarta har wani irin tafasa yake yi mata, sam bata san lokacin da ta ce mashi. "Allah zai saka mun duk abin da suka mun, na so su, na kaunacesu tsakani da Allah, babu abin da na yi masu, babu abin da na tare masu, Allah ya gani ina yin iyakacin bakin ƙoƙarina wajen ganin na yi komai na tsakanina da Allah, amma me nayi masu da suke son sai sun cutar dani a rayuwata? Me nayi masu? Ya Ubangiji kamun sakayya cikin gaggawa!". Tana magana tana hawaye, ta kai karshen maganar tare da miƙewa tamkar zata faɗi kasa, saboda tukukin bakin ciki, a hanzarce ta wuce izuwa cikin bedroom nata tana kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Already baban Zainab yasan za'ayi hakan, fin haka ma ya yi tsammani, dan yasan ta tsani kishiya, bata son maganar, yanzu shi yana cikin wani hali, duk ta in da ya je babu sauki, maman Zainab ta yi fushi, mahaifiyarsa ma ta fusata, kota ina babu daɗi, duk sai ya ji ba zai iya komawa kasuwar bama, haka zali ka ba zai iya tunkarar Maman Zainab a yanzu ba, zai barta ne sai ta huce kaɗan, yanzu ko ya tunkarata ba zata saurare shi ba, ba kuma zai sami abin da yake so ba, idan ba sa'a bama sai su yi faɗa sosai a tsakaninsu, shi mai ilimi ne, yasan idan ran mace ya ɓaci to kada ka tunkareta a lokacin, dan zaku yi ɓarattciya ne kawai, saboda a lokacin kome zaka gaya mata ba zata fahimta ba, idan ka samu ta saurareka ma kenan, zuciyar mace karama ce, kuma a kusa zuciyar take, idan ranta ya ɓaci babu abin da ba zata iya aikatawa ba, sai dai daga baya ta yi dana sani.......(Kamar aljanu haka muke idan ranmu ya ɓaci😅😅😅 mun san komai 🥱) Dan haka sai ya koma ya kishingiɗa a saman kujerar yana tunanin rayuwa, kansa sai wani irin sara mashi take yi tamkar zata fashe gida biyu, har wani irin jiri yake gani, idanuwansa duk sun yi jajir saboda ɓacin rai, ya rasa me yake yi mashi daɗi a duniyar nan, bugu da ƙari ga auren Khadija and Haidar, sannan ga shi mamarsa ta ce nan da wata ɗaya da ita da amarya zasu koma sabon gidansa in da ya ci burin ya rayu da maman Zainab rayuwa mai daɗi, dan ta juri akwai da babunsa, ta zauna da shi tun yana talaka bai da komai, kai akwai lokacin da ita ma take ciyar da shi, harta maman Haidar ta ciyar, amma saboda rashin godiyar Allah shi ne suka saka mata ta wannan hanyar, abin sam babu daɗi, ya so ya aurar da Khadija da Zainab ga nagartattun maza da suka san ciwon kansu, sai ya zauna daga shi sai mamansu a sabon gidansu su sake more amarcinsu a karo na biyu babu kowa, babu wanda zai damesu, suyi rayuwar farinciki, ya saka mata da abin alkharin da ta yi mashi a baya, amma duk mamarsa ta rusa komai, ina shi ina soyayya mamarsa tana gidan fisabilillahi? Ai babu wannan zance!. A haka su Khadija suka dawo daga school a tare da Sadiq da ya je ya ɗauko su suka sami baban nasu. Hajiya Zainab sarkin raki tun daga harabar gidan take kiran sunan maman tata, sai kace wata tsohuwar makauniya, sai kwala kira take yi, sai da Khadija ta ce. "Ni kam ke kam Zainab yaushe zaki yi hankali ne? Wai ba cikin ɗakin zamu shiga bane? Ki bari mu shiga mana sai ki gaya mata duk abin da zaki faɗa mata, amma kin wani tsaya daga tsakar gida kamar wata makauniyar da sandar dogarawarta ta ɓata kina kiran neman taimako?". Turo bakin nan tayi kamar biro, sannan ta wuce izuwa cikin parlourn fuuuu kamar wata kumfa a saman ruwan teku, Khadija ta cika shisshigi a cewarta. Tana shiga da ta ga babanta a kwance a saman kujera bata san time ɗin da ta saki school bag ɗin nata ya faɗi ƙasa ta ƙariso wajensa da gudu, kamar wata under 10 years tana ambatar sunansa. "Baba, baba ya aka yi yau ka dawo da rana? Da muka tambayi kawu Sadiq ina kake ya ce mana kana kasuwa fa, ashe kana gida". Khadijah tana ƙoƙarin cire takalmar makarantar tata a wajen ajiye takalmarsu ta tsinkayo muryar Zainab tana faɗin baba, baba, ai a ɗari ta yi maza ta ƙarisa cire takalmar ita ma ta faɗo cikin parlourn, bayin Allah suna matuƙar kaunar baban nasu sosai, dan uba ne na gari shi ɗin, yasan ciwon kansa dana iyalansa, yana koyi da fiyayyen halitta sosai da sosai. Jin muryar Zeezeensa yasa ya buɗe idanuwansa da suke jajir da su kamar wuta. Ɗan zaro idanu Zainab ta yi kafin ta ce. "Baba baka da lafiya ne?". "Kai'na ne yake mun ciwo Zeezeena, shi ne yasa kika ga na dawo kasuwa da wuri, jeki ki cire uniform kuyi wanka kuzo mu ci abinci a tare, yau a gida ma zan ci abincin rana". Da yake har yanzu yarinta sosai yana a kanta, sai ta miƙe cike da murna yau zasu zauna da babansu da rana su ci abinci, ɗakinsu ta nufa tana yi mashi addu'ar Allah ya sawwaƙa mashi ciwon kan nasa. Khadijah dake a tsaye a bakin kofar shigowa tana kallonsu ne ta ƙariso cikin parlourn, a ƙasa saman carpet ta zauna kusa da baban nata, gaisuwa ta fara ɗaga mashi cikin nutsuwa kafin ta ɗaura da cewa. "Baba ka dai'na sakawa ranka damuwa, zai iya taɓa lafiyarka, ni nasan kana damuwa ne a kan ni da yaya Haidar, to na yi maka alkawari zan zauna da shi kuma na yi hakuri, amma sai ka dai'na damuwa ka ji?". Khadijah ba dai hankali ba, akwai shi kam, ga nutsuwa, bata shiga harkar kowa, kawar da kai da kawaici duk ta haɗa. Miƙewa zaune ya yi, cikin sanyin murya ya fara saka mata albarka kafin shi ma ya ɗaura da cewa. "Mamana ba zaki auri Haidar ba In Sha Allah, saboda ba shi ne irin mijin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce mu zaɓawa ƴaƴanmu ba, dan haka ni ba zan aura maki shi ba, ina jiran ne kawai ki rubuta Exams naki ki gama sai na san abin yi, dan haka ki kwantar da hankalinki ki rubuta Exams kuma ki ciyo mun first class kamar yadda kika saba kin ji ko?". Haƙiƙa ya gaya mata hakan ne kawai domin ta nutsu ta rubuta Exams nata na karshe a secondary school da kyau, tabbas bashi da mafita a kan aurenta da Haidar, amma kuma baya taɓa sarewa wajen cewa ba zai aura mata shi ɗin ba, a kullum yana da kwarin gwiwar cewa Allah zai kawo mashi mafita ya kawo sanadiyar hana auren, amma for now dai bashi da wata hanya ko wata zaɓi, kawai gaya mata yake yi ba zata aure shi ɗin ba dan hankalinta ya kwanta. "To baba ta ya za'ayi na dai'na damuwa na kwantar da hankalina bayan kai da kanka da kake cewa na dai'na damuwar kana cikin damuwa? Ni nasan yanzu haka damuwar ce ta ja maka wannan ciwon kai da har ka dawo gida da ranar nan bayan baka saba dawowa da rana ba, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba matuƙar iyayena suna a cikin damuwa". Tana magana idanuwanta a cike tab da kwallah. "Mamana kada ki damu, muma daga ni har mamarki mun dai'na damuwa a yanzu, kema ki kwantar da hankalinki, yanzu dai jeki ki cire uniform ki yi wanka kuzo muci abinci a tare, na yi maki alkawarin ba zaki sake ganin damuwa a saman fuskata ba kin ji ko?". Jinjina kai ta yi tana mai ƙoƙarin goge hawayen da suka cika mata idanun. "Baba kafin na cire uniform ɗin bari na sayo maka maganin ciwon kai ɗin, idan mun ci abinci sai ka sha ka kwanta ka yi barci zuwa la'asar zaka ji sauki ko?". Kamar zai ce mata ta bari, sai kuma ya tuna Khadija ba kamar Zainab take ba, Zainab ne zai cewa ta bar abu ba zata tambaye shi dalili ba zata bari, ita kuwa Khadija yanzu idan ya ce ta bari ma wani sabon rigima ne, dan sai ta ce mashi lallai sai ya sha magani ko kuma ta tsayar mashi da kuka, zaman lafiyar dai kawai ya barta ta je ta sayo ɗin, baya son fitarta, amma da yake lallaɓata yake son yi yanzu ta kwantar da hankali ta yi karatu, sai ya kyaleta ta je ta sayo ɗin, tun da shagon babu nisa, idan ya ce ta bari ya sayo ma zata ce a'a ya kwanta kansa na ciwo, su Zainab kam an tafi wanka, sai murna take yi yau zata ci abinci a tare da babanta da rana. Hmmmmm Allah ka bamu ƴaƴa waɗan da zasu iya fahimtar farincikinmu da kuma bakincikinmu ba sai mun gaya masu ba!. Har ta kai bakin kofa zata fita sai kuma ta juyo tana faɗin. "Baba ina mama kuma?". "Mamanku tana ciki tana barci". Ya bata amsa yana ƙoƙarin ciro kuɗi daga aljihun dakakkiyar shaddar jikinsa. Shiru Khadija ta ɗan yi tana tunanin, hakiƙa zuciyarta ta gaya mata ba lafiya ba, ace babanta ya dawo mamanta tana cikin ɗaki tana barci? Bata taɓa ganin hakan ba, idan ma barcin ne wlh a tare suke yi, dole dai akwai abin da yake faruwa, dan mamanta da zarar babanta ya dawo to tana tare da shi, duk abin da zai buƙata ita zata yi mashi cikin ƙanƙanin lokaci cikin kuma kulawa da nutsuwa, hakan ne ma yasa shi ma baban nasu baya son yi mata abin da bata so, yana burin ganinta cikin farinciki. "Ga kuɗin maganin karɓa ki je ki sayo ki dawo da wuri". Muryar baban nata ya katse mata tunanin da ta afka. Shi ma ya lura ta luluƙa duniyar tunani, kuma dama yasan halinta sarai da shegen iya saurin gano abu. "Baba akwai kuɗin break da kawu Sadiq ya bani da safe a hannuna, zan sayo maka da shi". Ta faɗa tare da sa kai ta fice da wuri. Da kallo kawai ya bita yana mamakin halin ƴar tasa, akwai hankali da nutsuwa, Maman Zainab ta iya tarbiya!. Ita kuwa maman Zainab kuka ta je ta ci mai isarta, a haka har barci ya ɗauketa a saman bed ɗin, shi ne yasa kuka ji ta shiru. Hajiya Zeezee sarkin wanka tuni ta yi wanka ta hau shiri abinta, ita dai bata san dawar garin ba, sai murna take baba ya dawo da rana, bata san wannan dawowa tasa tamkar bom ne da zai tarwatsa masu farincikinsu ba, ance ƙuruci dangin hauka, to shi ne a kan Zeezeen babanta. Khadijah kuwa, tana fita izuwa bakin babbar titi saura kaɗan wasu danƙara danƙara motoci su bi ta kanta, domin kuwa, tana tafiya ne tana tunanin me ya haɗa mamanta da babanta faɗa? Meyasa mamanta zata shiga cikin ɗaki ta bar baba a parlourn? Wannan abin ya tsaya mata a rai. Ta yi nisa cikin tunanin ne har ta isa bakin babbar hanya, tana isa kawai ta sa kai zata wuce, dan bata ma san ta isa wajen ba, hakan kuma ya yi dai'dai da dannowar hancin wasu danƙara danƙarar motoci na familyn Sir ALAUDDIN ABDUL RAHMAN, ɗaya daga cikin manya manyan masu murya a ƙasar, babban mutun ne mai kamfanoni a manya manyan ƙasashen ƙetare, babban mutun ne sosai, so haka motocin gidansa suke, idan suka hau titi fa ba ɗaga kafa, wucewa kawai suke yi abinsu, bare ma idan motocin sun ɗauko babban ɗansa FAROOQ ALAUDDIN ABDUL RAHMAN, yaron sam bashi da kirki, baya ɗagawa kowa kafa, duk wanda ya yi kuskuren bi ta gabansu take shi suke yi, hakan yasa saura kaɗan su take mana Khadijarmu Allah ya tsareta ta farga a in da ta ja baya da sauri tana mai bin motocin da kallon banza, dama haushi take ji, zuciyarta a cike da damuwa, sun wani zo zasu kara mata damuwa a kan damuwa, sun wani wuce kamar wasu walkiya. Sai kace mutane take gani a gabanta ta wani tsaya tana watsawa danƙara danƙarar motocin harara har suka wucewa ganinta duk yawan nan nasu, ko ciwo ma idanunta basu yi mata ba wajen jure harararsu har suka wuce. Suna wucewa ta sanya kai ta wuce abinta tana mai kare masu zagi, dan bata ga alamar hankali a tattare da su ba a cewarta. Pharmacyn dake a tsallaken titin ta je ta haɗowa babanta maganin ciwon kai, sannan ta kama hanyar dawowa gida, sai magana samarin layi suke yi mata, kamar dai kullum babu wanda ya isheta kallo daga cikinsu, in da ta sanya kai kawai take nufa abinta. Lokacin da ta dawo gida Zainab har ta yi wanka ta fito parlourn. A kusa da baban nata ta zo ta ajiye mashi magungunar tana wani aikin yamutse fuska, sannan ta wuce cikin ɗakinsu dan ita ma ta yi wanka ta shirya. Sai a lokacin kuma baban nasu ya miƙe jiki ba kwari ya nufi cikin bedroom na mamar tasu, da farko Khadija ta so ta shiga wajen mamar tasu kafin ta wuce ta je ta yi wanka, amma ganin babanta ya miƙe zai nufi ɗakin ne yasa ta wuce nasu dakin kawai. Ya shiga cikin ɗakin dai'dai lokacin da maman Zainab ta farka daga barcin da take yi na wahala, idanunta har sun kumbura saboda kuka ga kuma barci, har ta yi barci ta tashi ɗin ma zuciyarta bai yi sanyi ba, tafasa yake yi mata sosai, musamman idan ta tuna cewa kakansu Zainab ta ce a tare da ita da kuma Amarya zasu koma sabon gida, duk sai ta ji duniya tana juya mata, yanzu ma basu zaune gida ɗaya da su ba ya ta kare da balaja'un bala'in tsohuwar bare kuma suna zaune gida guda? Ya kuke tunanin zaman zai kasance?. Akwai aiki ba kaɗan ba. Kuma abin da baku sani ba a nan shi ne, duk abinda kakansu Zainab take yi fa zugin maman Haidar ce, ita ce nan take ƙoƙarin tura ƴar tsohuwar nan ga halaka, munafukar mata. A gefen gadon baban Zainab ɗin ya zauna yana ƙoƙarin fara yi mata magana. A daƙile cikin tsananin ɓacin rai ta ce. "Ba sai ka sake ce mun komai ba baban Zainab, wanda ka gaya mun ɗazun ma ya isheni har karshen rayuwata, dan girman Allah ka rabu da ni haka idan dai ba so kake kaga gawata ba". Ta kai karshen maganar tare da zuro kafafunta ta sauka kasa daga saman gadon, ta wuce ta fice ta bar mashi ɗakin. Bawan Allah duk sai ya rasa ina zai sanya ransa ya ji daɗi, haka dai jiki ba kwari ya sake miƙewa ya fito parlourn, nan ya isko tana shirya masu abinci, ɗaya daga cikin abin da yasa yake kara sonta kenan, komai ɓacin ran da take ciki baya hanata ta yi aikin da ta saba, baya hanata nemar aljannarta baiwar Allah. A saman sofa ya zauna yana ta kallonta, ita kuwa ko kallon in da yake bata yi ba, abincin kawai take kwasowa daga kitchen tana shirya masu a parlourn, duk in da ta yi sai ya bita da ido bawan Allah, tana gamawa kuma ta nufi hanyar komawa cikin ɗakinta, da alama ita ba zata ci abincin ba kenan. "Maman Zainab ina zaki je kuma? Ki zo mu ci abincin mana". Ya faɗa yana kallon Zainab dake rike da wayar mamar tasu. A takaice ta ce mashi. "Bana jin yunwa, so ku ci kawai". Ta kai karshen maganar tare da shigewa cikin ɗakin abinta, har da rufo kofa ta murza key. Tabbas yasan saboda ganin idon Zainab ne yasa ta bashi amsa, da Zainab bata parlourn ba zata kula shi ba bare ta bashi amsa. Macece mai hankali sosai, tasan duk in da yake mata ciwo, tasan da cewa abin da take yi wa babansu Zainab shi suma idan suka yi aure zasu rinƙa yi wa mazajensu, so bata son ginasu a kan turbar da bata dace ba, shiyasa kome babansu zai yi mata na ɓacin rai bata nuna hakan a gabansu, tana ƙoƙarin ta danne dan taga tarbiyar da take basu yana tafiya mata yadda ya kamata, ba wai tana basu tarbiya kuma tana sake rusawa da kanta ba, Allah yasa mata su gane illar faɗa da mazajensu a gaban ƴaƴansu, Allah yasa su gane cewa rugujewa ƴaƴan nasu tarbiya suke yi da kansu, Allah yasa su gane cewa duk abin da suke yi wa ubansu haka ƴaƴan ma zasu yi wa mazajensu idan suka yi aure, dan suna ganin mamarsu tana yi, so hakan zai sa su ce abu ne mai kyau. Yau dai shi ma ya ci wannan abincin ranar ne kawai saboda Zainab da Khadija, ba dan su ba tabbas ba zai ci ba, amma baya son su san halin da ake ciki, dan haka sai ya zage yana ta ƙoƙarin ƙaƙalo murmushin da kuma yake wadda aka ce tafi kuka ciwo, a haka suka kammala cin abincin ya tashi ya nufi kasuwa bayan ya ɗaukawa su Sadiq nasu abincin a kula. Bai sake komawa wajen Maman Zainab ba, dan yasan har yanzu bata sauko ta huce ba, so ba zata saurare shi ba, hakan yasa ya wuce kasuwa kawai da nufin kafin ya dawo kila zuciyarta zata huce kaɗan ta saurare shi. Haka su Khadija suka zauna a gidan har zuwa lokacin tafiya islamiya, lokaci na cika suka yi sallah tare da shirin islamiyar, ko da suka je yi wa mamar tasu sallama sam bata nuna masu kamar akwai wata damuwa ba, sai ma kuɗin sayan attarugu da Albasa tare da tumatir ta basu kamar yadda ta saba, sannan ta bisu da addu'a tare da fatan alkhari kafin ta ja masu kunne a kan biyewa ƙawaye ko kuma wani ya taresu a hanya su tsaya su kulashi, su kiyaye hakan dan su ƴan gidan mutunci ne, ba'a kan titi suke ba, wannan shi ne nasihar da take yi masu a kullum idan zasu tafi islamiyar, shiyasa kuka ga basu taɓa kula maza a hanya. Da haka suka wuce Islamiya ita kuma ta tashi ta fito ta nufi tsakar gida, alwala ta ɗauro ta dawo. Bayan ta gabatar da sallah ne ta nufi kitchen dan girka masu abincin dare, a haka Aunty Hauwa ta zo ta iskota. Kamar yadda suka saba a parlourn suka zauna da Aunty Hauwar suna hira tana zuwa tana duba girkinta da ta ɗaura, cike da damuwa ta sanar da Aunty Hauwar bala'in dake shirin tunkarota a karona biyu bayan na auren Khadija and Haidar. Aunty Hauwa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen kwashewa su maman Haidar albarka tare da banka masu tsinuwa kala kala, sannan ta ce mata to wlh gara ta tashi tsaye, idan ba haka ba tana ji tana gani zasu korata gidansu bayan kuma ita ce ta sha wahalar baban Zainab ta ci talaucinsa, yanzu kuma wata zata zo ta ci arziki, wlh kada ta yarda, ta miƙe tsaye, dan rayuwar yanzu ba'a zama........ Aunty Hauwa ba dai bala'i ba.😅 "Hauwa to ya kike son nayi da su? Kina dai jin abin da suke faɗa ko? Umarni Hajiya ta bashi fa". Nisawa Aunty Hauwar ta yi kafin ta ce. "To ai idan ba zaki iya fito na fito da su ba sai ki biyo masu ta ƙarƙashin kasa, duk kici uban shegu marasa amana butulaye kawai". Ta bata amsa rai a ɓace "Hauwa kamar yaya na biyo masu ta ƙarƙashin ƙasa? Yimun bayani na ji". Tana magana cike da damuwa a ranta, kamar zata yi kuka. "Abin da nake nufi da ta ƙarƙashin kasa shi ne, tun da ba zaki iya fito na fito da su ba kawai ki yarda muje wajen Malam sha yanzu magani yanzu, muje mu gaya mashi ya rufewa ƴan uwan mijinki baki a kanki, ya kuma sanya masu kaunarki na fitar hankali, sannan a ruguje batun auren da suke son yi wa baban Zainab ɗin, kinga fa nima haka na yi wa ƴan balaja'un ƴan uwan mijin nan nawa, baki ga yadda suke so na bane? Ai kamar su goyani suke ji saboda so, baki ganin ko da yaushe su Khalid suna wajensu bane? Suke shan reno ni kuma ina neman kuɗi, kamar su haɗiye su Khalid saboda so, dan haka kema abin da zaki yi wa ƴan iska kenan, ai in sun san wata basu san wata ba". Ɗan zaro idanu Maman Zainab ɗin ta yi, a ruɗe ta ce. "Hauwa kina nufin wajen boka kike zuwa?!". Wani kallon banza ta ɗan watsa mata kafin ta ce. "Sai aka ce maki boka ne shi ɗin? Ko kin ji nace maki boka ne? Malam sha yanzu magani yanzu fa nace maki, shi ba irin bokan da kika sani bane, malami ne". Shiru Maman Zainab ɗin ta ɗan yi kafin daga bisa kuma ta ce. "To Hauwa me marabansa da boka?". Da sauri ta amsa mata da "Wlh suna da maraba, kuma ke da kike wannan magana ma kin san me wadda zai auro maki ɗin take yi ne? Su hajiyar tasa kin san me take shiryawa ne? Ki zauna ke kam, kada ki tashi tsaye, wlh sai sun rabaki da jin daɗin rayuwa, kina ji kina gani ki zama ƴar aiki jaka a gabansu". KAI MY PEOPLE'S, WAI YA NAGA AUNTY HAUWA NA ƘOƘARIN GURBATA MANA TUNANIN MAMAN ZAINAB ƊIN MU NE?😥😳 BAN GANE BANE😳 TO SAI DAI MUN HAƊU ON MONDAY DAN MUJI ME MAMAN ZAINAB ZATA YI, WANI ACTION ZATA ƊAUKA A KAI, ALLAH DAI KASA MU DACE KA RABAMU DA JAHILAN KAWAYE!. 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 15/7/2024.....✍️📚🌹 For information 0816139058 Whatsapp me only!!. Dedicated to Abubakar Sadiq.❤️ Baki ba zai iya faɗar alkharinka a gareni ba, ina matuƙar farinciki tare da godiya da irin kwarin gwiwa da karfafa mun da kake yi, a kullum nace na gaji cewa kake yi ki kara hakuri ki dage, ki jure ki daure, ba'a cin nasara sai an dage, kwarin gwiwar da kake bani ba zan iya biyanka ba, ban biyaka ko sisi ba, amma haka ka zage kake karfafa mun gwiwa tsakaninka da Allah da zuciya ɗaya, wanda nasan a duniyar yanzu ko kuɗi ka biya mutun ba zai taɓa yi maka hakan tsakaninsa da Allah ba, sai dai ya yi ta yi maka kauce kauce! Amma kai ba ko sisi kake karfafa mun gwiwa, da nace zan ɗauki hutu koda na wata biyu ne kafin na ɗaura da rubutu, bawan Allah cewa ya yi a'a Fatima, kada ki yi haka, ko dan masoyanki kawai ki ɗaura, ki huta kada ya wuce two weeks. Saboda shi da A'ishah Baita Jidda na fara yin posting ɗin RAWANIN ZALINCI, i really appreciate gaskiya.💘 Aisha Baita Jidda, kema kwarin gwiwar da kike bani bakina ya yi kaɗan wajen zayyano shi, ba abin da zan ce maku face Allah ya bar kauna ya kuma bar zumunci. Hjy Halimatus Sadiya, Ubangiji Allah ya baki ƴaƴa masu albarka waɗan da zasu kasance alkhari a gareki har bayan ranki, alkharinki a gareni ba zai faɗu ba, mace mai farar zuciya.💘 My admins godiya da tarin jinjina a gareku.💘 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________14🔥 "Hauwa wannan fa bashi da maraba da boka wlh, in kuma haka ne ni ba zan iya zuwa wajen boka ba, mama zan iya neman wani abin a wajen wanin Allah ba, Hauwa kin canza, kamar ba Hauwar da na sani ba, ki ji tsoron Allah, wlh wanin Allah bai isa ya baki abin da Allah bai baki ba, ki sani in kina cikin ƙunci da bakin ciki kika nemi taimakon wanin Allah, to wlh kofofi sama da dubu ne na sabuwar ƙunci da bakincikin da baki taɓa zato ba zasu buɗe maki, matsaloli ta ko'ina zasu fara kunnu maki kai ki rasa yadda zaki yi da su, wlh Allah ne kawai zai iya warware maki halin kunci ba waninsa ba". Ta kai karshen maganar zuciyarta cike tab da damuwa, haƙiƙa ta yi matuƙar jin rashin daɗi na halin da Aunty Hauwar ta faɗa, a tare fa suka yi makaranta suka yi komai, amma ace Aunty Hauwa ta canza cikin ƙanƙanin lokacin nan, abin da ban mamaki kuma abu ne da dole a tausaya mata, babu daɗi sam. "Hmmmmm maman Zainab kenan, to ki zauna, wlh ki na ji kina gani bakin ciki zai kashe ki, yanzu an gaya maki ita wadda za'a auro ɗin haka take zaune ne? Ai ke yanzu ba cutar da kowa zaki yi ba, kare kanki zaki yi, to me laifi a kare kai? Baki cuci kowa ba, baki zalinci kowa ba, kawai kwatar hakkinki daga wajen waɗan da suka cuceki zaki yi, amma ki ke wannan magana ko? To ni babu ruwana, na yi maki iya abin da zan iya, kina ji kina gani dai zaki zama jaka a wajensu, kuma zaki ce na gaya maki, baban Zainab ma sai ya koma tsaginsu, sai dai ki zama ƴar kallo". A faɗa ce ta kai ƙarshen maganar, ita a dole ranta ya yi mugun ɓaci. Nisawa ta yi kafin ta ce. "Amma Hauwa in tambayeki mana?". "Allah yasa na sani". Ta bata amsa a takaice. "Idan kin ce ba cutar kowa zan yi ba kwatar hakkina zan yi, me zai haka ba zan roƙi Allah da ya kwata mun hakkin nawa ba? Kin dai sai babu wanda ya kai Ubangiji adalci da kwatawa mara karfi hakkinsa a hannun mai karfi ko?". Shiru Aunty Hauwar ta ɗan yi, da alama tana sake tunano abin faɗa ne, dan ita dai zuciyarta ta rigada ta yi nisa, ta yarda da bokaye za'a ce, dan waɗan nan ba malamai bane ba. "Maman Zainab ko kin roƙi Allah wlh ba za'a fasa wannan aure ba". Ta faɗa tana duba time a wayar hanunta kirar Infinix note 10. "Meyasa zaki ce ba za'a fasa auren ba?". Nan ma shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Maman Zainab kin taɓa ganin wanda ya yi addu'a ya roki Ubangiji da ya ruguje wani sunna na ma'aiki ko kuma wani abin da annabi ya halakta ya kuma kawata shi wa al'ummarsa kin taɓa ganin wanda ya roki Allah ya ruguje wannan abin kuma Allah ya amsa ya ruguje shi? Ai ba'a ta'addanci a cikin addu'a, Allah ba zai amsa ba, dan haka ko kin roƙi Allah a banza kika yi, Allah ba zai ruguje aure sunnar ma'aiki babu gaira babu dalili ba". Nan fa zuciyar maman Zainab ya shiga ruɗu da tunani, Aunty Hauwa anyi ƴar duniya, tabbas a nan tana da gaskiya, babu wanda ya isa ya sanya Ubangiji ya rusa faɗar manzon Allah (S.A.W) koda kuwa kwana dubu zaka yi kana sallah kana addu'a, idan ka yi wasa ma a kan hakan sai Allah ya hallakar da kai, sau nawa zaku ga rabon aure yana kisa, sai kuga mutum ya kafe a kan ba'a za'ayi wannan aure ba ko ba zai bada ƴarsa ga wani ba idan yana raye, to idan Allah ya ƙaddara akwai auren a tsakanin wannan family, sai kuga Allah ya kawar da wanda ya hana ayi auren ɗin, ya mutu kuma a ɗaura auren zam zam a zauna babu mai hanawa, so da dama hakan tana faruwa, sai kiga mutun yana mutuwa bai fi da sati biyu ba anyi bikin ƴarsa ko wani makamancin haka, so rabo tana kisa har lahira, dan haka mu guji kin abin da Allah ya halakta mu ce mu sai mun haramta. "To Hauwa in dai haka ne nima sai na hakura kawai na bari baban Zainab ɗin ya yi auren ko?". Ta yi maganar muryarta a sanyaye, da alama jikinta duk ya yi sanyi. Wani irin harara Aunty Hauwar ta wurga mata kafin ta sake fara wannan shegen dogon jawabin nata. "Hakura fa kika ce? Lallai maman Zainab har yanzu baki da hankali! To idan kin hakura ya yi aure hajiyarsa fa? Ita ma haka zaki zauna da ita a tare da amaryar suna yi maki cin kashin da suke so? Kin dai san ƴar cikin dangi zai auro ko? To tasu ce ita ɗin, zasu goya mata baya ne ta taka ki son ranta ba yadda zaki yi, bare kuma ke da basu son ganinki a gidan, ai kin shiga ɗari ma kenan ba uku ba, malama kawai idan zaki tashi tsaye ki nemawa kanki mafita ki tashi tsaye, idan kuma ba haka ba wlh bakinciki ne zai zama sanadiyar ajalinki kin ji na gaya maki, waye ya ce maki yanzu ana zama shiru? Ai a zamanin da ne aka yi wannan haukar, yanzu ko mahaukacin kura aka kwanto maki maza ki yi fito na fito da shege, ke baki ga ko aljani idan kika nuna baki da tsoro shakkarki yake yi ba? Ai kawai haukacewa ƴan iska zaki yi duk kici ubansu, ki gasawa shegu aya a hannu, barema wannan Uwar Haidar ɗin, shegiya mai kafa kamar na shamuwa, saboda ita mijinta soloɓiyo ne ko abinci baya iya neman masu, baya iya ciyar da ita shi ne take yi maki bakinciki da hasada, wannan da ace ba ubansu ɗaya da baban Zainab ba da tsab zata aure shi, shegiyar mata dangin mayu" Ta kai karshen maganar tana cikin kunar rai, ta kuma kai karshe tare da miƙewa da nufin tafiya. "To Hauwa ina kuma zaki je?". Still dai cikin sanyin murya ta yi maganar, da alama jikinta ya yi sanyi sosai. "Ina zan je kuwa maman Zainab? Gidana mana zanje, me zan zauna nayi maki? Ina ce maki ga shinfiɗaɗɗiyar hanya mai kyau kina ce mun lallai ke ta saman dutse zaki bi ki wuce, ba dole na kama kai'na ba, kuma kada ki sake gaya mun wannan kayan takaici na sirikan naki, tun da ke baki ji, ke kin zama kamar wata jaka kwandon shara, kowa ya ɗebo dattinsa a kanki zai juye, da anyi magana ki ce ke ta Allah, ai kowa ma na Allah ne, kuma a koda yaushe muna rokon Allahn da ya yafe mana zunubanmu ya bi mu da rahmarsa, ni bana cutar da kowa, idan kin ga na gayawa malamai damuwata to cutata aka yi zan kwaci hakkina, a hakan ki gaya mun wani laifi na yi?". Ta kai karshen maganar tare da nufar kofar fita daga parlourn, tana wani kara ɗaure fuska yadda kuka san ita aka ce za'ayi wa kishi. Aunty Hauwa ta yi nisa ba zata ji kira ba, ga shegen kaifin harshe, yanzu tana neman ta jefa maman Zainab ga halaka da sunan wai tana sonta, a ganinta da haukarta hakan ce so, saɓawa Allah da shirka ka tura mutun ya yi ai ba so bane. Shiru dai Maman Zainab ta ɗan sake yi kafin ta ce. "To Hauwa zan yi tunani a kai, gobe zan zo gidanki mu sake tattaunawa In Sha Allah". Tana fita waje daga cikin parlourn ta amsa mata da sai kin zo, daga haka ta nufi harabar gidan dan wucewa nata gidan, dama daga wajen kasuwancinta take, akwai wata dillaliya ce a nan unguwarsu Zainab ɗin, to tana zuwa wajenta duba kayayyaki, irin suna harka a taren nan ne, duk wadda ta samu kaya mai sauki zasu raba su sayar dan su sami alkhari, wannan dalilin yasa take yawan kawowa Maman Zainab ziyara, dan a unguwarsu dillaliyar take, so duk time ɗin da ta shigo sai ta biyo mata sun gaisa. Kamar dai kullum har kofar gida maman Zainab ta rakata tare da bata kuɗin mashi 1k kamar yadda ta saba, daga haka suka yi sallama Aunty Hauwar ta tafi ita kuma ta komo cikin parlourn ta zaune. Uban tagumi ta buga tare da haɗa gerar sama da ƙasa tana tunanin mafita, da alama zuciyarta ta fara yarda da zancen Aunty Hauwa, abinku da shaiɗan la'anannen Allah, sai ya rinƙa raya mata cewa ita ma amaryar da za'a auro ai tana can wajen malami tana ƙoƙarin a mallaka mata zuciyar baban Zainab, ya zama baya son kowa sai ita. (Baban Zainab bawan Allah yana can kasuwa yana tunanin maman Zainab ɗin, ita kuma tana nan tana tunanin wata na ƙoƙarin mallake mashi zuciyar😅 kai shaiɗan shege wlh, Allah dai ya kara tsine mashi ya kuma nesantamu da shi, yasa mufi karfin zuƙatanmu. Amma na ce ba yanzu shi ma Haidar fa ba za'a rasa matan da zasu yi kishi a kansa ba ko?😂😅 Mata mutanenmu) Sai tunane tunane na banza shaiɗan yake kawo mata, har ya sanya zuciyarta ta fara yarda da zantukan Aunty Hauwa, yau har girkinta ya fara ƙonewa tana nan ta afka duniyar tunani. A hanzarce ta miƙe ta nufi kitchen ɗin, dan kaurin abincin ya iskota har cikin parlourn, tana can tana tunanin lamarin Aunty Hauwa ƴar balaja'u, abin mamakin shi ne tana da mahaifiya a raye, mahaifinta ne ya rasu, a maimakon ta sanar da mahaifiyarta gafa halin da ake ciki, ko banza shawarar uwa ta wuci abin wasa, da ai yanzu zata sami shawara mai ɓille mata, amma ta je tana ƙoƙarin daka ta Hauwa, bayan kuma ita da kanta ta karanta ta san cewa ba'a taɓa cin nasara da saɓon Allah, duk abin da ka haɗa shi da shirka tare da saɓawa mahaliccinmu to wlh wannan abin ba zai taɓa yi maka kyau ba, sai dai ma ya zamar maka bala'i, sarai tasan da haka, amma kishi yana neman rufe mata ido, ga Aunty Hauwa a gefe, sannan ga shaiɗan yana can yana ta faman buga masu ganga, da alama kuma suna shiri takawa wannan gangar ta shaiɗan ɗin rawa. Allah dai ya kyauta ya kuma kara tsaremu da tsarewarsa. Girkin nata ta sauke tare da ɗaura tukunyar miya a saman gas ɗin. Kamar yadda ta saba haka ta haɗa masu miyar steew tare da zuba komai a cikin kula, sannan ta kwasa zuwa cikin parlourn, sai dai fa duk wannan aikin da take yi hankalinta da tunaninta dukka yana a kan maganganun da suka yi da Aunty Hauwa, tana ta saka da warwara a cikin ranta. A haka su Khadija suka dawo daga islamiya suka sameta, sosai Khadija ta lura da yadda mamar tasu take sukuku yau, amma bata yi ƙoƙarin tambayarta ko lafiya ba, ta barwa kanta tunanin kawai a cikin zuciyarta. Yau babansu bai shigo gidan ba har sai da ya yi sallah issha, da kullum sai ya shigo ya yi wanka kafin ya tafi masallaci, amma yau sai da ya yi sallah ya dawo, duk kuma dan baya son shigowa ya kalli face ɗin maman Zainab a ɗauke da damuwa ne, hakan yasa ya yi zamansa a waje sai da ya yi sallar, tun da ya je kasuwa a cikin damuwa yake bawan Allah, ita kawai yake tunani, wlh baya son ɓacin ranta ko kaɗan, kawai ba yadda zai yi ne. Maman Zainab dai yau ta ki ta ci abincin daren ma, dan bata jin yunwa saboda damuwa, haɗa masu komai dai ta yi sannan ta nufi cikin bedroom nata. Izuwa yanzu Khadija ta gama fahimtar lallai iyayen nata sun sami gagarumin matsala a tsakaninsu, hakan yasa sai ta yi ƙoƙarin jan babanta da hira dan ya saki jiki ya ci abinci sosai, tasan ba abin da ya fi so irin ya gansu suna karatu sosai, dan haka sai ta ɗauko mashi zancen karatu, ta rinƙa bashi labarin irin karatun da ta sha yau a school. Ai kuwa nan take ya ɗan ware suka fara maganar karatu suna cin abinci, a haka ta ja shi da hira har ya ci abinci sosai wanda bai zata ba, Zainab kuwa da yake hankali bai gama zama ba, da suran yarinta, sai ta zauna tana zuba kallo a Tv tana loda abinci abinta. A haka suka yi hira su kaɗai har zuwa karfe tara na dare, yau dai Sadiq shi ya shigo ya ɗauka masu abincinsu. Karfe tara na cika su Zainab suka miƙe suka nufi bedroom nasu bayan sun yi wa baban sallama. "Kada ku manta ku yi addu'a fa". Ya faɗa tare da miƙewa shi ma ya hau kashe kayan kallo da su wutar ɗakin, dan shi ma shiga zai yi tun da maman Zainab bata nan, ba wani hira da zai zauna yi kuma, gara mashi ya je ya lallaɓata ta daure ta fito ta ci abinci, ga shi ko na rana ma bata ci ba..............💔😥 Cikin bedroom ɗin nata ya nufa, ya kuma yi sa'a bata rufe kofar ba, bawan Allah yau ko wanka ma bai yi ba, kuma ta haɗa mashi ruwan wanka kamar yadda ta saba, shi ne kawai bai je ya yi ba, saboda damuwa. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin, tana kwance a saman bed kamar ɗazun da rana, maganganun Aunty Hauwa kawai take tunawa. A gefenta ya zauna da nufin ya fara yi mata magana. Amma ina yana zama ta miƙe a hanzarce ta fice daga cikin ɗakin ta bar shi zaune, bedroom nasa ta je ta shiga tare da rufo kofar ta murza key, sai ka ce shi ne ya yi mata laifi, abin da shi ma ba laifinsa bane, amma ta kasa yi mashi uzuri a kan kishin...........MATA MUTANENMU😅😅 Ji ya yi gabaɗaya duniya tana juya mashi, ya rasa menene ma yake yi mashi daɗi a duniyar nan, har wani kara sara mashi kansa yake yi, ya rasa me zai sake yi kuma, jingina da jikin headboard na gadon nata ya yi yana tunanin me zai sake yi kuma? Ni ma na rasa wannan abin da me ta yi kama, dan haka bari na bar waɗan nan ma'auratan na leƙa wani ɓangare, wata kila kafin mu dawo maman Zainab zata ɗan sauko kaɗan........😥💔 Amma kafin mu leƙa KINGDOM OF POWER bari na baku amsoshinku sannan na kara maku haske a kan labarin, masu tambayata mun koma baya ne, ma'ana yanzu labari nake bayarwa ne, amsa ita ce a'a, ni ban koma baya ba, ai idan da zan koma baya na bada labari zan sanar daku, gaba muka ci ba baya ba, masu cewa Gimbiya Zunaira ita ce maman twins saboda suna tunanin mun koma bada labarin baya da ta wuce ne to ba haka abin yake ba, ai kuna gani ina rubutu a kan Gimbiya Zunaira kuma ina rubutu a kan su pretty wato twins, su pretty fa shekarunsu goma a yanzu, ita kuma Zunaira shekarunta shaɗaya, da shekara ɗaya kawai ta fisu, to taya za'ayi ta haifesu fisabilillahi,🤔 so rayuwar FOREST daban rayuwar KINGDOM OF POWER daban, fatan kun gane? Ɓangare biyu ne a wajen ba wai ɗaya ba, so yanzu dai zamu fara shiga cikin sarautarmu domin mu nemo shin ina RAWANIN ZALINCI take? Sai muga ko zamu iya fafatawa da ita.🥱 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ KINGDOM OF POWER💪🔥 Wasu irin shegun shirga shirgan dankara danƙaran motoci masu numfashi ne suka danno hancinsu a cikin Masarautar. Tun da waɗan nan motoci suka danno kai a saman shinfiɗaɗiyar titin dake tsakanin babban gate na shiga da second gate kowani mayaki da kuma bayi suka nemi waje su tsaya, motoci goma ne cif, dukka launin motocin sun kasance maroon color, guda ɗaya na tsakiyar ne kawai black color, waɗan nan motoci tamkar wasu jirage da suka danno kai, kace ba'a kan ƙasa suke tafiya ba, saboda tsantsar kyau, ga ɗaukar idanu, sam kukan motocin baya fita sosai, ba zaka taɓa cewa suna kuka ba, saboda haɗuwarsu, na manyan kai ce. Kai tsaye part na BARDE suka nufa, basu ja burki a ko'ina ba sai a katafaren parking space na part ɗin mai matuƙar girman da zai iya ɗaukar motoci sama da guda 50. Suna kashe motocin ba'afi da ƴan sakanninba wasu shirga shirgan bodyguards masu shiga cikin dark ash suit suka firfito daga cikin motoci maroon colors ɗin, bodyguards ne da suka san aikinsu, karfafan gaske ne, babu alamar wasa a tattare da su, aikin kawai suka iya aikatawa, duk suna sanye da face mask a face nasu. Wani shirgegen bodyguard mai ji da lafiya da karfi ne ya zo ya ɓalle marfin black car ɗin nan, ya buɗeta cikin girmamawa. A take sauran bodyguards ɗin suka ja gefe guda suka tsaitsaya alamar suna jiran na cikin motar ya fito. Sun ɗauki a kallah good 5 mins da buɗe kofar motar, amma babu wanda ya fito, tamkar babu kowa a cikin motar, su kuwa bodyguards ɗin sun kame waje guda suna jiran ya fito. Sai da aka kara almost 2 mins, sannan ya sako kafafunsa waje a hankali kamar mai tsoron taka ƙasa. Sanye yake da wata haɗaɗiyar cover shoe irin na gidan sarauta, cover ta haɗu matuƙar haɗuwa, launin white color, sai kyalli duwatsun jikinta suke yi, kun dai san yadda takalmar sarauta suke dai ko? Takalma ne na gani na faɗa waɗan da ake narka maƙudan dukiya wajen sayansu, To haka na kafarsa take, daga ta cikin takalmar yana sanye da uncle sos a kafafun nasa, sai kafar wandonsa da ta kasance wandon jeans blue color. Koma wanenen a cikin motar nan da alama jinin sarauta na gudu sosai a jikinsa, duba da yadda fitowa daga cikin mota ma kawai sai an yi ta da isa da izza, ya shanya bodyguards ɗinsa a tsaye tamkar wasu mutun mutumi, kamar an sassaƙasu a tsaye, shi kuma yana zaune, da alama jinin King Zuhair ne da gasken gaske kuwa. Ko da ya zuro kafafunsa waje ɗin ma sai da ya ɗauki almost 2 mins kafin ya fito daga cikin motar. Hannunsa na riƙe da waya, da alama tun ɗazun da yake zaune a cikin motar wayar yake latsawa. Aka ce faɗa ɓatawa ko? To shi ne wannan, dan tsayawa zayyana haɗuwar wannan matashi ma ɓatawa ne. JAISH kenan. matashin saurayi ne da ba zai haura 25 years a duniya ba, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan cewa e lallai wannan yayan gimbiya Zunaira ce, saboda fuskarsa iri ɗaya da nata, sai dai kwayar idanuwansa da suka bambanta da nata, shi nasa kwayar idanun baki ne, ita kuma nata kunga hazel eyes ke gareta, banbancin idanu ne kawai ya bambanta face nasa da ita, kyakkyawar gaske ne, ga wani haɗaɗen saje da ta kara sawa ya fito a ainahin jinin Modarawan larabawa da gaske, Cikakken namiji ne mai cikar sura tare da haiba da kamala, da ganinsa kasan e lallai shi ma ya taɓa renon commander ZAFAR, gashin kansa na larabawa a kwance luf bakin kirin yana wani sheki, ya sha gyara, da alama ba ƙananan kuɗi yake kashewa gashin nasa wajen gyaranta ba, dan da gani ba tambaya ba gyaran kananan kai ba ce, ta manyan kan ne. Yana da innocent face sosai, so silent ne, sai dai da alama akwai zafin nama da kuma zuciya, baya shiga harkar kowa, nutsatse mutun ne shi ɗin, ga bala'in kamun kai da yasa ake yi mashi kallon mai bala'in girman kai, baya da yawan magana, ga kuma bala'in kunya ke gare shi, sannan baya son ɗaga idanu ya kalli mutane, wasu suna fassara hakan da kunyar da yake da shi, a gaskiya mutun ne mai kunya sosai, dan ko mahaifiyarsu gimbiya Rahilarh baya kallonta ido cikin ido, haka Allah ya yi shi. Bugu da ƙari komai zaka yi wa JAISH a duniya ba zaka wani burgesa ba, irin mutanen nan ne da komai suka fiya yawan burus da shi, ba kasafai abu ya cika burgesu ba, amma fa mayen shan coffee ne kuma, kusan za'a ce abin a jinin gimbiya Rahilarh yake, dukka ƴaƴanta mayun coffee ne na bugawa a jarida, ko tsakiyar rana zaka gansu da cup ɗin coffee mai zafi suna sha, harta gimbiya Zunaira ɗin ma haka take da shan coffee, sai dai kuma basu taɓa shan coffee ɗin kowa sai wanda mamarsu Gimbiya Rahilarh ko kuyanga Haulat suka haɗa, a cewarsu babu wanda ya iya haɗa coffee sai mutane biyun nan, ga su da shegen kyankyani, basu son datti ko kaɗan, saboda su wani lokacin Gimbiya Rahilarh take shiga kitchen ta yi coffee da kanta. JAISH yana kaunar ƴan uwansa da iyayensu sosai, idan kaga yana magana to da ƴan uwan nasa ne, bayan su baya ɗaga idanu ya kalli kowa a cikin gidan, ƴan matan cikin family duk sun saka mashi ido, sai dai kowacce bala'in tsoron tunkararsa take yi, saboda wannan rashin maganar tasa yasa suke ɗaukarsa mai zafin rai sosai, kuma yana da zafin rai ɗin ba sai na faɗa ba, dan kunsan duk mutun mai shiru shiru irin haka fa ba'a magana wajen zuciya da zafin rai, baya ɗaukar wasa, hakan yasa suke shakkarsa sosai, best friend ɗin Yah Jawad ne.........😅 Shigar kananan kaya ce a jikinsa, sai dai ya ɗaura wata haɗaɗiya kuma tsadaddiyar suit fara a ta saman rigar jikinsa, da suit ɗin da takalmar kafafunsa haɗe da rigar jikinsa duk iri ɗaya ne white colors, wando ce kawai blue jeans. Sai tashin wani daddaɗar fitinannen kamshi yake yi. Cikin takun jarumta haɗe da ƙasaita ta jinin sarauta ya nufi hanyar barin parking space ɗin nasu. A hanzarce bodyguards ɗin nasa suka yi yunƙurin rufa mashi baya. Kyakkyawar farar hannunsa ɗaya ya ɗaga masu ba tare da ya yi magana ba, alamar baya buƙatar su bi bayansa. Cak suka tsaya kamar gumaka, shi kuwa ya wuce izuwa cikin gida. Duk in da ya zo wucewa sai mayakan dake arear wajen su risinar da kai ƙasa alamar girmamawa, kuyangu kuwa kasa suke zube gwiwowinsu. Yadda kuka san JAISH bai san da mutane a duniyar nan ba haka yake cigaba da tafiyarsa ba tare da ya ɗauke waɗan nan sexy eyes ɗin nasa daga kan screen ɗin tsadaddiyar wayarsa da yake kallah ba. Kai tsaye babbar Fada ya nufa. Yana sako kafarsa Sallama ya fara zuba mashi kirari haɗe da jinjina kala kala. Sai dai kash, ko kallo sallama bai samu daga gare shi ba, ciki kawai ya wuce abinsa, dama na gaya maku dukka ƴaƴan BARDE KING haka suke, Zunaira ce mai kula irinsu sallama, amma saura ai ko kallo daga garesu su Sallama basu samu, dan iyayen zafin kai ne da nuna isa tare da izza, ga ji da kai, basa ɗaukar raini ko wargi. Kai tsaye wajen King Zuhair ya nufa. BARDE yana dake a saman kujerarsa, ya sha naɗin RAWANIN fara kal, rawanin ta zaune mashi tamkar dan shi aka yi ta, sai fifita da gashin jimina ake yi mashi, a kujerar dake gefensa wata haɗaɗiyar kyakkyawar gimbiya ce dake sanye cikin alkyabbarta fara tas, kyakkyawa ce sosai, da kallo ɗaya zaka yi mata kasan e lallai ita ce jaruma gimbiya MieMie, kamaninta ɗaya da King Zuhair ɗin, da alama yau zama na musamman za'ayi a fadar, dan daga jefe guda ga uncle Abbas da Jawad. Da ɗan mamaki Jaish yake kallon uncle Abbas and gimbiya MieMie, tunani yake yi a kan ko me ya faru suka haɗu a fada haka? Dan shi yanzu dawowarsa kasar ma kenan daga Dubai wato wajen kakaninsa da ƴan uwan mamarsa da kuma ƴan uwan Akka, so bai san komai ba. Gaisuwa ya je ya kwasa wajen King Zuhair kafin ya ƙarisa wajen uncle Abbas, bayan ya gaisheshi ya wuce wajen Aunty MieMie, tana dake cikin alkyabbarta, sarauta iya sarauta, da ganin face nata kasan babu wasa a tattare da ita, macece mai fara'a sosai, amma da yake tana da Tiger face wajen faɗa, sai yazama idan ka ganta sai ka yi tunanin bata da fara'a sam sam, kuma jarumtarta yana ɗaya daga cikin abin da yasa ake yi wa face ɗin nata kallon mai Tiger face. Bayan ya gaisa da Aunty MieMie ne ya miƙawa Jawad kyakkyawar farar hannunsa suka yi musaba, daga haka ya wuce saman sofa kusa da Jawad ɗin ya zauna yana binsu da kallon me ya tarasu a nan to?. Daga stage na kasa kuma su commander ZAFAR ne a zaune a saman nasu dankara danƙaran kujerun na alfarma, yau har da abin alfaharin KINGDOM OF POWER wato HOORAIN duk a cikin fada, HOORAIN shi ne mayaki na farko da wannan shifiɗaɗiyar masarauta take alfahari da shi fiye da tunaninku, saboda jarumtarsa da jajircewarsa. Da alama zama na musamman za'ayi. Gyaran murya King Zuhair ya yi, cikin izza da mulki ya fara magana a nutse. "Na taraku a nan ne ba dan komai ba sai dan muna da buƙatar shiga filin daga!". Ya kai karshen maganar tare da ƙara dakewa a cikin alkyabbarsa. Cikin nuna halin ko in kula Jawad da Aunty MieMie suka sauke ajiyar zuciya, da alama basu damu da jin hakan ba. Shi kuwa uncle Abbas cewa ya yi. "Yaya filin daga kuma? Na menene? Kuma su waye zaku yaƙa?". Nisawa Barde ya yi kafin ya ce. "Ai ka sani tun da muke da masarauta guda ɗaya kawai muke takun saƙa a duniyar nan, sune suke ganin cewa yanzu sun yi girma kuma sun bunƙasa sun kawo karfin da yakamata su bar ƙarkashinmu su fara cin gashin kansu wanda hakan kuma ba abu bane mai yiwuwa, dole su kasance a karkashinmu kamar yadda yake tun farko, idan kuma ba haka ba to a karo na biyu zamu sake yaƙarsu". Yana magana words nasa na fita one by one, cikin nutsuwa da tsantsar jarumta a voice nasa. "Amma yaya ba shekarun baya da suka wuce bane kuka yakesu har sai da suka yi mubaya suka miƙa wuya, suka kuma ce sun tuba ba zasu sake ƙoƙarin gwada kwanji da mu ba?! Yanzu kuma me ya sake shiga tsakaninku?!". Cewar uncle Abbas. Shiru Barde ya yi na a kallah 2mins kafin ya amsa da cewa. "Haka ne, a shekarun baya haka suka ce, amma yanzu suna ganin sun mayar da asarar da yakin baya ta ja masu, suna ganin yanzu sun sake kawo karfi a karo na biyu, duk wasu ƙaidoji da ya dace a yaki masarauta sun cika shi, duk wasu dokoki da idan masarauta ta taka ya kai a yaketa to sun takata, sun wuce iyakarsu ne yasa dole mu mayar da su kan hanya tun wuri, tun da sun yi abin da ya kai a yaƙesu ɗin". "To amma yaya ka fara tura masu da warning mana". Cewar uncle Abbas. Gimbiya MieMie ce ta karɓi zancen da cewa. "E daddy, ka daka masu warning a karo na biyu, tun da a doka ma sai an yi wa masarauta warning ɗaya biyu a na uku ne idan basu canza ba sai a yaƙesu, to mu daka masu warning a karo na biyu, idan basu ji ba sai a hura mana bososhin yaki kawai". Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanin kafin ya buƙaci jin ta bakinsu su Commander ZAFAR and su Malam lima da sauran manyan cikin fada. Dukka kowa ya amince da a sake tura masu da saƙon warning, idan ba su ji ba sai a yake su, dama kwanaki an tura masu da warning na farko, suka yi burus da shi tamkar basu ji ba. Jinjina kai Barden ya yi alamar gamsuwa da maganganun manya manyan cikin fada da kuma ƴaƴansa da kanin nasa, sannan ya rufe da cewa zai yi tunani a kan maganarsu. Miƙewa Jaish ya yi cikin girmamawa ya ce da mahaifin nasa zai shiga cikin gida ya ga Mommansa, dan da kewarta ya dawo. Jinjina mashi kai kawai Barde ya yi ba tare da ya yi magana ba. Nufar kofar da zata sada shi da cikin part ɗinsu ya yi. A tare gimbiya MieMie da Yah Jawad suka miƙe suka rufa mashi baya. Jerawa suka yi a tare, sai dai a tsakiya suka sanya Aunty MieMie, da haka suka nufi elevator da zata kai su izuwa part ɗin Mommansa. Sai tsokanar Jaish Aunty MieMie take yi wai ya ɗan yi ƙiba wannan tafiyar da ya yi, Dubai ta karɓesa sosai. Ko sannu bai iya ce mata ba, ya dai yi shiru yana jinta kawai, kamar wani gunki. Jawad ma da yake dama sun saba zama kamar kuramen, sai bai iya cewa komai ba, Aunty MieMie ce kawai take maganarta kuma ta bawa kanta amsa, dama ta iya sakosu a gaba kullum tana tsokanarsu a kan zata ga ta yadda zasu tunkari mace da sunan soyayya, bare ma shi Jaish sarkin kunya ga iya nuna halin ko in kula da iya yin banza da mutane, kullum idan suka haɗu suna hira sai ta saka shi a gaba wajen cewa zata ga karshen kunyarsa nan da lokaci kaɗan, zata ga zai iya cewa yana son mace ce ko zai tabbata babu aure, sai dai ya yi mata shiru kamar dai kullum, dan bashi da abin faɗa, maganarta ma sam bata shiga mashi cikin kunnuwansa. A haka har suka isa katafaren part ɗin Momma wanda ya fi na kowa kyau da ƙawatuwa a gidan, an fi zuba kayan alatu na more rayuwar sosai a cikin part ɗin, saboda ƴar sarki ce kuma jikan sarki, sannan matar sarki, bugu da ƙari kuma ƴaƴanta manya manyan biloniyas ne na duniya, Jaish ba ƙaramin mai kuɗi bane, babban kai ne wanda ake ji da shi na wuce misali, sannan ƴayƴun Mommar maza da mata dukkansu kamshaƙan masu kuɗi ne kuma masu muryar faɗa aji faɗin Dubai dama a sauran manya manyan ƙasashen duniya, hakan yasa take da gata na wuce misali, shiyasa part nata ma daban yake dana kowa. A saman wasu shegun luntsuma luntsumar sofas suka zauna, Aunty MieMie ta zauna a saman sofa mai zaman mutun biyu, Yah Jawad da Jaish ɗin kuma suka zauna a saman sofa mai zaman mutun uku. Kuyangu masu yi wa Momma hidima a part ɗin nata a kallah zasu kai goma, sai dai kuyanga mama Haulat ce kawai take iya shigo mata har cikin babbar parlournta, saura duk suna ta part ɗin kitchen da sauransu. A yanzu ma Kuyanga mama Haulat kawai suka samu a cikin katafaren parlourn tana aiki, ga wani haɗaɗɗen kamshi tare da sanyin Ac mai ratsa zuƙatar masu shaƙa dake tashi a cikin parlourn, ta ko'ina tsab tsab tamkar yanzu aka zuba komai na cikin parlourn, tamkar yanzu aka cirosu daga cikin ledarsu, white floor tiles nan sai wani ɗaukar idanu yake yi saboda haskensa, babu datti ko ɗigo, mayun tsabta ne, basa shiri da datti ko miskala zarratin daga Mommar har ƴaƴan nata, bare ma Omar, GUYSON suke ce mashi a gidan, saboda shegen iya ɗaukar wanka da gayunsa, mayen buga basketball kenan kuma sarkin shan coffee...... Ya dai kammala secondary school yana shirin dawowa mu dama da shi......😅 Mama Haulat tana ganinsu ta zube gwiwowinta a ƙasa ta hau kwasar gaisuwa. Aunty MieMie ce ta ɗan yi kokari wajen amsa mata kafin ta tambayeta ina Mamma?. "Ranki ya daɗe tana cikin bedroom nata a tare da auta gimbiya Zunaira". Ta basu amsa cikin rawar murya, tamkar ta yi masu laifi sun ce zasu hukuntata, duk ta firgice baiwar Allah. "Jeki sanar da ita cewa zan shigo". Cewar Jaish, ya yi maganar kasa kasa da wannan sexy voice ɗin nasa. A hanzarce ta amsa da toh cikin girmamawa, sannan ta miƙe da sauri ta nufi katafaren kofar da zai sadata da cikin luxury bedroom ɗin wanda kofar ma kawai abin kallo ne, tsadadden sosai. Irin wannan daula na part ɗin Momma tamkar ba za'a mutu ba, wani irin shegen king bed ne a cikin bedroom ɗin nata, yana da matuƙar girma bed ɗin, headboard nasa ya kai har kusan saman bangon, king bed ɗin nan ba kanana makudan dukiya Jaish ya zuba wajen sayarsa ba, daga ƙasar itali aka saye shi. Idan ka shiga cikin bedroom ɗin ma sai ka ɗauka ba'a duniya kake ba, ga wani hamshaƙin kamshin room perfume da yake tashi haɗe da daddaɗar sanyin Ac. Curtains dake jikin door and windows ma kawai abin kallo ne, baki ya yi kaɗan ya zayyano maku haɗuwarsu. Shinfiɗe wannan bed ɗin yake da shinfiɗa ta alfarma irin na gidan manya manyan sarakuna, komai na cikin wannan luxury bedroom ɗin launin dark ash and golden color ne, hakan ba ƙaramin ƙawata idanun mai kallo ya yi ba. Zaune Momma farar mace mai farar aniya, kyakkyawa kuma tauraruwar amaryar BARDE KING ZUHAIR ABDUL MALIK take a tsakiyar bed, shigar manya manyan ƴan gatan gimbiyoyi ne a jikinta, ga wani tsadadden alkyabba sky blue a jikinta, tana a sanye da hular alkyabbar a kanta, hakan yasa fuskarta bai bayyana sosai ba, ga shi ta sunkuyar da kai ƙasa tana kallon face ɗin Gimbiya Zunaira dake kwance a kusa da ita, ta tada kai da laps ɗin Mommar nata tana shafa jikin wani kyakkyawar wolf da yake a hannunta, wolf ɗin kyakkyawa ne sosai fari ƙal da shi, sai dai ɗan karami ne, amma yana da yelwar gashi sosai a jikinsa, hakan yasa Gimbiya Zunairar take jin daɗin shafa lallausan gashin jikin nasa. Sai hira suke yi tamkar ba uwa da ƴa ba, kamar wasu ƙawaye, Momma tana ta shafa wannan kyakkyawar dark black curly hair Zunairan, abin gwanin birgewa. Daga saman wani irin haɗaɗɗen luxury carpet wanda aka kawata samansa da wasu haɗaɗɗun throw pillows masu tambarin gidan sarauta Mama Haulat ta zube gwiwowinta a ƙasa, cikin girmamawa ta ɗan risinar da kai tana mai faɗin tana neman izinin yin magana. Cikin sanyin murya momma kyakkyawar mace mai farar zuciya ta tambayeta "Menene yake tafe dake Haulat?". . "Dama ranki ya daɗe Yah Jaish ne ya ce a sanar dake zai shigo". Tana magana tana ƙara risinar da kai, alamar girmamawa. Ai a dubu ɗari gimbiya Zunaira ta miƙe zaune daga kwanciyar da take jin Mama Haulat ta ambaci sunan Yah Jaish............ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 16/7/2024.....✍️📚🌹 For information 0816139058 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________15🔥 Ai a dubu ɗari gimbiya Zunaira ta miƙe zaune daga kwanciyar da take jin Mama Haulat ta ambaci sunan Yah Jaish. A hanzarce ta sauƙo kasa daga saman gadon, da gudu Wolf nata ya rufa mata baya, ɗan karami da shi gwanin ban sha'awa. "Haulat je ki ce mashi ya shigo". Momma ta faɗa cikin sanyin murya, sai dai fa ita ma voice ɗin nata akwai kaifin mulki a tattare da shi, dama kuma ai dole a samu haka, uba sarki, kaka sarki, sannan miji sarki, ai mulki ya gama bin jininta, fin haka ma za'a samu a tattare da ita, izza da isa take da taƙama a jininsu yake, bare dama su fa modarawa sun yi kaurin suna na wuce misali wajen nuna isa, izza da kuma zuciyar bala'i, jininsu a tafashe yake, basu yafiya kuma basa ɗaga ƙafa, amma fa sai an taɓosu, haka kawai basu faɗa. Miƙewa Mama Haulat ta yi tare da nufar waje bayan ta amsawa mommar da "Toh ranki ya daɗe Allah ya kara tsawon rai tare da nisan kwana farar mace mai farar zuciya". Ko sannu momma bata sake cewa ba, da alama ita ma dai so silent ɗin ce, alamu sun nuna gadon shiru shiru su Jaish suka yi. Gimbiya Zunaira kuwa tana fitowa parlourn bata nufi kowa ba sai wajen yayan nata, sai sakin uban murmushi take yi tamkar wadda aka yi wa albashir da kyautar gidan aljanna, baiwar Allah tana masifar son ƴan uwan nata, haka suma suna masifar kaunarta sosai. Tana zuwa ba tare da ta yi mashi magana ba ta faɗa jikinsa tana ƴar dariya har gaf teeth nata dake a tsakanin kyawawan fararen hakwaranta suka bayyana. Kyakkyawar hannunsa ya kai ya shafa kanta kafin ya ce. "Where's your hijab?". Ya yi maganar can kasa kasa. Tana mai cigaba da sakin ƙayatattcen murmushin nan nata mai kara fito da tsantsar kyanta ta bashi amsa da. "Na manta da shi a bedroom na Momma, ai tsabar murnar na zo na ganka ne yasa na manta, ina su mai ran karfe da su Yah Omar?". Shiru ya yi mata yana kallon face nata yadda take zuba murmushi, yana bala'in kaunar kanwar nan tasa, baki ma ba zai iya faɗar son da suke yi mata ba, saboda tana da kyan zuciya kamar dai Mommarsu Gimbiya Rahilarh kenan. "Auta wato Jaish kawai kika kallah a parlourn ko?". Cewar Aunty MieMie. Kwanciya ta yi a saman kirjin yayan nata tana faɗin. "Aunty MieMie yanzu fa Yah Jaish shi ne sabo, ke ba ɗazun da muka baro wajen uncle Abbas na je wajenki ba? Shi kuma Yah Jaish yanzu ya kai almost 2 weeks fa ban ganshi ba, ki bari na gama ganinshi sai na zo wajenki". "Kina da gaskiya". Cewar Yah Jawad. Mama Haulat ce ta katsesu da cewa tana neman izinin yin magana. Daga Jaish har Jawad babu wanda ya amsa mata, ko kallon in da take ma basu yi ba, su fa idan na ƴan uwansu ba to kowa a ƙasƙance mara galihu suke kallonsa. "Haulat me Momma ɗin ta ce?". Cewar Gimbiya Aunty MieMie kenan. "Yanki ya daɗe ta ce Yah Jaish ɗin yana iya shigowa". Jinjina kai kawai Aunty MieMie ta yi ba tare da ta sake ce mata ko sannu ba, sai dai ta ɗaga mata hannu alamar zata iya tafiya ta basu waje. Da gudu Wolf ɗin Auta ya zo ya haye jikin Jaish ɗin shi ma, ya manne da auta gam abinsa. "Ɗagani na tashi baby". Cewar Yah Jaish. Da sauri ta miƙe tsaye rike da ɗan Wolf nata dan su bashi damar ya miƙe ɗin shi ma. Tashi ya yi cikin nutswa ba tare da ya sake yin magana ba ya nufi katafaren kofar da zata sada shi da cikin bedroom ɗin. Da ido Jawad da Aunty MieMie suka bishi, basu ce da shi ko ubban ba, kuma basu da niyar tashi su bi bayansa, da alama su ba ganin Momma suka zo yi ba, sun rako shi ne kawai, kuma sai suka kyale shi ya shiga shi kaɗai, dan ɗa da uwa akwai sirri a tsakaninsu. Komawa jikin Aunty MieMie auta ta yi ta haye saman laps nata tare da kwanto da kanta a saman shoulder ɗinta tana murmushi. Da ɗan karfi Aunty MieMie ɗin ta ja dogon hancin nan nata har sai da autar ta ce. "Wash Allah na Aunty MieMie kin cire mun hancina". "Dama ai hancin naki ya yi tsawo sosai, gara na rage maki shi". Aunty MieMie ta bata amsa. Ɗan kawar da kai Jawad ya yi yana faɗin. "Aunty MieMie baki nemi zaman lafiya ba, ki rasa hancin wanda zaki rage a gabaɗaya gidan nan sai na babyn daddy?". Ya kai karshen maganar yana miƙewa tsaye saboda call ɗin da ta shigo mashi cikin wayarsa a yanzu. Karar wayar kawai ya ji, tun bai duba ya ga wanene mai kiran nasa ba ya miƙe kamar yasan mai kiran nasa already. Kofar fita daga parlourn ya nufa, da yake kofofin da naura suke aiki kuma suna amfani ne da motsin ɗan adam, yana zuwa wajen kofar ta buɗe kanta da kanta. Waje ya nufa ba tare da ya ce da Aunty MieMie ko uppan ba. Yana fitowa suka haɗu da Gimbiya Chuchu da ta fito daga cikin elevator a yanzu, ita ma wajen Momma zata je, dama renon Mommar ce ita, shiyasa kuka ga ta fi shaƙuwa da Gimbiya Zunaira sama da kowa a cikin gidan, a part ɗin Momma ta saba zama time da take karama, da ta girma ne ta koma part ɗin Akka, sam bata son zama a wajen mummy wato mamarta sosai, baiwar Allah da alama zama da Momma mace mai farar zuciya ne yasa ita ma take da saukin kai duk da bata kai Zunaira ba. Kamar dai kullum aikin da aka saba, tana fitowa daga cikin elevator ta fara ɗaukar kyakkyawar fuskarta a hoto da wayar Fanan da yake a hannunta, idan baku manta ba Yah Jawad ɗin ya kwace nata wayar, hoto dai ba zata fasa ɗauka ba, abin ya bi jininta, ita da ko barci ta tashi sai ta kashewa kanta hotuna kala kala bare kuma ace ta yi wanka ta yi kwalliya, ai abin ba'a magana, shi ne har da aro wayar Gimbiya Fanan. Tana aikin ɗaukar hoto tana tafiya, sai turo ɗan bakin nan take tana canza style kala kala, sam bata lura da mutun yana zuwa ba, da yake yanayin takalmar kafafunsa smooth shoes ne, irin na yawo a cikin gidan nan, suna da laushi sosai ta yadda sam basu kara idan mutun yana tafiya, hakan yasa sam bata ji tahowarsa ba. Shi kuwa tun da ta fito daga cikin elevator yake kare mata kallo, ta canza shigar da yake a jikinta ɗazun izuwa wasu haɗaɗɗu kuma tsadaddun kayan, dama ita ƴar wanka ce, ga masifar san kwalliya, kamshi da kuma gyaran jiki kamar me. Sai tinkarosa take yi kallonta na a kan screen ɗin wayar, sam bai kauce mata daga hanya ba kuma bai yi mata alamar tasan mutun yana gabanta ba. Karo suka yi ta bugu da faffaɗar kirjinsa a in da wayar Fanan ɗin ta faɗi ƙasa saman beautiful tiles ɗin, ji kake tas karar wayar. A razane ta ɗago da kallonta izuwa kansa, dan taga wanenen?. Shi kuwa ɗaure fuska sosai ya yi tamkar bai san me ake cewa sakin fuska ba bare murmushi. Ganin shi haka yasa ta yi wani irin ja da baya, murya na rawa ta fara cewa. "Kayi hakuri Yah Jawad wlh ban ganka bane, kuma......". Bata kai karshe maganar ba ta dakata sakamakon wani kallo mai kama da harara da ya watsa mata, shi dai bai san ya zai yi da Chuchu da Sarina a kan waya ba, su biyun nan idan suka rike waya sai sun baka haushi, bare ma ita chuchu mayyar hoto da videos, kana zaune baka sani ba sai dai kaga ta ɗaura maka camera a fuska tana yi maka video kamar ka aiketa, ita kuma Sarina mayyar chatting ce, shi ne yasa Yah Jawad ɗin ya kwace wayoyinsu ɗazun, sai kuma gata dana Fanan ta karɓo, kai Allah mai iko, yanzu haka idan ya karɓi na Fanan ɗin ma anjuma na Mummy ko Momma or Akka zata ɗauko, na Akka kuwa bai isa ya kwace ba, dan bala'in tsohuwar nan ba iya ta zai yi ba! Zaman ka lafiya kada ka bari Akka ta kamaka ka yi laifi, idan hakan ya faru ka shiga talatin, ta in da take shiga ba ta nan zata fita ba, ta iya faɗa. Irin dai faɗa na normal tsofaffi da jikokinsu. Shiru ta nutsu tana muzurai kamar wata maras gaskiya, sai wani ƴan kame kame take yi. Shi kuwa ya kafeta da ido yana tunani wai me zai yi ya raba yaran nan da cutar waya ne? Dan wayar ta zama cuta a garesu. Kunsan idan ana kallon mutun duk sai ya rasa nutsuwarsa, ko da kuwa kallon mutunci da soyayya ake yi wa mutun yana rasa nutsuwarsa bare kuma kallon neman kalar hukucin da za'ayi wa mutun, ai kunsan dole Gimbiya Chuchu ta tsargu ta rasa nutsuwarta sosai. "Wayar waye wannan?". Ya tambaya calmly kamar mai ciwon baki. "Am.....inm...... Wayar Aunty Fanan ce..." Tana magana words ɗin suna rarrabewa saboda tsoro. Miƙa mata hannunsa ya yi akan ta bashi wayar ba tare da ya sake yin magana ba. Jiki na kerma ta tsugunna kasa ta ɗauko mashi wayar tare da miƙo mashi ita. Bai kai ga karɓa ba call ya sake shigowa wayarsa da take a cikin aljihunsa, kira ta ɗaya da ta biyu duk sun katse, yanzu na uku ne ya shigo. Burus ya yi da call ɗin da ta shigon ɗin, ya kai hannunsa ya karɓi wayar da Chuchun take miƙa mashi, sannan ya ce. "Anjuma ki sameni a bedroom ɗina". Yana gama faɗar hakan yasa kai zai wuce ta. A hanzarce ta matsa ta bashi hanya. Wucewa ya yi ba tare da ya sake kallon in da take ba. Tsayuwa ta yi tana bin bayansa da kallo ranta a cike tab da takaicin abin da yake yi masu na kwace masu wayoyi ya hanasu sakata su wala, ji take kamar ta je ta ja kunnen nan nasa ko zata huce takaicin da yake a cikin ranta. "Allah Yah Jawad ɗin nan ya iya mugunta". Ta faɗa a fili tare da murguɗa baki kafin ta wuce ta nufi kofar shiga parlourn Momma. Shi kuma Jawad elevator ya hau zuwa second step. A ɓangaren Jaish kuwa, ɗan bakin nan nasa a ɗauke da sallama kasa kasa ya shigo cikin bedroom ɗin na Momma. A wannan karon bata a saman bed nata, ta sauko kasa samar shinfiɗin alfarma da ake yi wa gimbiyoyi a cikin bedroom nasu dan hutawa, yanayin shinfiɗin kamar da gashin ɗawisu ake yinsu, amma kuma ba gashin ɗawisu bane, carpet ne na alfarma da ake kyarasa haka kamar da gashin ɗawisu, ga bala'in laushi, sai tashin kamshi yake yi, sannan an zuba mata throw pillows manya manyan a saman shinfiɗin, dan kishingiɗa aka zuba mata su idan zata kishingiɗa sai ta yi amfani da su, ta fito a ainahin cikakkiyar gimbiyarta, alkyabbar yana kara fitar mata da kyanta sosai. Kusa da wani throw pillow dake a gabanta Jaish ya ƙariso ya zauna a saman shinfiɗar da take ɗin kenan. "Sannu da hutawa Momma". Ya faɗa kansa na'a ƙasa yana kallon shinfiɗar, dama na gaya maku muguwar kunya ke gare shi, sam baya son haɗa idanu da mutane. Gyara zamanta ta yi a in da ta kara dakewa a cikin alkyabbar. "Jaish ka dawo lafiya? Ya gajiyar hanya ya kuma ka baro mun su Abbana?". "Kowa yana lafiya Momma, and suna gaisheki sosai". Bawan Allah ko part nasa bai leƙa ba, yana dawowa kawai iyayensa ya fara buƙatar gani, sune sama da komai a garesa, baya wasa da su kuma bi haɗasu da kowa ba, idan ba ya zo ya gansu ba ko wanka ba zai iya zuwa ya yi ba, shi ne yasa ya fara da fada ya duba daddynsu sannan ya taho wajen Mommansa, a kullum idan ya dawo daga tafiya haka ko daga office sai ya bisu ɗaiɗai ya fara duba suna cikin aminci kafin ya tafi ya je ya yi abin da zai yi. "Ina amsawa ina Omar?". Ta yi maganar tana kai hannunta saman kyakkyawar bakin gashin kansa, a hankali ta fara shafa kan nasa tana saka mashi albarka. "Baka je part naka ba ko?". Ta sake jefo mashi wata tambayar tana mai do da kallonta a saman kyakkyawar face nasa. Nisawa ya yi kafin ya bata amsa da. Omar yana gidan uncle Rahab babban yayanta kenan, sai ku ya ɗaura da cewa. "Ban je part nawa ba, ai kinsan ba zan iya zuwa ko'ina ba har sai na zo na ganki". "Allah ya yi maka albarka my son, ina alfahari da ku". Da amin ya amsa mata kafin ya ce. "Momma kina lafiya ba wata matsala in wuce part nawa?". "Lafiyata lou Alhdulillah nake, amma da ka je gidan Yah Rahab ya kasami su Jannat?". Shiru ya ɗan yi na a kallah one mint kafin ya ɗago da kallonsa ya ɗan kalli face nata kaɗan, sannan ya sake sunkuyar da kan nasa ƙasa, sai ƙoƙarin tuna su waye kuma su Jannat a duniyar nan yake yi? Amma ina ya kasa tuna su waye su, dan bai ma san da su ba a duniya, ƴaƴan uncle ɗin nasa ne da shi bai ma san da zamansu a duniya ba, su kuwa sun san da shi, har ma sun saka shi a cikin zuciyoyinsu, dan muguwar farin jinin ƴan'mata ke gare shi sosai, duk in da ya shiga sai ya shiga can cikin zuciyoyinsu, amma shi sam baya kula kowa. E babbar magana kenan, lallai Jaish ka cika cikakken ɗan duniya, ƴaƴan uncle ɗin nasa ne ma bai sansu ba. "Ba dai su ma su Jannat ɗin baka sansu ba kam?". Ta yi maganar tana aikin kallon face nasa da ya wani sunkuyar da kai ƙasa. "Momma i don't know them". Ya bata amsa yana kai hannunsa ya riƙo nata guda ɗaya a cikin nasa. Shiru ta yi a kan maganar su Jannat ɗin, dan tasan fin haka ma zasu aikata, dama ta yi sa'a suka san uncle Rahab ɗin kenan, kaɗan daga aikinsu su ce basu san sauran uncles ɗin nasu ba. "Mommana zan iya tafiya?". Yana magana ya ƙoƙarin cire mata wani dankareran tsadadden diamond ring da yake manuniyar yatsarta, zoben ya kama mata yatsa sosai ne, har ya fara cin namar jikinta. "Meyasa zaka cire mun? Zoben Ummiee na ne fa". "Ummm shi ne yasa kika ki cirewa har ya fara cin maki namar jikinki ko? Tom ni dai ba zan iya ganin shi yana ƙoƙarin cutar mana da ke na barshi ba, zan cewa Ummiee ta aiko maki da wani, dan nasan nata daban ne". Ya kai karshen maganar tare da zare ring ɗin a hankali cikin dabara ta yadda ba zai yi mata zafi ba, tamkar ma bata san an cire ba, duk da kuma yake ya kama jikinta. Murmushi kaɗan ta yi a cikin zuciyarta tana ƙara godewa Allah da ya bata ƴaƴa masu matuƙar kaunarta har haka, sun san farincikita ko bata gaya masu ba, haka zalika sun san bakin cikinta ko bata bayyana masu ba, sun san abin da take so da wadda bata so. "Momma zan je na yi wanka na ɗan yi barci, inason gobe na fita office da sassafe, kinga almost 2 weeks bana nan, so yakamata na je office gobe dan naga me ake ciki". "Jaish barci yamman nan fa bashi da kyau, idan ka yi shiri yanzu zaka tashi da ciwon kai". "In Sha Allah zan kiyaye, but now am feeling to much of sleeping, zan yi kaɗan kin ji mommata?". Ya yi maganar in a low voice sosai!. "Tom shikenan, ka kula sosai Allah ya yi maku albarka". Da Ameen ya amsa mata kafin ya miƙe tsaye rike da ring ɗin nata, sannan ya nufi kofar fita da wannan taku nasa cikin nutsuwa haɗe da fadanci. Da idanu ta bishi har ya fice daga cikin ɗakin, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana mai kara godiya ga Allah a cikin zuciyarta. Yana fitowa ya iske Aunty MieMie da Gimbiya Chuchu and Zunaira suna ta hirarsu, Yah Jawad baya wajen, tamkar zai tambayi Aunty MieMie ina Jawad yake? Sai kuma ya fasa tambayar yasa kai kawai ya wuce ba tare da ya bi ta kansu ba. Ita ma Aunty MieMie bata ce mashi ko uppan ba, dan tasa da wuya ya amsa mata, Gimbiya Chuchu dama saboda ance mata yana cikin ɗakin ne yasa ta nemi waje a parlourn ta zauna, dan haka yanzu yana fita ta yi maza ta miƙe ta nufi cikin ɗakin da murnarta. A hanzarce auta ta miƙe ta rufa mata baya, suka bar Aunty MieMie ita kaɗai, gyarawa ta yi ta kwanta a samar sofar tare da fito da wayarta ta fara latsawa. Dai'dai Jaish zai shiga cikin elevator wasu kyawawan ƴan samari suka fito daga cikin elevatorn, kyawawa ne sosai, da gani ba tambaya ƴaƴan Gimbiya Rahilarh ne, wato Momma. Ƴan samari ne da basu fi 13 years ba a duniya, kana ganinsu kaga twins, saboda tsannin kamannin da take a tsakaninsu ta yi yawa, ba zaka iya banbantasu ba, idan ka gansu ma zaka ce mutun ɗaya ne, dan fa komai sak suke kama. Suna ganinsa suka ɗan ja da baya suna mai risinar da kai. "Good afternoon Yah Jaish, ka dawo lafiya?". Suka haɗa baki wajen faɗar hakan. Tsaresu da idanu ya yi ba tare da ya yi magana ba. Nan take suka sha jinin jikinsu suka fara ƴan kame kame. Obaid ne ya ce. "Wajen momma zamu je dama". Sai kace an tambaye shi, tsabar tsarguwa ce kawai, da gani sun aikata wani abin da ba dai'dai ba, dan wlh idan kana neman ƴan rigima ƴan haɗa cakwakiya fitinannu marasa jin magana idan ka samesu kai kam ka gama komai, su ɗin number one ne a harkar rashin jin magana, sam basu son zaman lafiya, idan ƴaƴan sarakuna suka zo neman auren Gimbiya Sarina da Fanan, to da su Gimbiya Sarina take haɗa baki su kulla munafurci su kori ɗan sarkin, yanzu sau uku ƴaƴan manya manyan sarakuna daga masarautu daban daban suna zuwa neman auren Sarina ɗin, amma duk ta haɗa baki da su Obaid ɗin ta kori samarin, a cewarta babu class nata a cikinsu, suna da wani uncle mai suna Taheer kanin Mama wato matar king ta biyu, wannan uncle Taheer ɗin mutun ne mai izza da ji da kai bala'in girman kai na wuce misali, tun yana ƙarami yake cikin masarautar, yana nuna isa da zafin rai, ga jarumta, amma duk da haka sai da ranar su Obaid suka kusa saka shi kuka, kuma har yau babu wanda ya gane su suka yi mashi wannan ɗanyen aikin, kuma Sarina ce ta saka su, dan uncle Taheer ɗin yana bata haushi, yana takura mata da faɗa akan ta yi sallah ta dai'na taɓa waya, shi ne nan ta je ta sanya wata kuyanga daga cikin masu yi mata hidima ta ɗebo mata wani irin azabbabben mai mai zafi da aka rubuta rob a jikinsa, ɗan iskan zafi ke gare shi, haka ta kawo mata, saboda rashin imani ta saka su Obaid suka san ta yadda suka yi suka zubawa uncle Taheer ɗin wannan rob ɗin a towel da zai goge fuskarsa idan ya yi wanka, haka kuwa aka yi, dama ga shi jajir da shi kamar tsada, ai kuwa yana goge fuskarsa da towel nan ya kara yin wata uwar ja fuskar tasa, nan take face ɗin nasa ta yi ruɗu ruɗu kamar wadda ya sha marika a hannun maza irinsu commander ZAFAR, kan ka ce me idanuwansa sun yi jajir kamar jini, fitsari ne kawai bai saki a wando ba ranar, saboda azaba, sai da ya kwanta a gadon asibiti, saboda rub ɗin tana da azaba sosai, ga shi sun zuba dayawa a jikin towel ɗin. Ƴan albarkar ƴaƴa har yau ba wanda ya iya gane su suka yi wannan aika aikar, sun iya haɗa sharri kamar ba jinin gimbiya Rahilarh ba su kam, babban abin haushin kuma muguwar shiga rai ke gare su, wlh idan ka gansu sai sun yi mugun burgeka, ka ji duniya kana kaunarsu, ga shi kuma idan suka yi laifi aka kamasu to fa ba za'a taɓa iya banbance wanene ya yi laifi a cikinsu ba, saboda tsananin kamar da suke yi, sai su yi ta rai'nawa mutane wayo, wannan ya ce wannan ne, wannan ma ya ce wannan ne, haka suke ruɗar da mutane. "Me kuka aikata?". Shi ne tambayar da Yah Jaish ya wurga masu. Kallon juna suka yi, a tare suka haɗa baki wajen cewa. "Yah Jaish bamu yi komai ba, daga part ɗin mummy fa muke" Sam bai yarda da maganarsu ba, dan yasan hali, yasan basu zama shiru, basa ji, auta da take kanwarsu 11 years ma tana nan nutsatsiya kamar wata waliyiya, amma banda su, ba dan ba dan ba da na ce waɗan nan renon shaiɗan ne.......😅 "Idan na ji kun aikata wani abin Allah sai jikinku ya gaya maku". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya shiga cikin elevator abinsa. Tsayuwa suka yi a wajen har sai da suka ga tashin elevator, sannan suka kalli juna suka kwashe da dariya a tare kamar wasu munafukai, tamkar masu aljanu a tsakar ka. Dariya harda rike ciki suka yi, tamkar basu ne yanzu suke muzurai a nan ba. Sai da suka yi mai isarsu sannan Omaid ya ce. "To mu idan ma mun yi laifi za'a iya gane mu ne? Ai ƙwaƙwalwar Star ne da mu, ba tunanin boss muke da shi ba, dan boss ne yake da ɗoɗaɗɗen ƙwaƙwalwa, a film kullum cikin rashin nasara yake saboda tunaninsa na banza, kullum shi ake kashewa ba actor ba, kafin mu yi abu sai mun yi tunani irin na actor, sai mun nemo hanyar da baza'a taɓa gane mumuka yi ba". Dukar wasa Obaid ya kai mashi a shoulder ɗinsa yana faɗin. "Amma kasan dai Yah Jaish and Yah Jawad they're acting like actors ko? Suma ba tunanin boss suke da shi ba, tunanin actors ke gare su, wlh tun da sun dawo sai mun kara dogon tunani ta yadda zamu rinƙa zulle masu". (Ka ji wani zance, wai masu 13 years ne zasu yi wa mai 25 years wayo😂 kai jama'a su Obaid basu da kirki, kaɗan fa suka samu gadon kaifin ƙwaƙwalwar King Zuhair, amma har suke ƙoƙarin yiwa manyan kai waɗan da su suka gaji ƙwaƙwalwar da gaske wayo fisabilillahi 🤌😂 lallai kuna ruwa, mu muna gefa idan suka riƙeku zaku san cewa tunanin actors kuke yi, amma fa da gaskiyarsu, suna da kaifin basira sosai wlh, sun iya saka mutun a tarko su zulle su barshi) "Kai Obaid mu wuce ciki hai, kada Yah Jawad ya isko mu a nan, kasan dai tun da ka kalli Yah Jaish ya wuce to Yah Jawad yana bayansa, dan kasan basu rabuwa, kullum suna a tare". Ya kai karshen maganar tare da wucewa izuwa wajen kofar shiga cikin parlourn Mommar. Da sauri Obaid ya rufa mashi baya, suna sanye ne fa da fararen jallabiyas tas kamar wasu limaman masallacin jumma'a, amma kun ji irin tsiyar da suke surfawa!. Yah Jais kuwa kai tsaye cikin wani luxury part ya nufa, idan kun ji ance luxury ai ƙarshen haɗuwa kenan, baki ba zai iya faɗar haɗuwar ba, ya ji komai ya more rayuwa wadda duk min girman burin ɗan adam aka bashi nan to sai ya mance da cewa a duniya ma yake. Akwai kuyangu biyu dattijawa da suke kula da part ɗin nasa, sune suke yi mashi gyare gyare da komai da komai, ɗayar ta fi manyata, dan zata kai 45 years a duniya, ɗayar kuma bata da wani girma sosai, bata wuce 35 to 40 years ba, sun san kan aikinsu sosai, kasancewar sun sansu da balai'n son tsafta yasa suke zagewa su yi aiki babu kakkautawa, ko'ina sai sun gyara, su goge su sake gogewa, dan sun san idan Jaish ya sami datti komai ƙanƙantarta to fa bala'i ne zai tashi ya tsaya a cikin gidan, hakan tasa basu wasa kuma basu ƙasa a gwiwa wajen ganin sun yi aiki yadda yakamata, shiyasa part ɗin take tamkar sabuwa, komai very very clear gwanin ban sha'awa, ga uban daddaɗar kamshin da yake tashi tun daga dosowar mutun part ɗin zai bule shi. Komai na cikin part ɗin launin milk color ne, sai ɗan ratsin ash a jikin tsadaddun curtains ɗinsa. Bed da yake kwanciya duniya ce guda, abu kamar ba za'a mutu ba, irin wannan daula. Yana shigowa kuyangun suka zube ƙasa a saman gwiwowinsu suna kwasan gaisuwa tare da zuba mashi kirari na ɗan sarki jikan sarki takawarka lafiya toron giwa, zaki kake kafi karfin kananun namun dawa, irin dai kirarin da ake yi wa Barde suke yawan yi wa ƴaƴan nasa ma. Ko kallon in da suke bai yi ba bare asa ran zai yi magana, cikin luxury bedroom ɗinsa kawai ya wuce abinsa, sai a lokacin ya tuna da cewa ya bar laptop nasa a cikin mota, dama kayan sakawa kam baya tafiya dasu, dan Dubai gida ce a wajensu, kamar yadda yake da part nasa a cikin masarautar nan tasu da komai da komai, to haka yake da shi a can masarautar kakan nasu ma, so idan ya tashi tafiya Dubai ɗin baya ɗaukar ko tsinke na kayan sakawa, tafiyarsa kawai yake yi, haka dawowa ma. Raba kansa da kayan jikinsa ya fara yi daga shiga cikin bedroom ɗin, waɗan nan kuyangu nasa sun iya gyara, katafaren bed ɗin nan nasa ya sha shinfiɗa ta alfarma ta wata dankarariyar luxury bed sheets, ga wata haɗaɗiyar duv mai girma sosai, idan ka haye saman bed ɗin nan ma ai ba za'a gane da mutum a wajen ba, saboda girmansa ga laushi over. Haɗaɗɗen toilet ɗinsa ya nufa dan ya yi wanka, tas ya cire kayan jikinsa ya rage daga shi sai short, yana da kyan surar jiki sosai kamar shi ya yi wa kansa. Bayan ya yi wanka cikin kayan shan iska ya shirya, ya yi wa kayan matuƙar kyau sosai, singlet ce and short, sannan ya haye saman katafaren bed nasa yana wani lumshe idanu, sai zuba kamshi yake yi, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi. After some hours. Babbar parlourn King Zuhair, wajen da suke haɗuwa su ci abinci kenan. Hayaniya ne yake tasowa a cikin parlourn ba kaɗan ba, tun daga nesa suke ta aikin kace na ce. Gabaɗaya su Momma suna a saman haɗaɗɗen family dining table nasu dake dining room a cikin parlourn, abincin dare suke ci, King bai fito ba tukun nan, yana cikin bedroom nasa, Jaish da Jawad basu wajen, daga Momma, Mama, Mummy, sai su Sarina, Fanan, Zunaira, Chuchu, Aunty MieMie, Aneesa ƴar Mama kenan, Akka ma bata kai ga ƙarisowa wajen ba, tana part nata, sai Obaid da Omaid da suma suke wajen. A dukka faɗin girman KINGDOM OF POWER kuyanga guda ɗaya king Zuhair ya aminta da ita da ta kula masu da shashin abincinsu, kakkarfar macece mai jini a jikan nan, idan ka ganta sai ka rantse da Allah ta karɓi horo waje commander ZAFAR, irin matan nan ne da ake cewa mace mai kirar maza, gata doguwa samɓal, akwai kuyangu biyu da suke tayata aiki irin goge goge kitchen da sauransu, ita kuma ita kaɗai aka yardanwa da ta yi masu girki, sannan ita kaɗai take serving nasu abinci. Amma abin da baku sani ba shi ne, ita fa Gimbiya Rahilarh ranar da king yake ɗakinta ita take yi mashi girki da kanta, hakan yana ɗaya daga cikin abin da yasa yafi sonta, saboda tana nuna mashi cewa yana da kima da girma tare da daraja a idanunta, tana nuna mashi cewa ya fi mata komai a duniyar nan, kunsan maza da shegen sun respect, nan take king ya zama mata kamar baby, ga shi dai zaki ne a waje, amma a cikin gida wajen Gimbiya Rahilarh ba'a magana, na yi shiru kada su jini a miƙa ni wajen commander ZAFAR ya ragargaje mun baki na rasa na shan Maltina mai sanyi. To wannan kakkarfar kuyanga mai suna Zubaida ita kaɗai ta samu damar iznin shigowa cikin parlourn king ta yi serving na family, sun aminta da ita sosai, so abin da ya tayar da hayaniya a dining room ɗin yanzu ba komai bane fa ce rigima a tsakanin Mama da Momma, Mama da Momma sam basu shiri, basu haɗuwa inuwa ɗaya, tamkar wuta da audiga suke, Mamma izzar bala'i ke gareta, ga shege nuna isa da iko, sai ta nuna kamar ita ce uwar gida ta fi kowa iko a gidan, kuma ba ita ba ce uwar gida Mummy mahaifiyar Gimbiya Aunty MieMie ce uwar gida, amma da yake a tare king ya auresu sai mamar take ganin ai babu abin da Mummyn ma ta fita da shi, so ita ma uwar gida ce, dan haka dole a sanyata a tsagin da za'a sanya Mummy. Kun san fa uwargidaye daban suke, koma ina za'aje azo sune ke da gida, ko rabuwa ka yi da uwargidanka wlh baku rabuba, in dai kuna da yara to ko zaka mutu ita ce kai, ko ka saketa ita ke da iko da kai, ka jira girman yaranta kawai malam kasha mamaki......😅 Shiyasa ake son murza kambun uwar gida, dan a gaskiya ita ɗin daban take musamman idan ta haihu a gida, ai hajiyata ki ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ki sha kuruminki tare da bin ƴaƴan nan naki da addu'a, duk wadda zata zo wlh daga baya ne, ko ya sakeki kece shi idan bai sani ba wahalar kawai ƴaƴan su girma ne! Mama dai ta dage ita ma uwar gida ce........ Allah mai iko 😅 Amma kuma Mama basu taɓa yin rigima da mummyn ba sai da Momma, saboda mummy mace ce da ko ka yi abu ma bata ɗaga idanu ta kalle ka, sau da dama Mamar tana takalarta da faɗa, amma ko kallon in da take bata yi, ita kuma Momma ainahin jinin Modarawa ne kada ku manta, basu barin kota kwana, hakan yasa bata bari idan Mama ta yi mata abu, abin a jininsu yake, kada kuga laifinta ku fara bincikar tarihin modarawa ku ji, basu yafiya. Abin da ya faru yanzu bayan sun zauna a saman table za'a fara cin abinci, sai Momma ta ce da kuyanga Zubaida ta zuba mata abinci kafin king ya fito, ta zaɓi kalar da take so a zuba mata, da yake mama sarkin neman magana ce, sai ta yi maza ta ce ai ina a matsayinta na babba bata bada damar kowa ya ci wani abin ko abinci ba har sai king ya fito ko ruwa bata bada izinin a sha ba, yadda kuka san ita ce ta ajiye kowa da yake a saman table ɗin, shegen son girma ke gateta. Jin haka yasa Gimbiya Aunty MieMie ta sanya baki, dan ita ma irin king ce, ba'a tauye hakkin wani a gabanta ta yi shiru, sai ta ce. "A'a Mama, Momma fa tana son cin abinci, kin sani ne ko yunwa take ji sasoi? Kuma ai shi daddy bai ce idan mun hau saman table mu rinƙa jiransa ba, mu ne nan muka ɗaurawa kanmu jiran nasa da muke yi kullum, dan haka idan wani yana jin yunwa yana da damar da zai ci abinci kafin dad ya fito, Zubaida ki zubawa Momma abin da ta buƙata yanzun nan ba tare da ɓata lokaci ba umarni nake baki!!". Shikenan daga yin wannan magana Mama ta tada bala'i wai Aunty MieMie ta rainata dan ba ita ta haifeta ba! To daga nan ne fa abin yake ƙoƙarin zamar masu faɗa, dan kusan dukkansu sarakan zafin kai ne, Mummy ce kawai so silent da bata saka masu baki a cikin hayaniyar tasu ba, amma Momma ma ta saka baki, dan ta ce bata ga dalilin da zai sa Mama ta ce bata bada izinin a zuba mata abinci ba, wacece ita? Ko Mummy da take uwargida ran gida ma bata isa ta hana su cin abinci wai dan king bai fito ba bare kuma ita Mama, bata isa ba!! izza+izza ne yake aiki a nan. Mama dai ta ce ta isa har ta yi yawa, dan haka dole a bi umarninta ko anki ko anso!!. Toh fa, dama ai ita da Momma ba'a shiri sam, basu haɗuwa waje guda!!. Ita dai kuyanga Zubaida an sakata a cikin code, ga umarni gimbiya Aunty MieMie da kuma Momma sun bata a kan ta zuba masu abinci su ci, ga kuma umarnin da Mama ta bata na kada ta yarda ta zubawa kowa komai har sai king ya fito..... Wannan shi ne cakwakiya, tana tsaka mai wuya baiwar Allah, ta rasa zancen waye zata bi!. Ga shi King kuma ya ce shi da kuyanga Zubaida kawai ya yarda, ita kaɗai zata rinƙa yin serving nasu abinci, babu wasu kuyangun da zasu zo masu kan abinci, baiwar Allah Zubaida tana ganin rayuwa, ita kaɗai take aikin zubawa wannan ta zubawa wannan, idan bata yi sauri ba su hauta da faɗa musamman Gimbiya Sarina da twins Obaid and Omaid sun fi kowa rashin kirki a cikin gidan...... Familyn king sun fara nasu kala kalar tsiyar, bari na haɗa kayana sai zuwa gobe muga ya za'ayi da wannan rikici na Mama da Momma, ga Kuyanga Zubaida dai a cikin wani hali, duk wanda bata bi umarninsa ba ta shiga uku, to ita ya zata yi da ranta kenan? Izza sam bata yi ba a rayuwa 😌 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 17/7/2024.....✍️📚🌹 For information 0816139058 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________16🔥 Momma dai ranta ya ɓaci sosai, hakan yasa ta miƙe da nufin ta bar parlourn dan ma kada su yi ɓatattciya, kuma ta sanya a ranta idan ta fita daga cikin parlourn nan ta dai'na cin abincin a wannan dining room ɗin kenan, sai dai wani, dama saboda mijinta take zuwa part ɗin nasa, shi ya tsara wannan tsari na a rinƙa haɗuwa a part ɗin nasa ana cin abinci. Bata kai ga motsawa daga in da take ba suka ji gyaran murya daga bayansu. Ko basu juya ba sun san wannen, kuma sun san halinsa fa, shi ɗin ba uba bane mai wasa, baya ɗaukar wargi, yana da wasa da dariya da ƴaƴan nasa, amma baya taɓa bari su wuce iyaka, ba sai na sake faɗa ba kun san shi da zafin rai ga iya adalci!. Jin gyarar muryarsa yasa kowa ya nutsu tsit, dama can basu saba irin wannan kace na ce ɗin ba, bama sa yi, yau ɗin ma Mama ce ta tada wannan balli, kamar wadda aka yi wa wani laifi ta zo zata huce a kansu, shi ne ya kunna wannan wutar, amma fa da gasken gaske mama da Momma basa shiri, basu zama waje guda, sai dai basu kace na ce a tsakani, iya dai kiyayyar ce kawai da harare hararen juna sai ɗan abin da ba'a rasa ba, sai kuma time to time idan sun haɗu Mama ta yaɓawa Momma ɗin magana. Ƙarisowa cikin room ɗin King ya yi, jikinsa na'a sanye da jallabiya fara kal, sai zuba uban daddaɗar kamshi yake yi kamar anyi ɓarin turare a jikin nasa. Saman dining chair ɗin aka ware mashi mai kwalliyar sarakuna ya zauna, komai nasa daban yake, harta bed nasa mai ɗauke da tambarin sarauta ne, saboda fa mulkin kingdom of power mulki ne mai matuƙar karfin gaske, suna da karfin iko da muryar faɗa a ji a duniya, ba mulki bace ta kananar kai, ba sa a ƙarƙashin kowa, sai dai ma jiga jigan masarautu dake a ƙarƙashinsu suna mulkarsu, kuma dole ayi masu biyayya! Idan ba haka ba commander ZAFAR ya busa busoshin yaki a tashi ƙasa! Wasu masarautu ma ba dan Allah suke yi masu biyayya ba, dan tsoron horarrun jiga jigan dangerous warriors nasu suke yi. Komawa Momma ta yi ta zauna ranta duk a ɓace. A gaskiya King Zuhair kyakkyawan balarabe ne na gasken gaske, da ya cire wannan rawanin naɗin sarautar tasa sai tsantsar kyan nasa ta bayyana, ai dole ma ƴaƴansa su yi gadon kyau, ga dimple nasa gwanin birgewa, kaɗan zai ɗan motsa bakinsa kuga ta lotsa, ga shi jajir da shi kamar Akka, yadda kuka san ku taɓa shi jini ya zuba, madarar kyau ce babu mix!. Kallon Mummy king ɗin ya yi ba tare da ya yi magana ba. Kamar tasan me yake nufi ta ce da kuyanga Zubaida ta fara serving na kowa, kowa sai ya faɗi abin da yake da buƙata ta zuba mashi, abinci ne kala kala sun fi kala goma sha biyu a saman katafaren table ɗin, ga kuma kayan fruits, kun dai san yadda cimar gidan sarauta take? Duniya ce guda saman table nasu a yayin cin abinci, kaga abubuwa kala kala. Kowa ya nutsu tsit daga fitowar King, hakan ne zai kara tabbatar maka ƴaƴan nasa ma masu tarbiya ne, kuma sarauta mai karfi aka bugawa ta gasken gaske!!. A yanzu Jaish da Jawad sun dai'na zuwa parlourn cin abinci da su king ɗin, a cewarsu mata sun yi yawa a wajen, damunsu da surutu suke yi, bare ma idan Aunty MieMie ta baro part nata ta shigo nasu, duk sai ta ishesu ta saka masu ido, shi ne yasa suka dai'na cin abincin ana, kai masu nasu a cikin part nasu kawai Kuyanga Zubaida take yi. Da yake kullum suna a tare sai yazama a cikin part ɗin Jaish kuyanga Zubaidar take zuwa ta jere masu abinci, kuma idan ta gama da su King zuwa take yi ta yi serving nasu Jaish ɗin ma baiwar Allah. Yanzu ma haka ta hau serving nasu kowa yana faɗin abin da zata zuba mashi, kamar wata engine haka take aiki, yadda kuka san bettery aka saka mata, abinku da ta saba, abin ya bi jikinta!!. Kowa ta yi serving ta tura mashi sai ya ɗauki spoon ya fara ci a nutse, masu zaɓar kasassun nama an tea ma suna fama da wukar yanka namar suna kaiwa baki, Obaid da Omaid a al'adarsu kafin su fara cin abinci sai Obaid ya bawa Omaid first spoon nasa, shi ma Omaid ɗin ya ɗeba ya basa a baki, haka suke, dan haka a yanzu ma abin da suka yi kenan kafin su fara cin abincin. Zunaira dai tana a kusa da daddynta tana shan kankana sarkin son fruits, ga abinci nan tasa an zuba mata, amma ta zauna tana shan fruits ba tare da ta ci abincin ba. Ita kuwa hajiya gorgeous Queen namu kuma fashion babynmu wato Gimbiya Aunty Chuchu, ta tasa abinci a gaba, kaɗan kaɗan take ɗeba tana kaiwa bakinta, hankalinta sam baya a tare da su, tana can ta afka duniyar tunanin abin da Yah Jawad zai yi mata da ya ce ta same shi a cikin bedroom nasa, tsoronta ɗaya kada ya yi mata faɗa, tasan dai baya duka kasafai, sai ka yi mashi laifi goma bai ɗaga hannu ya daki mutum ba, amma kuma ya iya bada punishment ga shegen iya faɗa da tsawa, ita kuma ta tsani faɗar nan a rayuwarta, gara mata ma a zaneta da a yi mata faɗa, to shi ne ta afka duniyar tunanin abin da zai yi mana. Sarina sarkin yanga yauki da iyayi sai cin abinci take yi tana wani kwaɓe fuska, kanwar Yah Jawad ce, kuma ita ce ma mai bi masa a wajen haihuwa, tana da 19 year a duniya, sai kanwarta Fanan mai shekaru 17 years a yanzu, ita kuwa Aneesa ƴar mama shekarunta 15 years, shekara ɗaya ta bawa Chuchu. Ita ma fa Aneesa ba tayar baya bace, ta iya faɗa ga tsantsar nuna isa da izza, hakan yasa basu shiri da Gimbiya Sarina ko kaɗan, dan duk sarakan ji da kai ne, kunga kuwa ai ba zasu zauna inuwa guda ba. Momma, mummy and Mama dukka kuyanga Zubaida ta yi serving nasu na abincin da ransu yake so, dukkansu sun ɗauki spoon and salad knife sun fara cin abincin a nutse. Shi ma King ya fara cin nasa abincin a nutse. Sai a yanzu kuyanga Zubaida ta samu damar sauke nannauyar ajiyar zuciya, dan ta samu ta gama zubawa kowa abin da yake buƙata, sai ta ɗan koma gefe ta tsaya, tana jiran masu cewa ta zuba masu ruwan sha ko kuma wani drinks ɗin, ko dai ta yanka masu fruits da sauran aikin da suke sakata a lokacin cin abincin nasu, duk cikin gidan Gimbiya Zunaira ce kawai bata saka kowa aiki, da kanta take yi komai, sai dai idan sun ganta zata yi aikin ne su yi maza su kwace su yi mata, amma ita ko fruits ɗaukar wuƙa take yi ta ce zata yanka da kanta, sai dai su kwace su yanka mata, ba zaka taɓa jin ko da sunan wasa ta ce wance or wane yi mun abu kaza ba, sam bata da girman kai kamar ba jikar cikakkun modarawa ba!. BARI MU LEƘA SU KAMRAN WATA KILA KAFIN MU DAWO SUN KING SUN GAMA CIN ABINCIN!!. 🏞️FOREST🏞️ KING OF THE FOREST. Aikin gyaran namar ya kammala tas, sannan ya miƙe ya shigarwa da Mammarsa ciki kamar dai yadda suka saba. Bayan ya jibge mata su a madafarta ya fito ya nufi wajen da yake yin wanka. A gurguje ya yi wankar nasa ya fito, kayansa da ya saba sakawa na sakar audiga na gonarsu da Mammarsa take saƙa masu ya ɗauko, zuciyarsa cike pam da tunanin su pretty, ita kuma Mamma zuciyarta a cike pam da tunanin me ya kawo mayaƙa cikin wannan daji da har suka farmaki Kamran ɗinta? Kenan hakan na nufin basu da nisa da Masarauta ne ko yaya?. Abin ya yi mugun bata mamaki ne, yau tsawon shekaru 25 zuwa 26 tana cikin wannan daji! Bata taɓa ganin mayaƙa ba sai yau, tana dai ganin manya manyan maharba suna giftawa time to time, suma tana kan jima bata gansu ba, bayansu kuma bata ganin kowa, sai dai idan hanya ta kwacewa wani ya afko cikin dajin bisa rashin sani. Wannan abin ya ɗaure mata kai kuma ya bata mamaki!. Fitowa tsab tsab cikin shigarsa mai kyau king of the forest ya yi, ya kara kyau sosai Kamran, sai dai daga ganinsa ba tambaya kasan tabbas yana da yare, dan yanayin fatar jikinsa dama shi kansa, yanayin su Mamma san basu yi kala da larabawa ko Hausa fulani or turawa ba, sai Allah sai kuma mammar tasa ce kawai suka san su ɗin ƴan wace ƙabila ce or daga wasu duniya suke? Nasan kowa a ransa yana tunanin me ya kawosu wannan dajin? Ina mahaifin Kamran tun da dai mace bata haihuwa ita kaɗai? Ni kai'na PRINCESS TEEMA waɗan nan tambayoyi shi ne a cikin rai'na, a wannan daji aka haifi Kamran, kuma da alama tun kafin a haifesa Mamma tana cikin wannan daji, ta yi rayuwa mai tsawo a ciki, to kenan before a tare suka yi rayuwa mai tsawo da baban Kamran ɗin har suka haifesa? Me yasami baban nasa? Ina ƴan uwansu? Idan ita Mamma bata da ƴan uwa to shi baban nasa fa? Ina nashi ƴan uwan? Kun ga dai Mamma jaruma ce, da alama kuma kamar yadda take bawa Kamran training ita ma haka aka bata horo a cikin wannan dajin, to waye kenan? WAƊAN NAN AMSOSHIN ALƘALAMIN PRINCESS TEEMA CE KAWAI ZAI IYA WARWARE MAKU SHI KU DAI KU KASANCE A TARE DA NI, BA ZAKU YI DANASANIN BIBIYAR WANNAN LABARI NA RAWANIN ZALINCI BA IN SHA ALLAH, ZAKU ILMANTU, KU WA'AZANTU, IN FAƊAKAR DA KU, KU NISHAƊANTU MATUKA, AKWAI ABUBUWAN DA IDAN MUKA SHIGA CIKIN LABARIN ZAKU SHA MAMAKI!!. "Mamma, Mammaaa, where are you?". Cewar Kamran ɗin kenan. Tana daga zaune a gefen bakin bed nata tana tunani a kan warriors ɗin nan ta amsa mashi da. "Here I am, what happened? Why kake nemana?". Yaye labulen sakar dake a bakin kofar ɗakin nata ya yi, kasancewar babu mai yi mashi aski a cikin wannan dajin hakan yasa gashin kansa take da yawa, sai dai mammarsa tana rinƙa yanke mashi tsawon gashin da wuƙa, saboda ya rage yawa kada ya rinƙa takura mashi. "Mamma i want to go to somewhere here, ba zan jima ba, only 1 hour is okey for me na dawo gida". Bin shi da kallo kaɗan ta yi kafin ta ce. "What about your food? Waye zai ci maka?". "Oh Mamma na manta da abincin ne, to zan ɗauki abincin na tafi da shi, dama wani babban kogi na gani mai ruwa sosai a cikinsa ta ganganren can, so the place is very very beautiful, can zan je in yi bule a cikin ruwa". Tun da ya fara magana tasan karya yake yi mata, domin tasan gaskiyarsa da kuma karyarsa, bai saba yin karya ba shiyasa idan ya yi dole a gane, a haka ma fa wai ya yi kasa da kansa baya son ta kalli cikin idanunsa, dan yasanta da kaifin ƙwaƙwalwa, so baya son ta gano shi, sai dai ya makaro, ita ta haife shi ta kuma renesa tsawon shekaru ashirin da biyar yanzu, dole ta iya gane shi ciki da waje. Amma sam bata nuna mashi cewa ta gane karya yake shirga mata ba, sai ma ta ce ya je ya ɗauki abincin nasa ya tafi, ta kuma yi mashi hakan ne ba dan komai ba sai dan ta jima tun ɓatar su twins bata gansa cikin farinciki da annashuwa ba sai yau, tun shekaru goma baya da maman twins ta ɓace mashi ya koma wani irin so silent over, daga e sai a'a kawai yake haɗa shi da mamar tasa, ya dai'na sakewa suna hira, ya shiga damuwa sosai ta yadda mammar tasa duk kaifin basirar nan tata ta kasa iya shawo kan damuwar tasa. So yau ta ga yana cikin annashuwa tare da farinciki, bata son ta ɓata mashi wannan farinciki da ya jima bata gani a saman fuskarsa ba, duk da cewa bata san murnar me yake yi ba, amma dai tasan Kamran ba zai taɓa yi mata abin da zai ɓata mata rai ba! So koma me silar shigarsa farinciki a yau tana maraba da shi, kuma ba zata yi abin da zai kawar masa da farincikin ba, shiyasa ta bar shi ya je duk in da yake so, tasan jarumi ne sosai shi ɗin, so zai kula da kansa. (Kada fa Mamma ta yi mana wayo, ta yi mana mage mai kwanciyar ɗaukar rai ta bi bayansa ta je ta raba shi da su pretty mu shiga uku💔😥 ni nasan halinta sarai😥) A hanzarce ya amsa mata da okey Mamma, kafin ya wuce ya nufi cikin wajen madafar tata ya ɗauko abincinsa a cikin wani mazubi mai kyau, sannan ya fito tare da ƙara kwala mata sallama daga bakin kofa akan ya tafi. Tana daga cikin ɗakin ta ce mashi take care. Daga haka ya fice daga cikin ƙogon, sam bai nemi Rocky ba, dan yasan yau Rocky yana can yana ta fama da cin nama, so ba kula shi Rockyn zai yi ba, gara mashi kawai ya yi tafiyarsa. Kai tsaye wajen su pretty ya nufa, sai daɗi yake ji a cikin ransa. Cikin nutsuwa a hankali ya shiga cikin wajen nasu, dan yana rike da abincinsa a hannu, kada ya yi ya zubar da abincin. Kwance ya iskosu a saman bed ɗin nasu, pretty tana karanta wani littafi wanda sai Allah sai kuma mum ɗinta tare da alkalamin PRINCESS TEEMA ne kawai yasan a ina suka samo wannan littafin, ga littafin dai na addu'oe ne. Jin motsin mutun yasa pretty ta ɗago kai, ɗan wannan ɗagowa da ta yi yasa kumatunta suka ɗan motsa, hakan ya bayyanar mata da kyakkyawar dimple nata da ya ƙara bayyanar da kyan fuskarta. Ganin shi ne yasa ta yi saurin miƙewa zaune tana binsa da waɗan nan idanun nata masu jefa bawan Allah cikin ruɗu ya kuma rasa nutsuwarsa. "Pretty motsin me nake ji haka ne?". Cewar Sweetie dake kwance. "Wannan mutumin na ɗazun ne ya sake dawowa". Ta bata amsa tana mai zuro ƴan kyawawan fararen kafafunta kasan gadon. Yunƙurawa Sweetie ɗin ma ta yi ta miƙe zaune tana jin wani irin babu daɗi a cikin ranta, yau karo na farko da ta ji zafin ciwon makantarta, da sam bata damu da dole sai idanunta sun buɗe ta kalli abu ba, saboda a cewarta to ko idanun sun buɗema ai daga mum ɗinsu sai pretty kawai zata gani, wadda kuma ta saba ganinsu kullum, amma yau an sami sabon mutun wadda bata sani ba kuma bata taɓa ganinsa ba, kash ba halin ta ganshi, abin ya yi mata mugun ciwo yau, har ga Allah tana son ganin wanene shi ɗin. A saman wata dutse mai ɗan girma kaɗan dake cikin wajen Kamran ya zauna yana faɗin. "How's your body Sweetie?". Kamar zata yi kuka, har idanunta sun ciko da ruwan kwallah na rashin gani ta amsa mashi da. Alhdulillah. Maimaita kalmar Alhdulillah ya yi kafin ya maido da kallonsa a kan pretty dake ta faman kallon kwanon abincin dake hannunsa, bata taɓa ganin irin kwanikan ba, shi kuma bai taɓa jin kalmar Alhdulillah ba, so dukkansu da abin da suke mamaki a yanzu. "Let's go now ko?". Cewar pretty sarkin sauri. "Go to where?". Ya tambaya yana mai da kallonsa a kan littafin da suke karantawa. Allah idanun Kamran suna da matuƙar kyau sosai, sai ma idan yana kallon abu, sai kaga idanun suna ɗaukar hankali sosai. "Neman wannan mutumin da mum ta ce mu nemosa, you forget that you said zaka taimaka mana to fine him ɗazun ba?". Har wa yau pretty ce ta bashi wannan amsa. "Yeah i will going to help you ku same shi, but now ku zo ku ci abincin Mammata". Da sauri Pretty ta mayar da kallonta a kan Sweetie dake faman girgiza kai alamar su ba zasu ci abincin ba, dan basu yarda da shi ba, kuma da alama mum ɗin su ta ja masu kunne a kan mutane, dan ga shi sai ɗari ɗari suke yi da shi, sam basu saki jiki da shi ba. Ganin Sweetie tana girgiza kai ba tare da ta yi magana bane yasa pretty ta ɗan shagwaɓe fuska kamar zata yi kuka ta bashi amsa da. "We can't eat". A shagwaɓe ta yi maganar. Hakan ba ƙaramin kara mata kyau ya yi ba, duk sai ta sa Kamran ya ji wani irin bawan Allah. Why?. Ya tambayesu yana mai do da kallonsa a kan Sweetie, dan ya lura ita ce mai sanya Pretty yin abu, idan ta ce ba zasu yi abu kaza ba to Pretty ma ba zata yi ba, idan kuma ta ce za su yi abu, to Pretty zata amsa su yi. Ita ce babba kamar yadda ya yi tunani tun farko, kuma ta fi Pretty tunani da nutsuwa, and then ita tun ainahi bata cika fita waje ba, koda yaushe tana a tare da mum ɗinsu lokacin da mum ɗin take nan, hakan yasa ta fi Pretty sanin abubuwa sosai, and kuma kafin mum ɗin su ta ɓace kullum tana gaya masu cewa Pretty ta bi Sweetie sau da kafa, idan ta bita tamkar ita mum ɗin ta bi, duk abin da Sweetien ta ce mata to maza ta yi shi, hakan yasa kuka ga idan Sweetie ta ce a'a, to Pretty ma zata ce a'a. "We can't eat your food be cause we don't know you, kuma mum ta ce kada mu yarda da kowa, kada mu yi magana da kowa, ko mutun ya yi mana magana kada mu amsa, sai dai ta ce mana akwai mutun ɗaya da idan muka ji zuciyarmu ta yarda da shi to mu yarda da shi, dan mai taimako ne, and kuma ta ce lallai mu nemo wani wanda ya taɓa taimaka mata a dajin nan". Cewar Sweetie kenan. "If that's the case then why kuka yi accepted nawa time da na shigo nan? Why kuka yi magana da ni? Kenan kun karya maganar mum ɗinku? Ba ta ce kada ku yarda da kowa ba? Kada ku yi accept nawa sai wannan da ta ce ku nemo, why ni kuka yarda da ni?". Sweetie ɗin ce ta sake amsa mashi da. "Bamu yarda da kai ba, and we didn't accept you, kawai bamu da yadda zamu yi ne?". Yana ƙoƙarin sake yin magana Pretty ta riga shi da cewa. "Ni dai ina ji a jikina kai ne wanda mum ta ce mu nemo, and kuma zuciyata ta yarda da kai, please don't play with our heart, idan kai ne wannan mutumin tell us, idan kuma ba kai bane please nan ma ka gaya mana, ni dai har cikin rai'na i really accepted you". Haƙiƙa hakance, ta yarda da shi, ita ma Sweetie ɗin har cikin zuciyarta ta yarda da shi, kawai ita Sweetie da yake ta fi Pretty dogon tunani sai ya zamana bata son gaya mashi cewa sun yarda da shi, a ƴan kananan shekarun nan nata wai zata bari ne sai taga gudun ruwansa sannan ta gaya mashi cewa ta aminta da shi, yarinya mai wayo. Shegen wayo ke gareta kamar me!. Tun a karon farko suka ji ya kwanta masu a cikin zuƙatansu, kuma kuwa kunsan Kamran yana da shiga rai, and then ko dan kyan zuciyarsa da son taimako dole a so shi, kada ku manta haɗuwarsu ta farko ma taimakon Pretty ya yi, badan shi ba ai da yanzu babu ita ta mutu, kunga kuwa ko dan wannan taimako da ya yi masu dole su ji suna son shi, and kuma dole su fara tunanin ko shi ne mai taimakon da mum ɗin su ta gaya masu? Sau da dama suna ganin maharba suna giftawa ta cikin dajin, idan sun gansu ɓuya suke yi dan kada su gansu, haka mum ɗinsu ta koya masu, kada su yarda wani ya gansu, su rinƙa ɓuya idan suka ga mutane, to a takaice dai duk maharban da suke gani suna giftawa basu taɓa jin koda mutun ɗaya daga cikinsu ya kwanta masu a cikin zuciyoyinsu ba sai Kamran ɗin, hakan yasa suka fara tunanin ko dai shi ne mum ɗinsu ta ce su nema?. "I can't play with your hearts Pretty, not even you, ni bana cutar da kowa ko mai ƙanƙantar cuta, so feel free with me, yanzu dai ku zo ku ci abincin Mammata sai mu fita waje neman mutumin ko?". Kallon Pretty Sweetie ta yi tana jiran ta ji me ƴar uwar tata zata ce. "Okey zamu ci, amma ba'a gabanka ba, sai ka fita waje". Cewar Sweetie ɗin. Da okey ya amsa masu kafin ya miƙe ya miƙowa Pretty abincin. Sai da ya ji wani irin shock da bai taɓa ji ba a jikinsa na haɗuwar hannayensu wajen karɓar abincin. Amma sai ya daure ya nufi hanyar fita daga cikin wajen. A wannan karon sam yaki yarda ya juyo su haɗa idanu da ita, dan ɗan taɓa hannunta da nasa hannun ya yi bisa kuskure ma tasa ya ji kamar ba shi ba, dan haka sai ya yi ficewarsa kawai abinsa. Yana fita Pretty ta kalli ƴar uwar tata kafin ta fara magana a nutse. "Sweetie Allah wannan mutumin shi ne Mum ta ce mu nemo, na ji hakan a jikina, dama kin ji mum ta ce idan mun gansa zamu ji zuciyoyinmu sun yarda da shi, to ni dai na yarda da shi, ban san ko ke baki yarda da shi ba". Nisawa ta ɗan yi kafin ta amsa mata da cewa. "Pretty na fiki yarda da shi, zuciyata ta aminta da shi, amma kada mu yi sauri, mu jira mu gani, kinga mum ta yi mana kashedi sosai a kan yin abu cikin gaggawa, gaggawa aikin shaiɗan ne, duk kuma wanda ya yi gaggawa a kan abu sai ya tabka danasani". "Hakane, to amma Sweetie idan dai har kin yarda da shi kema why not ba za mu bashi saƙon da mum ta ce mu bashi idan muka ganshi ba? Kawai na ɗauko mu bashi, nasan ya manta mum ne shiyasa ya ce mana ba shi ba ne muke nema, amma tun da mum ta ce saƙon yana ƙunshe da abubuwa dayawa masu girmaa cikinsa kila idan muka bashi yana dubawa zai tuna da mum ɗin". "Pretty kefa baki jin magana, wai ba yanzu na ce maki mum ta hanamu yin abu cikin gaggawa ba? Kina ji fa bai yarda cewa shi ne wanda muke nema ba, taya za'ayi mu ɗauki saƙon da mum ta ce mana sai lallai wannan mutumi da ya taimaka mata ɗin zamu bawa ki ce mu bawa wanda bai yarda shi ya yi taimakon ba? Kina son mu saɓa maganar mum kenan?". "A'a bana son mu saɓa maganarta, dama dai kawai dan na ji ta ce idan mun ji ya kwanta mana a rai to shi ne, shiyasa na ce ko ya manta da mum ne idan muka bashi saƙon zai tuna". Shiru Sweetie ɗin ta ɗan yi kafin ta ce. "A'a ba zamu bashi komai ba, ba zamu ma nuna mashi kamar an bamu wani abin mu bawa wanda muke nema ba, mu bari har sai ya amsa da bakinsa shi ne wanda muke nema, kuma sai ya rantse mana da Allah". (Ni kuwa na ce idan ya san Allah kenan ba! To fa ga shi shi Kamran ya ɓoye masu shi ne ya taimaki mamarsu dan wani dalili nasa na kansa wadda bai bayyana ba, ga shi su kuma mamar tasu ta basu saƙo su bashi, ko saƙon menene?.....🤔 Wannan sai alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana kawai zai warware maku wannan cakwakiyar, ku dai cigaba da bibiya, bamu fara komai ba, sai a gaba zamu yi ainahin shiga cikin labarin cikin labarinmu, yanzu duk muna faro foundation!!. Amma kuma fa da gaske idan bai gaya masu shi suke nema ba ba zasu taɓa bashi wannan saƙon ba, to fahhhhhhhhh) "Tom shikenan Sweetie yadda kika ce haka za'ayi, yanzu ya zamu yi da abincin da ya bamun nan?". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Jeki ki juye shi a cikin bowl, ki dawo mashi da kwanonsa, mu ba zamu ci abincinsa ba, na ce mashi zamu ci ne kawai dan kada ya yi wani mummunar tunani a kanmu, ko kuma ya ja baya da mu ganin kamar bamu yarda da shi ba, na nuna masa zamu ci ne dan ya kara sakin jiki damu har mu gane wanenen shi mu kuma san idan shi ne wanda muke nema". (Ka ji yara kanana da shegen wayo da kaifin ƙwaƙwalwa, kai Sweetie akwai dabara, wai ta nuna mashi zasu ci ne dan ya kara yarda ya saki jiki dasu, wai ƴan 10 years ne suke ƙoƙarin yiwa mai 25 years wayo fisabilillahi 🤌😂 to mu dai namu ido, a buga game ɗin mu gani!!.) Haka kuwa aka yi, suka juye abincin nasa suka ɓoye da sunan sun cinye, sannan Pretty ta nufi waje dan ta kira shi a kan ya zo sun gama cin abincin. Mu ɗan koma baya kaɗan, a lokacin da Kamran ya fito daga cikin wannan ramin, ya nufi samar wata bishiya kwantatciya ya zauna, irin waɗan nan itatuwanne da suke fitowa a kwance, zaku gansu kamar waɗan da aka kwantar, amma haka Allah yaka halittarsu, a kwancen suke. So ya nufi saman wannan itaciya ya zauna yana ta tunanin Pretty, har cikin zuciyarsa yake son yarinyar nan, tana da shiga rai, sai dai idanunta suna tsorata shi, dan bai taɓa ganin irinsu ba! Yau ga jarumi Kamran yana tsoron wani abu, bai ji tsoron giwa ba! Bai ji tsoron zaki ba!! Bai ji tsoron Damusa da macizai ba, bai ma san menene tsoron ba sai ga shi yau ya sani kuma yana tsoron kallon cikin sexy eyes ɗin Pretty, tab lallai akwai cakwakiya nan gaba. A hankali ya fara jiyo motsi daga ɗan nesa da in da yake zaune, Allah yasa bai yi zurfi a tunanin Pretty da yake yi ba kunnnuwarsa suka iya tsinkayo mashi sautin motsin. Jin hakan yasa ya yi maza ya haura saman itacen dake kusa da wannan wanda yake a tsaye, ya ɓuya a cikin ganyayyaki ta yadda shi zai iya kallon su wanenen ko kuma menene mai nufo in da yake, amma su ba zasu iya kallon shi ba, ya shige cikin ganyayyaki. Shiru ya lafe a jikin itacen yana jiran yaga su wanenen?. Ya jima a haka har ya fara tunanin sauƙowa ya je ya duba menene a wajen ƙoramar, dan har lokacin bai dai'na jiyo wannan motsi ba, ga shi a in da yake daga saman itacen baya iya hango komai, saboda dogayen ciyayi masu sunkuru da kuma bishiyoyi sun rufe wajen. Hakan yasa baya iya hango me yake motsi a wajen ƙoramar, sai ya yi tunanin bari ya sauƙa ya lallaɓa ya je ya leƙa. Sautin karar haniniyar dawakai da ya dira mashi a cikin kunnuwarsa ne yasa sai ya fasa saukar, ya zuba idanu yana jiran yaga ta ina zasu ɓullo mashi. Can kamar minti uku da jin haniniyar dawakan sai ya fara jin sautin takun tafiyarsu suna tinkaro ta wajen da yake. Kara ƙanƙame itacen ya yi tare da kara lafewa a jikinta ya ɓuya da kyau ta yadda ba zasu iya ganinsa ba, sai dai shi ya gansu!. Bayan wani ɗan lokaci suka bayyana a tsakiyar wajen. Wasu jiga jigan zataran warriors ne har guda takwas, sun horu sosai, dan sun fi waɗan da Kamran ɗin ma ya yi faɗa da su ɗazun, waɗan nan manya manya ne gasu da tsawo da kiɓa, duk da suke zaune a saman ƙosassu kuma lafiyayyun dawakansu hakan ba zai hana ka gane cewa e lallai tabbas cikakkun jarumai ne na kin ƙarawa ba, suna dai sanye da kayan yaki irin dai na jikin waɗan can warriors ɗin da Kamran ɗin ya kashe ɗazun, har wa yau fuskokinsu hular kayan yakin nasu ya rufe shi ba'a iya ganinsu, da alama daga masarauta ɗaya suka fito da mayakan da Rocky yake watandarsa da su. Zaro idanu sosai Kamran ɗin ya yi yana kallonsu, abin ya yi mugun bashi mamaki na ganin wasu mutane irin waɗan da ya kashe ɗazun, tambayar kansa yake yi kenan suna dayawa a cikin dajin? Kenan dama suma a cikin dajin suke? Ko yaya abin yake?. Bawan Allah bai taɓa ganin mutane irinsu ba, bai san cewa shigowa suke yi dan neman wani abin da su kaɗai suka san shi ba kuma suka san dalilin da yasa suke nemansa. Sai dai kuma babban abin ban mamaki da waɗan nan warriors ɗin shi ne, idan suna tafiya suka ci karo da mutun sai su far mashi, babu abin da ya yi masu kawai zasu hallakasa saboda tsabar zalunci da ya yi masu yawa, kun dai ga yadda suka farmaki Kamran ɗazun ko? Ba dan Allah yasa yana da karfi shi ma suka gwabza ba ai da kashe shi za su yi, babu dai abin da ya yi masu bawan Allah, to haka suke, ko maharbi suka ci karo da shi a wannan daji sai sun far mashi sun kashe shi babu gaira babu dalili, sai kace waɗan da aka turo su kashe duk wanda suka gani a hanya, ni kam ma wai daga ina suke zuwa ne? Akwai cakwakiya sosai my people. Suna zuwa dai'dai in da wannan itaciya da Kamran ɗin yake kai suka ja birki suka tsaya, kamar sun san da akwai mutun a wajen, tun da suka shigo arear wajen kuma suke hira, dan a hankali hankali suke kaɗa dawakan nasu ba da gudu ba, hakan ya basu damar suke zuba hira a tsakaninsu, sai dai kash suna magana ne da wata yare na daban wadda shi Kamran sam baya jin me suke faɗa, ya so ya ji zancen da suke yi ko zai iya fahimtar su waye su? Amma ina bai taɓa jin irin wannan yare nasu ba sai yau. Kamar daga sama Kamran ɗin ya hango kofar ramin da su pretty suke ciki yana motsi, alamar za'a buɗe wajen a fito kenan, a dai'dai lokacin ne Pretty ta nufo wajen zata fito ta zo ta kira shi a kan ya zo sun gama cin abincin....... Tashin hankali da ba'a saka mashi date!. Wani irin zaro idanu Kamran ɗin ya yi tamkar idanunsa zasu fito su faɗi ƙasa, tunani yake yi idan Pretty ta fito tabbas kasheta zasu yi, shi kuma da bai shiryawa yaki ba, ko wuƙarsa da yake fita da ita yau ma bai ɗauko ba, saboda zumuɗin ya zo wajensu ya mantata a gida. Waɗan nan shegun warriors da suke kamar wasu dodannin nan wlh cikin minti ɗaya tsab zasu hallaƙata mana Prettynmu, babu imani ko miskala zarratin a tattare da su, wasu bujumaye da su, waɗan nan idan ka gansu ma sai ka rantse da Allah suna cin namar bil adama, saboda yanayinsu babu imani tamkar duwatsune a cikin kirazansu ba zuciya ba, ko shi kansa Kamran ɗin a yadda yake ɗin nan ya kuskura ya sauko cinye namarsa ɗanye zasu yi bare kuma Pretty ƴar firitu da ita da ko cinyeta suka ce zasu yi namarta ta yi masu kaɗan. Kamran dai bai gama razana ba har sai da ya ga Pretty ta buɗe wannan kofar tasu tana ƙoƙarin fitowa waje, daga in da yake yana iya kallonta, dan har ta fara fitowa waje, kuma suma warriors ɗin tsab zasu kalleta tana fitowa, saboda suna fuskantar ta wajen da take ɗin ne, ita kuma da yake bata san komai ba sai ta yi yunƙurin fitowarta kai tsaye kamar yadda ta saba, har ma da karawa da saurinta dan ta fito ta kira Kamran........... Wayyo Rocky yana can yana watandarsa bare mu ce ya kawo masu agaji, yau take sallarsa ai ba zai kula Kamran ba, Wayyo ni kai'na kada waɗan nan azzaluman su cinye mana Pretty ɗanyarta fa......💔😥 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 18/7/2024.....✍️📚🌹 For information 0816139058 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________17🔥 Wayyo Rocky yana can yana watandarsa bare mu ce ya kawo masu agaji, yau take sallarsa ai ba zai kula Kamran ba, Wayyo ni kai'na kada waɗan nan azzaluman su cinye mana Pretty ɗanyarta fa......💔😥 Idan muka leƙa KINGDOM OF POWER kuma. Su Momma sun kammala cin abincinsu lafiya lou kamar yadda suka saba, sannan ƴan matan nasu suka miƙe kowacce ta mufi bedroom nata, su Sarina dukka a part na King suke ba a part na uncle Abbas, tare da su Aneesa suke, kowa da ɗakinsa, so dan haka suna kammala cin abinci kowacce ta wuce nata ɗakin. Sarina kamar zata yi kuka ta nufi part ɗin yayan nata wato Jawad, so take ta je ta bashi hakuri dan ya bata wayarta, ba zata iya zama babu waya a hannunta ba, kuma koda ta sayi wani wayar ba zai bata abin da take so ba, saboda akwai abubuwa dayawa a cikin natan da bata son yin loosing ɗinsa, so is better for her da ta je ta roƙesa. Sai wani yanga take yi tana tura baki, kamar akwai wani a gabanta take aikin harare harare, ga idanun nata kamar na Jawad ɗin, dara dara da su, wannan da ita ce ƴar Jawad ba shakka zai sha duka a hannunta yau.......😅 Ƙasa ƙasa ta yi sallama a kofar shiga parlourn nasa, kamar wadda aka sanya dole ta yi sallamar, ina da tabbacin ba dan tsoronsa da take ji ba da ba shakka ba zata yi wannan sallama ba, kawai tana tsoron shan duka ne. Shiru ba'a amsa mata sallamar ba, tsayuwa ta yi a wajen na almost 2 mins kafin ta sake kwaɗa mashi wata sallamar. Kuyangu guda biyu dake a parlourn ne suka amsa mata sallamar tata cikin ɗari ɗari, ga dukkan alamu suna tsoron amsa mata sallamar, dan bala'in ta ya yi yawa. Ai kuwa sun gudu basu tsira ba, dan kuwa tana shigowa sai da ta hau surfa masu uwar bala'i a kan ina ruwansu da sallamarta da zasu wani amsa mata? Shin su ta yi wa sallamar ne? Ko ta ce wata ƙasƙantacciyar baiwa ta tanka maganarta ne?. Ƙasa suka yi da kai suna mai bata hakuri tare da yin alkawarin ba zasu sake ba, bayin Allah a matsayinsu na musulmai ne suke ganin kamar rashin amsa sallamar ba dai'dai bane, kuma hakan ne, ba dai'dai bane kana matsayin musulmi ayi maka sallama baka amsa ba, koda kuwa baku shiri da mutum amsa sallama wajibi ne idan aka yi maka, amma ita amsa mata ɗin ma bala'i ne, wannan yarinya sai dai shirin Allah kawai, bata son talakawa ko kaɗan, ga shegen iyayi da kwainane, ita ko ƴaƴan manyan sarakuna ma ganin ƙasƙantattun mutane take yi masu, wannan da ita ce a kan kujera riƙe da karagar mulki zata mulki mutane da anga bone wlh, ina ga daga karshe jama'a ne zasu yi mata bore su sauketa daga kan kujerar. Sai da ta gama zagesu fes, da Allah yasa ma bata haɗa masu da mari ba, sannan ne ta nufi bedroom ɗin yayan nata, tana wani yamutse fuska kamar wadda ta kalli kashi ko wani abin kyamar, sai wani ɗage dogon hanci sama take yi, kada fa kuce mummuna ce, a'a wlh, Gimbiya Sarina kyakkyawace kamar uncle Abbas, jinin Akkas ce ai, kawai ita dai halinta ne masifa da bala'i sai shirin Allah, bata son ganin ƙasƙantattun mutane a arear da take, shiyasa mai aikin da take yi mata aikin gyaran bedroom nata tana ganin bala'i, tana ƙoƙari, duk cikin ƴan'matan gidan ita kaɗai aka sha canzawa masu yi mata hidima, dan sai ta ce sun cika ƙazanta bata son su a kawo wasu, kuma wlh suna da tsabta, kawai idan aka samu akasi ne ta ga datti komai ƙanƙantarta sai ta ce sun yi mata ƙazanta a cikin bedroom nata, dan haka ita ba zata zauna da su ba a canza su!! Haka Mummy take sanyawa a canza mata wasu, dama mummy ce mai goya mata baya tana abin da ta ga dama, komai ta yi bata laifi, a gidan gabaɗaya sun fi shiri da mum ɗin. Sallama a bakin haɗaɗɗen kofar shiga cikin bedroom ɗin nasa ta yi. Shiru bai amsa mata ba, su kuwa kuyangun nan suka cigaba da aikin da suke yi na yi mashi gyaran dare, dama sau uku suke zuwa gyara mashi part ɗin nasa, safe da rana da kuma dare, aiki ba hutawa, saboda ƴaƴan Akka da jikokinta na gaya maku basu shiri da datti, basu son ƙazanta, suna da balai'n tsabta sosai, shiyasa komai nasu yake fes fes, kuyangu masu yi masu hidima suna ƙoƙari sosai wlh!. Ta kai almost 5 mins a tsaye ba tare da ta ji motsin komai ba, kuma ga shi ba'a a amsa mata sallamar tata ba, hakan yasa ta yi tunanin bari ta shiga ciki ta duba shi, bata san cewa Prince Jaish ya dawo ba, idan ta san ya dawo ma ba zata zo neman Yah Jawad ba, domin tasan dole suna a tare basu rabuwa. A hankali ta tura kofar bedroom ɗin ta shiga, aljannar duniya, oooooo familyn King suna sha'aninsu, kowa ka leƙa part ɗinsa sai ka ji kamar ba'a duniya kake ba, sai ma ka rasa part ɗin waye zaka zaɓa a ciki, wannan ruwan ido ma sai ya hanaka zaɓar komai, dan idan aka ce ka zaɓa sai ka kwana ka wuni kana kewaye a Parts ɗin, duk wanda ka shiga kuma sai ka ga ya fi na wannan kyau, idan ka shiga wani shi ma sai kaga ya fi wadda ka fita yanzu kyau, sai ka yi wata baka iya zaɓar wadda zaka zaɓa ba, saboda dukka sun haɗu ne na wuce misali. Sai tashin daddaɗar kamshin da sanyin Ac bedroom ɗin nasa yake yi, komai tsab tsab kamar yanzu aka cirosu daga ledarsu, kuyangun sun iya gyara sosai, sun san aikinsu. Babu kowa a cikin bedroom ɗin sai haɗaɗɗiyar katafaren bed nasa da ya sha gyara da shinfiɗu na alfarma. Haka ma cikin bathroom shiru bata ji motsin kowa a wajen ba, a hankali kamar wata ɓarauniya ta lallaɓa izuwa balconynsa dan ta leƙa. Nan ma babu kowa, da alama dai baya a cikin part ɗin. Dawowa cikin bedroom ɗin ta yi ta ɗan fara dube dube ko zata ga wayarta, tsabar tsoro har ɗan kerma jikinta yake yi, saboda ta san idan ya kamata a cikin bedroom ɗinsa tana yi mashi leƙe leƙe sai ya bata punishment, jikinta ne zai gaya mata, kuma dai tasan bata isa ta ɗauki wayar tata ba koda ta gani, dan ko giyar wake take sha bata isa yayyun nata su kwace abu su ajiye kuma ta ɗauka ba, babu ma wanda ya isa ya yi hakan a cikinsu, kawai tana duba wayar ne idan ta gani ta ɗan ɗauka ta kunna ta ɗan duba cikin wayar, dan tana kewayar mutanenta da suke chatting! Idan ta gama gani kuma ta mayar ta ajiye a in da ta gani ta kama kanta har sai ranar da ya ɗauko da hannunsa da kansa ya bata, bata isa ta tafi da shi ba. Sai dai kash ta yi iya dube dubenta babu wani abin da ta gani, ko na Chuchu dana Fanan da ya karɓa daga baya ma babu su a cikin room ɗin bata gani ba. Kuma duk bala'in rashin kunyarta ba zata iya zuwa part na Jaish neman Yah Jawad ɗin ba, tana mahaukacin tsoron Jaish, dan shi bashi da wasa kuma baya ɗaukar wasa, yanzu zai haɗa mata jini da majina, gara Jawad sau dubu a kan Jaish, so tun da bata ga Yah Jawad ɗin ba ta san duk yadda aka yi yana part ɗin Yah Jaish, zuciyarta ya gaya mata tabbas Yah Jaish ya dawo, dan haka sai dai ta hakura da ta tunkari part ɗin yah Jaish, ai ko giyar wake ta sha ba zata iya zuwa can ba, part ɗin Yah Jawad ɗin ma shahada ta yi ta zo. Kamar zata yi kuka haka ta fito tare da janyo mashi kofar bedroom ɗin nasa ta nufi waje, sai kace kuyangun nan ne suka yi mata laifi, ta wani wurga masu uwar harara kafin ta sa kai ta bar part ɗin. Bayin Allan su kuwa ko alamar damuwa ba su nuna sun damu ba, sai ma suka ƙarisa aikinsu wanda yake da shi da babu duk ɗaya ne, domin kuwa part ɗin yana da haske babu datti, amma a haka sai sun zo sun sake gyarawa, kunga kuwa wannan aiki kusan da shi da babu duk ɗaya ne. Bayan sun kammala suka bulbula mashi turarukan ɗaki masu daɗin kamshi kafin su fita su ja mashi kofar su nufi nasu ɓangaren na kuyangu. Ita kuwa hajiya Gimbiya Sarina part nata ta nufa kamar zata yi kuka, tana shiga ta fara ɓallawa kuyangar dake yi mata hidima harara, sai ka ce su ne suka yi mata laifi. Kayan jikinta ta fara cirewa kafin ta ɗaura wani ɗan figalallen towel da bai gama rufe mata tsala tsalan jajir ɗin cinyoyin nan nata ba, a haka ta nufi cikin bathroom. A hanzarce kuyangarta ta zo ta fara kwashe kayan nata da ta cire ta barsu a saman katafaren bed ɗinta, tsab ta kwashesu ta ƙara gyara mata ɗakin da kyau. Bata wani jima sosai a cikin bathroom ɗin ba ta fito sanye da bathrobe fara kal a jikinta, ta nannaɗe wannan dogon gashin kan nasu na larabawan da farar karamar towel Gaban katafaren dressing mirrorta dake shaƙe da kayan shafa ne, su turaruka da su make up artis ɗinta ta nufa. Tsadaddun lotions nata ta murje jikinta da shi, kamar bata son taɓa jikin nata, saboda shegen kaunar skin ɗin nan nata da take yi, sam bata son abin da zai taɓa mata shi, kamar ba za'a mutu ƙasa ta cinye skin ɗin ba, kullum cikin gyaransa take, sai dai kuma ba karya fa yana nuna ana gyara shi ɗin, ya yi luwai luwai da shi sosai, ga tsantsi da sheki Masha Allah. Bayan ta kammala murje lotions ɗin nata ne ta shirya cikin wasu tsadaddun kayan barci, ɗan riga shara shara mara nauyi mai ƙaramin hannu ne da kuma wandonsa dogo shi ma mara nauyi, launin brown color, hand dryer ta jona ta hau busar da kyakkyawar bakin gashin kanta, duk son jiki irin nata da rashin son aiki to fa bata bari kuyangu su taɓa jikinta wajen yi mata irinsu busar da gashi ko makamancin haka, ɗan gara wankin kafama tana sakasu su yi mata, sai kuma tausa idan ta yi ra'ayi. Tana gama busar da gashin ta sake feshe jikinta da daddaɗar perfume ɗinta mai daɗin kamshi kafin ta faɗa saman lallausan katafaren bed nata da ya sha shinfiɗa ta alfarma da bed sheets ash color mai haske. Babu wani addu'ar barci kawai ta lume cikin bed ɗinta tare da janyo kananar pillows dake saman bed ɗin ta runguma, sannan ta ce da kuyangarta ta zo ta warware duv ɗin dake a saman bed ɗin ta rufeta da shi. Da yake kuyangar tana a cikin bedroom ɗin tana ƙoƙarin tattare towels ɗin da Sarinar ta yi amfani da su bayan fitowarta daga wanka. A hanzarce ta zo ta ware duv ɗin ta lulluɓeta da shi, yau kam babu waya barcin wuri ya kama Gimbiya Sarina, da wayarta na nan yanzu zata fara aikin latsa shi har zuwa tsakiyar dare, amma yanzu dole ta hakura ta yi barci. Tattare komai kuyangar ta yi tare da kara fesa mata air freshener mai daɗin kamshi sannan ta ɗan kara mata gudun Ac zuwa yadda take barin mata kullum. Bayan ta kammala mata komai ta kashe wutar ɗakin tare da kunna purple light dake a ɗakin, sannan ta fito ta ja mata kofar, asuba ta gari. Da yake kuyangun ƴan'matan gidan basu rabuwa da part na su Gimbiyoyin, suna da bedroom a cikin part ɗin, dan watakila wata Gimbiya zata buƙaci wani abin da daddare, hakan yasa wannan kuyanga ta nufi bedroom nata dake kusa dana Sarinar, basu da nisa, saboda ta jadadda aikinta!!. A ɓangaren Gimbiya Chuchu kuwa, wanka ita ma ta je ta yi, sannan ta yi shirinta cikin tsadaddun kayan barcinta masu kyau da ɗaukar hankali, ita ma dai riga ce da wando launin pink color da ratsin white kaɗan, ta yi kyau sosai, bayan ta kammala busar da kyakkyawar bakin gashin kanta ma sai ta sake shi har gadon bayanta, sannan ta zuba perfumes ɗinta masu daɗin kamshi sosai wadda Momma ta bata, daga Dubai ake aikowa da Momma turarurruka, shiyasa suke da daɗin kamshi mai sanyayya zuciya. Zama ta yi a gefen luntsumemiyar bed mattress ɗin nata tana tunanin me Yah Jawad zai ce mata idan ta je part nasa?. A wannan hali auta ta shigo ta sameta, sanye take da nata tsadaddun kayan barcin ita ma, ta sha kyau over, dama ita ba gwanar ɗaura ɗankwali ba, sai ta saki wannan dark black curly hair nata har tsakiyar baya, tana rungume da Wolf nata dake barci. Saman bed ɗin ta haye tana faɗin. "Aunty Chuchu what are you thinking?". Nisawa ta ɗan yi tare da faɗin. "Am thinking about Yah Jawad, he said i should meet him in his part, so now am thinking about the reason of the call he called me". "To ai babu abin da zai yi maki, so just fell free and go, ko dai kin yi mashi wani laifi ne?". Da sauri ta ɗan girgiza kai tana faɗin. "No ban yi mashi komai ba". "Okey tom ki je ba zai yi maki komai ba ai, wata kila ma aikanki zai yi wani wajen ko wajen Mammie". Ta kai karshen maganar tare da kwanciya rungume da Wolf ɗin nata. "Aunty Chuchu yau a bedroom naki zan kwana yau ma kamar jiya". Ta faɗa tana janyo duv ta rufe su ita da Wolf ɗin nata da take kiransa da sunan Felix. "A'a zo mu je ki rakani part ɗin Yah Jawad ɗin, mu je tare mu dawo tare mu zo mu yi barci". Ta yi maganar tana juyo da kallonta a kan autar. "Kai Aunty Chuchu, am tied fa, am feeling too much of sleeping, kuma kinga my felix ma also ya yi barci, kawai ki je, ai Yah Jawad baya da faɗa, and kuma yana da kirki, da ma dai uncle Taheer ne sai na ce to ki shirya". "Hmmmm a ganinki ne Yah Jawad bashi da faɗa ba? Ke ai auta a gidan nan ma kowa baya da faɗa ne a wajenki, saboda basa yi maki, for me uncle Taheer is better than Yah Jawad a saukin kai, seriously Yah Jawad he's acting like a tiger ne or Lion za'a ce, he can't talk at all sai zafin rai like Yah Jaish, amma uncle Taheer fa? Baya kwacewa mutane abinsu, kuma shi idan ka ce mashi sorry yana hakura". Ta kai karshen maganar tana turo baki kamar Yah Jawad ɗin yana a gabanta. "To ni dai Yah Jawad is better than uncle Taheer for me, dan haka ma ni good night". Ta kai karshen maganar tare da jan duv ɗin har izuwa saman fuskarta ta rufe ruf. "No auta please stan up let's go together, I can't go without you! Ina tsoro". "Kai Aunty Chuchu idan da ban shigo bafa? Da waye zaki je?". "Cikin bedroom naki zan je na kiraki mana, Please taso mu je". Turo ɗan bakin ta yi, a hankali ta yaye duv ɗin ta fito, har ga Allah bata son zuwa, amma ya zata yi da Aunty Chuchu nan nata? Dole kawai ta rakata. Da yake Felix ɗinta ya yi barci sai ta kyale shi a saman bed ɗin suka tafi, dukkansu kai babu ɗankwali, sun saki gashin nan har baya, da yake auta tana da tsawo sosai kamar Mommarta, sai ya zamana ta kusa kamo Chuchu ɗin tsawo. Kai tsaye part na Yah Jawad ɗin suka nufa, sai hira suke yi cikin nishaɗi kamar wasu ƙawaye. Ba su kai ga ƙarisawa part ɗin nasa ba suka ci karo da wani haɗaɗɗen matashi mai jini a jika, kyakkyawa kuma lafiyayye, yana da fusatatcitar fuska sosai, idan ka gansa ma sai ka ɗan razana, saboda yadda face ɗin take a ɗaure tamau, sai dai kuma ba karya akwai kyau, da alama akwai zafin kai da izzar jinin mulki, yana sanye da kayan barci shi ma a jikinsa masu bala'in kyau da tsada, sai tashin kamshi yake yi, yana tafiya yana latsa haɗaɗɗiyar wayar dake rike a hannunsa, a shekaru ba zai wuce 28 years ba. "Good evening uncle Taheer". Suka haɗa baki wajen faɗa. Ɗan dakatawa daga tafiyar da yake yi ya yi, sannan gentle ya kawar da kallonsa daga kan screen ɗin wayar izuwa kansu, kallo ɗaya ya yi masu ya mayar da kallonsa a kan screen ɗin tare da cigaba da tafiyarsa, ba tare da ya amsa masu gaisuwar tasu ba ya ce. "Baby zo mu je ki rakani wajen uncle Abbas, can zan je". Yana maganar ne yana cigaba da tafiyar da yake yi. Uncle Taheer kenan, ƙanin Mama ne, ba ɗan King Zuhair bane ba!. Kallon juna suka yi ita da Chuchu, kamar Gimbiya chuchu zata sa kuka, uncle Taheer zai sanya ita kaɗai ta je wajen Yah Jawad, zai wani ɗauke mata abokiyar tafiyarta, wayyo Allah, gaskiya bai kyauta mata ba. Ganin ya ɗan yi nisa da tafiyar da yake yi har ya kusa fita daga arear wajen ne yasa auta ta yi saurin barin Gimbiya Chuchu ta rufa mashi baya, dan ma kada ya sake kiranta. Da kallo our fashion baby Chuchu ta bisu da shi har sai da suka kurewa ganinta, sannan ta kara turo ɗan bakin nan nata, ji take yi kamar ta juya ta koma ta fasa zuwa wajen Yah Jawad ɗin, amma ina ba hali, idan ta fasa zuwa ma wani laifin ta jawa kanta da kanta. Hakan yasa ta ɓata rai tana turo baki ba dan ta so ba ta cigaba da tafiya. A bakin kofar shiga part ɗin nasa ta tsaya ta yi sallama. Shiru ba'a amsa mata ba, a lokacin ma kuyangun da suke yi mashi hidima a part ɗin nasa sun kammala aikinsu su tafi, so babu kowa a cikin parlourn, hakan yasa ba'a amsa sallamar ba. Jin shiru babu wanda ya amsa mata har tsawon mintuna biyu yasa ta ɗan turo kofar ta sako kyawawan kafafunta da suke sanye cikin bedroom slippers masu bala'in kyau, ta sako ƙafafun nata ne tana sake rangaɗa mashi sallama. Ganin babu kowa a parlourn yasa ta ɗan sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da nufar kofar bedroom nasa. A bakin kofar ta tsaya tare da dai'dai ta nutsuwarta tana sake sauke ajiyar zuciya, sannan ta yi sallama cikin nutsuwa. Shiru shiru ba'a amsa ba, a karo na biyu ta sake yin sallamar. Nan ma shiru ba'a amsa ba. Wani tunani ne ya faɗo mata a ranta na ko dai baya a cikin ɗakin ne? Ko kuma ya yi barci ne?. A hankali ta juya da nufin ta bar wajen ta koma part nata, sai kuma wani ɓangare na zuciyarta ya ce mata ta leƙa cikin bedroom ɗin mana ta gani ko barci yake yi ko kuma dai laifin da ta yi mashi ne yasa ba zai amsa sallamar ba. Yin wanna tunani yasa ta sake juyowa tare da ɗan tura kofar tasa a hankali. Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta sako kafarta a cikin bedroom ɗin, tana ɗari ɗari. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da taga babu kowa a cikin ɗakin, sosai ta ji daɗi, Allah ya ceceta ya tseratar da ita, dan haka sai ta juya a hankali da nufin ta fice daga cikin bedroom ɗin. Kome ta tuna kuma? Sai ta sake juyowa da sauri, ƙurawa wayoyin dake a saman bed nasa idanu ta yi, ga wayarta dana Fanan, sannan ga na Sarina sai nasa guda biyu a gefe, duk ya zubesu a saman bed ɗin, da alama bayan fitar gimbiya Sarina ya shigo cikin ɗakin kenan, dan kunga lokacin da Sarina ɗin ta shigo cikin bedroom ɗin babu wayoyin a saman bed ɗin. Ganin wayoyin yasa bata san lokacin da ta saki cool murmushi ba kamar Yah Jawad ɗin ya mai do mata da nata ne. Da sauri ta karisa wajen wayoyin tana ta kara faɗaɗa murmushin da yake a saman fuskarta. Tana zuwa wayarta ta fara ɗauka, dukka wayoyin nasu a kashe, wayoyinsa ne kawai a kunne. Wani irin daɗi ne ya lulluɓeta, ta manta ma a ina take, tuni ta hau kunna wayarta, sai kara sakin murmushi take yi, wayyo ta mance ma da wanenen ya kwace wayoyin nasu, ita dai burinta ya cika ta ga nata, laifi kan laifi kenan take ƙoƙarin karawa. Tana kunna wayarta ta sauke ajiyar zuciya, a hanzarce ta fara dube dube a cikin wayar, shap fa ta mance da cewa ba'a bedroom nata take ba, kuma yau ta manta da cewa tana tsoron Yah Jawad, daɗi ne ya yi mata yawa, kada ku ga laifinta. Saboda jaraba abin ya bi jini tana ɗan yi shige shige kaɗan a wayar ta fita ta shiga Camera dan ta ɗauki hoto. (Wanna jaraba ta Chuchu dayawa yake💔 yarinya mayyar hoto haka?🤔 Anya ba aljanun yin hoto ke gareta ba? Wai ma ina take kai hotunan ne?🤔 Me take yi da su?🤔) Hotuna ta fara ɗaukar kanta, tana yi tana canza style, ta turo ɗan bakin nan ta sake ɗaga kyakkyawar gerarta guda. Wani irin rashin sa'a aka samu ta juya ta canza style kenan zata ɗauki hoton sai camerar ya haɗo mata da Yah Jawad dake tsaye a bayanta wajen kofar shiga dressing room nasa. Daga shi sai towel and single a jikinsa, wanka ya fito ɗaure da towel, lokacin da ta shigo cikin bedroom ɗin yana cikin dressing room nasa zai fara saka kaya kenan, ya saka single bai kai ga ƙarisawa ba ya ji motsi a cikin bedroom ɗin nasa, hakan yasa ya fito leƙawa ya ga wannen? Sai ganinta ya yi tana ɗaukar hotuna, shi ne ga tsaya tare da harɗe hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa yana kare mata kallo yana ganin ikon god. Ganin shi ta cikin camerar wayar ba ƙaramin razana ta ya yi ba ta yadda har sai da ta zunduma wani irin ihu tare da juyowa a dubu ɗari dan ta tabbatarwa da kanta abin da ta kallah a cikin wayar, sai yanzu ta tuna ashe ba'a bedroom nata take ba baiwar Allah. Tsabar tsorata da ganinshi yasa ta sake wayar tata ta faɗi kasa a saman white tiles ɗin, kunsan ganin mutun un expect ba karamin razanarwa yake yi ba, barema ita da ta ganshi ta cikin camera, ai dole ta tsorata, ga shi dare ne, kuma ya kafeta da waɗan nan dara daran idanun nasa, ai tama yi ƙoƙari da bata sakar mashi fitsari a wajen ba. Shi kuwa tunani yake yi ko dai ruƙuya za'ayi mata ne? Watakila aljanun ɗaukar hoto ne suka shigeta!. Ganin ko motsi bai yi ba ya kafeta da idanu ne yasa ta ƙara sorata sosai, jikinta har ya suma kerma, ita tunani ma take yi shi ne ko kuma aljani ne? Dan a gaskiya yanayinsa ya tsoratata sosai, ga shi daga shi sai single ta sama, ta kasa kuma towel ne ɗaure a kugun nasa, yanzu ta gudu ne ko ta tsaya?. (Ni dai na ce wlh ki zunduma a guje kiyi waje abinki ato😅 kuma kada ki tsaya a ko'ina sai wajen Momma, dan ita kaɗai zata iya kwatarki.🥰😅) Almost 10 mins suna tsaye a haka an rasa mai bakin yin magana a cikinsu, sai kermar tsoro jikinta yake yi, shi kuma yana kare mata kallo. Sai da ya ga ta fara ruwan hawaye ta gaji da tsayuwar ne tunaninsa ya dawo jikinsa, nisawa ya yi kafin ya ɗan motsa lips nasa wajen furta. "What are you doing here by this time around?". Har ya manta da cewa shi ya ce ta zo ta same shi a cikin part ɗin nasa. Hawayen da yake a saman fuskarta ne ya kara karfin gudun nasa, murya na kerma ta ce. "Yah Jawad kai ne fa ɗazun ka ce na zo na sameka a part naka". "Sai kuma na ce idan kin zo ki shigo mun har cikin bedroom?". Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a. "Waye kuma ya ce ki fito sanye da kayan barci babu ɗankwali bare hijab? Ki ka wuce kowani part dake arear nan kizo har nan? Are you out of your sense?!". Ya kai karshen maganar cikin faɗa da kuma ɗan ɗaga murya. Nan ma girgiza mashi kai ta yi alamar a'a, ta kasa iya sake yi mashi magana, sai dai ruwan hawaye. "Waye kuma ya ce ki taɓa mun abin da na ajiye? Ke kika ajiye mun wayoyin ne?". Nan ma dai girgiza kan nata ta yi alamar a'a, wahayen face nata suna kara tsananta gudu, ta yi danasanin zuwanta ma, ashe shi ya manta ma da ya ce ta zo ta same shi a part nasa, ita ce take wahalar da kanta, yanzu ga shi ta kara laifi a kan laifi, ga laifin fitowa da kayan barci wanda ita ta manta da cewa sune ma a jikinta, sannan ga laifi ɗaukar wayar da ya ajiye da ta yi. A nasa ɓangaren kuwa, kukan da take yin nan ne baya son gani, saboda suna kaunar kannen nasu sosai, ƴan gata ne da ba'a son su yi kuka sai ya zama dole, dan haka sai ya sassauta muryarsa ƙasa ƙasa ya ce. "Okey maza goge hawayen nan kiyi neel down a wajen ina zuwa, idan kuma kika bari na fito naga hawaye a saman face naki you now the rest". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya koma cikin room ɗin dan ya kammala shirin da ya fara. A hanzarce ta kai hannu ta goge hawayen nata tare da zube gwiwowinta a ƙasa, ji take yi wasu kukan suna zuwa mata, amma sai ta danne dan gudun kada ta kara laifi a kan laifi, ji ta yi gabaɗaya ta tsani Yah Jawad ɗin nan, duk cikin brothers ɗinta shi ne ya fara sakata kuka, ko yayansa wato first born ɗin uncle Abbas mai runa Rizwan bai taɓa sakasu kuka ba, duk da yake suna ce mashi mugu, amma bai taɓa dukansu ba, sai dai harara da daka masu tsawa, yau kawai Yah Jawad ya sakata kuka dan mugunta. Ya ɓatawa fashion babynmu rai, gaskiya bai kyauta ba.....😥😅 To bari dai na koma wajen su Kamran, wata kila kafin mu dawo Yah Jawad ya kammala shirinsa, sai mu zo muga wani hukunci zai yi mata, ta yi laifuka har guda uku, zamu ga irin hukuncin da zai yi mata dai!!. 🏞️FOREST🏞️ Fitowa waje Pretty ta yi kai tsaye abinta, ta fito kuma tana mai kiran sunan Kamran a kan ina yake ya zo sun gama cin abinci!. Ai yana saman bishiyar nan bai san lokacin da ya furta kash ba!. Ita kuwa wani irin birki ta ja na ganin waɗan nan jiga jigan zakunan a gabanta, zaro idanunta ta yi tana kallonsu, sai kuma ta fara ɗan waige waige tana neman ta in da zata ga Kamran?. While su kuma warriors ɗin suka bita da kallon from head to toe!. Gabaɗaya wani irin mahaukacin tsoro ne ya kamata, bata taɓa ganin halittu irin waɗan nan ba, kamar ba mutane ba, bugu da ƙari ga hular kayan yakin nan nasu a kansu, kuma su nasu hular mai design ɗin kan ɓauna ce, hakan tasa kan nasu ya kara girma ta yadda ya yi matuƙar sakawa hantar cikinta ya kaɗa, ƴaƴan hanjinta ya yi masifar kaɗawa, tsoro ne ya dabaibayeta ta ko'ina, kan kace me jikinta ya fara kerma. Kobaka san su waye waɗan nan warriors ɗin ba idan ka gansu dole ka razana, dole hantar cikinka ta kaɗa, saboda basu yi kala da masu ɗigon imani ko miskala zarratin a cikin ransu ba, ga bala'in kwarjinin da yake lulluɓe da fatar jikkunansu, gasu wasu bujumaye da su kamar wasu zakuna, dole Pretty ta tsure na kin ƙarawa, Kamran ma ya tsorata da ganinsu bare kuma Pretty, ai tama yi ƙoƙari da bata sume masu ba. Kallon juna warriors ɗin suka yi a in da suka fara yin magana da wannan yaren nasu dai da bamu jin me suke faɗa, Kamran dai yana bala'in son ya ji me suke cewa, amma babu hali, hakan yasa ya zuba masu idanu kawai ya ga me zasu yi idan suka gama maganar nasu, sai alama yake yi wa Pretty da hannunsa a kan ta gudu ta wata hanyar, kada ta koma cikin ɗakinsu, hakan zai sa a gane maɓoyatsu. Amma ina ita Pretty sam bata ma san yana saman bishiyar ba, bata ganshi ba, ita dama take tsaye tana jiran kiris ta saki fitsari a wando saboda tsoro, ina ita ina wani kallon sama kuma? Har ma ta ganshi a saman! Ai babu wannan zance. Kamran ya yi nisa cikin tunanin mafita bai ankara ba sai gani ya yi warriors guda biyu sun diro kasa daga saman dawakansu, cikin takun tsantsar jarumta suna taka ƙasa tana amsawa dip dip dip suka nufi Pretty ɗin. Tana tsaye ta kasa iya guduwa, tamkar wadda aka sarewa gaɓɓan jikinta ko aka dasata a wajen, ba komai bane ya ja mata hakan kuma face tsoro, tsananin tsorata da ta yi ne yasa gabaɗaya gaɓɓan jikinta suka yi la'asar babu laka. Ganin sun tunkareta gadan gadan ne yasa Kamran bashi da wani zaɓin da ta rage mashi face ya sauko ya fiskancesu gaba da gaba wata kila su yi mutuwar kasko, dan ba zai iya bari su cutar da Pretty ba, ko da kuwa zasu kashe shi, shi da kansa yasan wlh waɗan nan jiga jigan warriors ɗin sun fi karfinsa, ba zai iya yin faɗa da su ba, dama dai su huɗu ne to zai iya cewa zai kashesu, amma har su takwas shi kaɗai ai kowa yasan idan ba aljani ne shi ba wane kaniyarsa ya iya faɗa da su, amma ya zai yi? Da dai su kashe Pretty gara mashi ya sauko su buga da shi ɗin, idan ya so Pretty ta gudu ta samu ta tsira!. Hakan yasa shi ya diro ƙasa daga saman bishiyar, bai yi tunanin wani hali Mammarsa zata shiga idan aka kashe shi ba, yasan shi kaɗai take da shi a duniyar nan, tana bala'in kaunarsa fiye da tunaninku, ya zata yi da ranta idan aka ce waɗan nan azzaluman sun kashe shi? Ai ina ga ita ma mutuwa zata yi ko kuma ta haukace kawai!!. Ganin dirowar mutun yasa warrior da suke tunkarar Pretty suka dakata daga tafiyar da suke yi, tare da ɗaura kallonsu a kan Kamran ɗin. Ya yi tsayuwar cikakkun jarumai! Babu alamar tsoro ko kuma sarewa a tattare da shi, yadda kuka san zai iya da su dukkansu. Ganin irin tsayuwar da ya yi cike da jarumta babu ko ɗar ɗar ne yasa warriors ɗin suka fara tunanin ko dai da akwai abin da ya taka ne?. Amma da yake a fagen daga ba'a ja da baya kuma ba'a nuna tsoro ko shakku, sai hakan yasa suma basu nuna kamar sun ɗan yi mamakin ganin ɗan ƙaramin kwaron ya yi irin wannan tsayuwa a gabansu ba, sai ma waɗan can warriors biyu da suke tunkarar Pretty ɗin suka juyo ta kansa, gadan gadan suka nufesa. Cikin harshen turanci ya ce da Pretty ta gudu ta wata hanyar ta daban. Ai kuwa yana yin magana ta ji karfi ya zo mata, dan haka sai ta juya a guje ta nufi wata hanya da take ta can gefe, bata koma cikin ramin nasu ba. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin ta gudu, sai dai kuma ɗaya daga cikin warriors da suke a saman dawakan nan ya bi bayanta da dokinsa, hakan ya kara tayarwa da Kamran ɗin hankali sosai, dan haka sai ya yi ƙoƙarin hango warriors ɗin dan ya faɗo kasa daga kan dokin. Sai dai kash, bai kai ga nasarar yin hakan ba warriors biyun nan suka capke shi, wani irin murɗe mashi hannu ta baya da suka yi ne yasa bai san lokacin da ya zube ƙasa a saman gwiwowinsa ba. Da gudu ɗaya daga cikin warriors da suke a saman dawakansu ma ya rufawa wanda ya bi Pretty baya, suka zamana su biyu ne suka bi bayanta, waɗan nan biyun kuma sun durƙusar da Kamran ɗin a saman gwiwowinsa suna ƙoƙarin cutar da shi, a in da ɗaya ya zaro karamar wuƙa yana son yanke mashi maƙogoron wuya, yadda kuka san ya yi masu wani laifi bawan Allah. Ganin hakan yasa Kamran ɗin ya fara ƙoƙarin kwatar kansa daga hannunsu, dan shi ma dai kun sani ba tayan baya bane wajen iya faɗa, ya san salo da dabarun faɗa sarai. Hakan yasa ya iya samu da kyar da suɗin goshi ya kwaci kansa a hannun warriors biyun nan, gadan gadan ya fara yin faɗa da su yana son kashesu ya bi bayan Pretty dan kada waɗan can su kamata su kasheta. Cikin zafin nama da zafafawa yake faɗa da mutun biyun nan, mutun huɗu kuma suma saman dawakansu suna ta kallon ikon god ikon gaske, basu taɓa tunanin cewa Kamran ya iya faɗa haka ba, kallon ɗan ƙaramin kwaro suke yi mashi, basu san shi ma babban shege bane. Cikin ikon Allah, Allah ya bashi nasara ya iya kashe mutun ɗaya daga cikinsu, amma fa ya sha abin da ake cewa bakar wahala na kin karawa a hannunsu!!. Ganin ya kashe mutun ɗaya yasa wani bujumin warriors ya diro ƙasa daga saman lafiyayyar dokinsa, yana dirowa kuma yasa kafarsa da karfin gaske cikin ɓacin rai za zafin nama haɗe da tafasar jini ya taka Kamran ɗin a kirjinsa, hakan yasa Kamran ɗin ya yi baya baya ya faɗi kasa cikin ciyayi, a fusace wannan warrior ɗin ya yi kansa, wata iriyar shaƙa da ya kai wa Kamran ɗin a wuyarsa ne yasa har idanunsa suka firfito waje kamar zasu faɗi ƙasa. Ran maza ne ya ɓaci, ace ɗan ƙaramin kwaro kamar wannan ya kashe masu mutun guda ɗaya? Ai dole ran maza ya ɓaci, dole su gwada mashi banbancin kwanji, dole su gwada mashi akwai maza a gabansa. Cikin fusata yasa hannu biyu ya ɗago Kamran ɗin sama, ga shi kuma ya shaƙe mashi wuya sosai, so yake ya daurasa a saman wuyarsa ya karya mashi baya shikenan ya kashe shi sun huta, shi ne yasa ya yi mashi irin wannan ɗagawa sama. Shi kuma ɗayan warrior da suka sha fafatawa da Kamran ɗin ya nufi kan gawar ɗayan da Kamran ɗin ya kashe yana ambatar sunansa yana kuma mai da numfashi. Saura kuma suna saman dawakansu, dan a cewarsu sun fi karfin su ɓata hannunsu wajen yin faɗa da Kamran ko su ce zasu kashe shi, ya yi masu kaɗan, kamar kiyashi suke kallonshi a gabansu su........ E manya manya maganin kanana ba, ya yi mazan fama. Sosai wannan bujumin mayakin ya ɗaga Kamran ɗin sama zai karya mashi baya, shi kuwa bawan Allah Kamran izuwa yanzu ya fita daga cikin hayyacinsa, saboda shake mashi wuya da wannan mayaki ya yi, sai fafutukar neman numfashinsa yake yi ya dai'dai tata.......... 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 19/7/2024.....✍️📚🌹 For information 0816139058 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________18🔥 Ya ɗaga shi sama da nufin ya sauke shi a saman wuyar tasa ya ɓalla mashi baya, sai dai bai kai ga yin hakan ba wata iriyar mahaukaciyar kifiya mai bala'in dafi ta sauƙa mashi tamkar sauƙar aradu a wuyar tasa, irin waɗan nan kifiyoyin ne wadda ake masu shiri na musamman wanda idan aka caki mutun da shi koda a in da ba zata iya kashe shi ba ne to dafin jikinta tsab zai kashe shi, in dai an harbeka da wannan kifiya to fa sai dai wani ikon Allah, amma wlh tsab zaka mutu, ba kai ba iya cigaba da rayuwa, dan da wasu irin poison masu haɗari ake dafa kifiyar na tsawon lokaci kafin a fara amfani da ita. Ai tana sauƙa a wuyarsa ma bai san lokacin da ya saki Kamran ɗin ya faɗi ƙasa ba, nan take bakinsa ta fara bulbular da wata farar kunfa fara kal kamar wadda ya ci dangerous poison. Kafin sauran warriors ɗin su yi wani yunkurin tuni ya zube ƙasa yana shure shuren mutuwa cikin raɗaɗin azaba tare kuma da kai hannunsa saman wajen da kifiyar ta cakesa, ga shi dai kifiyar ƴar marama ce ba kamar na sauran mayaka ko maharba ba, amma sai shegen ɓarna ke gareta kamar nuclear. A dubu ɗari sauran warriors biyar dake wajen suka fara waige waige suna neman ta ina aka jefo wannan kifiya?. Shi kuwa Kamran sai ƙoƙari ya ja numfashinsa ya dai'dai tashi yake yi, ya ci bakar wahala na shaƙar nan da ya sha a hannun wannan warrior ɗin, har ya fidda rai da rayuwa, sai kuma Allah ya ƙaddara ba zai mutu a hannun wannan bakin azzalumin mayakin ba!. Suna tsaka da waige waige basu ankara ba sai jin saukar wasu kifiyoyin har guda uku suka yi a saman wuyar dawakansu. Hakan yasa dawakan suka buga wani irin uban haniniya mai tashin kai tare da yin watsi da warriors ɗin da suke a saman nasu, kan ka ce me suma sun zube ƙasa tare da fara yin birgima suna sure suren mutuwa, already shi wancan warrior da aka fara harba a karon farko da kifiyar har rai ta yi hanlinta, ya mutu ya yi sanyi!. Sauran dawakai biyun kuwa bazama suka yi cikin dajin a haukace suna neman hanya. Su kuwa waɗan nan jiga jigan warriors ɗin mimmiƙewa tsaye suka yi suna masu cigaba da neman ta ina ake watso masu waɗan nan shegun miyagun kifiyoyin masu bala'in haɗarin wadda ba kowa yake iya mallakarsu ba sai shahararre kuma gawurtatcen mai kuɗi ko Basarake ko dai wani mai mulkin?!. Da kyar Kamran ya iya miƙewa zaune, yau ya ji hannun maza bawan Allah, idanuwansa sun yi jajir kamar wuta, jijiyoyin kan nan nasa duk sun mimmiƙe tsaye cirko cirko, har wasu siraran jijiyoyi ne suka fito mashi a wajen wuyarsa, ga wata uwar zufa da take tsastsafo mashi, gabaɗaya fuskarsa ta jike sharkaf da zufar, har wata ƴar canzawa ya yi cikin ƙanƙanin lokaci?. Abin mamaki a nan shi ne, duk wannan uwar wahala da Kamran ɗin yake ciki sam bai damu ba, hankalinsa ma yana a kan tunanin Prettya! Yanzu damuwarsa ɗaya shi ne ya samu ya miƙe ya bi bayanta ko zai iya cetonta daga hannunsu, shi ko ya damu wajen neman wanenen ya taimakesa ma bai yi ba, damuwarsa dai Pretty, hakan yasa ya yi ƙoƙari da kyar ta miƙe. Da kyar da suɗin goshi ya iya tattaro sauran karfin da suka rage mashi ya miƙe tsaye, har wani irin jiri yake gani yana gilma mashi, amma sabosa karfin hali sai ya daure ya cije ya fara ƙoƙarin ɗaga kafafunsa domin ya yi tafiya. Yana miƙewa warriors biyar da suke a wajen suka kewaye shi tare da zare takubansu, cikin wannan yare nasu suka yi magana a kan duk wanda yake harba masu wannan kifiya ya fito fili mana idan ba tsoro ba! Kuma idan ya cika cikakken namiji ya fito ne su gwabza gaba da gaba ba ya ɓuya yana harbinsu ba! Idan kuma bai fito ba to zasu kashe Kamran ɗin, sannan idan ya sake harbinsu da kifiya ya tabbata mace rago kuma lusari!. Shi dai Kamran ko kallonsu da kyau ma baya iya yi, wani irin ɗan duhu duhu yake gani, ƙoƙarin ɗaga mafafunsa kawai yake yi dan ya yi tafiya wajen Pretty. Cikin fusata ɗaya daga cikin mayaƙan ya nufi Kamran ɗin da wuƙa, dan a tunaninsa idan suka yi yunƙurin kashe Kamran ɗin wannan mai harbinsu da kifiya da ya laɓe a wani wajen zai fito. Ai kuwa hasashensu ya gaya masu gaskiya, dan kuwa wannan mayaki yana ɗaga takobinsa da nufin ya fillewa Kamran kai, kamar wani walkiya haka mutun ya bayyana a gabansa, sai dai lokacin da mutumin ya bayyana shi kuma mayakin baya da rai, domin kuwa wannan mutumi ya bayyane ne tare da fillewa wannan mayaki wuya da wata sharɓeɓiyar takobi dake hannunsa, irin mahaukatar takuban nan ne masu tsawo ga kaifin balai' na wuce misali a hannunsa. Matashin saurayi da a kallah ba zai wuce 35 years a duniya ba, dakakken jarumin ne na kin karawa, dan daga yanayin bayyanarsa da kuma tsayuwarsa a gaban waɗan nan warriors ɗin ya nuna cewa daka jiya ne shi ɗin bata yau ba, da alama shiga filin daga ba bakuwarsa bace, duk in da ake neman cikakken jarumin namiji to wannan mutumi ya kai, sanye yake da kaya kusan irin na jikin waɗan nan warriors ɗin, sai dai nasa ya sha banban da nasu, nasa ya fi nasu dakuwa sosai da sosai, sannan kuma shi bai sanya hular kayan yakin nasu a kansa ba, ya dai naɗa wata iriyar rawani a kan nasa wadda ta rufe mashi fuska kamar nikaf, sai kwayar idanunsa da suke sak irin na Pretty zaku gani, olive eyes ke gare shi shi ma, bayan waɗan nan idanun nasa babu kuma wani abin da zaku iya gani a jikinsa, kafafunsa suna sanye cikin wasu shegun takalma irin na mayaƙa masu matuƙar kyau ga karfi, a yadda ya yi wannan tsayuwa ya tabbata zaki ne shi ɗin a cikin zakuna. TO FAH, WAYE SHI?!!!. Gadan gadan ragowar warriors huɗun nan suka nufeshi da yaki, shi kuma ɗayan ya faɗi ƙasa gefe kansa ma ta yi gefe, domin kan nasa wannan matashin ya cire mai gabaɗaya. Faɗa suka farayi na gaske gaske, kai daga ganin wannan faɗa dukkansu kasan tsoffin hannu ne, sun saba da yaki, domin kowannensu yana faɗa ne cikin kwarewa da nuna fifikon iyawa. Shi kuwa Kamran bawan Allah, lallaɓawa ya yi a in da ya bar wajen nasu ya bi bayan Pretty, shi ita ce kawai a ransa, ita ce damuwarsa. Ya ɗan jima yana tafiya a kan wannan hanyar da ta bi ɗin, saboda a hankali yake tafiya, bashi da kuzarin iyayin sauri, dan fa babu karya ya wahala a hannun mayakin can, da an kara minti ɗaya zuwa biyu da sai dai gawarsa, shegu ne warriors ɗin can. Tafiya yake yi yana ƙoƙarin dawowa normal, yana jin jikinsa tana warwarewa, ya bar wannan matashi da basu san ko wanene shi ba yana ta fama da faɗa a wajen. Can ya hango Pretty zaune a saman wani dutse dake kusa da wata ƙatuwar dutse wanda wani dibgefen bishiyar ɗorawa ya fito a tsakanin duwatsun, sai bishiyar ta bada inuwa sosai a wajen, Allah mai iko, Allah mai yin yadda ya so a koma ina ne, yanzu bishiya ce ta fito a tsakanin duwatsu guda biyu kuma har ta girma haka tana bada inuwa, Allahu Akbar. Ganin ta a zaune a wajen yasa Kamran ɗin ya ji wani irin karfi ya zo mashi, sai ya ji wani irin daɗi da sanyi har cikin ransa, hakan yasa ya nufeta da sauri. Ita ma tana ganinsa ta miƙe tsaye daga zaman da take yi tana kallonshi har cikin ido. Ɗan kawar da kallonsa daga kan kyakkyawar kwayar idanun nata ya yi, dan kada ku manta suna birkita mashi lissafin ƙwaƙwalwa. Da sauri ya ƙariso wajen nata. Da ƴar gudunta ita ma ta ƙariso in da yake, tana zuwa kuma ta faɗa jikinsa tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, baiwar Allah dama duk a tsorace take, ta zauna a wannan waje ne kawai dan ba yadda zata yi, duk da cewa bata san wanenen Kamran ba, amma ya fi mata kowa dake a cikin dajin nan sau dubu, dan kuwa shi tun farko da suffar taimako ya zo masu, so hakan yasa take tsananin jinsa a cikin ranta sosai da sosai, wannan dalilin kuma yasa ta rungume shi tana kerman tsoro. "Pretty are you okey? Where's the warriors?!". Ya faɗa da wata iriyar kasalalliyar murya wadda da ka jita kasan ta karfin hali aka yi aka ƙaƙalota dan ayi magana. Ya yi magana kuma shi ma yana rungumarta da kyau a jikinsa, dan wani irin kukan da take yi sai ta baka tausayi, da alama taga mutuwa kusa da kusa ne!. Kasa amsa mashi tambayar da ya yi mata ta yi, sai ma kara ƙanƙame shi da ta yi tana mai kara sautin kukan nata tare da gudun hawayenta. Ɗan bubbuga bayanta ya fara yi yana mai faɗin. "Is okey Pretty, ki yi shiru". Ina ta kasa yin shirun. Ganin haka yasa ya raba jikinsa da nata tare da riƙo hannunta suka koma saman dutsen da ta tashi ɗin suka zauna. Nan fa ya shiga rarrashinta yana mai lallaɓata a kan ta yi shiru. Ɗan rungumota a gefen kirjinsa ya yi yana mai cigaba da bubbuga bayanta alamar rarrashi. Almost 10 mins suna a haka kafin ya samu ta fara yin shiru, sai wani irin shesshekar kuka mai ban tausayi take yi!. Sai da ya tabbatar da ta ɗan nutsu ya lallaɓata ta yi shiru, sannan ya sake tambayar a karo na biyu ina mayakan suke?. Fararen idanun nan nata sun yi jajir saboda kukan da ta sha, abinku da farar fata harta fatar face nata ya yi jajir da shi, hancin nan nata kamar wadda aka kama mata shi da clip na kama kayan na tsawon lokaci yanzu aka saki, ya yi jajir da shi, duk kuma saboda kukan ne. Kyakkyawar farar tafin hannunsa Kamran ɗin ya kai saman beautiful face yana goge mata hawayen, ta kwanta shiru a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya tare da mai da numfashi, ƴar kaniya taga bala'i ne yau. Ɗan shafa kyakkyawar bakin gashin kan nan nata ya yi kafin ya ce. "Pretty meyafaru ne? Where's the warriors?". Sai a lokacin ta ɗan ɗago kanta daga saman kirjin nasa, ɗan bakin nan nata har yanzu yana kerman tsoro, kyakkyawar red lips ɗin nan nata sai ɗan ɓari suke yi. Har yanzu ɗan siririn zazzaƙar voice ɗin nan nata rawa yake yi, da kyar ma ta iya bashi amsa da. "Someone killed them all, i don't know who's he, he closed his face with veils, only his eyes i saw". Ta bashi amsa tare da sake komawa ta kwantar da kanta a saman faffaɗar kirjin nasa, saboda shegen son jiki ne da ita kamar mage, ga bala'in tsoro, amma akwai wayo kuma sosai da sosai!. Ta wani lafe mashi a jiki, da yake shima yana cikin damuwa da tashin hankali sai bai yi mashi kamar a jikinsa ta kwanta ba, hankalinsa da nutsuwarsa basa a tarrare da shi!. Jin abin da ta ce ne yasa ya tuna da wannan mutumi da ya taimakesa a yanzu, wanda ya bari suna fafata yaki da warriors ɗin can kenan. Tunani ya fara yi na cewa in dai haka ne kenan wannan matashin shi ne ha taimaki Pretty ya kashe warriors da suka biyota kafin ya ƙarisa wajensa shi ma ya taimaka mashi kenan? To waye shi?. Ya tambayi kansa tambayar da bashi da amsarta. Kamar wadda aka mintsina ya ce. "Pretty let's go, I want to see that man, I have some questions that I want to ask him, and I want to see his face". Ya kai karshen maganar yana shafa kyakkyawa kuma lallausan curly hairnta!. "Kamran ina tsoro, i don't want to go they again, this people's aren't a human being at all!". Ya fahimceta sosai, ya fahimci ta yi tsananin tsorata ne, baiwar Allah bata taɓa ganin makamancin hakan ba. Abin da bata sani ba shi ne, waɗan nan warriors da suke shigowa cikin wannan daji duk su suke nema, idan baku manta ba tun farko mayaka ne suka biyo mummynsu, kuma da suka biyota ba ita suke son kamawa ko kashewa ba, abin da yake cikin cikinta suke son ɗauka, which means kunga su Prettyn kenan suke nema ido rufe ko ta halin ƙaƙa, tsawon shekaru goma kenan yanzu kullun sai sun shigo cikin wannan dajin neman su Prettyn, sun kasa hakura su yarda cewa mum twins da cikinta sun mutu tun lokacin da suka harbeta da kifiya, sun ki yarda ta mutu, da alama sun lura da cewa wannan mayakin da ya harbeta ɗin bai harbeta a in da zata mutu ba, hakan yasa suka kasa yarda da ta mutu ɗin, shi ne yasa kullum basa gajiyawa wajen zaryar neman su twin's ɗin! Sannan idan kuka yi duba da yadda Mamman Kamran ta ce bata taɓa ganin warriors a cikin wannan dajin ba sai yau, hakan zai sa ku gane e lallai dole akwai abin da suke nema wanda yasa a koda yaushe suke zuwa, to ba komai suke nema ba face su Pretty, a haukace suke suna nemansu ido rufe, ko araye ko amace, su dai kawai su gansu, sai dai kuma duk cikinsu babu wanda yasan su Pretty ɗin ai, basu san kamanninsu ba! Suna dai nemansu, a tunaninsu za su iya ganesu ta hanyar mum ɗin su tun da sun santa ita kam!!. Abin tambaya a nan shi ne, me zasu yi wa twin's ɗin idan suka kamasu? Meyasa basu buƙatar mamansu sai dai su? Meyasa zasu iya kashe mum ɗin tasu dan kawai su fasa cikinta su ɗauke su? Ina zasu kaisu? Shin turo su aka yi ne ko kuma bisa radin kansu ne? In turosu aka yi to wanene ya turo su?. Waɗan nan amsoshi duk sai alkalamina ne kawai zai warware maku wannan cakwakiya!!. "Pretty kada ki ji tsoro, mu je kawai". Ya faɗa tare da sanya hannunsa ya ɗago haɓarta. Jinjina mashi kai ta yi, magana ta gaskiya ta amsa mashi da okey ɗin ne kawai, amma wlh tana tsoron zuwa wajen fiye da tunaninku, mayyar tsoro ce ga shegen son jiki, yanzu da wuya idan bata yi mafarkin wannan abin da ya faru ɗin ba, kaɗan daga cikin aikinta ma ta yi mafarkin warriors ɗin sun kasheta, ga shi dai a zahiri basu kasheta ɗin ba, ko taɓata ma basu yi ba, amma a mafarki tsab zata yi mafarkin sun kasheta!. Miƙewa ta yi daga jikin nasa tare da saukowa kasa daga saman dutsen, sai narai narai da idanu take yi kamar zata yi kuka. Lallaɓata ya rinƙa yi yana karfafa mata gwiwa, sai dai ina, wannan bata san karfafa gwiwa ba, tsoro kawai ta sani a rayuwarta kamar farar kura, tana gani a gaban idanunta wannan matashi ya yi wa waɗan nan mayaka biyu da suka biyotan kisan killah na rashin imani, sannan ace mata ta sami kwarin gwiwa? Ai ba wannan magana, a dai yi sha'ani kawai...........😅 Hannunta ya riƙo cikin nasa suka nufi wajen da suka fito, izuwa yanzu ya warware ya koma normal, sai maƙoshinsa da ta bushe kwalam yana buƙatar ruwan sha, kishi yake ji sosai da sosai, sai dai babu ruwa a kusa, dole sai sun je wajen wannan ƙoramar zai iya samu ya sha. Pretty dai bata yarda da iya hannunta kawai da ya rike ba, gani take yi fa warriors ɗin nan zasu kasheta, dan haka sai ta matso jikinsa sosai ta rikesa ta wajen ƙugunsa domin ta rage tsoro. Wani irin shock ya ji a jikinsa na rungumo mashi kugu da ta yi, wannan yarinya akwai son jefa mutun cikin bala'i, ya faɗa a cikin ransa tare da ɗan riko shoulder ɗinta, saboda ta ɗan kara nutsuwa mashi!. A haka suka nufi wajen nasu, sai baya baya take yi duk da ta wani dungume mashi kugu kamar nata, da alama ma ita sam bata san amfanin wajen da ta runguma ɗin ba, ita fa kawai ta ɓuya kada mayakan nan su ganta, a kan haka koma inane zata runguma babu ruwanta, to bama dan Kamran ɗin ya yi mata daɗin baki ba ai wlh da babu in da zata je, sai dai duk wacce za'ayi ayi!........ Pretty manya! Yanzu ma da kuka ganta zaune a saman dutsen nan wannan matashin da ya kashe mayakan da suka biyota ɗin ne ya zaunar da ita a wajen, ya kuma ce kada ta tashi har sai Kamran ya zo! Shi ne yasa kuka ga ta daure ta zauna shiru a wajen, amma a tsananin tsorace take sosai kafin Kamran ɗin ya zo. Abin mamaki tun da suka doshi wajen suka ji shiru babu wani hayani ko kuma motsin wani bil adama, tsit kake ji kamar babu waɗan da suka taɓa yin faɗa a wajen. Hakan yasa Kamran ya kara saurin dan ya iso wajen. Wayam babu kowa a wajen, ga gawarwakin warriors ɗin dukka a zube a kasar wajen, amma babu wannan matashin a wajen, babu shi kuma babu gawarsa, hakan na nufin basu kashe shi ba kenan, shi ne ya kashesu kuma ya yi tafiyarsa, to wanenen shi?. Ɗan waige waige Kamran ya fara yi ko zai hango giftawa ko kuma wani motsi na wannan matashin. Amma ina, sam babu ko mai kama da shi a arear wajen. A hanzarce ya saki Pretty tare da faɗin. "Wait for me here am coming". Ina ai kara ƙanƙame shi ta yi tare da ƙoƙarin saka mashi kuka a kan kada ya tafi ya barta. "Pretty nothing will happen, you hear? Please be strong kin ji? Zan duba mutumin nan ne da ya taimaka mana, maybe bai yi nisa ba sai mu san who's he ko?". Ina ai kara ƙanƙame mashi ƙugunsa ta yi tare da kwantar da kanta a saman kirjinsa tana faɗin. "No Kamran, i can't stay here, ina tsoro sosai, let's go together kawai!". Tana magana hawaye na bin saman lallausa kuma jajir ɗin kumatun nan nata!. Ganin yadda ta tsorata sosai kuma har yanzu tana cikin tsoron ne yasa ya ji muguwar tausayinta ya kama shi, duk sai ya ji wani iri babu daɗi, ya ji ba zai iya tafiya nan da can ya barta ba, ta rigada ta tsorata sosai, dan haka sai ya rungumeta da kyau a jikinsa tare da kai hannunsa cikin dabara ya cire hannayenta data harɗesu a ƙugunsa, ya mayar mata da su saman cikinsa ta wajen kirji, saboda zaman hannayen nata a ƙugunsa fa suna saka shi yana jin wani irin yanayi. "Is okey Pretty, I can't go anywhere na barki, mu je mu duba Sweetie tun da mai taimakon ya tafi, kuma i promise you that zan kula da ku sosai, sannan zan rinƙa zuwa wajenku sosai da sosai, gobe ma idan zanzo zanzo tare da kwari da bakata in fara koya maki harbi kin ji ko?". Tana daga kwance luf a saman kirjin nasa ta ɗaga mashi kai alamar e ta ji. Shafa kanta ya yi har izuwa bayanta kafin ya ce to. "Let's go ko? Mu je wajen Sweetie". Nan ma jinjina mashi kai kawai ta yi, ita dai koma me ba zata rabu da jikinsa, dan gani take yi tana sakinsa tabbas waɗan nan warriors ɗin za su tashi su kamata, shiyasa ta kara ƙanƙame shi!!. Cikin ramin nasu suka nufa, tana rike da shi har suka je bakin wajen, sannan ne ya ce to ta sake shi ta fara shiga ciki. A hanzarce ta sake shi ta yi maza ta buɗe kofar ta faɗa ciki abinta, Allah ya rufa masu asiri warriors ɗin da suka kalli wajen ɓuyar tasu ma dukka an kashesu, yanzu babu wanda yasan in da suke. Sai da ta shiga shi ma ya rufa mata baya, kai tsaye wajen Sweetie suka nufa, baiwar Allah tana kwance a saman gadonsu shiru, kamar mai tunanin wani abin, ta ɗaga idanu tana kallon sama yadda kuka san tasan abin da take kallo. Jin motsin shigowa wajen ne yasa ta fara faɗin. "Pretty meyasa kika daɗe haka?". Da gudu ta ƙarisa wajen ƴar uwar tata tare da hayewa saman gadon, dai'dai lokacin ita kuma Sweetien ta miƙe zaune tana jiran amsar da Prettyn zata bata, tana zuwa ta rungumeta sosai tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. A matukar ruɗe Sweetien ta fara tambayarta. "Pretty lafiya kike kuwa? Meyafaru? Meyasa kike kuka? Please tell me kada kisa zuciyata ta buga!". Ƙarisowa wajen gadon Kamran ya yi tare da zama a kusa da su. "Pretty why zaki tayarwa da Sweetie hankali? Me kuma abin sake yin kuka a nan tun da komai ya wuce?". Cewar Kamran kenan!. Cikin kuka ta ce. "Dole zan yi kuka Kamran, da yanzu sun kashe ni shikenan ba zan sake ganin ƴar uwata ba? Shikenan mun rabu da ita? Da waye ita zata zauna idan bana nan? Waye zai kaita toilet? Waye zan bata abinci? Waye zai bata kayan sakawa? Waye........." Bai iya bari ya kai ƙarshen jero mashi maganganun nata ba yasa tafun hannunsa ya rufe mata ɗan bakin nata, wannan yarinya sai shirin Allah, kawai ta zo ta ɗagawa ƴar uwarta hankali a banza bayan komai ya rigada ya wuce. "Kamran Please tell me me ya sami Pretty? Who attack her? Who want to kill her da na ji tana faɗa? Meyake faruwa ne?". Tana magana kamar zata yi kuka baiwar Allah, har fararen idanunta su cika tab da kwallah, duk ta ruɗe!. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Sweetie calm down, nothing happen, kawai wasu ne suka so raunata mu". Daga nan ya kwashe labarin abin da ya faru ya gaya mata ba dan ya so ba, sam bai so ta san komai ba, dan baya son abin da zai ɗaga mata hankali har ya sanya kuka, saboda matsalar idanunta!. Jin abin da ya faɗa ne yasa ta kara ƙanƙame Pretty suka manne juna kamar zasu shige jikin juna, nan take ita ma jikinta ya soma kerma, ta tsorata, cikin damuwa take faɗin. "Nashiga ukuna, my Pretty kashe mun ke suke son yi kenan? Me kika yi masu? Wayyo mummynmu". Tana magana tana ruwan hawaye, ita ma Pretty ruwan hawayen take yi. Yau dai Kamran ya ga ikon Allah, haka ya hau rarrashinsu su biyun dukka, baya son Sweetie ta yi kuka ko kaɗan, dan yana gudun idanun nan nata su lalace gabaɗaya, yanzu a point ɗin da taken nan za'a iya yi mata magani, da Mammarsa zata yarda ma ai da ita ma zata iya yi mata magani, amma ba zata taɓa yarda ta taimaka masu ba, so yana so ne dama ya lallaɓa Mamar tasa ta gaya mashi menene maganin wannan itaciya mai gubar idan ta taɓa idanun mutun ya dai'na kallo, idan ta gaya mashi zai zo ya yi mata ganin da kansa, so idan tana kuka tana mussuƙe idanun wajen goge hawaye za'a iya samun matsala su lalace gabaɗaya su ki gyaruwa, hakan yasa hankalinsa ya tashi da ya ganta tana kuka. Ba kakkautawa ya hau rarrashinta yana bata hakuri, ga shi sun haɗu su biyu sai yi suke yi, ba abin ka sami bulala ka zanesu ba........😅 Kawai sun saka bawan Allah cikin damuwa, Sweetie ta ce kashe mun ke suke son yi, Pretty ta ce rabani dake suka so yi, haba sai su kara sautin kukan nasu tare da kara manne juna, na gaya maku kamar a sami bulala a zanesu, amma ya za'ayi? Dole ne kawai Kamran ya lallaɓasu ya basu hakuri ya samu su yi shiru!. Da kyar ya iya samu ya lallaɓasu suka yi shiru, sannan ne ya samu damar gaya masu cewa gobe zai zo ya fara koyawa Pretty harbi da kifiya, yanzu zai je gida kada Mammarsa ta nemesa, dan ya ce mata ba zai wuce one hour ba, yanzu kuma yasan awa ta wuce. Pretty kamar zata yi kuka, bata son ya tafi ya barsu, tana tsoro sosai, amma ya zata yi? Dole haka ta hakura suna ji suna gani ya tafi. Yana tafiya suka kara mannewa junansu saboda tsoro. Lallai da alama yau su Pretty babu ko iya cin abinci, dan naga alama tsoro ba zai barsu su iya raba jikinsu da juna ba😅 to mu dai bari mu leƙa KINGDOM OF POWER mu ga me ake ciki?. KINGDOM OF POWER💪🔥 Almost 10 mins Gimbiya Chuchu tana zube ƙasa a saman gwiwowinta, shi kuwa Yah Jawad yana cikin room ɗinsa yana shiryawa, kamar zata yi kuka, abin da bata sababa, duk kafafunta ciwo suke yi mata, sai wani irin raɗaɗi da zogi suke yi mata, tana son ta yi kuka ko zata rage jin raɗaɗi, amma kuma tana tsoron yin kukan kada Yah Jawad ya fito ya sameta, dan ya ce kada ta bari ya isko hawaye ko ɗigo ɗaya a saman face nata, so tana tsoron kara laifi a kan laifi, hakan yasa ta daure ta cije, amma fa ga fararen idanun nan nata sun yi jajir da su, alamar ta wahala. Sai da ta kara 5 mins a haka sai ga shi ya fito shirye cikin wasu tsadaddun kayan barcinsa wando da riga, rigar mai karamar hannu ce wandon kuma zuwa dai'dai gwiwowinsa ta tsaya mashi, ya yi wa kayan matuƙar kyau sosai, ga shi fari tas da shi, launin kayan kuma brown color, hakan ba ƙaramin kyau ya yi mashi ba, ya fito a balarabensa, ga gashin kan nan nasa da ya sha gyara sai kyalli yake yi, gashin yana kwance luf, sai suba wani irin daddaɗar kamshi yake yi, bai sanya takalma a kyawawan fararen kafafun nan nasa ba. Tun da ya fito sai kallonsa ta ƙasan ido take yi, ya yi kyau ba karya. A saman bakin bed mattress ɗin nasa ya zo ya zauna tare da kai hannu ya ɗauko ɗaya daga cikin wayoyinsa. Kamar zata yi kuka ta ce. "Yah Jawad dan Allah ka yi hakuri, na tuba ba zan sake ba". A hankali ya ɗaura waɗan nan dara daran idanun nasa a saman face nata, ta tsuke ɗan bakin nan nata kamar wadda aka yi yunkurin dallawa mari. Shiru ya ɗan zuba mata idanu na ƴan mintocin da a kallah zasu kai 3 zuwa 4, sannan a nutse ya fara motsa lips nasa ya fara magana in a low voice sosai. "Jannat tell me your problem first, what are you doing with all those pics that your talking anytime?". Jannat shi ne ainahin sunan Gimbiya Chuchu, kuma sunane na kakarta wadda ta haifi mahaifiyarta, shi ne yasa mamanta ta ɓoye sunan nata suke kiranta da Chuchu. Amma banda dukka brothers ɗin nasu, su kam da Jannat ɗin suke kiranta!. Narai narai da idanu ta yi, ita bata san me zata sake ce mashi ba, ita da kanta bata san me take yi da hotunan ba, ko kallon hotonan ma fa bata sake komawa ta yi idan ta ɗauki hoton, ita dai ta ɗauka ɗin ne kawai. Manya kuke ji kenan ita dai ta ɗauka kawai abinta..........😅 "Sorry Yah Jawad ba zan sake ba, na yi alkawari zan dai'na ɗaukar hoto daga yau". Ta kai karshen maganar cikin ɗan shagwaɓa. "Okey zaki dai'na ɗaukar hoto ne ma ba kin daina ba? Wato zaki cigaba kenan". A hanzarce ta girgiza mashi kai tana faɗin. "No I mean na daina not zan daina, nama dai'na, please yah Jawad". Shiru ya yi mata bai sake yin magana ba, sai ma kunna wutar screen ɗin wayarsa da ya yi ya fara latsawa. Shagwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka, har ga Allah ta gaji, ba zata iya jurewa ba. "Yah Jawad please am tired, ka yi hakuri dan Allah". Yadda ta yi maganar a shagwaɓe sosai ne yasa ya dawo da kallonsa a saman fuskarta. Slowly ya fara binta da kallo from head to toe, kallon one min ya yi mata kafin ya kawar da idanun nasa izuwa saman screen ɗin wayarsa. "We done with the case one, na ji na hakura, amma idan na sake kamaki a kan case ɗin pics zaki sha wahala, lest go to the second case, waye ya ce ki fito daga ke sai kayan barci? Are you out of your sense? Mutun nawa kika ci karo da shi before ki iso nan? And ina ɗankwalinki? Kin kalli irin dressing da yake a jikinki kuwa?". Kasa jure neel down ɗin ta yi, saboda zafin da gwiwowinta suke yi mata, hakan yasa idanuta suka ciko tab da kwallah, ta kuma kasa iya dakatar da kwallar daga zuba mata a saman lallausan kumatunta, tana ji tana gani suka fara zubowa wani na bin wani kamar an buɗe fanfo, ita yanzu me zata ce mashi? Shi ne abin da take tunani, tsantsar danasanin zuwanta part ɗinsa ne a cike a cikin ranta, ji ta yi gabaɗaya haushinsa ma take ji. "Am i not talking to you? Amsa me, tell me the reason why kika fito da kayan barci and without ɗankwali?". Ya faɗa still kallonsa na'a kan screen ɗin wayarsa. "Am so sorry Yah Jawad, na manta ne na fito a haka, amma ba zan sake ba, na tuba". Yadda ta yi maganar daga ji kasan a kule take har wuya da haushi. Jin yadda ta yi maganar ne yasa ya dawo da kallonsa a saman fuskarta. Ganin hawaye suna bin saman kyakkyawar kumatun nata ne yasa ya ɗan.............. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 22/7/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________19🔥 PLEASANT ATMOSPHERE🥰🕊️ Jin yadda ta yi maganar ne yasa ya dawo da kallonsa a saman fuskarta. Ganin hawaye suna bin saman kyakkyawar kumatun nata ne yasa ya ɗan zaro dara daran idanuwansa waje. "Bana ce kada na kara ganin hawaye a saman face naki ba? What are you crying for?". Jikinta na kerma ta nuna mashi wajen gwiwowinta da suke yi mata raɗaɗi tare da zogi. "Yah Jawad am tired for this kneel down, my kneel and my all leg's is paining me, please for give me, ba zan sake ba fa". Tana magana hawayen suna mai cigaba da bin kuncinta. Shiru ya ɗan yi na tsawon a kallah 1 mins, ganin hawayen nata na kara tsananta ne yasa in a low voice kamar mai raɗa ya ce. "Firstly tell me da su waye kika haɗu before you reach here?". Cikin kuka ga voice ɗin nata baya fita sosai ta ce. "Only uncle Taheer ne kawai". Shiru ya ɗan yi na a kallah two mins kafin ya ɗan kawar da kallonsa daga kanta, sannan ya ce mata. "Okey start up, ki zauna a saman bedside drawer nan". Ai tun bai kammala kai karshen maganar ba ta yi maza ta miƙe, gwiwowin nata sun yi jajir da su, saboda hasken fatarta, ga shi luwai luwai, ba zata iya jurar wahala ba komai ƙanƙantarta. Da kyar ta iya ƙarisawa wajen bedside drawer ta zauna tare da yin ƙasa da kanta tana mai cigaba da ruwan hawayenta. "This tears for what again?". Ya faɗa ba tare da ya kalli in da take ba, da alama ta wutsiyar idanu ya saci kallonta har yasan bata dai'na ruwan hawayen ba. Kyawawan fararen tafukan hannayenta ta kai saman face ɗin nata, share hawayen nata ta farayi tana mai jin haushinsa sosai a ranta, ya wani zo ya saka mata kafafunta suna yi mata ciwo a banza dan mugunta. "I will going to give you your phone now, but idan kika bari na sake kamaki a kan this case babu mai karɓarki a hannuna, kin sani ai, kinga irin punishment da nake bawa su Sarina ba? Irinsa zan yi maki kema, now ki wuce ɗaki kada ki kuskura ki sake fitowa sai da safe". Ya kai karshen maganar tare da miƙo mata wayar tata. Hannunta sai karma yake yi ta kai hannu ta karɓi wayar tare da faɗin. "Thank you, In Sha Allah I won't do it again". Shiru ya yi bai sake yin magana ba, haka zalika bai sake ɗago idanu ya kalli in da take ba, sai dai yasa hannunsa ya yi mata nuni da hanyar kofar fita, alamar zata iya tafiya. Duk da kafafunta suna yi mata zafi hakan dai ta daure ta miƙe a hanzarce dan ma kada ta kara yi mashi wani laifi, dan tasan halinsa sarai, baya yi wa su Gimbiya Sarina ta daɗi idan ya rikesu, idan suka yi laifi yana azabtar da su dai'dai gwargwado, dan haka tasan muguntarsa sarai a kan wasu, ƴaƴan King Zuhair ɗin ne dai basu taɓa shiga hannunsa ya basu punishment ba sai yau ita Chuchu ta shigo hannunsa, kuma da alama tana da sa'a ya yi mata hukunci sassauƙa. Kofar fita ta nufa a hanzarce, tana tafiya tana jan kafafu tare da ɗan ɗingisasu. Ta wutsiyar idanu ya bita da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, har sai da ta fice daga cikin ɗakin ne ya mai da kallonsa full a saman screen ɗin wayar tasa ya cigaba da abin da yake yi, daga karshe ma sai ya miƙe ya fice daga cikin bedroom ɗin izuwa na JAISH, dan wani lokaci ma a tare suke kwana, so sai ya tattare wayoyinsa dana Fanan and Sarina ya fice da su gabaɗaya. A bangaren JAISH ɗin kuwa, bayan sun kammala cin abincin daren, wanka shi ma ya shiga ya yi kamar yadda Yah Jawad ya yi, sannan ya shirya cikin wasu kaya na shan iska masu bala'in kyau da tsada, ya fito izuwa wajen daddynsu. Haɗaɗiyar elevatornsu ya haye izuwa part na King, dan daddyn nasu ne ya kira shi a kan ya zo part ɗinsa ya samesa, ya yi matukar kyau sosai, sai tashin daddaɗar kamshin yake yi kamar anyi ɓarin perfume a jikinsa. Ƙasa ƙasa ya yi sallama a bakin kofar shiga babbar parlourn King, in da su Momma suke haɗuwa kenan, a baƙin kofar da akwai wasu jiga jigan zataran warriors guda biyu da suke tsaron kofar. Babu kowa a cikin parlourn, sai wani fitinannen kamshi da ya bule ko'ina a cikin parlourn, ta ko'ina tsab tsab tamkar babu wanda ya taɓa taɓa komai dake cikin parlourn, da alama masu yi wa part ɗin hidima kwararru ne sosai wajen iya gyara. Kai tsaye wata siririyar stair case ya nufa, ita kanta wannan stair case ɗin abar kallo ce, ta haɗu iya haɗuwa! Ga wasu kwayayen lantarki dake bada wuta mai haske a jikin duk wani step ɗaya, hakan ba ƙaramin kara fito da golden color pentin da yake wajen ya yi ba, sai ya yi tamkar ginin ɗanyar gold, abin ya ƙayatar matuƙa, ga wasu decoration na wasu haɗaɗun tsararrun flowers dake a manne a jikin bangon wajen stair case ɗin, abin dai sai wanda ya gani, amma fa ba'a magana wajen haɗuwar part ɗin King. A bakin kofar karamar parlourn sama ya yi sallama. Ita ma parlourn ta ƙawatu da kayan alatu na more rayuwa wadda baki ya yi kaɗan ya zayyanosu. Ɗakuna ukku ne a cikin parlourn, sai dai da alama ɗayan ɗakin ganawa da baki masu matuƙar mahimmanci ne, duba da yanayin tsarinsa ɗauke da luntsuma luntsumar sofas set uku launika daban daban, ash, golden and milk, ga wani shegen rug a tsakiya, hakan yasa ya yi kama da ɗakin ganawa da manyan baki, biyun kuma bedrooms ne. Ɗakin dake a tsakiya ya nufa, yana taku cikin jarunta tare da nuna izzar sarauta, da alama hakan a jinunsu take. Sallama ya yi wa daddyn nasa a bakin kofar shiga bedroom ɗin. An ɗauki a kallah two mins kafin daga ciki king ya amsa mashi sallamar tare da yi mashi izinin shigowa. Shiga cikin ya yi bakinsa a ɗauke da siririyar sallama again. Hmmmm bedroom na King aljannar duniya kenan, ga shi ya sha gyara, iya katafaren King bed ɗinsa ne kawai a cikin bedroom ɗin, sai wasu tsala tsalar shinfiɗu na alfarma da suke har guda uku ta kowani ɓangare a cikin bedroom ɗin, da yake ɗakin yana da bala'in girma sosai, hakan yasa akai mashi shifiɗu na wasu shegun tsadaddun Turkey carpet masu bala'i laushi, kyau da kuma tsada har guda uku, tiles na floor ɗin bedroom ɗin kamar glass yake, sai kyalli yake yi fari kal da shi, dressing room na King glass ne mai kama da transparent, daga ciki shi zai iya hango na waje wanda ya shigo cikin bedroom ɗin, wanda yake a cikin bedroom ɗin kuma ba zai iya ganinsa ba, haka yanayin tsarin dressing room ɗin yake, ya tsantsaru iya tsantsaruwa, curtains for windows and doors ma kawai ya isa ya sanya mutun ya wuni yana kallonsu ba tare da ya gaji ba, saboda haɗuwarsu. Kusan yanayin design na bed ɗin nasa iri ɗaya dana Momma, sai dai nasa ya fi nata girma sosai, da kuma banbancin colors, nasa color dark navy blue ne sosai, idan ka gansu ma kace bakakene, so haka shinfiɗun carpet dake a tsakiyar room ɗin ma yake, kana taka saman carpet ɗin nan kafarka zata lume ciki lausasan gashin da aka kawata kwalliyar carpet ɗin da su, tamkar gashin jimina, da yake mafiya yawan shinfiɗun gidan sarauta dama da gashin jimina ake yinsu!!. Kofofi biyu ne a cikin room ɗin, daga na balcony sai na bathroom! Sai drawers dake gefe da gefen bed ɗin wanda aka ɗaura wasu ƙayatattun lamp masu kyau da kuma hasken gaske, babu dressing mirror a cikin room ɗin, da alama yana cikin dressing room. King na zaune a tsakiyar katafaren bed ɗinsa, sanye yake da kayan barci, da alama ya yi shirin kwanciya ne, da kamshin perfume ɗin jikinsa da kuma daddaɗar kamshin perfume na room ɗin sai suka haɗu suka bada wani irin kamshi mai kwantar da hankali, ga kuma sanyin Ac mai sanyaya zuciyar mai shaƙa. Sanye yake da wani haɗaɗɗen siririn farin glass a face nasa, ya tasa wata shegiyar tsadaddiyar laptop a gabansa yana aiki, dama idan baku manta ba na gaya maku shi King architecture ne, so da alama wani aiki yake fitarwa a cikin laptop ɗin, ga kuma wasu envelope wadda a kallah zasu kai guda ashirin a saman bedside drawersa ta kusa da in da yake zaune. A kusa da shi Jaish ya zauna yana ɗan yamutse fuska kamar wadda yake jin barci, hannunsa ya kai tare da ɗauko pillow babba guda ɗaya daga cikin pillows da suke jere a bayan King ɗin, ya ɗaura a saman laps ɗinsa yana mai do da kallonsa a saman laptop ɗin na daddyn nasu. "Good evening my lovely dad". Ya faɗa a sanyaye. "Evening my pleasure". King ya bashi amsa cike da so da kauna!. "Daddy what are you doing by this time around? You have to be sleep ka hutawa ranka, since morning you're working like watch, yanzu dare kam ka huta mana, and da sassafe kuma zaka sake fita fada ka yi attending mutane fa, gaskiya ka kwanta ka huta, koma wani aiki kake yi ka barshi ko kuma ka kawo na yi maka". Nisawa ya yi kafin ya ce. "Jaish i can't sleep now, a duk lokacin da naga al'umma cikin damuwa da tashin hankali bana iya barci har sai naga abin da zan iya yi a kai". "But daddy hakan zai yi affect na lafiyarka, at least ka rinƙa samun 12 hours kana barci". Wasu envelope guda goma King ɗin ya kwaso daga saman bedside drawersa, miƙa mashi su ya yi yana faɗin. "Take this envelope, na ƴaƴan talakawa guda goma ne, ka nutsu ka duba takardun da kyau, naka ne, ina son ka bawa biyar daga cikinsu aiki a companynka, biyar kuma karatun surgery dr suka yi, so ka miƙawa Raj su ya sama masu aiki cikin gaggawa, bana son su ɓata lokaci basu fara aiki ba, dan mu duk ɗan talakan da ya kawo kukansa gabanmu da izinin Allah ba zai tashi daga gabanmu ba sai mun saka shi dariya, dan haka a sama masu aiki cikin gaggawa, aiki kuma mai matuƙar kyau sosai wanda zai sa su ji suma masu gata ne a duniya". Ya kai karshen maganar yana mai cigaba da zanen da yake yi, wani katafaren ginin gidan marayu mai haɗe da kamarantar boko da islamiya a kusa da gidan yake zanawa, ga kuma masallaci ta gefe guda, duk na marayun ƴaƴa ne da yake son gina masu, domin marayu sun yi yawa ba wajen zama, a kallah irin wannan zane sun kai biyar yanzu ya yi, kuma kowani gida zata ɗauki yara marayu sama da 500, ga ingantaccen abinci da wajen kwana mai rai da lafiya da zai sama masu, makaranta kyauta, suma zasu yi karatu kamar sauran ƴaƴa masu iyaye kuma masu gata, komai a kyauta, abin ban sha'awa kuma dukka filayensa ne ya sadaukarwa da marayun dasu, King Zuhair ba dai farar zuciyar taimako ba, yana kaunar jama'arsa, shiyasa suma suke kaunarsa kuma suke kaunar mulkinsa, shi ɗin baya ne goya marayu, aiki yake yi tukuru ba dare ba rana duk domin yaga rayuwar jama'arsa ta inganta, idan aka ce maku farar zuciya ma ai an rage, King Zuhair ya wuce haka, baya kyaman talaka! Kowa nasa ne sai wanda ya kawo mashi wargi, dan baya ɗaukar raini! Yanzu zai haɗawa mutun jini da majina! Ga shi idan ya kamaka ka yi laifi babu sonkai babu komai a nan take zai yanke maka hukunci ba tare da ɓata lokaci ba, kamar yadda jininsa take a tafashe haka yake wajen zartar da duk abin da zai yi babu ɓata lokaci!. Sallamar Yah Jawad ce ta sanya suka mayar da hankalinsu a kan kofar shigowa. Prince Jaish ne ya amsa mashi sallamar yana mai dawo da kallonsa a kan King ɗin, domin ya ji me zai ce, shin Jawad ya shigo ne ko yaya?. Kyakkyawar gerarsa ɗaya king ɗin ya ɗaga mashi alamar ya ce da Jawad ɗin ya shigo. Ba ɓata lokaci ya sanar da shi hakan. Sake kwankwasa siririn sallama Yah Jawad ya yi kafin ya shigo ciki. A kusa da King ta ɗayan bangaren shi ma ya zauna, sai yazamana king yana a tsakiyarsu. "Barka da dare daddynmu, ya hutu?". Shi ne abin da Yah Jawad ya faɗa. "Barka dai my son, ya aikin barci?". King ya faɗa yana gyara glass dake a face nasa!. "Daddy barci kuma? Mu ɗin?". Jinjina masu kai ya yi yana faɗin. "Kuɗin fa, ku gaya mun aikin da kuke yi idan ba barci ba? Kai Jaish rabonka da office naka tun yaushe, ka wuce wajensu Akka ka yi zamanka ko? Duk na zuba maku ido ne ai ina son in ga gudun ruwanku". "Kai daddy Allah kaiko, to mu me zamu yi da ya wuce hakan?". Cewar Jaish kenan, ya yi maganar kuma yana ɗan satar kallon Yah Jawad, while shi ma Jawad ɗin shi yake kallo. Sauran envelope da suke a saman bedside drawersa ya kwaso tare da miƙawa Yah Jawad yana faɗin. "Zan sama maku abin yi ai nan bada jimawa ba, sai ku rage yawace yawacen ƙasashe da kuma barci, yanzu dai Jawad ga wannan, takardu ne na haziƙan student masu ilimi da mayar da himma a makaranta, ga fasaha, na duba result ɗinsu da suke a ciki dukka, yara ne da samun irinsu cikin al'umma ba karamar nasara bace, amma kai ma ka nutsu ka duba komai da kyau zaka gani, akwai guda biyu da suke da master a ciki, sauran dukka degree certificate ne, and takwas daga cikinsu ne civil engineers, biyun akwai computer engr ɗaya, sai kuma business, so su waɗan nan civil engineers ɗin idan akwai fili ka basu aiki a companynka, saura takardu biyun kuma ka bawa Abbas su ya sama masu aiki cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba". Duk wannan magana da yake yi hankalinsa na'a kan laptop dake a gabansa, aikin da yake yi kawai ya ƙurawa waɗan nan dara daran idanun nasa irin na su twin's Obaid and Omaid. Karɓar takardun Yah Jawad ya yi yana mai kara jinjinawa King, kullum burin daddyn nan nasu yaga ƴaƴan talakawa cikin farinciki da annashuwa, yaga marayu suna farinciki kamar sauran kowasu ƴaƴa masu iyaye kuma masu gata, ƴaƴan talakawa da yau aka mayar da su marasa galihu a duniya, su sha wahala da kyar da suɗin goshi, iyayensu su hana kansu abincin ci duk dan su samu su biyawa waɗan nan ƴaƴan kuɗin makaranta, amma sai dai kash, yaran zasu gama karatu babu aikin yi, babu mai tallafa masu ya nema masu aiki saboda sun fito daga gidan marasa galihu, ko sun nemi aikin ma babu wanda yake basu, babu ma wanda yake kulasu, wani ma su bada result nasu a wajen nema aiki ko kuma wajen wani babba mai muryar faɗa aji a kasar dan ya nema masu aiki, a haka wannan result ɗin take ɓacewa, saboda ba kulasu ake yi ba, amma shi King Zuhair muddin result na ƴaƴan talakawa zai gifta ta gabansa dan neman aiki, to da izinin Allah ba'a kwana ɗaya sai ya sanya an basu aikin yi a koma ina ne a kuma kowani irin caurse suka karanta, shiyasa da wuya King ya yi kwana uku ba tare da buƙatun ƴaƴan marasa karfin ta gifta ta cikin fadarsa ba! Haka yake bawan Allah mai farin zuciya!. "Okey daddyn angama In Sha Allah". Cewar Yah Jawad kenan, yana magana yana kuma bin takardun da kallon. Karfi da ya ji King ya koya masu taimako dan dole, saboda dayawan ayyukan marasa karfi ko marasa ghalihu su yake sanyawa su yi, basu isa kuma su ce mashi a'a ba, so yanzu abin ma har ya bi jikinsu. "Jawad akwai wasu ayyukan ginin gidan marayu guda biyar dana fitar, companynka ta shirya karɓar aiki, ku yi mun aiki da sauri, kuma a ƙawata mun shi kamar yadda na fitar da zanensu, bari dai na kammala tsare tsaren zan nemeka". Cewar King. JAISH dai ya yi shiru sai Allah kaɗai yasan me yake tunani. Shi kuwa Jawad haka suka cigaba da hira cikin tsantsar so da kauna shi da King, kai kace abokai ne ba uba da ɗa ba, wani lokaci King ya zolaye shi yana murmushi, dan gaskiya King yana da son zolayar ƴaƴan nasa idan suna hira, barema manyan yana sakewa su yi wasa da dariya kamar abokai, duk kuma hiran da suke yin nan King yana ta aikin act design ɗinsa abinsa. Daga karshe dai Jaish wayarsa ya fitar ya fara aikin latsawa, dan shi hirar King da Jawad ma bata shiga kunnensa, baya jin me suke faɗa, gara ya yi abin da ya saba, wato latsar waya!. Sai wuraren karfe 10 ne Yah Jawad ya miƙe hannunsa rike da envelopes ɗin. "Daddy am feeling sleeping, bari na je na kwanta, have a wonderful night our hero". Ya kai karshen maganar tare da ɗan rungume King ɗin yana manna mashi sumbata a goshi. "Have a great night my son, don't forget to pray before sleeping". In Sha Allah ya faɗa tare da juyar da kallonsa izuwa kan Jaish da kwata kwata baya a tare da su, hankalinsa ta yi nisa, ya tafi can duniyar latsa waya. "Bro am feeling sleeping, see you tomorrow morning". Ya yi maganar yana taɓa shoulder ɗin Jaish ɗin, dan yasa idan ba taɓa shi ya yi bama ba jinsa zai yi ba, ya yi nisa a duniyar latsar waya. "Take care my bro and good night". Shi ne abin da Jaish ɗin ya faɗa, sai dai daga jin yadda voice nasa ta fita in a low sosai ya nuna cewa yana jin barci shi ma, jikinsa duk a mace sosai. Wucewa Yah Jawad ya yi ya nufi waje abinsa. Shi kuwa Prince Jaish juyo da kallonsa a kan daddyn nasu ya yi. "Please dad you have to be sleep now, dare ya yi sosai fa". Ya kai karshen maganar tare da kai kyawawan fararen hannunsa ya ɗauke laptop ɗin dake a gaban King ɗin. Kasheta ya yi tare da ɗurata a saman bedside drawer, sannan ya maido da kallonsa izuwa saman fuskar daddyn nasa. "Daddy i don't want to see you suffering your self to much like that, please our hero dad ka rinƙa samun hutu". Nisawa King ya yi kafin ya ce. "My god bless you my son, ina alfahari daku dukkanku ƴaƴana, amma da ka bari na ƙarisa aikin ai, saura kaɗan ne". "No dad gobe zaka ƙarisa, now dai ka kwanta ka yi barci". Ya kai karshen maganar tare da mannawa dad ɗin sumbata a goshi cikin so da kauna tare da miƙewa tsaye. A zahirin gaskiya King yana matuƙar kaunar ƴaƴan Gimbiya Rahilarh fiye da dukkan sauran ƴaƴansa, domin suna da tarbiya na wuce misali, ga hankali da sanin yakamata, suna kuma kaunar iyayen nasu sosai, barema ita auta da ta ɗauko irin halin King na taimakon bayin Allah, shiyasa ta fi kowa farinjini a gidan, dukka ƴaƴan Gimbiya Rahilarh ba'a cikin kingdom ɗin suka girma ba, hasalima Gimbiya Rahilarh bata haihuwa a cikin masarautar, tun da ta yi haihuwarta ta fari a ciki, daga nan idan ta sami ciki ta kusa haihuwa Dubai take komawa wajen iyayenta, a can take haihuwa, dan a cewarta bata yarda da gidan ba, a duk lokacin da take da ciki tana yawan mugayen mafarkai, ga yawan tsoratata da ake yi, wani lokaci ta rinƙa ganin jini a cikin toilet ɗinta da abubuwa mabanbanta da suka yi kama da tsafi ko makamancin haka, abubuwa dai kala kala, wani lokaci har danneta ake yi a cikin jacuzzi idan tana wanka, a danneta a shaƙa mata ruwa har kamar zata mutu, duk kuma hakan baya faruwa sai idan tana da ciki, wannan dalilin yasa bata taɓa yarda ta haihu a cikin Masarautar, dan fa a haihuwarta ta fari ansha gwagwarmaya, bata yi tunanin abin da ta haifa zai rayuwa ba, tun da ta haihu take cikin masifa ita da ɗan har sai da ta koma Dubai na tsawon shekara biyu, a can ta reni yaron har ta yayesa kuma ta dawo ta barshi a can, saboda tana gudun wani abin ya samesa, a lokacin da take da cikin auta mutuwa ne kawai bata yi ba, amma ta azabtu iya azabtuwa, bata samun barci, bata iya cin komai, da ta fara cin abinci zata fara ganin wasu hayaniya suna yi mata yawo a kai, babban abin damuwar kuma da zarar ta fara addu'a sai ta ji ana karisar mata da addu'ar tata ko kuma an shaƙe mata maƙoshinta ta kasa iya cigaba da karanto addu'oin, abin dai ba'a magana, KINGDOM OF POWER idan ka kalli masarautar ta wata fuska masarauta ce mai zaman lafiya da kuma son kwanciyar hankali, ga kuma taimakon jama'a, amma kuma ba kowa bane yasan ainahin menene a cikinta, duk yadda kuke tunaninta ta wuce nan, amma lokaci ne zai gaya mana menene a cikinta, yanzu na ɗan fara gutsira maku labarin ne, sai mun afka ciki zamu ji menene yake gudana!. A takaice dai duk ƴaƴan Gimbiya Rahilarh harta auta a Dubai suka taso, ba kunji auta tana cewa Yah Omar ya kammala secondary school zai dawo ba? To haka ƴaƴanta suke, sai sun kammala secondary school nasu a Dubai sannan suke dawowa, auta ce kawai ta dawo bayan kammala primary school ɗinta, dan King ya kasa hakura ya barta a can, yana kaunarta fiye da kowa a gidan, so yana son ganinta a kusa da shi, yanzu tana jss one, Obaid da Omaid ma ba'a nan suke karatu ba, hutu kawai suke zuwa, yanzu haka suka Ss 1, saura masu shekara biyu su kammala su dawo masarautar mai gabaɗaya, hakan yasa tarbiyar ƴaƴan Gimbiya Rahilarh ya babbanta dana sauran familyn, daban suke, shiyasa King ya fi kaunarsu fiye da kowa, amma yana ƙoƙari wajen ganin ya ɓoye son nasu da yake yi, baya nuna banbanci a tsakanin ƴaƴan nasa. Sai dai fa da Yah Omar ɗin auta da kuma twins Obaid and Omaid a wajen kakansu mai rankarfe suka girma, shiyasa kuka ga Omaid and Omaid basa jin magana, kunsan girman kaka, hmmm ba'a magana sai dai kun gani da idonku, su Jaish and auta kuma a gidan yayan gimbiya Rahilarh wanda yake matsayin Secretary to government of federation suka girma. Cikin so da kauna Jaish ya yi sallama da daddyn nasa, amma kafin ya tafi sai da ya tabbatar da King ɗin ya kwanta, sannan ya lulluɓe shi da duv ɗinsa mai kyau da laushi, ya rage mashi gudun Ac tare da janyo mashi kofar bedroom ɗin, sannan ya wuce nasa part ɗin abinsa, bawan Allah yana ji da iyayen nan nasa sosai da sosai. Yana zuwa bedroom nasa ya ajiye takardun da King ya bashi a saman table dake a tsakiyar bedroom ɗin gaban wata sofa mai bala'in kyau da laushi, bayan ya ajiyesu ne ya nufi saman katafaren king bed ɗinsa, addu'a ya yi bayan ya haye, sannan ya kwanta tare da jan duv zuwa dai'dai cikinsa, ya ɗauko remote dake a saman bedside drawer, wutar ɗakin ya kashe, nan take duhu ta mamaye ko'ina, a hankali ya lumshe idanuwansa ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi!. ASUBA TA GARI!. Washegari da safe shirye cikin wasu shegun tsadaddun suit Jaish and Jawad suka fito domin zuwa office nasu, companynsu daban daban, Jaish shararren ɗan jarida ne na gaske gaske, babba ne sosai wanda ake ji da shi, shi kuma Yah Jawad civil engr ne, so kowa da aikinsa. Sun fito sosai abinsu, kayan jikin nasu ma iri guda ne, sun yi masifar yi wa kayan kyau, Jaish yana sanye da black glass a idanunsa, while shi kuma Jawad yana sanye da white glass ɗan siriri kamar medicated, sun fa haɗu iya haɗuwa. A babbar parlourn King suka ci karo da su Gimbiya Zunaira, Fanan, and Aneesa suna shirye cikin uniform nasu na makaranta mai bala'i kyau, riga da sket ce sai ɗan hijabi da bata wuce kirjinsu ba, sket ɗin navy blue ne, kuma bata kai masu har ƙasa ba, dai'dai singalalin kafafunsu ta tsaya, rigar kuma fara mai doguwar hannu ce, sai hijab fara, sun je sun gaishe da King ne sun fito. Suna ganin su Jawad suka hau zuba masu gaisuwa cikin girmamawa, auta ce kawai ta zo ta rungumi Yah Jaish tana murmushi. Shi ma rungumarta ya yi ba tare da ya yi magana ba. "Where's Jannat?". Cewar Jawad, ya yi maganar yana kallon auta, dan yasan ita ce mutuniyar Gimbiya Chuchu, kullum suna tare. "She's not feeling fine, and dama Akka ta ce na kira mata kai, wai kaje da sauri, Aunty Chuchu ɗin ma tana ɗakinta". Ta bashi amsa tana raba jikinta dana Jaish, dan ta bi bayansu Fanan da suka wuce izuwa part na Mummy dan su gaisheta kafin su je wajen mama ma su gaisheta sai Momma, daga haka sai su wuce a kaisu school, ita kuma Sarina yanzu tana two hundred level a jami'a, ba secondary take ba!. Jinjina mata kai Jawad ya yi yana tunanin yadda zasu kare da Akka, dan yasan cewa tabbas Chuchu ce ta kai kararsa a kan kneel down da ya sakata jiya, dama kuma ita Akka wlh ko su Sarina ya bawa punishment idan ta sami labari ya rinƙa shan ruwan masifa kenan, tsohuwar akwai rigima, bata bari a taɓa ƴan'matan, shiyasa ya kafawa su Sarina doka a kan idan suka kuskura dan ya basu punishment suka gayawa Akka sai ya ɓallasu, to yanzu ga Chuchu ta je ta faɗa, yanzu idan tsohuwar nan ta sako shi a gaba da bala'i sai ma ta ce mashi ai haka ubansa ya rinƙa yi mata rashin ji da yana ƙarami ta rinƙa hakuri da shi har ya girma, to shi waye da ba zai hakura ba dan kannensa sun yi masa ba dai'dai ba? Akka duniya ce, kada ka yarda ka bari ta kamaka ka yi laifi, zaka sha surfar masifa. "Jaish ka ƙarisa ku gaisa da dad bari na amsa kirar ƴar tsohuwar nan, zan sameka a nan". Cewar Jawad ɗin kenan, ya kai karshen maganar kuma tare da wucewa wajen elevator dan ya nufi part na Akkar ya ji me zata ce mashi kuma. Da okey Jaish ya amsa mashi kafin yasa kai ya wuce izuwa wajen King ɗin. To bari dai mu leƙa su Kamran, kafin mu dawo mu ji ya Jawad zai kare da Akka da kuma Chuchu!. 🕊️🔥🕊️🔥🕊️🔥🕊️🔥🕊️🔥🕊️🔥🕊️🔥🕊️ 🏞️FOREST🏞️🔥 A wannan rana dai da kyar su Pretty suka iya raba jikinsu da juna har suka samu suka haɗa abin da zasu cinwa cikinsu. Wani irin ɗan ƙaramin dutse mai masifar haske Pretty ta ɗauko ta fara daka masu kayan biya a saman wani dutse mai ɗan faɗi, wannan dutse da yake a hannunta tana dakar da shi haskensa sai ya bawa mutun tsoro, yana da haske sosai mai kashe idon mutun, design of star ne dutsen, kamar kuma ba dutse bane ba, to ga dai shi nan, sai Allah ne kaɗai ya san daga ina suka same shi, da shi suke daka abubuwa, ya zama kamar taɓaryarsu kenan. A haka dai cike da tsoro Pretty ta haɗa masu abin da za su ci, suka ci, ko da lokacin kwanciya ya yi yau a manne da juna sosai suka kwanta, alamar suna tsorace sosai kenan. Kamran kuma bai sake dawowa wajensu ba sai washegari da safe rana ta ɗan ɗaga, kamar yadda ya yi masu alkawari haka ya dawo tare da kwari da bakarsa, sai dai yau a tare da Rocky suka zo, Rocky ya zauna a bakin kofar shiga cikin ramin, dan idan baku manta ba jikinsa ba zata iya shiga cikin ramin ba, ya yi girma, so a baki ya zaune. Shi kuwa Kamran ya shigo ciki. Zaune a saman bed kamar kullum ya isko Sweetie, ita kuma Pretty tana wajen kayan sakawarsu tana aikin gyarawa. Jin motsin shigowa yasa ta yi saurin juyar da kallonta izuwa kan hanyar shigowar. Ganin Kamran ne yasa ta ɗan saki cool murmushi wadda sai da yasa dimples nata suƙa lotsa, sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, hankalinta ya kwanta, ta samu nutsuwa, dan idan Kamran yana nan to fa tana jin kwarin gwiwa sosai. "Pretty who's here?". Cewar Sweetie wadda ta jiyo motsin mutun a kusa da ita, ba kowa bane kuma face Kamran, takardar addu'oin da yake a kusa da ita wadda Pretty ta ajiye yake son ɗauka. "Sweetie it's Kamran, yanzu ya zo". Pretty ta bata amsa tana mai dawowa kusa da su. Ajiyar zuciya ita ma Sweetie ta sauke jin cewa Kamran ne, hankali ya kwanta. Shi kuwa takardan da ya ɗauka ya fara buɗewa yana dubawa, kamar wani wanda ya iya karatun larabci, dan ma dai akwai English translation a jikin littafin. "Kamran wai yaushe zamu je neman wancan mutumin ne?". Cewar Pretty sarkin rawan kai da giggiwa. Ɗan satar kallonta ya yi ta ƙasar ido dan yaga shin tana kallonsa ne ko kuma, idan bata kallonsa sai ya kalli face nata, idan kuma tana kallonsa sai ya hakura, dan ba zai iya kallon cikin kwayar idanunta ba, suna rikita shi. Aikuwa shi ta kafe da idanu tana ta kallo, dan yana burgeta, a cewarta yana yi mata kyau, haka zalika ita ma Sweetie duk da bata gani bata san ya kamannin Kamran ɗin yake ba, amma har cikin zuciyarta yana burgeta, bata da burin da ya wuce idanunta su buɗe ta kalli face ɗinsa. E to akwai kura dai kam!. Ganin cewa shi take ta kallo ne yasa bai ɗago idanu ya kalleta ba, sai ma ya kara yin ƙasa da kansa, cikin sanyin muryar nan tasa ya ce. "Yanzu zamu tafi, ku zo mu fita waje ko?". Da sauri Pretty ta miƙe tana murmushi kamar baki ba zai rufu ba, dan ta ƙosa taga sun gane wannan mutumin da mamarsu ta ce su nema, dan mamar nasu ta gaya masu in dai suka ga wannan mutumi zai kula da su sosai, hakan yasa ta ji duk ta ƙosa su gansa ta kuma bashi saƙon da mum ɗin tasu ta basu su bashi. "Sweetie kawo hannunki mu tafi, zaki fita waje kema yau". Cewar Kamran, ya yi maganar yana rufe littafin tare da mayar masu a in da ya ɗauka ya ajiye. Ba musu Sweetie ta miƙa mashi hannunta, dan tana jinsa har cikin ranta, ta kuma yarda da shi. Ita kuma Hajiya Pretty sarkin rawan kai, tuni ta yi gaba. Sanin cewa Rocky yana a bakin kofa ne yasa Kamran ɗin ya ce da Prettyn ta dawo su jera a tare, dan yasan halinta da tsoro, yanzu idan taga Rocky sai ta haukace masu. Ba musu ta dawo suka jera, sai satar kallonta yake yi, ta yi matuƙar kyau cikin shigar wata doguwar riga zuwa gwiwanta, rigar mai kyau ce sosai, daga gani kuma tana da tsada sosai da sosai, kasar rigar a buɗe kamar umbrella, yau ta sanya wani irin hula mai kyau ta rufe kanta da shi, hular ce mai gashi gashi a jiki, ta yi kyau sosai, shigarsu iri ɗaya da Sweetien, amma shi Kamran a iya jikin Pretty ne kawai shigar suka yi mashi kyau. Kamran ɗin ne ya fara fita daga cikin ramin kafin ya sanya hannu ya fito da Sweetie, ita kuma Pretty ta fito da kanta. Lokacin da suka fito Rocky baya a wajen, da alama ya ɗan kewaya wani wajen ne, dan shi ma ya iya yawo........ Yo dama da kafarsa da lafiyarsa gasas me zai zaunar da shi? Ai sai yawo kawai abinsa, ya nemi nama ya ci, idan ba haka ba kuma ya cinye Kamran da Mamma........🥱😅💔 Suna fitowa waje Rocky ya dawo wajen da ƴar gudunsa, dama ashe bai yi nisa ba. Ai kuwa Pretty tana ganinsa ta daka wata uwar tsalle tare da kurma ihu mai razanar da ƙwaƙwalwar mai sauraro tana ƙoƙarin guduwa ta bar wajen, ita sam ta manta Kamran ɗin ya taɓa gaya maya Rocky abokinsa ne kuma ba zai cinyeta ba. Ai kuwa tana zunduma wannan ihun shi ma Rocky ya zunduma nasa ihun, habawa kara haukacewa suka yi daga ita har Sweetie da bata gani kuma bata san ya girman Damusar take ba, ta dai ji kurnaninshi da kuma kukanshi mai tashin kan duk wata halitta mai rai. Da sauri Kamran ya riƙo Pretty dake ƙoƙari zundumawa a guje ta bar wajen, ya rikota ne kuma saboda yasan wlh tana gudu Rocky zai rufa mata baya ya damkota ba fashi, dan haka sai ya yi saurin rikota tare da jawota jikinsa yana ƙoƙarin yi mata magana akan ta nutsu babu abinda Rocky zai yi mata. Dama already yana rike da hannun Sweetie kam, suna neman haukasa bawan Allah. Ai kuwa bai kai ga yi mata magana ba Rocky ya iso wajenta ya fara bin jikinta da shinshina kamar wani tsahon maye. Habawa wani irin mahaukacin ihu ta sake zundumawa tana faɗin. "Shikenan ya cinyeni na shiga uku na gama yawo! Wayyo ya cinye mun kafata! Laa shikenan ya fara cin kun kafata, wayyo Allah nazama mara kafa, ya cinye dukka, wayyo na mutu na mutu mummyna". Wayyo cikina, Pretty zata kashe ni da dariya,😅 ga abin tausayi ga kuma abin dariya, to ni kam dai na shiga aljanna naki fitowa ne, sai dai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu, yau Rocky zai cinye Pretty mayyar tsoro...🥱 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 23/7/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________20🔥 Shi kuwa Rocky cigaba ya yi da taɓa mata jiki, tsoratar da ta yi sosai ne yasa take jin kamar wannan taɓa mata jikin da yake yi cin namar jikin nata yake yi, hakan yasa take wannan ihu na ya cinye mata kafa, shi kuwa ina ruwansa? Yasan ma me take cewa ne? Ai kawai taɓata yake yi da bakinsa, kuma ya saba yi wa Kamran ko Mamma irin hakan, shiyasa ita ma ya yi mata. Taɓa mata wajen cinyarta da ya yi ne yasa ta zunduma wani irin mahaukacin ihu, nan take kuma ta ɗauke dif kamar an ɗauke wutar nepa, da alama tsoro yasa ta sume, ta zaci cikye mata cinya zai yi. Ammafa ni banga laifin Pretty ba, Damusa fa aka ce? Kai ai tama yi ƙoƙari, wannan shegiyar dabba ki sabon? Tab ai Kamran ma badan ya buɗe idanu ya sami Mamma da Rocky ba da zai sha fama kafin ya saba da shi, hmmm waɗan nan dabbobi ba'a sake jiki da su, kuma ba'a sabo da su ato. Duk sun rikita Kamran bawan Allah, ya rasa ma ta kan waye zai fara, ga Sweetie tana ta rera nata kukan tana ambatar sunan Pretty, ga kuma Pretty wadda ta sume mashi a jiki ya tallabota da hannu ɗaya dan kada ta zube ƙasa. Shi kuwa Rocky duk wannan abin da ya faru bai sa ya dai'na taɓa jikinta da bakinsa ba. Dama kuma a kaidar dabbobi ire iren waɗan nan idan har ka nuna kana jin tsoronsu to fa sun rinƙa tsorata kenan, duk da shi Rocky ba da gangan ya yi mata hakan ba, kawai yana taɓata ne saboda ya saba yi wa su Kamran. "Sweetie please ki yi shiru babu abin da zai yi maki, Rocky ne fa, is my friend, baya cutar da mutane". Cewar Kamran ɗin kenan. "Ina Pretty take to? Ina ta tafi? Damusar ya cinye mun ita ne? Na dai'na jin kukanta ne!". Cewar Sweetien Tana magana gabaɗayanta a ruɗe take, duk ta rikice, muryar tata ma baya wani fita, sai in da in da take faman yi, ga hawaye wani na bin wani a saman ƙuncinta, ita da kanta bata san me take faɗa ba!. "Sweetie Pretty tana nan lafiya, wannan Damusan ba mai cin mutane bane, please ki yi shiru". Ya kai karshen maganar tare da kwantar da Prettyn a ƙasa, dan ya samu dama ya zaunar da Sweetie ɗin ma!. Shoulders ɗin Sweetien ya riƙo da hannunsa dukka biyu, cikin sigar rarrashi ya zaunar da ita a ƙasa wajen wannan farin yashin (ƙasa) yana mai cigaba da rarrashinta. Sai tambayarsa ina Prettynta? Take yi. Shi kuwa takaici yasa bai ma san time ɗin da ya wurgawa Rockyn wani irin ɗan iskan kallo mai kama da harara ba, Rocky ya kawosa har wuya saboda bakin ciki, to shi Damusa ina ruwansa?. Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya sake amsawa Sweetie magana ba, ya nufi hanyar ƙoramar nan dan ya ɗebo ruwa. Da sauri Rockyn ya bi bayansa yana tafiyar ƙasaita na cikakken Tiger mai lafiya a jiki. "Kada ka biyoni". Kamran ɗin ya faɗa cikin wannan yare tasa da ni kai'na na ƙasa gane wani irin yarene, wannan sai Mammarsa da kuma Alkalamina ne kawai suka san wace yarece!. Wani irin gurnani Rockyn ya yi alamar irin a banza Kamran ɗin ya yi magana, wato sai ya bishi kenan. Banza da shi Kamran ɗin ya yi bai sake bi ta kansa ba, dan gabaɗaya haushin shi ma yake ji. Sai dai kuma a dake Rockyn namu na amana ba zai daku ba, a zage ma ba zai zaku ba, sai dai Kamran ya yi ta fama da kuncin zuciya.....😅🥱 Har ya je wajen ƙoramar kuma sai ya rasa da me zai ɗebo ruwan, bai ɗauki komai ba, wani karin takaici ya ji kamar ya kifawa Rockyn wani wawan mari, amma haka dai ya daure ya juyo ya dawo. Har lokacin sai kuka Sweetie take yi tana ambatar sunan Pretty, baiwar Allah babu halin gani. Bai kulasu ba ya wuce izuwa cikin ramin nasu domin ya sami abin da zai ɗebo ruwa a ciki ya zo ya zubawa Pretty ta farfaɗo. Shi kansa da ya jima a cikin wannan daji tsawon shekaru ya sha madarar mamakin ganin wannan dutse da su Prettyn suke daka da shi, yana gani duwatsu masu abin al'ajabi, wasu ku ga kamar mutun, wasu kamar halittar wata dabba, amma bai taɓa ganin irin wannan ba, hannunsa ya kai ya ɗauki dutsen yana binsa da kallo, wani irin haske mai bala'i kashe kwayar idanuwa ne yake fita daga jikin ɗan dutsen, in dai zaka kalli dutsen kai tsaye, to kana kawar da idanunka ba zaka iya ganin komai ba na tsawon mintoci, haskensa zai kashe karfin ganinka, sannan yanayin abin dai ga shi nan ne kamar ba dutse ba. Kamran ya ɗauki tsawon a kallah 10 mins yana ta kallon wannan abin mamaki a cike fal ransa, tunanin su Pretty ɗin ne ma ya faɗo mashi a ransa yasa ya mayar masu da abinsu ya ajiye, sai Allah kaɗai yasan daga ina suka samo shi kuma menene wannan abin?. Yasha madarar mamakin ganin abubuwa dayawa a cikin wajen nasu, ciki kuma harda sarkar gold na mamarsu wanda ya ɓace mata time da ta haifesu, da alkyabbarta, da dai sauran abubuwa, duk gasu nan sun dawo, mamaki ne ya kama shi a kan to ya aka yi ta gane waɗan nan abubuwa nata dukka? Abin dai akwai ɗaure kai sosai, domin wani lokaci idan kaga wani abin sai ka rantse da Allah mum twins ba mutun bace, yanzu dai ga shi ta ɓata ɓat, sama ta yi ƙasa ta yi wallahu a'alam, amma dai a yadda take son twin's ɗin nan nata, a kuma yadda ta rayu dasu tsawon shekaru tara, ta basu kulawa fiye da kanta, ta sha bakar wahala, ta gudunwa mayaƙan nan saboda su, to mawuyacin abu ne ta yi tafiyarta haka kawai bisa radin kanta ta barsu, koda kuwa basu da mahaifi, ina nufin koda kuwa ba ta hanyar aure ta samesu ba, to ba shakka ba zata iya tafiya ta barsu ba, dole dai akwai abin da ya saɓa, sannan bugu da ƙari ga masu nemanta tun farko waɗan da suka yi sanadiyar shigowarta cikin wannan dajin ma har yanzu suna nemanta, har yau har gobe suna shigowa cikin dajin nemanta, hakan na nufin kenan har yau basu ganta ba, da sun ganta ba zasu biyo sahun nemanta ba, to wannan abin dai akwai ɗaure kai sosai, sannan kuma wanenen wannan Jarumin jarumai da ya taimaki su Kamran? Kada ku manta idanunsa ne kawai aka iya gani, kuma babu in da idanun nasa suka banbanta dana Pretty akwai fa ɗaure kai......🤔 Kamran da ya je ɗaukar abin da zai ɗebi ruwa, sai ya ɓige da al'ajabi tare da mamakin abubuwan da yake gani a cikin ɗakin nasu, abubuwa ne da bai taɓa ganin irinsu ba, kada ku manta shi bai taɓa fita daga cikin wannan daji ba, so kayan da Mammarsa take kerawa kawai ya sani, su Pretty kuma kayan da suke amfani dasu dukka kaya ne da aka kawosu daga gari, abubuwa ne masu bala'in tsada ba kaɗan ba, hakan yasa Kamran ɗin ya zama kamar wani ɗan kauye a cikin wajen, ya taɓa wannan ya taɓa wancan, ga mamaki sosai a saman fuskarsa. Wani irin ƙatuwar envelope ya ɗauko daga cikin wani waje da aka keɓe shi sosai, alamar wajen ajiyar abubuwa masu mahimmanci ne, da alama kuma wannan envelope ɗin yana da matuƙar mahimmanci fiye da tunaninku, in da aka ajiye shi ma dole babban mutun ne ya ajiye shi, ba irin ajiyar su Pretty bane, da alama mum ɗinsu ce ta yi wannan ajiya kafin ta bar wajen. Ya ɗauki tsawon a kallah two mins yana karewa envelope ɗin kallo kafin ya kai hannunsa ya fara ƙoƙarin buɗeta. Wani irin kukan da Rocky ya yi mai sautin gaske ne yasa ya dakata daga yunƙurin buɗe envelope ɗin, a hanzarce ya ɗaga kansa sama yana kallon wajen hanyar shigowa daga ramin. A karo na biyu Rocky ya sake yin irin wannan kukan. Ai kuwa ba shiri ya yi wurgi da wannan envelope ɗin, ba tare da ya ɗauko abin da zai ɗebi ruwan ba ya fice waje da gudu sosai domin ya je yaga menene yake faruwa?. Yana fitowa ya ja wani irin mahaukacin birki yana kallon wannan al'amari. Sweetie ma dai ta suma saboda tsoro, bayan shigar Kamran ɗin cikin ramin Rocky ya zo yana taɓa mata jiki da bakinsa kamar dai yadda ya yi wa Pretty, hakan ne ya tsoratata sosai har ta suma, shi fa Rocky idan yana wannan taɓa jikin burinsa kawai a rinƙa shafa mashi nashi jikin shi ma, shiyasa yake yi wa su Mamma ma haka, amma su Pretty basu gane ba. Sweetie ta suma, shi kuma Rocky ya farauci wani mayaki guda ɗaya da ya zo giftawa ta wajen, mayakin ya yi yunƙurin harbin Rockyn da kifiyarsa a ciki, kifiyar ta same shi sai dai bata ji mashi ciwo sosai ba, dan fatar dabba daban take da na mutun, ba ƙaramin abu bane yake hudata, hakan yasa bata jiwa Rocky ciwo sosai ba, shi ne yasa ya daka waɗan nan uban ihun da ya yi tare da buga tsalle ya capko wuyar mayakin, daga saman dokinsa ya janyosa kasa, nan take ya tsinke mashi agarar wuyarsa, shi ne fa ya hau cin nama abinsa. Shi dai Kamran a wannan point ɗin kansa ta ƙulle, tunani yake yi wai waɗan nan warriors ɗin basu karewa ne a cikin dajin nan?. Bai san cewa turosu ake yi ba, idan aka turo wasu, in aka ji shiru basu dawo ba, sai a sake turo wasu, haka suke yi, kuma a dokarsu duk wanda ya fita neman mum twins kada ya dawo ba tare da ita ba, idan ya dawo ba tare da ita bama kashe shi za'ayi, so yanzu haka wasu mayaƙa su takwas ɗin ne suka sake shigowa cikin dajin, shi ne suka rarraba hanya wai kowa ya yi nasa gun ko Allah zai sa su kama mum twins, ashe basu san rabon Rocky ne wannan da ya biyo ta hanyarsu Pretty ba, to ga dai shi nan Rocky ya ci nama abinsa, wani ma ya sake zuwa, ai shi Rocky ba zai gaji da cin nama ba.....😅 Izuwa yanzu Kamran ya fara tsorata da waɗan nan warriors ɗin, yaga yanzu almost goma sha biyu suka mutu amma wai wasu sun sake zuwa? Anya kuwa ba'a cikin dajin nan suma suke ba kuwa? Ya jefawa kansa tambayar da shi ma bashi da amsarta, tunani ya fara yi a cikin zuciyarsa na cewa yana da kyau ya kama warrior guda ɗaya ya ɗaure shi ya samu ya gaya mashi me yake kawosu cikin wannan daji, dan gaskiya ya fara tsorata da lamarinsu. Ya jima a tsaye a wajen yana kallon yadda Rocky yake watandarsa da namar wannan mayaki, ya kasa gaba ya kasa baya, har sai da ya fara jin motsi a kusa da shi, sannan ne hankalinsa ya dawo jikinsa, a hanzarce ya kai kallonsa wajen motsin. Pretty ce ta farfaɗo daga sumar da ta yi tana ɗan motsi. Da sauri ya ƙarisa wajenta tare da zube gwiwowinsa a kasa kusa da ita, sunanta ya fara ambata a hankali hankali, fatansa ɗaya Allah yasa ta tashi a nutse, kada ta tashi a birkice. Pretty akwai murya innalillahi, idan ta yi ihu sai dajin kusan gabaɗaya ya amsa, kada ku manta ranar da aka haifeta ma sai da dajin yasan da zuwanta, saboda kuka, Sweetie sarkin hakuri ita kuma, har suka girman nan Pretty bata da hakuri da cin abinci, idan ta ji yunwa ya fara damunta zata fara yi wa Sweetie kuka ne kawai abinta, gata da ruwan hawaye kamar famfo ake buɗewa, dan hakan ne yasa Kamran yake addu'ar ta tashi cikin nutsuwa ba da hayaniya ba. Jin muryar Kamran yana ambatar sunanta yasa ta yi wani irin zaro idanunta waje, kai tsaye sai cikin kwayar idanunsa, da yake ya tsuguna a gabanra ne yana kallon kyakkyawar face nata. Ɗan lumshe idanunsa ya yi tare da sake buɗesu amma ba'a kan nata idanun ba, sai ya ɗan kawar da kallonsa gefe guda. Ita kuwa ganin shi ne a kusa da ita yasa ta fara ƙoƙarin miƙewa zaune tana faɗin. "Kamran ina Sweetie take? Damisar bai cinyeta ba ko? Ina take?". Tana magana tana tattaɓa kafafunta ta ji shin Rocky ya cinye mata kafafun ne ko kuma dai suna nan. Ganin cewa bata lura da Rockyn dake can gefe yana watandarsa ba ne yasa Kamran ɗin ya ce mata. "Pretty kin manta na taɓa gaya maki cewa Rocky baya cin mutane ne? Ai baya cin mutanen da suke tare dani, abokina ne fa, ke baki ga ni ma bai cinyeni ba ne? Dan haka ki dai'na jin tsoronsa ku kullula abota kin ji ko?". Yadda ya yi mata maganar cikin sanyin murya yasa ta nutsu ta kuma fahimce shi sosai, dan haka cikin nutsuwa ta ce. "To ina Sweetieta take?". Da hannu ya yi mata nuni da ita yadda take kwance a gefensu a sume. Da sauri ta rarrafa ta ƙarisa wajen ƴar uwar tata, sunanta ta fara ambata tana kallon face nata. "Ta suma ne fa Pretty, ki barta sai an zuba mata ruwa". A ɗari ta juyo da kallonta a kansa, zaro idanu waje ta yi, ai a dubu shi kuma ya kawar da kallonsa daga kanta, dama yaya bare kuma ta zaro mashi ido? Wannan yarinya tana birkita mashi ƙwaƙwalwarsa sosai, sai ya rasa a wani point zai ajiyeta. "Meyasameta ta suma Kamran?". Ta yi tambayar ne a ruɗe sosai Ba tare da ya kalli in da take ba ya bata amsa da cewa "Tsoro ta ji ita ma, yanzu dai tashi muje wajen ƙoramar can mu ɗebi ruwa mu zuba mata, bari na ɗauketa ko?". Da sauri ta miƙe tana faɗin okey. Miƙewa shi ma ya yi tare da saɓar Sweetie ɗin a saman shoulder ɗinsa mamar baby, suka nufi wajen ƙoramar, ko kallon in da suke Rocky bai yi ba, ya samu nama ba ruwansa da su.......😅 Ita ma Pretty bata lura da Rockyn yana ɗan gefe yana cin namar ba, da ta gani ai kara haukacewa zata yi, za ta ce da Kamram ai ga shi nan Rocky yana cin mutane, ita ba zata yarda da shi ba, to sai Allah yasa bata gani ba, ta yi gaba shi kuma Rocky yana ta ɗan bayansu ne. A kusa da ƙoramar ya kwantar da Sweetien, sannan ya wuce ya ɗebo ruwa a cikin kyawawan tafukan hannunsa, a hanzarce ya zo ya yayyafa mata a saman fuskarta. A ruɗe ta farka tana mai kukan ambatar sunan Pretty, da saurin Prettyn ta ƙarisa kusa da ita tana ce mata gata nan babu abin da ya faru. Haba rungume juna suka yi suna sauke ajiyar zuciya,. Shi kam Kamran da ido kawai ya bisu, ya rasa a wani matsayi zai ajiye yaran nan, da zarar ɗaya ta yi abu to ɗayar ma sai ta yi, yara kamar wasu chewing gum. Sai kallon face ɗin Pretty yake yi, har ga Allah wannan ɗan bakin nata yana matuƙar yi mashi kyau, bakin kuka, a duk lokacin da ya kalli ɗan bakin nan nata abu ɗaya ne yake faɗo mashi a ransa, ba komai bane kuma face ranar da aka haifeta, irin ihun da ta rinƙa tsallarawa, da zarar ya tuna hakan kuma sai ya ɗan yi murmushi, yanzu ta girma kamar ba ita ba. Ɗago kai Pretty ta yi daga jikin Sweetie da nufin ta kalli Kamran ɗin tana son yi mashi magana. Ganin ta ɗago kai zata kalle shi ne yasa ya yi saurin kawar da kallonsa daga kanta, dan ma kada su haɗa idanu. "Kamran mutafi ko?". cewar Pretty. Sauke kwari da bakarsa dake a bayansa ya yi ya ajiye a ƙasa tare da nufar wata bishiyar ayaba dake ɗan nesa da ƙoramar kaɗan. "Ina zuwa Pretty, zamu tafi amma sai mun ɗan huta a nan". Ya bata amsa yana mai cigaba da tunkarar in da ya nufa. Ajiyar zuciya ta sauke tare da kafeshi da idanu tana kallon yadda yake tafiya a bubbuɗe cike da jarumta, shi ko tsoron namun daji baya ji, duk in da ya nufa tafiyarsa kawai yake yi ba tare da tunanin zai iya haɗuwa da muguwar dabba a wajen ba, babu ruwansa da wannan tunani, ɗan garama kwana biyun nan da yana samun saɓani da waɗan nan warriors ɗin sun fara jefa mashi tsoro da shakku a cikin zuciyansa, hakan yasa yanzu idan ya tunkari waje yana tafiya yana tunanin kada ya haɗu da wasu warriors ɗin, amma sam baya tunanin kada ya haɗu da wasu namun dawa. Har ya ƙurewa ganin Pretty bata kawar da kallonta a kansa ba, sai da ya kure mata ne ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da raba jikinta dana Sweetie tana faɗin. "Sweetie Kamran yana da kirki sosai". "Sosai kam Pretty, mutumin kirki ne, nafara tunanin shi ne wanda mum ta ce mu nemo". Miƙewa tsaye Prettyn ta yi tare da nufar wajen duwatsun da suke a bakin ƙoramar tana faɗin. "Sweetie bari na shiga cikin ruwa kaɗan ina zuwa, idan mun koma sai mu yi maganar Kamran ɗin, yanzu zai iya jin abin da zamu faɗa fa". Jinjina mata kai kawai Sweetien ta yi, zuciyarta a cike tab da tunanin ya Kamran yake? Ya kamanninsa yake? Tana burin taga face ɗinsa!. Shi kuwa abin tsakiyar ganyen ayaba ya ciro guda biyu dogaye, sannan ya dawo in da suke. A kusa da Sweetie ya zauna tare da fara gyara abin. Yana yi suna hira da Sweetien sama sama. Ita kuma Pretty ta zauna a saman wani ɗan madaidaicin dutse dake bakin ruwan da yake taruwa a ƙasar ƙoramar, ta zura kyawawan fararen kafafunta a cikin ruwan, har da wani ɗaga kai sama tana jin daddaɗar yanayi, ga ruwan ƙoramar yana ɗan watsuwa mata a face nata, ga kuma iska mai matuƙar daɗi, sai ta ji duniya na yi mata daɗi. Abin busa shi kuma Kamran ya gyara da waɗan nan abubuwan ayaba guda biyun da ya ciro ɗin, ya miƙawa Sweetie guda ɗaya ya ɗauki ɗaya ya nufi wajen da Pretty take zaune. Har ya kai wajen sai kuma ya dawo ya ɗauki kwari da bakarsa. A gefenta ya zauna ba tare da ya kalli in da take ba ya sanya wannan abin busar a bakinsa ya fara busa mai bala'in daɗin ji. A hanzarce ta juyo da kallonta haɗe da fuskarta a kansa, yana ganinta ta wutsiyar idanun, amma yaki yarda ya juyo su haɗa ido, saboda baya son ta sanya shi ya rikice. "Kamran waye ya koya maka wannan abin?". Cewar Pretty sarki kin gani a kyale, bata ganin abu ta yi shiru, sai ta tambaya. Ita ma Sweetie dake zaune a bayansu sai da ta ce. "Kai amma ta yi daɗi waye ya koya maka?". Sai a lokacin ya ɗan juyo da face nasa, kaɗan ya kalli face ɗinta ya ɗan kawar da kallonsa izuwa kan Sweetie kafin ya amsa mata da. "Mammata ce ta koya mun, amma bana yi, yau ma saboda ku kawai na yi". Matsowa kusa da shi Pretty ta yi sosai, cikin zumuɗi ta ce. "Zaka koya mun? Bani ma dai na gwada yi, zan iya ba sai an koya mun ba, ina hurawa ne kawai?". Ɗan bakin nata kawai yake kallo, ba dai magana ba kam, ga kauɗi. "Why not?". Ya faɗa yana mai miƙa mata abin da nufin ta busa ya ji. Sarkin kauɗi, a hanzarce ta karɓa kamar wata kwararriyar, ta ɗauka hura iska ake yi sai ya bada sauti mai daɗi, da sauri ta kai ɗan bakinta ta fara hurawa. Kash babu abin da ta iya, ko da ta busa iskar bakinta ne kawai yake fitowa ta ramin dayakamata ace sautin busa ta fita, ina nata ai iska ne kawai yake fita kamar ana sace tayar mota. Turo ɗan bakinta ta yi tare da cire abin daga bakin nata tana bin shi da kallo. "Kamran abin ya dai'na yi, ina ga ya lalace ne, sai ka sake haɗa mun wani". Ta faɗa tana turo baki, bata yarda cewa bata iya bane, sai dai ya lalace ne, ita irin kwararriyar nan!. Duk abin da take yi yana ganinta ta wutsiyar idanuwansa, dama yasan ba iya busawa zata yi ba, ya dai bata ne kawai dan kada ta ce ya hanata ko kuma ta ji babu daɗi, shi ne yasa ya bata, kunga idan ta gwada yaki yi ai ba zata dai ce ya hanata ba. Guntun murmushi ya saki, hakan ba ƙaramin kara bayyanar mashi da kyansa ya yi ba, wannan da a cikin gari yake ba makawa da wannan murmushin nasa zai sa ƴan'mata masu ji da kansu, masu class dayawa su fola mashi, bashi da fara'a, amma time to time yana murmushi kaɗan kaɗan idan suna yin hira da Mammarsa, kuma ba ƙaramin kyau murmushin take yi mashi ba, sai ka ji kamar ya yi ta yi kana kallonsa ba gajiyawa. Sosai ya yi matuƙar burge Pretty da ya yi wannan murmushin, kun san ta bata gani ta yi shiru, dan haka sai ta ce. "Kamran ka yi kyau sosai da ka yi wannan murmushin". Ɗan kara sakin wani murmushin ya yi yana faman sanya kifiya a jikin kwarinsa. "Da gaske murmushin ya yi maki kyau?". Ya tambaya A hanzarce ta gyaɗa mashi kai tana faɗin. "Ka yi kyau sosai". Juyo da waɗan nan kyawawan fararen eyes ɗin nasa ya yi a kanta, ya kalleta ido cikin ido yau kam. "In dai ya yi maki kyau to zan rinƙa yi, amma sai kina yin abin da zai sakani yin murmushin, dan yanzu ma ke ce kika sakani yi ai". Har ya kai karshen maganar bai kawar da kallonsa daga cikin kwayar idanunta ba, ita ma kuma bata ɗauke idanunta daga kallon nasa idanun ba. "To yanzu me na yi da na saka ka yin murmushin?". Ta faɗa tana mai cigaba da kallonsa sosai. Ji yake yi kamar ba zai iya jure kallon cikin idanun nata ba, amma kuma yau ya kuduri niyyar sai ya kure kansa, sai ya kalli cikin kwayar idanunta sosai ya gani ko zata dai'na rikita shi. "Da kika ce abin busar bata yin aiki mana, shi ne ya sakani yin murmushin, naga dai yanzu fa ina tsaka da busa tana yi na cire na baki ita, amma daga gwadawarki ɗaya ki ce mun ta dai'na aiki? Ai dole ki sakani yin murmushi". Ɗan kara turo ɗan bakin nata ta yi kafin ta ce. "To ai naga na busa iskace kawai take fitowa daga ramin da naka sautin busar take fitowa". Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, sai Allah kaɗai yasan me yake tunani a cikin zuciyarsa. "Ni yanzu ba busa nake son fara koya maki ba, ki koyi harbi da kifiya zai fi, idan kika koyi harbi da kifiya zaki rinƙa rakani yin farauta". A wannan karon ya kai karshen maganar tare da ɗan yin ƙasa da idanunsa daga cikin nata, ya mayar da kallonsa izuwa samar wannan haɗaɗɗen gurun wuyar tata da yake cike dam dam. (Yo bata wasa da cin abinci ba dole wuyarta ta cika dam dam ba fisabilillahi 🤌😅) Ba ƙaramin kyau wannan tsokar gurun wuyar tata take yi mashi ba, ya kara mata kyau over, yana ɗaya daga cikin abin da yake burgesa a tattare da yarinyar, sai kuma wayonta da shegen son tambaya a kan abu, bata ganin abin da bata sani ba ta yi shiru, sai ta tambaya dan ta kara ilimi, kuma tana da gaskiya, duk abin da baka sani ba ka tambaya. "To ka koya mun mana, ni komai ma ka koya mun ina so". "Komai kuma?". Ya faɗa tare da kai hannunsa ɗaya samar wuyar tata, wani ɗan kwaro da ya sauka a wuyar tata yanzu ya cire mata. "E komai zaka koya mun". Ta bashi amsa tana kai hannu zata karɓi kwari da kifiyar dake hannunsa. Ita dai Sweetie tun da ba ganinsu take yi ba, sai kawai ta yi shiru tana sauraron hirar tasu, abin gwanin ban tausayi, rashin gani akwai matukar ciwo wlh, Allah mun gode maka da ka bamu idanun gani, ya Allah ka hana waɗan nan idanun namu ganin saɓonka ko kuma su haske mana izuwa wajen aikata saɓonka, kamar yadda ka yi mana ni'ima ta gani ya rabbi kasa iya aikin alkhari kawai zamu rinƙa yi da ita. "Pretty kina nufin na koya maki har da faɗa zaki iya yi? Zaki iya koyan duk abin da Mamma ta koya mun?". Ya yi maganar yana dawo da kallonsa cikin kwayar eyes ɗin nata tare kuma da sakar mata kwari da bakar. "E zan iya, yanzu ma ka nuna mun ya ake amfani da wannan abin? Ga abin busar kuma ka ajiyeta a wajenka". Tana magana tana miƙo mashi abin busar. Karɓa ya yi ya ajiye a gefen dutsen, sannan ya sanya hannunsa a saman shoulder ɗinta ya zagayo da shi ta gaban face nata, ya riko hannunta ɗaya da yake rike da kwarin nasa, sannan ya sanya ɗayar hannunsa ya kama wannan hannun nata dake riƙe da bakar. Da kanta yasa ta haɗa kwari da bakar waje guda, duk da yana rike da hannayen nata amma bai tayata yin controlling nasu ba, ya bari ta saita da kanta, sannan suka ja kifiyar baya a tare suka saki ba tare da saita komai ba. Sai dai ko da suka sake kifiyar sam bata yi nisa ba, sai ma ta sauka a kusa da su, hakan kuma ya samo asali ne sakamakon sake kifiyar da wuri da Kamran ɗin ya yi, ya rigata sakewa, da ya sake mata kuma kunga ya saki gudun karfin jan da ya yi, so ita bata da karfi hakan yasa da taga ya saki sai ita ma ta saki daga baya, kifiyar ta ki yin gudu mai nisa, shi kuma ya kasa iya ce mata su sake a tare ne, ya kasa iya magana, saboda wani irin yanayi da yake ji a tattare da shi, shi da kansa bai san wani irin yanayi bane bawan Allah, ga Pretty da shegen son jiki, da ta ji ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman shoulder ɗinta sai ta saki jiki ta kwanta mashi a gefen chest ɗinsa, dama can yaya, rikita shi take yi, bare kuma ta kwanto a jikinsa? Hakan yasa ya shiga yanayin da shi kansa ba zai iya sanin menene bane, duba da in da ya taso, da ni da ku dukka mun san ba zai sani ba dama, dan ma dai wani abin ba sai an koyawa mutun bane.......🥱😅 Ɗauke hannunsa daga saman shoulder ɗin nata ya yi, duk sai ya ji wani irin sanyi ta rufe shi kamar mai jin zazzaɓi, tunani ya fara yi anya Pretty zata iya koyar abubuwan da zai koya mata kuwa? Anya shi kansa zai iya cigaba da koya mata kuwa? Saboda a duk lokacin da ya haɗa jiki da ita tana sawa ya ji sanyi ta rufe shi kamar mai jin zazzaɓi, so ya fara tunanin ba lafiya yake ba, dole idan ya koma yau ya tambayi Mammarsa meyasa idan ya taɓa jikin wata ba ita Mammar tasa ba yake jin sanyi ta rufe shi? To amma jikin waye zai cewa Mammarsa ya taɓa? Shi ne tambayar da wani ɓangare na zuciyarsa ta yi mashi, To fa Kamran yana tsaka mai wuya wlh. (Bawan Allah bai san me ake nufi da........🤐😅 Na dai yi nan, bari na koma KINGDOM OF POWER, wata kila kafin na dawo Kamran ya nemawa kansa mafita😅 Mamma baki kyauta ba da baki koya mashi soyayya ba😅 wai baki san zai girma bane?🤔 25 years fa😒 gaskiya da sake😌 amma ba komai, Pretty zata banbance mashi me yake ji ai🥱 shi ma ɗan kaniya idan ha taɓa Sweetie baya jin komai sai dai Pretty😒😅) KINGDOM OF POWER💪🔥 Baki ɗauke da sallama Yah Jawad ya shiga cikin bedroom ɗin Akka. Akka bata a cikin ɗakin, Gimbiya Chuchu ce kawai take kwance a saman katafaren bed ɗin Akkar, daga ita sai kayan barcin jiya a jikinta, bata ciresu ba, da alama ma ko wanka bata yi ba, tana kwance ruf da ciki ta wani rungumo pillows kamar zata mayar da su cikin kirjinta. Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kallonsa, a saman bedside drawer ya zauna tare da ɗaure fuska sosai. Ita kuma jin sallamarsa yasa ta ƙara nutsuwa tsit tare da haɗe malaman jikinta waje guda, nan take wani sabon tsoronsa ya dira mata a ranta, gabaɗaya ta rasa me zata yi, sai ta fara ƴan kame kame. "Good morning Yah Jawad". Ta faɗa murya na sarkewa. Bai amsa mata gaisuwar tata ba, sai ma kara ɗaure fuska da ya yi ya ce. "What are you doing here da baki je kin yi shirin zuwa school ba?". Kara tsorata ta yi, dan tasan yayyun nasu basu wasa da batun karatu, basu yi masu ta sauki in dai a kan makaranta ne. Shagwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka, ga tsoro cike fal a ranta ta fara magana. "Dama bana iya tafiya sosai da kafafuna ne, my legs is paining me to much, shi ne yasa na kasa iya........". Kasa karisa maganar ta yi saboda wani irin kallo da ya wurga mata da waɗan nan idanun nasa masu rikitarwa. "Baka gama da wancan case ɗin ba kake shirin kara yin wani laifin ko Jawad?." Cewar Akka dake tsaye a bakin kofar toilet, ta yi magana cikin harshen larabci. Harara ya wurgawa Akkar kafin ya ce. "Wani case kuma? Ke wannan tsohuwa kwata kwata baki son zaman lafiya ko? Ni yanzu da sassafen nan me zaki wani kirani?". Ita ma harara ta wurga mashi da waɗan nan farare tas ɗin idanun nata, da alama sun saba, ba yau bane farau. "Me Jannat ta yi maka da ka ci zalinta har bata iya taka kafafunta? Anya Jawad kai kam akwai wadda zata soka kuwa? Anya muguntarku zai barku ku sami abokan rayuwa kuwa? Mutane ne sai mugunta, ina ɗaya mai mugun halin kuma yake? Ai tare na ce kuzo, dan na ja maku kunne a kan azabtarmun da kishiyoyi da kuke yi, ni ba kishin zamani nake yi da kishiyoyina ba, na da nake yi, dan haka zan iya tare masu faɗa". Ta kai karshen maganar tare da ƙarisowa wajen nasu. A bakin bed ɗin ta zauna kusa da shi. "Jaish kam ai kin san daidai yake dake, ni wai Akka me ma ya hanaki komawa wajensu mai rankarfe ne? Sune suke buƙatarki mu mun gaji dake gaskiya". Cewar Yah Jawad ɗin kenan. "Innalillahi kun gaji dani, to ubanninku basu gaji da ni ba, kuma ni nan da kake gani na takalmin karfe ce mai take maza, kai ni ma kake cewa kun gaji da ni ko? Wlh nasan maganinka, maza kira mun Abbas a waya, yanzu ba sai anjuma ba ya zo ya yi mun maganinka". Shiru ya ɗan yi mata na ƴan sakani kafin ya ce "Ina wayarki take? Ni bani da number daddy, ki kirashi da kanki". Nan fa ta fara sababi wai dama da Jawad da Jaish sun rainata. Da dai yaga da gaske take yi sai ya fara lallaɓata dan sun rabu lafiya, kada ta je ta gayawa daddynsa ko kuma daddynsu Jaish, tasa su ɓata masu rai a banza, wannan tsohuwa ta iya tsiya ita ma!. "Shikenan Akkarmu ta ƴan gayu, yanzu dai gaya mun meyasa kika kirani? Kin ga dai zan je wajen aiki ko farincikin Familyn ABDUL MALIK?". "Ba in da zaka je har sai ka ɗauki Jannat ka kai mun ita asibiti an duba mun lafiyarta dana kafarta, dan na lura so kake ka mayar mun da ita gurguwa ka cuci mijin da zata aura, to wlh baka isa ba, kai ka je ka auro tsaleliya mai kafa ita kuma ka cuceta ko? Wane kai, idan ta zama gurguwa kai zaka aureta, ni ka tashi maza ka kai mun ita asibitin a duba mun ita". Girgiza kai kawai ya yi, rigimar Akka babu mai iyawa da ita sai ƴaƴanta su King kenan, sune zasu iya biye mata. Miƙewa tsaye ya yi yana faɗin. "To ta tashi muje asibitin a dubata ɗin, ba shikenan ba?". Ya kai karshen maganar tare da nufar hanyar fita waje. "Ai dawowa zaka yi ka ɗauketa, kafafun nata sun kumbura basu iya takawa, dan haka dawo ka ɗauketa har izuwa asibitin". Dafe kansa ya ɗan yi, wannan tsohuwa gara mashi ya rabu da ita lafiya, idan ba haka ba yanzu zata kira daddynsu Jaish a waya ta ɓallo masu ruwa, ta ja mashi wani aiki, dan haka gara ya yi abin da ta ce kawai su rabu lafiya. Dawowa ya yi kusa da gadon. Da sauri Gimbiya Chuchu ta runtse idanunta saboda wani irin kallo da ya wurga mata, kallo ne na zamu haɗu ne, irin zai kamata ɗin nan, ta ja Akka ta ɗaura mashi wahala, kuma dole ya yi idan yana son zaman lafiya, dan haka ita ma ba zai barta ba, sun saka kafar wando ɗaya kenan, ba mai kwatarta a hannunsa........ E mukam zamu ga wannan wasa ya zata kaya, namu eyes...... 👀😅 Ɗaukarta cancak ya yi, cikin sauri ya nufi waje da ita, yana jiyo Akka tana sababin tare da masifa a kan ya kula mata da Chuchunta sosai, kada ya bari wani abin ya sake samunta, kuma ya tabbatar an duba mata kafafun nan nata da kyau anyi mata abin da ya dace, sannan ya dawo mata da ita har saman gadon nan kamar yadda ya ɗauketa, sai surfa masifa take yi, ai kuwa ko sannu bai ce mata ba, sai ma sauri da ya kara ya bar room ɗin. Suna shiga cikin elevator ya sauketa ƙasa, cikin bada umarni ya ce maza ta taka da kafafunta, kuma anjuma da daddare ta same shi a cikin part ɗinsa, zata gane kurenta. Kuka ta saka mashi, saboda har ga Allah kafafun nata suna yi mata zafi, bata taɓa yin kneel down ba sai jiya, shiyasa suke yi mata ciwo. "Rufe mun baki ko kuma na karya kafafun mai gabaɗaya ki huta, da kafarki zaki taka har izuwa cikin hospital". Zaro dara daran idanunta ta yi, duk da cewa katafaren hospital ɗin a cikin masarautar take, amma tana da nisa sosai da part nasu, idan za su je sai sun shiga mota, shinfiɗaɗiyar mikekiyar titi ne daga part nasu har izuwa cikin hospital ɗin, asibitin masarautar ne, harta school ɗinsu a cikin masarautar take, sai dai ita ma tana da nisa da part nasu, sai sun shiga mota, sannan akwai manya manyan masu faɗa aji a kasar da suka sanya ƴaƴansu a school ɗin, ƴaƴan manya ne kawai suke karatu a cikinta, malamai daga manyan ƙasashe masu faɗa a ji a duniya aka ɗebosu suke karantar da yaran, from nursery one ne two Ss3, daga nan sai su fita waje karatu, haka suke yi, akwai komai a cikin KINGDOM OF POWER, ba masarauta ce ta wasa ba, ba ta kananan kai bace ba, masarauta ce da idan bata zo ta farko a duniya ba to zata zo ta biyu!, ga bala'in girma duniya guda!. "Please Yah Jawad i can't walk with my legs, zafi suke yi mun, na tuba ba zan sake gayawa Akka ba, kuma yanzu ma ita ce fa ta tambaye ni me ya sami kafafuna, shi ne na gaya mata, amma please for give me". Tana magana tana ruwan hawaye, wani na bin wani!. Tamkar babu shi a cikin elevator, ya yi banza da ita, sai ma wayarsa da ya ciro ya fara latsawa abinsa. Durkushewa kasa ta yi a saman gwiwowinta, wani irin azaban zafi da gwiwowin nata suka yi mata ne yasa ta saki ƴar kara tare da yin zaman dirshan a cikin elevator, ba zata iya cigaba da tsayuwa bane, ƙafafun nata ba zasu iya ɗaukarta ba. Cike da bada umarni ba tare da ya kalli in da take ba ya ce "Stand up! Kada kuma naga kin yi mun tsayuwa wani iri, stay straight kamar koda yaushe! Daga nan har cikin hospital zaki je da kafarki, and lastly clean all this tears da yake a saman kumatun nan naki, kada ki yarda ki bari na sake ganin wani tears a saman face ɗin naki komai ƙanƙantarsa". Kai Yah Jawad ma ya iya mugunta, Akka ce fa ta tambayeta ita kuma ta faɗa, shi ne zai kara azabtar da ita? Allah ya saka mana, sai mun haɗu gobe idan my dukka ya kaimu my people's, Love you all guy's ❤️💘🔥 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 24/7/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________21🔥 Kasa miƙewa ta yi, saboda yadda ta yi zaman dirshan ɗin ba zata iya tashi ba, ga kafafun nata ciwo suke yi mata sosai, hakan hasa ta kara sautin kukan nata tana mai cigaba da yi mashi magiya da ya yi hakuri ta tuba ba zata sake ba! Ya dubi girman Allah ya yi hakuri, gabaɗaya hawaye ya gama jike mata face nata izuwa yanzu, ta ci kukan har ta fara ƙoshi. Dai'dai lokacin kuma elevator ta yi ƙasa da su, buɗe kofarta ya yi da nufin ya fita waje in yaso sai ya yi abin da ya dace. Ai kuwa yana buɗe kofar suka yi ido huɗu da uncle Abbas, zai je wajen Akka ne daga nan ya wuce su gaisa da su Mummy, dan tun da ya zo bai leƙa su mum ba a matsayinsu na Aunty's ɗinsa matan wansa, so shi ne zai je wajensu, ga wani jibgegen ɗan'sanda shirye cikin kayan aiki rike da wata lafiyayyar jibgeiyar gun a hannunsa, fuskar nan tasa sam babu alamar mutunci a tattare da shi, ya haɗe gerar sama da ta ƙasa, face kamar an naushi kashi, no mutunci. "Good morning daddy". Ya faɗa ƙasa ƙasa, yaki yarda kuma ya ɗago kai su haɗa idanu da daddyn nasa, dan ya san zai sha harara tun kafin ma ya tambayesa me ya sami Gimbiya Chuchu ta yi zaman dirshan a cikin elevator kuma take kuma haka?!. Aikuwa ya gudu ne bai tsira ba, domin kuwa uncle Abbas bai amsa gaisuwar tasa ba, kwata kwata bai ma ji gaisuwar ba, hankalinsa gabaɗaya yana a kan Chuchu dake ta faman kuka, hakan yasa sam bai ma ji cewa Yah Jawad ya ɗaga mashi gaisuwa ba!. "Jawad what happened to her? What did you did to her?". Uncle Abbas ya faɗa fuskar a ɗauke da mamaki, dan kukan da ta yi ba kaɗan bane, ta sha kukan ta ƙoshi har wani shessheƙa take yi, ya yi maganar kuma tare da shigowa cikin elevator da sauri fuskarsa a ɗauke da alamun ɓacin rai. "Dad i don't do anything to her, kawai kafafunta ne suke yi mata ciwo, Akka ta ce na kaita hospital, wannan shi ne dalilin yin kukanta". Sam uncle Abbas bai sake bi ta kansa ba, yana shigowa ya tsuguna a gabanta tare da kai fararen tafukan hannayensa ya fara goge mata hawayen yana mai tambayarta me ya sameta? Me take yi wa kuka har haka?. Da farko kamar zata gaya mashi gaskiyar abin da ya faru, amma tuna cewa yanzu ma faɗawa Akka gaskiya da ta yi ga shi nan Yah Jawad ɗin ya sake wahalar da ita, hakan yasa ta ɓoye gaskiyar dan kada ta sake shiga wani azaban. Cikin rawar murya ta ce. "Uncle my legs, ciwo suke yi mun, na kasa iya takawa ne". Hannunsa ya kai saman kafafun nata yana faɗin. "Meyasameki a kafar taki har take yi maki ciwo haka?". Ɗan satar kallon Yah Jawad ɗin ta yi kafin ta sake sunkuyar da kai ƙasa. "Faɗuwa a bathroom na yi". Ta faɗa tana sunkuyar da kai ƙasa. Daga yanayin yadda take satar kallon Yah Jawad yasa uncle Abbas ya fahimci tabbas Yah Jawad ɗin ne ya yi mata wani abin, shi ne makasudin wannan ciwon nata, dan haka sai ya miƙe tsaye yana karewa Jawad ɗin kallo, da yake shi mutun ne mai ilimi sosai sai bai ce mashi komai a gabanta ba, dan kada ya ja mashi reni a tsakaninsu. "Tun da ba zata iya takawa ta yi tafiya da kafafunta zuwa parking space ba, kai kuma ba zaka iya ɗaukarta ba bari na kira Jaish ko kuma Taheer ɗaya daga cikinsu ya zo ya ɗauketa, sannan idan kun kaita asibitin duk abin da yake damunta you should let me know da sauri". Ya kai karshen maganar tare da ciro wayarsa daga aljihun rigarsa domin ya kira ɗaya daga cikin waɗan da ya kira sunansu su zo su ɗauketa. A hanzarce ya ce. "Daddy me zaka yi kuma?". "Taheer zan kira ya zo ya ɗauketa dan ba zata iya takawa ba, Jaish ma ba zan wahalar da kai'na wajen kiransa ba, dan nasan halinku ɗaya ne da shi, kuma idan ka dawo office kazo ina son yin magana da kai". Ya kai karshen maganar yana wurga mashi wani irin kallo wadda za'a iya fassarata da sai na rama mata. "Kai daddy ni yanzu na ce maka ba zan iya ɗaukarta bane? Nawa take kwata kwata?". Hararar wasa ya wurga mashi kafin ya ce. "Aww dama zaka iya ɗaukarta kenan? Shi ne ka bar mana ita zaune cikin sanyin nan tana kuka kana sauraron kukan ko? Ku canza hali wlh". Shiru dai ya yi bai sake yin magana ba, sai ma zura wayarsa a aljihu da ya yi tare da duƙowa kanta kaɗan, ya saɓeta sai saman shoulder ɗinsa, yasan idan ya biyewa daddyn nan nasa sai su ɓata sama da awa a wannan wajen, haka suke kamar abokai, uncle Abbas yana da wasa da dariya dasu sosai fiye da King Zuhair ma, shi kamar ba daddynsu ba, yadda kuka san abokinsu ne. "Da ka bari na kira Taheer ya ɗauketa ai". Uncle Abbas ya faɗa yana binshi da kallon zolaya. "Daddy have a wonderful day, love you more". Shi ne abin da ya faɗa tare da sa kai ya fice da sauri abinsa, dan kada daddyn nan nasa ya ɓallo mashi ruwa ana zaune kalau. Da kallo uncle Abbas ya bishi da shi, sai da ya kalli wucewarsu suka bar arear wajen, sannan ya ce. "Zaka zo ka same ni ne, sai na rama mata, ku baku da aiki sai azabtar da ƴaƴan mutane". Ya kai karshen maganar tare da gyara tsayuwarsa a cikin elevator, sannan ya gyara babbar rigar dakakkiyar shaddar dake a jikinsa, ɗinkin ta zauna zam zam a jikin nasa, ya yi wa kayan kyau, da alama wani waje mai muhimmanci sosai zai je, domin idan ba haka ba uncle Abbas bai cike saka manyan kaya har da babbar riga haka ba, ya fi yawan sanya suit sai kananan kaya, da yake ma yanayin jikinsa, suna da kyan jiki sosai, ba zaka taɓa cewa shi ne ya haifi su Jawad ba, idan ya shiga cikinsu ma sai ya saje da su abinsa. A bakin elevator ya bar wannan ɗan'sandan, domin babu wani security da ya isa ya keta ya shiga part na King. A ɓangaren shi kuwa Jaish, bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga cikin bedroom na King. Zaune saman wannan haɗaɗɗiyar carpet na gashin jimina ya isko King yana shan haɗaɗiyar hot coffee da Gimbiya Rahilarh wato Mommar Jawad ɗin ta haɗa mashi, ta saba bashi coffee da sassafe ya sha kafin lokacin yin breakfast ɗinsu ya yi. Kusa da daddyn nasa ya zo ya zauna. "Good morning daddy, how was your night?". Miƙa mashi cup ɗin coffee ɗin dake hannunsa yana sha King ɗin ya yi, dan yasan ƴaƴan Momma dukka mayun shan coffee ne, a jininsu yake, yanzu haka shigowar Gimbiya Zunaira cikin ɗakin sai da ya bata ta sha kafin ta fita, za kuma ta sake zuwa wajen Momma ta sha, kullum safiya aikin kenan. Sai tashin tiriri coffee ɗin yake yi. Karɓa Jaish ɗin ya yi tare da kaiwa saitin ɗan bakinsa, kaɗan ya ɗan kurɓa ya sake muƙowa da daddyn nasa abinsa. "Ya isheka ne?". King ya tambaya yana mai kai hannu zai karɓi cup ɗin. "No dad, bai isheni ba, sai dai nafi son kai ka sha ne, Momma kai ta kawowa, for sure nasan nawa yana cikin bedroom ɗinta yanzu haka". "To ai na Mommarka daban na daddynka ma daban, nawa ya fi nata daɗi ai". Yana magana yana tsare Jaish ɗin da idanun. Nisawa kawai ya ɗan yi, har gobe daddynsu ba zai canza ba, wai nasa yafi na Momma daɗi, bayan kuma ita ta haɗasu dukka, tsammashi fa shi ma ta yi, ba shi ya yi da kansa ba! Haka yake cewa, sai ma sun zauna da Momman waje guda, sai ya rinƙa ce mata dukka ƴaƴansa shi suka biyo, sai ya zaɓi waɗan da suka fi kyau sosai a cikinsu ya ce sune masu kama da shi, ai Momma ita bata da wani kyau sosai, ya fita kyau, kawai ya aureta ne saboda uncle ɗinsa, kuma fa ba haka bane, daga cikin KINGDOM OF POWER yake shiryawa ya tafi har Dubai zance a wajenta lokacin da yake neman aurenta, yana mutuwar sonta, amma yanzu saboda zolaya sai ya rinƙa cewa ai ya fita kyau, kuma ita ta makale mashi ta ce idan ba shi ba mutuwa zata yi dan taga kyakkyawa, wasu abubuwan ma ai ba za'a tunosu bane, da irin kaunar da ya nunawa Momma idan sauran matansa suka ji ai ba zaman lafiya, zasu ce ya yi son kai, ita kuma Momma idan ya ce bata da wani kyau hasken fata ne kawai, lallaɓawa yake yi da ita, sai ta yi ta biye mashi tana cewa ta fishi kyau, hakan ne kuma yake yi mashi daɗi yasa kullum sai ya zolayeta, abin gwanin birgewa!. "Daddy zan je wajen Momma daga nan zan wuce office". Kai mashi cup ɗin coffee ɗin a saitin ɗan bakinsa King ɗin ya yi yana faɗin. "Ka kara sha kaɗan". Wannan coffee dai da albarka take, Gimbiya Zunaira ta sha, King ɗin ya sha, ga Yah Jaish ma yanzu ya sha, da twins Obaid da Omaid za su shigo yanzu da su ma sai sun sha. Ba musu ya karɓa ya ƙara sha ba mai yawa sosai ba, sannan shi ma da kansa ya sawa daddyn nasa cup ɗin a baki yana faɗin. "Dad take it all, kasan kai fa Momma ta kawowa, idan har ta samu baka sha dayawa ba zata ɓata rai". Da sauri ya ce. "Ni kuma da ta ɓata rai ai gara na shiga filin daga mu buga yaki, dan haka bani kayana". Ya kai karshen maganar tare da karɓar cup ɗin daga hannunsa. "Dad you really love Momma fa over". Ya faɗa tare da fara yunƙurin miƙewa. "Kai idan ka ce love ma ai ka rage, ita ɗin rayuwata ce, ƴar albarka ce". Shi dai Jaish miƙewa tsaye ya yi abinsa tare kuma da ɗan duƙowa ya mannawa King ɗin sunbata a goshi, ba dan yasan wanenen Jarumin mahaifin nasa ba ai da ya bashi number ɗaya a matsayin masoyan duniya, ita ma Momma bata da wani magana sai nasa, shi dai Jaish suna cika masu kunnuwa da zancen love ɗinsu da suka yi a baya, shiyasa da sun fara yake kara gaba abinsa, dan ya lura kowannensu mutuwan wa juna yake yi. "Dad na wuce, pray for me". Ya yi maganar tare da nufar hanyar fita abinsa!. Addu'a sosai King ya yi mashi cike da so da kauna. A cikin zuciyarsa yake amsawa da Amin ɗin, daga haka ya fice waje. Yana fitowa suka haɗu da uncle Abbas da yake ƙoƙarin shigowa bedroom na King ɗin, gaisawa suka yi cikin girmama juna tare da nuna tsantsar so da kauna, suna kaunar uncle Abbas ba karya. Addu'a sosai shi ma ya kwarara masu kafin su yi sallama da Jaish ɗin ya wuce part na Mommarsa domin ya je ya sha coffee kamar yadda ya saba. Shi kuma uncle Abbas ya wuce ciki wajen King kenan. Shiru part ɗin nata babu kowa sai kuyangun da suke ta faman yi mata hidima, sai kai komo suke yi, part ɗin tsab tsab da shi, sai tashin kamshin room freshener mai kwantar da hankali yake yi. Ƙasa gabaɗaya kuyangun dake cikin parlourn suka zube a saman gwiwowinsu suka fara zuba mashi gaisuwa. Kamar dai yadda aka saba ne ko kallon in da suke bai yi ba, ya sa kai ya nufi saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna a parlourn kenan. Kuyanga mama Haulat ce ta ƙariso gabansa cikin sauri tare da zube gwiwowinta a ƙasa tana ɗibar gaisuwa. "Yi mun sallama da Momma". Shi ne kawai abin da ya faɗa, daga haka bai sake magana ba, kuma bai kalli in da take ba. A hanzarce cikin rawan jiki ta miƙe ta nufi cikin bedroom ɗin, ita kaɗai ce mai shiga har cikin bedroom ɗin Gimbiya Rahilarh, sauran kuyangun a iya parlourn kawai suke tsayuwa. Zaune saman waɗan nan shinfiɗu na alfarmar ta isko Momma, ta sha kwalliya cikin wata dakakkiyar tsadaddiyar lace mai bala'in kyau launin pink color mai ɗan duhu, ba ƙaramin kyau ta yi ba, farar mace da kaya pink color akwai ɗaukar idanu, kalar yana hawa da skin ɗinta sosai, hannayenta wuyarta dukka shake suke da abin ado na zallar madarar gold masu bala'in kyau da tsada, ga tsadadden haɗaɗɗen alkyabbarta launin white color, white ɗin ma irin up white ɗin nan mai haske sosai, sai ta kara tsantsara kyau na wuce misali. Wasu haɗaɗɗun Dubai set of cup's ne a gabanta, ga hot jug ɗinsu, cup ɗin sun haɗu makurar haɗuwa. Daga gefe kuma wani haɗaɗɗen kwandon kayan fruits ne mai shake da fresh fruits ɗin sosai a cikinsa. A gabanta Mama Haulat ta zo ta tsugunna, cikin girmamawa ta dukar da kanta ƙasa tana jiran izinin yin magana. "Haulat menene yake tafe da ke?". Ta faɗa cikin sanyin murya kamar Gimbiya Zunaira ce ta yi magana. "Dama Yah Jaish ne yake neman iso, yana parlourn". "Ki ce mashi ya iso". A hanzarce ta miƙe cikin rawan jiki ta nufi wajen. Kai tsaye gabansa ta sake komawa ta zube gwiwowinta a ƙasa kafin ta gaya mashi Momma ta ce ya shigo. Tun bata ƙarisa maganar ba ya miƙe ya wuceta abinsa, dan lokaci ya ɗan tafi, yana son ya je office da wuri. Baki a ɗauke da siririyar cikakkiyar sallama ya shigo cikin bedroom ɗin. Yadda Mama Haulat ta barta bata motsa daga wajen ba, tana zaune, daga zaunen ta amsa mashi sallamar tasa tare da yi mashi izinin shigowa. Kai tsaye kusa da ita ya zo ya zauna tare da ɗaura wayarsa a saman wani haɗaɗɗen throw pillow dake kusa da shi. "Good morning our lovely Momma". Ya faɗa yana kai hannu zai ɗauki cup ɗaya ya zuba coffee da yake a gabanta. Karɓar cup da ya ɗaukan ta yi. "Morning my son how was your night?". Ta faɗa tana zuba mashi coffee ɗin da kanta. Alhdulillah ya amsa mata da shi tare da tambayarta ta tashi lafiya?. Zuba mashi coffee ɗin ta yi dai'dai yadda tasan yake iya shanyewa, sannan ta fara bashi a baki kamar ƙaramin yaro, bai karɓa ya sha da kansa ba, dan idan da sabo ai ya saba, sau da dama idan zai ci abu, in dai a gabanta ne to ba shakka sai ta bashi a baki, hakan yasa bai ma damu ba, ya fara buɗe ɗan bakinsa yana karɓa kawai. Akwai soyayya mai karfi mai kuma kayatarwa a tsakanin King Zuhair, Gimbiya Rahilarh da kuma ƴaƴansu. Haka ta cigaba da bashi coffee ɗin suna hira cike da so da kauna, har gobe dai yana da matukar kunya, baya bari su haɗa idanu da mutane shi dai!. A ɗayan ɓangaren kuwa, Gimbiya Sarina ce zaune a tsakiyar katafaren bed ɗinta, da alama yanzu ba jimawa ta tashi daga barci, gabaɗaya wannan gashin nata na larabawan a watse, ya basu mata har ta gaban fuskarta, kayan barci riga da wando launin sky blue ne a jikinta. Wayar Mammie ɗinta ce a hannunta, call take ta aikin dannawa twins Obaid and Omaid, a kan su zo su sameta su shirya wani plant, dan yanzu Mammienta ta fita daga cikin bedroom ɗin, ita ce ma ta tasheta daga barci, yau a part ɗin iyayen nata ta kwana, uncle Abbas ya ce akwai wani ɗan amininsa da ya ganta ya ce yana so, dan haka zai zo suka ga juna ta shirya, ɗa ne ga Attorney general of the federation, dan haka ta shirya anjuma zai zo, ita kuma sam bata son kowa, bata kula samari, bama ta son a kawo mata zancensu, shiyasa duk wanda ya zo neman aurenta sai ta haɗa baki da twin's sun yi mashi wata muguntar da idan ya tafi ba zai sake dawowa ba, haka suke yi, to shi ne yanzu ma take kiran numbersu, su zo maza, duk tana wani birkice, dan uncle Abbas ya yi ta yabon yaron, wai yaron kirki ne, ga hankali da ilimi, kwata kwata shekarunsa 28, ya kammala degreensa a ƙasar England, yanzu yana master ɗinsa a America, ya nuna yana sonta sosai ne tun lokaci da ya raka daddynsa makarantarsu halaktar wani taro, daga lokacin ya ganta, sai yanzu Allah ya bashi ikon iya gayawa iyayensa har suka sami uncle Abbas da maganar. Ita dai Gimbiya Sarina ta rasa me ta tsarewa daddyn nan nata da bashi da aiki sai turo mata samari, ta kori wannan ya sake turo wani su san juna, daga ƴaƴan sarakuna sai ƴaƴan ƴan siyasa, to ita duk basu bane a gabanta, tana da zaɓin ranta wanda taki bari kowa yasan ko wanene shi, ta killace abin a iya cikin zuciyarta ita kaɗai, kuma da alama bata da niyar faɗar wanenen take so ɗin a yanzu, saboda a yanayinta ma dukka babu alamar son aure nan kusa a tattare da ita, uncle Abbas dai shi ya matsawa kansa, a cewarsa ai ta girma, gara ya aurar da ita kawai, kuma ya lura da Sarina ba kamar su Fanan take ba, ita idanunta a buɗe sosai suke, wayewarta ya fi shekarunta, hakan yasa yake tunanin yi mata aure dan ya tsira da mutuncinsa......... Gaskiya kam yana da gaskiya sosai ma. A tare twin's suka shigo cikin bedroom ɗin nata, shirye suke cikin shiga iri ɗaya, komai na jikinsu iri ɗaya ne, shigar kananan kaya suka yi, duk nacinka ba zaka iya banbance wanenen Obaid kuma wanene Omaid a cikinsu ba, komai nacinka wlh sai sun gaya maka ni ne wane, a gidan ma gabaɗaya daga Mommarsu sai King and Zunaira ce kawai suke iya rabesu, ko shi Jaish ba wani iya rabesu yake yi ba, bare ma idan suka yi shiga iri ɗaya, sai ka rantse da Allah mutun ɗaya ne ba biyu ba, sai Jaish ya kura masu idanu yake iya rabesu, suna da banbanci, akwai abin da ya banbantasu a face nasu, amma ba kowa ya san da hakan ba, shiyasa shi ma Jaish sai ya kura masu idanu yake iya banbantasu. Suna shigowa suka haye saman bed ɗin nata, har suna haɗa baki wajen cewa. "Aunty Sarina me ya faru kike nemanmu?". Hannu ta kai ta fara tattare kyakkyawar bakin gashin kan nata waje guda, tana turɓune fuska kamar wadda ta kalli kashi, a ƴamutse ta ce. "Abin da aka saba ne, daddy ne wai wani Yusuf ɗan amininsa zai zo wajena, kuma ni tun ban ganshi ba ma na ji na tsaneshi, dan zai rusa mun plan". Guntun tsaki Omaid ya ja, dama shi ya fi Obaid zafin jini da rashin ji. "Aunty Sarina shi ne zaki wani damu? Waɗan da suka fishi ma sun zo munyi maganinsu bare shi ƙaramin kwaro, ki kyale shi ba dai anjuma zai zo ba? Kafin ya zo mu zamu shirya shirin yin maganinshi, da kafansa zai gudu kamar yadda ya zo, ke dai kamar yadda aka saba ki shirya sosai dan ma kada ace baki son shi a gane shirinmu". Wani irin shu'umin murmushi ta saki, don tasan Omaid bayi da wasa, yanzu zai iya shirya abin da zai tarwatsa gungun taro, shape brain ke garesu twins ɗin nan, kuma wlh duk nacinka ba zaka taɓa gane cewa sune suka yi abu ba idan suka aikata, saboda komai cikin kwarewa da kuma ilimi suke yi, kun ji da bakinsu sun gaya maku su tunani suke yi irin na actors ba boss ba, waɗan nan yara sai dai shirin Allah, ai da mutun ya takura maka kawai ka gaya masu, cikin ruwan sanyi zasu sanya shi ya rabu da kai, sun iya shiri, yanzu dai zamu ga me zasu shiryawa Yusuf bawan Allah........😅 Sai murna Gimbiya Sarina take yi, har ta sami kwarin gwiwar zuwa ta yi wanka, cikin sauri ta diro ƙasa daga saman bed ɗin ta nufi cikin toilet dan ta yi wanka. Su kuwa kwanciya suka yi a saman bed ɗin tare da fara tattaunawa a kan yadda zasu ɓullowa Yusuf idan ya zo, nan take suka fara shirya mashi kitimurmura wadda da wuya ya tsallake, bama shi kawai ba, da wuya twins su shirya maka gadar zare ka tsallake, ba'a taɓa wanda ya taɓa tsalleke tarkonsu ba, da zarar sun haɗawa mutun tarko to sai ya afka ko yana so ko baya so, kamar wasu aljanu, akwai basira, sun gado ta ɓangare dukka biyu ne yasa har basirar ta fara yi masu yawa, sun gaji basirar King Zuhair and gimbiya Rahilarh. Gimbiya Sarina tana fitowa wanka ta hau shiryawa, fuskarta ɗauke da annuri, saboda tasan me suka kullah, har wani zumuɗi take yi, sai ka rantse da Allah tana son Yusuf ɗin, ita da bata murmushi ma sai ga shi har da murmushi yau, saboda zasu zalinci Yusuf......... Waɗan nan Team ɗin wato da Obaid and Omaid da kuma Sarina sai kun yi masu addu'ar Allah ya shiryi Team ɗin nan nasu. A ɓangaren Jawad da Chuchu kuwa. Tun da ya ɗauketa bai direta a ko'ina ba sai a cikin tsadaddiyar dandatsetsiyar motarsa mai tashin kai. Da gudu driversa ya ƙarisa wajen, a gidan baya ya sauketa shi ma kuma ya shiga gidan bayan, ba ɓata lokaci driver ya shiga gidan gaba, sai shessheƙar kuka take yi mashi, sam bai bi ta kanta ba, da ta ishe shi ma sai cewa ya yi ta yi mashi shiru ko kuma ya karya kafafun nata. Tafukan hannunta ta kai ta toshe ɗan bakin nata, gudun kada sautin shesshekar kuka nata ya fita. Wayarsa ya ciro ya kira number Mammie ɗinsa, bugu ɗaya ta ɗauka. Gaisheta ya fara yi kafin ya ce. "Mammie please ki bawa kuyanga hijab babba ta kawo mun parking space yanzun nan". Kamar zata tambaye shi me zai yi da hijab, sai kuma ta fasa ta amsa mashi da okey kawai. Daga haka ya katse kiran tare da kashe hasken screen ɗin wayar, ya jingina kansa da jikin haɗaɗɗiyar kujerar motar yana shakar kamshin perfume ɗin jikin Chuchun haɗe da sanyin Ac mai ratsa zuciya ta kuma kwantar da hankali. Ba'afi 5 mins da gama waya da Mammie ɗin ba sai ga wata kuyanga ta doso katafaren parking space ɗin hannunta na rike da leda. Ƙasa ƙasa ya ce da driver ya fita ya karɓo mashi hijabin. A hanzarce ya amsa da okey sir tare da ɓalle marfin motar ya fito da sauri. Kuyangar bata ƙariso wajen ba ya yi saurin isa in da take ya karɓo hijabin a cikin ledarsa, da alama sabo ne gal. Tun daga yanayin nauyin hijabin a cikin leda zaka fahimci babba ne sosai, hakan ne kuma, ko da driver ya kawo hijabin Yah Jawad ya karɓa ya miƙa mata a kan ta sanya a jikinta, tana ciro shi sai taga ya fi karfinta wannan hijabi, zai ja mata har ƙasa sosai. Ɗago idanu ta yi ta kalle shi, sam kallonsa baya a kanta, hasali ma idanuwansa a lumshe suke, bata da zaɓin da ya wuce ta sanya wannan zunbulelen hijabin haka a jikin nata. Kamar zata yi kuka ta ware ta sanya, ya yi mata yawa over, harta wuyar hijab ɗin yafi karfinta, sai zamewa yake yi yana sulluɓewa ƙasa, ga gashin kanta dama da masifar tsantsi. Haka dai ta kai hannu ta rike wuyar dan kada ya zame, sai satar kallonsa take yi ko zai ce a canzo mata wani, amma ina idanunsa a lumshen nan yaki buɗesu kawai ya bawa driver umarnin ya wuce da su hospital. Ba ɓata lokaci ya karɓi umarnin tare da kunna motar suka nufi asibitin nasu. Yah Jawad bai sake bi ya kanta ba har suka isa. Katafaren hospital ne na gani na faɗa, kusan za'a ce ma da wuya a sami hospital mai girmansa a ƙasar, manya manyan masu faɗa aji a ƙasar ne suke kwanciya jinya a cikinta. Abin mamaki dai baya karewa, da Yah Jawad suka shiga cikin hospital ɗin kuma sai yaki yarda likita namiji ya duba mashi kanwar tasa, wai sai dai mace ta dubata, ita dai tana fama da zunbulelen hijabin wadda ko matar limamin masallacin jumma'ar ƙasar saudiya bata saka kamarsa, ko kula shi shi da Drs ɗin ma bata yi ba, bama ta fahimtar me suke faɗa ba, ta dai kwantar da kanta shiru a saman gefen shoulder ɗinsa tana sauke numfashi a hankali hankali, duk gudun kada shessheƙar kukan da take yi ne ya bayyana, ya ja mata yanzun nan ya sauketa ya ce ta tafi da kafafunta, dan ƙaramin aikinsa ne ya sauketa ƙasa ya ce ta taka kafafun, hakan yasa ta kwantar da kanta shiru tana jin bakin ciki kamar ta shake shi, ya iya mugunta. Shi kuwa sai da ya zaɓi nurse ɗin da ta yi mashi, sannan ya buƙaci ɗaki domin ya kwantar da ita wannan nurse da ya zaɓa ta duba ta. Gabaɗaya ɗakunan da suke a cikin wannan katafaren hospital ɗin ba ɗakuna ne kamar ɗakunan sauran hospitals da kuka sani ba, waɗan nan ɗakuna sai ka rantse da Allah ɗakunan gidan wani ministar or governor ka shiga, saboda manyan kai ne suke kwanciya jinya a cikin hospital ɗin, kowane ɗaki ka shiga ɗauke yake da katafaren bed 6/7 wanda ya sha shinfiɗu na alfarma, sai ka rantse da Allah ba hospital bane, dan wasu shegun bed sheets dake saman beds ɗin ma kawai abin kallo ne, ga lafiyayyun freezers, Ac, kai harta shi kansa tiles na cikin wannan hospital ɗin na musamman ne, curtains da sauran kayan alatu na more rayuwa duk na musamman ne, kamar ba wajen yin jinya ba. Ka kwararrun likitoci da kuma kayan aiki masu inganci wanda ake kawosu daga kasar China, idan aka kwantar da kai jinya a wannan hospital ɗin kuma kaga baka sami sauki ba to sai in ciwon ajali ne wanda shi kuma bashi da magani ko kuma wani ikon na Allah, likitocin wannan asibitin kamar mayu haka suke, sun kware wajen iya aiki ne babu wasa. Hospital ɗin hawa har biyar ne, so da haɗaɗɗe kuma tsadadden elevator suke amfani. A hawa na biyu aka bawa Chuchu ɗaki, can Yah Jawad ya nufa da ita. Yana kwantar da ita a saman katafaren bed ɗin da za'a dubata wayarsa ta fara kara alamar shigowar kira. Zama ya yi a gefen bed ɗin tare da ciro wayar tasa. Jaish ne yake kiransa a kan ya zo su wuce office. Shiru ya ɗan yi yana kallon call ɗin har sai da ta katse, sannan ya ɗan saci kallon Chuchu ta wutsiyar idanunsa kafin ya fara rubutawa Jaish ɗin sako kamar haka. Daddy and Akka sun sakani aiki, just go kawai sai mun haɗu da yamma. Yana gama rubutawa ya tura mashi, sannan ya kashe wayar tasa ma mai gabaɗaya ya zura a aljihunsa, sai ya ciro ɗayar wayar kuma ya fara latsawa. Nurse manyan mata biyu ne suka zo suka fara duba Gimbiya Chuchu, yana zaune a in da yake bai motsa ba, duk abin da suke yi yana kallonsu, sam hankalinsa baya a kan wayar da yake katsawa, ya dai rike wayar ne kawai, amma a zahirin gaskiya hankalinsa yana a kansu. Gimbiya Chuchu tana son ta yi kuka saboda zafin da kafar tata take yi mata, amma kuma tana tsoron yin kukan, dan kada Yah Jawad ya kara nata wani punishment ɗin, idan baku manta ba ya ce idan ya sake kamata tana kuka sai ya hukun tata, hakan yasa ta nutsu tsit baiwar Allah, tana jin yadda waɗan nan nurse ɗin suke mammatsa mata kafafun nata, har zogi yake yi mata, sai aikin tsuke fuska da ɗan bakin nan nata take yi, amma babu halin yin kuka. Duk kuma abin da take yi a kan idanun Yah Jawad ɗin take yi, yana kallonta sarai, amma sai ya yi kamar bai san tana yi ba, dan mugunta, ko irin ya ce mata sorryn nan babu. A ɓangaren Gimbiya Sarina kuwa, shiryawa ta yi cikin shiga na alfarma, ta fito a ainahin jinin sarautarta, kyau iya kyau, kayan jikinta wasu shegun tsadaddun kaya ne masu bala'in kyau Dubai make, goduwar riga ce ta ƴaƴan sarakuna, sai haɗaɗɗen alkyabbarta launin pink color, ta fito ras da ita, wlh ko baka so in dai ka kalli Gimbiya Sarina ta ci kwalliya to fa sai ka fola, shegiyar kaya ce, ta san kan duniya, idanunta a buɗe suke, wannan idan namiji ya shiga hannunta sai ta Allah, ko mata ƴan uwanta idan ta fito sai sun kalleta sun sake waigawa bare kuma maza, bata cika yin dressing da ya yi dai'dai da addinin musulunci ba, yawancin shigarta na turawa ne, sai dai idan a cikin masarauta take takan ɗaura alkyabbar a kan shigar tata gudun kada ta haɗu da su Jawad su saɓa mata kamanni, amma idan ta bar masarautar ko ziyara ta je wajen yan uwan mamanta ko kuma school ɗinsu, to fa ta soke sanya alkyabba, shegiyar kaya ce ta gasken gaske, ta wuce yadda kuke tunani, bata tarayya ko abota da mutun sai mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira kamar twins Obaid and Omaid, kuma ita ɗin zata iya amfani da kai ta cinma burinta ba tare da ka sani ba, wayo gareta kamar dila, shiyasa da uncle Abbas ya lura da wayewarta ya fi shekarunta yasa yake son aurar da ita, bata bin maza, kai bama ta kula namiji duk haɗuwarsa da iliminsa ko kuɗinsa, ko ɗaga idanu bata yi ta kalli namiji, dan tana da wani abin da take shiryawa ranta za'a ce ne ko mamarta take shirya mata ne oho masu. A ɓangaren mahaifiyarta kuma burinta kawai shi ne da Sarinar da Fanan ɗin duk su auri ƴaƴan King Zuhair, saboda idan baku manta ba ita mamansu mayinwaciyar mulki ce, tana son taga ƴaƴanta a kan kujera mai matsayi, shiyasa take ƙoƙarin taga yayanta sun auri koda ɗaya daga cikin Prince na masarautar ne tunda uncle Abbas dai ya ce siyasa yake da ra'ayi. Kamar yadda ake tarban baki a gidan sarauta haka aka tarbi Yusuf Abdulaziz Takur wanda ya zo da abokinsa guda ɗaya mai suna AL Amin Muhammad Zayyad. A katafaren masaukin baki da yake ta ɓangaren King Zuhair aka sauke su, an kawata parlourn ya sha kyau, sai tashin kamshin yake yi, ga kayan cima kala kala wadda a kallah zasu kai kala 10 da aka shirge masu a sama katafaren dining table dake a cikin parlourn. Yusuf dai ya sami tarba ta musamman, dan uncle Abbas da kansa yasa aka shirya mashi abubuwa da dama, sai dai lokacin da ya zo uncle Abbas ɗin yana tare da King a fada, so kai tsaye masaukin da aka tanada masu aka wuce da su. Wlh babu laifi, Yusuf haɗaɗɗen matashi ne kuma lafiyayye mai jini a jika, kyakkyawa ne ga shi dogo da shi, duk in da ake neman cikakken namiji mai kamala da riƙo da addini to Yusuf ya kai nan, bashi da makusa, haka zalika abokin nasa ma, basu da makusa, ga naira ta zauna masu, wasu fresh da su kamar suma jinin larabawan ne. Tun da ya shigo cikin parlourn yake ta faman raba idanu ta ina zai ga tauraruwar tasa, haƙiƙa yana son Sarina sosai, ya sha suit ɗinsa launin navy blue mai bala'in tsada, kafafunsa suna a cikin cover shoe masu kyau, bashi da yelwar gashin kai sosai, amma ya sha gyara yana kwance luf gwanin birgewa. Sai raba idanu yake yi yana jira yaga isowarta, abokin nasa ma burinsa ya ga isowarta kawai, dan Yusuf ya gama zuzuta masu kyanta, kuma ba karya ya yi ba, jinin Akka ba dai kyau ba, sun haɗu ne, bare ƴan'mata masu tsantsara kwalliya irin Chuchu, Zunairar da kuma Sarinar, ai idan ka yi ido biyu da su sai ka kalla ka sake waigowa, idan ma baka yi hankali ba a garin kallonsu ka je ka faɗi ƙasa. Sautin takalmarta mai uban tsini ne ya fara dakar dodan kunnuwarsu, fuska ba yabo ba fallasa, irin waɗan nan high heel masu tsawo sosai ɗin ta sanya, gata da tsawo dama, sai dressing ɗin nata ya kara kawata idanun mai kallo, ta fito sosai fa ba karya. Tafiya take yi tamkar wata hawayniya, kamar bata son taka ƙasa, tana sanya kafafun nan nata ɗaya bayan ɗaya a ƙasa, kai daga ganin tafiyar kasan ba yau bane farau, ta saba yin wannan shu'umin tafiyar mai ɗaukar hankali. Ga wasu kuyangunta biyu da suke binta a baya, ɗaya hannunta rike da kwando mai shake da kayan fruits, ɗayar kuma hannunta rike da wani katon try mai ɗauke da wasu shegun haɗaɗun cup's masu bala'in kyau, ga robar ruwa a shirye a saman, ruwa ne masu sanyi sosai, duk kayan cima da aka shiryawa su Yusuf ɗin a parlourn basu isheta ba, saboda munafurci dan ta nuna cewa tana son shi kamar yadda suka shriya da su Obaid yasa ta zo mashi da wasu, irin ta nuna shi na musamman ne a wajenta, waɗan nan Team ɗin sai dai shirin Allah na gaya maku, sun san kan duniyanci........😅 Duk in da ta wuce sai kuyangu sun zube ƙasa domin kwasar gaisuwa, amma kamar kashi haka take wucesu, sai ma yamutse fuska da take yi idan ta gansu kamar wadda ta kalli kashi, akawai ta da izzar bala'i tare da jiji da kai yarinyar. Tana sako kafafunta a cikin parlourn Yusuf ya miƙe tsaye, kawai ido ya kafeta da shi yana kallonta daga sama har ƙasa. Ita kuwa da yake ƴar duniya ce sai ta basar kamar bata san yanayi ba, ta cigaba da wannan ɗan iskan takun nata mai tafiya da tunanin mutum. Shi kansa abokin Yusuf ɗin sai da ya miƙe tsaye yana kallon tsantsar kyan da Allah ya yi mata, bayin Allah sun faɗa tarkon jinin Akka, sai dai Allah ya fitar da su. Takowa ta yi har izuwa wajen tsala tsalar sofas na parlourn, kamar ba ta kalli Yusuf da ya saki baki yana kallonta ba, zama ta yi a saman ɗaya daga cikin sofas ɗin, ko da ta zo zaman ma sai da ta yi wani rangwaɗa mai kara birkita tunanin duk wani lafiyayyen namiji, sam bata sanya idanuta ta kalli Yusuf ɗin ba har sai da ta zauna a saman sofa ɗin. "Kana iya zama yanzu ai malam Yusuf". Ta faɗa cike da izza sosai a muryarta, ka kwainane da kisisina, tana magana tana wani dakewa. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke kafin ya iya komawa saman sofarsa ya zauna. "Barka da isowa gimbiya kuma tauraruwar mata". Ya faɗa muryarsa cike tab da tsantsar so da kuma kaunarta. Wani irin ɗan iskan shu'umin murmushi kaɗan ta saki wanda ya kara fito da tsantsar kyanta, hakan kuma ya kara tafiya da imanin bawan Allah Yusuf. Shi ma abokinsa ya ƙasa iya kawar da kallonsa daga kanta, gata ƴar caras da ita. Juya waɗan nan fararen dara daran idanuwan nata ta yi kafin ta ɗan ja gajeran numfashi. "Yauwa barka dai malam Yusuf, fatan ka zo lafiya?". Ina ai ta gama tafiya da imaninsa, kara rikicewa ya yi a in da ya amsa mata da lafiya lou da hanzari. "Bari na zuba maku ruwan sha ko?". Ta faɗa ba tare da ta kawar da waɗan nan shegun idanun nata daga kan Yusuf ɗin ba. Da mamaki kuyangun da suka rakota suka bita da kallo, wannan yarinaya akwai shegen makirci, ita da ko kanta bata zuwaba ruwan sha idan zata sha, komai yi mata kuyangun nata suke yi, bata son yin aiki ko kaɗan, amma wai take cewa bari ta zuba mashi ruwan sha? Duk dan ace tana son shi kenan? Kai Sarina duniya. Ni ko na ce ko ina su twin's? Ko me suke shiryawa Yusuf bawan Allah? Ga shi dai ya gama afkawa gogin sonta, sai Allah sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA ne kawai yasan me waɗan nan Team ɗin suke shiryawa, sai mun haɗu da ku gobe idan mai dukka ya kai mu, amma fa akwai kallo ba kaɗan ba, dan nasan za'ayi dirama a cikin wannan KINGDOM ɗin yau, dan haka ku gyara zama!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 25/7/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________22🔥 Malam Yusuf dai ya ƙasa iya cigaba da magana, kallonta kawai yake yi, ikon Allah ikon gaske, abokinsa da ya zo rakiya ma sai kallonta yake yi, wannan da a tare suka ganta to ba shakka zata raba abotansu, dan sai sun yi faɗa a kanta, yanzu ma waye san gaibu? Ai sai Allah, bamu san me gaba zata haifar ba, amma dai koma me wannan abokin ya faɗa dayawa, Allah kaɗai yasan me yake tunani a cikin zuciyarsa kuma. Saboda shegen makirci irin na Sarina har da ɗan saukowa ƙasa kaɗan ta hau zuba masu ruwa yadda kuka san irin tana son shi kamar ta cinye shi ɗanyen nan, shi ma ya zaci haka ne, har da wani cewa. "Gaskiya na jima ban shiga farinciki irin na yau ba, bana jin kishin ruwa, amma saboda ke ce zaki zuba mun ruwan ko dukka kika ce na sha zan shanye". Ya yi maganar a nutse, da alama yana da nutsuwa sosai. Wani ɗan iskan shu'umin murmushi ta yi mai kara rikita mutun, a zahirin gaskiya saboda ma bata saba da yin murmushi ba, sai yazama sam murmushi bashi da gurbin zama a saman face ɗinta, ko ta yi baya yi mata wani kyau, amma da yake malam Yusuf sabon shiga ne, sai yazamana shi murmushin nata ya zama mashi wani abin na musamman, kuma sai yake ganin kamar idan ta yi murmushin nan har wani haske parlourn yake karawa.......... E ba shakka kai kam ka shiga tarkon Team ɗin nan na marasa jin magana, duk kuma wanda ya shiga hannun waɗan nan team ɗin to wlh sai dai Allah ya fitar da shi, yara ne yadda kuka san babba mai shekaru 50 wanda ya sha gwagwarmayar rayuwa ne yake shirya masu plan, ba zaka taɓa yarda cewa su ne suke shirya wasu abubuwa ba, saboda abin ya wuce tunanin mutun, idan zasu yi mugunta sai su juye su zama na Allah, su zama mutanen kirki, tsabar kuma sun iya basajan idan suka zama mutanen kirkin ma ba wanda yake iya ganewa, kai waɗan nan yara idan suka girma kada ka yarda ka shiga hannunsu, dan mutuwa ba makawa zaka yi. Cikin tsantsar rangwaɗa mai jan hankalin ta miƙewa Yusuf cup mai ɗauke da ruwan da ta zuba mashi. Bawan Allah jiki na rawa ya karɓa, tuni ya kai bakinsa ya fara sha yana zuba mata godiya. Haka ta sake zubawa ta miƙawa abokin nasa ma. A hanzarce shi ma ya kai hannu ya karɓa, daga yanayin yadda take zuba wannan ruwa ma kawai ya isa yasa ka fahimci bata iya aikin siɗiɗi bare saɗaɗa ba, kawai iyayi ne. Saman sofar ta koma ta zauna tare da ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, cikin wata iriyar voice mai sanyaya zuciyar mai sauraro ta fara magana daki daki. "Malam Yusuf ka sauko ku ci abinci, ga abubuwa nan mun tanada maku". Irin wannan voice da ta yi magana da shi ɗin nan sam ba zai iya tsalleke tayinta ya ce ba zai ci wannan kayan cima ba, dole ya amsa mata da. "Okey gimbiyata". Wani irin fari da ido ta sake yi mashi kafin ta ce da kuyangunta dake tsaye ta bayansu su zuba mashi abin da yake ra'ayi, dan a gaskiya bata iya serving na abinci ba, ruwan ma da yaya ta yi? Already kun san ita ko tsinke bata ɗagawa, komai sai dai ayi mata, so bata iya ba, shiyasa tasa kuyangun su yi masu. A hanzarce suka karɓi umarninta, ba ɓata lokaci suka zo suka fara serving ɗinsu, a wannan lokacin ne kuma Yusuf ya sami damar iya gabatar mata da kansa tare da abokin nasa da suka zo a tare. Bawan Allah abokin nasa bai yi kasa a gwiwa ba kuma bai bari kansa ya yi marfi ba ya yi maza ya ce. "Gimbiyarmu Please kina da sister? Allah dai yasa ba ke kaɗai bace". Ba tare da ta kalli in da yakeba ta bashi amsa, idan baku manta ba ita bata cika ɗaga idanu ta kalli mutane ba, bare ma kuma mutanen da ta raina class ɗinsu, ai gani take yi ma kallonsu kamar ɓata idanuta zata yi, hakan yasa sam bata kalli in da yake ba, shi ma Yusuf ya ci sa'ar akwai abin da aka shirya mashi ne yasa ake kallonsa, ba dan haka ba ina mai tabbatar maku Sarina ba zata ɗaga idanun ta kalli in da yake. "Yes ina da sisters ma dai ba sister ba, sai dai sun tafi school, amma idan kana son ganinsu sai na nuna maka pic's ɗinsu ai". Cikin rawan jiki kamar wani mazari ya buƙaci da yana son kallon hotunan sisters ɗin nata, dan har ga Allah ya afka kogin madarar kaunar jinin Akka....... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce aikuwa kana ruwa, dan ba Sarina ba, duk wanda ya ce zai yi soyayya da jikokin wannan tsohuwa in ma mace or namiji wlh yana ruwa, dan wasu murɗaɗɗun mutane ne, ko Zunaira da kuke gani kamar shiru shirun nan idan aka zo batun maza bata da daɗin sha'ani, bare su hjy Chuchu, duk kusan haka suke, babu wanda ya taɓa kula wani namiji a cikinsu, gani suke yi ma kula maza zubar da class ne, bare ma Aneesa ƴar Mama, ita ma kusan halinta ɗaya da Sarina a ɓangaren rai'na mutane, Fanan kuwa cewa ta yi sai ta samu namiji kamar yayansu zata yi aure, yayansu wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya nake magana, yayan Jawad mai suna Rizwan kenan, yana ƙasar Dubai, to shi ne wai sai namiji irinsa idan ta samu zata yi aure, ko shi ɗin wani irin hali gare shi da yasa ta ce sai irinsa zata aura? Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA, koma wani irin hali gare shi lokaci ne zai nuna mana, ga shi kuma yayanta ne uwa ɗaya uba ɗaya bare ace a haɗasu aure kawai, hakan ba zai yi wu ba. Wayar Mammie ɗinta da yake a hannunta ta ciro ta fara duba mashi hotunan su gimbiya Zunaira, ko a jikinta bata damu ba zata nuna mashi hoton, dan tasan idan ma a cikin ƴaƴan King ne wato su Chuchu, Zunaira or Aneesa zai zaɓa ya yi a banza, dan wlh bai isa ya tinkari King da wannan zance ba ato. Fito mashi da hotunansu a lokacin da Gimbiya Chuchu ta kammala primary school zata shiga secondary ta yi, a lokacin sun shirya gagarumin party sosai, an gayyaci manya daga ƙasashe da dama, sun sha kyau iya kyau, an yi hotuna anyi kyaututtuka da abubuwa daban daban, so iya waɗan nan hotuna na partyn kawai ne a wayar Mammie ɗin nata, dan na gaya maku ita Mammie ba kaunar jinin King take yi ba, har ga Allah bata son su Zunaira, kawai dai dan ba yadda zata yi ne, amma ta tsanesu kamar ta kashesu, wanɗan nan hotuna da kuka ga ta ajiye su a wayarta ma ta ajiyesu ne saboda akwai ƴaƴanta Sarina and Fanan a cikin hoton, da na su Zunaira ce kawai wlh ba zata ajiye ba, tsab zata gogesu munafukar mata. Miƙa mashi wayar ta yi a kan ya karɓa ya kallesu, a dai'dai lokacin kuma su kuyangunsu suka gama zuba masu abincin. Ƙasa saman haɗaɗɗen carpet ɗin suka sauko domin fara cin abincin. Hannu ya kai ya karɓi wayar domin ya kalli hotunan. Yusuf kuwa abincin ya fara ci domin ta gaya mashi idan ya ci zata yi farinciki, ya ce ta sauko su ci tare, ta ce tom su fara zata sauko. Shi kuwa Abokin nasa yana kyallah idanu yaga hotunan taurarin King Zuhair haba sai ya ruɗe, idanuwansa suna a tsaye kyam a kan Gimbiya Zunaira ƴar auta, shi ai yaga mata, ina sai ya ga ashe Sarina ma ba wata kyakkyawa bace idan aka dangantata da Zunaira da kuma Chuchu, sun fita kyau nesa ba kusa ba, sai dai Zunaira karamar yarinya ce, kuma shi baya jin kamar zai iya jiranta ta girma, yanzu yana da 28 years a duniya, ita kuma 11, ace ya jirata nan da shekaru 7 zuwa 8 haka, gaskiya da kamar wuya, ita ma dai Chuchu koda ya ce yana so zai yi jiran shekaru 4 zuwa 5 kam, dan 14 years ke gareta, Aneesa mai 15 years ma nawa take? Duk cikinsu dai Fanan ɗin ce sai kuma Sarinar suka isa aure, shi kuma Fanan bata yi mashi ba, dan kyawun Gimbiya Zunaira da Chuchu sun dishashe kyan kowa da yake a cikin hoton, su biyu ne taurarin da suka haska kowa, so shi a ɗaya daga cikinsu yake so a bashi mata. Taɓa shi Yusuf ɗin ya yi yana faɗin. "Ya dai? Bata yi maka bane?". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Yi kai, ai ni naga mata". "To mu gani". Yusuf ɗin ya faɗa. Miƙawa Sarina wayarta ya yi yana faɗin. "A'a ba zaka gani ba, kai baga naka Gimbiyar a gabanka ba? Me kuma zaka ce zaka ga wata? Gaskiya ban yarda ba". Yaki nuna mashi su ne kawai dan yasan yana ganinsu zai kallin kyan Sarina ya dishashe a idanunsa kamar yadda ya gani a yanzu shi ma, hakan yasa ya ki bashi ya gani. Ko a jikinsa Yusuf bai damu ba, shi dai Sarina kawai yake kallo abinsa. Ƙasa saman carpet ɗin ita ma ta sauko, duk dan ta nuna mashi kulawa ta kuma nuna yes tana kaunarsa, shi kuwa ya saki baki ya ɗauka haka abin yake. A ɓangaren su twin's kuwa, kwance suke a saman katafaren bed nasu, Omaid yana rike da tsadaddiyar wayarsa yana latsawa, shi kuma Obaid ya yi shiru tare da ɗaura hannunsa ɗaya a saman lallausan kumatunsa, da alama duniyar tunani ya afka, ga dukka alamu jikinsa a mace yake, ya yi kwanciyar ruf da ciki ne, while ya saka wani haɗaɗen pillow na ƙayatattcen bedsheets da yake shinfiɗe a saman bed ɗin nasu a kirjinsa, hakan yasa ya ji daɗin yin kwanciyar ruf da cikin. Luxury bedroom kenan, ɗakinsu duniya ne, katafaren bed guda biyu ne a cikin room ɗin, komai na jikin bed's ɗin iri ɗaya ne, komai da yake cikin room ɗin bibbiyu ne kuma iri ɗaya, harta bedsheet iri guda kuyangunsu suke shinfiɗa masu a kullum idan suka zo yi masu gyaran ɗaki, idan muka leƙa cikin toilet ɗinsu ma komai bibbiyu ne, luxury jacuzzinsu guda biyu ne, haɗadɗen glass bathtub showernsu ma guda biyu ne, kai komai nasu dai guda bibbiyu ne iri ɗaya!. Jin shirun ya yi yawa ne yasa Omaid ya ɗago da kallonsa izuwa kan ɗan uwan nasa. Ɗan zaro ido ɗaya ya yi tare da ɗage gera guda. "Blood what are thinking like that naga ka zauna so silent?". Ya faɗa yana ƙoƙarin kashe wayarsa da yake latsawa, domin ya maido da hankalinsa a kan ɗan uwan nasa da kyau, dan ya ji me matsalar. "Pleasure am thinking about this our plan, you know Yah Jaish is around, kuma shi Yah Jaish he has a very very shape brain that within a few minute zai iya kamamu, ni bana son shan wahala fa, kafa san halinsa sarai da mugunta, zai bamu punishment over". Ya yi maganar cikin wata iriyar makirar murya, kamar wadda ya karaya da gaske! Ko da yake dama shi Obaid da sauki a kan Omaid, Omaid shi ne shugaba, bashi da tsoro ko shakka!. Shiry Omaid ya ɗan yi na ƴan sakani kafin ya ce. "Why are you worry your self like that? Ka manta da cewa mun yi shiri mai kyau ne? I think by this time ma yakamata ace komai ta fashe, kayi feel free blood". Ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan yin shiru kamar mai tunanin wani abin, yadda kuka san malamin islamiya ya faɗa jarabawar Ubangiji, irin ya fawwalawa Allah komai nashin nan, to haka Obaid ya yi, ya wani koma kamar Allah sarki bawan Allah. Hannu Omaid ya kai da nufin ya rungoma shoulder ɗinsa, dan yaga kamar ya shiga damuwa, sai dai bai kai ga taɓa shi ba sai ga Obaid ɗin nan ya fashe da wani irin makiri kuma shu'umin dariya kamar wani zararre, kamar ba yanzu yake cikin halin Allah sarki ba. Da kallo Omaid ya bishi da shi, dama yasan da wuya Obaid ya karaya a kan abu, kawai salon sabon iskanci ne suka samo. "Why are you laughing like that?". Cewar Omaid, ya yi maganar kuma yana kare mashi kallo. Cigaba da dariyarsa mai sauti ya yi, tsabar dariyar muguntar ma ta yi yawa har da birgima a saman lumtsumemiyar mattress ɗin nasu, ya wani dafe ciki, da alama wani shaiɗancin ya tuna. "Blood stop this laughing and tell me what are you laughing for?". Miƙewa zaune ya yi tare da dafe cikinsa sosai, tsabar dariya har da hawaye suka cika mashi idanu. Pillow Omaid ya ɗauka ya fara bugunsa da shi yana faɗin. "Please blood stop it now, ni bana son haka fa, ka gaya mun reason na dariyar sai nima na taya ka, amma kana ta yin abu kai kaɗai". Ya yi maganar cikin ƙaguwa na son ya ji me Obaid ɗin yake yi wa dariya haka har da hawaye. Ganin yadda ɗan uwan nasa ya ƙagu da ya ji menene yake yi wa dariyar yasa ya daure ya tsagaita dariyar. Murya cike da shakiyanci ga kuma dariya da yake faman dannewa ya fara magana. "Pleasure ba komai bane ya saka ni dariya face this guy called Yusuf, da wani gemunsa kamar na uncle Rahab, irin shi ustadz like Yah Muzaffar, kaga time da suka fito daga cikin car ɗinsu ina jinsa wai har da cewa baya son ɓata lokaci, da sauri zai sanya daddynsa asaka masu rana shi da Aunty Sarina, har da wani cewa tun da ita ta yi mashi ai ba wani jira da sun ga juna sai aure, wani useless da shi har yana da zaɓi, bari ma dai yanzu zai ji kansa a prison, a nan ne zai ga aure da wuri, hancinsa like Akka nose". (Innalillahi da ji kunsan waɗan nan twins ɗin basa shiri da Akka, wai harda zagin hancinta irin na Yusuf, kai twin's sai shirin Allah 😅 Akka ma ashe tana layin waɗan da basu kauna, yo dama su ina zasu kaunaci mafaɗaci wanda zai takura masu?) Dariya Omaid ya kwashe da shi, cikin dariya yake faɗin. "Not only nose ɗinsa ne like na Akka, even his head ma kato ne like Akka own, ka ji kazami wai zai auri Aunty Sarina, an gaya mashi ita ɗin class ɗinsa ne? Amma gaskiya i pity this guy more, ina ga yau gunduwa gunduwa da shi ma dad zai yi, ai prison ma ya yi mashi kaɗan". Shiru Obaid ya yi kamar mai tunanin wani abin, hannayensa dukka biyu ya kai saman kumatunsa ya tallabosu kamar mai tunanin wani abin, ya ɗan tsuke fuska alamar tausayawa. "Obaid are you okey?". Omaid ya yi maganar tare da ɗan matsowa kusa da shi ya kuma dakatar da dariyar da yake yi. "Pleasure yanzun nan naji tausayin guy ɗin ya shiga rai'na, yana ɗan masu muryar faɗa aji a ƙasar amma zai shiga prison? Gaskiya i pity him, amma dai ba zamu fasa yin abin da muka yi niya ba, gobe ya sake zuwa neman aure a gidan su zakuna bakwai, sai ya sha jibga wajen commander ZAFAR, daga nan dad ya ce a yanke mashi hukuncin zama gidan prison for 10 years". Yana kai karshen maganar kamar abin haɗin baki kamar kuma wasu munafukai suka kwashe da dariya a tare, har da rike ciki suna rungumar juna da hannu ɗaya, ai idan baka san halinsu ba wlh sai su haukataka, yanzu zasu canza fuska kamar masu tausayi da imani, cikin second ɗaya kuma zasu iya sake komawa tantiransu, yanzu dai kunga Obaid wai ya tausayawa Yusuf, amma a take kuma sun sake kwashewa da dariya har da cewa ba zasu fasa abin da suka yi niyya ba, kai Allah ya shirya mana su, goyon kaka ne, kada ku ga laifinsu!. A ɓangaren Gimbiya Sarina kuwa, suna tsaka da cin wannan abincin Yusuf ya matso kusa da ita kamar wanda zai yi mata raɗa a kunne. A hanzarce ta ja baya kaɗan, dan idan baku manta ba na gaya maku ita bata haɗa hanya da maza, bata bin maza, so ko kusa da ita bata yarda namiji ya zo. Kara matsowa kusa da ita Yusuf ɗin ya yi, da mamaki ɗauke a saman fuskarta ta ɗago ta kalle shi. Ta ɗan tsorata da ganin yanayinsa, idanunsa sun sauya sun yi jajir da su, amma bata nuna alamar ta tsorata ba, sai ma ta dake ta ce mashi lafiya kuwa yake matsota haka?. Shi ma abokinsa da mamaki yake binsu da kallo, dan yasan Yusuf dai ba zai matsa kusa da ita haka kawai ba, ba halinsa bane kusantar mata har haka, tare suka yi karatu suka yi komai, tun da yake bai taɓa ganin Yusuf kusa da mace har haka ba, amma da yake ita Sarina ya mace a kanta sosai, kuma abokin nasa ya sani, dan tun kan su zo ya bi ya cika masu kunnuwa da zancenta tare da yabon kyanta, hakan yasa abokin nasa ya yi tunanin ko dukka shaukin soyayya ne take ɗebarsa yasa ya matsa kusa da ita har haka. Kuyangunta da suke tsaitsaye a ɗan gefe ta bayansu ma baki suka saki suna ganin wannan ikon Allah. Ita ma Gimbiya Sarina shiru ta yi tare da zuba mashi idanu tana jiran taga gudun ruwansa, sam bata san komai da yake faruwa ba. Shi kuwa sai kara gaba yake yi, daga matsowa kusa da ita yanzu ya kai ya sa hannu ya rungumota jikinsa. A zabure ta ɗago da kanta daga jikin nasa tare da fara ƙoƙarin ture shi, saboda ita tun ainahi ma ta rai'na class ɗinsa, taɓa ta da ya yin nan sai take ganin ya cuceta ya zubar mata da class, ta fi karfin ya taɓa koda dan yatsarta. Shi kuwa abokinsa bai san time ɗin da ya miƙe tsaye yana kallonsu ba, sunansa ya fara ambata Yusuf, Yusuf ba tare da yasan yana ambatar sunan ba, kawai ruɗewa ce tasa yake kiran sunan. Ina ai Yusuf baya ji baya gani, kara ƙanƙameta sosai ya yi a jikinsa ya fara ƙoƙarin ta yadda zai yi ya rabata da kayan jikinta. Tashin hankali. Zaro idanu kuyangun nata suka yi suna kallon ikon Allah, ga shi su ba halin su yi magana. Abokinsa ma izuwa yanzu ya gama tsorata, bai san lokacin da ya yi kansu yana ƙoƙarin janye Yusuf ɗin ba, ita ma Sarina ƙoƙarin kwace kanta take yi daga gare shi, shi kuwa ƙoƙarin rabata da kayan jikinta kawai yake yi, idanunsa sun rufe baya ji kuma baya gani. Ko da abokin nasa ya zo kama shi ma ina ya kasa, domin Yusuf ɗin yaki bashi wani dama, sai ma hankaɗesa gefe guda da ya yi ya fara ƙoƙarin yin rapen ɗinta da iya karfinsa. Sosai abokinsa ya ruɗe tare da tsorata, ganin abin yake yi tamkar a mafarki, sam bai yarda cewa Yusuf ne yake aikata hakan ba. Da dai gimbiya Sarina taga da gaske yake yi zai yi mata fyaɗe ya keta mata mutunci, sai ta fara ihun neman taimako, ga shi kuma da iya karfinsa ya riketa babu halin ta kwaci kanta, duk ya sauya lokaci guda kamar ba shi ba, sai haɗa uban gumi yake yi, ya zama kamar wani mayunwacin zaki, ga wasu zafafan gumi da suke tsastsafo mashi daga gefe da gefen face ɗinsa, jikinsa har wani tsuma yake yi, burinsa kawai ya rabata da kayan jikinta. Ihu sosai take kurmawa tana neman taimako, kuma da iya gaskiyarta take yin wannan ihun, har ga Allah bata yi excepting haka daga gare shi ba, ganin ya yi shigar mutunci yasa ta yi tunanin yana da mutum koma yaya take, ashe ba haka bane. Abokinsa ya kasa iya kwatarta daga hannunsa, domin kuwa Yusuf ɗin ya saka dukka karfinsa ne a kanta. Ganin hakan yasa kuyangunta suka yi waje da gudu dan su je su sanar da family ga abin da yake faruwa. A hanya suka ci karo da commander ZAFAR da ya fito daga fada zai je wajen mayaƙa ƴan uwansa, kamar kullum yana shirye cikin kayan yakinsa. Ganin yadda suke a birkice suna gudu yasa ya tambayesu menene yake faruwa?. Ba dan shi ɗin bane da ba zasu saurari kowa ba sai fadan King zasu kai rahoto, amma da yake sun san wanenen Zafar, sai suka dakata daga gudun da suke yi, suna ta aikin mayar da numfashi, da kyar suka iya gaya mashi cewa bakon Gimbiya Sarina ce zai yi mata fyaɗe a cikin parlourn baki. Ai tun basu gama magana ba Zafar ya nufi wajen da sauri, su kuwa suka nufi fada da gudu dan su kai rahoto, duk suna ruɗe, sun ga abin da basu taɓa tunani ba, bako ya zo har cikin gida zai yi wa ƴar gida fyaɗe kuma a cikin parlourn iyayenta? Wannan wani irin abu ne? Lallai akwai kura ba kaɗan ba, za'ayi karamar yaki kuwa yau, King Zuhair da yake sanyawa a dandake gaban masu yi wa mata fyaɗe ne yau za'a zo har cikin gida za'ayi wa ƴar ɗan uwansa fyaɗe? Tab akwai rikici kuwa. Ko da Zafar dattijon arziki ya shigo cikin parlourn ya tararda Yusuf ɗin ya rabata da alkyabbar jikinta yana ƙoƙarin cire mata doguwar rigar tata, sai ihun neman taimako take yi, ga abokinsa ma a kansu yana ƙoƙarin janye Yusuf ɗin daga gareta, sai abin ya yi kama da shi ma abokin yana son ya yi mata fyaɗen ne, dan a yadda yake duke a kansu sai Zafar yaga kamar tare suke ƙoƙarin yi mata fyaɗe shi da Yusuf ɗin, duk sun wargaje kayan abincin da yake waje, sun watsa komai a ƙoƙarin kiciniyar faɗa a tsakanin su ukkun, parlourn ya yi kaca kaca. Cikin tafasar jini Commander Zafar ya ƙariso cikin parlourn, ransa idan ya yi dubu to ya ɓaci, nan take idanunsa suka kaɗa suka yi jajir, wannan ai rai'nin hankali ne ma, ace a samu wasu su iya keta duk wasu zaratar warriors da suke cikin KINGDOM OF POWER su sami damar shigowa wajen ƴar gida kuma har su yi ƙoƙarin yi mata fyaɗe? Lallai ma waɗan nan hukuncin da za'ayi masu karema ba zai shinshina ba, a gaskiya ran commander ya yi muguwar ɓaci, dan ganin rai'nin wayo ma ya yi wa abin. Yana isowa kansu da hannu ɗaya ya sa ya damko wuyar abokin Yusuf da yake ƙoƙarin janye Yusuf ɗin daga kanta. Cikin ɓacin rai Commander ya sanya kafa ɗaya ya take wuyar Yusuf ɗin, sai ga shi ya zube ƙasa wanwar, jinin Commander sai kara tafasa take yi, jikinsa har wani tsuma yake yi, kafarsa dake sanye da waɗan nan shegun takalmar yakin nasu masu kama da takalmar karfe yasa ya take wuyar Yusuf ɗin a kasan, shi kuma abokin nasa ya shakesa da hannu ɗaya. Maza kake ji, ai ba sai an gaya maku waye commander ba, dattijon kirki mai zafin nama haɗe da tafasashiyar jini da ya shafe sama da shekaru 20 yana bawa zaratan mayaƙa daban daban horo, namijin gaske jarumin jarumai kuke ji!. A guje Gimbiya Sarina ta samu ta miƙe tsaye zata nufi waje, ƴar kaniya idanu sun rena fata, ta yi wani narai narai, duk ta yi laushi. Bata kai ga fita cikin parlourn ba zaratan horarrun mayaka masu jini a jika da lafiya har guda goma ne suka shigo cikin parlourn, kowannensu ka gansa sai hantar cikinka ta kaɗa, a haka ma fa fuskokinsu na'a cikin hular kayan yakinsu, ba'a ganin ainahin fusatatciyar face ɗinsu, amma yadda kasan wasu mutuwa idan sun doso waje haka ake tsoronsu, saboda cikar halittarsu ga kwarjinin masifa mai razanarwa, sun sha horo wajen commander ai, dole su zama kamar wasu bujuman zakuna. Daga King har uncle Abbas sai da suka baro fada domin su zo su ga abin da yake faruwa, a tare suka zo da waɗan nan jiga jigan zataran warriors ɗin, hakan yasa Sarina tana ganinsu ta tafi wajensu da gudun gaske tana kuka hawaye bibbiyu. Daga King har uncle Abbas rige rigen tarbanta suka yi. Jikin King ta faɗa tare da kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, daga jin yadda take wannan kuka zaka fahimci da iya gaskiyar take kukan, ba wai na munafurci bane, ba'a taɓa yin yunƙurin yi mata fyaɗe ba a rayuwarta sai yau, abin ya yi mugun tsoratata ba kaɗan ba, haƙiƙa kuma ita bata san me su twin's suka shirya ba, dama ba gaya mata suke yi ba, shirya shirinsu kawai suke yi, sai dai ta gani a aikace, sau da dama idan zasu kori samarinta bata sanin plan ɗinsu, idan ta gaya masu bata son saurayin shikenan sai ta rabu da su su yi nasu shirin, hakan yasa bata yi excepting Yusuf zai yi ƙoƙarin yi mata fyaɗe ba, ƴar kaniya yau idanu sun rena fata, taga mutuwa kusa, ai badan kuyangun nan nata da take renawa ba da ta yabawa aya zaƙinta. Kafin su King su yi wa Zafar magana ma har Yusuf da abokinsa sun sume a hannunsa, shakar da ya yi wa abokin Yusuf ɗin ne yasa ya sume, shi kuma Yusuf taka mashi wuya da ya yi ne yasa shi ma ya sume, dan basu samu numfashin da zasu shaƙa ba, dole su suna, Allah Sarki abokin Yusuf da shi kwatarta ma ya je yi, wannan shi ne ya taka sahun ɓarawo, a wannan hali da ake ciki kuwa mai kwatarsu sai Allah, ko ubansu ne shugaban kasa yadda aka kamasu da hujjarnan wlh basu isa a barsu haka kawai ba, tab King Zuhair fa, lallai za'ayi yaki kuwa ba kaɗan ba, su Yusuf sai dai mu ce Allah ya kwaceku, dan sai dai ayi yakin duniya amma King ba zai barsu ba, koma ƴan uban waye!. Uncle Abbas ne ya ce da Commander Zafar ya barsu haka nan, a kwashesu a zubasu a prison na masarautar zuwa anjuma idan komai ya lafa sai asan abin yi. Cikin ɓacin rai King ya ce ina babu wannan magana ta a kai su prison, yanzu zasu karɓi hukunci, kun san halin King bashi barin ko ta kwana, jinin Modarawa ai basu da hakuri malam, su sha yanzu magani yanzu ne, ba ɗaga kafa, dama ga King da tafasasshen jini ai su Yusuf sai ta Allah kawai. "Yaya please ka bari tukun nan zuwa anjuma mu nutsu sai a yanke masu hukuncin da ta dace da su". Cewar uncle Abbas. Cikin nuna isa da izza rai a matuƙar ɓace King ya ce. "Malam liman ka karanto masu doka irinta addinin musulunci a kan wanda ya yi yunƙurin yi wa yarinya fyaɗe a cikin gidan iyayenta, Commander ka zartar masu da wannan hukunci ba tare da ɓata lokaci ba, Abbas na gama magana bana son sake jin wani abin kuma!". Yana kai karshen maganar ya juya rungume da Sarina dake ta faman kuka a jikinsa, ta tsorata sosai, kuka take yi ba kakkautawa, yadda take kukan nan sai ta baka tausayi ƴar kaniya. Kai tsaye part ɗinsa King ya wuce da ita dan ya rarrasheta. Tashin hankali, ga shi dai su Yusuf sun suma bare a iya fahimtar ko wani abin Yusuf ɗin ya sha, kuma kunsan idan ya farfaɗo a yanzu dai koma me ya sha zata sake shi, da bai suma bane to ko King zai iya fahimtar ba lafiya yake ba, amma yanzu babu wanda zai fahimci hakan, bugu da ƙari ga abokinsa da ake ganin cewa a tare suka yi ƙoƙarin yi mata fyaɗen, kunga kuwa hakan ma hujja ce da zata kara sanyawa ayi masu hukunci ba tare da anyi tunanin ko dai ba lafiya yake ba, a gaskiya dai Yusuf bashi da hanyar da zai wanke kansa a cikin wannan al'amari, sannan bugu da kari duk abin da ya ci a wannan waje tare da Sarina da abokin nasa suka ci, to shi ta yaya wannan abin ya faru da shi shi kaɗai? Da alama kuma dole wani abin aka bashi ya ci or ya sha, dan farkon shigowarsa ai ba haka yake ba, to idan wani abin aka bashi ta yaya aka yi hakan kenan? Ko dai dama ya zo da ɓoyayyar manufa ce? Anya kuwa hakan zata faru? KINGDOM OF POWER fa, masarautar da jin sunanta ma kawai yake sanya hantar manya ta kaɗa bare kananan kwarin irin su Yusuf ne zasu yi tunanin shiga har su yi ƙoƙarin yiwa ɗaya daga cikin gimbiyoyi masarautar fyaɗe? Masarautar da mayakanta suke tamkar ajali. Akwai cakwakiya gaskiya, ni dai bari na koma gidansu Khadija mu ga wani hali ake ciki, wata kila kafin mu dawo wasu abubuwa zasu ɗan yi sauki ta nan, amma dai a gaskiya twin's shegun kaya ne na bugawa a jarida, dan ni su nake zargi, suna shirya plan ne ta yadda duk bala'in nacinka ba zaka taɓa gane cewa su suka shirya shi ba, they're very very smart, suna da shape barin. Amma kuma anya zasu iya shirya wannan babban al'amari har haka kuwa? (Allah yasa akwai Camera a cikin parlourn 😅 dan a wanke abokin Yusuf 😌 amma ko akwai Camera shi dai Yusuf ba zai wanku ba gaskiya, dan ya riga da ya zurma, su twin's ma ko akwai camera ba zasu kamu ba, dan ai basu a waje kuma basu leƙo ba, ita ma Sarina ba zata kamu ba, dan ta nunawa Yusuf so da kulawa, babu wanda zai yi tunanin bata son shi dan haka zata iya yi mashi sharri, ta nuna so a fili, dan haka ta wanke kanta, gaskiya idan ka shiga hannun Team ɗinsu twins kagama yawo wlh💔) 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ GIDANSU KHADIJAH💔😥 Izuwa yanzu komai ya kara lalacewa maman Zainab, karin auren baban Zainab babu fashi, haka zalika auren Haidar da Khadija babu fashi, damuwa sun taru sun yi mata yawa, tsananin damuwa yasa ta manta da Allah take tunanin bata da mafita da ya wuce ta bi shawarar Aunty Hauwa, a haukarta gani take yi shi ne kawai the only way da ya rage mata domin tsira, ga shi kuma kamar daɗa hura wutar gaba a tsakaninta da sirikan nata ake yi, duniya ta yi mata zafi, ta manta da cewa duk wani mumuni baya rabuwa da jarabawa ta Ubangiji, idan kaga Allah bai jarrabeka da wata musifa bama to wlh ka binciki imaninka akwai tankarɗa, duk wanda Allah yake so da rahma to yakan zarabce shi, dan haka kada kuga kun shiga wata jarabawa ku yi tunanin ko Allah baya son ku ne, ko kuma ma ku manta da Allah ku fara tunanin wani kato, Allah yana jarraba bayinsa ne domin yaga shin a kowani hali suna tare da shi ne ko kuma dai yaya? To dan haka shawara shi ne kuyi kokari ko a wani hali kuka tsinci kanku ku kasance a tare da Ubangiji, kada ku taɓa yarda ku yi tunanin wasu. Ba tare da ta yi tunanin me zai je ya zo ba, bata yi tunanin ta gayawa mahaifiyarta halin da ake ciki ba, kawai ta kira Aunty Hauwa a waya a kan ta zo su je wajen malamin nan, dan gaskiya ta rasa mafita, zuciyarta na gab da tarwatsewa, gidan farinciki yanzu yana shirin zama gidan ƙunci koma ace ya zama. Baban Zainab yana ta ƙoƙarin yaga ya lallaɓa mamarsa ta janye daga maganar karin aurensa, amma ta tirje a kan lallai sai ya kara, ya ce mata in dai matsalar rashin haihuwar Maman Zainab ne damuwarsu da har yasa suka ce ya kara aure, to su yi hakuri In Sha Allah nan bada jimawa ba zata samu ciki ta haihu komai ya wuce a dawo kamar da. Ina ai wannan tsohuwa taki yarda, ta ce ita yanzu bata damu ba ko maman Zainab zata haifo yara ɗari ne wlh sai ya kara aure gara ma ya ji da kyau, ta faɗa da babban murya kuma umarnin take bashi ba shawara ba. Bashi da zaɓin da ya wuce ya amsa da to, amma yana cikin wani hali, duk ta in da ya juya babu daɗi, ga maman Zainab ta rike mashi wuta a gida, bata kula shi, za dai ta yi mashi duk abin da ya dace ta yi mashi, zata sauke nauyin da yake a kanta, amma ko sannu bata ce mashi idan ya dawo, bata yi mashi magana, wasan ɓuya ma take yi da shi, idan ta ji ya dawo zata shiga ɗaki ta rufe kofarta, ba zata fito ba kuma har sai ta ji ya fita, ya yi magiyar duniyar nan taki sauraronsa, yadda kuka san shi ya yi mata laifi, bawan Allah bata san shi ma yana tsaka mai wuya ba. A ɓangaren Haidar kuwa, sai shirye shiryen biki yake yi abinsa, duk ya sanar da mahaukan abokansa irinsa marasa kan gado, tsabar mugunta irin na Mammarsa ma har da wani cewa ai ba sai ya yi wa Khadijah ɗin kayan lefe ba, ai kanwarsa ce, kuma koba komai ya bautawa babanta a kasuwa, dan haka babanta ne ma yakamata ya yi komai na bikin, domin tun Haidar yana ƙarami yana wahala a shagonsa, dan haka lokacin da yakamata abiyasa ya yi, tsabar rashin imani irin na maman Haidar ɗin, yadda kuka san ba uwa ɗaya take da baban Zainab ɗin ba, yanzu so take baban Zainab ɗin ya yi wa Khadijah kayan ɗaki kuma ya dawo ya haɗawa Haidar lefen da zai kawowa Khadija, sannan ga nashi karin aure, bugu da kari ga shi hajiyarsa ta ce a sabon gidansu za'a kai amarya, dan haka dole ya ƙarisa gininsa cikin sauri, Allah ma yasa abu kaɗan ne ya rage a kammala ginin, amma duk da haka akwai cin kuɗi, duk basu ga hakan ba su kam, dan rashin adalci irin nasu. A yau ne Maman Zainab da Aunty Hauwa suka shirya zuwa wajen malamin Aunty Hauwa, zasu je ne kuma da nufi ya yi masu aiki guda uku, na farko hana karin auren baban Zainab, na biyu hana auren Haidar da Khadija, na uku a saka dangin baban Zainab su sota sosai sosai kamar su haɗiyeta, wannan shi ne aikin da za'ayi masu. Yau dai Maman Zainab ta ɗan saki fuska kaɗan, dan tana ganin kamar da sun je wajen malamin komai zai zama daidai cikin lokaci ƙaƙani kamar yadda Aunty Hauwa take ta faɗa mata, hakan yasa ta ɗan saki fuska yau. Su Khadijah dai izuwa yanzu sun gama fahimtar komai da yake faruwa a cikin gidan nasu, da yake sun sami tarbiya mai kyan gaske, sai suka fawwalawa Allah komai nasu, suka dukufa babu dare babu rana wajen yin addu'a, kuma kawunsu Sadiq kullum idan suka kai mashi kukan halin da suke ciki yana kwantar masu da hankali tare da kara masu kwarin gwiwa a kan su miƙawa Allah al'amuransu komai zai warware. Hakan yasa suke samun sassauci a kan halin da suke a ciki ɗin, Sadiq bawan Allah ne, ya yi ƙoƙarin nusar da Maman Zainab da ta yi hakuri ta fawwalawa Allah komai zai yi mata sakayya a lokacin da bata zata ba, amma ina kishi da takaici ya rufe mata idanu, bata ji bata gani, har saɓani suka samu da Sadiq ɗin a kan maganar, ba dan Sadiq yana da hankali ba kuma yana taimakawa baban Zainab ba da ya bar mata gidanta, dan ba ƙaramin zaginsa ta yi a kan case ɗin ba, ta ce babu ruwansa da ita, amma ya hakura saboda yana taimakawa baban Zainab, kuma ko ba komai baban Zainab ya yi mashi abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba, shi ya ɗauki nauyin karatunsa tun daga nursery har izuwa master da yake yanzu, so koda baban Zainab ya saki maman Zainab shi gaskiya ba zai iya juyawa baban Zainab baya ba, ya yi mashi abin da babu wanda ya yi mashi shi a duniya, domin ilimi shi ne mutun, ya tsaya mashi ya yi karatu kuma boko da islamiya dukka, hakan yasa ya hakura ya cigaba da zama a gidan. Misalin karfe 9 na safe bayansu Khadija sun tafi school, baban Zainab ya fita kasuwa, Sadiq duk basu nan suna kasuwa, sai ga Aunty Hauwa ta zo domin su je wajen wannan malami na kan dutse da ta faɗa. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) https://chat.whatsapp.com/LAEmIGs3z0KBdL3NQsRixW 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 29/7/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________23🔥 Misalin karfe 9 na safe bayansu Khadija sun tafi school, baban Zainab ya fita kasuwa, Sadiq duk basu nan suna kasuwa, sai ga Aunty Hauwa ta zo domin su je wajen wannan malami na kan dutse da ta faɗa. Maman Zainab bata gaya wa baban Zainab zata fita ba, kawai ta biyewa Aunty Hauwa ta saɓi mayafi suka fita. Ya Allah ka rabamu da makiran kawaye munafukai, rimi rimi zaka yi wa ƴarka tarbiya na tsawon lokaci, amma wata shegiya cikin ƙanƙanin lokaci zata zugata ta juyar mata da tunani, sai wadda Allah ya tsare ne kawai bata afkawa zugin ƙawaye, to a koma ina Allah ka haɗamu da mutane na Allah masu gaskiya da sommu da gaskiya!. Haka dai suka kama hanyarsu suka tafi, sai kara zugata Aunty Hauwa take yi, abin ku da shaiɗan, sai buga mata gangan yake yi abinsa, tana ganin kamar suna zuwa shikenan matsalarta ta warware, ta manta da cewa idan Allah bai kaddara abuba to wlh idan duniya dukka gatanka ne, in zasu taru duk duniya su baka wannan abu karɓama ba zaka iya yinsa ba, saboda Allah bai rubuto maka a kaddararka ba, amma ita ina idanunta sun rufe, kishi ga kuma takaicin da Maman Haidar take kunsa mata nan, ga takaicin auren Khadija da Haidar duk sai ya haɗu ya rufe mata idanu ruf, bata ji kuma bata gani!. Allah dai ya kyauta. To kafin su dawo daga wajen bokan nasu bari mu fara ƙutsawa cikin ainahin labarinmu, bari mu taɓo wani ɓangare kaɗan mu gani, dan ina son mu nemo in da RAWANIN ZALINCI yake, saboda har yanzu fa bamu ko alamun samo shi ba! A gefe gefe muke!. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ Bari mu leƙa UAE wato United Arab Emirates, a cikin UAE ma bari mu leƙa Dubai, a cikin Dubai ma bari mu leƙa prison na Al Aweer Juvenile AAJ, wato prison na yara under 18 years kenan. AAJ Prison ne kamar yadda kuka san kowani prison na yara waɗan da suka aikata laifi kuma ba su kai shekarun da za'a yanke masu hukunci ba, so ana ajiye su a AAJ ɗin zuwa su kai munzalin karɓar hukunci, ba kamar prison na manya yake ba, nasu yafi na manya kyau, tsaro, kula da lafiyarsu, lafiyayyen abinci, ɗakin kwana mai kyau, masu kula da lafiyarsu suna ƙoƙari sosai, da dai sauransu, ana basu kula sosai ba kamar manya ba, domin kunga su yara ne, wasu ma kaddara ce take afka masu su yi laifi ba'a son ransu ba, amma kowa yasan da cewa dokar kasar Dubai tana da tsauri sosai, musamman ma da ya kasance a yanzu jinin modarawa wato su Akka su ne suke rike da ƙasar, shi ne yasa dokar ta kara sauri over, dan kowa yasan jininsu basu da wasa kuma basa ɗaukar wasa, bugu da ƙari komai da zasu yi dai'dai da faɗar Allah suke yi! A ko'ina da akwai ɓata gari, akwai kuma na kirki, idan suka yanke hukunci fa to ba lallai ne su sake sauraran wani excuse ɗin ba kuma, sai dai idan ta ƙarƙashin kasa za'a bi kamar dai yadda aka saba idan wani ɗan masu hali ya yi wani abin, fatan kun gane?. Ɗaki ne na yara mai kyau, gadaje irin na sama da kasan nan har gado shidda ne a ɗakin, sama da kasa sama da kasa guda uku kenan shi ne zai kama gado shidda, mattress da suke a saman kadajen mattress ne masu kyau ga kuma laushi, harta bedsheet ɗinsu ma mai kyau ne, tiles mai kyau da tsada ne a kasar floor ɗin ɗakin, suna da Ac kamar ba prison ba, ga bargon da suke rufuwa a lokacin da sanyi ya sauko masu ma mai kyau sosai da shi, pillows ɗinsu duk masu kyau ne, dama na gaya maku su ana kula da su sosai fiye da manya, wajen cin abincinsu a cikin prison ɗin, in da kowa yake fitowa su haɗu su ci abinci ma an kawata shi da dinings tables daban daban sama da guda ashirin, kuma tables ne masu girma wanda kowanne yana da 24 to 32 chairs, da yake katafaren prison ne hakan yasa aka zuba tables ɗin dayawa a wajen cin abincinsu. Sai hada hada yara suke yi, suna ta kai komo kamar gida, wasu suna buga kwallo a filin ball da yake a cikin prison ɗin, dan harda fillin ball ne da su. Part na maza daban na mata ma daban, kun san dama ba'a haɗasu waje guda!. Ƴan matasan ƴan'mata da ba za su wuci 13 to 15 years bane su huɗu a cikin wannan ɗakin, da alama ƴan mata biyun cikon gadaje shiddan nan sun fita waje wasa, abinku da yara. Waɗan nan ƴan'matan uku daga cikinsu sai kai komo suke yi tsakanin toilet da wajen gadajensu, kowacce da abin da take yi, ɗaya tana sanya da blue AAJ uniform a jikinta, ɗaya kuma tana ƙoƙarin shinfiɗa bed ɗinta, ɗayar kuma tana ƙoƙarin naɗe bargonta, da alama yanzu suka tashi daga barci, su dai babu takura babu komai, kawai za'a tsaresu ne sai sun girma sun kai munzali su girbi abin da suka shuka. Dukka waɗan nan ƴan'mata uku dake a cikin ɗakin larabawa ne saɓanin ɗaya da take zaune a saman bed ɗinta ta buga uban tagumi, da alama tana cikin mawuyacin hali ne, saboda yadda ta yi wannan uban tagumi ya nuna tana a cikin damuwa sosai, ba balarabiya bace ba, saboda yadda take bakar fata a cikinsu, sai dai kuma ta fisu kyau sosai, kyakkyawar gaske ce na kin ƙarawa, chocolate color ce dangin Africa, kalar fatarta kala ce mai tsada a duniya wanda yanzu samunsa yake wuya, tana da dogon hanci har baka, ga ɗan madaidaicin bakinta da ya yi ɗas a saman ɓul ɓul ɗin kumatunta, idanunta farare tas dara dara, kyakkyawa ce ajin farko, face nata ɗan dai'dai, bata da wani ƙiba, ƴar dai'dai da ita, ba zata wuci 15 years ba a duniya, tana sanye da kayan AAJ ɗin wadda kowasu prisoners suke sanyawa, kanta babu ɗan'kwali, tana da yelwar bakin gashi mai tsawo, gashin nata a nannaɗe yake irin kamar rubber hair ɗin nan, amma gashin nata akwai tsawo da kyau sosai, duk da ya kasance tana zaune ne hakan ba zai sanya ka kasa iya gane cewa dirarriyar mace bace, tana da dirarren jiki mai kyau wadda kamar ita ta yi wa kanta, coca cola shape ne da ita sosai, kirjin nan nata a cike suke fam kamar ba ƴar 15 years ba, kamar mai 18 years haka, ta buga uban tagumi kamar wadda aka saukowa da wahayin yinsa, her face looks she's so silent, innocent face ke gareta. Wata yarinya wadda a kallah zata iya kai 17 years ce ta shigo cikin room ɗin, fara ce tas balarabiya, kyakkyawa ce sosai, amma bata kai wannan chocolate color ɗin yarinyar kyau ba, ita ma kanta babu ɗan'kwali, ta ɗaure gashin kanta two step, ta saki jelar gashin nata ɗaya ta bayanta, ɗaya kuma ta saman shoulder ɗinta ya yo gaba, kyakkyawa ce sosai ita ma, ga dara dara idanu farare tas, tana da sura mai kyan gaske. A kusa da wannan chocolate color yarinya ta zo ta zauna a saman bed ɗinta kenan. Cikin harshen larabci mai nuna cewa kwararriya ce a iya larabci ta ce "أنت لم تأخذ حماما Leesharh? (Leesharh bakiyi wanka ba)?" Ta yi maganar tana taɓa shoulder ɗin Leesharh ɗin. Ƴar firgita ta ɗan yi alamar ta ɗan razana, dan ta afka duniyar tunani ne bata ji shigowar yarinyar ba, shi ne yasa da ta taɓata ta firgita. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa, cikin muryarta da kwata kwata baya fita, tamkar wata bebiya ko mai koyar yin magana, idan ba su da suka saba da ita ba wani daga waje ba zai iya gane me take faɗa ba, sam muryar tata bata fita kamar irin wadda mura ta shaken sosai ɗin nan, ga in'ina a cikin maganarta abin gwanin ban tausayi. "اليوم أتذكر والدتي، ولهذا السبب مات جسدي كله، ولم أستطع الاستحمام (Yau na tuna mahaifiyata, shiyasa duk jikina ya mutu, kuma na kasa yin wanka Jasrah)" Ta bata amsa cikin harshen larabci ita ma. Ɗaya daga cikin yaran nan ne da suke a cikin ɗakin before shigowar Jasrah wadda take shinfiɗa bed ɗinta ɗazun ta ce. "To ba kin kashe mahaifiyar taki ba? Menene kuma abin wani sake yin tunata?". Ita ma cikin harshen larabci ta yi maganar, da alamu larabci kawai suke ji wata kila da turanci!. "Aaradiya wai meyasa kuke yin haka ne?". Cewar Jasrah dake dafe da shoulder ɗin Leesharh. Wani kallon banza wadda aka kira da Aaradiyar ta wurga masu daga Leesharh har Jasrar, sannan ta sa kai ta fice waje abinta ba tare da ta sake yin magana ba, dan ta gama gyaran gadon nata dama. "Leesharh ki yi hakuri, ki je ki yi wanka ki zo mu je mu ci abinci". Cewar Jasrah. Leesharh kenan wadda rahotonta yake a rubuce cewa ta kashe mahaifiyarta da hannunta a cikin kitchen suna tsaka da yin aikin girki ta caka mata wuƙa a ciki, nasan dai dukkanku zaku sha mamakin yadda aka yi yarinya kyakkyawa karama kamar wannan ta kashe mahaifiyarta har a kawota prison ɗin yara, na san za ku so jin ainahin labarinta da yadda aka yi ta kashe mahaifiyarta da kuma yadda aka yi ta zo gidan AAJ, meyasa zata kashe mahaifiyarta? Uwa fa? Hmmmmm mu je dai zuwa. "Jasrah bana jin zan iya cin komai yau, ki je ki ci abincinki, ni ki barni kawai". Ta yi maganar idanuwanta suna kawo ruwa, alamar dai da gaske yau bata cikin yanayi mai daɗi, ko dai tana nadama ko makamancin hakan. "Amma Leesharh yau tsawon shekara guda kenan tun shigowarki gidan AAJ kullun ina baki shawara da ki cire wannan tunanin a cikin zuciyarki, ki hakura ki rungumi kaddararki, ki manta da kowa da komai ki sake ki yi rayuwa kamar mu, ni dai kina gani na barwa Allah komai, Allah ya sani ni ba da gangan na kashe Ameer ba, amma saboda bani da hujja kuma iyayena basu da karfi kinga an kawoni nan wajen an tsare, kuma ni na hakura na rungumi kaddarata, a kullum ina tunanin iyayena sosai, amma bana bari hakan ya hanani farincikina, nasan akwai ranar sakayya, kullum da tunanin ƙanwata Alveena nake kwana nake tashi, amma ya zan yi to? An rigada an rabamu, sai idan Allah ya ƙaddara muna da rabon haɗuwa a gaba, idan kuma lokacin yanke mana hukunci ya cika ba'a gane gaskiya ba aka kashemu shikenan akwai lahira ai, akwai ranar da babu wanda ya isa ya yi karya ko ya cuci wani, rana ce ta kwatarwa waɗan da aka cuta hakkinsu ba tare da zalinci ko son kai ba!". Ta kai karshen maganar tana goge hawayen da suka fara zuba mata a saman fuskarta, gwanin ban tausayi. Zuba mata idanu kawai Leesharh ta yi tana kallon yadda take sharar kwallah, hawaye wani na bin wani kamar famfo, abin tausayi, wlh ba da gangan ta kashe shi ba, saboda wani saɓani da aka samu ne, kaddara ce ta faɗo mata kawai, dan iyayenta talakawa ne kuma yasa ba'ayi wani shari'a sosai ba, yanzu shekarunta uku a cikin wannan prison ɗin, tun tana da 14 years aka kawota, yanzu kuma tana da 17 years, saura mata shekara ɗaya ta cika 18 years a duniya shikenan sai a yanke mata hukunci wadda dani da ku dukka munsan dai wanda ya yi kisan kai hukuncin kisa shi ma ake yanke mashi, wannan ita ce dokar kasar Dubai, a kanta kuma suke tafiya, doka ce ta addinin Musulunci, duk wanda ya kashe rai shi ma a kashe shi! Dan rai bata fi rai ba!. Ainahin Jasrah iyayenta larabawan ƙasar Turkey ne, zama ne ya kawosu kasar Dubai, wahalar rayuwa yasa suka baro Turkey suka zo nan Dubai neman abin da za su rufawa kansu asiri, kasancewar Jasrah ita ce babba sai take zuwa gidajen masu kuɗi tana yi masu aiki suna biyanta, a lokacin ma kwata kwata bata wuci 14 years ba, tana dai yi masu ɗan aikin da karfinta zai iya, to ita yarinya ce mai hakuri sosai, ga sanyin hali da tausayi, kanwarta ɗaya Alveena, su biyu iyayensu suka haifa, basu zuwa makarantar boko saboda halin rashi da mahaifinsu yake fama da shi, amma suna karatun islamiya sosai a wajen iyayen nasu, da yake mahaifinsu babban malami ne, akwai ilimin addini, so sun sami ilimin addini sosai. A haka dai kullun tana zuwa wani babban gida na masu kuɗi da yake a unguwar tasu tana aiki, matar gidan sam bata kaunar Jasrah ɗin, amma mijinta kuma yana son yarinyar, saboda shiga ranta, tana da hankali sosai, suna da yara maza biyu da mace ɗaya, mazan manya ne, babban zai kai 20 years, sai mai bi mashi Ameer wadda aka ce ta kashe kenan, shi kuma yana da 17 years kamar dai ita a yanzu, macen kuma tana da shekaru 7, kullum idan ta je ta yi masu aikin goge gogen ma idan babansu baya gida basu bata komai, dan maman bata kaunarta, amma idan baban yana nan zai bata abinci dayawa ta tafi da shi gida su ci da iyayenta da kanwarta Alveena, zai kuma bata kuɗi. Wata rana idan baban ma baya nan korinta mamar take yi idan ta je yin wannan aiki, amma da yake tana samun abincin da suke ci da iyayenta da kanwarta, tana kuma samun kuɗi wajen baban sai yasa bata gajiya da zuwa gidan duk walaƙancin da suke yi mata, tana hakura ta je, damo ce sarkin hakuri. A haka suke rayuwa a takaice kwance tashi watarana suka sami saɓani da wannan Ameer ɗin, ya so ya lalata mata rayuwa ne taki yarda, duk da tana karama amma ta samu ilimin addini daga iyayenta, ta san illar yin hakan, shi kuwa a lokacin ya doshi 18 years yana ji da tashen balaga, kansa na rawa sosai yaron, ya fi yayansa ma bushewar idanu, da alama kuma yana yawan kallon fina finan batsa, hakan yasa ya yi ƙoƙarin lalata mata rayuwa. Da taki yarda ne ya ɗauki karan tsana ya ɗaura mata, kullum idan ta zo tana aikin goge gogenta in dai zai gifta ta kusa da ita sai ya kai mata mari a mazaunanta, kamar shi ya halitta mata su, tun tana kuka har ta saba. Wata rana ta ce ba zata sake zuwa gidan ba, dan ta gaji da azabtar da ita da Ameer ɗin yake yi, ga shegen sakata aiki da yake yi, ya yi ta dukanta kuma, wani lokaci a gaban mamarsa yake dukan nata, amma uwar bata cewa komai saboda zalinci, sai dai ta kawar da kai, dama na gaya maku uwar bata da hali mai kyau. Sai dai ko da ta ce ba zata sake zuwa gidan ba tana hakura ta sake zuwa, saboda abincin da take samo masu su ci da iyayenta, mahaifinsu ya manyanta sosai, baya iya yin aikin karfi, amma yana iyaka bakin ƙoƙarinsa!. Wata rana mamarsa tana ƙasa ita kuma Jasrah tana sama tana goge goge, sai ya ce ta je ɗakinsa ta gyara mashi, kamar zata ce ba zata je ba, amma saboda tsoron mamar tasa yasa ta je ta fara gyara masa. A nan ya iskota tana faman gyara mashi bed ɗinsa, ai kuwa yana zuwa ya turata saman bed ɗin tare da ƙoƙarin yi mata fyaɗe ta karfin tsiya, tana ƙoƙarin yin ihu ne ya yi saurin toshe mata baki da hannunsa. Hakan yasa ta fara ƙoƙarin kwatar kanta ta karfin tsiya a in da suka fara kokawa, ya sanya karfi zai yi mata fyaɗe ita kuma ta sanya karfi zata kwaci kanta. Da yake mummunar kaddara ta gifta a tsakani sai ta sanya hannu tana laluɓar abin da zata buga mashi, cikin ikon Allah ta ɗauko kwalbar mardbe da ya yi amfani da shi ya barshi a saman bedside drawer ba'a fitar ba, ai kuwa yana danne da ita yana ƙoƙarin cire mata riga, bata yi wata wata ba ta buga mashi kwalbar a kansa, hakan yasa ya tashi daga kanta a haukace, saboda azaban zafi da ta ziyarce shi. Abinku da yarinta, zuciyar kuruciya tana ɗebansa, cikin fusata ya kwace kwalbar daga hannunta tare da fasata a ƙasa, tana ƙoƙarin guduwa ta fita daga cikin ɗakin ya rikota da nufin ya kasheta da kwalbar, dan yana ɗaukarta a ƙasƙantacciyar ƴar aiki mara galihu, koma me ai baiwarsu ce ita ɗin, ko ya kwasheta ya kashe banza a banza. Wage baki ta yi a in da ta zunduma ihu da karfi, a zuciye ya kai mata duka a bakin nata da ta yi ihun, ba shi ta haɗiye ihun da take ƙoƙarin kurmawa a karo na biyu, gadan gadan ya yi niyar kasheta, sai dai cikin ikon Allah ta samu ta ɗauko ɗaya daga cikin kwalaben da suka yi saura a kasan wanda ya fasa, a ƙoƙarin ta yi mashi barazanar kada ya kara matsowa kusa da ita, sai kuma mummunar kaddara ta gifta ta caka mashi wannan kwalbar a cikinsa, wannan ita ce sanadiyyar mutuwarsa kenan. Wannan ihu da ta yi na farko yayansa ya ji ihun nata, hakan yasa ya nufo ɗakin, ya shigo kuma dai'dai lokacin da ta caki Ameer ɗin da kwalbar har ya faɗi a saman bed ɗinsa da yake yana a kusa da bed ɗin dama, hakan yasa yayan ma ya kurma ihu mai sauti wanda ya ja hankali kowa da yake gidan. A guje suka nufo ɗakin, kafin ma ayi wani yunƙuri Ameer dai ya ce ga garinku, rai ta yi halinta, wannan shi ne abin da ya faru, ko da aka kira jami'ai sai cewa mamansa ta yi ai daba Jasrah bata kaunar Ameer, kuma ta taɓa cewa sai ta kasheshi a baya lokacin da ya mareta, to shi ne yanzu ta bishi har cikin ɗakinsa yana kwance ta kashe shi. Da jami'an suka tambayi cewa ina shaidar maman na cewa Jasrah ta taɓa yin ikirarin zata kashe Ameer, sai ta gabatar da shaida na farko yayan Ameer ɗin, da kuma sauran ƴan aikinta wanda dan dole suka amsa da anyi hakan, dan kawai basu da zaɓi da ya wuce hakan in dai suna son cigaba da rayuwa su kuma cigaba da yin aiki, haka suka bi bayan karya suka rufawa Ameer asiri na cewa shi yake neman lalata Jasrah, suka ɓoye wannan magana, kuma kowa na gidan yasan da cewa tabbas Ameer shi yake neman Jasrah da faɗa, saboda wani lokaci idan tana tsaka da yin aiki tare da sauran ma'aikatan gidan ya zo wucewa zai kai mata mari a mazaunanta a gaban kowa, kuma ya wuce ya mari banza, so sun san komai, amma basu da zaɓin da ya wuce su amsa maganar maman Ameer ɗin a matsayin gaskiya. Wasu matan wlh munafukai ne na karshe, Maman Ameer dai da kanta ta goge ɗaukar CCTV camerar da yake parlourn wanda ya ɗauki video Ameer ɗin lokacin da yake cewa Jasrah ta je ta gyara mashi ɗaki, sai ta goge wannan ɗauka dan ta kara tabbatar wa da jami'ai cewa tabbas haka kawai Jasrah ta shiga ɗakin Ameer ta kashe shi saboda ƴar tsama da ta taɓa shiga tsakaninsu har ya mareta, ko da aka tambayeta wace tsama ce, sai ta ce ai Jasrah ɗin ce ta zubawa Ameer ɗin tea mai zafi a jiki bisa rashin sani, shi ne shi kuma ya fusata ya mareta, shikenan ta ce ba zata barshi ba. Haka dai suka shirya karya da gaskiya tare da shirya hujjojin da dole sai ka yarda da maganar tasu, wannan dalilin yasa aka kai Jasrah kotu ba tare da ɓata lokaci ba aka yanke mata hukunci kisa daga nan sai gidan AAJ za'a tsareta zuwa lokacin da zata kai munzalin karɓar hukunci kisa kamar yadda ta kashe Ameer ɗin. Iyayenta sun yi kuka ne har mahaifinta ya kwanta jinya na tsawon lokaci, haka kanwarta Alveena, mahaifiyarsu har yau bata dai'na kuka ba, suna zuwa AAJ ɗin ziyartar Jasrah ɗin, amma ba koda yaushe ba, saboda basu son zuwa su ganta a cikin wani hali, idan suka koma gida a ranar da suka ziyarceta kwana suke yi basu yi barci ba bayin Allah. WANNAN SHI NE LABARIN SUHANA DA KUMA DALILIN ZUWANTA AAJ, BA SAI NA TSAYA YIN DOGON BAYANI BA NASAN KUN FAHIMCI IN DA AKA DOSA!. Mu koma kan labarinmu.❤️‍🔥 "Shikenan Leesharh, bari na je lokacin cin abincin yana kurewa, kuma kin san komai yana da lokacinsa a cikin gidan nan, dan haka bari na je na ci nawa kada time ya kure banci ba a hanani". Cewar Jasrah. Ta kai karshen maganar tana miƙewa tsaye. Da idanu kawai Leesharh ta bita har ta fice daga cikin ɗakin, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sanya hannayenta dukka biyu ta dafe ƙuncinta, duniyar tunani ta afka, yau gabaɗaya tana cikin damuwa sosai da sosai. 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ IDAN MUKA WAIWAYA WAJEN SU KAMRAN KUWA WATO FOREST.🔥🤍 Zaune suke a ƙasar wata ƙatuwar dutse mai girma dake kusa da wannan ƙoramar na kusa da wajen su Pretty, da alama an fasa yin harbi da kifiyar kenan, akwai itatuwan mangori sosai a ta kusa da wajen, hakan yasa suka samu ishasshen ƴalwar inuwa sosai a wajen. Yana zaune ya jingina da jikin dutsen ya kuma lumshe idanunsa tare da ɗan ɗaga kansa sama kamar mai yin tunanin wani abin, Sweetie na zaune a gefensa na hagu saman farin yashin da yake a wajen. Hannunta na rike da lemun zaki tana ɓarewa duk da bata gani, Kamran ɗin ne ya ciro masu lemun a wata bishiya dake ɗan nesa da ƙoramar. Ita kuwa Pretty sarkin kauɗi tana zaune kusa da shi sosai, ta ɗaura ƴan kyawawan kafafun nan nata a saman nasa ƙafafun tana ɓare nata lemun, idan baku manta ba Kamran ɗin bai fito da wukarsa bane yasa suke ɓare remun da hannu, ba halin yankawa. Shi dai Kamran ya afka duniyar tunanin abin da yake damunsa tun daga haɗuwarsa da su Pretty, kullum yana yawan mafarkinsu sosai, ga shi a duk lokacin da ya haɗa idanu da waɗan nan sexy eyes ɗin nata sai ya ji gabansa ya faɗi, tana rikita shi, ya rasa me dalili. Haƙiƙa idanunta suna da rikita mai kallonsu, wasu irin shegun sexy eyes ke gareta, amma shi nasa rikitarwar na daban ne, har tsoron kallon cikin idanun nata yake yi, gata da shegen daddaɗar zazzakar murya wanda idan ta yi magana sai ya ratsa jikin duk wani mai sauraro, ko baka son haɗa idanu da ita idan ta yi magana sai ka ji duniya baka da burin da ya wuce ka ɗaga idanu ka kalli face nata, saboda muryar nan tata akwai ratsa zuciya, sannan ga ɗan banzan shiga rai garesu daga ita har Sweetie, bugu da ƙari ga ɗan banzan wayo kamar wasu renon tsofaffi. "Kamran ga lemun nagama ɓarewa". Cewar Pretty, ta yi maganar tana kai hannu zata taɓa lallausan kumatunsa. Ajiyar zuciya ya sauke tare da waro idanunsa a hankali, dai'dai lokacin ta kai ɗan kyakkyawan lallausan hannunta saman kumatunsa, a tunaninta barci ya ɗan yi shi ne zata tashe shi. Karaf idanunsa ya sauka cikin nata. Ɗauke hannunta daga saman kumatun nasa ta yi tare da miƙo mashi lemun da yake a ɗayan hannun nata tana mai do da kallonta izuwa saman gashin kansa, duk da yana sanye da hula baka iya ganin gashin kan nasa sosai, amma ya ɗan fito ta gaban goshinsa. "Kamran kana da gashi sosai kamar mu". Ta faɗa tana mai cigaba da kallon kan nasa. Nisawa ya yi tare da karɓar lemun. "Waye ya gaya maki gashina kamar naku ne?". Gyara zamanta ta yi tare da ɗauka kafafunta daga saman nasa, ta yi zama irin na masu cin abinci ta lankwashe kafafunta dukka biyu suna fuskantar juna. "Babu wanda ya gaya mun, kawai na gano yawan gashin naka ne duba da yadda ya cika hular kanka, hakan yana nufin gashin na dayawa sosai". "Pretty ke dai kin cika sa ido". Ya bata amsa yana mai raba lamun da ya karɓa daga hannun nata gida biyu. Bayan ya raba biyu sai ya miƙo mata rabi. Maƙe mashi ɗan kafadarta ta yi alamar bata so tana faɗin. "Ni bana saka ido, daga magana kawai sai ka ce na iya saka ido? Kuma ni ba zan sha lemun ba". Ta kai karshen maganar tare da yunƙurawa zata miƙe, ita a dole ta yi fushi tun da ya ce mata mai sa ido. Cikin hanzari ya kai hannunsa ya riƙo nata hannun yana faɗin. "To sarkin fushi yi hakuri, am so sorry baki da sa ido shikenan?". Tana ƙoƙarin sake yin magana Sweetie ta katsesu da cewa. "Hmmmm ita kam ma ai ta ji daɗi tun da tana da idon da zata yi kallo har ace mata tana sa ido, ni kam sai dai na kalli abu da zuciyata". Wani irin yanayi mara daɗi dukkansu suka ji da jin maganar Sweetien, haƙiƙa maganar ta taɓa zuciyar Kamran sosai, wani irin tausayinta ne ya kamashi, ya sani rashin ido babu daɗi sam, ga shi a yadda ta yi maganar kamar zata yi kuka sai ka ji kalaman nata sun ratsa maka zuciya sosai, sai ka tausaya mata duk taurin zuciyarka, ita ma Pretty da take sarkin kauɗi ta ji kalaman har cikin ranta bare shi Kamran da dama already yake sarkin tausayi mai zuciyar musulman farko, ai dole ya tausaya mata. "Our Sweetie idanunki zasu buɗe nan bada jimawa ba kin ji ko? Kada ki damu kanki, zan nemo maki magani". Cewar Kamran, ya yi Magana da wata iriyar murya wadda da ka ji ta zaka san lallai maganar tata ta taɓa mashi zuciya. "Allah yasa ka samu maganin Kamran, ina son idanuna su buɗe, ina son na ga ya fuskarka take? Ina son sanin kamanninka, saboda kai kawai nake burin idanuna su buɗe". Har lokacin yana rike da hannun Pretty bai saki ba ya bata amsa da. "Nan ba da jimawa ba our Sweetie, zaki samu lafiya sosai kamar baki taɓa yin ciwo ba". "In Sha Allah, zan tayata da addu'a sosai nima". Cewar Pretty. Maido da kallonsa a kanta ya yi yana kallon ɗan bakin nata da ta furta In Sha Allah ɗin. "Take your orange". Ya faɗa yana mai miƙo mata rabin lemun. Sarkin rigima kara maƙe mashi ɗan kafaɗar tata ta yi tare da girgiza mashi kai. "I don't want, ba ka ce mun sarkin fushi ba? So don't talk to me again". Tana magana tana turo baki. "Oh sorry ba zan sake ba ai". Ya faɗa tare da miƙo mata lemun. "To sake mun hannu na sai na karɓa". A hanzarce ya saketa, shi kwata kwata ma ya mance da cewa ya rike mata hannu, ya ji hannu mai laushi luwai luwai. Karɓar lemun ta yi tare da komawa ta gyara zamanta da kyau, sarkin rigima ce sosai Pretty. Ta ƙasan idanunsa yake satar kallonta yadda take tsala lemun nata tsala sala, a hankali take kai sala ɗaya ɗan bakinta, idan ta kai ɗin ma ba dukka take turawa a cikin bakin nata ba, sai ta gutsira ta raba biyu, ta rike rabi a hannu ta bar rabi a cikin ɗan bakin nata tana tauna a hankali hankali kamar bata son motsa ɗan bakin, da alama akwai yauki a tattare da ita, tana kara girma kuma hakan yana kara bayyana. Sosai yake jin daɗin kallon yadda take shan lemun, hakan yasa ya mance da nasa baya sha, saukar zazzaƙar voice ɗinta a dodon kunnuwansa ne yasa ya ɗan firgita tare da dai'dai nutsuwarsa cikin hanzari kamar wani mara gaskiya. "Kamran muje ka cigaba da koya mun harbin kwari da bakar ko?". Shi ne abin da ta faɗa wanda ya fargar da shi daga satar kallonta da ya lula. Ta yi maganar ita kuma ba tare da ta kalli in da yake ba. Ƙasa da idanunsa ya yi tare da sanya hannu ya fara sala lemunsa kamar yadda ya ga ta yi, bai taɓa shan lemu irin haka ba, bai ma taɓa ganin an raba lemu a haka ba sai yau da ya gani a wajenta, shi kullum Mammarsa ce take yanka masu da wuƙa sai su ɓare su sha, yau ya ga sabon salo na tsala ta tsala sala. "Pretty koya maki harbi da kifiya sai na shirya, gara mun na fara koya maki busa tukun nan". Ya kai karshen maganar tare da kai lemu sala ɗaya ɗan bakinsa ya tura ciki, a hankali ya fara sha. "Amma kuma ɗazun kai ne fa ka ce harbi da kifiya zaka fara koya mun?". Ta yi maganar a ɗan shagwaɓe kamar yadda take zubawa Sweetie shagwaɓa, sannan ta yi maganar tana kallon kyakkyawar fuskarsa tana aikin turo ɗan baki. A hankali ya ɗago idanunsa ya saukesu a saman kyakkyawar fuskarta. "Zan koya maki, amma ba yanzu ba gaskiya, sai na yi magana da mamana na tambayeta wani abin tukun nan, yanzun na ji na kasa ne, ba zan iya ba". Ya faɗa muryarsa a ɗan kasale, alamar kwata kwata dai baya son ya tuna da zancen koya mata ɗin, dan shi kaɗai yasan me yake ji a duk lokacin da suka haɗa jiki, komai ƙanƙantar haɗuwar fata da tsokan jikin nasu sai ya ji jikinsa ta amsa. Matsowa kusa da Sweetie ta yi tare da kwantawa a kasa a wajen ta tada kai da laps na Sweetie, dama kun santa sarkin son jiki ce kamar mage. "Ki tashi a jikin Sweetie kada ki ji mata ciwo sarkin rigima kawai". Cewar Kamran, yana magana yana cigaba da shan lemunsa. "Sweetie in yi kwanciyata ko?". Ta tambaya tana mai da kallonta izuwa samar fuskar Sweetien. "Kullum da kike kwanciya a jikin nawa izinina kike nema ne?". Sweetie ta bata amsa tana mai kai hannunta a saman fuskar Prettyn, dogon hancinta ta laluɓa ta ɗan ja. "Wash Allah na, Sweetie kin fara ko?". Ta faɗa tana rike hancin nata da hannu ɗaya, tana kuma turo baki. Shiru Kamran ya yi yana kallonsu gwanin birgewa, suna son junansu sosai, akwai fahimta sosai kuma a tsakaninsu, dan Sweetie tana da hakuri ga hangen nesa sosai yarinyar duk da bata gani, Pretty kuma shagwaɓa, kauɗi, saurin kuka, son jiki, rashin iya juriyar yunwa, da dai sauransu duk ta haɗa, hakan kuma baya sa su yi faɗa a tsakaninsu, duk kuma hakurin Sweetie yasa basu yin faɗar, da ace kamar Prettyn take ba hakuri ai da tuni kullum sai sun yi ta faɗa, ita fa Pretty ko yunwa ta fara ji sai ta yi kuka saboda rashin hakuri. "Daga yanzu ki dai'na kwanciya a jikin Sweetie tun da kin ga bata da lafiya, idan kina jin kwaɗayin kwanciya ki zo ki kwanta a jikina, kada ki kara mata nauyi kan nauyi". Cewar Kamran, yana magana idanunsa yana a kansu sosai, saboda sun burgesa sun kara burgesa sun kara burgesa over to over. "Yauwa Kamran gaya mata dai, ni yanzu ma ka duba mun ita ta yi ƙiba ne ko? Dan naji ta kara mun nauyi, da idan ta kwanta a kafata bana jin nauyi sosai, amma yanzu sosai take yi mun nauyi in ta kwanta". Cewar Sweetie. Lumshe idanunta kamar mai jin barci ma ta yi abinta ta kyalesu, kamar bata jin me suke faɗa, tana jin Kamran yana gayawa Sweetien ai ta girma ne yanzu shi yasa take kara nauyi, amma sam taki kulasu, dan barci barci ma take ji, yanayin weather wajen ya yi mata daɗi sosai. Sweetie da Kamran kuwa cigaba da hira a tsakaninsu suka yi cikin mutunta juna tare da nuna kula ga juna. Kamar daga sama gurnanin Rocky ya doki doduwan kunnuwansu. Ai a dubu ɗari Pretty ta waro idanunta. Cikin sanɗo ta miƙe daga kwanciyar da ta yi, abin gwanin ban dariya ta fara rarrafawa a kasa kamar wata mage ta nufi Kamran, tana rarrafawa tana zaro idanu nan nata kamar ka ruga a kuje idan ka gansu, tana kuma rarrafawa tana ƴan waige waige tana neman ta ina zata gano ɓullowar Rockyn?. Abin ya so ya bawa Kamran dariya, sarkin tsoro kenan, ji yadda take sanɗo tana rarrafawa kamar wadda ta je ta yi sata, kai wannan yarinya sai shirin Allah. Yana tsoron ya yi mata dariya abin ya zamar masu rigima, dan haka sai ya yi kamar bai ganta ba, ya kawar da kansa. Kusa da shi sosai ta zo ta zauna, har da sanya hannu ta riƙo nasa hannun a cikin nata, cikin dabara tana yi tana zaro idanu ta kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa, sai muzurai take yi tana jiran taga ta ina wannan damusa mai gurnanin zai bayyana? Cikinta har ya ɗuri ruwa. Ita ma Sweetie tsoro ne ya kamata, barema da ta ji Pretty ta tashi daga kafarta, sai ta ruɗe, a ruɗe ta fara ambatar sunan Prettyn da kuma tana tambayar Kamran Damusa ce ta sake dawowa zata cinyesu ko?. Ɗan satar kallon sarkin tsoro Pretty ya yi, ta wani kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa tsit da ita, kamar ba ita ba fa, duk ta nutsu, wasu malaman ladab ne suka shigeta lokaci guda ƴar kaniya, sai muzurai take yi. "Sweetie it's Rocky my friend, don't worry babu abin da zai yi maku". Ya bata amsa yana kai hannunsa izuwa kusa da fuskar Prettyn. Kyasta mata yatsun hannunsa guda biyu ya yi a dai'dai fuskarta, dan yaga ta kafe waje guda da kallo. Kara ƙanƙame shi ta yi sakamakon gurnanin Rocky da ta kara ji ya matso kusa, ta kara lefewa a jikin nasa da kyau. "Kamran wlh tsoro nake ji, ni dan Allah ka dai'na zuwa mana da wannan Rockyn, ina tsoronsa sosai". Ta faɗa kamar zata yi kuka, har idanunta sun ciko tab da kwallah. Hannun nasa da ya kyasta mata a saitin face nata a hankali ya ƙarisa kai shi saman fuskar tata, lallausan kumatunta ya ɗan fara shafawa kafin ya fara yin magana. "Pretty ko da na zo nan wajen ba tare da Rocky ba, ko na gudun mashi sai ya samoni ya biyoni, in dai a cikin dajin nan ne babu in da zanje na ɓuya mashi, kamshin jikina yake bi ya nemoni, ba dan haka ba ko dan ki yi farinciki zan dai'na zuwa da shi, amma hakan ba zai yi wu ba, yanzu dai abin da nake so da ke ki dai'na jin tsoronsa kin ji ko? Babu abin da zai yi maki". Cikin sigar rarrashi sosai ya yi maganar, ga tausasawa sosai a voice ɗinsa. Shiru ta ɗan yi kafin a shagwaɓe kamar zata sa mashi kuka ta ce. "To ka ce ya dai'na zuwa kusa da ni idan ya zo, kuma ya dai'na taɓani, ina jin tsoronsa sosai". Ta kai karshen maganar hawayen da suka taru a cikin idanunta suka fara bin ƙuncinta. Hannunsa da yake a saman kumatun nata ya fara goge mata hawayen da shi yana faɗin. "Please Pretty stop crying, ba na son ganin hawayen, in dai Rocky ne baki son ya zo kusa da ke ba zai zo ba, zan gaya mashi kada ya taɓaki, amma ki dai'na kuka kin ji? Baki ga Sweetie bata kuka bane?". Da yake ai suna da banbanci, ita Sweetie bata da tsoron da Pretty take da shi, tana da tsoro amma bai kai ko rabin na Pretty ba, kuma ta yarda da maganar Kamran ɗin, tun da ya ce Rocky babu abin da zai yi mata sai kawai ta yarda abinta, ta kuma nutsu ta kwantar da hankali saɓani hjy Pretty sarkin raki da rigima ga saurin kuka. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 30/7/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________24🔥 Kara matsowa kusa da shi sosai ta yi tamkar zata shige jikinsa. "Pretty na gaya maki babu abin da Rocky zai yi maki, kuma tun da baki so ne ya zo kusa da ke ko kuma ya taɓaki na gaya maki ba zai zo ba, please ki daina wannan kukan". Ya yi maganar muryarsa a cike da damuwa, alamar sam baya son kukan nata. Dai'dai lokacin kuma Rocky ya iso wajen, yana wani tafiyar ƙasaita, ya ci nama ya ƙoshi, har wani lashe baki yake yi abinsa, wasa wasa kwana biyun nan har wani ƙiba yake karawa, yana wani murmurewa. Kai tsaye Kamran ɗin ya nufo abinsa, yana wani numfashi mai haɗe da gurnani alamar ya ƙoshi sosai. Haba kara ƙanƙame Kamran ɗin sosai ta yi, ji take yi ma kamar ta haye jikinsa kawai, zuciyarta ta kasa yardan mata cewa Rocky ba zai yi mata komai ba, ta kasa iya yarda cewa ba zai cinyeta ba, ita dai tsan Tiger suna cin mutanen. Kasancewar a ƙoshe sosai yake, sai ya zo kusa da Kamran ɗin kawai ya kwanta, bai bi ta kan kowa ba, bai kula su Prettyn ba, dama sai yana ɗan jin sakalam a cikinsa ne yake neman tsokana, amma tun da yana ƙoshe sai ya yi kwanciyarsa, yau dai babu shinshinar jikin Pretty. "To kinga ma shi kwanciyarsa ya yi, ki dai'na kukan haka ya isa ko?". Yana magana yana cigaba da goge mata hawayen nata, duk wani iri yake ji a jikinsa, ji yake yi kamar mai zazzaɓi. Hannun nasa da yake goge mata hawayen da shi ta kai nata hannu ta riƙo shi cikin nata, a hankali ta lumshe idanunta ba tare da ta saki hannun nasa ba kuma bata tashi mashi daga saman shoulder ɗinsa ba, ta yi shiru kamar mai barci. Shiru shi ma ya yi yana tunanin lokacin da yakamata ya koma gida ya yi, dan kada Mamma ta nemesa. Jin saukar numfashinta irin na mai barci da ya yi ne yasa ya dawo da kallonsa daga kan Sweetie dake zaune shiru izuwa saman fuskarta, ta yi mashi barci a jiki, ga shi ta ƙanƙame mashi hannu kamar nata ne. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, zuba mata waɗan nan kyawawan fararen idanun nasa ya yi yana mai karewa fuskarta kallo, ba ƙaramin kyau wannan ɗan bakin nata yake yi mashi ba, sarkin raki har ta yi barci kamar ba ita ba, ya faɗa a cikin zuciyarsa. Can kuma ya sake cewa she's so very very beautiful more than anybody that I saw in my life. Ya yi maganar yana jan doguwar numfashi tare da saukewa a hankali. Jin shirun ya yi yawa ne yasa Sweetie ta ce. "Pretty ya naji kun yi shiru?". Ba tare da ya kalli in da take ba ya amsa mata da cewa. "Pretty ta yi barci". "Dama bata da wuyar barci ai rigimammiya kawai". Ta bashi amsa tana mai gyarawa ta kwanta a wajen ita ma. Ta wutsiyar idanunsa ya kalli ta kwanta, ya kasa iya kawar da kallonsa daga saman fuskar Prettyn ne, ji yake yi kamar idan ya kawar da kallonsa wani abin zai ragun mashi, dan haka sai ya kasa iya kai kallonsa kan Sweetien ma. Shi ma Rocky barci ya fara yi abinsa, an ci an ƙoshi sai me? Ai sai barci. Wajen ya rage saura Kamran ɗin ne kawai idanunsa biyu, dan da alama ita ma Sweetie ta yi barci............. PRINCESS TEEMA CE TAKU TA AMANA🤍🔥 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ KINGDOM OF POWER 💪🔥 Kamar yadda King ya umarta haka aka wuce da su Yusuf prison na cikin masarautar in da ake rufe bayi da mayaka ana horar da su idan sun yi laifi. Bayan King uncle Abbas ya bi domin ya je ya samu su tattauna, dan ya nemawa su Yusuf afuwa da sassauci a matsayinsa na wanda ya basu izinin shigowa, kuma a matsayinsu na ƴaƴa ga abokinsa, koma dai me tun da basu aikata fyaɗen ba ba zai so ayi masu wani tsastsauran hukunci ba. Bai san cewa shi ma King zuciyarsa a cike da tunani kan cewa ba lafiya su Yusuf suke ba, saboda yasan jin sunan masarautarsu ma kawai tamkar jin isowar mutuwa ga bawa ne, bare kuma jin sunan shi King ɗin da kansa, so ya fara tunanin ba lafiya Yusuf yake ba, dan yasan abu ne wadda ba zai yi wu ba ace a sami wani mai karfin zuciyar da zai iya tunkarar KINGDOM OF POWER har ya yi ƙoƙarin yiwa wata daga cikin gimbiyoyin masarautar fyaɗe, ko mahaukaci ne ba zai yi wannan gangancin da rayuwarsa ba!. A ɓangaren twins namu kuwa, sarakan sharp brain, suna kwance abinsu, duk bom da yake tashi a gidan suna sane da komai, suna jin hayaniyar komai, amma tamkar babu su a cikin gidan, sai shakiyancinsu kawai suke yi a saman bed, suna ta uban dariya kamar ba lafiya suke ba, Obaid sai ya yi kamar zai yi ladab ya sake kwashewa da dariya kamar zararre, shi kam Omaid dama ba gwanin yin dariya bane ba, sama sama yake ɗan taɓawa idan ɗan uwan nasa yanayi, dan ya fi Obaid iya mugunta shiyasa baya dariya sam sam. Su Gimbiya Zunaira kuwa suna school abinsu, bama su san me yake faduwa a cikin family part ba, su momma ma sam basu sami labari ba, amma ita Mama ta sami labarin daga bakin wata munafukar kuyangarta mai yi mata leƙen asiri, duk wani motsi a cikin gidan Mama tana sani, tana da CID da suke yi mata aikin leken asiri sosai, haka zalika Mammie mahaifiyar su Yah Jawad, duk wani abin da yake faruwa in ma a part ɗin King ko kuma a cikin fada dukka tana sani, kamar wata aljana, sai ta riga uncle Abbas jin labarin abin da aka zartar a fada, sai ka rasa ta ina take samo labaran, ta fi mama iya bala'i sau dubu, ita nata mai lasisi ne. Yanzu haka duk abin da yake faruwa a wannan part na bakin har Mammie ta samu labari, ta ji komai da ya faru daga farko har ƙarshe, zuciyarta fari kal abinta, wani irin sanyi ne ya ratsata, dama ba ƙaramin kai ruwa rana da uncle Abbas suka yi ba a kan cewa ita bata yarda wani Yusuf ya zo wajen Sarina ba, saboda idan baku manta ba ita burinta Sarina da Fanan su auri ɗaya daga cikin Prince na kingdom of power, so ita bata burin kowani namiji ya kusanci ƴaƴan nata, shiyasa ta kafewa uncle Abbas a kan lallai ita fa bata son wannan Yusuf ɗin. Shi kuma ya ce ba makawa Yusuf sai ya zo, idan kuma Sarina ta yi na'am da shi to aure babu fashi. Wannan dalilin yasa da ta ji cewa ga abin da ya faru da su Yusuf ɗin ta fara sakin wani irin shu'umin murmushi wanda babu mai iya fassara me murmushin yake nufi sai ita da ta yi shi, ita kaɗai tasan nufin kayanta, amma dai murmushi ne mai tattare da abubuwa da dama a cikinsa, dan bana alkhari bane. Haka zalika duk wani abin da kake son sani a dangene da fada to ka tambayi Aneesa ƴar Mama zaka samu labari dallah dallah idan ta yi niyar faɗa, sai ka rasa daga ina ita ma take jiyo labarin komai. Idan muka koma ɓangaren Yah Jawad da Gimbiya Chuchu a hospital kuwa, yana zaune rike da waya yana latsawa, amma shi da kansa bai san ina yake shiga a cikin wayar bama, bai san me yake taɓawa ba, saboda kwata kwata hankalinsa baya a kan wayar, yana kan waɗan nan nurses ɗin da suke ta faman shafawa Gimbiya Chuchu wasu mayuka a kyawawan kafafun nata. Baiwar Allah idanunta sun yi jajir sun ciko da kwallah, ji take kamar ta saka ihu, amma tana tsoronsa kada ya yi mata wani muguntar. Daga karshe kasa daurewa ta yi saboda wani mai mai zafi da suka sanya mata, hakan yasa ta kasa iya cigaba da rike hawayenta, nan take suka fara simtiri a saman ƙuncinta. Ta wutsiyar idanunsa yake kallon yadda take ruwan hawayen, ga gwiwowin nata sun yi jajir da su kamar zasu fitar da jini. Sam bai san lokacin da a takaice ya ce da nurses ɗin su kyaleta haka ya isa ba. Ɗago idanu suka yi suna kallonsa, sai a lokacin ya fahimci ashe ya yi magana, ɗan kara ɗaure fuska ya yi kamar ba shi ya yi maganar ba, ya wani tsare gida tare da miƙewa tsaye daga saman bed ɗin, ji yake yi kamar ya fita waje ya basu waje su cigaba da yin aikinsu, amma kuma ya kasa iya yin haka, kuma har ga Allah ba zai iya ganin abin da suke yi ba, hakan yasa ya ɗan juyo da kallonsa a kanta. Siraran hawayen azaba sai simtiri suke cigaba da yi a saman kumatun nata. "Jannat bana ce kada ki bari na sake ganin hawaye a fuskarki ba? This tears is for what again?". Ya yi maganar yana kara ɗaure fuska sosai irin shi boss ɗin nan kada a rai'na shi. Cikin jin zafin ciwon nata ta fara yarfe mashi hannayenta tare da kara tsuke ɗan bakin nan, hawayen suna tsananta gudu a face ɗin tata, a shagwaɓe ta fara magana. "Ka yi hakuri Yah Jawad, zafi sosai kafata take yi mun, ni ban san lokacin da hawaye suka zubo na, amma na tuba ba zan sake ba....." Da kyar ta iya kai karshen maganar tata, saboda wani irin kuka da ya so kubce mata. Wani irin tausayinta ne ya ji ya dira mashi a ransa, amma bai nuna hakan ba, sai ya danne ya ce. "Okey now goge hawayen kuma kada ki bari wani ya sake fitowa". Cikin hanzari ta kai hannunta ta fara goge hawaye da shi, sai dai tana gogewa wasu suna kara zubowa sosai, saboda zafin da kafafun nata suke yi mata na dalilin wannan mai da nurses ɗin nan suka shafa mata. Ganin hannayenta sun kasa iya goge hawayen ne yasa ya ciro wani kyakkyawar white handkerchief mai laushi kamar jikin mage daga aljihun suit ɗin jikinsa, sai tashin kamshi handkerchief ɗin yake yi, a hankali ya tako izuwa kusa da ita sosai ta wajen da kanta yake. Miƙa mata handkerchief ɗin ya yi a kan ta karɓa ta goge hawayenta da shi. Hannu ta miƙo da nufin ta karɓa, a nan ya lura da yadda yannunta ke kerma kamar mai kermar zazzaɓi. Ɗan guntun mamaki ne ya kamashi, a tunaninsa zazzaɓi ne ya rufeta, hakan yasa ya kai ɗayan hannunsa saman 4 head ɗinta dan ya ji ko jikin nata da akwai zafin zazzaɓi. Babu wani zazzaɓi a jikinta sai ma wani irin ɗumi mai daɗi da jikin nata yake da shi, kawai shegen tsoronsa ne yasa hannunta yake kerma. Fuskarta ya kallah da kyau kafin ya ce. "Jannat lafiyarki kuwa?". Karɓar handkerchief ɗin ta yi tare da fara goge hawayen nata tana mai gyaɗa mashi kai alamar e lafiyarta lou. Su kuwa nurses ɗin nan sun saki baki suna ganin ikon Allah, ya dakatar da su daga yin aikinsu, basu karisar da shafa mata magungunar ba, su ga shi bai basu izinin tafiya ba, duk ya sakasu a tsakiya, sai kawai suka saki baki suna ganin ikon god. Ɗan karemata kallo ya yi a yadda take kwancen na a kallah one mins kafin daga bisani ya ɗago ya kalli nurses ɗin. "Muna iya tafiya ko?". Calmly ya yi maganar. "Sir bamu kammala shafa mata magungunar ba ai". Satar kallonta yadda take aikin goge hawayen ya yi kafin ya ce. "Wajibi ne sai an shafa su dukka?". A hanzarce cikin girmamawa tare da ladabi da biyayya suka girgiza mashi kai alamar aa ba wajibi bane sai an sha dukka, sun rigada sun shafa masu muhimmanci. "Bayan waɗan nan abubuwa da zaku shafa mata ko nace wadda kuka fara shafa mata da akwai wani abin da zaku yi mata ne? I mean injection or drugs?". Nan ma a hanzarce suka girgiza mashi kai alamar a'a babu, iya waɗan nan mayukan ne kawai. Shiru ya yi bai sake yi masu magana ba, hannu ya miƙa masu a kan su nashi mayukan da suka rage basu shafa mata ɗin ba. Cikin rawan jiki suka ɗauko suka miƙa mashi. Karɓa ya yi tare da sa kai ya wuce ya fita waje. Jim kaɗan ya sake dawowa ba tare da mayukan a hannunsa ba, kai tsaye wajenta ya nufa, tana kanƙame da handkerchief ɗinsa a saman ƙuncinta ta kasa cirewa, saboda hawayen nata ya ki dai'na zuba, shi ne yasa ta bar handkerchief ɗin a face ɗin tata, da hawayen sun zubo sai ta yi maza ta goge dan kada ya gani, bata san cewa duk abin da take yi yana ganinta ba, yana ganinta sarai, amma ya nuna kamar bai ganta ba, tausayinta ma sosai yake ji a yanzu. Hannayensa dukka biyu yasa ya ɗauketa cancak ya saɓata a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye ya nufi waje da ita ba tare da ya sake bi ta kan nurses ɗin ba, sai cikin motarsa. A guje driver ya buɗe masa kofar motar tasa, a gidan baya ya zaunar da ita, sannan ya zagayo ta ɗayan side ɗin ya shiga. A hanzarce drive ya shiga tare da yi wa motar key, cikin kwarewa da iya aikin sosai ya figi motar suka bar hospital ɗin, kai tsaye family part suka nufa, dan wajen Akka zai mayar da ita kamar yadda ya ɗaukota, dan idan ba haka ba wannan tsohuwa ba zata rabu da shi ya zauna lafiya ba, so gara ya mayar mata da ita ya samawa kansa salama. Ko da driver ya yi parking ɗin motar a tampatsetsan parking space da yake a fam part ɗin, basu fito ba, tamkar Yah Jawad bai san da an iso family part ɗin ba. Ɗan satar kallonsa gimbiya Chuchu ta yi, dan ita tana son ta je ta kwanta, barci sosai take ji, Allah ya gani ba zata iya jurar zaman nan ba. "Sir zan iya tafiya ko kuma akwai in da zan kai ka?". Cewar driver. Da hannu ya yi mashi alamar yana iya tafiya ba tare da ya yi magana ba. A hanzarce ya fito daga cikin motar ya mai da marfin ya rufe. Sun ɗauki a kallah 10 mins a haka shiru yana taɓa waya wanda shi da kansa ma bai san me yake yi a cikin wayar ba, kawai taɓa ta yake yi. Sautin canzawar numfashinta daga dai'dai izuwa na wahala ne yasa ya ɗan nisa tare da juyo da kallonsa a kanta, ya wani sakata zunbula hijabi gwanin ban dariya, sai ta kara zama ƴar karama a ciki. Kallon second biyar ya yi wa face nata kafin ya fara magana a nutse. "Wannan punishment da na yi maki is for fitowa with sleeping dress da kika yi ne kawai, now saura na haɗani da Akka da kika yi and ɓata mun lokacin da kika yi kika hanani zuwa office, by 8:30pm ki sameni a part ɗina". Tsabar bakin ciki bata san lokacin da ta saka mashi kuka ba, dan tasan punishment ɗinsa shi da Yah Jaish babu kyau, ji na jiya ma da ya yi mata sai da ta dangana da asibiti bare kuma ya kara yi mata wani, wai tsabar mugunta har da wani cewa iya na fitowa da kayan barcin da ta yi ne kawai, to shi kuma na haɗa shi da Akka ya zai kasance? Ga hanashi zuwa office da ta yi, wlh ba zata yarda ba, hakan yasa ta kara sautin kukan nata sai dai ya kasheta kawai ya huta, tun da su dama basu iya komai ba sai mugunta. Zuba mata idanu ya yi yana mamakin yadda take kukan, ita kuwa ta rufe idanunta gam dan ma kada su yi ido huɗu ta ji tsoronsa ta yi shiru, ba shirun da zata yi!. Da dai yaga da gaske take yin kukan kuma bata da niyar dai'nawa, and kuma yasan yana ɗaukarta suka shiga ciki a haka tana kuka confirm sai ya haɗu da su uncle Abbas or uncle Taheer, ko ma dai King da kansa a hanya, da wuya ya gifta har ya kai part ɗin Akka bai haɗu da ɗaya daga cikinsu ba, barema Momma, idan ya haɗu da ita ai sai ta saka shi a kwana da masifa, dan bata son abin da zai taɓa mata autarta Gimbiya Zunaira da kuma Chuchu, tana ji da ƴan mata biyun nan, bare ma Akka, ai yana zuwa wajen Akka ya shiga talatin ma ba uku ba. Dan haka sai ya kai hannu dan dole ya jawota jikinsa dan ya rarrasheta ta yi shiru ya samu ya mayar da ita wajen Akka ya kama kansa, da dai Jaish ne wlh ko kukan mutuwa zata yi bata isheshi kallo ba, sai dai ma ya kara mata da mari, kuma hakan ba zai hana shi ya sakata ta taka da kafafunta har izuwa cikin gida ba, ai idan ma Jaish ɗin ne wlh asibitin ma ba zai kai ta ba, sai dai Akka ta yi ta surutu har ta gaji ta yi shiru, tafiya ma zai yi ya basu waje sai dai duk abin da zai faru ya faru, Jawad yana da saukin kai sosai a kan Jaish. Ɗan bubbuga bayanta ya fara yi alamar rarrashi, duk Akka ce sila, wannan tsohu ta koma Dubai su huta, yanzu sai ta kai karansu wajen iyayensu haka take yi, ta ja masu wahala, shiyasa dan dole suke lallaɓata. "Ya isa haka kukan! Ki yi shiru ki faɗa mun kukan me kike yi?". Ya faɗa can kasan maƙoshinsa. "To Yah Jawad ba kai ne ba, na ce ka yi hakuri ba zan sake ba, amma kaki ka hakura, ka ce zaka kara bani wani punishment ɗin, ga shi kuma kafata tana yi mun ciwo". Ta yi maganar cikin muryar kuka, da kyar da kyar ma take iya maganar saboda kukan, har da shessheka. "Yanzu da na ce kizo cikin part ɗina ki sameni cewa na yi zan baki wani punishment ɗin ne?". Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a tana daga kwance a kirjinsa ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman bayanta, ɗayan hannunsa kuma yana rike da wayarsa. "Kin san me zan yi maki idan kika zo part ɗin nawa ne?". Ya sake jefa mata tambaya yana mai cigaba da kallon face ɗinta. Nan ma girgiza mashi kai ta yi alamar a'a bata sani ba. "Amma kike yin kuka a kan abin da baki sani ba?". Shiru ta yi tare da fara goge hawayenta da handkerchief ɗinsa da yake a hannunta wadda ya bata ɗazun. "Ka yi hakuri ba zan sake ba, na tuba". Ta faɗa a kasale, saboda kukan da ta sha ma duk yasa barci take ji over. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin cewa ta dai'na kukan, sannan ya kai hannu ya ɗago haɓarta daga saman kirjin nasa, ya zama suna fuskantar juna. "Kada ki yarda ki bari na sake ganin hawaye a saman wannan kumatun naki, in kika bari hakan ta faru to zamu ɓata, yanzu dai mun shirya tun da kin ce ba zaki sake ba, sannan kamar yadda na faɗa anjuma ki sameni a part ɗina, ta shi mun a jiki mu wuce cikin gida". Ya kai karshen maganar tare da sakin haɓar tata yana mai kawar da kallonsa daga kanta. Ajiyar zuciya ita ma ta sauke tare da tashi mashi daga jikinsa cikin sauri, ta ji daɗi koba komai ya ce ya hakura ba zai yi mata hukunci ba, kuma ya ce sun shirya, amma fa har yanzu akwai sauran haushinsa a ranta. Buɗe kofar motar ya yi ya fito, ya zagayo ta side ɗin da take ya buɗe kofar, a saman shoulder ɗinsa ya saɓota suka nufi cikin gida. Bai direta a ko'ina ba sai a saman katafaren bed ɗin Akka, yana sauketa call ta shigo wayarsa, a lokacin kuma Akka bata a cikin ɗakin, tana part ɗin King saboda abin da ya faru da Sarina, ta sami labari, shi ne ta yi maza ta je ta duba ko dai da gaske anyi mata fyaɗen ne su shiga uku, Akka sarkin zafin rai, tana jin labari tun bata ƙarisa wajen ba ta ce ba makawa kashe Yusuf za'ayi, wannan tsohuwa tafi King zafin nama da zafin zuciya ga iya faɗa kamar me. Zama ya yi a gefen bed ɗin tare da yin picking na call ɗin saboda Mammie ɗinsa ce take kiransa, dama wayoyinsa guda biyu ne, wanda ya kashe a asibitin nan ita ce wayar da yake amfani da ita ma mutanen waje, wadda take hannunsa kuwa iya familynsa ne kawai suke da wannan number, su kawai yake kira kuma suke iya kiransa da shi, gabaɗaya ƴaƴan su King suna da tsari sosai a rayuwarsu, komai daki daki suke yinsa, basu haɗa abu kaza da kaza, kowanne suna ware mashi matsayinsa da ta dace da shi, wannan dalilin yasa a koma ina suke suke zama the most responsible parsons. "Yanzun nan ka same ni a part ɗina". Shi ne abin da Mammie ɗin tasa ta ce. Da akey ya amsa mata da shi tare da miƙewa tsaye, zura wayar a cikin aljihunsa ya yi bayan ya karse kiran kafin ya juyo da kallonsa a kanta. Idanunta a lumshe, da alama ta yi barci, dan dama barcin take ji. Ganin alamun ta yi barci ne yasa a hankali kamar wani mai sanɗo zai yi sata, hijabin jikin nata ya ɗan yaye sama dan ya kalli kafafun nata, wato ba zai dubata idan idanunta biyu ba, dan kada ta rai'na shi, shi ne sai da ta yi barci ne zai duba kafafun. Ajiyar zuciya ya sauke tare da mai da kallonsa a saman fuskarta, tana rungume mashi da handkerchief ɗinsa ga sauran guntun hawaye a face ɗin nata. Hannu ya kai ya ɗan shafi lallausan gashin kansa kafin ya furta "Am so sorry my sister, nasan babu wanda ya taɓa sakaki kuka a gidan nan sai ni, gaskiya ban kyauta ba". Ya yi maganar a fili kuma kasa kasa ta yadda babu wanda zai iya jinsa, shi da kansa yasan ya yi laifi. Cigaba da shafa gashin kan nasa ya yi yana mai tambayar kansa Jawad what's wrong with you ne? Ka tafi Mammie na jiranka, shi ne abin da zuciyarsa take gaya mashi. Nisawa ya yi kafin ya mayar mata da hijabin nata ya rufe mata kafafun nata, sannan ya janyo duv na Akka mai bala'in laushi, kamshi, kyau da kuma tsada ya rufeta da shi har izuwa wuyarta, kafin ya sa kai ya fice waje daga cikin ɗakin da sauri. Kai tsaye wajen Mammie ɗinsa ya nufa kamar yadda ta umarta. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga katafaren parlourn ɗinta, duniya guda, duk wannan Daula bai ishe Mammie ba har take sake neman duniya idanu a rufe, sai ka rasa me take da buƙata again, idan kuɗi ne sune suka jikata a yanzu, a cikin daula take, idan mulkin ne ai suna ciki, ta fannin siyasa ma ana damawa da su, amma ita duk fa bai isheta ba, bama shi bane a gabanta ba, burinta kawai koma yaya ɗanta ya zama shi ne the next king of kingdom of power, babbar magana akwai show, ga shi kuma da alama ita da mama kudurinsu ɗaya, kuma suna da ƴan leken asiri sosai da sosai a cikin masarautar, dan duk wanda zai yi motsi a kan idanunsu yake yi, ga dukkan alamu ma ita Mammie tasan da mama da ƴan leken asirinta sarai, saboda ta fi mama iya makirci da tsiya ba kaɗan ba. Izinin shiga bedroom ɗin nata ya ce da Kuyangun da suke yi mata hidima su nema mashi, ya yi maganar yana a tsaye, dan bai jin kamar zai zauna ma, duk baya jin daɗi a ransa, bai so ace ya jiwa Chuchu ciwo har haka ba, sam abin bai yi mashi daɗi ba. Yana tsaye har kuyangar ta dawo wajensa tare da bashi amsar Mammie ta ce ya shigo. Ba tare da ɓata lokaci ba bai bi ta kan kuyangur ba ya yi maza ya wuce ciki da sauri. Zaune saman sofa da yake set a cikin bedroom ɗin nata ya iskota. Cikin nutsuwa ya yi sallama tare da ƙarisowa kusa da ita. Saman carpet ya zauna tare da ɗaga mata gaisuwa cikin girmamawa. Tana shirye cikin wani arnen lace mai bala'in tsada, ta zuba gwala-gwalai a wuya da hannu, tana da son duniya over, idan ta zuba wani kwalliyar sai ka rantse da Allah ba za'a mutu ba, gata da iya shan kamshi kamar me, nuna isa da izza a kan abu. Allah yasa gabaɗaya su Sarina babu wanda yake kama da ita, su Jawad dukka uncle Abbas suka ɗauko a kamani, shiyasa suke kama da ƴaƴan King, saboda uncle Abbas da Akka yake kama haka shi ma King da Akka yake kama, sai suka cure waje guda kamar mahaifa ɗaya. A maimakon ta amsa gaisuwar tasa, sai ta jefo mashi tambaya kamar haka. "Menene a tsakaninka da Chuchu?". A hanzarce ya ɗago da kallonsa izuwa kanta. Ɗaure fuskar nan ta yi tamau kamar hadari, Allah dai yasa kyakkyawace ajin farko, badan haka ba yadda ta wani uban ɗaure fuska nan ai da ba zata yi kyan ganuwa ba. "Mammie akwai wadda ya ce maki akwai wani abin a tsakanina da Jannat ne?". "Tambayarka nake yi ka bani amsa ba ka sake jefo mun wata tambaya ba". Ta faɗa a dake, irin ita big star ɗin nan, babu wasa. Shiru ya ɗan yi yana mamakin abin, shi da kansa wlh bai san me a tsakaninsa da ita ba, kawai tana burgesa ya sani, duk cikin ƴaƴan King ita da auta ne suka fi burgesa, shiyasa in dai zasu haɗu sai ya ɗaga idanu ya kallesu, bayan haka bai san wani abin ba kuma. "Mammie Jannat is my sister, bayan haka kuma ni ban san wani abin ba, babu komai a tsakaninmu". Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wanda sai da ya bashi mamaki, to me matsalarta da Chuchu ɗin da har zata damu kanta har haka dan ta gansu a tare? Ita Mammie ɗin nan lamarinta akwai ɗaure kai. "Kana iya tafiya, amma kafin nan ka saurareni da kyau, naga kwana biyun nan kana yawan kasancewa tare da Chuchu, to bana da buƙatar hakan, bana son na sake ganinku a tare". Da yake shi bai kawo komai a ransa ba, kuma bayan cewa Chuchu sistersa ce babu wani abin a ransa, sai ya amsa mata da okey kawai, sai dai abin ya ɗan bashi mamaki yadda ta ɗauki zafi a kan abin, sai ka ce Chuchu ɗin wata bare ce, kamar ba kanwarsu ba, kamar ba ɗiyar King ba, ai wannan ko kuyanga ce sai haka, lokaci guda ta wani ɗauki zafi daga ganinsu a tare, to wai ma ta ina ta gansu a tare har take zargin da wani abin a tsakanin nasu? Idan ma da wani abin kenan hanawa zata yi? Iko dai sai Allah, wannan lamari da ɗaure kai da ban mamaki, ga shi dai burinta ne su Sarina su auri ƴaƴan King, to shi Jawad kuma laifin me ya yi da ba'a yi mashi wannan fata?............🤔 Miƙewa ya yi ransa fes ya nufi waje bayan sun yi sallama, to dama shi me zai dame shi tun da a ganinsa dama babu wani abin a tsakaninsu? Ai shi normal ne, a ganinsa ko ta ce kada ya sake haɗuwa da Chuchu ma normal ne ba wata matsala. Yana fita kai tsaye Company Jaish ya nufa, dan dama haka suke, wani lokaci sai su haɗe waje ɗaya su yi zamansu a office suna hira. Mammie kuwa yana fita ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da miƙewa ta haye saman bed ɗinta tana tunani, ko me take tunawa oho mata. After some hours. Da Gimbiya Sarina, Gimbiya Zunaira, Gimbiya Fanan da kuma Gimbiya Aneesa ne zaune a saman katafaren bed ɗin Akka, wai sun zo duba kafar Gimbiya Chuchu, Akka ce nan ta gaya masu cewa kafar tata har yanzu yana ciwo bai warke ba, dama idan baku manta ba na gaya maku cewa sun fi yawan zama a part ɗin Akka, so suna dawowa daga school suka shigo part ɗin, a lokacin ita kuma Akka ta gama shiri zata nufi fada, dan ta je ta yi magana da King a kan su Yusuf, saboda a dokance za'a yanke masu hukuncin ba a familance ba, so dole sai a cikin fadar. Sai hira auta da Gimbiya Chuchu suke yi, dama sun saba kamar wasu kawaye, Gimbiya Sarina tana latsa wayar Mammienta da ta shigo da shi, har yau Jawad bai bata wayarta ba, Fanan da Aneesa suna hira, dan suma suna shiri sosai. "Aunty Chuchu kin ki ki gaya mana menene ya sameki a kafa ko?". Cewar auta, ta yi maganar kamar zata yi kuka, sarkin son ƴan uwanta kenan. "Auta na gaya maki nima ban sani ba, da safe kawai na tashi naga kafar tawa tana ciwo, ba kema kin gani da safen ba?". Gyaɗa mata kai auta ta yi alamar e ta gani. Zata sake yin magana Gimbiya Aneesa ƴar mama ta rigata da cewa. "Ba wani nan ki faɗi gaskiya, ba Yah Jawad bane ya baki punishment?". Dama na gaya maku duk wani labari da kuke so ku tambayi Aneesa ta sani, ko daga ina ta jiyo wannan kuma oho mata dai, ahalin gidan nan lamarinsu sai su. Shiru kaɗan Chuchu ta ɗan yi kafin ta ce. "Haka ne, Yah Jawad ne ya saka kneel down, shi ne yasa kafafuna suke yi mun ciwo". Zaro idanu waje Auta, Sarina and Fanan suka yi, basu yi zaton hakan ba, Sarina da Fanan sun ɗauka su kawai Yah Jawad ya tsana yake horarwa idan sun yi laifi, to yau dai ga shi harda Gimbiya Chuchu ta hau layi, hakan yana nufin kowa daga cikin bai tsallake ya horar da shi ba. "A gaskiya Yah Jawad mugu ne". Cewar Sarina, ta yi maganar tana kwaɓe fuska, dama basa shiri sam sam, bata sonsa dan yana takura mata. "Wlh Aunty Sarina ni babu ruwana idan ya jiyoki, kema kin san sauran idan ya ji abin da kika ce mashi". Cewar Fanan, tana magana tana zare ido, alamar tsoron Jawad ɗin sosai take ji. Wani irin kallon up and down Sarinar ta wurga mata kafin ta ce. "Ni narasa ma meyasa su Yah Jawad suka zauna a gidan nan, kowa ya koma nasa gidan mana, ko kuma su tafi Dubai wajensu mai ran karfe sun fi buƙatarsu mu bama da buƙatarsu". Aneesa ce ta ce. "Zaki iya zuwa ki gaya masu su tafi su baki waje ai". "Dake nake magana ne? Ko mi sa'ar wasarki ce". Ta faɗa cikin izza. Dama nagaya maku da Sarina da Aneesa basu zama inuwa guda, kamar wuta da audiga suke. "Ba dani kike yi ba, amma kuma na baki amsa ko kina da abin yi ne? Ke har ma kin isa ki yi da ni?". Cewar Aneesar. A fusace Sarinar ta buɗi baki zata yi magana sautin tafiya ya daki doduwan kunnuwansu, wadda ya sanyasu nutsuwa tsit, da alama sun san mai wannan tafiya, dan harta ita kanta Chuchu dake kwance ɗan gefe da su sai da ta kara nutsuwa sosai, yadda kuka san waɗan da aka yi wa wahayin ganin mala'ikan mutuwa, duk suka wani yi tsit, Auta ce kawai bata canza daga yadda take ba. Ƙasa kasa ya yi sallama kamar mai ciwon baki, yana sanye da wando three cuter a jikinsa, daga ta sama kuma polo shirt mai bala'in kyau, wandon ash color ce rigar kuma fara kal, ya yi kyau sosai, da alama bai jima da dawowa daga office ba. Har suna rige rige wajen haɗa bakin cewa. "Good evening Yah Jaish". Kallo ɗaya ya yi masu ya kawar da kansa tare da tambayarsu ina Akka take ba tare da ya amsa gaisuwar tasu ba, yana magana kamar wadda bakinsa yake ciwo. Tsabar tsoronsa da suke yi sun kasa iya bashi amsa, Auta ce kawai ta ce. "Yah Jaish Akka tana fada". Bai sake yin magana ba ya miƙo mata hannunsa a kan ta zo su je ta raka shi. Da sauri ta sauƙo kasa daga saman bed ɗin ta nufesa, hannunta ya rike suka nufi waje, kowa a gidan bashi da ɗan rakiya biyun auta, ita ce mai raka kowa duk in da zai je a cikin gidan, babu ruwanta, ita fa kowa sonta yake yi, ita ma kuma tana son kowa abinta. Suna fita daga part ɗin suka ci karo da jarumi abin alfaharin KINGDOM OF POWER, wato HOORAIN yana tsaye shi da wani dakakken jarumin mayaki suna magana. Cool murmushin nan nata mai kara fito mata da tsantsar kyanta tare da ɗan dimples ɗinta ta sakar mashi tare da cewa. "Hoorain tun jiya ban sake ganinka ba". Jaish yana jinsu bai yi magana ba, bai ma ɗago yaga Hoorain ɗin ba, sai dai ya ɗan ji babu daɗi a ransa da autar tasu ta cika sakewa kuyangun gidan har ma da mayaka fuska, ita kowa nata ne, baya son hakan sam, amma bai nuna ba, yana rike da hannunta suka cigaba da tafiya kawai. Ƙasa da kai Hoorain ya yi, har wa yau yana cikin kayan yakinsa tare da wannan hula da ta hana a kalli face ɗinsa, sarai ya lura da Jaish bai so auta ta yi mashi magana ba, hakance ma tasa ya iya bakinsa bai amsa mata ba, sai dai ya bita da kallo ta ƙasan ido kawai, yarinyar tana burgesa yadda ta fito daban a cikin ƴan gidan, bata da girman kai ga girmama mutane. Sai da suka ɗan wucesu ne wannan mayakin da suke a tare ya taɓa shoulder ɗin Hoorain ɗin tare da faɗin. "Kabi a hankali abokina". Jinjina mashi kai Hoorain ɗin ya yi tare da cewa. "Nagode manta kawai mu cigaba da maganar mu". Ya yi maganar kamar dai yadda ya saba yinta cikin sanyin murya kuma ƙasa ƙasa kamar baya son yi. Ita kuwa auta a duniya tana son ganin face ɗin Hoorain, sai dai duk kuma lokacin da ta ce mashi ya cire wannan hula ta kallesa sai wani abin ya gifta a tsakaninsu ya hana shi cirewa, tana jin daɗin kasancewa da Hoorain ɗin a matsayin mai bata tsaro sosai, saboda yadda yake kula da ita ya fi sauran mayakan da suke kula da su Gimbiya Chuchu. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 31/7/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________25🔥 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ A ɓangaren su Aneesa kuwa, kamar dai yadda suka saba ne, kullum in suka haɗu da Sarina waje guda matuƙar iyayensu basu a kusa to fa rabuwarsu bata daɗi, dan haka a wannan karon ma Yah Jaish yana fita suka dasa daga in da suka tsaye da surutan nasu, ko wacce sai shegen son girma da nuna isa da izza. Fanan da ta lura zasu cika mata kunnuwa sai ta miƙe ta nufi waje abinta, dan ba zata iya ba, ba yau bane farau. Ita ma Gimbiya Chuchu gyara kwanciyarta ta yi tare da basu baya tana fuskantar headboard na gadon, dan ma kada su takura mata sosai sai ta janyo duvet ɗin Akka ta rufe har kanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, abokiyar hirarta wato auta ta tafi, dama ita idan ba da auta ba bata cika yin hira da kowa ba, ɗan gara ma Fanan, wani lokaci suna hira sosai, amma Sarina da Aneesa wlh babu mai iya halinsu sai su, murɗaɗɗun mutane ne wanda ba zaka taɓa gane ina alkiblarsu take ba. Duk kuma faɗar da zasu yi fa a iya baki ne kawai yake tsayawa, ko da sunan wasa basa daka hannu a jikin juna, ba wai kuma dan basu iya faɗar ba, ina ai su faɗa a jininsu ma take, kawai dai basu taɓa ko da gwadawa bane, dan sun san zasu daku dukar mutuwa ma kuwa a hannun Jaish in suka yi faɗa, ina ga bugun da zai yi masu ko ganga iyaka, hakan yasa sai suke tsayawa a iya surutan nasu kawai. Yanzu haka suka yi surutun nasu tsab suka kammala ba tare da ɗaya ya taɓa koda alkyabbar jinin ɗaya ba. Aneesa ce ta fara miƙewa ta fice daga cikin ɗakin. Ita kuwa hjy Sarina sai ta gyara ta kwanta a saman bed ɗin tare da cigaba da taɓa wayar Mammie abinta. Da daddare misalin karfe 9 kowa ya kammala cin abincin darensa, masu saurin yin barci ma har sun yi barci, wasu kuma suna shirin yin barci. Akka tana part na uncle Abbas, dan tun da yamma ya ce kansa na yi mashi ciwo, kuma gobe yake son komawa, so Akka tana wajensa, ta je duba ciwon kan nasa. Gimbiya Chuchu ce kawai kwance a saman bed ɗin Akkar, ita kuwa Gimbiya Zunaira tana wajen Mommarta yau, ta je ta wani haye mata saman bed tare da tada kai da cikyarta suna ta hira na tsakanin uwa da ƴa, kamar wasu ƙawaye, sai shafa lallausan bakin arab hairnta momma take yi, tana ta bata labarin ƴan uwata su uncle Rahab kenan da suke can Dubai. Ita dai Momma har ga Allah tana wahala rayuwarta a wannan masarauta, shiyasa take yawan zuwa Dubai, ko da kuma ta gayawa mahaifinta ga abin da yake faruwa da ita, sai dai ya ce mata ta kara tsananta addu'a sosai, yau tsawon shekaru talatin kenan tana fama da wannan matsala, sai dai yana yin sauki, ya fi taso mata ne a duk lokacin da ta samu ciki, har ta haifi wannan ciki tana fama da wannan mahaukacin razanar da ita da ake yi, ba kalar halittar da bata gani, wani lokaci idan abin ya yi tsamari har suma take yi, sai an danganata da likitoci, amma kuma idan bata da ciki tana fin shekara biyu zuwa uku bata ga wani abin tsoro ba, sai jefi jefi. Da yake tana tsananin kaunar gimbiya Zunaira sai aka fi yawan tsorata da fuskar Zunaira ɗin, da tsakar dare zata jiyo muryar autar tata tana ta faman kuka a cikin toilet, idan ta tashi ta je ta duba kuma sai ta ga yes fuskar Zunaira ɗin ce, amma kuma babu gangar jiki, sai jini dake zubo mata daga hancinta, bakinta izuwa wuyarta, wani lokaci idan ta taso daga kan gado da addu'ar tashi daga barci, sai bata tsorata zaka ji ta furta sunan Allah sai abin ya ɓace, amma duk ranar da ta manta bata tashi da addu'ar tashi daga barci ba to ba shakka tana mahaukacin razana har ta kurma ihu, kuma abin baya ɓacewa sai dai ya kara razanar da ita, baya rabuwa da ita har sai ta samu ta furta wata addu'a ko sunan Allah. Haka baiwar Allah take ta fama, ta kuma ƙasa iya gayawa King Zuhair ga abin da take fuskanta, mahaifinta kawai ta iya gayamawa, shi ma kuma da alama saboda babban malami ne sosai kuma sarki mai karfin iko ne yasa abubuwan basu iya rufe mata baki a kansa ba, ta iya gaya mashi. Ko mahaifiyarta bata iya gayawa ba. Sai hira suke zubawa kamar wasu ƙawaye, a haka Jaish ya shigo ya samesu, sanye yake da kayan barci masu bala'i kyau da tsada, already ya nemi izinin shigowa ta hanyar turo mata massages a wayarta, saboda ko da ya zo parlourn bai sami su kuyanga Mama Haulat ba, sai kawai ya turo mata sako, ta kuma amsa mashi da ya shigo, shi ne yasa ya shigo. Kasancewar suna a saman bed sai shi kuma ya zauna a saman bedside drawer kusa da lamp dake a kunne yana bada wuta light green. "Good evening my Momma". Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa. "Yah Jaish ɗazun baka bani amsata ba". Cewar auta. "Evening Jaish how was the night?". Cewar Momma. Alhdulillah ya bata amsa kafin ya ce da auta. "Which amsa kenan?". Ɗan turo baki ta yi kafin ta ce. "About my journey to Dubai, ina son dawowa a tare da yaya Omar ne fa". Shiru ya yi mata bai amsa ba, dan ya rigada ya yanke hukunci babu in da zata je, abin da next week Omar ɗin zai dawo, dan haka ta jira shi a nan kawai. Hannun Mommarsa da take ta faman shafa lallausan gashin auta ya riƙo cikin nasa, a hankali ya zura mata wani haɗaɗɗen dankareran diamond ring irin nata da ya cire mata ranar, dama idan baku manta ba ranar ya cire mata nata ring ɗin saboda ya yi mata kaɗan, to shi ne ya yi waya wa a powerful king of Dubai ya aiko mashi da wani irin wannan sak, wato kakansa kenan wanda ya haifi Momma ɗin kuma uncle ga King Zuhair kani ga Akka kenan, dama idan baku manta ba na gaya maku King Zuhair Momma ƴar uncle ɗinsa ce ya aura, aure dangi ne. Sosai ta ji daɗin wannan ring ɗin, wani sanyi ne ya ratsa mata zuciya yadda ƴaƴanta suke nuna mata so, ya cire wancan da kasa ya kuma kawo mata mai ɗan girma ya saka mata, baban abin birgewa ma ko da ya sanya mata ring ɗin sai da ya ɗan sumbaci hannun nata da wannan ɗan ƙaramin bakin nasa, sannan ya ce. "Momma ring bai taɓa burgeni ba before, but a hannunki is so very very beautiful da har na ji ina sha'awar sakawa ni ma, you're so special our Momma". Cikin nutsuwa tare da sanyin murya ya yi maganar. Wani irin madarar daɗi ne ta ji ya kara lulluɓeta, yabo yana da daɗi, amma kuma irin yabon da Jaish yake yi mata ya fi na kowa daɗi. Shi kuma Jaish ɗin a duniya iya ita da King kaɗai ya iya yabawa, ko auta idan ta yi kwalliya suka haɗu ta tambayesa ta yi kyau, kai kawai yake gyaɗa mata, wani lokaci ko kallon kwalliyar tata ma baya yi, amma idan Mommarsa ce ya rinƙa yabon kyanta kenan koda bata yi kwalliya ba, ita da King kaɗai ya iya yabawa a duniyarsa, bayan su ko kansa bai iya yabo ba, yo shi da a duniya ma kwata kwata da mutane huɗu zuwa biyar yake iya buɗe baki ya bawa amsa, saura sai dai ya bisu da ido ko kuma ya gyaɗa masu kai, idan kun ji ya buɗe baki yana magana voice nasa na ɗan fita da sauti kaɗan ma to da Mommar ce ko King, su biyun nan yake yi wa magana har voice nasa ta ɗan fita, saboda baya son ya zamana ya yi masu magana basu ji ba sai sun sake wahalar da kansu wajen sake tambayarsa me ya ce? Baya son haka shiyasa yake ɗan buɗe murya idan zai yi masu magana, bai ɗauki iyayen nasa abin wasa ba, sune komai nasa, yana bala'in kaunarsu fiye da komai, da da hali ma ina ga har abinci zai rinƙa tauna masu dan kada su sha wahala. "Yah Jaish baka yi magana ba". Cewar auta, ta yi maganar a shagwaɓe sosai. "Baby I will think about it, ki bari zuwa gobe". Ya bata amsa yana sakin hannun Mommar tasu. "Allah ya yi maka albarka my son". Cewar Momma. Da Amin ya amsa mata kafin ya sake cewa. "Momma zan iya tafiya ko kina buƙatar wani abin?". Girgiza mashi kai ta yi alamar bata buƙatar komai zai iya tafiya. Miƙewa tsaye ya yi tare da kai hannunsa ya shafi lallausan kumatun auta da ta tsare shi da idanu. "Sarkin kallon mutane ayi addu'ar barci kafin a kwanta". Ya faɗa haɗe da ɗan jan karan dogon hancinta. Wani irin cool murmushi ta sakar mashi har sai da dimples ɗinta suka lotsa, wani irin sihirtacen kyau ne ya kara bayyana a saman face ɗin nata, dama ita fa ba baya ba wajen kyau, wlh ta fi su Jaish ɗin dukka kyau, yadda kuka san duk an haɗe mata kyansu ne aka cure waje guda aka bata, idan ka gansu dai dukka zaka san cewa ƴaƴan Momma ce saboda jini ba wasa ba, amma dai ta fisu kyau har twins Obaid and Omaid, Yah Omar dukka, ita ce tauraruwarsu. Ɗan yatsarsa karami ya ɗan saka mata a ramin da dimples ɗin nata suka lotsa, ya ɗan danna wajen kafin ya ce. "Naki ya fi na kowa kyau a gidan, kin yi mana wayo". Ya yi maganar kasa kasa tare da ɗauke hannunsa daga saman face ɗin tata. Sai binsu da kallo Momma take yi, gwanin ban sha'awa abin, akwai soyayya da kauna mai karfi a tsakaninsu. Daga King har Momma dukka suna da dimples, hakan yasa gabaɗaya ƴaƴan Momma suke da shi, ita ma Gimbiya Chuchu tana da shi, amma Gimbiya Aneesa ƴar Mama bata da shi, uncle Abbas yana da shi, amma su Sarina duk basu da shi, Akka ce tushen dimple ɗin nasu, duk da ta tsufa idan tana magana zaka gansa a face nata ɓaro ɓaro. Hannunsa auta ta kama ta ɗan sumbata kafin ta ce. "Take care Yah Jaish, kaima kada ka manta ka yi addu'a, nima kuma zan yi, Momma zata kara yi mun kona yi barci, kuma nasan daddy ma sai ya zo ya yi mun, dan baya taɓa yin barci ba tare da ya zo ya yi mun addu'a ba, ina fa samun addu'oi sosai". Nufar kofar fita ya yi yana tafiya a nutse, sai da ya kai tsakiyar ɗakin ya kusa bakin door ɗin ya ce. "Ni ma baki san ina dawowa na yi maki addu'a bako? Ai ke ƴar gata ce, bana jin a gidan nan akwai wanda baya yi maki addu'a". Ya kai karshen maganar dai'dai lokacin da ya fice daga ɗakin, bai jira amsarta ba, dan baya buƙatar ji, idan ya biye mata zasu iya kwana a wajen, auta bata gajiya da magana. "Mommana dama Yah Jaish yana dawowa ya yi mun addu'a idan na yi barci?". Gyaɗa mata kai ta yi alamar e tare da faɗin. "Harda Yah Jawad duk suna zuwa bedroom naki su yi maki addu'a, amma idan a nan kika kwana basu zuwa, dan basu son takura mun suka ce". Shiru ta ɗan yi kafin kuma ta ɗan shagwaɓe fuska tare da faɗin. "Allah sarki suna sona sosai". Yadda ta yi maganar sai da ta sanya Momma sakin murmushi, wai Allah sarki suna sonta sosai, ashe ma ita bata san cewa ita ɗin kamar bugun zuciyarsu take ba, bata san cewa sun fi sonta fiye da kansu ba, saboda kyawawan halayenta irin na King yasa take da mugun shiga rai, harta Mama da take bata shiri da Momma tana kaunar Zunaira, wannan suna na Zunaira ma Mamar ce ta zaɓa mata a lokacin da aka haifeta, yarinyar ce dole ta shiga ran mutun, saboda yadda take bata ɗauki duniya a bakin komai ba, bata ɗauki abubuwa da zafi ba, komai nata very calmly and softly conduct. Cigaba da hira ita da Mommarta suka yi har izuwa lokacin yin barci, dama already tana shirye cikin kayan barcinta masu bala'in kyau da tsada, riga da wando launin maroon color. Barci ne ya ɗauketa kwance a saman laps ɗin mommar tata, fuskarta ɗauke da annuri tare da murmushi mai kara mata kyau ko da tana barci. Shiru Momma ta yi tana karewa face ɗin nata kallo kamar mai tunanin wani abin. Ta ɗauki a kallah tsawon mintuna 10 a haka tana kallon fuskar ƴar tata ba tare da kyafta idanu ba. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin nan cikin dabara ta sauketa daga saman laps ɗinta tare da sanya mata pillow, sannan ta sauko kasa daga saman bed ɗin, dan ta je ta yi wanka ta yi shirin kwanciya. Bata kai ga shiga toilet ɗin ba sallamar King kasa kasa ya daki dodon kunnuwanta, ya biyo sahun ƴarsa, ya je bedroom ɗinta bata nan, ya leƙa na Chuchu bata can, babu kowa ma a ciki, dan Chuchu ɗin ma tana wajen Akka, hakan yasa ya nufo nan kai tsaye kawai, ba zai iya yin barci ba idan bai yi wa Zunaira addu'a ya shafa mata ya kuma tabbatar tana cikin aminci ba. Sanye yake da arab jallabiya fara tas a jikinsa, ga arab hairn nan nasa a kwance luf har gaban goshinsa, King ba dai kyau ba, kyakkyawan balarabe ne ajin farko, ga wani bakinkirin ɗin saje mai bala'in laushi da kyau kwance luf a gefe da gefen face ɗinsa, kyakkyawar gemun nan nasa ta sha gyara, sai sheki take yi sosai, ga wani haɗaɗɗen gashi da ya kewayo ɗan red bakinsa, ba ƙaramin kyau ya kara mashi ba, farar fata da bakar gashi ku kunsa dole ya ɗauki ido, ga kuma dara daran idanu masha Allah, gashin gerarsa har kamar zasu haɗu da juna saboda cika, suna kwance luff suma kamar an zana mashi su, sai sheki suke yi........ (Har na ji zan iya yi wa Momma kwace🥱🌝 sai dai ina tsoron commander ZAFAR😥) Tsare Momma da waɗan nan dara daran idanun nasa ya yi yana kare mata kallo tare da harɗe hannayensa a saman wannan Lion chest ɗin nasa, King fa ansha fama a fagen yaki a lokacin da mahaifinsa King ABDUL MALIK yake raye yake kuma rike da karagar mulki, idan baku manta ba na gaya maku ya taɓa rike commander mayakansu a lokacin, so har yanzu a buɗe yake kamar yana mai cigaba da karɓar horon yakin. "Barka da shigowa ranka ya daɗe". Momma ta faɗa cikin girmamawa, sai kallon juna suke yi, ita bata cire idanunta daga kansa ba, shi kuwa dama kunsan ba kawarwa zai yi ba. (Ni kam na ce mada dai a manta auta tana ɗakin😌🌝) Shiru suka kurawa juna idanu na a kallah mintoci uku kafin kuma a tare su sakarwa da juna cool murmushi kamar abin haɗin baki. "Ka fara ko?". Momma ta faɗa tare da sa kai zata wuce cikin toilet abinta. "In dai zan shigo ki cigaba da yi mun irin wannan tarba to ba zan canza hali ba". Ya faɗa tare da nufar saman bed ɗin nata wajen Zunaira kenan yana cigaba da sakin murmushi kamar ba King sarkin zafin rai da iya tsare gida a fada ba. "Shi ne baki rufe mun sanyin idaniya ta da duv ba ko? Kika barta sanyin Ac na ratsa mun ita sai ta yi mura ko? Zan rama mata". Ya kai karshen maganar tare da hayewa saman bed ɗin, a kusa da ita ya zauna tare da fara tofa mata addu'a kamar yadda ya saba. Ita kuma Momma ta shige cikin toilet, dan in ta biye mashi tsab zasu iya kwana a tsaye suna yi, su ɗin ƴaƴan kawu da gwaggo ne, Akka gwaggon Momma ce, akwai wasa sosai a tsakaninsu, abokan wasa ne, hakan yasa wani lokaci King ɗin yake tsokanarta sosai da sosai kamar wasu yara, tun kafin su yi aure haka suke, har izuwa yanzu kuma basu canza ba, abin gwanin birgewa, ban sha'awa da kuma ɗaukar hankali tare da ɗaukar darasi. Ya ɗauki a kallah good 10 mins yana zubawa sanyin idaniyar tasa addu'oi kafin ya shafa mata, sannan ya janyo duv ya lulluɓeta bayan ya manna mata kiss a saman 4 ahead ɗinta, yana ji da ita sosai, ya ce ita ce ke kama da shi a dukka cikin ƴaƴansa, King akwai neman magana, kawai dan yasa Momma yin magana ne yasa yake cewa Zunaira ce mai kama da shi, dan yasan sai ta yi magana, saboda da ita Zunaira take kama ba shi ba, duk da cewa ita da shi ɗin ma suna kama kamar ba mata da miji ba, idan ka gansu sai ka zaci wa da kanwa ne, saboda jini guda ne dama. Bayan ya kammala tofa mata addu'a saukowa ƙasa ya yi tare da nufar door ɗin fita, dama abin da ya kawosa kenan, kuma ya gama, Momma zata same shi a part ɗinsa, dan yau dama kwananta ne. A ɓangaren Gimbiya Chuchu kuwa, barci ne mai nauyi ya ɗauketa tun bayan cin abinci da suka yi, ko wankan dare bata samu ta yi ba, da yamma ma da kyar ta iya yin wanka, sai da Gimbiya Fanan ta taimaka mata, tana sanye da doguwar riga mai ɗan nauyi a jikinta da haka barcin ya kwasheta, ita kaɗai ce a bedroom ɗin, idan baku manta ba na gaya maku Akka tana part ɗin uncle Abbas. Ƙasa ƙasa Yah Jawad ya yi sallama ya shigo cikin bedroom ɗin, hannunsa na rike da waɗan can kwalaben magunguna daya karɓo daga hannun waɗan can nurses ɗin. Tun ɗazun yake ta jiranta ta zo ya bata ta shafa a kafafun nata amma shiru bata zo ba, shi ne ya biyo sahu, dama idan baku manta ba ya ce ta same shi a part ɗinsa, baiwar Allah barci ɓarawo yasa ta manta gabaɗaya. A saman bedside drawer ta kusa da ita ya zauna tare da ɗaura wayarsa a saman gefen bed ɗin ta kusa da ita, da waya guda ɗaya ya fito, ya baro ɗayar ta jama'a a ɗaki, dama ya fi yawan fita da ta family, dan kada ya yi missing call ɗin kowa daga cikin ƴan uwansa. Hannu ya sanya ya yaye duv da take lulluɓe da shi, sai sharara barci take yi kamar babu gobe, ta ɗan ƙudundune hannayenta a saman kirjinta. Face ɗinta ya ɗan ƙurawa idanu na ƴan sakani kamar mai nazarin wani abin. Can kuma sai ya gangarar da hannunsa ƙasa ya ɗan ɗage mata dogowar rigar jikin nata izuwa santala santalan cinyoyinta. Sai da gabansa ya yi wani irin mummunar faɗuwa, na ganin kyakkyawar farar fatan tsala tsalan cinyoyin nata da suke luwai luwai suna sheki, sai ji ya yi kamar Akka zata zo ta same shi, idan kuma ta same shi a haka to ya shiga talatin, sai ta addaba mashi da surutun ko dai yana son Chuchu ne? Ba zata barshi ya zauna lafiya ba, wannan tsohuwa akwai baki, so shi surutun ne baya da buƙata, dan haka sai jikinsa ya fara ɗari ɗari, ya ji kamar kada ya shafa mata ganin ya barshi kawai. Amma kuma ina ba zai iya ba, ba zai iya barinshi ɗin ba, saboda abin da ya fito da shi kenan, ya kasa iya rintsawa ne, har ya yi shirin kwanciya ya kwanta, sai kuma ya kasa iya rintsawa, saboda yana tunanin in dai bai kula da ita ta samu lafiya ba to bai kyauta ba gaskiya, dan koma me shi ne silar jin wannan ciwo tata, so yana da kyau ya kula da ita ta samu lafiya, hakan yasa ya kasa rintsawa har sai da ya fito. Mayukan ya buɗe tare da fara ɗebowa da nufin ya fara shafa mata, abin mamaki hannayen nasa ne suka fara kerma, ji yake yi kamar ba zai iya shafa mata ɗin ba, da mamaki yake kallon hannun nasa yadda yake kerma kamar wadda akacewa ya taɓa wuta. Ajiye kwalbar maganin da yake a ɗayan hannunsa ya yi, ya kai hannun ya ɗan shafa lallausan arab hairnsa tare da furta why? A hankali. Nisawa ya ɗan yi kafin ya yi ta maza ya ƙarisa kai hannunsa ya shafa mata. A hanzarce kamar mara gaskiya ya yi sauri ya shasshafa mata sama sama, duk gudun kada Akka ta zo ta kama shi ta janyo mashi jangwangwan ga kuma tsikar jikinsa dake ta faman tashi na taɓata da yake yi. Ganin Chuchun ta fara ɗan motsawa kamar tana son farkawa ne yasa ya yi saurin miƙewa ya ɗauki wayarsa tare da nufar door ɗin fita ba tare da ya ɗauki ragowar magungunar ba. Har ya kai tsakiyar ɗakin kuma ko me ya tuna ya yi saurin juyowa ya dawo, a hanzarce hannunsa na kerma ya sauke mata rigarta ya mayar mata da shi dai'dai tare da janyo duv ɗin ya rufeta, da sauri ya nufi door ya fice, sai motsawa Chuchun take yi tana son farkawa daga barci. 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ UAE💘 AAJ PRISON💔😥 After two dys. Zaune yau ma Leesharh take a saman bakin bed ɗinta, ta buga uban tagumi kamar dai ranar, ta yi shiru, da alama bata a tare da mutane, ta luluƙa duniyar tunani, kamar ko da yaushe suna cikin uniform na AAJ ɗin, kala biyu ne uniform ɗin nasu, akwai fari kuma akwai blue, yau su canza wannan gobe su canza wannan. Jasrah ce ta shigo ɗakin cikin shigar fararen uniform ɗinta ta sameta. A kusa da ita ta zo ta zauna tana mai faɗin. "Queen of thinking, yau kuma waye kika tuna a cikin familyn naku?". Sam sam babu alamar murmushi ko mai ƙanƙantarsa a saman fuskar Leesharh, da alama yarinya ce da since before bata dariya, saboda bata ma yi kama da wadda take ko yaƙe bane, duk abin da za'ayi na dari wlh bata taɓa yi, Jasrah ta taɓa ɗaukar 30 mins tana surutan banza duk dan ta sanyata ko da murmushi ne, amma ina ko yaƙe ta kasa sakata, a tsawon shekara ɗaya na zaman da ta yi a gidan AAJ wlh sai dai suga hakwaranta idan tana magana ko tana yin brush, amma ba dai dariya ba, sam walwala da farinciki baya a saman fuskar yarinyar na, kullum cikin kuncin zuciya take, daga tagumi sai kwanciyar rigingine, abinci ma wani lokaci sau ɗaya take ci a rana, na safe kawai, bata wani damuwa da cin abinci, sai yawan tunani kamar me. Ita kuwa Jasrah ta ce tun da nan da shekara guda za'a kasheta kamar yadda doka ta yanke mata, gara mata ta ci abincinta ta yi duk abinda tasan zata yi, dan tasan dokar nan ba zai kau daga kanta ba, sai dai wani ikon Allah, amma babu wanda ya isa ya sanya a fasa kasheta, kisa ba fashi, so dan haka gara mata ma ta saki ranta ta samu ta yi bankwana da duniya da kyau da kyau. Ita kam Leesharh saura mata shekaru uku ta kai munzalin ɗaukar hukuncin da aka yanke mata........ Hmmmmm ni ko na ce hmmmmm. "Ni kam a duniya waye nake da shi da zan yi tunaninsa da ya wuce mamata?". Leesharh ta bata amsa tana mai dawo da kallonta a kanta su fuskanci juna kenan. "To amma Leesharh where's your father? And you Said you're from Africa, so what brought you here Dubai?". Jasrah ta jefa mata tambaya. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin yin magana Aaradiya dake kwance a saman bed ɗinta ta rigata da cewa. "Shima baban naki kashe shi kika yi ko? Dan naga ke horuwa ce, tun da kika zo gidan nan ko hakwaranki ba'a gani a waje, ke anya ma ba mayya ba ce Leesharh? Dan naga duk gidan kin fi kowa manya manyan idanu kamar ball". Cike da shakiyanci da isgilanci sosai Aaradiya ta yi maganar. Ɗayar yarinyar da take kasan bed ɗin Aaradiyar ce mai suna Sarah ta ce. "Kuma fa Aaradiya kina da gaskiya, kila mayya ce, ta kashe babanta, yanzu kuma ta kashe mamanta, muma fa kada ta kashe mu". Ta kai karshen maganar tana zaro idanu. A ɗan fusace Jasrah ta ce. "Ko ta kashe ku ko bata kashe ku ba nan da lokaci ƙalilan kasheku za'ayi, kuma idan ma ta kashe ku a yanzu ai saukaka maku zata yi". Jasrah damo sarkin hakuri, bata magana a kan kome za'ayi mata, amma bata son taga irin cin fuskar da suke yi wa Leesharh a gidan, dan ita ce kawai aka kawo wadda ta kashe mahaifiyarta da hannunta, hakan yasa yaran da kansu suke tsangwamanta, yara ma kenan sun san daɗin uwa bare kuma manya, shiyasa sam sam Leesharh bata fita waje, dan idan ta fita kowace yarinya da kalar zagin da take yi mata, ƴan manyan cikinsu ma sai ku ji suna cewa Allah ya tsine maki la'ananniya, la'ananniya ce kawai zata kashe uwar da ta yi silar zuwanta duniya. Wannan dalilin yasa bata fita, ta gwammaci ta yi ta ƙunsuwa a cikin ɗaki kamar daddawa, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa kullum take cikin ƙuncin zuciya da ɓacin rai tare da tunani. Ga shi kuma taki buɗe baki ta gayawa kowa ya aka yi ta kashe mahaifiyarta da kanta, ko da jami'ai suka tambayeta ma iya e kawai ta amsa masu da shi, anyi anyi ta yi magana ta bada labarin yadda aka yi, amma ina taki yarda ta buɗe baki. "Ai munsan zaku iya kashe mu ba sai kin gaya mana ba, ke da kika kashe Ameer bai yi maki komai ba". Cewar Sarah kenan. Shiru Jasrah ta yi bata sake bi ta kansu ba, dan in ta biye masu faɗa zasu yi sosai, kuma dukkansu zata girme masu da shekara guda, amma saboda su basu da kirki sun rainata, sun mayar da ita kamar wata kanwarsu suna yi mata cin kashi. "Leesharh amsa me where's your dad?". Cewar Jasrah. Nisawa Leesharh ta yi tare da ƙoƙarin fara yin magana kenan wata ganduroba mace ta shigo cikin ɗakin nasu bakinta a ɗauke da siririn sallama, tana sanye cikin uniform ɗinsu na aiki. "Who's Leesharh?". Shi ne abin da ta faɗa tana mai binsu da kallo. Miƙewa tsaye Leesharh ɗin ta yi tana faɗin gata nan. Wucewa matar ta yi ta fita tare da cewa. "Follow me". Da sauri Jasrah ta miƙe tana faɗin. "Ina zaku kaita?". Abin da kun rigada kun sani ne ba amsa mata zasu yi ba, dan ba sha'aninta bane su ɗin, dan haka sai ta yi wucewarta ba tare da ta sake juyowa ta kallesu bama. Leesharh kuwa bata da zaɓin da ya wuce ta bi bayan matar. Komawa Jasrah ta yi ta zauna tare da buga uban tagumi tana tunanin to me zasu yi wa Leesharh da suka wani zo suka kirata? Ko dai wani nata ne ya kawo mata ziraya? Ko kuma wani aikin zasu sakata? Ka dai za'a canza mata ɗaki a rabasu ne?. Tunani dai kala kala take ta yi a wajen. Da kallon banza Sahra and Aaradiya suka bita da shi tare da binsu da addu'ar Allah yasa a kashe Leesharh ɗin ma a yau kowa ya huta, yadda kuka san a kansu Leesharh ɗin nan take zaune, sam basu kaunarta. Kai tsaye office na shugaban gandurobobi wannan mata ta wuce da Leesharh dake ta faman jan kafa kamar zata faɗi a ƙasa, sam babu kuzari a jikinta, da alama bata ci abincin rana ba yau ma, dik a galabaice take baiwar Allah. Da alama a baya Leesharh tana da ɗan ƙiba kaɗan, saboda yanayin shape ɗin jikinta ya nuna rama ta yi, da ta fi hakan cikar bom bom and hips. Shugaban gandurobobin tana a zaune a saman kujararta, ta yi crossing na leg's ɗinta, sanyin Ac na dukanta, office ɗin nata ya kawatu iya ƙawatuwa, tana sanye cikin haɗaɗen jallabiyarta launin sky blue a jikinta, yau bata sanya uniform ba, ta sanya wani ɗan ƙaramin please call me hijab da bai wuce kirjinta ba, ƴar siririya da ita, bata da ƙiba ko kaɗan, amma akwai kyau sosai da sosai, balarabiya ce ta usli, ga manya manyan idanu farare tas. Sai uban tulin takardu a gabanta kamar wata mai MD na Company, idanunta sanye suke da wani haɗaɗɗen farin glass mai ɗan girma, sai kamshi take zubawa ita kanta, ga kuma kamshin da office ɗin yake zubawa shi ma. Wata macece zaune a zaman kujerar zaman baki idan suka zo a cikin office ɗin, daga sama har ƙasa idan ka cire nikaf da yake a fuskarta sanye wannan mata take da fararen kaya, nikaf ɗinta ne kawai baki, amma komai da ta sanya a jikinta fari ne tas, harta luxury hand fashion bag ɗinta ma fari ne, ta yi rolling na veil a kanta, ƴar dai'dai da ita, ba zaka kirata da mai ƙiba ba, haka zalika ba zaka kirata da siririya ba, ta dai ci ta ƙoshi, babu yunwa a tattare da ita, da alama kuma daloli bama nerori ba daloli sun yi mata mugun jiƙo, dan babu alamar gurbin talauci a tattare da ita, diamond ring da yake ɗan ƙaramin yatsan hannunta ma kawai ya haura 10 million, idanunta suna a sanye da black glass kamar wata mara gaskiya, ga nikaf ga kuma glass. A ƙasa saman carpet Leesharh ta zo ta zauna a gaban ogar tasu, ita kuma wancan gandurobar da ta je ta zo da ita juyawa ta yi ta fita bayan ta isar da saƙon ga Leesharh nan ta kawota. Cikin girmamawa da muryarta da sam kwata kwata bata fita sosai kamar wata mai koyon magana Leesharh ta ce. "Ganin nan". Cikin harshen larabci ta yi maganar. Kallon wannan mata dake zaune a saman kujara ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya shugaban gandurobobin ta yi, da hannu ta nunawa Leesharh wannan mata tana faɗin. "Bani ne nake kiranki ba, ga mai buƙatarki nan". A hanzarce Leesharh ta juyo da waɗan nan dara daran idanun nata a kan matar, tun shigowarta bata kalli matar ba sai yanzu da aka nuna mata ita, hankalinta na'a kan shugaban gandurobobin ne kawai baiwar Allah. Cikin girmamawa ta sake ce da wannan mata gani nan Aunty. Kallon shugaban gandurobobin wannan matar ta yi, ɗan guntun numfashi ta ja tare da saukewa a hankali kafin ta ɗan ja ƴan mintoci da a kallah zasu kai biyu ba tare da ta ce komai ba, sannan calmly ta fara magana cikin kwararriyar laraɓcinta da zazzaƙar muryarta mai daɗin sauraro. "Bismillah Abida kina iya bamu waje a yanzu". Ta faɗa cikin sanyin murya, sai dai da alama akwai isa sosai da ji da kai a tattare da muryar tata. Miƙewa shugaban gandurobobin ta yi ba tare da ta sake cewa komai ba, ta nufi out door, sai dai da alama ranta bai so fitar ba, kawai an fi karfin ta ne. Bayan fitarta da kamar minti biyar haka, suna zaune shiru, wannan mata sai karewa Leesharh kallo take yi ta cikin black glass ɗinta, ita kuma Leesharh ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da hannunta. Tana son ta ɗago kai ta saci kallon wannan mata, amma kuma tana tsoron su haɗa ido ko kuma ta ganta, hakan yasa ta sunkuyar da kan nata shiru kawai. "Shin kina son fita daga cikin wannan bakin gida da zuwansa ba alkhari bane Leesharh?". Ta tambayeta cike da fargabar amsar da zata bata, tana tsoron Leesharh ɗin ta ce bata sha'awar fita daga gidan, hakan zai sa buƙatarta ba zai biya ba......... Ko wani buƙata take da shi a kan Leesharh? Muje dai zuwa.🤔😥 Tamkar saukar aradu haka Leesharh ta ji sautin zazzaƙar voice ɗin wannan mata ya daki dodon kunnuwanta. A wani irin hanzarce ta fara gyaɗa mata kai in doubling. Baiwar Allah da alama bata da wani burin da ya wuce ta fita daga cikin wannan gida na AAJ........ Ba dolema ta so fita ba ko dan yadda sauran yaran suke tsangwamanta suka takura mata. Wani irin cool ajiyar zuciya wannan mata ta sauke, ta cikin nikaf ɗinta ta saki wani irin shu'umin murmushi wadda fassara shi zai yi matukar wahala, da alama haƙarta zai cinma ruwa. "Very good Leesharh, na ji matuƙar daɗi da ya kasance kina son fita daga cikin wannan gida". Ta faɗa muryarta cike da tsantsar farinciki saɓanin ɗazun da magana kawai take yi babu walwala a tattare da ita. "Aunty ina son na fita daga nan sosai, ko dan saboda tsangwamanta da suke yi suna kyarata, ga zagina da suke yi, kuma bana son a kasheni a nan, ina son na koma kasarmu, ina son na je wajen kabarin mamata na ganta". Ta yi maganar idanunta suna cikowa tab da kwallah, muryar Leesharh sam baya fita sosai idan zata yi magana, yadda kuka san harshenta a naɗe yake, kamar mai koyan magana, gata kyakkyawa ajin farko, amma sam bata iya yin magana ya fita, a wani daddame maganar tata yake fita, idan ba ka nutsar da hankalinka sosai ba ba zaka taɓa iya gane me take son cewa ba ko me ta ce ba. Shiru wannan mata ta ɗan yi tana ƙoƙarin iya fahimtar me Leesharh ta faɗa, dan bata wani gane me ta ce ba bayan cewa da ta yi mamanta, iya kalmar maman kawai ta iya ji a cikin maganar nata. Da kyar ta iya fahimtar wasu daga cikin abin da Leesharh ɗin ta ce, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Idan kina so yau ba sai gobe ba zan fitar dake daga cikin wannan gidan, kuma zan kai ki asibiti a gyara maki voice ɗinki, zan ƴantaki ki zama mai gata, zaki zama ƴa kamar kowa, zaki samu farinciki da jin daɗi fiye da ƴaƴan shugaban ƙasa, zaki samu rayuwa mai cike da jin daɗi, zaki ci abinci mai rai da lafiya a kullum da ko yaushe kike da buƙata, zaki kwanta a ɗaki mai Ac, zaki kwanta a katafaren bed ɗin da nasan da idanunki ma baki taɓa ganin gado irinsa ba, zaki saka suturuna na alfarma wadda ƴaƴan manya suke sakawa, ke har da gida da mota zan iya saya maki mai kyau da tsada, idan kina son yin karatu ma zaki yi, kome kike so zan yi maki amma da sharaɗi, kin amince?". A wannan karon a hanzarce Leesharh ta ɗago da kanta, jiki na kerma ta fara gyaɗa mata kai alamar ta yarda ta amince tun ma bata ji wani irin sharaɗi bane, ita dai burinta ma kawai ta bar wannan gida, ko bara zata yi a bakin titi in dai zata bar wannan gida to zata amince da koma wani irin sharaɗi za'a sanya mata, bata damu da sai wannan mata ta bata dukka wannan daula da ta lissafa mata ba, ita dai ta fita daga gidan nan kawai. "Good girl, wani aiki zaki yi mun, ba aiki bane mai wahala, kuma ba jimawa zaki yi kina yin aikin ba, da zarar kin yi mun shi dai'dai shikenan angama zaki sami duk waɗan nan abubuwa dana kirga, kina amincewa ko yanzu ne zaki bar wannan gida ba tare da kin kara one mins ba, amincewarki ne kawai yanzu zai fitar dake a yau ɗin nan". With full confidence matar ta yi maganar. Shiru Leesharh ta ɗan yi, kamar zata ce wani abin, sai kuma bata yi wani tunani ba ba kuma ta ji wani irin aiki bane, idanunta ya rufe da son fita daga AAJ, hakan yasa ta gyaɗa kai alamar ta amince zata yi wannan aiki da bata san menene bane. "Kin amince zaki yi mun wannan aiki?". Matar ta tambaya muryarta cike tab da tsantsar farinciki mai nuna alamun ta jima bata shiga farinciki irin haka ba, ga tsantsar ƙaguwa a voice ɗin nata. Ƙara gyaɗa mata kai Leesharh ta yi alamar yes ta yarda ta amin zata yi wannan aiki da bata ji ko menene ba. "Kin san wani irin aiki zaki yi mun ne? Bashi da wata wahala fa". Matar ta sake faɗa cike da murna da farinciki. Girgiza kai Leesharh ta yi alamar bata san wani aiki bane. "Ba wani aiki mai wahala bane, so nake............. Ko masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu, amma ku wani aiki kuke ganin wannan mata zata sanya Leesharh da har ta yi mata alƙawarin maƙudan dunbin dukiya har haka?🤔 Anya wannan mata akwai alkhari a tattare da ita kuwa?🤔 Ga shi dai ta rufe ko'ina nata ba'a iya ganin wacece!🤔 To dai shikenan su kuma nasu wasan yanzu zai fara kenan, 🥱 na yi ta nan. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 1/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________26🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼 "Ba wani aiki mai wahala bane, so nake kawai ki shiga jikin wani, ina son ki shiga jikinsa ta yadda duk wani abin da yake yi zan samu labari, na sha wahala sosai kafin na samu yarinya irinki wadda take da duk wasu qualities da nake da buƙata wanda kuma nake ganin zai iya jefa Ramish a cikin tarkonmu". Ɗan dakatawa da yin magana ta yi cike da fargabar kada Leesharh ɗin ta ce ba zata iya yin wannan aiki ba, ta kafeta da idanu ta cikin glass ɗinta tana karewa fuskarta kallo tare da karantar yanayin ta, bata san ya zata yi ba idan Leesharh ɗin ta ce ba zata iya yin wannan aiki ba. Cike da kirsa tare da ƙoƙarin yin amfani da ƙarancin shekarun na Leesharh ɗin ta cigaba da yin magana kamar haka. "Na san da cewa baki jin daɗin zaman wannan gida, na san da cewa kina cikin kunci da takura, na san da cewa kina cikin wahala, na san da cewa baki da burin da ya wuce ki fita daga cikin wannan gida, to dukka wannan zai faru ne kawai idan kika amince da tayi na, bafa cutar da kowa zaki yi ba" Sake dakatawa da yin maganar ta yi tana jan numfashi tare da kara kurawa face ɗin Leesharh idanu. Ni kuwa nace babu rami me ya kawo maganar rami? Me ya kawo zance ba cutar da kowa zata yi ba?......🤔 Anya wannan mata ta kulla gaskiya kuwa? Anya ba so take ta kai Leesharh ta barota ba? To wai waye ma shi Ramish ɗin? Kuma meyasa take son a yi mata leƙen asiri a kansa? Me suke nema daga garesa?. "Leesharh zaki samu jin daɗin rayuwa sosai da sosai, zaki samu farinciki fiye da tunaninki, zaki sami kuɗi ki taimaki duk wanda kike so, just kawai amsa me with your full confidence that zaki iya, nasan cewa zaki iya shiyasa na zo wajenki, ban zo nan ba sai da na binciki tarihin rayuwarki, and ke ƙaramar yarinya ce, babu wanda zai yi tunanin ga abin da kika je yi a gidan, taimako fa zaki yi, wasu ne suke son cutar da shi mu kuma zamu bashi kariya ta hanyar sanin duk wani motsinsa, ta hakance kawai zamu taimakesa, kinga kema kin taimaka mashi kenan". Cike da kwarewa a iya juyar da tunanin mutun ta yi maganar, sai dai fa tana magana ne tana fargabar amsar da Leesharh zata bata, domin ta gama saka duk wani hope ɗinta tun kafin ta zo a kan cewa lallai Leesharh zata yi mata abin da take so, amfani zata yi da karantar shekarun Leesharh, dan tasan ƙaramar yarinya kamar Leesharh babu wanda zai yi tunanin leƙen asiri ta je yi, da alama wutar ɗaukar fansa ne yake ruruwa a cikin zuciyarta, shi ne kuma take son ta yi amfani da Leesharh domin cikar burinta. Hmmmm akwai babban yaki da cakwakiya kuwa a gaba, ga shi ko face nata bata bari an sani ba, wato idan ma an kama Leesharh ita kaɗai ayi mata duk hukuncin da za'ayi mata, wannan mata bata kullah gaskiya ba, akwai babban wasa a wannan waje. "Leesharh say something now, shin kin amince?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ɗago da idanunta da suke cike taf da kwallah, muryarta na rawa, da alamar tsoro sosai a saman face ɗinta, hannayenta dukka kerma suke yi, hakan zai kara tabbatar maka da tana tsorace. Magana ta fara yi cikin rawar murya ga shi dama ba fita sosai voice ɗin nata yake yi ba, sai abin ya kara kwaɓewa. "Ni Aunty duk wata dukiya bata dameni ba, ni bana da buƙatar komai a duniyar nan da ya wuce na je naga kabarin mamata daga nan na koma ƙasarmu, ƙasarmu nake da burin na koma naje na nemo ƴan uwana da kuma mahaifina, please Aunty ki taimaka mun na koma ƙasarmu zan yi duk abin da kika ce". Wani irin nannauyar ajiyar zuciya wannan mata ta sauke da jin amsar da Leesharh ɗin ta bata, ranta ya yi haske da jin cewa Leesharh zata iya yin komai domin ta bar wannan gida ta koma kasarsu, har wani walwala ne ya bayyana a face nata, da yake tana sanye da nikaf hakan yasa ba za'a gane ba, hankalinta ya kwanta yanzu, ta samu damar da zata cinma burinta da abin da take hari a nata tunanin kenan, ko da yake bata zo wannan gidan yarin wajen Leesharh ba sai da ta shirya ta kuma san labarin Leesharh ta san da cewa zata iya aikata komai idan aka bita ta yadda ya dace, idan aka yi wasa da tunaninta, dan yarinya ce mai jajircewa a kan burinta da aikinta. "Good Leesharh, haka ake son mutun mai zuciyar jajircewa juriya da hazaƙa, naji matuƙar daɗi da ya kasance zaki yi komai domin mahaifinki, kada ki damu kina gama aiki zan mayar dake ƙasarku ba tare da ɓata lokaci ba, ai uba ya wuce wasa Leesharh, ke ɗin yar baiwa ce Allah ya yi maki albarka". Ɗan dakatawa da kalaman yaudarar tata ta yi tana kara kallon face ɗin Leesharhr, dan kowa yasan dai waɗan nan kalaman nata na yaudara ne, so take yi ta yi amfani da ƙarantar shekarun Leesharhr haƙanta ya cinma ruwa, daga gani bata ƙullo gaskiya ba. Da Amin kawai Leesharh ta amsa mata ba tare da ta ɗago da kallonta ba, tunanin a ina zata yi wannan aikin kawai take yi. "Kina jin yadda aikin zai kasance, zaki je gidan ne a matsayin ƴar aikinsu, suna da masu aiki da a kallah zasu kai mutun 50, amma dukka wannan ba damuwa bane, ni nasan ta yadda zan shigar dake gidan a matsayin mai yi masu aiki, zan saya maki sabuwar waya, ba kin iya amfani da ita ba?". Ta dakata tana jiran amsa. Girgiza mata kai Leesharh ta yi alamar a'a bata iya amfani da wayar ba. "Okey wannan dukka ba matsala bane, ni zan sanya a koya maki komai, dama ba'a haka zaki je masu ba, dan su masu yi masu aiki ma sai wanda yake da degree or diploma, ba kananan kai bane suke yi masu aiki, sai na sanya an koya maki abubuwa na a kallah wata guda, kafin nan na shirya ta yadda zaki yi ki shiga gidan, babu ruwanki da kowa a cikin gidan, ko sauran ma'aikatan gidan ban yarda ki rinƙa yi masu magana ba, kada ki yarda ki sake da kowa, muna da ma'aikata a gidan da zasu kula da ke, dukkansu manyan mutane ne da ba zasu iya shiga jikin Ramish ba, shiyasa na zaɓoki, Ramish kawai zaki saka mun ido a kansa, ban ce ki kira kowa da wayar da zan baki ba, haka zalika ban ce ki bawa kowa number wayar ba, nima kuma ba zan kiraki ba, idan ina da buƙatar yin magana dake ni nasan ta in da samu haɗu mu gana, wayar da zan baki zan baki ita ce kawai dan abu biyu, na farko domin akwai abin da zan sanya a cikin wayar dan ya tayaki aikin da zaki yi domin mu kammala da wuri, na biyu kuma wani lokaci ki rinƙa ɗauka mun Ramish ɗin a video idan suna irin tattaunawa mai mahimmancin nan, kuma da zarar kin turo mun video ki goge shi a wayar, ko da yake ma time to time zan rinƙa canza maki wayar, wannan ba abin damuwa bane na san ta yadda zan shirya komai". Ɗan dagatawa da maganar ta yi tana jiran ta ji me Leesharh ɗin zata ce. "Aunty to ni da nake matsayin ƴar aiki ya za'ayi na iya sanin lokacin da suke tattaunawa mai mahimmancin? Kuma ai idan zasu yi tattaunawa ba'a ko'ina zasu yi ba ko? In dai haka ne ya za'ayi na san in da zasu yi tattaunawar?". Ɗan ƙaramin tsaki ta ja kafin ta cigaba da cewa. "Aikin da zan samo maki ba kamar sauran ƴan aikin gidan bane, an gaya maki a banza na zaɓeki ne? Akwai dalilan da yasa na zaɓeki wadda ban gaya maki ba, kina da kyau, kina da diri da sai an tara mata 100 ba'a sami goma masu irin dirinki ba, da wannan zamu yi amfani mu sanya shi ya saki jiki da ke ko kuma ku sami kusanci sosai har haƙanmu ya cinma ruwa". Shiru Leesharh ta ɗanyi, abinku da kananan shekaru, sai bata kawo komai a ranta ba, bata ma san waye zata yi wa wannan shisshigin da leƙen asirin ba, ita dai tun da ance mata taimako zata yi ai shikenan, bata san me za'ayi mashi da ake buƙatar sanin duk wani halin da yake a ciki ba, ita dai burinta na son komawa ƙasarsu ya rufe mata idanu da har take jin cewa tabbas zata iya yin komai a kan hakan.... Babbar magana, in kuwa haka ne akwai kura ba kaɗan ba. "Tunanin me kike yi Leesharh?". Ta faɗa a ɗan tsorace, tana tsoron kada Leesharh ta ce ba zata iya ba ko ta karaya. Girgiza mata kai ta yi tana faɗin. "Bana tunanin komai". Kada ku mance duk maganar da Leesharh zata yi sai wannan mata ta ɗan ɗauki lokaci mai ɗan tsawo tana jujjuya maganganun a cikin ranta, dan ta fahimci abin da Leesharh ɗin ta faɗa da kyau da kyau, na gaya maku maganar tata ne baya fita sosai, hakan yasa ba'a gane me take cewa sosai. "Kada ki yi tunanin komai my sister, ba wani abin da zai faru In Sha Allah, zaki gama wannan aiki lafiya ki kuma koma ƙasarku wajen babanki da ɗinbi dukiya sosai lafiya lou, ba zan bari wani abin ya sameki ba, na yi maki alkawarin, ki yarda da ni taimakon zaki yi". "Na yarda dake Aunty, na kuma yarda da duk abin da kika faɗa, sannan na yarda da zan yi maki wannan aiki". Wani irin cool ajiyar zuciya ta sauke jin kalaman yarinyar, sai kuma ta ɗan ji wani irin yar a ranta, ba komai bane yasa ta ji hakan face tasan da cewa in dai asirin Leesharh na leken asiri ya tuno to ba makawa kasheta zasu yi har lahira, hakan yasa ta ɗan ji wani iri a cikin ranta, amma da yake abin da suke buƙata kuma yake a gabansu suna ganin cewa yafi ran Leesharh ɗin mahimmanci, sai ta saki wani irin shu'umin murmushi tare da cewa. "Tom shikenan jeki ɗakinku ki shirya ki kuma yi bankwana da kawayenki anjuma zan dawo na ɗaukeki mu tafi". Yadda ta yi maganar with her full confidence sai ka rantse da Allah ba'a gidan yari Leesharh take ba, wai zata dawo ta ɗauketa kamar ba ita aka yankewa hukuncin kisa ba, hakan na nufin koma wacece wannan mata ba kananan mutane bane, dole manyan kai ne suke ƙoƙarin tura Leesharh ga halaka. Miƙewa Leesharh ta yi jiki ba kwari, dan yunwa take ji sosai, da kyar take iya jan kafafun nata ta nufi kofar da zai mai data izuwa ɗakinsu. Da idanu matar ta bita da shi tana yi mata wani irin kallo mai wuyar fassaruwa. Har ta kai tsakiyar office ɗin, sai kuma ta juyo tare da cewa. "Aunty a gidan waye zan yi aikin?". Wani shu'umin murmushi ta ɗan saki kafin ta ce. "A gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen zaki yi aiki". Jinjina mata kai kawai ta yi da yake ita ba ƴar ƙasar ba ce, bata san wanenen Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen. Wucewa ta yi ta nufi waje ranta fes zata fita daga wannan gida a yau. Nannauyar ajiyar zuciya wannan mata ta sauke kafin ta ce. "Lokacin ka ya fara daga yanzu Ramish, time ɗimu ya yi". Ta yi furucin nata a fili, cike da farinciki tare da full confidence sosai ta yi furucin nata. Ita kuwa Leesharh sai murna take yi ta koma room ɗinsu. A yadda ta bar Jasrah haka ta dawo ta sameta, ta buga uban takumi tana tunanin ina aka kai Leesharh. Tana ganinta ta yi maza ta miƙe tsaye, nan take farinciki ya bayyana a samar face ɗin tata, har wani ƴar murmushi ta sakar mata kafin ta ce. "Alhdulillah nagodewa Allah da yasa ba ɗaki suka sauya maki suka rabani dake ba. A hanzarce Leesharh ta ƙariso ta zo ta rungumeta tana murnar lokacin fitarta daga gidan ya yi. "Leesharh is there any good news? Naga like you're so happy like ba yadda kika fita ba, ke matsalar ma baki yin dariya bare mutun ya iya fahimtar kina cikin farinciki or not, amma dai a haka nake son kayata, baki dariya ko kina dariya dukka abu ɗaya na sani shi ne i really like you". Wani irin faɗuwar gaba Leesharh ta ji na jin kalaman Jasrah, ba yau ta fara jin kalaman da suka fi haka daɗi da kyau daga gareta ba, amma na yau ɗin sai ta ji sun ɗaga mata hankali kuma sun jefata cikin damuwa, sai yanzu ta tuna cewa zasu rabu da Jasrah kenan? Shikenan ita zata fita ta bar Jasrah? Kuma nan da one year kashe Jasrah kenan za'ayi? Ba zasu sake haɗuwa ba? Sun rabu kenan har abada?. Ya ilahi ya lillilahi, a duniya duka bayan iyayenta babu wanda ya taɓa nuna mata tsantsar kauna tsakani da Allah kamar yadda ƴar tahaliƙan nan Jasrah ta nuna mata, bata taɓa zama da yarinyar kirki biyun Jasrah ba, yarinya so silent, ga hakuri da tawakkali, ilimin addini da yin aiki da shi, nutsatsiya, ta nuna mata kauna kamar ƴar uwarta na jini, wani lokaci har a baki take bata abinci idan ta ki ci, shikenan yau alaƙarsu zata zo karshe na har abada?. Wani irin sara mata ta ji kanta ya yi, nan take murnarta ya rikiɗe izuwa bakin ciki, damuwar da bata taɓa shiga makancinsa bane ya lulluɓeta, nan take ta ji wani irin karayar zuciya ya dira mata a ranta, idanuwanta ne suka yi wani irin ciwowa da kwallah tab, nan take kuma idanun nata suka yi jajir kamar wuta. Sai tambayarta Jasrah take yi akwai labari ne suna a rungumi da juna, amma ina Leesharh ta ƙasa yin magana, sai ma wani irin ciwo da nauyi da kanta ya yi mata, ji take yi kamar kan nata zai faɗi ƙasa. Jin alamar saukar hawaye a saman shoulder ɗinta ne yasa Jasrah ta yi saurin raba jikinsu domin taga face ɗin Leesharh ɗin da kyau. Su Sarah dai sai binsu da kallon walaƙanci suke yi, sun tsani Leesharh a rayuwarsu yaran nan, babu abin da ta yi masu, kawai bakar zuciya ce irin tasu. "Subhanallah Leesharh what's happening? This tears is for what?". A ruɗe ta yi tambayar tata, tana magana tana zaro idanu, alamar tana ɗan tsorace, dan ita ma bata jin zata iya rabuwa da Leesharh a yanzu, duk da cewa tasan lokaci ƙalilan ne ya rage mata a duniyar ma bakiɗaya, amma bata sanya a ranta zata rabu da Leesharh a yanzu ba, ta fi yin tunanin kasheta da za'ayi ne kawai zai rabasu. Zama a gefen bed ɗinta Leesharh ta yi tare da buga uban tagumi, kan kace me har hawaye sun jike mata fuska, sai simtiri suke yi, sun wanke mata fuska sosai, wani irin kukan zuciya ma da take yi tun da uwarta ta haifeta bata taɓa yin irinsa ba, sai dai kuma duk da haka bata jin akwai wani abin da zai dakatar da ita daga fita wannan gida, tana son ta koma wajen ƴan uwanta, ba zata iya hakuri da mahaifinta tare da ganin kabarin mamarta saboda Jasrah ba, haka zalika bata jin kuma kamar zata iya rabuwa da Jasrah ɗin. Tashin sense, dole kuma a ciki ta ɗauki ɗaya. A ruɗe Jasrah ta zauna a kusa da ita, duk ta rikice tana son ta ji me ƴar uwar tata take yi wa kuka? Me yasameta ko me suka ce mata a office ɗin da ta je. Shoulders ɗinta ta rungumo tana mai cigaba da faɗar subhanallah. Da taga dai Leesharh ba zata iya gaya mata me suka ce mata ba, dan yarinya ce mai zurfin ciki, sai ta yanke shawarar bari ta yi mata nasiha wata kila idan nasiha ya ratsata zata sami nutsuwa har ta gaya mata abin da yake faruwa, a nutse ta fara magana kamar haka. "Leesharh duk tsanani yana tare da sauki, duk abin da yake da farko dole yana da karshe, kuma ki sani duk wata second ɗaya da zata wuce a rayuwarmu Ubangiji baya barci yana sane damu, ni bansan me suka ce maki a cikin office ɗin ba, amma dai koma menene nasan ba mai daɗin ji bane, dan abin da yake sanyaki kuka ba ƙaramin abu bane, to koma dai me suka ce maki ina son ki yi hakuri ki fawwalawa Allah al'amuranki, da sannu zai yi mana sakayya, ni har cikin zuciyata ban taɓa yarda da cewa ke kika kashe Oummunki ba, kin kuma ki gaya mun gaskiya yau tsawo shekara guda kenan, amma dai koma me Allah ya fimu sanin dai'dai da ba dai'dai ba da kuma abin da ya dace damu, shiyasa na miƙa mashi ragamar rayuwata, ni bance dole sai kin gaya mun abin da suka gaya maki ba, abin da nake so dake kisani a nan shi ne komai ya yi zafi koda ya fi wuta zafi to maganinsa Allah, duk abin da suka ce maki idan alkhari ne a gareki Allah ya tabbatar maki, idan kuma sharrine to Allah ya wargazar da shi, amma please ki dai'na wannan kuka, mu yi addu'a komai zai koma dai'dai da izinin Allah". Ta kai karshen maganar ita ma idanunta suna cikowa da kwallah. Sosai Leesharh ta samu saukin raɗaɗin da take ji a cikin zuciyarta da jin kalaman Jasrah. Haƙiƙa duk abin da Jasrah ta faɗa gaskiya ce, hakan take babu wata tantanma, sai ta ji ta ɗan sami kwarin gwiwar da zata iya gaya mata abin da ya sanyata kuka, dan haka sai ta kai hannu ta goge hawayen da suke a saman fuskarta, cikin voice ɗinta kamar wata yarinya yar shekara huɗu a duniya ta fara korawa Jasrah bayanin abin da yake faruwa daga farko har karshe kamar yadda wannan mata ta gaya mata da yadda suka yi dukka. Da Aaradiya da Sarah sun mayar da su Tv na kallo, kallonsu kawai suke yi babu kyafta idanun, tunani kawai suke yi da ace sune suka sami wannan damar mana, ai da shikenan komai shar abinsu su bar gidan. Shiru Jasrah ta yi tana sauraronta, har sai da ta kai aya a maganar tata, tana yi wasu hawaye suna ƙara bin ƙuncinta sosai. Da yake Jasrah babu mugunta ko ɗigo a ranta, ita ɗin tana sowa ɗan uwanta abin da take sowa kanta ne, sai ta saki cool murmushi ga ragowar hawaye a fuskarta. "Leesharh ai wannan abin farinciki ne bana kuka ba, ke da zaki fita daga wannan gida, kuma ke da zaki koma wajen iyayenki da ƴan uwanki, to me abin kuka? Ai godewa Allah ma zaki yi sosai, alwala yakamata mu tashi mu yi dan mu nunawa Ubangiji murnarmu, Addu'arki ce ta karɓu wata kila". Tana magana ne da dukka iya gaskiyarta, tabbas zata sha kukar rabuwa da Leesharh, kuma zata shiga damuwar da bata taɓa shiga ba, domin da ita kawai ta saba a gidan, amma kuma hakan ba shi zai sanya ta tauye gaskiya ko ta hanata cigaba saboda son zuciyarta ba, sam ba haka take ba ita. Wani irin confidence Leesharh ta kara ji ya dira mata, sai ta ji kaso sittin na damuwar da ta shiga duk ya gudu, ta lura da cewa tabbas Jasrah ta shiga damuwa, amma kuma ta yi ƙoƙarin danne damuwar tata dan kada ta sarewa Leesharh ɗin gwiwa. Aaradiya da Sarah da yake bakaken zuciya ne da su, kuma basu son Leesharh ta fita gidan ta barsu, sun fi son a kashesu a tare kamar yadda aka yanke masu hukunci tun farko, sai abin ya sosa masu rai over, nan take suka ji koma ta halin ƙaƙa ba zasu bari Leesharh ta fita ta barsu su a kashesu ba, dan haka har suna haɗa baki wajen cewa. "Ke Leesharh baki da hankali ne da zaki yarda da wannan mata? Wlh kada ki yarda da ita, kila ma kasheki zata je ta yi, gara maki ki zauna a nan wlh yafi maki". Da yake ita Jasrah ta fisu shekaru kuma ta fisu wayo da ilimi, sai ta fahimci in da suka dosa, ta ganosu hassadace kawai take cinsu, dan haka sai ta ce. "Da can baya babu wadda ta taɓa bawa Leesharh shawara a cikinku ko? Kuma babu wadda ta taɓa yi mata maganar da zai amfaneta ko? Babu wadda ta taɓa shiga harkarta a cikinku ko? Sai yanzu ne kuke ganin yakamata ku bata shawara kenan?". Da yake Leesharh har yanzu da sauranta, yarinta yana a kanta sosai, sai taga kamar amsar da Jasrah ta basu bai dace ba, a wawtarta ita gani take yi ai sonta suke yi tun da har suka bata shawara. Wannan shi ne da gaske ne ta yaro kyau take yi bata ƙargo. Wani kallon uku saura kwata Aaradiya ta wurgawa Jasrah ɗin kafin ta ce. "To uwar kanzagi, ai da yake sunan Jasrah muka kira ba Leesharh ba, ina ruwanki da mu? Dole ne mu bata shawara dan munga zata faɗa halaka". (Ni kam na ce su shawara manya, Aaradiya manyan kasa😅🥱) A takaice Jasrah ta amsa mata da cewa. "Ko kuma dan kunga zata fita ba za'a kasheta ba, zata fita ta barku ba, shi ne hankali duk ya bi ya tashi". A harzuƙe Aaradiya ɗin ta miƙe zaune, nan take ta hayyako da hayakin masifa kamar wadda dama take wuya tana jiran kiris ta zazzageta. Jasrah bata sake bi ta kanta, ba kuma ta sake maida hankali ta saurari hayakin masifar da take barbalo masu ba, ta toshe kunne tare da maido da hankalinta a kan Leesharh da take ta faman binsu da idanu. "Leesharh baki gaya mun a gidan waye zaki yi aikin ba? And kuma baki gaya mun wasu irin bayanai na mutumin zaki kwasa ki bawa wannan mata ba, sannan ina son kafin ki tafi ki gaya mun kasar da kike da sunan iyayenki ko da baki bani labarinki ba, zan gayawa kanwata Alveena idan sun kawo mun ziraya watarana ko bana raye ta je ƙasarku ta kai maki ziyara idan ta girma". Duk wata zuciya mai tausayi sai ta tausayawa Jasrah a wannan gaɓa, sai ta ji wani irin mugun tausayinta, saboda daga jin yadda ta yi maganar kasan kawai ta ƙaƙalo ta ne dan dole, daga jin muryarta kasan e lallai tana cikin matsananciyar tashin hankali da damuwa. "Aikin da zan yi mata ta ce mun duk wasu motsi nasa tana son ta rinƙa sani, kamar in da zai je da kuma idan ya fita gida, yaushe yake fita? And kafin ya fita tana son sani? Yaushe yake dawowa gida, and idan ya dawo gida ma tana son ta sani da dai sauran dukkan motsinsa, and duk wani muhimmin tattaunawa da zai yi da ma koma waye shi ma tana son ta sani, iya aikin da zan yi mata kenan, batun wajen da zan yi aikin kuma ni ban san a ina bane, ban san wani gida bane, ni dai ta ce mun gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen, so ban san waye shi ba, sai dai ta kaini na gani, batun iyayena da ƴan uwana kuma zan baki..........." Wani irin jan birki ta yi, ta tsaya cak da maganar tata sakamakon wani irin mimmikewa tsaye da ta ga Jasrah, Aaradiya and Sarah sun yi. Ɗan zaro idanu ta yi tana kallonsu a cike da mamaki. Ai a dubu ɗari Aaradiya ta diro ƙasa daga saman bed ɗinta, cikin sarkewar murya ta ce. "A gidan waye zaki yi aiki?". Da wani irin kallon mamaki ta bita da shi kafin ta maimaita mata kalmar gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen. Wani irin kara Aaradiya ta fasa kamar wadda aka tsinkawa mari, sai kuma ta sake cewa. "Tab Allah ya bada sa'a, ai Leesharh ki je kawai abinki, ashe banza muƙa ɓata bakinmu wajen baki shawarar karki je ma, ai baikamata mu hanaki tafiya ba, ni yanzu ba zaku sake jin bakina a wannan case ɗin ba, lastly dan girman Allah Leesharh kada ki sake yin tunanin kin sanni a rayuwarki, please koda watara za'a tambayeki wa da wa kika sani a rayuwarki ki ce ke baki sanni ba bama ki taɓa ganin mai kama da ni ba". Tana kai karshen maganar tana wuce ta haye saman gadonta. A hanzarce Sarah ta karɓi zance da cewa. "Ki haɗa da ni Leesharh, dan girman Allah ko da sunan wasa kada ki taɓa sake tunanin cewa kin sanni". Ita dai ta yi kasake tana kallon ikon Allah, daga ambatar sunan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen duk sun ruɗe haka? To waye shi?. Dafa shoulder ɗinta da aka yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka. "Jasrah wannen Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ɗin?" Ta wurga mata tambayar a ɗan ruɗe, dan ta tsorata na ganin yadda su Sarah duk suka bi suka ruɗe daga jin sunan mutumin. Wani irin dogon numfashi Jasrah ta ja tare da saukewa a hankali, shiru ta ɗan yi na a kallah mintuna uku kafin ta sake nisawa ta fara magana a nutse. "Tabbas ni ba haifaffiyar nan Dubai bace, amma kuma duk wanda ya kwana ya tashi a cikin Dubai dole zai san familyn Badeen, dole zai san wannen Shaikh Abu Abdussalam bin Badeen, magana ta gaskiya ni yanzu na ji ban ma yarda da cewa wannan mata zata iya shigar dake cikin wannan gida ba farko kenan, gidan da aka ce maki tun daga farkon titin da zai kaika cikin unguwar da gidan yake wasu mahaukatan securitys ne wadda ganinsu tamkar ganin mutuwa haka yake, ban taɓa zuwa gidan ba, amma babana yana bamu labarin gidan, ke in takaice maki ko tsuntsuwa waɗan nan securitys ɗin da da hali ba zasu bari ta gifta ta sararin samaniyar wannan gida ba, babana ya ce duniya ne guda gidan, ma'aikata masu yi masu aiki kawai sun fi mutun 50, a hakan ne zaki shiga cikinsu a matsayin mai aiki? Zaratan mata ne masu lafiya da jini a jika, mata masu kirar maza su suke yin girkin wannan gida, to ina mai tabbatar maki duk wani motsin ma'aikatan wannan gida suna sane da shi, wlh Leesharh gwara maki mutuwa a cikin wannan gidan yarin da ki je ki karɓi aikin leƙen asirin gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen, dan naratse maki da wanda rai'na yake hannunsa idan suka kamaki wani irin kisan walaƙancin da zasu yi maki ko kare ba zai shinshini namarki ba, yafi maki sauki ki tabbata a cikin nan da ki fara tunanin zuwa gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ziyara ma kawai, wannan mata da ta kawo maki wannan aiki ma sam sam babu ƙwaƙwalwa a cikin kanta, da alama mahaukaciya ce". Izuwa yanzu cikin Leesharh ya gama ɗuran ruwa, ta tsorata sosai da jin maganganun Jasrah, sai zaro idanu take yi, amma sai ta daure ta ce. "To Jasrah wanenen shi ɗin?". Da sauri Aaradiya ta ce. "Ni ne nan zan baku wannan amsa, dan ko ita Jasrah magana kawai yake yi bata san wa ake kira da Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ba, ku saurara ku ji wanenen shi ɗin. Shi ɗin ɗane ga the most powerful King of Dubai, babban Yayan Shaikh Abu Abdussalam shi ne president mai ci a yanzu, shi kuma Abu Abdussalam Defence minister ne, shiyasa securitys kala kala suka yawaita a gidansa, domin duk wani security da kuka sani a faɗin Dubai, duk wani mai kaki (uniform ) da kuka sani to dole da umarninsa zai yi aiki, a ƙarƙashinsa suke, dole umarninsa zasu bi kafin aiwatar da wani abin, yana da manyan brothers har guda uku masu rike da manyan muƙamai masu karfin faɗa a ji a duniya bakiɗaya, amma babban yayansu baya kasar nan ma bakiɗaya, King of Dubai ƴaƴansa maza biyar ne mace ɗaya ita ce Gimbiya Rahilarh (Mommar Zunaira) ita ce kuma auta, su Abu Abdussalam bin Badeen duk yayyunta ne, Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen matarsa ɗaya yayansa uku, mata biyu namiji ɗaya, wannan shi ne kaɗan daga cikin labarin gidan da zaki je leƙan asiri, familyn da manyar ƙasar nan suke tsoron haɗa hanya da su, sai dai muce Allah ya bada sa'a yasa ki samu mutuwa mai sauki a hannunsu......" Tana rufe baki Jasrah ta karɓi zancen da cewa. "Wlh Leesharh gara maki ki mutu a cikin wannan gidan yarin da ki mutu a hannun ƴan gidan can in suka kamaki, tab akwai ma wanda ya isa ya shiga gidan leƙen asiri ne?! To wlh ki shafawa kanki ruwan sanyi, meyasa ita matar bata je ta yi aikin da kanta ba? Sai ke zata saka bakar muguwa azzaluma! Kuma meyasa ba zata saka maza manya ko kuma mata manya ba? Sai ke ƴar ƙaramar yarinya? Ai naga manya ne ma zasu yi mata abin da take da buƙata daidai, sune suke da girman da sun san ta yadda zasu zulle kada a kamasu". Sosai Leesharh ta kara tsorata over, muryarta na rawa ta ce. "Ni ai kinga ta ce mun taimakonsa zasu yi, wai wani ne ma yake son cutar da shi su kuma zasu taimaka mashi, kuma ta ce mun wai manyan maza ko mata ba zasu iya samun damar shiga har cikin gidan ba bare su sami kusanci da shi, da alama baya yarda da kowa, amma ni karama ce babu wanda zai yi tunanin leƙen asiri na je yi, zasu yarda na shiga cikin masu aikin da suke aiki a can cikin gida ba tare da wani damuwa ba haka ta ce mun". "Hmmmmm Leesharh ya tabbata baki da hankali, waye ya ce maki taimakonsa suke son yi? Idan har taimakonsa suke son yi menene na neman information a kan duk wani motsinsa? Su fito mana kai tsaye kawai su sanar da shi cewa ga wani zai cutar da shi in gaskiya ne, wlh babu wani taimakonsa da zasu yi face cutarwa, sannan maganarki gaskiya ce da kika ce ke kamar yarinyar ce ba wanda zai kawo wani bad tunani a kan ki, kuma za'a iya barinki ki shiga cikin ma'aikatan da suke aiki a can cikin gidan, amma ki sani hakan ba mai ɓulle maki bane wlh, dan yadda kika san aljanu haka familynsu suke, kin san takun sakar da ake bugawa da su a duniya kuwa? Kin san adadin makiyan da suke son kaisu kasa kuwa? Ta ko'ina tarin makiya suke da shi sakamakon riko da gaskiya da suke da shi, suna sane da tarin makinyan su, a haka kuma kuke tunanin zasu yi zaman shiru har wani ya iya shiga cikin ya leƙa asirinsu? Lallaima Leesharh na tabbata makiyan familynsu ne suke son yin amfani dake dan cinma burinsu, ki sake yin tunani da kyau, na tabbata sun hango cewa amfani dake zai basu nasara ne yasa suka buƙaceki, wlh idan kika shiga hannunsu ina gaya maki gawarki ma ba za'a gani ba, mahaukatan karnikan gidan ne kawai zasu cinye namarki ɗanya, wata ƴar figaggiya dake a wajen ne zaki ce zaki je leƙar asirin shegun duniya ko?". Shiru Leesharh ta yi, gabaɗaya ta shiga ruɗani kanta ya ɗaure, duk ta rasa me yake yi mata daɗi, yanzu ya zata yi?..... Masu karatu ku bawa Leesharh shawarar ya zatayi, shin ta yarda ta yi wannan aiki ne ko kuma ta hakura a kasheta a wannan gidan yarin kawai? Ni dai bari na leƙa su Kamran namu na amana mu gani, wata kila kafin mu dawo Leesharh ta samu mafita, amma kam tana ruwa kusa da kada..........🥱 🏞️FOREST🏞️ Kamran ba dan ya so ba ya tashi Sweetie daga barci, dan su koma gida, saboda ya haura lokacin da yake komawa, ya tabbata idan ya ɗan kara ƴan mintoci Mamma zata fito nemansa, dan haka sai ya tashi Sweetie daga barci, ita kuma Pretty sai dai ya ɗauketa cak, dan san kai irin nasa sai bai tasheta daga barcin ba, ko da yake abokiyar rigimarsa ce, ba son kai bane...........😅 Hannun Sweetie ɗin ya riko bayan ya saɓa Pretty a saman shoulder ɗinsa, da haka suka nufi maɓoyar tasu, ya bar Rocky a wajen yana aikin zuba barci, yasan duk lokacin da ya tashi daga barcinsa zai komo gida. Da kyar ya iya shiga da Prettyn cikin wannan rami, sai barci take zubawa, da alama yau barcin nata ya yi nauyi sosai. A saman gadon nasu ya kwantar da ita, ita kuma Sweetien ya zaunar da ita a bakin bed ɗin, ba tare da ɓata lokaci ba ya yi maza ya kama hanya tare da yi wa Sweetie sallama. Kai tsaye gida ya nufa, bai sake bi ta kan Rocky ba, sai sauri yake ta zuba wa kada Mamma ta yi faɗa. Yana shigowa cikin ƙogon nasu ya wuce ɓangarensa, tunanin Pretty ce kawai a cikin zuciyar tasa. "Mamma where are you?". Ya faɗa yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa. Mamma dake wajen madafarta tana ta aikin soka nama a jikin itace tana saƙalewa a saman dutsen, ta amsa mashi da. "Sai yanzu ka dawo ko?". "Kai Mamma ban fa jima ba". Wasu duwatsu guda biyu ta ɗauko masu karfi tare da fara ƙoƙarin kunna wuta ta hanyar haɗa duwatsun tana bugawa, suna bada wuta. "Ba shakka kam baka jima ba, kazo ka ɓare ɓawon masaran nan". Tana magana tana ƙoƙarin kunna wuta da waɗan nan duwatsun. "Am coming Mamma, but before na zo let me ask you something, dan na ƙagu na ji amsar, abin yana damuna". Yana magana yana cire kayan jikinsa. "Okey ina jinka sarkin tambaya". Ta faɗa tare da ɗauko wani tukunyar ƙasa ta ɗaura a saman wutar da ta kunna ɗin, sannan ta duba ruwa ɗan dai'dai misali. "Mamma this two dys am feeling something da ban san ya zan gaya maki ba, ban taɓa jin hakan a jikina ba sai this time around, and hakan yana faruwa ne...............🥱 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________27🔥 "Mamma this two dys am feeling something da ban san ya zan gaya maki ba, ban taɓa jin hakan a jikina ba sai this time around, and hakan yana faruwa ne if i........... " Sai kuma ya ja birki da yin maganar, saboda ya kasa iya ƙarisar da cewa hakan na faruwa ne idan ya taɓa wata mace ba ita ba. Da yake ita Mamma tasan wani lokaci questions ɗin da yake yi mata ba wasu masu amfani bane, kawai ya sanyata magana ne, sai da ta ji ya yi shiru bata sake bi ta kansa ba, ta cigaba da aikin girkinata na dare, ga nama da take gasa masu a gefe, namar gwanin ban sha'awa, kana gani sai ha kaɗiyi yawu. Shi kuwa kammala cire kayansa ya yi tare da nufar in da zai yi wanka zuciyarsa a cike tab da tunanin yadda zai yi da mamma ta gaya mashi menene yake damunsa ba tare da ta san cewa jikin wata ya taɓa ba, a nasa tunanin gani yake yi bashi da lafiya ne, kada kuma ku manta Mamma babbar likitar gargajiya ce, shi ne ma dalilin da yasa yake son ya tambayeta ko akwai wani magana da zata taimaka ta bashi.......... E lallai ni kuwa nace zaka ga magani...😅 Wankarsa ya je ya yi tare da fitowa ya shirya cikin wasu haɗaɗɗun kayansa masu matuƙar kyau, tas tas da su, Mamma ba dai tsabta ba, shi ma Kamran a yadda ta rainesa kenan, baya kaunar datti ko kaɗan, suna da tsabta sosai da sosai. Itatuwan da take saƙar kayan sakawa irin na mutanen da ya ɗauko tare da audigar da take saƙawa ya nufo waje gabaɗaya, bai je in da take ba, sai tubka da warwara a cikin zuciyarsa yake yi, yana ta saƙa ta yadda zai yi mata ta gaya mashi me yake damunsa?. Can wata dabara ta faɗo mashi ya gaya mata yanayin da yake shiga kawai ba sai ya ce mata wata ta taɓa shi ba, tuna wannan dabara yasa ya ɗan saki face ɗinsa keɗan. Kafa itatuwar sakar tata ya yi tare da zama a saman wata dutse da Mammar tasa take zama idan zata yi saka, shi ma izuwa yanzu ya iya sakar sosai, so ya ɗauko ne domin ya saƙawa Pretty sket da riga masu shegen kyau, bai taɓa saƙa kayan mata ba sai nasa, yau ne farau, so ya sanya a ransa idan ya saka ta yi kyau sai ya sakawa Sweetie ma, idan kuma bata yi kyau ba sai ya hakura. Yasan ba yanzu Mammarsa zata fito waje ba, zai iya kammala saƙa sket ma Mamma bata leƙo ba, dan tana girki, idan ta kammala kuma wanka zata yi ta gyara madafa da sauran sassa na cikin ƙogon, so sai can yamma sosai zata fito, yasan cewa yana saurin yin sakar shiyasa bai ji tsoron kada ta fito ta same shi yana saka kayan mata ta tambayesa waye zai sakawa ba, bai wani damu ba, a hanzarce ya fara saka mata sket, dan shi ya fi girma da cin lokacin. Sai dai fa yanayi kuma yana fargabar kada Mamma ta faɗo mashi babu wani excuse. Sam ya manta Mamma ta ce ya zo ya ɓare mata masara, da dai baya mantawa da maganar Mamma komai ƙanƙantarta, yanzu kuma su Pretty sun shigo cikin tunaninsa da ƙwaƙwalwarsa suna raba mashi hankali gida biyu, har ya fara mancewa da wasu kalaman Mamma, duniya kenan. Da sauri sauri yake sakar kamar wani mara gaskiya. Sket ya saƙa mata white color, dan Mamma bata rina audigar ba, farace kawai, sket ɗin ya yi masifar kyau, sai dai ɗan guntu ne da ba zai wuce mata gwiwowinta ba, kamar umbrella ya yi yanayin design ɗin sket ɗin, ta yi kyau sosai. Cikin sauri ya cireta ya sake mayar da audigar ya fara sakar sket ɗin Sweetie ma. Good one hour ya ɗauka yana yi, iri ɗaya dana Pretty ya sakasu kamar yadda yaga Mamma tana yi wa kanta, sai dai nata manya ne har kasa take yi, shi kuma ya yi masu ƙanana, dan yana ganin kamar zata iya kai masu kasan gwiwa kaɗan. Rigar Pretty ya fara saƙawa kamar yadda ya fara da sket ɗinta, yana yi yana fargabar kada Mamma ta fito ta same shi yana sakar mata, dan ma ya kwashe skets ɗin ya kai cikin ɗakinsa ya ɓoye, idan Mamma ta gani ta tambayesa kayan waye bai san me zai ce mata ba, bashi da amsa, hakan yasa ya kwashe skets ɗin ya kai room ɗinsa. Yana kammala rigar Pretty ya jiyo motsin Mamma tana shirin fitowa, ta kammala duk wasu ayyukanta da ta saba yi, a hanzarce ya cire rigar daga jikin itatuwar ya cusata a cikin rigarsa ya ɓoyeta a wajen plat tummynsa, sannan ya saka wata audiga ya kama sakar hula ta karya. Wasa wasa Kamran ya fara koyan karya tun bayan haɗuwarsa da su Pretty, ya kuma koyi ɓoyewa Mamma abubuwa saɓanin da can baya kafin ya haɗu da su Pretty, sam baya ɓoye mata komai. Sarai Mamma ta lura da cewa yana ɓoye mata abubuwa da dama, amma ta zuba mashi idanu ne tana son taga gudun ruwansa, abinku da uwa kuma abin da bai saba ba, bai saɓa ɓoye mata komai ba, rana tsaka ya koya harda karya kunga kuwa dole ta fahimci canzawar ɗan nata, da yake ita macece mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira sai bata wani damu ba tana bin komai daki daki taga iya ina abin zai kaita. Shiru ta tsaya a bakin kofar fitowa daga kogon tana kare mashi kallo, ta zuba mashi idanu tamkar mai nazarin wani abin a face ɗinsa. Sarai yasan da tsayuwarta a wajen, amma sai ya yi kamar bai sani ba, tamkar bai ji motsinta ba, saboda kada ta fara zarginsa, yasan halinta sarai. Ta ɗauki a kallah good 10 mins tana kallonsa babu ko kyaftawa, shi kuma ya zage yana ta saƙa hula ta karya kamar bai san da ita a wajen ba. Haƙiƙa wannan kallo da take yi mashi kallo ne da ya ƙunshi abubuwa da dama, kallo ne da ya ƙunshi abubuwa da ba zasu fassaru a bakin wani ɗan adam ba face ita, yanayin fuskarta ya nuna cewa da akwai abin da take tunani sosai da ta tsare shi da ido haka. "Kamran". Ta ambaci sunansa in a low voice sosai. Sarai ya ji kiran nata, amma sai ya yi kamar bai ji ba, saboda idan ya nuna ya ji zata fahimci cewa lallai akwai wani abin, zata ce kenan yasan da tsayuwarta a wajen. Da yake shi ma ba tayan baya ba wajen basira, ya ganota, wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya. "Kamran". Ta sake ambatar sunansa da ɗan ɗaga murya kaɗan. Sai da ya dai'dai ta nutsuwarsa ta yadda ma kada ta gano shi ya yi sakar mata ko ya ɓoye kayan mata a jikinsa, kafin ya juyo da kallonsa a kanta. "Mamma why are you standing there?". Ya faɗa cikin nutsuwa. Shiru ta ɗan yi kafin kuma ta ce. "What's wrong with you?". Ta yi maganar ne tana kallon cikin kwayar idanunsa da suke ja a yanzu saɓanin a baya da ta san idanunsa farare ne tas. Wani littafi da ya taɓa karantawa a cikin takardun da take koya mashi karatu ne ya faɗo mashi a ransa, Kamran ya iya reading sosai kamar ba girman Forest ba, Mamma ta koya mashi, tunawa da wani part na short story of love da ya karanta a cikin littafin ya yi, nan take ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ɗan kwaɓe fuska ya ce. "Now Mamma kin daina damuwa dani, kina gani na dawo ban ci abinci ba amma ko ki damu, before fa har a baki kike bani abinci idan nace ba zan ci ba". Wannan magana ba daga zuciyarsa ta fito ba, a cikin wannan littafi ya tuno da ita. "Yanzu dai tambayarka na yi what's wrong with you ba wai cewa na yi ka gaya mun na damu da kai or not ba". Ta bashi amsa tare da ƙarisowa in da yake. "Kanaso ka doje mun ko Kamran? Me kake ɓoyewa?". Ta yi maganar tare da cire hular da yake a kansa, nan take uban tulin gashin kansa ya watse har bayansa, bashi da mai yi mashi aski bawan Allah, Mammar ce take datse mashi gashin nasa da wuƙa idan ta yi yawa sosai, ga shi kuma da halittar gashi sosai, ya fi mata dayawa gashi, ga gashin nasa a kwance luf yana sheƙi. Tara mashi kashin nasa ta fara yi tana son ta haɗa ta ɗaure waje guda sai ta ɗauko wuƙa ta rage mashi tsawonsa, dan ta lura ya yi tsawo sosai har izuwa bayansa, hakan yana sanya shi ƴar rama, ita kuma bata son hakan, ta fi son ta gansa ɓul ɓul da shi, wannan dalilin yasa take datse mashi gashin a kai a kai. "Mamma this two days ina jin canji a jikina sosai, sometimes ina jin kamar sanyin zazzaɓi yana ratsani, and kuma......" Sai kuma ya yi shiru ya kasa iya gaya mata karshen maganar na cewa gabansa yana tashi ba kamar da ba, bai san me zai ce mata ba. Sarai ta gane me matsalar tasa tun ma kafin ya sanar da ita, tun ba yau ba ta fahimci yana da karfin sha'awa sosai, sai dai ta zuba mashi idanu ne kawai domin ta ga ko zai iya gane wa ko akasin haka, bata yi zaton zai tunkareta ya tambayeta ba, saboda tasan yana da kunya sosai, ba komai yake iya yin magana a kai ba, yanzu ma idan da yasan menene wlh ba zai yi magana ba bawan Allah. "Baka barisar da maganar ba ai, and kuma me?". Ta yi maganar cikin zolaya. A hanzarce ya ce. "Mammaaaaaaaaa zaki fara ko? Na san kin gane me nake nufi fa, because i know who's my mother, ke ɗin special ce, just kawai ki gaya mun ganyen da zan ciro maki ki haɗa mun maganin, dan gaskiya abin yana damuna". Ya kai karshen maganar tare da juyowa suna fuskantar juna. "Ni babu wani abin da na gane, ni likita ce?". Ta yi maganar tana ƙoƙarin barin wajen ta koma cikin ƙogon, dan ta ɗauko wuƙa ta zo ta datse mashi gashin nan nasa. Cikin hanzari da zafin nama ya riƙo hannayenta cikin nasa. "Mamma wai yanzu kin dai'na sona ne? Kwata kwata baki kulani sosai". "Kai da ka girma ni yanzu wani kula ka zan yi? Yanzu fa ka gama mun bayanin lallai da gaske ka girma, shi ne kake son kulawata kuma? Ai sai dai ka kula da ni yanzu". Ta bashi amsa tana ɗaga mashi gera guda. Ƴar murmushi ya sakar mata kafin ya miƙe cike da so da kuma kaunarta ya rungumeta a jikinsa, cikin dabara ya zame rigar Pretty da ya ɓoye a wajen plat tummynsa ya mayar ta bayansa, dan kada Mamma ta ji ya ɓoye abu. "My Mamma you're my world, you're my happiness, you're my everything, ina kaunarki sosai". Ya faɗa yana kwantar da kansa a saman shoulder ɗinta. "Kamran this two days ɗin nan kana yin abubuwan da ban saka ka ba sosai". Ta faɗa tare da raba jikinsu ta nufi cikin ƙogon. Da sauri shi ma ya nufi ɗakinsa domin ya ajiye rigar na Pretty ya fito, zuciyarsa cike tab da tunanin maganar Mamma na cewa kwana biyun nan yana yin abin da bata sanya shi ba, me hakan yake nufi? Duk sai ya bi ya tsargi kansa, ya afka duniyar tunani. Kun san ance mutun idan bashi da gaskiya ko yana ɓoye wani abin to fa haka yake, kome zai gani sai ya rinƙa zargin kansa, yanzu dai ita Mamma bada wata manufa ta yi maganar nan ba, hasali ma ta yi mashi harshen damo ne a maganar, abin da take nufi shi ne kwana biyun nan baya yin abin da take saka shi, kunga ɗazun ta ce ya ɓare masara, amma bai yi hakan ba ya zauna saka kayansu Pretty, jiya ta ce ya kawo masu fruits, ya fita ya je wajensu Pretty ya yi zamansa ya manta, kuma da zai dawo ma bai ciro ba, and ya dai'na kawo masu nama a kai a kai, to shi ne harshen domon da ta yi mashi na baya yi mata abin da ta saka shi, amma da yake shi yasan yana ɓoye wani abin, duk sai ya tsargu ya ruɗe yake ganin kamar ta gano shi ne. "Kamran lafiyarka kawa?". Voice ɗinta ya daki dodan kunnuwarsa. Ƴar razana ya yi tare da amsa mata da ba komai. Sam bata son ta fara zarginsa a kan komai, amma zuciyarta ta kasa yarda da canzawar da ya yi kwana biyu, sai take jin lallai akwai abin da yake ɓoye mata, shekaru ashirin da biyar suna a tare bata taɓa ganin canji a tattare da shi ba sai wannan karon, kunga kuwa dole ta damu. Cike da tunani a zuciyarta ta fara datse mashi gashin kan nasa da kakkaifar wukarta. Shi ma duniyar tunani ya luluƙa, amma fa tunanin Pretty yake yi, face nata yadda take barci a saman shoulder ɗinsa ɗazun kawai yake gani tana yi mashi gizo. Sam bai san lokacin da ya furta sarkin rigima a fili ba. Sai da ya ji voice ɗin Mamma a cikin kunnuwansa ne ya gane ashe ma a fili ya yi maganar. "Wacece kuma sarkin rigima?" Shi ne tambayar da ta yi mashi. Ƴan kame kame ya fara yi ya rasa waye zai cewa Mamma ita ce ƴar rigimar. Canza mashi topic na hirar Mammar ta yi, saboda ta sanya a ranta tabbas in zai fita zata bi bayansa domin ta ga menene ya canza mata yaro, ta fara tunanin ko dai ya gano wannan mum twins da yake ta yawan maganarta a baya ne a kan ta ɓata, yanzu kuma ya dai'na yin magana tata, to dole da akwai dalili. Jansa da hira irin na uwa da ɗa ta yi, cike da so da kauna yake amsa mata suna zuba hirar, sai datse mashi gashin take yi tana zubarwa. Sai da rana ta faɗi suka shiga cikin ƙogonsu, abinci suka ci tare da namar da ta gasa masu, ya kara kyau sosai da Mamma ta datse tsawon gashin nasa ta rage mashi, sai face ɗinsa ta kara wani irin haske. Bayan sun ci abinci ne suka ɗan taɓa hira kamar yadda suka saba kafin nan kowa ya yi nasa waje ya kwanta. Mamma tana kwanciya ba jimawa ta yi barci, shi kuwa bai yi barci ba har dare ta tsala sosai, sai juye juye yake yi a saman gadon nasa, shi da kansa ya rasa menene ya hana shi yin barci bawan Allah. Tunaninsa ɗaya kawai shi ne ya tashi ya lallaɓa ya je ya leƙo su Pretty, su kawai yake son gani yasa ya shiga damuwa haka. Sam baya tsoron dare. Saukar ruwan sama da ya fara gudana a cikin dajin ne yasa ya hakura da tunanin zuwa ganinsu a cikin wannan duhun dare, ya kwanta shiru yana ta tunaninsu har wayewan gari barci ta gagara. Da gari ta fara wayewa ne ya yi maza ya ɗauko abin sakar Mamma ya saƙawa Sweetie rigarta, ya haɗa kayan waje guda ya ɓoye da nufin anjuma in ya fita zai kai masu!. Da safe kamar yadda suka saba idan suka tashi daga barci haka suka yi, Mamma ta dafa masu abin da zasu ci, ba komai bane face gasasshen nama da kuma ruwan gayyayakin tea masu inganci da ƙara lafiya a jiki. A cikin tea ɗin Kamran sai ta sanya mashi wani ganyen magani green color, kasancewar da zuma suke haɗa tea ɗinsu ba sugar ba, sai yazama ruwan tea ɗin nasu ya yi wani irin orage color mai ɗan duhu, ganyen shayin da suke amfani da shi ya kasance ja ne sosai, so idan suka zuba zuma sai ya ɗan dishashe karfin jan ya ɗan yi kamar orage color, suna da yelwar zuma sosai a cikin dajin, Kamran ne mai ciro masu Mamma kuma ta tace ta zuba a mazubi mai kyau ta ajiye masu suna amfani da shi, zuman da babu mix ko ɗigo a ciki, su ina ma suka san anayi mata mix? Ina suka ga sugar a cikin wannan daji? Ai babu ita. Kamar yadda suka saba yin breakfast bayan sun yi wanka cike da so da kauna haka suka yi yau ɗin ma, suna gamawa Kamran ya ce mata zai je cikin daji yawo, ba tare da jan mashi rai ko ta ce ba zai je ba ta amsa mashi da sai ya dawo ya kula da kansa. Cike da murna ya nufi ɗakinsa domin ya shirya, ya ɓoye Kayan da ya sakawa su Pretty a jikinsa sannan ya fito ya nufi waje. Da ido Mamma ta bishi har sai da ya fice, sannan ta fara bin bayansa a sese'sese domin taga ina ya nufa. E TO LALLAI AKWAI CAKWAKIYA, BARI DAI MU JE MU DAWO. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ KINGDOM OF POWER 💪🔥 Zaune Gimbiya Zunaira take a cikin katafaren lambun da yake a cikin family part. Zaune take a saman ɗaya daga cikin wasu haɗaɗɗun chairs da suke a wajen da aka tanada dan zama a cikin lambun, an kawata wajen sosai da sosai, ga wani irin iska mai matuƙar daɗi da yake kaɗawa a wajen, iska ne ba mai sanyin cutarwa ba, ɗan dai'dai. Ta tsantsara kwalliyarta cikin shiga ta alfarma ta ƴaƴan manya manyan sarakuna da ake ji dasu, wata shegiyar Dubai gown ce a cikinta launin pink color, rigar ta sha kyau har ta gaji, yanayin tsarin rigar ya yi kama da masu tula tulan breast ne kamar su Gimbiya Chuchu, dan rigar yana da breast part a jikinsa duk da ba mai girma bane, ita Zunaira yanzu ma ta fara kirgan dangi, amma ta sanya shi a jikinta, hakan kuma ya samo asaline saboda tsawon da take da shi, tsawonta ya fi shekarunta, hakan yasa ake saya masu kaya dai'dai girman na su Chuchu, dan shi ne yake yi mata dai'dai tsawon, da kaɗan Chuchu ta fita tsawo, to kun ji in da matsalar take. Ta yi shiru tana kallon kyawawan tsuntsayen da suke a cikin ɗan kejin dake kusa da ita, irin kananan tsuntsayen nan ne waɗan da suke three colors, akwai brown, akwai blue, sannan yellow, haka kalarsu yake, suna da matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ƴan kanana da su. Cikin takun jarumta Hoorain ya shigo cikin wajen. Tun daga bakin kofar lambun ta tsare shi da waɗan nan kyawawan fararen hazel eyes ɗin nata tana kare mashi kallo yadda yake taka ƙasa cikin zafin nama, yana shirye cikin kayan yakinsa, hannunsa na rike da wani ɗan ganye kamar flower yana ɗan murzawa. Ga wata shegiyar sharɓeɓiyar takobi a ƙugunsa. A kusa da ita ya zo ya tsaya tare da ɗan sirinar da kai ya furta. "Sannu da hutawa ranki ya daɗe". Cikin harshen larabci ya yi maganar. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan saki ƙayatattcen murmushi mai kara fito da tsantsar kyanta tare da faɗin. "Waye ya gaya maka ina nan Hoorain?". Ƙara yin kasa da kansa kaɗan ya yi kafin ya bata amsa da cewa. "Abbie ne ya faɗa mun". Idan ba ka kasa kunne sosai ba ba zaka taɓa jin me Hoorain yake faɗa ba idan yana magana, in a low voice sosai yake magana ɗan tahaliƙin nan, kamar baya son motsa laɓɓansa. Da yake ita auta ta saba da shi sosai, dan tun tana karama take tare da shi, sai ta saba da maganar nasa, ko yaya zai yi magana tana iya gane me ya faɗa kuma tana jinsa, ita tama saba da jin magana ƙasa ƙasa sosai ai, ga Yah Jaish da Yah Jawad ma, wannan ba shi bane farau. "Kai Abbie ya cika sa ido, yaushe wai ya ganni na fito har ya gaya maka". Ta faɗa tana turo baki. Bai amsa mata ba, dan bai san me zai ce maya ba, shi ba wani iya surutu ya yi ba, idan ka gansa yana magana ma to ka kan yaki ne da sauransu, bayan haka baya wata magana, ko da mahaifinsa commander ZAFAR wato wanda ya kira da Abbie yanzu basa hira, ko dare ne basa wani hira a tsakaninsu, dukkansu sarakan shiru shiru ne, kuma a tare suke kwana, basu taɓa rabuwa, suna manne da juna, amma ba zaki taɓa jin suna wani hira mai tsawo ba, daga tambaya sai amsa kawai ne a tsakaninsu. "Hoorain kai kullum idan muka haɗu sai na ce maka ka zauna ne?". Ta faɗa tana mayar da kallonta izuwa kan Gimbiya Chuchu da ta shigo cikin lambun a yanzu, kafa ya ɗan sami sauki, sai wani turɓune fuska take yi kamar wadda aka yi wa dole ta zo wajen, tana sanye da kaya irin na jikin Autar, sai dai ita ta ɗaura kyakkyawar alkyabbarta a saman kayan, ita kuma auta bata ɗaura komai ba, sai ɗan ƙaramin lallausan hula da ta sanya a kanta ta rufe arab hairnta. Ganin bai amsa mata bane yasa ta sake ce mashi. "Hoorain ka zauna mana". Cikin girmamawa ya karɓi umarnin nata tare da zama a saman ɗaya daga cikin kujerun da suke a wajen in da take zaune ita ma kenan, wasu irin chairs ne masu bala'in kyau a wajen, a baya idan ta ce mashi ya zauna sai dai ya ce zai zauna a ƙasa, ita ta hana shi zama a ƙasan, ta gaya mashi da shi da su duk ɗaya ne a wajen Allah, dukkansu mutane ne halittun Ubangiji, babu wanda ya fi wani a duniya sai wanda ya fika tsoron Allah, dan haka ita idan yana son su shirya kada ya kara zama a ƙasa, ya zauna a in da take zaune ita ma, hakan yasa yanzu idan ta ce ya zauna sai ya zauna a in da ta zauna ita ma, dan kada ya ɓata mata rai. A kusa da su Gimbiya Chuchu ta ƙariso ta zo ta zauna, sai turo baki take yi kamar wadda aka yi wa wani abin, da ace Sarina ce ta shigo wannan waje kuma ta sami Hoorain zaune a saman irin chair ɗin da auta take zaune, da rashin mutuncin da zata yi mashi kare ma ba zai shinshina ba, sai ta zagesa fes, sannan ta buga mashi warning a kan kada ya sake, kuma ya sani shi ɗin bawansu ne, a karkashinsu yake, dole a kasansu zai zauna ba wai ya jera da su ba. Amma da yake gimbiya Chuchu ce, sai bata wani damu ba, bama ta bi ta kansa ba, zama kawai ita ma ta yi. "Aunty Chuchu meyafaru naga kina ɓata rai ne?". Cewar auta. Kara tsuke ɗan bakin nan ta yi kafin ta ce. "Ni da Yah Jawad ne mana, na je wajen daddy yanzu dan na roke shi zan je Dubai, shi ne Yah Jawad wai na tafi daga nan babu in da zan je, kamar shi na je tambaya". "Yauwa kin ma tunaninmun bari na je wajen Yan Jaish ya gaya mun ya gama tunanin da zai yi, nima dai ina son zuwa Dubai ɗin ne ai" Ta kai karshen maganar tare da yunƙurawa ta miƙe. "Jirani mu fita tare, daga nan na wuce wajen Akka, Allah zan je na gaya mata ta sa daddy ya barni na je". (Chuchu dai bata daddara ba zata sake kai karan Yah Jawad wajen Akka, da alama ta manta punishment ɗin ne😅 mu dai namu ido) A tare suka miƙe. "Hoorain zan je wajen Yah Jaish, zaka jirani a nan ne ko zaka tafi?". Ta faɗa tana kallonsa. Ƙasa ya yi da kansa kafin ya amsa mata da cewa. "Yadda kika ce ranki ya daɗe". "Auta sunana ba ranki ya daɗe ba, ko kace mun Zunaira". Ta faɗa a ɗan ƙule. "Ai babu wanda zai kiraki da Zunaira sai mara kunya". Cewar Aunty MieMie da ta shigo cikin lambun a yanzu. A hanzarce suka kai kallonsu a kanta, tana shirye cikin kayan masu bala'in kyau da tsada, ga wani dankareran alkyabbarta a sama, daga wuya zuwa hannunta dukka gwala-gwalai ne masu tsada ta kawata kanta da su, ga wani haɗaɗɗen ɗan kunnen hancinta na gold shi ma da ta sanya ɗan karami, sai kyalli yake yi, hakan ba ƙaramin kyau ya kara mata ba, cover irin na hamshaƙan matan sarakuna ne a kafafunta launin golden color, haɗuwa iya haɗuwa, jinin larabawa. Da sauri auta ta taho ta faɗa jikinta tana sakin murmushi, ita ma Chuchu a hanzarce ta ƙarisa wajenta tana faɗin. "Aunty MieMie ina kika je two days?". Rungume auta ta yi tare da sanya hannu tana shafa kan Gimbiya Chuchu ta basu amsa da. "Na je na halakci taron makarantarsu Omar da aka gudanar ne na kammala secondary school ɗinsu, yau na dawo". "Shi ne Aunty MieMie baki tafi da mu ba?". Cewar Chuchu. "Ban san kuna son zuwa ba ai, nima na wakilci daddy ne, saboda ba zai samu zuwa ba, akwai abubuwa da suka sha mashi kai sosai, uncle Abbas ma bashi da lokaci shi ne na wakilcesu duk da su uncle Rahab sun je". Gimbiya Zunaira zata yi magana wata kuyanga da ta shigo cikin lambun a yanzu ta katsesu da cewa. "Allah ya kara sawon kwana ranki ya daɗe, Momma tana kiranki, wai ki je parlourn mai martaba ki sameta". Har suna haɗa baki wajen tambayar waye ake kira? Dan ranki ya daɗe ta ce, kuma dukkansu haka ake ce masu. "Princess Aunty MieMie ke ake kira". Kuyangar ta basu amsa. Shi dai Hoorain yana zaune yana binsu da kallo, sai dai ba kowa zai iya gane cewa yana binsu da kallon ba, baza ma kataɓa yin tunanin yana kallonsu ba. Raba jikinta dana auta ta yi tare da riƙo hannunta tana faɗin su je su ji me ake kiransu. Ta yi maganar tare da riƙo hannun Chuchu da ɗayan hannunta. Kai tsaye part ɗin King suka nufa, suka bar Hoorain a zaune a wajen bawan Allah. Sun sha madarar mamaki na ganin gabaɗaya family a wajen, harda su Sarina, ga Yah Jaish da Yah Jawad ma nan, dukkansu manyan suna zaune a saman tsala tsalar sofas dake a cikin parlourn, su Sarina kuwa suna zaune a saman Dubai carpet dake a tsakiyar sofas ɗin, ga twins Obaid and Omaid a kusa da Gimbiya Fanan. Cikin mutuntawa Aunty MieMie ta yi sallama tare da wucewa ta zauna a saman sofa mai zaman mutun biyu da yake a kusa da King, tare da zaunar da auta a gafenta kafin ta ɗagawa su Momma gaisuwa. Kowacce tana dake a cikin alkyabbarta, kowacce kuma tana zaune a saman nata sofar na daban, Mama ta wani tsare gida kamar hakan ce zai sa su ji tsoronta, har da Mammie Yah Jawad a wajen, kowa yana cikin shiga ta alfarma. Gimbiya Chuchu kuma kusa da King ta zo ta zauna a saman carpet ɗin, ta kwantar da kanta a saman laps ɗin King ɗin. Tana turo baki kamar anyi mata wani abin, sai dai rashin sa'arta na yanzu yasa ta zauna a in da suke fuskarta juna ita da Yah Jawad, da zarar ta ɗago kai shi zata fara kallah, shi ma kuma haka, sam bata lura da hakan ba har sai da ta ɗan ɗago da kanta da nufin ta kalli su waye da suwaye ne ma a cikin parlourn, tana ɗago kai kawai karaf suka haɗa idanu da shi, a dai'dai lokacin shi ma ya ɗago idanu dan ya saci kallonta, dan shigarta ta yi mashi kyau. Cikin sauri ta yi ƙasa da nata idanun ta fara ƙoƙarin matsawa daga saitinsa ko da kaɗan ne. Shi ma kawar da nasa kallon ya yi izuwa kan King, ga mamakinsa sai ya ga King ɗin ma shi yake kallon, abin gwanin ban dariya. Duk sai ya ji ya tsargu kuma, sai yake ganin kamar kallon tuhuma King yake yi mashi, alhalin kuma ba haka bane, shi ma King ɗin ya ɗago ido ne kawai sai kallonsa ya sauƙa a kansa, ba wai haka kawai ya kalle shi ba. Kamar dai wani mara gaskiya sai ya yi saurin kawai da kallonsa daga kan King ɗin yana jin gabaɗaya a takure yake, izuwa yanzu shi da kansa ya fahimci ba iya burgesa kawai Chuchu take yi ba, sama da hakan ne, akwai dai abin da yake ji dangane da ita. Shi kam Jaish da tun ɗazun yake aikin latsa waya bai ma san me ake ciki ba. Twins kuwa sai wani ƙus ƙus suke yi ƙasa ƙasa, wani lokaci su yi ƴar kurma kurma kamar wasu munafukai. Gyaran murya King ya yi tare da fara yin magana a nutse. "Nataraku a nan ne kan abubuwa biyu zuwa uku. Na farko shi ne akan abin da ya faru da Sarina, abin sam bai yi daɗin ji ba, ga shi har ya saka mun ɗan uwana (uncle Abbas) ciwon kai, sam ban ji daɗin hakan ba, shiyasa na taraku domin na ja maku kunne a kan ban yarda wani ya sake zuwa wa wani daga cikinku da zancen yana son ƴaƴana har kuma ku yi mashi jagora zuwa cikin gida na wajen ƴaƴan nawa ba, ban yarda da hakan ba! Ku kyaleni idan sun kai munzalin aure ni zan zaɓa masu maza da kaina, koma ya kuke da mutun bana da buƙatar ku kawo mun shi cikin gidan nan da sunan wai yana son ƴa ta, dukka dukka ma nawa Sarinar take da Abbas zai takura kansa da zai ta yi aure? To ni bana da buƙatar irin hakan ta sake faruwa, ku kyale mun ƴaƴana su huta, sai dai ni ina tunanin wannan yaro Yusuf ba lafiya yake ba, amma dai koma menene Zafar zai yi masu abin da ya dace, wannan shi ne maganata ta farko. Ta biyu kuma Obaid and Omaid zasu koma Dubai gobe, duk da ba'a buɗe makarantarsu ba ko ma nace basu wuci sati ɗaya da yin hutu ba, amma za su koma bisa son hakan da mahaifiyarsu take yi, ta ce tana son su koma yafi mata, so zasu koma. Sai magana ta uku, Omar zai dawo nan da kwana uku, Mommynku ta buƙaci da zata shirya mashi gagarumin walima na murnar dawowarsa, na kuma bata izinin yin hakan, ina gaya maku ne domin na fita hakkin kowa". Ɗan dagatawa ya yi da maganar yana sauke numfashi tare da bin fuskokin matan nasa da kallo. Shi dai Jaish har ga Allah bai ga wani abin da zai sa a kirashi cikin wannan al'amari ba, shi ba aboki yake da shi bama bare ace ko abokinsa zai ce yana son kanne nasa har ya yi mashi jagora zuwa gidan, to shi ko da ace yana da aboki ma ya isa ya yi mashi jagora zuwa neman aure ne? Wlh bai ga wanda ya isa ya sanya shi ya yi mashi jagora zuwa wajen mace ba, a ganinsa ba'a haifi mutun ba. "Akwai wani mai abin faɗa ne?". King ya katse su da wannan tambayar. Siririn tsaki Mama ta ja kafin ta ce. "Ranka ya daɗe ni ina son a gaya mun menene banbancin su Chuchu da su Obaid da duk wanda Rahilarh zata haifa sai ta ce bata son ya zauna da ƴan uwansa a nan sai dai a Dubai? Menene a gidan da nata ƴaƴan ba zasu zauna ba sai namu? Ko mu namu ƴaƴan ba mutane bane? Ko dai nata ƴaƴan sun fi namu daraja ne?". Da iya gaskiyarta ta yi maganar. Ita kuwa Momma ba wani dalili bane yasa ta buƙaci su Obaid su koma Dubai face wannan matsala dai da take fuskanta a cikin gidan, kwana biyun nan tana yawan mafarkinsu a cikin wani mawuyacin hali ne yasa ta buƙaci da su koma kawai ko hankalinta zai kwanta. (Ni kuwa na ce bama dole ki gansu a cikin mawuyacin hali ba, yara basu ji, sai dai su yi ta kwasa wa kansu alhakin mutane suna biyewa Sarina suna kwasan hakkin waɗan da basu ji ba basu gani ba, yara kamar an canza maki su lokacin da kika haifesu🤔 ai in a kansu ne ma fin haka zaki gani baiwar Allah😅) Da yake Momma jinin Modarawa ce ba'a masu su kyale, sai ta ce da Mama ɗin. "To ai naga duk tushe ɗaya ne ko? Kina iya mayar da su Chuchu ɗin Dubai ɗin kema idan kina da buƙata, saboda suma ai kakaninsu ne a can ɗin, babu wanda ya hanaki yin haka, dan haka sai ki cire idanunki a kan rayuwata, haka nake son ƴaƴana su kasance, tun da ba ke kika haifa mun su ba kina iya jan baki ki yi mun shiru". Akka dake zaune saman nata sofar ta wani dake tare da ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ne ta karɓi zancen da cewa. "Idan ma baku yi haka ba ai sai na ce Zuhair ba mata ya aura ba". Karo na farko da Yah Jawad ya ji dariya ta so ta kubce mashi, wannan tsohuwa Akka akwai iya tada bom, a maimakon ta shiga cikin lamarin ta sasanta, amma kun ji wai idan basu yi hakan bama ba mata bane. Shi dai Jaish haushi har wuya yake ji ta iso mashi, dan shi sam baya son zama a taron mata, yasan fin haka ma zasu aikata, su yi abinsu su bar mutun da ƙuncin zuciya ba abin da ya damesu, ai mata duniya ne, kome za'ayi masu kishin nan dai yana nan, ba zai taɓa tafiya ba, kai ko cire zuciyar mace ka yi ka wanketa fes da ruwan zam zam ka sake dawo mata da shi a kan kishi gobe sai kaga wani bakin halin........😅 "Daddy zamu iya tafiya?". Cewar Yah Jawad, dan ya lura abin na mata ne take shirin motsawa, wato kishi, dan haka gara su kama kansu kada a kashesu da kuncin zuciya. Shiru King bai basu amsa ba, ya dai zuba masu idanu yana ganin su, dama haka yake yi, sai sun yi sun gaji yaje saka baki. "Bayan kin asirce shi ya zama ƴaƴanki kawai yake gani da daraja ta ina muke da ƴan cin zaɓarwa ƴaƴanmu in da muke son su yi rayuwa? Ai ke kaɗai ce mai wannan dama, zalunci dai komai daren daɗewa yana da karshe". Cewar Mama. Omaid ne ya kalli Mama ɗin cikin ɓacin rai ya amsa mata da. "Mama ko Momma ta zaɓa mata in da zamu yi karatu ko bata zaɓa mana ba mu dama bamu da ra'ayin yin rayuwa a cikin kingdom ɗin nan, wajen su mai ran karfe su Uncle Rahab and uncle Abu Abdussalam muke son zama, dan haka ba laifin Momma bane, kuma..........." Wani irin ɗan iskan kallo da Yah Jaish ya wurga mashi ne yasa ba shiri ya haɗiye sauran maganar nashi, dan sun san Jaish ba kanwar lasa bane, ba shi bashi da hakurin Yah Jawad, yanzun nan zai sa su ji kamshin ma'aika azarailu, dan haka sai ya yi shiru tsit kamar babu shi a parlourn. Ita kuwa Mama kallon walaƙanci ta wurgawa Momma ɗin kafin ta ce. "Kina iya yin fin hakan ma ai, kisa yaranki basu daraja kowa". Shiru gabaɗaya parlourn ya yi, kallon Obaid ta ƙasan ido Omaid ɗin ya yi, burinsu kawai su bar parlourn nan su je su shiryawa Mama ɗin nan wani munafurcin da sai ta yi kuka, dan wlh idan ba haka suka yi mata ba ba zata rabu masu da Mommarsu ba, shi kuma Yah Jaish zai taka masu birki, wlh ka ana ha maza ha mata basu ga dalilin da zai sa su bar wata banza tana yi wa mahaifiyarsu kutse a cikin al'amura ba, a cewarsu sun lura Yah Jaish ɗin nan baya son Momma sam sam, tun da yana zaune Mama ta zageta bai iya cewa komai ba, to su dai ba za su ɗauki wannan iskanci ba, dole kowa ya san matsayinsa a gidan, kafin su koma Dubai sai sun yi maganinta....... Hmmmm lallai akwai kura!. Shi kuma Jaish ya ja bakinsa ya yi shiru ne saboda King yana wajen, koma dai menene yasan da cewa King zan yanke hukuncin da ta dace, kuma dama a matsayinsa na babba mai ilimi da hankali me ruwansa da faɗan kishiyoyi fisabilillahi? Ai wanan ba layinsa bane, amma fa sosai abin ya sosa mashi zuciya, ji ya yi tamkar ya buge Mamar sai ta sume ko ta mutu a wajen, amma ya danne saboda kannensu dake a cikin parlourn ga kuma King and uncle Abbas sannan ga Akka a kwana!. Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya bi ta kan kowa ba ya nufi hanyar fita, domin idan ya ce zai cigaba da zama a wannan tattaunawa ba makawa tsab zai yi wa Mamma one slap seven death, so gara mashi ya yi gaba tun bai hasala ba. "Where are you going Jaish?". Cewar uncle Abbas. Duk yadda yake kaunar uncle Abbas ɗin ya kasa iya bashi amsa, dan zuciyarsa a kusa take, idan ya ce zai buɗe baki ya yi magana zai iya haɗiyar zuciya ya mutu, so sai ya yi kamar bai ji me uncle Abbas ɗin yake cewa ba, a hanzarce ya fice daga cikin parlourn dan ma kada King ya dakatar da shi. Already shi kuma King dama bai yi niyar dakatar da shi ɗin ba, saboda yasan halin ƴaƴan nasa da zuciyar bala'i, shi kansa ya ji zafin maganar Mamar bare kuma ƴaƴan Momma, ai dole abin ya sosa masu rai. "Sarina, Fanan, auta, Jannat, Obaid and Omaid duk ku tashi ku tafi". Cewar Aunty MieMie. A hanzarce kusan a tare suka miƙe suka nufi waje. Mummy kam tana zaune kamar mutun mutumi tana binsu da kallo, ita sam sam ma bata son hayaniya a rayuwarta, ba zaka taɓa jin maganarta a irin wannan abin ba, da girmar kujerarta hajiya uwargidan King Zuhair Abdul Malik ba. King ya ɗauki a kallah 5 mins yana kallonsu tun bayan fitarsu Sarina, kafin ya ɗan nisa tare da fara yin magana cike da bada umarni da kuma izza. "Kada wanda ya sake yin magana a kan hukuncin da Rahilarh ta yankewa ƴaƴanta na girmansu a hannun ƴan uwanta, kowacce a cikinku tana da damar da zata ce mun Zuhair a wajen kakaninsu nake son ƴaƴana su girma, iyayena da yayyuna haɗe da kannena sai kakanina ne fa a Dubai ɗin, me dan ƴaƴana sun girma a hannunsu? Ƴaƴana mata ne na ce bana buƙatar su matsa daga kusa da ni, amma maza ina iya turasu ko'ina su je su yi karatu, ita Zunaira da take mace ba ga shi tana gabana ba? To me wani sabon abu a ciki? Me abin ta da hankali? Bana son wannan hayaniya dukka, ba'a kan haka na taraku ba, abin da na tara ku a kai shi ne, kada ku kuskura ku gayyato mun wani cikin gidan nan da sunan yana son ƴaƴana, sannan Obaid and Omaid zasu koma Dubai gobe, Omar yana dawowa nan da kwana uku, Mummynsa zata shirya mashi walima, idan akwai wadda take buƙatar wani abin ta yi mun magana zan shiga ciki". Ya kai karshen maganar tasa cikin nuna cewa tsantsar umarnin yake basu. Mummy baiwar Allah, Omar dai ba ɗan ta bane, ɗan Momma ne yayan Zunaira, amma kun ji har walima ta nemi izinin shirya mashi dan zai dawo, ita dukka ƴaƴan nasu abu guda ta ɗaukesu saɓanin Mama. "Zan iya tafiya?". Cewar Mama, da alama ranta bai so maganar da king ya yi ba sam. Akka ce ta ce "Kowa ma zai iya tafiya a yanzu". A hanzarce Mama ta miƙe ta yi waje, Momma ce ta biyu a fita ta rufa mata baya, sai Mummy ta uku, princess Aunty MieMie ta rufa masu baya. Parlourn ya rage daga Akka, uncle Abbas sai King. Uncle Abbas ma miƙewa ya yi tare da sanar da su zai je ya shirya dan zai koma baƙin aikinsa. Sallama suka yi ya wuce, ya rage saura Akka da King, su kuma suka cigaba da hira na tsakanin uwa da ɗa. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 5/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________28🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼 AAJ YARI.💔😥 Shiru Leesharh ta yi, gabaɗaya ta shiga ruɗani, kanta ya ɗaure, duk ta rasa me yake yi mata daɗi, yanzu ya zata yi?. Dafa shoulder ɗinta da kyau Jasrah ta yi tare da fara magana cikin nutsuwa da ƙoƙarin nuna mata illar da abin da zata aikata zai haifar mata ita da danginta gabakiɗaya, dan wlh idan aka kamata ko mahaifinta da take burin take ikirarin ta koma gida ta je ta gani ba barinsa za'ayi ba, babu wanda zai iya tsira daga cikin familynta, babu wanda zai tsallakewa Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen, duk sai ya ragargazasu, to babban abin tambayar ma a nan shi ne wanenen shi wanna Ramish ɗin kam? Ya yake? Meyasa ake farautar rayuwarsa har haka da ake ƙoƙarin leƙar asirinsa? Kuma kun ji matar ta ce suna da ma'aikata a gidan, hakan na nufin ba ita Leesharh ɗin bace ta farko, kenan an jima ana sanya mashi idanun? Da alama har yanzu haƙarsu bai cinma ruwa bane yasa suka buƙaci Leesharh a wannan aiki, idan kuka yi duba da yadda matar ta ce ma'aikatan nasu a iya harabar gidan suke ba su sami damar shiga ciki ba, hakan yasa basu iya sanin me Ramish ɗin yake ciki, ita kuwa Leesharh karamar yarinya ce da ba za'a barta a harabar gida ta yi aiki ba, dole idan za'a ɗauketa aiki a can cikin gida zata yi aikin, kila ma a ta fannin kitchen ko kuma gyaran ɗaki or wani abu makamancin haka, babu wanda zai kawo wa ransa ita ɗin leƙar asiri ta zo yi, kunga zata sami damar sanin wanenen Ramish da kuma motsinsa a cikin gidan, ina ga tabbas kafin su tunkari Leesharh da wannan magana sai da suka yi gagarumin bincike a kanta, sai kuma da suka shirya sosai. Amma kuma matsalar a nan shi ne, ita Leesharh idan ta amince ta karɓi wannan aiki da ankamata fa shikenan ita da danginta ne zasu girbi laifukan da basu suka shuka ba! Domin bata san wannan mata ba! Tab akwai cakwakiya na gasken gaske kuwa, yanzu nasu wasan kuma zai fara kenan, zamu ga wanene zai yi nasara a wannan game ɗin da za'a buga kuma!!!. "Leesharh a wannan magana babu wani tunani da zaki yi, domin kuwa baki da wata mafitar da ya wuce ki ce mata ba zaki je ba, idan kuma kika ki, to wlh karnikan gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ne zasu cinye gawarki a ɗanyarta, kuma ki sani sun cinyeki sun cinye banza, ke bama wannan ba, wlh duk danginki babu wanda zai iya tsallakewa, babu wanda zai sha a hannun Ramish idan asirinki ya tonu, kuma yadda suke da mahaukatan cameras a gidan kin san kuwa dole asirinki zai tunu, ke ta ina ma zaki fara yin wannan aikin fisabilillahi Leesharh? To ina mai tabbatar maki ganin waɗan nan mugayen fusatattun securitys ɗin da suke gadin kan titin da zata ratsa ta shigar dake unguwar da gidan yake ma ya isa ya sanya ki saki fitsari a wando, duk rashin tsoron nan naki da ƴan gidan nan suke faɗa wlh baki ga abin tsoro bane, bare ace ki ga securitys ɗin da suke gadin ainahin gidan, ina ga daga nan zaki sume, ke ni fa ban ma yarda matar nan zata iya shigar dake wannan gida ba, gidan ɗaya daga cikin ƴaƴan the most powerful King Badeen da duniya take magana a kansa, kowa idanunsa naa kansa, ga karfin iko kamar shi ya bawa kansa, kuma defence minister da duk wani mai kaki yake a ƙarƙashinsa, sai da izininsa kaki zata motsa, lallama kam, ni dai a matsayina na ƴar uwarki ban baki goyon baya ba, ko da bamu da alaƙa ta jini addinin Musulunci ya haɗa mu mun zama ƴan uwan, kuma ba zan zuba maki idanu ina ganin abin da zai cutar dake da familynki na yi shiru ba, dole na gaya maki gaskiya koda zaki gujeni". Ta kai karshen maganar tana mai cigaba da kallon fuskar Leesharh da tsoro ya gama bayyana a samansa sosai. Bata taɓa shiga irin wannan yanayi ba, ko lokacin da aka kawota gidan da sunan ta kashe mahaifiyarta babu irin makamancin wannan tsoro a face ɗinta, bata taɓa tsorata a cikin wannan gida ba duk da ta san hukuncin kisa ne a kanta, tasan kasheta za'ayi, amma babu tsoron hakan a ranta, yau dai ta tsorata da jin wannan irin bala'i na aikin da zata je. "Ke fa Jasrah baki da mutunci, yanzu saboda mugunta ne kike son hanata fita daga cikin wannan gida, kina ji Leesharh? Wlh duk abin da Jasrah take faɗa karya ne, kawai bata son ki kuɓuta daga hukuncin kisa da yake a kanki ne, bata son ke kifita ita a kasheta ne, shiyasa take ƙoƙarin sare maki gwiwa, dan haka kada ki yarda, ki je kawai Allah ya bada sa'a, zamu tayaki da addu'a". Cewar Sahra dake makale a saman gado kamar wata mage........ Mugunta dai babu kyau Sahra!!. Taɓe baki Jasrah ta yi tana mamakin irin wannan kiyayya, kiyayya ido da ido suke nunawa Leesharh babu ko sakayawa! Sai ka ce ba musulmai ba, yaran nan sam sam basu da mutunci, sun tsani Leesharh over, duk wani munafurci ƙoƙari suke yi suga sun kullah mata, su basu ki ba ma a matso da hukuncin kisan da yake a kanta ya dawo yau yau a kasheta su huta, ko me ribarsu idan an kasheta?..............🤔 "Sahra laifin me kika yi ma aka kawo ki gidan nan?". Cewar Leesharh, daga jin yadda ta yi magana ƙasan zuciyarta ta gama karaya, gwiwowinta duk sun sage, ta tsorata sosai da wanna al'amari, ita tunaninta ma ɗaya shi ne ya zata yi ta cewa wannan mata ba zata yi wannan aiki ba ta, fasa?. "Dole ki tambaya mana wani irin laifi ta yi aka kawota gidan yarin nan, dan na lura babu Allah a ranta". Cewar Jasrah. Wani irin matsiyacin kallo Sahra ɗin ta watsa masu kafin ta ce. "Baku kai na baku amsa ba, bani ma da lokacinku ƴan wahala kawai". Sahra kenan wadda ta turo yaron mai aikin gidansu daga saman bene ya faɗo ƙasa ya mutu, kuma cameras na harabar gidan nasu da wanda yake a balcony duk sun ɗauketa time da take tura yaron ƙasa, yaro ɗan ƙarami wanda bai wuci 5 years ba a duniya, abinku da yarinta, kawai dan ya ɗauki Teddynta yana wasa da shi a wajen balcony shikenan ta wurgoshi ƙasa babu imani bare tausayi, ko da yake ina zata ga imani yarinya mara kunya har haka? Shi ne laifin da ta aikata, gata da uban rashin kunya kamar wadda shaiɗan yake yi wa busar sarewa a kunne, ga shegen rai'na na gaba da ita, iyayi da manyance, ga kauɗi da rawan kai, bata ganin kowa da gashi, bata jima da shigowa cikin gidan ba, yanzu haka iyayenta suna can suna ta faman ta yadda za'ayi su fito da ita, sai faman rokar ƴan aikin suke yi da ta yafewa ƴarsu, dan ita kaɗai suka haifa, suna can suna wahala suna kashe kansu a kanta, ita kuwa tana nan tana tsula tsiyarta son ranta, da yake iyayen nata sun gaya mata ai ba za'a kasheta ba, sun kusa yin nasarar fitar da ita, shi ne nan rashin kunya ya karu sanka sanka, ta zagi uban kowa a cikin gidan babu mai tanka mata, saboda suna tsoron ruwan bala'inta, bata da mutunci, kwata kwata 15 to 16 years ke gareta. Kawar da kai Jasrah ta yi daga kan Sahrar tare da dawo da kallonta a kan Leesharh da nufin su cigaba da maganarsu dan ganin sun samowa kansu mafitar yadda zasu yi da wannan bala'i da yake shirin tunkarosu. Bata kai ga buɗe baki ta yi maganar ba sai ga wata ganduroba tana ƙoƙarin buɗe kofar ɗakin nasu zata shigo. Jan baki Jasrah ta yi ta yi shiru tare da bin gandurobar da kallon mamaki tare da kara tsorata sosai, saboda bata san me ya kawo matar ba, abin da ta sani dai shi ne a duk lokacin da kaga wata ganduroba to ba alkhari bane ya kawota, ammafa a nasu ganin kenan. "Leesharh let's go". Shi ne abin da gandurobar ta faɗa bayan ta gama buɗe kofar, ta yi maganar kuma tana wurgawa Jasrah wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, kamar dai ba kallon lafiya ba. Miƙewa Leesharh ta yi jiki ba kwari, ga shi babu halin ta tambaya ina zata je kuma? A tsorace take kada ace matar ce ta dawo ɗaukarta ko kuma makamancin hakan. Ita ma Jasrah tsoro sosai ya kara bayyana a saman face ɗinta, fargabarta ɗaya shi ne kada ace matar ce ta zo ɗaukar Leesharh ɗin, sai addu'a take yi Allah yasa Leesharh ta gayawa matar ba zata je ba idan ma ita ɗin ce ta dawo, Allah kuma yasa idan ta gaya mata ba zata je ba ta hakura ta kyaleta, gara masu su kare rayuwarsu a nan har izuwa lokacin da wa'adin hukuncinsu zai cika a kashesu kawai, a kan wannan aikin, dan yafi mutuwa haɗari, fargaba da tsorata tare da faɗuwar gaba ne ma kawai zai Kasheka a gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen. Salun alum Leesharh ta wuce gaba, jikinta sai kerma yake yi, saboda tsoro, ta yi gaba matar ta rufa mata baya. Dai'dai Leesharh zata wuce office na ɗazun in da suka yi magana da matar can, wannan gandurobar ta dakatar da ita ta hanyar cewa. "Ba nan zaki shiga ba ai". Da mamaki sosai tare da tsoro Leesharh ta juyo da kallonta a kan gandurobar. Ɗaure fuska matar ta yi tare da nuna mata wani hanya da yake a tsakanin wasu ɗakuna na wasu yaran dake dakon lokacin hukuncinsu ya cika su girbi abin da suka shuka. Bata da zaɓin da ya wuce dole ta bi wannan hanya, domin ko damar yin magana ma ba'a bata ba. Wucewa kawai ta yi gaba matar ta rufa mata baya, suna tafiya matar tana waige waige kamar wata maras gaskiya, da alama dai ba gaskiyar bane aka kullah. To koma dai menene mu kam namu ido, zamu so ganin wannan cakwakiya, dan da alama zai ƙayatar ya kuma rikitar tare kuma da tarwatsa ƙwaƙwalwale, ya hargitsa tunani gami da ruɗar wa!!. Sun yi tafiya mai nisa kafin su isko wani ɗan siririn hanya da yake a daf karshen wannan hanya, zuciyar Leesharh sai harbawa da karfi karfi yake yi, ji take yi kamar ta ce zata koma wajen Jasrah, amma ina babu bakin yin magana, tana tsoron gandurobobin sosai, saboda basu da sakin fuska ko kaɗan, kullum rai a haɗe kamar waɗan da aka yi wa wahayin mutuwa tare da lokacin da zasu mutu ɗin. Wannan kwana suka bi, suka sake tafiya mai ɗan dogon zango kaɗan kafin su isko wani kofa a ƙarshen hanyar. Wasu irin makullai matar ta ciro daga aljihunta, makullai ne masu tarin yawa sosai da a kallah sun fi guda 70, ga su kala kala. Wanda ya fi ƙanƙanta a cikin makullan ta sanya a kofar ta buɗeta, nan take haske ya bayyana a wajen. Da mamaki Leesharh take ganin wajen. Da akwai dogayen bishiyoyi masu tarin yawa a wajen, kowa dai yasan yadda bayan dayawan prisons suke, kamar daji daji wajen haka yake. Da hannu matar ta nunawa Leesharh hanya a kan ta fita. Kamar zata musa taki fita, sai kuma bata ga fuskar yin hakan a tattare da matar ba, dan haka salun alum ta lallaɓa ta kama kanta ta rufawa kanta asiri ta nufi waje. Tana fita matar ta mayar da kofar ta rufe tare da murje key ɗin, sannan ta juya ta koma cikin prison ɗin ta baro Leesharh a waje. To fa babbar magana!!. Wani irin bugu da kirjinta ya yi ne yasa Leesharh bata san lokacin da ta sanya hannu ta dafe kirjin nata ba, ji take yi kamar zuciyarta zai fasa kirjinta ya fitowa waje, saboda tarin tsoro da kuma danasani na amsawa wannan mata da e zata yi wannan aiki da ta yi, ga kuma tunanin rabuwa da Jasrah! Ko sallama basu yi ba abin gwanin ban tausayi, sannan ga shi yanzu an kawota waje an barta ita kaɗai. Juyawa ta yi gabas da yamma kudu da arewa bata ga alamar wani halitta mai rai a arear wajen ba, wani sabon tsoron ne ya kara dira mata a cikin ranta. Juyowa ta yi tana kallon wannan prison door ɗin, ji take yi kamar ta yi knocking na door ɗin da karfi har sai an zo an buɗe mata ta koma ciki, dan komawarta ciki shi ne mafi a'ala a gareta. Sai dai kuma tana tsoron yin knocking na door ɗin, gudun kada ya haifar mata da wani gagarumin matsala. To wai me mutanen nan suke nufi da ita ne da suka barta a wajen gidan yarin?. Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana.💘 Ta kai almost 10 mins tsaye katsake a wajen, ta kasayin gaba ta kuma kasa yin baya, ta rasa duk wani ƙata ɓus, tunani da tsoro duk ya dabaybayeta baiwar Allah. "Let's go". Tamkar saukar aradu ta ji wannan murya ta bayanta an faɗi ta zo su tafi. A razane ta juyo mai gabaɗaya. Wata jibgeiyar hajiya ce da daloli suka yi mata mubaya'a, kuɗi suka jiƙata sharkaf ne tsaye a bayanta sanye cikin wata dakakkiyar tsadaddiyar bakar jallabiya tare da nikaf a face ɗinta, kafafunta na a sanye cikin booth mai tsada, ga wani bakin glass a face nata, kusan dai irin shigar matar ɗazun, sai dai matar ɗazun ƴar siririya ce, wannan kuma jibgegiya, tana da tsoka a jiki sosai, ta ci ta ƙoshi, wannan irinsu ake kira da hajiya two seater, masu haɗiye sofa two seater a wajen zama. Sosai Leesharh ta ƙara razana fiye da tunanin mai tunani, sam bata ma san lokacin da ta fara kallon matar from head to toe ba, saboda ita dai bata taɓa kallon mace mai kibar wannan mata ba, wani irin kerma na tsoro jikinta ya fara yi, ta kasa koda iya ɗaga kafafunta bare ta isa ga wannan matar. Ganin haka yasa ita matar ta ƙariso gareta tare da riƙo hannunta, ta jata da nufin su bar wajen. Ƙasa iya tafiya Leesharh ta yi, da alama suman tsaye a wajen ta yi, yau taga tashin hankali, babban damuwarta ma shi ne kada ace shikenan an rabata da Jasrah ba tare da sun yi sallama ba, in kuwa haka ne wlh ancuceta an zalunceta, haka ake yi ne? Zasu rabasu babu ko excuse!. Ganin Leesharh fa ba iya tafiya da kafafunta zata yi ba dan duk jikinta ya yi wani irin muguwar la'asar kamar wadda aka zarewa laka, hakan yasa wannan mata ta sanya hannu ta ɗauketa cancak kamar baby ta wuce da ita!. Kara razana Leesharh ta yi da wannan mata, duba da yadda ta ɗauketa cak abinta. Cikin wani ɗan ƙurƙuran abin hawa wannan mata ta sauke Leesharh, abin hawan anyisa kamar bayan kunkuru tare da wata ƴar runfa a samansa, ta gaban kuma kamar keƙen hawa yake. Lokacin da wannan mata ta shiga cikin wannan ɗan ƙurƙuran abin hawan sai da ta jijjiga sosai, saboda ƙibar matar nan Masha Allah kawai za'a ce. Cikin harshen larabci ta ce da mai abin hawa ya ja su tafi. Ba ɓata lokaci ya ja suka wuce. Sun yi tafiya mai nisa har sai da suka bar arear AAJ, sannan wannan mata ta buƙaci da mai wannan ƴar ƙurƙuran abin hawan da ya dakata su sauka. Ba musu ya dakata suka sauka, ga mamankin Leesharh sai taga matar bata biya mai abin hawan kuɗinsa ba kawai ta saɓeta a shoulder ɗinta suka fara takawa da kafa. Shi kuwa mai wannan ƴar ƙurƙura ya gurgura abarsa ya kara gaba, da alama bakinsu ɗaya, duk cikin basaja ne. Bata sake sauke Leesharh a ko'ina ba sai a gaban wasu irin jiga jigan motoci masu masifar kyau da ɗaukar hankali. Sai dai sun ɗan yi tafiya mai nisa kafin su iso wajen waɗan nan motocin, ba zaka taɓa cewa waɗan nan motoci wata alaƙa ce ta kawo su AAJ ɗin ba, ita kuwa ainahin matar da ta fara yin magana da Leesharh ɗin tana cikin AAJ ɗin tana cike wasu takardu tare da bawa shugaban gandurobobin wasu takardu da ta zo da su ta sanya hannu, da alama yarjejeniya ce a kan sun karɓi Leesharh, ga dukkan alamu takardun da matar ta zo da su daga sama suka fito, ma'ana daga manyan madafun iko suka fito. Gaskiya akwai cakwakiya ta gasken gaske kuwa, ku dai gyara zama sosai!. Cikin ɗaya daga cikin waɗan nan shirga shirgan dankara danƙaran motocin wannan mata ta sauke Leesharh a gidan baya kenan. Idan ka kalli motocin in the first place ba zaka taɓa yin zaton da akwai mutane a cikinsu ba, saboda bakar glass da suke da shi, sannan babu wani motsi da zai nuna maka cewa akwai mutane a cikinsu. A tunanin Leesharh dukka babu mutane a cikin waɗan nan motoci, sai da aka sauketa a cikin ɗaya daga cikinsu ne taga wani shirgegen bodyguard, farin balarabe tas da shi sanye da face mask a fuskarsa, shi ne driver wannan mota da aka sanyata. Ita kuwa wannan mata hajiya two seater, wata mota na daban ta shiga, tana shiga kuma ko second ɗaya ba'a ƙara ba motocin suka tashi a jere kamar abin haɗin baki. A wani irin haukace suka tashi, da wani irin mahaukacin gudu suka bar arear wajen. Izuwa yanzu Leesharh ta gama saddakarwa da cewa lokacin mutuwarta ne kawai ya yi ba makawa, jikinta sai ɓari yake yi kamar mai zazzaɓi. Motoci guda goma ne cif dama, haka suka rinƙa sharara uban gudu kamar zasu tashi sama, kai daga gani kasan ba lafiya. Cikin ikon Allah suka samu damar isa katafaren shinfiɗaɗiyar titin da zata sadasu da unguwar Dubai Hills Estates, a luxurious area kenan, area ce ta manya manyan shegu masu faɗa aji a faɗin ƙasar, area ce da tun farkonta har izuwa karshenta take da matakan tsaro sosai, lafiyayyun securitys masu jini a jika ne suke tsaron arear, dogayen benaye masu matuƙar haɗuwa ne a ko'ina na faɗin yankin, babu karamar gida ko ɗaya a arear, dukka gidan manyan kai ne, tsayawa zayyana maku haɗuwar wannan unguwa ma ba zai yuwu ba, ku dai kawata a ranku ya zai kasance, amma dai ya haɗu iya haɗuwa. Tun da waɗan nan motocin suka danno kai cikin unguwar duk securitys dake arear suke aikin sara masu, da alama motocin gidan wani babban shegene mai faɗa a ji!. Kai tsaye wani tampatsetsan gida na gani na faɗa waɗan nan motoci suka nufa, tun daga kan yanayin tsarin ginin wannan gida kasan ba na ƙananan mutane bane, gini ne da ya amsa sunansa aljarnar duniya, hawa ɗai ɗai har hawa huɗu ne ginin, ga wani irin fitillu masu haske da suka kara fito da ainahin tsantsar kyan wannan gidan. Da akwai abubuwar kawata idanu sosai a wannan area da kuma wannan gida da waɗan nan mutane suka shiga da Leesharh, dan idan ka tsaya kalle kalle ma sai ka kwana ka wuni baka yi abin da ya kawoka ka wuce ba, saboda haɗuwa ta ko'ina fa ya haɗu. Kai tsaye tampatsetsan harabar parking space na gidan motocin suka nufa. Izuwa yanzu Leesharh ƙwaƙwalwarta ta dai'na gane mata komai, ta daina ɗaukar komai, sai dai ido kawai take bin ko'ina suka gifta da shi. Suna kashe motocin wasu mata guda biyu da suke sanye cikin jallabiyas dark blue har ƙasa, da kuma nikaf a face nasu suka ƙariso wajen motocin. Tamkar sun san motar da Leesharh take a ciki, ita kawai suka nufa, suna zuwa ba ɓata lokaci suka ɓalle marfin motar suka buɗe, ɗaya daga cikinsu ne ta roki hannun Leesharh ta fito da ita. Suna fito da ita kuma waɗan nan motoci suka sake tashi ba ɓata lokaci suka bar wannan gida tare da hajiya two seater a ciki, ita bata fito ba. Cikin katafaren gidan suka nufa da Leesharh da ta zama kamar mutun mutumi, bayan idanu da kuma numfashinta babu wani abin da yake motsawa a jikinta baiwar Allah, sai jan kafafu take yi ta bisu izuwa cikin, suma sai jan hannayenta kawai suke yi, basu da karfin iya ɗaukarta, dan ƴan sirara ne su ɗin ma, basu da wani ƙiba saɓanin hajiya two seater, hakan yasa suka jata izuwa ciki kawai. Duk wata mace da zaka gani a cikin wannan gida to tana sanye da nikaf, duk da cewa hakan kusan ɗabi'ar wasu dayawan larabawan ne, amma su waɗan nan nasu akwai ayar tambaya sosai. Mata sosai ne a cikin gidan, sai ayyukan gabansu suke yi, babu mai kula wani!. Lafiyayyun securitys ne masu gadin wannan gida, daga gani kasan gidan wani shegen ƙusa ne a ƙasar. Kai tsaye wani haɗaɗɗen elevator suka nufa da Leesharh, hawa na karshe suka haura da ita. A wani katafaren luxury parlour suka dakata, parlourn ya ji komai na more rayuwar ɗan adam. Wata hamshaƙiyar macece take zaune a saman sofa set mai matuƙar kyau da laushi, ita ma sanye take da wani haɗaɗɗen jallabiyarta launin white color, sannan ga nikaf a face ɗinta ita ma, baka iya ganin komai nata face yatsun hannayenta da suke farare kal kal kamar madara, kafafunta ma na sanye cikin safa baka, iya yatsun hannun ne kawai a waje. A gabanta waɗan nan mata suka kawo Leesharh suka zaunar, sannan suka sanya kai suka nufi waje ba tare da sun furta ko uppan ba. Wani irin kerma da jikin Leesharh yake yi ne yasa hankalin wannan mata gabaɗaya ya karkata izuwa kanta. Ɗan kyafta idanunta ta yi alamar tana son tabbatarwa shin da gaske ne take ganin jikin Leesharh na kerma haka?. Ganin da gaske ne yasa ta ɗan yi gyaran murya, cikin harshen larabci ta fara magana. "Yunwa kike ji ne A'isha? Naga jikinki na kerma". Jin muryar matar tare da jin yadda ta ambaci ainahin sunanta yasa Leesharh ta kara tsorata sosai, sai kuma a yanzu ta sami dama tare da jin cewa zata iya yin magana, ta ɗan ji kwarin gwiwa kaɗan, a ruɗe take faɗin. "Dan girman Allah ku mayar da ni AAJ, wlh ni nafasa yin wannan aiki, ba zan iya ba, ku mayar dani wajen ƴar uwata Jasrah". Magana take yi amma bata san me take faɗa ba, saboda a tsananin ruɗe take, tana magana tana zaro waɗan nan dara daran idanuwan nata. Daga ta bayanta ta ji wata murya mai kamar saukar aradu ya daki dodon kunnuwanta tana cewa. "A'isha Aliyu Haidar, calm down mana, menene abin ruɗewa da tada hankali har haka?". A matuƙar razane ta juyo da kallonta izuwa wajen da wannan murya ta fito. A hankali matar take saƙo kafarta tana taka haɗaɗɗen tiles na floor ɗin kamar bata son takawa, daga ɗaya daga cikin bedroom da suke a cikin parlourn ta fito, sanye take da wasu kananan kaya da suka kama jikinta sosai, wandon jeans fari tas da ƴar riga mai karamar hannu, ta ɗaura after dress a saman kayan, sai dai bata ja zip ɗin after dress ɗin ba, ta barshi ana ganin kayan da yake a ciki, ga wani munafikin nikaf da yake a face ɗinta. A ruɗe Leesharh ta miƙe tsaye jiki na kerma ta fara faɗin. "Yauwa Aunty dan girman Allah ku mayar da ni AAJ, wlh ni ba zan iya wannan aiki ba, tsoro nake ji". Tana magana tana zaro idanu kamar an tare ɓera a lungu, dama ga idanun nata dara dara ba'a magana, duk wanda ya ganta a wannan hali da take a ciki sai ya tausaya mata, dan ta ruɗe sosai baiwar Allah, tana tsaka mai wuya. Duk da a AAJ wannan mata da nikaf ta je wa Leesharh, hakan bai hana Leesharh ta iya gane ta ba ta hanyar jin muryarta, sarai ta gane wannan mata da ta yi magana a yanzu ita ce ta je wajenta a AAJ, shi ne ma yasa ta miƙe a ruɗe take sanar da ita cewa ita ta fasa yin wannan aiki. "Very very sharp brain little girl! Gaskiya Leesharh kina da ƙwaƙwalwa, a cikin nikaf kika kalleni a karon farko, haka zalika yanzu a karo na biyu ma a cikin nikaf muka haɗu, amma kin iya gane ni? Abin da mamaki kuma is so nice, wonderful and interested, hakan ya kara tabbatar mun da zaki iya yin wannan aiki, saboda kaifin brain ɗinki". Matar ta yi magana cikin wani irin salo da ɗan adam ba zai iya fassara wani irin hasashe ko kuma kudurine a cikin zuciyarta ba, komai kaifin ƙwaƙwalwarka ba zaka gane ina suka dosa ba, saboda yadda suke fitar da magana sai sun taunata sosai da sosai suke sakinta, daki daki one ofter the other. "Aunty please ki tausaya mun, wlh ba zan iya wannan aiki ba, na fasa yi, ki ji tausayin maraicina". Ta faɗa hawaye zafafa suna bin ƙuncinta, sai a yanzu ta sami damar yin kwallah baiwar Allah. Sheeeee. Matar ta furta tare da sanya yatsarta ɗaya a saman lips nata dake cikin nikaf, a hankali ta ƙariso gabar Leesharh ɗin. "Leesharh why are you suffering yourself for what you know you have to do it, tun da kika amsa zaki yi wannan aiki har kuma kika bari muka gaya maki wani irin aiki ne to fa dole sai kin yi shi! Babu wanda ya taɓa jin sirrinmu kuma ya ce ba zai yi aikin ba, kin yi kaɗan". Cewar wannan hajiya da take zaune. My people's ina da wani tantama, anya idan Leesharh Allah yasa ta kammala masu wannan aiki ba'a kamata ba asirinta bai tunu ba ta tsira daga gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen da ranta su zasu barta da ranta kuwa? Ga dukkan alamu sun nuna duk wanda ya ji sirrinsu baya rayuwa, to kenan ita Leesharh me makomarta idan ta yi wannan aiki ta kuma samu nasarar kammalawa lafiya ba'a kamata ba? Kunga kuwa ita dai ta ji sirrinsu, ta ji komai, idan wani abin ya sami Ramish ma ta san sune sila. Shiyasa fa na ce maku wlh akwai cakwakiya da yaki ba kaɗan ba a part ɗin su Leesharh ɗin nan. Riƙo hannunta wannan mata da ta je wajenta a AAJ ta yi, a saman sofa ta zaunar da ita tare da cewa. "Mummy ki bari na yi magana da ita mana, kada ki saka baki please, ai zata yi. Leesharh kina ji ko? Ki saki jikinki, anjuma wadda zata koya maki aiki da abubuwan da suka dace dan ki yi basaja da kyau zata zo ta fara koyar dake komai, zaki zauna a gidan nan a kallah one to two weeks kina koya, sai kin goge sosai zamu san ta yadda zaki shiga gidan Sheikh Abu Abdussalam, kada ki damu babu wani abin da zai faru kamar yadda na gaya maki tun farko, ai na gaya maki zan kula dake koda kina a gidan Sheikh Abu Abdussalam ɗin ne, kin manta na ce maki muna da ma'aikata a can gidan ne? To kada ki damu babu abin da zai sameki, ki saki jikinki, na yi maki alkawarin lafiya lou zaki koma gida wajen ƴan uwanki tare da ɗimbin dukiya mai tarin yawa da zaku je ku gina rayuwarku ta inganta". Tana zuba kalaman yaudarar tata zuciyarta na fargabar jin amsar da Leesharh ɗin zata bata. "Aunty ni wlh ba zan iya ba, tsoro nake ji, dan girman Allah ki mayar dani wajen ƴar uwata Jasrah". Tana magana har wa lokacin hawaye na cigaba da bin ƙuncinta, zara zaran gashin idanun nan nata sun jike sharkaf da hawaye, idanun nata sun yi jajir da su gwanin ban tausayi. A dake wannan hajiya dake zaune saman sofa wadda wannan matashiyar mata ta kira da mummy ta ce. "A'isha kina son Aliyu Haidar ko baki son shi?". A ruɗe kuma a hanzarce Leesharh ta amsa masu da. "Wlh Aunty in son babana sosai kamar yadda shi ma yake sona". "To in dai kina son Aliyu Haidar dole sai kin yi wannan aiki, idan ba haka ba zaki rasashi rasawa ta har abada". Ƙara ruɗewa sosai Leesharh ta yi, cikin tsananin tashin hankali ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta da yake harba mata pat, pat kamar zai fasa kirjinta ya fito, ba komai bane ya hassasa mata hakan face tsoro. "Aliyu Haidar yana hannunmu, ba kuma zamu sake shi ba har sai kin kammala mana aikin mu, abu ɗaya idan kika saɓa mana ki sani a jikin babanki zamu fanshe". Hajiyar ta sake yin wannan magana cike da iya gaskiyarta. A ɗan shagwaɓe wannan matashiyar matar ta ce. "Why now mummy? Ai da kin barni da ita ma zata yi aikin ba sai kin saka baki ko kin gaya mata babanta yana a wajen mu ba". "Ki ɗauketa ku bar parlourn nan, bana son na sake ganinta har sai an gama koya mata komai idan za'a kaita gidan Abu Abdussalam sai mu yi bankwana". Cewar Hajiya, tana kai karshen maganar kuma ta miƙe ta nufi ɗaya daga cikin bedroom da suke a cikin parlourn. Binta da kallo wannan matashiyar matar ta yi har sai da ta shige ciki, sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da miƙewa tsaye, cikin mutunci ta riƙo hannun Leesharh ɗin a kan ta zo su tafi ta kaita room ɗinta. Bata da wani zaɓin da ya wuce ta bita, dan tun da ta ji furucin wannan hajiya a kan babanta sai ta ji ta sanyawa ranta dole zata yi wannan aiki, dole ta aikata shi ko dan ta tsiratar da rayuwar mahaifinta da shi kaɗai ya rage mata a duniya. Ni kuwa na ce to Allah yasa idan kin kammala aikin su cika maki alkawarinsu na sake ku ku koma ƙasarku lafiya ke da baban naki, amma fa akwai cakwakiya, ace irin wannan tampatsetsen gida da dollars ta zauna masu sosai ɗin nan ne suke neman leƙar asirin wani? Daga gani kun san ba dan kuɗi zasu yi hakan ba, dole sai dai ransa ko wani abin makamancin hakan, da alama mummunar gaba ce a tsakaninsu, dole akwai abin da Ramish ɗin nan ya aikata masu da suke neman ɗaukar fansa, to koma dai menene lokaci zai nuna mana...... Mu dai bari mu leƙa FOREST mu dawo, wata kila kafin nan hankalin Leesharh mu ya ɗan kwanta, baiwar Allah marainiyar Allah duk da bamu san asalinta ba. 🏞️FOREST🏞️ Tafiya Kamran yake yi cikin jarumta, amma kuma zuciyarsa na raya mashi kada ya je wajen su Pretty, haka nawai ya tsinci kansa da zargin cewa Mammarsa ta biyo bayansa. Kawar da wannan zargin ya yi daga zuciyarsa, dan yana ganin kamar karya ce kawai, ba dai'dai bane, Mamma ba zata biyo bayansa ba. Ƙara tsanan ta mashi zargin hakan zuciyarsa ta yi, lokaci guda ya ji jikinsa ya mutu da tunkarar wajen na su Pretty, da yake yana da kaifin ƙwaƙwalwa ya kuma san wacece Mamma, sai ya fara tunanin irin tattaunawar da suka yi da ita jiya da kuma yadda aka yi yau daga ce mata bari ya je cikin daji babu musu ba komai ta amince, ita da wani lokaci sai sun kai ruwa rana take aminta ta barshi ya fita, amma yau kai tsaye ba wata kwana kwana or ƙunbiya ƙunbiya ta ce ya je kawai? Dole akwai abin da take shiryawa. Tuna hakan ne yasa ya canza hanya daga kan hanyarsa na zuwa wajen su Pretty izuwa wata hanya ta daban. Yana tafiya yana kasa kunne yadda ko zai jiyo motsin Mamma a bayansa. Amma shiru bai jiyo ba, kuma yaki yarda ya juya baya dan kada idan ta biyo shi ma ta gane ya fahimci tana binsa, hakan yasa ya samu waje a ƙarƙashin wata itaciyar ɓaure ya zauna tare da ɗan jinjina da jikin itaciyar. Laɓewa Mamma ta yi a can nesa da shi in da take iya hangosa daga wajen, ta laɓe tana kallonsa yadda ya jingina da jikin itaciyar tare da lumshe idanu. Shiru ta ɗan yi tana tunanin dama nan wajen yake zama kenan?....... Wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya, yau Kamran ya yi wa Mamma wayo duk kaifin ƙwaƙwalwar tan nan, tab akwai cakwakiya kuwa duk ranar da ta kama shi tsamo tsamo a wajen su Pretty, ina ga daga ranar rabasu zata yi, kuma da wuya idan bata koresu daga cikin Forest ɗin ba, dan ita fa bata da ɗigon tausayi a ranta. Almost 20 mins suna a haka, daga karshe dai tsabar basaja da iya waskiya na Kamran harda kwanciya, ya karkata ya gyara ya kwanta a wajen, domin tun zamansa a wajen ya hango Mammar tasa a can bayan itaciyar da ta laɓe, yaga kayan jikinta, amma bai ga face ɗinta ba, shi ne har da kwanciya dan ya tabbatar mata da shi babu in da yake zuwa. Sanɗo Mammar ta fara yi tana son ta lallaɓa ta koma wajen kogonsu tun da taga babu in da yake zuwa. Tana sanɗo yana kallonta da mamaki, tunani ɗaya kawai yake yi yadda aka yi wannan tunani na tana bin bayansa ya faɗo mashi a cikin ransa, kullun yana zuwa wajen su Pretty, amma bai taɓa jin irin wannan zargin a ransa ba sai yau, ga shi shi bai san Allah ba bare ya ce Alhdulillah, sai dai kawai ya miƙe cikin sanɗo ya fara lallaɓawa zai je ya leƙa ko Mammar ta yi nisa. A hankali yake tafiya har izuwa bayan wata itaciyar mangoro ya laɓe, yana ganin Mammar tasa har sai da ta kurewa ganinsa, sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da juyawa da sauri ya bar wannan yankin. Kai tsaye wajen su Pretty ya nufa abinsa, sai dai yana tafiya yana fargabar kada ace ita ma Mamma wayo ta yi mashi ta yi kamar ta koma alhalin bata koma ba, ta bari ne taga ko zai je wani waje. Yana tafiya zuciyarsa na harbawa cike da tsoro. Ko da ya isa wajen su Pretty ɗin ma sai da ya jima a tsaye a waje kafin cikin sauri kuma cikin dabara ya buɗe ramin nasu ya afka ciki a hanzarce. Zaune ya isko Pretty a saman dutse ta buga uban tagumi, ita kuma Sweetie tana kwance a saman bed. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanuwansa suka sauka a kansu, Allah ya gani yana kaunar yaran nan sosai da sosai, jinsu yake yi har cikin ransa. Ya ɗan ji wani irin ba daɗi a ransa na ganin Pretty zaune ta buga uban tagumi saɓanin yadda ya saba samunta a kullum cikin nishaɗi da annasuwa. Jin motsin mutun yasa Pretty ɗago da waɗan nan idanun nata ta bi hanyar shigowa da kallo, ganin cewa shi ne yasa ta miƙe a hanzarce, kana ganin face nata kasan a matuƙar tsorace take. Da sauri ta nufe shi tun kafin ya ƙariso, tana zuwa kuma ta faɗa jikinsa tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Miƙewa zaune ita ma Sweetie ta yi, baiwar Allah da yake bata gani sai ta fara cewa. "Pretty meyasa kike sake yin kuka kuma? Ko dai mutanen ne suka biyoki har cikin nan mun shiga uku?". A ruɗe ta yi maganar, daga jin muryarta kasan ta sha kuka ta ƙoshi. Sosai Kamran ya ruɗe tare da shiga tashin hankali na ganin Pretty tana kuka ita kuma Sweetie daga jin voice ɗinta kasan ta sha kukan ne har ta ƙoshi. "Pretty what happened? Why are you crying? Please stop this crying and tell me what happened". Ya yi maganar cikin tsananin damuwa, dan a yanzu ya fi shiga damuwa idan aka taɓasu sama da idan aka taɓa shi, ya fi shiga ɓacin rai idan su suna cikin ɓacin rai sama da ace idan shi ne ransa ya ɓaci. Jin zazzaƙar voice ɗinsa yasa Sweetie sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da lumshe idanuta kamar wadda aka jefa a cikin ruwan sanyi a sahara mai tsananin zafi. "Pretty talk to me now?". Ya yi maganar a hankali sosai. Cikin kuka ta amsa mashi da cewa. "Ba waɗan nan mutanen da ka yi faɗa da su ranar bane na je ɗebo mana ruwa a ƙoramar nan suka kamani". Zaro idanu waje ya yi, a hanzarce ya ce mata. "To da suka kamaki sai me ya faru? Ya aka yi kika kuɓuta daga hannunsu har kika dawo nan?". A ruɗe ya yi maganar. "Wannan mutumi mai rufe fuskar ne wanda ya taimakemimu ranar ne ya zo ya kashesu dukka, sai ya ce mun na gudu na tafi, na gudu shi kuma ya fara faɗa da su". "Ina mutu min yake?". Ya tambayeta cikin ƙaguwa. "Nima ban kara ganinsa ba ai, daga ya ce in gudu shikenan na gudu na dawo, ban san ya suka kare ba". Sarkin tsoro ta tsorata ne sosai, dan a wannan karon kamata suka yi zasu tafi da ita, ta je ɗebo masu ruwa, su kuma mayakan sun je wajen domin dawakansu su sha ruwa suma, shi ne suka ganta, sai suka kamata, wannan mutu da ya taimaka masu ranar ne yau ma ya zo ya taimaketa ya kuma ce ta gudu, shi ne ta gudo ta dawo. Toh fah! Ko waye wannan mutumi? Wannan sai alƙalamina ne kawai zai warware maku wannan cakwakiya, kedai kada ki bari a baki labari, yanzu labari zai fara ɗaukar zafi. Rarrashinta Kamran ɗin ya fara yi yana ɗan bubbuga bayanta a hankali a kan ta yi shiru to tun da ta samu ta tsira. Sarkin son jiki, kara kwanciya mashi a jikinsa ta yi tana tunanin yadda waɗan nan mayakan suka damko gashin kanta, da yake tana nan ƴar piritu ba nauyi sai suka ɗagata da gashin kai saboda rashin imani, yau ta ga bone ai ƴar kaniya, shi ne yasa ta tsorata sosai. Da kyar Kamran ya samu ta yi shiru, sai dai bata tashi daga jikin nasa ba, ta cigaba da kwanciyarta a saman kirjinsa tana mai da numfashi. Daga Kamran har su Prettyn dukkansu fa babu wanda yake tunanin yana da uba a cikinsu, dan dukkansu uwa kawai suka buɗe idanu suka kallah, basu san da ma cewa sai mutun biyu bane suke haifan ƴaƴa, su dai kawai iyayensu mata suka sani, basu san me aure ba, kuma basu ma san a cikin ciki mahaifiya yaro yake rayuwa har izuwa wata tara a haifesa ba, duk basu san wannan ba, saboda idan kuka yi duba da yanayin yadda suke dukkansu basu da kanne bare ace sun san lokacin da mahaifiyarsu take da cikin kannen nasu, duk basu san wannan ba, gara ma shi Kamran ya yi karatu wajen Mamma, amma fa ba ta wannan fannin ya karanta ba, ya dai san abin da ya sani, kuma ya taɓa kallon wani maharbi yana wucewa rike da ƙaramin yaro a hannunsa, a nan ne ma ya fara sanin ashe akwai kananan yara a duniya, shi da duk a tunaninsa kowa da girmansa kamar yadda ya yi wayo ya gansa da girmansa a tunaninsa kowa a haka yake zuwa duniya......... Da kuwa an shiga uku😅 Su Pretty sune mutane na uku da ya taɓa gani suna kanana a rayuwarsa, su kuwa su Prettyn basu taɓa ganin kananan yara ba, shi kawai suka sani sai mum ɗinsu, sai kuma yanzu da suke ganin waɗan nan warriors ɗin time to time, shiyasa kuka ga dukkansu suke a haka, basu taɓa yin tunani ina iyayensu maza ba? Ba su taɓa yin wani tunani makamancin hakan ba........ E lallai akwai cakwakiya kuwa, ko waye zai koyar dasu sanin hakan?.....🤔 Sweetie da take a saman gado ne ta ce. "Kamran sannu da zuwa". Sai a lokacin ya kai kallonsa a kanta, amsa mata da yauwa ya yi kafin ya ɗaura da cewa. "Pretty sakeni bari na je na duba wannan mutumi a wajen ƙoramar ko? Ko zaki rakani?". A hanzarce ta fara girgiza mashi kai alamar ita ba zata je ba. Hannu ya kai ya ɗan shafa lallausan gashin kanta da yake bakin kirin ta ɗaure shi kashi biyu gwanin birgewa kafin ya ce. "To bari na je na dawo, na kawo maki wani kyauta, ki jirani ko?". Gyaɗa mashi kai kawai ta yi ba tare da ta amsa ba. Raba jikinsu ya yi tare da juyawa a hanzarce ya nufi waje, ita kuma ta yi maza ta koma saman gado tare da kwanciya ta tada kai da cinyar Sweetie tana goge hawayen nata. Kai tsaye wajen ƙoramar Kamran ɗin ya nufa ba tare da tsoro ko shakkar komai ba, cike da jarumta tare da fata da kuma yakinin son ganin wannan mutumi ya nufi wajen. Yana ƙarisawa wajen ya wani ja uban birki babu shiri, a razane ya zaro fararen idanuwan nan nasa waje kamar zasu faɗi ƙasa........ Bamu fara komai ba, dan har yanzu ba mu kai ga nemo RAWANIN ZALINCI ba tukun nan, yanzu labarinmu zai fara, ga Leesharh ta baro gidan AAJ babu shiri, ya Jasrah zata ji a ranta idan ta ji shiru Leesharh bata dawo ba? Shikenan sun rabu kenan? Wani irin rabuwa ne wannan mai tsananin ciwo haka? Leesharh dai zata yi aikin dole domin ta ceci rayuwar mahaifinta, ya kuke tunanin zata gudanar da wannan aiki? Shin asirinta zai tonu a kamata ne ko zata yi nasarar kammala aikin? Idan ta kammala waɗan nan unknown mutanen zasu cika mata alkawarin da suka ɗauka mata na sakar mata babanta da kuma maƙudan dukiyar su kuma mai da ita ƙasarsu?. WAJEN SU KAMRAN. Ya kenan idan Mamma fifikon wayo ta nunawa Kamran ta yi kamar ta koma alhalin bata koma ba? Ya makomar su Pretty, su waye su? Ina ne usulinsu? Ina mum ɗinsu? Suna da uba ko babu? Meyasa ake farautar rayuwarsu kamar yadda ake kafautar ruwan sanyi a sahara mai tsananin zafi?. KINGDOM OF POWER meyasa Momma take fuskantar barazana a cikin masarautar?. Meyasa Mammien Yah Jawad bata son shi a tare da Gimbiya Chuchu? Meyasa da Mamma da Mammie ɗin dukka suke kamar ƴan leƙen asiri a cikin kingdom ɗin? Ya makomar su Yusuf? Me su twin's Obaid and Omaid zasu ƙullawa Mama?. GIDAN SU KHADIJA. ya makomar rayuwarsu a yanzu? Maman Zainab ya tabbata ta je wajen boka? Shin idan ma ta je zai sa a fasa auren baban Zainab da kuma Haidar and Khadijah? Zai sa su maman Haidar ɗin su fara sonta ne?. Kai akwai tarin tambayoyi amma bari na barku da iya waɗan nan ku farata caza brain naku zuwa gobe idan Allah ya kai mu mu ji me ake ciki. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 6/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________29🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ 🏞️FOREST🏞️ Kai tsaye wajen ƙoramar Kamran ɗin ya nufa ba tare da tsoro ko shakkar komai ba, cike da jarumta tare da fata da kuma yakinin son ganin wannan mutumi ya nufi wajen. Yana ƙarisawa wajen ya wani ja uban birki babu shiri, a razane ya zaro fararen idanuwan nan nasa waje kamar zasu faɗi ƙasa. Fara bin gawarwakin warriors ɗin da idanunsa ya yi, mamaki ne sosai ya kama shi na yadda ya ga gawarwakin nasu, babu wata gawa da zaka iya kallah da mutuncinta, kisan walaƙancin wannan mutumi ya yi masu, da alama fa wannan mutumi an sha fama da shi a fagen yaki, da alama ya sha gwagwarmayar rayuwa, domin daga ganin yadda yake farautar mayaƙannan yake kashesu kisa mafi muni ba makawa shahararren jarumi ne na kin karawa. A hanzarce Kamran ya fara juyawa gabas da yamma kugu da arewa yana dube dube ko Allah zai sanya ya ga wannan mutumi. Amma ina babu shi babu alamarsa. Mutum kamar aljani, nan take yake iya yaƙan mayaƙa komai yawansu, zai tarwatsasu kuma ya yi tafiyarsa abinsa, sai ka rasa ina ya shiga? Ko alamarsa baka sake gani. Abin akwai ɗaure kai, anyama mutun ne ma kuwa? Na fara tantanma!. Kamran ya jima tsaye a wajen yana ta jimamin abin, kafin daga bisani kuma ya hango robar da Pretty ta zo ɗeban ruwa da shi ɗazun. Ɗauko robar ya yi tare da ƙarisawa wajen da ruwan ƙoramar yake zubowa daga saman dutsen, a nan ya ɗeba masu ruwa mai haske, sannan ya juya ya nufi cikin ramin nasu, zuciyarsa a cike tab da tunanin wanenen wannan Jarumin sadaukin? Su waye waɗan nan warriors ɗin? Meyasa ake ta kashesu kuma basu gajiya da sake shigowa dajin? Wanda yake turosu kuwa anya yana da imani? Duk wanda ka turo cikin dajin basa komawa, amma a haka kullum yake cikin turo wasu dan su nemo mashi kananan yaran da su kansu basu san kansu ba? Abin da ɗaure kai sosai gaskiya. Cikin ramin ya koma gabaɗaya jikinsa a mace, tunanin canzawa su Pretty maɓoya kawai yake yi, sai dai shi kaɗai ba zai iya ba, ba zai iya irin wannan gini da Mammarsa ta yi a cikin ƙogonsu ba, suma su Pretty wannan gini da yake ramin nasu dakakkun jaruman maza suka yi shi, ba mum ɗinsu bace ta yi shi, dan wane ita, bata isa ta yi shi ba, dole maza madaka katti ne suka yi shi, dan ba ƙaramin aiki bane, ba aikin yara bane ba. Shi ma zai iya yi, amma za'a ɗauki tsawon lokaci yana yin wannan aiki, kuma ba lallai aikin ya kai ko rabin na mammarsa da ta yi ƙargo ba. Sai tunanin mafita na ya zai yi yake yi har ya ƙarisa wajensu, a gefe ya ajiye masu ruwan tare da zama a saman dutsen da ya saba zaba. Tun da ya shigo Pretty ta tsare shi da waɗan nan idanun nata masu rikitar da shi. Da yake shi ma hankalinsa baya a jikinsa sai ya tsareta a ido a zahiri, amma a baɗini ba ita yake kallah ba, hasalima bai san in da yake kallah ba, ya luluƙa duniyar tunani. "Kamran ka kalli wani abin maras kyau ne a wajen?". Cewar Pretty sarkin ba'a gani ayi shiru. Ta kalli face ɗinsa ya sauya daga yadda ya bar cikin ramin ne, ya fita da annuri a saman fuskarsa, ya dawo cikin tunani da jimamin al'amarin, hakan yasa yanayin face ɗinsa ta sauya gabaɗaya. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, jin muryarta yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka. "No I didn't see anything, kawai am thinking ta yadda zan yi na sauya maku waje ne". A hanzarce Prettyn ta miƙe daga kwanciyar da take tare da cewa. "Do you see the man?". Girgiza mata kai ya yi alamar a'a bai gansa ba. Shiru ta ɗan yi kafin ta miƙe ta diro ƙasa daga saman gadon, wajen wani ma'ajiya da aka gina da taɓo ta nufa. Da kallo Kamran ya bita kawai. Ita kuwa Sweetie ta jingina da jikin bangon dutsen baiwar Allah, bata iya ganin komai, sai dai shiru kawai take yi tana sauraron maganganunsu a kullum, abin gwanin ban tausayi, rashin idanu babban cuta ce. Allah Alhdulillah da ka bamu ji da kuma gani haɗe da lafiya, kafafu da kuma hannaye. Ƴan dube dube ta fara yi a wajen kamar mai neman wani abin. "What are you looking for?". Kamran ya jefa mata wannan tambayar. Ba tare da ta kalli in da yake ba ta amsa mashi da. "Am looking for my mum pen and book, I want to draw something, ina ganin zan iya zana face ɗin mutumin nan, with his eyes like mine". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Waye ya koya maki rubutu ma bare kuma zane Pretty?". Sai a lokacin ta juyo da kallonta a kansa, dan bama ta ga abin da take nema ba. "Mum ɗin mu mana, ai da tana koya mana abubuwa sosai har da su karatun Alqur'ani mai girma". Maimaita sunan Alqur'ani mai girma ya yi tare da tambayarta wani littafi ne kuma Alqur'ani mai girma?. Ɗauko wani ƙaramin Alqur'ani na mum ɗin nasu mai English translation ta yi tare da dawowa kusa da shi ta miƙa mashi tana faɗin ga Alqur'ani nan. Da yake yarinya ce babu ruwanta da yana da tsarki ko bashi da shi, kawai ta miƙo mashi full Alqur'ani izu sittin abinta. Shi kuwa da yake bai ma san menene bane sai ya sanya hannu kawai ya karɓa tare da fara dubawa. "Kamran you said that you have some surprise for me, kuma baka bani ba". Ta kai karshen maganar tana zama a kusa da shi. Yana kan duba farko farkon Alqur'ani ya amsa mata da close your eyes na baki. Ba musu ta kai ƴan kyawawan fararen tafukan hannunta ta rufe fuskarta tana ɗan murmushin da yasa dimples ɗinta suke lotsawa sosai. Juyo da kallonsa a kanta da kyau da kyau ya yi tare da rufe Alqur'ani ya rike da hannunsa na dama. Ganin yadda take ɗan murmushin dimple ɗinta yana lotsawa ne yasa ya sanya karamar yatsarsa a ramin dimple ɗin nata yana faɗin. "Irin na Mammana". Idan baku manta ba Mamma tana da dimples. Kara faɗaɗa murmushinta ta yi idanu a rufe. "Ka kaini in ga mammarka ɗin". Ta faɗa ba tare da ta buɗe idanu ba. Ɗauke hannunsa daga saman face ɗin nata ya yi tare da fito masu da kayansu da ya ɓoye a ƙugunsa wajen da yake ɗaure wuƙarsa. "Mamma ba zata zama abu mai daɗi da zamu iya gani ba, haɗuwarku ba zata yi kyau ba, dan haka ki bar batun yanzu, maybe wani lokaci zan gwada". Daga jin yadda ya yi maganar zaka san ya yi ta ne kawai, amma ba cikin daɗin rai ba, Pretty tasa ya ji wani irin a ransa, sabuwar tunani a kan meyasa mamma bata son yin taimako ne ya dawo mashi a cikin kwakwalwarsa, ya yi iya tunanin da zai yi domin ya gano dalilinta na kin taimakawa mutane, amma ya kasa iya ganowa, kuma babban abin ban mamakin a nan shi ne, ita tana bala'in kaunar Kamran ɗin kamar ta yi mashi numfashi, amma bata son kowa, bata tunanin cewa kamar yadda take son ɗan nata kowa ma haka yake son nasa? Ita dai a'a nata ɗan ne kawai mutun, saura duk a banza suke, wannan abin da ɗaure kai sosai wlh. "Meyasa ka ce haka?". Cool voice ɗin Sweetie ne ya katse mashi tunanin da yake yi. Nisawa ya yi kafin ya ce. "Wani lokaci zan gaya maku, now Pretty open your eyes?". A hanzarce ta janye tafukan hannayenta da ta rufe fuskar nata tare da waro idanun nata waje. Miƙa mata kayan dukka ya yi tare da bin face ɗinta da kallo, yana fargabar ta ce kayan basu yi mata ba, dan ita fa na gaya maku bata suturta abu, in dai bai yi mata ba ƙaramin aikinta ne ta dubi idanunsa ta ce bata so basu yi kyau ba, da dai Sweetie ne zata hakura ko da basu yi mata ba ta yaba su, amma Pretty wlh ba zata yabi abin da bata so ba, tab ai ko a gaban abin zata ce bai yi mata ba, sai dai dik abin da zai faru ya faru. Wani irin cool murmushi ta saki wanda ya kara bayyanar mata da kyanta sosai. "Kamran kamar kasan irin kayan nan naka yana yi mun kyau sosai idan na gansa a jikinka". Ta faɗa tana warware kayan ta gani. Ɗan yatsarsa ya kai saman wannan ɗan ƙaramin lips ɗin nata na kasa, a hankali ya ɗan shafi lips ɗin nata tare da faɗin. "Me ya ji maki ciwo a nan Pretty?". Ɗan turo bakin ta yi kafin ta amsa mashi da. "Waƴan can mugayen dodannin ne mana, da suka ɗaga ni sama da gashin kai'na zasu ɗaurani a saman dokinsu, sai wannan mutumi ya harbesu da wani abin irin naka da zaka koya mun harbin nan, da ya harbesu shi ne suka sake ni na faɗi kasa bakina ya ɗan fashe, da mutumin ya zo ne sai ya ɗaga ni ya ce na gudu". Shoulder ɗinta ya ɗan rungumo tare da ɗan jawota jikinsa kaɗan, sannan ya sanya yatsunsa guda biyu na hannun da ya rike da Alqur'ani nan ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, sam yaki yarda ya kalli cikin idanunta, hannunsa kawai ya sanya ya ɗan buɗe ɗan bakin nata domin ya ga ciwon da ta jin da kyau. Hakorinta ne suka ji mata ciwo a lips ɗin tata, amma ta ciki ne, kaɗan ne ya fito ta waje, sai ka lura sosai ma zaka iya gane cewa ta ji ciwo a wajen, da yake shi Kamran ɗin tana a cikin ransa shiyasa ya yi saurin gane cewa an ji mata ciwo, kuma sau da dama ya fi yawan kallon ɗan bakin surutun nan nata, idan ya kallah yana tuna ranar da aka haifeta ta rinƙa ihu, hakan yana sanya shi shiga cikin nishaɗi........😅 Kamran dai ya kasa mantawa da ranar da aka haifi Pretty ta rinƙa ihu, wato har nishaɗi yake ji idan ya tuno da ranar, lallai kuwa Pretty zata sha gori idan ta girma ta zama ƴan mata ta fara yi mashi yanga, zai ce ke dallah mai kuka kawai yi mun shiru......😅 Kallonsa sosai take yi har cikin idanu, shi kuma ya zubawa ciwon nata idanu yana kallon yadda hakwaranta guda biyu suka haɗu suka datse namar wajen har ya yi jini, ga wajen ya yi jajir ya kuma ɗan kumbura, tunanin ciro mata magani ya fara yi, dan ba ya jin zai iya jure komai ƙanƙantar ciwo a jikinta ba tare da ya nema mata magani ba. Slowly ya dawo da kallonsa a saman face nata gabaɗaya, ta wani tsare shi da idanu tana jiran ta ji me zai ce, har da wani kara kwanciya mashi a jiki, dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo? Dama bai janyota jikinsa bama ta iya kwanciya bare kuma ya janyota da kansa, ai shikenan kuma ta samu gado da katifa har ma da pillow. Ganin yadda take kallon cikin kwayar idanunsa sosai ne yasa ya hura mata iskar bakinsa a ido, a tunaninsa hakan zai sanya ta rufe idanun nata. Ga mamakin sa kuma sai yaga ko kyafta idanun ma bata yi ba bare asa ran zata rufe su, yadda kuka san ta sume ido a buɗe, kawai kallonsa take yi...... Dole ya ce idanuta suna rikita shi, wanna yarinyar akwai abubuwan mamaki sosai a tattare da ita, koya aka hurawa mutun iska a cikin idanu sai ya ɗan ji wani iri, wani ma harda kwallah yake yi saboda iskar, wani kuma a take zai datse idanun, amma ita kunga ko kyaftawa ma bata yi ba bare asa ran zata rufesu. Ba ƙaramin mamaki ta bawa Kamran ɗin ba, sake hura mata iskar ya yi a karo na biyu yana mai cigaba da kallon idanun nata. Ko gezau bata kyafta ba. Tsoro ne ya ɗan kamashi kada ace sume mashi a jiki ta yi, da sauri ya ɗan girgizara tare da ambatar sunanta. Nisawa ta yi tare da amsawa tana sakin wani irin cool murmushi. Nannauyar ajiyar zuciya shi kuma ya sauke tare da cewa. "Kekam ba mai iya maki, yanzu me kika tsareni da ido haka?". Hannunta ɗaya ta kai ta dafa shoulder ɗinsa ta gaba tare da gyara kwanciyarta a jikin nasa ta ce. "Yanzu me na yi?". Yadda ta gyara kwanciyar tata sai gurun wuyarta ya fito sosai. Yatsunsa biyu na hannun da yake rike da Alqur'ani mai girma ya kai saman wuyar tata yana faɗin. "Pretty wannan tsokar da take a wuyar nan taki tana yi mun kyau over, tana kara maku kyau sosai har Sweetie, amma kuma kamar mum ɗinku bata da shi ita". Girgiza kai Pretty ta yi, cikin sauri ta ce. "Kasan mum ɗin mu ne?". Sai a lokacin ya san ya yi suɓutar baki, ƴan kame kame ya fara yi yana son waske mata kada ta gane shi ne wanda mum ɗin nasu ta ce su nemo. Tsare shi da ido ta yi, sai gabaɗaya ya tsargu ya rasa me zai ce. Ƴan hannunta ta kai saman karan dogon hancinsa ta ja da ɗan karfi har sai da ya ce wash. "Amsa me, kasan mum ce?". Girgiza mata kai ya yi alamar a'a bai san ta ba, kawai tunani yake yi kamar ita bata da gurun wuyar. Da yake dukkansu yara ne sai ya yi wasa da ƙwaƙwalwarsu ya waskar da zancen, sai dai fa ita Sweetie ta fahimci akwai abin da baya son su sani, tabbas ko dai shi ne wanda mum ta ce su nemo, ko kuma dole da biyu yake zuwa wajen nasu, ko dai yama san in da mum ɗinsu take kawai baya son gaya masu ne, shi ne tunanin da Sweetie take yi. "Kamran bari na ɗauko maka wani rubutu da Mum ɗinmu ta yi, ta ce mu bawa wannan mutumi idan muka gansa, sai kuma wani littafi karami da ta ce shi ma mu bashi, yanzu bari na ɗauko maka takardan tun da ka iya karatu sai ka karanta mana mu ji me mum ta rubuta". Cewar Pretty sarkin kauɗi, ta yi maganar tare da yunƙurawa ta bar jikinsa. Da kallo kawai ya bita, har cikin ransa yake jin duk wani magana da zata yi, zazzaƙar voice ɗinta yana ratsa shi sosai da sosai. Wannan envelope ɗin da ya ɗauka ranar shi ta ɗauko mashi, a saman gado ta zauna tana faɗin. "Sweetie in nunawa Kamran ya karanta mana mu ji me mum ta ce?". Sam Sweetie bata so hakan ba, bata so ace Pretty ta ɗauko wannan ajiya ba, saboda mum dai ta ce sai wannan mutumi kawai zasu bamawa, amma ta je ta ɗauko shi, ga shi ba halin ta ce mata ta mayar da shi kada ta nuna mashi, zai ji babu daɗi tun da yana wajen, da baya nan ne, amma a gabansa ba zata iya cewa kada a nuna mashi ba, dan haka bata da wani zaɓin da ya wuce ta ce. "Ki nuna mashi iya takardan kawai, sauran abubuwan kuma duk ki barsu a cikin envelope ɗin". To ta amsa mata da shi, cikin hanzarce ta fara fito da abubuwan da suke a ciki, ba iya takardan da aka yi rubutu bane kawai a ciki, har da wasu ring guda biyu iri ɗaya sak, da wasu chain suma gida biyu irin ɗaga, irin siraran chain ɗin nan ne, kansu akwai tambarin ɓauna kamar tambarin gidan sarauta, haka shi ma ring ɗin da yake a cikin, shi ma yana ɗauke da wannan tambari, akwai dai karikitai a ciki, sai wani littafi mai kama da diary, da alama tarihin rayuwarta ta rubuta a ciki ko makamancin haka. Wata farar takarda dake nannaɗe ta fito da shi, sannan ta kwashi duk sauran abubuwan ta mayar ciki tare da rufe envelope ɗin ta ajiye a gefe guda. Warware takardan ta yi tare da cewa Kamran zo ka gani. Ba musu ya taso hannunsa rike da Alqur'ani ya dawo kusa da su ya zauna. Ita dai Sweetie shiru abinta baiwar Allah. Shinfiɗe takardan a gabansu ta yi tare da cewa ya karanta masu su ji. Fara karanta rubutun da aka rubuta cikin harshen turanci ya yi, amma kafin ya fara karantawa sai da ya tsaya ya tsare rubutun da idanu sosai, yadda kuka san ba hanu bane ya rubuta shi, kamar computer ce ta rubuta, rubutun ya tsaru sosai da sosai, komai daki daki. "Gaisuwa da fatan alkhari a gare ka Kamran, nasan da izinin Allah saƙona zai iso gareka, ban yarda da kowa ba a rayuwata sai kai, ga amanar ƴaƴana na baka, na san zaka kula mun da su sosai, a yanzu basu da kowa a duniyar nan sai Allah sai kuma kai, zan so kasan tarihin rayuwarsu ko in ce rayuwata, akwai wata littafi da na ajiye maka a tare da wannan saƙo da kuma wasu abubuwa, a nan zaka sami dukkan wata amsa a kan rayuwata, daga karshe ina mai yi maku fatan alheri tare da yi maka albishir da idan Pretty ta girma na baka aurenta duniya da lahira, ita kuma Sweetie ka rike mun ita tamkar kanwarka na jini, na gode sosai godiya mara iyaka". Shi ne abin da yake rubuce a jikin wannan takarda. Slowly ya ɗago da idanunsa bayan ya kammala karanta saƙon, saman face ɗin Pretty ya sauke fararen idanun nasa, while ita ma shi take kallo har cikin idanu. Cikin nutsuwa da sanyin muryar ya ce mata. "Pretty menene kuma aure? Na ji mum ɗinku ta ce ta bani aurenki". Ya kai karshen maganar yana cigaba da kallonta. "Kamran ɗan sake karanta mun layin farko na sakon bari na kara ji". Cewar Pretty, ta yi maganar kamar wata mai cike da ɓacin rai. Bai kawo komai a ransa ba, sam bai fahimci ya yi suɓul da baka ba, kawai ya sake fara karanta mata. "Gaisuwa da fatan alkhari a gareka Kamran........" Dakatar da shi ta yi a wajen tare da sake tambayarsa wani suna ya karanta a wajen?. Sai a lokacin ya fahimci ya saki layi wajen karanta sunansa da yake rubuce a wajen, abin gwanin ban dariya, shi gabaɗaya ma ya mance da cewa ya ɓoye masu shi ne wanda suke nema, to yau dai fa Pretty ta kamo shi tsamo tsamo, ba sauran waskiya kuma. Ƙasa ya sunkuyar da kansa tare da ɗan fara shafa hular da yake a kansa, ƙasa ƙasa ya ce. "Kila wani Kamran ɗin ne mai irin sunana, amma bani bane". A ƙule Pretty ta yi kansa tare da kai hannunta dukka biyu ta riƙo kunnuwarsa, da karfi ta fara ja tana faɗin. "Ashe ma wani Kamran ɗin ne ko? Har yanzu baka tuba ba kenan? Ba zaka dai'na yi mana wasa da hankali ba?". Da yake da karfin take jan mashi kunnuwan nasa hakan yasa ya ji zafi ya ziyarcesa, da sauri ya janyota ta faɗa jikinsa tare da cire ƴan hannayen nata daga kunnuwar nasa yana faɗin. "Haba mana, ki bari kada ki cire mun kunnuwa, da zafi fa". Kuka ta saka mashi har da hawaye, ita a dole ta ji haushi ya yi masu karya. Ita kuwa Sweetie cikin nutsuwa ta ce. "Kamran da gaske kai ne ko ba kai bane? Please kada ka yi wasa da zuciyoyinmu ka ji? Kai mutumin kirki ne sosai, na tabbata ba zaka so ka ganmu cikin ƙunci ba, so please ka gaya mana gaskiya". Yana ƙoƙarin ƙanƙame Pretty dake son tashi daga jikinsa ta nufi waje, sai kuka take yi hawaye wani na bin wani ya amsa mata da cewa. "Da gaske ne Sweetie, ni ne, na ɓoye maku hakan ne ba dan komai ba sai dan naga zaku iya ganeni da kanku ne ko ba zaku gane ba, amma kuyi hakuri kin ji?". Ya kai karshen maganar dai'dai lokacin da Pretty ta kwace kanta tare da barin jikin nasa, ta diro kasa daga saman bed ɗin ta nufi waje tana kuka sosai. "Pretty sarkin rigima, to me abin kuka kuma? Ai daɗi ma yakamata ta ji tun da mun ganoka yau, shiyasa mana kake kula damu sosai, dama mum ta gaya mana zaka kula damu sosai" Cewar Sweetie. "Haka ne Sweetie, amma ku yi hakuri da ce maku bani bane da na yi". Yana magana hankalinsa na a kan Pretty da ta bar cikin ramin, burinsa kawai ya bi bayanta ya je ya rarrasheta. "Ba komai Kamran, ai kai yakamata ma mu bawa hakuri". Cewar Sweetie baiwar Allah. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe tsaye tare da ɗaukar kayan da ya kawo masu wadda Pretty ta zubar da su a kasa ta nufi waje, ya ɗaura kayan a saman gadon tare da ajiye Alqur'ani hannunsa a kan gadon yana faɗin. "Bari na bi bayan Pretty ina zuwa yanzu". Yana kai karshen maganar bai tsaya jiran me zata ce ba ya nufi wajen shi ma. Yana fitowa ya fara waige waige ta ina zai hangota, a hankali ya fara takawa yana naman ta ina take wannan yarinyar. Can saman dutse wajen ƙorama ha hangota, ta takure jikinta waje guda, da alama a tsorace take da zamanta a wajen, kawai dai karfin hali ne yasa ta zauna, irin ita ta yi zuciyar nan, ta yi fushi. Dariya ma ta bashi, gata da tsoro kuma ga ban tsoro. A hankali ya lallaɓa ya nufi wajen nata, har lokacin kuma gawarwakin warriors ɗin yana wajen, sai dai ba ta gefen da Prettyn ta zauna ba, ta can gefe ita Pretty ta je ta zauna, da yake wajen yana da matuƙar girma sosai. Ta yi shiru ta zubawa ruwa idanu tana kallon yadda yake zuba gwanin ban sha'awa, ga hawaye a saman fuskarta. Ruwan wannan ƙoramar yana da matuƙar haske sosai, tankar yake. Sam bata ji motsin mutun ba sai ji ta yi an rufe mata idanu ta baya. A tunaninta warriors ɗin ne suka dawo, dama a tsorace take da zama a wajen, kawai dan tasan Kamran yana nan, kuma zai biyo bayanta ne ma yasa ta daure ta cije ta zauna a wajen, ba dan haka ba ina ba ita ba fitowa yau. Wani irin ihu ta kurma har sai da arear wajen ya amsa, a dubu ɗari ta fara ƙoƙarin tashi ta gudu, dan kwata kwata bata kawowa ranta cewa Kamran ne ya rufe mata idanu ba. Ganin a garin gudunta tana ƙoƙarin faɗawa cikin ruwan yasa Kamran ɗin ya yi saurin zame hannun nasa daga idanun nata ya yi maza ya riƙo kugunta ta baya. Jikinsa ya janyota dan kada ta faɗa ruwan. Sai ƙoƙarin kwace kanta take yi, dan bata san waye bane, ga shi yana ta bayanta babu halin taga fuskarsa. "Sarkin tsoro ai sai ki nutsu ni ne to". Ya faɗa yana ɗagata sama zai sauko da ita kasa daga saman dutsen, dan ma kada ta yi ta afka cikin ruwan nan ta sanya shi faɗawa ba shiri, bai shirya shiga ruwa da safiyar nan ba. Yana sauƙo da ita kasa ta juyo tare da fara kai mashi duka a kirji na tsoratata da ya yi, ya wani zo ba excuse ya tsoratata a banza, ya sa ta kusa sumewa. Ƴan hannayen nata da take dukan nasa ya riƙo tare da cewa. "Sorry our rigimammiya, wai ma da kika fito wajen nan idan warriors ɗin nan wasu sun zo fa? Idan suka kamana mana ke ya kike son mu yi ni da Sweetie? Kin san fa za mu iya mutuwa idan suka kamaki suka cutar dake". "Ni kada ka yi mun magana mun ɓata". Ta faɗa a shagwaɓe tana ƙoƙarin raɓawa gefensa ta wuce. A hanzarce ya riƙo hannunta yana faɗin. "To ai ni bance mun ɓata ba, ki bari sai nima na faɗa sai ki tafi". "Ni bawani jiranka da zan yi kawai mun ɓata". "To shikenan am so sorry, zo ki gaya mun menene aure? Dan na ji mum ta ce ta bani ke na aure! Sannan ki gaya mun menene mum take nufi da ta ce da izinin Allah, menene Allah?" Ya yi maganar cike da ƙaguwar son jin amsa, dan duk abin da zai fito daga bakin mum twins yana ɗaukar hakan da mahimmanci kamar maganar Mammarsa yake ji. "Nima ban san menene aure ba, amma dai nasan Allah, Allah shi ne wanda ya haliccemu dukkanmu, shi ne wanda ya halicci wannan daji da komai da komai, shi ne abin bauta da gaskiya shi kaɗai, bashi da abokin tarayya, ba'a haɗa shi da wani, shi ne mai riƙe da rayukanmu da komai dai da kasani". Hannunta ya riƙo suka zauna a saman dutse domin ta cigaba da yi mashi bayanin wanenen Allah, shi kuma batun aure ya barwa ransa cewa zai tambayi Mammarsa idan ya koma gida, ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce lallai akwai case idan ya tambayi Mamma, jiya ya gaya mata yana jin feeling a jikinsa, yau kuma ya tambayeta menene aure? Me kuke tunanin zai faru? Me kuke tunanin zata ɗauke shi ko zata yi tunani a kansa? Ai dole ta zargesa sosai ma. To bari dai mu leƙa KINGDOM OF POWER, daga baya zamu dawo mu saurari hirarsa da Pretty mu ji ya zasu kaya. KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 Kwance twin's Obaid and Omaid suke a saman katafaren bed ɗin Obaid, dama kullun a gado ɗaya suke kwana, basu rabuwa duk da kowa da gadonsa. Omaid dai yana aikin latsa waya, chatting suke yi da sistersa Jannat ƴar uncle Rahab dake a Dubai, dama itace kawarsa, suna mugun shiri sosai, idan suka koma Dubai kullum tana tare da su a gidan King Badeen, wato kakansu, sun fi yawan zama a gidan, basu cika zuwa gidansu Abu Abdussalam bin Badeen ba, a cewarsu su Yah Ramish suna takura masu, ko gidan uncle Rahab ɗin ma basu zuwa, sun fi son zama da mai ran karfe, wato kakarsu mace kenan, ita kuwa ba kamar Akka take ba, sam bata da tsauri, goya masu baya take yi suna tsula tsiyarsu, ita ce nan ta koya masu kada su yafe laifi idan aka yi masu, ita ma tsohuwar ƴar yi ce. Obaid ya buga uban tagumi kamar mai tunanin wani abin, ya yi kwanciyar ruf da ciki, ga wani haɗaɗɗen pillow da ya sanya a dai'dai chest ɗinsa ya kwanta a kai. Kullun dai cikin tashin daddaɗar kamshi suke, haka zalika bedroom ɗin nasu ma, kullum cikin ƙamshi yake zubawa, kuyangunsu sun iya gyara sosai. Ganin alamar Obaid fa ya luluƙa duniyar tunani ne yasa Omaid ya yi wa Jannat voice na karshe a in da yake ce mata cikin harshen larabci yana zuwa two mins. Yana tura mata ya ajiye wayar tare da fara bin Obaid da kallo, dukkansu daga short sai single ne a jikinsu. "What are you thinking blood?". Omaid ya faɗa yana zare pillow da yake a tsakanin chest na Obaid ɗin da kuma bed. Mirginawa Obaid ya yi ya sake mirginowa kafin ya ce. "Am thinking about Mama, kasan me zan yi mata kuwa?". Tsare shi da waɗan nan shegun eyes ɗinsa masu shegen rikita mutun idan suna kallonkan nan Omaid ɗin ya yi ba tare da ya yi magana ba. Jira kawai yake yi ya ji me Obaid ɗin ya shirya. Wan nan munafukin dariyar tasa ya saki, har da kara kwanciya a saman pillow, da alama mugun abu sosai yake shriyawa. "Please Obaid stop this laughing mana, ka fara ko? Please i ƙage nake da na ji me kake tunani a kanta". Ya yi maganar yana ɗaure fuska kuma cikin ƙaguwa da son jin me blood ɗin nasa yake shiryawa, nan take kamanninsa da Jaish ta kara bayyana sosai, twin's ɗin nan idan suka ɗaure fuska sai ka kalli kamar Yah Jaish ne a wajen. "Wait mana pleasure, i will tell you dolena ka sani ai, but please ka barni kaɗan, let me laugh more so that na samu damar iya ɗaure fuska idan abin ya faru, kasan we can't laugh a wajen da abin zai faru, kada a gane mu, dan haka ka barni na yi dariyar tun daga nan". "You're a bad boy Obaid like Akka". Omaid ya faɗa (Hasbunallahu lallai yaran nan sun tsani Akka 😅 wato ita mutuniyar banza ce a gabansu 😅 kash wayyo ciki, idan kunji ance dariya ya kasheni to su twin's ne sila.) Tsabar dariyar mugunta har da hawaye ne yake fita mashi a cikin idanunsa izuwa saman lallausan kumatunsa, ya dafe ciki, kamar wani zararre, da kyar ya iya cewa Omaid ɗin. "I think I'm even better than Akka ma ai". Dukan wasa Omaid ɗin ya kai mashi a shoulder ɗinsa yana faɗin. "To is okey, now gaya mun me ka shirya?". Da kyar ya iya dakatar da dariyar tasa tare da haɗe nutsuwarsa waje guda, sannan ya fara magana. "Snake mana zamu sakar mata ko kuma scorpion, kuma sai cikin dare zamu yi hakan, ya cijeta ko sau ɗaya ne". "Obaid you're not serious fa, so kake ka kasheta ko? Idan snake ko scorpion suka cijeta ai kafin a kaita hospital ma ta mutu, kuma tsabar kai you're a very very bad boy sai cikin dare za mu yi mata hakan ko? Wlh Yah Jaish yana nan, idan ya rikemu ina ga ko daddy ba zai iya kwatarmu a hannunsa ba, kuma kowa ya sani a cikin gidan nan mune kawai muke da su scorpion, muna sakar mata su za'a san aikin mu ne, ina ga kafin wayewan gari ni kam ina hanyar Dubai da kafafuna, ba zan jira jirgi ba, dan da punishment ɗin Yah Jaish gwara na je Dubai da kafa". Dariya sosai Obaid ya sake kwashewa da shi kafin ya ɗan tsagaita kuma, ko me ya tuna sai kuma ya sake cewa. "Yakamata sai mun shirya zamu bar ƙasar nan mu sakarwa Yah Jaish ma scorpion guda ɗaya". A wannan karon Omaid bai san time ɗin da ya fashe da dariya ba. Waɗan nan yara wlh anyi ƴan albarka, ba'a faɗin ɗayan, sai dai shirin Allah kawai zamu yi masu fata. "Amma ni ban taɓa sanin cewa blood kai mugu bane sai yau, wato sai mun shirya barin ƙasar zamu sakarwa Yah Jaish ɗin ma nasa scorpion ko? Ai wlh ina ga ko cikin momma muka koma sai Yah Jaish ya bi mu". Cewar Omaid. Yana magana yana ɗan dariya, da yake shi na gaya maku bai cika yawan dariya sosai ba, Obaid ya fishi yawan dariya. "Ai Yah Jaish ɗin ne ya cika takurawa mutane, yakamata mu ɗan ɗan ɗana mashi azaba kaɗan, shiyasa fa ni bana son zuwa gidan uncle Abu Abdussalam, saboda muguntar su Yah Ramish". Obaid ya faɗa yana janyo wata pillow ya rungume. "Kai mu yi magana serious me yakamata mu yi wa mama kafin mu koma? I really hate this woman, da idonta kamar na Akka". (Wai kowani kayan tsiya yaran nan suka ɗebo sai su ce irin na Akka?🤔😅 Ita dai Akka tana shan zagi a hannunsu ba tare da saninta ba.) "I think this night mu je mu san ta yadda zamu yi mu saka mata diaza a cikin drink nata or water ta sha". Cewar Obaid. Wani irin zaro idanu waje Omaid ya yi, dama ga idanun dara dara a waje, yadda ya zarosu a yanzu idan ka gansu sai ka ruga a guje dan tsorata. A hanzarce ya ce. "Real bad boy without a mix, kai Obaid wani irin bakin mugu ne wai? Yanzu Mamar zamu bawa diaza ko? So kake yi ka zubarwa da daddy mutunci kawai. Tab wayaga mama ta sha diaza? Wai da kuwa KINGDOM OF POWER ya ɗauki jan launi". Ya kai karshen maganar tare da kwashewa da wani ɗan iskan dariya. Cikin dariya yake faɗin. "Har na hango Mama tana bin jikin bangon kingdom ɗinnan dukka tana wankewa, kai amma kuma da ta taimaka fa". Cike da shakiyanci da iyashege ya yi maganar. A hanzarce Obaid ya karɓi zancen da cewa. "Ba iya jikin bango ba, ai wlh idan ta sha diaza ina ga harta motoci da dawakan gidan nan ba zata bari ba sai ta wanke, har mu ba barinmu zata yi ba sai ta wanke mu, komai na gidan nan babu abin da zata bari, caf zata wanke komai, 24 hours tana aiki". Shi ma cike da shakiyanci ya yi maganar. Sun zauna sai tsiya suke zubawa Mama ƴan albarka. Kara fashewa da dariya Omaid ya yi tare da ɗaukar pillow yana kaiwa Obaid duka, da kyar yake iya faɗin. "Please blood ka barni haka kada kasa dariya ta kasheni, dan ka tuna mun da uncle Muslim da muka bawa diaza a school, bawan Allah har bangon jikin class namu sai da ya wanke, gobe ya kara yi mana faɗa har ma ya raba mana wajen zama uban diaza a aiki zamu bashi ". Wani irin bushewa da dariyar iskanci Obaid ya yi, kamar wasu zararru suna ɓaɓɓaka dariya mai sauti ba tare ma da sun san sautin yana fita ba, sun kulla mugunta kala kala yaran nan, uncle Muslim uncle nasu ne a school wanda kullum yake yi masu faɗa a kan su dai'na ana yi masu magana suna yin banza da mutane. A gaskiya su idan kaga suna magana to a gida ne da su Sarina, amma wlh a waje ko uncles ɗinsu a school basa yi masu magana su amsa, kamar wasu masu aljanu haka suke, sai ayi ta magana su yi banza da mutane, idan kaga twin's ɗin nan suna dariya to sai sun haɗu su biyu irin haka, su biyu suke hira, su yi dariya, to shi ne fa uncle ɗin ya yi masu faɗa sosai dan ya ji haushin yana yi masu magana sun ki amsa mashi kuma suna ta hira a tsakaninsu a cikin class ɗin, izzar bala'i ke garesu suma, jinin sarauta na gudu a jikinsu. Har uncle ɗin ya so ya zanesu ma kuma sai ya hakura ya kyalesu, daga nan sai ya raba masu wajen zama a class ɗin, dan idan suna a tare wlh ko malami yana class suka so yin magana sai sun yi, basu jin magana ne na wuce misali, ga shariya da mannin hauka game da izza. To su wannan raba masu wajen zama da ya yi ne ya baƙanta masu rai, ba zasu iya rabuwa da juna ba ko dede da minti ɗaya, hakan yasa suka shammaci bawan Allah suka sanya mashi diaza a cikin ruwan shansa, yana sha ya haukace a school ɗin, 24 hours yana aiki kamar computer, ko barci bai iya yi ba, bawan Allah ya wahala a lokacin, abin gwanin ban tausayi kuma gwanin ban dariya idan kuka kalli yadda yake tiƙar aikin. Diaza wata shegiyar kwaya ce mai haukatar da mutun, yasa ka yi ta aiki kamar jaki babu gajiya. Ko a ina suke samo abubuwan kulla muguntar tasu? Ƴan yara da su, abin da mamaki, dole akwai mai basu wasu abubuwa, dan dai su idan ba shopping ba basu zuwa ko'ina bayan school, ko gidan uncles nasu kaisu ake yi a kuma dawo dasu, basu driving da kansu ma bare ace sun ɗauki mota sun fita sun je sun sayi wani abin, idan zasu fita sai da driver and bodyguards masu rai da lafiya da zasu yi tsaron lafiyarsu, su kaisu su kuma dawo da su gida lafiya, to a ina suke samo kwayoyi masu haɗari haka? Akwai matsala kam babba ma kuwa..........🤔 Za dai mu gani, lokacin zai nuna mana komai, amma dai twins Obaid and Omaid kamar ba ƴaƴan Momma ba wlh, basu ji sam. Yah Jawad ya zo wucewa ta saitin bedroom ɗin nasu zai je wajen Akka ya jiyo sautin dariya kamar wasu zararru. Ƴar mamaki ce ta kama shi, dan shi dai yasan twin's basa dariya, kuma basu da yawan magana, bai san a waje ne suke haka kamar malaman islamiya ba, idan suna ɗaki su biyu kamar ƴaƴan shaiɗan haka suke, su yi ta tuna muguntar da suka yi a baya wa mutane suna ɓaɓɓaka dariya kamar waɗan da aljanu suka shafa. Room ɗin nasu ya nufo, handle ɗin door ɗin ya rike tare da murɗawa a hankali ya sanyo kai. Suna jin an buɗe kofar suka wani irin nutsu sit. Wani irin kallo ya wurga masu. Nan take suka sha jinin jikinsu, tsuru tsuru suka yi da idanu. "Me yake damunku haka?". Shi ne tambayar da ya jefa masu yana ɗaure fuska. Omaid ne ya ce. "Nothing Yah Jawad, kawai we're watching some comedys in my phone ne yake bamu dariya". "Shi ne kuke dariya haka like you're out of your sense?". Obaid ne ya ce. "Sorry Yah Jawad ba zamu sake ba". Juyawa ya yi ba tare da ya sake yi masu magana ba ya fice daga ɗakin. Kallon juna suka yi tare da sake kwashewa da dariya ƙasa ƙasa suna toshe baki kada sauti ya fita Yah Jawad ya dawo ya karairayasu. Shi kuwa Yah Jawad yana fita part ɗin Akka ya nufa. Gimbiya Chuchu ta tsantsara kwalliyarta cikin wani abaya pink color mai shegen kyau, ta yi kyau sosai, arab hair ɗin nan nata ta ɗaure shi part biyu, Kuyanga mama Haulat ta kitse mata jelar gashin nata gwanin birgewa, sai sheki yake yi ita kuma tana ta tashin kamshin daddaɗar perfume mai sanyaya zuciyar mai shaƙa wadda Momma ta basu ita da auta Zunaira. Sam ta manta da yarjejeniyar da suka yi da Yah Jawad, ta tsaya sai ɗaukar kanta hoto da videos take yi a wayarta abinta, dan ba karya ta yi kyau over......... Dama ai mai hali baya fasawa, da wuya ta dai'na ɗaukar hoton nan lokaci guda haka, abin da ta saba yabi jininta ai ko zata dai'na ba lokaci guda haka ba, sai a hankali. Yana shigowa ɗakin ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana binta da kallo tare da jingina jikinsa da jikin door ɗin shigowa room ɗin, tunani yake yi yadda zai yi da yarinyar nan a duniya.............. Nima tunani nake yi lokacin da zan dasa aya ya yi, sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu da rai da lafiya, zamu ji ya Yah Jawad zai yi da Gimbiya Chuchu? Wani hukunci zai yanke mata?....🤔 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 7/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________30🔥 Yana shigowa ɗakin ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana binta da kallo tare da jingina jikinsa da jikin door ɗin shigowa room ɗin, tunani yake yi yadda zai yi da yarinyar nan a duniya. Sam bata ji motsinsa ba, videonta kawai take ɗauka, ta turo bakin nan ta sake ɗaga jera ɗaya, sai style kala kala take yi. Kamar a mafarki ta gansa ta cikin camerar wayar tata. Ai a dubu ɗari ta juyo har wayar tata sai da ya faɗi ƙasa. Tana juyowa suka haɗa idanu, ko kyafta idanu daga kallonta bai yi ba. Tana juyowa sai da ya ji gabansa ya faɗi, saboda kyan da ta yi, kun santa da shegen iya make up, dama kuma ga kyau kamar su suka yi wa kansu. Ƙasa da kai ta yi kamar wata mumina sahabiya. Tun bai yi mata magana ba ta fara ƴan kame kame tana in'ina ta ce. "Am.... Im so sorry Yah Jawad...... Na mance na ce ba zan sake bane". Tana magana kirjinta na dukan uku uku. Kamar mutun mutumi ne a wajen ba shi ba, ko motsawa bai yi ba bare tasa ran zai amsa mata, in fact ko kallonsa daga kanta bai kawar ba, ya tsareta da ido kamar wadda aka yi wa guduma a tsakar kai ya yi tsumar tsaye. Duk baiwar Allah ta tsargu, tana son ta ɗago kai ta saci kallonsa, amma tana tsoron su haɗa idanun, ga shi ta ji ya yi shiru bai yi magana ba, tana son ta ga action da ya ɗauka, shin yana harararta ne ko kuma dai yaya? Face ɗinsa a ɗaure take ne ko kuma dai a ɗan sake? Duk tana son sani, amma ba halin ta ɗago kai, saboda tsoronsa. Sai addu'a take yi Allah ya kawo Akka, idan Akka ta shigo shikenan ta tsira. Har kerma ƴan hannayenta suka fara yi, ba abin da take tunawa irin punishment na ranar, narai narai ta yi da idanun tana shirin fara yin kuka kawai. Almost 10 mins yana tsaye a haka, sai da ya ga hawaye ya fara bin kyakkyawar kumatunta yana ɓata mata make up nata ne, a nan ne ya ɗan sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanunsa ya sake buɗesu. A hankali ya fara takowa izuwa cikin ɗakin. Datse idanunta gam ta yi tana jiran kawai ta ji saukar mari. Gabanta ya ƙariso yadda ta tsaya kamar wadda aka sassaka. Ɗan sunkuyawa ya yi ya ɗauko wayarta da ta yasar a kasar, pause ɗin video da take ɗauka ya yi, sannan ya yi saving video, yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi mata magana ta raɓa gefensa da gudu da nufin ta yi waje. Cikin sauri ya riƙo hannunta tare da ɗaure fuska sosai. "Where are you going?". Ya faɗa cikin sanyin murya. Bai san cewa uncle Abbas ta gani a bayansa yasa zata gudu ta je wajensa ba, yanzu ya shigo room ɗin, sallama ya zo yi da Akka zai wuce, shi ne da ta ga ya tsaya a bakin kofa yana kallonsu zata gudu ta je wajensa, hankalinta ya ɗan kwanta uncle nata ya zo shikenan ta tsira, shi kuwa Yah Jawad bai san da uncle Abbas ɗin ya shigo ba. Janyota ya yi ta dawo ta gabansa, kara ɗaure fuska sosai ya yi irin ba wasan nan. Gabaɗaya hankalinta na'a kan uncle Abbas ɗin, shi ma ya harɗe hannu a saman kirjinsa yana kallonsu. Ganin hankalinta na'a kansa yasa ya yi mata alama da ta yi shiru bari ya ga gudun ruwan Jawad ɗin. Ganin uncle Abbas ɗin ya yi mata alamar ta nutsu ne yasa ta nutsu tare da yin ƙasa da kanta. "Am i not talking to you?". Yah Jawad ya yi maganar yana sakin hannun nata da ya riƙe. "Am so sorry babu in da zanje". Ta bashi amsa tana ɗan satar kallon uncle Abbas. "Wai Jannat anya babu wata matsala a tattare da ke kuwa? Ban hanaki ɗaukar hoto ba?". "Mantawa na yi, amma ka yi hakuri ba zan sake ba". Nisawa ya ɗan yi kamar wani wadda ya yi wani aikin ya gaji. "Yanzu wani hukunci kike son na yi maki?". Sai a lokacin ta ɗan ɗago da kanta, a hankali ta kai kallonta izuwa saman face ɗinsa, while shi ma face ɗin tata yake kallo, hakan yasa suka kalli juna a cikin idanu. "Dan Allah Yah Jawad kada ka yi mun komai, Allah ba zan sake ba, na tuba, wlh bana son kneel down ɗin nan, please Yah Jawad, gwara mun ka kwace wayata na har abada akan ka ka bani punishment ka ji?". Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar, a shagwaɓe kuma ta yi maganar, ga ragowar guntun hawayen ɗazun a saman fuskarta. Lumshe idanunsa ya yi, har cikin ransa ya ji voice ɗin nan nata. "Last time bana ce ki sameni a part ɗina ba? Meyasa baki zo ba? Kin rai'na ni ko?". A hanzarce ta girgiza mashi kai alamar a'a tana mai cigaba da maimaita mashi kalmar sorryn nan dai da ta saba faɗa kullum. "Ina Akka?". A hanzarce ta amsa mashi da. "Bata nan ta fita, ina ga ko tana wajen daddy ko kuma wajensu mummy". "Meyasa kika ce mata ni na hanaki zuwa Dubai?". Zaro idanu waje ta yi, ita kwata kwata ma ta mance da cewa ta kai karansa wajen Akka ɗin, wannan shi ne laifi a kan laifi, dan kuwa Akka ta je har part ɗinsa wai sai ya gaya mata dalilin da yasa ya hana Chuchu zuwa Dubai?. Da kyar ya shawo kanta ta rabu da shi, wannan dalilin yasa ya biyo Chuchun, yasan confirm zai sameta a nan ɗin, shi ne ya zo. "Ba zaki bani amsa ba kenan ko? Wai ni Jannat yaushe na zama abokin wasanki ne?". Cigaba da girgiza mashi kai ta yi, nan take idanunta suka sake ciko da kwallah, kan kace me sun fara bin kumatunta. "Another case kenan, bana hanaki kuka ba?". Da sauri ta sanya hannu ta fara goge hawayen nata. "Okey jeki part ɗina ki yi kneel down ina zuwa". Okey ta amsa mashi da shi tare da raɓawa jefensa ta wucewa da sauri. Tana wucewa ya juyo da kallonsa a kanta domin ya kara tsareta da idanu. Mugun jin daɗin kallonta yake yi ɗan rainin wayo, amma tsabar walaƙanci da mugunta sai ya rinƙa baƙanta mata rai, ya yi ta takura mata yana sakata kuka. Yana juyowa suka yi ido huɗu da uncle Abbas da ya saki baki yana ganin ikon Allah, shi dai yasan babu wanda ya taɓa yi wa su Jawad ɗin makamancin haka, amma su sun zo suna cin zalin kannesu. Ɗan zaro idanu ya yi yana kallon daddyn nasa, yana son ya san yaushe uncle Abbas ɗin ya shigo room ɗin, adduarsa ɗaya Allah yasa bai ji abin da ya ce da Chuchu ba, dan yasan halin uncle Abbas sarai, idan kana son kaga ɓacin ransa to ka taɓa mashi ƴan matan nan nasa, sam baya son yaga an taɓasu, ƴan lelene, shagwaɓasu yake yi over, shiyasa suma suke matuƙar kaunarsa sosai, ba dan ba dan bama sai mu ce sun fi kaunarsa sama da daddynsu King Zuhair. "Welcome daddy yaushe ka shigo?". Ya faɗa yana satar kallon Chuchu da ta fita a yanzu, yana magana yana fargabar kada ace daddyn nasa ya ji maganganunsu da ita. Shiru uncle Abbas ɗin ya yi har sai da Chuchu ta yi nisa da room ɗin, sannan ya ce. "Tun lokacin da kake sanya mun ƴata kuka na shigo". Ɗan shafa arab hairnsa ya yi tare da ɗan sunkuyar da kai ƙasa. "Kai daddy ni yaushe na sakata kuka? Kawai sune sun cika yin kuka banza banza, kuma duk kai ka shagwaɓasu ai, ni iya faɗa kawai nake yi mata". "Jawad wlh ina jiye maka tsoron kar ka tabka kuskure". Uncle Abbas ya faɗa tare da ƙarisowa cikin room ɗin. A saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna tare da ɓalle botir na suit ɗin jikinsa. "Daddy kuskuren me kuma?". Ya faɗa da iya gaskiyarsa, dan shi bai san wani kuskure daddyn nasa yake hango mashi ba. "Zaka ce mun baka san abin da nake jiye maka tsoro bane?". Ya yi maganar yana wurga mashi wani irin kallo da waɗan nan idanun nasa irin na Akka. "Kai daddy wannan kallon fa?". Ya kai karshen maganar tare da dawowa kusa da daddyn nasa ya zauna a saman sofar. "Ai dole na kalleka da kyau tukun nan, na tabbatar lafiya kake da zaka ce mun baka san tsoron da nake jiye maka ba". Ɗaura wayar Chuchu a saman hannun sofar ya yi tare da cewa. "Daddy da gaske ban san wani irin kuskure kake ji mun tsoron na tabka ba". "Jawad kenan, to ina jiye maka tsoron ranar da zaka bayyanawa Jannat gaskiya ita kuma ta ce bata so bazata yarda ba saboda kana mata mutunta, a ranar ne zaka gane ka yi kuskure". Ɗan zaro idanu ya yi, ƴar mamaki ce ta bayyana a saman face ɗinsa. "Daddy wace gaskiya kuma zan bayyanawa Jannat har da zata ce bata so?". Hararar wasa uncle Abbas ɗin ya wurga mashi kafin ya ce. "Yanzu zaka ce mun ba son Jannat kake yi bane?". "So kuma daddy? Ni ɗin?". Ya faɗa cike da mamaki sosai. "A'a ba kai ba ni, wai Jawad lafiyarka ma kuwa?". Shiru ya ɗan yi yana tunani, sake furta cewa son Jannat ni kuma, ya yi tare da nuna kansa, mamaki abin ya bashi ne. "Baka yardanwa kanka kana sonta ba ko? To bari na baka wani Assignment ka je ka aiwatar da shi yanzu, idan ka kammala sai ka kirani a waya ka sanar da ni amsa". Dawo da kallonsa a kan daddyn nasa da kyau ya yi kafin ya ce. "Okey daddy ina jinka wani Assignment?". Kallon shi da kyau uncle Abbas ɗin ya yi kafin ya ce. "Ba ka ce ta je ta yi kneel down a part ɗinka yanzu ba?" Gyaɗa mashi kai ya yi almar e ya ce. "Okey in ka je part ɗin naka yanzu ka barta ta yi one hour tana kneel down, kuma kada ka hanata yin kuka, ka barta ta yi kukanta, sannan idan ta cika one hour ɗin ka ce ta tafi room ɗinta da kafafunta, idan ta kasa ka ce dole ta tafi, ko kukan jini zata yi kada ka kulata ta taka da kafafunta dole, idan ka iya aikata hakan ka kirani ka gaya mun.....". Ya kai karshen maganar yana kallon ɗan nasa har cikin ido, dan shi dai yasan tun Chuchu bata kai haka ba yasan da cewa Jawad ɗin yana sonta, shi ne dai bai gane hakan ba, amma yanzu zai gane ne dolensa, uncle Abbas yasan ko dede da minti ɗaya Jawad ba zai iya jure kukanta ba, amma dai koma me yanzu zai gane ai. "Daddy wai yau da kanka kake cewa na bawa ƴan gatanka punishment? Kuma kace ko ta yi kuka na barta ta yi ta yi? Anya daddy kai ne kuwa?". Ɗan murmushi ya yi tare da faɗin. "Ni ɗin ne dai, Abbas ɗin da kasani ne, ni nace ka je ka yi ai, kawai ka je ka aikata, idan ka iya sai ka kirani ka sanar da ni, dan ni daga nan wucewa zan yi......". Girgiza kai ya fara yi yana faɗin. "No daddy banda kuka kam, ni bana son ganin kukanta, amma zan iya sanyata kneel down sosai, har ma fin one hour, amma ba zan iya jure ganin kukan nata ba". Harararsa uncle Abbas ya yi kafin ya ce. "Okey tom shikenan na janye wannan Assignment ɗin bari na baka wani, idan ka koma part ɗin naka yanzu, ka kalleta ido cikin ido na a kallah one mint, duk tunanin da ya zo zuciyarka a wannan lokacin ka kirani ka gaya mun, dan shi ne gaskiyar abin da yake a tsakaninku". "Daddyyyyyy kai ni wlh wahalar dani kawai kake son yi, Jannat is my sister that's all, bayan haka ni babu wani abin, to daddy Jannat ma nawa take? Yaushe ta girma ma? Me zan yi da ita? Ai ta yi mun ƙanƙanta, ni bani ma da lokacin mata a yanzu". Ya kai karshen maganar yana turɓune fuska, shi sam bai ma san cewa ya saki layi a maganar tasa ba, ko da yake shi dama bai kai Jaish kunya ba. "Babu abin da zaka yi da ita, kuma bata girma ba amma a haka kullum kake tsare mun ita da ido, idan kana kallonta ma har mantawa kake da in da kake, jiya ma fa a parlourn Yah Zuhair ina ganinka sai kalle mun ita kake yi kamar ka samu Tv, gaskiya zan gayawa yaya ma duk ku bar family part ɗin nan ku koma gidajenku, saboda kun sakawa ƴaƴana ido, ku barmun su su sakata su wala". Da yake gidajen nasu dukka a cikin kingdom ɗin yake, sai dai yana da ɗan nisa da family part gaskiya. "Kai daddy wai ni yaushe na kalleta ne? Kai da uncle Taheer da dad kun saka mun ido fa, shi ma dad daren jiya har da ce mun wai yanzu aure zai yi mun ni da Jaish ya huta, to mu laifin me muka yi yanzu fisabilillahi da kuke neman ɗaura mana wahala?.". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ɗauki wayar Chuchu ɗin da ya ajiye, sannan ya nufi waje. "Allah ya kiyaye hanya daddy". "Zaka ga mun saka maka idanu ne, sai na yi mata miji cikin ɗaya daga cikin ƴaƴan abokaina ba tare da saninka ba za'a ɗaura auren, a nan ne zaka san mun saka maka ido, ka jira ka gani". Shiru ya yi, dan har ya ji ransa ya ɗan ɓaci da last zancen daddyn nasa, da sauri ya wuce ya fita dan kada ma daddyn ya ƙara yi mashi magana mara daɗi irin haka. Da kallo uncle Abbas ya bishi, sai da ya fice ne ya ce yaro yaro ne, zaka yi bayani ne, ai ita so ba'ayi mata wargi. Part ɗinsa kai tsaye ya nufa, sai saƙa kalaman daddyn nasa yake yi a cikin ransa. Ƙasa ƙasa ya yi sallama kamar mai ciwon baki. Babu kowa a parlourn nasa, sai tashin kamashi da ko'ina yake yi, kai tsaye cikin room ɗinsa ya nufa. A nan ya isko Gimbiya Chuchu ta yi kneel down sai aikin sharar kwallah take yi, har idanunta sun yi jajir saboda kuka. A kusa da ita saman katafaren bed ɗinsa ya zo ya zauna tare da ajiye wayoyinsa haɗe da nata a gefensa. Zancen daddy nasa ne kawai yake yi mashi yawo a cikin kansa. Ji kawai ya yi zuciyarsa ta aminta da ya yi abin da daddyn nasa ya faɗa. Slowly ya kai hannunsa ya ɗago haɓarta daga yadda ta sunkuyar da kai ƙasa tana ruwan hawaye. Datse idanunta gam ta yi saboda tsoron su haɗa idanu da shi. Sai da ya ji tsikar jikinsa ya wani irin tashi na ganin face nata kawai da ya yi, a haka ma ba cikin kwayar idanun nata ya gani ba, ga shi face ɗin nata ma ya yi jaga jaga da hawaye, duk ya ɓata mata kwalliyarta. In a low voice sosai ya furta. "Open your eyes". Bata da zaɓin da ya wuce ta buɗe idanun nata, slowly ta warosu waje, sai dai taki yarda su kalli juna ido cikin ido, sai ta kawar da kallonta gefe guda tana mai cigaba da ruwan hawayenta suna bin gefe da gefen face ɗinta kasancewar ya ɗaga mata kanta sama. Wani irin shock ya ji tun daga tsakiyar kansa har izuwa tafin kafafunsa, yana kallon face nata sosai a duk time ɗin da suka haɗu, amma bai taɓa jin yanayi irin na yau ba, anya ba baki uncle Abbas ya yi mashi ba kuwa? Ya tambayi kansa da kansa. Luluƙawa duniyar tunani kawai ya yi, ji yake yi har cikin ransa yana sha'awar ya yi ta kallon face nata ba gajiyawa. Kyawawan laɓɓanta ne suka fara kerma saboda yadda ya ɗaga mata wuya sama ya fara yi mata zafi, hakan yasa ta tsananta kukan nata da take yi, shi ne dalilin ja mata kermar laɓɓan nata. Slowly ya mayar da kallonsa a saman lips ɗin nata, yadda suke kerman nan ba ƙaramin kyau suka yi mashi ba dan mugunta, har shaiɗan yana ƙoƙarin raya mashi wani abin na daban a cikin zuciyarsa. Ganin ya fara tunanin ya yi kissing na lips ɗin tata ne yasa ya yi saurin sakar haɓar tata tare da dafe kansa da hannu ɗaya. "Tashi ki tafi Jannat". Ya faɗa cikin wata iriyar murya mai kama dana mai jin barci. Da sauri ta miƙe, ba tare da ta kalli in da yake ba ta yi saurin nufar waje. Da idanu ya bita da kallo har ta fice. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya kwanta a saman bed ɗin, tunanuka kala kala ne a cikin ransa wanda bai bama kowa damar sani ba. A haka barci ta yi awon gaba da shi, ba shi ya farka ba sai da ringing ɗin wayarsa ta tashesa, cikin barci ya ji wayar tana ƙara, da kyar ya iya buɗe idanuwansa da suka yi mashi bala'in nauyi, jikinsa duk a mace, wannan barci da ya yi tun daga farkonta har izuwa ya tashi mafarkin Gimbiya Chuchu kawai ya rinƙa yi, ta tsaya mashi a rai kamar uncle Abbas ya yi mashi baki. Da kyar ya iya laluɓar wayar tasa, ɗaukota ya yi tare da bin saman screen ɗin da kallo. Ɗan zaro idanuwansa waje ya yi lokacin da idanunsa suka sauƙa a kan time. Karfe 8:30 pm, ko sallar mangariba bai yi ba ga issha ta wuce. Shafa arab hairnsa ya yi tare da yunƙurawa zai miƙe. Ina kasa miƙewar ya yi, duk jikinsa a mace, ga barcin yamma ga kuma mafarkin Chuchu, abin ya haɗu ya yi mashi yawa, dama kuma da tunaninta ya yi barci. Call na biyu ne ya sake shigowa wayar tasa, dan wancan ta katse kafin ya ɗauki wayar. Ganin sunan my daddy ne yake yawo a saman screen ɗin yasa ya yi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnensa. "Hello daddy". Ya faɗa cikin murya ƙasa ƙasa, dan bai wastsake ba. Daga ɗayan ɓangaren uncle Abbas ya ce. "Barci kake yi ko my son?". "Wlh daddy barci ne ya ɗaukeni sai yanzu na farka". "Oh ka ci abinci dai ko?". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya amsa da no bai ci ba. "To ka tashi ka ci abinci, amma kafin nan bani amsata na Assignment dana baka a kan Jannat". Miƙewa zaune daga kwanciyar da yake ya yi. "Daddy i didn't feel anything ni kam, na kalli cikin idanunta ban ji komai ba". Ya faɗa yana kwaɓe fuska. Sarai uncle Abbas yasan ba gaskiya ya gaya mashi ba, dan shi yasan wlh tun Chuchu tana ƴar shekara 5 yake daƙon sonta, idan anyi magana sai ya ce kawai sistersa ce, bayan haka babu komai, wannan soyayya ba ta yau bace, ta jima, tsohuwar zuma ce. "Okey tashi ka ci abincin zan zo next month ai". Uncle Abbas ya faɗa, shi kwata kwata ma bai san cewa ko sallah ɗan nasa bai yi ba, yana can duniyar mafarkin babynsa, ya tashi kuma tsabar bushewar ido wai shi bai ji komai ba, bayan kuma har da mafarki, kai maza duniya.........🤔 "Okey dad take care". Ya faɗa tare da katse kiran, a hankali ya zuro kafafunsa kasan bed ɗin tare da miƙewa tsaye ya nufi toilet dan ya yi wanka tare da ɗauro alwala. Da alama uncle Abbas yana son haɗa Gimbiya Chuchu da Yah Jawad aure, ga shi Mammie kuma kun ji ta dakawa Yah Jawad ɗin warning a kan Chuchun, ta ce bata sonta, to ko ya zasu kare? Akwai cakwakiya babba kuwa, dan kuwa Mammie idan bata son abu babu abin da ba zata iya aikawa dan ta rabu da wannan abin ba...... Hmmm akwai rikici nan gaba ba kaɗan ba. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🕊️🌼🕊️🌼🕊️🕊️ UAE💔😥 DUBAI HILLS ESTATES💔😥 Kai tsaye cikin wani haɗaɗɗen bedroom wannan matashiyar matar ta kai Leesharh. Tun da suka sanya kafafunsu cikin room ɗin Leesharh ta saki baki tana kallon irin dukiyar da aka narkawa wannan room ɗin, kamar room na hajiyar gidan gabaɗaya, amma a haka ace ɗakin ƴar aiki? Wai me mutanen nan suke so ne a rayuwarsu? Irin wannan uban tarin dukiya dukka kuma suke neman leƙar asirin wani, wannan ya tabbatar ba kuɗin suke yi wa ba, sai dai idan wutar ɗaukar fansa ce take ruruwa a cikin zuƙatansu, kuma da alama ba waɗan nan mata ne kawai suke shirya wannan abin ba, da alama akwai shegun manyan kai daga sama, idan kuka yi duba da yadda hajiya two seater ta kawo Leesharh kuma bata shigo cikin gidan ba ta juya tare da waɗan nan motocin, dole ita ma nata team ɗin daban, sannan suma waɗan nan motoci da alama bana wannan gida bane, suma na wani team ne na daban, abin dai akwai ɗaure kai sosai. Ƙananun shekarun Leesharh yasa ta kasa iya gane cewa ba komai ake yi dan kuɗi ba, ba kuma komai ne kuɗi yake iya saya ba. "Leesharh this is your room, ki je ki yi wanka, zan kawo maki kayan sakawa da abinci ki ci ki ƙoshi kin ji? Sai ki kwanta ki ɗan huta zuwa anjuma mai koya maki aiki zata zo, don't mind about what my mum said kin ji? Babu abin da zai sami daddynki, zaki koma wajensa lafiya lou, babu wani abin da zamu yi mashi, yadda kika ga kina cikin wannan room ɗin cikin daula haka shi ma yake, mun ajiye shi ne kawai a ɗaya daga cikin gidanjenmu yana cin arziki shi ma, so dan haka ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki koyi duk abin da za'a koya maki, sannan ki yi aikin ki cikin natsuwa da iya taku ta yadda ba za'a ganeki ba, idan ma kika mayar da hankalinki two months ya yi ti yawa ki kammala mana aikinmu ki koma gida kin ji ko?". Allah sarki yarinyata, kai kawai Leesharh ta gyaɗa mata alamar ta gansu da maganganunta. Juyawa matar ta yi ta fita domin ta bata waje ta yi wanka. A hankali kamar mai tsoron taka ƙasa ta ƙarisa bakin shinfiɗaɗiyar bed ɗin ta zauna, sai buɗe hanci take yi tana shakar daddaɗar kamshin perfume ɗin dake room ɗin, tunani kala kala ne a cikin ranta, sai dai zantukan babanta ya fi yi mata yawo a cikin kanta sosai, tana kaunar baban nata sosai, musamman ma da ta zauna da Jasrah yarinya mai ilimin addini, ta koyar da ita abubuwa da dama, a nan ne ta gane cewa babanta yakamata ta so sosai ba mamanta ba, domin baban nata ya fi mamarta gaskiya. Ta kai a kallah 30 mins a zaune a wajen tana aikin tunanin zantukan babanta dana mamar tata, lokacin da tunanin Jasrah ya ratso mata ta cikin ƙwaƙwalwa tata, nan take wasu siraran hawayen ya fara bin ƙuncinta, har ga Allah bata kawowa ranta rabuwa da Jasrah ba, sam bata taɓa yin wannan tunani ba, amma rana tsaka an rabasu, rabawa mara daɗin ji, ta tabbata yanzu haka Jasrah tana can tana ruwan hawaye, ga shi bata da wata kawa a gidan AAJ, ba kowa, yanzu haka zata yi zaman kaɗaici cikin kunci?. Kara tsananta gudu hawayen face ɗin nata ya yi, a gaskiya tana kewar Jasrah over. Dafa shoulder ɗinta da aka yi ne ya fargar da ita tare da dawowa cikin hayyacinta. A hanzarce ta ɗago da dara daran idanun nata da suka yi jajir saboda kuka da damuwa. "Leesharh baki yi wankar ba kin zauna a nan kina kuka? Kukan me kuma kike yi?". Cewar wannan matashiyar matar, hannunta na rike da wasu kaya masu shegen kyau da tsada, abaya ne da mayafinta launin brown color, ya ji stones jikinsa sosai, sai kyalli yake yi. "Aunty ina kewar Jasrah ce, and ina son ganin babana da kuma kabarin mamata". Zama a kusa da ita matar ta yi, cikin mutawa tare da nuna fifikon ilimi da shekaru ta fara tsara mata magana kamar haka. "Leesharhi i promise you that idan kika tsaya kika fara aikin nan da kyau, kika yi one to two weeks kina aikin na ga yadda kike tafi da komai, komai ya tafi dai'dai, idan kika mayar da hankali naga kina ƙoƙari, to na yi maki alkawari zan zo na ɗauke ki daga gidan Abu Abdussalam muje na kai ki ki kalli babanki, sannan mu wuce AAJ ki kaiwa Jasrah ɗin ziyara, idan muka dawo naga kina ƙoƙari a kan aikin sosai to duk end of the week zan rinƙa kai ki wajensu kuna ganawa". Yadda ta yi maganar kana ji kasan kalaman karya da yaudara tare da makirci ne, amma da yake ita Leesharh ba ilimi ishasshe ne ke gareta ba, ga kuma ƙarancin shekaru, sai ta yarda da zancen, kuma da alama ta yarda da wannan mata sosai. Cigaba da lallaɓata matar ta yi tana kwantar mata da hankali har sai da taga ta samu nutsuwa, sannan ne ta riƙo hannunta suka miƙe ta raka cikin toilet, da kanta ta haɗa mata ruwan wanka saboda makirci, duk cikin taku ne. Bayan ta haɗa mata ta nuna mata yadda zata yi komai ne ta nufo waje ta barta a cikin toilet ɗin. Sai da Leesharh ta ɗauki almost 30 mins a tsaye a cikin toilet ɗin tana tunane tunane kafin ta fara wanka. Sosai ta wanke jikinta tsab da tsadaddun shower gels ɗin da suke a cikin toilet ɗin, har wani ɗan haske ta kara yi, dattin gidan AAJ ya fita. Daga yanayin yadda take amfani da abubuwan cikin toilet ɗin zaka fahimci ba yau ta fara ganin ire-irensu ba, da alama ta saba gani, so bata wani nuna kauyanci ba, towel ma ta ɗauro ta nufo waje bayan ta kammala, sai tashin kamshin take yi. Lokacin da ta fito sai ta tarar da an kawo mata abinci kala kala na larabawa masu shegen tashin kamshi, an geresu a saman rug da yake a cikin room ɗin. Da ido ta fara bin abincin da kallo, wajen kala huɗu ne abinci, duk kuma ita kaɗai aka kawowa, kara jinjinawa wannan al'amari ta yi kafin ta wuce ta ɗauki kayan da yake a saman bed ɗin wanda wannan mata ta ajiye mata. Ba tare da ɓata lokaci ba ta sanya kayan a jikinta. Sun yi mata kyau sosai, sun kuma zauna a jikinra kamar sun san size ɗinta, har jikinta ya fara sanin cewa ta fara samun canji. Zama ta yi a gaban abinci, ta zaɓi wanda zata iya ci, ta zuba a plate, hannu baka hannu kwarya ta fara kai abincin nan bakinta, dan a yunwace take baiwar Allah, hakan yasa ta ci sosai da sosai. Wani irin ƙoshi da ta yi ma har sai da ta ji numfashinta yana yin sama sama, da kyar ta iya tattare wajen ta haɗa kayan abin waje guda. Kaɗan ta sha ruwa dan gudun kada ta yi amai, sannan ta ɗan sha lemu kaɗan. Bayan ta kammala ne ta tashi ta fara gabatar da sallolin da suke a kanta a wajen saman rug ɗin, dan ta ɗauro alwala tun daga cikin toilet da ta gama wanka. Tana idar da sallar a wajen ta ɓige da barci, anci an ƙoshi me ya rage? Ai sai barci, dama ga wahala da gajiyar gidan AAJ a jikinta. Ba ita ta farka ba sai da yamma, nan ma wannan matar ce ta zo ta tasheta a kan ta tashi ga mai koya mata aiki ta zo. Da kyar ta iya buɗe idanunta, yau ta kwanta a waje mai laushi ga sanyin Ac haɗe da daddaɗar kamshin perfume, sannan ta ci abinci mai rai da lafiya ta ƙoshi, barci ya yi daɗi har da munshari, duk jikinta sai ta ji ya yi mata nauyi, sam barcin bai isheta ba. Idanuta sun ɗan kumbura sun kuma yi jajir, alama ce ta barci bai isheta ba. Ba ƙaramin madarar mamaki ta shaba lokacin da ta kalli mai koya mata aikin, ita ma matar tana sanye da nikaf, wannan batu na nikaf ɗin ya fara ɗaurewa Leesharh kai sosai, kowa ka gani a gidan da nikaf? Ita a yanzu bata san face ɗin ko mutun ɗaya daga cikin ƴan gidan ba, su kansu securitys ɗin gidan sanye suke da face mask a fuskokinsu, abin da alamar tambaya sosai, duk da yarinta irin na Leesharh yanzu ta fara tunanin anya akwai gaskiya a wannan gida kuwa?. Fita wannan matashiyar matar ta yi ta basu waje, ya rage daga Leesharh sai mai koya mata aiki, ita ma matashiyar macece wadda ba zata wuce 30 years a duniya ba, tana tare da wani haɗaɗɗen echolac ɗinta ɗan ma dai'dai ci, hakan ya nuna cewa tare zasu rinƙa kwana da Leesharh a wannan ɗakin kenan. Sannu da zuwa Leesharh ta yi mata tana ƙoƙarin miƙewa tsaye, ga mamakinta sai taga duk an kwashe kayan abincin da ta ci ta bari, babu komai a room ɗin. Sam matar bata amsa mata ba, yadda kuka san wasu abokan gaba, sai wucewa da ta yi ta sanya echolac ɗinta a cikin katafaren wardrobe da yake a cikin ɗakin, sannan ta nufi toilet. Cike da mamaki sosai Leesharh ta bita da kallo, ta sha madarar mamakin ganin yadda matar bata amsa sannunta ba, tunani ta fara yi to ko dai matar bata jin larabci ne? Ga dukkan alamu kuma balarabiya ce, duk da cewa baka iya ganin komai na jikinta sai ido, saboda kayan da ta sanya ta rufe ko'ina nata, amma da alama ba bakar fata bace ba, ko meyasa ta ki amsa mata? Allah masani. Cike da tunani Leesharh ta wuce wajen katafaren windown da yake fiskantar harabar gidan dan ta leƙa taga ko zata iya samun damar ganin fuskar ɗaya daga cikin ƴan gidan. Ta kai 10 mins a tsaye a wajen, amma shiru bata ga giftawar wani ɗan adam a harabar gidan ba, jin motsin alamar wancan mata tana ƙoƙarin fitowa daga cikin toilet ɗin ne yasa ta yi saurin barin jikin window ta koma bakin bed ta zauna. Fitowa matar ta yi a in da ta zo ta ciro dadduma daga cikin echolac ɗinta ta shunfuɗa a kasa saman tiles ɗin ɗakin tare da tada sallah. Sai ƙure mata kallo Leesharh take yi, dama ita fa ba baya ba wajen iya yi wa abu kallon ƙurilla, ba kallon wasa take yi wa abu ba, ƙure mashi kallo take yi ta haddace komai. Tana ta ƙurewa wannan mata kallo har ta idar da sallarta cikin nutsuwa tare da dai'daito kamar yadda addini ya faɗa, daga ganin yadda wannan mata take sallah tabbas addini ya ratsata sosai, to amma meyasa duk da tana da sani take yi wa waɗan nan unknown mutane aiki? Wannan amsa sai alƙalamina ne kawai zai warware maku, ku dai kasance a tare da ni dan mu warware komai a tare, nasan kuna da tarin tambayoyi sosai a kan rayuwan kowani part na cikin wannan littafi, to kada ku ji komai, sannu a hankali zan nemo bakin zaren kowace part in warware maku dukkan wasu amsoshinku my people. Bayan wannan mata ta idar da sallah ne ta miƙe ta nufi wajen bed in da Leesharh take a zaune kenan, cikin harshen larabci ta umarceta da ta tashi su nufi cikin gidan, domin ta je ta fara nunnuna mata abubuwa, shi ne abu na farkon da zata fara koya mata, zasu koya mata hakan ne kuma saboda kada Leesharh ɗin ta je ta yi masu kauyanci, dan duk ba ƴan kauye bane suke yi wa familyn Abu Abdussalam bin Badeen aiki, sai mai kwalin maratu suke ɗauka aiki, dan basu son shirme da shiririta, dan haka duk sai an wayarwa da Leesharh kai sosai da sosai, ta zama kamar cikakkiyar ƴan boko, an kara buɗe mata idanu, kada a samu matsala. Gaba matar ta yi ba tare da ta jira ta ji me Leesharh zata ce ba. Jiki ba kwari ta tashi ta bi bayanta tana mamakin hali irin na wannan mata, ita kuma haka rayuwarta yake kenan? A haka kuma zasu zauna har tsawon sati ɗaya zuwa biyu? Tab akwai matsala kuwa. To nima dai bari na motsa na leƙa wani bangare kafin mu dawo watakila Leesharh ta iya aikin da suke son ta iya. 🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH💔😥 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 8/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________31🔥 🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH💔😥 Sai can rana wuraren karfe 2 su Maman Zainab suka dawo daga wajen malamin nasu, gidanta Aunty Hauwa ta wuce, ita kuma Maman Zainab ta nufo nata gidan. Tun da ta kamo hanyar gida take jin gabanta yana faɗuwa, amma bata kawo komai a ranta ba, a duk lokacin da ta tuna alkawarin da wannan malami ko ace bokan ya yi mata na cewa tana komawa gida zata ga result ɗin aikinta, sai ta ji wani sanyi ya ratsa zuciyarta. Kuɗi raina na dukan naira har naira 200k ta kwasa ta bawa wannan bokan, Aunty Hauwa ce nan ta yi ta zugata a kan ta bada kada ta wani damu tun da buƙatarsu zai biya, da yake tana da kuɗi issassu, da ni da ku duk mun san da cewa baban Zainab dai bai rageta da komai ba, tana samun kuɗi a hannunsa sosai, wani lokaci haka kawai zai dunƙule dubu ɗari ya bata ya ce ko zata yi wani buƙata, to tara kuɗin take yi, dan kunga bata sayan komai a gidan, ko ashana shi yake sayowa dayawa ya ajiye, hakan yasa take da isassun kuɗaɗe a cikin account ɗinta, shiyasa bata nemi ko sisi daga hannunsa ba da zasu je wajen malamin, sai dai single ɗinsa da ta ɗauka da kuma hularsa, dan Aunty Hauwa ta ce mata ta ɗauki wasu daga cikin abubuwan da yake amfani da su, domin bokan nasu zai buƙaci hakan, ita ma haka wai aka yi mata na mijinta, to shi ne yasa ta ɗauki wannan ma. Ko da ta iso gida cike da murna, ga mamakinta sai ta ga kofar gidan a buɗe sabanin fitarta, ta dai san ta rufe gidan kafin ta fita, kuma lokacin dawowar su Khadija daga school bai yi ba bare ace kawunsu Sadiq ne da ya dawo da su ya buɗe masu gidan, kowa na gidan daga kan Baban Zainab, Haidar, Sadiq duk suna da key ɗin kofar gidan. Ciro wayarta ta yi ta fara duba time, nan take kirjinta ya fara dukan uku uku na ganin cewa lokacin dawowar su Khadija bai yi ba, to kenan waye ya buɗe gidan? Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsarta. Fargabarta ɗaya kada ace Baban Zainab ne ya yi masu dawowar rana irin na kwanaki biyu da suka wuce, idan kuwa shi ne to fa akwai cakwakiya, dan kuwa zata sha faɗa ba kaɗan ba na fita bada izininsa ba, ya fita kishi sosai, kawai dai kawar da kai wani lokaci yake yi dan a samu zaman lafiya, amma ita nata kishin nafila ne a kan nasa. Cike da fargabar abin da zata tarar a cikin gidan ta turo kofar ta shigo. Tsoro da mamaki ne suka kara kamata lokacin da ta turo kofar ta ji ko jam lock ba'a sanyawa kofar ta ciki ba. Ta san da cewa tabbas suna sanya jam lock ta ciki, saboda matasan marasa tarbiyar da suka yi yawa a unguwar, ga shaye shaye, kana zaune baka san hawa ba baka san sauƙa ba zasu faɗo maka cikin gida, sun sha sun bugu ba hankali a tattare da su, basu san ma sun faɗo gidan ba, hakan yasa suke rufe kofar duk wanda ya zo sai ya yi knocking azo a buɗe mashi. Amma yau sai ta ji kofar a buɗe, hakan yasa ta kara fargaba da shiga tsoro, sai yanzu ta fara danasanin fita bata tambaye shi ba da ta yi. Sai kuma yanzu ne abubuwan da suka faru ɗazun ɗin suka fara dawo mata cikin kanta, gabaɗaya sai ta ji jikinta ya saki, duk sai ta ji ta yi nadama kuma ta ji babu daɗi. Kutsawa cikin gidan ta yi tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, ita kaɗai tasan me take tunani. Ƙasa ƙasa ta yi sallama a bakin kofar shiga parlourn. Shiru babu wanda ya amsa mata, cike da fargaba ta sanya hannu ya yaye curtain ɗin kofar. Kwance yake a saman doguwar sofa mai zaman mutun uku, ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman fuskarsa, ɗayan hannun nasa kuma yana riƙe da remote na Tv, ga Tvn yana magana ƙasa ƙasa, sanye yake da brown ɗin jallabiya wadda ta sha guga sosai, har wani kyalli take yi saboda an saba gogeta sosai, ga karin gugan nan a jikinta ya fito ɓaro ɓari, sam ba barci yake yi ba, yana jin sallamar tata, a cikin zuciya ya amsa, magana ne baya son yi mata. Wani irin dum dum ta ji gabanta ya faɗi, tunani ta fara yi a kan tun yaushe ya dawo? Idan bai jima da dawowa ba in ya tambayeta ina ta je sai ta yi mashi karyar maƙota nan ta shiga, tasan cewa ko gidan Aunty Hauwa bai yarda ta je ba, idan tana son zuwa shi yake kaita da mashin ɗinsa, idan ya kaita kuma zai gaya mata ga time ɗin da zai dawo ya ɗauketa, lokaci na cika kuma ɗan halak zaku ga ya zo ya ɗauketa sun dawo, bata zuwa ko'ina ita kaɗai ko da kanta, saboda yadda ya ɗaukota daga garinsu ya kawota nan garin da bata da kowa sai ƴan uwansa da basu sonta sai kuma Aunty Hauwa, hakan yasa yake kula da ita sosai, saboda ya sauke hakkinta da yake a kansa, akwai shi da ilimin addini sosai, kuma yana aiki da ita, duk wani hakkin mace ya sani, kuma yana ƙoƙari wajen saukewa iya iyawarsa. Cikin parlourn ta shigo jiki ba kwari, sai faɗuwa gabanta yake yi, tun da ta shigo take binsa da kallo, ko gezau bai yi ba, bai yi kamar ma yasan da mutun ya shigo ba, hakan yasa ta fara jin fargaba da faɗuwar gaba. Room ɗinta ta wuce da sauri dan ta je ta ɓoye abubuwan da bokan ya bata da ta sanya a cikin jakarta. Tana ajiyewa ta yi maza ta dawo parlourn, da yake bata da gaskiya ko da ta je ajiye jakar sai taga kamar baban Zainab ɗin ya biyo bayanta yana leƙarta, hakan yasa ta yi saurin ajiyewa ta fito, abin ku da bata saba ba, duk sai ta bi ta tsargu tana neman tonawa kanta asiri, ta rasa a ina zata sanya ranta. Saman sofa mai zaman mutun ɗaya ta zo ta zauna tare da ce mashi sannu da dawowa, tsoro da fargaba yasa ta manta da cewa faɗa suke yi, ta manta da cewa tana fushi da shi bata yi mashi magana. Yana jinta amma bai amsa ba, ya yi kamar bashi a parlourn, dan iya ɓacin rai ta ɓata mashi rai, tun karfe 11 ya dawo gidan domin ya ɗebe mata kewa, ya dawo ya cigaba da rarrashinta tare da bata hakuri kamar yadda ya saba, amma sai ya zo ya ga bata nan, kuma bata sanar da shi ga in da zata je ba, ya kira numberta a lokacin suna kan dutse babu network, ya gwada numberta ya fi sau hamshin, amma bata shiga, ya kira number Aunty Hauwa ma bata shiga, ya je gidan Aunty Hauwar Khadija kanwar mijin Aunty Hauwar ta ce mashi Aunty Hauwa bata nan tana wajen business ɗinta na yawon bin gidan dillalai, ita kuma maman Zainab bata zo gidan ba, bawan Allah ya shiga damuwa sosai a kan to ina ta je tun da bata je gidan Aunty Hauwa ba? Ya dai san bata san kowa ba, bata kuma zuwa gidansu Haidar, gara ma gidan hajiyarsa wani lokacin yana kaita su kuma dawo a tare, baya yarda ya barta a can, dan yasan hajiyarsa zata takura mata, a tare suke zuwa su gaisheta su kuma dawo a tare. Bawan Allah nan ya yi tunani sun fi kala ɗari a kan ina taje? Wani zuciya ya rinƙa raya mashi cewa kila ta yi fushi ne ta shiga mota ta koma gidansu, ya kira mamanta cikin hikima ta yadda ba zata yi zargin komai ba ya tambayeta ko ta yi magana da maman Zainab da safe ne? Da maman ta tambayesa lafiya? Sai ya ce lafiya lou kawai dama maman Zainab ɗin ce ta tambayesa a kan zata je gida shi kuma ya hana, shi ne ta ce sai ta gayawa mama, to shi ne ya kira ya ji idan ta kawo kararsa ya bada hakuri. Bawan Allah. Murmushi kawai mahaifiyar tata ta yi tare da gaya mashi bata kira ta kawo kararsa ba ya kwantar da hankalinsa, rabon ma da su yi waya tun shekaran jiya, hakan yasa ya fahimci lallai ba garinsu ta tafi ba, dan da garinsu ta nufa dole zata sanar da mamarta, ya kira Sadiq da ya baro a kasuwa ya tambayesa ko ta gaya mashi zata je wani waje?. Mamaki ne sosai ya kama Sadiq ɗin, domin kuwa bai taɓa jin maman Zainab ta fita har baban Zainab ɗin ya nemeta ba, abin ya ɗaure mashi kai, haka dai ya bawa baban Zainab ɗin amsa da a'a ai shi ta kwana biyu ma bata yi mashi magana tun lokacin da suka yi wannan faɗar. Da okey kawai baban Zainab ɗin ya amsa mashi tare da katse kiran. Yana katse kiran Sadiq ɗin ya hau kiran numberta dan ya ji a ina take? Amma ina number bata shiga, babu network. Tunani baban Zainab ya fara yi a kan to kodai dama haka take yi kullum ne? Abin ku da shaiɗai ko ya ya samu kofa sai ya cusa maka wani mummunar tunanin, sai ya fara raya mashi cewa ai dama kullum idan ya fita ita ma fita take yi ta tafi yawonta, sai yau ne Allah ya nufa dubunta ya cika ya kamata, wannan tunani shi ne yafi tsaya mashi a ransa sosai, kawai burinsa yanzu ya ji ina take zuwa to? Kamar zai yi hauka haka ya rinƙa nemanta har wajen karfe 1 na rana, sannan ne ya hakura ya dawo gida ya kwanta, sallar azahar ma yau a gida ya yi, damuwa tasa ya kasa iya zuwa masallaci ya bi jam'i, ya rasa ina zai sanya ransa bawan Allah nan, ta ko'ina ba sauki, ga hajiyarsa a gefe ga kuma maman Haidar, yanzu kuma maman Zainab ta kawo mashi sabuwar bala'i, kunga kuwa ai bai yi laifi ba da ya shareta da ta dawo! Yana ma da ƙoƙarin da kuma hakuri tare da juriya, idan wani namijin ne wlh kina yin sallama zai fara sauke maki buhu buhun masifa a kan gidan uban waye kika je ba tare da izininsa ba? Amma shi sai ya yi shiru yana mai cigaba da haɗiyar bakin cikinsa a ransa, ya yi kamar bai ganta ba, da alama kuma ya yi hakan ne dan baya son ya yi magana da ita cikin fushi da ɓacin rai, yana da ilimi, yasan cewa idan mutun yana cikin fushi ya buɗe bakinsa to tabbas sai ya yi danasani, hakan yasa bai kulata ba, sai ya huce tukun nan. Ta kai almost 20 mins a zaune a wajen bai ko ɗago idanun ya kalleta ba, idanunsa na a kan Tv kamar mai yin kallo da gaske, alhalin ba wani kallon da yake yi, duniyar tunani ma ya afka, yo bakinciki ma ina zata barshi ya iya yin wani kallo? Ai babu wannan zance kuma. Da dai taga bashi da niyar kallon in da take ma bare ya yi mata magana sai ta miƙe ta nufi kitchen domin ta girkawa ƴaƴanta abinci sun kusa dawowa daga school. Farar shinkafa ta dafa masu, already tana da miyar steew ɗin da ta yi da safe, so sai ta ɗauko shi ta sake ɗumamawa, ta zubesu a kulolinta kamar yadda ta saba ta kwasa izuwa cikin parlourn. Tana kokarin shirya abincin su Khadija suka shigo, sun dawo daga school, lemun kankana da abarba ta haɗawa baban Zainab na daban kamar yadda ta saba haɗa mashi, sai dai a yau ta zuba mashi maganin da boka ya bata, tana zuba maganin jikinta na kerma, hannunta na ɓari har ta ɗan zuzzubar da maganin a wajen, abinku da bata saba ba, tana yi tana leƙo wajen kitchen ɗin, dan sai taga kamar baban Zainab ɗin yana yi mata laɓe ne, sai taga kamar ya ganta, duk ta ruɗe zata tonawa kanta da kanta asiri, shi kuwa baban Zainab bawan Allah yana can cikin parlourn suna zuba hira da su Khadija, sai dai daga jin yadda yake magana zaka fahimci kawai ƙaƙalo maganar dan dole yake yi, dan kawai yaga ya kwantarwa da ƴaƴan nasa hankali kuma matsalar da yake a tsakaninsa da mamarsu bata shafesu ba, yana ƙoƙarin yaga bai ɗauko matsalar mamarsu ya shafa masu ba, yasa su rasa farincikinsu da kulawar da suke samu daga garesa a kullum ba. Bayan ta kammala haɗa mashi lemun ta shirya a saman try ɗin jug ɗin tare da cup's ta ɗauka sai cikin parlourn, sam bata ji tsoron kada su Khadijah su sha ya zamar masu matsala ba, ita dai bukatar ta ya biya taga abubuwa sun dai'dai ta mata kamar da....... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce ki kauce hanyar Allah kuma ki yi tunanin abubuwa zasu dai'dai tun maki? Lallai kin tabba babban kuskure kuwa, domin wane mutun, babu wanda ya isa ya ga dai'dai idan ya sauƙa daga kan haryar Allah, ai yama kullah da rashin daidai kenan har sai ya tuba, idan kuma bai tuba ba haka zai mutu cikin ƙunci da baƙinciki, ya je lahira kuma ya girbi abin da ya shuka, Allah ka kiyashemu sauƙa daga kan hanyarka, Allah ka tsaremu kaucewa faɗar ma'aiki, ka kare mu daga sauka daga turbar da ma'aikinka ya ɗauramu, duk wuya duk daɗi ya Allah ka tausaya mana ka barmu da imaninmu, ya Allah cikin jarabarwa da zaka yi mana kada ka haɗa mana da raunin imani tare da tawakkali. Kamar yadda ya saba shan lemun ya kuma ci abincin haka yau ma ya ci ya sha, sai dai fa yau ɗin ya ci ne kawai saboda su Khadija, ba dan haka ba bai da niyar cin girkinta yau, bama yau ba bai da niyar sake cin girkinta har sai ta gaya mashi in da take zuwa, idan ta gaya mashi kuma sai ya bincika yaga da gaske ne ko karya, dan haka kawai ya ji hankalinsa sam yaki ya kwanta. Bayan sun kammala cin abincin, har da su Khadijah duk sun sha lemun baban nasu, miƙewa ya yi tare da nufar room ɗinsa, ita kuma maman Zainab jiki ba kwari ta zo ta tattare wajen, ta shiga damuwa sosai na ganin yaki ya kulata, har ta yi tunanin ta bisa ɗaki ta bashi hakuri, sai kuma ta sake cewa bari ta barshi tun da ya sha maganin nan, wata kila zai sauko ya zo ya fara yi mata biyayya................ Babbar magana, akwai case kuwa ba karama ba, ga su Khadija ma dai sun sha magani, ko me zai faru? Mu dai je zuwa zamu ga komai dallah dallah, kun san ni dama da iya yi maku komai dallah dallah ta yadda zaku fahimta da kyau da kyau, to mu dai je zuwa, na yi gaba sai kunzo!. Shirin komawa kasuwa ya je ya yi tare da fitowa, bai yi mata sallama ba ya sa kai ya fice izuwa harabar gidan. Da sauri Zee and Khadijah suka bi bayansa.1k ha ciro daga cikin aljihunsa ya basu a kan su sai wani abin idan sun je islamiya, ya san ba'a rabasu da kayan kwalama. Sai zuba mashi godiya tare da adduar a dawo lafiya suka rinƙa yi, ita kuwa maman Zainab ta maƙale a windown parlourn tana leƙansu, ji take yi kamar ta je ta bashi hakuri, amma kuma idan ta tuna ya sha magani sai ta ce ina babu wani hakurin da zata bashi, da kansa zai kawo kansa gabanta yana mai ƙasƙantar da kansa a ƙasa, a nan ne zata zuba mulkinta ita kuma. Babbar magana. Tana ji tana gani ya fice ya tafi kasuwa, su Khadijah kuma suka dawo cikin parlourn, room ɗinsu suka nufa domin su yi wanka tare da ɗauro alwala su yi shirin zuwa Islamiya, dan lokacin sallar la'asar ta kusa, saura kaɗan, suna yin sallah kuma zasu wuce Islamiya. Ita ma mamar tasu nata room ɗin ta shiga ta kwanta, dan ta huta, duk a gajiye take, dutsen nan da suka hau ya ja mata ciwon kafafu................ Ni kuwa nace har da uban ciwon kafafu ma zai ja maki ai, ai kafafu ma kaɗan ne ba dai saɓon Allah ba?. Sai da suka kammala shiri cikin uniform ɗin islamiyarsu, sannan suka yi sallar la'asar, dan a lokacin an kira, bayan sun idar da sallar lafiya lou suka zo suka yi mata sallama a kan sun tafi islamiya, kuɗin kayan miya kamar yadda suka saba ta basu su sayo mata a hanya idan suna dawowa, daga haka bata sake yi masu magana ba, suma karɓa kawai suka yi suka wuce abinsu, dan sun san kwana biyun nan fa gidan nasu sai addu'a kawai. Yara masu hankalin manya kenan, kullum cikin yiwa iyayen nasu addu'a suke yi bayin Allan!. Tamkar Khadija zata dawo ta ce mata an kira sallar la'asar, sai kuma ta fasa saboda kada ta yi mata faɗa ta ce ai ita ba kurma bace tana ji. Haka suka wuce Islamiyarsu, gwanin birgewa idan suna tafiya islamiya, cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kai daga ganinsu kasan tarbiya ta ratsasu sosai. Maman Zainab kuwa barcinta ta hau yi ba tare da ta yi sallah ba, dan ta ci mugun wuyar hawa dutsen, duk gaɓɓan jikinta ciwo yake yi mata, hakan yasa da ta kwanta ta ƙasa iya tashi, sai kawai ta hau barci ƴar kaniya. Ɗan tsokaci, saɓon Allah komai ƙankantarsa yana mugu mugun nesanta bawa da Ubangiji tare da raba shi da imani, barema saɓon Allah mafi girma wato shirka, haɗa Allah da wani kenan, kun dai san maman Zainab tana da ƙoƙari wajen yin ibada, amma da yake ta saɓawa Allah kunga har abin ya fara shafar ibadarta, ko a jikinta ta kwanta tana barci lokacin sallah, to haka saɓawa Allah yake, kishiyoyi ne da rabaka da Ubangiji, daga nan kuma zaka ga komai yana taɓarɓare maka, please ƴan uwana mata, zan yi amfani da wannan dama na ja hankulanku sosai, duniya dai ba matabbata bane, kwana nawa ya rage? Lahira ita ce madauwamiya, kada ki je garin neman duniya ki ɓata lahirarki wadda kuma ita ce madauwamiya, duniya tamkar kasuwa muka zo ci mu koma gidan gaskiya, duk daɗi duk wuya kada ki taɓa yarda ki rasa lahira, gara maki ki rayu cikin ƙunci na tsawon rayuwarki da ki lalata lahirarki, Allah ka karemu da kariyarka, ka shiga cikin lamuranmu, ka dafawa musulmi da musulunci, ka kara ɗaukaka musulunci da musulmai bakiɗaya, ya Allah ka jikanmu, ka tausaya mana, kai mana rahmarka, dama kai arrahman ne kuma arrahim, ka gafarta mana, dama kai algaffar ne, mai gafartawa bayinsa a duk lokacin da suka ƙasƙantar da kai suka nemi afuwa, ya Allah ka kawo mana zaman lafiya a duk in da muke. Ku ce amin a cikin zuciya!. Bari mu leƙa wani wajen, wata kila kafin mu dawo baban Zainab ya dawo mu ga result ɗin maganin bokan ya ake ciki?!. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ 🏞️FOREST🏞️🌼 After some days. A cikin ƴan kwanakin nan da suka suɗe, Kamran sun yi muguwar sabo da su Pretty, kullum yana zuwa kamar yadda ya saba, har yau kuma ya kasa iya tambayar mammarsa menene aure, tun da ya tambayeta menene Alhdulillah ta ɓata rai sosai kamar zata maresa, ta kuma tsare shi a kan dole sai ya gaya mata a ina ya jiyo wannan kalmar ta Alhdulillah? Da kyar ya iya shawo kanta ya gaya mata cewa wasu maharba ne suna wucewa ya ji suna faɗin Alhdulillah, shi ne yake son sanin ma'anarta, warning ta yi mashi sosai a kan babu ruwansa da jin abubuwan da mutane masu wucewa zasu faɗa, a wannan rana dai sam bai je wajen su Pretty ba, saboda mamma ta yi mugun ɗaukar zafi na jin kalmar Alhdulillah ta fito daga bakinsa, hakan yasa ni PRINCESS TEEMA na kara sakawa mamma ayar tambaya a kai, duk yadda aka yi tana da sani a kan addinai ba iya musulunci kawai ba, tana da sani sosai a kan har sauran addinan, dole akwai wani abin da yasa ta ce ita bata yarda da addini bama kwata kwata, ita bata da addini, yadda ta ɗauki zafi daga jin kalmar Alhdulillah ya nuna tasan ma'anar kalmar. Shi kuwa Kamran a bakin su Pretty yake yawan jin wannan kalma ta Alhdulillah, sai ya yi gangancin tambayar mamarsa bai tambayi su Pretty ɗin ba, tun da yaga ta ɗauki zafi sosai haka sai ya ji tsoron yi mata tambaya a kan menene aure, dan gudun kada ya zamana shi ma auren wata magana ce babba da zai ja mashi a rabashi da su Pretty, duk abin da zai sanya a rabasu baya kaunar ko jin makamancinsa, dan sun zama wani ɓari na rayuwarsa, wani abu guda ɗaya da ya lura da shi shi ne, duk wani abin da zai fito daga wajensu Pretty yana cin karo da ra'ayin mammarsa, ma'ana zaka tarar da Mammarsa ta tsani jin makamancin wannan abin, abin har ya fara bashi mamaki yana kuma ɗaure mashi kai sosai, hakan yasa ya fara zargin lallai Mammarsa tana da sani a kan irin wannan addini nasu su Pretty, sai dai ya barwa zuciyarsa wannan tunani, saboda baya son ya ɓallo ruwan da zai rabashi da sanyin idaniyarsa wato su Pretty, ga shi mum ɗinsu ta bashi amanarsu, ai kunga nauyi ya karun masa a ka, dole ya zage dantse wajen kula da su. A ƴan kwanakin nan da suka shuɗe sun yi muguwar sabo da shi na ƙin karawa, har ta kai ta kawo yanzu sai ya zo suke cin abinci a tare, suna fita waje filin ƙoramar nan su yi ta wasa, a yanzu yana koyawa Pretty harbi da kifiya, sakamakon ya rage jin feeling da yake yi, hakan kuma ya samo asaline saboda maganin da mammarsa take basa ba tare da saninsa ba, so yanzu idan ya taɓa Pretty baya jin abin sosai. Yanzu ya koya mata busar wannan sarewar tasa da yake kyarawa da abin ayaba, ya koyawa Sweetie ma, idan suka zauna a wajen ƙoramar nan yana koyawa Pretty harbi da kifiya ita kuma Sweetie tana yi masu busa mai daɗi, abin gwanin birgewa, wani lokaci ya goyi Pretty su hau saman bishiya su ciro mangoro, Sweetie tana ƙasa tana yi masu busa, sai dai su ciro su zo su wanke mata su bata ta sha. Sai dai fa har yau har gobe Pretty dai taki yarda da Rocky, taki yarda su zama abokai, ta ce babu wannan magana, kowa ya tsaya a matsayinsa, Kamran dai bashi da zaɓin da ya wuce ya yi masu iyaka idan yana son zaman lafiya, baya yarda ya bar Rocky ya taɓata, dan yana taɓata zata haukace masu ne a wajen. Taƙa tsantsan sosai Kamran yake yi wajen zuwa wajen nasu, dan kada Mamma ta gane shi. A yanzu warriors ɗin nan sun ɗan rage shigowa cikin wannan dajin, yau tsawon kwanaki biyar kenan Kamran bai haɗu da ko mai kama da su ba. Gawarwakin warriors ɗin da wannan jarumin sadaukin mutumin ya kashe su ma duk Kamran ɗin ya jefasu cikin ruwan dake gudu har izuwa wajen babban teku ruwan ya tafi da su. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ Gari ya yi sanyi, rana ta yi yamma ta kusa faɗuwa, inuwa ta sauko a dajin, ƴelwar ni'imar iska tana kaɗawa a ko'ina, iska ce mai matuƙar daɗi da ratsa jiki, dogayen bishiyoyin sai kaɗawa suke yi, ba iska bace ta ruwan sama, ba kuma iska bace ta hunturu, iskace ta bishiyoyi suke kaɗawa, yanayin gari ya yi matuƙar daɗi musamman ace ga masoya, dajin ta yi shiru sai sautin kukan tsuntsaye ne yake tashi da kuma sautin zubar ruwan koramu, gari babu hadari. Rocky yana kwance a kasar wata jibgegiyar bishiyar ɗorawa da take a kusa da ƙoramar wajen su Pretty, da alama ma barci yake yi. Sweetie tana zaune a kusa da shi, kasancewar bata gani baiwar Allah bata san a kusa da ita Rocky yake kwance ba, kayan marmari ne a gabanta take sha cikin nutsuwa. Su kuma sarakan suna saman dutse, Kamran yana zaune ya miƙe kafafu ruwan koramar tana sauƙa a saman kafafun nasa, ita kuma Pretty tana zaune a ta gabansa, sai dai ta bashi baya ta ɗan kwanto a jikinsa, ita ma ta miƙe waƴan nan ƴan guntayen kafafun nata, ko wajen ƙoramar kafafun basu iya kaiwa ba saɓanin nasa da yake cikin ruwa tsulumdum, sai takura mashi take yi a kan su matso baki bakin dutsen dan ita ma kafarta ya shiga cikin ruwan. Shi kuwa ya ce ai ita gajera ce ko sun matso kafafun nata ba zasu iya taɓa ruwan ba, ta bari sai ta zama babba kamar shi. Mai hali dai baya fasawa shi ne ta sa mashi kuka tare da miƙewa tsaye wai zata faɗa cikin ruwan mai gabaɗaya. Jawota ya yi ta zauna, dukkansu biyu hannunsu na rike da abin busar suna busawa ne dama, sun yi harbi da kifiya har sun gaji ne suka koma yin busa. "Kai our Pretty kin iya rigima fa". Ya faɗa yana jan hancinta. "Ba wani rigima, ni ka matso nima kafata ta rinƙa taɓa ruwa". "Sai ki yi mun busar da ta fi ta jiya daɗi zan matso". Ya yi maganar yana tattare mata gashin kanta da iska ke kaɗata tana rufe mashi fuska. "Idan na yi maka zaka goyani mu hau kan Giwa?". Ƙulle mata gashin nata ya yi yana faɗin. "E amma ai ba yau bako? Dan yau ba zamu je wajen giwayen can ba, kinga lokacin komawata gida ta kusa". Turo baki ta yi kafin ta ce. "To ba kai ne ka je ka jima wajen cirowa Sweetie fruit ba? Ni Allah ba zan yarda ba sai mun sake zuwa wajen, akwai daɗi hawa bayan giwa......" Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Akwai daɗi kuma kike yi mana ihu? Jiya duk kin yagushe mun wuya da waɗan nan faratunan hannun naki, duk saboda tsoron giwa, kin wani ƙanƙameni kamar idan zasu cinyeki ba zasu haɗa da ni ɗin dukka su cinye ba, kin sa na koma mamma tana tambayata me ya jimun ciwo, sai da na ce mata mage ne ta yakusheni". Ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar kamar mai raɗa. Sweetie dake shan fruits ɗinta ne ta amsa zancen da cewa. "Ai ba zaka kara kaita ba Kamran, jiya da daddare muna barci sai ta yi ta kurma ihu cikin tsakiyar dare wai ga giwa ya buɗe baki zai cinyeta na ceceta, sai da na rinƙa tofa mata addu'oi sosai kafin na samu ta yi barci". A hanzarce Prettyn ta ce. "To waye ya ce ki gaya mashi? Ya tambayeki ne? Ni ba wani ihun da na yi, sharri ne kawai dan baki son a kaini, kuma sai ya kaini ɗin". Shi dai dariya suke bashi idan suka fara wannan diramar tasu, ita Pretty bata son ace ta gaza a kan wani abin, ta fi son ace ta iya komai, ita kuma Sweetie sai iya faɗar gaskiya bata rufawa Prettyn asiri......... 😅 "Nikam Kamran ka kammala karanta littafin da mum ta baka ɗin ne?". Sweetie ta tambaya, dan a cewarta ba zata biyewa Pretty ba, haka dama take yi kullum, bata biyewa Prettyn. "No na dai fara karantawa, amma ban samun ishasshen lokaci sosai ba, ni kai'na ina son na kammala karantawa, a ƙage nake da na karanta, dan naga duk wani abin da ta bar mun a cikin saƙo kama daga waɗan nan ring ɗin da komai da komai akwai labarinsu a cikin littafin, shiyasa nake son karantawa na ji me zan yi mata da su, amma da na fara marantawa ne sai Mammata ta zo, bana son kuma taga littafin da kuma kayan, shiyasa sai na ɓoye, bana samun lokaci a gida na karanta, a waje kuma ina tare da ku, da daddare kuma ban isa in kunna wuta a ɗaki na ce zan yi karatu ba, mamma zata ce me nake yi ban yi barci ba, amma soon zan karanta". Yana magana yana ta murɗawa Pretty kyakkyawar dark black curly hairnta. Ita kuma ta wani kwanta mashi a jiki sarkin son jiki. Sweetie tana ƙoƙarin yin magana Prettyn ta rigata da cewa. "Ni Kamran ka matso bakin dutsen nan please, ina son kafata ta taɓa ruwa, kuma gobe zaka kaini wajen Giwa, Allah Sweetie babu ruwanki, tun da ke kin ce ba zaki je ba ai sai ki barni ya yi ta kaini yawo nikam". Dogon hancinta ya ɗan ja tare da faɗin. "Ki yi ta wahalar da ni ina goyaki ko? Saboda tsoro sai ki ce ba zaki tafi da kafafunki ba, kisa na goyaki duk na gaji". Sweetie ce ta ce. "Katuwa da ita zata yi ta karya maka baya ko ta saka ka ciwon kwankwaso ba?". "Allah Sweetie bana so, babu ruwanki da ni, ni ƴar karama da ni ɗin ne zaki ce zan karya mashi baya? To ni yaushe ma nake da ƙiba? Baki fini girma bane? Kin fini ai, kuma a haka shekaran jiya ya goyaki muka tsallake duwatsun can, ke baki ɓalla mashi baya ba sai ni? Kamran kada ka kulata sharri take yi mun ko? Ina bani da nauyi?". Yadda ta yi maganar gwanin ban dariya, irin ita ma wai zata yi mashi wayon nan ta saka mashi magana a baki. Shiru ya yi bai amsa masu ba, dan yanzu idan ya amsa da cewa tana da nauyi Sweetie zata ji daɗi, ita kuma Pretty ba sai na faɗa ba kunsan kuka zata yi mashi ance tana da nauyi, idan kuma ya amsa bata da nauyi, to Prettyn zata yi dariya har ma ta yi wa Sweetie gwalo, ita kuma Sweetie bara ta ji daɗi ba ga watsa mata ƙasa a ido, dan haka sai ya yi shiru ya kyalesu, haka suke yi mashi wani lokaci, sai su saka shi a tsakiya ya rasa bayan waye zai bi bawan Allah. Idan ya bi bayan wannan, sai wannan ta yi fushi, idan ya bi na wannan, wannan ta yi kuka, shirun dai shi ne mafita a gare shi!. Rayuwarsu gwanin birgewa sosai da sosai, sai sun baka sha'awa idan ka gansu, sun ɗauki Kamran tamkar ɗan uwansu na jini, shi ma duk da yana jin son Pretty a ransa sosai da sosai baya taɓa yarda ya nuna masu banbanci, ya fi nunawa Sweetie ma kulawa, saboda akwai ranar da ta ce mashi Kamran saboda bani da ido bana gani ne yasa baka hira da ni sai Pretty kawai ko? Wannan maganar tata ta taɓa mashi zuciya sosai da sosai, hakan yasa ya ɗaura ɗamarar koyan zama dasu su dukka ba tare da nuna masu wani babanci ba, sai ma ya fi bawa Sweetie kulawa dan kada ta ji babu daɗi ta ji kamar cewa ita ba mutun bace dan bata da ido, yana janta a jiki sosai yanzu. Ita kuwa Pretty ta daban ce a cikin zuciyarsa, yana bala'in kaunarta, kome ta yi kyau take yi mashi, amma kuma abin da bai sani ba shi ne Sweetie ce take son shi ba Pretty ba, ita Pretty da kauɗi ya yi mata yawa a kai ina ma take wani bi ta kansa sosai, ta dai shaƙu da shi fiye da Sweetien, tana kuma kaunarsa a matsayin ɗan uwa da suka ɗaukesa, bayan haka babu wani abin, amma watakila a gaba zata iya fahimtar tana son shi. Akwai cakwakiya sosai kam, domin ita Sweetie da iya gaskiyarta take son shi, bata san ya kamaninsa yake ba, amma zuciyarta ta kamu da kaunarsa, wannan ita ce ma kauna ta gaskiya duk da ita ma bata san me kaunar ba a yanzu, saboda ƙananun shekarunsu. Hmmm akwai case ba kaɗan ba, mum ɗinsu ma auren Pretty ta bashi bana Sweetie ba, Allah sarki baiwar Allah ga cutar makanta gana soyayya, to Allah ya baki ikon cin jarabawarki. Bari mu leƙa DUBAI mu dawo. 🌼DUBAI🌼 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________32🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ 🌼DUBAI🌼 After some days.🕊️ LEESHARH🌼 Kwance take a saman bed ɗin nata, idan ka kalleta zaka yi zaton ba ita bace, ta goge ta yi wani kyau da ita, dattin gidan AAJ duk ya fita, ta ɗan yi dumurmur da ita, alamar ta samu huta da kula, ba karya suna kula da ita sosai, dan a halin yanzu ita ce kawai hope ɗinsu, ita ce zata biya masu buƙatarsu da suke ƴinwace wajen nema, kula da ita sosai suke yi tamkar kwai a saman bajajjen plate. Mayuka da sabulan gyaran jiki kala kala masu kyau da tsada suka saya mata take amfani da su, wannan mata dai ta zage sai koya mata aikin take yi kamar yadda suka gaya mata. Sai dai kuma har yau bata iya samun damar ganin ko face ɗin mutun ɗaya daga cikin gidan ba, ta yi iya ka baƙin ƙoƙarinta wajen ta samu ta ga face ɗinsu, amma abin ya ci tura. Daga harshe dai sai ta hakura ta fawwalawa Allah komai... Hmmm ga shi ita da kanta bata san a wani location wannan gida yake ba, an dai keto da ita cikin unguwa, ga gidajen da yake a unguwar duk ginin iri guda ne, in fact bama ta san wace unguwar bace ba, bata san komai dan gane da su ba. Duk nacinta da yadda ta so ta iya sanin wani abin a dangane da su to fa hakura ta yi, domin ance duk wanda ya rigaka kwana to zai rigaka tashi, wannan haka yake, sun ko fita wayo, idan juranta sammako to su a tafe suka kwana, sun ki yarda su bata wani dama, a shirye suka tsab kafin su fara duk abin da za su yi. Ta kwanta shiru tana tunanin duniya, mahaifinta ne kawai a cikin ranta, ta ƙurawa sama idanu kamar wata mai kallon wani abin, dama kun san akwai ta da ido kam, tafi kowa manyan idanu a gidan AAJ. Wani irin jiniya ne ya karaɗe gabaɗaya unguwar ta su, jiga jigan motoci ne suka saki jiniya tun daga nesa da wannan gida, ya karaɗe ko'ina, tun da Leesharh ta zo wannan gida bata taɓa jin jiniya makamancin hakan ba, wani lokaci jefi jefi tana jin karar jiniyar motar ƴan'sanda ya wuce, da yake unguwa ce ta manya, akwai irinsu ƴan majalisu, ciyamomi da sauransu, hakan yasa wani lokaci motocin ƴan'sanda da sojoji suke giftawa tare da motar wani ɗan majalisa, to amma na yau jiniyar ta daban ce, domin ta karaɗe ko'ina a faɗin unguwar, daga ji kasan wasu manyan shegu ne suka dimfari arear. Kamar wadda aka tsira ta miƙe zaune a tsakiyar bed ɗin, tunani ta fara yi akan wannan jiniya kuma na menene? Waye ne kuma ya zo?. Bata ankara ba sai jin jiniyar ta yi har tsakar kanta kamar zasu tashi gidan nasu, alama ce ta motocin cikin wanna gida suka shigo. Ai a dubu ɗari ta diro kasa daga saman bed ɗin, da gudu ta nufi wajen window dan taga wanene? Sai addu'a take yi Ubangiji Allah yasa su basu rufe face ɗinsu ba, ta samu dai taga koda mutun ɗaya ne, dan tasan ya kamanin ƴan gidan yake. Jikinta na kerma ta ɓalle labulen window, har tana ƙoƙarin faɗuwa saboda sauri. Kurawa parking space ɗin gidan idanu ta yi kamar idanun nata zasu faɗi ƙasa. Danƙara danƙarar motoci masu numfashi har guda goma ne suka keto cikin wannan gida, kai daga ganin motocin kasan na manyan shaggu ne, sun haɗu iya haɗuwa, ga motar polices biyu a baya ɗaya a gaban jerin gwanon motocin nasu. Gabaɗaya bodyguards ne a cikin motocin da suka kasance launinsu bakake, mota ɗaya ce ta kasance launinta fari a cikinsu, mamallakin wannan mota kuma bai fito ba, bodyguards ne kawai suka firfito tare da tsaitsayawa a gefe da gefen motocin, ƴan'sanda kuma suka diro ƙasa daga saman bayan motocinsu hannayensu a riƙe da wasu shegun bindigu waɗan da basa saɓa saiti. Daga bodyguards ɗin har ƴan'sanda dukka akwai face mask a face ɗinsu, su bodyguards ɗin ma sun kara da black glass a idanunsu, jiga jigai ne bodyguards ɗin, suna ji da ƙoshi da lafiya. Ƙara kura masu idanu sosai Leesharh ta yi tana jiran taga wanenen mamallakin wannan luxurious white car ɗin, ga shi bodyguards sun buɗe mashi kofar motar amma shiru bai fito ba, yana zaune a ciki. Ji Leesharh take yi tamkar ta fita ta je ta janyoshi ya fito daga cikin motar koma wanene ta gansa. Amma ina ba hali, dole ta yi jira sai lokacin da aka ga damar fitowa. An ɗauki a kallah tsawon good 10 mins kafin nan ya sako kyawawan kafafunsa waje, wadda yake sanye cikin wani haɗaɗɗen black booth mai matuƙar kyau da tsada, kai daga ganin wannan shoe ɗin kasan bana ƙananan kai bane. Ko da ya sanya kafafun nasa waje ma sai da ya ɗan ɗauki 2 mins kafin ya fito waje mai gabaɗaya, nan take bodyguards ɗin suka fara sara mashi. Matashei ne mai ji da lafiya, cikakken namiji ne wanda a kallah zai iya kai 27 years a duniya, sanye yake da ƙananan kaya, wandon jeans dark ash and white polo shirts, arab hairnsa yana kwance har wajajen bayan wuyansa, ya gyara gashin nasa sosai da sosai, farin balarabe ne tas da shi, kyakkyawa ne ajin farko, duk da kansa a sunkuye yana kallon ƙasa hakan ba zai iya hana ka gane kyakkyawan gaske bane. Hannunsa ɗaya na ɗaure da wani dankareran diamond watch, ɗayan hannunsa kuma babu komai yana riƙe da wayarsa, arab skin ɗinsa sai sheki yake yi, ya ji hutu har ya gaji. Daga yanayinsa zaka fahimci jininsa a tafashe yake. Cikin tafasar jini ya taku ya nufi cikin gidan kai tsaye, Leesharh bata samu damar ganin face ɗinsa da kyau sosai ba, amma dai tabbas ta gansa, saboda bai rufe face ɗinsa da komai ba, da alama ba ɗan gidan bane, duba da rashin amfani da face mask da ya yi kamar yadda su suke yi. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙara mannewa da jikin windown tana tunanin to wanenen kuma wannan haɗaɗɗen guy ɗin? Kamar saukar aradu daga bayanta ta ji an ce. "What are you doing there?". A razane ta juyo da kallonta kirjinta na dukan uku uku. Wannan mata ce mai koya mata aiki, ita ce ta jefo mata wannan tambaya. Ƴan kame kame ta fara yi na rashin gaskiya tana zaro waɗan nan idanun nata kamar ball ɗin mota, cikin rawar murya ta amsa da nothing tare da sakin labulen window ta bar wajen. Da kallo ta cikin nikaf matar ta bita da shi har ta isa saman bed ɗinta, sumui sumui kamar munafuka da asirinta ya tonu aka kamata tana munafurci haka ta haye saman bed ɗinta ta takure waje guda. Wucewa wannan matar ta yi ta nufi cikin toilet ba tare da ta sake yi mata magana ba. Shiru Leesharh ta yi tana binta da kallo, ita ta kasa iya gane halin wannan mata, yau ka ganta kamar mutuniyar kirki, gobe kuma sai kaga wlh ta ma fi shaiɗan iya shaiɗanci, ga bakin hali, mugunta da rashin son magana, idan ka yi mata magana ko ka tambayeta wani abin, sai dai ta nuna maka da hannu ko ta ɗaga maka kai, amma ba zaka ji tana magana ba, sai ayi magana goma bata amsa ɗaya da muryarta ba, sai dai da hannu ko kai kamar ƙadangaruwa, yadda kuka san mai ciwon baki. Jim kaɗan ta fito daga cikin toilet ɗin ta nufi kofar fita. Ko sanu bata sake cewa Leesharh ba, dama ita kuma Leesharh ba magana take yi mata ba, a haka suke rayuwa a cikin wannan ɗaki, sai dai fa ba'a nan matar take kwana ba, da dare ya yi zata bar ɗakin, ba zaka sake ganinta ba sai gobe da safe, tun abin yana bawa Leesharh mamaki har ya dai'na, yanzu ita ta riga ta saba da ahalin wannan gida. Matar na fita ba'afi da minti biyu ba sai ga wannan matashiyar matar ta shigo cikin room ɗin bakinta a ɗauke da sallama. Amsa mata sallamar Leesharh ta yi tare da ɗan sakin fuskarta kaɗan, domin sun saba da wannan mata, ita kaɗai ce Leesharh take ganin ta Allah a gidan, ita kaɗai ce mai yi mata magana mai daɗi, ƙananun shekarunta yasa ta kasa iya banbanci kalaman soyayya da kuma kalman yaudara, ita dai a ganinta wannan matashiyar matar tana sonta tsakani da Allah..... Hmm yaro yaro ne bai san wuta ba sai ya taka. Wannan hali na matar shi ake kira da makirci kuma kisan karkashin ƙasa or mummuƙe! Leesharh dai bata gane ba, bata san suwa ye ake cewa makiran mutane ba. A bakin bed ɗin wannan mata ta zauna, cikin nutsuwa ta ce. "Leesharh gobe za'a kaiki gidan Abu Abdussalam bin Badeen, ki tsaya sosai ki jajirce ki yi aikinki, ki mai da hankali ki yi abu da wuri dan ki samu ki je wajen babanki ku koma ƙasarku, kada ki yi wasa, kin dai ɗauki duk abin da aka koya maki ba?". Kai ta gyaɗa mata kamar kan ƙadangaruwa alamar e ta ɗauki komai. "Good girl, to kada ki yi wasa kin ji? Ga wannan wayar idan kin je ki tabbatar kin ɓoyeta kada kowa ya gani, zan kara jan kunnenki Leesharh, ban yarda ki yi hira da ma'aikatan gidan ba bare har ki je kiyi suɓutar baki ki saki layi ki sanar da su abin da ya kaiki, nasan ma'aikatan gidan ba kakanun masu ilimi bane, wasu ma zasu yi maki dabara su bugi ruwan cikinki, kin dai ji abin da mai koya maki aikin nan ta ce ko? Kada ki yarda ki saki baki kiyi hira da wata, idan ya wuce gaisuwa ina wuni shikenan kada ki kara kada ki rage, sannan bayan Ramish ban aminta da ki kula kowa a cikin gidan ba, shi kaɗai zaki sakawa ido, kibi a hankali". Ta kai karshen maganar tana kallon Leesharh har cikin ido. "Aunty zan yi duk abin da kika ce da kuma abin da kuka koya mun In Sha Allah, amma Aunty ya za'ayi na gane wanene Ramish ɗin? Sannan kuma a wajensa zan yi aiki ne?". Ta yi tambayar cike da fargaba, tsoro take yi kada Aunty tata ta ce mata ta cika tambaya sosai. Shiru matar ta ɗan yi kafin ta ce. "Ramish! Ramish! Ramish, kina ganinsa a jikinki zaki ji cewa shi ne, domin shi ɗin ganinsa ba kowace zuciya take iya ɗauka ba, amma dai zan turo maki hotonsa ki gani a cikin wayar, ki kula sosai, and yana da wasu kanne da ba zasu wuce mate ɗinki a shekaru ba, i think ba zasu wuce 13 years ba, kin ma fisu shekaru, they're twins, (Obaid and Omaid) and they're very very stubborn, basu cika zuwa gidan ba, amma na tabbata duk ranar da suka je idan kika yi wargi kaɗan zasu iya gano cewa ke ƴar leƙen asiri ce ko kuma akwai abin da ya kawoki gidan, because they're very very talented and suna da sharp brain fiye da tunaninki, kamar aljanu haka suke, ki kula sosai, idan sun zo gidan kada ki yarda ki yi wani kwakkwaran motsi, idan da dama ma kada ki bari ku haɗu da su kin ji?". "To Aunty amma ta yaya zan gane sune har na guji haɗuwa da su ni da ban sansu ba?". "Ai waɗan nan twins ɗin idan suka je gidan dole ma kisan sun je, saboda kamar yadda na gaya maki yadda kika san aljanu haka suke, kuma kowa a gidan sonsu yake yi, har shi kansa mai girma Abu Abdussalam bin Badeen kaunarsu yake yi, idan suka ce zasu je gidan ma har wani shagalin murna ƴaƴan Abu Abdussalam suke haɗawa, dan suna kaunarsu, ai zaki gani idan kika je, yawanci weekend ne suke zuwa gidan su ɗan yi hutu, kwana biyu kawai suke yi a gidan Saturday and Sunday, amma wlh sai ki rantse da Allah wani shugaban ne yaje gidan, saboda kauna da ake nuna masu, ke dai ki kula dasu, dan sun fi bala'i iya bala'i, makirai ne na karshe!". (Yo ai dole ayi mata kashedi a kan Obaid and Omaid 😅 hmmm yaranda kamar ba mutane ba, anya Momma lafiya aka bar maki ƴaƴan nan naki kuwa?🤔 Na fara tantanma, dan sun fita zakka a cikin ƴan uwansu, ai kuwa Leesharh tana yin wani wargi zasu kamata waɗan nan yara, da kuwa sunanta sorry wlh baiwar Allah) Da okey ta amsa mata, saboda a yanzu an koya mata dabaru kala kala. Ji take yi kamar ta tambayi Auntyn nata wanene wanda ya zo yanzun nan? Sai kuma ta basar da maganar gudun kada ta jama kanta wani abin. Miƙa mata dalleliyar wayar hannunta matar ta yi, waya ce mai tsada ga kyau, sannan ta miƙe ta nufi waje tana gaya mata cewa mai koya mata aiki ta tafi, aikinta ya kare yau. Haka kawai Leesharh ta tsinci kanta da jin faɗuwar gaba a lokacin da ta ji zancen mai aikin..... Ni kaina na ji wannan faɗuwar gabar, fatana dai shi ne Allah yasa ba kashe mai aikin zasu yi ba, dan sun ce babu mai jin sirrinsu kuma ya rayu, kunga kuma ita mai aikin ai ta ji sirrinsu, dan sai da suka gaya mata abin da zata koyar da Leesharh ɗin, to Allah dai ya nuna mana lokaci ya kai mu mu ji komai a tare. Zubawa wayar idanu sosai Leesharh ta yi tana kallonsa, a cikin wannan sati biyu da suka yi an koya mata yin amfani da waya, sai dai abin da bata sani ba shi ne an saka mata abubuwa biyu zuwa uku a cikin waya. Na farko an saka mata na'urar bi diddigi a cikin wayar, na biyu ansaka mata abin sauraren magana, matuƙar wayar tana kunne ta yi magana a kusa da wayar to waɗan da suka bata wayar suna sauraren duk abin da zata faɗa, abu na uku kuma shi ne anyi setting na wayar ta yadda duk wanda ta ki zasu sani. Hmmm wlh akwai cakwakiya ba kaɗan ba a wannan part ɗin. Duk Leesharh bata san da waɗan nan abubuwa da suka sanya mata ba fa tab! Waya sani ma kila akwai wasu abubuwan da basu bari muma mun sani ba. Yanzu ita Leesharh duk bama wannan bace a gabanta, face ɗin wannan mutumi da ya shigo a yanzu take son ta sake gani, tana son sanin wanenen shi? Ko ba komai yau karo na farko ta ɗan ga face ɗin wani a cikin gidan, duk da tasan tabbas ba ɗan gidan bane, dan a yanayin yadda ya shigo ya nuna cewa koma wanenen ya fi ƴan gidan nan kuɗi da ji da isa, saboda idan ka lura da irin kallon da yake yi wa gidan, kallo ne na raini da kuma ƙasƙanci, kuma fuskarsa ta nuna kamar dole aka yi mashi zuwa wannan gida ba da son ransa ba, sannan idan ka kalli yanayin motocin da suka rako shi da masu tsaronsa, haɗe da motocin ƴan'sanda har guda uku zai nuna maka ba ƙaramin mutun bane, ya fisu komai da komai, kuma yana bala'in ji da kansa sosai, duba da yadda ya shanya waɗan nan shirga shirgan bodyguards ɗin suna a tsaye suna jiransa tsawon lokaci yana cikin mota, sai lokacin da ya ga dama ya fito, ko mutun ɗaya daga cikin waɗan nan ƴan'sanda da bodyguards ɗin babu wanda ya nuna alamar ya ji wani abin, alamu sun nuna cewa lallai ba yau bane farau, halinsa ne shanya mutane suna jiransa, sai dai a jirasa amma shi baya jira. Sosai Leesharh tasa ƙwaƙwalwarta a cikin tunanin tana ƙoƙarin haɗa abin da tasan sam ba zai yi wu ba, dan wannan matashi shi ne kawai ta kalli face ɗinsa a cikinsu, shi ma ba sosai ba, ba lallai ma idan ta sake ganinsa a wani waje ta ganesa ba, amma ta dage tana ta ƙoƙarin haɗa idanun ƴan gidan, ita a yanzu da idanu da kuma murya take son ta gwada iya gane su wanene su, shiyasa take ta ƙoƙarin haɗa idanun wannan guy da bata gani da kyau ba da kuma idanun wannan matashiyar mata tare da mamarta, dan ta gane shin wannan matashi yana da alaƙa ta jini da su ko kuma bashi da shi? Leesharh kenan, akwai ƙwaƙwalwa, wani lokaci kuma akwai iya shirme da shiririta, ga yarinta da yake ratsowa ta cikin ƙwaƙwalwar tata. Ta jima tana kallon wayar da aka bata ba tare da ta shiga cikin wayar ba, bata ma sha'awar shiga cikin wayar, saboda tasan babu komai a ciki. Sai hidima take ji ana ta famar yi a cikin gidan, amma ita babu halin ta fita taga me ake yi, dan idan bada izinin wannan hajiya ba ko kofar ɗakin bata leƙawa baiwar Allah. Tana ƙunshe a ciki kamar daddawa!. Tana dai ji anata kai komo tsakanin hawan kasa da sama, elevator sai zarya yake yi, amma haka ta cigaba da kwanciya shiru. Wunin ranar dai haka ta wuni a takure, ta takure kanta da burin son fita ta leƙa me ake yi a cikin gidan, amma babu hali, haka ta wuni babu wanda ya leƙo in da take har can yamma. Kamar daga sama ta ji motsin jama'a a harabar gidan. Ai a dubu ɗari ta diro ƙasa daga saman bed ɗinta ta nufi wajen window dan taga menene?. Wannan matashin saurayin ne zai tafi, ga mamakinta sai taga mata wajen huɗu ne suka rako shi wajen motarsa, ita dai tasan mata biyu kawai ta sani a cikin gidan, sai mai koya mata aiki wadda kuma tun da rana ta koma, to su kuma saura mata biyun nan daga ina? Ta tambayi kanta. Ga wannan Hajiya da kuma ƴarta waɗan da already Leesharh ta rike kamaninsu ta yanayin idanunsu duk da suna cikin nikaf, kuma wata basira irin tata ko basu yi magana ba tana iya gane da waye take a tare ta hanyar idanunsu. Sam basu kawowa ransu cewa Leesharh zata iya yi masu wannan sani ta haka ba, a tunaninsu ai ba zata taɓa iya ganesu ba. Kamar dai ɗazun, yana sunkuye da kansa yana kallon ƙasa ya nufi motarsa, sosai Leesharh ta baza idanu tana son kallon face ɗinsa da kyau da kyau, amma sam hakan bai samu ba, saboda yana ƙasa ita kuma tana sama, ya kuma sunkuyar da kansa ƙasa, ba halin ta gansa sosai!. Tana ji tana gani suka bar wannan gida, sam ranta baiso haka ba, ta so dai taga wannan haɗaɗɗen guy ɗin mai cike da shegen isa da izza. Sai da ta ga tafiyar motocin nasu ne ta juyo ta koma wajen bed ɗinta cike da haushi, sai kuma ta fara tambayar kanta a kan cewa kenan ko da wannan matashi ya zo basu cire nikaf ɗin da yake face ɗinsu ba? Ko dai sun cire a cikin gida da zasu rakoshi waje ne suka sake sanyawa? Waɗan nan tambayoyi shi take ta jerawa kanta wadda kuma har lokacin sallar mangariba ta yi bata samu amsarsu ba. Jiki ba kwari ta tashi ta yi sallah ta dawo ta cigaba da kwanciya tana tunanin irin rayuwar da suke son jefata a ciki, ga shi sun yi mata kashedi da kada ta yi kusa da kowa a wannan gidan aiki da zata je, sannan kuma sun ce kada ta yarda ta rinƙa sanya hijab irin nasu na Africa, a kayan da zasu saya mata ma ba za'a sayi irinsa ba, sai dai arab hijab zata sanya wanda iyakansa kirjinta ya tsaya, abin ya ɗan ɗaure mata kai da har ta fara tunanin kenan tallar jikinta zata yi wa Ramish ne ko yaya? Ta ƙasa gane komai, waɗan nan mata akwai shegu, duk sun birkita mata ƙwaƙwalwa ta yadda ta kasa iya kamo zaren bakin abu guda ɗaya a cikin waɗan nan matsaloli ta warware ta gani, anya kuwa waɗan nan mata su suke shirya wannan plan ɗin kuwa? Saboda abin ne ya wuce tunani, dole akwai sama da su, to waye? Wannan tunani Leesharh ta fara yi a cikin ranta. Kamar a mafarki muryar babanta ya fara yi mata yawo a cikin kunnuwanta in da yake ce mata. "A'isha duk abin da zaki yi a rayuwar nan ki riƙe gaskiya da amana, in dai kika rike waɗan nan abu biyun to Allah ba zai taɓa bari ki taɓe ba, Allah zai ji ƙanki, ki tabbata baki cutar da kowa ba a rayuwarki, hakan zai sa Allah ya sanya bargon ni'imarsa ya lulluɓeki daga kowani irin cuta da ɗan adam zai yi maki, kada ki bari mutuncinki ya zube ta hanyar cutar da wani, gara maki ace mutuncinki ya zube wajen ƙoƙarin tsayar da gaskiya". Sai gizo kalaman babanta suke yi mata a cikin kunnuwanta, gabaɗaya ta rasa madafa, hankalinta ya yi mummunar tashi gobe za'a kaita gidan aiki, ji take yi kamar ba zata iya ba, duk da wannan mata ta ce mata ba cutar da kowa zata yi ba, amma ita a jikinta tana jin cewa kamar cutar Ramish ake son yi, to amma koma cutar ce a wannan gaɓa dai bata da zaɓin da ya wuce dole ta yi wannan aiki, idan ba haka ba ita kuma zata rasa babanta wanda shi kaɗai ya rage mata a duniya. Tashin hankali, duniya ta ɗau mata zafi fa. Cikin ƙoƙarin neman mafita da tunanin ina zata sanya ranta ne Jasrah ta ratso mata ta cikin tunaninta, daɗaɗan kalam Jasrah ta fara tunawa a in da take ce mata. "Leesharh a duk lokacin da kika rasa mafita, kika shiga damuwa, kina ganin kamar baki da mafita, kina ganin kamar komai ya lalace maki, a dai'dai wannan lokaci ki fara furta Hasbunallahu wani'imal wakil, domin babu wanda zai iya kawo maki ɗauki sai Allah, kada ki tunkari kowa da ya ya ye maki damuwarki, ki tunkari mahaliccinmu kawai ta hanyar ɗauro alwala ki yi nafila raka'a biyu tare da karanta Alqur'ani mai girma koda shafi biyu ne, zaki ji sauki sosai a ranki, domin Allah shi ne kawai mai kowa kuma mai komai, shi ne kawai zai iya fitar dake daga zafi izuwa sanyi, duk tsananin da zaki shiga kada yasa ki manta Allah". Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, zamanta da Jasrah babban alkhari ce a gareta, ta koyar da ita abubuwa da dama. Tunano da kalamar ƴar uwar tata ne yasa ta yunƙura zata tashi ta ɗauro alwala kenan wannan matashiyar matar ta shigo cikin room ɗin bakinta a ɗauke da sallama. Tare suke da wani babban likita da yake biye da ita a baya, yana sanye cikin ƙananan kaya ya ɗaura rigarsa na likitoci a saman kayan, hannunsa na ɗauke da A box, babban mutun ne da zai iya haura shekaru 45 a duniya, farin balarabe ne tas da shi. Leesharh matar ta nuna mashi da hannu tare da zama a saman bedside drawer tana faɗin. "Doctor Suhail this is the patient". Ɗan zaro idanu Leesharh ta yi tana tunanin ita a yaushe ta ce bata da lafiya to? Ita dai tasan lafiyarta ras, to me za'ayi mata kenan?. "Zaki iya bamu waje". Dr Suhail ya yi maganar cikin harshen larabci. "No Dr, ka yi aikinka kada ka damu da ni, ina son bata kulawa ne sosai". Ta faɗa cike da nuna mashi cewa tana kaunar Leesharh ɗin sosai. Sai kallon face ɗin Dr da yake sanye da farar face mask na likitoci a face ɗinsa Leesharh take yi. Ko kaɗan alamu basu nuna cewa waɗan nan mata suna da wata alaƙa ta jini da wannan Dr ba, saboda shi yanayin idanunsa daban da nasu, amma fa a tunanin Leesharh ne hakan. Jinjina kai Dr ya yi tare da cewa Leesharh ta gyara kwanciyarta bari ya dubata ya kuma duba maƙogoronta me yasa maganarta baya fita sosai?......... NI KAM NA CE ANYA BA WANI ABIN ZA SU SANYA MATA BA KUWA?🤔 BAFA A YARDA DA IRIN WAƊAN NAN MUTAEN!. Ba musu ta gyara ta kwanta, dan ma dai bata da wata zaɓin da ta wuci hakan. Alluran barci Dr ya ciro daga cikin A box ɗin ya fara haɗawa, amma kafin ya yi mata sai da ya tambayeta ya akayi maganarta bata fita sosai? Shin haka aka haifeta ne ko dai daga baya ne ta samu wannan cuta?. Kallon wannan matar ta yi alamar tana jiran ta ji me zata ce. Cikin sanyin murya matar ta ce. "Ki saki jikinki ki bawa Dr duk wani amsar tambayar da zai yi maki, ta hakance kawai zai sa a iya yi maki magani cikin sauki, ba sai an shawahalar wani dogon bincike ba". Cikin harshen larabci ta yi maganar. Bayani Leesharh ta fara ƙoƙarin yi masu, sai dai ga dukka alamu a tsananin razane take da maganar da ta fara yi ɗin, alamu sun nuna bata son yin maganar, in fact bala'in jin tsoron yin maganar take yi, hakan zai tabbatar maka da cewa akwai babban abu dangane da ita da take tsoron faɗarsa ga duniya, dole akwai abin da ya faru da ita a rayuwarta ta baya, baiwar daga tambayar meyasamu voice ɗinta duk ta ruɗe, ta shiga tashin hankali kamar ba ita ba. Kasa iya yi masu bayanin ma ta yi, daga fara wa sai ta fara kuka da hawaye bibbiyu. Ganin hakan yasa wannan mata ta matso kusa da ita tare da ɗan rungumota ta fara rarrashinta a kan ta yi hakuri. Cikin kuka take faɗin. "Ni dan Allah kada ku tambayeni meya samu voice ɗina, kawai dai abin da nasani shi ne ba'a haka aka haifeni ba, last year ne ma abin ya faru da ni, kuma garwashin wuta ne silar komai, garwashin wuta ne ya shiga bakina har maƙogorona ya kona mun baki da yasa muryara bata fita, please kada ku tambayeni wani abin kuma". (Garwashin wuta zai shiga bakin mutun da kafafunsa ne?🤔) Ganin yadda ta ruɗe ta fita a hanyacinta daga cewa ta bada labarin abin da yafaru da muryarta ta dai'na fita yasa Dr Suhail ya fahimci lallai yarinyar nan gabaɗayanta tana under barazanar mutane ne, dole dole akwai gagarumin abin da ya faru da ita a rayuwarta ta baya wanda kuma take a ƙarƙashin barazanar kada ta yarda ta tona wannan abin da ya farun, hakan yasa da suka tambayeta ta yi wannan ruɗewa har haka, da alama kuma wannan dalili yasa ta ƙasa iya buɗe baki ta yi magana a kan mutuwar mahaifiyarta da ake ta cewa ita ta kasheta, dole wani abin ya saɓa, rayuwarta akwai abin dubawa sosai, amma kada ku ji komai, ni PRINCESS TEEMA ba zan gaji ba sai na je na leƙo masu asiri na binciko maku tarihin rayuwarta koma ta halin yaya ne, ai ba za'a barmu a baya ba, daga jin wannan abin kasan tarihin rayuwarta akwai darasi da abubuwan karuwa, dan haka dole na binciko mana dan muji komai mu kuma ƙaru..........😎 "Dr Suhail ina ganin kada ka sake yi mata wani tambayar kuma, tun da ta ce ba'a haka aka haifeta ba, kuma ta ce last year ne abin ya faru da ita sannan garwashin wuta ne ya shiga bakinta yasa voice ɗin nata baya fita, ina ganin ka bata magani kawai ba sai ka sake yi mata wasu tambayoyi ba". Cewar wannan mata da take aikin gogewa Leesharh ɗin hawaye. "Tayaya zaki ce mun kada na tambayeta? Idan na bata maganin da bai yi dai'dai da ciwon nata bafa? In fact ma kin taɓa ganin garwashin wuta yana da kafa ne da zai tashi ya shiga bakin mutun haka kawai? Ke baki ga yadda ta ruɗe daga tambayarta ba, dole akwai abin da ya faru a rayuwar wannan yarinya na shekara ɗaya da ya wuce, yana da kyau mu san menene". Dr ya bata amsa. "Dr Suhail bana son jin dogon magana, kawai kayi aikinka kada ka sake tambayarta, idan kuma ba zaka yi aikin bane sai na kira Dr Bakir na sanar da shi ya turo mun wani likitan". Ta yi maganar a gasale. Da alama ranta ya ɗan sosu da jin kalaman Dr na neman son jin tarihin Leesharh, ta ga alama kamar ya ji tausayin yarinyar kuma yana son janta a jiki ya taimaka mata, shi ne ta yi saurin taka mashi birki!. "Am sorry, bari na dubata na yi mata abin da ya dace". Ya bata amsa tare da fara gyara alluran barcin. Da kyar Leesharh ta tsaya aka yi mata alluran. A takaice dai Dr Suhail ya dubata ya kuma yi mata abin da ya dace, sannan ya basu magunguna da zata rinƙa sha, a hankali hankali voice ɗinta zai koma normal, daga haka ya yi masu sallama ya tafi. Ita kuma wannan matashiyar mata miƙewa tsaye ta yi tare da zubawa Leesharh dake ta faman barci idanu tana kallonta, kamar mai tunanin wani abin, kamar kuma tana ɗan jin tausayinta. Ta ɗauki a kallah 5 mins a haka kafin ta sa kai ta nufi waje. Leesharh kuwa, babu sallar mangariba bare issha, sai barci take yi sakamakon wannan allura da aka yi mata, ba ita ta farka daga wannan barcin ba sai wuraren asuba. A hankali ta waro idanunta da suke jajir dasu saboda barci, jikinta duk ya yi mata nauyi, da kyar ta iya miƙewa zaune, har wani irin jiri ta fara ji, kanta na sara mata, cikin matsananciyar kasala ta miƙe ta nufi cikin toilet. Alwala ta ɗauro ta zo ta yi sallar mangariba, dan a tunaninta yanzu mangariba ce, saboda taga ɗan haske haske, sai take ganin kamar yammace irin an fara kiraye kirayen sallar mangaribar nan. Baki a ɗauke da sallama Auntyn tata ta shigo cikin room ɗin, hannunta na a rike da akwati mai bala'in kyau da kuma wata envelope mai ɗan girma. Leesharh dake zaune a saman dadduma ce ta fara binta da kallon mamaki. A bakin bed matar ta zauna tare da faɗin. "A'isha idan kin idar da sallar ki zo". Miƙewa ta yi daga kan daddumar tare da naɗeta ta mayar cikin wardrobe ɗin, sannan ta zo gaban matar ta tsugunna tana faɗin gata nan, duk jikinta ciwo yake yi mata tana son ta je ta yi wanka, dama bata yi wanka bane wai dan kada lokacin sallar mangariba ta wuce ta, kun san shi gajeran lokaci ne da shi, to a tunaninta yanzu mangariba ne ta yi sauri ta ɗauro alwala kawai da nufin idan ta yi sallah sai ta yi wanka tare da ƙara ɗauro wani alwala ta yi sallar isha. "Tashi ki zauna a saman bed ɗin". Matar ta faɗa. Ba musu ta miƙe ta haye saman bed ɗin abinta. "To A'isha, wannan akwatin kayan sakawarki da zaki yi amfani da su ne a gidan Abu Abdussalam idan kin je, akwai komai a ciki, na tabbata ba zaki buƙaci komai ba, wannan envelope ɗin kuma takardun makaranta ne a ciki, dama na gaya maki mai girma Abu Abdussalam baya ɗaukar jahilai aiki, daga irin masu diploma ne suke mashi aiki, kema ba karamar wahala muka sha ba kafin mu samu su amince su karɓeki aiki da kwalin secondary school, dan ma dai muna da hanyar da ba za'a iya kin bukatarmu bane yasa Abu Abdussalam ya yarda, dan haka ki mayar da hankali, ga takardun makaranta nasa an buga maki, nasan kin yi karatu from primary two Jss two, babanki ya gaya mana, so yanzu dai waɗan nan takardu har da result na waec ne a ciki, na primary da komai da komai yana ciki, kuma da first class kika fito, already takardunki sun kaiga mai girma Abu Abdussalam, ya gani kuma ya yarda ya shaida, yanzu zan damkamaki su a hannunki ne kawai dan wata kila watarana za'a buƙacesu a gidan, so ki ajiyesu da kyau a wajenki, sannan ki yi ƙoƙari wajen aiki cikin nuna wayewa da ilimi, kinga result ɗinki sun nuna ke first class ce mai ƙoƙari sosai, so kada ki je ki yi masu kauyanci da shirme". Jinjina mata kai Leesharh ta yi tare da yi mata alkawarin In Sha Allah zata kula sosai. Shafa kanta matar ta yi tare da sanya mata albarka. A takaice dai haka ta kara gaya mata komai da komai tare da gaya mata wasu dabarun, sannan ta bata takardun tare da ce mata ta yi wanka ta shirya yanzu za a kaita gidan wadda zata kaita gidan Abu Abdussalam ɗin.......Tirƙashi! Wadda zata kaita gidan ma gidanta daban?.🤔 Miƙewa matar ta yi ta nufi waje, ita kuwa Leesharh toilet ta nufa, a gurguje ta yi wanka ta zo ta hau shiri, a nata tunanin fa lokacin sallar isha bata yi ba, saboda tana cikin room, bata ganin rana. Ɗaya daga cikin tsofaffin kayan da ta saba sakawa ta sanya, abaya ce black color mai kyau, ta gyara gashin kanta da ya sha wanki da gyara a wajen wannan mata mai koya mata aiki, ta feshe jikinta da perfume mai daɗin kamshi, ita da kanta tasan ta yi kyau sosai, amma sai fargaba da faɗuwar gaba take ta ji a ranta. Bayan ta kammala shirinta fes ne ta nufi wajen window dan ta leƙa wajen harabar gidan. Tana yaye labule ta buɗe window me zata gani? Sai ganin rana ta yi ɓaro ɓaro, a lokacin ma karfe bakwai ta kusa. Zaro idanu waje ta yi tana mamaki, ita da take jiran lokacin sallar isha ta yi? Ashe bata san tuni asuba ma ta wuce ba. A hanzarce ta dawo cikin room ɗin tare da shinfiɗa dadduma ta tada sallah. Isha ta fara biya kafin ta yi asuba, tana idarwa bata kai ga yin addu'a bama sai ga wannan mata ta shigo, ta zo ɗaukarta ne su tafi. A hanzarce ta yi addu'a ta shafa tare da naɗe daddumar matar ta riƙo hannunta suka nufi waje bayan ta ɗauka mata wayarta da yake a saman bed in da ta ajiye tun daren jiya bata sake bi ta kai ba. Wasu mata guda biyu ne suka zo suka ɗauka mata akwatin kayanta izuwa harabar gidan. Sai kallonsu da mamaki take yi, ta gane masu aikin gidan ne, dan a aikin kitchen da aka koya mata tana ganinsu a kitchen ɗin suna nasu aikin suma, yanzu ita damuwarta ɗaya shi ne taga ina waɗan can hajiyoyi guda biyu da suka rako wannan matashin jiya? Tasan dai su ba ƴan aiki bane, duba da yanayin kayan jikinsu, hamshaƙai ne a gidan, to ina suke?!. Suna tafiya wajen parking space na gida wannan mata tana yi mata bayanin aikin da aka ɗauketa zata yi a gidan, ba komai bane face yin mopping na babbar parlourn gidan in da family suke haɗuwa su ci abinci, daga nan sai gyaran bedroom na yaran gidan, shikenan aikinta, banda wankin toilet, akwai masu wankin toilet, iya gyaran room ɗin ne kawai. Sosai ta kasa kunnuwa tana sauraron matar har suka isa wajen motar da zai ɗauketa izuwa gidan wadda zata kaita gidan aikin. Rungumarta matar ta yi tare da yi mata fatan nasara kafin ta kara karfafa mata gwiwa, sannan ta bata wayarta da ta kashe mata shi already, daga haka suka yi sallama ta shige cikin motar, wancan hajiyar mahaifiyar wannan bata ko leƙo in da suke ba. Har motarsu ya bar gidan bata kalli wannan hajiya ba, yau kwana uku kenan ma bata haɗu da wannan hajiya face to face ba, ko ina take zuwa oho mata. A takaice dai wani dakareran gida aka sake kai Leesharh, a nan ne wani mota ya ɗauketa tare da wata hamshaƙiyar hajiya dake sanye cikin abaya tare da nikaf ita ma suka nufi gidan ABU ABDUSSALAM BIN BADEEN tare da wasu bodyguards guda biyu da suka yi masu rakiya......... Kai tsaye unguwar............. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 12/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________33🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼 Kai tsaye unguwar.............EMIRATES HILLS motarsu Leesharh ta nufa........ Ku daga jin sunan arear kun san bana ƙananan kai bace ba, area ce wadda take da gamayyar kera keran haɗaɗɗun high rise building da manyan ƙasashen duniya take ji da su, duk wata ƙasa da ta amsa sunanta ƙasa to tana takama da ire iren waɗan na high rise building ɗin, gini ne wadda zaku gansa kamar da glass zallah aka yi sa, luxurious area ne dake ta farko a cikin faɗin DUBAI, babu ƙananan gine gine ko guda ɗaya a gabaɗaya arear, dukka luxurious gine gine ne na manyan shegu a ƙasar, ta ko'ina shinfiɗaɗiyar titi ne mai ji da lafiya har kofar gidaje, ga hasken lantarki ta ko'ina, tsayawa zayyana maku haɗuwar wannan area ma sam ba zai yi wu ba, domin baki ma ya yi kaɗan ya faɗesa, ga wasu mahaukatan cameras ta ko'ina dake ɗauko duk wata abu da zata gifta a wannan area, gabas da yamma kudu da arewa Cameras ne. Wasu irin jiga jigan zaratan lafiyayyun securitys dake tsaron arear tun daga farkonta har karshenta kawai ma ya isa ya sanya hantar cikin bawa ya kaɗa, kowani security ka gani fuskar nan tasa kamar ta saniya, a tuɓune, a fusace, kamar waɗan da aka aikowa da saƙon bakar takarda ta albishir da shiga cikin wutar jahannama, sam babu annuri ko miskala zarratin a tattare da su, ga wasu shegun bindigu a hannunsu. Sai dai securitys ɗin kala kala ne, ciki akwai ƴan'sanda ma, abin ku da Defence minister, duk wata kaki a kasarsa take, dole ai kuga kaki kala kala a gidansa. Sai kai komo suke yi wasu daga cikinsu, da alama komai ƙanƙantar motsi suka ji sai sun duba. (Ni kam nace dole waɗan can ƴan leƙen asiri na matan can su kasa iya basu information a kan gidan Abu Abdussalam bin Badeen, irin wannan tsaro dake a arear ma kawai?🤔 Ina ga gidan kuma?🤔) Ganin waɗan nan securitys kawai sai da ya sanya hantar cikin Leesharh ya yi wani irin kaɗawa, duk da tana cikin mota amma ta tsare hanya da kallo, da alama tana son sanin tsakanin gidan da aka ɗaukota da wannan gidan ya tazararsu take, Leesharh ba dai wayo ba. Sai dai ganin waɗan nan securitys ɗin yasa ta mance duk wasu abubuwan da ta gani a hanyar zuwa dan riƙesu a matsayin yadda zata gane hanya ko watarana, ta manta komai tsabar shiga tashin hankali, sai ma da ta ji cikinta ya yi wani irin murɗawa mai bala'i zafi, nan take ta nemi nutsuwarta ta rasa, tunani ta fara yi asirinta ya tonu gata can a hannun waɗan nan dodannin securitys ɗin suna cin namar jikinta ɗanye. Ai bata san lokacin da ta kurma ihu a cikin motar ba, ta ɗauka da gaske ne ake yagar namar jikin nata. Sai da matar ta taɓa ne ta farga ashe dai tunani ne. Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye tare da fara yin danasani mafi muni na karɓar wannan aiki da ta yi tun daga yanzu, tun ma bata kai ga shiga cikin gidan ba ta fara yin nadamar zuwanta duniya, tunani take yi kawai ta shiga uku ta lalace! Shikenan karshenta ne ya zo, idan asirinta ya tonu a irin wannan gida ace gata an kamata a matsayinta na ƴar leƙen asiri ai shikenan ko gata namar jikinta ba zai samu na agasa shi ba, a ɗanye zasu cinyeta, yau ta shiga uku ta lalace!! Ashe su Jasrah sun yi gaskiya, sune ainahin masoyanta da suka hanata karɓar wannan aiki!. Duk da sanyin Ac dake a cikin wannan danƙareriyar mota ita fa Leesharh zufa ce ta fara tsastsafo mata a gabaɗaya face ɗinta, kukan mutuwa a cikin zuciyarta kawai take yi, ta yi tsuru tsuru idanu sun rena fata, har buƙatar shiga toilet ta fara ji ya kamata saboda yadda cikinta yake murɗa mata ga kuma dukan uku uku da kirjinta yake yi, kunsan mara gaskiya fa shi tsoratarsa daban take da kowa!. Sosai wannan mata ta lura da halin da Leesharh ta shiga, amma sam bata kula taba, domin kuwa tasan duk wanda zai shiga gidan Abu Abdussalam bin Badeen to fa sai ya razana makamancin haka, bare kuma ita da tazo da zallar rashin gaskiya? Ai tama yi ƙoƙari da bata saki fitsari a wando ba, leƙen asiri ta zo yi wa masu farautar ran ɗan gidan fa aka turota ta yi, tab ai kunga idan akwai abin da ya fi fitsari a wando ma yi zata yi. Bata ma kara tsananin tsorata ba sai da ta ga sun dimfari wani katafaren luxurious High rise building wanda ya fita daban da sauran gine ginen dake arear, kuma jiga jigan securitys sun fi yawa sosai a wajen, design na ginin ma kawai abin kallo ne, ba wai gini ne da aka yi shi dogon bene kamar na yau da kullum ba, a'a shi wannan idan ka gansa sak design ɗin world, wato duniya yake, ya yi matuƙar ƙawatuwa kuma ginin ya zauna ya zanu da kyau, ya fita iya fita. Duk ba shi bane ya ƙara ɗagawa Leesharh hankali, masu tsaron titin da zata sadaka da cikin wannan hamshakin ginin ne suka ƙara ɗaga mata hankali da har suke ƙoƙarin sanya zuciyarta ta buga. Wasu irin jiga jigan bodyguards ne waɗan da kallonsu a wajen Leesharh da sauran marasa gaskiya kai har ma da masu gaskiya waɗan da suke da karamar zuciya dai'dai yake da kallon mutuwa, fusatattun fuskokinsu kawai ya isa ya sanya mutun tsumar tsaye. Sanye suke cikin baƙaƙen kaya sidif, wasu irin shegun securitys shoes ne a kafafunsu, shi ma baki, irin waɗan nan takalmar ne da idan sun takeka da shi sai mutuwa, ga wasu uban black glass da suka zuba a ido kamar ka kurma ihu idan ka gansu, fararen larabawa ne tas waɗan da babu ɗigon baki ko kaɗan a fatarsu, dayawansu suna da dogayen gemu bakin kirin, sannan gasu da tsawo tare da cikar halitta ta jarumai. Tun daga ɗan nesa da katafaren gate na gidan wani shirgegen bodyguard ya ɗagawa motarsu Leesharh jan wuta, alama su dakata daga in da suke kada su ƙariso, aikin wannan bodyguard ɗin kenan, idan sun san da zuwanka to wannan bodyguard zai ɗaga maka wata farar wuta dake a hannunsa jikin wata kyakkywar na'ura mai bala'in haske, to idan kaga ya ɗaga wannan farar wutar alama ce ta sun sami labarin zuwar wannan mota mai kira kaza da numberta kaza, shi ne zai ɗaga maka wutar alamar ka ƙariso bakin gate su cajeka, ba wai zaka wuce ciki bane, no, wannan farin wutar iso ake maka izuwa bakin gate, sannan wasu bodyguards ɗin su caje motarka tsab ta hanyar amfani da na'urori da komai ƙanƙantar abin zargi bata ɓoyewa, idan suka gama caje motarka tsab, sannan su baka damar wuce gate na farko izuwa na biyu, a nan ma sai ka sake tsayuwa amsa wasu tambayoyi tare kuma da a kara dubaka da kyau, sai sun tabbatar lafiya lou sannan su baka hanya ka wuce ciki izuwa katafaren parking space na gidan. Idan kuma suka ɗaga maka jan wutar nan, to alama ce ta basu san da zuwan wannan mota ba, ba a gaya masu mota kaza mai number kaza zata zo ba, so dan haka tun kana dimfaro gate ɗin gidan zasu ɗaga maka jan wuta, idan kaki dakatawa a wajen to fa zasu sanya bindiga su harbi tayar motarka ne babu ruwansu, so is better for you da ka dakata tun wuri, in kaƙi jiki magayi. Da yake ita wannan mata tasan da dokar gidan sanka sanka, sai ta sanya driver ya dakatar da motar. Wani irin kukan kura cikin Leesharh ya kara yi na tsoro, dan a tunaninta ko asirinta ne ya tonu, tun bata ma fara aikin ba har ta fara tunanin asirinta ya tuno, kai a gaskiya rashin gaskiya sam bai yi ba a rayuwar nan, idan baka da gaskiya a waje dai kana cikin tsaka mai wuya, fargaba da faɗuwar gaba ba zasu barka ka zauna lafiya ba, kullum kana cikin tunanin asirinka zai tonu, Allah ka rufa mana aisiri kasa mu kasance cikakkun masu gaskiya a duk in da muke, ko dan mu samu zaman lafiya da zuƙatanmu. Wayarta matar ta ciro daga cikin jakarta mai shegen kyau da tsada. Massage ta shiga kan wani contact da aka rubuta Hajiya Babba. Gajeran rubutu ta rubuta mata tare da tura mata, sannan ta koma ta jingina da jikin kujerar motar. Ita dai Leesharh sai haɗiyar wahalallen yawu take yi dan bushewa da wuyarta ya yi saboda tsoro, fargaba da razana yasa maƙoshinta ya bushe ta fara jin ƙishi, ga tsoro yasa bata iya haɗiyar yawun nata ma, bama ya fitowa ta nemesa ta rasa. Almost 10 mins da tura saƙon da wannan mata ta yi sannan ne wannan bodyguard ɗin ya ɗaga masu farin wuta alamar su ƙariso ya samu saƙon zuwansu. A hanzarce wannan mata ta ce da driver ya tada mota su ƙarisa. Leesharh ƙwaƙwalwarta ya daina iya gane komai, kwata kwata ma bata san wani doka ce ta dakatar da su na tsawon mintuna goman nan ba, bata san se da izini ake nufar gidan ba, ita dai ta yi wiki wiki da ita kamar an tare ɓera a tarko. Gaban bodyguards dake a bakin gate ta waje ma tukun nan suka paka motar nasu. Wasu ƙosassun zaratan bodyguards su biyun ne suka zo suka fara bincikar motar da wata haɗaɗɗiyar na'ura da take a hannunsu. Kada kuso ku ji yadda kirjin Leesharh yake dukan uku uku baiwar Allah, ta sanya hannu ta dafe kirjin nata ko zata ji wani sassauci, ga fitsari da take ji kamar zai zubo mata a wando, ta rasa ina zata cusa ranta, ta datse idanunta gam wai dan kada ta kalli waɗan nan bodyguards ɗin, suna matuƙar razana ta, baiwar Allah da alama fargaba da faɗuwar gaba ne zai kasheta!. Tsab waɗan nan bodyguards ɗin suka gama caje motar, babu komai na barazana a cikinta. (Ni kuwa nace basu san mutanen da suke a cikin motar sune barazanar ba, rashin sani ya fi dare duhu.) Umarni suka basu a kan su wuce ciki. Kunna motar driver ya yi tare da nufar gate ɗin. Yana ƙarisawa dab da gate ɗin sai gata ta wangale kanta da kanta, da na'ura take aiki, babu wanda yake control ɗinta wajen buɗewa da rufewa, da zarar bodyguards sun baka izinin shiga ciki gate ɗin kuma zata buɗe maka kanta, haka aka yi setting ɗin na'urar ta.................. (Wayyo Allah ka yi mana arziki mai albarka mai amfani, har na ji na fara kamuwa da tausayin Abu Abdussalam bin Badeen🥱 tausayi fa na ce😅) Kutsa motarsu cikin gidan suka yi, a nan Leesharh taga duniya, zantukan su Jasrah ce kawai suke yi mata yawo a kunne yadda suke bata labarin gidan Abu Abdussalam bin Badeen, ashe duk basu faɗa dai'dai bama, gani da ta yi a yanzu yasa ta ji su Jasrah basu san komai a dangane da gidan ba, dan makurar haɗuwa ne wannan gini. Parking space na wannan gida kawai ya ci plot 5 girma, amma kuma duk girman nan nasa cike yake maƙil da luxurious cars kala kala masu zafi, kowani mota ka gani sai ka zaci sabo ne, saboda wani irin ɗaukar idanu da suke yi dan tsabta. A can gefe driversu Leesharh ya samu ya saƙala motarsa ya yi parking ɗinta,. Da farko Leesharh tana ganin motar nasu kamar wani abi ne, sai da ta shigo parking space na Abu Abdussalam sai ta ga ashe motarsu kam banza ne ma, babu ma irinsa a cikin kerarrun motocin da suke parking space ɗin, saboda ƙarami ne. "A'isha mu je ko?". Cewar wannan mata, ta yi maganar tare da sanya kai ta fito waje daga cikin motar, already driver ya buɗe mata mota. Gabaɗaya gidan tiles ne har harabar gidan, tiles mai mugun kyau launin sararin samaniya wato sky blue, hakan yasa ya haɗe da haske ya kara ƙawata gidan sosai da sosai. Ga haɗaɗɗun flowers masu bala'in ƙamshi da kamshinsu ya karaɗe ko'ina a harabar gidan, kamshin nasu irin mai daɗin shaƙar nan. Duk Leesharh sai ta ji ta rai'na class ɗin matan ma gabaɗayansu, har mamaki ne ya ɗan kamata na ganin driver ya buɗewa wannan mata kofar motar, a ranta ta ce ashe ma gidan talakawa aka kai ni da farko, ina cewa ba dan dukiya zasu farauci rayuwar Ramish ba dan suna da ɗinbin dukiya, ashe ni mahaukaciya ce ban san komai ba, ashe ma talakawa ne na ƙarshe a gaban familyn Abu Abdussalam, lallai na yarda son kuɗi zai iya sawa su farauci rayuwar Ramish, wannan shi ne gaba ma da gabanta wai aljani ya taka wuta. (Ku kuwa daga ganin irin wannan gida yakamata ku gane cewa dole Mommar Gimbiya Zunaira ta fita daban a cikin sauran matan King, nan fa gidan yayanta ne uwa ɗaya uba ɗaya, kuma ita ce kaɗai mace a cikinsu, kunga kuwa dole su kaunace ta over, dole komai nata ya fita na daban a cikin KINGDOM OF POWER.) Tana can tana tunane tunane sai ji ta yi an janyo hannunta tare da fito da ita daga cikin motar suka nufi ciki. Gidan bashi da wata hayaniya, ma'ana ba part part bane, a cure yake waje guda gwanin birgewa. Kai tsaye elevator suka nufa wadda zai kaisu izuwa katafaren ginin da family suke. Leesharh an saki baki, ido hanci, kunnuwa da komai da komai ana bin ko'ina da kallo, bata wahalar da kanta wajen ɓoye kauyancinta ba, ta fito da shi fili tana morewa idanunta kallo abinta, ta ki bari kanta ya yi marfi ato, har ta manta da cewa wancan mata ta ce kada ta yarda ta nuna kauyanci, kome zata gani ta dake irin ita ƴar birnin nan, tab aiko dai ga shi nan ta saki baki tana baza kauyancinta son ranta. Ai bata ma karasa sakin bakin nata mai gabaɗaya ba sai da suka shiga katafaren parlourn gidan, a nan ne ta fito da tsantsar kauyancinta tana ganin royal furniture dake a ciki, ta buɗe kofofin hancinta dukka tana shaƙar wani ni'imantaccen haɗaɗɗen arab air freshener dake kwantar da hankalin mai shaƙa wadda ya karaɗe gabaɗaya parlourn da kamshi, ga tsabta da sanyin Ac. Wata hamshaƙiyar hajiya kyakkyawa fara tas ne take zaune a saman sofa mai zaman mutun biyu, babbar macece ba yarinya ba, tana sanye cikin arab jallabiya, fara tas da ita, ta yi rolling veil a kanta, yatsun hannunta na sanye da wasu shegun ring na diamond masu bala'in tsada har guda uku, ta haɗu iya haɗuwa, ta ji hutu har ta ƙoshi, da alama itace matar gidan, ga wata kyakkyawar matashiyar yarinya da take kwance a kusa da ita ta tada kai da laps ɗinta, a shekaru yarinyar ba zata wuce mate na Leesharh ɗin ba, kyakkyawa ce sosai ita ma, tana da ɗan yanayi da wannan hajiya, da alama mahaifiyarta ce, da alama ita ce ƴar Abu Abdussalam da aka ce yana da ƴaƴa maza biyu da mace ɗaya, yarinyar ma arab jallabiya launin white ne a jikinta, kanta babu ɗan'kwali, wannan kyakkyawan arab hair ɗin nata an ɗaure mata shi gida biyu kamar yadda Gimbiya Zunaira da kuma Chuchu suke yawan ɗaure nasu gashin, haka ita ma aka yi mata. Fuska ba yabo ba fallasa ta tarbi wannan mata da ta zo da Leesharh. Saman sofa matar ta zauna, ita kuma Leesharh ta zauna a ƙasa saman wani haɗaɗɗen Turkey carpet mai bala'in laushi, har wani lumewa zaka ji kafafunka sun yi idan ka taka carpet ɗin. Cikin girmamawa wannan mata ta ɗagawa hajiya babba gaisuwa. Cikin mutunta zuna hajiya ta amsa, da alama tana da kamala da dattaku, babu alamar walaƙanta mutane a tattare da ita duba da yadda ta karɓi su Leesharh cikin mutunci duk da tasan cewa tabbas Leesharh ƴar aiki ce, domin tun kafin Leesharh ɗin ta zo gidan tasan da hakan, kada ku manta kafin ma su zo sai an san da zuwansu an kuma san su waye su, so tasan aiki Leesharh ta zo yi, amma bata nuna irin kyama ko kyara ba, ta tarbesu da mutunci. Sosai Leesharh ta ji jikinta ya yi sanyi na ganin yadda matar ta mutuntasu, ko ba'a gaya mata ba ta san cewa wannan mata itace hajiyar wannan aljannar duniyar bakiɗaya, amma ji yadda ta tarbesu kamar wasu ƴan uwanta, duk sai ta ji jikinta ya yi la'asar da ta fara tunanin to meyasa ake son cutar da su tun da dai alamu sun nuna su ɗin mutanen kirki ne?. Yarinta bai bari ta iya gane cewa yanzu ai masu kirki ake cutarwa ba, da zarar kana da kirki neman ganin bayanka ake yi, musamman idan ta haɗo da kana cikin siyasa, sarauta, da dai sauransu, idan ka ce zaka yi adalci ko ka yi wa al'umma hidima ai kana tsaka mai wuya a hannun abokan gaba sai dai Allah ya tsare!. A fili ta furta Allah masani wadda sam bata san maganar ma ya fito ba, sai da ta ga hajiyar tana kallonta ne ta fahimci ashe ta yi magana. Cike da tsoro ta yi ƙasa da kanta. Ita kuma hajiyar sai ta ce. "Turai yanaga kamar ƴar aikin namu bata da lafiya ko kuma wani abin yana damunta?". Wani irin dum dum Leesharh ta ji gabanta ya bada bugu. Matar da suka zo a tare ɗin ne wadda Hajiya Babba ta kira da Turai ta ce. "Hajiya Babba ai dole ki ganta a birkice haka, kema kinsan duk wanda zai shigo wannan gida sai ya razana, securitys ɗin nan naku masu fusatattun fuska da babu amnurin nan ba dole su birkita mutum komai jarumtarsa ba!". Ƴar murmushi Hajiya Babba ta yi kafin ta dubi ƴar matashiyar yarinyar da ta tada kai da laps ɗinta ta ce. "Sharifat jeki ki kira mun Radia ta zo ta wuce da wannan yarinyar izuwa part na ma'aikata dan ta je ta huta, da alama akwai gajiya da firgici a tattare da ita". Miƙewa zaune yarinyar ta yi, ɗan waro idanu waje ta yi irin mamakin nan lokacin da ta kalli Leesharh, da ƴar siririyar zazzaƙar voice ɗinta ta dubi Hajiya Babba. "Ummie she's so beautiful, Allah kyakkyawace sosai, harta kalar fatarta ya yi mun kyau". Ƙasa da idanu Leesharh ta yi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, yanzu ta kara tabbatarwa da kanta waɗan nan mutane mutanen kirki ne, ji yadda yarinyar gidan ma ta karɓeta kamar ba ƴar aikinsu ce ita ba. Allah wadarar mummunar aikin da ta zo aikatawa a kansu ta fara yi, sai dai kuma bata fa da wani zaɓin da ya wuce dole ta yi wannan aiki ko zata mutu kuwa, dan mahaifinta shi ne duniyarta. Babbar magana, wlh akwai cakwakiya da tashin hankali ba kaɗan ba a wannan part ɗin!. Sharifat kyakkyawar yarinya ce sosai, amma a rayuwarta tana kaunar kyawawan mutane, idan taga mace kyakkyawa sai ta ce su ƙullah abota, haka take yi, shiyasa take kaunar yayanta Omar, yayan gimbiya Zunaira kenan, saboda fa kyakkywa ne sosai kamar Zunaira ɗin shi ma, idan kuka gansa kamar shi ya yi kansa, ga idanun nan nasa ba'a magana, so suna mugun shiri da Sharifat sosai! Shi ma a gidan nan yake, ba'a gidan kakarsa yake zama ba, ya fi jin daɗin zama a gidan nan saboda Sharifat ɗin babbar kawarsa kenan. "Sharifat kenan, ai haka Aisha take da kyau, sai ma ta yi make up". Cewar Turai. Murmushi Sharifat ta saki tana faɗin. "Kai bari Yah Omar ya zo zan gaya mashi ankawo ƴar aiki kyakkyawa wadda ta fishi kyau". Girgiza kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce. "Da kuwa kinci bugu a hannunsa, GUYSON ɗin namu ne zaki ce wata ta fishi kyau? Kin manta me ya gaya maki na cewa babu wanda ya kaisa kyau a duniya ko? Faɗa mashi wata ta fisa kyau ina ga yau ko Abbunki ba zai iya kwatarki a hannunsa ba". Ɗan turo baki ta yi tare da miƙewa ta nufi wani haɗaɗɗen curtain, yaye shi ta yi ta shige ta kofar da yake a wajen, tana tafiya tana ɗan juyowa ta kalli Leesharh, ita dai har ga Allah Leesharh ta yi mata kyau ba kaɗan ba, ga shi a tsawo ma tsawonsu zai iya zuwa ɗaya, shekaru ma haka, sai take jin dama ace Leesharh ƴar uwarta ce ta jini, kasancewar ita kaɗai ce mace a gidan, hakan baya yi mata daɗi, ƴan uwa maza kawai take da su, ita sam bata damu da kalar African skin ɗin Leesharh ɗin ba, ita dai kawai ta burgeta tunda kyakkyawa ce. (Ni kuwa na ce a'a Sharifatu baiwar Allah, ki nesanta zuciyarki da Leesharh, dan ita ɗin kyan ɗan macijine a gareku keda ƴan uwanki, cutarku tazo yi, duk da cewa ba laifinta bane, amma dai ku yi nesa da ita, kada ma ku jata a jiki, idan kuka jata a jiki ne ma zata samu damar cutar da kuɗin yadda yakamata, amma dai nayi shiru......🥱) Shiru parlourn ya yi na tsawon lokaci, har Sharifat ta dawo daga wajen kiran Radia. A tare suka dawo da Radia ɗin, tana gaba tana binta a baya. Saman sofar da ta tashi ta koma ta kwanta tare da tada kai da laps ɗin Ummie ɗin nata. Ita kuma Radia a gabansu ta zo ta tsugunna, balarabiya ce ita ɗin ma. Cikin girmamawa ta ce. "Ummie gani nan". Nuna mata Leesharh da hannu Ummie ta yi tare da faɗin. "Ki wuce da ita part ɗinku, already ɗakinta is ready tun da Abbu ya gaya mun za'a kawo wata ƴar aiki nasa su Fadila suka gyara mata room ɗinta, dan haka ki ce Fadila ta nuna maki room da suka gyara mata ki kaita can". Ta kai karshen maganar tare da dawo da kallonta a kan Leesharh. "A'isha ko?". Ta tambayeta. Da sauri ta gyaɗa mata kai alamar e kanta na'a ƙasa kamar wata sahabiya. "Okey tashi kuje ta kaiki room ɗinki, ki yi wanka ki kwanta ki huta, su Fadila zasu baki abinci, yau ki huta gobe sai ki fara aiki ko?". Cikin sanyin murya Ummie ta yi maganar, tana da cool voice sosai kamar yadda yanayinta ya nuna ita ɗin so silent ce. Duk maganar da suke yi cikin harshen larabci suke yinsa. Da okey Leesharh ta amsa mata tare da yi mata godiya, sannan ta miƙe tsaye, Radia ma ta miƙe ta yi gaba Leesharh ɗin ta rufa mata baya, sai kallonsu Sharifat yarinyar kirki take yi, taga Leesharh kyakkyawa jinin Africa tamu ta gida!. Cigaba da hira sama sama Hajiya Babba da Turai suka yi, da alama sun saba. Ita kuwa Sharifat ta cigaba da kwanciyarta shiru abinta!. KO YA RAYUWAR LEESHARH A WANNAN GIDA ZATA KASANCE?🤔 LOKACI NE ZAI NUNAMANA, ALKALAMINA KUMA YA BAYYANA MAKU KOMAI, AMMA DAI AKWAI GAGARUMIN CAKWAKIYA BA KAƊAN BA, DAN KUWA LEESHARH DOLEN UBANTA TA YI WANNAN AIKI IDAN TANA SON MAHAIFINTA!!. 🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH 💔😥 Maman Zainab tasha madarar mamaki sosai lokacin da Baban Zainab ya dawo daga kasuwa, yadda kuka san bai san da zamanta a gidan ba, ko ɗaga idanu ya kalleta yaki yi, da alama ma haushinta yake mugu mugun ji, ko kallon in da take bai son yi. Ko da ta kawo mashi abincin dare ma a yau kam bai ci ba, yaki ko kallon abincin nata ma, abin ya yi mugun ɗaga mata hankali na ƙin karawa, hakan yasa ta shiga gagarumin tashin hankali a in da ta shige cikin room ɗinta tare da rufo kofa, ta murzaki, sannan ta ɗauki wayarta tana kuka hawaye bibbiyu ta kira Aunty Hauwa a waya ta sanar da ita maganin nan fa bai yi aiki ba, hasali ma baban Zainab yaki yi mata magana, ko sannu yaki ce mata, in fact ma yaki kallon in da take, yaki ya ci abincin dare, su Khadijah ɗin ma ya sharesu yau kam, dama wani lokaci saboda su yake daurewa ya danne zuciya idan ta yi mashi laifi ya ci, to yau dai a gabansu ya ce ba zai ci ba, ya kuma wuce cikin bedroom ɗinsa ya kwanta, wannan abin ya yi matuƙar ɗagawa Khadija hankali, da yake ita hankali da ilimi ya ratsata sosai a yanzu, ga nutsuwa da sanin yakamata, tasan baban nata bai taɓa yin makamanciyar haka a gabansu ba tun da suke da shi, to me ya sauya shi lokaci guda haka kenan?. Zeezee da take karama ma hankalinta ya tashi yau, ta shiga damuwa, haka dai suka hakura suna ɗan ci abincin kaɗan, sannan suka nufi nasu ɗakin suma, domin mamarsu ta rufe nata bedroom ɗin tana ciki, shi ma baban nasu haka. Har sun kwanta Khadija ta gagara yin barci, barci ya ƙaurace daga idanunta baiwar Allah, damuwa sun taru sun yi mata yawa, hakan yasa ta miƙe ta sauke ƙasa daga saman bed ɗin nasu. A lokacin Zainab barci ya fara ɗaukarta, lallaɓawa ta yi ta ɗauki hijabin sallarta ta sanya a jikinta ta nufo waje. Tana tsoron fitowa saboda Haidar, amma bata da zaɓi dole ta je wajen kawunta Sadiq ta gaya mashi abin da yake faruwa, dan shi ne kaɗai zai iya gaya mata kalaman da zasu sanyata jin daɗi har ta samu barci, amma sai fargabar haɗuwa da Haidar take yi, addu'a take yi Allah yasa ya yi barci, dan idan bai yi barci ba ta je room ɗinsu a yanzu tabbas sai ya tsayar da ita in ta gama magana da Sadiq, idan kuma ya tsayar da ita ba makawa sai ta taɓa mata jiki, sai ya yi ƙoƙarin taɓa mata breast ɗinta ko ya ce zai yi kissing ɗinta, sam bashi da hankali ko na sayan pure water. Sai dukan uku uku kirjinta yake yi, amma haka ta daure ta fito harabar gidan. Ai kuwa tana fitowa ta yi sa'ar cin karo da Sadiq ɗin yana tsaye a harabar gidan wajen fampon tsakar gida yana waya, da alama da mamarsa yake waya, shi ne ma yasa ya fito waje dan su sami keɓewa da sirri, ba zai yi waya da ita a gaban Haidar ba kenan, yadda ya nutsu sosai yake magana cikin mutunci da girmamawa ne zai tabbatar maka da cewa tabbas da mahaifiyarsa yake waya, dan idan da budurwace ba zai yi irin wannan nutsuwa ya bata dukkan hankalinsa tare da magana cikin girmamawa haka ba. Yaron kirki mai hankali da sanin darajar iyayensa. A hankali kamar wata mai raɗa ta yi mashi sallama, tun fitowarta dama ya ganta, shiyasa yake ƙoƙarin yin sallama da mamar tasa, saboda yasan Khadija bata zuwa wajensa haka kawai, kuma idan ma kaganta a waje harabar gidan to fa girki take taya Mammarta, idan ba haka ba kullum tana ƙule a ciki abinta, ɗan gara ma Zainab tana fitowa waje jefi jefi. So yasan bazata fito haka kawai ba, barema a daren nan yasan dole da akwai matsala, hakan yasa ya yi sallama da mamar tasa a kan gobe da safe zai sake kiranta, daga nan ya kashe wayar tare da bawa Khadijahr dukkan attention ɗinsa. Cikin sanyin murya ta fara gaya mashi halin da ake ciki, ta shiga damuwa sosai na ganin baban nata yaki ya ci abinci, bata ɓoyewa Sadiq komai ba ta gaya mashi tas, sannan ta kara da cewa abin ya hanata yin barci ne yasa ta fito. Zama ya yi a bakin dakalin da aka kewaye fampon da shi, sannan ya ce ita ma ta zauna. Ba musu ta zauna a gefensa, hakika ya shiga damuwa sosai, irin wannan matsala yake gujewa maman Zainab tun tuniya yasa yake ta ƙoƙarin ganin bata sauka daga kan hanya ba, amma ta yi busur da zancensa ta yi son ranta, ga shi yanzu wankin hula yana neman kaita dare, tura ta kai bango baban Zainab ya fara juya mata baya, yanzu wa gari ya wayanwa?. Rarrashin Khadija ɗin ya fara yi tare da bata hakurin, sannan ya sanar da ita dama a tsakanin mata da miji ana iya samun wannan matsala, aure ya gaji hakan, babanta mutumin kirki sosai da yake ɓuye masu ire iren wannan faɗa na mata da miji yasa basu san da hakan na faruwa ba, dan haka kada ta sanya damuwar kowa a ranta, ta yi hakuri zuwa da safe In Sha Allah babanta zuciyarsa zata sauko, dan shi mutun ne mai hakuri, ta yi hakuri komai ya yi zafi maganinsa Allah, ta koma cikin room ɗinsu ta ɗauro alwala ta gabatar da nafila raka'a biyu tare da rokan Ubangiji da ya kawo mata mafita, In Sha Allah zata samu dama ta yi barci, komai kuma zai wuce. Haka dai ya cigaba da rarrashinta yana bata kwarin gwiwa har ta ji sanyi a ranta. Sai da ya tabbatar ta ji daɗi damuwarta ya gudu, sannan ya ce ta tashi ta shiga ciki. Duk da rashin yawan magana irin tata sai da ta ce. "Kawu Sadiq ka bari mu ɗan yi hira kaɗan, zan kara samun nutsuwa na sani". Bai musa mata ba ya jata da hira har wuraren karfe 10, sannan ne ya ce ta tashi ta shiga ciki. Ba musu ta miƙe ranta a sake, fuska ba yabo ba fallasa ta wuce ciki tana yi mashi zai da safe. Shi ma sai da safe ya yi mata kafin ya miƙe ya koma cikin room ɗinsu a in da ya sami Haidar yana riƙe da wayarsa yana kallo, ko shakka bayayi fina finan batsa yake kallo duba da yadda ya takure jikinsa waje guda, kuma yasha kamasa yana kallon fina finan batsa dama, sau da dama yasha yi mashi nasiha a kan hakan babu kyau ya daina, amma ina ya yi nisa baya jin kira, hasalima idan bai kalli batsan ya samarwa da kansa nutsuwar hankalinsa da ya ɗaga ba baya iya yin barci, hakan yana ɗaya daga cikin abin da yasa yake son taɓa jikin Khadija sosai, shi bai kima ta dawo kwana a ɗakinsu ba, ɗan iska saboda yana kalle kalle batsa kullum yana cikin ɗagawa kansa hankali, dole ya yi ta ƙoƙarin latsa ƴar mutane. A kullum idan Sadiq ya fara yi mashi nasiha a kan ya dai'na kallon film irin haka, to wlh faɗa ne yake biyowa baya, basu wanyewa lafiya, hakan yasa Sadiq ɗin yanzu bai ci bi ta kansa ba, ya sharesa kawai tun da baya ji kuma ai ba yaro bane shi, ya fi Sadiq ɗin shekaru da shekaru biyu, kamata ya yi ace shi yake yi wa su Sadiq ɗin faɗa da nasiha, amma ina, ina ma yaga hankali ne wannan kam, sai dai Allah ya kyauta. Yanzu ma girgiza kai kawai Sadiq ɗin ya yi tare da nufar nasa gadon, already da alwalar barcinsa a tattare da shi, dan har ma ya kwanta mamarsa ta kirasa ya tashi ya fita, so yanzu yana dawowa addu'ar barci kawai ya yi tare da kashe wayarsa ya kwanta, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi. A ɓangaren Khadija ita ma bayan ta yi sallar nafila raka'a biyu kamar yadda kawun nata ya ce, sannan ta rufe da shafai da witiri, hankalinta ya kara kwanciya sosai, ta ƙara samun nutsuwa sosai da sosai in da ta zo ta haye gadon ta kwanta, cikin ƙanƙanin lokaci barci ya ɗauketa, dama ita Zee already ta yi barci abinta. Mamarsu kuwa, cikin kuka ta sanar da Aunty Hauwa halin da ake ciki. Hakuri Aunty Hauwar ta bata tare kuma da ce mata ta kwantar da hankalinta gobe da safe zata zo gidan, kada ta ji ta wani damu zasu yi maganin baban Zainab. Da haka dai ta rinƙa rarrashinta har ta hakura a nan barci ya yi awon gaba da ita, in takaice maku labari dai bata yi sallar mangariba bare isha, a haka barci ya saceta saboda kukan da ta sha. (A gaskiya ina jin labarin gidansu Khadija tamkar true life story, wato tamkar gaskiya, wlh duk idan na zo rubuta part ɗin ji nake yi kamar gaske, saboda abu ne da yake faruwa yau da gobe a zahiriya sosai da sosai, Allah dai ka ƙara tsaremana imaninmu ka rabamu da ƙawaye jahilai.) Washegari da safe kamar yadda suka saba haka Maman Zainab ta tashi tare da biyan bashin sallolin da suke a kanta na tun jiya, sannan ta nufi kitchen da nufin ta yi masu girki, kasancewar farar shinkafa da miya ta dafa masu daren jiya wadda basu ci ba, sai ta ɗauko shi ta sake ɗumama masu, saboda bai yi komai ba, kuma yana da yawan da bai kamata su zubar ba, so sai ta sake mayar da shi wuta ta ɗumama, shi ta sanyawa su Khadija a kulolin makarantarsu. Suma su Khadijah suka yi wanka suka shirya kamar yadda suka saba, baban su ne kawai yaki fitowa, da yake dama sai maman Zainab ta haɗa mashi ruwan wanka sannan take tashinsa daga barci, to jiya dai ya rufe room door ɗinsa da key, koda ta kammala shirya masu komai kamar yadda ta saba ta nufi room ɗin nasa dan ta tashesa, sai ta ji kofar a rufe da key. Kamar zata yi knocking, sai kuma ta hakura ganin cewa su Khadija suna nan, kuma tasan halinsa tun suna saurayi da budurwa, damone sarkin hakuri over, amma kuma idan ya zuciya wlh abin da zai sanya shi ya sauko ba karamar abu bace, kuma duk yadda yakai ga kawar da kai ga abu idan fa ya zuciya tura ta kai bango to fa mantawa yake yi da wata kawaici ko makamancin haka, yanzu haka a yadda yake cikin fushi sosai ɗin nan yana iya yi mata faɗa tatas sosai koda a gaban su Khadijah ɗin ne, zai manta da wani tarbiya. Tuna hakan yasa ta fasa yin knocking na kofar ta juya izuwa nata room ɗin, bata sake bi ta kan su Khadijah ɗin bama ita ma. Bayin Allah da suka ga lokaci na ƙurewa zasu yi latti ga Khadijah suna dab da fara rubuta Exams, sai suka fito suka nufi wajen kawunsu Sadiq, dan ya kai su school kamar yadda ya saba, yau dai sun hakura da yin sallama da baban nasu tun da bai fito ba. Knocking suka yi masu Sadiq a kofar ɗakin, ba'afi second ashirin ba sai ga Sadiq ɗin nan ya buɗe kofar ya fito. Shirye yake cikin dakakkiyar shaddar mai shegiyar kyau, da alama yau ma yana da class. Har suna haɗa baki wajen cewa Uncle Sadiq ina kwana. Murmushi ya yi yana kallon Zainab sarkin tsiwa kafin ya amsa masu gaisuwar, yarinyar nan Zainab ba dai iyayi ba, haka take zama ta karewa maman Haidar da kakansu zagi fes kamar an aikota, bata da sauki, Khadija kam daga e sai a'a, sai kuma gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa. "Dama na shirya ku nake jira, ina da class karfe 7:30 dai'dai mu je ko?". Sadiq ya faɗa yana kai hannunsa ya ɗan bugi bakin Zee da take aikin turo shi kamar wadda aka zaga. "Kai kawu Sadiq menayi maka to?". Ta faɗa tana ɗaure fuska. Khadijah ce ta amsa mata da. "Kwaɗayin duka yake ji yasa ya dake ki, ko dai bai kai bane?". Wani irin harara ta bi Khadija da shi. Shi dai Sadiq wucewa ya yi izuwa wajen mashin ɗin baban nasu, da yake key na a hannunsa, fito da mashin ɗin ya yi kamar yadda suka saba, ba ɓata lokaci ya ce su yi sauri su hau su tafi lokaci yana ƙurewa. Da sauri suka hau Zainab sai raki take yi. Da haka suka bar gida, shi kuwa Haidar yana can yana barcin asara, wani lokaci ma sai 10 yake tashi ya tafi kasuwa ko kuma wajen mamarsa or kakarsa, kullum aiki ɗaya, ya kusa yin aurema bai canza hali ba, ko waye zai ciyar mashi da matar idan ya yi auren? Shi da kasuwar ma sai yaga dama yake zuwa. Akwai matsala sosai, akwai case ba kaɗan ba. Misalin karfe 9 dai'dai sai ga Aunty Hauwa ta nufo gidan kamar yadda ta faɗawa maman Zainab zata zo jiya. A lokacin baban Zainab bai fita ba, yana ciki, da alama yau ba zai je kasuwa da wuri ba, ita ma maman Zainab tana cikin ɗakinta ta yi zaman ƴan bori a saman tsakiyar gado, ta haɗa hannayenta ta buga uwar tagumi kamar wadda aka aikowa da wahayin yinsa, ta luluƙa duniyar tunanin ya zata yi da rayuwarta, har yanzu ta kasa iya gane cewa damar da Allah ya bata a baya ne take wasa da shi son ranta, tana yi kuma ba tare da godiya ga Allah ba, to yanzu damar tana neman kubce mata, ta kasa iya gane hakan ma bare ta yi ƙoƙarin dawo da damar izuwa gareta..... Tirƙashi, akwai matsala fa my people's, mu je dai zuwa. A parlourn Aunty Hauwa ta zauna, ta tsantsara kwalliyarta cikin wata shegiyar lace mai kyan gaske, da alama ma case ɗin maman Zainab ɗin bai wani dameta ba, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya a kanta irin yau ba mutuncin nan, sai wani kwaɓe fuska take yi kamar wadda taga kashi. Fitowa maman Zainab ta yi daga room ɗinta cike da damuwar halin da take a ciki, tsawon shekarun nan da suka yi aure baban Zainab bai taɓa yi mata makamancin haka ba, har ya share tun jiya bai yi mata magana ba har yau, abin dole ya jefata cikin damuwa sosai, a maimakon ta kira mahaifiyarta ta sanar da ita abin da yake faruwa, sai ta sake kirawo Aunty Hauwa kuma. "Hauwa ki zo mu shiga cikin bedroom, baban Zainab yana nan fa". Maman Zainab ta faɗa murya ƙasa ƙasa. Okey Aunty Hauwa ta amsa tare da ɗaukar wata ƴar figaggiyar jakarta irin na dillalai, ga gyalenta dama a kafaɗa ta yafo shi kamar ba matar aure ba, burinta kawai su shiga ciki ta tambayi maman Zainab ɗin baban Zainab ya sha maganin? A ƙage take da ta ji ya sha ɗin ko bai sha ba?. A haka ta miƙe da nufin su shiga cikin bedroom ɗin dan rashin hankali irin na maman Zainab da kuma damuwa da ya rufe mata idanu. Tana miƙewa tsaye sai ga baban Zainab ya fito cikin shirinsa na shadda mai shegen kyau launin sky blue, ɗinkin manyan kaya ne, so ya ɗaura babbar rigar ma a sama, a takaice dai makurar shigar mutunci ya yi, da alama yau ma ba zai ci abincin maman Zainab ba, kamar dai daren jiya, dan dai ga shi ya kammala shirin fita abinsa. "Sannu da fitowa, ina kwana?". Aunty Hauwa ta faɗa cikin sanyin murya. Turus ya ja birki ya tsaya tare da juyo da kallonsa a kanta, wani irin faɗuwar gaba ya ji a lokacin da ya sauke idanunsa a kanta. Da ni da ku duka mun san cewa baban Zainab in ya shigo ya sami maman Zainab da bakuwa wlh ko kallon in da suke baya yi, baƙin suna gaishesa ma baya tsayawa, wani lokaci kafin ya amsa masu gaisuwar nasu ma ya kai bakin kofar ɗakinsa, amma yau sai ya tsaya tare da juyowa yana kallon Aunty Hauwa. Maman Zainab ta ɗan yi mamaki, amma sai ta ce kila zai tambayi Aunty Hauwa ɗin ina ta je jiya ne, dan haka sai bata wani damu ba. "Sannunki da zuwa Hauwa ya gida ya yara?". Ya faɗa yana bata full attention ɗinsa. Murmushi ta sakar mashi kafin ta amsa mashi da komai lafiya lou. Shiru ya ɗan tsaya tare da zuba mata idanu yana ta kallonta. Maman Zainab kuwa sai ta taɓe baki tana ganin abin kamar a Tv a gabanta, ita kuma Aunty Hauwa sai wani irin murmushi take yi mashi. "Yanzu zaki tafi ne na kai ki gida?". Baban Zainab ya tambaya. Wani irin zaro idanu maman Zainab ta yi, abin da bata taɓa ji ba, ba kuma ta taɓa gani a tattare da shi ba, kai ina bata yarda ba, a mafarki ta ɗauki abin, dan haka sai ta kai hannunta saman face ɗinta ta ɗan mari kumatunta wai idan mafarki take yi ma ta farka. Amma ina sai ma ji da ta yi Aunty Hauwa tana cewa. "E zamu iya tafiya a tare duk da ba yanzu naso tafiya ba, amma tun da zaka mayar dani ai komawa ta kamani". "To muje ko?". Ya faɗa yana mai cigaba da kallon face ɗinta sosai, sai wani uban murmushi take yi. Maman Zainab bata ankara ba tana can tana tunanin mafarki take yi ne ko ba mafarki ba kawai sai ganin Aunty Hauwa ta yi sun jera da baban Zainab sun nufi wajen parlourn. Ai bata san lokacin da ta bi bayansu ba, a harabar gidan ta ce. "Hauwa menene haka kuma?". Dakatawa daga tafiyar da suke yi Aunty Hauwa ta yi tare da juyowa ga maman Zainab ɗin, ɗaure fuska ta yi sosai kafin ta ce. "Wacece kuma Hauwa? Ni kike kira ko dai wata?". Tashin hankali da ba'a sanya mashi date kenan!!. Wani irin zaro idanu waje maman Zainab ta yi, tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa, cikin tashin hankali ta ce. "Hauwa ban gane me kike faɗa ba? Ban gane me kike nufi ba? Ko dai kunnuwana sun dai'na ji ne? Ko dai har yanzu a cikin mafarki nake ne?". Kallon baban Zainab Aunty Hauwar ta yi tare da cewa. "Abu Zee mu je ko? Bani da lokacin A'isha ni kam". Da okey kawai ya amsa mata ba tare da ya kalli in da maman Zainab ɗin take tsaye ba, kamar bai taɓa saninta ba a duniya.... Tashin sense kenan yau ake yinta a wannan gidan. Gaba Aunty Hauwa ta yi tana wani rangwaɗa tare da kara gaya mashi su je ita fa bata da lokacin maman Zainab a yanzu. Rufa mata baya ya yi da nufin su tafi ɗin. Ai tsabar kishi da bakin ciki yasa Maman Zainab bata san lokacin da ta yi kukan kura ta damko wuyar Aunty Hauwar ba, idanunta sun rufe, wani irin bakin cikin take ji kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, wani irin cin amana ne wannan mai azaban raɗaɗin zafi haka?. Cikin sauri baban Zainab ya fara ƙoƙarin kwatar Aunty Hauwar daga shaƙar da maman Zainab ta yi mata, da alama mafa baban Zainab ya manta wacece maman Zainab. Tirƙashi. Maman Zainab kuwa ta shaƙeta da iya karfinta na karshe tana faɗin wlh sai ta kasheta, azzaluma maciyi amana, su taso a tare su yi karatu a tare, komai a tare suke yi ne zata nemi ta ci amanarta haka? To wlh ba zata barta ba, kasheta zata yi sai dai duk abin da zai faru ya faru. Wani irin mari da baban Zainab ya sakar mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wuyar Aunty Hauwar ba tana zunduma ihu kamar zararriya. Wani irin kukan kura ta sake yi ta................ Tashin hankali, akwai babbar cakwakiya na kin ƙarawa a wannan gidan, kenan Aunty Hauwa amanar maman Zainab ta ci? Ta kaita wajen malami da sunan samun mafita kenan kanta ta shiryawa hanya mai kyau ba maman Zainab ɗin ba?🤔 Ita kuma maman Zainab cikin rashin sani ta bashi maganin kaunar Aunty Hauwar da hannunta ya sha?🤔 Ga shi har da ƴaƴanta su Khadijah ta bawa suka sha dan rashin hankali da rashin tunani? To kenan ya makomarsu take su kuma? Suma zasu bi ayarin Aunty Hauwa kamar babansu kenan? Bala'in nan, wannan shi ne bala'i, akwai yaki gagarumi a cikin wannan gida, ya makomar maman Zainab? Farkoma ya makomar auren Aunty Hauwar? Da ni da ku dai duk mun san tana da aure? Alamu kuma sun nuna baban Zainab dai ya kamu da sonta, kuma ga dukkan alamu ita ma hakan take so, to ya kenan batun nata mijin?🤔 Ina su maman Haidar? Zasu yarda da hakan kuwa? Kada ku manta sun yi mashi mata fa a cikin family, lallai akwai rikici da rikita rikita, yau akan Aunty Hauwa baban Zainab ya mari Maman Zainab, tab duniya kenan, amana ta yi ƙaranci, ni dai PRINCESS TEEMA na haɗa kayana sai mun haɗe daku gobe dan jin yadda wannan bala'in yakin da ta tinkaromu zata kaya!! RAWANIN ZALINCI ya fara ɗaukar tafasa ma ba zafi ba, Zalunci ta ko'ina😥💔 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 13/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________34🔥 Wani irin mari da baban Zainab ya sakar mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wuyar Aunty Hauwar ba tana zunduma ihu kamar zararriya. Wani irin kukan kura ta sake yi ta damko wuyar Aunty Hauwar, idanunta sun rufe, ita dai ta kashe Aunty Hauwa kawai hankalinta ya kwanta. A karo na biyu baban Zainab ya kara mata wani zazzafar mari, sai dai a wannan karon ko da ya mareta bata saki Hauwar ba, sai ma kara ƙanƙame wuyarta da ta yi, yadda ta ji zafin wannan mari haka ta kara shaƙe mata wuya gam. Kafin baban Zainab ya samu ya kwaceta daga hannunta har Hauwa ta sume, saboda azaba, tasha shaƙar manya, ga shi cikin fushi aka yi mata shaƙar. Fara ƙoƙarin dukan maman Zainab ɗin ya yi, amma ina, ai bata tsaya ya daketa ba, sai ma kwasawa da ta yi a guje ta nufi cikin kitchen, muciyar tuƙa tuwonta ya je ta ɗauko, hauka hauka ta nunawa baban Zainab a in da ta fara ƙoƙarin dukan Hauwa dake sume yashe a ƙasa da wannan muciya, ta sumar da ita ɗin ma ba zata kyaleta ba. Da baban Zainab da ya ga haka sai shi ma ya sanya mata karfi da nufi ya yi mata duka ya kuma karewa Hauwa dake sume faɗar. Amma ina maman Zainab taki yarda ta bari ya sake ɗaura hannunsa a jikinta, sai zulle mashi take yi, shi kuma yaki barinta ko sau ɗaya ne ta kwalawa Hauwa wannan muciya da ta ɗauko. Daga karshe dai ya yi nasarar kwace muciyar tare da kamata ya turata cikin ɗaki, ya kuma rufo kofar ta waje ya barota a ciki. Kamar zararriya haka ta rinƙa dukan kofar nan da iya karfinta na karshe, tamkar zata ɓalle kofar, hakan yasa Haidar ya farka daga barcin asararsa da yake yi. Shi kuwa baban Zee bai ma sake bi ta kanta ba, ruwa kawai ya ɗebo a kitchen ya zo ya yayyafawa Hauwa ta farfaɗo. A haukace ta farfaɗo tana ambatar ta shiga uku yau zata mutu. Hakuri ya fara bata kamar wani ɗanta, harda tsugunnawa a gabanta ya fara rarrashinta. Ji maman Zainab take yi zuciyarta zai iya fasa kirjinta ya fito waje, hakan yasa ta fara neman abin da zata karya wannan kofar da shi ta fito waje, yau ji take yi idan bata kashe Hauwa ba ba ita ba zaman lafiya, kada ku manta dama baban Zainab ya ce tana da balai'n kishi na wuce tunani, bare kuma ace irin wannan cin amana mai bala'in zafin da Hauwa ta yi mata ai dole ne ta haukace masu, kawarta ce fa da suka taso tun yarinta, duk da tun suna yara halinsu ya sha banban, amma hakan bai sa sun rabu ba, kawance ta ɗaure har girma izuwa aure, ace rana tsaka ta yi mata irin wannan ɗanyen aiki ɗanyen cin amana, ai dole zuciya ta sosu over. Fatana a nan dai shi Allah yasa mata kun ɗauki darasi! Duk abin da yake faruwa da maman Zainab ita ta jawa kanta, kama daga abin da su maman Haidar suke yi mata har wadda Hauwa ta yi mata a yau, duk ita ce da laifi, ta ya za'ayi ki rinƙa sakin baki kina gayawa wata cewa mijinki yana kula dake hundred over hundred? Kuma sai ma ki rasa wadda zaki rinƙa gayawa hakan sai wadda ita mijin nata baya yi mata hakan, a haka kike tunanin zaki samu zaman lafiya? Ke kina tunanin cewa ai kawarki ce, kun taso tare ba zata ci amanarki ba, to ai ga shi nan kun gani ido da ido, ita tana can tana fama sai ta sha rana ta yi kasuwanci tukun nan ta iya biyawa kanta dukkannin buƙatun da take so, ke kuma kina daga kwance ake yi maki komai, sannan kizo kina bata labarin irin daɗin da kike ji ki ce ba zata yi tunanin ita ma bari ta yi join ɗinki kuci daɗin a tare ba? Waye baya son daɗi? Waye yake son wahala? Kin yi kuskure babba idan ma haka kike tunani, wata ma domin hasada da bakin cikin bata samun abin da kike samu ko ba zata auri mijin naki ta shigo kuci daɗin a tare ba zata yi duk yadda zata yi ta rabaki da mijin, idan kuma hakan bai samu ba to zata yi duk yadda zata yi ta ga ya dai'na kyautata maki kin koma wahala kamar ita. Ai a zamanin yanzun nan duk yadda kuke tare da mutun da ya tambayeki ya mijinki? Alhdulillah kawai zaki ce mashi, daga wannan Alhdulillah ɗin kada ki kara kada ki rage, bakinki kanin kafarki, idan kuma kin ki ji to fa ba kyaki gani ba. Idan muka koma muka yi duba da abin da yake a tsakaninta da su maman Haidar nan ma ita ta jawa kanta, domin kuwa ita ce nan tun farko ta sakewa Haidar ya san komai ɗinta da har yake kwasan sirrin gidan yana kaiwa kakarsa da kuma mahaifiyar tasa. Kunga ita ma maman Haidar ɗin ba samun jin daɗin nan wajen mijinta take yi ba, baban Zainab ɗin ne ma mai ciyar da ita, saboda mutuwar zuciya irin na mijinta, ai dole ita ma zata ji haushin bata samun abin da maman Zainab take samu, dole ta yi mata hasada da bakin ciki, shiyasa take zuga kakan su Khadijah dan kawai ta takurawa maman Zainab ɗin kuma ta ƙuntata mata. Yaushe zaki bari har familynsa su san irin kyautatawar da yake yi maki? Ai a irin haka ne ma wata daga cikin family zata maƙale ta ce idan ba shi ba ba zata yi aure ba, haka kina ji kina gani za'a sanya ya aurota kamar dai yadda kuka ga aya a kan maman Zainab. Ai ko mijinki ya ɗauko kaninsa ya kawo maki ki rike, sai ki san ta yadda zaki zauna da shi baki cuce shi ba kuma baki bari ya cuceki ba, kada ki yarda ki bari yasan cewa ga abin da yayansa yake yi maki, ki koyawa mijinki ko abu zai baki to ya baki tun daga cikin bedroom ba sai anzo parlourn bama bare har a kai ga tsakar gida. Fatana dai my people's kun ɗauki darasi na farko a kan maman Zainab?. Sosai baban Zainab ya rarrashi Hauwa, sai kukan makirci da kisisina take yi, ita kuma maman Zainab tana can tana ƙoƙarin haɗiyar zuciya kofa yaki buɗewa. Tana ji tana gani baban Zainab dai ya saka Hauwa a gaba suka bar gidan, sai lallaɓata yake yi. Dama kun san shi ya iya sosai..........😅 Suna fita gidan Haidar kuma ya fito daga cikin nasu ɗakin, dukar kofar parlourn da maman Zee ke yi ne yasa ya farka, sai dai bai yi nasarar ganin menene ya faru ba, baban Zee ya ja Hauwa sun yi gaba. Ko da ya fito waje bai ga kowa a harabar gidan ba, ita ma Maman Zee a lokacin ta dai'na buga kofar parlourn ta kwasa a guje ta nufi cikin bedroom ɗinta, dan taga tafiyarsu ta window, sun riga sun fita, ko ta buga kofar ba amfani, dan haka sai ta kwasa da gudu ta yi cikin room ɗinta. Jikinta har wani irin kerma yake yi saboda bakin ciki, wani irin zufar wahala yana tsastsafo mata a gabaɗaya face ɗinta, kuka take yi hawaye bibbiyu, idanunta sun yi jajir kamar wata ƴar shaye shaye. A gigice ta ɗauko wayarta, har wani yana yana take gani a cikin idanunta, bata ganin screen ɗin wayar da kyau saboda kuka. Number mahaifiyarta ta fara kira a haukace, sai yanzu ta tuna da cewa ta kira mahaifiyar tata, da can duk bata tuna ba, sai da abu ya kwaɓe mata. Bugu biyu mamar tata ta ɗauka. Cikin kuka ta fara faɗin. "Nashiga uku mama, na mutu na lalace Hauwa ta cuceni". A gigice ƴar tsohuwa ta ce. "A'isha lafiyarki kuwa? Babu sallama sai ihu haka? Menene yake faruwa? Me Hauwa ɗin ta yi maki?". Da gaji maganar tsohuwar nan kasa ta firgice, baiwar Allah maman Zee ta ɗaga mata hankali babu shiri. "Mama Hauwa ta cuceni, ta kaini wajen boka, da kai'na kuma tasa na bawa baban Zainab maganin da zai sota, da kuɗina kuma muka karɓo maganin, yanzu shikenan sonta yake, ga shi can ya ɗauketa sun tafi, na shiga ukuna, mama ki taimakeni kada na mutu". Yadda take maganar zaka fahimci cewa tabbas ba'a cikin hayyacinta take ba, bata ma san me bakinta yake faɗa ba, kawai sambatun surutai barkate take yi. Ƙara rikicewa ƴar tsohuwar nan ta yi, sai cewa take yi. "A'isha ki nutsuwa ki yi mun magana a nutse ta yadda zan fahimta, yanzu ni bana iya gane komai da kike faɗe". Ita ma tana magana tana haɗe words, saboda a rikice take, kun san irin wannan call ɗin ma sai mai dakiyar zuciya yake iya jurewa baya suma, amma a kiraka irin haka ana kuka ga shi ba gari ɗaya kuke ba, baka san halin da ake ciki ba kuma baka san kan zance ba, in fact bata ma taɓa kiranka ta ce maka tana cikin wata damuwa ba, rana tsaka kawai ayi maka irin wannan kira ai dole bawa ya rikice, idan akwai abin da ya fi rikicewa ma yi zai yi. Sai sambatu maman Zee take yi ta kasa iya nutsuwa, a haka dai ta kwashe duk abin da ya faru tun daga farko kan auren Khadija da Haidar har izuwa yau ta gayawa mamar tata, tana yi tana kuka hawaye bibbiyu. Cikin tsananin tashin hankali mamar tata ta ce. "A'isha kin tabka baban kuskure da gyara shi zai yi matukar wahala a yanzu, da hankali da tunaninki har wata zata kaiki wajen wani boka? Shin bana duniyar ne da ba zaki kirani ki sanar da ni ga abin da yake faruwa ba? Ga halin da gidanki yake a ciki? Tun farko ma ban hana ki yin shawara da wata ba? Tun kuna yara na yi na yi na rabaki da Hauwar nan, amma kika ki rabuwa da ita, yanzu ba ga shi ta kai ki ta baroki ba, to ita ina ma mijinta yake? Da auren nata ta biyo baban Zainab ɗin kenan ne ko yaya?". Ta yi maganar cikin maƙurar ɓacin rai!. "Mama bansani ba, ban san ina aurenta yake ba, ni dai kawai nasan dai tana da miji da yara, ni ba zuwa gidanta nake yi ba, nafi wata 8 ban leƙa gidanta da ƙafafuna ba, mama nashiga ukuna". A ɗan fusace mamar ta ce mata. "Ai baki shiga uku bama tukun nan A'isha, ba dai shirka haɗa Allah da wani kika yi ba, laifi mafi girma a duniya, ai kin rinƙa shiga masifu kala kala kenan Allah ya kiyaye ba baki nake yi maki ba, amma wlh kin tabka baban kuskure, kuma abin da zan gaya maki a nan yanzu shi ne tun wuri ki fara istigifari kafin abin ya yi nisa ki fara fuskantar fushin Ubangiji, kin taɓa ganina da ko da sassaken itace na jiƙa na sha ne da zaki kama hanyar zuwa wajen boka? Wato duk nasihar da nake yi maki kullum abanza yake ko? Kishi haukace? To tun wuri ki yi gaggawar tuba, ki nutsu ki koma ga Allah, hankalinki ya dawo jikinki kafin mu san abin yi". Ta kai karshen maganar ranta a matuƙar ɓace sosai. Kuka ne da ya ci karfinta yasa ta ƙasa iya amsa maganar maman, danasani ne kawai a cike a cikin ranta, nadamar sanin Hauwa a rayuwarta ne kawai ya cika mata zuciya. Sam bata san lokacin da mahaifiyar tata ta karaci yin faɗarta ta katse kiran ba. Ita dai ta luluƙa duniyar tunani mafita, a wajen ta sulale ƙasa ta kwanta tana mai cigaba da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Shi kuwa Haidar dama can kun san ba shiri da ita yake yi ba, dan haka ko da ya ji kukanta ma tsaki ya ja ya koma cikin ɗaki abinsa, ya je ya haye gado ya cigaba da yin barcinsa, dama lokacin tashinsa bata yi ba, kawai sun tashesa ne. Baban Zainab kuwa da yake ba yin kansa bane, abin hawa ya tara masu shi da Hauwa suka nufi gidanta, da alama ya manta da cewa tana da aure.... Tirƙashi, akwai cakwakiya kam ba kaɗan ba wlh. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ 🌼DUBAI🌼 Ɗaki mai matuƙar kyau aka kai Leesharh, tamkar ba ɗakin ƴar aiki ba, ya ji komai na more rayuwa, ga bed ɗinta ma katafare da shi, yana shinfiɗe da shinfiɗa ta alfarma, ita kaɗai ce a room ɗin, ba'a haɗata da kowa ba, ta ji matuƙar daɗin kasancewar ita kaɗai ga kuma room ɗin ya ji komai, ga wani haɗaɗɗen sanyin Ac dake ratsa jiki gwanin daɗi. Ai tana shiga cikin room ɗin bayan Radia da Fadila sun fita, saman gadonta ta kwanta tana mai da numfashi, sai yanzu ta samu damar sauke nannauyar ajiyar zuciya, godiya ta yi wa Allah da ya kawota cikin irin wannan daula, addu'a kawai take yi da Allah ya bata nasara ta kammala aikinta cikin ƙanƙanin lokaci ta koma wajen babanta. Nan take kuma face ɗinta ya canza, tunawa da ta yi da irin aikin da ya kawota, duk sai ta ji ta shiga gagarumin damuwa, yanzu da gaske haka zata yi wannan aiki na leƙan asiri Ramish? Tukun nan ma waye shi? A ina kuma yake? Shi ma a wannan part ɗin yake ko yaya?. Jin motsin an shigo mata cikin room ɗin nata ne yasa ta yi saurin kai kallonta zuwa bakin kofar shigowa. Fadila ce ta dawo ɗauke da akwatinta, ta je ta ɗauko mata ne. Sannu da hutawa ta yi mata kafin ta ce mata ga akwatinki nan. Nagode Leesharh ta yi mata tare da binta da kallo, daga haka basu sake ce da juna ko sannu ba har ta ajiye mata akwatin ta fita waje. Barci mai shegen daɗi ne ya ɗauki Leesharh, ba ita ta farka ba sai wurare karfe 1 na rana, kasancewar yanayin gidan baka iya gane rana ko dare ya yi sai dai ka duba time, sai ya zamana bata iya gane cewa wani lokaci bane a yanzu. Miƙewa ta yi cikin kasala irin na mai barci ta nufi cikin toilet. Haɗaɗɗene toilet ɗin nata, ita a nata ganin sai take ga kamar wannan room ɗin ai dai'dai yake dana ƴar gida, saboda ta ga ya haɗu ne sosai, da alama ta mance a gidan waye take da har take ƙoƙarin haɗa room ɗinta dana ƴar gida, tab bata san duk wannan haɗuwa na room ɗin nata su shi suke kallo a matsayin na masu aiki ba, kila idan ta shiga bedroom na ƴar gida sumar tsaye zata yi dan haɗuwa. Akwai komai a cikin toilet ɗin na buƙata, harta su kyawawan towels masu kyau na wanka, ga jacuzzinta ma mai ɗan girma da shi. Wanka ta fara yi kafin ta ɗauro alwala ta fito, tun asali ita Leesharh tana yawan son zama da alwala, shiyasa a duk lokacin da ta shiga toilet bata fitowa sai ta ɗauro alwala ko da ba lokacin yin sallah bane ba. Akwaitin kayanta ta jawo bayan ta fito daga cikin toilet. Dukka Arabian dressing ne a ciki, daga dogayen riguna, sai riga da sket, riga da wando. Leesharh mayyar son riga da wando ce, tana da son yin gayu sosai, kawai halin babu da suke ciki ne yasa take hakura, amma idan ba haka ba tana da son yin gayu, lokacin da take gaban iyayenta mafiya yawan kayanta riguna da wanduna ne, ta ci gayu gwanin ban sha'awa, ga ta kyakkyawa kuma dirarriyar mace. A yanzu ma riga da wando ta ɗauko tare da mayar da sauran kayan da ta fitar ciki. Riga da wandon sun haɗu makurar haɗuwa, Arabian dressing ne, wando ne mai kyau dogo har ƙasa, sai rigarsa da ya tsaya mata izuwa gwiwowinta, sannan wani ɗan ƙaramin veils mara girma sosai. Da alama Leesharh ta jima a tare da larabawa, domin kuwa tsab ta iya dressing nasu ya zauna a jikinta da kyau da kyau, kamar wata balarabiyar gaske, a yanzu ma haka ta shirya cikin wannan kaya ta fita ras abinta, ta yi rolling veil ɗin nan a kanta kamar yadda suke yi, sai kyanta ya kara fitowa sosai. Wayarta ta ɗauko ta kunna da nufin ta duba time, haka kawai ta tsinci kanta da shiga fargaba da faɗuwar gaba na kunna wayar, sai take jin kamar kada ta kunna wayar ta kyale shi a haka. Amma haka ta kunna ta duba time. 2:5 pm. Ganin har karfe 2 ta ɗan wuce ne yasa ta zaro waɗan nan manya manyan idanun nata waje. Cikin hanzari ta miƙe tare da fara waige waigen ina ne gabas dan ta yi sallah?. Sallamar da aka yi daga bayanta ne yasa ta yi saurin juyawa izuwa kofar shigowa room ɗin. Fadila ce ta shigo hannunta ɗauke da abinci a wani katuwar try, ɗazun ma ta kawo mata abincin, sai ta sameta tana barci, shi ne ta koma da abincin, yanzu kuma na rana ne ta kawo mata. Fadila fa babbar budurwa ce wadda a kallah zata kai 25 year, amma saboda tarbiya irin na gida Abu Abdussalam yasa suma masu yi masu aiki suke ɗaukar kansu kamar dukka ƴan uwa ne, basu nuna banbanci ko fifikon shekaru, suna aiki a tare sun zama kamar ƴan uwan abin gwanin ban sha'awa, yanzu na tabbata kun ji sha'awar yadda Fadila bata nuna cewa ai ta fi Leesharh shekaru dan haka ba zata kawo mata abinci ba, da wasu ne za su ce sai dai ta zo da kanta ta ɗauka, amma a gidan Abu Abdussalam ba'a yin haka, masu yi masu aiki ma suna da tsari na bin doka haka ina kuma ga ƴan gida? Masu aiki ma an koya masu haɗin kai har haka ina kuma ga ƴan gida? Ya kuke tunanin haɗin kan ƴan gidan zai kasance?. A saman carpet ta ajiye mata abincin tare da sake yi mata sannu da tashi daga barci. Kasancewar ita Leesharh tana under umarni da kashedi na kada ta kula kowa a cikin gidan, sai ya zamana ciki ciki ta amsawa Fadila ɗin, tana yi kuma tana kawar da kanta, dan a wawtarta hakan ce zata sanya ta yi nesa da ƴan aikin kada ta kulla abota da kowa. Fadila kuwa, ta yi tunanin saboda Leesharh bakuwa ce yasa bata sake da ita ba, ta yi mata wannan uzurin, a in da ta ajiye mata abincin kawai tare da nufar kofar fita waje tana faɗin. "Idan kin kammala cin abincin zanzo na ɗaukeki mu je ki ga wasu gurare a cikin gidan, daga nan sai ki ga parlourn da zaki yi aiki a ciki, sai bedroom ɗin Aunty Sharifat da zaki rinƙa gyara mata, nata ita da Guyson, bedroom biyu ne kawai zaki rinƙa gyarawa, Ummie ta sanar da ni shi ne aikinki". Nan ma ƙasa ƙasa Leesharh ta amsa mata da. "Okey amma dan Allah ina ce alkibla a wannan gida?". Da hannu Fadila ta nuna mata gabas tare da sa kai ta fice abinta. Saman carpet ta yi tsaya ta fuskanci alkiblar, sannan ta tada sallah da iya wannan veil na kanta da ta yi rolling. Bayan ta idar ta yi addu'oi sosai da sosai, lokacin da ta ɗauka tana zuba addu'ar ma ya fi lokacin da ta ɗauka wajen gabatar da sallar. Bayan ta shafa ta matso kusa da abincin nata, dama yunwa take ji, tun safe bata ci komai ba, sai kuka ƴaƴan hanjin cikinta suke yi. Abincin ta fara zaɓar wanda zata ci, cikin nutsuwa ta zuba a cikin plate, ba ɓata lokaci hannu baka hannu kwarya ta fara cin abincin. Wani tunani ne ya faɗo mata, tunawa da yadda taga yawan Cameras tun daga kan titin da zai kawoka gidan nan har izuwa cikin gidan ta yi. A hanzarce ta ɗaga kanta sama ta fara neman camera a cikin room ɗin nata, dan ta tsorata, a tunaninta akwai camera, kada ya zamana duk abin da take yi masu gidan suna kallonta. Ganin bata ga alamar camera a room ɗin bane yasa ta cigaba da cin abincinta tana tunanin yadda zata kaya mata a wannan gida. After some minutes. Ta kammala ci tas, ta ci abincin sosai, sannan ta tattare komai kamar ba'a taɓa cin abinci a wajen ba, ta kwaso kayan abincin ta fito waje. Nan ta bar wayarta a saman bed ɗin tata, ita da aka ce ta ɓoye wannan wayar, kada ta fitar kowa ya gani, ta bari za'a bata wayar amfani a gidan, dan duk masu aikin gidan suna da wayoyi da Ummie ta saya masu wanda zasu iya kiran ƴan uwansu, haka tsarin gidan yake, amma ita Leesharh tun ba'a je ko'ina ba ta baro wayar sirrinta a saman bed wangalam ba sakayawa ta yi waje abinta.... Toh fah, akwai fa ƙura, da alama Leesharh dai ita da kanta zata tonawa kanta asiri a wawtarta da shiriritarta. Fitowa haɗaɗɗen parlourn nasu ta yi, yadda part na masu aikin gidan yake ma sai ya baka sha'awa, parlourn ne haɗaɗɗe mai cike da komai na more rayuwa, sai bedroom manya manya guda huɗu a cikin parlourn a hawa na farko kenan, a na biyun ma hakan ne har karshe, so ƴan aikin da suke hawa na farko suna amfani da part ɗin, ƴan aiki na hawa na biyu ma haka, in da Leesharh zata yi aiki shi ne ainahin family part, in da ɗakin barcinsu da komai da komai nasu yake kenan, to masu aiki uku ne kacal a wajen, da Leesharh ta zo yanzu sun zamana su huɗu, Fadila da Radia ƴan mata ne da a shekaru ma zasu iya zuwa mate, sai kuma babbar su wadda take kamar matsayin uwa a garesu, ita kam bazawarece wadda a kallah zata kai shekaru 40 haka a duniya, ita take kula da su da kuma aikin da suke yi idan ya yi kyau, sannan tana ɗaya daga cikin masu yin girki a gidan, a hawa na ƙasa ake yin girki ba'a family part ɗin ba, dan Ummie ta ce bata buƙatar kamshin ingredients komai ƙanƙantarsa a hawan nasu, dan haka ba za'ayi amfani da kitchen na part ɗin ba, sai dai ayi girkin a kasa a ɗauko a hauro da shi sama a jere masu a saman table, haka tsarin gidan yake, suna da tsari sosai da sosai, kuma a kan tsarin suke tafiya. So kowani hawa ƴan aiki huɗu ake ɗauka kamar yadda part ɗinsu yake ɗauke da bedroom guda huɗu. Leesharh tana fitowa ta ci karo da su Fadila suna kallo Arabians film a makeken Tvnsu da yake a cikin parlourn nasu. Sannu ta yi masu, Fadila ce ta miƙe ta karɓi trayn kayan abincin daga hannunta tare da ce mata ga waje ta zauna mana. Okey kawai ta amsa da shi tare da nufar saman sofa ta zauna, ita kuma Fadila ta yi waje da kayan abincin. Shiru ta yi bata yi magana ba, Radia ce ta ce "Ke baki yin magana ne? Gaki kyakkyawa". Ƙasa kaɗan ta ɗan yi da kanta kafin ta amsa da tana yi. Kasancewar muryarta baya fita sosai yasa Radia bata iya gane me ta faɗa ba, sai kawai ta mayar da kallonta a Tv da suke kallah. Ko a iya kan masu aikin gidan kawai ya isa yasa ku fahimci shi Abu Abdussalam bin Badeen shugaba ne adali, duba kuga yadda masu aikin suke shanawarsu, idan sun kammala aikinsu suna da damar zuwa part ɗinsu su yi wanka su sha kwalliya kamar ƴan gida, su kunna Tv da Ac su samu waje su zauna suna kallo. Akwai emergency phone a gidan ta ko'ina wadda duk wanda yake buƙatar wani abin daga wajen wata ƴar aiki koma a hawa na nawa yake zai iya kiran emergency phone ɗin nan, cikin ƙanƙanin lokaci masu aikin zasu bayyana su kawo mashi abin da yake buƙata, sam Abu Abdussalam bai ƙasƙantar da ƴan aikinsa dake a ƙarƙashinsa kamar yadda saura suke yi ba, ya basu jin daɗi da hutu suma kamar ƴaƴa, har sun dai'na jin kansu a matsayin ƴaƴan talakawa marasa gata, ga shi a duk karshen shekara yana basu dama su je ganin iyayensu bayan ya cikasu da alkhairai dayawa, zai basu abubuwa da dama su kaiwa iyayen nasu, a kaisu da mota a kuma dawo da su, ita ma Ummie ta kara masu, Sharifat da Omar ma wato Guyson ba'a barsu a baya ba, suma in dai masu aiki zasu je ganin gida sai sun basu kyauta mai tarin yawa su ce su kaiwa ƴan uwansu, Sharifat yarinyar kirki, haka zalika shi ma Omar ɗin Gimbiya Zunaira, yana da kirki shiyasa suke shiri da Sharifat sosai, duk gidan su biyun nan ne suke shiri sosai, bayan shi Sharifat bata shiri da kowa, ko sauran brothers ɗin nata, dan basu wasa da ita, kallo ma bata ishesu ba, amma fa suna bala'in kaunarta over, kawai dai basu wasa da ita ɗin ne. Fadila ce ta dawo cikin parlourn baki a ɗauke da sallama, ta kai kayan abincin cikin kitchen ne ta dawo. "A'isha muje ki ga yadda abubuwa da kuma dokokin gidan suke ko? Daga nan sai na nuna maki parlourn da zaki yi aiki a ciki". Da mamaki Leesharh ta ce. "Dama ba'a parlourn da muka shiga ɗazun zan yi aiki ba?". Kallonta da kyau Fadila ta yi tana mamakin yadda take magana, ta ji voice ɗinta baya fita sosai, abin sai ya bata mamaki. Amma sai bata ce komai a kan yanayin maganar tata ba. Sai ta ce. "Wannan parlourn ai na hutawar Ummie ne, ainahin babban parlourn gidan mai ɗauke da part na kowani ɗan gida yana gaba dana Ummie, muje zaki gani". Ba musu ta miƙe, Fadila ta ɗan yi gaba kaɗan ta na ce da Radia ko zata zo su je ne. Sai kun dawo Radia ta yi mata alamar ba zata je ba kenan. Fitowa suka yi Fadila tana nuna mata komai daki daki tare da yi mata bayanin yadda komai yake dallah dallah. Sosai Leesharh ta kasa kunne take naɗan komai da ake gaya mata tare da hanyoyin da suke bi. A haka har suka isa izuwa babban parlourn, sai dai sun ɗan sha tafiya sosai daga part ɗinsu zuwa parlourn, sannan ne suka isa. Ai a nan ne Leesharh ta zama cikakkiyar ƴar kauye sosai, ko a film bata taɓa ganin parlourn mai girma da haɗuwar wannan ba, gari guda, ya haɗiye sofa set kala kala har set biyar, ya ƙawatu iya ƙawatuwa kamar parlourn shugaban ƙasa. A nan ne part ɗin kowane ɗan gida yake wadda shi ma akwai ɗan madaidaicin parlourn a cikinsa kafin sleeping room ɗinsu. Ganin yadda Leesharh ta saki baki tana karewa parlourn kallo ne yasa Fadila ta ɗan yi dariya kaɗan kafin ta ce. "A'isha wannan parlourn zaki rinƙa gyarawa, amma ba ke kaɗai bane, Ummie ta gaya mun ke kaɗai ba zaki iya ba, ta ce na rinƙa tayaki, sai kuma part ɗin Aunty Sharifat wanda ga shi can shi ne na tsakiya, na Guyson shi ne a kusa da nata, su ne zaki rinƙa gyarawa ke kaɗai, parlourn kuma zamu gyara a tare". Jinjina mata kai kawai Leesharh ta iya yi, amma ta kasa yin magana, haɗuwar wannan parlourn ya ruɗar da ita. Ta yi shiru tana kalle kalle ne can idanunta suka hango mata wani katafaren frame na hoto, yana da girma frame ɗin, an ƙawata shi ya yi kyau sosai. Wani irin zaro idanu waje sosai Leesharh ɗin ta yi a lokacin da idanunta suka sauka a kan hoton da yake a jikin frame ɗin, a hanzarce ta runtse idanunta ta sake warosu a kan hoton. Sam Fadila bata lura da yanayin da Leesharh ɗin ta shiga na ganin wannan hoto ba, hankalinta ita yana can kan yi mata bayanin lokutan da zata yi aiki, bata san Leesharh kam bata a tare da ita ba. Hoton wani kyakkyawan matashi ne number ɗaya, kyakkyawa ne sosai ɗan wanka, ya sha wanka da idan ka gansa sai ka so ka sake ganinsa, ya fita iya fita a hoton, kamar ka kirasa ya amsa, kansa na sunkuye a ƙasa ya ɗago da dara daran fararen idanunsa, yanayin smooth skin ɗinsa kamar madara, dark black arab hairnsa kamar wadda aka kifawa hula har gaban goshinsa, yana da ɗan ƙaramin lips sosai, hasken fatarsa tasa launin lips ɗinsa ya kara fitowa sosai, a shekaru ba zai wuce 15 to 16 years ba, ya sanya wata ƙatuwar Bluetooth a kunne, da alama dai ɗan gayun ne na gasken gaske, ko kaki ko kaso daga ganinsa kasan ya ci sunan da suke kiransa da shi wato Guyson, dan fa guy ɗin ne da gaske. So ita Leesharh ba wai kyansa ne ya ruɗata ko kuma wankar daya ɗauka ba, dukka ba wannan ba, abin da ya ruɗa ta shi ne yanayin kamaninsa, tabbas yana kama da wancan matashin da ta gani a gidansu masu nukaf wanda ya je ranar, duk da bata sami damar ganin face ɗinsa da kyau ba kasancewar kansa na kallon ƙasa, amma tabbas a yadda Guyson ya duƙar da kansa ƙasa tare da ɗago waɗan nan kyawawan idanun nasa ba makawa sun yi yanayi da wancan guy ɗin, tabbas sun yi mata kama, wannan shi ne abin da ya ruɗar da ita. Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye tare da fara tunanin wanene ma Guyson ɗin nan tukun nan? Idan har da gaske ne abin da idanunta suka gaya mata na yanayin kamanceceniya a tsakanin Guyson da wancan matashi hakan na nufin kenan already dama makashin Ramish yana nan a tare da shi? Ko dai yaya abin yake ne? To amma idan har makashin nasa yana a tare da shi meyasa za'a turota leƙen asirin motsinsa? Kai ina hakan ba zai yi wu ba. Wani tunanin ta sake yi a kan to anya wancan matashin da ya je gidansu mai nikaf ɗin nan yasan da abin da suke shiryawa kuwa? To wannan wani irin al'amari mai bala'in rikitarwa ne?. Ya ilahi ya lilliahi, shi ne abin da Leesharh ta furta a cikin zuciyarta tare da dafe kanta da yake yi mata barazanar tarwatsewa. Sai magana Fadila take ta yi mata, amma ina ko kalma ɗaya bai shiga mata cikin kunnenta ba. Haka Fadila ta gama surutun bayanan nata abanza, ta ce su tafi. Ta yi maganar tare da wucewa gaba. Ganin tana tafiya ne yasa Leesharh ta rufa mata baya, yadda kuka san wadda kwai ya fashewa a ciki haka take jan kafafunta, duk jikinta ya yi sanyi, sai tunani take yi a kan masu nikaf ɗin nan, faɗi take yi a cikin ranta anya masu nikaf ɗin nan basu da wata alaƙa da wannan gida kuwa? Anya ba ƴan uwan juna bane?. Nima dai PRINCESS TEEMA an jefani a cikin ruɗani, dan haka bari na bar part ɗin su Leesharh ɗin nan kada su sanya ƙwaƙwalwata ta tarwatse, bari na je na sha Maltina mai sanyi sannan na leƙa mana su Kamran, wata kila kafin na dawo ƙwaƙwalwata zata ɗan huta na samu na cigaba da kwaso maku labarai a kan Leesharh tamu... Amma dai akwai cakwakiya ba kaɗan ba!. 🏞️FOREST🏞️ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 14/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________35🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼 🏞️FOREST🏞️ A zaune suke wajen ƙoramar nan, Kamran yana zaune a saman dutse mai ɗan faɗi ita kuma Pretty tana tsaye a bayansa tana ta famar yamutsa mashi kyakkywar gashin kansa, sai busa mai daɗi yake yi masu da abin busarsa. Sweetie kuma tana cikin raminsu tana barci, bata fito ba yau, ta ce zata kwanta ta huta. Kayan sakar da ya kawo masu Pretty ta sanya a jikinta, ta yi matuƙar kyau over, sai ta zama kamar wata ƴar tsana a cikin kayan, ta kara zama ƴar karama da ita, kamar dai kullum kyakkywar dark black curly hairnta a ɗaure kashi biyu, ta saki jelar gashin har bayanta, sket ɗin kayan ya tsaya mata a iya gwiwarta. Sai watsa mashi gashin kansa take yi kamar an aiketa, wai zata ɗaure mashi irin yadda mum ɗinsu take ɗaure masu nasu, haka take ɗaurewa Sweetie ma nata, to shi ne wai shi ma zata ɗaura mashi nasa. Ta yi mamakin ganin yadda gashin nasa yake da yawa bakin kirin da shi, ya yi baki sosai kamar tata. Sai fama take yi, gashin ya fi karfin ƴan hannayenta, shi kuwa sai busa yake yi masu. Da kyar ta iya samu ta raba gashin nasa gida biyu, kitsa mashi ɗayan ta fara yi, sam bai san me take ta faman yi mashi ba, shi dai har cikin ransa yana jin matuƙar daɗin wasa da gashin nasa da yake yi, dan a tunaninsa wasa da shi take yi, so hakan daɗi yake yi masa. Ita kuwa kitsa mashi su ta yi kamar yadda mummynta ta koya masu, sannan ta nannaɗe jelar gashin nasa ta cusa mashi a ƙarƙashin kitson kafin ta mayar mashi da hularsa ta rufe mashi kan nasa. A ta gabansa ta dawo ta zauna tare da kwantowa a jikinsa ta kai hannu ta karɓi abin busar. "Kawo bari na busa mana". Ta faɗa cikin sanyin murya. Ba musu ya miƙa mata, dan shi ma yana jin daɗin busar tata sosai. Hannayensa dukka biyu ya ɗaura a saman shoulders ɗinta a in da ya zuro da su ta gaba ya kara jawota jikinsa yana faɗin. "Rocky fa yana nan zuwa?". Kai abin busar ɗan bakinta ta yi tana girgiza kai, kafin ta fara busar ta ce. "Yazo nan sai na mare shi, gara mashi tun wuri yasan in da dare ta yi mashi". Cikin tsiwa ta yi maganar, dan fa ita bata kaunar Rocky, sam jininsu bai haɗu ba, har yau har gobe razana take yi idan ta ganshi. Ɗan murmushi kaɗan ya ɗan yi wadda ba za'a iya kiranta da murmushi bama, dan sam bata fito ba, sannan ya sauke hannunsa ɗaya daga saman shoulder ɗin tata izuwa saman ɗan shafaffen cikinta. "Rocky fa baya da faɗa, kece nan kike sawa yake baki tsoro". "Ko baya da faɗa bana sonsa, kuma ba zan taɓa sonsa ba". Tana kai karshen maganar ta fara busarta cikin kwarewa, a yanzu ta iya busar sosai da sosai, ga shi kala daban daban ta iya rera busar, har wani lumshe idanu suke yi daga ita har shi idan tana busa masu. Akwaita da ƙwaƙwalwa, cikin ƙanƙanin lokaci take iya koyan abu ta haddace, akwai su da baiwa twin's ɗin nan sosai. Yanzu ma tsabar daɗin busar yasa suka lumshe idanu su dukkansu, ta kara lafewa a jikinsa tana mai cigaba da busawa. Wajen ya yi shiru tsit, sai karar sautin zubar ruwa da kuma kukan tsuntsayen dake shawagi a wajen zaka ji, a hankali hankali sautin busar tata yake tashi a arear wajen, hakan ba ƙaramin daɗi da ƙawa ya yi ba, a yanzu akwai wata busa da suke yi wa junansu, wanda Kamran ɗin shi ne ya koya masu, idan suka cutsa cikin daji yawo, da wannan busar suke kiran juna, wani lokaci idan suka je yawon nasu Kamran da Sweetie suna zama a ƙarƙashin bishiya suna hira, ita kuma Pretty yawo take tafiya abinta, so idan Kamran zai nemota sai ya ciro abin busarsa ya fara busawa, idan tana kusa da shi zata mayar mashi da martanin irin wannan busar da tata abin, shi kuma zai bi sautin karar busar tata har zuwa in da take. Idan kuma ta ji shiru bata mayar mashi da martani ba to ta ɗan yi nisan zango, sai ya kara gaba har sai ya samota. Wani kyakkyawan parrot ne ya sauka a kusa da Pretty da ta lumshe idanu tana aikin busa mai kwantar da hankalin mai sauraro. Cikin dabara Kamran ya shammaceta tare da shammatar parrot ɗin ya damko shi. Tana jin alamar hakan ta yi maza ta waro idanunta waje tare kuma da dakatawa daga busar tata. Aikuwa tana yin ido biyu da wannan parrot ɗin ta fara yunƙurin miƙewa a guje dan ta bar wajen, dama Kamran yasan za'ayi hakan, shiyasa ya shammaceta ya kama parrot ɗin, yasan idan ta ji saukar shi a kusa da ita haukace mashi zata yi, kaɗan daga aikinta kenan sarkin tsoro. A hanzarce ya riƙota yana faɗin. "Zauna ki ji". Bata ankaraba sai ji suka yi parrot ɗin ya maimaita abin da Kamran ɗin ya faɗa na zauna ki ji, sai dai maganar akun bata fita sosai. Hakan na nufin akun mai magana ce, kun san akwai waɗan da basa magana, to shi wannan yana yi, sai dai maganar bata fita. Wani irin zaro idanu waje Pretty ta yi na jin yadda wannan Parrot ɗin ya maimaita maganar Kamran, waɗan nan olive eyes ɗin nata kamar zasu faɗo kasa saboda zarosu da ta yi, cike tab da mamaki ta ce. "Kamran magana fa na ji ya yi......" Ai bata kammala rufe ɗan bakin nan nata ba Parrot ɗin ya maimaita abin da ta faɗa na cewa Kamran magana fa na ji ya yi, still dai maganar bata fita sosai, amma ana iya gane me ya ce. "Na shiga ukuna, Kamran dama tsuntsaye suna magana ne?...." "Na shiga ukuna, Kamran dama tsuntsaye suna magana ne?......" Parrot ɗin ya maimaita abin da ta faɗa. Ina ai a dubu ɗari ta yunƙura zata tashi, dan ita bata taɓa ji ko gani ba, ta dai san dabbobi basa magana. Kamran dai sai kallonta yake yi, dama da gangan ya kama parrot ɗin, dan kawai ta sanya shi yin nishaɗi, yana jin matuƙar nishaɗi idan yana kallon wannan kyakkyawar face ɗin tata cikin tsoro, idan ta tsorata ba ƙaramin kyau take karawa ba, sai ma ta zaro idanun nan nata, sai ka ji kamar ka yi ta kallonta kada ka gaji, hakan yasa wani lokaci har Allah Allah yake yi ta tsorata ya kalleta da kyau yana nishaɗi. Kara janyota jikinsa ya yi tare da matso mata da parrot ɗin kusa da ita, ƙasa ƙasa ya fara yi mata magana bayan ya ɗan sunkuyo da kansa a dab da kyakkyawan razanannen face ɗin tata. "Tsuntsaye basa magana Pretty, amma shi parrot yana magana sosai ma, kada ki ji tsoro babu abin da zai yi maki". Yana maganar yana kallon face ɗinta. Ai kuwa yana rufe ɗan bakinsa Parrot ɗin ya maimaita abin da ya faɗa mata shi ma. Sanya idanunta cikin nasa ta yi da kyau. Calmly ta ce. "Kenan ba aljani bane?". Yadda ta yi maganar a kusa da shi sosai hakan yasa sai da ya ji wani iri, ga shi kuma ta yi maganar tana zaro mashi waɗan nan dara daran idanun nata masu rikitar da shi, sannan tana magana kyakkyawan lips ɗinta yana ɗan kerma, dan already ta rigada ta razana tun farko. Kafeta da idanu ya yi ya kasa iya bata amsa, shi kaɗan yasan a wani hali yake shiga a duk lokacin da zata yi magana kusa da kusa da shi har haka, bare ace maganar ta haɗu da tana cikin firgici ta yi sa tana zaro idanun nan, ai abin ba'a magana. "Kuma ba zai cinyeni ba Kamran?". Ta sake jefa mashi tambaya tana mai cigaba da zaro idanun nata alamar mamaki abin ya bata. Sam bai san lokacin da ya saki parrot ɗin nan ya tashi sama abinsa ba, ya luluƙa duniyar sama jannati na kallon ƴar diramarsa. Ganin ya saki tsuntsun ne yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ƙara shigewa jikinsa tana hamdala ga Allah daya sanya Parrot ɗin bai cinyeta ba. Sam bata lura da duniyar tunani da kuma kallonta da Kamran ɗin ya afka ba. Ita dai da ta ga ya saki parrot ɗin ya tashi sama sai ta juya ta cigaba da busar da take yi. Wannan shi ne yana yi bata san yana yi ba, ita dai babu ruwanta da wani abu wai soyayya, yo Allah na tuba dama nawa take? Ga rashin nutsuwa a tattare da ita, ita kanta Sweetie nutsatsiyar ma yaushe ta san menene soyayya bare wata Pretty, ai ita Pretty bata da wata damuwa a rayuwarta da ya wuce ta ci abinci, ta yi wanka ta kuma yi sallah, dan suna yin sallah a kan lokaci kam, kuma da rana suke auna lokaci, wani lokaci kuma da yanayin garin suke auna lokaci kamar yadda mum ɗinsu ta koya masu, bayan sallah kuma shikenan sai Kamran ya kaita yawo, iya abin da ta sani a duniyarta kenan ƴar albarka. Sweetie ita ce mai zama ta yi tunani a kan gobensu da kuma makomarsu, wani lokaci har tana gayawa Kamran cewa tana ji a jikinta tabbas wannan dajin ba iya shi kaɗai bane a duniya, akwai wani waje, sannan shi ma wajen tana ganin kamar mutane suna rayuwa a ciki. Tun Kamran baya wani ɗaukar maganganunta da mahimmanci har abin ta fara shiga zuciyarsa shi ma, hakan yasa shi ma ya fara tunanin ƙure wannan dajin a wajen tafiya ko zai iya ganin makamancin abin da Sweetien take hangowa na wasu mutane da suke rayuwa a duniya........ Tirƙashi, lallai Sweetie tana son ɓallowa Mamma ruwa, dan kuwa idan ya fita wannan dajin dai kunsan zai haɗu da mutane, idan kuma ya haɗu da mutane ku da kanku readers kun san labarin dole ya canza salo, dan kuwa ba karamar dirama zasu buga shi da Mamma ba, idan ma ya dawo a kan lokaci kenan, akwai fa cakwakiya idan har Kamran ya yarda da wannan hasashe na Sweetie, zai iya cewa ma Mamma munafurtarsa take yi ta ki gaya mashi bayan wannan dajin akwai wata rayuwa ta daban, kuma ina da tabbacin zai ce ba zai cigaba da zama a wannan daji ba, dan kowa dai baya son wahala sai dole, bare shi da yake bai yi kalar ƴan kauye masu duhun kai ba, da wayonsa da kuma iliminsa dai'dai gwargwado, kunga kuwa ai dole zai so canjin rayuwa, akwai cakwakiya, Sweetie ta zo da wata al'amari mai girman gaske wanda zai iya tarwatsa zuciyar Mamma, domin kuwa da ni da ku dukka mun san Mamma bata da kowa a duniya sama da Kamran, tana kaunarsa fiye da yadda take son kanta, kuna dai ganin yadda take kula da shi, ko nan da can bata son taga ya matsa, ace rana tsaka ya fita cikin wannan dajin, sannan ya dawo ya ce mata shi ba zai sake zama a nan ba wajen mutane zai tafi ya yi rayuwa? Kuna tunanin zuciyarta ba zai tarwatse ba? Hmmmm akwai case!. "Pretty". Ya ambaci sunanta a hankali, ƙasa ƙasa kuma a ta cikin kunnuwanta. Dakatawa da yin busar ta yi tare da juyowa gare shi. "Kamran lafiya ka kirani?". Ta yi tambayar tana riƙo hannayensa dukka biyu. Abin busar ta sanya mashi a hannunsa ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ta ɗaura shi a saman a shoulder ɗinta ta ɗan kwanto a saman kirjinsa. "Pretty kin san menene soyayya?". Tana daga kwance a jikinsa ta ce. "A'a ban sani ba, shima wani kalar abincin na Mammarka ko kuma fruits ne?". Ta yi maganar ba tare da ta ɗago ta kalle shi ba, tana kwance tana ganin zubar ruwar ƙorama abinta. Ajiyar zuciya ya sauke, jiya wuni zunbur ya yi yana bincike cikin littatafan Mammarsa ba tare da sanin Mammar ba, a nan ne ya ci karo da wata littafi mai suna true love never end, da yake litattafin bata da yawa sosai, short story ne da bata wuci pepar ashirin ba, sai ya nutsu ya karanta, a nan ne ya samu abubuwa da dama har amsarsa na dan gane da aure, kasancewar a littafin ya karanta duk wahalar da jaruma da jarumin suka sha daga karshe sun yi aure sun mallaki juna, kuma sun haifi ƴaƴa, a nan ne ya fara tunanin kenan shi ma dai yana da baba? Ba iya mama bace kawai?. Ya dai samu abubuwa da dama a ciki littafin, ya kuma yi masu kyakkyawar fahimta, ya kuma tarawa kansa uban tarin tambayoyin da ƙwaƙwalwarsa take ƙoƙarin kasa ɗauka, ya kasa iya tambayar Mammarsa ina babansa? Ya kasa iya gaya mata labarin su Pretty, ya kuma rasa ta ina zai iya sanar da ita cewa an bashi auren Pretty, kuma da ya karanta wannan littafin ya fahimci yana son yarinyar nan Pretty, kuma zai aureta ɗin kamar yadda mum ɗinta ta bashi aurenta, duk ya kasa samun kwarin gwiwar iya sanar da mamma komai, ya shiga damuwa na wuce misali, sai saƙa da warwara yake yi na yadda zai ɓullowa da Mamma ta bashi amsoshinsa a kan waɗan nan al'amura. Lallai akwai cakwakiya, finally ga shi dai Kamran yasan menene aure da ma ita kanta soyayyar, sannan kuma yasan cewa yanzu mace bata haihuwa ita kaɗai, har ya fara tunanin to shi ina nasa uban? Ga wani sabon cakwakiya kuma da Sweetie ta matsa mashi a kan su kurewa dajin nan tafiya ko akwai wasu mutane a wajen dajin, dan ita bata yarda da cewa suma warriors ɗin nan a cikin dajin nan suke ba. To Kamran fans ya kuke tunanin makomar Mamma idan har Kamran ya fita daga cikin wannan dajin yaga akwai mutane a wajen? Anya zai sake yarda ya zauna a dajin kuwa? Anya zai iya yin hakuri ya danne ba tare da ya buƙaci sanin ina mahaifinsa yake ba kuwa? One day one time da wuya idan bai tambayi Mamma da ta fito mashi da babansa ba, duk da yanzu yana tsoron tambayarta, amma dakamar wuya ya iya hakuri da babansa... Tashin hankali kenan, babbar magana!!. Forest ma ya kusa kamawa da wuta da alama!. "Pretty soyayya ba abinci bane sarkin son cin abinci, kuma soyayya ba kayan fruits bane, wani abin ne na daban". Ya bata amsa ta hanyar raɗa mata a kunne. Jin cewa ba abinci bane kuma ba kayan fruits bane soyayya yasa ta yi saurin ɗago da kanta daga saman kirjin nasa ta juyo garesa. "To menene kenan?". Yadda ta ɗago da kan nata sai ya zama suna fuskantar juna. Tsura mata ido ya yi yana kallonta, tun da ya fahimci sonta yake yi sai ya dai'na jin wani irin yanayi tare da fargabar kallon cikin idonta, sai ya zamana ma idan bai kalli cikin idanun nata ba sam baya jin daɗi. "Ya kake ta kallona haka Kamran? Na ce maka menene soyayyar baka bani amsa ba? Wajen yawo ne to? Ko dai wasu dabbobin ne?". A hankali ya motsa kyawawan lips ɗinsa ya furta. "Kece soyayyar mana". Kyafta idanunta sau biyu ta yi tare da sakar mashi wani irin cool murmushi mai kara mata matuƙar kyau, har dimples ɗinta suka lotsa. "Kai kam Kamran wani lokaci ka iya maganar banza, ni ce soyayya kuma? To ni dai sunana Pretty ba soyayya ba". Tun daga yanayin maganar Pretty zaka fahimci duk wanda zai auri wannan yarinya yana ruwa kusa da kada, sai ya shirya shanye duk wani shirmenta har Allah ya gyara mashi ita, ko da yake yarinta ne sosai a kanta, ƴar shekara goma zuwa shaɗaya nawa take dama? Ai yarinya ce sosai. Da yake shi Kamran ya saba da halin kayarsa, sai ya ɗan matso da face nasa dab da tata, ƙasa ƙasa kamar mai tsoron wani kada ya jisu ya ce. "Ai ban ce maki sunanki ne soyayya ba bare ki ce mun sunanki Pretty, duba idonta a wajen kamar na raƙumin dawa". Da yake ba'a yi mata ta kyale sai da ɓallah mashi harara tare da faɗin. "Ai garani ma idon Raƙumin dawa ce da ni, kai kuma idonka kamar na wannan Rocky ɗin naka". Ta kai karshen maganar tana kara ɓallah mashi harara. Murmushi kaɗan ya ɗan sakar mata kafin ya ce. "Na ji to, yanzu dai koma menene ki sani dai ina sonki". Shiru ta ɗan yi, sai yanzu kalmar ina sonki ya fara dawo mata a cikin ƙwaƙwalwata, mum ɗinsu tana yawan gaya masu cewa ina sonku ƴaƴana, kune duniyata kuma kune komai nawa, ina alfarhari daku kuma ina son yin rayuwa da ku, na kasance da ku na kuma kula da ku, na baku tarbiya irin ta addinin Musulunci na kuma baku ilimin addini dana zamani, ina kaunarku fiye da yadda nake son kai'na. Sosai maganganun mum ɗinta suka rinƙa yi mata zarya a cikin kunnuwanta zuwa ƙwaƙwalwarta, kenan yanzu shi ma Kamran irin son da yake yi mata kenan? Irin son da mum ɗinsu take yi mata? Ganin ta luluƙa duniyar tunani ne yasa ya kai hannunsa ya ɗan shafi lallausan kumatunta haɗe da dogon kyakkyawar hancinta da ya zauna ɗas a face ɗinta. "Kema kina sona ko?". Ya faɗa a hankali. Kara kallon cikin kwayar idanunsa da kyau ta yi kafin ta ce. "Ni ban san menene ma'anar kalmar ina sonki ba, mum ɗinmu tana faɗa mana shi, so ni ban san me take nufi ba". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fara yi mata bayanin menene soyayya kamar yadda ya karanta a wancan littafin, sai dai ya ɓoye mata menene aure da kuma ganowa da ya yi cewa suna da iyaye maza, dukka ya ɓoye mata wannan, saboda a ƙananun shekarun nan nata ba fahimtar komai zata yi ba, sai dai ta kara tabka mashi shirme, dan haka sai ya yi mata bayanin abin da zata gane kawai cikin sauki. Ɗan taɓe baki ta yi a lokacin da ya gama yi mata bayanin menene soyayyar. "Dama wannan ce soyayya? To ai ina sonka nima". Ta bashi amsa tana kallon cikin idonsa. Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗi da sakar mata cool murmushi mai matukar kyau, ya ji daɗi sosai. Tabbas kamar yadda ta faɗa tana son shi haka ne, tana son shi amma ba kamar yadda shi yake sonta ba, kunsan kowace zuciya tana son mai kyautata mata, to hakance, dole zasu so Kamran sosai, dan a yanzu shi ne komai nasu. Cigaba da hirarsu mai shegen daɗi a tsakaninsu suka yi, yana kara fahimtar da ita yadda soyayya take, ta wani kasa kunne tana ɗaukan bayanai, ita kuwa Sweetie tana can tana barci abinta, ba ruwanta da hayaniya. Sun jima a haka kafin nan ya ce mata zai koma gida ta tashi ya rakata wajen maɓoyarsu da yamma zai dawo su sha hira da soyayyarsu. Sam bata so tafiyarsa ba, kawai dan ba yadda zata yi ne, tana matuƙar jin daɗin kasancewa da shi, idan ya ce zai koma har ji take yi kamar ta yi kuka ko kuma ta bi bayansa su tafi a tare, amma ba hali. Haka ta miƙe tana turo baki, sai hakuri yake bata, har da goyata a bayansa ya yi izuwa wajen bakin ramin nasu, duk dan baya son ganin fushinta, duk dan ya lallaɓata ta yi farinciki kafin su rabu. Da kyar ya iya sakata dariya kafin su rabu, sai da ta yi dariya mai sauti ma tukun nan, sannan ya ce ta shiga ciki kuma kada ta yarda ta tashi Sweetie daga barci, sannan kada ta sake fitowa waje sai ya dawo da yamma. Da okey kawai ta amsa mashi kafin ta sa kai ta wuce ciki. Shi kuma bayan ya tabbatar da ya rufesu da kyau sai ya nufi gida. A bakin kofar shiga ƙogonsu ya ci karo da Rocky dake ta faman barci, da alama ya ci ya ƙoshi ne, wucewa ciki ya yi izuwa cikin ɗakinsa. Ga mamakinsa sai ya isko Mammarsa a cikin ɗakin nasa tana yi mashi bincike. Bai nuna mata ya yi mamakin hakan ba, ya wuce kawai ya haye saman gadonsa yana faɗin. "Mamma sannu da hutawa ina abincina?". Zuba mashi idanu sosai ta yi na ƴan sakanni kafin ta ce. "Kamran cire hular kankan nan bari na gani". Da yake ya manta shap da zancen cewa Pretty ta yi mashi kitso, sai bai wani damu ba, yana kallon face ɗin mammar tasa ya cire hular. Kun san fa idan mutun ya yi kitso koma ya take sai face ɗinsa ta ɗan canza, shi ne yasa Mamma ta iya ganewa, kuma da yake taga wannan uban tulin gashin nasa da idan ya sanya hula take cika hular duk ta ɓace, hakan yasa ta fahimci an taɓa mashi gashin, shi yasa ta ce ya cire hular ta gani, sam bata kawowa ranta cewa kitso ma aka yi mashi ba, ta dai fi tunanin cewa shi ne ya datse gashin nasa ya zubar. Zaro idanu waje ta yi sosai tana kallon kitso guda biyun, tun da take da shi ko da sunan wasa bata taɓa yi mashi kitso ba, bata taɓa kwatanta yin kitso bama, dan ita gashin kanta baya kitsuwa saboda tsantsi, to a ina kuma ya samo kitso? Tasan dai ba shi ya yi wa kansa ba, dan bai iya ba. Shi kuwa ganin yadda ta zaro idanun nan nata tana kallon kan nasa ne yasa ya yi saurin kai hannunsa saman gashin nasa dan ya ji menene ya sanyata zaro idanu haka?. Ai bai san lokacin da ya miƙe tsaye a dubu ba time da ya ji kumbusa kumbusar kitson da rigimammiyarsa Pretty ta yi mashi. Yau ya shiga uku! Wani amsa zai bawa Mamma kenan? Me zai ce yau kuma? Ya mance da kitson ne da tun a hanya zai warwareta........ (Kamran fans yau ba zata yi maku ta daɗi ba😅 baku da amsar da zaku bawa Mamma, kuna tsaka mai wuya, Pretty ta kai ku ta baroku 😅 ku daɗi soyayya ba? To yau zaku ga soyayya kuwa😅) Readers me kuke tunanin Mamma zata ce mashi? Wani action zata ɗauka? Shi ma wani action zai ɗauka dan kare kansa kada a raba shi da Pretty? Ga shi ya bayyanawa Pretty ɗin soyayyarsa, ya kenan zata kaya?. To ni dai bari na leƙa KINGDOM OF POWER na dawo, wata kila kafin nan Kamran ya samowa kansa mafita. 𝗞𝗜𝗡𝗚𝗗𝗢𝗠 𝗢𝗙 𝗣𝗢𝗪𝗘𝗥💪🔥 Haɗe gabakiɗaya family suke a saman dining table dake dining room ɗinsu na part ɗin King. Kuyanga Zubaida ta yi serving ɗinsu, cikin nutsuwa suke cin abincin nasu. Kowa yana saman table ɗin amma banda Yah Jawad, Yah Jaish and Gimbiya Chuchu dake cikin part ɗin Akka, taki fitowa, Akka ta fito daning room ta barta kwance a saman gado, wai sai anjuma kaɗan zata sha complex or coffee ko dai wani abin mara nauyi, dan bata jin yunwa a yanzu. Obaid and Omaid duk suna a saman haɗaɗɗiyar dining table ɗin, abincinsu kawai suke ci cikin natsuwa, sai ka rantse da Allah babu su a cikin room ɗin, auta duk ta damu na rashin ganin gimbiya Chuchu a room ɗin, ita kuma Sarina sai faman hararar Aneesa take yi sarakai waɗan da basa shiri, sai mayar mata da martanin hararar Aneesa ɗin ma take yi. Obaid and Omaid dai har yanzu suna nan suna shirya kalar azabar da za su yi wa Mama, basu janye wannan kuduri nasu ba. King ne ya ɗan yi gyaran murya tare da fara yin magana kamar haka. "Omar dai uncle Abu Abdussalam ya ce ba zai dawo this week ba, na yi na yi amma ya ce wlh na fita idonsa na bar mashi guyson ɗinsa ya kara mashi hutun koda na one month ne kafin ya dawo ya cigaba da karatu, so mummynsa sai ki yi hakuri da shirya mashi walimar sai next month, ku kuma Obaid and Omaid sai next week zaku koma, dama saboda Omar zai dawo ne yasa na yarda zaku koma, to tunda an sake riƙe mun shi nima bari na sake riƙeku a nan kaɗan tun da ma ku baku koma school ba, ke kuma Sarina ina son ki mayar da hankalinki da kyau, kada na kara ji ko ganin wani bako ya zo wajenki, nasa a saki su Yusuf bayan Zafar ya horasu da kyau". Ya kai karshen maganar yana kallon Mommar Zunaira. Momma ɗin dai bata ce komai ba, domin yayanta ne Abu Abdussalam ɗin, kuma shi ya hana Omar dawowa, ya zata yi da ya wuce ta yi shiru, bata da ta cewa, ita kuma mummy sai cewa ta yi. "Kai gaskiya uncle Abu Abdussalam ya yi hakuri ya bar nana Guyson ɗin mu ya dawo, muna kewarsa sosai fa". Mama ce ta wani ɓalle masu kallon banza tare da turɓene fuska kamar wadda taga wani abin kyamar. "Daddy please ka barni mana na je wajen su Uncle ɗin, ba sai mu dawo a tare da Yah Omar ɗin ba". Cewar auta, ta yi maganar tana turo baki. "Wani zuwa kuma bayan an buɗe school?" King ya bata amsa. Turo baki kawai ta yi, ta ji babu daɗi, tun kafin a buɗe makaranta take ta son zuwa, amma aka hanata. "Bari na dubo Aunty Chuchu". Cewar autar, ta yi maganar tare da miƙewa ta nufi hanyar fita daga room ɗin. Sauri sauri ta yi ta fita dan ma kada daddyn nata ya ce ta zawo sai sun ƙarisa cin abinci, dan Akka ta gaya mashi cewa Chuchu ta ce tana ƙoshe bata jin yunwa da ya tambaya. Kai tsaye part ɗin Akka ta nufa, dan tasan a can zata sameta, bata jin daɗi ne a duk lokacin da take waje ba tare da Chuchu ba, sun yi matukar shaƙuwa. Ta zo wucewa ta part ɗin Yah Jaish ne Yah Jawad ya fito daga ciki, bayan ya yi sallolin da suke a kansa ne ya yi wanka ya yi shirin barci sai ya nufi part ɗin Jaish kamar yadda suka saba, a nan suka ci abincin dare suka ɗan yi hira kaɗan, kasancewar yana da aikin da zai yi sosai shi ma kuma Jaish ɗin akwai wani bincike da yake yi a kan wata ma'aikata da suke zargin tana haɗa kwayoyin cuta da kwayoyin magunguna na shan al'umma, suna watsa cutar ta wannan hanyar, a matsayinsa na babban ɗan jarida ya kuma samu information sosai a kan ma'aikatan, shi ne yake ƙoƙarin bincikarsu ya tabbatar da abin da jama'a suke zargin gaskiya ce kafin ya fitar da bayanan, wannan dalilin yasa yau suka yi sallama da juna da wuri, saboda duk suna da tulin aiki a gabansu. Yana fitowa suka ci karo da auta. "Good evening Yah Jawad". Ta faɗa tana ƙoƙarin wucesa. "Zunaira ina zaki je kike sauri haka? And then ban hanaku yawo da kayan barci babu hijabi haka a cikin gidan nan ba?". Dakatawa ta yi daga tafiyar da take yi, ɗan turo baki kaɗan ta yi kafin ta ce. "Kayi hakuri ba zan sake ba, na manta ne". Shiru ya ɗan yi mata na ƴan sakani kafin ya ce. "To ina zaki je haka?". "Wajen Aunty Chuchu zan je, bata zo dining room bane, tana part ɗin Akka, shi ne zan je in dubota". Ta bashi amsa. "Idan kin je ki ce ta zo ina son ganinta, ta same ni a part ɗina". Yana kai karshen maganar yasa kai ya wuce abinsa. Ita ma cikin sauri ta wuce izuwa wajen elevatorn da zai kaita part ɗin Akka. Kwance ta isko Chuchu a saman bed, tana sanye cikin kayan barci riga da dogon wando masu kyau launin maroon color, kayan barcin yana da hula mai kyan gaske, so ta sanya hular a kanta, sai latsa wayar Akka take yi dan Yah Jawad ya kwace mata nata wayar idan baku manta ba. Saman bed ɗin auta ta haye tare da cewa. "Aunty Chuchu shi ne baki nemeni ba ko? To Yah Jawad yana kiranki". Zaro idanu waje Chuchu ta yi tare da miƙewa zaune. "Nashiga ukuna! Me kuma na sake aikatawa Yah Jawad da yake nemana?! Ni wlh Allah sai na kai shi kara wajen daddy in dai ya sake bani punishment, kuma sai na gayawa Akka ma, na gaji da shan wannan bakin azaba, haba wai ni kaɗai ce a gidan?". Cikin tsiwa ta yi maganar. Kwanciya ita dai auta ta yi tare da jawo pillow ta rungume haɗe da karɓar wayar Akka dake hannun Gimbiya Chuchun, sannan ta ce. "Allah ni ban san meyasa Aunty Chuchu kike ganin laifin Yah Jawad ba, yana da saukin kai fa, kuma yana da kirki". Duka ta kaiwa autar a baki tana faɗin. "Tun wuri ki yi istigifari, dan Yah Jawad kam sam bai bi hanyar da saukin kai ya bi ba, mugu ne na karshe, kuma wlh sai na gayawa uncle Abbas duk muguntar da ya yi mun, Allah har na fara tsanarsa sosai, amma fa kada ki gayawa kowa na ce na tsanesa fa". Hannu auta ta kai ta toshe ɗan bakinta da shi tare da zaro idanu waje. "Yah Jawad ɗin kika tsana Aunty Chuchu? Yayan mu ne fa, innalillahi". Tana magana tana zaro idanu!. "Ke zaki yi mun shiru ne ko dai kina gaya mun yayan mu ne? To ni dai bana son shi, mugu ne, kuma idan kika faɗawa wani ko wata nace hakan daga yau mun bata". Girgiza kai auta ta fara yi tana faɗin. "Ba zan gayawa kowa ba, amma dan Allah Aunty Chuchu ki dai'na cewa kin tsanesa, please, wlh ni bana son jin wannan kalma". Ƙoƙarin sauka kasa daga saman bed ɗin ta yi tana faɗin. "Zan daina faɗa, amma dai ba zan cire tsanarsa a rai'na ba, sai ya yi ta azabtar da mutane dan mugunta, Allah bari na je na amsa kiransa, idan ya bani wata punishment ɗin kamar a gaban uncle Abbas aka yi, sai na gaya mashi, kuma in gayawa Akka da daddy dukka". Tana kai karshen maganar ta sauko kasa, sai turo baki take yi ta nufi waje, haushi yasa ta manta da cewa kayan barci ne a jikinta kuma bata ɗauki hijabi ba, haka ta nufi part ɗinsa tana kunkuni a cikin ranta, sai faɗi take in dai ya ci zalinta yau to wlh sai ta kai kararsa wajen uncle Abbas, sai dai ya yi duk abin da zai yi mata mugu kawai. Bakinta a ɗauke da sallama ta shigo part ɗin nasa. Daga jin yadda ta yi sallamar kasan a ƙule take da bakinciki har wuya. Babu kowa a parlourn, kuyangu masu yi mashi gyara ma sun kammala aikinsu sun fice. Kai tsaye bedroom ɗinsa ta nufa. Ƙasa ƙasa ta yi sallama tare da tura kofar ta shiga ba tare da jira izininsa ba, dan ita fa haushin da take ji yasa ta manta ma a ina take tukun nan, sai kunkuni take yi tana tsine mashi a cikin ranta. Yana zaune a saman bed ɗinsa, ya tasa laptop a gaba yana aiki a kan aikin da King ya ba wa Companynsa na gina gidan marayu, aikin yake ta fama da shi. Ta wutsiyar idanunsa ya kalleta. Wani irin bakinciki da kishi ne ya taso mashi, hakan yasa ya ɗaure fuska sosai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa, yauma da kayan barci ta fito kenan? Ya.................. Lokacin shan Maltina ta yi🥱 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 15/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________36🔥 Yana zaune a saman bed ɗinsa, ya tasa laptop a gaba yana aiki a kan aikin da King ya ba wa Companynsa na gina gidan marayu, aikin yake ta fama da shi. Ta wutsiyar idanunsa ya kalleta. Wani irin bakinciki da kishi ne ya taso mashi, hakan yasa ya ɗaure fuska sosai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa, yauma da kayan barci ta fito kenan? Ya tambayi kansa da kansa a cikin zuciyarsa. Ita kuwa gabansa ta nufo, sam bata tuna komai ba. A ɗan nesa da shi kaɗan ta tsaya tare da cewa. "Yah Jawad gani nan". Tamkar bai san da shigowarta room ɗin ba, aikin gabansa kawai ya cigaba da yi, sai dai kuma a zahirin gaskiya ya kasa yin aikin dai'dai saboda ɓacin rai, hankalinsa kuma yana kanta, tunanin kalar hukuncin da zai yi mata kawai yake yi. Ta jima a tsaye a wajen almost 10 mins bai ko ɗaga idanu ya kalleta ba, aikinsa kawai yake yi na latsa laptop ɗin buge dan kada ta gane hankalinsa baya a kan aikin. "Yah Jawad in ta fi ne?". Ta yi maganar kamar zata fasa kuka, saboda ta gaji da tsayuwa, ta ga bashi da niyar kulata, kuma yau ta sha alwashin wlh ba zata tsaya a cuceta ba, idan ya ce ta yi kneel down ko makamancin haka to wlh guduwa wajen Akka zata yi, sai dai ya bita can ya kakkaryata idan yana so...... Lallai Chuchu ta fara girma, abin ya fara kureta........😅 Sai da suka kara good 5 mins a haka kafin nan ya ɗan ture laptop ɗin daga gabansa izuwa gefensa, ba tare da ya ɗago ya kalli in da take ba ya ce. "Zo nan ki yi mun kneel down, domin yau sai na koya maki hankali sosai, ke kunnanki baya jin magana ko Jannat? To yau zai fara jin magana dole........" Bai gama rufe baki ba ta watsa a guje zata nufi waje, dama ta ce wlh ba wani hukuncinsa da zata karɓa yau, yana yin yunkurin hukuntata zata gudu, aikuwa sai ga shi ta ruga a guje zata yi waje. Wani irin miƙewa ya yi babu shiri, dan yasan idan ya barta ta gudu ya shiga tara da Akka na farko, na biyu kuma bai ga dalilin da zai sanya yana yi mata magana zata gudu ba, a cikin kannen nasu ma fa ita da auta sune kanana, amma tsabar ta rai'na shi ne yana magana zata gudu? Lallai yau dole ta ci duka, ba ma zai yiwu ya barta ta gudu ba ai, dole ya kamota ta karɓi hukuncin dama bai taɓa yi ma kowa daga cikin kannen nasu ba, ko Sarina da take sarkin rashin ji yau hukuncin da zai yi wa Chuchu bai taɓa yi wa Sarina ɗin ba, sannan ya ja mata kunne a kan idan ta gayawa Akka ko uncles Abbas sai ya karairayata........ (Ku ji mun mugunta, a dakeka a hanaka kuka, ya azabtar da ita kuma ya ce kada ta gayawa kowa🤔 Allah Yah Jawad ma mugu ne) Bata kai ga isa kofar ɗakin ba ya damkota ta baya, duk da tasan cewa ko ta yi ihu babu wanda zai iya jinta a cikin gidan, saboda ainahin kofar shiga part ɗin nasa ma a rufe, tana shiga kofar ta rufe, ga shi izuwa yanzu tasan kowa ya rufe kofofin part ɗinsa, koda bama haka ba yanayin tsarin ginin gidan mawuyacin abu ne tana cikin wani part ta yi ihu a jita a wajen, hakan ba zai yi ba. Amma duk da haka hakan bai hana ta waje baki zata kurma mashi ihu ba, domin ta tsarorata da kamota da ya yi, bata yi tsammanin zai yi yunƙurin bin bayanta har ma ya kamata ba, ta yi tunanin zata iya tsira ne ma yasa ta fara gudun, tasan ba komai yake kulawa ba, so a tunaninta idan ta gudu ma zai kyaleta ya ce wata kila da safe zai kamata, amma sai ta ji an damkota ta baya, shi ne abin ya razanata da har yasa ta waje baki da karfin gaske zata zunduma ihu, ga tsoron kalar hukuncin da zai yi mata, yanzu ma bata gudu ba ma ya ce ta yi kneel down bare kuma ya ce ta yi ta ki yi zata gudu? Ai ita da kanta tasan hukunci ya karu sosai!. Ina duk da yasan ba wani jin ihun nata family zasu yi ba, amma bai bari ta yi shi ba, tana waje ɗan bakin yasa hannu ya toshe mata bakin nata, ransa ya sosu matuƙa, duk cikin sisters ɗinsu babu wanda ya taɓa yi mashi makamancin abin da ta yi mashi, bai san cewa idan ka cina takurawa mutun dama ya kansa ya rage tsoronka idan ma yana ji ba, takura mata da yake yi ne yasa ta rage jin tsoronsa da har ma take kiransa da mugu, yanzu da Yah Jaish ne ya kirata ai ko yankata yake yi ba zata tsallake abin da ya ce ba, saboda me? Saboda da ni da ku dukka mun san Yah Jaish dai ba wanda ya ishe shi kallo a cikin kannen nasa, baya kulasu kuma baya bi da kansu, kunga kuwa dole a ji shakkarsa sosai, shi ma dai Yah Jawad ɗin chuchu kawai ya sakawa ido, kuma dani da ku duk mun san dalilinsa na yin hakan. "Stay quiet, if not a cikin daren nan zan kakkaryaki na zubar da kasusuwanki a dustbin". Ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar, ya kuma kai karshen maganar tare da zame hannunsa daga saman ɗan bakin nata. Wani irin kermar tsoro jikinta ya fara yi, danasanin abin da ta aikata ta fara yi, yau dai ta shiga uku ta lalace, haka take ta faɗi a cikin ranta. Saketa ya yi tare da juyo da ita suna fuskantar juna, sannan ya kai hannunsa ya damko wannan arab hair ɗin nata, saboda hular kanta ya cire tun lokacin da ta watsa a guje zata yi waje, so sai ya zamana babu ɗankwali a kan nata, hakan ya bashi damar damko mata kyakkyawar gashinta da ta ɗaure shi kashi biyu. Da karfi ya danki gashin nata tare da jan shi baya sosai, hakan yasa dan dole babu shiri sai da ta ɗago kanta sama, wani irin azaba ne ta ji ya ziyarceta lokaci guda. "Kin girma ko Jannat? Har inai maki magana zaki gudu ko?". Kai ta fara girgiza mashi ba bakin yin magana, sai wasu zafafan hawayen azaba da suka cika mata idanu, kan ka ce me sun fara wanke mata fuska, amma fa a cikin ranta faɗi take yi wlh yana sakinta sai ta sake watsawa a guje, kuma yau ba sai gobe ba sai ta gayawa uncle Abbas muguntar da yake yi masu ita da su Sarina, sannan zata gayawa Akka da daddy, wlh ba zata hakura da kudurinta na gaya masu ba, ko dan su samu sassauci a kan irin cin zalinsu da yake yi, duk sai ta ji ta kara tsanarsa sosai. "Zaki yi mun shiru ne ko sai na ɗauko belt?". Ya yi maganar yana kai kallonsa izuwa saman bed ɗinsa, wayarsa ce take kara alamar shigowar kira. Kara jan mata gashi baya ya yi da ƙarfi, tare da dawo da kallonsa a kanta. Ba komai ne yake kona mashi rai ba face fitowa da kayan barci da ta yi, kishi ne kawai yake cinsa a zuciya yasa yake azabtar da ita har haka. Izuwa yanzu shi da kansa ya fahimci cewa tabbas uncle Abbas gaskiya yake gaya mashi na cewa yana son Jannat, domin kuwa idan har baya sonta ba zai yi kishinta har haka ba, wannan kishi ya wuce na yaya da kanwa sai dai mata da miji, kuma ba zai rinƙa damuwa da son ya ganta har haka ba, yanzu da yasa auta ta kirata a fili idan ta zo dama wayarta zai bata, a zahirin abin da yake cikin zuciyarsa kuma ba wayar yake son bata ba, ganinta yake son yi, dan yana kewarta, shi ne gaskiya!!. Amma kuma shi fa wai a haka so yake ya cire son nata a ransa, saboda a cewarsa ita ɗin sistersa ce kawai, kuma ta yi ƙanƙantar da zai iya cewa yana so, bugu da kari ba zai iya jawa kansa rai'ni na cewa zai aureta ba, idan ya yi haka ai yagama da kansa, ya jawa kansa rai'ni, shi ne yasa tun farko yake kaucewa yaki yarda da cewa yana sonta, dan bai son rai'ni, yanzu kuma da ya fahimci hakan yake ƙoƙarin cire son nata a ransa. Akwai cakwakiya ga Mammie ɗinsa ma kun dai ji bata kaunar wannan haɗin, uncle Abbas kuma fatansa kenan, wai ma to meyasa Mammien bata son haɗin Jawad ɗin da Chuchun? Akwai dai wata a ƙasa gaskiya. Kasa iya yi mashi shirun ta yi, sai ma kara karfin gudu hawayen nata suka yi, sakamakon ya kara ja mata gashi kanta baya, zafi ya karu, dan haka ita ma sai ta kara kukan nata. Har cikin ransa yake jin zafin wannan kuka da take yi kamar yadda ita kuma take jin zafin jan mata gashin da yake yi. Ya yi iya kar yinsa, ya yi mata iya barazanar da zai yi mata akan ta yi shiru amma taki, bashi da zaɓin da ya wuce ya sakin mata gashi idan har yana son ta yi shiru, zuciyarsa ba zata iya jurar ganin kukan nata ba, dan haka sai ya zame hannunsa daga kan nata tare da gyara tsayuwarsa da nufin ya fara magana, ya gaya mata kalar hukuncin da zai yi mata a yau, dan ba zai barta ba. Ai kuwa yana saketa ta sake watsawa a guje ta nufi waje. Ba shiri ya sake rufa mata baya a karo na biyu. Tana fitowa parlourn ya damkota, da hannu ɗaya ya ɗagata sama, ɗayan hannunsa kuma yasa ya toshe mata baki saboda waje bakin da ta yi zata zunduma mashi ihu. Kai tsaye sai saman carpet dake a gaban bed ɗinsa ya sauketa, wani irin ɗaure fuska sosai ya yi kamar hadari, tamkar bai taɓa sanin me ake kira da murmushi ba. Tsawa ya daka mata a kan ta zube gwiwowinta a kasa ko kuka ya karairayata a cikin daren nan, ashe abin nata har ya kai haka? Dole ya yi mata hukunci mai zafi tun da rai'ni ya fara shiga tsakaninsu, irin wannan rai'nin yake gudu yasa yaki yarda da yana sonta yake kuma ƙoƙarin yin patali da soyayyar tata daga cikin zuciyarsa, sai ga shi tun ma bai bayyana mata yana son nata ba, tun bai bayyana wa kowa bama rainin ta fara shiga tsakaninsu, dole ya ɗauki mataki!. Jikinta na kerma ta zube gwiwowinta a ƙasa tana mai cigaba da yin kukanta. Remote na door room ɗinsa ya ɗauka ya rufe kofar mai gabaɗaya, yau ba ita babu fita kenan, sannan ya wuce dressing room ɗinsa ya ɗauko ɗaya daga cikin belt ɗinsa mai mugun zafi yadda kuka san da gaske zai iya zaneta ɗin, ya wani ɗaure fuska irin babu wasan nan, bai san shi so ba'a kawo mashi wargi ba, ba ruwansa da shekaru ko girma, in dai ya shiga zuciya to sai ya yi pata pata da duk wasu dokoki ko matakan da mutun yasawa kansa, so ai bashi da adalci wani lokaci, sai ya kaika ga son wadda kai da kanka kasan ka kusa haifarta, dan bala'i ya barka ka yi ta fama kana ɗawainiya, to wannan irin shi ne a tsakanin Yah Jawad dan Aunty Chuchunmu fashion babynmu ƴar wanka. Yo ko dan shegen iya ɗaukar wankarki da iya gayu, ki yi gayu ya zauna a jikinki kamar dan ke aka yi ba dole ma Yah Jawad ya sarara maki ba, dole ba zai iya jure wuni bai sanyaki a idanunsa ba, irin wannan haɗuwa da kike yi, ga zuba kamshi kamar me, duk wasu perfume na Momma ke da auta sai kun bi kun karar mata, ai dole ki sanya zuciyar bawan Allah cikin tunaninki kullum da ko yaushe, dole ya rinƙa fakewa da kwace maki waya dan ya rinƙa sami damar ganinki, shiyasa yake zuwa part na Akka wai ya je duba Akkar da ba shiri suke yi ba, ba wani nan mun san komai ke yake zuwa gani, me zai yi da ganin fuskar Akka da daddare fisabilillahi? Salon ya yi mafarkin wannan masifaffitar tsohuwar? Gimbiyarsa yake zuwa gani ya fake da Akka, to yanzu dai mu kam mu gano komai ato, sai dai ya ɓoyewa su daddy, Momma, mummy, Mammiensa, da kuma su Jaish, amma ba dai ya ɓoyewa PRINCESS TEEMA da tawagarta ba ko my people's? Ba zai ɓoye mana komai ba!. A bakin bed ɗin ya dawo ya zauna ta yadda suna fuskantar juna. Ganin shi da belt a hannu yasa ta ƙara ruɗewa sosai, nan take jikinta ya kara tsananta kerman da yake yi. A hanzarce ta kai hannu ta riƙo kyawawan fararen tafukansa ta wajen gwiwowinsa, kuka mai sauti ta fashe mashi da shi tana faɗin. "Dan girman Allah Yah Jawad kada ka dakeni, ba zan sake ba, wlh na duba, bana son duka, last week ma da uncle a school ya mun bulala ɗaya a hannu Allah sai da hannuna ya kumbura, wlh tsoron duka nake ji, ba zan sake ba, ka bani wani punishment ɗin amma banda duka, wayyo Allah Momma na na shiga uku, uncle Abbas kazo ka ceceni". Tana yin magana tare da ƙara ƙanƙame kafafun nasa sosai, tana kuma tsananta kukan da take yi. Zafi sosai zuciyarsa take yi mashi na jin kukan nata, amma a maimakon ya rarrasheta ta yi shiru, sai ya jefa mata tambaya kamar haka. "Me kika yi wa uncle ɗin naku ya dakeki? Kuma wani uncle ɗin naku ne?". Tana kuka sosai kamar ranta zai fita, dan ita harga Allah bata son zancen duka, tun da take ma a makaranta ne kawai aka taɓa dukanta, muguwar tsoron duka take ji, "Babu abin da na yi mashi, ƴan class ne suna ta surutu shi ne ya zo ya haɗe mu gabaɗaya ya yi mana bulala ɗai ɗai". Ta bashi amsa tana ɗan kwantar da kanta a saman kafafun nasa, domin zafi wuyarta yake yi mata, ta ci kuka sosai, sannan ga jan mata gashi da ya yi yasa ta ɗage wuyarsa sama da har ya kusa sagewa a haka, so zafi yake yi mata da ba zata iya jurar cigaba da ɗaga shi ba. Wani irin yanayi ya tsinci kansa a ciki, abubuwan sun haɗe mashi, ga kukanta da yake taɓa mashi zuciya, ga kishin ta fito da kayan barci a gefe, sannan ga ɓacin ran uncle nasu ya dakar mashi ita, ta wani bangaren kuma ba haushin abin da ta yi mashi na yana magana ta watsa a guje, yanzu kuma ta kwantar mashi da kanta a jikinsa, duk sai ya ji wasu damuwar sun ragun mashi ma.......🙄 Muryarta ne ya dagi dodan kunnuwarsa cikin kuka take faɗin. "Yah Jawad na tuba ba zan sake ba, dan Allah kada ka dakeni, na yi alkawarin ba zan sake ɗin ba". Bai san lokacin da ya sassauta muryarsa a gareta ƙasa ƙasa ya ce. "Sau nawa kike ce mun ba zaki sake ba kuma ki sake kara yin abin da na hanaki ɗin Jannat?". Kara kwantar da kanta da kyau a saman kafafun nasa ta yi, tana shessheƙar kuka hawaye na zuba ta fara magana da kyar da kyar. "Yanzu da gaske nake yi ba zan sake ba, wlh na tuba......" "Kenan da can baya duk ba da gaske kike yi ba ko?". Ya katseta ta hanyar jefa mata wannan tambayar. Girgiza mashi kai ta shiga yi tare da kara ƙanƙame kafafun nasa ta shiga bashi hakuri. "A'a dukka da gaske nake yi, amma wannan shi ne babban da gaske, ba zan sake ba........". (Oho Allah Chuchu kenan, wai shi me babban da gaske 😅 to my people's kun dai ji babbar da gaske 😅) "Kina saka mun ciwon kai sosai Jannat". Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya, zuciyar tasa ta ɗan yi sanyi a yanzu. "In Sha Allah ba zan sake saka maka ciwon kai ba, na tuba". "Promise?". Ya faɗa kamar mai yi mata raɗa. Da sauri ta gyara mashi kai alamar e ta yi alkawari. (Ni dai na ce Allah yasa wannan alkawari ta ɗaure, dan Chuchu da ɗaukar hoto sai Allah, ga shegen mantuwa) Hannu ya kai saman dark black arab hairnta, a hankali yake shafa kan nata ya furta. "My God bless you my lovely sister". Ɗan ɗago kanta ta yi a hankali dan ta saci kallonsa, ta ji yadda ya yi maganar ne alamar ya huce, har wani sanyi ita ma ga ji a ranta na jin abin da ya faɗa na Allah ya yi mata albarka, yanzu kenan ba zai bugeta ba? Amma abin ya yi mata matuƙar daɗi sosai. Shiru suka ɗan yi kowannensu da abin da yake tunani, sai shafa kyakkyawar arab hairnta yake yi. Kasancewar ta ci kuka sosai hakan yasa barci ya fara ƙoƙarin ɗaukarta a wajen, saboda sun yi shiru suna tunani, ita tana jiran ta ji me zai sake ce mata, shi kuma ya luluƙa wata duniya ta daban. A haka har barci ya ɗauketa, bai ankara ba sai ji ya yi tana ƙoƙarin salalewa ƙasa saboda barci. Cikin hanzari yasa hannunsa dake saman gashin kanta ya tallabota tare da ɗan kura mata ido yana mamakin yadda barci ya ɗauketa cikin ƙanƙanin lokaci haka. Ganin yadda face ɗinta ya yi jajir da shi, abin ku da farar fata, ta sha kuka fuska ya yi jaga jaga da hawaye ya kuma yi jajir da shi, duk sai ya ji babu daɗi, sai ya ji sam bai kyauta mata ba. Ƙasa ƙasa ya furta "Am so so sorry my sister". Ya yi maganar ta yadda koda idanunta biyu ma ba zata ji me ya faɗa ba, dan ƙasa ƙasa sosai ya yi ta. Hannunsa ya kai saman ƙuncin nata ya ɗan shafo ruwan hawayen nata kaɗan a yatsunsa, nisawa ya yi tare da miƙewa tsaye, cak ya ɗauketa ya saɓa a shoulder ɗinsa. Remote ya ɗauko ya buɗe kofar room ɗin. Mutsu mutsu ta fara yi mashi alamar tana son farkawa, amma da yake barci ya sha kanta sosai ga kuma kukan da ta sha hakan yasa ta saƙalo wuyarsa da hannunta ɗaya tare da kara kwantar da kanta a saman shoulders ɗin nasa. Yana jinta a haka ya nufi room ɗinta da ita. Babu kowa a room ɗin, kuyangu sun gyare ko'ina tsab, da yake ita ƴar son kamshi ce over, sai ya zamana kamshin room ɗinta ma ya fita daban da nasu Sarina, ita a wajen Mommar Zunaira take ɗauko perfume na jiki da na ɗaki, momma kuma kunsan daga Dubai ake kawo mata komai nata, so yana da daɗin kamshi sosai, shi kansa Jawad ɗin da ya shaki kamshin sai da ya ji hankalinsa ta kara kwanciya ta wani fannin, ta wani fannin kuma hankalinsa a tashe yake, fannin kamshin room ɗin dai lafiya lou ne, kamshin ta yi mashi daɗi over, sai dai sauran fannin kuma sai a hankali. Ita fa Chuchu kullum kuyangun nan sai sun gyara mata room ɗinta, su zuba turaruka kala kala, amma yarinyar nan sai ta fi kwana uku bata kwana a cikin room ɗin, tana can wajen Akka, ko Momman Zunaira, ko kuma dai ɗakin Zunairan, bata cika zuwa wajen mummynta bama sai jefi jefi, na gaya maku sun fi sabawa da Momman Zunaira dama, idan baka sani bama sai ka ce ai Momma ita ce ta haifeta ba mummy ba. Saman haɗaɗɗen bed ɗinta dake shinfiɗe da shinfiɗa ta alfarma ya shinfiɗeta, sai sauke ajiyar zuciya take yi, ƴar kaniya ta ci kuka har ta ƙoshi. Zuba mata idanu sosai ya yi yana kare mata kallo from head to toe. A nan ne ya kalli ta yi mashi girma da yake renata kullum, kawar da kallonsa daga jikinta ya yi izuwa saman kyakkyawar face ɗinta. Shi kaɗai kome ya tuna sai ya ɗan yi wani guntun murmushi tare da kai hannu ya janyo duv ya lulluɓeta da shi, sannan ya ɗan duƙo da jikinsa izuwa dai'dai saitin face ɗinta. Can kasan maƙoshinsa ya furta. "You're so cute, very very beautiful my sister and my wife to be In Sha Allah". (Wato shi Yah Jawad ya mance da cewa Mammiensa ta daka mashi warning a kan babu shi babu Chuchu ko?🤔 Har da wani cewa my wife to be In Sha Allah, zaka ga wife kuwa, dan Mammie dai ta fika bala'i ato, ga shi ita ma Chuchun ba sonka take yi ba, hasalima duk cikin brothers ɗinta kai ta tsana bata so sosai, mu dai ana yi muna shan Maltina mai sanyi.) Ya kai karshen maganar tasa tare da kai hannu ya goge mata hawayen da yake a saman face ɗinta, ji yake yi mamar ya sumbaci lallausan kumatun nan nata, amma kuma ba zai iya yin hakan ba, yana cikin yanayi haka ya miƙe tsaye tare da ɗaukar remote ya rage mata gudun Ac sosai, sannan ya zauna a saman bedside drawer ya hau kwaranyo mata karatun addu'oin barci da bata samu damar yi ba barci ya yi mata shigar sauri. Tsab ya kammala addu'ar ya tofa a hannunsa, lokacin da ya zo zai shafa mata addu'ar a jikinta sai hannunsa ta fara kerma, kamar mai tsoron taɓata, kamar kuma wadda yake tsoron wani abin a jikinta. Haka dai ya kai hannu ya shafa mata addu'ar from head to toe, amma fa ya ji a jikinsa kam. Miƙewa ya yi da sauri ya nufi wajen switch, kashe wutar room ɗin ya yi tare da nufar waje ya janyo mata ƙofa. Yana ɗan matsawa daga saitin kofar tata da nufin ya tafi part ɗinsa sai ga King sun ci karo, yana sanye da farar jallabiya mai bala'in kyau sosai, ga arab hairn nan nasa ba'a magana, tana kwance har gaban goshinsa, sai sheki wannan kyakkyawar gemu da sajen nasa suke yi. Dama idan baku manta ba King fa kafin ya kwanta ya yi barci sai ya bi ƴan'matan nan nasa dukka ya duba ya suka kwanta? Ya tabbatar da suna cikin aminci, sannan ya yi masu addu'a ya koma part ɗinsa. Zubawa Yah Jawad waɗan nan idanuwan nasa King ɗin ya yi, bai ce da shi ko uppan ba, shi kuwa Yah Jawad sai ya wani sunkuyar da kai yana ƴan kame kame kamar wani mara gaskiya. A hankali ya ɗago ido dan ya saci kallon King ɗin, sai ya kalli still dai kallonsa King yake yi, da suka haɗa ido ma sai King ya ɗaga mashi gera guda alama ya aka yi ne, abin gwanin ban dariya. "Kai daddy to me kuma na yi?". Ya faɗa yana ɗan murmushi. "Ashe kenan ka yi laifin tun da har kake tambayar me ka yi, me ka zo yi a room ɗin ƴata cikin daren nan?". Ya yi maganar yana ɗaga mashi gera guda. "Kai daddy wai ba sisters ta bace ba? Ni fa kun saka mun ido a gidan nan". Yana kai karshen maganar yasa kai yana son zullewa King ɗin. Yasan halin daddyn nasu sarai, yanzu zai saka shi faɗar abin da bai yi niya ba, King ya iya basaja sosai, ya fi uncle Abbas kaifin ƙwaƙwalwa, yanzu zai yi maka dabara ka faɗi magana ba tare da kasan ka faɗeta ba, yanzu dai kunga da ido kawai ya tsare Yah Jawad amma har ya ruɗe ta yadda ya ce shi bai yi laifin komai ba, kunga kuwa babu rami me ya kawo maganar rami? Ya yi laifin kenan, shiyasa dukkansu basu cika son yin doguwar hira da King ɗin ba sam sam, cikin ruwan sanyi yake kamasu a hannu, bare ma Jaish da yake shiru shiru, duk shiru shirunsa King yana iya buga cikinsa yasa shi yin magana ba tare da yasan ya yi ba. "Zonan, ai ban sallameka ba". King ya faɗa. "Kai daddy barci fa nake ji, Allah kafara ko? To ni yanzu ma wai me na yi?". "Sai ka gaya mun me ya kawoka room ɗin ƴata, and kuma ka gaya mun wai ma a naira nawa ne kullum kake kalle mun yarinya? Ka biya Abbas sadakinta ne? Ko dai kawai a free kake kalle mun ita?". "Kai daddy kai daddy kai ko, zaka fara kenan ko?, to ni yanzu yaushe ma na kalleta? Ni ina ga zuwa zan yi na koma Dubai, kawai kun saka mun ido a gidan nan". Yana magana kuma yana ɓoye fuska, dan baya son su haɗa ido da King ɗin, yasan idan suka haɗa ido sai ya yi dariya. Shi kuwa King ya tsaresa da kallo sosai yana faɗin. "A'a ba abin da ya haɗaka da ita, ai kasan yanzu ma ba kai na kama a room ɗinta ba, kai Jawad Allah ku kuyayeni". "To shikenan daddy na yarda ni aka kama a room ɗinta, amma to ni da sister ta? Dan nazo wajenta kawai sai ace mun wani abu, addu'ar barci to na zo yi mata ba shikenan ba?". Yana kai karshen maganar ya ɗago ido tare da sauke kallonsa a kan King ɗin. Wani irin kallo da King ke wurga mashi ne yasa bai san lokacin da murmushi ta kubce mashi ba, dama yasan sai dai idan ba su haɗa ido ba, sai ya saka shi dariya, irin kallon da King ɗin yake yi mashi irin kallo ne na e ba shakka addu'a kam ka yi mata naga zahiriyya. "Kai daddy wai kallon fa?". Yana magana yana murmushi. "Kai daddy haka kake yi, sai ka tsare mutun da kallo har kasa ya yi karya". Ko sannu dai King bai sake cewa ba bayan ido da ya tsare shi da shi tare da ɗaga mashi gera guda sama. "To ni yanzu daddy in tafi tun da na gaya maka gaskiyar abin da ya kawoni, addu'a nazo na yi mata, kuma yanzu ma room ɗin auta zan je na yi mata nata addu'ar kafin na wuce nawa room ɗin na kwanta". Shi da kansa fa yasan maganar da ya faɗa ɗin nan ba yarda da shi King ya yi ba, amma ya zage sai ƙoƙarin yiwa maganar tasa kwaskwarima yake yi. "Ba shakka Jawad da kai da Jaish na kusa aurar da ku a gidan nan, dan na gaji da ganin abubuwa kala kala". King ya faɗa yana karewa Jawad ɗin kallo from head to toe, dama da kallo ɗaya zaka yi mashi idan kana da hankali zaka faminci yana cikin yanayi, bare kuma shi King da dama already dole ya gane cewa Yah Jawad fa to sai dai shiru. "To wai daddy fisabilillahi me muka yi kuma? Shi Jaish ma yana da budurwa ce da zaka yi mashi aure? Allah daddy mu fa......" Sai kuma ya yi shiru. "Idan Jaish bashi da budurwa kai kam ba kana da ita ba? Shi ma kuma kwanan nan zan je Dubai na samo mashi mata, na gaji da ganinku tsakar dare kuna yi mun yawo kun kasa barci". "Wai daddy ko su Yah Rizwan fa basu yi aure ba sai mu? Gaskiya a'a ka bari dai idan suka yi aure sai mu duba mu gani idan zamu iya, kuma ma wai daddy mu munce maka rashin samun barci ne yake fito damu tsakar dare? Kawai fa shan iska muke fitowa yi, sai mu ɗan lelleƙa mu gani ko akwai wanda bai yi barci ba a gidan, kaga tsaron kannanmu muke yi". "E haka ne babu shakka, to zo ka wuce na ji bayananka, ka jira nawa kuma, yanzu zaku yi tsaro da tushe". King ya faɗa tare da wucewa zai shiga room ɗin Chuchu. "Daddy to wani mataki zaka ɗauka ne wai?". Ya tambayesa a ƙage, dan yasan halin King ƙaramin aikinsa ne da safe suji wata zancen da basu yi tsammani ba. "Good night son ka yi addu'a kafin ka kwanta, babu ruwan ka da matakin da zan ɗauka". Yana kai karshen maganar ya shige cikin room ɗin. "Kai daddy Allah ka iya jefa mutun cikin tunani, to yanzu wai wani mataki zaka ɗauka a kan mu kuma?". Ya tambayi kansa tare da sa kai ya wuce izuwa nasa part ɗin. Yana shiga ya haye saman bed ɗinsa tare da jawo bargo mai laushi ya shige ciki, sannan ya kashe wutar ɗakin ta hanyar amfani da remote, ya ɗaura hannayensa ɗaya a saman cikinsa, ɗayan kuma a saman fuskarsa, nan take tunanin Gimbiya Chuchu ya faɗo mashi cikin ransa, yadda take kwance take sharara barcin nan kawai yake hangowa, da alama dai yanzu ma sai ya yi mafarkinta, dama yaya lafiyar kura bare ace ta yi zawo?. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ Idan kuma koma ɓangaren su Kamran kuwa wato Forest. 🏞️FOREST🏞️ "Kamran me nake ganin a kan nan naka haka?". Mamma ta faɗa tana ɗaure fuska sosai, domin bata taɓa zaton ganin kitso a kansa ba. Shiru ya ɗan yi yana tunanin me zai ce mata ya tsira? Yau dai bashi da mafita gaskiya. "Kamran am i not talking to you? What's this I said?". Kame kame ya fara yi, tsabar ruɗewa ma har in'ina ya fara yi a magana. "Mamma i don't know, kuma ni ban san ta ya aka yi ya zo kai'na ba, and Mamma please don't ash me any questions again now, am feeling to much of hungry, and my Head is penning me". Yadda yake maganar rashin gaskiya ce ƙarara ta bayyana a tattare da shi, ya yi wani tsuru tsuru da shi. "Kamran am i your mate?". Girgiza mata kai ya yi alamar a'a yana faɗin. "Sorry Mamma". "Na yi maka kalar wadda zaka yi wasa da hankalinta?". Nan ma girgiza mata kai ya yi alamar a'a. "Okey now tell me who did this thing to you? Dan nasan dai kai kam baka iya ba". Wani irin tsoro ne ya kamashi, yasan da cewa tabbas idan tasan da su Pretty sai ta rabasu babu makawa, shi kuma har ga Allah ba zai iya rabuwa da su ba, gara ta kashe shi kawai ta huta da ta rabasu, sun zamar mashi wani ɓari na rayuwarsa. Har wani zufar tsoro ce take tsastsafo mashi, duk ya ruɗe ya rasa abin faɗa. Voice ɗinta ne ya katse shi da cewa. "I'm waiting for your amsa ne fa Kamran". Ɗago da idanuwansa izuwa kanta ya yi, sannan ya koma bakin bed ɗin ya zauna, ko zai mutu ba zai gaya mata ga wadda ta yi mashi wannan kitso ba, sai dai yau duk abin da zai faru ya faru. Dan haka shiru ya yi mata bai iya sake cewa ko uppan ba, yana jinta sai tambayarsa take yi, da yaga zata matsa mashi sosai ma sai ya miƙe da sauri ya nufi waje da nufin ya barmata kogon ma mai gabaɗaya. "Where are you going?". Ta jefa mashi tambaya. Ina ai bai tsaya ba, da sauri ya nufi waje irin shi ya yi fushin nan. Da sauri ita ma ta rufa mashi baya. Kusan a tare suka fito wajen kogon. Damko gashin kan nasa da karfi ta yi har sai da ya furta wash. Ai kuwa yana furta wash ɗin nan Rocky da yake kwance ya yi tsalle da nufin ya haye kanta. A hanzarce ta kauce mashi, kamar dama tasan zai aikata hakan, ko da yake tasan cewa ko ita ta taɓa Kamran Rocky baya barinta, dan yafi sabawa da Kamran ɗin sama da ita, so in dai zata taɓa shi sai ya yakusheta da waɗan nan shegun faratunan hannun nasa dake fasa fatar mutun. Ko da ta kauce mashi kuma bata saki gashin Kamran ɗin ba, kaucewar da ta yi kuma yasa ta ja mashi gashin da karfi ta yadda ya sake furta wash da karfi, hakan yasa Rockyn ya sake daka tsalle ya yi kanta da karfi a karo na biyu. A wannan karon kam dan dole ta saki Kamran ɗin tare da yin baya baya. Tana sakinsa kuma bai bi ta kanta ita da Rocky ɗin ba yasa kai ya sauka ƙasa daga saman dutsen. Sunansa ta fara kira da karfi karfi, amma ina Kamran yaki ko juyowa ya kalleta, yasan idan ba haka ya yi mata ba ba zai rabu da ita lafiya a kan su Pretty ba, yasan yanzu idan ya nuna mata ya yi fushi ya tafi wuni zunbur bai dawo ba, to da kanta zata fita nemansa, idan kuma ta nemosa lallaɓasa zata fara yi tana rarrashinsa, daga haka zata mance da zancen kitso......... (Ashe dai Kamran ma ya iya tsiya😅) To bari dai mu leƙa gidansu Khadija mu je mu dawo. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH 💔😥 Lokacin shan Maltina ta yi🥱 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 19/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________37🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH 💔😥 Duk yadda Maman Zainab ta yi tsammani abin ya wuci nan, the thing is getting out of hand, ya sha gaban tunaninta, wasa wasa dai da gaske baban Zainab ya juya mata baya, komai ya lalace mata, ga Zainab bata jin maganarta, saboda maganin Aunty Hauwa ya taɓa Zainab ɗin, amma bai taɓa Khadija ba, saboda da ni da duk mun san Khadija da Zainab akwai banbanci sosai a tsakaninsu, Zee yarinya ce, and kuma bata wani riƙo da addini kamar Khadija, bata kai Khadija ilimi ba, so ita abin ya ɗan taɓata duk da ba sosai ba, bata dai'na son mamar tata ba, amma kuma bata jin magana, ko kina yi mata magana sai ta ga damar amsawa, idan mamanta zata yi mata magana sau dubu sai lokacin da ta ga damar amsawa take amsawa, wani lokaci maman tana magana ma tana mayar mata da martani..... Abin akwai tsananin ciwo sosai. Da farko har Sadiq ya so dukanta sosai a kan hakan, sai maman ta hana shi, dan tasan ba laifin Zee ɗin bane, bama ta san tana yi ba. Duk abin da ya faru from A to Z maman Zainab ta kwashe ta gayawa Sadiq ɗin, shi kansa sai da ya ji kansa ta yi wani irin sara mashi, ya jima yana guje mata irin wannan matsala, amma sam taki yarda, duk wani abin da zai gaya mata sai ta saka kafa ta shure, yanzu yadda komai ya lalace ɗin nan ta ina zasu fara neman mafita ma tukun nan?. "Ki kira mama ki gaya mata batu a kan Zainab, watakila akwai abin da zata taimaka maki da shi". Cewar Sadiq da yake tsaye a bakin kofar parlournta, ya dawo daga school ne, ya shigo kenan ya samu tana kuka, shi ne ya je jin ba'asi, a nan ne take sanar da shi ai ga abin da ya faru duka. Haƙiƙa ya yi matuƙar tausaya mata sosai da sosai, sai dai kuma bashi da wani abin yi a yanzu face ya taya da addu'ar samun mafita. Duk ta wani uban rame kamar ba ita ba, bata cin abinci, sai idan ta ji yunwa sosai ne zaka ganta tana shan ruwan tea, ba yadda Khadija bata yi ba wajen rarrashinta, amma ina taki ta hakura, a yanzu fa shi baban Zainab yana yin kwana uku ma bai leƙo gidan ba, to a ina yake kwana kenan? Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana. Kasuwar ma baya wani zuwanta, ko maman Zainab ta tambayi Sadiq baban Zee ya je kasuwa, sai dai ya ce mata a'a, Sadiq ne mai kula da komai yanzu, shi kuma baban Zee sai a hankali, ƴan kwana biyun nan ma kamar baya garin ne gabaɗaya, domin kuwa idan da yana garin baya kwana uku huɗu haka yana zuwa ya ɗauki abin da ba'a rasa ba a room ɗinsa. Sai dai ko ya zo gidan yadda kuka san bai taɓa sanin yana da wata mata da ƴaƴa a duniya ba, ko kallon in da suke bayayi, ko maman Zainab ta yi mashi magana tamkar da mutun mutumin da aka sassaƙa take yi ba shi ba, kamar yadda bango baya magana haka shi ma baya kulata, wannan abin shi ya fi komai ɗaga mata hankali. A kowani lokaci ta kira mamarta a waya ta sanar da ita, amsa ɗaya take bata shi ne ta cigaba da yin istigifari tana tuba har izuwa lokacin da Allah zai karɓi tubanta ya dubeta da idon rahama, kuskure dai ta rigada ta tapka shi, shirka haɗa Allah dawani ai dole taga sakayya, dan haka ta yi hakuri ta cigaba da tuba tana gayawa Allah kukanta one day one time komai zai wuce In Sha Allah. Haƙiƙa maman Zee ta shiga tashin hankali na kin karawa, bare ma kuma idan ta tuna harda ƴarta Zainab abin ya shafa, wannan abin yana kara ɗaga mata hankali ta yadda take jin har wani juya mata duniya take yi, sannan ga batun aure Khadija da Haidar da yake ta kara matsowa, kun dai san ba fashi wannan aure, koda baban Zainab baya nan kuma baya a cikin hayyacinsa dole za'a ɗaura auren in ji hajiyarsa, saboda already anrigada an bawa Haidar ita, maman Zee dai a yanzu ita kam jira kawai take yi taga ranar da zuciyarta zai fashe ta mutu kowa ya huta, abin gwanin ban tausayi. Ta ce da mamarta zata dawo gida da zama, maman ta ce mata a'a kamar yadda ta zauna a ɗakin mijin nata ta ruguje komai ta lalata farincikinta dana ƴaƴanta, hakan zata zauna a yanzu ma a buga da ita ta gyara komai kamar yadda ta lalata. Wannan dalilin yasa ta hakura ta cigaba da zama. Tun daga ranar da abin ya faru bata sake saka Hauwa a idanunta ba, ta aika Sadiq gidan ya fi sau a kirga, amma ko ya je kullum gidan a rufe da kwaɗo, abin ya yi mugun ɗaure mata kai, to ina Hauwa ta tafi? Tana son samun amsa, ga shi mamarta ta ce bata yafe mata ba idan har ta sake saka kafafunta ta fita waje ba tare da izinin baban Zee ba, kuma bata yafe mata ba idan ta kuskura zata fita ta yi mashi karyar ga in da zata je ta je wani wajen na daban, domin kuwa duk shi ne ya jefata cikin wannan bala'i, fita bada izininsa ba, da ya sani ai baya bari ta je ba, yanzu ga shi tana kuka tare da danasani maras amfani. "To shikenan Sadiq, bari na kirata na gaya mata halin da ake ciki a kan Zainab ɗin". Ta bashi amsa kamar zata fasa ihu, duk ta yi wani futu futu da ita yadda kuka san ba maman Zee ƴar kwalliyar nan ba, duk ta fice daga hayyacinta. Khadijah na zaune a saman sofa a gefenta, ita kuma Zainab tana cikin dakin, ba kasafai ta cika fitowa ba a yanzu, duk kuma saboda wannan magani ne. Nasiha sosai Sadiq ɗin ya kara yi mata tare da haɗawa da Khadija da take a zaune, daga karshe ya rufe masu da cewa. "Maman Zainab dama akwai maganar da nake son mu yi dake, shi ne ma ya dawo dani ta nan, ba dan haka ba kasuwa na so wucewa tun da kinga yanzu komai ya dawo kai'na, baban Zainab baya zuwa kasuwar". Da kyar ta iya amsa mashi da. "Ina jinka Sadiq, faɗi duk abin da kake so". Nisawa ya ɗan yi tare da gyara tsayuwarsa kafin ya ce. "Maman Zainab sanin kanki ne bani da wani iko a kan su Khadija, babansu yana raye kuma danginsa ma suna raye, ni kaninki ne kawai, a halin yanzu sai dai na basu shawara a matsayina na kawunsu, ba wata magana zan gaya maki ba face na tuna maki da abin da kika manta, ki sani ke kika haifi yaran nan, duk in da za'a je a dawo kina da iko da kayanki, babu wata daga cikin ƴan uwan babansu da zata nuna maki iko a kansu, addini bai ce hakan ba, kina da damar buɗe murya ki yi magana a kansu! Ba wai zan haɗaki faɗa da ƴan uwan baban Zainab bane, amma ki sani shirunki zai iya ja maki danasani mafi girma a kan yaran nan, su suka haifa maki su ne da zasu rinƙa tsara maki ga yadda suke son rayuwar yaran ta kasan ce? Dukkansu ba mata bane? Ba suna da yara ba? Akwai wanda ya isa ya ce ga abin da zasu yi wa ƴaƴansu ne? To meyasa sai ke kawai suke tsarawa naki yaran abin da suke so? Ke kuma kin zuba masu ido kina ganinsu, ko kin manta da cewa ƴaƴa amana ce da Allah ya bawa iyaye? Ko kina tunanin idan Allah ya tambayeki meyasa kika tauyewa ƴaƴan nan naki hakkinsu idan kika ce mashi maman su Haidar ne sila shikenan sai Ubangiji ya yafe maki? To idan ma haka kike tunani kin yi kuskure, ba Maman Haidar Allah ya bawa amanar su Zainab ba, ita Maman Haidar tana da nata amanar da zata amsa tambayoyi a kansu ranar gobe ƙiyama, babu wanda zai amsa na wani, kowa nasa zai amsa, dan haka yana da kyau ki buɗe baki ki kuma tsaya komai zai faru ya faru amma ki tabbatar baki jefa rayuwar yaranki cikin kunci ba". Ɗan dagatawa ya yi da maganar yana mai da numfashi kafin kuma ya cigaba da cewa. "Khadijah bata ɓoye mun komai ba, ta gaya mun duk wani abin da Haidar yake yi mata, to ina son ki sani ni daga nawa ɓangaren na hanata tsayawa hira da Haidar, na gaya mata ko ya tsayar da ita kada ta sake kula shi dan bashi da hankali ko kaɗan, sannan na gaya mata in dai ya sake ɗaura hannunsa a jikinta to kada ta yi tunanin komai ta koya mashi hankali, na bata goyan baya da ta zabga mashi mari, nasan zai iya cewa zai daketa dan ba hankali ne da shi ba, dan haka na ce mata ko kusa ko alama kada ta tsaya ya daketa, sannan kuma kada ta sake nuna cewa tana jin tsoro ko shakkarsa, ina son ki buɗe kunnuwanki kema ki saurateni, ko a cikin parlourn nan Haidar ya zo yin hira da Khadija kada ki sake bari, kada ki yarda, ki ce mashi kin hana hirar daga yau, ya bari sai anyi auren, sannan shiru da kike yi kina zuba wa Haidar ɗin da uwarsa ido ya isa haka, ba wai na ce ki yi wa yar mijin rashin kunya bane, a'a, kada ki manta yarsa ba uwarsa bace ba, dan haka ba kowani irin takaki zata yi ki yi shiru ba, lokacin da ya dace ki yi fito na fito da su ya yi, yanzu ne yakamata ki gyara masu zama su san da cewa kema ƴa ce, kuma dan zaman aure ya kawo ki cikin familynsu ba hakan yana nufin kema naki familyn basa sonki ba, ƴa ce kamar kowa, kuma kamar yadda kowasu iyaye suke son ƴaƴansu haka kema ake sonki, dan haka yana da kyau ki mayar da hankali, a yanzu baban Zainab hankalinsa baya a kanku gabaɗaya, yanzu ne lokacin da ya dace ki taka masu birki dukkasu, ki zana masu jan layi, su shiga taitayinsu da kyau......". Sake dakatawa ya yi yana sauke ajiyar zuciya, yau ya samu ya fitar da abin da ya jima yana cinsa a cikin zuciyarsa, ya jima yana son gayawa yayar tasa da wannan shirun nata a kan ya yi yawa, amma taki bashi dama ta saurare shi, ta biyewa Hauwa a tunaninta hakan ce mafita, to Alhdulillah a yanzu dai ya samu ya fitar da abin da yake cikin cikinsa, ya huta. Bai ɓoye mata komai ba, duk abin da Haidar yake yi wa Khadijah ya sanar da ita tas, sannan ya ɗora da cewa. "Ga Khadija ɗin a zaune a gabanki, ki binciketa da kyau a iya haka abin ya tsaya ko kuma ya wuci hakan, kin tsaya biyewa Hauwa har ya zama ƴarki bata samun damar da zata iya gaya maki halin da take ciki sai dai ta zo ta sameni ta sanar da ni, kinyi kuskure babba, kuma yanzu lokacin ɗaukar mataki ne.......". Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon knocking na kofar gida da suka ji ana yi. "Khadijah je ki duba wanenen mai buga kofar nan". Cewar Maman nasu. "No ta barshi bara na dubi". Sadiq ya faɗa tare da sa kai ya nufi wajen. Shiru maman Zainab ta yi tana tunanin maganganun ɗan uwan nata, duk abin da ya faɗa zancensa haka ne, yana a kan gaskiya, tun farko ma ita ta yi masu sake, yanzu ga shi wankin hula ya kaita dare. Wani irin mamaki ne ya kama Sadiq a lokacin da ya buɗe kofar gidan, ba kowa bane yake knocking face baban Zainab a tare da Hauwa, dukkansu sun ci uwar kwalliya, ko daga ina suke haka oho dai. Sannu da zuwa Sadiq ya yi wa baban Zee ɗin yana bin Hauwa da kallo, sai wani yauki da yange take yi, tana sanye cikin shadda da ya sha ɗinki mai kyau, ko rantsuwa Sadiq ya yi ba zai yi kaffara ba wannan shadda daga shagonsu aka ɗauketa, wato kayan da baban Zainab ɗin ya kwasa ranar da ya je shagon ita ya kaiwa kenan? Sadiq ya tambayi kansa da kansa, lallai akwai cakwakiya ba kaɗan ba. Sai zuba kamshi suke yi suka nufi cikin gidan. Saboda tsabar mugunta irin na Hauwa ce ta ce sai dai baban Zainab ɗin ya rakota ta gaisa da maman Zainab, dan tana kewar kawar tata, kawai ta yi hakan ne dan ta kara kunsawa maman Zainab bakin ciki, yanzu fa Hauwa bata gidan mijinta, da alama kashe auren ta yi ko wani abu makamancin hakan, yanzu haka daga gidan kanin mahaifinta ta fito, garinsu maman Zainab kenan, ita ma Hauwa dama mahaifinta ya jima da rasuwa, ya riga baban su maman Zainab ɗin ma rasuwa, so already dama a hannun kanin mahaifin nata take, ku ma shi ba mutun ne mai karfi ba, kusan kaso saba'in na matsalolin gidansa ma Hauwar ce take ɗaukar nayinsu, shiyasa duk abin da zata yi yake ganin tana a kan dai'dai, dan yana tsoron kada ya ce bata yi dai'dai ba ta ɗauke mashi tallafi, Allah ka rabamu da mutuwar zuciya. Yanzu ta zubar da ƴaƴan nata wa dangin mijinta ta koma garinsu. Suna sako kafarsu a cikin parlourn aka sake yin knocking na kofar gidan, a lokacin shi kuma Sadiq yana ƙoƙarin shiga room ɗinsu, dan ya je ya ɗan kwanta ya huta kafin ya fita kasuwa. A dubu ɗari maman Zainab ta miƙe tsaye na ganin Hauwa a tare da baban Zainab da ta ɗauki kwanaki bata sanya shi a idanunta ba. Wani irin shu'umin murmushi Hauwa ta sakar mata tare da faɗin. "Gaskiya nayi kewarki sosai maman Zee, yau dai na ce dole baban Zee ya rakoni na zo mu gaisa, zan iya zama a kujerar taki ne?". Cike da kirsa da makirci ta yi maganar, daga jin yadda take magana kuma ba sai an faɗa ba kunsan da biyu ta yisa, ta yi ne duk domin da kara jefa zuciyar maman Zainab cikin ƙunci. Kallon baban Zainab kawai maman Zee take yi, tamkar bata san da Hauwa a wajen ba. Shi kuwa Baban Zee tamkar bai san da mama Zee ɗin a cikin parlourn ba, wucewa ya yi ya zauna a saman sofa yana faɗin. "Hauwa me ya tsayar dake a tsaye? Ki samu wuri mana ki zauna......". Yanzu fa har su Khadija ma ya mance da su bawan Allah. Bai gama rufe baki ba aka banko labulen parlourn aka shigo ciki. Ba kowa bace face su maman Haidar, dama tsawon kwanaki yau suna neman baban Zee ɗin basu samu ganinsa ba, shi ne nan suka sanya Haidar da ya saka masu ido duk idan ya ga giftawarsa ya sanar da su, sun zo gidan ya fi sau a kirga suna cin mutuncin maman Zee a kan wai ita ta hanashi zuwa wajensu, basu san ita kanta bata samu ganinsa da ido ba, amma haka suke cin mata mutunci son ransu, sai dai ta bisu da ido kawai. To yanzu kafin baban Zainab ɗin ya zo gida sai da suka fara zuwa kasuwa Hauwa ta kwashi abin da take so, sannan ne suka nufo gidan, a nan ne kuma Haidar ya gansu, shi ne ya yi maza ya sanar da mamar tasa ta hanyar kiranta a waya ya ce mata to ga baban Zainab ya nufi gidansa, shi ne suka biyo sahunsa dan su zo su ji dalilinsa na kin zuwa in da suke, su kira wayarsa ba zai ɗauka ba, ga batun aurensa da suke ta jiran ya zo ya je su gaisa da bappan nasa a samu a saka rana, ayi komai cikin ƙanƙanin lokaci, ƴar bapparsa suke son aure mashi dama, to fa shi ne suke ta nemansa amma shiru, sai yau Allah ya yi suka ji labarin ga shi a gida, shi ne suka kwaso ayari suka yi maza suka zo. Ko sallama babu suka faɗo cikin parlourn fuskoki babu mutunci, shi kuma Haidar ya tsaya daga bakin kofa. Baban Zainab yana zaune a saman sofa tamkar bai san da shigowarsu ba. Maman Zainab ce ta ce masu. "Sannunku da zuwa". Ita kuwa Hauwa wani irin kallon sama da ƙasa ta wurga masu kafin ta ce. "Ya zaku wani shigowa mutane cikin ɗakin babu ko sallama kamar wasu dabbobi? Ko dai ba musulmai bane ku?". Ɗan zaro idanu maman Zainab ta yi tana kallon Hauwar da mamaki a saman face ɗinta, shi kam baban Zainab ko gezau, bai ma ɗaga idanu ya kallesu ba. Maman Hanif wato kanwar maman Haidar ita ce ta ce. "Ke kuma wacece? Daga ina kuma?". Kallon uku saura kwata Hauwa ta watsa masu kafin ta buɗe baki zata yi magana maman Haidar ta rigata da cewa. "Ke maman Hanif ai da baki bata amsa da baki ba, buge bakin shegiya ya kamata ki yi har sai ya fitar da jini, an gaya mata mu sha'anin yinta ne da zata nemi ta gaya mana magana ko ta yi mana rashin kunya?". A walaƙance Hauwa ta basu amsa, dan dama a kule take da su har wuya, musamman ma maman Haidar, ta tsani matar sosai, tasan labarinsu dukka a bakin maman Zainab, tasan duk irin cin kashin da suke yi wa maman Zee ɗin, shiyasa ita ta ɗaura ɗamarar cin ubansu one by one, da gangan kuma dama ta zagesu daga shigowarsu, dan tana son su fara gwabzawa ne da su tun daga yanzu, duk sai ta saita masu zama tun da su basu da lissafi. "Ke tsohuwar kokon giya dallah ki rufewa mutane baki, kada ki sake sanya mun baki a maganata, an gaya maki ni Aisha maman Zainab ce? Ba zan ɗauki iskancin ku ba, yanzun zan sanya mata ta san matsayinta, bani da mutunci ko miskala zarratin kuma ban san hanyar in da mutunci take ba, dubeki wata a koɗe dake futu futu kin yi tsufar kokon giya, wlh na zabga maki mari idan baki mai da hankalinki ba, an gaya maki ruwa sa'ar kwando ce? Ke baki ga kalar ba? Na yi kala da waddan tsofaffin kokon giya zasu kawowa wargi ne? Yanzu zan sa ki gane annabi ya faku". Cewar Hauwa. Yadda take magana tamkar wadda ake karantowa tana faɗa ko kuma wadda aka sanyawa battery, daga ji kasan wannan dama tun ainahi ƴar tijara ce, bala'i da masifa ya jima da samun matsuguni a wajenta. Tsit maman Haidar ta nutsu, dama tsoron bala'i ke gareta, kawai dan sun rena maman Zainab ne yasa suke cin mutuncinta dai'dai gwargwado, amma banda haka mugayen matsorata ne, to yau dai sun sami dai'dai da su. Maman Zainab kam sake baki ta yi tana ganin ikon god, ashe dama akwai abin da zai sanya maman Haidar yin shiru a duniyar nan? Wannan shi ne gaba ma da gabanta wai aljani ya taka wuta, duk iskancinta da balai'nta yau dai ga shi ta nutsu tsit ana kwashe mata albarka ba bakin tankawa. Babbar magana, ana dirama a cikin wannan gida. Haidar dake a tsaye a bakin kofa ne ya yi kanta cikin fushi da nufin dukanta, a cewarsa bai ga dalilin da zai sanya ya tsaya wata ta tsaya tana gayawa mahaifiyarsa maganganu marasa daɗi son ranta ba. Wani irin tsawa ta daga mashi wadda ya sanya shi jan birki babu shi, a walaƙance ta ce. "Dakata ƙaramin maras kunya, ai kai taka rashin kunyar nafila ce tun da iya nan gidan kawai ka iya baje ta, wlh idan ka yi kuskuren sanya hannunka a jikina duk danginka babu mai kwatarka, sai kun yi danasani mafi girma a rayuwarku". Sai a lokacin baban Zainab ya saka baki a in da ya dakawa Haidar ɗin tsawa da ya fita mashi daga cikin parlourn ko kuma yanzun nan ya canza mashi kamanni. Babbar magana, a kan Hauwa fa babu abin da baban Zainab ba zai aikata ba, lallai akwai rikici ba kaɗan ba. Ba ƙaramin kara tsorata su maman Haidar suka yi ba na ganin yadda baban Zainab ɗin ya hayayyako masu dan kawai Haidar ya yi yunƙurin taɓa Hauwa, yana gani Hauwar ta ci masu mutunci bai saka baki ba, amma daga za'a taɓata ya wani hayayyaƙo masu kamar zai cinyesu ɗanye, lallai akwai matsala babba ma kuwa. Ita kam maman Zee komawa ta yi saman sofa ta yi zamanta tare da buga uban tagumi tana ganin wannan cakwakiya. Tatas baban Zainab da Hauwa suka yi wa su maman Haidar, daga karshe baban Zee ya koresu ma daga cikin gidansa, basu kuma da zaɓin da ya wuce su tafi, dan kuwa a yadda yake ɗin nan tsab zai iya yi wa mace ɗan banzan duka, Allah ma ya rufa asiri basu zo da hajiyarsu ba, abin ya tsaya a iya kansu kawai, ai da anyi ba daɗi. Haka suka kwashi jiki cikin ruɗu tare da mamaki haɗe da tunanin baban Zainab kam anya lafiyarsa kuwa, a haka suka bar gidan suka nufi gidan Hajiyarsu, dan su sanar da ita halin da ake ciki. Ita kuwa Hauwa bata bar wannan gida ba sai da ta tabbatar ta ƙunsawa maman Zainab abin da zai hanata yin barci a yau, sannan ta ce da baban Zainab su tafi. Shi kuwa bawan Allah kamar raƙumi da akala haka ya bita zalau zalau suka bar gidan kamar yadda suka zo. Suna fita maman Zee ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tun daga saman kujera ta zubo kasa saman gwiwowinta tana kuka, Khadija dake zaune komai ya faru a kan idanunta ne ta zo ta rungumeta tana rarrashinta ita ma kuma tana nata hawayen, abin gwanin ban tausayi. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ Idan muka waiwaya Dubai kuwai. GIDAN ABU ABDUSSALAM BIN BADEEN🔥🌼 Lest cut the story, tsawon wata guda Leesharh tana aiki a cikin wannan gida, amma kuma ko kusa ko alama bata samu ganin wanda ta zo aiki a kansa ba, wato Ramish kenan, bayan Ummie and Sharifa ma sai su Radia babu wani bakon fuska da ta sake gani a cikin gidan, abin ya ɗaure mata kai, ji take yi kamar ta tambayi su Radia ina Ramish yake kuma wanenen shi? Amma da yake bata saki jiki da su ba, bata shiga cikinsu, kuma tana tsoron su zargeta a kan wannan tambaya yasa ta ja bakinta ta yi shiru, kawai ta zubawa sarautar Allah idanu, amma kullum da wannan tunani take kwana, da shi kuma take tashi, ga wayar da aka bata kullum a kunne yake, amma babu wanda ya taɓa kiranta ko ya turo mata saƙo, waɗan da suka bata wannan aiki da alama sun san da cewa ganin Ramish da ido ma kawai ba ƙaramin aiki bane, shi ne yasa basu nemetaba tukunnan, da alama suna samun information a kan wani hali take ciki sosai ba tare da saninta ba, amma su waye masu basu information a kanta? Allah masani. ita dai a yanzu bata san a wani matsaya ma take ba baiwar Allah. A bangaren shi kuwa Ramish yana nan a cikin gidan, sai dai samin damar ganinsa ne ba kowa ba, ko ita kanta Ummie tana fin sati biyu bata sanya shi a idanunta ba, ba wai kuma dan baya nan ba, no a cikin gidan yake kwana yake tashi, sai dai yadda kuka san wani aljani haka yake, tamkar yasan akwai mayunwatan kuraye dake farautar rayuwarsa a cikin gidan, bawan Allah nan baya tashi dawowa sai tsakar dare yake shigowa cikin gidan, duk balainka da nacinka baka isa kasan lokacin da Ramish yake fita ko yake dawowa ba, zaka iya zaman shekara guda a cikin wannan gida baka haɗu da shi ba, shi ɗin ba kamar sauran mutane yake ba, and kuma ba shi kaɗai bane, matasa ne su huɗu wadda dukkansu babu wanda ya kai 30 years a duniya, cikinsu kuma harda Rizwan yayan Yah Jawad, first born ɗin uncle Abbas kenan, amma fa dukkansu kafin ka samu damar ganinsu wlh kana iya fin shekara a cikin wannan gida, su ɗin ba mutane ne kamar kowa ba na gaya maku. Wai wanenen Ramish? Bari mu ɗan ji wanenen shi kaɗan wata kila zamu iya fahimtar dalilin da yasa ake nemar rayuwarsa ruwa a jallo. Ramish dai ɗan King Zuhair ne ba ɗan Abu Abdussalam bin Badeen bane, yayan gimbiya Aneesa ƴar mamace uwarsu ɗaya, wato ɗan mama ne shi kenan. Ramish fa Special weapons and tactics. Wato SWAT, kuma shi ne operation lieutenant ɗinsu gabakiɗaya. Special weapons and tactics, ku daga jin sunan special kun san they're special ɗin ne da gasken gaske, su ɗin wasu irin jami'ai ne da ake basu horo na musamman fiye da duk sauran jami'ai da kuka sani, saboda su idan ka gansu a waje ma to fa abu ya lalace, sai special waje ake turasu aiki, ba kamar jami'an air force, jami'an soja, jami'an ƴan'sanda da sauran masu kaki suke ba, no su they're very special, da farko kasar America ce ta fara kaddamar da Special weapons and tactics, daga baya sauran manyan ƙasashe ta duniya suka kwaikwayesu suma suka kaddamar da su, aiki suke yi kamar agogo, ga ɗan banzan fikira dake garesu, ga zafin nama, cikin ƙanƙanin lokaci suke aiwatar da duk abin da zasu yi, ba iya karfin dantse ne kawai suke da shi dan an basu horo na musamman ba, no su ɗin aiki suke yi da kwakwalensu cikin kwarewa tare da tunani mai zurfi, duk fa idan suka yanke hukunci a kan abu to ko gwamnati bata ja da su, domin ansan gaskiya ce, suna da uban tarin makiya ta gabas da yamma kudu da arewa, saboda sun yi aiki tukuru, sun kashe iyayen wasu, sun kuma jefa iyayen wasu gidan prison, su fa har manya manyan ƙusoshin gwamnati basu bari ba, duk wanda ya keto ta cikin aikinsu to ba makawa zai jisa a in da sai ya yi danasanin zuwansa duniya, wannan takaitaccen bayani ne a kan wanene Ramish, sauran bayanai ya biyo daga baya, kada ku manta shi ɗin jinin Modarawa ne, ɗa ne ga King Zuhair. To amma meyasa ake farautar rayuwarsu har haka? Lokaci ne zai nuna mana komai. Ramish yana da kani mai suna Bilal wanda ya kasance yaya ne ga Gimbiya Chuchu uwarsu ɗaya, wato ɗan mummy kenan, Bilal air force ne shi, ba sai na tsaya yi maku dogon bayanai a kan su waye air force ba, kun san jami'ai ne da suke sadaukar da rayukansu a kan ƙasarsu, sun fi sojoji shiga haɗari nesa ba kusa ba, su ɗin jami'an sama ne, yakin sama ake turasu, jami'ai ne da ba kowa yake iya yin aikin da suke yi ba, jajirtattun ne kuma jarumai na gasken gaske. Bayan Bilal kawai Dr Raj wanda ya kasance shi ma ɗan mama ne, Kanin Ramish kenan uwa ɗaya uba ɗaya, shi kuma hamshaƙin Medical Dr ne, mutun ne shi da ya san aikinsa, baya kuma wasa da aikinsa, bama sai na ɓata bakina wajen gaya maku cewa yaran King Zuhair basu da wasa ba, ku da kanku kun san jininsu a tafashe yake, sun gada wajen mahaifinsu, Akka da take mace ma da yake jinin Modarawa ne ke gudu a jikinta ita ɗin ma, baku ganinta a zafafe take ne? Tana da zafin nama bare kuma su maza, sam basu da wasa ko kaɗan, kuma idan ka kuskura ka kawo masu wasa a cikin lamuransu yanzun nan zasu saɓa maka kamanni. Rizwan kuma wato yayan Yah Jawad, kamshaƙin ɗan kasuwa ne wadda yake business tsakanin manyan kasashen duniya, yana da kamfanonin a ƙasashe daban daban, baya da ra'ayin siyasa ko sarauta, haka zali baya ra'ayin kaki, duk da cewa kowace irin kaki ya yi ra'ayi zai iya sanyawa ga jikinsa ya yi aiki, domin kada ku manta da muƙamin uncle ɗinsu wato uncle Abu Abdussalam bin Badeen, shiyasa su Ramish ɗin ma suke da manyan muƙamai a wajen aikinsu, kuma ya haɗu da basu da wasa, jajirtattu ne su ɗin. To shi Rizwan ya zaɓi kasuwanci ne abinsa, shi ne ra'ayinsa. Dukkan ƴaƴan King Zuhair idan ka kallesu ba sai an ce maka ƴaƴansa bane, akwai alamar kamanni ta jini a tsakaninsu, musamman Ramish da kaninsa Dr Raj, suna kama sosai, duk kuma kamannin Akka suka ɗauko, shiyasa suke sajewa da su Abu Abdussalam bin Badeen, sun zama dai duk iri ɗaya. Wannan shi ne takaitaccen labarin waɗan nan zaratan samari na Abu Abdussalam bin Badeen wanda kuma ya renesu kamar wasu zakuna, suka taso a haka, tun suna kanana suke a hannunsa, shi kuma ƴaƴansa maza biyu basu a tare da shi, suna gidan the most powerful King Badeen, wato gidan mahaifinsa kenan, ƴarsa Sharifat ce kawai a gidan, sai Ummie, yana kaunar King Zuhair ne over, hakan yasa yake kaunar ƴaƴansa ma. To mu koma kan labarinmu tun da kun ji su waye su Ramish, ɗan mama ne dai, mama sarkin masifa, ƴaƴanta maza biyu ne sai Aneesa ta uku, kuma ga duka yayan nata da Ramish da kuma Dr Raj ɗin duk a Dubai, amma a haka kullum take tsayar da bala'i a kan ita King baya yi mata adalci, ya fi son Momman auta, ɗan adam kenan, ba'a iya mashi, ita fa ƴaƴa maza manya har biyu ke gareta saɓanin Mummyn Gimbiya Chuchu da take da iya Bilal kawai, amma Mummy bata wani damu ba, ita kuma mama sarkin haɗama so take ace ita kaɗai ce take da ƴaƴa maza, kuma fa su Ramish ɗin nata sune manya a kan Bilal ɗin Mummyn Gimbiya Chuchu, idan ma mulki take so ai su zasu karɓi mulki, amma ita dai duk bai yi mata ba, sai ka rasa me take so a duniyar nan kuma, mummy ma fa tana da babban ɗanta na fari kafin Gimbiya Aunty MieMie wanda ya rasu, rasuwa ya yi shiyasa yanzu su Ramish sune manya a kan Bilal ɗinta da yake matsayin ɗanta a uku, sai Chuchu auta. Fatan dai kun gane?. A kullum baza idanu Leesharh take yi tana tunanin ta in da zata kalli Ramish, amma shiru babu shi babu labarinsa. Yauma dai kamar kullum, ta gama aikin gyaran parlourn ita da su Fadila da suka tayata, tana shirye cikin arab jallabiya ash color, ta yi kyau matuƙa, yanzu ta kara gogewa ta yi wani fresh da ita, ta kuma ɗan yi kumatu, amma kullum tana cikin zulumi tare da fargabar ya zata kalli Ramish? And ya zata kaya da wannan aiki da yau tsawon wata guda kenan bata fara shi ba? Yaushe zata kammala wannan aiki har ta koma ga mahaifinta?. Kullum tana cikin yin wannan tunani. "Leesharh ki je ki gyara room ɗin guyson and na Aunty Sharifat bari mu kuma mu fara shirya kayan abinci kamar yadda muka saba". Cewar Fadila. Da okey ta amsa masu tare da nufar room ɗin nasa, shi kansa Omar ɗin yau tsawon wata kenan bata samu damar ganinsa ido da ido ba, sai dai a wannan hoton, kuma kullum ita take gyara mashi room ɗin nasa, amma suna samun saɓani sosai da shi, wani lokaci sai ya fita take shigowa ta gyara ɗakin, wani lokaci kuma tana gama gyara ɗakin ta fita shi kuma zai shigo, Sharifat ta so ta haɗata da shi dan ya ga kyakkyawa, amma ina ba dama, dan kuwa bai zauna ba, yana shirye shiryen komawa KINGDOM OF POWER, so dayawan lokuta yana gidan King Badeen, yanzu bai cika zama a gidan Abu Abdussalam ba, shiyasa basu haɗu ba. Room ɗin nasa ta nufa, hannunta na rike da mooper da abin share share. Duk da ta san cewa ba lallai ta sami mutun a cikin room ɗin ba hakan bai hanata ta yi sallama cikin sanyin murya ba. Tana yin sallamar kuma ta afka cikin room ɗin. A tsakiyar ɗakin ta ajiye kayan share share da goge gogen nata. Kai tsaye ta nufi saman katafaren bed ɗinsa na alfarma mai matukar girman gaske, room ɗin nasa ya ji komai na more rayuwa, sai tashin kamshi yake yi, ko'ina tsab tsab, amma a haka sai ta sake gyarawa ta goge ko'ina. Jibgegiyar duv ɗinsa dake a saman bed ɗin nasa ta sanya hannu tana ƙoƙarin janyewa, domin ta cire ta canza mashi wani, kullum sai ta sake wani bedsheet ɗin, bata da tabbacin ana kwanciya a gadon ne ko ba'a kwanciya, amma dai kullum sai ta canza. Tana ganyo duv ɗin mutun ya bayyana kwance a saman gadon, da yake duv ɗin yana da girman da idan mutun ya kule a ciki ma ba lallai kasan yana a cikin ɗin ba, ba zaka yi zaton akwai shi a ciki ba, shiyasa ta zo ta janye kawai. Tana janyewa kuma kamar wadda aka yi wa allura ya fara mutsu mutsu haɗe da murkusoso kamar wadda yake shirin mutuwa, tamkar ana zare mashi rai, juyi ya fara yi a saman bed ɗin, jikinsa na a sanye da farar jallabiya tas da shi, farar kyakkyawar fuskarsa ta yi kal kal da ita, ya yi wani fayau, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin mawuyacin hali, kyakkyawar arab hairnsa da ya zubo mashi har ta gaban goshinsa yasa ba'a ganin face ɗinsa da kyau, ga shi kwanciyar ruf da ciki ya yi, so ya bawa Leesharh ɗin baya, ko ba'a gaya mata wanene bane tasan shi ne guyson, saboda room ɗinsa ne, kuma tasan hotonsa, kullum idan ta shigo babbar parlourn da face ɗinsa take fara cin karo, yana sakin ƙayatatcen murmushi, so tasan shi ne. Ganin shi cikin wannan mawuyacin hali ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, a razane ta zaro dara daran idanun nan nata tana kallon yadda take juyi kamar ba zai rayu ba, idanuwansa a rufe ruf, yama datse idanun nasa ne sosai tamkar zai fasasu, da alama yana jin tsananin azaba, kuma da alama ma baya a cikin hayyacinsa, sai wasu siraran hawaye da suke fita mashi daga idanuwansa suna bin gefe da gefen face ɗinsa, hakan zai kara tabbatar maku da yana cikin mawuyacin hali. Sam Leesharh bata taɓa kallon irin hakan ba, hakan yasa hankalinta ya yi mummunar tashi, cike da ruɗu ta........... 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 26/8/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________38🔥 *Assalamu alaikum everyone ina fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya?! Allah yasa! Ina yi wa kowa da kowa fatan alkhari tare da fatan kasancewa cikin ni'ima da kuma rahmar Ubangiji, a duk in da kuke Allah ya cigaba da dafa maku yana kara tsareku da tsarewarsa, Allah ya jiɓanci al'amuranmu bakiɗaya, ina matuƙar farinciki tare da godiya da irin tarin addu'oinku dana samu daga bakunanku masu albarka, na kuma ga tasirin addu'oinku wlh, Allah ya amsa jikina ya warware Alhdulillah, babu abin da zance maku face in ce Allah ya bar kauna ya kuma cikaku da farincikin da babu bakinciki a bayansa, arxikin da babu talauci a bayansa, daga karshe Allah ya bar kauna ina godiya 💘 taku PRINCESS TEEMA ta amana✍️💘* E____________38🔥 Sam Leesharh bata taɓa kallon irin hakan ba, hakan yasa hankalinta ya yi mummunar tashi, cike da ruɗu ta kai hannunta ta mayar mashi da duv ɗin da nufin ta gudu ta fice daga room ɗin kada ace ita ta yi mashi wani abin, kunsan maras gaskiya da shegen tsarguwa, sai yaga kamar komai ƙanƙantar motsi idan ya yi asirinsa zai iya tonuwa. Sannan kuma kunga tana janye mashi duv ɗin ne ya fara wannan murkusoson, so sai tana ganin kamar za'a ce ita ce sila. Har ta juya zata fita ta tsinkayo zazzaƙar voice ɗinsa ya daki dodan kunnuwarta, idanunsa a datse gam yana ruwan hawaye, voice nasa ɗan siriri kamar na mata, ga shi cool voice gare shi sosai, akwai daɗin saurara, bare da ya haɗu da yana cikin ciwo, sai maganar tasa tana fita wani iri. Cikin harshen larabci ya fara faɗin. "Shareee.... Shareee zo ki bani drugs ɗina, kada ki kira su Ummie kin ji?". Yana magana ne a tunaninsa Sharifat ce, da alama ya ji shigowarta kenan. Kamar zata gudu, dan tana tsoron kada ace ita ta yi mashi wani abin, bare kuma yadda ta ji kowa a gidan yana yawan maganarsa tasan tabbas ɗan gata ne da ake ji da shi, to tana tsoron kada wani abin ya haɗasu tun bata fara aikinta ba ta shiga uku. Amma kuma tana da tausayi da raunin zuciyar da ba zata iya tafiya ta barshi a cikin wannan hali ba. Juyowa ta yi a hankali tare da kai kallonta saman gadon, har lokacin yana murkusoson nan dai yana ambatar sunan Sharifat come and give me my drugs. Shiru ta ɗan yi tana tunanin Sharifat dai bata nan, tana school, koda kuma tana nan ita a ina tasan zata nemota a cikin wannan gida har ta kira mashi ita? Yau watan ta guda kenan a gidan idan ba time to time ba ko Ummie bata wani samun damar gani sosai a wannan hawa da suke, Sharifat ɗin ma ita take zuwa in da suke dan ta ce Leesharh na yi mata kyau, yarinyar tana da saukin kai, so ita take zuwa wajen Leesharh ɗin ta ce ta zo su ɗan yi hira, Leesharh ta bata labarin ƙasarsu, so dani da ku duk mun san a kan dokar da Leesharh ɗin take na ja mata kunnuwa da aka yi a kan kada ta yarda ta yi hira da kowa, hakan yasa bata taɓa yarda ta saki jiki da Sharifat ɗin bare ma har su yi hira, bata yarda da hakan, sai dai ta yi shiru. Idan Sharifat ɗin ta ce mata to ki yi magana mana, sai ta ce ai bata san me zata ce ba, murmushi kawai Sharifat take yi ta ce na lura baki da yawan magana amma zan koya maki, iya murmushi kaɗan kawai take yi daga haka bata sake yin magana, to haka suke rayuwa a cikin gidan, Leesharh tana yawan janye jikinta ga mutane sosai, bata taɓa yarda ta buɗe baki ta yi magana, izuwa yanzu voice ɗinta ya koma yadda yake sosai da sosai, maganarta na fita da kyau da kyau, tana da daɗin murya sosai, ta gama shanye magungunan da Dr Suhail ya bata. Sanin cewa ba zata sami Sharifat bane kuma tana da zuciyar tausayi sosai, ta ji ba zata iya guduwa ta bar shi a cikin wannan mawuyacin halin ba ne yasa ta juyo da sauri ta dawo wajen bed ɗin. Kaɗan ta sake janye duv ɗin kasa. Sosai da sosai yake kuka, har wa lokacin kuma idanuwansa a rufe ruf. Matsowa kusa da shi kaɗan ta yi tare da duƙowa kansa, cikin kwararriyar laraɓcinta tare da yi mashi magana ƙasa ƙasa a tawajen kunnuwansa ta tambayi ina magungunan nasa suke?. Duk da yana cikin raɗaɗin ciwo hakan bai hana ya gane cewa wannan ba voice ɗin Sharifat bane, hakan yasa ya ɗan yi jim kaɗan kafin kuma ya ce. "Who're you?". Dum dum ta ji gabanta ya bada bugu, sai ta ji ta yi nadamar zuwanta wajen nasa ma, a cewarta da ta gudun kawai abinta, ta tsorata sosai saboda bata kullo gaskiya ba. Kai ya Allah kasa mu kasance masu gaskiya a duk in da muke, rashin gaskiya bai yi ba, domin kuwa idan baka da gaskiya ka rinƙa shiga fargaba da faɗuwar gaba koda sunanka kawai aka kira a waje, duk karasa sukuni ka takura kanka, ka rasa walwala ka kasa iya rayuwa kamar kowa, koda iya wannan kawai aka barka kana cikin masifa wlh, jama'a mu riki gaskiya da amana domin samun rabauta duniya da lahira!!. Jin ta ɗan yi shiru ne yasa ya sake maimaita mata tambayar da ɗan kausasshiyar murya tare kuma da fara ƙoƙarin buɗe idanuwansa da suka yi mashi tsananin nauyi saboda ciwo, ga kuma kukan da ya sha, har wani sara mashi kansa yake yi. Ƙoƙarin juyawa ta yi dan ta gudu, a shirmenta zata je ta tonawa kanta asiri, ko me abin guduwa a wajen oho, ta tsargu ne. Bata bar wajen ba ya damko hannunta da ɗayar hannunsa tare kuma da ƙarisa waro waɗan nan manya manyan idanuwan nasa masu kama da na Auta Gimbiya Zunaira. Idanun nasa sun yi jajir da su kamar wuta saboda kuka. Nutsuwa ta yi tsit tare da sunkuyar da kanta ƙasa, tsoro ne karara a saman face ɗinta, sai dai hakan bai hana ta rinƙa satar kallonsa ta ƙasan ido ba, kullum ma idan ta shigo babbar parlourn sai ta yi ta karewa hotonsa kallo, yana yi mata kyau sosai da sosai, bare ma iya ɗaukar wankarsa, guy ne sosai, in dai ɗaukar wanka ne to daga kansa an rufe kofa, gwani ne, kowani irin kaya ya saka zama mashi suke yi ɗas a jikinsa kamar dan shi aka yi su. "Who're you?". Ya sake tambaya yana ciza laɓɓansa, alamar yana jin azaba. Ga hawayen kuma suna cigaba da wanke mashi fuskarsa. Cikin in'ina ta gaya mashi wacece ita da kuma matsayinta a cikin wannan gida nasu. Sake mata hannunta ya yi tare da mayar da idanunsa ya datsesu gam. Shiru ya ɗan yi na ƴan sakani kafin ya ce ta buɗe drawers ɗinsa ta ɗauko mashi drugs ɗinsa and bottle water mai ɗumi ba mai sanyi ba. A hanzarce ta amsa mashi da okey, har lokacin jikinta yana ɗan kerma ta fara bubbuɗe drawers ɗin, dan bai gaya mata a cikin wanne drawer magungunan suke ba, ya dai ce kawai ta buɗe drawers ta kawo mashi magungunan. Tana buɗe drawers ɗinsa na wajen bed ɗin ta ci karo da uban tulin hotuna sosai, kala kala, wanda yake a saman kawai ta kurawa idanu ne, hotonsa ne shi da twins Obaid and Omaid ƴan albarka jikokin hajiya Akka tamu......😅 Da yake su twin's ɗin suna da tsawo sosai sai yasa da kaɗan Omar ɗin ya fisu tsawo a hoton, sun yi matuƙar kyau sosai da sosai, a gidan kakansu King Badeen suka ɗauki hoton, dukkansu suna cikin arab alkyabba bakake, while daga ta ciki suna sanye da farar arab jallabiya, sun naɗa rawani irin na sarauta fari tas, Omaid yana rike da sandar sarauta mai matuƙar kyau mai kuma tambarin kan zaki, Obaid da Omar fuskokinsu ɗauke da cool murmushi, shi kuwa Omaid fuska a ɗaure sosai, dama idan baku manta ba shi bai cika dariya ba sai sun shirya mugunta sosai. One thing about this twin's da baku sani ba shi ne, su fa ba normal makaranta suke yi ba, tun suna yara they're very very stubborn, hakan yasa Ramish ya sanya su special swat academy, a tunaninsa idan suka shiga nan zasu nutsu in sun ci kwakwa, bai san cewa kuskure ya tabka ba, domin kuwa ƙaro rashin ji over tare da taurin zuciya da rashin imani suka yi, sun zama basu da tausayi, ga ɗan banza rashin ji! Mugunta kuwa ba'a magana kuma shaida ne, kun ganewa idanunku, da alama duk wasu kayan muguntar da suke amfani da shi daga school suke tahowa da shi, domin dai in ba daga school ba babu in da zasu samo shi. (Yah Ramish ne ya kaisu special swat academy, wato makarantar koyar irin aikinsa kenan, ya kai su ne dan ya samu su nutsu, amma kun dai ji yanzu ga shi mahaifiyar Yah Ramish ɗin wato maman Gimbiya Aneesa ita suke shiryawa mugunta da zasu yi mata idan zasu dawo Dubai😅 hmmm ba zan yi magana ba, amma wlh idan Ramish ya kamasu ko King Zuhair sai ya yi da gaske zai iya gane su, saboda irin ragargazar da Ramish ɗin zai yi masu😅 Allah dai ya kwacesu, mu dai ana yi muna shan Maltina ko my people's?.🥱) Kasancewar tasan halin da yake a ciki ne yasa bata tsaya gulmar ganin hotunan ba, amma dai ta so duba hotunan ko zata kalli hoton Ramish ko dai na wani daga cikin ƴan gidan, amma haka ta hakura ta rufe drawer ta miƙe. Kusa da shi ta dawo, a nutsu ta ce. "Guyson ban ga drugs ɗin naka ba". Ciza lips ɗinsa ya yi da karfi, alamar azaban zafi yake ji, juyi ya yi ya sake kifawa a kan cikin nasa, idanuwansa a lumshe ya sanya ɗayan hannunsa yana laluɓar saman bed ɗin kamar mai neman wani abin. Cike da tsoro tab a ranta ta ce. "Wani abin kake nema ne?". Ƙasa ƙasa ya amsa mata da. "My phone". Ɗan juye juye ta fara yi tana neman mashi phone ɗin, hannu ta kai ta kara janye duv ɗin nasa ƙasa. Can wajen kyawawan fararen ƙafafunsa ta hango haɗaɗiyar wayar tasa. Cikin hanzari ta ɗauko mashi, hannunta sai kerma yake yi. Miƙa mashi ta yi tare da ce mashi "This is the phone". In a low voice sosai ya ce. "Check my contacts, ki duba Yah Ramish or Yah Raj ki kira mun ɗaya daga ciki". Wani irin muguwar faɗuwar gaba ta ji jin sunan Ramish, har wani irin haɗiyar wahalallen yawu ta yi, a duk lokacin da kunnuwanta suka ji sautin sunan Ramish har cikin ranta take jin kanta a matsayin gawa, ji take yi kamar shi ne ajalinta, ita da bata ma san wanene bane, amma a yadda ta kalli yanayin gidan da kuma yanayin yadda take tsintar maganarsa time to time a bakin su Radia yana mugun sakawa ta ji cewa in dai asirinta ya tonu to tabbas Ramish shi ne ajalinta!. Tana shiga contacts ɗinsa da sunan My baby (Gimbiya Zunaira) kenan ta fara cin karo, ƙasan numberta kuwa number Dr Raj ne da ya yi saving da Yah Raj. Dialling na number ta yi, gabanta sai dukan uku uku yake yi. Ringing wayar ta fara yi har ta kusa katsewa, sannan ne aka yi picking call ɗin. A hanzarce ta miƙa mashi wayar. Sam ya kasa iya kai hannunsa ya karɓa. Ganin hakan yasa ta matso mashi da wayar a kusa da ɗan bakinsa tare da sanya wayar a speaker. Daga ɗayan ɓangaren wani irin cool voice ya fara magana da. "Assalamu alaikum Guyson". Sautin kukansa ya kara tare da cewa. "Yah Raj come and help me........ My". Sai kuma ya yi shiru yana goggoga kansa a jikin pillown da ya kwantar da kansa. Sosai Leesharh ta tsorata lokacin da Dr Raj ya yi magana a karo na biyu. "Omar where are you?!". Ya yi maganar ne cikin ɗaga murya, hakan ne ya tsoratata, tamkar bashi ne ya yi magana cikin sanyin murya da farko ba. "Yah Raj am in my room". Da kyar ya furta hakan. Diff aka kashe kiran ba tare da an sake yin magana ba. Ajiye mashi wayar tasa ta yi a kusa da shi, a hankali ta lallaɓa ta nufi kofar fita daga cikin room ɗin. Tana sanya kai zata fita suka yi karo da mutu, baya baya ta yi ta faɗi ƙasa. Shi kuwa shigowa ciki ya yi bai bi ta kanta ba, da alama ma bai san ya buge mutun ba, dan hankalinsa kacukam yana a saman bed ɗin guyson, tun da ya shigo waɗan nan eyes ɗin nasa irin na King Zuhair suna a saman bed ɗin kawai, sanye yake da wando three cuter milk color, sai t-shirt sky blue mai haske sosai, ƴaƴa King sun gado tsawo kam, dogaye da su, so shi ma Dr Raj yana da tsawo sosai, ga cikar halittar sai ka rantse da Allah renon commander ZAFAR ne shi ɗin, tsayayye ne sosai mai ji da lafiya, kyakkyawar gaske ne sosai, duk dai Akka suka ɗauko. Da alama yau bai je hospital ba, domin kayan shan iska ce ma a jikinsa, arab hairnsa ba dai kyau ba kam, ya sha gyara sai kyalli yake yi. Bin shi da kallo Leesharh ta yi gabanta na dukan uku uku, tunani take yi kenan dama suna cikin gidan? Amma kuma shi ne ba'a taɓa ganinsu? To a ina suke zama kenan? Ita a tunaninta ai basa nan ne yasa ba'a ganinsu, bata san dukkansu wani lokaci ma a gidan suke wuni basa fita ba, kawai ganin nasu ne sai wane da wane, daga Abu Abdussalam sai Ummie, ita ma Ummie ba kullum ba, gara ma Sharifat tana zuwa ɓangarensu jefi jefi, musamman ma wajen Rizwan suna shiri da shi sosai, so tana yawan zuwa room ɗinsa, ita bata jimawa sosai bata gansu ba. Kai tsaye wajen bed ɗin ya nufa. Yana zuwa ya janye duv ɗin da guyson yake lulluɓe, gabaɗaya ya cire duv ɗin. Hannu yasa ya tallabo kan Guyson ɗin. Ƙanƙame shi guyson ɗin ya yi, hawaye suna bin kyakkyawar kumatunsa. "Omar did you take your drugs?". Ya tambaye shi cikin sanyin murya, yana magana yana goge mashi hawayen nasa da kyawawan fararen tafukan hannunsa. Girgiza mashi kai ya yi, cikin raɗaɗin ciwo ya ce. "No Yah Raj". "Why?". Ya jefa mashi tambayar tare da miƙewa tsaye ya saɓe shi a saman shoulder ɗinsa, ya wani saɓesa kamar baby, kamar ba shi ne mai kanne har uku ba, wato da twin's da auta Zunaira, dukka fa kannensa ne, amma da alama duk sun fi shi jarumta, dan dai shi kam ga shi yana ruwan hawaye abinsa, abin da kunsa Obaid and Omaid kam ba zasu aikata hakan ba, waɗan nan yara ma ai sai addu'a, dan abin da zai saka su yi kuka ba ƙaramin abu bane gaskiya............😅 Leesharh tana zube a kasa ta kasa motsawa daga in da ta faɗi ɗin har Dr Raj ya fice waje da guyson a saman shoulder ɗinsa, sai binsu da kallo take yi, sun yi matuƙar burgeta over, sai ta ji tana sha'awar da ace tana da ɗan uwa ita ma. Nan take kuma mood nata ya sauya, jiki ba kwari ta miƙe ta dawo cikin room ɗin ta fara aikin gyaranta kamar yadda ta saba, tana yi tunanin yadda ta kalli Dr Raj wanda yake a matsayin kanin Ramish, abubuwa da dama a tattare da shi sun rikitata, tunani take yi to shi kuma Ramish ya zai kasance kenan? Ace Dr Raj kaninsa ne haka ga shi kyakkyawa, to shi ya zan kasance kenan? Tunanuka sosai ne a cikin kanta har ta kammala aikinta ta fito ta nufi wajensu Radia. Yau gabaɗaya sukuku ta wuni, sai tunanin ya jikin Omar take yi, idan ta rufe idanu sai ta rinƙa kallon fuskarsa a yayin da yake ruwan hawaye, tausayinsa ne sosai a ranta, da shi ta wuni, tsabar ƙoƙari irin tata har da yi mashi addu'a da ta yi sallah, ta yi mashi fatan Allah ya bashi lafiya. Da daddare misalin karfe 9 na dare, ta fito daga room ɗinta ta nufi kitchen, dan ta ɗan sha wani abin, yunwa take ji, sam ta kasa iya cin abincin dare ne, saboda tunani da ya taru ya yi mata yawa, na farko tana tunanin in dai Dr Raj haka yake to ya Ramish kuma yake? Na biyu kuma tunani a kan me yake damun Omar? Yanayin yadda yake cikin ciwo ya tsaya mata a rai, waɗan nan tunane tunane ne suka hanata cin abinci, so shi kuwa yunwa ai bai da sabo, ta fara jin ana yaki a cikinta, haka yasa ta yi maza ta fito nemanwa kanta mafita. Elevator ta hau zuwa ƙasa, ta sanya ɗan hijabinta a kanta, riga da wando na barci ne a jikinta, farare tas masu laushi sosai. Kai tsaye kitchen ta nufa, tana tafiya tamkar wadda kwai ya fashewa a cikin ciki, kamar wadda aka zarewa laka. Ko da ta shiga cikin kitchen ɗin pina colada kawai ta ɗauko daga cikin fridge, sannan ta ɗauki glass cup guda ɗaya ta fito. Sama ta koma, kamar zata wuce part ɗinsu, sai kuma ta ce bari ta leƙa living room ta gani ko Sharifat tana ciki su ɗan gaisa, yau throughout basu haɗu ba. A hankali ta nufi parlourn, da alama ma a tsorace take. Ƙasa ƙasa ta yi sallama. Shiru ba'a amsa ba, parlourn tsit, da alama babu kowa, sai daddaɗar kamshin da yake tashi ga sanyin Ac. Shigowa ciki kaɗan ta yi, ganin babu kowa yasa ta juya da nufin ta koma, kamar daga sama ta ji ance. "Hey come here". Da sauri ta juyo da kallonta izuwa in da ta ji sautin muryar, tun bata juyo ba tasan wanene, saboda duk da yana cikin ciwo ya yi mata magana a ɗazun to ta rike voice ɗin nasa. Zaune yake a saman ɗaya daga cikin wasu haɗaɗɗun sofa set kanana marasa girma da suke ta can gefe guda, sai ka yi zaton ma ba'a parlourn suke ba, saboda girman parlourn kuma su suna ta can gefe ne, set ɗin suna da kyau, kanana haka aka yi su gwanin birgewa, ga decoration na flowers masu kyau da ɗaukar hankali da aka ƙawata wajen da su. Zaune yake, daga shi sai wata ƴar riga mai karamar hannu ƴar shara shara fara tas da ita, daga kasa wando ce three cuter ita ma fara tas, kafafunsa suna cikin wasu kyawawan slippers sky blue masu laushi sosai, arab hairn nan nasa dai tana nan kamar wadda aka kifawa hula, bakinkirin da shi har gaban goshinsa, sai kyalle yake yi. Ƴar ƙaramar haɗaɗɗiyar cup ce mai ɗauke da capacino a hannunsa, a hankali yake sha ga laptop a gabansa yana yin video call da auta, a duniyarsa bayan iyayensa babu wanda yake so biyun gimbiya Zunaira, sai Sharifat kawarsa ɗaya tilo........😅 Ita ma auta kun san tana son shi sosai ai. Gabansa Leesharh ta ƙariso tare da yunƙurawa zata tsugunna, da hannu ya nuna mata saman sofa dake fuskantar tasa a kan ta zauna ba tare da ya yi magana ba. Ba musu ta zauna a in da ya nuna mata, domin Fadila ta gaya mata cewa su ƴan gidan nan basa son ayi masu musu, komai suka ce kawai ace masu to, idan ka yi masu musu yanzun nan zasu hau su fara faɗa kamar wasu mayunwatan zakuna dake jiran a taɓosu dama, amma idan baka yi masu musu ba lafiya lou zaku zauna. Daga cikin laptop ɗin auta ta ce mashi. "Yah Omar kai da waye kuma a daren nan? Ko dai Aunty Sharif ce?". Girgiza mata kai ya yi tare da juya mata laptop ɗin izuwa saman fuskar Leesharh. "I don't know her kawai she is the one who helped me in the morning, that's why I called her now domin in tambayeta ya sunanta". Sai satar kallonsa Leesharh take yi, kamar shi ya yi kansa, yana da kyau sosai, sai ma idan yana magana, lips ɗinsa suna da kyau sosai, ga yadda gashin gerarsa suka zauna sosai a face nasa, bakinkirin da su a kan farar fata kamar madara. Ɗan zaro idanu auta ta yi tana kallon Leesharh ɗin, kwance take a saman gadon mommanta, da alama mommar bata nan. "Sannunki". Auta ta faɗa tana sakar mata murmushi, har ta ji tana son Leesharh ɗin tun da ta taimaki yayanta, kun san halin auta dama da son mutane, ita bata da walaƙanci ko kaɗan. Juyo da laptop ɗin ya yi ta saitinsa yana tambayar Leesharh menene sunanta kuma wacece ita?. Sake maimaita mashi wacece ita ta yi kamar yadda ta gaya mashi ɗazun da yake a halin ciwo. Guntun murmushi ya sakar mata kafin ya ce mata shi kuma sunansa Omar kuma ya gode da taimakon da ta yi mashi ɗazun, ta gaya mashi me take son ya bata a matsayin gift na taimakon da ta yi mashi. Girgiza mashi kai ta yi tare da ce mashi ita bata son komai, dan Allah ta yi. Kara ɗan sakin murmushi kaɗan ya yi kafin ya miƙa mata cup ɗin da yake a hannunsa. "To karɓi wannan ki sha, good night zaki iya tafiya". Bata yi mashi musu ba, dan tasan dokansu, dan haka sai ta karɓi cup ɗin ta miƙe tare da yi mashi godiya ta nufi hanyar fita. Cigaba da yin hiransa da auta ya yi suna ta sakin murmushi, duk auta ta ƙosa ya dawo, Abu Abdussalam kuma ya hana shi komawa, sai fakewa da ciwonsa Abu Abdussalam ɗin yake yi yana kara rike shi, baya son rabuwa da shi ne, shi ma kuma King Zuhair yaki hakura ya bar mashi guyson ɗin, dan bayan auta ba wanda yafi so biyun Omar, yana kaunarsa, amma ya zai yi? Dole ya hakura ya cigaba da lallaɓa yayan nasa har ya yarda ya barshi ya dawo, shi kuma King Zuhair ɗin yaki barinsu twin's su dawo, ga shi yanzu an buɗe school nasu this week, so ya zama dole su dawo, shiyasa King Zuhair duk ya bi ya damu sosai, Abu Abdussalam kuma yaki kula shi. Har Leesharh ta kai tsakiyar parlourn sai kuma ta juyo, cike da tsoro ta ce. "Yah Omar me yake damunka ne?". Kansa na'a duke kan laptop ɗin ya ɗago da dara daran idanun nan nasa. "Ciwon ciki nake fama da shi since ina da two years a duniya, amma ina taking drugs yanzu da sauki, and Yah Raj yana treating ɗina very very well". Ya bata amsa fuska ba yabo ba fallasa. Addu'a sosai ta yi mashi na Allah ya bashi lafiya, sannan ta wuce zuciyarta a cike tab da tunani, Allah sarki ciwon ciki tun yana ƙarami, Allah yasa dai ba da shi ma aka haifesa ba, ashe dole ya yi kuka, ciwon ciki waje ƴa mace ma mugun muni garesa bare kuma namiji, ciwon cikin ɗa namiji ai babban haɗari ne ba kaɗan ba, suna shan bakar azaba sosai, wani ma nan take yake kashe shi, amma Alhdulillah shi Omar nasa tana jimawa bata tashi ba, sai ya kai wata shidda bai ji ciwon ba, sai dai idan ta tashin mashi kuma kamar ba zai rayu ba, Dr Raj ne likitansa, shi yake kula da shi sosai da sosai, shiyasa basu yarda su yi nisa da shi sosai, dan a kowani lokaci ciwon tana tashi, shiyasa suke lallaɓa shi suna kula da shi sosai, komai yake so suna yi mashi ba ɓata lokaci, shi kuma yana da kirki sosai, kusan halinsa ɗaya da Zunaira, sai dai shi baya taɓa yarda ace mashi bai iya abu ba, idan kana son ka yi faɗa da shi to ka ce ka fishi iya abu, yanzu zaku ɓata, shi dai gani yake jarumi ne shi ya iya komai ato. Sosai ya ji matuƙar daɗin addu'oin da ta zuba mashi, harta auta da ta kasan kunne tana sauraronsu ta ji daɗin addu'ar, sai ta ji ta kara son Leesharh ɗin sosai, ita dai tana kaunar mai son ƴan uwanta. Tas Leesharh ta shanye cappucinon da ya bata, sai ta ajiye nata pina colada da ta ɗauko, ta ji nasa yana da wani irin shegen daɗi sosai, kamar a kara mata ta ji, sai tunani take yi ko waye ya haɗa mashi wannan gaɗaɗɗen haɗin haka? Bata san shi guyson in dai ba Ummie ce ta girma mashi abu ba to ba zai ci ba, sannan shi abincinsa ba kamar na sauran ƴan gidan yake ba, dan shi yana kan tsarin magani, so abincinsa ya banbanta da nasu, Ummie da kanta take haɗa mashi komai da zai buƙata. Sai tanɗe baki take yi, da haka ta kwanta zuciyarta cike da tunanin kirki irin na Guyson, ga shi fuskarsa ba yabo ba fallasa, ga shi kuma ya iya murmushi mai kara mashi kyau sosai, ta wani ɓangaren kuma idan ta tuna yadda taga Dr Raj sai ta ji gabanta ya yi wani irin bugawa, tsoro ya kamata, da haka dai barci ɓarawo ya saceta. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ KINGDOM OF POWER 💪🔥 Mammien Yah Jawad. Zaune take a saman wani irin shinfiɗa ta alfarma irin na gidan sarauta mai kwalliya da gashin jimmina, shinfiɗar ta haɗu sosai da sosai, tana cikin alkyabbarta, ta zuba gwala-gwalai ɗin nan a hannu da wuya dam kamar ba za'a mutu ba, daga samanta har kasa dukiya ne aka narka. A in da take zaunen nan cikin minti ɗaya idan ta buƙaci kuɗi sama da 100 million a take za'a bata, kada ku manta Rizwan ɗan farinta ne, ga Yah Jawad shima yana da nasa company's ɗin, uncle Abbas ba'a magana, kuɗi ta ko'ina, amma ita fa duk basu a cikin plan ɗinta, sai ka rasa me take nema a duniyar nan to. Ta ɗaura kafa ɗaya biya ɗaya, ta baza alkyabbar nan tata a wajen gabaɗaya, ta wani dake sai ɗage hanci sama take yi, tana zaune ne a wajen shan iskan uncle Abbas da yake a cikin part ɗinsu, uncle Abbas ɗin kuma baya nan, ga wasu ƴan matan kuyangu biyu a kusa da ita, ɗaya tana zaune ta gefenta na dama, ɗayar kuma tana zaune a gefenta na hagu, ga wasu uban tulin kayan marmari dake a cikin wani kyakkywar kwando da suka jibgemata a gabanta, very fresh kayan marmari ne, sai wani fadanci take yi kamar ita ce Queen of the Kingdom ɗin na ainahi, ko mummyn Gimbiya Chuchu uwar gidan King Zuhair bata irin wannan fadanci sai ita. A hankali iskar bishiyoyin dake wajen suke kaɗata, ga kuyanga ɗaya tana yi mata fifita da maficin gashin jimina, an kawata in da take zaune ɗin da luntsuma luntsumar throw pillows masu girma. Wata Kuyanga ce ta shigo cikin wajen, sai sauri take zubawa kamar zata kife kasa, da alama an ɗebo gulma fal ciki, shiyasa ake sauri kada ciki ya fashe gulmar ta zube a hanya. A gaban wannan shunfuɗa ta zo ta zube gwiwowinta tare da fara zuba kirari na girma ga Mammie ɗin. Kara dakewa ta yi cikin alkyabbar nan tata. Sai da ta ɗauki a kallah minti biyar tana sauraran wannan kirarin kafin ta ɗagawa kuyangar hannu alamar ya isa haka ta dakata, sannan cikin nuna isa ta yi wa kuyangun dake wajen nata umarni da su bata waje zata yi magana da wannan kuyanga da ta shigo a yanzu. Cikin hanzari suka miƙe suka fice daga wajen. Akwai sadaukan yaki biyu dake gadin kofar shigowa wajen shan iskan, dan tsaro. Ko da suka fita sai da ta sake ɗaukar good two mins kafin ta ce. "Bintu meyafaru kika shigo da sauri haka?". Ƙasa ta ɗan yi da kai kafin ta ce. "Allah ya kara maki tsawon rai, farar mace mai farar zuciya, Allah ya ja da ranki wlh yanzu ne ma Yah Jawad yake ƙara kula Gimbiya Chuchu sosai, daga majiya mai karfi na jiyo cewa har yanzu bai dai'na kulata kamar yadda kika hana shi ba, yanzu ma sai abin da ya cigaba sosai". Cikin girmamawa ta yi maganar. Shiru Mammie ta ɗan yi kafin ta ce. "Shikenan je ki ki cigaba da yin aikinki, ki saka ido sosai, sannan kada ki kuskura ki kawo mun maganar da ba haka ba, ki tabbatar da ingancin magana kafin ki kawo mun". "In Sha Allah ranki shi dade, Allah yaka maki girma da ɗaukaka". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye ta nufi waje. Da kallo Mammie ta bita har ta fita, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Bintu tana fita sai ga kuyangu biyun can sun dawo ciki. Wajen zamansu suka koma suka zauna, suna zama wayarta dake saman throw pillow dake kusa da hannunta ne ta fara ruri alamar shigowar kira. A hanzarce ɗayar kuyangar dake ta wannan bangaren ta yi sauri ta ɗauko wayar ta miƙa mata. Sai da ta sha kamshi kafin ta karɓi wayar. My son, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar, ajiyar zuciya ta sake saukewa kafin ta ɗauki kiran. Sallama ta yi cikakke. Daga ɗayan ɓangaren Rizwan ya amsa mata cikin girmamawa tare da ɗaga mata gaisuwa. "Lafiya lou Alhdulillah my son, ya aiki?". Da Alhdulillah ya amsa mata kafin shi ma ya jefa mata tambayar ya gida ya kowa da kowa. "Kowa yana nan lafiya, amma ka tambayeni kowa baka tambayeni ya matarka ba?". Cikin nuna halin ko in kula ya ce. "Wacece kuma matata?". "Wai kai Rizwan kullum sai ma na tuna maka wacece matar taka ko? Ya yi maka kyau, ka cigaba da yi mun kamar ni kakarka ce". "Kai Mammie bafa haka bane, duk lokacin da zaki gaya mun wacece hankalina yana kan wani abin ne, but yanzu gaya mun zan rike ba zan manta ba". Shiru ta ɗan yi kafin ta amasa masa. "Jannat mana ko in ce Chuchu tun da da shi kuka fi saninta, tana ta kara girma, yakamata fa ka kawo mana ziyara, ni kam yanzu fa kun kai almost 12 to 14 years haka rabonku da masarautar nan fa ko? To yakamata ku zo gaskiya, matarta ta girma kuzo ku yi aure sai ku koma". Chuchu kuma?! Tashin hankali to me Mammie take nufi? ta dai san Yah Jawad yana son Chuchu, kenan dama da gangan take hana shi kulata dan Rizwan take sonwa? To amma menene banbancin Rizwan ɗin da Jawad ɗin da zata hana kanin ta yi wa yayansa sha'awarta? Akwai matsala babban kuwa in dai haka ne, domin kuwa in dai tasa Rizwan ya fara son Chuchu shi kuma Jawad fa? Wai ni kam me Mammie take so ne a duniyar nan? Ita sam bata son zaman lafiya! Ba'a taɓa gane ina ta dosa sam sam! Mata kamar wata aljana ko shaiɗaniya! Sai iya haɗa makirci da faɗa! So take ta kashe Jawad ne ko me? Bawan Allah shekara kusan 11 yana dakon soyayyar Chuchu? Anya wannan abin ba zata tarwatsa mashi zuciya ba? Yayansa uwa ɗaya uba ɗaya, tashin hankali akwai rikici kam ba kaɗan ba, Mammie da alama zata kashe ɗanta da hannunta, ko me dalilinta na yin hakan kuma? Mu dai je zuwa, sannu a hankali komai zai warware. Hmmm ga shi shi kuma Jawad bai sani ba, yana ta wahalar da Chuchu har yasa ta fara tsanarsa, akwai rikita rikita ba kaɗan ba kuwa a nan gaba! Da alama nan gaba kaɗan kingdom of power zata kama da wutar bala'i, kai tabɗijam!!!. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Kai Mammie yanzu waye yake da lokacin yin wani abu wai shi aure? Ki bari idan lokacin yi ɗin ya yi zamu zo, but now ayyuka sun yi mana yawa, bamu da lokacin kanmu ma bare na wata mace, just ki bari kawai.........". Cikin hanzari ta katse shi da cewa. "Naki na bari ɗin, sai fa anyi, bari ma zan turo maka hoton Chuchun sai kaga yadda ta girma ta kara kyau, nasan ma kana ganinta zaka ce ka yarda kawai daddynku ya ɗaura maka aure, dan ta girma, kuma nan da two weeks kawai na baka kazo ka ganta da idonka". A takaice ya amsa mata da. "Okey Mammie yadda kike so hakan za'ayi, yanzu dai aiki nake yi, anjuma zamu yi waya, dama nakira ne na ji ya kike? Tun da kina lafiya shikenan". Da haka suka yi sallama, wani irin murmushi mai wuyar fassaruwa ta saki tare da miƙawa wannan kuyangar wayar, sannan ta gyara ta ɗan kishingiɗa a saman wani throw pillow dake kusa da ita, ta kai hannu ta ɗauki tuffa guda ɗaya, a hankali ta fara jujjuya tuffa ɗin tana sakin murmushi, sai Allah kaɗai yasan tunanin me take yi. A can cikin gid kuwa, kwance Auta da Gimbiya Chuchu suke a saman bed ɗin Akka, dogayen riguna iri guda ne a jikinsu, kayan ya yi masu kyau sosai, babu ɗan'kwali a kansu, kamar kullum ɗauri biyu suka yi wa arab hairnsu, sai hira suke zubawa kamar wasu ƙawaye, sai labari Gimbiya Chuchu take bawa autar a kan yadda suka yi da Yah Jawad, sai murmushi auta take yi mata. Jin wani daddaɗar kamshin perfume ya daki hancinsu ne yasa suka ɗan ɗago kai a tare suna bin kofar shigowa da kallo. Yana tsaye ya harɗe hannu a kirji yana ta kallonsu, Allah ya gani yana kaunar kannen nan nasa sosai, ko su Sarina da suke uwa ɗaya uba ɗaya ma baya jinsu sosai a ransa kamar yadda yake son Chuchu da Zunaira, saboda kyan halinsu, sam baya shiri da Sarina, ya fi kaunar Fanan a kan Sarina, ita ta cika rashin ji ne sosai shiyasa. Cikin hanzari suka miƙe zaune a tsakiyar gadon. "Yah Jawad good evening". Cewar auta. Ɗan sake fuskarsa kaɗan ya yi tare da ƙarisowa cikin room ɗin yana amsa mata gaisuwar. Saman bedside drawer ya zauna tare da tambayar su ina Akka?. Still auta ce ta bashi amsa da Akka tana fada, suna can suna zama ne a kan yakin da King Zuhair yake son su yi da wancan masarautar, so Akka tana wajen, kunsan halinta sarai ba wasa, Akka bata son wargi, akwai zafin nama, tana can tana bada shawarar ayi yaki, nan ko takobi ba iya riƙewa zata yi ba, sai baki .........😅 "Auta jeki room nawa ki kwaso mun wayoyina dukka kin ji?". Ya faɗa yana dawo da kallonsa kan fuskar chuchu da ta yi ƙasa da kai, ko gaisuwa bata ɗaga mashi ba, ta tsorata ne dan tana tunanin ya ji hirarta ita da auta, idan ya ji tasan zai hukuntata, saboda ya ce kada ta gayawa kowa ya bata punishment, amma ta zo ta bawa auta labari har da cemata ai ta tsani Yah Jawad ɗin nan, to tana tsoron ace ya ji ne, dan basu san tun yaushe ya shigo ba, ita kuma a gaskiya ba zata iya ɓoyewa auta komai ba, komai aka yi mata sai ta bata labari, haka ita ma autar take, komai sai ta gayawa Chuchu ɗin. Saukowa kasan gadon auta ta yi tare da nufar kofar fita tana faɗin okey. A hanzarce ita ma Chuchu ɗin ta sauko da nufin ta fake da raka auta ta gudu. "Come here". Ya faɗa a sanyaye. Jiki ba kwari ta juyo ta dawo. Da hannu ya nuna mata saman bed ɗin ta kusa da drawer da yake kai a kan ta zauna. Ba musu ta zauna tare da takure jikinta waje guda ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Yau ba zaki gaishe ni bane Jannat?". Ya yi maganar yana mai da kallonsa a kan ƴan yatsun hannunta dake ta faman ƴan kerma. "Ka yi hakuri na manta ne good evening". In a cool voice ta yi maganar. Hannu ya kai ya riƙo ƴan hannayen nata cikin nasa. "Meyasa kike jin tsorona har haka Jannat?". Girgiza kai ta yi tare da cewa babu komai. "Meyasa kika gayawa auta na baki punishment? Kuma meyasa zaki ce mata kin tsaneni? Me nayi maki da zaki tsaneni?". Yadda ya yi maganar ƙasa ƙasa kamar wadda aka yi wa dole yasa ta yi saurin ɗago kanta. "Meyasa kika ce kin tsaneni e Jannat?". Ya sake jefa mata tambaya a karo na biyu. Kai ta fara girgiza mashi tare ce mashi.......... *Masu tambayata cewa sunan Raj na musulmai ne koma krista, sunansa ba Raj ba ne, SURAJ ZUHAIR ABDUL MALIK yake, ƴan uwan nasa ne suka yanke sunan daga DR SURAJ zuwa RAJ, so sunan musulmai ne fatan kun gane?. Duk wani suna da na saka a cikin littafin nan suna ne masu ma'ana mai kyau, sunan larabawa ne, kuma kowanne zan rubuta maku ma'anoninsu, zaku iya sakawa yaranku idan ya yi maku.💘🌼* 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 27/8/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________39🔥 Those who are asking me for complete of RAWANIN ZALINCI babu complete ɗin, yanzu nake posting ɗinsa, hakuri zaku yi ku cigaba da bibiyar su Kamran ɗin nan har muga me Allah zai yi🥱 much love my people's 💘🔥 "Meyasa kika ce kin tsaneni e Jannat?". Ya sake jefa mata tambaya a karo na biyu. Kai ta fara girgiza mashi tare ce mashi. "A'a ban tsaneka ba Yah Jawad". "Amma ai na ji da kunnuwana kin cewa auta baki sona, duk cikinmu ni kika fi tsana why?". Shiru ta yi bata da bakin magana, ta kuma kara yin ƙasa da kanta sosai. "Ɗago idanunki ki kalleni sai ki bani amsa ta ko?". Bata iya ɗago idanun nata ba, sai dai ta ce mashi. "Ka yi hakuri ba zan sake ba, kuma ni na dai'na tsanar taka daga yanzu". "To amma me nayi maki da yasa tun farko kika fara tsanar nawa?". Ya kai karshen maganar tare da sakin hannunta guda ɗaya, ya kai hannun nasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. Ƙasa ta yi da idanunta tare da yin shiru. "Me na yi maki tun farko Jannat da yasa har kike ikirarin kin tsaneni?". Ɗan turo baki ta yi kafin ta amsa da. "To Yah Jawad ba kai ne kake saka ni kneel down ba, kuma sai ka rinƙa ja mun ga shi kan......". Shiru ta yi ta ƙasa ƙarisa maganar sakamakon ji da ta yi ya saki ɗayar hannun nata ma, a tunaninta wani laifi ta sake yi yasa ya saki hannun nata zai daketa. "Shi ne yasa kika ce kin tsaneni ni?". Yana magana yana kara ɗago haɓarta da kyau. Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar e. "Okey to buɗe ido mu yi magana". Ba musu ta ɗan buɗe idanun nata, sai dai taki yarda su haɗa ido. "Am so so sorry da punishment da na rinƙa baki, na yi haka ne nima ba'a son rai na ba, amma ki mun alƙawarin abu guda ɗaya, ni ma kuma ba zan sake baki punishment be kin ji?". Ɗago idanu ta yi zata saci kallonsa, sai ta tarar da ita yake kallo. "Na yi maka alkawari In Sha Allah". Ta amsa mashi tun ma bata ji me zai ce ba ko akan me zata yi alkawari ba ta riga da ta yi. Shiru ya yi bai gaya mata alkawarin me yake son ta yi ɗin ba, tun da ta amsa mashi da ta yi sai ya kawar da zancen da cewa. "Kada ki sake cewa kin tsani wani daga cikin gidan nan, bama ni ba koma waye, mu ba ƴan uwanki bane? Idan kika tsanemu to su waye zaki so? Amma tukun nan ma anya Jannat kin san me kalmar tsanar nan take nufi ma kuwa?". Shiru ta yi tana tunanin ya zata gaya mashi yadda ta ɗauki tsana a nata tunanin. "Me tsanar mutun yake nufi?". Ya jefa mata tambaya yana sakin haɓar tata ya koma ya riƙo hannayen nata a cikin nasa kamar ɗazun. "Tsana yana nufin kamar idan mutun yana yi maka abin da baka so sai kana jin babu daɗi sai kawai ka tsane shi". Ta bashi amsa a kwakkwaɓe. Sai yanzu ma ya fahimci ita bama ta san ainahin menene ma'anar tsanar ba, haushin mutun shi take ɗauka a matsayin tsana, tsana kuma daban jin haushin mutun daban, mutun zai iya yi maka abin da baka so a lokacin ka ji haushinsa, daga baya idan ka huce komai ya wuce ku koma normal, shi kuma tsana daga zuciya yake, idan mutun ya tsaneka da gaske to mawuyacin abu ne ya dawo daga baya ya soka ko me zaka yi mashi kuwa. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan matsowa kusa da ita kaɗan, sannan ya kai hannunsa ɗaya yana shafa arab hairnta. "Da ga yau ba zan sake baki wani punishment ba, amma kema ki dai'na yin duk wani abin da bana so kin ji?". Cike da murna ta ce. "Da gaske Yah Jawad ba zaka sake bani wani punishment ba?". Kai ya gyaɗa mata alamar e. Cikin sauri ta faɗa jikinsa tana dariya, kamar ba ita bace yanzun nan take ƙoƙarin saka mashi kuka, Allah sarki ashe wannan punishment ɗin da yake bata abin yana matuƙar damunta, yana yi mata ciwon da kullum yana ranta, to yau dai an dena, ai sai murna kawai. Ɗan rungumeta kaɗan ya yi tare da cewa. "To ai ni kuma baki tambayeni me bana so ba domin ki dai'na aikatawa". Tana kwance a jikinsa ta amsa da. "Ai na dai'na komai ma, amma dai tom gaya mun sai na kara dai'nawa". Shirmenta ya fara saka shi farinciki da murmushi, wai komai ma ta dai'na, ita da bata san ainahin dalilin da yasa a kullum suka haɗu sai sun sami saɓani da shi ba, amma wai ta dai'na, har da wani zata kara dai'nawa. Murmushi kaɗan ya ɗan sakar mata kafin ya ce. "To promise me that za'a rinƙa sanya ɗan'kwali one! Two kuma za'a rinƙa sanya hijab idan za'a fito da sleeping dress!". Ita dai tun da babu zancen punishment a yanzu ai shikenan, dan haka sai ta ce "I promised you ba zan sake yi ba dukka". Kara rungumeta da kyau ya yi. "Yah Jawad to hoto fa?". Ƙasa ƙasa ya amsa mata da. "Ki cigaba da ɗaukar kayanki, ba zan takura maki ba, dan kada ki sake tsanata". Ƴar dariya ta yi tana faɗin. "A'a ba zan kara tsanarka ba ai". "Promise?". In a low voice sosai ya yi maganar. Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar e. "Okey tom shikenan jeki shirya sai kizo ki rakani wani waje, amma kada ki bari kowa fa yasan cewa zaki rakani wani waje, kawai idan kin gama shi sai ki kirani a waya zanzo mu tafi". Cike da murna ta zaro idanu tana faɗin. "Yah Jawad wajen Kingdom zamu fita?". Basu taɓa fita waje haka wai yawo ba, sai dai idan Dubai zasu tafi, shi kuma Dubai daga cikin gida idan suka shiga mota sai airport kai tsaye, shi ma Dubai suna jimawa sosai, school nasu ma kunga a cikin kingdom ɗin yake, ba su taɓa leƙa waje su ga gari ba, suna son zuwa yawo suga gari, amma ba hali, ko shopping za su je yadda kuka san menene, a mota za'a kaisu, a jira su ɗauki abin da suke so, sannan a dawo da su har cikin gida, basu fita ko nan da can, su ko irin taro na sarakuna da ake yi kowa ya je da iyalensa King baya yarda, baya son yaga suna yawo cikin mutane, shi King ai sai dai a zo a same shi a cikin kingdom ɗinsa, ba kowani taro yake zuwa ba bare ma har ya je da ƴaƴansa, yana da doka mai tsaurin gaske ne shi ɗin, ga bala'in ji da kai kamar me, baya ɗaukar rai'ni ko wargi. "Wajen Kingdom kike son mu je?". Yana magana yana cigaba da shafa arab hairnta. A hanzarce ta ɗago kai daga kirjinsa tana faɗin. "E ina son mu fita waje naga ya yake?". "Tom shikenan jeki shirya, kada dai ki bari kowa yasan zamu fita". Tana ƙoƙarin miƙewa sai kuma ta dawo ta ce "Harda auta kada na gaya mata?". Ya fahimci bazata iya ɓoyewa auta komai da ya danganceta ba, so ko ya hanata ma sai ta faɗa mata koda a sace ne, is better for him da ya kyalesu a yadda suka taso kada ya ce zai yi ƙoƙarin sakawa lallai sai chuchu ta ko ɓoyewa auta wani abin nata, idan ya ce zai yi hakan to tabbas zai haifar da matsala a tsakaninsu, gara ya kyalesu kawai, akwai gaɓar da idan anzo wajen da kansu ma zasu ɓoyewa juna wani abin ba sai an ce masu sirrinsu bane. So dan haka sai ya ce. "Ki ɓoyewa kowa amma ban da auta, kin manta ke da ita ɗin hanta da jini ne? Ai bazama ki iya ɓoye mata ba na sani, da wani ɗan bakinki a wajen kamar da gaske idan na ce kada ki gaya mata ɗin ba zaki faɗa ba, ni da nasan ko a ɓoye sai kin gaya mata". Ƙara shigewa jikinsa ta yi tana dariya kamar bakinta ba zai rufu ba, ya harbo jirginta, domin kuwa dama ko ya ce kada ta gayawa auta sai ta faɗa mata koda a ɓoyene kamar yadda ya faɗa ɗin, so sai abin ya bata dariya. A haka auta ta shigo ta samesu, a kusa da chuchu ɗin ta zauna tare da miƙo mashi wayoyinsa kamar yadda ya ce ta ɗauko mashi. Karɓa ya yi ita kuma Chuchu ta tashi daga jikinsa tana mai cigaba da murmushi. "Aunty Chuchu dariyar me kike yi?". Auta ta tambaya. "Yah Jawad ya ce zamu je wani waje". Ɗan zaro ido autar ta yi tare da kai kallonta kansa. "Yah Jawad waje zaka kai mu?". Gera kawai ya ɗaga mata yana ƙoƙarin kunna hasken screen ɗin wayarsa. "Zunaira jeki ki fara shiryawa ba ɓata lokaci kinga yamma ta yi". Ya faɗa yana kan bin screen ɗin wayarsa da kallo, miss call ɗin Yah Rizwan ya gani har uku a wayar tasa. Da sauri autar ta miƙe ta nufi waje, sai murna take yi. Miƙewa ita ma Chuchun ta yi zata nufi waje da ɗan saurinta. Yana ƙoƙarin kiran number Rizwan ɗin ya riƙo hannunta da hannunsa ɗaya. Juyowa ta yi tana kallonsa, da ido ya nuna mata wajen da ta miƙe a kan ta koma ta zauna. A hanzarce ta koma ta zauna sai sakin ƙayatattcen murmushi take yi. Murza ƴan yatsun hannunta a cikin nasa ya fara yi dai'dai lokacin da Rizwan ya yi picking na call ɗin. "Assalamu alaikum Yah Rizwan". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a saman face ɗinta. Murmushin nan nata yana ƙayatar da shi matuƙa. Daga ɗayan ɓangaren ɗan uwan nasa ya amsa mashi da. "Jawad ina ka yasar da wayar taka kuma tun ɗazun nake kira baka ɗauka ba?". "Sorry yaya na barota a ɗaki ne ina wajen Akka, amma lafiya kuwa?". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "E to kusan hakan dai, ɗazun na kiraka mu yi magana baka ɗauka ba, but yanzu ina yin wani aiki idan na gama zuwa dare sai mu yi magana". "To amma Yaya lafiya dai ko? Ko dai na zo ne?". "Kazo kuma?". Ya jefo mashi tambaya a takaice. "E mana yaya nazo idan da wata matsala". "Ni nace maka da wata matsala? Ba zan kiraka mu yi magana ba sai idan da akwai wata matsala?". A'a ya amsa mashi da shi. "Okey tom babu wata matsala, nima ai na kusa kawo muku ziyara, Mammie wai ta yi mun mata, kuma wai dole na zo naga matar ido da ido, ka dai san halinta idan ta sako mutun a gaba, bani da lokacin yin aure a yanzu, amma zan zo ɗin kamar yadda ta buƙata, dan farincikinta kuma nasan ma ba kyaleni zata yi ba idan ban zo ba, ta rinƙa takura mun kena, idan na yi wasa ma sai ta shirya mun abin da ba haka ba, akan ta yi mun abin da zai sani ɓacin rai na har abada gara dai na bi umarninta a hankali mu rabu lafiya". Guntun murmushi Jawad ya saki kafin ya ce. "Wlh gara kazo ka yi abu da kanka, idan ba haka ba kana can Mammie zata iya sanyawa a aura maka yarinyar da baka ma santa ba, kuma dole ka karɓa ba yadda zaka yi da ita, kaga kuwa idan hakan ya faru kana cikin ƙunci, so is better kazo kaga matar idan bata yi maka ba sai ka ce ta duba maka wata....." Tarar numfashinsa Rizwan ɗin ya yi da cewa. "Ai kasan zaɓin Mammie ba yadda na iya da ita, dole zan karɓa, kuma nima ai ban isa in ce bana son matar ba ai, a cikin yaran daddy wai ta yi mun mata, kuma dai yarinyar like zata yi dai'dai da ra'ayina duk da cewa ban wani kalli pic's ɗinta da kyau ba, muna hira da Ramish lokacin da Mammie ta turo mun hotunanta, amma dai zuwa anjuma idan na nutsu zan sake duba hotunan da kyau, ko a iya yanzu naga yarinyar like ba laifi". "Awww wai dama a cikin yaran daddy ta yi maka mata? Tab to ai wannan zaɓi babu canji kenan, baka isa ka ce baka so ba, dole ka karɓa, shikenan Allah ya kawo lokacin yin aurenka na yi farinciki sosai da hakan, amma kasan me yaya?". A'a Rizwan ya amsa mashi da shi. Ɗan murza yatsun hannun Chuchu dake cikin nasa da ɗan karfi ya yi, hakan yasa ta ɗago kanta tare da kallonta izuwa kansa tana mamakin wai dama yana magana har haka? Bata san sai dai idan basu haɗu ba, ko shi da Jaish suna hira sosai idan suka zauna. "Ina ga idan kazo tare kawai za'a haɗa auren namu ayi a wuce wajen". Yana magana yana kallon face ɗinta. Ita ma ta lula duniyar tunani tana kallon face ɗinsa a zahiri, a baɗini kuma tana duniyar tunani tare da mamaki a kan yau dai ɗaya ta ji yayyunta suna maganar aure, abin da bata taɓa ji ba a bakunansu. "Kai Jawad a ina ka samu mata kuma? Ko dai kaima Mammie ta yi maka irin abin da ta yi mun ne? Ita ta zaɓa maka ko?". Girgiza kai ya fara yi kamar yana a gaban ɗan uwan nasa, sannan ya saki hannun Chuchun tare da ɗan rungumo shoulder ɗinta, ya dai'dai nutsuwarsa kafin ya cigaba da yin magana. "Babu wanda ya zaɓa mun ita, ni da kai'na na zaɓota, ita ɗin ta daban ce". "E lallai Jawad ba shakka kana cikin soyayya, to dai shikenan zamu yi waya anjuma". Yana kai karshen maganar ya katse kiran diff, da alama yana yin wani abin ne. Shiru shi kuma Jawad ɗin ya yi yana jin wani irin a cikin zuciyarsa, haka kawai yau tun da suka fara waya da yayan nasa yake jin babu daɗi a cikin zuciyarsa, yanzu kuma Rizwan ɗin yana katse kiran sai ji ya yi ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, bai taɓa jin irin hakan a tattare da shi ba. Hasbunallahu wani'imal wakil ya furta a cikin zuciyarsa tare da sakin shoulder ɗinta, ya miƙa mata ɗayar wayarsa yana faɗin. "Wayarki babu caji ta mutu, ki rike wannan nawan idan kin gama shiri sai ki kirani da ita, bari nima na je na duba daddy sai na je na shirya yamma tana yi". Yana kai karshen maganar ya miƙe tsaye tare da nufar hanyar fita haka kawai yake jin zuciyarsa babu daɗi tun da suka yi waya da yayan nasa. Cike da murna ta miƙe tsaye hannunta rike da wayar tasa, bin bayansa da kallo ta yi har ya fice hannunsa na rike da wayarta da ɗayar tasa. Yana fita ta dawo da kallonta a kan wayar tasa, kunna hasken screen ɗin wayar ta yi, a hankali ta kai hannu ta fara taɓa wayar, da alama sai da ya cire password ɗin wayar kafin ya bata, domin babu password. Cikin wayar ta fara shiga kamar ya aiketa, dube dube ta rinƙa yi mashi har ta shiga cikin gallerynsa, ita da ya ce ta shirya da wuri. Ta sha madarar mamakin ganin uban tulin pic's ɗinta a cike a gallery ɗin nasa, iya pic's ɗinta da kuma design na gine gine da companynsa take fitarwa ne kawai suka cika galleryn nasa, sake baki ta yi tana kallon pic's ɗin, mamaki take yi a ina ma ya samosu? Wasu pic's ɗin ma bata sani ba aka ɗauketa, wani suna saman dining table suna cin abinci tun bata kai shekarun haka ba, wani tana sanye da uniform zasu tafi school, wasu tana kwance a gadon Akka, wasu kuma a fada wajen King, hotuna ne dayawa iri daban daban da duk ba wanda ta san da su a cikinsu. Ta jima a tsaye tana ta ganin hotunan, wani waje ita da kanta idan ta gani sai ta kwashe da dariya, dan duk hotunane da aka ɗaukesu a sace, so dole wani ya baka dariya. Ta ɓata lokaci sosai wajen ganin hotunan kafin ta tuna cewa yana jiranta, dan haka sai ta yi sauri ta wuce izuwa room nata da yake a ɓangaren Akka ɗin dan ta shirya. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ 🏞️FOREST🏞️ Kamar yadda Kamran ya tsara hakan ya yi, ya yi tafiyarsa har sai da Mamma ta sauko daga dokin zuciya da ta hau ta bazama nemansa a cikin dajin, dama ashe yasan ba zata iya hakura ta share shi ba, shiyasa ya yi mata wannan tsiya, yasan halinta in and out. Ai kuwa ko da ta je ta same shi kwance a saman irin bishiyoyin nan masu fitowa a kwance, cikin sanyin murya ta fara lallaɓa shi a kan ya tashi su koma. Amma da yake ya san lagonta, yana fa jin yunwa kamar me, amma dan tsiya sai ya kafe mata a kan shi babu in da zai je ta kyalesa kawai a nan tun da bata sonsa, komai ya yi mata sai ta yi magana, yanzu ta dai'na sonsa, shi wai me ya yi mata ne da ko waje bata son ya rinƙa leƙawa? Shin ita bata son farincikinsa ne? Ba zata barshi ko ɗan yawon nan ya rinƙa zuwa yana rage kewa ba?!. Lallaɓa shi dai ta cigaba da yi, tuni ta mance da batun kitson da Hajiya Pretty ikon Allah ta yi mashi, yanzu burinta kawai ya dawo gida, dan tasan shi da shegen zuciya, ba ƙaramin aikinsa bane ya kwana a wajen nan, tana matuƙar kaunarsa, dama annabi ya ce abin da kake so a nan jarabawarka take, duk abin da ka sanya a ranka kana son shi to wlh a nan Allah yake gwada imaninka, nan jarabawarka take, to ita ma dai Mamma Kamran shi ne rauninta gaskiya, bata iya jure ganinsa cikin ɓacin rai, dan dole take hakura idan ya yi fushi ta hau lallashinsa. Yana jin yunwa kamar me, amma sai da ya tsaya ya ja mata rai sosai, sannan ya miƙe suka nufi gida. Yana zuwa bai tsaya yin wanka ba kawai ya fara neman abinci, dama a hannu yake, kawai juriya ce saboda ya waskewa mamma, amma yunwar tana nan. Sai da ya ci ya ƙoshi sannan ne ya miƙe da nufin ya je ya yi wanka. Da ido kawai Mamma take binsa, sai dai ba irin kallon yau da kullum take yi mashi ba, wannan kallo akwai alamar tambaya sosai a cikinta. Wanka ya yi ya wuce makwancinsa ya kwanta abinsa, zuciyarsa cike da tunanin su Pretty barci ta yi awon gaba da shi. Can cikin barci da yamma sosai rugugi da tsawar ruwan sama suka tada shi daga barci, a hankali ya waro idanuwansa da suka yi mashi nauyi sosai saboda barci. Jin yadda garin yake ta famar haɗewa da hadari ga tsawa da walkiya ta ruwan sama yasa ya kara waro idanuwansa waje tare da miƙewa zaune, a hanzarce ya zuro kafafunsa ƙasa tare da miƙewa tsaye. Kamar wadda ya yi wani ajiya a waje haka ya nufo wajen da zafinsa. Mamma tana barci, dan ta sha aiki ta gaji. Kai tsaye fita ya yi, gari ta yi bakinkirin da hadari, sai walkiya dake tashi, iska suna ta kaɗa manya da kananan bishiyoyi, ruwan ƙoramar na kaɗawa. Da sauri ya sauko kasan tsaunin nasu, Rocky baya nan, da alama ya yi gaba abinsa, ya tafi yawo. Kai tsaye wajensu Pretty ya nufa, dan da tunaninsu ya yi barci, da kuma su ya farka a ransa, yana son kafin ruwan saman nan ta sauƙo ya je ya duba su, dan yasan wannan ruwa idan ta zubo tofa takan iya kai cikin dare tana zuba, so gara mashi ya je wajensu in ya so ya dawo cikin ruwan ta jiƙa shi, amma dai ya je ya gansu kam. Sosai yake zuba sauri cikin takun jarumta, babu tsoro ko ɗigo a ransa. Yana zuwa ya yi maza ya afka cikin ramin nasu. Sweetie ce kawai zaune a saman wani dutse hannunta na rike da wannan abin mai haske da suke farfasa abu da shi ko su daka wani abin da shi, ɗayan hannunta na rike da wani irin nau'in fruits mai kama da ruman tana sha. Baiwar Allah tana sanye da kayan da Kamran ɗin ya kawo masu na sakar audiga, ta yi matuƙar kyau sosai da sosai, kayan suna yi masu kyau, ga idanunta tas, wlh sai ka rantse da Allah tana gani, gasu tankar da su a buɗe, amma ba abin da take iya gani face duhu, yana ya rufe idon daga ta ciki. Jin motsi yasa ta fara faɗin. "Kin dawo kenan? Dama na gaya maki ba zaki iya zuwa in da Kamran yake ba, ke da bama kisan daga ta ina yake zuwa ba, kawai ki ce ke kina kewarsa zaki je ki kirasa, Allah Pretty baki jin magana, wai da can kece kike kiransa ya zo ne? Ba shi da kansa yake zuwa ba? Sai kin je kin ɓata hanya ai zaki yi bayani". Zaro idanu waje sosai ya yi tare da faɗin. "Sweetie ina Pretty ɗin ta tafi?". Ita ma ɗan zaro ido ta yi kafin ta ce. "Kamran kai ne?". E ya amsa mata tare da sake tambayarta ina Pretty ɗin ta je?. "Wai ta tafi nemanka dan tana kewarka sosai, tun ɗazun da ka tafi baka dawo ba shi ne wai ba zata iya hakura ba ta je nemanka". Dafe kansa ya yi tare da juyawa a guje domin ya bi bayanta. "Kamran! Kamran!". Sweetie ta fara kiran sunansa. Ina ai tuni ya fice, bai sake bi ta kanta ba, dan kada ma ya biye mata Pretty ta je ta faɗa wani wajen. Yana fitowa ya fara ƴan waige waige yana tunanin to shi yanzu ta wani hanya zai bi ya je ya nemo wannan rigimammiyar yarinyar?. Fara nemanta a ɗan kewayen wajen ya yi ko Allah zai sa ya ganta bata yi nisa ba, har haɗa zufar dole ya fara yi, damuwarsa ɗaya shi ne kada ta je a garin nemansa ta isa ga in da Mamma take. Sosai ya fara nemanta ta yankin waje, ya je ya dawo ya je ya dawo, duk ya wahala ya galabaita, ya kuma shiga cikin tsananin tashin hankali da damuwa, duk ya ruɗe, har idanuwansa sun yi jajir saboda shiga damuwa, ga hadarin ruwan sama yana ta kara tsananta. Idan ka gansa sai ya baka tausayi, sai ka rantse an raba shi da Pretty ɗin kenan, wannan ya kenan idan aka ce za'a rabasu? Ya zai yi da ransa? Ina zai sa kansa? Sun rigada sun zama jinin jikinsa, suma ba zasu iya rabuwa da shi ba, kunga dai bai wani jima sosai da barin wajen nasu ba, barci ne ya dauke shi har lokacin da yake dawowa ya yi bai dawowa ba, amma Pretty ta kasa iya hakura har ta tafi nemansa, hakan zai kara tabbatar maku da suma ba zasu iya rabuwa da shi ba, dukkansu biyu suna kaunarsa sosai. Babbar magana akwai case ranar da Kamran ya bayyana da gaske waye yake so a cikinsu tab!!. Sosai ya galabaita sai haki yake yi, amma babu ita babu alamarta, kai kamar ma ba'a taɓa yin mai kama da ita ba a duniya. Har kusa da gidansu ya je nemanta, amma shiru. Nufar wajen ƙoramar da suke zama ya yi yana ta mayar da numfashi tare da sauke ajiyar zuciya. Tun daga nesa ya hangota kamar wata macijiya tana tsaye a samar dutse kamar ƴar tsana tana aikin data saba, wato dai tana sanya hannunta a cikin ruwan koramar ruwan yana fallatsuwa mata a saman fuskarta, hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, mayyar son ruwa ce sosai, ko da yake dama dole ai su so ruwa sosai, duba da in da suka taso. Ita ma Sweetie ba baya ba wajen shegen son ruwa, shi ne abin wasansu da kuma ɗebe masu kewa, idan suna jin kewa cikin ruwan ƙoramar suke zuwa su shiga yana jiƙasu suna jindaɗi. A dubu ɗari ya ƙariso wajen yana sauke numfashi dan ya tabbatar da cewa ita ɗin ce ko ba ita ba. Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya kalli cewa ita ɗin ce, tana sanye da riga da sket wanda ya fara ganinta da shi, ta ɗaure gashin kanta kamar dai ranar da suka fara haɗuwa. Cikin wani irin farinciki ya ambaci sunanta tare da ƙarisowa wajen yana murmushin da shi kansa bai san yana yi ba, ya ji daɗin ganinta, da bai ganta ba yau ina zai sa kansa? Ta wahalar da shi ashe tana nan tana aikin da ta saba. Jin voice ɗinsa yasa ta juyo tare da dirowa kasa, da gudu ta faɗa jikinsa tana dariya tare da gaya mashi ta yi kewarsa sosai. Rumgumeta ya yi shima yana murmushi mai ƙayatarwa, alamar suna cikin tsantsar farinciki da ganin juna. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 28/8/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________40🔥 Rumgumeta ya yi shima yana murmushi mai ƙayatarwa, alamar suna cikin tsantsar farinciki da ganin juna. Ruwan sama ne mai karfin gaske ya kece kamar da bakin kwarya. A ɗari ta sake shi tana faɗin. "Kamran mu gudu cikin raminmu ruwan sama". Hannunta ya riƙo shi ma yana faɗin. "Me ruwan saman zai yi maki sarkin tsoro? Babu komai, zu mu zauna a saman dutsen nan kina mana busa ruwa na jiƙamu". Ɗan turo baki ta yi. "Kamran akwai sanyi fa ruwan". Jan hannunta ya yi suka koma saman dutsen suka zauna. "Ai haka kike so, shi ma ruwan ƙoramar da kike shiga kullum ai akwai sanyi". Kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi tana faɗin. "Not like rain, shi sanyinsa daban ne, but is so sweet kuma fa". Tafukan hannunsa ya buɗe ruwan na zuba a samansu. "The water is so very very fresh and cool". Ya yi maganar yana ɗan watsa mata shi a saman face ɗinta. Jinjina mashi kai ta yi. "Yah ikon Allah kenan, ko iya ruwan saman nan idan ka kallah ya isa ya sanyaka ka kara jin tsoron Allah, ka kara ganin girman Allah, Allah buwayi gagara misali, yanzu idan ka ɗaga kanka ka dubi sararin samaniya sai ka rasa ta ina ruwan yake fitowa, hmmmm wani abin sai Ubangiji, yanzu fa a saman nan akwai ruwan da zai iya cinye duniya da abin da yake a cikinta, kaf duniya babu wanda ya isa ya tare ruwa kada ya wuce idan ya doso waje, amma shi Ubangiji ya rike ruwan da zata iya cinye duniyar nan tas ba tare da ta zubo ta cinye duniyar ba, kai komai ma fa ka gani a duniyar nan idan kana da hankali ya isa yasaka ka kara jin tsoron Allah!!". Yadda ta yi maganar kamar wata babbar mace, ta kwantar da kanta shiru tana zayyano bayanai cikin natsuwa, ruwan saman na sauka a kansu, abin sai ya ƙayatar da masu kallon. "Pretty ina son sanin wanene Allah? And ina son samun karin sani sosai a kan abubuwan da kuke yi keda Sweetie". Ya yi maganar tare da juyowa da kallonsa izuwa saman face ɗinta. "Kamran Allah shi ne wanda ya halicceni ya kuma halicceka tare da sauran mutanen da kake gani suna giftawa a cikin dajin nan, sannan ya halicci sammai da ƙassai, halittun Ubangiji ba zasu kirgu ba, dan sun wuce gaban tunanin kowa". Juyowa da kyau ya yi ta yadda zai sami damar ganinta da kyau da kyau. "To meyasa Ubangiji ya haliccemu kenan?". "Bauta, domin mu bauta mashi, kuma sallah da ka tambayeni a kan mecece ita ranar da kasame ni ina yinta to ɗaya ce daga cikin abin da Ubangiji ya haliccemu muzo mu yi mashi, kuma ita ce ma a kan gaba, sai karatun Alkur'ani mai girma, ita ce littafin nan da ka ɗauka a wajenmu ranar, akwai azumi da sauransu, amma ni dai bana yin azumi gaskiya, ba zan iya yunwar nan ba, Sweetie ce kawai take yi, ni kam wlh dana ji yunwa zan ci abinci na, so ban taɓa yin azumi ba". (Sarkin cin abinci ba, yo dama ke a yanzu ai ba zaki iya yi ba, wata kila idan ya zama wajibi a kanki kyayi dan dole😅) "E ina karanta littafin dana ɗauka a wajenku, kuma yana da matuƙar daɗi sosai, sai dai ban yi nisa a karatun ba, wannan littafin ma yana ɗaya daga cikin abin da ya hanani karanta diaryn da mummynku ta bani, wannan Alqur'anin ya ja ra'ayina sosai, ya ɗauke mun hankali da a kullum a ƙagare nake dana karanta shi". Murmushin ta sakar mashi tare da kai hannunta ta ja karar dogon hancin nan nasa. "Ka yi ƙoƙari ka karanta zaka ji daɗinsa, aduniya babu abin da ya kaisa daɗin karantawa da kuma sauraran mai karantawa". Shafa kumatunta ya yi kafin ya ce. "To ɗan karanta mun kaɗan na ji". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannunsa a cikin gashin kanta dake ta zubar da ruwa sosai, ga hadari sai kara haɗuwa yake yi, ruwan sama yana kara tsananta karfin zubarsa kamar da bakin kwarya, ga walkiya mai hasken gaske da yake haske arear wajen a duk lokacin daya wanzu a sararin samaniyar, sai tsawa ya biyo baya. Hankalinsu a kwance suke zaune a wajen abinsu, ko kaɗan basu damu da ruwan da yake zuba masu a kansu ba. Rera mashi karatun Alqur'ani mai girma ta fara yi cikin suratul iklas, ga voice ɗin nata da zaki ga shegen daɗi. Shiru ya saurara yana jinta, har wani irin ni'imantaccen ajiyar zuciya ya sauke, Alqur'ani akwai daɗin saurara, ga kwantar da hankalin mai sauraro. Ƙarar da suka fara jiyowa daga can nesa da su ne yasa Pretty ta dakata da karatun, a lokacin already ta kammala suratul iklas ta shiga falak, dan ƙasa ta yo. Dakatawa da yin karatun ta yi tana zaro idanun nan nata da suke kara fito da tsantsar kyanta. "Kamran menene yake kara har haka?". A tsorace ta yi maganar. "I don't know, amma mu je mu duba mana mu gani". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta, shi fa ko tsoro baya ji, wai su je su duba, ita dai Sweetie baiwar Allah tana ciki abinta, ba ruwanta da yawace yawace har sai idan ya zama dole. "Kamran ina tsoro fa". Ta faɗa tana ƙanƙame hannunsa tare da kara zaro idanu. Sauƙowa ƙasa daga saman dutsen ya yi tare da juya mata faffaɗar bayansa a kan ta hau ya goyata yana faɗin. "Kada ki ji tsoron komai my Pretty, ina tare dake, mu je muga menene yake kara har haka?". Ba musu ta haye bayan nasa tana murmushi, idan da sabo ai ya saba goyonta, dan haka sai ta ɗale abinta tare da saƙalo wuyarsa ta kwantar da kanta a gefen shoulder ɗinsa, sai murmushi take saki dimple ɗinta na lotsawa, ga ruwa na zuba mata daga tsakiyar kai, kyalkyawar gashin kanta sai zubar da ruwa yake yi. Kai tsaye Kamran ya nufi ta wajen da suke jiyo wannan kara a tare da ita. Sai hira suke yi gwanin birgewa har suna ɗan yi nisa. Suna tafiya suna kara jiyo wannan sauti tana kara matsowa kuma tana kara karfin kara. Sai da suka sake matsawa kusa sosai suka fahimci ashe sautin ƙugin igiyar ruwace mai karfin gaske ne, da alama katafaren teku ce a wajen wadda ta cika take ambaliya sanadiyar wannan ruwan saman, igiyar ruwace ke ƙugi. A hanzarce ya ƙarisa matsowa sosai, babu ko shakka bare tsoro ya nufi waje. Wannan katafaren tekun nan wanda mum ɗinsu ta faɗo daga ɗaya daga cikin duwatsun dake kewaye da tekun nan ne, sai dai a yanzu iya gane daga ta ina mum ɗin nasu ta fito har ta faɗo ta wannan waje abu ne da ba zai yi wu ba, su bama su san daga ta wajen ta fito ba, so sai basu wani damu ba. Mamaki ne kawai ya bayyana a saman fuskokinsu na ganin tekun a dajin bai sani ba. Duk zaman Kamran a wannan daji bai taɓa sanin wannan teku ba, sai dai kananan ruwa dake ta wajen tsauninsu, ashe akwai teku mai girman da idan ka bi cikinta zaka je ƙasashe da dama. "Kamran saukeni na ga tekun nan da kyau". Ta faɗa tana zaro idan, yadda igiyar ruwa ke juya tsakiyar ruwan tekun kawai take kallo. Shi ma Kamran ɗin abin da yake gani kenan, abin ya ƙayatar da su kuma ya basu mamaki sosai. Ba musu ya sauketa dan ta yi kallo da kyau. "Pretty ina ganin kamar wannan teku ta nan ce hanyar fita daga cikin wannan Forest ɗin ko?". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a kanta, ya jima yana neman hanyar da zata fitar da shi wannan Forest ɗin cikin sauki, ita kuma wannan teku abin da bai sani ba ta kasance kamar border ce, iya kar ƙasashe da damane a wajen, sai dai tabbas ita ce hanyar da zata iya kaisu cikin babbar ƙasar, kuma dai kada ku manta su su Pretty ta nan mum ɗinsu ta fito, kunga hakan na nufin koma dai me ta nan garinsu or ƙasarsu yake. Akwai cakwakiya kenan, da alama su Pretty zasu kai kansu in da ake nemansu ruwan ajallo idan suka yi wasa. Sai hira suke yi suna ta kallon yadda igiyar ruwa yake jan ruwan har sama sai kuma ya sake sake shi, hakan yakansa ruwan ta bada sauti mai karfin da har suka iya jiyowa ɗazun, sai zancen neman hanya suke yi, Kamran ya kafe a kan shi dai lallai wannan teku a akwai hanya a kusa da ita, ita kuma Pretty ta ce bata ga alama ba, domin kuwa ita dai ruwa take kallo maras iyaka, kuma wlh ita ko kasheta za'ayi bafa zata shiga cikin ruwan nan ba........😅 (Kunga laifinta? Da gaskiyar ruwa ba iyaka haka ace su shiga su ketare?🤔 Ni dai ina bayanta, ko za'a kwasheta kada ta yarda ta shiga😅 ta bar Kamran da Sweetie su je, idan suka isko mutane sai azo da jirgin ruwa a ɗauketa😅😅 saura naji wata magana, shawara na bata🥱😎) Sun jima tsaye a wajen ruwan sama na jiƙasu, sai da Pretty ta fara rawan sanyi ne ta dube shi. "Kamran sanyi nake ji sosai". Juyowa ya yi da kallonsa a kanta. "Zo na goyaki mu koma, gobe dole mu dawo wannan waje". Da sauri ta faɗa jikinsa, sai rawan sanyi take yi sosai, shi ma dai zubar ruwa yake yi. Ɗagata sama ya yi tare da maida ita bayansa, ya goyata kamar yadda suka zo, dan wannan yarinya ba iya tafiya da kafafunta zata yi cikin bishiyoyi da ciyayin nan ba, sai ta ɓata masu lokaci basu isa in da za su je ba, kuma dama shi Kamran yana jin daɗin goyata idan zasu je yawonsu, saboda hakan zai sa su yi tafiya mai nisa ba tare da ɓata lokaci ba. Nufar hanyar komawa suka yi, ta kwanta shiru a bayansa tana rawan sanyi, ta wani ƙanƙame mashi wuya. Shi kuma sai tafiya yake yi. Ko da suka isa bakin ramin nasu sai ya sauketa, miƙo mata wani irin nau'in fruit nasu dake a cikin dajin mai kama da ruman mai kuma kama da Apple haka yake ya yi, ya miƙo mata tare da cewa. "Ina sonki sosai Pretty, ki koma ki cire kayan jikinki ki canza wasu kada sanyi ya kamaki, nima zan je gida, sai gobe, kada fa ki sake fitowa, gobe za mu je yawo sosai". (Ko a ina ya samo wannan fruit ɗin?🤔 Kila a hanya ya ciro da suna dawowa) Karɓar fruit ɗin ta yi tare da cewa. "Nima ina sonka Kamran, amma fa gobe kazo da wuri ka ji?". Jinjina mata kai kawai ya yi, sam baya son rabuwa da su, ji yake yi a wannan yanayi kamar kada ya koma gida, amma ina babu dama, ba hali dole ya koma idan yana son cigaba da kasancewa da su. Shiru ya ɗan tsaya ya kasa tafiya. "Kamran lafiya ka tsaya shiru? Ka tafi mana". Ta faɗa tana kallon face ɗinsa. Ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan ƙaƙalo murmushi kaɗan. "Babu komai Pretty, kawai ina tunanin rabuwa da ku ne, bana son komawa gida na barku". Shiru ta ɗan yi itama, jikinta ya yi sanyi, har ga Allah bata son rabu da shi ita ma, amma ya zasu yi? Dole su rabu, idan ba haka ba su jawa kansu rabuwa ta har abada. "Nima bana son ka tafi Kamran, nafi son kullum ka kasance a tare da mu, idan ka tafi bana jin daɗi, ina jin kamar bani da lafiya, duk sai in ji wajen zamanmu ya yi mun zafi babu daɗi, shiyasa ka kallah ina fitowa waje in zauna idan baka nan, bana jin daɗin zaman cikin ne". Tana magana kamar zata yi kuka. Ɗan rungumota a jikinsa kaɗan ya yi tare da shafa kanta dake ta zubar da ruwa. "Idan nazo gobe zamu yi magana, yanzu kinga kije ciki kada sanyi ya kama mana ke, ki canza kaya kin ji ko? Ki gaishe da Sweetie sosai". Rungume shi ita ma ta yi kafin ta sake cewa. "Goben fa kada ka daɗe, kazo da wuri". Okey ya amsa mata da shi, sannan ya saketa tare da ce mata ta shiga ciki. Ba musu ta shige ciki, sai dai ta shige ne tana ruwan hawaye, kuma ya lura da hakan, kawar da kansa kawai ya yi, saboda dalilai guda biyu, na farko baya son ya cigaba da tsayar da ita cikin ruwan nan ga kuma ɗanyen kaya a jikinta, sanyi zai kamata, na biyu kuma baya son kara jan lokaci da su kada mamma ta tashi daga barci ta farga baya nan, hakan yasa ya kawar da kai tamkar bai ga tana kuka ba, amma ya ji zafin hakan sosai a cikin zuciyarsa, sai ya ji kamar shi ma ya yi kukan ko zai ɗan ji sanyi a ransa. Haka ya juya jiki ba kwari ya nufi nasu gidan, yana tafiya yana tunanin hanyar da zai bi ya isa ga mutanen dake wajen dajin nan, sannan yanzu kuma tunanin mahaifinsa ta yawaita mashi a cikin zuciyarsa, ji yake yi lokaci ya yi da yakamata ya tambayi Mamma ina babansa? Tun da yanzu ya gano cewa ba iya macece kawai take haihuwa ba, dole yana da baba, to ina baban nasa? A gaskiya yakamata Mamma ta gaya mashi in da mahaifinsa yake, kullum da wannan tunani yake kwana kuma yake tashi, sai dai ya rasa ta ina zai fara tunkara Mamma da zancen. Tashin hankali kenan. Tafiya yake yi sam bashi da wani kuzari a jikinsa, da haka ya isa gida. Yana zuwa ya wuce nashi makwancin, kayan jikinsa ya fara kwaɓewa tas. Yana da kyan jiki kam kamar madara duk da Mamma ta fishi haske nesa ba kusa ba, da alama babansa ya yo a kalar fata, fari ne fa shi ɗin ma, amma a gaban mamma gaskiya ba fari bane. Canza kaya ya yi tare da kwashe waɗan nan ya kai su in da suka dace, ya sanya kaya masu nauyi sosai saboda sanyi, sannan ya kwanta ya ɗauko Alqur'ani da ya ɗauka wajen su Pretty ya fara dubawa yana karantawa, bai leƙa Mamma ba. A lokacin ita kuma ta tashi daga barcin tana cikin madafarta, tana aiki, tasan da cewa ya fita bayanan, domin tana farkawa daga barci makwancinsa ta fara leƙawa dan ta duba shi, sai ta taras baya nan, so bata wani damu ba, dan dama da lallami ta lallaɓa shi ya dawo, so ba zata takura mashi ba. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼 GIDANSU KHADIJAH😥💔 Maman Khadija tana durkushe a wajen tana kuka Khadija na rarrashinta, bata tashi daga wajen ba sai ji ta yi an sake banko masu kofar gida. Bata kula ba, haka zalika bata bi ta kan son sanin su waye bane, ita masifar da take a ciki ma ya isheta, dan haka sai ta cigaba da rera kukanta da sauti baya fita sai dai ruwan hawaye. Banko labulen kofar aka yi aka shigo, maman Haidar ce da Maman Hanif sai Hajiyarsu, Haidar yana tsaye daga bakin kofa, shi ma Sadiq ya fito ya tsaya a bakin kofar ɗakinsu yana kallon cikin parlourn, abin da ya fito da shi kuma shi ne irin yadda ya ji sun banko masu cikin gida babu mutunci, so yana tsoron kada su yi wa ƴar uwarsa wani abin, shiyasa ya fito, shi dai yana ganin bala'i kala kala bawan Allah, daga nasu maman Haidar yanzu kuma an koma na Hauwa, wannan irin jarbawa sai ka dage zaka iya cinta, Allah yasa maman Zee tana da juriya da karfin imanin iya cinye jarabawarta. Tana durkushe tana kuka maman Haidar ta fara surfa mata ruwan bala'i a kan ina su Hauwa ɗin suke? Ta fito masu da baban Zainab ita kuma. Wani irin kallon takaici mai haɗe da tsananin ɓacin rai maman Zee ta wurga masu. Cikin ɓacin rai da fusata ta ce. "Saboda ni kuka raina shi ne dan kinga ni kaɗai ce zaki fara mun hargagin banza ko? Meyasa ɗazun da kika samu Hauwar baki yi mata ba kika yi shiru? Yanzu dan kinga bata nan ne zaki ce na fito maku da baban Zainab? To na cinye shi ɗanya, sai ku fasa cikina ku ciro shi!!". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye, idanunta jajir kamar wuta, yau tasha kuka, kuma a cike take har wuya da bakinciki, idan su maman Haidar suka yi wasa tana iya yi masu hauka, dan Hauwa ta sanya zuciyarta yanzu ya fara bushewa ta dai'na ganin mutuncin kowa, zuciyarta ta kusa fashewa ta fito waje. Tashin hankali, yanzu wasan zai fara!!. "Ke Aisha ni kike gayawa magana yau? Ni nake magana kike mayar mun da amsa? A lallai kam kan mage ya fara wayewa". Cewar maman Haidar. "Ke ɗin nake gayawa, an gaya maki ɗin, zaki iya yin duk abin da ya zo maki cikin wannan banzar ƙwaƙwalwar taki, sannan kuma ke dama a tunaninki rashin wayewa yasa bana mayar maki da martanin duk abin da kika yi mun ko? Ko kina tunanin ina jin tsoron ki ne? To idan ma haka kike tunani kin makaro, tarbiya da ilimi dana samu daga wajen iyayena ne yasa nake darajaki a matsayinki na yar miji, nake baki girma kamar yayata uwa ɗaya uba ɗaya, nake kuma ganin mutuncinki, amma yanzu tun da abin yazama babu mutunci, to kuwa zaki ga ainahin wacece A'isha! Yanzu baki isa kiyi mun na kyale ki ba wlh, a baya kin ci banza, amma yanzu zan nuna maki ba wai ban iya rashin kunyar bane, tarbiya muka kwankwaɗa muka ƙoshi, a gidanku kuma kuka shayar da ni ruwan kwatar ƴancina, to yanzu na sha na ƙoshi, duk wanda ta shirya mu buga to ta zo mu buga daga nan har illa Masha Allah, in dai bata gaji ba, to nima ba zan gaji ba! Duk wadda ta ce mun kule sai na ce mata cas, na dai'na yin shiru tun ba mutuncin kuke so ba!!". Shiru ita dai maman Hanif ta yi, dan ita dama ba wai ta cika shiga irin wannan shirgin bane, kawai ba yadda ta iya ne, idan maman Haidar ta yayuɓota dole ta biye mata, ko dan ma Hajiyarsu, idan bata shigarwa maman Haidar ba ya zama dole ta shiganwa Hajiyarsu. Gadan gadan cikin fushi maman Haidar ɗin ta nufeta da nufin ta kai mata mari. Ai kuwa maman Zee bata yi ƙasa a gwiwa ba ta yi cap ta rike hannun nata. "Wlh idan kika kuskura kika ɗaura hannunki a jikina sai na rama, ashe rashin kunyar taki sai kinga wargi kike yi, meyasa baki yi wa Hauwa ba? Kika yi shiru ta gama cin maki mutunci baki da wani kataɓus! Meyasa kika ja baki kika yi shiru a gabanta? Sai ni zaki yi wa hargagin banza? To nima na dawo daga rakiyarku wlh!!". Ƙoƙarin kwace hannunta ta fara yi, amma ina maman Zee taki sakar mata hannun, ji take yi ma kamar ta kife munafuka da mari, so take ta sauke haushin da Hauwa ta cusa mata a kansu. A fusace Haidar ya shigo cikin ɗakin, a haukarsa da rashin hankalinsa wai zai daki maman Zainab ɗin. Ai kuwa yana zuwa Sadiq ya tare shi, dan kuwa ya biyo bayansa, saboda yasan halinsa sarai, tun da yaga ya shige cikin parlourn yasan ba zasu yi da kyau ba, shi kuwa ba zai bari su taɓa mashi ƴar uwa ba, tun da faɗar ba'a kan ƴaƴa bane tsakaninsu da ƴar uwarsa ce yana da damar saka baki ya tare mata, da ace faɗar a kan su Khadijah ne to fa bashi da bakin magana, amma a kan ƴar uwarsa yana da bakin magana. Aikuwa ya tare mata a in da ya ce wlh in dai Haidar ya ɗaura hannunsa a jikinta yau sai ya gwada mashi banbancinsu, jahili wanda bai san me yake yi ba, angaya mashi ana taɓa matar aure ne? Matar mutun kawai kasa hannu kace zaka daketa, ai ko kotu aka je in dai shari'ar musulunci za'a bi sai a ɗaureka har igiya ta yi saura a kan hakan. Da farko Haidar ɗin ya so kama Sadiq ɗin da kokawa. Amma ina Sadiq ya nuna mashi ya fishi hankali da sanin ciwon kansa a in da ya ce da maman Zee ta wuce cikin bedroom ɗinta ta rufe kofa ta rabu da su, idan suka gama hauƙarsu ba'a kulasu ba za su kama kansu. Da sauri ta wuce cikin room ɗinta, ta bi maganar ɗan uwan nata. Tana jiyo muryar Hajiyarsu tana cewa to ai ba gidan ubanki bane da zaki shige cikin ɗakin, ki fito ki tafi gidan ubanki marasa kunya marasa tarbiya, wlh sai kin bar gidan nan tun da ku baku da albarka dangin matsiyata, dole ya zo ya sakeki ki wuce gidan ubanki tun da har da ni zaki yi wa rashin kunya, dan kin rai'na taki uwar. Wato ita fa Hajiyarsu bata san cewa yanzu fa baban Zainab bayan Hauwa baya jin maganar kowa ba, har da wani cewa zata sa ya saki maman Zainab, wlh ana show a wannan gida, ana rikici, ko ya tsohuwar nan zata ji lokacin data ga Hauwa na juya mata ɗa? Mu dai ana yi muna shan Maltina. Ko juyowa maman Zee bata yi ba bare ta kallesu har ma ta kulasu, tana jin hajiyar tasu ta ce kada ta yarda ta shiga cikin bedroom ɗin nan ta zo ta wuce gidan ubanta, amma ina ta wuce ciki ta banko masu kofa da karfi tare da murza key abinta, irin bata da lokacin sun nan. Shi ma Sadiq sa kai ya yi ya wuce ya fita abinsa, dan bashi da lokacin biyewa haukarsu a cewarsa, shi a mahaukata ma yake kallonsu, idan sun ga dama su kwana a cikin parlourn suna surfa masifa su dai suka sani, shi dai ya kama kansa abinsa. Baban Zainab ma yanzu ba samun damar ganinsa zasu yi ba bare har su ce ya saki maman Zainab ko su gaya mashi ta yi masu rashin kunya, idan ma sun sami damar ganinsa to ko kallo basu isheshi ba, shi da yake ta Hauwa ina ruwansa da su? Idan ma suka yi wasa sai ya haɗa masu da zagi da kuma duka koma ya ce bai san su ba. Tirƙashi, ana cakwakiya a gidan baban Zainab fa sosai. Haka suka yi ta surfa uban masifa mai isarsu, da dai suka ga ba mafita sai suka kama kansu, dama shi Haidar already ya bi bayan Sadiq da nufin ya je ya kama shi da faɗa, amma ina Sadiq ɗin yaki biye mashi, dama yaga zai takura mashi sai ya ɗauki wayarsa ya fice daga cikin ɗakin, ya bar masu gidan ma gabaɗaya, sai dai bai yi nisa da gidan ba, dan yana tsoron ya yi nisa kada su yi wa maman Zainab ɗin wani abin. Haka suka yi ta haukarsu har suka gaji suka hakura suka tafi. Ita kuma maman Zainab tana shiga cikin ɗaki ta ɗauki waya ta kira mamanta dan ta sanar da ita halin da ake ciki na batun Zainab. Khadija kuwa wadda tun da taga ƴan uwan baban nata sun zo ta gudu ta shige cikin room nasu ta rufe kofa kamar basu a gidan, dan haka Sadiq ya gaya mata, ya ce kada ta sake tsayawa a wajen da ƴan uwan babanta suke faɗa da mamanta, idan taga sun zo ta shige cikin ɗakinsu su rufe kofa babu ruwansu. Bugu ɗaya mamarsu ta ɗauki wayar, ƴar dattijuwa tana zaune a saman dadduma, kullum cikin yiwa ƴar tata addu'a take yi a kan Allah ya kawo mata mafita. Bayanai ta kora mata dan gane da halin da Zainab take a ciki kamar yadda Sadiq ya ce ta gaya mata. Ajiyar zuciya maman tata ta yi tare da kara yi mata nasiha mai ratsa jiki sosai, daga karshe ta rufe fa ce mata. "A duk in da kike Aisha ki kasance mai jin tsoron Allah, in ma a lokacin kaɗaicewarki ko a cikin mutane, ki sani idan kowa baya ganinki to shi Allah yana ganinki kuma baya barci, dan haka kada ki ji tsoron kowa ki ji tsoron Allah shi kaɗai, sannan ita kuma Zainab ki samu ganyen magarya guda bakwai, ki daka shi a wajen da babu ya ji, sannan ki zuba shi a cikin ruwan da zai ishata wanka, sai ki karanta mata suratul baƙra aya biyar ɗin farko, ki haɗa da ayatul kursiyu kafa ɗaya, sai wattabau ma tattlusshayaɗini ala mulki sulaimanu waman kafara sulaiman har dai zuwa karshen ayar, sai amanarrasulu kafa ɗaya, sai ayoyin sihiri wato wa auhaina musa zuwa karshe, sai kala musa attakiluna maja'akum sihirulhazakulyan shi ma har karshe, sai kulhuwallahu kafa uku, falak da nasi kafa uku uku, daga karshe ki rufe da fatiha ki tufa a cikin ruwan ganyen magaryar, a bata ta yi wanka da shi". Wannan duk girman sihirin da aka yi wa mutun manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce in dai ka yi hakan to ba shakka wannan sihiri duk girmanta sai ta warware, koda kuwa da me aka haɗata wlh sai Allah ya kwance ta, sai ta warware, so wannan ba iya Zainab na bama ba, gabaɗaya al'ummar Annabi na bawa, Allah ka tsaremu da tsarewarka, ka shiga tsakanin nagari da mugu. Idan kin ji daɗi kafin ki wuce ki mun addu'a ko wace iriyace in dai ta alkhari ce a gareni ina so. Godiya maman Zainab ɗin ta yi mata tare da yi mata fatan karin samun lafiya, sannan suka yi sallama. Shiru ta yi bayan ta ajiye wayar a gefen gado tana tunanin da zata samu ace baban Zainab ma ya yi wanka da wannan haɗi da zata yi wa Zainab ɗin, ai da shikenan kashin Hauwa ya bushe, asirin zai karye asirinta ya tonu, komai da zai dawo daidai, amma ina babu halin ta yi wa baban Zainab ɗin, ina ma ta gan shi da ido ma bare har ta haɗa mashi wannan haɗin? Ai bata ma ga alama ba, hakuri kawai zata yi ta cigaba da addu'a har Allah ya kawo mata mafita, ita kuma Zainab da izinin Allah zata samu lafiya komai ya wuce ya dawo normal. Gyarawa ta yi ta kwanta zuciyarta cike taf da tunanin mafita, sai addu'a take yi na Allah ya kawo mata saukin al'amura da haka barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ ABU ABDUSSALAM BIN BADEEN EMPIRE.🌼 Sosai Leesharh take yin aikinta na gyare gyare kamar yadda aka umarceta, sai dai tana taƙa tsantsan da ƴan gidan sosai. Kwance take a saman bed ɗinta daga ita sai doguwar riga mara nauyi, hular rigar ce a kanta, ta yi shiru tana tunani, ta kammala aikinta na yamma, ta yi sallar la'asar. Ta yi nisa cikin tunanin da take yi kamar daga sama ta ji wayarta ta ɗan yi kara alamar shigowar sako, wayar da tun da ta zo gidan bata taɓa amfani da shi ba bayan duba time, ba'a taɓa kiranta ba, sai ga shi yau saƙo ya shigo ciki. Cikin hanzari ta janyo wayar har hannunta na kerma, a ƙage take da taga wani saƙo ne?. Unknown number ce wadda aka rufeta da kyau, da ita aka turo mata sakon. Cikin hanzari ta fara duba saƙon ba tare da damuwar sai ta kalli number ba, ita dai me saƙon ya ƙunsa kawai take son sani, ba wani karatu sosai can can ta iya ba, amma dai ba laifi. Jikinta har yana kerma wajen buɗe saƙon, miƙewa ta yi daga kwanciyar da take ta zauna tare da fara karantawa. Saƙo ne da aka turo mata a kan su Sharifat, ya tabbata dai duk wani motsinta suna sane da shi, rubutu ne kamar haka. A'isha tun da Sharifat ta nuna tana son samun kusanci dake to dama mu haka muke fata, dan haka ki saki jiki da ita ta yadda zaki shiga jikinta sosai, ta hanyarta ne kawai zaki iya samun damar isa wajen da Ramish yake, domin kuwa ta hanyar mutun ɗaya zaki samu kusanci da Ramish, ta hanyar Omar ne kawai, shi kuma dole sai ta kasancewarki kusa da Sharifat, idan kika shaƙu da Sharifat tabbas shi ma zaki shaƙu da shi, dan su ɗin abokai ne, idan kuma kika shaku da shi to tamkar kin shaƙu da kowa na cikin gidan ne, kin ga kuwa zamu samu abin da muke so, kema zaki kammala aikinki da wuri ki zo ki koma ƙasarku, ammafa ki kula sosai, kada ki saki baki, ki dai shiga jikinta sosai, kuma kin yi ƙoƙari taimakon Omar da kika yi, hakan ma wata dama ce da zata sa ki samu kusanci da shi, ko na ce ma yanzu ma kin samu kusanci da shi tun da har ya kulaki, ki cigaba da dagewa saura kiris mu isa in da muke so. Wannan shi ne saƙon da aka tura mata, shiru ta ɗan yi tana nazari a kan waɗan nan maganganu, ita sam ta ƙasa ganewa mutanen nan, addu'ar da yazo bakinta kawai ta karanta tare da miƙewa ta sauƙo kasan gadon, wajen drawer kayanta ta nufa ta ɗauki ɗan ƙaramin hijabi ta sanya a jiki, ta nufi waje, dan ta je wajen Sharifat su ɗan yi hira, dama tana son biye mata su yi hira saboda Sharifat ɗin ta nuna ra'ayin hakan, amma saboda dokar da take tafiya a kai yasa take shareta bata kulata, yanzu tun da ta samu dama ai shikenan kuma, yanzu ne zata shiga jikinsu da kyau ta samu ta yi aikinta da wuri ta bar gidan a cewarta. Ni kuwa na ce akwai cakwakiya kuma sosai. Wai ma ta ina mutanen nan suke sanin motsinta ne?........🤔 Muje dai zuwa. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ KINGDOM OF POWER 💪🔥 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 29/8/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________41🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ KINGDOM OF POWER 💪🔥 Shiri sosai Chuchu ta yi, ta tsantsara kwalliya, kun san halinta dama da iya tsara shegen kyalliya kamar me, part ɗin Momman Zunaira ma ta je ta kwaso wasu perfumes ɗin masu zafi, ita da kanta ta yi wa kanta kyau, ta tsaya a gaban mirror tana ta kallon kanta, ta yi wa kanta kyau, sai murmushi take yi ta kasa dai'nawa, kamar wata wadda take ba ita kaɗai ba. Doguwar riga haɗaɗɗiya mai bala'in tsada na ƴaƴan manya manyan sarakuna ta sanya a jikinta, launin pink color ce rigar, sai dai akwai ratsin white color kaɗan, and kuma duwatsun jikin rigar ma white color ne, daga ta sama rigar ta kamata dai'dai da jikinta, daga ta wajen ƙugunta kuma zuwa ƙasa ya yi wani irin bala'in buɗewa sosai da sosai. Alkyabbarta mai bala'in kyau launin white color ta ɗaura a saman kayan tare da sanya hular alkyabbar a kanta, ta haɗu kam ba karya, ta gyara gashin kanta sannan ta cigaba da tsayuwa a gaban mirror tana ganin kanta, ta mance da cewa ya ce idan ta kammala shiri ta kirasa, ta tsaya kallon kanta. Almost 10 mins tana tsaye shiru tana ta kallon kanta, sai kwashe kyan nata take yi da idanunta, ga wani ƙamshi da take zubawa mai kwantar da hankalin mai shaƙa. "Ba sai kin kalla kin sake kallan kan naki ba, kin yi kyau sosai na wuce misali ai my sister" kamar daga sama ta jiyo voice ɗinsa ta bayanta. A hanzarce ta kai kallonta a bakin kofar shigowa. Yana tsaye cikin shigar ƙananan kaya, da alama shi ma ya yi wanka ya shirya, ya yi kyau sosai. Murmushi ta yi tare da kai tafukan hannunta ta rufe face ɗinta. "Ina auta?". Ya yi maganar hankalinsa na'a kan wayarsa dake hannunsa. "Bata dawo ba tun da ta tafi shiryawa". Ta bashi amsa. "Okey ku sameni a wajen Aunty MieMie idan kun kammala, ta ce nazo yanzu". Yana kai karshen maganar ya juya ya nufi wajen elevator dan ya yi ƙasa ya je ɓangaren Gimbiya Aunty MieMie wato first born na King Zuhair kena, yar mummyn Gimbiya Chuchu ce kada ku manta, yayar Chuchun kenan. Da kallo ta bishi da shi har ya ƙurewa ganinta, Yah Jawad ɗin nan yana yi mata kyau, ta faɗa a cikin zuciyarta tare da sauke nannauyar ajiyar, sannan ta nufi bakin bed ɗinta domin ta ɗauki ɗayar wayar tasa. Auta ce ta shigo cikin ɗakin bakinta a ɗauke da sallama tana rike da wayar mommanta a hannunta, da alama video call take yi da wani daga cikin ƴan uwanta. Ta yi kyau sosai cikin shigar riga da sket Indian dressing, da wani katon mayafinta da yafi karfinta har yana jan ƙasa, kayanma gabaɗaya kamar sun ɗan yi mata yawa, dan sket ɗin ma yana jan ƙasa, amma ta yi kyau matuƙa, kamar ka saceta ka je ka ajiye ka yi ta kallonta kawai. A kusa da chuchun ta zo ta zauna tana faɗin. "Ai Yah Jaish ne ya hanani zuwa da fa zan zo, nima na yi kewarku sosai Allah kuma". Daga ta cikin wayar ya ce. "To yanzu ai baki gaya mun ina zaki je ba da kika yi wannan kwalliya haka? Kin yi kyau sosai". Ƴar dariya ta yi kafin ta ce. "Yah Rizwan kai da ka ce aiki kake yi kuma ka biye mun ko? Ni kam dai babu ruwana ga shi ma Yah Omar ɗin ya gudu ya haɗamu ya dakatar maka da aikinka". "Omar bai gudu ba, ga shi can a kwance a gadon Raj, ya barmu ne mu yi hira". Ya yi maganar tare da ɗan juya mata wayar izuwa kan Guyson dake kwance a saman katafaren bed ɗin Dr Raj ya yi ruf da ciki tare da sanya pillow a wajen kirjinsa yana danna laptop ɗin Dr dake a saman bed ɗin, shi kuma Rizwan yana zaune ne a saman sofa set dake a cikin room ɗin na Dr Raj ɗin, gabansa shi ma laptop ɗinsa ne yana aiki yana kuma shan cappuccino mai zafi dake cikin wani haɗaɗɗen cup dake a gabansa. Su dai a duniyarsu suna kaunar coffee da cappuccino, sun ma fi son cappuccino a kan coffee gaskiya. Gabaɗaya su Rizwan sun san auta, kuma suna kaunarta kamar yadda suke son Omar, su chuchu ne dai basu sani ba, domin idan baku manta ba ita fa auta tana zuwa Dubai sosai, kuma Abu Abdussalam bin Badeen uncle nata yayan mommanta, duk idan aka yi hutun school a can wajen dangin mommanta take hutu har sai an buɗe makaranta, wannan karon ne kawai aka hanata zuwa, su Chuchu kuwa dama basa zuwa sai jefi jefi, ko sun je kuma a gidan kakansu King Badeen suke zama, basu cika zuwa wajen sauran ƴan uwa ba, ko sun je ma basa wuce su wuni su koma gidan kakansu, ko kwana basa yi bare har su saba da sauran ƴan uwan nasu, so su gaskiya su Rizwan basu wani sansu sosai ba, ko shi Bilal da yake uwa ɗaya uba ɗaya da Chuchun ba wani saninta sosai ya yi ba, rabonsa da ita ya kai shekaru 10, Gimbiya Aunty MieMie kawai suka yi wa farin sani kuma suke waya da ita a koda yaushe, dan ita ɗin babbar yarsu ce, ta girmesu dukka, kuma tana yawan zuwa Dubai wajensu, su Chuchu kam shiru ne, kunga kuwa ai ko Bilal ɗin ba ya shaidata ba, auta kam ai dole ma su santa, ita take zuwa har in da suke ko basu nemeta ba. "Kai Yah Omar har da tafiya ya kwanta, tom muma dai unguwa zamu je". Ta faɗa tana bin Chuchu dake ƙoƙarin kwanciya a saman bed ɗin da kallo. "Ina zaku je?". Rizwan ɗin ya tambayeta. "Nima ban sani ba, Aunty Chuchu ce ta ce na shirya Yah Jawad zai kai mu wani waje". Jin ta ambaci sunan Chuchu yasa ya kawar da kallonsa daga kan laptop dake a gabansa izuwa kan wayar da kyau, shiru ya ɗan yi yana tunanin sunan Chuchu, can ya ɗan tuna ashe ita ce wadda Mammie ta zaɓa mashi. "Ina Chuchun take?". Ya tambaya tare da zame farar glass da yake face ɗinsa, dama ɗazun bai wani duba hotunanta da Mammie ta turo mashi da kyau ba, aiki yake ta fama da shi, yanzu ma dan auta ce yasa ya tsaya yake hira da ita, video call Omar ya shigo yana yi da ita, shi ne ya zauna kusa da Rizwan ɗin, da ta gansa kuma sai ta ce. "Yah Rizwan inawuni". Daga haka suka fara hira ya karɓi wayar daga hannun Omar ɗin, shi ne yasa kuka ga suna waya, amma hankalinsa dukka yana a kan aikin da yake yi. Juyar da wayar ta yi izuwa kan Chuchu dake kwance tana cigaba da yi wa Yah Jawad bincike a cikin wayarsa kamar ya aiketa. "Aunty Chuchu ga Yah Rizwan yana magana". Da sauri ta juyo da fararen idanun nan nata tare da miƙewa zaune. "Ina wuni Yah Rizwan". Ta faɗa tana kashe wutar screen ɗin wayar Yah Jawad. Shiru ya ɗan zuba mata idanu kamar mai tunanin wani abin, ta yi mashi kyau sosai, ga shi kuma ya yi sa'a gani ta ci kwalliya zasu fita, ai dole nema kowa ya ganta ya ji yana sha'awar cigaba da kallonta. Sai da ta sake maimaita mashi kalmar inawun sannan ne ya ɗan kawar da kallonsa daga kanta tare da amsa mata da lafiya lou Alhdulillah. Sannan ya ɗaura mata da tambayar cewa ita ce Chuchu daman?. E ta bashi amsa da shi. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tambaye ya school da kowa da kowa?. Miƙa mata wayar auta ta yi tare da miƙewa ta koma gaban mirror ta zauna, kwalliyar face ɗinta ta fara gyarawa, dan Omar ya ce mata da ta sanya janbaki bata yi kyau ba, ta bar launin kalar lips ɗinta haka sun fi kyau, ta sanya lips balm kawai, to shi ne ta je gyarawa. Ita kuwa Chuchu karɓar wayar ta yi suka cigaba da yin hira da Rizwan, dan shi dama yana da saukin kai sosai ba kaman su Dr Raj ba, shiyasa ma Sharifat take zuwa wajensa suke shiri, dan bashi da zafi sosai. Dan haka sai ya biyewa chuchu suka shiga hira, har da tambayarta ya yi ina wayarta, ta ce mashi yana hannun Yah Jawad. "Me ya kai wayarki hannunsa kuma?". Ya yi tambayar yana matsar da laptop dake a gabansa ya miƙe tsaye. "Kwace wayar ya yi dan na cika ɗaukar hoto dayawa". Ta bashi amsa tana ɗan turo baki, domin ta tuna da abin da Yah Jawad ɗin ya rinƙa yi mata a kan ɗaukar hoto. Shiru ya yi a cikin ransa yana faɗin Jawad ka cika cin zali sosai, dan kawai tana ɗaukar hoto sai ka kwace mata waya?. A fili kuma sai cewa ya yi. "Tom shikenan idan ya dawo maki da wayar sai ki karɓi numberta a hannunsa ko a hannun auta ki kirani da numberki". Okey ta amsa mashi da shi tare da tambayarsa ina su Yah Bilal. Cikin zolaya ya ce mata. "Bilal kawai kika sani ba?". Da sauri ta fara girgiza mashi kai tare da cewa. "A'a nasan su Yah Ramish mana, nasanku dukkanku ai". Nufar hanyar fita daga cikin room ɗin ya yi, jikinsa na sanye da farar arab jallabiya, dukkansu dai kalar Akka ɗin ne, kyawawan gaske, soft skin kamar madara, sai ka rantse da Allah basu fita waje, saboda yadda skit ɗinsu yake sun ji hutu sun ƙoshi. Cikin zolaya ya sake cewa. "A'a baki sanmu ba kam, Bilal kawai kika sani, dan ga shi shi kaɗai kika tambayi ina yake? To ya baya ƙasar ya yi tafiya". Murmushi kawai ta sakar mashi, dan tasan zolayanta yake yi, ai babu bambanci a tsakanin ƴaƴan King, duk da cewa iyayensu basa shiri, to su dai basa faɗa, dan haka ita da yayanta Bilal da su Ramish ƴaƴan mama duk ɗaya ne a wajenta. "Aunty Chuchu kizo mu tafi mana, Yah Rizwan kai da ka ce mun aiki kake yi ɗazun shi ne kuma ka sake biyewa Aunty Chuchu ko? Idan ka biye mata ba zata barka ka yi aiki ba". Cewar auta dake dake a saman mirror chair ta gama gyara kwalliyarta, ita dai kafarta na mata kaikayi, su tafi kawai, burinta taga sun je wannan yawon. "Auta ai chuchu ta rigada ta hanani yin aikin ma, baki ga ma na fito waje na bar aikin ba? Sai kuma dare zan ƙarisa, yanzu dai bari mu ɗan yi hira da ita ko my sister?". Ya faɗa yana tsare Chuchun da waɗan nan idanun nasa wanda da ka gansu ba tambaya kasan tsatso ɗaya suka fito da Jawad, dan kuwa wlh idanunsu iri ɗaya sak, kamar Akka ta samu sabo ta basu tsoho..........😅 Murmushi ta sakar mashi tana ƙoƙarin yin magana auta ta rigata da cewa. "Ni gaskiya Yah Rizwan ban yarda ba, nifa nagama shirina tafiya kawai zamu yi kace zaku yi hira? Wlh idan ba so kuke na fara kuka na kai karanku wajen daddy ba Allah ku bar hiran sai mun dawo". "Wai ina zaku je nema?". Rizwan ya tambaya. Chuchu ce ta bashi amsa da. "Nima dai ban sani ba, kawai Yah Jawad ya ce mu shirya mu same shi a part ɗin Aunty MieMie....." Katseta auta ta yi da cewa. "Wai dama Yah Jawad ya ce mu same shi a wajen Aunty MieMie ne kika zauna a nan ban sani ba, baki gaya mun ba, to ni dai na tafi". Tana kai karshen maganar ta miƙe da sauri ta nufi hanyar fita daga room ɗin mayafin kayan na jan ƙasa, ta tattaro ƙasan sket ɗin da hannunta ɗaya kamar dole. Da sauri ita ma Chuchun ta miƙe tana faɗin. "Yah Rizwan in tafi ko?". Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya dai tsareta da ido yana ta kallonta. Katse kiran ta yi ba tare da ta sake yi mashi magana ba. A hanzarce ta rufawa auta baya tana murmushi. Kai tsaye ƙasa suka yi tare da nufar part ɗin Aunty MieMie, suna tafiya suna hira, kamar wasu taurari. A kan hanyarsu na tafiya ta wajen tsakanin part ɗin uncle Abbas da part ɗinsu suka ci karo da commander ZAFAR tare da Sadauki Hoorain da kuma wani jarumin mayaki ɗaya suna tsaye suna tattaunawa, da alama magana mai mahimmanci suke yi. Cikin girmamawa Sadauki Hoorain da wannan mayaki suka ɗan dukar da kansu ƙasa tare da yi masu sannu, shi kuma commander Zafar bai duka masu ba, amma cikin mutunci ya yi masu sannu tare da tambayar ina zasu je?. Chuchu ce ta basu amsa da cewa part ɗin Aunty MieMie zasu je, ita kuwa Auta tuni hankalinta ya koma kan mutuminta wato Sadauki Hoorain, ta tsaya ne ma tana tambayarsa wai ina yake shiga ne kwana biyun nan bata ganinsa sosai?. Cikin girmamawa ya yi ƙasa da kai, da wannan sanyayyar muryar tasa ya amsa mata da cewa. "Kece kika dai'na fitowa lambu ranki shidaɗe, shiyasa baki ganina, amma ina nan". Kallon commander Zafar ta yi kafin ta ce. "Abbu kai ma fa na dai'na ganinka sosai". Duk cikin masarautar kowa da commander Zafar yake kiransa, ɗansa Hoorain ne kawai yake kiransa da Abbu, sai kuma auta da take bin bakin Hoorain ɗin, ita kaɗai take bashi wannan darajar, shiyasa yake kaunar yarinyar, shiyasa shi ma Hoorain yake kula da ita sosai, tana da girmama manya. "Gimbiya ina nan, kamar yadda Hoorain ya gaya maki ne, muna nan kece baki fitowa yasa baki ganinmu". Hannunta Chuchu ta ja tana faɗin. "Ke idan mutun ya biye maki sai ki kwana a nan, wuce mu tafi, ke kowa kika gani sai kin tsaya tambayarsa ina ya shiga kwana biyu? Bayan kina kule a cikin room ta ina zaki gansu dama?". Da kallo kawai su commander suka bisu da shi, auta tana son tsayawa ta ɗan yi magana da Hoorain and commander, amma Chuchu ta hanata, haka ta hakura ta bi bayan Chuchun suka nufi ɓangaren Aunty MieMie da mijinta kenan. A babban parlourn kasa suka isko Aunty MieMie zaune a tare da Jawad suna tattaunawa. Aunty MieMie tana shirye cikin kayan sarauta kusan kamar kullum, ga alkyabbarta dake jan ƙasa a jikinta. Suna shigowa suka haye jikin Aunty MieMie, har suna rige rigen kwanciya a kafarta. "Ni ku tashi kada ku karyani, yanzu kun zama ƴan'mata har ma kun kusa zama matan wasu". Cewar Aunty MieMie. Ta yi maganar tana kallon Jawad, da alama akwai abin da ya gaya mata dangane da chuchun, shiyasa da ta yi maganar sun kusa zama matar wasu sai ta ɗago tana kallonsa. Kawar da kansa ya yi kamar bai ganta ba. "Ku tashi mu fita ta part ɗin Aunty MieMie nan, bani key ɗin motarki Aunty Babba". Cewar Yah Jawad ɗin, ya yi maganar kuma yana miƙewa tsaye. "Ni dai ba zan bada key ɗin motata ko guda ɗaya ba, haka kawai za'a fitarwa da daddyna ƴan'matansa waje bada saninsa ba, to sai dai a bani cin hanci ko kuma na tona asiri". Cewar Aunty MieMie. Auta ce ta ce. "Aunty MieMie ni zan baki cin hancin kin ji? Please ki bamu kin motar mana, amma fa idan daddy ya kamaki kina karɓar cin hanci babu ruwana". "Sarkin son yawo ba, da anyi hutun school ki ce Dubai, yanzu kuma a nan ma zaki fara ko? Bari daddy ya kamaku zaku yi bayani". Aunty MieMie ta faɗa tana kallon auta. Dariya kawai suka yi ita da Chuchu, shi kuwa Jawad ya tsaya yana ta satar kallon Chuchun, a ƙagare yake Aunty MieMie ta basu key su tafi, dan ya fitar da su ya je ya yi ta kallonta a wajen, amma Aunty MieMie kuma ta tsaya tana ta wani ja mashi rai, ya sani da gangan take yi mashi hakan. Sai da ta ja masu rai sosai sannan ta ɗauko mashi keys dayawa ya zaɓi guda ɗaya. A hanzarce ya wuce gaba yana cewa su zo su tafi. Da sauri suka miƙe suka bi bayansa suna dariya, sai addu'ar Allah ya dawo da su lafiya Aunty MieMie take yi masu suna amsawa da Amin. Bayan sun shiga cikin motar ne ya tambayesu meyasa suka jima kafin su zo?. Auta ce ta bashi amsa da cewa. "To ba Aunty Chuchu bace ta tsaya biyewa Yah Rizwan suna ta hira...." Da sauri Chuchu ta tari numfashinta da cewa. "Waye ya fara yin hira da shi? Ba kece kika shigo mun room da wayar kuna yin video call ba? Ai kece nan kika zauna tun a room ɗinki kika rinƙa hira da shi, ni babu ruwana kada ki yi mun sharri, ina gaisawa kawai muka yi, kuma bai wuci 5 mins ba muka gama......". Auta ta buɗe baki zata yi magana. Katsesu ya yi da cewa. "To dai shikenan ya isa haka, yanzu dai kusa seat belt ɗinku zamu tafi". Dukkansu gidan gaba suka shiga, da kansa zai ja su kenan. Ba ɓata lokaci ya tada motar bayan sun sanya seat belt ɗin, kai tsaye ya nufi tampatsetsan gate da zai fitar da shi daga ɓangaren Aunty MieMie, suka ratsa ta bangaren uncle Abbas sannan suka nufi katafaren gate one na kingdom ɗin. Sai daɗi su auta suke ji kamar me, ya ji daɗi sosai shi ma na ganin suna a cikin farinciki har haka. Suna fita daga masarautar Jaish ya kira shi a wayarsa dake hannun Chuchun. Miƙa mashi ta yi, kamar ba zai ɗauki kiran ba, sai kuma dai ya ɗauka. Daga ɗayan ɓangaren Jaish ɗin ya ce mashi ina yake ne?. Shiru ya ɗan yi kafin ya bashi amsa da baya nan kuma ya ɗan yi nisa, uncle Abbas ne ya aikesa, amma ba zai jima sosai ba zai dawo. Sosai Jaish ya yi mamakin jin hakan, domin ya gano karya yau Jawad ya yi mashi, daga yanayin maganarsa ya fahimci ba gaskiya ya faɗa ba, yasan halinsa sarai, tare suka taso. "Jawad me kake ɓoye mun?". Cewar Jaish. "Mekuma zan ɓoyemaka Jaish? Babu komai, amma meyasa ka ce na ɓoye maka wani abin". Shiru Jaish ɗin ya yi na ƴan sakani kafin ya ce. "Saboda ba gaskiya ka gaya mun ba shiyasa na ce me kake ɓoye mun? Kai kanka kasan ba gaskiya ka faɗa ba, kawai ka gaya mun ina kake?". "Kai my blood kana saurin gane abubuwa, na ɗan je wani waje ne to, but idan na dawo zamu yi magana". Hmmmm kawai Jaish ya ce mashi. A hanzarce ya katse kiran, a cewarsa ko hauka yake yi ba zai bari Jaish ya gano cewa yana son chuchu ba, dan ba zasu wanye lafiya ba, Jaish ɗin zai ce shikenan ya gama ja masu raini a idanun kannensu, ya gama zubar masu da mutunci, ya gama da su, ba karamar dirama zasu yi ba, dan wlh Jaish ba zai yarda ba, bare ma shi da ba sanin darajar soyayyar ya yi ba, ba yinta yake yi ba, bai taɓa yi ba bare yasan zafinta ko sanyinta, ai kunga ba zai ɗauketa da mahimmanci ba, zai ce Jawad ya haukace, ina ai bama zai yarda ba, Jawad ɗin yasan da hakan shiyasa yake ɓoye mashi, kuma shi ma Jawad ɗin a rashin sa'arsa da ya tashi ɓoye abin sai ya ɓoyewa har da ita Chuchun, a cewarsa yanzu ta yi karama, idan ya gaya mata cewa yana sonta na farko zata rai'na shi, na biyu kuma a gaskiya ta yi ƙanƙanta da batun soyayya, karatu yake son ta yi, shiyasa ya barta a duhu bai sanar da ita ba, ya dai ce zai koyawa kansa shakuwa da ita, zai na sakar mata fuska su saba, amma banda zancen soyayya, dan a ganinsa tana jin cewa yana sonta shikenan ta rai'na shi. Tashin sense!. Akwai cakwakiya ba kaɗan ba, da alama Rizwan zai riga shi bayyana mata soyayyarsa, ita kuma dai kunga bata taɓa yin soyayya ba bare ta ce akwai son wani a ranta, so a yadda take a yanzu duk wanda ya ce yana sonta daga cikin ƴan uwanta zata iya amince mashi, bare kuma a yadda suke son juna dukkansu, babu nuna banbanci a tsakani. (Yah Jawad yana ruwa kusa da.....🥱🤔 Akka😅🤭) Tuki yake yi yana kallonta ta wutsiyar idanunsa, wannan kwalliya tata ta tafi da imaninsa sosai da sosai. Ita kuma sai kallon hanya suke yi ita da auta, suna farinciki yau dai ga su a wajen Kingdom, kamar bakinsu ba zai rufu ba. Kai tsaye wani haɗaɗɗen wajen da suke yawan zuwa shi da Jaish su zauna su huta idan pressure ya yi masu yawa a kai ya nufa da su, idan sun tarawa kansu aiki ko kuma Jaish yana son su tattauna ba'a office ɗinsu ba kuma ba'a gida ba, sai su zo wannan wajen hutawar mai cike da kayan alatu su zauna su yi duk tattaunawar da za su yi cikin sirri. Jaish ɗan jarida ne babba, so ba kamar Jawad yake ba, kwakwalwarsa kullum tana cikin aikin ƙaƙale ƙaƙale, shiyasa yake son keɓewa shi kaɗai dan ya rinƙa zurfafa tunaninsa tare da faɗaɗata. Shi kuwa Jawad ai kunga har lokacin soyayya yake da shi abinsa. "Yah Jawad ka kaimu zoo mu kalli namun dawa, daga nan ka kaimu wajajen wasanni mu ɗan yi wasa". Cewar Chuchu. Ɗaga mata gera guda ya yi kafin ya ce. "Jannat har yanzu baki yi girma da zuwa wajen wasanni ba ko?". Ya yi maganar yana zama a ɗaya daga cikin tsala tsalar sofas dake part na musamman a wajen, part ne na musamman wanda sai wane da wane suke zuwa wajen, babu hayaniya sam sam a wajen. "Kai Yah Jawad to duka duka shekaruna nawa? Ko sha shidda fa ban kai ba". Ta faɗa tana turo baki. Auta ce ta ce. "Yah Jawad tun da yau mun fito ka kaimu har da gidan kallo mu kalli Film". Girgiza kai ya yi, kwata kwata su auta basu da wata matsala a rayuwarsu, wai gidan kallo, su dai tun da yau sun fito shikenan kuma, sai abin da Allah ya yi, akuyar ɗaure an samu sake. "Zaku ci abinci a waje yau?". Ya tambayesu yana kallon face ɗin chuchu. Har suna haɗa baki wajen amsawa da e zasu ci, basu taɓa cin abincin waje ba. Bai sake yi masu magana ba ya buga masu oder kawai, a kawo masu kayan cima da abinci mafi tsada a wajen. Ba'a ɓata lokaci ba aka kawo masu. "Bismillah ku ci abincin waje yau ku ji ya take". Ya faɗa yana ciro wayarsa, sai kuma ya kawar da kallonsa daga kansu, dan ba zai so ganin yadda za su yi da fuska ba, sai ɗauki su kuma suke yi yau dai za'a ci abincin waje. Chuchu ce ta fara ɗaukar spoon ta ɗebo madbe dake a saman plate na gabanta. Madbe ba sabon abinci bane a wajensu, amma yau ji suke yi kamar sabon abu aka kawo masu, saboda na waje ne ba su kuyanga Zubaida ne suka haɗa ba. Fuska a ɗauke da murmushi ta kai shi bakinta, ta zuba ta fara tauna. Nan take ta kwaɓe fuska kamar wadda ta tauna wani abin mai ɗaci. A hanzarce ta tufo shi waje tana kara kwaɓe fuska. Dariya ne ya so kubce wa Yah Jawad ɗin, dama yasan za'ayi hakan shiyasa ma ya kawar da kansa, ba zai so ganin sauyawar fuskar masoyiyarsa daga murmushi zuwa ƙunci ba. "Aunty Chuchu what happened naga kin fito da abincin?". Cewar auta. "Isn't sweet at all auta, like coffee and salt". Ai kuwa Jawad bai san lokacin da dariyar da yake ɓoyewa ta kubce mashi ba, bama abin da ya bashi dariya kamar yadda ta ce wai kamar coffee da gishiri, innalillahi Chuchu anji ɗanɗano kam tab. Ganin yana yi masu dariya ne yasa Chuchu ta gane da gangan ya yi masu hakan, kenan yasan ɗanɗanon babu daɗi ya barsu suka ci? Har da wani ɗaukinsu zasu ci wani abinci na daban bana kingdom ba. Hakan yasa Chuchun ta fashe da kuka mai sauti, ta ji haushin dariyar da yake yi masu. Ita kam auta mamakin ganinsa yana dariya ya sa ta ƙasa iya yin magana, ta dai san yana ɗan yin murmushi time to time, amma dariya mai sauti haka bata taɓa ganinsa yana yi ba sai yau. Ita kuwa Chuchu zagewa ta yi da gaske tana kuka har da hawaye. Ganin hakan yasa ya dakatar da yin dariyar tasa, sannan ya fara ƙoƙarin rarrashinta. Ƙin yin shiru ta yi, ta cigaba da yin kukanta. Da yaga da gaske fa take kukan sai ya miƙe ya dawo saman nasu sofan, dama su sun zauna ne a mai zaman mutun uku, shi kuma ya zauna a mai zaman mutun biyu, so sai ya miƙe ya dawo kusa da ita. Ɗan rungumota ya yi yana faɗin. "Sorry my sister, tuba nake yi, kuma ai dama ba laifina bane, da nace maku babu daɗi kada ku ci ai da zaku ce na hanaku, kuma nasan halinku sarai zaku yi ta jin haushi na, amma kuma dana barku kuka ɗanɗana ai kunji da kanku ko?". Cikin kuka ta ce. "To Yah Jawad meyasa zaka yi mun dariya?". "To na tuba, ba zan sake ba". Yana magana yana ƙoƙarin goge mata hawaye, ita dai auta da Allah ya rufa mata asiri bata ɗanɗana ba lafiya lou ɗanɗanon bakinta yake. "Yanzu ga shi ɗanɗanon bakina ya ɓaci". Ta faɗa tana fito da harshe domun ta goge harshen nata. Sake guntse dariyar ya yi. (Ni ina tantanma ma, anya da ya tashi buga oder nan bai ce a ɓata abincin Chuchu ba kuwa?🤔 Dan wannan dariyar dai na mugunta yake yi, da biyu gaskiya, da gangan ya yi mata hakan.) Hannu ya kai yana tayata goge ɗan harshen nata yana faɗin. "Bari ma na tayaki gogewa". Yana magana yana guntse dariya. Kome auta ta tuna sai ita ma ta kwashe da dariya kamar wadda aka tsikara. "Me kike dariya ke kuma?". Chuchu ta tambayeta. Cike da zolaya ta ce. "Aunty Chuchu ɗanɗana nawa madbe ɗin ki ji kamar ya fi naki daɗi....." Ƙasa ƙarisa maganar ta yi sakamakon harara da Yah Jawad ɗin ya wurga mata, da alama dai ya tabbata da gaske da gangan yasa aka ɓata na Chuchu dan ya tsokaneta. "Ba zata sake ɗanɗana komai ba, salon ɗanɗanon bakinta ya kara canzawa ko?" Ya tari numfashin auta da sauri, dan ma kada Chuchun ta ce zata ɗanɗana ta ji akwai banbanci da nata, idan ta ji hakan kuwa kuka zata sanya masu ta ce sai ta ji dalilin da yasa nata ɗanɗanonsa daban. Ganin irin hararar da ya yi mata ne yasa autar ta gane shi ya shirya komai, dan haka sai ta ja bakinta ta yi shiru, amma fa a cikin zuciyarta ta ƙuduri niyar sai ta gayawa Chuchun gaskiya idan suka je gida. Cigaba da rarrashinta ya yi, ya kuma goge mata ɗan harshen nata tas, sannan ya ɗauko mata ruwan da ta zuba a cup da nufin ta sha idan ta gama cin abinci, yana ɗan rungume da shoulder ɗinta ya kawo mata cup ɗin saitin bakinta. Da sauri ta fara girgiza mashi kai tare da ce mashi ita ba zata sha ruwansu ba, kila ruwan ma sun zuba gishiri. Dariya ne cike fal ransa, amma ya danne ya ce auta ta ɗauko mashi ruwa a mota bari ya bata ta kuskure baki. Ita dai auta ƴar ba ruwana, koma me za'ayi sai ayi ta yi babu ruwanta. Auta na fita ya ce. "To juyo naga harshen naki ko ya fita?" Ba musu ta juyo suna fuskantar juna, sakin shoulder ɗin nata ya yi tare da ƙurawa face ɗinta idanu. "Yah Jawad har sai da harshena ya yi ja fa nasani". Ta faɗa tana mayar da harshen nata. Jin ya yi shiru bai amsa mata bane yasa ta ɗago dan ta kalli meyasa ya yi shirun. Tana ɗagowa suka haɗa ido. Dariya ne ya so kubce mashi, domin da suka haɗa idon sai ya tuna da lokacin da ta ɗanɗana madbe ɗin ta kwaɓe fuska. Yankar salar lemu ya ɗauko daga cikin kayan ciman da aka kawo masu ya sanya mata a ɗan bakin nata yana faɗin. "Ɗan kuskure baki da wannan tukun nan". A hanzarce ta fara ƙoƙarin turo shi waje, dan a tunaninta duk kayan wajen akwai gishiri a cikinsu. Ɗan riƙo shoulder ɗin nata ya yi yana faɗin. "Kisha babu komai". Make mashi kafaɗa ta yi tare da faɗin. "A'a Yah Jawad babu daɗi kayan waje, gaskiya ni na ƙoshi". Yana ɗan murmushi kaɗan kaɗan ya yi ƙasa da murya. "Sorry ki sha kaɗan ki ji". Ya yi maganar tare da ɗauko mata wani lemun, dan ta tufar da wancan da ya bata da farko. A bakin ya sake saka mata, bata yi musu ba ta karɓa. Yana rumgume da shoulder ɗinta auta ta dawo wajen ta same su. "Yah Jawad babu ruwa fa a cikin mota". Ta faɗa tana komawa mazauninta ta zauna. Dama yasan babu ruwa a motar, kawai ya aikata ne. Dan haka sai ya karɓi key ɗin motar kawai ya cigaba da lallaɓa Chuchun tana shan fruits ɗin dan ɗanɗanon gishirin ya bar bakinta. Idan muka waiwaya kingdom kuwa. Jaish yana zaune a saman ɗaya daga cikin haɗaɗɗun sofas da suke lambun King, ya miƙe kyawawan kafafunsa a saman throw pillow dake saman shinfiɗaɗiyar Turkey carpet dake gaban sofas set ɗin. Gabansa kayan cima ne kala kala, yana sanye da arab jallabiya launin sky blue, ya yi matuƙar kyau yau ɗin nan, har yanzu yana nan yana aikin bincike a kan wannan Company na haɗa magunguna, su ya sakawa ido yanzu. Wayarsa ce a gefensa, saman laps ɗinsa kuma laptop ɗinsa. Ya yi nisa cikin abinda yake yi. Ga wasu kuyangu biyu dake ɗan gefe nesa da shi kaɗan, aikinsu shi ne su tsaya kusa da shi ko zai buƙaci wani abin. Gimbiya Fanan kanwar Jawad ce ta shigo wajen bakinta a ɗauke da sallama. Sallamar kawai ya amsa mata saboda sanin darajar sallamar, bayan haka ko in da take bai ɗago ya kallah ba. Ƙasa a gabansa ta durƙusa, cikin girmamawa ta ce. "Yah Jaish Mammiena ta ce in kiraka". Kai kawai ya gyaɗa mata alamar ya ji ba tare da ya yi magana ba. Jiki a sanyaye ta miƙe ta nufi hanyar fita, sai kallon shi take yi, suma kuyangun da suke a wajen sai kallonsa suke yi, shi kuwa sai kallon laptop yake yi yana aiki, ni kuma sai kallon ink ɗin bairona nake yi, ban anakara ba na ji ya kare ɗiff........🥱 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 30/8/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________42🔥 Jiki a sanyaye ta miƙe ta nufi hanyar fita, sai kallon shi take yi, suma kuyangun da suke a wajen sai kallonsa suke yi, shi kuwa sai kallon laptop yake yi yana aiki. Ya ɗauki a kallah 30 mins zaune a wajen yana ta aikinsa, tamkar bai san cewa Mammien Yah Jawad ta aika ya zo ba, dama shi sam sam jininsa bai haɗu da ita ba, shi fa Jaish bayan mommarsa wlh jininsa bai haɗu da kowa ba a cikin matan nan, harta mummy da take sonsu ɗin ma, shi kowa ma bai ishe shi kallo ba, yana dai kaunar Yah Jawad sun fi shaƙuwa, kuma yana kaunar uncle Abbas sosai kamar ransa, amma ya tsani Mammie, baya son haɗa hanya da ita da kuma Mamma and Mummy. A hankali ya miƙe tare da ɗaukar wayarsa, ya baro laptop ɗin a wajen bayan ya kashe wutar screen ɗinta, cikin gida ya nufa. Cikin nutsuwa yake tafiya. Kai tsaye part ɗin mommarsa ya nufa, da alama ba zai je kiran Mammie ɗin ba, dan ba part ɗin uncle Abbas ya nufa ba. Zaune a parlourn ya isko mommar tasa tare da wasu kuyangunta guda biyu da suke zaune a gefe da gefenta, ga mama Haulat kuyanga ta musamman wadda momma ta aminta da ita, ita kaɗai take iya shiga har cikin bedroom ɗin momma, tana zaune a gaban mommar tana tsantsara mata zanen flowers lalle masu matuƙar kyau, zanen ya fita, abinku da farar fata ga zanen lallen baki da ja, sai ta yi wani irin kyau na musamman, ta fito a amaryar King ɗin da gaske. Kusa da ita ya kariso saman sofar da take ya zauna, da yake a saman sofa mai zaman mutun uku take zaune, ta ɗaura kafafunta a saman throw pillows dake a gabansa, hannayenta da aka yi mata zanen flowers ɗin ta ɗaura su a saman wasu ƙananan throw pillows wadda kuyanga Mama Haulat ta ɗaura mata su a saman sofar da take zaune ɗin. Zama ya yi ba tare da ya yi magana ba, cikin hanzari dukkan kuyangun har da Mama Haulat ɗin ma suka miƙe tsaye, a hanzarce suka nufi waje, dan su basu waje ita da ɗanta su tattauna. "Jaish lafiya na ganka haka? Ko dai wani abin yana damunka ne?". Ta yi maganar tana dawo da kallonta a kansa. "Momma lafiya lou, me kika gani?". ya yi maganar yana kamo hannunta dake ta kusa da shi. "Momma waɗan nan flowers ɗin sun yi maki kyau sosai da sosai". Ya faɗa yana kallon face ɗinta. "Na ganoka waskewa kake son yi, ba wani kyau da flowers suka yi, kana son ne ka mantar dani daga tambayar me yake damunka da na yi ko?". "Kai momma ba haka bane, da gaske flowers ɗin sun yi maki kyau, ayiwa auta ma zata yi kyau sosai, kuma da gaske babu wani abin da yake damuna, gajiya ce kawai, kuma nasan dana ɗan huta zan wastsake". Wani irin kallo ta wurga mashi wadda ya ɗan sanya shi kajeriyar murmushi. "Kai momma da gaske fa nake yi, wai meyasa ke da daddy idan mutun ya yi maganar da baku gamsu da ita ba kuke yi mashi irin wannan kallon da sai kun saka shi murmushi ne?". Haƙiƙa murmushi da ya yi a karon farko yau ta yi mashi kyau matuƙa, kyansa ta kara bayyana sosai, sai ya yi kama da ita mommar da ya yi wannan murmushin. "Hakan zai tabbar mun da ba abin da ka faɗa bane yake damunka, idan da shi ne da gaske in na yi maka irin wannan kallo ba zaka yi murmushi ba, sai dai ka ɗaure fuska, dan gaskiya ka faɗa". Ta bashi amsa tana murmushi. "Oh momma dama wannan kallon tarko kenan kuke haɗa mana ko? Kusa mu faɗar gaskiya ba shiri, to yau na gano sirrin, amma momma daddy ne ya koya maki ko? Dan nasan ke ba haka kike ba tun farko......" Tarar numfashinsa ta yi da cewa. "A'a ni dai na koya mashi, kasan ai ni ta daban ce". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Kai momma daddynmu fa na daban ne, ni nasan shi ya koya maki". "To duk dai ba wannan ba, gaya mun menene yake damunka kada ka mantar da ni?". Ta yi maganar tana ƙoƙari janye hannunta daga riƙon da ya yi mata, dan ta lura suna hirar nan zai iya kyaɓe mata flowers ɗinta, saboda yana magana yana mancewa da cewa hannunta ya rike. "Kai momma keko? Ba zaki bar mutun ba sai dai ya gaya maki ɗin, wai ma ni ya aka yi kika gane cewa ina da damuwa ne?". "Saboda ni na haifeka mana, kuma ba zan bari ba sai na ji me yake damun mun kai". Shiru ya ɗan yi yana jin kaunar mahaifiyar nan tasu, tun jiya yake fama da damuwa a kan aikinsa, ya so su zauna da Jawad su yi magana, amma ina bai samu dama ba, Jawad yana can yana soyayya, babu wanda ya iya gane cewa yana a cikin damuwa sai mommarsa, ya je wajen King almost sau uku, amma King bai iya gane yana cikin damuwa ba, ita kuma da kallo ɗaya ta yi mashi ta harbo jirginsa. "Tunanin me kake yi?". Ta katse shi. Ɗago da kallonsa ya yi izuwa saman face ɗinta, ba zai iya gaya mata abin da yake bincike a kai ba, saboda yasan halinta da zafin zuciya, yanzun nan sai ta ce da King dole a rufe wannan Company kuma dole a kama masu haɗa magunguna da kayan mayen nan, momma fa bata da sauki ko kaɗan wani lokaci, ko da yake su dama modarawa ina suka ga sauki? Ai da manya da yara duk a jininsu abin yake, akwai su da ɗaukar zafi ba wasa. "Momma wani bincike nake yi yake saka mun zafin kai, ina ganin ma zan yi tafiya na ƴan kwanaki". "Dubai zaka je?". Girgiza kai ya yi alamar a'a. Baya son gaya mata in da zai je, sannan kuma baya son ya yi mata karya, domin bai san me zai je ya dawo ba, saboda Company ne da suke da haɗaka da manyan campanoni daga ƙasashen turawan yamma, reshe suka zo suka kafa a nan, amma ainahin daga waje ake shigo da duk wasu gurɓatattun kayan aikin da sauransu, to idan ya banƙaɗo sirrin bai san a iya ina rigimar zata tsaya ba, dan abu ne na manyan kai, baya son ɗagawa mahaifiyar tasa hankali. "Brazil zaka je?". Ta sake jefo mashi tambayar. "Momma ban fa tabbatar da zan yi tafiyar ko ba zan yi ba, ina tunani ne kawai, sai na tabbatar". Ya faɗa a fili, a cikin zuciyarsa kuma ƙudurin tafiya binciken daga wani kamfani ne na waje ke turo waɗan nan kayayyakin, zai yi hakance kuma domin ƙara samun hujja, kunsan cikakken ɗan jarida komai da hujja yake yi, sai ya riƙe hujjoji masu zafi yake fasa kwai, to shi ma hakance. Sallamar Obaid and Omaid ne ya katse masu hirar ta su. Ji suka yi tamkar su juya su koma na ganin Jaish a parlourn da suka yi, sam basu son haɗuwa da yayan nasu inuwa guda, domin kuwa ya rinƙa tuhumansu kenan, kuma ya rinƙa yi masu nasiha kenan, su kuma basu so. Amma da yake sun rigada sun shigo, sai suka ƙariso ciki kawai. A kusa da mommar tasu suka zo suka zauna, sai dai a ƙasa saman carpet, sun wani nutsu tamkar wasu alaranmomi daga babban masallacin Madina, irin Jaish ya ce yanzu suna da nutsuwar nan, waɗan nan ƴaƴa sun san kan duniya. Cikin girmamawa suka ce. "Yah Jaish ina wuni?". Bai yi mamaki ba, dan shi fa yasan su waye su, fin haka ma zasu aikata in dai su ne. Da lafiya ya amsa masu sannan ya ɗaura da cewa. "Me yau kuma kuka aikata?". Ajiyar zuciya suka sauke a tare, faɗi suke yi a cikin zuciyarsu cewa ko zamu mutu sai Yah Jaish ya ɗaura mana ayar tuhuma, mu dai mun shiga uku, wai kullum mu cikin aikata abu muke yi. A fili kuwa sai cewa suka yi. "Yah Jaish babu abin da muka aikata fa, mu fa yanzu we're so silent, innocent and babu ruwanmu da kowa". Ita dai Momma sai murmushi take yi, dan tasan halin kayanta, tana da tabbacin sun yi wani abin kamar yadda Jaish ya zarga, baya zargi a banza ai. Kuma da gasken ne sun yi wani abin kamar yadda ya faɗa, mugunta suka shiryawa mama a daren yau, dan gobe zasu koma Dubai an buɗe school, shi ne ma yasa suka zo yin hira da mommsrsu, dan zasu koma, to tabbas sun aikata wani abin ne, shi ne dan iya shege har da wani kara nutsuwa kamar wasu limaman masallacin harami. "Kun gama shirin ku ko?". Jaish ya tambayesu. Har suna haɗa baki wajen ce mashi e sun kammala shiri. "To ku dai tsaya ku yi karatu, kuma a duk in da kuke ku sani Allah yana ganinku idan mu bama ganinku, ku rage rashin ji, ku nutsu ku dai'na zalintar kowa, na gaji da jin sunanku a bakunan mutane, yadda kuka san ku kaɗai ne student a makarantar nan naku, ko ziyara na kai maku sauran students har tsayawa suke yi suna satar kallona, saboda yayanku ne ni, duk kun takurawa yayan mutane a makaranta, ku akwai wanda ya takura maku ne? To wlh ku nutsu, idan ba haka ba Allah next time na sake jin wani abin kun aikata, to ba makawa sai na miƙaku ga kasar Faransa ku je ku zama sojojinta na dai gaya maku, tun da ku dama wahala bata yi maku komai, kun saba da yin up and down". Zaro idanu waje suka yi, har suna haɗa baki wajen cewa. "Allah Yah Jaish mu mun nutsu yanzu, ba zaka sake jin komai ba, mun tuba, dan Allah ka bar maganar ƙasar France ɗin nan, mu bama son ji". "In dai baku son ji to ku nutsu, idan ba haka ba kun san dai bana magana biyu". Omaid ne ya ce. "Ni dama can babu ruwana, Obaid ne baya ji" (Tab wai kun ji Omaid babu ruwansa🤔 bayan kuma ya fi Obaid iya mugunta da rashin ji😅) "Kai Omaid ni ma ai babu ruwana". Momma dai murmushi kawai take binsu da shi, dan ita bata da ta cewa, yaran nan nata sai addu'a, dan ma yayyunsu maza sun tsaya tsayin daka a kansu ne, da wlh Obaid and Omaid sai Allah, rashin jinsu ba zai tsaya a iya nan ba, amma Alhamdulillah, a cikin kingdom of power idan suka zo su Jaish basu kyalesu ba, suna kula da su tare da yi masu faɗa da nasiha, dan nasiha tafi tasiri a zukatan mutane sama da faɗa ko duka, wani ma idan ka dake shi sai ya ce ba zai yi abin da kake so ɗin ba sai dai ka kashe shi, amma koya mutun ya kai ga taurin kai wlh nasiha tana tausasa zuciyarsa koda a iya wunin ranar ce kawai, bare kuma nasihar idan aka haɗa da annabi Muhammad (S.A.W) ta fi shiga cikin zuciya ta tausasa zuciyar bawa, karya ne a kirawa mutun Allah da annabi a sake kira bai ji zuciyarsa ta risina ba, sai dai kafurar zuciya ta kafuran farko. So a gaskiya nasiha ta fi faɗa ko duka tasiri musamman ga zuƙatan yara, ku rinƙa nuna masu Allah da annabi cikin ruwan sanyi tare da dabara ta yadda zasu fahimta ya kuma nutsa cikin zuƙatansu, hakan zai sa su taso cikin kamala da nutsuwa. A Dubai kuwa ga su Ramish, suma a kullum suna yin nasu iyaka baƙin ƙoƙarin wajen ganin kannenen nasu sun nutsu sosai. Amma kuma abin mamaki yadda kuka san ba lafiya ba, kullum rashin jinsu da taurin zuciyarsu karuwa yake yi, sun iya shirya mugunta daki daki babu ko ɗar ɗar, yanzu ga shi Yusuf saurayin Sarina da mu readers muke zargin su suka shirya mashi wannan mugunta, ga shi bawan Allah nan kafin a sakesa ya koma gida baya iya tafiya da kafafunsa, commander Zafar sai da ya ragargajesu kamar ba gobe, takawa da kafafunsu dai sun ƙasa iya yinsa, a haka aka kwashesu zuwa hospital, bayan sun sami lafiya aka sallamesu zuwa gida, wai a haka ma sboda uncle Abbas an yi masu da sauki, ba dan haka ba kaciya ta biyu za'ayi masu, commander baya ɗaukar wasa ai, kuma ba abin da iyayen Yusuf ɗin suka isa su yi, domin kuwa ba wanda ya isa ya ɗaga yatsa a kan wannan masarauta kuma ya zauna lafiya, sannan kuma ai hannu dumu dumu aka kama Yusuf ɗin ba zarginsa ake ba, so dole su ja baki su yi shiru. Sosai Jaish ya yi masu nasiha mai rasa zuciyar mai sauraro, amma kuma su dai bai wani ratsa su ba, tabbas sun ɗan yi ladab, amma dai ba wai can can ba, abin nasu kamar dai ba lafiya ba. Sun ɗan jima suna hira a tare da mahaifiyar tasu kafin su miƙe su ukun dukka, sannan suka yi mata sallama suka fita. Addu'a da fatan alkhari ta yi masu har suka fice. Suna fita kuyanga Mama Haulat ta dawo cikin parlourn domin ta ƙarisar mata da lallenta, sannan ta wanke mata tare da yi mata hayakin turaren lallen da sauransu, lalle mai turare take yi mata, shi kwaɓinsa na musamman ne, ya fita daban da sauran dukkan lalle da kuka sani, shi yana yin two months kafin ya goge, kuma kullum zaka gansa kamar sabo yana kyalli, kuma zaki yi ta zuba ƙamshi mai bala'in daɗi har sai ranar da ya goge, larabawar Dubai ne suka fi yawan amfani da shi, yana da tsada sosai, ba ko'ina ake samunsa ba sai gidan mulki, shi ma sai wane da wane, to ita dai momma kowani lokaci irinsa ake yi mata, haka Gimbiya Zunaira da Chuchu ma. A bangaren Mammien Yah Jawad kuwa, haka ta yi ta jiran Jaish amma ina shiru bai zo ba, dama tasan da wuya ya zo, saboda sau da dama tana aikawa a kirasa baya zuwa, idan kunga ya je kiranta to an aiko ya zo ɗin suna a tare da Yah Jawad ne, shi ne zai je, domin kada Jawad ɗin ya ji babu daɗi, amma idan Jawad baya nan wlh baya zuwa, ko kallo ma bata ishe shi ba. Ranta ya sosu sosai da sosai, ga shi a duniya bata da burin da ya wuce Jaish ɗin ya auri Fanan, wato ƴar autarta kenan, kanwar Sarina, shi kuma abin da yasa ma kenan baya kaunar zuwa in da take, dan in dai ya je sai ta yi mashi zancen Fanan, bata ma san shi haushi Fanan ɗin take bashi ba, kai shi fa baka gane mashi, kowa ma haushi yake bashi.........😅 Tana burin Fanan ta auri Jaish ɗin ne saboda dalilai da dama, kaɗan daga ciki sun haɗa da kasancewar Jaish jika ne ga the most powerful King Badeen, and kuma ƴan uwansa daga sama har kasa part na mommarsa daga masu mulkin siyasa sai masu sarauta, sannan Jaish yana da tarin dukiya duk da bai kai mommarsa ba, momma ta fi shi kuɗi sosai, amma dai shi kuma ya fi uncle Abbas kuɗi, sai kuma kasancewar ƴaƴan Momma sun fi zama mafi soyuwa a wajen King, wannan ma yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa take son Jaish ya auri Fanan, a ganinta idan Allah yasa Jaish ya auri Fanan zasu samu dama sosai a cikin masarautar, King zai zo Fanan kamar yadda yake son Jaish ɗin, ƙudurin da take da shi na son ganin ɗanta ne a kan kujeran King zai iya cika, amma fa a nata tunanin. Sam ranta bai ji daɗi ba na rashin zuwansa, da alama akwai abin da ta shirya mashi ne wadda bata son ya tsallaka, sai kuma ga shi ya tsallaka, ranta ya sosu sosai, cikin fushi ta ƙuduri niyar sai ta yi maganinsa, zata gyara mashi zama, shi da yana can bai ma sani ba tana nan tana haukarta, har da wani ɗaukarwa kanta alkawarin ko yana so ko baya so sai ya auri Fanan, bata fa da tabbacin cewa ita Fanan ɗin tana son Jaish ɗin, ita dai tsarinta kawai take tsarawa kamar yadda take ƙoƙarin ruguje soyayyar Jawad ta gina na Rizwan, abin nata dai sai ita ta san me take nufi da bayin Allahn nan, duk so take taga kowa a cikin ƙunci ne ko yaya ne oho mata dai, lokaci ne zai nuna mana ainahin me take da buƙatar cinmawa a ranta. A bangaren su Jawad kuwa, kamar yadda ya sakata kuka ta hanyar sanyawa a ɓata mata abinci, haka ya sake sakata dariya ta hanyar kaita yawo duk in da take so, sai dai duk in da suka je sai ya tsokaneta ta ɗan yi kuka hankalinsa yake kwanciya, ita dai auta ta tara abubuwan da zata gayawa Chuchun wanda Yah Jawad ya yi mata da gangan idan suka koma gida. Ko da suka je gidan zoo ma sai da ya tsokaneta, sun je wajen wasu irin macizan mesa masu haɗiye mutane, macizan suna cikin wani irin glass mai kyau aka sanyasu, sai yawaro wasu daga cikinsu suke yi, wasu kuma sun haɗiyi saniya suna ƙawance bata gama narkewa a ciki cikinsu ba, so sun zo wajen suna kallo, sai ɗaukarsu a video suke yi, auta ta tsaya sai magana take yi wa macizan wai su nannaɗu kamar taya yadda take gani a film bari ta gani a zahiri, sai ka ce an ce mata macizan dama magana ake yi masu sai su nannaɗu ɗin, ita kuma Chuchu ta tsaresu da ido tana kallon ikon Allah, idanunsu kawai take kallo, sai dai ta takure jikinta waje guda, da alama tsoro take ji, kawai ta dake ne ta cije ta tsaya a wajen. Cikin zolaya ya ce mata. "Jannat menen a wajen kafafunki kamar kamar snaka? Kamar fa ɗan snake ɗin dake cikin glass ɗin ne ya fito......." Bai iya kai karshen maganar ba ya dakata saboda wani irin ihu da ta zunduma, a guje ta bar wajen tana ƙoƙarin cire alkyabbar jikinta kamar ance mata a jikin alkyabbar macijin yake, kunsan irin wannan abin sai ka ji kamar da gaske yana taɓa maka jiki, musamman ma idan tun farko kaga macijan da idon ka, to wlh ko baa tsoratar da kai ba sai ka rinƙa jin kamar suna taɓaka, to ita ma haka ta ji, sai ta ji kamar da gaske yaron macijin ne yake taɓa mata kafa, ai kuwa ta rinƙa tsalle tana kakkaɓe kayan jikinta tana ƙoƙarin cire kayan ma gabaɗaya, sai ihu take yi. Cikin sauri ya bi bayanta, da gudu ita ma auta ta bar wajen, dan ma kada su kamata. Yana zuwa in da take ya riko wuyar alkyabbar tata dan ya hanata cirewa. Ƙanƙame shi ta yi tana faɗin. "Na shiga uku, Yah Jawad dan Allah ka cire mun shi, wlh na ji yana taɓa mun kafa". Dariya kamar zata kashe shi, yau ba karya ya yi nishaɗi over to over, bare ma idan ta zaro ido tana faɗin. Ya yi sauri ya cire mata ta ji yana haura mata saman kafafu wajen cinyarta, innalillahi Jawad kamar zai mutu da dariya, bayan rike wuyar alkyabbarta da ya yi dan kada ta cire, ya kasa iya aikata komai, saboda dariyar da yake dannewa ta hana shi ko da ɗaga hannunsa bare ya yi rarrashi. Ma'aikatan da suke wajen ne suka yi saurin ƙarisowa in da suke domin su ji ko lafiya. Hannu kawai ya ɗaga masu alamar su tafi babu komai. Cikin kuka ta ce. "Kada ku tafi, ku zo ku cire mun macijin nan kada ya kasheni, Wayyo mummyna, Yah Jawad ka mayar dani gida, ni ba zan sake fitowa ba, na shiga uku daddy yau zan mutu, idan ya cije ni shikenan na mutu". Ai a wannan gaɓar dariyar ba zata dannu ba, ta ci karfinsa a in da ya fara tikar dariya kamar wani zararre. Ita kam auta ta rigada ta gane ba wani maciji da gangan ya yi wa Aunty Chuchunta haka, dan haka sai ta sanya hakan ma a cikin lissafin abin da zata gayawa Chuchu idan suka koma gida, zata gaya mata cewa da gangan ya yi mata hakan. Ganin yana tikar dariya har da tsugunnawa a ƙasa yasa ita ma Chuchun ta ɗan tsagaita kukanta tana binsa da kallon mamaki. Da kyar ya iya tsayar da videon da yake ɗaukarsu tun farko, har murɗa mashi cikinsa ta yi saboda dariya. Jin ta ɗan tsagaita kukan ne yasa shi ma ya yi ƙoƙarin ya danne dariyar tare da miƙewa tsaye. Ɗan rungumota ya yi yana faɗin. "Ai tun ɗazun snake ɗin ya sauka daga kafafunki, ya koma wajen ƴan uwansa, kece baki gani ba". Yana magana yana guntse dariya. Duba kafafunta ta fara yi da sauri tana mai cigaba da kuka. Rarrashinta ya hauyi yana yi mata sorry. Ita dai auta ta harɗe hannaye a kirji tana ganin ikon god. "Sorry my sister, yanzu mu je muga su zaki dasu zamisa sai mu koma gida ko?". Ai a ɗari ta ce mashi. "Ni Yah Jawad ka mayar da mu gida kawai babu in da zan sake zuwa". Ɗan kara rungumeta ya yi yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi. Sai a lokacin kuma ya haɗa ido da auta da ta harɗe hannaye a kirji tana ganinsu. Ido ɗaya ya kashe mata tare da ɗaga gera guda, irin alamar Malama ya ne?. Dariya ta ɗan yi mara sauti kafin kuma ta ɗan kawar da kanta tana faɗin. "Yah Jawad gida zaka mayar damu daga nan, mun yafe sauran wajen yawon". Alama ya yi mata da hannu a kan ta zo. Ba mutu ta ƙariso wajen nasa da sari, haɗata ya yi da chuchun dukka ya rungume yana kara rarrashin chuchu, sai ajiyar zuciya take saukewa, ta sha zunduma ihu kam. Sun dan ɗauki a kallah minti goma a haka kafin ya rabasu da jikinsa ya ce su wuce gidan tun da sun ce yawon ya ishesu. Chuchu ce a gaba, ta yi sauri ta wuce zuwa wajen motarsu, taki ɗagowa ta sake kallon komai a wajen, wai dan ma kada wani abin ya sake bata tsoro. Sai murmushi kaɗan kaɗan yake yi ya riƙo hannun auta suka rufa mata baya. Har suka shiga cikin mota bata dai'na sauke ajiyar zuciya ba, a haka ya tada motar suka nufi gida, sai janta da hira auta take yi, amma bata wani kulata ba, saboda hankalinta ya yi gida, so take ta koma ta cire kayan jikin nan nata, ta yi alkawarin ba zata sake saka kayan ba, zata bawa kuyangarta dake gyara mata ɗaki kyauta, dan ita tun da maciji ya taɓa kayan bata so kuma. Suna isa gida ba ɓata lokaci ta fice daga cikin motar, Jawad ya yi mamakin ganin irin saurin da take yi, ko sallama basu yi ba, bai san tana son zuwa ta cire kayan jikin nata bane. A hanzarce auta ta rufa mata baya bayan ta yi mashi sallama, har lokacin wayar momma yana hannun autar, ta haɗa kuma da wayar da Yah Jawad ya bawa Chuchun ɗazun, domin Chuchun ta bata ajiyar wayar tun da suka fita, so sai ta haɗa da wayar ta nufi cikin gida, shi kuma bai lura da ta tafin mashi da waya ba, kawai ya fito ya nufi nasa part ɗin yana ɗan murmushi. Ita kuwa auta sai sauri take yi dan ta je ta gayawa Chuchun cewa da gangan yah Jawad ya yi mata duk abin da ya yi mata ɗin nan. A ɓangaren su Kamran kuwa, wato Forest. Washegari da safe kamar yadda ya saba zuwa wajensu haka ya nufo in da suke bayan ya kammala yi wa mama dik abin da ya saba yi mata. Yana tafiya yana tunanin yadda zai yi ya fita wajen dajin nan da kuma yadda zai yi da mama ta barsa ya fita ɗin, ba zai iya tafiya bai tambayeta ba, domin yasan zata shiga tashin hankali na wuce misali, yana kaunarta over, amma kuma ya kasa iya gaya mata, domin yana tsoron kada hakan ya ja mashi rabuwa da su Pretty, ta hana shi zuwa in da suke ma kwata kwata, ƙaramin aikinta ne ta hana shi fita ma kwata kwata idan ta ji yana da burin barin wannan dajin. A kan hanyarsa na zuwa wajensu ya cikaro da Rocky, bai wani kula shi ba ya cigaba da tafiyarsa kawai, rufa mashi baya Rockyn ya yi suka jera kamar yadda suka saba, sai wani miƙa yake yi da alama ya ci nama ya ƙoshi ne ya yi barci ya tashi. Dajin gabaɗaya akwai danshi danshin ruwa, saboda ruwan saman da aka yi jiya, da wasu ganyayyakin itace suna zubar da ruwa, wasu ramukan sun cika da ruwa, idan suka zo wucewa sai Rockyn ga tsallaka Kamran yake bin bayansa, haka suka cigaba da tafiya har izuwa wajensu Pretty. A waje Rocky ya kwanta, already kunsan baya iya shiga ciki, kofar ta yi mashi ƙarami. Ciki shi kuma Kamran ya shige, ga mamakinsa sai ya tarar basu a ciki dukkansu. Zaro idanu sosai waje ya yi yana tunanin to ina kuma suka tafi? Yasan dai Sweetie ita bata fita, koda Pretty ta ce tazo suje waje, in dai ba da shi bane bata yarda ta je, kullum tana cikin abinta, to ina suka je yau kuma?. Ya jefawa kansa tambaya. Ganin babu mai bashi amsa ne yasa ya yi saurin juyawa cikin zafin nama ya nufi wajen. Rocky na kwance kamar yadda ya barshi. Bai bi ta kansa ba ya nufi wajen ƙoramar nan, dan ya duba su. Da sauri Rocky ya miƙe ya rufa mashi baya. Tun daga nesa yake baza idanu ko zai gansu, amma kuma bai ga alamar su a kusa ba, hakan yasa ya yi saurin ƙarisawa wajen, dayawan lokuta tun daga nesa yake hango Pretty a saman durse tana wasa da ruwa, to yau dai bai ganta a wajen ruwan ba. Har yana haɗawa da gudu ya ƙarisa wajen. Zaune suke a ƙarƙashin bishiya, Sweetie tana magana ita kuma Pretty ta buga uban tagumi tana kallon ruwan dake gudu a ƙasar ƙoramar. A hankali Kamran ɗin ya lallaɓo kamar wani ɓarawo, ya ce da Rocky ya tsaya yana zuwa, da yake sun saba sai Rockyn ya tsaya, sanɗo ya fara yi kamar mai son yin wani abin, da yake Pretty ta bawa hanyar da yake zuwa baya sai bata gansa ba, ita kuma Sweetie dake fuskantar hanyar bata gani, so basu san da zuwansa ba. Sanɗo ya cigaba da yi har ya iso kusa da Pretty, dama tana zaune ne a saman jijiyar bishiyar, irin bishiyoyin nan ne masu jijiya manya manya kamar jikin wani bishiyar, to a saman jijiyoyin suka zauna daga ita har Sweetien. Yana ƙarisowa wajen cikin dabara ya sanya hannunsa ya capke kan black snake dake ƙarƙashin jijiyar bishiyar ta bayan Pretty ta kuma gaban Sweetie kenan, yanayin yadda suka zauna kamar suna fuskantar juna ne, Pretty tana fuskantar ruwa, ita kuma Sweetie tana fuskantar hanyar dake bayan Prettyn, so Pretty ta bawa macijin baya shiyasa bata gansa ba, ita kuma Sweetie bata gani ma bare ta ganshi, ga shi kuma a gabanta, sai dai bai yi yunƙurin cizonsu ba, yana kwance ne shiru shi ma macijin, da alama ma kamar bai ji motsinsu ba, kuma dai hira suke yi a kan mum ɗinsu, suna tattaunawa a kan ina take? Ina ta shiga? Ina ta tafi ta barsu? Ta mutu ne ko tana raye? Suna kewarta. Yana damke kan maciji, macijin ya harɗe mashi hannunsa da bindinsa, matse kan ya yi da karfi dan ma kada ya fito da waɗan nan shegun harshen nasa mai baki biyun ya caka mashi dafi. Kusa da Prettyn ya zauna tare da ɓoye hannunsa da ya riƙe macijin ta bayansa dan kada ta gani. Jin an zauna a kusa da ita yasa ta juyo da sauri. "Lah Kamran kai ne?". Ta faɗa cikin tsantsar farinciki tana sakin murmushi. Sweetie ma cewa ta yi. "Malam Kamran ya aka yi kasan muna nan? Sannunka da zuwa". "Ai nasan ba zaku wuce nan ɗin ba shiyasa da naje can baku nan na zo nan, ya karfin jikinki?". Ya yi maganar kamar wanda shock na wutar lantarki ta kama, ba komai yasa hakan ba kuma face wannan maciji dake ta faman harɗe mashi hannu da bindinsa. "I really missed you Kamran, yanzu ma am thinking of you, na ce baka zo ba har yanzu, ashe kana hanya". Cewar Pretty. Sweetie ce ta amsa da cewa. "Kamran yesterday bamu yi sallama ba, you just go without telling me, pretty kawai ka gayawa". Juyowa ga Sweetien ya yi da nufin ya bata hakuri. Ihun da Pretty ta zunduma ne yasa ya dakata da yin maganar, ya manta ya juya ta kalli macijin da yake ta faman harɗe mashi singalalin hannunsa izuwa sama, dan macijin yana da tsawo sosai, ga jikinsa sai kyalli yake yi, bakin kirin da shi, mugun maciji kenan, kumurci da idan ya cijeka minti biyar ta yi maka yawa a duniya idan ba'a kawo agajin gaggawa ba. Ihun da ta zunduma yasa Rocky ya ƙariso wajen da gudu. Ita kuwa ta miƙe da gudu zata bar wajen, ta ruɗar da Sweetie da ba gani take yi ba, sai faman tambayarta take yi Pretty lafiya kike ihu, amma ina ita ƙoƙarin guduwa ta bar wajen ma take yi. Cikin hanzari ya riƙota da hannunsa ɗaya yana ƙoƙarin ya yi mata magana, ai ina wani irin ihun da ta saki sai da dajin ya amsa, kan kace me kuma ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutar nema, akwai ta da shegen tsoro, kuma shi fa maciji kwarjini ne da shi, ba kowa yake iya kallonsa kuma ya wuni cikin walwala ba, bare kuma ace mutun yana da tsoro dama, idan ka kalle shi sau ɗaya a wuni sai ka rinƙa jin kamar fa yana nan tare da kai, koda kuwa an kashe shi a gabanka, duk sai ka ji kana takure. Ai kuwa sume mashi a jiki ta yi. Yana ƙoƙarin sauketa ƙasa ya miƙe dan yasan ya zai yi da macijin, sai ga Rocky ya ƙariso wajen. Gabansa ya zo ya fara buɗe mashi baki a kan ya bashi kan macijin ya rike mashi sai ya zame hannunsa daga harɗe shi da macijin ya yi, da alama sun saba yin hakan. Ba musu Kamran ɗin cikin dabara ya bashi, ko tsoro bai ji ba ya warware hannunsa daga naɗin da macijin ya yi masa. Da gudu Rockyn ya bar wajen da macijin sai wintsila bindi yake yi. Shi kuma ya kwantar da Prettyn a kasa a wajen ya miƙe tsaye ya riƙo Sweetie dake ƙoƙarin miƙewa tana ta ambatar sunan Pretty lafiya kuwa, duk ta ruɗe. Riƙota ya yi yana faɗin ta yi shiru babu abin da ya sami ƴar uwarta, kawai ta ga maciji ne ta tsorata. Aikuwa ita ma Sweetien tana jin sunan macijin ta kara rikice mashi tana tambayarsa ina macijin yake? Ya cizan mata ƴat uwa ko? Nan take ta fara yi mashi ruwan hawaye. Rarrashinta ya fara yi babu kakkautawa tare da gaya mata babu abin da macijin ya yi masu, sumewa kawai Prettyn ta yi. Subhanallah ai kuwa sake rikice mashi ta yi tana faɗin. "Na shiga uku sumewa kuma? Suma fa kanin mutuwa kenan, dan Allah Kamran ka tasan mun ƴar uwata kada ta mutu". Dafe kansa ya yi yana danasanin gaya mata cewa suma ta yi, shi wlh idan abu ya rikice tsakaninsa da twin's ɗin nan suna rikita shi sosai, kusan buɗa mashi ƙwaƙwalwarsa suke yi, ba Sweetien ba ba Prettyn ba dukkansu idan abu ya rikice halinsu iri ɗaya ne. Da kyar ya samu ta yi shiru, sannan ya zaunar da ita ya koma wajen Pretty, ɗaukarta cancak ya yi ya ƙarisa bakin ƙoramar da ita, a saman wani dutse mai ɗan faɗi ya kwantar da ita tare da sanya hannunsa ya ɗebo ruwa mai haske daga cikin ruwan dake gudu. A fuska ya shafa mata ruwan. A haukace ta........ 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________43🔥 FOREST🏞️🔥 A haukace ta farfaɗo tana ihun kada Kamran ya bari macijin ya kamata. Da kyar ya samu ta nutsu ya iya gaya mata ai macijin baya nan ya tafi. Kin yarda ta yi, ta ce ita lallai su bar wajen, ba zata sake zama a wannan wajen ba. Shiru ya ɗan yi yana tunanin da bai zo ba fa idan macijin ya farga da suna wajen zai iya yi masu illah, kuma ita Pretty ita zai fara yi wa illar, dan ta fi kusa da shi, tab ai kuwa da yau dajin nan babu zaman lafiya, da kowani namun dawa sai ya san da zamansu a cikin wannan daji, dan wannan ɗan bakin nata idan ta fara kurma ihu ina ga har Mamma yau sai ta jiyosu. Ganin ya yi shiru ya afka duniyar tunani ne yasa ta miƙe da sauri tana faɗin. "Bari na je na kama hannun Sweetie mu koma, ba zamu sake zuwa wajen nan ba". A hanzarce ya miƙe ya rufa mata baya, bai ce da ita komai ba, dan yasan ko ya ce zai yi magana ma ba zata saurare shi ba, ta rigada ta yanke hukuncin, kuma a yadda take uwar tsoron nan ai kuwa ba ita ba sake zuwa wannan waje kamar yadda ta faɗa, sai dai su sake wajen zama dan shan iska amma ba nan ba! Ta. Tana zuwa ta riƙo hannun Sweetie tana faɗin. "Tashi mu tafi Sweetie, Allah there's snake's here, ba zamu sake zuwa ba". Da sauri Sweetien ta miƙe tare da faɗin. "I hope snake ɗin bai yi maki komai ba?". "Yeah bai mun komai ba, let's go kawai". Tana kai karshen maganar ta ja hannunta ta mata jagora suka nufi hanyar komawa, ko kula Kamran ɗin taki yi, kamar shi ne ya kawo macijin wajen, wannan yarinya idan baka san halinta ba sai ka ce aljanu ne a kanta, wanda ya yi laifi daban, wanda kuma ake fushi da shi daban. Bata tsaya ko'ina ba sai mazauninsu. Ciki suka shige. Bayansu ya bi, bawan Allah shi tunanin zuwa wajen wancan tekun ma yake yi, bai wani damu da kin kula shi da suka yi ba, dan in da sabo ai yasaba da halin Pretty, sai dai hakuri. Bayan sun zauna ne shi ma ya zauna a saman dutsen da ya saba zama. Cikin sanyin murya ya ce. "Pretty zaki rakani?". Tana ƙoƙarin kwaso kayan cimarta haɗe da su fruits da ba'a yanyanka ba, dama bata wani ci abu sosai da safen nan ba, dan tana jiran ya zo sai ta ci, idan tana kewarsa bata wani jin yunwa sosai, sai dai Sweetie ta ci abin da zata ci, ita kuma sai ta jira ya zo. "To where?". Ta faɗa tana zube kayan a kusa da Sweetie dake zaune a bakin gadonsu. "Wajen wancan teku na jiya, daga nan zamu je......". Sai kuma ya dakata da yin maganar, da ya so ne ya ce mata daga nan sai su je gonar Mamma su ciri masara da sauransu, sai ya tuna in dai ya bari Pretty ta san hanyar mazauninsu to wlh da ta ji kewarsa zata nufi wajen, idan mamma ta ganta kuma kun san me zai biyo baya, lokacin rabuwarsu ya yi kenan, kuma gonar na mamma idan baku manta ba bashi da nisa da in da ƙogonsu yake, so idan ya kuskura ya je da ita wajen tamkar ya kai ta mazauninsu ne da kansa, hakan yasa ya dakata da yin maganar bai ƙarisa ba. Da yake ita ma ta abinci take yi bata tasa ba, sai bata wani mayar da hankalinta a kan ya dakata da yin wata magana bama, sai ta ce mashi. "Kamran I can't go anywhere today, am very scared for seeing this snake, so today am here no going out again". Tana magana tana ɓare wasu ƙosassun ayaba, sun ƙosa sosai, kuma a jikin bishiyarsu suka nuna, hakan yasa suke da zaƙi sosai, ga matuƙar kyau a ido ɓul ɓul, ai dole ne ma jikin Sweetie da Pretty ya yi kyau tamkar waɗan da suke rayuwa a cikin Ac cikin wata Daula mai girma, jikinsu luwai luwai saboda shan kayan marmari, ga su kuma ta ko'ina a cike ɓul ɓul, tsokar jikinsu masha Allah, shiyasa kullum Kamran yake karewa gurun wuyar nan nasu kallo, barema na Pretty, tsoƙar wuyar tata ya fi na Sweetie cikowa sosai, kun san fa ita dama acici ne mala'ikun tauna, bata wasa da ci, kuma a koda yaushe ka ganta sai ka ganta rike da ayaba ko lemu or kwakwa tana ɗan motsa baki, ita dai bata son zaman shiru, shiyasa ga shi nan tafi Sweetie cikowa ta ko'ina ɓul ɓul kamar wata mai shekaru 13 zuwa 14, alhalin nan ko 11 years basu cika ba. "Haba Pretty please escort him mana". Cewar Sweetie. Tana aikin tura ayaba a ɗan bakinta ta bata amsa da. "I can't, amma ke zaki iya miƙewa ku je ai, ni an ce maki na shirya mutuwa ba tare da na sake kallan mum ɗina bane? Ai sai mum ta dawo tukun nan koma me zai faru ya faru". Ta kai karshen maganar tare da miƙowa Kamran ɗin nonan ayaba guda ɗaya mai ɗan girman da akallah ayaba 12 ne a jikinsa. Karɓa ya yi tare da ajiyewa a gefensa, dan shi kansa ayabar ta burgesa, kamar zai tambayeta a ina suka samo ayabar, sai kuma bakinsa ta yi mashi nauyi ya kasa iya tambaya. Shi dai yasan ba shi ya kawo masu wannan ba, wanda yake kawo masu ba irin wannan bane, red banana yake kawo masu, su ne suka fi yawa ta wannan yankin, wannan da ta bashi kuma green ne. "Pretty yau Kamran ɗin kike gudu ko? To ni dai ban apple ɗaya bari na sha na kwanta na yi barci, malam Kamran yau dai Pretty na gudunka". Cewar Sweetie. Yake ya ɗan yi mai kama da murmushi kamar Sweetien tanan kallonsa, sannan ya ce. "Bani take gudu ba, snake take gudu, ni bari na je zan dawo yanzu ba jimawa, zan duba tekun nan ne". Ya kai karshen maganar tare da ɗaukar ayabar da ta bashi ya miƙe tsaye. "Kamran". Pretty ta ambaci sunansa a hankali. Zuba mata ido ya yi ba tare da ya amsa ba. "Kuma tafiya zaka yi?". Ta tambaya ita ma tana kallonsa, kun san idan ya zo tafiya dama bata son rabuwa da shi, kuma tana jin tsoron rakasa, zai ta fi shi kaɗai kuma tana jin kamar ba zata iya zama ya tafi ya barta ba, bata son ya matsa daga kusa da ita ko nan da can. Da e ya amsa mata, shi kansa baya son matsawa daga kusa da ita kun san haka, amma kuma neman hanyar da zata ɓulle masu abu ne mai matuƙar muhimmanci a garesa, so dole ne ya je domin neman mafita. Narai narai da ido ta yi mashi zata yi kuka, ga gwandar daji a rike a hannunta ta sha rabi bata ƙarisa sha ba. "Please Pretty don't let your tears to come out, zaki sanya zuciyata ta yi mun zafi, yanzu fa zan dawo". Ya yi maganar cikin wata iriyar murya wadda da ka ji ta zaka san shi ma baya cikin jin daɗi, dan sun shaƙu sosai har ta kasance in sun haɗu suka zo rabuwa zuciyarsa kuka take yi, ita kuma Pretty kuka a zahiri take yi, Sweetie ma kukan zuci take yi bana zahiri ba idan zasu rabu, Pretty ce sarkin hawaye mai yi a fili kowa ya gani. "To Kamran ka bari mana sai zuwa gobe sai ka je ka yi checking na abin da zaka duban, now ka zauna da mu please". Cewar Sweetie da a kullum kaunar Kamran ɗin karuwa yake yi a ranta, mutumin da bata san shi ba, bata taɓa ganin face ɗinsa ya yake ba, bata san ya zuciyarsa na ainahi yake ba, ta iya yiwuwa a wajensu ne yake mutumin kirki, a bayansu ba haka yake ba, duk bata san wannan ba, ita dai zuciyarta na sonsa, shi kuma zuciyarsa na son Pretty, son da yake yi wa Pretty ma ai ko kansa baya yi wa hakan, ta zama tamkar bugawar numfashinsa, komai yake yi yana tunaninta, tun ranar da aka haifeta, ya ɗauketa tana tsallara wannan ihu, tun da lokacin ta shiga cikin zuciyarsa, sau da dama idan zai yi tunaninta yana tunaninta ne a ranar da ya ɗagata tana jaririya ko cibiya ba'a yanke mata ba, ya ɗauketa ya kudunduneta a cikin rigar da ya cire daga jikinsa, tana ta tsallar ihu da wannan red lips ɗin nata suna ta kerma saboda sanyi, tun da lokacin ta dasu mashi a cikin zuciyarsa wanda cireta kuma ba abu ne mai yiwuwa ba, sai dai idan za'a haɗa da zuciyar tasa dukka a cire. To fah, babbar magana kenan, akwai cakwakiya ba kaɗan ba. "Sweetie ba zan jima ba zan dawo kin ji? Kada ku damu". Da okey kawai ta amsa mashi, amma daga jin yadda ta amsa kai kasan rai bai so ba, kawai ta amsa ne dan bata son ja in ja da shi. Ita kuwa Pretty tuni idanunta sun ciko da kwallah, tasan cewa idan ya je zai ɗan jima kafin ya dawo, idan kuma ya dawo ba zai wani jima a wajen nasu ba zai ce masu zai koma, shikenan yau ba zasu jima a tare da shi ba, zai tafi ya barsu da kewa, in ya tafi kuma sai yamma zai dawo, wannan dalilin yasa duk ta ji babu daɗi. Kawar da kansa ya yi tare da ficewa da sauri, dan baya son ganin kukanta, kuma shi gaskiya yana son sanin hanya cikin ƙanƙanin lokaci, dan a gaskiya ya gaji, yana son ganin duniya ya take. Zuciyarsa sai yi mashi kuna take yi, amma a haka ya sa kai ya wuce hannunsa rike da ayabar da ta bashi. Ita kuwa Pretty goge hawayen face ɗin nata ta yi tare da ture kayan cimar da suke a gabanta gefe guda, sannan ta miƙe ta koma kusa da ƴar uwarta tana faɗin. "Sweetie sam sam i don't want Kamran to go anywhere ya bar mu, am not happy at all, and am feeling very very bad mood idan baya nan". Ta kai karshen maganar tare da kwanciya ta tada kai da laps na Sweetien. "Same here Pretty, ina jin kuna a cikin rai'na idan zai tafi". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "But Sweetie why not mu fara neman mum da kanmu? Maybe fa tana a cikin Forest ɗin nan kusa da mu". "E kince wani abu, let Kamran come back sai mu gaya mashi, zai tayamu nemanta, maybe tana nan wani abin ne ya riƙeta, kinga idan muka ganta zata rage mana kewa, idan Kamran ya zo tafiya ba zamu damu sosai ba". Allah sarki bayin Allah, ai ko dan kasancewarsu su kaɗai a cikin wannan ramin ma dole su rinƙa kuka idan Kamran zai tafi ya barsu, abin akwai taɓa zuciya, babu uwa babu uba, babu wani ɗan uwa, babu motsin halittar ɗan adam sai dai na dabbobi su tsuntsaye da sauransu, babu gida gaba babu gida baya, su biyun nan suke rayuwarsu kafin Allah ya kawo masu Kamran, gwanin ban tausayi sosai, dole ma su sha kuka a duk lokacin da zai tafi wajen Mammarsa, Allah sarki. Cigaba da hira suka rinƙa yi suna neman mafita a tsakaninsu, da haka har barci ya ɗauke Pretty, ya rage Sweetie kawai da ta kasa yin barcin, tunanin mafita ta shiga yi tana ɗan shafa kyakkyawar gashin kan Prettyn wadda yake a saman laps ɗinta, tana matuƙar kaunar ƴar uwar tata, ita ma Prettyn tana matuƙar kaunarta, su biyun nan su ne duniyar juna, ita ce duniyar Pretty, Prettyn ma Sweetien ne duniyarta, komai nata, so suna tsananin kaunar juna. Kamran kuwa tafiya ya yi wajen wannan teku na jiya dan ya duba ko akwai wata hanya mafi kusa ta gefe gefen tekun. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH 💔😥 After some days. A cikin waɗan nan kwanaki da suka shuɗe dai maman Zainab ta yi nasarar samun sa'a wannan asiri na jikin Zainab dai ya karye, ta tsaya ne tsayin daka wajen ganin ta yi wannan haɗin maganin da mamanta ta gaya mata, so Allah da ikonsa Zainab ta dawo normal. Sai dai kuma wani tashin hankali shi ne tun ranar da baban Zainab ya fita gidan a tare da Hauwa bai sake dawowa gidan ba, su maman Haidar sai nemansa suke yi, amma ina basu gansa ba, sosai maman Zainab ta shiga damuwa maras misaltawa, ta yi mummunar rama sosai da sosai, kamar ba ita ba, har duhun wahala da damuwa sai da ta yi, sun dawo yin rayuwa daga ita sai su Zainab da Sadiq, Haidar ma yanzu sai gefi gefi yake shigowa gidan, watarana a gidan kakarsa yake kwana. Ga wani bala'i da hajiyarsu ta taso masu da shi shi ne wai auren Khadija and Haidar za'a yi shi kafin ta rubuta Exams ɗin, sun fasa bari sai ta rubuta, saboda Haidar ya matsa masu sosai, shi fa sam bai damu da rashin sanin in da babanta yake bama, bai wani damu da halin da suke ciki ba, ko a jikinsa, abin da yake gabansa kawai yake yi. Maman Zainab ji take yi kamar ta kwashi ƴaƴanta su koma wajen mahaifiyarta, Sadiq kuwa ya ce mata a'a ta yi fito na fito da su ta gaya masu Khadija bata son Haidar, dan haka ba za'ayi wannan auren ba, idan sun ki sun ce sai anyi aure to ta shigar da su kara ga hukuma a kwantar ma yarinya hakkinta, tun da yanzu baban Zainab ma ba ta su yake yi ba, dan haka ta tsaya ta kwatarwa ƴarta yanci. Ta ɗauki kwanaki tana tunani a kan zance Sadiq ɗin, daga karshe dai ta kira mamarta a waya ta sanar da ita ga wani lukutar masifa da suke ciki, sannan ga shawarar da Sadiq ya bata. Da yake mahaifiyar tata dattijuwan arziki ce sai ta ce mata. "A'isha duk abin da zaki yi ki rinƙa kallon Mamarsa tamkar ni ce, ki girmamata kada damuwa ko ɓacin rai or zuciya haɗe da shaiɗan ya ja ki ki yi mata wani abin da ba zaki iya yi mun ba, kada ki manta zamanku da ɗanta a baya, na baki izini ki kwatarwa ƴaƴanki yanci, amma kada ki wuce gona da iri, uwa bata fi uwa ba, mahaifiya dai mahaifiya ce, kada ki riƙi hujjar cewa hankalinsa baya a kanki ki ce zaki walaƙanta mahaifiyarsa, ki sani in shi baya nan Allah yana nan, kada ki yi wannan kuskuren, komai zaki yi ya kasance tsakaninki da Allah zaki yi, baki san me gobe zata haifar ba, Allah ya kyauta ya saita maki al'amuranki, ki cigaba da yin addu'a tare da yin azzumi komai ya kusa warwarewa In Sha Allah". Sosai Ouumar tata ta yi mata nasiha mai ratsa jiki, daga karshe suka yi sallama. Tana ajiye wayar ta ɗaura ɗamarar rusa wannan aure ta Haidar da Khadija koma ta yaya ne. Da misalin karfe uku na yamma, Sadiq ya dawo da su Khadija daga makaranta, ya bawa maman Zainab ɗin kuɗin cefene, ya zama dai kamar shi ne mai gida, ya rikewa baban Zainab komai nasa da amana, yana kula da komai, kowani karshen sati zai zauna su buga lissafi shi da maman Zainab ɗin, ya ware ribar da kasuwa ta bayar ya zuba a cikin account ɗinsa, uwar kuɗi kuma ya koma da ita kasuwa, a cikin kuɗinsa da yake cirewa na sallamar da baban Zainab ya saba basu tun farko yake cirewa ya bawa maman Zainab ɗin kuɗin cefene, sam ba'a kuɗin baban Zainab ɗin yake ciyar da su ba, daga aljihunsa hakkinsa ya riƙesu bawan Allah. Zai wuce ya nufi kasuwa maman Zainab ta dakatar da shi, ta ce ya zo su yi magana. Ba musu ya shigo cikin parlourn. A saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna, su Khadija kuma suka wuce cikin ɗaki domin su cire uniform su yi wanka kamar yadda suka saba. Cikin rashin kwarin jiki ta gaya mashi yadda suka yi da mamar tasu, sannan ta ɗaura mashi da cewa idan sun ki rushe auren nan tabbas kara zasu kai su daga nan har kotu. Ajiyar zuciya ya sauke, cikin nuna tsantsar kula tare da tausayawa ƴar uwar tasa ya buɗe baki zai fara magana kenan suka fara jiyo bugun kofar gida. Haka kawai maman Zainab ta tsinci kanta da fargaba tare da faɗuwar gaba, kirjinta ne ya fara bugawa kamar wadda ta jiyo dukan kofar gida da tsakar dare. Hannunta ta kai ta dafe saitin kirjin nata, sannan ta furta Hasbunallahu wani'imal wakil. "Sadiq duba su wanene?". Ta faɗa cike da fargabar su waye zata gani, ita a yanzu buga kofar gidan nasu ma bala'i ce a gareta, dan tasan ba alkhari take gani ba, wani lokaci bala'in su maman Haidar, wani lokaci baban Zainab da Hauwa, dukkansu kuma ganinsu tamkar ganin gagarumin bala'i ne a gareta, da zarar sun zo fa to shikenan ɗan sauran walwala da ya saura a tattare da ita ma zai tafi, zata faɗa sabon kuncin da sai ta fi kwana uku bata fita ba, so ganinsu ba alkhari bane a wajenta. Miƙewa Sadiq ɗin ya yi hannunsa na rike da key ɗin mashin din baban Zainab da kuma keys ɗin shago a jiki, haka ya nufi wajen dan ya duba su wanene?. Shi kansa sai da ya shiga fargabar abin da zai gani idan ya buɗe kofar, dan ya gaji da kallon wannan fitina da bala'i shi ma, amma da yake namiji ne shi sai ya ɗanne ya zare jam lock ɗin kofar. Yana buɗe kofar ta fara zazzaga mashi buhun bala'i kamar dama ta tara bala'i ne tana jiran ta samu wadda zata zazzagewa shi a kansa. "Wani irin iskanci ne wannan kusan minti uku kun bar mutane a tsaye a waje? Ku baku da tarbiya ko? Baku san darajar ɗan adam ba zaku barmu a tsaye!!". Wani irin ƙululun bakinciki ne ya tokarewa Sadiq maƙoshi, ji ya yi tamkar ya tsinka mata mari sai ta sume a wajen, wata ƴar gajera da ita a gabansa, ba dan ganin baban Zainab da yake a tare da ita ba wlh yau ba abin da zai hana shi dalla mata mari shegiya. Amma haka ya danne ya kawar da kansa, ko sannu bai ce mata ba ya sa kai zai wuce cikin ɗakinsu kawai, ɓacin rai yasa ya mance bai gaishe da baban Zainab ɗin ba ma. "Kai zo nan". Ta faɗa tana wani ɗage hanci sama. Da alama rashin mutuncin da take ji da shi yau yafi na kullum, da alama yau rabon babin rashin mutuncin ta buɗe. Ɗan zaro idanunsa kamar na Zainab ɗin nan ya yi tare da juyowa ya kalleta. "Yeah da kai nake yi, na ce ka zo nan! Ko ba zaka zo bane?". Hauwa duniya, akwai ta da son nuna isa da taƙama! Burinta ta ganta tana fadanci a waje jama'a suna yi mata biyayya, tana da son duniya da sharholiya sosai!. Sai kace Sadiq ɗin ɗanta ne, ta wani kirasa kamar ita ta haifesa, kira ma na walaƙanci. Kai kallonsa a kan baban Zainab dake tsaye a gafenta ya yi. "Ba zaka zo bane tana kiranka?. Ka tsaya kana ganina?". Cewar baban Zainab ɗin. Ɗan lumshe idanunsa ya yi yana ƙoƙarin danne zuciyarsa, dan wlh in ya biyewa zuciya harda baban Zainab ɗin zai haɗa duk ya ci ubansu, dama a wuya yake da su, suna son kashe mashi ƴar uwa ɗaya tilo, duk time da suka zo gidan idan suka tafi sai ta fi kwana uku tana fama da ciwon kirji, Allah ne kawai yake tsareta wani ciwon bai kamata ba, so a ƙule yake da su, idan ya biyewa zuciyarsa tsab zai sumar da su dukkansu biyu wlh. Juyowa ya yi ya dawo gabanta. "Gani". Ya faɗa yana kawar da kallonsa gefe guda. "Ba zaka tsugunna ba ka wani tsaya a gabana, so kake wuyana ya yi ciwo wajen ɗaga kaina na kalli fuskarka idan zan yi magana ne? Wannan ai rashin tarbiya ne, haka kake tsayawa a gaban mamanka gangan da kai ka sakata ɗaga kai sama dan ganin fuskarka kafin ta yi magana........." Aikuwa bata kai karshen maganar ba ya dallah mata wani irin gigitattacen mari. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce. "Iskancinki ya tsaya a iya kan maman Zainab, dan itace kuka haɗa wani abin da ita, kuma ko ita ɗin ma idan kika sake kuna wani magana da ita kika saƙo mamarmu a ciki sai kin gane ke karamar maras kunya ce! Mahaifiyarmu ba sa'ar ki bace, idan baki ɗauki taki da daraja ba mu tamu tana da daraja.......". Shi ma bai kai karshen maganar ba baban Zainab ya dalla mashi mari tas a kumatu. Wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaura hannunsa ɗaya a kumatun nasa, nan take idanunsa suka yi jajir kamar jini, da alama ransa ya ɓaci sosai. A hanzarce ya sanya kai ya fice daga gidan, domin gudun kada abin ya kwaɓe masu sosai, yasan idan ya tsaya zuciya zata ɗebesa ya daki baban Zainab ɗin ma, idan ya yi hakan kuma sam bai kyauta ba, yana da halinki sosai, baya manta alkhari, ba irin Haidar bane shi ɗin, yanzu ma ba dan ya lura Hauwa na ƙoƙarin saka mahaifiyarsu a cikin rai'nin wayonta ba da ba zai sanya mata hannu ba, yasan idan bai dakatar da ita ba tabbas zata cigaba da kiran mahaifiyarsu a cikin maganarta, shiyasa ya yi saurin taka mata birki, ban da haka da zai danne zuciyarsa ya shanye walaƙancinta ko dan saboda baban Zainab ɗin. Kafin baban Zainab ya yi wani magana tuni ya fice daga gidan da sauri. Kukan munafurci Hauwar ta saka mashi, cike da makircin tana kukan munafurcin ta fara magana. "Wlh baban Zainab ni ba zan yarda ba, kana gani wani ƙato ya dakeni ina matsayin matarka, dole a bi mun hakkina". (Matarsa kuma?🤔 Yaushe aka yi hakan?🤔 Dole su yi mana bayani) Hakuri ya fara bata tare da gaya mata to ba ga shi ya rama mata marin ba. Kafewa ta yi a kan ita fa ba zata yarda ba, wannan marin da ya yi masa ya yi mata kaɗan, idan yana son ta hakura dole ya karɓi komai nasa daga hannun Sadiq ɗin, ya karɓi keys ɗin shagonsa da komai nasa, sannan Sadiq ba zai bisu sabon gidan da ya gina ba, maman Zainab kawai zasu ɗauka, Sadiq ɗin ya koma gidansu. Tirƙashi da alama da biyu ta takali Sadiq ɗin da faɗa, da alama tana da manufa sosai a kan dukiyar baban Zainab ɗin, so ta lura Sadiq ɗin zai kawo mata cikas shiyasa ta takalo faɗar, ga shi kuma da alama burinta zai cika, wanna Hauwar anyi makira wlh. "Duk yadda kike so haka za'ayi, zan karɓi komai na, shikenan?". Ya yi maganar yana goge mata hawayen munafurcin da take zubarwa. Kai ta gyaɗa mashi alamar e hakan ya yi mata. "Tom shikenan mu je cikin ko?". To ta amsa mashi da shi tare da wucewa gaba tana mai tambayarsa to yaushe zai karɓi keys ɗin daga hannun Sadiq ɗin. Amsa mata ya yi da duk lokacin da take so. Tana ƙoƙarin shiga cikin parlourn ta yi saurin amsa mashi da yau take so. Babu damuwa ya amsa mata da shi tare da shigewa ciki. Maman Zainab tana zaune a in da take bata tashi ba, already ta jiyo wannan shegiyar muryar Hauwar mai kama da muryar babanin akuya, jin muryar ma yasa bata motsa daga in da take ba, ta cigaba da zamanta kawai, dan yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani ganin fuskar Hauwa a rayuwarta. "Ana sallama maman Zainab ba zaki amsa mana ba sai kace ba musulma ba? Ko dai kin manta da muhimmancin sallama ne? Ina karatun islamiyar da kika yi? Ko dai ya zube ne?". Cewar Hauwar, ta yi maganar tana ƙoƙarin zama a saman sofa, cike da iyashege da shakiyanci tare da son ganin ta bakantawa maman Zainab ɗin rai ta yi maganar tata. "Kada ki kuskura ki zauna mun a saman kujera Hauwa, idan kuma kika zauna wlh zan yi maki ɗanyen aiki, kin san halina!". Maman Zainab ta faɗa tare da miƙewa tsaye. Kallon baban Zainab Hauwar ta yi ta ce. "Honey waye ya sayi kujerar ne? Kai ne ko kuma daga gida ta zo da su?". Zama ya yi a saman kujerar mai zaman mutu ɗaya. "Ni na saya Hauwa'u na". Wani irin shu'umin murmushi ta saki kafin ta ce. "To maman Zainab ashe kujerar na mijinmu ne ma ba naki ba, to ki bari sai kin sayi naki sai ki hanani zama, amma wannan ai nima nawa ne tun da mijinmu ya saya!". Wani irin murmushi wanda ya fi kuka ciwo maman Zainab ta yi, ƙoƙari take yi ta ɓoye ɓacin ranta, saboda ta lura burin Hauwa ne kullum taga ta cusa mata baƙinciki, in kuwa haka ne to bai kamata ta bari Hauwar tana ganin ɓacin ranta ba, hakan yasa ta yanke shawarar fito da nata makircin na mata, ai ba Hauwar ce kawai ta iya makircin ba, kowa ma ta iya. "Hauwa kenan, to ki zauna a kai ki ga ɗanyen aiki, idan kika zauna ne kuma zaki san ainahin wanene mamallakin kujerar". Ta faɗa tana mai cigaba da ƙaƙalo murmushi dole, daga ta ciki kuma zuciyarta kamar zai fashe, barema da ta ji Hauwar ta ambaci baban Zainab da sunan mijinsu, hakan ya tsaya mata a rai sosai, sai dai taki yarda ta fitar da ɓacin ran a fili bare ma Hauwar ta gani ta ji daɗin ta ɓata mata rai. Kasancewar Hauwar ta san halin ƙawar tata sarai, sai bata zauna a saman kujerar ba, sai ta fake da jan magana, irin kada ace ta tsorata ta ƙasa zama a saman kujerar, ta fake da kananan maganganu tana ta soki burutsu tana ƙoƙarin ta cusawa maman Zainab ɗin ɓakin ciki ta hanyar nuna mata cewa ai baban Zainab yanzu mijinta ne, har da wani cewa kila ma yanzu sun sami ɗan tayin ciki da bai wuce sati ɗaya ba. Ba yake maman Zainab ɗin ta gama fahimtar dan ta ƙuntata mata ta zo gidan, sai bata nuna kamar ta damu ba, sai ma murmushi da ta saki tare da cewa. "To ai dama shi namiji mijin mata huɗu ne, me a ciki dan ya aureki? Yanzu ma ai akwai sauran gurbin mata biyu a tattare da shi, so yana iya cike gurbin ya rufe kofa kawai, idan ma bashi da ƴan matan da zai cike gurbin da su ba sai mu samo mashi ba, ki samo mashi ɗaya in samo mashi ɗaya ya kara ya rufe kofa me a ciki?!". Sam sam Hauwa bata so hakan ba, ta so maman Zainab ɗin ta tada balli dan su ji daɗin yi, ko kuma ta hau kuka burinta ya cika, amma ina maman Zainab ta gwada mata cewa ai ita ma ta iya makircin, ta shanye ɓacin ran tsab ta ɓuye kayanta. Meyake faruwa a tsakanin Hauwa da kuma baban Zainab ne? Nasan kowa tana son sani, to ku matso ku kasa kunne. Hauwa dai sara ce ta zo mata a kan gaɓa, dama already ta kashe aurenta saboda ta auri baban Zainab ɗin, zaman idda take yi a gidan mijinta da ta mayar da shi wani soloɓiyo, dama tana can tana shirin yadda zata yi ta mallaki baban Zainab ɗin cikin sauki, ta kai sunansa wajen wannan bokan nata na kan dutse, sai bokan ya ce mata aikin ba zai taɓa yiwuwa ba dole dole sai da wani abinsa da ya taɓa amfani da shi, ko dai single ɗinsa ko short ɗinsa, ko wani abin nasa, to tarasa taya zata yi ta sami wannan, tana ta tunani, kwananta uku da gama idda ta sake komawa wajen wannan boka, a nan ma ya sake jaddada mata aiki ba zai yiwu ba dole sai ta kawo abin da ya gaya mata ɗin nan. Hakan ta kwaso jiki kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta dawo, kwananta biyu da dawowa daga wajen bokan maman Zainab ta kirata a kan matsalar da take ciki, ta yi matuƙar farinciki da jin hakan, domin ta samu damar da zata cinwa burinta, hakan yasa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen bawa maman Zainab ɗin shawarar su je wajen wannan boka, ta kuma zagaya ta gayawa bokan nata ga abin da take son ya yi mata zasu zo a tare da maman Zainab ɗin, kada ya nuna kamar ita zai yi wa aiki, ya nuna cewa maman Zainab ɗin zai yi wa aiki, idan ya yi mata hakan komai ya tafi dai'dai zata bashi maƙudan kuɗaɗe. Da yake bokan mutuminta ne sun saba, ba yau ya fara yi mata aiki ba, shi ya yi mata aiki ta mayar da mijinta soloɓiyo sai abin da ta ce zai yi, ya kuma yi mata aiki ta mallake dangin mijin nata basu da bakin magana a kanta, so sun jima a tare da bokan, hakan yasa ya aminta da wannan aiki da ta kawo mashi, cikin sirri suka shirya komai ta munafurci maman Zainab. Bayan sun zo an yi aikin ne sai Hauwar ta kwashe kayanta daga gidan mijinta ta koma gidan iyayenta a garin Kaduna garinsu maman Zainab ɗin kenan, dama already ta gama iddarta da tsawon sati ɗaya ma kenan, burinta ya cika da samu kan baban Zainab, so a Kaduna baban Zainab ya je ya nemi aurenta, dama na gaya maku ƙanin babanta da take a hannunsa mayen son kuɗi ne, sai abin da Hauwar take so yake yi, dan ita take ɗaukar nauyinsu, dan haka bai wani ja ba da Hauwa ta ce ga mijin da zata sake aura, a takaice dai yanzu sati guda kenan da ɗaurin aurensu, shi baban Zainab iyayensa basu sani ba, ita ma maman Zainab bata sani ba, shi kuma kanin baban Hauwa kuɗi kawai yake so ba ruwansa da tambayar daga ina Hauwar ta samo miji ko ya halinsa yake ko kuma ina iyayensa, shi dai kawai ya bi umarnin Hauwar gudun kada ta cire masu tallafi ya shiga uku, zuciya ta mutu ba zai fita ya yi sana'a ba, Allah ka rabamu da matatciyar zuciya. In short wannan shi ne abin da ya faru a tsakanin Hauwa da baban Zainab, yanzu maganar da nake maku sun tare a sabon gidansa, shi ne fa tsabar mugunta irin na Hauwa, dan son ta kuntatawa maman Zainab ne yasa ta cewa baban Zainab ɗin lallai dole dole su zo su ɗauki maman Zainab su koma sabon gida a tare. Da alama so take ta kashe maman Zainab da bakinciki, wato su koma sabon gida a tare dan ta je ta cigaba da cusa mata kayan takaici, wannan Hauwa tamkar green snake under green grass take, shegiya silent killer, ta san ta kan duniya, cikin ruwan sanyi zata dama mutun. To mata ina fatan wannan yazama darasi a garemu, duk wanda zata ce maki ki je wajen boka wane kaza, ko kije wajen wane ya biya maki bukatunki, hakan yana nufin tasan bokan kenan, sun jima a tare, idan baki ji tsoron Allah kin koma ga Allah mahaliccin kowa da komai ba kika biye mata ta kan iya yi maki irin ta Hauwa, ni labarin gidansu Zainab yi mun yake yi kamar true life story wlh, kamar gaske haka nake jinsa, dan mata dayawa suna tabka irin wannan babban kuskure, yaushe zaki yarda bawa mai kafa biyu! Hannu biyu irin naki, mai yin kashi da fitsari, mai cin abinci kamar yadda kike ci, mai kwanciya ya yi barci ya kuma tashi ya yi tafiya, yaushe zaki yarda mutun kamar ke zai iya biya maki buƙatar da ke ba zaki iya biya ba?! Wannan magana hankali zata ɗauka kuwa?! Mutun ne fa kamar ki! Komai da yake da shi kina da shi! Amma kike yarda da cewa shi ne warakar matsalarki?! To dai ga Hauwa ta nuna maku aya, idan baku kuji bin shawarar kawaye domin Allah ba, zaku guda dan gudun cin amana, bare ma ace kinfi kawar komai, kin fita jin daɗi da morewar rayuwa! Ai abin da kuka ga Hauwa ta aikata wlh kaɗan ne ma a kan wata idan ta tashi tabka maki nata son zuciyar, babu mai sanin mutun sai Allah, Allah shi kaɗai yasan ɗan adam in and out, ko shekara ɗari kika yi a tare da mutun baki isa ki ce kin san shi in and out ba, dan a kowani rana, a kowani lokaci zuciyar ɗan adam tana juyawa tamkar juyin agogo, dan haka mata gareku sai ku kiyaye, kun dai ga aya ƙarara, babu mai yi sai Allah, kuma babu mai hanawa sai Allah, ki miƙa lamuranki ga Allah ki jira ki ga ikon Allah, ba wai ki dogara da wani ƙaton banza mai kashi da fitsari ba!!!. Allah yasa mu fi karfin zuƙatanmu. Mu koma kan labarinmu tun da kunji menene yake faruwa a tsakanin Hauwa, baban Zainab da kuma maman Zainab da yadda aka yi waɗan nan abubuwa suka faru, dan haka mu koma kan cakwakiyar domin ganin ya wasan zata kaya. Gyara tsayuwa Hauwar ta yi, ta dai kasa iya zama a saman kujerar, dan fa ba karya tana tsoron maman Zainab sosai, tasan halinta sarai, macece mai hakuri da kawaici, amma kuma idan ka kureta, dama ance mai hakuri fa bai iya fushi ba, so a gaskiya maman Zainab tana da zuciya over, faɗarta kuma babu daɗi idan ta fara shi, hakan yasa Hauwar bata zauna a saman kujerar ba, sai ta ce. "Allah ko maman Zainab, gaskiyarki haka ne, namiji mijin mata huɗu ne, to amma fa banda honey, shi daga ke sai ni mun ishe shi". Sake sakin murmushi wanda ya fi kuka kuna Maman Zainab ta yi kafin ta ce. "A'a ki barshi ya cike huɗun kawai zai fi, ko dai kina jin tsoron yin kishi da su ne idan suka shigo? Kada ki damu ai ni zan tsaya maki". Ta yi maganar tana jefa mata wani irin kallo mai wuyar fassaruwa. Yau fa ake yinta a wannan gida, kowacce ashe ba tayar baya bace. Ajiyar zuciya Hauwa ta sauke. "To ai ni bana kishi, nafi karfin na yi kishi da mace, ke baki gani bane, yanzu duk bama wannan ba, munzo ɗaukarki ne ke da yara mu koma sabon gida, mu je mu haɗu a can mu zama cikakkun family ai yafi, nasan kuma kina kewar honey sosai, bai kamata ya barki a nan kina ɗaukar kwanaki baki sanya shi a idanunki ba, shi ne naga ya dace na zo na ɗaukeki mu koma can tare, at least a kowace rana zaki sanya shi a cikin idanunki ko sau ɗaya ne kam". Cike da mugunta sosai ta yi maganar, ta kuma yi maganar ita ma tana wurgawa maman Zee ɗin wani irin kallo na nuna tsantsar isa da rai'nin wayo. So take dole dole sai ta kuntatawa maman Zainab ɗin, burinta kawai taga bacin rai ya bayyana a saman fuskarta. "Allah ko?". Maman Zee ta faɗa tana binta da kallo. Wannan shi ne idan mutun yana son ganin kukanka to kada ka yarda ka bari ya tafi ba tare da ka nuna mashi dariyarka ba, sai dai bakin ciki ta kashe shi!. Hura chewing gum dake a bakinta Hauwar ta yi kafin ta ce. "Yeah hakan naga ya dace, ai bai kamata mu barki kina zaman kaɗaici tare da gauranci ba, dan haka ki shiga ki ɗauko mayafinki kawai mu tafi ko honey?". Ta kai karshen maganar tare da juyo da kallonta a kansa. Shi dai ya zubawa wayarsa ido yana aikin latsawa, da alama ma hankalinsa baya a kansu. A takaice ya ce mata. "Yadda kika ce hakan za'ayi". Wani irin tauna chewing gum ɗin nata ta yi sai da ya bada sautin kas kas tare da sakin wani shaiɗanin murmushi. "Tom maman Zainab kin ji honey ya ce yadda nace haka za'ayi ba sauran ja, to na ce ki shiga ki ɗauko mayafi mu wuce, waɗan nan tsofaffin kayan ɗakin naki duk ki barsu a nan ko kuma ki turawa mama Kaduna ta yi amfani da su, akwai komai a sabon gida an zuba, so bamu buƙatar tsofaffin kaya". Haƙiƙa a wannan gaɓar maman Zainab ta kulu da bakinciki, ta zo har wuya, kiris take jira ta fashe, amma sai ta kara daurewa, duk da ta rasa me zata sake cewa da Hauwar, hakan bai hana ta ƙaƙalo murmushin dole tare da sauke ajiyar zuciya ba. Sannan ta sanya kai zata wuce izuwa cikin ɗakinta. "Kiyi sauri, kada ki bata mana lokaci, dan ba zan iya jimawa a wannan gidan ba, zafi ya yi yawa babu Ac, kuma yanzu lokacin cin abincin honey ya kusa". Cewar Hauwa. Tamkar maman Zee bata ji ta ba, sam bata juyo gareta ba, ta nufi cikin ɗakinta kawai zuciyarta na tafasa tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje. Tana shiga cikin ɗakinta Zainab ta fito daga nasu ɗakin zata nufi waje. "Ke Zainabu abu zo nan". Hauwa ta faɗa, har lokacin kuma tana tsaye, ta kasa iya zama a saman kujerar, da alama tana mutuwar tsoron maman Zainab, kawai dan taga baban Zainab yana bata goyon baya ne ma yasa ta tsaya har ta iya gayawa maman Zee ɗin magana, ban da haka tana tsoronta sosai, alamu sun nuna a lokacin kuruciyarsu Hauwa ta sha kashi a hannunta sosai. Wani irin matsiyacin kallo Zainab ta wurga mata kafin ta sa kai ta wuce waje, taki zuwa, dama fa ita Zainab kun san ba kamar Khadija take ba, bata da kunya ko kaɗan, kuma idan baku manta ba tun suna yara Zainab ɗin tafi kowa tsanar Hauwar, bata son ganinta ko su haɗa hanya, bare kuma yanzu da ta ji abubuwan da suka faru, mamansu ta gaya masu komai bata ɓoye masu ba, dan gudun kada su aikata irin kuskuren da ita ma ta aikata, hakan yasa ta sanar da su, so sun san komai, shiyasa Zainab ta kara tsanar Hauwar over ta kuma ɗaura ɗamarar yi mata rashin mutunci idan ta shiga gonarta. Kawai cakwakiya kam. Girgiza kai Hauwar ta yi ba tare da ta sake yin magana ba, da alama akwai abin da zata ƙullawa Zainab ɗin kenan. In short haka Maman Zainab ba musu ta ɗauko mayafinta tare da sanya su Khadija suka ɗauko nasu mayafan domin su tafi, abin da yasa zata je sabon gidan kuma domin su gwabza ne, a cewarta yanzu ta dai'na yin shiru, duk uban da ya ce mata kule sai ta ce mashi cas, sannan kuma tasan tun da Hauwar ta zo ta ce su tafi to fa ko ta ce ba zata je ba baban Zainab zai ce lallai dole ta shirya su tafi, ga shi mamanta ta hanata sake yi mashi musu a kan abu, so gara kawai kada ta yi wani ja in ja ta kara zubar da mutuncinta a gaban Hauwar, dan tasan a yanzu idan ta yi ja in ja da baban Zainab ma yana iya saka mata hannu ya kai mata duka, kunga kuma ai mutuncinta ya kara zubewa a idon Hauwar, dan haka gara mata kawai ta bisu, ta nunawa Hauwar ita ma a shirye take da su je sabon gidan ai. E lallai yanzu kam maman Zainab ta shirya gwabza faɗar domin kwatar ƴancinta. Suna fita daga gidan ba jimawa sai ga su maman Haidar sun zo, dan sun sami labarin yau ya zo gida. Sai dai ko da suka zo kofar gidan a rufe, already su baban Zainab ɗin sun tafi, baban Zainab ya sayi sabuwar mota ba tare da sanin ƴan uwansa ba, Hauwa ce nan ta sanya shi ya sayi motar wai dan ya koya mata, idan ta iya sai ya bar mata kyauta, aikuwa ya saya kuma yana ɗan koya mata a hankali hankali, so a yanzu da motar suka zo suka ɗauki su maman Zainab, Hauwa an dake a kujerar gaba, sam maman Zainab bata nuna kamar ta wani damu ba, ta shiga gidan baya a tare da Zainab da Khadija. Su maman Haidar kuwa ganin gidan a rufe yasa suka juya suka nufi kasuwa ita da maman Hanif, a tunaninsu zasu same shi a kasuwa, ba a tare da hajiyarsu suke ba yau, Hajiyar tasu ta ce idan sun gan shi su ce yazo tana son ganinsa, shi ne ma yasa suka zo nemansa. To bari mu leƙa kasar TUNISIA, wato KINGDOM OF POWER muga me ake ciki. KINGDOM OF POWER. 💪🔥❤️ Yau ta kasance ranar jumma'a, kuma a yau su Obaid jirginsu ya ɗaga zuwa Dubai kamar yadda King ya bada umurnin komar tasu, sai dai fa jirgin nasu bai ɗaga da wuri ba, jirgin karfe 6 na safe zasu bi, amma saboda abin da ya faru a cikin kingdom ɗin yasa suka bi jirgin 11 na rana, shi ma dai da kyar suka tafi ɗin, sai da Jaish ya kaisu airport da kansa, domin yau kingdom babu lafiya, ɗaya daga cikin matan king bata da lafiya, hankalin kowa a tashe ban da Jaish da shi ko a jikinsa, ba abin da ya damesa tun da ba mommarsa bace abin ya shafa, shiyasa ma ya iya raka su Obaid airport hankalinsa a kwance, shi ma Yah Jawad bai wani damu sosai ba, ya dai ji babu daɗi, ita kuma Mammaien Yah Jawad ɗin har wani farinciki da rashin lafiyar na mama ta yi............. To me ya sami mama kuma?🤔 King kuwa yana............. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 3/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________44🔥 KINGDOM OF POWER. 💪🔥❤️ King kuwa yana room ɗin na mamar, saboda ya duba jikin nata, hankalin kowa a cikin kingdom ɗin nan a tashe, kowa sai tunani yake yi a kan me ya sami ɗaya daga cikin matan King ɗin, bayani kuma bai fita a kan me ya sameta ɗin ba, an dai sanar da cewa bata da lafiya. Abin da yasa aka sanar da cewa bata da lafiyar ma shi ne, kingdom of power tana da wata gasa da take gabatarwa na dawakai a kowani jumma'a, kowacce sati suna gabatar da wannan gasa na tseren dawakai wanda jaruman mayaka zasu fito a gabza gasar, wanda ya yi nasar zuwa na ɗaya yana da gagarumin kyauta daga hannun King, daga ɗaya zuwa na goma ake bawa kyauta, ana gabatar da gasar ne domin nishaɗi. A gabaɗaya tarihin kingdom of power ba'a taɓa yin jarumin mayaki biyun HOORAIN ba, shi ne a kullum yake zuwa na ɗaya, kuma kowani sati sai ya shiga wannan gasa, na gaya maku shi ɗin abin alfaharin KINGDOM OF POWER ne, suna ji da shi, haka zali babu yakin da za'a tafi ba tare da shi da commander ne suka ja ragamar rundunar mayakan ba, kuma ko ciwo Hoorain bai taɓa ji a wani yaki da suke zuwa ba, gara commander ya taɓa jin ciwon da sai da ya kwanta jinya, saboda jikin tsufa ya sha wahala sosai, shi kuwa Hoorain sabon jini ne, jininsa a tafashe yake, lafiya lou yake jan ragamar rundunar sadaukan yaki sama da dubu biyar ya jagorancesu su je yaki su dawo, basu taɓa fita yaki basu yi nasara ba, duk girman daula in dai Hoorain da Commander suka jagoranci rundunar mayakan to fa sai sun jijjige wannan daula sun jefar da ita, basu gudu kuma basu ja da baya a fagen yaki komai tsanani kuwa. Idan ka kalli Hoorain ta wata fuska zaka gansa so silent haka, baya da magana kuma baya son hayaniya, amma fa da zaka same shi cikin abokansa mayaƙa ƴan uwansa, yana hira da su sosai, idan ka kalle shi ta fuskar assistant commander kuwa ba zaka so ka sake yin ido huɗu da shi ba, domin kuwa ganinsa a wannan siffar fa bata da kyau, wasu suka ce tamkar ganin mutuwa ne ganin Hoorain a siffar assistant commander, gara ku haɗu da shi a Hoorain ɗinsa a kan ku haɗu da shi a assistant commander. So a kullum a tseren gasar dawakai ma shi yake zuwa na ɗaya, kunsan ita fa doki tana gudu ne kusan dai'dai da bugawar zuciyar wanda yake a kanta, iya karfin da ka sanya mata iya gudun da zata yi kenan, iya yadda zuciyarka take harbawa domin muradin cin nasara, iya power da zata baka kenan, so shi Hoorain yana da zafin zuciya sosai, bugu da kari akwai karfin dantse kamar dokin, idan ya hau kanta yana bata wuta sosai da sosai ta yadda idan ya zo na ɗaya ma ratar dake tsakaninsa da wanda zai zo na biyu ba ƙaramar rata bace, yana kere masu sosai, ko kamshinsa basa jiyowa a gasar. Shi fa har wani wasa yake yi da dokinsa a hanya ma idan ya kusa iso wa, har wani irin karkatawa yake yi kamar zai faɗo kasa, amma har ya dawo cikin kingdom ɗin babu mai iya cin masa bare ma ya wucesa. Sosai Gimbiya Zunaira da kuma Gimbiya Chuchu suke jin daɗin kallon wannan gasa, saboda Zunaira ma yasa King ya kara karfafa wannan gasa ta zama kamar al'ada a masarautar, wajen da ake yin wannan gasa a cikin masarautar take, amma ba ta bangaren fada ba, ta baya ne, an ƙawata wajen sosai, babban fili ne sosai da sosai, tsawon wajen gasar har ta fita daga cikin kingdom ɗin, basa iya ganin karshen filin daga in da suke, kafin a fara gasar dama already za'a ɗaurewa wata lafiyayyar bujumar doki wani jan kyalle mai ɗauke da tambarin kingdom of power wadda kowa yasan tambarinsu shi ne kan zaki, so za'a ɗaurawa wannan lafiyayyar dokin wannan kyalle, sannan a saketa kamar da minti 20 haka, sannan su Hoorain su bi bayanta da nasu dawakan, wanda ya riga kama wannan dokin ya ciro wannan jan kyalle ya kuma ɗaure dokin dan kada ta yi wani wajen, sannan ya dawo da kyallen wajen King shi ne ya yi nasara, abin fa ba sauki ne da shi ba, ba ƙaramin abu bane, har faɗa mayaƙan suke yi a tsakaninsu, su jiwa juna ciwo, amma a haka kullum sati Hoorain ne yake yin nasarar zuwa na ɗaya, duk masu yin wannan gasa fa matasan sadaukan mayaƙa ne masu jini a jika, dukkansu basu wuce sha'anin Hoorain ɗin ba a shekaru, amma shi ya kerewa tsara, renon Commander Zafar ai dama ba za'a haɗa shi da kowa ba, ɗan commander da kansa ai dole dama ya kerewa tsara, horon da ya samu na musamman ne, tun yana ɗan ƙaramin yaro Commander yake koyar da shi dabarun yaki da sauransu. So a takaice dai saboda wannan gasa yasa labarin rashin lafiyar mama ya fita, King ya tsoke yin wannan gasa a wannan sati saboda rashin lafiyar tata, hakance yasa kowa ya sami labarin bata da lafiya, amma babu wanda ya san me ya sameta sai ƴan cikin gida. Nasan kuma kuna son jin me ya sami mama, to ku saurara, daren jiya ne aka samu wasu mayun kwari da babu wanda yasan daga ina suka fito, suka rinƙa ɗana mata harbi kamar zasu kasheta, kafin ta yi ihu a samu a kawo mata agaji duk sun yi mata ruɗu ruɗu da jiki, duk in da suka ɗana mata harbi sai wani kuraje ya bayyana a wajen tulele da shi jajir, abin ku da farar fata, duk jikinta ya yi ruɗu ruɗu, hakan ya saukar mata da mummunar kuma zazzafar zazzaɓi sosai, ga kurajen sai yi mata zogi da raɗaɗi suke yi, ga azaban kaikayi, babu kuma halin ta sosasu, idan ta ce zata sosa sai raɗaɗin azaba ya kasheta, wannan shi ne halin da take a ciki, harta face ɗinta waɗan nan shegun kuraje basu bari ba, har face kwarin suka cijeta, fuskarta ya kunbura kamar cincin puk puk. Tun a wannan dare da abin ya faru, family gabaɗaya suka taru a room ɗinta lokacin da take ihun neman taimako, ba wasu masu yawa bane fa kwarin, basu fi su goma ba amma suka yi mata wannan aika aikan, kuma baa iya gane menene ya cijeta ɗin ba, domin kuwa kwarin basu da yawa, gasu ƙanana ido baya ganinsu. Sai dai tun a daren Momman Zunaira ta fahimci tabbas wannan cizon na waɗan nan kwarin na su Obaid ne, sai dai bata nuna kamar ta gane nasu ɗin bane, domin kuwa tasan idan kowa yasan nasu ne ba ƙaramin rikici abin zai zamar masu ba, mama tana da yara ita ma, so suma za su ce ba zasu bari ba sai sun ɗauki fansa, saboda dai suma jinin Modarawa na gudu a jikinsu, akwai jinin Akka, ba sai na sake faɗa ba kun san dai Modarawa basu barin bashi, ko ya ka taɓosu sai sun rama, babu yafiya, idan baka taɓosu ba kusan za'a ce sun fi kowa iya zaman amana da adalci ga mutane, amma ka kuskura ka taɓosu fa sai sun rama, ba ɗaga kafa, idan kowa ya ce zai ramawa mamarsa to fa daga nan gida kuma ya dai'na zaman lafiya, duk da cewa dama yanzu ma ba wani zaman lafiya iyayen suke yi ba, ɗan garama yaran nasu da yake basu ne masu yin kishinba, su kansu a haɗe yake, amma iyayen dai sai a hankali, kun san da hakan. Wannan dalilin yasa momma ta ɓoye cewa kwarin nan nasu twin's ne suka ciji Mama, amma dai ta ƙuduri niyar sai ta yi masu faɗa sosai, zata tsawatar masu ta yadda ko da sunan wasa ba zasu sake yi wa wani makamancin irin hakan ba, domin wannan irin cizon kwarin ba ƙaramin azaba ne da shi ba. Amma kash bata samu damar ganawa da su ba har suka wuce Dubai, hakan kuma ya samo asali ne saboda suna a tare da mamar ita da Mummyn Gimbiya Chuchu da Mammiensu Yah Jawad, sai kuyangun da suke yi wa mamar aiki, su ne a tare da ita. Kwararrun likitoci kala kala har kala wajen biyar ne suke a kan mamar suna kula da lafiyarta, ba'a kaita hospital ba duk da a cikin kingdom ɗin asibitin yake, King ya ce likitoci su zo har cikin room ɗinta su yi treating ɗinta. Hakan kuwa aka yi, suka zo suna kula da ita, so su Momma suna a tare da ita. King ma yau bai fita fada ba, yana a tare da ita, bata iya gane wanda yake kanta ma saboda zafin zazzaɓi, tasha bakar azaba, har da suma ta yi kafin likitocin su zo, a sume suka zo suka sameta. Da kyar da taimako Allah suka bata taimakon gaggawa ta farfaɗo. King bai bar wajenta ba sai da lokacin tafiyarsa masallacinsa na jumma'a ya kusa, sannan ya nufi part ɗinsa domin ya je ya shirya. Akka ma tana cikin room ɗin, ita ma Akka ta so ta gane cewa waɗan na kwari na su twin's ne suka ciji mama, saboda ita ma Akkar ƴan biyu ce, daga wajenta aka gado twin's ɗin nan, sai dai ita ɗan uwanta namiji ne, amma kuma sai zuciyarta ya raya mata a kan me su twin's zasu yi wa mama wannan aika aikan? Ganin babu wani dalili ne yasa ta kawar da tunanin su suka yi wannan aikin. King bawan Allah yana can yana tunanin ta ina aka samu irin waɗan nan shegun kwarin masu cizon har cikin room ɗinta saman gado? Dan ya gano waɗan nan kuraje da suka feso mata a jiki cizon wasu halittune daga cikin halittun Ubangiji, sai dai bai san ya aka yi aka sami kwarin ba, bai kuma ga kwarin da idanunsa ba, yasa an cire komai na gadonta an kakkaɓe, amma basu ga komai ba! Ya ɗaura tuhumarsa a kan kuyangun da suke gyara mata ɗaki, bai san shakiyan ƴaƴansa suka yi aika aikan ba, sun koma Dubai sun barsu da jidali. Wannan rashin lafiya ta mama ai jidali ne suka ɗaurawa family, dan kowa sai jikinsa ya gaya mashi, zasu sha wahala kafin mamar ta sami lafiya. Sosai King ya yi shirinsa kamar yadda ya saba zuwa masallacin, ya haɗe a cikin farar alkyabbar wadda kwalliyar jikinta ma duwatsun gold ne, sai kyalli suke yi, haka zali takalmar sarautar da suke a kafafunsa kwalliyar jikinsu da zallar madarar gold aka yi su, ya sha naɗin na wani haɗaɗɗen farar rawanin, ya yi masifar kyau sosai, haka ya fito domin zuwa masallacin. Already an ƙawata mashi dokin da zai hau, ta sha kwalliya da kayan ado na dawakai masu bala'in kyau da tsada, kuɗin kayan kwalliyar dokinsa kawai ya isa ya sayawa mutun katafaren gida a babban birnin tarayya Abuja Nigeria. Tun ba'a buɗe kofar fada ba kilishi da sallama suka fara zuba kirarin sarki zai fito, masu busa suka hau yin busa, tun kafin a buɗe kofar fada da take fuskantar harabar kingdom ɗin mai sanarwa ya sanar da fitowar sarki ta hanyar amfani da amsakuwa. Hakan yasa kowani bawa mai rai da yake cikin masarautar sai da ya nutsu jin sarki zai fito. Nan take masu busar dake a wajen fadar suna dakon fitowarsa suka fara buga busar tasu, masu kirari ma suka fara rera kirarinsu, abin gwanin ban sha'awa, komai cikin tsari da bin ka'ida tare da ƙayatarwa, mayaka duk sun nutsu, ga wasu jiga jigan mayaƙa da a kallah zasu kai su 100 da suka jeru tun daga farkon kofar fadar har izuwa karshen stage na haurawa wajen kofar katafaren fadar, duk waɗan nan mayaka suna a ƙarƙashin kulawar Hoorain ne tare da bin umarninsa, already dama sun saba yin hakan, suna tsayawa a wajen ne domin tabbatar da sun bawa King tsaro har ya hau saman dokinsa zuwa masallaci. Commander kuwa dama shi a cikin Fada yake zama kun sani, da shi ake tattauna duk wata zance da ta shafi fada dama kingdom ɗin gabakiɗaya. Bawan Allah tsufa ta ɗan fara kama shi, yana da ƙoƙari da jajircewa ne sosai, assistant commander yana kula da mayakan sosai, shi kuma yana cikin fada, idan ma zasu je yaki to yana ciki zasu tattauna, idan King ya tsayar da zance sai ya kira Hoorain ya gaya mashi, shi kuma ya hau shirya sadaukai kawai, so haka tsarin yake. Sai da komai ta kankama sannan aka buɗe katafaren kofar fadar, su Galadima ne a gaba shi da malam liman, sannan su makama suka biyo baya, King yana a tsakiya an rufe shi, wasu jiga jigan mayaƙa biyu suna take mashi baya, Hoorain and commander kuma suna ta gabansa, su ne masu bashi tsaro ta gaba. A haka suka fito suka nufi wajen dokin da aka shirya mashi dan zuwa katafaren masallacinsa da yake a cikin kingdom ɗin, sai dai masallacin yana da nisa da family part. A haka King ya nufi masallacinsa masu busa suna ta aikin busa tare da zazzaga mashi kirari kala kala. Dakarun kwararrun mayaka ne suka yi gaba domin sharar hanya kada ko tsinke ya taɓa mai girma King. Ni kuwa na haɗa kayana zuwa DUBAI dan kwaso maku labaran can kuma, mu je muji wace wainar ake toyawa kafin mu sake dawowa mu duba jikin Mama......🥱 DUBAI🔥🤍 Sosai Leesharh ta sha mamakin ganin irin hidimar da ake yi a gidan yau, ta ga gidan nasu sai baki suke yi, jiniyar motoci ne suke ta dira a cikin gidan duk bayan ɗan lokaci, manya manyan baki suke ta yi, ministocine abokan Abu Abdussalam suke ta faman zuwa. Sai tsantsara girke girke kala kala ake yi, a koda yaushe girki kala kala ake yi a gidan kun sani, to amma yau na musamman ake yi. Wanka ta tsantsara ita ma tare da shiryawa cikin wani malesian gown mai bala'in kyau launin up pich, ta ɗauki ɗan ƙaramin please call me hijab ɗinta white color mai kwalliyar duwatsu masu haske a jikinsa ta sanya a jikinta, malesian gown ɗin ya zauna a jikinta sosai, ya bi coca cola shape ɗinta kamar dan ita aka yi sa. Sam sam Leesharh bata damu da yin make up ba, bata yin sai jefi jefi, natural beauty gareta, dan haka a yanzu ma bata yi make up ba, natural beautynta ya kata fitowa sosai saboda zama a Ac ga cima mai kyau, sannan ga sabulai masu zafi da suke kara gyara mata skin ɗinta, sai chocolate colornta ya kara fitowa sosai yana wani glowing. Sai dai fa duk da hakan tana ɗan rame, kuma tana firgice, dan a kullum cikin fargaba da zulumi take, kullum tana tsorace asirinta zai tonu, tana cikin tunanin ya zata kasance ranar da akace asirinta ya tonu, ita sam bata taɓa yin tunanin ya za'ayi ta fita daga cikin gidan ma idan ta kammala aikin ba, bata taɓa kawo wannan tunanin bama a ranta, burinta kawai ta kammala aikin ta koma kasarsu. Hmmmm ni kam na ce akwai gagarumin yaki kuwa a gabanki, dan kuwa kin shiga in da babu fita ne, ko dai my people's kun gano mata hanyar fita bayan ta gama aikin da ya kawota ɗin?. Akwai gagarumim cakwakiya, dan kuwa fita daga cikin gidan Abu Abdussalam ba duk kai ba wlh, wane mutun in ji mutuwa! Ba yadda take tunanin abin bane, ya wuci tunanin mai tunani. Tana shirin nata tana tunanin ta je wajen Sharifat ta tambayeta ko biki za'ayi a gidan ne da yasa ake ta shirye shirye haka, ga motocin ƴan'sanda da sojoji birjin da suka rinƙa rako ministoci gidan. Ta yi kyau sosai, waje ta nufo. A parlourn ta isko su Fadila suna aikin gyaran parlourn nasu. Sannu ta yi masu tare da sanya kai zata fice daga part ɗin nasu. "Leesharh ki shirya da misalin karfe huɗu zamu yi serving na baki drinks da sauran kayan cima a cikin hall ɗin Abbie na yin walima". Cewar Fadila. Kamar zata tambayeta biki za'ayi a gidan ne? Sai kuma ta fasa ta amsa mata dawo okey kawai, a cewarta gara ta je ta tambayi Sharifat zai fi mata kuma zata fi samun cikakken bayani a matsayinta na yar masu gida. Tana amsawa ta wuce izuwa waje. Da kallo su Fadila suka bita har sai da ta fice, sannan ne Radia ta ce. "Gaskiya Leesharh kyakkyawa ce ajin farko, gata kuma black beauty". "Faɗe ma ai ɓatawa ne". Cewar Fadila, ta yi maganar tana shirya pillows dake a saman sofas ɗin nasu. Ita kuwa Leesharh kai tsaye bedroom na Sharifat ta nufa, dan tasan tabbas a nan zata sameta. Sharifat yarinya ce da bata cika son hayaniya ba, dayawan lokuta idan bata a tare da Ummienta to zaka sameta a cikin room ɗinta ta haye saman katafaren king bed ɗinta tana aikin karance karance, ita ɗin macece mai ra'ayin karance karance da bincike bincike kamar yayanta Jaish, wato kamar ƴar jarida, sai iya kaƙale kaƙale. Baki a ɗauke da sallama ta tura kofar room ɗin ta shigo, yau ba ita ta gyara babbar parlourn ba, saboda yau gyara na musamman aka yi mashi, manya manyan masu aikin da suke aiki a hawa na ƙasa ne suka zo suka gyara, ya kuwa sha gyara, kusan komai na parlourn sai da aka canza, aka zuba sabbi, sai tashin fitinannen kamshi parlourn yake yi, kun san larabawa da shegen son turarukan wuta, ƙamshi mai kwantar da hankalin duk wani mai shaƙa ne yake tashi. Kwance ta isko Sharifat a saman gadonta, ta ci kwalliya kamar ba ita ba, arab dressing ta yi kamar yadda ta saba, ta yi rolling veil a kanta, kasancewarta farar fata hakan yasa bakaken kayan suka yi mata kyau sosai. Ta nutsu cikin karanta wani ɗan littafi da yake riƙe a hannunta, littafin larabci ne. Guyson na zaune a saman sofa a cikin room ɗin nata, yana latsa wayarsa, bai jima da gama magana da su Obaid ba, sun gaya mashi jirginsu ya sauka, suna gidan King Badeen, ya ce yaushe zasu zo, suka ce mashi ai ba za su zo ba sai an yi hutun school, saboda ba lokaci, za su je wajen uncle Rahab kafin su koma school, so ba zasu zo gidan Abu Abdussalam ba. Sarai Guyson yasan da cewa gudun haɗuwa da su Yah Ramish suke yi, hakan yasa basu son zuwa, amma bai wani damu ba ya ce masu shi yana nan zuwa gobe su ga juna kafin su wuce school ɗin, on Monday zasu koma school, daga haka suka yi sallama a kan shi zai je gidan King Badeen ya same su. Gaisuwa ta ɗagawa Guyson cikin girmamawa. Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mata gaisuwar tata cikin mutunci. A yanzu shi ma ya fara sabawa da ita saboda ganinta a tare da Sharifat da yake yawan yi, so ya fara sakin jiki da ita, ita kuma Sharifat already dama kunsan ita ta fara neman sabo da Leesharh ɗin ma, so a yanzu sun saba sosai, sun zama kamar wasu ƙawaye. Leesharh kuma har yau har gobe tana aiki ne bisa umarnin masu nikaf, duk abin da kuka ga ta aikata sune nan suka bata umarni, a yanzu suna yawan waiwayarta, suna turo mata saƙonni ba kamar da can baya da suka zuba mata idanu ba, da alama a yanzu sun ɗa gano wani haske dan gane da aikin da suka sanyata ɗin ne yasa suke waiwayar tata. A saman bedside drawer ta zauna tana ɗagawa Sharifat ɗin ma gaisuwa bayan Guyson ya amsa mata gaisuwar tata kenan. Rufe littafin hannunta Sharifat ɗin ta yi tare da miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin, fuska a ɗauke da ƙayatattcen murmushi ta ce. "Leesharh kin yi kyau sosai, kamar kin san yau Yah Bilal zai dawo, shi da Yah Ramish za su je ƙasar Tunisia duba jikin Queen Mama, kowa na gidan nan ya yi kwalliya sosai, kinga Yah Guyson ma ya yi kwalliya". Ta kai karshen maganar tana nuna Omar ɗin da hannu. Haƙiƙa kuwa ya sha kwalliya fiye da kullum, duk da cewa shi dama tun ainahinsa ɗan kwalliya ne, babban yaro ne ɗan kwalisa, shegen son gayunsa ma yasa suke ce mashi Guyson, amma fa gayun da ya ci yau na musamman ne, ƙananan kaya ne a jikinsa, wandon jeans and polo shirts masu bala'in kyau launin white color up and down ɗin dukka, ya gyara kyakkyawar dark black arab hairn nan nasa, abin ba'a magana, kamshi kuwa duk yadda ka kai ga sonta ina ga Guyson ya fika sonta, yana bala'in son kamshi sosai. Wani irin faɗuwar gaba Leesharh ta ji da jin sunan Yah Ramish a bakin Sharifat. "Kai Masha Allah, Allah ya dawo da shi lafiya, shiyasa naga anata hidima a gidan". Cewar Leesharh. "E ai dole kiga ana hidima, da Yah Ramish, Yah Rizwan, Yah Bilal, Yah Raj su ɗin na musamman ne a wajen Abbie, yana ji da su fiye da tunaninki, kamar shi ya haifesu, shekaru dayawa fa suna nan ya ki yarda ya bari su je ƙasar Tunisia, saboda ba ya son su yi nisa da shi, yanzu ma ba dan Queen mama bata da lafiya ba da ba zai iya barinsu su yi nisa da shi har haka ba, ko tafiyar da kika ga Yah Bilal ya yin nan dan saboda aiki ne, badan haka ba suna nan a tare da Abbie". Ta kai karshen maganar tare da zuro kyawawan kafafunta kasan bed ɗin. Miƙewa Guyson ya yi yana faɗin. "Is time, Shareefat lokacin zuwa airport ya yi". Ya kai karshen maganar tare da nufar hanyar fita. Da sauri ta miƙe ita ma tana faɗin. "Wait for me mana Yah Guyson, Leesharh zan bisu airport, sai na dawo, idan kuma zaki bini ki zo muje, a jerin tawagar motacin Yah Ramish zamu tafi". Da sauri ta girgiza kai tare da faɗin. "A'a ina tsoron binki, sai dai kun dawon kawai". "Me kike tsoro?". Cewar Guyson. Ya yi maganar tare da tsayawa daga tafiyar da yake yi, ya ɗan juyo gareta. "Ina tsoron waɗan nan securitys masu face mask ɗin, da kuma waɗan can masu manya manyan bindigun, fuskokinsu tsoro yake bani". Murmushi ya yi har sai da haɗaɗɗiyar dimple ɗinsa ta lotsa. "Kada ki ji tsoronsu, babu abin da za su yi maki, kawai face ɗinsu ne kullum a fusace, amma ai ba zasu yi wa mutun komai ba ba tare da ya yi masu laifi ba, dan haka ki dai'na jin tsoronsu". Da okey kawai ta amsa mashi, amma fa tsoro kam dole ta ji, waɗan nan fusatattun mutane masu kama da dodannin, ita idan aka ce mata waɗan nan securitys ɗin suna cin namar jikin mutun ɗanya ma ba zata musa ba, domin kuwa fuskokinsu babu ɗigon annuri ko sauki a kansa, waɗan nan idan suka kama mutun ya yi masu laifi Allah sarki, sai dai wani ba shi ba, sun iya ganawa bawa azaba. Wucewa Guyson ɗin ya yi ya nufi waje, da sauri Sharifat ta riƙo hannunsa tana murmushi, a haka suka fice daga ɗakin suka bar Leesharh. Ta ɗan jima a zaune tana tunanin saƙon da aka turo mata yau da safe, saƙo ne da masu nikaf suka turo mata a kan lallai ta nemi wanene or wacece take kaiwa Ramish abinci a cikin ma'aikatan dake gidan, idan ta gano wanene to lallai ta san ta yadda zata yi su ƙullah alaƙa, su sami kusanci sosai, idan suka saba shikenan akwai wani aikin da zasu bata, wannan shi ne saƙon, yanzu ya za'ayi ta nemo mai kaiwa su Ramish abinci a cikin ma'aikatan gidan nan fisabilillahi? Ma'aikata ba ɗaya ba biyu ba, kowani hawa da nasa ma'aikatan, ita da kwata kwata ma bata san a wani hawa su Ramish ɗin suke ba, ba ta taɓa ganinsu ba, yanzu ya zata yi kenan? Wannan shi ne abin da ya tsaya mata a ranta take ta aikin tunani a kansa tun safe. Daga karshe dai ta miƙe ta nufi waje domin ta koma cikin room ɗinta, sai tunanin take yi ko dai ta tambayi Sharifat wacece take yi wa su Ramish aiki ne? Ko kuma ta tambayi su Radia? Tana tsoron tambayarsu kuma kada hakan ya zamar mata matsala, kada wani abin ya zo ya faru ace ai ita ce ta taɓa neman masu yi mashi aiki ta shiga uku. Babbar parlourn ta fito tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Wani irin razana ta yi tare da zaro idanu tana kallon Ummie dake a zaune a saman sofa mai zaman mutun uku tare da wata jibgegiyar hajiya ita ma tana zaune a saman sofa mai zaman mutun uku. Sosai Leesharh ta zaro waɗan nan manya manyan idanun nata tana ganin wannan mata. "Wlh ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan ita Hajiya two seater da ta ɗauko ni daga AAJ House". Ta faɗi wannan magana a cikin zuciyarta tana mai cigaba da kallon matar. Matar bata lura da ita ba, haka zalika ita ma Ummie bata lura da ita ba, da yake parlourn yana da matuƙar girma, daga in da suke zaune da in da take akwai rata sosai da sosai, so basu san da ita a cikin parlourn ba, su suna a saman sofas da suke ta kusa da dining room ne, ita kuma kunga tana ta ɓangaren ɗakinsu Sharifat, akwai rata a tsakaninsu. Hannu ta kai ta sake goge idanuta sosai domin ta tabbatar da abin da take gani. Tabbas dai wannan mata ce a cewarta, duk da tasa nikaf lokacin zuwanta AAJ House ta ɗauketa, hakan bai sa yau da tazo gidan nan babu nikaf ta ganeta ba, LEESHARH akwai ƙwaƙwalwa sosai, da idon wannan mata ta iya ganeta babu nikaf, idan baku manta ba dama tana iya banbantasu da yanayin idanunsu, to fa hakance yasa take tunanin wannan jibgegiyar hajiya ita ce hajiya two seater. Lallai akwai cakwakiya, kenan makashin Ramish suna a tare da shi? Meya kawo wannan hajiyar gidan? Wacce iriyar alaƙa yake a tsakaninta da familyn Abu Abdussalam? Ya abin yake? Anya tana da alaƙa ta jini da su kuwa? Wacece ita?. Alƙalamin na ne kawai zai warware maku wannan cakwakiya, ku dai mu cigaba da tafiya, mun kusa cinwa ainahin in da RAWANIN ZALINCI yake........🥱 Salallaɓawa Leesharh ta yi ta nufi hanyar fita daga parlourn ba tare da sun ganta ba, tunani take yi kenan haka kamannin masu nikaf ɗin nan yake? Haka kamanin hajiya two seater yake?! Kanta ya ɗaure sosai, ta kuma shiga ruɗani, ji ta yi ta dai'na gane komai, a haka ta fice daga parlourn cikin dabara ba tare da sun ganta ba. Sai hira suke zubawa a tare da Ummie, da alama suna cikin farinciki tare da annashuwa. Leesharh tana shiga cikin room ɗinta ta nufi wajen windownta dake fuskantar harabar gidan, ta zuge windown tare da janye labule ta tsaya tana kallon cikin gari, tunani ya taru ya yi mata yawa a cikin ƙwaƙwalwata, har ji take yi kanta yana yi mata ciwo, wannan wace iriyar bala'i ce? Ta tambayi kanta da kanta. Tana tsaye a wajen jerin gwanon danƙara danƙarar motocin masu zafa suka fara fitowa daga cikin parking space na gidan, sun kasance a jere cikin tsari, hakan ba ƙaramin burjewa ya yi ba, motocin ƴan'sanda uku ne suka yi gaba, sannan waɗan nan jerin motoci suka rufa masu baya, sai motocin sojoji uku suka take masu baya. A kallah motocin zasu kai 15, da alama airport suka nufa, da kallo kawai ta bisu har suka fice. Da fitarsu bai fi da minti biyu ba wasu jeren danƙara danƙarar motocin ma suka sake danno kai daga parking space ɗin, taɓe baki ta yi tana mamaki tare da kara jijjinawa girman gidan Abu Abdussalam, bata san daga ina parking space na gidan ma yake ba, ita dai tana ganin motocin kawai suna ketowa ta harabar gidan wadda kuma take da yakinin daga parking space suke fitowa, dan duk motocin gidan ne, duk suna ɗauke da tambarin gidan. Motocin da suka fita na farko na su Ramish, Dr Raj and Rizwan ne, na biyun nan kuma na sauran ƴan uwa, duk airport suka nufa dan tarbo Bilal, ga motocin dukkansu suna da tinted, ba zaka iya ganin waɗan da suke a ciki ba. Cikin kwanciyar hankali suka hau saman wannan haɗaɗɗiyar shinfiɗaɗiyar titin da ta fita zuwa babban gate na fita unguwar tasu, yadda motocin suke tafiya kai ɗaya sai sun burgeka. Ba normal airport suka nufa ba, kai tsaye AL MINHAD AIR BASE suka nufa, wato airport na AIR FORCE kenan, kada ku manta shi Bilal AIR FORCE ne. Ko da suka isa airport ɗin jirgin su Bilal ɗin bai sauƙa ba, saura five mins ya dira. Hakan yasa suka yi parking a katafaren parking space na airport ɗin, sai dai babu wanda ya fito daga cikin motar tasu, duk suna ciki. Babban airport ne sosai, kalar fentin bangon airport ɗin ma kalar uniform na air force ɗin ne, dan airport ɗinsu ne, ga jiragen yakinsu bitjik ta ko'ina. Ta ko'ina idan ka juya dakakkun jami'ai masu sanye da kakin air force ne cike a cikin airport ɗin, sai kai komo suke yi, kowannensu ka ɗaga ido ka gani ba zaka so ka sake ganinsa ba, saboda yadda kyawawan fuskokinsu suke a turɓune a kuma fusace, dakon jiran jirgin ƴan uwansu jami'an kawai suke yi, kowannensu ka gani a shirye yake da a mutu ko ayi rai, sun riga da sun sayar da rayukansu, yanzu fa idan suna yaki da zarar an yi bombing na jirginsu an jefe shi daga sama fa shikenan, kashesu bai da wuya, shiyasa ba kowa yake yarda da aikin ba, gara sojoji sau dubu, su sojoji suna iya ɓuya a sunkuru idan ana yaki, su kuwa air force da suke sararin samaniya kowa yana gani, ana jefa nakiya zata yi bombing na jirgin yakin nasu, ko gawarsu kuma ba'a samun gani, dan tarwatsewa suke yi, wasunsu kuma jirgin mai ɗauke da ƙananan nakiya ake tasa ta bi tasu ta yi bombing su tarwatse, musamman idan ƴan ta'addan da suka je yaƙan shegun kai ne, abin baya masu ta daɗi, sai mai taurin rai yake yarda ya yi wannan aiki. Ko shi Bilal Mummynsa ta so ta hanashi yin wannan aiki, King ne ya ce a'a namiji da jarumta aka san shi, shi bai haifi rago ba, jarumai ya haifa, dan haka Bilal zai yi wannan aiki tun da ita ya zaɓa, kun san halin King ai, akwai tafasasshen jini, ita ma Akka ta zage har da karawa abin armashi, wai idan Mummy ba zata iya ganinsa a gabanta yana wannan aiki ba to ya haɗa kayansa ya koma Dubai, wannan shi ne dalilin da yasa tun farko suka dawo Dubai da zama abinsu, Akka ce nan ta hurawa abin wuta, kun santa ita ma akwai son sabgar jarumta, bata da wasa, bata son ragwaye, wannan da namiji ne ita ban san a iya ina zata tsaya ba, duk ta reni su King sun taso da Barden zuƙata, babu tsoro sai ma ban tsoro da suke da shi. Jiga jigan Fighter Jets ne suka dinfaro airport ɗin. Jiragen A400M Atlas da C-130J Hercules, sune a gaba da suka fara saukowa a filin saukar jirgi na airport ɗin. Da saukarsu kamar da two mins haka sai ga wasu Typhoon FGR4 da F-35B Lightning suma suka yi landing, dukka jirage ne na AIR FORCE. Jirgin F-15 Eagle ce a tsakiya, wadda kuma ta kasance ita ce na Bilal ɗin, a cikinta yake, sannan jiragen Typhoon FGR4 da F-35B Lightning suka rufa mashi baya wajen sauka, su ne suke takewa F-15 Eagle na Bilal ɗin baya, so nasa tana dira da kamar minti biyu suma suka dira. Nan take jami'an Air force ɗin da suke cike a wajen suka fara cincirindon ƙarisawa wajen jiragen. Jaruman Jami'an Special weapons and tactics guda biyar ne suka fito daga cikin jerin gwanon motocin su Ramish. Gabaɗaya fuskokinsu a matuƙarn turɓune, kamar waɗan da aka aikowa da saƙon cewa wutar jahannama zasu shiga, kun ga kuwa ai ba zaman lafiya mutun ya ji zai shiga wuta.........😅 Duk suna sanye cikin bakaken kaya ne, harta takalmar dake a kafafunsu bakake ne, ga su dai fararen arab guy's kyawawa, amma kada ku so kuga yadda suka haɗe rai kamar ba lafiya ba. Bubbuɗe kofofin motocin nasu Ramish su ka yi, hannayensu na sanye cikin black hands gloves, from up to down dai shagar bakake ne, ba uniform ɗinsu suka sanya ba. Omar da Sharifat ne suka fara fitowa kafin su Dr Raj su rufa masu baya. Ramish shi ne a karshen fitowa, sai da ya kalli kofar F-15 Eagle na Bilal ta buɗe sannan shi ma ya zuro kafafunsa dake a sanye cikin wasu tsadaddun shoes masu matukar kyau waje. Da alama yana son su fito a tare da Bilal ɗin ne, Dr Raj da Rizwan sun yi gaba abinsu, shi kuwa ko da ya sako kafar tasa waje ma sai da ya nuna wannan, izza da fadanci tasu ta jinin sarautar kafin kuma a cikin nutsuwa ya fito waje.............. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 4/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________45🔥 Masha Allah. Sanye yake da tsadaddun suit masu zafa, idanunsa a sanye da white glass kamar medicated, dogo ne sosai kamar King Zuhair, kyakkyawar gaske ne ajin farko, da gani kasan jikan Akka ne, ya fi kama da King sosai, sai dai fa ya fi King Zuhair hasken fata gaskiya, shi fari ne tas har ya ɗan yi yellow yellow, King Zuhair kuwa ya ɗan yi ja, yana da kirar jaruman maza sosai, kamar renon Commander Zafar, arab hairnsa ba'a magana, ta sha gyara sai kyalli take yi, tana kwance luf ka tsantsi, kun dai san yadda gashin larabawa yake, to haka suma dai ƴaƴan King dukkansu gashin kan nasu yake, daga matansu har mazan dukka akwai gashi mai matuƙar kyau kam. Taku yake yi cikin natsuwa, sai dai da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan e lallai jarumin namiji ne sosai mai jini a jika, duba da yadda yake a buɗe kuma yana tafiya ne da jikinsa sosai, ba shi da kiɓa sosai, yana dai murmure, Rizwan ya ɗan fisu kiba a cikinsu. Kai tsaye wajen F-15 Eagle ya ɗin ya nufa, a daidai lokacin shi ma Bilal yake ƙoƙarin saukowa, shi yana sanye da kakinsu na air force, sai dai kakin yaki ne a jikinsa ba normal ba. Special weapons and tactics uku ne suka takewa Ramish ɗin baya izuwa wajen F-15 Eagle jet ɗin. A lokacin da ya isa wajen Bilal ɗin ya fito sun rungumi juna da Rizwan har ya sake shi ya rungumi Dr Raj suna ƙoƙarin raba jikinsu. Yana ƙarisawa wajen, shi kuma Bilal ɗin ya yi saurin sakin Dr Raj suka yi hugged ɗin juna shi da Ramish ɗin, da ka gansu ba tambaya kasa lallai waɗan nan jinin King Zuhair ne, da shi da Bilal banbancinsu kaɗan ne, ya fi Bilal tsawo, haka zalika ya fishi da shekaru, sannan ya ɗan fi Bilal hasken fata da kyau, amma aka ce jini ba wasa ba, akwai kamar jini sosai a tsakaninsu. Da yanayinsu zaka fahimci suna cikin farinciki, sai dai dukkansu babu alamar murmushi a saman fuskokinsu. "Yah Bilal nafa riga Yah Ramish ƙarisowa wajenka, amma shi ne ka rungumesa kaki kulani ko?". Cewar Guyson dake tsaye kusa da Sharifat yana ƙoƙarin tura wayarsa a cikin aljihunsa. "Our Guyson ai naga waya kake yi tun da ka ƙariso nan, da waye kake magana?". Bilal ɗin ya bashi amsa, voice nasa sak na King Zuhair, da alama jinin King ya fi na su Mummy karfi sosai, hakan yasa dukka ƴaƴa suke kamanceceniya da shi. "Waya na yi da daddy, shi ya kirani, shiyasa na ɗauka, ai kasan idan ba daddy ko su Momma ba ba zan ɗauki call ɗin kowa ina murnar ganinka ba". Ya faɗa yana ɗan tuɓune fuska, irin shi gaskiya ba'a kyauta mashin nan ba. Raba jikinsu suka yi, sannan Bilal ya rungumi Guyson ɗin haɗe da riƙo hannun Sharifat dake tsaye ta yi shiru kamar wata mai sauraran kira'ar Alqur'ani mai girma, sai binsu da kallo take yi. "Shikenan our Guyson". Cewar Bilal ɗin. "Yah Bilal sannu da dawowa". Cewar Sharifat ɗin. Yana riƙe da hannunta ya amsa da. "Yauwa lil sis, fatan kuna lafiya?" Sai sakin ƙayatattcen murmushin take yi ta amsa da. "Lafiya lou Yah Bilal". Sakin hannun nata ya yi yana ƙoƙarin raba jikinsa da Guyson. "Wato Yah Bilal lil kawai ka gani ko? Ita ce kawai ka tambaya ya take? Ni baka damu da kasan ya nake ba ko?". Cewar Guyson ɗan rigima. Ya yi maganar kamar zai yi kuka. Idan da sabo sun daba da mitarsa, shi dai kada a nuna wani ya fishi a gabansa, sai shegen kishi tun yana ƙarami, yanzu wai dan me za'a tambayi Sharifat ya take shi ba a tambayeshi ba, kenan anfi damuwa da Sharifat a kan shi, shi ne yake yi wa raki. Kallonsa da ido kawai Bilal ɗin ya yi ba tare da ya yi magana ba, domin idan ya biyewa Guyson sai su kwana a nan. Tsayawa Guyson ɗin ya yi a kan shi ba zai tafi ba tun da dai sun nuna sun fi damuwa da Sharifat a kan shi har suna tambayarta ya take shi ba wanda ya tambayi ya yake?. Ramish ne yasa hannu ya ɗauke shi cak kamar ɗan baby ya saɓa a shoulder ɗinsa suka nufi wajen motocinsu, domin ba biye mashi zasu yi ba, idan ya fara raki kamar wata kaza mai kwanci yake. Jiga jigan jaruman jami'an air force guda shidda ne suka ƙariso wajen Bilal ɗin, dai'dai lokacin da shi kuma y ƙarisa wajen jerin gwanon motocin su Ramish domin su koma gida. Cikin girmamawa suka ɗaga hannu suka sara mashi, sannan ɗaya daga cikinsu ya ce "Sir office zamu wuce ne?". Yana riƙe da hannun Sharifat da ya kama tun lokacin da Ramish ya ɗauki Guyson suka nufo wajen motocin, shi kuma sai ya riƙo hannun Sharifat ɗin ya rufa masu baya. Yana riƙe da hannunta ya amsa masu da. "No gida zan wuce, ni da office sai next week kila". Cikin harshen larabci suke maganar. A cikin mota gidan baya Ramish ya sauke Guyson yana jefa mashi wani irin kallo mai kama da harara. Murmushi Guyson ɗin ya sakar mashi domin yasan ma'anar wannan kallo. Wucewa Ramish ɗin ya yi ya zaka ta ɗayan side ɗin ba tare da ya yi magana ko ya sake bi ta kan Guyson ɗin ba. Buɗe mashi kofar motar jami'in Special weapons ya yi, ya shiga kusa da Guyson ɗin ya zauna, shi ma Bilal wannan motar ya shiga suka sanya Guyson a tsakiyarsu, ita kuma Sharifat ta shiga wata motar na daban. Kamar yadda motocin suka shigo a jere haka suka tashi a jere bayan su Rizwan dukka sun koma cikin nasu motocin. Da haka suka nufi gida. Jami'an air force mota guda suka yi masu rakiya zuwa gida, dan Bilal ya ce ba zai je office nasu ba, gida zai wuce, shi ne zasu yi mashi rakiya su tabbatar da ya isa gida lafiya, sannan su koma headquarter ɗinsu. A wannan karon gudu sosai motocin suke shararawa a saman shinfiɗaɗiyar titin. Hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gida. Leesharh dake kwance a saman gadonta ne ta ji diran motoci a cikin gidan, jiniya ya karaɗe ko'ina, motocin ƴan'sanda da sojojin dukka sun saki jiniya kamar zasu tafi filin daga, hakan yasa jiniyar take tashin kai, ta yawaita sosai. A hanzarce ta diro kasa daga saman bed ɗin nata, da sauri ta nufi wajen window domin ta leƙa taga su waye ne?. Sai dai kash, bata samu damar ganin motocin ba, dan already sun wuce izuwa parking space na gidan, shi kuma parking space ɗin yana ta can gefe ne, bata iya ganinsa daga wannan window tata, dan haka bata sami damar ganinsu ba. Mai da windown ta yi ta rufe tare da sakin labulen, sannan ta nufi waje. Babu kowa a parlournsu, kai tsaye ta nufi barin part ɗin nasu mai gabaɗaya, yau ƙasa ma take son sauƙa. Elevator ta je ta haye ta nufi ƙasa kamar wadda zata ɗauki wani abin. A hawa na biyu ta tsaya, ma'aikata sai hidima suke yi, sai kai komo suke yi, ta sha madarar mamakin ganin ma'aikatan wannan hawa suna da yawa, sai dai bata wani damu ba ta nufi cikin hawar da kyau dan ta sha kallo, ta gaji da kwanciya a ɗaki ne babu abokin hira, ga shi ba da kowa aka yarje mata ta yi hirar ba. Su Ramish kuwa kai tsaye part ɗinsu suka nufa, shi da Bilal sun jero kamar wasu tagwaye, sai dai Ramish ya ɗan fi tsawo na gaya maku, Dr Raj and Rizwan ma sun jero kansu ɗaya. Ramish yana rike da hannun Guyson dake ta faman kunbure kunbure na anfi damuwa da Sharifat a kansa. Ita kuma Sharifat Bilal ne ya riƙe hannunta suka nufi elevator. Sam basu leƙa Ummie ba, ita ma bata leƙasu ba sai can yamma da misalin karfe huɗu, a lokacin dakkansu sun yi wanka sun shirya cikin wasu tsadaddun suit masu bala'in kyau, zasu halarci waliman da Abbie nasu ya haɗa ne domin dawowar Bilal ɗin, sai a wannan lokacin ne Ummie ta leƙasu, ita ma ta tsantsar kwalliya cikin wani Turkey gown, kun san yawancin dogayen rigunar mutanen Turkey suna nan da kauri sosai kamar cuit, yadikansu kusan kamar yadikan suit ne, so haka rigar da ta sanya ɗin ma yake, ga rigar ta fita shape ɗinta sosai, ta sha ado kam ba'a magana, ta yi rolling gyalen a kanta. Part ɗinsu ta isko su, kowanne a cikinsu da abin da yake yi. Ramish yana tsaye a wajen windown parlourn part ɗin nasu yana waya, da alama da King Zuhair yake waya, duba da yadda yake maganar cikin nutsuwa da kuma respect, yana wayar hannunsa na rike da wani haɗaɗɗen cup mai ɗauke da cappuccino a ciki yana sha. Shi kuma Bilal yana zaune a saman sofa ya tasa waya a gaba yana latsawa yana kuma shan cappuccino dake a saman ɗan table ɗin dake gabansa. Rizwan da Dr Raj sai hira suke yi, jefi jefi Bilal yana saka masu baki a cikin hirar tasu, sun kammala shiri tsab, fita ne kawai basu yi ba, ga shi kuma wajen walimar ya cika da manya manyan baki, ministoci da ƴan majalisu da dai sauran masu muƙaman gwamnati haɗe da ƙananan da manyan sarakuna duk sun hallara, su da aka shirya walimar dan su kuma suna nan zaune a parlournsu suna hira, da alama ma basu so halartar walimar ba, Abbie ɗin ne ya matsa masu a kan lallai su zo, basu son ɓata mashi rai ne yasa suka aminta zasu halarci wajen. Guyson da ya fi kowa tsantsara kwalliya a cikinsu yana kwance saman doguwar sofa, ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin, ita ma Sharifat tana cikin room ɗinta tana tsantsara nata kwalliyar, ita kam sai murna take yi za'a yi walima. Baki a ɗauke da sallama Ummie ta shigo cikin parlourn nasu. Dr Raj ne ya amsa mata sallamar. Cikin parlourn ta ƙariso, a saman sofan da yake fuskantar Bilal ta zauna. "Good evening Ummie". Bilal ya faɗa yana kashe hasken screen ɗin wayarsa domin ya bata attention ɗinsa. "Evening Yah Bilal ya hanya ya kuma aiki? Hope komai normal". Da yes normal ya amsa mata, sannan ya yi shiru. "Ya baku fita zuwa hall ɗin ba? Zaku fara halin naku ba?". Cewar Ummien. Dr Raj ne ya amsa mata da. "Ummie kema dai kin san bamu son zuwa, tun da Abbie ya yi mana dole kuma sai an kusa tashi zamu je". "Gaskiya a'a banyarda ba, kawai tun da kun shirya ku je, yana jiranku fa, nima can zan wuce sai na ji motsinku alamar kuna nan baku tafi ba shi ne na shigo, dan haka ku tashi kawai mu jera a tare, kun fa san Abbienku bashi da burin da ya wuce ya ganku a kusa da shi, nasan yanzu haka yana cikin damuwa na rashin zuwanku, yana son ya ganku kusa da shi yana nunawa abokansa ku yana kuma alfaharin yin hakan". Ransu bai so ba, Dr Raj, Rizwan, Guyson and Bilal ɗin suka miƙe, basu son yin ja in ja da ita ne kawai yasa zasu je, shi kuwa Ramish da tun da ta shigo yake waya bai ko kalli in da take ba, sai da ta miƙe zasu fita ne ta ce mashi idan ya gama wayar ya biyosu fa, kada ya ce zai kwanta yaki zuwa dan tasan halinsa. Kai kawai ya gyaɗa mata alamar to, tare da binsu da waɗan nan dara daran idanun nasa. Sakata a tsakiya suka yi suka nufi hall ɗin. Shi kuwa Ramish ya jima yana magana da King a waya, da kyar suka yi sallama, da alama King ɗin bai so su yi sallamar ne, sai dai Ramish ɗin ya ce mashi. "Kai daddy gobe fa zamu zo, ka bari idan muka zo sai mu yi ta hiran, yanzu Abbie yana jirana ne fa". Da haka dai ya samu suka yi sallamar da kyar. Yana kashe wayar ya ɗaurata a saman sofa mai zaman mutun biyu, ya kuma ajiye cup ɗin cappuccino dake a hannunsa a saman table, sannan ya nufi cikin katafaren room ɗinsa. Jim kaɗan ya fito sanye da three cuter jeans trousers sky blue, sai wata farar shirt mai karamar hannu maras nauyi mai laushi sosai, ya cire suit ɗin jikinsa, da alama ba zai je walimar ba kenan. Wayarsa dake a saman sofa ya ɗauko ya nufi waje. Kai tsaye babban parlourn ya nufa. A saman sofas set da suke kusa da dining room ya zauna, sannan ya ɗauki wayar dake kusa da wajen na emergency ya kira masu aikin dake kitchen ɗin kasa suna girki. Bugu ɗaya aka yi picking call ɗin, dan already akwai wadda aikinta ne kawai ta zauna kusa da wayar, idan an kira ta ɗauka ta ji me ake buƙata, idan an gaya mata sai ta isarwa da masu aiki a kitchen ɗin saƙon abinda ƴan gida suke da buƙata, nan take su kuma ma'aikatan zasu karɓi umarni su fara aiki, wannan ɗaya ne daga cikin tsarin gidan Abu Abdussalam. A takaice ya sanar da wadda ta ɗaga kirar cewa yana da buƙatar kayan marmari haɗe da ferfesu mai ruwa ruwa kuma mai zafi yana babban parlour. Already tasan wanda ya kirata, domin aikinta ne dama lallai ta tabbatar da ta riƙe muryar kowa, yana ɗaya daga cikin dokokin aikinta, kuma yau a kallah ta shafi shekaru 7 zuwa 8 tana wannan aiki, so ta san voice na kowa a cikin gidan, shiyasa na gaya maku Abu Abdussalam baya ɗaukar ma'aikata jahilai, sai waɗan da suka yi karatu sosai, dan ba'a saɓa mashi dokokin gidansa, sannan aikin gidansa yana buƙatar masu ilimi ne sosai. Tab irin wannan abu haka.....🤔 Cikin girmamawa ta karɓi umarninsa tare da sanar da masu aiki a kitchen ɗin ga saƙon Ramish nan, kuma jira yake yi, dan haka su yi sauri. Kitchen na gidan Abu Abdussalam kawai abin kallo ne, girmansa ya wuci tunaninku, ma'aikatan da suke aiki a cikinsa kawai zasu kai su 20, girki kala kala ake yi a kowani lokaci, kowacce da kalar abincin da take girkawa kuma da kalar aikin da take yi a cikin kitchen ɗin. Idan mace tana ta ɓangaren gas wata kuma tana ta ɓangaren freezers sai ka yi zaton ba'a waje guda suke ba, saboda girman kitchen ɗin, ratar da yake a tsakaninsu ba kaɗan bane, girma ne da kitchen ɗin sosai, tsakanin wajen jera pots da kuma wajen su baker ovens ma ba karamar rata bace ba, girman kitchen ɗin ya kai girman gidan wani ko in ce ya kai girman fili plot guda. emergency phones har guda biyar ne a kowani ɓangare na cikin kitchen ɗin, duk domin saƙon ƴan gida su faɗi abin da suke da buƙata a girka a kawo masu, abin fa ba sauki bane, Daular gidan Abu Abdussalam ya wuci tunaninku, maƙudan dukiya suke narkawa, albashin ma'aikin gidan a kowani wata ma kawai abin a saki baki ana kallo ne. Da yake dukka ƴan gidan manyan kai ne, duk shaggun masu maƙudan dukiya ne, hakan yasa suke pacaka son ransu, ga jiga jigan masu kuɗi su Ramish duk suna nan ai dole su more rayuwa son ransu...... Allah ka yi mana arziki mai albarka. Ajiye wayar ya yi bayan ya isar masu da saƙonsa, sannan ya jingina kansa da jikin head na sofar, a hankali ya lumshe kyawawan idanunsa kamar mai jin barci. A can cikin hall kuwa sai jiransa su Bilal suke yi, kowa ya dake a saman nasa haɗaɗɗen sofa da aka kawata da kwalliya na alfarma kuma mai tsada, an tanadi waɗan na sofas ɗin ne domin family, sauran bakin da suka halarci walimar kuwa kowanne yana saman nasa sofar, sofas da aka tanadawa family a saman stage suke, na baki kuma a ƙasa. Hall ɗin a cikin gidan yake, Abu Abdussalam yasa aka gina mashi ita domin yin walima ko wani taro nasa kamar dai yau, ba karamar dukiya aka narka wajen haɗa wannan hall ɗin ba, kamar ba za'a mutu ba, tsadaddun sofa set da ya zuba a cikin hall ɗin kawai kuɗinsu ya isa ya riƙe wani har karshen rayuwasa shi da iyalansa, amma duk shi a kan sofa kawai ya karar da kuɗin, ga kayan alatu da aka zuba domin kara ƙawata hall ɗin, kowani abu idan ka gani a cikin hall ɗin nan aka gaya maka kuɗinsa sai ka saki baki, gabaɗaya bangon hall ɗin ma na glass ne, abin dai sai wanda ya gani, dan faɗar tsaruwar hall ɗin nan da baki ma ba zai yiwu ba. Sosai Leesharh tasha kwalliyarta cikin wasu dogon wando da riga, dama na gaya maku ita ma abokiyar son wando da riga ne, malesian dress ne, wandon yana da faɗi sosai kamar palazo, rigar kuma ya fitar mata da shape ɗinta, rigar zuwa gwiwanta ya tsaya, sai ɗan ƙaramin veils ɗinsa, sannan rigar yana da igiya ta wajen cikinta, ta ɗaure igiyar a baya hakan yasa rigar ta kara fito mata da shape ɗinta sosai, flat tummyn nan nata shape nasa ya bayyana sosai. Ɗaura veil ɗin a kanta ta yi ɗauri mai kyau, da yake chocolate color ce ita sai launin kayan da suka kasance red color ya yi mata kyau sosai. Fitowa ta yi daga part ɗinsu domin ta je wajen walimar su rabawa baki drinks da abubuwan da suka da ce, already an shirya glass cups masu tarin yawa da za'ayi amfani da su a wajen, masu zuba lemuka a cikin glass cup's ɗin ma har sun fara aikinsu, masu jera glass cups ɗin a try bayan an zuba drinks ma suna nasu aikin, so su Leesharh kuma aikinsu kawai su ɗauka su rinƙa rabawa waɗan da suke zaune shiru basa motsa baki. Kamar zata nufi ƙasa, sai kuma ta tuna to ai ita bata san ma a ina hall ɗin yake ba a cikin gidan, bata san ta wani bangare yake ba, hakan yasa ta yanke shawarar tunkarar room ɗin Sharifat ko zata sameta sai su tafi a tare, sai zuba daddaɗar kamshi take yi. Kasancewar tasan babu kowa a cikin babbar parlourn ne yasa ta yi sallama a ƙasa ƙasa, kai tsaye room ɗin Sharifat ta nufa, sam bata lura da shi a parlourn ba, kasancewar tsakaninsu akwai rata sosai, sai dai kuma tasha madarar mamakin jin ƙamshi parlourn ya sauya daga yadda ta saba ji, kamshin perfume ɗinsa ya rinjayi na parlourn saboda karfin da perfume ɗin nasa yake da shi. Amma bata kawo komai a ranta ba ta wuce wajen Sharifat kai tsaye. Tana tura kofar room ɗin Sharifat, ita kuma Sharifat ɗin tana sanyo kai zata fito kenan suka yi karo, gwara kansu suka yi ta yadda har sai da dukkansu suka furta wash da ɗan karfi. Baya kaɗan Sharifat ɗin ta yi tana murje goshinta da Leesharh ta gwara mata kai. A ɗan ruɗe Leesharh ta yi mata sannu tare da ja da baya ita ma. Ba komai Sharifat ɗin ta ce mata sannan ta ɗaura da cewa. "Kin yi kyau sosai Leesharh, ke kam kowani kaya kika sanya sai sun yi maki kyau, wajen walima zaki je ko?". Kai ta gyaɗa mata tare da faɗin. "E can zanje mu rabawa mutane drinks, sai dai ban san a ina wajen yake ba, kafin na gama shirina kuma su Radia sun tafi, shi ne nazo tambayarki wajen". Nisawa ta yi kafin ta ce. "Can zan je nima, muje a tare". Ta kai karshen maganar tare da sanyo kai ta fito, tasha kwalliya sosai cikin abaya, ta yi rolling gyalen a kanta, ta fita ɗas da ita abinta, launin navy blue ya yi mata kyau sosai dan tana da hasken fata. Juyowa Leesharh ta yi suka nufi dawowa cikin babban parlourn, Sharifat ta sanya takalma mai tsini wato high heel sosai, sai kwas, kwas, kwas take yi a white tiles na parlourn, ita kam Leesharh plat shoe ne a kafafunta, suma plat shoe ɗin Sharifat ɗin ce ta bata kyautarsu kala goma sha biyar, ciki harda high heel guda biyar, amma bata saka high ɗin ba, sai ta ɗauki flat ta sanya, duk da haka ta yi kyau sosai. Suna ƙarisa zuwa cikin parlourn Sharifat ta tsaya tana ƴan waige waige. "Lafiya Sharifat kika tsaya?". Leesharh ta tambayeta tana binta da kallo. "Naji kamshin perfume ɗin Yah Ramish ne shi ne nake neman ta ina yake?". Ta bata amsa tana nufar wajen kofar dining room. Da farko kamar Leesharh ba zata bita ba, amma tunawa da ta yi tana matukar son taga Ramish ɗin yasa ta yi saurin rufa mata baya, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, yau zata kalli wanda ta zo yin aiki a kansa, fargaba da faɗuwar gaba ne cike tab a ranta, ta takure jikinta waje guda saboda rashin gaskiya da kuma tsoro. Ganinsa yasa Sharifat ta saki wani cool murmushi kamar budurwar da ta ɗauki shekaru tana begen ganin saurayinta sai yau ta gansa, kunsan ba ƙaramin daɗi zata ji ba, to haka ita ma Sharifat ɗin ta ji daɗi sosai har yasa ta saki murmushi ba tare da ta sani ba. Ita kuwa Leesharh ganinsa yasa ta haɗiyi wani irin wahalallen yawu duk da bata da tabbacin cewa shi ne, amma lallai ba shakka ta ji a jikinta shi ɗin ne kamar yadda masu nikaf suka gaya mata cewa in dai ta gansa to zata ji a jikinta cewa shi ne, haƙiƙa kuwa ta ji hakan, nan take bugawar zuciyarta ya karu, faɗuwar gaba da fargaba suka karu, kanta har wani irin sara mata ya yi, a take a wajen ta ji wani irin karayar zuciga a kan wannan aiki, ji ta yi ina wlh in dai wannan shi ne Ramish to ba zata iya bin diddiginsa ba, wannan ganinsa kawai yana sanyata faɗuwar gaba, iya faɗuwar gabar kuma kawai ya isa ya kasheta, ai wlh idan bata yi hankali ba da kanta zata tonawa kanta asiri, bare ma ace su haɗa ido da shi, wannan tun bai yi magana ba zata ruɗe ta fara ce mashi ba laifinta bane turota aka yi, ta tonawa kanta asiri, har wani irin zufar tsorata da ganinsa ne ya fara tsastsafo mata, yau almost 2 month kenan tana gidan tana son ganinsa, ta jima tana begen ganinsa, yau ta gansa kuma sai ta fara danasanin ganin nasa da ta yi, duk sai ta ji dama ace bata gansa ba da ya fi mata alkhari, yanzu ganinsa da ta yi zai sanya mata fargaba, yanzu zata kasance kullum cikin fargaba da tsoron ranar tonan asiri, dama gata duk a firgice. "Yah Ramish sannu da hutawa". Cewar Sharifat da take tsaye a kusa da shi. Ba tare da ya buɗe idanunsa ba, ya kuma ɗauki tsawon minti ɗaya kafin ya amsa mata da. "Yauwa lil sis". Sosai Leesharh ta kara jin faɗuwar gaba da jin voice ɗinsa, yana da sanyin murya sosai, sai dai muryar tasa akwai kaifi sosai a cikinta, daga ji kasan manyan maza ne suke magana. A ɗan tsorace Sharifat ta sake cewa. "Yah Ramish ya baka je wajen walima ba?". Ta yi maganar tana ɗan ɗari ɗari, domin tasan halinsa baya son tambaya kuma baya son yawan magana, idan magana ta wuci biyu zuwa uku to baya amsawa koda kuwa Ummie ce ta yi maganar. Ai kuwa ta gudu bata tsira ba, dan kuwa bai amsa mata ɗin ba, kamar babu shi a wajen. Ganin hakan yasa Sharifat ɗin ta ce da Leesharh su tafi kawai. A hanzarce Leesharh ta juya ta yi gaba, har mamaki ta bawa Sharifat ɗin na yadda ta juya a hanzarce kamar wata maras gaskiya. Amma bata kawo komai a ranta ba, sai ma tunani da ta yi na cewa kodai tsoron Yah Ramish ɗin ne yasa ta birkice haka? Bayanta ta bi kawai suka fita parlourn suka nufi elevator dan su sauƙa kasa. Sai dafe saitin zuciyarta Leesharh take yi, dan ji take yi tamkar zuciyar tata zai fasa kirjinta ya fito waje, a gaskiya ta tsorata da ganin Ramish, wannan ma fa ba ido cikin ido ta kalle shi ba, akwai aiki kenan. Hall ɗin kai tsaye suka nufa, yau gidan ya kara cika da jami'ai kala kala saboda ministocin da manyan bakin da suka halarci walimar, an kara tsaro sosai da sosai. Suna zuwa Sharifat ta wuce saman stage wajen ƴan uwanta ta zauna a kusa da Guyson, ita kuwa Leesharh ta nufi wajensu Radia dake can gefe guda wajen shirya drinks. Tana zuwa ta tsaya idanunta suna a kan stage da Sharifat ta hau. Izuwa yanzu ta shiga ruɗani sosai, faduwar gaba kuma yana neman kasheta har lahira, ba komai kuma ya hassasa mata hakan ba face ganin, Rizwan, Bilal, Dr Raj da ta yi a saman stage ɗin, ta ruɗe ta yadda har ta kasa iya banbance kamanninsu da Ramish da suka baro a cikin gida, yau rana ta farko da ta fara ɗaura idanunta a kan Abu Abdussalam bawan Allah, tana jin labarin kirkinsa bata taɓa ganinsa da ido ba, ta haura wata biyu a gidan, to yau dai ga shi nan a tsakanin ƴaƴansa. Da ka gansa ba tambaya kasan yayan Mommar Zunaira ce, yana kama da Guyson sosai, sai ka rantse da Allah Guyson ɗan cikinsa ne ba ɗan kanwarsa ba. Ya sha farar arab jallabiya mai tsada da alkyabbarsa, rawani ya yafa daga kansa zuwa kafaɗunsa, daga sama har ƙasa fararen kaya ne a jikinsa, ɗan gara alkyabbar jikinsa ma akwai ratsin baki kaɗan a jiki, half cover shoe ne a kafafunsa masu bala'in tsada, suma launin fari, waɗan nan family yau sun haɗu iya haɗuwa. Sai dakon jiran Ramish suke yi, shi kuwa basu san ma ya tuɓe ya sanya kayan shan iska yana zaune abinsa ba, yama mance da wani zancen walima da ake gudanarwa a cikin gidan. Leesharh dai yau fargaba da faɗuwar gaba ne suka kusa yin ajalinta, duk in ta ɗaga ido ta kalli Dr Raj and Bilal sai taga kamar Ramish ɗin take kallah, ta kasa iya ɗaukar try ɗin drinks ɗin ta kaiwa mutane, saboda kerma da hannayenta suke yi, tana tsoron ta ɗauki try ɗin ta je ta ɓarar da shi, glass cups ɗin su tarwatse a wannan haɗaɗɗen tiles ɗin, ga shi kuma yadda aka jera cup's ɗin wasu kan wasu ɗorin ɗosalo tamkar yadda ake jerawa a party na manya manyan shugabannin manyan kasashen ta duniya, sun yi kyau a ido kam, amma ɗaukarsu sai ka shirya, sai mai nutsuwa. So ita dai Leesharh ta kasa iya ɗauka, domin fargaba da faɗuwar gaba sun ja mata kerman jiki. Waje ta samu ta karshen hall ɗin ta zauna, ta rasa dalilin da yasa kawai ta ji hawaye sun fara gangaro mata a saman face ɗinta, har wani irin shesshekar kuka take yi mai tsuma zuciyar mai sauraro, ita wannan bala'i ya fi karfin shekarunta, ta rasa ya zata yi, ji take yi kawai kamar ta yi wani laifin da zai sanya a kasheta kawai ta huta da wannan bala'i, tana kewar babanta, tana son sake ganinsa koda sau ɗaya ne, idan ta tuna cewa babanta yana hannun masu nikaf, kuma zasu cutar da shi idan bata mayar da hankali ta yi aikinta da kyau ba, sai ta ji wani irin kuka mai karfi ya zo mata haɗe da karfin gwiwar zata iya yin komai a kan baban nata, idan kuma ta tuna wanene Ramish da yadda ta kalli suffarsa da kirarsa sai ta ji zuciyarta ya karaya ta fara yi wa kanta fatar mutu. Ta rasa ina zata saka rayuwarta ta ji sanyi. Sosai take kuka, kasancewar babu jama'a a wajen yasa ba'a san tana kukan ba, can kashen hall ɗin ta je ta zauna, wajen babu kowa sai camera dake iya ɗaukar hoton wajen, murzan kukanta take yi son ranta wata kila ta huce takaici. Kamar daga sama ta ga an miƙo mata handkerchief fari tas wanda kamshinsa ya daki kofofin hancinta har sai da yasa ta ɗan lumshe idanunta. Waye kuma da karfin halin miƙo mata handkerchief? To bari dai mu leƙa KINGDOM OF POWER kafin mu dawo sai mu duba wanene da ƙoƙari ya miƙo mata handkerchief ɗin. KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 Kwance Gimbiya Chuchu take a saman bed ɗinta a cikin room ɗinta bayan an sauko daga sallar jumma'a kenan, ta bawa kofar shigo cikin room ɗin nata baya, tana maƙale da waya a kunne tana magana ƙasa ƙasa kamar wata maras gaskiya, yadda kuka san mai yin soyayya. A ruɗe Gimbiya Zunaira ta shigo cikin ɗakin idanunta a cike tab da kwallah, ga farin cikin idanun nata sun ɗan yi ja, kwayar Hazel eyes ɗin nata kuma ya kara launi sosai, da alama ta ɗan sha kuka kafin ta zo room ɗin, face ɗinta da ɗan danshin ruwa alamar ta wanke fuska kafin ta zo. Tana zuwa ta haye saman gadon tana faɗin. "Aunty Chuchu ki tashi na shiga ukuna!". A tsorace Chuchu ta juyo, dan bata yi tsammanin shigowar mutun ɗakin nata ba, kuma bata ji shigowar autar ba, so hakan ya ɗan tsoritata. "Auta lafiya?!". Ta tambayeta a ruɗe, ta yi maganar kuma ba tare da ta cire wayar daga kunnenta ba. Daga ta cikin wayar tata da yake hannunta Rizwan ya tambayeta da lafiya ita da waye?. A takaice ta amsa mashi da. "Auta ce ta shigo mun ɗaki babu sallama ta tsoritani, ina ɗan zuwa Yah Rizwan bari mu yi magana da ita". Da okey ya amsa mata. Cikin hanzari ta katse kiran nasa tare da ajiye wayar a gefe, sannan ta juyo da jikinta gabaɗaya ga autar. Ganin idanun kanwar tata cike tab da kwallah ga alamar ta sha kuka kuma yasa ta zaro idanu tare kuma da kara ruɗewa. "Auta lafiya idanunki suke cike da hawaye? Meyake faruwa ne?". Ta yi maganar tana miƙewa zaune. A tsananin ruɗe autar ta fara yin magana. "Aunty Chuchu na shiga uku, wani abin ne ya fito mun a kirjina, wanka na je yi sai na jishi ya fito mun kamar dutse, ko dai asiri aka yi mun ne? Dan na ji ance ana iya yi wa mutun asiri kala kala". Tana magana hawayen suna ganganro mata a saman fuskarta. Hakika akwai shaƙuwa mai karfi a tsakanin Zunaira da Chuchu, duk abin da yake damun Zunaira ba zata tinkari kowa ba sai ta fara tunkarar Chuchu ta gaya mata kafin ma ta gayawa Mommarta, basu ɓoyewa juna komai, yanzu haka abin da Yah Jawad ya yi wa Chuchun jiya auta tana nan da shi a ranta zata gayawa Chuchun bata manta ba, abin da yasa jiyan bata sami damar gaya mata ba barci ne ya ɗauketa, lokacin da suka dawo daga wajen yawon nasu, suna shigowa cikin gida suka isko su Sarina a parlourn, shi ne suka zauna yin hira da su har lokacin cin abinci ya yi, ita kuma Chuchu ta shiga ɗaki ta canza kaya, bayan sun ci abinci ne suka wuce ɗakin Chuchun da nufin in sun je auta zata gaya mata ga abin da Yah Jawad ya yi mata a gidan zoo da kuma sauran guraren da suka je, to suna shiga cikin ɗakin kuma Yah Jawad ya kawowa Chuchu wayarta, bayan ta karɓa sai ta ce ya bata number Yah Rizwan, ba musu ya bata, bai kuma kawo komai a ransa ba dan yayansu ne ai, ita kuwa ta sanya number a wayarta ta kira Rizwan ɗin, bai ɗauki call ɗin ba a lokacin, hakan yasa ta ajiye wayar ta nufi toilet dan yin wanka. Ita kuma auta tana kwance a saman gado tana jiran ta fito ita ma ta shiga, yau a ɗaki ɗaya zasu kwana. Bayan ta fito ta yi shirinta cikin kayan barci masu kyau da tsada, sannan ta haye gado, ita kuma auta ta miƙe ta shiga toilet ɗin da nufin idan ta yi wanka ta yi shirin kwanciya sai tazo su yi hira ta sanar da Chuchun. Sai dai ko da ta fito daga wanka sai ta tarar da Chuchun tana waya da Yah Rizwan, hakan yasa da ta gama shiri ta zo ta kwanta a kusa da chuchun, tun tana sauraron hiran da suke yi da Yah Rizwan ɗin har barci ya yi awon gaba da ita, washegari da safe kuma suka tashi da batun rashin lafiyar mama, wannan dalilin yasa autar bata samu damar gaya mata ba. To mu koma kan labarinmu. "Menene ya fito maki ɗin in gani?". Chuchu ta faɗa tana zaro idanun nan nata waje kamar zasu faɗo ƙasa, ta tsorata ita ma tun kafin tasan menene. A hanzarce auta ta fara zuge zip ɗin rigarta ƙasa tana faɗin. "Ga shi nan ki kallah". Ta yi maganar tana sauke wuyar rigar tata kasa tare da nunawa Chuchun breast ɗinta. Wani irin dariya ne ya kubcewa Chuchun, dariya ta shiga yi har da rike ciki. Baki auta ta saki tana kallonta. Sai da taga dariyar tata ba mai karewa bane yasa ta fasa mata kuka mai ɗan sauti wadda hakan yasa dan dole Chuchu ta tsayar da dariyar tata. "Yanzu me kuma abin dariya a nan? Kina ganin abu ya fito mun amma kike mun dariya". Autar ta faɗa cikin kuka. "To auta ba dole na yi dariya ba". A kule ta ce. "To idan kika tsaya kina dariya na mutu fa?". Murmushi kaɗan Chuchun ta sake yi kafin ta ce. "Ba zaki mutu ba, ai ba wani abin bane, girma ne ya zo maki, ke baki yi mamakin ya aka yi ni da su aunty Aneesa muke da breast manya ke baki da shi ba? To kema naki ne ya fara fitowa, sai a dai'na wasa da su Hoorain, a dai'na yi wa maza magana, yanzu an girma, eyee autarmu ta girma ta fara kirgan dangi". Tana magana tana guntse dariya. Sai yanzu auta ta fahimci menene, nan take ta ji wani irin kunya ya kamata, da sauri ta mayar da rigarta tana turo baki, danasanin meyasa ta nunawa Chuchun ma ta fara yi, har da wani cewa da tasan haka ne ai ba zata gayawa kowa ba, da farko ma Yah Jaish ta so fara zuwa ta gayawa kafin ta gayawa Chuchun sai ta gayawa Mommarta, ashe Allah ya taimaketa ma da bata je ta gayawa Yah Jaish ta kuma nuna mashi ba. Nima na ce amma da ta je ta gaya mashi zan yi mata dariya kam, yanzu ma n yi mata, Chuchu ta kalle mata tula tulanta da suka fara fitowa😅😅😅😅😅 bye my people's sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu..... 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 5/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________46🔥 "Meyafaru our Auta?". Ta tambayeta tana ɗan murmushin. "Babu komai Aunty Chuchu". Ta yi maganar kamar zata fasa kuka, ta kuma yi maganar tana sanya hannu ta goge kwallar da yake a saman face ɗinta. Ɗan rungumota kaɗan Chuchun ta yi tare da ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi tana ɗan tsokanar. "Sai ki sanar da Yah Omar ko?". Cikin zolaya ta yi maganar. "Allah Aunty Chuchu ki bari mana bana so". Ta yi maganar kumatu a kumbure kuma cikin shagwaɓa. "To na bari, amma kin manta ke da Yah Omar akwai amana ne? Bafa ki ɓoye mashi komai shi ma kamar yadda baki ɓoye mun, wannan ne yanzu ba zaki iya gaya mashi ba? Lallai Auta kenan yanzu babu amana da nuna kauna? Kin manta yawan gaya mashi da kike yi cewa shi ne pleasurenki? Tun ba'a je ko'ina ba an fara ɓoyewa pleasure abubuwa". Still cikin zolaya ta yi maganar. "E ɗin Aunty Chuchu na ɓoye mashi ɗin, kuma kema Allah da ban nuna maki abuna ba". Wani irin dariyar iyashege ta tuntsure da shi, cikin dariyar take faɗin. "Kai menene kuma abunki ɗin to? Bashi da suna ne". A ƙule Autar ta raba jikinta dana chuchun tare da ɗaukar wata jibgegiyar pillow da ta sha rigar bedsheet mai matuƙar tsada da nufin ta fara dukan Chuchun da shi. Ai da gudu Gimbiya Chuchu ta sauka daga gadon tana faɗin. "Bari ma na je na gayawa su Aunty Sarina har da Aunty MieMie cewa Auta ta fara kirgan dangi, ta girma". Da gudu Autar ta biyota tana faɗin. "Allah Aunty Chuchu ba zan barki ba kuma mun ɓata, kada ki sake yi mum magana, babu ruwana dake daga yau". Tana magana tana binta da gudu. Kai tsaye part ɗin King Chuchu ta nufa sai dariya take yi kamar wata zararriya, yau Auta na neman kasheta da dariya. Tana gudu tana waigo Autar taga ko ta kusa isota har ta shiga parlourn King, sai waigowa take yi bata ankaraba ta ji fa bugi faffaɗar kirjin mutun. Baya baya ta yi tana ƙoƙarin faɗuwa tare da ƙoƙarin dakatar da dariyarta da yake shirin zama kuka duba da yadda ta yamutsu fuskarta, da alama ta bugu sosai saboda gudu take yi. Wuyar doguwar rigar jikin nata ya riƙo tare da janyota gaba ya tsayar da ita a kan kafafunta bai bari ta faɗi ƙasa ba. Auta ko a jikinta da gudu ta ƙariso wajen ta fara sauke mata wannan pillown a gadon bayanta tana faɗin. "Kuma ko na dakeki ba zan huce ba, mun ɓata kenan, tabbas mun ɓata da gaske!". A hanzarce Jawad ɗin ya sanya hannunsa ya tare dukar da Autar take kawo mata ba kakkautawa. Saura kaɗan Chuchun ta kifa a kan kirjinsa saboda dukan da Autar ta yi mata ta baya da pillown na ƙarshe yasa ta yi gaba kamar zata kifa, shi kuma a lokacin yana sanya hannunsa zai tari pillown kenan, hakan yasa ta kusa kifawa a kirjin nasa. "Sorry our Auta tuba muke yi". Yah Jawad ya faɗa yana riƙo pillown da hannunsa ɗaya. "Allah ya Jawad ni na zan yi sorry ba, yau mun ɓata da Aunty Chuchu baram baram!". Tana magana tana kwaɓe fuska tare da turo baki. Cike da iya shege da tsokana tana murje gaban goshinta ta ce. "Yah Jawad to ka tambayeta me nayi mata da zata kama dukana haka?". Tana kai karshen maganar wani dariyar ne ya so kubce mata duk da turɓune fuska da ta yi lokacin da ta buge da kirjinsa, maganar a tambayi Autar yasa ta ji dariya ya zo ya kori kukan da take ƙoƙarin yi wa yayan nata. Kuka Autar ta sanya masu tare da juyawa zata bar wajen dan ta ji cewa Yah Jawad ya tambayi me Gimbiya Chuchu ta yi mata. A hanzarce ya riƙo hannunta bai bari ta bar wajen ba. Cikin sanyin murya ya ce. "Zo Autarmu, zo ki gaya mun me ta yi maki in rama maki yanzun nan". Habawa me Chuchu zata yi face dariya, shi Yah Jawad fa bai san tambayar me Chuchun ta yi mata bane yasa zata gudu ya zo yana wani tambaya shi ala dole zai rarrasheta kuma ya rama mata. Hawayen gaske ta fara yi mashi bata ce komai ba, sai wani irin harara da take wurgawa Chuchun da waɗan nan dara daran idanuwan nata. Shi dai Jawad ya rasa gane me matsalar, sun saka shi a duhu. "Ki faɗi me na yi maki Yah Jawad ya rama maki ya ce". Chuchu ta faɗa ita ma tana jefa mata hararar. Bakinciki kamar Auta ta sanya hannu a kai ta kurma ihu. Faɗawa jikin Yah Jawad ɗin ta yi tana ɓoye fuska tare da fara yin hawayen gaske, dan ranta ya ɓaci sosai, Chuchu ta kureta. Wani irin kallo mai wuyar fassaruwa Yah Jawad ɗin ya jefawa Chuchun kafin ya sassauta muryarsa kasa sosai. "Me kika yi mata Jannat?". Da sauri Autar ta ce. "Babu abin da ta yi mun Yah Jawad". Tana magana tana goga kanta a kirjinsa. Izuwa yanzu ya fahimci abin sirri ne a tsakaninsu Chuchu take yi mata wasa da hankali take kuma sanyata kuka a banza. Dan haka sai ya ce. "Shikenan our Auta, jeki abinki yanzu zan bata punishment ba tare da na ji ma me ta yi maki ba". Ya yi maganar yana shafa kyakkyawa arab hairnta da ko ɗankwali bata ɗaura ba ta shigo room ɗin na Chuchun a ruɗe, dan a tunanin wani abin ne ya sameta. Da sauri ta raba jikinta da na shi tare da nufar hanyar komawa room ɗin na Chuchun rike da pillown tana faɗin. "Allah Aunty Chuchu ba zan yafe ba idan kika gayawa wani". Juyawa da gudu ita ma Chuchun ta yi da nufin ta bi bayanta dan ta ji Yah Jawad ɗin ya ce zai bata punishment, ba zata iya ɗaukar punishment ɗinsa ba. Aikuwa bai bari ta bar wajen ba ya yi saurin riƙo hannunta tare da janyota ta dawo in da take tsaye ta tsaya. Ƙasa da murya sosai ya yi kamar wani na yi mashi laɓe, kamar kuma maras gaskiya ya fara magana, ita kuma Auta ta yi tafiyarta sai kumbure kumbure take yi. "Me kika yi mata? Meyasa zaki saka mana ita kuka?". Yana magana yana kallon cikin kwayar idanunta, while ita kuma tana ɗan satar kallonsa ta wani yi ƙasa da kai kamar wata mai ɗaukar darasin hadisi a islamiya!. "Babu fa komai Yah Jawad". Ta faɗa a sanyayye. Shiru bai sake yin magana ba, domin ya shagaltu da kallonta, gaskiyar uncle Abbas da King da suke cewa in dai zai haɗu da chuchu sai ya karewa ƴarsu kallo tsab sannan yake kama kansa, ashe dai sun san komai. Jin ya yi shiru bai sake yin magana bane yasa ta ɗago ido dan ta ɗan saci kallonsa. Ai kuwa tana ɗagowa suka yi four eyes. "Yah Jawad in tafi?". Ta faɗa ba tare da ta kawar da kallonta daga saman fuskarsa ba, sai dai ba kallon cikin kwayar idanunsa take yi ba. "Ban gama kallonki ba ai my Jannat". Ya faɗa ba tare da yasan lokacin da hakan ya fito daga bakinsa ba, sai da ya ji ta ce. "Kallona kuma Yah Jawad? Na yi kyau ne?". Nisawa ya yi, kamar mai jin barci ya furta. "Over ma kuwa kika yi kyau". "To Yah Jawad ka mun hoto". Cike da zumuɗi ta yi maganar. Wani irin cool ajiyar zuciya ya sauke tare da ciro wayarsa ɗayar. "Where's my other phone da na baki jiya?". Sai a lokacin ta tuna da wayar. "The phone is in my room, in je in kawo shi yanzu?". Murya a warware ta yi maganar. Girgiza mata kai kawai ya iya yi alamar a'a, bai iya sake furta komai ba sai matsowa da ya yi kusa da ita tare da shiga camerar wayarsa, sannan ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman shoulder ɗinta. Zafafan hotuna ya fara ɗaukarsu, ita da ta ce ya ɗauketa ita kaɗai ya ɓige da ɗaukarsu a tare. Sai canza style suke yi sun manta da cewa a parlourn King fa suke, ga shi yau King yana da baki sosai saboda zuwan su Ramish da za su yi gobe, jama'a suna ta kai koma a part ɗin, already kun san dama akwai part na saukar muhimman bakinsa na kusa sosai a cikin part ɗin nasa, so su Jawad suna tsaye ne a tsakanin wannan ɓangare na saukar bakin da kuma hanyar nufa master room na King. Canza style ya yi daɗi harda kwanciya a saman kirjinsa ta yi, yau abin nema ya samu, Chuchu mayyar ɗaukar hoto, to ga dama ya samu, mai hanata ɗaukar hoton ya takura mata yau da kansa yake ɗaukarta, ai style kuwa sai abin da kuka gani. Suna tsaka da kashe hotunansu basu ankareba kawai sai tsinkayo muryar Akka suka yi a cikin kunnuwansu tana sababi, ta nufo parlourn ɗin ne tana ta surfa sababi da masifa, da alama wani ya taɓota. Tun daga nesa take faɗin. "Ai Zuhair shi ne ya mori aure, ku cigaba da yi, har ku kwanta a gadon ajalima kada ku dai'na, yo ni idan baku yi haka ba ai sai nace sam sam Zuhair ba mata ya aura ba, kuma idan baku yin haka ai sai na sa a bincika mun ku ko da wata munafurcin a ƙasa, dan cikakkun mata kam dole sai sun ɗana wannan kishi, shi kuma Abbas ba yadda ban yi da shi ba dan ya ƙara aure ya ji daɗin aure amma yaki, shi sam ba aure ya yi ba, dan idan baka haɗa mata biyu a gida suna nuna kishi karara kamar dai matan Zuhair suna faɗa a kanka ba to ba aure ka yi ba, ku ta yi abinku shi ne dai'dai, wadda ta fi sanin kan duniya ta kwace Zuhair ɗin ya tattare a wajenta". Sai sababi take yi. (Jama'a kun ji mun wannan tsohuwa da bala'i 🤔 ita fa har dattijon arzikinta wato mijinta King Abdul Malik ya kwanta dama ita kaɗai ce matarsa, bata da kishiya, amma take cewa uncle Abbas ya karo aure, Akka sam bata son zama lafiya, ga rikicin tsufa, mata suna faɗa tana kara hura wuta 😅) Jin motsinta tana surfa wannan uban sababin yasa Jawad yaja hannun Chuchun da sauri suka haura izuwa master room na King, domin idan ya bari Akka ta kama shi da Chuchu a ɗan wannan lungu to fa ya shiga uku, ai ta rinƙa takurawa rayuwarsa kenan, idan ma bata ce zai lalata mata jika ba, dama kun san ba shiri suke yi ba, kullum cikin faɗa da samun saɓani suke, kuma idan baku manta ba Akkar ta sha shiga tsakaninsa da Chuchun tana rabasu faɗa, so tasan basa shiri sam sam, yanzu kwatsam ta gansu a tare a wannan ɗan hanya na zuwa master room ai shikenan ya shiga uku a cikin wanna kingdom ɗin, ba zata barshi ya zauna lafiya ba, kuma abin da yake gudu na kada Jaish ya san halin da ake ciki na tsakaninsa da Chuchun fa to sai ya sani idan Akka ta gansu, bugu da kari Mammiensa ma sai ta sani, kuma ɓoye mata yake yi dan yasan bata son alƙarsa da ƴaƴan King Zuhair, shi kuma a part ɗin ya taso ya girma, ya fi sabawa da su fiye da ƴan uwansa su Sarina ɗin ma, amma bai san dalilin Mammaien ɗin tasa na bata son taga yana alaƙa da ƴan uwan nasa ba, jini ɗaya suke amma tana son raba jini da karfi da yaji. Kai tsaye room na King suka nufa da gudu, wajen hawa ƴan ƙananan stage da suke a bakin kofar room ɗin na King Chuchu ta yi tuntuɓe ta faɗi, gudun da suke yi ne yasa bata lura da sun iso wajen ba. Cak Yah Jawad ya ɗauketa suka ƙarisa shiga room ɗin. A lokacin da suka shigo kuma King yana wanka, bai jima da dawowa daga masallacin jumma'ar ba, so shi dama kayansa na zuwa masallaci daban suke da sauran kayansa, saboda daraja da girma da yake bawa ranar, a ranar kwalliya na musamman yake yi, saboda jumma'a babbar rana ce, kayan zuwa masallacin nasa ma na musamman ɗin na musamman ne, idan ya dawo daga masallacin kuma yana yin wanka ya canzasu izuwa wasu na musamman ɗin dan komawa fada ya zauna zuwa yamma irin karfe 5 ɗin nan bayan sallar la'asar kenan, sai a fita yin wannan gasa tasu da suke yi. Coz yau ba zuwa fada zai yi ba, saboda abin da yake faruwa da Mama, yanzu haka idan ya yi wanka ya shirya wajen Mamar zai wuce, domin idan bai yi haka ba sai ta ce bai yi mata adalci ba, idan Momma bata da lafiya ko Dubai ta koma can yake tarewa, kunga kuwa idan yana son zaman lafiya dole ya zauna kusa da Mamar ma, idan ba haka ba a tashi gidan gabaɗaya da ruwan bala'i......... 😅 Akka dai ta ce idan basu yi haka ba to ba mata Zuhair ya aura ba, da alama fa Akka tana jin daɗin wannan diramar tasu, suna ɗebe mata kewa. Ganin cewa King na cikin toilet yana wanka, ga kuma Akka a bayansu tana zuwa yasa Yah Jawad ɗin ya sauketa a tsakiyar room ɗin saman shinfiɗar tsakiyar ɗakin, sannan ya riƙo hannunta da sauri suka faɗa cikin dressing room na King. A bayan wajen glass na jera watch ɗinsa suka tsaya suna mayar da numfashi......... Akka kuwa cikin room ɗin ta shigo tare da zama saman shinfiɗar King ɗin in da yake zama ya huta. A nan ta zauna tana jiran ɗan nata ya fito daga wanka, da alama su Momma sun bakanta mata rai ne yasa ta nufo wajen King dan su yi magana, har ta zauna saman wannan sofa da aka kawata da shinfiɗu na alfarma na gashin jimina bata dai'na zance su Momma ba, sai sababi take yi, aikuwa Allah ya rufawa Yah Jawad asiri, dan a yadda take kan tsini tana surfa sababin nan ta gansu shi da Chuchun a yadda suke ɗin nan ai shikenan rayuwarsa tana kwale kwale, dan ya shiga talatin ma ba uku ba. Ni kam na ce to su yanzu da suka shigarwa King cikin dressing room ɗinsa ku gaya mun idan ya fito daga wanka zai sanya kaya ya kenan?.🤔 Ya zasu yi idan zai shigo sanya kayansa?🤔 Ga dai Akka a cikin ɗakin, King kuma zai shigo nan, my people's kuna ganin a gudun nan da suka yi sun tsira kuwa?🤔 To ni dai bari na leƙa Daular Abu Abdussalam wato Dubai in dawo, sai naga zasu tsira ne ko asirinsu zai tonu. Abu Abdussalam empire🤍🔥 LEESHARH....✍️💘 A hankali ta ɗan waro idanun nata waje, from down ta fara kallonsa, a maimakon ta ɗaga idanu ta kalli face ɗinsa, sai ta fara kallon kafafunsa da suke sanye cikin cover shoe masu kyau da tsada launin baki. In a slow ta fara ɗaga idanunta tana binsa da kallon from down ɗin har up. A tsananin razane ta miƙe tsaye tana zaro idanu waje kamar za su faɗi ƙasa. Domin kuwa a karya na idanunta face ɗin Ramish yake nuna mata, shi ya yi mata gizo a kan fuskar guy ɗin, wannan guy ɗin daban, amma da yake tunanin Ramish ne a ranta sai take ganin kamar shi ne. Cikin harshen larabci wannan guy ɗin ya ce mata lafiya ta yi irin wannan miƙewa haka? Meyasa kuma ta tsorata da ganinsa? Ko dai ta san shi ne?. Bai san cewa face ɗin Ramish ta gani a tattare da shi ba. Wannan magana da ya yi ne yasa ta dawo cikin hankalinta, nan take idanunta suka kallan mata ainahin kamannin guy ɗin wannan da yake cikakken arab men, fari tas da shi kuma kyakkyawa. Miƙa mata handkerchief ɗin ya yi yana mai sake ce mata lafiya take kuwa?. Bata karɓi handkerchief ɗin ba sai dai ta raɓa ta gefensa da sauri domin ta wuce. A dai'dai lokacin kuma Guyson ya iso waje, zai je duba Yah Ramish da ya ki halartar taron ne, zai wuce sai ya hangota tana kuka, shi ne ya ce bari ya ƙariso ya ji me ya sameta ko dan Sharifat sai ya kulata. Ganin Guyson a gabanta yasa ta ja birki tare da sanya hannu ta hau goge hawayen face ɗin nata da sauri sauri. Wani irin kallo Guyson ɗin ya bi matashin da ya miƙa mata handkerchief ɗin nan da shi kafin ya ce da shi. "Meka yi mata?". Cikin harshen larabci ya yi maganar. Yadda ya yi maganar kuma sai ka rantse da Allah Bilal ko Ramish ne suka yi maganar, ya yi maganar a dake irin babu wasa a tattare da shi ɗin nan, ya yi ta kuma yana ɗaure fuska sosai. Kai kai kai, Guyson fa akwai madarar kyau kam, kamar Gimbiya Zunaira yake, sai ma daya haɗe rannan, sai kyan ta kara bayyana so masha Allah, kamar ka yi ta kallonsa ba gajiyawa, da ya ɗaure fuska sai ga shin gerarsa suka haɗe waje guda, hakan ba ƙaramin kara tsatso mashi kyansa ya yi ba, waɗan nan fararen idanun nasa idan ya zaro maka su sai ka gudu saboda girma ga kyau. Cikin girmamawa wannan matashi ya amsa mashi da babu abin da ya yi mata, haka ya iskota tana kuka shi ne yake rarrashinta. Da alama wannan matashi yasan Guyson sosai duba da yadda ya bashi amsa cikin girmamawa. "Leesharh meyasameki kike kuka?". Ya yi tambayar yana maido da kallonsa a kanta. Tana kan goge hawayen da suka ki dagatawa da zuba, ta ruɗe ta rasa wani amsa zata bashi. Shin ta ce mashi kewan babanta ne yasa take kuka ko yaya? Amma idan ta ce mashi kewar babanta ne zai iya sanyawa ya ce a kaita wajen baban nata ta gansa sai a dawo da ita, to a ina zata ga baban nata kenan? Ta sake jefawa kanta tambaya, ta rasa me yakamata ta ce mashi, tasan ƙaramin aikinsa ne duk abin da ta ce ga shi shi ya sakata kuka shi kuma ya ce a nemo wannan abin, ya zata yi kenan?. Can wata wani dubara ta faɗo mata, cikin hanzari ta amsa mashi da. "Wani kwaro ne ya shiga mun cikin idona, shi ne ya sanya ni yin kuka". Murya a ɗan kausashe ya ce. "Ta ya aka yi aka samu kwaro a cikin hall ɗin nan? Dole masu gyaran hall ɗin nan su sha punishment, domin kuwa basu yi aikinsu yadda ya dace ba ga shi suna cutar da mutane". Ya kai karshen maganar tare da ciro handkerchief daga aljihunsa ya miƙa mata a kan ta goge hawayen nata, sannan ya yi mata sannu kafin yasa kai ya wuce ya barta tsaye a wajen, ya sha alwashin in aka gama taro dukka masu aikin gyaran hall ɗin sai sun sha punishment, a kan me basu yi aikinsu da kyau ba har suka bar kwari suka iya shigowa cikin wajen suna cutar da bayin Allah?. Da alama Guyson yasan darajan ɗan Adam sosai da sosai. Ita kuwa tsoro ne ya kamata na ganin cewa zata ɗauki alhakin masu gyaran wajen, bayin Allah basu san komai ba zasu sha punishment a banza, ta shiga damuwa sosai a kan hakan, danasanin yin wannan karya da ta yi ta fara yi, tana yi tana goge hawayen nata da handkerchief ɗin da ya bata, tana kuma shaƙar daddaɗar kamshin dake jikin handkee ɗin. Katseta da yi mata sannu wannan matashi na bayan nata ya yi. A ɗan razane ta juyo da kallonta a kansa, da alama ta manta da shi yana wajen, hakan ne ya razanata. Sannu ya kara yi mata yana wani binta da kallo kamar wani tsohon maye. Da yauwa kawai ta amsa mashi, cike da tsoro tasa kai zata bar wajen. Ƙoƙarin dakatar da ita ya yi, da alama yana da wani plan a kanta. Kin tsayawa ta yi domin idan baku manta ba ita Leesharh tana aiki ne bisa umarnin masu nikaf, sai abin da suka ce take yi, dan haka kula maza baya daga cikin tsarin aikinta, hakan yasa ta yi saurin barin wajen. A hanzarce ta fito daga hall ɗin, tana tafiya tana waige waige kamar maras gaskiya, kirjinta sai dukan uku uku tara tara yake yi, addu'a take yi kawai Allah yasa wannan matashin kada ya biyota, sai zuba uban sauri take yi, a ƙagare take da ta isa wajen elevator ta koma sama ta je ta yi kwanciyarta a room nata dan yau dai aiki ba zai yiwu mata ba. A garin waige waigen baya da take yi bata ankara ba sai ji ta yi ta yi karo da mutun. Har wani irin jiri ta ji tana ƙoƙarin faɗuwa saboda bata rike jikinta da kyau ba. Da kyar ta iya kama kanta ta tsaya tare kuma da ƙoƙarin ɗaga idanu dan ta kalli da waye ta yi karo. Daddaɗar kamshin perfume ɗinsu ne ya daki kofofin hancinta. Kusan kamshin perfume ɗin irin na Ramish, hakan ne ya haifar mata da faɗuwar gaba tun bata kalli wanene bane. Cikin tsoro ta ɗago idanunta da suke jajir har sun ɗan kunbura saboda kuka. Dai'dai lokacin da ta ɗago kai shi kuma Obaid ya yi yunƙurin kai mata mari saboda buge shi da ta yi, har ta sanya wayarsa ya faɗi a ƙasa. Riƙesa Omaid ya yi dan yasan wlh marinsu ba shi da daɗi sam sam, idan ya mari yarinyar nan ai sai ta suma, duk wanda waɗan nan twins ɗin suka mara fa baya sha ta daɗi, sam marinsu bashi da daɗi. Hakan yasa Omaid ya riƙesa. Ita sam bata damu da yunkurin kai mata marin da Obaid ya yi ba, ruɗani ma suka jefata, tunani take yi wai shin a gaban madubi take kallon mutun biyu maimakon ɗaya ne ko dai yaya ne? Taga sun yi muguwar kama, ka rantse da Allah mutun ɗaya ne, sun ruɗar mata da ƙwaƙwalwa...... Ni kuwa na ce ba ke kaɗai ba, yayyunsu ma ba iya rabesu suke yi ba bare ke bare, ai su kaɗai suke iya rabe kansu sai Mommarsu, ko King da yake matsayin ubansu baya iya rabesu, sai ya kira Obaid da sunan Omaid, ya kira Omaid da sunan Obaid, Allah ya yi masu halitta ne iri guda sak, ta wannan kamanceceniya da take a tsakaninsu suke amfani su ruɗar da mutane a kullum, baka isa ɗaya daga cikinsu ya yi maka laifi ka ce zaka iya gane wanda ya yi ɗin ba, wane kai, sai dai idan zaka haɗesu dukkansu biyu ka basu punishment, amma gane mai laifi a cikinsu ba abu bane mai yiwuwa. "Who're you and what are you doing here?". Cewar Omaid ɗin, ya yi maganar kuma bai saki hannun Obaid da ya rike da kada ya mareta ba. Da farko dai sun cewa Guyson ba zasu zo gidan ba, amma daga baya suka ce zasu halarci walimar, shi ne fa Abu Abdussalam ya tura tawagar motoci aka ɗaukosu. Sun ci gayu cikin ƙananan kaya, ga wasu booth da suka sanya a kafafunsu masu kyau da tsada, already kunsan su komai masu iri ɗaya suke sanyawa, harta gyaran gashin kansu iri ɗaya suke yi. "She looks like a criminal, ban yarda da ita ba". Cewar Obaid, ya yi maganar yana zame hannunsa daga riƙon da ɗan uwan nasa ya yi mashi. Su suna ta maganarsu ita bata ma a tare da su, duniyar tunani ta luluƙa, ta ruɗe ta rasa gane wai mutun biyu ne a gabanta ko dai ɗaya ne a gaban mirror, sam bata jin abin da suke faɗe ma. Na gaya maku waɗan nan twins ɗin giveted ne, ƙwaƙwalwarsu kaifi gare shi ga saurin gudun aiki, cikin lokaci ƙanƙani suke iya gane abin da babba baya ganewa, da kallo ɗaya Obaid ya yi mata ya ji ya fara zarginta, bai ma san wacece ita ko me take yi a cikin gidan ba, amma har cikin ransa ya ji tabbas wannan yarinyar maras gaskiya ce. (Da su twin's a gidan Abu Abdussalam suke da kuwa akwai cakwakiya, dan kuwa cikin minti ɗaya zasu gano Leesharh.😅 Yara kamar wasu aljanu🤔😅) "Yeah you're right blood, the way she's walking she's totally criminal, and see her eyes like she want to kill someone innocent". Cewar Omaid. Tsawa Obaid ya daka mata a kan wacece ita?. Can masu dai, ita bata ma jin me suke faɗe, hankalinta ya yi nisan kiwo. Wani irin raɗaɗin azaba da ta ji ya ziyarci dukkannin ilahirin sassan jikinta ne yasa ta dawo daga tunanin da ta afka. A wani irin mahaukacin razane ta sanya hannu ta dafe ƙuncinta in da Obaid ya sakar mata mari, ji take yi kamar ba'a duniya take ba, nan take ta fara ganin wani haske yana mamaye ko'ina a wajen, ɓangaren da ya mareta ɗin kunnenta ya daina jiyo mata sautin komai. Dama twin's basu shiga aikin special weapons and tactics bama ya marinsu yake da azaban zafi bare kuma su da suke karɓar horo kullum, ga aikin wahala, ai dama idan suka mareka sai ka ji kamshin lahira, to ita dai Leesharh ta ɗan ɗana. Ƙoƙarin kara mata wani marin Obaid sarkin saurin hawa ya yi, dai'dai lokacin Guyson ya iso wajen, ya fito daga cikin gida wajen Yah Ramish. "Kai Obaid me ta yi maka zaka mareta?". Guyson ya jefa masu tambaya, while shi kuma Omaid ya riƙe hannun Obaid ɗin dan kada ya kara mata wani marin, yasan idan ya barshi ya kara mata to fa sai dai a kwasheta ranga ranga bayan ta zuba kashi da fitsari a wando. "Yah Omar who's she?". Cewar Omaid. Omaid fa da kuke ganin nan ya iya takunsa, ya fi Obaid iya tsiya, sai dai shi yana danne zuciyarsa baya saurin hawa, baya yarda ransa ta ɓaci har zuciya tasa ya fita hayyacinsa, sarai yasan me yake yi, da ƙwaƙwalwarsa yake aiki over, ya iya takunsa sanka sanka, yanzu dai kunga shi Obaid har ya arzuƙa, dan sun yi magana bata amsa masu ba har ya fusata ya mareta, shi kuwa Omaid kun ga kamar ma bai san ana yi ba, saboda tsabar iya taku da basaja. "Ayya she's our new house girl, sabuwar maaikaciya ce fa, kuma innocent girl ce, bata da hayaniya, kawar Lil sister ce ma fa". Cewar Guyson. Kawar da kansa Obaid ya yi tare da sauke hannunsa daga yunƙurin kara mata marin da ya yi niyar yi Omaid ya tare, cikin ɓacin rai ya ce. "Wannan ba house girl bane ba, criminal ce maras gaskiya, she looks like green snake under green grass". Omaid zai yi magana Guyson ya riga shi da cewa. "Anyway, koma dai menene kuzo mu tafi cikin hall, wai bama kunce ba zaku zo ba? Ya aka yi kuma kuka zo?". Guyson bawan Allah, yasan da cewa halin kannen nasa sai su, shi sam bai ɗauki zancensu da wani mahimmanci ba na kiran Leesharh da green snake under green grass da suka yi, dan yasan su fa yaran nan sam sam basu son zaman lafiya, idan basu kaunar mutun ba kalar sharrin da ba zasu yi mashi ba, dan haka sai ya ɗauki abin a zaman cewa basu kaunar Leesharh ce kawai yasa suka laƙa mata wannan suna. Bai san sun fishi gaskiya ba, su fa jami'ai ne, yau tsawon almost shekaru 8 suna a special weapons and tactics academy, a matsayin horon da suke yanzu zasu iya gane ɓarawo cikin dubbannin mutane, horo mai rai da lafiya suke samu, ba makarantace ta kananan kai ba, kun san su kuma da basira, hakan yasa makarantar take alfahari da su sosai da sosai, su ɗin su kaɗai ne tamkar ya dubu a cikin school ɗin nasu. Shi kuwa Guyson da yake karatun computer engineering ina zai gane hakan? Ai babu wannan magana, ba abin da zai gane, su kam sun san duk wasu lago na mutun maras gaskiya. Da kyar Guyson ɗin ya iya jansu suka bar wajen, har suka bar wajen kuma Leesharh bata dawo cikin hayyacinta ba, ta maru kam ba karya, duk da take chocolate color sai da shatin yatsu biyar ɗin Obaid ya fito ruɗu ruɗu a face ɗin tata, ta ji hannun manya, wannan ma dan ba marin Omaid ta sha ba, da na shi ne ina ga suma zata yi ko mutuwa mai gabaɗaya, dan Omaid ya fi Obaid sanin gurbin mugunta, dama kunsan ko da twin's ɗin a mahaifa guda suka fito ba daban daban ba dole ɗaya yana fin ɗaya wasu abubuwa, to Omaid dai ya fi Obaid wayo, iya shege, iya taku, zafin zuciya, iya sarrafa zuciyarsa, kai da komai ma. Ta jima sosai a wajen kafin ta fara jin kamshin dawowa cikin hayyacinta. Sai a lokacin kuma ta iya durkushewa kasa a saman gwiwowinta a wajen ta saki wani marayar kuka, wani irin zogi da azaba ne yake ratsa kashi da ɓargon jikinta, har yanzu kuma ta kasa iya tantance wai Obaid da Omaid mutun biyu ne ko dai mutun ɗaya ta gani?. Ta ɗauki a kallah tsawon good 30 mins s wajen kafin nan ta iya miƙewa tsaye, tana sharar kwallah ta nufi cikin gida. Allah sarki Jasra mai cewa Leesharh bata da saurin kuka to yau ta zo taga Leesharh na sharɓar kwallah kamar ruwan fanfo aka buɗe. Elevator ta haye ta nufi sama, sai goge kwallar take yi amma yaki dakatawa daga zuba, zogin wannan mari nasa yaki sakinta, tunani take yi su waye su Obaid kuma?. Can zancen wannan matashiyar mata mai nikaf ɗin ya faɗo mata a ranta in da take cewa. "Akwai wasu twin's a gidan, kada ki yarda ki haɗa hanya da su, kada ki takalesu ko wata gardama ta haɗaku, saboda kaifin ƙwaƙwalwarsu zasu iya harbo jirginki". Tuna tattaunawarta da matar yasa ta fara zargin to ko sune waɗan da aka yi mata gargaɗi a kansu? In kuwa sune to ai ta kwaɓe aiki, dan kuwa ga shi dai gardama ce ta fara haɗasu, kuma tun da suka fara cewa suna zarginta to da wuya su kyaleta, idan ma basu fara yin practical na aikinsu a kanta ba... Akwai cakwakiya kam. Tana haurawa sama ta nufi hanyar da zai sadata da part ɗinsu, tana tafiya zalo zalo kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Kamar daga sama ta tsinkayo muryar Ramish da tun da ta ji ta sau ɗaya ɗazun ya tsaya mata a ranta. Waya yake yi cikin harshen turanci, da alama kuma da abokan aikinsa yake wayar, yana tsaye a gabanta in da take tunkara kenan, sai dai bata ƙarisa wajen ba, da alama wayar ce ta fito da shi daga babbar parlourn izuwa wannan waje. Cikin hanzari ta ɗan ja da baya kaɗan ta laɓe wajen wani ɗan lungu na kusa da babban parlourn, tattara dukkan nutsuwanta ta yi ta kasa kunne tana sauraron abin da yake faɗa, ba wani gane turancin sosai take yi ba, amma Allah yasa yana maganar yana haɗawa da larabci, hakan yasa tana fahimtar abin da yake faɗa sosai da sosai, ta fahimci ina maganar tasa ta dosa. NI KAM NA CE LEESHARH FA TA FARA AIKINTA KENAN, TO KAFIN MU JI ME RAMISH YAKE FAƊE BARI MU LEƘA SABON GIDAN BABAN KHADIJA MUGA ME AKE AIKATAWA SAI MU DAWO. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH 💔😥 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________47🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH 💔😥 Ana dirama a wannan gida dai'dai gwargwado, domin kuwa Hauwa fa ita ce ta bawa maman Zainab ɗakin da zata zauna, gini ne da baban Zainab ya yi ta gabaɗaya rufi ɗaya, manya manyan bedrooms guda huɗu ne a cikin ginin, kowanne da toilet ɗinsa daga ciki, sai parlor a tsakiyarsu, akwai katafaren kitchen a cikin, kofar kitchen ɗin yana ta wajen dining area. Daga waje ta baya kuma akwai Bq, ginin dai ya tsaru sosai, gini ne na zamani, kasa tiles sama pop, ga manya manyan Ac a parlourn da kowa room na gidan. Kitchen ɗin ma already anyi fixing na komai, drawers ɗin duk an yi fixing ɗinsu, harta gas da komai da komai an sanya. Hauwa da kanta ta zaɓawa maman Zainab ɗakin da yake ta kusa da dining area, wai shi ne ɗakinta, sannan ta bawa su Zainab ɗakin da yake kusa da na mamar tasu wai shi ne nasu, sura room guda biyun kuma ta ce ɗaya nata ita da baban Zainab, ɗayan kuma a bar mata shi zata yi amfani da shi ba yanzu ba. Nan fa maman Zainab ta ce bata isa ba, dan bata ga dalilin da zai sa ace Hauwa ce zata zaɓa mata ɗakin da zata zauna ba, kunsan mu fa mata haka halinmu yake, mun tsani muga wata macen tana nuna mana ta fimu iko da abin da muka san mu muka sha wahala a kansa, da farko maman Zainab ta ce zata danne zuciyarta ta hakura kome Hauwar zata yi ba zata kulata ba, zata kawar da kai, amma ina ba zata iya yin hakan ba, domin kuwa mu mata bamu da karfin zuciyar jurar ganin kishiya ta nuna ta fimu iko da komai na gida.........😌🙃🌝 Hakan yasa maman Zainab ta ce ina wlh Hauwa bata isa ta zaɓa mata ɗakin da zata zauna ba, ta gama shan wahalar baban Zainab ɗin, su juri wahala a baya domin su gina kansu rana tsaka kawai wata banza ta zo ta ce zata nuna mata ta fita iko da wannan ribar wahala da suka sha? Wlh wannan ne kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba. Ita kuwa Hauwa ta ce yama yiwu ya gama. Baban Zainab wanda tun da suka shigo gidan ya kama hanya ya wuce room ɗinsa bai ma san me ake ciki ba, ya barosu a parlourn ne suna ta dirama. Cikin gatse Hauwa ta fara gaya mata magana. "Wannan ɗakin shi na zaɓa maku, kuma a cikinsa zaku zauna, idan ba haka ba sai dai ku kwana a waje, dan ba zaku kwana mun a parlour bama, saboda wani lokaci tsakar dare ina fitowa mu ɗan yi hira da mijina idan barci yaki zuwa, so ba zaki kwana mun a parlour mu fito hira mu sameku ba, dan haka in baki son ɗakin da na baki ki san abin yi, ke bari ki ji ko shi kansa mai gidan idan na ga dama yau a waje zai kwana, kuma haka dole zai kwana babu yadda ya iya da ni, ni fa babu yadda kuka iya da ni, na zame maku ƙashin wuya, na fi karfinku sai gani sai hange daga nesa". Zainab dake tsaye kusa da mamar tata ce ta ce. "Idan kin fi karfinsu ai baki ki fi karfin Allah bako? To da izinin Allah sai rayuwarki ta walaƙanta tun a duniya kafin ki je lahira ki girbi abinda kika shuka, maciyi amana kawai, In Sha Allah idan baki yi hankali ba ni ce nan zan gyara maki zama!". Ta yi maganar tana wurga mata kallon up and down irin wanda take yi wa Haidar idan ya ɓata mata rai, kun san fa Zee ta kware a iya irin wannan ɗan iskan kallo na rai'nin wayo, kamar dan ita aka yi kallon, ga idanun nata kuma manya farare tas, idan ta fara wannan kallo ba'a magana, kallo ne na ƙasƙanci wanda idan ka yi wa mutun sai ya ji kamar bashi da gata, to ita dai Zainab ta kware a wannan part ɗin. Sai ƙoƙarin rufe mata baki Khadija take yi a kan ta yi shiru kada ta sake jangwalo masu wani bala'in, amma ina Zainab fa taki rufe bakinta har sai da ta kai aya a maganarta. "Eyeee lallai Zainab kin girma, wuyarki ya yi kwari ya kai yanka, ke ɗin ce zaki gyara mun zama? To uwarki ma mecece a gaba bare ke? Ubanki ma bai wuce na aikesa ya je ya dawo ba bare ke, lallai yarinya kinzo da abin da dukka familynki ba zasu iya ɗauka ba, wato faɗa da ni!!". Cigaba da wurga mata wannan matsiyacin kallo ta yi tare da cewa. "Ke ɗin wacece ke? Ke ɗin banza ke ɗin hofi, babanmu dai zaki iya aikansa ya je ya dawo kamar yadda kika faɗa ɗin, dan kin shanyesa, amma ni dai wlh nafi karfinki algunguma kanwar shaiɗan kawai!!". Cikin fushi tare da jin zafin kalaman nata Hauwar ta yi kanta zata daketa. Da sauri maman Zainab ta shiga tsakaninsu ta mayar da Zainab ɗin bayanta. Cikin ɓacin rai ta fara magana. "Wlh Hauwa idan kika ɗaura hannunki a jikin Zainab sai kin gane baki da wayo, sai na tuno maki da lokacin da muke zuwa Islamiya!". Khadija dai tana tsaye shiru tana ganin wannan iko na Allah, ita kanta ma ciwo yake yi mata, ta gaji da tsayuwa tana son ta zauna. Birki Hauwar ta ja, cikin kunan rai ta juya fuuu kamar wata kunfa ta nufi ɗakinta in da baban Zainab ya shiga kenan, da alama tana matuƙar tsoron yin faɗa da maman Zainab ɗin, duk da ta san cewa baban Zainab yana nan kuma zai tare mata faɗar, sai dai tasan kafin ya fito ya tare mata ɗin maman Zainab idan ta yi mata duka ɗaya sai ta yi jinya, hakan yasa bata yarda ta yi faɗa da ita idan baban Zainab ɗin ya matsa ko kaɗan ne. "Zainab ku shiga wancan ɗakin da ta ce naku ɗin ku zauna ina zuwa, ku fa rufe kofa idan kun shiga, kuma ko an buga kofar kada ku buɗe har sai idan ni ce na dawo". Cewar maman Zainab. Cikin wani irin kasalalliyar murya mai sanyi Khadija ta ce. "Mama ina zaki je?". Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. "Ba zan yi nisa ba, yanzu zan dawo, idan na dawo zan gaya maki in da na je". Tana kai karshen maganar bata jira jin me zasu sake faɗa ba ta nufi waje da sauri. Su kuma suka nufi cikin ɗakin a hanzarce kamar yadda ta umarcesu, suna shiga kuma suka dannawa kofar key. Da shigansu ɗakin ba'afi da minti ɗaya ba sai ga Hauwa da baban Zainab sun fito daga nasu room ɗin. Sai cika Hauwa take yi tana batsewa, da alama wani munafurcin ta je ta haɗa, ta kwashi karya da gaskiya ta sanar da shi, bawan Allah shi kuwa da already an rigada an shanye mashi ruwan kansa, sai yazama kamar wani yaronta, duk abin da ta faɗa shikenan ya yarda, haka kuma zata taso shi a gaba zalo zalo yana biye da ita, duk abin da ta faɗa ya hau kai ya zauna da shi yake aiki. Ganin babu kowa a parlourn ne yasa Hauwar ta fara surfa uwar masifa a kan ita lallai ba zata yarda ba sai baban Zainab ya daki Zainab ɗin dan ta yi mata rashin kunya. Shi kuwa bawan Allah sai hakuri yake ta bata babu kakkautawa, kafewa ta yi a kan lallai sai ya gurzan mata bakin Zainab har sai ya yi jini. Allah sarki Zee baiwar Allah, babanta bai taɓa ɗaura hannunsa a jikinta da sunan duka ba, baya dukansu sai dai rarrashi da lallama tare da nuna soyayya, amma yau Hauwa tana son lallai sai an dirzan mata bakin Zee, akwai cakwakiya kenan. Sai hakuri yake bata yana gaya mata ai shi bai ga su Zainab ɗin ba, tun da kuma basa nan ta yi hakuri kawai. Sam bata san sun shiga cikin ɗakin ne sun rufe kofa ba, da ta leƙa ɗakin da ta baiwa mamar tasu taga ba kowa sai ta yi zaton fita suka yi, bata yi yunƙurin leƙa ɗayan ɗakin ba. Ita kuwa maman Zainab tana fita kai tsaye bakin titi ta nufa, da yake gidan nasu bashi da nisa da bakin babban titin. Yau a karo na biyu Maman Zainab ta sake fita ba da izinin baban Zainab ba, hakan kuma ya faru ne saboda tsananin kunan rai da take ji, idanunta sun rufe bata ji bata gani, shiyasa ake son bawa a kowani lokaci ya rinƙa yawaita addu'ar Allah yasa ya fi karfin zuciyarsa, sannan ku kasance a duk lokacin da ranku ya ɓaci ku yawaita istigfari kuna ambaton sunan Allah, hakan zai sa duk ɓacin ran da zaku shiga ba zaku taɓa yin aikin danasani ba, dan haka ni dai shawarata a gareku ƴan uwana mata har ma da maza, kada ku bari zuciyarku ta fi karfinku, duk wuya duk daɗi kuma kada ku bari ambaton sunan Allah ya kubce daga bakunanku, yawan ambaton Allah ya kan sa ku fi karfin zuƙatanku, kuma yakan kai ku ga nasara tare da cinma burikanku da kuma samun babban rabo duniya da lahira, dan haka kada ku yarda ambaton Allah a kowani irin yanayi ne ya kubce daga gareku!!. Abin hawa ta hau ba tare da ta gayawa kowa ba ta nufi bayan gari. Zuciyarta tafarfasa yake yi mata tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje, ranta ya yi bakin kirin, idanunta sun rufe sosai, burinta kawai ta isa in da take da buƙata, sai sauke wani irin ajiyar zuciya take yi wanda da gajisa kasan na tsananin ɓacin rai ne, wai ace Hauwa ce ma zata zaɓa mata in da zata zauna ita da gidan mijinta, gidan mijin nata ma wanda ta sha wahala ta juri komai dan su gina gidan? Abin da ciwo kam matuƙa, duk kuma macen da aka yi wa haka ba lallai ta iya ɗauka ba, za'a tara mata ɗari da wuya a samu biyu da zasu iya danne irin hakan su shanye, akwai matuƙar ciwo sosai. Kai tsaye bayan gari suka nufa, ba tare da ɓata lokaci ba ta yi wa mai mashin ɗin kwatance wajen wannan boka na Hauwar, sai kutsawa cikin dajin yake yi ita kuma tana kara yi mashi kwatance. Da kyar dai suka iya isowa wajen dutsen. Sauka ta yi ta ce ya jirata bari ta je ta fito, dama sun yi da shi tun kafin ta hau a kan zai kai ta ne ya kuma dawo da ita, hakan yasa ya samu waje ƙarƙashin wata bishiyar kuka mai girma ya yi zamansa bayan ya kashe mashin ɗin nasa kenan. Zuciyarsa cike tab da tunani tare da tarin tambayoyi haɗe da mamaki a kan maman Zainab ɗin. Bai san wacece ita ba, amma ta bashi mamaki yadda ta ce ya kawota wannan ƙungurmin dajin, tunani ya rinƙa yi tare da tambayar kansa me ta zo yi a nan? Sam bai san da cewa a saman wannan dutse ta baya akwai wani la'anannen Allah ba wai shi boka, wani tsinanne wanda wutar jahannama ke jiran gangar jikinsa idan bai tuba ba, shi dai mamaki yake yi kawai na me zata yi a daji, tunani ya yi ko dai ya salallaɓa ya bi bayanta ya je ya leƙa me zata yi ne domin ya samu abin labartawa a gari. Hakan kuwa a ka yi, ya miƙe daga zaunen da yake ya fara salallaɓawa ya haye saman dutsen shi ma. Tun bai ƙarisa zuwa wajen ɗan kogon da ya gani a wajen ba ya fara jiyo muryarta tana magana kamar haka. "Ba ni ce na kawo maka aikin ba dama? Ai kuɗina na biya, dan haka na ce ka warware wannan aiki, idan kuma ba haka ba zan shigar da kai kara ga hukuma, macuci kawai azzalumi, wlh da kai da Hauwa ba zaku ga annabi idan baku tuba ba". Yana daga zaune saman ɗan buzunsa na tsafin ya amsa mata da. "Ke ɗin ganin annabin zaki yi ne aka ce maki? Nasan kin san da cewa idan mutun ya je wajen boka ba tare da ya yi aiki da abin da bokan ya faɗa ba, zuwa kawai ya yi sallarsa ta kwana arba'in Allah baya karɓa, kin san da haka kuma ai kika zo nan har kika yi amfani da abin da na faɗa na kuma baki, ke muma fa ba wai jahilai bane, bari ki ji in gaya maki gaskiya kafin ka zama cikakken boka sai kana da hadda Alqur'ani mai girma a kanka, sannan sai ka san fassarar ayoyin cikinta, babu wanda Allah ya kafurta a Alqur'ani mai girma har sau biyar sai boka!! Mun san komai kawai take sanin muke yi domin biyan buƙatar kanmu! Kuma hakan ce kaddararmu, Alqur'ani da kike ganin nan tun daga farkon duniya har karshenta akwai magungunar duk wasu cuta da suke a duniya a zamanin da ya shuɗe da kuma yanzu har ma da cutar da zata bayyana nan gaba wadda namu sani ba, Allah bai saukar da cuta ba sai da ya saukar da maganinta, kowacce aya a cikin Alqur'ani da kike ganin nan tana da dalilin sauketa, dan haka ki sani ba wai da ka muke komai ba, duk wani sihiri da zamu haɗa in dai da gaske so muke taci to dole sai da Alqur'ani, dole sai da wasu ayoyin da Ubangiji ya saukarwa mutanen da suka gabata domin kawar da matsalarsu, to mukuma da ita muke amfani domin hassasa matsala cikin al'umma, sihirin da yake jikin mijin kurciya ce, sihiri mai wuyar warwaruwa kenan, ba kamar sauran sihiri da kika sani wadda zata yi kwana arba'in ko makamancinta ta kwance bane, wannan babban aiki ne, dole idan za'a kwanceta sai an dawo da kurciyar, sannan tsakanina da Hauwa akwai amana, dan tana mun abin da ba kowa ba, sai dai idan zaki yi mun abin da take yi mun sai na duba na gani.......". Zaro ido maman Zainab ta yi tun lokacin da ya fara jawabinsa, kenan dama sun san gaskiya shegu?. Ni kuwa na ce kwarai kuwa babu abin da basu sani ba, shiyasa idan Allah ya tashi kamasu suke cin ubansu! Domin da sanin komai suke aikata duk abin da suke aikatawa, Allah baya kama bawa a cikin aikin rashin sani, amma ka sani ka take sani babban laifine wanda idan Allah ya tashi kamaka baya yi maka ta daɗi, babu wani ɗan iskan boka da ya isa ya yi sihiri ba tare da ayoyin Alkur'ani ba, dan haka ilimi ne da su sarai la'anannun tsinannu, kafirtasu da Ubangiji ya yi har sau biyar a cikin Alqur'ani ma duk sun san da haka shegu, sun karanta kuma sun karanci tafsiri, sun san fassarar ayoyi da dama, wasu ma sun san fasarar kowace aya shegu, amma a haka suke take sani suna cutar da bayin Allah, su yi asiri su ɗaurawa wata cuta, wata su haukatata ta shiga duniya a sake samun wasu la'anannu su yi amfani da ita a haukace dan biyan buƙatarsu suma, kuma duk bokayen ke saka hakan, ga shi nan dai abubuwa kala kala, ga cin zarafin Alqur'ani mai girma da suke yi, wata zasu rubuta mata suratul ali'imran su haɗa da magungunansu su ce ta wanke gabanta da shi, wannan ɓangaren sun fi yiwa karuwai wai dan su kara ɗanɗano, kun ga laifi kan laifi, ga bokanci ka taimakawa zinace zinace ta kara yaɗuwa, wani lokaci su rubuta wata sura daga cikin Alqur'ani mai girma su wanke suce mace ta yi wanka da shi, haka zata je cikin toilet wajen najasa ta yi wannan aiki, wani lokaci da jinin al'ada kazanta zasu rubuta Alqur'ani mai girma su wanke su bawa mace ta baiwa namiji, wani lokaci su rubuta wata sura a paper su ce mace ta sanya a gabanta, aiki dai kala kala na cin zarafin Alqur'ani mai girma duk yinsa suke yi, kuma sarai sun san hukuncin da yake jiransu na yin wannan ɗanyen aikin, amma da yake sheɗan ya yi wa Allah alkawarin sai ya samu parsinjoji na tafiya wutar jahannama, sai ya bi ya yi ta kaɗa masu gangan a kunne yana gaya masu cewa kada su damu su yi ta aikata fin hakan ma, idan sun zo mutuwa sai su tuba, haka sheɗan yake ruɗarsu, su yi ta tsula siyarsu a zuwan zasu tuba kafin mutuwa, sai su fake da cewa ai Allah gafurun rahim ne, sai dai sun manta shi Allah ba'a yi mashi wayo, wane mutun, san da zasu mutu ma basa sani bare har su tuba, time da zai kamasu ma basa sani bare su tuba shegu!!!. Ganin maman Zainab ta zaro idanu tare da luluƙawa duniyar tunani ne yasa bokan ya sake ce mata. "Kada ki damu mu wannan ita ce kaddararmu da Allah ya kaddaro mana". Wani irin matsiyacin kallo ta bishi da shi kafin ta ce. "Kuka dai kaddarawa kanku, Allah kam bai ɗaura maku wannan kaddara ba, kowani ɗan iska sai ya gama shirga iskancinsa, ya tsula tsiyarsa son ransa sai ya ce kaddararsa da Allah ya kaddaro masa kenan, to shi dai Allah baka isa ka yi mashi karya kuma ka zauna lafiya ba, azzaluman banza kawai..........." Dakatar da ita ya yi ta hanyar daka mata tsawa ba tare da ya bari ta gama amayar da zafafan zantukan da suke ƙunshe a cikin cikinta suna cizonta ba. Maman Zainab akwai karfin hali, ko tsoron wannan boka bata ji ba, ɓacin rai yasa ta fara zazzaga mashi masifa ba tare da jin tsoron kada ya yi mata wani abin ba, bugu da kari tana zaune a cikin muhallinsa tana kwashe mashi albarka. "Dakata Hajiya, idan maganganu marasa daɗi kika zo gaya mun to tun wuri ina umartarki da ki fita a cikin wajen nan tun ban sauya maki halittar jikinki ba, sha sha sha kawai, ke har kin isa ki zo har in da nake ki ce zaki gaya mun magana? To idan ba aiki zaki kawo mun ba kada na kara ganinki a nan, idan ba haka ba kuma sai na mayar dake kwaɗo ko kunkuru". Yana maganar yana wani irin muzurai da ido, yadda kuka san kwarton da soja ya kama a gidansa, irin shi zai tsoritatan nan, ga idanun nasa jajir da su kamar mutun ya kwakwalesu ya jefar saboda muninsu, hancin nan nasa ba'a magana, a bage yake a saman fuskarsa kamar kan fanfo, ga shi bakin kirin kamar zunubi, bakinsa kamar waga. Kasancewar ta zo ne domin a kwance wannan aiki da hauwa ta yi wa baban Zee, sai ta ɗane zuciyarta, ta daure ta sassauta muryarta tare da ƙoƙarin kawar da ɓacin ranta ta fara magana a nutse. "Ni ba dukka wannan ne ya kawoni ba, aikin da ka yi wa mijina kawai nake son ka kwance shi kamar yadda ka yi". To kun san bokaye basu da sirri, dan haka sai ya ce mata. "Ni da Hauwa akwai amana a tsakaninmu, amma idan zaki bani abin da take bani sai na warware". Da sauri ta amsa mashi da. "E zan baka menene?". Ba wani ɓoye ɓoye bare kunya ya baje mata komai a faranti. Kanta zata bashi, dan shi ne abin da Hauwa take bashi yasa ya riƙe mata amana, har da wani ɗaurawa da cewa. "Ke kin ma fi Hauwa sura da kaya, kin ga da kin bani sai na warware aikin, kuma zan riƙe maki amana". Ni kuwa nace wani amana kuma? Na tabbata ita ma Hauwa hakan ya ce mata idan ta bada kanta zai riƙe mata amana, amma ga shi yanzu saboda yaga maman Zainab ta fi hauwa komai da komai har ya tonawa Hauwar asiri, kuma idan da maman Zainab zata bashi kan nata tsab zai iya kwance aikin nan da ya yi wa Hauwar, kun ga kuwa a nan ina amana fisabilillahi? Ko da yake duk aikin da aka ce maka ya saɓawa Allah da Manzonsa ai babu wani amana da tausayi a cikinsa face danasani da nadama maras amfani!!. Wani irin mahaukacin razana maman Zainab ta yi da jin maganganunsa, nan take ta ji wani irin jiri yana neman kwasanta, wa'iyyazubillah ta furta kusan sau uku. Wani irin tsinanne kallo ta fara bin bokan da shi, wani ƙazami da shi, ai wannan da ta haɗa shinfiɗa da shi gwara ta mutu, da wasu garmar hakwaransa da baya brush kamar na shanu. Wani irin muguwar tsanan Hauwa haɗe da baban Zainab ɗin ne dukka ya kamata, ji ta yi wlh zata iya hakura da baban Zainab har abada tun da ya haɗa shinfiɗa da Hauwa da ta sallamawa wannan ƙazamin la'anannen Allah kanta, waye ya sani ma ko yana ɗauke da wata cuta tun da ya nemeta hakan yana nufin ba da iya Hauwar kawai yake kwanciya ba, yana keta mutuncin mata da dama, daga gani halinsa ne, da wuya kuma idan bai da wata cutan. Wani irin ƙululun bakinciki ne ta gangaro mata har wuya, kanta dake sara mata tun ɗazun ne ya fara yi mata barazanar tarwatsewa, sam bata san lokacin da zafafan hawaye suka fara bin ƙuncinta ba, ita kanta bata san hawayen me take yi ba. Cikin kunar rai ta juya da sauri kamar zata kifa ta fice daga cikin wajen ba tare da ta sake ce mashi ko uppan ba. Unexpect wannan mai mashin ɗin da yake yi masu laɓe ya ganta a gabansa, bai yi tunanin zata juya tafito cikin ƙankanin lokaci haka ba, ya saki baki yana kallonsu kuma ya afka duniyar tunani a kan cewa kenan mata idan suka je wajen bokaye haka suke yi? Dama haka ake abin, bawan Allah bai taɓa gani ba sai yau, ya luluƙa duniyar tunani kwatsam ya ganta a gabansa ta fito. Cikin hanzari ya ɗaga jikinsa daga jikin dutsen ta bakin kofar kogon in da ya samu damar leƙan nasu. Ƴan kame kame ya fara yi irin na marasa gaskiya. Bata bi ta kansa ba ta yi saurin wucewa zata sauka kasan dutsen. A hanzarce ya rufa mata baya. Da kyar ta iya jiransa har yazo ya hau mashin ɗin ya tayar, kamar zata faɗi ƙasa zaboda jirin da take gani. Tsana da kyamar Hauwa da baban Zainab ne cike fal a ranta, bata da tabbacin cewa baban Zainab ɗin ya taɓa kwanciya da Hauwar, amma da yake zuciya bata da ƙashi sai ta ɗaurawa har da shi ma karan tsana. Kunna mashi mai mashin ɗin ya yi suka bar wajen, suka nufi hanyar da suka zo domin komawa, sai sake sake take yi a cikin ranta, tana ta tufka da warwara........... 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ 🏞️FOREST🏞️🕊️🌹 Sosai Kamran ya sha wahala wajen yawo a bakin wannan tekun domin neman hanya, sai dai kash bai iya samun hanyar da yake ganin e ya aminta da ita ba, ya samu hanyoyi da dama a wajen, sai dai duk yana ganin kamar zasu yi mashi wahalar bi, sannan yana ganin kamar ba za su ɓille mashi ba, domin kuwa dukka hanyoyin daji ne gaba daji baya, babu kamshi alamar gida ko motsin wata halittar ɗan adam, hakan yasa yake ganin kamar har yanzu bai samu hanyar da ta dace ya bi ba. Komawa ya yi wajensu Pretty jiki duk ya yi tsami saboda wahalar neman hanya, a kasale yake tafiya, yanayi yana tunanin mafita. Lokacin da ya koma wajen nasu Pretty tana barci, ita kuma Sweetie tana karatun husnul Muslim da kai ba tare da littafi ba. Kasancewar Prettynsa ta yi barci sai ya ji babu daɗin zaman wajen nasu, domin kuwa babu abokiyar rigimarsa, babu wanda zai tsokana ta yi mashi rigima ko kuka ya rarrasheta, hakan yasa ya ce da Sweetie bari ya je wajen mammarsa kada ta nemesa. Sam Sweetie bata so tafiyarsa ba, ta so su yi hira sosai, amma ina ba dama. Da okey ta amsa mashi kawai, daga jin yadda ta amsa mashi kuma kasan ba har cikin zuciyarta wannan okey ɗin yake ba, ta dai amsa ne kawai rai bai so ba. Miƙewa ya yi ya nufi hanyar fita. Yana tafiya yana waigo Pretty dake kwance, ji yake yi kamar ya mayar da yarinyar nan cikin cikinsa ko zai huta da irin kaunarta dake azalzalar zuciyarsa. Ita kuma Sweetie ji take yi kamar da sanya hannu ta buɗe idanunta ta fara gani domin ta ga mutumin da take jin tana kauna a duniya sama da komai nata a halin yanzu. Yana fitowa ya cikaro da Rocky ya dawo daga yawonsa. Bai kula shi ba yasa kai ya yi gaba, baya Rockyn ya rufa mashi suka cigaba da tafiya kamar yadda suka saba, a haka suka nufi gida wajen mamma. Pretty kuwa tana barci tana mafarkin Kamran ɗin, ita kuma Sweetie idanunta biyu tana tunaninsa, shi kuma yana tunanin Pretty tare da tunanin babansa da kuma yadda za'ayi ya samanwa Sweetie maganin idanun nan nata, yau ya ƙuduri niyar tambayar mamarsa maganin, in ta gaya mashi kuma tabbas ko a ina ne komai wahalar da zai sha wajen nemowa zai nemo mata, a cewarsa ya gaji da ganinta bata gani, so gara ya nemo mata maganin idanunta zu buɗe ko dan su rinƙa zuwa yawo a tare. Wani ɓangare na zuciyarsa kuma yana tunanin meyasa Mamma take ɓata rai sosai a duk lokacin da ya yi maganar addinin su Pretty? Wato a duk lokacin da ya yi mata wata kalma da ta danganci musulunci irin su Alhamdulillah da dai sauran word's da yake tsinta a bakin su Prettyn.......... 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 "Yah Jawad meyasa zamu ɓuya to?.....". Bata ƙarisa maganar ba ya yi saurin sanya tafin hannunsa ya rufe mata baki yana mai kallon cikin idonta, har yanzu basu dai'na sauke ajiyar zuciya ba daga shi har ita. Ƙura mashi ido ta yi tana jiran ta ji me zai ce, tana kuma mamakin meyasa suka ɓuya? Meyasa bai bari ta yi magana ba ya rufe mata baki. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 10/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________48🔥 KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 Ƙura mashi ido ta yi tana jiran ta ji me zai ce, tana kuma mamakin meyasa suka ɓuya? Meyasa bai bari ta yi magana ba ya rufe mata baki. Matsowa kusa da ita sosai ya yi, cikin murya wadda za'a iya kiransa da kamar raɗa, in a low sosai kenan ya fara magana. "Kada ki sake yin magana kin ji ko?". Ya yi maganar tare da zame hannunsa daga saman bakin nata. Sai binta da wani irin kallo yake yi. Ƙasa sosai ita ma ta yi da murya kamar yadda ya yi. "To Yah Jawad meyasa muka ɓuya?". Bin ɗan bakin nata da kallo ya yi kafin ya ce. "Because of Akka mana, kin san wannan tsohuwa da bala'i, yanzu sai ta samun hawan jini, so stay quiet har sai ta tafi zamu fita, don't let anyone to know abin da ya faru". "Har da Auta?". Ta faɗa tana ɗan zaro ido. Hannu ya kai ya ɗan matse ɗan bakin nan nata har sai da ta ce wash. "If i say don't tell someone anything about me and you doesn't means har da Auta a ciki, i know kece Auta, sannan Auta ce ke, dan haka ki dai'na raba kanki da ita, coz nasan ma ko na ce kada ki gaya mata sai kin faɗa ɗin, so is better na ce ita kam a gaya mata". Yana magana yana ɗan wurga mata hararar wasa. Zata yi magana suka ji motsin mutun yana tinkaro dressing room ɗin wanda ko basu ga waye bane sun san King ne, dan sun san ya shiga wanka. Jawad ba zai damu sosai ba idan kin ya gansu, saboda shi da daddyn nasa kun san yadda suke ai, gwara mashi King ya yi ta ganinsu a haka sau dubu a kan Akka, Akka ce matsalarsa shi. Cikin hanzari ya sanya hannu ya toshe mata baki dan kada ta yi maganar, sannan ya fara matsawa a hankali kusa da ita, ita kuma ta fara ja da baya a hankali har suka matsa daga wajen glass ɗin suka ɓuya a bayan wani shirgegen drawer dake shaƙe tab da haɗaɗɗu kuma tsadaddun King shoes kala kala. Cikin nutsuwa King ya shigo room ɗin waist ɗinsa na'a ɗaure da wata tsadaddiyar towel sky blue mai haske, yana shigowa cikin kuma yana magana a in da yake ce da Akka ta jira su je a tare, bari ya sanya kaya five minutes yana zuwa. Mannuwa da jikin bangon wajen Chuchun ta yi, a hankali ya zame hannunsa daga saman bakin nata, sannan ya kara matsowa kusa da ita sosai, ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa a in da suka bawa King baya kenan. Cikin nutsuwa shi kuma ya fara shirinsa tare da fitar da kayan da zai sa, sai dai yana yi yana ɗan yin sauri saboda ya tsayar da Akka a kan ta jirasa. Sosai Yah Jawad ya kura mata ido, ita kuma hankalinta na can wajen tunanin daddyn nata dake a cikin room ɗin, dan ma Allah yasa room ɗin yana da matuƙar girma, sannan wajen jera takalmar sakawarsa har drawer kala uku ne, kuma ba'a waje guda suke ba, dukkansu suna da ɓangarori daban daban, haka shi ma glass na jera watch ɗin nasa ma manya manya ne har guda uku, dukkansu kuma a shaƙe suke da tsadaddun agoguna kala kala, mafiya yawancin komai da yake cikin room ɗin guda uku uku ne, da alama wannan tsarin su Momma ne, shi kuma dan ya yi adalci ya biye masu kowacce ta jera nata kalar abubuwan da take buƙata ya rinƙa yi mata kwalliya da shi, ranar da yake wajen Momma sai ta shirya shi da kalar kayanta da ta sanya aka shirya mashi, haka idan yana ɗakin su mama kenan, yana ƙoƙarin kamanta adalci kam, shi ne yasa komai nasa uku uku ne kala daban daban, kowacce da kalarta, kuma kowacce a ranarta duk kalar da ta zaɓa mashi baya reject koda baya son wannan kalar, dan zaman lafiya, yana hakuri ya nuna yana matuƙar so ya kuma yi amfani da shi fuska ba yabo kuma ba fallasa!!. Shiru ya ɗan dakata daga ƙoƙarin zura ash color arab jallabiyarsa da yake ƙoƙarin yi, kunnuwansa ne suka jiyo mashi kamar alamar motsi a cikin room ɗin. Ƴan waige waige ya fara yi da mamaki fal a saman fuskarsa. Jin haka yasa Yah Jawad ɗin ya ƙara matsawa kusa da ita sosai ta yadda har suna iya jiyo sautin numfashin juna, dan gudun kada King ya gansu, still idanunsa yana a kan face ɗinta ya kasa kawar da kallonsa, ɗan rage gudun sautin fitar numfashinsa ya yi ta hanyar ɗan rike numfashin da yake yi kafin daga baya ya ɗan saki a hankali, duk gudun King ya gansu ne, yanzu sun ji ya fara waige waige dan yana ɗan jin motsi, so sun san zai iya ganosu, kuma fitar sautin numfashin a wajen da ya kasance babu hayaniya yana bada sauti mai ɗan karfi da har mutun zai iya ji kamar motsin wani abin!. Ganin bai ga alamar komai bane yasa ya cigaba da yin shirinsa cikin natsuwa. Daga karshe dai jawota jikinsa mai gabaɗaya ya yi tare da rage tsawonsa kaɗan, sannan ya sunkuyo da kansa izuwa kunenta, cikin raɗa ya ce mata. "Ki rage sautin fitar numfashinki, ki rinƙa sakin numfashin a hankali hankali......". Still wannan ɗan magana da ya yi yasa King ya sake jin alamar motsi a karo na biyu, a lokacin kuma yana sanya alkyabba a saman jallabiyar jikinsa. Dakatawa ya yi shiru, cus cus ya ji yo kamar ɓera na fasa ledar indomie, mamaki ne ta kara bayyana sosai a saman fuskarsa a in da ya fara waige waige a karo na biyu, sai kuma ya ajiye rawanin da ke hannunsa a saman wani haɗaɗɗen show glass dake shake da hatiman masarautar wadda suke dukka iri guda ne masu kan zaki kenan. Fara ƴan dube dube ya yi ko zai gano ta ina yake jiyo wannan ɗan motsin. Jin ya zo ta kusa da drawer da suke ɗin ne yasa Jawad ɗin ya kara mannata da jikinsa sosai suka yi wani tsit kamar babu wata halitta mai rai a wajen. Yan dube dubensa King ya gama yi tsab, sannan ya juya ya koma wajen da yake shirinsa. A hanzarce ya ƙarisa shirin dan Akka na jiransa kuma ya ɓata lokaci wajen tsayawa da ya yi ta yi dan jin motsin da ya yi, dan haka sai ya ƙarisa shirin a hanzarce ya fice daga room ɗin. Yana fita a tare suka sauke wani irin nauyayyar ajiyar zuciya, kara ƙanƙameta ya yi yana fitar da numfashi da sauri da sauri saboda rike numfashin nasa da ya yi ta yi dan kada King ya gansu. Ita ma da sauri sauri take sakin numfashin tata. Hannunsa ɗaya ya ɗaura a saman bayanta dai'dai tsakiya. "My Jannat mun tsalleke rijiya da baya, da Akka ko daddy sun ganmu am in trouble wlh". Ya faɗa da wata kasalalliyar murya kamar mai jin barci. "To Yah Jawad meyasa kake gudun su ganmu? Ai naga sun saba ganinmu a tare, bare ma shi daddy da a can baya kai da Yah Jaish kuke zuwa cin abincin a dining room ai kullum suna ganinmu a dining room ɗin a tare ko?....." Ɗaga kansa sama ya yi tare da jinginta da jikin drawer, a wahalce ya ce. "Banda irin wannan kallon kam, ai idan suka ganmmu a irin wannan yanayi akwai matsala, musamman Akka sai ta saka mun hawan jini...." "To meyasa?". Ta tambaya da mamaki sosai a saman face ɗinta, ta kuma yi maganar tana ɗan ɗago kanta daga saman chest ɗin nasa. Slowly ya sauƙo da kansa daga ɗagata da ya yi, ya zamana suna fuskantar juna sosai saboda ta ɗan ɗago kanta ita ma. Kura mata idanu ya yi kamar wani ya ce zai kwace mashi ita. A hankali ya motsa lips ɗinsa wajen furta. "Kina son sanin dalili?". Da sauri ta gyaɗa mashi kai haɗi da cewa e. Rankwafo da face nasa dab da tata ya yi, ɓangare ɗaya na zuciyarsa tana azalzalarsa da ya faɗa mata kawai, ya furta mata saboda yana sonta ne, ɗayan ɓangaren kuma yana ƙoƙarin hana shi yin hakan ne ta hanyar bijiro mashi da tunanin cewa zata rai'na shi, zakuma ya samu matsala da Jaish da dai sauran tunani marassa kan gado. "Yah Jawad ka faɗamun mana". Ta katse mashi tunanin da yake yi. Ji yake yi kamar ya yi kissing ɗinta idan tana magana a kusa da shi, kuma ji yake yi kawai ya daure ya gaya mata yana sonta. Amma ina ko kusa ko alama ba zai iya yin hakan ba. Nisawa ya yi tare da sumbatar goshinta, sannan ya ɗan ja baya kaɗan tare da raba jikinsu. "Wani lokaci zan gaya maki, but now come let us go". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta cikin nasa da nufin su fice daga room ɗin. Ba musu ta bi bayansa, hankalinta yanzu gabaɗaya ya karkata izuwa room ɗinta, tana son ta koma can ta je ta cigaba da yin waya da Yah Rizwan wanda yanzu shi ne tauraronsa yake haskawa a idanunta tun daren jiya, ya tsarata ne da wasu shegun love word's, shi da yake cewa Jawad a yanzu ba shi da lokacin mace, amma kuma ashe ya iya zafafan kalamai masu tsayawa a rai, ko daga ina ya koyo? Allah masani sai kuma shiɗin haɗi da alkhalamina........💘 A cikin room na King suka tsaya, hannun nata ya saki tare da juyowa gareta da kyau. Zuba mata idanun ya yi na ƴan mintocin da basu wuci biyu ba, kafin ya nisa tare da cewa. "Jeki room naki". Da sauri ta juya zata ta fi, har ta kai tsakiyar room ɗin kamar a mafarki ta tsinkayo muryar can ƙasa ƙasa ya furta sunanta. Da sauri ta juyo tare da dakatawa daga tafiyar da take yi. Siririn murmushi ya sakar mata mai matuƙar ƙayatarwa wadda idan aka yi maka shi dole ka mayar da martani ko kana so ko baka so, dan time ɗin da martanin zai bayyana a saman fuskarka ma ba zaka sani ba sai dai kawai ka ji ka yi. Ita ma kuwa hakance ta faru da ita, sam bata san lokacin da ta dawo mashi da martanin nata siririn murmushin wadda ya kara jefa shi cikin yanayi ba. "Ki kula sosai my sister, bana son dai mu rabu, amma ki je ni zan je wajen Jaish tun jiya yake nemana ban samu mun haɗu ba". Ya faɗa yana kallon cikin idonta. "Tom Yah Jawad zan kula sosai". Ta yi maganar tare da juyawa, yanzu tana jin Yah Jawad ɗin nan nata a matsayi na musamman a cikin zuciyarta, haka kawai take jin daɗin ganin fuskarsa musamman idan yana ɗan murmushi. Zuciyarta cike tab da tunanin Yah Rizwan ɗinta ta nufi kofar fita. Tsareta da kallo Jawad ya yi babu ko kyaftawa, ita kuma tana tafiya tana tunanin zafafan kalamai Rizwan bare ma yadda ya rinƙa yabon kyanta tare da nuna mata ya mace a kanta, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, tana son taga ana nuna mata so ana kuma yabon duk abin da ta yi, ta wannan hanya Rizwan ya yi nasarar sace zuciyarta, kuma a nan ne suka sha banban da Jawad, shi Jawad koda yaushe sai faɗa ya iya yi mata a kan kada ta yi kaza ko idan ta yi kaza sai ya bata punishment, amma shi Rizwan jiya da ta ce mashi zata je wajen Momma da daddare, cikin nutsuwa ya tambayeta da kayan barcin zata fita? Da e ta amsa mashi, ƙasa ya kara yi da murya tare da kara nutsu kafin ya ce mata a'a shi bai yarda ba yana da kishi sosai, ta sanya hijabi har ƙasa, kuma me zata je yi a wajen Momma da daddaren nan? Gaya mashi ta yi zata je ɗebo turaruka. A sanyayye ya ce mata ta bari sai da safe mana, shi yanzu gaskiya ba zai iya hakura da hiran nan nasu ko na minti ɗaya ba, bai shirya dai'na jin zazzaƙar voice ɗinta ba, ta yi hakuri ko dan soyayyarsu ta bari sai zuwa da safe. Cikin rarrashi da nuna soyayya ya yi mata magana ba kamar yadda Jawad ya ce idan ta sake fitowa da kayan barci sai sun ɓata kuma ya bata punishment ba, wannan shi ne banbancin da yake a tsakaninsu, Rizwan da daɗaɗan kalamai yake amfani wajen hanata yin abu. Sai da ta kurewa kallonsa da kamar minti biyu sannan ya rufa mata baya, kai tsaye part ɗin Jaish ya nufa. Ga mamakinsa sai ya ga ɗan uwan nasa sai shirga aikin shiri yake yi alamar zai yi tafiya. "Travel without telling me, why? And where are you going?". Ya yi maganar tare da zama a gefen gado idanunsa na'a kan ɗan uwan nasa babu ko kyaftawa. Sai da ya kammala zuba kayayyakin da yake zubawa a cikin haɗaɗɗiyar echolac ɗinsa mai bala'in tsada kafin ya juyo da kallonsa izuwa kan ɗan uwan nasa. "How do you expect me to tell you that I want to go to somewhere bayan gabaɗaya you're totally useless now, wai ma ni this two day's what's wrong with you? Where are you going that very important better than my issues?......" Katse shi ya yi da cewa. "Woooo zaka fara halin naka ko Jaish? To wai ni mema na yi ne? Am with you bro, i didn't give anyone my attention or my time, kawai dai lokacin haɗuwarmu mu tattauna a kan issues ɗin naka ne bai yi ba........". Hararar da Jaish ɗin ya wurga mashi ne yasa ya dakata da yin maganar yana son fahimtar wani abu, shin da gaske ran ɗan uwan nasa ya ɓaci ne? Ko dai wasan da suka saba yi ne?. "Since day before yesterday nake binka a kan kazo mu yi magana, amma you're always try to show me you're busy, you don't have my time, you're doing something or you go to somewhere, you're not around and some miscellaneous excuse". Cikin zolaya ya ce da Jaish ɗin. "Meyasa ba zaka tambayi uzurin nawa ba? Do you know maybe I fall in love with someone ne yasa am going up and down since that time you said?". Cigaba da kwaso wasu abubuwan buƙatarsa da zai buƙata ya yi yana zubawa a cikin echolac ɗin nasa ba tare da ya sake bi ta kan Jawad ɗin ba. Ganin hakan yasa shi Jawad ɗin ya ce bari ya janyo attention ɗinsa ko baya so, dan haka sai ya ce. "I think fa auren gida ma zan yi, dole na dawo cikin kannena na sami mata, bari mu gani wacece zata ɗan dace dani...." Still dai Jaish bai kula shi ba, sai harkar gabansa yake yi cikin zafi zafi. Shiru ya ɗan ɗaga kansa sama irin mai tunanin nan, yana tunanin abin da zai cewa Jaish ɗin. Can kuma sai ya sauko da kan nasa haɗe da kallonsa a kan ɗan uwan nasa. "I think Jannat zata dace dani ko my blood bro?". A wani irin hanzarce Jaish ɗin ya ɗago da idanunsa izuwa kan shi. Dariya ce ta so kubce mashi saboda yadda Jaish ɗin ya zaro ido, amma sai ya danne ya ɗagawa Jaish ɗin gera guda alamar ya ne Jannat ɗin ta yi ko?. "A'a ba Jannat ba, cewa zaka yi dai ka gaji da kallona da mutunci ne kawai a cikin gidan nan, ai gara ka ja mutuncin nawa a kan titi sai ka fi jin daɗi, please get out from my side ma, am very very angry wlh, I don't want to talk to much, idan ka matsa mun kuma Allah you know the rest, i will make you regret". Yana magana yana banka mashi harara da waɗan nan idanun nasa na gado wadda da ka gansu kasan yes yaran Momma ne ba tambaya, dan ita idanun yaranta sun sha banban da na kowa a gidan, sun fi na kowa dara dara a gidan, saboda ita da King ban san waye za'a ce ya fi wani manyan manyan kyawawan ido ba, da yake dai shi da ita duk tushe ɗaya ne sai suka gaji idon daga wajensu King Badeen. Harararsa Jawad ɗin ma ya fara yi kafin ya ɗaura da cewa. "I can't go anywhere, wai da kake ce mun baka son yin magana sosai ni zaka yi wa iskanci? Kaga malam ni ka bar dukka wannan zance let's talk serious, bar wasa, what's going on? What's wrong with you? I know ban kyauta maka ba, amma ka sani jiya wlh naso zuwa mu yi magana, amma sai na sha'afa gabaɗaya da zancen kace nazo mu yi magana, am sorry about that..." Wani irin kallo Jaish ɗin ya wurga mashi kafin ya janyo zip ɗin echolac ɗin ya rufeta tare da cewa. "Bani da mahimmanci a gabanka ne yasa ma zaka sha'afa da zancena". "Kai bro, ni ban san kalarka ba, gaka da saurin fushi, gaka kuma da balai'n kunya, sannan idan ka yi fushi baka sauƙowa da wuri, ayi ta yin magiya amma duk a banza sai time da ka ga dama kake saukowa, ga zuciyar bala'i, kuma a haka wai baka son haɗa ido da mutane saboda kunya, yanzu na gano ba kunya bane ne yake damunka tsantsar rashin kunya ne yake damunka, ni mu bar wasa please, a ƙage nake da na ji me yake damun ɗan uwana, if not zuciyata zata buga". Ya kai maganarsa ta karshen nan cikin serious babu wasa. Bayan harara babu abin da Jaish ɗin ya bisa da shi, sannan ya zauna a gefensa. In short ya bashi labarin abin da yake faruwa da kuma tafiyar da zai yi, daga karshe ya rufe mashi da cewa kada ya gayawa kowa ya yi wannan tafiya har da Momma, dan ba zai wuce kwana ɗaya ba, gobe zai dawo. Sosai Jawad ɗin ya yi mashi fatan alkhari tare da addu'oi masu karfi. Cike da son ɗan uwan nasa ya amsa da amin. Daga haka suka shiga hirar duniya har zuwa lokacin da jirgin Jaish ɗin zai tashi. Kafin ya tafi zuwa airport sai da ya je cikin dabara ya ga Momma, sannan ya je wajen King, daga haka ya nufi in da Auta take, dan ba zai iya tafiya ba tare da ya sanyata a cikin idanunsa ba. Sosai ya tsareta da idanu kamar wadda yake yi mata kallon bankwana, har sai da ta tambaye shi lafiya? A lokacin kuma Gimbiya Chuchu tana kwance ta shige cikin bargo tana waya da Yah Rizwan, Autar tana kwance tana fuskantar kofar shigowa tana latsa wayar Yah Jawad da ya bari a wajensu. Lafiya lou ya amsa mata da shi kafin ya buɗe mata hannu a kan ta zo. Da sauri ta diro ƙasa daga saman gadon ta tafi ta faɗa jikinsa tana murmushi, duk wannan bidiri da ake yi Chuchun bata da labari, hira ya yi daɗi ga shi tana ƙule a cikin bargo ne yasa sam bata jiyo komai sai kalman yayan nata da yake zazzaga mata tana kara macewa haɗe da narke mashi. Sosai ya rungumi Autar a jikinsa yana jin tsantsar kaunar ƴar uwar nan tasa, ita kaɗai suke da shi mace a ɗakinsu, suna ji da ita kamar me, da kyar ya iya raba jikinsa da nata sannan ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba. Ta ɗan yi mamakin ganin hakan da ya yi, amma bata kawo komai a ranta ba ta koma cikin ɗakin tare da hayewa gado ta kwanta. A wannan rana dai Jaish ya bar kasar ba tare da sanin kowa ba sai Jawad ɗin da yake tamkar jinin jikinsa, kun san shakuwar da take a tsakaninsu tun suna yara. Ko airport ma Jawad ɗin ne ya kaisa a sirrance, sun jima sosai a lokacin da suka yi hugged na juna kafin jirgin ya ɗaga, ba yau bane farau na su yi tafiya ba tare da sanin kowa ba, su je su dawo, amma su kansu yau ji suke yi kamar waɗan da zasu yi rabuwa ta har abada. Jiki ba kwari Jawad ya juya ya dawo gida, duk sai ya ji wani iri, yana tukin mota yana tunanin Jaish ɗin kamar yau suka saba rabuwa. Yana dawowa gida room ɗinsa ya shige ya yi kwanciyarsa dan ya ɗan huta. Da misalin karfe 8 na dare gabaɗayansu sun haɗu a saman table a dining room domin cin abinci, Mama dai tana can room nata ta sha allurar barci, saboda azaban da take ji a jikinta na raɗaɗɗin cizon kwarin nan da kuma tsakanin kaikayi da wajen yake yi mata, ga shi babu halin sosawa, hakan yasa da kanta ta buƙaci ayi mata alluran barci ko zata huta da azaban!. Kasancewar yau Jaish baya nan sai Jawad ya halarci dining room ɗin, ba zai iya cin abinci shi kaɗai ba, dama kun san a tare da Jaish ake kai masu nasu part ɗin ɗaya daga cikinsu, so yau baya nan sai ya ji gara mashi ya fito su haɗu a dining room ɗin ko ya rage kewar ɗan uwan nasa. Sosai King ya yi mamakin ganinsa a room ɗin, bai yi nauyin bakin tambayarsa yau kuma a nan ya ga damar cin abincin ne? Da e kawai ya amsa mashi. Sosai King ya lura da yadda jikinsa yake a mace, ya yi wani sukuku da shi, nan ma bai yi nauyin bakin tambayarsa ko bashi da lafiya bane yake yi kamar wani mai jin barci?. Sam basu kawo a ransu cewa Jaish baya gidan ba, dan kowa yana da ra'ayin zuwa in da yake so ya ci abinci, sun yi zaton Jaish ɗin yana ɗakinsa. A'a lafiyarsa lou ya amsa da shi. Shiru King ya kyalesa da nufin idan sun gama cin abinci sai ya tasashi gaba ya gaya mashi me yake damunsa? Dan dai ga damuwa kam nan karara a saman fuskarsa. Kowa ya hallara a room ɗin ban da Gimbiya Chuchu dake cikin room ɗinta tana ta aikin zuba soyayya da Yah Rizwan, waya suke ta yi ba kakkautawa, ya gaya mata gobe zai biyo su Ramish domin kawai ya zo ya ganta, sai daɗi take ji. Da alama Rizwan ya iya soyayya sosai, sai zuba uban murmushi take yi fuska cike fal da annuri. Allah sarki shi kuma Yah Jawad yana can daning room yana tura abinci kamar dole yana fama da kewarta da kuma tunanin Jaish. Da dai ya gaji sai ya ce da Auta. "Auta ina Jannat ne?". Ya tambayi in da take ne kuma domin yana da buƙatar ta zo nan ko zai rage kewa da tsananin tunanin ɗan uwan nasa da ya tsaya mashi a rai sosai, bai san meyasa ya damu har haka ba. "Aunty Chuchu tana ɗakinta". Auta ta bashi amsa. King ne ya ce. "Meyasa bata fito cin abinci ba?". Still dai Autar ce ta bashi amsa, domin babu wanda zai iya ce maka yasan halin da Chuchu take ciki a gidan biyun Autar. "Daddy nima ban sani ba, ina ganin kamar bata jin yunwa ne ko kila sai ta yi shirin kwanciya zata sha wani abin mara nauyi kamar shekaran jiya da jiya". Jawad ne ya ce. "Go and call her for me". Ya yi maganar ba zato ba tsammani yana kawar da kallonsa daga kan Autar suka haɗa ido da King. Wani irin kallo King ɗin ya jefa mashi wanda ya ɗan sanya shi sakin siririn murmushi. Hannunsa ɗaya ya kai ya ɗan shafa sumar kansa yana cigaba da ɗan murmushi. Hararar wasa King ya wurga mashi yana mai cigaba da kai abinci bakinsa. Sai kallonsu a sace momma take yi, ta fahimci akwai wani abin dai da King bai gaya mata ba dan gane da Jawad, dan yadda yake binsa da irin wannan kallo akwai wata a ƙasa. Shi kuma Yah Jawad sai ya kawar da kallonsa daga kan King ɗin ya cigaba da cusa abincinsa cikin baki wanda yake jinsa kamar magani saboda rashin daɗi. Miƙewa Auta ta yi ta nufi fita daga room ɗin. Ko da ta je manne da waya ta isko Chuchu, sai zuba hira suke yi, tana ta kashe Yah Rizwan da shagwaɓa, soyayya ta yi daɗi tama mance da abinci. Kiranta Autar ta yi sannan ta juya bata tsaya ta jirata ba, dan yunwa take ji Allah ya gani. "Yah Rizwan daddy na kirana in je in ci abinci, ka bari sai na dawo ko?". Daga other side ɗin ya amsa mata da. "Bari na zo to na baki a baki ko? Dan bana son ki sha wahala, da akwai yadda zan yi in tauna maki ma sai na tauna maki". Wani irin sihirtatcen murmushi ta saki kafin ta bashi amsa da. "Kai Yah Rizwan, ai zan ji kunyar su daddy idan ka ce zaka bani abinci a baki, ba zan iya ci ba, har da Akka fa da su Mummy dukka a wajen, kuma sai ka iya bani a baki ba zaka ji kunyarsu ba?". Nisawa ya ɗan yi. "Wacece kuma Akka? Ina ruwana da ita? Zan dai ɗan ji kunyar Mummy, amma banda daddy". (Da alama Akka fa dukka jikokinta ne basu kaunarta 😅 kun ji Rizwan da walaƙanci wai wacece kuma Akka😅 ko da yake wannan tsohuwa zama da ita sai irinsu Guyson ne za su iya, wato masu mugu mugun hakuri sosai kenan 😅 babu ruwana dai ni kam kada ace na ce, to ban ce ba.🌝) Ɗan zaro idanu ta yi na jin ya ce wacece kuma Akka da kuma ba zai ji kunyar daddy ba sai Mummynta. "Yah Rizwan ni kuma na fi jin kunyar daddy a kan Mummy fa". Ta faɗa tana sauƙowa ƙasa daga saman gadon. "To bana son gimbiyata ta zauna da yunwa, jeki ki ci abinci ki ƙoshi sosai, hirarmu ba zata kare ba, idan kin dawo zan baki wani labari kin ji ko?". Da okey ta amsa mashi tana ƙoƙarin katse kirar ta tsinkayo muryar can ƙasa ƙasa yana faɗin. "I love u my sister, ki kula mun da kanki, i will going to miss this your sweet voice wadda idan kina magana yana sanya na rinƙa jin mamar barci zai ɗaukeni, bana........" Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon shigowar Ramish da Bilal cikin room ɗin nasa. Ita kuwa jin ya dagata yasa ta mayar mashi da kalmar i love u too tare da katse kiran ta nufi waje. Kai tsaye dining room ta nufa. A saman kujera kusa da Auta ta zauna, ya zama suna fuskantar juna ita da Yah Jawad ɗin, shi kuma daddy da kujerarsa take a gaba yana iya ganin fuskar kowa, a side ɗin kujerarsa ce kawai a wajen. "Meya hanaki fitowa ki ci abinci?". Jawad ya tareta da wannan tambayar. Gaisuwa ta fara ɗagawa daddyn nasu, bayan ya amsa ta gaishe Akka sannan su Momma haɗe da Akka, sannan ta bawa Jawad ɗin amsa da tana waya ne, da yake bata iya karya ba, amma bata gaya mashi da waye take yin wayar ba. Bayan ta bashi amsarsa ne ta ɗagawa su Sarina gaisuwa a matsayinsu na sister ɗinta. Cikin nutsuwa suke cin abinci. Kuyanga Zubaida ta zubawa Chuchun abin da take buƙata. Room ɗin ya yi tsit kamar ba mutane, sai sautin spoon ɗai ɗai zaka ji yana tashi. A hankali Chuchun ta ɗauki cup mai shake da pina colada zata kai ɗan bakinta, tana jin ra'ayin shansa kaɗan ba dayawa ba. Bata ƙarisa kai shi bakin nata ba ta ɗan yi ƴar ƙara tare da sakin kofin ya faɗi a saman table ɗin. A hanzarce gabaɗaya kowa dake saman dining ɗin ya ɗago da kansa tare da kai kallonsa kanta. Auta ta riga kowa tambayarta lafiya me ya sameta?. Autar bata rufe baki ba King ya jefo nashi tambayar. Nan take kowa ya fara jefo nasa tambayar, sun tsura mata idanu suna jiran amsa. A hankali ta ɗan ɗago idanunta ta saci kallon Jawad da suke fuskantar juna, ya yi wani yin ƙasa da kai kamar babu shi a room ɗin. Bin in da take kallo da kallo King ya yi, ganin Jawad take kallo yasa ya cigaba da cin abincinsa ya fita shirginsu, dan yasan in ya biye masu ma shi zai ji kunya a banza. Su Momma sai tambayarta suke yi ta ƙasa yin magana, kowa ya ruɗe yana ta cewa lafiya kuwa? Amma ina ta ƙasa magana. King ne ya ce. "Wai ku ku rabu da ita mana, Zubaida ki sake zuba mata wani pina colada domin ta sha dan naga shi take ra'ayi". A hanzarce kuyanga Zubaida ta zo ta fara kwashe wanda ya zube ta gyara wajen, sannan ta zuba mata wani ta turo mata shi gabanta. Ɗauka ta yi tana ta kallon fuskar yayan nata. Shi kuwa kamar babu shi a wajen. Tana ƙoƙarin kai cup ɗin bakinta a karo na biyu ya sake yi mata abin da ya yi mata ɗazun yasa ta zubar da wancan pina ɗin, ba tare da ya ɗago ya kalleta ba. Ba komai yake yi mata ba face babbar yatsar kafarsa yake zurowa ta ƙasar table ɗin yana ɗan yi mata kamar tafiyar tsutsa a kafafunta, da yake doguwar riga ce a jikinta, ta ƙasar rigar yake zura kafar tasa yana taɓa mata tata. To da ya yi mata na farko tsoratata ya yi, dan bata yi expect na jin hakan ba, ta tsorata. Yanzu ma a hankali ya sake zuro kafar tasa ya fara yi mata kamar ɗazun. Still yanzu ma ta tsorita, sai dai bai kai tsoron da ta ji ɗazun ba, ɗan lumshe idanunta ta yi tare da kai cup ɗin ɗan bakinta. Bata cire cup ɗin daga bakin nata ba ta waro idanun nata a saman fuskarsa, a lokacin shi ma ya zuba mata idanu yana kallonta, wani irin kyau ta yi mashi lokacin da ta lumshe idanun nata, sai ya ji ta gama tafiya da shi mai gabaɗaya, da babu kowa a room ɗin ba abin da zai hana shi rungumota. Cigaba da yi mata tafiyar tsutsa a kafar tata ya yi yana mai cigaba da kallonta, ita ma tana shan pina ɗinta tana kallonsa tana ɗan murmushi. A hankali ya gangaro da kafar tasa izuwa dai'dai sai tin tata, sannan ya sanya ƴatsun kafafun nasa ya riƙo nata babbar yatsar kafar yana wasa da shi. Duk abin da suke yi King yana kallonsu, amma ya cigaba da cin abincinsa tamkar bai ga komai ba, tunanin abin da zai yi kawai yake yi a ransa, tunanin kalar hukuncin da zai yanke masu yake yi. Matse mata babbar yatsar kafar tata ya yi a cikin tsakiyar nashi yatsun. Har sai da ta ɗan yamutse fuska alamar zafi, ɗan turo mashi baki ta yi tare da ajiye cup ɗin pinan nata, kamar zata sanya mashi kukan shagwaɓa. Ganin hakan yasa ya ɗan sakar mata ƴatsun nata, yana saki ita ma tasa nata wai zata kamo nashin ta matse ya ji idan da daɗi. Amma ina ƴan yatsunta ba za su iya kama na shi ba, ya yi mata girma. Kamar zata yi kuka take binsa da kallo tare da turo baki. Wani siririn cool murmushi ya sakar mata wanda ya sanyata sauke ajiyar zuciya, sannan ya kashe mata ido ɗaya. Plate ɗin abinci da kuyanga Zubaida ta zuba mata ta jawo ta fara ci tana sakin murmushi, tana jin daɗin kasancewa da Yah Jawad a yanzu, saboda yana sakar mata fuska kuma yana mata wasa sosai, so tana jin daɗin kasancewa a tare da shi sosai da sosai. Bayan sun kammala cin abincin ne ya janye kafarsa daga kusa da tata, a hankali ya miƙe tsaye. "Jannat ki kawo mun wayata da na baki room ɗina". Yana maganar unexpect again kallonsa ta sauka a kan King, tun ma daddyn nasu bai yi wani yunƙurin ba ya sakar mashi murmushi tare da sa kai da sauri ya wuce. Sai dai kafin ya fita muryar King ɗin ta daki dodon kunnuwansa da cewa. "Ka sameni a room ɗina yanzu Jawad". Da okey kawai ya amsa sannan ya fice. Da ɗaiɗai da ɗaiɗai kowa ya watse a room ɗin. Akka tana shigowa cikin room ɗinta wayarta dake saman bed ya fara ruri. A hanzarce ta ƙarisa ta kai mashi agaji. Picking ta yi tare da hayewa saman gadon mai gabaɗaya. Daga can ɓangaren Rizwan ya fara tsantsara mata sallama tare da ɗaga mata gaisuwa. Sai da ta zage shi kafin ta amsa, wai yau kuma wani munafurcin yasa ya kirata? Dan rabon shi da kiranta tun last year sallah da ya kirata ya yi mata happy sallah, to yanzu kuma gulmar me yasa ya kirata?. Hakurin ya fara bata tare da rarrashi yana gaya mata aiki ne ya yi mashi yawa. Tatas ta zage shi daga shi har su Ramish ɗin gabaɗaya kafin ta saurare shi, Akka akwai dirama tsohuwar nan. Cikin zumuɗi ya sanar da ita dalilin kirata, ya kira ne ya sanar da ita ya samu mata kuma ba kowa bace face Chuchu, dan haka ta taya shi kafin ya zo. Wani irin matuƙa fari tas ɗin farinciki ne ya mamaye mata cikin zuciya. Haƙiƙa ta ji daɗi kuma ta yi murna, amma sai ta ɓoye murnar tata, ta fara zazzaga mashi masifa a kan ai dama tasan yanzu ma buƙatar kansa ne yasa ya kirata, to dan haka ya sani ba zata bashi Chuchu ba, kuma dai yasan ita ce mai zartar da hukuncin a kan komai. Lallaɓata ya fara yi yana magiya tare da marairace murya, yasan Akka ita ce nan take da iko da su da iyayensu, yasan idan ta bashi Chuchun to fa babu uban da ya isa ya hana, haka zalika idan ta hana shi, wannan dalilin ma yasa ya biyo ta wajenta kai tsaye bai je wajen daddy ba, dan ko ya je ga daddyn ma zai ce mashi sai abin da Akka ta zartar ne, so shiyasa ya fara bi ta wajenta, kuma Mammaiensu ce ta bashi wannan shawara, ta ce kai tsaye ya tunkari Akka, kuma kada ya wani ɓata lokaci wajen jira, ya yi saurin tunkararta ya gaya mata, hakan yasa ya gaya mata ɗin......... Lallai da gaske Mammie ta shirya raba Jawad da soyayyar Chuchu karfi da ya ji, domin kuwa hanyar da ta biyo mai karfi ne wanda ya fi na Jawad karfi, tun da Rizwan ya gayawa Akka shikenan kuma, Akkar zata tambayi Chuchun tana son yayan nata ne ko bata sonsa, idan har ta amsa da tana son shi fa shikenan babu wanda ya isa ya sa a fasa wannan aure sai mutuwa sai kuma wani ikon na Allah. Ku ma dai kun san Chuchu dai tana son yayan nata, dan haka da e tana son shi zata amsa. Akwai cakwakiya ba kaɗan ba, akwai tashin hankali. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼 ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥 Nutsuwa sosai Leesharh ta yi tana sauraron abin da yake faɗa. Daga yadda yake fitar da word's ɗinsa kai kasan nutsatsen mutun ne mai ji da izza haɗe da class, ba karya jinin King Zuhair yana gudana a jikinsa. Magana yake yi a kan lallai a cikin daren nan dole zasu yi wannan meeting ɗin, domin gobe da safe za su wuce ƙasar Tunisia, so ya zama dole a daren nan su haɗu, umarni ya baiwa wanda suke yin wayar da shi a kan lallai karfe takwas ya samesu a wani katafaren luxurious guests house ɗinsa. Ba taro ne da zasu yi a ma'aikatarsu, taro ne na team guda ba na gabaɗaya special weapons and tactics ba, manya manyan zakarun gurayen mazan dake cikin Team na Ramish ɗin su sha biyu ne dai'dai, kowanne daga cikinsu kuma yana da yaran aikinsa a karkashinsa, hakan yasa waɗan da suke a ƙarƙashin Ramish ɗin sun fi mutun 200, waɗan nan maza sha biyun sune jiga jigai masu kula da kannar dake cikin team ɗin, su suke karɓar umarni daga wajen Ramish ɗin su zartar wa da na kasa da su ɗin, so haka suke, team, team, suke, sai dai team na Ramish ya fi na kowa shahara a cikin special weapons and tactics, saboda bashi da wasa, duk kuma wanda za su kasance a cikin team ɗinsa to ba karamar horar wa yake sakawa a basu ba, domin kuwa shi baya ɗaukar faɗuwa, burinsa a kullum cin ma nasara, baya wasa da aikinsa, waɗan nan gurayen maza guda sha biyu na cikin team ɗin nasa ba karamar horar da su ya yi ba kafin su kai matsayin da suke kai a yanzu, ba shi da aboki daga waje sai cikin gida, su ne kuma Bilal, Rizwan and Dr Raj, haka zalika bashi da wani kusanci da wani a wajen aiki, duk da ya kasance cewa ƴan team ɗin nasa horonsa ne, amma baya yarda da kowa, dan yasan farautar rayuwarsa ake yi kamar yadda ake farautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana, yasan komai hakan yasa bashi da wani makusanci biyun Bilal, Rizwan and Dr Raj, a waje baya yarda da kowa, kallo da ido kawai ta raba shi da kai. A ko da yaushe yana yawan zaman meeting da waɗan nan gurayen mazan ƴan cikin team ɗin nan nasa domin kara karfafa team ɗin nasu ya cigaba da kasancewa shi ne na ɗaya a cikin hukumar special weapons and tactics, yana son ya kasance a sahun gaba kullum....... Yo dama jinin King Zuhair jinin Akka ai dole ya zama haka, su fa basu ɗaukar wasa a lamuransu, wai kun manta me Akka ta ce ne a kan jarumta?..........😅 Sosai Leesharh ta tsumaya da sauraron zazzaƙar muryarsa, tana naɗar duk abin da yake faɗa tana kuma jin daɗin yadda yake yin maganar one by one. Bata bar wajen ba har sai da ta dai'na jin maganarsa alamar ya bar wajen kenan. Cikin hanzari ta fito daga in da ta laɓe ɗin ta nufi room nata, jikinta sai kerma yake yi kamar wadda ta aikata wani abin rashin gaskiya....... Ko da yake rashin gaskiyar ai ta aikata tun da ta yi wa wani laɓe ta ji abin da yake faɗa. Tana shiga ta haye saman gadonta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, kirjinta sai bugawa da sauri sauri yake yi. Zuciyarta sai harbawa pat, pat, pat, yake. Wani irin razana ta yi jin vibrate na wayar dake ƙarƙashin pillownta, dama can a razane take tsabar rashin gaskiya, da wayar ta fara vuuu kuma sai ta kusa rugawa a guje. Dafe kirjinta ya yi tana furta Hasbunallahu wani'imal wakil cikin rawar murya. A hankali ta kai kallonta kan pillown, jiki a sanyayye ta janyo pillows tare da ɗauko wayar. Da farko kamar ma ba zata ɗauki wayar ba, amma tuna cewa number ɗaya ce take kirarta a wayar kuma wannan number babban barazanace ga rayuwar mahaifinta yasa ta hakura ta janyo wayar. Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye lokacin da idanunta suka sauka a kan wannan number, ji take yi kamar ta maka wayar da ƙasa ko ta haɗiyi zuciya da mutu kawai huta, ta fara gajiya da fargaba da faɗuwar gabar da suke jefata a ciki, idan ta cigaba a haka wlh faduwar gaba ne zai zama sanadiyar rayuwarta. Picking ta yi tare da kara wayar a kunnanta jiki kamar wadda aka zarewa laka. Daga other side ɗin aka fara magana cikin sanyin murya. "A'isha na manta ne ban sanar dake wani abin ba, idan kin je wajen walimar nan ki mayar da hankalinki sosai a kan mutane, babu ruwanki da yin magana da kowa, sannan kada ki manta wajen a cike yake tab da camera's sosai". A tunanin matar yanzu ne Leesharh zata tafi wajen walimar, bata san ita kam har ta je ta dawo ba abinta, zama ya gagareta a wajen walimar saboda rashin gaskiya. Da kyar ta ɗan iya saita nutsuwarta tare da fara gayawa matar duk abin da ya faru tun daga zuwan ta wajen walimar har izuwa yanzu da take zaune a bakin bed dinta. One thing about Leesharh yarinyar nan bata karya, kome zaka yi mata in dai zata buɗi baki ta yi magana to gaskiya zata faɗa, sai dai idan tasan gaskiyar bashi da amfani a wajen ko kuma tana tsoron faɗarsa kada ya zame mata illa to a nan kuma shiru zata yi sai dai a kashe ta, amma ba zata taɓa yin karya ba!!. Wani irin sautin dariya ne ya fito daga ta cikin wayar, a hankali sautin yake tashi, da alama sun ji matuƙar daɗin news da Leesharh ɗin ta basu. Shiru baiwar Allah ta yi tana sauraron dariyar matar har na tsawon minti ɗaya. Ɗan taɓe baki ta yi tana mamakin ko me ya sanya matar yin dariya? Ta tambayi kanta. Ta shagala da tunane tunane ta tsinkayo muryar matar tana faɗin. "A'isha Allah ya yi maki albarka, ashe da rabon kin kusa komawa wajen babanki, yau kin gaya mun labari mai daɗi, amma kin tabbatar a guests house ɗinsa ya ce zasu yi zaman?". Gyaɗa mata kai Leesharh ta yi tamkar tana a gabanta kafin ta ce e ta tabbatar. "Good! Kenan Ramish zai fita gida kafin karfe takwas na dare, dan shi baya wasa da lokaci, hakan ma dai'dai ne, yanzu dai abin da nake so da ke shi ne, akwai wata magani da zan sanya a kawo maki, ko in ce ki fita ki je ki nemo wacece zata kai wa Ramish abincin dare? Idan kin dawo zan kiraki karfe 6 dai'dai dan na gaya maki a in da zaki ga wannan maganin, abin da nake so da ke lallai lallai ki shammaci mai kai mashi abincin nan ki zuba mashi wannan maganin a cikin cappuccinonsa, dan na san ko bai ci abinci ba tabbas ba zai fita daga gida ba tare da ya sha cappuccino ba, dan haka zai sha maganin kafin ya halarci wannan taron, idan kika yi komai cikin nuna taka tsantsan da kulawa tabbas gobe zan haɗaki da babanki a waya ku gaisa, idan komai ya tafi yadda muka tsara kam ma a cikin daren nan zaki bar gidan, kina barin gidan kuma sai ƙasarku zaki koma....." Zubur ta miƙe tsaye tare da zaro idanu tana faɗin. "Aunty da gaske zaki haɗani da babana a waya? Kuma da gaske zan koma ƙasarmu?". Tabbatar mata da hakan matar ta yi kafin ta katse kiran kit. Wani irin farinciki Leesharh ta ji ya rufeta, nan take ta ji kwarin gwiwa, tabbas in dai zata gaisa da mahaifinta a waya to ba shakka yanzu ba sai anjuma ba zata nemo waye zai kai wa Ramish abincin dare. Lallai ba shakka matan nan sun san lagon Leesharh, sun san da cewa idan suka ce zasu haɗata da babanta to fa zata yi masu abin da suke so cikin sauri, basu zaɓota a kan wannan aiki haka kawai ba sai da suka tabbatar da lallai tana da jajircewa akan abu idan ta sanya kanta, in dai ta ce zata yi abu fa to wlh sai ta yi shi, haka take, sun san zata iya ne yasa suka fara, da sun san ba zata iya ba ba zasu fara wannan aikin da ita ba. (Ni kuwa na ce tom Leesharh kada dai ki manta Our twin's Obaid and Omaid na Maman Sultan suna nan😌 ki bi dai a sannu.) Miƙewa ta yi cikin kwarin gwiwa da azamarta har ta ji karfi ya zo mata ta nufi waje, sai murna take yi zata yi magana da babanta, sam bata san illar da abin da zata aikata zai haifar ba. Kasa ta sauko domin neman wacece zata kai mashi abincin dare kuma da wani lokaci zata kai mashi. Tsabar rashin tsoron irin na yarinyar nan da muradin cin ma burinta karara a saman fuskarta, ba tare da shakkar komai ba ta tinkari kitchen ɗin dake ƙasa kai tsaye abinta, cikin jajircewa take yin komai tare da burin cinma nasara.......... Akwai kura kuwa ba kaɗan ba, kura mai tashi har sararin samaniya ma kuwa. Leesharh fa tana ganin kamar samun gane mai kaiwa Ramish abinci abu ne mai sauki a gareta! Sannan tana gani aiki mai sauki ne ta iya zuba mashi wani abin a cikin abinci ba tare da an gane ba! Ta manta da cewa a Abu Abdussalam empire take. To wai ma me zata zuba mashi? Me amfanin hakan? Kuma da alama so suke ya ci maganin kafin ya fita! Me suke nufi?. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH 💔😥 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 11/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________49🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ GIDANSU KHADIJAH 💔😥 Kai tsaye gida Maman Zainab ta nufo, ranta sai tafasa yake yi, tana tunanin hukuncin da ya dace ta yanke wa kanta. Tun daga ɗan nesa da gate ɗin gidan nasu ta fara jiyo hayaniya a cikin gidan kamar gidan biki, kamar kuma gidan dambe ne ko filin yaki za'a ce ne oho. Ruwan bala'i take ji ake ta zazzagawa wanda sam ta kasa iya tantance muryoyin su wanene?. Sai da ta shigo cikin gidan ne ta fahimci muryoyin masu yin maganar. Wani irin sanyi ta ji a ranta jin suna hayaniya. A fili ta furta ku kashe kanku ma idan kun ga dama ƴan iskan kawai. Cikin parlourn ta shigo abinta. Kamar bata gansu ba ta wuce fa nufi saman sofa ta yi zaman, bata son shiga in da su Zainab suke ne, dan tasan ba shakka sai ta samesu suna kuka, Allah sarki bayin Allah, a duk lokacin da suka ji wannan bala'i na familyn baban nasu sai sun shiga cikin ɗaki sun sha kukansu son ransu, suna shiga tashin hankali, sam abin baya yi masu daɗi, ace kullum da familyn babansu da mahaifiyarsu basu shiri, kullum cikin faɗa kamar masu ganin hanjin junansu, abin kam babu daɗi kwata kwata. Zama maman Zainab ɗin ta yi tare da zuba masu na mujiya tana kallon faɗar tasu, ta mayar da su Tv abinta. Maman Haidar ce da maman Hanif sai Hajiyarsu suka zo, sun tasa Hauwa a gaba, Hajiyarsu sai tsinewa Hauwar albarka take yi, ita ma Maman Haidar yanzu da yake taga Hajiyarsu ta zo sai ta samu bakin zazzagawa Hauwar rashin kunya dai'dai gwargwado, domin a tunaninta Hajiyar tasu zata tare mata faɗa. Sai da ina, Hauwa ai ba tayar baya bace, bata da mutunci kuma bata san mutunci ba, ka yi mata halacci ma ta ci amanarka bare kuma ka nuna mata iya shege? Ai wlh tsab zata warware maka zani ta yi maka zigidir a tsakar kasuwa, bata da albarka. Da farko dai ta yi shiru tana jin Hajiyar tasu tana ta kwashe mata albarka tare da tsine mata bata ce komai ba, ta danne bata tanka ba. Amma da abin ya isheta sai ta fara zazzagawa Hajiyar tasu kwandon bala'in, ta yi wa Maman Haidar zazzajen attarugun masifa, ta haɗesu ta cinye masu mutuncin tas!!. Sai da suka yi tsit kamar waɗan da ruwa ta cinyesu!. Baban Zainab dai bawan Allah ko sannu bai iya cewa ba, hakan ba ƙaramin konawa Hajiyarsu rai ya yi ba, har ta kusa yi mashi baki saboda bakinciki, ace wai ɗanka yana zaune wata ƴar gantali titi tana zaginka! Ai abin da ciwo over. Ita kuwa Hauwa yadda kuka san daga tsatson fir'auna ta fito, tsabar rashin tarbiya har da cewa sai ta tsinke Hajiyar da mari har sai ta ga wuta yana bata taurari a face ɗinta. Maman Zainab dai wannan abin ya sanyaya mata zuciya, duk wani tukukin bakinciki da ta kwaso daga wajen bokan nan sai ta ji ya gudu, ranta ya ɗan yi haske, ai dama maganin shege sai ɗan banza. Ta saki baki tana kallon film abinta, dan wannan bala'in da ake bugawa a cikin wannan gida film ne mai zaman kansa. Hajiyarsu ce ta tambayi wacece Hauwa?. Baban Zee da bakinsa ya amsa mata da matarsa ce. Ai kuwa idan ran Hajiya ya kai dubu to sai da ya ɓaci a wannan lokaci, cikin fusata tare da bada umarni ta ce maza yanzun nan ba sai anjuma ba ya saki wannan maras albarka!. Kai tsaye ya ce mata ba zai yiwu ba, babu saki a tsakaninsu, dan haka ba zai saketa ba, su fice su bar mashi gidansa ma tun ransa bai ɓaci ba, sun zo sun ɓatawa matarsa rai sun sa tana ta faɗa a banza. Saura kaɗan Hajiyarsu ta yanke jiki ta faɗi ƙasa saboda mamaki game da bakinciki, ta san dai tun da take da baban Zee, tun da ya kai shekaru goma a duniya, ya fara mallakar hankalin kansa ba ta taɓa yin magana ya ce a'a ba, komai ta ce mashi da daɗi da ba daɗi hakura yake yi ya amsa mata da to, kuma ya aikata abin da ta ce ɗin cikin biyayya matuƙar bai saɓawa Allah ba, dan ba'a bin umarnin kowa a aikata saɓon Allah, ko alamar ɓacin ran baya so ma ba zaka gani a face ɗinsa ba, kawai zai aikata umarninta, amma yau rana tsaka shi da bakinsa da girmasa yake mayar mata da martani? Abin da bai taɓa yi tun yana yaro ba!. Wannan abin ya gigitata kuma ya zame mata izina a rayuwarta, yau ta ga ayar Allah ƙarara. Shiru ta yi tana tunani, gani take yi laifinta ne, sam bata kawo a ranta cewa Hauwa ta asirce shi bane, faɗi take a cikin zuciyarta koma me ya yi a halin yanzu laifinta ne, bawan Allah mai biyayya, ta takurawa rayuwarta shi da familynsa, ta hana shi sakat, ta ɓata mashi farincikinsa bayan kuma shi kullum ƙoƙari yake yi ya ga ya sanya ta farinciki, ta cusa mashi damuwa da tunani, duk wani walwala da yake yi sai da ta toshe mashi wannan kofa ya dai'na samun yinta, yanzu ga shi tura ta kai shi bango har ya juyo yana iya kallonta ido cikin ido ya gaya mata ta ɓatawa matarsa rai dan haka ta fita mashi daga gida? Wato ya gaji da irin cin mutuncin da suka rinƙa yi wa Maman Zainab shiyasa yanzu ba zai bari su yi wa amaryarsa ba, yau ga ayar Allah ido da ido ta gani..... Ita fa take wannan tunanin a cikin zuciyarta. Wannan ba aya ce ga iya Hajiyarsu ba, ina fatan ya zama izina a garemu mata gabakiɗaya, idan yaro yana yi maki biyayya, yana binki sau da kafa, to fa ki yi ƙoƙari kiga kin kyautata mashi kema, kuma ki yi ƙoƙari taya shi neman farincikinsa kamar yadda yake yi maki, in dai ba abin cutarwa kika ga zai aikata ba kada ki matsa mashi wajen ganin kin hana shi yi, zuciya wani lokaci wawan abu ne, kuma wannan ɗabiarmu ce mata, idan munga mutun yana yi mana biyayya yana kyautata mana sai kawai mu yi ta bashi umarni ba kakkautawa, komai sai mu nuna mashi iko, mu hana shi sakat, tabbas wannan ɗabi'ar kaso tamanin cikin ɗari na mata suna aikatata. Ki sani idan kika takura mashi, yana yi maki biyayya kika matsa mashi ke kuma, kika hana shi sakat da wasu umarninki da ba wahayi ne daga sama ba, wlh a kwana a tashi zuciyarsa zata juya maki baya, musamman idan ya haɗu da abin da yake matuƙar so ke kuma kika hana shi, tabbas zuciya bata da ƙashi, ko bai yi maki rashin kunya ba zai ja baya dake, zai ji baya sha'awar ya rinƙa zuwa in da kike, zai ji kin fita a ransa!. Ga kuma shaiɗan a gefe da zai ƙara ingiza zuciyarsa da ya gujeki!!. To dan haka ni dai shawarata a gareku iyaye masu ƴaƴa ƴan albarka masu biyayya, da ma mata da basu rigada sun zama iyaye ba, shawarar da zan baku shi ne, duk wanda yake sonku yake kyautata maku, yake yi maku biyayya, yake bin umarninku, ku daure ku so duk abin da yake so matuƙar ba cutarwa ce a gare shi ba, ku daure ku so nashi farincikin shi ma, kada ku yi la'akari da ku kuka haifesa dole ya bi umarninku, Allah da ya halicci mu gabaɗaya ma bai ce dole dole mu bi abin da ya halicci mu dominsa ba, saboda yana da wuta da aljanna! Ki sani idan har zaki daure ki bi farincikin ɗanki mai yi maki biyayya, ki so shi ki so abin da yake so, wlh a kullum sonki karuwa zai rinƙa yi a cikin zuciyarsa, zai ji yana son ganinki a kusa da shi, zai ji shi idan ba gida ɗaya tare da ke bama ba zai iya zama ba, bare ace kina son familynsa, ƴaƴansa ma suna sonki, wlh duk yadda zai yi sai ya dawo dake kusa da shi domin ya cigaba da samun farinciki, ba ƙaramin daɗi yake ji ba idan yaga kina kaunar familynsa, ji yake kamar ya haɗiyeki dan soyayya, zaki ga komai kika ce cikin rawar jiki zai amsa maki, sai kiga ya fi umarnin da kike zama ke Hajiya two seater ki ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ki zayyana mashi su kamar wadda aka saukowa da wahayinsu, ke sam ba zaki yi tunanin halin da zai shiga ba, bukatarki kawai dai ta biya kamar dai Hajiyarsu baban Zainab....... Abin da yasa na yi maku wannan magana saboda rayuwar gidansu Zainab abu ne wanda yake faruwa a cikin al'umma sosai da sosai, to fisabilillahi mata ku ɗauki hanyar gyara domin farincikin kanku da ƴaƴanku haɗe da jikokinku, Allah ka yafe mana kura kuranmu ka iya mana da iyawarka, ka jikan iyayenmu da suka rigamu gidan gaskiya, waɗan da suke raye kuma Allah ka kara masu lafiya da nisan kwana, Allah kasa mu cika da imani, na so na bawa ƴan'mata ma shawara, amma babu lokaci zaku cinye mun filin page ɗin, sai wani lokaci idan alkalamina ya zago ta makamancin hakan. Sosai Hajiyarsa ta shiga yin danasanin abubuwan da ta yi wa Maman Zainab, dan ita a tubaninta ita ce ta hasasa komai, kuma ba shakka tana da hannu a ciki kam, domin idan da bata biyewa son zuciyarta ba, ta tsaya ta yi mashi addu'a, tana son ganin farincikinsa wlh da wane mutu, wane kaniyar Hauwa ta iya yi cin nasara a kansa, wai kun san karfin addu'ar iyaye kuwa? Musamman ma uwa! Wlh da tana yi mashi addu'a ko shi baya yi sosai babu abin da ya isa ya taɓa shi, amma ta tsaya biyewa son zuciyarta maras amfani, to yanzu ga shi an raba ta da shi, kuma shi ɗin nan dai shi ne mai ciyar da su, shi yake rike da ita da ƴan uwansa su maman Haidar, to yanzu ba dukkansu sun yi rashi ba? A yadda yake ɗin nan ina wani zance kula da su? Ai sai dai kowacce ta ciyar da kanta a yanzu, dan yanzu dai Hauwa ce mai mulki da komai, kuma kunsan Hauwa ƴar tijara kam ba yi masu zata yi ba, sai dai ma ta hana ayi masu! To mata bana son ko wacce readers ɗin litattafaina ta faɗa irin wannan aikin danasanin maras amfani, kun ga aya a fili, da mamarsa tana son abin da yake so, tana zaune cikin kwanciyar hankali da shi tana zuba mashi ruwan addu'oin ai da wane uban Hauwa ta yi nasara a kansa. Dan Allah mata mu gyara. ...........Ni kam anya Hajiyarsu ma bata fi shekaru goma rabon da ta yi mashi addu'a ba kuwa?🤔😅 Mata kullum cikin mashifa da kuntatawa familynsa, bata san idan ta kuntatawa familynsa shi ta kuntatawa ba, ta biyewa su Maman Haidar sun kaita sun baro, kai wato mu mata akwai shegen son girma🤔 kawai ki dake a saman kujera ki ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya kina jerowa yaro umarni babu ruwanki da halin da zai shiga🤔 Allah dai ya shiryamu wlh............... Jiki a mace Hajiyar tasu ta ce da su Maman Haidar su zo su koma gida. Da mamaki suke kallonta, a tunaninsu ai umarni zata bashi a kan lallai dole ya saki Hauwa, amma sai suka ga akasin haka!. Juyawa ta yi ta nufi hanyar fita ba tare da ta sake yi wa su maman Haidar ɗin magana ba. Har ta kai bakin kofar parlour sai kuma ta juyo da kallonta a kan maman Zainab dake zaune shiru ta mayar da su Tv tana kallo. Allah sarki maman Zainab sarkin tausayi, gabaɗaya sai ta ji mugu mugun tausayin tsohuwar ya kamata, amma ko sannu bata ce masu ba, dan koma me ya faru su suka ja wa kansu!!. Ƙasa iya yi mata magana Hajiyar tasu ta yi, gabaɗaya kunyar Maman Zee ɗin ma take ji, sai kawai ta juya ta fice daga parlourn zuciya cike tab da danasani maras amfani. Da sauri su Maman Haidar ɗin suka rufa mata baya. Suna barin gidan Hauwa ta dawo da tijararta a kan maman Zainab dake zaune shiru. Ai tsabar tsanar da maman Zee ɗin ta yi masu ma ko tanka mata bata yi ba, dan cewa ta yi magana da Hauwa ma zunubi ne babba, dan haka ita bata sake buɗe baki ta kulata. Sai tijara Hauwar take yi! Ko ci kanki Maman Zainab bata sake ce mata ba, yadda kuka san ta zagi sama ko kuma da mutun mutumi take magana ba Maman Zee ba. Da dai taga ba kulata zata yi ba, sai ta ce da baban Zainab lallai lallai yau sai ya zane Zainab a gidan nan ko kuma ta bar mashi gidansa. Ta yi hakan ne dan ta ƙuntata zuciyar Mamam Zee, sai dai nan ma dai kamar babu Maman Zee a parlourn, sam bata nuna kamar ma ta ji me suke faɗa ba. Da ta ga hakan sai ta ce da Baban Zee ɗin su je ɗaki su tattauna a kan batun auren Khadija da Haidar, dan wannan aure babu fashi wlh. A wannan karon ne maman Zainab ɗin ta ɗan ɗago idanu ta kalleta amma bata ce komai ba. Wani irin shu'umi kuma munafukin murmushi Hauwar ta sakar mata, dan ta ƙara kona mata rai. A cikin zuciyarta kuma tana faɗin ai wlh tun da baki son Khadijah ta auri Haidar to ba shakka sai anyi auren nan cikin satin nan tun ubanta a hannuna yake, bani da burin da ya wuce in ga ina ƙuntatawa rayuwarki!!............Tashin hankali!! Hauwa fa ƴar iskace bata da mutunci ko kaɗan wlh!! Kowa yasan ko yau ta ce a ɗaura auren nan sai an ɗaura ba fashi, dan uban gayya umarninta yake bi!. Akwai matsala. Kawar da kallonta Maman Zee ɗin ta yi, still dai bata tanka mata ba. Cikin ɗaki suka shige da baban Zainab tana gaya mashi yadda za'ayi tsare tsaren bikin, duk dan ta bakantawa baiwar Allah maman Zee rai. Shi kuma baban Zainab komai ta ce sai ya ce yadda kike so haka za'ayi ai Hauwa'u na!. Suna shiga cikin ɗakinsu ita ma Maman Zee ta miƙe ta nufi ɗakin da su Khadijah suke a ciki. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 Zaune Yah Jawad yake a kusa da King saman bedside drawer, while King ya saman katafaren bed ɗinsa, suna ɗan fuskantar juna, King dai yana aiki ne a laptop ɗinsa kamar yadda ya saba, dama idan baku manta ba ya ce Jawad ɗin ya zo ya same shi. Shiru Yah Jawad ya yi alamar ya luluƙa duniyar tunani, gabaɗaya yana jinsa babu daɗi, haka kawai yake jin baya son zuwan ƴan uwan nan nasa da za su yi gobe. Sau uku King yana yi mashi magana bai amsa ba, ya luluƙa duniyar tunani. Sai da ya ɗan taɓa shi ne ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da ɗago idanunsa zuwa saman face ɗin daddyn nasu. "Daddy ka kammala aikin ne?". Ya tambaya yana tattaro hankalinsa da nutsuwarsa waje guda. "Jawad menene yake damunka har haka? Tunanin me kake yi haka da har na yi magana baki uku baka ji ba?". Ɗan zaro idanu ya yi yana mamakin jin daddyn nasu ya yi magana har baki uku yana can yana tunanin da shi kansa bai san me yake tunawa ba..... Tirƙashi. "Daddy wlh ni ma fa ban san tunanin me nake yi ba, kawai dai ban ji me ka ce ba". Shiru King ya zuba mashi idanu ba ƴan sakanni kafin ya ce. "Jawad ka gaya mun me yake damunka? Ina Jaish yake kuma yau bai shigo ba?". Ɗan shafa arab hairnsa ya yi tare da ƙaƙalo murmushin dole. "Daddy babu abin da yake damuna, Jaish kuma i think ya fita shiyasa bai shigo ba, idan ya dawo da wuri nasan zai zo". Ajiyar zuciya King ɗin ya sauke kafin ya ce. "Jawad meyasa baka jin tausayin maraicin ka ne? Meyasa kake son ɗaurawa kanka damuwa? Matsalar wajen aiki ce ko ta cikin gida? Ni fa daddynka ne, duk duniya baka da biyuna, ko Abbas bai kai ni kusanci da kai ba, dan shi kansa Abbas da hakwaranka sama da goma ya zo ya sameka tun bayan da ya miƙa mun kai kana cikin tsumma, a tunanina babu wanda ya fini sanin halinka, dan haka kawai ka gaya mun gaskiyar me yake damunka? Ko dai kana da wani mahaifin bayan ni ne?". Da sauri ya fara girgiza mashi kai bawan Allah. "Daddy tabbas babu wanda ya kaika sanin halina, kuma tabbas bani da wani mahaifin da ya kaika, haka zalika babu wanda nake kauna number one a duniyarnan sai kai, kai ne farincikina daddy, kuma nasan ka sanni in and out, tabbas nasan kaga damuwa a tattare da ni ne yasa ka matsa mun sai na gaya maka menene? Amma daddy ka yarda da ni wlh ni ma ban san me yake damuna ba". "Kana kewar mummynka ne?". King ya jefa mashi tambaya cike da tsantsar tausayinsa, yana kaunar Jawad over, kuma yana tausaya mashi saboda wasu abubuwa da suka faru a shekarun baya. Guntun murmushi ya yi kafin ya amsa da. "Daddy ni da ban san ya kalar mum ɗin nawa ma yake ba meyasa zan yi kewarta har haka? Ina kewarta amma ba har haka ba, wanda ya rayu da uwa na ɗan lokaci ne idan bata nan zai yi kewarta, ni da na tabbata ko rayuwar 30 mins ban yi da ita ba ya za'ayi na ji kewarta har haka? Ban san daɗinta ba kuma ban santa ba, kai da Momma kune komai nawa, idan akwai wata uwa da zan yi kwatarta to Momma ce, kuma tana part ɗinta, a duk lokacin da na ji kewarta zan je in ganta, dan haka daddy ni bana wani kewar mum". Haƙiƙa King ya yarda da maganarsa na cewa shi kansa bai san me yake damunsa ba, amma kuma abin ya tsaya mashi a rai sosai. Ƙoƙarin kawar da zancen King ɗin ya yi ta hanyar sako wani topic dan ya ga ya kore mashi damuwar da take kwance a saman face ɗinsa. "Aure kake so ko?". Ya jefa mashi tambayar yana kura mashi ido. Zaro idanu sosai Jawad ɗin ya yi, sai kuma ya saki siririn murmushi sakamakon gera guda da King ɗin ya ɗaga mashi. "Daddy ni fa ba wani auren da nake so". Ya yi maganar yana ƙoƙarin tuɓune fuska irin shi da gaske yake yin nan. "Ai duk wanda zaka gansa a cikin damuwa, ka tambaye shi me yake damunsa ya ce maka bai sani ba, to tabbas aure yake so, aure kawai zan yi maka kai da Jaish, shi ne maganin damuwar da ba'a san mecece bace". "Daddy aure fa? To ina zaka samo matan da zaka aura mana ɗin? Ni kam ma dai bana so gaskiya daddy, wata kila dai Jaish, kuma ni daddy Allah ba damuwar aure bace take damuna". "To me yake damun naka? In dai baka gaya mun me yake damunka ba to ba shakka damuwar rashin aure ce take damunka, kuma zan yi maganin abin, dan ba zan iya cigaba da zuba ido ina ganin my son cikin damuwar da shi kansa bai san na mecece ba". "Daddyyyyyyyyyy ka fara ko? Ni fa da gaske ba rashin aure bane yake damuna, wai daddy su Yah Ramish da suke manya ma basu yi aure ba sai mu ƴan yara? Kawai salon ka ja mu tsufa da wuri, ni Allah bana so". Yana magana yana kawar da kai, dan kada su haɗa ido da daddyn nasa ya saka shi dariya, saboda ya turɓune fuska ne irin ace da gaske yake yin nan. "Da gaske baka so?". Kai ya gyaɗa mashi alamar e da gaske yake yi. "To shikenan, amma gaya mun me a tsakaninka da Jannat?". Da sauri ya dawo da kallonsa kan daddyn nasu. "Jannat kuma daddy?". Gera guda kawai King ya ɗaga alamar e ita dai. "Kai daddy kai daddy, ni babu abin da yake a tsakanina da ita, sister mafi soyowa ce a gareni ita da auta, bayan haka babu komai". "Da gaske?". King ya yi mashi gatse. "Kai daddy wai ba zaka bar tsokanata ba? Da gaske mana babu komai". Ɗaure fuska sosai King ya yi alamar babu wasan nan, cikin nuna isa ya ce. "Me kaje yi a bedroom ɗinta ranar wuraren karfe 11, ka san dai na kamaka a bedroom nata ba sau ɗaya ba sau biyu ba ko? Haka zalika na kamaka da ita a room na Akka, kai har room ɗin nan nawa baku bari ba, daning room ma baku bari ba, and da kuka fita ranar ina kuka je?". Yana magana yana kara ɗaure fuska. "Daddy ni fa addu'ar barci nake zuwa yi mata a room ɗinta, kuma ba ita kaɗai ba har da Auta, wai to daddy laifine dan yaya ya ɗauki kannensa sun fita yawata gari? Kuma ai kaga a tare da auta muka je, ni daddy ba zaka barni na huta ba ko?". Wani irin kallo ya wurga mashi wanda sai da ya saka shi sakin murmushi. "Kai daddy kai daddy ka fara ko? Ni Allah wani lokaci kamar nayi kuka nake ji idan kana yi mana irin wannan abin, gaskiya fa na gaya maka babu komai a tsakaninmu". "To ka ji nace karya ka gaya mun ne? Ko dai ka tsargu ne? Babu rami me ya kawo maganar rami? Kai da kanka da yake kasan ba gaskiyar ka faɗa ba duk ka tsargu, ka ruɗe kana ta maimaita kalmar gaskiya ka faɗa, to shikenan na ji addu'a kake zuwa yi mata a room ɗinta, shi kuma room ɗin Akka da nawa room ɗin fa? Ko nan ma addu'a kake zuwa yi mata?". Kamar zai yi kuka ya ce. "Daddyyyyy tom shikenan duk yadda ka ɗauki tsakanina da Jannat haka ne, amma dai ni nasan babu abin da yake a tsakaninmu, kuma zaka iya tambayarta ma ka ji, amma please daddy ka bar zancen auren nan ga su Yah Ramish a gaba". "Tom shikenan tun da baka son zancen, nasan maganinku ai, bari su Ramish ɗin su zo, kun kusa dai'na yi mun yawon tsakar dare a cikin gida". Guntun murmushi ya yi kafin ya ce. "Wai ni daddy daga ina ma kake samun information a kanmu ne? Wai duk yadda muka yi fitar sirri ranar sai da kasan mun fita ko? Kuma wai ya aka yi kasan ina hira da Jannat a ɗakin Akka?". Cikin zolaya ya amsa mashi da. "Ka bari Akka ta kamaka a cikin room nata kana soyayya, a nan ne zaka gane ta in da nake samun information, kasan halinta ai, zaka yi bayani randa ta riƙeka". "Daddy soyayya kuma? Ni fa kawai hira muke yi da su, dan su ɗebe mun kewa". "Hirar ce har da yiwa autata wayo ku korata ta tafi ta baku waje ko?". Shafa kansa ya yi yana murmushi, yanzu dai kam ya rasa abin faɗe domin ya kare kansa, shi dai ba zai yarda soyayya suke yi ba, dan ba yanzu ya so bayyana soyayyarta ga kowa ba, ita kanta ma bai bayyana mata bare sauran familyn, ai ba yanzu ba a cewarsa. "Ka rasa abin faɗe don cigaba da kare kanka ne?". Ya yi maganar yana ɗaga mashi gera. "Ni daddy barci ma nake ji, kuma da gaske ni da Jannat babu wani abin da yake a tsakaninmu, wai ni yaushe na kori auta ne ma? Daddy masu baka bayanin nan sun yi mun sharri". Hararar wasa ya wurga mashi kafin ya ce. "Ko? To ce maka nayi akwai masu bani bayananku ne? A kan me zan buƙaci mai saka mun ido a kanku bayan ina da rai'na da lafiyata? Kawai duk abin da kuke yi ne yana cin karo da a lokacin ina wajen, da idona nake ganin komai, wai shin anya ma amsar da ka bawa Abbas gaskiya ce kuwa? Jawad sanadiyyar Jannat ka fara koyan karya ko?". "Daddy barci nake ji sosai, in je in kwanta please?". Ya yi maganar ƙasa ƙasa irin a ce da gaske yana jin barcin. Gefensa King ɗin ya nuna mashi tare da cewa. "Zo mana ka kwanta, yau kuka fara yin barci a nan ne? Zo mu kwana tare". A hanzarce ya girgiza mashi kai yana faɗin. "No daddy zan je room ɗina in kwanta......." Katse shi cikin zolaya ya yi da cewa. "Ba zaka iya yin barci ba sai ka yi wa Jannat addu'a ko? To je kayi mata sai kazo mu kwana tare". Miƙewa ya yi tare da nufar kofar fita yana faɗin. "Allah daddy kai da daddy idan kuka saka mutun a gaba babu daɗi, ni yanzu fa na gaya maka gaskiya babu komai a tsakaninmu". Still cikin zolaya King ya ce. "To ai dama ni bance ba gaskiya ka gaya mun ba, sannan kuma ni ban ce akwai komai a tsakaninku ba, kawai dai idan ta yi tsami zanji ai". Ficewa ya yi yana murmushi, daddy ya gama gane komai, amma ya tsaya sai waske mashi yake yi saboda wata banzar dalilinsa na cewa sai gaba zai bayyanar da soyayyarsa................... Allah sarki rashin sani yafi dare duhu, da yasan bala'in da yake tinkarosa a gabansa da cikin daren ba sai gobe ba zai gayawa King gaskiya ya kuma ɓukaci da a ɗaura masu aure gobe da safe, amma bai sani ba!. Yana fita part na King kai tsaye nasa part ɗin ya nufa, wanka ya je ya yi tare da shiryawa cikin tsadaddun kayan barci riga da dogon wando launin brown, ya yi kyau sosai a cikinsu kasancewar yana da hasken fata, yau sai ya kara fitowa sak uncle Abbas, shi ma gashin gerarsa ta kusa haɗewa irin na Jaish, sai zuba kamshin perfume mai daɗi yake yi. Wayarsa ya ɗauka tare da fitowa waje. Bai zame ko'ina ba sai ɗakin Chuchun kamar yadda kin ya faɗa kuwa. Yau auta bata cikin ɗakin, tana tare da Mommarta tun bayan da suka gama cin abincin daren. Tura kofar ya yi ya shiga tare da yin sallama ƙasa ƙasa. A lokacin kuma ta kammala shiri cikin kayan barcinta kenan, ta hau gadon hannunta rike da waya tana ƙoƙarin kiran layin Rizwan, dama hira suke yi ta ce mashi bari ta yi wanka kada dare ya yi sosai, shi ne ya ce idan ta kammala ta kira shi. Ta yi matuƙar kyau sosai cikin riga da wandon barcin nata, ga su launin dark purple, kasancewar jajir yasa kalar ya yi mata kyau, sannan sleeping dress ɗin nata sun zauna a jikinta cif cif, ta ɗaure arab hairnta kashi biyu, a kowani bakin jelar gashin nata ta ɗaure shi da rebbon white color, saboda kada ya warware, gashin nasu yana da tsantsine sosai, hakan yasa dole suke ɗaure bakin jelar gashin da rebbon. Da alama sleeping dress ɗin nata basu da hula, dan bata sanya ba. Jin sallamarsa haɗe da turo kofar yasa ta kai kallonta bakin kofar tare da dakatawa daga kiran Rizwan da take ƙoƙarin yi. Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Yah Jawad baka yi barci ba?". Cool murmushi shi ma ya maido mata tare da maido mata da tambayar tata. "Kema baki yi barci ba?". Kai ta gyaɗa mashi tare da ajiye wayar tata a gefe ta juyo da kallonta mai gabaɗaya a kansa. "Yah Jawad to meyasa baka yi barcin ba?". Ta tambaya tana zuro da kafafunta kasan gadon. "Kasa yin barcin na yi, barci yaki zuwa, shi ne na ce bari na zo mu yi hira". Ya yi maganar tare da harɗe hannayensa a saman kirjinsa, sannan ya jingina da jikin door ɗin kofar, hakan yasa kofar ta rufe kirif sosai. Wani irin daɗi ta ji da jin kalamansa na cewa ya kasa yin barci ne ya zo su yi hira, tana son kasancewa a tare da shi yanzu da ya dai'na takura mata. Vibrate ɗin wayarta da ta ji ne yasa ta kai kallonta kan wayar. Yah Rizwan, shi ne sunan da yake yawo a saman screen ɗin wayar, ji ta yi ba zata iya ɗaga kiran ba, saboda a gaskiya tun da har Yah Jawad ya tako kafarsa ya zo har in da take domin su yi hira dan ya kasa yin barci, to dole ta bashi lokacinta su yi hirar. Dan haka sai bata ɗauki kiran ba har ya yanke, yana yankewa kuma ta kashe wayar gabaɗaya tare da dawo da waɗan nan fararen idanun nata a kansa. Ya zuba mata idanu yana ta kare mata kallo ya jingina da jikin door. "Yah Jawad meyasa kake ta kallona haka?". Kamar bakinsa na yi mashi ciwo, a hankali ya motsa lips ɗinsa ya furta. "Saboda kin yi kyau sosai". Daga in da yake ya jiyo saukar ajiyar zuciyarta, alamar ta ji daɗin maganar. "To Yah Jawad ka shigo mana". Tana magana tana murmushi mai kara mata kyau. Girgiza mata kai ya yi alamar a'a, kasa kasa ya ce. "Ba sai na sai na shigo ba, ganinki daga nan ma ya wadatar". "To ni in zo ne?". Girgizara mata kai nan ma ya yi. "Ba zaki juri tsayuwa ba ai, dan haka yi zamanki a saman bed ɗinki daga nan ma ina iya kallonki da kyau". "Yah Jawad zan iya tsayuwa mana, bari na zo, dan ni bana ganinka da kyau". Ta kai karshen maganar tare da sauƙowa kasa ta nufo shi. Tun da ta miƙe ya kara kura mata ido from head to toe yana kallonta, kayan barcin sun yi mata kyau sosai. A kusa da shi ta zo ta tsaya tana faɗin. "Yah Jawad Allah kai ma kayi kyau sosai, kalar sleeping dress ɗin nan naka ya yi maka kyau". Can kasa kamar mai raɗa ya ce. "Da gaske?". Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e. Ji ya yi duk jikinsa ta yi la'asar, ya kasa motsawa daga jikin door ɗin, yana son ya ɗan karkato su fuskanci juna da kyau, amma ya kasa, saboda wani irin kasala da ta rufe shi. "Yah Jawad ya naga kuma kamar kana jin barci?". Ta faɗa tana jingina da jikin bangon kusa da door ɗin. Nisawa ya yi kafin ya ce. "Ke ki ka ja mun jin barcin ai". Zaro idanu ta yi tare da cewa. "Ni kuma?". Lumshe idanu ya yi dan ba ƙaramin kara tafiya da imaninsa ta yi ba da ta zaro idanu. "Ganinki yasa har na fara jin barci". Ya bata amsa da ɗan buɗe murya. "Tom ka je ka kwanta". Girgiza mata kai ya yi alamar a'a. "Meyasa?". Ta tambaye shi da mamaki. "Saboda ganinki ya fi barcin daɗi". A wannan karon ta ɗanyi mamakin jin hakan, bata damuwa a duk lokacin da ya ce mata ta yi kyau, dan tana ɗaukar hakan a matsayin yabo na yaya da kanwa ne, amma yanzu da ya ce ganinta ya fi barci daɗi sai ta ji kamar Rizwan ne ya yi maganar, dan shi ma yana gaya mata hakan wani lokaci, idan ta ji yana hamma alamar mai jin barci, idan ta ce ya kwanta ya yi, sai ya ce mata hira da ita ya fi barcin daɗi....... Tirƙashi. Ta luluƙa duniyar tunani bata ankara ba sai ganin hannunsa ta yi saman fuskarta, shafa face ɗin nata ya yi yana faɗin. "Tunanin me kike yi my sister da har ina magana baki ji ba". Da yake dai akwai yarinta sosai a tattare da ita sai ta kawar da wancan tunanin tare da sakin cool murmushi. "Babu tunanin da nake yi". Ƴan hannayenta ya riƙo cikin nasa hannun guda ɗaya, wasa da yatsun hannun nata ya fara yi yana faɗin. "Jannat da gaske yau kin yi mun kyau fiye da kowacce rana". Zata yi magana suka ji knocking na kofar room ɗin. A tare suka zaro ido ita da shi dukka. Abin gwanin ban dariya. Janyota jikinsa ya yi, a kunne ya raɗa mata koma wanene ya zo kada ta yarda ta gaya mashi ita da waye a cikin ɗakin, bari ya ɓuya a cikin toilet ɗinta. Shi a cikin zuciyarsa yana tunanin King ne ko kuma Mummynta, cikin biyun nan, dan yasan auta kam izuwa yanzu ta yi barci, ba zai lamunci wani ya kama shi a ɗakinta almost 11 na dare ba, duk da suke matsayin iyayensa sun san halinsa ciki da waje, su suka renesa, amma dole shaiɗan zai raya masu wani zargin a ransu idan suka gansa a irin wannan lokacin a ɗakinta, so maganin bari kada a fara, kada ya bari su kama shi ma bare shaiɗan ya raya masu wani abin. Da sauri ya saketa tare da raba jikinsa da jikin door ɗin ya nufi cikin toilet. Sai da ta ga shigarsa sannan ta dai'dai nutsuwarta tare da ɗan ja baya daga wajen kofar, ƙasa ƙasa ta ce. "Wanene?". Murɗa handle ɗin door ɗin aka yi tare da turo kofar, dama ɗazun kofar taki buɗuwa ne yasa aka yi knocking, saboda kunga Jawad ya jingina da ita, shiyasa taki buɗuwa. Jin ba'ayi magana ba an turo kofar ne kawai yasa ta ɗan zaro idanu.............. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 12/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________50🔥 Jin ba'ayi magana ba an turo kofar ne kawai yasa ta ɗan zaro idanu tana jiran kawai taga wanene?. Tun kafin ya shigo kamshin perfume ɗinsa ya isar mata da saƙon wanene, hakan yasa ta ɗan sauke ajiyar zuciya tare da ɗan sakin fuska. "Jannat me kike yi har yanzu baki kwanta ba? Almost 11 something fa yanzu, kuma me ya tsayar dake a tsakiyar ɗakin?". Ya jefa mata tambayar tun bai ƙarisa shigowa ciki ba. Ƴan kame kame ta fara yi, bata iya karya ba, bata son kuma ta karya maganar Yah Jawad, ta rasa me kuma zata ce. "Jannat ba da ke nayi magana bane? Ko baki da lafiya ne?". Lokacin guda ta gyaɗa mashi ta sake girgizawa, alamar e bata da lafiya kuma a'a lafiyarta lou. Shiru ya ɗan tsaya ya zuba mata ido da kyau yana kallon yadda take ƴan kame kame, zallar rashin gaskiya ne a tattare da ita. "Ina Jawad?". Ya jefa mata tambayar ne dan yana son fahimtar wani abin!. A ɗan ruɗe ta ce. "Daddy ni ma ban gan shi ba". "Keda waye a room ɗin da naga kamar alamar ba ke kaɗai bane? Kuma na je room ɗin Rahilarh na tatda Auta a can bare nace ke da ita ce". A hanzarce ta amsa da. "Daddy bani da kowa bane, ni kaɗai ce a ciki, ban jima da fitowa wanka bane, yanzu na gama shirin kwanciya, dama yanzu zan kwanta". Da hannu ya yi mata nuni da saman bed ɗinta. "Jeki kwant to bari na yi maki addu'a, ita ce ta kawoni dama". A hanzarce ta juya kamar dama jira take yi ya ce ta je ta kwanta. Binta da kallo ya yi zuciyarsa na ayyana mashi ba ita kaɗai ce a cikin ɗakin ba, koma ita kaɗai ce to tabbas Jawad bai jima da barin ɗakin nan ba, dan akwai kamshin perfume nasa a ɗakin, ga rashin gaskiya dake tattare da ita sosai. A gefen bedside drawer ya zauna tare da karanto addu'oin kamar yadda ya saba yi masu kullum, ya tofa a hannunsa ya shafeta da shi, sannan da kansa ya janyo mata lallausan katuwar bargonta ya lulluɓeta. Cike da tunani a ransa ya miƙe ya ɗauki wasu remote guda biyu dake cikin bedside drawer. Ya yi amfani da ɗaya wajen kashe wutar ɗakin, ɗayan kuma ya yi amfani da shi wajen rage gudun Ac. Cike da kaunar ƴaƴan nasa ya yi mata good night. Tana daga cikin bargo ta amsa mashi da daddy Allah ya tashe mu lafiya. Amin ya amsa da shi kafin yasa kai ya fice izuwa ɗakin Gimbiya Aneesa ƴar Mama. A kowacce dare haka yake binsu ɗaya bayan ɗaya yana yi masu addu'a tare da dubasu ya tabbatar suna cikin aminci, abin gwanin ban sha'awa, yana sauke hakkinsa a matsayinsa na uba, ƴaƴa mata sai da kula sosai!. Yana ƙoƙarin janyo mata kofar ɗakin nata ya rufe ne wayar Jawad daga cikin toilet ta fara kara alamar shigowar kira. Ɗan dakatawa ya yi yana son tantance kirar waya ce ko menene? Da yake wayar bata da ƙara kamar android phone. Mamaki ne sosai ya bayyana a kan fuskarsa, shiru ya ƙasa kunne yana sauraro. Bai kai ga tantance komai ba Jawad ya yi saurin ciro wayar daga aljihun wandon sleeping dress ɗin nasa, cikin hanzari ya katse karar yana sauke ajiyar zuciya. Jin shiru ne yasa King ɗin ya yi tunanin ba ringing na waya ya ji ba, kila gizo abin ya yi mashi, dan haka sai ya ja mata kofar ɗakin nata ya wuce, sai dai har ga Allah zuciyarsa na tunanin kamar Chuchu ba ita kaɗai bace a cikin ɗakin, amma sai ya yi ƙoƙarin kore tunanin tare da shiga wajen Aneesa. Ɓangaren Jawad ɗin kuwa. Ganin sunan Yah Rizwan ne yake yawo a saman screen ɗin wayar tasa yasa bayan ya ji fitar King ya rufo kofa sai ya yi ƙoƙarin picking. Sai dai bai kai ga ɗauka ba wayar ta katse. Fara ƙoƙarin bin call ɗin ya yi sai ga kiran ya sake shigowa. Kallon kansa a jikin mirror dake gabansa ya yi, hannu ya kai ya ɗan shafi face ɗinsa kafin ya yi picking. "Ka fara barci ne my brother?". Rizwan ya jefa mashi tambayar bayan ya yi sallama kenan. "A'a Yah Rizwan ban yi barci ba, lafiya?" Daga ta cikin wayar ya jiyo saukar ajiyar zuciyar ɗan uwan nasa. "Lafiya lou, amma Jawad ya na ji voice ɗinka haka? Baka da lafiya ne?" Cike da kulawa sosai ya yi maganar. Rizwan da Jawad suna kaunar junansu fiye da tunaninku, yanzu haka King ne ya gayawa Rizwan ɗin yana zargin kamar akwai abin da yake damun mashi marayarsa, shi ne yasa Rizwan ɗin ya kasa barci ya kira shi domin ya ji menene yake damun ɗan uwan nasa, ba zai iya yin barci ba in dai bai san menene yake damun Jawad ɗin ba. One thing da ban gaya maku akan Rizwan and Jawad ba shi ne, Jawad and Rizwan fa uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, dukkansu ba Mammie bace ta haifesu, Mammie matar uncle Abbas ta biyu ce, Sarina ita ce ƴarta ta fari sai Fanan wadda take son Jaish ya aura kenan, ita bata da ɗa namiji. Jawad King Zuhair ne ya renesa, tun ranar da aka haifesa yana cikin tsumma uncle Abbas ya baiwa King shi, shiyasa kuka gansa baya a part ɗin uncle Abbas yake tare da Jaish, tsakaninsa da Jaish kwana uku ne kacal ratar, kusan rana ɗaya aka haifesu kenan, so a tare suka taso, tare suka yi wasa, dan King ya haɗawa Momma sune a Dubai, dan kun san ita a can taken haihuwa, haka kawai King ya zaɓi da ya bata Jawad ɗin ta haɗa da Jaish, ita ma tana ra'ayin rikesa yasa ta roƙa, ko da zata dawo sai ta barosu a can, tare suka yi komai, makaranta da komai har zuwa lokacin da suka dawo ƙasar, wannan dalilin yasa kuka ga suna kaunar junansu shi da Jaish ɗin over. Sannan Rizwan yana kaunar Jawad fiye da tunaninku, dan shi kaɗai yake da shi, ban san dalilin Mammaien na son haɗasu faɗa a kan mace guda ba, suna matuƙar kaunar junansu, ta zo ta cusawa Rizwan kaunar Chuchu bayan tasan Jawad yana sonta. Shi kuma Rizwan yana yi mata biyayya ne saboda a ganinsa ta riƙe shi tsakani da Allah, bata taɓa nuna mashi wani mugun abu ba tun yana yaro, ta riƙe shi kamar ɗan cikinta, bai san da cewa Allah ne ya taimakesa yake tsalle rijiya da baya daga tarkonta har ya kawo yanzu da Allah yasa ya girma ba, bai taɓa kamata tana ƙoƙarin cutar da su ba ko da sunan wasa, to wannan soyayya da ta nuna masu a zahiri kamar uwarsu yasa suke yi mata biyayya sosai. Baɗininta kuma Allah ne kaɗai masani, Allah ne kaɗai yasan me take shirya masu na mugunta? Kuma menene kudirinta a kan Kingdom namu, Allah masani sai alƙalamina, makirar mata ce sosai, ta iya makirci ta yadda ko baka so sai ka yarda da ita ba muguwa bace ta Allah ce, ta iya takunta sosai. So a takaice dai yanzu ga shi tasa dukkansu biyu suna matuƙar kaunar Chuchu ba tare da sun san da cewa ɗaya yana sonta ba, ita kanta Chuchun tana kaunarsu dukkansu biyu, sai dai kaunar da take yi wa Jawad na matsayin yaya da kanwa ne, shi kuma Rizwan bayan yaya da kanwa akwai na masoyi a gefe, wlh Mammie ta cucesu over, a yanzu haka duk wanda ya auri Chuchu daga cikinsu zuciyar ɗayansu wanda bai aureta ba sai ya cutu, koma dai ya zama sanadin ajalinsa, kuma su biyun duk randa ɗaya ya gane ɗaya yana sonta to ba shakka ɗayan zai hakura ya barwa ɗan uwansa..... Akwai matsala kam babba ma kuwa. Gaskiya Mammaien ba ƙaramar muguwa bace wlh! Ta cika bakar azzaluma! Dan ba ƴaƴanta bane shi ne ta gwara kansu a kan mace ɗaya! Ko me dalilinta na yin hakan? Wato su mutu idan ma zasu mutu, Allah sarki shi kuma Rizwan yana ganin kaunarsa take yi sosai har yasa ta zaɓa mashi kyakkyawar mata na gani na faɗa, wadda duk namiji mai lafiya dole ya sota! Har da kara kaunar Mammaien ya ji yana yi da ta yi mashi hakan, bai san rami mai zurfi ta tona ta kuma kunna wuta a cikin ramin sannan ta tura shi ciki ba, shi ya ɗauka madarar kauna ce zalla. (Wai nikam na ce ba ko dai so take duk su haɗiyi zuciya su mutu dan ita bata ɗa namiji ne? 🤔 Ku tayani duba my people's) STORY🔥 "Babu komai Yah Rizwan". Daga other side Rizwan ya ce. "A'a Jawad, babu komai kuma? Ni zaka ɓoyewa abin da yake damunka? Idan baka gaya mun ba waye zaka gayawa? Ko kana son ne nima ka hanani yin barci, ka hanani yin komai? Kasan ba zan iya aikata komai ba matuƙar kana cikin damuwa ko?". "Yah Rizwan please kada ka kwana da damuwa, zan gaya maka, bana son naji wani abin yana damunka". Ya yi maganar tare da nufo kofar fita. Har zai fita kuma sai ya tuna kada Chuchu ta ji abin da zai ce, dan haka sai ya koma ya tsaya a in da yake tsaye ɗazun. "To gaya mun menene yake damun zinariyar zuciyar ɗan uwana?". Rizwan ya faɗa. "Yah Rizwan ba komai bane face kewar ɗan uwana Jaish, haka kawai na ƙasa samun nutsuwa a tafiyar da ya yi, kada ka gayawa kowa fa ya yi tafiya, tafiyar sirrice, amma duk na damu sosai, sai nake jin kamar na bishi, mun yi waya da shi ɗazun yake ce mun yana kewata sosai, da tunanina ya yi barci ya tashi, ina jin kamar bani da lafiya ne haka". Shiru Rizwan ɗin ya ɗan yi na ƴan sakani kafin ya ce. "Shikenan my pleasure, ka yi mashi addu'a, kuma ka cire duk wani banzar tunani a ranka, babu komai In Sha Allah, bana son ganinku cikin damuwa, amma idan kaga ka damu sosai to da safe ka bishi kawai, dan ba zan lamunci ganinku cikin damuwa ba" "In Sha Allah Yah Rizwan zan dai'na damuwa kuma zan yi mashi addu'a". Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya. "To shikenan ka kula mun da kanka sosai da sosai". Da okey ya amsa kafin shi ma ya ce yayan nasa ya kula mashi da kansa, suna kaunar juna sosai, da haka suka yi sallama. Suna sallama ya nufo waje. Kasancewar ɗakin da duhu dan King ya kashe wutar yasa sai ya kunna hasken wutar wayarsa, nan take haske ta gauraye wajen, gaban bedside drawerta ya je ya zauna. Hannu ya kai ya yi ƙasa da bargon da King ya rufeta da shi ita kuma ta kara ja har sama ta rufe kanta gabaɗaya. Ƙasa ya ɗan ja bargon zuwa dai'dai kirjinta, hasketa ya yi da hasken wayarsa, ta lumshe idanu kamar mai barci. Zubawa kyakkyawar fuskarta idanu sosai ya yi, a nan ne ya fahimci ba barci take yi ba, da gangan ta lumshe mashi idanunta. Siririn murmushi ya saki kafin ya kai hannu ya ɗan shafi face ɗinta. "Tashi to, na gano baki yi barci ba". Kin kula shi ta yi, irin ita a dole ta yi barci da gasken nan, ga kuma idanunta yana gani suna rawa duk da suke lumshe. Jin taki kula shi ta dake a zaman dole ta yi barci ne yasa ya kifa wayarsa a saman bed ɗin ta wajen hasken, nan take duhu ya karaɗe ko'ina. Hannu ya kai ya toshe mata hanci saboda tsokana. A firgice ta buɗe idanun haɗe da cewa. "Wayyo Yah Jawad zaka kashe ni, wai me nayi maka?". Zame hannunsa ya yi ba tare da ya yi magana ba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da yunƙurawa ta miƙe zaune. Wayarsa ya ɗauko daga kifata da ya yi, haske mata fuska ya yi tana ta aikin turo baki. "Awww ashe baki yi barcin ba, amma meyasa kika yi mun barcin karya?". Tana aikin turo baki ta ce. "Ni fa wasa na yi maka, amma shi ne ka kusa kashe ni?". "Da gaske wasa aka mun?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "Jannat ya za'ayi in kashe ki? In na kashe ki ai kai'na na kashe! Dan nima ba zan kai labari ba! Kina mutuwa zan biki! Nima da wasa na toshe maki hanci, baki ga na sakeki da wuri ba? Ai na sake ki da wuri ne dan ma kada wani abin ya samun min ke". Yana magana yana kara kare mata kallo daga sama har ƙasa, dan iya shege sai kalle mata kirji yake yi a cikin sleeping dress ɗin, da yake kayan sun zauna a jikinta dai'dai ita, sai alamar komai ya bayyana. Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Amma fa Yah Jawad akwai wahala idan aka toshewa mutun hanci!". Ɗan zaro idanu ya yi tare da cewa. "Kunji wahala ne?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "Kaɗan fa na ɗan rike maki hancin, amma kin ji wahala?". Kai ta gyaɗa mashi still tana turo baki. Hannu ya kai ya ɗan shafi kumatun nata. "Sorry my Jannat, ba zan ƙara ba, to yi murmushi". Haɗaɗɗen murmushi ta sakar mashi wadda ya sanya shi sakin murmushi shi ma. "To shikenan ni zan wuce bedroom ɗina, sai da safe ko?". Ƙasa ƙasa ta ambaci sunan. Lafiya ya amsa mata da shi. "Allah Yah Jawad bana son ka tafi, ina jin daɗin yin hira da kai". Ajiyar zuciya ya sauke tare da duba time a wayarsa. 11:44, "Jannat dare ya yi fa, ki kwanta ki yi barci akwai school gobe". Ɗan turo mashi baki ta yi kafin ta amsa mashi da to. Miƙewa ya yi zuciyarsa cike tab da tunanin zai yi kewarta, ɗan matsowa ya yi ya bata sumbata a goshinta kafin ya ce ta kwanta bari ya mayar mata da bargonta ya lulluɓeta. Ba musu ta kwanta, ya lulluɓeta, zuciyoyinsu bai so rabuwa ba, amma haka ya yi mata sallama sai turo baki take yi ya fice zuwa nasa room ɗin. Yana tafiya ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita ba tare da ta kunna wayarta ba, daɗin hira da Yah Jawad yau yasa ta manta da hira da Yah Rizwan. Shi kuwa a nasa ɓangaren ko da ya kwanta bai iya yin barci ba, tunani ne kala kala cike tab a ransa, har wuraren karfe 2 ya gagara barci, daga karshe ya miƙe ya ɗauro alwala ya zo ya fara gabatar da nafilfilu. Washegari da safe misalin 6:30. Shirye yake cikin wandon Jeans baka, daga ta sama t-shirt fara ce tas, sai ya ɗaura long coat zuwa gwiwarsa a saman kayan, ita ma coat ɗin baka ce kalar wandonsa, takalmar kafafunsa ma bakake ne, matsayinsa na farar fata sai bakaken kayan suka yi mashi kyau, ga arab hairnsa bakin kirin da shi ya sha gyara. Kai tsaye part ɗin Akka ya nufa sai zuba kanshi yake yi, office zai je yau da wuri, amma yana da buƙatar sanya ta a idanunsa kafin ya tafi, yasan kuma a part ɗin Akka kawai zai sameta by this time around. Dai'dai zai shiga part na Akkar shi kuma uncle Taheer kanin Mama yana fitowa, kusan karo suka yi, da sauri ya ɗan ja da baya yana faɗin good morning uncle. Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mashi tare da tambayarsa ya ya kwana ya kuma ya wayi gari. Da Alhdulillah ya amsa kafin ya wuce ciki, shi kuma uncle Taheer ɗin ya fice ya nufi part na mama dan ya duba jikinta............. Allah sarki mama, su Omaid sun ja mata bala'i, sun barta da jinya, suna can gidan Abu Abdussalam, ko me suke aikatawa yanzu?...🤔 Baki a ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin. Babu kowa sai Chuchu dake ta ƙoƙarin sanya uniform ɗinta, yanzu Akka ta shiga toilet bayan sun gama gaisawa da uncle Taheer, ita kuma Chuchu uncle Taheer ɗin yana fita ta hau shirin zuwa school, dama ta yi wanka shigowarsa ɗakin yasa ta zauna suka gaisa. Ta zura rigar a kanta tana kokawar sauke shi ƙasa, da yake rigar dai'dai ita yake hakan yasa sanya shi yake ɗan yi mata wahala. Cike da tsokana Jawad ɗin ya ƙariso ciki, samar rigar ya rike ya hanata janyo shi ƙasa. Ja da karfi ta yi sai ta ji kamar an rike, ga shi bata iya gani bare taga wanene? Dan ta zura rigar a kanta. A ƙule ta ce. "Auta bana son walaƙanci fa, zaki sakar mun riga na samu na sauke shi kasa na shaki numfashi ne ko sai kin kashe ni?". Shiru bai amsa mata ba, sai ma da shaiɗan ya ɗan ruɗesa ya zura hannunsa daga ta bayan nata izuwa saman plat tummynta. Janyota ya yi ta zo jikinsa. Sai surutu take yi a tunaninta Auta ce, sai da ya ɗan wahalar da ita kafin ya sakar mata rigar tare da jan mata shi ƙasa har lokacin hannunsa yana saman cikinta. Yana sakar mata rigar bayan ya sauke mata a hanzarce ta fara ƙoƙarin juyowa domin taga wanene? Hanata juyowa ya yi ta hanyar ƙara ƙanƙame mata ciki. A garin ƙanƙame ta ɗin kuwa hannunsa ya ɗan haura sama izuwa kusa da kirjinta, hakan yasa ta kurma ihu mai sauti wadda tasa dan dole ya saketa a ɗari ya shiga dressing na Akka. Yana shiga Akka kuma ta fito daga cikin toilet cikin zafi tana faɗin. "Nashi uku! Jannat lafiya? Ihun me kike yi?". Ƴar waige waige ta fara kamar mai neman wani abin, kuma fa ta gansa lokacin da ya shiga room ɗin, amma ta rasa ita kanta waige waigen me take yi, ta kuma rasa me zata gayawa Akkar. Shi kuwa sai addu'a yake yi Allah yasa kada Jannat ta gayawa Akka shi ne ya taɓata ta yi wannan ihun, yasan halinta sarai, idan ba shi ya ce kada ta faɗa ba Akka na tambayarta zata shi ne ya zo ya taɓa mata kusa da kirji, yasan yanzu da wuya idan ba gaskiya zata gayawa Akkar ba, ya shiga talatin yau ba uku ba. Da alama addu'ar King na daren jiya ne ta kama shi, dama King ya gaya mashi one day one time Akka zata kama shi yana yi mata soyayya a ɗaki, kuma idan ta kama shi ya shiga uku, to da alama yau ranar tonon asiri ne....... 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥 Ko da Leesharh ta shiga cikin kitchen ɗin sai ta rasa ina zata nufa, ma'aikata ne birjik suke maƙare a ciki suna ta aikin dake gabansu, babu wadda ta ɗaga idanu ta kalleta ma bare ta sa ran zata iya tambayarta. Da farko a tunaninta abin da sauki ne, sai yanzu ta fahimci isn't easy ooooo, damuwa ta shiga sosai, ta rasa wa zata tinkara da zancen?. Ta juya gabas da yamma gudu da arewa a cikin kitchen ɗin nan bata ga ƴar aikin da fuskarta yake a sake bama bare ta tinkareta, ga shi babu wadda ta kulata, sai ka ce basu ji shigowar mutun ba. Ita fa Leesharh bata ma san da cewa masu girki daban, masu shirya abinci a parlourn daban, sannan masu serving ƴan gida abinci suma daban, bugu da kari masu kaiwa zaratan samarin gidan abinci suma daban suke. To a gabaɗaya cikin kitchen ɗin nan a yanzu dai iya masu yin girke girke ne a ciki, a lokaci guda sai a girka abinci almost kala sha biyu, kunga kuwa dole masu yin girkin su kasance suna da yawa, kowacce da aikin da take kamawa, haka zalika kowacce da kalar girkin da take yi, kun san laraba da iya shirya abinci kala kala a saman table. Idan suka kammala yin girkin ne sai masu kwasa su kai dining room su shirya a saman table kuma su zo su fara aikin jidansu su kai, masu kaiwa su Ramish suma su zo su kwasa nasu, haka tsarin gidan yake, Ta kai almost 30 mins a tsaye a tsakiyar kitchen ɗin babu wadda ta ce mata ko ci kanki. Da dai taga tsayuwa ba zai amfana mata da komai ba sai ta duba a cikinsu ta ga mai ɗan dama dama dan ta nufeta. Can ta hango wata ƴar matashiyar yarinya da ba zata wuci 17 year ba a duniya, sai aikin yanka kayan lambu irin su Chinese cabbage, cucumber da dai sauransu take yi. Ita kuma sune aikinta, sai ta wuni tana aiki ɗaya, dan duk girkin da za'ayi ana amfani da haɗin salad dan cin abincin, da rana haka da daddare haka, ga gidan da girma da kuma yawa, cikin wani katon kwando mai girma take yankawa, da yake ta saba sai sam bata ganin wahalar aikin. Sannu Leesharh ta yi mata, yauwa ta amsa da shi, ta amsa kuma ba tare da ta ɗago ta kalli Leesharh ɗin ba, saboda aikin da yake gabanta, daddatsa su cabbage ɗin take yi babu wasa, cikin sauri sauri saboda ta kware, kwararriya ce. Shiru ta yi tana tunanin ta yadda za'ayi ta tambayi wannan yarinyar abin da take buƙata. Ta ɗan yi nisa cikin tunanin da take yi kawai ta tsinkayo muryar yarinyar a kunnenta tana faɗin. "Kina buƙatar wani abin ne? Da me zan iya taimaka maki?". Tana ƙoƙarin yin magana wani tunani ya faɗo mata a cikin ranta, ba komai bane kuma face tunawa da ta yi da akwai cameras sosai a cikin kitchen ɗin, tambayar mai kaiwa Ramish abinci a wajen babbar barazace a gareta, dan ana ganinsu. Tuna haka yasa ta yi maza ta juya ta fita ba tare da ta sake cewa yarinyar ko sannu ba......... Kai Leesharh fa tana da basira sosai yarinyar. Kai tsaye room nata ta nufa domin ta je ta sake yin tunani a kan mafitarta. A dai'dai lungun da ta yi wa Ramish laɓe ɗazun suka ci karo da mutun, kasancewar wajen babu wadatatcen haske dan a tsakanin ɗakuna yake, kuma wajen babu Camera. Rashin haske yasa bata san da waye ta yi karo ba, sai dai koma wacece tabbas macece, dan karon da suka yi kirjin wancan ta buji kafaɗunta, to ta ji tana da breast. Wucewa ta yi da sauri ba tare da buƙaci sanin da waye ta yi karo ba. Ita ma wadda suka yi karon a hanzarce ta wuce kamar maras gaskiya. Dakatawa da yin tafiya Leesharh ta yi tare da juyowa ta bi yarinyar ne ko matar za'a ce ne da kallo, haka kawai sai ta ji gabanta ya faɗi, ji tayi bata yarda da matar ba, duba da yadda ta wuce da sauri kuma bata yi magana ba, ita ce ta bugi Leesharh ɗin, amma bata ce mata ko uppan ba ta wuce da uban sauri har haka, hakan yasa Leesharh zarginta sosai. Da sauri ta juyo domin ta bi bayanta ko idan suka fita haske zata iya ganin wacece?. Sai dai kash! Kafin ta fito wajen haske sam bata ga ko mai kama da alamar matar ba, ta ɓacewa ganinta, da alama wani lungu ta shiga ko kuma wani wajen. Jiki ba kwari ta juya ta nufi hanyar koma ɗakin nata. Tana barin wajen matar ta fito daga in da ta laɓe ta kusa da hanyar shiga part ɗin su Ramish, ashe tasan Leesharh ɗin ta biyo bayanta, da gaskiyar Leesharh matar bata da gaskiya, kuma ɗaya ce daga cikin masu aikin gidan wadda take a hawa na biyu, ko me ya kawota nan? Ko me ta aikata take wannan uban sauri har da ɓuya haka?. A bakin gadonta ta zauna tare da buga uban tagumi tana tunanin yadda zata ɓullowa wannan al'amari. Wayarta ta janyo domin ta duba ko matan nan sun turo mata wani saƙo. Tana kunna hasken screen ɗin wayar sai ga saƙon kuwa ta ci karo da shi sun turo. Buɗewa ta yi ta fara karantawa duk da ba wani kwarewa ta yi a karatun ba. Ba wani saƙo suka tura mata ba face cewa da suka yi ta duba cikin akwatinta sun ajiye mata maganin da suke son ta zubawa Ramish a cappuccino, dan haka ta ɗauko maganin kuma ta kula. Zaro idanu ta yi tana mamakin ta ya akayi suka iya kawo mata maganin kuma? To ko dai suna tare da ita a cikin gidan ne bata sani ba?. Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufi wajen akwatin nata. Tana zuwa ta buɗe akwatin da wuri, ga mamakinta sai ga maganin a saman kayanta kamar yadda suka faɗa. Ita dai tasan ɗazun da ta ɗauki kayan sakawarta babu magani a ciki. Maganin a cikin wani ɗan ƙaramin kwalba yake, kamar kwalbar maganin ciwon idanu, zubawa maganin ido ta yi tana kallonsa, tana son sanin maganain menene? Sai dai ba dama, dan basu gaya mata ba, ita kuma bata isa ta ce zata nunawa Sharifat ta ce zata tanbayeta ko ta san na menene bane, kada ta zo ta ɓata aikinta, amma tabbas tana son sanin maganin menene kafin ta zubawa bawan Allah. Zuciyarta na ta ayyana mata maganin nan cutar da shi zai yi, zantukan babanta take yawan tunawa a kullum in da yake yawan gaya mata kada ta kuskura ta cutar da wani a duniyar nan, da ta cuci wani gara a cuceta, wannan dalilin yasa duk wani aiki da zasu sakata take yawan shiga zulumin a kan kada ta je ta cutar da wani. Ta jima sosai a wajen tana tsugunne tana kallon kwalbar maganin kafin daga bisani ta miƙe da maganin riƙe a hannunta, sannan ta rufe akwatin nata, shi kuma maganin ta tura a cikin aljihun wandon jikinta. Waje ta sake nufa domin kudurinta na neman mai kaiwa Ramish abinci, tana da jajircewa da kuma kafiya a kan abin da ta sanya a gaba, kuma bata taɓa sanyawa ranta sarewa ko karaya. Sai dai a wannan karon tana yi tana fargaba tare da tsoron kada ta cutar da bayin Allahn da basu ji ba basu gani ba, mutanen da suka karɓeta hannu bibbiyu, suka yi mata gatan da bata taɓa samun makamancinsa ba a rayuwarta, bata taɓa yin tunanin zata taɓa samun irin wannan gata ba, sun bata bedroom haɗaɗɗe, ga cima mai kyau, ga sabulai masu zafi na gyaran jiki, ga haɗaɗɗun kayan sakawa duk bayan wata guda ana sayo masu dayawa, gasu da halacci da kirki sosai. Amma idan ta tuna mata mai nikaf ɗin can ta ce mata ba cutar da shi zasu yi ba, taimakonsa zasu yi, sai ta ji sanyi a ranta, sai ta ji zata iya aikata komai dan ita ma ta taimaka da nata gudunmawar. Amma wani ɓangare na zuciyarta ya ki yarda a kan taimakonsa suke son yi. Tana da ƙwaƙwalwar da basira sosai, amma akwai yarinta sosai a tattare da ita. Masu nikaf kuma da wannan yarinta tata suke amfani dan cika burinsu!!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 13/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________51🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼 KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 "Jannat lafiyarki kuwa?". Akka ta sake faɗa cike da damuwar son sanin me ya sami jikar tata ta zunduma ihu haka. Dawo da kallonta a kan Akkar ta yi, a hankali ta sake satar kallon dressing room ɗin, da farko kamar zata gaya mata gaskiya, amma sai wani tunani ya faɗo mata a rai, tunawa ta yi cewa to idan har Yah Jawad zai gudu ya ɓuyan wa Akka bai kamata ta gaya mata cewa yana nan ba, yin hakan zai sanya ya ji babu daɗi. Wannan tunani yasa ta dawo da kallonta kachokam kan Akkar. "Akka babu fa abin da ya sameni, ji nayi ne kamar wani abin ya shiga mun cikin rigata yana tafiya, shiyasa na yi ihu" Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke daga in da yake tsaye, sanyi sosai ya ji tana ratsa zuciyarsa, ba ƙaramin daɗi ya ji da bata faɗi gaskiya ba, sai albarka yake saka mata a cikin zuciyarsa. Matsowa kusa da ita a hanzarce Akkar ta yi, riƙota ta yi tana faɗin bari ta duba cikin rigar tata ta gani kada ya zamana akwai wani abin a ciki ya ji mata ciwo, ko ya cutar da ita. Ƙanƙame rigarta ta yi bata son Akka ta kalle mata tula tulanta, mamaki ne ya kama ƴar tsohuwan. "Jannat lafiya? Ki bari na duba mu gani". Girgiza kai ta fara yi. "Akka ni ba sai kin duba ba, koma menene ya tafi, kuma ma babu komai a ciki ni ce na ji kamar da akwai wani abin". Ta faɗa tana turo baki. Haba da yake Akka sarauniya ce wajen iya magana, tuni ta fara sababi. "Ah ah ah lallai Jannat, ƴan nonuwar naki ne baki son in gani ko menene?" Nan fa ta fara jero mata kan cewa ai ba ita ba su Aunty MieMie duk taga nasu bare ita, dan haka sai ta duba..........😅 Dariya ne ya so kubcewa Jawad dake laɓe cikin room, yana jiyo duk abin da suke faɗa, yau yaga ikon Allah, yarinya da kayanta Akka ta ce sai ta duba, duk sai ya ji haushi za'a kalle mashi abin da shi ma bai taɓa kalla ba, wai shi ya zai yi da Akkar nan ne? Mata idan ka nuna baka son abu sai ta ce sai ta yi shi, ita fa idan taga kana kin abu ka ce baka so, sai ta ce rashin gaskiya ka kullah a wajen, dan haka sai ta ce sai ta gani!!. Jawad dai bai ji daɗin hakan ba, dan yasan ran Chuchunsa zai ɓaci sosai, babu wata budurwa da take tasowa wadda zata so a kalle mata abinta, bare ma idan tana da kunya, wannan dabi'a ce ta mata, a jininmu yake. Ita kam Akka ta kafe sai ta duba cikin rigar, ita kuma Chuchu taki yarda har da kukanta, ran Jawad ya ɓaci sosai, kamar ya kifawa Akkar nan mari yake ji, sai dai ba hali, ya suka iya da ita? Ai dole sai hakuri. Da Akkar ta ga da gaske kuka Chuchun take yi da hawayenta, sai ta kyaleta ta koma cikin toilet dan dama wanka zata yi, tana shirin farawa kenan ta jiyo ihunta, so sai ta koma kawai tana yi mata sannu haɗe da surutun Chuchu na ɓoye mata ƴan nonuwa. Tana shiga cikin toilet ɗin ya fito da sauri, ransa a ɓace saboda sanya mashi beb ɗinsa kuka da tsuhuwar nan tasu ta yi. Ya ɗaure fuska kamar hadari. Yana zuwa in da take ya riƙo hannunta tare da ɗauka mata school back ɗinta dake saman gadon Akkar wadda ta ajiye da kanta. Ya riƙo hannunta tare da nufar kofar fita. Har lokacin ƴan siraran hawaye suna bin saman ƙuncinta. Kai tsaye part ɗinsa ya wuce da ita ba tare da ya ce mata ko uppan ba, ya kuma yi sa'a bai ci karo da kowa a hanya ba har ya isa part ɗin nasa, kasancewar da safe ne kowa yana can yana ta faman aikin shiryawa, masu zuwa school suna nasu shirin, masu zuwa office suna nasu, masu yin breakfast suna fama, kowa dai yana room nasa yana abin da yake yi. A bakin bed ɗinsa ya zaunar da ita tare da ciro handkerchief mai kyau daga aljihunsa, ya zauna saman bedside drawer, a gefenta ya ajiye mata jakarta kafin ya kai hannu a hankali ya fara goge mata hawayen nata. "Am so so sorry my sister, duk ni na ja maki yin kuka da sassafen nan, kyale Akka hai ki dai'na kuka ba zata gani ɗin ba". Ya faɗa ƙasa ƙasa. Ƙasa ta yi da kanta, kunyarsa take ji sosai saboda ya ji yadda suka yi da Akka, ga Akka bakinta babu full stop ta rinƙa kiran sunan tula tulan a tsiraransu, abin ku da tsoffi sam bata wani sakaya sunan ba, ta rinƙa ambatarsa ba kakkautawa, wannan dalilin yasa Chuchun ta ji tana bala'in kunyar yayan nata, dan ya ji komai. Shi ma ya fahimci kunyarsa take ji, sai ya kawar da zancen da cewa. "Yau na kai ki school da kai na ko?". Ya yi maganar yana ƙurawa jikinta ido, gani yake kamar gizo idanunsa suke yi mashi, kamar kuma da gaske ne bata sanya vest a ciki ba, kuma bata sanya bra ita. Yana son ya tambayeta kuma yana jin fargabar yadda zata ɗauki abin, tsoro yake ji kada ta kalli hakan da wata manufa ko kuma ta fara gudunsa ko dai ta fara jin kunyarsa sosai. Idan ɗaya daga ciki ya faru ba zai ji daɗi ba!. Wani tunani ne ya faɗo mashi cikin ransa, idan ya tashi daga office ya je ya yi masu shopping na vest dayawa ita da Auta, sai ya bawa Autar ya gaya mata kada su sake saka kaya ba tare da sun saka vest a ciki ba, wannan ce tunanin da ya yi, yanzu haka sam ransa bai so ta tafi school a haka ba, amma ba yadda zai yi, idan ya ce zai yi mata magana a yanzu to tabbas zata haɗa maganar da abin da Akka ta yi mata ta kwaɓesu, daga haka zata fara ja baya da shi. Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e ya kaita school da kansa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Kin yi breakfast ne?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a. Waya ya ɗauko ya kira kuyanga Zubaida a kan ta kawo mashi kayan breakfast yanzu. Yana ajiye wayar ya hau janta da hira dan ta saki jiki ta mance da abin da Akka ta yi mata ta koma walwalarta. Ba'afi minti biyu da kiran da ya yi wa kuyanga Zubaida sai gata ta iso baki ɗauke da sallama. Izinin shigowa ya bata ba tare da ya kawar da kallonsa daga kan Chuchu dake ta faman murmushi ba, har ya mantar da ita kuncin da take ciki, ya sanyata farinciki. Saman carpet ya yi mata umarnin ta ajiye mashi abincin, a hanzarce ta karɓi umarninsa tare da aiwatarwa. Bayan ta fita ne ya ce da Chuchun ta zo su je su yi breakfast a tare. To ta amsa mashi da shi, hannunta ya riƙo suka nufi wajen kayan abincin. Zama ya yi tare da zaunar da ita a kusa da shi. Cup mai shake da coffee mai zafi ya ɗauko ya kai mata bakinta. Ba musu ta buɗe baki ta fara karɓa. Wayarsa ce ta fara kara daga cikin aljihun coat ɗin jikinsa. Hannu yasa ya ciro wayar tasa. Yah Rizwan, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Cigaba da bata coffee ɗin ya yi yana haɗa mata da pepper soup na kaza mai bala'in daɗi. Cike da kaunar yayan nasa ya ɗauki wayar yana kuma mamakin kiran da yayan nasa ya yi mashi da sassafe haka. "Assalamu alaikum Yah Rizwan barka da safiya". Ya faɗa cikin nutsuwa, yana magana yana yanko tsokar kazar yana cusa mata a baki. Ta saki jiki sai ci take yi abinta. "Jawad ka tashi lafiya?". Rizwan ya tambaya, daga jin muryarsa kasa yana kaunar ɗan uwan nan nasa sosai, sannan muryarsa da alama damuwa matuƙa a tattare da ita. Da lafiya lou Alhdulillah ya amsa mashi da shi, sannan ya ɗaura da cewa. "Yaya ya naga ka kirani da sassafe haka? Ko dai akwai wata matsala ne?". Sai a lokacin Chuchu ta ɗago idanu tana kallonsa jin ya ambaci matsala. Daga ɗayan ɓangaren ya amsa mashi da. "E akwai matsalar babba ma kuwa, amma ba ita ce tasa na kiraka ba, na kiraka ne dan naji ya ka kwana? Ya kuma ka tashi? Jiya ban samu ishasshen barcin kirki ba, saboda tunaninka". Miƙawa Chuchun cup ɗin coffee ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye ya nufi hanyar fita yana faɗin. "Matsala kuma Yah Rizwan? To matsalar me? Meyake faruwa?" Bin shi da kallo ta yi har ya ficewa ganinta. Cigaba da cin abin nata ta yi tana tunanin to matsalar me aka samu kenan?. After some minutes ya dawo cikin ɗakin fuskarsa babu annuri ko kaɗan, da alama Rizwan ɗin ya gaya mashi wani abin da ya ɗaga mashi hankali sosai, jikinsa duk ya yi sanyi sosai kamar ba shi ba. Kusa da ita ya koma ya zauna yana faɗin. "Jannat ci abinci da wuri na kai ki school akwai in da zanje". Cikin sanyin murya ta ce. "Yah Jawad kai fa? Ba zaka yi breakfast ɗin ba ne?". Kai ya gyaɗa mata alamar e ba zai ci ba, sannan ya ɗaura da cewa. "Sauri nake yi, ki ci da wuri in kaiki school ke dai, idan na dawo daga in da zan je zan yi breakfast ɗin". "Yah Jawad meyasameka naga fuskarka ta sauya haka". Ta faɗa tana kallon face ɗin nasa. Babu komai ya amsa mata da shi, sannan ya fara ƙoƙarin kiran number Jaish domin su gaisa su kuma yi magana, dan basu yi wayaba, ya so ya kira shi tun farkawarsa daga barci, amma bai samu dama ba, ya sha'afa. Ringing wayar ta yi har ta katse ba'a ɗaga ba, duba time ya yi a danƙareriyar watch dake hannunsa. 7:05 am, yakamata ace Jaish ya tashi barci yanzu ai. Ya faɗa a bayyane tare da sake gwada kiran number. A karo na biyu ma ba'a ɗaga ba. Knocking na kofar ɗakin da aka yi ne ya ja hankulansu shi da ita izuwa bakin kofar. Kasa ƙasa ya furta wanene?. Daga wajen kuyangarsa ta amsa mashi da ita ce, tazo tana son fara yin aikinta ne na gyaran ɗaki. "Ki je sai anjuma ki dawo". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a kan wayarsa da call ya shigo ciki yanzu. Mammie, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗauki call ɗin, yana sonta, ya ɗauketa kamar uwa, saboda yana ganin cewa tana son su kuma ta rike su kamar ƴaƴan cikinta. "Good morning Mammie". Ya faɗa cikin sanyin murya. Tana daga zaune saman sofa a fatafaren parlournta, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, kamar kullum tana cikin haɗaɗɗen kwalliyar nan nata na alfarma, ga ruwan madaran gwala gwalai da ta zuba wuya da hannu, ta fito a hamshakiyarta, ta ko'ina dai bata da makusa sai bakar zuciyarta, kyakkyawar macece ga iya ɗaukar wanka, sai dai kash, kyan ɗan macijine. Daga gefenta wata hamshaƙiyar budurwace take zaune mai tsananin kama da ita, daga gani ba tambaya kasan kanwarta ce, dan sun yi kama sosai, yarinyar ba zata wuci 25 to 27 years a duniya ba, ita ma kyakkyawace, ga shi ta iya ɗaukar wanka kamar Mammie ɗin, yanzu haka ta sha wanka, duk wanda ya kalleta sai ya sake waigowa ya kalleta, da alama abin ya samo asali ne, duk yadda aka yi ainahinsu ƴan son gayu ne sosai. "Morning Jawad how was your night?". Ta faɗa tana kallon kanwar tata. Bayan ya amsa mata sai ta ce. "Kafin ka tafi office ka sameni a parlour mu ɗan yi magana". Da okey kawai ya amsa mata, katse kiran ta yi tana bin kanwar tata da kallo. "Aliyah lafiya kike cunkushe rai haka?". Kara tunɓune fuska kanwar tata ta yi kafin ta ce. "Aunty ba dole na turɓune fuska, ni ban san ya zan yi ba, saboda King nake zuwa gida nan, amma har in je fadarsa in gaishesa in fito baya ɗaga idanu ya kalleni, kuma ni ina matuƙar sonsa Aunty"............. Tashin hankali kenan, yau ake yinta, ita King ɗin da kansa ma take so ba ƴaƴansa ba, lallai wannan ta ɗebo da zafi, kai bama da zafi ba ta ɗebo mai tafasa!!. Wani irin zaro idanun Mammaien ta yi, tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa. "Amma dai Aliyah baki da hankali! Ko dai kin sha wani abin ne yau kafin ki zo gidan nan! King Zuhair ma kike magana ko wani King ɗin da ban sani ba?!". Cikin tashin hankali ta yi maganar. Kara turɓune fuska sosai ta yi. "Aunty idan ba King Zubair ba wani King muke da shi mai power a ƙasar Tunisia? King Zuhair nake magana a kai mana, kuma shi nake so, shi nake burin aura, In Sha Allah kuma ni ce cikon matarsa ta huɗu! Da ni zai rufe kofa, ko ana ha maza ha mata wlh sai King ya aureni!!". Babbar magana!. "Aliyah lallai mutuwa kike nema, wlh idan baki yi hankali ba a ɗanya ƴaƴansa zasu cinye namarki, wai ke Aliyah ni da nake nan ina ta faman yadda zan yi in ga King auri Jahiz ɗan autan su King ɗin, shi ne bashi da aure, bai taɓa yin aure, matashi saurayi ne mai jini a jika, ga shi shararren mai kuɗi, duk duniya ta san shi, ya fi Abbas fa kuɗi nesa ba kusa ba, ke in takaice maki ma wlh zai iya fin King Zuhair ɗin ma kuɗi, ga shi sabon jini, shararrene da duniya dukka suna san shi, shi ba iya ƙasar Tunisia ne kawai aka san shi ba, duniya gabaɗaya ta san shi, shararren ɗan kwallo ne da yake bugawa Real Madrid, ke kanki kin san da haka, kin san Jahiz ganinsa da ido ma ba abu bane mai sauki, ko a cikin family na kusa kusa ba kowa yake samun damar ganinsa ba, ni kai'na da nake matsayin matar yayansa ma idan ya zo gidan nan ba samun ganinsa nake yi ba, idan kinga na gansa to yayansa yana nan, nan ne zai shigo wajen yayan nasa, a nan nake samun damar ganinsa, kuɗi iya kuɗi yana da shi, ga shi sabon jini matashi, me kuma zaki buƙata....." Katseta Aliyah ta yi da cewa. "Sarauta! Yana da sarauta ne? Duk kuɗinsa a banza idan ba shi da mulki, burin mulkar ƙasar Tunisia nake da shi ni ba kuɗi ne a gabana ba, burina in yi mulki, in zama mai faɗa aji, dan haka yasa nake son zama mace ta huɗu da zata rufe kofa a zuciyar King Zuhair....." Tashin sense!!. "To idan mulki kike so ai magajin masarautar zaki ci burin ki aura, magajin wannan powerful seat ɗin zaki kwaɗaitu da son aura, ga Ramish! Ga Bilal! Ga Suraj! Ga Jaish! Sannan ga Aryan! Ɗaya daga cikinsu yakamata ki zaɓa ai, dan sune zasu gaji wannan kujera mai matuƙar power da karfin ikon, in dai burinki ki zama mai faɗa a ji a faɗin ƙasar Tunisia ne to ɗaya daga cikinsu zaki buƙata........" Kara kwaɓe fuska ta yi tare da wurgawa Aunty tata wani irin kallo mai kama da zargi. "Gaskiya Aunty kanki baya kawo wuta sam sam, ni fa ba ce maki na yi ina son in auri wanda zai yi mulki a nan gaba ba, so nake na haifi wanda zai yi mulki a nan gaba, kina tunanin ko na auri ɗaya daga cikin ƴaƴan King zan samu yadda nake so ne? Gaskiya Aunty sam baki tunani mai kyau, ai ko na auri magajin kakkarfar kujerar izza buƙatata bata biya ba, dan dai ke da kanki kin san ƴaƴansa ba masu juyuwa bane, baki isa ki juyasu yadda ranki yake so ba! Amma idan kika auri uban kika haifi naki ƴaƴan, ko ba yanzu ba nan da shakaru 20 zuwa da 25 zaki zama yadda kike burin ki zama, zaki zama mai karfin iko, a duk lokacin da aka ce ɗanki ne a saman wannan the most powerful seat ɗin, sannan ya sanya powerful Crown a kansa, ai kinga daga nan zaki murza kambunki son ranki a faɗin ƙasar, amma idan kika biyewa ƴaƴan nan nasa sai su ce maki basu son sarauta kamar dai Yah Abbas, kin ga shi ma ya ce maki baya sha'awar sarauta, to nasan ƴaƴansa ma yadda suke shararrun ƴan bokon nan ba wani mulki da za su yi, shiyasa bana son na auri magajin mulki, nafi son na haifi magaji wadda ko ya ce baya son ya yi mulki zan tursasa shi dole ya yi, sannan shi Jahiz da kike magana kada ki manta bashi da gadon mulkin nan a yanzu, dan King yana da yara, da bashi da yara ne sai kaninsa ya hau kujera........" Kallon tsab Mammie ta yi mata. "Lallai Aliyah kin girma, waye ya ce maki Jahiz bashi da gadon mulki? Yana da shi mana, idan su Ramish suka kekashe ƙasa suka ce basu da ra'ayin mulkar ƙasar Tunisia ai dole idan King ya tsufa Jahiz ya karɓesa tun da Abbas baya ra'ayi". Cike da rashin respect a maganar tata ta furta. "Aunty koma dai menene ni magajin nake son haifa, magajin da ko baya son mulki zan tursasa shi yi dan cinmma burina, dan haka ni King Zuhair ne burina, shi nake son aura!". "Aliyah King Zuhair ya fi karfinki, Jahiz shi ne zaɓin da na yi maki, dan haka ki dai'na maganar King!!". Cigaba da wurga mata kallon zargin ta yi, a ƙule ta ce. "Aunty saboda kema kina da burin auran King Zuhair ɗin shi ne kike son hanani ko? To ki bari mana kowacce ta gwada sa'arta, a cikinmu duk wadda ta samu nasarar mallakarsa ai shikenan duk ɗaya muke, ni dai ba zan hakura da burina kuma muradina ba"............... Tashin sense, lallan yanzu KINGDOM OF POWER zai kama da wuta, na ce ba my people's mu gayawa Aliyah wacece Momma ne ko dai mu bari ta Momma ta gwada mata karfin jinin Modarawa?🤔 Tab kuna tunanin da Momma King ya fara aura ma zai kara aure ne? Ai da ba wannan magana kuma kun sani, hmmm Hajiya Aliyah momma kam dai'dai take da zamaninki, ga Mama a gefe, sannan ga mummy, uwa uba ga su Ramish, wai kuna tunanin su Ramish zasu yarda King ya auri wadda suka girma ne?🤔 Gaskiya akwai rikici a wanan gida ba kaɗan ba. "Aliyah ni kike gayawa ina son auran King Zuhair? A yaushe muka yi hakan dake?". Ta yi maganar cike da mamaki tana kuma zaro idanun. "Kina mamakin ya aka yi nasan burinki ne Aunty? To bari ki ji ranar da kika je gida ina jinki ke da mama kuna magana a kan ke dama ba Yah Abbas kike so ba, King Zuhair kike so, dan burin mulki kike da shi, kuma ko za'a mutu ko za'ayi rai, ko rai nawa zaki iya salwantarwa domin ki auri King ki haifi maganin Crown of Kingdom of power!!". Kara zaro idanu sosai Mammie ta yi, bata taɓa tunanin bayan mahaifiyarsu akwai wadda tasan da wannan magana ba, sirrinta ne kuma burinta!. "Aunty ki dai'na yin mamaki fa, kuma ki dai'na ƙoƙarin hanani mallakar abin da zuciyata take so, Crown na kingdom of power rawani ne da kowani basarake yake burin samunsa, kujerar mulkin kingdom of power kujerace da jiga jigan sarakuna masu karfin iko suke fatan su zauna a kansa, masarautu ba adadi ne a ƙarƙashin wannan masarauta, duk wani karfin ikon mai karfi a faɗin ƙasar nan dama maƙota ƙasashe duk a ƙarƙashin King Zuhair suke, a haka kike son nayi wasa da wannan dama? Sanin kanki ne fa shiga in da King Zuhair yake ma ba ƙaramin abu bane, ke kanki kin san ko da yatsa ka nuna gate na farko na shigo cikin masarautar nan sai an datse maka hannu, duk wani karfin iko da isa tana nan! Wlh kamar yadda kika ce ko rayuka nawa zaki iya salwantarwa domin ki mallaki King, ni ma hakance, zan iya aikata komai dan na mallakesa, dan haka da ni dake lokacin buga wasa a tsakaninmu ya yi, kowacce ta gwada sa'arta kawai....." E lallai akwai cakwakiya ba kaɗan ba!. Tana kai karshen maganar ta miƙe fuuu abayar jikinta na ja a ƙasa ta nufi waje, bata zame ko'ina ba sai family part ɗin King, kai tsaye wajen mummy ta nufa, dan ita mummy ƴar baruwa na ce, kowa nata ne, kowa ya zo gidan hannu bibbiyu take tarbansa, shiyasa suke sonta, tana da hakuri haɗi da kawaici, ainahin mahaifiyarta ƴar Nigeria ce, kuma ita ba yar kowan kowa ba ce, tana da taimakon mutane da kuma saukin kai sosai, ba kamar Mama da Momma ba, ku kunsan Momma tana da kyan zuciya, wargi ne kawai bata ɗauka! Iadan ka kawo mata ba dai'dai ba yanzu zata nuna maka cewa jinin Modarawa ne yake gudu a jikinta. Mama kuma sai ka rasa me matar nan take so a duniya, sai bala'in masifar tsiya, ga ɗan banzan kishi na masifa. Da kallon mamaki Mammie ta bi Aliyah har ta kurewa ganinta, mamaki da al'ajabi ya hanata yin magana, tunani take yi wai yaushe Aliyah ta girma da har take cewa su ƙara ko wacce tata ta fisheta?. Ita ma fa Mammien ba wata babba bace take wani cewa yaushe Aliyah ta girma, Aliyah ɗin ce fa mai bi mata a wajen haihuwa, kada ku manta Sarina ce ƴarta ta farinta, so ita ma ba wata babbar mace can can bace, iyayi ne kawai. Wayarta ta ɗauka tare da miƙewa ta nufi cikin bedroom ɗinta tana faɗin. "Dani kike yi Aliyah, yaushe ma aka haifeki da har zaki ce mu ƙara akan muradina? Ke har kin isa ina son abu kuma a yunwace nake da na cinma burina a kansa ki ce kema kina son shi? Wlh ba'a haifeki ba! Tsab zan gyara maki zama, zan gwada maki banbancin shekaru..." Ta kai karshen maganar tata tana zama a gefen bed ɗin nata, dai'dai lokacin kuma wadda take kira a waya ya ɗauki kiran. "Misalin karfe 1 dare mu haɗu a in da muka saba haɗuwa". Shi ne abin da ta gayawa wanda ta kira ɗin. Tana gama faɗin hakan ta katse kiran tare da buga uban tagumi tana tunani. (Ni kam na ce uncle Abbas da King sun ga ta kansu, shi yanzu uncle Abbas kenan ya Mammie zata yi da shi tun da ta ce yayansa take so? Shi kuwa King yaga ta kansa kowa son shi yake yi, bawan Allah bai ma san ana yi ba, momma ki shirya ga kishiyar karfi da yaji na dole nan Aliyah tana zuwa, zaki tashi daga amarya 😅 Mama kuma kishi zai karu😅 family part ɗin King zai kama da wuta, 🔥 mummy baiwar Allah dai babu ruwanta, da rabon za'ayi yaki ba kaɗan ba, da rabon su Ramish zasu yi kisan kai ko na ce kashe kashe😅 hmmmm KINGDOM OF POWER kuma yanzu nasu wasan zai fara🔥 ina commander ZAFAR sai ku shirya, ni dai bari na tafi Nigeria gidansu Zainab dan jin ya ake ciki). GIDANSU KHADIJAH 😥💔 Hakura maman Zainab ta yi ta karɓi wannan ɗaki da Hauwa ta zaɓa mata, a ciki ta kwana, bakinciki kamar zai kasheta, ta fara danasanin zuwanta sabon gidan nan, dan bakinciki kala kala Hauwa take kunsa mata, tsabar mugunta dan ta kuntata mata ma da daddare tasa baban Zainab ya sanyata ta yi masu girkin dare, har da gaya mata kalar abincin da take son ta girka masu Hauwar ta yi. Idan ran maman Zainab ya yi dubu to ya ɓaci, amma haka ta daure ta yi girki tare da taimakawar su Khadija, ita kuwa Hauwa tun yamma da ta gaya mata ga abin da zata yi masu, suka ci wanka ita da baban Zainab ɗin suka nufi kasuwa, ta tasa shi a gaba wai sai dai su je ya karɓi komai nasa daga hannun Sadiq, haka ya shirya suka tafi, maman Zainab ta yi girki tare da su Khadija. Sai can wuraren karfe 9 na dare su Hauwar suka dawo, a lokacin maman Zainab sun kammala girki ta zubawa su Khadija sun ci nasu, ita ma ta ɗan tsakuri kaɗan ta ci, bakinciki ya hanata cin abincin na kirki, so kaɗan ta tsakura. Tana gama cin abincin bayan sun yi sallar mangariba da isha'i ta wuce ɗakinta ta kwanta, su Khadija ma suka wuce nasu da Hauwa ta basu suka kwanta, Zainab ta yi addu'ar barci ta kwanta, ita kuma Khadija ta ɗauro alwala, dan kwanciya bai ganta ba iyayenta suna cikin masifa. Maman Zainab tana kwanciya sai ga kiran Sadiq ya shigo cikin wayarta, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi da ganin kiransa. Ɗauka ta yi cike da fargaba. A hankali ta yi sallama kamar mai jin tsoron wani abin ko wadda bakinta yake ciwo. "Assalamu alaikum Maman Zainab na manta ban gaya maki ba ni fa ina hanyar Kaduna, da farko massages naso in tura maki, amma sai dai nace bari kawai na kiraki". Cewar Sadiq ɗin. A zabure ta miƙe zaune a tsakiyar gadon, zaro idanu waje ta yi. "Sadiq me zaka je yi a Kaduna? Kuma sai ka tafi baka sanar da ni ba? Yanzu da ka tafi ya kake son na yi da rai'na? Da waye zan yi shawara? Waye zai rage mun raɗaɗin da yake damuna a rai'na?! Ina kake son na sanya rayuwata na ji daɗi? Mutuwa kuke son nayi ne?". Tana magana wasu zafafan hawaye suna biyo ƙuncinta. "Ki yi hakuri maman Zainab, dole ce tasa na tafi, amma kinsan ni ma ba zan so rabuwa dake a irin wannan hali da kike ciki ba, shiyasa nace maki da farko sms naso in yi maki ba kira ba, saboda kada na ji kukanki, da ina turo maki sms zan kashe wayata, amma ki yi hakuri Allah yana tare da ke!!". "Sadiq to me yayi zafi da zaka tafi ka barni? Kana da wata ƴar uwa a duniyar nan biyu na ne? Ko dai ka dai'na sona ne". Cikin raunin murya haɗe da karyewar zuciya ta yi maganar. "Ko ɗaya maman Zainab, ban dai'na sonki ba, yama za'ayi na dai'na sonki? Ai ba zai yiwu ba, yanayi ne yazo da dole na yi nisa dake, idan ba haka ba zan iya aikata kisan kai wadda kema kanki ba zaki so na yi hakan ba, ba zan iya jurar cin kashin da suke yi maki ba, baban Zainab ya zo kasuwa da yamma, ya karɓi komai da komai nasa, mun yi lissafi da shi da Hauwa, komai ya fita yadda yakamata, kuma mun yi a rubuce yasa hannu na sa hannu a kan na mayar mashi da komai ɗinsa, shi ne naga ya dace na koma gida in je in kula da mama". Magana ta gaskiya ba hakance tasa Sadiq ya bar garin Kano ya kama hanyar Kaduna ba, abin da yasa shi ne, wani irin mummunar cin mutunci baban Zainab da Hauwa suka yi mashi a kasuwa, ga lissafi sun yi dallah dallah amma Hauwa ta ce da baban Zainab karya ne ya saci wasu kuɗaɗen, wai ba zai yiwu ace iya wannan ribar kawai aka samu a shagon ba, gudun irin haka fa yasa Sadiq ɗin yake ciyar da su maman Zainab ɗin da kuɗinsa, harta su maman Haidar idan suka zo kasuwa a kan basu da abincin ci daga aljihunsa yake cire kuɗin ya basu, duk dan kada ya taɓa naira biyar ɗin baban Zainab, amma da yake Hauwa makirace, kuma tana jin haushin marin da ya yi mata, sai da ta sa baban Zainab ya ci mutuncinsa a bainan nasi, ya yi mashi kaca kaca, shi kuma Sadiq ga shegen zuciya kamar ɗan kuturu, hakan yasa ya haɗa kayansa ya nufi gidan iyayensa in da zai bugi kirji yace ya isa a can, har police Hauwa ta ce baban Zainab ya kira su zo su tafi da Sadiq ɗin, da kyar masu shagunan kusa da su suka bata hakuri ta hakura, mata kamar wata kanwar shaiɗan. Wannan shi ne a takaice abin da ya faru a tsakaninsu da yasa Sadiq ɗin ya bar Kano, yaki gayawa ƴar uwa tasa gaskiya ne kawai dan baya son ya ɗaga mata hankali, baya son kara mata zafi a kan zafi, shiyasa ya ce mata sun yi lissafi lafiya lou!!. Sosai maman Zainab ta rinƙa kuka, sai hakuri yake bata ita kuma tana yi mashi magiyar ya dawo dan Allah, daga shi sai su Khadija take gani ta ji daɗi a rayuwarta, sune kaɗai suka rage mata, sune kaɗai farincikinta a yanzu. Duk magiyar da ta yi mashi ya kafe a kan lallai shi ba zai dawo ba, ta yi hakuri kawai, daga ƙarshe dai ya bata hakuri tare da kashe wayarsa ya yi switch off ɗinta mai gabaɗaya dan ma kada ta sake kiransa. A wannan daren dai sai da barci ya kasance ɓarawo ya saci maman Zainab, nan ma har wuraren karfe 2, bakinciki da ɓacin rai ya hanata rintsawa baiwar Allah. Washegari da safe haka ta farka idanunta a kumbure luhu luhu, saboda kuka da ta sha ga kuma rashin barci, tana farkawa ta fito kuma Hauwa ta ce lallai lallai ita zata yi masu kayan ƙarin kumallo, rai a ɓace ta ce ba zata yi ba, baban Zainab ya ce ta yi ko ranta ya ɓaci. Danne zuciyarta ta yi ta girka ba dan ta so ba, yau dai su Khadijah basu je school ba, dan basu taho da uniform ɗinsu sabon gidan ba, ga shi yau jumma'a, so basu taho da uniform ɗin da suke amfani da shi ranar Friday ba. A takaice dai babu daɗi suka yi ƙarin kumallo a gidan, duk wanda ka gani ransa a cunkushe banda Hauwa da take cikin farinciki, ranta fes, sai daɗi take ji tana kuntatawa maman Zainab. Da misalin karfe ɗaya na rana tana zaune a parlour ita da su Khadija, Zainab tana kallo a Tv, Khadija kuma ta buga uban tagumi kamar yadda mamanta ta yi. "Mama ina kawu Sadiq ne? Ba zai zo gidan nan bane?". Cewar Zainab. Wani irin ƙululun bakinciki maman ta ji ya taso mata. "Khadija tashi ki je ɗakina ki ɗauko mun wayata bari na gwada numbersa ko yanzu kam zata shiga, tun safe nake gwadawa bata shiga". Da to Khadija ta amsa mata. Bata kai ga miƙewa ba sai ga Hauwa da baban Zainab sun fito. Yana shirye cikin wata haɗaɗɗiyar shadda chocolate color, ya yi kyau sosai, da alama masallacin jumma'a zai je, ita ma Hauwa ta ci kwalliya cikin abaya brown color. Gaisuwa Khadijah ta ɗagawa baban nata, a takaice ya amsa ba tare da ya bi ta kanta ba ko ya ɗaga idanu ya kalleta ba. Zata wuce cikin kenan ya ce. "Khadija ki shirya Hauwa ta ce lallai yau a ɗaura aurenki da Haidar bayan mun sauko sallar jumma'a, dan haka ki shirya su Maman Haidar zasu zo su ɗaukeki". Wani irin kuka Khadijan ta fashe da shi mai matuƙar tsuma zuciyar mai sauraro, da gudun gaske ta afka cikin ɗakin maman nata, wani irin jan numfashi da take yi cikin kuka sai ta baka tausayi, kamar zata haɗiyi zuciya. Da gudu Zainab ta tashi ta bi bayanta. Ita kuwa Hauwa wani irin murmushin mugunta take ta faman saki. Miƙewa tsaye maman Zainab ta yi, cikin wata iriyar murya da ba zaka iya fassara halin da take ciki ba ta furta. "Baban Zainab kada ka yi wannan kuskuren, wlh billahi Haidar ba zai aura mun ƴa ba, kada ka bijiro da abin da zai sanyaka yin danasani, wlh a kan farincikin ƴaƴana na yarda komai ya faru, zan iya barin maka gidanka a kan wannan aure". Hauwa ce ta ce. "To me laifi dan yarinya ta auri ɗan uwanta na jini? Kyamar dangin nasa kike yi ne? Amma kuma ke kin haɗa jini da shi ko?......" Cikin ɗaga murya tare da zafin rai haɗi da ɓacin rai maman Zainab ta ce. "Hauwa ban kasa dake ba, a wannan gaɓa idan kika saka mun baki a maganata zan ci uban, wlh wlh wlh idan kika sake saka baki a maganar nan babu uban da ya isa ya dakatar da ni daga sumar dake a cikin gidan nan, sai na yi maki dukan uwar ala tsine, ke sai na yi maki abin da wlh ke da kanki ba zaki iya gane kanki ba, kin san halina bani da full stop idan aka kureni, in dai ba so kike hajiya ta haifi wata Hauwar ba, ki sake saka mun baki shegiya mai kama da kazar mayu". Juyowa ta yi ta kalli baban Zainab ɗin. "Honey ka tafi masallaci abinka, kada ka dakata kowa, idan an ɗaura auren ka kirani ka sanar da ni". Cewar Hauwa. Ta yi hakan ne kuma dan tana tsoron maman Zainab, tana tson sake yi mata magana, amma tana da bakin yin magana da baban Zainab ɗin kam ai, a ranta kuma ta ƙuduri niyar yau sai an ɗaura auren nan ko dan taga ya maman Zainab zata yi. Kai Hauwa dai anyi sheɗaniya makirar mace. Sa kai baban Zainab ɗin ya yi zai wuce ya fita ba tare da ya ce da maman Zee uppan ba, ko kallon in da take ma bai yi ba. A ɗari maman Zainab ta sha gabansa tana faɗin. "Kada ka haɗa wannan aure, zaka yi danasani". Wani irin mari ya zabga mata wai dan ta sha gabansa, rai a ɓace ya daka mata tsawa ta bashi hanya ya wuce. Ɓacin rai iya ɓacin rai yau ranta ya ɓaci, dama ga baƙincikin tafiyar Sadiq, sannan ga bakincikin da ya ƙunsa mata da safe na sanyata ta yi girki da ya yi, ga na jiya da daddare, sai abin ya haɗu ya yi mata yawa, yanzu kuma ga marin da ya dalla mata, sannan ga future yarta da yake ƙoƙarin lalatawa ta hanyar aura mata Haidar, ta ƙuduri niyar ba zata bari hakan ya faru ba!!. Hauwa dake tsaye a bayansa kaɗan ne ta ce. "Yes honey, wlh ka kyauta da ka mareta, kai sa'arta ne da zata tare maka gaba?". A wani irin kaunace maman Zainab ta ɗauketa da wani irin wawan mari wadda sai da ta ga wani haske ya gifta a gabanta idanunta, yau ɓacin rai ya rufewa mmn Zee ido. Cakumo wuyar rigarta ta yi da nufin ta yi mata ɗan iskan duka. Baban Zainab bai bari hakan ta faru ba ya fara ƙoƙarin kwatarta, wasa wasa yaga idan bai saka karfi ba ba zai iya kwatarta ba. Cikin fushi yasa kafa ya kwashe kafafunta sai ga mmn Zee a kasa rigijib, har lokacin kuma bata saki wuyar Hauwar ba, a tare suka yi ƙasar, ta ƙanƙame wuyar tata kamar mage a saman ɗan siririn reshen bishiya da idan ta sake saza faɗo, kunga dole ta ƙanƙame da kyau. To haka maman Zainab ta ƙanƙame wuyar Hauwa!. Mari baban Zainab ɗin ya sake kai mata, daga karshe ya fara haɗa mata da duka, Hauwar ma ta fara kai mata duka domin ta kwaci kanta, ta ji shaƙa shegiya, ta ji kamshin lahira, dole ta fara kai duka dan ta samu ta tsira da ranta. Dukan da baban Zainab yake kai mata ne ya yi mata tsananin zafin da yasa ta saki Hauwar, a guje ta miƙe ta nufi kitchen, sabuwar wuƙa ta ɗauko wadda ba'a taɓa amfani da shi ba, dan komai na cikin kitchen ɗin sabbi ne. Da gudun gaske ta yi kansu da wukar faɗi take yi yau ko sama zata haɗu da ƙasa sai ta kashe Hauwa, sai dai duk abin da zai faru ya faru. Sanin halinta da balai'n bakar zuciya yasa Hauwar ta ruga a guje ta yi ɗakinta. Da mahaukacin gudu ta rufa mata ba, kamar wata mahaukaciya haka maman Zainab ta zame masu, hauka take yi masu kamar wadda take da aljanun kukar buluhi a kanta. Da gudu baban Zainab ya bi bayansu. Ihu Hauwa ta fara yi tana kewaye ɗakin dan ta ceci rayuwarta, ita kuwa maman Zainab yadda kuka san bata san menene hankali bama yau, binta take yi kawai tana faɗin. "Yau idan kinga baki mutu ba to ni ce nan na mutu, shegiya mugun iri, ina kika ce ke shaiɗaniya ce? To ki tsaya dan ubanki, yau sai dai hajiya ta haifi wata Hauwar!!" Sai kewaye ɗakin suke yi, a hau gado a sauka, duk maman Zainab sai farfashe abubuwan cikin ɗakin take yi. A haka baban Zainab ya iskosu, da gudu ya yi ƙoƙarin shiga tsakaninsu dan ya rabasu, ai kuwa maman Zainab zata cakawa Hauwa wukar sai ta caka mashi a tsakiyar cikinsa wajen cibiya. Dama da Hauwa taga ya shigo sai ta tsaya a saman gadon, dan tasan zai tare mata, shi ne maman Zainab ta nufota da wukar, zata caka mata shi kuma ya shiga tsakani. Nan take jininsa ya fara yin wani irin tartsatsi kamar wutar welder, ga wukar ta cakesa har can cikinsa, gabaɗaya kaifin wukar ta lume a cikin nasa. Kan kace me ya zube ƙasa a kan gadon, jini ne yake zuwa kamar an buɗewa ruwa hanya. Wani irin mahaukacin ihu maman Zainab ɗin ta saki tare da yin kansa tana kiran sunansa, ita kuwa Hauwa waje ta nufa a guje kamar mahaukaciya tana kurma nata ihun. Da gudu su Khadija suka fito daga ɗakinsu jin irin ihun da mamansu take kurmawa, kai daga jin wannan ihu kasan bana lafiya ba, dan ihu take kurmawa tamkar maƙoshinta zai ɓalle, sai ambatar sunansa take yi. Gwanin ban tausayi shi kuma sai shure shure yake yi kamar wadda ransa yake fita, ƙafafunsa sai kaɗawa suke yi, ko'ina na jikinsa kakkarwa yake yi, harta gashin kansa sai da suka mimmiƙe tsaye, wani irin zara zaran jijiyo ne suka fito ɓaro ɓaro a hannunsa zuwa ƙafafunsa har gaban goshinsa da kuma wajen wuyarsa, wahala ta fito da su, nan take ya yi wani irin fari kamar ba shi ba, har lokacin jini na feshi kamar wutar welder, haka zalika har lokacin yana ta shure shure, idanunsa sai juyawa sama suke yi, bakin ciki sai ƙoƙarin ɓacewa yake yi, wani irin zufa dake tsastsafo mashi yana wanke ko'ina na jikinsa sai ya baka tausayi, fuskarsa kamar an watsa mashi ruwa, ya jike sharkaf da zufa, kayan jikinsa duk sun jike da zufar azaba!!. Ai Khadija na leƙowa taga abin da yake faruwa sai ta yi waje da gudu domin ta kira mutane su zo su taimaka masu kada babansu ya mutu, ita kuwa Zainab ta yi kansa da gudu tana ihu, Hauwa kuma sai Allah kaɗai yasan in da ta nufa...... Tashin sense!!! Akwai matsala fa my people's😥💔 Shin baban Zainab zai mutu ko zai rayu? Ina Hauwa tsohuwar makira? Ya makomar maman Zainab?. Zuciyata ba zata iya jurar ganin tashin hankalin da waɗan nan ahalin suke ciki ba, bari dai na leƙa Dubai muga me yake faruwa a can, my people's yanzu littafin RAWANIN ZALINCI zai fara ɗaukar 🔥 dan yafi karfin ɗaukar zafi sai dai wuta, mun dai kusa isa ga RAWANIN ZALINCI da gaske!. Second to the last page of book 1 my people's. 💘🔥 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 14/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________52🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🕊️🌼🕊️ ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥 A karo na biyu ma wahala Leesharh ta sha sosai wajen neman mai kai abinci, sai dai kuma bata ci nasara ba har yanzu, sake dawowa cikin ɗakinta ta yi, a bakin gado ta zauna, uban tagumi ta buga tana tunanin mafita, mahaifinta ne kawai a ranta, shi kaɗai take tunawa, ta ci burin yau ta yi magana da shi. Sallamar Sharifat a cikin room ɗin ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka. Da kallo ta bita, ta kasa iya amsa mata sallamar, dan hankalinta baya a jikinta, duk ta yi la'asar. Kusa da ita Sharifat ta zauna, cikin sanyin murya ta ce. "Leesharh Yah Guyson ya gaya mun kin yi kuka a kan wani abin ya shiga maki cikin ido ko?". Kai ta gyaɗa mata alamar e haka ne. "Eyya sorry, amma kuma dan wani abin ya shiga cikin idanun ki hakan doesn't mean sakacin masu aiki ne, i told Yah Guyson kada ya ce laifinsu ne, kada a hukuntasu, be cause yau rana ce ta taro, baki dayawa sun zo, a wajen shige da fice ma za'a iya samin kwari ai". Da sauri ta amsa mata da. "Yauwa Sharifat, even me abin da na gani kenan, please ki rarrasheshi kada ya ce za'a hukunta masu aikin nan, please ya yafe masu". "Leesharh tell me the truth, what's wrong with you? I already saw many problems in your eyes, so please feel free and tell me!". Tsuru tsuru ta yi da idanu, yanzu me zata ce da Sharifat? Ta tambayi kanta da kanta. "Leesharh from which country you came here?". Ta sake jefa mata tambaya, Sharifat tana zargin ko Leesharh tana kewar iyayenta ne yasa take shiga damuwa haka, kamar dai yadda Guyson ya yi hasashe ɗazun, suna ganin yarintarta sosai, suna ganin bata kai a rabata da iyayenta ba, shiyasa suke yawan tambayarta ko tana kewar iyayenta ne, basu ma san ita Leesharh ai ta jima rabonta da iyayenta ba, idan da sabo yanzu ta saba da kaɗaicinsu. "Am from Nigeria". Ta bata amsa a takaice, ta yi maganar kuma kanta na'a ƙasa tana kallon ƴatsun hannunta. "Do you mean Nigeria African?". Ta faɗa tana zaro idanu alamar mamaki. Kai ta gyaɗa mata alamar tabbatarwa daga Nigeria take. "From Nigeria you came here because of work? Kai dole ki yi missing na parents naki, dole ki shiga damuwa, but why your parents zasu yarda su barki ki zo nan aiki? Su ba zasu ji kewarki bane? And su basu ga akwai nisa bane?". Tana maganar still mamaki ne sosai a saman face ɗinta. Shiru ta ɗan yi mata, kamar zata fashe da kuka take ji, zuciyarta na yi mata zafi, Sharifat ta taɓo mata in da yake yi mata kaikayi, ta tuna mata da iyayenta, duk sai ta ji wani irin. "Sorry ko Leesharh, dole ki rinƙa kuka na kewar parents ɗinki, in saya maki waya ki rinƙa magana da su dan ki rage damuwa da kewa?". Sai a lokacin ta zaro nata idanunta da suka girmewa na Sharifat a girma, idan ta zarosu kamar ka ruga a guje. Ko me ta tuna sai kuma ta ɗan yi ƙasa da kai. "Leesharh meyasameki kuma? Is there any problem again?". Kai ta girgiza alama a'a babu komai. "Leesharh talk to me now! should I buy phone for you? Saboda ki rinƙa kiran parents ɗinki, I don't want to see you always crying and worried". A takaice Leesharh ta ce mata. "I don't have anyone in my life, I don't have a mother and i don't have a father, they're not alive, they're all dead". Ta faɗa kamar zata yi kuka, kuma ta gaya mata hakan domin Sharifat ɗin ta rabu da ita da zancen saya mata wayar nan, kada ta zo ta saya mata waya hakan ya zame wa babanta babbar baraza, dan masu nikaf basu bata damar yin amfani da wata waya ba bayan wanda suka bata, shi ma kunji sun gargaɗeta a kan kada ta kuskura ta kira kowa da shi, so hakan yasa ta ce bata da har da uba, ni da ku mun san iya mamanta ce kawai bata raye, amma ta haɗa harda babanta dan tsira daga wajen Sharifat kada ta saya mata waya. Tasan cewa duk abin da zata aikata a kan mahaifinta masu nikaf zasu ɗauki fansa, idan ta yi kuskure babanta ne zai ji a jikinsa! Hakan yasa take taka tsantsan sosai!. Wani irin mugun tausayinta ne ya kama Sharifat ɗin na jin cewa bata da iyaye, Allah sarki duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, ji ta yi zata yi ƙoƙari ta ɗauketa kamar yar uwarta dan ta rage mata raɗaɗin rashin iyaye, da yake ita da Guyson akwaisu da zuciyar zinari na tausayi sosai, ga hakuri kamar damo, basu da faɗa kuma basu son hayaniya, kowa ya zauna da su sai ya ji yana tsananin kaunarsu, saboda kyawawan halayensu. Ɗan matsowa ta yi ta rungumeta tana yi mata sannu a kan rashin iyaye. "As from today i am your sister kin ji? Sorry ko?". Ta faɗa tana mai kara jin tausayinta sosai. Ita ma Leesharh ɗin duk jikinta ya yi sanyi, tana jin kaunar Sharifat ɗin tamkar ƴar uwarta na jini, saboda kauna da ta nuna ma, duk sai ta ji bai kamata ace ta yi abu komai ƙanƙantarsa dan ta cutar da bayin Allah nan ba, ita tama rasa a wani matsayi zata ajiye Sharifat da Guyson, babu ruwansu da girman kai, mahaifinsu yana da murya mai karfin faɗa aji kuma dole ayi abin da ya ce a faɗin ƙasar, ga ɗimbin dukiya da shi kansa bai san adadinsu, ga matsayi a siyasance, sannan ga matsayi a sarauce, ga tarin masu kaki kala kala a ƙarƙashinsa, duk wata kaki a faɗin ƙasar bata isa ta motsa ba ba tare da izininsa ba, karfin iko gare shi ba kaɗan ba, amma su Sharifat duk basu ɗauki hakan a bakin komai ba, abin duniya bata damesu ba, basu ɗaurawa kansu girman kai ba, Guyson kam ma ai shi ta ko'ina ma jinin mulki ne yake gudana a jikinsa, ta sama da ta ƙasa, amma babu ruwansa da girman kai ko kyamar talaka, yana son kowa da zuciya ɗaya. A can wajen walima kuwa. Tun da suka je wajen Guyson yake ta ƙoƙarin dannar twins Obaid and Omaid, shi Omaid ma ya hakura ya barwa cikinsa abin da yake tunani dan gane da Leesharh, dama shi kun san ya iya takunsa. Obaid kuwa sarkin bakar zuciya, sai cika yake yana batsewa, shi lallai lallai dole sai Guyson ya yarda Leesharh criminal ce, har da wani cewa su basa hasashen abu kuma ya zama karya. Shi kuma Guyson ya ce sam ba zai yarda a kan ita mai laifi bace kuma abin zargi, saboda shi baiga laifin da ta yi masu ba, kuma shi ba zai yarda ya zargeta ba, ya kafe masu a kan lallai ita ɗin mai gaskiya ce, sune kawai basu sonta. Tun da suka shigo wajen yayyun nasu suke yi masu kallon tuhuma except Abu Abdussalam da ya buƙaci su zo kusa da shi su zauna ya yi kewarsu, Abu Abdussalam yana bala'in kaunar Momma da King Zuhair, shiyasa yake kaunar ƴaƴan nasu. Kusa da shi suka zauna cikin manya manyan ministoci da ƴan majalisu, Guyson yana ta gefen damansa, su kuma ta gefen hagu suka zauna, basu taɓa raba wajen zama, duk in da ka gansu a tare suke, kai su basu raba komai ma ba wajen zama kawai ba, in dai ba zaka basu abu a tare ba gara ma ka barshi, dan ɗaya ba zai karɓa ya bar ɗaya ba. Abbie ne ya ce. "Guyson where's Ramish?" Ya yi maganar cikin kwararriyar laraɓcinsa, yare biyu Abu Abdussalam yake ji a duniya, daga turanci sai larabci. Cikin sanyin murya haɗe da nutsuwa ya ce. "Abbie wai kansa na yi mashi ciwo, he can't come here, dan kara mashi ciwon kai za'ayi da surutu, so ya kwanta". Kallon Bilal Abbie ya yi. "Jeka duba mun shi, Dr Raj ka kula da lafiyarsa sosai". Da okey suka amsa mashi kafin su miƙe su nufi hanyar fita. Tun da suka miƙe maza da mata kallonsu suke yi, ba dai haɗuwa ba kam, sun fito ba'a magana, kyau iya kyau. Shi kuwa Rizwan ya kafa kansa a kan waya yana chatting da Chuchu, sai zuba mata kalaman soyayya yake yi, ita kuma sai narke mashi take yi!. Bayan anci an sha, kowa yasan da cewa lallai yau Abu Abdussalam empire ya zo, biki aka yi na girma da girmamawa, rakuma har biyar ma'aikata suka gasa, nama kamar hauka, da nama na magana yau da ya yi a gidan Abu Abdussalam, drinks da ruwa suma da sai sun yi magana, abinci kala kala, a yau ba wata ma'aikaciya ko ma'aikacin masu yin girki waɗan da basu ji a jikinsu ba, yau sun sha aiki sun kuma wahala, jiki duk ya yi tsami. Rera karatun Alkur'ani mai girma manyan baki suka fara yi, kun san fa larabawa akwai iya rera ƙira'a, Abu Abdussalam ne ya buƙaci da a yi karatu sosai kafin a tashi daga taron. Duk wanda zai yi karatu saman stage yake hawa, abin ya yi tsari sosai ya kuma bada ma'ana, sannan ya ƙayatar matuƙa. Lokacin da Guyson ya fara rera kira'arsa sai da gabaɗaya jama'ar cikin hall ɗin suka bar abin da suke yi suka zuba mashi idanu, tsantsar madarar kyau suke gani, ga zakin murya kamar me, karatu yake rerawa cikin kwanciyar hankali cikin suratul Yusuf, yadda yake fitar da kowani baki, kowani gunna sala sala yake fitar da ita, baya mance wasali ko yaya, dai'dai yake zayyanosu ga nutsuwa matuƙa a tattare da shi sai ya tafi da imaninka, dama ga yaran Momma da bala'in farin jini kamar su suka bawa kansu. Wasu kyan da Allah ya yi mashi suke gani, wasu kuma kyakkyawan arab hairnsa suke gani, dan fa kunsan gwani ne wajen iya gyaran gashi, ga shi ɗan wanka, wasu daga cikinsu kuma wankarsa suke kallo, wasu zazzaƙar voice ɗinsa ne ya tafi da imaninsa, wasu kuma yadda yake rera karatun cikin nutsuwa ne ya tafi da imaninsu, yaro mai farinjini, dayawa daga cikin manyan bakin nan sun kwaɗaitu da son samu ɗa kamar sa, ji suke yi dama ace ɗansu ne. A hankali zazzaƙar muryarsa ta fara rikiɗewa daga yadda ya faro karatun cikin zaki da nutsuwa zuwa muryar mai kuka, da kaɗan da kaɗan fararen idanunsa suka fara rikiɗewa izuwa ja saboda kukan, siraran hawaye ne suka fara bin kyakkyawar farar kumarunsa, ba komai ya ja hakan ba kuma face sanin fassarar surar da yake karantawa da ya yi, zuciyarsa tana kara jinjinawa girman Allah, jikinsa har tsuma yake yi yana kerma a lokacin da yake karanta gudurorin Ubangiji da ya yi ta yi wa annabi Yusuf. Kukansa kara tsananta ya yi lokacin da ya zo in da aka raba annabi Yusuf da mahaifinsa, sanin fasarar surar tasa shi kuka sosai da yake karantota. Guyson bai kai 17 years ba a duniya, amma Allah ya bashi baiwa ta ilimi fiye da tunaninku, ba boko ba ba Arabic ba, dukka akwai tarin ilimin a kansa, shiyasa yake da saukin kai sosai, saboda ya san girman Allah sosai, yasan duniya ba'a bakin komai take ba, a wajen Allah duniya kamar wuni guda ce. A ƴan shekarun nan nasa ya san farrasarar rabi da kwana na surorin dake cikin Alqur'ani mai girma, kun san larabawa fa ba baya ba wajen iya karatu, basu wasa. A bangaren littafan addini ɗan tahaliƙin nan ba'a magana, yasan dayawa daga ciki, ya haddace dayawa, kuma har yanzu bincike yake cigaba da yi yana kara nutsawa cikin karatun addini, yana ta ƙoƙarin ya haddace fasarar Alqur'ani gabaɗaya, ɓangaren bokon ma baya wasa, yanzu kunga ya kammala secondarynsa, jam zai rubuta kai tsaye ya shiga babban makaranta da kananun shekarunsa, shiyasa ƴan uwansa dukka suke sonsa, saboda jajircewarsa wajen neman ilimi. Su Omaid kuwa, akwai tarin ilimin suma, amma sai shegen shakiyanci, iyashege, da tarin rashin ji, ga ɗan banzan shiga rai garesu kamar me, ga farin jini kamar su suka yi wa kansu, amma duk da hakan baya hanasu karatu, duk iskancin da suke yi basa wasa da karatu, dan idan suka kuskura suka yi wasa wlh zasu kwashi kashinsu a hannun idan su Ramish suka riƙe su, shiyasa kome zasu yi banda wasa da karatu kam. Kai in takaice maku labari gabaɗaya jinin King Zuhair babu jahili, sai dai ilimin wani ya fi na wani, wani ya fi wani kaifin basira, ga tafasasshen jini, dagiya da kafiya, jarumta da jajircewa, babu jahili sam sam! Suna da dagiya wajen neman ilimin boko dana addini basa wasa!. Kukan Guyson a cikin hall ɗin nan yasa dayawan mutane kuka, masu raunin zuciya sun taya shi kuka, shi kansa Abu Abdussalam sai da idanunsa suka ɗan yi ja. Kasancewar a nutse yake karatun sai ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya kammala. Yana kammalawa Abbien nasu ya miƙe ya rungumo shi tare da fara goge mashi hawaye, kabbara jama'a suka fara yi suna zuba mashi ruwan albarka sosai da sosai. Omaid ne ya miƙe ya fara rera nasa kira'ar cikin suratul ma'ida, dama kun san su sarakan shiga rai ne, ga farinjini, nan take jama'a suka fara binsa dana mujiya, sai santin kyansa da muryarsa kusan irin na Guyson suke yi. Shi kam Omaid saboda dakiya da taurin zuciya ko ɗigon hawaye babu a idonsa, sarai kuma yasan fassarar surar da yake karantawar, amma akwai taurin zuciya, ko alamar hawaye ma babu a idanunsa, idanun suna bushe karau yake rera karatunsa har ya kammala, har lokacin kuma Abu Abdussalam bai saki Guyson ba, yana bala'in kaunarsa, duk da sun koma sun zauna yana ƙanƙame da hannunsa suna sauraron kira'ar Omaid ɗin. Bayan ya kammala Obaid ma ya miƙe ya fara rero nasa cikin suratul Maryam. A wannan gaɓar ma sai da Guyson ya yi hawaye, saboda yasan fassararta, sosai kuma ya kara jin tsoron Allah matuƙa, sai goge mashi hawaye Abu Abdussalam yake yi. Shi kuwa Obaid da ya karanta surar ma idanunsa a bushe karau, Guyson sai sharar kwallah yake yi shi da ba shi yake karatun ba, mai karatun kuwa idanu a bushe karau, ga gashin idanun nasa zara zara a tsaitsaye na rashin kunya da rashin jin magana, kowa ya ga idanun Obaid da Omaid ya san akwai tarin rashin tsoro da rashin kunya game da mugunta a cikinsu, basu tsoron a mutu. Bayan Obaid ya kammala karatun ne ƴaƴan manyan baki suka fara rero nasu. A can cikin gida kuwa, Leesharh ta saki jiki sosai suna ta hira da Sharifat. "Leesharh anata gudanar da abubuwa a wajen walima ni kuma ina nan a tare da ke, ki tashi mu je can mana? Kin ga ai sai mu yi hira a can ko?". Cewar Sharifat. Make mata kafaɗa ta yi. "A'a Aunty Sharifat ni bana son zuwa, ban son shiga cikin mutane sosai, ki barni a nan kawai". Gyara zama ta yi. "To shikenan Leesharh mu zauna tare a nan ɗin kawai ko? Mu cigaba da hirarmu ni ma na fasa zuwa duk da nasan Yah Guyson zai damu idan bai ganni ba". Da sauri ta girgiza mata kai tana faɗin. "A'a Aunty Sharifat, kada ki sa ya ji babu daɗi, idan kin san zasu damu da rashinki a wajen kawai ki tafi". Gyarawa ta yi ta kwanta a saman gadon tare da miƙe kafafunta. "Kawai mu cigaba da yin hirarmu Leesharh ba zasu damu ba, ai na gayawa Yah Guyson bari na je wajen ki tun lokacin da ya gaya mun kin yi kuka". Okey ta amsa mata da shi haka suka cigaba da yin hirar duniya cikin nishaɗi abinsu. Sun shagala da hirar duniya mai daɗi Sharifat ta dubi ɗan siririn diamond watch dake manne a hannunta. "Kai Leesharh karfe 7 ta yi bamu yi sallar mangariba ba! Sannan karfe 7: 30 dai'dai zan kaiwa Yah Ramish abincinsa da cappuccino, kin san shi bai yarda da kowa ba, bai yarda da ƴan aikin gidan nan ba, abincin da zai ci ma wanda yake girka mashi na musamman ne, bai yarda wata ko wani mai aiki ya keto cikin ɗakinsa ya kawo mashi abinci ba, garama idan da rana ne yana zaune a babban parlourn haka zai iya cewa a kawo mashi, nan ma sai idan yasan na tafi school ko bana kusa ne zai yarda wata ta kawo mashi abinci, duk wata ƴar aiki da kika gani a cikin gidan nan sai da Abbie ya aminta da ita kafin ta fara aiki, amma shi ya Ramish bai aminta da kowa ba sai ni da su Yah Rizwan, ke ni ina ganin ma kamar Ummie ma bai yarda da ita ba fa, dan naga baya wani sakin jiki da ita kamar yadda su Yah Rizwan suke yi". Shiru Leesharh ta yi tana sauraron tun da ta fara maganar, wani irin sanyi ta ji yana ratsa mata zuciya, tsuntsu daga sama gasasshe! Ta sha wahala wajen neman mai kai mashi abinci cikin room ɗinsa, ashe dai tana tare da ita bata sani ba, wannan shi ne tsuntsu daga sama gasashe! Sosai abin ya yi mata mugun daɗi, har wani sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke. "Leesharh tunanin me kike yi?". Ta yi maganar tare da ɗan taɓata. Ƴar razana ta yi tare da cewa. "Babu komai, amma meyasa Yah Ramish ɗin baya yarda da kowa?". "Saboda ya ce yana da tarin makiya, kuma fa na gaya maki dukka masu aikin gidan nan daga maza har matansu amintattu ne, shi ne dai kawai bai aminta da su ɗin ba". Shiru Leesharh ta yi tana jinjinawa kaifin ƙwaƙwalwarsa, yana da gaskiya, su suke ganin kamar dukka ma'aikatan gidan amintattu ne, shi da ya san da cewa ɗan adam yanzu ba a abin yarda bane, ya san kan duniya ai ga shi bai yarda da su ɗin ba, ita kanta Leesharh ai kunga ba amintatciya bace, ƴar leken asiri ce, ƴar ɓadda kama!. Miƙewa Sharifat ta yi. "Bari na ɗauro alwala Leesharh, kema ki tashi lokacin sallah ya yi, ki yi sallah mu je ki rakani wajen Yah Ramish mu kai masa abinci, idan mun je sai ki jirani a kofar shiga part ɗinsu, dan idan kika shiga na shiga uku na, ba kowa yasan in da part ɗinsu yake ba a cikin gidan nan, kuma Yah Ramish baya son wata ma'aikaciya ta zo arear part ɗinsu, wai kyamar ƴan aikin yake ji, idan sun zo in da yake zai yi amai, so sai ki jirani a waje". Sharifat baki abin magana, ta aminta da Leesharh ta saki baki sai gaya mata sirrin gidan take yi, bata san cewa Leesharh dai green snake under green grass bace, ƴar ɓadda kama kuma ƴar basaja. Rashin sani bai yi ba a rayuwar nan. Okey ta amsa mata da shi, nan take ta ji kwarin jikinta ya dawo, wani irin daɗi ta ji ya kamata, duk yadda zata yi ta zuba mashi maganin nan yau sai ta yi, dole ta san yadda zata yi ta shammaci Sharifat ta aiwatar da aikinta. Waje Sharifat ɗin ta nufa, ita kuma Leesharh ta nufi cikin toilet, alwala ta ɗauro tare da zuwa ta shimfiɗa dadduma ta tada sallah, bayan ta idar ta sanya hannu ta taɓa aljihun wandanta dan ta tabbatar maganin yana ciki. Jin cewa yana ciki yasa ta saki cool murmushin da bata san lokacin da ya fito ba, faɗi take yi a cikin ranta shikenan da ta zuba mashi maganin nan masu nikaf zasu haɗata da babanta ta yi magana, yau tsawon shekara kusan biyu bata ji muryarsa ba, tana kewarsa sosai, tun lokacin da aka kaita prison ta kashe mamanta, tun ma kafin lokacin take kewar muryarsa, sun ɗan kwana biyu basu a tare, shiyasa take ɗaukin jin muryarsa, take begen hakan. Sallamar Sharifat a cikin ɗakin yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka. Ɗago idanun nan nata ta yi tare da saukesu a kanta, rike take da katon luxurious tray, shake yake da kulolin abinci masu bala'in kyau da tsada, ga cup dake shake da cappuccino, sannan ga cup na coffee mai zafi a gefe, duk suna rufe da ƴan ƙananan plate na set ɗin cup's ɗin. Sai sauran snacks dake saman wani luxurious plate. Zubawa trayn idanu ta yi tana kallonsa sosai, ayyana yadda zata zuba mashi maganin a ciki kawai take yi. Muryar Sharifat ɗin ce ya katseta da cewa. "Let's go Leesharh". Miƙewa ta yi suka jera a tare. Allah sarki tausayin maraicin Leesharh da Sharifat take yi yasa zata tabka kuskure ba tare da sanin ta ba, burinta ta ja Leesharh ɗin a jiki ta yadda zasu saba sosai, duk dan ta mantar da ita damuwar da take ciki na rashin iyayenta, tana son su saba sosai su zama kamar ƴan uwa, shi ne harda gayyatota ta rakata wajen ƴan uwanta. Hmmm bata san aiki dama ta zo yi a kansu ba, rashin sani ya fi dare duhu. A tare suka tafi, cikin dabara Leesharh ta ciwo maganin daga aljihunta, ko tsoro bata ji ba, kamar mai son gyara zip ɗin wandonta haka ta yi ta buɗe ɗan gwalbar ganin. Sai da suka shiga wajen wannan ɗan hanya in da ta yi karo da mai aikin ɗazun ɗin nan, kun san wajen akwai ɗan duhu. Saboda jajircewa da karfin hali haɗe da ƙoƙari irin nata, ga taurin zuciya da rashin tsoro, cikin dabara ta kai hannu ta bude plate ɗin cappuccino ba tare da Sharifat ta jita ba, sai hira Sharifat ɗin take zuba mata, tana bata labarin kyan Yah Ramish ɗin. A hanzarce ta zuba maganin kaɗan a ciki, ta sake zubawa a cikin coffee ɗin ma kaɗan sabosa ƙoƙari irin nata. Tana yi kirjinta na dukan tara tara, ita kuma Sharifat sai surutu take zubawa suna tafiya a hankali cikin natsuwa, saboda girman tray ɗin yasa bata ji an taɓa komai ba. Kaɗan kaɗan ta zuba maganin kamar yadda suka umarceta, ta yi maza ta dunƙule kwalbar a hannunta kasancewar sun fito wajen haske. Fargaba da faɗuwar gaba ne ya kusa kasheta, zuciyarta sai bugawa da karfi karfi yake yi, da kyar ta haɗiyi yawun wahala, wani irin jan numfashi da ta yi har sai da tasa Sharifat ɗin ta ɗan ci birki tare da tambayarta lafiya kuwa?. Cikin dakiya ta ce babu komai su je kawai, duk a ruɗe take, gabanta na faɗuwa, sai karanto addu'oi take yi dan ta ji sassauci a cikin zuciyarta...... Kai Leesharh ba dai karfin hali da dakiya haɗe da taurin zuciya ba, kai irin wannan ɗanyen aiki haka? Ko tsoron asirinta ya tonu bata ji yarinyar nan, idan ta sa kanta zata yi abu, to fa sai ta yi. Ashe ba'a banza masu nikaf suka ɗaukota ba, ashe sun san wa suka ɗauko, yo dama Allah na tuba mu jinin ƴan Nigeria ai fin haka ma zamu aikata ba tare da tsoro ko shakka ba, ai mu karfin halinmu tare da jajircewa a jininmu yake, dan haka kada ku yi mamakin idan Leesharh ta aikata fin haka, yauwa jininmu a tafashe yake, babu abin da baza'a samu a Nigeriarmu ba, mu ai ba'a isa a mana gorin komai ba ato...........🥱 (Jinjina gareki Leesharh jikar baba bola Ahmad tinunbu🥱 kina da karfin hali irin na jikokin tinunbu,🔥 kin ci lambar ya bo, dole villa ta san da zamanki, irinki ake turawa aikin soja🥱) Cigaba da tafiya suka yi. Sun ɗanyi tafiya mai nisa kafin su kai bakin haɗaɗɗen katafaren part ɗin nasu. "Leesharh ki jirani a nan ina zuwa". Ta faɗa tare da nufar cikin part ɗin. Ita kuma Leesharh ta tsaya a bakin stair case da ya yi ƙasa. Shiru ta yi tana tunanin me zai faru idan bawan Allah Ramish ya sha wannan maganin?. Tana son buɗe hannunta ta kalli maganin, amma tana tsoron yin hakan, dan tana zargin wajen da take ɗin da akwai camera. A hankali ta fara jiyo takun sahun mutun yana haurowa saman stair case ɗin, kuma daga jin wannan taku kasan bana ƙananan yara bane. Wani irin tsoro ne ya kamata wanda yasa ta watsa a guje ta bar wajen, kai tsaye hanyar da suka bi suka zo ta nufa. Ita kuwa Sharifat ta kaiwa yayan nata cikin parlournsa, yana zaune saman sofa, jikinsa na sanye da hoodie mai bala'in tsada launin milk color, ya sanya hular rigar a kansa, kasancewar hular rigar ta gaba akwai gashi gashi kamar jikin mage, hakan yasa ba'a ganin face ɗinsa da kyau, ya yi matuƙar kyau sosai a cikin kayan, sai dai kayan kusan kalar fatarsa ce. Kyawawan fararen ƙafafunsa na'a saman haɗaɗɗen carpet ɗin tsakiyar parlourn mai bala'in laushi, ya mike kafafun yana latsa waya, da alama shirin fita ya yi abincinsa kawai yake jira. A gabansa saman center table ta ɗaura tray ɗin, cikin girmamawa ta ce "Yah Ramish ga abincin nan". Ajiye wayar ya yi a gefensa, ba tare da ɓata lokaci ba ya kai hannu ya ɗauki cup ɗin cappuccino ya fara sha. Ita kuma Sharifat ta zauna a gefensa saman sofan da yake ɗin tana faɗin. "Yah Ramish fita zaka yi ne?". Da alama ta mance da cewa ta ajiye Leesharh a bakin kofa tana jiranta. Kai kawai ya gyaɗa mata alamar e fita zai yi ba tare da ya yi magana ba. Cikin nutsuwa ya fara shan cappuccino. Ita kuma ta mayar da hankalinta kan Tv dake magana. Tas ya shanye cappuccino kafin ya miƙe ya nufi cikin master room ɗinsa. Dawo da kallonta kansa ta yi tana son ta tambayesa ba zai ci abincin bane? Sai dai kafin ta tambayesa ya wuce cikin ɗakinsa. Jiransa ta yi har sai da ya fito sanye da haɗaɗɗun takalma a ƙafafunsa, wayarsa ya zo ya ɗauka. "Ki barmun abincin a nan sai na dawo zan ci". Ya faɗa a sanyaye tare da nufar waje da sauri. Kafin ta amsa mashi da okey ma ya fice. Sai lokacin ta tuna da cewa Leesharh na waje ga kuma Ramish zai fito, da sauri ta miƙe ta bi bayansa, dama dayawan lokuta idan ta kawo mashi abinci yin zamanta take yi a part ɗinsa, wani lokaci ma har barci ya ɗauketa, idan da daddare ne ta yi mashi barci a ɗaki sai lokacin da ya gama abin da yake yi sai ya mayar da ita room nata, idan su Bilal sun shigo kuma sai ya ce su mayar da ita. Magana ta gaskiya Sharifat tana son Ramish sosai, shi take burin aura, sai dai shi bai san da hakan ba, kuma babu hakan a gabansa, ita kuma ta kwallafa rai a kansa sosai, shiyasa take son zuwa in da yake, idan tana wajensa mantawa take yi da kowa da komai........,....... Lallai kuwa Sharifat tana kwale kwale, amma kuma idan ta ce shi take so anya zai iya yi wa Abu Abdussalam musu kuwa?🤔 Amma kuma ina tausayawa Sharifat gaskiya, dan son wanda baya sonta take yi, wanda ma bata isheshi kallo ba, kai suma dai da nasu cakwakiyar kunji my people's, mu fita harkarsu, kowa ma da nashi cakwakiyar a littafin nan, yanzu kuma kowa zai fara buga wasansa iya wasa, yanzu game zai fara, zamu ga winners, idan kun ji ana cewa tseren mutuwa to wannan cakwakiyar na cikin littafin nan ne, yanzu dai zamu afka cikin ainahin labarinmu da kuma cakwakiyoyinmu kala kala. A ɓangaren Leesharh kuwa, tana watsawa a guje ta nufi hanyar koma ɗakinta. Dai'dai zata fita cikin wannan ɗan siririn hanya mai ɗan duhun suka ci karo da mutun, hakan yasa kwalbar maganin hannunta ya faɗi ƙasa ya fashe. Wani irin baya baya ta yi tana ƙoƙarin faɗuwa. Da kyar ta iya riƙe kanta ta tsaya, goshinta ya bugu da nashi ne sosai. Kirjinta kara tsananta bugu ya yi saboda tsoro da tunanin da waye ta yi karo? Ga kwalbar maganin ya faɗi ya fashe, shikenan asirinta ya gama tonuwa, yanzu idan aka ga maganin kuma idan wani abin ya sami Ramish kashinta ya bushe!. Shi kuwa Obaid da farko ya ɗauka da Sharifat ce suka yi karon shiyasa bai yi saurin dalla mata mari ba, sai da ta ɗan ja baya ya gane ba Sharifat bace, cikin fusata ya matso tare da sharara mata wani gigitattacen mari a karo na biyu wanda ya sanyata dai'na gane komai. Wani irin azaba ya ji a ƙafarsa lokacin da ya matsa kusa ya mareta, ba komai ne yasa hanan ba kuma face taka kwalbar maganin da ya fashe ya yi, ƙafafunsa suna da laushi sosai, hakan yasa kwalbar ta yi saurin fasa mashi namar cikin tafin kafar tasa ta shige ciki. A hanzarce ya kai kallonsa kasa kan............... To fa akwai cakwakiya, Ramish ya sha maganin nan! Ko maganin menene? Ga Obaid kuma ya kara dallawa Leesharh mari a karo na biyu! Da alama asirin Leesharh zai tonu! Dama kunsan Obaid yana zarginta, ya kuma kafe lallai lallai ita mai laifi ce abar zarga, ga kwalbar maganin ya faɗi ya fashe, bugu da ƙari ya fasa mashi kafa, akwai cakwakiya ba kaɗan ba, dama da Guyson suka ci karo ne, to da da sauki, amma Obaid fa, tab Leesharh kina ruwa wlh, sai dai muce Allah ya ceceki!.. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ FOREST🏞️ 🔥 Zaune Pretty take a cikin Raminsu tana daddaka ganye da wannan farar abin mai kama da lu'ulu'u nasu da suke daka, ita kuma Sweetie tana kan gado ta yi shiru tana tunanin Kamran. Wani irin sauti Pretty ta ji ta bayanta yana fita suuuuu, sirrrrrrrr haka, da sauri ta juyo domin taga menene?. Ai kuwa tana juyawa suka yi ido huɗu da wani murtukeken kumurcin maciji bakin kirin da shi kwance a kusa da dutsen da Kamran yake zama idan ya zo. Macijin yana da girma sosai da sosai, ga shi bakin kirin. Wani irin ihu ta kurma tare da miƙewa tsaye. Ihu da ta yi yasa macijin girgiza jikinsa ya kuma miƙe daga kwanciyar da ya yi, sannan ya yi wani irin kananannaɗa kamar ba lafiya ba, wannan maciji kamar ba maciji ba. A guje ta miƙe tare da rugawa wajen ƴar uwarta, hannunta ta riƙo tana faɗin. "Tashi mugudu Sweetie, mun shiga uku maciji a ɗakinmu". Da karfi ta yi maganar cikin ihu. Ai a dubu ita ma Sweetien ta miƙe, hannunta Pretty ta riƙe gam suka nufi waje da gudu. Ai kuwa macijin yana ganinsu ya rufa masu baya. Da gudun gaske suka fito cikin ramin, sai jan hannun Sweetien take yi, baiwar Allah bata iya ganin komai sai yadda aka yi da ita. Gudu suke yi basu san ina suka nufa ba, shi kuma macijin da kyar ya fito daga cikin ramin, saboda hawace tana yi masu wahala, ko da ya fito babu alamarsu a arear, habawa Pretty sarkin tsoro tuni ya ja Sweetien suka bar arear wajen. Waige waige snake ɗin ya fara yi kamar yadda macizai suke yi idan suka bi mutun ko idan zasu yi mugunta. Ya fasa kai tare da ɗago kan yana nemansu. Ganin babu alamarsu a wajen ne yasa ya kwantar da kansa ƙasa ya fara bin cikin ciyayi suuuuuuuu ya tafi. Su kuwa gudu suke yi babu kakkautawa, basu fa san ina suka dosa ba bayin Allah, sai fincikar Sweetie pretty take yi suna tiƙar uban gudu. Basu fargaba sai ganin wata bakar damisa suka yi a gabansu. Wani irin birki Pretty ta ja har sai da Sweetien ta kusa faɗuwa, a hankali ta fara ja da baya da baya. Suna ta zuba uban haki Sweetie ta tambayeta lafiya suka tsaya?. Ƙasa iya yin magana ta yi, dara daran idanunta na'a kan hakwaran wannan damisa da yake ta faman buɗe baki. Ai bata san lokacin da ta saki fitsari a jikinta ba, zuuu fitsarin ya ganganro ƙasa, tana son ta yi kuka, amma ta rasa ina kukan nata ma ya tafi, wani irin kakkarwa jikinta ya fara yi kamar wadda sanyi ya kama, ji take yi shikenan yau kwananta ya kare. Sai yau ta tuna da addu'ar da mun ɗinsu ta koya masu na idan sunga miyagu zasu cutar da su, sai dai ta ƙasa iya furta addu'ar ma. Sambatun Sweetie na tambayarta lafiya ne ya dawo da ita cikin hayyacinta. Kuka ta fashe da shi mai tsananin sauti tare da cewa. "Sweetie mun mutu yau, damusa ce a gabanmu, baki ji gurnaninta ba? Mun mutu yau kam!". Tana kai karshen maganar ta kara sautin kukan nata. Sweetie na ƙoƙarin yin magana kirjinta na dukan uku uku duk da ita bata kalli damisar ba, bata san ya take ba, amma ta tsorata, tana ƙoƙarin tambayarta damisar Kamran ne wato Rocky. Bata kai ga yin maganar ba damisar ta daka wani uban tsalle ta haykewa Sweetien wanda hakan yasa ta zube ƙasa hannunta dana Prettyn ya rabu, Prettyn ta saketa dan dole ta faɗi ƙasa a gefensu ita ma. Ƙoƙarin capko wuyar Sweetien damisar ta yi, baiwar Allah bata gani sai ƙoƙarin kwatar kanta take yi, tana ta buge buge da hannunta. Ganin hakan yasa Pretty ta miƙe tsaye, zuciyarta tafasa yake yi kamar an ɗaura dalma a wuta, jikinta na tsuma, da taga yadda Sweetie ke buge buge da hannu da kafa, ga shi jikin damisar ya rufe jininta ba'a iya ganinta sai hannu da kafar da take ta bubbugawa a ƙasa tana neman yadda zata kwaci kanta. Ganin haka yasa Prettyn ta yi tunanin ko damisar cin namar Sweetien take yi, ta kara tsorita over! Jikinta na tsuma tana tsotace, nan take ta ji wani karfi ya zo mata, zuciya ba zata iya gani a kashe mata ƴar uwa ba, da wani irin mahaukacin gudu ta nufi damisar, ita kanta bata san ta nufe shi ba, jini ba wasa ba, tashin hankalin kada ƴar uwarta ta mutu ne yasa ta nufi damisar ba tare da saninta ba, bata san tana da karfin zuciya har haka da zata iya tinkarar damisa ba har sai da taga Sweetien a gaɓar mutuwa. Wani irin kukan kura ta yi ta haye saman bayan damisar ta fara kai mashi duka da ƴan hannayenta da basu wuce a kama a karya ba, duka take kai mashi har da su cizo, tana yi tana sambatu a kan ya rabun mata da ƴar uwarta, kada ya kasheta, wlh ita kaɗai kawai take da shi a duniya. (Ni kam na ce ko yaushe damisa yasan duniya bare har yasan yar uwa kuma yasan ita kaɗai kike da shi a duniya? Jama'a ku taya jin abin da Pretty ke gayyawa damisa fisabilillahi 🤌 Allah sarki, duk wata zuciya mai imani ne ba zata ɗauki ganin a kashe mata nata a gabanta ba, barema su da suka taso a tare, basu da kowa, kullum suna manne da juna, suka kwanta ciki ɗaya kuma suka sha nono lokaci guda, ai fin haka ma Prettyn zata aikata) Baiwar Allah ihu take tamkar maƙoshinta zai ɓalle, komai rashin imanin zuciya ta gansu a wannan hali sai ta tausaya masu. Wani irin girgiza damisar ta yi sai ga Pretty ta faɗo ƙasa tim. Ɗago kai damisar ta yi daga kan Sweetien tana kallonta, duk ta farfasawa Sweetie wuya da faratunan hannunta, sai dai bata kai ga tsinke mata maƙogoro ba, har yanzu akwai rai a jikinta. Ihu Prettyn ta sake kurmawa ganin jinin dake malala daga wuyar ƴar uwar tata, da karfi ta miƙewa tsaye, cikin dakiyar zuciya da ita kanta bata san tana da shi ba sai yau data ga bone, da Sweetie ta mutu gara mata ta rinkari koma wace iriyar masifa ce. Wani katon itace dake kusa da ita yashe a ƙasa ta ɗauko, idanunta ya rufe sosai, gadan gadan ta nufi damisar, a lokacin kuma damisar ta mayar da kanta kan Sweetie tana ƙoƙarin lamusheta. Da karfi Prettyn ta daddage ta bugawa damisar itacen a kai. Hakan yasa ta ɗaga kanta sama ta saki wani uban gurnani mai tarwatsa ƙwaƙwalwale masu sauraro. Ita kanta Pretty sai da ta jefar da itacen ta sanya hannu ta toshe kunnuwanta, tare da runtse idanunta ta ɗan yi baya. Wani irin dip da ta ji a kusa da ita ne yasa ta yi saurin buɗe idanunta. Damisar ce a gabanta, ta baro kan Sweetie ta tinkarota, shi ne ta yi tsalle daga kan Sweetien ta diro a gabanta hakan yasa ta ji wannan dip ɗin. Sai a lokacin kuma ta dawo cikin hankalinta ta gane ashe fa damisa ce a gabanta, duk buga mata itace da ta yi bata cikin hayyacinta ne, tsoron rasa ƴar uwarta yasa ta yi duk abin da ta aikata. Yanzu kuma da ta juyo ta kanta sai ta fara tunanin mutuwa zata yi, nan take ta fara hawaye. Cikin takun ƙatsaita damisar ta tunkarota. Habawa kafa me naci ban baka ba? Da wani irin mahaukacin gudu ta juya ta nufi barin wajen, da gudu damisar ta rufa mata baya, gudu take kamar walkiya, kamar zata tashi sama, tana gudu kuma tana ihun a kawo mata ɗauki. (Gaskiya duk da sun ban tausayi a wannan waje, kuma na yi kwallah, amma wlh sai da Pretty ta sake bani dariya😅 dan ni kaɗai naga irin gudun da take yi kamar walkiya😅 Allah sarki gudun cetan rai😥💔 ko in da take kawa bata sani ba, yi take kamar zata fire sama kawai) Ita kuma Sweetie jin damisar ta bar kanta ne yasa ta miƙe jini ba ɓulɓula daga wuyar tata, ta kai hannu ta rike wajen tana kuka gwanin ban tausayi, ga shi bata iya gani, haka ta bazama cikin dajin nan tana layi tana kiran sunan Pretty, kuka take yi sosai gwanin ban tausayi, sai kutsawa cikin dajin take yi ba tare da ta san ina ta nufa ko in take takawa ba. Hanyar yamma ta nufa dan neman Prettyn tana kuka, ita kuma Pretty ta yi gabas ne, so kwata kwata ma basu haɗa hanya ba. Bata yi nisa a lalluɓen hanyar da take yi tana tafiya ba sai ga wasu jiga jigan zaratan matasan maza da mace ɗaya masu ji da lafiya sun sha gabanta, dukkansu sanye suke da fararen kaya tas except macen, kumma dukkansu suit ne a jikinsu, macen kuma wani irin kaya ne mai kama dana mayaƙa ta sanya, macece da a shekaru ba ba zata wuci 22 years ba, mazan kuma zasu iya haura 30 haka. Face ɗinsu da wani irin bakin fenti na zanen bakar damisa, ba zaka taɓa iya gane su wanene bane, maza ne majiya karfi madaka katti. Su goma ne cif sai macen. Daga sama har ƙasa su da gani kasan daga wani ɗaular suka fito, dan babu harkar karanta a tattare da su, sun jiku da naira, sai dai kuma babu alamar imani ko ɗigo a tattare da su, sannan babu annufi a kan fuskokinsu, duk yadda aka yi waɗan nan basu ƙunso alkhari ba!! Dan daga ganin yanayinsu kasan babu lafiya!. Macen cikinsun lafiyayyar mace ce wadda da kallo ɗaya zaka yi mata kasan e lallai ta karɓi horo iya horo bana wasa ba, macece amma damtsen hannunta kamar na Assistant commander wato HOORAIN, daga ganin wannan mayakiya ce ko dai wani abin makamancin hakan. Macen ce ta matso ta ɗauki Sweetie cak ta saɓa a saman shoulder ɗinta, da alama nemanta ne ya kawosu cikin wannan daji, duk yadda aka yi sun san face ɗin Sweetien kuma ita suke nema, dan suna ganinta babu wata wata suka nufeta, duk yadda aka yi ita ce dalilin zuwansu wannan dajin. (Da alama Sweetie ce zata kai mu ga RAWANIN ZALINCI) Gaba da ita macen ta yi, waɗan nan zaratan mazan suka rufa mata baya, da alama itace shugabansu, kuma itace karama a cikinsu, duk sun fita shekaru, amma yadda suke yi mata biyaya sun yi mubaya'a zaka gane e lallai duk yadda aka yi ta fisu matsayi. Gata jajircecciya, daga gani jininta a tafashe yake. Tafiya suka yi da Sweetien ta hanyar da suka fito, sai sambatu take yi tana kiran sunan Kamran da kuma Pretty, Allah sarki bata ma san wanene ya ɗauketa ba. Su kuma sam babu wanda ya ce mata ko sannu a cikinsu, kuma ba kayan mayaƙa ne a jikinsu ba bare muce mayakan da suke nemansu su da mum ɗinsu ne suka kamata, ko dai su ne suka sake yin ɓadda kama da fararen suit? To lokaci ne zai nuna mana koma su wanene. A ɓangaren Pretty kuwa, tana tsaka da tikar gudu wannan damisa ta daka wani uban tsalle da nufin ta sauka a kanta, sai dai bata kai ga yin hakan ba Kamran ya shiga tsakaninsu, dan kuwa hanyar da Pretty ta biyo hanyar kogonsu ne, yana zaune a saman dutsen a waje suna hira da Mammarsa ya jiyo ihu tun daga nesa, ko ba'a gaya mashi ba yasan ita ce, dan muryarta hadda ya yi mata. A ɗari ya miƙe Mamma na kiransa amma ina, ko kallonta bai yi ba, da gudun gaske ya nufi in da ake ihu, to kun ji yadda aka yi. Ai kuwa yana shiga tsakaninsu damisar ta sauka a kansa, rigizib ya zube ƙasa. Habawa hayke mashi damisar ta yi, kokawa da ita ya fara yi yana ƙoƙarin kwatar kansa, ita kuma damisar da waɗan nan shegun faratu nan nata duk ta farfashe mashi fuska, so take ta damki maƙogwaransa ta tsinketa ta kashe shi. Ita kuwa Pretty da bata san ma da cewa Kamran ya zo ba, cigaba da tikar gudunta kawai ta yi tana ihu, a tunaninta damisar na binta, gudu take yi sosai har ta bar yankin mai gabaɗaya, ta yi nisan kiwo. Kamran kuma gabaɗaya damisar ta gama da shi, ko motsin kirki baya yi, duk ta farfashe mashi fiska jini na malala, tana ƙoƙarin capko wuyarsa da bakinta dan ta ƙarisa kashe shi kwatsam ba zato ba tsammani sai ta ɗaga kai sama ta kurma wani irin gurnanin azaba sakamakon wani irin kaifaffen wuƙa da Mamma ta caka mata a ciki. Wani irin gurnani ta saki take da girgiza jikinta. Mamma dake tsaye a dake kamar wata commander mayaka ta fara kalla. Ko alamar tsoro babu a fuskar Mamma, tana tsaye cikin jarumta, ko shakkar damisar bata ji ba, zuciyarta tafasa yake yi, wani irin bakinciki ta ji na jiwa ɗanta ciwo da damisar ta yi, burinta kawai ta zo su gwabza ta kashe banza, dan ita ba yau ta fara faɗa da damisun dake cikin wannan dajin ba, kafin Kamran ya girma ta sha gwagwar maya kafin su shafa mata lafiya, so Mamma ta wuce tunaninku, ita kaɗai tasan wacece ita kuma me yake ranta. Kanta damisar ta yi cikin zafin nama. Ai kuwa bata yi wata wata ba ta sunkuya ƙasa tare da daba mata wata kaifaffiyar wukar a wuya wajen maƙogwaranta. Kun san damisa da zaki taurin rai ne da su, basu mutuwa ta daɗi, dan haka suka fara kokawa da Mamma babu kakkautawa. Ganin haka yasa Kamran ya lallaɓa da kyar da makyarkyata ya miƙe, yana ta layi ya fara nufar hanyar da take ta kudu domin neman Pretty, bawan Allah shi bama ta rayuwarsa yake yi ba, Pretty ce kawai a ransa. Ita kuma Pretty gabas ta yi, Mamma kuma na faɗa da damisa tana ƙoƙarin ƙarisa kashe ta, yau Rocky baya nan, su suke kwatar kansu da kansu, Allah sarki ga Sweetie dai an tafi da ita, ko su wanene?............ Wai yau ina wannan jarumin mai irin idon su Pretty wanda yake kawo masu ɗauki kullum ne?😥💔 To wannan shi ne sanadiyar rabuwar waɗan nan bayin Allah da suka shafi tsawon lokaci a tare, Sweetie, Pretty, Kamran, shin zasu sake haɗuwa? Ya Kamran zai yi idan aka ce yau babu Pretty? Anya zai iya cigaba da rayuwa? Kun san kaunar da take a tsakaninsu fa! Shin Kamran zai je neman babansa? Wanenen ma shi? Wacece Mamma? Ina mum twins ta tafi ta barsu a cikin wannan dajin? Su waye su Pretty? Suwaye suke neman rayuwarsu? Su waye suka biyo mamansu time da take da cikinsu? Meyasa su kaɗai ake da buƙata ban da mamarsu? Meyasa lokacin da aka biyota waɗan da suka biyota cikin nata kawai suke da buƙata? Ina babansu? Ina baban Kamran? Waye wannan jarumi mai irin idon Prettyn? DUBAI. Menene makomar Leesharh? Shin asirinta zai tonu? Maganin me Ramish ya sha? Shin zai cutu da gaske?. Idan Allah yasa Leesharh ta gama aiki shin masu nikaf zasu cika alkawarin da suka ɗaukar mata na haɗata da babanta kuma su mayar da ita kasarsu? Shin da gaske Leesharh ita ta kashe mahaifiyarta? Idan ita ce menene dalili? Wacece ita ma? Ya makomar tsakaninta da Obaid a yanzu? GIDANSU KHADIJAH. Menene makomar maman Zainab? Baban Zainab ya mutu? Ina Hauwa? Idan baban Zainab ya mutu ya maman Zainab zata yi? Zata tsira kuwa? Kisan kai ta yi kenan? Hukuma zasu barta?. KINGDOM OF POWER. Nan ba sai na yi magana ba, cakwakiyar dake ciki ya wuce tunaninku, abin ya wuce zatonku. Shin da gaske Sweetie ce zata kaimu ga RAWANIN ZALINCI? Suwanene waɗan da suka ɗauketa? Ina kuma zasu kaita?. Amsoshinku yana step two, yanzu zamu afka cikin labarinmu, kada ki bari a baki labari, labari ne da yazo da salo na daban, zalinci, cin amana, hainci, cutarwa, zanba cikin aminci, tauye yarda, tauye hakki, cin hakki, cin zarafi, mugunta, keta, da kuma zazzafar soyayya mai cike da kaddarori haɗi da nasarori da kuma fafutukan cikar buri. 500 Naira kacal kuɗin karatun littafin RAWANIN ZALINCI from step one to end, da 500 naki zaki cigaba da karatunsa cikin aminci da kwanciyar hankali, trust me ba zaki taɓa yin danasanin karanta littafin RAWANIN ZALINCI ba, zaki ilmantu matuƙa, zaki nishaɗantu matuka, zaki wa'azantu matuƙa, ku kunsan yadda alƙalamina yake, akwai tarin abubuwa a tattare da shi, ba sai na ɓata bakina wajen sake gaya maku ba. Duk wadda ta shirya biyan kuɗin karatun littafin RAWANIN ZALINCI zata tura kuɗinta ta wannan account ɗin 1882812910 Musa Fatima Zahra access bank. Sai ta tura mun shaidar biya ta nan. 08161390581, kina biya zaki afka cikin tafiyar nan, ayita dake, kada ki yarda a baki labari!!. TAƁA KA LASHE STEP TWO🔥💔😥 KAMRAN AND MAMMA. "Kamran idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu, mutuwa kuma mafi muni a rayuwa, kamar yadda ka taso baka san kowa ba, sai ni, to haka zaka riƙe ka manta da duk wasu tunanin banza". "But Mamma why? I want to know my father ko da kuwa hakan ce zata zama sanadiyar numfashina na karshe, just tell me where's he? Ni zan je in da yake koda kuwa ya fi wuta zafi dole na tunkaresa!! Na kusancesa!!". Tsawa ta daka mashi mai sauti, cikin fusata, idanunta sun kaɗa sun yi jajir, jijiyon kanta har wani mimmikewa suka yi, da alama ranta ya kai kololuwa wajen ɓaci, har wani huci take yi kamar zakanya. "Kamran ina gaya ma zaka yi mutuwar walaƙanci in dai ka sake yin magana a kan babanka! Kai ba mutun ne kamar kowa ba! Kai ba kamar sauran mutane kake ba! Kai na daban ne, farautarka ake yi kamar yadda ake karautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana! Zaka mutu idan ka fita! Zaka mutu kamar dabba! Dan haka ka tsaya a in da na tsayar da kai!!". "Mamma i can't! I can't gaskiya! Idan kuma kina son na bi maganarki so tell me who I am?! Where's my father and my family?! Why are you hiding our life anytime?! Am tired! Am tired Mamma! I want to see my father and my family, cos I can't stay with you again! Tafiya zan yi na nemo babana and Prettyta even wannan shi ne ganina dake ta karshe!". Tashin hankali kenan, ɗan tsokaci a tsakanin Mamma da Kamran kenan, menene dalilin Mamma na hana shi sanin tarihin babansa bayan ya buƙaci sani? Waye shi? Ina mahaifin nasa yake? Meyasa take cewa zai mutu idan ya sake yin magana a kan babansa? Meyasa?!!. SWEETIE.🔥 "Ɗago idanunki da kyau ki kalleni, sannan kuma ki yi mun shiru, a nan ba'a son hayaniya, kada ki bari a jiyo ki". Shiru dole ta yi ba dan ta so ba, sai dan tsoron irin muryar da ta ji anyi mata magana da shi, tabbas wannan murya da ta ji ba muryar wasa bace, kuma da alama babu imani a tattare da mai wannan murya ko ɗigo. "Ina Spender yake? Shi kawai muke da buƙatar ki bamu, kina bamu zamu sakeki, mu bamu da bukatarki a nan wajen!". Wannan murya ce ta sake katseta da faɗin hakan. Su waye su? Meyasa suka ɗauketa? Menene Spender? Ina kuma yake? Me zasu yi da shi?. Murya a dashe saboda kukan da ta rinƙa sha tun safe, murya ya dashe, da kyar ta iya furta. "Menene Spender?". A fusace Delisha ta ɗaga wannan katakon hannu nata zata zabga mata mari, dan a ganinta Sweetien ta raina masu wayo ne, ta isa tace bata san Spender ba? Ba zai yiwu ba dole ta basu yau, abin da suke haukace suke nema, nemansa suke yi kamar hauka, kuma sun san yana wajenta, sama da shekaru biyar suna nemanta, da kyar suka ganota, sun sha bakar wahala a nemanta, amma ta nuna masu bata ma san shi ba? Tama isa?!!. Tana ƙoƙarin sauke mata wannan katakon hannun nata a saman lallausan kumatunta kwatsam ta ji hannun nata ya sage a saman iska bai ƙarisa kai saman kumatun Sweetien ba. Yar karar azaba ta saki kafin ta furta............. Kai kai kai taɓa ka lashen ya isa haka my people's, sai dai mun haɗu a step two kawai, akwai cakwakiya over. Hanzarta ki biya kuɗin karatu dan ki morewa ganin wannan cakwakiyar!.🤸💃💃 Ƴan Niger kuma ban barku a baya ba, ku mun magana ta wannan numberta ɗin dan na gaya maku ta yadda zaku yi naku payment ɗin. 08161390581 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels