Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [10/03, 08:30] Zeey Kumurya: https://chat.whatsapp.com/K8mrKzSJTP1CYMAj1ci1of *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ _*Da sunan Allah mai kowa mai komai, Allah ka sa yanda na fara rubuta Littafinnan lafiya na gama shi Lafiya, Allah ka ba ni ikon rubuta abun da zai amfanar da Al'umma Ameen.*_ ```Kamar yadda na yi alƙawari yau zan fara sakin sabon book ɗina NEEHAL, gashi na cika alƙawarin, sai dai ba na jin daɗi hakan ya sa za ku ga page d'in kaɗan, nima ba haka na so ba, ina buƙatar addu'ar ku🙏🙏😥 Masoya.``` 0️⃣1️⃣ ............A ƙaton parking space d'in gidansu driver'nsa wanda ya kasance soja kamarsa ya yi parking rantsatstsiyar motar da suke ciki, driver'n ya fito da sauri ya zagaya ɓangaren da yake ya buɗe masa motar, ya ɗan ja baya tare da sara masa irin nasu na sojoji, a hankali ya ziro da santaleliyar ƙafarsa ta dama, bayan 3 seconds ya ziro ta hagun itama tare da fitowa gabad'ayansa fuskarsa babu walwala ko kaɗan kamar kodayaushe, kai kawai ya gyad'awa driver'n ya fara tafiya cikin takunsa na ƙasaita da isa, part ɗin mahaifiyarsa ya nufa direct, duk inda ya gilma sojojin dake kai kawo a farfajiyar gidan na sara masa, kasancewar mahaifinsa shima GENERAL ne na sojoji, hannu kawai yake d'aga musu. Da sallama ƙasa_ƙasa ya shiga main parlour na part d'in Mama, Mama da mahaifiyarta Hajiya dake zaune a parlorn suka amsa masa suna binsa da kallo, Hajiya tana washe baki ta ce "Aminullahi! sannunka da zuwa, ashe da rabon zamu haɗu da tuni yau na tafi baffanku ya ce in bari sai Monday zai zo mu tafi" ya ɗan saki fuska ya ce mata "Yawwa, ina yini" idanunta na kansa ta ce "Lafiya k'alau, ya aikin?" ba tare da ya amsa mata ba, ya zauna a kujerar dake fuskantar ta su ya dubi mahaifiyarsa wadda suke tsananin kama da shi tamkar an tsaga kara ya ce "Ina yini Mama" ya ƙarasa zancen yana dafe kansa tare da taune lips d'insa na ƙasa dan maganama wahala take masa" Mama data k'ura masa ido ganin yanda ya rame ta ce "Lafiya k'alau, yau sai yanzu kazo har ina shirin kiranka in tambayeka ko this week ba za ka zo ba, Dad ma kafin ya fita yanata ta tambayarka" ya gyad'a mata kai kawai tare da kwantar da kansa a jikin kujera ya lumshe fitinannun idanunsa, Hajiya data saki baki da hanci tana kallonsa ta ce "Aminullah cuta kayi acan Lagos ɗinne naga duk ka zabge ka rame haka, kamar wanda ke zaune cikin guggun mayu?" Shiru yay mata kamar ba da shi take ba , A ɗan fusace Hajiya ta ce "Nifa matsalata dakai jarababben miskilancinka na tsiya, ana maka magana kana yiwa mutane banza" nanma shirun ya kuma mata, Mama ta tab'e baki ta maida kanta akan wayarta dake hannunta, Hajiya ta dubeta ta ce "Ke kuma Fatima wacce irin uwa ce ke? Kina kallon yaro ya dawo a haka, ai kya tambayesa ki ji me ya samesa ya yi irin wannan zabgewa haka" Mama ta d'ago da kanta tana duban Hajiya ta ce "Amma fa Hajiya kinsan halinsa, ko zan kwana ina tambayarsa abin da ke damunsa idan bai ga dama ba, ba faɗamun ze yi ba, kema kuma gashi kin tambayesa ya miki shiru" cikin faɗa Hajiya ta ce "To kuma sai abiye masa, ai ba dan shi zaki yi ba" Mama ta ce "Hmmm, Hajiya Ameen fa ba yaro ba ne yasan ciwon kansa" Hajiya ta ce "Sai kuma ki yi, amma dai wannan rashin kula ne gaskiya, ace kiga yaro haka ki nuna masa halin ko in kula, ni tunda ya rainani ai ba ze bani amsa ba dama, amma ke tunda ke kika haifeshi dole ya sanar miki" Mama ta mata shiru ta cigaba da sabgarta, Hajiya ta cigaba da mitarta da masifarta. Wata kyakkyawar budurwa ce take sakkowa daga kan steps d'in dake parlour'n, sanye take cikin wani wandon jeans dark blue wanda ya kama jikinta sosai, sai riga t_shirt pink colour, babu ɗankwali akanta, kawai ta tufke gashintane cikin ribbom, hannunta riƙe da waya tana latsawa da earpiece sanye a kunnenta, Mama ta d'ago jin takunta tana kallonta fuska a daure ta ce "kar ki kuskura ki ƙarasomun nan a haka" NEEHAL ta d'ago da kanta daga kallon wayarta da take ta kalli Mama sannan ta juya ta koma inda ta fito ta na turo baki gaba, Hajiya ta keb'e baki ta ce "Oh ni Zainabu, Allah kanunamun ranar da wannan yarinya za tai hankali ta san ta girma" Neehal ta koma ɗakinta tana kwab'e fuska ta ɗakko after dress ta ɗora a kan riga da wandon jikinta tare da sanya hula a kanta ta ƙara fitowa ta dawo falon ƙasan, Hajiya ta ce "To ba ki fi kyan gani ba yanzu, amma da kinfito kamar wata y'ar arna" Neehal ta turo baki gaba, ta na ƙoƙarin zama kusa da Mama ta lura da Ameen dake zaune yanda yake tun d'azu, waro manyan idanunta tayi waje cikin murnar ganinsa ta ce "Yayana yaushe ka zo?" Ameen wanda tun sanda ta ƙaraso falon ya buɗe idonsa yake kallonta ta ƙasan ido baice komai ba, Neehal ta koma kusa dashi ta zauna, dama tunda ta shigo falon taji k'amshinsa amma bata lura da shi ba saboda mitar da Hajiya take mata, ta tattaro duka nutsuwarta saboda sanin halinsa ta ce "Yaya ina yini" bai tanka mata ba, sai idanunshi daya mayar ya lumshe kawai. Neehal ta ɓata fuska ta tashi daga kusa dashi ta koma kusa da Mama, Hajiya ta ce "Wannan mugun hali naka Aminu Allah ya sauya maka shi da gaggawa, yarinyar ta taho da murnarta tana maka magana amma ka shareta, saboda baƙin hali irinnaka" Mama ta dubi Neehal data kwanta mata a jiki ta ce "To mage, sai yanzu kika tashi daga baccin?" Neehal ta ce "Um" Mama ta ce "K'arfe nawa zaki aiki?" Neehal ta ce "Around 4" Mama ta ce "Sai ki tashi ki shiga kitchen for lunch, kinga 2 ta kusa" Neehal ta kwab'e fuska sosai tana barin jikin Mama ta ce "Tom" Arayuwar Neehal bata k'aunar aiki ko kaɗan, musamman ma girki ta fi tsanarshi, gashi in dai tana gida ita take yi, Mama ba ta yi, masu aiki dama wanke_wanke da shara kawai suke yi sai kuma ɗan tayayyar aiki, dan ko Neehal tana School ko gurin aiki Mama ke girkinta da kanta. Neehal ta mik'e tana duban Mama ta ce "Me zan dafa?" Mama ta ce "ki yi abun da zai yi sauri dan kar ki yi late gurin aiki, akwai ma soyayyen kayan miya na soya ɗazu, ki haɗa miya kawai sai ki dafa wani abun simple a ci da miyar" Neehal ta ce "Toh" tare da nufar hanyar kitchen. Hajiya ta ce "ki yi sauri da'Allah kar yunwa ta kashemu" Neehal bata bi takanta ba ta shige kitchen. Mama ta mik'e tana duban Ameen ta ce "Mit me in my room" batajira amsarsa ba tayi hanyar step, a hankali ya mik'e ya bi bayan Maman, Hajiya ta bishi da kallo cikin tausayinsa kamar zatayi kuka ta ce "Aminu Allah ya baka lafiya, bari jenal ya dawo gaskiya a san abin yi, tunda ita uwarta ta ka shashashace" Mama tana duban Ameen dake zaune a gefenta a bakin gado fuskarta babu wasa ta ce "Ameen me ke damunka?" Shiru ya yi tare da sunkuyar da kansa, Mama cikin takaicin shirun da yay mata ta kuma cewa "Ameen da kai nake fa, ko ba ka jina ne, kasan bana son wannan iskancinnaka ko, ana maka magana ka na jin mutane ka yi musu banza" Jin yanda Mama ta yi magana a fusace ya sa shi d'agowa ya na duban Maman cikin muryarsa mai daɗin amo da sanyi ya ce "Babu komai Mum" ya ƙarasa zancen ya na taune Pink lips d'insa na ƙasa tare da maida idanunshi ya lumshe ya na sauke numfashi a hankali. Mama ta bishi da wani irin kallo cike da takaici gami da mamakin halinsa na zurfin ciki, tun yana ɗan ƙaraminsa haka yake, miskilancinsa da zurfin cikinsa ya yi over. Mama ta sauke numfashi cikin ƙoƙarin ganin ta danne tata damuwar, cikin sanyin murya mai nuni da rarrashi ga wanda akewa ta fara magana, "Al'Ameen!" Ta kira sunanshi a ɗan kausashe, bata jira amsarsa ba ta cigaba da magana da faɗin, "Ameen, Ni mahaifiyarkace duk duniya ba ka da kamata kamar yadda nima ba ni da kamarku, ko kaɗan ba na son ganinka cikin damuwa, amma kuma 2 years kenan idan ban manta ba kullum cikin damuwa nake ganinka, ka faɗamun menene damuwarka ko na samu nima hankalina ya kwanta" buɗe idanunsa da suka yi nauyi ya yi ya saukesu akan fuskar Mama wadda take kallonsa itama, matsowa jikinta ya yi ya kama hannayenta zuciyarta cike da tausayinta ya ce, "Babu komai fa Mum, ni babu wani abu da ya ke damuna, idanma da akwai addu'arki kawai nake buƙata" kallonsa kawai Mama ta tsaya ta na yi, duk wannan uwar ramar da ya yi amma ya ce mata babu abun da yake damunsa. Ajiyar zuciya ta sauke, dan tasan tunda ya faɗa mata haka ba zai taɓa faɗa mata abun da yake damunnasa ba, kome zata masa kuwa, kamar yadda ya faɗa addu'ar kawai za ta cigaba da masa. Ganin yanda take kallonsa ya ce "ki yi haƙuri UMMUNAH, ba na son ki sa damuwa a ranki, dagaske nake miki babu abun da yake damuna ki yarda da ni mana" Mama ta nunfasa ta ce "Shikenan, Allah ya sa mu dace" a saman lab'b'ansa ya amsa da "Amin" tare da sakin hannun mahaifiyartashi. Mama ta ƙara fuskantarshi ta ce "Saura kuma maganar da muka yi kwanaki, na gaji da yawo da hankalin da kake mini Ameen, ka fitar da mata ka ƙi" ɓata fuska ya yi ya ce "Har yanzu ban sami wadda tamun ba ne" Mama ta masa wani kallo ta ce "Ita kuma Hamidan da take jiranka kusan shekaru goman fa, koma ba Hamidan bama ai ba rasa masu sonka ka yi ba, dan haka banason wani zancen banza, wannan itace last Maganar da zan yi maka akan ka fitar da matar Aure, zan d'aga maka ƙafa zuwa bayan bikin Neehal, idan ba ka zaɓi mata da kanka ba Ni zan zab'a maka, danni da son raina ne ma a yi bikinka tare da na Neehal" jinjina mata kai kawai ya yi ya mik'e ya fice daga ɗakin, dan kwata_kwata baya son maganar Auren da Mama take yi masa a kodayaushe. Mama ta bishi da kallo zuciyarta babu daɗi. Neehal ta na shiga kitchen ta dakko tukunya ta d'aurayeta ta zuba ruwa ta kunna gas ta ɗora, wayarta dake kan locker kitchen ce ta fara ringing, dakkowa ta yi ta sauri ta duba sunan *HEART CRUSH* ta ga ya na yawo akan screen ɗin, ɗagawa ta yi da murmushi akan fuskarta ta ce "Aloo" daga ɗaya ɓangaren Haneefah ta ce "Na bi Aloo d'in da gudu, dan iskanci na kiraki tun ɗazu amma shine ba za ki iya biyo bayan kirannawa ba" Neehal ta na murmushi mai sauti ta ce, "Sorry Bestynah, time ɗin da kika kira ina bacci ne, ban jima da tashi ba mama ta tura ni kitchen girki, so nake na ɗan rage aikin dama na kira ki ke da MY HUSBAND" Haneefah ta tab'e baki ta ce "To me miji, mun dai kusa miƙa ki gidansa kowa ya huta da rashin kunyarki" Neehal ta yi 'yar ƙaramar dariya ta ce "Na ji ɗin, ya kike ya Mommy?" Haneefah ta ce "Mommy tana Lafiya nima haka, ya Mama da Hajiya da Husband d'in naki?" Neehal ta ce "Suna lafiya ƙalau" Haneefah ta ce "Masha Allah, dama kiran ki na yi in ji ko kin dawo daga school" Neehal ta ce "Tun 12 na dawo" Haneefah ta ce "Da wuri haka?" Neehal ta ce "Kin manta yau Saturday lecture ɗaya gareni 10_12" Haneefah ta ce "Hakane fa, na sha'afane" Neehal ta ce "Yaushe za ki fito ne?" Haneefah ta ce "Ni yanzuma na gama shiryawa shiyasa na ƙara kiranki" Neehal ta ce "Toh ki zo mana, sai ki tayani na ƙarasa girki sai mu wuce kawai" Haneefah ta ce "In zo in taya ki girki ko kuma ki ce in zo in ƙarasa Miki girki?" Neehal ta ce "Ni dai koma yaya ne ki yi sauri ki zo" Haneefah ta ce "Toh Mommy ganinan" Neehal ta yi dariya ta ce "Sai kin ƙaraso" ta kashe kiran ta lalubo number'n masoyinta kuma mijinta nan da watanni biyu masu zuwa insha Allah wato ANWAR, kiransa ta yi amma no Answer, ajiye wayar ta yi batare data ƙara kirannasa ba, dan tasan ya na wani uzurinne da ya hanashi d'aga wayar tata, komawa ta yi ta cigaba da aikinta. After 15 minutes Haneefah ta ƙaraso gidan, Mama tana sama har time ɗin, Hajiya ce kawai kwance akan kujera bacci ya ɗauketa, Ameen kuwa part ɗinshi ya yi bayan ya dawo daga ɗakin Mama. Kitchen Haneefah ta nufa bayan ta ajiye handbag d'inta da mayafinta a kan kujera, Neehal tana cikin slicing d'in cabbage da za ta yi co'slow da shi Haneefah ta yi sallama a kitchen d'in, da sauri Neehal ta ajiye abun hannunta tare da juyawa cikin farin cikin ganin besty'ntata ta amsa mata sallamar, itama Haneefah cike da murnar ganinta ta ƙaraso inda take, rungume juna suka yi Neehal tana faɗin "Welcome dear" Haneefah ta saketa tana faɗin "Thank you" Neehal ta ce "Yau gabad'aya ban ji d'uriyarki da takurarki ba, na yi missed ɗin ki" Haneefah ta ce "Nima haka diarling, ina Mama fa?" Neehal ta ce "Ta na sama may be" Haneefah ta ce "Na ga mutuniyartamu ana ta shan bacci ai" Neehal ta ce "Hajiya rigima, ta kusa tafiya ai mu huta da magana, yawwa dear dan Allah ɗan ƙarasa mini girkinnan na je na shirya kar mu yi latti" Haneefah ta harari Neehal ta ce "Ba wani dan ki shirya, kawai dai ki ce kin ga ji da aikin" Neehal ta b'ata fuska ta ce "Kamar kin sani kuwa" Haneefah ta ce "Hmm, yarinya idan ma za ki daure ki na girki ta daɗin rai ki daure, dan idan aka kai ki gidan ki dole ki yi" Neehal ba ta ce komai ba ta fice daga kitchen d'in. Ta na fitowa falo ta ji mayen k'amshin turaren Ameen da har time ɗin bai bar falon ba, tunawa ta yi ashe fa ya dawo, kallon saman steps ta yi ta juya kamar wata mara gaskiya tana tafe ta na waige ta buɗe ƙofar falon a hankali ta fice ta nufi part d'in Yayannata dake kusa da nasu part d'in.......✍️ *Neehal it's free book, your comments and share kawai nake buƙata* *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *0️⃣3️⃣* .............Lumshe idanunta ta yi tana shaƙar daddaɗan kamshinsa da ya mamaye falon, numfashi ta sauke ta buɗe idanunta a hankali cikin ƙoƙarin dai_daita nutsuwarta ta cigaba da tafiya kanta a ƙasa, sallama ta yi masa cikin siririyar muryarta tana kyab'e fuska ita a dole fushi take da shi, ba tare da ya d'ago ba ya amsa mata sallamar a can ƙasan mak'oshi, har ta ɗan wuce shi za ta haura saman steps ya kirata ta hanyar faɗin "Miemah!" Tsayawa ta yi tare da juyowa amma ba ta ƙaraso inda yake ba, kamar ba shi ya kira ta ba ya wani waske abunsa yana ta aikin latsa wayarsa, sanin halinsa ya sa ta ƙaraso inda yake ta zauna a ƙasan kujerar da yake ta ce "Ga ni Yayah" Be kulata ba, kusan 2 minutes kamar ya manta da ita a gurin, sai kuma ya d'ago ya mata wani kallo, cikin daddaɗar muryarsa mai daɗin sauraro ya ce "Sau nawa zan hanaki bulbula turare a jikinki idan zaki fita?" Turo baki ta yi gaba ta ce "Kaɗan fa na saka" ya ce "Ƙarya na miki kenan?" Girgiza kanta ta yi alamar a'a, maida hankalinsa ya yi kan wayarsa, Neehal na son wucewa sama amma ta na tsoro tun da bai bata umarni ba, shikuma ya cigaba da al'amuransa kamar ya manta da ita a gurin, kuma ya na sane umarninsa take jira, ɗayar wayarsa da ke ajiye a kusa da shi ce ta yi ƙara alamun shigowar kira, dubawa ya yi, ganin sunan Dad na yawo akan wayar ya sa shi d'agawa da sauri. Dad ya ce "Muhammad ka dawo daga masallacin ne?" Ameen ya ce "Eh" Dad ya ce "Daughter din ta dawo ne" ya ce "Eh" Dad ya ce "Ok, ina son ganinka yanzu a part ɗina" Ameen ya ce "Ganinan zuwa yanzu" ya katse wayar tare da miƙewa ya nufi part d'in Daddy wanda akwai ƙofar da za ta sadaka da part d'in Daddy'n ta cikin falon Mama. Neehal ta mik'e da sauri kamar wadda ke zaune a kan ƙaya ta haye sama. Ɗakin da Hajiya take ta lek'a, Hajiya dake zaune kan darduma ta na lazimi ta dubi Neehal ta ce "A'a kin dawo ne?" Neehal ta ce "Ba gashi kin ganni ba" Hajiya ta ce "To sannunki da dawowa, ina ja'irar ƙawar taki?" Neehal ta ce "Ta wuce gida, Mama ba ta dawo ba?" Hajiya ta ce "Sai bayan magriba fa ta tafi, na yi_na yi ta haƙura da zuwa asibitinnan ta huta itama amma ta ƙi, kamar wadda aka yi wa wahayi haka ta tafi a darennan, dan ma aikin Allah za ta yi, tun da duba marasa lafiya ne" Neehal ba ta ce Komai ba ta juya ta fice ta nufi ɗakinta. Tana ajiye jakarta ta fito ta nufi kitchen, cake ta ɗauko da meatpie saboda wata irin yunwa ta ke ji, ɗakinta ta koma bayan ta ɗau drink a falo, sai da ta ci ta yi k'at, sannan ta tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala dan yin sallar isha'i. Tun da Ameen ya shigo Dad yake binsa da kallo cikin mamakin irin ramar da ya yi, duk da Mama ta masa bayani a waya amma bai yi zaton abun ya kai haka ba, Ameen ya zauna a ƙasan kujerar da Abba yake tare da sunkuyar da kansa ƙasa, Dad ya nisa ya ce "Muhammad cuta ka yi a can barrak ɗinne ba mu sani ba?" Ameen ya ce "A'a Daddy" Dad ya ce "To wannan ramar fa ta menene?" Shafa lallausar sumar kansa ya yi tare da lasar lips d'insa na ƙasa, cikin girmamawa ya ce "Dad yanayin aiki ne kawai" Dad yay shiru ya na kallonsa ba tare da yarda da abin da ya ce ɗin ba, sanin halinsa koda zai kwana yana tambayarsa ba faɗa masa abin da ke damunsa zai yi sai ya kyale shi kawai, amma tabbas ya san akwai abin da ke damun ɗan nasa. Sauke numfashi Dad ya yi ya ce "Shikenan Captain, Allah ya taimaka ya ba da sa'a" Ameen ya amsa da "Amin" Dad ya gyara zama ya ce "Ɗazu kafin na fita mun yi magana da Doctor akan shirye_shiryen bikin Daughter, tunda bikin ya matso, ya kamata mu san abin yi mu fara shiri" Ameen ya ce "Hakane, Allah ya kai mu Lokacin da rai da lafiya, ya kuma sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya" Dad ya ce "Amin ya Allah, ta mun Magana kuma a kanka kaima, ya kamata a ce zuwa yanzun kaima ka fitar da matar Aure, dan mu da son samu ne ma a haɗa bikinka da na Daughter" Ameen ya d'ago kansa da sauri ya na duban mahaifinnasa amma bai ce komai ba, Dad ya ce "Kayi shiru Captain" Ameen ya sauke Numfashi ya ce "Dad a dan ƙara mini time, zuwa bayan bikinnata insha Allahu zan fitar da mata nima" Dad ya ce "To shikenan, Allah ya kai mu da rai da lafiya, ya kuma haɗa ku da abokan zama na gari, Allah ya muku Albarka" Ameen ya ce "Amin ya Allah" Wata hirar suka shiga daban akan aikinsu na sojoji. Neehal tun tana sallah take jin wayarta na ringing, sai da ta idar ta yi shafa'i da wutri sannan ta ɗakko wayoyinnata dake cikin jakarta. Wayarta da personnal sim ɗinta yake ciki ake kira, missed call ɗin Mama ta gani da na masoyinta, Layin Mama ta fara kira, ringing daya Mama ta d'aga, Neehal ta ce "Hello Mama" Mama ta ce "Wato Neehal har yanzu ba ki koyi sallama a waya ba ko?" Neehal ta ce "Sorry Mamanah" Mama ta ce "Sorry for your self, kin dawo gida ne?" Neehal ta ce "Eh tun ɗazu" Mama ta ce "Dad fa?" Neehal ta ce "Shima na ga car ɗinsa a parking space, amma ban je part d'in shi ba, na tsaya Sallah ne" Mama ta ce "Ok, kin ci abinci dai ko? Dannasan halinki da zama da yunwa" Neehal ta ce "Na ci snaks" Mama ta ce "Haka dai ki ka iya, Ina Hajiya?" Neehal ta ce "Ta na ɗakinta, Yaushe za ki dawo Mama?" Mama ta ce "Sai 10, dama kira na yi in ji ko kin dawo, zan yi abu yanzu ki kula" Neehal ta ce "Toh Mama sai kin dawo" daga haka ta katse wayar. Number'n Anwar ta dannawa kira, sai da ta kusan katsewa ya ɗauka, Neehal ta ce "Amincin Allah ya tabbata ga farin cikin zuciyata, dafatan ka wuni lafiya, kaina bisa wuya na, yau nasan Queen ta yi lefi" Anwar ya lumshe idansa cikin jin daɗin kalamanta da tsananin farin cikin jin muryarta ya ce "Tare da ke tauraruwar da ke haskaka birnin zuciyata, amma tabbas yau kam Queen ta mini laifi babba ma" Neehal ta waro kyawawan idanunta waje tana murmushin jin daɗin kasancewarta da masoyinnata ta ce "Haba my Habibi, a yi haƙuri mana insha Allahu Queen ba za ta kuma ba" Yanda ta yi maganar cike da shagwab'a ya sa sai da tsigar jikin Anwar ta tashi, ya ɗan sauke numfashi ya ce "Shikenan ai Queen ɗita ta wuce gaban komai a gurina, amma dai yau ta mini k'wauron jin muryarta wanda hakan ya sa na rasa nutsuwata gabad'aya" Neehal ta ce "Am so sorry mijin, missed call ɗin farko da ka mun ina bacci ne, da na tashi kuma na kira ka ba kai picking ba, har na je gurin aiki na dawo ba ka kira ba, sai yanzu" Anwar ya ce "Sarkin bacci, to ya kike?" Neehal ta ce "Alhamdulillah sai kewarka da ta cikamun zuciya da gangar jikina" Anwar ya ce "Missd You too my love, ya Mamana da Yayanah da Dad ɗinmu?" Neehal ta ce "Duk sunanan lafiya k'alau, ya Amminah?" Anwar ya ce "Masha Allah, Ammi tananan klu" Neehal ta ce "Ka gaidata Please da sauran 'yan gidan" Anwar ya ce "Za su ji Insha Allah, yaushe zan zo in ganki ne na yi missing kyakkyawar fuskarnan taki" Neehal ta ce "Gobe mana" Anwar ya ce "Allah ya kai mu amaryata" Hira suka ci gaba da yi irin ta masoya mai cike da nishad'i da farin ciki, ba su wani jima ba su ka yi sallama Neehal ta ce za ta part d'in Dad ne. Da sallama ta shiga falon Dad, Dad na zaune akan kujera ya na karatun jarida time ɗin Ameen ya fita, Dad ya d'ago tare da amsa sallamar Neehal ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi, Neehal ma murmushin ta ke yi ta ƙaraso cikin falon tana faɗin, "My Dad yau na yi missing ɗinka over" Dad ya ce "Nima haka my daughter, ya aikin" Neehal ta ce "Alhamdulillah" tare da zama a gefen Dad d'in, Dad ya ce "Ɗazu bayan mun fito daga meeting na kunna TV na ce bari in ga daughter nah, time ɗin ki na labaran yamma" Neehal ta yi murmushi "Dad ya ce, yanzu nake shirin kiranki na ce ki had'o mini fruits" Neehal ta Mik'e tana faɗin "Bari na had'o maka to" Dad ya ce "Yawwa ɗiyar albarka" Neehal ba ta wani jima ba, ta dawo ɗauke da vowl wanda ta yayyanka fruits d'in a ciki, ta ajiye akan Centre table ɗin dake gaban Dad, Dad yana dubanta da murmushi a kan fuskarsa ya ce "Thank you Amarya" Neehal ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Tare su ka sha fruits d'in da Dad, ya na ta zolayarta da yake Dad mutum ne mai barkwanci, hirar su suke irin ta ɗa da mahaifin da ya ja ƴaƴansa a jiki, har sai da Mama ta dawo sannan Neehal ta koma part ɗinsu. Sau da ta biya ɗakin Hajiya ta mata sai da safe sannan ta wuce nata ɗakin, wanka ta fara yi sannan ta ɗauki wayoyinta ta kwanta akan lumtsumeman gadonta bayan ta kashe light d'in ɗakin, data ta kunna ta shiga yanar gizo, sai wajen 1pm ta kashe datar bayan ta gama shan hira da masoyinta Anwar da besty'nta Haneefah da sauran freinds ɗinta da 'yan'uwa da abokan aiki. Misalin ƙarfe uku da ƴan mintuna na daren Mama ta kirata, ɗagawa ta yi muryarta cike da bacci ta yi sallama, Mama ta amsa mata tare da faɗin "Ki tashi ki yi Sallah toh" Neehal kamar za ta yi kuka ta ce "Mama dan Allah ki bar ni na yi bacci na, gobe fa da safe za ni aiki, kuma ban daɗe da kwanciya ba" Mama ta ce "Ni na hanaki kwanciya da wuri, ai kin san da sallar ki ka tsaya chat" Neehal ta ce "Ba fa chat na yi ba, karatu na yi, kin san 2 weeks ya rage mu fara exam" Mama ta ce "Na ji, ki tashi ki yi Sallar dai, ko raka'a biyu ce, kin ga auren ki ya kusa, ki roƙi Allah ya kawar muku da fitintunu a zama auranku, yanda auren yanzu ya zama na zamani, dole sai mun dage da addu'a" Neehal ta ce "To Mama" Mama ta ce "Yawwa my daughter, ki yi addu'a sosai, sharrin mutum da Aljan Allah ya kare mu" Neehal ta ce "Ameen, bye" Mama ta katse wayar, Neehal ta yunk'ura ta tashi ta shiga toilet dan d'auro alwala. Washegari, bayan ta idar da sallar asuba ta yi karatun Alkur'ani mai girma izifi biyu, sannan ta ɗauko materials ɗinta na school ta ɗan dudduba, gari na fara haske ta tashi ta gyara ɗakinta, sannan ta faɗa toilet ta yi wanka. 7:30 ta sakko ƙasa cikin shirinta na zuwa gurin aiki, ta na sanye da hijabinta wanda ya zo mata har ƙasa, Mama ta na kitchen ta na haɗa break fast, ƙarasawa kitchen d'in ta yi ta ce "Morning Mum" Mama ta ce "Morning dear, har kin fito" Neehal ta ce "Ehh, kin san yau Sunday za mu haɗa labaran week d'in gabad'aya dole sai na je da wuri" Mama ta ce "Amma dai ki tsaya ki yi break" Neehal ta ce "Idan na je can zan ci, bari na ɗiba cake" Mama ta ce "A'a ki dai tsaya ki ci abincin ko kaɗanne nasan halinki ba ci za ki yi ba" Neehal ba ta musa ba, ta haɗa tea a ƙaramin cup ta d'ebi soyayyayen phatatoe d'in da Mama ta soya kaɗan, ta koma falo ta ci. Kayan ta dawo kitchen ta ajiye bayan ta gama ci, ta yi wa Mama sallama, Maman ta mata addu'a ta fice. Sai da ta biya part d'in Dad sharp_sharp ta gaishesa sannan ta fito ta tafi........✍️ *Ku cigaba da haƙuri, ina yin garau za ku na samun Read more da yawa insha Allah.* *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL ⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *0️⃣2️⃣* .............A hankali ta tura ƙofar falonsa, ta yi sa'a kuwa ƙofar a buɗe ya barta, shiga ta yi gabanta na ɗan fad'uwa saboda sanin halin Yayannata da kuma tsoronsa da take masifar ji. Ya na zaune a kan kujera 2 seater ya jingina bayansa a jikin kujera idanunshi a lumshe hannunshi dafe da kanshi, Neehal ta ƙaraso kusa da shi a hankali idanunta k'ur a kansa, gabantane ya fadi ganin irin ramar da ya yi, dan ɗazu kwata_kwata bata lura ba, a ɗan ruɗe ta ce "Yaya!" Bai motsa ba balle ya nuna ya ji ta. Ba ta damu ba ta zauna a kusa dashi kamar za ta yi kuka ta kuma faɗin "Yayah ba ka da lafiya ne?" Shiru yay mata kamar ba zai amsa ba, sai kuma can ya d'ago da kansa ya na ɗan sauke numfashi ya dubeta, kallon ta ya yi na 3 seconds kafin ya daukey idonshi daga kanta tare da girgiza mata kai alamar a'a. Idanunta na kawo ruwa ta ce "Gashinan ka rame, Please yaya mai ke damunka?" Haɗe rai ya yi sosai har sai da gabanta ya fadi amma bai ce komai ba, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta wanda ta kasa tantance na banzan da ya yi da ita ne ko kuma na ganin shi cikin damuwa da ta yi?" Ta na hawayen ta ce "Yay......" cikin tsawa ya dubeta ya ce "Kin san bana son takura ko? tashi ki fita" turo ɗan karamin bakinta ta yi gaba ta na share hawayen fuskarta ta tashi ta fita, Bin ta ya yi da kallo ta ƙasan ido har ta fice, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya maida idanunshi ya lumshe zuciyarsa na masa ɗaci. Haneefah ta dubi Neehal da ta tsaya jiki a sanyaye tun da ta dawo kitchen d'in ta ce "Besty me ya faru na ganki haka?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya idanunta na cikowa da k'walla ta ce "Yaya ne" Haneefah ta ci gaba da juya miyar da take dan in da sabo ya ci ace ta saba da rashin shirin Neehal da Yayannata, kamar ba za ta kula da zancen ba sai kuma dai ta ce "Me yay miki kuma yau" Neehal cikin raunananniyar murya ta ce "Besty ba ki ga yanda Yaya ya rame ba, amma na tambayeshi meke damunshi shine ya ce mun bakomai, na roƙe shi ya faɗamun shine ya koro ni" Ta ƙarashe zancen hawaye na zubo mata akan kuncinta, Haneefah ta juyo ta fuskance ta, ta ce "Ni fa daɗina dake saurin kuka, yanzu mene abun kuka anan?" Neehal ta ce "Ba za ki gane ba ne Besty, amma ba ki ji yanda nake ji araina ba, ganin shi cikin damuwa da na yi" Haneefah ta ce "Tom shikenan ki yi masa addu'a, koma me ya ke damunsa Allah ya yaye masa ya kuma bashi lafiya" Neehal ta ce "Ameen" Haneefah ta ce "Yawwa ko ke fa, to share hawayennaki 'yar Mama, kin san fa ke amarya ce ba na son na ga kina damuwa, kar mu kaiwa ya Anwar ke a rame" Neehal ta yi Murmushin yaƙe, saboda fad'uwar da gabanta ya yi, ta rasa me ya sa a duk lokacin da a ka yi zancen bikinta sai ta ji fad'uwar gaba, daurewa kawai ta ke yi, fita ta yi daga kitchen d'in domin ta je ta shirya, ɗakin Mama ta shiga ta tarar da Mama zaune ta na karatun Alkur'ani mai girma, zama ta yi har Maman ta kai ƙarshen aya, Mama ta d'ago ta dube ta, ta ce "Kin gama girkinne?" Girgiza mata kai Neehal ta yi, Mama ta ce "Toh menene kuma na ganki haka?" Cikin damuwa Neehal ta ce "Mama Yaya ne na ga kamar bashi da Lafiya, kuma na tambayesa me ke damunsa ya ƙi faɗamun sai ma koroni ya yi" Mama ta ce "To ke halin Ameen ɗinne ba ki sani ba ko me? Kin san ba faɗa miki zai yi ba, wa ya aike ki?" Neehal ta b'ata fuska ta ce "To ba Yayana ba ne?" Mama ta ce "Kin ga Yayanki ai, Ni tashi ki je ki ƙarasa mun girki kar time ya k'ure ki bar Ni da shi" Neehal ta tashi tana turo baki gaba ta fita. Bedroom ɗinta ta shiga, rage kayan jikinta ta yi ta shiga toilet dan yin wanka. K'arfe uku dan wasu mintuna Neehal ta gama shirinta cikin wata rantsatstsiyar doguwar rigar abaya maroon colour, wadda ta ji kwalliyar stones milk colour, rolling mayafin abayar ta yi, ta yi kyau sosai duk da ba wata kwalliya ta yi ba, daddad'an turarenta mai daɗin ƙamshi ta feshe jikinta da shi, zoben gold ta zira a ɗanyatsanta na tsakiyar hannun damanta, na kusa da shi kuma ta zira zoben azurfa mai kyan gaske, yatsun hannun hagunta suma fashion ɗin zobuna masu kyau ta sa musu guda biyu, tsadadden agogon hannu milk colour ta zira tare da abun hannu mai kyau, flate shoe mai kyau milk colour ta zira, wayoyinta dake kan mudubi ta kwasa ta zuba a cikin handbag ɗinta mai kyau itama milk colour. Light din ɗakin ta kashe ta janyo ƙofar ta fito ta sauko ƙasa. Haneefah ta kammala girkin cus_cus ɗin da Neehal ta ɗora, ta na zaune a falo Neehal ta sakko, Haneefah ta bita da ido tana murmushi ta ce "Kaga amaryar ya Anwar, kin yi kyau sosai" Neehal ta yi murmushi ta ce "Har na kai ki yin kyan?" Haneefah ta ce "Wane Ni, ke fa harkin fara irin shining ɗinnan na amare" Neehal ba ta kulata ba, ta nufi kitchen, Haneefah ta tashi ta koma kusa da Hajiya ta fara tashinta. Hajiya ta buɗe ido a hankali tana salati, tashi zaune ta yi tana mutsitstsike ido, duban Haneefah da take dariya ƙasa_ƙasa ta yi ta ce "Ai dama nasan sai ke, dan Neehal dai ba za ta yi mun wannan muguntar ba, To ke da Allah, ina cikin baccina mai daɗi kin katsemun ko uban me zan miki idanna tashin Oho?" Haneefah ta tsuke fuska ta ce "Hajiya dan na tashe ki ki ci abinci ki yi Sallah, shine za ki ce mugunta, gani na yi ke bakya wasa da Sallah kuma lokacinta ya kusa" Hajiya ta ce "To yi haƙuri ai ban sa ni ba, yaushe ki ka zo gidan? ya kuma Maryam ɗin?" Haneefah ta ce ɗazu na zo ai, na tarar ki na ta sharar baccinki, Mommy kuma tananan Lafiya k'lu" sakkowar Mama ƙasa ya katse musu maganar da suke, Haneefah ta mik'e ta je ta yi hugging Mama. Mama na murmushi ta ce "Welcome, yaushe ki ka zo?" Haneefah ta ce "Na ɗan jima" Mama ta ce " sannunki Ya Barrister?" Haneefah ta ce "Tananan klu" Mama ta kalli kofar kitchen ta ce "Neehal ba ta gama girkin ba ne, ta yi ta fito ku shirya ku tafi kar ku yi late" kafin haneefah ta ce wani abu Neehal ta fito daga kitchen d'in, Mama ta bita da kallo fuskarta ɗauke da mamakin ganin ta a shirye, Neehal ta ƙaraso kusa da su ta ce "Mama na gama abincin" Mama ta mata wani kallo ta ce "To sannu" Sannan ta juya ta kalli Haneefah ta ce "Kin taya ta girki ko?" Haneefah ta sunkuyar da kanta ƙasa ba ta ce komai ba, Mama ta ce "Ba magana nake miki ba Haneefah?" Haneefah ta ce "Mama ƙarasa mata miya kawai na yi, na ce ta je ta shirya dan mu yi sauri mu tafi" Mama ta ce "Ba na ce ko sauke abu ki dena taya ta da shi ba, ki barta ta dinga yin komai da kanta" Haneefah ta gyad'awa Mama kai. Neehal ta ɗan turo baki gaba ta wuce za ta ɗauki jakarta, Mama ta ce "Kun ci abincinne?" Haneefah ta ce "Na k'oshi Mama, ina gama cin abinci na fito, sai dai idan mun dawo" Mama ta dubi Neehal ta ce "Ke fa?" Neehal ta ce "Ni ma haka" Mama ta ce tunda kin cika cikinki da kayan zak'i ba, ki wuce kitchen ki d'ebo abinci ki ci kar na ɓata miki rai" Neehal ta ɓata fuska, amma ba ta da zaɓi sai bin umarnin Maman, kitchen d'in ta koma ta d'ebo abinci kaɗan a plate ta dawo falon ta zauna a ƙasa ta fara ci kamar ba ta so, ta na ci ta na yamutsa fuska, kaɗan ta ci Mama ta ce ta tashi su tafi, tun da ɓata musu lokaci kawai take ba cin abincin za tay ba. Neehal na duban Mama da Hajiya ta ce "Sai mun dawo" "Mama ta ce ƙarfe nawa za ku dawo?" Neehal ta ce "8" Mama ta ce "8 ina Hospital" Neehal ta ce "Mama yau fa Saturday me za ki yi a Hospital kuma?" Mama ta ce "Akwai patients d'in da zan duba ne" Neehal ta ce "Toh, idan mun tashi zan biya Zoo road na siyo popcorn a'one" Mama ta ce "In ma a 10 ne ba damuwata ba ce, kin san Yayanki na gida ai, 8: 15 in ba ki dawo ba, ke da shi ne" Neehal ta ɓata fuska ta yi gaba, Haneefah ta yi wa su Mama sallama, Mama ta musu addu'a suka tafi, Hajiya na faɗin "Wai yaushe zaku kai ni gidan talabijin d'innan naku ne nima a hasko Ni a ciki?" Suna jin ta suka mata shiru. Parking space suka nufa suka shiga Mota Driver'n Neehal ya ja su zuwa *ASTV* fitaccen gidan TV'n da ya shahara a nan ƙasarmu Nigeria dama nahiyar Africa baki ɗaya. Ƙarfe 8 kamar yadda Neehal ta ce suka tashi daga gurin aiki, bayan sun gama gudanar da shirin *'Yancin mata* wanda suke yinsa duk Ranar Asabar da misalin ƙarfe 7 na dare zuwa 8. Su na gamawa suka yi sallama da ma'aikatan gidan TV suka nufo gida, Neehal ta yi_ta yi Haneefah ta bita ta gidansu kamar yadda take yi wani lokacin amma ta ce ita gida za ta wuce, sai da suka biya suka fara sauke ta sannan suka wuce, da yake duk ba su da nisa, gabad'aya a cikin Nasarawa G.R.A suke har ASTV'n. Driver na parking Neehal ta fito, ganin Motar Dad a gurin alamun ya dawo ta ji daɗi a ranta, dama yau gabad'aya ta yi missing ɗinsa. Part d'in Mama ta nufa, ta shiga falon bakinta ɗauke da sallama, gabantane ya faɗi ganin Ameen zaune shi kaɗai a falon ya na latsa waya..........✍️ *Ku yi haƙuri da wannan, har yanzu jikinnawa ne sai addu'a, dan kar ku ji shiru ma yasa na yi wannan ɗin, insha Allah next page za mu shiga cikin gundarin labarin, Nagode da addu'oinku Masoya.🙏❤️* *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ [10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *0️⃣5️⃣* .............Tab'e ɗan ƙaramin bakinsa ya yi tare da ɗauke kansa daga inda suke. Neehal ta janye hannunta ta na sauke Numfashi ba ta ce komai ba, saboda abun ya mata wani banbarakwai, duk da Anwar ko hannunta bai taɓa riƙe wa ba amma sai ta ji wata irin kunyarsa ta rufe ta. A hankali ta daure ta ce "Nagode sosai Ya Anwar" Anwar ya yi murmushi ya ce "Kin ga yanda hannunki ya yi wa zoben kyau kuwa?" Neehal ta yi ɗan murmushi idanunta na kan hannunta da zoben yake sanye dass kamar an gwada ta ce "Hannun nawa ne ma ya yi wa zoben kyau, ba ma zobenne ya yi wa hannuna kyau ba?" Anwar ya ce "Eh mana, ai ke ko kwalliya ki kai ke ki ke wa kwalliyar kyau ba ita take miki ba" kafin Neehal ta ce wani abu Ameen ya ƙaraso kusa da su, Anwar ya yi sauri ya ce masa "Yayanmu Barka da dare" Ameen ya ɗan saki fuskarsa ya na mik'owa Anwar hannu ya ce "Yawwa barkan mu" suka yi musabaha Anwar ya gaisheshi ya amsa sannan ya wuce ba tare da ya kalli ko inda Neehal take ba, saɓanin ita kuma da ta zira masa na mujiya. Anwar ya kalle ta ganin ta bi Ameen da ido ya ce "Ya dai Queen?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya, zuciyarta babu daɗi ganin yanda Ameen ya shareta, ya ƙi kulata, Alhalin yau ba su haɗu ba kwata_kwata, ta rasa me yasa kwana biyunnan yake mata haka, duk da ma can shi mutum ne ba mai sakewa ba kuma ga miskilanci, amma ya na nuna mata kulawa sosai a matsayinta na k'anwarshi tilo guda ɗaya...... Anwar ya katse mata tunaninta ta hanyar faɗin "Wai me yake farune na ga kamar kina cikin damuwa Neehal?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya a karo na biyu ta ce "Bakomai Ya Anwar" ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai kawai tare da ƙoƙarin boye damuwarta dan kar ya fuskanci wani abu. Anwar ya duba tsadadden agogon hannunsa ya ce "Shikenan Queen bari na je gida na ga time ɗin Sallah ya yi" Neehal ta ce "Ba ka ci cake din ba kuma?" Ya ce "Na k'oshi ne" Neehal ta bata fuska ta ce "Please ya Anwar ka ci mana" ba tare da ya ce komai ba ya buɗe Plate d'in da'aka rufe cake d'in ya d'au 1 ya gutsira ya ajiye, ya na kallonta ya ce "Thank you" Neehal ta ce "Ka ƙara Mana, wannan ai baka ci ba" ya ce "I'm sorry dear, ciki na ya cika ne" Neehal ba ta kuma komai ba, Anwar ya Mik'e ya ce "Bye sai mun yi waya?" Neehal ta mik'e ta na faɗin "Mu je in raka ka" Suka jera su na tafiya har inda ya yi parking Motarsa ta raka shi, tsayawa su ka yi ta dubeshi ta ce "Thank you so much ya Anwar for your time, da kuma kyautar da ka ba ni, Allah ya sa ka da Alkhairi ya ƙara buɗi" Anwar ya ce "Ni ma Nagode sosai dear, kuma na ji daɗi, Allah ya barmu tare" Neehal ta ce "Amin, Allah ya kiyaye hanya ya tsare, ka gaida Ammi" ya ce "Amin, za ta ji Insha Allah bye" Neehal ta ɗaga masa hannu ta na murmushi, shima d'aga mata hannun ya yi ya buɗe motar sa ya shige" Neehal ta juya ta koma cikin gida. Su Dije ta faɗa wa su je su ɗauko cake ɗin su cinye, Mama da Hajiya duk suna ɗaki tasan jiran Sallah su ke yi, itama ɗakinta ta shiga ta faɗa toilet ta dauro alwala ta fito ta bi jam'i itama. Misalin ƙarfe tara na dare Hajiya ce zaune a falon sama ita da Ameen, Hajiya sai washe baki take tana zubawa Ameen hira, da alama dai ya cika mata aljihunta da kuɗi, Neehal ce ta fito daga ɗakinta, ganin Ameen ta ɓata fuska tare da turo baki gaba, Hajiya ta bi ta da kallo ta ce "Har Auwar ɗin ya tafi?" Neehal ta gyad'a mata kai kawai, Hajiya ta ƙara faɗin "To kuma mene ki ke ta ɓata rai, kamar za ki kai duka?" Neehal ba ta kula ta ba ta zauna a kasan kujerar da suke. Ameen ya d'ago ya na kallonta a hankali ya ce "I saw your missed call since?" Neehal ta ce "Uhm" kawai, ya ce "What Happen?" muryarta na rawa ta ce "Nothing" ƙoƙarin maida kwallar da ta cika mata ido ta yi, wadda batasan dalilin ta ba. Ameen ya maida hankalinshi kan wayarsa bai ƙara cewa komai ba, Neehal ta tashi ta koma ɗakinta. Ta na shiga ta hango wayarta na haske alamun a na kira, ɗauka ta yi ta duba ta ga Anwar ne, ɗaga wa ta yi ta kara a kunnenta ya yi sallama ta amsa masa ta ƙara da faɗin "Ka je gida lafiya?" Ya ce "Lafiya ƙalau" Ta ce "Nagode fa ya Anwar sosai" Ya ce "Kin san fa ban san yawan godiyar nan, kin kai na miki komai Neehal a rayuwarnan, kuma kin san wani abu?" Neehal ta ce "A'a" Ya ce "Wannan ring d'in kyautar da na ajiye zan miki ce ranar aurenmu, kuma kawai sai na canza shawara na ce bari na kawo miki kawai" Neehal ta ce "Aiko na ji daɗi sosai Ya Anwar ɗina, Allah ya bar k'aunah." Ya ce "Ameen My Queen." Hirarsu suka cigaba da yi cikin nishaɗi, duk da Neehal ba ta wani jin daɗi a ranta kawai daurewa ta ke yi. Washegari gari Uncle Mahmud k'anin Mama ya zo da sassafe ɗaukar Hajiya za su wuce Gombe, Neehal kafin ta wuce School suka yi Sallama dan lecture din safe gareta. Kwanaki na ta tafiya Rayuwa ta na wucewa, sai gashi har satika huɗu sun shud'e, a wannan week ɗinne kuma su Neehal za su gama exam ɗinsu ta second semester Level two (2), sosai Neehal ta zama silent saboda kusantowar bikinta, Tsakaninta da Ya Ameen kuwa ba ta sauya zani ba, tsakaninta da shi gaisuwa ce kawai sai kuma kyauta da tsarabar da yake yo mata a duk satin duniya idan ya dawo gida weekend bai fasa mata ba, amma kwata_kwata ba ya sakewa da ita, ita kuwa Neehal hakan ba ƙaramin damunta ya ke ba. Yau Laraba ƙarfe 12 Neehal ta fito daga exam, ta na cikin tafiya ta ji a na kiranta da faɗin *"Fateema Tafeedah*" juyawa ta yi ta ga best freind ɗin ta ce a school ɗin Zee, tsayawa ta yi har Zee ta ƙaraso inda take, Zee ta ce "Fateemah tafiya za ki yi" Neehal ta ce "Ehh" Zee ta ce "Tun yanzu, yau ba shiga Library kenan?" Neehal ta ce "Na gaji ne, bacci ma nake ji, da daddare kawai na yi karatun" Zee ta ce "Ok sai mun yi waya tunda gobe bamu da exam" Neehal ta ce "Ba za ki zo ke da su Meesha ku karb'i Ankonku ba?, gobe fa Aunty Sadiya za ta kawo duka" Zee ta ce "Allah ya kai mu goben, za mu shigo da yamma mu karb'a insha Allah" Suka yi sallama Neehal ta tafi. Ta na zuwa gida ta wuce sama ta shiga ɗakinta ta kwanta ta na tunanin rayuwarsu tun daga k'uruciya, haka kawai ta ji kuka ya kufce mata ta shiga rera shi, sai da ta ga ji dan kanta ta yi shiru, dan babu mai rarrashin ta a kusa, Toilet ta shiga ta dauro alwala ta dawo ta zauna kanta na mata wani irin ciwo, ga yunwa dake nuk'urk'usar cikinta dan bata karya ba ta tafi school. Da k'yar ta daure ta yi Sallar sannan ta sakko ƙasa, tea ta haɗa mai kauri tasha, duk da tasha tea d'in amma ba ta dena jin ba daɗi a jikinta ba, haka dai ta daure ta shiga kiciniyar ɗora girki kar Mama ta dawo ta tarar ba ta yi ba. Washegari ta tashi ba ta jin daɗin jikinta ko kaɗan, amma ta ta'allak'a hakan da period ɗinta da ya kusa, dan ta na cin wahala ba kaɗan ba idan za ta yi. Ta na kwance a kan gadonta lullub'e da duvet Mama ta shigo ɗakin, Janye duvet d'in Mama ta yi ta na faɗin "Neehal wanne irin bacci ki ke haka har 10 ta wuce ba ki tashi ba?" Neehal ta buɗe idonta a hankali ta ce "Ba na jin daɗi ne Mama" Mama ta ce "Ayya sorry Daughter, Month ɗinki ya yi ko, ki tashi ki lallaɓa ki yi wanka ki sha ko tea ne, sai kisha magani" Neehal ta ce "Ai bai zo ba,ciwon kawai na ke ji" Mama ta ce "Ki dai tashi ki sha" Neehal ta yunk'ura ta tashi zaune tana taune lips d'inta. Ƙarfe 12 Aunty Sadiya ta ƙaraso gidan da atamfofi da leshuka da yadin bridal shower na k'awayen amarya, aka zube su a falo. Neehal ta na kwance a kan doguwar kujera ba ta ko motsa ba duk da ta na jin duk budurin zuwan Aunty Sadiyan, sai ma runtse idanunta da ta ƙara yi zuciyarta na bugawa. Aunty Sadiya ta kalli sashen da take ta ce "Neehal lafiya kuwa take bacci da ranar nan?" Mama ta ce "Ba ta jin daɗi ne, ciwon mararta ne ya tashi, amma na bata magani tasha, shine bacci ya ɗauketa" Aunty Sadiya cike da tausayawa ta ce "Ayya Allah ya ba ta lafiya, Amarya ba lafiya ai babu kanta, dan ma insha Allahu ta na yin Aure za ta dena ciwon marar" Mama ta ce "Allah ya sa, kin san ta da shegen shan zak'i kamar me, na hanata na hanata amma ta ƙi denawa" Aunty Sadiya ta ce "Allah ya sauwak'e, bari na kira Haneefah ta zo ta ɗibi na freinds ɗinsu" Mama ta ce "Ya kamata kam, tunda bikin ya matso su kai ɗinkuna, nima bari na ɗibi na mutanena." Su na duba kayan su na cigaba da tattaunawa akan bikin, Mama ta na sanar da Aunty Sadiya Abubuwan da za'ayi, ba wani jan bikin za'ayi ba, Events uku kawai za'ayi, daga Kamu/Mother's day, sai Dinner da Yini, sai bridal shower na k'awayen Amarya. Gabad'aya sun riga da sun yi bucking na events din da za'ayi, duk wata siyayya ta Amarya itama sun kammala ta, yanzu lefe kawai suke jira sai a sanya satittikan bikin. Sai da Haneefah ta zo sannan ta tashi Neehal daga baccin gasken da ya d'auketa, ta tashi zaune ta na taune lips ɗinta, ka na ganinta ka ga mai cuta, Aunty Sadiya da Haneefah suka shiga yi mata sannu. Mama ta kawo mata abinci ta ɗan tsakura ta ci ta ƙara shan magani, ranar dai haka ta wuni ba ta jin daɗi, Anwar da su ka yi waya hankalinshi ya tashi da ya ji ba ta da lafiya, sai da ya zo ya duba ta da daddare hankalinsa ya ɗan kwanta, tun da ya ga jikinta ba rijib take a kwance ba. Washegari, ta tashi jikin nata da sauƙi, dan period d'in nata bai zo ba har yau, yau ma exam d'in safe ce da su, amma ba ta dawo ba gida da wuri ba, saboda sun tsaya ɗaukar pics da friends ɗinta, tunda sun gama exam d'in sai dai fatan samun result mai kyau, suka yi sallama da freinds ɗinta su na faɗin sai sun zo bikinta, ita dai Neehal yaƙe kawai take yi dan zuciyarta babu daɗi ko kaɗan. Ta na dawowa gida Mama ta sanar mata da zuwan wadda za ta mata gyaran jiki daga Maiduguri gobe Insha Allah, Hajiya ma goben za ta zo tunda ran Lahadi za'akawo lefe amma maza ne za su kawo. Da daddare Neehal ta na kwance a ɗakin Mama, sai juyi take akan gado saboda murd'awar da cikinta yake mata, hawaye ne kawai yake fita daga idanunta, wani amai ne ya taho mata ta tashi da gudu ta nufi toilet ta shiga kelayashi, ta na yin aman ta na jin fitar jinin a jikinta, Ta na sassauke Numfashin azaba ta gyara jikinta ta sanya pad, kuskure bakinta ta yi ta janyo ƙafarta da ta fara riƙe mata ta dawo ɗaki ta kwanta. Mama ta shigo ɗakin ta dube ta cikin tausayawa ta ce "Sannu Daughter ya jikin?" Neehal ta ɗaga mata kai kawai, Mama ta ce "Allah ya ƙara sauƙi" Sosai Mama take tausayin Neehal lokacin period ɗinta, saboda azaba take sha ba ta wasa ba, ciwon mara, baya, k'ugu duk take yi, ƙafafunta duka su riƙe, yau ko gurin aiki ba ta je ba, sai Haneefah ce ta je ta maye gurbinta. Time ɗin da Dad ya zo dubata bacci ya ɗauke ta. Washegari dai da ta tashi jikin nata da sauƙi sai dai ba ta warware tas ba. Da safe ta na cin Irish da soyayyen kwai ɗin da Mama ta kawo mata ta tilasta mata ta sha Ameen ya shigo ɗakin, jin kamashin turarensa ya sa ta d'ago kanta da sauri ta na kallonsa, gabanta ne ta ji ya fad'i ba ta san dalili ba, satar kallonsa ta shiga yi ta ga ya canza sosai ba kamar kwanaki ba, ramar da ya yi duk babu ita sai ma wani fresh da haske daya ƙara, lumshe idonta ta yi a hankali ta ce "Ina kwana?" Kamar bai ji ba sai kuma can ya ce "Lafiya, ya jikin? Ba ta yi mamakin sanin ba ta da lafiya da ya yi ba, domin kowa na gidan ya san time ɗin period ɗinta saboda azabar da take sha a lokacin yin period ɗin nata. Cikin raunin murya ta ce "Da sauƙi" Juyawa ya yi ya fita ganin Mama batanan, a falon ƙasa su ka haɗu da Mama ta dawo daga part din Dad, Mama ta na dubanshi ta ce "Welcome, har ka zo kenan?" Ya ce "Ehh, ina kwana?" Mama ta ce "Lafiya ƙalau, ya aiki" Ya ce "Alhamdulillah, ya naku?" Mama ta ce "Lafiya ƙalau" Zai nufi part d'in Dad Mama ta ce "Idan ka dawo ina son ganinka" Ya ce "Toh." Misalin ƙarfe goma na safe Aunty Sadiya da Aunty A'isha da yarinyar gurinta Maryam su ka zo gidan, domin yin snacks na karɓar kayan lefe, Neehal dai ta na shan Magani ta kwanta bacci ya ɗauketa dan jiya ba ta samu wani baccin kirki ba, saboda ciwo. Yauma ba ta samu damar zuwa gurin aiki ba, Hajiya da yamma ta ƙaraso gidan da tulin kayanta dan sai bayan biki za ta tafi, wadda za ta yi wa Neehal gyaran jiki Mama ta kira ta, ta ce ta bari sai Monday tun da Neehal ɗin ba ta jin daɗi. Bayan sallar isha'i bayan su Mama sun gama aiki ta samu Ameen a ɗakinsa, Ameen ya tattara duka hankalinshi akan Mama jin ta ce za su yi Magana. Mama tana dubanshi ta ce "Gobe za ka koma Lagos ko jibi?" Ya ce "Gobe da safe" da mamaki Mama ta ce "Da safe kuma?" Ya ce "Ehh" Ta ce gobe fa za'akawo lefen Neehal kuma sai da yamma, kuma maza ne za su kawo" Ya ce "Am sorry Mum, amma ba zan samu damar tsayawa ba, dan akwai wani important thing da zan yi" Mama ta ce "Sunday ce fa, saboda gudun haka fa ya sa aka sa weekend, kar wani uzurin ya tsaida wani" ya yi shiru bai ce komai ba, Mama ta mik'e ta ce "Dole ne koma uzurin mene da kai ka jira a karb'i kayan da kai, ka ji na faɗa maka" Ta na faɗin haka ta fice daga ɗakin, Ameen ya bita da kallo. Washegari Sunday Ranar kawo kayan lefe, tun safe su Mama su kai packagin kayan snacks d'in da soyayyen naman kaza gami da lemuka, yamma kawai suke jira masu kawo kayan su zo. Neehal yau ta lallaɓa ta shirya ta tafi gurin aiki, duk da Mama ta so hanata amma ta ce mata ta ji sauƙi za ta iya zuwa. Mama na kitchen Ameen ya shigo ya same ta da shirinsa na tafiya. Mama ta masa wani kallo bayan ta amsa sallamar da ya yi, Ya ce "Ina kwana Mum" Mama ta ce "Lafiya k'alau" Ya ce "Am sorry Mum zan wuce Lagos yanzu, nima ba son raina ba ne uzurin da zan yi a can mai ƙarfi ne" Mama ta ce "Uhm, uzurin har na fi umarnina kenan a gurinka?" Ya ce "A'a Mum, kar ki ce haka Please" Mama ta yi shiru kawai ta na kallonsa, Ya ce "Am sorry" Mama ta ce "Na yi sorry ɗin ka je Allah ya kiyaye, amma ka sani ko kananan ko ba kanan ba za'a fasa komai ba, idan ma ka ga dama karka halacci taron bikin" ya yi murmushi kawai ya ƙaraso kusa da ita ya yi hugging d'inta tare da faɗin "Thank you Mum, Allah ya sa su zo lafiya su tafi lafiya bye" Mama ba ta ce komai ba, ya sake ta ya fice. Mama ta bishi da kallo, abinda ya sa ta barshi ya tafi tasan uzurin da yake faɗa ba ƙarami ba ne, dan Ameen ba ya taɓa mata musu a kan duk wani abun da za ta sa shi ya yi, komai wuyarsa kuwa. Ƙarfe 12 na rana Mama su na zaune a falo ita da Hajiya da uncle Mahmud da ya zo shima dan karɓar lefen ɗin, wayar ta shiga ringing, ɗauka ta yi ta duba ta ga Ammin Anwar ce ke kiranta, murmushi ta yi ta d'aga wayar ta kara a kunnenta tare da yin sallama, ba tare da Ammi ta amsa sallamar da Mama ta mata ba, cikin tsananin ruɗu da matsanancin tashin hankali ta ce..........✍️ _*Duk mai son shiga group ɗin NEEHAL FAN'S ta mun magana ta Number na 09066710753, amma in kin tabbatar za ki na comments and share.*_ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *0️⃣4️⃣* .............Mama bayan ta gama haɗa break fast din ta ɗibi na Dad ta haɗa masa a cikin tire, tana ƙoƙarin fita Dije mai aiki ta shigo kitchen d'in, ta risina ta ce "Ina kwana Hajiya, dafatan kin tashi lafiya" Mama ta ce "Lafiya kalau Dije, yawwa dama na gama sai ki haɗa wanke_wanke ki yi ki gyara kitchen d'in" cikin girmamawa Dije ta ce "Toh Hajiya" Mama ta fita daga kitchen d'in, Zulai mai aiki ta na mopping a falon, ganin Mama ya sa ta ajiye mopper ɗin hannunta ta taho da sauri ta na faɗin "Sannu da fitowa Hajiya" Mama ta ce "Yawwa mun tashi Lafiya" Zulai ta ce "Lafiya ƙalau Hajiya" tana ƙoƙarin karɓar kayan hannun Mama, Mama ta ce "Ki barshi ki je ki ci gaba da aikin ki kawai, idan kun gama sai ku ɗibi abinci a kitchen ku karya" Zulai ta ce "Toh Hajiya" ta koma ta cigaba da aikinta, Mama kuma ta nufi part din Dad. Dad ya na bedroom d'insa, Mama ta ajiye masa break fast d'insa a kan dinning sannan ta nufi bedroom d'innasa, da sallama ta shiga ya na zaune akan gadonsa ya na operating system, d'agowa ya yi ya na duban Mama tare da amsa mata sallamar da ta yi, Mama ta zauna a gefensa ta na faɗin "Your break is ready" Dad ya yi murmushi ya ce "Godiya nake matar Aljannah" Mama ta yi murmushi ta tashi ta ɗauke system ɗin gabansa ta ajiye a kan bedside locker ta ce "Mu je ka yi break idan ka gama sai ka cigaba da aikin" Dad ya yi murmushi ya mik'e ya bi bayan Mama suka fita zuwa falonsa, Mama ta koma ta ɗauko tea plaks ta dawo ta yi sarving ɗin su suka fara cin abincin cikin nutsuwa. Bayan sun gama Mama ta yi hamdala ta na goge bakinta da tissue ta ce "Wai Ni kuwa Dad ya ku ka yi da Son jiya?" Dad ya ce "Na masa magana a kan ya kamata zuwa yanzu a ce ya na da iyali shima ya ce Insha Allah bayan bikin daughter zai fitar da mata shima" Mama ta sauke numfashi ta ce "Amma Dad me ka fuskanta ya na damun Ameen, tun jiya da yawo gabad'aya hankalina ya kasa kwanciya da yanayin da na gan shi" Dad ya ce "Nima a nawa ɓangaren hakane Doctor, abun da ya ƙara tayar mun da hankali da Muhammad ramar da ya yi da kuma yanda ka na kallonshi za ka hango zallar damuwa a tattare da shi, kuma duk abin da yake damun Muhammad ba ƙaramin abu ba ne, dan kin san Muhammad tun ya na ɗan ƙaramin shi, yaro ne mai juriya, haƙuri, kawaici gami da tawakkali, zai yi wuya ka gane ya na cikin damuwa ko ka fuskanta, idan har ba shi ya furta maka ba, wannan dalilin ya sa nasan lallai abin da yake damunsa ba ƙaramin abu ba ne" Mama ta sauke wani gwauran numfashi tare da dafe kanta ba ta ce komai ba, Dad ya kama hannunta cikin lallami ya fara mata magana da faɗin "Kinga Doctor ki kwantar da hankalinki, Insha Allahu ba wata matsala ba ce, ba na son in ga kina damuwarnan, kamar yadda ya ce mu dinga masa addu'a ki dinga masa, Insha Allahu koma meke damunsa Allah zai yaye masa" Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya sa" Dad ya saki hannunta tare da mik'ewa ya na faɗin "Yawwa ko kefa, ba na son na ga ki na yawan damuwarnan ko kaɗan, dama naga kwana biyu kin ɗan fa ɗa" Mama ta mik'e itama ta na faɗin "To ba dole ba Dad ka ga ina rama, autatah za ta tafi, ai ahakanma ina ƙoƙarin b'oye damuwata dan kar ta damu itama" Dad da ya fara tafiya ya ce "To ya za'ai sai haƙuri, Ni kaina na fara kewar daughter tun yanzu" Bayan Mama ta gama gyara part d'in Dad ta haɗa masa ruwan wanka ya yi, ta dawo part d'inta ta baro shi ya na aiki tun da Yau Sunday ba fita zai yi ba. Ɗakin Hajiya ta shiga ta tarar da ita ta na haɗa kaya, Mama ta zauna a gefen gado ta ce "Hajiya ashe kin tashi, har General ya na cewa zai zo ya gaishe ki, na ce ya bari sai anjima dan nasan da k'yar in kin tashi" Hajiya ta ce "Na tashi mana, ko zan zauna ina ta barci har wannan lokacin kamar wata marar aikin yi" Mama ta ce "ai na san ki ne Hajiya da son bacci" Hajiya ta ce "To yau ban yi ba, tun ɗazu na tashi nake haɗa kayana ba sai goben ta yi Mahmud ɗin ya zo ba in yi ta kame_kamen ban gama shiri ba" Mama ta ce "Ai da kin barshi Hajiya na haɗa miki ko kuma na turo su Dije su haɗa miki, tun da ko karyawa ba ki yi ba" Hajiya ta kama hab'a ta ce "Rufa mini asiri, masu aiki da haɗa mun kaya, lalacewar tawa bata kai haka ba, kema na hutashsheki tun da ba wani abu na aiki nake a gidan ba, dan haɗa kaya dai ba zai mun wahala ba" Mama ta ce "Shikenan bari na kawo miki abincinki" Mama ba ta jira amsar Hajiya ba, ta mik'e ta fice. Ƙarfe 11 Ameen ya shigo falon Mama, su na zaune ita da Hajiya suna kallo, Mama ta bishi da kallo har ya zauna a gefenta, cikin muryarsa kamar baya son magana ya ce "Morning Mum, dafatan kin tashi lafiya" Mama ta ce "Lafiya k'alau and you?" Ya ce "Fyn" Mama ta ce "Masha Allah, yau za ka wuce Lagos ɗin ko sai gobe?" A hankali ya ce "Tomorrow in the morning" Mama ta ce "Allah ya kai mu" Hajiya dake saurarensu ta keɓe fuska ta ce "In Mutum bai kula ni ba, sai me? Daga yau ma ba ƙara gani na za ka yi a gidanku ba, sai wani lokacin kuma" ɗan Murmushi Ameen ya yi bai ce komai ba, sai ma mik'ewa da ya yi ya nufi part d'in Dad, Hajiya ta bishi da harara" Mama ba ta ce komai ba, sanin da ta yi ba'a shiga tsakanin Hajiya da Ameen, dan Hajiya ko wata ta yi ba ta zo gidan ba, da kanshi ya ke zuwa har Gombe ya ɗaukota. Kafin la'asar Neehal ta dawo gida, tare suka taho gidan yau da Haneefah, a falo suka tarar da su Mama da kannenta guda biyu mata masu kama da ita, sun zo yiwa Hajiya sallama, Aunty A'isha da Aunty Sadiya, Neehal ta tafi da sauri ta rungume Aunty Sadiya dan tafi kusa da kofa, Haneefah kuma ta rungume Aunty A'isha, Neehal ta ce "Aunty Sadiyata welcome" Aunty Sadiya na murmushi ta ce "Yawwa my daughter, ya aiki?" Neehal ta ɓata fuska cike da shagwab'a ta ce "Alhamdulillah, sai gajiya" Aunty Sadiya ta ce "Sorry dear, za ta tafi itama" sakin Aunty Safiya ta yi ta koma ta yi hugging Aunty A'isha tare da gaisheta" Aunty A'isha na murmushi ta ce "Lafiya k'alau, Neehal yanzu an gujeni ko, yaushe rabonku da gidana" Neehal ta ce "Kai Aunty ko wata fa ban yi da zuwa ba" Aunty Aisha' ta ce "To ai da ko sati ba kya yi ba ki zo ba, ko Anwar d'inne ya hana ki fita?" Haneefah tay karaf ta ce "Baruwan Angonmu, Mama ce ke hanamu fita" Mama ta harare ta ta ce "Ta yaya zan bar ku ku fita ba'amun aiki ba, duk randa fa ba su je aiki ba ko school, wuni suke a d'aki su na shiririta, sai na je na fatattako suke saukowa su yi abun da ya dace, can gidan Barrister ma ta ce in sun je haka suke, kamar wasu yara" Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba, ta zauna kusa da Hajiya, wadda ta ƙurawa TV ido ta na kallo. Aunty A'isha ta yi murmushi kawai, Haneefah ta dubi Aunty Sadiya ta ce "Aunty Sadiya dama ina shirin kiranki, wasu freinds ɗinmu sun turo mun kuɗin ankon Neehal bari na miki transfer yanzu" Aunty Sadiya ta ce "Toh, na atamfa ne ko na less?" Haneefah ta ce "Duka" Neehal ta lumshe idonta gabanta na faɗuwa, tunawa da ta yi nan da 2 months fa inda rai da lafiya an yi aurenta, shikenan za ta bar Mamanta da Yayanta da Dad ɗinta mutane mafi soyuwa a gareta, ƙoƙarin mai da kwallar da ta ciko idanta ta yi ta mik'e ta wuce sama. Da yamma bayan su Neehal sun ci abinci sun yi wanka suka tafi gidansu Haneefah, Mommy ta na zaune a falo suka shigo gabad'aya suka yi kanta suka ruk'unk'ume ta, Mommy ta ce "Uhm, Allah ya kawo ku, Kwana biyu bakina shiru amma yau za ku zo ku samun ciwon kai" Neehal ta ɓata fuska ta ce "Kai Mommy ko irin yar tarb'ar nan ma babu" Mommy ta ce "Ban san ta ba, ba kuma zan yi ba, a ɗaga mun jiki Ni, ba daɗi nake ji ba" Haneefah ta tashi daga jikin Mama tana faɗin "Shiyasa wlh gwara gidan Mama sau dubu da nan" ta ƙarashe zancen ta na shigewa kitchen. Mommy ta ce "Ni da za ki tattara kayanki, ki koma gidan Maman da kin taimaka mun" Neehal ta yi dariya ta ce "Ai ba za ki iya kwana 2 ba ki ga Besty ba, abun da ko kwana ɗaya ta yi kinta kiranta a waya kina ta dawo" Mama ta ce ''Ai dan ba Ni da mai mun aiki ne, amma ba wai kewarta nake ba" Haneefah ta dawo falon ta na duban Mama ta ce "Mama cake za mu yi wa ya Anwar, na gidan Mama kwananne ne, kuma na duba kitchen kamar ba ki da butter" Mama ta ce "Babu kam, amma bari na ba wa idi ya karb'o, tun da ɗana za'aiwa" Neehal ta ce "Au da mu za mu ci, ba za ki bayar a siyo ba?" Mommy ta ce "Sai dai ku siyo da kanku ko kuma ku haƙura da cin" Haneefah ta ce "Mommy nan da wasu watanni fa kin dena ganinmu a kai a kai, ki dinga lallaɓamu fa" Mommy ba ta kula ta ba ta shige ɗakinta dan ɗakko kuɗi. Neehal ta dubi Haneefah da damuwa a fuskarta ta ce "Besty Yau gabad'aya ban ga Yayana ba, ba na jin daɗi" Haneefah ta ce "Why?" Neehal ta ce "Da safe da zan fita, na san ya na bacci, da muka dawo kuma ban ga car ɗinshi ba, na tambayi Mama shi, ta ce sun fita tare da Dad" Haneefah ta ce "ki kirashi mana" Neehal ta ce "Good idea" ta ƙarashe zancen tare da zaro wayarta daga cikin small handbag ɗinta mai kyau, kiran duka numbobin sa ta yi amma bai ɗauka ba. Bayan Magriba Neehal na zaune a gaban madubin ɗakinta ta na d'aura ɗankwalin atamfar da ke jikinta, dawowarta kenan daga gidansu Haneefah ta sauya kaya ta fara shiryawa kafin Anwar ya ƙaraso. Wayarta dake kan mudubinne ta fara ringing cikin amon sautin wak'a mai daɗi irin ta masoya, murmusawa ta yi ta kai hannu ta ɗauki wayar dan tasan Anwar ne ya ƙaraso tun da shi kaɗai ta sawa wannan ringintone ɗin, ta ɗaga kiran tare yin sallama cikin siririyar muryarta, Anwar ya amsa tare da faɗin "Gimbiyata na ƙaraso" ta yi murmushin jin daɗi mai sauti ta ce "You Are Welcome Sir" shima murmushin ya yi tare da katse wayar, Neehal ta ƙarasa daurinta ta feshe jikinta da da daɗaɗan turarukanta masu sanyin ƙamshi, wanda idan mutum ba matsowa kusa da ita ya yi ba, ba zai ji k'amshin ba. Ɗakin Mama ta lek'a ta sanar mata Anwar ya zo ta fita, Mama ta ce sai ta dawo, ta kuma gaishe da Anwar ɗin, a falon ƙasa ta tarar da su Dije su na kallo, ta dube su ta ce "Aunty Dije dan Allah idan babu damuwa ki ɗan biyo ni da cake ɗin can, zan ɗau drinks ne" Dije ta je "Haba uwar ɗakina babu damuwar komai" Neehal ta yi murmushi ta ce "Toh Nagode" Zulai ta ce "Kawai ki wuce zamu kawo miki har ruwanma, kar yay ta jiranki" Neehal ta ce "Toh Nagode sosai" Ya na zaune a kan fararen kujerun da suke zama koyaushe dan yin zancen, ya na latsa wayarsa, ya na sanye cikin wata shadda light blue, da ta haska choculate colour ɗin fatarsa wadda ta nuna zallar jin daɗin da yake ciki, Anwar Kyakkyawane a jin farko a sahun kyawawa, dogo ne amma bashi da jiki sosai. Neehal ta ƙaraso gurin tare da yin sallama, Anwar ya d'ago ya na bin ta da wani kallo k'auna, wadda ya sata saurin sunkuyar da kanta ƙasa cikin jin kunya, ya amsa mata sallamar ya na ƙara k'ura mata ido, Neehal ta turo baki gaba cikin shagwab'arta ta ce "Ina yini" ya yi murmushi ganin yanda ta yi, kasancewar gidansu Neehal akwai wadatuwar haske sosai komun dare, shiyasa ya ke kallonta tar" ya ce "Lafiya k'alau, ya Mama" ta ce "Tananan k'alau ta na gaisheka" ya ce "Ina amsawa tare da ajiye wayarsa a kan ɗan table ɗin robar da ke gabansu, cike da soyayya da kulawa ya ce "Me ya faru ne, na ga kamar Queen na fushi da Ni" Neehal ta ƙara shagwab'e fuska ta ce "Nothing, kawai kai ne na ga ka na ta kallo na" murmushi Anwar ya yi me sauti ya ce "Dan mutum ya kalli matarsa laifine, ni fa gaskiya kunyar nan ta ki ta na cutata, dan ma kwanaki kaɗan suka rage ki zama mallakina na cire miki ita gabad'aya" Neehal ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa ba ta ce komai ba, saboda fad'uwar da gabanta ya yi, a dalilin zancen auransu da Anwar ya yi, ta rasa me ya sa tun da auransu ya matso take jin hakan a tattare da ita, a da kuma farkon soyayyarsu ba ta jin komai, burinta kawai a lokacin a ce sun mallaki juna, saboda tarin k'aunar da take masa, amma yanzu duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi da auran. Anwar bai yi tunanin wani abu a shirun da Neehal ta masa, dan ya riga ya saba da halinta na jin kunya idan suna tare, saɓanin idan suna waya ko chat da take zagewa ta na rattabo masa kalaman soyayya, amma idan ya zo gurinta sai dai ya yi ta hirarsa shi kaɗai, ita daga um sai um'um, in kuma ta so wani lokacin ta zage su sha hirarsu. Anwar ya ƙara cewa "Yau ko um ɗinma ba zan samu ba Queen, sai dai shiru?" Neehal ta yi murmushi a ƙoƙarin ta na ganin Anwar din kar ya yi tunanin wani abu ta d'ago kanta tana kallonshi amma ba ido cikin ido ba ta ce "Za ka samu mana, harma fiye da haka" ƙarasowar su Dije gurin ya hana Anwar maganar da yake son yi, su ka yi sallama Neehal da Anwar suka amsa musu a tare, gaishesa suka yi tare da ajiye kayan hannunsu a gaban Anwar din, Anwar ya amsa musu tare musu godiya suka juya suka tafi. Neehal ta mik'e ta tsiyaya masa ruwa da lemo a glass cup, sannan ta koma ta zauna suka cigaba da hirarsu ya na shan drink d'in kaɗan_kaɗan. Can Anwar ya dubeta ya ce "Queen ni fa yau na zo miki da babbar tsaraba" Neehal ta ce "Ta me kenan?" Bai ba ta amsa ba sai hannunsa da ya zira a aljihun rigarsa ya ɗakko wani abu da Neehal ba ta gane mene ba, buɗe ɗan ƙaramin case ɗin ya yi wani zobe mai kyau ya bayyana, Neehal ta waro manyan idanunta ta ce "Wow ya Anwar ring ɗin nan ya yi kyau sosai fa" ya ce "Sai ma kin san a wannan kyakkyawan finger ɗin naki, na san sai ya ƙarawa zoben kyau" Neehal ta yi murmushi, Anwar ya ɗakko zoben dake ta k'yalk'yali ya ce "Kawo Hannunki in saka miki, na ki ne na kawo miki" Neehal ta ce "Nagode sosai Ya Anwar, amma Ni dai ka ba ni in saka da kaina" Anwar ya ce "A'a my Queen ni dai ki barni na sa miki" Neehal ta yi shiru ba ta ce komai ba, domin ba za ta iya musu da Anwar ɗin ba, hannun damanta ta kalla, a hankali ta sa hannun hagunta ta cire zoben dake babban ɗanyatsanta ta ajiye, sannan ta miƙa masa ɗanyatsan, murmushi Anwar ya yi ya matso ya zira mata zoben, hakan ya yi dai_dai da fitowar Ameen daga part ɗinsa domin tafiya Masallaci dan anfara kiran sallar isha'i, karaf a idanunsa Anwar ya zirawa Neehal zobe...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ 0️⃣6️⃣ ............Doctor an..an...an ka..kashe An...Anwarrrr!' ta fad'i maganar a rarrabe saboda tsananin tashin hankali. Mama suman zaune ta yi zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu, Ammi ba ta jira amsar Mama ba ta katse wayar. Ita kuwa Mama wayar ma sakin ta ta yi ta fad'i ƙasa. Ganin yanda Mama ta k'ame kamar gunki ga kuma wayarta da ta saka ta faɗi ya sa Hajiya a ruɗe ta ce "Ke lafiyar ki kuwa, ki ka zuba mana na mujiya ga waya kin saki ta fad'i ƙasa?" Uncle Mahmud da ya fuskanci da akwai wata matsalar ya taso ya dawo kusa da Mama, ganin yanda ta sandare sai ya ɗan girgiza ta, wani nannauyen numfashi Mama ta ja ta sauke, saitin zuciyarta ta dafe da hannunta jin yanda ta ke bugawa tamkar za ta yi tsalle ta fito daga k'irjinta, sai a sannan wani uban gumi ya fara tsatstsafo mata ta ko wanne k'ofofin gashi na jikinta, duk da sanyin Ac'n dake falon. Kallo ɗaya za ka yiwa Mama a wannan lokacin ka hango zallar tashin hankali da ɗimuwar da take ciki, gabad'aya ta rasa a duniyar da take jinin jikinta ya tsaya, ƙwaƙwalwarta ta cak da aiki. Ganin yanayin Mama Uncle Mahmud ya ƙara tabbatar da ba k'alau ba, a ɗan ruɗe ya ce "Doctor lafiya kuwa, me ke faruwa ne?" Mama ba ta bashi amsa ba, numfarfashi kawai take sauke wa. A ruɗe Hajiya ta ce "Na shiga uku Ni Zainaba, Fatima ki faɗa mana me ya faru mana, yanayin da ki ka koma Lokaci ɗaya ya tada mana hankali" Mama ta runtse idanunta ta ce "Anwar ya rasu" A gigice Hajiya ta mik'e tsaye ba tare da ta shirya wa hakan ba, ta ce "Innalillahi_wa'inna'ilaihirraji'un, wanne Anwar d'in?, kar dai ki ce mun na Neehal" Uncle Mahmud innalillahi kawai ya shiga maimaitawa a fili domin mutuwar ta bige shi ba kaɗan ba, Hajiya ta saka kuka ta na salati ta ce "Allah ya ji ƙanka Anwar yaron kirki, mai biyayya, Allah ya sa aljannah ta zamo makoma a gareka, Ni Zainabu yaya Neehal za ta ji mutuwarnan?" Dai_dai nan Dad ya shigo falon a firgice, ganin yanayin su Mama ya tabbatar masa da suma sun ji mutuwar. Mama ta shafe wasu mintuna a zaune a gurin, abu biyu ne yake ƙara dugunzuma mata hankali a kan mutuwar Anwar, na farko cewa da Ammi ta yi an kashe shi, na biyu kuma halin da Neehal za ta shiga idan wannan mummunan labarin ya riske ta. Hajiya kuwa ban da kuka babu abin da take, Dad ma kallo ɗaya mutum zai masa ya gane ya na cikin tsananin tashin hankalin mutuwar Anwar ɗin, musamman idan ya tuna halin da daughter d'insa za ta shiga idan ta ji mutuwar, Uncle Mahmud ne ma mai dauriyar cikin su, amma babu ƙarya wannan ahali mutuwar Anwar ya dake su ba kaɗan ba. Da k'yar Mama ta yi ƙarfin halin kiran Aunty Sadiya da Aunty A'isha ta sanar musu, suma sun shiga tashin hankali da jin mutuwar Anwar d'in ba kaɗan ba, Ameen kuwa ta yi ta neman Number'nsa amma ba ta shiga, kuma duka layikansa ta yi ta gwadawa amma sun ƙi tafiya, dole sai haƙura ta yi ta ajiye wayar ta fara tunanin hanyar da za ta sanar da Neehal. Neehal yau tunda ta tashi take jin wata irin faduwar gaba na riskar ta, shi ya sa ma ta shirya ta tafi gurin aiki, ko idan tana cikin mutane za ta ji sauƙin abin da yake damunta, amma tunda ta je gurin aikin ta kasa tab'uka komai, wayar da su ka yi da Anwar ne ma da safen nan ta ɗan sanyaya mata rai, kowa ya ganta sai ya mata sannu, dan su duk ɗaukarsu rashin lafiyar da take ne. Haneefah na tsaka da aiki, Mama ta kira ta, ba ta d'aga ba ta bari idan ta gama sai ta kira ta, ganin kiran da Maman take mata ba k'ak'k'autawa ya sa ta ɗaukar excuse ta fita ta d'aga kiran,Mama cikin dauriya dan kar Haneefah ta fuskanci da wata matsalar tace "Haneefah ku taho gida yanzu ke da Neehal" ba ta jira amsar Hannefan ba ta katse wayar, duk da Mama ta yi ƙoƙarin b'oye damuwarta amma sai da Haneefah ta fuskanci akwai wani abu a Muryar Maman, office d'in da Neehal ta ke ta nufa da sauri, Neehal ta na zaune ta kwantar da kanta a kan table ɗin office Haneefah ta shigo, taɓa ta yi ta na faɗin "Neehal taso mu koma gida tunda ba ki da lafiya" Neehal ba ta yi musu ba dan ita ma ta na bukatar zuwan gidan, dan har wani jiri_jiri ta ke ji daga zaunen da take, d'ago da kanta ta yi a hankali, wayarta ta ɗauka jikinta a matukar sanyaye ta zira a cikin jakarta, ganin yanda take Haneefah ta kama ta suka fito daga office din, Manager d'in gidan TV Haneefah ta sama ta masa bayani, sannu ya yi wa Neehal sannan ya haɗa su da ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan TV'n ya kai su gida. Mama ce kaɗai a falo tana zaune ta na hawaye, su Dad sun wuce gidansu Anwar harda Hajiya da ta dage sai ta bisu. Jin shigowar su Neehal ya sa tai saurin share hawayen fuskarta ta mik'e tsaye, ganin yanayin Neehal gabanta ya faɗi, dan ta yi tunanin ko ta ji mutuwar ne, Haneefah ta ce "Mama ga ta mun dawo, nima dama tun d'azu nake son na ce mata ta dawo gidan saboda jikinta, sai kuma gashi kin kira ni" Mama ta kama Neehal a jikinta ta rungume, ta na sakin ajiyar zuciya jin ba su ji mutuwar ba, Haneefah kallon Mama kawai take yi ganin yanayinta, hakan ya tabbatar mata da tabbas da akwai wata matsalar ba iya ciwon Neehal ɗinne ya maida Mama haka ba, Neehal kuwa luf ta yi a k'irjin Mama ta na sauke ajiyar zuciya, wayar Mama ce ta yi ƙara, hakan ya sa ta sakin Neehal da sauri ta zaunar da ita, Dad ne ke kiran ta, ɗagawa ta yi ta kara wayar a kunne, daga ɗaya ɓangaren Dad ya ce "Doctor, Neehal d'in sun dawo?" Mama ta ce "Eh." Dad ya ce "To ku taho yanzu an kawo gawar." Mama ta ce "Ohk ga mu nan." Daga haka ta katse wayar, dama ta ce wa Dad idan ankawo gawar su kirata dan gawar ta na asibiti fiye da awa biyu Police na binkice a kanta, sai yanzu aka ba da ita. Mama da ma da hijabinta a jikinta, mukullin Motor kawai ta ɗauka ta dubesu ta ce "Ku taso mu je" Kallon ta Neehal ta yi cikin mamaki amma ba ta ce komai ba, sai Haneefah ce ta ce "Ina zamu Mama?" Mama ta ɓata rai ta ce "Siyar da ku zan yi" Haneefah ba ta ƙara cewa komai ba, ta kama hannun Neehal suka bi bayan Mama, a tunanin Haneefah asibiti za su itama Neehal haka. A bayan Motor suka tarar da Mama, sai driver a gaba, suma bayan suka shiga. Tunda suka shiga Motar idanun Neehal a lumshe suke, Haneefah ce ma take ɗan kallo hanya, a tunaninta Nasarawa Hospital za su sai ta ga sun yi hanyar Hotoro ba ta kawo komai a ranta ba, sai da ta ga sun shiga layinsu Anwar sannan ta fara tambayar kanta a kan mai kuma za su yi a gidan su Anwar d'in, gabanta ne ya yanke ya faɗi Lokacin da driver ya yi parking a ƙofar gate ɗin gidansu Anwar, ga mutane an taro a na ta d'aura rumfuna, duk wata alama da za nuna mutuwa a ka yi a gidan Haneefah ta gan ta, sai dai ko kaɗan ba ta yi tunanin Anwar ne ya mutu ba, ta yi tunanin dai wani dabanne a gidan, tunda mahaifinsu already ya rasu balle ta ce ko shine. Mama ta buɗe Motar ta fita, Neehal ta biyo ta itama ta fito, sai da ta fito ta gane inda suka zo, Mama ta kama hannunta kawai ganin yanda take jujjuya idanunta ta na bin layin da kallo kamar wata doluwa suka nufi cikin gidan, Haneefah jiki a sanyaye ta fito ta bi bayansu. Bin Mama kawai suke zuciyoyinsu na bugawa har suka shiga part ɗin Mahaifiyar Anwar inda suka tarar da Mutane damk'am a falon an yi jugum_jugum, masu kuka na yi masu salati na yi, Kakarsu Anwar ta na hango su Neehal ta rushe da kuka, cikin kukan ta ce, "Allah sarki, ga yarinyar da Anwar zai aura nan, Allah ya ji ƙanka Anwar, Anwar ya saka mana, ya tona asirin azzaluman da suka kashe ka" ta ci gaba da rizgar kukanta, wani irin wul Neehal ta ji a kanta kamar an ɗora mata dutse, k'wace hannunta ta yi daga na Mama ta yi baya za ta faɗi, cikin dauriya Mama ta ruk'ota da sauri, Haneefah kuwa tuni ta durk'ushe a ƙasa dan ƙafafuwanta ba za ta su iya ɗaukar ta ba, jin wai Anwar ne ya mutu. Mama ta na riƙe da Neehal har suka ƙarasa gurin da Mahaifiyar Anwar take, Neehal ta kwace jikinta daga na Mama ta je ta tsugunna a gaban Maman Anwar ta ce "Ammi ke kaɗai ce za ki faɗa mun Anwar ya rasu in yarda, Ammi dan Allah ki faɗa mun dagaske Anwar ya mutu, dagaske wannan taron na rasuwar Anwar ne?" Ammi ta share hawayen fuskarta ta kama hannun Neehal cikin lallami da dangana ta ce, "Neehal, Allah shi ya bamu Anwar kuma ya fimu sonshi ya karbi abinsa, Addu'a kawai Anwar yake buƙata daga gurinmu" Tunda daga Allah ya karb'i ran Anwar da Ammi ta ce, Neehal ba ta ƙara fahimtar komai da yake wakana ba, sai farkawa ta yi ta ganta a jikin Mama ta na shafa mata ruwa a fuska, ga Haneefah a gefenta ta na kuka, dafe kanta da yay mata mugun nauyi ta yi, ga kirjinta ma kamar an ɗora mata dutse saboda nauyin da yay mata. Mahaifiyar Anwar ta na hawaye sosai ta zo ta d'aga Neehal ta na faɗin "Mu je ki ganshi kafin a fita dashi" Neehal ta bita kamar wani mutum_mutumi jiri na kwasarta su ka shiga wani ɗaki, gawar Anwar ta hango kwance samb'el an gama shiryashi har an sanya shi cikin makara, jini gaba-daya ya ɓata likafanin ta saitin k'irjinsa, wata ƙara Neehal ta k'walla ta ƙarasa inda gawar take a gigice ta fara faɗin, "Anwar dagaske ka mutu, kai ma za ka tafi ka barni, mutuwa me ya sa zaki mun haka, me ya sa za ki ɗauke mun Anwar ɗina, dan Allah Anwar ka tashi kar ka tafi ka barni, ka tashi ka ce musu ba ka mutu ba, ka....." Mama da ta shigo ɗakin saboda ƙarar da Neehal ta k'walla, ta rufe mata baki, ta na hawaye ta ce "Addu'a za ki yi masa Neehal ba surutai da kuka ba, addu'arki ya fi buƙata a halin yanzu" Neehal ta ture hannun Mama daga bakinta ta ce "To..to, zan masa addu'ar" Ka na ganin yanayin Neehal ka san ba ta cikin hayyacinta a wannan lokacin. Mama ta dubi Ammi dake tsiyayar da hawaye kamar an buɗe famfo ta ce "Wuk'a aka soka masa ne?" Ammi ba ta iya ba ta amsa ba saboda halin da take ciki, sai wani k'anin mahaifin Anwar ne dake tsaye a ɗakin ya ce "Harbin sa aka yi da bindiga" Neehal ta kalli Mama a matuƙar firgice ta ce, "Mama shi ma harb'e mun shi a kai, kamar yadda a ka harb'e mun JAMIL ɗina da....." Mama da ita ma kalmar Harbin ta firgita ta, ta rungume Neehal a jikinta ba ta ce komai ba, zuciyarta na wani irin bugu. Neehal kuka take a jikin Mama ta na sumbatu na fitar hayyaci. a haka a ka shigo a ka ɗauki gawar Anwar a ka fita da ita dan kai sa gidansa na gaskiya😭 (Ya Allah ka sa mu cika da kyau da imani🙏.)...........✍️ _*Manage please 🙏*_ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:31] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *0️⃣7️⃣* ..........Neehal ta k'wace jikinta daga jikin Mama ta yi falo da gudu a matuƙar gigice ganin dagaske dai Anwar ɗin ya mutu har za'a tafi da shi, riƙe ta a ka yi ganin ta na ƙoƙarin bin masu ɗauke da gawar, bin gawar kawai ta yi da ido hawayen idanunta ya ƙafe ƙaf kukanma ta kasa yi, kawai gani a ka yi ta yi ƙasa ta fad'i sumammiya. Farkawa kawai ta yi ta ganta a cikin wani d'aki kwance a kan gado, ƙoƙarin tashi zaune ta yi amma ta kasa saboda nauyin da kanta ya yi mata. Muryar Mama ta ji ta na faɗin, "Sannu Neehal kin tashi?" Neehal ta gyad'a mata kai ta na bin d'akin da take da kallo, ƙoƙarin ƙara tashi ta yi Mama ta taimaka mata ta sa mata filo a baya ta jingina da shi, ta na sauke Numfashi, Aunty Sadiya ce ta shigo ɗakin ita da Maman Haneefah, Aunty Sadiya ta ce "Sannu Neehal" Neehal ta ɗaga mata kai kawai, Mommy ma sannu mata. Neehal ta dubi Mama ta ce "Zan yi Sallah Mama" Mama ta taimaka mata ta kaita toilet ta yi alwala, kafin su fito Mahaifiyar Anwar da ta ci kuka ta k'oshi ta shigo ɗakin, sannu ta yi wa Neehal sannan ta shimfid'a mata darduma ta yi Sallah. Bayan ta idar Haneefah ta kawo mata wayarta da'ake ta zuba mata uban kira, ajiye wayar kawai ta yi ba tare da ko dubawa ta yi ba, domin ba ta ita take ba a wannan lokacin, rashin Anwar ba ƙaramin rashi ba ne a gare ta, wayar da su ka yi da safiyar yau ta shiga tunawa bayan sun gaisa ya mata ya jiki sai ya ce mata. _Neehal kwana biyun nan na lura kamar akwai wani abun da yake damun ki, ba zan matsa miki a kan dole sai na ji ba, Amma ki sani, ita rayuwa ba ta taɓa tafiya dole sai ka na fuskantar wani K'abule ko kuma jarrabawa daga Ubangiji, kuma komai ya same ka muk'addari ne daga Ubangiji kuma babu mai yaye maka sai shi a kuma lokacin da ya so, dan haka a kodayaushe ki zama mai kaiwa Allah kukanki, kuma ki zama mai haƙuri a kan dukkan wata jarabawa da ta same ki, domin dukkan mai haƙuri ya na tare da Nasara a rayuwarsa._ Hawaye mai dumi ne ya zubo daga idon Neehal cikin ranta ta fara faɗin "Ashe dama Anwar mutuwa zai yi, shiyasa ya mata yar gajeriyar nasiha a zantawarsu ta ƙarshe da shi a duniya, Ya Allah ka ji k'an Anwar, ka gafarta masa zunubansa kasa Aljannah ta zama makoma a garesa." Kafin Yamma labarin Mutuwar Anwar ya karad'e ko'ina a garin Kano, dama jahohin Nigeria da wasu ƙasashen, kasancewar harbeshi a ka yi, kuma gashi ya na shirin angoncewa nan da wata ɗaya, gashi kuma shahararriyar 'ƴar jaridar da duniya ta santa zai aura, hakan ya ƙarawa labarin armashin yayatawa. Sosai mutuwar Anwar ta girgiza Mama, musamman idan ta tuna mutane masu Mahimmanci a rayuwar Neehal duk kashe su akai ta hanyar harbin su, zuwa yanzu Mama ta tabbatarwa da kanta akwai wata a ƙasa a rayuwar Neehal ɗin, tausayin ɗiyarta ta ne ya ƙara cika mata zuciya, tun ta na 'yar ƙaramar ta za'a ɗora mata abin da ya fi ƙarfinta. A ɓangaren su Aunty Sadiya da Aunty Aisha, suma tunanin da suka wuni da shi kenan a ransu, musamman Aunty Sadiya da ta kasance Barrister, tunanin abun take cike da nazari, Maman Haneefah ma haka. Har wannan time ɗin Mama ta na ta trying number'n Ameen, amma ba ta sameshi, abun ya bata mamaki ba kaɗan ba, domin Ameen ko cikin dare ka kira shi sai ka same shi ba ya taɓa kashe wayoyinsa. Neehal kuwa ta na zaune kawai ta na bin mutane da ido, amma ita ko tunanin ma ta kasa, Mutanenta maza da mata ana ta zuwa yi mata gaisuwa, amma abun da ya bata mamaki rashin ganin Yayanta har zuwa wannan lokaci da yamma ta yi Magriba ta gabato. Bayan isha'i su Mama suka tattara suka koma gida, duk da Neehal ta so a barta ta kwana amma Mama ta ce ta bari gobe da sassafe sai su dawo, tunda yanzu gidan damk'am yake da mutane 'yan'uwan Mahaifin Anwar da na Mahaifiyarsa. Neehal har dare ko ruwa bata kai bakinta ba, ga ciwon mara da yake murd'a mata kaɗan_kaɗan, ta na daga zaune ma jiri take ji. Gabad'aya gidan Mama suka wuce, su Haneefah dai gidansu suka wuce. Neehal ta na kwance akan gadonta Mama ta shigo ɗakin da cup a hannunta, ajiye shi ta yi akan bedside locker sannan ta zauna a gefen gado, a hankali ta ce "Daughter!" Neehal ta buɗe idanunta a hankali ta sauke akan Mamanta, Mama ta ce "Tashi ki sha tea" Neehal ta girgiza mata kai alamar a'a, Mama ta ce "Haba Neehal ki tashi kisha ko kaɗan ne, ko haka za ki kwanta da yunwa" cikin raunin murya Neehal ta ce "Ba zan iya sha ba ne" Mama ta ce "Ki daure ki gwada dai" ƙoƙarin tashi Neehal ta yi Mama ta taimaka mata ta shi, kanta ta dafe da sauri alamun ya na mata ciwo, Mama ta ce "Sannu" sannan ta tashi ta ɗauko tea d'in ta fara bata a baki, Neehal shan tea ɗin kawai take yi amma babu test ko ɗaya a bakinta, tamkar ruwan mad'aci haka take jin sa, tasha kusan rabi kafin ta ture cup d'in daga bakinta har ruwan tea d'in ya d'an zuba a jikinta, Mama ta na shirin yi mata magana, amma ganin ta tashi da gudu ta nufi toilet ya sa Maman ajiye cup d'in ta bi ta, amai take k'wararawa sosai, hankalin Mama a tashe ta shiga yi mata sannu, bayan ta gama ta wanke mata bakinta sannan ta kamata ta mayar da ita ɗaki, ta kwantar. Sosai hankalin Mama ya tashi ganin yanayin jikin Neehal ɗin, ga zazzaɓi mai zafi da ya rufe ta, lullub'a mata duvet Mama ta yi, sannan ta fita ta haɗo allura ta mata, duk rashin son Allura irin ta Neehal wannan kam ba ta ma sam an yi ta ba, ba jimawa kuwa bacci ya ɗauke ta. Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta ƙara gyara mata kwanciya gami da tofa mata addu'a, cike da tsananin tausayinta, ta san a daren yau Neehal ba za ta taɓa rintsawa ba shiyasa ta mata allurar bacci dan ta samu ta rintsa. Falo ta koma inda su Aunty Sadiya suke, Hajiya kuwa ta na ɗakinta itama baccin ya ɗauke ta, ba tare da ta shirya masa ba. Aunty Sadiya ta na duban Mama ta ce "Yaya Fateemah me ki ka fahimta a kan kisan Anwar?" Mama ta sauke Numfashi ta ce "Sadiya na Fahimci kamar yadda a ka kashe Jamil haka a ka kashe Anwar, kuma idan har hakane to saboda Neehal ake kisan" Aunty Sadiya ta jinjina kai ta ce "Hakane, amma shi Jamil ɗin an gano waɗanda suka kashe shin?" Mama ta ce "A'a, dan ko last week mun haɗu da Mahaifiyarsa a asibiti mun daɗe ma, har nake faɗa mata bikin Neehal ya kusa, kuma na tambayeta ya maganar kisan Jamil ta ce mun, an yi binkicen, an yi binkicen amma shiru har yanzu babu wani labari, shiyasa su sun ma haƙura sai addu'a kawai suke, koma waye ya yi kisan Allah ya bi musu hakkinsu" Aunty Sadiya ta ce "Tabɗijan, ni tsoro na ɗaya idan har aka cigaba da bincike a kan mutuwar Anwar, za'a gano a baya Neehal an taɓa kashe mata wanda za ta aura, dan haka gabad'aya binkicen kanta zai koma fa." Mama ta yi shiru dan ta ma rasa me za ta ce, Aunty Aisha dake saurarensu ta ce "To wai abun tambayar ma a nan Sadiya, idan har saboda Neehal ake wannan kisan waye ya ke yi?" Aunty Sadiya ta ce "Ba mu da amsa Ya A'isha" Mama ta ce "Wannan abun shine babbar damuwata, yau tunanin da na wuni kenan ina yi, akan waye ya kashe wa Neehal duk mijin da za ta aura, kuma me ta yi masa yake mata hakan, me ne ribarshi na yi mata Hakan?" Aunty Sadiya ta ce "Hmmm sai Allah, amma na yi wa kaina alƙawari daga yau zan fara zurfaffen binkice akan wannan abun, insha Allahu ko ma waye yake bibiyar rayuwar Neehal sai mun binciko shi" Mama ta ce "Ba na jin ki a kan aikin ki Sadiya, na san ki na da k'warewa da kuma Sa'a gami da jajircewa, amma kuma sai na ji zuciyata ta na tsoron ki yi aikin nan, kar su gano ki na binkice akan su su yi miki wani abun." Aunty Sadiya ta yi wani guntun Murmushi ta ce "Kar ki damu Ya Fateemah, insha Allahu babu abin da zai faru da ni, kuma da ma harkar Shari'a a ƙasar nan indai kai me gaskiya ne, sai addu'a kawai, ku dai kawai ku taya mu da addu'a." Mama ta yi shiru kawai, dan ita kaɗai ta san me yake damun zuciyarta akan wannan baƙon al'amari da ya shigo cikin rayuwarsu yake ƙoƙarin tarwatsa masu farin cikinsu, ita fatan ta ma a ce kisan ba saboda Neehal ake ba, duk da tasan hakan da wuya, domin Neehal ba iya samarinta kawai aka kashe mata ba har da...... Shigowar uncle Ahmad mijin Aunty Sadiya ya katse wa Mama tunaninta, amsa masa sallamar da ya yi suka yi. Ya zauna suka gaisa, sannan suka ƙara tattaunawa a kan al'amarin kasancewar shima Barrister ne, kamar matar tasa, Dad ma ya shigo falon aka cigaba da tattaunawar da shi. Misalin ƙarfe goma da rabi na dare Mama ta na ɗakinta a zaune a kan darduma ta na lazimi, domin babu d'igon bacci ko kaɗan a idonta, bayan tafiyar su Aunty Sadiya gidajensu Dad ya koma part ɗinsa, ita kam Mama yau ko part d'in nasa ba za ta iya zuwa ba, saboda damuwar da take ciki, sosai Mama ta damu da wannan al'amari, domin ba ta k'aunar abin da zai taɓa Neehal ko kaɗan a rayuwar nan, balle abin da zai taɓa farin cikinta, amma tasan ba ta isa ta goge rubutacciyar ƙaddarar da Ubangiji ya zana wa Neehal ɗin ba, a rayuwarta. A hankali ta ji an buɗe ƙofar ɗakinta an shigo, a tunaninta Dad ne, amma jin k'amshin turaren Ameen ya sa ta d'ago kanta da sauri ta kalle shi, kansa a ƙasa ya yi sallama tare da nufo inda take, Mama ta ɗauke kanta daga Kallonsa tare da amsa masa sallamar da ya yi a zuciyarta. Kusa da ita ya zauna kansa na ƙasa still ya ce "Mum!" Mama ta ɗan kallesa ta watsar amma ba ta ce komai ba, ya ƙara faɗin "Ya haƙurinmu?" Mama ba ta amsa masa ba sai cewa ta yi "Me ya samu phones ɗinka?" Ba tare da ya yarda sun haɗa ido ba ya ce "Switch up d'insu na yi" Mama ta ce "Akan wanne dalili" ya ɗan yi shiru na wasu sakanni ita kuma Mama ta tsura masa ido. Cikin dakiyarsa ya ce "Aikin da ya kaini Lagos ne ba ƙarami ba ne, kuma ina so in gama shi a yau gobe kawai sai dai a rabawa masu yi, that is why na katse wayar kar a kira ni a tsayar da ni." Mama ta yi shiru dan ita ta damuwarta take a halin yanzu, shima shirun ya yi, amma ba ka isa ka gane ko wani abu ya na damunsa ko akasin haka ba a halin yanzu. Washegari Neehal ta tashi jikin nata da ɗan dama, dan Mama a gurinta ta kwana, tun dare jinin ya ɗauke mata, hakan ya sa da asuba ta yi wanka ta yi sallar ta, ta daɗe ta na wa Anwar addu'ar samun dacewa, da waɗanda kullum da koyaushe cikin yi musu take, da Jameel da ma dukkan Musulman da suka rigamu gidan gaskiya baki ɗaya. Zuwa yanzu zuciyarta ta gama tsinkewa ta haƙura ta fawwalawa Allah komai, Amma kallo ɗaya Mutum zai mata ya hango ramar da ta yi lokaci ɗaya, bayan ta gama addu'o'inta ta janyo wayarta wadda rabonta da ita tun jiya, missed calls d'in da akai mata take dubawa, Numbobin da ta sani da wanda ba ta sani ba gasunan rututu har ta rasa kiranwa ma za ta bi. Aranta ta ce "Da waninta ne ya mutu ba Anwar ba, da har da missed calls d'inshi za ta gani, kuma shi kaɗai za ta iya bin kiranshi, wani abu ta ji ya tokare mata a k'irji, a hankali ta shiga App din free kur'an ta buɗe ta fara karanta Suratul Baƙara, domin ta san shi kaɗai zai mata maganin abun da yake damunta. Ta yi nisa a karatun Ameen ya shigo ɗakin, ba ta ma san ya shigo ba har ya yi sallama, saboda hankalinta gabad'aya ya na kan karatun da take, a ƙoƙarin ta na ganin ba ta ba wa damuwa damar zama a cikin zuciyarta ba, sai dai k'amshin turarensa da baya b'uya ya sanar mata da zuwan nashi, ta d'ago da kanta da sauri cikin mamaki dan ba ta san ya kwana a gidan ba, gabanta ya faɗi haɗa idon da suka yi da shi, ta ɗauke idonta da sauri daga kallon shi bugun zuciyarta na ƙaruwa ba tare da tasan dalili ba, nufar inda take ya yi cikin takunsa na ƙasaita da burgewa..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:31] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ 0️⃣8️⃣ ..........Tsugunnawa ya yi a gabanta ya na kallon ta, ƙasa ta yi da kanta zuciyarta na cigaba da bugawa, lumshe idonta ta yi saboda daddad'an k'amshinsa da ya mamaye mata hanci, numfashi ta ja tare da lumshe idanunta, a hankali ya kama tattausan hannunta da nasa, cikin sanyin murya ya ce "Miemerh! Ya hakurin rashin Anwar?" Cikin muryarta da ta ɗan dashe saboda damuwa ta ce "Alhamdullah" fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Allah ya ji k'an shi, ya sa ya huta." Neehal ta d'ago kanta a hankali tare da buɗe idanunta da suka cika taf da hawaye, ta ce "Amin, amma Yayah me ya sa ba ka zo tun jiya ba?" Ta k'arashe zancen hawaye na zubo mata, ba tare da ya saki hannunta ba ya shiga share mata hawayen fuskarta da ɗayan hannun nasa, cikin murya mai nuni da rarrashi ya ce "Am sorry, ban samu labarin mutuwar da wuri ba ne." Neehal ba ta ce komai ba, sai hawaye kawai take kamar jira take a taɓa ta dama. Ameen ya ce "Kukan na mene kuma? Kin san dai mamaci ba ya buƙatar kuka ko?" Neehal ta na kuka ta ce "Dole in yi kuka Yaya, me Anwar ya yi aka kashe shi, haka ma fa a ka kashe mun Jameel, shima Anwar d'in ba za su bar mun sh......." Rungumeta Ameen ya yi tsam a jikinsa cikin tsananin tausayinta, sosai shima al'amarin ya rud'a shi, Ajiyar zuciya Neehal ta shiga saukewa ta yi luf a kirjinshi tare da dena kukan. Shigowar Mama d'akin ya sa ta janye jikinta daga na shi da sauri, Mama ta kalle su ta ce "Me ya faru?" Ameen ya mik'e tsaye ya ce "Babu komai" Sannan ya sa kai ya fice. Mama ta zauna a bakin gado ta na duban Neehal ta ce "Kukan me ki kay?" Neehal ta girgiza mata kai alamun babu, Mama ta ce "Shikenan tashi mu je ki yi breakfast, Haneefah na hanya idan ta zo sai ku wuce gidan su Anwar" Neehal ba ta yi musu ba ta mik'e suka sauka k'asa tare da Mama. Tea kawai tasha kaɗan, shima dan kar Mama ta mata fad'a ne, Mama ta ce "Shikenan abin da zaki sha kuma ki ce kin k'oshi?" Neehal ta ce "Eh Mama ba zan iya ƙara cin komai ba" Mama ta ce "Daurewa za ki, ki ci ko Irish ne kaɗan" Neehal ta ɓata fuska, sannan ta d'ibi Irish d'in kadan ta ci, ta na kokarin barin falon Haneefah ta shigo da sallamarta, suka amsa mata ta gaida Mama, sannan ta dubi Neehal ta ce "Besty ya hak'urinmu?" Neehal ta ce "Alhamdulillah, ya kuka je gida jiya?" Haneefah ta ce "Lafiya k'alau" Sama suka hau tare, suka je d'akin Hajiya suka gaisheta. Neehal ta ɗauki wayoyinta suka fito suka yi wa Mama sallama, sannan suka je part d'in Dad suka gaisheshi. Yau ma Neehal an zo mata ta'aziyya sosai, Uncle Mahmud da ya koma gida jiya yau ma ya dawo har da matarsa da 'yarsa budurwa kamar su Neehal, sai dai Neehal ta ɗan girme ta. Ameen da Dad yau da su a ka wuni gurin zaman makoki. Da yamma Police masu fararen kaya suka zo gidan mutuwar domin yin tambayoyi ga ahalin Anwar, bayan sun gama da mutanen waje suka shigo cikin gidan, inda suka ce a kai su gurin Mahaifiyar Anwar. Ammi ta na ɗakinta ta ce su shigo, su su uku ne kuma duk maza ne, ɗaya daga cikin su wanda da alama shine babban su ya dubi Ammi ya ce "Hajiya ina yini, ya ƙarin hak'uri kuma?" Ammi ta ce "Lafiya k'alau Alhamdulillah" Ya ce "Allah ya ji k'an shi ya gafarta masa" mutanen d'akin suka amsa da "Amin" gabatar wa da Ammi kansa ya yi da na abokan aikinsa sannan ya ɗora da faɗin "A daren ranar da ana washegarin Anwar zai mutu, kun zauna da shi? Ma'ana kun yi doguwar hira?" Ammi ta ɗan yi jim na wasu sakonni kafin ta ce "Eh mun yi hira amma ba wata me tsayi ba" Mutumin ya ce "Ko a cikin hirar taku ya faɗa miki sun yi faɗa da wani ko kuma sun samu ɗan sabani haka?" Ammi ta ce "Gaskiya A'a, dan gaba-da'ya ma hirar a kan kai lefen sa da za'a kai ne washegari" Mutumin ya jinjina kai ya ce "Kuma ba ki ga wata alamar ɓacin rai ko damuwa a tattare da shi ba?" Ammi ta ce ko kaɗan, sai ma tarin farin cikin da ya kasa b'oye shi, abun ma da na san ya faɗa mun wanda ya ɗan dame shi, sai rashin lafiyar da ita yarinyar da zai aura take yi, harma ya ce mun zai je ya gano jikin nata a wannan lokacin" Mutumin ya ce "Daga nan ba ku sake haɗuwa ba a wannan daren?" Ammi ta ce "Eh, sai dai sallama da ya zo ya mun, lokacin wajen 11 na dare" Mutumin ya ce "Kuma a nan ma ba ki ga ya na cikin wani yanayi ba ko kuma damuwa haka?" Ammi ta ce "Gaskiya ko kaɗan ban ga haka ba" Mutumin ya gyara zama ya ce "Ki yi hak'uri da tambayoyi na fa, sha'anin aiki ne" Ammi ta ce "Babu komai, ka ci gaba insha Allah zan faɗa maka duk abin da na sani" Mutumin ya gyad'a kai sannan ya ci gaba da magana "To a baya fa, ya taɓa faɗa miki ya na da wani wanda ba sa shiri da shi, ko a makaranta ko gurin aiki ko unguwa ko wani guri daban?" Ammi ta yi shiru na wani gajeren lokaci ta na tunani, sai kuma can ta girgiza kai ta ce "Gaskiya babu, domin Anwar tunda ya girma ba zan ce ga abokin faɗan sa ba, ko cikin abokansa da 'yan'uwa da unguwa harma gurin aikin na su, idan ma da akwai bai taɓa faɗa mun ba, kuma gaskiya ba ya b'oye mini duk wani abu nashi, komai zai faɗa mun ya ce Ammi ki ta ya ni da addu'a." Mutumin ya jinjina kai ya ce "A ranar da zai rasu ya yakasance ya tashi kamar kullum da ya saba ko da wani canji?" Ammi ta sauke Numfashi muryarta na ɗan rawa ta ce "Lafiya k'alau muka tashi kamar kodayaushe, Misalin ƙarfe 7 da k'wata kamar yadda ya saba ya zo nan gurina, muka gaisa k'annensa suka kawo masa abincin kari ya ci, sannan ya mun sallama ya tafi gurin aiki, kuma kamar yadda ya saba da ya ƙarasa wajen aikin ya kira ni ya ce mun ya je lafiya, daga nan sai mummunan labarin da muka j......." Ta fashe da kuka mai ban tausayi. Mutumin ya jinjina kansa a karo da yawa ya ce "Sai hak'uri Hajiya, Allah ya ji k'an shi, Mun gode da haɗin kai da ki ka ba mu, Insha Allah za mu yi iya ƙoƙarin mu wajen ganin an gano waɗanda su kai kisan kuma an bi muku hakkin ran ɗanku, idan da buƙatar sake zuwa mu miki wasu tambayoyin za mu dawo" Ammi ta gyad'a masa kai ta na share hawayen fuskarta. Mutumin ya dubi ɗaya daga cikin wanda suka zo tare mai rubuce_rubuce ya ce "Ya kamata mu ga yarinyar da zai Aura ita ma" Ɗayan ya ce "Haka ne Sir" Ammi ya tambaya ina Neehal ta ce ta na falo bari a kira masa ita, bayan ta zo sun gaisa ya mata ta'aziyya sannan ya dubeta da kyau ya ce. "Malama Neehal, a zamanku da Anwar ko ya taɓa faɗa miki cewa ya na da wani abokin faɗa ko kuma wanda ba sa jituwa?" Neehal da kanta ke ƙasa cikin sanyin murya ta ce "Gaskiya bai taɓa faɗa mun ba, Ni tunda nake da shi ma bai taɓa ce mun yau sun yi faɗa da wani ba, ko kuma wani ya ɓata masa rai ba" Mutumin ya ce "Ke ce wadda ya yi waya da ke ta ukun ƙarshe kafin rasuwar sa, shin da kuka yi waya kin ji wata alama da take nuni da ba ya cikin wani firgici ko damuwa? duba da a gurin aikinsa har cikin office d'insa a ka je a ka kashe shi, kuma wayar ki da shi ko 2 hour ba'ayi ba hakan ta faru" Neehal ta ce "Ko kaɗan ban ji alamar hakan ba gaskiya" Mutumin ya jinjina kai ya ce "Shikenan Malama Neehal bari na barki haka, next time idan buƙatar mu ƙara tattaunawa da ke ta taso, za mu nemi ki" Neehal ta gyad'a masa kai kawai, zuciyarta na bugawa. Haka a ka ci gaba da zaman makokin mutuwar Anwar, Neehal kullum su na zuwa gidansu Anwar da safe sai dare suke tafiya har a ka yi sadakar uku, daganan kuma bata ƙara komawa ba saboda ita ma ana zuwa gida yi mata gaisuwa, sai ranar sadakar bakwai suka kuma komawa. Yau Juma'a wanda ya kama kwana goma sha biyu da rasuwar Anwar, zuwa yanzu Neehal ta sakawa zuciyarta dangana game da mutuwar Anwar, Anwar ya riga ya tafi ya zama tarihi addu'ar su kawai yake buƙata, duk da wani lokacin ta na damuwa sosai har ta zauna ta yi ta kuka, Mama,Dad, Haneefah sune 'yan rarrashin ta da bata baki gami da nasihohi, Ameen ma yanzu wata kulawa yake bata ta musamman saboda tausayi take basa sosai, ta zama wata so silent wannan rigimar da neman magana gurin Mama duk ta daina, Magana ma ba sosai take yinta ba, ga rama da ta yi. Misalin ƙarfe Biyar na yamma Neehal ta na zaune a falon ƙasa ita kaɗai ta na kallon Sunna TV, gani ta yi Dije mai aiki ta fito daga dakinsu da sauri, ashe ƙarar bell ta ji, ita ba ma ta ji ba ta na can duniyar tunani. Dije ta na buɗe door d'in ta ga kanwar Dad ce ta zo tare da 'yarta, hanya ta ba su ta na musu sannu da zuwa cikin girmamawa, Matar ce kawai ta amsa mata a wulak'ance amma 'yarta ta ko kallon ta ba ta yi ba, ta wuce ciki ta na taunar cingum ƙas_ƙas ga takalmin ƙafarta mai shegen tsini sai ƙara yake a kan tiles ɗin falon, k'amshin turarenta mai hawa kai ya cika falon, fara ce tass kamar ka tsaga jikinta jini ya fito amma gajeriya ce ta na da madaidaicin jiki, ta na sanye da wata doguwar riga 'yar kanti, ta yafa mayafi kalar rigar kanta babu ɗankwali sai fuskarta da ta sha uban make up. Neehal ta bita da kallo fuskarta ba yabo babu fallasa, ita kuwa wani matsiyacin kallo take bin Neehal da shi. Neehal ta yi ɗan murmushi ta ce "Sannunku da zuwa Aunty Hamida" kamar ba ta ji ba, ta yi banza da ita, Neehal dama ta san za'a rina, duk da kasancewar Hamida 'yar gidan k'anwar Dad ce amma ba sa shiri ko kaɗan, ko dan hakan ya samo asali ne daga rashin shirin Mahaifiyar Hamidan da Mama ne?. Neehal ranta ya ɓaci a kan abin da Hamida ta mata, dama shi ya sa bata son shiga sabgarta, Mama ce ke tursa sata dole, ta rasa me ta yi wa Hamidan ta tsane ta over. Hamida ta zauna ta na kar kaɗa ƙafa, Mahaifiyarta wadda suke k'ira da Mumy ta ƙaraso cikin falon ta zauna ita ma ta na huhhura hanci, Neehal ta dube ta ta ce "Sannu da zuwa Mumy ina yini?" Ta mata wani kallo ta ce "Lafiya k'alau, ya hak'uri kuma?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Daga haka suka yi shiru, Neehal ta maida hankalinta a kan kallon da take, bayan wasu mintuna Mama suka sakko ita da Hajiya da Dije da ta je kiranta. Mama ba yabo ba fallasa ta ce "Sannunku da zuwa" Mumy ta ce "Yawwa" Mama ta ce "Ya gida Suwaiba?" Mumy ta ce "Lafiya k'alau" Mama ta ce "Masha Allah" tare da zama a kan kujera, Hajiya ma ta zauna. Hamida kamar ba ta so ta ce "Ina yini Mama?" Mama tace "lafiya k'alau, Hamida ya aiki" tace "Fine Mama" Hajiya yadda ba su mata magana ba, itama ba ta musu ba, TV kawai take kallo hankalinta kwance. Su Dije suka dawo falon da ruwa da lemo gami da drinks, Zulai ta gaishe su kamar yadda Mumy ta amsa wa Dije haka ta amsa wa Zulai a wulak'ance. Can dai Mumy ko me tuna sai ta dubi Hajiya ta ce "Ina yini Hajiya?" Hajiya ta ce "Lafiya" tana keb'e fuska, Hamida da ke ta latsa wayarta ita ma ta gaishe ta a yangance. Mumy ta gyara zama ta dubi Mama ta ce "Sai muka ji kuma an kashe saurayin Neehal" Mama ta ce "Eh ƙaddara ta riga fata." Mumy ta ce "To Allah ya ji k'an shi, amma ni fa ina ganin wannan abun kamar da sa hannu, a ce yarinya duk wanda maganar aure ta shiga tsakaninsu sai an kashe shi, sai ka ce firlm ko labaran tatsuniya?" Mama ta yi shiru ba ta ce komai ba, domin da rainin hankali Mumy ta yi maganar. Hamida ta tab'e baki ta ce "Hmmmm gaskiya dai Mumy, dan Ni na ma fi tunanin ko wani baƙin Aljanin ne ya aure ta.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:31] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ 0️⃣9️⃣ ...........Hajiya ta dubi Hamidah ta na mitsi_mitsi da ido ta ce "Ke! Ki iya bakinki, mugun nufinki Insha Allahu ba dai a kan Neehal ba, ato, bakinki ya sari ɗanyen kashi" Hamida za ta kuma magana Mommy ta girgiza mata kai, tab'e baki ta yi ta ci gaba da latsa wayarta a gadarance, Mama kuwa kamar ba ta ji su ba, ta musu banza. Neehal ma ko d'aga kanta ba ta yi ba, balle ta nuna ta san me su ke cewa. Hakan kuwa ba ƙaramin k'ona ran Mommy ya yi ba, domin kuwa ta so Mama ta kula ta su yi ta yi, ko kuma Neehal ta tankawa Hameedah Dad ya dawo ta haɗa mata sharri, sai kuma ba ta samun haɗin kai ba. Mama tashi ma ta yi ta wuce sama abin ta, Neehal ma bin bayanta ta yi dan zaman falon ya ishe ta. Hakan kuwa ya ƙara kona ran Mommy. Ɗakin da suke sauka idan sun zo Mama ta sa su Dije suka gyara musu, da yake daga Abuja suke a can suke da zama, su Dije suka kwasar musu kayansu zuwa d'akin. A gadarance su Mommy da Hameedah suke yin komai a gidan, Mama kuwa ba ta tanka musu haka ma Neehal, Hajiya ce ma sarkin magana, amma Mama ta roƙe ta a kan ko me za su yi kar ta kula su. Ko da Dad ya dawo part d'insa suka je su na hira, har sai da dare ya yi sosai sannan ya ce ya kamata su je su kwanta, Mama kuwa dama ta san hali shi ya sa ba ta je ba, sai da ya kira ta da kansa a waya. Washegari Neehal tun safe ta wuce gurin aiki, dama tun ranar mutuwar Anwar ba ta koma ba sai yau. Misalin ƙarfe 11 na safe Ameen ya shigo gidan, kamar yadda ya saba part d'in Mama ya nufa direct, da key d'in hannunsa ya yi amfani ya buɗe kofar, da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga. Hameedah ce kwance a kan kujera ta na latsa waya, Mahaifiyarta kuwa ta fice gidan k'awayenta. Da sauri ta tashi zaune jin sallamarsa tare da faɗaɗa fara'arta wadda tun da ta zo gidan ba ta yi kamarta ba. Ameen ya kalle ta sau ɗaya ya kau da kansa, har ya ƙaraso cikin falon kallon sa take kamar za ta lashe shi bakin ta ya ƙi rufuwa dan farin ciki. Cikin kaud'i da iyayi ta ce "Sannu da zuwa Ya Ameen." Ta ƙarashe zancen tare da mik'ewa ta koma kusa da shi. Ya kalle ta ba yabo ba fallasa ya d'aga mata kai. Hameedah ba ta damu ba ta ce "Yayanah I missed you so much, na manta when last da na ganka, last zuwan da na yi ba mu haɗu ba, gashi kai kuma ba ka zuwa gidanmu." Ameen ya banzatar da zancen nata ya ce "Yaushe ki ka zo?" Cike da jin daɗin ya biye mata suna hira ta ce "Yesterday, ni da Mommy mun zo gaisuwa ne?" Ameen ya ce "Tun yaushe aka yi rasuwar amma sai yanzu za ku zo?" Hameedah ta ɗan shagwab'e ta ce "To ai Yaya ka ga ina zuwa aiki, sai weekend nake da time." Ameen ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma can ya ce "Neehal as she is your cousin sis, amma a mata rasuwa ki ce sai kin samu time za ki zo mata gaisuwa?" Hameedah ta tab'e baki tare da ɓata fuska ba ta ce komai ba, sai kuma can ta ce "Kasan Mommy ma ba ta ji dad'i ba time ɗin shi ya sa ba mu zo ba, kuma na ga ita gaisuwa ai ba ta tsufa, tun da mun masa addu'a ai is ok." Ameen bai kuma ce mata komai ba ya mik'e ya nufi sama gurin Mahaifiyarsa. Mama ta na operating system ya yi knocking k'ofar ɗakin, Mama ta ba da umarnin a shigo. A hankali ya buɗe k'ofar bakin sa ɗauke da sallama. Mama ta d'ago ta na duban sa ta amsa masa, ya ƙaraso ya zauna a gefen ta ya ce "Gud Morning Mum, how are you?." Mama ta ce "Lafiya, ka zo lafiya? Ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah, ina Neehal fa?" Mama ta ce "Ta je aiki." Ya gyad'a kai kawai tare da ƙoƙarin mik'ewa. "Koma ka zauna ina son magana da kai." Muryar Mama ta katse masa hanzarinsa. Ya gyara zama tare da bata duka hankalinsa. Mama ta ture laptop d'in gabanta ta na dubansa da kyau ta ce "Ameen me kake tunani a kan al'amarin Neehal? Ba ka ganin kamar wasu ne suke bibiyar rayuwarta? Duba da a baya an kashe Jameel ma" Shiru ya yi alamun nazari kafin ya sauke Numfashi ya ce "Mum, babu irin tunanin da ban yi ba a kan wannan al'amarin, tun lokacin na ci karo da labarin mutuwar Anwar dake ta yawo a media, amma kuma da na yi wani nazari da lissafi sai na ga kamar kisan Anwar da Jameel ba shi da alaƙa da Neehal." "Saboda me ka ce haka?" Cewar Mama ta na kallon sa. Ameen ya ce "Idan ba ki manta ba Mum, shi Jameel dama can ya na da 'yan adawa a rayuwarsa duba da yanayin aikinsa." Mama ta ce "Hakane, domin kuwa tun a wancan lokacin da aka kashe Jameel ko kaɗan ban yi tunanin kisan ya na da alaƙa da Neehal ba, dan some times Idan ya zo gaishe ni ya na yawan cewa a taya su da addu'a saboda magauta da mahassada, amma kuma kashe Anwar da aka yi ya birgita mun duk wani lissafi na Ameen." Ameen ya ce "Duk da an kashe Anwar amma ba na tunanin kisan Anwar ya na da alaƙa da na Jameel" Mama ta yi shiru ta na jin dama furucin Ameen zai tabbata da sai tafi kowa farinciki, za ta so a ce ba dan Neehal ake kisan ba, amma kuma abun da kamar wuya musamman idan ta yi duba da....... "Kar ki sa wa ranki damuwa Please Mom, kuma ki cire tunanin wai ko dan Neehal aka kashe Anwar" Ameen ya katsewa Mama tunaninta da faɗin haka. Mama cikin damuwa ta ce "Ameen! Ka na so ka kwantar mini da hankali ne kawai kamar yadda ka saba a kodayaushe idan ka ga ina cikin damuwa, amma ba ni kaɗai ba ma, ko A'isha da Sadiya mun yi maganar da su kuma suma duk tunanin su haka ne." "To ai dama tunanin ku duk ɗaya ne ku mata." Cewar Ameen ya na murmushi. Mama ta ɗan harara shi ta ce "Su kuma sauran mazan da muka yi maganar da su fa?" Kamar a ɗan rud'e ya ce "Su wa kenan?" Mama ta masa wani kallo ta ce "To mene na yin hakan kuma, kamar wanda aka zabura?" Ameen ya ɗan lumshe idonsa ya ce "Nothing, kawai ban so ki ka yi maganar da wasu ba" Mama ta ce "Ahmad ɗin Sadiya ne fa sai Mahmud, su kuma ka ga ai duk na gida ne." Ameen ya ce "Hakane, Insha Allahu ko ma yaya ne Allah zai warware mana, kuma Insha Allahu problem ɗin ba daga wurin Neehal ta ke ba." Mama ta ce "Ameen ya Allah." Ameen ya mik'e ya na faɗin "Ina Hajiya fa?" Mama ta ce "Tun safe driver ya kaita gidan Sadiya yau can za ta wuni." Ya ce "Ok" har ya juya Mama ta ce "Ka ga Hameedah kuwa" ya gyad'a mata kai alamar Eh ba tare daya juyo ba, Mama ta yi murmushi kawai dan tasan tun da ya yi haka ba ya son zancen Hameedan ne. Neehal ta na zaune a office d'inta ta na duba wasu takardu Haneefah ta shigo office d'in bakinta ɗauke da sallama. Neehal ta amsa mata tare da dire da takardun a kan table ɗin gabanta. "Har kun gama editing ɗin?" Neehal ta tambayi Haneefah dake ƙoƙarin zama. Haneefah ta ce "Eh, ai time ɗin labaran ya kusa" Neehal ta ce "Hakane" sannan ta gyara zama ta na duban Haneefah ta ce "Haneefah!" Haneefah ta dube ta da mamaki domin tasan tunda Neehal ta kira ta da sunanta abu mai mahimmanci za ta faɗa mata. Neehal ba ta jira amsar Haneefah ba ta cigaba da magana. "Haneefah zuciyata ta na cikin fargaba gami da zullumi da tsoro a kan kisan Anwar, Ina tsoron a ce ta dalilina aka kashe Anwar" Haneefah ta ce "Me ya sa ki ke cewa haka ne wai Neehal, ta yaya kisan Anwal zai zama saboda ke?" "Saboda an kashe Jameel ma a baya." Haneefah ta ce "Ki dena tunanin saboda ke aka kashe su, na faɗa miki wannan maganar tun kafin yau amma kin k'i ki daina ta, akan me za'a na kashe miki samari?" Neehal ta ce "Shine ban sani ba Haneefah." Haneefah ta mik'e ta koma kusa da Neehal ta dafa kafad'arta, cikin son kwantar mata da hankali ta ce "Kin ga Neehal kar ki saka wannan abun a ranki har ya yi tasiri a cikin zuciyarki, Jameel da Anwar lokacin mutuwar su ne ya yi, da lokacin su bai yi ba babu wanda ya isa ya kashe su. Kawai Allah ya yi ajalinsu ya na hannun waɗanda suka kashe sun ne, amma wlh Neehal ni har yanzu zuciyata ba ta yarda saboda ke a ka kashe su Anwar ba." Neehal ta sauke numfashi ta ce "Amma kuma Haneefah yanayin yanda ake kashe sun ɗaya ne, duk harbe su ake fa." Haneefah ta ce "Kar ki yi la'akari da wannan, duba da yanda zamani ya sauya, yanzu ai ko barayi ne za su yi sata zai yi wahala ki gansu da wuk'a ko wani makamin, sai dai yara, amma waɗanda suka shahara da bindigu suke zuwa, Dan haka idan an harbe Anwar da Jameel ba hakan ya na nufin mai kisan ɗaya ba ne." Neehal ta yi shiru kawai ta na kallon Haneefah tare da auna maganganunta a mizanin nazari. Bayan kamar minti uku ta ce "To Haneefah ko dai aljanu ne?" "Haba Neehal, wanne aljanu kuma? Kar ki ɗauki alhakin bayin Allah, idan aljanu ne kuma sai su dinga harbe mutum, su da suke da hanyoyin cutar da mutane kala_kala." Haneefah ta katse Neehal da faɗin haka cikin tarar numfashi. Neehal ta runtse idonta kawai tare da dafe kanta cikin kullewar kwanyarta. Haneefah ta saki kafadunta ta koma kujerar da ta taso sannan ta ce "Da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, idan da rabon shan numfashin mutum a duniya ko a na yanka naman jikinsa sai ya rayu, idan kuma kwanan mutum ya ƙare ko da lafiyar sa k'alau dole sai ya amsa kiran mahaliccin sa, ki sa wannan a ranki Allah shine mai yin komai a kuma sanda ya so." Neehal ta ja wani gwauron numfashi ta ce "Tabbas maganganunki gaskiya ne Haneefah, kuma Insha Allahu zan cire wannan tunanin daga raina, amma zan dage da addu'a a kan Allah ya bayyana gaskiyar al'amari." Haneefah ta ce "Ko ke fah, su kuma sai ki ta musu addu'ar neman gafara da dacewa a gurin Ubangiji" Neehal ta ce "Insha Allah, Ni kuma tawa ƙaddarar kenan duk wanda na so ba ma kasancewa tare sai mun rabu." Yanda Neehal ta yi maganar sai da Haneefah ta murmusa ba tare da ta sani ba, Neehal ma murmushin ta yi domin kalaman Haneefah sun fara sanyaya mata zuciya. Ta na murmushin ta ce "Dariya ma na baki ko?" Haneefah ta ce "Ai yanda ki ka yi maganar ne kamar wata sabuwar marainiya." Neehal ta ce "Me ne marabata da sabuwar marainiyar?" "Marabar ku ki na da iyaye samari kawai ki ka rasa, kuma suma za ki samu wasu nan gaba wanda har za ki manta da na baya." Neehal ta mata wani kallo ta ce "Hmmmm, ki na tunanin zan iya ƙara son wani ɗa namiji a duniyar nan ne? ai ni da soyayya kuma sai dai na ga a na yi" Haneefah ta yi wani ɗan murmushi ta ce "Zance ma kenan, za ki yi ta zama ne ba ki yi aure ba? Ko kuma za ki yi Aure ba tare da soyayya ba? Ni na faɗa miki ki rubuta ki ajiye sai kin so wani fiye da son da ki ka yi wa Jameel da Anwar." Neehal ta tab'e baki ba ta ce komai ba, dan ita ba ta ɗauki maganganun Neehal da mahimmanci ba, ban da haka ta yaya za ta so wani fiye da son da ta yi wa Anwar d'inta? Ai tun ranar da Anwar ya rasu ta yi wa kanta alƙawarin ta bar soyayya har abada. Yau ma gidan Mama Haneefah suka wuce bayan sun tashi daga aiki, suna shiga ta ga Hameedah ita ba ma tasan ta zo ba, dan Neehal ta ma manta da zuwanta ba ta faɗa mata, ita kuma rabonta da gidan tun ranar Alhamis. Suka yi sallama, Hameedah ta d'ago ta musu wani kallo kamar ta ga kashi ta ƙi amsa musu sallamar. Haneefah da ta fi Neehal saurin ɗaukar zafi ta ce "Sai ka ce mutum ba musulmi ba a yi sallama ya na ji ya ƙi amsa wa." Aiko Hameedah dama kaɗan take jira, dan ta je part d'in Ameen za ta masa shirme ya korota, gashi dama ta tsani Haneefah kamar yadda ta tsani Neehal. Mik'ewa tsaye ta yi kamar wata sabowar kamu ta fara ɗura_ɗuran ashar ta na zagin Haneefah har ma da Neehal da ta bata kula ta ba. Haneefah za ta biye mata Neehal ta ja ta su ka hau sama. Bayan sun shiga daki Neehal ta dube ta ta ce "Mai ya sa ki ka kula ta dan Allah? Kin san halin ta fa." Haneefah ta na ware rolling d'in kanta ta ce "Amma dai ai gaskiya na faɗa mata, ita say ta yi ta yi wa mutane kallon banza ta na musu masifa, ni kuma zan mata shiru ne, ai ba tsoron ta nake ba." Neehal ta ce "Na san bakya tsoron ta dama, amma dan Allah ki dai na kula ta, kome za ta yi." Haneefah ta ce "Shikenan Insha Allahu haka ba za ta kuma faruwa ba." Washegari tun safe su Hameedah suka shirya suka wuce Abuja. Mama ta haɗa musu tsaraba kamar yadda take wa kowa idan ya zo gidanta. Hameedah kuwa kamar karta tafi saboda ganin Ameen da take, shi kuwa ko kallo ba ta ishe sa ba. Hameedah ta na bala'in mutuwar son Ameen, shekarun ta kusan 30 amma ta ƙi aure wai jiran shi take, Family kowa ya ɗauka soyayya suke nan kuwa ita kaɗai take haukan ta. Mahaifiyarta kullum ta zo sai ta ce wa Dad ya kamata a saka ranar bikin su, a duk lokacin da ta fadi haka sai Dad ya yi murmushi ya ce "Suwaiba Na fi so Ameen ya yi maganar Hameedah da kansa, ko kuma so ki ke ya raina mini 'yar tawa ya ga kamar neman kai muke da ita." Ita kuwa Suwaiba (Momy) sai ta kada baki ta ce "Yoo tunda shi ya ƙi magana ai mu sai mu yi, abu duk na gida ai duk ɗaya ne." Da daddare Mama ta na part d'in Dad suna tattaunawa akan maganar Ameen ɗin da Hameedah, ya na faɗa mata yanda Mommy'n Hameedah ta takura masa da zancen ayi_ayi aurensu. Mama ta ce "Ni kaina Gen. na matsu Ameen ya yi aure, na gaji da yawo da hankalin da yake mana." Dad ya ce "Hakane, nima ina son na ga ya yi auren, amma bari na kirashi na ji ra'ayinsa a kan Hameedan, tunda ni bai taɓa mini batun ta ba da kansa." Mama ta ce "Toh." Dad ya kira Ameen a waya ya sanar masa ya na son ganinsa yanzu. Bayan 10 minutes sai gashi ya zo, ya zauna a ƙasa ya na duban Dad ya ce "Ga Ni Dad" Dad ya ce "Dama akan maganar Hameedah ne, tunda auren Neehal ɗin Allah bai nufa ba, dama shi muke jira a yi sai mu yi zancen naka, to yanzu ka na son Hameedan ne?" Ameen ya d'ago ya dubi Dad, cikin nutsuwarsa ya ce "Ni fa Dad ba na son Hameedah, Ina da wadda nake so!" Da sauri Mama da ta k'ura masa ido ta ce "Kamar ya ba ka son ta?" Dad ya d'aga mata hannu ya na ɗan murmushi, sannan ya dubi Ameen ya ce "Wa ce wacce ka ke so ɗin?"..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:33] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ 1️⃣0️⃣ ............ Ameen ya yi shiru tare da sunkuyar da kansa ƙasa. Mama ta na duban Dad ta ce "Kai ka biye masa ai, ban da haka mene aibun Hameedan da zai ce ba ya sonta?" Dad ya ce "Haba Doctor, kin san dai ba zan yi masa auren dole ba tunda ba ya sonta Shikenan." Dad ya maida dubansa ga Ameen ya ce "Kai muke sauraro." Ameen cikin dakiyarsa ya ce "Hafsah!" "Hafsat kuma?" Mama ta tambaya cikin mamaki. Ameen ya gyad'a mata kai. Mama ta ce "Dama har yanzu ku na tare da ita ?" Nan ma kan ya kuma gyad'a mata. Dad ya na murmushi ya ce "Masha Allah, A Ina ita Hafsan take? 'Yar waye?" Mama ta ce "Hafsat fa 'yar gidan Alhaji Nuhu Ɗan gaske" Dad ya ce "Allah sarki, to Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, Insha Allahu a satinnan zan samu shi Mahaifinnata mu yi magana, a san abun yi." Mama ta ce "To Allah ya tabbatar da Alkhairi" Dad ya ce "Amin" Ameen ya mik'e kansa a ƙasa ya fice daga falon, Mama ta bishi da kallo cikin mamakin shi, maida kallonta ta yi ga Dad bayan ya fice ta ce "Al'ameen halinsa sai shi, yarinyar nan Hafsat ba irin son da ba ta nuwa masa ba a baya, amma ya nuna ba ya son ta, yanzu kuma da bakin shi ya dawo ya ce ya na sonta" Dad ya ce "Haka Al'amarin Allah yake, kin san matar mutum kabarinsa, wata ƙila duk wannan abun da ake itace matar tasa" Mama ta ce "Hakane, Allah ya sa Albarka ya sa da mu za'a yi." Dad da fara'a ta ƙi bacewa daga fuskarsa ya ce "Amin." Mama ta ce "Um, sai wata fara'a kake kamar an maka wani albishir ɗin." Dad ya yi 'yar ƙaramar dariya ya ce "Wlh ba ki ji yanda farin ciki ya lullub'e ni ba da Ameen yau ya furta mun ya fidda mata, dama ni tsoro na kar mu bashi mata a zo a samu matsala zumuncinmu ya ɓaci." Mama ta ce "Gaskiya kam, amma Ni na so Ameen ya auri Hameedah, ko dan yanda take k'aunarsa, ga ta kuma jininsa ce, yanzu idan Family suka ji zancen nan ya kake ganin za su ɗauki maganar, tunda kowa ya na tunanin Ameen Hameedah zai aura, ita kanta Hameedan ban san wanne hali za ta shiga ba idan ta ji wannan zancen." Dad ya gyad'a kai ya ce "Nima na so hakan Doctor, Amma kin san yaran yanzu ba'a musu dole, ni ba na so a samu matsala ne, shi ya sa ban tursasawa Ameen a kan lallai sai ya Auri Hameedah ba, itama Allah ya fito mata da miji na gari ta yi auranta." Mama ta ce "Amin ya Allah." Wayar Dad ce ta fara ringing, dubawa ya yi sai kuma ya saci kallon Mama, ƙin d'aga wayar ya yi har ta katse, aka kuma kira ya kuma ƙin d'agawa. Mama ta ɗauke kai kamar ba ta gani ba, kiran da aka kuma yi ya sa Mama mik'ewa tsam ta zagaya ta ɗauki wayar ta duba, Dad ya yi murmushi ya na kallonta ya ce "Ba wata ce take kirana ba sarkin kishi." Mama ta haɗe rai ta ce "Hubby! Har yanzu dama ka na tarayya da Alhaji *Kabir Ginyau* ?" Dad ya riko hannun Mama tare da zaunar da ita a gefensa ya ce "Ehh, amma ba tarayya irin wadda muka yi da ba, kawai dai mu na gaisawa ne sama_sama." Mama ta ce "Amma..." Dad ya d'aga mata hannu cikin lallami ya ce "Kin ga Doctor, Dan Allah kar ki tada hankalinki a kan dan Kabir ya kira ni, yanda kike tunanin abun kwata_kwata ba haka yake ba." Mama ta yi shiru kawai ta na kallonsa. Washegari da safe Neehal ta na kitchen ta na yin breakfast Ameen ya shigo part d'in, ganinta a kitchen d'in ya sashi shiga kitchen d'in. Neehal ta juyo ta na kallonsa jin k'amshin turarensa, a hankali ta ce "Ina kwana Yaya?" Ameen ya ce "Lafiya k'alau, ina Mama fa?" "Ta na d'akinta" Neehal ta bashi amsa ta na satar kallonsa, shima kallon nata yake yi hakan ya sa suka haɗa ido. Neehal ta ɗauke idonta da sauri ta na turo bakinta gaba. "Idan kin gama ki kawo mun nawa breakfast d'in part d'ina." Ya fadi haka tare da juyawa ya fice, Neehal ta bishi da kallo kawai. Mama ta na zaune a kan darduma ta na karatun Alkur'ani mai girma ya shigo d'akin, sai da ta kai ƙarshen aya sannan ta rufe ta d'ago tare da amsa masa sallamar da ya yi. Ameen ya zauna a gefenta ya ce "Ina kwana Mom, dafatan kin tashi lafiya?" Mama ta ce "Lafiya k'alau, and you?" Ya ce "I'm fine." Mama ta ce "Masha Allah, am Ameen dama ina son na tambayeka." Ameen ya dubi Mama amma bai ce komai ba. Mama ta ajiye Kur'anin hannunta a kan bedside locker, sannan ta fuskance shi da kyau ta ce "Me ya sa ka ce ba ka son Hameedah?" Ameen cikin nutsuwarsa da sanyin muryarsa ya ce "Mama! Kin san wace Hameedah kuma kin san halinta, kwata_kwata ba ta da qualities d'in matar da zan iya aura." Mama ta ce "Na san da haka Ameen, amma ba ka tunanin yanda Family'n Dad d'inka za su ɗauki abun? Kowa zai yi tunanin Ni na hanaka auren Hameedah saboda ba ma shiri da Mahaifiyarta." Ameen ya tab'e ɗan ƙaramin bakinsa sannan ya ce "Kar ki damu kanki Mama da su, su faɗi duk abun da za su faɗa." Mama ta tsura masa ido kawai ba ta ce komai ba. Kawar da zancen ya yi ta hanyar faɗin "Yaushe wacce old Woman d'in za ta tafi?" Mama ta ce "Bansani ba, tunda uwar tawa ce Old Woman." Ameen ya mik'e ya na faɗin "Tunda ba za ki faɗa mun ba zan tambaye ta da kaina." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa daga d'akin. D'akin Hajiya ya leƙa ya tarar da ita a kan darduma ta na lazimi ta na gyangyad'i, ya yi murmushi kawai ya juya ya fice. Neehal ta na gab da kammala aikin da take Mama ta shigo kitchen, Neehal ta kwab'e fuska tare da turo baki gaba. Mama ta dube ta, ta ce "Sannu Daughter." Neehal ta ce "Yawwa Mama, kin fito." Mama ta ce "Eh, amma ba yanzu zan fita ba, kawo na ƙarasa aikin ki je ki yi azkar ɗin safe dan nasan ba ki yi ba." Neehal ta ce "Toh Mama." Harta fita daga kitchen d'in sai kuma ta dawo, Mama ta kalleta da alamun mamaki amma ba ta ce komai ba, Neehal kanta na ƙasa ta ce "Yaya ya ce in kai masa break ɗinsa part ɗinsa." Mama ta ce "Yanzu dawowa ki kai masa?" Neehal ta ce "Ehh." Mama ta ce"Ki wuce ki yi abin da na ce miki, zan bayar a kai masa." Neehal ta turo baki sannan ta juya ta fice. Bayan ta gama azkar ɗin ta sakko ƙasa ta na break Mama ta ce mata, "Za ki aiki ne yau?" "A'a." Neehal ta bata amsa. Mama ta ce "Idan kin gama ki shirya ki je gidan Sadiya, daga nan sai ki biya gidan A'isha, su na ta complain kin dena zuwar musu 2 days." Neehal ta yi murmushi ta ce "To Mama, bari na kira besty mu je tare." Kafin azhar su Neehal sun je gidan Aunty Sadiya, Aunty Sadiya ta tare su da fara'a sosai, bayan sun gaisa ta kawo musu drinks su na zaune a falo Aunty Sadiya ta dubi Neehal ta ce "Ni kuwa Daughter Ina son in miki wata tambaya." Neehal ta maida hankalin ta duka a kan Aunty Sadiya ta ce "Ina jin ki Aunty." Aunty Sadiya ta ce "Ki na da saurayi bayan Anwar ne?" Neehal ta ce "A'a, dan gaskiya ba na kula duk masu nuna suna so na, tun daga lokacin da a ka yi Engagement ɗinmu da Anwar." Aunty Sadiya ta ce "Babu wani wanda yake son ki tun da dad'ewa kafin haɗuwar ki da Jameel, kuma har yanzu ya na nuna ya na sonki?" Neehal ta ce "Ban gane ba Aunty?" Aunty Sadiya ta ce "Ina nufin kamar shekaru Biyar da suka wuce, ba ki yi wani saurayi da ya nuna ya na sonki ba, kuma har yanzu bai daina son ki ba.?" Neehal ta yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce "Gaskiya ba na jin akwai, idanma da akwai na manta." Aunty Sadiya ta gyad'a kai sannan ta maida dubanta ga Haneefah da take saurararsu ta ce "Ke fa Haneefah ko kin sani?" Haneefah ta ce "Gaskiya samarin Neehal na baya duk sun hak'ura da ita, wasu ma sun yi Aurensu." Aunty Sadiya ta ce "Alright." Neehal ta ce "Amma me yasa ki ka mun wannan tambayar Aunty?" Aunty Sadiya ta ce "Kawai." Daga haka suka shiga wata hirar. Sai bayan la'asar suka bar gidan Aunty Sadiya, wadda cikin hikima take yi wa su Neehal tambayoyi domin samun wani information d'in da zai taimake ta gurin binkicen da take. Kamar yadda Mama ta ce gidan Aunty A'isha suka wuce, nanma sun sha hira da Aunty A'isha sai bayan sallar Magriba suka yi haramar tafiya, shima sai da Mama ta kira su ta ce "Ko kwana za su yi a nan ɗin ne?" . Neehal ta na ɗaukar hand bag d'inta ta ce "Toh Aunty mun tafi sai gani na biyu." Aunty A'isha ta ce "Yanzu ba za ku jira driver'n ya dawo ya kai ku ba tafiya za ku yi?" Neehal ta ce "Gwara mu tafi Aunty, tunda ba mu sani ba ko ba zai dawo da wuri ba, gashi kin kira wayarshi ta ƙi shiga balle mu ji in ya na kusa mu jira shi." Aunty A'isha ta ce "Toh Shikenan, ku gaida gida, ku gaida su Hajiya da Yaya Fatimah." Neehal ta ce "Za su ji Insha Allah." Haneefah ta yi wa Aunty A'isha sallama, Aunty A'isha ta ce ta gaida Mamanta sannan suka tafi. Suna fitowa daga gidan Haneefah ta dubi Neehal ta ce "Wai me ya sa ba za ki kira driver'nki ya ɗauke mu ba?" Neehal ta ce "Kawai yau Napep nake so mu hau." Haneefah ta ce "Kin shiga uku da tsurfa, ko mai ciki haka ta ganki ta k'yale." Neehal ta ce "Na ji ɗin." Suna tafiya suna hirarsu, sun zo dai_dai ƙarshen layinsu Aunty A'isha za su fita titi wata had'ad'd'iyar Mota ta shigo layin, kamar ance Neehal ta kalli Motar suka haɗa ido da ma mallakin motar wanda ya kasance saurayi, kuma a ka yi sa'a ya zuge glass d'in Motar, wata irin fad'uwar gaba Neehal ta ji dalilin haɗa ido da suka yi da shi, da sauri ta ɗauke kallonta daga gurin Motar bugun zuciyarta na sauyawa...........✍️ *Ku yi hak'uri da wannan Please, wlh na shiga wani uzurinne, sai yanzu na samu time, da k'yar ma na iya typing ɗinnan saboda ciwon kai da nake fama dashi.😥🙏* *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:33] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ 1️⃣1️⃣ *BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽 *500MB* 200 *1GB* 300 *2GB* 600 *3GB* 900 *6GB* 1800 (CHECKING BALANCE * 461*4# ) VALIDITY : 1 MONTH For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951* ...........Ƙoƙarin b'oye baƙon yanayin da ya risketa lokaci ɗaya ta yi dan kar Haneefah ta fuskanta. Yanda take ta sauke numfashi a kai_a kai ya sa Haneefah dubanta da mamaki ta ce "Ya dai?" Neehal ta girgiza mata kai. Haneefah ta ce "Mu tsaya a nan mu samu Napep ɗin, tunda kin samu tafiyar ƙasa, gashinan ba'aje ko ina ba kin gaji." Neehal ta ce "Ni na ce miki na gaji?" Haneefah ta ce "Ba ki faɗa ba, amma na ga alama, sai sassauke numfashi ki ke kamar wadda ta yi tseren gudu raguwa kawai." Neehal ta harareta ba ta ce komai ba, suka tsaya domin duba abun hawa. A hankali yake yo baya da Motar tasa cikin tsananin zak'uwa da son ƙara ganin fuskar Neehal, tabbas idan har idanunsa ba gizo suke masa ba, matashiyar 'yar jaridar nan ya gani wadda take matuƙar burge sa tare da abokiyar aikinta. Duk yadda ya so ya wuce ba tare da ya musu magaba amma ya kasa, duk da tarin gajiyar dake addabar gaɓɓan jikinsa, hakan ya sashi bin shawarar zuciyarsa na bin su domin ya musu magana. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya hango su tsaye a bakin titin, da alamun abun hawa suke jira. Neehal da har lokacin zuciyarta ba ta daina bugawa ba ta ga Mota kamar daga sama ta yi parking a gabansu. Kallon juna suka yi ita da Haneefah da sauri da alamun mamaki. Ba su gama mamakinsu ba suka ji wata daddadar murya mai sanyi daga cikin Motar ta na faɗin "Assalamu alaikum." Haneefah ce ta yi ƙarfin halin amsa wa, Neehal kuwa ƙasa ta yi da kanta gabanta na ci gaba da fad'uwa. "Ina yininku?" Ya gaishe su idanunshi a kan Neehal. Haneefah ta yi ɗan murmushi haka kawai ta ji Matashin ya burgeta, "Lafiya k'alau, amma na ji kunyar amsawa, saboda mu yakamata mu gaishe ka, tunda ka na gaba da mu." Cikin jin daɗin kalaman Haneefah ya ce "Haba k'anwata kar ki ji komai, ai durk'usawa wada ba gajiyayawa ba ne." Haneefah ta ce "Hakane." "Ita k'awar taki ba ta magana ne?" Ya yi maganar idanunsa a kan Neehal. Haneefah ta ce "Hmmm, gajiya ta yi ne daga ɗan......." "Ke! ki zo mu tafi, ki na sane Mama ta ce kar mu yi dare, a hakan ma kin san sai ta yi faɗa." Neehal ta katse Haneefah a ɗan zafafe. Murmushi ya yi har yanzu ya kasa ɗauke idonsa daga kanta, cikin wani irin salo mai narkar da zuciya ya ce "Gaskiya ba na so Mama ta muku faɗa, idan babu damuwa ku shigo in kai ku gidan mana." Neehal ta yi sauri ta ce "A'a mun gode." Ta ƙarashe maganar ta na turo baki gaba ganin yanda ya tsareta da ido, duk ya bi ya wani dabaibaye ta." "Please and please, ba danni ba, 'yar k'anwata." Ya fadi maganar cikin marairaicewa. Haneefah ta ce "Ka yi hak'uri, idan ka kai mu gida za'a yi mana faɗa." Ya ce "Waye zai muku faɗan?" Haneefah ta ce "Mama, za ta ce me yasa ba mu kira an ɗauko mu ba." Ya ce "Sai in shiga in mata bayani, In ce sabon ɗa ta yi shine ya kawo k'annensa gida." Haneefah za ta kuma magana ya katse ta da faɗin "Kar mu tsaya ja_in_ja daku, ku shigo kawai mu tafi, kunga kun ce za'ai muku faɗa idan ku kai dare, ni kuma bazan barku ba sai na kai ku gida." Haneefah ta yi murmushi ta ce "To Mun gode." Neehal ta ɓalla mata wata uwar harara, Haneefah ta mata gwalo ta wuce ta zagaya ta buɗe murfin Motar ta shiga, ita ma Neehal ba ta da zaɓi wanda ya wuce ta shiga Motar tunda Haneefah ta riga da ta shiga. Karon farko a rayuwarta da ta shiga Motar wani wanda ba ta sanshi ba, amma fa ta ɓata rai sosai alamun ba ta so. *Sadik* ya yi murmushin jin dad'i, wani irin nishad'i yake ji a ransa, gajiyar da take damunsa tuni ya neme ta ya rasa. Neehal ta lumshe idanunta ta na sauke numfashi saboda k'amshin da ta shak'a da ta shiga Motar, wanda ya haɗe da sanyi Ac. K'amshin ya mata daɗi sosai domin har shige ta ji ya mata da na Yayanta. Sadik ya tambayi Haneefah unguwar su ta faɗa masa, kunna Motar ya yi suka hau titi suka fara tafiya. Su na tafiya su na hira da Haneefah wadda ta saki jiki sosai da shi kamar sun dad'e da sanin juna, Neehal kuwa sai harara take bankawa bayan Haneefah, ita ko ba ta ma san ta na yi ba. Har layinsu Neehal ya kai su, daidai k'ofar wawakeken gate d'in gidan Haneefah ta ce ya tsaya, bayan ya yi parking Haneefah ta ce "To new Bro, mun gode sosai fa." Sadik ya na murmushin da ya ƙi bacewa daga fuskarsa ya ce "Haba sai kace wani abun, ai nine da godiya da har kuka yarda kuka shigo 'yar akwalar Mota ta, kuna Manyan 'yan jarida." Haneefah ta yi murmushi ta ce "Kai Yaya na akwai ka da zoyala." Neehal ta tab'e baki, kamar ba ta son magana ta ce "Mun gode, Allah ya saka da Alkhairi." Ba ta jira amsar sa ba ta buɗe Motar ta fice ta fara tafiya. Sadik ya bita da kallo wani abu na yawo a cikin zuciyarsa game da ita, Haneefah ma fita ta yi tare da yi masa sallama. Mai da dubansa ya yi gareta ya ce "Sai yaushe kuma?" Haneefah ta ce "Sai ransa Allah ya kuma haɗa mu." Complimentary card ɗinsa ya mik'a mata, Haneefah ta karb'a ta ce "Bye bye, Insha Allahu zan kiraka." A falo Neehal ta tarar da Mama zaune ta na kallo, Neehal ta ƙarasa kusa da ita ta zauna a gefen ta, Mama ta juyo ta kalle ta ta ce "Sai yanzu?" Neehal ta ce "Ki yi hak'uri Mama akasi a ka samu." Mama ta ce "Da Ameen ya na nan sai ki faɗa masa akasi a ka samu, kin san ba ya nan shi ya sa ki ka yi daren ai." Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba, "Ina Haneefan Kuma?" Mama ta tambayeta ta na maida duban ta ga TV. Kafin Neehal ta ba ta amsa Haneefah ta shigo falon bakin ta ɗauke da sallama, suka amsa mata a tare. "Ina ki ka tsaya kuma?" Cewar Mama ta na kallonta. Haneefah ta yi wani munafukin murmushi ta na kallon Neehal. Neehal ta ɗauke kanta daga kallonta ta na ɓata rai. Mama ta tab'e baki ta maida hankalinta ga kallon da take. Haneefah ta ƙaraso ta zauna a saman carpet ta ce "Mama mun dawo, duk su na gaishe ku." Mama ta ce "Muna amsawa, ya kuka baro su?" Haneefah ta ce "Lafiya k'alau." Neehal ta tashi ta haye sama, Haneefah ta bi bayanta. Ta na ajiye card d'in da Sadik ya bata a kan mudubi ta ce "Ga card nan ya bani, ashe ma Barrister ne." Neehal ta tab'e baki ta ce "Sai ki nemi ma'ajiya ki killace shi ai, daga ganin mutum ba ki san shi ba, sai uban surutu ki ke zuba masa." Haneefah ta ce "Kin manta ne, I'm Jornalist fa." Neehal ta ce "Ke dai ki ka sani." ************************ Rayuwa na ta tafiya kwanaki na ta wucewa, cikin ikon Allah har an yi sadakar arba'in Anwar, su Neehal har wannan lokacin cikin hutu suke ba su koma school ba. Sosai Haneefah suke zumunci ita da Sadik, tamkar 'Yan'uwan juna tun da, dan Mama da Mommy'n Haneefah duk san Sadik a bakin Haneefah. Neehal ce dai sama_sama suke gaisawa, shima sai dai idan suna tare ya kira Haneefah sai ta bata su gaisa. Dad sun je sun samu Mahaifin Hafsat sun yi magana, sai dai har yanzu Hameedah da mahaifiyarta da sauran Family ba su da labarin Ameen ba Hameedah zai aura, kuma ƙarshen watan nan Insha Allahu za'a kai kuɗi gidansu Hafsat ɗin. Haneefah ta na kitchen ta na dafa Indomie da daddare ta ji Mommy dake zaune a falo ta na k'wala mata kira. Haneefah ta amsa tare da faɗin "Ina zuwa Mommy." Sai da ta kammala ta juyo Indomie'n a plate sannan ta fito. Ta na ajiye Indomie'n a kan Centre table ta ce "Ga ni Mommy." Mommy ta ce "Wayar ki a ke ta kira." Haneefah ta ƙarasa inda ta ajiye wayar ta ɗauka ta duba missed call d'in, Saurayinta ne wanda za ta aura ya mata 1 missed call sai kuma Sadik da ya mata 2 missed call, kiran Saurayinta ta fara bi amma bai d'aga ba, bayan ta katse ta kira Sadik. Ringing biyu ya yi rejected ya kira ta. Haneefah ta d'aga tare da yin sallama, ya amsa mata ya ƙara da faɗin. "K'anwata Ya kike? Ya Mommy?" Haneefah ta ce "Ina lafiya Yayanah, Mommy ma haka, kai fa?" Sadik ya ce "Lafiya k'alau nake, am Haneefah dama ina so mu yi wata magana dake yanzu idan babu damuwa." Haneefah ta ce "Alright, to bari na ci abinci minti goma i will call you back." Sadik ya ce "Ok sai kin gama." Bayan ta gama ci ta koma d'akinta sannan ta kira sa, rejecting ya ƙara yi sannan ya kira ta. Bayan ta d'aga ya ce"Haneefah, Magana za mu yi a kan k'awarki Neehal." Haneefah ta yi ɗan murmushi domin tun kafin yau ta gano nufin Sadik a game da Neehal. Ta ce "Ina jin ka Ya Sadik." Sadik ya ɗan numfasa ya ce "Haneefah, tun kafin nu haɗu da ku na san ku a Television, kasancewar ni ma'abocin kallon labaranku ne, Sosai ku ke burgeni saboda yanda ku ke yin komai na ku cikin nutsuwa, ga shiga ta mutunci da kamala wanda yake nuna kun fito daga gidan tarbiyya. Ranar da na ganku a unguwarmu ji na yi tamkar mafarki nake dan farin ciki, hakan ya sa na kasa hak'uri har sai da na tsaya na muku magana, kuma wannan ita ce rana ta farko da na taɓa tsaida mace na mata magana." Ya ɗan numfasa sannan ya cigaba da magana. "Haneefah maganar gaskiya, zuciyata ta kamu da matsanancin son k'awarki, amma ban san me ya sa nake tsoron tunkarar ta da maganar ba............✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:33] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *1️⃣2️⃣* ...........Ya ƙara yin shiru a karo biyu sannan ya cigaba da magana kamar haka. "Abun da ya sa nake tsoron tunkarar Neehal da maganar saboda ina tunanin kamar ba za ta amince ta karb'i tayin soyayyata ba." Haneefah ta ce "Ya Sadik na ji batun da ka zo mun dashi, kuma na ji dad'i sosai, amma maganar gaskiya tunkarar Neehal da maganar soyayya a yanzu abu ne mai matuƙar wahala, domin har yanzu ba ta warware daga rasuwar tsohon saurayinta Anwar ba." Sadik ya ce "Allah sarki, ai dole dama sai a hankali za ta warware daga rad'ad'in mutuwar ta sa, Allah ya ji k'an sa ya gafarta masa." Haneefah ta ce "Amin, amma kar ka damu Ya Sadik ka bar komai a hannuna zan san ta yadda ta ɓullo mata." Ta yaya kenan?" Anwar ya tambaye ta. Haneefah ta ce "Ka bani nan da wani lokaci, na san me zan yi." Sadik ya ce "Shikenan Na gode, sai na jiki." Daga haka suka yi sallama. Haneefah ta yi shiru kawai ta na tunanin ta yanda za'a yi Neehal ta amince da soyayyar Sadiƙ. Ta dad'e ta na tunanin abun kafin ta mik'e ta koma falo. Mommy har yanzu ta na zaune a falon, Haneefah ta zauna a kusa da ita ta ce "Mommy kin san me?" "Sai kin faɗa." Cewar Mommy da ta juyo ta na kallonta. Haneefah ta ce "Ya Sadik ne ya ce min wai ya na son Neehal." Mommy ta faɗaɗa fara'a a fuskarta ta ce "Kai Masha Allah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Neehal ta ce "Amin, amma fa Mommy akwai matsala." "Matsala kuma tame Haneefah?" "Mommy Neehal mana, na san ba za ta taɓa amincewa da soyayyar Ya Sadik, saboda kwanaki mun yi magana da ita, ta ce mun ita ba za ta ƙara kula wani ɗa Namiji da sunan soyayya ba, Tun da Anwar ya rasu." Mommy ta ce "Zancen banza, to haka za ta yi ta zama ba ta yi aure ba ko kuma me take nufi? Mace ma take yin Aure mijinta ya rasu kuma ta sake wani auran su zauna lafiya, balle ita da yake Saurayinta, yarinta ce kawai ke damunta." Haneefah ta ce "To ai ita Mommy dan ta ga ankashe Jameel da Anwar wai karta ƙara yin soyayya da wani shima a kashe shi." Mommy ta ce "Wannan duk ba hujja ba ce, mutuwa da rayuwa duk na Allah ne, su ma da suka mutun kwanan su ne ya ƙare, Allah dai ya ji k'an su, ita kuma Allah ya fito mata da miji na gari ta yi auranta." Haneefah ta ce "Amin." Washegari da yamma Neehal ta zo gidansu Haneefah suna zaune a d'akin Haneefah Neehal ta dubi Haneefah ta ce "Besty ban baki labari ba." Haneefah ta ce "Labarin me?" Neehal ta ce "Yayanah ya kusa aure." Haneefah ta waro ido waje ta ce "Wow, nice story, ki ce su Aunty Hamida an kusa shiga daga ciki.?" Neehal ta ce "Hmmm, na yi farin ciki sosai da Yaya zai yi aure, sai dai kuma harna fara kewar shi." Haneefah ta ce "Iskancin banza, abun da ba kullum ki ke ganin sa ba." Neehal ta ce "Duk da haka, amma i will miss him over." Haneefah ta ce "Sai ki bishi gidan nashi, dama ba kwa shiri da Aunty Hamida sai ku yi ta fafatawa." Neehal ta ce "Ke ba fa ita zai aura ba." "Kamarya. Haneefah ta tambaya cikin mamaki. "Kamar yadda Allah ya yi, wata tsohuwar budurwarsa zai aura, Hafsat." Neehal ta bata amsa da faɗin haka. Haneefah ta jinjina kai ta ce "Allah sarki Aunty Hamida ta bani tausayi wlh, yanda take son Yaya ban taɓa tunanin ba ita zai aura ba." Neehal ta ce "Nima haka Besty, na yi mamaki, Mama ma duk ta damu." Haneefah ta ce "Allah ya sanya Alkhairi ya kai mu da rai da lafiya mu sha shagali." Neehal ta ce "Amin dai." Haneefah ta numfasa ta ce "Dama a haɗa a muku auren tare da Yaya." Neehal ta mata wani kallo ta ce "Sai dai a haɗa dake, dama na ji Mama ta na cewa Month d'in bikin da za a sa kamar ɗaya da naki." Haneefah ta ce "Sai a haɗa mu duka a mana tare." Neehal ta tab'e baki ta ce "Ke nifa na cire wani zancen aure a tsarina, karatuna kawai zan yi ta yi." Haneefah ta ce "Zance ma ki ke, idan ke kin yarda kin zauna ai Mama ba za ta yarda ki zaunar mata ba aure ba." Neehal ta ce "To za ta mun aure ba miji ne? Ina dai sai na kawo mata mijin?" Haneefah ta ce "Ai miji ba zai miki wahalar samu ba, duk tarin masoyan da ki ke da su." Neehal ta ce "Kan ki ake ji, ni dai na riga na hak'ura da wata maganar soyayya a rayuwata balle kuma har na kai ga aure." Haneefah ganin yanda Neehal take magana bil hak'k'i, ya sa ta saki baki kawai ta na kallon ikon Allah, amma ta mata uzuri, domin ta san har yanzu Anwar ya na nan a cikin ranta, shi ya sa take ganin kamar ba za ta iya ƙara tarayya da wani ɗa Namijin ba..... *********** *ABUJA* *********** Mommy'n Hameedah ce tsaye a falonta ta na zarya cikin tsananin ɓacin rai da damuwa. K'awarta mai suna Haj. Saratu dake zaune a falon ta dube ta da mamaki ta ce "Wai Suwaiba lafiya kuwa, na ga kin fito daga d'aki kin hau zarga kamar wata me fareti?" Mommy ta ja wani dogon numfashi ta sauke cikin tsantsar ɓacin rai ta ce "Ina fa Lafiya Saratu, waccan munafukar matar 'yar abu ta kazar uba ta shirya makircin da ta saba." Haj. Saratu ta ce "Wake nan.? Mommy ta ƙaraso kujerar da Haj. Saratu take ta zauna a gefenta, cikin ɗacin rai ta fara magana. "Yanzu nan Yaya Gen. ya kira ni, ya ce mun za mu yi wata magana, na tattara hankalina duka na bashi dan na ɗauka wata maganar arzik'in ce, buɗar bakinsa sai ce mun yayi. Suwaiba! Magana za mu yi a kan yaran nan Ameen da Hameedah. Na gyara zama cikin jin daɗi na ɗauka zai ce mun za a yi maganar bikin su ne, amma sai na tsinkayi muryarsa da faɗin akasin haka, wai ya kira Ameen ya masa maganar Aure ya ce ya fitar da mata, shine Ameen ɗin ya ce ba ya son Hameedan wata yake so, yanzu maganar da yake mun har sun je gidan su yarinyar an yi magana, next week za su kai kuɗi a yi Engagement ɗinsu haɗe da sa rana." Wani uban ashar Hajiya saratu ta narka ta ƙara da faɗin "Eh, lallai kam dole ki ce makira ta yi markici, dan wannan ko tantama ba na yi shirin wannan Matar tasa ne, me ji da kanta kamar tafi kowa." Mommy ta ce "Ai dama ni na san za a rina, domin matar nan ba ta k'auna ta da ni da ƴaƴana, amma wlh wannan karon ba ta isa ba, zan nuna mata asalina za ta san ko wacece Suwaiba, shima Yayan dan takaici kashe wayata na yi, ya tsaya ya na mun wata nasiha wai matar mutum kabarinsa, komai na Allah ne, Ni ko gama saurararsa ma ban yi ba." Haj. Saratu ta ce "To yanzu mene abin yi?" Mommy ta ce "Ni na san me zan yi, dan idan kinga ba a yi auran Ameen da Hameedah ba to wlh sai dai in ba na numfashi. Amma kafin na yi abin da zan yi bari na fara kiran ita makirar na ci mata mutunci." Mommy ta ƙarashe Zance tare da mik'ewa ta shiga d'akinta ta ɗauko wayarta, jikinta har tsuma yake ta nemo number'n Mama ta danna mata kira. Mama ta na asibiti ta na ƙoƙarin tafiya gida ma tunda yamma ta yi kiran Mommy ya shigo wayarta. Ba tare da tunanin komai ba ta ɗauka, dan ita ba ta masan Dad ya kira Mommy'n ya mata maganar ba. "To makira, munafuka Algunguma, wato kin yi halin naki da ki ka saba kin hana ɗanki Auren 'yata, dan nasan Ameen haka kawai ba zai ce ba ya son Hameedan ba, wa ya sani ma ko hadda siddabarunku na Fulani ki ka haɗa masa saboda ya ƙi amincewa." Kalaman da Mama ta ji kenan lokacin da ta kai wayar kunnenta, wani ɗan guntun murmushi ta yi, cikin maganarta mai cike da aji da nutsuwa ta ce "Na isa ne ai Suwaiba na hana Ameen abu kuma ya hanu, dan haka ki yi duk abin da za ki yi a kan hakan." Kamar mahaukaciya Mommy ta ce "Wlh kuwa za ki ga abun da zan yi, za ki san da ni Suwaiba ki ke maganar." Ta ƙarashe zancen ta na bubbuga k'irjinta. Mama ta yi tsaki ta na ƙoƙarin cire wayar daga kunnenta ta ji Mommy na faɗin. "Kuma nasan duk saboda me ki kai haka, dan tun ba yau ba na fuskanci wannan figaggiyar yarinyar da danginta suka kasa riƙe ta ki ke son bawa Ameen." Mama harda za ta bata amsa sai kuma ta kashe wayarta, domin ba ta da time ɗin Mommy'n. Mommy kuwa jin Mama ta katse wayar hakan ya ƙara k'ular da ita, ta yi ta masifa da d'uran_d'uran ashariya kamar sabuwar kamu. Haj. Saratu na ƙara zugata. Daf da Magriba Hameedah ta dawo gidan daga gurin aiki a matuƙar gajiye kamar wadda ta yi aikin ƙarfi. Jakarta da mayafinta ta cillar a kan kujera sannan ta zauna tare da faɗin "Wash, Mommy na gaji." A dak'ile Mommy ta ce "Sannu" Hameedah ta kalli mahaifiyarta ta, yanayin da ta mata magana ta gane ba k'alau ba, da mamaki ta ce "Mommy what happened na ga kamar ranki a ɓace?" Mommy ta ce "Akwai matsala ne Daughter babba ma kuwa." A ɗan firgice Hameedah ta ce "Me ya faru Mommy? Har kin sa hankali na ya fara tashi." Mommy ta ce "Hmmm, bari kawai Hameedah, ni da waccan matar ne Fateema matar Yaya......." Labarin duk abun da ya faru Mommy ta faɗawa Hameedah. Wani irin ihu Hameedah ta yi tare da mik'ewa tsaye cikin tashin hankali ta ce. "Wallahi Momy ba zai yiyu ba, shekara nawa ina zaman jiran shi sai yanzu a ce ba ni ze Aura ba." Ta ƙarashe zancen tare da fashewa da kuka. Mommy ta taso ta zo kusa Hameedah, dafa kafadunta ta yi cikin lallami ta ce "Share hawayenki Daughter, indai Ina raye babu abun da zai hana auranki da Ameen, ki kwantar da hankalinki." Cikin kuka Hameedah ta ce "Mommy Dan Allah ki san abun yi, wlh ba zan iya rayuwa babu Ya Ameen" Mommy ta zaunar da ita a kan kujera ta ce "Ki kwantar da hankali kamar tsumma a cikin ruwa, ki sa a ranki ma auranku da Ameen tamkar an yi angama." ******************* Neehal ta na kitchen ta na girkin dare Mama ta dawo gidan, ta fito daga kitchen d'in ta yi hugging d'inta ta na faɗin "Welcome sweet Mom." Mama ta yi murmushi ta ce "Thanks You Daughter, ya gida?" Neehal ta ce "Alhamdulillah, sai gajiyar aiki." Ta ƙarashe maganar a ɗan shagwab'e. Mama ta ce "Sannu, me ake girka mana ne, na ji k'amshi duk ya baɗaɗe ko'ina?" Neehal ta murmusa ta ce "Sai kin zo ci za ki gani." Mama ta yi murmushi ta wuce sama jin a na kiran sallar Magriba.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:33] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *1️⃣3️⃣* ..........Neehal ta koma kitchen ta cigaba da aikinta. Bayan Sallar Magriba Mama ta na zaune a ɗakinta a kan darduma ta na lazimi wayarta ta yi ƙara, ɗauka ta yi ta duba ta ga Mommy'n Hameedah ce ke kuma kiranta. Tsaki ta yi cikin takaici ta maida wayar ta ajiye, dama ta san Mommy'n Hameedah za ta yi abun da yafi haka ma indai ta ji maganar Ameen ba zai auri Hameedah ba. Kiran Mama Mommy ta yi_ta yi, amma Maman ta ƙi d'agawa. Hakan ba ƙaramin ƙara tunzura Mommy ya yi ba, ta yi ta masifa ta na kiraye_kirayen 'yan'uwa ta na faɗa musu abun da ke faruwa. Hameedah kuwa kiran layin Ameen tayi_tayi amma shima be d'agawa ba, hakan ya ƙara ta da mata da hankali ta zauna tayi ta rufzar kuka. Mama ce zaune a falon Dad dake shan fruits, Dad ya na duban ta da murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce "Kamar da magana a bakin nan naki Doctor." Mama ta ce "Babu maganar komai Hubby, Idan ma da akwai ba ta wuce ta zancen bikin Ameen ba, yaushe za ku kai kuɗin ne.?" Dad ya ce "Ranar Sunday Insha Allah." Mama ta ce "Allah ya kaimu." Dad ya ce "Amin, ina Daughter ne?" Mama ta ce "Tana can ta na hutawa wai yau a gajiye take." Dad ya ce "Bari na kirata a waya na yi missed ɗinta yau.'' Neehal ta na kwance a kan luntsumemen gadonta ta yi nisa a cikin tunanin rayuwarta, wayarta dake gefenta ta fara vibrate, ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi tare da share hawayen da yake zirarowa daga idanunta, tashi zaune ta yi ta na cize lips d'inta zuciyarta na mata zafi. Duba wayar ta yi ta ga Dad ke kiranta, cikin sanyin jiki ta d'aga wayar tare da karawa a kunnanta. Dad ya ce "Daughter bacci ki ke ne?" Neehal ta ce "A'a, ina kwance dai." Dad ya ce "Yau tun safe ban gan ki ba, na dawo kuma na jiki shiru, ko yau ba za ki zo mu yi hirar ba ne." Neehal ta yi murmushi cikin daɗi da kuma k'aunar Dad d'in nata ta ce "Zan zo My Dad, gani nan." Dad ya ce "Yawwa d'iyar albarka sai kin ƙaraso." Neehal ta ajiye wayar bayan ya kashe kiran ta na sauke ajiyar zuciya, sosai take kewar Anwar a cikin zuciyarta, musamman idan ta kaɗaice ita kaɗai babu abun da take sai tay ta tunanin sa, addu'a ta masa ta samun dacewa sannan ta mik'e jiki a sanyaye ta fice ta nufi part d'in Dad. Da sallama ta shiga falon, Mama ta kalle ta tare da amsa mata, kusa da Dad ta je ta zauna ta na faɗin. "Abbunah barka da dare." Dad ya shafi kuncinta ya ce "Yawwa Daughter, Mamanki ta ce kin gaji yau ni kuma na taso ki ko?" Neehal ta ce "A'a Dad ba komai ai na huta." Dad ya ce "To ya aikin na ku? Dafatan dai babu wata matsala.? Neehal ta ce "Babu Dad." Dad ya ce "Masha Allah." Neehal ta Kalli Mama ta ce "Mama ina son na je gidansu Ammin Anwar gobe in gaishe ta." Mama ta ce "Allah ya kai mu." Dad ya ce "Ai ko ni yakamata na kai ki da kaina, daga nan sai ki rakani zance, gurin...." Ya ƙarashe zancen da kannewa Neehal ido. Neehal ta yi murmushi ta ce "Gurin wannan kyakkyawar matar mai kirkin nan ta unguwar da muke zuwa?" Dad ya ce "Ehh ita fa, kin san ta iya girki sosai na yi kewar abincinta." Neehal ta yi dariya ta na kallon Mama. Mama ta tab'e baki domin ta saba da zolayar Dad da Neehal, sun maida ita kamar wata kakarsu, idan 'yan nishad'in na kansu haka za su yi ta tsokanarta, idan ta ga dama wani lokacin ta biye musu idan kuma ta so sai ta yi musu shiru. Yau ma biye musu ta yi sukai ta yi, hakan ya rage wa Neehal damuwar da take ciki ba kaɗan ba, dan Dad akwai shi da barkwanci. Sai wajen 10:30 Mama ta raka Neehal ta koma part ɗinsu. Dad ya na zira kayan bacci bayan fitowarsa daga wanka ya ce "Doctor ban faɗa miki yanda muka yi da Suwaiba ba a kan batun su Ameen." Mama ta ce "Ya ku ka yi." Dad ya ce "Ai ko maganata ba ta gama saurara ba ta kashe wayarta, ina idar da Sallar Magriba kuwa sai ga kiran Yaya na Abuja, na d'aga muka gaisa ya ce mun wai ya ji wata magana a bakin Suwaiba, na ce masa dama ina shirin kiran shi a kan maganar, jibi Insha Allahu zan je har Abujan." Mama ta ce "Allah ya kyauta ya kaɗe fitina." Dad ya ce "Amin." Mama ba ta faɗawa Dad Mommy'n Hameedah ta kira ta ba saboda gudun Fitina, dan tasan halin Dad bai iya ɓacin rai ba, yanzu sai ya kira ta ya ɓata rai. Neehal ta na fitowa daga wanka ta ga a na kiranta a waya, d'agawa ta yi da sauri ganin Yayanta ne. "Hello Yaya!" Neehal ta faɗa bayan ta d'aga. "Sallamar kenan ko?" Shima ya faɗa cikin daddadar muryarshi mai cike da nutsuwa. Neehal ta ce "Sorry duk murnar ka kira ni ce fa Yaya." Ameen ya ce "Ba ki yi bacci ba?" Neehal ta ce "Uhm" "Me ki ka tsaya yi?" "Ina part d'in Dad muna hira, yanzu na dawo zan kwanta." Ameen ya ce, "Ya yi kyau." Cikin shagwab'a Neehal ta ce "Yaya ina Aunty Hafsat?" Ya ce "Wacece haka?" Neehal ta ce "Aunty Hafsat d'inka fa." Cikin basarwarshi ya ce "Oh tananan k'lu." Neehal ta ce "My regard please." Ya ce "Insha Allah, Bye." Neehal ta ce "Gud night." Daga haka suka yi sallama ya kashe wayar. Neehal ta shirya cikin kayan baccinta masu taushi white color sannan ta rage light d'in ɗakin ta kwanta, hotunan Anwar ta lalubo a wayarta ta shiga kalla, saboda gajiyar dake addabar jikinta ba ta san sanda bacci ya yi awon gaba da ita ba. Washegari ya kama Talata Neehal ba ta da aiki ranar, bayan sallar la'asar ta fito cikin shirinta na fita. Ɗakin Mama ta je domin yi mata sallama. Mama ta ce "Har kin shirya kuma Haneefan ba ta zo ba." Neehal ta ce "Yaya Faruq ya na gari fa, shi yasa yanzu ganin ta sai an cike Form." Mama ta ce "Shi yasa 2 days na ji ta shiru, yanzu ke kaɗai za ki tafi.?" Neehal ta ce "A'a zan biya na ɗauke ta mu wuce." Mama ta ce "Shikenan amma kar ku yi dare fa, kin ga ke za ki yi driving, ban san ki na hawa manyan titi da daddare." Neehal ta ce "Insha Allah Mama ba za mu jima ba." Mama ta ce "Allah ya kiyaye, kar ki manta da addu'a dai idan za ki fita da kuma hawa Mota." Neehal ta ce "Ba zan manta ba Mama." Mama ta ce "Yawwa, sai kun dawo, ki ɗauki saƙon fa, a gaishe su." Neehal ta amsa da "Toh" tare da ficewa daga d'akin. Sun je gidansu Anwar lafiya, tarb'a sosai Ammi ta musu kamar yadda ta saba. Su na zaune a falo bayan sun gama gaisawa da Ammi Najwa k'anwar Anwar ta shigo falon hannunta ɗauke da tire, ta dire a gaban su Neehal ta na faɗin "Aunty Neehal ku sha ruwa." Neehal ta ce "Toh mun gode." Hira suka shiga yi da su Najma da Ammi, can Haneefah ta dubi Ammi ta ce "Ni ko Ammi ya batun mutanen da suka kashe Anwar, an gano su kuwa.?" Ammi ta ce "Har yau dai shiru babu labari ba'a gano ko suwaye ba." Haneefah ta ce "Allah ya bayyana su cikin gaggawa." Suka amsa Amin gabad'aya. Kafin Magriba suka musu sallama suka tafi. *After 2 weeks* Su Dad sun kai kuɗin Auren Ameen gidansu Hafsat, inda a ka tsaida ranar biki wata huɗu masu zuwa. Maganganu sun yi ta yawo a cikin Family'n su Dad sosai, wasu na faɗin Ameen ya yaudari Hameedah, wasu kuma na faɗin Ameen kuɗin mahaifin Hafsat ya bi zai aure ta, wasu kuma suna faɗin ai gwara ma da ba Hameedah zai aura ba, dan sam ba su dace ba. Mommy'n Hameedah kuwa kamar za ta yi hauka, duk da an kai kuɗin amma ƙara kwantarwa da Hameedah hankali take da faɗin indai ta na raye Ameen ba shi da mata sai ita. Su Neehal da Haneefah da sauran cousins d'in Neehal murna suke sosai da baikon Yayansu. Next week su Neehal za su yi resuming school, ta na cikin d'akinta ta na guge hijabs ɗinta Mama ta shigo d'akin. "Neehal yau fa Muna da baƙi a gidan nan." Neehal ta ce "Suwa kenan Mama?" Mama ta ce "Ameen ya ce Hafsat za ta zo ta gaishe ni, ki bar gugar nan ki taso mu ki musu ɗan abun taɓawa." Neehal cikin murna ta ce "Yanzu kuwa Mama, ashe yau mu na da manyan baƙi." Mama ta ce "Ki dai yi sauri kar time ya k'ure." Sosai Neehal ta zage jikinta ta shiryawa su Hafsat kayan ciye_ciye kala_kala ita da su Dije da suka taya ta. Bayan sun gama aikin ta na nunawa Mama abubuwan da suka yi Mama ta ce. "Um lallai Neehal, da ni na saki wannan aikin na san har kuka sai kin mun, amma da yake budurwa Ameen ce za ta zo ko nuna alamun gajiya ba ki yi ba." Neehal ta yi murmushi kawai. Mama ta ce "Ki je ki yi wanka kafin su ƙaraso, su Dije za su jera musu abincin a dinning." Neehal ta ce "Toh." Hafsat 'Ya mace ɗaya tilo a gurin mahaifinta wanda ya kasance hamshaqin mai kuɗi, Hafsat ta so Ameen kamar ba gobe, amma Ameen ya nuna sam ba ya ra'ayinta. A wancan lokacin haka za ta yi ta zarya gidan Mama tun suna Abuja ta na gaishe ta, daga baya ne da ta ga Ameen ɗin dai ba ya k'aunar ta sai ta hak'ura ta k'yale shi amma ba don ta dena k'aunar shi ba. Cikin wata rantsatstsiyar Mota suka ƙaraso gidan, driver'nta a gaba ya na driving ɗinsu sai ita da k'awarta mai suna Fadeela a bayan Motar. Bayan ya yi parking Motar ya fito da sauri ya buɗe mata mota, cikin izzarta ta fito ta na kallon harabar gurin. Duk da kasancewar mahaifinta ya fi Dad kuɗi amma babu abun da gidansu zai nunawa gidansu Ameen a kyau da tsaruwa, sai dai ya fishi girma. Cikin takunta ɗai_ɗai ta fara tafiya k'awarta na bin bayanta. D'aya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya musu jagora zuwa part ɗin Mama. Hafsat sosai take farin ciki da zuwanta gidansu Ameen ɗin, domin wannan zuwan ta zo ne a matsayin suruka ba kamar baya ba da take zuwa dan neman samun guri. Fadeelah ta dube ta tace "Hafsy na lura yau wani farin ciki ki ke na musamman kamar yau ne ranar auran naku." Hafsat ta faɗaɗa fara'ar fuskarta ta ce "Hmmm Fadeelah kenan, wannan zuwan fa da na yi gidansu Ameen a matsayin suruka na zo, saɓanin da da nake zuwa da k'ok'on barata." Fadeelah ta ce "Gaskiya ki na son Ameen da yawa."Hafsat ta ce "Faɗar irin son da na kewa Ameen ms ɓata baki ne saboda tarin yawansa a cikin zuciyata." Fadeelah ta ce "Amma me yasa be bari sai ya dawo daga Lagos ki zo yana nan ba?" Hafsat ta ce "Ni na matsu sai na zo na gaida Mum ɗinsa, shi ma da yaso na bari sai ya dawo na ce ni dai sai na zo......." Buɗe k'ofar da Zulai ta yi ya katse mata maganar da take. Zulai ta ce "Sannunku da zuwa, ku shigo." Fadeelah ce kawai ta amsa da "Yawwa" amma ita Hafsah ɗan yatsina fuska ta yi ta wuce ciki. Gurin zama Zulai ta nuna musu sannan ta haura sama domin ta sanarwa da Mama zuwansu. Hafsat ta dinga satar kallon falon dan ba ƙaramin kyau da burge ta ya yi ba, ga wani sassanyan k'amshi da yake tashi a cikin sa. Neehal Mama ta turo ta hawo da su sama. Neehal da murnarta ta taho dan tarar Aunty'n tata. Tun da ta fara sakkowa Hafsat ta ƙura mata ido cikin fad'uwar gaba, domin ta gane ita ce Neehal ɗin da kullum sai Ameen ya yi zancen ta, dama ta santa a ASTV amma sai ta ga kamar a TV'n ma rage mata kyau a ke a fili ta fi kyau. Haɗe rai ta yi sosai tare da ɗauke kanta daga kallon Neehal ganin ta ƙaraso cikin falon. Da fara'a sosai Neehal ta ce "You are highly Welcome Dear, sai dai ban san Aunty'n tawa ba da nake ta ɗokin zuwan ta, wacece acikin ku?"." Fadeelah ta yi murmushi dan ita kam yanda Neehal ta musu ta burgeta, nuna Hafsat ta yi ta ce "Gata nan, tunda kin kasa hak'uri na gabatar miki da ita." Neehal ta yi murmushi ta na kallon Hafsat ta ce "Masha Allah, gaskiya Yayanah ya iya zaɓe." Ta ƙarashe zancen tare da ƙoƙarin rungume Hafsat ba tare da ta damu da ɗauke kan da ta mata ba. Wani kallon wulak'anci Hafsat ta jefa wa Neehal ta na yatsina fuska kamar ta ga kashi..............✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:34] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL ⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ 1️⃣5️⃣ Ina ma'abota karatun littattafan HAUSA masu ilimantarwa ,nishaɗantarwa,wa'azantarwa gami da sa canjin rrayuwa🗣️🗣️🗣️. AƘIDATA! AƘIDATA!! AƘIDATA!!!. Idan baki karanta ba inason nabaki shawarar ki nemi naki . AƘIDATA! Labarin wata haɗaɗɗiyar hamshaƙiya ƴar hamshaƙin mai kuɗi ce😍gata da izzah, taƙama,gadara,iko,ilimi,wayo da sauransu🥳Amma duk da wannan halaye nata tana da wasu wanda taɗaukesu AƘIDARTA, Akwai takun saƙa tsakaninta da matar babanta da kuma agololin da tazo dasu🥺 Ana bibiyar rayuwarta ta ko'ina hakan yasa rayuwarta taƙare aƙasar waje🥳 Bata da abokai da suka wuce dabbobi zomaye,maguna,tattabaru,dasauransu🥳sune abokan dariyarta da kukanta kuma suke ɗebe mata kewa🥳🥳🥳🥳 Bata tausasa lafazi ga kowa ciki kuwa hadda ma'aifinta ciki 🥳🥳🥳 🥳🥳🥳🥳Cikin rashin yaddarta tasaki jiki da direbanta wanda shine masomin ƙaddararsu 😳😳bata yafewa wanda yayi mata ƙarya koyaci amanarta🥳🥳shin mezai faru idan tasan direbanta ma'aikacin sirri ne❔❔❔❔❔ Kutsen ƙaddara ya kutso rayuwarta ba tare da ta shirya ba, rayuwarta takoma wani gari dako ruwan famfo babu, sedai kududdufi wanda ake wanka da wanki aciki shine ruwan amfanin garin.... 😳alhalin ita idanba ruwan jarka ba batasaba shan wani ruwaba🥳🥳🥳🥳🥳 Sabulun wanka kansa babu semai ƙarni alhalin tasaba wanka da shower jell🥳🥳🥳🥳🥳 Akwai tarin sarƙaƙiya da ƙulle ƙulle a cikin wannan labari me ban al'ajabi ƘAƘA ƘARA ƘAƘA🥺🥺🥺 WIDAD🥳WIDAD🥳WIDAD🥳 Duk me son jin cikakken kabarin Widad da mahaifinta NASIR DAULA yanemi 2&3 akan farashi ƙalilan🥳🥳🥳🥳🥳daman part 1🥳🥳kyauta ne meso taimin magana nabata🥰🥰💞💞 LALLAI 🥳AYSHERCOOL ✍🏻ta dabance basirarta bazaka ganeta ba seka kranta AƘIDATA domin ta farantawa mu masoyanta fie da yadda tay AWATA KISSAR........! SAI MATA😊😊. 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻AƘIDATA TAYYI DABAN DATA KOWA🥳🥳 Normal gro duka littafi biyun #300 Idan kuma laya zaki siya #200 Vip #500. Idan kuma se angama zaki siyi complete documment #700. Account Number Aisha Adam 0009450228 Ja'iz Bank Se aturo evidence of payment through 07063065680. Share please🙏🏻🙏🏻🙏🏻. .......... Neehal ce zaune a office d'inta ta na operating system, sai sauke numfashi take akai_akai alamun wani abu na damunta. Haneefah dake zaune a kujerar da take fuskantar ta ta na latsa waya, lokaci zuwa lokaci ta na d'agowa ta na kallon ta. Ajiye wayar ta yi a kan table ɗin gabanta cikin kulawa ta ce "Wai Neehal meke damun ki ne.?" Ba tare da Neehal ta d'ago ba ta ce "Babu komai, me ki ka gani.?" Haneefah ta ce "Yanayinki ya nuna kamar wani na damun ki." Neehal ta ce "Babu gaskiya, idan ma da akwai ba zai wuce Rashin jin Ya Sadik ba ne da banyi ba yau." Haneefah ta ce "Kamarya rashin Ya Sadik.?" Neehal ta sauke numfashi ta ce "Tun jiya da yamma da muka yi waya har yanzu bai ƙara kira na ba, gashi last seen ɗinsa a WhatsApp tun 6:44 pm na jiya" Haneefah ta yi wani munafukin murmushi ganin haƙansu ya kusa cimma ruwa ita da Sadik, domin ita ta bashi shawarar ka da ya nunawa Neehal ya na sonta a yanzu, ya bari sai ta shak'u da shi sosai sai ya sanar mata. Ita kuwa Neehal baiwar Allah, maganarta take bil hak'k'i ba tare da tunanin komai ba. "To ki kira shi mana ki ji ko lafiya." Cewar Haneefah cikin nazartar ta. Neehal ta ce "Kuma fa hakane, bari mu koma gida zan kira shi." Haneefah ta ce "To, Allah ya sa lafiya dai." Neehal ta ce "Amin." Bayan sun koma gida da yamma wanka kawai Neehal ta yi ta kira layukan Sadik amma duka ba sa tafiya. Zama ta yi a bakin gado tare da dafe kanta cikin damuwa, can kuma ta ja ɗan ƙaramin tsaki ganin damurwar na neman hanata sukuni. A fili ta ce "To mene ma na damuwar haka akan shi.?" "Sadik ya cancanci ki damu dashi fiye da haka ma, duba da tarin kyautatawarsa a gare ki, gami da kulawar da yake nuna miki." Wata zuciyar ta ba ta amsa da faɗin haka. Mik'ewa tsaye ta yi zumbur kamar an tsikareta ta na sauke ajiyar zuciya, saboda wani tunani da ya ɗarsu a ranta. Wata doguwar rigar abaya purple color ta ɗakko ta zira a jikinta, turarukanta ta mutstsika ta yane kanta da ɗankwalin abayar, wayoyinta kawai ta kwasa a hannunta ta fice daga d'akin. A falon ƙasa ta tarar da Mama. "Ke ina zaki haka ki ke sauri kamar za ki tashi sama.?" Mama dake kallon Neehal tunda ta fara sakkowa daga kan steps ta fad'i haka." Neehal ta tattaro nutsuwarta ta na ɗan sosa kanta ta ce "Gidan Aunty za ni, kuma sauri nake saboda in yi in dawo da wuri." Cikin mamaki Mama ta ce "Gidan Aisha kuma da wannan sakaliyar yammar? Daga dawowarki daga aiki ko abinci ba ki ci ba.?" Neehal ta yi shiru tare da sunkuyar da kanta ƙasa. Mama ta ce "Me ma za ki yi a gidan A'ishan?" Neehal ta ce "Gaishe ta zan yi, na dad'e ban je ba." Mama ta mata kallon tsaf ta ce "Ki bari gobe kya je." Neehal ta ce "Gobe fa sai six zan dawo daga school." Mama ta ce "To kya je wani time ɗin." Neehal ta marairaice ta ce "Please Mama." Mama ta ce "Ba fa za ki fita ba Neehal a yamman nan, idan Dad ɗinki ya dawo me zan ce masa.?" Neehal ta turo baki gaba ta juya za ta koma sama. Mama ta katse ta ta hanyar faɗin. "Ki shiga kitchen ki zubo abinci ki ci." Neehal ta yi hanyar kitchen ba tare da ta ce komai ba, abincin ta ɗebo kaɗan ta koma sama. Ta na shiga ɗakinta ta ajiye shi a kan bedside ta hau gado ta kwanta, sosai ta ji takaicin hana ta zuwa da Mama ta yi harda 'yar k'wallarta, kiran Sallar Magriba ne ya tada ta. Bayan ta idar da Sallah ta ɗakko abincin ta fara ci, sai kuma yanzu take jin haushin kanta na damuwar da ta yi akan kawai yau rana ɗaya dan ba su yi waya da Sadik ba, tambayar kanta ma ta yi inda ta je unguwar su Aunty A'ishan gidansu Sadik ɗin za ta je neman sa ko kuma yaya? Sakin ranta ta yi ta cigaba da sabgarta duk da kewar Sadik ɗin na nuk'urk'usar ranta. Neehal na na kitchen ta na yiwa Dad pepper chicken Mama dake falon a zaune ta na kallon labarai ta shigo kitchen ɗin ta na faɗin. "Neehal kin kusa gamawa.?" Neehal ta ce "Ehh na kusa." Mama ta ce "Kawo in ƙarasa ki je falo Sadik ya zo." Neehal ta juyo da sauri ta na duban Mama cikin fad'uwar gaban da ba ta san dalilin ta ba." Mama ta ƙaraso cikin kitchen, Neehal ta na Ƙoƙarin fita Mama ta ce "Ki zuba masa abinci mana." Neehal ta ce "Toh, hijab zan ɗauko." Jiki a sanyaye ta ƙaraso ta zauna a kujerar kusa da shi bayan ta ajiye masa abinci a gabansa. Kanta a ƙasa ta ce "Ina yini." Sadik da yake ta binta da kallo ya ce "Lafiya k'alau ya aiki." Neehal ta ce "Alhamdulillah." Sadik ya gyara zama cikin kulawa ya ce "Ba ki da lafiya ne na ganki wani iri.?" Neehal ta ce "Lafiya ta k'alau." Sadik ya ce "Uhm, ko ki tambaye ni yau ina shiga.?" Neehal ta ce "Ai zan tambaye ka, dafatan dai Lafiya.?" Sadik ya ce "Lafiya lau, sha'anin aiki ne ya kawo haka." Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba. Sadik ya yi murmushi cikin tsokana ya ce "Fushin me ki ke yi to.?" A shagwab'e ta ce "Ni ba fushi nake ba." "Uhm rigimar autanci ce ta motsa kenan." Neehal ta yi murmushi saboda yanda yay maganar ya bata dariya. Hirar su suka cigaba da yi cikin nishad'i, wani irin daɗi take ji saboda ganin Sadik, cikin lokaci kaɗan ta ware suka shiga hirarsu. Sadiƙ mutum ne da ya san takan bi da duk wanda yake mu'amala da shi, mutum ne mai tsananin kirki da hak'uri, gashi da sanyi kamar ba lawyer ba, sai dai akwai kaifin tunani da saurin fahimtar abu, ga uwa uba nutsuwa da addini. Abun da yake ƙara burge Neehal da shi nasiha da faɗin gaskiya a kodayaushe, ko yaya kuka ɗan zauna dashi sai ya tunatar da kai wani abu na addini da mu'amalar rayuwa. Mama ma yaron ya na burgeta, ta yaba da hankalinsa da nutsuwarsa, shi yasa ba ta hana mu'amalar su da Neehal. Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah, yau gashi bikin Ameen ya matso saura satittika, shirye-shiryen biki ake ba kama ƙafar yaro, ɓangaren gidan amarya da gidan Ango, ba yama kamar gidan su Amarya, dan su yanda suke tsara bikin ma sai anfi sati ana shagali, ango ne yake neman ba su cikas dan shi ya ce bashi da lokacin ɓatawa a yawon zuwa events, amarya dai ta na ta lallab'ashi a kan ya amince amma ya ƙi. Su Mama shirin su suke sosai ita da 'yan'uwanta, Ameen ya saki kuɗi an haɗa lefe na gani na faɗa, Aunty Sadiya da Aunty A'isha ne suka haɗo masa. Ƴan'uwan Dad ma masu murna da auren ba a barsu a baya ba gurin nasu shirin. Yau Saturday Misalin ƙarfe goma na safe Neehal ta na kwance a kan gadonta ta na bacci ta ji ana tashin ta, a hankali ta buɗe idanunta dake cike da barci ta na karanta addu'ar tashi daga bacci a zuciyarta. Ameerah 'yar gidan Uncle Mahmud ta gani tsaye a kanta, yunk'urawa ta yi ta tashi zaune ta na mutsitstsika ido, Ameerah ta na murmushi ta zauna a bakin gadon ta na faɗin. "Bacci har wannan ranar Yaya Neehal." Cikin murya mai cike da bacci Neehal ta ce "Kin san jiya muka gama exam, baccin da ban yi ba ne kwana 2 saboda karatu nake ramawa, yaushe ku ka zo?." Ameerah ta ce "Yanzun nan, Mama ta ce in shigo in tashe ki." Neehal ta ce "Welcome, ke da Ammi ku ka zo.?" Ameerah ta ce "Ehh, suna falo suna kallon lefe." Neehal ta sauka daga kan gadon ta na faɗin, "Kin san nima har yau ban samu nutsuwar ganin lefen nan ba, saboda exams d'in da muke, gashi har za a kai gobe." Ameerah ta ce "Ai dama exam akwai caza wa mutum kai, Allah dai ya ba da sa'a." Neehal ta amsa da "Amin" tare da shigewa toilet. Bayan ta shirya suka sauko ƙasa inda suka tarar da Mama,Hajiya,Ammi,Aunty Sadiya da Aunty A'isha sun baje kayan lefen a falon suna kalla, Ammin su Ameerah sai yaba kayan take ta na faɗin "Masha Allah kaya sun yi sosai". Neehal ta ƙarasa ta rungume Hajiya cikin murnar ganinta ta ce "Hajiyata Oyoyo na yi miseed ɗinki." Hajiya ta ce "Kamar da gaske, ina ja'irar k'awarki.?" Neehal ta ce "Daɗina dake ba'a miki gwaninta sai ki gwale mutum." Hajiya ta ce "Na ji ɗin." Neehal ta sake ta ta ƙarasa kusa da Amminsu Ameerah ta rungume ta tare da gaishe ta, Ammi ta amsa mata cikin fara'a da kulawa. Gaishe da su Mama da Aunties ɗinta ta yi. Mama ta dubeta ta ce "Ki je ki haɗa break fast ki kaiwa Yayanki, kema ki haɗa ki ci." Neehal ta ce "Mama bari na ga kayan nan sai na kai masa." Hajiya ta tari numfashinta da faɗin "Kayan da sun kusa sati a gidan nan, mak'ota da ƴan'uwa duk sun zo sun gani amma ke ki na kwana a gidan baki gani ba." Mama ta bata amsa da faɗin "Ba ta wani gani sosai ba saboda ta na exam, kin san Neehal idan ta na exam ba ta da nutsuwa." Aunty Sadiya ta ce "Yanzu dai an gama, sai a bita da addu'a Allah ya ba da sa'a." Suka amsa gabad'aya da "Amin." Neehal bayan ta gama ganin kayan ta mik'e ta shiga kitchen ta haɗawa Ameen break fast kamar yadda Mama ta bata umarni, tunda Ameen ɗin a gida ya kwana yau. Ta ɗauki kayan ta na duban Ameerah da ta taya ta haɗa kayan ta ce "Mu je ki raka ni na kaiwa Yayan." Ameerah ta riƙe hab'a tare fito da idanunta waje ta ce "Wa? ki je ke kaɗai dai, kin san halin kayanki fa." Neehal ta ce "Kar ki je ɗin, kuma sai na faɗa masa in ce kince masa masifaffe." Ameerah ta ce "Allah ya na gani dai." Ammi ta bi Neehal da kallo bayan sun fito harta fice daga falon, Ammi ta sauke Numfashi ta ce "Neehal har yanzu ba ta maida jikinta ba tun ramar da tayi lokacin rasuwar Anwar." Mama ta ce "To bata son cin abinci, ba dole tai ta rama ba." Ammi ta ce "Duk da rashin cin abincin ma, amma mutuwar na damunta a rai har yanzu." "Ai dole ne ta damu Aunty Bilki, Samari har biyu sai an kusa bikinku duk su mutu." Cewar Aunty Sadiya cikin jimantawa. Mama ta ce "Wlh nima abun na damuna ina tsoron kar ace sanadin Neehal ake kisan nan." Cikin tarar numfashi Hajiya ta ce "Ashsha, faɗima ba na hanaki wannan zancen ba, yanzu idan wani ya ji ba sai ya samu abun ɗorarwa ba, tunda kema uwarta ki na faɗa, kun san mutane ba sa rasa abun fad'i, yanzu sai a gogawa yarinya baƙin fenti aita jifanta da sharruka kala_kala." Mama ta sauke numfashi ta ce "Shikenan Hajiya Insha Allahu na dena faɗar haka, shima Dad ranar da na faɗa masa haka sai ya hauni da faɗa wai a kan me zance haka, Neehal ɗin me taiwa wani da zai dinga bibiyarta ya na kashe mata samarinta?" Aunty A'isha da ba ta ce komai ba tunda suka fara maganar sai yanzu ta ce. "To mu dai muna ga Allah, kuma shi zai warware mana gaskiyar al'amari, duk ma mai nufin wani da sharri Allah ya mayar masa kansa." Suka amsa gabad'aya da "Amin." Ameen ya na cikin bedroom ɗinsa ya na shiryawa ya ji a na knocking k'ofar falo, sai da ya ƙarasa shirinsa a tsanake sannan ya fito dan zuwa ya buɗe, zuwa lokacin Neehal ta gaji da tsaiwa ga kaya a hannunta. Ya buɗe k'ofar tare da yin baya dan bata damar shigowa, Neehal ta yi sallama sannan ta shiga. "Yaya a ina zan ajiye maka?" Ta tambaye shi bayan ya amsa mata sallamar. Kan carpet d'in dake tsakiyar falon ya nuna mata, ajiyewa ta yi ta na sauke numfashi. Juyowa ta yi Ameen dake kallonta yay saurin ɗauke kansa tare da zama a kan kujera 2 seater. Neehal ta zauna a kusa da shi ta na kallonsa a ranta ta na gulmarsa ganin kamar ƙara kyau yake ya yi wani fresh abinsa, Neehal a ranta ta ce "Tun kafin a yi auren, wannan ina ga anyi auren." "Ina kwana Yaya" ta faɗa cikin nutsuwarta. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Lafiya, Ya exams.?" Neehal ta ce "Mun gama jiya." Ameen ya jinjina kai ya na dubanta ya ce "Allah ya ba da sa'a." Neehal ta ce "Ameen." Daga haka suka yi shiru, Neehal ta na son ta tambaye shi abu amma ta kasa saboda sanin halin halinsa, wannan ƴar sakewar da ta samu ya mata yanzu sai ta nemeta ta rasa. Wayarta dake cikin aljihun rigarta ce ta fara vibrate, hannu ta zira ta ɗauko a tunanin Mama ta ce amma sai ta ga Sadik ne. D'agawa ta yi ta na murmushi ta kara a kunnenta. "Wa'alaikassalam Yaya Sadik ɗina." Ta fad'i haka cikin murmushi mai sauti alamun ta na cikin nishad'in kiran da a ka mata. Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Lafiya k'alau and you." Ameen dake kallonta ya tab'e ɗan ƙaramin bakinsa tare da ɗauke kansa daga kallon nata, da sauri kuma ya juyo amma cikin basarwarshi yanda ba za a gane saurin nashi ba jin ta na magana cikin shagwab'a "Dan Allah da gaske kake Ya Sadik? Kar fa kasa na fito kuma ba ka zo ba." Sosai Ameen yake kallonta, Ƴar dariya ta yi sannan ta mik'e ta na faɗin "Gani nan to." Kallon Ameen ta yi ta ce "Yaya ina zuwa, bari in je in dawo." Ba ta jira amsarshi ba ta fara tafiya. Bin ta da kallo kawai ya yi cikin ransa ya na ƙissima abubuwa, har ta kai bakin k'ofa ya tsayar da ita ta hanyar faɗin...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:34] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *1️⃣4️⃣* ........... Neehal duk da ta ga irin kallon da Hafsat ta mata amma ta danne zuciyarta ta rungume ta, sai dai jikinta ya yi sanyi ba kaɗan ba. Kamar yadda ta rungume Hafsat haka ta rungume Fadeelah. Fadeelah da ba ta ji daɗin abun da Hafsat ta yi ba ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce "Ai na yi fushi, tunda Aunty'nki kawai ki ka sani ita ki ka fara tarb'a." Neehal ta yi murmushin yaƙe ta ce "Sorry ai kema Auntyna ce." Fadeelah ta yi murmushi dan sosai ta ji ta na son Neehal, yarinyar ta burgeta daga gani ba ta da d'abi'ar wulak'anta mutane duk da kasancewar ta celebrity. Neehal ta ce "Mama ta na sama mu ƙarasa." Fadeelah ce kawai ta amsa mata suka mik'e suka bi bayanta, Hafsat sai hararar bayan Neehal take. Neehal ta shiga d'akin Mama ta sanar mata da isowarsu sannan ta fito ta wuce ɗakinta. Kafin Mama ta fito Fadeelah ta ce wa Hafsat "Haba Hafsah, gaskiya ban ji daɗin abun da ki ka yi wa yarinyar nan ba ko kaɗan wlh." Hafsat ta mata wani kallo ta ce "Yarinyar ba ta mun ba ne shi ya sa." Fadeelah ta ce "Hmmmmm, me yarinyar nan ta yi da za ki ce ba ta miki ba? Yarinya ta taho da murnarta da ɗokin ganin ki ka amma ki mata wannan wulak'ancin, gaskiya ban ji dad'i ba." Hafsat ta tab'e baki ba ta ce komai ba, domin ita kaɗai ta san baƙin cikin dake cin ranta na ganin Neehal, ashe duk kyawunta da mutane suke faɗa na ganin da suke mata a TV a fili tafi haka, yarinya ga dirin jiki kamar ita ta yi kanta, tafiyar ta ma kaɗai abun kallo ce ga zazzak'ar murya.... Fitowar Mama ya katse mata tunanin da take. Cikin girmamawa suka ɗan zamo daga kan kujerar da suke suna amsa sallamar da Mama ta musu. Mama ta zauna ta na faɗin "Sannun ku da zuwa." Suka amsa da yawwa tare da gaisheta, Mama ta amsa musu cikin fara'a ta ƙara da faɗin. Ya mutanen gida.?" "Suna lafiya, suna gaishe ku." Cewar Fadeelah. Mama ta ce "Masha Allah, muna amsawa." Hafsat dai kanta na ƙasa ta na satar kallon Mama, domin Maman kamar ba ta tsufa, a 'yan shekarun da ta yi ba ta ganta ba sai ta ga ta ƙara kyau da gayu, ba za ka taɓa cewa ta haifi Ameen ba. Mama ta mik'e ta na faɗin "Bismillah ku ƙarasa dinning ku ci abinci, bari na kira Neehal ta yi sarving ɗinku." Neehal ta na shiga ɗakinta ta zauna a bakin gado hannunta dafe da kanta, mamaki take sosai a kan abun da Hafsat ta mata, dan ta ji haushi ba kaɗan ba kawai ta danne zuciyarta ne, domin ita mutum ce wadda bata son wulak'anci ko kaɗan kuma ba ta son a yi mata, hakan ya sa itama ba ta yi. Kawar da tunanin Hafsah ta yi daga ranta ta na ƙoƙarin tashi kira ya shigo wayarta, ta daga tare da karawa a kunnenta. Cikin daddad'ar muryarshi ya mata sallama, Neehal ta amsa tare da faɗin "Ina yini Yaya." Ameen ya ce "Lafiya k'alau, su Hafsat sun zo kuwa.?" Neehal ta ce "Ehh." Ya ce "Ok" tare da kashe wayar, ya bar Neehal da mitar faɗin ya kira Hafsan mana ya tambaye ta. Su Hafsat sun ɗan jima a gidan Mama kafin su tafi, sosai Neehal suka sha hirarsu ita da Fadeelah, dan da ta fito ma ko ƙara kallon inda Hafsat take ba ta yi ba, hakan kuwa ya burge Fadeelah dan ko ba komai Neehal ta nunawa Hafsah tafi ƙarfin raini. Da za su tafi Mama ta basu turaruka da kayan kwalliya. Suna Mota Hafsat ta dinga yi wa Fadeelah masifa a kan wai me yasa ta sakarwa Neehal fuska su ka yi ta hira kamar wata sa'arta salon ta jawo ta rainasu. Fadeelah kallon Hafsat kawai ta tsaya ta na yi cike da mamakinta, kawai daga ganin mutum sai ka ɗauki k'iyayya ka ɗora masa ba tare da wani dalili ba.?" Bayan Magriba Mama ta na kitchen Dije ta zo ta sanar mata ta yi bak'o, Mama ta ce ta je ta shigo da shi gata nan zuwa. Ta na fitowa falon ta ga ashe Sadik ne. Ta na dubansa ta ce "Sadik ashe kai ne?" Ya ɗan sosa kai kansa na ƙasa ya ce "Ni ne Mama." Mama ta ce "Shine kuma ka tsaya a waje ba za ka shigo ba, sai ka ce wani bak'o.? Sadik ya yi murmushi kawai tare da gaishe da Mama, Mama ta amsa cikin fara'a sannan ta mik'e ta hau sama dan ta kira masa Neehal. Neehal ta na duba abu a system Mama ta shigo d'akin ta ce "Ba ki gama abun da ki ke ba har yanzu?" Neehal ta ce "Ehh, amma na kusa." Mama ta ce "To ki sauko ƙasa kin yi bak'o." Neehal ta d'ago da sauri ta na duban Mama da mamaki ta ce "Mama bak'o kuma?" Mama ta ce "Eh, ya na ƙasa ya na jiran ki." Ba ta jira amsar Neehal ɗin ba ta juya ta fice. Neehal ta mik'e ta na turo baki ta ɗauki Hijabinta ta zira ta sauka ƙasan. Babu kowa sai shi kaɗai ya na latsa wayarsa, Neehal ta ƙaraso cikin falon ta na kallonsa, a hankali ya d'ago kansa suka haɗa ido, gaban Neehal ya yanke ya fadi. Ƙasa ta yi da kanta da sauri bugun zuciyarta na sauyawa, dama tun da ta shigo falon ta ji kamar tasan baƙon k'amshin da ta ji a falon, ashe shine. Zama ta yi a kujerar dake fuskantar sa kanta na ƙasa ta ce "Ina yini." Ba tare da ya ɗauke idonsa daga kanta ba ya ce "Lafiyar k'alau, ya aiki." Neehal ta ce "Alhamdulillah." Shiru suka yi na tsawon mintuna biyu, Sadiƙ ya katse shirun nasu da faɗin "Kun kusa komawa school ko?" Neehal ta ce "Ehh." Ya ce "Yaushe." Cikin k'osawa ta ce "This coming Monday." Sadiƙ ya jinjina kai ya ce "Allah ya taimaka." Suka ƙara yin shiru na wasu mintuna, Sadik ya na lura da Neehal gabad'aya a takure take sai turo baki gaba take. Neehal ganin bashi da niyyar tafiya ta ɗan d'ago kanta ta ce "Gashi kuma ka zo k'anwar taka ba ta nan." Sadik ya yi murmushi ya ce "Ok, you mean Ke ba k'anwata ba ce.?" Neehal ta yi shiru tare da ƙara mai da kanta ƙasa, Sadik ya ƙara yin murmushi ya ce "Shikenan bari in tashi in tafi." Neehal cikin shagwab'arta da ta zame jiki ta ce "Am sorry ba haka nake nufi ba." Ya ce "To ya.?" Ta yi shiru ta na wasa da yatsun hannunta dan ba ta da abun cewa. Mama ce ta sakko ƙasa za ta ɗauki abu, da mamaki a kan fuskarta ta ce "Neehal ya ba a kawo masa ruwa da abinci ba.?" Kafin Neehal ta yi magana ya riga ta da faɗin "Ba komai Mama a k'oshe nake ma." Mama ta ce "No, ba za a yi haka ba, Neehal tashi ki kawo masa abinci." Neehal ta mik'e a hankali ta nufi kitchen, Mama kuma ta ɗauki abun da za ta ɗauka a falon ta koma sama. Neehal ta fito da k'aton tire a hannunta ta ajiye a gaban Sadik, sannan ta koma ta ɗakko drinks ta kawo masa. Shi dai kawai bin ta yake da ido. Neehal ta koma ta zauna, ganin bashi da niyyar taɓa abincin ta ce "Ka ci mana." Ya ce "Na k'oshi." Neehal ta marairaice ta ce "Dan Allah Ya Sadik ka ci, idan ba ka ci ba Mama faɗa za ta mun." Ya yi murmushi a karo da yawa ya ce "Shikenan zan ci." Neehal ta yi murmushin itama. Ruwa kawai ya tsayaya ya sha, Neehal tayi_tayi ya ci abincin amma ya ƙi, dole ta hak'ura ta k'yale shi. Jin an fara kiran Sallah ya mik'e ya na faɗin "Ni zan wuce." Neehal ta ce "Bari na kira Mama ku yi sallama." Ya ce "A'a ki ce mata na wuce kawai." Neehal ta ce "Sai da safe ka gaida gida." Daga haka ta wuce sama. Ɗakin Mama ta leƙa ta sanar mata ya tafi. Mama ta ce "Ok, zan kira shi, kema ya kamata later ki kira shi ki ji ya ya koma gida." Neehal ta ce "To" kawai, amma ita Mama ba ta ma san ko Number'nsa ba ta da shi ba. Ɗakinta ta koma domin yin Sallah. Bayan ta idar da Sallar, ta ɗakko wayarta da niyyar kiran Haneefah ta faɗa mata Sadik ya zo sai ta tarar da missed call d'in Ameen har 3, waro manyan idanunta ta yi cikin mamaki dan ta san ze yi wuya ka ga ya kira ka ba ka d'aga ba kuma ya ƙara kiran ka, amma gashi ita ya mata har 3 missed call. Bin bayan kiran ta yi, ringing biyu ya d'aga tare yin da sallama. Neehal ta amsa masa ta ƙara da faɗin "Ina yini Yaya." Ameen bai amsa mata ba, sai cewa ya yi "Ina ki ka shiga.?" Neehal ta ce "Ina ƙasa wayar kuma ta na sama a ɗakina." Me ki ke yi a ƙasan?" "Bak'o na yi fa Yaya, ina...." "Alright Gud." Ya katseta da faɗin haka tare da kashe wayar. Neehal ta bi wayar da kallo bayan ta cire ta daga kunnenta, dama tunda suka fara wayar ta ji kamar ransa a ɓace yake, bakinta ta tab'e ta ajiye wayar ta koma ta cigaba da abun da take yi a laptop d'inta. Ta na cikin aikin a ka ƙara kiran wayarta, ba dan taso ba ta tashi ta ɗauko wayar, baƙuwar number ta gani, kamar ba za ta d'aga ba sai kuma dai ta d'aga. Sallama a ka mata cikin murya mai tattare da nutsuwa, Neehal ta amsa ba tare da ta gane mai magana ba, sai dai kuma ta ji kamar ta san muryar. "Tunda ba ki kira ni kin ji ya na je gida ba, ni na kira ki na ji dafatan na barki lafiya." Neehal ta sauke ajiyar zuciya dan ta gane Sadik ne, a hankali ta ce "Am sorry, tunda muka rabu aiki nake yi ne shi yasa." Sadik ya ce "Ok, amma ko ba haka ba nasan ko Number ta ba ki da shi." Neehal ta yi shiru ba ta ce komai ba. Sadik jin ta yi shiru ya ce "Ki je ki cigaba da abun da ki ke yi, sai da safe." Neehal ta ce "Allah ya kai mu, thank you." Sadiƙ ya ce "Gud night daga haka ya kashe wayar." .Washegari Friday Neehal ta dawo daga gurin aiki da yamma, ta na shiga Falon Mama ta ga Ameen zaune a kan kujera ya na latsa wayarsa, Neehal ta waro manyan idanunta cikin mamakin ganin sa, domin ba ya dawowa Ranar Friday sai dai Saturday or Sunday. Cikin murnar ganinsa ta nufi gurin shi ta na faɗin "Yaya yaushe ka zo.?" Kamar ba da shi take ba, ko d'ago kai ya kalleta ma bai yi ba, balle ya ba ta amsa. Neehal ta turo baki gaba ta wuce sama. Wannan weekend d'in gabad'aya Ameen ya ɗauke wa Neehal wuta, ko gaishe sa ta yi ba ya amsawa. Ita kam Neehal ko a jikinta domin ta saba da wannan halin nasa, idan muskilancin nasa ya motsa. ***************** Neehal sun koma school inda suka ɗora karatunsu a first semester Level 3, Neehal da Haneefah tare suke tafiya a matakin karatu, sai dai ba department d'aya suke ba, Neehal ta na Department of Mass communication, ita kuma Haneefan ta na karantar Law ne. Neehal zuwa yanzu ta fara sabawa da Sadik, domin Sadik cikin 1 Month sai da yasan yanda ya yi ya shiga jikin Neehal sosai, sam bai nuna mata sonta yake ba, suna mu'amalane a matsayin Yaya da K'anwa. Sosai Neehal take jin daɗin tarayya da Sadik, kusan kullum sai ya zo sun sha hira, ya yi ta bata labaran ban dariya da nishad'i, wani lokacin kuma idan an bata assignment a school tare suke yi, wani lokacin kuma ya yi ta tsokanarta ita kuma tai ta ɓata rai ta na turo baki gaba, haka za su rabu ta na fushi da shi, sai bayan ya tafi ya kira ta ya lallab'ata su shirya. A hankali kaso mafi yawa na damuwar rashin Anwar ya fara barin zuciyarta a sanadiyyar shigowar Sadik cikin rayuwarta.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:34] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ 1️⃣6️⃣ INAYI MUKU ALBISHIR 💃💃💃💃DA SABON LITTAFINA NA KUD'I MAI SUNA(sarauniya SADDIK'A) PAID BOOK NE GA MASU SO SUYI MIN MAGANA NAN DA NEX WEEK 16 October, 2021 Ranar Asabar IDAN ALLAH YAKAIMU 😍😍😍😍😍😍 GAMAI BUKATAR KARANTA LITTAFIN SARAUNIYA SADDIKA YAMIN MAGANA TA PC GA NUMBER (07089540330 Asmeety) Sai najiku kadda kubari abaku labari 😍😍😍💕💕💕💕💕 (Hot Sexy 🍌, Love❤️,and💞 Romantic 👄 than Funny 🤣)💞 All in this Book (SARAUNIYA💞 SADDIKA)💞 KADDA KUBARI ABAKU LABARI💞 😍 LOVE YOU FAN'S GOOD LUCK💞 BY ASMEETY💞 ............"Ke!" Neehal ta juyo da sauri jin yanayin da ya yi maganar a zafafe. Ganin yanda ya haɗe fuska tamau ya sa ta shiga nutsuwarta, cikin raunin murya ta ce "Na'am." Ɗauke kansa ya yi kamar ba shi ya kira ta ba, dawowa cikin falon tay ta tsaya a gabansa tare da faɗin "Gani Yaya." Abincin da ta kawo ya nuna mata da hannunsa, cikin rashin fahimtar abun da yake nufi ta ce "Ɗaukewa zan yi na kai dinning?." Wani kallo ya watsa mata, ƙasa tay da kanta da sauri idanunta suka cicciko da k'walla, ta na ƙoƙarin mai da k'wallar ta ji ya ce "Da kike ƙoƙarin fita ki na rawar jiki saboda za ki gurin wani, Ni zan zuba wa kaina abincin.?" Neehal ta ce "Ka yi hak'uri ban san yanzu za ka ci ba." Ta ƙarashe zancen hawaye na zubawa a kan kuncinta, a rayuwar Neehal kwata_kwata ba ta san a mata faɗa ko tsawa, shi kuma Yayan nata ta fuskanci ya na k'aunar hakan. Ta na share hawayen fuskarta ta tsugunna ta haɗa masa tea a ƙaramin cup d'in da ta haɗo da shi, miƙa masa tay ya karb'a tare da faɗin "Thanks." Sauran kayan soye_soyen ta zuba mata a cikin plate ta ajiye masa a gefensa ganin ya sakko ƙasa ya fara shan tea d'in. Harta mik'e ya dawo da ita, ya na kallonta fuskarsa a ɗan sake ya ce "Kukan me ki ke.?" Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba. Hannunsa ya zira a aljihun wandonsa ya ɗakko handkerchief ɗinsa dake tashin daddad'an k'amshinsa ya mik'a mata, ba ta yi musu ba ta karb'a ta share hawayennata. Cikin sanyin murya kamar ba shi ya gama mata magana cikin faɗa yanzu ba, ya ce "Rigimammiya kawai, tashi ki tafi." Neehal ta mik'e zumbur ta na ƙara turo baki gaba, Ameen ya bi ta da kallo har ta fice. Parking space ta nufa kamar yadda Sadik ya ce mata ya na can. Sadik ya hangota ya buɗe Motarsa ya fito ya jingina da ita ya na kallonta, gabad'aya fushin da take a kan abun da Ameen ya mata nemar sa tay ta rasa a dalilin ganin Sadik, murmushi ne kawai yake bayyana a kan fuskarta. "Assalamu alaikum." Neehal ta faɗa lokacin da ta ƙaraso inda Sadik yake, cikin sauke numfashi Sadik ya ce "Wa'alaikissalam." Neehal ta na murmushi ta ce "Ashe da gaske ka zo, Ni fa na ɗauka wasan da ka saba mun ne, ba zuwa kai ba." Sadik dake kallonta ta ce "Shi yasa ki ka shanya ni kenan.?" Neehal ta ce "A'a, Yaya ne ya saka ni abu fa, am sorry." Sadik ya ce "Babu komai, kin san ai yanda amarya ba ta lefi ango ma haka, dan haka tunda aikin Yaya ki ka yi na hak'ura." Neehal ta ɗan murmusa ta ce "Mu shiga ciki mana." Sadik ya ce "Ai tunda ki ka ga na tsaya a nan wucewa zan yi, dan sauri nake, sak'o na biyo in kawo miki." Neehal ta ce "Ba za ka shiga ba kenan.?" Ya ce "Eh, bari na baki na wuce ina sauri ne ana jira na." Bai jira amsar ta ba ya buɗe murfin Motar ya ɗakko abu a cikin wata leda ya mik'o mata. Neehal ta karb'a ba tare da ta gane mene a ciki ba. "Me ne wannan Ya Sadik."? Ta tambaye shi bayan ta karb'a. Ba tare da ya amsa mata tambayar ba ya ce"Ki gaida Mama sai mun yi waya." Ya faɗa ya na shigewa cikin Motar sa, Neehal ta bi shi da kallo kawai cikin mamaki. Reverse ya yi ya d'ago mata hannu, itama hannun ta d'aga masa ta juya ta fara tafiya. Buɗe ledar ta yi kafin ta ƙarasa part d'in Mama, kuɗi ta gani bandir ɗin 1k, zaro ido waje tay cikin mamaki, da sauri kuma ta maida ledar yanda take sannan ta ɗauko wayarta tay dialing number'n Sadik amma bai d'aga ba. Part d'in Mama ta ƙarasa, Mama ba ta falon ƙasa hakan ya sa ta wuce sama, dakin Maman ta nufa direct, bayan ta yi sallama Maman ta amsa mata ta shiga. Mama ta ce "Sai yanzu Neehal daga kai abinci?" Neehal ta ce "Mama Ya Sadik ne ya zo, gurinshi na je." Mama ta ce "To ya shigo mana, sai kuma ku tsaya a waje kamar wani bak'o." Neehal ta ce "Har ya tafi ai, yace sauri yake yi, kinga ma ya bani wannan." Mama ta karb'i ledar ta buɗe, ganin kuɗi ya sa ta d'ago ta na duban Neehal ta ce. "Kuɗin me ne wannan?" Neehal ta ce "Bani kawai ya yi ya wuce bai mun bayani ba." Mama ta ce "Ke kuma ba sai ki tambaye shi ba." Neehal ta ce "Ya na mik'o mun ya shige Motar ya tafi." Mama ta ce "To ki ajiye may be wani abun za ki masa da su, idan kun yi waya sai ki tambaye shi." Neehal ta ce "Toh." Dan ita ko kaɗan ba ta yi tunanin kyauta Sadik ɗin ya bata ba." Mama ta ce "Ki je ki ci abinci Driver ya kaiku ku karb'o ragowar ɗinkunanku ke da Ameerah." Neehal ta amsa mata tare da ficewa daga d'akin. Bayan sun dawo daga karb'o ɗinkin Sadik ya kira ta, maganar farko da ta fara masa a kan kuɗin nanne, ya ce mata nata ne ai ita ya bawa ta yi hidimar biki. Neehal ta ce ya dawo ya karb'i kuɗin, Mama ta sai mata komai, kuma itama ta na da kuɗi a hannunta tunda duk wata ta na ɗaukar albashi. Sadik ya ce ya riga da ya bata ba zai karb'a ba, Neehal tai ta masa magiya a kan ya zo ya karb'a kamar wani abun, da ya gaji da magiyar ma sai ya kashe wayarsa. Da Neehal ta faɗa wa Mama abun da ya ce, sai Maman ta ce ta masa godiya tunda ya riga ya bata ba za a matar masa ba, itama za ta kira shi ta masa. Kamar yadda Sadik ya bawa Neehal kuɗi 100k haka ya je ya bawa Haneefah ita ma. ************ABUJA************ Yau tun sassafe Hameedah da ta tashi take ta rufzar kuka kamar wadda aka ce uwarta ta mutu, sosai hankalinta ya tashi ganin dagaske bikin Ameen za'a yi. A haka Mommy ta shigo ta same ta Misalin ƙarfe shida na safe, ganin irin kukan da take Mommy ta fara mata magana cikin faɗa. "Haba Hameedah, wai kukan nan ba zai ƙare ba ne, sai kin je wani ciwon ya kama ki a aikin banza, ki barmu da wahala." Cikin kuka Hameedah ta ce "Mommy ta yaya ba zan damu ba, bikin Ya Ameen fa za'a yi da wata ba da ni ba, Mommy ba ki san Yadda nake ji a cikin zuciyata ba ne, wlh Mommy kamar zan mutu haka nake ji." Mommy ta ce "To ba nace ki kwantar da hankalinki ba, indai Auren ku da Ameen ne kamar an yi an gama." "Tun yaushe ki ke faɗin haka Mommy, amma babu abun da ki ka yi akai gashi har auren ya matso, kuma kin ce mun za ki san yadda za ki yi auren nan bai yiyu ba, amma ban ga wata alamar hakan ba." Mommy ta sauke numfashi ta ce "Hameedah ki dena damuwa da matsowar auren kusa, ai ba ki ga an ɗaura Auren ba, kuma wallahi ko da an ɗaura Ni Suwaiba ba zan bari su samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman auran nasu ba, sai na zame musu masifa da bala'i wadda za su yi da na sanin yin auren." Hameedah ta ce "To Mommy ai idan sun yi auran Ya Ameen ba zai aure ni ba, domin ya sha faɗa ba shi da ra'ayin auren mace biyu." Mommy cikin tarar numfashi ta ce "Kar ki damu da wannan, duk zancen banza ne, shi ya ma isa, ki rubuta ki ajiye Ameen dole sai ya aure ki indai ina numfashi." Hameedah ta yi shiru ta na sauke ajiyar zuciya, maganganun mahaifiyarta ta sun ɗan sanyaya mata zuciya, domin ta san ta idan ta ce za ta yi abu tofa sai ta yi shi. Mommy ganin Hameedah ta yi shiru ta dena kukan sai ta ce mata, "Yanzu zan shirya zan tafi nemo mafita daga nan zan biya Kano ganin kayan lefen." Da sauri Hameedah ta kalle ta ta ce "Yanzu Mommy sai kin je kin ga kayan, ki na farin ciki da auran kenan.?" Mommy ta ce "Ba ki ji ina na ce miki zani ba ne, yanzu daga nan Katsina zan wuce gidan Haj. Rakiya daga nan za ta rakani gurin wani malami, ta sanar mun aikinsa tamkar yankan wuk'a yake, sai na gama da nan sannan in wuce Kanon, kin san idan ban je ba yanzu sai ya zama abun magana, tun kwana uku da suka wuce Yaya ya kira ni akan in je inga kayan, ina sane na ƙi zuwa a washegarin ranar dan Family duk yawanci ranar suka je, ɗazu ma Yayan ya kuma kirana ya ce mun ya ban zo ba? gashi har gobe za'akai kayan. Shi ya sa zan je kar a ce Yayanka Uwa ɗaya Uba ɗaya ɗansa zai yi aure ba ka je ganin lefe ba, yanzu sai ya zama abun magana." Hameedah tay shiru ba ta kuma cewa komai ba jin abun da mahaifiyar tata ta faɗa. Kafin ƙarfe 7 Mommy ta gama shirinta na tafiya Katsina, bayan ta cewa Abban Hameedah Kano za ta ganin lefe. Sai washegari da safe Mommy ta je Kano, Mama ta tarb'e ta ba yabo ba fallasa harma ta tambaye ta ina Hameedah ita ba ta zo ba.? Mommy ta kada baki ta ce "Ba ta da lafiya ne, itama rashin lafiyar Hameedan ne ya hana ta zuwa tuntuni ganin kayan." Mama ta mata addu'ar samun sauƙi. Baƙin cikin da Mommy ta ji a ranta lokacin da ta na kallon kayan ba zai misaltu ba, saboda ganin yanda aka kashewa lefen kuɗi, zuciyarta na faɗa mata da tuni wannan uban kayan ƴar ta za'a kaiwa fa, Takaici da hassada bai barta ta gama ganin kayan duka ba. Washegari a ka kai kayan inda aka tsaida Ranar biki sati uku masu zuwa. Shirye-shiryen biki ya kankama ta ko ina, kasancewar mahaifin Hafsat Babban Mutum ne a ƙasar nan kuma sananne ya sa tun saura sati bikin a ka fara sanarwa a gidajen Radio, amarya an shirya events kala_kala, shi dai ango ya sanar mata ba kowanne zai halarta ba. Ɓangaren Mama kuwa Events biyu kawai za ta yi, daga Dinner sai Yini/Mother's day. Su Neehal kam k'annen Ango suma suna ta shirye-shiryensu. Kasancewar wannan shine karon farko da Mama da Dad za su fara aurar da ɗa ya sa tun ranar Larabar satin bikin gidan ya fara cika da baƙi ta ko ina zuwa ake, Dangin Mama da dangin Dad. Hameedah wadda har rama tay saboda damuwa da ta sawa ranta itama ta zo bisa tilastawar mahaifiyarta wadda take ta kwantar mata da hankali akan ta daina damuwa ko anyi Auren Ameen ɗinma babu inda auren zai je zai lalace, ganin yanda Mommy'n take ta sintiri gidan Malamai sai hakan ya ƙara kwantarwa da Hameedah hankali. Yau Alhamis, yau ne kuma Ranar Dinner d'in da Aunty Sadiya ta shirya musu su Dangin Ango, Dangin Amarya kuwa tuni suka fara shagulgulan bikinsu.............✍️ *A yi hak'uri da typing error, ban yi edit ba ne.* *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:39] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *1️⃣7️⃣* _*Alhamdulillah am back*_ *🔥🔥 FITATTU HUƊU🔥🔥* _Zangon farko 2022_ _Allahamdulillah kuna ina💃🏽! Nace kuna ina?? Masoya wa ƴan nan shahararrun Marubutan wanda ake masu take da *(TAURARI MASU HANNUN LU'U LU'U)*_ _Uhm kada na cika ku da magana, nasan kun matsu kuji wannan taurarin kuma Jaruman wannan shekarar ta 2022 wanda suka wasa alƙalaman su domin farantawa masoyan su rai_ _Munyi duba da halin rayuwa na rashi da ake fama dashi, wannan dalilin ya sanya muka haɗe kanmu tare da Alƙalamanmu, waje guda, wajan ganin mun sauƙaƙa kuɗin da zaku sayi wannan FITATTU HUƊUN da zasu zama Abun ƙwatance a gareku, muje zuwa💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽._ *AUTAR MANYA* _fitacciya ƴar zamani wacce ta nishaɗan tar daku a littafin ta mai suna *AURAN BARE* a yanzu ta shirya tsaf domin bawa masoyanta farin ciki a cikin littafin ta mai taken 💃🏽💃🏽🔥 *BAƘAR FATA* kuna jin sunan kun san na musamman ne kada ku bari ayi babu ku_ *RAHMA REAL LADINGO* _Marubuciyar *RUWAIDA* ba sai na tsaya baku labarin Wacece ita ba, sunanta kaɗai zai sanya ku san cewa tayi fice a duniyar marubuta yanar gizo yanzu ta shirya tsaf domin kawo maku Nagartaccen littafin ta mai suna *DATTIJON ARZIƘI* 💃🏽🔥 Uhm Kuna jin sunan kun san daban yake_ *NIMCYLUV SARAUTA* _matashiyar marubuciyar wacce alƙaminta yake kan ci, wacce ta faɗa kar daku a littafin ta mai taken *MOON* *AURAN FANSA* yanzu ma ta shirya tsaf a cikin littafinta mai taken *TSINTACCIYA* 💃🏽🔥 Kuna jin sunan ba sai an tsaya magana ba_ *MSS FLOWER BATOOL* _Ƙasaitacciyar marubuciyar nan wacce littattafan ta suka karaɗe nahiyar makaranta littattafan Hausa, wacce ta wa'azantar daku a *ƳAR SO* yanzu ma ta shirya ta gyara Alkalamin ta, ta ciro maku littafinta mai suna 💃🏽💃🏽 *SULTAN* Uhm sunan kaɗai zai sanya kusan akwai????????_ _Zaku iya fara payment a yanzu haka domin samun damar zama mace ta farko wacce ta siyi wannan littafan, nasan a kullum masoyan mu a shirye kuke da ganin labaranmu, nasan ba zaku bamu kunya ba, zaku iya biyan naku ta hanyar👇🏾_ *GUDA ƊAYA 300* *GUDA BIYU 500* *GUDA UKU 600* *GUDA HUƊU 800* ACCT NO: 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 0814 210 5218 MASU TURA KATI KUMA SU TURA TA NAN👇🏾 0816 788 8934 GA MUTANAN NIGER KUMA SUYI MAGANA TA NAN👇🏾 +227 96 51 58 05 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽Mun shirya tsaf domin sanya zuƙatan masoyan mu farin ciki, Muna fatan zaku fara bibiyar FITATTU HUƊU tun a ZAGON FARKO👏🏻😍. Dan Allah share fisabilillahi Habibaties👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻. FITATTU HUƊU ✍🏾 *Team fittattu huɗu*🥰 ............Misalin k'arfe hud'u da mintuna na yamma Neehal ce ke shiryawa a bedroom d'in Mama saboda d'akinta cike yake da bak'i 'yanmata, sauri take ta yi ta gama shirin nata saboda su Haneefah dake jiranta za su gurin kwalliya. Doguwar rigar abaya ta zira ta d'ora hijabi akai, turarukanta masu sanyin k'amshi ta feshe jikinta da shi, tana gama shiryawa wayarta dake kan mudubi ta fara vibrate, d'auka ta yi ta duba ta ga Ameen ne yake kiranta, a fili ta furta "Yaya kuma?" Kafin ta d'aga wayar ganin tana k'ok'arin tsinkewa ta kara a kunnenta bakinta d'auke da sallama. Ameen ya amsa mata ya k'ara da fad'in, "Ki kawo mun coffe part d'ina yanzu." Neehal ta ce "Ok gani nan." Kamar za ta yi kuka ta yi maganar, domin a haka ma tasan sai ta sha jarabar su Haneefah na jiranta da suke, gashi Yayan nata ya k'ara tsayar da ita, zata k'ara b'ata musu time. Fitowa ta yi daga d'akin ta shiga d'an k'aramin kitchen d'in dake saman wanda ba su fiya amfani da shi ba dan dafa masa coffee d'in. Cikin mintuna qalilan ta gama had'a masa coffee ɗin, kafin ta gama ta window'n kitchen d'in ta hango Haneefah ta zo ta shiga d'akin Mama fuskar nan tata a cukule, ta san bayanta ta biyo. Bayan ta juye masa a k'aramin tea flaks ta d'auka ta nufi part d'in nasa tana ta sauri. Da sallama ta shiga falonsa bayan ta k'arasa, ba ya falon sai k'amshinsa kawai ke tashi a ciki, bedroom d'in sa ta nufa ta tsaya a bakin qofa ta fara knocking, mintuna biyu ya bud'e qofar tare da tsayawa yana kallonta. Neehal ba tare da ta kalle shi ba ta mik'a masa flaks d'in, cikin d'akin ya koma yana fad'in "Kika sake sa ya fad'i ya zube wani zaki sake had'awa." Neehal ta d'ago tana duban bayansa tare da turo bakinta gaba, shiga d'akin ta yi ta ajiye masa a kan bedside, ta juya zata fita ta tsinkayi muryarshi yana fad'in ta d'auko masa cup, ba tare data amsa masa ba ta je ta d'auko masa ta dire, zata kuma fita ya ce ta zuba masa coffe d'in a cikin cup, Neehal kamar ta zunduma ihu dan takaicin tsaida ta da Ameen yake gashi har 5 ta kusa, gashi Haneefah tana ta kiranta a waya, zuba masa ta yi ta mik'a masa, ya karb'a yana bin hannunta da ya sha jan lalle da kallo, lallen ya kama ya yi kyau gwanin sha'awa. "Ki jira ni a falo." Ya fad'a cikin had'e rai, Neehal ta marairaice ta ce "Yaya gurin kwalliya za mu tafi fa, su Haneefah na jiran...." Wani kallo ya watsa mata wanda yasa ba shiri ta had'iye sauran managarta ta juya ta nufi qofa ta fice daga d'akin. Tana fita kiran Haneefah na k'ara shigowa cikin wayarta, sai da ta zauna a kan kujera sannan ta d'aga wayar, cikin k'ufula Haneefah ta ce "Wai Neehal ina kika shiga ne tun d'azu inata neman ki amma ban ganki ba, kuma kin san jiran ki muke fa amma kika shanya mu, idan ba za ki taho ba mu za mu yi tafiyarmu." Neehal ta ce "Ki yi hak'uri Haneefah Yaya ne ya kira ni ina part d'in shi." Haneefah ta ce "Yaya kuma? Me kike masa toh?" Neehal ta ce "Coffe na had'o masa, yanzu kuma ya ce na jirashi a falo ban san me zai kuma sani ba." Ta yi maganar kamar za ta yi kuka, Haneefah ta ce "Yanzu dai kinga 5 ta kusa, kuma muna da yawa wad'anda za'ayiwa make up d'innan, bana so mu yi late a gurin zuwa dinner nan." Neehal ta ce "Idan 5 d'in ta yi ku wuce kawai zan taho ni kad'ai ko'a Napep ne." Haneefah ta ce "Shikenan." Tare da katse wayar. Neehal tana zaune a falo Ameen ya shanya ta, har k'arfe biyar ta wuce, su Haneefah sunyi wucewarsu gurin kwalliyar, gashi dinner d'in k'arfe bakwai na dare ne, kuma bata son ta yi African time. Ameen bai fito daga dakinshi ba sai da 6 ta wuce, zuwa lokacin Neehal harta fara hawaye, gashi Haneefah nata kiranta ita har angama mata make up d'inta, kuma kayan da zata saka yana gurin Haneefah ta tafi da shi a had'e da nata, da sai ta hak'ura da kwalliyar ta zira kayanta kawai ta tafi, get past d'inta ma dana Sadik duk yana hannun Haneefan." K'amshi turarensa da ta ji ya k'ara cika mata hanci shi yasa ta d'agowa da sauri ta kalle shi, shima ita d'in yake kallo hakan yasa suka had'a Ido, Neehal ta d'auke idanta da sauri tana yaba tsananin kyawun da ya yi a cikin zuciyarta, ya fito sak angonsa cikin dakakkiyar shadda mai tsadar gaske sky blue wadda aka maka aiki da Kalar Royal blue, tunda Neehal take ba zata iya tuno ranar da ta ganshi da hula ba a rayuwarta, domin shi mutum ne ma'abocin saka k'ananun kaya, idan ka ganshi da manyan kaya Juma'a ce ko kuma Sallah ko kuma idan za shi d'aurin aure, kuma suna masa kyau sosai idan ya saka, yau kam gashi harda babban riga (Malin_Malin) a kan kayan. Kiran shi ake tayi a waya amma ya k'i picking, Neehal kanta na k'asa ta ce "Yaya dan Allah ka barni in tafi, su Haneefah fa har an gama musu kwalliyar za su tafi ni kaɗai na rage." Ameen ya mata banza tamkar ba da shi take ba, tsadadden agogon hannunsa kawai ya kalla sannan ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun falon ya shiga latsa wayarsa hankali kwance. Sosai ran Neehal ya b'aci a kan abunda Ameen ya mata, haka kawai ya tsaidata kuma babu abunda zata masa, ita kuma bai barta ta je ta yi uxurin gabanta ba. Kiran Sadik ne ya shigo wayarta domin sun yi da shi zai d'auko su daga gurin kwalliyar ya kaisu gurin bikin, ba ta san me zata fad'a masa ba, shi yasa ta k'i d'aga wayar ta barta harta gaji ta katse. 6:30 pm, Ameen ya mik'e ya dubi Neehal dake ta hawaye ya ce "Tashi mu je." Fuskarsa babu walwala ko kad'an ya yi maganar, Neehal ta mik'e da sauri kamar wadda ke zaune a kan k'aya ta yi gaba, sai da ya kulle qofar part d'in sannan ya bi bayanta, har ta nufi part Mama ya tsayar da ita Neehal ta tsaya cike da mamakinsa gami da tsoro, domin ta kasa gane me yake nufi da ita, bayan zaman banzan daya sa tayi na fiye da awa ɗaya bai ishe shi ba sai ya k'ara tsayar da ita, to me yake nufi da ita ne? Gurin bikin ne baya son taje ko kuma me?" Dan ita zuwa yanzu ta hak'ura da kwalliyar kayanta kawai take so taje ta saka ta tafi tunda lokaci ya k'ure, gashi Sadik sai kiranta yake a waya ta k'i d'agawa, tafi son sai taje gurin kwalliyar sai ta kira shi ya je ya d'auke ta su wuce. Ameen ya nufi parking space bayan ya mata alamar ta biyo shi, harabar gidan Neehal ta kalla taga duk babu mutane an tafi gurin kwalliya wasuma sun fara tafiya gurin bikin. Bata da zab'i wanda ya wuce bin nasa, Motarsa ya shiga mazaunin driver, hakan yasa ita kuma ta shiga gurin mai zaman banza ta zauna zuciyarta na mata k'una, tana rufe murfin Motar ta fashe da kuka, Ameen ya dube ta da sauri ya ce "Me ne haka?" Neehal cikin kuka ta ce "Yaya wai me kake so na maka ne kake ta tsaida ni? alhalin kafi kowa sanin inda za ni, ga mutane suna ta jira na, kasan Mama ma Idan tasan ina gida har yanzu sai ta yi fad'a." Ameen ya tab'e bakinsa bai ce komai ba, yay wa Motar key suka fice daga gidan. Neehal ta cigaba da kukanta, a d'an fusace ya dube ta ya ce "Kar na k'ara jin kukan nan, yana cika mun kunne." Yanayin yanda yay maganar yasa Neehal ba shiri ta had'iye kukanta, Handkerchief d'insa ya zaro daga aljihu ya mik'a mata tare da fad'in "Share hawayenki, kuma kar na k'ara ganin ko d'igonsu." Ba musu Neehal ta karb'a ta share hawayen ta ci gaba da kukan zuci. Tafiyar mintuna k'alilin suka yi ya faka a gaban wani shago, wayarsa ya d'auka ya yi kira, mintuna uku wata matashiyar mata ta fito fuskarta d'auke da fara'a, Ameen ya zuge glass d'in Motar bayan ta qaraso suka gaisa tana tsokanarsa da ango ka sha k'amshi, nuna mata Neehal wadda idanunta ke lumshe ya yi ya ce "Gata nan, sai ki yi sauri please dan time ya qure." Matar ta yi murmushi ta ce "Kai dama wa ya fad'a maka sai i'yanzu ake zuwa make up? ai tun rana ake zuwa." Neehal wadda ta yi dif kamar bata Motar ta bud'e idanta da sauri jin an ambaci make up Tana kallon Matar, a hankali ta sauke numfashi ta ce "Ina yini." Matar ta amsa fuskarta d'auke da fara'a, ta k'ara da fad'in "Kai Masha Allah qanwar taka kuma kyakkyawa da ita, harma ta so ta fi ka kyau." Ameen ya yi murmushi kawai ya juyo da dubansa ga Neehal ya ce "Ki je ta miki, inanan ina jiran ki." Neehal ta ce "Amma Yaya kayana fa suna gurin Haneefah." Yana latsa wayarsa da ake ta kira ya ce "Zan kawo miki wasu." Neehal ta waro Ido ta ce "Yaya wasu kayan kuma? Anko ne fa wanda zan saka, kenan ni daban zan tashi?" A ɗan hasale ya ce"Kin san bana son musu ko?" Neehal ta turo Baki gaba cikin qoqarin maida hawayen da ya tarar mata a Ido ta bud'e Motar ta bi bayan Matar wadda ta koma cikin shagon nata tun sanda Ameen suka fara magana da Neehal. Ameen ya bita da kallo harta shige shagon sannan ya ja Motarsa ya tafi dan zuwa masallaci jin an fara kiran Sallah. Neehal ma sai da ta yi Sallah tukunna aka fara mata make up d'in, zuwa lokacin wayarta ta gaji da shan kiran Haneefah da Sadik harda ma da Mama. Matar da kanta ta yi wa Neehal kwalliya, sab'anin wasu a shagon da yaranta ne suke musu, gata da sauri cikin abun da bai wuce 40 minutes ba ta tsantsarawa Neehal kwalliya irin light d'innan amma ta yi masifar kyau, kowa dake shagon sai da ya furta "Wow, Masha Allah." Har wasu na tambayar ko Neehal amarya ce? Matar na ba su amsa da fad'in "K'anwar wani class mate d'inta ce da suka yi Secondary school, auransa ake shine ya kawo ta, ta yi mata kwalliya." Bayan kammalawa Neehal kwalliyar ta kira Ameen a kan ya kawo mata kayan Neehal, ya shaida mata ta fito bakin shagon ta karb'a. Neehal ta cika da mamaki ba kad'an ba ganin kayan da Ameen ya kawo mata ta saka, wata had'ad'd'iyar wedding gown ce sky blu, sai head Royal blue da takalmi da su sark'a harda pos wanda duk bata san da su ba, babu b'ata lokaci ta zira kayan me make up ta kafa mata had'ad'd'en d'aurin da ake yayi, nan fa Neehal ta qara fitowa bayan ta gama shiryawa tsaf, babu ta yanda za a yi ka ce ba amarya ba ce, matar ta ba ta turaruka masu sanyi da dad'in k'amshi ta feshe jikinta da shi. Neehal ta kasa d'auke idanunta saga kan mudubi saboda ganin kyawun da ta yi, sai tambayar kanta take a ranta tana fad'in "Ashe make up zai mata kyau sosai irin haka?" Matar ta mata pictures a wayarta sannan suka fito, dan itama matar zata je bikin, Ameen ya yi invited d'inta. Tunda suka fito Ameen ya kafe Neehal da Ido, ganin wani irin sihirtaccen kyau da ta yi, tana tafe tana faman rik'e Riga saboda jan k'asar da take ta baya, duk da kuwa takalmin k'afarta yana da tsini. Neehal ta bud'e front seat ta shiga, Matar kuwa ta shiga baya, zuciyar Neehal cike take fal da tarin tambayoyi ga Ameen, akan hanata zuwa gurin kwalliyar da ta yi niyya da ya yi, ya kawota wani wajen daban, sannan kuma ya bata wasu kayan daban wanda suka yi colour d'aya da nashi, Amma dole tabar tarin tambayoyinta a ranta saboda ba su kad'ai ba ne a Motar kuma ba taga fuskar hakan a gurin shi ba dan tana shigowa ya wani tsare gida. Wurin biki ya cika ya tumbutsa da 'yan'uwa da abokan arziqi, anata cashewa amma har takwas na dare ta yi amarya da ango ba su qaraso ba. Haneefah kuwa tana gurin ne kawai amma hankalinta gabad'aya yana gurin Neehal, gashi sai kiranta take a waya ba ta d'auka, Sadik ma ya zo ya fi mintu talatin a harabar gurin, ganin Neehal ba ta zo ba kuma yana ta kiranta ta qi d'auka sai kawai ya tafi, kuma bai yi tunanin kiran Haneefah ya ji ko suna tare ba. Amarya Hafsat kuwa da tawagarta sun dad'e da qarasowa gurin, ango kawai take jira su shiga cikin gurin, ranta idan ya yi dubu ya b'aci saboda kiran Ameen da take ta yi amma ya k'i d'auka, gashi bata san me ya tsayar da shi ba ya qi qarasowa gurin har wannan lokacin, har ta gaji da d'adin bakin da abokanan Ameen suke mata na fad'in ya kusa qarasowa. Fadeelah dake zaune gefenta a bayan Motar da suka zo ta dube ta ta ce "Ki qara kiran Al'ameen ki ji wai yana ina ne har yanzu be ƙaraso ba?" Hafsat da ranta ya kai qololuwar b'aci ta ce "Sau dubu nawa zan kira shi yana qin d'aga mun waya Fadeelah? ni na gaji da kiran shi, Idan aka qara wasu mintinan bai zo ba zan koma gida ne kawai, haba wannan ai wulaqanci ne." Kafin Fadeelah ta kuma cewa wani abu wani abokin ango mai suna Salman ya leqo ta glass ɗin Motar yana faɗin "Ranki ya daɗe angon naki ya ƙaraso ki fito." Hafsat ta saki ajiyar zuciya tare da gyad'a masa kai. Neehal kuwa yana parking Motar ta yunƙura za ta buɗe murfin Motar ta fito amma sai ta ji ya riƙe hannunta, ta juyo tana kallon shi cikin tsananin mamaki sai ta ga ya ɗauke kansa, sai da matar da ta yiwa Neehal make up ta fita daga cikin Motar sannan shima ya fito bayan ya sakar wa Neehal hannun, bai bi takan abokansa da suke ƙoƙarin cinye shi d'anye ba na rashin zuwansa da wuri ba ya zagaya ya buɗe wa Neehal Motar, a hankali ta ziro k'afarta ta fito cikin tsananin mamakin Ameen da ya kusan kashe ta da shi na abubuwan da yake mata a yau kamar ba shi ba, dai_dai lokacin itama Hafsat an buɗe mata Mota ta fito, akan idonta Ameen ya buɗe wa Neehal Mota.............✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:39] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *1️⃣8️⃣* *JERIN LITATTAFAN ELEGANT ONLINE WRITERS MAI TAKEN ELEGANT 5STARS* ✨🔥 *IDAN ZUCIYA TAYI WAKE*- Meerah *TUGGU BIYU*-diamond Aleesha *ZUBAR HAWAYE*-Gimbiya Ayush *MATA A YAU*-Aphserteen khairee *NIHLA*-Mammy Kabeer Akan farashi mai sauki 5_500 4_400 3_300 2_200 1_150 Zakuyi payment d'inku ta 0623151889 AISHA NURA MURTALA GT BANK sai evidence of payment ta wannan no 08148360851 Kati waya na MTN 09067211352 SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA 🤝🏻 ...........A razane Hafsat take kallon Ameen cikin tsananin mamakinsa, wani irin baƙin ciki na mamaye zuciyarta. Tunanika da yawa ne suka ziyarci zuciyarta a wannan lokacin, "Kenan Ameen jiran yarinyar nan mai kama da aljanu ya tsaya shi yasa bai zo da wuri ba? Kan uba! Dress ma colour ɗaya suka yi?" Hafsat ta faɗi haka a fili cikin tsananin kaɗuwa da takaici. Fadeelah ta dafa ta cikin rarrashi ta ce "Calm down Hafsat, dan Allah kar ki nuna ɓacin ranki a dai_dai wannan lokacin, yau ranarku ce kar ki yi abinda zaki zo kina da na sani, nasan abun da ciwo amma ki ɗaure." Hafsat ta yiwa Fadeelah wani kallo tare da yin ƙwafa cikin takaici amma ba ta ce ba komai ba,wata irin tsanar Neehal na ƙara cika mata zuciya. Neehal kuwa tana gama fitowa daga Motar ta dubi Ameen ta ce "Thank you." Ameen dake kallonta kamar zai cinye ta ya ce "Jira ni anan, kar ki je ko'ina." Bai jira amsarta ba ya nufi gurin Hafsat ya barta da baki a sake. Fadeelah ta sakar masa murmushi bayan ya ƙarasa inda suke tana faɗin, "Haba Ango ya zaka mana haka, gaskiya mun yi fushi." Ameen yana duban Hafsat wadda ta haɗe rai tare da ɗauke kai ya ce "Afuwan." Fadeelah ta yi murmushi kawai tare da matsawa ta koma gurin sauran ƙawayensu. Ameen ya kama hannun Hafsat ya ce "Ba magana." Hafsat ta d'ago ta kalle shi ba ta ce komai ba sai ƙura masa ido da ta yi ganin irin kyawun da ya mata, a hankali ta ce "Ka yi kyau sosai." Ya kashe mata ido tare da faɗin "Ke ma haka amaryata." Hafsat ta saki murmushi cikin tsananin farin ciki, gaba-d'aya ɓacin ranta ta neme shi ta rasa kasancewar Ameen a kusa da ita, dan sosai take farin ciki da Allah ya cika mata burinta na mallakar Ameen a matsayin miji. Neehal dake kallonsu ta tab'e baki tare da maida dubanta a kan wayarta, lalubo Numbern Sadik ta yi ta danna dialing. A lokacin ne kuma mutane suka fara zuwa inda Ameen da Hafsat suke suna ɗaukar su a hoto, Neehal dai bata motsa daga inda take ba takaicin Ameen ya kusa kashe ta na tsayar da ita da ya yi, gashi ta kira layin Sadik har sau biyu bai ɗauka ba, kiran Haneefah ta yi ringing uku ta d'aga, hayaniyar gurin yasa Neehal bata jinta sosai hakan yasa ta katse wayar. Haneefah ta fito daga cikin hall ɗin zuwa harabar gurin sannan ta kira Neehal, Neehal ta d'aga da sauri ta kara wayar a kunnenta. Haneefah ta ce "Wai ina kika tsaya ne Neehal? Tun d'azu nake ta baza ido ko zan ga kin shigo amma shiru, kuma na kikkira ki baki ɗauka ba." Neehal ta sauke numfashi ta ce "I'm sorry sai yanzu na ƙaraso ne." "Kina ina?" Haneefah ta tambaye ta cikin zak'uwa, Neehal ta ce "Ina harabar gurin tare da Yaya." Haneefah ta ɗan kalli gabanta inda take hango mutane ta ce "Gurin da nake hango mutane?" Neehal ta ce "Eh." Haneefah ta ƙaraso gurin tana duba Neehal, Neehal ta hango ta ta je kusa da ita tare da dafata tana faɗin "Ga ni nan fa." Haneefah ta juyo amma ta gaza cewa komai sai bin Neehal da ido kawai take ganin kayan dake jikinta da kuma irin kyawun da ta yi. Neehal ta ce "Ya dai, wannan kallon fa?" Haneefah ta ce "Na mamaki ne sai kuma kyawun da kika yi kamar ke ce amaryar, amma yana ga kin saka wasu kayan ba irin namu ba." Neehal ta shagwab'e fuska ta ce "Rigimar Yaya mana." Ta kwashe duk yadda suka yi da shi ta faɗa wa Haneefah a tak'aice. Haneefah ta yi murmushi ta ce "Kuma wallahi kin yi kyau sosai, make up ɗin naki ma ya fi namu kyau." Neehal ta ce "Kuma takun ta yi kyau, ina su Ameera fa?" Haneefah ta ce "Suna ciki suna cashewa, nikam tunda na zo ko rawar ban yi ba, hankalina yana kan ki, musamman da kayan ki suke wurina, har fa Mama sai da na kira na faɗa mata, shima Yayan na kira shi bai ɗauka ba." Neehal ta ce "Shi yasa na ga missed call ɗin Mama." Haneefah ta ja hannun Neehal tana faɗin "Zo mu shiga ciki, kafin su amarya su shigo." Neehal ta kalli inda su Ameen suke ta ga anyi arranged ƙawayen Amarya da Abokanan Ango, domin shiga wurin. Ameen duk abun da ake hankalinsa na gun Neehal da ya tsaida ta, domin so yake su shiga gurin tare, amma suna zuwa inda ya barta ya neme ta ya rasa. A cikin halla kowa ya zazzauna filin rawa ma babu kowa, sai Mc dake ta karaɗin isowar ango da Amarya. Neehal kuwa gurin cousins ɗinta suka nufa, tana zuwa kowa ya fara yaba kyawun da ta yi, hotuna suka shiga ɗauka kowa yana so ya yi da ita. A nutse ƙawayen Amarya suka fara shigowa suna ɗan rausayawa abun gwanin sha'awa, nan fa mutane suka mik'ewa suna video a wayoyinsu, ga masu Camara ma nata fama ko ta ina, shigowar Ango da Amarya aka sauya sauti zuwa wak'ar masoya, a hankali suke tafiya har suka ƙarasa mazauninsu. Nan fa wurin ya fara cika da jama'a kowa yana so ya ɗauke su a hoto, da ƙyar Mc ya samu mutane suka ragu. Amarya da ango sun yi kyau sosai, abu ɗaya ne ya musu cikas rashin dacewar kalar kayansu, dan ita Hafsat gown ɗin jikinta purple colour ce. Hafsat har ta gaji da ciwon bakin da ƙawayenta suke mata akan me yasa ba su saka kaya kala ɗaya ba ita da Ameen? Itama ba ta ji daɗin hakan ba ko kaɗan, kuma ta tambayi Ameen ɗin tun kafin yau amma bai faɗa mata kalar kayan da zai saka ba. Neehal tana zaune dan su ba su tashi ba saboda cikowar mutane, ji ta yi kamar wayarta tana vibrate tana dubawa ta ga Ameen ne ke kiranta. Da mamaki ta ce "Yaya kuma, yana high table amma yana kira na, to me zan masa?" Haneefah dake gefen ta ta kama hannunta ta ce "Taso mu je, sai a mana hotuna ma da su." Neehal ba dan ta so ba ta mike tana faman riƙe riga suka je. Ta zauna a gefen Ameen Haneefah kuma ta zauna a gefen Hafsat aka ɗauke su a hoto, Neehal ta dubi Ameen ta ce "Yaya na ga ka kira ni." Ameen ya harare ta ya ce "Me na ce miki?" Neehal ta ɗan turo baki gaba ta ce "To ai na ga shigowa za ku yi shiyasa kawai na taho." Duk maganganun da suke masu ɗaukar hoto nata musu ba tare da sun sani ba, domin sai suka zama tamkar suke Ango da Amaryar. Neehal ta tashi ta zagaya bayan kujerar da suke ta ɗan sunkuya tsakanin Hafsat da Ameen ta ce "Aunty ina yini." Hafsat ta saci kallon Ameen ta ga ita yake kallo hakan yasa ta ɗan saki fuska ta ce "Lafiya k'alau." Neehal ta ce "Ya taro." ta ce "Alhamdulillah." Kusa da ita Neehal ta je ta zauna ta ɗan rungumo ta aka musu hoto, Hafsat kuwa ji ta yi tamkar Neehal wuta ta sa mata a jikinta da ta taɓa ta. An cigaba da gudanar da shagalin biki yanda ya kamata, Amarya da Ango sun fito tsakiyar fili anata zuba musu lik'i. Neehal ma ta yi liƙi da kuɗin da Ameen yasa wani abokinsa ya bata bandir ɗin 200. Neehal tana gurin bikin ne amma hankalinta gaba-d'aya yana gurin Sadik, sai kiran shi take amma ba ya picking. Mama ma ta zo gurin ita da tawagarta ta yi kyau sosai cikin wani haddadden less kalar orange and black, Maman Hafsat ma ta zo. Neehal da taje yiwa Mama lik'i Maman tai ta kallonta cike da mamakin kayan da ta gani a jikinta, amma bata mata magana ba, kuma ko shakka ba ta yi tasan duk shirin Ameen ne wannan. Ƙarfe 9:30pm Neehal ta ja Haneefah gefe cikin damuwa ta ce "Besty Ina ta kiran Ya Sadik ba ya picking, Allah ya sa lafiya." Haneefah ta ce "Nima tun d'azu nake son na ce miki banga Ya Sadik ba, amma bari na kira shi na ji." Neehal ta ce "Ya kikkira ni fa, time ɗin ko gurin kwalliyar ba mu tafi ba, ina tunanin fa ya zo da ya kira ni ban ɗauka ba shine ya tafi." Haneefah da hankalinta ke kan wayarta ta ce "To ke me yasa kika ƙi d'agawar?" Neehal ta ce "I think in ya ji ban d'aga ba zai kira ki shi yasa." Haneefah ba ta kuma cewa komai ba jin wayar Sadik ta shiga, har ta yi zaton ba zai d'aga ba sai kuma ta ji ya d'aga tare yin sallama. Ta kalli Neehal tare da amsa masa, ta ƙara da faɗin "Ya Sadik ina yini." Ya ce "Lafiya k'alau, Ya taro?" Haneefah ta ce "Alhamdulillah, ya na ga ban ganka a wurin bikin ba?" Sadik ya ce "Na zo ai na kira Neehal ba ta ɗauka ba, kawai na wuce." Haneefah ta ce "Ayya da ka kira ni ai, dan get pass ɗinka ma yana wurina." Sadik ya ce "Don't worry, Allah ya sanya Alkhairi." Haneefah ta ce "Ameen." Tana shirin ce masa ga Neehal ta ji ya katse wayar, Neehal dake kallon Haneefah ta ce "Me ya ce?" Haneefan ta ce "Ya zo ya tafi." Neehal cike da damuwa ta ce "Fushi ya yi da ni kenan? Shi yasa ma naita kiran shi ya ƙi pick." Ta ƙarashe zancen kamar zata yi kuka." Haneefan ta ce "Ki kuma kiran shi yanzu nasan zai d'aga, d'azun ma may be ba ya kusa da wayar ne." Neehal ta ce "Toh." Sai da ta fice daga hall ɗin saboda hayaniya sannan ta kira shi amma still bai ɗauka ba. Text ta tura masa kamar haka. _I'm sorry Ya Sadik, Please ka d'aga wayata_ Sadik ya yi murmushi lokacin da ya ga text ɗin Neehal, kafin ya kirata har wani kiran nata ya kuma shigowa, rejected ya yi sannan ya kira ta. Ta d'aga da sauri cikin shagwab'a Ta ce "Ya Sadik I'm sorry please, time ɗin da ka ki......" "Kar ki damu ba komai, ya taron?" Sadik ya katse ta da faɗin haka. Neehal ta turo baki gaba ta ce "Ai na yi fushi tunda baka dawo ba." Sadik ya ce "Haba 'yar ƙanwata a yi mun afuwa mana." Neehal ta ce "Um, um nidai sai ka zo zan haqura." Sadik ya ce "Shikenan ki ba ni 15 minutes gani nan zuwa." Neehal ta ce "Yawwa Yayanah sai ka zo." Sadik ya katse wayar yana murmushi, yana jin farin ciki a cikin zuciyarsa. Neehal tana yin taku kaɗan ta ga wasu maza biyu a gabanta a tsaye, ta canza hanya da sauri ta ga sun ƙara shan gabanta, ɓata fuska ta yi sosai tare da tsayawa ta ce "Lafiya?" Suka yi murmushi sannan wani a cikinsu ya ce "Lafiyar kenan ƴan'mata." Neehal ta ja ɗan ƙaramin tsaki ta wuce da sauri ta bar su a gurin. Tunda ta koma cikin hall ɗin ta ji kanta na mata ciwo, ta yi tunanin ko yunwa ce dan rabon ta da abinci tun safe hakan yasa ta nemo abinci ta ɗan ci, amma a banza kamar ma ƙara mata ciwon kan aka yi har wani jiri_jiri take ji, gaba-d'aya gurin bikin ya gundure ta, so take kawai ta ganta a gida. Gurin Aunty Sadiya ta je ta ce mata "Aunty dan Allah ara mun key ɗin Motarki idan da ita kika zo." Aunty Sadiya ta ce "Me za ki yi da shi?" Neehal ta ce "Wata Friend ɗina zan kai gida yanzu zan dawo." Aunty Sadiya ta ce "Ina?" Neehal ta ce "Anan cikin Narasawan suke." Aunty Sadiya ta ce "Ta bari a tashi mana, ai an kusa tashi sai a kaita." Neehal da take magana cikin dauriya saboda ciwon kai ta ce "Ana ta kiran a gida ana cewa ta dawo, a hakan ma sai an mata faɗa." Aunty Sadiya ta buɗe Pos ɗinta ta ɗauko key ɗin Motar ta bawa Neehal tana faɗin "Take it, amma ki yi sauri, ki kuma kula da hanya sosai kin ga dare ne." Neehal ta ce "Insha Allahu Aunty, thank you." Aunty Sadiya ta faɗa mata inda ta yi parking Motar ta fito ta nufi gurin. A hankali take driving saboda ciwon kai gashi kuma dare ne, ta cikin layika take bi saboda ta yi saurin zuwa gida, abunka da G.R.A ko ina tsit babu mutane, amma akwai wadatuwar haske, tana shiga wani layi ta taka wani wawan burki da ƙarfin gaske cikin tsananin razana saboda abun da ta gani, ƙara dallare gabanta ta yi da hasken filitar Motar dan ta ƙara tabbatar da abun da idanunta suke gane mata..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:40] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *1️⃣9️⃣* ...........Dafe kanta dake barazanar tarwatsewa ta yi saboda yanda yake sara mata, tattaro dukkan dauriyarta ta yi ta buɗe Motar ta fito ba tare data kashe ba, da fitilar wayarta ta haske Yaran mata guda biyu wanda suke ta kuka manne da juna, ga haushin da wasu karnuka suke yi wanda ga dukkan alamu shike ƙara firgita Yaran. Neehal addu'a take acikin ranta zuciyarta cike da tsoro, domin ba tasan yaran mutane ba ne ko aljanu, ƙura musu ido ta yi cike da tausayawa a ranta tana faɗin "Idan har Yaran nan mutane ne to duk wanda ya ajiye su anan bai da imani ko kaɗan, yanda duniyar nan ta lalace ace yara ƙanana a daren nan amma su kaɗai a bakin layi, layin ma irin wannan da babu mutane, ga su ƴaƴa mata, yanda duniyar nan ta lalace idan wani mugun ya ƙyalla ido ya gansu ai sai ya ɓata musu rayuwa.' Lokaci ɗaya Neehal ta nemi ciwon kan dake damunta ta rasa tunanika kala_kala ta shiga yi akan yaran, cike da faragaba ta kama ƙafar ɗaya daga cikin yaran ta duba, jin kamar ƙarar tahowar Mota cikin layin yasa ta yi addu'a ta kamo hannun yaran wanda ganin tana haska su yasa suka ƙara rukunkume junansu. Babu musu yaran suka biyo ta still suna cigaba da kuka, Neehal ta buɗe bayan Motar ta saka su sannan ta shiga gaba ta tada Motar ta nufi gida, har suka je gida yaran ba su dena kuka ba tare da kiran sunan *Daddy* a kofar part ɗin Mama ta yi parking Motar, ta fito da sauri ta fito da yaran suma da har yanzu ta gaza ce musu ko ƙala, ɗaukar ɗaya ta yi ta ja hannun ɗaya suka shige ciki, babu mutane sosai a gidan duk suna gurin dinner, sai tsoffi kawai da waɗanda ba a rasa ba. Neehal ta gaida mutanen data tarar a falo sannan ta wuce sama, babu wanda ya tambaye ta game da yaran tunda biki ake za su yi tunanin ko ƴaƴan wata ne. Direct Neehal ɗakinta ta nufa ta sauke yarinyar dake hannunta wadda ta yi shiru tare da yin luf a jikinta, Neehal ta zauna a gefen gado tasa yaran duka a gabanta tana kallo, koda ba'a faɗa mata ba tasan yaran twins ne, saboda komai nasu da ya kasance iri ɗaya. Kyawawa ne kuma farare ga gashi an musu two babies, babu alamar talauci a jikin yaran, fatarsu luwai_luwai ga dukkan alamu daga gidan kuɗi suke, sai k'amshin turaren yara mai daɗi suke. Neehal ta fara tambayar kanta da faɗin "To wa ya ajiye su a waje a wannan daren? Ko dai fitowa suka yi suka kasa gane gida, ko kuma sato su aka yi? Gashi yaran da shigarsu tsaf cikin doguwar riga ƴan kanti masu kyau da tsada, ƙafafuwansu ne kawai babu takalmi ga....." "Aunty ki kai mu gurin Daddy." wadda da Neehal ta ɗauka da za su shigo ta katse ta da faɗin haka cikin maganarta ta yara. Neehal ta sauke numfashi tare da shafa kan yarinyar ta ce "Ina Daddy'n yake?" Ɗayar da hanyar yanzu bata daina kuka ba tace "Yana gida." Neehal ta janyo ta jikinta ta ce "Wa ya ajiye ku a waje?" Yarinyar ta ce "Wasu ne." Neehal ta ce "Ina mom ɗinku." Suka haɗa baki gurin faɗin "Daddy ya ce ta tafi ba zata dawo ba." Neehal ta yi shiru kawai tana kallon yaran, lokaci ɗaya suka cigaba da kuka suna kiran "Daddy Daddy, su dai akai su gurin Daddy'nsu." Neehal ta rungume su a jikinta tausayin yaran na ratsa dukkan jikinta, domin ta fahimci ba su da uwa saboda yanda suke kiran sunan Daddy kawai da kuma abun da suka ce mata. A hankali kuma ta d'ago su daga jikinta ta shiga goge musu hawayen fuskokinsu, tsabar kuka idanunsa sun yi jajir fuskarsu ma haka. Neehal cikin lallashi ta ce "Ku yi hakuri da safe zan kai ku gurin Daddy kun ji." Yaran suka d'aga mata kai suna sakin ajiyar zuciya. Neehal ta ce "Kun ci abinci?" Suka girgiza mata kai alamar a'a, Neehal ta shafi fuskokinsu ta ce "Bari na dafa muku indomie da tea, kuna ci ko?" Wadda tafi magana ta ce "Eh, Daddy Yana dafa mana every Morning." Neehal ta ce "Bari in dafa muku to." Ta mik'e ta cire ɗan kwallin dake kanta, tana cire ɗan kunne yarinyar ta ce "Aunty amarya ce ke.?" Neehal ta yi murmushi tare da d'aga mata kai, Ta lura yarinyar na da wayo da surutu saɓanin ɗayar data fahimci miskila ce. Neehal ta cire gown ɗin jikinta ta ɗauko wata riga mara nauyi ta nufi kitchen yaran na biye da ita a baya, ta lura duk a tsoro ce suke. A can gurin biki kuwa Sadik ya ƙaraso ya kira wayar Neehal ba ta ɗauka ba, sai ya kira Haneefah ta zo ta shigar da shi, Haneefah ta kai shi suka gaisa da Mama da Ya Ameen ya musu Allah ya sanya Alkhairi. Haneefan tana ta neman Neehal amma bata ganta ba, ta kira wayarta kuma bata ɗauka ba, ta bawa Sadik hakuri ya ce babu komai. Sai wajen 11 aka tashi daga dinner, Aunty Sadiya tana ta neman Neehal itama dan ta bata car key ɗinta. Mama ta kira Haneefan ta ce mata "Ina Neehal ne? Ta zo mu wuce gida." Haneefan ta ce "Mama tun d'azu ban ganta ba, da Ya Sadik ma ya zo nay ta neman ta za su gaisa amma ban ganta ba." Mama ta ce "Kin kira wayarta kuma?" Haneefan ta ce "Eh, bata ɗauka ba." Mama ta yi shiru kawai tana sauke numfashi. Sai da za su shiga Mota Aunty Sadiya take faɗa mata yanda suka yi da Neehal, Mama tay ta faɗa tana cewa Aunty Sadiya "Me yasa zata bawa Neehal Motar a daren nan ta yi driving?" Aunty Sadiya ta ce "Mu yi fatan Allah yasa tana lafiya kawai." Ameen ma yana ta baza ido ko zai ga Neehal su tafi tare amma bai ganta ba. Kallon yanda yaran suke cin abinci kawai Neehal cike da tausawa, a nutse suke ci amma kana gani ka san suna tattare da yunwa, sun ci sosai ɗaya ta fara kakarin amai, Neehal ta yunk'ura ta dauke ta da sauri ta yi toilet da ita, aikwa suna shiga ta fara kela amai, kafin ta gama itama ɗayar ta shigo tana yi, Neehal sai sannu take musu cike da tausayawa. Ta wanke musu baki bayan sun gama, ta cire musu rigunan jikinsu saboda sun ɓaci, ta dawo da su ɗaki suna ta sauke numfashi, Neehal ta lallaɓa su da ƙyar suka sha tea kaɗan, sannan ta kai su toilet ta musu wanka, dan duk sun yi kashi a cikin pampers ɗin jikinsu. Neehal tay ta mamakin yanda yara sun girma kamar waɗannan amma ake sa musu pampers, kuma da bakinsu za su iya cewa za su yi kashi. Komai na yaran iri ɗaya ne, babu wani abu daya bambanta a jikin su, harta da fingers ɗinsu iri ɗaya ne. Neehal ta naɗo su da ƙananun towels ɗinta, ta shafe su musu jiki da lotion sannan ta karkaɗe gado ta kwantar da su, har sun kwanta wadda tafi magana ta tashi kamar za ta yi kuka ta ce "Aunty ki kai mu gurin Daddy." Neehal ta matso ta janyo su jikinta sannan ta ce "Zan kai ku insha Allah, amma yanzu dare ya yi ku kwanta ku yi bacci da safe sai na kai ku." Yaran suka yi lamo a jikin Neehal ba su ƙara cewa komai ba, cikin 5 minutes ta ji saukar Numfashinsu alamun bacci ya ɗauke su, sai sakin ajiyar zuciya suke. Neehal ta raba su da jikinta a hankali tare da gyara musu kwanciya, ƙura musu ido ta yi zuciyarta cike da tunanika kala_kala. Jin hayaniyar mutane sun fara dawowa ta sauke ajiyar zuciya tare da tashi zaune, addu'a ta tofa musu sannan ta tashi ta ɗauko blanket ta lullub'e musu dukkan jiki da shi kansu ne kawai a waje. Toilet ta shiga, rigunan yaran ta fara wanke wa sannan ta goge make up ɗin fuskarta da tissue, tana cikin wanke fuskarta da sabulu Haneefan ta shigo ɗakin tana kiran sunanta. Turus Haneefan ta tsaya bayan ta ƙaraso tsakiyar ɗakin tana kallon yaran dake bacci akan gadon cikin mamaki, a hankali ta ƙarasa gadon ta zauna tana duban yara cike da sha'awa, a rayuwar Haneefan tana bala'in son twins, kan yaran ta shafa tana addu'ar Allah ya bata twins itama. Neehal ta fito daga toilet tana faɗin "Kiran me kike mun haka kamar sabuwar makauniya?" Haneefan ta harare ta tace "Makauniyar ce, ashe kina nan hankalinki kwance mu muna can namu a tashe." "Akan me?" Neehal ta tambaya tana shimfida Darduma domin yin Sallah. Shigowar Mama dakin ya hanata tada Sallar, Mama ta tsaya kawai tana bin ta da kallo. Neehal ta ce "Sannu da zuwa Mama." Rai a ɓace Mama ta ce mata "Kin kyauta Neehal Na gode." Neehal data san kwanan zancen ta ce "Ki yi haquri Mama, wallahi kaina ne ke ciwo kamar zan mutu shi yasa na dawo gida dan na huta." Mama ta ce "Shine ba za ki faɗa a dawo dake gidan ba sai kin yi ƙarya." Neehal ta yi ƙasa da kanta ta ce "I'm sorry ban san na wahalar da kowa ne." Mama ta tab'e baki ba ta ce komai ba, ta juya zata fita idanta ya sauka akan *twins* dake bacci akan gado. Ta dubi Haneefan wadda ta kasa ɗauke idanunta daga kansu ta ce "Haneefan Waɗannan Yaran fa ?" Haneefan ta ce "Nima anan na zo na same su Mama." Mama ta maida dubanta ga Neehal wadda gabanta ke fad'uwa dan bata san ya Mama zata karb'i zancen yara ba, ta ce "Ƴaƴan waye?" Neehal ta sauke numfashi ta ce "Mama long story ne." "Long story kuma?" Mama ta tambaya cikin rashin fahimta, Neehal ta gyaɗa mata kai tare da bata labarin yanda ta samu yaran. Ta ƙara da faɗin, "Na ji tsoro sosai a time ɗin da na gan su, har da zan wuce na barsu sai kuma na yi tunanin kar na barsu wani abun ya cutar da su, gashi sai kuka suke suna kiran Daddy." Mama ta yi shiru kawai tana kallon Neehal, tana son gano gaskiyar abun da Neehal ɗin ta faɗa, ta san Neehal bata mata ƙarya dan ko ta yi ma sai ta gano ta. Mama ta ce "Neehal kin san bana son ƙarya ki faɗa mun gaskiya yaran waye?" Neehal ta ce "Wallahi Mama abun da na faɗa miki shine gaskiya ki yarda mana." Mama ta ce "A ina kika gan su?" Neehal ta ce "Titin Ahmadu Bello ta cikin layika amma." Mama ta yi shiru tana tunani tare da kallon yaran cike da tausayawa, Haneefan ta ce "Allah sarki ko dai sato su aka yi Allah ya yi nufin kub'utar da su shine aka yarda da su a gurin." Mama ta sauke numfashi ta ce komai ma zai iya faruwa, ɗauko ɗaya Haneefan bari na ɗauki ɗaya mu kai su part ɗin Daddy, tunda nan akwai baƙin da za su kwana, kafin safiya mu san abun yi akan su." Haneefan ta ce "Toh." tare da lallaɓawa ta ɗauki ɗaya, yarinyar ta ɗan firgita cikin bacci ta ce "Daddy." Haneefan ta rungume ta ajikinta tana shafa bayanta. Mama ta ce "Babu kaya ajikinsu dama?" Neehal ta ce "Akwai, ya ɓaci da amai ne shine na wanke suna toilet." Mama ta ɗauki ɗayar itama suka fice daga ɗakin. Neehal ta bisu da kallo kafin ta tada Sallah, tana hamdala a ranta da Mama ta fuskanci lamarin Yaran cikin sauƙi. *▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️* *ABUJA* *▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️* Wata matashiyar budurwa ce ke kai kawo a cikin wani madaidaicin bedroom hannunta riƙe da waya ƙirar iPhone, yanayinta ya nuna tana cikin wani tashin hankali, wayar hannunta ce ta ɗau ruri wanda hakan yasa ta ɗan firgita tare duba wayar da sauri, jikinta har rawa yake ta d'aga wayar ta kara a kunne. A ɗan zafafe ta ce "Haba Gaye ya zan yi ta kiran ku amma ku ƙi d'aga mun waya, kun sa hankalina gaba-d'aya ya tashi ina tunanin ko an samu matsala ne a aikin." Gayen ya ƙyalƙyale da dariya cikin wata ƙatuwar muryarsa ta ƴan shaye_shaye ya ce "Haba haba, ki yi hanzarin tofar da yawunki domin ni bana taɓa yin aiki a samu matsala kuma bana son ana ambata mun ita a cikin aikina, yanzu nan yarana suka kira ni akan aiki ya kammala yanda ake so, yanzu ke kawai nake jira da cikon kuɗina." Wata doguwar ajiyar zuciya budurwa ta sauke ta sharce gumin dake goshinta ta ce "Baka da matsala Gaye indai kuɗi ne yanzu nan zaka ji alert har da ƙari ma akan wanda na ce zan baka." Gaye ya yi murmushi ya ce "Sai na jiki." Tare da kashe wayar. Wani tsalle budurwar ta yi ta faɗa kan gado tana ƙyalƙyala dariyar farin ciki da samun nasara. A fili ta fara faɗin "Ahmad dole yanzu hankalinka ya dawo gare ni tunda na rabaka da abun da yake hanaka kallon mata da sunan soyayya." Ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya tare latsa wayarta domin turawa Gaye kuɗinsa. Had'ad'd'en asibiti ne wanda daga gani babu tambaya na masu hannu da shuni ne, wata mata ce tsaye a Emergency ward tana kaiwa da komo wa tare da karanto duk addu'ar da ta zo bakinta cikin kuka, kallo ɗaya za kai mata ka fuskanci tana cikin tashin hankali ba kaɗan ba. A gefe guda kuma wata yarinya ce zaune akan kujerun dake gurin wadda ba za ta wuce shekara 15 ba, tana rufzar kuka da dukkan ƙarfinta. Wani Babban Mutum ne ya ƙaraso gurin tare da wasu mutane biye a bayansa, matar na ganinsa ta ƙara fashewa da kuka tana faɗin, "Alhaji ba a gansu ba ko? Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, ya ALLAH ka bayyana mana yaran nan a raye ko a mace, Allah ka kare su da kariyarka a duk inda suke, Allah kasa suna hannu na gari, Allah ka dubi maraicinsu." Sai kuma ta fashe da kuka abun gwanin ban tausayi. Ta ƙarasa inda mutumin yake ta riƙe hannunsa tana faɗin "Alhaji dan Allah ka taimake ni kasa a nemo yaran nan, ko dan mummunan halin da mahaifinsu yake ciki sanadiyyar ɓatansu, dan Allah Alhaji karna rasa ɗanaa." Mutumin wanda ga dukkan alamu mijinta ne cikin lallami ya ce, "Police suna can suna iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun nemo yaran, kuma insha Allahu muna saran za a gansu, ki kwantar hankalinki kin ji." D'ago da jajayen idanunta da suka ci kuka suka koshi ta yi tana duban sa ta ce "Ta yaya hankalina zai kwanta Abbansu, alhalin ga yarona can kwance rai a hannun Allah, jikokina kuma an neme su an rasa ka faɗa mun ta yaya hankalina zai kwanta!" Ta ƙarashe maganar cikin tsananin kuka. Mutumin ya sauke numfashi cikin ƙoƙarin ɓoye tasa damuwar ya ce "Allah yana sane da mu Fatima, kuma insha Allahu shi zai kawo mana mafita, ke dai kawai ki dage da addu'a." Ta gyaɗa masa kai tare da sakin hannunsa ta zauna saboda jirin dake neman yar da ita, mutumin ya nufi gurin da yarinyar dake ta kuka take ya zauna tare da janyo ta jikinsa ya fara rarrashinta. Mutanen da suka zo tare da mutumin suka jinjina kai zuciyoyinsu cike da tausayin wannan ahali. Matar ta d'aga hannunta sama a fili take faɗin, "Ya Ubangiji na roƙe ka ka tashi kafaɗun *AHMAD* ɗina, ka bayyana masa yaransa da gaggawa a duk inda suke, Allah duk wanda yake da hannu a ɓatan yaran nan Allah ka tona asirinsa." Gaba-d'aya mutanen wurin suka amsa da "Amin ya Allah.".........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:40] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *2️⃣0️⃣* ..........Bayan wasu mintuna wani likita ya fito daga ɗakin da Ahmad yake yana goge fuskarsa da handkerchief, Matar ta riga kowa mik'ewa tana faɗin "Doctor, ya ya jikin nasa?" Likitan ya sauke numfashi yana dubanta ya ce "I'm sorry to say Hajiya, just pray." Bai jira amsarta ba ya juya ga Alhajin ya ce "Ka biyo ni office Alhaji." Matar tana sheshshek'a ta ce "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, likita me kake nufi? Har yanzu kenan Ahmad be farfaɗo ba?" Alhaji ya dube ta ya ce "Ki zauna ki yi addu'a kamar yadda Doctor ya ce, zan je inji bayaninsa." Matar ta gyaɗa kai tana salati ta koma ta zauna jagwab, yarinyarta ta matso kusa da ita tana sauke numfashi ta ce "Ummi, tunda har yanzu ba'a gansu ba ki kira gidan su Ammi ki sanar musu, ya kamata zuwa yanzu su ma su san halin da ake ciki." Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Tun d'azu naso kiran su Zahra, Abbanku ne ya hana ya ce kar a tayar musu da hankali a bari aga abun da hali zai yi, amma yanzu tunda ba a gansu bari na kira Yaseer na faɗa masa, kin san Ammin tana da hawan jini yanzu in ta ji sai ya tashi, amma shi Yaseer ɗin ya san ta yanda zai faɗa mata hankalinta ba zai tashi ba sosai." Zahra ta gyaɗa mata kai kawai cikin sanyin jiki. ▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️ *KANO* ▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️ Jiki a sanyaye su Mama suka kwantar da yaran a wani ɗaki dake part ɗin Daddy, sosai al'amarin yaran ya girgiza kwanyar Mama, tafi 5 minutes tana kallon yaran kafin ta sauke numfashi ta juya ta fita bayan ta lullub'a musu bargo, Haneefah dama suna kwantar da yaran ta fice. A falo suka ci karo da Aunty Sadiya da Aunty A'isha. Aunty Sadiya ta dubi Mama ta ce "Ya Fatima kin ga Neehal ɗin?" Mama ta ce "Eh, ashe gida ta dawo wai kanta na ciwo." Aunty A'isha ta ce "Ayya, hayaniya ce Allah ya sauwaaqe." Aunty Sadiya dake kallon Mama ta ce "Lafiya kuwa na ganki wani iri?" Mama ta sauke numfashi ta ce "Ina fa lafiya Sadiya." A rude Aunty Sadiya ta ce "Me ya faru?" Mama ta ce "Ku zauna maganar ba ta tsaye ba ce." Sosai Aunty A'isha da Aunty Sadiya suka jimanta al'amarin, zargika kala_kala suka yi akan yarda yaran da akay, Mama ta ce "Sanin gaibu sai Allah." Ɗakin da yaran suke suka shiga suka gan su, Amma Mama ta roƙe su a kan kar su sanar da kowa hatta da Hajiya kuwa. Bayan Neehal ta idar da Sallah ta ɗauko wayarta ta kira Sadik, rejected yay kamar ko da yaushe sannan ya kira ta. Tana d'agawa ta ce "I'm sorry Ya Sadik Please." Sadik ya kwaikwayi yanda take magana ya ce "Um um, ba zan yi sorry'n ba." Neehal ta yi murmushi me sauti jin yanda ya yi ta ce "Haba Yayanah na kaina, idan baka hakura ba kuka fa zan yi." Ta ƙarashe maganar cikin shagwab'a. Sadik ya sauke numfashi ya ce "Shikenan komai ya wuce dear, amma ina kika shiga?" Neehal ta ce "Kaina ke ciwo shi yasa." Cikin tausayawa Sadik ya ce "Subhallah, sannu Allah ya sauqaqe, amma dai kin sha magani ko?" Neehal ta ce "Yanzu dai zan sha." Sun taɓa hira kaɗan suka yi sallama, saboda ta samu ta sha magani ta kwanta ta huta. Hameedah ce zaune ta ɗora kanta akan cinyar mahaifiyarta tana kuka ƙasa_ƙasa, ganin tabbas ta rasa Ameen tunda gobe zai angonce da wata. Mumy wadda ta gaji da rarrashi tun a gurin bikin ta ce "Wai Hameedah meke damunki ne? so kike har sai mutane sun fuskanci halin da kike ciki, masu dariya su yi miki suna Allah ya ƙara, na ce miki daure zuciyarki za ki yi ki nuna kamar baki damu ba, a yi bikin nan a gama." Hameedah ta d'ago kanta cikin sheshshek'a ta ce "Mumy na yi iya yina nayi ƙoƙarin hakan amma na kasa, wallahi Mumy ba ki ji yanda nake ji a cikin zuciyata ba kamar ana rura mun garwashin wuta." Mumy ta ce "Na san abun da ciwo, kuma nima ina jin yanda kike ji, amma ki daure dai, na faɗa miki ko mai daren daɗe wa sai kin auri Ameen in dai da bokaye a cikin duniyar nan, yanzu dai ki share hawayenki in faɗa miki wani abu kin ji My daughter." Hameedah ta gayd'a mata kai ta fara share hawayen nata. Misalin ƙarfe 12:30 na dare Ameen ne zaune a falon Daddy shi da Mama da ta kira shi, ya tattara duka hankalinsa yana sauraren abun da zata faɗa masa. Mama ta ce "Dama d'azu kai ka tsayar da Neehal?" Ya ce "Eh." Mama ta ce "Akan wanne dalili?" Ya yi shiru, Mama ta ce "Ka yi shiru ina maka mgn." Ya ce "Babu komai Mama." Mama ta girgiza kai ta ce "To me ne dalilin da yasa ka bata kayan data saka? bayan ga wanda suka ɗinka za su saka ita ƴan'uwanta." Ameen ya ce "Mama wai dama wannan shine kiran da kika mun? wallahi na ɗauka wani babban abunne ya faru." Mama ta harare shi ta ce "Ban sani ba." Shigowar Neehal falon ya hana Ameen faɗar abun da zai faɗa. "Ke kuma daga ina?" Mama ta tambayi Neehal tana kallonta, Neehal ta turo baki gaba ta ce "Bacci zan yi a nan saboda ina son na kwana tare da yaran." Mama ta nuna mata dakin da suke da hannu tana faɗin "Suna nan, zaki wani kwaso jiki a daren nan ki taho kamar da tare da su kike kwana." Neehal ba ta ce komai ba ta shige, Ameen da ya bita da kallo har ta shige dakin sannan ya dubi Mama ya ce "Wanne Yara ne kuke magana akansu." Mama kamar ta share ta ƙi faɗa masa sai kuma dai ta sanar masa, don abokin kuka shi ake fadawa mutuwa. Shima ya girgiza da lamarin, amma dai ya ce wa Mama da safe sai akai yaran gidan Radios da Televisions a bada cikiyarsu ko za a dace a samu iyayensu. Mama ta yi na'am da shawarar shi. Neehal ta daɗe kafin bacci ya ɗauke ta, tana ta aikin kallon yaran, tana jin ƙaunar su na mamaye mata zuciya. Washegari da safe Neehal tana tattare ɗaki Yarinya ɗaya ta tashi tana kiran sunan Daddy, Neehal ta ajiye tsintsiyar hannunta ta ƙarasa gadon ta d'ago ta tana faɗin "Kin tashi, mu je ki yi fitsari to." Yarinyar dake binta da kallo ta gyaɗa mata kai. Bayan ta yi fitsarin Neehal ta wanke mata baki da fuska suka fito, suna fitowa ta ga itama ɗayar ta tashi zaune tana ta mutsitsika ido, Neehal ta kama ta itama ta kaita toilet, Bayan sun fito ta kalle su ta ce "What is your names?" Wadda tafi surutu ta ce "Afrah, amma Daddy yana ce mun Princess, a lesson da islamiyya kuma *FATIMA AHMAD*." Neehal ta jinjina kai ta ce "Nice name Darling." Sannan ta juya ta kalli Ɗayar ta ce "Ke fa." Yarinyar ta ce "Amrah, amma Daddy yana ce mun Jewel a lesson da islamiyya kuma *AISHA AHMAD*." Neehal ta Jinjina kai tana murmushi ta ce "Nice name sweetheart." Afrah ta ce "Aunty safiyar ta yi zaki kai mu gurin Daddy ko?" Neehal ta gyaɗa mata kai zuciyarta cike da k'aunar yaran. Mama ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da tea flaks da ƙananun cups, yaran suka bita da kallo kafin su haɗa baki a tare su ce "Ina kwana." Mama ta ajiye kayan hannunta tare da amsa musu, ta ƙaraso ta shafa kansu da cike da kaunarsu, dan yaran sun matuƙar burge ta ba kaɗan ba, musamman da suka gaishe ta, ga dukkan alamu daga gidan tarbiyya suke. Mama ta dubi Neehal ta ce "Ɗauko musu kayansu a saka musu, bari na haɗa musu breakfast su yi." Neehal ta amsa mata tare da ficewa daga ɗakin, yaran suka bita da kallo kamar za su bita. Bayan sun yi breakfast Neehal ta musu wanka ta shirya su cikin rigunansu na jiya. Kasancewar yau ne d'aurin Aure yasa gidan ya ƙara cika da baƙi mata da maza, duk inda Neehal ta ɗora k'afarta su Afrah na biye da ita a baya, duk wanda ya tambaye ta yaran waye sai ta ce na wata Friend ɗinta ne. Ɗaya daga cikin sojojin gidan ta bawa kuɗi ya siyo wa musu kayan sakawa da takalma da panties, kafin Azhar ya kawo mata ta shirya su tsaf suka yi kyau sosai. kowa so yake ya ɗauke su ko ya musu hoto, amma yaran sun ƙi yarda da kowa sai Neehal, saboda ganin taron jama'a, ita kuwa ta cika su da kayan zaƙi dangin su chocolate da sweet suna ta sha. Mama kanta ya ɗau caji tana da hidima da mutane, hakan ya sa ba ta bi takan zancen yaran ba, dama kuma da taywa Daddy maganar su ya ce a bari bayan biki sai a san abun yi. Ƙarfe biyu na rana aka ɗaura Auren AL'AMIN MUHAMMAD TAFIDA da amaryarsa HAFSAT AHMAD ƊAN GASKE. Anan babban masallacin Juma'a dake cikin Narasawa G.R.A. Yau ma Neehal ta yi kyau sosai, shadda ta saka da safe Wadda aka mata akai mai kyawun gaske, ta kafa ɗaurinta. Su Afrah sai faɗin "Kin yi kyau Aunty." suke, Murmushi Neehal take idan suka faɗi haka. Ta ce musu "Thank you Dearies." Wajen ƙarfe uku Sadik ya ƙaraso gidan. Neehal ta fito tare da twins ɗinta, tunda ta fito ya ƙura mata ganin irin kyawun da ta yi. Neehal ta gaishe shi ya amsa yana kallon yaran, Neehal ta ce "Ya su Maamah da Abba?" Sadik ya ce "Suna Lafiya, Ya taro?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Allah ya sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya, saura naki kuma." Neehal ta yi murmushi ta ce "Yau har na gaji da jin wannan furucin, kowa muka haɗu sai ya ce sai mun zo naki kuma." Sadik ya ce "To ai gaskiya ne, gwara Mama ta aurar dake ta huta da rigimarki." Neehal ta ce "hmmm." Kawai, Sadik yace "Wannan cutes babies ɗin fa?" Neehal ta ce "Yaran wata Friend ɗina ne." Sadik ya ce "Masha Allah, Allah ya raya su." Neehal ta ce "Ameen." Tare da dubansu ta ce "Ba ku gaida Uncle ba." Amrah ce ta fara gaishe shi da faɗin "Ina kwana." Sannan itama Afrah ta gaishe shi, ya kama hannunsu tare da amsa musu. Bai wani jima ba ya tafi saboda Ameerah data zo kiran Neehal. Suna tafiya Ameerah ta ce "Amma Yaa Neehal wannan saurayinki ne?" Neehal ta girgiza kai tare da faɗin "Ko ɗaya, he is just Friend." Ameerah ta yi shiru amma ba dan ta yarda ba. Ƙarfe huɗu aka tafi gurin da za ai Mother's Day, sai bayan magriba aka tashi. Yau kam amarya ba ta zo ba, tana gida suna nasu suma, shima Ameen ɗin bai je ba, hakan yasa yau kwata_kwata ba su haɗu da Neehal ba. Twins kam ganin hada_hadar mutane yasa ba su ƙara takurawa Neehal akan ta kai su gurin Daddy'nsu ba, sai da suka zo bacci nema suka so yi mata rigima ta lallaɓawa su da faɗin sai an gama biki zata kai su. Washegari ma anyi taro a gida inda akai kidan ƙwarya manyan mata suka cashe, tun kafin Azhar aka fara har bayan la'asar ana yi. Yau za a miƙa Amarya gidan angonta, misalin ƙarfe biyar na yamma Neehal dake jin duk jikinta a sanyaye ba tare da tasan dalili ba ta barwa Haneefah twins ta nufi part ɗin Ameen............✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:40] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *2️⃣1️⃣* ..........A hankali ta buɗe ƙofar falonsa ta shiga bakinta ɗauke da Sallama, kanta na ƙasa ba ta yarda ta d'ago ba saboda falon cike yake da abokanansa. Suka amsa mata suna binta da kallo, Salman ganin yanda ta takure a tsaye ya dube ta ya ce "Shiga mana Neehal, yana ciki ai." Neehal ta ce "Toh." Tare da gaishe su a lokaci ɗaya, ba ta jira amsarsu ba ta wuce. Wani a cikinsu da ya bita da kallo ya ce "Salman, wannan kamar ƴar jaridar nan ta ASTV?" Salman ya ce ba kama ba ce ita ce." Ya ce "Wow yarinyar me kyau tana burge ni wlh." Kafin ya ce wani abu ya ji wani a cikinsu yana faɗin "Ita ce wadda suka zo tare da Al'ameen ranar dinner ai, dama ƙanwarsa ce?" Salman ya ce "Yeah." Wanda ya fara magana da farko ya ce "To ai ni ranar na ɗauka ita ce ma Amaryar saboda ta yi kyau sosai har ma tafi Amarya....." Haka dai sukaita magana akan Neehal. A hankali take knocking ƙofar bedroom ɗinsa kamar me tsaron wani abu, Ameen dake shiryawa a gaban mudubi don bai jima da fitowa daga wanka ba ya ɗan yamutsa fuska ya ce "Waye?" Neehal tay shiru yanayin da take jin jikinta da zuciyarta na ƙara tsananta, Ameen ya taho ya buɗe ƙofar zuciyarsa cike da masifa, a tunaninsa a cikin abokansa ne wani ya zo zai ƙara masa ciwon kai akan wanda suka sa masa d'azu. Cike da mamaki yake kallonta, kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, Ameen ya koma ciki yana faɗin "Come in." Neehal ta shiga kamar munafuka ta zauna a gefen gado, yana fesa turare ya ce "What happened." Ganin ta ƙi cewa komai tunda ta shigo. A hankali ta d'ago ta kalle shi amma yanda ba za su haɗa ido ba ta ce "Yaya..." Sai kuma ta yi shiru hawaye ya fara zuba daga idonta, Ameen ya sauke numfashi sannan ya dawo kusa da ita ya zauna ya kama hannunta murya ƙasa_ƙasa ya ce "Tell me what happened?" Neehal ta share hawayenta ba ta ce komai ba, Ameen ya ƙura mata ido domin yasan dalilin kukanta a hankali ya ce "Kin fara missing Yayanki ko?" Neehal ta d'aga masa kai da sauri sannan ta ce "Shikenan Yaya na dena ganinka every weekend?" Ameen ya girgiza mata kai tare da faɗin "Wa ya faɗa miki? Zan dinga zuwa kodayaushe." Neehal ta ce "Na san baza ka zo ba tunda ka yi aure." Ameen ya ce "Dolena ma inzo inga my Mum da little sis ɗina." Neehal ta ce "Dagaske?" Ya d'ago kanta ya saka idanunsa a cikin nata yana mata wani kallo ya gyaɗa mata kai, Neehal ta kumshe idanta da sauri gabanta na fad'uwa. Ameen ya sakar mata fuska yana sauke numfashi, tashi ya yi ya ɗauko wayarsa ya shiga gallery ya miƙa mata, ta karb'a tana dubawa. Waro idanta ta yi tana murmushi ta ce "Wow Yaya pics ɗin sun yi kyau sosai." Ya yi murmushi kawai yana kallonta, ita kuma ta cigaba da kallon hotunan. Pictures ɗinsu ne wanda aka musu ranar dinner ita da shi, wani suna zaune wani kuma a tsaye lokacin da ta je yi musu lik'i, sosai hotunan sukai kyau, kuma babu ta yanda za'ai ka gani ka ce ba Neehal ce amaryar ba. Ta ajiye masa wayar bayan ta gama ta gani tare da mik'ewa ta ce "Yaya Bari in koma." Ameen ya mata wani kallo ya ce "Ba za ki raka ni gidan Amaryata ba?" Neehal ta waro Ido ta ce "Ni kuma Yaya? ga Freinds ɗinka nan." Ya kau da zancen da faɗin "Ina new kids ɗinki?" Neehal ta ce "Suwa?" Ya ce "Twins." Neehal ta ce "Oh, suna gurin Haneefah." Ya ce "Me yasa ba ki zo mun da su ba?" Ta ce "Na ga baka son hayaniya ne kar su dame ka." Ameen ya ce "Ok, me kike so in baki a ɗakin nan?" Neehal ta hau juya ido a ɗakin ganin babu abun da zata buƙata a ɗakin, ta ce "Nothing." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai, sai kuma ta kalli kan mudubi ta ɗan shagwab'e fuska ta ce "Na tuno, your perfumes." Ya ce "Ai is only for male." Ta turo baki gaba ta ce "Ai ba ajikina zan dinga sawa ba, kawai zan dinga jin k'amshin ina tunawa da kai." Ameen yay murmushi ya buɗe wata jaka ya ɗauko mata turaruka kala uku ya bata, Neehal ta karb'a da murnarta ta ce "Thank you so much." Tare suka fito daga ɗakin, Neehal ta fice shi kuma ya zauna yana haɗe rai dan kar su cigaba da tsokanarsa, aikwa kamar ma ya ce su yi suka fara, daga baya kuma suka koma zancen Neehal kowa yana faɗin yana kamu. Shi dai ko kanzil bai ce musu ba. Neehal tana koma Haneefah ta miƙa mata su Afrah da suke ƙoƙarin saka kuka ganin shiru_shiru ba su ga Neehal ɗin ba, Neehal ta kama hannunsu suka shiga ɗakinta, ta adana turarukan. Bayan Magriba aka tafi ɗaukar Amarya, su Neehal kam ba a je da su ba, Mama ta ce sa je daga baya. Bayan isha'i mutane suka fara watsewa, gidan ya rage daga su Aunty Sadiya sai na nesa waɗanda za su tafi gobe da safe, Hameedah ma da Mamanta suna nan. Sai yau Mamansu Anwar ta zo ita da k'annenshi, ba ta jin dad'i ne shi yasa tunda aka fara bikin ba ta zo ba. Neehal dai tana kwance a ɗakin Mama tana ta matsar kwalla, Twins na manne a jikinta suna cin Cheese, tunda ta idar da Sallah ta haye gadon tay kwanciyarta. Hajiya ce ta shigo ɗakin tana ƴan mitocinta da ba ta rabo da su, kallon Neehal ta yi ta ce "Ke kuma lafiya kike kwance?" Neehal tay mata shiru, ta tab'e baki ta ce "Wai waɗannan Yaran ina uwarsu ne?" Daidai nan Mama ta shigo ɗakin, Hajiya ta ce "Yawwa, Ta Abuja (Da yake haka take ce mata idan fulatancin ya motso mata) yanzu nake tambayar wannan uwar langwan ta mun shiru, waɗannan Yaran waye ne haka, take ta wahala da su?" Kafin Mama ta ce wani abu Neehal ta juyo da sauri idanunta da guntun hawaye ta ce "Ƴaƴan ƙawata ne, ba ta da lafiya ba ta samu zuwa ba shine ta aiko aka kawo mun su." Mama ta kalle ta kawai, Hajiya ta ce "Ayyo, ga su kuwa kyawawa kamar Ƴaƴan Turai." Mama dake kallon Neehal ta ce "Kukan me kike?" Kafin ta yi magana Afrah ta yi karaf ta ce "Ba ta da lafiya." Da yake haka Neehal ɗin ta ce musu da suka dame ta da tambaya ganin tana kuka. Mama ta ce "Allah ya sauwaqe." Ta juya ta fice. Hajiya ta ce "Sannu gajiyar biki ce." Ciki_ciki Neehal ta ce "Yawwa." Hajiya ta fara yiwa su Afrah surutu da tambayoyi kamar wasu manya, su dai shiru kawai suka yi suna kallonta tare da ƙara lafewa a jikin Neehal, ta gaji ta tashi ta fita. Da daddare wajen 12 Mama suna zaune ita matar Yayan Daddy da Hajiya dake ta gyangyad'i, ance ta koma ɗaki ta ƙi. Neehal ce ta fito daga ɗakin Mama wadda bacci ya ɗauke ta bayan ta gama shan kukanta, yanzu ma Amrah ce ta tashe ta, idanunta kuwa har sun kumbura. Mama ta bita da kallo kafin ta ce "Wai lafiyarki kuwa Neehal, me aka miki kike kuka?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba, Mama ta ce "Ba na son halin kin nan fa, ana miki magana kina ji ki yi shiru." Neehal ta ce "Ba komai kawai dai.." sai kuma ta yi shiru, Mama ta ce "Kawai dai me?" Neehal ta ce "I start missing Yaya." Mama ta tab'e baki ta ce "Shine kuma zaki zauna kina kuka, kamar wanda ya mutu, ko ce miki aka yi ya tafi kenan?" Neehal ta ce "To ai ba zai dinga zuwa kodayaushe ba." Mama ta ce "So you can follow him ai, tunda tare aka haife ku." Matar Yayan Dad wadda ake kira da Umma ta ce "Ai da gaskiyarta dole ta yi kewar ɗan'uwanta." Hajiya data wartsake tun fitowar Neehal ta ja tsaki ta ce "Wai dama akan Ameen kike asarar hawayenki saboda baki san ciwon kanki ba, Ameen ɗin da ba wani k'aunarki yake ba, ai daɗi ma ya kamata ki ji yanzu zaki wataya babu mai ƙara takura miki a gidan nan, kafin kema Allah ya kawo miki miji ki tafi." Neehal ta turo baki gaba ta nufi kitchen dan haɗawa Amrah tea. Washegari tun safe sauran baƙi suka tafi, su Aunty Sadiya ma suna gama gyaran gidan kafin Azhar suka wuce nasu gidajen, Hajiya ma ta bi Ammin Amirah sun wuce Gombe. Gida ya rage daga Mama da Neehal sai su Dije masu aiki da Twins, sai Hameedah da Mom ɗinta da Umma wanda suma da Yamma za su wuce Abuja. Driver Mama ta aika ya kaiwa su Ameen breakfast, da rana ma haka. Neehal kam wuni ta yi a ɗaki ita da Twins ɗinta. Sai can yamma Haneefah ta zo gidan. Da daddare bayan kowa ya tafi Mama ta je part ɗin Dad su yi magana akan su Afrah, Mama tana duban shi ta ce. "Daddy yanzu sai mu san abun yi akan yaran nan, dan yanzu na san duk inda hankalin iyayensu yake a tashe yake ba kaɗan ba." Daddy ya ce "Hakane, tunda gobe Monday idan Neehal zata aiki sai mu tafi tare mu bada a yi cikiyar iyayensu, na san Insha Allahu za'a samu iyayen nasu ko a'ina suke a ƙasar nan, tunda babu inda ba'a kallon ASTV, daga nan sai mu biya wasu gidan Radios ɗin duk mu bada cikiya. Mama ta ce "Allah ya kai mu goben lafiya. Dad ya ce "Ameen, kira mun Neehal ɗin ma tunda aka fara biki haɗuwar mu ta yi wuya." Mama ta ce "Kuma a part ɗin nan take kwana, dan dai ana sha'anin biki ne." Mama ta kira Neehal a waya ta ce ta zo part ɗin Daddy. Ba jimawa ta ƙaraso tare da Twins. Mama ta ce mata "Kai Neehal kina cika wa yaran nan kayan zaƙi, duk sanda zan gansu da sweet ko chocolate a hannunsa." Neehal ta yi Murmushi tare da zama a kusa da Daddy. Ta gaida Daddy suma su Afrah suka gaishe shi, ya amsa musu cike da fara'a. Sun ɗan taɓa hira da Daddy har su Afrah suka fara bacci. Mama ta dubi Neehal ta ce "Gobe za mu je mu yi report akan yaran nan, daga nan mu biya mu ba da cikiyar iyayensu." Gaban Neehal ya faɗi, dan bata k'aunar abun da zai rabata da yaran ko na second ɗaya, ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mama data kula da yanayinta na canzawar da fuskarta ta yi ta ce "Sai ki shirya da wuri, dan ke zaki yi bayanin yanda kika tsince su." Neehal da idanunta suka ciko da k'walla ta ce "Mama gobe ya yi wuri a bari a ƙara wasu kwanaki sai a...." Kallon da Mama ta watsa mata yasa ta had'iye maganarta. Mama ta ce "Kina cikin hankalinki kuwa? Yanzu kin san irin tashin hankalin da iyayensu suke ciki na rashinsu har na kwana biyu ba su san inda suke ba." Neehal ta ce "To ni Mama ban san rabuwa da su." Mama ta ce "Uhm, ke da kika same su sama ta ka kenan, kuma dudu kwana biyu kawai kuka yi tare, amma ba kyasan rabuwa da su, balle kuma mahaifiyarsu da ta haife su ta raine su na shekaru." Neehal ta ce "Ai ba su da Uwa, ta rasu." Mama ta ce "Who told you?" Neehal ta ce "Su ne, suka ce mun Daddy'nsu yace their Mom ta tafi ba za ta dawo ba for ever." Mama ta ce "Allah ya ji k'anta, amma ai suna da Uba da dangi ko?" Neehal ta yi shiru ba ce komai ba sai hawaye take. Daddy dake kallon su Ya ce "Daughter me yasa bakya son su tafi?" Neehal ta ce "Dad I love them and kuma bana son na rabu da su, na ji ina son su sosai, kuma ga su marayu ina tausayin Maraya sosai because....." Mama ta katse ta da faɗin "Shut up, Stupid, komai za ki ce yara dai sai an maida su gurin iyayensu, duk yanda kike son su ba ki kai iyayensu ba." Tana gama faɗar haka ta mik'e ta shige bedroom ɗin Daddy. Dad ya rarrashi Neehal ta bar kukan da take sannan ya rakata part ɗin Mama da Afrah a hannunsa, ita kuma ta ɗau Amrah. Ko wanka ba ta yi ba ta kwanta rungume da yaran gam a jikinta kamar wanda za'a k'wace mata su..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:43] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *2️⃣3️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ..........Cikin ƴan mintuna suka ƙarasa gidan Ameen dake Lamido Cresent. Driver ya danna horn mai gadi Ya zo ya buɗe masa madaidaicin gate ɗin gidan, tun daga farfajiyar gidan zaka tabbatar da gidan ya haɗu gami da tsaruwa. Bayan ya yi parking Neehal ta fito Twins suka biyo bayanta, sallama suka yi da driver sannan ta nufi inda take hango ƙofar shiga ainihin cikin gidan, Mota ɗaya ta gani a harabar gidan, hakan yasa take tunanin da ƙyar in Ameen yana gidan. Hafsah tana ɗakinta a kwance ta ji ƙarar door beil, a tunaninta Ameen ne ya dawo daga masallaci hakan ya sata tashi da sauri ta fito ta sakko ƙasa ta buɗe ƙofar falon. Kamar a mafarki ta ga Neehal tsaye a bakin ƙofa, haɗe rai ta yi sosai kamar ba ta taɓa dariya ba ta shiga ƙarewa Neehal kallo, wadda ke sanye cikin doguwar riga pink colour, an mata ado da blue color, rigar ta ci guga har wani ɗaukar ido take, ta yi sosai kamar ka sace ta. Neehal ta danne zuciyarta tana murmushi ta ce "Sannu da gida Aunty Amarya." Ƙara haɗe rai Hafsat ta yi ta ce "Yawwa." Sannan ta juya ta koma ciki, Neehal ta shiga Falon bakinta ɗauke da Sallama Twins na biye da ita, suna ta murna sun zo unguwa. Kan kujera suka yi da gudu suka haye, Hafsah ta dube su kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa. Amrah ta dubi Hafsah ta ce "Ina kwana." Kafin ta gama rufe baki Afrah ma ta gaishe ta, ta amsa musu tana bin su da kallo. Neehal ta ƙaraso cikin falon ta zauna jikinta a sanyaye, a hankali ta ce "Ina yini Aunty." Hafsah kamar an mata dole ta ce "Lafiya." Daga haka ta wuce warta sama. Neehal ta bi ta da kallo duk murna da dokin zuwan da take ya koma ciki, gaba-d'aya ta ji dama ba ta zo ba, kamar ta tashi ta koma gida haka take ji, amma ta daure saboda idan ta koma gida ba ta san me zata cewa Mama ya dawo da ita ba. Falon ta shiga ƙarewa kallo, babu ƙarya falon ya haɗu, domin kuwa an narkawa Hafsah kaya. Komai dake cikin falon Dark and light purple colour ne. Neehal ta ɗauko wayarta daga cikin handbag ɗinta ta kira layin Haneefah ta sanar mata ta je gidan Ameen yau amma Haneefan ba ta ɗauka ba. Su Afrah kuwa tsalle_tsalle suka hau yi a falon, Neehal ta musu mgn su bari, ta nuna musu kusa da ita ta ce su dawo su zauna. Suka dawo suka zauna suna turo baki gaba. Har mintuna goma suka wuce Hafsah ba ta dawo gurinsu Neehal ba, kamar ma ba baƙi ta yi ba ta koma ta yi kwanciyarta. Afrah da ta gaji zama ta dubi Neehal ta ce "Aunty bari na kira Aunty'n data hau sama." Neehal ta ce "Ban aike ki ba." Yarinyar ta ɓata fuska. Neehal ta bi ƙasan Falon da kallo, tiles ɗin ta gani kamar da datti. A hankali ta tashi ta shiga duba falon ko za ta ga tsintsiya, a bakin ƙofa ta ganta tare da mopper, ɗauka ta yi ta shiga share falon, bayan ta gama ta yi mopping ɗin shi, tana cikin yi Hafsah ta sakko, da mamaki take duban Neehal, can kuma ta tab'e baki ta ce "Ina kika samu ruwan da kike mopping?" Toilet ɗin dake falon Neehal ta nuna mata da hannunta ba tare da ta yi magana ba, Hafsat ta wuce kitchen tana tab'e baki. Amrah ta dubi Neehal ta ce "Aunty zan ci abinci." Neehal ta mata shiru, har sai da yarinyar ta ƙara maimaita mata sannan ta ce "Ba ki ci abinci ba ne a gida?" Amrah ta gyaɗa mata kai tana keɓe fuska, Neehal ta yi shiru kawai dan bata san me zata ce mata ba. Hafsah ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da ruwa da lemo ta ajiye a gaban yaran, ta dubi Neehal a yatsine ta ce ki shiga kitchen ki dafa muku abin da zaku ci. Neehal ta mata wani kallo sannan ta ce "Toh." a ranta tana faɗin 'Ai ba yunwa na ce miki ina ji ba.' Daga haka Hafsah ta koma sama, ashe Ameen ne ya mata waya yana hanya shi yasa ta yi sauri ta sakko ta kawo wa su Neehal drinks dan kar ya dawo ya ga bata basu ba. Bayan Neehal ta gama mopping ɗin ta koma ta zauna tana duban su Afrah dake shan lemo, Hafsah ta ƙara sakkowa hannunta ɗauke plate ta ajiye a gaban Neehal, A hankali Neehal ta ce "Thank you." Hafsat ba ta ce komai ba ta juya ta koma sama. Cake ne da cin_cin da Donot a cikin plate ɗin, Neehal ta ce su Amrah su sakko su ci, ita kuwa ko kallon snacks ɗin bata ƙara yi ba. Su ma kaɗan suka ci suka ce sun k'oshi. Neehal ta duba time a wayarta ta ga uku saura, lumshe idonta ta yi ta kwanta akan kujera tana jin cikinta na juya mata, zuciyarta kuwa cike take da mamakin dalilin ya sa Hafsah ba ta k'aunarta, dan ita ba ta taɓa tunanin irin wannan tarb'ar daga gare ta ba, yanda tasan amare idan ka je gidajensu kamar su mai da mutum ciki dan murna amma..... Ƙarar buɗe ƙofar falon ya katse mata tunanin da take. Da Sallama ya shigo falon duk da be yi tunanin da mutane a ciki ba, dan yasan Hafsah ba ta zaman ƙasa. Waro ido ya yi ganin Twins fuskarsa na nuna mamakinsa na ganinsu. Su ma suna ganinshi suka nufe shi da gudu suna faɗin "Uncle !." Dan ɗan zuwan da Ameen yake gida sun saba da shi. Ameen ya d'aga su ɗaya bayan ɗaya ya shilla yana murmushi, yaran suka shiga ƙyalƙyala dariya sannan suka gaishe shi, ya amsa musu cikin kulawa. Afrah ta ce "Uncle nan gidanka ne?" Ameen ya mata murmushi tare da gyaɗa mata kai. Neehal wadda ta tashi zaune tun shigowar shi, cikin boye ɓacin ran Hafsah da dauriyar ciwon cikin da take ji ta ce "Sannu da zuwa Yaya." Ameen ya zauna a gefen ta yana kallonta cikin nazarta yanayinta ya ce "Yawwa." Neehal ta yi ƙasa da kanta ganin yana binta da wani irin kallo, a sanyaye ta ce "Ina yini." Ya amsa da "Lafiya k'alau, ya aiki?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Ina Haneefah fa, kika zo ke kaɗai?" ta ce "Tana Abuja ta je gidan Yayan Abbansu sai Sunday zata dawo." Ameen ya gyaɗa kai tare da bin falon da kallo, sai kuma ya dawo da dubansa ga Neehal ya ce "Ina matar gidan?" Neehal ta ce "Yanzu ta hau sama." Ameen ya miƙe hannayensa riƙe dana Twins suka hau saman, Neehal ta bi su da kallo tare da jan numfashi. Duk murna da d'okin ganin Yayan nata da take takaicin Hafsat ya sa ta ma dena. Ko minti biyar Ameen be yi da hawa saman ba suka sakko tare da Hafsah, wadda ta faɗaɗa fara'a akan fuskarta. Tana duban Neehal ta ce "Sister na bar ki ke kaɗai ko? Sorry toilet na shiga ne." Mamakin Hafsat ne ya kusa kashe Neehal, shanye mamakinta ta yi ta kirkiro murmushi ta ce "Ba komai Aunty." Hafsah ta dubi Ameen da ya zauna yana kallonsu ta ce "Honey Ka ga hira da Sister ta ɗauke mun hankali ko girki ban daura ba, duk da ma na tambaye ta mai za su ci ta ƙi faɗa mun, na ce kuma ta shiga ta girka da kanta ta ƙi, sai ka ce wata bakuwa." Ameen yana duban Neehal ya ce "Why?" Neehal ta ce "Yaya mun ci fa snacks mun k'oshi." Ameen ya ce "Snacks ai ba abinci ba ne, ki shiga kitchen ki dafa muku abun da zaku ci." Neehal ba za ta iya musu da Yayan nata ba, hakan yasa ta miƙe ta nufi kitchen ɗin." Hafsah na murmushi ta ce "Ko ke fa yar ƙanwata, amma da kin ƙi sakin jiki kamar wata baquwa." Neehal dai bata yanka mata ba ta shige kitchen zuciyarta cike da mamakin kissa irin ta Hafsah. Duk da bata jin dadi haka ta dafa musu jallop ɗin sphagetti, kafin ta gama an shiga sallar Asr, hakan yasa da ta gama ta juye a warmer sannan ta dawo falon, Twins ne kawai a falon suna kallon cartoon ɗin da Ameen ya kunna musu, Ameen ya fita Masallaci ita kuma Hafsat tana sama. Ɗakin dake falon Neehal ta shiga ta yi Sallah, bayan ta idar ta fito falo ta tarar har Ameen ya dawo, Hafsah ma ta sakko. "Sannu da aiki my sister, Allah ya saka da Alkhairi ya baki miji na gari, bari na je na ga me aka girka mana haka ne, duk muna nan k'amshi ya buɗaɗe mu yawun mu sai tsinkewa yake." Hafsah ta faɗi haka cikin iyayi tana murmushin da be kai zuci ba. Neehal ta yi ɗan murmusa kawai, dan mgn ma bata son yi saboda yanda take jin cikinta. Hafsah ta miƙe ta shiga kitchen ɗin, ɗauko warmer ta yi gaba-d'aya tare da plates da pork ta ajiye akan dinning, sannan ta ɗauko drinks shima ta aje. Ta dube su duka ta ce "Ku taso mu ci abincin." Neehal dai kamar ta ce ta k'oshi, amma ta san ko ta faɗa Ameen ba kyale ta ze yi ba sai ta ci, hakan yasa ta miƙe tana taune lips d'inta ta nufi dinning ɗin. Ameen dai kallonta kawai yake amma ya gane akwai abun da ke damunta. Duban Hafsah ya yi ya ce "Ku ci kawai am full." A karamin plate Hafsah ta zuba wa Twins na su abincin ta ajiye musu ƙasan carpet ɗin dake tsakiyar falon. Da kanta ta zuba wa Neehal abincin sannan ta zuba nata itama, ba kunya ta shiga durawa cikinta taliyar dan ta mata daɗi ba kaɗan ba. Neehal ta kasa cin abincin sai juya pork ɗin take a cikin taliyar, har taliyar ta fara sanyi. Da ƙyar dai ta daure ta tsakura ta kai bakinta, a hankali ta shiga taunawa cikin nutsuwa, Hafsat kuwa tana zuba lauma tana harararta a fakaice. Cokali uku Neehal ta ci ta ajiye pork ɗin da sauri saboda murd'awar da cikinta ya mata, dafe cikin ta yi tare da taune lips ɗinta sosai, duk yanda taso daurewa amma ta kasa, Ameen dake latsa wayarsa amma hankalinsa gaba-d'aya yana kanta ya ce "What happened?" Hafsah cikin nuna damuwa itama ta ce "Sister me ya faru?" Neehal cikin sanyi ta ce "Cikina." Ameen ya miƙe da sauri ya ƙaraso dinning ɗin yana mata sannu, miƙewa ta yi ta nufi toilet ɗin dake falon da gudu ta fara kela amai. A rude Ameen yake faɗin "Sannu, Sorry, dama ba ki da lafiya?" Neehal dai bata samu damar ba shi amsa ba, bayan ta gama ya taimaka mata ta fito tana numfarfashi ta kwanta a ƙasa, Twins suka bita da kallo. Sai da ya tsaftace toilet ɗin sannan ya fito, sai a sannan Hafsah ta yiwa Neehal sannu, tana pretending kamar ta damu, nan kwa a zuciyarta ji take kamar ta ƙarasa ta dan tsanar da take mata. Neehal ta fara nuk'urk'usu a ƙasa tana hawaye, sosai Ameen ya rude dan ya san wahalar da take sha a ciwon ciki, hakan ya ƙara konawa Hafsah rai, dan ko first night ɗinsu da bata da lafiya be rude haka ba sai a kan wannan figaggiyar yarinyar. Neehal ta riko hannun Ameen a wahalce ta ce "Yaya cikina kamar zan mutu, ka kai ni gurin Mama Please." Ameen ya tashi ya haura sama da sauri ya ɗakko car key ɗinsa ya ɗauki Neehal kamar jaririya ya yi waje da ita, Twins da ganin halin da Auntinsu take ciki yasa su kuka suka bi bayanshi da gudu. Takaici kamar ya kashe Hafsah ganin yanda Ameen ya wani gigice, tsaki ta ja ta ɗauki handbag da takalman su Neehal ta bi bayansu. Har ya kwantar da Neehal a bayan Motar su twins kuma yasa su a front seat. ajiye takalman ta yi a gaban Motar fuskarta ɗauke da jimamin ƙarya, Ameen bai bi ta kanta ba ya ja Motar ya danna horn, mai gadi ya taso da sauri ya buɗe masa gate ya fice daga gidan...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:43] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL ⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *2️⃣2️⃣* .........A ɓangaren Ango da Amarya kuwa komai ya tafi yadda ya kamata a daren da aka kaita, sai dai Ameen ya sha rawar kai a gurin Hafsat, daga baya kuma ta koma raki da shagwab'a. Sai dai abu na farko da Ameen ya fuskanta dangane da Hafsat tana da ƙarancin ilimin Addini da shi kanshi addinin ma, dan Sallah ma da asuba har ya je masallaci ya dawo ba ta yi ba tana kwance, da ƙyar ya tashe ta ta yi, duk ya san bata jin dad'i amma ai ba cutar da zata hanata Sallah take ba. Haka ɓangaren gyaran gida ma babu abun da ta taɓa da sunan gyara,duk da jikin nata ya warware, sai da ƴan'uwanta suka zo da yamma ne ma suka gyara mata gidan. Da daddare Mama ta aiko musu da dinner, bayan sun gama ci ta tashi ta bar kayan a wurin, Ameen ya bita da kallo cikin mamaki zuciyarsa cike da takaicinta, amma ya danne bai nuna ba ya kwashe kayan ya kai kitchen, wurin da suka ci abincin kuwa ko arzik'in tattarewa bai samu ba haka ya kwana. Washegari misalin ƙarfe Takwas da ƴan mutuna na safe Mama tana zaune a falonta tana karatun Alkur'ani da bata samu ta yi ba sai da ta gama haɗa musu breakfast saboda fitar da za su yi, Neehal ce ta shigon falon, tana ɓata fuska wai ita a dole fushi take ta zauna a kusa da Mama tana jiran ta gama karatun. Mama ta kai ƙarshen aya ta d'ago tana dubanta. A hankali Neehal ta ce "Ina kwana." Mama ta ce "Lafiya k'alau, Ina yaran?" Neehal ta ce "Bacci suke." Mama ta ce "Bacci kuma har yanzu? Kin san fa za mu fita." ta ce "Yanzu za su tashi sai na musu wanka." Mama ta ce "Ki sauka ƙasa ki yi break." Neehal ta miƙe ta ce "Bari na fara musu wankan sai mu yi tare." Tana komawa ɗaki ta tarar sun tashi duka suna zauna, ta ƙarasa gadon da sauri tana dubansu. Afrah ta ce "Aunty yau za mu gurin Daddy ko?" Neehal ta ce "Insha Allah." Amrah ta ce "Zaki bi mu ko Aunty?" Neehal ta ce "Ehh." Tana cire musu kaya ta ce "Wa yake muku wanka a gida?" Amrah ta ce "Baaba talatu, idan mun je gidan Mommy kuma Aunty zahrah." Neehal ta gyaɗa kai ta ce "Ku da wa kuke bacci." Amrah ta ce "Mu da Baaba Talatu." Neehal ta ce "A gidanku take itama?" Suka haɗa baki suka ce "Ehh." Bayan ta musu wanka tana shafa musu lotion Afrah ta ce "Aunty ba mu yi karatu ba, kuma kullum Daddy yana mana idan mun tashi." Neehal ta ce karatun me?" Afrah ta ce "Qur'an." Neehal ta ce "Ku biya mun naji to." Suka haɗa baki sukai basmala cikin karatun yara suka fara karanto Suratul Nas." Harta gama shirya su ba su gama karatun ba. Neehal ta jinjina wa yaran sosai a ƙananun shekarun su amma sun iya karatun, sai da ɗan gyararraki da ba za a rasa ba. Neehal ta kamo hannunsu suka sakko ƙasa suka yi break, suna gamawa ta haye sama dan yin wanka su kuma ta barsu a falon suna kallo tare da su Dije. Wajen ƙarfe tara Ameen ya kira Mama, ya gaisheta ta tambaye shi lafiyar Hafsah ya ce tanan k'lu. Kafin ƙarfe goma sun fita, duk inda ya kamata su je sun je dan bayar da cikiyar su Afrah, Neehal dai kamar ta zunduma ihu haka take ji, a hanyarsu ta dawowa kuwa suna Mota ta saka kuka, dan ji take kamar har anga ƴan'uwan su Afrah sun karɓe su, Mama ta mata tsawa ta ce "Ta rufe musu baki kar ranta ya ɓaci." Daddy kuma ya rarrashe ta. Wajen 1 suka koma gida, ɗakinta ta yi wucewarta da Twins ta kulle suka kwanta, hakan yasa baccin dole ya ɗauke su dukan su. Sai da 3 ta wuce Mama ta buga mata ƙofa dan su tashi su ci abinci. Bayan Sallar la'asar ma ta ƙara jan su daki ta samu game a wayarta ita kuma ta kwanta, Mama dai kallonta kawai take duk abun da take ba ta kuta ba. Har Ameen ya zo gidan da Yamma ya tafi ba ta sani ba tana ɗaki. Wunin yau ko kiranta aka yi a waya sai gabanta ya faɗi saboda tunanin ko ƴan'uwan su Afrah ne, dan Numbern'ta aka bada idan iyayen yaran sun ji cikiyar su kira. Bayan Magriba Mama ta kwankwasa mata ƙofa, ta taso ta buɗe, Mama ta ce mata "Ki sauka ƙasa Sadik yana jiranki, ya kira wayarki dan iskanci kika ƙi d'agawa." Neehal ta ce "Ban gani ba wayar na silent." Mama ta ce "Ke kika sani, kuma ki fito da Yara su shaƙata in ke kin zaɓi zaman ɗaki su ba za su yi ba." ta ce "Toh." Mama ta yi wucewarta. Hijabi ta zira ta kamo hannunsu suka fito, suna ta murna sun ɗauka fita za su ta yi. Sadik yana zaune yana latsa waya, k'amshinsa ya cika falon gaba-d'aya, Mama ta sa su Dije sun kawo masa drinks da abinci. Neehal ta yi masa sallama tare da zama a kujerar dake gefen ta sa, ya amsa mata yana kallonta. Su Afrah kuwa suna can gefe sun samu kallo. Sadik ya ce "Ya gajiyar biki kuma?" Neehal da ta ƙi d'agowa ta ce "Babu gajiya, ya kaje gida.?" Ya ce "Lafiya k'alau." Suka yi shiru, ita tana wasa da yatsun hannunta shi kuma yana danna waya, can dai ya katse shirun da faɗin "Na yi tunanin ma bakya nan dana kira wayarki ba ki ɗauka ba, shigowa na yi in gaida Mama sai ta ce kina ciki." Neehal ta ce "Uhm ina kwance ne." Ya ce "Ba ki da lafiya ne?" Ta ce ",Lafiyata k'alau." Ya yi shiru yana kallonta na wasu sakanni, duk ta ƙi d'ago kanta amma ya fahimci tana cikin damuwa. Murya ƙasa_ƙasa seriously ya ce "Me ke damunki to?" Numfashi ta ja jin yadda ya yi maganar ta girgiza masa kai, ya ce "Neehal!." Ta d'ago da kanta a hankali ta ce "Na'am." Ya ce "Har yanzu baki saki jikinki da ni ba, baki ɗauke ni a matsayin brother ɗinki ba kamar yadda na ɗauke ki as my sister." Neehal ta yi shiru, Sadik ya ce "Okay thank you." Ganin yana ƙoƙarin miƙewa ta marairaice ta ce "I'm sorry ya Sadik, dan Allah kar kace haka, wlh ba haka ba ne." Ya ce "Ya ya ne?" Ta sauke numfashi cikin rashin sanin ta ina zata fara masa bayanin damuwarta, dan tabbas tana buƙatar share problem ɗinta da wani ko zata ji sauƙi a ranta, ita kanta tana mamakin yanda aka yi take son yaran haka." Sadik ganin ta yi shiru ya ce "Kar ki damu ba sai kin faɗa mun abunda ke damunki ba, but i promise you zan taya ki da addu'a." Neehal ta ce "No I will tell you now." A hankali ta shiga bawa Sadik labari tun daga time ɗin data tsinci su Afrah har zuwa yau. Sadik dake kallon ta ya ce "Gaskiya Mama take faɗa Neehal, ki yi imagine ace yaran nan yanda suke hannunki yanzu kawai ki tashi ki neme su ki rasa, na san hankalinki zai tashi ba kaɗan ba, to duk tashin hankalin da zaki yi ba za ki kai iyayensu ba, dan haka Mama ta fiki gaskiya. And please kuma ki dena damuwa akan hakan, yaran nan ko da sun koma gurin iyayensu ai hakan ba yana nufin kun rabu ba kenan, duk time ɗin da kike son ganinsu zaki je ki gan su kin ji." Neehal ta jinjina kai cikin gamsuwa da bayaninsa, ya ce "Yawwa sisina, ki kuma je ki bawa Mama hak'uri." Neehal ta ce "Insha Allah, na gode." Ya yi mata murmushi mai taushi yana jin sonta tamkar zai fasa masa zuciya. Cikin kankanin lokaci Neehal ta saki jikinta suka shiga hira da Sadik, sai gata tana ƙyalƙyala dariya kamar ba ita ce take ta k'unci ba d'azu." Har kusan Tara da rabi Sadik bai tafi ba, duban agogon hannunsa ya yi da waro ido cikin mamaki ya ce "Haka dare ya yi ba mu yi Sallah ba, lallai yau hira ta yi daɗi." Neehal ta turo baki gaba ta ce "Yanzu sai ka ce zaka tafi ko?" Ya ce "Ehh mana, ko so kike Maamah ta rufe mun gida." Neehal ta ce "Sai ka kwana anan." Ya mata wani kallo ya miƙe ya ce "Wataran zan kwana not now." Miƙewa ta yi itama ta ce "Allah ya kai mu wataran ɗin, mu je in raka ka." A bakin part ɗin Mama suka tsaya suka yi sallama, har cikin ranta take jin dama kar ya tafi, dan yana ɗebe mata kewa ba kaɗan ba." Tana dawowa falo ta lek'a ɗakin su Dije ta ga ba su yi bacci ba hirarsu suke yi hakan yasa ta ce musu su kawo mata su Afrah sama, wanda tuni sun yi bacci. Ɗakin Mama ta shiga ta tarar da ita tana operating system. "Sannu da aiki Mama." Ta faɗa lokacin da take zama a kusa da ita, Mama ta ce "Yawwa sai yanzu ya tafi?" Ta ce "Eh." Mama ta ce "Ina yaran?" "Sun yi bacci." Neehal ta amsa, Mama ta ce "Sun dai ci abinci ko?" Neehal ta ce "Na basu popcorn kafin mu fito." Mama ta ce "Popcorn abinci ne?" Neehal ta ce "Da yawa suka ci ai, kuma da suna jin yunwa za su faɗa mun." Mama ta ce "Alright." Neehal ta ɗan yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce "Mama ki yi haquri akan abin da na yi, na gane gaskiya kika faɗa." Mama ta ce "Shikenan na ji dad'i da kika gane haka, wai har yanzu ba'a kira ki ba akan Yaran nan? tun d'azu nake so na tambaye ki kuma sai na sha'afa." Neehal ta ce "Ba a kira ba." Mama ta d'ago ta dube ta karon farko tun shigowar ta ɗakin ta ce "Bana son ƙarya fa Neehal kin sani, ki faɗa mun gaskiya ko sun kira." Neehal ta ce "Allah Mama ba'a kira ba, sai dai ko yanzu da na sauka ƙasa." Mama ta ce "Amma na yi mamaki, more than five Radios banda Televisions amma a ce ba'a samu wanda ya san su ba, Sadiya ma ta kira ni ta tambaye ni, Dad ma haka." Neehal ta ce "Nima Mama na yi mamaki, dan ko kirana akai sai na yi tunanin ko su ne." Mama ta jinjina kai kawai, Neehal ta ce "Mama kun yi waya da Yaya kuwa?" Mama ta ce "Ya zo ma d'azu." Neehal ta waro Ido ta ce "Amma shine bai neme ni ba." Mama ta ce "Ya tambaye ki na ce kina ɗaki a kwance, ko kina ta k'uncin zan je in kira ki ne." Neehal ba ta ce komai ba ta tashi ta fice tana turo baki gaba, cikin takaicin Ameen ya zo amma ba su haɗu ba, shima kuma ko ya shigo ɗakin ya ganta. Gyarawa su Amrah kwanciya ta yi ta cire Hijab ɗin jikinta ta shiga toilet dan ɗauro alwala. Goma saura Sadik ya ƙarasa gida, kamar yadda ya yi zato duka ƴan gidan nasu suna zaune a falon har Abbansu, bakinsa ɗauke da Sallama, gaba-d'aya suka zuba masa ido tare da amsa masa sallamar. Kusa da mahaifiyarsa ya je ya zauna a ƙasan kujerar da take ya mata sannu da gida, sannan ya gaishe da Abbansa da kishiyar Maamah wadda suke kira da Umma, k'annenshi kuma suka gaishe shi. Abbansa ya ce "Abubakar daga ina haka?" Sadik ya yi ƙasa da kansa tare da shafa sumar kansa, Abban ya kalli Maamah Wadda ke murmushi ƙasa_ƙasa yana murmushin shima, Umma kuwa tab'e baki ta yi ta ce "Hmmmm, Sadik dai ya soma ɓata wayonsa da yawon dare, da dai ba ya yi amma yanzu....." "Wacce irin magana ce wannan Ruqayyah kike yi?" Abba ya katse Umman a ɗan fusace, Maamah da annurin fuskarta ya ɗauke lokaci ɗaya jin kalaman Umma ta sauke numfashi cikin jin daɗin yanda Abban ya katse Umman ga aikabata mata ɗa da take ƙoƙarin yi." Sadik ma ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin yanda zugar Umman bata samu shiga ba a gurin Abban kamar yadda ta saba kodayaushe. Umma ba ta da aiki sai yi masa sharri a gurin Abbansa, kuma Maamah ba ta isa ta yi magana ba sai ta saka kuka ta ce tana nuna mata iko akan Sadik dan ta ga ita ba ta ƴaƴa maza, ai itama ɗanta ne ba zata cutar da shi ba. Shiru Umma ta yi ganin yanda Abban ya haɗe rai. Shima Abban shiru ya yi ganin yaransu na falon, miƙewa Sadik ya yi ya nufi bedroom ɗinsa dan yana da aikin da zai yi akan wani case da yake bincike akai. Asalin Mahaifin Sadik mutumin Kano ne, ɗan kasuwa ne da yake da rufin asirinsa dai_dai gwargwado. Mahaifiyar Sadik kuma ƴar asalin garin Maiduguri ce kabilar Shuwa, aure ne ya kawo ta Kano. Fara ce kyakkyawa ga gashi har baya, a gurinta su Sadik suka gado kyau. Umma kuwa ƴar asalin jihar Kano ce, iyayenta a cikin gari suke, Maamah ba ta fi shekara 5 da aure ba Abba ya auro Umma, lokacin an haifi Sadik yana yaro. Ana zaton wuta a mak'era sai aka same ta a masak'a, domin kuwa Umma ce take da tsananin kishi da shegen makirci, ita kuwa Maamah da zuciya ɗaya take zaune da Umma, kuma duk kasancewarta Shuwa ba ta nuna wannan kishin na hauka, ga ta da haquri da addini. Su Sadik su biyar ne kawai a gurin mahaifinsu, a ɗakinsu su uku ne, Shine babba sai k'aninsa mai bi masa Bashir, sai autarsu Batul. Ita kuma Umma ƴaƴanta biyu kuma duk mata ne, kuma ta fi shekara goma kafin Allah ya bata haihuwar. Makirci kala_kala Umma ta dinga haɗawa Maamah a gurin Abba kafin ta haihuwa, wai Maamah tana mata gorin haihuwa. Hakan yasa Abba ya ce ƴaƴan Maamah itama ƴaƴan ta ne tunda Ƴaƴansa ne dan haka tana da iko akansu. Tun daga wannan rana fa Umma ta samu damar yiwa Sadik sharri iri_iri a wajen Abbansa, a matsayin tana faɗa masa gaskiya wadda Maaman take bo'yewa a cewar ta, kasancewar Abba matafiyi ne bai fiya zama a gari ba, saboda sha'anin kasuwancinsa. Haka Abba zai samu Sadik yay ta masa faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, itama Maamah bata tsira da faɗan Abban. Inda Allah ya taimaka kakarsu Sadik mahaifiyar Abba tana son su sosai, to wani sharrin idan Umma ta k'ulla ita take taka mata burki ta ci mata mutunci, ta kuma hana Abba ɗaukar hukunci akan Sadik ko Maamah. Ita kuwa Maamah kullum cikin tausar Sadik take tana ba shi baki akan Abinda Umma take masa, duk da abun na damunsa amma haka yake haquri ba ya nuna ɓacin ransa saboda nasihar mahaifiyarsa. Bashir ne ma sarkin zuciya wataran yake ƙoƙarin tankawa Umma idan ta ƙure shi akan abun da takewa Mahaifiyarsa da ɗan'uwansa, duk da shi ɗinma tana masa ba tsira ya yi ba, amma shi tana ɗan shayin shi ganin yaron a tsaye yake, Sadik kuwa haqurin mahaifiyarsa ya ɗauko shi yasa tafi raina shi kuma tafi tsanar shi. Misalin ƙarfe 11 na dare Maamah ta kwankwasa masa ƙofa, yana zaune gaban laptop, ya d'ago ya dubi ƙofa tare da faɗin "Come in." Maamah ta shiga bakinta ɗauke da Sallama, ya amsa mata ya ƙara da faɗin "Au Maamah ke ce, na ɗauka ma Basheer ne." Maamah tana murmushi ta ce "Ni ce Son ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah gashi muna ta fama." Maamah ta ce "Allah ya taimaka ya bada sa'a." Ya amsa da "Ameen." Cikin ladabi. Maamah ta dube shi ta ce "Daga ina kake ne Sadik?" Sunkuyar da kanshi ya yi yana murmushi ya ɗan sosa kai ya ce "Gidan su Neehal." (Da yake Maamah ta san Sadik yana zuwa gurin Neehal.) Maamah ta yi murmushi ta ce "Ka baro su lafiya?" Ya ce "Eh, tana gaishe ki ita da Mama." Ta ce "Ina amsawa." Ta miƙe tay masa sai da safe sannan ta fice zuciyarta fal da farin ciki, kullum addu'arta Allah ya bawa Sadik mace ta gari yay auransa ko ya huta da addabar Umma da kuma faɗan mahaifinsa, tunda ba su isa dai sun bi shi gidansa sun masa ba. Washegari Mama ta koma bakin aiki, Neehal kuma gidansu Haneefah ta je dan yi musu ban gajiya ita da Twins ɗinta. Bayan sati ɗaya, Neehal ta koma gurin aiki, kuma har yanzu babu wanda ya kira akan su Afrah. Kullum Mama cikin saka ran kira take amma sai ta ji shiru, abun yana ɗaure mata kai sosai, dan yanda aka baza hotunan su Afrah a gidajen Televisions ya ci ace wani nasu ya gani, kuma kullum sai an yi cikiyar iyayensu a gidajen rediyo da Talabijin. Yau Juma'a Neehal aikin safe ta yi, 12pm da mintuna ta dawo gida, kasancewar Ran Monday za su yi resuming School Mama ta ce ta shirya ta je gidan Ameen, kar ta koma School ta zo bata samu damar zuwa ba, tunda every weekend tana gurin aiki, Monday to Friday kuma tana school. Ameen ɗin kuma yana ta yiwa Mama mitar ta hana Neehal zuwa gidansa. Neehal murna kamar ta kashe ta dan ba ƙaramin kewar Yayan nata ta yi ba, dan tunda yay aure ko waya ba su taɓa yi ba, kuma kusan kullum sai ya zo amma ba sa haɗuwa, duk time ɗin da zai zo tana gurin aiki. Cikin Sauri ta shirya Twins ɗinta itama ta shirya, ana sakkowa daga masallaci Driver ya tafi kai su, dan ita ba ta san gidan ba, duk da tana jin mararta na mata ciwo kaɗan_kaɗan amma ta daure, dan tana faɗa Mama cewa za ta yi ta fasa zuwan wani lokacin ta je, ita kuwa zuciyarta cike take da kewar Yayan nata............✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:44] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *2️⃣4️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ...........Direct gida Ameen ya nufa da ita, domin ya san duk taimakon da za a bata a asibiti Mama za ta bata. Mama tana zaune a falo tana azkar ɗin yamma ta ga Ameen ya shigo mata da ƴa a hannu, a ruɗe a tashi tana dubansa ta ce "Al'ameen me ya same ta?" Sai da ya kwantar da Neehal a kan kujera sannan ya ce "Mama ciwon cikinta ne ya tashi." Mama ta ƙarasa inda take tana mata sannu, Neehal dai hawaye kawai take. Mama ta ce Ameen ya kai mata ita sama bari ta haɗa allura ta mata, insha Allah ciwon zai lafa mata yanzu. Bayan 10 minutes Neehal har ta samu bacci saboda allurar da Mama ta mata, Mama dake zaune a gefen ta ta sauke ajiyar zuciya cikin tausawa Neehal ɗin, gyara mata kwanciya ta yi daga ruf da cikin da ta yi sannan ta fice. Ameen yana falo tare da Twins har time bai tafi ba. Ameen ya dubi Mama ya ce "Ya jikin nata?" Mama ta ce "Alhamdulillah ta samu ya lafa mata har bacci ya ɗauke ta, dama haka ciwon nata yake kamar aljanu, lokaci ɗaya zai zo amma tana shan magani ko aka mata allura zata ji sauƙin shi 70%." Jinjina kansa ya yi kawai, a ransa yana mamakin wannan ciwon nata da baya jin magani, dan idan bai manta ba kusan 10 years kenan Neehal take fama da shi. Sun ɗan taɓa hira da Mama akan rashin bayyanar wanda ya san su twins har yau, sannan yay wa Mama Sallama ya tafi. Ko da ya koma gida Hafsah bata nuna masa komai na ɓacin rai ba, sai ma tambayarsa jikin Neehal da ta yi. Washegari da Neehal ta tashi lafiya k'alau ta tashi, sai dai ɗaurewar ciki kawai wanda duk lokacin period ɗinta haka yake mata, sai ta gama take jin ta normal. *ABUJA* Tun ranar da aka ba da cikiyar su Afrah misalin ƙarfe goma 12 na rana, budurwar nan ce zaune a falon gidansu tana kallon ASTV, 12 na yi aka fara labaran rana. Hankalinta ba ya kan TV'n dan bata damu da kallon labarai ba, kamar an ce ta d'ago idanunta suka sauka a kan hotunan twins ana cikiyar iyayensu. Wata muguwar zabura ta yi gabanta na tsananta bugu, ba ta san sanda ta cillar da wayar hannunta ba a matuƙar razane cikin ƙaraji ta ce "What?" Mahaifiyarta ce ta fito daga bedroom tana dubanta da kyau ta ce " *Safeenah*! Ke da waye na ji kamar kina ƙara?" Tattaro nutsuwarta ta yi ta lalubi remote ta kashe TV dan kar mahaifiyartata ta ga cikiyar su Afrah da ake, ta sunkuya ƙasa ta ɗauki wayarta sannan ta dubi Mahaifiyartata ta ce "Ba komai Momma." Daga haka ta miƙe ta shige ɗakinta gumi na karyo mata ta ko ina a jikinta. Tab'e baki Momma ta yi ta wuce kitchen. Wani narkeken ashar Safeenah ta danna ta fara zarya a ɗakin a fili take faɗin "Lallai Gaye ya ha'ince ni, amma wallahi sai ya yi dana sanin cin amanata da ya yi." Ganin surutu ba mafita ba ne a gareta yasa ta ɗauki wayarta data cillar akan gado ta lalubo Numbern Aminiyarta kuma abokiyar shawararta. Bugu ɗaya ta ɗauka cikin tsananin tashin hankali Safeenah ta fara mata magana. "Na shiga uku Saudart, Gaye ya cuce ni ya ha'ince ni ashe Yaran nan be kashe su ba yar da su ya yi." "Ke wa ya faɗa miki haka?" Saudat ta tambaye cikin tarar numfashi. Safeenah na kuka ta ce, "Gashi nan na gani ana cikiyarsu a gidan TV an tsince su a Kano, yanzu ya zan yi ƙawata dan Allah ki ba ni shawara, ina tsoron kar asirina ya tonu." Ta ƙarashe zancen tamkar Numfashinta zai bar jikinta saboda tashin hankali. Saudat ta ce "Kin ga ƙawata ki kwantar da hankalinki, in dai ina raye ba zan bari hawayenki ya zuba ba, ki bani nan da zuwa yamma zaki sha mamaki, Gaye kuma zamu haɗu da shi zai san mu ya ha'inta." Safeenah zata yi magana ta ji wayar ta katse, zama ta yi a ƙasa dab'as tare da dafe kanta cikin rashin sanin abun yi. Ta san Saudat shu'umar kanta ce, yarinya ce mai buɗaɗɗan ido, ga shegen bin bokayen tsiya, a makarantar ABU Zaria suka haɗu da Safeenah har suka zama abokan juna. Ita Saudat ƴar cikin garin Zaria ce, ita ta bawa Safeenah shawarar tasa a sace su Afrah a kashe su, ita kuma ta haɗa ta da su Gaye sukai mata aikin. Yinin ranar cikin fargaba da tsoro Safeenah ta wuni, har wata yar ƙaramar rama ta yi, kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin firgici. Kamar yadda Saudat ta mata alƙawari da yamma ta kirata ta shaida mata ta je gurin wani boka ya mata aiki akan ko da mutum ya ga cikiyar su Afrah a rufe bakinsa ya kasa magana akai, kuma ta tabbatar mata aikin bokan tamkar yankan wuk'a yake. Wannan magana ta Saudat ita ta sanyaya wa Safeenah rai, domin kuwa ta tabbatar aikinsu ya ci tunda gashi har an fi sati amma babu wanda ya yi magana akan ya ga cikiyarsu Afrah da ake ta yi, kuma inda an gani za ta ji labari tunda gidansu ɗaya da Kakarsu Afrah ta wajen uwa, Safeenah ƙanwar mahaifiyar Su Afrah ce ubansu ɗaya. (Tsafi gaskiyar mai shi, Allah ka tsare mana imaninmu, Ameen ya Allah.) Su kam gidansu Mahaifin su Afrah ba su da nutsuwar wani kallon TV, kodayaushe suna zaryar asibiti hakan ya sa ba su ga cikiyar da ake ta yi ba. A ɓangaren su Kakarsu Afrah ta wajen uwa ma haka ne, tashin hankali bai barsu damar wani kallon TV ko sauraren Radio ita ƴaƴanta ba, hakan ya sa suma ba su ga cikiyar ko sun ji ta ba. Ranar Laraba Neehal ta dawo daga school da yamma ta tarar da Aunty Sadiya wadda zuwanta kenan gidan daga wurin aiki ta biyo ta gidan. Neehal ta rungume ta tana faɗin "Auntyna oyoyo." Aunty Sadiya na murmushi ta ce "Oyoyo my Daughter, Ya school?" Neehal ta ce "Alhamdulillah, sai yau ma ni na koma." Aunty Sadiya ta ce "Allah ya taimaka, saura semester uku ku gama ko?" Neehal ta ce "Insha Allah." Mama ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da ruwa da glass cup, ta ajiye a gaban Aunty Sadiya, Aunty Sadiya ta ɗauki ruwan tana faɗin "Sannu Yaya, kamar wata baquwa sai kin kawo mun drinks." Mama ta ce "Ai na ga daga gurin aiki kike, kuma yanayinki ya nuna kin gaji." Aunty Sadiya ta ce "Hmmm bari kawai Yaya, yau tun 7 na fita office sai yanzu na samu kaina, case ɗin wannan Yarinyar da na ce miki an mata fyaɗe ne har yanzu ya ƙi ƙarewa, so kike ku murd'e gaskiya ƙarshe ma idan ba ai wasa ba su kori shari'ar." Mama ta ce "Ai Allah ya fi su, kuma insha Allahu zai baku nasara." Aunty Sadiya ta ce "Allah ya amsa." Neehal ta dubi Mama tana turo baki gaba ta ce "Mama na dawo fa." Mama ta ce "Ai na ganki." Neehal ta ce "Ai ba ki yi welcoming ɗina ba." Mama ta ce "To bari in ɗauke ki in goya ki uwata." Neehal ba ta ce komai ba ta tashi ta wuce sama tana ɓata rai. Aunty Sadiya ta yi murmushi zuciyarta cike da tausayin Neehal. Neehal tana shiga ɗakinta ta tarar da twins sun ba je kayan kwalliyarta akan gado suna ta yaɓa wa fuskarsu. Suna ganin ta shigo suka fara kifkifta idanuwa, dan tasha yi musu faɗa akan in ta fita su daina yi mata b'arna a ɗaki. Cike da takaici take kallonsu, ganin yanda suka bata jikinsu da bedsheet da janbaki, ta ƙaraso cikin ɗakin tana faɗin "Sannun ku da aiki." Afrah ta nuna Amrah ta ce "Aunty ita ta ɗakko miki." Amrah tai sauri ta ce "Ba ni ba ce ita ce." Neehal ta ce "Ku sauka ni ku bari guri." Sauka suka yi daga kan gadon da sauri suna mutsitstsika janbaki a ƴan'yatsunsu. Tattare kayan da suka barbazar mata akan gadon ta yi, sannan ta cire zanin gadon ta kai toilet. sai da ta sake wani sannan ta kamo su Afrah ta cire musu kayan jikinsu ta musu wanka, sukwa sai murna suke an ƙara yi musu wanka, dan suna k'aunar wanka a rayuwarsu suga suna ta facal_facal da ruwa. Bayan Mama ta kawo wa Aunty Sadiya abinci ta ci, sannan ta tattara duka hankalinta akan Mama ta ce, "Yaya maganar Neehal ce fa ta biyo da ni." Mama ta ce "Ina jinki Sadiya me ya faru." Aunty Sadiya ta sauke numfashi cikin jimanta al'amarin ta ce "A binkicen da na yi ya nuna mun Mutum ɗaya ne yake kisan Jamil da Anwar!" Dammmm! Gaban Mama ya yanke ya faɗi, a razane ta ce "Ke ko Sadiya wacce shaida kika gani data tabbatar miki da haka? Kuma waye yake kisan?" Aunty Sadiya ta ce "Alamomi da yawa ne suka nuna hakan Yaya, sai dai kuma har yanzu ba mu gano wanda yake kisan ba, amma muna nan muna binkice a kan hakan kuma insha Allahu sai mun gano ko waye." Mama ta ce "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, wannan wanne irin abu ne? wanene yake bin yarinyar nan da irin wannan sharrin? Me tai masa yake ɗaukar wa rayuwarta wannan mummunan matakin?" Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce "Shine abun da muke son sani muma." Ƙarshen tashin hankali Mama ta shiga da jin wannan batun, da har hankalinta ya kwanta ta fara tunanin ko ba dan Neehal ake kisan ba, amma kuma jin wanda ya kashe Jamil shi ya kashe Anwar ya tabbatar mata da sanadin Neehal ake kisan. Duk yanda Aunty Sadiya ta so kwantar wa da Mama hankali amma hakan ya gagara, dan sosai hankalinta ya tashi da jin wannan K'ADDARAR da ta shigo cikin rayuwar Neehal, abun da yake ƙara tadawa Mama hankali shine idan ta tuna ta yanda MAHAIFAN Neehal suka bar gidan duniya, ta matsu Daddy ya dawo ta labarta masa wannan mummunan labarin dan su san ta inda za su ɓullo wa al'amarin. Misalin ƙarfe goma sha ɗaya da mintuna na dare, Neehal ce kwance akan makeken gadonta Amrah kwance a kirjinta tana bacci, Afrah kuma ta rungume ta ta baya itama tana baccin. Hotuna take kallo a wayarta idanunta na zubar da hawaye tamkar an kunna famfo, a fili ta fara magana kamar haka, "UMMANAH, ABBANA, JAMIL ƊINA, ANWAR ƊINA, Allah ya ji k'anku ya gafarta muku, ya sa kuna cikin aljannatur firdausi, Allah ya toni asirin duk wanda yake da hannu a kisanku." Kuka ta shiga rerawa ƙasa_ƙasa cikin tausayin kanta, rayuwarta ta baya na dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, kewar mahaifanta na ƙara mamaye dukkan zuciyarta, ta rasa me yasa yau suke ta faɗo mata a rai tun da ta tashi, ta daɗe tana kukan kafin bacci barawo ya yi gaba da ita. *ASALIN LABARI..........✍️* _*Ku yi haquri da wannan, yau na yi busy ne.*_ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:44] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *2️⃣5️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ............Alhaji *Muhammad Gabasawa*, Haifaffen garin Kano ne a wani ƙauye dake ƙaramar hukumar Gabasawa, mahaifiyarsa da mahaifinsa duk na can ne. Neman kuɗi ne ya kawo shi cikin birnin Kano tun yana saurayi gurin wani cousin ɗin mahaifinsa wanda suke kira da Baffa. Su biyu rak iyayensu suka haifa a duniya, daga shi sai Yayarsa mace, itama tana zaune a Gabasawan anan take aure. Gidansu babban gida ne a garinsu kuma sananne, kasancewar gidan yawa ne kuma kakansu na da arzik'i. Kayan masarufi suke siyarwa a ƙofar Nasarawa shi da k'anin Babansa wanda yake zaune a gurinsa, kuma Alhamdulillahi suna samu sosai. K'anin baban nasa (Baffa) wanda yake gurinsa yana riƙon yarinya sunanta *FATIMA* ƴar wansa ce uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, Fatima marainiya ce mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama, da a gurin kakarta wadda ta haifi su Baffa take a Gabasawa, daga baya kuma Baffa ya ɗauko ta ya ci-gaba da riƙon ta. Soyyayyace ta shiga tsakanin Fatima da Muhammad har ta kai su ga yin aure suka tare a nan qofar Nasarawa, Muhammad ya kama musu hayar gida ɗaki ɗaya. Fatima ita kaɗai ce Ƴa a gurin mahaifinta, amma a gurin mahaifiyarta su uku ne, kasancewr mahaifinta ya rasu da dadewa har mahaifiyarta ta ƙara aure a wani gidan ta haifi maza guda biyu. Shekar Fateemah biyu da aure ta haifi ɗanta Namiji, sai dai bayan suna ba jimawa ya dinga wani irin ciwo har ya ce ga garinku nan. A lokacin ne kuma Muhammad ya samu aiki a Company'n wani hamshaqin Alhaji, kasancewar ya yi karatun boko amma iya secondary ya tsaya saboda halin rayuwa. Bayan shekara Fatima ta ƙara haihuwar ƴarta mace, sai dai itama watanni ta yi ta ce ga garinku nan. Hankalin Fateemah ya fara tashi garin tana haihuwa yaran na mutuwa, Muhammad ne ma ke tausar ta yana bata baki. A ƙauye kuwa mahaifiyarta da Kakarta suna ta aiko mata magungunan Hausa, a cewarsu jeji ne ke kashe yaran nata. A wannan lokacin suka tashi daga ƙofar Nasarawa suka koma Gadon k'aya inda Muhammad ya gina gidansa madaidaici mai kyau. Lokacin ne kuma arzik'i ya fara bunƙaso masa, saboda mutumin da yake aiki a wajensa mutumin kirki ne ga kyauta ga jama'a, kuma yana jin dad'i aiki da Muhammad kasancewar sa mai gaskiya da riƙon amana, hakan yasa ya ƙara masa matsayi a Company'nsa da suke sayar da takin zamani. A wannan shekarar ne kuma Muhammad ya ziyarci ƙasa mai tsarki ya sauke farali. Sai da aka kusa shekara biyu sannan Fateemah ta ƙara samun wanin cikin, addu'a suka duk'ufa ita da Alhaji Muhammad akan Allah ya yara mata abun da zata haifa, wannan karan ma mace ta haifa, cikin ikon Allah yarinya ta fara girma ba kamar sauran ƴan'uwanta ba, farin ciki a gurin Fateemah da Muhammad da ba zai faɗuba, sai dai watannin yarinyar bakwai ta ce ga garinku nan. Ko kaɗan Fateemah bata nuna damuwarta sosai ba, zuwa lokacin ta sare ta karbi ƙaddarar da Ubangiji ya dora mata, k'annenta Umar da Usman su ta karb'o daga gurin mahaifiyarta ta ci-gaba riƙe su a gurinta, dan gidan da mahaifiyartata take aure ba wani jin daɗin shi take ba, ana dai zaman haquri ne kawai. Umar da Usman suka ci-gaba da zama a gurin yayarsu cikin jin daɗi, lokacin ma sun fara zama samari. Alhaji Muhammad shi yake musu komai babu abun da ya rage su da shi. Fateemah ba ta yi boko ba amma ta yi ilimin Addini dai_dai gwargwado, dan da auranta ma ta yi saukar Alqur'ani mai girma a makarantar matan auren da take zuwa. Fateemah macece mai haquri ga kawaici babu ruwanta, shiyasa mijinta yake jin daɗi zama da ita. Watarana cikin dare Fateemah ta tashi da wani irin murd'awar ciki, tayta nurququsu ba tare da Alhaji Muhammad ya sani ba, har ta samu cikin ya lafa mata, sai dai kuma tana koma wa ta kwanta ta ji wani irin amai ya taso mata, da gudu ta tashi ta yi toilet ta shiga kelaya aman, kakarin amanne ya tashi Alhaji Muhammad daga bacci, sosai ya tausaya mata yay mata sannu. A wannan daren ta yi aman ya kai sau uku, ga zazzaɓi mai zafi daya rufe ta. Da safe kuma cikin ikon Allah sai ta tashi jikin da sauk'i sosai. Haka tai ta yi har kwana uku tana zazzaɓin dare, ranar na huɗu Alhaji ya ɗauke ta suka je asibiti aka dubata, gwajin farko likita ya tabbatar musu tana ɗauke da juna biyu. Murna a gurin Alhaji Muhammad ba a magana, Fateemah kam yak'e kawai take duk da ba ta san abun da Allah ze yi ba. Sosai Fateemah take shan wahala a wannan cikin kamar ba za ta kai ba, laulayi take mai wahala, ba ta iya bacci cikin dare sai kusan asuba yake ɗauke ta, kakarta ita ta zo daga Gabasawa take zaune da ita, dan ko aiki ba ta iya wa. Haka suka cigaba da rainon cikinsu har ya shiga watan haihuwa, tun cikin yana wata bakwai idan ka ga Fateemah sai ka zata ta kusa haihuwa saboda girman cikin. Ranar wata Juma'a ta tashi da nak'uda, cikin ikon Allah kuma ba ta wani sha wahala ba ta santalu ƴaƴanta guda biyu duk mata. Zo ku ga murna gurin Alhaji Muhammad da Fateemah dama sauran ahalinsu baki ɗaya, yaran kyawawa kamar Fateemah sak suka yo, sai dai ɗaya fara ce ɗayar kuma chocolate color kamar Fateemah. Wadda ta fi farin ita aka haifa sannan mai duhun. A ranar aka sallame su suka dawo gida. Kusan ɗaki guda Alhaji Muhammad ya cika da kayan babies saboda tsananin farin ciki, kodayaushe cikin addu'ar Allah ya bar masa rayan yake. Bayan kwana uku da haihuwarsu da daddare ɗaya daga cikin yaran Allah ya amshi abarsa, Hussainar ce ta rasu mai duhun kenan. Kuka sosai Fateemah ta yi akan rasuwar yarinyar, domin ba ta taɓa jin k'aunar ƴaƴan da take haifa ba kamar waɗannan Twins ɗin, ga fargabar itama ɗayar kar ta mutu. Alhaji Muhammad ya ji mutuwar yarinyar sosai shima, haka dai aka yi sunan ɗayar, Ranar suna ta ci Sunan mahaifiyarta *Fateemah Zahra* amma *NEEHAL* za'ana kiranta da shi. An sha Suna sosai wanda duk haihuwar Fateemah ba'a taɓa yin kamarsa ba. A wannan lokacin ne kuma Umar k'anin Fateemah ya gama karatun Secondary ɗinsa, bayan Result ya fito kuma an samu Alhaji Muhammad ya sama masa gurbin karatu a Bayero University Kano. Fateemah kullum cikin godewa Alhaji Muhammad take ita da mahaifiyarta na yanda baya gajiya da dawainiyar k'annenta, kama daga cinsu,shansu,surarsu,iliminsu na boko dana addini duk baya gajiya da yi musu. Dama Alhaji Muhammad mutum ne shi mai kyautatawa ƴan'uwansa na birni dana ƙauye, hakan yasa kullum yake ganin cigaba a al'amuransa. Kowa ya tashi da buƙatarsa sai ya zo gurinsa, shi kuma indai ba ta fi ƙarfinsa ba zai maka. Neehal irin yaran nanne masu shegen Kuka, musamman cikin dare ba ta barin iyayenta su rintsa, Fateemah idan ta gaji da rarrashi takance "Allah ya nuna mun ranar da zaki bar ni na huta nikam, tun daga cikin ki har yau bana samun isasshen bacci." A duk lokacin da ta faɗi haka Alhaji Muhammad sai dai ya yi murmushi kawai. Watan Neehal bakwai kacal a duniya amma sai wayon tsiya, a lokacin rarrafe take ɗan yi amma akwai son yawo, Abbanta kullum da wayo yake fita daga gidan dan idan zai fita ta dinga ihu Kenan. Uncle Usman shine mai d'aukar ta idan ya dawo daga makaranta ya fita da ita, shi yasa tafi sabawa da shi akan Uncle Umar. Shekarta ɗaya da wata biyu Umma ta yaye ta, dan zuwa lokacin ta yi ƙafa ta fara tattakawa ga surutu duk da gwaranci take yi maganar ba ta fita sosai, ga kuma masifa, dan Yaro ɗan shekara uku ma dan tsaurin ido sai ta dinga dukansa, musamman idan aka zo gidansu, ga ta'adi komai aka ajiye sai taɓa. Neehal yarinya ce mai farin jini dan kowa sonta yake, kullum zaka ganta fess Ummanta bata barinta da k'azanta, Abbanta kuwa ba ya gajiya da yi mata siyayyar kayan sawa masu kyau da tsada. Tun tana ƙarama ba ta son hula, ana sa mata zata cire ta yar, gata da gashi mai yawa da tsayi kuma baƙi sidik. Shekararta biyu bakinta ya buɗe cui_cui sai ɗan banzan surutu kamar ta ci aku, ga tsokana kamar me. Umma kullum sai dai ta kalle ta mata addu'ar shiriyar Ubangiji. Sosai mahaifinta yake nuna mata gata kasancewar ta yarsa guda ɗaya tilo a duniya, sai dai ba irin gatan da zai ɓata ba, kuma suna mata tarbiyya dai_dai gwargwado. Shekarar Neehal uku a duniya lokacin ta fara zuwa islamiyya da boko, mahaifinta ya sai filin kusa da gidansu ya haɗe da nasa ya gina wani part ɗin, nan ma da suke ciki ya ƙara gyarashi. Dan zai ƙara aure ne ba dan ya dena don Matarsa ba, sai dan yana da halin yi kamar yadda Allah ya ce. Umma ko kaɗan ba ta damu ba akan za a mata kishiya, addu'a take kawai Allah ya kawo mata ta gari,kuma ta toshe kunnuwanta daga duk wata zuga ta k'awaye da ƴan'uwa. Neehal kam sai murna take Abbanta ya ce ya kusa kawo mata Aunty. A'isha Sunan Matar da Abba zai aura, Ƴar asalin garin Gombe ce, mahaifanta duka na can ne kuma Fulani ne. Ƴan'boko ne na bugawa a jarida, amma bokon bata hana su yin ilimin Addini ba, ga su ƴan'gayu kyawawa. Bautar ƙasa ce ta kawo ta Kano har Allah ya haɗa ta da Abba suka fara soyayya. Su A'isha su Huɗu ne a gurin iyayensu, Fateemah (Mama) ita ce babba sai Mahmud (Uncle Mahmud) sai A'isha (Aunty A'isha) sannan auta Halimatus Sadiya ( Aunty Sadiya.) An yi bikin Abba da Aunty A'isha lafiya an gama Lafiya, a garin Gombe a ka yi komai, sai kuma ranar D'aurin Aure da Ƴan Gabasawa suka zo aka yi wuni a gidan Umma, Neehal daɗi kamar ya kashe ta ana taro a gidansu, tana ta b'arna Umma ba ta hana ta ba, balle ta faɗa ko ta dake ta. Ƴan kawo Amarya sun zo sosai daga Gombe, kwanan su ɗaya suka koma, suma ƴan Gabasawan ranar suka tattafi. Tun a washegari Aunty A'isha ta fara hidima da Neehal, duk da Umma ta hanata amma ta ƙi. Bayan kwana biyu shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Neehal da Aunty A'isha, dan Aunty A'isha ba ruwanta ita take mata komai, Neehal kam abun da yasa take son Aunty A'isha idan ta yi ta'adi bata faɗa kamar na Umma, Umma kuwa idan ta gaji da magana har make ta take. Da tafiya ta yi tafiya ma Neehal gurin Aunty'n ta koma da zama gaba-d'aya, Umma ta ce "Ala raka taki gona, ta huta da ciwon bakin bari_bari." Zaman lafiya ake tsakanin Umma da Aunty A'isha, Abba kuma yana yin adalci a zamansu, hakan yasa ba'ajin kansu kwata_kwata. Duk inda Aunty A'isha zata da Neehal take zuwa ko da kuwa tafiyar kwanaki za ta yi, hakan yasa danginta duk sun saba da Neehal tamkar jininsu haka suke kallonta. *Bayan shekara biyu* An yi bikin Uncle Umar k'anin Umma, inda ya tare da amaryarsa a unguwar Sabuwar gandu, bayan ya gama degree ɗinsa ya yi service Abba ya samar masa teaching a wata secondary school. Gidan da zai zauna ma Abban ne ya siya masa, Umma ta ce gaskiya ba zai karb'a ba abun ya yi yawa, dawainiyar ta yi yawa. Abba ya ce mata "Idan ba zai musu ba wa zai yi wa? Ko tana so ta nuna masa k'annenta ba nasa ba ne." Umma da ta ji ya faɗi haka sai ta haqura, amma fa ranar ya sha godiya da addu'oi a gurinta. Har yanzu da Neehal ta yi shekara biyar Umma ba ta kuma samun ciki ba, Aunty A'isha ma haka. Neehal kullum cikin mitar ita a haifa mata k'ani take, wataran har da kukanta, saboda Freinds ɗinta na makaranta duk yawanci suna da k'anne. A duk lokacin data faɗi haka Abba kan rarrashe ta ya ce ta yi addu'a Allah ya kawo. Neehal ta ƙara girma iyayi da surutu sun ƙaru. Ranar wata Saturday da yamma ta dawo daga islamiyya, part ɗin Aunty'nta ta nufa direct tana k'wala mata kira, tana shiga falo ta yarda jakarta wadda Exercise book ne kawai a ciki sai pencil, ta cire ɗan mutsin hijabin jikinta shima ta yar, kanta babu d'ankwali saboda bata k'aunarshi ko kaɗan, fakakken gashin kanta da Aunty A'isha ta tsefa mata da safe ya bayyana, wanda ya sauka har ƙasan wuyanta. Har ta nufi bedroom ɗin Aunty ta tsaya turus saboda ganin wani matashi wanda ba zai wuce 17_18 years ba a zaune akan kujera yana latsa system ɗin Aunty A'isha. Neehal ta waro Ido dan bata taɓa ganinshi ba ta ce "Kaii! Waye kai, wa ya kawo ka gidanmu?" *AMEEN* Da bai masan da shigowar ta ba sai muryarta kawai ya ji ya mata banza, kasancewar sa muskili na bugawa a jarida. Neehal ta matso kusa da shi da ɗan ƙarfi ta ce "Kai baka ji ina maka magana." Ko d'agowa bai yi ba balle ya kulata, Neehal ta hau kan kujerar da yake ta kai bakinta dai_dai kunnansa da iya ƙarfinta ta ce "Kai ba ka ji ne, ko kai kurma ne!" Ameen ya d'ago a mugun fusace jin zata kashe masa dodon kunne ya wurga mata wani mugun kallo tare da hankad'e ta daga kusa da shi, Allah ya so kujerar da yake kai doguwa ce ta faɗa a kanta. Da sauri ta tashi zaune tana keɓe fuska tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Sauka ta yi daga kan kujerar ta yi bedroom ɗin Aunty da gudu tana kukan shagwab'ar da babu hawaye, Aunty A'isha ta tare ta da sauri tana faɗin "Me kuma ya faru Daughter?" Neehal ta keɓe baki ta ce "Wani ne a falo ya dake n......" Hango Mama da ta yi zaune a gefen gado yasa bata ƙarasa maganar ba ta nufe ta tare da d'ane mata cinya tana faɗin "Maman Abuja, yaushe kika zo?" Mama ta shafa kanta tana murmushi ta ce "D'azu na zo Daughter, wane ya kika ce ya dake ki?" Neehal ta turo baki ta ce "Ni ban san shi ba, wani yaro ne a falo." Aunty A'isha ta ce "Ba yaro ba ne Neehal Yayanki ne." Neehal ta ce "Aini ban da Yaya, kuma su Annur da Aslam duk suna da Yaya." Ta ƙarashe maganar kamar za ta yi kuka, Mama ta shafa kanta tana murmushi ta ce "Ke ma Daughter ga Yayanki nan na kawo miki kin ji? Daga yau kema kina da Yaya." Neehal ta gyaɗa mata kai tana murmushin jin daɗi an ce ga Yayanta. Mama ta dubi Aunty A'isha ta ce "Nikam A'isha da zaku bar mun Neehal ai da naji daɗi sosai wlh, ina son yarinya mace amma Allah bai bani ba." Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Tab' Wannan kam Ubanta ba zai iya bayar da ita ba, dan tsoka ɗaya ce a miya." Mama ta ce "Ni shaidace kam akan k'aunar da Alhaji Muhammad yake mata." Aunty A'isha ta kama Neehal ta cire mata uniform ɗin jikinta ta saka mata best da dogon wando. Neehal ta ce "Aunty kin dafa mun macaroni na?" Aunty A'isha ta ce "Yana kitchen na dafa miki, bari na zubo miki." Bayan Aunty ta zubo mata macaronin da miya ta fice falo da shi a hannu, gurin Ameen ta nufa tana faɗin "Yayanah! Yayanah, Maman Abuja da Aunty sun je kai Yaya ne ko?" Cike da murna take maganar, Amma Ameen ya ƙi kulata kamar tana magana da dutse. Neehal ta matso kusa da shi sosai ta d'ebo macaronin da ya ji miya sosai a ƙaramin spoon ɗin da take cin abinci da shi ta kai bakinsa tana cewa "Yayanah ungo ka ci." Ai macaronin be kai ga shiga bakinsa ba ya zube a jikinsa, miyar jiki ta b'ata masa white T_shirt ɗin dake jikinsa............✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:45] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *2️⃣6️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* .........Cikin tsananin takaici ya d'ago yana jifan ta da wani irin kallo, ita ma kallon nashi take da kyawawan idanunta cikin shock ta turo small pink lips ɗinta gaba. Tsaki ya ja tare da ɗauke idonsa daga kanta, ajiye abincin hannunta ta yi a ƙasa ta kai hannunta jikinsa inda abincin ya zuba tana faɗin "Sorry Yayanah bari na goge maka." Shi dai be ce mata komai ba sai harara da yake ta banka mata, maimakon ta goge masa kamar yadda ta ce sai ma ƙara damula masa miyar take a inda babu, cikin k'ufula ya buge hannun nata tare da jan wani wawan tsaki ya tashi fuuu ya nufi ɗakin da Aunty A'isha ta sauke shi, shi fa shiyasa tun farko bai so Mama ta yo wannan tafiyar da shi ba, sai da ya ce mata ba zai biyo ta ba amma ta takura masa sai ya zo, gashi nan daga zuwan shi wata tsaregar yarinya ta fara ɓata masa rai. K'wafa ya yi lokacin da yake cire rigar jikinsa, ba dan ya kai zuciyarsa nesa ba da sai ya gaggaura wa yarinyar maruka, dan ta gane shi ba sa'an wasanta ba ne. Neehal kuwa ɗakin Aunty ta yi da gudu tana kuka, Mama kuwa tana ganin Neehal ta shigo da kuka ko da ba a faɗa mata ba tasan ita da Ameen ne, dan tasan halin kayanta sarai. Tashi ta yi ta fito falo, Aunty A'isha kuwa rarrashin Neehal ta shiga yi. Ba ta ganshi a falon ba hakan yasa ta bi shi har ɗakin da yake, ta tura ƙofar ta shiga da Sallama, trolley ɗinsa da ya ɗauko riga a ciki ya saka yake zipping, ya amsa mata sallamar cikin muskilar muryarsa. Mama fuska ɗaure ta ce "Ameen! Me yarinyar mutane ta maka kake dukanta? dan na saka ka zo sai ka huce a kanta?" Kamar ba zai yi magana ba sai kuma dai ya ce "Mum ni ban dake ta ba, kawai ta zo tana samun ciwon kai ne shine na ɗan maketa." Mama ta ce "Uhm lallai, ai gwara daka ɗan maketan, to tunda ka make ta kuwa kai zaka zo rarrashe ta." Tana gama faɗin haka ta juya ta fice, cize lips d'insa na ƙasa ya yi, ya tashi ya fito falo. Da Mama ta koma ɗaki ta tarar Neehal ta yi shiru tana bawa Aunty A'isha labarin dalilin kukanta. Aunty A'isha ta ce "To ki yi haquri kin ji, kuma ai ke kika ɓata masa kaya dole ya dake ki, ki je ki bashi haquri ki ce masa ba za ki kuma ba kin yi yarinyar kirki tah." Neehal ta gyaɗa mata kai ta fice daga ɗakin da saurinta. Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Neehal rashin ji Ameen kuma babu haquri." Mama ta ce "Dama da abunsa, har yanzu fushi yake na taho da shi, na rasa irin wannan muskilanci na Ameen da baya son shiga cikin mutane, ya fi son in barshi a gida yay ta fama da system da takarda, kamar a kansa aka fara study." Aunty A'isha ta ce "Ameen halinsa sai shi kam." Neehal tana fita ta ɗan nutsu saboda tsoron Ameen da ya dirar mata a zuciya. A hankali ta ƙaraso kusa da shi cikin sanyi ta ce "Yayanah ka yi haquri ba zan kuma ba." Ameen ya sauke numfashi ya kamo hannunta ya ce "Shikenan na haqura, amma ki daina rashin ji da yiwa mutane ihu kin ji." Neehal ta gyaɗa masa kai, cikin murnar ya ce ya haqura ta ce "Yayanah za ka kai ni islamiyya gobe? Nima ince wa su Noor ga Yayanah." Ameen ya ɗan murmusa tare da gyaɗa mata kai. Ganin fa ya sake mata sai ta shiga yi masa hira tana bashi labarai kala_kala, shi dai kallon ɗan ƙaramin lips ɗinta da kyawawan idanunta kawai yake, a zuciyarsa yana mamakin surutu irin na Neehal sai ka ce Radio, ko ya ta motsa bakinta sai dimples ɗinta sun lotsa abun sha'awa. Kiran Sallar Magriba ne ya tada shi, tare suka fita da ita bayan ya yi alwala ita kuma ta yi part ɗin Ummanta. Washegari da safe Mama ta je part ɗin Umma suna hira, kamar ko wacce Sunday Aunty A'isha ta kamo Neehal ta fara yi mata kitso duk da zillewar da tai ta yi, saboda a rayuwarta ba ta k'aunar a taɓa mata kai ko kaɗan, kitso kuka, tsifa kuka, wankin kai kuka, haka Allah ya yi ta. Yauma gaba-d'aya ta cika part ɗin Aunty A'isha da ihun kukan kitson, Ameen yana daga ɗaki a kwance amma yana jiyo ihun nata, dan ware murya ta yi iya ƙarfinta, kamar wadda ake yankar naman jikinta. Da abun da ya ishe sa ne ya fito a fusace ya daka mata tsawa, ba shiri ta yi tsit sai tsiyayar hawaye kawai take, daga baya kuma sai bacci ma ya ɗauke ta. Haka rayuwa tay ta tafiya, Neehal tana girma kyawunta na ƙara fitowa, gata ƴar gatan Abbanta babu abunda ya rage da shi, Haka ma mahaifiyarta da Aunty'nta. Tana zuwa Gabasawa sosai musamman lokacin hutu, haka ma tana zuwa Abuja gidan Mama, amma tun daga time ɗin da Ameen suka zo gidansu ba ta ƙara ganin shi ba, saboda ya tafi Turkey karatu. Tun tana tambayar Mama shi harta manta da shi ma. Neehal yarinya ce mai ƙoƙari ga iyayi da son gayu, hakan yasa take da farin jini a ko'ina, duk inda ta shiga sai an k'aunace ta. Tana da shekara takwas kakarta Inna mahaifiyar Umma ta rasu, mutuwar Inna ta girgiza mutane da yawa, Umma ta yi kuka ita da su Uncle Umar, Neehal ma duk yarinya ce a time ɗin Amma ta ci kuka ta gode Allah. Shekarta goma sha biyu ta zana commen entrance, a lokacin ne ta samu hutun makaranta mai tsayi kusan na 3 months, Gabasawa ta fara zuwa ta yi 1 week daga nan ta dawo gida ta je gidan Baffa ƙofar Nasarawa ta musu kwana uku, daga nan ta je gidan Uncle Umar ta yi kwana biyu, dan duk da Uncle Umar yana da ƴaƴa guda biyu amma Neehal ba ta jin daɗin zaman gidan saboda matarsa ba ta da kirki, shi ma Uncle Umar ɗin kuma dama ba ya wani sakar mata fuska, hakan yasa babu wata shak'uwa mai ƙarfi a tsakaninsu, sai masifar tsoransa ma da take ji. Daga nan Gombe ta wuce gidan Hajiya (Mahaifiyar su Aunty A'isha), time ɗin ba'ayi auren Aunty Sadiya ba, kuma ga Ameerah ƴar gidan Uncle Mahmud suna wasa tare, shi ya sa take jin daɗin zaman Gombe. Satinta ɗaya a can ta wuce inda tafi jin daɗin zamansa akan ko'ina wato Abuja gidan Mama. Daga cewa za ta yi 2 weeks sai gashi tar tafi wata ba ta dawo ba, su Abba da Umma da Aunty sun yi kewarta, kullum suna waya a wayar Mama, idan suka tambaye ta yaushe zata dawo sai ta ce musu ta kusa amma kuma ta ƙi dawowar. Ameen ya dawo Naija time ɗin, amma ba ya Abuja yana Lagos acan ya fara aiki, zuwa time ɗin ya zama cikakken saurayi mai cikar zati da kwarjini, miskilanci kuwa da tsare gida sai abun da ya yi gaba. Neehal tana jin daɗin zama a Abuja sosai, saboda yanda Mama da Daddy suke tarairayarta tare da nuna mata tsantsar k'auna tamkar su suka haife ta. Ita kam babu abun da za ta ce da dangin Aunty A'isha sai godiya da sam barka, ƴan'uwan kishiyar babarta ne amma har sun fi wasu ƴan'uwan Abbanta kula da ita, dan idan ta je Gabasawa a yanzu da babu ran Kakarta Yayar mahaifinta wadda take kira da Ummi ita kaɗai take kula da ita, sauran cousins ɗin Abbanta kuwa tsakaninta da su gaisuwa ce kawai, amma idan zata shekara a garin babu mai aiko mata da abun biyar, amma su komai na su sa kwashi jiki su tafi gurin Abbanta ya biya musu buƙatar su. Gwara ƴan'uwan Umma su ko ba su bata komai ba, amma akwai sakin fuska kuma suna janta a jiki. Ƴaƴan Baffa kuma wanda ya rik'i Ummanta da Abbanta suma dai ba wani jin daɗin su take ba, Ƴaƴansa duka maza ne guda huɗu, duk sun yi aure sun hayayyafa, wasu ma sun haifi wanda suka girme ta, Baffan ne dai ya nuna mata k'auna da ya raye, ba ya banbanta ta da sauran jikokinsa. (Da yake tun Neehal tana shekara goma Allah ya masa rasuwa.) Akwai wani cousin ɗin Abba da yake nan Kano Yaya ne a gurin Abban, mutumin yana da kirki ga ilimin Addini, kaf cousin ɗin Abba ya fi zumunci da Abba sosai, dan tamkar uwa ɗaya uba ɗaya haka suka ɗauki junansu. Mutumin yana son Neehal sosai, dan Abba yana yawan kai masa ita, to shi kuma matsalar matarsa ce makira kuma muguwa, zata nuna babu ya kai a zahiri, amma a cikin zuciyarta ba haka ba ne, da wani abu na sharri zai same ka sai ta fi kowa murna. Duk da haka dai suna Zumunci sosai da Umma da Aunty A'isha. Dangin Abba haushin yanda Neehal take da ƴan'uwan Aunty A'isha suke ji, a cewar su wai itama Umman kwad'ayi ne yasa ta bar Neehal take shige musu, dan ta ga suna da kuɗi. Ita kuwa Umma daɗin yanda Aunty A'isha da danginta suke son Neehal take ji, ga kuma tausayin Aunty A'ishan na rashin haihuwa da Allah bai bata ba, shi yasa ta bar mata Neehal ɗin, dan komai na Neehal yana hannun Aunty A'isha, dan in ba faɗa maka aka yi ba za ka ce ba Aunty A'isha ce ta haife ta ba, dan Umma tana mata kawaici sosai akan Neehal, dan ko abu ne za ta cewa Neehal je ki gurin Mamanki ta miki kaza, Mamanki kaza, Aunty'n Neehal ma take cewa Aunty A'isha. Abba kam sosai yake jin daɗin yanda Umman take wa Aunty A'isha, hankalinsa a kwance yake tun da kan matansa a haɗe yake. Ita kuwa Aunty A'isha sosai take girmama Umma, haka ma ƴan'uwanta, babu ruwansu da wai su masu kuɗi ne ƴan'boko, ita kuma Umma ƴar talakawa ce talakawan ma na ƙauye balle su wulak'anta ko suna mata gani_gani. Ranar wata Laraba lokacin Neehal satin ta shida da kwanaki a gidan Mama, da yamma tana bitar haddadarta da zata bayar ranar Asabar, da yake tun bata fi sati da zuwa ba Mama ta nemi islamiyya ta saka ta, da ta je sai ta ɗora daga inda ta tsaya a haddarta ta gida. Gabanta ne ta ji ya yi wata mummunar fad'uwa, runtse idanta ta yi da sauri tana karanto Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, mike wa ta yi tsam ta nufi bedroom ɗin Mama. Bayan ta yi sallama ta shiga Mama ta amsa mata ta ƙara da faɗin. "Har kin gama haddar?" Jiki a sanyaye ta zauna a gefen Mama sannan ta ce "Eh." Mama ta ce "To ki je ki wanke panties ɗinki kar Magriba ta yi, dan nasan halinki da k'ailula sai ki yi awanni a wankin panties kawai." Ta ce "Toh." har ta miƙe sai kuma ta koma ta zauna ta ce "Mama yaushe zan koma gida?" Mama ta dube ta cikin mamaki ta ce "Gida kuma? Ke da kullum aka miki zancen komawar sai ki ce ba yanzu ba, amma yau kuma da kanki kike tambayar yaushe zaki koma." Shiru ta yi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, Mama ta cigaba da kallonta cikin nazartar ta, ta lura kamar wani abu na damunta dan wata nutsuwa ta ga ta yi, alhalin ta san Neehal da rawar kai da surutu, babu yanda za'ayi ta shigo bata ishe ta da hira ba, sai dai idan da wani dalili. Mama ta kira sunanta a hankali tare da kama hannunta ta ce "Neehal! Meke damunki? Ko baki da lafiya ne?" Girgiza mata kai ta yi alamun babu komai, Mama ta ƙara tambayarta da faɗin "Wani abun aka miki?" Nan ma girgiza kan ta ƙara yi, Mama ta ce "To me yasa kike son tafiya gida?" Neehal ta ce " Kawai ina son ganin Ummata da Abbana da Aunty." Mama ta sauke numfashi ta ce "To Shikenan, gobe Yayanki Ameen zai dawo, Ranar Saturday insha Allah sai na saka shi ya kai ki gida." Neehal ta gyaɗa mata kai cikin gamsuwa duk da bata san wanda Maman ta ambata mata a matsayin Yayanta ba. Tashi ta yi ta koma ɗakinta dan yin abun da Mama ta sata. Washegari ma haka ta tashi tana jin kanta wani iri, gabanta kuma bai dena fad'uwa, Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un kawai take maimaita wa kamar yadda Mama ta koyar da ita a duk lokacin da ji ko ta ga wani abun tashin hankali. Ranar Ameen ya dawo gidan da yamma, shima ba wani jima wa ze yi ba, Ranar Sunday da zai koma. Neehal ba su haɗu ba ranar saboda wuni ta yi a ɗaki a kwance, Mama ta mata tambayar duniya ta faɗa mata me yake damunta amma amsar ɗaya ce babu komai, ƙarshe ma sai ta saka kuka, sai da suka yi waya da Abbanta da Ummanta da daddare, ta ji suna lafiya k'alau sannan ta ɗan ji daɗi a ranta. Duk da Neehal a lokacin yarinya ce amma tana da hankali, shi yasa Mama take jin daɗin zama da ita. A Kano kuwa bayan su Umma sun gama waya da Neehal, Umma ta dubi Aunty ta ce "Aunty'n Neehal kin ga ikon Allah, yau kuma Neehal ce take cewa tana so ta dawo gida." Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Kin san halin Neehal sai ita, may be ta gaji da Abujan ne take so ta dawo." Umma ta ce "Hakane, amma da fa da kuka take baro Abujan." Abba ya ce "Ai kin san ba ta taɓa dadewa kamar wannan lokacin ba, shi ya sa." Umma ta gyaɗa kai tana faɗin "Sai dai haka, amma yanzu tana dawo wa ana mata abu zaku ji tana ita gidan Mamanta zata koma dan tafi sonta." Abba ya yi murmushi ya ce "Ai soyayyar Yaaya da Neehal sai Allah, Allah ya haɗa jininsu." Aunty A'isha ta ce "Ai ita Yaaya tana son yara ne, musamman mata, Allah kuma bai bata ba, gashi duk yarinyar data ɗauka a Family'nmu tana ɗan yin kwanaki sai su ce su gida za su koma, kin san yara ba sa son zaman gida shiru kuma gashi ba'a fita, daga makaranta sai gida, haka take komar da su gurin iyayensu." Umma ta ce "Allah sarki, Allah ya bata nata itama, ai ba'a fitar da rai da rabo a rayuwa." Abba ya ce "Allah ya kawo masu albarka." Suka amsa da Ameen gaba-d'aya. Ranar sun jima suna hira a falon Umma gwanin sha'awa, da yake ranar girkin Umma ne, sai Kusan 12pm Aunty A'isha ta koma part ɗinta. Misalin ƙarfe biyu da mintuna na dare, Abba yana zaune akan sallaya yana lazimi bayan ya idar da sallar Nafila, Umma kuma tana kan gado a kwance amma ba barci take ba, tun da suka baro falo ta kwanta amma bacci ya ƙi zuwar mata, sai wata irin faduwar gaba ce take riskarta akai_akai, addu'ar neman tsari daga sharri ta shiga karantawa a cikin zuciyarta, ana haka kawai suka ji an banko musu ƙofar ɗakin baram............✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:46] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *2️⃣7️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ...........A firgice Umma ta yaye bargon data lullub'a tare da tashi zaune tana kallon bakin ƙofar k'irjinta na dukan tara_tara. Abba kuwa ko kaɗan bai nuna razana ba, kallon mutanen da suke shigo musu ɗakin kawai yake a ransa yana faɗin, "La'ilaha'illa'anta subhanaka'inni'kuntu'minazzlimuun." Su su biyar ne, suna sanye cikin bak'ak'en kaya, fuskokinsu a ɗaure da wani baƙin k'yalle, hannunsa ɗauke da bindigu. Sosai hantar cikin Umma ta kad'a, addu'ar da take yi a zuci bata san sanda ta fito fili ba. Abba kuwa kallonsu kawai yake amma bece musu komai ba kamar yadda suma ba su ce ba, sai ƙare wa ɗakin kallo kawai suke. Cikin wata irin tafiya ta ƙasaita ɗaya daga cikinsu ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan bedside locker ya ɗan sunkuyo da fuskarsa dai-dai inda Abba yake. Cikin wata irin shakakkiyar murya ya ce "Na gaida Jarumi uban Jarumai." Sannan ya saki wata uwar dariya ya maida dubansa ga Umma ya ce "Ke! ki adana addu'arki zatai miki amfani a gaba dan yanzu baza ta hana mu yin abun da mukai niyya ba." Umma ta tab'e baki duk da yanayin tsoron da zuciyarta take ciki amma ta dake ta cigaba da karanto addu'arta, domin ta san ita ce kaɗai makaminta a wannan lokacin. Mutumin ya juyo ya yi wa ɗaya daga cikin yaransa inkiya da ido, cikin sauri yaron ya zagaya ta bayan Abba ya ƙarasa kan gado inda Umma take ya damk'o ta, Umma tana cizewa Abba kuma yana faɗin su sakar masa mata cikin tsananin ɓacin rai ganin wani k'aton banza yana taɓa masa mata, ganin Abba ya zabura zai miƙe wani daga cikin yaran ya riƙe shi, tare da ɗora masa bindiga a goshi, Umma ganin haka ta ruɗe ta fara kuka, a kusa da Abba yaron ya cillar da ita, shi kuma wanda ya riƙe Abba ya sake shi tare da koma wa baya. Babban nasu ya ƙara sakin wata kafirar dariya, ya daɗe yana dariyar sannan ya tsagaita ya zira hannunsa a aljihun gaban rigarsa ya ɗauko waya ya latsa ya haska wa su Abba da Umma yana faɗin "Kun san wannan?" A tare Umma da Abba suka kalli juna cikin al'ajabi, Abba ne ya fara ɗauke kallonsa daga kan wayar ya mayar ga mutumin ya ce "Eh na san sa, farin sani ma kuwa." Mutumin ya yi wani guntun murmushi sannan ya matso da fuskarsa kusa da su Abba sosai ya fara magana ƙasa_ƙasa wanda ni dai zeey ban ji ba. Zuwa can dai na ji Abba cikin d'aga murya wadda ke nuni da tsantsar ɓacin rai ya ce "Ba zan iya wannan haukan da shirmen ba, ƴar tawa guda ɗaya zan yarda in ɓata mata rayuwa in jefa ta a halaka, to bazan yi abun da kuke so ba ku yi duk abunda zaku yi, Allah ya fiku kuma da shi na dogara." Mutumin ya jinjina kai ya mai da dubansa ga Umma ya ce "Kema kin zaɓi mutuwa akan amincewa da buƙatar mu?" Umma ta saka kuka, cikin kukan ta ce "Ko me zaku mun ba zan taɓa amincewa da buƙatarku ba, kuma ƴarmu ko da bama raye Allah zai kare mana ita daga mugun nufinku, kuma da ku da wanda ya turo kun mun kai ƙarar ku gurin mai duka, shi zai mana maganin ku ya kawo ƙarshen ku da duk wasu irin hali da mummunar d'abi'arku, kuma......." Ƙarar harbin da ta ji ya katse mata zancenta ta runtse idanta da sauri, kafin ta yi wani yunk'uri ta ƙara jin wani saukar harbin, buɗe idonta ta yi zuciyarta na wani irin bugu tamkar zata faso kirjinta ta fito, wata gigitacciyar ƙara ta saki ganin duk harbin da ta ji a ƙirjin Abba aka yi su, rungume shi ta yi k'am ajikinta tana kiran sunansa cikin fitar hayyaci, amma ko motsi ba ya yi, jini har ya fara ɓata farar jallabiyar dake jikinsa. Janye Abba suka yi da sauri daga jikinta itama suka sakar mata harbin a ƙirji, a take Umma ta bi bayan Abba ta zube a gurin babu alamun numfashi a tattare da ita. kafin kiftawar ido suka fice daga ɗakin a guje suka bi ta inda shigo suka fice daga gidan gaba-d'aya. Aunty A'isha tana part ɗinta tana bacci ƙarar harbin ne ya tashe ta, amma ko kaɗan ba ta yi tunanin a cikin gidan ba ne, ta yi tunanin wani gidan custom ne da suke mak'ota b'arayi suka shigar masa. Amma duk da haka sai da ta ji gabanta ya faɗi a lokacin da akai harbin ƙarshe, wayarta ta ɗauka ta kira Numbern Abba amma bai ɗauka ba, jin shiru kusan minti talatin da yin harbin Ba'a kuma ba ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta, amma sai ta nemi bacci a idonta ta rasa, haka kawai ta ji jikinta wani iri, zuciyarta har wani rawa take dan fargaba. Ƙara kiran wayar Abba ta yi amma bai d'aga ba, hakan yasa ta kira Umma itama ba ta ɗauka ba, gashi Uncle Usman ba ya nan ya yi tafiya balle ta kira shi, dan ita ta rasa mai yasa hankalinta ya kasa kwanciya da harbukan da akai. Ranar Aunty A'isha bata iya bacci ba, ga wani irin tsoro da ya rufe ta, wadda ko kwakwkwaran motsi tsoron yi take. Sai da aka shiga Sallar Asuba sannan ta iya tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta tada Sallah, tana idarwa kuwa ta yi part ɗin Umma. Da Sallama ta shiga falon Umma amma ta ji shiru, corridor ta nufa inda ɗakunan Umma guda biyu suke suna facing juna, tun daga bakin ƙofar ta fara hango jini ta ƙasan ƙofar, wani mummunar fad'uwa gabanta ya yi, da gudu ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, wata gigitacciyar ƙara ta k'walla ganin Umma da Abba kwance cikin jini, kamar kuma wacce aka tsikara ta fito da gudu ta yi waje tana k'wala wa mai_gadi kira, mai gadi da dawowarsa kenan daga masallaci ya fito da sauri yana tambayar "lafiya Hajiya?" Part ɗin Umma kawai Aunty A'isha take nuna masa amma ta kasa mgn, hakan yasa ya nufi part ɗin da sauri a zatonsa ko wuta ce ta kama a ciki. Gigitar da mai_gadi ya shiga baza ta faɗu ba, ga mamakin ta ya ya aka iya shigowa gidan har aka aiwatar da wannan mummunan aikin, dan shi ko da za shi masallaci ma ƙofar gidan a rufe take shi ya bude ta da hannunsa, kuma gidan baza a iya haurowa ba saboda tsayin katangar gidan. Kuka sosai Aunty A'isha ta shiga yi lokacin da mai_gadi ya sanar mata babu numfashi a tattare da su Umma, tana faɗin "Su waye suka kashe ku? Me kukai musu?" Mai_,gadi kuwa da sauri ya fita ya faɗa wa mak'ota, nan da nan kuwa mazan layin suka fara shiga gidan cikin tashin hankali, dan kuwa duk yawanci sun ji harbin da akai, babu ɓata lokaci custom ɗin dake layin ya kira Police aka sanar musu, kafin gari ya yi haske har sun zo gidan. Aunty A'isha kuwa tuni ta suma, wata makociyarsu ce da ta shigo ta ɗauki ƙaramar wayar Umma ta shiga kiran ƴan'uwanta tana sanar musu, haka ma wayar Abba mai_gadi ne ya ɗauka ya kira ƴan'uwa da abokan arziki yana sanar musu. Aunty A'isha bayan an shafa mata ruwa ta farfaɗo itama tana kuka ta shiga kiran mutane tana sanar musu wannan mummunan labarin wanda take ganin tamkar al'amara ko kuma mafarki take zata farka. Mutuwar su Abba ta girgiza zuk'atan mutane, kafin ka ce me, labari ya fara baza gari, musamman da matasan unguwar suka yaɗa a social media. Lokacin da Aunty A'isha ta sanar da Mama rasuwar Umma da Abba kusan zaucewa ta yi ita kaɗai a ɗaki, saboda tsananin kaɗuwa dan mutuwar ta dake ta ba kaɗan ba, wayar da suka yi jiya da daddare kawai take tuna wa. Da ƙyar ta samu yar nutsuwa ta fara dawo mata sanadiyyar karanta Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, da ta shiga maimaitawa a fili. Miƙewa ta yi da ƙyar ta fito ta nufi part ɗin Daddy, tana shiga ta tarar da shi yana waya. Sai da ta jira ya gama wayar sannan ta rattabo masa abun da faru, iya rudewa shi ma Daddy ya ruɗe, ba shiri ya yi kira a waya dan asamar musu Visa zuwa Kano shi da Mama, da Ameen da Neehal. Neehal tana kwance a ɗaki Mama ta shigo ta same ta. "Neehal, tashi ki shirya zamu unguwa." Mama ta faɗi haka cikin sanyi da raunin murya. Neehal ta tashi zaune tana duban Mama ta ce "Ina zamu Mama? Ni fa Umma da Abba nake son gani." Ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka, Mama ta daure dan kar Neehal ɗin ta gane wani abu ta ce "Daga can zamu biya gida ki ga su Umman." Neehal ta sauke ajiyar zuciya sannan ta miƙe ta shiga toilet, Mama ta bita da kallo cikin tsananin tausayinta. Tashi ta yi ta fice daga ɗakin da sauri jin kuka na neman kufce mata. Neehal kam cikin sanyin jiki sosai ta fito ta shirya, ta rasa me yasa ta ji bata wata murna duk da Mama ta ce mata za su biya ta ga Su Ummanta. Kafin ƙarfe tara su Mama sun ƙarasa Airport, cikin mintuna aka gama komai suka shiga jirgi suka yo Kano, Neehal sai kallon Ameen take cikin zuciyarta tana mamakin tsakanin kamarsu da Mama, daga gaisuwa babu abun da ya kuma haɗa su, dan shi ko kallonta bai kuma yi ba. Sai dai cikin zuciyarsa cike take taf da tausayin ta, dan Mama ta sanar masa rasuwar Mahaifan nata. Driver'n Abba ne ya je ya ɗauko su lokacin da suka sauka a Kano, Neehal ta yi mamakin hakan amma ba ta ce komai ba. Yanda Neehal ta ruɗe, ta gigice tare da firgicewa ba zai misaltu ba, balle ya faɗu, lokacin da ta yi arba da gawar iyayenta kwance duk jini ya ɓata likkafanunsu, duk da Kasancewar ta yarinya a time ɗin amma tasan mutuwa, ta san shikenan ba zata ƙara ganin Ummanta da Abbanta ba sun tafi kenan, ta yi kuka ta yi kalamai wanda sai da suka karya zuciyar duk wanda yake gurin tare da zubar mata da hawaye, haka ta rungume Aunty A'isha sukai ta kuka abun tausayi. Mama ma duk dauriyarta ranar ta ci Kuka. Saboda tsabagen Kukan da Neehal ta sha kafin dare zazzaɓi mai zafi ya rufe ta, sai da aka mata allura sannan jikin nata ya ɗan yi dama, da safe kam jikin sai ya ƙara rikicewa, sai da ta yi kwana biyu ana saka mata drip tare da allurori sannan ta ji sauƙi. Umma da Abba sun yi jama'a sosai wanda suka raka su gidansu na gaskiya, dan Abba mutumin k'warai ne, kowa sai faɗar Alkhairinsa yake, haka ma Umma, gashi kuma sun yi sa'ar dace wa da Ranar Juma'a. Tun daga Ranar da akai kisan jami'an tsaro suka duk'ufa da binkice dan gano waɗanda suka yi nisan, dan har mai_gadi sun kama a tunaninsu ko da haɗin bakinsa, amma daga baya sun sake sa da suka gane babu haɗin bakinsa a kisan, ta ƙofar baya ma waɗanda suka yi kisan suka shigo gidan. Bayan sadakar bakwai kowa ya watse gida ya rage daga Neehal sai Aunty A'isha da hajiyarsu da Yayar Abba. Nan fa mutuwar ta dawowa da su Aunty A'isha da Neehal sabuwa, sai ya kasance Kullum sai sun yi kuka. Nasiha sosai Hajiya da Yayar Abba suke musu akan su yi haquri, dama duk mai rai mamaci ne, kowa jiran mutuwarsa yake fata dai kawai Allah yasa mu cika da kyau imani. Uncle Umar da Uncle Usman ma mutuwar ta dake su ba kaɗan ba, dan suma kuka wurjanjan suka dinga yi. Aunty A'isha kullum tunaninta su waye suka kashe su Umma, kuma akan wanne dalili? Dan a binkicen da akai ya nuna wanda suka yi kisan ba b'arayi ba ne turo su akai, dan babu abunda suka ɗauka a gidan. Kafin a yi arba'in Yayar Abba ta koma Gabasawa, sai Hajiya ce kaɗai take zaune da su Neehal. Kusan kullum suna waya da Mama da Daddy, Mama ta ƙara zuwa sau ɗaya ta duba su. Sosai Ubangidan Abba ya sa aka tsananta bincike dan gano wandanda suka yi kisan su Abba, amma shiru babu wani information, duk da jami'an tsaron na iya bakin ƙoƙarinsu a binkicen. Washegari garin Arba'in Uncle ya zo da wata magana wadda ta gigita Su Aunty A'isha ta kuma ba su mamaki, ya zo ya same su suna zaune da Mama, da Yayar Abba da Aunty Sadiya, da Ammi matar Uncle Mahmud wanda duk sun zo ne saboda sadakar Arba'in su Umma. Maganar da ya musu kuwa itace akan rabon gado, wai nan da kwana uku insha Allah za su zo da Alk'ali a raba a bawa kowa nasa. Kuka Aunty A'isha ta saka tana faɗin "Ita bata son wani gado, dan ta riga ta yi rashin da har abada ba zata mai da kamarsa ba, rashin adalin mijinta da kuma Abokiyar zamanta salihar mace." Hajiya da Yayar Abba suka ce "Haba saurin me ake, ya bari Aunty A'isha ta fita daga takaba mana." Amma ya ƙi, wai hakan shine dai_dai. Uncle Usman kuwa k'ala bai ce ba akan maganar ba. Maganar fa ta girmama har gurin manya, dole ba son ran su Aunty A'isha ba aka raba gadon. Kasancewar Neehal ita kaɗai ce 'yarsu Abba ya sa a cikin kadarorin Umma da Abba ya mallaka mata kafin ya rasu sai da aka raba da su Uncle Umar, haka ma na Abba sai da aka raba da Yayarsa. Aunty A'isha ma aka bata tumunin takabarta. Gidan da suke ciki a gadon Neehal ya zo. Sai dai kuma wata sabuwa batun riƙon Neehal, da farko Yayar Abba ta so tafiya da ita Gabasawa amma akace hakan ba zai yiyu ba saboda ƙauye ne, ga kuma karatun Neehal ɗin, idan ta koma Gabasawa zata tawaya. Ƴan'uwan Abba kuwa da suke cikin Kano kowa ƙin ɗaukar ta ya yi, a ganinsu wahala zata zamar musu. Aunty A'isha kuwa tun farko ita ta ce a bata Neehal ɗin zata cigaba da riƙon ta, amma Uncle Umar yay ruwa yay tsaki ya ce ba za su ba da Neehal ga bare ba, tunda ba rasa dangin da za su rike ta ta yi ba, dan haka shi zai ɗauke ta. Ai Neehal na jin haka ta dinga kuka tana faɗin Ita "Gurin Aunty'nta zata zauna, babu inda zata je." Amma Uncle Umar ya sawa idonsa toka, ya ce "Ko kukan jini za ta yi wallahi a gidansa zata zauna, shi zai cigaba da riƙon ta." Aunty A'isha dama ba wani shiri take da shi ba, ta san ko zata mutu tana roƙon sa ya bata Neehal ba zai bata ba, kuma babu yanda zata yi da shi tunda ɗan'uwan mahaifiyarta ne, yafi ta kusanci da Neehal ɗin. Neehal tana ji tana gani Aunty A'isha suka haɗa kayansu ita da Hajiya suka wuce Gombe, tana kuka Aunty A'isha na yi, mutuwar Abba da Umma ta dawo musu sabuwa, duk mai imani idan ya gansu a wannan lokacin yanda suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi sai ya zubar musu da k'walla, amma Uncle Umar ko ajikinsa, Neehal har shid'ewa take saboda kuka. A ranar da suka tafin da daddare yasa ta itama ta haɗa kayanta kaf ya tasa ƙeyarta suka tafi gidansa tana ta faman tsiyayar hawaye, dan ya mata tsawa akan kar ya ƙara jin kukanta............✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:46] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *2️⃣8️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ..........A falon gidan suka tarar da matarsa Aunty Fauziyya hakimce akan kujera suna kallo, yaranta guda biyu mace da Namiji suna ta wasansu akan doguwar kujera. A hankali Neehal ta shiga Falon tana goge hawayen fuskarta dan kar Uncle Umar ya gani, kan kujera ta nufa zata zauna Aunty Fauziyya ta buga mata wata uwar tsawa tana faɗin "Kar ki kuskura ki zauna mun akan kujera zauna nan ƙasa." Ba musu Neehal ta zauna a ƙasan cikin mamaki, dan ta saba ita a gidansu da gidan Mama akan kujera take zama. Uncle Umar ya zauna yana hararar Neehal ya ce "Hmmmm, yarinyar nan ai sai an dage mata, gaba-d'aya waccan matar da Ƴan'uwanta sun ɓata mata tarbiyya, Ni wlh Yaaya ta ban mamaki da ta yarda suke riƙe mata ƴa." Fauziyya ta tab'e baki ta ce "Kai kwa kuɗii, kuɗi fa aka ce maka, ta ga suna da kuɗi ne shi yasa, ka ga in an ɗan yi Zakka a dinga tunawa da ita ai." Shiru Uncle Umar ya yi jin abun ya fara komawa cin fuska. Yaran su Aiman da iman suna wasa suka fado tim akan Neehal, Uncle Umar ya ce "Subahanallah, Aiman ban hana ku wasan banza ba? gashi nan kun faɗo wa Aunty'nku akai." Aunty Fauziyya dake ta aika wa Neehal harara ta ce "Kamar ya sun faɗo mata? Ita bata gani ne, makauniya ce ita, ai tana kallonsu zasu faɗo ɗin dan baƙin hali ta ƙi matsawa, salon ace daga zuwanta an fara cutar da ita." Neehal dai ba ta ce komai ba, kanta na ƙasa tana ta hawaye. Su Aiman suka kwantar da trolley ɗinta suka buɗe suka fara zak'ulo mata kaya suna yar wa a dakin, Uncle Umar cikin tsawa ya ce musu "Wai wanne iskanci haka, ko kun mata ajiya a cikin kaya ne.?" Cikin tarar numfashi Aunty Fauziyya ta ce "Ka ga, ka dena dakawa ƴaƴana tsawa irin haka, nan gidan ubansu ne ba cin arziki suka zo ba, dan haka dole su sakata su wala san ransu." Tsaki Uncle Umar yay ya ce wa Neehal ta tashi ta tattara kayanta ta shiga ɗakin yaran. Aunty Fauziyya ta ce "Kar kuma ki hau mun kan katifar ƴaƴa, a ƙasa zaki zauna, anan kuma zaki dinga kwana." Neehal dai ba ta ce komai ba ta tashi ta shiga ɗakin tana janye da trolley ɗinta da ƙyar. A ƙasan ta zauna kamar yadda Fauziyya ta ce ta rafka tagumi, kanta ne ke mata wani irin ciwo hakan yasa ta kwanta a ƙasan, amma gaba-d'aya sai ta ji kwanciyar bata mata daɗi ba, ita data saba kwana akan luntsumemiyar katifa da lallausan bed sheet ta lullub'a da lallausan bargo, ta yaya zata iya kwanciya akan dandaryar ƙasa kan tayis? A hankali ta miƙe dak'yar ta buɗe trolley ɗinta ta ɗauko kayanta ta shimfid'a a ƙasan ta kwanta akai, amma duk da haka bata wani ji daɗin kwanciyar ba, ya dai fi ta kwanta a ƙasan ne kawai. Allah ya so ma Aunty A'isha ta saka mata bargo acikin kayan nata, da yake ita ta haɗa mata kayan. Amma saboda garin da ɗan zafi shi yasa bata lullub'a ba, ɗakin kuma da fanka amma bata wani ba da iska, ko dan ta saba da Ac ne a gida. Tafi awa da kwanciya amma ta kasa bacci sai juyi take, idanunta dai a lumshe suke kamar mai bacci, tana jin Aunty Fauziyya ta shigo ta kwantar da ƴaƴanta akan katifa ta daura musu Net sannan ta kashe musu light ɗin ɗakin, nan fa sauro ganin duhu ya ce wa Neehal salamu alaikum, ita kuwa bata saba da sauro ba, nan da nan ya gigita ta, ta tashi zaune tana hawaye, ga ciwon kai tamkar ana ƙara mata ake, lallaɓawa ta yi ta shige Net ɗin su Aiman dan bata da wata mafita, katifar ma zata ishe su amma ɗan baƙin halin Aunty Fauziyya ta hanata kwanciya akai. Tana shiga ta sauke ajiyar zuciya, ba jimawa baccin wahala ya kwashe ta. Sanyin asuba ne ya tashe ta, cizon sauron da tasha jiya da kukan da tay ya haifar mata da zazzaɓi, cikin rawar ɗari ta sauko daga kan katifar ta dunk'ule a waje ɗaya tana numfarfashi, kayanta data shimfid'a a ƙasa ta rarumo ta rufe jikinta saboda sanyin da take ji. Sai wajen ƙarfe 7 su Iman suka tashi daga bacci, kamar wasu ƴaƴan karnuka da faɗa suka tashi, gashi sun tsutstsula fitsarinsu a kwance, Allah ya taimaki Neehal ba su ɓata ta ba. Da ƙyar Neehal ta iya tashi ta ƙarasa toilet ɗin dake ɗakin ta yi fitsarin da ya matseta, da ƙyar take tafiya saboda jiri, ga yunwa dake nuk'urk'usar hanjin cikinta, rabonta da abincin tun lunch ɗin jiya da ta yi a gida. Aunty Fauziyya kamar kullum tana jiyo hayaniyar yaranta ta shigo ɗakin da sauri, dan kullum da hakan take gane tashinsu, Neehal na rakub'e jikin kayanta tana ta rawar sanyi, cikin muryar marasa lafiya ta ce "Ina kwana Aunty." Wani mugun kallo Aunty Fauziyya ta watsa mata, a harzuk'e tana zazzaro ido kamar sabuwar kamu ta ce "Yana gidan Ubanki shi kwanan." Neehal bata kuma cewa komai ba, ita kuma Fauziyya ta ja ƴaƴanta sukai toilet, wanka ta musu ta shirya su cikin uniform ɗinsu, sannan suka fita falo dan karyawa. Uncle Umar ya ce wa Fauziyya "Ina Neehal ɗin, itama ta fito ta karya mana." A fusace Aunty Fauziyya ta ce masa "Ka san yar gold ce bata tashi ba har yanzu." Sai wajen ƙarfe tara Aunty Fauziyya ta ƙwalawa Neehal kira lokacin Uncle Umar ya fita, cikin hanzari Neehal ta taso dan wani bala'in tsoron matar take ji, k'osan Talatin ta bata da wani ɗan bread da ruwan bunu rabin ƙaramin cup a matsayin breakfast. Neehal ta bi abun da aka bata da kallo sannan ta fara ci tana yamutsa fuska saboda bakinta babu daɗi, yunwa ce kawai ta sa take ci, ga shi ita k'osai ba mutuminta ba ne, gara ma bread ɗin. Ruwan bunun kuwa ko kurb'a ba ta yi ba, dan tasan baza ta iya sha ba. Bayan ta gama cikin faɗa Aunty Fauziyya ta ce "Tunda ciki ya ɗauka, sai ki tashi ki haɗa kayan nan, ki kai tsakar gida ki wanke, sannan ki dawo ki share mun falo ki yi mopping, ɗakin da kika kwana ma haka." Cikin sanyi Neehal ta ce "Aunty ban da lafiya, kuma ban iya b......." "Ai ko cutar mutuwa kike yau sai kin mun aikin nan, dan Ubanki Jakar uwarki ce ni zan dafa miki ki ci kina daga kwance, zaki tashi ko sai na miki dukan mutuwa a gidan nan." Jiki na b'ari Neehal ta tashi ta fara haɗa kayan, duk da zazzaɓin dake damunta, amma saboda tsoron Fauziyya da take ji dole ta yi. Ba ta taɓa wanke_wanke ba a rayuwarta, sai a gidan Mama ne ma idan ta ci abinci Mama take sata ta dauraye flate ɗin da taci abincin. Ai kuwa Fauziyya ta sha asarar omo, gashi kafin ta gama ta jik'a jikinta jagab da ruwa, a haka ta yi share_sharen da mopping, Fauziyya kuwa tuni ta fice yawon mak'ota. Tana gama aikin ta yi daki ta kwanta akan tiles, zazzaɓi mai zafi ne ya rufe ta. Da Fauziyya ta dawo ta ga b'arnar Omon da Neehal ta mata, ta dinga surfa mata ashariya da masifa, da dukanta ma zata yi wata makociyarta data shigo ta hanata, ganin yanda Neehal ɗin take rawar sanyi. Da rana ma kiranta Aunty Fauziyya ta yi ta bata wata shinkafa da wake ƴar kaɗan a roba, ko man kirki babu a ciki. Lauma ɗaya Neehal ta yi ta ture ta koma ɗaki ta kwanta, Fauziyya ranar wuni ta yi tana zagin Neehal. Da daddare Uncle Umar ya lek'a ɗakin da Neehal take ganin Shiru_shiru bai ji motsinta ba tunda ya dawo, ganin ba ta da lafiya ya bata panadol da Paracetamol ta sha, ya kuma kawo mata lemo da ayaban daya shigo gidan da su har ɗaki, ta kuwa ci ayabar ba laifi dan tana sonta sosai. Fauziyya tayta kumbure_kumbure tana huci kamar zata naushi iska ganin abun da Uncle Umar ya yi wa Neehal. Washegari ma Neehal ce ta yi wanke_wanke da shara, jikin nata ya yi sauƙi tunda ta sha magani, sai dai bata warke sumul ba, ranar kam sai da Fauziyya ta mare ta akan ta'adin omon data mata. A daren Ranar Uncle Usman ya zo gidan yi musu sallama dan zai koma garin da yake aiki ne. Tsaraba sosai yayo wa Neehal da su Aiman ta sweet da chocolate, da zai tafi Neehal tai ta Kuka, Aunty Fauziyya ta tab'e baki a ranta ta ce 'Munafurcin banza.' Tun daga ranar Neehal ce take wanke_wanke da shara da mopping da aiken gidan, yanda ka san baiwa haka Fauziyya ta mayar da ita, ga masifa da tsawa da bala'i. Wani matsifaffen tsoronta Neehal take ji, gashi idan Uncle Umar ya dawo ta haɗa wa Neehal sharri a gurinsa wai ta zage ta, haka zai zo yay mata masifa shi ma kamar zai dake ta. Kullum Neehal sai ta ci kuka ta gode Allah, kuma duk wani abu na amfani da Aunty A'isha ta sako mata acikin kayanta Fauziyya ta k'wace, kama daga MacLean, sabulan Wanka hatta bargonta duk ta k'wace. Yau kwanan Neehal goma sha biyu a gidan Uncle Umar, amma gaba-d'aya ta rame ta yi duhu saboda wahala, baza ka taɓa cewa itace yar gatan Ummanta da Abbanta ba. Kitson dake kanta ya tsufa ya dugurguje, ga farcenta ya fara taruwa, ta saba duk ran Friday Aunty'nta tana yanke mata, haka ma Mama idan tana gidanta, nan kuwa wanka ma ba kullum ake barinta ta yi ba. Ga rashin ishashshen abinci, abincin da yaro ɗan shekara biyar zai ci shi ake bata, shima kuma mara daɗi. Kullum da safe tana jin k'amshi ana soya k'wai da dankali amma ita ko ganin shi bata yi, haka ma naman miya ba'a bata ko gutsire. Misalin ƙarfe Uku na yamma Neehal ce tafe tana ta zuba sauri saboda gargadi'n da Aunty Fauziyya na mata akan kar ta daɗe, kayan miya zata siyo mata a can bakin titi, kuma daga gida zuwa bakin titi da ƴar tafiya, gaba-d'aya a gajiye take saboda aikin da tasha yau har da wankin kayanta ta yi, ga rana da ake k'walla wa a garin, gashi ba ta ci abincin rana ba kuma tana jin yunwa sosai gami da ƙishirwa, Aunty Fauziyya ta ce sai ta siyo mata kayan miyar sannan zata ci abincin. Ta shiga wani layi wanda daga shi sai titi, ta ga wani k'aton gida mai kyau, wani kyakkyawan matashi da ba zai wuce shekara 25 ba ne ya fito daga ƙaramar ƙofar gidan hannunsa ɗauke da robar ruwan faro mai sanyi. Tsayawa Neehal ta yi ta ƙura wa ruwan hannunsa ido tana maida Numfashi saboda gajiya, sau ɗaya matashin ya kalleta ya ɗauke kai ya nufi Motar dake fake a gaban gidan, Neehal ganin haka yasa ta ƙarasa kusa da shi da sauri ta ce...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:47] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *2️⃣9️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ..........."Uncle please zan sha ruwa." Kallonta ya yi fuska a sake ya ce "Oh sorry Dear take it." Neehal ta karb'i ruwan da yake miƙa mata tare da faɗin "Thank you." Murmushinsa Mai kyau ya mata, Neehal ta buɗe robar ruwan da sauri har tana yar da kuɗin kayan miyan bata sani ba, kai robar ta yi bakinta zata sha ruwan ya katse ta da sauri ta hanyar faɗin. "No, go there ki zauna sai ki sha." Ya ƙarashe maganar tare da nuna mata wani dakali dake kofar gidansu. Da sauri Neehal ta ƙarasa ta zauna ta fara quqqutar ruwan, sai da ta shanye tass sannan ta yarda robar. Matashin yana tsaye yana kallonta, haka kawai ya ji ya kasa tafiya, Neehal ta dafe cikinta saboda k'ullewar da ya fara mata saboda yunwar da take ji. Cike da tausayawa Matashin ya sunkuya ya ɗauki kuɗin da ta yar a ƙasa ya ƙarasa inda take, cikin tausayinta da ya d'arsar masa a zuciya lokaci ɗaya ya ce "Are you Ok?" Neehal ta girgiza masa kai ta ce "I'm felling hungry." Ya ce "Okay, sorry, wait for me here, I will come now." Neehal ta gyaɗa masa kai tana ƙara dafe cikinta. Cikin 5 minutes ya shiga gidansu ya fito hannunsa ɗauke da Cake wanda aka yi rapping ɗinsa, sai kuma lemon jarka guda ɗaya. Miƙa mata ya yi ta karb'a da sauri tare da kallonsa, a hankali ta ce "Thank you so much." Sannan ta fara cin Cake ɗin, ƙura mata ido ya yi ganin yanda take cin cake ɗin cikin nutsuwa tana lumshe ido, ita kuwa Neehal daɗi Cake ɗin ya mata ba kaɗan ba. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta ɗauki leman ta sha fiye da rabin jakar, ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ce "Alhamdulillah." Sai kuma ta miƙe zumbur kamar wadda aka tsikara ta fara ƙoƙarin tafiya, katse ta ya yi ta hanyar faɗin "Zo ki ɗauki sauran mana." Neehal ta ce "Na k'oshi ne." Ya ce "Are you sure?" Ta gyaɗa masa kai, ya ce "To ki tafi da shi gida anjima sai ki ci." Neehal ta waro ido waje ta ce "Aunty zata dake ni idan na je da shi gida." Miƙa mata kuɗin data yar ya yi ya ce "You forget." Neehal ta karb'a da sauri ta wuce. Cake ɗin data bari da lemo ya ɗauka ya shige Motarsa, yana fita titi ya hango ta a gurin mai kayan miya, an yi sa'a ita ma ta juyo suka haɗa ido, d'aga mata hannu ya yi yana murmushi itama ta mayar masa da murmushin tare da d'aga masa hannun, a gurin ya samu almajiri ya bashi ragowar Cake ɗin da lemon. Cikin sauri Neehal ta siyi kayan miyan ta koma gida, zuciyarta cike da tsoron Aunty Fauziyya, wani ɓangaren na zuciyarta ta kuwa farinciki take yau ta ci Cake ta sha lemo. Da masifa Aunty Fauziyya ta tare ta, ita dai tay shiru kawai tana kallonta tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Aunty Fauziyya cikin bala'inta ta ce "Shegiyar yarinya mai kama da aljanu, ana miki magana ki tsare mutum da wasu idanunki kamar na mage." Ta kamo kunnen Neehal ta murd'e da ƙarfi tana faɗin, "Gobe ma in ƙara aiken ki ki kuma zuwa ki zauna." Neehal ta saka kuka saboda zafin da ta ji a kunnenta, Aunty Fauziyya ta dungurar da ita a wurin tare da daka mata tsawar ta rufe mata baki. Kayan miyan ta wanke ta bata ta kai markad'e, ko tunanin bata abinci bata yi ba gashi har la'asar ta yi. Cikin mintuna ƙalilan Neehal ta dawo daga kai markad'en da yake anan mak'otansu ake babu nisa. Sai a sannan Aunty Fauziyya ta bata abinci a wani ɗan kwano, jallop ɗin shinkafa ce da cavage ce akai. Neehal ta kai abincin ɗaki ta ajiye a bayan kayanta, dan a koshe take. Aunty Fauziyya bata barta ta huta ba, sai da ta bata wankin uniform ɗin su Aiman, Neehal ta jijjik'a ta shanya dan ba wani iya wanki ta yi ba, sai dai tai ta goggoga sabulu ajikin kaya in ta ga ya yi kumfa sai ta d'auraye ta shanya. Bayan isha'i tana zaune a ɗaki tana yi wa su Aiman Homework, dan Yaran babu abun da suka iya sai dambe da zagi, ashar kala_kala sun iya narkawa kamar ƴaƴan maguzawa. Tun da Neehal ta zo gidan ita take musu Homework da Assignment ɗin islamiyya. Jin Uncle Umar ya shigo ta miƙe ta shiga falon ta gaishe shi, Allah ya so Aunty Fauziyya tana ɗakinta da sai ta k'ulla mata wani sharrin a gurinsa. Bayan ya amsa ta ce "Uncle Ina son na koma School da Islamiyya." Uncle Umar ya ɗan bata rai ya ce "To je ki sai na duba." Neehal ta tashi ta koma ɗaki ta cigaba da abun da take. Aunty Fauziyya ta fito daga ɗakinta tana yamutsa fuska ta ce "Me na ji yarinyar can tana ce maka ne?" Uncle Umar ya ce "Wai Makaranta take so ta koma." Aunty Fauziyya ta haɗe sosai ta ce "Kai kuma saka ta a makarantar zaka yi?" Ya ce "To ya zan yi, tunda Allah ya ɗora mun." "Ka dai ɗora wa kanka." Aunty Fauziyya ta faɗa tana keɓe fuska. Uncle Umar ya ce "Hmmm, tunanin ma makarantar da zan kaita nake, amma ina ga makarantar su Aiman zan kai ta." "Me? Makarantar su Aiman fa ka ce, dubu ashirin da biyar ɗin zaka biya mata? Tab'! To wallahi ka nemarwa kanka sauƙi, ka nemi Government School ka kaita." Uncle Umar ya ce "Ai na ga babu Government School a kusa ne shi ya sa." Aunty Fauziyya ta ce "Ga ta nan ana ginawa, ka bari idan an gama ginin sai ka kai ta mana." Daga haka suke rufe wannan chapter, suka kama wata. Washegari bayan Neehal ta gama shan akinta kamar kullum aka aike ta siyan kayan miya, yau ma ba ta ci abinci ba ta tafi, gashi abun da bata ci ma Aunty Fauziyya ta yi wato tuwo, tuwon ma miyar kuka. Ta zo dai_dai layin da suka haɗu da mutumin jiya wanda ta rad'a masa suna *Uncle mai kirki* , har ta wuce gidan ta dawo ta tsaya a ƙofar gidan tana kallon gidan, a hankali ta ƙarasa jikin ƙofar ta fara knocking, 2 minutes tana tsaye sannan aka buɗe ƙofar. Faɗaɗa fara'a ta yi sosai kamar yadda shi ma yake fara'ar cike da mamakin ganin ta, yana sanye cikin ƙananan kaya wanda suka masa kyau sosai, sai tashi daddad'an k'amshinsa yake. Neehal ta ce "Ina yini." Yana murmushi ya ce "Lafiya k'alau." Juya wa ya yi ya ce "Come in." Neehal ta tsaya ba tare data bishi ba, ya juyo ya ce "Ya kika tsaya? Ki shigo mana." Neehal ta girgiza masa kai alamun a'a, ya ce "Why?" Ta ce "Ina jin tsoro." Da ƙyar ya lallaɓa ta ta shiga gidan, a BQ yake har ciki ta shiga ta zauna a falo a d'arare, haɗadd'iyar pride rice ya kawo mata a plate da bottle water da juice, da murna Neehal ta karb'a ta fara ci. Zama ya yi yana kallonta cikin tausayinta. Sai da ta ci ta yi ƙat sannan ta ce "Uncle ina Mamanka?" Ya ce "Tana cikin gida." Ta ce "Nan part ɗinka ne?" Ya ce "Ehh." Shiru ta yi tana ƙarewa falon kallo, cikin kulawa ya ce "What is your name?" Neehal ta ce "Neehal." Ya ce "Wow Nice name, real name ɗinki fa?" Ta ce "Fateemah." Ya ce "Wow! My mother's name." Neehal ta ce "And you?" Ya yi murmushi ya ce "Ahmad." gyaɗa kai ta yi tare da tashi da sauri ta ce "Zan tafi Uncle, zan siyo wa Aunty kayan miya, idan na daɗe zata zane Ni." Ya ce "To Princess, gobe ma zaki zo ko?" Neehal ta yi shiru can kuma ta ce "Ehh." Har bakin titi ya raka ta sannan ya dawo gida. Yau ma data koma gida sai da ta sha bala'in Aunty Fauziyya. Tun daga wannan ranar kullum sai aka aike ta sai ta biya gidansu AHMAD, ya bata lafiyayyen abinci ta ci da drinks, wataran kuma ice cream da snacks yake bata, choculate da sweet kam kullum sai tasha su ta more, idan ta koma gida kuma Aunty Fauziyya tay ta mata masifa, wataran har da duka akan dad'ewar da take, amma ko sau ɗaya bata taɓa tambayarta inda take zuwa ba. Idan ta bawa Neehal abinci sai ta k'ulle a leda ta faki idon Aunty Fauziyya ta fita ta bawa almajiri, tunda yanzu kullum a k'oshe take wuni, abincin dare ma kullum sai ta rage kaɗan take ci. Breakfast kawai take yi full a gidan. A hankali shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Neehal da Ahmad, kullum ta zo yana mata tambayoyi a game da rayuwarta, a haka ya gane marainiya ce kuma bata haɗu da uwar riƙo ta gari ba, hakan ya ƙara masa tausayinta a zuciyarsa sosai, kullum yana mata ƙarin haddarta na Alqur'ani tunda Uncle Umar ya ƙi saka ta a Islamiyya da School, haka karatun boko kullum yana mata lesson, sai ta yi fiye da awa biyu a gidansu, ta koma gida kuma ta ci duka, amma duk da haka gobe sai ta karsi zuwa. Yau Sunday da misalin ƙarfe biyu na rana Neehal tana zaune ita kaɗai a ɗaki tana bitar haddarta, su Aiman kuma sun tafi Islamiyya. Uncle Umar ma baya nan, duk da yau Sunday amma ya fita tun safe shagonsa da yake sayar da kayan masarufi, kuma ba ya dawowa sai dare, kullum haka yake dama, Monday to Friday ma bayan sun tashi daga School ɗin da yake koyarwa can shagon yake wuce wa. Aunty Fauziyya ta tak'wala wa Neehal kira, Neehal ta miƙe da sauri ta fito waje. Aunty Fauziyya tana mata wani mugun kallo ta cilla mata kuɗi ta ce "Ɗauki kuɗin nan, ki je ki siyo mun kayan miya, kuma yau ma ki biya yawon naki da kika saba, wallahi dukan dana miki jiya Nafila ne akan wanda zan miki yau idan kika daɗe. Neehal ta ɗauki kuɗin ta koma ɗaki ta ɗauko Hijab da hula ta saka sannan ta fito ta tafi. Duk da gargadi'n da Aunty Fauziyya ta mata sai da ta biya gidansu Ahmad, dan dukan Aunty Fauziyya zuwa yanzu har jikinta ya saba da shi. Kamar kullum bayan ta yi knocking ya zo ya buɗe mata ƙofa ta shiga. Yau ba BQ ya kai ta ba, ainihin cikin gidan ya nufa da ita. A falon gidan ya zaunar da ita sannan ya nufi kitchen yana kiran sunan Mamy, Mamy wadda takasance ƙanwar mahaifiyar Ahmad ta fito daga kitchen tana amsa masa. Ya tsaya tare da faɗin "Sannu da aiki Mamy." Mamy ta ce "Yawwa son." Nuna mata Neehal ya yi ya ce "Ga yarinyar da nake baki labarinta na kawo miki ita." Mamy ta washe baki tana duban inda Neehal take ta ce "Ita ce wannan, Masha Allah, ga ta kyakkyawa da ita." Ta ƙarasa kusa da Neehal ɗin, Neehal ta durqusa ta ce "Ina yini Mama." Mamy ta ce "Lafiya k'alau, sannunki yarinya ya sunanki?" Ta ce "Neehal." Mamy ta ce "Masha Allah, Allah ya miki albarka ya inganta rayuwarki." Ahmad dake tsaye yana fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa da "Ameen." Mamy ta kawo wa Neehal lafiyayyen abinci da ruwa da juice, Neehal ta mata godiya sannan ta zauna ta ci. Mamy sai kallonta take cike da tausayawa, dan Ahmad ya tsakura mata labarin Neehal. Bayan Neehal ta gama cin abinci ta dubi Mamy ta ce "Please Mama ki tsefe mun kaina, na ce Aunty ta tsefe mun ta ce inyi da kaina, ni kuma ban iya ba." Mamy ta yi murmushi ta tashi ta ɗauko kibiya ta ce Neehal ta cire hijabin jikinta ta tsefe mata, Neehal tana cire Hijab sai ga shatin bulalar jiya ruɗu_ruɗu a jikinta, kasancewar hannun rigar jikinta k'arami ne. Mamy tay salati ta ce "Neehal wa ya dake ki haka?" Neehal ta ce "Aunty ce." Mamy cikin tsananin ɓacin rai ta ce "Amma kuwa wannan matar bata da imani ko kaɗan, yanzu wannan yar yarinyar ita akewa irin wannan dukan kamar wani qaton gard'in? Wai duniya ina zaki da mu ne, dan bake kika haifi 'ya ba sai ki dinga zaluntar ta, menene abun damuwa a riqon ƴar wannan yarinyar da za'a dinga azabtar da ita haka?" Cikin takaici Ahmad ya ce "Hmm, kin ga wannan dukan kullum sai an mata shi, kuma Mamy wanke wanke, shara, mopping, wanki ta ce mun kullum ita take yi, sannan tai aike, kuma sun ƙi sata boko da islamiyya." Mamy ta ce "To kuwa wannan mata ta kiyayi duniya, dan wallahi cutar da Maraya ba ƙaramin abu ba ne, ta kiyayi randa Hakkin yarinyar nan zai kamata, kuma itama uwa ce ta haifa ko zata haifa nan gaba, kuma ba ta san inda ƴaƴanta zasu ƙare rayuwarsu ba, tunda ba'a mata alƙawari zata rayu da su har abada ba." Sosai ran Mamy ya ɓaci tai ta faɗa kamar zata ari baki, da gidan Fauziyyan ma ta ce zata je ta mata tatas duk da bata san ta ba, da ƙyar Ahmad ya taushe ta ta haqura ta fasa zuwan. Tass ta tsefe wa Neehal daddaud'an kanta da tunda ta dawo gidan Uncle Umar kusan 2 months Sau ɗaya wata mak'ociyarsu ta taɓa mata kitso. Mamy ta wanke mata kan tass ta busar da shi ta shafa wa gashin mai, ta mata wanka ta shafe mata jiki da mai, har yankan farce da cire dattin kunne sai da Mamy ta mata ranar. Tana yi tana mitar baƙin ciki Aunty Fauziyya take dan ta ga Neehal kyakkyawa ce shi yasa bata kula da ita. Ahmad kam daga baya dariya Mamy'n ta fara ba shi da mitartata, sai ga Neehal ta fito fess da ita sai k'amshin turaren da mamy ta saka mata take. Sai wajen ƙarfe biyar Ahmad ya raka Neehal ta siyo kayan miyan, suna tafe yana ta aikin maimaita mata "Ta yi kyau sosai." Dan har cikin zuciyarsa ta masa kyau ba kaɗan ba. Ita kam Neehal sai dai tay masa murmushi kawai. Har kusa da layinsu ya rakata sannan ya juyo, ita kuma ta ƙarasa gida..........✍️ _*Yau ban yi edit ba, sorry for the typed error.*_ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:47] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *3️⃣0️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* .........Sosai Ahmad yake jin nishad'i da farinciki a duk lokacin da suka kasance tare da Neehal, sai ya ji kamar kar ta tafi ta zauna tay ta masa hirarta da muryarta mai daɗin sauraro gami da sassayan murmushinta. Har cikin ransa yake jin wani abu game da yarinyar, a da yana tunanin tausayi ne kawai, amma yanzu duk da da akwai tausayin amma da wani abu daban da ya kasa gane ko menene. Babban tashin hankalinsa yanzu befi 1 month ya rage masa ya koma gidansu ba, dama a Abuja suke wani course ne ya kawo shi Kano, dan shi bai taɓa zuwa Kano ba sai wannan time ɗin, saboda duk Relatives ɗinsu a Abuja suke both na Mamanshi dana Dad ɗinsa. Mamy ma da a Abuja take, a wurin aiki ne aka yi posting ɗin mijinta zuwa Kano shine suka dawo, itama ba tafi two years da dawowa ba. Zuciyarsa babu daɗi ya ƙaraso gida, zama ya yi akan kujera yana sauke numfashi, a hankali ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa ya latsa ya shiga kallon pictures ɗin da yay wa Neehal d'azu, ta yi kyau sosai tana ta zuba murmushi. Zuciyar Neehal cike da tsananin tsoro da fargaba ta ƙarasa gida, ba ta ga Aunty Fauziyya a tsakar gida ba, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙarasa kitchen ta ajiye kayan miyan sannan ta nufi falo, nan ma ba ta ga Aunty Fauziyyan ba, hakan ya sa ta wuce ɗakinsu tana sauke ajiyar zuciya. Yau wani daɗi take jin jikinta ya mata, to mamy ta dirje ta tass ta fitar mata da duk wani datti da daud'a dake jikin nata. Sai wajen magriba time ɗin su Aiman sun dawo daga islamiyya ta ji maganar Aunty Fauziyya, gabanta ya yanke ya faɗi saboda tsoro. Fauziyya wadda tun kafin la'asar ta kwanta take baccin asara sai yanzu yaranta suka tashe ta, ko sallar la'asar ba ta yi ba. "Neehal! Neehal!!" Ta shiga ƙwalawa Neehal kira, Neehal ta fito da sauri tana faɗin "Na'am Aunty." Wani mugun kallo Aunty Fauziyya ta jefe ta da shi kamar kodayaushe, ta ce "Ina aiken dana miki?" Neehal ta ce "Na ajiye a kitchen." Aunty Fauziyya ta ce "Yau ma sai da kika gama yawon naki sannan kika dawo ko?" Neehal ta girgiza mata kai cikin tsoro. Aunty Fauziyya ta ce "Hmm, munafukar yarinya, zaki yi bayani ne idan wanda ya ajiye ki ya dawo gidan, zaki faɗa masa inda kike zuwa ne, in ma iskanci kike zuwa ki yi duk za ki masa bayani." Neehal dai tay shiru kanta na ƙasa. Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ƙara cewa "Taso ni mu je ki mun tsinta." Neehal ta tashi ta bi bayan ta, a k'aton farantin silver ta zubo shinkafa yar Hausa ta ajiye a gaban Neehal ta ce ta tsince mata, Neehal ta kalli shinkafar ta kalle ta, ta ce "Aunty ban iya ba." Rank'washinta Aunty Fauziyya ta yi sannan ta nuna mata yanda zata yi. Neehal fa ta duk'ar da kai ta fara tsinta, ga duhun Magriba ya kawo kai da ƙyar take gani. Fitila Aunty Fauziyya ta bata ganin magriba ta yi, Neehal ta ce "Aunty bari na yi sallah sai na cigaba." Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ce "Dalla ni ki cigaba da mun aikina, algungumar yarinya kawai, sai ka ce da Sallar kike, ko kuma in kin yi lada zaki samu." (Allah ka raba mu da jahilci.) Neehal ta turo baki gaba ta cigaba da tsintar, Nasihar Abbanta da yake mata a kodayaushe ta tuno, inda yake ce mata "Ƴar albarkata ko me kike yi idan kika ji an kira Sallah ki bar shi ki je ki yi Sallah, idan kin idar sai ki ci gaba." Tun tana ƴar k'ank'anuwarta yake faɗa mata haka. Hawaye ne ya zubo daga cikin idanunta, da sauri ta share su dan kar Aunty Fauziyya ta gani, Allah ya rufe wa Aunty Fauziyya ido ba ta ga canzawar da Neehal ta yi ba na gyara ta da Mamy ta yi, gashi kanta da hula shi yasa ba ta lura da gashinta da ya sha gyara ba, da yau Neehal ta shiga uku. Sai wajen isha'i ta gama tsintar, duk da shinkafar bata da tsinta sosai, amma saboda bata saba ba shi yasa ta daɗe, aiko da ƙyar ta iya tashi dan bayanta ya k'age, ga cizon sauro da ta sha, Aunty Fauziyya kuwa ko sannu sai ma tukwuicin harara ta samu. Kan kujera ta je ta kwanta, yau ta ci sa'a ba'a ce ta sauka ba. Bayan Uncle Umar ya dawo yana ɗakin baccinsu yana marking papers Aunty Fauziyya dake goge Uniform ɗin su Aiman ta dube shi ta ce "Baban Iman inata zuci_zucin ka dawo in faɗa maka wani hali da yarinyar can ta tsira." Ba tare daya d'ago ba ya ce "Wacce yarinya kenan?" Ta ce "Neehal mana." Ya ce "Me kuma ta yi." Ta tab'e baki ta ce "Hmm, yawon banza ta koya, idan na aiketa sai ta yi awa uku a waje, ƴar ƙarama da ita har ta san wani bin maza." Da sauri Uncle Umar ya d'ago ya dubi Aunty Fauziyya ya ce "Haba Fauziyya, yarinyar da ba ta fi shekara goma sha ɗaya ba ita zaki ce tana bin maza? Ki dai sake wata maganar ba wannan ba gaskiya." Aunty Fauziyya ta ce "Lallai Umar me kake nufi? Sharri zan mata ko me? Kuma idan ba maza take bi ba gidan ubanwa take zuwa idan na aike ta, har ta yi awanni." Uncle Umar ya ajiye red biron dake hannunsa tare da miƙewa a fusace ya ya fito falo. Neehal dake kwance rub da ciki akan kujera har lokacin, ta ɗan samu baccin gajiya ya ɗauke ta ji murya Uncle Umar a tsawace yana cewa "Ke Neehal! Neehal!" A firgice ta farka tare da buɗe ido, cikin muryar bacci ta amsa masa tana ƙoƙarin tashi zaune cikin tsoro. "Gidan uban wa kike zuwa idan an aike ki?" Uncle Umar ya tambaye ta cikin tsawa, Neehal ta manne jikinta ba ta ce komai ba, Uncle Umar ya ƙara daka mata wata tsawar da faɗin "Ba dake nake ba." Neehal bata iya ƙarya ba, hakan yasa ta fashe da kuka dan ta san idan ta faɗawa Uncle Umar inda take zuwa sai ya kusa kashe ta da duka. Masifa ya dinga surfa mata, ya kuma ce aka kuma aiken ta ta daɗe sai ya karya k'afarta. Ba ƙaramin tsorata Neehal ta yi da Uncle ɗin nata ba, hakan yasa washegari bata biya ta gidansu Ahmad ba. Shi kuwa tun da ya yawo daga inda yake zuwa aiki yake ta zuba idon ganinta amma ya ji ta shiru har yamma. Yau data koma da wuri Aunty Fauziyya ta ce "Ehh lallai, wato ni kika raina shi yasa ba kya jin maganata, shi da kike tsoronsa gashi ai kin ji faɗan sa." Ta ƙarashe zancen tare da jan k'wafa. Neehal kam tunanin Uncle ɗinta Ahmad ta shige ɗaki tana yi, ta san yanzu ya siyo mata kayan daɗinta yana jiran ta je ta ci. Yau kwana uku Neehal bata je gidansu Ahmad ba, kullum sai dai ta kalli gidan ta wuce. Misalin ƙarfe 2/30mp Aunty Fauziyya ta aiki Neehal siyan kayan miyan gado, dan shi kaɗai ne aikenta tunda komai na abinci Uncle Umar ya siyo ya dire, sai kuma markad'e idan babu wutar Nepa. Babu musu ta karb'a kamar kodayaushe ta tafi. Yau ma kallon gidansu Ahmad ta yi ta wuce duk kuwa da yanda zuciyarta take azalzalarta akan ta shiga, amma tsoron abun da Uncle Umar zai mata idan Aunty Fauziyya ta faɗa masa yasa take ƙin shiga. Tana shan kwana Motar Ahmad na shigowa layin, cikin tsananin murnar ganinta Ahmad ya taka burki wanda har yasa ta tsorata ta yi baya. Da sauri ya buɗe murfin Motar ya fito, da mamaki ya ce "Princess." Neehal ta washe baki ta ce "Uncle ɗina ina yini." Ya ce "Lafiya k'alau Princess, me yasa kwana biyu ba kya zuwa." Neehal ta ce "Uncle ne ya hana ni, ya mun faɗa sosai, He said in aka ƙara aike na na daɗe sai zane ni." cikin rashin jin daɗi Ahmad ya ce "Ayya I missed you alot dear." Neehal ta ce "Me too Uncle." Ahmad ya ce "Mu je gida in baki cake da sweet ɗinki." Da murnarta ta ce "Toh." Yanayin garin damuna ta fara shigowa dan shekaran jiya ma an yi ruwa, yau ma garin ya yi luf kamar hadari_hadari. Gashashshiyar kaza Ahmad ya bata da yoghurt, Neehal ta zauna ta ci ta k'oshi tay hamdala. Mantawa ta yi da wani tsoron Uncle Umar ta zauna ta shiga yi wa Ahmad hira, shi kuma yana ta aikin murmushi cikin jin daɗi da nishad'i, sai yanzu da ya ganta ma ya ƙara tabbatar da ya yi kewar ta sosai. Kiran sallar la'asar ne ya tashe su, Ahmad ya yi alwala suka fita tare ya rakata ta siyi kayan miyan sannan ya wuce masallaci ita kuma ta nufi gida. Zuwa lokacin hadari ya ƙara haɗuwa sosai har an fara Iska, sauri Neehal tay ta yi kar ruwa ya sauko tana waje, aiko ana idar da Sallah aka fara yayyafi, da gudu ta ƙarasa gidan dan har ta fara jik'ewa, kitchen ta nufa zata ajiye kayan miyan amma sai ta tarar da shi a kulle da mukulli, ga ruwan ya fara ƙarfi. Ƙofar falon ta dawo ta fara bugawa da ƙarfi tana faɗin, "Aunty! Aunty, na dawo ki buɗen ƙofa!" Amma Fauziyya tana ji ta ƙi buɗe ƙofar, gashi kaf tsakar gidan babu gurin fakewa, dan ko toilet babu duka suna cikin ɗaki, kitchen ne kawai kuma ta kulle. Gashi irin gidan nan ne da kana buɗe gate ɗinsa sai tsakar gida babu soro. Haka Neehal ta takure jikinta cikin ruwan dan bata da yanda zata yi, cikin ikon Allah kuma ruwan ya tsuge kamar da bakin kwarya, Neehal ta runtse ido tana jin saukar ruwan ajikinta. A hankali kuma ya fara ɗaukewa, sai da ya ɗauke dif sannan Aunty Fauziyya ta buɗe ƙofar falon ta fito, Neehal na tsugunne a bakin ƙofar sai rawar ɗari take saboda sanyi ta ci kuka ta gode Allah. Aunty Fauziyya ta ɗauke kayan miyanta tare da faɗin "Kar ki shigar mun ɗaki kina yarari, ki jik'a mun ɗaki." Neehal ta miƙe ta cire komai na jikinta ta shanya a igiya, pant kawai ta bari sannan ta shige falon da sauri. Aunty Fauziyya tay dariyar mugunta ta ce "Gobe ma kya ƙara tafiya gantali Shegiyar yarinya kawai." Ita kam tana shiga ɗaki ta yi toilet ta cire pant ɗin jikinta ta rarumi towel ta ɗaura a jikinta sannan ta tsugunna ta yi fitsarin daya matse ta. Tana fitowa ta hau kan katifa ta ja bargonsu Aiman ta lullub'a. Aiko kafin dare mura ta mata mugun kamu, ranar da tari ta kwana. Washegari duk masifar Aunty Fauziyya ba ta saka ta aiki ba, dan jikin nata ya yi zafi ba kaɗan ba, ta san ma ko ta saka ta ba iyawa zata yi ba shi yasa. Amma ta sha zagi da masifa, a cewarta cutar ma ta ƙarya ce da shegen rakin tsiya. Kwana huɗu ta yi a kwance, a ran na biyar ne ta fara samun sauƙi, shi ma sai da Uncle Umar ya ga ciwon ya ƙi ƙarewa sannan ya kaita chemist aka bata magani, aiko suna tafe yana mitar ta ja masa asarar kuɗin da ya siya mata magani, maganin da ko 1K bai kashe ba, alhalin kuma dukiyarta da duk wata kadararta tana hannunsa. Bayan ta warware aka cigaba da aikenta, kullum sai sun haɗu da Ahmad amma ta daina shiga gidansu sai dai su haɗu a ƙofar gida, yasan lokacin da ake aikenta, dan haka time ɗin yana yi zai fito ƙofar gida ya zauna zaman jiranta, saboda ta bashi labarin dukan da ruwa ya mata har ya sata zazzaɓi akan ta daɗe ranar, shi kuma saboda tsananin tausayinta shi yasa ya daina tsayar da ita, dan kar a ƙara yi mata wata muguntar. Amma duk da haka bai daina bata abubuwan da yake bata abaya ba, idan ta je gurin mai kayan miyan akwai benci wanda dan customers aka tanade sa, anan take zama ta yi sauri ta cinye abun da ya batan sannan ta koma gida. Haka rayuwa tay ta tafiya da Neehal a gidan Uncle Umar cikin wahala da azaba kala_kala a gurin Aunty Fauziyya, gurin Ahmad kawai take jin daɗi, gashi ta yi magiyar a saka ta a makaranta an ƙi, har ta gaji ma ta dai na, sai ɗan lesson ɗin da Ahmad yake mata atsaitsaye. Yau ma bayan Neehal ta gama shan ayyukanta tana zaune a kitchen tana juya miyar da Aunty Fauziyya take soyawa, ta shiga ɗaki ne shine ta ce Neehal ɗin ta cigaba da juya mata dan kar ta roqe. Wayar Aunty Fauziyya dake kitchen ɗin ce ta fara ringing, cikin ɗan daga murya Neehal ta ce "Aunty ana kiran ki a waya." Aunty Fauziyya bata amsa mata ba sai turo Aiman ta yi ya ɗauko mata wayar, kasancewar yau Friday ce suna gida. Aiman yaro ne mai k'iriniya baya abu cikin nutsuwa ko kaɗan, da gudu ya shigo kitchen ɗin ya ɗauki wayar, ya zo fita ya b'arar da taliyar da Aunty Fauziyya ta tace kafin ta bar kitchen ɗin, fiye da rabin taliyar ya zube a ƙasa. Neehal ta tashi da sauri tana faɗin "Ka ga ka yi ɓari ko?" Aiman bai saurare ta ba ya yi ɗaki da gudu yana kiran uwarsa, Aunty Fauziyya ta taso da sauri tana faɗin "Mene ne." Ya ce "Aunty Neehal ce ta b'arar miki da taliya." Ai bai ƙarasa ba Aunty Fauziyya ta fito a fusace ta shiga kitchen ɗin, Tafa hannuwa ta shiga yi tana faɗin "Eh lallai, tun da ba Ubanki ne ya nemo ba ba kuma Uwarki ce ta dafa ba ai dole ki b'arar." Neehal ta ce "Aunty ba fa ni na b'arar ba Aiman ne." Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ce "Rufe mun baki zaki ne bayani ne, shegiya mai baƙin hali, kwashe mun ita tass da hannunki, idan kin gama kuma ki zo ɗaki ki karb'i hukuncinki." Neehal ta sa hannu ta fara kwashe taliyar, ga taliyar sai tururi take saboda ba a daɗe da sauke ta ba, Aunty Fauziyya tana barin kitchen ɗin Neehal ta ɗauki serving spoon ta cigaba da kwashe wa da shi, saboda hannunta zafi. Sai da ta kwashe duka sannan ta debo ruwa ta d'auraye ta. Ɗakin ta nufa cikin tsoro ta ce "Aunty na gama." Aunty Fauziyya tay wani murmushi ta ce "To ƙaraso mana kika tsaya a bakin ƙofa." Cikin ɗari ɗari Neehal ta ƙarasa idanunta taf da ruwan hawaye. Aunty Fauziyya ta kamo hannunta, kuka ta saka ta ce "Aunty dan Allah ki yi haquri." Aunty Fauziyya ba ta kula ta ba, ta kamo hitar data jona a jikin socket ta ɗora a ƙafar Neehal. Wani irin zirrrrr Neehal ta ji ajikinta na shock ta ji kamar an d'aga ta sama. Ai bata san sanda ta k'wala ihu mai ƙarfi ba tare da fizge jikinta ta fice daga Falon da mugun gudu, gaba-d'aya jikinta rawa yake kamar mazari, cikin fitar hayyaci ta fice daga gidan gaba-d'aya, gudu take da dukkan ƙarfinta gani take kamar Aunty Fauziyya ta biyo ta zata ƙara sa mata shock ajikinta. A ƙofar gidansu Ahmad sukai cikibus, ya dawo daga masallaci da Darduma a hannunsa. Neehal ta ƙarasa gare shi ta riƙe shi gam tare da sakin kuka, har lokacin jikinta rawa yake. A ruɗe Ahmad ya shiga kiran sunanta "Princess! Princess what happened to you?" Yana ƙoƙarin d'agota daga jikinsa, ita kuwa ƙara k'ank'ameshi ta yi. Fahimtar da ya yi a firgice take sai kawai ya sunkuce ta ya shiga cikin gidan da ita. A kan kujera ya kwantar da ita, cikin kulawa ya ƙara tambayar ta da faɗin "Princess mene ya faru? kika fito ko takalmi babu a ƙafarki." Cikin kuka ta ce "Un... Uncle shocking Aunty ta samun a jikina." A ruɗe ya ce "Subhanallah shocking kuma Princess?" Bai jira amsar ta ba ya miƙe da sauri ya nufi ƙaramin kitchen ɗin dake falon ya ɗauko gwangwanin pick milk ta ruwa ya fasa ya juye ta a glass cup, sannan ya fito ya dawo gurin da take a kwance tana ta sauke numfarfashi. Ɗago kanta ya yi ya kafa mata cup ɗin a baki. Ba musu ta shiga sha. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta lumshe idanunta ta koma ta kwanta, Ahmad nata jera mata sannu cikin tsananin tausayinta. Ranshi ba ƙaramin ɓaci ya yi ba yau game da Aunty Fauziyya, ya rasa matsayin da zai ajiye matar akan rashin imani, da Mamy zata ji maganar nan yanda take da zuciya ya san tsaf zata iya kaita a kulle. Ƙura mata ido ya yi da idanunsa da suka fara canza launi saboda ɓacin rai, yana jin wani abu na fizgar zuciyarsa game da Neehal ɗin. Ajiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta akai_akai alamun bacci ya ɗauke ta, gyara mata kwanciya ya yi yanda zata fi jin daɗin baccin. Babbar damuwar Ahmad a duniya ɗaya ce a halin yanzu, jibi Sunday zai koma gidansu Abuja, tun last week ya gama abun da ya kawo shi Kano, amma saboda Neehal ya kasa koma wa gida, gashi parent ɗinsa sun matsu ya dawo, kasancewar shi kaɗai ne ɗansu Namiji, dama su biyu ne a gurin iyayensu daga shi sai ƙanwarsa mace, ƙanwar tashi ma ƙarama ce bata fi 4_5 years ba, 20 years ya bata. Sai bayan la'asar Neehal ta farka, ya je masallaci ya dawo ya tatar ta tashi. Ya ƙarasa kusa da ita ya ce "Kin tashi." Ta ce "Ehh, Uncle ka kai ni gurin Mamy na yi wanka, jikina babu daɗi." Ya ce "Mamy bata nan, amma bari na kai ki ki yi anan." Ta ce "Toh." Toilet ɗin dake cikin bedroom ɗinsa ya kai ta, Brush ya bata sabo da MacLean ta wanke bakinta, sannan ya haɗa mata ruwa mai dumi ta yi wanka. Bayan ta shirya ya kawo mata abinci da drinks ta zauna ta ci. Tana gamawa ta ce "Uncle Thank you so much." Tattausan murmushinsa ya mata ya ce "Say Alhamdulillah." Itama murmushin ta masa ta ce "Alhamdulillah." Sannan ta tashi ta kwashe kayan ta kai kitchen, ta so tafiya gida amma ya zaunar da ita wai ta masa hira, ba musu ta zauna tana shan choculate tana masa hirar, shi kuma sai murmushi yake yana mata video a wayarsa. Sai gab da magriba suka fito daga gidan, a ƙofar gidan ya tsaya tare da hard'e hannayensa a ƙirji ya zuba mata ido. Neehal ta ce "Uncle bye." Tare da d'aga masa hannu, numfashi ya sauke cikin wata irin murya ya ce "Princess!" Ta ce "Na'am Uncle ɗina." Kusa da ita ya matso sosai ya kama hannunta cikin sanyin murya ya ce "I love You!" Neehal ta yi murmushi ta ce "Love You too Uncle." Lumshe idonsa ya yi cikin jin daɗi, a hankali kuma ya sunkuyo ya yi picking forehead ɗinta sannan ya sakar mata hannunta, har ta fara tafiya ya ƙara kiranta, ta dawo da sauri, tsugunna wa ya yi dai dai tsayinta yana kallon cikin idonta ya ce "Princess, promise me you will never forget me in your life." Neehal ta ce "I promised you Uncle." ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai. Fuskarta ya shafa ya ce "Thank you dear." Neehal ta masa bye_bye sannan ta juya ta fara tafiya, haka kawai ta ji jikinta ya mata wani irin sanyi. Shi kam Ahmad tsayawa ya yi yana kallonta yana jin jikinsa kamar babu laka ba tare da yasan dalili ba. Duk wannan abun da ya faru tsakanin Neehal da Ahmad Uncle Umar yana farkon layin akan machine ɗinsa yana kallonsu cikin tsananin ɓacin rai, yana shago Aunty Fauziyya ta kira shi akan ya zo gida babu lafiya, dan tun safe Neehal ta fita kuma har yanzu bata dawo gida ba, shine fa ba shiri ya baro shagon ya taho, yana shigowa layinsu Ahmad dai-dai lokacin su kuma su Neehal sun fito daga gidansu Ahmad, cikin shock ya tsaida machine ɗinsa ya tsaya yana kallonsu. Neehal ta juyo ta ga ko Ahmad ya shige gida idanunta suka sauka akan Uncle Umar wanda ya figo machine ɗinsa a fusace..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:47] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *3️⃣1️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ...........Ba ƙaramin kaɗuwa da firgita Neehal ta yi ba da ganin Uncle Umar, juya wa ta yi ta falfala a miliyan ta nufi gida. Ahmad dake tsaye yana kallonta ya cika da mamakin abun da yasa ta gudu da firgita lokaci ɗaya, bai gama mamakin ba ya ji tsayuwar babur a gabansa kamar yaƙi, kafin ya yi magana Uncle Umar ya sauko daga kan babur ɗin, yana ƙarasa wa kusa da shi bai yi wata_wata bae ya cakumi kwalar rigar Ahmad cikin zaro ido waje ya ce "Kai ne kake hure wa ƴata kunne dama, munufinki Allah yau Allah ya toni asirinka, kune irin mutanen nan masu ɓata ƴaƴan mutane wato, to ka sani wallahi sai na yi shari'a da kai, kotu ce zata raba mu." Kallon shi kawai Ahmad yake yi cikin rashin fahimta, k'wace jikinsa ya yi ya ce "Malam lafiya zaka zo ka ci kwalata kana faɗar maganganun da ban gane musu ba tare da jifana da munanan kalamai." Uncle Umar dake kallon gidansu Ahmad ganin gidan ƙato yasa ya yi baya dan ya san bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne. A harzuk'e yake faɗin "Zama ka gane ne, idan ka ga sammaci." Babur ɗinsa ya hau a fusace ya tayar da shi ya nufi gida. Ahmad ya tab'e baki sannan ya juya ya shige gida, a zuciyarsa yana Addu'ar Allah ya kare Neehal daga muguntar waɗannan azzaluman mutanen ya kuma hana su cutar da Ita. Da gudu Neehal ta shiga gida ta yi ɗaki dan neman gurin b'uya, domin ta san idan Uncle Umar ya kama ta yau mai k'watar ta a hannunsa sai Allah. Aunty Fauziyya jin motsinta ta fito daga ɗakinta, jijjiga kai ta hau yi ta ce "Sannunki, shegiya karuwar banza, ƴar ƙaramarki dake kin san bin maza, to yau zan yi maganinki dan Uwarki, gaban naki zan k'ona sannan in miki tsarki da jajjageggen attaruhu, sai in ga da abun da zaki yi iskancin gobe." Ta ƙarasa zancen tare da fizgo Neehal da ƙarfi. Neehal ta fasa kuka ta ce "Dan Allah Aunty ki yi haquri, wallahi ba zan ƙara ba." Wani wawan mari Aunty Fauziyya ta zabga wa Neehal. Neehal ta fasa ƙara ta ce "Wayyo Allah, Ummanah, Auntynah...." Wani marin Aunty Fauziyya ta ƙara kifa mata wanda yasa ta kifawa a ƙasa, Aunty Fauziyya ta ce "Uwarkin da Aunty'n su zo su cece mana shegiya mai kama da aljanu." Tsakar gida Aunty Fauziyya ta fita ta ɗauko wata igiya ta ɗaura a jikin windon kitchen sannan ta dawo falo inda Neehal take durk'ushe har lokacin ta janyo ta kamar wata tinkiya ta ɗaure k'afarta da igiyar, Neehal ta ƙara volume d'in kukanta tana ba ta haquri, amma Fauziyya bata saurare ta ba ta shiga kitchen ta ɗauko wayoyin wutar data haɗa dan zane Neehal. Dai_dai lokacin Uncle Umar ya shigo gidan a babur ɗinsa, kafe babur ɗin ya yi a fusace tare da sauko wa, bai bi takan sannu da zuwan da Aunty Fauziyya take masa ba ya k'wace wayar hannunta ya zabgawa Neehal a ƙafa yana faɗin "Dan Ubanki dama ashe bin maza kike har gida kuna iskanci, tarbiyyar dana baki kenan, yaushe ma aka haife ki da har zaki lalace haka ehe!." "Wayyo dan Allah Uncle ka yi haquri ba zan kuma ba, wayyo Allahna, Abbana......." Magiyar da Neehal take ta masa kenan cikin kuka, amma ya rufe idonsa ya dinga tafkar ta da waya. Aunty Fauziyya daɗi kamar ya kashe ta, duk wani makusancin Neehal a duniya sai da ta kira shi sunansa dan ya neman taimakonsa saboda azabar duka, tun tana kuka da da ƙarfin murya har muyar ta dashe. Wata mak'ociyarsu mai suna Binta wadda ta taɓa yi wa Neehal kitso ce ta shigo gidan a guje saboda ihun Neehal da take jiyo wa, ganin yanda Uncle Umar yake tafkar ta kamar an aiko sa yasa ba ta san lokacin data ƙarasa ta hankad'e shi gefe ba. Uncle Umar ya taso a fusace ya ce "Ki ƙyale ni in kashe ta data jawo mun abun kunya." Matar tana hawaye ta ce "Ba zan ƙyale ka ba, Kuma wallahi baza ka ƙara dukan yarinyar nan ba, sai dai ka haɗa ka dake mu tare." Ta fashe da kuka ta ce "Wannan wanne irin zalunci ne da rashin imani? Me yarinyar nan ta muku kuke azabtar da ita haka? Idan baza ku iya roqon ta ba kukai ta gurin waɗan da zasu iya mana, wallahi da wannan muguntar da kuke mata gara ta gwammace a gidan marayu ta tashi." Uncle Umar da sai huci yake kamar zaki ya yar da wayar hannunsa ya ja ƙwafa ya fice daga gidan. Aunty Fauziyya ta dubi Binta ta ce "Hmmm, Maman ikram dan baki san abun da yarinyar nan ta yi ba ne, da kin san abun da ta yi da kin bar Baban Iman ya cigaba da dukan ta." Binta ta ce "Ko me ta yi bata cancanci wannan cin zalin ba, kuma wallahi sai Allah ya saka mata, haqqin yarinyar ba zai taɓa barin ku ba." Aunty Fauziyya ta tab'e baki ta ce "Bin maza fa take dan...." "Sai dai ki gani akan ƴaƴanki Insha Allahu wannan alkaba'in ba dai akan marainiyar Allah ba, kuma ko wanne hali yarinyar ta shiga laifinku ne, kun quntata wa rayuwarta da izaya da matsi haka kawai saboda ba ku kuka haife ta ba. Me tay muku? Me ta tsare muku a rayuwa? Wallahi ku bi a hankali da duniya, kuma ku ma kun haifa indai ƴaƴa ne, kuma baƙu san hannun wanda ƴaƴan nawku za su faɗa ba tunda rayukanmu ba a hannunmu suke ba, inda iyayen yarinyar nan suka je kuma zaku je ne, ina jiye muku ranar nadama da dana sani akan cutar da yarinyar nan da ku kai, ku kiyaye gamuwarku da Ubangiji Fauziyya daga ke har mijin naki." Aunty Fauziyya ta ɓata fuska ta ce "A'a, a'a Binta kar kuma ki yi wa ƴaƴana baki, ki faɗi duk abinda zaki faɗa amma kar ki kuma jawa ƴaƴana alkaba'i gaskiya ba zan ɗauka ba." Binta ta bita da kallon tausayin bin rud'in shaid'an da take wanda har take ganin hakan kamar ba komai ba ne. Ba ta kuma cewa komai ba, ta juya ta tallafo Neehal jikinta tare da kiran sunanta, amma ko motsawa ba ta yi ba, balle ta amsa. A gigice Binta ta shiga jijjiga ta tare da kiran sunanta cikin bugawar zuciya ganin babu alamar numfashi a tattare da ita. Dai_dai lokacin Uncle Usman ya yi sallama tare da shigo wa gidan...........✍️ _*Da babu gwara ba daɗi*_ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:47] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *3️⃣2️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ..........Aunty Fauziyya ta amsa masa sallamar cikin mamakin ganin sa a dai-dai wannan lokacin, Uncle Usman da idansa ya sauka akan Neehal wadda Binta keta jijjiga ta a jikinta. Da sauri ya zubar da manyan ledodin dake hannunsa a ƙasa yana tambayar "Lafiya me ya same ta?" Binta tana hawaye ta ce "Dukan tsiya ya mata, wanda har ya kai ta ga suma." Wani irin sarawa Uncle Usman ya ji kansa ya masa, yana ɗago Neehal daga jikin Binta ya ce "Duka kuma? Wa ya dake ta?" Binta ta ce "Babansu Aiman." Uncle Usman ya yi shiru kawai yana bin jikin Neehal da kallo, ganin yanda shatin duka ya fito b'aro_b'aro a jikin lallausar fatarta, wadda wahala ta sa yanzu ta fara canzawa. Lokaci ɗaya idanunsa suka kad'a tsantsar ɓacin rai ya bayyana akan fuskarsa. Cikin rawar jiki ya miƙe da Neehal a jikinsa amma sai ya ji sun koma ƙasa, da mamaki ya kalli k'afarta wadda a zatonsa wani abun ne ya riƙe ƙasan kayanta amma sai ya ga ashe ɗaure mata ƙafar akay. Cikin sauri Binta ta kwance mata igiyar tana Allah wadaran hali irin na Uncle Umar da Aunty Fauziyya. Wani kallo Uncle Usman ya yi wa Aunty Fauziyya sannan ya fice daga gidan cikin k'unar zuci. Aunty Fauziyya ta dubi Binta rai a haɗe ta ce "Kin ji daɗi kin haɗa ƴan'uwa uwa ɗaya uba ɗaya." Binta kamar zata tanka mata sai kuma ta fasa ta fice daga gidan. Aunty Fauziyya ta ja dogon tsaki ta shige ɗakinta. Uncle Usman yana fita direct titi ya yi da Neehal saɓe a kadararsa cikin sauri_sauri gudu_gudu. Yana fita titin ya tsari a daidaita ya ce ya kai shi asibiti mafi kusa da sauri dan Allah, bayan ya shiga mai a daidaitan ya ja suka tafi. Cikin mintuna ƙalilan suka ƙarasa wani private Hospital, bayan ya sallami mai adaidaita ya shiga ciki rungume da Neehal a jikinsa. Cikin sauri wasu Nurses guda biyu suka karb'i Neehal suka nufi wani ɗaki da ita dan bata taimakon gaggawa. Uncle Uwar ya zauna a reception ɗin asibitin tare da dafe kansa da hannunsa ɗaya, a hankali yake fuzgar da zazzafan numfashi cikin tsantsar ɓacin rai. Tabbas kowa ya shaida Uncle Usman yana da haquri da sanyin hali gami da sauqin hali, amma fa bai iya ɓacin rai ba. Har aka kira Magriba likitocin dake duba Neehal ba su fito ba, hakan yasa ya miƙe ya nufi masallaci. Bayan ya dawo ɗaya daga cikin Nurses da suka karb'i Neehal ta ce masa "Yawwa malam ka shiga wancan office ɗin Doctor zai yi magana da kai." Uncle Usman ya ce "Toh." Tare da nufar office ɗin. Bayan ya shiga sun gaisa likitan ya dube shi ya ce "Kai waye ɗinta?" Uncle Usman ya ce "K'anin mahaifiyarta ne." Doctor ya ce "Ina mahaifiyarta ko mahaifinta?" Uncle Usman ya ce "Sun rasu." Doctor ya jinjina kai ya ce "Allah ya ji k'ansu da rahama." Uncle Usman ya ce "Ameen, amma ya jikin nata Doctor?" Doctor ya ce "Alhamdulillah, dan ta farfaɗo daga suman da ta yi sanadiyyar dukan da aka mata, kuma mun mata allurar rage zugi da zazzaɓin daya rufe ta lokaci ɗaya, ga wannan magunguna ne muka rubuta za a siyo yanzu kafin ta farka, sannan kuma zaka je ka biya kuɗin gado da sauran abubuwa." Ya ƙarashe zancen tare da miƙewa Uncle Usman wata takarda. Uncle Usman ya sauke numfashi ya karb'i takardar ya ce "Zan iya ganin ta yanzu Doctor?" Ya ce "Eh, idan ka fita daga nan room mai kallo ka nan zaka shiga." Uncle Usman ya ce "Toh Na gode sosai Doctor." Likita ya ce "Allah ya ƙara sauƙi, nan gaba kuma a kiyaye da dukan ƙananun yara irin haka dan wataran ba za su tashi ba." Ƙasa Uncle Usman ya yi da kansa ya ce "Insha Allahu." Tare da ficewa daga office ɗin. Tana kwance a kan gadon asibitin tana bacci an saka mata drip. Kallonta yake cike da tausayawa, sai ajiyar zuciya take saki a kai_kai alamun ta ci kuka ta k'oshi. Ko ina ka kalla a jikinta ya yi jajur saboda duka. Uncle Usman ya shafa kanta ya ce "Allah ya baki lafiya my baby." Sannan ya fice dan siyo mata magani. Ba jimawa ya dawo da katan ɗin ruwan jakar da yoghurt da kayan fruits. Ganin bata farka ba ya dubi Nurse ɗin da take duba ruwan da aka saka mata ya ce zai je ya dawo. Sai da ya yi Sallar isha'i sannan ya dawo bayan ya siyo mata Balango mai yawa a leda. Zama ya yi akan kajerar dake fuskantar gadon da take a kwance ya zaro wayarsa daga aljihu wadda ake ta kira tun zuwansa asibitin ba jima wa. Missed call ɗin Ummi (Yayar Abba) ya gani sai na Uncle Umar rurutu da kuma na wani abokin kasuwancinsa. Bai bi bayan kiran ɗaya daga cikinsu ba saboda wani dalili nasa, sai ma Numbern budurwarsa daya kira. Ringing biyu ta d'aga, bayan sun gaisa ya ce "Halima dan Allah idan babu damuwa zan zo gida na karb'i aron blanket da darduma, muna asibiti ne Neehal babu lafiya." Halima ta ce "Subahanallah, me ya same ta?" Uncle Usman ya ce "Zazzaɓi take shine aka bamu gado." Halima ta ce "Allah ya sauqaqe, ka zo ka karb'a babu matsala." Godiya ya mata sannan suka yi sallama ya katse wayar. Wata Nurse ya ƙara ba wa amanar Neehal sannan ya bar asibitin. Gidan su Haleemah da ɗan nisa daga asibitin, hakan yasa sai da tara ta wuce ya dawo da kaya a hannu, dan har da su plates da cups da spoons sai da Halima ta haɗo shi da su, shi kuma ya biya ya siyo wa Neehal sabon brush da sosan wanka da su sabula da ƙaramin macLean gami da takalmi slifas. Sai wajen goma Neehal ta farka a zabure cikin dashashshiyar muryarta take faɗin "Uncle ka yi haquri dan Allah ba zan kuma ba." Uncle Usman ya tashi da sauri yana cize lips ɗinta saboda takaici ya ƙasara gaban gadon. Kama hannunta ya yi ya ce "Neehal!" Neehal ta buɗe kumburarrun idonta da sauri ta ce "Uncle ɗina." Uncle Usman ya ce "Na'am Neehal, sannu kin ji, ya jikin naki?" Gyaɗa masa kai ta yi tana bin shi da kallo alamun tana cikin mamakin ganin sa. Shafa fuskarta ya yi ya ce "I'm coming Baby." Fita ya yi da sauri ba jimawa sai ga shi sun dawo da likita, dudduba ta ya yi bayan ya mata sannu sannan ya cire mata drip ɗin hannunta da ya ƙare a lokacin. Magungunan da Uncle Usman ya siyo Doctor ya nunnuna masa wanda zai bata yanzu. Uncle Usman ya masa godiya sannan ya fita. A hankali Neehal ta ce "Uncle zan sha ruwa." Uncle Usman ya tayar da ita zaune ya sa mata filo a bayanta ta jingina da shi yana mata sannu. Ruwa ya dauko ya buɗe mata sannan ya kafa mata a baki, kaɗan ta sha ta cire robar daga bakinta. Lumshe ido ta yi ta ce "Uncle ina Uncle Umar da Aunty Fauziyya?" A dak'ile Uncle Usman ya ce "Suna gida." Neehal ta buɗe idonta da ya cika da hawaye ta ce "Please Uncle ka ba su haquri su daina duka na." Uncle Usman ya ce "Shikenan kar ki yi kuka kin ga baki da lafiya." Neehal ta gyaɗa masa kai ta ce "Uncle ka kira mun Aunty, idan na cewa Uncle Umar ya kira mun ita baya kiran ta." Uncle Usman ya ce "Yanzu dare ya yi ki bari sai da safe in Allah ya kai mu." Zata kuma magana ya katse ta da faɗin "Ki yi shiru haka kin ga baki da lafiya." Neehal ta ce "Toh." Ya ce "Yawwa good girl mu je in kai ki ki yi brush sai ki ci abinci." Kamata ya yi a hankali ganin yanda take yamutsa fuska alamun tana jin ciwon jikinta ya kai ta toilet ɗin ya taimaka mata ta yi brush, sannan ta yi fitsari ya kama ta suka fito. Zaunar da ita ya yi ya ɗauko balangon da ya siyo ya juye a plate ya janyo kujera gabanta ya fara bata a baki, kaɗan ta ci ta ce ta k'oshi saboda bakinta da babu daɗi. Banana ya bata ta ci ɗaya da ƙyar, sannan ya bata magungunanta ta sha ta kora da ruwa. Bayan 5 minutes ya kwantar da ita sannan ya dauk'o blanket ya lullub'e mata jikinta. Neehal tana duban sa ta ce "Yaushe ka zo Uncle?" A tak'aice Ya ce "D'azu, inane yake miki ciwo yanzu?" Neehal ta ce "Kaina da duka jikina." Uncle Usman ya ce "Ki rufe ido ki yi bacci, Insha Allahu in kin tashi da safe zaki ji kin warke." Neehal ta gyaɗa masa kai tare da murmushi cikin jin daɗin ganin sa. Shi ma murmushin ya yi ya ce "Ki yi addu'a kin ji daughter." Neehal ta gyaɗa masa kai tare da lumshe idonta. Washegari bayan Uncle Usman ya dawo daga masallaci ya tarar Neehal ta tashi zaune. Da mamaki ya ce "Har kin tashi?" Neehal ta ce "Ehh, ina kwana Uncle." Uncle Usman ya ce "Ai sai an yi Sallah ake gaisuwa." Neehal ta fara ƙoƙarin saukowa daga kan gadon tana faɗin "To bari na je na yi alwala sai na yi sallah." Cikin jin daɗi Uncle Usman ya ce "Jiki ya yi sauqi kenan Masha Allah." Neehal ta sauko daga kan gadon ta shiga toilet, duk da bata gama jin jikin nata dai-dai ba amma zazzaɓin da ciwon kai sun mata sauqi sosai, jikinta ne dai take jin shi da ɗan tsami saboda dukan da ta sha. Bayan ta fito ta tayar da Sallah akan darduma, duk da bata da Hijab sai ɗan kwalinta ta yafa. Uncle Usman ya zuba mata yughurt ɗin da ya siyo jiya a cup ya bata. Ta sha sosai kuwa saboda da yunwa ta tashi. Wajen 7 da wani abu sai ga Haleemah da ƙanwarta sun zo duba Neehal, dan jiya da Uncle Usman ya je ya faɗa mata asibitin da suke, amma ya yi mamaki lokacin data kira shi ta faɗa mishi ta shigo asibitin ya zo ya ɗauke ta, domin bai taɓa tunanin zuwanta da safiya haka ba. Da k'aton tea flaks ɗinta kuwa wanda ta ciko da ruwan zafi kamar ta san za su buƙata. Basu wani jima ba suka tafi. Tea mai kauri Uncle Usman ya haɗa wa Neehal ta sha sannan ya bata magungunanta suma ta sha. Cikin dabara Uncle Usman yake tambayar Neehal tana faɗa masa irin zaman da take a gidan Uncle Umar. Sosai ransa ya ɓaci fiye da jiya da ya ji irin azabtar da Neehal da Aunty Fauziyya take. Wayarsa ya ɗauko ya bi kiran da Uncle Umar ya masa jiya, ringing ɗaya Uncle Umar ya d'aga tare da faɗin, "Usman wannan wanne irin iskanci ne, zaka ɗauke yarinya tun jiya kuma dan wulaqanci inta kiran ka ka ƙi d'agawa, ina ka kai ta to?" Uncle Usman ya ce "Asibiti na kai ta dan ceto rayuwarta." Ya faɗa masa sunan asibitin sannan ya kashe wayar. Da ruwan zafin da Halima ta kawo Uncle Usman ya haɗa wa Neehal ruwan wanka ta yi, kayan jikinta da ta cire ya ce ta mayar anjima zai ɗauko mata wasu a gidan Uncle Umar. Wajen 8:40 Likita ya zo ya ƙara duba ta sannan ya mata allura, tana kukan allurar bacci ya ɗauke ta. Ganin ta yi bacci Uncle Usman ya lalubo Numbern Aunty A'isha ya kira ta, sai da ta kusa katsewa sannan ta d'aga bakinta ɗauke da Sallama. Uncle Usman ya amsa ya ƙara da faɗin "Ina kwana Aunty dafatan kin tashi lafiya, ya su Hajiya?" Aunty A'isha ta ce "Lafiya k'alau Uncle Usman, su Hajiya suna nan k'alau, ya kwana biyu da bayan saduwa? inata kiran wayarka data Uncle Umar duk bana samun ku dafatan dai lafiya?" Uncle Usman ya ce "Lafiya k'alau, ai yanzu na koma Niger da kasuwancina ne, to idan ina can sai na sauke wannan layin, ina ta son na kira ki amma sabgogi sun sha mun kai, jiya_jiya ma na shigo garin." Aunty A'isha ta ce "Allah sarki, Allah ya taimaka ya ba da sa'a, wancan satin ai na fita daga takaba." Uncle Usman ya ce "Ikon Allah, lokaci ba wahala har kin fita, Allah ya ji k'an su Yaya." Aunty A'isha ta ce "Ameen ya Allah, a satin nan ma nake son shigowa Kano zamu zo siyayya bikin Sadiya ya kusa, ya labarin Neehal kuwa? kana zuwa kana ganin ta? Kullum da ita nake kwana nake tashi a raina, kwanaki ma na so zuwa na ganta Hajiya ce ta hana ni ta ce in bari na fita daga takaba tukunna." Uncle Usman ya ce "Hmm, bari kawai Aunty wallahi Neehal wahala kawai take sha a gidan Ya Umar gurin Matarsa, yanzu ma muna asibiti bata da lafiya saboda dukan da suka mata jiya." A ruɗe Aunty A'isha ta ce "Subahanallahi, Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, asibiti kuma? Wannan wanne irin duka ne haka? ashe shi yasa jiya na wuni da tunaninta a cikin zuciyata, har na kasa daurewa sai da na yi zancenta a gida, Hajiya ta ce na kwantar da hankalina ai na kusa zuwa na ganta, ya jikin nata yanzu?" Uncle Usman ya ce "Da sauƙi Alhamdulillah, yanzu ma bacci take yi, Nima shekaran jiya na kira Ummi mun yi waya ne ta ce dan Allah in daure in je in dubo mata Neehal, ta tura ƴaƴanta sun ce ba su san gidan ya Umar ɗin ba, ita kuma tana fama da ciwon ƙafa baza ta iya zuwa ba, shine na zo na tarar da wannan abun takaicin. Wallahi Aunty A'isha baki ga ni ba, abun tausayi gaba-d'aya Neehal ta lalace ta yi baƙi ta rame duk ta fita hayyacinta." Aunty Aisha tana hawaye ta ce "Shi yasa naso tafiya da ita amma Uncle Umar ya hana ashe rabon wahala ne yake kiranta." Uncle Usman ya ce "Kar ki damu Aunty daga nan Gombe zamu zo na kawo miki Neehal da zarar ta ji sauƙi, ai kuma ta gama zama a gidan Ya Umar." Aunty A'isha ta ce "Kana ganin Uncle Umar ɗin zai yadda Neehal ta dawo gurina da zama?" Uncle Usman ya ce "Kar ki damu da wannan na san me zance masa kuma dole ya bari. Amma dan Allah Aunty kar ki tada hankalinki fa komai ya zo ƙarshe ai dan zuwa gobe ma za'a iya ba mu sallama tunda ta ji sauƙi sosai." Aunty A'isha ta ce "Shikenan Usman na gode sosai, idan ta tashi daga baccin ka kira ni dan Allah." Uncle Usman ya ce "insha Allah zan kira ki, a gaishe da su Hajiya da Amarya, ace ina mata fatan Alkhairi kafin na zo." Aunty A'isha ta ce "Duk za su ji, sai anjima." Daga haka ya katse wayar. Ummi ya kira ya sanar mata halin da ake ciki, amma ya ɓoye mata wasu abubuwan dan kar hankalinta ya tashi sosai tunda ba ishashshiyar lafiya gare ta ba. Itama ta jajanta abun sosai ta kuma yi Allah wadai da halin Umar da Fauziyya, har ma da Ƴan'uwansu na cikin Kano wanda ko waiwayar Neehal ɗin ba sa yi alhalin suna gari ɗaya. Ta kuma yi na'am da mayar da riqon Neehal hannun Aunty A'isha da Usman ya ce mata zai yi, amma kafin su tafi Gomben ta ce ya kai mata Neehal ɗin ta gan ta..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:48] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *3️⃣3️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ...........Wajen ƙarfe goma na safe sai ga Uncle Umar a asibitin, Uncle Usman ya je ya shigo da shi. Tun kafin su shigo ɗakin ya fara masifa, Uncle Usman dai bai tanka masa ba. Har lokacin Neehal bacci take abunta. Uncle Usman ya zauna yana yi wa Uncle Umar wani kallo ya ce "Wallahi Ya Umar ka matuƙar ba ni mamaki ka kuma ba ni kunya da har kake kallo ana azabtar da Neehal amma baza ka hana ba sai ma tayawa da ka yi. To idan ka manta bari in tuna maka, mahaifin yarinyar nan shi ya fito da mu daga cikin duhun rayuwa zuwa mai haske, cinmu, shanmu, suturarmu, iliminmu, bai taɓa nuna gazawar sa ba ko a fuska balle a aikace, alhalin kuma mu ba dolensa ba ne kyautatawa ce kawai irinsa. Mutumin da yay maka duk waɗannan abubuwan sannan ya ɗora da samar maka aiki ya baka muhallin zama, hidimar bikinka rabi da kwata shi ya yi ta, dan ba ya raye ɗiyarsa guda ɗaya tak a duniya ta cancanci azabtarwa daga gare ka? A tunani na ko wani ka ga yana mata haka sai inda ƙarfin ka ya ƙare a ɗaukar mata mataki." Uncle Umar ya yi shiru kawai yana kallon Uncle Usman amma ya rasa bakin magana. Uncle Usman ya Tab'e baki ya ce "Abu na ƙarshe daga rana irin ta yau Neehal ta bar hannunka da zama, zata koma inda ake sonta da k'aunarta saboda Allah, tun da dama kai dan dukiyarta ka karb'i riqon ta, to ka riƙe dukiyar amma ita dai baza ta ƙara kwana a gidanka ba." Cikin fusata Uncle Umar ya ce "Ni kake faɗa wa waɗan nan maganganun Usman? Uban wa ya faɗa maka dan dukiyarta na karb'i riqon ta, wato an zugo ka zaka mun rashin kunya ko?" Uncle Usman ya yi murmushi ya ce "Calm down bro, abun duk bai kai haka ba, karɓe Neehal daga hannunka ba ya nufin za a karɓe dukiyarta daga hannunka ba ne, za'a bar maka kacigaba da juya ta domin wadda zata ɗauki Neehal bata buƙatar dukiyarta dan a gurinta ba komai ba ce." Uncle Umar ya mike tsaye ya ce "Wai me kake nufi da nine Usman eye? Wato kana so ka ce son cinye dukiyar Neehal nake son yi ko? To wallahi babu inda zata a hannuna zata cigaba da zama har auranta." Uncle Usman ya ce "Hmmm sai ku ji daɗin kashe ta kenan kai da matarka da duka ko? Yaya Umar, Yaya Fateemah bata cancanci haka daga gare ka ba, ka ji tsoron Allah ka tuna kai ma zaka mutu kuma kai ma ka haifi ƴaƴan nan. Yarinyar nan mai ta sani a rayuwa me ta tsare muku da kuka mayar da ita baiwa a gidanku, kuma wallahi bana ganin lefin Fauziyya sosai na fi ganin naka dan da ka tsawatar mata ba ta isa ta yi wa Neehal haka ba, amma babu komai rayuwa ce Duk *abin da mutum ya shuka shi zai girba* ." Uncle Umar cikin borin kunya ya ja tsaki ya fice daga ɗakin. Sai wajen 12 Neehal ta tashi daga baccin, bayan ta wanke baki Uncle Usman ya bata abincin da ya siyo mata ta ci sannan ta sha maganinta. Wayar Aunty A'isha ya kira ya haɗa su, Neehal ta dinga murna jin Muryar Aunty'nta, ta dinga tambayarta ina Maman Abuja. Bayan sun gama wayar ya kira Ummi ya haɗa su itama. Da kansa ya je har gidan Uncle Umar ya tattaro duk wani abu na Neehal ya haɗa a trolley ɗinta ya baro su daga gidan. Aunty Fauziyya ta tab'e baki ta ce "Umma ta gai da Ashsha, ala raka taki gona." A yammacin ranar aka sallame su daga asibitin tun da Neehal ɗin ta warware sosai, sai dai zata cigaba da shan magungunanta. Gidansu Haleemah suka je ya kai mata kayayyakin da ta ba shi tare da yi mata godiya sannan suka wuce Gabasawa. Ummi ta yi kuka sosai ganin yanda Neehal ta lalace ga shatin duka b'aro_b'aro ajikinta. Kwanan su ɗaya suka wuce Gombe, nan ma Su Aunty A'isha sun sha kuka da ganin yanda Neehal ta koma. Hajiya ta dinga ja wa su Aunty Fauziyya alkaba'i. Lokacin da Neehal ta koma Gombe Mama ba sa garin ta je Saudiyya Umara daga nan ta wuce London, sai daf da bikin Aunty Sadiya ta dawo. Lokacin Neehal ta fara dawo wa hayyacinta saboda kulawar da take samu a gurin Aunty A'isha da Hajiya, har an saka ta a makaranta boko da islamiyya. Mama ta yi murna sosai da ta ga Neehal ta dawo gurin Aunty A'isha da zama. Bayan bikin Aunty Sadiya Neehal ta mak'ale wa Mama ta bita Abuja, wannan zuwan shine sanadiyyar komawarta hannun Mama gaba-d'aya da zama. Dama zuwa Kano siyayya da su Aunty A'isha suka yi ta haɗu da wani Alhaji da Allah ya yi wa matarsa rasuwa shekarar da ta wuce, shima bai taɓa haihuwa ba ya ce yana son ta kuma baya son a ja bikinsu da nisa tun da su ba yara ba ne. Cikin wata biyu bayan fahimtar juna da sukai da kuma duk wani binkicen da ya kamata aka ɗaura Auran Aunty A'isha da mutumin ta tare a nan Kano. Neehal tana jin daɗin zama a gurin Mama sosai dan babu abun da suka rage ta da shi na jin daɗin rayuwa ita da Daddy. Makaranta mai tsada Daddy ya saka ta. Cikin lokaci kaɗan Neehal ta koma Neehal ɗinta ta ainihi mai rawar kai da surutun tsiya, hakan ya sa ba sa shiri ko kaɗan da Ameen, a duk lokacin da ya zo gida to ba ta da sukuni ta dinga kumbure_kumbure a ɗaki tare da Allah Allah ya yi ya tafi. Tun Neehal tana tunawa da Ahmad a ranta har ta fara mantawa shi. Neehal ta tashi yarinya mai hankali da nutsuwa da biyayya, ga addini da tsafta, dan Mama duk ba baya ba ce a cikin waɗannan abubuwan. Dawowar Neehal hannun Mama sai dangin Mama suka ninka soyayyarsu a gareta, kowa ka ji yana Neehal ɗin Maman Abuja. Nan da nan Neehal ta ƙara saba wa da su, shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, saɓanin dangin Daddy da ba kowa ke son ta ba, musamman Maman Hameedah ƙanwar Daddy k'iri_k'iri take nuna tsanarta ga Neehal. Watarana Mama suka shirya ita da Neehal suka zo Kano, duk wani makusancin Neehal da Mama ta sani sai da ta kai ta gidansa dan ta gaishe shi, amma babu inda suka samu tarb'ar arzik'i sai gurin Ummi yayar Abba sai gidan wani cousin ɗin Abba wanda suke shiri da Abba sosai mai suna kawu Musa, shi ma dan yana gidan suka je ne, da dan ta matarsa ne ita ma baza su samu tarb'ar arzik'i ba. Uncle Umar kuwa da suka je gidansa cewa ya yi kar Neehal ɗin ta ƙara zuwa inda yake tun da ta zaɓi bare akan sa. Haka dai suka dawo Abuja rai babu daɗi, sosai Mama ta ji takaicin yanda ƴan'uwan mahaifan Neehal suka banzatar da ita, ta yi Allah wadai da zumuncin wannan zamani na ganin ido, dan ta san da iyayenta suna raye baza su mata haka ba. Neehal cikin danginta na Uwa da Uba da Uncle Usman da Ummi kawai suke waya, sai kawu Musa wani lokacin, lokaci zuwa lokaci kuma tana ziyartar Ummi. Riqon da Mama take wa Neehal ko ɗan data haifa da cikinta iya shi zata masa, Mama tana k'aunar Neehal sosai har cikin ranta, haka ma Daddy. Babu yanda za ai ka gane ba su suka haife ta ba, wanda bai sani ba ma ba ya gane wa. Dan ko a school da *Fateemah Muhammad Tafida* take amfani. Sunan Daddy kenan (Muhammad Tafida) amma Neehal da sunan Abbanta take amfani, Tafidan kawai ta ƙara, da yake sunan ɗaya ne duk Muhammad shi yasa ba'a gane wa. Daddy yana da kuɗi sosai kasancewar ya riƙe matakai na soja kala_kala har zuwa matakin ƙarshe wato General, kuma dama can zuri'arsu masu arzik'i ne. Asalin su Daddy su ma fulanin Gombe ne kuma ƴan'uwa ne na jini da su Mama, da Mahaifin su Daddy da Hajiyar su Mama cousin ne. Su Daddy su uku ne a wajen mahaifinsu, Yayansa Namiji mai suna Hamza sai shi, Haj.Saratu Maman Hameedah ita ce Autarsu. Iyayensu duka sun mutu ba jima wa, su ma su Mama mahaifinsu ya rasu daf da bikin Aunty A'isha da Abba. Daddy ya fara harkar siyasa, amma ganin siyasar ƙasar nan babu Allah a cikinta Mama ta ce gaskiya ya daina tun da dama bai yi wani suna acikinta ba, ba dan ya so ba haka ya haqura sai dan farincikin Maman kawai. Ameen shi kaɗai Mama da Daddy suka haifa a duniya, daga kan shi Allah bai ƙara ba su haihuwa. Kamar Ameen da Mama ɗaya sak tamkar an tsaga kara, bambamcinsu kawai shi Namiji ne Mama kuma mace ce, haka ma a halaye da d'abi'u duk nata ya yo, kama daga kan tsafta, addini, kyauta, iya mu'amala da mutane, tsare gaskiya ko mai ɗacinta, da kuma rashin tsoro. Ko dan shi Namiji ne,har ya fi Mama rashin tsoro da dakiyar zuciya, sai kuma Allah ya ɗora masa miskilanci tun yana ƙaramin sa. A ɓangaren aiki ne ya gaji Daddy shi ma ya zama soja. Sosai Neehal take tsoronsa, idan ya zo gida weekend sai ta zama salihar ƙarfi da yaji, dan abu kaɗan za tay ya balbale ta da faɗa dan yana da zafin zuciya, amma fa duk zuwan da zai yi da ƙatuwar ledarsa ta tsarabar Neehal yake zuwa, idan ƴan fara'ar suna kansa wataran yana sakar mata fuska. Neehal kam tana son Yayanta sosai, tana jinsa tamkar yayanta uwa ɗaya Uba ɗaya. Komai nata Yayanta Yayanta, sai dai wani lokacin in ta je gurinsa ya koro ta, ta dawo tana aikin turo baki, Mama ta ce mata "Dama wa ya aike ki gurinsa kin san hali." A hakan dai shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su. Shekarar Neehal shida a gurin su Mama Daddy ya yi retire, hakan yasa suka dawo Kano da zama gaba-d'aya, lokacin Neehal ta gama Secondary school tana 17_18 years. Ta yi saukar haddar Alqur'ani mai girma shekara biyu da suka wuce. A gurin registration ɗin Jamb suka haɗu da Haneefah, har suka yi musayar contact ɗin juna, sai da za su tafi gida suka gane ashe ma unguwarsu ɗaya. Tun daga time ɗin suka zama k'awaye sosai har Mama suke zumunci da Mommy'n Haneefah, ita ma Haneefah marainiya ce, mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama. A wannan lokaci Allah ya yiwa Ummi Yayar Abba rasuwa, Neehal ta ji mutuwar sosai kuma ta sha kuka. Duk da tarb'ar da Mama ta samu a gurin dangin Neehal bata daina kai ta tana gaishe da su ba, tun da jininta ne su, babu yanda zata yi da su, daga baya da Neehal ɗin ta girma da kanta ta cewa Mama dan Allah ta daina kai ta, ganin yanda suke wulaqanta ta da nuna halin ko'in kula a gareta kamar wadda ta je neman wani abu gurinsu, ko sau ɗaya babu wanda ya taɓa tako wa gidan Mama da sunan ya zo ganin Neehal. Ita kuwa Neehal tuni ta cire su daga ranta, yanda suka manta da ita a rayuwarsu itama ta manta da su. Da Uncle Usman ɗinta kawai take zumunci wanda shi ma ya yi aure suna zaune da matarsa a can Niger. Neehal kyakkyawa ce doguwa mai dirin jiki dai_dai misali da dogon gashi, ga ta ƴar gayu ce dan tana son gayu sosai, ko da yake ba ta ɗauka a ƙasa ba dan Mama ma akwai gayu da kwalliya, zai yi wahala ka ga hannu da ƙafarta babu jan lalle idan ka ganta baza ka ce ta haifi Ameen ba, ga iya girki, shi yasa duk ta kanainaye zuciyar Daddy, ba ya ganin kowacce mace sai ita. Aunty A'isha ta haifi yarinyarta mace mai suna Maryam, Aunty Sadiya ma ta haihu ɗanta Namiji. Tun da Neehal ta fara zama budurwa Ameen ya daina sakar mata fuska kwata_kwata, wani lokacin kuma sai ta fito zata unguwa sai ya ce sai ta koma ta canzar shigar da ta yi ba zata fita a haka ba, babu yanda ta iya haka zata koma ta sake. Sannan ko ya ya ji k'amshin turare a jikinta kuwa sai ta koma ta sake wanka wai babu kyau ba zata fita tana k'amshi ba, janbaki wannan idan tasa sai ya ce sai ta goge shi. Mama da ta ga abun na shi bana ƙare ba ne ta taka masa burki ta ce bai isa ya takurawa Ƴarta ba, tun da ba shi ya haifar mata ita ba. Sannan fa Neehal ta samu salama ya ɗan sararara mata. Allah ya ba wa Neehal farin jinin samari tun da ta fara tasowa, amma bata kula su saboda ba a bata damar hakan ba a gida. Jameel shine saurayin data fara kulawa da sunan soyayya, ɗan Kano ne amma a Abuja suka haɗu a wani Mall, a lokacin ya takura mata da naci har sai da ta ba shi phone Number ɗinta. Tun yana kiranta tana ƙin d'aga wa har dai ta fara sake masa. Jameel matashi ne Black beauty, gashi da nutsuwa hakan yasa Neehal ta ji ya kwanta mata a rai. A hankali soyayyarsa ta fara mamaye zuciyarta. Tun kafin tafiyarsu ta yi nisa ta gabatarwa da Mama shi, Mama ta yi murna sosai ta kuma sanar da Daddy dan a san abun yi. Mahaifin Jameel ba boyayyen mutum ba ne kasancewarsa ɗan siyasa ne, Daddy ma ya san sa. Soyayya sosai Neehal suka sha da Jameel kamar ba gobe, sai dai bayan an yi Engagement ɗinsu ba jimawa ya fita aka bishi aka harbe sa ya mutu. Mutuwar Jameel ta girgiza duk wani makusancinsa ciki har da Neehal kuwa, dan tun daga lokacin da ya rasu ta zama so silent. A lokacin ne kuma Jamb ɗinsu ta fito, sai dai Neehal ba ta ci point sosai ba duk da Kasancewar tana da ƙoƙari, Haneefah kuwa ta ci point da yawa, amma ganin Neehal bata ci ba harma ta yi apply a Kano state polytechnic sai itama Haneefah ta ce can zata ta fasa zuwa University tun da besty'nta ba can zata yi ba, ita ma ta yi apply a poly. Sun fara karatu cikin nasara a Management kasancewar su duka ƴan art ne, department of mass communication suke, dama ita Neehal choice d'inta kenan, burinta a rayuwa ta ga ta zama Jonorlist. Da wata shekarar ta zagayo suka sake yin Jamb, wannan karan ma Haneefah ce ta ci Neehal ba ta ci ba. Dole tasa Haneefah ta yi apply a Bayero University Kano inda ta fara karantar law, Neehal kuma ta ci gaba da Polytechnic ɗinta. Tana siwes suka haɗu da Anwar, da farko shi ma ba ta kula shi sosai, sai daga baya ta saki jiki da shi suka fara soyayya fiye da ma wadda suka yi da Jameel. Cikin ikon Allah Neehal ta gama school ɗinta successfully, bata taɓa carry over ba balle spill, tun kafin ta gama ta siyi D.E Form a Bayero ta cike da waiting result. Bayan ta karb'i result ɗinta suka bata admission direct level two ta ɗora karatunta, lokacin ita ma Haneefah ta shiga level two ɗin, sai matakin karatunsu ya zo ɗaya. Ba jimawa da shigar ta Bayeron aka yi Engagement ɗinsu da Anwar. Duk kawo kuɗin Neehal ɗin da za'ai sai Mama ta aikawa ƴan'uwan Neehal, amma daga ƴaƴan Baffa har Uncle Umar babu mai zuwa, Kawu Musa ne kawai yake zuwa a karb'i kuɗin da shi, Uncle Usman kuma ya yi nisa ba ya samun zuwa, ya kance sai bikin Neehal ɗin zasu zo shida iyalansa. A lokacin da aka yi engaged ɗin Neehal aka buɗe gidan Television na ASTV. Wani abokin Daddy ne ya buɗe, hamshaqin mai kuɗi ne kuma sananne ne a ƙasar nan. Da kwalin Deplomer aka ɗauki Neehal aiki a gidan TV'n, Haneefah kuma da S.S.C.E Daddy ya sa aka mata alfarma ita ma aka ɗauke ta. Neehal abun nema ya samu ta zama Jonorlist sai murna. Kafin Neehal ta fara aiki sai da aka kai ruwa rana da Ameen, dan da farko cewa ya yi baza ta yi ba. Mama ta ce, A nan bai isa ba kuwa, wanda zai aure ta ma bai hana ta ba sai shi ɗan karere. Har wannan lokacin dukiyar Neehal tana hannun Uncle Umar yana juya ta, babu wanda ya ce masa k'ala a kanta, su Fauziyya da aka ga Neehal a gidan TV baƙin ciki kamar ya kashe ta, musamman da ta ga yanda ta ƙara kyau ta zama ƴar gayu wanke hannu ka taɓa, gashi ko ta ina samun masoya take rututu a faɗin ƙasar nan. *CIGABAN LABARI.............✍️* *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:48] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *3️⃣4️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* .............Washegari bayan an yi sallar asuba, Daddy ya dawo daga masallaci Mama ta sanar masa abun da Aunty Sadiya ta faɗa mata, dan jiya bai dawo da wuri ba shi ya sa bata faɗa masa ba. Zarya yake ta yi a ɗakin baccinsa, Mama kuma tana zaune a gefen gado ta yi tagumi cikin tunanin mafita. A hankali ta ɗago da idanunta da ba su samu isasshen bacci ba a daren jiya saboda fargaba ta dubi Daddy ta ce "Daddy ka zauna mana, ka bar wannan safa da marwar ka zo mu nemi mafita akan wannan al'amarin." Daddy ya sauke numfashi tare da goge gumin da ya kwanta a kan goshinsa ya ce "Al'amarin ne ya girgiza ni ba kaɗan ba Doctor." Mama ta sauke tagumin data rafka bata ce komai ba. Daddy ya zauna a kan bedside locker yana fuskantar Mama ya ce "Zuciyata ta kasa yarda da wannan abun Doctor, ba zan taɓa yarda saboda Daughter ake wannan kisan ba gaskiya." Cikin karaya Mama ta ce "Saboda me zaka ce haka? Kar fa ka manta mahaifan Neehal ma fa kashe su a kai, kuma har yau an kasa gano waɗanda suka yi kisan da kuma dalilin da yasa aka kashe sun. Haka su Jameel suma har yau an kasa gano waɗanda suka kashe su, ai ko aljanu ke kisan nan ya ci ace zuwa yanzu asirinsu ya tonu." Daddy ya ce "Ka da ki la'akari da haka, zata iya yiyuwa mahaifan Neehal b'arayi ne suka kashe su ko kuma wani mak'iyin Abbanta, kin san idan mutum ba ya k'aunar ka a shirye yake da ya aikata komai a kanka. Sannan na biyu kuma Jameel, mahaifinsa ɗan siyasa ne abokan hamayya babu abun da baza su iya ba suma a kan mutum, tun lokacin da aka kashe Jameel tunanin da kowa ya yi kenan ciki har da mahaifinsa. Sai kuma Anwar, wanda shi kaɗai ne ma babu wani dalili a rayuwarsa da a yi tunanin zai sa a kashe sa." Mama ta sauke numfashi ta ce "Yanzu dai a takaice kana son ka ƙaryata abun da Sadiya ta faɗa kenan? Ko kuma kana son ka kwantar mun da hankali ne kamar yadda ka saba a kodayaushe idan ka ganni a cikin damuwa? Daddy! Wannan maganar ba fa ƙaramar magana ba ce, ina tsoron abun da Sadiya ta faɗa ya tabbata." Daddy ya ce "Ko kaɗan ba ina nufin na ƙaryata Sadiya ba ne domin akan aikinta take, kuma ban san hujjar data gani ta faɗi haka ba, kawai dai ina son nusar dake wani abu ne." Mama ta ce "Wanne abu zaka nusar da ni? Hmm Daddy kenan, ni fa na riga na gano ka, kawai kana san kwantar mun da hankali akan wannan al'amarin ne." Daddy ya yi shiru domin tabbas abun da Mama ta faɗa haka ne, yana son ya kwantar mata da hankali ne kawai amma tabbas shi ma maganar ta girgiza zuciyarsa ba kaɗan ba, ya manta rabon da ya ji abun da ya firgita zuciyarsa irin wannan. Mama ta ce "Ya Allah ka bayyana mana gaskiyar wannan abun, ka tona asirin duk wanda yake da hannu a cikin wannan al'amari da gaggawa." Daddy ya ce "Ameen ya Allah, abun da ya dace dama mu dage da yi kenan addu'a, Insha Allahu gaskiya zata bayyana." Kusa da Mama Daddy ya dawo ya kama hannunta ganin damuwa ƙarara a fuskarta ya ce "Please Doctor ki rage damuwar nan da kike, kin san Neehal ɗin ma idan ta ganki a haka itama zata shiga damuwar ne, ina jarumtar dana san ki da ita ne? Haba matar soja uwar soja." Mama ta sauke numfashi ta ce "Idan ka ga na daina damuwa to naga na aurar da Neehal, shine kawai hankalina zai kwanta." Daddy ya miƙe ya ce "Insha Allahu zaki gani, ai shi aure hab'o ne idan lokacinta ya yi dole sai ta yi, fata kawai Allah ya kawo mata miji na gari, wanda zai riqe mana ita da amana ko bayan ranmu." Mama ta ce "Ameen ya Allah." Daddy yana buɗe wardrobe ɗinsa ya ce "Yanzu ita Neehal ɗin akwai wanda take kulawa ne?" Mama ta ce "Gaskiya a sani na babu kowa." Daddy ya ce "Wannan yaron da yake zuwa fa wani ɗan fari dogo haka?" Mama ta ce "Sadik kake nufi wai?" Daddy ya ce "Ehh, Barrister ne shi ko?" Mama ta ce "Ehh, a unguwar su A'isha gidansu yake." Daddy ya ce "Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Mama ta ce "Ameen." Car key Daddy ya miƙawa Mama ya ce "Gashi ki ba wa Daughter." Mama ta karb'a cikin mamaki ta ce "Mota ka sai mata?" Daddy ya ce "Ehh mana, alƙawarin dana mata ne tun sanda ta gama Polytechnic kika hana a bata a time ɗin." Mama tana murmushi ta ce "Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi ya tsare, ai yanzu ta ƙara hankali zan bar ta ta yi driving ɗinta. Mun gode sosai fa Allah ya ƙara buɗi mai albarka" Daddy ya ce "Ameen ya Allah. Mama ta miƙe ta ce "Bari in je inwa Daughter albishir, na san zata yi farin ciki sosai." Daddy ya yi murmushi cikin jin daɗin ganin Mama na murmushi, saɓanin d'azu da damuwa ke kwance a kan fuskarta. A duk duniya abun da ke d'aga masa hankali kenan ya ga iyalinsa a cikin damuwa, da yana yanda zai yi da sai ya magance wa Neehal wannan K'ADDARAR data shigo cikin rayuwarta, amma babu yanda zai yi komai rubutacce ne tun fil'azil daga Ubangiji Mai girma da ɗaukaka, amma ya ɗaukar wa kansa alk'awari sai inda ƙarfinsa ya ƙare a game da binkicen wannan al'amari, a matsayinsa na k'wararren soja. Zaune a kan darduma Mama ta tarar da Neehal ta jingina jikinta a jikin gado, Sallamar Mama yasa ta ɗago da kanta tare da amsa mata. Mama ta zauna a bakin gado tana dubanta. Neehal ta ce "Ina kwana Mama." Mama ta ce "Lafiya k'alau, me ya samu idanki?" Neehal ta girgiza mata kai, Mama ta ce "kuka kika yi ko? kuka dai ba ya maganin duk wata damuwa, addu'a ita ce kawai mafita." Neehal ta gyaɗa mata kai. Mama ta kalli su Afrah dake bacci ta ce "ƴan rigimart taki ba su tashi ba kenan?" Neehal ta ce "Ehh ni Mama dama ina son na faɗa miki me zai hana a saka su a makaranta kafin Allah ya bayyana iyayensu, kin ga idan na tafi school ko aiki kema in kin tafi asibiti sai su kaɗai fa a gidan, su Aunty Dijee ma kin ga suna zuwa islamiyya da yamma." Mama ta ce "Hakane kin kawo shawara mai kyau, ranar Asabar in Allah ya kai mu sai a kai su tahfiz, ranar Monday kuma sai na kai su school." Neehal ta ce "Allah ya kai mu." Mama ta ce Ameen, ga saqo in ji Dad ɗinki." Neehal ta miƙa hannu dan karɓar abun da Mama take miƙo mata tana faɗin "Saqon mene?" Kafin Maman ta bata amsa ta gani da idonta, waro ido ta yi waje tana murmushi ta ce "Mama kar dai ki ce mun wannan nawa ne Dad ya siya mun Mota?" Ita ma Mama tana murmushin ta ce "Ban ce ba to, amma ni dai saqo aka bani kuma na isar." Neehal ta rungume Mama da sauri cikin farin ciki ta ce "Alhamdulillah, amma fa Dad ya iya surprise." Mama ta ce "D'aga mun jiki ni, sai a kula da titi sosai tare da kasancewa cikin addu'a a kodayaushe." Neehal ta ce "Insha Allah Mamana." A take Neehal ta tafi part ɗin Daddy ta masa godiya sosai, Mama ce ta yi musu breakfast yau dan ta san murna ba zata bar Neehal ta musu cikin nutsuwa. Ƙarfe tara da ƴan mintuna Neehal ce zaune a gaban mudubi tana ɗaura d'ankwalin atamfar dake jikinta, ɗinkin riga da skirt ne ya mata das a jikinta. Bayan ta gama ɗaura d'ankwalin ta saka ɗan kunne fashion mai kyau kalar one colour na jikin atamfar, sannan ta ɗaura agogo a left hand d'inta, ta zira abun hannu a right. Masha Allah ta yi kyau sosai small pink lips ɗinta sun sha white lipstick sai k'yalli suke. Su Afrah dake zaune a kan carpet ɗin bakin gado suna break, ganin ta miƙe ta ɗauki mayafinta dake kan gado suka miƙe su ma da sauri suna haɗa baki gurin faɗin "Zan biki Aunty." Neehal ta kalle su ta yi murmushi sannan ta kama hannuwansu ta ce "Bana faɗa muku school zani ba, ku bari idan na dawo da yamma za mu je unguwa Insha Allah." Suka gyaɗa mata kai ba dan ransu ya so ba. Neehal ta yi picking goshinsu sannan ta ce su tafi ɗakin Mama ta musu wanka idan sun gama break ɗin. Ta yafa mayafinta wanda ya kasance babba ne amma ba me kauri sosai ba, sannan ta ƙara fesa perfumes ɗinta ta zira plate shoe d'inta ta ɗauki jakarta da car key ɗinta ta fice daga ɗakin tana yi wa su Afrah bye_bye. A falo ta tarar da Mama ta ce mata "Mama zan tafi sai na dawo." Mama ta ce "Allah ya kiyaye ina yaran fa?" Ta ce "Suna ɗaki suna break in sun gama na ce su zo ki musu wanka." Mama ta ce "To Allah ya bada sa'a, ki kula da titi fa kuma kar ki manta da addu'a." Neehal tana fita daga falon ta ce "Insha Allah Mamana, bye." A parking space kamar yadda Daddy ya ce mata Motar ta tana can, a nan ta ganta. Ta sa key ɗinta ta buɗe murfin Motar da bismillah sannan ta yi addu'a ta shiga zuciyarta cike da farin ciki, gaba-d'aya damuwar data kwanta da ita daren jiya a ranta ta ji duk ta gushe, Daddy ya faranta mata ba kaɗan ba, a rayuwarta tana son ta ga tana driving, tun da Daddy ya so siya mata Motar amma Mama ta hana. A hankali take driving ɗin cikin nutsuwa da kula, sai dai ba ta yi nisa da tafiya ba ta ga wata Motor kamar tana binta a baya, ba ta kawo tunanin komai a ranta ba, tafi zaton may be hanya ce ta haɗa su ɗaya da mai motar, sai dai yanda take driving ɗin a hankali ya ci a ce mai Motar ya zo ya wuce ta kamar yadda wasu motocin ke yi. Cikin ikon Allah ta ƙarasa har cikin Bayero lafiya, kuma har ta zo bakin gate ɗin makarantar Motar na biye da ita a baya. Ƙarfe biyu suka gama last lecture ɗinsu, ko Sallah bata tsaya yi ba ta yi wa Freinds ɗinta sallama ta yo gida, saboda tana son ta je gidansu Haneefah ta nuna mata sabuwar Motarta.Tana fita daga get ɗin makarantar ta hau kan titi kenan ta mudubi ta ga kamar motar d'azu ce ke kuma binta, ita tama manta da batun wata motar d'azu, dan ta yi tunanin mai Motar shima Bayeron zai je a d'azun. Gabanta ya yanke ya faɗi tsoro ya fara ziyartar zuciyarta, hakan yasa ta shiga karanto Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, da hasbinallahu'wani'imal'wakil. Har ta ɗan samu nutsuwa a ranta ta cigaba da driving ɗinta. Wata zuciyar na faɗa mata ƙila ma ba Motar d'azun ba ce irinta ce kawai. Sai dai kuma kamar ɗazun duk inda ta yi nan Motar itama take bi, har tafiya ta fara yi a slow wai dan ta ga ko Motar zata zo ta wuce ta amma still dai motar tana bayan tata..........✍️ *Na so page ɗin ya fi haka tsawo, amma tun daren jiya ban jin daɗi, yanzu ma dauriya na yi na muku wannan ɗin* *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:50] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *3️⃣5️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ...........Har ta ƙarasa gida Motar tana biye da ita a baya. Sunayen Allah tsarkaka take ambata a ranta, kuma cikin k'udurarsa da ikonsa ya kawo ta gida lafiya. Sai da ta shiga layinsu sannan ta ga Motar ta daina bin ta. Tab'e baki ta yi a fili ta ce "Allah kai ne sarki, Allah ka kare ni daga dukkan wani mai nufi na da sharri, Allah da kai na dogara kuma kariyarka nake roqa a kodayaushe." Da haka ta shiga cikin gida ta yi parking motar sannan ta fito a gajiye ta yi cikin gidan. Zulai ce ta zo ta buɗe mata ƙofa, "Sannu da zuwa." Ta faɗa tana bata hanya. Neehal ta ce "Yawwa Aunty zulai, ya gida." Zulai ta ce "Lafiya k'alau." Daga haka Neehal ta wuce sama. Ɗakinta ta nufa ta ajiye handbag ɗinta, ganin su Afrah ba sa dakin ta fito ta nufi ɗakin Mama. A kan gado ta tarar da su sun baje suna bacci, da alama kaɗaici ne ya ishe su, tunda ta san ba su fiya baccin rana ba. Mama bata nan ta je aiki, dama ta san ba zata dawo ta same ta ba. Ɗakinta ta koma ta shiga toilet ta ɗan watsa ruwa tare da yin tsarki ta ɗauro alwala, bayan ta idar da Sallah ta sauka ƙasa ta zuba abinci a ƙaramin plate ta ci. Ganin har uku ta wuce yasa ta koma sama da sauri dan shiryawa. Wayarta ta ɗauka ta ga missed call na Uncle Usman, murmushi ta yi sannan ta siyi kati daga banki a sim ɗinta na 5k sannan ta kira shi. Yana d'agawa ta ce "Assalamu alaikum." Uncle Usman ya amsa mata, ya ƙara da faɗin "Daughter kin manta da ni ko?" Neehal ta shagwabe fuska kamar yana ganin ta ta ce "Haba Uncle ni na isa in manta da kai a rayuwata? ai ɗiyar kirki bata taɓa mantawa da ubanta ko dan neman albarkarsa." Uncle Usman ya yi murmushi mai sauti ya ce "To ƴar gidan Uncle, ya school ya office." Neehal ta ce "Lafiya k'alau Alhamdulillah, ina Auntynah da takwarata?" Ya ce "Suna nan k'alau, dafatan dai komai lafiya ko Neehal?" Ta ce "Lau lau my Uncle, ya kasuwa?" Ya ce "Kasuwa Alhamdulillah, gashi ma ta hana ni zuwa in ga ƴata." Neehal ta ce "Babu komai Uncle, Allah ya taimaka. Nima Insha Allahu wannan hutun da zamu yi zan yi ƙoƙari in zo Niger ɗin." Uncle Usman ya ce "Allah ya kai mu ya kawo ki lafiya." Neehal ta ce "Ameen." Ya ce "Ya Mama da Daddy da Aunty A'isha da Aunty Sadiya da wajen su Hajiya?" Ta ce "Duk sunanan lafiya k'alau." Uncle Usman ya ce "Masha Allah, haka ake so Allah ya yi mana jagora. Ni kwa na ce Neehal har yanzu ba kya zuwa gidan Ya Umar da Gabasawa?" Neehal ta had'iye wani abu da ya tsaya mata a mak'oshi ta ce "Bana zuwa Uncle, tun da duk sun nuna ba sa son na rab'e su, kowa na je inda yake sai ya dinga wulaqanta ni kamar wadda ba jininsu ba, na rasa me nay musu, mutuwar iyayena ce lefi a gare su ko kuma riqona da Mama take yi? Dama Uncle idan iyayen mutum sun rasu sai ya zama abun ƙyamar a cikin zuri'arsu?" Ta ƙarashe zancen hawaye na zuba akan kuncinta. Uncle Usman ya danne ɓacin ransa ya ce "Don't cry Daughter please, ba dan na saki kuka na tambaye ki ba, na tambaye ki ne saboda ina son sanin ko an samu cigaba sai dai kash bayananki sun tabbatar mun jiya i_yau ake bata sauya zani ba, amma har su Mubarak ɗin Ummi suma ba kya zuwa wajensu?" Neehal ta ce "Ai Ka san yanzu ba sa Gabasawa suna Lagos acan suke neman kuɗin su, amma Mama ta ce Insha Allahu watarana zata kai ni gurinsu da kanta, tunda ba ni da kamar su a duk faɗin duniyar nan." Uncle Usman ya ce "Allah ya ba da iko." A ransa yana jinjina ƙoƙari irin na Mama da kullum ita dai burinta ta ga Neehal tana zumunci da danginta kamar kowa, wani b'arin na zuciyarsa kuwa cike yake fal da tausayin Neehal. Ganin har yanzu kamar bata saki ranta ba da zancen su Uncle Umar da yay mata sai ya kawar da zancen inda cikin sigar tsokana ya ce "To a bani labarin sabon surikina." Murmushi ne ya zubce mata ba tare da shirya yin sa ba sai dan yanayin yanda Uncle Usman ya yi maganar, don sosai take jin k'uncin da ɓacin rai a duk lokacin data tuno da yanda danginta suka manta da rayuwarta a cikin tasu rayuwar. Uncle Usman ya ce "Ko baza a bani ba, na ji kin yi shiru!" Neehal ta ce "Ai babu ne Uncle." Ya ce "Kai haba, Ni dai na san my Daughter bata da baƙin jini, sai dai idan korar surukan nawa take." Neehal ta ce "Dagaske babu Uncle." Uncle Usman ya ce "Allah ya kawo na gari to, mu sha biki mu rak'ashe." Neehal ta yi murmushi cikin jin kunyarsa, wani b'arin na zuciyarta kuma fargaba ce fal a ciki, dan ita ba ma ta kawo wa kanta aure a yanzu, to idan ma zata yi auren wa zata aura? Sun ɗan taɓa hira kaɗan wanda gaba-d'aya zolayarta Uncle Usman yake, har sai da ya ji ta ware tana ƙyalƙyala dariya sannan suka yi sallama bayan ya ce ta gaisar masa da Mama da kyau. Bata ajiye wayar ba ta kira layin Haneefah sai da ta katse wa sannan Haneefah ta d'aga. Neehal ta ce "Matar nan kin yar da ni." Haneefah ta ce "Faɗi da babbar murya, bacin yarwa ma har bi takanki na yi na take ƴar rainin hankali kawai." Neehal ta yi murmushi ta ce "Me yay zafi haka Besty?" Haneefah ta ce "Abun kan wuta mana, tun jiya na kira ki amma sai yanzu zaki kira ni." Neehal ta ce "Ki yi haquri ƙawata, yanzu dai ba ma wannan ba kina gida in zo in nuna miki wani abu." Haneefah ta ce "Ina gida, Nima da ma akwai abun da nake son faɗa miki." Neehal ta ce "To gani nan zuwa." Daga haka ta katse wayar. Kukan twins ta jiyo a falo, da sauri ta fita dan ganin mene ne. Abun da bata taɓa gani sun yi ba wato faɗa shi ta tarar suna yi, Amrah tana ta dukan Afrah ita kuma tana kuka. Ɗaukar Afrah ta yi tare da hararar Amrah ta ce "Me tay miki kike dukanta?" Amrah ta ce "Ita ta fara duka na." Afrah cikin ta ce "Ƙarya take ban dake ta ba." Neehal ta sauke Afrah ta tsugunna ta rungume su duka a jikinta ta ce "Ku daina faɗa kun ji babu kyau." Suka gyaɗa mata kai, Amrah ta cewa Afrah "Am sorry." Afrah ta ce "Me too." Neehal ta rungume su cikin k'aunarsu tana murmushi. A hankali kuma ta raba su da jikinta ta miƙe tsaye tana faɗin "Mu je in shirya Ku mu tafi unguwa." Afrah ta ce "Aunty gurin Daddy'nmu za mu?" Neehal ta ce "A'a ai ban san inda yake ba." Cikin sauri Amrah ta ce "Abuja, a Abuja yake." Neehal ta ce "Tom Shikenan, soon za mu je Insha Allah." Wanka ta musu ta shirya su sannan itama ta shirya tay wa su Dije sallama suka tafi. Ta kira layin Mama bata d'aga ba sai text message ta mata ta sanar mata ta tafi gidansu Haneefah. Abun mamaki da ɗaure kai gidansu Haneefan ma sai da ta ga Motar nan tana bin ta a baya. Kamar ɗazu addu'a ta shiga yi a ranta har suka ƙarasa. Haneefah ta yi murna sosai da ganin sabuwar Motar Neehal, kamar ita yi Motar. Bayan ta gama tsallen murna suna zaune a kan gadonta su Afrah kuma suna falo gurin Momy, Neehal ta cewa Haneefah "Me kika ce zaki faɗa mun idan na zo?" Haneefah ta ce "Hmm, jiya Abban Abuja ya zo (wan mahaifinta kenan) ya cewa Mommy Iyayen ya Faruq sun je sun tsaida ranar bikinmu nan da three months masu zuwa." Neehal ta waro ido tana murmushi ta ce "Dagaske kike Haneefah?" Haneefah ta ce "Zan miki ƙarya ne to." Neehal tana dariya ta ce "Ban iya guɗa ba dana rangad'a ta yau, Ya Faruq ya ga ji da iskancinki kenan na ja masa rai da kike, amma na ji daɗi sosai ƙawata, Allah ya kai mu lokacin ya sanya Alkhairi." Haneefah ta ce "Amin, ni kuma ban ji daɗi ba, na so an fara bikinki kafin nawa na rak'ashe son raina." Neehal ta mata gwalo ta ce "Sai kuma Allah ya yi ni zan rak'ashe ɗin a bikinki." Haneefah ta ce "Ba komai, idan bikin naki ya zo nima aje auran zan yi a gefe in sha sha'ani na." Neehal ta ce "Allah ya sa lokacin kina da tsohon ciki ma, sai mu ga ta tsiya." Haneefah ta jefe ta da filo tana faɗin "Ba Amin ba muguwa ƴar buk'ulu." Sai bayan Magriba suka koma gida, a koma wa gida dai Neehal bata ga Motar nan tana binta ba, in ma tana binta ɗin ita dai bata gan ta ba, ko dan duhu ya fara ne oho. Washegari Friday bayan Neehal ta dawo daga school da yamma Mama ta ce ta shirya su je ita da su Afrah ta yi musu shopping ɗin kayan sawa da duk wani abun buƙata. Suka shirya suka tafi, kaya sosai Neehal ta jidar wa su Afrah, sannan suka biya suka sha Ice cream sannan suka dawo gida. Yau dai ba ta ga Motar nan ta bi ta ba kwata_kwata, ko da safe da zata school. Hakan yasa ta ji hankalinta ya ɗan kwanta ba kamar jiya ba da ta kwana cikin zullumi da fargaba. Bayan Sallar Magriba Neehal tana sama tana yin wani Assignment Amrah ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama, Neehal ta amsa mata ba tare da ta ɗago ba. Amrah ta ce "Aunty Mama ta ce ki zo Uncle Sadik ya zo." 'Sadik kuma?' ta tambayi kanta gabanta na fad'uwa ba tare da ta san dalili ba. A hankali ta dubi yarinyar ta ce "Ki ce ina zuwa." Amrah ta juya ta fice daga ɗakin da gudunta. Neehal ta tattara takardun gabanta ta ajiye akan bedside locker sannan ta ɗauko mayafi ta yafa ta fito falo. Mama tana zaune tare da su Afrah suna kallo a Falon. Neehal ta dube ta, ta ce "Mama wai Ya Sadik ne ya zo?" Mama ta ce "Eh, yana ƙasa yana jiran ki." Bata kuma cewa komai ba ta nufi ƙasa. Yana zaune a kan kujera as always idan ta sakko gurinsa yana ta latsa waya, k'amshinsa ne ya ziyarci hancinta, ta lumshe ido tana jin wani irin yanayi na bin jikinta tare da canzawar bugun zuciyarta. Sosai Sadik ya mata kyau ba kaɗan ba, yana sanye cikin ƙananun kaya, sumar kansa baƙi sidik sai k'yalli take. Cikin sanyin jikin data rasa na mene ta ƙarasa ta zauna a kujerar kusa da shi tare yin ƙasa da idonta tana sauke numfashi a hankali. Murya ƙasa_ƙasa ta yi masa sallama. Ya d'ago kansa a hankali fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mata tare da mayar da wayarsa cikin aljihu. Kamar bata son magana ta ce "Ina yini." Idanunsa na kanta Ya ce "Lafiya k'alau, ya study?" Ta ce "Alhamdulillah, ya su Maamah?" Ya ce "Suna lafiya, ta ce na gaishe ki ma." Still kanta na ƙasa ta ƙi d'agowa ta ce "Ina amsawa, ya aiki?" Ya ce "Aiki gashi nan muna ta fama Alhamdulillah." Ta yi shiru ba ta ce komai ba, shi ma shirun ya yi yana jiran ya ji ko zata tambaye shi dalilin yasa kwana 2 bai kira ta ba kuma bai zo ba. Tsawon three minutes suna haka, katse shirun na su ya yi da faɗin "Neehal !Kamar wani abu na damunki ko?" Lumshe idonta ta yi tana jin yanda sunanta ya ƙara daɗi a cikin muryarsa, sai ta ji kamar ta ce ya ƙara maimaitawa. Girgiza masa kai ta yi alamun a'a. Ita kanta ba zata ce ga abun da yake damunta ba, amma tabbas daga lokacin da Amrah ta zo ta faɗa mata Sadik ya zo ta ji sauyi a zuciyarta wanda bata san ko na mene ba. Sadik ya yi ƙoƙarin jan ta da hira amma ta ƙi sakin jikinta, ko d'ago kanta ta kasa yi, amma sai ta tsinci kanta da son jin muryarsa a wannan lokacin, ta ji bata son ya yi shiru da magana ko na second ɗaya ne. Shi kuwa Sadik jikinsa ne gaba-d'aya ya yi sanyi, dan yau da shirinsa ya taho na bayyana wa Neehal abun da ke zuciyarsa game da ita, amma kuma yanayin da ya ganta a ciki ya kashe masa gwiwa. Suna haka kamar a mafarki Neehal ta ji k'amshin Ameen, da sauri ta d'ago kanta ta kalli ƙofa. Shine kuwa yake ƙoƙarin shigowa falon, samun kanta ta yi da ƙura masa ido fuskarta ɗauke da murmushin da bata shirya masa ba, rabon data gan shi tun ranar da ta je gidansa, sati ɗaya kenan yau, sai ta ga ya ƙara mata kyau da haske ya yi wani fresh abunsa, alamun angoncin ya karɓe shi. Ameen ya ƙaraso inda suke fuskarsa ba yabo ba fallasa ya yiwa Sadik sallama tare da miƙa masa hannu. Cikin fara'a Sadik ya miƙa masa nasa hannun suka yi musabaha sannan ya gaishe shi. Ko kallon inda Neehal take bai yi ba ya nufi sama, Neehal data kasa ɗauke idonta daga kansa cikin sanyin murya ta ce "Yaya ina wuni." Ba tare da ya juyo ba ya ce "Fine." Tare da wucewa sama abinsa ya bar musu daddad'an k'amshinsa a falon...........✍️ _*Yanzu labarin zai fara sauya salo, sannu_sannu bata hana zuwa.......*_ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:51] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *3️⃣6️⃣* ............Runtse idanunta ta yi tana jin ba daɗi akan abun da Ameen yake mata, ta rasa wanne irin mutum ne shi da ba'a gane gabansa balle bayansa, tamkar mai aljanu wata rana faran_faran, wataran kuma akasin haka. Buɗe idonta ta yi tare da daidaita nutsuwarta jin muryar Sadik yana mata magana. Da Sallama Ameen ya shiga falon sama, Mama ta d'ago tana dubansa tare da amsa masa. Su Afrah suka tashi da sauri suka nufe shi suna faɗin "Oyoyo Uncle." Ameen ya kama hannuwansu yana murmushinsa mai k'ayatarwa. Shafa kansu ya yi ya ce "How are you?" Amrah ta ce "We are fine Uncle." Ya shafa fuskarta ba tare da ya kuma cewa komai ba sannan suka ƙarasa ya zauna a gefen Mama. Cikin kulawa Mama ta ce "Welcome." Ya gyaɗa mata kai tare da faɗin "Ina yini Mum." Mama ta ce "Lafiya k'alau, ya Hafsah?" Ya ce "Tana nan k'alau." Mama ta ce "Komai dai lafiya babu wata matsalar ko?" Ya ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa sannan ya ce "Babu matsalar komai, Dad ba ya nan ne?" Mama ta ce "Bai dawo ba, ka san sai ya yi isha'i yake shigowa." Ameen ya jinjina kai tare da mai da kallonsa ga Twins wanda suka ba da hankalinsu a kan kallon cartoon ɗin da suke. Mama ta ce "Bari na zubo maka abinci." Ya ce "No, am full." Mama ba ta kuma cewa komai ba ta cigaba da latsa counter ɗin dake jikin finger d'inta bakinta na ɗan motsi alamun lazimi take. Ameen ya dawo da dubansa gare ta ya ce "Who is that boy?" Mama ta ce "Wanne yaron kenan?" Ya ɗan yi shiru na sakanni sannan ya ce "Wanda na gan shi a downstairs yanzu." Mama ta ce "Sadik ɗin ne baka sani ba ko ya?" Ya yi shiru bai ce komai ba. Sai ma kawar da zancen da ya yi da faɗin "Ya wajen su Hajiya, da Uncle?" Mama ta ce "Sunan nan k'alau, Next week ma Insha Allahu zani Gomben." Ameen ya ce "Allah ya kai mu, nima Sunday Insha Allah zan tafi Lagos." Mama ta ce "Da Hafsah zaka tafi amma?" Ya ce "No." Tare da ɗan girgiza kansa. Mama ta ce "Kamar ya No? Zaka bar ƴar mutane ita kaɗai k'wal ne a gida? Ai ba zai yiyu ba." Ya ce "Za'a zo a taya ta kwana daga gidansu." Mama ta ce "Alright, Allah ya kai mu." Ameen ya ce "Amin, but in kin je Gomben tare zaku dawo da Hajiya ko?" Mama ta ce "Da ƙyar gaskiya, dan ta ce ita da Kano sai bikin Neehal kuma." Ya ɗan kalli Maman kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya mai da dubansa ga agogon hannunsa ya ce "Mum ni zan koma, ki gaishe da Dad." Mama ta ce "Zai ji, Allah ya kiyaye hanya, ka gai da Hafsan." Ya amsa mata yana miƙewa sannan ya fice. Mama ta bishi da kallo a ranta tana cewa 'He will never change daga shegen muskilancinsa, ta yi zaton idan ya yi aure abun zai ragu, amma kamar ma ƙaruwa ya yi. Da ya sakko zai wuce Sadik kawai ya kula, shi ma dan ya masa sai da safe ne. Ganin lokacin Sallah ya yi Shi ma Sadik ya yi wa Neehal sallama ya tafi, bayan ya sanar mata zai turo mata da saƙo ta waya anjima, ba ta yi tunanin komai ba ta ce sai ya turo tana jiran shi. Lokacin data koma sama Mama bata falo, sai su Afrah da bacci ya kwashe su, dama lokacin baccin nasu yayi, dan da wuri suke bacci, amma asubar fari sun tashi. Neehal ta shiga ɗakin Mama tana turo baki gaba, Mama dake shimfid'a Darduma ta dube ta amma ba ta ce komai ba. Neehal ta zauna a bakin gado kamar zata yi kuka ta ce "Mama yau Yaya bai kula ni ba, ban sani ba ko wani laifin na masa." Mama ta ce "To nice shi da zaki zo kina cuno mun baki, ko kuma halin Ameen ɗin ne baki sani ba?" Neehal ta ƙara bata fuska ba ta ce komai ba. Mama ta ce "Tashi ki je ki yi Sallah ki ci abinci, in kin gama ki zo i want took to you." Neehal ta ce "Toh." Tare da tashi da fita. Bayan ta idar da Sallah ta ci abinci ta kai su Afrah ɗaki sannan ta koma ɗakin Mama. Ganin yanda Mama ta yi serious alamun magana za su yi mai mahimmanci sai ta bata duka hankalinta. Mama ɗan numfasa ta ce "Neehal! Zan tambaye ki wani abu, kuma ina son ki faɗa mun gaskiya." Ta ɗan ji gabanta ya faɗi, amma ta daure ta ce "Insha Allah Mama zan faɗa miki gaskiya in dai na sani." Mama ta ce "Wanne matsayi Sadik yake a gurinki?" Neehal ta dubi Mama da sauri cikin mamakin tambayartata sannan ta ce "Like Brother or Friend." Kamar Mama zata kuma magana sai kuma ta fasa. Neehal ta ce "Wani abu ya faru ne?" Mama ta ce "Babu komai." Neehal ta ce "Daddy bai dawo ba ne?" Mama ta ce "Ya dawo yanzun nan." Neehal ta yi murmushi ta ce "Bari na je part ɗinsa mu yi hira." Ta miƙe ta fita, Mama ta bita da kallo cikin tausayinta. Ba dan ta mata maganar Sadik ta kira ta ba, ta kira ta ne ta mata wata tambayar daban akan abun da yake damun a zuciyarta a kwanakin nan, amma kuma da ta yi wani tunani a yanzu sai ta fasa. Sai wajen ƙarfe goma Neehal ta dawo part ɗin Mama daga gurin Daddy. Toilet ta shiga ta watsa ruwa sannan ta fito ta zira doguwar rigar bacci, ta kashe light ɗin ɗakin ta kunna bedside lamp sannan ta kwanta a kusa da twins. Wayoyinta ta ɗauko domin shiga yanar gizo. Message ta gani akan wayarta da Numbern Sadik, ta ma manta ita ya ce zai turo mata sak'o. Ta text ɗin kai tsaye ta fara karantawa kamar haka: _*Amincin Allah ya tabbata a gare ki yake ma'abociyar kyawu da nutsuwa gami da hankali. Neehal! Na daɗe ina tunanin ta yanda zan Bayyana miki abun da yake raina game da ke, amma fargabar abun da zai biyo baya yasa na kasa bayyana miki tun tuntuni, na cigaba da dakon sa a cikin zuciyata. Neehal! Ina son ki! Tun kafin na sanki a zahiri mu fara mu'amala k'aunarki ta cika duk wani gurbi na zuciyata sai dai.......*_ Ai ba ta ƙarasa karanta message ɗin ba ta tashi zaune da sauri zuciyarta na wani irin dokawa da sauri da sauri. Ajiye wayar ta yi a gefenta ta runtse idanunta hannunta dafe a ƙirjinta, a ranta tana addu'ar Allah yasa mafarki take ba gaske ba ne Sadik ya mata text ya sanar mata wai yana sonta. Vibration ɗin da wayarta ta fara yi ne yasa ta buɗe idanunta da sauri ta ɗauki wayar ta duba, sunan Sadik taga yana yawo akan screen ɗin wayar. Kallon wayar take tare da girgiza kanta, a fili ta fara faɗin "No, no Sadik soyayyata da kai ba zata taɓa yi yu ba, dan ban shirya shiga wani tashin hankalin ba a rayuwata bayan wanda yake manne a cikin zuciyata, ban shirya ƙara rasa masoyi a karo na uku ba, ka yi haquri Sadik dan babu batun ƙara soyayya a rayuwar Neehal har abada." Tana gama faɗar haka ta kashe wayar gaba-d'aya ganin kiran ya katse wani ya ƙara shigowa. Komawa ta yi ta kwanta tana jin haushin kanta da har ta bari suka saba da Sadik sosai haka. Tabbas biri ya yi kama da mutum, ya kamata a ce tun kafin yanzu ta gane Sadik sonta yake, idan ta yi la'akari da yanda alaƙarsu ta fara, lokacin da farko da Haneefah suke mutunci ba ita ba. Amma tunda ya samu ta fara sake masa sai kuma suke shiri fiye da wanda suka yi da shi da Haneefan ma. Me yasa tun ranar da suka fara haɗa ido da shi ta ji sauyi a cikin zuciyarta, ko kuma hakan yana nufin shine wanda zai shigo cikin rayuwarta a karo na uku a matsayin wanda zai zamo abokin rayuwarta. Tabbas idan cancanta zata duba Sadik ya cancanta ya zamo abokin rayuwarta, domin yana da duk wasu qualities ɗin da take so mijin da zata aura ya kasance yana da shi. Sai dai bata tunanin *ƙaddarar* data raba ta da Jamil da Anwar zata bar mata Sadik. Bata son ta jefa rayuwarta data iyayenta a cikin wani tashin hankalin, shi yasa duk wata ƙofa da wani zai nuna yana sonta ta rufe ta a rayuwarta, da zarar ta ga take_taken mutum zata taka masa burki. Ita yanzu burinta a rayuwa taga ta yi karatu mai zurfi, domin ta san shikaɗai ne zai zama gatanta a nan gaba. Wasu zafafan hawaye suka ziraro daga idanunta.Ta lumshe ido tana jin hawayen na diga akan filon da tay matashi da shi. Fuskar Sadik, murmushinsa, tafiyarsa, su kawai idanunta suke hango mata, ga muryarsa dake mata kuwwa a cikin kunnenta. Wata irin fad'uwar gaba ta ji bugun zuciyarta na ƙaruwa. Tana ƙoƙarin cire Sadik daga rayuwarta amma zuciyarta tana hasaso mata komai nasa, kenan hakan yana nufin ta kamu da sonsa ne ita ma ko kuma dama can tana son shine ne? Ta tambayi kanta, a fili ta ce "Impossible!" Cikin muryar kuka. Ta san soyayya, tunda ta yi ta kar karo biyu, ta san daɗinta kamar yadda ta san ɗacinta. A rayuwarta tana son soyayya tana son ta ga masoya, a kullum addu'arta Allah ya bata mijin da ya iya soyayya, amma zuwa yanzu ta yiwa kanta alƙawarin koda zata yi aure ta ajiye babin soyayya a rayuwarta. Saboda ita bata iya so ba, idan tana son mutum tana son shi ne da dukkan zuciyarta, irin zufaffaffen son nan take yiwa mutum mai game jiki da zuciyar ɗan'Adam. Haka tay ta tunane_tunane da sak'e_sak'e a wannan daren, bacci kam yau duk iya satarsa ya kasa sure Neehal. Washegari bayan ta yi Sallar Asuba ta ɗauko Alqur'ani ta shiga karantawa kamar kowacce Asubahi. Kafin ta gama karatun su Afrah sun tashi daga bacci, jikinta suka zo suka ɗane suna zuba mata surutu, ta ce su yi mata shiru ba su ga karatu take ba ne. Bayan ta gama ta musu wanka ta shirya su saboda yau Asabar Mama zata kai su Tahfiz. Ita ma wankan ta yi bayan ta gama shirya su dan ƙarfe tara zata fita gurin aiki. Ta kama hannunsu suka sauka ƙasa, a kitchen ta hango Mama tana haɗawa Daddy kayan karinsa. Su Afrah suka ƙarasa kitchen ɗin da gudu suna kiran sunan Mama. "Mama! Mama! kin ga Aunty ta saka mana sabon Hijabi, ta ce yau da mu zata fita." Mama tana dubansu da murmushi akan fuskarta ta ce "Kun yi kyau sosai ƴaƴan Aunty, ku je ga Aunty Dije can a falo ta zuba muku abinci ku yi breakfast, maza!" Da murnarsu suka juya suka fita, Neehal ta bi su da kallo sannan ta ƙarasa shiga cikin kitchen ɗin jikinta a sanyaye. "Sannu da aiki Mama, ina kwana." Neehal ta faɗa tana duban Maman. Mama ta ce "Yawwa har kun fito kenan?" Neehal ta ce "Ehh, ina tunanin ma tafiya zan yi kar na yi late kya kai su Tahfiz ɗin kawai." Mama ta ce "Amma dai kya tsaya ki ci abinci ai." Neehal ta ce "A'a, yau na tashi da azumi ne, na manta ana bina wani guda ɗaya sai jiya na tuna ashe azumi bai fi saura 1 month ya rage ba, shi yasa na ga gwara in yi kar na manta kuma......" Kallon da Mama take bin ta da shi tunda ta fara magana ne yasa ta yin shiru ba tare da ta kai aya ba. Mama ta ce "Yaushe kika ko yi ƙarya Neehal ban sani ba?" Neehal ta yi ƙasa da kanta ba ta ce komai ba. Mama ta cigaba da Magana "Jiya kin tashi da kumburarrun ido alamun kin sha kuka kafin ki yi bacci, yau ma ga idanunki nan da alama ba ki yi bacci ba jiya, kuma still kin yi kuka, yanayinki da maganarki sun tabbatar mun da damuwar da na gani kwance akan fuskarki. Ba zan takura miki ki faɗa mun abun da yake damunki ba tunda ba ki yi niyyar faɗa mun ba tun farko, amma zan miki addu'a Allah ya yaye miki." Mama tana gama faɗar haka ta juya ta cigaba da abun da take fuskarta na nuna ɓacin ranta. Neehal ta matso kusa da ita ta rungume ta tare da sakin kuka, cikin kukan ta ce "Ki yi haquri dan Allah Mama kar ki yi fushi da ni." Mama ta sanyaya muryarta ta ce "Ba zan taɓa iya fushi dake ba Neehal, amma kin san ba zan juri ganin damuwarki ba ko?" Neehal ta gyaɗa mata kai. Mama ta ce "To share hawayen ki faɗa mun me yake damunki." Neehal ta share hawayen sannan ta ce "Babu komai Mama, kawai ki mun addu'a." Mama ta bita da kallo ba ta ce komai ba. Neehal ta kama hannunta ɗaya ta ce "Ki yarda Mamana seriously ba komai, idan ma da akwai ganinki da na yi yanzu ya shafe mun duk wata damuwata." Mama ta ce "Shikenan, amma dai always ina faɗa miki kuka ba maganin damuwa ba ne, addu'a ita ce magani, kin ji?" Neehal ta ce "Insha Allah zan daina kukan." Mama ta ce "Ki je ki ci abinci to, sai ki je ki gaida Daddy." Neehal ta ce "Toh." Sannan ta juya ta fita, Mama ta bita da kallo cikin tsananin tausayinta gami da k'aunarta. Neehal ta daure ta cuccusa bread da k'wai ta kora da ruwan tea, ba ɗan tana jin yunwa ba ko ɗan tana jin daɗin abincin a bakinta ba sai dan kar Mama ta mata faɗa. Bayan ta gama ta faki idon su Afrah ta shiga part ɗin Daddy, daga nan ta wuce gurin aiki. Sai dai wani ƙarin damuwar tana fita ta ga Motar data bi bayanta shekaran jiya tana bin ta yau ma still. Tun daren jiya bata kunna wayarta ba saboda bata so ta kunna ta ga kiran Sadik ko text ɗinsa. Sukuku ta wuni yau, abokan aikinta kowa sai ya tambaye ta lafiya take kuwa? Ita kuma sai ta ce musu kanta ke ciwo, fatan samun sauqi su kai mata.Tare suka wuce gida yau da Haneefah, amma Haneefan bata jima ba ta wuce gidansu. Mama ta kai su Afrah Islamiyya kamar yadda ta ambata, islamiyyar weekend kawai ake yinta, 8_5. Babu nisa kuma daga gidan. Ɗaya daga cikin sojojin gidan Mama ta aika ya ɗauko su da time ɗin tashin su ya yi. Neehal tana kwance akan gado suka shigo, suka haye jikinta cikin murna suna ba ta labarin Islamiyyarsu, murmushin da bai kai zuci ba kawai take bin su da shi amma ta gaza ce musu ƙala, har suka haqura suka ƙyale ta suka koma gurin Mama suke ba ta labarin ita, tunda Auntin ta ƙi kula su. Da daddare tana gani Sadik yana ta kiran wayarta amma ta ƙi d'agawa, daga baya sai ga text ɗinsa, ta buɗe ta karanta amma ta ƙi yi masa reply. Haka rayuwa tay ta tafiya, Neehal ta daina d'aga kiran Sadik kwata_kwata, shi kuma ba ya gajiya kullum sai ya kira ta ba a daɗi gami da yi mata daɗaɗan text, na kalaman soyayya addu'a da fatan Alkhairi. Duk text ɗin da ya turo sai ta karanta amma fa bata reply, kuma ba ta yi block ɗinsa ba, saboda babu block ɗin mutane a tsarin rayuwarta, in dai ba abun da bai dace ba mutum yake turo mata ba. Mama ta je Gombe ta yi kwana uku ta dawo, gidan Aunty A'isha su Neehal suka koma kafin Mama ta dawo, su Zulai da Dije kuma garinsu suka je. Da tana gidan Aunty A'isha sai ga Sadik ya zo, Allah ya so tana ɗaki ba falo ba. Ashe ya saba zuwa gidan yana gaishe da Aunty A'ishan ita ba ma ta sani ba. Da Aunty A'isha ta ce a kira ta, sai ta ƙi fitowa ta ce ace bacci take yi. Duk wannan abun da Neehal take dauriya kawai take yi a ƙoƙarinta na ganin ta cire Sadik daga cikin rayuwarta, sai dai zuciyarta ta ce sam bata san wannan batun ba, dan da tunanin sa take kwana take tashi. A kwanakin nan da ta yi babu Sadik ta tabbatar wa da kanta tana son Sadik, so ba na wasa ba ma kuwa, Amma ta yi alƙawari ko son nasa zai kashe ta ba zata taɓa bari su yi soyayya ba. Ameen kuwa tun ranar da ya zo ɗin nan bata ƙara sa shi a idanta ba, tunda ya koma aiki sai weekend yake gari, weekend ɗinma idan ya zo gidan ita tana gurin aiki, bare ma ta ji Mama ta ce sau ɗaya ya ƙara zuwa tun ranar. Sai dai ita Hafsah ta zo sau biyu ta wuni, bata nuna wa Neehal komai ba saboda ganin idon Mama, ita ma Neehal ɗin haka, sai dai ba sa shigewa juna sosai. Dan Munafurci Hafsah harda cewa Mama wai Neehal bata zuwa gidanta, kamar so take ta je ɗin, Mama ta ce bata da lokaci ne shi yasa ga aiki ga school. Kamar yadda Mama ta kai su Afrah Islamiyya ta kai su makarantar boko, wadda haɗe take da islamiyya itama, Monday to wednesday sai 5:pm ake tashin su, Thursday and Friday kuma 12: pm. Yau Talata wanda ya kama azumi saura kwana shida ga mai rabon gani. Da yamma bayan Neehal ta dawo daga school tana ɗaki tana gugar Uniform ɗin su Afrah Haneefah ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama. Neehal ta d'ago tana dubanta ta amsa mata sallamar, "Amarya ke ce a gari yau? inji maƙi baƙo." Haneefah ta ce "Ni ce nan, na zo mu yi wata magana ne, da zan bari sai gobe sai kuma kawai na ce bari in zo tunda babu abun da nake yi yanzun." Neehal ta ce"Gwara da kika zo ai, Ya Mommy?" Haneefah ta ce "Tana nan k'alau." Suka ɗan taɓa hira kafin Neehal ta ƙarasa gugar sannan ta koma bakin gado kusa da Haneefah ta ce "Wacce maganar zamu yi Besty?" Haneefah ta ce "Akan Sadik ne." Neehal ta ɓata fuska ta ce "Me ya faru?" Haneefah ta ce "Yanayin da kika koma yanzu shi ya tabbatar mun da kin san koma menene." Neehal ta ce "I don't know any thing." Haneefah ta ce "Any way dai, Jiya Sadik ya zo gida ya same ni and he told me duk yanda kuka yi, wanda kin fini sani ba sai na ƙara maimaita miki ba, amma Neehal na tambaye ki mana." Neehal ta ce "Ina jin ki." Haneefah ta ce "Me yasa kika yi ignoring ɗinsa? Ko kin manta Sadik ɗin ne?" Neehal ta ɗan tab'e baki ta ce "Saboda bana buƙatar sa a cikin rayuwata." Haneefah ta yi ɗan murmushi ta ce "Bakin ki dai ya furta haka, amma fuskarki da yanayinki sun tona asirin zuciyarki. Neehal kina son Sadik! Kuma kema kin sani." Neehal ta yi shiru saboda ba ta san me zata ce ba, sai ma k'walla data cika mata ido. Haneefah ta cigaba da magana "Ina lura dake a kwanakin nan walwalarki ta ragu sosai, kuma na san duk akan haka ne. Amma Sadik yana da wani aibu ne da ba za ki iya soyayya da shi ba? Ko kuma yana da wani halin ne mara kyau da kika fuskanta wanda mu ba mu sani ba?" Neehal ta girgiza kai cikin karaya ta ce "Ko ɗaya." Haneefah ta ce "To me yasa ba za ki yi accept ɗinsa a cikin rayuwarki ba? Wallahi Neehal baki ga yanda Sadik ya koma ba, gaba-ɗaya ba ya cikin nutsuwarsa, kuma duk saboda ke ne." Haneefah ta sassauta murya ta ce "Please Neehal dan Allah ki amincewa Sadik ku yi soyayya, ki tausaya masa ke ma kuma ki bawa zuciyarki abun da take so, kar ki cutar da ku dukanku." Neehal tana hawaye ta ce "I can't, ba zan iya ba Haneefah, na san ina son Sadik amma ba za mu yi soyayya ba, bana son na kuma yiwa iyayen kowa asarar ɗansu. Haneefah na rufe babin soyayya a rayuwata, ba zan ƙara soyayya da kowa ba!" Cike da tausayawa Haneefah ta ce "Kar ki yi haka Neehal, na sha faɗa miki ki daina faɗar irin wannan maganar, ke a karan kanki kina faɗar haka idan wani ya ji ya samu abun ɗorarwa fa?" Neehal ta ce "An yi na farko an yi na biyu, idan aka yi na uku Haneefah dole hankalin mutane zai dawo kan al'amarin, ko na faɗa ko ban faɗa ba, dole za a fara faɗar maganganu a kai na, ko so kike duk inda na yi a dinga nuna yi ana gata can, duk wanda zata aura sai ya mutu, sai....." Haneefah ta rufe mata baki ta ce "Insha Allahu haka ba zata faru ba, in Allah ya yarda za a yi auranku da Sadik lafiya babu abun da zai faru. Ke dai ki miƙawa Allah al'amuranki, sannan ki dage da addu'a. Su ya Ammar ma kwanansu ne ya ƙare a duniya, amma ba wai dan ke aka kashe su ba." Neehal zata yi magana Haneefah ta katse ta da faɗin "Dan Allah Neehal kar ki ɗauko abun da baki da tabbas akai ki saka a ranki Please!" Neehal ta sauke numfashi ba ta ce komai ba, sai kallon ƙanwartata kawai take tana hawayen tausayin kanta. Haneefah ta baibaye Neehal da kalamai masu kwantar da hankali gami da wa'azin da ya ratsa mata zuciyata. Ta nuna mata babu wani mahaluƙi da ya isa ya maka abun da Allah bai maka ba. Neehal ta ji zuciyarta ta yi mata sanyi, kuma ta ji zata karb'i Sadik a matsayin masoyi a karo na uku a rayuwarta. Sai dai wani ɓangaren na zuciyarta cike yake fal da tsoro da fargabar rashin sanin abun da zai biyu baya a soyayyar tasu. Za su yi Aure da Sadik ɗin ne kamar yadda Haneefah ta faɗa ko kuma shima za'a kashe mata shi ne?..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:51] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *3️⃣7️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ...........Sai da Haneefah ta tabbatar da bayananta sun shiga Neehal kuma sun ratsa ta sosai sannan ta miƙe dan tafiya gida tana faɗin "Mu je in yiwa Mama Sallama na ga magriba ta taho." Neehal ta shagwaɓe fuska ta ce "Ki bari ki yi sallah mana." Haneefah ta ce "Tafiya zan yi, zan je in yi girkin dare." Neehal ta ce "Please dear!" Haneefah ta ce "Ikon Allah, to ki adana shagwab'arki idan yaya Sadik ya zo sai ki yi masa, amma bani zaki wa ba." Ta ƙarashe zancen da dariyar tsokana. Neehal ta ɓata fuska ta ce "Na ji ɗin zan masa." Suka fita daga ɗakin Haneefah tana ta tsokanarta. A ɗakin Mama suka tarar da twins suna cire uniform. Haneefah ta ce "Ashe kun dawo yanzu nake shirin tambayar su." Mama ta ce "Yanzu nan aka ɗauko su." Twins suka gaishe da Haneefah ta amsa, Afrah ta cewa Neehal "Aunty zamu biki." Neehal ta harare ta ta ce "Sarakan son yawo, to ba fita zan yi ba." Amrah ta kalli Haneefah ta ce "To Aunty ke zamu biki." Haneefah ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ku saka kaya sai mu tafi." Suka shiga tsallen murna, Mama ta ce "Babu inda za su Assignment za su yi." Lokaci ɗaya Suka ɓaɓɓata fuska kamar za su yi kuka. Neehal ta ce "Don't cry My babies, gobe zan kai ku unguwa." Sai suka saki ransu suka ci-gaba da sabgarsu. Haneefah ta dubi Mama ta ce "Mama zan wuce, sai da safe." Mama ta ce "Allah ya kai mu, ki gai da gida da Mominki, Insha Allah kafin tafiyarmu Saudiyya zan zo gidan naku." Neehal ta marairaice ta ce "Wai Mama baza ki tafi da ni ba?" Mama ta ce "In na tafi dake Neehal mu bar yaran nan a ina? Kuma ga makarantarki ma, ki bari Lokacin Hajji idan Allah ya kai mu sai ki je indai kun yi hutun school." Haneefah ta ce "ki ƙyale ta Mama, rigima ce kawai ke damunta, yaushe ne tafiyar taku?" Mama ta ce "Biyar ga azumi Insha Allah." Haneefah ta ce "Allah ya kai mu, sannan ta yiwa Mama Sallama suka fice ita da Neehal wadda zata ɗan taka mata. Bayan Sallar Magriba Neehal ta yiwa Sadik text kamar yadda suka yi da Haneefah zata masa. A ɓangaren Sadik kuwa tun ranar da ya yiwa Neehal text bata masa reply ba kuma yana kiranta bata ɗauka, sai hankalinsa ya tashi. Gaba-d'aya ya ji duniyar ta masa zafi, ga wani sabon son ta dake ƙara mamaye masa zuciya da gangar jiki. Cikin kwanaki kaɗan ya rame saboda damuwar da ya saka a ransa. Hotunan Neehal su suka zama abincinsa, dan kodayaushe cikin tasa wayarsa a gaba yake yana kallon pics ɗinta. Duk wani program da take a gidan TV kuwa ba ya wuce shi. Mahaifiyarsa ta tambaye shi me yake damunsa haka duk ya fita daga hayyacinsa? Sai ya ce mata "Wani case yake ne mai wahala, ta taya shi da addu'a kawai." Ganin abun Neehal bana ƙare ba ne shine jiya ya shirya ya je gidansu Haneefah, ya faɗa mata duk abun da ke faruwa, Haneefah ta kwantar masa da hankali ta ce zata je ta samu Neehal ɗin, kuma ta san ta yanda zata ɓullo mata kar ya damu. To bayanin Haneefah ne ma ya ɗan kwantar masa da hankali. Yau kuma yana masallaci ya ji message ya shigo wayarsa, ya yi zaton ma kamfani ne amma da ya duba sai ya ga Neehal ce ta turo masa. Jikinsa har rawa yake yi wajen shiga ya karanta message ɗin zuciyarsa cike da fargaba. Wani sanyi ya ji ya ratsa zuciyarsa gami da farin ciki mara misaltuwa ganin abun da Neehal ta turo masa, a fili ya furta Alhamdulillah yana sakin murmushi shi kaɗai. Duk wannan murnar da Sadik yake ba fa wani abu Neehal ta ce masa ba a cikin text ɗin. Ta tambayi lafiyarsa ne kawai, a ƙarshe kuma ta nuna tana son ganinsa Yau idan babu damuwa. Amma shi a gurinsa hakan alamun nasara ne, dama tun d'azu zaman jiran kiran Haneefah yake domin ta sanar masa yadda suka yi da Neehal ɗin, sai kuma ya ga text ɗin Neehal ɗinma a lokacin da bai taɓa tsammani ba. Cikin sauri ya tashi ya nufi gida, jikinsa har rawa_rawa yake dan zumud'i. Shaf_shaf ya shirya cikin wani yadi milk colour ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin k'amshi ya fito ya ɗauki hanyar gidansu Neehal. Itama Neehal ɗin ba'a barta a baya ba, wanka ta yi ta shirya cikin wata gown purple colour wanda ta zauna das ajikinta, ta kuma haska farar fatarta. Ta shafa powder a fuskarta gami da White lipsticks a lips ɗinta. Ta yi kyau sosai fuskarta sai annuri take, ita kanta ta san She Missed him over, zuciyarta cike take da d'okin ganin kyakkyawar fuskarsa ɗauke da murmushinsa da ba ya rabo da shi kodayaushe. Tana jin wayarta ta yi ƙara ta ji gabanta ya ɗan faɗi, kamar yadda ta yi zato tana dubawa ta ga shine, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta d'aga amma ba ta ce komai ba. Lumshe idonta ta yi tana sakin ajiyar zuciya a hankali jin muryar Sadik yana mata sallama, a sanyaye ta amsa masa masa. Yana jiran ta a waje kawai ya sanar mata sannan ya kashe wayar, kamar ya san kuwa da ya ce wani abun ba zata iya ce masa komai ba. Ta yafa mayafinta sannan ta fito falo, anan ta tarar da Mama ta tasa su Amrah a gaba suna Assignment. Kanta a ƙasa ta ce "Mama zan sauka ƙasa Yaya Sadik ya zo." Mama ta bita da kallo sannan ta ce "Okay ki gaishe shi." Su Afrah sarakan son yawo suka bi ta da kallon a tafi da su, Neehal tay murmushi ta shafi kuncinsu sannan ta fita. Inda suke zance da Anwar ta saka aka kai musu kujerun roba, tunda yau Sadik ɗin ya ƙi shigowa falo. Allah sarki rayuwa har ta tuna da sanda Anwar yake zuwa zance, ta hango zuwansa na ƙarshe gidan, sai ta ji zuciyarta ta mata rauni kamar zata yi kuka. Sai da ta mayar da k'wallar data tarar mata a ido sannan ta ƙarasa gurin cikin sanyin jiki. Tun da ta taho ya ƙura mata ido cikin shauƙin k'aunarta yana sakin ajiyar zuciya. Sai ya ga kamar ta ƙara kyau da iya tafiya a kwana biyun da bai ganta ba. Kanta a ƙasa ta ƙarasa tare da yin Sallama cikin siririyar muryarta. Sadik ya amsa mata cikin kulawa da k'auna yana jifanta da wani irin kallo da murmushin nan nasa manne a kan fuskarta. Ta zauna cikin tsananin jin kunyarsa akan abun da ta yi masa, kuma dama can ita naturally ɗinta tana da jin kunyar wanda take so. A hankali ta ce "Ina yini." Ya ce "Lafiya k'alau sarauniyar birnin zuciyar Sadik." Ta ɗan kalle shi amma ba yanda za su iya haɗa ido ba, sai ta ga ya ɗan rame duk da manyan kaya ya saka. Tausayinsa ta ji ya cika mata zuciya. Ganin yanda ta takure ta hana kanta sakewa sai Sadik ya fara da zolayarta da ya saba, har ya samu ta ɗan fara sakin jiki amma duk da haka ta ƙi d'ago kanta ta kalle sa. Cikin sanyin murya ta ce "Dan Allah Yaya Sadik ka yi haquri da abunda na maka, nima ba son raina ba ne, sai dan wani dalilin daban." Sadik ya yi murmushi mai sauti ya ce "Kar ki damu Neehal, tun farko dama na fahimce ki kuma na san haka zata faru, dan haka wannan ba komai ba ne, ki manta kawai. Alfarmar da kika mun ma har na samu ganin kyakkyawar fuskarki a yau ya tabbatar mun da ina wani matsayi a gare ki, ko da kuwa matsayin mai goge miki takalmin ƙafarki kika bani zan yi farin ciki da hakan." Neehal ta d'ago da sauri ta kalle sa, ya kashe mata ido ɗaya wanda yasa ta ji tsigar jikinta ta ɗan tashi hakan yasa ta yi saurin mayar da kanta ƙasa. Ya cigaba da magana da faɗin "Kina mamaki dan na ce miki ko da matsayin mai goge miki takalmi nake a gurinki zan yi farin ciki sosai da hakan? Neehal a yanda nake jin sonki a cikin zuciyata ko da bawanki kika mayar da ni zan yi farin ciki da hakan sosai, ni indai zan kasance dake a kodayaushe ina ganin kyakkyawar fuskarki to zan yi farin ciki gami da alfaharin haka." Neehal ta ce "Haba Yaya Sadik ka daina faɗar haka, matsayin da kake da shi a gurina kafi ƙarfin na mulke ka sai dai kai ka mulke ni." Cikin jin daɗin kalamanta ya ce "Are you Sure! Neehal matsayina har ya kai haka agurinki?" Ta yi murmushi tare da rufe fuskarta da hannunta. Kafin Sadik ya tafi yau sai da suka gama fuskantar junansu yanda ya kamata, har tahirinsa ya bata a tak'aice. Har sai da Mama ta kira ta a waya sannan suka yi sallama ya tafi bayan ya ce ta gaishe da Mama, tun da a suruki ya zo gidan yau ya ƙi shiga ciki. Soyayya sosai Neehal da Sadik suke, Haneefah kuwa ta samu abun tsokanarta, matar Barrister ma ta koma ce mata. Mama ma tana lura da ita a kwanakin nan Sadik ya bar Friend or brother ya koma Habibi. Ta kuwa ji daɗin hakan sosai, sai ta ƙara dagewa da k'aimi gurin yi musu addu'a akan Allah yasa Sadik shine mijin Neehal. Sadik ya iya tafiyar da mace yanda ya kamata, ga tarin kyautatawa da daɗaɗan kalamai wanda suke ƙara dulmiyar da Neehal a kogin k'aunarsa. Ranar Asabar ta kasance ranar farin ciki ga kowane musulmin duniya, saboda tashi da azumin watan Ramadana mai girma da ɗaukaka da akai. Ranar da aka ɗauki azumi na Shida su Mama suka tashi zuwa ƙasa mai tsarki ita da Aunty Sadiya dan yin Umrah. Gidan Aunty A'isha su Neehal suka koma kafin Mama ta dawo, wannan karon har da su Dije suka tafi. Mama ta yi addu'a sosai a gaban ka'aba akan Allah ya kawo ƙarshen ƙaddarar Neehal gami da tona asirin duk masu hannu a kisan su Anwar............ *THREE MONTHS LATER* Neehal ce ta fito cikin shirinta na tafiya school, a kitchen ta tarar da Mama tana yin lunch, ta cewa Maman. "Mama zan tafi school." Mama ta ce "Har kin gama karatun?" Da yake Neehal ɗin sun fara exam ɗin second semester level three. Ta ce "Eh, na ga 2 ta wuce, kuma ƙarfe 3 zamu shiga exam ɗin. Mama ta ce "Allah ya kiyaye ya ba da sa'a, ki biya fa ki dubo Yayanki kar ki manta." Neehal ta ce "Zan je Insha Allah, zan kira Haneefah ma idan tana free sai mu je tare, idan ma tana School ɗin sai mu wuce ta can kawai." Mama ta ce "Shikenan ki masa sannu." Neehal ta ce "Zai ji." sannan ta juya ta tafi. Kamar kodayaushe tsawon watanni ukun nan da suka wuce kullum Neehal ta fita sai Motar nan ta bita a baya, idan zata school,aiki,shopping da unguwa duk tana biye da ita a baya. Ita har mamakin ma yanda mai Motar yake sanin time ɗin fitarta dana dawowarta take sai ka ce aljani. Kuma har yau bata taɓa faɗa wa kowa ana bin ta ba, Ubangijinta kawai take faɗawa, dan babu mai bata kariya sama da tasa. Bata son kuma ta d'agawa Mama hankali shi yasa bata faɗa mata ba, duk da a zahirin gaskiya a tsorace take da bin ta da ake yi ɗin. Watarana ta kai su Afrah shopping a hanyarsu ta dawowa motar tana bin ta sai ta ce a ranta bari ta gwada wani abu. Parking ta yi a gefen titi ta kulle su Afrah a cikin motar sannan ta shiga wani shago da ake sayar da zobuna da agogo, ta ɗauki zobe ɗaya ta siya duk da bata fito da niyyar hakan ba. Bayan ta fito daga shagon ta kalli titi ta bayanta ko zata ga motar nan amma bata ganta ba. Amma abun mamaki bayan ta shiga tata motar bata fi 3 minutes da fara tafiya ba ta hango motar tana bin ta a baya. Hakan ya tabbatar mata da abun da take tunaninta akan wani ne yake bibiyarta, kuma koma waye Allah ya fi shi. Ƙarfe huɗu ta fito daga exam ɗin kuma Alhamdulillahi ta mata sauƙi, masallaci ta nufa ta yi sallah sannan ta kira Haneefah dan su je su dubo Ameen dake fama da zazzaɓi. Haneefah ta sanar mata bata gida sun fita kasuwa da ƙanwar Mommy, kasancewar bikinta ya gabato saura sati uku, dan ma exam ɗin da suka fara ne da tuni an yi bikin. Yanzu sai bayan Babbar Sallah da sati biyu za'ayi. Sallama Neehal ta yiwa k'awayenta ta tafi. Sai wajen biyar ta ƙarasa gidan. Babu kowa a falon ƙasa hakan yasa ta nufi sama, a nan ta tarar da k'awayen Hafsat su uku zaune a falo. Ta musu sallama ta shiga, suka amsa suna bin ta da kallo. Ta zauna a kujera sannan ta gaishe su. Cikin fara'a Fadeelah ta ce "Laa Neehal ke ce, ai ban gane ki ba da farko sai yanzu." Neehal ta yi murmushi ta ce "Aunty Hafsan tana ciki ne?" Fadeelah ta ce "Eh wanka take, ki shiga Yayan naki yana cikin ɗakinsa." Neehal ta ce "Toh." Tare da miƙewa ta shiga ɗakin. Ɗaya daga cikin k'awayen Hafsat ta ce "Wannan yarinyar kamar mai aiki a ASTV ko?" Fadeelah ta ce "Ita ce, ƙanwar Ameen ce fa." Wadda tai maganar ta ce "Allah sarki, Ni kam tana burgeni, yarinyar a nutse take bata da rawar kai." Fadeelah ta ce "Ga ta da kirki wallahi so friendly babu ruwanta." Neehal ta tura ƙofar ɗakin Ameen a hankali bakinta ɗauke da Sallama, k'amshinsa ne ya fara mata Welcome. Yana kwance akan gado jikinsa sanye da jallabiya brown colour idanunsa a lumshe. Neehal ta ƙarasa ta zauna akan bedside locker tana kallonsa cikin tausayawa, ya ƙara haske kuma ya ɗan faɗa. Hannunta ta kai a hankali ta taɓa wuyansa ta ji jikin nasa da zafi, a tunaninta bacci yake. Ta zare hannunta a hankali daga jikinsa ta ce "Allah ya baka lafiya Yayana." A hankali ya buɗe lumshashshun idonsa ya sauke su a kanta. Ta ce "Yaya! Sannu, ya jikin?" Bai amsa mata sai tashi zaune da ya yi yana taune lips ɗinsa. Cikin murya mara sa lafiya ya ce "Yaushe kika zo?" Neehal ta ce "Yanzu na zo, ya jikin naka?" Ya ce "Da sauƙi, ina Mum?" Ta ce "Tana gida daga school na biyo ta nan." Ya jinjina kansa tare da lumshe idonsa, daga gani babu tambaya ka san yana jin jiki. Neehal ta ji duk hankalinta ya tashi dan baza ta iya tuna sanda ya kwanta ciwo irin haka ba, hannun damansa ta kalla ta ga abun ƙarin ruwa alamun ya sha drips. Kamar zata yi kuka ta ce "Yaya me yake damunka? Mama ta ce mun zazzaɓi kake, kuma na ga kamar ba iya zazzaɓin ba ne kawai." Kafin Ameen ya bata amsa wayarta dake cikin jakarta ta fara vibrate, ta zuge jakar ta ɗauko wayar tare da d'agawa ganin Sadik ne. "Hello Yaya Sadik." Jin haka yasa Ameen ya juyo da sauri ya kalle ta, ta ce "Eh na dawo, ina gidan Yaya na je duba shi." Ta ɗan yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce "Tom sai ka zo." Tare da kashe wayar. Ameen ya mayar da idansa ya lumshe a hankali ya ce mata "Bani ruwa." Da sauri ta ɗauko ruwan dake gaban gadon ta buɗe sannan ta tashi ta miƙa masa tare da faɗin "Sannu Yaya Allah ya sauwaqe." Ya d'aga mata kai tare da karɓar ruwan ya sha. Ganin yanda ta damu sai ya kamo hannunta a cikin nasa yana kallon fuskarta ya ce "Menene?" Ta yi ƙasa da idonta ba ta ce komai ba, ya d'ago hab'arta da ɗayan hannunsa ya ce "Don't cry." Dan ya san halinta, ai ko kamar zugata ya yi sai ta fara hawaye, ita haka Allah ya halicce ta idan ta ga mutum ba shi da lafiya duk sai ta ji ta damu sosai, musamman ma Yayan nata da take jin kamar ta mayar da ciwon nasa jikinta. Ya ɗan tauna lips ɗinsa murya ƙasa_ƙasa ya ce "Kukan na mene?" Ta ce "Yaya baka da lafiya, na ga duk ka rame." Ya ce "Ai na ji sauƙi, kuma soon zan warke Insha Allah." Ta gyaɗa masa kanta. Ya yi ɗan murmushi sannan ya shiga goge mata hawayen fuskarta da tattausan tafin hannunsa ɗaya, ɗayan kuma yana riƙe da hannunta har lokacin. Dai_dai time ɗin Hafsah ta turo ƙofar ɗakin ta shigo.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:52] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *3️⃣8️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ..........Turus ta tsaya a bakin ƙofar cikin shock, wani abu mai tsananin ɗaci ya tsaya mata a mak'oshi, dama a fusace ta taho saboda Fadeelah ta sanar mata Neehal ta zo tana cikin ɗakin, sai da ta mata masifar me yasa zata bar wata ta shigar mata ɗakin miji sannan ta taho ɗakin. Neehal ta yi ƙoƙarin zame hannunta daga cikin na Ameen jin ƙarar buɗe ƙofar ɗakin, kuma ko tantama ba ta yi Hafsat ce, amma ya ƙi bata damar hakan, sai ma ƙara matse hannunta yake a cikin nasa duk da shim ya ji shigowar Hafsan. Sai da ya goge mata hawayen fuskarta tass sannan ya saki hannunta yana murmushi ya ce "Mommy's girl, rigimammiya kawai." Neehal ta koma kan bedside locker ta zauna ta turo ɗan bakinta gaba. Duk yanda Hafsah taso daurewa kasawa ta yi, sosai fuskarta ta nuna ɓacin ranta. Ta janyo ƙafarta data ji ta mata wani iri tana bankawa Neehal harara ta ƙaraso cikin ɗakin, ji take kamar ta janyo ta ta shak'e ta dan tsananin ƙiyayyarta da take ji a ranta. Neehal ta dube ta da murmushi akan fuskarta ta ce "Ina yini Aunty Hafsah." Kamar an mata dole ta amsa da faɗin "Lafiya." Neehal ta ce "Ya mai jiki?" A ranta ta ce ''Gashi nan a gabanki ai, kin ga jikin nasa munafuka' Amma a fili sai ta ce "Da sauqi." Daga haka Neehal ta ja bakinta ta tsuke sai ma ƙoƙarin tashi da ta yi dan ta ba su guri. Hafsah ta ɗan saki fuska ta zauna a kan gadon ta kai hannunta jikin Ameen wanda idanunsa ke lumshe ta ce "Baby ya jikin naka?" Ameen ya buɗe idanunsa ya kalli Neehal ba tare da ya amsa mata ba, ya ce "Ki bata abinci, daga school take." Neehal ta miƙe ta ce "No Yaya am full." Wani kallo ya wurga mata wanda yasa ta yin ƙasa da kanta. Hafsah ta had'iye wani malolon baƙin cikin da ya tsaya mata a mak'oshi, 'wato ba ma zai amsa mata magana ba, sai ma bata umarnin da bawa wata banzar yarinya abinci. Amma da yake makira ce sai ta dake kamar ba ta ji komai ba. Cikin kissarta ta ce "Ayya, ai ban sani ba sisina, mu je na baki abinci ki ci" Neehal zata yi magana wayarta dake hannunta ta hau vibrate, ta duba tare da d'agawa ganin Mama ce. Mama ta ce "Kin je gidan Ameen ɗin." Neehal ta ce "Ehh." Mama ta ce "Ya jikin nasa." Ta ce "Da sauqi." Mama ta ce "Is he sleeping?" Neehal ta ce "A'a, idonsa biyu yana ma zaune." Mama ta ce "Okay, bashi wayar." Neehal ta miƙa masa ba tare da ta yi magana ba, ya karb'a tare da kara wayar a kunnensa, ko da ba'a faɗa masa ba ya san Mama ce. Gaisawa suka yi, Mama ya masa ya jiki? Sannan ya bawa Neehal wayar. Ameen ya dubi Hafsah wadda ke kallonsa ya ce "Ina kika ajiye mun my phone's? Mum said ta kira ni ban yi picking ba." Hafsah ta ce ,"Suna Bedroom dina, bari na ɗauko maka." Sai kuma ta marairaice fuska ta dafa kafaɗunsa tare da faɗin "Babyna duk ka rame, ciwon nan yana wahalar mun da kai, nice mai cikin amma kai ne da laulayin." Neehal ta ɗan tab'e baki tare da fita daga ɗakin. Ameen bai cewa Hafsah komai ba, sai idanunsa da ya mayar ya lumshe. Neehal ta fito falo ta zauna ta ɗauko wayarta ta shiga latsawa, su Fadeelah kuwa sai hirarsu suke. Hafsah ta fito ta shiga bedroom ɗinta ta ɗauko wayoyin Ameen ta kai masa, sannan ta fito ta zauna kusa da k'awayenta ba ta ko kalli inda Neehal take ba. Fadeelah ce ma take ɗan sako ta a cikin hirar tasu, ita kuma sai dai ta yi murmushi kawai. Ganin Magriba ta kusa ta miƙe ta dube su ta ce "Aunty Hafsah zan wuce Allah ya ƙara sauƙi." Bata jira amsarta ba ta mai da dubanta ga su Fadeelah tana murmushi ta ce "Sai anjimanku." Fadeelah ta ce "Har zaki tafi Neehal? To ki gai da gida da Mama." Neehal ta ce "Mama zata ji." Sannan ta juya ta fice daga falon. Hafsah ta bita da harara tare da jan dogon tsaki bayan ta fita. Fadeelah ta kalle ta ba ta ce komai ba, a ranta tana mamakin wannan hali na ƙawartata. Neehal tana koma wa gida Mama ta kalle ta, ta ce "Kuka kika yi ko Neehal?" Neehal ta yi shiru, Mama ta ce "Allah ya shirye ki, ya jikin nasa?" Kamar zata kuma wani kukan ta ce "Da sauqi, amma Mama daga gani Yaya yana jin jiki sosai, duk ya rame." Mama ta ce "Ki masa addu'a, ba kuka ba." Ganin idanunta har sun fara ƙyallin k'walla. Da daddare Sadik ya zo suka sha zancensu, sun daɗe suna hira wanda kusan gaba-ɗaya hirar a kan bikin Haneefah suka yi ta. Lokacin da Sadik ya koma gida kamar kodayaushe idan mahaifinsu yana gari, iyayensa duka suna zaune a main Parlour, sai dai yau babu k'annensa. Ya shigo da sallama kan sa a ƙasa, suka amsa masa baki ɗaya. Umma ta ce "Um su Sadik yanzu kullum sai an je zancen ne?" Ran Maamah ya ɓaci amma ba ta ce komai ba. Abbansa ya ce "Idan ya je zance laifi ne?" Cikin kissarta da son ɓata Sadik ɗin a idon mahaifinsa ta ce "Ba laifi ba ne Abbansu, kawai dai na ga ya kamata a san inda yake zuwa zancen ne, domin a tabbatar da tarbiyyar yarinyar." Abba ya kalli Sadik dake tsugunne ya ce "A ina gidansu yarinyar da kake zuwa yake?" Cikin ladabi Sadik ya ce "A Nasarawa gidansu yake, sunan mahaifinta Alh. Muhammad Tafida." Abba ya maimaita sunan kamar mai son tuno wani abu "Alh. Muhammad TAFIDA? kamar na san sunan nan, amma dai zan bincika, dan kamar Yadda Ummanku ta faɗa ya kamata mu san inda kake zuwa ɗin, idan gidansu yarinyar gidan tarbiyya ne sai ka cigaba da zuwa, idan kuma akasin haka ne kasan sauran." Ya ƙarashe zancen yana kallon Sadik. Sadik ya gyaɗa masa kai zuciyarsa babu fargabar komai, dan yasan babu wani abu bad da za a samu a gurin Neehal ko iyayenta Insha Allahu. Washegari da safe sai ga Hajiya ta zo wai ta zo duba Ameen ne. Neehal tana bacci ta ji Maganar Hajiya a kanta. A hankali ta buɗe idanunta dake cike da bacci, cikin muryar bacci ta ce "Kai tsohuwar nan baza ki bar mutum ya yi ƙiba ba, daga zuwanki ina baccina mai daɗi kin katse mini." Hajiya ta ce "Wanne irin baccin asara ne wannan har tsakar rana? Yaushe Faɗiman ta lalace har ta barki kike irin wannan baccin? Haka zaki je gidan mijin kina sakin baki kina sharar bacci." Neehal ta tashi zaune tana ƴar miƙa tare da yin salati. Hajiya ta ce "Ni ki yi ki tashi ki shirya ki raka ni gidan Aminu yaron kirki irin albarka in dubo sa, duk da ma sai jiya Uwartasa ta faɗa mun rashin lafiyar tasa, ban da haka da tuni ban zo ba." Neehal ta kalli agogon dake bangon ɗakin ta ce "Taɓ, sai dai direban Mama ya kai ki, ni school zan tafi yanzu ina da exam 12." Bata bi takan mitar Hajiya ba ta tashi ta shige toilet. Tana fitowa ta ga wayarta dake kan gado tana haske, ta ɗauka ta ga Ameen ne yake kiranta. Ta d'aga da sallama a bakinta, Al'ameen ya amsa mata. Ta ce "Ina kwana Yaya, ya jikin naka?" Ya ce "Da sauqi, me yasa jiya kika taho baki mun sallama ba?" Ta ce "I thought ka yi bacci ne lokacin." Ya ce "Ko dai kina sauri ki tafi saboda saurayinki zai zo?" Neehal ta ce "Allah ba haka ba ne Yaya" ya ce "Amma ai yazo ɗin ko?" Neehal ta yi shiru tana murmushi ƙasa ƙasa, ya ce "Uhm, to me yasa yau baki kira ni kin ji lafiyata ba?" Sai ta ji abun wani iri, ita da tun yana gida ma basa wata waya balle yanzu da ya yi aure, ko yana nufin dan bashi da lafiya ne bata kira ta ji jikin nashi ba? ta ce "Yanzu na tashi daga barci ne am sorry" Ya ce "Alright, i will call you later" Daga haka ya kashe wayar. Ta bi wayar da kallo kamar zata gan shi a ciki, daga baya kuma ta ajiye ta cigaba da sabgarta. Hajiya tana duban Mama bayan ta gama rattabo mata yanda suka yi da Neehal ta ce "Wai niko Faɗima har yanzu yaran nan shiru babu labarin wani nasu?" Mama ta ce "Babu Hajiya har yanzu, tun muna zuba idon ganin kira har mun gaji." Hajiya ta ce "Ikon Allah, to ko dai ba ƴan ƙasar nan ba ne?" Mama ta ce "Waya sani ne, sai Allah." Hajiya ta ce "Allah ya kyauta, suna inane ma ban gansu ba." Mama ta ce "Suna makaranta, sai yamma suke dawowa." Hajiya ta ce "Allah sarki Janar, Allah ya saka masa da Alkhairi, shi da ba ya gajiya da aikin Allah" Har Neehal ta shirya ta fito Hajiya bata tafi gidan Ameen, Mama ta tsayar da ita, ta ce idan ta gama girki sai ta raka ta da kanta. Tana falon ƙasa tana kallo, da Neehal zata wuce ta ce "Au baki tafi gidan Yayan ba?" Hajiya ta ce "Ban sani ba, tunda baza ki raka ni ba meye naki na tambayata na je ko ban je ba?" Neehal ta ce "Allah ya baki haquri, amma dai zaki zaunar mana har bikin Besty ko?" Hajiya ta ce "Gobe goben nan zan koma inda na fito, dubiya ce ta kawo ni dama." Neehal ta ce "Kai Hajiyarmu ki zauna ki yi babbar Sallah a nan." Hajiya ta ce "Um'um, in zauna ku ce na cinye muku nama, gidana zan tafi in yi sallah ta a can." Neehal ta ce "Tom Shikenan, Ni na wuce school." Hajiya ta ce "Allah ya tsare." Washegari kuwa kamar yadda Hajiya ta faɗa ta koma Gombe, ko gidansu Aunty Sadiya ba ta je ba sai su suka zo gidan Maman suka gan ta. Babbar Sallah saura kwana Biyar aka kawo lefen Haneefah, Masha Allah kaya sun yi kyau, Faruq ya yi ƙoƙari sosai, kaya masu tsada ya zuba mata, akwati goma ya mata cike taf da kaya. Ranar Haneefah ta sha tsokana gurin Neehal, tun tana biye mata tana ramawa har jikinta ya fara yin sanyi ta yi shiru. Ana i gobe Sallah mai ƙunshi ta zo har gida ta yiwa Mama da su Afrah, Neehal dai ba ta yi ba saboda kar ya ƙi fita kafin bikin Haneefah. An yi bukukuwan Sallah lafiya an gama Lafiya, Neehal kam babu inda ta je saboda aikin nama, gashi hutun school kwana uku ne kacal, dan ran huɗu ga Sallah ma tana da exam. Kuma ta so wannan Sallar ta zazzaga danginta, duk da basa nemanta amma ita baza ta biye ta su ba, kamar yadda Mama take faɗa mata a kodayaushe, Ta yi zumuncinta dan Allah ba dan su ba, shi zumunci dole ne. Ranar Asabar ɗin data kama saura kwana huɗu a fara bikin Haneefah su Neehal suka gama exam, hakan yasa ta kama hidimar bikin ƙawarta gadan_gadan. Ranar Thursday akai bridal shower, Amarya ta yi kyau sosai ita da k'awayenta, an yanka Cake an cashe. Ranar Friday kuma Kamu, shima Ranar Amarya ta yi kyau har tafi jiya ma. Su Neehal ƙirjin biki an cashe sosai, dan ma Sadik yana hana ta rawar gaban hantsi duk inda ta yi yana biye da ita, wai dan kar wani ya kula ta. Ranar Asabar kuma akai Mother's Day da yamma, da daddare kuma akai Dinner. Tunda aka fara bikin Ameen bai je ba sai ranar Dinner suka je shi da Hafsah. Aiko ranar Neehal ta ga takura, dan hana ta sakat ya yi. Tana shiga filin rawa zata hango idanunsa yana banka mata harara, ga shi ita ma kamar an mata asiri sai tay ta kallon inda yake. Ƙarshe ma tashi yay ya ja hannunta ya fara mata masifar wai tana ganin Maza a gurin amma sai Safa da Marwa take, gashi kayan jikinta sun kama ta. Allah ya taimake ta ranar Sadik bai zo ba, da bata san a gurin wa zata fi shan takura ba tsakanin shi da Ameen. Hafsah kuwa bata ma san me ake yi ba, tana can tana bawa idanta abinci, da Ameen ya tashi ma ta ɗauka waya ya tafi yi. Wata cousin ɗin su Haneefah ta cewa Neehal "Kai amma guy ɗin nan naki ya haɗu, kuma daga gani yana sonki sosai, gashi kun dace." Neehal ta yi murmushi tace mata "Yayana ne fa, kin ga matarsa can a gefensa." Yarinyar ta jinjina kai kawai, amma ita ta hango tsantsar kishin Neehal a tattare da Ameen. Washegari Ranar Lahadi da misalin ƙarfe Sha ɗaya na rana aka ɗaura Auran Haneefah da Angonta Umar Faruq. Tun lokacin ta fara kuka saboda tsokanarta da abokan wasa suka fara yi, jikinta ya yi sanyi duk rawar kan nan babu. Neehal ta ce "Ashe zan ga ranar da bakin tsiwar nan zai mutu." Duk da itama jikinta ya yi sanyi dauriya kawai take. Ranar kiɗan ƙwarya aka sha a cikin gida. Kafin Magriba ƴan ɗaukar Amarya sun zo, a lokacin kukan Haneefah ya tsananta kamar zata shid'e, Neehal ma tuni ta fara kuka. Mommy ma duk yadda taso daurewa amma sai da ta yi Hawaye da za'a fita da ƴartata tilo ɗaya a duniya. Sadik ne ya kai su Neehal gidan Amarya ita da wasu k'awayen Haneefah guda biyu, sai Ameerah ƴar Uncle Mahmud da ta zo bikin itama. A lokacin Neehal ta yi ƙoƙari ta daina kukan, amma kana ganinta ka san tana cikin bad mood, Suna Mota Sadik yana mata magana ma bata responding, ta kwantar da kanta a jikin kujera idanunta a lumshe. Sai da su Afrah dake kan cinyarta yake hirar. Sune na ƙarshen barin gidan Amarya, a haka ma da dabara suka fito saboda Haneefah riƙe Neehal ta yi wai ba za su tafi ba. Gidan Amarya ya yi kyau Masha Allah, Mommy da dangin Abban Haneefah sun mata kaya na ƴaƴan gata, komai ya ji Masha Allah. Sai fatan Allah yasa gidan zamanta ne na har abada, ya kuma ba su zaman lafiya ya kau da fitina a tsakaninsu. Da wani irin ciwon kai Neehal ta dawo gida, sallah kawai ta yi ta bi lafiyar gado, ba jimawa bacci ya ɗauke ta saboda tarin gajiyar dake addabar jikinta. Yau Laraba misalin ƙarfe huɗu da mintuna Neehal ce zaune akan darduma, ta idar da sallar la'asar. Tunanin besty'nta da ta yi kewarta take yi, tana tuna yanda suke yin komai tare, idan ɗaya zata unguwa sai ta kira ɗaya ta raka ta, idan yau wannan bata zo ba gobe sai wannan sai ta zo, su je gurin aiki tare su dawo tare. Yanzu gashi aure ya raba su, tunda Haneefah baza su wuce 1 month a Kano ba, zasu koma Kogi state, a can mijin nata yake aiki. Wayarta ce ta shiga ruri ta kai hannu ta ɗauka, murmushi ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta. Bayan ta yi picked ta ce "Ƴar halak, tunaninki nake a raina sai gashi kin kira ni." Haneefah ta ce "Ba wani nan, ba cin ma kin manta da ni, ko kirana akai_akai bakya yi." Neehal ta ce "So kike Yaya Faruq ya fara jin haushina kenan, yana tsaka da cin amarcinsa ni kuma ina damunsa da kira." Haneefah ta ce "Na ji, yaushe zaki zo?" Neehal ta ce "Ran Friday Insha Allahu." Haneefah ta ce "Allah ya kai mu, ina Mamana da twins?" Neehal ta ce "Duk suna nan lafiya k'alau." Haneefah ta ce "My regard to them." Neehal ta ce "Za su ji insha Allah." Sun ɗan taɓa hira sannan suka yi sallama. Neehal ta miƙe ganin biyar ta kusa ta ɗauki car key ɗinta ta fita dan ɗauko su Afrah, Mama bata nan tana gurin aiki. A bakin gate ɗin makarantar ta yi parking motar, sai da ta duba agogon hannunta sannan ta fito ta shiga cikin school ɗin. Tana shiga ana kaɗa musu beil, yara suka fara fitowa daga classes ɗinsu da gudu. A bakin class ɗin su Afrah ta hango su, ta ƙarasa ta kama hannuwansu. Suka juyo suka kalle ta, Afrah ta ce "Aunty yau ke kika zo ɗaukar mu?" Neehal tana karɓar lunch box ɗinsu ta ce "Gashi ko kin gani." A hankali suke tafiya har suka fito daga school ɗin, ta nufi inda ta yi parking Motarta. Wani matashi dake waya a gefe ɗaya ya ƙurawa su Afrah ido cikin tsananin mamaki. Katse wayar ya yi bayan ya cewa wanda suke wayar yana zuwa, ya nufo inda Neehal take. Neehal ta buɗe bayan Motar ta ajiye lunch box ɗin sannan ta shigar da su Afrah cikin Motar. Tana rufe musu murfin Motar matashin ya ƙaraso, kawai sai ganin mutum ta yi a gabanta. Ta ɗan ja baya ta ce "Malam lafiya?" Matashin ya mayar da dubansa ga su Afrah dake cikin Mota ta glass ya ce "Dan Allah ina kika samo waɗannan yaran?" Gaban Neehal ya faɗi amma ta dake ta ce "Kamarya? Wannan wacce irin tambaya ce." Matashin ya ce "Na san su ne shi yasa na tambaye ki." Neehal ta ɓata rai sosai ta ce "To ba su ka sani ba gaskiya, watakila ɓatan kai ka yi." Bata jira amsar sa ba ta juya ta buɗe gaban Motarta ta shige, ta bar shi nan tsaye. Matashin ya matso da nufin ƙara yi mata magana, amma ganin ta yi reverse yasa shi yin baya da sauri, sai kuma ya nufi titi da gudu ya tsayar da na mai napep ya shiga, cikin sauri ya ce "Dan Allah malam waccen Motar zaka bi mun bayanta duk inda ta yi, zan biya ka ko nawa ne." Mai napep ɗin ya ja suka tafi da sauri dan kar motar Neehal ta ɓace musu. Suna shiga layin su Neehal ita kuma ana buɗe mata gate ta shige cikin gidan. Matashin ya cewa mai napep ɗin ya tsaya, ya sauko tare da Sallamar mai napep ɗin. Sannan ya nufi gidan da ya ga ta shiga. Sai da ya fara Ƙarewa gidan kallo sannan ya nufi gate ɗin gidanya fara knocking, mintuna biyu ya ga wani soja ya buɗe ƙaramar ƙofar gidan. Ya dubi sojan dake masa kallon tara saura k'wata ya ce "Barka da yamma yallaɓai, dan Allah idan babu damuwa ka mun magana da mai_gidan nan." Sojan ya bishi da kallo daga sama har ƙasa sannan ya ce "Baya nan." Matashin ya ja numfashi ya ce "Matar gidan fa? Dan Allah ka mun magana da ita to." Sojan ya ja tsaki ya ce "Malam kafin na yi counting ten ka bar gurin nan, ko kuma yanzu jikinka ya faɗa maka." Matashin ya ce "Please I have important t...." Sojan yana jijjiga kai ya ce "Baka ji ba kenan? To ka cigaba da tsayawa." Ya juya ya rufo ƙofar da ƙarfi. Dafe kansa matashin ya yi sannan ya juya ya fara tafiya, yana tafe yana waigen gidan, a ransa yana faɗin daga ganin wannan tamfatsetsen gidan mai gidan ba ƙaramin mutum ba ne. Sai da ya bar layin sannan ya ɗauko wayarsa ya shiga kiran wata Number...... Yana kwance rigingine akan makeken gadonsa, dawowarsa kenan daga office. Idanunsa a lumshe yana jin yanda zuciyarsa take bugawa a hankali, duk bugun da zata yi tana bugawa da tunanin kids ɗinsa a ransa. A kullum kewarsu na ƙara cika zuciyarsa, duniyar gaba-ɗaya ta yi masa zafi, yana jin gidan da yake ciki ya yi masa girma saboda rashin kids ɗinsa. Da suna nan da tuni yanzu suna jikinsa suna basa labarin abun da ya faru a school ɗinsu. Ya taune lips ɗinsa cikin k'unar zuci. "I missed you alot my kids." Ya furta hakan a fili cikin sassanyar muryarsa mai nuni da damuwar da zuciyarsa take ciki. Ɗaya daga cikin wayoyinsa da ya ajiye akan mudubi ce ta fara ruri, yana ji amma bai ko motsa ba da niyyar ɗauka har ta katse, wani kiran ya ƙara shigowa. Tashi zaune ya yi yana sauke numfashi sannan ya sauko daga kan gadon ya je ya ɗauki wayar. Musbahu! Sunan da ya gani yana yawo akan screen ɗin wayar kenan, ya yi picking tare da kara wayar a kunnensa. Daga ɗaya ɓangaren ba tare da gaisuwa ba Musbahu ya ce "Doctor! Na ga su Afrah yanzu." "What?" Ya faɗa cikin dokawar zuciya. Musbahu ya ƙara maimaita masa abun da ya faɗa, duk da ya san ya ji. "Musbahu! A ina ka gan su?" Ya tambaya cikin sark'ewar harshe. "A Kano." Shima Musbahun ya bashi amsa cikin hanzari. Ya ce "Kano kuma? A Kano a ina?" Musbahu ya bashi labarin duk abun da ya faru na ganin su Afrah tare da Neehal da bin bayanta da ya yi zuwa gida. Ahmad ya zauna dab'as a bakin gado ya ce "Soldier kuma? Kuma ya hana ka shiga gidan? Kuma ta tabbatar su Afrah ka gani?" Musbahu ya ce "Wallahi Doctor sune, ai na san su sosai, tunda kana zuwa da su gida gurin Yaya." (Musbahu k'anin wani Freind ɗin Ahmad ne mai suna Sagir.) Ahmad ya ce "Shikenan, gobe ƙarfe goma na safe Insha Allahu ina cikin garin Kano, idan na shigo zan kira ka." Musbahu ya ce "Shikenan Doctor sai ka zo, Allah yasa a dace." Ahmad ya ce "Ameen." Dafe kansa ya yi yana jin kamar mafarki yake, zuciyarsa ta kasa yarda da abun da Musbahu ya sanar masa, duk da idan hakan ya kasance bai san wanne irin farin ciki zai yi ba, his kids sun kusa dawowa gare sa kenan? Addu'ar da ake ba dare ba rana ita ce Allah ya amsa yau ya bayyana masa inda yaransa suke. 'Ya Allah! Ka tabbatar da abun da Musbahu ya faɗa.' ya faɗi hakan a ransa yana jin kamar ya zuk'o gobe ta yi........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:55] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *3️⃣9️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ............A ɓangaren Neehal kuwa bayan sun koma gida tana cire musu kaya Amrah ta ce "Aunty yaushe zamu gurin Daddy?" Neehal ta sauke numfashi har yanzu gabanta bai far faɗuwa ba ta ce "I don't know." Afrah ta ɓata fuska ta ce "Aunty We Missed him alot, please ki kai mu gurinsa." Ta yi shiru ba ta ce musu komai ba. Har ta gama cire musu kayan ta saka musu wasu zancen Daddy'nsu suke, suna ta lissafin abubuwan da yake siyo musu da abubuwan da yake musu, har wak'ar da yake musu idan za su yi bacci sai da suka bawa Neehal labari, ita dai kawai jin su take, amma zuciyarta cike take da fargabar da bata san ko ta mecece ba. Da Mama ta dawo bata faɗa mata gamuwarta da matashin nan ba, ta san idan ta sanar mata faɗa zata mata sosai akan rashin saurararsa da bata tsaya ta yi ba. Washegari da safe ta shirya su Afrah suka tafi school, ita kuma bayan ta gama breakfast ta koma ɗaki ta kwanta....... Ƙarfe goma da mintuna na safe Doctor Ahmad ya sauka a garin Kano, garin da ya yi shekaru masu yawa rabon sa da shi, sai yau sanadiyyar kids ɗinsa Allah ya kawo shi. Babu wanda ya faɗawa abun da zai je yi Kano, daga shi sai Musbahu ne suka sani, saboda ya fi so ya musu surprise, kuma ma baya so sai ya gama faɗar anga twins a Kano kawai ya zo ya ga ba su ba ne, duk da baya fatan haka. Yana sauka ya kira Musbahu ya sanar masa ya sauka yana airport ya zo ya ɗauke sa. Mintuna ƙalilan Musbahu ya je airport ɗin, saboda dama a shirye yake, kuma daga inda yake babu nisa zuwa airport ɗin. Bayan sun gaisa Ahmad ya shiga cikin motar da musbahu ya zo a ciki suka nufo gidansu Neehal. Suna tafe Ahmad yana tambayar Musbahu ƙarin haske akan ganin su Afrah da ya yi, har da nuna masa hoton su Afrah wai ya tabbatar su ɗin kuwa ya gani? Abun da ɗaure wa Ahmad kai da Musbahu ya ce masa cikin uniform ya ga su Afran, ɗaukar su ma aka zo yi daga school. Kenan waɗanda suka tsince su ne suka saka su a makaranta? Ko kuma dai ba su Afrah ɗin Musbahu ya gani ba wasu masu kama da su ne? Tunda gashi ya ce ya yiwa wacce ta zo ɗaukar tasu magana ta ce ba waɗanda ya sani ba ne. Tambayoyi dai barkatai Ahmad yake ta yiwa kansa wanda ba shi da amsoshin su, a gefe guda kuma yana jin wani irin sauyi a cikin zuciyarsa, a haka har suka ƙarasa gidansu Neehal. Horn Musbahu ya yi a bakin makeken gate ɗin gidan, Ahmad ya ƙurawa gidan ido cikin fad'uwar gaba. Ƙaramar ƙofar gidan wani dogon soja ya buɗe yana kallon Motar tasu, a hankali Ahmad ya bude murfin Motar ya fito Musbahu ma ya biyo bayansa. Ahmad yana zuwa ya miƙawa sojan hannu cikin kamilalliyar muryarsa ya ce "Good Morning." Musbahu ya saki ajiyar zuciya ganin ba sojan jiya ba ne, wanine daban. Sojan ya ce "Morning." yana bin Ahmad da kallo." Ahmad ya ce "Masu gidan suna nan?" Sojan ya ce "Mai gidan dai baya nan, amma matar gidan tana nan." Ahmad ya ce "Idan babu damuwa a yi mana iso a gurinta." Sojan ya ce "Wa za'a ce mata?" Ahmad ya ce "Baƙi ne daga Abuja." Sojan ya yi shiru yana ƙarewa su Ahmad kallo, sannan ya juya ya koma cikin gidan ba tare da ya yi magana ba. Musbahu ya ce "Hmm, Daga ganin gidan nan na wani babban Sojan ne." Ahmad ya sauke numfashi bai ce komai ba, yadda yake jin zuciyarsa kamar ya bi ta cikin gini ya shiga gidan saboda zak'uwa...... Mama tana falon ƙasa tana operating system Dije ta ƙaraso inda take bayan ta buɗe ƙofa, cikin ladabi ta ce "Hajiya wai kin yi baƙi daga Abuja." Mama ta d'ago cikin mamaki ta ce "Baƙi kuma? Maza ko mata?" Dije ta ce "Ina tunanin dai Maza ne." Mama ta ce "Kuma suka ce ni suke nema?" Dije ta ce "Haka sojan ya ce mun." Mama ta ce "Okay ki ce a kaisu Guest part, ganin nan zuwa." Dije ta amsa mata tare da komawa bakin ƙofa ta sanar da Sojan. Su Ahmad suna tsaye fiye da mintuna goma sannan Sojan ya dawo ya ce su shigo. Wata irin ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke ya zura ƙafarsa cikin gidan da Bismillah, tare da fatan dacewa. Suna tafe Musbahu yana bin gidan da kallo, a zuciyarsa yana mamakin girma irin na gidan da kuma tsaruwarsa. Ahmad kuwa hankalinsa ba ya kan wannan, shi dai burinsa ya gana da masu gidan su tattauna akan kids ɗinsa. Ba su fi 5 minutes da zama ba Mama ta ƙaraso falon fuskarta ɗauke da fara'a tana musu sannu da zuwa. Ta zauna akan kujerar dake fuskantar wadda suke a zaune. Cikin ladabi Ahmad ya gaishe ta, musbahu ma haka. Ta amsa tare da faɗin "Sai dai ban waye ku ba ƴan samari?" Ahmad ya kalli Musbahu amma bai ce komai ba saboda yanda ya ji bugun zuciyarsa na ƙaruwa. Ganin haka Musbahu ya ɗan muskuta ya ce "Daga Abuja muke ." Ya ɗan yi shiru sannan ya cigaba da magana yana nuna Ahmad. "Wannan Abokin yayana ne, watanni kusan biyar da suka wuce aka zo har gida aka ɗauke masa yaransa, anyi cikiyar anyi cikiyar amma babu labarinsu babu labarin wanda ya ce ya gan su, to ana tunanin kidnappers ne suka sace su sai akai ta tsammanin kiransu, amma har kawo yau babu wanda ya kira game da yaran. To shekaran jiya na shigo Kano gurin wani abokin kasuwancina zan karb'i kaya a hannunsa, jiya kuma kamar a mafarki sai na ga yaran wata budurwa ta zo ɗaukar su daga makaranta da yamma." Nan ya bawa Mama labarin yanda suka yi da Neehal da biyo ta da ya yi wani soja ya kore shi. Ya ƙara da faɗin "Shine ban yi ƙasa a gwiwa ba na kira mahaifin Yaran na sanar masa, shine ya zo Kanon yau domin mu zo nan gidan mu bincika ko sune." Tun da ya fara magana Mama take kallon Ahmad cikin tsananin shock, wata zallar kama take hango wa a fuskarsa da yaransa, wadda ita kaɗai ma ta tabbatar mata da shi ɗin mahaifinsu su Afrah ne kamar yadda Musbahu ya faɗa. Amma abin da ya bata mamaki, a ce suna nan_nan Abuja duk cikiyar su Afrah da akai ba su gani ba. Ganin yanda Mama ta yi shiru sai jikin Ahmad ya fara yin sanyi, a ransa yana faɗin "Ko dai ba su Afrah Musbahu ya gani ba, wasu yaran ne daban. Mama ta sauke numfashi ta ce "Mu ga hoton yaran nasa." Da sauri Musbahu ya zaro wayarsa a aljihu ya shiga gallery ya lalubo pictures ɗin su Afrah wanda yay ta yawo a media lokacin da aka neme su aka rasa ya tashi ya kaiwa Mama. Mama ta ƙurawa hoton ido a ranta tana faɗin "Alhamdulillah." Yalwataccen murmushi ta saki ta dubi Musbahu ta ce "Tabbas su ka gani jiya, kuma yarinyar da ka gani ta je ɗauko su ita ta tsinto su, kusan wata biyar da suka wuce." Ahmad ya waro ido tare da sakin ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske, lumshe kyawawan idanunsa ya yi a fili ya ce "Alhamdulillah³" sai kuma ya zamo daga kan kujerar da yake kai ya yi sujjada a ƙasa. Musbahu cikin murmushin farinciki shi ma ya ce "Alhamdulillah, Masha Allah, yau Allah ya bayyana mana inda su Afrah suke." Mama ta dubi Ahmad cike da tausayawa wanda farinciki ya kusa kashe shi, wasu sanyayan hawaye ne suka zirnano daga idanunsa, jinsa yake kamar ba shi ba, kamar mafarki yake zai farka ya ga ba haka ba. A hankali ya d'ago daga sujjadar da ya yi ya dubi Mama zai yi magana amma sai ya kasa, ya ma rasa me zai ce mata saboda tsananin farin ciki. Mama ta ce "Masha Allah, nima na yi farin ciki sosai da bayyanar ku, dan kullum da fatan hakan muke kwana muke tashi, kusan kullum sai yaran sun yi zancen Daddy'nsu suna tambayar yaushe za a kai su gurinsa." Mama ta ƙarashe zancen tare da latsa wayarta dake kan cinyarta, Numbern Daddy ta kira, bayan ya d'aga ta sanar masa abun da yake faruwa, shi ma ya yi farin ciki sosai ya ce gashi nan zuwa gidan yanzu_yanzu. Mama ta dubi Ahmad ta ce "Yaran suna School yanzu, amma bari nasa a ɗauko su, dan nasan yanda kuke zumud'in ganin su baza ku iya jiran 1 hour baku gansu ba. Ahmad ya yi murmushi mai bayyana tsantsar farin cikinsa, a ransa yana girmamawa karamci irin na waɗan nan bayin Allah, daga tsintar yara har sun saka su a school. Musbahu ya yi ƙoƙarin kiran gida ya sanar musu, amma Ahmad ya hana shi, dan yasan tsaf zai iya ganin ƴan'gidansu a Kano sun taho ganin su Afrah. Mama ta kira direbanta ta faɗa masa ya je ya ɗauko su Afrah a school, zata kira shugabar makarantar ta mata bayani kafin ya ƙarasa. Kafin direba ya dawo Mama ta bawa su Ahmad labarin yanda Neehal ta tsinci su Afrah. Musbahu ya jinjina kai cike da Al'ajabin abun ya ce "Amma al'amarin nan akwai ɗaure kai, sato su akayi kenan Allah ya kub'utar da su ko kuma yaya sai Allah." Nan dai sukaita jimanta abun, Ahmad ya bawa Mama labarin yanda suka nemi su Afrah suka rasa lokaci ɗaya. Suna haka direba ya shigo da su Afrah, Yaran da basu lura da mutanen dake falon ba suka nufi gurin Mama, Afrah ta ce "Mama ba'a tashi daga school ba fa aka ɗauko mu." Ahmad wanda ya ƙura musu ido cikin tsananin murnar ganinsu kamar a cikin mafarkin da ya saba yi da su, ya ce "Princess!, Jewel!" A tare yaran suka juya suka kalle shi da alamun shock a tattare da su. "Daddy,!" Suka haɗa baki gurin faɗa tare da nufar inda yake da gudu suna dariyar farinciki. Ahmad ya rungume su a ƙirjinsa yana sakin ajiyar zuciya, bai san da wacce rana zai kwatanta wannan ranar ta farinciki ba a rayuwarsa. Babu irin neman da bai musu ba, ya sha wahala ya sha jinyar rashinsu kamar ba zai rayu ba, sai da ya fitar da rai da ganin su ya sakawa ransa dangana da haqurin rashin su sannan Ubangiji ya bayyana masa su cikin aminci, bai taɓa zaton ko da zai ga yaransa zai gan su cikin kwanciyar hankali haka ba. Ya ƙara rungume su a ƙirjinsa kamar zai mai da su ciki hawayen farinciki na bin fuskarsa. Su kuwa su Afrah sai dariyar murnar ganinsa suke, suka shiga jero masa tambayoyi. "Daddy wa ya faɗa maka muna nan gidan? Ina Ummi da Aunty Zahra da Ammi da Uncle Yaseer? Suma za su zo nan gidan mu gan su? Har da Baaba Talatu? Daddy zaka tafi da mu gida ko?" Mama sai kallon su take cike da tausayawa, haka ma Musbahu da bakinsa ya kasa rufuwa dan murna. Ahmad ya manta da kowa da yake gurin yaransa kawai yake biyewa suna hirarsu, wani irin wasai yake jin zuciyarsa ta masa, gaba-ɗaya damuwar dake cikinta ta gushe sai wani sanyi ne yake ratsata. Su Afrah sai labarin new Aunty'nsu (Neehal) suke bashi da kuma school ɗin da suke zuwa. Tun kafin ya ga Antin tasu ya ji yana k'aunarta saboda kulawar da ta yi da sanyin idaniyarsa, ya fara tunanin mai zai mata a duniyar nan wanda zai faranta mata a matsayin tukuici. Lokaci ɗaya ya koma ainihin Ahmad ɗinsa mai yawan fara'a da saurin sabo da mutane. Kasa daurewa ya yi ya kira Mahaifiyarsa ya sanar mata wannan abun farinciki. Farincikin data tsinci kanta a ciki ba zai misaltu ba, ta cewa Ahmad kar ya taho Abuja ya jira komai dare za su zo Kano su yiwa gidan da suka riƙi su Afrah godiya. Suna gama wayar kuma ta shiga kiran ƴan'uwa da abokan arziki tana sanar musu anga su Afrah. Hajiya Neehal tana kwance tana chatting da Habibinta bata san mai yake faruwa a gidan nasu ba. Shigowar Mama yasa ta tashi zaune. Mama ta ce "Har yanzu bacci kike ne?" Ta ce "A'a idona biyu, yanzu ma so nake na tashi na je saloon a wanke mun kai na." Mama ta ce "Jiya da kika je ɗauko su Afrah ashe kin gamu da wani yace miki ya san su?" Gabanta ya faɗi ta dubi Mama da sauri ta ce "Eh, amma wa ya faɗa miki?" Mama ta ce "Da kansa ya zo ya faɗa mun, yanzu haka ma suna part ɗin baƙi shi da Mahaifin su Afran." Neehal ta waro Idanunta sosai ta ce "Ta yaya suka san suna gidan nan to? Mama anya kuwa dagaske mahaifin nasu ne? Kar fa wasu su zo su miki ƙarya." Mama ba ta ce komai ba ta girgiza kai kawai ta juya ta fice. Neehal ta sauko daga kan gadon da sauri ta biyo bayan Mama ƙirjinta na dokawa. A falo ta ci karo da Amrah sanye cikin uniform, cikin murna Amrah ta kama hannunta ta ce "Aunty Daddy ya zo, ki zo mu je ki gan shi ya ce mu kirawo ki, ashe dama ya san gidan nan?" Neehal ta shafa fuskar yarinyar ta ce "Dagaske Daddy'nku ya zo? Yana ina?" Amrah ta ce "Yana wani falo, mu je ki gan sa." Neehal ta tsaya cak cikin tsananin shock, zuciyarta cike da murnar bayyanar iyayensu. Ta kama hannun Amrah tana murmushi suka koma ɗakinta ta ɗauko Hijab ta zira, sannan ta ƙara kamo hannunta suka fito. A kitchen ta tarar da Mama da su Dije suna ƙoƙarin haɗa girki dan tarb'ar baƙi, dan Ahmad ya sanar mata su Umminsu suna nan tafe. Haka Kawai Neehal ta tsinci kanta cikin farinciki, duk da ta san lokacin rabuwa da twins ɗinta ya yi za su koma gurin iyayensu, tunda Allah ya bayyana su. Sai dai kuma suna zuwa part ɗin baƙin ta ji gabanta ya faɗi, ta ɗan tsaya a bakin ƙofar falon tana jin jikinta wani iri. Amrah ta ce "Aunty Daddy'n yana cikin falon nan mu je ki gan shi." Neehal ta ce "Toh." Cikin sauke numfashi, sannan ta ƙarasa ta tura ƙofar falon a hankali ta shiga bakinta ɗauke da sallama cikin zazzak'ar muryarta. Ahmad wanda yake ta murmushi yana sauraren hirar da Afrah take masa ya d'ago ya dubi ƙofar falon, karaf idanunsa suka sauka akan Neehal wadda kanta ke ƙasa, hannunta riƙe da na Amrah........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:55] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *4️⃣0️⃣* ...........Samun kansa ya yi da kafe ta da ido kamar mai san gano wani abu a tattare da ita. Afrah ta sauka daga jikinsa ta tafi gurin Neehal da gudu cikin murna tana faɗin "Aunty! Daddy'nmu ya zo, kin gan shi." Ta ƙarashe maganar tare da kamo hannunta tana nuna mata Ahmad. Neehal ta d'ago kanta tana murmushi ta shafa kan Afrah ta ce "Thank God." Ai Ahmad ji ya yi gaba-ɗaya yawun bakinsa ya ƙafe ƙaf tare da wani irin bugawa da zuciyarsa ta yi. Ƙara ware idanunsa ya yi a kanta dan tabbatar da abun da yake gani kar ya je ko idon ne yake masa gizo, har abada ba zai taɓa manta wannan kyakkyawar fuskar ba. Neehal ta ɗan saci kallonsa a hankali cikin sanyin muryarta ta ce "Ina yini." Ahmad ya sauke wani dogon numfashi yana murmushi ya ce "Lafiya k'alau Aunty." Neehal bata kuma ce masa komai ba saboda tsintar kanta da ta yi uncomfortable tun shigowar ta falon, ta mayar da kallonta ga Musbahu wanda yake ta aikin latsa waya, posting ɗin hotunan su Afrah yake a social media tare da yin note ɗin bayyanarsu. Gaishe sa ta yi, ya d'ago ya dube ta tare amsa mata cikin fara'a, ita kuwa duk sai ta ji kunya ta kama ta saboda abun da ta masa jiya dan ta shaida sa. A hankali ta ƙarasa kan kujera ta zauna, su Afrah na jikinta suna mata hirar Daddy'nsu, duk da gashi nan a zaune a gabanta ya zuba mata na mujiya, ko kifta idanunsa ba ya yi. Amrah ta koma jikinsa tana masa surutu, amma ba ya ma saurarar abun take cewa, zuciyarsa gaba_ɗaya tana gurin Neehal. Ita kuwa Neehal tun tana daurewa tana biyewa Afrah har ta yi mata shiru tare da turo bakinta gaba, duk d'agowar da zata yi sai sun haɗa ido da shi, gashi idanun nasa sun sa ta fara jin wani iri ajikinta, gaba-ɗaya ya dabaibaye ta da kallonsa. Gajiya ta yi da kallon nasa ta miƙe ta fice daga falon a ranta tana faɗin "Wannan kuwa lafiyarsa k'alau? Ko dai ganin yaransa ne ya zautar da shi?" Ahmad ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da lumshe idonsa bayan ta fice. *Fateemah,Neehal,Princess.* Ita ce ko mai kama da ita? Dagaske ita ya gani ko kuma dai mafarki yake? Idan ita ce wacce irin *lucky day* ce wannan a rayuwarsa? "Oh my God!" Ya faɗa cikin siririyar murya, at the first da ya ganta ji ya yi kamar ya je ya rungume ta, ba ƙaramin control ɗin zuciyarsa ya yi ba wajen ganin bai aikata hakan ba, sai dai duk yadda ya so ɗauke idonsa daga kanta kasawa ya yi, wani maganaɗisun abu ya ji yana fizgar zuciyarsa a game ita, wadda bai taɓa jin irinsa akan wani mahaluƙi ba. Neehal ta koma part ɗin Mama tana ɓaɓɓata fuska, a ranta tana ta gulmar Ahmad. Sosai ta ga kamminsa da yaransa kamar ma ya fi su kyau. Kitchen ta shiga suka cigaba da aiki tare da su Mama. Sai da su Ahmad suka tafi masallaci sannan su Afrah suka dawo part ɗin Mama, a lokacin ne kuma Daddy ya ƙaraso gidan. Bayan sun dawo daga masallaci Mama ta aika musu da drinks da ɗan abun tab'awa. Neehal tana cikin Sallah Afrah ta shigo ɗakinta tana faɗin "Aunty ki zo in ji Daddy'nmu." Ganin tana Sallah sai yarinyar ta fita. Ko da ta idar ƙin fita ta yi, ta ɗauko wayarta dan kiran Haneefah da Sadik ta sanar musu bayyanar iyayensu Amrah. Kafin la'asar Su ummi sun ƙaraso Kano zuciyoyinsu cike fal da farinciki, Ahmad da kansa ya je ya ɗauko su a Airport. Su uku suka zo, da Ummi da wata ƙanwarta Aunty Mardiyya sai Zahra ƙanwar Ahmad. Cikin fara'a da mutuntawa Mama ta karɓe su hannu bibbiyu. Aunty A'isha ma ta zo a lokacin, Aunty Sadiya ce dai ba ta zo ba tana gurin aiki. A part ɗin Mama aka sauke su, hakan yasa su Ahmad su ma suka dawo nan. Ummi ta rungume su Afrah a jikinta tana hawaye tare da godiya ga Ubangiji, murnarta guda biyu ce a wannan rana, ta farko bayyanar jikokin nata, na biyu kuma ta san yanzu farinciki da walwalar ɗanta za su dawo, kuma lafiyarsa zata samu Insha Allah. Su Afrah kam yau take Sallah a gurinsu, kowa sai rungumar su yake da murnar ganin su, suma daɗi suke ji ba kaɗan ba na ganin su cikin ahalinsu. Bayan an gama murnar, su Ummi sun yi sallar la'asar Mama ta gabatar musu da abinci. Ahmad kuwa duk wannan abun da ake rabin hankalinsa ne a gurin, rabi yana gurin Neehal, gashi ko wulgawarta bai ƙara gani ba, ya tura su Afrah ya kai sau biyar su kira ta amma Neehal ta ƙi fitowa, sai dai su dawo su ce masa bacci take. Bai taɓa tunanin akwai abun da zai iya ɗauke masa hankalin murnar ganin Ƴaƴansa ba, sai gashi tozalin da ya yi da Neehal ya raba masa hankali, wani irin farinciki yake ji a cikin ransa, burinsa kawai yanzu ya samu ya tattauna da ita dan ya tabbatar ita ɗin ce. Bayan su ummi sun gama cin abincin aka zauna zaman mai da zance. Ummi ta dubi Mama ta ce "Yanzu duk tsawon watannin nan yaran nan suna tare da ku a gidan nan? Tsintar su kuka yi ko yaya?" Mama ta bawa Ummi labarin yanda Neehal ta tsinci su Afrah, da yanda akai ta cikiyar neman iyayensu . Cikin al'ajabi Ummi ta ce "Ikon Allah, Ubangiji ne ya kub'utar da yaran nan daga hannun azzaluman da suka ɗauke su, domin kuwa duk wanda ya ɗauki yaran nan da wani mugun nufin ya ɗauke su sai kuma Allah bai bashi nasarar cimma abun da ya yi niyya ba akansu." Aunty A'isha ta ce "Fita suka yi waje aka ɗauke su ko kuma a makaranta ne?" Ummi ta ce "Ba ɗaya, har cikin gida har falonsu aka shigo aka ɗauke su. Ita mai kula da su ta shiga wanka a ɗaki, su kuma suna falo suna kallo, sai fitowa ta yi ta ga babu su a falon, ta shiga ƙwala musu kira tana zaga ko ina na gidan amma bata gan su ba, ta fito ta tambayi mai gadi a ruɗe ko ya ga fitarsu ko kuma shigowar wani ya fita da su, amma ya ce babu wanda ya shigo kuma babu wanda ya fita. Hankali a tashe ta kira ni ta sanar mun, na kira mahaifinsu na tambaye shi ko shi ya dawo ya ɗauke su, ya ce shi bai ma koma gida ba yana office, na kira gidan kakaninsu nan ma suka ce ba su zo ba. Wasa_wasa ƙaramin abu ya zama babba, muka fahimci yara fa sace su akai, tunda har dare babu su babu labarinsu. Tashin hankalin da muka shiga ba zai misaltu ba, mahaifinsu kuwa yanke jiki ya yi ya faɗi a sume ciwonsa ya tashi. In tak'aice miki zance ya sha jinya kamar ba zai rayu ba, har waje sai da aka fita da shi, daga baya kuma Ubangiji ya kawo masa sauƙi, har ya warware. Ba mu fi wata da dawowa daga India ba, satinsa biyu ma da komawa gurin aiki." Mama ta ce "Allah sarki, yaran mahaifiyarsu ta rasu ko?" Ummi ta ce "Ehh, a gurin haihuwar su Allah ya mata rasuwa." Mama ta ce "Allah ya ji k'anta ya gafarta mata." Nan dai sukai ta tattaunawa akan batun, Ummi ta kira Ammi kakar su Afrah ta haɗa ta da Mama, ta yi mata godiya sosai, sannan ta bawa su Afrah wayar ta ji muryar ƴan jikokin nata kafin ta gan su. Ummi ta kalli su Afrah ta ce "Ni fa tun d'azu ana ta bani labarin Aunty amma har yanzu ban gan ta ba." Mama ta ce "Au bata sakko ba, ban ma lura ba muna ta hira bari na kira ta." Mama ta miƙe ta hau sama su Afrah na biye da ita a baya. Fitowarta kenan daga wanka Mama ta shigo ɗakin, Mama tana kallonta ta ce "Kakannin su Afrah sun zo amma shine baki sauko kun gaisa ba dan iskanci." Neehal ta ce "Mama bacci ne fa ya ɗauke ni, yanzu na tashi." Mama bata ce komai ba ta juya ta fita. Afrah ta ce "Aunty, Ummi da Aunty Zahra sun zo suna falon ƙasa." Neehal ta ce "To bari na shirya mu je na gan su." Tare suka sauko da su Afrah, tunda ta fara sakkowa ya zira mata na mujiya yana sakin ajiyar zuciya, sai ya ga kamar ta ƙara yi masa kyau fiye da d'azu. Neehal bata lura da shi ba ma a falon, ta gaishe da Ummi cikin girmamawa, Ummi ta rungume ta tana sanya mata albarka tare da yi mata godiya cikin k'aunarta. Tana dariya ta ce "Zauna anan kusa da ni kin ji d'iyata ƴar albarka." Neehal ta yi ƙasa da kanta cikin jin kunya. Zahra ta waro Ido ta ce "Laaa kamar Neehal ɗin ASTV." Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Ita ce." Zahra ta dawo kusa da Neehal tana murmushi ta ce "Nice to meet you Aunty Neehal and I love You." Ta yi murmushi itama ta ce "Thank you, ya kike?" Zahra ta ce "Lafiya k'alau." Hira Zahra ta shiga yiwa Neehal, dan ba laifi akwaita da surutu. Neehal kuwa gaba_ɗaya jinta take a takure, ta rasa dalili kuma, nan kuwa kaifin idanun Ahmad ne yake yawo a jikinta. Ta ɗan juyo dan ta gaishe da Aunty Mardiyya karaf suka haɗa ido da shi ya mata ƙuri, ta ɗauke idanunta da sauri a ranta tana mitar yau ta gamu da gamunta, mutum daga zuwa ya mayar da ita TV'nsa. Bayan sun gaisa da Aunty Mardiyya ta janyo Afrah ta mata raɗa a kunnenta da faɗin "Je ki cewa Daddy ya daina kallo na." Yarinyar ta kalle ta zata yi magana Neehal ta ce "Shiiii, go and tell him I will give you chocolate." Afrah ta tafi da sauri ta haye jikinsa, cikin raɗa kamar yadda Neehal ta ce mata ta ce "Daddy, Aunty ta ce ka daina kallon ta." Ahmad ya ja hancin yarinyar ya ce "Go and tell her, ciwo idona yake mun idan ban kalle ta ba." Afrah ta ce "Daddy kasa glass ɗinka zai daina ciwon." Ya girgiza mata kai ya ce "No, idan ina kallon Aunty ne kawai zai daina." Afrah ta tashi daga jikinsa ta koma gurin Neehal ta faɗa mata abun ya ce. Neehal ta kalle shi tana turo baki gaba, shi kuma ya wani marairaice fuska yana ƙara tsare ta ido tare da sakar mata murmushinsa wanda yasa ta ji gabanta ya faɗi, da sauri ta ɗauke kanta daga kallon sa tana ɓata fuska. Wajen ƙarfe biyar suka fara shirin tafiya, Mama ta ce Su bari sai gobe mana, amma Ummi ta ce "Ba zai yiyu ba, dan Family suna can suna jiran dawowar su, kowa yana d'okin ganin su Afrah, tun yanzu an fara addabarta da kira inaga sun kwana." Mama ta dubi Neehal ta ce "Je ki haɗowa su Afrah kayansu." Ta miƙe da sauri dama duk a takure take da kallon da Ahmad ya addabe ta da shi, Zahra ta bi bayanta dan taya ta haɗa kayan. Jiki a matuƙar sanyaye ta shiga haɗa musu kayan, tare da ƙoƙarin danne kukan da yake ƙoƙarin k'wace mata. Bata taɓa tunanin zata rabu da twins ɗinta nan kusa ba, tana son yaran sosai ta shak'u da su over, suna matuƙar ɗebe mata kewa, yanzu gashi rana ratsa Allah zai raba su kamar yadda ya haɗa su. Ta haɗa musu kayan sawarsu a wata ƙatuwar jaka, suka kama ita da Zahra suka sauka da ita ƙasa. Ahmad ya taso da sauri ya karɓe su yana faɗin "Sannu Aunty, thank you so much." Ta masa shiru ba ta ce komai ba sai ma juyawa da ta yi ta koma sama. Ummi ta dubi Zahrah ta ce "Ta tattara kayan da suka ci abinci ta kai kitchen." Ahmad ya faki idon mutanen falon ya bi bayan Neehal da sauri. Yana shiga falon sama ita kuma tana rufo ƙofar ɗakinta, hakan yasa ya gane nan ta shiga ya nufi ɗakin cikin murna ya tura ƙofar ya shiga. Tana shiga ita kuma kukan da take ta dannewa ya kufce mata, ta kwantar da kanta a jikin gado ta shiga rera shi. Ya tsaya a bakin ƙofa tare da hard'e hannuwansa a ƙirjinsa yana sauraren sautin kukan da take, wanda ko ba'a faɗa masa ba ya san na rabuwa da twins ne........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *4️⃣1️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ..........A hankali ya fara takawa ya ƙarasa inda take, tsugunnawa ya yi a daf da ita cikin sanyin murya tare da marairaicewa ya ce "Please Aunty stop crying." Neehal ta d'ago kanta da sauri tare juyowa a tsorace dan ba ta ji shigowar sa ba, sai maganarsa kawai ta ji. Ta ɗan ja baya tare da kallonsa cikin mamakin ƙarfin hankalinsa na shigo mata har cikin daki. Ya marairaice fuska kamar ƙaramin yaro tare yi mata alamar rok'o da hannunsa. Ta tsaida kukan da take cikin jan numfashi tare da ƙoƙarin miƙewa tsaye, hannu ya zira a aljihun wandonsa ya ɗauko handkerchief ɗinsa ya miƙa mata, ta karb'a ba tare da ta ce komai ba, ta shiga share hawayen fuskarta. Wani sassayan k'amshi ya daki hancinta wanda yasa ta sakin ajiyar zuciya ba tare da ta shirya ba tare da lumshe idanunta. "Princesss!" Ya faɗa murya ƙasa_ƙasa tare da jan sunan, buɗe idonta ta yi da sauri ta sauke su akan fuskarsa cikin nazartar wani abu. 'Princess?' ta maimaita sunan a ranta kamar mai son tuno wani abu, kusancin da suka samu a yanzu yasa ta samu damar ƙarewa fuskarsa kallo sosai, sai ta ga kamar ta san fuskar, amma ta rasa a ina ta santa, ko kuma dan yana kama da su Afrah ne shi yasa. Ta kawar da kanta da sauri ganin yanda yake sakar mata wani murmushi wanda yake ƙoƙarin zautar da zuciyarta. 'He is Handsome.' ta faɗa a ranta tare da miƙewa tsaye da sauri kamar wadda aka tsikara, shima miƙewar ya yi still idanunsa na kanta. Ba tare da ta kalle shi ba ta miƙa masa hancky ɗinsa tare da faɗin "Thank you." Ya karɓa tare da faɗin "You are welcome, and I want to talk to you." Da sauri ta kalle shi ta ce "Ni kuma." Ya gyaɗa mata kai, ta ce "Okay ina jinka." Ya ɗan ja numfashi sannan ya fara magan "Tun d'azu nake son na miki godiya akan tsintar yarana da kikai a titi kika ɗauke su ba tare da ƙyama ko tsoron wani abu ba, and....." "Kar ka damu ai yiwa kai ne." Ta katse shi da faɗin haka. Ya yi murmushi ya ce "Duk da haka ba kowa ne zai iya abun da kika kai ba, hakan ya nuna kina da kyakkyawar zuciya mai cike da tausayi da jin ƙai. Allah ya biya ki ya albarkaci rayuwarki, ya yaye miki duk wani abu da yake damunki a cikin rayuwarki, ya yi miki tukuci da gidan Aljanna." Cikin jin daɗin addu'arsa ta ce "Ameen ya Allah na gode sosai, Allah ya raya mana twins." Ya ce "Amin, and secondly I......" Turo ƙofar ɗakin da akai ya katse masa maganar da yake yi. Zahra ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama. Da mamaki ta ce "Yaya Doctor dama kana nan, muna ta nemanka zamu tafi, Ummi ta kira wayarka baka d'aga ba." Ya juya ya nufi ƙofa yan faɗin "Ina nan ina yiwa Aunty godiya." Zahra ta yi murmushi ta ce "Gaskiya ne." Neehal ta ƙirƙiro murmushi tana kallon Zahra bayan ya fice ta ce "Har kun fito?" Zahra ta ce "Ehh, sai tafiya." Neehal bata kuma cewa komai ba ta ɗauki wata leda dake cike da kayan wasan su Afrah suka fice daga ɗakin zuwa downstairs. Babu kowa a falon duk sun fice. a parking space suka tarar da su tsaitsaye suna sallama. Su Afrah suna hango Neehal suka rugo gurinta suna faɗin "Aunty Daddy ya ce dake zamu tafi, zaki je gidanmu ko?" Neehal ta shafi kuncinsu tare da gyaɗa musu kai. Zahra ta karb'i ledar hannunta ta zira a Mota sannan ta dawo ta karb'i phone Numbern'ta. Cikin matuƙar dauriya Neehal ta ƙarasa bakin Motar da za su tafi a cikinta ta cewa Ummi. "Ku gaida gida, Allah ya tsare." Ummi ta ce "Ameen d'iyata, sai mun kuma dawowa ko kuma in kin zo ganin ƴaƴanki." Neehal ta murmusa bata kuma cewa komai ba, dan tana buɗe baki ta san kuka ne zai kufce mata. Ta buɗe murfin Motar ta zira su Afrah wanda suka mak'ale mata su sai da ita zasu tafi. Ganin bata shigo motar ba tana ƙoƙarin rufewa suka fasa kuka tare da ƙoƙarin fitowa. Ummi ta ce "Ah ah, me ya faru?" Afrah ta ce "Aunty, ni gurin Aunty zani." Cikin rarrashi Ummi ta ce "Ba ga Auntin nan ba ai tare zamu tafi da ita." Amrah ta ce "Ai bata shigo cikin Mota ba." Neehal da k'walla ta tarar mata a ido ta yi murmushi tare da shafa fuskar Afrah ta ce "Kayana zan ɗauko yanzu zan dawo sai mu tafi." Yarinyar ta ce "To zan biki." Ummi ta ce "A'a Afrah ku jira ta, ta dawo." Yaran suka saka kuka dan sun gane wayo ake musu, Neehal ta juya da sauri ta bar wajen hawaye na zuba daga idonta. Ahmad dake tsaye yana kallonsu ya bita da kallo, da sauri kuma ya bi bayanta ya sha gabanta. Ta tsaya ba tare data d'ago kanta ba. Fuskarsa cike da damuwa ganin tana kuka ya ce "I'm sorry na raba ki da yaranki ko?" Ta d'ago ta kalle shi cikin mamakinsa, shi da yaransa amma yana bata haquri. Ya yi mata murmushin nan nasa mai shegen kyau, tare da girgiza mata kai alamun ta daina kukan. Jin kukan su Afrah a kusa da ita yasa ta juya da sauri, ashe fitowa sukai daga cikin motar suka taho gurinta. Ta tsugunna ta rungume su a jikinta, sannan ta d'ago su ta musu pick a goshinsu tana murmushi. Afrah ta ce "Aunty ki zo mu tafi Please, mu dake zamu tafi." Kafin Neehal ta ce wani abu Ahmad dake tsaye yana kallonsu cikin burgewa ya kama hannun yaran ya ce "Aunty zata ɗauko kayanta ne, mu je Mota mu jira ta." Neehal ta miƙe tare da juyawa da sauri ta d'agawa Zahra hannu sannan ta nufi cikin gidan zuciyarta cike da kewar yaran, bayan tafiyarta ba jimawa su Ahmad suka fice daga gidan suna d'agawa su Mama hannu, sai da suka fice sannan su Mama suka koma cikin gidan. Neehal ba ta yi kuka sosai ba kamar yadda Mama ta zata, tana komawa ɗakinta ta shiga toilet ta wanke fuskarta, sannan ta sakko ƙasa gurin Aunty A'isha suka sha hira, bayan Sallar Magriba Aunty A'isha ta tafi, tana tafiya ba jimawa Sadik ya zo. Shima ya yi tunanin zai zo ya same ta cikin damuwar rashin su Afrah, amma sai ya tarar da akasin haka, suka sha hirarsu kamar kodayaushe. Washegari da hantsi ta shirya ta je saloon aka mata wankin kai, daga nan ta wuce gidan Haneefah kamar yadda ta mata alƙawari. Sai Bayan Magriba ta dawo gida, a hakan ma dak'yar Haneefah ta barta ta taho suna ta shan hira. Bayan Sallar isha'i Zahrah ta kira ta a waya, bayan sun gaisa ta musu ya suka je gida ta haɗa ta da su Afrah. Sun daɗe suna wayar suna ta bata labarai, bayan ta sha complain ɗin rashin bin su da bata yi ba..... Ranar Monday ta fara zuwa siwes ɗinta na school, a gidan TV'nsu take yi, hakan yasa abun ya zo mata da sauk'i. Bayan tafiyar su Afrah kullum sai sun yi waya a wayar Zahra, dan yanzu duk abun Ahmad ya haqura ya bar su a gidan Ummi su cigaba da zama anan saboda abun da ya faru. Neehal ta rasa meyasa fuskar Ahmad ta ƙi bacewa daga idanunta, musamman murmushinsa da yay ta kashe ta da su a ranar, kullum sai ta yi imagine ɗinsa a cikin ranta, a gefe guda kuma tana son tuno inda ta san fuskarsa, dan tabbas ta taɓa ganinta a rayuwarta ko da a hoto ne kuwa. Ranar Asabar da yamma ta dawo daga gurin aiki ta tarar Hameedah da Mommy'nta sun zo gidan. A gajiye take amma duk da haka ta zauna a falon ƙasa inda ta tarar da su da fara'arta ta ce "Sannunku da zuwa." Hameedah ta mata wani shegen kallo ta ɗauke kanta. Haj. Saratu ba yabo ba fallasa ta ce "Yawwa." Neehal ta ce "Ina yini Mommy." Hajiya Saratu ta ce "Lafiya, ashe an yi bikin ƙawar nan taki mara kunya?" Neehal ta ce "Eh." Cikin rashin jin daɗin mara kunyar data kira Haneefah da shi. Hajiya Saratu ta tab'e baki ta ce "Ke kuma yaushe ne naki bikin?" Neehal ta ce "Mommy idan an saka bikina ai zaku ji." Hajiya Saratu cikin baƙin ciki ta ce "Au da akwai wanda kike kulawa yanzu kenan?" Neehal ta ce "Eh." Cikin takaici Haj.Saratu ta ce "Wanne me rabon ɗorawa iyayensa asararsa ne? Ko kuma munafuntarsa akai ba a gaya masa matsalar da kike da ita ba?" Neehal ta yi shiru dan ta gane inda maganar Haj Saratu ta dosa. Hameedah ta ce "Kema dai Mommy banda abinki ai kin san baza a faɗa masa ba tunda ana neman a shiga daga ciki kar a tsufe a gida." Haj. Saratu ta ce "Hakane fa daughter, shi dai Yaya Muhammad Allah ya haɗa shi da masifa, yana zaman zamansa za'a ɓata masa suna a idon duniya, daga ya fito a dinga nuna shi ana yarinya ce a gidansa ta zama annoba duk wanda zata aura sai ya mutu." Mama dake sakkowa daga sama karaf maganganun Mommy a kunnenta, ta yi wani murmushi ta ce. "Saratu kenan." Haj Saratu ta ce "To ƙarya na faɗa ne, ai gaskiya ce, wa ya sani ma ko dama can dangin nata sun san annoba ce ita shi yasa suka ƙi riƙe ta karta zame musu masifa." Har Mama zata kuma magana sai kuma ta fasa, ta san dama haka Haj. Saratu take so ta tanka mata su yi ta yi, ita kuma bata da wannan lokacin. Ta dubi Neehal da take kuka sosai na kiranta annoba da Hajiya Saratu ta yi ta ce "Tashi ki wuce sama." Ta miƙe ta zari jakarta tana share hawaye ta yi sama, Mama ta bi bayan ta, ta bar Haj. Saratu tana cigaba da faɗar bak'ak'en maganganu marasa daɗi akan Neehal. A kan kujera ta tarar da Neehal ta kifa kanta tana kuka. Mama ta janyo ta jikinta ta shiga lallashinta tana faɗin "Ki yi shiru haka kukan ya isa, kar ki ɗauki maganganunta na banza ki saka a ranki har su zo suna damunki, na san halinki da saka abu a rai." Ta d'ago ta, ta shiga share mata hawayen fuskarta. Sosai maganganun Haj.Saratu suka daki zuciyar Neehal, musamman idan ta tuna kalmar annoba da Hajiya Saratu ta kirawo ta da ita, hakan yasa hawayenta suka ƙi tsayawa. Mama ta tashi ta shiga dakinta ta barta a falon. Haj. Saratu tana cikin mitar ta Ameen ya shigo falon, tana ganinsa ta yi shiru. Hameedah ta faɗaɗa fara'a cikin iyayi ta ce "Yaya Ameen sannu da zuwa." Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa tare da amsa mata ciki_ciki. Ba yabo ba fallasa ya gaishe da Haj. Saratu sannan ya haye upstairs abinsa. A falo ya tarar da Neehal durk'ushe inda Mama ta barta tana kuka, ya bita da kallo tare da faɗin "What happened to you?" Neehal ta d'ago kanta jin muryarsa amma ba ta ce komai ba, ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta a ɗan ruɗe ya ce "Tell me what happened?" Neehal ta share hawayenta ta ce "Mommy ce, ta kira ni da annoba." Sai ta kuma fashewa da kuka. Shiru ya yi cikin ɓacin rai, ya rasa uwar me Neehal ta tsarewa Haj. Saratu a rayuwa ta tsane ta. A hankali ya matso daf da ita ya janyo ta jikinsa ya rungume ta tsam a ƙirjinsa ya shiga rarrashinta..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *4️⃣2️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ..........Lamo ta yi a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya tare da barin kukan da take. A hankali ya d'ago ta daga jikinsa yana dubanta da murmushi akan fuskarsa ya ce "Je ki wanke fuskarki ki zo ki raka ni unguwa." Ta gyaɗa masa kai tare da miƙewa ta shige ɗakinta. Ya bita da kallo cikin sauke numfashi. Miƙewa ya yi shima ya shiga ɗakin Mama. Bayan ya yi sallama ta amsa sun gaisa ya zauna a gefenta tare da faɗin "Mum ki taya ni murna, next month zan dawo Kano da aiki Insha Allah." Mama ta ce "Masha Allah, na ji daɗin hakan sosai, ka ga an huta da fargabar barin Hafsah ita kaɗai a gida." Ya ce "Hakane, bari in je masallaci na ga lokacin Sallah ya gabato, idan na dawo zamu fita da ƴarki." Mama ta ce "Fita kuma? Zuwa ina?" Ya ce "Unguwa." Ta ce "Ita unguwar bata da suna?" Yana miƙewa ya ce "Sirri ne tsakanin Yaya da ƙanwarsa." Mama ta tab'e baki ta ce "Kamar gaske." Ya yi murmushi kawai tare da ficewa daga ɗakin. Itama Neehal data shiga toilet bayan ta wanke fuskarta ganin Magriba ta gabato sai ta ɗauro alwala ta fito. A gaban mudubi ta tsaya ta ɗan gyara fuskarta ta saka kwalli a idanunta saboda kukan da ta yi. Bata canza kaya ba, mayafi kawai ta ɗauko ta yafa ta ajiye hijabin da yake jikinta. Ɗakin Mama ta shiga dan sanar mata Ameen ya ce za su fita, zuciyarta cike da mamakinsa dan ta manta rabon da su je unguwa ko wani gurin tare da shi, dan tun da ko Mama ta ce ya kaita School ko gurin aiki sai ya haɗa ta driver, ya ce shi ba direbanta ba ne. Ta tarar Mama tana toilet tana alwala, ganin ƙofar toilet ɗin a buɗe ta ƙarasa bakin ƙofar ta ce "Mama Yaya ya ce zamu fita yanzu." Mama ta ce "Ya faɗa mun, amma ai kya ci abinci kafin ku tafi." Ta ce "Bana jin yunwa." Mama ta ce "Shikenan ai, ki je ki yi sallah kafin ya dawo, shima ya je masallaci." Neehal ta ce "Toh." Ta dawo cikin ɗakin ta ɗauki darduma ta shimfid'a ta zira hijabin Mama ta tayar da Sallah. After some minutes Ameen ya shigo ɗakin, yana duban Neehal ya ce "Tashi mu je kar dare ya yi." Mama ta ce "Allah ya tsare, saura kuma kafin ku dawo ka samun ita kuka, dan na san hali." Ya yi ɗan murmushi bai ce komai ba. Neehal ta yiwa Mama Sallama suka fice a tare. Yanda ta bar Haj.saratu da Hameedah haka suka sauko suka same su, da alama ko tashi sun je sun yi sallah ba su yi ba. Ba suce musu ƙala ba suka fice, su kuma su Hameedan suka raka su dana mujiya. Bayan fitarsu Hameedah ta dubi Mahaifiyarta ta ce "Sabon salo b'arawo da sallama, ko ina kuma za su a daren nan?" Haj Saratu ta ce "Oho musu, amma ni fa na fuskanci take_taken Haj. Fatima so take ta aurawa Ameen shegiyar yarinyar can." Hameedah ta lailayo ashariya ta ce "Tab'dijan, da kuwa an yi ƙaramin yaƙi a family wallahi, ta hana shi aure na sannan kuma ta aura masa wata can bare." Haj Saratu ta ce "Hmmmm, ba dai tak'amarta ita ta haife shi ba, to ai ba ɗanta ba ne ita kaɗai, wallahi matuƙar ta ce zata aurawa Ameen yarinyar nan da taƙi auruwa sai na yi sanadin barinta gidan nan, mu zuba mu gani ni da ita." Cikin damuwa Hameedah ta ce "Mommy ni duk ba wannan ba ma, wai ya batun aure na da Ya Ameen ne? kin ce mun wannan zuwan da mukai akan maganar auren ne, kuma ban ga wata alama data nuna hakan ba, ni fa gaskiya na gaji da gafara sa ban ga k'aho ba." Ta ƙarashe maganar cikin botsarewa. Mommy ta ce "Me kike ci na baka na zuba ne? Ki bari ki ga me zan yi mana, akwai shirin da nake yi, da zarar ya kammala zaki sha mamaki, ke dai ki kwantar da hankalinki bana son kina damuwar nan." Hameedah ta sauke numfashi cikin damuwa, ita yanda Ameen yake nuna halin ko in kula da ita yafi komai d'aga mata hankali, gashi ita babu wani wanda yake zuwa gurinta a yanzu da sunan saurayi. K'awayenta duk sun yi aure, ita ga kuɗin ga aiki tana yi amma babu mashinshini duk da uwar maganin farin jinin da uwarta take dirka mata. Sai da suka shiga Mota sannan Neehal ta dubi Ameen ta ce "Yaya ina zamu?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Siyar dake zan yi." Jin haka yasa ta ja bakinta ta tsuke. Har suka ƙarasa wani had'ad'd'en Bakery dake cikin Nasarawa babu wanda ya ce uffan. Ya yi parking ɗin Motar ya fito itama ta biyo bayan shi suka shiga gurin. K'amshin abinci irin me tsinka yawun nan ne ya fara musu welcome. Gurin ya haɗu sosai kuma babu hayaniya ko kaɗan. Suka zauna a kujerun dake zagaye da table suna fuskantar juna. Ameen ya ɗauko wayarsa ya shiga latsawa, ita kuma ba ta fito da waya ba ta baro ta a gida, kallon gurin kawai take cike da burgewa. Wani ma'akaicin gurin ya kawo musu takarda mai ɗauke da duk wani abu da suke siyarwa a gurin tare da price ɗinsa. Ameen ya karɓa ya duba tare da selected ɗin abun da za'a kawo musu. Bayan mintuna biyar ma'aikacin ya dawo ɗauke da madaidaitan plates guda biyu a hannunsa, a gaban Neehal ya ajiye su duka kamar yadda Ameen ya ce masa. Neehal ta kalli snacks ɗin yawunta na tsinkewa saboda k'amshin daya bugi hancinta. Plate na farko meatpie ne a ciki da Spring rolls da samosa. Plate na biyu kuma Pizza and shawarma ne a ciki. Sai kuma Juice and bottle water a gefe, sai tissue. Ba tare da Ameen ya kalle ta ba yana cigaba da latsa wayarsa ya ce "ki yi sauri ki ci." Ta dube shi ta ce "Kai fa?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. Ba ta kuma cewa komai ba, ta yi Bismillah ta fara ci cikin nutsuwa. Cin abincin Neehal babu sauri, kafin ta gama fiye da mintuna ashirin sun wuce, kuma bai fi rabin abun da aka ajiye mata ta ci ba. Bayan ta gama, ya je ya biya kuɗin tare siyan wasu snacks ɗin, a leda biyu aka masa packaged, ya karbo suka baro gurin. Daga nan gurin shan Ice cream da siyar da su chocolate ya kai ta, suka shiga ya ce ta ɗibi abun da take so. Neehal masoyiyar choculate da wafer ta diba son ranta ya biya kuɗin suka fito suka nufo gida, lokacin har an yi isha'i. Suna hanya Hafsah ta kira shi, da ya duba ya ga ita ce sai ya ƙi d'agawa. Sun kusa zuwa gida ta ji Muryarsa ba tare da ya juyo ba ya ce "Ko mu ƙara zuwa wani gurin?" Neehal ta ce "A'a dare ya yi." Ya ɗan kalle ta ya ce "Ko dai wannan saurayin naki ne zai zo kike sauri ki koma gidan?" Ta ce "A'a wallahi, ka san idan muka daɗe Mama za ta yi faɗa." Ya ce "Hmmm." Kawai. A parking space ya ajiye ta bayan sun ƙarasa gida, ya bata ledodin ta ya ce ta gaishe da Mama shi ya wuce, ta yi masa godiya sannan ta nufi part ɗin Mama. Tana jin zuciyarta ta mata sanyi akan bata mata ran da Haj Saratu ta yi. Sosai ta ji daɗin fitar nan da sukai, ko dan ta daɗe bata fita irin guraren nan ba ne? Bata tarar da su Hameedah a falo ba, da alama sun shige ɗaki, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi ya mata ba. Ɗakin Mama ta nufa ta tarar da ita tana shirya kaya a wardrobe. "Mama na dawo." Ta faɗa tana zama a gefen gado. Mama ta ce "Sannunki da zuwa, ina Ameen ɗin?" Ta ce "Ya wuce gida." Mama ta ce "Ina kuka je ne?" Neehal ta ce "Wani Bakery ya kai ni, sai kuma muka biya muka siyi Ice cream." Mama ta ce "Shine dan wulaqanci ba zai je da Matarsa ba sai dai ya zo ya ɗauke ki." Neehal ta yi dariya ta ce "Kai Mama, itafa ta zama cuss yanzu tunda matar Aure ce, da ƴan mata ake fita, kuma itama ya siya mata nata, kema ga naki ya ce na kawo miki." Mama ta ce "Ko ma da jarirai ake fita daga yau ya dinga fita da matarsa." Mama ta ƙarasa zancen tana duba ledar da Neehal ta ajiye. Neehal ta miƙe ta ce "Bari na je na yi sallah." Mama ta ce "Alright." Tana shiga bedroom ɗinta ta dauko wayarta, kamar yadda ta zata missed call ɗin Sadik ta gani har biyu. Tana ƙoƙarin bin bayan kiran nasa wani kiran ya shigo amma da new Number. Ta d'aga ba tare da ta ce komai ba. Muryar Amrah ta ji ta ce "Hello Aunty." Neehal tana murmushi ta ce "Sweetheart, ke ce? ya kike?" Amrah ta ce "Lafiya k'alau Aunty, yaushe zaki zo?" Neehal ta ce "Soon Insha Allah, ina Afrah?" Ta ce "Tana toilet tana pupu." Neehal ta ce "Ina Ummi da Aunty Zahra?" Amrah ta ce "Suna gida, mu kuma muna gidan Daddy." Neehal ta ce "Anan zaku kwana?" Ta ce "A'a, idan Afrah ta fito daga toilet Daddy zai mayar da mu gidan Ummi." Neehal ta ce "To ƴar gidan Daddy ina Daddy'n?" Amrah ta ce "Gashi nan, yana jinki." Ta ce "To ki gaishe shi." Muryarsa ta ji a maimakon ta Amrah, cikin marairaicewa ya ce "Uhm, ke baza ki gaishe ni da kanki ba kenan?" shiru ta yi, jin muryarsa a bazata yasa ta ji wani abu a cikin zuciyarta, har da lumshe idanunta ba tare data sani ba, tare da tunanin a ina kuma ya samu Numbern'ta? 'A gurin Zahra.' zuciyarta ta bata amsa. A kasalance gami da shagwab'arta ta ce "Ina yini." Ya kwaikwayi muryarta ya ce "Lafiya k'alau Aunty, ya Mama." Ta turo baki gaba kamar yana kallonta ta ce "Tana nan k'alau." Ya ce "My regard to her." Daga haka ya miƙawa Amrah wayar jin Afrah tana kwad'a masa kira daga toilet. Suka ci-gaba da hira da Amrah tana bata labarin school ɗin da aka mayar da su, har Afrah ta fito daga ta karb'i wayar tay ta mata surutun ta itama, ganin dare yana yi Ahmad ya ce su mata sallama zai mayar da su. Bayan sun gama wayar ta bi wayar da kallo kamar zata ga yaran a cikin wayar. Sosai take jin kewarsu a cikin ranta, musamman in ta zo bacci sai ta ji gadon ya mata faɗi ita kaɗai, ta saba da, da twins manne a jikinta. Tashi ta yi ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da dauro alwala ta fito ta yi Sallar isha'i. Bayan ta idar ta kira layin Sadik amma bai ɗauka ba, hakan yasa ta kunna data ta shiga yanar gizo. Jimawa kaɗan Sadik ya kira ta, ta d'aga da sauri dan yau gaba- ɗaya ba su yi waya ba, ta yi kewarsa ba kaɗan ba....... Washegari Sunday tana gida through out saboda ita kaɗai ce ranar hutunta a week, tunda ta fara siwes Monday to Saturday take zuwa gurin aiki. Tunda ta tashi da safe bata huta ba tana ta aikin gida. Mama sun fita gidan wata Freind ɗinta ita da su Dije tun wajen 11, daga nan kuma za su wuce kasuwa su siyo kayan girki. Suma su Hameedah tun safe suka wuce Abuja, saboda gobe Monday Hameedan zata je gurin aiki. Bayan Sallar la'asar tana kitchen tana girki ta ji ƙarar door beil. Ta fito tana kwab'e fuska saboda gajiyar da ta yi, a tunaninta su Mama ne suka dawo, amma tana buɗe ƙofar sai ta ga wanda bata taɓa tsammanin ganin sa a wannan lokacin ba. Cikin matuƙar mamaki ta tsaya tana kallonsa. Ya sakar mata murmushinsa wanda ya kasa bacewa idanunta tun ranar da ya tafi har kawo yau. Ta yi ƙasa da kanta tare da faɗin "Sannu da zuwa." Ta ƙarashe zancen tana matsawa baya dan ta ba shi hanya. Ya ce "Yawwa Aunty." Tare da shigowa cikin falon bakinsa ɗauke da Sallama. Ta koma kitchen zuciyarta cike fal da mamakin zuwansa. Plate ta ɗauko ta ɗora masa drinks akai ta dawo falon, ya bita da kallo still fuskarta d'auke da murmushi. Ta ajiye plate ɗin a gabansa ba tare da ta ce komai ba. Ya ce "Mama bata nan ne?" Ta ce "Eh, ta je unguwa, amma na san yanzu tana hanyar dawowa, ina su Afrah?" Ya ce "Suna gida, ba su ma san zan zo ba dan kar su mun rigima." Neehal ta ce "Ai da ka zo mun da su, ya su Ummi?" Ya ce "Suna nan k'alau." Ta mik'e tare da faɗin "Ga ruwa ka sha, bari na ƙarasa girki." Ya ce "Okay thank you." Tare bin ta da kallo har ta shige kitchen ɗin, ya lumshe idonsa yana jin k'aunarta na ƙara mamaye dukkan wani gurbi dake cikin zuciyarsa. Ba jimawa da shigar ta kitchen ɗin ya ji shigowar su Mama falon ita da su Dije tare da wasu ma'aikatan gidan maza guda biyu hannunsu ɗauke da manya_manyan ledodi. Mama ta ƙaraso cikin falon da mamaki take duban Ahmad, cikin fara'a ta ce. "Doctor! Kai ne a gidan namu?" Cikin girmamawa ya ce "Nine Mama, sannu da zuwa." Mama tana ƙoƙarin zama ta ce "Yawwa, sannunka kai ma." Ya sauko daga kan kujerar da yake ya ce "Ina yini." Mama ta ce "Lafiya k'alau, ina ƴan tagwayena da su Ummi?" Ahmad ya ce "Suna nan k'alau." Mama ta ce "Masha Allah, ina Neehal ɗin ne ta bar ka kai kaɗai a zaune." Yana sosa kai ya ce "Ai babu komai Mama.,'" Mama ta miƙe ta nufi kitchen jin k'amshin girki ta gane Neehal ɗin tana can. "Oyoyo, Sannunku da zuwa." Neehal ta faɗa lokacin da Mama ta shiga kitchen ɗin. Mama ta ce "Yawwa, Sannunki da aiki." Ta shagwab'e fuska ta ce "Yawwa Mama, yau na sha aiki na gaji, jikina har ya fara mun ciwo." Mama ta ce "Allah ya baki lada kin ji ƴar albarka." Neehal ta ce "Ameen." Mama ta ce "Ki je gurin Doctor, bari na ƙarasa girkin. Babu daɗi a bar mutum shi kaɗai a zaune." Neehal ta ce "Na ma gama girkin, saukewa kawai zan yi, da kitchen ɗin zan gyara." Mama ta ce "Barshi, idan su Zulai sun huta sai su zo su gyara, ki zuba abincin ki kai masa." Neehal ta ce "Toh." Mama ta juya ta fita, ita kuma ta shiga zuba masa abincin kamar yadda Mama ta umarce ta. Sai da ta hau sama ta sako hijabi tare da ɗauko wayarta sannan ta dawo downstairs ɗin. Yana zaune yana latsa waya ta yi Sallama ta ajiye masa abincin a gabansa, ganin bai sha drinks ɗin data ajiye masa ba. Ta ce "Ya baka sha ruwan ba." Ya d'ago yana kallon fuskarta da murmushinsa na gado ya ce "Zan sha yanzu." Ba ta ce komai ba ta buɗe ruwan ta tsiyaya masa a cikin glass cup ta miƙa masa. Ya karɓa tare da faɗin "Thank you." Neehal ta koma kujerar gefensa ta zauna ta shiga wasa da yatsun hannunta. Bayan ya gama shan ruwa ya fuskance ta a hankali ya ce "Gurinki na zo Neehal." Ta dube shi da sauri amma bata yi magana ba. Ya gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa. Ya miƙe tsam daga kujerar da yake ya koma wadda take zaune ya zauna a gefenta. Ta lumshe ido da sauri saboda shaƙar sassayan k'amshinsa da ta yi. Muryar Ahmad da ta ji yana magana yasa ta buɗe idanunta. Wayar hannunsa yake miƙo mata, ta karɓa da alamar tambaya akan fuskarta. Hoton da ta gani akan screen ɗin wayar yasa ta waro Idanunta waje cikin tsananin mamaki. Hotonta ne tana ƙarama wanda bata san a inda ya same shi ba. Kafin ta yi magana ya riga ta da faɗin "Ki wuce kiga na gaba." Ba tare da ta yi magana ba ta wuce kamar yadda ya ce zuciyarta cike da al'ajabi, Wannan karon ɗan zabura ta yi tana ƙara kallon hoton, hoton tane ita da shi, tana murmushi shi kuma yana kallon fuskarta da murmushi ɗauke akan fuskarsa...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *4️⃣4️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* *🌈NIMCY'S LIBRARY🌈* _Readers gareku, masu tambayar old books na NIMCYLUV SARAUTA, tayi shiru ne domin tana bada bunus kafin azumi, to Finally the day is here, tana sai da littafan ta gaba ɗaya akan 3k gaba ɗaya littafan guda 14 ne, to bisa Bunus ɗin da tayi na tsayin sati guda dukkan mai so zai biya 1500 mai makon 3k😍, nasan baku karanta littafan ta na baya ba, da am sure za kuce sunma fi na yanzu daɗi❤️🤨_ So what are waiting for.....??? Go and subscribe your own... Abu Maleek Sirrin mu Uncle ne The new emir Izzar so Sai na aureta😍 Tsintacciya E.t.c guda 13 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 a biya asha karatu Tabbas za kuyi farin ciki littafan babu baya #Love #Romance #Destiny Bunus ya fara 6/2/2022 Share fisabilillahi😍 .........Ahmad ne ya fara juyawa ya kalli ƙofa jin ana sallama tare da amsa Sallamar. Neehal kuwa bata san time ɗin data miƙe tsaye ba jin sallmar Ameen cikin kamilalliyar muryarsa. "Yaya! ga mahaifin su Afrah." Ta faɗa a diririce ba tare data san ta yi hakan ba. Ameen dake tahowa inda suke ya mata wani kallo bai ce komai ba. Ahmad kuwa bai lura da yanayin da Neehal ta shiga ba wanda ita kanta in za'a kashe ta baza ta ce ga dalilin da yasa ta haka ba, idanunsa suna kan Ameen. Ameen ya miƙa masa hannu bayan ya ƙaraso inda suke ba tare da ya ce komai ba. Da fara'a Ahmad ya miƙa masa nasa hannun suka yi musabaha. Ahmad ya ce "Barka da yamma." Ameen ya ce "Yawwa, ina maka murnar bayyanar kids ɗinka." Still fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Thank you." Ameen ya juya ya nufi sama ba tare da ya ƙara cewa komai ba. Neehal ta sauke numfashi tare da komawa ta zauna tana bin bayan Amee da kallo, wanda ya tafi ya bar musu k'amshinsa a falon. Muryar Ahmad da ta ji yana faɗin "Princess." Shi yasa ta juyowa ta kalle sa. Ya ce "Zan wuce, na ga time ɗin sallah ya yi." Ya ƙarasa maganar tare da duba agogon hannunsa. Neehal ta ce "Gidan Mamy zaka koma?" Ya ce "Eh." Ta ce "Ka gaishe ta Please." Ya ce "Zata ji Insha Allah." Ya miƙe tsaye yana jifanta da wani kallo mai cike da tsantsar k'auna. Ta miƙe itama kanta a ƙasa ta ce "Thanks for the visited." Ya ce "Thank you more and more Princess, nine da godiya ba ke ba, kasantuwar mu yau a tare ya sanya ni a cikin farincikin dana manta rabon da na yi kamar sa." Ta d'ago ta kalle shi amma ba yanda za su iya haɗa ido ba ta ce "Nima na yi farin cikin kasancewa da kai Uncle." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai alamar tabbatarwa. Ya tsaya kawai yana kallonta yana jin kamar ya tafi. Kiran Sallar da aka gwad'a a masallacin dake cikin layin nasu ne ya sa ya sauke ajiyar zuciya. A hankali ya matso daf da ita, hannunta ya kama cikin murya kamar mai rad'a ya ce "I love You....!" Ta lumshe idonta tare da ƙoƙarin zame hannunta daga nasa jin taku ana sakkowa daga sama, amma ya ƙi bata damar hakan, sai ma hannunta da ya kai saitin bakinsa ya mata pick tare da faɗin "Bye." Sannan ya sakar mata hannun ya juya ya nufi ƙofa ya barta anan sandare cikin wanin yanayi da bata san ya zata fassara shi ba. A hankali kuma ta buɗe idonta ta ga har ya fice daga ɗakin. Ta juya dan ɗaukar wayarta tana sauke numfashi suka yi 4 eyes da Ameen tsaye a cikin falon. Ta yi kamar bata gan shi ba, ta sunkuya ta ɗauki wayarta ta nufi upstairs. Ameen ya bita da kallo sannan ya tab'e ɗan bakinsa ya fice daga falon. Sai da ta zauna akan kujera bayan ta ƙarasa falon sama sannan ta latsa wayarta, message ɗin Sadik ta gani 11 minutes ago. Ta buɗe da sauri ta karanta. Ajiyar zuciya ta sauke ganin ya ce, tunda abu take yi yanzu zai je ya yi Sallah ya dawo tunda lokacinta ya gabato. Ta miƙe ta shiga ɗakin Mama. "Mama! Mama!" Ta shiga kiran sunanta bayan ta shiga, Mama ta fito daga toilet fuskarta da ruwa alamun alwala ta yo ta ce "Na'am Daughter wannan kiran fa?." Neehal ta yi murmushi ta ce "Wani labari zan baki mai daɗin gaske." Mama ta ce "To bari mu yi Sallah sai ki bani, Ahmad ɗin ya tafi ne?" Neehal ta ce "Eh, ya tafi yanzu nan." Mama ta ce "Amma ba a yau zai koma Abujan ba?" Neehal ta ce "Eh, akwai ƙanwar Ummi a nan Kano gidanta zai koma, amma gobe zai wuce Abujan." Mama tana shimfid'a Darduma ta ce "Alright." Neehal ta juya ta fice daga ɗakin zuwa nata dan yin Sallah. Bayan ta idar ba jimawa wayarta ta fara vibrate, ta ɗauko kamar yadda ta zata Sadik ne yake kiran ta. Ta d'aga tare yin sallama, ya amsa mata. A hankali ta ce "I'm sorry Yaya Sa..." Ya katse ta da faɗin "No Darling kar ki damu, na san abu kike yi time ɗin. Daga unguwa ma nake na biyo in ganki in kuma yi miki sallama." Neehal ta ce "Sallama kuma?" Ya ce "Eh, gobe in Allah ya kai mu zan tafi ibadan sai ranar Friday zan dawo." Neehal ta ce "Allah ya kai mu, ya tsare hanya ya kiyaye mun kai." Ya ce "Ameen ya Allah, na ce miki zan dawo kuma bayan mun yi Sallah Abba ya kira ni ya sanar mun in zo gida zamu fita tare da shi yanzu." Neehal ta ce "Idan kun dawo ba sai ka zo to." Ya ce "Idan mun dawo da wuri zan zo insha Allah." Cikin shagwab'a ta ce "Idan baku dawo da wuri ba sai nan da 5 to 6 days zan gan ka kenan?." Ya ce "Um'um Dear, ai za mu yi video call ko?" Ta ce "Shikenan Husby nah." Ya ce "Yawwa wifey." Daga haka suka yi sallama ya kaste wayar. Ta tashi ta tafi ɗakin Mama ta fara fara labarin Ahmad tun farkon haɗuwar su, duk da wasu abubuwan ta manta wanda ta riƙe kawai ta faɗa mata. Mama ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, Allah ya biya shi taimakon da yay miki." Neehal ta ce "Ameen, shi yasa nake son twins over, ashe....." Sai kuma ta yi shiru. Mama ta ce "Uhm? Ashe soyayyar Mahaifinsu ce ta shafe su." Neehal ta rufe fuska tana murmushi. Mama ta ce "Gobe idan ya zo ya kamata ki bishi ki je ki gaishe da ƙanwar Ummin nasu." Neehal ta ce "Gaskiya kam, dan tana da kirki kuma tana sona, har wanka ta taɓa mun." Cikin takaici Mama ta ce "ita matar Umar ɗin duk zuwa gidansu Ahmad ɗin da kike bata taɓa bibiya ta ji me kike zuwa yi ba, yanzu da ba shi da hali fa cutar dake yake babu ruwanta ko? Saboda ba ita ta haife ki ba, halin wasu mutanen sai dai mu ce Allah ya shirye su kawai yasa su gane." Neehal ta ce "Ameen Mama." Mama ta ce "A cikin week ɗin nan ya kamata ki je gidan A'isha da Sadiya, kin jima ba ki je ba." Ta ce "Toh Mama Insha Allah zani, ni Gombe ma nake son zuwa, duk sanda Hajiya ta zo sai ta mun complain akan rashin zuwa na." Mama ta ce "Na ji Ameen yana cewa yana son zuwa Gomben nan kusa shi ma, sai ku tafi tare. Ga Abuja ma kin daɗe baki je ba, Jiya da muka yi waya da Umma ma sai da ta ce ƙin daina zuwar musu yanzu." Neehal ta ce "Insha Allah, duk a cikin month ɗin nan zan je musu." Mama ta ce "Allah ya yarda, shi ma Uncle ɗin naki ya kamata ki lek'a musu." Neehal ta ɓata fuska dan ta gane Uncle Umar Mama take nufi. Ta ce "Ni fa Mama bana son zuwa yana kora ta da cin mutunci." Mama ta ce "Ki je dai, ai ba zama zaki yi ba, ganin su kawai zaki yi ki dawo, kin fi shekara biyu fa baki je ba." Ba don ta so ba ta ce "Toh." Mama ta ce "Yawwa my Daughter, ki yi haquri watarana sai labari, nina faɗa miki watarana sai sun zo suna neman ki har inda kike, komai lokaci ne. Kuma har abada su jininki ne ba'a taɓa sauya wa tuwo suna." Neehal ta gyaɗa mata kai cikin gamsuwa. Mama ta ci gaba da yi mata nasiha cikin taushin murya, daga ƙarshe kuma ta saka mata albarka tare da tarin addu'oi. Kiran Sallar isha'i ne ya tayar da su suka yi Sallah. Bayan sun idar ba jimawa Ameen ya dawo gidan kamar yadda Mama ta ce masa in an yi isha'i ya dawo Daddy yana neman sa. Ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo da sallama. Suka amsa masa a tare. Kan Neehal a ƙasa ta ce "Ina yini Yaya." Ko kallon inda take bai yi ba balle ya amsa mata, ya samu gefen gado ya zauna fuskar nan a haɗe. Neehal ta tashi ta fice daga ɗakin. Bayan ta fita Mama ta dube shi ta ce "Kana ji tana gaishe ka amma ka ƙi amsa mata." Ya ɗan yi murmushi bai ce komai ba. Cikin takaicin wannan halin nasa Mama ta ce "Bari na kira Dad ɗin, na ji bai shigo ba har yanzu." Ya ce "Tom." Tare da miƙewa ya fice daga ɗakin. Ɗakin Neehal ya buɗe ya shiga, tana kwance a kan gadonta tana latsa waya. Bata san ya shigo ba sai k'amshinsa ta ji ya cika mata hanci. Ta juyo da sauri sukai ido huɗu fuskar nan a haɗe, ta tashi zaune da sauri cikin tsoron yanayin data gan shi ta ce "Yaya!" Bai amsa mata ba sai harara da ya zabga mata. Tayi ƙasa da kanta da sauri. Ya fi mintuna biyar a tsaye bai ce komai ba, daga baya kuma ya juya ya fice daga ɗakin. Ta sauke ajiyar tare da tashi ta je ta kulle ƙofar ɗakin dan yanayin data gan shi a ciki na ɓacin rai ta ɗauka dukan ta ma zai yi, duk da bata san abun da ta yi masa ba. A ranta tana mitar ya yi auren ma amma ba zai barta ta huta da masifarsa ba, gashi shi mutum ne wani iri da baka sanin lokacin daka masa laifi, abun da kai a tunaninka ba laifi ba ne shi a gurinsa laifi ne. Duk da ta san yana da haquri, musamman ma ita ya yi haquri da ita a baya, ta saka masa ciwon kai lokacin da ya dawo daga karatu kafin ta saba da shi, dan a lokacin duk abun da ta san baya so shi take yi, shi kuma idan ya gaji da ɗauke kai daga abubuwan da take yi, ya kamata yay punishied ɗinta. Daga baya kuma da ta ƙara girma ta yi hankali sai ta ci maganin zama da shi, ta gane mutum ne shi mai sauƙin kai da kawaici, shi abun da kawai ba ya so a rayuwarsa raini, idan har zaka raina shi to baza ku taɓa shiri ba. Gashi da kyauta kamar mahaifiyarsa, bata neman komai ta rasa saboda kafin ma ta buƙata ya siyo mata, duk weekend ɗin duniya idan ya dawo daga Lagos da guzurin tsarabarta yake tahowa. Sometimes idan yana gari shi yake koya mata Assignment idan bata iya ba, haka ma hadda yana jiye mata ko kuma ya ƙara mata inda bata iya ba. Daga shekara biyar zuwa yanzu ne ya sauya mata gaba-d'aya, ya fara shashshare ta over dama gashi muskili, sai ran da ƴan mutuncin suke kansa shine zai ɗan sakar mata fuska......... Wayarta dake gefenta ce ta katse mata tunanin da take ta hanyar yin vibrate, ta sauke numfashi sannan ta saka hannu ta ɗauka tare da duba mai kiran. Number ce babu suna, amma da yake da sim ɗin da ba kowa ne yake kiran ta da shi ba sai makusantanta yasa ta d'aga. Cikin sassanyar muryarsa ya mata sallama hakan yasa ta gane shi ne. Ta amsa tare yin shiru ya ce, "Are you Ok?" Ta ce "Eh, me ka ji?" Ya ce "Na ji muryarki so cool." Ta ce "Ba komai, ya ka je gida?" Ya ce "Lafiya k'alau, duk da baki kira ni kin ji ba sai da na kira ki." Ta ce "I'm sorry, bani da Numbern ka ne." Ya ce "Alright." Suka yi shiru gaba-d'ayan su, ita ta rasa me yasa ta ji gaba-d'aya zuciyarta babu daɗi, kuma daga shigowar Ameen ɗakinta ne mood ɗinta ya canza, amma da tana cikin farin ciki sosai. Fahimtar hakan da Ahmad ya yi yasa ya shiga bata labarin rayuwarsu ta da cikin sigar tsokana, nan da nan ta ware ta shiga ƙyalƙyala dariya. Ahmad He is so funny at all, amma idan ya shagwab'e sai ka ɗauka yaro ɗan shekara uku ne. Sosai ta ji daɗin wayar da sukai kamar kar su daina, sai da ta ga Sadik yana ta kiran ta sannan ta masa sallama ta kira Sadik bayan ta gama haɗa kalaman da za ta yi amfani da su gurin ba shi haquri akan kiran ta da ya yi ya ji waiting call......✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *4️⃣3️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* .........Da sauri ta d'ago ta kalle shi gabanta na fad'uwa ta ce "Doctor! wa...." Ya katse ta da faɗin "Kin yi mamaki ba, na san yanzu kina tambayar kanki ina na samo waɗannan hotunan, kuma yaushe aka yi su?" Ya ɗan ja numfashi ya ce "Neehal! Na yi mamaki sosai da kika kasa gane ni a lokacin da kika ganni, duk da nasan shekarun da yawa kuma lokacin da muka haɗu kina yarinya ƙarama, amma na san yanzu waɗannan pictures ɗin sun tuna miki da ni a rayuwarki." Kallon fuskarsa ta shiga yi ko kiftawa ba ta yi, lokacin ɗaya idanunta suka ciko da k'walla, ta yi minti uku a tana kallonsa kallo irin na k'urilla sannan ta ce. "Uncle Ahmad! Are you the one please?" Ta faɗa cikin raunin murya da tsantsar mamaki. Ya yi murmushi cikin jin daɗin yanda ta iya tuno shi da wuri haka ya ce "Yes, kin manta ni a rayuwarki ko? kin karya alƙawarin da kika mun." Ta girgiza masa kai cikin ƙoƙarin mai da k'wallar data tarar mata ta ce "Ban manta ka ba a cikin raina, domin a duk lokacin da zan tuno da rayuwata ta gidan Uncle Umar sai na tuna da kai da irin taimakon da ka ba ni." Ya ce "Amma me yasa da kika ganni kika kasa gane ni." Ta ce "I don't know, amma kasan shekarun da yawa, kuma ranar dana ganka na ga kamar na san fuskarsa, amma na rasa a ina na santa." Ahmad ya juyo ya fuskance sosai ya ce "Neehal, duk tsawon shekarun nan da suke wuce dai_dai da rana ɗaya ban taɓa mantaki ba a cikin raina, kodayaushe ina tunanin ki tare da fatan na sake haɗuwa dake a rayuwata, ashe ta sanadin twins Ubangiji zai ƙara haɗu mu, haɗuwar da bana fatan mu rabu har abada." Neehal ta sauke numfashi ta ce "Ina Mamy?" Cikin mamaki ya ce "Baki manta Mamy ba?" Ta ce "Eh mana, kamar yadda ban manta ka ba itama ban manta ta ba, amma na san idan na ganta a yanzu ba zan gane ta ba, har yanzu tana unguwar su Uncle Umar?" Ya ce "A'a sun tashi daga unguwar, amma suna Kanon dai. Sai dai ita tafi shekara bata ƙasar nan, ta je Turkey, shekaran jiya ta dawo, yanzu ma daga gidanta nake." Ya ɗan ɓata fuska sannan ya cigaba da magana "Ni fa ban ga kina murnar gani ba, ko ba ki yi farinciki da sake haɗa mu da Allah ya yi ba?" Neehal ta yi murmushi ta ce "Hmm, wlh Uncle farincikin da yake cikin Zuciyata a yanzu na haɗuwa da kai a karo biyu a rayuwata ba zai misaltu ba, kawai tsananin mamaki ne ya hana murnar tawa bayyana, gani nake ma kamar mafarki nake, Uncle Ahmad, mutumin kirki, mai taimakon bayin Allah ba tare da ya san su ba, shine mahaifin Twins ɗina? Abun kamar almala Uncle." Ahmad ya yi murmushi yana jin zuciyarsa ta masa wasai ya ce "Ikon Allah ya fi ƙarfin komai Princess." Ta yi shiru kawai tana kallon sa, ta kasa ɗauke idanunta daga kansa. Ya d'age mata gira ɗaya ya ce "Wannan kallon fa?" Da sauri ta rufe fuskarta da hannunta tana murmushi, wani irin farinciki take ji a cikin ranta, kamar ta tashi tai ta tik'ar rawa haka take ji. Ya yi ƙasa da murya ya ce "Ya zaki rufe mun maganin ciwon idona? Please ki buɗen wannan kyakkyawar fuskar da idanuna ba sa gajiya da kallon ta" Ta buɗe fuskar amma sai ta yi ƙasa da kanta, wata irin kunyarsa take ji ba kaɗan ba. Ahmad da yake jin kamar ya rungume ta saboda wutar k'aunarta da take ƙara ruruwa a ransa ya ce "Now tell me, me ya faru bayan rabuwar mu." Ba tare data d'ago ba ta ce "Ka fara faɗa mun naka, da yanda har ka yi aure ka....." Sai kuma ta yi shiru. Ya ce "Uhm, ƙarasa faɗar abun da zaki ce mana." Ta ɗan turo baki ta ce "Babu." Ya gyara zama tare da faɗin. "Ranar da muka haɗu dake last, bayan na koma gida na kasa aiwatar da komai saboda tunanin ki, na farko ina tunanin kar a miki wani abu a gida saboda Uncle ɗinki ya ganmu tare. Na biyu kuma wanda shi ya fi sani cikin damuwa komawa Abuja da zan yi in yi nesa dake. Tun kafin ranar nake wannan tunanin, da farko na ɗauka tausayin ki ne yasa nake wannan tunanin, amma daga baya na gane na shak'u dake shak'uwa mai tsanani. A ranar ko baccin kirki ban iya yi ba saboda tunani. Da safe bayan na gama shiryawa kafin na fita sai da na je wajen gidanku ko Allah zai sa in ganki, amma ko me kama dake ban gani ba. Gashi ni ban san gidanku ba tunda bana ƙarasawa a hanya muke rabuwa. Haka na dawo gida jiki a sanyaye, gashi washegarin ranar ne tafiyata Abuja. Tun da na je Masallaci na yi sallar Azhar har aka kira la'asar ban koma gida ba, ina ƙofar gida ina jiran ki, ki zo wucewa, ranar ko abincin kirki ban iya ci ba. Bayan na yi Sallar la'asar na je gurin mai kayan miyan da kike siya a gurinsa na masa kwatancenki na tambaye shi ko kin zo siyan kayan miyan ranar ya ce mun A'a baki zo ba. Hankalina fa ya tashi matuƙa na ƙara komawa layinku ko zan gan ki, na tambayi wasu yara ko sun san gidanku suka ce mun bama su san ki ba. Ranar dai haka na kwana cikin tsananin damuwa. Washegari tun safe na wuce Abuja zuciyata babu daɗi ko kaɗan. Wata na uku da komawa Abuja na tafi India na yi wani course na shekara ɗaya, bayan na dawo da some weeks na fara aiki. A'isha ƴar gidan wani abokin Daddy ce, na santa sosai suna zuwa gidanmu tun kafin mu fara soyayya da Ita. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa, shine abun ma da ya ja hankalina a game da Ita. Mun kai 3 years muna soyayya kafin mu yi aure, dan sai da na jira ta ƙarasa karatunta na degree. Na ji daɗin zaman aure da A'isha sosai, saboda macece mai haquri da biyayya ga ilimin addini, ta bani kulawa da kowanne ɗa Namiji yake fatan samu a gurin Matarsa ta sunna. A'isha ta san labarinki tass a gurina, saboda yawan zancen ki da nake mata, a duk lokacin da na mata zancenki sai ta ce mun ita dai tana son ta ga Neehal ɗin nan, Allah ya nuna mata ke kafin ta mutu. Ashe baza ku taɓa haɗuwa domin a haihuwar twins Allah ya mata rasuwa. Mutuwar A'isha ta dake ni ba kaɗan ba, sanadiyyar mutuwar ta hawan jini ya kama ni saboda damuwar da na saka a raina da yawan tunani. Idan na kalli twins ne kawai nake jin sanyi a raina. Afrah suna biyu ta ci a gurina, da sunan Ummi da sunanki, Amrah kuma A'isha na yiwa takwara. A hankali radadin mutuwar A'isha ya fara raguwa a zuciyata, sai dai up to now ban ƙara kallon wata mace da sunan soyayya ba balle na yi tunanin ƙara aure, shekara biyar kenan da rasuwar A'isha. Yarana sune farincikina, su suke ɗebe mun kewar Mahaifiyarsu, kuma tun suna jarirai ni na riƙe su, Ummi ta so ɗaukar su ita da Ammi na ce bazan iya yin nesa da ƴaƴana ba su yi haquri zan riƙe su a gurina. Aka samo mun wata dattijuwa (Baaba Talatu) ita take taya ni kula da su, tun suna jarirai har time ɗin da aka sace su." Ya sauke numfashi tare da kallon Neehal cikin ido ya ce "Duk waɗannan abubuwan da suka faru, kamanninki da tunaninki suna manne a zuciyar *Ahmad Aliyu Bulama*. Lokaci zuwa lokaci ina kallon pics ɗinki wanda na adana su a Email ɗina. Ni ba ma'abocin kallon TV ba ne, dan tun ina ƙarami na kallo ba ya gabana, shi yasa ban san ki ba. Na yi mamaki sosai da Aunty Mardiyya da Zahra suka ce mun shahararriyar ƴar jarida ce ke domin ban taɓa sani ba. Dan da nasani kafin yanzu da tuni na binciko inda kike na zo mun haɗu. Tun Ranar da na bar Kano ban ƙara zuwan ta ba sai last zuwan da mukai dalilin su Afrah. Ina sauka a cikin garin Kano ke kika fara faɗo mun a cikin raina, amma ko kaɗan ban yi tunanin ganinki a nan kusa ba, duk tunani ma zuwa yanzu kin yi aure. Lokacin da na yi 2 eyes dake yanayin dana tsinci kaina a ciki na shock ɗin ganin ki ba zai misaltu ba, na kasa banbance tsakanin bayyanar su Afrah da ganin ki da nayi a bazata wanne ya fi sakani farinciki, sai dai rashin gane ni da baki yi ba shi ya kashe mun gwiwa, kuma a ranar ba mu da ishashshen time ɗin zan miki bayanin da zaki iya tunawa da ni. Tunda muka koma gida tunanin ki ya hanani sakat, so nake kawai na ƙara saka ki a cikin idona, amma saboda yanda mutane suke zuwa mun murnar ganin su Afrah that is why ban samu dama na zo ganin ki ba sai yau." Ya yi shiru yana sauke numfashi. Neehal ta d'ago da kanta wanda yake ƙasa tunda ya fara bata labarin, cikin sanyin jiki ta ce "Allah ya ji k'an Aunty A'isha ya gafarta mata." Ahmad ya ce "Amin ya Allah." Suka yi shiru na wasu mintuna kowa da tunanin da yake a cikin ransa. Ahmad ne ya katse shirun da faɗin "A zak'e nake in ji labarin abun da ya faru da ke bayan rabuwar mu, gashi kuma na ga magriba ta gabato." Neehal ta ce "Next time idan muka haɗu sai na baka labarin, dan yana da tsayi." Ya ce "Gobe zan wuce Abuja, amma kafin na tafi zan biyo ta nan Insha Allah." Neehal ta ce "Allah ya kai mu." Ya ce "Amin." Ta ce "Bari na zuba maka abinci, tun d'azu muna ta hira baka ci ba." Ya ce "No, kar ki zuba am full." Ta shagwab'e fuska tare da turo baki gaba. Ya yi murmushi ya ce "Kin san me?" Ta girgiza masa kai ita a dole fushi take da shi, tun da ba zai ci abinci ba. Ya ce "Kin ƙara kyau sosai da zaƙin murya, sai dai shagwab'arki mai kyau tun ta yarinta tana nan har yanzu, tun last zuwan da muka yi na lura da hakan, sai nake tuno da, idan na zaunar dake a gidan Mamy, sai ki shagwab'e mun ki ce, Uncle please zan tafi gida, idan na daɗe Aunty zata dake ni." Ta rufe fuska tana murmushin da ya kufce mata ba tare da ta shirya masa ba saboda yanda ya yi maganar yana kwaikwayon muryarta. Shima ƴar dariya ya yi wadda ta ƙara fito da zallar kyawunsa. Wani irin nishad'i yake ji yau a cikin zuciyarsa, wanda rabon da ya ji irinsa tun kafin rasuwar A'isha. Neehal ita ce first love ɗinsa a duniya, a kanta ya fara sanin menene so. Wayarta dake gefenta ce ta shiga vibrate, ta duba ta ga Sadik ne yake kirancta. Ta ɗan saci kallon Ahmad ta ga ita yake kallo, sai ta ji baza ta iya d'aga wayar a gaban sa, ta ƙi pick. Tana katsewa wani kiran ya ƙara shigowa, shima har ya katse bata d'aga ba. Ahmad ya ce "Ba kiran ki ake ba, ki d'aga mana." Zata yi magana ta ji shigowar sak'o cikin wayar, ɗauka ta yi ta cire key ta duba, ganin Sadik ne ta shiga karantawa a zuciyarta. _Where Are you sweetheart inata kiran ki baki ɗauka ba, gani kuma a cikin gida na zo na ganki._ 'Ya Sadik kuma da sakaliyar yammar nan?' ta faɗi haka a cikin ranta. Reply ta masa da faɗin _Ina abu ne, na zo zan yi pick kafin na ɗauka ta katse, Okay ka ƙaraso ciki mana._ Ta ajiye wayar tare da d'agowa ta kalli Ahmad wanda ya ƙura mata ido. Ta shagwab'e fuska ta ce "Ni fa kallon nan naka yana sa in ji wani abu a jikina, Please ka daina." Ya ce "Idan kina kusa da ni ba zan taɓa iya daina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki ba Princess." Ta yi ƙasa da kanta ba ta ce komai ba. Ya ɗauki wayarsa dake kan cinyarta ya shiga Camera ya fara ɗaukarta a hoto ba tare data sani ba. Ta d'ago zata yi magana ya katse ta sauri da faɗin, "Please Princess ko ɗaya ne." Ta yi murmushi saboda yanda ya wani marairaice fuska. Ya ce "Yawwa, Wow da murmushin ya fi kyau." Ya ƙarashe maganar tare da ɗaukarta hoton tana murmushin. Dai_dai nan Ameen ya buɗo ƙofar falon ya shigo...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *4️⃣5️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ...........Washegari tun kafin 7 na safe Neehal ta bar gida zuwa gurin aiki. Kafin ƙarfe ɗaya kuma ta dawo gida. A gajiye ta dawo ga yunwa dake nuk'urk'usar hanjin cikinta dan babu abun da ta ci ta tafi gurin aikin, da ta je can ma ba ta ci komai ba, gashi jiya kafin ta kwanta ta so cin abinci amma wayar da suka yi da Ahmad da Sadik yasa bata ci ba, saboda dare da ya yi. A falo ta ajiye jakarta ta zarce kitchen dan samarwa kanta abun da zata ci. Tea ta fara haɗawa ta sha, bayan ta samu nutsuwa ta fara tunanin abun da zata girka mai sauƙi for lunch, dan Mama bata nan ta je aiki, sai 2 zata dawo. Indomie ta fara dafawa ta ci a cikinta sannan ta ɗora girkin ta fito daga kitchen ɗin dan zuwa ta yi Sallah ta watsa ruwa a jikinta. A falo ta tarar da Zulai tana kallo, ta zauna tana duban Zulan ta ce "Aunty Zulai sannu da gida." Zulai ta juyo cikin fara'a ta ce "Yawwa Neehal, kin dawo ashe? Muna daki muna ta barci ban ma ji shigowar ki ba, yanzu ma tashi na yi nay Sallah, na ce bari dai na fito in yi kallo." Neehal ta ce "Ban ma jima da dawowa ba, bari na ƙarasa upstairs na yi Sallah, na ɗora girki dan Allah ki duba mun kafin na sakko." Zulai ta ce "Shikenan a sauko lafiya." Neehal ta ɗauki jakarta ta wuce sama. Wanka ta fara yi sannan ta fito ta yi sallah, bayan ta idar tana cikin shiryawa ta ji ana knocking ɗin ƙofar ɗakin. "A shigo." Ta faɗa ba tare data tambayi waye ba. Zulai ce ta shigo bakinta ɗauke da Sallama. Ta amsa mata. Zulai ta ce "Kin yi baƙo." Neehal ta ce "Waye?" Zulai ta ce "Babansu Afrah ne, yana falon ƙasa." Ta ce "Okay ki ce masa gani nan zuwa." Zulai ta amsa da "Toh." Sannan ta juya ta fita. Ta ƙarasa simple d'aurin d'ankwalin da take yi, sannan ta ɗauki mayafinta ta yafa a ƙafaɗa ta fice. Tunda ya jiyo taku ana sakkowa ya ƙurawa step ɗin ido cikin zak'uwa da son ganin ta. Cikin nutsuwarta ta ƙaraso cikin falon kanta a ƙasa saboda kallon da yake jifan ta da shi. Ta zauna a kujerar dake gefen sa a hankali ta ce "Ina yini Uncle." Ya ce "Lafiya k'alau Princess." Ta ce "Ya Mamy?" Ya ce "Tana nan k'alau, Mama bata nan ne?" Ta ce "Eh tana gurin aiki." Ya jinjina kai tare da miƙewa ya dawo gabanta ya zauna a saman carpet." Ta d'ago kanta da sauri ta ce "Uncle ka koma kan kujera ka zauna mana." Ya ce "No, barni a nan, sai nafi ganin wannan kyakkyawar fuskar taki yanda ya kamata." Ta ce "A kan kujerar ma fa zaka gani Uncle." Ya ce "Ba kamar nan ba princess." Saukowa ƙasan ta yi itama ta zauna a ɗan nesa da shi ba ta ce komai ba. Ya yi murmushi ya ce "Kin yi kyau sosai Princess!" A hankali ta ce "Thank you." Ya kwaikwayi muryarta ya ce "Nima thank you." Ta yi ɗan murmushi ta ƙara yin ƙasa da kanta, kunyarsa take ji sosai har yanzu moment ɗinsu na jiya ya kasa ɓacewa daga zuciyarta. Zulai ce ta ƙaraso inda suke hannunta ɗauke da tire mai ɗauke da drinks ta ajiye a gaban su. Ahmad ya dube ta ya ce "Na gode." Ta ce "Babu komai yallaɓai." Sannan ta juya ta koma kitchen dan ƙarasa girkin da Neehal ta ɗora. Neehal ta ɗan matsa kusa da tire ɗin ta ɗauki juice ta tsiyaya masa a cikin glass cup, sannan ta matso kusa da shi ta miƙa masa ba tare da ta kalli fuskarsa ba. Ƙin karɓa ya yi ya tsaya yana kallon fuskarta, ta d'ago ta kalle shi cikin sa'a suka haɗa ido, kashe mata ido ya yi wanda yasa tay saurin yin ƙasa da idonta tana turo baki gaba. Ya karɓa cup ɗin data miƙo masa tare da yin murmushi mai sauti, dama so yake ta kalle shi su haɗa ido kuma ya yi nasara. Ta koma inda take d'azu tana satar kallon sa ƙasa_ƙasa, shi kuma yana kurb'ar juice ɗinsa hankali kwance. Ya yi mata kyau ba kaɗan ba, yana sanye cikin ƙananan kaya wanda suka amshi jikinsa, sassayan k'amshinsa mai daɗin shak'a ya cika mata hanci. 'Yana nan a ɗan gayun sa up to now' ta faɗi haka a ranta. Ya sha juice ɗin fiye da rabin wanda ta zuba masa sannan ya ajiye cup ɗin, ya dube ta ya ce "Idan kin gama kallon nawa sai ki cika mun alƙawari na." Ta ɓata fuska ta ce "Ni ba kallon ka nake ba." Ya yi murmushi ya ce "Tom Shikenan, now start from where we stopped yesterday." Ta ce "Da me fa?" Ya mata kallan ƙasan ido ya ce "Your story mana." Ta ja numfashi a hankali tare da runtse idonta, sannan ta fara ba shi labarin abun da ya faru bayan rabuwar su a tak'aice, daga time ɗin data farka ta gan ta a asibiti Uncle Usman ya kai ta up to now, sai dai ta ɓoye masa abu ɗaya a labarin nata, shine kashe su Anwar da akai, ta ce masa dai kawai rasuwa suke. Bai katse ta ba, har sai da ta kai aya ta yi shiru da kanta. Ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin bata kuma shan wata wahalar ba bayan rabuwar su, sai ma cigaba na rayuwa data samu. Abu ɗaya ne ya ɗan taɓa masa zuciya a labarin nata har ya ji tausayinta over da ta ce masa samarinta biyu duk sun rasu, dan ya san ɗacin mutuwar masoyi tunda ya ɗanɗana da A'isha ta rasu. Cikin sanyin murya mai cike da alhini ya yiwa su Anwar da Jameel addu'ar dacewa da samun Rahamar Ubangiji. Neehal ta amsa da "Ameen Na gode, ƙarfe nawa zaka wuce Abujan?" Ya ce "Ƙarfe Shida na yamma." Ta ce "Alright, ina son ka kai ni da gaishe da Mamy idan babu damuwa." Ya ce "Kamar kuwa kin san tana son ta gan ki, dan na bata labarin ki." Neehal ta ce "Har ka bata labarina?" Ya ce "Eh mana, tun a waya ma kafin na zo na ce mata aike kika tsinci su Afrah." Ta ce "Kuma ta tuna ni?" Ya ce "Ina mata bayanin ki ta gane ki." Ta jinjina kai sannan ta miƙe tare da faɗin "Ina zuwa." Upstairs ta hau ta ɗauko wayarta ta kira Mama, dan ta sanar mata za su je gidan Mamy, amma Maman bata ɗauka ba. Ta duba agogo ta ga 2 ta wuce, hakan yasa ta yi tunanin may be Maman tana hanya ne, dan in tana driving bata ɗaukar waya. Sauran wayoyinta ta ɗauko ta zira a aljihun doguwar rigar jikinta, kasancewar rigar mai aljihu ce. Ta fito ta dawo downstairs, kitchen ta shiga ta duba ko Zulai ta ƙarasa abincin ta zubawa Ahmad. Ganin ta kammala har ta bar kitchen ɗin ma, sai ta ɗauko plate ta zuba masa, ta rufe da wani plate ɗin ta ɗora akan tire. Sannan ta ɗauko bowl ta zuba masa kayan salad a ciki, shima ta ɗora akan tire ɗin ta saka spoon ta ɗauko ta fito. Yana ƙasa a zaune har time ɗin bai koma kan kujera ba, ta ajiye tire ɗin a gabansa ta ce "Ga abinci Uncle." Ya d'ago yana duban ta ya ce "Thank you so much." Neehal ta juya ta bar falon dan bashi guri ya ci abincin ta shige ɗakinsu Dije. After some minutes ta hango Mama ta window ta shigo falon suna gaisawa da Ahmad. Ta miƙe ta fito falon. "Welcome Mama." Ta faɗa cikin murnar dawowar Maman. Mama ta ce "Yawwa Neehal, ina hanya na ga kiran ki." Neehal ta ce "Eh, dama za mu je gidan Mamy ne da Uncle Ahmad shine na kira na faɗa miki." Mama ta ce "Okay to sai kun dawo ku gaishe ta." Ta juya ga Ahmad wanda kansa ke ƙasa tun shigowar Mama ta ce. "Idan kun dawo ka shigo zan baka sak'o ka kaiwa Ummi." Cikin girmamawa ya ce "Toh Mama Insha Allah." Mama ta wuce sama, ita kuma ta ƙarasa inda yake. Ta kalli tiren abincin data ajiye ta ga ko taɓa shi ba ai ba, yanda ta bar shi haka yake. Ta ɓata fuska sosai ta ce "Uncle baka ci abincin ba ai." Ya miƙe cikin son kawar da zancen abincin ya ce "Tashi mu tafi." Ta miƙe bata ce komai ba ta je ta yiwa sallama sannan ta sakko suka tafi. Har ya fice daga falon, a waje ta tarar da shi suka jera suka ƙarasa parking space. Ya buɗe mata motar da ya zo a cikin ta ta shiga, bayan ya rufe mata murfin ya zagaya ya shiga driver seat ya kunna Motar suka fice daga gidan. Har suka ƙarasa gidan Mamy babu wanda ya ce kala a cikin su, sai cool music ne yake tashi a cikin motar. Ita fushi take a kan ya ƙi cin abinci, shi ma kuma yasan laifinsa shi yasa shi ma ya yi shiru, ya barta ta ɗan huce sai ya rarrashe ta. Bayan ya yi parking ta buɗe murfin Motar ta fito, shi ma ya biyo bayan ta ya fito. Ya zagayo inda take tsaye a jikin Motar ya kama hannunta yana kallon ta ya ce "Princess what happened?" Ta girgiza masa kai tana ƙoƙarin k'wace hannunta. Ya sakar mata hannun tare da matsowa daf da ya marairaice ya ce "I'm sorry Dear." Ta sauke numfashi ganin kamar zai rungume ta, ta ce "Babu komai fa Uncle." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa tana murmushi. Ya sauke ajiyar zuciya tare da kama hannunta suka nufi cikin gidan, ta yi ƙoƙarin k'wace hannun nata amma ya ƙi sakar mata. Mai aikin Mamy ce ta zo ta buɗe musu ƙofa bayan ya danna beil. Neehal ta samu ta k'wace hannunta ta bi bayan sa suka shiga cikin falon da sallama. Ahmad ya nuna mata kujera ya ce ta zauna, ta zauna, amma a ƙasa kan carpet. Ba jimawa Mamy ta fito daga ɗakinta mai aikinta da ta kira ta na biye da ita a baya. Da fara'a haɗe da murna Mamy ta ce "Sannu da zuwa yarinyar kirki, d'iyata ashe zan ƙara ganin ki?" Neehal ta yi murmushi cike da kunya ta gaishe da Mamy. Mamy ta amsa mata tare da rungume ta a jikinta cikin kulawa, tana tambayar ta su Mama. Neehal ta ce "Tanan nan lafiya, ta ce a gaishe ki." Mamy ta ce "Ina amsawa." Ahmad ya miƙe yana duban Mamy ya ce "Bari in je in dawo tunda yau bata ni kike ba." Mamy ta ce "Sai ka dawo, ina ta murnar ganin Ƴata ina zan tuna da kai." Ahmad ya ce "Shikenan ai." Sannan ya kalli Neehal ya kashe mata ido ya ce "Sai na dawo Princess." Bata iya ce masa komai ba saboda kunya har ya fice. Mai aikin Mamy ta kawowa Neehal abinci da drinks da su snacks. Mamy kam sai nan_nan take da Neehal. Da ƙyar ta tilasta mata ta tsakuri abinci cikin jin kunya. Mamy kam sai janta take da hira. Da lokacin Sallar la'asar ya yi ta kai ta bedroom ɗinta ta yi Sallah. Bayan ta idar ba jimawa Ahmad ya dawo gidan, ta fito suka tafi. Mamy ta bata leda mai ɗauke da turaruka da kayan shafe_shafe, shi ma dak'yar ta karɓa dan Ahmad ne ma ya karɓar mata. Kafin biyar sun ƙarasa gida, ta fito ta bar shi a Mota dan karɓo masa sak'on da Mama ta ce zata ba shi. Sai da ɗauko tsarabar data yiwa su Afrah sannan ta biya ɗakin Mama dan karɓar sak'on Ummi. Mama ta bata wata leda wadda bata san mene a ciki ba ta kay masa, ta buɗe bayan Motar ta ajiye sannan ta shiga cikin motar kamar yadda ya ce mata, tana shiga ya kulle motar sannan ya tasa ta a gaba da kallo, ganin lokaci yana tafiya ta ce "Uncle kar fa time ya ƙure baka tafi ba, kuma ka ce sai ka koma gidan Mamy kafin ka wuce airport." Ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce "Ban gaji da kallon ki ba ko kaɗan Princess, kamar na d'aga tafiyar haka nake ji." Ta juya masa ido ta ce "Ni dai nafi son ka tafi yau, saboda na san yanzu twins ɗina suna can suna damuwar rashin ganin ka two days." Ya ɓata fuska ya ce "Kin fi son yaranki akaina kenan?" Tana dariyar tsokana ta ce "Eh mana." Ya marairaice fuska kamar wani maraya ya tallafi fuskarsa da hannayensa biyu ya tsura mata ido. Ta ce "Me nene?" Ya nuna mata kanta da hannunsa, a shagwab'e ta ce "I'm sorry My Uncle." Ya lumshe ido ya buɗe bai ce komai ba, seriously kamar ya fasa tafiyar saboda ita haka yake ji. Amma ya san hakan ba zai yiyu ba, saboda aikinsa da kuma yaransa da su Ummi. Ya duba agogon hannunsa sannan ya dube ta ya ce "Zan wuce Princess." A sanyaye ta ce "Sai yaushe?" Dan itama ta fara jin ba daɗi saboda tafiyar da zai yi. Ya ce "Next week idan na samu chance, idan kuma ban zo ba sai upper week." Ta ce "Amma zaka taho mun da Yarana in gan su ko?" Ya ɗan matso kusa da ita ya ce "Idan ma cewa kikai in dawo miki da su gurin ki gaba-ɗaya da zama zan iya Princess." Ta kalle shi da sauri cikin mamakinsa, ya gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa, ya ƙara da faɗin "In dai a kan farincikin ki ne Princess babu abun da ba zan iya ba." Cikin murna ta ce "To ka dawo mun da su Please ka ji Uncle?" Ta yi maganar da iya gaskiyar ta har cikin ranta. Ya yi murmushi ya ce "An gama Princess, next zuwan da zan yi Insha Allahu zan taho miki da su da kayan su gami da komai na su." Cikin jin daɗi ta ce "Thank you so much Uncle." Ya ja dogon hancinta ya ce "You deserve everything from me my Baby." Ta yi murmushi ba ta ce komai ba, ya kama hannunta tare yi mata pick a kuncinta, so romantic voice ya ce "Bye Princess I will miss you." Ta lumshe idonta murya ƙasa_ƙasa ta ce "Allah ya kiyaye hanya ya kai ku lafiya." Ya amsa da Ameen tare da sakar mata hannunta. Ta buɗe murfin Motar a hankali ta fito cikin sanyi jiki, bayan ta rufe ta d'aga masa hannu. Yana murmushi ya ce "I love You!" Ta juya da sauri ta nufi part ɗin Mama cikin matsananciyar kunyar sa, zuciyarta cike fal da murnar ya ce zai dawo mata da twins ɗinta su cigaba da zama a gurin ta........✍️ _*A yi haquri da wannan hilis*_ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *4️⃣6️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* .........Mama tana kitchen tana girkin dare, Neehal ta shiga kitchen ɗin ta rungume Mama tana murmushin farinciki. Mama ta ce "Lafiyarki kuwa zaki zo ki ɗane mun jiki, ina cikin aiki?" Neehal ta bar jikinta cikin murna ta ce "Mama Uncle Ahmad ya ce zai dawo mun da su Afrah." Mama tabar abun da take ta juyo ta fuskance ta, ta ce "Kamar ya fa?" Ta ce "Mama zai dawo mun da su, su cigaba da zama a gidan nan." Mama ta ce "Uhm, na san Ahmad zai yi haka ne saboda da ke, ni kuma ba zan taɓa yarda da hakan ba, saboda Ahmad da Family ɗinsu sun fi mu buƙatar twins a kusa da su, especially ahalin mahaifiyarsu data rasu, tunda su suke kallo su ji daɗi a madadin mahaifiyarsu." Neehal ta shagwab'e fuska ta ce "Mama wlh na yi kewar twins over, kawai ina daurewa ne saboda karki mun faɗa ki ce ina damuwa." Mama ta ce "Nima ai na yi kewar su, sometimes ina zaune sai inga kamar za su zo su haye mun jikina kamar yadda suka saba, amma ya za mu yi dole mu haqura mu barwa danginsu su." Neehal kamar zata yi kuka ta ce "To ai za suna zuwa gurin Family ɗin nasu akai_akai." Mama ta ce "Sai kuma ki yi, amma ba dani za ai wannan son zuciyar ba." Ta juya ta cigaba da aikin ta. Neehal ta matso jikin Mama kamar zata yi kuka ta ce "Ki yi haquri Mama idan ranki ya ɓaci, zan je masa ya fasa dawo su ɗin kawai." Mama ta sassauta murya ta ce "Shikenan kar ki mun kuka, je ki ki huta idan na gama girki za mu yi magana." Neehal ta ce "Bari in taya ki aikin." Mama bata hana ta ba suka ci-gaba da aikin tare Mama na ƙara yi mata Ƴar nasiha akan rayuwa. Bayan Sallar isha'i suka yi waya da Sadik ya sanar mata sun isa ibadan lafiya. Ba su yi wata doguwar waya ba saboda Sadik ɗin yana tattare da gajiya yana son ya kwanta ya huta. Bayan sun gama wayar ta nufi part ɗin Daddy, two days ba ta je sun yi hira ba, da safe idan ta je gaisawa kawai suke saboda yana sauri zai fita. Sai da goma ta wuce Mama ta koro ta, ta ce hirar ta isa haka dare ya yi kuma. Bayan ta dawo ɗaki kamar zata kira Ahmad ta ji yaa ya sauka sai kuma ta fasa, ta kunna data kawai ta shiga media. Haka kawai ta ji Ameen ya faɗo mata a rai da yanayin data gan shi jiya na ɓacin rai, har tay bacci bai daina faɗo mata a rai ba. Washegari ma fitar safe ta yi zuwa gurin aiki, data dawo kamar time ɗin jiya ta shirya ta tafi gidan Aunty A'isha, sai bayan Magriba ta dawo gida. Tana cikin yin Sallar isha'i ta ji wayarta na ringing, bayan ta idar ta yi lazimi ta ɗauko wayar domin ta duba mai kiran nata. Wani kiran ne ya ƙara shigowa, 'Uncle Ahmad' sunan data gani yana yawo akan screen ɗin kenan. Ta d'aga tare karawa wayar a kunne, muryar su Afrah ta ji kowa na rige_rigen kiran sunan ta, "Aunty! Aunty!" Cikin farinciki ta ce "Na'am my kids ya kuke?" Suka haɗa baki gurin faɗin "Lafiya k'alau." Neehal ta ce "Ya school da Islamiyya? Kuna dai karatu sosai ko yaran kirki?" Afrah ta ce "Eh Aunty, exam ma zamu fara next week." Ta ce "Allah ya ba da sa'a Daughter, ina Ummi da Aunty Zahra?" Ta ce "Suna gida." Neehal ta ce "Ki ce ina gaishe su." Amrah ta zo ta karɓe wayar daga hannun Afrah tana faɗin "Aunty ki yi hirar da ni nima, ai kin gama da ita ko?" Neehal ta ce "Toh Daughter ina Daddy?" Amrah ta kalli Ahmad dake zaune yana sauraren hirar da suke, da yake a handsfree ya saka wayar. Ya gyaɗa mata kai, Amrah ta ce "Gashi nan." Ahmad ya ɗauki wayar ya ce musu su je su cigaba da Assignment ɗinsu. Ya kara wayar a kunnensa bai ce komai ba. Neehal ta ce "Ina yini." Ya ce "Bana amsawa." Tun ma kafin ya faɗa mata abun da ta masa ta san laifinta, dan haka ta ce "I'm sorry bazan kuma Uncle, ya ka je gida?" Ya ce "Lafiya k'alau, ya Mama da Daddy?" Ta ce "Suna nan k'alau." Ya ce "Masha Allah." Tare da kwanciya akan gadon da yake kai, murya ƙasa_ƙasa ya ce "Princess ki bani labari mai daɗi mana." Ta ce "Uhm, kasan me Uncle?" Ya ce "A'a." Ta yi shiru, ya ce "Uhm? ina jin ki?" Ta ce "Ka fasa kawo mun su Afrah, ka bar su a gurin Ummi ta cigaba da riƙe su kawai." Ya ce "Why?" Ta ce "Mama ta ce, kun fi mu buƙatar su a kusa da ku." Ta faɗa masa duk yanda suka yi da Maman. Ya yi murmushi ya ce "Allah sarki Mama, ta hango abun da mu ba mu hango ba, kuma ta fi mu gaskiya." Neehal ta ce "Amma idan sun yi hutu zaka na kawo mun su." Ya ce "Insha Allah Princess, kafin kuma mu yi aurenmu su dawo hannunki da zama gaba-ɗaya." Ta yi shiru tana maimaita kalmar Auren daya ambata a cikin ranta, gabanta na fad'uwa. Ya ce "Hello Princess!" Ta sauke numfashi ta ce "Na'am Uncle." Ya ce "Kin yi shiru." Ta ce "Ba komai." Sun ɗan taɓa hira sannan suka yi sallama..... *SAFEENAH* Tun ranar da su Afrah suka gida anata murnar ganin su yan'uwa da abokan arziki, yayin da a ɓangaren Safeenah kuwa akasin haka ne. Dan wani irin tashin hankali mara misaltuwa ta tsinci kanta a ciki, lokacin ɗaya cikinta ya kaɗa ta tsure sai toilet. Da yake sai a washegarin ranar da su Ahmad suka koma da safe sannan suka samu labarin bayyanar su Afran. Ranar wuni ta yi a ɗaki cikin zullumi da fargaba, lokacin ɗaya ta zabge ta rame ta fita daga cikin hayyacinta. Gashi tana ta kiran wayar ƙanwarta Saudart bata shiga wayar a kashe. Ranar da su Afrah suka zo gidan ta ja su ɗaki ta tambaye su cikin bugar ciki, yanda aka ɗauke su. Afrah data fi surutu ta ce mata "Suna falo suna kallo, wasu suka zo fuskokinsu a rufe suka ɗauke su." Tashin hankalin ta ne ya ƙaru, tunda gashi yaran za su iya bayanin yadda aka sace su idan an tambaye su, hakan yasa a washegarin ranar ta yi sammako ta tafi Zariya bayan ta yiwa mahaifiyarta ƙaryar Saudat ɗin ce bata da lafiya zata je duba ta. Tana zuwa Zariya ta ƙara tarar da wani tashin hankalin, domin kuwa kwance a gadon asibiti ta tarar da Saudat cikin mummunan yanayi, bata ma san waye a kanta ba. Ƙanwar Saudat ɗin ce take sanar mata wasu ƴan_daba ne suka mata duka ba tare da an san me ta yi musu ba. Amma ana ta bincike ana ce ƙoƙarin gano ko su waye. Cikin fitar hayyaci Safeenah ta dawo gida da daddare, tana zuwa ta kwanta zazzaɓi rigijib ya rufe ta saboda tsananin tashin hankali. Tana tsoron kar ta yi biyu babu, ita bata samu soyayyar Ahmad da take bala'in son sa ba gashi kuma Ƴaƴansa sun dawo gare sa cikin k'oshin lafiya. Ta yi da na sani da nadama mara amfani data biyewa rud'in shaid'an da zugar ƙawa har ta kaita ta baro ta, yau gashi ta barta a ciki, duk da itama gata can kwance cikin mawuyacin hali, amma ita ta san idan asirinta ya tonu kashe ta za'a yi. Tunda kwangilar kisan kai ta bayar a yi. Ta kira Gaye wanda yasa yaransa suka masa aikin ɗauke su Afrah amma wayar ta shiga bai ɗauka ba. Sai bayan kwana biyu ta ga text ɗinsa ya turo mata, inda yake sanar mata. Shine yasa yaransa suka yiwa Saudat dukan mutuwa, saboda ta yi masa barazanar zata tona masa asiri tunda ya ci amanar su a aikin da suka ba shi. Itama matuƙar ta yi ƙoƙarin aikata gangancin da Saudat ta aikata sai ya mata abun da ya fi wanda ya yiwa Saudat. Ƙarshen tashin hankali da damuwa Safeenah ta shiga da ganin wannan text ɗin, amma ta yiwa Allah godiya da ba'a kashe su Afrah ba, may be in an tashi yi mata hukunci a mata da sassauci. J inya sosai ta kwanta har sai da ta kaita ga kwanciya a gadon asibiti....... A cikin week ɗin nan Neehal ta je gidan Aunty Sadiya kamar yadda Mama ta umarce ta, ta kai mata ziyara. Aunty Sadiya ta yi amfani da wannan damar ta ƙara yiwa Neehal tambayoyi a game da binkicen da take na kisan su Anwar, kuma Alhamdulillahi ta ƙara samun wasu evidence ɗin. Ranar Friday kamar yadda Sadik ya ce suka dawo lafiya daga Ibadan. Delicious sosai Neehal ta haɗawa masa na tarb'ar sa, ta bayar aka kai masa har gida, tunda bai samu zuwa gurinta ba saboda sai yamma lik'is suka dawo. Sai washegari Saturday ya zo suka sha hirar su. A kwanakin nan da suka wuce kullum Neehal sai sun yi waya da Ahmad every Morning and Night. Ranar Sunday tun ƙarfe goma sha ɗaya na safe ta shirya dan zuwa gidan Uncle Umar bisa tilastawar Mama. Tana aikin turo baki gaba ta shiga ɗakin Mama dan yi mata sallama. Mama ta dube ta, ta ce "To Haka zaki je musu hannu Rabbana." Ta ƙara ɓata fuska ta ce "Toh Mama me zan kai musu, ni fa dak'yar ma idan zan gane gidan." Mama ta ce "In kin je kar ki gane ɗin, ki ɓata, da duk da muke zuwa wani ne yake raka mu ai." Neehal ta ce "Toh Mama ai yanzu na daɗe ban je ba." Mama ta ce "Ko me zaki yi fa sai kin je, gwara ma ki bar wani kame_kame. Ki duba cikin drower ɗin can zaki ga kuɗi ki ɗauki 10k, sai ki biya ta Mall kafin ki tafi ki yiwa yaransu tsaraba." Ta ƙarasa ta ɗauki kuɗin tana faɗin "An gode." Mama ta ce "Kin haɗa kayan wankin da na ce ki haɗa?" Ta gyaɗa mata kai alamar eh. Mama ta ce "Har su bedsheet da labulayen?" Ta ce "Eh duk na haɗa." Mama ta ce "Shikenan ki wuce ki tafi, Allah ya kiyaye, ki gaishe su." Ta amsa tare da ficewa daga ɗakin. Two days bata ga Motar da take bin bayanta ba, ta yiwa Allah godiya tare da addu'ar Allah ya yi mata iyaka da koma su waye. Sai da ta biya ta siya musu kayan su chocolate duk da ta san yanzu su Iman sun girma, ta haɗa musu da turaruka da sabulan wanka, dan rasa me zata yi musu tsarabar da shi ta yi. Sha biyu da ƴan mutuna ta ƙarasa ƙofar gidan, ita kanta ta yi mamaki data iya gane layin, ko da yake layin ba shi da wahalar ganewa tunda miƙa ɗaya za kai daga titi har gidan. Da shagon wani mai aune_aune take gane gidan Uncle Umar da yake pacing ɗin gidan . Tabbas inda ta tsaya nan ne gidan, amma abun da ya bata mamaki ganin yanda gidan ya ƙara girma da kyau, filin kusa da gidan aka haɗe da gidan aka gine. A ranta ta ce "Ko sun tashi daga gidan ne? Ta day yi k'undunbala ta fito daga cikin Motarta hannunta ɗauke da ledar data musu shopping ta ƙarasa ta fara knocking ƙofar gidan. Muryar da ba za ta taɓa mantawa da ita ba a rayuwarta ta ji ta ce "Waye?" Ta sauke numfashi ta ce "Ni ce." Aunty Fauziyya ta ce "Turo ki shigo." Kanta a ƙasa ta tura ƙofar ta shiga tare da yin Sallama. Aunty Fauziyya da wata bak'uwar murya a gurinta suka amsa mata. Ta d'ago karaf suka haɗa ido da Aunty Fauziyya. Cikin mamaki Aunty Fauziyya ta ce "Neehal!" Ta ƙirƙiro murmushi ta ce "Na'am Aunty." Tare da bin ta da kallo ganin yanda ta zabge ta rame ta yi wani uban baƙi. Ɗayar matar da Neehal bata san ta ba cikin fara'a ta ce "Sannu da zuwa, ki ƙaraso mana." Neehal ta ƙarasa ta inda suke sannan ta ɗan tsugunna ta gaishe su. Ɗayar ce kawai ta amsa, Aunty Fauziyya kuwa mamaki ne ya sandarar da ita. Matar wadda ke sanye cikin atamfa doguwar riga tayi shar abunta ta ci d'aurinta ta kamo hannun Neehal ta yi hanyar sabon ginin da Neehal taga an yi a gidan tana mata lale marhabin. Sai a lokacin Aunty Fauziyya ta yi magana ta ce "To ai ba gurinki ta zo ba, tunda ba ma sanin ki ta yi ba, zaki wani janye ta daki." Matar ta juyo ta yiwa Aunty Fauziyya wani kallo sannan ta juya hannunta still riƙe dana Neehal suka shiga ƙofar part ɗin nata bayan ta buɗe. Ta nunawa Neehal guri a falon ta ce "Bismillah ki zauna bari in kawo miki ruwa." Neehal ta ɗan murmusa sannan ta zauna zuciyarta cike da tarin tambayoyi, ko shakka bata yi Uncle Umar ne ya ƙara aure, dan kwanaki suna waya da Uncle Usman ya fara mata zancen kuma sai wayar ta katse, data bi bayan shi kuma wayar ta ƙi shiga. Ita kuma bata wani riƙe zancen a ranta ba saboda a ganinta ba sabgarta ba ce. To an ma auren da Uncle Umar ya ƙara shine ya mayar da Aunty Fauziyya haka ta lalace ta zama kamar wata tsohuwa, ko kuma cuta ta yi... Dawowar matar falon ya katsewa Neehal tunaninta. Matar ta ajiye mata ruwa da juice a gabanta, sannan ta ƙara shiga kitchen ta dawo hannunta ɗauke da abinci. Neehal ta ce "Na gode." Matar ta ce "Babu komai, dan ma bamu san da zuwanki ba kawai ganinki mu kai, ai da an tanadar miki ko ɗan wani abu ne." Neehal ta ce "Babu komai, hakan ma Na gode sosai." Matar ta ce "Neehal ko Yar gidan Yayar Umar?" Bata jira amsar Neehal ba ta cigaba da faɗin "Ai na ji labarin ki a bakin Binta mak'ociyarmu da kuma shi kansa mai gidan namu." Neehal ta yi shiru cikin mamakin jin Uncle Umar ne har yake na zancen ta, ashe yana sane da ita kenan. Neehal ta ce "Ina su Iman fa ko basa nan?" Matar ta ce "Suna islamiyya, amma sun kusa dawowa, ɗaya tana yi zaki gan su sun dawo." Ta jinjina kai ta ce "Uncle fa? Sai dare yake dawowa shi ko?" Matar ta ce "Zaki iya ganinsa ya dawo anjima da yamma." Neehal ta yi shiru dan ba ma ta so su haɗu da shi. Haka matar ta yi ta jan Neehal da hira cikin fara'a da karamci, ta takurawa Neehal ta ci abinci tana mata tsiyar kamar ba gidansu ba ta ƙi sakin jikinta. Bayan ta ci abincin kaɗan ta yi Sallah sannan ta bawa Matar ledar data shigo da ita. Matar ta karɓa ta mata godiya ta debi abubuwan cikin ledar kaɗan ta bawa Neehal ta ce ta kaiwa Aunty Fauziyya sauran. Neehal ta fito ta tarar har lokacin Aunty Fauziyya tana tsakar gidan a zaune akan kujera yar tsugunne. Kallo ɗaya zaka mata ka fuskanci tana cikin damuwa. Aunty Fauziyya Ta shigar da Neehal ɗakinta cikin fara'ar data bawa Neehal mamaki. Bayan sun ƙara gaisawa ta ce "Neehal kin ƙara girma da kyau Masha Allah." Neehal ta yi murmushi kawai. Aunty Fauziyya ta cigaba da bin ta da kallo cike da sha'awa, a ranta tana faɗin kamar ba'a Nigeria take rayuwa ba saboda kyawun fatar ta da hasken ta, ga k'amshin ta mai daɗi daya cika mata hanci irin na ƴan gayu. Ta sauke ajiyar zuciya ta fara bawa Neehal labarin abubuwan da Uncle Umar yake mata yanzu dan ya ƙara aure. Wai wulaqancin yau daban na gobe daban suke mata shi da matar tasa, har da k'wallar ta. Neehal ta ce "Ta yi haquri kawai." Dan bata san me zata ce mata ba, bayan haqurin. Daga ƙarshe kuma ta fashe da kuka wai Neehal ta yafe mata ko alhakin ta ne yake bibiyar ta. Ta ce ita ta yafe mata, dama can bata riƙe ta ba. Sai kuma ta bata labarin ɓacin da Iman ta yi, wai yarinyar bata ji har bin maza take. Haka dai tay ta yiwa Neehal zance kamar wadda aka tambaya. Ita kuma duk sai ta ji tausayinta ya kamata har da zubar mata da hawaye. Suna cikin hirar su Iman suka dawo daga islamiyya, kallo ɗaya Neehal ta mata ta tabbatar da abun da mahaifiyarta ta faɗa. Yarinyar ta ci uban bleaching har da b'ular hanci, sai taunar cingum take ƙas_ƙas. Neehal tay ta mamakin ta a cikin ranta, yarinyar da bata fi 16 years ba amma ita ta yi wannan budewar idon haka. Ta ji ba daɗi sosai akan halin yarinyar, ko ba komai jininta ce bata so ta yi wannan lalacewar haka ba. Addu'ar shiriya ta mata a gurin Ubangiji, domin ita ce kawai mafita. Ta shiga har gidan Binta ta gaishe ta, Binta ta karɓe ta hannu bibbiyu duk da bata gane ta ba da farko, sai da Neehal ɗin ta mata bayanin kanta sannan ta gane ta. Cikin mamaki ta ce "Neehal ke ce? Kin canza gaba-d'aya ai shi yasa ban gane ki ba." Neehal ta yi murmushi ta tambayi yaranta, tace mata duk suna nan k'alau. Binta ta gyara zama ta ce "Kin ga yanda Ubangiji ya yi da Fauziyya ko? Ko shakka babu alhakin ki ne ya fara bibiyarta, dan kaɗan ma ta fara gani. Umar ya ƙaro Aure da macen kirki Ƴar gidan manyan mutane da tarbiyya da ya gane Fauziyya ba matar k'warai ba ce. Gaba-d'aya ta canza shi ta mayar da shi mutumin k'warai, Fauziyya tay ta haukanta na kishi ta gama dan Umar ya watsar da ita a kwandon shara. Daga baya kuma da taga ba sarki sai Allah sai ta risina, tunda bata da inda ya fi nan ɗin, dan iyayenta ba ƙarfi gare su ba suma ta kansu suke, ita ce ma take taimakon su. Yarinyarta kuma Iman! kullum sai uban ya mata dukan tsiya akan yawon banzan da take, amma kamar ma ƙara tura ta yake, har ya gaji ya daina dukan nata ya koma yi mata addu'a. Da taimakon Hauwa (Amaryar Uncle Umar) an samu yarinyar ta ɗan rage yawon har tana zuwa makaranta yanzu. Amma Fauziyya kullum cikin yawo take da ita a unguwa tana faɗin Ita ta yiwa Ƴarta asiri ta lalace." Neehal ta jinjina kai kawai zuciyarta babu daɗi akan rayuwar da Iman da jefa kanta a ciki. Gashi ita ba ci ta rasa ba balle ta ce wahalar rayuwa ce, Uncle Umar babu abun da baya yiwa iyalinsa na buk'atun rayuwa. Ta ɗan daɗe a gidan Binta kafin ta mata sallama ta fito bayan ta bata kuɗaɗen dake cikin jakarta duk da da ƙyar Bintan ta karɓa. Wajen ƙarfe uku ta ce zata tafi, amma Aunty Hauwa ta ce baza ta tafi ba sai ta jira Uncle Umar ya dawo sun gaisa. Haka ta zauna ba dan ranta ya so ba, dan bata san irin tarb'ar da zai yi mata ba. Can yamma kuwa sai gashi ya dawo, Aunty Hauwa ta sanar masa da zuwan Neehal. Abun mamaki sai Neehal ta ga yana murna da zuwan nata, tare yi mata magana cikin salama da kulawa. Ya zauna a falon Aunty Hauwa yana ta jan ta da hira, ya tambaye ta matakin karatun ta a yanzu da kuma sauran wasu abubuwan na rayuwa. Daga ƙarshe kuma ya mata maganar dukiyarta dake hannunsa, ita da yake ma babu abun da ta nema ta rasa a rayuwa tama manta tana da wata dukiya a gurinsa. Sai kusan Magriba ta baro gidan, sunyi_sunyi ta tsaya a yi Magriba kafin ta tafi amma ta ƙi, ta sanar musu Mama zata mata faɗa idan ta yi dare. Sai ga su Uncle Umar da Aunty Fauziyya rakiya har bakin Motar ana ta dashare mata baki. Sai bayan Magriba ta ƙarasa gida, zuciyarta cike da zumud'in ta je ta bawa Mama labarin canzawar da Uncle Umar yay mata. A falon ƙasa ta tarar da Mama da Ameen har da Hafsah a zaune sune hira. Ta ƙaraso cikin falon da sallama. Suka amsa mata, Hafsat ta bi ta da kallo cikin tsananin tsanar ta, Ameen kuwa bai ko d'ago ba hankalinsa yana kan wayarsa da yake ta aikin latsawa. Mama ta ce "Sai yanzu." Ta ce "Eh Mama, sai da na jira Uncle ɗin ya dawo muka gaisa." Mama ta ce "Kin kyauta kuwa, suna nan k'alau dai?" Ta ce "Lafiya k'alau suna gaishe ki." Ta mai da dubanta ga Ameen ta ce "Yaya Ina yini." Ciki_ciki ya amsa da faɗin "Lafiya." Ta mayar da duban ta ga Hafsat itama ta gaishe ta. Hafsah ta amsa da fara'ar munafurci akan fuskarta, har da tambayarta ya aiki. Ko zama bata yi ba ta wuce upstairs dan yin sallar dake kanta. Ameen ya bi ta da kallo ta ƙasan ido. Bayan 10 minutes ya miƙe ba tare da ya kalli inda Mama da Hafsah suke ba, ya bi bayan ta upstairs ɗin.........✍️ _*A yi haquri da typing error, ban yi edit ba ne.*_ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *4️⃣7️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* .........Idar da Sallar ta kenan ta ji an turo ƙofar ɗakin an shigo. Ta juyo da sauri dai_dai lokacin da ya yi Sallama a can ƙasan mak'oshinsa. Ta amsa masa cikin nazartar yanayin sa. A hankali ta ce "Yaya!" Ya amsa mata da ido ba tare ya yi magana ba. A hankali kuma ya fara takowa ya ƙaraso inda take ya tsugunna a gabanta tare da zuba mata narkakkun idanunsa da suke a lumshe. Ta yi ƙasa da kanta gabanta na fad'uwa saboda fargaba, a tunaninta wani laifin ta yi ya zo ya yi mata masifa kamar yadda ya saba. Ji ta yi Gaba-d'aya ta takura da kallon da yake bin ta da shi, sai cukuikuye hannuwanta take a cikin hijabin dake jikinta. Ta d'ago kanta ma ta dube shi ta kasa, ga k'amshinsa kamar ƙara buɗe mata kofofin hancinta a kai saboda yanda take jin sa. "From where are you?" Ta ji muryarsa a ɗan zafafe yana tambayar ta. Ba tare data yi wani k'wakwk'waran motsi ba ta ce "Gidan Uncle Umar." Ya yi shiru na wasu sakanni kamar ba zai tanka ba sai kuma ya ce "Mene haɗin ki da wannan guy ɗin?" Ta d'ago ta kalli fuskarsa cikin rashin fahimta ta ce "Wanne guy ɗin Yaya?" Ya ɗan taune lip ɗinsa ya ce "Baban twins kika ce ko wanene ma oho? Ya yi maganar irin i don't care ɗin nan. Ta ɗan yi murmushi ta ce "Oh Yaya wai Uncle Ahmad kake nufi?" Ya kalle ta kallon mamakin Uncle data kira Ahmad da shi. Ya ce "Eh shi." Ta girgiza kai tana kifkifta idanuwa ta ce "No.. nothing." Ya wurga mata wani kallo ya ce "Tarbiyyar da Mama ta yi miki kenan ki dinga tsayawa wani k'ato yana riƙe miki hannu ko?" Ya ƙarashe maganar a ɗan tsawace. Ta tsorata sosai dan bata taɓa tunanin ya ga lokacin da Ahmad ya riƙe mata hannu ba. Ya sassauta murya ya ce "Why Miemerh? Idan da Mama ta fito a time ɗin fa Me zaki ce mata?" Jikinta ne ya yi sanyi ta rasa me zata ce, tabbas da ace tsautsayi ya sakko da Mama ta ga sanda Ahmad ya riƙe mata hannu da kashinta ya bushe a gurin Maman, tunda ta sha nusar da ita akan illar hakan ga ƴa mace. Sai ta ji haushin kanta dana Ahmad ɗin ya cika mata zuciya. Zata yi magana kenan suka ji an buɗe ƙofar ɗakin. Mama ce ta shigo, ta dubi Ameen ta ce "Me kake yi anan?" Ya miƙe ba tare da ya yi magana ya nufi ƙofa, Mama ta matsa masa ya fice tana bin sa da kallon tuhuma. Ta mayar da duban ta ga Neehal bayan ya fice ta ce "What happened?" Cikin rashin gaskiya ta ce "Nothing." Mama ta tab'e baki ta ce "Ku kuka sani." Sannan ta juya ta fice. Neehal ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idonta, haka kawai ta ji wata irin kunyar Ameen ta rufe ta, yanzu bata san irin kallon da yake mata ba a cikin ransa na ganin Ahmad ya riƙe mata hannu. Ta yiwa kanta alƙawari ba zata ƙara bari haka ta faru ba. Tunda dama hakan bai taɓa faruwa a gare ta da wani ɗa namiji ba sai Ahmad ɗin, shi ma dan tana masa kallon kamar jininta ne, kuma ta san ba da wata mummunar manufa yake riƙe mata hannun ba. Hafsah ta cika ta yi fam kamar zata yi bunduga saboda baƙin cikin bin bayan Neehal da Ameen ya yi, a haka ya sakko ya same ta. Ta yi saurin ɓoye ɓacin ranta ta k'ak'alo murmushi ta ce "Baby har ka sakko." Ya zauna a kusa da ita cikin kulawa ya ce "Eh, bari na je na yi sallah, idan na dawo sai mu wuce gida ko? Ta ce "Ai na ɗauka a nan zamu kwana." Ya yi mata wani kallo bai ce komai ba. Ta yi murmushi cikin ranta tana jin wata irin k'aunarsa na ƙara cika mata zuciya. Ita kanta ta san ta yi dace da mijin kere sa'a, dabi'un Ameen suna bala'in burge ta, more especially muskilancinsa yana bala'in tafiya da imaninta. Yana ɗaya daga cikin abun da ya ja hankalinta a kansa, gashi ya iya kula da mace, ta tabbatar za a bashi lamba ɗaya a wannan fannin, ta san sai a tara maza ɗari kafin a samu wanda iya tarairayar mace da nuna mata tsantsar k'auna kamar Ameen ɗinta. Ya miƙe ya fice daga falon, ta bi shi da kallo. Komai nasa kyau yake mata, tafiyarsa ma kaɗai abun burgewa ce. Tana son Ameen over shi yasa bata son ɓacin ransa ko kaɗan, duk abun da ta san zai ɓata masa rai ko yaya ne gudun shi take. Shi yasa take danne duk abun da take ji a ranta a duk lokacin data gan su tare da Neehal, dan ta san bata isa ta nuna masa ɓacin ranta ba akan haka. Ta tsani Neehal over, tsanar da ita kanta bata san adadinta ba, tun lokacin data samu labarin ba su Mama ne suka haife ta ba ta ji yarinyar gaba-d'aya ta fice mata a rai.. Maganar Mama data dawo falon ne ya katse mata tunanin da take. Mama ta ce "Au Ameen ɗin fita ya yi?" Hafsah ta ce "Eh ya je masallaci." Mama ta ce "To mu je sama kema ki yi Sallar, na ji an fara kira." Hafsah ta miƙe ta bi bayan Mama. Bayan ta idar da Sallah Mama ta kawo mata abinci, tana cikin ci Ameen ya dawo gidan. Neehal kuwa tana ɗakinta ta ƙi fitowa, har sai da ta tabbatar sun bar gidan sannan ta fito falo. Anan ta tarar da Mama, ta zauna a kusa da ita ta shiga bata labarin zuwan ta gidan Uncle Umar. Cikin farin ciki Mama ta ce "Masha Allah, na ji daɗin wannan labarin, dama kullum fata na da addu'a ta Allah ya waiwayo da hankalin danginki gare ki, ku dinga zumunci kamar kowan ne ahali." Neehal ta ce "Nima Mama na ji daɗi sosai, ba ki ga yanda Uncle Umar yake mun magana ba, cikin kulawa kamar ma kunya ta yake ji akan abubuwan da yay mun a baya." Mama ta ce "Haka muke so dama, Allah ya ƙara shirya mu ya nuna mana gaskiya da sani akan abubuwan da muke aikatawa ba dai_dai ba." Neehal ta ce "Ameen." Mama ta ce "Ki je ki ci abinci, bari na je part ɗin Daddy." Neehal ta ce "Toh." Tare da miƙewa, ɗakinta ta koma ta ɗauko wayarta ta kira Uncle Usman ta sanar masa sauyawar da Uncle Umar yay mata. Daren yau ba su yi waya da Ahmad ba, tana ganin yana kiran ta ƙi pick. Washegari da safe ma tana ganin kiran sa lokacin tana gurin aiki shima ta ƙi ɗauka. Bayan Magriba Sadik ya zo gidan kamar yadda ya saba zuwa, sun jima suna hira a gurin da suka saba zama. Har yake mata zancen shi kam zai turo iyayensa a yi maganar aurensu ya matsu ya ganta a cikin gidansa a matsayin matarsa ta sunna. Cikin jin kunya ta ce masa babu matsala zata yiwa Mama maganar idan ta koma ciki. Zuciyar Sadik Cike da farinciki ya koma gida, a main Parlour ya tarar da iyayensa da k'annensa kamar kodayaushe. Ya yiwa iyayen nasa sannu da gida ƙannansa kuma suka yi masa sannu da zuwa ya shige ɗakinsa. Bayan shigar sa ɗakin ba jimawa Batul ta zo ta ce ya je Abbansu yana kiran sa a part ɗinsa. Ya amsa tare da tashi ya biyo bayanta suka fito. Abba yana zaune shi da Umma da Maamah, kamar yadda tsarinsa yake idan zai yi magana da ƴaƴansa a gaban su Maamah yake yi. Sadik ya samu guri ya zauna a ƙasa bayan ya ƙarasa falon Abban. Abba ya dube shi cikin kulawa ya ce "Abubakar na kira ka ne akan maganar yarinyar da kake zuwa gurinta, kamar yadda na ce zan yi bincike akanta da iyayenta na yi, kuma Alhamdulillahi na samu kyakkyawan sakamako kamar yadda ake fata dama. An tabbatar mun yarinyar tana da tarbiyya, mahaifinta kuma mutumin kirki ne. Dan haka na yarje maka ka cigaba da zuwa gurin ta." Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Maamah na farinciki. Sadik kuwa ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin bayanan Abba, daman ya san babu wata matsala da za'a samu a gurin Neehal. Maamah ta ce "Masha Allah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Abba ya ce "Ameen." Tare da mayar da duban sa ga Sadik wanda kansa ke ƙasa ya ce "Ashe ma yarinyar nan ce mai aiki a gidan TV na ASTV?" Sadik ya shafa kansa ya ce "Eh ita ce Abba." Abba ya ce "Masha Allah, Allah ya yi mana jagoranci." Umma da baƙin cikinta ya kasa b'oyuwa akan fuskarta ta tari numfashin Abba ta ce "Alhaji wacce yarinya na ji kana magana a kanta? Ba dai Neehal ɗin nan ba ta gidan Alh. Tafida?" Abba ya ce "Ita mana, ai yarinyar da mahaifinta sanannun mutane ne a ƙasar nan." Umma ta jinjina kai irin ta ga mugun abun nan ta ce "To gaskiya Alhaji baka yi bincike yanda ya kamata ba, indai akan yarinyar nan ne?" Abba ya ɗan canza fuska ya ce "Kamar yaya kenan?" Umma ta tab'e baki ta ce "Ita yarinyar fa su Alhaji Tafidan ba su ne asalin iyayenta ba." Sadik ya d'ago da sauri ya kalle ta, Maamah zata yi magana Abba ya riga ta da faɗin "Kamar ya ba su ne iyayenta ba Ruqayyah? Ban gane me kike son faɗa ba." Umma ta ce "Ina nufin riqon ta suke Alhaji ba ƴarsu ce ta cikinsu ba, riqonta kawai suke amma ko dangi ba su haɗa ba." Abba ya ce "Wannan ai ba wata matsala ba ce, indai tana da asalinta ai shikenan." Umma ta ce "Hmm, hakane. Amma kuma akwai wata matsalar bayan wannan." A harzuk'e Maamah ta ce "Wai ni Rukayya dan Allah me Yaron nan ya tsare miki a gidan nan ne, duk abun da zai yi sai kin san yanda kikai kika kawo masa cikas, akan wane dalili zaki takurawa ɗana? Me ya tsare miki?" Abba ya d'aga mata ya ce "Ya isa haka Kaltum, barta ta ƙarasa maganarta." Umma ta harari Maamah sannan ta cigaba da magana. "Abu na biyu Alhaji, wanda na same sa daga majiya mai ƙarfi akan yarinyar, na so in ɓoye maka kar in faɗa a mun wata fassarar daban, amma na kasa saboda yanda ba zan bari a cutar da ɗan cikina ba, haka ba zan bari a cutar da naka ba. Ita yarinyar ce duk wanda zata aura sai an kashe shi..." A zabure Sadik ya miƙe tsaye yana duban Umman, zuciyarsa na wani irin bugu ba tare da ya ji ƙarshen zancen nata ba." Abba ya haɗe rai sosai ya ce "Kin ga Rukayya, bana son shirme wannan wacce irin magana ce mara ma'ana?" Umma ta ce "Wlh Alhaji ba ƙarya ba ne, nima na girgiza da na ji zancen dan da farko ma ban yadda ba sai da aka tabbatar mun, samari har biyu sai an saka ranar Aurensu sai a wayi gari a tarar an kashe su idan....." A fusace Abba ya katse ta da faɗin, "Wannan duk ba hujja ba ce Rukayya, Babu mai kashewa da rayawa face Ubangiji, suma waɗanda suka rasun kwanansu ne ya ƙare. Dan samarin yarinya guda biyu sun rasu baza a ce daga ita ba ne, Ubangiji ne ya karb'i abinsa. Dan haka kar na ƙara jin wannan maganar mara kai da tushe, kuma wannan dalilin ba zai sa na hana Sadik cigaba da neman Auren yarinyar ba." Yana gama faɗar haka ya tashi ya shige ɗakin baccinsa. Maamah ta sauke ajiyar zuciya cikin jin daɗin yanda mai gidan nasu bai goyi bayan abokiyar zamantata ba a wannan karon. Miƙewa ta yi ta kama hannun Sadik dake tsaye kamar an dasa shi suka bar falon, ba tare da ta kuma kallon inda Umman take ba. Umma ta yi ƙwafa tare da raka su da harara, a fili ta furta "In kun san wata baku san wata ba ai, wallahi indai ina raye Sadik ba zai auri wannan yarinyar da Ubanta yake da arzik'i ba, mu zuba mu gani, shege ka fasa." Har ɗakin Sadike Maamah ta kai shi ta zaunar da shi a bakin gadonsa. Cikin tausasawa ta ce "Kar abun da Rukayya ta faɗa ya d'aga maka hankali Sadik, ka dai san halinta ba sai na faɗa maka, zata iya yin ko wanne irin sharrin dan ganin auran ka da yarinyar nan bai yiyu ba. Ka dogara da Allah, ka kuma dage da addu'ar neman zab'insa ka ji." Sadik ya d'aga mata kai yana sakin ajiyar zuciya. Sai da kwantar masa da hankali sannan ta bar ɗakin. Kwanciya ya yi bayan fitar Maamah zuciyarsa na tariyo masa abun da Umma ta faɗa akan Neehal, tabbas ya san Sauratinta ya rasu kafin su haɗu, har Haneefah ma ta tabbatar masa da an kusa bikinsu lokacin da ya rasun. Amma bai san da wani ba bayan shi ba. Wani b'arin na zuciyarsa kuwa cike yake da mamakin cewa wai ba su Mama ne suka haifi Neehal ba, shi ko kaɗan ma bai yarda da wannan batun ba. A yanda yake jin Neehal a cikin ransa koma me za'a faɗa a kanta ba zai iya rabuwa da ita ba, ko yaya take yana son abarsa kuma a haka zai aure ta. Balle ma ya san bata da wani aibu. Tashi zaune ya yi a ransa yana faɗin 'Dole ma ya yiwa Maamah magana ta faɗawa Abba ayi_ayi a saka ranar bikinsu kowa ma ya huta.' Ko da suka yi waya da Neehal yau sai da ta gane kamar yana cikin damuwa har ta kasa shiru ta tambaye shi. Amma ya ce mata babu komai, dan Maamah ta gargad'e shi akan kar ya sake ya yiwa Neehal zancen. Umma kuwa bayan ta koma ɗaki Yayan Abban su Sadik wanda suke kira da Kawu ta kira ta sanar masa ƙarya da gaskiya akan yarinyar da Sadik yake nema. Kawu ya dinga masifa a waya kamar zai ari baki yana faɗin "Shi Surajon (Abba) ba shi da hankali ne yana ji yana gani zai salwantar da rayuwar ɗansa har zai da ce wannan abun ba wata matsala ba ce? To ina nan zuwa a cikin satin nan in same shi, domin kuwa wannan yarinyar dole Sadik ya rabu da ita." Cikin jin daɗi Umma ta masa sallama, zuciyarta fari k'al kamar takarda. Bayan kwana biyu Ranar Laraba Neehal ta dawo daga gurin aiki da Yamma, tana zaune a ɗakinta tana operating system Mama ta shigo ɗakin, bayan ta yi Sallama Neehal ɗin ta amsa mata ta ce "Neehal Ahmad ya zo, yana ƙasa." Ta d'ago kanta da sauri ta ce "Uncle Ahmad kuma?" Mama ta ce "Ki yi sauri ki je kar ki bar shi yay ta jiran ki, na san ki da shiririta." Neehal ta ce "Toh." Sannan ta miƙe ta ɗauki Hijabi ta zira ta fito. Haka kawai ta ji zuciyarta na d'okin ganin sa, ko dan ta kwana biyu rabon ta da shi ko a waya ne. Yana zaune hannunsa tallafe da fuskarsa idanunsa akan steps, wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke jin takun tafiyarta. Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon. Ya miƙe tsaye da sauri kamar wanda aka tsikara ya ƙarasa gabanta ya tsaya daf da ita kamar zai rungume ta, cikin wata irin murya ya ce "Princess!" A hankali ta ce "Na'am Uncle." Ya kamo hannunta tay saurin k'wacewa tare da yin baya ta zauna akan kujera. Ya ƙarasa ya tsugunna a gabanta ya ce "Princesss mai ya faru idan na kira wayarki bakya ɗauka, ko wani laifin na miki?" Ganin yanda yake magana cikin damuwa sai ta ji tausayinsa mai tsanani ya cika mata zuciya, har ta fara da na sanin abun da ta yi masa. Cikin raunin murya ta ce "I'm sorry Uncle, ka koma ka zauna akan kujera." Ya girgiza mata kai tare da faɗin "No Princess, please tell me me ya faru." Ta ce "Seriously babu komai Uncle ɗina." Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa jin yanayin da ta yi magana ya tabbatar masa babu komai ɗin. Ya koma ya zauna sosai tare da zuba mata idanunsa. Cikin marairaicewa ya ce "But Princess why? Na shiga damuwa sosai da ƙin d'aga kira na da kike, har na fara tunanin ko ba lafiya ba. Na karb'i Numbern Mama a gurin Ummi na kira ta, dan nasan in ma ba lafiya zata sanar mun, amma jin bata ce mun akwai matsalar komai ba sai hankalina ya ɗan kwanta, amma kewarki gaba-d'aya ta hana ni sukuni. Kwana ukun nan da ban ji muryarki ba gaba-ɗaya bana cikin nutsuwata, yau dai na kasa jurewa na ce sai na zo na gan ki." Ta lumshe idonta cikin sanyin murya ta ce "Nima na yi kewar ka Uncle." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai. Ya ce "To me yasa kika daina ɗaukar kira na." Ta buɗe idonta tana kallon fuskarsa ta ce "Babu komai fa Uncle ka yarda da ni." Ya ce "Uhm, salon ki tayar mun da hankali ne kawai ko?" Ta ce "A'a, i'm sorry ba zan kuma ba." Ya ce "Shikenan Princess." Ta ce "Ina yarana, me yasa baka zo mun da su ba?" Ya ce "Bari na yi sai next week idan sun yi hutun school sai na kawo miki su." Ta ce "Allah ya kai mu, Ya su Ummi?" Ya ce "Duk suna nan lafiya lau." Hira suka sha sosai yau, dan ita kanta sai yanzu ta tabbatar ta yi kewarsa ba kaɗan ba. Anan ya yi Sallar Magriba, yau kam ya ci abinci kaɗan a gidan saboda gudun ɓacin ran Princess ɗin tasa. Sai kusan isha'i ya tafi zuciyarsa cike da nishad'i, saɓanin kwana biyun da suka wuce wanda ya yi su cikin damuwa. Itama Neehal anata ɓangaren cike take da farincikin kasancewa da Uncle ɗin nata a yau. Bayan ya koma gidan Mamy tai ta tsokanarsa tana faɗin "Ai fa yanzu dole yay ta musu zarya a Kano tunda zuciyarsa tana nan." Murmushi kawai yake mata baya cewa komai. Bayan Sallar isha'i Mama tana falon sama tana kallo wayarta dake hannun kujerar da take kai a zaune ta fara ringing. Ta ɗauko ta duba tare da d'agawa ganin Aunty A'isha ce ke kiran. Ba tare da gaisuwa ba Aunty A'isha ta ce "Adda Fateemah! Yanzu Mai_gidan su Abban Neehal ya kira ni ya sanar mun cewar an samu nasarar kama mutanen da suka kashe Abban Neehal ɗin da Ummanta........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *4️⃣8️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ```Ku yi haquri da rashin ganin update akan lokaci, kun san an ce idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi.``` ..........Cikin hanzari mai nuni da tsantsar mamaki Mama ta tari numfashin Aunty A'isha da faɗin. "Da gaske A'isha?" Aunty A'isha ta ce "Dagaske mana Adda, shi Alhaji Alin ne tun bayan rasuwar su Abban Neehal ba jimawa ya kamu da rashin lafiya, aka fitar da shi Saudiyya ake masa magani. Ashe duk wannan shekarun da suka wuce abun yana ransa, sai a ƴan watannin da suka wuce ya samu lafiya ya dawo Nigeria. Shine yana dawowa yasa aka duk'ufa da binkicen waɗanda suka yi kisan a lokacin da ya samu labarin har yanzu ba'a gano su ba. Yanzun nan shi ya kira ni da kansa muna gama waya da shi na kira ki, ya sanar mun cewa tunda ya dawo ƙasar nan yake neman mu, amma bai samu labarin inda muke ba, sai daga baya tunanin ya je gadon ƙaya inda muka zauna ya zo masa, to a wurin wata mak'ociyarmu aka samo masa Number ta." Mama ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Alhamdulillah, Allah mun gode maka, yanzu ya ake ciki game da waɗanda suka yi kisan? Ya sanar miki ko su waye suka yi?" Aunty A'isha ta ce "A'a bai sanar mun ba, ya dai ce mun suna hannun Police a halin yanzu, ranar Monday za'a shiga kotu a yanke musu hukunci tunda sun amsa laifunsu, sauran bayani kuma ya ce sai mun haɗu." Mama ta ce "Ki ji wani ikon Allah A'isha, shekara fiye da goma sai yanzu Allah ya toni asirinsu, Allah ya ƙara tona asirin duk wasu masu laifi a cikin duniyar nan." Aunty A'isha ta ce "Ameen ya Allah, wallahi adda ba ki ji yanda na ji daɗi ba, Alhaji Ali ya cika ubangida na gari da ya tsaya tsayin daka ganin jininsu Abban Neehal bai tafi a banza ba." Mama ta ce "Allah ya saka masa da Alkhairi ya biya shi da gidan Aljannah." Aunty A'isha ta ce"Amin ya Allah, ya ce akai masa Neehal yana son ya gan ta." Mama ta ce "Aiko bai faɗa ba dole mu je har gida mu yi masa godiyar wannan jajircewar da ya yi, gobe gobe ma Insha Allahu za mu je, a wacce unguwa yake da zama?" Aunty A'isha ta ce "A rijiyar zaki, ya turo mun da address ɗin gidansa ta message." Mama ta ce "To Insha Allahu da safe za mu je, bari in je in sanar da Daddy wannan abun al'ajabi da farincikin." Aunty A'isha ta ce "Tom shikenan da safen zan biyo ta nan sai mu wuce, nima bari in je in sanar da Abban Maryam, in kira Sadiya itama in sanar mata." Mama ta ce "Allah ya kai mu goben, sai mun yi waya." Daga haka suka yi sallama. Mama ta dafe kanta tana sauke numfashi, zuciyarta cike da d'oki da zumud'in jin asalin zancen, domin ta san wa ya kashe su Abba ko kuma wa ya turo a kashe su, da kuma son sanin ko mutum ɗaya ne ya yi kisan su Abba da su Anwar? A ɓangaren Aunty A'isha itama tunanin da take yi kenan. miƙewa Mama ta yi ta nufi part ɗin Daddy cikin sauri dan ta sanar masa halin da ake ciki. Cike da mamaki da kaɗuwa Daddy yake duban Mama bayan ta gama sanar masa da abun da yake faruwa. Zuwa can ya nisa ya ce "Allah buwayi gagara misali, dama an ce duk wanda yay kisan kai da wuya ya mutu Ubangiji bai toni asirinsa ba, saboda haqqin rai ba ya taɓa barin mutum ya zauna lafiya a duniya." Mama ta ce "Wannan haka yake, Allah ka raba mu da mummunar ƙaddarar da zata kai mu ga dana sani, su kuma azzaluman mutane irin waɗannan Allah ka cigaba da tona musu asiri!" Daddy ya ce "Amin Amin Doctor." Mama ta cigaba da magana. "Mutum bai ji ba bai gani ba kawai saboda rashin imani a zo har cikin gidansa a kashe shi saboda neman duniyar da kowa sai ya bar ta, mutane ba sa tuna Allah a ransu, ba sa tunanin inda suka kashe mutum ya je suma komai daren dad'ewa za su je." Cikin jimantawa Daddy ya ce "Ai ke dai ki bar mutum kawai Doctor, amma in dai duniya ce gata nan ta ishi kowa, kuma Duk *abin da mutum ya shuka* dai *shi zai girba* , walau na sharri ko na Alkhairi." Sun zanta akan al'amarin sosai sannan Mama ta miƙe dan zuwa ta sanar da Neehal itama. Tana kwance ruf da ciki akan gadonta, system ɗinta na gabanta tana latsa ta cikin kwarewa, idanunta sanye da siririn glass mai ɗan duhu, wanda bata fiya amfani da shi ba, sai irin wannan lokacin idan zata yi using system. Mama ta shigo ɗakin tare da zama a bakin gadon bayan ta yi sallama. Neehal ta amsa mata tare da tashi zaune ta cire glass ɗin fuskarta ta ajiye a gefen ta. Mama ta ce "Aikin ne har yanzu baki gama ba." Ta ce "Na kusa ƙarasawa saura kaɗan, zuwan Uncle Ahmad ne ma ya tsayar da ni." Jinjina kai Mama ta yi tare da juyowa ta fuskance ta sosai ta ce "D'azu Auntinki ta kira ni take sanar mun an kama waɗanda suka kashe su Ummanki." Neehal ta waro Ido waje cikin kaɗuwa ta ce "Su waye Mama?" Mama ta kwashe duk yanda suka yi da Aunty A'isha ta sanar mata. Kuka ta saka cikin kukan take faɗin "Mama me su Umma suka musu da suka kashe su? Su waye waɗannan mutanen da suka raba ni da mahaifana rabuwa ta har abada a rana ɗaya? Me nay musu suka zaɓi mayar da ni marainiya?" Kuka take sosai mai ban tausayi, mutuwar su Umma ta dawo mata sabuwa fil a cikin ranta, duk da a lokacin da suka rasu tana ƙarama amma har yanzu gawar iyayenta kwance cikin jini bata daina hango ta acikin idanunta ba, kuma har ta koma ga mahaliccinta ba zata taɓa mantawa ba. Mama ta rungume ta a jikinta cikin tsananin tausayinta, tare da rarrashinta da kalamai masu taushi har ta samu ta bar kukan. Mama ta d'ago ta tana share mata hawaye ta ce "Komai rubutacce ne daga Allah, Ubangiji ya riga ya tsara rana ɗaya Umma da Abba za su rasu kuma a lokaci ɗaya, ko da waɗan can Mutanen ba su kashe su ba idan kwanan su ya ƙare dole su bar duniya. Dan haka addu'ar mu kawai suke buƙata a halin yanzu, ita ce kawai soyayyar da za mu nuna musu. Mutuwa dole ce Neehal, mu ma nan zaman jiranta muke, fatanmu Allah yasa ta zo mana cikin sauqi." Cikin matuƙar sanyin jiki Neehal ta ce "Haka ne Mama, Allah ya ji k'an Umma da Abba da ma dukkan musulmin da suka riga mu gidan gaskiya, mu kuma Allah yasa mu cika da imani." Mama ta ce "Ameen dan darajar Annabi." Lumshe idonta ta yi bata kuma cewa komai ba, cikin zuciyarta kuwa ji take dama a bata dama ta kashe azzaluman mutanen da suka kashe mata iyaye da hannunta, saboda wata muguwar tsanar su data cika mata zuciya. A hankali ta yi baya ta kwanta akan gadon saboda sarawar da ta ji kanta ya yi mata lokaci ɗaya. Mama ta janyo system ɗin da take amfani da ita ta yi saved na aikin da take sannan ta kashe ta, ta ɗora ta akan bedside locker. Shafa fuskar Neehal ta yi cikin raunin zuciya da tausayinta, cikin kulawa ta ce "Ki yi addu'a idan kina jin zuciyarki babu daɗi ba wai ki yi kuka ba, idan kin kasa barci kar ki kwanta ki yi ta tunane_tunane, ki tashi ki kaiwa Allah Kukanki." Ta gyaɗa mata kai ba tare data buɗe idonta ba. Mama ta kashe mata light ɗin ɗakin sannan ta fice zuciyarta babu daɗi. Iyayenka ko da ace baka san su ba kana jariri suka rasu idan ka girma aka baka labarinsu dole ka ji feeling a kansu da son kasance tare da su, balle ita da tana da ɗan wayonta suka rasu, dole abun ya dinga taɓa mata zuciya. Kuma da a ce mutuwa suka yi kamar kowa ba kashe su a kay ba, abun ba zai dinga damun ta over ba. Amma yanzu gani zata dinga yi kamar da ba'a kashe su ba da suna raye har yanzu.... Washegari kafin ƙarfe goma sha ɗaya na safe sun gama shiryawa dan zuwa gidan Alhaji Ali, Neehal dai kamar mai cuta komai a sanyaye take yin sa. Daren jiya kam ko wayar love ɗin data saba bata iya yi ba, da ta tashi da safen nan ma ko bi takan wayar bata yi ba. Sai da Mama ta ce mata ta kira gurin aikinsu ta sanar musu ba zata samu damar zuwa yau ba sannan ta ɗauki wayar. A time ɗin ne ta ga missed call ɗin Sadik, Ahmad har ma da Ameen wanda kiran nasa ya bata mamaki. Ahmad kam har da text yay mata ya sanar mata ya wuce Abuja, dama tun jiya ya faɗa mata da sammako zai yi ya koma. Bata bi kiran ko ɗaya daga cikinsu ba saboda tana cikin mood ɗin da ko doguwar magana bata son yi. A lokacin itama Aunty A'isha ta ƙaraso gidan, bayan sun gaggaisa suka rankaya suka tafi a Motar Mama wanda direban Maman ne zai kai su. Suna tafe suna ƙara jimanta al'amarin a tsakanin su. Neehal dai ta yi shiru kawai tana sauran su. Aunty A'isha ta dube ta, ta ce "Daughter baki da lafiya ne?" Mama ce ta bata amsa da faɗin "Tun jiya dana faɗa mata zancen nan shine duk ta koma haka." Aunty A'isha da itama dauriya kawai take dan mutuwar tsohon Mijin nata da abokiyar zamanta ta dawo mata sabuwa a ranta. Ta kwantar da kan Neehal a ƙafaɗarta bata ce komai ba. Mama ta ce "Na kira Hajiya na faɗa mata, ta ce zata zo kafin Monday a yi zaman kotu da ita." Aunty A'isha ta ce "Allah ya kai mu, ya kuma sa a ƙarƙare shari'ar a ranar, kin san shari'ar ƙasar nan tsaf zasu iya cewa sun d'age shari'ar." Mama ta ce "Ai tunda waɗanda suka yi laifi sun amsa babu buƙatar wani jan magana na daban, hukunci kawai za'a yanke musu dai_dai da abun da suka aikata." Aunty A'isha ta ce "Haka muke fata dama." Bayan sun ƙarasa gidan Alh Ali Aunty A'isha ta kira shi ta sanar masa, ɗaya daga cikin ma'aikatan gidansa ya aiko ya shigar da su. A wani babban falo aka sauke su, dattijuwar matarsa ta karɓe su hannu bibbiyu dan ta san da zuwan nasu. Alh.Ali ya yi mata bayanin komai. Kuma ta shaida fuskar Aunty A'isha dan kafin Abba ya rasu suna ɗan zuwa tsohon gidansu idan abu ya samu. Tana ganin Neehal ta ce "Wannan yarinya kamar an tsaga kara ita da mahaifiyarta." Da kanta ta musu jagora har falon Alhaji Ali. Yana zaune shi kaɗai a falon yana kallon labarai suka yi sallama, ya amsa musu cikin sakin fuska. Suka ƙarasa suka zauna matar tasa ta ce "Ga iyalan Alh.Muhammad sun ƙaraso." ya yi murmushi yana duban Neehal ya ce "Masha Allah, wannan ce Amaryar tawa?" Suka yi murmushi dukan su, Neehal ta ƙarasa ta tsugunna a gabansa ta gaishe shi. Ya amsa mata cikin fara'a da kulawa, su Mama ma suka gaishe shi, ya amsa musu. Aunty A'isha ta ce "Ya jiki kuma Alhaji? Ashe cuta ka sha Wlh ba mu da labari." Ya nuna ƙafarsa ya ce "Ciwon Ƙafa ne ya sako ni a gaba, na fi shekara biyar a zaune bata takuwa, kuma tunda muka je Saudiyya ake ta maganin, sai yanzu Ubangiji ya kawo sauqi." Mama ta ce "Subhallahi, Lallai kasha jinya Alhaji, Allah Ubangiji ya ƙara sauƙi yasa kaffara ne." Suka amsa da "Ameen." Ya dubi Aunty A'isha ya ce "Ya ƙarin haquri rashin su Alhaji Muhammad, tun bayan rasuwar su ba mu ƙara haɗuwa ba, na samu labarin ma kin yi aure." Aunty A'isha "Haquri Alhamdulillah, ai tun bayan dana gama takaba na yi aure." Ya ce "Masha Allah, Allah ya raya zuri'a ya ƙara haqurin zama da juna. Su kuma Alh. Muhammad Ubangiji Allah ya ji k'ansu ya gafarta musu." Suka amsa da Ameen gaba_ɗaya. Daga nan suka shiga tattaunawa akan abun da ya kawo su. Inda Alhaji Ali ya sanar musu da cewa. "Bayan ya dawo daga Saudiyya ne ya bibiyi al'amarin, inda aka tabbatar masa har yanzu ba a gano wand'anda suka yi kisan ba, hankalinsa ya tashi ya dinga faɗa akan rashin tsaurarara bincike na ƙasar nan da ba'ayi, sannan ya saka lauyoyi da jami'an tsaro su binkito masa. To ana cikin haka ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kisan su Abba ya fito daga gidan yari bayan shekaru takwas daya shafe a gidan yarin, bisa laifin fashi da makami da aka kama shi da shi, dama irin ƴan daban nanne da masu kuɗi da ƴan siyasa suke amfani da su dan cimma wata buƙata ta su, daga zarar buƙatar tasu ta biya kuma da su da banza duk ɗaya ne a gurinsu. Bayan ya fito ya nemi wanda sukay kisan su Abban tare wanda shine yakasance kamar babbansu a jan ragamar aikin, ya buk'aci daya ba shi cikon kuɗin aikinsa, shi kuma wancan ɗin sai ya hana shi ya ce ya cinye. To saboda baƙin cikin cinye masa kuɗin da aka yi shine ya ɗauki alwashin sai ya tona musu asiri in ya so kowa ya rasa duk a kama su. Da kansa ya kai kansa Police station ya faɗi laifinsa, aka kuwa yi ram da shi nan take, sannan ya faɗi inda sauran biyun suke su ma aka je aka kamo su. Da farko su sun musa, amma da suka ji duka sai suka fadi gaskiya, suka ce tabbas su sukai kisan amma su ma wani mutum ne ya ba su kwangilar yin kisan. Yanzu haka suna Bamfai a tsare, Ranar Monday Insha Allahu za'a yi shari'ar a babbar kotun jiha, dan yanke musu hukunci dai_dai da abun da suka aikata. Sai dai har yanzu sun ƙi faɗar wanda ya saka su aikin, dan su yaran biyun dama ba su san shi ba, babban nasu ne ya san shi. Amma ana saka rai Insha Allah za su faɗi koma waye a zaman kotu, lauyoyinmu suna ta faɗi tashi akan haka. Na samu duk wannan bayanan ne ta bakin amintaccen lauyana wanda shi ne lauyan da zai tsaya a gaban kotu a matsayin lauyan iyalan Alhaji Muhammad Gabasawa dan ganin kotu ta bi musu hak'k'in su." Sai bayan Azhar su Neehal suka baro gidan nasa zuciyoyinsu cike da al'ajabi. Ranar Asabar sai ga Hajiya ta zo Kano kamar yadda ta faɗa. Kwanakin nan da zazzaɓi mai zafi Neehal ta yi su, dan ko falo bata iya takowa ba tana kwance, ko toilet zata sai Mama ta taimaka mata. Ranar Monday ranar shiga kotu ta tashi jikin nata da ɗan dama, har ta yi wanka da kanta ta shirya. Daa Mama ta ce ta zauna a gida ba sai ta je court ɗin ba, amma ta ce zata iya zuwa ai ta ji k'warin jikin nata. Ƙarfe tara da ƴan'mintuna suka bar gidan gaba-ɗayansu har su Dije da Daddy zuwa court, dan ƙarfe goma za'a saurari ƙarar. Duk wannan abun da yake faruwa Ahmad da Sadik ba su sani ba dan Neehal bata sanar da su ba, tunda ko waya bata yi da ɗayan su ba saboda rashin lafiyar da take. Idan sun kira ta Mama ce take d'agawa. Sadik ya zo har sau biyu ya duba ta, Ahmad ma ya zo sau ɗaya ranar Sunday. Mama ta ce masa, dama bai wahalar da kansa ya zo ba tunda yana da nisa kuma dududu kwanansa uku da barin garin. Ameen kuwa tun ranar Friday da ya dawo garin every morning and night sai ya zo ya duba ta.... Ƙarfe goma dai_dai court ta cika ta tunbatsa da mutanen Daddy da suka samu labari da mutanen Alhaji Ali gami da wasu daga cikin abokan Abba, sai ƴan jarida da sauran mutane, har da su Uncle Umar da iyalansa da Kawu Musa. Uncle Usman ne bai samu damar zuwa ba. Shigowar Alk'ali yasa kotun yin tsit daga hayaniyar dake tashi a cikin ta, hakan kuma ya yi dai_dai da shigowar jami'an tsaro da waɗanda ake ƙara akan laifin kisan su Umma........✍️ _*Page ɗin yau bana soyayya ba ne, bare a cika mana kunne da team ɗin anace dana k'anin kurma.*_🏃‍♀️😉 *By* *zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *4️⃣9️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ...........Bayan Alk'ali ya zauna a mazauninsa aka miƙo masa wani ɗan abun rubuta da pen. Bayan 2 minutes wani mutum ya miƙe ya ɗan rankwafawa ya yi gaisuwa ga Alk'ali sannan ya fara karanto takardar dake hannunsa kamar haka "Zamu saurari shari'a ta gaba akan gisan gillan da wasu mutane suka aikata wa marigayi Alhaji Muhammad Gabasawa tare da mai ɗakinsa, shekara goma sha ɗaya da watanni da suka wuce." Sannan ya koma ya zauna. Neehal ta lumshe idonta bayan ta gama ƙarewa wadanda suka yi kisan kallo, zuciyarta na mata k'una. Barrister Murtala Gaya (Lauyan Alhaji Ali) ya miƙe ya kai gaisuwa ga Alk'ali sannan ya fara magana. "Sunana Barrister Murtala Gaya, Ni ne lauyan masu ƙara, ina roƙon wannan kotu mai adalci da ta yankewa waɗan nan azzaluman mutanen da suka yiwa Alhaji Muhammad Gabasawa da mai ɗakinsa gisan gilla hukunci dai_dai da abun da suka aikata." Ya rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Alk'ali ya ɗan yi rubuce_rubuce sannan ya d'ago ya dubi mutane ya ce "Ko akwai lauyan da yake kare masu ƙara?" Wani Barrister ne ya miƙe cikin girmamawa ya ce "Eh akwai ya mai girma mai shari'a. Sunana Barrister Garba Dan_ladi, nine lauyan dake kare waɗanda ake ƙara." Sannan shi ma ya ɗan rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya koma ya zauna. Barrister Murtala Gaya ya miƙe a karo na biyu yana duban Alk'ali ya ce "Ya mai girma mai shari'a ina son zan yi magana da waɗanda ake ƙara." Alk'ali ya ce "Kotu ta baka dama." Ya rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya yi fito daga gurin da yake ya ƙarasa inda masu laifin suke ya ɗan kare musu kallo na wasu sakanni sannan ya ce. "Kotu tana son sanin sunayenku da kuma yanda kuka gudanar da kisan kai ga Alhaji Muhammad Gabasawa da iyalinsa, tare kuma da son sanin wanda ya turo ku aikata hakan." Da sauri Barrister Garba ɗan ladi ya miƙe ya ce "Ina da ja ya mai shari'a, bai kamata Barrister Murtala ya dinga tambayar waɗanda ake ƙara wanda ya turo su aikata laifin da sukay ba, saboda ba don haka ake zaman wannan kotun ba." (Da alama dai wanda ya turo a kashe su Abba shine ya ɗauki Barrister Garba.) Barrister Murtala ya tari numfashinsa da faɗin "Dole ne in musu wannan tambayar ya mai girma mai shari'a, saboda waɗanda ake ƙara sun sanar da jami'an tsaro cewar turo su akay, amma sun ƙi faɗar ko waya ne, da alama an musu babban gargadi' ko barazana mai tsoratarwa. Mu kuma muna so mu sani saboda shi ma a nemo shi a duk inda yake a hukunta shi." Alk'ali ya dubi Barrister Garba ya ce "K'orafi bai karbu ba Barrister Garba." Ya mayar da dubansa ga Barrister Murtala ya ce "Barrister Murtala cigaba da tambayarka kotu na sauraren ka." Ya yi murmushi ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya ƙara maimaita tambayar da ya yi wa waɗanda ake ƙara. Ɗaya daga cikinsu ya ce "Sunana Hakim ilyasu." Sai babban nasu shi ma ya ce "Sunana Bilyaminu saminu." Na ƙarshen kuma ya ce "Sunana Zakari Mu'azu." Barrister Murtala ya jinjina kai ya ce "Kotu tana sauraren ku, Malam Zakari da Bilyaminu da Hakim." Wanda ya fara faɗar sunansa wato Hakim ya ce "Watarana muna zaune da yamma ni da abokina Zakari......ya nuna Bilyaminu sannan ya cigaba da magana. Bilyaminu ya zo ya same mu a kan yana so zamu yi wani aiki tare da shi, ya tabbatar mana da za mu samu kuɗi mai tarin yawa a wannan aikin, cikin zumud'i muka ce masa za mu yi ko wanne irin aiki ne. Da farko da ya sanar mana aikin kisan kai ne mun tsorata, muka ce gaskiya baza mu iya ba, domin ba mu taɓa aikata hakan ba, iyakacinmu k'wace da haurawa gidan mutane, ko kuma raka irin su Bilyaminu fashi da makami. Amma Bilyaminu ya nuna mana ruwan kuɗi ya ce, mutumin da zamu yiwa aiki hamshaqin mai kuɗi ne, zai ninka mana kuɗin da muka gani a gurin Bilyaminu sau goma. Nan fa muka ruɗe mun ji zamu kuɗi, muka je mun amince amma fa muna tsoron kar a samu matsala. Bilyaminu ya ce babu matsalar da za'a samu, koma da an samu wanda ya samu aikin zai tsaya mana dan Babba ne a ƙasar nan, dan haka mu kwantar da hankulanmu babu abun da zai faru. Da jin wannan batu sai muka amince." Hakim ya ɗan numfasa, Barrister Murtala ya ce "Dama already kum san shi Bilyaminun ne kuna da alaƙa dashi?" Hakim ya ce "Ehh, babba ne shi a daba kuma kamar oga yake a gurin mu." Barrister Murtala ya jinjina kai ya ce "Cigaba kotu na saurarenka ka sanar mata yanda kuka gudanar da kisan." Hakim ya cigaba da magana. "Tun a ranar Bilyaminu ya fara ba mu kuɗaɗe masu kauri, ya ce sauran kuma sai aiki ya kammala zai ba mu. Muka amince cike da k'warin gwiwa da murnar za mu samu kuɗaɗe. Bayan kwana biyu da daddare Bilyaminu ya zo ya ɗauke mu a wata Mota shida wasu mutane guda biyu, gaba-ɗayansu fuskokinsu a rufe da baƙin k'yalle. Wani ɗan gida ya kai mu ya ba mu wasu kaya bak'ak'e muka saka a jikinmu tare da baƙin k'yallen muma muka ɗaure fuskokinmu. Sannan ya bamu bindigu muka zira a aljihun wandunanmu. Bayan dare ya tsala muka fita a wannan Motar zuwa gidan mutumin da muka kashe, ta bayan gidan Bilyaminu ya yi parking motar muka fito ya buɗe ƙofar dake bayan gidan muka shige, shi ya yi mana jagora har cikin ɗakin baccinsu. Dama Bilyaminu ya sanar mana za su yi magana da mutanen, idan sun amince da buƙatarsa wadda ba mu san ta mene ba kar mu yi musu komai, idan kuma mun ji sun yi gardama mu sakar musu harbi. Bayan ya gama rad'a musu maganar da zai faɗa musu muka ji mai gidan cikin ƙaraji yana cewa ba zai taɓa amincewa da buƙatar su ba, da ido Bilyaminu yay mana inkiya. Babu jira ni da Zakari muka sakar musu bullet bibbiyu a ƙirjinsu, Bilyaminu ya ƙara musu ɗai_ɗai. Sauran mutum biyun da su zo ɗaukar mu tare da Bilyaminu waɗanda ba mu san su ba, su ba su yi harbin ba. Suna dai tsaye riƙe da bindigu a hannunsu. Mu ukun nan mu kai kisan." Ya yi shiru yana jan numfashi. Neehal ta runtse idanta hawaye mai zafi na zuba daga cikinsu. Aunty A'isha ma runtse idanunta tay tana tuno sanda ta ji ƙarar harbin a cikin kunnenta. Hajiya kuwa tsinuwar Allah take ja musu a cikin zuciyarta. Barrister Murtala ya jinjina kai cikin k'warewar aiki ya dubi Zakari ya ce "Ka ji duk abun da ɗan'uwanka ya faɗa, gaskiya ne?" Zakari ya ce "Eh haka ne." Barrister Murtala ya mayar da dubansa ga Bilyaminu wanda ko cikin duhu mutum yay gamo da shi zai tabbatar da rikak'k'en ɗan ta'adda ne. Saboda zubinsa da yanke yake muzurai da ido da kuma tabo_tabon yanka dake jikinsa. Ya ce "Malam Bilyaminu ka ji duk abun da Hakim ya faɗa haka ne?" Cikin shakak'k'iyar murya ya ce "Eh Haka ne." Barrister ya jinjina kai ya ce "Kotu tana san sanin wanda ya turo ku ku kay wannan ɗanyen aikin da kuma sanin ina sauran mutum biyun da ku kay aikin tare?" Bilyaminu ya ce "Sauran mutum biyun da mukay aiki tare ɗaya ya shek'a barzahu a cikinsu, ɗayan kuma yana kurkuku a halin yanzu sakamakon wani kisan da yay aka kama su, an yanke masa hukuncin d'aurin rai da rai. Batun wanda ya samu wannan aikin kuma wani babban mutum ne kuma sananne a ƙasar nan. Shi ya bani address ɗin gidan da za mu yi kisan, har yanda tsarin gidan yake da hanyoyin da zamu bi har zuwa ɗakin baccinsu, kuma shi ya ba ni mukullin da na yi amfani da shi na buɗe ƙofar gidan ta baya. Ban san dalilin da yasa ya ce mu je mu kashe mutumin da matarsa ba, ya dai faɗa mun kawai idan na je na nuna musu hotonsa, na ce masa za su amince da buƙatar da yake da ita a kan ƴarsu ko a'a? Idan sun je za su amince kar mu yi musu komai, idan kuma sun ƙi amince mu kai su k'iyama, dan za su iya tona masa asiri. A halin yanzu mutumin ba ya numfashi a doron ƙasa ya mutu shi ma. Kuma na riga na yi masa alƙawari bisa wani sharad'i namu na sirri ba zan taɓa faɗar sunansa ba a cikin wannan aikin ko me za'a mun kuwa." Barrister Murtala ya jinjina kai cikin gamsuwa ya ce "Ko zaka iya faɗawa kotu alaƙar dake tsananinka da mutumin da ya saka ku aikin." Ya ce "Eh, alaƙa ce kawai irin ta mai kuɗi da ƴan hark'alla irin mu, idan suna buƙatar aiki irin wannan su saka mu su biya mu da ƴan silalla." Barrister Murtala ya juyo ya kalli Alk'ali ya ce "Ya mai girma mai shari'a, ina son wannan kotu ta bani dama in gayyato wani bawan Allah wanda yake da masaniyar komai akan wanda yasa su Bilyaminu kashe su Alhaji Muhammad Gabasawa da matarsa. Tunda shi Bilyaminu ya ƙi faɗa" Alk'ali ya ɗan yi rubuce-rubuce ya d'ago ya ce "Kotu ta baka dama Barrister Murtala." Ya rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya ce "Ina son gayyato *Hashim Isma'il na_kowa* ." Alk'ali ya dubi mutane ya ce "Kotu na san ganin Hashim Isma'il na_kowa a gabanta." Alhaji Ali ya maimaita sunan a cikin zuciyarsa "Hashim Isma'il na_kowa?" Mamaki bai gama kashe shi ba sai da wani magidancin mutum da aƙalla zai yi shekaru arba'in a duniya ya fito gaban kotu, domin kuwa ɗan amininsa ne Alhaji Isma'il na_kowa, tsohon sanatan Kano ta tsakiya, kuma mutumin da yake matuƙar son Alhaji Muhammad Gabasawa. Aunty A'isha ma mamakin ne ya kusa kashewa domin ta san mutumin a gurin Abban Neehal, mutuminsa ne sosai. Ba iya Aunty A'isha da Alhaji Ali kawai ambatar sunan Isma'il na kowa ya bawa mamaki ba, mafi yawan mutanen gurin sun cika da mamakin ganin ɗan *senator Na_kowa* a matsayin wanda zai ba da shaida. Wata mata kuwa har zabura ta yi ta miƙe, na kusa da ita su kay saurin mayar da ita ta koma ta zauna. Barrister Garba ɗan_ladi ma ya firgita ba kaɗan ba, dan har gumi ya fara gogewa, sai dai babu bakin magana tunda ba shi da abun cewa da kotu zata saurara. Bilyaminu ma ido k'walalo waje alamun razana yana kallon Hashim. Cikin nutsuwa Hashim ya faɗi sunansa kamar yadda Barrister Murtala ya ce masa. Sannan ya buk'aci da ya ba da shaida kamar yadda ya fito da nufin hakan. Ya gyara tsayuwa ya ce "Mahaifina Senator Na_kowa shine wanda ya saka su Bilyaminu yin wannan kisan." Kafin ya gama rufe bakinsa kotu ta barke da hayaniya gami da sallallamun jama'a. Alk'ali ya buga gudu ma tare da faɗin "Order." Nan dan kotun ta ƙara yin tsit kamar ba mutane a ciki. Alk'ali ya dubi Hashim ya ce "Cigaba da baya nanka kotu na sauraren ka." Ya cigaba da magana. "Watarana tun ina saurayi kafin na yi aure na je part ɗin mahaifina dan amsa kiran da yay mun. Ina shiga falonsa na ji yana waya a balcony inda yake cewa. "Kar ka damu mutumina, ko Alhaji Muhammad Gabasawa ya yarda ko kar ya yarda sai na biya buƙata ta da ƴarsa tunda zuciyata ta ƙwadaitu da ita, kasan bana had'iyar yawu a banza. Ya yi shiru na wasu sakanni sannan ya kece da dariya ya ce, Kar ji komai na waje na kamar kaima ka huta da wannan yarinyar nan ne, kasan dama muna neman yarinya ta cikon goma kamar yadda boka ya ce mana akan aikin mu, to ina tabbatar maka da ita za'a za mu cike, zan biwa Gabasawa ta tallama ya bani ƴarsa in cika shi da ƴaƴan banki, idan kuma ya yi taurin kai kawar da shi a doran ƙasa ba wahala zai mun. Ya ƙara yin shiru na wasu sakanni sannan cikin dariya ya ce, Ah, to dan yana mutumina ai bai kai ya biyan buƙata ta ba a gurina. Ni fa dama dan na yi mu'amalar jin daɗi da shi na shiga cikin rayuwarsa, to kuma na fuskanci ba zai taɓa amincewa da buƙata ta ba, wai shi mai tsoron Allah, dan haka kawai zan huta ƴarsa ma ya wadatar. Wani irin juyawa na ji kaina yana mun, na yi baya da sauri na fice daga falon cikin tsananin tashin hankalin jin abun da mahaifina yake aikawa. Da ƙyar na iya ƙarasawa part ɗina na zube a kan kujera. Tun daga wannan ranar na fara bibiyar al'amuransa ba tare da ya sani ba. Anan na gane mahaifina cikakken ɗan luwaɗi ne sannan kuma k'wararre a rapping ƙananan yara mata, duk a saboda neman duniya da mulki. Lokacin dana samu labarin rasuwar Alhaji Muhammad Gabasawa da matarsa ko tantama ban yi ba na san aikin mahaifina ne, amma ban sanar da kowa ba saboda yanda idonsa ya rufe a neman duniya nima zai iya sawa a kashe ni matuƙar na faɗa. Sai dai cikin ikon Allah bayan rasuwar Alhaji Muhammad Gabasawa da wasu kwanaki shima Dad Allah ya saukar masa da ciwo wanda aka rasa gane kansa da gindinsa. Ciwo kullum ƙara tsanani yake ana magani amma kamar ba'ayi. Ya shafe fiye da shekara biyu yana jinya kafin ya mutu, mutuwar da bana fatan duk wani wanda na sani a duniya ya yi irin ta. Domin kuwa babu alamar dacewa a tafiyar." Sai kuma ya yi shiru na wasu sakanni sannan ya cigaba da magana cikin raunin murya. "Ganin ya rasu sai na bar abun a raina ban sanar da kowa ba, sai a cikin satin nan muka haɗu da Barrister Murtala ta sanadin wani abokina wanda shi ma Barrister ne, a nan ya ji yana bashi labarin case ɗin dake gabansa. Gabana ya faɗi amma ban sanar da shi komai ba a lokacin har muka rabu, sai daga baya dana koma gida na kasa zaune na kasa tsaye, na rasa abun da yake mun daɗi. A jiya ne na yanke shawarar na nemi Barrister Murtala na faɗa masa gaskiyar cewa mahaifina ne ya saka a yi wannan kisan, ko iyalan mamacin za su yafe masa dan ya samu sassauci daga azabtar Ubangiji. Da taimakon abokina kuma abokin Barrister Murtala na gano inda Barrister Murtala yake da zama na je na ba shi wannan labarin, shine ya buk'aci dana zo kotu yau na faɗa a gaban Alk'ali." Kotun ta yi shiru kamar ruwa ya cinye mutanen ciki, ba ƙaramin tashin hankali Alhaji Ali ya shiga ba da jin wannan labarin, tabbas da wanine ya faɗa masa wannan maganar ba ɗan cikin Senator na_kowa ba, ba zai taɓa yarda ba. Saboda yanda yake mutum na k'warai a idon al'umma, da kuma yanda yake nuna yana matuƙar son Alhaji Muhammad Gabasawa. Lallai ka ji tsoron ɗan Adam ka kalle shi kawai, domin ba kowa ka san abun da ke cikin zuciyarsa ba. Neehal kuwa toshe bakinta ta yi saboda kukan da ya taho mata, kifa kanta ta yi hawaye na zuba a kan kuncinta kamar an buɗe famfo. 'Dan kare mutuncinta da ganin bata tozarta ta wulaqanta ba, aka kashe Ummanta da Abbanta? Tabbas babu wanda ya kay iyayenka k'aunarka a duk duniya, har abada ba zata yafewa Senator na_kowa ba da su Bilyaminu, ko da kuwa zata ga ana babbaka naman jikinsu a gabanta. Aunty A'isha ma kuka take yi, Mama kam ta daure zuciyarta sai jujjuya kai take tana da Allah wadai da wannan halin rashin imanin da zallar zalunci. Hajiya kuwa sai matsar hawaye ake tana ƴan maganganunta ƙasa_ƙasa. Sauran mutane wanda suka san yanda Abban Neehal suke mutunci da Senator na_kowa abun ya girgiza zuk'atansu. Barrister Murtala ya dubi Hashim ya ce "Kotu tana godiya bisa ga shaidar da ka bayar, zaka iya komawa ka zauna." Sannan ya dubi Bilyaminu dake ta aikin zazzare ido ya ce "Ka ji abun da Hashim ya faɗa, gaskiya ne Senator Na_kowa ne yasa ku wannan aikin?" Bilyaminu ya ce "Eh shine." Barrister Murtala ya yi murmushi ya mayar da dubansa ga Alk'ali ya ɗan rank'wafawa ya ce "Ya mai girma mai shari'a, ina roƙon wannan kotu mai adalci data yankewa waɗanda ake ƙara hukunci dai_dai da abun da suka aikata, bisa ga shaidun da aka gabatar da kuma amsa laifunsu da sukai da bakinsu. Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya juya ya koma inda yake a zaune d'azu ya zauna. Alk'ali ya ja gwauron numfashi dan shi kan shi abun ya daki zuciyarsa ba kaɗan ba sannan ya d'ago daga rubuce-rubucen da yake ya ce. "Bisa tarin hujjoji da bayanai da wannan kotu mai adalci ta tattara ta yankewa Bilyaminu,Zakari da Hakim, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an ba su horo mai tsanani a gidan kaso. Sannan kuma kotu ta yabawa Hashim Isma'il na_kowa k'warai bisa yanda ya bayar da shaida ga abun da mahaifinsa ya aikata. Shi kuma Senator Na_kowa da wand'anda suka yi kisan tare da su Bilyaminu tunda sun riga mu gidan gaskiya hukuncinsu yana gurin mahaliccin su." Alk'ali ya buga guduma gum!gum! Har sau uku. Sannan mutane aka haɗa baki gurin faɗin "Koto! Su Bilyaminu kuwa ido ne ya raina fata ganin yanda gandirobobi (Ma'aikatan gidan yari) suka ƙaraso inda suke suka fara daurawa musu ankwa a hannuwansa, a gefe guda kuma ga turmutsitsin ƴan jarida kowa na son ɗaukar rahoto. Barrister Murtala kuwa sai gaisawa mutane suke zuwa suna yi da shi, shi kuma yana murmushin samun nasara. Hajiya ce ta fara miƙewa a cikin su Mama tana faɗin. "Wannan la'anannen Senator ɗin Ubangiji ya ƙara masa azabar k'abari, mutane sai son zuciyar tsiya da rashin imani, wannan irin zalunci haka har ina?" Sai kuma ta kalli Neehal da har yanzu bata d'ago kanta ba ta ce "Wannan yarinya Allah ya bi miki haqqinki na marainiyar ƙarfi da ya ji da aka mayar da ke baki ji ba, baki gani ba." Aunty Sadiya ta taso daga inda take zaune ta dawo gurinsu tana murmushin takaici ta ce "Masha Allahu, an gano waɗanda suka kashe su Abban Neehal an hukunta su, saura kuma wanda yake kashe su Anwar shi ma." Kafin wani a cikin su ya yi magana Alhaji Ali da Daddy da sauran abokan Abba sun ƙaraso gurin, ƴan jarida na bin su yuu a baya dan son jin tofa albarkacin bakinsu a game da wannan al'amari a matsayin su na iyalan waɗanda aka kashe. Alhaji Ali ya dubi Aunty A'isha ya ce "A'isha! kin ji abun da bamu taɓa tsammani ni ba ko? Lallai ka ji tsoron duniya da mutanen cikinta, saboda ko mafarki na yi aka ce mun Na_kowa zai yiwa Gabasawa haka zan farka in yi tunanin ko addu'ar bacci ce ban yi ba, shaid'an ya kawo mun ziyara." Aunty A'isha ta girgiza kai ta ce "Yanda Abban Neehal yake yawan zancen mutumin nan da k'aunarsa da faɗar kirkinsa da mutuncinsa ashe shi zai yi sanadin barin sa duniya." Aunty Sadiya ta ce "Mutane sai addu'a kawai, amma wanda baka taɓa zaton zai iya cutar da kai ba, sai a wayi gari ya maka abun da ko mak'iyin ka na fili ba zai maka ba." Nan dai suka ci-gaba da tattauna al'amarin, su Uncle Umar ma sun ƙaraso ana jimanta abun da su, dan ya san Senator Na_kowa mutumin Abba ne sosai. Mama kuwa magana ma ta kasa yi, sai bin su da ido kawai take. A hankali Ameen yake takowa cikin takunsa mai ɗaukar hankali zuwa inda Neehal take, wadda bata ma san ya zo court ɗin ba tunda ba tare suka zo ba. Hannunsa yasa ya d'ago fuskarta bayan ya ƙarasa daf da ita, tun kafin ta kalli fuskarsa ta san shine saboda k'amshinsa da baya buya da ya ziyarci hancinta. A hankali ta d'ago ta dubi fuskarsa idanunta taf da ruwan hawaye, sai kuma ta miƙe da sauri ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kuka. Yasa hannunsa ɗaya ya zagaye bayanta yay mata kyakkyawar runguma ba tare da ya ce komai ba, sai lip ɗinsa da yake taunewa alamun abun ya taɓa masa zuciya sosai shi ma. Tsahon mintuna biyu tana jikinsa sannan ya d'ago ta a hankali ya rabata da jikinsa. Bai ce komai ba ya saka tafin hannunsa ya shiga share mata hawayen. Ta sauke ajiyar zuciya tare da yin ƙasa da kanta, ya kalli gefensa inda su Mama suke har yanzu gurin a cike yake da mutane. A hankali ya kama hannunta, bata musa ba ta bi shi suka fice daga cikin court ɗin. Da kansa ya buɗe mata Motarsa ta shiga ta zauna, sai aikin sassauke numfashi take. Ya zagaya ya shiga driver seat ya zauna shi ma. Yana ƙoƙarin kunna Motar wayarsa ta fara ringing, ya ɗauko ta daga aljihun gaban rigarsa, ganin Mama ke kiransa ya yi picked. Mama ta tambaye shi yana tare da Neehal ne. A takaice ya ce mata "Eh." Ya mayar da wayar aljihu tare da kallon Neehal wadda ta dunk'ule kanta a waje ɗaya saboda zazzaɓin jikinta dake son dawo mata sabo. Hannunsa ya kai ya taɓa goshinta ya ji da zafi, jikinta kuwa sai rawar ɗari yake. A hankali ya janyo ta ya kwantar da kanta a kan ƙafaɗarsa cikin tsananin tausayinta. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tare da lumshe idanunta, hannunta ɗaya ta saka ta zagaye bayansa da shi. Ya ɗan lumshe ido ya buɗe sannan ya kunna Motar ya yi reverse suka bar harabar court ɗin. A haka suka ƙarasa gida tana jikinsa har bacci ya fara ɗauke ta. Bayan ya yi parking ya d'aga kanta a hankali daga kan ƙafaɗarsa ya ɗan tsurawa beauty face ɗinta ido, gigirarta ya shafa da finger ɗinsa a hankali gami da ɗan bakinta da ya ɗan turo gaba saboda baccin da take. Hakan yasa ta buɗe idonta dake cike da bacci, dama baccin ba wani nisa ya yi ba. Yatsina fuska ta yi saboda kanta da ta ji yana sara mata, cikin muryar wanda ya ci kuka ya k'oshi ta ce "Yaya kaina ciwo." Ya shafi kuncinta ya ce "Sorry dear, mu je ciki ki sha magani." Ta gyaɗa masa kai tare da barin jikinsa cikin harfin hali, dan sosai take jikin nata babu daɗi. Ya buɗe Motar ya fita sannan ya zagayo ya buɗe mata itama ta fito. Hannunta ya kama suka nufi part ɗin Mama. Ya yi amfani da key ɗin hannunsa na part ɗin ya buɗe musu ƙofa suka shiga. Ta saki hannunsa da nufin ta kwanta anan falo kan kujera, fahimtar hakan yasa ya ƙara kama hannun nata ya ce "Mu je daki sai ki kwanta." Bata musa ba, amma bata ce komai ba. Har bedroom ɗinta ya raka ta ta kwanta akan gado. Yana ƙoƙarin fita ta ce "Yaya zan yi fitsari." Bai ce komai ba ya dawo ya taimaka mata ta tashi ya rakata har bakin toilet, ta shiga ta yi ta fito, ya ƙara kama hannunta zuwa bakin gado sannan ta hau ta kwanta tare da jan bargo ta lullub'e jikinta da shi. Fita ya yi daga ɗakin, ba jima sai gashi ya dawo hannunsa ɗauke da drug da ruwa. Ya zauna a bakin gadon cikin kulawa ya ce "Tashi ki sha magani." Ta tashi zaune da ƙyar tana yamutsa fuska, ya bare mata maganin ya bata ta sha ta kora da ruwa. A hankali ya ce "Allah ya sauwaqe." Ta kalle shi idanunta cike da hawaye ta ce "Ameen, Thank you." Ta koma ta kwanta. Ya matso kusa da ita ya shafi gefen fuskarta cikin wata irin murya ya ce "Don't cry, bana son inga kina kuka, bana jin daɗi." Ta tsura masa ido kamar me mamakin abun da ya faɗa, shima kallon nata yake yi. Ta kama hannunsa a hankali ta ce "Insha Allah Yaya na daina kukan tunda baka so." Ya yi mata ɗan murmushi ya ce "Sleep well." Itama murmushin ta masa ta mayar da idanunta ta lumshe. Ya zare hannunsa a hankali daga cikin nata, ya gyara mata hijabin jikinta da ya ɗan shak'e mata wuya, sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin.........✍️ _*Long page, amma ban yi edit ba, a yi haquri da typing errors.*_ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *5️⃣0️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951* ..........Falo ya koma ya zauna, ya lumshe idonsa hannunsa ɗaya dafe da kansa. Sai aikin taune lip ɗinsa na ƙasa yake alamun something is hurting his heart cikin sauke numfashi kaɗan_kaɗan. Ya fi mintuna goma a zaune ba tare da ya motsa ba, jin an buɗe ƙofar falon yasa ya ɗan buɗe idanunsa kaɗan. Mama ce ta shigo, cikin sanyin jiki ta ce "Ina Neehal ɗin." Ya d'ago ya dube tare da nuna mata ƙofar ɗakin Neehal ba tare da ya yi magana ba. Bata ce komai ba ta shige ɗakin. Bacci ta tarar Neehal ɗin tana yi wanda ga dukkan alamu bana daɗi ba ne. Ta yaye mata bargon data lullub'a ganin yanda take zufa ga jikinta ya yi zafi zau. Cire mata hijabin jikinta ta yi ta ɗan goge mata gumin fuskarta sannan ta juya ta koma falo. Ta dubi Ameen ta ce "Ka bata Magani ne?" Ya ce "Eh, na ɗauko mata a dakinki." Mama ta ce "Ashe ka je court? ban ma ga zuwanka ba." Ya ce "Ina ciki ma kuka zo." Mama ta jinjina kai ta ce "Ina Hafsat fa, me yasa baku zo tare ba?" Ya ce "Bata jin daɗi ne." Mama ta ce "Ayya, Allah ya bata lafiya." Kafin ya amsa Hajiya ta shigo falon tana faɗin "Ina Neehal ɗin ta shiga ne? ko ba gida Aminun ya kawo ta ba?" Mama ta ce "Tana ɗakinta, zazzaɓi mai zafi ne a jikinta, allura ma zan haɗa in mata yanzu." Hajiya ta ce "Subhallahi, dama jikin nata bai gama warware wa ba, gashi ta je ta jiyo wannan abun tashin hankalin ai dole zazzaɓi ya dawo baya." Mama ta ce "Allah ya bata lafiya kawai." Sannan ta nufi ɗakinta. Hajiya ta dubi Ameen ta ce "Au Aminu, ina matar taka ne? Ban ganta a kotu ba, ai yanzu an zama ɗaya ya kamata ace ta zo, duk abun da ya samu Neehal ai ya shafe ka, ko ma ince kamar kai ya sama, tunda ba ka da kamarta a duniyar nan. Koda yake ba zan yi mamakin ƙin zuwan nata ba dan ba wani son mutane take ba. Dan ranar da na je dubo ka..... "Allah ya kawo ki zaki cika mun kunne." Ameen ya katse ta da faɗin haka fuskar nan a haɗe." A zafafe Hajiya ta zauna ta ce "An cika maka kunnen, na ce an cika maka kunnen, dan k'wal uba kawai, laifin matarka ne baka son a faɗa kuma sai na faɗa ɗin!" Hajiya ta cigaba da mitarta tana faɗar Abun da Hafsat ta mata na rashin kyautawa da ta je gidan. Idan kujerar da take kai a zaune ta tanka mata to Ameen ma ya tanka mata. Mama ce ma data fito ta ji tana mitar ta sanar mata Hafsan ce bata jin daɗi shi yasa bata zo ba. Kiran sallar Azhar da akai yasa ya miƙe dan tafiya masallaci. Hajiya ta ce "Idan ka dawo sai ka kai ni na dubo jikin Hafsan." Ko juyowa bai yi ya kalle ta ba ya fice abinsa." Ya bar Hajiya tana faɗin, "Dan Allah zani ba don halinta ba." Har wajen la'asar su Aunty Sadiya suna gidan Mama suna cigaba da tattaunawa akan al'amarin. Yayinda a ɓangaren al'ummar gari ba'a wani yayata zancen ba, saboda ba'a lokacin akai kisan ba. Kafafen watsa labarai ma ba su yaɗa labarin sosai ba, saboda gargadi'n da akay wa kowacce kafar yaɗa labarai daga sama, musamman waɗanda suke zaune a ƙarƙashin gwamnati. Masu zaman kansu ne suka faɗi hukuncin da akaywa su Bilyaminu, amma suma an gargad'e su akan kar sunan Senator Na_kowa ya fito a cikin al'amarin. Alhaji Ali kuwa bayan ya koma gida ko ruwa kasa kurb'a ya yi balle akay ga cin abinci, saboda tsananin al'ajabi da ɗimauta shi da al'amarin ya yi. Sai bayan la'asar ta farka daga baccin, a hankali ta yunƙura ta tashi zaune, kanta ta dafe da hannunta saboda yanda ta ji yay mata dimm, amma babu ciwo kamar ɗazu. Jikin nata ma ta ji sauƙin sa babu zafi sosai kamar ɗazu, sai dai rashin k'warin jiki da kuma abun da baza a rasa ba. Ta ja ƙafa ta sakko daga kan gadon tana yamutsa fuska ta miƙe, taune lip ɗinta ta yi saboda yanda ta ji saman cinyarta ta hagu a ɗan daure, alamun Mama ta mata allura kenan da tana baccin. Toilet ta nufa cikin rashin k'warin jiki ta yi wanka da brush tare da dauro alwala ta fito. Tana fitowa Mama na shigowa ɗakin, dama ta shigo ta tashe ta ne ganin yamma ta yi sai kuma ta ga ta ma tashin. Mama tay sauri ta ƙarasa ta kamata ta kai ta kan gado ta zaunar. Mama ta ce "Sannu Daughter ya jikin?" Cikin muryar marasa lafiya ta ce "Da sauqi." Mama ta ce "Allah ya ƙara sauƙi, bari na shimfid'a miki darduma ki yi sallah sai ki ci abinci ki ƙara shan magani." Ta jinjina mata kai kawai. Mama ta ɗauko mata lotion ta shafa mata a hannu da ƙafafuwanta, sannan ta ɗauko mata wata gown mara nauyi ta bata ta saka a jikinta. Mama tana shimfid'a mata dardumar ta ce "Me zaki ci a dafa miki?" Ta yi shiru alamun nazari sannan ta ce "Babu komai, bakina babu daɗi." Cikin lallami Mama ta ce "Ai dole sai kin daure kin ci wani abun, cuta ba cin abinci ai bazai yiyu ba. Ga abubuwan da Ameen ya siyo miki can a dawnstairs, bari na ɗauki miki na san ba'a rasa abun da zaki iya ci ba." A hankali ta ce "Yayan ya tafi?" Mama ta ce "Eh, yakai Hajiya gidansa zata dubo Hafsah, itama bata jin daɗi." Ta ce "Su Aunty ma sun tafi?" Mama ta ce "Duk sun wuce tun d'azu." Bata kuma magana ba, dan wadda ta yi ma cikin dauriya ta yi ta, ta miƙe ta ɗauki hijabin da Mama ta ajiye mata ta saka ta tayar da Sallah. Kafin ta idar Mama ta je ta ɗauko siyyayar da Ameen ya yo mata ta kawo mata. Ledoji ne guda biyu, ɗaya kayan fruits ne cike a cikinta, ɗayar kuma Popcorn ne da wafer da shawarma da yoghurt. Ta yi murmushi lokacin da Mama take fito da su daga cikin ledar, gaba-d'aya favourites things d'inta ya siyo mata, sai dai yanda take jin bakinta babu daɗi da ƙyar zata iya ci. Yoghurt d'in ta ce Mama ta bata, shima kaɗan ta sha ta ajiye. Sai ta ɗauki wafer ɗaya ta koma kan gado tana gutsira kaɗan kaɗan tana ci. Mama ta miƙo mata wayoyinta ta ce "Anata kiranki tun d'azu, Haneefah ma ta kira, amma na d'aga nata kiran." Ta karb'i wayoyin tare da faɗin "To bari na bi bayan missed calls ɗin." Mama ta juya ta fice daga ɗakin. Ta latsa wayar ta duba ta ga Sadik da Ahmad ne suka kira ta, sai wasu daga cikin abokan aikinta sai kuma Uncle Usman. Ahmad ta fara kira saboda missed call ɗinsa ya fi yawa. Kamar jira yake ringing ɗaya ya yi rejected ya kira ta. Ta d'aga tare da yi masa sallama. Ya amsa tare da faɗin "Princess!" cikin sauke ajiyar zuciya da jan numfashi. Ta ce "Na'am Uncle, ina yini?" Ya ce "lafiya lau, jikin naki ne har yanzu?" Ya yi maganar cikin damuwa. Ta ce "Na ji sauƙi Uncle." Ya ce "Um,um Princess, sound ɗin muryarki ya tabbatar mun da baki da lafiya har yanzu, ko jikin ne ma nay ta kira baki pick ba." Ta ce "Ciwon kai ne, kuma na sha magani, time ɗin da ka kira ni kuma bacci nake." Ya ce "Oh God! Allah ya baki lafiya Princess sannu kin ji." Ta ce "Amin na gode Uncle, ina twins ɗina?" Ya ce "Suna nan k'alau, suna ta missing Auntinsu, da a cikin week ɗin nan zan kawo miki su, to kuma baki da lafiya, sai kin warke zan kawo su." Ta ce "Dan bani da lafiya baza ka kawo mun su ba." Ya ce "Eh mana, kar su zo su damar min ke." Cikin shagwab'a ta ce "Ni dai na warke, ka kawo mun su." Ya ce "Shikenan Princess zan kawo miki su, suna dawowa daga gidan Ammi, sun je can zasu kwanar mata biyu ne." Neehal ta yi murmushi cikin murna ta ce "Thank you." Ya ce "Uhm, ni fa na gane kin fi son yaranki da ni, da ni na ce zan zo baza ki yi wannan murnar ba." Ta yi murmushi mai sauti bata ce komai ba. Ya ce "Insha Allahu, inna samu chance gobe zan zo na ƙara duba jikinki." Ta ce "Uncle, Jiya fa ka zo, ka yi zamanka Please na ji sauƙi fa." Ya ce "In bakya son gani na ni ina son ganinki." Ta ce "I'm sorry ba haka nake nufi ba Uncle, na ga kana ta wahala...." Ya katse ta da faɗin "Babu wata wahala a zuwa ganin ki Princess, don't worry kin ji." Ta ce "Toh Shikenan Allah ya kawo ka lafiya." Ya ce "Ameen, sai ma in duba jikin naki da kaina in ga me yake damar mun ke haka." Ta ce "Kafin ma ka zo na warke Insha Allah." Ya ce "Allah ya amsa Princess." Daga haka suka yi sallama ya ce bari ya barta ta huta tunda bata jin daɗi. Bayan ya katse kiran ta kira Sadik amma bai ɗauka ba, ta san dama by now yana gurin aiki. Uncle Usman ta kira, yay mata ya jiki da nuna jin daɗin sa akan hukuncin da kotu ta yanke akan su Bilyaminu, dan sun yi waya da Uncle Umar ya sanar masa da komai. Bayan sun gama wayar da shi ta bibbi bayan sauran missed calls ɗin da akay mata. Bayan Sallar Magriba Haneefah suka zo gidan ita da Mijinta Faruq, ta ƙara kyau abinta kana ganinta ka ga amarya. Mama ta tarbe ta cikin mamakin ganin ta tana faɗin "Yau Amarya ce a gidan namu?" Haneefah tana murmushi ta ce "Ni ce Mama, dama ina so in zo muku sallama jibi zamu wuce Kogi, ga kuma rashin lafiyar Besty, shine na ce mu zo yanzu kawai na duba jikin nata." Mama ta ce "Har tafiyar ta zo? Sai yaushe kuma zaku dawo?" Haneefah ta ce "Sai week ɗin da za'ai resuming School." Mama ta ce "To Allah ya kiyaye hanya, ki hau sama tana ɗakinta." Ta amsa sannan ta wuce upstairs. Tana kwance rigingine tana latsa waya Haneefah ta shigo ɗakin da sallama. Ta d'ago kanta da sauri ido waje ta ce "Amarya!" Haneefah ta ce "Na'am Ango." Neehal ta tashi zaune tana murmushi ta ce "Welcome dear." Haneefah ta zauna a bakin gado kusa da ita ta ce "Yawwa ya jikin naki? Gaskiya kina jin jiki Besty duk kin rame." Neehal ta ce "Da sauqi, ai na yi kyan gani ma yanzu." Haneefah ta ce "Sannu, Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffara ne." Ta ce "Amin ƙawata, ina Yah Faruq?" Haneefah ta ce "Yana cikin Mota, tare muka zo." Neehal ta ce "Shine kuma kika bar shi a waje, ki ce ya shigo mana." Ta ɗauko wayarta a jaka ta kira shi ta ce ya shigo ciki. Neehal ta ce "Ko ke fa, ya amarci?" Haneefah ta ce "Mu sauka ƙasa ki tambayi Ya Faruq zai baki amsa." Neehal ta yi murmushi. Sun ɗan taɓa hira Haneefah ta sanar mata tafiyarsu Kogi, Neehal ta musu fatan sauka lafiya. Sannan suka sauka ƙasa inda suka tarar da Ya Faruq da Mama suna hira. Haneefah ta ɗauki juice ɗin dake gaban Ya Faruq tana duban Mama cikin zolayarta ta ce "Mama shi ne ni ba'a kawo mun ba sai shi?" Mama ta ce "Ɗana kawai na sani, ke ai gidan ba baƙon ki ba ne." Haneefah ta ce "Allah sarki ni Mama ta daina yina yanzu." Faruq ya yi murmushi tare da yiwa Haneefah gwalo a fakaice. Sannan ya dubi Neehal suka gaisa yay wa Neehal ya jiki yana tsokanarta gawa ta ƙi rami. Ana kiran sallar isha'i suka tafi saboda daga nan gidan iyayen Faruq za su biya. Bayan fitarsu Mama ta zubowa Neehal abinci ta tilasta mata ta ci, tunda ta ji sauƙi har tana iya surutu abincin ma zata iya ci. Tana tutturo baki ta fara cin abincin kamar bata so, kaɗan_kaɗan take tsakurar sa tana kaiwa baki kamar mai irgawa, gashi Mama ta ce sai ta cinye wanda ta zubo mata duka. Tana zaune ita kaɗai a falo fiye da mintuna ashirin akan abincin da ba wani yawa ne da shi ba, Ameen da Hajiya suka shigo Falon. Hajiya ta ce "Ke kaɗai ina Faɗiman? ta bar ki ke kaɗai kuma ke da ba lafiya ba" Ciki_ciki ta ce "Tana sama." Hajiya ta ce "To ya jikin naki?" Ta ce "Da sauqi." Hajiya ta ce "Ke gashi kin warware, ita kuwa waccan da na je dubowa tunda na je tana nad'e akan gado, sai masu aiki ne ke ta kai kawo." Neehal ta saci kallon Ameen wanda ya zauna akan kujera yana kallon Hajiya. Ta mayar da duban ta ga Hajiyan ta ce "To ai bata da lafiya ne." Hajiya ta ce "Duk da rashin lafiyar, amma kuma da rakin tsiya ma, sai langwab'ewa take kamar lagwani." Neehal ta ce "Dan ciwon ba'a jikin yake ba dole ki ce haka." Hajiya ta wuce sama bata tanka ba. Ameen ya tashi ya koma hannun kujerar da Neehal take kai ba tabo ba fallasa ya ce "How was your body?" Kanta a ƙasa ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Na ga kin ji sauqi har da magana haka." Ta ce "Ya jikin Aunty Hafsat?" Ya ce "Da sauqi." Ta ce "Allah ya ƙara sauƙi, ka yi mata sannu." Idansa akan abincin da take ta juyawa da spoon ya ce "Zata ji." Suka yi shiru dukan su, ita bata cigaba da jin abincin ba, shi kuma ya zuba mata ido. A hankali ta ji ya ce "Ki ajiye abincin mana idan kin k'oshi." Ta ɓata fuska cikin shagwab'a ta ce "Mama ta ce dole sai na cinye, kuma da ƙyar nake ci bakina babu daɗi." Sai kuma ta kalli fuskarsa iya gaskiyarta ta ce "Yaya ka cinye sauran Please kafin ta sauko." Ya ce "Uhm, jagwalgwalon naki zan ci?" Ta kalli abincin dan ita bata ga wani jagwalgwalawa da ta yi ba, ta turo baki ta ce "Taimakona fa zaka yi Please." Ya yi wani ɗan murmushi ya ce "Sai dai in zaki bani a baki." Ta kalle shi da sauri ta ga fuskarsa babu alamun wasa ya sha mur, kamar bashi ya gama maganar yanzu ba." Ta yi shiru ta rasa me zata ce, shi kuma ya tab'e baki irin zaɓi ya rage natan nan." Jin taku ta d'aga kai ta kalli steps, ganin Mama ce ke saukowa sai ta ɗibi abincin ta kai baki tana yamutsa fuska kamar mai cin kashi. Mama ta dube ta bayan ta ƙaraso cikin falon ta ce "Tashi ki kai kitchen ki rufe, cin ɗan wannan abincin fiye da 30 minutes kamar mai cin gandar da bata gama dahuwa ba." Ta miƙe da sauri ta nufi kitchen ɗin. Ameen ya raka ta da ido. Mama ta ce masa "Ya jikin Hafsan?" Ya ce "Da sauqi." Ta ce "Allah ya ƙara sauƙi, da safe Insha Allahu zamu zo ni da Dad mu duba jikin nata." Ya ce "Allah ya kai mu." Daga haka ya miƙe yay mata sallama ya tafi. Bayan Neehal ta yi Sallah suka yi waya da Sadik, sannan ta kwanta. Kafin ta kai ga yin baccin Mama ta shigo ta yi mata allura wanda da ƙyar ta bari aka yi dan bata son allura ko kaɗan, gwara ta sha magani duk da shi ma ba wani son shi take ba, amma duk da gwara shi sau dubu akan allurar. Tana cikin rakinta da shagwab'arta bacci ya yi awon gaba da ita.........✍️ *By* *Zeey kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *5️⃣2️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ..........A hankali take tafiya kamar bata son taka ƙasa, as always shi kuma tunda ya hango ta ya ƙura mata ido. Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon ta zauna a kan carpet ɗan nesa da shi tare da kawar da kanta gefe, su Afrah kuwa gurinsa suka nufa, wayoyinsa guda biyu ya basu bayan ya kunna musu game, cikin murna suka karb'a suka fara yi. Ba tare da ta kalli inda yake ba kamar an mata dole ta ce, "Ina yini." Bai amsa ba sai tashi da ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna ganin yanayinta ya kira ainihin sunanta. "Fateemah." Ta d'ago ta dube shi cikin mamaki dan ko da can bai taɓa kiran ta da Fateemah ba. A hankali ta ce "Na'am." Ya ce "Jikin naki ne har yanzu?" Ta girgiza masa kai, ya ce "To me ya faru na ga ranki a ɓace, ko nine ba kya son gani ko kuma kawo miki su Afrah da na yi ne ba ki ji daɗi ba?" Ta ɗan saki fuskarta ta ce "A'a ba komai Uncle." Ya ƙara matsowa kusa da ita ya sassauta murya ya ce "To me yasa ba kya farin ciki, Please be happy, bana so na ganki a haka Pleaseee.." ya ƙarashe maganar da jan kalmar ƙarshe cikin wani irin wani salo da yasa ta ji wani iri a jikinta. Ta ɗan yi murmushi tana kallon shi ta ce "To na yi Uncle, ya kuka baro Mamy?" Shima yana murmushin ya ce "Lafiya k'alau, tana ta tambayar ki, ta yi zaton ma tare zamu zo." Bata kuma cewa komai ba ta miƙa masa wayarsa dake hannunta, ya karɓa tare da faɗin. "Oh, na ma manta, thank you." Yana ƙoƙarin zira wayar a aljihu ba tare daya latsa ta ba ta ce "An kira ka fa." Ta yi maganar cikin ɓata fuska. Cikin mamaki ya zaro wayar ya duba dan ba permanent sim ɗinsa ba ne a ciki bai yi tunanin wani zai kira shi a wayar ba. Tab'e baki ya yi bayan ya ga mai kiran ya saka wayar a aljihu ba tare da ya bi bayan kiran ba. Neehal ta ɗauke kanta daga kallon sa ta ɗan turo baki gaba. Ya saka tafin hannunsa ya taɓa goshinta ya ce "Har yanzu da sauran zazzaɓi a jikinki Princess, kina shan magani kuwa?" Ta ce "Uhm." Kawai. Ya ƙura mata cikin nazartar ta, ya lura kamar akwai abun da ke damunta tunda ta fito, ko kuma wacce ke cikin ɓacin rai. Ya ɗauke hannunsa daga goshinta ya d'ago hab'arta be serious ya ce "Neehal me yake damunki?" Ta lumshe idonta tare da girgiza masa kai tana ƙoƙarin saka hannunta ta cire nasa daga fuskarta. Ya riƙe hannun nata ya ce "Please talk to me Princess, ko kina so ki ganni a cikin damuwa nima?" Ta yi shiru. Ya ƙara tambayar ta, nan ma bata tanka masa ba. Ya sauke numfashi ya cire hannunsa daga hab'arta tare da sakar mata hannunta ya ce "Okay, Good bye Dear, tunda na fuskanci kamar nine ba kya son gani." Ta buɗe idonta da sauri sai hawaye sharr wanda bata san sanda suka zubo ba. Ya dafe kansa tare da faɗin "Oh my God, Dan Allah Princess me yake damunki ne, ko na miki wani abun ne da baki ji daɗi ba?" Ya yi maganar a ɗan ruɗe yana kallon ta. Ita kanta bata san me ya saka ta a cikin wannan yanayin ba, kuma ta yi ƙoƙarin ta danne kar ya fuskanta amma ta kasa. Ta turo baki gaba sosai ta ce "Ka ce mun tunda Maman twins ta rasu baka ƙara kula wata mace ba, and now kuma naga wata ta kira ka harda text, who is she?" Ta yi maganar iya gaskiyar ta. Sai yanzu ya gane bakin zaren, shi dariya ma ta ba shi ba kaɗan ba, amma yanda take a sama ɗin nan in ya dara ya san da matsala, musamman yanda ta tsare shi da kyakkyawan idanunwan nan nata tana jiran amsa. Ya danne dariyarsa ya ce "Oh wai Jamila, she is my cousin, ƴar ƙanwar Dad ce." Ta juya masa idonta ba tare da ta ce komai ba, amma bata gamsu da abun da ya faɗa ba. Ya yi ɗan murmushi tare da matsowa daf da ita, ya kai bakinsa dai_dai saitin kunnenta ya ce "Princess ce kaɗai a zuciyar Uncle ɗinta, since, now and for ever, daga ita kuma babu ƙari." Ta rufe fuskarta da hannunta cikin jin kunyar gano ta da ya yi. Ya yi ƴar dariya ya ce "Ashe Babin Uncle ta fara sonsa har da su kishi?" Ta juya masa baya a shagwab'e ta ce "Ni ba kishi nake ba?" Ya ce "To me kike? Jealous? Kamar zata yi kuka ta ce "Ni fa Allah ba kishi nake ba." Ya juyo da ita da hannunsa ya sa tafin hannunsa ya share mata hawayen data zubar d'azu, zuciyarsa fess da yanda ta nuna tana kishin nasa. Ya zubawa fuskarta ido yana jin kamar ya mayar da ita cikin jikinsa saboda k'auna. Jin maganar Afrah a kusa da shi yasa ya ɗauke idonsa daga kallon ta ya mayar kan yarinyar da take miƙo masa wayarsa tana faɗin "Daddy kiran Sallah ake a cikin wayar." Ya karɓa ya ce "To aje a yi alwala a yi Sallah." Ta ce "Tom Daddy." Ya yi mata kiss a goshi itama ta mayar masa tana dariya sannan ta nufi upstairs da ɗan gudunta tana cewa Amrah sai ta riga ta hawa saman. Jin haka itama Amrah ta kawo masa ɗaya wayar ta bi bayan ta. Neehal ta bi su da kallo cikin k'auna. Ya ce "Princess zan wuce?" Ta juyo ta ce "Sai yaushe?" Ya ce "Gobe da safe Insha Kafin na wuce." Ta ce "Allah ya kai mu." Ya miƙe tsaye yana faɗin "Amin." Itama miƙewar ta yi, ya ja karan hancinta ya ce "Bye, I love You." Ta ce "Allah ya kiyaye." Ya ɓata fuska tare da langwab'ar da kansa ya ce "Ba feedback?" ta yi murmushi bata ce komai ba, ya ce "Shikenan." Ta ce "Thank you for coming, and..." "Kawo miki twins ko?" Ya ƙarasa mata dan ya san haka zata faɗa. Ta yi murmushi tare da gyaɗa masa kai. Ya yi mata murmushin nan nasa mai kyau tare daga mata hannu sannan ya juya ya tafi. Ta sauke ajiyar zuciya bayan ya fice, a ranta tana faɗin 'Ko sallama bai yi da ƴaƴansa ba.' Ta juya ta haye upstairs, ɗakin Mama ta shiga ta tarar da ita tana ƙoƙarin shimfid'a darduma, su Afrah suna taya ta. Amrah ta ce mata "Aunty ina Daddy? Ya tafi?" Ta ce "Eh ya tafi gidan Mamy, amma gobe da safe zai dawo." Mama ta ce "Ki je ki yi alwala ki zo ki yi Sallah, tunda kin warke sai ki shiga kitchen ki yi masa something special gobe in ya zo sai ki ba shi ya tafi da shi" Ta ɓata fuska ta zauna a bakin gado ta ce "Mama ban fa warke ba, cikina ma tun safe ya fara mun ciwo." Mama ta ce "Allah ya sauwaqe." Daga haka ta tayar da Sallar ta. Miƙewa ta yi itama ta shiga toilet ta fito ta tayar da Sallar. Daf da Magriba Sadik ya shigo gidansu a gajiye, a falon Maamah ya tarar da Hajiyarsu da Batul, Maamah kuma tana bedroom ɗin Abba tana gyara saboda ta karɓi girki da yammar nan. Ya zauna a kusa da Hajiya cikin mamakin ganin ta ya ce "Ƴar tsohuwar nan ke ce a gidan namu? Zuwa babu sanarwa, ai da kin faɗa dana taho miki da tsarabar goruba." Ta rank'washi kansa ta ce "Giginya zaka siyo mun ba goruba ba, ɗan nema kawai." Ya yi murmushi tare da miƙewa yana faɗin "Kin yiwa kanki tunda ba kya so, bari na shiga ciki na fito." Ta ce "To a fito lafiya." Batul ta ce "Sannu da zuwa Yaya." Ya ce "Yawwa, ina Maamah?" Ta ce "Tana ɗakin Abba." Bayan ya dawo daga masallaci Maamah ta kawo masa abinci yana ci suna hira da Hajiya har ta sako masa zancen Neehal inda ta ce "Abubakar ashe ka fara yunƙurin yi mini kishiya ban sani ba?" Ya yi murmushi ya ce "Har kin samu labari kenan?" Ta ce "Shine ma abun da ya kawo ni gidan nan yau?" Ya ce "Kamar ya Hajiya, ko duk kishin ne?" Ta sanar masa yanda suka yi da su Abba da Kawu a tak'aice." Sadik ya ajiye cokalin hannunsa fuskarsa na nuni da damuwa ya ce "Hajiya wannan zancen fa ba gaskiya ba ne, shati faɗin mutane ne kawai." Hajiya ta ce "Koma mene ne dai mahaifinka ya ce zai bincika, in ma gaskiya ne in ma ƙarya ne duk zai gano, amma kafin nan ka fara tuntubar ita yarinyar da zancen, idan har tana sonka da gaskiya saboda Allah kuma ba su da wata manufa akan kisan ake yi zata faɗa maka gaskiya da bakinta." Sadik ya marairaice ya ce "Insha Allahu Hajiya zan tambaye ta, Amma dan Allah Hajiya ko me zai faru karki bari su Abba su hana ni Aurenta, ina sonta sosai wallahi." Maamah dake sauraren hirar tasu cike da tausayin ɗan nata ta ce "Sadik, ka yi addu'a kawai, idan Alkhairi ce a gare ka Allah ya baka ita, idan kuma ba Alkhairi ba ce Allah ya baka wadda ta fita, sautari wani abun da muke so ba shine Alkhairi a gare mu ba, rashin sa a tare mu ya fi zama Alkhairi." Ya kalli mahaifiyar tasa ya ce "Shikenan Maamah, Insha Allahu zan cigaba da addu'a akan wacce nake yi." Hajiya ta ce "Shi ya fi dai, muma zamu taya ka da addu'ar, abun da mahaifiyarka ta faɗa gaskiya ne." Ya yi shiru cikin damuwa, amma a cikin ransa yana jin ba zai iya rabuwa da Neehal ba, kuma Insha Allahu itace matarsa." Bayan su Neehal sun idar da Sallah ba jimawa Ameen ya zo gidan. Su Afrah suka tafi da gudu gurinsa suna faɗin "Oyoyo Uncle." Ya d'aga su ɗaya bayan ɗaya ya shilla yana murmushi. Sannan ya kamo hannunsu zuwa bakin gado ya zauna ya gaishe da Mama. A hankali Neehal ta dube shi ta ce "Ina yini Yaya." Ya kalle ta ya ce "Lafiya k'alau." Ta ce "Ya jikin Aunty Hafsah?" Ya ce "Da sauqi, ya naki jikin?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya mayar da duban sa ga su Afrah ya ce "Yaushe kuka zo?" Afrah ta ce "D'azu Daddy ya kawo mu." Ya shafi kuncinsu bai ce komai ba. Mama ta ce masa "Ya aikin naku? Ya ce "Alhamdulillah, Hajiya ta wuce kenan?" Mama ta ce "Eh, tun safe ba ku yi waya ba ne?" Ya ce "Na ga missed call ɗinta tun safe, na kira ta kuma d'azu bata ɗauka ba." Mama ta ce "May be time ɗin suna hanya, amma mun yi waya kafin Magriba ta ce sun ƙarasa." Ya ce "Okay." Mama ta dubi Neehal ta ce "Zubo masa abinci, na san da ƙyar in ka ci tunda Hafsah bata da lafiya, suma su Afrah ki zubo musu." Ta ce "Toh." Tare da miƙewa ta fice. Ya ce "Allah yasa ina cin abin da kuka dafa." Mama ta ce "Koma mene haka zaka ci, har yanzu baka daina zaɓe zaɓen abinci ba ko Ameen? To tuwo na yi, itama Neehal yanzu ta gama cewa baza ta ci ba, na ce mata ta kwana da yunwa kuwa dan babu mai sake mun wani sabon girki yanzu, tunda ku tsurfar ku ta muku yawa." Ya yi ɗan murmushi tare da miƙewa ya fice daga ɗakin. Kitchen ɗin ya shiga inda ya tarar Neehal tana ƙoƙarin zuba miya. Ya ce "Kar ki zuba." Ta juyo ta dube shi ta ce "Ka fasa ci?" Ya gyaɗa mata kai. Ta ce "Na manta ashe fa baka cin tuwo, in dafa maka wani abun to?" Ya ce "Like what?" Ta ce "Akwai miya, sai ka faɗi abun da kake so in dafa maka." Ya ce "Okay, dafa mun ko mene ma." Ta ce "Toh." Ya juya ya fice. Ta dauko tukunya ta ɗauraye sannan ta zuba ruwa ta kunna gas ta ɗora. Ta buɗe frizer ta ɗauko kayan salad ta zauna ta fara yankawa kafin ruwan ya tafasa. Mama ce ta shigo kitchen ɗin ta dubi tukunyar data ɗora ta sannan ta dube ta, ta ce. "Me kike yi haka?" Ta ce "Yaya zan dafawa abinci, kin san ba ya cin tuwo." Mama ta ce "Oh, yanzu kin warke kenan zaki iya girki?" Ta ce "To Mama naga bai ci abinci ba, kar ya zauna da yunwa, kuma ba wani girki mai wahala zan yi ba." Mama ba ta ce komai ba ta juya ta fice. Mintuna kaɗan ruwan ya tafasa, ta ɗauko macaroni ta zuba fiye da rabin leda. Bayan ta gama ta juya a plate ta kai masa falo ta ajiye a gaban sa. Ya dube ta ya ce "Thank you." Sannan ya sauko daga kan kujerar da yake ya zauna a kan carpet, ya dubi abincin ya ce "Take another spoon." Ta koma ta ɗauko ta kawo masa, bai karɓa ya ce "Zauna mu ci." Ta ce "Yaya na k'oshi." Yay mata wani kallo, ba shiri ta zauna suka fara ci tare. A takure take sosai saboda ba su taɓa cin abinci tare ba, kanta a ƙasa take cin abincin ta kasa d'agowa ta kalle shi. Shi kuwa kallon ta ya ma fi cin abincin nasa yawa. Ba su fi rabin abincin ba ta ce ta ƙoshi, ya ce bata isa ba sai sun cinye duka. Dama Mama ta gama masa mitar tunda yasa a yi masa girki, to kar ya bar mata sauran abinci ko d'igo ya cinye duka. Haka ta haqura suka ƙarasa ci. Bayan sun gama ta ɗauke plate ɗin ta kai kitchen, su Afrah ta zubawa ragowar abincin a plate ɗin, kafin ta fito har ya fice daga falon. Ta wuce sama ta kai musu abincin, ta tarar su Cake ma suke ci da yoghurt. Ta ajiye abincin ta ce in sun gama sa ci, sannan ta fita zuwa ɗakinta. Tana ɗaukar wayarta ta tarar da missed call ɗin Sadik har huɗu, da chaji ma zata saka wayar, amma dai ta kira shi duk da ta ji an fara kiran isha'i, ya d'aga ya ce mata idan ya dawo daga masallaci zai kira ta. Bayan an yi Sallar ya kira ta, ta daga suka gaisa ya tambaye ta jikinta ta sanar masa ta ji sauƙi. Cikin damuwa ya ce "Wifey wai me yake faruwa ne?, kwana biyu naga gaba-ɗaya kin canza mun, kafin ki yi rashin lafiyar nan idan na kira ki sometimes da daddare sai in ji call waiting, ina tsoron kar wani ya mun ƙafa fa." Ta yi shiru dan ita kanta ta san tunda Ahmad ya shigo cikin rayuwarta ta canzawa Sadik, dan ma yana da haquri da wani ne da tuni sun yi faɗa, ko kuma inda ita ce yake mata haka bata san ya za tay ba. Cikin sanyin murya ta ce "Ka yi haquri Husby, ni kaina na san ban kyauta maka ba, amma babu abun da ya faru, kuma babu wanda yay maka wata ƙafa balle hannu, har yanzu kai kaɗai ne a zuciyar Neehal." Cikin jin daɗi ya ce "Dagaske Wifey?" Ta ce "Gasken gaske ma, Ya Sadik ina da kai me zan yi da wani ɗa_namiji kuma?" Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Har na ji daɗi a raina, dan bana son abun da zai raba ni da ke." Ta ce "Insha Allahu Husby zamu rayu tare har ƙarshen rayuwarmu." Ya ce "Amin Amin Wifey." Suka Cigaba da hirar su ta masoya Sadik ya sanar mata Insha Allahu gobe zai zo, akwai maganar da yake son su yi. Ta ce Allah ya kai mu lafiya sai ya zo ɗin. Bayan sun gama wayar ta yi tagumi ta fara tunani, tabbas ta san zuciyarta Sadik take so, so mai tsanani ma kuwa, amma abun da ta rasa ganewa matsayin Ahmad a gurin ta, da farko tana masa kallon like ɗan'uwanta na jini, amma a kwanakin nan lissafin yana ƙoƙarin sauyawa a cikin zuciyarta game da shi. Ga kuma tausayinsa mai tsanani da take ji, saboda koda bai faɗa ba tana hango sonta mai tsanani a cikin kwayar idonsa, ga kuma yaransa da Allah ya ɗora mata kaunarsu, bata jin zata iya jurar Ahmad ya auri wata matar ta riƙe masa su Afrah, ta san kuma koda bata aure shi ba in ta ce masa ya bar mata su zai bata, amma ta san Mama baza taɓa yarda da hakan ba. Last abu kuma da yake damunta shine, ko zata yi auren at this time ko baza ta yi ba sai Allah, za'a barta da wanda zata aura ɗin ne ko za'a kashe mata shi kamar su Anwar?.... Shigowar su Afrah ya katse mata tunanin da take. Suka haye jikinta suka ce ta kira musu su Ummi, ta kira Zahra bayan ta ɗauka sun gaisa ta ba su wayar, suka yi mata surutun su sannan ta kaiwa Ummi wayar itama suka yi magana, har Dad ɗin su Ahmad yau sun gaisa da Neehal. Ta gaishe su cikin girmamawa su kuma su kay ta saka mata albarka. Bayan sun gama wayar ta ja su toilet tay musu wanka, tana shirya su suka dame ta akan ta kira musu Daddy'nsu. Ta kira shi kuma bai d'aga ba. Bayan ta shirya su, ta kama hannunsu suka nufi part ɗin Daddy dan su gaishe shi. Sai da goma ta wuce ta dawo part ɗin Mama ɗauke da Amrah a hannunta, Mama kuma ta biyo ta da Afrah dan har sun yi bacci. Bayan ta yi wanka ta sha magungunanta ta kwanta, lokacin sha ɗaya saura ƴan mintuna, ta ɗauko wayarta ta tarar da missed calls ɗin Ahmad, ta bi bayan kiran nasa, sai da ta kusan katsewa ya ɗaga cikin muryar bacci suka ɗan yi magana kaɗan, ya sanar mata fita suka yi da Mamy bayan ya koma gida, shi yasa bai kira ta ba, sai bayan sun dawo ya ga missed call ɗinta. Suna gama wayar itama bacci ya ɗauke ta. Washegari Neehal ta tashi da ciwon cikinta, amma bai yi tsanani sosai ba. Sai wajen ƙarfe goma na safe ya tasar mata sosai, gashi Mama bata nan ta tafi gurin aiki tun 8. Ganin yanda take nuk'urk'usu da juyi akan gado su Afrah suka sauka ƙasa da gudu suka kira su Dije. A tare suka dawo da yaran. Dije ta riƙe mata hannu cikin tausayawa ta ce "Sannu Neehal, ina maganinki yake a ɗauko ki sha?". Tana hawaye ta buɗe baki da ƙyar cikin rawar murya ta ce "Yana ɗakin Mama." Zulai ta tafi da sauri ta duba amma bata gani ba. Ta dawo ta cewa Neehal "A ina take ajiyewa ban gani ba." Neehal ta taune lip ɗinta ta tashi zaune da ƙyar ta nuna musu wayarta, Dije ta ɗauko da sauri ta miƙa mata, ta karɓa ta cire key ta yi dialing ɗin Numbern Mama ta miƙa musu, ba tare da ta yi magana ba ta koma ta kwanta, hannunta dafe da mararta dake barazanar fashewa dan ciwo da murd'awar da take mata. Har wayar ta katse Mama bata ɗauka ba, suka ƙara kira bata ɗauka ba. Cikin damuwa Zulai ta ce "Bata ɗauka ba Neehal." Ta fashe da kuka saboda azabar ciwo, dama Maman ta ce mata yau surgery zata yiwa har mutum uku, ta san may be ta shiga theatre room ɗin shi yasa bata ɗauki wayar ba. Cikin Kukan ta ce "Ku kira Yaya ko Daddy su zo mutuwa zan yi." Su Afrah suka saka kuka ganin yanda take kukan itama. Zulai ta yi searching sunan Yaya ta kira. Sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka. A gaggauce Zulai ta sanar masa abun da yake faruwa, yana gurin aiki amma ya ce gashi nan zuwa gidan. (This week Ameen ya dawo Kano da aiki kamar yadda ya sanar da Mama, and an ƙara masa matsayi from captain to lieutenant Colonel.) Dije ta riƙe hannun Neehal tana zuba mata sannu, Zulai ta sauka ƙasa dan ɗauko ruwa ta tofa mata addu'a ta sha ko Allah zai sa a dace kafin Ameen ɗin ya ƙaraso. Bata kai ga ɗauko ruwan ba ta ji ƙarar door beil, ta nufi ƙofar da sauri ta buɗe cikin addu'ar Allah yasa wanda zai iya taimakon Neehal ɗin ne Allah ya kawo musu. Ahmad ta gani, ta bashi hanya ya shigo falon, cikin girmamawa ta gaishe shi. Ya amsa mata da fara'arta sannan ya tambaye ta Neehal, ta sanar masa bata da lafiya tana sama kuma Mama bata nan. A rikice ya ce su je ya ga jikin nata. Suna shiga ɗakin, su Afrah suka tashi da gudu suka nufe shi. Amrah ta ce "Daddy Aunty bata da lafiya, sai kuka take." Bai bi takan yaran ba ya ƙarasa bakin gadon ya kamo hannun Neehal a ruɗe, lokacin ta galabaita matuƙa sai numfarfashi take kamar zata shid'e. Ya sunkuyo a hankali ya ce "Princess! Me yake damun ki?" Zulai ce ta faɗi amsa da faɗin "Ciwon ciki take." Ya ce "Okay." Ta buɗe idanunta da ƙyar ta kalle shi, sai kuma ta saka kuka cikin azabar ciwo ta buɗe baki da ƙyar ta ce "Uncle ka kai ni gurin Mama Please mutuwa zan yi." Ya shafa fuskarta cike da tausayawa ya ce "Sorry dear, zaki samu sauqi soon Insha Allah." Ya dubi su Dije ya ce "Dama tana yin irin haka?" Suka ce "Eh." Ya miƙe da sauri dan ya gano mai yake damunta, ya ce musu yana zuwa zai je ya dawo yanzu. Afrah ta ce "Daddy ta kai ta hospital please." Ya ce "No yanzu zan dawo na bata magani." Cikin sauri ya fice daga gidan ya je wani pharmacy ya siyo allura ya dawo gidan. Kafin ya dawo har ta yi amai a ƙasan gadon, su Dije suna cikin gyara wurin ya dawo. Ya haɗa allurar sannan ya hau kan gadon ya d'ago ta a hankali. Ta faɗa jikinsa ta k'ank'ameshi sosai cikin gigitar ciwo. A hankali ya d'aga rigar jikinta tare da ɗan zame dogon wando jikinta yay mata allurar. Ta saki gwauron numfashi tare da ƙoƙarin barin jikinsa, ya ƙara riƙe ta da kyau da ɗaya hannunsa, ɗayan hannun kuma yana mulmula mata wurin allurar. Fita su Dije su ka yi da kayan da suka gyara inda tay aman. After 5 minutes har lokacin tana jikinsa, ta yi lamu a jikinsa tare da lumshe ido, ga dukkan alamu ta fara samun relief, sai ajiyar zuciya take saukewa akai_akai. Amrah ta ce "Daddy ta ji sauqi ko? tunda ka yi mata injection?" Ya gyaɗa mata kai. Afrah ta saki ajiyar zuciya ta ce "Thank God." Neehal ta fara ƙoƙarin tashi daga jikinsa dan tun sanda ta yi amai ta ji jinin ya fara zuba a jikinta, kuma gashi bata saka pad ba tana tsoron kar ta yi stain a jikinsa. Ya ƙi bata damar hakan sai ma ƙara gyara mata kwanciya da ya yi a jikinsa, ji yake kamar ya mayar da ciwon jikinsa, a hankali ya ce "Princess ya jikin?" Ta gyaɗa masa kai kawai, ya fara gyara mata gashin kanta wanda ya ɗan barbaje har saman fuskarta ya ce "Allah ya baki lafiya Baby." Ta jinjina masa kai kawai, ita so take ta bar jikinsa amma ya hanata, gashi sai ƙara jin zubar jinin take a jikinta, tana tunanin ma ta ɓata shi. Turo ƙofar ɗakin akai da ƙarfi hakan yasa ta buɗe idonta da sauri ta kalli ƙofar, Ahmad ma ƙofar ya kalla. Ameen ne ya shigo ɗakin, yana sanye cikin uniform ɗinsu na sojoji wanda suka ƙara fito masa da kwarjininsa, suka kuma matuƙar yi masa kyau.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *5️⃣1️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ..........Washegari da misalin ƙarfe goma na safe, Neehal tana cikin bacci ta ji muryar Hajiya tana tashin ta. Ta buɗe ido da ƙyar tana duban ta cikin muryar bacci ta ce "Bani da lafiyar ma ba zaki bar ni na huta ba?" Hajiya ta ce "To tafiya zan yi na tashe ki mu yi sallama ƴar nema." Ta tashi zaune tana hamma tare da yin salati. Ta dubi Hajiya ta ce "Kai Hajiya yanzu tafiya zaki yi kamar wadda ake kora? Ki ɗan ƙara mana kwana biyu mana." Hajiya ta ce "Ba zan zauna ba, yau a Gombe mahaifata zan kwana, in kuma na ƙara dawowa garin nan to sai dai in bikin na zo insha Allah." Neehal ta ce "Zaki yi shekaru kuwa baki zo ba, indai bikina ne." Hajiya ta riƙe baki ta ce "Ikon Allah, ka ga shashashar yarinya zatai wa kanta mugun baki, to in ba ki yi aure ba jiƙa ki su Faɗiman za su yi su shanye? ko kuma zama zaki yi kuna goga ƙafaɗa da ita a gidan?" Neehal ta sauko daga kan gado bata tare da tankawa Hajiya ba ta shige toilet. Hajiya ta ce "Kya shige banɗaki mana ja'irar kashi kawai, da kai kamar k'ullin magani." Ta ƙaraci mitarta sannan ta fice daga ɗakin. Bayan Neehal ta fito daga toilet ɗin ta saka kaya sannan ta hau gyaran dakin nata, tana cikin gyaran Mama da Daddy suka shigo. Daddy ya ce "Daughter da kanki kike gyaran ɗaki ke da ba ishashshiyar lafiya ce da take ba." Ta yi murmushi tare da ajiye filon dake hannunta ta ce "Ai na ji sauƙi Daddy na." Mama ta ce "Masha Allah, Allah ya k'aro sauƙi." Ta amsa da Amin, sannan ta gaishe su. Daddy ya ce "Jiya da daddare na zo ganin jikin naki na tarar kina ta bacci, ƙwaƙwa da dabidon da kika ce mun kina so yana cikin fridge na bawa Mamanki ta ajiye miki." Neehal ta ce "To Daddy na, na gode sosai." Ta kalli Mama ta ce "Allah yasa dai babu wanda ya ci mun." Mama ta ce "Tunda kowa irin ki ne ba, Ki sauka ƙasa ki yi break zamu je gidan Ameen yanzu mu dubo Hafsah." Neehal ta ce "Hajiya ta tafi ne?" Mama ta ce "Tana falo yanzu dai zata tafin." Bin su Mama ta yi suka sauka ƙasa tare, har parking space ta raka su, tay wa Hajiya sallama wadda direban Mama zai kai ta gidansu Aunty A'isha da Aunty Sadiya daga can zai wuce ya kai ta Gomben. Bayan ta koma cikin gidan ta haɗa tea ta sha ta ɗan ci Irish sannan ta sha maganinta. Suna zaune a falon ƙasa suna hira da su Dije suka ji ƙarar door beil, Zulai ta tashi ta je ta buɗe, a zaton Neehal Mama ce ta dawo amma sai ta ji muryar waɗanda bata taɓa tsammani ba wato Afrah da Amrah suna kwad'a kiran sunanta. Ta tashi tsaye da sauri tana kallon su cikin shock. Suka taho da gudu suka rungume ta. Ta tsugunna itama ta rungume su duka cikin tsananin farincikin ganin su. Ta d'ago su daga jikinta har lokacin fuskarta na ɗauke da mamaki ta ce "Sweethearts wa ya kawo ku?" Suka haɗa baki gurin faɗin "Daddy ne, Aunty ina Mama?" Ta ce "Ta fita unguwa amma yanzu zata dawo." Afrah ta ce "Aunty ya jiki? Daddy ya ce baki da lafiya kar mu zo mu cika miki kunne da surutu." Ta shafi kuncin yarinyar ta ce "Da sauƙi Dialing ina Daddy'n." Amrah ta nuna mata bakin ƙofa inda yake a tsaye hannunsa hard'e a ƙirjinsa yana kallon su, ga trolley ɗin kayan su Afrah a gefen sa." Ta ƙura masa ido tunda suna ɗan nesa da juna baza su iya haɗa ido ba, yau sanye yake cikin manyan kaya wanda suka yi masa kyau sosai, tunda take bata taɓa ganin sa da manyan kaya ba sai yau. Ya fara takowa a hankali zuwa inda suke, ganin haka yasa su Dije suka tashi suka nufi kitchen dan kawo masa drinks. Ta ɗauke idonta daga kallonsa da sauri ta mayar ga su Afrah tana murmushi ta ce "Welcome dear, I missed you alot." Amrah ta ce "Missed you too Aunty." Ta ce "Ya school? Dafatan dai kuna karatu sosai?" Suka gyaɗa mata kai. Ta ce "That's is good, ina Ummi da Aunty Zahrah da Ammi?" Afrah ta ce "Suna gida mun bara su, Aunty Zahrah ta ce zata biyo mu Ummi ta hanata." Ta zauna sosai a kan carpet ɗin falon ta ɗaura su duka akan cinyarta suna yi mata hira, ko ƙara kallon inda Ahmad yake bata yi ba. Shi ma bai ce mata komai ba sai zama da ya yi yana kallonsu. Har su Dije suka dawo falon suka ajiye masu drinks da snacks. Ganin da gaske ba kula shi zatai ba ta yaranta kawai take sai ya cewa su Afrah su tashi daga jikinta ba su ga bata da lafiya ba. Yaran suka tashi da sauri suna faɗin "I'm sorry Aunty." Neehal ta ɓata fuska ba ta ce komai ba, ta miƙe ta kamo hannunsu da nufin su wuce sama, a hankali kanta na ƙasa ta ce "Ina kwana." Ya k'ank'ance ido yana dubanta ya ce "Lafiya, ya jikin naki?" Ta ce "Da sauƙi." Ya ce "Allah ya ƙara sauƙi." Tare da miƙewa ya ce wa su Afrah su ya kai su gidan Mamy, da yamma sai ya dawo da su. Neehal ta ce "Daga zuwanku, dan Allah ka bari idan Mama ta dawo sai mu je tare." Ya ce "Ke da baki da lafiya kuma zaki fita, idan kin ƙara warwarewa sai ku je, tunda za su kwana biyu a nan." Bata ce komai ba ta saki hannun yaran ba don taso ba. Ya kama hannunsu suka juya za su tafi, ta kalli abubuwan da su Dije suka ajiye masa ta ce "Uncle ko ruwa baka sha ba zaka tafi?" Ya yi mata ɗan murmushi ya ce "Idan na dawo zan sha." Ta ce "Shikenan sai kun dawo ɗin, Allah ya kiyaye." Ta d'agawa su Afrah hannu tana faɗin su gaishe mata da Mamy. Bayan fitar su ta zauna akan kujera zuciyarta cike da farincikin zuwan yaran. Ta miƙe dan kai trolley ɗinsu ɗakinta sai ta ga ƙaramar waya keypad akan kujerar da Ahmad ya zauna, da alama dai tasa ce ya manta ta. Wayarta ta ɗauko akan centre table da sauri ta kira shi dan ta sanar masa ya manta wayar tunda bai yi nisa ba ya dawo ya ɗauka. Ringing biyu ya d'aga, ta ce "Uncle ka manta ƙaramar wayarka a nan." Ya ce "Ohh, ki ajiye mun ita kawai Princess, idan na dawo anjima sai na karb'a." Ta ce "Tom Allah ya kai mu." Daga haka ta katse kiran. Ta ɗauki wayar ta ja trollin su Afrah ta yi upstairs. Tana shiga ɗakinta ta ji cikinta ya fara juya mata hakan yasa ta kwanta, ba jimawa da kwanciyar tata bacci ya ɗauke ta. Sai wajen Azhar Mama ta dawo gidan, ita kaɗai ta dawo Daddy ya wuce gurin sabgoginsa. Kitchen ta faɗa ta ɗora girki, sannan ta barwa su Dije su ƙarasa dan ita Hospital zata tafi aiki, ta bar musu sallanun idan Neehal ta tashi su ce mata ta wuce office, a bakinsu take jin labarin zuwan su Afrah da mahaifinsu, ta ji daɗi itama sosai ta ce Insha Allahu zata dawo da wuri kafin su dawo daga gidan Mamy...... A gidan su Sadik kuwa yau tun safe Kawunsu ya zo gidan shi da Hajiyarsu (Kakar su Sadik) wadda kawun ya biya ya taho da ita. Maamah ta tarb'e su cikin mutuntawa da girmamawa. Umma kuwa yau ita ce da girki tana ɗakin Abba tana zuba masa kissa da kisisina, zuwan su Hajiyan yasa suka fito tare da Abban. Bayan an gama gaggaisa sun taɓa abun da Maamah ta kawo musu Kawu ya gyara zama ya dubi Abba ya ce. "Surajo Rukayya ta kira ni ta sanar da ni wani zance mara daɗin ji da ma'ana." Abba ya kalli Umma ya ce "Wanne zance kenan Yaya?" Kawu ya ce "Zancen yarinyar da Abubakar yake neman Aurenta mana." Hajiya ta tari numfashin Abba da faɗin "Au Sadik ɗin har ya fara neman Aure ba mu da labari?" Abba ya ce "A'a, soyayya dai kawai suke, tunda shi batun Aure dole sai an fahimci juna kafin akai ga maganar yin sa." Hajiya ta ce "Gaskiya ne, To Allah ya taimaka. Amma me ya faru da ita yarinyar?" Kawu ya kwashe duk abun da Umma ta sanar masa ya faɗa musu. Hajiya ta zaro ido tana jinjina kai ta ce "Kai! Gaskiya kuwa matuƙar haka ne da matsala, to ya rabu da ita mana ya nemi wata, ga ƴan mata nan burjik da yawa a gari sai ya zab'a ya darje." Maamah ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin rashin jin daɗi, Umma kuwa murmushin farinciki ta saki a ɓoye." Abba ya ce "Ni fa Hajiya a gani na wannan duk ba matsala ba ce, yarinyar nan na yi binkice a kanta da iyayenta sosai mutanen kirki ne, mahaifinta ba b'oyayyen mutum ba ne, dan ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa, daga baya kuma ya daina siyasar kwata_kwata. Duk da dai ba shi ya haife ta ba, amma a matsayin mahaifi yake a gurinta tunda shi yake riqon ta." Maamah tay saurin d'ago kanta a karon farko ta ce "Au ba shi ɗin ne ya haife ta ba dagaske?" Abba ya ce "Ehh, amma itama yarinyar an tabbatar mun mahaifinta kafin ya rasu mutumin kirki ne, kuma ɗan asalin jihar nan ne a ƙaramar hukumar Gabasawa." Kawu ya ce "Wane ne marik'in nata?" Abba ya ce "General Alhaji Muhammad Tafida." Kawu ya jinjina kai ya ce "Tabbas na san sunan mutumin sananne ne, to amma mu yanzu ba nasabarta ce abun damuwar mu ba, damuwar mu batun kashe duk wanda ya ce zai aure ta da ake yi." Hajiya ta ce "Gaskiya fa, abun nan abun dubawa ne, dan watakila aljanu ne da ita suka aure ta." Umma ta ce "Nima abun da na gani kenan Hajiya, hankalina gaba-d'aya ya tashi har na kasa haquri na kira Yaya na sanar masa dan a yiwa tufkar hanci, tunda shi Abban nasu ya ƙi saurara ta." Abba ya ce "To, gaskiya ni dai duk a iya binciken da na yi ban ci karo da wannan labarin ba, kuma itama Rukayyan ban san a ina ta samo shi ba." Umma tay karaf ta ce "Ai ita marik'iyar yarinyar akwai ƙanwarta a nan unguwar, nan gaba kaɗan ne da mu babu nisa, to a gurin wata mak'ociyarta na ji wannan labarin, kuma babbar mace ce baza tay mun ƙarya ba." Abba ya ce "Ka ji fa, watak'ila ma ba gaskiya ba ne zuzutun abu ne irin naku na mata." Hajiya ta katse shi da faɗin, "Ba wani zuzutun mu na mata, maganar nan fa ya kamata a duba ta, kar mu zo mu yi abun da za'ai dana sani daga baya." Kawu ya ce "Ato, faɗa masa dai Hajiya." Abba ya ce "Shikenan, zan yi sabon bincike akan hakan Insha Allahu, idan ya tabbata haka ne sai ya haqura da ita ya nemi wata kawai." Daga haka suka rufe wannan chapter suka kama wata...... Sai da ƙarfe biyu na rana ta wuce sannan Neehal ta tashi daga baccin da take, shima ƙarar wayar Ahmad da ake ta kira ne ya farkar da ita. Tashi zaune ta yi tana kallon agogon bangon dake ɗakin, mamaki ne ya cika ta ganin ta yi fiye da awa uku tana baccin. Ta sauke numfashi a ranta tana tunanin may be a cikin magungunan data ke sha akwai na bacci, dan wannan baccin nata daga jiya zuwa yau ya yi yawa. Ta sauko daga kan gadon domin yin Sallah, wayar Ahmad ce ta ƙara yin ringing alamun shigowar kira. Kamar ta share sai kuma ta ɗauki wayar ta duba mai kiran, *Jamila* sunan da ta gani kenan akan ɗan screen ɗin wayar. Ta mayar ta ajiye sannan ta nufi toilet dan yin alwala. Bayan ta fito ta ji still ana kuma kiran wayar, bata bi takan ta ba dan dama dalilin da yasa ta kira shi ya dawo ya ɗauka kenan kar ayi ta kiransa a wayar ba'a same shi ba. Har ta yi Sallarta cikin nutsuwa ta idar ba'a daina kiran wayar ba. Ta yi ɗan tsaki ta tashi ta je ta ɗauki wayar, 17 missed calls ta gani kuma duk mutum ɗaya ce wato Jamila. Ta tab'e baki ta ajiye ta sauka ƙasa. Ƙwaƙwa da dabinon da Daddy ya siyo mata ta ɗauko a cikin fridge ta zauna ta fara ci bayan ta ɗibarwa su Dije. Bayan ta gama ci ta ɗebo abinci kaɗan ta ci. Koda ta koma ɗakinta dan yin sallar la'asar sai tarar wayar tana ringing, still a fili ta ce "Kai wannan mai kiran akwai naci, tunda ta kikkira ta ga ba'a ɗauka ba ai sai ta haqura." Ta d'aga wayar a kufelen da ita kanta bata san ko ta mecece ba ta ce "Mai wayar ba ya kusa." Bata jira amsa ba ta katse wayar. 5 missed calls ta gani bayan na d'azu, kuma duk dai mutum ɗaya ce, sai kuma 4 unreaad message data gani. Har zata ajiye wayar sai kuma ta shiga message ɗin ta gani, ɗaya na kamfani ne sauran ukun kuma duk na Hajiya Jamila ne. Ta shiga na farko ta ga abun da ta turo, _*Please Dear pick my call.*_ ta fita ta shiga na biyu ta ga shi kuma haka ta rubutu, _*Dama kiran ka nay in ji lafiyar ka, dafatan kana lafiya Habibi?*_ bata karanta na ukun ba ta ajiye wayar saboda takaici. Haka kawai ta ji ranta ya ɓaci ba tare data san dalili ba. Ta nufi kan darduma ta tada ik'amar Sallah dan tana da alwalarta. Ƙarfe biyar da ƴan mintuna Mama ta dawo, ɗakin Neehal ta leqa ta tarar da ita zaune a kan gado tana latsa waya. Ta d'ago ta dubi Maman ta ce "Sannu da zuwa." Mama ta ce "Yawwa ya jikin?" A hankali ta ce "Da sauqi." Mama ta ce "Ashe su Afrah sun zo, har yanzu ba su dawo ba ne?" Ta gyaɗa mata kai kawai. Mama ta juya ta fice ganin kamar bata son magana, ita kuwa ranta ne a ɓace har lokacin, sai taune lip ɗinta take. Kafin Magriba Ahmad ya dawo da su Afrah, da gudu suka je suka rungume Mama dake zaune a falon ƙasa. Mama ta shafa kanwunansu tana murmushi ta ce "Welcome yarana." Ahmad ya zauna a kan carpet ya gaishe da Mama cikin girmamawa. Ta amsa masa tare da tambayarsa yanda ya baro Mamy da su Ummi. Su Amrah suka bar jikin Mama suka nufi upstairs dan sun san Auntin nasu tana can. Tana nan yanda Mama ta bar ta suka shigo ɗakin suna kiran sunanta. Ta d'ago ta kalle su bata ce komai ba, suka hawo kan gadon da murnar su, Afrah ta ce "Aunty mun dawo, Mamy ta ce mu gaishe ki." Ta yi ɗan murmushi ta ce "Sannun ku da dawowa, to ina amsawa." Amrah ta ce "Daddy yana ƙasa shi da Mama." Ta yi shiru bata ce komai ba, yaran suka cigaba da yi mata hira. Kiran Ahmad ne ya shigo wayarta, ta ɓata rai kamar yana gabanta ta ƙi d'agawa, haka kawai ta ji tana jin haushin shi ba tare da ta san dalili ba. Bayan kiran ya katse wani ya ƙara shigowa, still ƙin ɗagawa ta yi. After three minutes Mama ta turo ƙofar ɗakin ta ce mata ta je Ahmad yana jiran ta. Fuska a cukule ta ɗauki wayarsa dake kan bedside locker ta fice daga ɗakin, su Afrah suka mara mata baya........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *5️⃣3️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........Cikin sauri ta zare jikinta daga na Ahmad, shima bai yi musu ba ya sake ta tare da faɗin "Ki yi a hankali Princess." Ganin yanda ta zare jikin nata cikin gaggawa ta koma ta kwanta a kan gadon, wani irin fad'uwa gabanta yake kamar zata yi fitsarin sa gami da matsanancin tsoron da ya cika mata zuciya saboda ganin Ameen, ta runtse idanta tare da jan bargo ta lullub'e jikinta. Cikin matuƙar shock Ameen yake kallon su, tun daga turo ƙofar da ya yi ya kasa ko da d'aga ƙafarsa ne, shi mutum ne da ba kasafai ake gane halin da zuciyarsa take cike ba, amma a yanzu kallo ɗaya zakai masa ka san ran Maza ya kai matuƙar ɓaci. Afrah ta waro Ido ta ce "Uncle are you a soldier? Dama Aunty Zahran mu zata gan ka, she like soldiers over." Amrah ta ce "Uncle show me your gun, I want to see it." Ahmad ya ɗauke idonsa daga kan Neehal ya dube su ya ce "Ba ku gaishe shi ba sai surutu ko?" Yaran suka rufe baki a tare suna murmushi. Ameen bai bi ta kan zancen yaran ba ya tako zuwa inda Neehal take, Idanunsa akan Ahmad yana masa wani kallo ta gefen ido. Ahmad ya miƙe tsaye, Allah ya taimaka Neehal bata ɓata shi ba kamar yadda ta yi zato. Hannu ya miƙawa Ameen yana murmushi ya ce "Barka da zuwa Babban Yaya." Ba tare da Ameen ya kalle shi ba ya miƙa masa nasa hannun suka yi musabaha amma bai ce komai ba. Ahmad ya lura da yanayin da Ameen ɗin yake ciki, sai ya danganta hakan da halin sojoji ne kodayaushe fuska a cukule, ko kuma wani ne ya ɓata masa rai, amma ko kaɗan rashin maganar bai dame shi ba. Neehal wadda tun sanda Ahmad ya yiwa Ameen magana ta buɗe idonta ta kalle shi hawaye na zuba daga cikin idanunta, ganin ya zauna a kusa da kanta ta runtse ido da sauri cikin saddaqarwar zata ji duka a jikinta saboda ganin yanayinsa, ta san Ameen ta san waye shi, ta kuma san ɓacin ransa babu kyau. Saboda tsabar fargaba da tsoron da zuciyarta ke ciki da wani irin gudu ta ji jinin yana fita daga jikinta, ga gefen mararta da ya k'ulle. Zuba mata ido kawai ya yi bai ce komai ba, wanda hakan yasa ta kuma runtse idonta da sauri tare da jan bargo ta rufe har fuskarta. Ahmad daga tsayen da yake ya ce "Princess bari na je na kawo miki magani ki sha, Allah ya baki lafiya." Bai jira amsar ta ba ya nufi ƙofa, Ameen ya bi shi da kallo har ya fice, yaransa suka mara masa baya cikin gudu wai sai sun bi shi. Ya dauke idonsa daga bakin ƙofar yana ɗan furzar da numfashi, akan syringe ɗin allura dake ƙasan gadon idanunsa suka sauka, ya ɗauke kansa ya mayar kan Neehal wadda ƙirjinta ban da bugawa babu abun da yake. Ya ɗan lumshe idonsa ya buɗe sannan ya janye bargon daga kanta tare da ɗora hannunsa ɗaya akan goshinta. Ta buɗe ido cikin tsoro wanda hakan yay dai-dai da zubar wasu sabbin hawayen, cikin muryar marasa lafiya ta ce "Yaya!" Cikin muryar da bata taɓa zaton zai mata magana ba nan kusa ba ma yanzu ba ta ji ya ce "Na'am." A matuƙar sanyaye. Ta kama ɗayan hannunsa tare da fashewa da kuka ta ce "I'm sorry." Ya taune lip ɗinsa sannan ya ce "For what?" Ta yi shiru sai kukan ta cigaba da yi tana ƙara k'ank'ame hannunsa cikin nata. Ya shafa kuncinta da ya jik'e da hawaye ya ce "Stop crying Miemerh, kin ga baki da lafiya, kuma You promised to me kin daina." Cikin matuƙar mamakin yanda yake mata magana cikin sanyin murya mai cike da tsantsar kulawa ta tashi zaune tana yamutsa fuska tare da goge hawayen fuskarta da bayan hannunta. Ta kwantar da kanta akan ƙafaɗarsa, tana sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da ƙara lafewa a jikinsa. A hankali ya ce "Ya jikin naki?" Ta ce "Ya yi sauqi, Uncle ya mun allura." Ya ce "Na gani ai." A zaton ta gatse yay mata sai ta ce "Dagaske fa Yaya." Bai kuma magana sai hannunsa da ya ɗora akan cikinta ya ɗan danna cikin. Ta ce "Aushh! da zafi fa Yaya." Ya ce "Ba haka Mama take miki ba?" Ta matso k'walla ta ce "Ai itama yana mun zafi idan tay mun." Ta cire hannunsa daga kan cikin tare da ƙoƙarin saukowa daga kan gadon, jikinta lullub'e da bargo. Ya riƙe ta tare da faɗin "Where are you going?" Ta ce "Toilet." Ya sake ta, ta sauko tana ƙara rufe jikinta da bargon, locker mudubi ta nufa tana jan ƙafa da ƙyar ta janyo ta ɗauki abu a leda, ba tare da juyo ba ta shige toilet. Ya bita da kallo har ta shige sannan ya dawo da idonsa kan gadon, abun da ya gani a zanin gadon dai-dai inda ta tashi ya ƙurawa ido. A hankali ya tashi ya cire zanin gadon gaba-ɗaya ya ajiye a ƙasa. Ta yi kusan 30 minutes a toilet ɗin sannan ta fito, har lokacin yana zaune a ɗakin idanunsa a lumshe. Tana yamutsa fuska ta ƙaraso, ganin zanin gadon a ƙasa ta ji wata irin kunya ta lullub'e ta domin ta gane ɓaci ya yi, bata kalli inda yake ba ta faɗa kan gadon ba tare data saka wani zanin gadon ba, kwanciya ta yi tare da juya masa baya. Sai a lokacin ya buɗe idonsa ya kalli bayanta. "Miemerh!" Ya kira sunanta, ta ce "Na'am." Ya ce "Juyo." Ba musu ta juyo, amma bata iya kallon fuskarsa ba. Cikin muryar da idan yay mata magana da ita take bala'in tsorata ta ji yana cewa. "Ina gurin aiki aka kira ni baki da lafiya kuma Mama bata nan, hankalina a tashe na baro abubuwan da nake na taho dan taimakon ki, amma ina zuwa na tarar dake a jikin wani." Ya ɗan taune lip ɗinsa sannan ya miƙe ya zuba hannayensa duka a aljihu ya ce "I will punish you, kin san ba ay mun laifi in ƙyale." Ta saka kuka zata yi magana ya ce "Shiiii." Sannan ya ɗan sunkuyo da kansa kusa da fuskarta a hankali ya ce. "Just Sleep." Ta had'iye kukan nata tare da lumshe ido. Ya shafi gashin gigirarta ya ce "I will go, idan ya dawo ma still ki kuma ɗane jikinsa." A firgice ta ce "Wallahi Yaya allura yay mun, kuma su Aunty Dije suna nan yay mun ka tambaye su ka ji, dan Allah Yaya ka yi haquri kar ka faɗawa Mama." Bai ce komai sai iska da ya shiga hura mata a fuska daga cikin bakinsa. Ta ja hanci tare da turo baki gaba tana cigaba da tsiyayar da hawaye, a hankali ta ji wani irin bacci na fizgarta, 80% na ciwon cikin d'azu ya tafi, yanzu kaɗan_kaɗan yake mata. Jin saukar numfashinta alamun ta tafi duniyar bacci, ya gyara mata kwanciyar kanta akan pillow sannan ya juya fice daga ɗakin. A falo ya tarar da su Dije, ya sanar musu ta yi bacci su kula da ita. Suka amsa masa cikin girmamawa tare da fatan Allah ya tsare hanya. Da Ahmad ya dawo ko saman bai kuma hawa ba, ya bawa su Dije magungunan da ya siyo mata bayan sun sanar masa ta yi bacci. Ya kuma ba su sallahun idan ta tashi su ce mata ya wuce Abuja. Ba dan wayar da ake ta zabga masa ba a gurin aiki da babu abun da zai sa ya koma Abuja a yau, ko dan rashin lafiyar Neehal. Dan ma ciwon nata na lokaci ɗaya ne, ya san nan da anjima zata wartsake Insha Allah. Amma sosai tausayinta ya cika masa zuciya, na ganin tana cikin mata masu shan wahala a lokacin al'adar su. Sai bayan Azhar ta farka, lokacin Mama ta kikkira wayarta bata ma sani ba. Ta tashi ta ɗauke bedsheet ɗin dake gaban gadon ta kay toilet, sannan ta dawo ta ɗauko wani ta shimfid'a. Ta ɗauki wayarta ta bi bayan kiran Mama, ringing uku ta d'aga da sallama. Neehal ta amsa mata tare da turo baki gaba kamar tana ganin ta, ta ce "Mama nay ta kiran ki baki ɗauka ba, kuma ban da lafiya na kusa mutuwa." Mama ta ce "Sorry dear, na shiga surgery ne, ciwon ciki ko? Ya jikin naki? Amma dai kin sha maganinki?" Ta ce "Ni ina kwance na kasa tashi, Aunty Zulai ta je ta duba ɗakin ki bata gani ba." Cikin damuwa Mama ta ce "Subhallahi, amma dai ciwon bai wahalar dake sosai ba?" Ta ce "Na wahala sosai, sai da Uncle Ahmad ya zo yay mun allura sannan ya lafa mun." Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki Doctor ashe ya zo? Allah ya biya shi." Ta ce "Amin." Mama ta ce ta je ta ɗauki magungunanta duka dake ɗakinta, ta dawo da su nata ɗakin. Daga yanzu a nan zata na barin su, saboda gaba kar irin haka ta kuma faruwa. Bayan sun gama maganar ta k'waso magungunan ta dawo da su ɗakinta. Duk second ɗaya zuciyarta na bugawa da tsoron punishment ɗin da Ameen ya ce zai mata. Ta sauka upstairs ta tarar da su Afrah baje akan carpet suna bacci, ga chocolate ɗin da Ahmad ya siya musu da suka fita barbaje a kusa da su. Dije ta fito daga kitchen tana duban ta, ta ce "Har kin tashi? Ya jikin naki?" Ta ce "Alhamdulillah, waɗannan bacci su kai kenan." Ta ce "Eh, da Babansu ya dawo da su zasu hau sama ya hana su, ya ce su zauna a nan kar su je su dame ki. Na kunna musu kallo, sun fara kuma bacci ya ɗauke su." Ta ce "Ya daɗe da dawowa?" Dije ta ce "Eh, ga magani ma ya kawo ya ce in kin tashi a baki shi ya wuce Abuja." Sai ta ji daɗin tafiyar tasa, dan idan suka ƙara haɗuwa a yau bata san da idon da zata kalle shi ba saboda kunya. Sai la'asar Mama ta dawo gida, Neehal ta haye jikinta tay ta zuba mata shagwab'ar ita bata da lafiya, cikinta ciwo da ƙafarta da kanta. duk da ta ji sauqi sosai rigimarta ce kawai. Da Maman ta gaji da mitar ta_ta, sai ta ce bari ta ɗauko allura tay mata, zata ji sauqi. Sai ta bar jikin nata tana faɗin ta ita ta warke ai. Kafin Magriba ta ware abunta tana harkokin ta, sai ɗan abun da baza a rasa ba. Da yamma wasu daga cikin abokanan aikinta mata suka zo suka duba ta. Bayan Magriba ta yi wanka ta shirya cikin wata brown abaya mai kyau, ta yi kyau amma fuskarta ta yi fayau saboda cutar ta da ta yi. Ta fesa sassanyan turarenta mai daɗin k'amshi. Su Afrah suka mak'ale mata dan a zaton su fita zata yi. Ta zauna tana latsa wayarta kafin Sadik ya ƙaraso. Amrah ta ce "Aunty Unguwa zamu?" Ta ce "A'a." Bayan abun da bai fi mintuna biyu ba Sadik ya kira ta ya sanar mata ya ƙaraso. Ta miƙe ta kama hannun yaran suka fita. A falon sama ta tarar da Mama tana operating system. Ta saki hannun yaran tare da faɗin "Mama ga ƴan tayin aiki na kawo miki." Mama ta d'ago ta dube ta, ta ce "Sadik ɗin ya zo ne?" Ta ce "Eh." Mama ta ce "Sai ki ɗauki drinks ki tafi masa da shi, tunda ke ki shiga kitchen ki yi masa ko da snaks ne ma baza ki iya ba saboda ganda, sai dai mutum yay ta zuwa yana tafiya haka." Ta turo baki ta ce "To Mama baki ga ban da lafiya ba." Mama ta ce "Haka ne, duk watannin da ya yi yana zuwa ma a cutar kike ai? Wuce ki tafi ni kar yay ta jiran ki." Ta ɓata fuska, Afrah ta ce "Aunty zan biki." Mama ta ce "Ku zauna a nan, zata je gurin Uncle Sadik ne." Suka koma suka zauna kusa da Mama ita kuma ta fice bayan ta ba su wayarta ta ce su yi game. Bayan ta ƙarasa inda suka saba zama, ta gaishe shi cikin mutuntawa ya amsa tare da tsokanarta kamar yadda ta saba har ta yi fushin wasa, shi kuma ya rarrashe ta. Sai da suka shirya sannan ya gyara zama yay mata tambayar dake damun sa a rai. "Neehal Please dan Allah karki ɗauki tambaya da wata manufa i want know something ne." Ba tare da tunanin komai ba, ta ce "Karka damu Ya Sadik, ka tambaye ni ko me kake so, ni kuma indai na sani Insha Allahu zan baka amsa." Ya sauke numfashi ya ce "Neehal kafin mu haɗu, na ga sanarwar rasuwar tsohon saurayinki wanda a lokacin ma an kusa bikinku, bayan mun haɗu da ku Haneefah ta ƙara tabbatar mun da hakan, lokacin dana nuna mata ina son ki. Already na riga na san wannan, amma kafin shi akwai wani saurayin naki da ya rasu ne?" Neehal ta ƙura masa ido cikin tsananin bugawar zuciya dan bata taɓa zaton tambayar da zai mata ba kenan. Hawaye masu d'umi suka fara zuba a kan kuncinta, cikin raunin murya mai haɗe da kuka ta ce. "Sadik! Har an kai maka wannan labarin? ko kuma in ce an kai muku kai da ƴan gidanku, har lokaci ya yi da za'a fara yawo da ni a gari ana duk wanda zai aure ni kashe shi ake, har lokacin ya yii?" Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi. Gaba-d'aya Sadik ya ruɗe cikin dana sanin tambayar tata ya shiga bata haquri da ban baki, amma ina kuka kawai take yi, dama ta san wannan ranar sai ta zo a rayuwarta, ranar da wani zai zo neman auranta a ce masa ya janye kar ya zama gawa. Da ƙyar Sadik ya rarrashe ta ta yi shiru, sai da ya yi kamar zai rungume ta sannan ta haqura. Cikin tsananin damuwa ya ce "Dan Allah Wifey ki yi haquri, wlh ba da niyyar ɓata miki rai na yi miki wannan tambayar ba, amma mu bar maganar kawai tunda har ta samun ke kuka haka." Ta ce "Na sani Sadik, na sani kuma ko kaɗan ban ga laifinka ba, tun kafin yau na shirya tarb'ar wannan ranar a rayuwata dan na san dole zata zo. Sadik! Kafin Anwar Jameel ya kawo kuɗin aurena, sai da bikinmu ya rage saura watanni aka kashe shi, aka harbe shi and shima Anwar haka." Sai ta kuma ta fashewa da kuka. Gaba-d'aya Sadik ya ruɗe ganin yanda take kukan da dukkan zuciyarta, kuka ne irin wanda an fama wa mutum wani gyambon ciwo a cikin zuciyarsa. At the first time a tarayyar su ya kama hannunta, tare da tsugunnawa a gabanta ya fara magana cikin rarrashi. "Dan Allah, Neehal ki yi shiru ki saurare ni." Ta yi iya yinta ta ga ta bar kukan da take, ya zaro handkerchief ɗinsa ya shiga share mata hawayen fuskarta zuciyarsa cike da matsanancin tausayinta. Da yasan samarinta biyu ne kacal suka rasu Wlh ba zai tambaye ta ba, shi duk a tunaninsa sun kai irin biyar ɗin nan, amma saboda tsabar gulma irin ta mutane har an saka wa rayuwarta ido. Ba tare da ya saki hannunta ba ya ce "Neehal! Ina son ki fiye da yanda nake son kaina, komai rintsi komai wuya ba zan taɓa iya rabuwa dake ba, ki saka wannan a ranki." Ta kalle shi cikin wadataccen hasken dake wurin, cikin raunin murya ta ce "Bana son na rasa ka Sadik, bana son kaima a kashe mun kai." Ya ce "Allah ne mai rayawa da kashewa Neehal, kisa a ranki zamu yi aure kamar yanda kowanne masoya suke yin auransu, jikina yana bani zamu yi aure, mu rayu cikin farinciki da annashuwa, har ma da tuk'wucin kyawawan yara kamar ki da yardar Allah." Ta sauke ajiyar zuciya tare da zare hannunta daga cikin nasa, tana jin sanyi ya fara ratsa zuciyarta. Sadik ya cigaba da faɗa mata daɗaɗan kalamai masu kwantar da zuciya, gami da ƴar nasiha. Lokaci ɗaya ta ji ta samu nutsuwar zuciya, ta kuma tabbatar Sadik ya cancanci zama miji a gare ta, ko dan tarin Alkhairinsa da k'aunarsa a gare ta. A part ɗin Mama kuwa, ba jimawa da fitar Neehal Mama ta miƙe ta shiga ɗakinta, a lokacin ne kuma kiran Ahmad ya shigo wayar Neehal dake hannun su Afrah. Suka dinga shafa wayar har Allah ya ba su sa'a su kay pick ba tare da sun sani ba. Amrah ta ƙara danna wayar a ƙoƙarin ta na ganin sun koma game ɗin da suke, ashe gurin speaker ta danna. Jin muryar Mahaifinsu yana sallama suka ruɗe da murna. "Daddy! Daddy! Daddy!" Kowacce na son ya yi magana da ita. Ya ce "Oh, sweethearts zaku kashewa Daddy kunne fa." Afrah ta ce "Daddy Aunty ta ce ka tafi ka bar mu." Ya ce "Ai zan dawo in ɗauke ku soon, ko baku san zama a gurin Aunty." Suka ce "Muna so." Ya ce "Yawwa yaran kirki, ina Aunty? Ko bacci take?" Amrah ta ce "Ta fita gurin Uncle Sadik." A kwance yake amma bai san sanda ya tashi zaune ba. A fili ya ce "What? who is he?" Ya yi maganar a gigice. Afrah ta ce "Daddy yana zuwa gida gurin Aunty, yana da kirki yana ba mu chocolates." Amrah ta karɓe zancen da faɗin "Shi ya kai mu gidan Aunty Haneefah da ana bikinta." Ahmad ya had'iye wani abu da ya tsaya masa a mak'oshi, da ƙyar ya iya cewa "Unguwa suka je?" Afrah ta ce "No, Mama ta ce suna waje a zaune." Ya cize lip ɗinsa da ƙarfi, tare da faɗin "Damm it." Yaran suka ce "Hello Daddy." Ya sauke numfashi ya ce "Bye Dear, I will call later." Ya kashe wayar ya cillar akan gado. Kansa ya dafe da hannunsa yana zancen zuci. Me yasa tun farko bai yi tunanin Neehal tana da wani saurayin ba? a age ɗinta dama dole a ce tana da samari ba ma saurayi ɗaya ba. Hankalin Ahmad fa in ya yi dubu ya tashi, ya maimaita sunan Sadik a cikin ransa ba a dadi, kamar mai neman wani abu a cikin sunan. Ji yake kamar ya yi tsintsuwa ya gan shi a Kano, ya ga wane Sadik ɗin nan da his future wife take kulawa. "Kenan tana son shi?" Ya faɗi haka a fili cikin tsananin damuwa. 'Tana son shi mana tunda har take kula shi.' Zuciyarsa ta ba shi amsa da haka. "Ya Allah!" Ya furta haka a fili wani irin kishi na nuk'urk'usar zuciyarsa. Sai wajen 9 Sadik ya tafi, bayan ya gama wanke mata zuciyarta tass, ya kuma roƙe ta kar ta sanar da Mama abun da ya tambaye ta, bare itama hankalinta ya tashi. Tay masa alƙawarin ba zata faɗa mata ba. A bakin part ɗin Mama tana ƙoƙarin danna door beil, ta ji k'amshin Ameen ya cika mata hanci, ta juya bayanta da sauri suka yi 4 eyes da shi.........✍️ *NOTE: For just of you that are thinking Ameen zai yiwa Ahmad wani abu na rashin mutunci or something else, har da masu tunanin duka.🤔🤣 Let me tell you something, Namijin duniya baya hukunci da faɗa ko wani hargagi, da ido ma kaɗai ya isa ya hukunta mutum, ato, Mama bata haifi sakaran Namiji ba, Jarumi ta haifa mai dakakkiyar zuciya. Har na hango su oo suna washe baki na yabi gwaninsu, to ba Ameen na kare ba, dan Mama na yi.😎* *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *5️⃣4️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........Gaba-ɗaya sai ta duburburce ta rasa ina zata saka ranta saboda tsoro da kunya. Ya ƙaraso ba tare da ya ce komai ba ya buɗe ƙofar da key ɗin part ɗin dake gurinsa ya shige. Ta turo baki tare da bin bayansa, a ranta tana faɗin. 'Ya bar gidan ma amma har yanzu yana tare da key ɗin part ɗinsu.' Ya tsaya bayan ya shiga falon yana kallon ta, ta sunkuyar da kanta ta ce "Ina yini?" Ya ce "Lafiya, Ya jikin?" Ta ce "Da sauƙi." Ya ce "Allah ya ƙara sauƙi." Bai jira amsar ta ba ya nufi upstairs. Ta d'ago kanta tare da sauke ajiyar zuciya ta bi bayan shi zuwa saman. Babu kowa a falon hakan yasa ta nufi bedroom ɗinta, a nan ta tarar da su Afrah kwance akan gado suna bacci. Ta ajiye mayafin jininta tare da kwanciya ta lumshe idonta ta faɗa duniyar tunani. Ameen kuwa ɗakin Mama ya shiga, bayan sun gaisa ta ce "Neehal ta ce mun ka zo da safe ina gurin aiki." Ya ce "Eh." Ta ce "Ya jikin Hafsan?" Ya ce "Ta ji sauqi." Mama ta ce "Allah ya ƙara sauƙi." Ya miƙe ya ce "Ameen, bari na je gurin Dad." Mama ta ce "Okay." Bayan fitar sa Mama ta ɗauki wayar Neehal data karɓa a hannun su Afrah ta nufi ɗakinta, dan dubawa ko ta dawo." Turo ƙofar ɗakin da Mama ta yi yasa ta buɗe ido, Mama ta ce "Har kin dawo kin kwanta kenan?" Ta ce "Ban jima da dawowa ba." Mama tana mata kallon tsaf ta ce "Are you Okay?" Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Kaina ke mun ciwo." Mama ta ce "Allah ya sauqaqe sai ki tashi ki ci abinci ki sha magani." Ta ce "Toh." Tare da karɓar wayarta da Mama ke miƙo mata." Mama ta ce "Sai kiran ki ake, waye yake miki wannan kiran ne haka?" Tana latsa wayar ta ce "Uncle Ahmad ne, yaransa yake son magana da su." Mama ta ce "Sai ki kira shi ki sanar masa sun yi bacci." Ta gyaɗa mata kai, amma bata jin zata iya kiran nasa. Mama ta juya ta fita bayan ta ƙara jajjada mata ta fa tashi ta ci abinci ta sha magani. Ta fi awa bayan fitar Mama tana sak'awa da kuncewa sannan ta miƙe ta fito ta sauka ƙasa. Abinci ta ɗebo ta ci, sannan ta dawo ta sha magani. Har time ɗin bata kira Ahmad ba, shi ma bai ƙara kiran ta ba. Ta shiga toilet tay wanka ta fito ta shirya cikin kayan bacci masu taushi ta kwanta, text kawai ta yiwa Sadik ta yi addu'a ta tofa wa su Afrah sannan ta shafa a jikinta, ba jimawa bacci ya ɗauke ta. Bayan kwana biyu ranar Juma'a da safe ta samu Mama a ɗakinta ta ce mata. "Mama Ya Sadik ya matsa wai sai na je gidansu na gaishe da Maamah." Mama ta ce "To ki shirya anjima ki je mana." Ta ce "Ni dai Mama kunya nake ji, kuma ba zan iya zuwa ni kaɗai ba." Mama ta ce "Maganin rashin zumuncin ki kenan, da kina zuwa ki kaiwa Freind's ɗinki ziyara da yanzu sai ki kira wata ta raka ki ku je." Ta ce "Bari in kira zee ta B.U.K." Mama ta ce "Tunda baki da kunya ba, yarinyar nan haka tay ta zuwa gidan nan amma saboda ba kya zuwar mata itama ta gaji ta daina zuwa, yanzu kuma sai ki kira ta ki ce ta zo ta raka ki ko? Tunda zaman ki take." Ta marairaice fuska ta ce "Allah sarki, Haneefah tah, ga ranarta ta zo." Mama ta ce "Bari na kira Hajiya Rabi, idan Salma tana free yau sai ta zo anjima ku je." Neehal ta yi murmushin jin daɗi ta ce "Yawwa Mamana." Mama ta ɗauko Wayarta ta kira Hajiya Rabi wadda ta kasance ƙawarta ce, Salma kuma ƴarta ce baza ta fi mate ɗin Neehal ba. Bayan sun gaisa Mama ta roƙe ta alfarmar zuwan Salman idan babu abun da take. Hajiya Rabi ta ce, zata zo insha Allah bayan an sauko daga masallaci. Mama tay mata godiya su kay sallama. Ta dubi Neehal ta ce "Sai ki kira shi ki sanar masa ya zo da yamma ya kai ku." Ta ce "Toh Mama, amma duk da haka ina jin kunya in na je me zance?" Mama ta ce "To ai ba zama zaku yi ba, gaishe su kawai zaki ku dawo." Ta ce "Tom, bari na je na kira shi." A safiyar Ahmad ya kira wayarta, ta d'aga ta saka a speaker sannan ta bawa su Afrah. Tun ranar Larabar nan da ya tafi ba su kuma magana ba, idan ya kira sai dai ta bawa ƴaƴansa, shima kuma ba ya cewa su bata wayar, ko zancen ta ba ya musu, sai dai su in sun masa maganarta yana biye musu. Ta yi shiru tana sauraren voice ɗinsa a cikin wayar, yana magana da ƴaƴansa cikin nishad'i. Sai ta ji ba daɗi sosai a ranta, na ƙin kulatan da yake kwana biyu, ta turo baki kamar yana ganin ta, jin yana cewa su Afrah ranar Sunday zai zo ya ɗauke su. Afrah ta kalle ta, ta ce "Aunty Daddy ya ce zai zo ya ɗauke mu ranar Sunday." Ba ta ce komai ba, sai lumshe idonta da ta yi. Ahmad ya ɗan lumshe idonsa cikin tsananin kewarta, ambatar sunan ta da Afrah ta yi kawai yasa ya ji ba zai iya jurewa ba sai ya ji muryarta a yanzu. A hankali ya ce "Ina Aunty?" Amrah ta ce "Gata nan, a kwance." Ya ce "Ku bata wayar." Suka matso jikinta suna kiran sunan ta, "Aunty, Daddy ya ce ki karb'i wayar." Tana jin su tay musu shiru, ta kuma ƙi buɗe idonta. Amrah ta ce masa. "Daddy ta yi bacci." Ya san ba baccin take ba, kawai wayar ce baza ta karɓa ba. Sai yay wa yaran sallama ya katse wayar ya tura mata text. Sai bayan sun gama surutunsu sun fita falo sannan ta tashi ta ɗauki wayar, a lokacin ta ga text da Numbern sa. Cikin sauri ta shiga karanta abun da ya turo. _Princess, ya jikin naki, da fatan kin samu lafiya. I MISSED YOU ALOT._ Ta ji wani murmushi ya subce mata, ko ba komai ya nuna care a kanta, duk da bata san me yasa 2 days ya daina kula ta ba, ita kuma tsananin kunyarsa ce tasa in ya kira take kasa pick. Tay masa reply da, _Ina lafiya Uncle, dafatan kai ma haka?_ Ta rungume wayar a ƙirjinta zuciyarta na azalzalarta akan ta kira shi, ta ji muryarsa. Duk da ta ji yanzu da suna waya da su Afrah, amma ta yi missed ɗin yanda yake mata magana da ita a cikin kunnenta cikin salo mai narkar da zuciya, tana ta tunanin nasa bata san bacci ya ɗauke ta ba. Sai ƙarfe ɗaya saura Mama ta tashe ta. "Ki tashi, ki shirya ki shirya su Amrah, ko kin manta zaku fita ne?" Ta tashi zaune cikin muryar bacci ta ce "Ban ma san sanda baccin ya ɗauke ni ba." Mama ta ce "Sai ki tashi yanzu, kafin Salma ta ƙaraso, gidan A'isha zaku fara zuwa sai ya je ya ɗauke ku a can." Tana sakkowa daga kan gadon ta ce "Toh." Kafin ƙarfe biyu Neehal ta gama shiryawa cikin wani plan cotton material mai kyau, milk colour an masa ado da coffee colour, ɗinkin Baby gown ta yi das a jikinta. Ta yi simple d'auri da d'ankwalin material ɗin, sannan ta yafa mayafi coffee colour. Ta yi kyau sosai, hannunta ya ci zobuna da abun hannu, sai tashin sassayan k'amshinta take. Ta zira plate shoe coffee colour a farar ƙafarta, sannan ta ɗauki ƙaramar handbag itama coffee colour ta zira wayoyinta a ciki. Ta kalli kanta a mirror tana tambayar kanta 'Shigar jikinta ta dace data zuwa gidan surukai? Tun kafin tay wanka take ta tunanin kayan da zata saka a jikinta, da a niyyar ta Hijabi zata zumbula ta tafi, amma kuma data zo saka kayan sai ta fasa ta ɗauko na jikinta wanda bata taɓa saka su ba ta sa. Ta sauke numfashi tana jin zuciyarta wani iri akan zuwa gidansu Sadik ba tare data san dalili ba, ba yau ne first time ɗinta zuwa gidan surukai ba, ta je gidan su Anwar da Jameel, amma wannan sai ta ji kamar ta ce ta fasa zuwan. A hankali ta juya ta fice jikinta a sanyaye, a falon ƙasa ta tarar da Mama da Twins data shirya su tun d'azu, ta kora su gurin Mama dan ta samu damar shiryawa a tsanake. Afrah ce ta fara ganin ta, cikin kaud'inta ta ce "Aunty You look so beautiful." Neehal ta yi murmushi, Amrah ta juyo itama ta ce "Kin yi kyau Aunty." Tay mata murmushi ta ce "Thank you dears." Ta ƙarasa ta zauna a kusa da Mama dake kallon ta, ta ce. "Mama shiga ta bata yi komai ba?" Mama ta ce "Babu abun da ta yi, Daughter sai ma kyau da tay miki." Ta yi murmushi kawai, Mama ta ce "Na ga jikinki duk a sanyaye, ki saki jikinki Daughter babu abun da zai faru sai Alkhairi, Insha Allahu, wannan shine last zuwan ki another in-laws Family." Ta ce "Allah yasa." Ba jimawa da zamanta Salma ta iso gidan, cikin shiga ta mutunci. Mai kyau ce, Black beauty da ita. Ta gaishe da Mama sannan suka gaisa da Neehal, Neehal ta kawo mata drinks ta sha kaɗan bisa takurawar Mama. Kafin ƙarfe uku sun isa gidan Aunty A'isha, Salma da yake she is so friendly tay ta tsokanar Neehal da suna tafiya, dan Mama ta mata bayanin inda za su je, Neehal kam sai dai tay mata murmushi kawai. Sai bayan la'asar Sadik ya zo ya ɗauke su dan kai su gidansu, har da Maryam ɗin Aunty A'isha suka tafi. Ta so barin su Afrah a gidan Aunty A'isha, amma suka saka ihun sai sun bita, Aunty A'isha ta ce ta je da su kawai. Duk uban warning da ta ja musu akan kar su yi surutun su in je gidan, amma tun a Mota suka fara yiwa Sadik zuba, shi kuma yana biye musu cikin fara'a. Parking ɗin Sadik a compound ɗin gidan su, ya yi dai_dai da fad'uwar gaban Neehal. Ta lumshe ido a ranta tana fatan wannan gidan ya zama na ƙarshe a zuwa gaisuwar surukai a rayuwarta. Salma ce ta fara fita daga cikin Motar su Afrah suka bi bayan ta cikin zumud'in sun zo unguwa sai kuma Maryam. Sadik ya dubi Neehal ya ce "What happened Wifey?" Ta ce "Nothing, me ka gani?" Ya girgiza kai tare da faɗin. "Babu komai." Ya buɗe Motar ya fita sannan ya zagaya ya buɗe mata. Ta ɗan ɓata rai tana masa kallon bata so hakan ba. Ya yi murmushi ya ce "To naga sai jan aji kike, Maamah kuma na san zuciyarta ta cika taf da d'okin ganin ki." Ta fito tana faɗin, "Like me." Ya ce "Sure?" Ta ce "Sosai ma, waye ba zai so ganin Mamansa ba?" Ya yi murmushi, suka jera suka nufi cikin gidan, Salma na bin bayan su tare da tsokanar su tana faɗin. "Gaban dai Mama za'a je, a rage rashin ta ido." Neehal ta harare ta. Sadik ya ce "A'a gwara dai ta gani da idonta irin son da sirikar ta takewa ɗanta, ko Baby?" Neehal ta ɓata fuska ta ce "Kar ka sa in kasa shiga, ni ka yi gaba ma." Ya yi murmushi tare da yin gaban kamar yadda ta ce. Sadik ne ya buɗe musu ƙofar part ɗin suka shiga bakunan su ɗauke da Sallama, kan Neehal a ƙasa, da ƙyar take iya d'aga ƙafarta, sosai take jin wata irin kunya tun ba ta yi tozali da surukan nata ba. A ƙasan carpet suka zauna dukan su. Afrah tana kallon falon ta ce "Uncle Sadik gidanka ne nan?" Ya kamo hannunta yana murmushi ya ce "Gidanmu ni da my Family ne." Neehal ta janyo ta tana hararar ta, ta zaunar da ita a gabanta. Sadik ya zauna a kusa da ita ya ce "Me tay miki kuma?" Kamar zata yi kuka ta ce "Ni dai ka tashi daga kusa da ni dan Allah kar Maamah ta fito." Ya tashi yana mata dariyar tsokana, sannan ya nufi ɗakin Maamah. Tare suka fito shi da Batul da Maaman, cikin fara'a Batul ta tarb'e su, suka gaisa. Maamah ma da fara'a ta zauna a Falon, suka gaishe ta cikin girmamawa. Daga yanda kan Neehal yake ƙasa Maamah ta gane ita ce sirikar ta_ta, and 100 💯 ta yaba da Neehal a matsayin surukarta. Batul ta cika musu gaban su da kayan ciye_ciye da na sha, wanda aka tanada domin su. Maamah ta ja su Afrah ɗakinta dan yaran sun burge ta ba kaɗan ba, gashi ba su da wahalar sabo. Maryam da Salma ne kawai suka ci abubuwan da aka kawo musu, amma Neehal ƙin ci ta yi, duk da Maamah ta bar falon, Batul ma korar ta Sadik ya yi duk dan Neehal ta sake amma ta ƙi sakin jikinta. Sadik ya dawo kusa da ita ya zauna ya ce. "Ki ci abincin mana Wifey, Maamah fa da kanta ta yi girkin nan musamman dan ke, ko in baki a baki?" Ya ƙarashe zancen da kashe mata ido. Ta harare shi dama ciki take da shi, ya nuna wa Maamah ita sai ka ce haka aka ce masa ana yi. Da ƙyar ta kurb'i juice ɗin da ya zuba mata a cup, ganin yanda ya wani marairaice mata. Kafin su tafi Abban Sadik da yake yana gari ya zo sun gaisa cikin fara'a da nuna jin daɗin ganin su. Umma ma ta zo sun gaisa ita ƴaƴanta ƴan'mata guda biyu, su kay ta satar kallon Neehal kuwa, amma duk kallon nasu ba su ga makusa a jikinta ba. Sai kusan Magriba suka tafi, Maamah ta sa Batul ta juye musu Gaba-ɗaya sauran kayan ciye_ciyen da suka bari, Abba kuma ya bawa su Afrah kuɗi wanda da farko ƙin karɓa su kay, sai Sadik ne ya karɓar musu. Sosai Abba ya yaba hankali da tarbiyya gami da kunyar Neehal. Suna fita Batul ta ce, "Gaskiya Yaya ya iya zaɓen mata, mai kyau da kunya." Maamah ta yi murmushi cikin jin daɗi, Umma kuwa tab'e baki ta yi. Gidan Aunty A'isha Sadik ya mayar da su, bayan ya shigar musu da kayan ciki, Neehal ta rako shi bakin Mota tana ɓaɓɓata fuska. Ya shiga cikin motar, amma ya bar murfin a buɗe ya ce mata, "To ba mun baro gidan Maaman ai, ki saki jikinki mana." Ta turo baki ta ce "Ina ruwanka da ni, ai mun ɓata." Ya marairaice ya ce "Ni ɗin Wifey, Please ki yi haquri na tuba." Ya ƙarashe zancen yana haɗa hannunsa biyu guri ɗaya. Ta kalli fuskarsa wadda take bayyana farincikin da zuciyarsa take ciki a yau. Ta ce "Sanda ka bani kunya a gaban su Maamah ai baka san da haqurin ba." Da ƙyar dai ya lallaɓa ta, ta haqura suka yi sallama. Bayan ya mata godiyar zuwa gaishe da su Maamah. Ana yin Sallar Magriba suka bar gidan Aunty A'isha, saboda Salma da zata wuce gida. Suna zuwa gida Salma ta fara bawa Mama labarin irin kyakkyawar tarb'ar da suka samu a gidan su Sadik, Mama ta ji daɗin hakan sosai. Salma bata jima ba ta tafi bayan Mama ta cika ta da Alkhairi, Neehal ma ta bata turaruka da sabbin undies. Ranar Sunday kamar yadda Ahmad ya faɗa da hantsi ya sauka a Kano a gidan Mama. Neehal tana bacci su Afrah suka tashe ta cikin murna. Ta tashi da ƙyar dan bata jima da kwanciya ba, suka sanar mata Daddy ya zo. Sai ta ji gabanta ya faɗi, dan har yau ba su kuma magana da shi ba, tun ɗan chat ɗin nan da sukay ta message. Ta tashi ta shiga toilet ta wanke baki da fuska, sannan ta fito ta ɗauki Hijabi ta fice. A falon sama ta gan shi yaransa a jikinsa suna masa surutu. Ta zauna akan carpet kanta a ƙasa ta ce "Sannu da zuwa Uncle." Ya d'ago ya dube ta cike da d'okin ganin ta, ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani sanyi na ratsa zuciyarsa. Sauke su Afrah ya yi daga jikinsa ya ce su tafi gurin Mama, sannan ya sauko daga kan kujerar da yake ya zauna a kusa da ita. "Princesss!" Ya kira sunanta a hankali. Ba tare da d'ago kanta ba ta ce "Na'am." Ya lumshe ido ya buɗe ya sauke su akan fuskarta ya ce "I missed you so much." Ta d'ago ta kalli fuskarsa itama saboda azalzalar da zuciyarta take mata akan hakan, ta yi murmushi ba ta ce komai ba. Ya tallafi fuskarsa da hannunsa ɗaya ya ce, "Wow, Princess kin ƙara kyau, Please karki daina mun wannan murmushin." Kamar zuga ta ya yi sai ta ɓata rai tare da ɗauke kanta daga gare sa. Cikin damuwa ya ce "Why Princess?" Ta turo baki ta ce "Babu komai." Ya ce "No, akwai Princess, tell me what happened? Bana son na gan ki cikin damuwar nan." Ta yi shiru, ya kamo hannunta ya ce "Please." Ta k'wace hannunta ta ce "Ba kai ne ka daina kula ni ba, yanzu ma na san dan su Afrah ka zo ba dan ni ba." Ya yi shiru yana kallonta, yana tunanin abun da yasa yay mata hakan ko kuma ya ce sukai wa juna." A hankali ya ce "Ke kika fara daina kula ni Princess, idan baki manta ba ranar dana tafi na kira ki da daddare Twins suka ɗauka, nay ta jiran kiran ki idan kin dawo tunda sun ce mun ba kya nan, amma baki kira ni ba, dana kira da safe kuma sai na ji Twins ne suka ɗauka again. That is why na ƙyale ki, may be haka kike buƙata, i thought ina takura miki ne. But I'm sorry." Sai ta ji bata kyauta masa ba, amma ita kunyarsa ce tasa ta yi haka, yanzu ma kawai daurewa ta yi har ta iya kallon sa bisa tilastawar zuciyarta. Ta marairaice ta ce "Ka yi haquri Uncle." Ya yi murmushi ya ce "Babu komai Princess, Princess bata taɓa laifi a wajen Uncle ɗinta." Cikin shagwab'a ta ce "Kuma ni baka takura mun ba." Ya ce "To me yasa kika daina kula ni?" Ta juyar da kai gefe ta ce "Kunyar ka nake ji, ban san ta yaya zan maka magana a time ɗin ba." Ya matso ya juyo da fuskarta ya ce "Let me hug you, sai ki daina jin kunya ta." Ta ja baya da sauri kamar zata yi kuka ta ce "Ai na daina since." Ya yi murmushi yadda duk ta tsorata ya ce "Shikenan, amma idan kika ƙara mun haka, i know what I did." Ta kawar da zancen da faɗin, "Ya su Ummi?" Ya ce "Suna nan k'alau, Mamy ta ce "Kun je gidanta jiya." Ta ce "Uhm." Sai kuma ta shagwab'e fuska ta ce "Wai dagaske tafiya zaka yi da Twins yau?" Ya ce "Eh mana, Gobe za su yi resuming School, hutun nasu babu yawa 2 weeks ne kawai." Ta ce "Shikenan, but i will miss them." Ya ce "Ki bi mu, mu tafi tare." Ta ce "Soon, Insha Allah zaku ganni, Relatives ɗin Dad ma suna ta complain bana zuwa." Ya ce "I was so surprised fa, ace kin zauna a Abuja for some years amma Allah bai taɓa haɗa mu ba." Ta ce "To ai bana fita, daga gida sai School, in kuma zan fita tare da Mama ne." Ya ce "Haka ne, Mummy's girl." Sai ta yi murmushi, ta tuno Ameen saboda shi yake yawan faɗa mata haka. Sai bayan Azhar suka tafi suka bar Neehal cikin kewar su, su ma yaran kuka suka saka da za su tafi, wai sai da ita za su tafi. Da ƙyar Ahmad ya lallashe su ya ce zata biyo su itama soon. *A WEEK AFTER* Ranar Friday da safe Mama tana gyaran part ɗin Daddy Ameen ya kira ta a waya, ta ɗauka suka gaisa, daga yanda ta ji muryarsa ta san ba k'alau ba. Ta ce "Ya jikin Hafsan?" Cikin damuwa ya ce "Muna asibiti Mum, ta yi Miscarriage." Mama ta ce "Subahanallahi, yaushe?" Ya ce "Cikin daren jiya." Cikin jimantawa da damuwa Mama ta ce "Allah ya bata lafiya, yanzu tana ina?" Ya ce "Hospital." Mama ta ce "Wanne?" Ya faɗa mata wani private Hospital ne dake kusa da su." Mama ta ce "Bari ta shirya ta zo." Daga haka su kay sallama. Ta kira Daddy ta faɗa masa, sannan ta ƙarasa aikin da take cikin sauri ta shirya ta tafi ita kaɗai, tunda Neehal tana wurin aiki. Jikin Hafsan da sauƙi ta tarar da ita, tunda tun daren jiyan akay mata ƙarin jini da wankin ciki. Tana kwance akan gadon marasa lafiya, sai mahaifiyarta da mahaifinta a ɗakin. Mama tay mata ya jiki, suka gaisa da parent ɗin nata cikin fara'a da mutunta juna. Kusan wuni Mama ta yi a Hospital ɗin tare da mahaifiyar Hafsah, Daddy ma ya zo ya duba ta da rana, da yamma kuma su Aunty A'isha da Aunty Sadiya suka sun zo. Mama ta kira Driver ya kawo su Dije tare da abincin data saka su, su girka. Ƴan'uwan su Hafsat ma suna ta zuwa duba ta. Tun zuwan Mama ta fuskanci Ameen yana cikin damuwa da b'arewar cikin Hafsat, ko tantama bata yi ya k'walla fa ransa akan cikin ne Allah kuma ya yi ba mai fitowa doron ƙasa ba ne. Tay masa addu'ar Allah ba su wani. Sai can yamma Mama ta dawo gida, lokacin Neehal itama bata jima da dawowa ba. Mama ta sanar mata abun da ya faru, ta ji ba daɗi sosai akan barewar cikin itama, dan duk sun san Hafsan na da ciki, har tana ta murna a ranta sun kusa samun new Baby. A daren ranar aka sallame su Hafsah, mahaifiyarta ta so tafiya da ita gida amma Ameen ya nuna bai so hakan ba, Mahaifin Hafsah kuma ya goya masa baya, ya ce tunda jikin nata da sauk'i ta wuce gidanta kawai. Dole mahaifiyar ta_ta, ta haqura, ta ce zata samo mata dattijuwar da zata na kula da ita har ta samu sauƙi, kamar wata wadda ta haihu, bayan kuma already tana da masu aiki ƴan'mata har guda biyu. A daren Mama tana part ɗin Daddy suna hira ya ce mata. "Son fa ya kira ni d'azu in nemar masa alfarma a gurin ki." Mama ta ce "Alfarmar me?" Ya ce "Wai Daughter yake son ki ba su ta je ta musu ɗan kwana biyu, kafin Hafsah ta gama warwarewa." Mama ta ce "Ba tana da masu aiki ba, me kuma Neehal zata je tay musu?" Daddy ya ce "Kin san ɗan naki, ba ya cin abinci masu aiki." Mama ta ce "Ohh girki zata je tana yi masa kenan? To ban yarda ba, idan dan abinci ne zan na badawa akai musu." Daddy ya ce "Dama sai da ya ce mun baza ki bari ba, shi yasa ma ya kira ni, in lallame ki, ki barta ta je Doctor, kin ga akwai abubuwan da dole masu aiki baza su iya yi masa ba tunda matarsa bata da lafiya, amma ita Neehal ɗin zata iya masa." Mama tay shiru, Daddy ya ce "A taimaka mana ƴar Amaryata." Ya ƙarashe zancen da dariya. Mama ta ce "Ka ce mun amarya mana tunda zaku yaudare ni kai da ɗanka." Ya yi dariya sosai ya ce, "Yanzu dai kin bari ya zo ya ɗauke ta da safe? Just 1 week za ta yi ta dawo." Mama ta ce "Ka san ba zan iya har 1 week babu ƴata a gabana ba." Ya ce "Idan kuma da Allah yasa an yi auranta fa?" Ta ce "Aure daban, wannan na san gidan miji na kai ta ba gidan Ameen da basa shiri ba, Neehal rigima da shiririta shi kuma masifaffe, ta yi abu kaɗan ya rufe mun ƴa da masifa, na yarda dai tay musu kwana biyu ta dawo." Daddy ya ce "To hakan ma, mun gode, bari na kira shi na sanar masa. Washegari wajen ƙarfe tara na safe Neehal tana breakfast a ɗakin Mama. Maman kuma tana karatun Alkur'ani mai girma, bayan ta kammala ta ce "Ki yi ki gama uwar janjani, Ameen zai zo ya ɗauke ki, ki je gidansa ki musu kwana biyu." Neehal ta d'ago da sauri har tana k'warewa ta ce "Mama kwana biyu kuma?" Mama ta ce "Eh, kin ga Hafsan bata da lafiya, zaki ɗan taimaka mata da wasu ayyukan, ita kuma ba k'annena ba bare su je su taya ta." Kamar zata yi kuka ta ce "Amma Mama tana da masu aiki fa." Mama ta ce "Ki je dai Neehal, mene in kin je kin taimaka mata, Dad ne da kansa ya ce ki je." Neehal ta fara hawaye tare da ture abincin gabanta, ita ba zuwan ne damuwarta ba, yanda zata zauna gida ɗaya da Ameen har na wasu kwanaki ne damuwarta, dan tun ranar da ta dawo daga gurin Sadik suka haɗu a bakin part bata ƙara bari sun haɗu ba, wasan b'uya take da shi, saboda tsoron punishment ɗin da ya ce zai mata. In ya zo gidan tana nan har ya tafi bata fitowa daga ɗakinta. Tana matsar hawaye ta ce "Mama aikina fa, kin ga ban jima da komawa ba, kuma ina siwes." Mama ta ce "In kin je can ɗin ma zaki na zuwa ba wai daina zuwa zaki ba, kina gama ayyukan ki sai ki tafi, idan Ameen ɗin yana gida da kansa ma zai dinga kai ki." Ta saka kuka ta ce "Ni dai Mama....." Mama ta haɗe rai ta ce "Bana son iskancin banza, mene a gidan Ameen ɗin da baki son zuwa? Ko yayyanka naman jikinki za'ai in kin je? Ki tashi ki je ki yi abun da na ce, tunda kin gama cin abincin. In kuma ban isa ba ne to." Ta tashi tana kuka ta fice daga ɗakin. Mama ta bi ta da kallo, tana sane da su kwana biyu ita da Ameen ɗin, da wasan b'uyan da take da shi, shi kuma idan ya zo gidan ya dinga baza ido kenan yana neman ta inda zata ɓullo. Ta girgiza kai tare da yi musu addu'ar shiriya a cikin ranta.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *5️⃣5️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........Tana Kuka ta janyo small trolley ta zuba kayanta da bata ma tsaya zab'a ba kawai buɗe wardrobe ta yi ta kwaso. Ta saka hijabai guda biyu a ciki ta zuge. Ta ɗauki wani ta zira a jikinta, ta koma bakin gado ta zauna tana cigaba da kukan ta. A haka Mama ta shigo ta same ta. Cikin takaici Mama ta ce "Neehal kukan ne har yanzu kamar wadda akaiwa wani mugun abun, haka zaki je gidan mutane kina musu kuka?" Ta yi shiru tare da daina kukan. Mama ta tab'e baki ta ce "Ki fito yana falo yana jiran ki, kuma ki cigaba da kukan kin san halinsa dai." Ta goge hawayen fuskarta ta ce "Ki yi haquri Mama na daina." Mama ta ce "Allah ya shirya mun ke, ya nuna mun ranar da zaki girma ki daina wannan kukan, ko jariri haka ya gan ki ya bari a kuka Neehal." Ta turo baki ba ta ce komai ba, ta miƙe ta kwashi wayoyinta ta zuba a small handbag. Mama ta kama hannunta ta ce "Ki saki ranki mana Daughter, ko kuma kin fi so idan kewarki ta dame ni in dinga tuno fuskarki a cukule." Ta yi murmushi saboda yanda Maman ta yi magana. Itama murmushin ta yi ta shafa kuncinta ta ce, "Je ki wanke fuskarki maza ƴar albarka ta." Ta gyaɗa mata kai tare da tashi ta shige toilet. Mama ta miƙe ta fita, a falo ta tarar da Ameen zaune inda ta bar shi. Ta zauna a kusa da shi ta ce "Gata nan zuwa, saura kuma a dinga ci mun zalin yarinya idan an je." Ya yi murmushi ya ce "Ƴar taki ce bata ji ai ba daga ni ba ne." Mama ta ce "Ni dai na faɗa maka, inna ji ba dai-dai ba da kaina zan zo in ɗauke ƴata." Ya ce "Baza ma ki ji ba Insha Allah." Dai-dai nan Neehal ta fito daga ɗaki tana jan trolley, Ameen ya bi ta da kallo. Ba tare data kalle shi ba ta ce "Ina kwana." Ya ce "Lafiya." Tare da miƙewa ya karb'i trolley'n hannunta ya fice daga falon. Ta dubi Mama ta ce "Daddy ya fita ba mu yi sallama ba." Mama ta ce "Sauri yake ne, amma ya ce idan ya dawo da daddare zai zo har gidan Ameen ɗin ya gan ki." Ta shagwab'e fuska ta ce "Please Mama ku zo tare." Mama ta ce "To Allah ya kai mu, make sure dai kin ɗauki komai na zuwa gurin aikin ki?" Ta girgiza kai tare da faɗin. "Mama wai kwana nawa zan yi ne?" Mama ta ce "Just 2 days." Ta gyaɗa mata kai sannan ta juya ta koma ɗakinta, ta ɗauko laptop ɗinta da duk wani abu da zata buƙata a gurin aiki, sannan ta fito. Mama ta bata kuɗi ko zata buƙata, ta ce mata a'a ta ɗauki ATM ɗinta, idan tana buƙata zata ciro. Har waje Mama ta raka ta, amma iyakacin ta bakin part ɗinta ta koma. Gabanta na fad'uwa ta nufi parking space inda ta san yana jiran ta, a hankali take tafiya har ta ƙarasa. Kafin ta ƙarasa gurin Motarsa ya buɗe ya fito ya buɗe mata baya, ba tare da ya ce komai ba ya karb'i laptop ɗin hannunta ya saka a bayan Motar, ya mayar ya rufe sannan ya buɗe mata gaban Motar. Cikin mamaki take kallon sa zuciyarta cike da tsoro, gani take kamar wani abun yake shirya mata na punishment ɗin da ya ce zai mata, sai ta kasa shiga Motar. Ya haɗe rai amma cikin sanyin murya ya ce "Ko sai na ɗauke ki na saka ki ne?" Ta kalle shi ta turo baki sannan ta shiga Idanunta cike da k'walla. Ya zagaya ya shiga mazaunin driver, ya yi looked Motar sannan ya kunna ta ya yi reverse suka fice daga gidan. Ta lumshe idonta tare da kwantar da kanta a jikin kujera. Ji take kamar garin zata bari saboda damuwa, dan ita bata taɓa yin tafiyar kwanaki ba tare da Mama ba, and kuma tana tunanin yadda zata yi kwanaki a gidan matar da bata k'aunarta ko kaɗan, Matar dake mata fuska biyu a gurin Yayanta da Mamanta. Har suka je gidan babu wadda ya yi magana a cikinsu, sai karatun Alkur'ani ne yake tashi a cikin Motar. Ta buɗe idonta jin Motar ta tsaya, idanunta suka sauka a cikin nasa saboda juyowa ya yi sosai yana kallonta, harara ta yi tsammanin samu daga gare shi amma sai ta ga saɓanin haka, wani tattausan murmushi ya sakar mata, murmushin da tun tana yarinya yake matuƙar burge ta, kuma bata tunanin akwai na biyun shi a kyau a idonta. Ta mayar da idonta ta lumshe cikin jin bugun zuciyarta na sauyawa, gaba-ɗaya ya juye mata ya koma Mamanta data baro a gida, kamar Ameen da Mama ta ɓaci, babu abun da ya baro nata, hatta yanayin kallon su iri ɗaya ne, the only difference is shi Namiji ne ita kuma mace ce. A hankali ya ce "Cry cry girl, kukan ne dai?" Ta buɗe ido tare da turo baki gaba ta ce "I start missing my Mum." Ya ce "Sorry, ai taimakon mu zaki yi Mummy's girl." Ta ɓata fuska ba ta ce komai ba, shi ma bai kuma magana ba ya buɗe Motar ya fita, itama bin bayan shi ta yi ta fito hannunta riƙe da handbag ɗinta. Ya buɗe bayan Motar ya ɗauki laptop ɗin sannan ya fara tafiya ta bi bayan sa. Babu kowa a falon ƙasan da suka shiga, amma fess yake a gyare sai tashin k'amshi yake, sama ta ga ya hau hakan yasa itama ta bi bayan sa. Bedroom ɗin Hafsah ya shiga ita kuma ta zauna a falo, ba jimawa ya fito ya ce ta shiga ɗakin. Ta tashi ta shiga a tunaninta Hafsan tana ciki, amma sai ta ga babu kowa, ga laptop ɗinta ya ajiye mata akan bedside locker. Ta zauna a bakin gado tana bin ɗakin da kallo, dan bata taɓa shigar sa ba sai yau. Knocking ƙofar da akai yasa ta tashi ta je ta buɗe, ɗaya daga cikin masu aikin gidan ce, cikin girmamawa ta gaishe da Neehal sannan ta bata trolley ɗinta tana faɗin. "Gashi mai gidan ya ce akawo miki." Ta karɓa tare yin murmushi ta ce "Na gode." A ɗakin Hafsat zata zauna kenan? A fili ta ce "Lallai ma Yaya." Sai kuma ta tab'e baki da ta yi tunanin wani abu. Tana ajiye trolley'n ya turo ƙofa ya shigo da sallama, ta amsa masa, ya dube ta ya ce "Ki zo ku gaisa." Ba ta ce komai ba, dan ta gane wadda yake nufi, ta fito ta biyo bayan sa suka shiga ɗakinsa, Hajiya Hafsat na kwance akan gado idanunta akan ƙofa. Already ta san da zuwan Neehal gidan dan Ameen ɗin ya sanar mata tun jiya, kuma ko kaɗan bata ji daɗin hakan ba, babu yanda zata yi ne kawai. Neehal ta ƙarasa bakin gadon ta ce "Ina kwana Aunty Hafsah, ya jikin?" Cikin fake smiling Hafsah ta ce "Lafiya k'alau sisina, ai na yi fushi tunda sai yau zaki zo duba ni, da haihuwa na yi ma sai Babyn ya kwana sannan zaki zo ki gan shi ko?" Neehal ta saci kallon Ameen da ya zauna a kusa da matarsa ta ce "A yi mun afuwa Aunty, na je gurin aiki ne, sai bayan da Mama ta dawo take faɗa mun abun da ya faru, I hope dai jikin naki da sauƙi." Hafsah ta ce "Jiki da sauƙi, Welcome, Yaya ya ɗauko ki zai wahalar wa da Mama ke da aiki ko?" Ta ƙarashe zancen da kallon Ameen, yay mata wani kallo bai ce komai ba. Neehal ta yi murmushi ta ce "Babu komai Aunty, mene abun wahala a aikin gida?" Hafsah ta ja tsaki a ranta cikin tsanar Neehal ɗin, maganar nan da suke yi ma daure zuciyarta kawai take yi, tsanar yarinyar kullum ƙaruwa take a ranta, ko dan yanda Ameen yake nuna caring a kanta ne? Gashi duk ganin da zatay mata sai ta ga kamar ƙara kyau take, ga iyayi a idan tana magana, ita a dole mai class. Ta ja ɗan ƙaramin tsaki ba tare da ta san a fili ta yi ba tare da yamutsa fuska, kallon da Ameen yay mata ne ya fargar da ita, ta taune lip ɗinta tare da dafe cikinta dan ya yi tunanin ciwon cikin ne ya sata tsakin. Ya ɗauke idonsa daga kanta a kallon da yake mata data rasa yaren da zata fassara shi, shi ba kallon tuhuma ba shi ba na gargadi' ba. Neehal ta ce "Sannu Aunty, ko kina buƙatar wani abun ne?" Hafsah ta girgiza mata kai alamar a'a. Ta ce "Allah ya sauwaqe." Sannan ta da juyawa ta fice daga ɗakin. Hafsah ta bi ta da kallon tsana, tana juyowa suka haɗa ido da Ameen yana mata irin kallon d'azu. Sai ta hau borin kunya ta fara yamutsa fuska tana faɗin. "Baby cikina na damuna da ciwo." Ameen ya janyo ta jikinsa ya ce "Sorry, bari na kira Mama ko akwai maganin da za'a baki ya daina ciwon." Ta gyaɗa masa kai, tare ƙara shigewa jikinsa. A falo Neehal ta zauna bayan ta fito, bata koma bedroom ba. Tana zaune a nan Ameen ya fito daga ɗakin. Ta kalli agogon dake falon ta ga goma na safe ta wuce, ta ce masa "Yaya me za'a girka for lunch?" Ya zauna a kujerar dake fuskantar ta, ya ce. "Tun yanzu?" Ta ce "12 za ni gurin aiki ne, shi yasa." Ya ce "Ki dafa ko me kike so." Ta ce "Ka faɗa dai, kar in dafa abin da baka ci, ko kuma wanda Aunty Hafsah bata ci." Ya ce "Ita ai bata iya cin abinci, for me kuma ko me kika dafa i will eat." Ta ce "Ko tuwo ne?" Ya harare ta. Ta tashi tana dariya ta sauka ƙasa, ya bi ta da kallo. A falon ƙasa ta samu ƴan'mata guda biyu masu aikin gidan, ta shiga kitchen ba tare data musu magana ba. Kamar yadda ta tsokani Ameen tuwon ta ɗaura, duk da itama bata wani ci sosai amma kawai sai ta ji shi take son yi. Tuwon semo ta yi, miyar zogale tare da taimakon ƴan'mata nan, wanda bayan shigowar ta kitchen ba jimawa suka biyo ta wai za su taya ta aikin, ta ce musu to bismillah. Suna aikin suna mata hira, dan surutu ne da su ba kaɗan ba, farkon hirar kyawunta suka fara yabawa, har suna cewa sun kasa gano waya fi kyau tsakanin ita da Ameen. Yanda suke acting a hirar sai suke bata nishad'i, ta dinga murmushi, wani abun kuwa idan sukay dole sai ta dara, because they are so commedians. Sai ta ji daɗi a ranta ta samu masu ɗebe mata kewa a gidan, kuma ga su yara ne ba za su wuce 18 years ba. Ta tambaye su sunayensu suka sanar mata, Harira da Saude. Ba ta gama girkin ba sai kusan 12, saboda da ɗan yawa ta yi saboda ta san za'a iya yin baƙi ƴan zuwa dubiya, ta kwasawa Ameen nasa daban a cikin ƙaramar warmer, ta ce wa su Saude idan ya zo neman abincinsa gashi nan. Ta ɗibi kaɗan ta ci saboda saurin da take yi ta tafi gurin aiki dan ta yi late, bayan ta gama ci ta hau sama ta shirya cikin sauri ta fito ta shiga ɗakin Hafsah ta sanar mata zata tafi, kamar an mata dole ta ce ta je driver ya kai ta. Direban gidan ne ya kai ta gurin aiki kamar yadda Hafsan ta faɗa, ba ta ga Ameen ba kuma bata ga Motarsa a parking space ba, hakan ya tabbatar mata da baya gidan kenan. Ƙarfe Shida na yamma ta tashi daga aiki, tun kafin ta fito daga office aka aiko an zo ɗaukarta. Bayan ta fito ta ga direban gidan Ameen ne, dama da ya kawo ta ya tambaye ta ƙarfe nawa zata ta tashi ta sanar masa. Bayan ta koma gidan ta shige ɗaki bata fito ba har akay Magriba, saboda baƙin da ta ga an yi. Tana zaune akan sallaya suna chat da Sadik aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, ta d'ago tana dubansa tare da amsa masa sallmar da ya yi. Ta ajiye wayar ta ce "Sannu da zuwa Yaya." Bai amsa mata ba ya zauna a kusa da ita. Ta ɗan lumshe ido ta buɗe saboda k'amshinsa da ya cika mata hanci. Ta yi ƙasa da kanta saboda yanda ta ga yana kallon ta, lokuta da dama tana mamakin yanda yake yawan kallon ta, ta kan tambayi kanta ko kallon na mene ne? Ganin ba shi da niyyar magana ta ce "Mun yi waya da Mama ta ce, idan tana free za su zo anjima ita da Daddy." Ya ce "Allah ya kai mu." Sai kuma ya ɓata fuska ya ce "Dama zuwa kika yi dan kina bari na da yunwa?" Ta masa kallon mamaki ta ce "Yunwa kuma Yaya?" Ya ce "Eh." Ta yi murmushi dan gano bakin zaren, ta ce. "Amma dai ka ci wani abun?" Ya girgiza mata kai, ta ɓata fuska cikin rashin jin daɗi ta ce, "Da ka ci tuwon Yaya ko kaɗan ne, ya yi daɗi fa, nima na ci, amma shine ka zauna da yunwa." Ya ce "Ai baki so in ci ba dama." Ta ce "To yanzu bari in tashi in dafa maka wani abun ka ci, me kake so in dafa maka Yayana?" Ya ce "No ki huta I knew you are tied." Ta ce "Zan iya fa Yaya, ai na huta." Ya ce "No ki bar shi, mu je dai ki raka ni unguwa." Ta ce "Toh Yaya." Ya miƙe ya fita, ta tashi ta cire hijabin jikinta ta ninke, sannan ta ɗauko mayafin abayar dake jikinta ta yane kanta da shi, ta fesawa jikinta turare kaɗan sannan ta ɗauki wayoyinta ta bi bayan shi. A falo ta zauna jiran shi, ba jimawa ya fito daga ɗakinsa inda Hafsat take a yanzu. Da ido yay mata alamar ta tashi su tafi, ba tare ta ce komai ba ta miƙe ta bi shi a baya. A falo ta tarar da su Harira suna kallo, su kai musu a dawo lafiya. Restaurant suka je ya siyo musu abinci, daga nan kuma ya biya ya siyo mata ice-cream da choculate da ya san tana matuƙar son su. A hanyar dawowa ta shagwab'e fuska ta ce "Yaya ka kai ni in ga Mama, sai mu dawo." Ba tare da ya dube ta ba ya ce "Ba ta ce zasu zo ba?" Ta ce "Ai na san da ƙyar za su zo, dama haka ta ce sai ta samu time." Bai kuma magana ba bai kuma kaita gidan ba, gidansa suka koma. Bayan an yi Sallar isha'i ta ci abinci sai ta sauko ƙasa gurin su Harira dan su yi hira. Saude ta ce "Mai kyau, d'azu na gan ki a talabijin." Neehal ta yi murmushi ta ce "Ni kuma? ba ni ba ce gaskiya, sai dai mai kama da ni." Saude ta ce "Alkur'an ke ce, da na je kaiwa Hajiya kifin data ce in sake d'umama mata ne na ga mai_gidan yana kallo, kuma har ɗan tsayawa na yi na ga kayan da kika fita da su ne a jikin wadda na gani." Neehal ta yi ƴar dariya saboda yanda Sauden ta yi maganar ta ce "Ƴan biyu ce ni ai, to ɗayar kika gani ba ni ba." Saude ta ce "Tab' amma kuna kama sosai, har fa yanda kike yi da idonki haka take yi." Neehal ta ce "Ya nake da idon?" Harira ta gyara zama ta ce "Ni zan gwada miki." Sai ta wani lumshe ido ta buɗe tare da keɓe baki ita a dole iyayi take tana gwada yanda Neehal take magana. Neehal ta yi dariya sosai wadda ta ƙara fito da kyawun fuskarta, kumatunta suka lotsa kamar an cire naman gurin. Saude ta taɓa dai_dai gurin cikin santi ta ce "Ke kam ki godewa Allah, ya baki kyau, wannan abun yana ban sha'awa, tun ɗazu in kina magana shi kawai nake kallo." Neehal ta ce "Allah ya baki miji mai irinsa, sai ki yi ta kallon sa." Saude ta washe baki ta ce "Allah ya amsa bakin ki mai kyau." Suna cikin hirar su mai daɗi dake sanya Neehal nishad'i Ameen ya shigo falon, sai ta ga su Harira cikin sauri sun tashi sun shige ɗakin da suke bayan sun masa sannu da zuwa. Neehal ta bi su da kallo, sannan ta mayar da idonta kan Ameen dake kallon ta hannunsa riƙe da leda, ta ɗan ɓata fuska ta ce "Sannu da zuwa." Ya ce "Yawwa." Tare da shiga kitchen ya ajiye ledar hannunsa, ya dawo falon ya ce wa Neehal. "Miemerh Please ki shiga kitchen ki soyawa Hafsah kajin can." Neehal ta ɓata fuska amma bata ce komai ba ta tashi ta shiga kitchen ɗin dan babu musu a tsakanin ta da shi. Ya bi bayan ta zuwa kitchen ɗin, ta juyo ta kalle shi, ya nuna mata inda kajin suke. Ta ɗauko tana turo baki gaba ta juye su a abu, a yayyanke suke a wanke tass. Ta ƙara ɗauraye su, ta ɗauko tukunyar da zata cinye su ta ɗauraye ta juye su a ciki, sannan ta saka musu magi da spices da ɗan yaji ta kunna gas ta ɗora. Duk abun da take yana tsaye yana kallon ta, ya jingina da ƙofar kitchen ɗin. Bayan sun mata yanda take so ta sauke ta tsame su ta zuba a cikin colander, sannan ta tsiyayo mai a jarka ta zuba a kasko ta ɗora akan gas ɗin. Ta ƙara juyowa ta ga har lokacin yana kitchen ɗin, ta turo baki ta cigaba da abun da take. Har ta fara soyawa bai fita ba, ita kuma duk ta takura kamar ta ce masa ya fita. Sai da ya gaji dan kansa ya fita. Tana soya na ƙarshe ya dawo kitchen ɗin, naman ya yi irin ƙarar nan da yake yi a cikin mai, har man ya ɗan fallatso mata a hannu. Ta ɗan ja baya tare da yarfe hannun, ya matso kusa da ita da sauri ya kama hannun yana dubawa. Ta shagwab'e fuska kamar zata yi kuka. Murya ƙasa_ƙasa ya ce "Sorry dear, don't cry." Ta kalli fuskarsa tana turo baki gaba tare da gyaɗa masa kai, Idanunsa suna kan hannunta hakan yasa ta ƙurawa fuskarsa ido kamar mai neman wani muhimmin abu a fuskar, sai da ya d'ago sannan ta yi saurin lumshe idonta tare da sakin ajiyar zuciya a hankali. Ta matsa daga kusa da shi tare da zare hannunta daga nasa. Ya ce "Zaki iya ƙarasa suyar kuwa?" Ta d'aga masa kai alamar eh. Ya juya zai fita cikin siririyar murya ta ce "Yayah.!" Ya juyo ya kalle ta ba tare da ya amsa ba. Ta yi shiru dan ta kasa faɗar abun da yake ranta, ba yabo ba fallasa ya ce "What happened?" Ta ce "Nothing." Yay mata wani kallo sannan ya juya ya fice. Ta sauke numfashi tana jin zuciyarta na mata wari irin lugude, wani b'arin na zuciyar kuma mamakin Ameen take, yanda yake mata magana babu faɗa bare haɗe rai, ko dan ta zo gidansa ne? Jiki a sanyaye ta kwashe sauran naman da ya fara k'onewa. Sai da ta kimtsa kitchen ɗin sannan ta fice. Tana komawa ɗaki ta tarar da missed call ɗin Mama da Ahmad. Mama ta fara kira, tana ɗauka ta ce mata. "Shine ba ku zo ba Mama?" Mama ta ce "A gajiye Dad ya dawo ne shi yasa, sai gobe Insha Allah, ina kika shiga nay ta kiran ki?" Ta ce "Ina ƙasa, wayar kuma tana sama a ɗaki." Mama ta ce "Ya jikin Hafsan?" Ta ce "Da sauƙi." Mama ta ce "Babu matsalar komai dai?" Ta ce "Nothing Mama, ina Dad?" Mama ta ce "Ya kwanta bacci, saboda gajiyar dake damun sa, shi yasa ni kiran ki ɗazu ai, kuma baki d'aga ba, yanzu kuma ya yi bacci." Neehal ta ce "Ki gaishe shi idan ya tashi, har na fara kewarku Mama." Ta ƙarashe maganar cikin shagwab'a. Mama ta ce "Rigimarki da yawa take Daughter, yau ma fa kin gan mu." Ta ɓata fuska ta ce "Ni dai dan Allah ku zo gobe in gan ku." Mama ta ce "Allah ya kai mu goben lafiya, daga haka suka yi sallama ta katse wayar. Ahmad ta kira, kamar mai jiran kiran ringing ɗaya ya katse ya kira ta. "Princesss.!" Ya kira ta cikin shauƙi after she picked, ta ce "Uhm, Uncle ina yini?" Ya ce "Ga shi nan, babu daɗi tunda yau throughout ban ji muryarki ba." Ta ce "To yanzu ai ka ji ai, sai ka ji daɗin." Ya yi murmushi mai sauti ya ce "Ni da jin daɗi Baby ai sai ranar da aka kawo mun ke gidana a matsayin mata, na san zan yi farincikin da ban taɓa yin irinsa ba a rayuwata Princess, na san a ranar i war haka masu kawo mun ke sun tafi, sai mu kaɗai a gidanmu, muna making love." Ta rufe fuska kamar yana gabanta cikin jin kunya, ya ce "Princess ban san irin son da nake miki ba, kuma na san duk bayanin shi da zan miki baza ki gane ba, amma da zarar kin zama tawa, I know you will understand more." Ta sauke numfashi ba ta ce komai ba, Ahmad da Sadik suna ɗaure ta da jijiyoyin jikinta, ga abun da yake ƙara bata haushi idan tana tare da kowannen su Heart ɗinta shi kaɗai take tuna mata, ta rasa gane wa take so da k'auna a cikin su, zuciyarta ta kasa tantance mata wanda ya kamata ta zab'a a matsayin abokin rayuwarta. 'Na barwa Allah zaɓi, Allah ka zaɓan mafi Alkhairi.' Ta faɗi haka a cikin ranta. Ahmad ya cigaba da yi mata hira mai daɗi cikin iya tsara kalamai masu kwantar da zuciya. Har bacci ya fara cin ƙarfin ta, saboda gajiyar dake tattare da ita. Jin hakan yasa yay mata sai da safe ya katse wayar, tashi ta yi dak'yar tana lumlumshe idanuwa ta rage kayan jikinta sannan ta kashe hasken ɗakin, ta kunna fitilar gado. Har ta kwanta ta ƙara tashi ta kunna light ɗin ɗakin sannan ta shiga toilet ta yi fitsarin da ya matse ta, bayan ta fito ta kulle ƙofar ɗakin tare da kashe light, sannan ta hau kan gadon ta ware bargon dake ninke a gefen gadon daga gurin bango ta lullub'e jikinta. Da ƙyar ta iya yin addu'ar kwanciya bacci, saboda baccin dake cin ta. Cikin dare ta yi juyi, haka Allah ya halicce ta indai zata yi juyi a bacci sai ta ɗan farka, kamar an ce ta buɗe ido sai ta ga kamar an turo ƙofar ɗakin an shigo, ta ware idanunta dan tabbatarwa gabanta na dokawa a million. kamar a mafarki ta ga ana nufo gadon ta ɗan hasken bedside lamp. Ta ƙara waro idonta ganin dagaske fa ita ake tunkarowa har anzo bakin gadon, ta yunƙura ta tashi zaune cikin rawar jiki tare da ware baki da nufin ta ƙwala ƙara, amma sai ta ji ana fesa mata wani abu a fuska kamar shantos, ta fara jujjuya kai a ƙoƙarin ta na nemo iskar Ubangiji ta shak'a ba wannan abun mai wari da ake fesa mata ba. Cikin sakanni ƙalilan hankalinta ya gushe daga jikinta, daga nan bata ƙara sanin inda kanta yake ba.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *5️⃣6️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........Alarm ɗin da ta saita wayarta da shi wanda yake tashin ta idan ta koma bacci bayan sallar asuba shi ya tashe ta ƙarfe 6:30 am. Ta ja gwauron numfashi sannan a hankali ta buɗe idonta da sukai mata nauyi, ɗakin data ke ta fara bi da kallo, a hankali ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo mata inda take da kuma abun da ya faru a farkawar da tay daren jiya. Ta yunƙura ta tashi zaune da sauri cikin matuƙar tsoro zuciyarta na mata wani irin bugu kamar zata faso ƙirjinta ta fito. Ta kalli ƙofar ɗakin ta ga babu alamar an buɗe ta a rufe take ruf, ta dawo da idanta kan gadon da take ta kalli gefen ta, shima babu alamar an yi wani abu a gurin. Ta yaye bargon dake lullub'e a jikinta da sauri ta shiga duba jikinta, amma babu alamar ko hannu an ɗora a jikin nata. Ta miƙe cikin rawar jiki ta sauko daga kan gadon ta yi taku uku ta ji ta rass, babu alamar wani ciwo a jikinta. Dafe kanta ta yi da hannunta a fili ta ce "Ko mafarki na yi ne?" Ta ja numfashi mai ƙarfi hakan yasa ta ji warin abun da aka fesa mata jiya ta cikin mak'oshinta. Ta kai hannu ta shafa fuskarta sai ta ji wani abu mai maik'o a fuskar kamar ta shafa mai. Ta goga hannunta sosai a fuskar sannan ta kai hannun hancinta ta shinshina. Tsoron ta ne ya ƙaru jin warin abun da aka shak'a mata, hakan ya tabbatar mata da ba mafarki ta yi ba, da gaske wani ko wata ya shigo ɗakin nan jiya, kuma ga dukkan alamu cutar da ita ake son yi tunda gashi an fesa mata abun da ya gusar mata da hankali. 'To waye? Kuma me yake nema a gurin ta?' Tsoron ta ne ya ƙaru sosai kamar a yanzu ne aka shigo ɗakin, ta nufi ƙofa da sauri cikin kyarmar jiki ta buɗe ta fita falo da gudu a gigice. Ameen yana zaune akan carpet yana karatun Alqur'ani a hankali, ya ji an buɗe ƙofa da ƙarfi, ya juya da sauri idanunsa suka sauka a kanta. Ta ƙaraso inda yake da gudu ta faɗa jikinsa ta baya tare da fashewa da kuka. A ruɗe yake tambayar ta me ya faru ganin gaba-ɗayanta a firgice take. Ta kasa magana sai ƙofar ɗakin kawai take nuna masa. Ya matsar da Alkur'anin gaban sa gefe, ya dawo da ita gaban sa, tana ƙoƙarin ƙara ruk'unk'ume shi ya riƙe ta, cikin damuwa ya ce "Miemerh! Mai ya faru? Talk to me please." Cikin sheshshek'a ta ce "Wani ne ya shigo ina bacci, ya fesa mun wani abu a fuskata, dan Allah Yaya ka mayar da ni gurin Mama kar ya ƙara dawowa." Ta ƙarashe zancen tare da faɗawa ƙirjinsa ta k'ank'ame shi, ilahirin jikinta rawa yake. Fuskantar da ya yi a tsorace take sosai, sai ya saka hannunsa ya zagaye bayan ta da su, a hankali ya shiga karanto addu'a yana tofa mata, dan ya fi zaton mafarki ta yi wanda ya firgita ta. A hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya, rawar da jikinta yake ta ragu. Jin haka yasa ya d'ago ta daga jikinsa, ta buɗe idonta dake shatatar da hawaye ta ce "Ni dai ka kaini gurin Mama dan Allah Yaya." Yana gyara mata gashin kanta da ya barbazo saman fuskarta ya ce "Relax Miemerh, babu komai fa, may be mafarki kika yi, dan babu wanda zai iya shigowa cikin gidan nan, saboda gaba-d'aya doors ɗin a rufe suke, ni da kaina na rurrufe su. Kuma babu ta yanda za'a iya haurowa a shigo, bare na ce ko haurowa akay." Cikin kuka ta ce "Wallahi Yaya ba mafarki na yi ba gaske ne." Ta bashi labarin duk abun da ya faru, cikin tashin hankali yake kallon fuskarta. Ta kai hannunsa kan fuskarta_ta, ta ce "Ka taɓa ka ji Yaya zaka ji wani abu kamar mai yana wani irin wari, kuma ni ban shafa komai ba kafin na kwanta." Bai ce komai ba ya sake ta ya miƙe ya nufi ɗakin, ta miƙe itama da sauri ta bi bayan shi. Dudduba ɗakin ya yi gami da toilet amma bai ga kowa ba, bai kuma ga wata alamar an shigo ba, ya tsaya yana sauke numfashi, shi kansa hankalin shi ya tashi ba kaɗan ba, saboda tabbatarwar da ya yi an shigo ɗin ba ƙarya ta yi ba, ya gane hakan ne ta ƙofar bantlation ɗin ɗakin da ya tura ya ji ta a buɗe, kuma shi ya san a rufe suke barin ta, tunda suka zo gidan ma zai iya k'irga time ɗin da aka buɗe ta. Neehal kam duk inda ya ɗora ƙafarsa nan take ɗora ta_ta, hannunta riƙe da nasa tana faman tsiyayar hawaye. Ya kamo fuskarta yana kallon idonta cikin tashin hankali ya ce "Kuma baa ki gane kowa ne ya shigo ba?" Ta girgiza kai ta ce "Ban gane ba Yaya, ai time ɗin ɗakin babu haske sosai, kuma cikin bacci ne idona bai gama washewa ba, da ƙyar ma na iya tashi zaune." Ya saki fuskarta ya ɗan lumshe idonsa a hankali tare ciza lip ɗinsa, tsawon wasu sakanni sannan ya buɗe idon ya ce "Kin yi Sallah?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. Ya ce "Je ki yi." Ta ce "Toh Yaya karka fita dan Allah, ka jira ni in fito tsoro nake ji." Ya gyaɗa mata kai kawai sannan ya koma bakin gado ya zauna tare da tallafe kansa da hannayensa guda biyu ya faɗa duniyar tunani. Harta fito ta zira abayar data cire jiya ta zira hijabi ta tayar da Sallah bai yi ƙwaƙkwaran motsi ba. Sai bayan ta idar ya tashi ya fita ba tare ya ce komai ba, ta bi bayan shi da sauri dan gani take kamar tana kadaicewa za'a kuma zuwar mata. Dawnstairs ya sauka ya fice daga part ɗin gaba-ɗaya. Ganin su Harirah suna kaikawo a falon ƙasa sai ta zauna a nan dan jiran shi. Wata irin kalasa take ji a jikinta, ga wani bacci_bacci dake fizgar ta, da alama abun da aka shak'a mata har yanzu bai bar ta ba, amma tsoro da fargaba sun hana baccin ɗaukar ta. Ameen ya jima a wajen kafin ya dawo, dan sai wajen 8 ya dawo. Neehal ta takura masa da kukan ita dai ya mayar da ita gida gurin Mamanta, dole ba dan yaso ba ya mayar da itan, ko kayanta bata tsaya ɗauka ba balle su yi sallama da Hafsah, dan ko saman ƙin komawa ta yi. Cikin mamaki ganin su a wannan lokacin Mama ta tarb'e su, bayan sun zauna Neehal ta mata bayanin abun da ya faru cikin kuka. Hankalin Mama fa ya tashi ba kaɗan ba, ta je ta taso Daddy ta faɗa masa abun da yake faru. Cikin damuwa ya ƙaraso part ɗin Mama ya ƙara tambayar Neehal ƙarin bayani, ta faɗa masa. Daddy ya ce, ta kwantar da hankalinta Insha Allahu koma waye Allah zai toni asirinsa. Ameen kuwa ya tabbatarwa Mama da Daddy cewar, akwai binciken da zai yi koma mene ne zai gano da yardar Allah. Mama kuwa sai da ta caje ƴarta ciki da waje ta ga babu abun da akai mata sannan hankalinta ya ɗan kwanta. A daren ranar Neehal ƙin kwanciya ta yi a ɗakinta ita kaɗai, saboda a tsorace take, sai a ɗakin Mama suka kwana tare da Maman. Washegari da safe Ameen ya kawo mata kayanta, tare da saƙon Hafsah na ta tafi babu ko sallama, dan Ameen bai sanar mata abun da ya faru ba. *AFTER FOUR MONTHS* Neehal sun koma school inda suka ɗora karatunsu na final year first semester, 8 weeks da suka wuce, and now suna shirye_shiryen fara first semester level Four exam. A ɓangaren soyayyarta da Ahmad da Sadik kuwa kowa yana nan yana zuba mata gwanintar sa, ita kuma ta dage da addu'ar neman zaɓin Allah. Every weekend sai Ahmad ya zo Kano ya gan ta, sai da randa aka samu wani akasi ne ba ya zuwa, jiki da jini sai Allah. wani Ikon Allah ba su taɓa haɗuwa da Sadik ba, sai dai sun haɗu da Ameen ba iyaka, dan shi kullum sai ya zo gidan da daddare. Har wata rana ya kasa haquri ya tambayi Mama, wai me Ahmad yake zuwa yi gidan ne, A tak'aice Mama ta ce masa zumuncin Allah yake zuwa. Kafin Neehal su koma school ta je Gombe ta kwanar musu biyu, haka ma ta je Abuja gidan Yayan Dad da gidansu su Hameedah, har gidan su Ahmad ta je. Ta ga karamci da k'auna a gurin ahalin Ahmad, twins suka dinga murna Aunty ta zo gidan su. A ɓangaren Sadik kuwa, bayan mahaifinsa ya gudanar da binciken da ya ce zai yi ya zo ya sanar musu cewar gaskiya ne abun da Umma take faɗa akan Neehal. Hajiyarsu da Kawu suka ce dole sai dai Sadik ya rabu da Neehal ya nemi wata yarinyar ya aura. Shi kuma ya ce ba zai iya ba, dan ba zai iya rayuwa babu ita ba, ya ƙi ci ya ƙi sha, ya tada hankalinsa, damuwar da ya sanya wa ransa gami da yunwa suka taru suka haifar masa da ciwo mai tsanani, wanda har ya kai shi ga kwanciya a gadon asibiti. Hankalin Maamah dana Abba ya tashi ba kaɗan ba, Maamah ta kira iyayenta ta sanar musu halin da ake ciki. Mahaifin Maamah da ya zo duba Sadik ya ji abun da yake faruwa yay ta faɗa, ya ce wannan ba hujja ba ce wadda za'a hana Sadik auren Neehal, da mutuwa da rayuwa duk a hannun Allah suke, sai ya rabu da Neehal ɗin kuma idan kwanansa ya ƙare dole ya tafi, dan haka shi zai tsayawa Sadik ɗin a auransa da Neehal, tunda ita yake so. Wannan magana ta Abeey (mahaifin Maamah) ita ta sanyayawa Sadik rai gami da ƙwarara masa gwiwa, har ya fara kwantar da hankalinsa ya samu lafiya. Hajiya da Kawu kuwa suka ce babu saka hannunsu a wannan al'amarin, dan haka duk abun da ya faru da Sadik babu ruwan su. Abeey ya ce "Babu abun ma da zai faru Insha Allahu sai Alkhairi." Abbansa kuwa bin al'amarin kawai ya yi da addu'a, dan ita ce mafita. Sadik ya so tun lokacin a zo a yi maganar auran su da Neehal, amma Maamah ta dakatar da shi ta ce, ya bi komai a sannu, ya bari ya ƙarasa ginin gidansa and kuma akwai lefe, dan haka idan ya gama shiryawa sai aje a yi maganar auren, a saka lokaci ƙanƙani a yi a wuce gurin. A month ɗin da ya wuce ne asirin Safeenah wadda tasa aka sace su Afrah ya tonu. Ta hanyar Gaye wanda jami'an tsaro suka samu nasarar kama su shi da yaransa akan dukan da suka yiwa Saudart. Bayan an kama sun ne ya yi bayanin dalilin dukan da sukay mata. Daga Zariya aka je har Abuja aka kamo Safeenah, wadda zuwa lokacin duk ta fige ta rame saboda zullumi da tsoro. Babu wanda bai yi mamakin jin Safeenah ce ta saka a sace su Afrah ba, kasancewar ta ƙanwar Mahaifiyarsu ta jini. Mamanta tay ta kuka tana Allah wadai da halin ta, duk da ba shiri suke da Ammi kishiyar ta ba, amma bata taɓa tsammanin ƴarta zata cutar da ahalinsu har haka ba. Ahmad ma ya sha mamaki ba kaɗan ba, duk da ya san Safeenah tana sonsa amma bai taɓa tunanin son zuciyarta har ya kai haka ba, dan shi a gurinsa wannan hauka ne da jahilci ba so ba, dan duk mutumin da yake k'aunarka to zai so ƴaƴanka. Safeenah ta yi nadama mara amfani ita da ƙawarta Saudat, dan har ita Alk'ali ya tisa prison bayan an gabatar da su a gaban kotu bisa laifin bayar da kwangilar kisan kai, duk da bata gama warkewa daga jinyar dukan da yaran Gaye sukay mata, sai dai an cigaba da ɗora ta akan magani a gidan kason. Yau ta kama ranar Alhamis, misalin ƙarfe huɗu da mintuna na yamm Neehal ta dawo gida daga school. A falo ta ajiye handbag ɗinta da sauran tarkacen school, kitchen ta nufa saboda hango Mama da ta yi a ciki. "Mama sannu da aiki, am back." Ta faɗi haka bayan ta shiga kitchen ɗin. Mama ta ce "Sannunki da zuwa, shine zaki shigo mun babu sallama." Ta ƙarasa ta rungume Mama ta baya a shagwab'e ta ce "Na yi sallama fa ba ki ji ba ne. Mama duk na gaji yau ɗin nan." Mama ta shafi kuncinta ta ce "Ki je ki yi wanka ki sakko ki abinci, idan kin huta akwai maganar da za mu yi." Ta bar jikin Maman tare da faɗin "Tom Mamana, Yaya ya kawo miki saqo ki bani?" Mama ta ce "Ya kawo tun safe, ki duba kan mudubi zaki gani." Ta ce "Me ya kawo mun?" Mama ta ce "Ban duba ba, ki je ki gani, zaki gan shi a cikin leda." Ta juya cikin murna ta fice daga kitchen ɗin. Ɗakinta ta fara shiga ta yi wanka, bayan ta shirya ta je ɗakin Mama ta ɗauki ledar da Ameen ya kawo mata ta buɗe. Kwalin sabuwar waya ta gani kamfanin iPhone, ta shiga buɗe kwalin da sauri ta zaro sabuwar wayar ta shiga jujjuya ta a hannunta cikin tsananin murna, da sauri ta tashi ta sauka ƙasa ta shiga kwad'awa Mama kira. Mama ta fito falo da sauri jin kiran tana faɗin, "Ke lafiya kike mun wannan kiran?" Ta rungume Mama tana murmushin farinciki ta ce "Mama Yaya ya siyo mun sabuwar phone." Mama ta yi murmushi tare da zare ta daga jikinta ta karɓi wayar tana kallo ta ce "Congratulation Dear, Ameen ya hutar da ni, na huta da mitar kullum Mama anyo sabuwar waya kaza ki siya mun ko ki sa Dad ya siya mun." Neehal ta yi dariya ta ce "Mama tun sanda result ɗinmu na last semester ya fito na nuna masa, da ya gani shine ya ce na yi ƙoƙari sosai me nake son na siya mun? Na ce masa kome ne ma ina so. Ni har na manta mun yi haka da shi, ashe shi bai manta ba yana sane. Jiya da ya zo da daddare shine ya ce mun zai kawo mun sak'ona yau na alƙawarin da yay mun." Mama ta ce "Ya kyauta sosai, sai kira shi ki yi masa godiya." Ta ce "Toh Mama bari na saka wayar a chaji." Mama ta bata wayar ta koma sama. Bayan ta saka chajin ta sauko ƙasa ta ɗebo abinci ta ci. Tana gama cin abincin ta ɗauki wayarta ta kunna data, ko 5 minutes ba ta yi da ɗaukar wayar ba kiran Ahmad ya shigo. Ta yi murmushi sannan ta d'aga ta kara a kunnenta, muryar su Afrah ta ji a maimakon ta Ahmad, suna kiran sunanta cikin karaɗin su. "Aunty! Aunty!" Ta ce "Na'am, Yaran kirki dafatan kuna lafiya?" Amrah ta ce "Lafiya k'alau Aunty." Ta ce "Ina Ummi da Aunty Zahra da Abba?" Suka ce "Suna gida." Ta ce "To ku gaishe su." Suka shiga yi mata hirar makarantarsu da bata labarin kayan wasan da Daddy ya siyo musu. Ta ce "Lallai ƴan gatan Daddy, ina Daddy'n yake?" Amrah ta ce "Gashi nan a kwance, bashi da lafiya." Cikin damuwa ta ce "Bashi da lafiya kuma, me yake damunsa?" Ahmad dake kwance yana sauraren su ya tashi zaune tare yi musu alamar su kawo masa wayar. Amrah ta ce "Ya tashi Aunty, ya ce na bashi wayar." Yarinyar ta miƙa masa wayar, ya karɓa ba tare da ya cire ta a speaker ba ya ce "Princesss.!" Cikin kasalalliyar murya. Ta ce "Na'am Uncle, meke damun ka?" Ya sauke numfashi ya ce "Babu komai." Cikin shagwab'a ta ce "Please Uncle ka faɗa mun, hankalina gaba-d'aya ya tashi da aka ce mun baka da lafiya." Ya ce "Ba ciwo nake ba Princess, kawai ina jin wani iri a cikin zuciyata kamar zan rasa ki." Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Twins dake kallon sa suna sauraren su duk da ba fahimta suke ba, Afrah ta ce "Daddy Aunty ta yi shiru, ko ta kashe wayar ne?" Ya ce "A'a bata son magana da ni ne, Aunty ku kaɗai take so bata so na." Yarinyar ta waro Ido ta ce "She like you Daddy." Ya ce "No, ask her?" Yarinyar ta ɗauki wayar da sauri tare da ɓata fuska ta ce "Aunty wai bakya son Daddy'n mu?" Amrah ta tari numfashin ƴar'uwarta da sauri da faɗin "Daddy yana da kirki fa Aunty." Neehal ta sauke numfashi tare yin murmushi domin ta gane wayo Ahmad ya shirya mata. A hankali ta ce "Ina son Daddy sosai Yarana, wasa yake muku." Ahmad ya lumshe idonsa tare yin wani sassanyan murmushi, duk da ba direct shi ta faɗa wa tana son shi ba amma kalmar ta doki zuciyarsa. Afrah ta kama hannunsa ta ce "Daddy Aunty ta ce tana sonka." Ya girgiza kai ya ce "Ai bata faɗa mun ba, ku ta faɗa wa." Cikin shagwab'a Amrah ta ce "Aunty please ki cewa Daddy kina son shi, tunda kina son mu ai kina son Daddy'n mu ko?" Ta ce "Eh mana, bawa Daddy wayar za mu yi magana da shi." Ya karɓa ya cire ta a speaker sannan ya kara a kunnensa ya ce "Uhm? ina jin ki." Ta ɓata fuska kamar yana ganin ta, ta ce. "Uncle meke damun ka?" Ya ce "Babu komai sai son ki Princess." Ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Ya yi ƙasa da murya ya ce "Princess please say you love me, baki taɓa faɗa mun ba fa." Ta ce "Gashi nan kai ka faɗa, kuma already You know I....." Sai kuma ta yi shiru. Cikin zak'uwa ya ce "Please Princess say it, ko zan ji daɗi a raina." Ta lumshe ido cikin shauƙi tare da yin ƙasa da murya sosai ta ce "I Love You Doctor Ahmad!" Sai kuma ta yi saurin zare wayar daga kunnen ta, ta yi hanging up. Sai jin ɗil ya yi alamun ta kashe wayar. Ya yi murmushi cikin tsananin farinciki ya ajiye wayar a gefen sa, sai ya tuno lokacin da tana ƙarama da ya ce mata I love You, ta ce "Love You too Uncle." Ya janyo ƴaƴansa da suka fara wasan su da sabbin teddy's ɗin da ya siyo musu ya rungume su a jininsa ya ce "Aunty ta kusa dawowa nan gidan mu zauna tare da ita." Yaran suka waro suka ce "Daddy When?" Ya ce "Soon Insha Allah." Sai suka bar jikinsa suka fara murnar Aunty zata dawo gidansu." Ahmad ya bi su da kallo yana tunanin farincikin da kids ɗinsa za su yi idan ya auri Neehal, da shi da his kids suna buƙatar ta a cikin rayuwar su, yaran suna sonta sosai dan har mamakin hakan yake, dan yanzu komai za su yi sai sun ambaci sunan Aunty, in unguwa suka ce suna dawowa za su je akira musu Aunty su bata labari, idan makaranta ce ma haka ne. Ya koma ya kwanta tare da janyo pillow ya rungume a ƙirjinsa gami da lumshe idonsa. A daa ya bar Neehal ta ƙarasa school ɗinta kafin ya tura a yi maganar auransu, amma a yanzu sai yake ganin kamar ba zai iya jiran watannin da suka rage mata ba ta ƙarasa karatun, ba tare da ya mallake ta a matsayin matarsa ba. A ɓangaren Neehal itama lumshe ido ta yi ta kwanta a jikin a kujera bayan ta katse wayar da murmushi ɗauke akan fuskarta. 'Uncle rigima.' Ta faɗi haka a ranta. Ƙarar shigowar text message cikin wayarta yasa ta buɗe ido ta ɗauki wayar ta duba, kamar yadda ta zata shine yay mata text ɗin, ta shiga karantawa a zuciyarta kamar haka. _Thank You so much Princess, you make me Happier, I love you so much._ Ta yi murmushi ba tare da ta yi masa reply ba ta tashi ta haye upstairs.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *5️⃣7️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........Bayan Sallar Magriba Neehal tana zaune a falon ƙasa tana sauraren karatun Alkur'anin dake tashi a cikin speaker, wanda ta yi connecting ɗinsa da wayarta. A hankali take bin karatun idanunta a lumshe. Ameen ya buɗo ƙofar falon ya shigo tare da yin Sallama cikin kamilalliyar muryarsa. Bata ji sallamar ba ma hankalinta yana kan karatun, har ya nemi guri ya zauna, k'amshin turarensa ne ya fargar da ita zuwan sa. Ta buɗe idonta da sauri tare da tashi daga kishingid'en da take. Ta waro Ido cikin murmushi tana kallon sa, kamar yadda shima yake kallon ta. Ta saka stop a karatun, sannan ta tashi ta koma ta zauna a kusa da shi. A hankali ta ce "Ina yini Yaya." Ya ce "Lafiya k'alau." Ta ce "Ya Aunty Hafsah?" Ya ce "Tana nan k'alau." Ta murmusa ta ce "Yaya na ga sak'on ka, thank you so much, Allah ya ƙara buɗi mai albarka." Ya lumshe ido ya buɗe a kanta ya ce "Amin." Ta miƙe tare da faɗin, "Bari na kira Mama." Bai ce komai ba har ta haye upstairs. Ta shiga ɗakin Mama da sallama, Mama dake shiryawa ta amsa mata, ta ce "Mama Yaya ya zo, yana ƙasa." Mama ta ce "Okay I will come." Ta juya ta koma ƙasa ta zauna a kusa da shi, ta shiga aikin kallon sa, shi kuma yana ta aikin latsa waya. Sai ta ga kamar ƙara kyau yake, ko dan ƙarshe ne shi a iya wanka da iya ɗaukar dressing. Ta kalli bak'ar sumar kansa wadda daga gani babu tambaya ba ƙaramin kuɗi ake kashe mata ba. Ta lumshe ido a ranta tana faɗin 'Ba a ƙasa ya ɗauki gayu ba, dan Mama ƙarshe ce itama a wannan fannin. Mama ta shigo falon tare da faɗin, "Neehal ki kawo masa abinci mana." Ta miƙe tare da amsawa ta nufi kitchen ɗin. Mama ta zauna a kujerar dake fuskantar sa, fuska a sake ya ce "Ina yini Mum." Mama ta ce "Lafiya k'alau, ya Hafsah?" Ya ce "Tana nan k'alau." Mama ta ɗan ƙura masa ido na wasu sakanni sannan ta ce "Ameen! Is everything okay?" Ya ce "Komai lafiya Mum, me kika gani?" Mama ta ce "You look so worry." Ya yi murmushi ya ce "Nothing Mum, idan ma da akwai wani abu yanayin aiki ne kawai." Mama ta ce "Allah ya taimaka ya bada sa'a, sai a cigaba da dagewa da addu'a." Ya ce "Insha Allah Mum." Dai-dai lokacin Neehal ta fito daga kitchen ta ajiye tray a gabansa, ta tsugunna dan sarving ɗinsa, Mama ta dakatar da ita da faɗin. "Barshi Daughter, je ki gyara mun bedroom i will save him." Ta ce "Toh Mama." Tare da nufar sama. Mama ta sakko ta zuba masa abincin a plate, ta dube shi ta ce "Sakko ka ci, and no more excuse or saying you are full." Ya yi murmushi tare da saukowa ya zauna a kusa da ita, ya jawo abincin gaban sa ya ce "Yaushe da rabon da ki yi save ɗina Mum?" Mama ta harare shi ta ce "Kasan jariri ne ai kai, da sai na zuba maka abinci zaka ci." Ya yi murmushi ya ce "Before you getting a Daughter ai kina mun, tunda kika yi ƴa kika daina yayi na." Mama ta yi murmushi ganin yanda ya wani marairaice ta ce "Au har wani daina yayin ka na yi?" Ya lumshe kyawawan idanunsa ya buɗe ya ce "Eh mana." Mama ta ce "Never Ameen, ai babu wani abu da zai yi replacing ɗinka a zuciyata, kai ɗin ne sometimes nima ba gane kanka nake ba." Ya yi murmushi bai ce komai ba ya yi Bismillah ya fara cin abincin sa. Mama ta bishi da kallo cike da k'auna, a ranta ta ce "My Son you will never change daga miskilanci." Ta yi zaton idan ya yi aure zai rage, amma sai ta ga jiya i yau, kamar ma ƙara masa a kay. Kaɗan ya ci abincin ya ajiye spoon ya ce ya k'oshi, sannan ya sha ruwa yay mata sallama ya tafi. Mama ta tattara kayan ta kai kitchen bayan ya fice. Sai da suka yi Sallar isha'i sannan Mama ta zaunar da Neehal a ɗakinta akan maganar da ta ce zasu yi. Tana duban ta seriously ta ce "Neehal ɗazu kawunki Malam Musa ya zo, yaso ya zauna ya jira ki dawo ku gaisa amma akai masa kiran gaggawa a gurin aikin su. Kuma dalilin zuwan nasa ya zo ne akan ya kamata idan kina da tsayayye ya fito a yi maganar auran ku." Ta d'ago ta dubi Mama da sauri amma batai magana ba. Mama ta cigaba da magana da faɗin, "Na ce masa akwai wanda yake zuwa gurin ki, dan kun ma daɗe kun kusa shekara tare, amma mu da muna jiran ki kammala karatun ki ne sai mu yi masa magana idan da gaske yake sai ya fito a yi maganar biki." Neehal ta sauke numfashi tare da yin ƙasa da kanta, Mama ta ce. "Ya ce duk wannan ba matsala ba ce, idan gasken yake ya turo a yi maganar auran naku, bayan kin kammala karatun naki sai a yi bikin." Neehal ta d'ago ta dubi Mama gabanta na fad'uwa ta ce "Mama duk yanda kuka yanke dai-dai ne, kuma duk abun da kuka ce shi zan bi." Mama ta ce "Haka ne Daughter, Allah yay miki albarka, yanzu idan Daddy ya dawo zamu tattauna ni da shi, yanda muka yi zan sanar miki sai ki faɗawa Sadik ɗin." Neehal ta gyaɗa mata kai, tana son tay mata maganar Ahmad amma kuma ta rasa ta ina zata fara. Mama dake nazartar ta, ta ce "Neehal me kike son cewa? Ko baki son Sadik ɗin ne?" Ta girgiza mata kai cikin sanyin jiki. Mama ta ce "To ya na ga gaba-ɗaya yanayinki ya sauya, kamar ba ki yi farinciki ba, kin ga Daughter idan da akwai wata matsalar ki faɗa mun." Ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce "Uncle Ahmad." Mama ta yi murmushi ta ce "Me ya faru da shi?" Ta buɗe baki kamar zata yi magana sai ta fasa. Mama ta ce "Na san soyayya kuke yi da shi ai, na zuba miki ido ne kawai in ga iya gudun ruwanki." Ta rufe fuskarta da hannunta cikin jin kunya. Mama ta ce "Amma Neehal me yasa kina tare da Sadik kike kula Ahmad da sunan soyayya? Hakan ba dai-dai ba ne." Ta sauke numfashi ta ce "Mama i can't reject him, saboda shi ma ya taimake ni a lokacin da nake buƙatar taimako." Mama "You are right, but you did a mistake." Ta ce "Mama na sani, amma ban san yaya zan yi ba ne a time ɗin." Mama ta ce "Shikenan, yanzu shi kike so ko Sadik ɗin. Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mama ta ce "Uhm? Ke nake sauraro." Ta ce "Mama na rasa wanda zan zab'a a cikin su, kowanne a cikin su yana da good quality, amma Mama ki zaɓar mun ɗaya a cikin su Please, duk wanda kika zaɓar mun i will accept him." Mama ta girgiza kai tare da dafa ƙafaɗarta ta ce. "Neehal miji fa, abokin rayuwarki wanda zaku yi rayuwar da baku taɓa yin irinta da kowa ba a duniyar nan. Dan haka ke ya kamata ki zab'arwa kanki wanda hankalin ki ya fi kwanciya da shi. Wanda kika yaba nagartar shi kuma kuka fahimci juna, wanda kike ganin zai baki farinciki ya kuma riƙe ki amana. Duk da mazan yanzu sai addu'a, amma ba duka aka haɗu aka zama ɗaya ba, akwai nagari wanda muke fatan Allah ya haɗa ku da su. Dan haka ki je ki nutsu ki yi shawara ki tantance wanda kike ganin hankalinki ya fi kwanciya da shi, kafin mu gama magana da Dad sai ki sanar mun wanda kika fitar, sai na faɗa musu a san abun yi. Sannan kuma ki dage da addu'a da neman zaɓin Allah." Neehal ta sauke numfashi cikin rashin sanin abun yi ta gyaɗawa Mama kai. Mama ta tashi tana faɗin. "Bari na je part ɗin Daddy." Ta gyaɗa mata kai kawai still bata yi magana ba. Bayan fitar Mama ta kwanta akan gado ta faɗa duniyar tunani. Ta fara tuno farkon haɗuwar su da Sadik da irin mutuncin da yay mata, ta kuma tuno irin tarin soyayyar da yake mata, da kuma damuwar da yake shiga a sanadin ta, domin ta san komai da ya faru a gidansu ya sanar mata babu abun da ya ɓoye mata. Ta tuna alkawarin da tay masa lokacin da ta je asibiti dubo shi da ba shi da lafiya, ya kama hannunta ya ce mata. "Neehal dan Allah duk runtsi karki bari a raba mu, Wlh idan na rasa ki mutuwa zan yi." Tana hawaye ta ce masa "Baza ka mutu ba Ya Sadik ɗina Insha Allahu kai ne mijina, na maka alƙawarin indai kana raye ba zan taɓa aurar wanin ka ba." And then ta komar da tunanin nata kan Ahmad, mutumin da yay ta dakon soyayyarta tsawon shekaru, kuma ya taimaka mata a lokacin da take da buƙatar taimako, ga kuma Ƴaƴansa wanda suke k'aunarta take k'aunar su, zata so ta auri Ahmad ko dan ta kula da twins, ta maye musu gurbin mahaifiya da suka rasa. Ta gyara kwanciyarta tana son ta tantance wa tafi so a tsakanin su amma ƙwaƙwalwarta ta kasa yi mata wannan aikin. Ganin ta kasa samun mafita sai ta yanke shawarar zata tunkari ƴar'uwa kuma Aminiyarta wadda bata da kamar ta wato Haneefah da wannan maganar, domin ta bata shawara. Da wannan tunanin ta miƙe ta koma ɗakinta. Mama kuwa sai da ta zubawa Daddy abinci ya ci sannan ta sanar masa da zuwan Kawu Musa da kuma yanda suka yi da shi. Daddy ya numfasa ya ce "Haka ne, kuma abun da ya faɗa gaskiya ne, nima da na so na ce ta turo mun shi yaron mu yi magana, amma sai na ce mu bari ta gama karatun ta, ta ɗan huta tukunna. Ko dan damuwar da ta shiga kwanaki akan rasuwar sauran samarinta." Mama ta ce "Haka ne, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi ya kawar da duk wata fitina a wannan karon a yi lafiya a gama lafiya." Daddy ya ce "Amin, yanzu ta fara turo mun shi yaron mu yi magana da shi, kafin akai ga maganar turo magabatansa." Mama ta ce "To ai ita yanzu wai ta rasa wa zata zaɓa, ka san baban Twins shima son ta yake." Mama ta kwashe duk yanda suka yi da Neehal ta sanar masa. Daddy ya yi murmushi ya ce "Daughter mai farin jini." Mama ta ce "Hmm, Allah ya kyauta, amma ni nafi mata sha'awar Ahmad ɗin, tunda shi babba ne, ga kuma yaransa suna buƙatar kulawar uwa, amma kuma idan ta zaɓe shi ta bar Sadik shi kuma bata kyauta masa ba, tunda ya riga Ahmad ɗin zuwa." Daddy ya ce. "Allah ya zaɓa mafi Alkhairi kawai." Mama ta ce "Amin Amin." Dad ya ce "Ɗazu Saratu ta kira ni, tana mun shirmen ku na mata." Mama ta ce "Shirmen me kuma?" Dad ya ce "Ita fa har yanzu bata haqura da batun Ameen da Hameedah ba, na ce mata ban da abunta Ameen fa ko shekara bai rufa da yin aure ba, idan ma auran zai ƙara ai ba yanzu ba, ballantana ma na san halin Ameen da ƙyar zai yarda ya ƙara aure." Mama ta ce "Allah ya kawo mata miji nagari ta yi auranta, amma Ameen a farko ma ya ƙi auren ta balle kuma yanzu." Daddy ya ce "Nima shi na gani dai Doctor." Mama ta ce "Allah ya kyauta." Washegari ta kama Friday lecture ɗin safe gare ta 8_12. Kafin ɗaya ta dawo gida, bayan ta yi Sallah ta ci abinci ta shirya tay wa Mama Sallama ta tafi gidan Haneefah kamar yadda ta k'udurta. Haneefah tana kitchen tana suyar wainar fulawa ta ji ana knocking ƙofar falo, bata fita ta falo ba ta buɗe ƙofar kitchen ta baya ta lek'a dan ganin waye. Hango Neehal da ta yi yasa ta waro ido da ƙarfi ta ce, "Kan uban nan, zuwa babu sanarwa." Neehal ta yi murmushi tare da ƙarasowa ƙofar kitchen ɗin ta juya ido ta ce. "Ko in koma ne?" Haneefah ta rungume ta cikin murnar ganin ta ta ce, "Wa ya isa ke da gidan ki." Neehal ta ce "Shi na gani dai." Haneefah ta jata suka shiga kitchen jin wainar data bari akan wuta tana kamawa. Neehal ta riƙe hab'a ta ce "Unborn me cin wainar fulawa ne kenan?" Haneefah ta ce "Rufa mun asiri da wani batun unborn, ina da sauran shekara biyu da watanni kafin na kammala school, a hakan ma idan ba'a tafi strike ɗin ƙasar nan na gado ba. Wannan wainar fulawar ta Ya Faruq ce ya saka ni in yi masa, kin san masoyiyarsa ce." Neehal ta ce "Faɗi gaskiya dai, wannan murjewar da kyawun da kika yi duk na mene ne?" Haneefah ta ce "Auran kenan Yarinya." Neehal ta waro Ido ta ce "Hmm, ya kk ya gida da school?" Haneefah ta ce "Lafiya k'alau, Alhamdulillah ya Mamana? Duk da fushi nake da Mama ta ƙi zuwa gidana." Neehal ta ce "Kin san Mama, ita fita wahala take mata." Haneefah ta ce "Daga gida kike ko school?" Ta ce "Daga gida mana, takanas na zo dan na gan ki." Haneefah ta yi murmushi ta ce "Kin kyauta kuwa, ki shiga falo ki huta kafin na ƙarasa." Neehal ta ce "Toh, Ya Faruq yana nan ne?" Haneefah ta ce. "Eh yana ɗaki, da na ji shigowar mota ma na ɗauka abokansa ne, ashe my Besty ce ta mun surprised." Neehal ta yi murmushi ta wuce ciki. Bayan Haneefah ta kammala wainar ta kaiwa Ya Faruq ɗaki tare da sanar masa zuwan Neehal, ya fito suka gaisa cikin fara'a. Haneefah ta kawowa Neehal abinci da drinks da wainar data toya, tana ci suna hira. Sai da suka yi Sallar la'asar lokacin Faruq ya fita sannan Neehal ta zayyanowa Haneefah problem ɗinta. Haneefah data ƙura mata ido tana sauraren ta, ta numfasa ta ce "Yanzu Neehal ke a karan kanki kin kasa zaɓar wanda zuciyarki ta fi so, ta yaya wani zai iya zaɓar miki? Ke baki san wa kika fi so a cikin su ba?" Cikin damuwa Neehal ta ce "Wallahi ban sani ba Besty, na kasa tantancewa, idan ina tare da wannan sai in mata da waccan." Haneefah ta ce "To duk ba son su suke ba." Neehal ta dube ta cikin mamaki tare da faɗin "Kamar ya?" Haneefah ta ce "Kamar yadda kika ji na faɗa, ai shi wanda zuciya take so baya b'uya, Neehal da ace kina son Sadik ko Ahmad idan kina tare da ɗayan su ba zaki taɓa mantawa da wanda kikewa son gaskiya a ba a cikin su. Daga Sadik har Ahmad tausayin su kawai kike ji, ko kuma wani a cikin su yana miki wani abu da yake burge ki, and kuma kina duba halacci ko kyautatawar da sukay miki a rayuwarki, amma so dai da k'auna na soyayya ba kya yiwa Sadik da Ahmad. Ni nafi tunanin akwai wanda zuciyarki take so, wanda ke kanki baki sani ba." Neehal ta ɓata fuska ta ce "Ni babu wani wanda nake so daban kuma, to wani saurayin ne dani bayan su da zan so shi?" Haneefah ta ce "Wanda ba kya taɓa mantawa da shi a cikin ranki, ko da kuwa kina tare da Sadik da Ahmad. Indai akwai wanda kike jin haka a kan shi to shi kike so." Neehal ta tab'e baki ta ce "Babu shi gaskiya, kema kin sani." Haneefah ta ce "Lokaci ne zai faɗa mana haka, amma now back to our business, wa kike ganin hankalinki ya fi kwanciya da shi a tsakanin su?" Neehal ta ce "Wannan ita ce tambayar da Mama tay mun, kuma na kasa tantancewa, shi yasa na zo mu haɗu mu tantance." Haneefah ta ce "Indai a yanda kika bani labari ne gaskiya zan fi so ki auri Sadik, saboda yanda yake da rauni akan soyayyar ki, kece mace ta farko da Sadik ya fara so a rayuwarsa, idan kika rabu da shi saboda Ahmad kin zalunce shi, saboda sai da ya gama sakankancewa ya samu mata sannan kuma ki canza zance. Time ɗin da Ahmad ya dawo cikin rayuwarki already kuna tare da Sadik, dan haka yanzu idan kika bar shi kin yaudare shi, kuma hak'k'in shi ba zai barki ba. Sannan kuma ki duba yanda danginsa ba kowa ke son ku tare ba, idan kika rabu da shi kika watsa masa ƙasa a ido za ai masa dariya, ace shi yana ta wahala a kanki ashe ma ke ba k'aunar sa kike ba, kuma Sadik ya riga Ahmad fara sonki." Neehal ta yi sauri ta ce "Uncle Ahmad ya riga, na faɗa miki fa tun ina yarinya farkon haɗuwar mu yake so na." Haneefah ta ce "Ai wancan lokacin daban, kuma ya wuce. Zancen yanzu ake da girmanki, amma ni dai shawara nake baki, dan ni Baban twins ɗin nan ma bai wani mun ba, ya miki tsufa, gwara ki auri saurayi ɗan shawalwali wanda zaku fi jin daɗin rayuwar auranku. Kuma na lura kalaman Ahmad da iya tsara mace ne suke rud'ar ki a kansa, dan na san ki da son soyayya, da son a nuna miki k'auna." Neehal ta ce "Ni duk ba wannan nake dubawa ba, ina duba taimakon da yay mun a baya, ni kuma yanzu yana buƙatar nawa sai in ƙi taimaka masa? Kuma ga yaransa da muka shak'u da su, bana son rabuwa da su" Haneefah ta ce "Idan dan Allah yay miki ba zai yi wannan tunanin ba dan baki zaɓe shi ba, su Afrah kuma dan kin yi aure ai ba yana nufin kin rabu da su ba kenan, zaki cigaba da zumuncin ki da su, tunda Allah ne ya haɗa ku." Neehal ta yi shiru na tsawon mintuna biyu, sannan kamar zata yi kuka ta ce. "Haneefah! Uncle Ahmad yana so na Sosai, kuma duk abun da kika faɗa akan Sadik gaskiya ne, ya cancanci zama miji a gare ni, amma ban san da idon da zan kalli Uncle Ahmad na faɗa masa wannan maganar ba, Allah na yi dana sanin haɗa two dating at one time." Haneefah ta ce "Haka nan Sadik ɗin shima idan kika zaɓi Ahmad zaki ji nauyin sanar masa kin zaɓi wanin shi a matsayin miji. Neehal! matar mutum kabarinsa, tun kafin ki zo duniya Allah ya riga ya rubuta wanda zaki aura, ki yarda da wannan, ki kuma dage da addu'a da neman zaɓin Allah, tunda kin san dai baza ki auri maza biyu ba ko?" Neehal ta ce "Haka ne ƙawata, daren jiya ma kusan kwana na yi ina kaiwa Allah kukana tare da neman zaɓin sa." Haneefah ta ce "Yawwa, kisa a ranki kawai wanda kika zab'a shine mafi Alkhairi a gare ki, kuma shi Allah ya rubuta zai zamto mijinki." Neehal ta ji wani ɗan sanyi a ranta, lallai ta yarda shawara tana daɗi. A hankali kamar wadda aka tilasta mata ta ce "Na zaɓi Ya Sadik, Allah yasa haka shi yafi Alkhairi." Haneefah ta ce "Amin ya Allah, shi kuma Ahmad Allah ya bashi tasa matar mai Alkhairin." Kamar zata yi kuka ta ce "Amin, amma ban san yanda zai ɗauki wannan al'amarin ba, ina jin kamar ban kyauta masa ba." Haneefah ta ce "He is a Muslim, kuma ya san qaddara mai kyau da mara kyau, Insha Allahu zai fahimce ki. But I'm not forcing you Neehal akan Sadik, kawai ina baki shawara ne kamar yadda kika nema daga gurina, idan kin ji zuciyarki ta fi k'aunar Ahmad karki cuci kanki, ki zaɓi wanda kike so ki aura, dan aure ba abun wasa ba ne." Neehal ta ce "Hmm, Allah yasa ya fahimta ɗin. No, ni da Ya Sadik da Uncle Ahmad duk ɗaya ne a gurina, duk wanda na zab'a dai-dai ne, saboda duk sun cancanta." Ta yi shiru tare da ɓata fuska, sannan cikin damuwa ta ce. "Ni duk ba wannan ba ma, ina tsoron abun da ya faru a baya ya kuma faruwa." Sai ta fara hawaye sannan ta cigaba da magana. "Ina tsoron a kuma kashe mun wanda zan aura yanzu ma." Haneefah ta ɓata fuska ta ce "Oh my God, Neehal har yanzu baki daina wannan banzan tunanin ba, kin manta Allah ne me rayawa da kashewa." Neehal ta girgiza kai kawai ba ta ce komai ba, hawaye na cigaba da shatata a fuskarta. Haneefah ta matso ta rungume ta, cikin lallami ta ce. "Insha Allahu, Besty babu abun da zai faru sai Alkhairi, Allah yana sane da ke, ki miƙa masa k'ok'on bararki, shi kuma da yardarsa na san zai kawo miki ɗauki. Kuma duk wanda yake kisan nan matuƙar dan ke ake yi bisa zalunci da son zuciya Ubangiji zai saka miki cikin gaggawa, dan Allah yana karɓar addu'ar wanda aka zalunta. Kuma rayuwar mumuni bata tafiya sai da jarrabawa, ke kuma wannan ita ce taki jarabawar, amma in kika yi haquri sai ki ga komai ya wuce tamkar bai taɓa faruwa ba, be a good Muslim please Dear." Haka dai Haneefah tay ta nusar da Neehal da nasihohi da kalamai masu daɗi gami da ƙara mata k'warin gwiwa akan Sadik, daga baya kuma ta koma tsokanarta da matar Barrister, an kusa shiga daga ciki. Har ta ji zuciyarta ta mata sanyi, kaso mafi yawa na damuwar da take ciki ya tafi. Shi yasa take son Haneefah, because she is a good person, kuma ta san baza ta taɓa bata shawarar da zata cutar da ita. Amma wani b'arin na zuciyarta sai tambayar ta yake akan anya ta yiwa Ahmad adalci kuwa? Sai bayan Magriba sannan ta bar gidan, shi ma sai da Mama ta kira ta a waya, dan sosai ta ji daɗin kasancewa da Besty'nta_ta.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *5️⃣8️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........A falon sama ta tarar da Mama tana kallo. Ta tafi da murnarta ta faɗa jikinta tare da faɗin. "Oyoyo Mamana." Mama ta harare ta, ta ce. "Aina na ɗauka a can zaki kwana." Ta ƙara ruk'unk'ume ta tana murmushi ta ce "Sorry My Mum, hira ce ta yi daɗi." Mama ta ce "Ya yi kyau, idan da Daddy ya dawo sai ki faɗa masa hira ce ta yi daɗi shi yasa kikai dare." Ta yi dariya kawai, Mama ta ce "Ya kika baro Haneefan?" Neehal ta ce "Lafiya k'alau, tana gaishe ki." Mama ta ce "Ina amsawa." Neehal ta miƙe ta shige ɗaki. Kwanciya ta yi akan gado bayan ta ajiye handbag ɗinta da mayafinta. Ta kwanta rub da ciki tare da tallafe kanta da hannunta. Tunanin Ahmad take da irin tarin soyayyar da yake mata, har yanzu ta kasa amincewa da zaɓin da ta yiwa kanta, tana ganin kamar ba zata iya barin Ahmad ba a rayuwarta. To amma Sadik fa, kamar yadda Haneefah ta faɗa idan ta bar shi ta zalunce shi, ta cuce shi ta yaudare shi. Ta runtse ido cikin tsananin damuwa, ita bata taɓa dating two persons at one time ba sai wannan karon, ta yi dana sani mara iyaka, amma kuma babu yanda zata yi wannan ma is another addiction in her life. Ta tashi ta ɗauko jakarta jin wayarta na ringing a ciki, Sadik ne yake kiran ta. Ta d'aga cikin ƙoƙarin ganin bai fuskanci tana cikin wata damuwa ba, gaisawa kawai sukai ya tambayi lafiyarta saboda lokacin Sallah da ya gabato. A daren ranar ta sanar da Mama Sadik ta zaɓa, Mama ta ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Washegari da safe Mama ta ce mata gobe Sunday ta cewa Sadik ya zo Daddy yana son ganin sa. Kamar zata yi kuka ta ce, "Toh Mama zan faɗa masa, amma Mama har yau na kasa sanar da Uncle Ahmad, wallahi ban san ta yaya zan faɗa masa ba, kuma na san zai yi wahala ya ƙi zuwa yau ko gobe." Mama ta ce "Shikenan idan ya zo ni zan masa bayanin da zai fahimta da kaina." Ta gyaɗa mata kai tana ƙoƙarin ganin bata bar hawayen idonta ya zubo ba. Ta tashi ta koma ɗakinta dan zata iya fashewa da kuka saboda yanda take jin zuciyarta, ita kuma bata son ta yi kuka a gaban Mama. Tana hawaye ta yiwa Sadik text ta sanar masa abun da Mama ta ce ta faɗa masa. Ta kwanta tana kukan da bata san dalilin shi ba. Tana jin wayarta tana ringing amma bata bi ta kanta ba. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi shiru, ta tashi ta ɗauki wayar ta duba ta ga Sadik ne ya kira ta, da ya ga bata ɗauka ba yay mata reply ɗin text ɗinta, tare da daɗaɗan kalaman soyayya a ƙarshe. Ta yi ɗan murmushi, sannan ta tashi ta je ta wanke fuskarta. Bayan Sallar Azhar tana zaune a ɗakinta da materials ɗin karatun ta tana dubawa. Mama ta shigo ɗakin ta ce mata. "Neehal Ahmad ya zo." Ta d'ago da sauri gabanta na wani irin fad'uwa saboda razana. Mama data kula da yanayin da ta shiga ta ce. "Ki je ku gaisa, yana ƙasa yana jiranki, kuma karki nuna masa wani abu, idan zai tafi i will explain to him." Neehal ta gyaɗa mata kai kawai. Kamar wadda k'wai ya fashewa a ciki ta tashi cikin sanyin jiki ta yane kanta da mayafin abayar dake jikinta. Ta ɗan gyara fuskarta sannan ta fesa turare kaɗan, sannan ta fice daga ɗakin cikin matuƙar sanyin jiki. As always yana zaune akan carpet idanunsa akan steps. Ta sakko cikin nutsuwarta kanta a ƙasa, gabanta na cigaba da faɗuwa ta zauna a kusa da shi tare yin sallama. Yana murmushi ya amsa mata. Ta ce "Ina yini Uncle." Ya ce "Lafiya k'alau Princess, ya weekend?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Ya School da aiki?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya gyara zama tare da juyowa ya fuskance ta sosai ya ce. "Kin yi kyau, kullum kamar ƙara miki kyau ake Princess." Ta d'ago tare da ƙirƙirar murmushi akan fuskarta a ƙoƙarin ta na ganin bata nuna masa akwai wata damuwa ba, ta ce. "Ni ɗin kuwa?" Ya ce "To da wa?" Ta sake yin murmushi ta ce. "Ina Yarana?" Ya ce "Suna gida." Ta ce "Da fatan dai suna lafiya, kuma baka barin wani abu yana damar mun su?" Ya kafe ta da ido ya ce. "Suna lafiya, ni kam me zan bari ya damu ƴaƴan Aunty? Ai lallaɓa su nake kar Aunty ta ce ta fasa Aure na." Ta yi ƙasa da kanta da sauri saboda yanda ta ji bugun zuciyarta ya sauya, ta hasaso yanda yake cikin farincikin nan da nishad'i ya zai ji idan Mama ta yi masa bayanin ta kusa zama mallakin waninsa, daga yau ba zai ƙara zuwa su yi irin wannan zaman ba, duk soyayyar da ya nuna mata ta zama tahiri, a...... "Princess.!" Ya katse mata tunani ta hanyar kiran sunanta. Ta d'ago tay masa kallon cikin ido cikin dakiya. Ya lumshe ido ya buɗe su a cikin nata ya ce. "Tunanin me kike?" Ta ce "Babu komai Uncle." Ya karyar da kai ya ce, "Let me snap you, kin mun kyau sosai yau." Ya ɗauko wayarsa yay mata pictures, ita kuma tana ta murmushi, sannan ya ɗauke su tare. Ta karɓi wayar tana dubawa, hotunan sun yi kyau sosai. Ta yi murmushi ta cigaba da kallon pictures ɗin wayar, wanda fiye da rabi na twins ne. Ta tura wanda yay musu yanzu sannan ta tuttura wasu na twins da nasa ta whatsapp. Mama da kanta ta sakko ta shiga kitchen ta zubo masa abinci ta kawo masa, ya dinga yi mata godiya cikin jin kunya. Bayan Mama ta koma sama ya dubi Neehal ya ce. "Ina son Mama sosai, saboda kirkinta, da sanin darajar ɗan Adam gami da karamci." Ta yi murmushi kawai, sannan ta zuba masa abincin, yana ci suna hira, wanda Neehal ta ji kusan rabin damuwarta ta tafi. Sai da aka kira Sallar la'asar sannan ya tashi ya je masallaci ya dawo. Neehal bata sakko ba tana ɗakinta akan darduma bayan ta idar da Sallah, addu'a take yi akan Allah ya sanyayawa Ahmad zuciyarsa, Allah yasa kar abun da Mama zata faɗa masa ya yi hurting heart ɗinsa over. Jin dawowarsa Mama ta sakko ta zauna akan kujera sannan cikin kulawa ta ce. "Neehal ta faɗa maka za mu yi magana ko Doctor?" Cikin fad'uwar gaban da bai san ko ta mecece ba ya ce "Eh Mama." Mama ta danne tausayinsa dake cikin ranta ta fara yi masa bayani, cikin tausasan kalamai ta yanda zai fuskanta. Da farko ji yay kansa ya masa wani irin juyawa, yawun bakinsa ya kafe kaf, dak'yar ya iya had'iye wani abu mai ɗaci da ciwo daya tsaya masa a mak'oshi ya ce. "Babu komai Mama, na fahimce ki, Allah kuma yasa hakan shi ya fi Alkhairi a gare mu gaba-ɗaya." Ya yi maganar cikin tsananin dauriyar zafin da zuciyarsa take masa. Bai kuma fuskantar abun da Mama take kuma faɗa masa ba, ya dai ji kamar haquri take ba shi da kuma ƴar nasiha. Ya gyaɗa mata kai kawai, ita kuma ta tashi ta nufi upstairs tana faɗin bari ta turo masa Neehal ɗin su yi Sallama. At the first bayan barin Mama falon ya d'ago kansa tare da lumshe idonsa yana fatan ya kasance mafarki yake ba gaske ba ne abun da Mama ta sanar masa. Ya yi imagine wai hakan na nufin ya rabu da Princess ɗinsa kenan har abada, nan da wani ɗan lokaci za'ai mata aure da wani ba shi ba. Innalillahi,wa'inna'ilaihirraji'un ya shiga maimaita a fili cikin sanyin murya mai cike da damuwa, har ya ji ya fara ɗan samun salama a cikin ransa. Neehal wadda da ƙyar Mama ta yaƙo ta, ta fito saboda ta ce bata san da idon da zata kalle shi ba, ta ƙaraso falon idanunta na shatatar hawaye, da ƙyar take iya ganin gabanta. Ya ƙura mata ido cikin sarewa da karayar zuci, karon farko a rayuwarta ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kuka. Ya runtse ido ya buɗe saboda yanda kukan nata yake taɓa masa zuciya. Ya tsotsi lips ɗinsa da suka bushe lokaci ɗaya saboda damuwa cikin marainiyar murya ya ce. "Please Princess Stop crying, ko so kike nima in yi kukan?" Ta girgiza masa kai. Ya d'ago kanta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ya shiga share mata hawaye da shi. Ta bar jikinsa tana sakin ajiyar zuciya. Cikin muryar kuka ta ce, "I'm so sorry Uncle, I..." Ya katse ta da faɗin. "Me kikai mun Princess da zaki bani haquri? Na fuskanci bayanin Mama kuma na gamsu. Princess! Ba mu muke da ikon tsarawa kanmu rayuwa ba, Allah ne yake tsara mana. I'm a Muslim, na yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, tabbas rasa ki a cikin rayuwata ba ƙaramin rashi ba ne, amma kuma babu yanda zamu yi da ikon Allah. Karki damu akan wannan Please Princess, I knew you love me so much." Ta kalli fuskarsa yay mata murmushin da ya fi kuka ciwo tare da kamo hannunta ya ce. "Princess! Sau da yawa abun da zuk'atansu suke so ba shine Alkhairi a gare mu ba, sai mu ga wanda bama so ɗin ya fi zama Alkhairi a gare mu. Duk da na san kina son guy ɗin da zaki aura ba wai auren dole za'ai miki ba. Amma ko kaɗan ban ji a raina kin yaudare ni ba or something like this, abun da kikai shine dai-dai, kuma shine adalci. Tunda shi guy ɗin he came first before I came, abun da baza ka so ai maka ba kaima karka so kaiwa wani, dan haka ki daina damun kanki indai ni Ahmad ne na haqura, dama rayuwa cike take da farinciki da baƙinciki, idan ka yi haquri kuma zaka ga ribarsa a gaba, kuma komai zai wuce kamar bai faru ba." Ya yi shiru yana sauke numfashi, dan shi kansa ya san ba ƙaramin dauriya yake ba wajen ɓoye mata damuwarsa. Ta ƙura masa ido cikin mamakin kalamansa zuciyarta cike da tsantsar tausayinsa, ta san daurewa kawai yake dan ya ga ta damu kar ta tashi hankalinta. A hankali ta ce "Thank you so much Uncle, for your cares and everything to my life." Ya yi irin murmushin d'azu ya ce. "Nima na gode da k'aunar da kika nuna mun Princess, and I will never forget you in my life. Na gode Na gode sosai, da k'aunar kike wa ƴaƴana. Allah ya yiwa rayuwarki albarka, ya baku zaman lafiya ke da mijinki idan kun yi aure, ya kuma baku zuri'a d'ayyiba." Ta ce "Amin Uncle tare da kai." Ya ja karan hancinta ya ce, "Zan wuce sai mun zo biki." Dan ba ƙaramin dauriya yake ba, so yake kawai ya kadaice ya rarrashi zuciyarsa. Ta lumshe ido hawaye ya zirnano daga cikin idanunta. Kamar zai yi kuka ya ce. "Oh My God Princess, dan Allah ki bar kukan nan, baki san yadda nake jin zafi a cikin raina ba idan kina yi. Ta share hawayen bayan ta zare hannunta daga cikin nasa ta ce. "Na daina Insha Allah Uncle." Ya ce "Promise to me ko na tafi baza ki yi kuka ba." Ta ja hanci a hankali ta ce. "Ba zan yi ba Uncle Insha Allah." Ya shafi kuncinta ya ce, "Good lady, yanzu fa kin girma Princess, ko kina so twins ɗinki su gan ki kina kuka?" Ta girgiza masa kai. Ya ƙara kamo hannunta ɗaya ya ce. "Tashi mu je ki raka ni." Ta kalle shi sannan ta tashi ganin shima ya miƙe. Ya taune lip ɗinsa jin kamar zai faɗi tare da dafa hannun kujera yana ambaton sunan Allah. Ta ƙura masa ido kawai cikin damuwa. Ya d'ago yana murmushi ya ce, "Wannan kallon fa?" Ta ƙara waro masa manyan kyawawan idanunta haɗe da juya masa su sannan ta lumshe su a hankali. Salon nata ya shige sa ba kaɗan ba, bai san sanda ya dafa kafaɗunta ba ya yi kissed saman idanun, a hankali kuma ba tare da ta taɓa zato ba ta ji saukar lips ɗinsa akan nata. Ta sauke wani gwauron numfashi lokacin da ta ji yana kissing ɗinta, kafin a hankali ya janye fuskarsa daga ta_ta. Cikin raunin murya ya ce, "Good bye Princess, I love You.!" Sannan kamar wanda aka tsikara ya juya da sauri ya fice daga falon. Sai buɗe idanunta ta yi ta ga babu shi sai k'amshinsa da ya bar mata a jikinta da falon. Ta ja ƙafafuwanta da sukay mata nauyi ta ƙarasa kujerar dake kusa da ita, ta faɗa kanta ta fashe da kuka, a ranta tana faɗin. 'This means daga yanzu mun rabu da Uncle, rabuwa ta har abada.' Ta cigaba da kukan ta a gurin, ta ma manta da alƙawarin data ɗaukar masa na baza ta kuma yin kuka ba, akan rabuwar ta da shi. Da ƙyar Ahmad ya iya jan ƙafarsa ya je parking space, yana zuwa ya buɗe Motar da ya zo da ita ya shiga ya zauna ya ɗora kansa akan sitiyarin Motar, yana jin zuciyarsa tamkar zata soye saboda zafin da take masa. Ganin abun yake tamkar almara, domin bai taɓa tunanin zai ƙara rasa Neehal a karo na biyu ba. Amma ya yadda da ƙaddara, ya kuma yarda wani ba ya taɓa auran matar wani. Zai dage da addu'a akan Allah ya cire masa sonta ko da ba duka ba daga cikin ransa, ya kuma bashi mace ta gari wadda zata kula da shi da marayun ƴaƴansa. Sai dai ya rasa me yasa wani b'arin na zuciyarsa yake tabbatar masa da bai rasa Neehal ba, yake nuna masa zai mallake ta. Ya sauke numfashi tare da addu'ar idan rabonsa ce ita, Allah ya bashi, zai je ya dage da addu'a. Sunan Allah yay ta maimaita a ransa, har ya ɗan samu nutsuwa. Cikin dauriya ya kunna Motar ya fice daga gidan bayan an buɗe masa gate ya nufi gidan Mamy. Yanda Mamy ta ganshi ya shigo a sanyaye kamar mai cuta ta san da matsala, a ɗan rikece ta tambaye shi me nene? Kamar zai ɓoye mata sai kuma ya sanar mata. Itama Mamy ta ji ba daɗi a ranta sosai, domin ta yiwa Ahmad sha'awar Neehal, dan ta yaba da hankalinta da nutsuwarta. Amma sai ta kwantar masa da hankali, ta ce ya je ya dage da addu'a Allah ya zaɓa masa abun da ya fi Alkhairi. Har bayan Magriba Neehal bata daina kuka ba, Mama ta yi rarrashin ta yi nasihar ta yi faɗan amma ta ƙi barin kukan, har ta gaji ta ƙyale ta. Tana jin wayarta nata vibrate ana ta kiran ta amma ta ƙi bi ta kanta. Ga kanta dake ciwo saboda kukan da take. Bayan Magriban ne Ameen ya zo gidan, lokacin tana ɗakinta a kwance akan gado. Bayan sun gaisa da Mama ya tambaye ta Neehal ɗin, ta sanar masa tana ɗaki tana kuka, ko abinci bata ci ba tun safe. Bai tambaye ta dalilin kukan ba ya tashi ya shiga ɗakin. Ya zauna a gefen gadon ya kira sunanta, ta tashi zaune da ƙyar tana goge hawayen fuskarta, idanunta sun yi jajur. Cikin sanyin murya mai nuni da rarrashi yay mata Ƴar nasiha, akan kuka ba maganin damuwa ba ne, komai yake damun ka, ka kaiwa Allah kukan ka, shi zai maka magani. Sai gashi ta yi shiru, ya ce ta je ta wanke fuskarta ta zo ta ci abinci. Bata musa ba, ta tashi ta yi abun da ya ce. Mama ta cika da mamakin ganin cikin mintuna ƙalilan ta saki ranta, Alhalin ita tun yamma take fama da ita. Sai da ta ci abincin ta sha maganin ciwon kai sannan Ameen ya bar gidan. Washegari kamar yadda Dad ya ce, Sadik ya zo gidan da yamma. Har part ɗin Daddy'n akai masa iso ya je ya same shi. Daddy yay masa ƴan tambayoyi, sannan ya ce ya bashi auran Neehal ya turo magabatansa. Ai Sadik ji ya yi kamar ya rungume Daddy dan tsananin farin ciki, yay ta zuba masa godiya. Ranar Neehal ta sha kalamai da soyayya a gurin shi kala_kala, ita kuwa tay ta masa dariya tana tunanin ranar da aka ɗaura musu aure kuma sai ya kusa mutuwa dan farinciki. Bayan sati ɗaya mahaifinsa da abokinsa da Yayan Maamah suka zo nema masa auren Neehal, tare da kuɗin na gani ina so. Daddy da Kawu Musa da Uncle Mahmud, da mijin Aunty A'isha, su suka karb'i kuɗin, aka saka ranar biki bayan ƙaramar Sallah da yardar Allah, lokacin Neehal sun yi graduation ba jimawa. Su Sadik baki ya ƙi rufuwa, saboda farincikin nan da watanni biyar zuwa shida zai angonce da masoyiyarsa. A ɓangaren Ahmad kuwa a washegarin ranar da ya zo ya koma Abuja, yana zuwa ya sanar da su Ummi abun da yake faruwa. Sun ji ba daɗi sosai har Abban su Ahmad, amma suka ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Ahmad ya bawa zuciyarsa haquri, bai bari damuwa ta masa illa ba, duk da ko d'igo babu abun da ya ragu na son Neehal a cikin zuciyarsa. Daga ya ji abun zai dame sa sai ya dinga maimaita kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un da hasbunallahu'wani'imal'wakil, ga zuciyarsa kullum cikin ƙarfafa masa gwiwar Neehal tasa ce take, kar ya fidda rai da samun ta. Kuma babu abun da ya canza wa Neehal daga yanda suke before, idan ya kira wa su Afrah ita a waya, ta ce su ba shi wayar yana karɓa su yi magana har da ƴar tsokana wani lokacin, sai dai ba ya mata zancen soyayya ko kaɗan, zumunci kawai suke yi. Itama Neehal ɗin ta yi ƙoƙari ta cire damuwar rabuwa da shi daga ranta. Ta yadda cewa Allah ya yi Sadik ne mijinta tun fil azal, ba Jameel, Anwar da Ahmad ba, tunda su sun rasu, Ahmad kuma shi yasa Allah ya raba su tun a farko, dan da ace ba su rabu da shi ba a lokacin da take gidan Aunty Fauziyya, da ko soyayya ba zata yi da Jameel da Anwar ba, tunda ga shi kuma tun lokacin yake son ta. Ta kwantar da hankalinta suna shan soyayyar su da Sadik. Sai dai tunda aka tsayar da lokacin bikin su take jin wani irin feeling a cikin zuciyarta, feeling ɗin data kasa tantance ko na mene ne, sai dai yana mata yanayin kamar tsoro ko fargaba, amma kuma tsoron da fargabar na mene? Sai kuma wani abu guda ɗaya, ɗan sakin fuskar data fara samu daga gurin Ameen da kulawa ya daina mata yanzu, sai ta gaishe shi ma ya ƙi amsawa, ita kuma hakan na damunta matuƙa, bata son ta ga yana yi mata irin wannan shariyar, sai ta ji duk ranta babu daɗi........✍️ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *6️⃣0️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........Da yamma Haneefah ta zo gidan, duk da tana fama da laulayi amma ta ce ba zata iya kwana bata ga lefen Besty ba. Bayan sun gaisa da su Mama ta hau sama gurin Neehal. A falo ta tarar da ita idanunta a lumshe tana sauraren karatun Alkur'anin da tasa a speaker. Haneefah ta ƙarasa inda take ta taɓa ta, tare da faɗin. "Amarya." Neehal ta buɗe idonta ta dube ta, ta yi murmushi ta ce. "Na'am Ango." Haneefah ta zauna a kusa da ita, ta ce. "Ya na ganki wani iri, ko baki da lafiya ne?" Neehal ta ce. "A'a k'alau nake, kawai yanayi ne." Haneefah ta ce, "Yanayin me? Ke da ya kamata a zo a tarar kina cikin farinciki da annashuwar kin kusa aure." Ta ƙarashe maganar da dariya. Neehal ta harare ta, ta ce. "Zan bar Maman shine zan dinga farinciki?" Haneefah ta ce. "Wannan duk na ɗan lokaci ne, kina jin zaƙin auren zaki ware, wuyarta ki shiga daga ciki, ke Auran fa da daɗi." Neehal ta ƙara hararar ta, ta ce. "Allah ya shirye ki, kin fi ƙarfi na." Haneefah ta yi dariya ta ce. "Ina Barrister? Na ɗauka zan shigo in same ki kina waya da shi kuna soyewa." Ta sauke numfashi ta ce. "Yana nan k'alau, ba mu jima da yin waya ba, ina Yah Faruq?" Haneefah ta ce. "Yana can Kogi State." Neehal ta ce. "Yaushe zaki koma ke?" Ta ce. "Next week insha Allah, tunda by Monday zamu gama exam." Neehal ta gyaɗa mata kai cikin ƙoƙarin ganin ta ɓoye Mood ɗin da take ciki. Ta tashi ta sauka ƙasa ta ɗebo mata snacks ɗin da akaiwa masu kawo kayan lefen, ta haɗo mata da drinks. Bayan Magriba kamar yadda aka ce, su Daddy suka karb'i lefen Neehal a gurin magabatan Sadik, suka kuma saka lokacin biki sati takwas, bayan Babbar Sallah da sati biyu kenan. Ba su wani jima ba suka tafi, Daddy yasa ma'aikatan gidan suka shigar da kayan part ɗin Mama, aka baje su a falon ƙasa. Aunty Sadiya ta rangad'a guda, gudar da Neehal dake ɗakinta ita da Haneefah sai da suka jiyo. Wata irin fad'uwar gaba ce ta ziyarci Neehal, ta runtse idanunta ta shiga ambaton Hasbunallahu'wani'imal'wakil a cikin ranta. Haneefah dake gwagwiyar goruba ta ajiye ta miƙe tsaye cikin tsananin farin ciki ta fice daga ɗakin da saurin ta. Neehal ta ji wasu hawaye masu d'umi sun zubo a kan kuncinta, wanda ta kasa tantance na farinciki ne ko akasin haka, yau ita ce aka kawo lefen ta, hakan ya nuna mata ta kusa zama mallakin Sadik kenan? Ta kusa aure itama? Kamar amsar tambayar ta sai ga kiran shi ya shigo wayarta. Ta saka hannu ta ɗauki wayar tare da buɗe idonta, ta ƙura wa screen ɗin wayar ido da idanunta dake ganin dishi_dishi saboda hawayen dake cikin su, ganin Sadik ne yake kiran sai ta mayar ta ajiye wayar, haka kawai ta ji bata son yin wayar da shi. Set ɗin akwati ɗai ɗai ɗai har goma sha biyu Sadik ya yo, sai kuma takalma da jakunkuna a cikin manyan basket ɗin kaba da ake yi yanzu. Su Aunty A'isha fa suka shiga bubbud'ewa suna dubawa cikin farinciki, Haneefah kuma ta shiga yiwa kayan video. Kaya na gani na faɗa masu tsada da kyau aka zuba a lefen, Sadik ya yi ƙoƙari sosai, dan ya kashe kuɗi ba kaɗan ba. Mama ta rasa inda zata saka ranta dan farinciki, ashe za ta ga lefen ƴarta_ta kafin ta mutu, ta shiga addu'ar Allah ya nuna musu ranar bikin lafiya. Har bayan isha'i suna ta aikin kallon kayan, ba su kuma da alamar dainawa, su Dije ma sun fito suna kallon kayan. Sai kod'a kayan da faɗar kyawun su suke. Haneefah dai tana tsakiyar kayan zaune tana ta aikin ɗaukar hotunan su. Suna cikin duba kayan Haneefah ta dubi Mama ta ce. "Mamana yau kina cikin farinciki, dan haka bari na yi amfani da wannan damar na ƙara roƙar ki abun da nake ta nacin roƙon ki in ƙi yarda." Mama ta yi murmushi ta ce. "Haneefah da naci kike amma." Ta yi dariya ta ce. "Ni dai Mama ki amince mu ɗan warwasa, biki lami ai babu daɗi, kamar wadda za ai wa auren dole." Aunty Sadiya ta ce. "Gaskiya Ya Fateemah ki bar su, su warwasa, muma ma je a warwasa da mu." Aunty Aisha ta ce. "Gaskiya dai." Mama ta ce, "Shikenan tunda kun dage, sai a yi kamu kawai." Haneefah ta ce. "Yeee, yawwa Mamanmu, thank you so much, bari mu zo mu zaɓi atamfa mai kyau mu fitar da anko, dan event da anko ya fi kyau." Mama ta ce, "Kina fama da kanki, amma sai shegen son bidiri." Haneefah ta yi murmushi ta ce. "Mama bikin Besty ne fa, aiko jego nake na ajiye ɗan a gefe na wasu kwanaki in sha shagali na." Suka yi dariya Gaba-d'aya, Aunty Sadiya ta ce. "Allah ya shirya ki Haneefah." Suka ci-gaba da tattaunawa akan yanda bikin zai kasance, a nan Haneefah ta sanar musu Sadik ma ya ce za'a yi dinner, Aunty Sadiya ta ce, itama Dinner ya kamata a fitar mata da nata ankon. Anan suka zaɓi atamfar da za'a yi ta kamu da kuma kalar yadin da k'awayen amarya za su yi na ranar Dinner." Haneefah ta haɗa video na kayan lefen da ankunan bikin ta saka a story. Tare da yin ɗan note na Allah ya sanya Alkhairi da kuma nuna farincikin da take ciki. Har da cewa, Yau tana cikin farinciki bikin besty ya kusa, dan haka ko marin ta akai ba za ta ji haushi ba. Neehal dai tana ɗaki bata san me suke ba, Sallar isha'i ce kawai ta tashe ta, ta tashi ta yi sannan ta koma ta yi kwanciyarta. Sai da tara ta wuce sannan Haneefah ta shigo ɗakinta. Ta rungume ta cikin murna tare da faɗin. "Besty kin ga lefen ki kuwa, ya haɗu Masha Allah, Yaya Sadik ya yi ƙoƙari sosai wallahi, Allah ya sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya." Neehal ta janye jikinta daga nata tana murmushi amma bata ce komai ba. Haneefah ta latsa wayarta ta miƙa mata. Ta karɓa ta shiga kallon videon kayan. Sai ta ji wani irin daɗi ya lullub'e zuciyarta, yanzu duk wannan uban kayan nata ne? Gaskiya dole duk wacce aka kaiwa lefe ta yi farinciki. Ta d'ago ta dubi Haneefah ta ce. "Yanzu har kin musu video?" Haneefah ta ce. "Me zan jira, har na watsa su a media ma." Neehal ta ce. "Sannu uwar azarbabi." Haneefah ta ce, "Na ji ɗin, ki yi gaba akwai wanda na haɗa da atamfar ankon da muka zab'a yanzu a wayar Aunty Sadiya, ta ce next week zata yi order, duk mai so sai ya siya. Ki tura videon sai ki yiwa duka friends ɗinki sending, ki faɗa musu date ɗin bikin, 8 weeks aka saka." Neehal ta ce. "Toh." Tare da ƙara kallon videon. Ta janyo wayarta, first abun da zata yi kafin sending videon ta fara yiwa Sadik godiya. Ta shiga contact ɗinsa ta rubuta masa text mai cike da tarin godiya da kuma addu'oi, sai kuma kalaman soyayya. Sannan ta tura video's ɗin ta shiga yiwa k'awayenta sending. Nan fa mutane aka yi caaa a kanta, "Dama bikin ki za'ai Neehal babu labari? Wow kaya sun yi Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi. Ai dole mu yi anko bikin ki guda." Maganganun da ta yi ta sha kenan, ta dinga murmushi kawai. Haneefah tay ta tsokanarta bayan ta yi Sallah. Mama da kanta ta zo ta kama hannunta suka sauka ƙasa ta ga kayan, su Aunty nata tsokanarta. Ita kuma wata irin kunya take ji, bata ma san tana da kunya haka ba sai yau. Ganin yanda Mama take cikin farinciki, sai hakan ya ƙara mata nata farincikin itama. Ta dinga kallon kayan a cikin ranta tana ƙara yabawa Sadik gami da jinjina masa. Sai kusan ƙarfe goma su Aunty A'isha suka tafi gidajensu, Haneefah kuwa ta yiwa Faruq waya, ta ce masa ta yi dare a gidansu zata kwana. Da Daddy ya shigo gidan ya zauna Mama tana bubbud'e masa kayan yana gani, shi kuma yana ta tsokanar Neehal dake cin abinci. Sai dai ta yi murmushi kawai kanta a ƙasa, sosai take jin farinciki, bata jin ko baccin kirki zata iya yi yau, duk wani feeling na damuwa da take ji kusan rabi ya tafi. Ranar kusan raba dare suka yi suna tattauna yanda bikin zai kasance ita da Haneefah, bayan kowacce ta gama shan waya da masoyinta. Da yake Neehal har Zahra ƙanwar Ahmad ta tura wa lefen, data kunna data sai ta ji voice ɗin su Afrah wanda ya sata dariya ba kaɗan ba. Dan gaba-d'aya yaran sun ruɗe da murna ganin kayan, sai zaɓar abubuwan da suke so a cikin kayan suke tun kafin su zo. Washegari tun safe mak'ota suka fara shigowa ganin kayan, ranar wuni su kay cikin karɓar baƙi ƴan ganin kaya, k'awayen Neehal da k'awayen Mama gami da ƴan'uwa, cikin baƙin har da Hafsat da Hajiya da Matar Uncle Mahmud, da matar Kawu Musa. Neehal dai ta sha tsokana a gurin mutane. Ummin su Ahmad da Mamy sun kira ta a waya sun mata Allah ya sanya Alkhairi. Shima Ahmad ɗin ya kira ta, yay ta tsokanarta kuwa. Da daddare Ameen ya zo gidan, Mama ta bubbud'e masa kayan ya gani, duk da, da farko cewa ya yi ba sai ya gani ba. Amma Mama ta ce, ya dai gani ɗin yasa Albarka. Haka su kay ta shan baƙi ƴan ganin kaya, ƴan aikin gurin su Neehal dana gurin su Mama. Amaryar Uncle Umar ta zo, amma banda Aunty Fauziyya. A gurinta Neehal take jin ashe Uncle Umar ɗin ya saki Aunty Fauziyyan, a dalilin cikin shegen da Iman ta yi, ya haɗa su duka ya kore su. Neehal bata ji daɗi ba har da kukan ta. Shi kuma Uncle Umar ya gama haɗa kuɗaɗen sa zai yo sarin kaya ya zuba a shago b'arayi suka tare shi suka k'wace kuɗaɗen. Aunty Hauwa tana faɗawa Neehal har cuta ya yi saboda tashin hankali da damuwa. Ita kuma ta k'wace duk wasu takardun kadarorin Neehal, kuɗaɗen ta kuma suna account ɗinta. Ta ce ba zai ci kuɗin marainiyar Allah ba, sai dai ya fita ya nemi nashi ko dako ne ya yi. Neehal ta cewa mata ta ba shi dukiyarta ita ta bar masa duniya da lahira, Aunty Hauwa ta ce. Abun da ba zai yiyu ba kenan, dan ta gama yanke shawara ana yin bikin Neehal ɗin zata tattaro mata dukiyarta ta damk'a mata a hannunta, ta juya abunta ta nemi kuɗi. Shi kuma Uncle Umar tunda yana koyarwa zasu cigaba da jalautawa a haka. Neehal dai bata ji daɗin abun ba sam, dan sosai tausayinsu ya cika mata zuciya. Babbar Sallah saura sati ɗaya Mama ta ɗauko matar da zata yiwa Neehal gyaran jiki daga Maiduguri, sunan matar Hajja Gana, dan Mama so take a gyare mata ita sosai ciki da waje. Da ƙyar Neehal take zama a yi mata gyaran jikin, sai Mama ta mata jan ido tukunna, mai gyaran jikin tay ta dariyar dramar Mama da Neehal, wadda tunda bikin ya matso ta koma so silent, abun kaɗan sai kuka da k'unci. Mama kuwa ta tattara ta, ta watsar shirye-shiryen biki kawai take ba kama hannun yaro. Siyayya ba kaɗan ba take jibgowa Neehal ta kayan kitchen. Daddy kuwa ya ce, a je a duba gidan Sadik sannan Neehal da Mama su je duk inda take so ta zaɓi kayan ɗakinta da kanta wanda zai cika gidan. Ameen kuma Mama ta ɗaura masa nauyin siyayyar duk wani kaya da Neehal zata saka na fitar biki shi zai siya mata, tun daga kan ɗan'kunne da sarka har zuwa takalma, ta ce ba zata saka komai a cikin kayan lefen ta ba. K'awayen Neehal da ƴan'uwa suna ta kara suna ta siyen anko, ƴan NEEHAL FAN'S GROUP ma ba'a bar su a baya ba, sun ce ba'ayi ba su ba. Neehal ta kasa tantance yanayin da take ciki, bikin na ƙara kusantowa tsoron da zuciyarta take ciki na ƙara tsananta. Ta rasa tantance tsoron ko na mene ne, tana jin kamar wani abu mara daɗi na shirin faruwa, duk da kullum Aunty Sadiya cikin rarrashin ta da ƙara jaddada mata cewar haka kowacce amarya haka take jin irin wannan feeling ɗin, ta kwantar da hankalinta ba wani abu ba ne. Ita dai ta ƙara k'aimi gurin dagewa da addu'a, kamar yadda Mama take tunatar da ita a kullum. A ɓangaren Sadik kuwa zai iya cewa tunda ya zo duniya bai ɓata riskar kansa a farinciki irin na wannan lokacin ba, kullum cikin lissafin kwanakin bikin da suka rage yake, tare da ƙara dagewa gurin farantawa Neehal da nuna mata k'auna. Zuwa yanzu Ahmad ya cire rai da samun Neehal, kuɗi masu kauri ya turo mata a matsayin gudunmawarsa, dan ya rasa mai zai sai mata. Da tay masa complain ɗin kuɗin ya yi yawa sai ya yi fushi ya ce bata ɗauke shi a matsayin Uncle ɗin da take kiran shi ba kenan. Da ƙyar ta lallaɓa shi ya haqura sannan tay ta zuba masa godiya kamar ba gobe, Mama ma ta kira shi tay masa godiya. Bayan Babbar Sallah da sati ɗaya an gama soyasoyen nama da shan bukukuwan Sallah wanda ya kama bikin Neehal saura sati ɗaya. Ranar Alhamis da daddare Neehal tana ɗakinta tsaye a gaban mudubi, fitowarta kenan daga wanka bayan da aka gama mulke mata jikinta da haɗin gyaran jiki da ake mata. Tana shafa mai amma kallon fatar jikinta kawai take yi, yanda ta canza ta yi wari irin laushi hami da haske, har wani pink_pink jikinta yake yi saboda an mata halawa. Ita kanta bata gajiya ta taɓa jikinta, dan ji take kamar ba jikinta ba tsabar sulb'i da kyau, dan tana shan gyara bana wasa ba. Ga wani irin fitinannen k'amshi dake tashi a jikinta, duk inda ta gilma kuwa sai an ji shi. Dan ma bata fita yanzu kwata_kwata, tun satin da za'a fara mata gyaran jiki ta ɗauki hutu a gurin aiki. Jiya da Sadik ya zo kawo mata invitations card kamar zai cinye ta saboda santi da kyawun da tai masa. A hankali ta ji an buɗe ƙofar ɗakin tare da yin Sallama, ta juyo ta kalli ƙofar da sauri. Ganin Ameen ne ta yi saurin tashi ta ɗauki hijabin dake gefen gado ta zira a jikinta cikin rawar jiki. Shi ko bai ko kalli inda take ba, ya ajiye ledodin hannunsa a kusa da ƙofa. Ya juya yana ƙoƙarin fita ta ce. "Yaya!" Ya tsaya ba tare da ya juyo ba. Ta ƙarasa ta tsaya a kusa da shi. A hankali ta ce. "Thank you so much, Allah ya ƙara buɗi." Ya juyo ya zuba mata ido, itama idanun ta zuba masa ganin yanda yake kamar wani mara lafiya. Lokaci ɗaya idanunta suka kawo ruwa, cikin damuwa ta ce. "Yaya baka da lafiya ne? ko kuma wani abun ne yana damun ka?" Ya yi mata ɗan murmushi tare da girgiza mata kai. Ta fara hawaye ta ce. "Yaya i know baka da lafiya, ko kuma wani abun yana damun ka, Yaya You look so worry." Ya tako a hankali ya matso daf da ita, a hankali ya kama fuskarta da hannuwansa duka ya saka idanunsa cikin nata ya ce. "Nothing Miemerh, Just pray for yourself and me." Ta gyaɗa masa kai a hankali cikin rashin fahimta. Ya saki fuskarta sannan ya kuma yi mata murmushi ya juya ya fita. Ta bi shi da kallo tana maimaita abun da ya faɗa a cikin zuciyarta, a ƙoƙarin ta na ganin ko zata gane mai yake nufi amma bata gane ba. Addu'a abu ne mai kyau akan kowanne mutum, may be shi yasa ya ce tay musu addu'a ita da shi. Ta sauke numfashi ta ƙarasa inda ledodin da ya ajiye suke ta tsugunna ta shiga fito da kayan ciki tana dubawa. Kayan da zata yi fitar biki ne da su, kuma gaba-d'aya kalolin da ta ce masa tana so ya siyo. Babu abun da zata saka wanda bai sako ba, har da su undies da pant da bra. Ta yi murmushi ita kaɗai cikin jin kunya. Wedding gowns ɗin da zata saka ranar kamu, Dinner da ranar D'aurin Aure da safe. sun fi komai burge ta da yi mata kyau a cikin kayan, gashi daga ganin su masu tsada ne. Ta cire hijabin jikinta cikin murna ta fara gwada kayan. Ameen kuwa ɗakin Mama ya shiga bayan ya fita, ya tarar da ita da Aunty Sadiya suna haɗa kayan da suka siyo d'azu a kasuwa. Tunda bikin ya gabato ba'a kwana biyu ba su je kasuwa ba. Bayan ya yi sallama ya zauna a kujerar dake gefen gado. Suka bi shi da kallo, Ba tare da Mama ta amsa gaisuwar da yay mata ba ta ce. "Al'ameen! Meke damun ka ne?" Ya lumshe idonsa bai ce komai ba. Mama ta shiga yi masa masifa akan wannan shegen muskilancin nasa da zurfin ciki, idan wani abu ke damun shi ai sai ya sanar mata, ko baza ta magance masa ba sai tay masa addu'a, amma ya gwammace ya bar abu a ransa yay ta damun sa, ita mahaifiyarsa ce baza ta so ta dinga ganin shi cikin damuwa ba, idan ma wata matsalar ce tsakanin sa da matarsa ai ya kamata ya sanar mata a san abun yi. Tunda ba shi da kamar ta a duk duniyar nan. Faɗa sosai Mama tay masa, Aunty Sadiya na bata haquri amma bata yi shiru ba sai da ta kai aya. Ganin yanda ran Mama ya ɓaci ya dinga bata haquri, ya sanar mata yanayin aiki ne kawai. A k'ufule Mama ta ce. "Aiki, aiki. Daga an yi magana ka ce aiki, kamar kai kaɗai ke aikin duk duniyar nan, a gurin aikin yankar naman jikinka ake ai. Amma ka cigaba idan ganin ka cikin damuwa ya haifar mun da wata damuwar nima ai ka ji daɗi." Bata jira amsar shi ba ta tashi ta fice daga ɗakin, Ya bita da ido. Aunty Sadiya ta dawo kusa da shi ta zauna cikin rarrashi ta ce. "Ameen! Rayuwar nan cike take da k'alubale da kaddda kala_kala, kowa ka gan shi ka kalle shi kawai, amma shi kaɗai ya san abun da ke damun sa, kuma bawa ba ya taɓa kaucewa ƙaddarar sa, ka saka wannan a ranka, sannan kuma ka rage damuwa, Please Ameen." Ya sauke numfashi ya ce. "Insha Allah Aunty Sadiya I will try." Aunty Sadiya ta tsaya kawai tana kallon sa kamar yadda shi ma yake kallon ta, kallo mai kama da na tausayi tare da jiman ta wani al'amari." Ta ɗauke idonta daga kallon sa cikin raunin murya ta ce. "Ka je ka bawa mahaifiyarka haquri, ka ga ranta ya ɓaci sosai." Ya ja numfashi mai huci ya sauke sannan ya miƙe bai ce komai ba ya fice, Aunty Sadiya ta girgiza kanta cikin damuwa, alamun something is hurting her heart. Bayan ya tafi Aunty Sadiya suna falo zaune ta cewa Mama. "Ki yi haquri Yaya Fateemah akan al'amarin Ameen, na ga kamar har yanzu ranki a ɓace yake." Mama ta girgiza kai cikin sanyin jiki ta ce. "Ko ɗaya Sadiya babu d'igon ɓacin ran Ameen a raina, dan ya wanke mun shi tass kafin ya tafi. Amma Sadiya ni na haifi Ameen, na san halinsa ciki da waje, tabbas ko tantama bana yi akwai abun da ke damar mun yaro." Aunty Sadiya ta ce. "Tunda ya ce miki babu, a matsayin ki na mahaifiyarsa wadda babu hijabi a tsakanin addu'arki a gare sa, ki yi masa addu'a, Insha Allahu in ma da akwai abun da ke damun sa to Allah zai yaye masa." Mama ta ce, "Haka ne, Allah yasa mu dace. Mu je kiga kayan fitar bikin da ya kawo wa Neehal kafin ki wuce, ya ce mun ya kawo mata." Aunty Sadiya ta ce. "Masha Allah, Allah ya saka masa da Alkhairi. Mama ta ce, "Amin." Tare da miƙewa. Washegari Neehal suka fita da Freind's ɗinta guda biyu na B.u.k rabon I.v, ba'a son ranta ta fita ba Mama ce ta tilasta mata. Da cewa ta yi zata turawa kowa ta waya, gate pass ɗin dinner kuma zata wakilta wasu su bayar a ranar. Mama ta ce, bata isa ba yara su yi mata anko sannan ta ƙi kai musu kati har gida. Sai yamma liss suka dawo, tana cin abinci kuma aka ɗora mata daga inda aka tsaya a gyaran jiki. Washegari ma ta fita, ta je gurin aikin su ta kai musu katin, sai kuma sauran Freind's ɗinta da ba su ƙarasa jiya ba. Ranar talata mai ƙunshi ta zo har gida tay musu ita da Mama da su Aunty Sadiya da Haneefah. Saboda Washegari ran Laraba za'a fara bikin, a yi Kamu Laraba, Alhamis a yi Dinner, Juma'a a daura aure akai ta gidan mijinta. Tun yau da taga an yi mata lalle ta ga tabbas da gaske dai auren zatai zata bar gaban Mama ta fara kuka sosai. Mama ta tsaya kawai tana kallon ikon Allah, ta rasa hali irin na Neehal, ta ga dai yara ma ƴanv17_18 years ana musu aure amma basa damuwa haka, sai ita mai 24_25 years. Aunty A'isha ce mai aikin rarrashinta. Tun yau gidan ya fara wadatuwa da baƙi, ciki har da Uncle Usman da matarsa da yaransa guda biyu. Neehal ta rungume shi cikin tsananin farincikin ganin sa. Ta ce "Uncle ɗina na yi kewar ka sosai." Ya yi murmushi ya ce, "Nima haka Daughter, rabo na dake tun kina ƙarama, gashi har kin girma kin zama ƙatuwa." Ta yi dariya cikin jin kunya. Aunty Hauwa ma amaryar Uncle Umar tun yau ta zo, su Hajiya ma da wasu ƴan Gombe haka. Ƴaƴan Ummi (Yayar Abba) Maza guda biyu su ma sun zo tare da matansu daga Lagos. Can yamma kuma sai ga Zahra da twins. Farincikin ganin yan'uwa da mutane anata zuwa ya ɗaukewa Neehal hankalin damuwar da take ciki. Ga Ameerah ƴar gidan Uncle Mahmud da Haneefah da Zahra, duk inda ta yi suna biye da ita, dama amarya akwai farinjini. Ranar Kamu da safe sai ga Hameedah da Mommy'nta sun zo, abun ya bawa Mama mamaki amma bata nuna ba, ta karɓe su hannu bibbiyu. Saboda yanda suke nuna tsana ga Neehal bata yi zaton za su zo tun yau ba, ta ɗauka sai ranar D'aurin Aure za su zo. Kafin ka ce me gida ya ƙara cika da baƙi, ƴan'uwan su Mama da ƴan'uwan Daddy. Ba ya ma na Mama, dan Familyn su Mama suna da yawa Masha Allah. Ga shi dama Mama ita ta kowa ce, ko bata je inda kake akai_akai ba, akwai kira a waya ta sadar da zumunci. Hafsah ma ranar tun safe ta zo. Mama zuciyarta fari k'al da farinciki, yau Allah ya nuna mata zata fara taron bikin Neehal, duk da ba'a daura aure ba, amma yanzu zuciyarta babu fargabar komai kamar a baya da suke cike da tsoron kar a kuma kwata kashe wanda Neehal zata aura. Duk da sun fi alaƙanta hakan da shawarar da Uncle Mahmud ya bayar ta ɓoye batun auren sai da ya zo daf sannan aka bayyana. Gidansu Sadik ma ya fara harama da baƙi ƴan biki, suna ta nasu shirye-shiryen su ma. Amma fa har yanzu Hajiyarsu da Kawu ba san bikin suke ba, babu yanda za su yi ne kawai dan suna matuƙar jin kunyar Mahaifin Maamah, baza su iya yin jayayya da shi ba. Umma kuwa ta yi makircinta da kisisina akan ganin an fasa Auren amma bata yi nasara ba. Tun a jiya da safe bayan an gama yiwa su Aunty ƙunshi suka tafi gidan Neehal dake unguwar Tarauni yi mata jere, yau da sassafe kuma suka koma dan ƙarasawa. Masha Allah Gidan ya yi kyau, falo biyu ne da three bedrooms. Sai kitchen da store. Sai kuma ɗakin mai gadi kana shigowa gate daga gefe. Su Mama da Daddy kuma sun cika mata gidan da kaya na gani na faɗa. Ƙarfe biyu na rana Aunty Sadiya ta saka Neehal ta yi wanka. Ta fito ta zira doguwar riga ta saka hijabi suka ɗauki kayan da zata saka suka tafi gurin kwalliyar da already an yi bucking. Aunty Sadiya ta ce, ta kira Sadik ana yin Sallar la'asar saboda ba su san African time, ƙarfe huɗu aka saka a jikin kati amma kamar biyar haka su taho. Neehal ta amsa mata sannan ta je ta yiwa Mama Sallama suka tafi ita da Haneefah. Gurin kwalliyar ya haɗu sosai, shago ne a cikin wata ƙatuwar plaza dake nan cikin Nasarawa. Suna zuwa babu ɓata lokaci aka fara yi musu kwalliyar, dan ba mutum ɗaya ce ke yi make up ɗin ba. An riga gamawa Haneefah saboda ita casual make up akay mata. Neehal kuma bridal ake mata. Masha Allah Haneefah ta yi kyau sosai, sai ma data saka kayanta akai mata dauri. Sai biyar aka gama shirya Neehal, faɗar irin kyawun da ta yi ɓata baki ne. Ta yi kyau ƙarshen kyau. Ita kanta ta kasa ɗauke idonta daga kan mirror, sai tambayar kanta take anya kuwa ita ce, ba wata aka canza ba. Aka yiyyi mata pictures da video's, sai 5:30 Sadik ya zo ɗaukar su shi da wani abokin sa. Ya yi kyau abunsa cikin dakakkiyar shadda sai maik'o take, kalar adon jikin kayan Neehal da head ɗinta. Zuwa lokacin Aunty Sadiya har ta fara kiran su akan su yi sauri su taho, saboda gurin biki fa ya ɗauki harama an fara shagali, amarya da ango kawai ake jira. Mai kwalliyar tasa dole sai da Sadik ya shiga cikin gurin, tana son tay musu pictures tare da Neehal and kuma tana son ta caze shi kuɗi. Yanda Sadik ya ruɗe da ya ga Neehal ba zai misaltu ba. "Wifey ke ce kuwa? Kai Masha Allah na yi dace da kyakkyawar mace." Su Haneefah da masu kwalliyar su kay tay masa dariya. Ya zaro kuɗi masu yawa a aljihun sa ya bawa mai kwalliyar, duk da already su Neehal sun biya ta, amma ya ƙara mata. Wai ta iya kwalliya babu ƙarya, bayan auran su zaina kawo Neehal ta dinga yi mata. Ita dai Neehal murmushi kawai take, a ranta tana jin abun kamar a mafarki. Wai yau ita ce a matsayin amarya, yanda take zuwa bikin wasu itama an zo nata. Sai 6 suka bar a wajen. Haneefah da abokin Sadik sune a gaban Motar, ita kuma da shi suna baya, ya addaba mata da kallo kamar zai cinye ta. Haneefah kuma na yi musu video da pictures daga inda take a wayarta. Suna isa gurin bikin ta ji gabanta ya faɗi, ta lumshe ido tana ambaton sunan Allah, tare da ƙoƙarin ganin ba ta yi kuka ba. Tana jin Sadik yana mata magana, da kai kawai take iya amsa masa. Sun yi 15 minutes a Motar kafin a gama arranged k'awayen Amarya da abokan ango da za su shiga tare da Amarya da Ango. Daga cikin ball ɗin kuma MC nata b'ab'atun sanarwar isowar ango da amarya. Aka buɗe mata Motor ta fito, tun daga lokacin Camera ta ce mata salama alaikum, aka fara ɗaukar ta a hoto. Kowa na yaba kyawun da ta yi. Ta ƙarasa ta tsaya a inda aka ce mata, Sadik na gefen ta yana ta zuba murmushi. K'awayen amarya ne a gaba, suka fara tafiya cikin tsari suna ɗan yin rawa ta cool music ɗin da aka saka, wadda ta dace da shigowar amarya da ango. Su Neehal suka mara musu baya cikin taku ɗai_ɗai, abokan Ango na take musu baya. Abun dai gwanin burgewa mutane duk an tattashi ana musu video. Ango da amarya suka ƙarasa gurin zaman su, mutane da masu hoto suka baibaye su, kowa na san ya ɗauke su. Sai a lokacin Neehal ta ga twins ɗinta Zahra ta kawo mata su, wanda suke ta kuka tun yamma su sai an kai su inda take. Sun yi kyau sosai cikin shigar da akai musu, hannayensu da ƙafafuwansu sun sha lalle. Afrah ta zauna a gefen Neehal, Amrah kuma a gefen Sadik. Haka aka cigaba da gudanar da shagali a gurin, amarya da ango suka shigo tsakiyar fili aka dinga zuba musu lik'i kamar kuɗin ba su da wahalar samu. Su Haneefah da sauran k'awayen Neehal sun jajige sun ci rawa abin su, amarya dai ƙin takawa ta yi. Shigowa ta musamman aka yiwa Mama wadda ta yi kyau abun ta sosai, kana ganin ta ka ga uwar amarya. Duk yadda Neehal ta so daurewa sai da ta yi hawaye a lokacin, ana saka wak'ar wayyo Allah Mamana ta Ali jita ta ji zuciyarta ta karye, ta tuno Ummanta da Abbanta da basa raye, Allah ya yi baza su ga Auren ta ba. Hawaye take yi sosai, da ƙyar Aunty Sadiya ta lallaɓa ta, ta bar kukan. Mama ta yi musu lik'i sosai ita da Sadik su ma su kai mata, k'awayen Mama sun mata kara sun musu lik'i ita da Neehal. Sai a lokacin Neehal ta ga Ameen ya zo ya yiwa Mama lik'i, haka kawai ta ji daɗi a ranta dan bata yi tunanin zai zo ba, saboda sanin halin sa. Suka haɗa ido yay mata murmushi ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa, ya matso kusa da ita ya shiga yi mata lik'in rafar ƴan dubu_dubu. Itama ta zari wasu a hannunsa ta dinga lik'a masa suna kallon juna cikin wani irin yanayi. Ahmad ma ya zo, ta yi mamakin zuwansa dan bai faɗa mata zai zo ba. Haka dai akay ta gudanar da shagali a gurin, a gefe guda kuma masu rabon abinci da drinks suna ta yi. Can na hango ƴan NEEHAL FAN'S GROUP an ci anko an kame akan kujera, su Meerah, Rachel, Ummu Hanif, Hany, Zainab AA, Zainab Aliyu kkm, Miemie Afreen, Aunty ruky, Maman Zahrah, Hauwa'u Sani, Fulani, Hafsat Garba da sauran team ɗin Ameen suna ta kai laumar shinkafa baki suna korawa da drinks. (🤣😅😂)Sai hararar Sadik suke tare da gulmar sa wai ko kyau bai yi ba, bai ma dace da Neehal ba. Gefe guda kuma su Ummul Amina ne ana ta yagar naman kaza. (🤣🤣🤣🤣😂😂😂) Ita da sauran team ɗin Ahmad irin su, Aysha Rawayau, mrs Suraj, mrs Jay, Ruk'ayya, Momyn ruky, A'ishat Abubakar, Aysha Khalil da sauran su dai. Su kuma Ameen suke zabgawa harara dan shi ya tsole musu ido. (🤣😂) Ummul Amina har da gulmar sa wai dan baƙin hali a gurin bikin ma ba zai yi fara'a ba sai haɗe rai yake. Sai da tara ta wuce aka tashi daga taron, bikin yau ya yi daɗi Alhamdulillah an yi lafiya an tashi lafiya saura kuma na gobe. Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare, bayan Neehal ta yi wanka ta saka kayan bacci, tana ƙoƙarin kwanciya duk da ƴan'matan dake ɗakin suna ta hira ba su da niyyar kwanciyar su, ita kuwa ta gaji bacci kawai take buƙatar yi a yanzu. Mama ta aiko Aunty Sadiya ta kira ta. Ta zira hijabi ta fito ta nufi part ɗin Daddy inda Maman take. Ta same ta zaune a falo da kayan fruits a gaban ta. Ta zauna a kusa da ita tare da kwantar da kanta akan ƙafaɗarta. Mama ta ce. "Bacci kika fara ne?" Ta girgiza kai. Mama ta ce. "To sauka ki sha fruits ɗin nan, na san yau ba ki ci wani abincin kirki ba." A hankali ta ce. "Bana jin yunwa." Mama ta ce. "Ai ba cewa na yi kina jin yunwa ba, cewa na yi ki sauka ki ci." Ta zare jikinta daga na Mama a hankali ta sauka ta janyo plate ɗin da suke ciki a yayyanke ta ɗauki yankan Apple ta fara ci, ta yamutsa fuska lokacin da take taunawa. Mama ta ce, "Ya dai?" Bata ce komai ba sai hawaye. Mama ta girgiza kai ta ce. "Oh Allah, Neehal meke damun ki ne? Dan zaki yi aure sai ki koma kamar wadda aka cewa zaki mutu, haba Neehal karki ki kaini bango fa da wannan banzan kukan naki, sai kace a kanki aka fara Aure, duk wanda ake yiwa Auran haka kika ga suna yi?" Neehal ta fashe da kuka ta ce. "To ni Mama id'ont want to leave you." Mama ta yi murmushi kamar ba ita ta gama faɗa yanzu ba, ta sakko ta zauna a kusa da ita, tare da janyo ta jikinta. Tana ɗan bubbuga bayanta kaɗan ta ce. "Haba ƴar Mamanta, ai kina tare da Mama babu wanda zai raba ki da Ita, dan kin yi aure Neehal ai hakan ba yana nufin kin daina gani na ba ne. Nima dauriya kawai nake, dan ban ma san irin kewar ki da zan yi ba in kin tafi. Amma kuma ina cikin tsananin farincikin nuna mun lokacin Aurenki da Allah ya yi. Neehal burin kowace uwa idan tana da ƴa wadd ta girma ta isa aure to ta aurar da ita, ki yi haquri kin ji, kowa da haka yake sabawa, ai Aure ya zama dole." Neehal ta gyaɗa mata kai tana ƙara matso hawaye. Mama ta d'ago kanta ta yago tissue ta share mata hawayen. Cikin tsokana ta ce. "Ki rage wannan kukan naki, ko haka zaki haifa mun jikoki suna kuka ke kina yi?" Ta mayar da kanta jikin Mama tana murmushin jin kunya tare da turo baki. Mama ta ƙara d'ago ta, ta ce. "Taso in baki a baki, kin ji ƴar autar Mama." Ta tashi zaune, Mama ta fara bata fruit ɗin a baki. Sai da ta sha sosai sannan Mama ta ƙyale ta, ta koma part ɗinsu ta kwanta. Mama ta shiga ɗakin Daddy ta tarar da shi yana kaiwa da komowa cikin damuwa. Mama ta dafe kai ta ce. "Yanzu na gama da ƴarka kai ma gaka, sau nawa zan faɗa maka Gen. Ka kwantar da hankalinka, babu abun da zai faru Insha Allahu sai Alkhairi, za'a yi bikin nan lafiya a gama lafiya." Daddy ya zauna a bakin gado cikin damuwa ya ce. "Wallahi Doctor bana son a kuma samun wata matsalar at this time, na rasa me yasa hankalina ya ƙi kwanciya, bana son a ƙara cutar da marainiyar Allah." Mama ta ƙarasa kusa da shi ta ce. "Ka saka abun a ranka ne shi yasa, ni duk damuwata tunda na ga bikin ya matso na kwantar da hankalina, addu'a kawai nake kuma na san Ubangiji yana sane da mu, duk wani mai ƙoƙarin cutar da mu Allah ya mayar masa da cutar kansa." Daddy zai kuma magana Mama ta hana shi, ta hanyar kama hannunsa tana faɗin. "Mu je ka yi wanka, ji bi yanda duk ka haɗa zufa." Ya miƙe ya bi bayan ta zuwa toilet ɗin, amma shi kaɗai ya san abun da yake ji a ransa na damuwa. Washegari aka yi Dinner bayan Magriba, a wani had'ad'd'en hall. Yau Neehal har tafi jiya kyau, gurin bikin ma ya fi na jiya tsaruwa sai dai bai kai shi girma ba, da yake ba kowa aka gayyata ba, bai fi rabin mutanen jiya ne suka je ba. Shima an warwarsa an ci an sha, Haneefah dai yau bata more da rawa ba kamar jiya, saboda zuwan Faruq gurin. Ya zaunar da ita ya ce baza ta ce ta jawo masa asarar ɗa/ƴa a banza ba. Ta zauna ta dinga ɓata fuska shi kuma yana mata dariya. Yauma kamar jiya Sadik ne ya kawo ta gida da aka tashi daga gurin bikin, time ɗin 11 na dare ta wuce. Suna zaune a bayan Mota abokinsa da ya yi driving ɗinsu yana gaba. Sadik ya ƙura mata ido tare da kama hannunta. Ta yi ƙoƙarin k'wace wa amma ya ƙi sakar mata. Ta turo masa baki gaba. Ya yi murmushi murya ƙasa ƙasa ya ce. "Wifey gobe by this time muna tare a gidana an kawo mun ke." Ta d'ago ta kalle shi tana murmushi, sun jima suna kallon juna ido cikin ido, kallo mai cike da k'aunar junan su. A hankali ta fara janye nata idanun tare da lumshe su. Sadik ya lumshe nasa shi ma tare da sakar mata hannu. Cikin matuƙar sanyin murya ya ce. "Mu je in raka ki, kar Mama ta ga kin daɗe, duk da dai na san baza ta damu ba, tunda ta san kina tare da mijin ki." Tay masa wani kallo ta ce, "Ka bari a ɗaura dai." Ya yi ƴar dariya sannan ya ce. "Yau da gobe duk ɗaya ne a gurin Allah." Bata ce komai ba, ya buɗe Motar ya fita sannan ya zagaya ya buɗe mata ta fito itama. Sai da ya raka ta har bakin part ɗin Mama sannan ya juya, yana jin kamar kar su rabu. Dare ya tsala amma Neehal ta kasa bacci, duk hirar ƴan ɗakin sun gaji sun yi bacci. Ita kuwa sai juyi take akan gado, sosai gabanta ke faɗuwa duk bayan sakanni, ta rasa na mamaki ne ko na tsaron Ɗaura mata auren da za'a yi gobe. Sai tambayar kanta take wai da gaske ita za'a d'aurawa aure gobe, abun kamar almara haka take jin sa. Jin wayarta na vibrate ta tashi zaune da sauri ta ɗauka dan ganin wake kiran ta cikin tsakiyar daren nan. Ganin Sadik ne ta cika da mamaki, ta yi pick sannan ta ƙara a kunnenta amma bata yi magana ba. Cikin raunin murya ta ji ya ce. "Neehal baki bacci ba?" A hankali ta ce. "Uhm." Ya ce, "Why? Ko d'okin za'a kawo ki gidana gobe ne?" Cikin shagwab'a ta ce. "Ni ba haka ba ne, kawai na fara missing Mama ne." Ya ce. "Ki daina damuwa Wifey, idan Mama ce koyaushe kike so ki gan ta zan kaiki ki gan ta, I promised." Ta yi shiru tana sauke numfashi. Ya ce, "Nima zumud'i da farinciki sun hana ni bacci, idona murtsitsi babu alamar d'igon bacci, amma yanzu zan je in yi alawala in yi sallah in roƙa mana Allah ya wanzar mana da zaman lafiya a zaman auren mu, ke ma idan kin ji baccin ya ƙi zuwa ki je ki yi, mu raya daren kin ji Wifey." Ta ce. "Toh Husby." Suka yi sallama ta katse wayar, duba time ta yi ta ga uku na dare saura. Ta kunna light ɗin wayarta sannan ta sakko daga kan gadon, dan ta san ko ta cigaba da kwanciya baccin ba zuwa zai yi ba, gwara ta bi shawarar Sadik ɗin.....✍️ _*6k plus words, ten read more. Gaskiya na yi typed yau, sai dai ban yi edit ba, ku yi haquri da typing errors.*_ *By* *Zeey Kumurya* [10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *5️⃣9️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........Haka rayuwa tay ta tafiya, bikin Neehal na ƙara kusantowa. Ɓangarorin biyu na amarya dana ango suna ta shirye-shiryen bikin, duk da dangin Angon ba kowa ke son auren ba. Sai dai kamar yadda Uncle Mahmud ya roƙi alfarma tun ranar da aka kawo kuɗin Auren, akan a ɓoye batun auren sai abun ya matso daf sannan a bayyana saboda tsaro, a cewar sa idan ma wani ne yake kashe samarin da Neehal zata aura kamar yadda ake hasashe, to lokacin da zancen bikin zai fito kafin ya gama duk wani shirinsa an yi bikin an gama Insha Allah. Hakan ce ta kasance kuwa domin ba kowa ya san da maganar bikin ba, sai na jiki_jiki wanda ya zama dole. Ita Mama kam ta ce babu wani shagali da za'ai da bikin, ɗaurin Aure kawai za'ayi akai amarya gidan ta. Sai dai fa shi Ango Sadik da bai san da shirin Mama ba yana ta shirye-shiryen haɗa gagarumar dinner shi da abokanansa. Haneefah ma ta ce baza su yi biki lami ba, sai sun cashe ko da na rana ɗaya ne, tana nan tana ta yiwa Mama naci da magiya akan ta amince. Ita kam Neehal tsarin Maman ya mata dai-dai, dan ita ba gwanar son harkar taro ba ce dama. A wannan azumin na bana Neehal suka ziyarci ƙasa mai tsarki ita da Mama, Mama ta cika alƙawarin data ɗaukar mata tun last year. Sun je sun yi Umrah, satin su biyu a can suka dawo. Bayan Sallah da sati ɗaya suka fara final exam ɗinsu. Neehal ta maida hankalinta sosai akan karatu, ta watsar da duk wani feeling da take ji a cikin ranta ta duk'ufa ga karatu, domin tana son yanda ta fara karatun ta successfully ta gama successfully. A gefe guda kuma zuciyarta cike take da murnar kammala karatunta da zata yi this year. Yau Friday wadda ta kama sati uku da fara exam ɗinsu, kuma yau ne za su yi final exam. Exam ɗin safe gare su, hakan yasa tun asuba ta fara shirinta. Ta shirya cikin Black Tomy skirt ɗin da suka yi anko na ƴan class ɗinsu da farar t_shirt wadda aka yi rubutu a gaban rigar, aka rubuta sunan department ɗinsu da year da suka gama school. Ta zauna ta tsara ɗaurin ɗan_kwali a kanta da wani plan yadi Black. Ta saka ɗan kunne mai rawl white colour. Ta ɗaura tsadadden agogon hannu mai kyau Black a left hand ɗinta, sannan right kuma ta saka white abun hannu da k'aton zobe mai stone a ɗanyatsanta na tsakiya. Ta kalli kanta a mirror tare da yin murmushi, kallo ɗaya zakai mata kasan tana cikin farinciki a yau. Ta tashi ta ɗauko sabon Black shoe ta zira kyakyawan ƙafuwanta dake sanye cikin socks a ciki. Bayan ta feshe jikinta da sanyayan turarukanta masu daɗin k'amshi ta ɗauko madaidaicin mayafi white colour ta yafa a jikinta, sannan ta ɗauki ƙaramar handbag mai ɗauke da exam card ɗinta da pen da kuɗi da phone's ɗinta a ciki.Ta riƙe jakar a hannun damanta, hannun hagunta kuma leda ta riƙe mai ɗauke da rigar graduation ɗinta a ciki. Ta fito ta nufi part ɗin Daddy domin Mama tana can. A falo ta tarar da su a zaune akan carpet Daddy yana breakfast. Ta ajiye kayan hannunta ta tafi da gudu ta rungume Mama tana murmushi. Mama tana murmushin itama ta shafi gefen fuskarta ta ce. "Congratulation my Daughter, Allah ya albarkaci karatunki da rayuwarki baki ɗaya." Tana murmushi ta ce "Amin, Thank you so Much Mum." Sannan ta tashi ta koma kusa da Daddy ta zauna ta ce. "Good Morning Dad." Yana murmushi cike da kulawa ya ce. "Morning Daughter, how was your preparation of been a graduate?" Ta ce "Alhamdulillah." Daddy ya ce, "To Masha Allah Daughter, Allah ya bayar da sakamako mai kyau, ya nuna mun ranar da zaki zama professor." Ta ce "Amin My Dad, than you so much." Ya ce "You are welcome Dear." Mama ta dube ta, ta ce, "Dafatan kin yi breakfast, ba saurin tafiya school ba." Ta girgiza kai ta ce. I'm full." Daddy ya ce, "A'a Daughter, ba'a yi celebration ciki babu abinci ba, zauna mu ci a nan taree." Ta ce "Toh Daddy na." Ta haɗa tea ta sha tare da bread. Ƙarfe bakwai da mintuna tay wa su Mama sallama ta tafi, su kuma suka bi ta da addu'a tare da fatan samun nasara. Bayan ta ƙarasa school ta tarar da classmates ɗinta cikin irin shigar jikinta, mata da skirt maza da wando. Cikin farinciki Freind's ɗinta suka tarb'e ta, kowacce tana yaba kyawun da ƴar'uwarta ta yi. Ƙarfe takwas da mintuna suka shiga ɗakin jarrabawa, Alhamdulillah exam ɗin ta yi mata sauƙi dan jiya kusan raba dare ta yi tana karatu. After 1 hour waɗan da suka gama suka fara submit na exam sheet, itama submitted ta je ta yi dan already ta gama. Tana fitowa suka rungume juna ita da wasu classmates ɗinta da suka riga ta fita, suna taya juna murna. Ta ɗauko wayarta ta shiga WhatsApp ta yi story da *Alhamdulillah.* Dai-dai nan sak'on text message ya shigo wayarta daga Ameen. Ta buɗe da sauri ta karanta. Murnar graduation yay mata tare da tarin addu'oin nasara a rayuwarta. Ta yi murmushi cikin jin daɗi, a ranta ta ce. "One like no other, My Yaya." Tay masa reply da thank you. Daga nan suka shiga ɗaukar pictures ita da classmates ɗinta, har time ɗin gama exam ɗin ya yi, kowa ya fito daga exam hall, suka sassaka rigunan su na graduation mai ɗauke da sunayen kowa a jikin tasa. Rigar white and black colour ce, sai ta dace da dress ɗin jikinsu. Sun sha hotuna yau kamar ba gobe, Haneefah ta zo mata har yamma suna tare a school, whites t_shirt ɗin jikinsu gaba-ɗaya ta ɓaci da sign out, dan ma ita Neehal bata bari an mata ba sosai ba, k'awayenta mata ne kawai su kay mata. Sai kusan Magriba ta koma gida, ta tarar Mama ta haɗa delicious for Dinner na taya ta murnar graduation. Sai bayan ne Magriba ta kunna datar wayarta dan tun safe da tay posted pics ɗinta bata kuma kunnawa ba, ta tarar da tarin messages daga mutane ana mata congratulations, ciki har da Sadik da Ahmad, sai kuma waɗanda suka ɗora ta a status da pics ɗin da ta yi posted. Ta yiyyi screenshot ta ɗora a story tare da godiya. Sosai take cikin farinciki yau, today is another unforgettable Day in her life. Bayan ta yi wanka ta canza kaya tana zaune a falon ƙasa kan dinning table tana cin delicious ɗin da Mama ta haɗa mata Ameen ya shigo falon. Kasancewar tana dinning area hakan yasa bata ga shigowar shi ba. Ya zauna suka gaisa da Mama. Sai da ta miƙe domin ɗauko juice dake ɗan nesa da ita akan dinning ɗin, sannan ta hango shi. Ta ɗauko juice ta tsiyaya ta sha idanunta na kansa, sannan ta ajiye cup ɗin ta nufo inda suke. A kusa da shi ta zauna duk zuciyarta cike take da tsoron kar ya share ta, amma sai ta ga saɓanin abun da ta yi tsammani. Ya juyo yana kallon ta fuskarsa ɗauke da murmushin da ta manta rabon da yay mata, kafin ta yi magana ya riga ta da faɗin. "Congratulation." Ta yi murmushi cikin daɗi ta ce. "Thank you Yaya." Ya gyaɗa mata kai sannan ya ɗauke kansa daga gare ta. Ta gaishe shi ya amsa mata cikin kulawa, sannan ta tashi ta ɗauki wayarta ta tafi upstairs dan amsa kiran da Sadik yake ta zuba mata. Tana shiga ɗakinta wani kiran nasa yana ƙara shigowa. Ta d'aga tare yin sallama. Ya amsa mata tare da faɗin. "Graduate." Ta yi fari da ido tana murmushi ta ce. "Yes Barrister." Ya yi murmushi ya ce. "Congratulation once again Dear." Ta ce "Thank you, Husband to be." Ya ce, "Wow kina fasa mun kai fa, idan kika ce Husband to be ɗin nan." Ta yi ƴar dariyar dake bayyanar da farincikinta ta ce. "To na daina faɗa maka." Ya kwaikwayi muryarta ya ce, "Ai bakinki ne ya iyar faɗar Husband, ina son ki kira ni da sunan." Ta murmusa ta ce, "To Husby, Ya Maamah da Abba?" Ya ce "Suna nan k'alau, suna taya surukar su murnar been a graduate." Ta ce "To ina godiya sosai." Ya ce "Diarlin ya kamata mu haɗa wani ɗan special party fa, na taya ki murna." Ta ce, "Hmm Daddy ya so haɗa mun amma Mama ta hana, ta ce ita bata son wannan bidi'a_bidi'an, ka san halin Mama sai ita. Sadik ya yi dariya ya ce. "Mama tamu, Allah ya bar mana ita." Ta ce. "Amin." Suka ci-gaba da hirar su, suna cikin wayar kira ya shigo wayarta, ta duba ta ga Ahmad ne yake kiran ta. Ta cewa Sadik zata ɗan d'aga waya mintuna kaɗan, ya ce babu damuwa. Ta d'aga kiran cikin sauri ganin yana ƙoƙarin katsewa. Ahmad ya ce "Princess!" Ta ce "Na'am my uncle." Ya ce "Kina waya da my in-law shine kika katse kika daga kira na?" Ta yi murmushi ta ce. "To ai kai Uncle ɗina ne, dole ya yi haquri in yi waya da kai, tunda cikin biyayya yake karka fasa ba shi auren ƴarka." Ya yi murmushi mai sauti ya ce. "Yaranki ne suka ce na kira ki they want to congratulate you." Neehal ta ce. "Allah sarki ƴaƴan albarka, amma fa sun so su yi late." Ahmad ya ce, "Lefin Daddy ne bai kira musu Aunty da wuri ba, yau kuma a gidan Ammi suka wuni babu mai Numbern ki a gidan." Neehal ta ce. "To a basu wayar in ji muryoyinsu ko hankalina zai kwanta, in ji sa'idar kewarsu dake cike a raina." Ahmad ya cire wayar daga kunnensa ya saka a speaker, ya ajiye a gaban su Afrah da suka zuba masa ido amma babu damar su yi magana, dan ya ce duk wanda ya yi masa surutu yana waya ba zai yi magana da Aunty ba, kuma ba zai ci cake ɗin celebration ɗinta ba. Cikin rige_rigen Magana suka ce. "Aunty congratulation." Neehal ta yi murmushi ta ce, "Thank you so much my kids, Allah yay muku albarka, yaushe zaku zo Aunty ta gan ku, dan I missed you over." Afrah ta yi saurin fara magana da faɗin. "Aunty Daddy ya ce sai bikin ki zamu zo, wai kin kusa zama amarya." Neehal ta murmusa ta ce. "Toh Shikenan Daughter, ya school?" Amrah ta ce. "Aunty now we are in primary one." Neehal ta ce "Masha Allah, yarana sun girma har sun shiga primary, what about islamiyya?" Afrah ta ce. "Muna suratul Jin." Ta ce, "Masha Allah, ku dage da karatu kun ji yaran kirki, ban da over play, idan kuna karatu sosai I will give you something special." Suka ce. "Toh Aunty, Daddy ya ce zaki yanka Cake for your celebration, Aunty ki kawo mana mu ci." Na ce. "Insha Allah, zan kawo muku." Ahmad ya ɗauke wayar jin za su kuma wata maganar ya ce. "Ya'isa haka kar a ƙarar mun da credit." Neehal ta ɓata fuska kamar yana ganin ta, cikin shagwab'a ta ce. "Kai Uncle, muna hirar mu mai daɗi zaka katse mana?" Ya ce. "Sorry Aunty, zan mayar da su gidan Ummi ne, idan na bar su kuma surutunsu ba ya ƙarewa sai mu yi dare, kuma i want to tell you something." Neehal ta ce. "What?" Ya lumshe ido ya buɗe ya ce. "I was engaged today." Cikin razana ta waro Idanunta waje tare da dafe saitin zuciyarta da hannunta, saboda wani abu da ta ji mai zafi ya soki zuciyarta. A hankali ta shiga sauke numfashi amma ba ta ce komai ba. Ahmad ya cigaba da magana. "Neehal! Zuwa yanzu na riga na fitar da ran samun ki a rayuwata, duba da yadda bikin ki ya rage bai fi saura 1 month ba. Amma kuma zuciyata ta kasa daina tunanin ki, ta kasa rage sonki ko da kaɗan ne. Neehal! Ina tsoron ki yi Aure na dinga tunanin ki ina kwasar zunubi, hakan yasa na yanke shawarar yin aure nima nan da watanni kaɗan, na san idan ina da mata zata ɗauke mun hankalin tunanin ki." Ta lumshe idonta hawaye ya biyo ta ƙasan idon, ta sani ita macece mai kishi, yanzu ma kuma ta san kishin Uncle ɗin nata ne yake damun zuciyarta. Ta daure sosai dan ganin bai fuskanci halin da take ciki ba, ta ce. "Masha Allah My Uncle, Allah ya sanya Albarka, Allah yasa matar rufin asirinka ce, Allah ya kau da duk wata fitina dake cikin auren ku. Allah ya bata ikon riƙe ka da amana kai da twins." Cikin jin daɗi ya ce. "Amin, Amin Princess, na gode sosai. But one thing Princess, Twins naki ne, babu matar da zan iya bawa ta riƙe mun su matuƙar kina raye. Dan haka bayan aurenki idan kun gama cin amarcin ku, Indai mijinki ya amince zan kawo miki su, ki riƙe ƴaƴanki har auransu idan Allah ya nufa." Ta buɗe idonta hawaye na cigaba da zuba daga idanun, bata jin zata samu wanda zai so ta kamar Uncle ɗinta, tana son twins sosai, amma ta san duk k'aunar da take musu ya fita son su, amma ya sadaukar da nasa son saboda ita, saboda ta yi farin ciki a rayuwarta. "Me yasa baza mu yi aure ba mu mori soyayyar da muke wa juna?" Ta yi maganar da a tunaninta a zuci ta yi, sai da ta ji Ahmad cikin raunin murya ya ce. "Allah ne bai yi ba Princess." Sannan ta yi realising ashe a fili ta yi maganar. Ta ja gwauron numfashi tana hasaso irin kulawar da zata samu a gurin Ahmad data aure shi. A hankali ta ce. "Thank you so much Uncle, Allah ya biya ka da Aljannah." Ya ce "Amin Princess, and you too." Ta kawar da damuwar dake cin ranta ta ce. "Ya sunan Auntin tawa?" Ya ce, "Kina so ki sani?" Ta ce. "Eh mana, idan da hali ma har da pics ɗinta domin in ga ko ta dace da kyakkyawan Uncle ɗina, one in the million." Ya yi murmushi ya ce. "Yanzu kuwa Princess, dan idan ba tay miki ba dole a canza ta, a samo duk kalar wadda kike so." Ta yi ɗan murmushi mai ciwo, a ranta ta ce. 'Da son samu ne ni nake so ka aura Uncle.' amma a fili sai ta ce masa. "Na san ma ta yi, Uncle ɗina ba zai yi zaɓen da zai bani kunya ba." Ya murmusa ya ce, "Sai dai kin gani zaki tabbatar, zan tura miki pics ɗinta yanzu ta WhatsApp." Ta ce. "Toh Uncle." Ya ce, "Good night, ki je ki cigaba da waya da in-law kar ya yi fushi, ga yaranki har sun fara bacci." Ta ce, "Ka shafa mun kansu, and my regard to Ummi, Abba, Zahra and my Aunty." Ya ce "Duk za su ji Insha Allah, ki gaishe da Mama." Ta ce, "Zata ji Insha Allah." Daga haka suka yi sallama ya kashe wayar. Ta zare wayar daga kunnenta tare da zuba mata ido, tana jin zuciyarta babu daɗi sosai akan auren da Ahmad zai yi. Kenan duk soyayyar da yake cewa zai nuna mata idan sun yi Aure yanzu wadda zai aura zai yiwa ita. Sai ta ji wani kishi ya ƙara cika mata zuciya, a ganinta kamar ya yi sauri, ai da ya bari ya ga an ɗaura mata Aure sannan sai ya fara tunanin yi shi ma. Ta ɓata fuska tare da kunna data ta shiga WhatsApp dan ganin pics ɗin da ya ce zai tura mata. Ya turo kuwa kamar yadda ya faɗa, da sauri ta buɗe ta kalla, wata Black beauty ce, amma daga gani ta girme mata. Tana ta zuba murmushi a hoton, tana da kyawunta dai-dai gwargwado. Ta yi back, ta karanta gajeran bayanin da yay mata akan yarinyar, Nurse ce a asibitin da yake aiki, a nan suka haɗu sunanta Khadijah. Neehal ta masa reply da Allah ya tabbatar da Alkhairi. Sannan fita daga WhatsApp ɗin ta kira Sadik suka ci-gaba da hirar su. Washegari Sadik ya kawo mata prame mai ɗauke da hotonta, tare da banner mai ɗan girma, da turaruka as her graduation gift. Ranar Sunday wanda ya kama kwana biyu da yin graduation ɗinsu, ranar za su yi Graduation dinner da suka haɗa iya ƴan class ɗinsu, a wani tsadadden hall ƙarami. Ƙarfe biyar da mintuna na yamma ta sakko cikin shirinta na tafiya. Tana sanye cikin wani had'ad'd'en less kalar black and red. Ɗinkin riga da skirt akai mata wanda ya zauna dass a jikinta. Ta kafa kwatancen dauri mai V a kanta. Ta yi kyau sosai kayan ya ƙara haska farar fatarta. Turus ta tsaya a falon ganin Ameen zaune shi da Mama, dan ɓata tunanin ganin shi at this time ba, tunda ba ya zuwa gidan sai dare. Mama ta dube ta, ya ce. "Me ya faru na ga kin tsaya? ke da tun d'azu kike ce mun sauri kike." Ta ƙaraso cikin falon tana kallon sa wanda sai a lokacin ya d'ago ya dube ta. Kamar mara gaskiya ta ce. "Yaya Ina yini." Bai amsa ba sai cewa ya yi. "Where are you going?" Ta kalli Mama ba ta ce komai ba, Mama ta ce. "Party suke yi yau na graduation ɗinsu." Ya dubi Neehal yana ɗan haɗa rai ya ce. "Party kuma na me?" Mama ta ce. "Na ƴan class ɗinsu mana." Ya kafe ta da ido bai ce komai ba, tay saurin yin ƙasa da kanta cikin tsoron kar ya hana ta zuwa, dan ta san kaɗan daga aikinsa ne ya hana tan." A hankali ta ce. "Mama zan tafi." Mama ta ce, "Allah ya kiyaye a hanya, ki kula fa sosai kuma karki yi dare." Ta miƙe tana faɗin. "Insha Allah Mama, sai na dawo." Ameen ya haɗe rai sosai yana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ce. "Wai wanne irin party ne da ba'a yi shi tun rana ba sai daf da Magriba za'a tafi? A dawo yaushe kenan?" Neehal ta yi raurau da ido kamar zata yi kuka, dan ta saddaqar hana ta zai yi." Mama ta ce, "Bayan Magriba zata dawo." Sannan ta mayar da kallonta ga Neehal ta ce. "Wuce ki tafi Daughter, saura ki bari hawayen idonki su zubo ki ɓata kwalliyar ki." Ta gyaɗa mata kai. Ameen ya miƙe yana faɗin, "Mu je in kai ki." Ta kalle shi ta ce, "To Yaya wa zai dawo da ni?" Ya mata wani kallo ya ce. "Ban sani ba." Mama ta ce, "Ku je Daughter, zan zo in ɗauko ki, kafin ku tashi ki kira ni." Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fice daga falon. Mama ta dube shi tana taɓa baki ta ce. "Yarinya tana cikin farincikinta zaka canza mata mood, ta kusa dai hutawa da takurar ka, tunda in ta yi aure baza ka bi ta gidan mijinta ka nuna mata iko ba." Bai ce Komai ba, ya fice daga falon. A bakin Motarsa ya tarar da ita tsaye tana jiran sa. Bai mata magana ba ya buɗe Motar ya shiga, itama buɗewa ta yi ta shiga tana tutturo baki gaba. Ya kalle ta sau ɗaya ya ɗauke kai sannan ya kunna Motar suka tafi. Sai da suka hau kan titi ya tambaye ta gurin da za su, ta faɗa masa. Suna cikin tafiya ta ce, "Yaya." Ya ce. "Uhm." Sai kuma ta yi shiru, ya ce. "Mene ne?" Jin yanda ya yi magana cikin sanyin murya sai ya bata k'warin gwiwar tambayarsa abun da yake damunta a rai. "Yaya wai dan Allah me nake maka sometimes sai in ga kana ta shashshare ni." Ta yi maganar kamar zata yi kuka. Ya juyo ya kalle ta, sannan ya yi ɗan murmushi ya ce. "Kina son in daina miki hakan ne?" Da sauri ta ce. "Eh." Ya mayar da duban sa ga titi sannan ya ce. "Why?" Ta ce. "Saboda kai kaɗai ne Yayana, ina son na ga muna rayuwa kamar kowanne Yaya da ƙanwarsa." Ya yi shiru na tsawon mintuna biyu, kamar ba zai tanka ba sai kuma ya ce. "Yanzu kamar yaya muke rayuwar? Ai kamar kowa ne dama." Ta ce. "Ni dai bana son yanda muke, sai nake ganin kamar wani laifin nake maka." Ya juyo ya mata wani kallo da lumshashshun idanunsa, cikin wata irin so cool voice wadda tasa Neehal lumshe ido ba tare data shirya ba, ya ce. "Yes akwai abun da kikai mun." Ta buɗe ido da sauri tare da waro su cikin mamaki ta ce. "Mene Yaya, ka faɗa mun ba zan kuma yi maka ba, Insha Allah." Ya murmusa ganin yanda ta ruɗe ya ce. "I will tell you, but not now, kuma don't ask me again, idan lokacin da ya dace ki sani ya yi zan sanar miki da kaina ba tare da kin kuma tambaya ta ba." Ta shagwab'e fuska ta ce. "Please Yaya ka faɗa mun yanzu." Ya ɓata rai ya ce, "Ba ki ji mene na ce ba ne?" Bata kuma magana ba, a ranta tana jinjina halinsa, yanzu zaka gan shi faran_faran take kuma sai ya canza. Ta kwantar da kanta a jikin kujera tana tunaninta ita kuwa wanne irin abu tay masa da yake mata haka? Har suka ƙarasa gurin babu wanda ya kuma magana. Sai bayan ya yi parking ne ta ce masa. "Thank you." Ya ce, "Saura kuma ki je ki ta rawa." Ta turo baki a ranta tana faɗin. 'Ko yaushe ya taɓa ganin ta tana rawa ma da zai ce kar ta yi." Ta buɗe ƙofar ta fita, ta kalle shi ta d'aga masa hannu. Ya gyaɗa mata kai kawai tare da bin ta da kallo harta shige gurin. Sai bayan isha'i sannan aka tashi, partyn ya yi musu daɗi da armashi yanda suke so. Ga mamakin Neehal Ameen ne ya dawo ya ɗauke ta, sai ta yi tunanin ko Mama ce ta tilasta masa ya zo, dan ta san halinta zata iya cewa tunda shi ya kai ta sai ya koma ya ɗauko ta........ Bayan Kwana Uku ya kama ranar Laraba, ranar ne kuma za'a kawo lefen Neehal daga gidan su Sadik. Tun safe tana kwance akan gado ko falo bata fito ba, balle ta sauka ta ci abinci. A kwanaki ukun nan da suka wuce gaba-ɗaya bata jin daɗi, yanayin feeling ɗin data ke ji a cikin zuciyarta na ƙaruwa. Ji take kamar ta ce ta fasa Auran Sadik Ahmad take so, amma akan me to? Idan so ne ta san tana son Sadik, kuma babu wani abu da yake mata wanda bata jin daɗin sa, kullum cikin ƙoƙarin faranta mata yake, bare ta ce ga dalilin da yasa ta fasa auren sa. Sai daga baya ta gane Auren take tsoro gaba-ɗaya ba Sadik ɗin ne bata so ba. Mama bata bi ta kanta ba ayyukan ta kawai take, ta lura abun nata har da iskanci. Aunty Saudiya ce da suka zo tun safe ita da Aunty A'isha dan taya Mama aiki da kuma jiran masu kawo kayan lefen, duk da Maza ne za su kawo, amma sai an kawo za su tafi. Wajen sha biyu na rana ta shiga ɗakin Neehal, ganin tunda suka zo ba ta ga gilmawar ta ba. Ta zauna a gefen gadon tare da yaye bargon data lullub'e jikinta da shi, ta ce. "Neehal baki da lafiya ne?" Ta buɗe ido jin muryar Aunty'n, ta yunƙura ta tashi zaune tana hawaye. Aunty Sadiya ta ce. "Subhallahi! Neehal meke damun ki?" Ta girgiza kai ta ce, "Babu komai Aunty." Aunty Sadiya ta ce. "Babu komai amma kike kwance kin ƙi tashi kuma gashi kina kuka?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Aunty Sadiya ta kamo hannunta ta ce, "Please talk to me, ko da akwai wata matsala ne?" Ta ce. "No Aunty, just I'm scared" Aunty Sadiya ta ce. "Tsoron me kuma Neehal?" Ta ce. "Na auren nan." Aunty Sadiya ta yi murmushi ta ce. "Ki daina jin wani tsoro babu abun da zai faru Insha Allah, wannan emotions ne da kowacce mace take feeling idan Aurenta ya gabato, wani lokacin kuma shaid'an ne, sai yay ta saka maka wasu abubuwa a cikin ranka game da Auran, ka ji kamar a fasa." Ta shiga share mata hawayen fuskarta tana faɗin. "Ki daina damuwa, ki yi ta addu'a kawai, muma duk mun ji irin wannan yanayin a namu lokacin Auren." Neehal ta gyaɗa mata kai. Aunty Sadiya ta ce, "Yawwa Daughter, ke fa amarya ce, farinciki ya kamata ki dinga yi, kin kusa tafiya gidan masoyinki." Ta rufe fuskarta da duka hannayenta biyu, Aunty Sadiya ta yi dariya tare da miƙewa ta ce. "Ki tashi ki shirya, sai ki sakko ƙasa ki yi breakfast, yau ai ranar farinciki ce bata damuwa ba." Ta amsa mata, tare da saukowa daga kan gadon ta nufi toilet. Zuciyarta na tuna mata exactly day like this, ranar da za'a kawo lefen ta daga gidan su Anwar, amma Allah bai nufa ba aka kashe mata shi. Ta tambayi kanta da faɗin. 'Ko wannan karon za'a bari a kawo mata lefen har a yi bikin nata? ko kuwa shima Sadik ɗin kashe mata shi za'ai?.........✍️ _*Ban yi edit ba Yau, a yi haquri da typed errors.*_ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *6️⃣1️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* .........Toilet ta shiga ta ɗauro alwala ta fito, tun a toilet ɗin ta ji wayarta ta yi vibrate alamar shigowar message. Bata bi ta kanta ba, ta tayar da Sallah. Har aka fara kiraye_kirayen Sallar Asuba tana kan darduma tana lazimi, zuwa lokacin ta fara jin bacci na fizgar ta, daurewa kawai take saboda bata so ta rasa Sallah akan lokaci. A lokacin ne kuma ƴan ɗakin suka fara tashi daga bacci. Tana nan zaune har aka yi kiran assalatu aka shiga sallah. Ta miƙe dak'yar dan jin ta take kamar mai cuta ta yi Sallah, tana idarwa ta haye gado ta kwanta, tana jin tsiyar da su Haneefah suke mata ta share su, cikin mintuna ƙalilan bacci ya ɗauke ta. Sai da bakwai na safe ta wuce sannan Aunty A'isha ta shigo ta tashe ta. Ta tashi ba dan baccin ya ishe ta ba, dan har ciwo kanta ya fara mata. Aka cigaba shirye_shirye ana ta dafe_dafen abinci a bayan gidan, kowa nata hada_hada cikin farinciki, amma ita tana zaune ta yi tagumi, so take ta yi kuka ko zata ji sauƙin abun da take ji a ranta, amma bata son faɗan Mama dana su Aunty Sadiya shi yasa take ta daure kukan. Ta ɗakko wayarta ta kunna data ta shiga media. Ƴan'matan dake ɗakin suna ta tsokanarta tare da yin hirarsu, amma ko ƙala bata ce musu ba, dan ta san tana buɗe baki da nufin magana kukan da take ta ƙoƙarin dannewa ne zai taho. Haneefah ta shigo ɗakin da plate ɗin wainar shinkafa ɗauke a hannunta. Ta zauna a gaban Neehal ta fara ci tana faɗin. "Bebinki ya mayar da ni uwar ci, duk abincin dana ci kafin na kwanta amma ina tashi na ji cikina na mun ƙugi". Neehal ta d'ago daga lallatsa wayar da take, cikin sanyin murya ta ce. "Dama can ke acici ce, karki yiwa ɗana ko ƴata sharri." Haneefah ta ce. "Hmmm, kwana nawa ne kema kin yi inda rai, a lokacin zaki tabbatar sharri na yi ko gaskiya na faɗa." Neehal ta ce. "Me zan yi?" Haneefah tana dariyar mugunta ta ce. "Cikin mana." Neehal ta ɓata fuska bata ce komai ba, a ranta tana tunanin abun da Haneefah ta faɗa, kamar tana mamakin abun. Haka kawai ta ji tana son jin muryar Sadik, ta shiga phone ta yi dialing Numbern shi, tay ta ringing amma bai ɗauka ta ba. Sai ta yi tunanin wataƙila bacci yake tunda jiya bai samu ya yi ba. Ta lumshe idonta kawai tana sauke numfashi. Haneefah ta dube ta da kyau ta ce. "Lafiya kike kuwa Neehal? yau fa ranar farinciki ce a gare ki, amma na ga duk kin yi kamar wata mai cuta." Ta buɗe idonta tare da girgiza mata kai. Haneefah ta ce. "Are you sick? Ko kewar Maman ce kika fara tun yanzu?" Kamar zuga ta, ta yi sai ga hawayen da take ta ƙoƙarin mayarwa sun zubo. Cikin lallami Haneefah ta ce. "I'm sorry Besty, Dan Allah ki bar kukan nan kar hankalin mutane ya dawo kan ki." Ta share hawayen tare da gyaɗa mata kai. A hankali ta sakko daga kan gadon ta shiga toilet ta yi brush, sannan ta fito ta tafi part ɗin Daddy, dan anan kayanta na sakawa suke. Mama da kanta ta kawo mata ruwan zafi da kayan haɗin tea, ta haɗa mata ita da su Afrah dake mak'ale da ita suka sha. Sannan ta kawo musu abubuwan toye_toye irin su, waina, sinasir, funkaso suka ci. Duk da ita Neehal kaɗan ta ci, dan da ƙyar suke iya wuce mak'oshinta, cusawa kawai take ganin idon Mama. Wajen ƙarfe tara Aunty Sadiya tasa ta, ta yi wanka, ta shirya cikin wani had'ad'd'en less ɗinkin riga da zani, ta yi kyau sosai duk da ba ai mata make up ba. Sai anjima mai make up ɗin zata zo har gida tay mata, tunda d'aurin Auren sai ƙarfe biyu na rana za'a yi, bayan an idar da sallar juma'a za'a daura. Ta dawo part ɗin Mama ta zauna suna ta yin pictures da su Haneefah. Abokan wasa nata tsokanarta. Ƙarfe goma na safe sai ga Aunty Fauziyya da Iman da Aiman sun zo. Neehal ta tarb'e su cikin fara'a, har da musu tsiyar shine tunda aka fara bikin ba su zo ba sai yau. Aunty Fauziyya ta bata haquri da cewar Iman ce bata jin daɗi shi yasa ba su zo ba. Neehal tay mata sannu cikin tausayawa, yarinyar duk ta rame ta d'ashe, ana kallon ta an ga mai ƙaramin ciki, itama Aunty Fauziyyan kamar me jinya ta k'anjale ta yi baƙi. Sai ga Hafsah ba kunya ta zo tana yiwa Neehal magana cikin fara'a, abun ya bawa Neehal mamaki, amma sai ta ɗauki hakan a matsayin fuska biyun da take mata. Kamar ta tambaye ta Ameen da kuma dalilin da yasa bai zo dinner jiya ba sai kuma ta fasa. Gida fa sai ƙara cika yake da baƙi mata da maza. Neehal har ta fara gajiya da gaisawa da mutane. Ƙarfe goma sha biyu na rana mai make up ta zo gidan ta fara yiwa Neehal kwalliya, wadda zuwa lokacin hankalinta gaba-ɗaya yana kan angon ta. Ta ƙara kikkiran sa bayan kiran da tay masa na safe amma bai ɗauka ba kuma bai kira ta ba har yanzu. Duk da ta masa uzurin may be ya shiga cikin hada_hada da mutane ne. A dai-dai lokacin Mama tana bedroom ɗin Daddy tana shiryawa cikin shigarta ta biyu a ranar, fuskarta ɗauke da farincikin nuna mata ranar D'aurin Auren Neehal da Allah ya yi. Tana zira sark'a Daddy ya shigo dakin kamar an jeho shi, kallo ɗaya tay masa ta cikin mudubi ta san akwai matsala. Gabanta ya yi mummunar fad'uwa, ta miƙe tsaye har wayarta dake kan cinyarta na faɗuwa a ƙasa ta juyo tana kallon Daddy dake ta goge gumin fuskarsa, in ba gizo idanunta ke mata ba har yar rama ta ga ya yi. A ruɗe ta ce. "Gen. Lafiya kuwa?" Daddy ya sauke zazzafan numfashi cikin tsananin damuwa ya ce. "Akwai matsala Doctor." Wani irin sarawa Mama ta ji kanta yay mata, jikinta har rawa ya fara, cikin rawar murya ta ce. "Matsalar me?" Daddy ya kamo hannunta kamar zai yi kuka ya ce. "Yanzu Mahifin Sadik ya kira ni, wai an neme shi an ransa." Mama ta waro Ido waje tare da k'wace hannunta daga na Daddy, cikin matuƙar tashin hankali ta ce. "Kamar ya an neme shi an rasa? Ina kuma zai tafi ranar Auren sa?" Daddy ya ce. "A yadda ya sanar mun ya ce, suna zargin sace shi aka yi, dan jiya har cikin dare yana gida cikin ƴan'uwa, amma tunda asuba mahaifin nasa ya shaida mun aka lura baya gidan, kuma ga wayoyinsa duka da komai nasa a ɗakin da ya kwana, harta silifas ɗinsa gashi nan a bakin toilet." Mama ta ji wani abu luuu ya gilma ta ƙwaƙwalwarta, zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfin gaske, cikin sark'ewar numfashi ta ce. "Me hakan yake nufi Daddy? Dan Allah karka ce mun an sace Sadik a yau ranar Auransa da Neehal, dan Allah Daddy kace mun kunnena ne bai ji dai-dai ba." Daddy ya riƙe ta ganin tana ƙoƙarin faɗuwa suka zauna a bakin gado. A gigice ya ce. "Calm dawn Doctor, jikina yana ba ni Insha Allahu za'a gan shi kafin time ɗin d'aurin Auren, may be wani gurin ya tafi zai dawo." Mama ta girgiza kai cikin hawaye ta ce. "Tunda har Mahaifinsa ya kira ka ya sanar maka to da akwai babbar matsala." Bata jira cewar Daddy ba, ta tashi cikin sauri ta ɗauki wayarta data faɗi ƙasa, ko gani bata yi sosai saboda tashin hankali ta shiga contact ta lalubo Numbern Maamah ta yi dialing. Kamar yadda ta yi zato bata ɗauki kiran ba. Ta juyo tana duban Daddy amma bata ce komai ba, Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un kawai take maimaitawa a cikin ranta. Ta dafe bango saboda jirin da take ji yana ɗibar ta. Aunty Sadiya ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, a tunaninta Mama ce kaɗai a ciki kamar yadda ta fita ta bar ta. Da mamaki take kallon su, ganin fuskokinsu cikin tashin hankali. Da mamaki ta ce. "Yaya Tafida lafiya?" Daddy ya sauke numfashi ya ce. "Babu lafiya Barrister, an sace Sadik." Aunty Sadiya ta yi jimm tana kallon Daddy sannan ta ce. "Sadik dai Ango wanda za'a d'aura musu aure da Neehal yau? Na ma kasa gane wane Sadik ɗin." Daddy yay mata bayanin abun da Abban Sadik ya sanar masa kamar yadda yay wa Mama bayani. Aunty Sadiya ta dafe kai tana ambaton Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un a fili. Kusan 5 minutes suna haka babu wanda ya kuma magana, Mama dai sai addu'a take a ranta Allah yasa mafarki take, ba gaske ba ne abun da yake faruwa yanzu. Wayar Daddy ce ta dau ƙara, suka kalle shi gaba-ɗaya cikin alamar tambaya. A sanyaye ya zaro wayar ya duba, sannan ya dube su ya ce. "Alhaji Suraj ne." A hanzarce Mama ta ce, "D'aga mu ji ko an gan shi ne." Daddy ya yi picked ya saka wayar a handsfree. Cikin damuwa ya ce. "Alhaji Suraj an gan shi ne?" Cikin muryar dake nuna tsantsar damuwa Abba ya ce. "Har yanzu dai babu wani labari ranka ya daɗe, duk inda muke tunanin zai iya zuwa an je baya nan, ga dukkan alamu fa sace Abubukar akai, dan ƙofar ɗakin da ya kwana a ciki a ɓalle muka tarar da ita." Daddy ya ce, "A ɓalle kuma? Kenan ɓalla ta akai aka shiga?" Abba ya ce. "Haka muke tunani, ga darduma nan a shimfid'e alamun abu na ƙarshe da ya yi sallah ce." Daddy ya ce. "Hasbunallahu'wani'imal'wakil, Alhaji gani nan zuwa gidan naka, wannan maganar bata waya ba ce, bari na kira a haɗa mun jami'an sojoji su zo mu san abun yi, Insha Allahu za'a gan shi." Mama ta durk'ushe a gurin da take tsaye numfashinta na fita da ƙyar. Ta rasa tunanin me ma zata yi, ƙwaƙwalwarta gaba-ɗaya ta toshe, ta ma daina fahimtar abun da Daddy yake faɗa. Aunty Sadiya ta yi wani murmushin takaici ta ce. "An canza salo kenan? saboda a ɗauke hankalin mutane." Cikin rashin fahimta Daddy ya ce. "Kamar Yaya?" Aunty Sadiya ta ce. "Lokaci da ikon Ubangiji na tonar asirin duk wanda yake da hannu a cikin wannan al'amari zai bayyana." Daddy ya ce. "Me kike nufi ne Barrister, dan Allah karki danganta ɓatan Sadik da mutuwar su Anwar." Aunty Sadiya ta ce. "Ban danganta ba, amma ina zargin haka." Daddy ya miƙe yana gyara hular kansa ya ce. "Bari na je na dawo sai mu yi magana, yanzu hankalina ba ya jikina." Bai jira amsar ta ba ya fice daga ɗakin. Dan shi damuwar Daddy ɗaya kar a ce an fasa d'aurin Auren nan a yau. Aunty Sadiya ta ƙarasa inda Mama take ta riƙo ta, Mama tana duban ta, ta ce. "Sadiya an sace Sadik kamar yadda aka kashe Jameel da Anwar, kenan hakan yana nufin akwai wani da yake bibiyar rayuwar Neehal da wata mummunar manufar? Me tay masa haka da ya zaɓi cutar da ita da mu da iyayen yaran da yake kashewa? Akan me ba'a son aga ta yi Aure kamar kowacce mace?" Aunty Sadiya ta ce. "Yaya Fateemah yanzu duk ba wannan ne a gaban mu ba, addu'a kawai zamu yi Allah ya bayyana mana Sadik a duk inda yake. Kila ma abun da muke tunani ba haka ba ne, wani gurin Sadik ɗin ya je. Ko kuma idan ma sacen shi aka yi hakan ba shi da alaƙa da Neehal." Mama ta sauke wani gwauron numfashi mai tattare da tsantsar damuwa ta ce. "Ya Allah ka bayyana mana yaron nan, ya Allah ka kare shi a duk inda yake, Allah ka bayyana mana gaskiyar wannan al'amari." Aunty Sadiya ta ce. "Ameen ya Allah." A gidansu Sadik kuwa, tun bayan da k'aninsa Bashir ya je tashin sa da asuba dan su tafi masallaci kamar yadda suka saba kullum, duk wanda ya riga ɗan'uwansa tashi shi zai je ya tashe sa. Tun daga ganin ƙofar ɗakin a ɓalle a ƙasa ya san da matsala, cikin mamaki ya shiga ɗakin yana k'wala masa kira da tambayar sa dalilin ɓalle ƙofar. Jin shiru kusan mintuna biyar yasa ya lek'a toilet inda yake tunanin Sadik ɗin yana ciki, amma sai ya ga wayam babu kowa. Ya fito ya dinga dudduba ɗakin har bayan labule amma babu shi babu alamar sa. Ya fito hankali a tashe ya duba bayan ɗakunan, nan ma babu shi. Sai ya yi tunanin ko masallaci ya tafi ya bar shi, duk da wata zuciyar na faɗa masa ba haka ba ne, amma dai ya nufi masallacin. Yana ta dube_dube amma ko mai kama da Sadik bai gani ba har aka idar da Sallah. Bayan sun fito daga Masallacin sun gaisa da Abban su ya sanar masa. Ba tare da damuwar komai ba, Abban ya ce masa su duba ɗakinsa na part ɗin Maamah may be yana can, tunda dama a can suke kwana saboda baƙi ne yasa suka dawo BQ. Wasa_wasa dai Bashir da Abba sai da suka duba ko'ina na gidan amma ba su ga Sadik ba. Suka dinga kiran wayar shi amma bai ɗauka ba, sai da suka koma ɗakin da ya kwana suka gan ta. Tun daga nan Abba ya san da matsala, Bashir ya ɗauki wayar da yake ya san pin ɗin Sadik ya buɗe wayar, ya duba last wanda suka yi waya ya ga Neehal ce. Har zai kira ta amma ya hana shi, dan ya san Sadik ba zai je gurinta ba tun asuba. Abokanansa suka dinga kira ana tambaya ko suna tare amma kowa sai ya ce A'a. Duk inda Abba yake tunanin Sadik zai je sun kira baya nan. Hankalin su fa ya ƙara tashi, Bashir ya fara kuka. Abba ne ma mai dauriya, ya fita ya tambayi mai gadi ko ya ga alamar wasu sun shigo gidan ko kuma ya ga Sadik ya fita? Mai gadi ya ce, Gaskiya babu wanda ya shigo ko ya fita daga cikin gidan, dan shi ya buɗe gidan ma da kansa da asuba. Hankali a tashe Abba ya kira ƴan'uwansa maza ya sanar musu dan su san abun yi, amma ya roƙe su kar su sanar da kowa, Bashir ma ya gargad'e shi kar ya sake ya sanar da Maamah, Insha Allahu za'a ga Sadik ɗin. Babu jimawa Ƴan'uwan Abba suka zo cikin tashin hankali, kowa na tambayar ina yaron nan ya tafi shi kuwa da sassafe ranar Auransa? Duk wani gidan abokan Sadik da Abba da Bashir suka sani sai da suka je neman sa, duk da sun kira su a waya sun ce basa tare, amma Abba sai yake ganin kamar ɓoye masa suke, Sadik ɗin yana tare da su. Har gurin telan dake masa ɗinki suka je, akan ko nan ya je can karɓar ɗinki, amma telan ya ce bai zo ba, dan tun last week ya gama masa ɗinkunansa duka ya ba shi. Mata na gida suna can suna cigaba da harkar girke_girke da harkokin biki basu san mai yake faruwa ba. Sai Maamah ce ma da ta ga har kusan 11 bai shigo cikin gidan ba ta yi mamaki, amma ko kaɗan bata yi tunanin wani abu ba. Duk wani abu da zai tabbatarwa da su Abba sace Sadik akai ya bayyana, dan haka wani k'ani a gurin Abba ya ce ya kamata a kira iyayen Amaryar a sanar musu halin da ake ciki. Shine Abba ya kira Daddy ya sanar masa. Bashir yana kuka wiwi ya shiga cikin gidan ya sanar da su Maamah abun da yake faruwa, faɗar irin rud'ewa da tashin hankali da Maamah ta shiga ba zai misaltu ba, ƙarshe ma sumewa ta yi saboda tsabar firgici. Cikin lokaci k'ank'ani zancen ɓatan Sadik ya baza gidan, nan fa aka fara koke_koke gidan biki ya koma kamar na zaman makoki. Umma ta dinga faɗin dama ta san haka zata faru, shi yasa ta ce kar a yi bikin nan amma Sadik ya dage, gashi nan ai. Hajiya kuwa iska ta tayar tana faɗin sai ta je gidansu Neehal sun fito mata da jika, kurwar jikanta ta fi ƙarfin su in ma su mayu ne. Da ƙyar aka riƙe ta dan sai fizge_fizge take tana ƙoƙarin k'wacewa ta fita. Ana cikin haka Su Abby (Mahaifin Maamah) suka ƙaraso gidan, sun taho da shirin d'aurin Aure suka tarar da wannan abun tashin hankalin. Daddy da shi da Yayansa da Kawu Musa da Uncle Usman da Uncle Mahmud suka je gidansu Sadik hankali a tashe. Har ƙarfe ɗaya ta wuce lokacin masallaci ya yi babu labarin Sadik, tuni Daddy Ya yi report ga Police da duk wani gurin da ya dace. Tashin hankalin da ahalin Sadik suke ciki a wannan rana ba zai misaltu ba. Kamar yadda ahalin Sadik suke cikin tashin hankali haka su Mama suke ciki, sai dai su har wannan lokacin ba su bayyana labarin ɓatan Sadik a gidan ba. Daga ita sai Aunty A'isha, da Aunty Sadiya, da Ammi matar Uncle Mahmud sai Umma matar wan Daddy ne kaɗai suka sani, dan ko Hajiya ba su sanarwa ba, ita Mama Babban tashin hankalinta bata san ya Neehal zata yi ba in ta ji labarin ɓatan Sadik. Mama ta kira Daddy yafi sau 20 tana tambayar sa ko an ga Sadik, amma amsar ɗaya ce yake bata A'a. Sauran ƴan biki kuwa suna ta harkokin su, duk da ana ta neman Mama da tambayar ta dan tana part ɗin Daddy bata fito ba, saboda ana kallon ta za'a gane tana cikin tashin hankali. Mommyn Haneefah data fuskanci da akwai wata matsalar ita take replacing ɗinta, tana faɗawa masu tambayar ta cewa suna ɗan tattaunawa ne da ƴan'uwanta, yanzu zata fito. Duk da halin tashin hankali da ake ciki amma haka su Daddy da su Abba suka tafi masallacin Juma'a, masallacin da aka saka za'a yi d'aurin Auren a can. Ai kuwa masallacin ya cika ɗank'am da jama'a, mutanen Daddy da ƴan'uwa dana Abba kowa ya hallara ana jiran a ɗaura Aure bayan an idar da Sallah. Daddy ya dubi Abba ya ce. "Amma Alhaji ina fata dai ɓatan Sadik ba zai saka a fasa wannan d'aurin Auren ba? duba yanda muka tara wannan dubban jama'ar." Abba ya nuna Kawu dake gefen sa ya ce. "Ga waliyyin shi nan ku yi magana da shi, ni bani da ta cewa akan wannan maganar." Daddy ya ja Kawu da Kawu Musa wanda shine waliyyin Neehal ya faɗa musu abun da ya cewa Abba. Kawu da dama jiran k'iris yake tunda ba k'aunar Auren yake ba, ya shiga masifa yana faɗin. "Tunda dama ba ɗansu ba ne ya ɓata ai dole ya faɗi haka, to wallahi ko Allah ya bayyana Sadik a yanzu baza a yi Auren nan ba, su sun fasa, wannan tashin hankalin ma kaɗai ya ishe su, a yanzu ma an sace shi in aka ɗaura Auran kuma ai sai kisa kamar yadda aka yiwa na baya, tunda ƴar tasu ta zama annoba, duk wanda zata aura sai an kashe shi." Duk da ran Daddy ya ɓaci amma ya dinga ba shi haquri akan ya amince a ɗaura Auran, Insha Allahu Sadik ɗin zai bayyana a yau cikin k'oshin lafiya har su tare da matarsa. Duba da yadda jama'a suka taro dan halartar d'aurin Auren, yanzu kuma kawai sai a ce musu an fasa." Kawu ya ce, ai kamawa ta yi dan haka batun wani d'aurin Aure ma a bar shi bai taso ba, su yanzu ta ɓatan ɗansu suke bata wani d'aurin Aure ba. Kawu Musa ya lallmi Daddy ganin yanda ya damu, ya ce masa ya bari a idar da Sallah sai su san abun yi, Insha Allahu baza a tara wannan Jama'ar a banza ba. A dai-dai wannan lokacin aka gama yiwa Neehal make up ɗin, ta shirya cikin wani rantsatstsen farin less, an yi masa ado da golden colour, an ɗaura mata head golden, ta ci ɗan'kunne da sark'a da awarwaro na gold sai walwali suke. An yafa mata wani farin mayafi mai kamar net, sai tashin k'amshi dake. Hajiya tunda aka fara kwalliyar take ɗakin tana ta zuba santin kwalliyar. Kowa na ɗakin sai faɗin. "Masha Allah, amarya kin yi kyau, anya kuwa wannan angon naki zai gane ki in ya gan ki." Neehal dai murmushin yaƙe kawai take, amma ita kaɗai ta san halin da zuciyarta take ciki. Gashi haka kawai ta ji ta fara damuwa da rashin kiran ta da Sadik bai yi ba, shi da kullum tun safe yake kiran ta, wataran ma shi yake tashin ta daga barci. Amma yau ranar farincikinsu a ce har yanzu bai kira ta ba, yanda yake ta zumud'in nan ta yi tunanin ba ƙaramin addabarta zai yi da kira ba, amma sai ta ga saɓanin haka. Hafsah ce ta shigo ɗakin yanayin ta kamar tana cikin damuwa. Hajiya ta dube ta ta ce. "Ke wai ina mijin naki ne? ban gan shi ya zo yau ba." Cikin damuwa alamar an sosa mata inda yake mata k'aik'ayi ta ce. "Wallahi Hajiya ban sani ba, rabo na da shi tun jiya da yamma, dama ya ce mun dak'yar in zai je gurin dinner. To kuma yau tun safe nake kiran wayoyinsa duka a kashe." Hajiya ta ce. "Subhallahi, an shiga uku, kar dai baƙin halin Aminu har ya kai ya ƙi zuwa d'aurin Auren Yar'uwarsa guda ɗaya jal a duniya." Neehal tay karaf ta ce. "Ni Yayana ba shi da baƙin hali." Ta yi maganar cikin turo baki. Hajiya ta tab'e baki ta ce. "Toh mai Yaya, zamu gani ai in zai zo, halin Aminun ne ban sani ba, kaɗan daga cikin aikinsa ne ya ƙi zuwa." Hafsah dai bata kuma cewa komai ba. Neehal ta tsugunna ana musu hotu ita da twins ɗinta. Salma Ƴar ƙawar Mama wadda suka je gidansu Sadik tare tana gefen ta a bakin gado tana latsa waya, kallon status take. Da yake sun yi exchanging number ita da batul da suka je gidan sai ta ga ta yi story just now. Ta shiga da sauri dan ganin pics ɗin Namiji ne, a tunaninta kwalliyar Sadik ta ɗora ta angonci. Rubutun da ta gani akan hoton yasa ta waro Ido, ta kalli hoton tare da maimaita karanta rubutun kan hoton ya fi sau biyar. Da sauri ta taso ta miƙawa Neehal wayar tana faɗin. "Neehal! Duba mun hoton nan ba Sadik ɗinki ba ne?" Neehal ta karɓa cikin tashin hankali, hannunta har rawa yake tun kafin ta ga mene a hoton Sadik ɗin. Kowa na ɗakin ya zuba mata ido. Hajiya ta ce. "Me kuma ya samu Sadik ɗin?" Neehal ta zauna dab'as daga tsugunnen da take idanunwanta duka sun yo waje. A fili ta maimaita rubutun da ta karanta a jikin hoton Sadik. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Be safe Big brother, Allah ya bayyana mana kai ya kare ka a duk inda kake. Yan'uwa musulmai muna barar addu'arku, yau mun tashi cikin tashin hankalin ɓatan Yayanmu Barrister Abubakar Sadik, wanda wasu alamomi suka tabbatar sace shi aka zo akay har cikin gida. Dan Allah a taya mu da addu'ar Allah ya bayyana mana s....." Ta yarda wayar ba tare data ƙarasa karanta rubutun ba ta hau girgiza kanta kamar dolowa tana faɗin. "No, no ba Sadik ɗina take managa akai ba, wani mai kama da shi ne. Sadik ba zai taɓa ɓata ranar Auren mu ba." Sai ta fashe da kuka tare da miƙewa zumbur numfashinta na wani irin fuzga. Da sauri aka yo kanta aka riƙe ta, Haneefah ta zo ta ɗauki wayar ta duba ta ƙara karanta abun da Neehal ta karanta a fili cikin tashin hankali. Hakan ba ƙaramin ƙarawa Neehal tashin hankali da razani ya yi ba tare, lokaci ɗaya ta ji kamar an janye iskar da take shaƙar numfashi da ita, idanunta suka daina ganin komai sai duhu, kawai gani aka yi ta tafi luuu ta faɗi a gurin sumammiya. Yan ɗakin gaba-ɗaya suka yo kanta suna kiran sunanta, twins suka fashe da kuka. Hajiya wadda ita kaɗai ce bata motsa ba sai bin su da ido kawai take cikin tsananin shock, ta miƙe tsaye tare da rafka salati cikin d'imuwa.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *6️⃣3️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........Mama ta ja baya da sauri tana kallon sa kamar yadda shi ma ya tsaya yana kallon ta cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. Mama ta sauke ajiyar zuciya gaba-d'aya kwandon bala'in data tanada domin sauke masa idan ya dawo ta nemi shi ta rasa saboda yanayin tsantsar damuwar data gan shi a ciki. Cikin sanyin murya ya ce. "Mum.!" Mama ta haɗe rai ta ce, "Malam bani hanya in wuce, ka zo ka wani tsaya mun a kai." Ya sauke numfashi mai huci ya ce. "Please Mum I want to talk to you." Mama ta harare shi ta ce. "Bani da wannan lokacin, bani da lokacin magana da kai Ameen, So ka bani hanya in wuce ana jira na, and i have important something to do now." Ya kama hannunta tare da marairaicewa ya ce. "Please Mum, na san ni mai lefi ne a gurin ki, amma just 5 minutes ki tsaya ki saurare ni." Mama ta kalle shi tana sauke ajiyar zuciya, ko ba komai ta ji daɗi data gan shi cikin k'oshin lafiya. Ta zare hannunta daga nashi ta juya ta koma cikin falon, ya yi ɗan murmushi tare da bin baya ta sannan ya ce. "Thank you." Bayan sun zauna Mama ta fara magana cikin sanyin murya mai nuni da damuwa. "Yanzu Ameen abun da ka yi ka kyauta mana kenan? More especially ma ni da ka san zan damu over, muna cikin wannan halin tashin hankalin amma a nemeka a rasa, sannan ka kashe wayoyinka, bayan ka kunna kuma in an kira ka sai ka ƙi d'agawa." Ya lumshe ido ya buɗe ya ce. "I'm sorry Mum."Mama ta ce. "I don't want your stupid sorry, ka riƙe haqurin ka, abun da nake so kawai just tell me what happened to you? Ina ka shiga through out today? And me yasa kuma ka kashe wayoyinka?" Ya kalli fuskarta ya ce. "Nothing Mum, kuma babu abun da ya faru da ni." A fusace Mama ta ce. "You are lier Ameen, like every time if I asked you to tell me what is wrong with you. Amma yanzu ma i will not force you to tell me kamar kodayaushe, zan barka tunda haka kake so, just i will pray for you kamar yadda kake buƙata." Ta miƙe tana sauke numfashi da sauri alamun ranta a matuƙar ɓace yake. Ya miƙe shi ma tare da kamo hannunta cikin tsananin damuwa ya ce. "Bana son na ga kina ɓata ranki a kaina Mum, sai in ji gaba-d'aya na tsani kaina, dan Allah ki koma ki zauna mu yi magana." Mama ta ce. "I think five minutes Ka ce, kuma ta yi har ma ta wuce." Ya ce. "Please Mum." Mama ta sauke numfashi cikin sanyin murya ta ce. "Ameen! Ni mahaifiyarka ce?" Ya ce. "Yes you are." Ta ce. "To meyasa baka son faɗa mun damuwarka? Ameen barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa, ni na san akwai abun da yake damun ka, kuma ba ƙaramin abu ba ne, yanayinka ya tabbatar mun da haka, amma ban san dalilin ka na ƙin sanar mun ba, ni kuma indai zanke ganin ka a haka bazan taɓa iya haquri ba sai na tambaye ka. Ameen da damuwarka zan ji ko da ta Neehal?" Ya zaunar da ita shi ma ya zauna cikin damuwa ya ce. "Mama! wani abun da yake cikin ciki wuta ne, wanda idan ya fito zai cinye mutane da yawa, barin shi a cikin shi ya Alkhairi." Mama tay masa wani kallo ta ce. "Tunda ka san wutar ne me yasa kai zaka bar shi a cikin cikinka? ya cinye ka kenan?" Ya ce. "Ba zai cinye ni ba Insha Allah, I know." Mama zata kuma magana ya katse ta da faɗin. "Just pray Mum." Mama ta jinjina kai cikin raunin murya ta ce. "Shikenan Allah yasa mu dace, Amma Ameen ina jin wani iri a raina something so bad, bana son na rasa ka kai da Neehal a rayuwata, ku kaɗai ne garkuwata a duniyar nan, ku kaɗai nake kallo in ji sanyi a raina bayan mahaifiyata, more especially You!" Ya kwantar da kansa akan ƙafaɗarta bai ce komai ba, sai lumshe idonsa da ya yi. Mama ta shafa lallausar bak'ar sumar kansa ta ce. "Ameen! ka ji ƙaddarar data kuma samun mu ko? ban san me marainiyar Allah nan tay musu suke cutar da ita." Can ƙasan mak'oshi ya ce. "Akwai Allah!" Mama ta ce. "Da shi muka dogara." Ya janye kansa daga jikin Mama ya ce. "Where is she?" Mama ta nuna masa ɗakin Daddy da hannu dan ta gane Neehal yake nufi ta ce. "Tana can." Ya miƙe ba tare ya yi magana ba ya nufi ɗakin. Mama ta bi shi da kallo zuciyarta cike da son sanin abun da yake damun tilon ɗan nata k'waya ɗaya jal a duniya da ya sanyaya shi over haka. Ta miƙe tana sauke ajiyar zuciya ta fice daga falon. Neehal tana kwance idonta a lumshe tana tunanin da bata san ranar daina shi ba. A hankali ya turo ƙofar dakint ya shigo, ya tsaya yana kallon ta tare da hard'e hannayensa a ƙirji. Bata ji shigowar shi ba saboda bata duniyar da yake, daddaɗan k'amshinsa da ba ya taɓa buya matuƙar yana guri shi yasa ta buɗe idonta, saboda yanda ta ji gaba-ɗaya ya mamaye mata hanci. Ta waro Idanunta waje waɗanda babu d'igon hawaye a cikin su, tunda ta kwanta take son ta yi kukan ko zata ji daɗin radadin da zuciyarta take mata amma kukan ya ƙi zuwa, sai yanzu ta gane ashe kukan ma rahama ne, ashe idan damuwa ta kai damuwa nemar shi ake a rasa? ta yunƙura tana ƙoƙarin tashi zaune cikin matuƙar dauriya. Ganin haka ya ƙarasa bakin gadon da sauri. Cikin marainiyar murya ta ce. "Yaya!" Ya rank'wafawa ya ce. "Na'am Miemerh!" Ta faɗa jikinsa da sauri tare da fashewa da kukan da take ta fatan ya zo mata tun d'azu sai yanzu ta ji sa. Ya runtse idanunsa tare da taune lip ɗinsa da ƙarfi, a hankali ya saka duka hannayensa ya zagaye bayan ta da su. Kuka take yi sosai mai taɓa zuciya gami da karyar da zuciyar mai saurarensa, wanda idan mutum mai saurin kuka ne zai iya taya ta. Numfashinta har wani sama_sama yake kamar zai ɗauke. Da sauri Ameen ya zare ta daga jikinta jin yanda take kukan kamar zata mutu, ya zauna akan gadon sosai sannan ya d'ago fuskarta yana fizgar da huci mai zafi ya shiga girgiza mata kai. Ta kwantar da kanta akan ƙafaɗarsa ta cigaba da rera da kukan ta. Ya jinjina bayansa da prame ɗin gado tare da lumshe idonsa zuciyarsa na wani irin bugawa. Bai ce mata komai ba kuma bai yi yunƙurin hana ta kukan ba, sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi shiru ta shiga sauke ajiyar zuciya. Jin ta yi shiru ya buɗe idonsa ya zuba su akan fuskarta, wadda ta yi jajur saboda kuka. Ya ɗora hannunsa akan fuskar ya ji zafi zau kamar garwashi. Ta cire hannunsa daga kan fuskarta ta rike da nata hannun ta d'ago kanta daga jikinsa, cikin magana da ƙyar ta ce. "Yaya sun sace Sadik, Yaya me nay musu? Please Yaya ka karb'o mun shi dan Allah kar su cutar da shi, kar su kashe mun shi kamar sauran, ka ji Yaya." Ameen ya shiga goge mata hawayen fuskarta ya ce. "I promised to you Miemerh, zan nemo miki Sadik a duk inda yake Insha Allah." Ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tana ƙara riƙe hannunsa. "Thank you Yaya, dama na san kai kaɗai ne zaka dawo mun da shi, Yaya ka je ka karb'o mun shi yanzu_yanzu karka bari ya kwana su kashe shi, Yaya in ya mutu nima mutuwa zan yi, ka yi sauri ka ji Yayana." Ya ƙura mata ido ganin yanda take magana kamar bata cikin hayyacinta, ga dukkan alamu tashin hankalin da take ciki ya rud'ar da ita ba kaɗan ba. Ta saki hannunsa ta mayar da kanta ta kwantar a jikinsa tare da lumshe idanunta tana sassauke ajiyar zuciya akai_akai. A lokacin Mama ta dawo ɗakin da ledar drugs a hannunta, kallo ɗaya tay musu ta ɗauke kanta. A hankali Ameen ya zare Neehal daga jikinsa ta koma ta kwanta, wadda ta yi wani irin shiru jikinta kamar na wadda ta suma duk ya shika, sai numfashinta dake fita da sauri da sauri. Mama ta ɗauki mug ɗin tea tana faɗin. "Taso ki sha Daughter kar ya yi sanyi." Neehal ta buɗe idonta a hankali ta zubawa Mama su, Mama ta dubi Ameen ta ce. "Taimaka mata ta tashi zaune." Ya amsa mata da kai sannan ya tayar da Neehal zaune, ya saka mata pillow a bayan ta Sannan ya miƙe. Mama ta ce. "Ka je gurin matarka kuwa? Yarinyar nan yau gaba-d'aya cikin zullumi ta wuni." A hankali ya ce. "Yanzu zan je na gan ta, daga nan sai mu wuce gida." Mama ta ce. "Shikenan Allah ya kiyaye hanya." Ya amsa da Amin sannan ya fice daga ɗakin. Mama ta zauna a bakin gadon tare da miƙawa Neehal mug ɗin hannunta ta ce. "Take it." Neehal ta girgiza mata kai, Mama ta ce. "Ki yi haquri ki daure ki sha ko kaɗan ne, baki da lafiya Neehal ba zai yiyu ki zauna da yunwa ba." Ta buɗe baki da ƙyar ta ce. "Bakina ɗaci Mama, ba zan iya sha ba, ko na sha ma amai zan yi." Da ƙyar Mama ta lallaɓa ta, ta sha tea ɗin kaɗan, sai dai kamar yadda ta faɗa kurb'a uku kawai ta yi ta dawo da shi. Dole Mama ta haqura ta ƙyale ta, magungunan ma fasa bata ta yi, dan ta san su ma in tasha amansu zata yi. Tana son tay mata allura amma saboda cikin ta babu abinci yasa batai mata ba dan kar ta galabaitar da ita. Sai ruwa ta ɗebo ta goga mata a jikinta da towel saboda zafin da jikin nata ya yi, ta kuma kama mata kanta ganin yanda take ta dafe kan da hannunta. Goma saura Hafsat ta zo ta yiwa Mama Sallama, wai za su wuce gida ita da Ameen. Mama tay musu addu'ar Allah ya kiyaye hanya. Neehal dai tana kwance idanunta a lumshe amma ba barci take ba, tunanin Sadik da rashin sanin halin da yake ciki a yanzu kawai take. Ko yana raye ko a mace sai Allah. Tana ji su Aunty A'isha da Aunty Sadiya da Hajiya suka shigo ɗakin suna tambayar jikinta tare da yi mata sannu, amma ko ido ta kasa buɗewa ta kalle su. Sha ɗaya saura Daddy ya shigo ɗakin, Mama tana zaune ita kaɗai akan darduma tana jan carbi. Ya zauna a bakin gado yana duban Neehal ya ce. "Bacci take ne?" Mama ta ce. "Ehh." Daddy ya girgiza kansa ya ce. "Allah ya kawo miki ƙarshen wannan abun Daughter." Mama ta ce. "Amin, bari na kawo maka wani abun ka ɗan saka a cikinka, na san yau babu abun da ka ci." Ya ce. "Doctor bar abun cin nan, babu abun da zai iya shiga cikina a yanzu." Mama ta ce. "Daurewa zaka yi ka ci ko kaɗan ne, yau ɗaya amma ba ka ga yadda ka faɗa ba." Daddy ya ce. "Ina cikin tsananin tashin hankali ne Doctor." Mama ta ce. "Addu'a ce mafita Gen." Daddy ya ce. "Haka ne ita muke ta yi, yanzu ma masallaci zan tafi, na saka a kwana yau ana karatun Alkur'ani, to na san ko na zauna a gida ba bacci zan yi ba, shi yasa na ce gwara na je kawai a yi karatun tare da ni, ko na ji daɗi a raina." Mama ta ce. "Shikenan, Allah ya amsa mana addu'oin mu, ya bayyana mana wannan yaro." Daddy ya ce. "Amin Amin." Sannan ya shafa kan Neehal yay wa Mama Sallama ya tafi masallaci. Daren yau mutane da yawa ba su rintsa ba, Mama kwana ta yi tana Sallah tana kaiwa Allah kukan ta, haka ma Maamah mahaifiyar Sadik da Abbansa, Aunty Sadiya ma kwana ta yi tana bincike a system ɗinta da wayarta. Neehal kuwa wannan daren da tunanika ta raya shi. Ta fara tunanin farkon haɗuwar ta da Jameel har zuwa lokacin da ya rasu ya bar ta da tarin k'aunarsa a ranta, ta tuno Anwar shi ma da irin soyayyar da suka sha kamar babu gobe, ta tuno Ahmad da tarin k'aunar da ya nuna mata, ƙarshe kuma suka rabu. Sai Sadik wanda ta saka a ranta shine mutum na ƙarshe wanda zata yi soyayya da shi a rayuwarta, ta sakankance shi zai zamto abokin rayuwarta na har abada. Amma shi ma sai da *BAK'AR ƘADDARA* ta raba su a ranar d'aurin Auren su. Ta gane bata da sa'a a soyayya kamar yadda ta fitar da rai da yin aure a rayuwarta. Ta haqura da soyayya balle har ta yi tunanin yin aure, tunda aka sace Sadik a ranar Aurensu to babu makawa ko da ta yi aure mijin data aura ma ba zai tsira ba, za'a iya biyo shi har cikin gidansu a kashe shi. Ita kuma abun da zuciyarta baza ta kuma ɗauka ba kenan, ta san idan hakan ta faru bugawa zuciyarta_ta zata yi ta mutu. Ta gaji da sai ta shak'u da mutum sannan a raba su, rabuwa ta har abada. She accepted her destiny, zata k'are rayuwarta a haka babu aure, wannan ita ce *ƙaddarar ta*. Tana fata da kuma addu'ar Allah ya bayyana Sadik cikin k'oshin lafiya, amma ba dan ya dawo su yi aure ba, sai dan farincikin ahalinsa. Sai wajen asuba bacci mai kama da suma ya ɗauke ta, a cikin barcin mafarkai ta dinga yi barkatai, wani wai gashi an ga Sadik cikin mawuyacin hali, wani kuma gawarsa aka gani an kashe sa, wani kuma ya dawo cikin k'oshin lafiya har an yi auransu suna rayuwarsu cikin farinciki. Duk mafarkan nata dai akan Sadik ne da kuma halin tashin hankalin da ake ciki game da ɓatan sa. Da asuba da Mama ta tashe ta da ƙyar ta iya tashi ta yi Sallah a zaune. Kafin safe jikinta ya rikice sosai da zazzafan zazzaɓi, jikinta har rawa yake ga matsanancin ciwon kai. Hankali a tashe Mama da Aunty A'isha suka ɗauke ta suka nufi asibiti da ita. Suna zuwa aka ba su gado, wanda zuwa lokacin Neehal ta galabaita matuƙa. A asibitin suka wuni, yayin da ƴan dubiya da suka samu labarin ciwon nata suke zuwa ko ta ina duba ta. Ahmad da su Ummi ma sun zo sun duba ta, Ahmad ya tsaya a bakin gadon marasa lafiyar da take kwance yana kallon ta cikin tsananin tausayin ta. Ya shafi gefen kuncinta ya ce. "Allah ya baki lafiya Princess." Kamar kar ya tafi ya zauna yay jinyar ta haka yake ji. Sai can yamma Ameen da Hafsat suka zo asibitin amma har dare ba su tafi ba. Da daddaren Mama ta matsa aka sallame su daga asibitin, ta ce zata cigaba da kula da ita a gida. Neehal dai bata um bata Um'um, sai dai tay ta kallon mutane. Hajiya ta ce, al'amarin nan nata fa sai an haɗa mata da rubutun dangana ta sha. Haka kuwa aka yi Daddy yasa akai mata rubutun ya zamto ruwan shan ta. Kwana uku da ɓatan Sadik amma shiru babu wani labari har yanzu, addu'a kam an dage yinta ake, a gefe guda kuma jami'an tsaro suna ta aikin nasu binciken. Zuwan su biyu gidan Mama domin yiwa Neehal tambayoyi a matsayin ta na wadda suka yi wayar ƙarshe da Sadik kafin a sace shi, amma halin da take ciki yasa ba su samun damar yin magana da Ita ba. Baƙin da suka yi saura a gidan tuni kowa ya koma gidan sa, su Aunty ma sun koma gidajensu amma kullum sai sun zo, dan ita kanta Maman tausayi take ba su, dan za'a bata gado tsaf Ita ma zata kwanta, dauriya da ƙarfin hali kawai take. Hajiya ce kaɗai bata tafi ba. Mommyn Hameedah ma ta gama yada habaibaice_habaicen ta tasa tuzuruwar ƴarta a gaba sun tafi. Uncle Usman da iyalansa ma basu koma Nijar ba, suna gidan Uncle Umar, a part ɗin Aunty Fauziyya suke zaune tunda bata gidan. Neehal ta fara magana kaɗan_kaɗan, idan aka yi mata magana yanzu tana amsawa da um ko um'um. Doguwar maganarta kuwa sai idan Ameen ya zo gidan, ta dinga ce masa. "Yaya ka karb'o mun Sadik ɗin? dan Allah Yaya ka karb'o shi kar su cutar da shi." Shi kuma sai ya lallaɓa ta tare da tabbatar mata da Insha Allahu Sadik zai dawo cikin k'oshin lafiya. Sai karatun Alkur'ani da kullum suke yi tare da Mama safe da dare, shine yake ɗan sanyaya mata zuciya yasa ta ji damuwarta na raguwa. Haneefah ma idan ta zo gidan tana iyakar ƙoƙarinta wajen ganin ta rage mata damuwar dake ranta, ta hanyar yi mata hira da nasihar yadda da ƙaddara cikin sigar rarrashi. Ranar juma'a wanda ya kama sati guda cif da ɓatan Sadik, da yamma Maamah suna zaune a main Parlour'n gidan ita da ƴan'uwanta da ba su koma gida ba har yau, sai Hajiya kakarsu Sadik. Suna zaune jigum_jigum kamar gidan zaman makoki, ko da yake su da mutuwa ma Sadik ɗin ya yi sai hankalinsu ya fi kwanciya tunda sun san ba ya raye, akan wannan zullumun da fargabar rashin sanin halin da yake ciki da suke. Mai gadin gidan ne ya faɗo Parlour'n yana ta zuba haki babu ko sallama. Hajiyarsu Sadik ta ce. "Lafiya kuwa malam Ayuba ka faɗo mana cikin gida a ruɗe babu sallama?" Sai a lokacin Maamah dake jan carbi ta d'ago kanta tana jin zuciyarta na wani irin bugu. Waje malam Ayuba yake nuna musu da hannunsa amma ya kasa magana sai rawar baki yake alamun yana so ya ce wani abu maganar ce ta ƙi fitowa. Hajiya ta buɗe baki zata kuma magana amma shigowar Sadik Parlour'n a matuƙar sanyaye ya hana ta faɗar abun da tay niyya........✍️ _*Na so page ɗin ya fi haka tsayi, amma rashin caji ya hana yiyuwar hakan, and ban yi edit ba a yi haquri da typing errors.*_ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *6️⃣2️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ..........Kafin Yamma Labarin sace Sadik ya baza ko ina a cikin jihar nan da ma mak'wabtan ta. Sakamakon hotunansa dake ta yawo a social media tare da note ɗin ɓatan da ya yi. Abun da yake ƙarawa labarin nasa armashin yaɗuwa sace shin da akai a ranar D'aurin Auren sa, and kuma amaryar tasa wadda yake shirin angoncewa da ita fitacciyar ƴar jarida ce wadda duniya ta san ta. Su Daddy sun so a ɗaura Auran a yau ko dan jama'ar da aka tara amma dangin Sadik suka ƙi amincewa, haka suka dawo gida jiki a sanyaye. Kawu Musa ya ce, suna da gaskiya, kuma ko waɗanne iyaye ne ɗansu ya ɓata abun da zasu yi kenan, suna cikin zullumi da damuwar ɗansu baza su bi takan wani d'aurin Aure ba. Uncle Usman ya bayar da shawarar a ɗaurawa Neehal Aure da wani saurayin idan tana shi kowa ya huta da wannan fargabar. Amma Daddy ya ce baza a yi haka ba, domin Dangin Sadik zasu ga kamar ba su damu da ɓatan Sadik ba, tunda har suka iya ɗaurawa Neehal Aure a yau, idan suka yi haka ba su yi musu kara ba. Gidan bikin Mama ma ya koma kamar na zaman makoki like gidansu Sadik, Haneefah ta ci kuka ta k'oshi, haka ma Aunty A'isha da Hajiya. Aunty Sadiya mai ɗan dauriya a cikin su, Mama kuwa ko magana bata iya yi, tana zaune kawai ta tafka tagumi. Neehal kam tun bayan data suma aka dinga shafa mata ruwa a fuska da ƙyar ta farfaɗo tana ambaton sunan Sadik tare da roqon kar ya tafi ya bar ta. Ganin bata cikin hayyacinta kuma a firgice take yasa wata abokiyar aikin Mama tay mata allurar bacci, aka ɗauke ta aka kaita ɗakin Daddy aka kwantar. Bayan Sallar la'asar gaba-ɗaya ƴan'uwa na jiki suka hallara a main Parlour'n Daddy dan tattaunawa akan al'amarin, tunda zuwa yanzu sun fuskanci saboda Neehal aka sace Sadik. Daddy, Kawu Musa, Uncle Usman, Uncle Umar, Uncle Mahmud, Uncle Ahmad (Mijin Aunty Sadiya) Abba, (Yayan Daddy) Mama, Hajiya, Aunty Sadiya, Aunty A'isha da Umma. Kawu Musa ya yi gyaran murya sannan ya fara magana kamar haka. "Zamu fara da Addu'ar Ubangiji Allah ya bayyana mana wannan yaro a duk inda yake, ya kuma kare shi yasa yana hannu na gari, idan kuma kamar yadda ake tunanin sace shi aka yi, to Ubangiji Allah ya toni asirin waɗanda suka sace shin cikin gaggawa." Gaba-ɗaya suka amsa da "Amin ya Allah." Daddy da hannunsa ke dafe da kansa ya d'ago yana girgiza kai ya ce. "Amma fa wannan abun akwai rikitarwa da tayar da hankali ba kaɗan ba." Mama ta sauke numfashi tare da janye tagumin data rafka, cikin sanyin murya mai nuni da tsantsar damuwar da take ciki ta ce. "Tabbas a yau na yarda da maganar Sadiya 100%, ko shakka babu wanda ya kashe Jameel shi ya kashe Anwar, haka nan kuma shi yasa aka sace Sadik yanzu ma, kuma duk saboda Neehal." Daddy ya ce, "Ni kuma bana tunanin hakan gaskiya." Cikin takaici Uncle Usman ya ce. "To idan ma hakan ne waye yake aikata hakan? kuma akan me? Me yarinyar nan tay masa?" Cikin dashashshiyar muryar da ta ci kuka ta k'oshi Aunty A'isha ta ce. "Na fi tunanin koma waye son ta yake, shi yasa baya son kowa ya aure ta." Aunty Sadiya ta ce. "So?" Sai kuma ta yi ɗan murmushi ta ce. "Hmm, duk wanda yake aikatawa Neehal wannan abun ba son ta yake ba, wata mummunar manufar ce da shi a gare ta." Uncle Mahmud ya ce. "Me yasa zaki ce haka Haleemah? Nima zuciyata ta fi yarda da abun da A'isha ta faɗa na wani ne yake son Neehal ɗin, shi yasa yake kashe duk wanda zata aura, yanzu kuma sai ya sace Sadik ya canza salo." Aunty Sadiya ta miƙe ta yi taku hannayenta cikin juna tana zira yatsunta a tare tana zarewa, sannan ta ce. "Idan har dagaske son ta yake son Allah ba ƙoƙarin cutar da ita ba me yasa ba zai bayyana kansa a gare ta ba? Me yasa ya san idan har ya bayyana kansa a matsayin wanda yake kashe mata duk wanda zata aura saboda yana son ta ya san baza ta taɓa amincewa da auren shi ba, amma kuma yake aikata hakan? Ya kamata Ku yi tunani da kyau akan wannan idan har son ta yake da gaske ba zai taɓa aikata mata haka ba, kamar yadda na faɗa wata mummunar manufar ce da shi a gare ta, ko kuma akwai wani abun da yake son gudanarwa da ita, amma kuma Allah bai ba shi sa'a ba har yau, kuma ga dukkan alamu mummunan kudirin sa a kan ta da zarar ta yi aure ba zai samu ba, shi yasa yake aikata hakan." Gaba-ɗaya suka yi shiru suna kallon ta kowa yana auna maganganun ta a mizanin hankali. Ta koma ta zauna sannan ta dubi wani sashi na Falon ta ce. "A binciken da nake gudanarwa fiye da shekara akan al'amuran Neehal akwai wanda nake zargi, kuma a Ƴan kwanakin nan wasu alamomi suka ƙara ƙarfafa mun zargin nawa a kansa." A hanzarce Daddy ya ce, "Wa kike zargi Barrister? Ki yi gaggawar sanar mana in saka a damk'o sa a bincike sa." Uncle Umar ya ce, "Wannan haka ne, kuma shine abun yi, domin kuwa wannan abun ya yi yawa, mun gaji, muna san sanin gaskiyar al'amarin." Suka gyaɗa kai gaba-d'ayan su alamun haka ne. Aunty Sadiya ta ce. "Zargi nake ban tabbatar ba, shi yasa ba zan sanar muku a yanzu ba, na fi son sai na samu cikakken evidence k'wakwk'wara." Uncle Mahmud ya tari numfashinta da faɗin, "Amma ai a tsarin doka ma ana gudanar da wanda ake zargi a gaban shari'a, ko da ba'a tabbatar ya aikata lefi ba, ke me yasa baza ki faɗa ba?" Hajiya da bata yi magana ba tun d'azu sai yanzu ta ce. "Gaskiya ne, ya kamata ki faɗi wanda kike zargin, in ma ba shi ba ne wataƙila sanadiyyar hakan sai ki ga an gano gaskiya." Umma ta ce. "Haka ne, Sadiya ya kamata ki faɗa mana wanda kike zargi domin a san abun yi a kansa." Aunty Sadiya ta numfasa ta ce. "Ku yi haquri, na san zuciyoyinku a zak'e suke da sanin ko waye, amma ku sani wannan case ɗin na Neehal ya sha banban da case ɗin laifukan da muka saba ji da gani, idan har ban yi takatsantsan ba to zan iya kwana a ciki." Abba ya ce. "Kamar ya? Ba bincike ba ne? Ai idan aka gane mutum ba shi da hannu a ciki sakin sa za'a yi." Aunty Sadiya ta ce. "Ku dai yi haquri, Insha Allahu nan ba da jimawa komai zai bayyana, mu dai kawai mu dage da addu'a." Kawu Musa ya ce. "To Allah yasa mu dace, amma ba kwa tunanin ko akwai wani da suka samun saɓani da yarinyar nan ya k'ullace ta yake aikata mata wannan abun?" Mama ta ce. "Bana tunanin haka gaskiya, dan Neehal bata da abokin faɗa a rayuwarta, na san wani lokacin bata da haquri idan aka ɓata mata rai, amma bana jin zata yiwa wani babban abun da zai sa ya dinga bin ta da wannan mummunan abun a matsayin ɗaukar fansa ko hukunci." Kawu Musa ya ce. "To idan ba haka ba kuwa zata iya yiyuwa ko shi Gen. da ya kasance babban mutum mai tare da ƴan adawa a ƙasar nan saboda shi ake aikata wannan abun, domin a ɓata masa suna ko kuma dan wata manufar daban." Suka yi shiru cikin alamun nazari. Daddy yana jinjina kai ya ce. "Kuma fa Alhaji Musa zancen ka akwai k'amshin gaskiya, dole ne in tsaurara bincike akan wannan al'amarin, domin kuwa na san zuwa yanzu sunana dana iyalina ya fara ɓaci a idon duniya." Uncle Mahmud ya ce. "Wannan shawarar ta yi, kuma ita ma Neehal ɗin ya kamata a tuntube ta akan maganar da Alhaji Musa ya yi ta farko, akan ko sun taɓa samun matsala da wani, like criminal person haka, ko kuma wani da suka samu saɓani ya taɓa yin wani mummunan ƙudiri a kanta a matsayin ɗaukar fansa." Abba ya jinjina kai ya ce. "Ya kamata kam, domin komai zai iya faruwa, tunda mu har yanzu lalube muke a cikin duhu, muna neman gaskiyar al'amari." Umma ta ce. "Har wannan ƙawarta_ta itama a tuntube ta ko san wani abu akai, tunda kodayaushe suna tare." Aunty A'isha ta ce. "Wai Haneefah kike nufi?" Umma ta ce. "Ehh." Aunty A'isha ta ce. "Insha Allahu duk zamu yi ƙoƙarin yin hakan, Allah Ubangiji dai ya toni asirin masu aikata wannan abun da gaggawa, ko zuciyoyinmu zasu samu salama." Suka amsa da Amin, kuma kowa ya yi na'am da wannan shawarwarin da aka bayar. Aunty Sadiya dai kawai kallon su take bata ce komai ba, cikin ranta tana tunanin wani abu daban. Uncle Usman ya ce, "Ni Neehal ɗin ma nake tausayawa, yarinya duk za'a sa ta tsani kanta da rayuwarta, dan babu wanda zai so a ce ana rasa rai ta dalilin sa, ko kuma an cutar da wani." Kawu Musa ya ce. "Wallahi fa, tunda k'uruciyarta za'a ɗora mata tension ɗin da ya fi ƙarfin kanta." Umma ta ce. "Ƙaddara ce, wadda ta riga fata, babu yanda zamu yi, sai dai mu yi addu'ar Allah ya tsayar haka, kuma da izinin Allah komai zai zo ƙarshe, zai kuma zama tarihi kamar ba'ai ba." "Haka muke fata." Cewar Uncle Umar. Hajiya ta ce. "Tana kwance har yanzu ko?" Aunty A'isha ta ce. "Eh, tunda akai mata allurar bacci bata farka ba har yanzu." Mama ta ce. "Bari mu gama sai in je in tashe ta, na ga yamma ta yi sosai Magriba ta gabato, gwara ta tashi ta yi sallolin dake kanta." Hajiya ta ce. "Ni fa da wannan abun ya faru na yi zargin ko dai aljanu ne da yarinyar nan." Kawu Musa ya ce. "Zata iya yiyuwa su ɗin ne ma, amma kuma shi sha'anin jinnu ba haka yake ba akan al'amarin Aure, yawanci tun kafin maganar aure ta yi nisa suke tarwatsa abun, ko kuma ki ga yarinya ta girma sosai babu mashinshini, amma indai ba turo su akai ba zai yi wahala su yi kisa, in ma zasu yi kisan ba ta hanyar harbi ba, sai dai kawai a wayi gari a ga mutum ya rasu." Umma ta ce. "Tabbas haka ne, dan na taɓa ganin yarinyar da irin wannan ya faru da ita, ita auranta aljanin ya yi, da farkon ƴan'matancinta tana samari, daga baya kuma sai suka daina zuwa dif, sai daga baya aka gane aljanin ne ya aure ta." Aunty A'isha ta ce. "Subhallahi, Allah ya kiyaye mu da zuri'armu baki ɗaya. Suka amsa da Amin. Uncle Mahmud ya ce. "Hakan ma zata e yiyuwa, kin san su ma aljanun babu abun da ba za su iya ba, sai a gwada yi mata magani a ga ko Allah zai sa a dace." Kawu Musa ya ce. "Allah yasa mu dace, yasa mu fi ƙarfin zuk'atanmu, ya kare mu daga abun da yafi ƙarfin mu, ya raba mu da mummunar ƙaddara." Suka ƙara Amsawa da Amin. Abba ya nisa ya ce. "Ni fa ina da wata shawara, a gani na tunda duk wannan abun da ake yi mun fahimci saboda kar yarinyar ta yi aure ne, auren ne ba'a son ta yi, me zai hana a ɗaura mata Auren kawai ta tare a gidan mijinta ba tare da duniya ta sani ba, kun ga kenan daga lokacin da tai auran koma waye yake bibiyarta da mugun nufinsa ta yi auranta, magana ta ƙare." Uncle Usman ya ce. ,"Tunanin dana yi d'azu kenan nima, na ce a ɗaura mata auran a yau, amma Daddy'n ta ya hana." Dad ya ce. "Ba wai na ƙi ba ne, abubuwa guda biyu na duba, na farko iyayen yaron Sadik nan baza su ji daɗi ba idan muka ɗaurawa Neehal Aure a yau, zasu yi tunanin ba ma mu damu da ɓatan ɗansu ba ta auran ƴarmu kawai muke, alhalin kuma duk mun fuskanci ko na ce muna tunanin saboda da ita aka sace shi, duk da ba ma fatan hakan. Na biyu kuma ita kanta yarinyar bazai yiyu tana cikin halin baƙin ciki da tashin hankalin ɓatan Sadik sannan mu ƙara mata da wata damuwar mu daura mata aure da wanin sa ba da sanin ta ba, may be wanda zamu aura matan bata son shi, kun ga mun jefa ta a cikin wata damuwar bata gama fita daga wata ba." Suka jinjina kai gaba-d'aya cikin gamsuwa da bayanan Daddy. Mama ta ce, "Maganar ka gaskiya ce Gen. Amma in dan wanda Neehal zata aura ne ba mu da matsala da wannan, dan ta son yaron nan Ahmad Baban twins, shima kuma yana son ta, gashi yaron kirki ne ba shi da matsalar komai haka ma iyayensa, amma kamar yadda ka faɗa koda za'ai mata auran ba yanzu ba, mu ɗan jira zuwa wani lokaci kafin nan Insha Allahu mun warware daga cikin wannan matsalar, dan yanzu babban burin mu Allah ya bayyana mana Sadik cikin k'oshin lafiya." Haka dai suka ci-gaba da tattaunawa, shi Daddy yana ganin gwara a jira bayyanar Sadik idan ma Auren za'ai wa Neehal a aura mata shi. Uncle Mahmud ya ce, kamar hakan da wuya, tunda a rabuwar da suka yi ɗazu da danginsa sun nuna ko Allah ya bayyana shi ba zai auri Neehal ba, kuma ba ya jin yanda suka ɗauki zafi akan al'amarin zasu amince ta cikin ruwan sanyi. Suna cikin tattaunawar ne Aunty Sadiya ta ce. "Wai ina Ameen ne? Yau gaba-d'aya duk wannan abun da ake ban gan shi ba." A ɗan firgice Daddy ya ce. "Bai zo gidan nan ko da safe ba? Ni sai ma yanzu da kikai magana na yi released ban gan shi ba yau kwata_kwata ko a gurin d'aurin Auren." Cikin damuwa Mama ta ce. "Nima rabo na da shi tun jiya da rana, to ina yaron nan ya shiga?" Hajiya ta ce. "Matar shi ma haka ta ce, kuma tun safe take kiran wayarsa a kashe." Kawu Musa ya ce. "Subhallahi, Allah dai yasa lafiya yake." Uncle Ahmad ya ce. "Insha Allahu yana lafiya k'alau, kun san halin Ameen, may be ya samu wannan labarin ne shi yasa bai zo ba saboda tashin hankali." Daddy ya ce. "To kuma sai ya kashe wayoyinsa, Ameen da koyaushe wayoyinsa a kunne suke." Mama da gabanta ke faɗuwa ta ce. "Bari na dauko wayata na kira shi mu ji ko zata shiga yanzu." Uncle Mahmud ya ce. "Bari na kira shi ba sai kin tashi ba." Ya ƙarashe zancen tare da zaro wayarsa daga aljihun gaban rigarsa. Yana kira ta shiga, sai dai har ta katse bai ɗauka ba. Mama ta ce, "To ina Yaron nan ya shiga ya bar wayar tasa kuma?" Daddy da yanayinsa ya nuna rud'ewa ya ce. "To shi kuma me ya faru da shi?" Umma ta ce. "Babu komai Insha Allahu, tunda wayar ta shiga zai biyo bayan kiran ko anjima ne, wataƙila ba ya kusa da wayar ne, ku kwantar da hankulanku, kar ƙarawa kanku wata damuwar, mu yi masa addu'a kawai." Sukay shiru kowa da tunanin da yake a cikin ransa. Kiran Sallar Magriba ne ya tashe su. A ɓangaren su Abban Sadik su ma bayan dawowar su daga masallaci suka zauna zaman cigaba da tattaunawa akan al'amarin. Suma kamar su Daddy sun amince dalilin Neehal aka sace Sadik, har wasu k'annen Abba na cewa k'ila ma da haɗin bakinta, tunda ita ce last wanda ya yi waya da ita cikin dare. Abba ya ce, ya yarda ta sanadin Neehal aka sace Sadik, shi ma hakan zargi yake ba wai ya tabbatar ba ne, amma sam ba zai taɓa yarda da saka hannunta ko haɗin bakinta a sace shin ba, dan ya san baza ta taɓa cutar da Sadik ba. Kuma batun waya da suka yi, ai idan aka duba Sadik ɗin ne ya kira ta ba ita ta kira shi ba, bare ace akwai abin da ta shirya a wayar suka yi. Abby ya ce duk wannan maganganun ba su ne mafita ba, mafita kawai a dage da addu'ar Allah ya bayyana Sadik. Maamah ta farfaɗo, amma ko magana bata iya yi, ƴan'uwan ta na kanta suna yi mata firfita. Ƴan'biki kuwa duk an watse cikin alhakin abun, sai ƴan'uwa na jiki ne da baƙin nesa sukay saura, al'amarin dai babu daɗin ji ko kaɗan, abun tausayi da rud'ani. A ɓangaren Ahmad al'amarin ya rud'a shi fiye da tunanin mai karatu, musamman da Zahra ta sanar masa abun da ta ji ana faɗa a gidansu Neehal lokacin da suka riski labarin ɓatan Sadik, cewar samarinta biyu na baya ma kashe su aka yi. Abun ya matuƙar ɗaure masa kai da jefa shi cikin tunani, Neehal ta sanar masa samarinta biyu sun rasu, amma bata ce masa kashe su akay ba. Idan kuwa har haka ne ya tabbatar da akwai wata b'oyayyiya kenan a rayuwar Neehal ko kuma ya ce wata babbar matsala. A gefe guda kuma tausayinta mai tsanani ne ya cika masa zuciya, a ransa ya dinga faɗin wannan wanne irin zalunci ne ake mata haka? Wunin yau gaba-d'aya cikin tunanin al'amarin ya yi shi, ya kulle kansa a ɗakin da yake sauka a gidan Mamy, Sallah ce kawai take fito da shi. Hankalinsa in ya yi dubu yau a tashe yake, ba ya son wani mummunan abun ya samu Princess ɗin sa, yanda yake jin zuciyarsa ba abun da yake buƙata sama da ya je ya ga halin da take ciki, dan ya san tana can tana kukan nan nata, ya san hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, abun da yake ƙara d'aga masa hankali da Zahra ta ce har suma ta yi. Twins ma waɗanda su Ummi suka taho da su gidan Mamy sai kuka suke suna kiran Aunty, da ƙyar Ummi ta lallame su suka ci abinci. Ummi saukar su kenan ita da Abban su Ahmad suka tarar da wannan mummunan labarin, hakan yasa ba su wani jima ba a gidan Mama suka yo gidan Mamy tare da Mamin da ta je bikin ita ma, tunda maganar biki kuma ta tashi tunda babu Ango. Zuciyoyinsu babu daɗi ko kaɗan, wuni suka yi suma suna jimanta wannan al'amarin mai rikitarwa. Neehal da ahalinta sun ba su tausayi sosai, more especially ma Neehal da ƙarshe komai a kanta zai ƙare. Mama tana zaune a bakin gadon Daddy, ta saka Neehal dake kwance a gaba tana kallon ta cikin tsananin tausayawa bayan ta idar da Sallah. Tunanin rayuwar Neehal kawai take da irin jarrabawoyin da take gamuwa da su a rayuwarta, tun tana ƙarama aka kashe mata iyayenta, ta tashi a wahalce a hannun iyayen riƙon ta, bayan ta dawo hannunta da zama kuma danginta suka nuna suna ƙin ta ƙuru_ƙuru ba k'aunarta suke ba, ta san wannan abun ma yana damun ta, boyewa kawai take tana barin abun a cikin ranta. Bayan ta isa aure kuma ta fara fuskantar wannan challenges ɗin, abun ya yi mata yawa a ƙananun shekarunta. Daga nan Mama ta fara tunanin abun da suka tattauna d'azu, and she noticed one thing a zaman d'azu da akai game da Aunty Sadiya, tana magana ne kamar mai habaici a gurin, tana kuma yin wani irin kallo kamar na gargadi' ko kuma na tuhuma. Gashi ta ƙi faɗar wannan ta ce tana zargin, Mama ta kasa gane me Aunty Sadiyan take nufi da kuma inda ta dosa, amma ta k'udurce a ranta zata tambaye ta idan sun keɓe. Sai kuma ta juyar da akalar tunanin nata kan Ameen bugun zuciyarta na ƙaruwa, tana tambayar kanta ina ya shiga? Me yake yi har yanzu bai zo gidan ba? Kuma ana ta kiran shi ba ya pick. Bayan shigowar ta ɗakin ta masa kira ya kai sau biyar amma bai ɗauka ba. A hankali Neehal ta buɗe idonta da yay mata nauyi ta sauke su akan fuskar Mama. Cikin muryar marasa lafiya dake fita da ƙyar ta ce. "Mama!" Mama ta sauke wahalallen numfashi muryar Neehal ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi. A hanzarce ta ce. "Na'am, Daughter kin tashi? sannu kin ji." Ta ƙarashe zancen da kama hannayen Neehal duka a cikin nata. Neehal ta gyaɗa mata kanta wanda take jin sa kamar dutsen dala saboda nauyin da yay mata, ta fara hawaye ta ce. "Mama da gaske ne ba mafarki na yi ba Sadik ya ɓata an sace shi?" Mama ta mayar da k'wallar data tarar mata a ido dan kar ta ƙara karyar wa Neehal zuciya ta ce. "Eh Daughter, amma za'a gan shi Insha Allah, ana nan anata neman sa da cikiyar sa tare da addu'a." Neehal ta fashe da kuka mai karyar da zuciya ta ce. "Me nay musu Mama? Su waye suka ɗauke mun Sadik? Me yasa basa san na yi aure kamar kowa? Ya Allah in wani laifin nay maka ka yafe mun w....." Mama tay saurin rufe mata baki tana faɗin. "Ya isa haka Neehal, ki bar wannan maganganun kar ki je ki yi sab'o, gashi baki da lafiya. Ki yi haquri komai kika gani ya samu bawa rubutacce ne a rayuwarsa tun fil azal daga Ubangijin sa, wannan abun ƙaddarar ki ce da mu baki ɗaya, amma baza mu gaji da kaiwa Allah kukan mu ba, da shi kaɗai muka dogara kuma shi zai yaye mana, jarrabawa ce Neehal, kowanne Mumini akwai irin tasa, ki kwantar da hankalin ki Insha Allahu za'a ga Sadik." Ta lumshe ido hawaye masu d'umi na zubo mata, bata taɓa jin ta tsani rayuwarta irin yau ba, ta gaji da cutar da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da ake yi saboda ita. "Ya Allah kar ka ba su ikon cutar mun da Sadik, My Sadik where you? Ka dawo gare ni karka tafi ka barni kamar yadda su Anwar suka tafi suka bar ni Please, i'm in needing you in my life, please my Sadik come back to your wife." Abun da take faɗa a ranta kenan cikin ɗacin zuciya, kamar ta cire zuciyarta ta yar haka take ji saboda zafin da take mata. Har yanzu bata bar fatan ace zata farka daga wannan mummunan mafarkin da take ba, zuciyarta ta kasa yarda cewar da gaske ne abun da yake faruwa. Mama ta d'ago ta tana faɗin. "Tashi mu je ki yi wanka ko zaki ji daɗin jikinki, ki kuma rama sallolin dake kanki, sai ki sha ko tea ne ki sha magani, na ji jikin naki da zafi zau alamun zazzaɓi." Bata musa wa Mama ta ɗaure ta sakko dak'yar tana cize lip ɗinta hannunta dafe da kanta, Mama ta taimaka mata ta kai ta toilet ta yi wanka tare da brush ta ɗauro alwala sannan suka fito, kayan data cire ta mayar ta zira hijabin Mama ta tayar da Sallah, a zaune ta yi sallolin da ake bin ta duka ta haɗa isha'i da ake yi yanzu, ta daɗe tana addu'a cikin kuka a sujjadarta ta ƙarshe akan Allah ya bayyana Sadik, ya kuma kawo mata ƙarshen wannan al'amarin. Bayan ta idar ta lallaɓa ta koma kan gado ta kwanta, Mama bata ɗakin ta fita hado mata tea, wanda tana da yaƙinin a halin k'uncin da take ciki a yanzu ba zai iya shiga bakinta ba balle har ya wuce ta mak'oshinta ya tafi cikinta. Bata san musawa Maman ne kawai, amma ita a yanda take jin zuciyarta da Allah zai ɗauki ranta a yanzu da ta yi murna da hakan fiye da wannan rayuwar da take ciki. Mama ta dawo ɗakin ta ajiye mug ɗin hannunta ba tare da yi magana ba, sannan ta juya ta kuma fita dan ɗauko mata magani, sauri take saboda tana son ta yi ta kawo mata maganin sannan ta je gurin baƙin da suke rage a gidan, dan fiye da rabin mutanen d'azu duk sun koma gidajensu tunda maganar biki ta tashi. Ta buɗe ƙofar falon kenan da nufin fita suka yi karo da Ameen dake ƙoƙarin shigowa...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *6️⃣5️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ..........Bayan Sadik ya gama cin abinci suka haɗu gaba-ɗaya a Parlour'n Abbansa, shi, Abba, Maamah, Umma, Hajiya, Kawu da mahaifiyar Maamah da ƙannen Abba guda biyu. Abba ne ya fara magana da faɗin. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Masha Allah, muna ƙara godewa Ubangiji buwayi gagara misali, mai mayar da farin ciki zuwa baƙin ciki, da mayar da baƙin ciki zuwa farin ciki. Kwana takwas i war haka zuk'atanmu cikin tsananin farin ciki suke, amma cikin ikon Allah washegari sai ya canza mana zuk'atanmu zuwa baƙin ciki da fargaba da tsoro gami da zullumi. A yau kuma sai ya sauya mana su da tsananin farin ciki, muna fata kuma ya yarje mana mu cigaba da kasancewa cikin farin ciki har ƙarshen rayuwarmu, Ubangiji Allah kar ka ƙara maimaita mana irin wannan tashin hankalin da muka shiga har ƙarshen rayuwarmu." Suka amsa da Amin gaba-ɗayan su. Kawu ya kalli Sadik ya ce. "Masha Allah Abubukar, mun ji daɗin dawowar ka cikin k'oshin lafiya wanda ba mu taɓa zaton haka ba, babu irin sak'e_sak'en da ba mu yi ba akan ɓatan ka, mu ce kidnappers ne, mu ce ko masu satar mutane ne, mu ce ko kai ka gudu da kanka, mu ce ko asiri akai maka ka bazama duniya, babu abun dai ba mu ayyana ba, sai daga baya muka gane bakin zaren, amma duk da haka muna son jin ƙarin bayanin abun da ya faru daga gare ka wanda shi zai sa mu ƙara tabbatar da abun da muke zargi." Sadik ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce. "Misalin ƙarfe uku na daren ranar ina cikin yin Sallah na ji kamar motsi a bayan ɗakin da nake, wanda ga dukkan alamu ƙofar BQ ta baya ake bugawa da ƙarfi. Na cigaba da Sallah ta ba tare da tunanin komai ba a raina, amma kafin na sallame Sallar na ji an banko ƙofar falo da ƙarfi, gabana ya faɗi ba shiri na sallame Sallar na tashi na je na lek'a window, bana ganin Parlour'n sosai saboda babu wadataccen haske, amma ina iya hango alamun mutane a Parlour'n, kuma ɗakin da nake ciki suke tunkarowa. Na tsaya ina cigaba da kallon ikon Allah, cikin mintuna ƙalilan na ji ana dukan ƙofar ɗakin da nake, na koma bakin ƙofar da sauri na ƙara locked ɗinta, sannan na koma ƙarshen ɗakin ina ambaton sunan Allah tare da neman ɗaukin sa. Kawai sai gani na yi an banko ƙofar ɗakin ta faɗi ƙasa an ɓalle ta ɓal. Na firgita sosai tsorona ya ƙaru, ban gama zullumun ba na ga ana haske ɗakin da wata fitila mai hasken tsiya, sannan aka dallare mun fuskata da ita, hakan yasa ban tantance adadin mutanen da suka shigo ba, balle naga kammanin su, na fara kare idona saboda hasken fitilar dake ƙoƙarin yi masa illa, ba tare da sun ce mun k'ala ba na ji sun watsa mun wani abu a fuska kamar powder, lokaci ɗaya na ji numfashi na yana ƙoƙarin ɗaukewa, kaina ya fara wata irin juyawa, na ji ƙafafuna sun kasa ɗauka ta, na tafi luuu zan faɗi ƙasa, daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba. Sai farkawa na yi na gan ni a wani ƙaramin ɗaki a kwance akan wani ƙaramin gadon ƙarfe. Na shiga bin ɗakin da kallo kwanyata na tariyo mun last abun da ya faru, na yunƙura da sauri da nufin in tashi amma sai hakan ya gagara, na ji jikina kamar ba nawa ba, kamar an zare mun lakar jikina, kamar an zuk'e mun jinin jikina, na kasa d'aga ko da ɗanyatsana ne duk iya ƙoƙarin yin hakan da na yi kuwa. Idanuna ne kawai suke iya aiki a jikina suma ba kamar da ba, dan sun mun wani irin nauyi. Na shiga ƙarewa ɗakin kallo a tunanina ko zan iya tuno ɗakin da nake, ko na taɓa zuwan sa a rayuwata. Amma babu abun da na gane, na kasa tantance dare ne ko rana lokacin. Na lumshe ido ina tunanin me na yi aka kawo ni nan? Su waye suka zo har gida suka ɗauko ni saura awanni kaɗan d'aurin Aure na? Bayan ku san minti talatin ina ta yiwa kaina tambayoyin da ba ni da amsar su na ji an turo ƙofa a hankali an shigo ɗakin, na buɗe idona da sauri ina kallon mai shigowar, wani ƙaton mutum ne dogo fuskarsa a rufe da bak'ar face maks ta roba, ƙwayar idanunsa kawai ake gani wanda suka kasance jajaye ne. Na buɗe bakina da na ji ya mun nauyi da ƙyar na ce. "Who are you? What do you want to me?" Kamar da dutse na yi magana bai ce mun k'ala ba, ƙarasowa kawai ya yi ya tattab'a jikina, ni kuma ina cigaba da yi masa tambayoyin dalilin da yasa suka kawo ni gurin. Ya fita bayan ya gama tattab'a jikina, jimawa kaɗan ya dawo da abinci da ruwa a hannunsa, ya ajiye a gefen gadon sannan ya tayar da ni zaune, ya buɗe abincin ya turo mun gabana sannan ya tashi ya fita. Na bi shi da kallo har ya fice, ban ko kalli inda abincin yake ba balle na yi tunanin ci. Bayan wasu mintuna ya ƙara dawowa ɗakin, ganin ban ci abincin ba sai ya kalle ni kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya rufe abincin ya kamani na tashi ina jin jikina kamar ba nawa ba saboda rashin k'wari, wata ƙofa dake cikin dakin ya nufa da ni, yasa hannu ya tura ƙofar ta buɗe sannan muka shiga, ashe toilet ne. Ya zaunar da ni akan toilet sannan ya juya ya fita, na gane mai yake nufi in ina jin wani uzurin in yi kenan. Na tashi da ƙyar ina layi na kunna pampon sink na yi alwala, duk da ban san ƙarfe nawa ba, ban kuma san sallar da zan yi ba, amma na san a lokacin baza a rasa sallar da ake bina ba wadda ban yi ba. Bayan na idar da alwalar na fito dak'yar ina jin kamar iska zata ɗauke ni saboda rashin k'warin jiki. Na tarar da darduma a shimfid'e a tsakiyar ɗakin, bangon ɗakin kuma ta inda dardumar take fuskanta alamun nan ne gabas an saka wani ƙaton agogon bango mai 24 hours a jikinsa, na ga a lokacin ya nuna ƙarfe bakwai da mintuna na safe. Sai dai na kasa gane time ɗin na wacce rana ne, safiyar ranar juma'ar d'aurin Aure na ce ko kuma wata ranar ce daban? Na ƙarasa gaban agogon sai na ga ashe har da rubutun days mitsi_mitsi a cikin sa, a yanda ya nuna kuma safiyar ranar juma'a ce. Na sauke ajiyar zuciya sannan na tayar da Sallah, na yi Sallar asubahin dake kaina. Bayan na idar na zauna na rafka tagumi zuciyata cike da tsantsar tashin hankalin sabon al'amarin da ya same ni, wanda ban san dalilin sa ba amma na fawwalawa Allah komai, na shiga roƙon sa akan ya kare ni daga dukkan wani mai nufi na da sharri mutum ko na aljan. Sai kuma na fara tunanin gida da mahifina da sauran ƴan'uwa, dan na san zuwa yanzu an farga da rashin gani na a gidan, an fara nema na hankali a tashe. Ina zaune inata tunanen gida da dalilin sato ni da aka yi aka kawo wannan gidan har goma na safe ta yi. Na tashi da sauri kamar wanda aka tsikara na nufi ƙofar ɗakin na fara ƙoƙarin buɗewa amma na jita a kulle gam, ni kuma jikina babu k'wari balle na yi yunƙurin buɗe ta. So nake in yi ihu ko wani zai jiyo ni ya kawo mun ɗauki amma k'warin muryar ihun ma bani da shi. Idan na tuna ranar ne fa d'aurin Aure na sai hankalina ya ƙara dugunzuma ya kai k'olokuwar tashi. Na zube a bakin ƙofar jin jiri na neman yarda ni, babu irin tunanin da ban yi ba akan kawo ni gurin da akai. Na ce ko wani abokin aikina ne yake jin haushina yasa a sato ni? Ko kuma kidnappers ne? Ko kuma wani case ɗin na yi daya ɓata wa wani rai ya k'ullace ni? shine zai saka a zato ni ranar Aure na a matsayin ɗaukar fansa. Ni kaɗai a ɗakin babu alamar wani yana inda nake, ko kukan tsuntsu ban ji ba balle na wasu dabbobin ko na mutum. Ina nan zaune aka buɗe ƙofar ɗakin aka shigo, na d'ago da sauri sai na ga mutumin d'azu ne, hannunsa ɗauke da take away da ruwa da lemo, ya ajiye a gabana ba tare da ya yi magana ba ya juya ya fita. Ni kuma kamar an ɗaure mun baki na kasa yi masa magana, duk da tarin tambayoyin dake raina. Na yi ball da abincin da ƙafa cikin tsananin takaici, na san zuwa lokacin ahalina da abokan arzik'i da amaryata suna can cikin tashin hankalin ɓata na. Haka na wuni ni kaɗai a ɗakin cikin tunanin mafita, Sallah ce kawai take tayar da ni idan na ga lokacin ta ya yi. Har bayan Magriba ko ruwa ban kurb'a na saka wa cikina ba, yunwar ma da ƙishirwar ko jin su bana yi, ko ma ina ji bata su nake ba. Kafin isha'i mutumin ya ƙara dawowa ya kawo mun wani abincin da ruwan. Na tashi da sauri cikin ƙarfin hali dana zuciya na cakumi mutumin ina tambayar sa dalilin yasa suka kawo ni nan? Me nay musu? Kamar wani kara haka mutumin ya yakice ni daga jikinsa ya dank'wafar da ni a ƙasa ya juya ya fice. Na rarrafa a ƙoƙarina na ganin na riƙe ƙofar kafin ya rufe, amma tuni ya ja ta sai motsin saka mukulli a jikinta na ji. Na kwanta akan carpet ɗin dake malale a ɗakin cikin tsananin damuwa. Sai da takwas ta wuce sannan na miƙe ina layi na shiga toilet na ɗauro alwala na yi Sallar isha'i, na ƙara da nafila a cikin kowacce sujjada ta ina roƙon Allah ya fitar da ni daga cikin wannan riskin da nake ciki. Ina kan sallaya mutumin ya sake shigowa, na zuba masa ido in ga mai kuma ya shigo yi, da yake ɗakin akwai hasken wani farin k'wan wuta guda ɗaya dake sak'ale a bango. Ga mamakina sai na ga ya kama ni ya kai ni kan gado ya kwantar, na bishi da kallon mamaki, ban gama mamakin ba na ji ya juya ni gefe ya d'aga jallabiyar jikina ya tsikara mun allura. Daga nan na fara ganin bibbiyu, cikin mintuna ƙalilan bacci ya yi gaba da ni. Ban farka ba sai ƙarfe shida saura na safe, na bi ɗakin da kallo, sai na ga fankar sama tana wulwulawa, na juya b'arin damana sai na ga Television ta bango manne a bangon dakin, sai wani abu mai kama da GO TV a ƙasan ta da remotes biyu a kansa. A gefen ta kuma wani ɗan table ne an ɗora Alkur'ani izifi sittin akai. Mamaki fa ya kusa kashe ni, na shiga tambayar kaina abun da mutanen nan suke nufi da ni? Ko duk a cikin salon cutarwar da za su mun ne? Ko kuma wani abu suke nema a guri na? Na yunƙura na tashi sai a lokacin na lura da bargon dake lullub'e a jikina, kaina kuma ashe akan pillow yake. Sai na rasa da yaran da zan fassara wannan al'amarin da na tsinci kaina a ciki. Haka na yunƙura na sakko daga kan gadon, jikina a matuƙar sanyaye kamar jiya na nufi toilet. In tak'aice muku zance haka na kasance a cikin ɗakin nan, kullum za'a kawo mun abinci da ruwa da lemo safe, rana, dare. Da farko bana ci, sai daga baya dana ji yunwa na neman yi mun illa sannan na fara ci ba don daɗi ba. Kuma duk dare sai mutumin nan ya mun allurar nan, wanda na fuskanci ta bacci ce, amma asuba tana yi zan farka. Hakan yasa jikina kodayaushe babu k'wari, ya yi mun wani irin lagwab. Ban taɓa wanka ba sai sau ɗaya da na ji kamar zan mutu saboda k'aik'ayin da jikina yake mun, a toilet ɗin akwai kat'on soap na wanka da toothpaste da brush sabo. Tun ina tambayar mai kawo mun abinci wanda ban taɓa ganin fuskarsa ba dalilin da yasa suka ɗauko ni suka ajiye ni a gurin, har na haqura na daina na zubawa sarautar Allah ido da ganin iya gudun ruwan su, amma har na baro gurin ba su taɓa ƙoƙarin cutar da ni ba, Alkur'ani nan shi ya zamo abokin hira ta, shine nake karantawa wuni guda cur, hakan yasa nake samun nutsuwa a cikin zuciyata. Kwana na huɗu aka kawo mun jallabiya guda biyu da ƙaramin wando, da har na ƙi sakawa sai kuma na ɗauka na saka, da na yi tunanin ina Sallah kar kayan jikina su yi dattin da baza su yi Sallah ba, Tunda ban san ranar fita ta daga gurin ba. Jiya da ya kasance kwana na shida a wannan ɗakin na lek'a waje ta window, sai na fuskanci kamar gida ne inda nake ciki, saboda dana lek'a like bayan gida na gani. Yau na tashi kamar kullum na yi Sallah na ɗan taɓa abincin da aka kawo mun kaɗan, sannan na ɗauki Alkur'ani na fara karatu. Wajen sha biyu lokacin na ajiye Kur'anin inata ta tunane_tunane na, mutumin nan ya shigo ɗakin. Ya ɗauke Alkur'anin gaba na ya ajiye akan table ɗin nan, sannan ya fito da wani baƙin k'yalle ya ɗaure mun idanuna tamau, ina tirje_tirje da yi masa ihun ya rabu da ni amma bai kula ni ba. Na ji an ƙara buɗe ƙofar ɗakin an shigo, daga nan kuma sai ji na yi sun kama ni mun fice daga ɗakin. Inata tambayar su ina zasu kai ni, amma babu wanda ya ce mun kanzil. Har suka saka ni a cikin mota suka ɗaure mun hannuna ta baya muka fara tafiyar da ban san inda za'a kai ni ba. Addu'ar neman tsari kawai nake karantawa a raina. Mun yi tafiya sosai sannan na ji mun tsaya, suka fito dani muka shiga wari guri, sai da muka shiga suka kunce mun daurin fuskata dana hannuna, suka buɗe wata ƙofa suka kaini bakinta, ina shiga na ga toilet ne. Mamakin waɗan nan mutanen nake da basa wasa da Sallah, dan na gane tsayawa suka yi da tafiyar dan na yi Sallah. Na ɗauro alwala na fito na tayar da Sallah akan carpet ɗin dake tsakiyar gurin mai kama da ɗaki, amma babu komai a cikin sa, ko labule babu. Na tayar da Sallar kenan ɗaya daga cikinsu ya taso ya juyar da ni, da alama ban fuskanci alk'ibla dai-dai ba, tunda dama shata kawai na yi. Ina idarwa suka mayar mun da k'yallen fuskata suka kuma ɗauren hannuna, suka kama ni muka fice daga gurin. Muka koma motor aka cigaba da tafiya, wadda har sai ana la'asar muka shigo cikin gari, nan ma sai da suka tsaya suka shigar da ni wani gida da babu kowa a cikinsa na yi Sallah, sannan muka fito, tafiya kaɗan muka yi suka sauke ni tare da kunce mun d'aurin fuskata dana hannuna cikin sauri sannan suka juya suka shiga cikin Mota suka manne ta da mugun gudu. Na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi lokacin dana fuskanci a bayan gidan nan nake. Jikina har rawa yake dan murna da zumud'i na miƙe na nufo gida, ina son na yi gudu dan ƙarasowa da wuri amma rashin k'warin jikina ya hana ni, dole sai a hankali na tako na zo, ina tafe ina tunanin mutanen nan da tambayar kaina menene fa'idar ɗauke ni da sukay? Kuma gashi sun dawo da ni gida ba tare da cutarwar ko ƙwarza ne a jikina ba? Wannan shine abun da ya faru da ni." Gaba-ɗaya mutanen Parlour'n suka yi shiru kowa yana jimanta al'amarin a cikin ransa cikin tsananin mamaki. Abban Sadik ne ya fara magana a cikinsu cikin matuƙar mamaki ya ce. "To fa, ka ji kuma wani ikon Allah, amma wannan abun da ɗaure kai yake, to su waye waɗan nan mutanen, mene kuma fa'idar su na yin hakan?" Kawu ya ce. "Shine abun tambayar." Hajiya ta ce. "Yo wanne abun tambaya kuma ga abu nan a zahiri? An sace Sadik ba dan komai ba ne sai dan kawai akan wannan yarinyar, saboda kar auransu ya yiyu, Allah ya rufa mana asiri shi ba'a kashe shi ba kamar na bayan da aka kashe." Cikin sauri Sadik ya kalle ta amma bai ce komai ba. Hajja (Mahaifiyar Maamah) ta ce. "Gaskiya ne zargin mu ya zama gaskiya, saboda yarinyar ne." Kawu ya ce. "Lallai Sadik ka auna arzik'i, Allah ya yi da sauran kwanan ka a gaba kana da rabon shan ruwa, Eh, Alhamdulillah mun godewa Allah, fatan mu Allah ya baka wata matar ta gari, wannan yarinya kam ba matar Aure ba ce." Abba ya ce. "Nima na tsorata gaskiya, gwara da ba mu yarda an ɗaura Auren ba, wataƙila da waɗan da suka sace shin sun ji labarin an ɗaura Auren da tuni sun kashe shi." Hajiya ta ce. "Zancen yaushe kuma? Ai Allah ne yay mana gyaɗar doguwa, gobe in Allah ya kai mu sai a karb'o kaya da kuɗin da aka kai gidansu yarinyar, maganar aure kuma ta ruguje, tunda yarinya ta zama annoba." Abba ya dubi Sadik dake cikin tashin hankali ya ce. "Ka yi haquri Abubukar, tun kafin ka dawo mun gama yanke hukunci baza ka auri yarinyar nan ba, dan alamu sun nuna kota yi auren ma za'a iya bi har gida a kashe mijin." A ruɗe Sadik kamar zai yi kuka ya ce. "Abba ni na san ba domin Neehal aka sace ni ba, abun da kuke tunani ba haka ba ne Abba, ka manta aikina, ka manta wani zai iya yin komai dan yana jin haushi na, may be mun samu wata matsalar akan wani case daban, ko kuma....." A zafafe Hajiya ta katse shi da faɗin. "Lallai Sadik na yarda baka da hankali, ka ci akai ka dawanau a duba ƙwaƙwalwarka, yarinyar da kafin kai samarinta biyu an kashe su, kai kuma aka sace ka ana i gobe d'aurin Auren ku shine kake ƙoƙarin kare ta? Saboda Kai ne Majnoon sarkin soyayya, ko kuma in ce sarkin hauka? To yarinyar nan in ma mayya ce ta lashe maka kurwa sai ta sake ka wallahi, kai da ita kuma haihata_haihata kun rabu, rabuwa ta har abada, in ma zaka cire ta daga ranka ka cire ta, na san wannan farar fatar ta_ta da dogon hanci da manyan idanu su suke rud'ar ka a kanta, to indai wannan ne zaka samu wadda ta fita sau dubu a duniyar nan." Sadik ya dafe kansa dake sara masa kamar zai tsage lokaci ɗaya. Abba ya ce. "Abubakar ka yi tunani da hankalinka mana, idan dan jin haushin ka ko dan ɗaukar fansa aka sace ka baza a barka lami lafiya ba sai an cutar da kai, amma wannan fa dubi yadda aka kula da kai, harda saka maka kayan kallo dan su ɗebe maka kewa. Amma na jinjinawa koma waye ya sace ka, yanda bai bari ka yi wasa da Sallah ba, kuma yake baka abinci akai_akai, tabbas ya san darajar ɗan Adam. Sai dai ba mu san mene a cikin zuciyarsa ba daya aikata hakan." Ɗaya daga cikin k'annen Abba ya ce. "Abun da mamaki ba kaɗan ba, ita kuwa wannan yarinya wa yake yiwa rayuwarta haka, ni tausayi take ba ni dan na san su ma ba su da masaniya akan mai aikata mata wannan al'amari." Hajja ta ce. "Abun da tausayi gaskiya." Umma ta ce. "Wataƙila aljanu gare ta." Kawu ya ce. "Koma mene ne Allah ya yaye mata, mu dai an yi walk'iya mun gani, ɗanmu ba zai aure ta ba, fak'at." Sadik zai yi magana Kawu ya katse shi cikin faɗa ya ce. "Karka ce komai, indai mun isa da kai daga yau ba kai ba wannan yarinyar." Sadik ya kalli Maamah da bata ce k'ala ba tunda ta zauna yana marairaice fuska, a ƙoƙarin na son ta roƙar masa su Kawu akan kar su raba shi da Neehal, amma sai ya ga ta sunkuyar da kanta ƙasa alamun tana bayan su Kawu, ta goyi bayan a raba shi da Neehal kenan ita ma? Ya ɗauke kansa daga kanta cikin ƙarfin halin radad'in da yake ji a zuciyarsa ya ce. "Shikenan Kawu, Allah yasa haka shi yafi Alkhairi." Yana gama faɗar haka ya miƙe cikin sanyin jiki kamar zai faɗi ya fice daga falon. Suka bi shi da kallo dukan su. Maamah ta ji tausayin ɗan nata ya cika mata zuciya, sai ta ga kamar su Kawu ba su kyauta masa ba, daga dawowar shi su tarye shi da zancen rabuwa da abar son sa, wanda kowa ya san zai ji ciwon hakan ba kaɗan ba. A ganin ta aida sun bari an kwana biyu ya ƙara hutawa ya dawo cikin nutsuwarsa. Baza ta iya barin ɗanta a cikin halin damuwa ba tare da rarrashe shi ta faɗa masa abun da zai ji sanyi a ransa ba, hakan yasa ta miƙe ba tare data kalli kowa ba ta bi bayan shi. Umma ta tab'e baki. Hajiya ta shiga mita da masifar Neehal ba haka ta bar mata jikan ta ba, asirce shi ta yi, ban da haka mutum yana ganin mutuwa muraran amma yana ƙara kai kansa gare ta. Yana kwance akan gadon ɗakinsa ruf da ciki Maamah ta shiga ta same shi, idanunsa a lumshe sai faman sassauke numfashi yake. Maamah ta zauna a bakin gadon tare da ɗora hannunta a kansa cikin sanyin murya ta ce. "Ka yi haquri Sadik, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, ka miƙawa Allah komai zaka ga ya warware maka damuwar ka cikin sauƙi, ta hanyar da baka taɓa tsammani ba. Ka saka a ranka idan Neehal matar ka ce duk runtsi duk wuya sai ka aure ta, just pray hard my son everything will be Okay by the grace of God." Sadik ya gyaɗawa mata kai tare da sauke ajiyar zuciya. Maamah ta ce. "Dan Allah karka damu kanka da tunani, ka kwantar da hankalinka, ka ga yau ka dawo kana murna muma muna murna, karka ɓata Mood ɗinka ka ɓata namu." Ya gyaɗa mata kai. Maamah ta shafi sumar kansa ta ce. "Allah yay maka Albarka, ya baka ƴaƴa masu biyayya kamar yadda kake mana, ya zaɓa maka abun da yafi Alkhairi a rayuwarka." Ya buɗe ido cikin daɗin addu'arta ya ce. "Amin Maamah ta, thank you so much." Maamah ta yi murmushi ta miƙe ta fice. Ya bita da kallo cikin matsananciyar k'aunar ta, uwa uwa ce, mai sanya farinciki a zuciyar ƴaƴanta akodayaushe, dole duk wanda ya rasa uwa ya yi kuka. Ya lumshe ido a ransa yana faɗin, dole ya yiwa iyayensa biyayya ya rabu da Neehal, duk da ya san zai cutu, cutuwa ba kaɗan ba, bai ma san ya zai kwatanta rayuwarsa babu Neehal ba, bai sani ba ko zuciyarsa zata ɗauki rayuwa babu ita ko ba zata ɗauka ba? A fili ya furta. "I'm sorry Neehal, dole zan bar ki ba dan san raina ba." Ya sauke ajiyar zuciya tare sakawa a ransa ya rabu da Neehal rabuwa ta har abada kamar yadda iyayensa suke zo, zai dage da addu'ar Allah ya rage masa soyayyarta a cikin zuciyarsa ko da rabi ce, dan ya san ba zai taɓa daina son ta ba har abada. Amma Neehal fa? Yaya zata ji idan ta ji ya bar ta akan ƙaddarar da ba ita ta ɗorawa kanta ba? me yasa mutane baza su yi mata uzuri ba? Me yasa za'a ƙyamace ta a hana a aure ta? Mene laifin ta a cikin ƙaddarar ta? Hawaye masu d'umi ne ya ji suna zarya akan kuncinsa, na tausayin kansa da tausayin abar k'aunarsa, masoyiyarsa, muradin ransa, wadda ya saka ran zata zamto matarsa uwar ƴaƴansa amma *ƙaddara* ta raba su, a lokacin da ba su taɓa tsammani ba, lokacin da suke gab da mallakar junan su, su zamto abu ɗaya. Ya share hawayen fuskarsa wanda ya manta rabon da ya gan su akan fuskarsa sai yau, shi musulmi ne ya yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, haɗuwar su da Neehal wani shafi ne a cikin shafin littafin ƙaddarar rayuwarsa da Ubangiji ya rubuta masa, haka ma rabuwa da ita, dan haka He accepted it, Rayuwar mumuni dole sai da jarrabawa daga Ubangijin sa. Fata kawai Allah yasa mu iya cinye dukkan jarrabawoyin rayuwar mu, wanda muke fatan hakan ya kai mu ga samun dacewa a duniya da lahira baki ɗaya........✍️ _*Not edit, sorry for the typed errors.*_ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *6️⃣7️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ..........Tun ƙarfe biyar da ƴan mintuna Mama suka yi waya da Neehal ta sanar mata ta taho gida, amma har shida ta wuce bata dawo ba, abun ya bawa Mama mamaki dan daga ASTV zuwa gidansu bai fi tafiyar 10 minutes ba, indai ba mugun go slow mutum ya tarar a hanya ba, shi ma ba zai tsayar da kai har kusan 1 hour ba. kiran wayar Neehal Mama ta yi dan jin abun da ya tsayar da ita amma sai ta ji switch up. Ta kira another sim ɗinta shi ma ta ji shi a kashe, Numbobin Neehal huɗu gare ta amma duk ta kira abu ɗaya ake maimaita mata is switch up. Sai ta ji kawai hankalinta bai kwanta ba, ta miƙe daga zaunen da take gabanta na fad'uwa ta lulubo Numbern ɗaya cikin abokan aikin Neehal mai suna Rahama ta kira. Cikin sa'a wayar ta shiga ringing biyu ta ɗaya tare yin sallama. Mama ta amsa mata ta ƙara da faɗin. "An wuni lafiya Rahmah ya aiki?" Rahmah ta ce. "Alhamdulillah." Mama ta ce. "Na ji kamar baki gane mai magana ba, Maman Neehal ce." Da fara'a a muryar Rahmah ta ce. "Laa Mama ke ce, ina yini, wallahi ban gane ki ba, Numbern babu save da yake na canza waya ne." Mama ta ce. "Babu komai, kin baro gurin aiki ne?" Rahmah ta ce. "Eh, tare ma muka fito da Neehal." Mama ta sauke numfashi ta ce. "Mun yi waya da ita tun d'azu ta ce mun ta taho saboda bana son ta yi dare a waje tunda ba ishashshiyar lafiya ce da ita ba, to kuma har yanzu na ji ta shiru bata dawo ba, ga magriba ta kawo kai, na kira wayoyinta duka a kashe." Rahmah ta ce. "Too, kuma bata ce miki zata biya ta wani gurin ba, saboda sai da ta shiga Mota sannan direbanmu ya zo ya ɗauke ni." Mama ta ce. "Kina nufin ta ma riga ki fita?" Rahmah ta ce. "Eh, buɗe mata gate ɗin ma da akai ta fita kafin a rufe direbana ya shigo, da ya ɗauke ni muka fita daga cikin gidan TV'n babu ma motar ta a layin har ta ƙarasa titi." Mama ta ce. "Toh shikenan Rahmah na gode, dama na yi tunanin ko ta yi mantawa ne ta koma." Rahmah ta ce. "Gaskiya ban ga komawar ta ba, amma bari na kira wani a cikin masu night duty in ji ko bayan mun fito ta koma." Mama ta ce. "Yawwa Rahmah na gode sosai, yanda kuka yi sai ki kira ni ki faɗa mun." Rahmah ta ce. "Insha Allahu." Mama ta ajiye wayar a hannun kujera bayan ta katse kiran ta shiga kaiwa da komowa a falon idanunta akan makeken agogon bangon dake manne a kusurwar Parlour'n, duk second ɗaya da yake tafiya akan idonta, haka kuma duk second ɗin yana tafiya ne da ƙaruwar bugun zuciyarta na tsoron kar wani mugun abun ne ya samu Neehal. Girki take a ƙasa amma ta kasa sauka ta ƙarasa, girki na musamman take shiryawa Neehal ɗinta dan ta ci abinci sosai in ta dawo, dan ta san mawuyacin abu ne ta ci a gurin aikin, amma kuma rashin dawowar Neehal ɗin akan lokaci ya sanya mata wani irin abu a zuciyarta, duk da ba yau Neehal ta saba ƙara lokaci ba idan ta fita amma yau ɗin sai ta ji hankalinta ya kasa kwanciya da hakan, ko dan yanayin damuwa da Neehal ɗin take ciki ne yasa take tsoron kar wani abu ya faru da ita? Like accident or something like that. Abun da yake ƙara d'aga mata hankali kuma jin wayoyinta gaba-d'aya a kashe, ta san ba zai yiyu a ce duka wayoyi ukun da Neehal take amfani da su babu charge ba, ta san kuma Neehal bata kashe wayoyinta haka kawai, dole sai da wani dalilin....... Ringing ɗin wayarta ne ya katse mata tunanin da take, ta ƙarasa ta ɗauka cikin sauri tare da karawa a kunne ganin Rahmah ce take kiran. Rahmah ta ce. "Mama wai bata koma ba tunda ta fita." Ƙirjin Mama na tsananta bugu ta ce. "Shikenan Rahmah, na gode." Rahama ta ce. "Kuma bata ce zata biya ta wani gurin ba?" Mama ta ce. "Bata faɗa ba, amma bari na kira Auntie's ɗinta na ji ko ta je gurin su." Rahama ta ce. "Toh Mama, Insha Allah ma tana can ɗin." Mama ta ce. "Allah yasa." Sannan ta katse wayar ta kira Aunty A'isha. Cikin dabara yanda Aunty A'ishan baza ta gane da wata matsalar ba, Mama ta tambaye ta ko Neehal ɗin ta zo gidanta, Aunty A'isha ta ce bata zo ba, har take tambayar ta Neehal ɗin ta fara fita ne? Mama ta ce mata yau ta fara fita. Bayan sun gama wayar ta kira Aunty Sadiya ita ma ta tambaye ta, Aunty Sadiya ta ce bata zo ba, ita yanzu ma ta dawo daga gurin aiki. Mama ta zauna dab'as cikin tsananin tashin hankali, zuwa yanzu kam ta tabbatar da akwai matsala, gashi Haneefah bata nan suna Kogi state bare ta ce ko gidanta ta tafi. Ta yi tunanin ko gidan Ameen ta tafi, ko kuma gidan su wasu k'awayen nata. Duk wanda Mama take tunanin Neehal zata iya zuwa gidansa a cikin garin Kano sai da ta kira ta tambaya ko ta je, su Aunty matar Uncle Umar, da matar Kawu Musa, da k'awayen Maman da suke zuwa gidajensu da Neehal ɗin, da Maman Haneefah, har mak'ota sai da Mama ta kira amma ko ina babu labari. Ta kira few Freind's ɗin Neehal da take da Numbern su, su ma babu labari. Data kira Ameen bai ɗauka ba sai ta kira Hafsat ta tambaye ta, and amasar duk ɗaya ce nan ma Neehal bata je ba. A gigice Mama ta sauko ƙasa ta shiga duba all Apartments ɗin gidan ko Neehal ta dawo ta wuce can, duk da wasu a kulle suke amma duk sai da Mama ta duba, su Zulai na taya ta suma hankali a tashe da Mama ta labarta musu abun da yake faruwa, duk bayan mintoci Mama tana ƙara kiran wayar Neehal ko za'a dace, amma still a kashe. Har parking space Mama ta duba ko zata ga Motar ta amma bata gani ba, Mama ta tambaye yi masu gadi ko Neehal ta shigo ta kuma fita suka ce tunda ta fita bata dawo ba. Har an fara kiran Sallar isha'i amma Mama bata yi Magriba ba saboda tashin hankali, ita da bata wasa da Sallah. Ta kira Daddy ta sanar masa Neehal fa bata dawo gida ba, kuma ta kira duk inda take tunanin zata iya zuwa amma an ce bata je ba. A gigice Daddy ya ce gashin nan zuwa gidan yanzu_yanzu. Sai da Mama ta ji ana kiran ishar sannan ta tuna bata yi Magriba ba, ta miƙe cikin sauri ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta tayar da Sallah. A kowacce sujjada tana roƙon Allah ya dawo mata da Neehal gida, tana cikin Sallar ta ji anata kiran wayarta. Tana idarwa ta ɗauko wayar cikin addu'ar Allah yasa Neehal ce take kiran ta ko kuma wani da zai ce mata ya ga Neehal ko kuma ya tsince ta, ita a yanda take ji ma ko ce mata aka yi Neehal tana asibiti ta yi accident zata fi jin daɗi fiye da rashin sanin inda take da halin da take ciki. Amma tana dubawa sai ta ga Ameen ne yake kiran ta. Ta yi pick cikin sanyi jiki ta saka wayar a speaker, muryar Ameen ta karede ɗakin da yin sallama a wayar, Mama ta amsa masa cikin raunin murya. Ya ce. "Mum, I saw your missed call, time ɗin ina yin abu, hope dai ba wata matsalar ba ce na ji muryarki with so concern." Sai a lokacin Mama ta ji hawaye masu d'umi sun zubo daga cikin idanunta, muryarta da alamun kuka ta ce. "Ameen! Neehal has missed." A ruɗe Ameen ya ce. "What? Kamar ya?" Mama ta labarta masa abin da yake faruwa. With so concern ya ce mata gashin nan zuwa gidan. Mama ta ajiye wayar tare da rafka tagumi tana hawaye tare da tunane_tunane. Ganin tunanin ba zai kai ta ba ta kira Aunty A'isha da Aunty Sadiya ta sanar musu halin da ake ciki. Ƙarshen rud'ewa su Aunty sun ruɗe, su ma suka sanar da Mama gasu nan zuwa gidan. Ameen ne ya fara zuwa gidan a gigice, ya tarar Mama tana kuka sosai abun da ba zai iya tuna ranar da ya ta yi ba, kasancewar ta mace mai juriya da dauriya. Ya kama hannunta ya ce. "Please Mum stop crying, Insha Allahu za'a gan ta." Mama ta girgiza masa kai cikin kuka ta ce. "Ameen duba time ka gani har tara fa ta kusa, sai yaushe zata dawo? Ina tsoron yarinyar nan kar damuwa tay mata yawa ta yanke shawarar guduwa wani gurin." Ameen ya ce. "Miemerh will never do that I know, tarbiyyar da kikai mata baza ta taɓa yanke shawarar guduwa ba, may be Gombe ta tafi ko kuma Abuja, ko dai wani gurin daban." Mama ta kalle shi cikin sauri ta ce. "Abuja? Gombe? A daren nan zata ɗauki hanya ita kaɗai, amma kuwa idan haka ne yarinyar nan bata kyauta mun ba, ta san hankalina zai tashi sosai, kuma sannan ta kashe wayoyinta." Ameen ya ce. "No Mum, hasashe na ne kawai ba wai na tabbatar da hakan ba, a halin da ake ciki everything will happen." Mama ta sauke gwauron numfashi bata ce komai ba. Ameen ya ce. "Let me check har room, ko zan samu something like jotter da take rubuta Numbers a ciki, sai mu kira Freind's ɗinta da baki da Numbers ɗinsu, mu ji ko suna tare." Mama ta gyaɗa masa kai cikin gamsuwa da shawararsa. A dai-dai lokacin Daddy ya shigo ɗakin a gigice, hankalinsa a matuƙar tashe. Ameen ya gaishe shi amma ko iya amsawa bai yi ba ya shiga tambayar Mama ƙarin bayanin abun da ya faru. Ameen ya fice dan zuwa bedroom ɗin Neehal, Mama tana ƙara yiwa Daddy bayani tana trying Numbers ɗin Neehal, but still wayar a kashe. Daddy ya shiga maimaita Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un sannan ya ce. "Ina wannan yarinyar ta tafi a dai-dai lokacin da bata cikin normal mood? Bata tunanin wani abun ya faru da ita? Ko dai accident ta yi?" Mama ta ce. "Na yi tunanin haka nima Gen. Amma da haka ne da tuni an kira mu an sanar mana, kusan 4 hours fa da yin wayar mu." Daddy ya jinjina kai with so concern ya ce. "Yanzu zan bayar da cikiyar ta a duk wata kafar sadarwa dake garin nan, sannan kuma zan baza yarana su bi asibiti_asibiti su duba mun ko an kai ta." Mama ta ce. "Allah yasa a dace." Ya ce. "Amin." Tare da zaro wayarsa a aljihu ya shiga kiran mutane......... Gudu na fitar hankali waɗanda suka ɗauke Neehal suka dinga shararawa akan titi, duk inda suka gilma sai an yi maganar su da irin gudun gangancin da suke yi kamar basa san rayukansu. Tafiya suka yi takai ta mintuna hamsin sannan suka tsaya a wata unguwa mai kama da jeji, saboda babu gidaje sosai kuma tsit take babu mutane. A gaban wani ƙaton gida wanda shi kaɗai ne a layin ba gida gabansa babu a bayansa suka tsaya, suka danna horn, ba jimawa wani buzu da ya sha rawani ya zo ya wangale musu gate ɗin gidan suka kutsa kai ciki. Girman compound ɗin gidan ya ninka na gidan Mama sau biyu saboda girman sa, sai da suka je har bakin ƙofar da zata sada su da ainihin cikin gidan sannan suka yi parking. Wanda yake cikin Motar Neehal ya ɗauki jakarta cikin sauri ya buɗe ya ciro wayoyinta duka ya kashe su, duk da kafin su tafi farautar Neehal sun katse network ɗin gidan, amma saboda tsaro kuma sun san ogansu zai yi magana anjima da Neehal ta waya, to za'a iya dawo da network ɗin akodayaushe shi yasa ya kashe wayoyin nata kamar yadda aka ba shi umarni. Ya buɗe Motar ya fita ya tarar already har ɗan'uwansa ya fita ya tafi buɗe musu kofofin gidan. Ya ciccibi Neehal ita da jakarta kamar wata yaririya ya nufi cikin gidan da ita. Corridor mai ɗan tsayi zaka tarar kana shiga ciki mai ɗauke da k'ofofi a jejjere, sai da suka kusa zuwa ƙarshen sa sannan suka buɗe wata ƙofa suka shiga da Neehal dake kwance tamkar gawa. Madaidaicin d'aki ne da ya ji komai na buƙatar rayuwa, akan k'aton gadon dake ɗakin suka shimfid'e ta. sannan wanda ya ɗauko ta ya kwashe wayoyinta suka fice daga ɗakin suka kulle ta. Bata farka ba sai kusan goma na dare, a hankali ta buɗe idonta da ƙyar ta shiga bin ɗakin da kallo, tana jin kanta yay mata wani irin dumm, ga warin wani abu a hancinta. So take ta tuno inda take da abun da ya faru da ita amma ta kasa, ƙwaƙwalwarta gaba-ɗaya ta cunkushe ta ƙi yin tunanin da take son tay mata, sai kayataccen ɗakin data gan ta a ciki wanda ya ji komai take bi da kallo, ta dai gane dare ne lokacin duk da wadataccen hasken dake ɗakin. A hankali cikin ikon Allah ƙwaƙwalwarta ta dawo dai-dai, ta fara tariyo mata last thing da ya faru da ita. Ta k'walla razananniyar ƙara tare miƙewa zaune a matuƙar hanzarce ƙirjinta na bugawa a million. Ta sauko daga kan gadon kamar zata kifa tana magana a fili cikin matuƙar rud'ewa da razana. "Ina ne nan? A ina nake? Wa ya kawo ni? Me na zo yi a nan? Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." Ta ƙarashe maganar tare da ɗora hannayenta duka a kanta. Ta fashe da kuka tare da faɗin. "Su waye ku da kuka kawo ni nan? Me nay muku? Me kuke so da ni? Nan kuma ƙaddarata ta kawo ni? Ya Allah ka fitar da ni daga gurin nan, Allah karka ba su ikon cutar da ni." Sai ta nufi gurin da take tabbacin nan ne ƙofar shigowa ta kama handle ɗin ƙofar tana murd'awa da ƙarfi tare da bubbuga ƙofar da ɗayan hannunta tana kuka tana faɗin su zo su mayar da ita gida. Ganin babu alamun akwai ma me jin ta balle ya taimake ta, ta zube a bakin ƙofar tana ƙara volume d'in kukanta. Tana jin zuciyarta kamar zata tarwatse saboda tension, tana jin dama Ubangiji ya zare ranta a yanzu ta huta da wannan masifar da bala'in da yake riskar ta daga wannan sai wannan. Nan kuma ina ne waɗannan mutanen suka kawo ta? Ta d'ago kanta a fili ta ce. "Why Neehal? Why? Me yasa na buɗe my car na yi magana da mutanen nan? Da na yi zama na a cikin Motar har Allah ya taimake ni ya kawo wanda zai iya taimako na, ko kuma Daddy ko one of our staff soldiers sun zo sun kori mutanen. Wanne ganganci ne ya kai ni zuge glass ɗina?" Zuciyarta ta bata amsa da faɗin. 'Tsautsayi da rashin sani.' Tabbas tsautsayi ne wanda ba ya kaucewa ranar sa. Da kuma wata sabuwar ƙaddarar a cikin jerin ƙaddararorin rayuwarta. Jin ana buɗe ƙofar ɗakin ta waje ta tashi da gudu ta nufi kan gadon ta faɗa ta kudundune jikinta guri ɗaya tana cigaba da kukanta. Aka turo ƙofar ɗakin aka shigo aka mayar aka rufe, ɗaya daga cikin wanda suka kawo ta gidan ne, Neehal ta bi shi da kallo da jajajen idonta tsoro mai tsanani na ƙara lullub'e ta, ta ƙara makurewa a jikin gadon bugun zuciyarta na ƙaruwa kamar zata faso ƙirjinta ta fito. Abinci ne a hannunsa ya ajiye mata a kan bedside locker, yana duban ta da wani shegen murmushi ya ce. "Ki ci abinci ƴan'mata." A zafafe ta ce. "Ba zan ci ɗin ba, ku mayar da ni gida, me yasa zaku kawo ni nan, ku mayar da ni gurin Mamata, me nay muku? Me kuke so a wajena?" Ta fashe da kuka mai ban tausayi. Bai ce komai ba ya juya da niyyar fita, ta tashi ta biyo shi ta riƙe hannunsa ta fara ihu da ƙarajin ya mayar da ita gida ita dai. Ya hankad'a ta, ta faɗi a ƙasa, kafin ta yi yunƙurin tashi ya buɗe ƙofar ya fice. Ta ƙurawa ƙofar ido kamar idanun nata ne za su buɗe mata ƙofar. Ta tashi da ƙyar ta faɗa kan gado cikin rashin sanin mafita, "Mama." Ta furta a fili. Ta san tana can hankalinta a tashe, tana can cikin damuwar rashin dawowar ta gida. Ta tashi zaune da sauri ta janyo hand bag ɗinta dake tsakiyar gadon ta buɗe da niyyar ɗauko wayoyinta ta kira ta, amma sai ta ga babu ko ɗaya. Ta zazzage jakar hoping ko zata ga wayoyin sun mak'ale a wani gurin, amma kuɗi da earpiece da i.d card ɗinta na gurin aiki ne kawai suka fado. Ta yi cilli da jakar ƙasa ta kuma fashewa da wani sabon kukun, tana ambaton sunan Allah a ranta tare da neman taimakonsa. Tunawa ta yi bata yi Sallah ba hakan yasa ta d'ago kanta, idanunta suka sauka akan agogon bangon dake ɗakin wanda ya nuna sha ɗaya da rabi na dare. Ta miƙe ta sauko kamar zata fadi ta nufi ƙofar da take da tabbacin toilet ne, tana turawa ta ga ta buɗe, kuma kamar yadda ta zata toilet ɗin ne mai matuƙar kyau a tsabtace, ba ta shi take ba abun da ya shigo da ita kawai ta yi ta fito, ta gyara hijabin jikinta ta tayar da Sallah. Bayan ta idar ta rafka tagumi a gurin, tana tunanin ko kidnappers ne suka sace ta, ko kuma gidan masu yankan kai aka kawo ta. Tana nan zaune aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, bata ko motsa ba balle ta d'ago ta kalli mai shigowar, ta fawwalawa Allah komai, ta san duk abun da ya rubuta zai same ta babu makawa sai ya same ta, kuma shi kaɗai ne zai iya kare ta daga dukkan wani sharri da mutanen nan suke nufi da ita. Mutumin d'azu ne ya ƙara dawowa da waya a hannunsa, ya tsugunna a kusa da ita tare da miƙa mata wayar yana faɗin. "Oga zai yi magana da ke." Wata uwar harara ta zabga masa sannan ta ce. "Bazan yi maganar ba, ku mayar da ni gida na faɗa muku, ku kai ni gurin Mamata." Bai ce komai ba ya saka wayar a handsfree, wata murya mai kaushi ta karaɗe kunnen Neehal da dariya, daga baya kuma aka daina dariyar ya fara magana da faɗin. "Fateemah Zahra! Neehal! ƴar Mamanta. Ki kwantar da hankalinki zaki koma gurin Mama nan kusa, amma kafin nan zai mun amshi abun da muka kusa shekara goma muna dakon sa a gurinki, abun da *ƘUNGIYA* Mai daraja take da buƙatar sa shekara da shekaru, abun da bata taɓa shan wahala gurin mallakar wani abu kamar sa ba, yau gashi lokaci ya yi, dama an ce komai nisan dare gari zai waye. Yau ƙungiya tana cikin farincikin da bata taɓa kasancewa a cikin irin sa ba, yau zata kwana tana shan shagalin da murnar mallakar *BUDURCIN NEEHAL.* Tun da ya fara magana babu abun da Neehal ta fahimta sai kalmar virginity ɗinta, ta ji dai yana ambatar ƙungiya. Cikin rud'ewa ta ce. "What? Wacce ƙungiyar? Me kuke so a gurina?" Mutumin ya kuma ƙyalƙyalewa da dariya cikin ƙatuwar muryarsa sannan ya ce. "Zaki gane komai daga daren yau zuwa safiyar gobe, zan so ace ni ne zan ratsa kyakkyawar yarinya ƴar hutu wadda ƙungiya take girmamawa da tattalin budurcin ta, sai dai kash dole sai mamallakin budurcin ne zai amshi abun sa." Zuwa yanzu Neehal ta soma gane inda maganganun sa suka dosa, sun ɗauko ta nan ne domin yi mata fyade akan wata buƙatar su ta banza. Cikin ƙaraji da rashin tsaro ta ce. "Ƙarya kake munafukin Allah, Ubangiji ba zai taɓa baku nasarar cutar da ni ba, mushrikai kawai!" Mutumin ya ƙyalƙyale da wata muguwar dariya sannan ya ce. "Yaro man kaza, yaro baka san wuta ba sai ka taka. Dole a gobe ɗaya cikin ƴan ƙungiya ya mallaki budurcin ki, dole a gobe sarauniya ta sha sperm ɗinki da take ta ƙwadayin shi shekara da shekaru, ƙungiya bata taɓa neman abu ta rasa ba, ki hutawarki ƴan'mata." Daga haka wayar ta yi ɗil alamun an yanke. Neehal ta shiga jujjuya kanta dake barazanar fashewa, ta ɗora hannunta a ƙirjinta da yay mata wani irin nauyi tana ambaton sunan Allah cikin fitar hayyaci. Bata ma san time ɗin da baƙin mutumin nan ya fice daga ɗakin ba. Ta d'au tsawon lokacin da bata san yawansa ba a cikin wannan halin, a hankali cikin Ikon Allah ta fara dawowa cikin nutsuwarta. K'azaman maganganun mutumin da sukay waya na yi mata kuwwa a cikin kanta tamkar yanzu yake faɗa mata, ta shiga auna maganganun nasa a mizanin hankali, idan ta fahimta wannan kungiyar da yake magana akai ta matsafa ce masu asiri dan neman duniya, idan ta fahimta mitumin da suka yi magana ba shi zai amshi budurcin nata ba kamar yadda suke so, wani ne daban wanda ya alaƙanta shi da mamallakin budurcin nata. "To waye wannan?" Ta tambayi kanta a fili, bata da amsa ba kuma ta san inda zata samo ta ba, hakan yasa ta tafi point na gaba. Wanda ya ce kusan shekara goma suna d'akon virginity ɗinta, idan ta fahimta su ne suka kashe su Jameel kenan dan sun san idan ta yi aure zata rabu da abun da suke dakon shi a gurin ta? Me tay musu da zafi haka to suke bibiyar ta da wannan mummunar manufar? Su waye ƴan ƙungiyar da sarauniyar su? A ina suka san ta da har suke son cutar da ita? Tambayoyi barkatai ta shiga yiwa kanta, daga baya ta fara addu'ar kar Allah ya basu ikon cimma mummunan kudirin su a kanta. Sai kuma ta koma tunanin abun da Mama tay ta tambayar ta a cikin kwanakin nan, ko ta taɓa samun saɓani da wani shine yake ta bibiyarta rayuwarta dan ɗaukar fansa, amma kuma ta kasa tunowa tunda babu, bata jin ta taɓa samun babban saɓani da wani a rayuwarta. Ta kawar da wannan tunanin ta koma tunanin samarinta da ba su ji ba, ba su gani ba an kashe su saboda ita, ta tuno Jameel wanda da an yi auransu da tuni yanzu sun yi 6 years da aure yanzu, Anwar kuma 3 years da watanni, sai Sadik da sun kusa wata biyu. Idan har waɗan nan mutanen suka samu nasarar cimma burinsu a Kanta rayuwarta ta zo ƙarshe, bata ga amfanin sauran rayuwarta_ta ba, tunda an raba ta da abu mai kima da martaba da daraja a tare da ita. Ta girgiza kanta tare da addu'ar Allah ya ɗauki ranta kafin safiya, ko ta huta da wannan bala'in. A tak'aice yanda ta ga rana yau haka ta ga dare.......... Kamar yadda Neehal bata iya runtsawa ba yau haka ma Su Mama ba su runtsa ba, dan Ameen ma sai ɗaya saura na dare ya bar gidan. Tashin hankalin da Mama take ciki ba zai misaltu ba, kwana ta yi tana kuka Daddy da Aunty Sadiya suna kanta suna bata baki, Aunty A'isha kuma tana gefe tana Sallah da roƙon Allah ya kare Neehal a duk inda take. Da yake su Auntie's ɗin a gidan suka kwana ganin halin da Mama take ciki. Jiya har ɗaya na dare suna buge_bugen wayar mutane suna tambaya ko Neehal ta je gurin su, duk wata Number da Neehal ta rubuta a cikin jotter data rubuta Numbers da Ameen ya yi nasarar gani a ɗakinta, ya kira amma babu wanda ya ce ta je gurinsa, kafin ƙarfe goma na daren kuwa cikiyar Neehal ta baza garin Kano kamar yadda Daddy ya bayar da sanarwa a kowacce kafar yaɗa labarai dake garin Kano. Sai da asuba sannan Mama suka kira mutanen Gombe da na Abuja ko Neehal ɗin ta je can, nan ma aka sanar musu bata je ba. Da sassafe Uncle Mahmud ya haɗo Hajiya da driver zuwa Kano wadda ta matuƙar gigice jin ɓatan Neehal, Yayan Dad ma asubanci ya yi ya taho hankali a tashe. Duk gidan ƴan'uwa da kawu Musa yake tunanin Neehal zata je ya kira an ce bata je ba, har Gabasawa sai da ya kira nan ma babu wani labari. Wajen ƙarfe shida Mama ta kira Wayar Uncle Usman ta ji ko Niger ɗin Neehal ta je, ko kuma tana hanyar zuwa idan ta ƙarasa ya kira su ya sanar musu amma sai ta ji wayar tasa bata shiga. Ta kira Haneefah ko Kogin Neehal ta je amma Ita ma ta ce bata zo ba. Idan ka ga Mama sai ka tausaya mata ko ka zubar mata da k'walla, saboda yanda duk ta fita hayyacinta lokaci ɗaya. Ƙarfe bakwai na safe Daddy ya bar gidan dan zuwa Hospital's da kansa duba Neehal, gani yake kamar yaran da ya saka aikin basa dubawa da kyau shi yasa tun jiya har yau ba'a gan ta ba.......... Neehal tana rakub'e a gurin da ta yi Sallar Asuba har gari ya waye, ta rafka tagumi tana jiran ganin ikon Allah, bata taɓa riskar ranar data tsinci kanta a cikin tsoro da fargaba irin na yau ba, ta sadaqar ta karaya yau sai yanda Allah ya yi da ita tunda ya nufa ta wayi garin yau da ranta, ita kaɗai a cikin wannan gida tare da waɗannan azzaluman mutanen ai sai yanda suka yi da ita, amma bata daina addu'ar neman ɗauki a gurin Ubangijin ta ba. Wajen ƙarfe takwas aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, ta runtse idanta cikin matsananciyar fad'uwar gaba da murd'awar ciki, a hankali ta ce. "Shikenan, sun zo ida mummunan baƙin nufinsu a kaina, shikenan rayuwata ta zo ƙarshe." Jin an ajiye abu a gabanta yasa ta buɗe ido tare da d'ago kanta zuciyarta fal tsoro, wani farin saurayi ta gani tsaye yana kallon ta, gabanta kuma tire ne mai ɗauke da abinci, da alamun shi ya ajiye mata. Hawaye ya taru a cikin idonta ta fara kuka ta ce masa. "Fuskarka bata yi kala data masu cutarwa ba, ta yi kala data masu imani, dan Allah bawan Allah ka fitar da ni daga gidan nan kafin su gurɓata mun rayuwata, ni marainiya ce bani da kowa sai Allah, ka taimake ni dan Allah, na san baza ka so a wayi gari ka ga an ɓata rayuwar ƙanwarka ba, to ka ɗauke ni kamar haka ka fitar da ni daga gidan nan." Saurayin ya lumshe ido a hankali ya buɗe, kamar zai yi magana sai ya tuna ba'a ba su umarnin hakan ba, kuma akwai CCTV camera a ɗakin, sai ya juya cikin wani irin yanayi ya fice daga ɗakin. Neehal ta fashe kuka tare da saka ƙafa ta yi ball da abincin gabanta. Cikin kukan take faɗin. "Yaya where are you? Ka zo ka fitar da ni daga gidan nan kar su cutar da ni, kar su yi abun da zai sa zuciyar Mama ta buga, Daddy......." Haka ta dinga kiran sunan duk wani makusancinta tare da neman taimakon su, abun tausayi ta zama kamar wata zararriya. Ƙarfe goma saura wasu maza majiya ƙarfi guda biyu suka shigo ɗakin, Neehal ta tashi da gudu ta haye kan gado ta koma can ƙarshen gadon ta takure jikinta dake karkarwa kamar ana kad'a mata mazari. Gifd'a_gifd'an mutanen nan guda biyu suka bi ta gadon suka kamo ta tana ihun su sake ta har su kai ta inda za'a *keta mata haddi* amma kamar da dutse take magana abun da aka saka su kawai sukay. Fitar da ita suka yi daga ɗakin, wata ƙofa dake ƙarshen corridor ɗin gidan suka buɗe suka shiga, steps ɗin bene ne ya bayyana suka fara hawa da ita. K'ofofi uku ne a upstairs ɗin da suka hau, ta farko suka buɗe suka tura ta tana tirjewa sannan suka ja ƙofar suka fice. Ta d'ago kanta ta kalli mutumin dake tsaye a gaban gado yana saka face maks ta bogi a fuskarsa, sai dai kafin ya gama zirawa ta ga ainihin fuskar tasa, kuma ta gane shi. Ta miƙe cikin matuƙar dimaucewa daga fad'uwar da ta yi lokacin da mutanen nan suka yarda da ita. Dai-dai lokacin mutumin ya gama saka fake face maks ɗin, suka haɗa ido da shi ta cikin face maks ɗin da ya saka. Ko a cikin magagin bacci take ta ga mutumin nan sai ta gane shi, ko makancewa ta yi ta shafa fuskarsa sai ta gane shi, tsayuwarsa da siffar jikinsa kaɗai idan ta gani sai ta gane shi ko da ya juya mata baya ne, ko a cikin duhu ne, balle yanzu da yake tsaye a gabanta cikin haske suna pacing ɗin juna, ba fuskar bogi ba ko jikinsa duka ya ɓoye a cikin kayan ƙarfe sai ta gane shi, balle kuma ta riga ta ga fuskarsa ba tare da ya sani ba, ga kuma k'amshinsa da ba baƙo ba ne a gurin ta da ya mamaye ɗakin. Amma ita duk ba wannan ne damuwarta ba, damuwarta me ya kawo shi gidan? Me yake yi a cikin gidan da ake ƙoƙarin keta mata haddi? Me yasa k'artan mazan can suka kawo ta inda yake? Ko shine wanda mutumin da suka yi waya jiya ya ce zai aiwatar da mummunan ƙudirinsu a kanta? Ta d'aga hannunta dake karkarwa kamar an jona masa shock da ƙyar kamar yadda zuciyarta take fat fat fat kamar zata faso ƙirjinta ta fito ta nuna shi, cikin rawar murya numfashinta na fita da ƙyar kamar ana zarar ranta ta ce. "Ya..........✍️ (😭🙄 *Neehal wa kika gani ne!?* ) *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *6️⃣6️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........Sai kusan ƙarfe goma na dare Daddy ya dawo gidan, Yana cikin cire kaya Mama ta shigo ɗakinsa. Ta zauna akan stoll tana duban shi ta ce. "Daddy yau ina ka je ka daɗe haka? Gashi ina ta kiran wayarka bata shiga?" Daddy ya ce. "Au har kin manta inda na ce miki zan je da safe kenan?" Mama ta ce. "Sorry na sha'afa, sannu da zuwa da fatan kun dawo lafiya kuma an dace da abun da aka je nema?" Daddy ya ce. "An dace kam, bari na ci abinci nay wanka sai nay miki bayani." Mama ta yi murmushi ta ce. "Ga dukkan alamu dai baka da labarin an ga Sadik." Daddy ya ce. "What? Yaushe? Wallahi ban sani ba." Mama ta ce. "Tun yamma aka gan shi ko in ce ya dawo, dan Mamansa ta ce mun da kansa ya shigo gida cikin k'oshin lafiya." Daddy ya ce. "Alhamdulillah, kai Masha Allah for this nice story, to ya akai ya dawo?" Mama ta ce. "Bata faɗa mun ba, da zamu je gidan kuma rashin dawowar ka da wuri yasa bamu je ba, su Sadiya ma duk sun zo d'azun, amma gobe da safe Insha Allah zamu je gaba-d'ayan mu." Daddy ya zauna yana murmushin farinciki. Mama ta ce. "Kwanan masallaci ana sauka ya ƙare, yau sai ka more bacci ko zaka ciko, dan ba ƙaramar rama ka yi ba a Ƴan kwanakin nan." Daddy ya yi murmushin dake bayyanar da farin cikinsa ya ce. "Dole ai, bari na kira baban yaron na fara yi masa murna." Mama ta ce. "Toh, bari na kawo maka abincin ka nan ka ci." Daddy ya ce. "Ina Daughter ɗin ne da Hajiya?" Mama ta ce. "Sun kwanta tuntuni, Neehal ta sha kuka kanta sai ciwo yake mata." Daddy ya ce. "Sarkin kuka kenan, ta cancanci award ta wannan fannin." Mama ta ce. "Rashin duka ne da iskancin banza, abun kuka da bana kuka ba ita duk kuka take musu." Daddy ya yi dariya ya ce. "Duka kuma Doctor? Tab' ai ba me taɓa mun ƴa ya kwana lafiya, saurin kukanta kuma ai halitta ce, da yawan mutane haka suke musamman ku mata." Mama ta ce. "To Allah ya yaye mata." Tun bayan isha'i Neehal take saka ran ganin kiran Sadik a wayarta amma ta ji shiru, tun tana jira har bacci ya ɗauke ta. Data tashi da asuba ta ɗauka zata ga text ɗinsa ko missed call ɗin sa, amma ko ɗaya bata gani ba. Bata yi tunanin komai ba sai ta yi tunanin ko yana cikin dangi ne anata murnar ganin sa, ko kuma a gajiye ya dawo ya yi bacci da wuri. Kafin ƙarfe goma na safe sun gama shirin su na zuwa gidansu Sadik dukan su, Aunty Sadiya ma ta zo, Aunty A'isha ce dai tunda a unguwar take sai dai su biya gidanta su ɗauke ta. Mama da Daddy da driver a Mota ɗaya, Neehal da Hajiya kuma suna Motar Aunty Sadiya. Sun fara tafiya Mama ta dubi Daddy ya ce. "Jiya Ameen bai zo gida ba, yanzu kuma na kira shi ya zo mu je gidansu Sadik da shi wai ba zai samu damar zuwa ba, sun fita operating tun safe wani ƙauye." Daddy ya ce. "Allah sarki Son ba dai jajircewa a aiki ba." Mama ta tab'e baki ta ce. "Ni ban ma yarda da sun fita wani aiki ba, yau fa Saturday." Daddy ya ce. "Ina ruwan aikin tsaro da weekend Doctor, ko kin manta yanda na yi da ne, sai kina kira na kina Hamma Tafida wai baza ka dawo gida ba, idan ma kin same ni a wayar kenan." Mama ta yi murmushi tana tuna lokacin farkon Auren su ita da Daddy, lokacin suna faman yawon gari_gari a Nigeria idan an yi posted ɗinsa, wani gurin ma ba zai yiwu ya tafi da ita ba sai dai ya bar ta a gida. Cikin mintuna ashirin suka ƙarasa gidansu Sadik. A compound ɗin gidan suka tarar da Abban Sadik shi da Kawu. Suka gaisa cikin mutuntawa tare da yi musu murnar bayyanar Sadik da addu'ar Allah ya tsare gaba, Sannan su Neehal suka shige cikin gidan suka bar Daddy a gurin su Abba. Da fara'a sosai Maamah da ƴan'uwanta suka tarb'e su, suka gaisa cikin mutunta juna tare da ƙara jajanta abun da ya faru, su Mama sukay musu murnar bayyanar Sadik. Neehal dai tana ƙasa zaune akan carpet kanta a ƙasa, Hajja tana ta tsokanar ta, sai dai ta yi murmushi kawai, wata ƙanwar Maamah na tare mata. Ƴan'uwan Maamah suna da kirki sosai, kuma suna son Neehal da ɗansu, kawai babu yadda zasu yi dan su kansu al'amarin na ba su tsoro. Batul ƙanwar Sadik ce ta shigo falon, ta gaishe da su Mama sannan ta zauna a kusa da Neehal ta gaishe ta. Murya ƙasa_ƙasa yadda Neehal ɗin ce kaɗai zata ji ta, ta ce. "Aunty Neehal Yaya ya ce ki zo." Cikin d'oki Neehal ta ce. "Yana ina?" Batul ta ce. "Yana bayan gida nan." Neehal ta yi shiru dan bata san ta yanda zata iya tashi ta tsallake su Maamah da Mama ta tafi gurin Sadik ba. Maamah data fahimci abun da ke faruwa sai ta cewa Neehal. "Ƴata ku je da Batul ki ga jikin Sadik ɗin." Cikin jin kunya ta ce. "Toh." Sannan ta miƙe a hankali ba tare da ta kalli kowa ba ta bi bayan Batul wadda ta riga ta tashi. A wata rumfa dake bayan part ɗin Maamah suka same shi zaune akan ɗaya daga cikin kujerun robar dake gurin. Ta ƙura masa ido kamar yadda shi ma ya zuba mata nasa, sai ta ga ya rame ya ƙara haske. Ta zauna a kujerar dake fuskantar wadda yake kai, Batul kuma ta juya ta koma cikin gida. Sadik ya yi murmushi ya ce. "Neehal!" Ta mayar masa da matarnin murmushin ta ce. "Sadik!" Ya ce. "Na'am da fatan kina lafiya?" Ta ce. "Lafiya k'alau, Alhamdulillah Yaya Sadik, na gan ka cikin k'oshin lafiya ba kamar yadda muka yi zato ba, na ji daɗin hakan sosai sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba." Sadik ya ce. "Amin ya Allah, Are you sick?" Ta ce. "Lafiya ta k'alau, me ka gani?" Ya ce. "Duk kin rame Neehal." Ta ce. "Tashin hankalin ɓatan ka ne kawai amma yanzu ai komai ya wuce, tunda Allah ya dawo mana da kai lafiya." Sadik ya danne duk wata damuwa dake cikin ransa suka cigaba da hira da Neehal, har yake bata labarin yanda aka sace shi da inda aka kai shi. A Parlour'n Maamah kuwa bayan fitar su Neehal ba jimawa Hajiyarsu Sadik ta shigo Parlour'n. Bacci take a part ɗin Umma aka taso ta aka ce mata iyayen Neehal sun zo. Su Mama suka gaishe ta cikin girmamawa. Ta amsa ba yabo ba fallasa sannan ta ce. "To Alhamdulillah, yaron mu ya dawo lafiya, mun gode da zuwar mana murna da kuka yi, amma ku sani babu batun Aure yanzu a tsakanin sa da ƴarku." Cikin mamaki Hajiya ta ce. "Saboda da me kuma?" Ta ce. "Saboda mu tsiratar da rayuwarsa daga faɗawa halaka mana, dan wannan yar taku ba matar aure ba ce, yawwa, dan haka baza mu ɗauki ɗanmu mu aura masa ita watarana kawai mu wayi gari mu ga an kashe mana shi ba." Mama ta kalli Aunty A'isha dake gefen ta da sauri suka haɗa ido. Cikin rashin jin daɗin abun da Hajiyarsu Sadik ta faɗa, Hajja ta ce. "Haba Hajiya, wannan wacce irin magana ce?" Hajiya data saki baki tana kallon ta, ta ce. "Ko mutuwa tana kunyar idon iyaye, amma ke matar nan ki dubi tsabar idon mu ki faɗa mana haka? Saboda mun zo inda kike." Maamah ko kaɗan bata ji daɗin abun da Hajiyar ta ce ba, ta dubi su Mama ta ce. "Dan Allah ku yi haquri." Hajiyarsu Sadik ta ce. "Haqurin me zaki ba su, kar ma su yi haqurin gaskiya ce dole a faɗe ta, ƴarsu annoba ce wadda zaman ta ma a cikin al'aumma bala'i ne, wa ya sani ma ko mayya ce take lashe kurwar samarin nata." Wannan kalmar ta maita da Hajiya ta danganta Neehal da ita ta bala'in k'ona ran su Mama ta yi ba. Hajiya ta ce. "Insha Allahu sai dai ki ga maita a zuri'arki ba dai a tamu ba, kuma Allah sai ya sakawa yarinyar nan k'azafin maita da kikai mata, ɗanku kuma ku kwad'anta shi ku cinye ko ɗan gold ne Neehal baza ta aure shi ba." Ganin abun yana neman ya zama babban faɗa Maamah ta yiwa Abba text akan ya zo, dan duk haqurin da Hajja take ba su akan ɗan Allah su bar maganar haka amma sun ƙi saurarar ta. Aunty Sadiya da baza ta iya jure cigaba da sauraren munanan kalaman Hajiyarsu Sadik akan Neehal ba ta miƙe tana duban Hajiyar ta ce. "Yarinyar nan ƙaddara ce Allah ya ɗora mata wadda babu wanda ya fi ƙarfin ya ɗora masa ita, ita ma ba yin kanta ba ne. Dan haka karki sake danganta ta da maita, idan kin manta bari in tuna miki shari'ar maita ba ƙaramin abu ba ne, wallahi idan kika sake alaƙanta Neehal da maita zaki sha mamaki." Tana gama faɗar haka ta ɗauki jakarta a fusace, ta cewa su Mama su tashi su tafi. Kafin su kai ga tashin Abban Sadik ya shigo falon a ruɗe, bai tambayi ba'asi ba dan ya san halin mahaifiyarsa ya shiga ba su haquri. Hajiyarsu Sadik kuma sai ta saka kuka wai ƴar cikinta wadda ta yi jika da ita ta zage ta amma ya zo yana ba su haquri. Su Neehal suna can suna hira ba su san me yake faruwa ba, ita Neehal kanta gaba-d'aya ya kulle da labarin da Sadik ya bata, a yanda ta fuskanta waɗanda suke kawo masa abinci a inda aka ajiye shi su suka fito da shi suka dawo da shi gida. Kenan wanda yasa aka ɗauke sa shi ya saka aka dawo da shi, sai ta shiga tambayar kanta ta yaya Ameen ya fito da Sadik? Ko kuɗi ya bawa masu tsaron nasa fiye da yadda wanda ya saka su aikin ya ba su suka fito da Sadik ɗin? Ko kuma ƙarfi ya nuna musu ya tsoratar da su? Ko da hukuma ya haɗa su? Amma idan da hukuma ya haɗa su ai hukumar ce zata fito da shi su kuma a kama su. To ko dai ya san wanda ya sace Sadik ɗin ne? Sai ta girgiza kai a ranta tana cewa hakan ma ba zai taɓa faruwa ba, ta bar yiwa kanta tambayoyin tun kafin ta fara rubbish ɗin tunani akan Yayan nata wanda ta san ba za'a taɓa haɗa baki da shi a satar Sadik ba, ta k'udurce a ranta zata tambaye shi ya warware mata yanda abun ya kasance, duk da ta san halinsa da ƙyar ya bata amsa. Sadik yana ƙoƙarin faɗa mata abun da yake ransa na raba sun da aka yi dan kar ta ga lefin sa ta ga kamar ya zalunce ta ya yaudare ta, amma zuwan Batul kiran Neehal ɗin ya hana shi yi mata zancen, Batul ta ce ta zo su Mama suna jiran ta za su tafi. Neehal ta miƙe suka yi sallama da Sadik, ta lura da yanda jikinsa ya yi sanyi k'alau da kuma yanda yake bin ta da wani irin kallo. Ta tafi tana jin ba daɗi a zuciyarta kamar kar su rabu, sai ta tarar su Mama har sun shishshiga Mota zuciyoyinsu babu daɗi. Ta buɗe Motar Aunty Sadiya ta shiga, bata lura da yanayin da suke ciki ba saboda bata bari sun haɗa ido da kowa ba, har suka je gida babu wanda ya ce k'ala, sun yi shiru kowa da tunanin da yake a cikin ransa. A Parlour'n Mama suka zauna gaba-ɗayan su, sai a lokacin Neehal ta lura kamar duk suna cikin ɓacin rai. Daddy ya sauke wani gwauron numfashi yana duban Neehal cike da tausayawa. dan shi ma Abba ya faɗa masa komai akan fasa Auren ta da Sadik. Mama ta janyo ta jikinta cikin damuwa ta ce. "Ya kika ga jikin Sadik ɗin?" A hankali ta ce. "Lafiyar sa k'alau." Mama ta sauke numfashi ta ce. "Ki yi haquri Neehal da rayuwa a duk yanda ta zo miki, duk abun da kika ga kin rasa ba Alkhairi ba ne a gare ki, idan kika yi haquri da tawakkali sai ki ga Ubangiji ya sauya miki da wanda ya fi wanda kika rasa ɗin, komai lokaci ne da shi kuma komai mai wucewa ne, na daɗi ko na wahala. Neehal iyayen Sadik sun ce ba zai aure ki ba." Ai Neehal ji ta yi kamar Mama ta soka mata mashi a ƙirjinta, ta runtse idanta a ƙoƙarin ta na ganin hawaye sun zubo mata kamar kodayaushe idan tana cikin damuwa ko zata ji abun da ya tokare mata ƙirji ya yi ƙasa, amma sai hawayen suka ƙi zuwa wannan karon. Ta buɗe idonta tare yin murmushi mai ciwo wanda ya matuƙar bawa su Mama mamaki ta ce. "Shikenan Mama, Allah yasa haka shi Alkhairi, dama na san haka zata iya faruwa." Bata jira amsa ba ta miƙe dak'yar ta nufi upstairs, ko ganin gaban ta bata yi sosai saboda tsananin damuwa. Suka bi ta da kallo gaba-d'ayan su cike da tsantsar tausayawa Aunty A'isha har da k'walla. Hajiya ta fashe da kuka ta ce. "Gaskiya duk mai aikatawa yarinyar nan wannan abun Allah ka wulaqanta rayuwarsa ta duniya da lahira, Allah ka saukar masa bala'in da ya fi ƙarfin sa." Mama ta lumshe idonta wani tunani na d'arsuwa a cikin ranta wanda take ganin Insha Allahu shine ƙarshen matsalar Neehal. Aunty Sadiya ta ce. "Komai ya kusa zuwa ƙarshe da yardar Allah." Aunty A'isha ta ce. "Allah yasa." Suka cigaba da jimanta al'amarin, suna jinjina wulaqanci irin na Hajiyarsu Sadik. Aunty A'isha ta ce. "Ni ban ji daɗin maganganun da kika faɗa mata ba Sadiya, tunda babbar mace ce ta haife ki." Aunty Sadiya ta ce. "Ai bata da wani girma sai na jikinta, dan abun da ta yi halin ƙananun mutane ne." Hajiya ta ce. "Gwara da kikai mata hakan ai, da za ji zancen Shari'ah ai shiru ta yi ta kama kukan munafurci, yanzu sai a tattara musu kayansu da kuɗaɗen su a mayar musu." Daddy ya ce. "Insha Allahu gobe zan kira Alh. Musa da su Usman sai su zo mu mayar musu." Suka amsa da Allah ya kai mu. Su Aunty's ba su wani jima a gidan ba suka tafi, saboda yanda zuciyoyinsu gaba-d'aya babu daɗi, Hajiya ma ta ce gobe zata wuce Gombe. Dak'yar Neehal ta iya ƙarasawa ɗakinta saboda juyawar da kanta yake mata. Ta faɗa kan gado tana maimaita Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un cikin sark'ewar harshe. Jikinta gaba-ɗaya rawa yake kamar yadda take jin zuciyarta na bugawa da ƙarfi, ba rabuwa da Sadik ne yafi damun ta ba, *Baƙin tabon* da aka yiwa rayuwarta ne ya fi komai damun ta, ta san shikenan an fara kenan, duk wanda ya ƙara fitowa da niyyar Aurenta mutanen gari zasu hana shi ko kuma idan ya ƙi jin maganar mutane iyayensa wanda ya zama dole yay musu biyayya su hana shi, shikenan kuma wataƙila ita da Aure sai a lahira. Ta tuno gawar Jameel data gani lokacin da za'a kai shi makwancinsa na gaskiya, sannan ta tuno Anwar ma, ta tuno Ahmad ranar da suka rabu a soyayya sannan ta tuno moment ɗinsu da Sadik na d'azu, ta tuna yanda yake kallon ta da yanda ta ga jikinsa a sanyaye da damuwar data hango ƙarara akan fuskarsa, ashe duk na rabuwa da ita ne, hirar ƙarshe suka yi, kallon ƙarshe yake mata ashe. Sai a lokacin ta ji wasu hawaye masu d'umi suna bin kuncinta, wanda take jin kamar a zuciyarta suke sauka suna ƙara mata zafin da take ji a cikin zuciyarta_ta. Ta daɗe a cikin wannan halin mai wuyar fassaruwa, wanda ta kasa bambance a sume take ko a normal rayuwa saboda tsananin damuwa. Bata san mintunan data ɗauka ba ko awanni ba sai ji ta yi Mama tana mata magana. Ta d'ago kanta da yay mata nauyi ta dubi Maman, Mama ta taɓa jikinta ta ji ya yi zafi. Ta shafa fuskarta ta ce. "Ki tashi ki yi Sallah, ko baza ki iya ba?" Ta yunƙura ta tashi zaune dak'yar, a zaunen ma sai ta ji kamar jiri yana ɗibar ta, amma saboda kar tayar da hankalin Mama ta ce. "Zan iya." Mama ta ce. "Sannu kin ji, ki yi Sallar sai ki ci abinci ki sha magani, ki yi ta maimaita sunan Allah da Hasbunallahu'wani'imal'wakil, Insha Allahu zaki ji sauƙin zafin zuciyarki." Ta gyaɗa mata kai kawai. Mama ta bi ta da kallon tausayawa sannan ta tashi ta fice. Bayan ta yi Sallar a zaune Mama ta kawo mata abinci, favourite ɗinta Mama ta yi hoping zata iya ci, amma lauma ɗaya ta yi ta ji abincin ya kasa wucewa ta mak'oshinta, sai ta ji kamar ƙasa ta watsa a bakin nata, ba shiri ta furzar da abincin. Sai tea Mama ta haɗa mata ta sha shi ma da ƙyar ta iya shan kaɗan. Mama tay mata allura ta kwanta ta samu bacci ya ɗauke ta. Tana cikin baccin ta ji muryar Haneefah a kanta. Ta buɗe ido sai ta gan ta zaune a gefen ta. Haneefah ta ce. "Yau kuma bacci ake, na ɗauka zan zo in tarar kuna hira da Habibin naki." Neehal ta tashi zaune bata ce mata komai ba ta sauka ta shiga toilet saboda fitsarin data ji ya ɗaure mata mara. Bayan ta fito ta cewa Haneefah. "Yaushe kika zo?" Haneefah ta ce. "Na kai 30 minutes, na gaji da jiran ki har sai kin tashi da kanki shi yasa na tashe ki." Neehal ta ce. "Kin kyauta ai, gashi nan kin ja mun ciwon kai." Haneefah ta ce. "Sharri kayan k'walba." Sai kuma ta yi murmushi ta ce. "Ashe an ga Ya Sadik, dan iskanci shine baki kira ni kin faɗa mun ba." Neehal ta ce. "Sorry ƙawata, wallahi babu wanda na faɗawa, farinciki ya mantar da ni." Haneefah ta ce. "Sai fa Mommy ce da muka yi waya d'azu take mun zancen, ta ɗauka ma na sani. Na ce mata ban sani ba wallahi, ta ce mun Mama ce ta kira ta, ta faɗa mata." Neehal ta ce. "Ya dawo, cikin k'oshin lafiya ma." Haneefah ta ce. "Masha Allah, haka muke fata dama, yanzu sai k'unci da damuwa su ƙare Tunda Ango ya dawo." Haneefah ta ƙarashe zancen cikin sigar tsokana. Neehal ta yi murmushi mai ciwo ta ce. "Mu fara yin Sallah Haneefah, na ji an shiga a masallaci sai in baki labari." Haneefah ta ce. "Toh." Duk yanda Neehal take tunanin Haneefah zata ruɗe idan ta ji an fasa Auren su da Sadik sai ta ruɗe fiye da haka, ta miƙe tsaye kamar wata zautacciya tana ambaton Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Idanunta a waje. Neehal ta kama hannunta ta zaunar da ita ta ce. "Karki tada hankalin ki Haneefah nina barwa Allah komai, domin shi yake tsara mun rayuwa kuma ya fi ni sanin dai-dai a cikin ta, ki taya ni da addu'a Allah ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar tawa." Ta ƙarashe maganar cikin matuƙar raunin murya. Haneefah ta girgiza kanta idanunta fal da hawaye ta ce. "Abun ya yi yawa Neehal, daga wannan sai wannan, amma ba komai, komai na Allah ne kuma aure lokaci ne da shi idan lokacin yinki ya yi dole ki yi, babu wani mahaluƙi da ya isa ya hana yiyuwar sa." Neehal ta ce. "Hmmm, Haneefah ni ƴar jarida ce cikakkiya, a kullum cikin jin labarin halin da duniya take ciki nake, haka kuma ina jin labarin ƙaddarar mutane da dama, kowa da irin tasa, wasu matsalar talauci, wasu ciwo, wasu matsalar gidan aure ga suna nan dai matsalolin da yawa barkatai. Amma ban taɓa jin irin nawa ba, Ni kam Haneefah na fitar da rai da Aure har abada, zan cigaba da rayuwata ni kaɗai, in dage da bautawa Ubangiji nah domin samun rabauta a k'iyama. Amma Haneefah na gaji da wannan tashin hankalin, ƴan'uwa da abokan arziki kowa babu kwanciyar hankali. Ki kalli Mama fa, matar da ba ita ta haife ni ba, amma na tabbata damuwata ta kusa saka mata wani ciwon, haka ma Daddy jibi yadda gaba-d'aya ya rame duk saboda ni, ga su Aunty su ma cikin damuwa suke saboda ni, ga ki kema da sauran mutane. A kwanakin nan sai na ji gaba-ɗaya na tsani kaina da rayuwata, amma da nai wani tunani d'azu sai na yi istigfari, na tuna Ubangiji ya bar ni cikin k'oshin lafiya, ga wasu can kwance a gadon asibiti cikin jinya, wanda da zasu ganni na san zasu ce ina ma sune ni yanda nake da lafiyar nan. Rayuwa cike take da k'alubale kala-kala, kuma kowa da irin tasa ƙaddarar, ni kam na karb'i tawa hannu bibbiyu, yanzu addu'a kawai nake Allah ya cire mun son Sadik da tunanin sa daga cikin raina, na san hakan zai rage mun damuwar da nake ciki." Haneefah ta ja gwauron numfashi ta zare hannunta daga cikin na Neehal ta ɗora su akan ƙafarta, cikin confidence ta ce. "Insha Allahu Neehal zaki yi aure da mijin kere sa'a nan ba da jimawa ba, duk wannan k'uncin da kike ciki zai wuce ya zamto tamkar firlm a gare ki." Neehal ta lumshe ido tana jin kamar abun da Haneefah ta faɗa ba zai taɓa tabbata a gare ta ba........... ****************************** Sabuwar rayuwa Neehal ta buɗe a shafin rayuwarta, a ƙoƙarin ta na ganin ta manta da dukkan abubuwan da suka faru da ita a baya a rayuwarta. Ta yi ƙoƙari sosai wajen cire Sadik daga cikin zuciyarta tare da dagewa da addu'a. Ta koma shiru_shiru a rana bai fi ta furta kalmomin daza a iya irgawa ba. Kafin ka ga murmushi a fuskarta kam za'a daɗe. Alkur'ani da azkar su suka zamto abokan hirar ta, wani lokacin kuma takan taɓa karatun Hausa novels wanda Aunty Sadiya ta tuttura mata dan su ɗebe mata kewa. Tana kuwa jin daɗin karatun littafan sosai. Bata fita ko'ina, saboda a ganin ta tana fita za'a fara nuna ta ana gata nan ita ce duk wanda zata aura sai an kashe shi. Mama da Daddy sun yi sun yi ta koma gurin aikinta amma ta ƙi, da suka takura mata sai ta saka musu kuka, dole suka haqura suka ƙyale ta. Duk wani abu da Mama ta san zai sata farinciki shi take yi, haka zata fita da kanta ta jido mata su sweets wanda ada ita take hanata shan su, amma yanzu duk dan ta yi farinciki take siyo mata. Tun ranar da aka mayar wa da Sadik kayansa gidansu ya turo mata text ɗin ban haquri da nuna mata ba laifinsa ba ne ba su ƙara magana ba. Ahmad ya zo tun cikin week ɗin da ya samu labarin bayyanar Sadik, yay mata murna ya sanar mata bikinsa watan malaudi. Bata sanar masa an fasa bikinsu da Sadik ba dan ta san tsaf zai iya dawowa cikin rayuwarta a matsayin masoyi, ita kuma bata son hakan, ta riga ta cire babin soyayya a rayuwarta. Kuma baza ta so yabar yarinyar da zai aura saboda ita ba, dan ko ita akaywa haka baza ta ji daɗi ba. Ameen kuwa sai ya zo gidan ya tafi ma ba su haɗu ba saboda wunin ɗaki take, babban dalili ne yake fito da ita falo ko ya saukar da ita ƙasa. Yau ta kama Monday, wanda ya yi dai-dai da wata ɗaya da fasa Auren su da Sadik. A jiya ne kuma ƙawarta Zee ta Bayero ta sanar mata result ɗinsu na last semester is on the corner. Hakan yasa ta shirya yau zata je gurin aikin su, saboda ta ciccike wasu takardu na promotion ɗin da za'ai mata, tunda yanzu zata bar aiki da k'walin Deplomer ne ta koma da na Degree, kafin result ɗin ya fito komai ya yi ready sai ta haɗa ta yi linking ɗinsu. Dama zaman gidan ya fara isar ta, kuma wannan aikin shine gatan ta a duniyar nan, baza ta so ta rasa shi ba.Ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa, ta yi kwalliya sama_sama a ƙoƙarin ta na ganin kar mutane su gane halin damuwar da take ciki. Sai dai a fuska ne kawai ta iya pretended amma damuwar na nan kwance a cikin zuciyarta. Ta tsaya tana kallon kanta a mudubi, sai ta ga ta rame musamman ta wuya da saman ƙirjinta. Hakan yasa ta cire mayafin jikinta ta ɗauko hijabin da zai shiga da kayan jikinta ta saka. Ta ɗauki jakarta wadda wayoyinta ke ciki ta nufi ƙofa, har ta buɗe ƙofar zata fita ta dawo ta ɗauki wata ƙaramar wayarta keypad wanda bata fiya amfani da ita sosai ba, ta saka ta a cikin aljihun rigar jikinta sannan ta fita. A falo suka ci karo da Mama, Mama ta yi murmushin jin daɗin yanda ta gan ta. Ta kama hannunta ta ce. "Kin tashi lafiya Daughter." Neehal ta ce. "Lafiya k'alau Mamana, ina kwana." Mama ta ce. "Lafiya k'alau, ko kefa Neehal har na ji daɗi da zaki koma aikin nan, zai ɗebe miki kewa ba kaɗan ba, jiya da Ameen ya zo kin yi bacci yay ta faɗa wai iskancin me ya hana ki komawa aiki." Neehal ta yi murmushi ta ce. "Mama ɗan nan naki halinsa sai shi, Yaushe ya daina masifar zuwa na aikin, amma yanzu dan bana zuwa zai ce in koma." Mama ta ce. "Nima na yi mamakinsa, wai zama guri ɗaya babu fita gara kina fita kina ganin jama'a hakan zai rage miki damuwa." Neehal ta ce. "Haka ne, shi yasa yau na shirya komawa, Daddy ya fita ne?" Mama ta ce. "Yana nan yanzu dai zai fitan." Neehal ta ce. "Bari na je na gaishe shi." Mama ta ce. "Okay." A falo ta tarar da Daddy zaune yana waya, ta zauna a ƙasan kujerar da yake a zaune, sai ya katse wayar ya dube ta da murmushi ya ce. "Daughter an fito? Ta ce "Eh Daddy ina kwana?" Ya ce. "Lafiya k'alau ƴar albarka, dafatan kin yi breakfast?" Ta ce. "Na yi Daddy." Ya ce. "To Masha Allah, sai yaushe zaki dawo?" Ta ce. "Zan kai yamma saboda cike_ciken da zan yi." Daddy ya ce. "To Allah ya taimaka, ki kula fa sosai kin ji." Ta ce. "Insha Allah Daddy." Sannan ta miƙe tay masa sallma ta fita, ta koma ta yiwa Mama Sallama ta tafi. Ta ji daɗin fitar da ta yi yau sosai, sai ta ji duk rabin damuwarta ta kau, tana ta hada_hada cikin jama'a ko time ɗin tunani bata samu ba, balle ta tunano abun da zai dame ta. Duk inda ta gilma ma'aikata na yi mata magana, wasu na tsokanarta da wata sabon gani wasu kuma suna yi mata ya jiki, saboda abun da ta cewa Manager ɗinsu kenan da bata zuwa bata da lafiya ne. Sai yanzu ta ƙara tabbatar da abun da Mama take faɗa mata kullum akan ta dinga fita zata ji sauƙin damuwar dake ranta. Sai yamma ta baro gurin aikin tana jin zuciyarta wasai. Ta shigo farkon layin su ta ga wata Mota tana tahowa daga cikin layin, ta yi b'arin left inda masu shiga suke bi, masu fita kuma right side suke bi, amma sai ta ga Motar saitin da take bi nan ita ma take bi, kuma layin nasu yana da faɗi sosai, three motors zasu iya wucewa a lokaci ɗaya ba tare da sun takura ba, kuma babu kowa a layin balle ta ce an tsare masa hanya ne. Ta cigaba da tafiya slowly tana kallon ikon Allah, sai ta koma right side ta bar masa left side ɗin, sai ta ga shi ma ya canza ya koma inda ta koma. Ta yi tsaki ta cigaba da tafiyar ta, a ranta tana faɗin baza ta kuma matsawa ba, sai dai shi in ya ga zasu yi karo ya matsa. Amma me, sai kawai ganin Motar ta yi ta sha gaban ta kamar zata buge ta. Ta taka burki cikin sauri gabanta na fad'uwa. Kafin ta yi wani yunkurin ta ga maza guda biyu sun fito daga cikin Motar cikin sauri, ta yi looked Motar ta_ta da sauri cikin mamakin dalilin da yasa waɗan nan mutanen zasu tare mata hanya, ta shiga ambaton Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un a cikin zuciyarta. Suka ƙaraso inda take suka yi mata knocking glass ɗin Motar. Da farko ta tsorata sai ta ƙi buɗe musu, amma daga baya kuma da ta ga suna bata mata time sai ta zuge glass ɗin Motar ƙasa ta dube su cikin dakiya da son ɓoye tsoron da take ciki ta ce. "Me kuke buƙata a gurina, da zaku taren hanya and then ku zo kuna mun knocking?" Ɗaya daga cikin su ya juya yana kallon layin da babu kowa sai su kaɗai, ɗayan kuma ya bata amsar tambayar ta da watsa mata wani abu a fuska. Ta rufe idanunta tare kare fuskarta_ta da hannunta tana jujjuya kanta saboda juyawar da ta ji ya fara mata, cikin wasu sakanni kanta ya langwab'e a jikin kujerar da take. Da sauri wanda ya watsa mata abun ya zira hannunsa ta saman glass ɗin ya yi unlocked ɗin Motar, sannan ya ja murfin ya buɗe ya shiga, ya mayar da Neehal kujerar mai zaman banza sannan ya zauna a driver seat ya rufe Motar ya tayar da ita ya yi reverse ya fice daga layin da mugun gudu. Ɗayan wanda ya kasance kamar mai yi masa gadi ya juya cikin gudu ya shiga Motar da suka fito daga ciki ya kunna ta ya bi bayan ɗan'uwansa a guje.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *6️⃣8️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ........."Ya...ya... Al...lah kasa mafarki nake ba gaske ba ne abun da yake faruwa." Ta sauke hannunta tare da runtse idonta tana girgiza kai, cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ta buɗe ido ta ga babu shi a gurin, Allah yasa idan ta buɗe idon ba shi zata gani ba wani daban zata gani idanunta ne ke mata gizo. Ta buɗe idonta a hankali kamar mai tsoron buɗewa bugun zuciyarta na ƙaruwa. Shi ɗin ne dai tsaye a gaban ta yana kallon ta. Ta sake nuna shi tana ƙoƙarin yin magana amma ta kasa sarrafa harshenta ta yi maganar, sai rawar baki kawai take. Ta juya cikin fitar hayyaci ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice da gudu, ƙofar dake kusa da dakin ta murd'a ta buɗe ta shiga, cikin ikon Allah kuma ƙofar a buɗe take. A cikin wani ɗan ƙaramin ɗaki da babu komai a cikinsa ta tsinci kanta, ta zube a bakin ƙofar cikin matsanancin tsoro da fargabar wanda ta gani, shirun sa da yanda ya tsaya yana kallon ta ya tabbatar mata da shine wanda yake ƙoƙarin keta mata haddi, me ya haɗa shi da wannan ƙungiyar wadda bata tantama ta matsafa ce? Ko shi ma member ne a cikinta? Ta tambayi kanta. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." Ta shiga maimaitawa a fili cikin sark'ewar numfashi. Addu'a da fatanta ɗaya Allah ya farkar da ita daga wannan mummunan mafarkin da take, dan ta kasa yarda a gaske ne wannan baƙin al'amarin yake faruwa da ita. Wanda take masa kallon jigon rayuwarta anya zai aikata mata haka? Wanda take kallo a matsayin bangon rayuwarta a ce da shi ake ƙoƙarin gurɓata mata rayuwa, wannan wacce irin ƙaddara ce ta kuma samun ta? Wacce irin rayuwa take yi ne a duniyar nan? A fili ta furta. "Ya Allah idan wani laifin nai maka kake jarabta ta Allah ka yafe mini ka sassauta mun wannan jarabawar, Ya Allah karka tabbatar da abun da nake zargi, Allah karka ɗora mun abun da ya fi ƙarfi na." Ta zauna akan gwiwoyinta ta shiga bubbuga kanta a jikin kofar ɗakin cikin rashin sanin mafita da abun yi, ƙwaƙwalwarta_ta ta tushe gaba-d'aya ta ƙi bata space ɗin ma da zata yi tunani, idanunta kamas ko k'walla babu a cikinsu, kukan ma ya ƙi zuwar mata balle ta ji sauqin yaƙin wutar da ake a cikin zuciyarta....... Tunda bayan fitar Daddy su Mama suke ta amsa kiran wayar mutane, ƴan'uwa da abokan arzik'i ana ta tambayar ko an ga Neehal. Mak'ota da wasu mutanen suna ta zuwa jaje. Ƙarfe sha ɗaya da mintuna Hajiya ta ƙaraso gidan, ta zube a falon ƙasa inda su Mama suke da Abba yayan Daddy wanda bai jima da zuwa gidan ba shi ma. Salati kawai Hajiya take yi tana hawaye. Mama tay mata sannu da zuwa cikin muryarta dake fita da ƙyar saboda tsananin damuwa. Su Aunty ma suka gaishe ta tare da bata baki akan ta yi haquri. Hajiya ta ce. "Wanne irin haquri zan yi? Ku daina bani wani haquri ni, ku bar ni in yi kukana, wannan wanne irin bala'i ne yake bibiyar yarinyar nan? Dan na tabbatar sace ta aka yi." Mama ta jinjina kai tare da sauke numfashi. Dan itama zuwa yanzu ta fi zargin sace Neehal ɗin akay. Gashi Daddy shiru tunda ya fita bai dawo ba, ana ta trying Numbers ɗinsa basa tafiya. Gajiya Neehal ta yi da bubbuga kan nata ta zauna dab'as tana sauke numfashi, sai ta ji kamar wani abu yana tokarinta a cinya. Ta kai hannu ta taɓa gurin sai ta ji abu a cikin aljihun rigarta. Cikin sauri ta dage hijabin jikinta ta zira hannu ta zaro ƙaramar wayarta da tashin hankali ya mantar da ita tana jikinta. Hannunta har rawa yake wajen kunna wayar, sai kuma ta kama waige_waige kamar mai tsoron kar wani ya gan ta. Numbern Mama ta lalubo da ƙyar saboda ko gani bata yi sosai ta yi dialing, amma sai kiran ya ƙi tafiya, tay ta trying kusan sau 20 amma ya ƙi tafiya, wayar ma gaba-d'aya emergency ta koma, sim ɗin ya ɗauke alamun babu network. Cillar wayar ta yi gefenta cikin takaici, ta zauna sosai ta jingina kanta dake barazanar fashewa saboda ciwo a jikin ƙofar ɗakin, bata san kuma mai zai faru da ita next ba, ko zasu biyo ta har nan ɗin ne su cimma buƙatarsu a kanta? Ko kuma wani sabon shirin muguntar suke kuma yi a kanta? Duk wannan ba shine abun da ya fi damunta ba a yanzu, damuwarta me ya kawo mutumin data gani a ɗakin da aka kaita? Ko fitar da ita ya zo yi daga gidan? Amma me yasa da ya gan ta ya ƙi magana? Ya ƙi ce mata komai? Me yasa data fito bai biyo ta ya kama hannunta sun fice daga gidan nan ba? Me yasa? A fili ta ce. "Dan Allah ka zo ka ce mun zuwa ka yi ka cece ni ba wai da kai ake ƙoƙarin cutar da ni ba, idan har hakan ta kasance ƙwaƙwalwarta baza ta ɗauki wannan al'amarin ba, zuciyata bugawa zata yi in mutu......!" Tun daren jiya da Ameen ya bar gidan Mama ya koma gidansa ya kulle kansa a ɗakinsa dan a halin da yake ciki ba ya buƙatar takurar Hafsat. Wata ƴar ƙaramar laptop ya ɗauko ya shiga operating, ga dukkan alamu aikin da yake yi mai matuƙar mahimmanci ne duba da yanda ya bayar da hankalinsa duka a kan aikin, yana yi yana kiran Numbobin Neehal tare da addu'ar Allah yasa su shiga, ya ɗaukarwa kansa alƙawarin duk inda Neehal take sai ya nemo ta ko da zai rasa ransa a gurin yin hakan, saboda dalilai guda biyu. Na farko saboda Mahaifiyarsa, ba zai iya jurar ganin Mama cikin wannan tashin hankalin da take ciki ba, wanda bai taɓa ganin ta a cikin irinsa ba tsawon rayuwarsa, dan haka dole sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Na biyu kuma yana son sanin gaskiya akan wani al'amari da yake zargi, al'amarin da idan abun da yake zargi ya tabbata to tabbas da akwai babbar matsala, matsalar da zata girgiza rayukan mutane da yawa. Har asuba yana operating system, sai da aka kira sallah sannan ya tashi duk ya haɗa zufa duk da A.C dake ɗakin, sai da ya watsa ruwa sannan ya ɗaura alwala ya fito ya tafi masallaci. Hafsah ta cika ta yi fam akan shiga ɗaki da Ameen ya yi ya kulle, kishi ya cika ta dan ko tantama bata yi saboda ɓatan Neehal ya aikata hakan. Kwana ta yi tana jan tsaki da ƙwafa tare da addu'ar Allah yasa kar a ga Neehal ɗin shegiyar yarinya, ko kuma in an gan ta a gan ta a mace kowama ya huta. Dan tun gabatowar bikinta da Sadik ta rasa gane kan Ameen, har yanzu kuma bai dawo dai-dai ba, kullum cikin damuwa da shegen bincike_bincike yake, wanda ta san duk akan al'amarin Neehal ɗin ne. Bayan ya dawo daga Masallacin ɗakin Hafsat ya zarce, ya tarar da ita kwance lullub'e da bargo babu alamun ta tashi ta yi Sallah. Ya shiga tashin ta a hankali. Ta buɗe ido da yake baccin nata ba wani nisa yay ba, sai da aka shiga sallah ya ɗauke ta. Ta riƙe hannunsa idanunta ƙur a kansa, cikin kissa ta ce. "Baby." Tana tashi zaune. Bai amsa mata ba sai zare hannunsa da ya yi daga cikin nata yana haɗe rai, ta kuma san dalilin hakan saboda bata tashi ta yi Sallah akan lokaci ba ne. Sai ta ƙara riƙe hannunsa cikin damuwa ta ce. "Baby a kwana ɗaya har ka faɗa, nima jiya kwata_kwata ban samu bacci ba, saboda damuwar ɓatan sister, sai yanzu gab da Asuba na ji ya ɗauke ni, dan Allah ka kira Mum ka tambaye ta ko an ga Neehal ɗin, ko kuma an samu labarin inda ta je, hankalina gaba-d'aya a tashe yake." Ya saka ɗayan hannunsa ya shafi gashin kanta cikin sanyin murya ya ce. "Go and pray First." Ta gyaɗa masa kai cikin nuna tsantsar damuwa. Ta sakar masa hannunsa ta sauka daga kan gadon ta shiga toilet zuciyarta fal da murna, dan yanda ta ga yanayin Ameen ta san babu wani daddaɗan labari, ta k'udurce a ranta tana idar da Sallah zata kira Mama dan jin ƙarin bayani, a zuwan da damuwar abun ta kwana kamar yadda ta nunawa Ameen. Shi kuwa da ya koma ɗakinsa ɗorawa ya yi daga inda ya tsaya a aikin da yake yi, babu alamun yana da niyyar fita yau..... Neehal tana nan zaune a bakin ƙofa ta ji ana taɓa handle ɗin ƙofar ta waje. Ta zabura ta miƙe tsaye ta manne a jikin bango jikinta na ƙyama, jin an turo ƙofar ɗakin ta runtse idanta a tunaninta sun biyo ta nan ne domin su far mata. Jin shiru har na wasu sakanni bayan turo ƙofar yasa ta buɗe ido, farin saurayin nan da ya kawo mata abinci d'azu ta gani yana kallon ta. Ya tako a hankali zuwa gaban ta ya kama hannunta ya ce. "Ki nutsu ƴan'mata, zan fitar dake daga gidan nan yanzu amma sai kin nutsu kin kuma yi komai cikin lura. Da sauri Neehal ta gyaɗa masa kai alamun gamsuwa. Ya ce. "Ki zauna anan, yanzu zan je na lalata wutar gidan haske ya ɗauke, kafin su gyara Insha Allahu zan fitar da ke. Cikin marainiyar murya Neehal ta ce. "Na gode, na gode sosai bawan Allah." Ya jinjina mata kai sai kuma ya juya da niyyar fita idanunsa suka sauka akan wayarta dake tsakar ɗakin, ya waro Ido cikin alamun mamaki. Da sauri Neehal ta zo ta tattare wayar data tarwatse ganin yanda yake kallon ta, ta haɗa ta ta kunna ta. Bai ce komai ba ya juya ya fita. Neehal ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ƙara dialing Numbern Mama, amma still bata tafiya network is not available ake rubuta mata. Kamar ta yar da wayar sai kuma ta zira ta a cikin aljihun rigarta. Ta koma ta rakub'e a kusurwar ɗakin tare da rafka tagumi da hannu biyu. Bayan mintuna biyar ta ga hasken ɗakin ya ɗauke sai duhu dumɗum, ta ƙara mannewa a cikin bango jikinta na ƙyarma. Ko minti biyu ba'ai ba ta ji an turo ƙofar ɗakin an shigo, muryar saurayin ta ji yana faɗin. "Taso da sauri ba mu da ishashshen time." Neehal ta tashi cikin sauri kamar yadda ya ce ta yi inda ta ji sautin muryarsa saboda bata ganin sa, sai da ta matso kusa da shi ne ma ta ga alamar duhun mutum a tsaye, ya kamo hannunta cikin raɗa ya ce. "Duk inda nasa ƙafata ki saka taki, amma sai kin yi sauri fa dan yanzu zasu gyara wutar, kuma gidan nan gaba-d'aya a zagaye yake da CCTV camera, duk inda muka gilma akwai masu kallon mu." Neehal ta gyaɗa masa kai. Ya buɗe ƙofar suka fita yana jan ta, dan gudun ma gagarar ta ya yi ta kasa yin sa, sai faɗuwa take musamman idan suka zo gurin shan kwana, amma kuma sai ta miƙe zumbur saboda tamkar gudun ceton rai take. Suna fitowa daga corridor ɗin gidan wutar gidan ta dawo, saurayin ya waro ido waje cikin alamun tsoro, dan ya san kafin sukai bakin gate waɗanda suka gyara wutar sai sun gan su, ya tsaya ya fara tunanin mafita. Neehal ta shiga kalle_kalle a makeken harabar gidan. Bai gama tunanin ba ya ji alamun tafiya, ya yi saurin jan hannun Neehal suka zagaya baya, suna zuwa bayan ya hangi mutum uku suna tahowa, ya yi saurin yin ƙasa tare da jan Neehal suka b'uya a bayan wani gini. Ta daf da ginin mutanen ukun nan suka zo suka wuce, ɗaya daga cikinsu har da juyowa, ai kaɗan ya rage Neehal bata saki fitsari ba. A tare suka saki ajiyar zuciya bayan mutanen sun ɓace wa ganin su. Saurayin ya miƙe hannunsa cikin na Neehal ya ce. "Gudu zaki yi sosai mu samu ki fita daga gidan nan, dan na san zuwa yanzu sun fara nemanki, mintuna kaɗan kuma ya rage ragowar ƴan ƙungiya da sarauniya su ƙaraso gidan nan dan bikin murna." Neehal da zuwa yanzu ta fara sarewa ta gyaɗa masa kai numfashinta na fita da ƙyar. Ya ja hannunta suka falfala da gudu yana yi yana waiwaye, cikin ikon Allah har suka ƙarasa gate ɗin gidan babu wanda ya gan su. Sai dai gate ɗin a kulle yake da gark'amemen ƙwado. Saurayin ya dafe kansa cikin takaici dan gaba-d'aya ya manta da akwai sauran rina akaba, wato ta yanda zasu fice daga gidan. Kallon ɗakin mai gadi ya yi sannan ya juyo ya kalli Neehal wadda ke ƙoƙarin sumewa. Ya ja ta dan tafiya ma neman gagarar ta take, a bakin ƙofar ɗakin mai gadi suka tsaya, ya zaunar da ita shi kuma ya tura ƙofar ya shiga. Mai gadin yana zaune kishingid'e, jin an shigo ya tashi zaune sosai. Saurayin ya ƙaƙaro murmushi ya ce. "Malam Buba ana hutawa ne?" Malam Buba ya washe baki ya ce. "A'aa, Malam sagiru kai ne, sannu da zuwa farin mutum ganin ka Alkhairi ne." Sagir ya ce. "Yau an gama abinci da wuri, kuma baka zo ka kawo kwano ba." Buba ya ce. "Ai na ga lokaci bai yi ba ne shi yasa." Sagir ya ce. "Ka san yau muna da shgali fa shi yasa aka gama da wuri, yanzu dai ɗauko kwanan naka kar wanda ya fi maik'on ya ƙare." Buba ya ƙyalƙyale da dariya ya tashi ya ɗauko flaks ɗin da ake zuba masa abinci ya miƙawa Sagir, Sagir ya karɓa ya buɗe ya ce "Dan daurayo shi dai a bayan gida Malam Buba, na ga da ɗan maik'o a cikinsa." Buba ya ce. "Toh Sagiru daɗina da kai akwai tsafta." Sagir ya yi murmushi kawai yana wurwurga idanunsa a ɗakin yana neman inda zai ga makullan gidan. Cikin sa'a ya ga malam Buba ya ajiye su akan wani ɗan table ya shige toilet. Jikinsa har rawa yake ya ɗauka tare da juyawa ya fice daga ɗakin da mugun gudu, inda ya bar Neehal anan ya tarar da ita. Ya kama hannunta suka nufi get ɗin da gudu, ya lalubo key ɗin ƙofar ya shiga bubbud'e makullan gidan kusan guda goma, yana yi yana waiwaye. Yana gama buɗewa ya hango Buba ya fito daga ɗakinsa a gigice, ya kama ƙaramar ƙofar gate ɗin ya buɗe ya tura Neehal waje sannan shi ma ya fita, ya damk'i hannunta suka falfala suka yi gabas da mugun gudu. Tafiya sosai suka yi sannan Neehal ta faɗi tana numfarfashi, cikin magana da ƙyar ta ce. "Ruwa, ruwa." Sagir ya ce. "Ki yi haquri ban san inda zan samu ruwa in baki ba, kuma dole anan zan barki in koma gidan da muka fito in karɓi hukunci na." Neehal ta ƙura masa ido ta ce. "Me yasa ka san za'a hukunta ka, ka taimake ni? Me yasa zaka koma gidan da da mutanen cikinsa babu Allah a ransu? Ka zo mu gudu tare mana." Sadik ya girgiza mata kai ya ce. "Duk inda na shiga a faɗin duniyar nan sai sun nemo ni, idan ban koma ba a yanzu za su tsotse jinin mahaifiyata wadda ita kaɗai ta rage mun a duniya, ni kuma da haka ta faru gwara ni su kashe ni." A ruɗe Neehal ta ce. "Tsotse jini kuma? Suna shan jini ne?" Sagir ya gyaɗa mata kai ya ce. "Eh suna shan jini, matsafa ne, kuma nima ina cikin su." Neehal ta waro Ido ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, me ya kaika cikinsu? kuma gashi ba kai kala da marasa imani ba." Sagir ya ce. "Baza ki gane ba ƴan'mata, amma abun da zan faɗa miki rashin imanin yan ƙungiyar nan ya wuce duk inda kike tunani, ni zan koma kafin azzaluman ƙungiyar da sarauniya su ƙaraso." Neehal ta ce. "Me yasa ka taimake ni?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce. "Saboda Yayanki Al'ameen, ya taɓa mun wani taimako da bazan taɓa mantawa da shi ba a rayuwata, kalamanki na d'azu a lokacin da na kawo miki abinci su suka tunzura ni akan na taimake ki, domin na san kamar yadda kika faɗa da ƙanwata ce na ga ana ƙoƙarin keta mata haddi sai inda ƙarfina ya ƙare a ceton ta duk da bani da ƙanwar ban san daɗinta ba ni kaɗai iyayena suka haifa. Dan haka na yi amfani da wannan damar gurin sakawa Ameen da Alkhairin da yay mun na taimake ki, domin na san da zarar sauran ƴan ƙungiya sun zo babu abun da zai hana su aiwatar da ƙudirinsu a kanki sai dai wani ikon Allah. Ni ne na bar ƙofar ɗakin da kika shiga a buɗe saboda na san idan kin samu kin kub'uta nan zaki fara tunkara dan neman tsira." Ta ce. "Ta ya ya ka san ni ƙanwar Ameen ce?" Sagir ya yi murmushi ya ce. "Na sani kawai." Neehal ta ce. "Ya sunan ka?" Ya ce. "Sagir." Ta ce. "Na gode sosai Yaya Sagir da taimakon da ka mun, amma ina tsoron kar su kashe ka saboda ka fito da ni." Sagir ya ce. "Karki damu baza su taɓa kashe ni ba." Neehal ta sauke ajiyar zuciya numfashinta na fita da sauri_sauri. Sagir ya miƙe da niyyar tafiya Neehal ta tsayar da shi da faɗin. "One more question." Ya tsaya yana kallon ta bai ce komai ba. Ta ce "Wanda waɗannan mutanen suka kaini ɗakinsa shine wanda yake ƙoƙarin keta mun haddi? Shine wanda aka ce mun my virginity is for him? Shi ma ɗan ƙungiyar ne? Yana shan jini?" Sagir ya ce. "Kin ci sunanki ƴar jarida, Tamboyoyinki kuma amsar su gaba-d'aya *Eh* ce." A razane Neehal ta ce. "Real him ɗin shi fa, not fake face maks ɗin daya saka, kasan kuwa matsayin shi a gurina?" Sagir na ce. "Na sani kuma shi ne." Neehal ta dafe ƙirjinta da sauri saboda wata irin bugawa da zuciyarta ta yi a million. Hakan ya yi dai_dai da jin vibration ɗin wayarta da ta yi. Sagir ya juya ya tafi cikin sauri. Ta zaro wayar daga cikin aljihun rigarta da ƙyar saboda yanda kanta yake juya mata, ta danna gurin picking ba tare data duba mai kiran ba. Ameen wanda tun safe ya ɗora da kiran Numbobin Neehal sai yanzu cikin sa'a ya ji ɗaya ta shiga. A hanzarce ya ce. "Miemerh." Cikin magana da ƙyar ta ce. "Yaya...!" Ya ce. "Where are you?" Ta ce. "I dont know, please Yaya ka zo ka ɗauke ni." Ameen ya sauke doguwar ajiyar zuciya ya ce. "Okay I will come now Insha Allah, ki bar wayar a kunne." Bai jira amsar ta ba ya katse kiran. Ya miƙe da sauri ya ɗauko wata laptop ɗinsa ya kunna ta ya shiga latsawa yana kwafar Numbern da suka yi waya da Neehal yanzu yana sakawa a ciki, sannan ya ɗauko wani abu mai kama da waya ya yi connecting ɗinsa da system ɗin, ya soka wani abu a jikin socket ya shiga lallatsa su a tare, in ya taɓa wannan sai ya taɓa wancan, a gaggauce yake yin komai. After 5 minutes ya sauke doguwar ajiyar zuciya a fili ya ce. "Alhamdulillah." Sannan ya ɗauko wani abu a cikin takarcensa mai kamar agogon hannu ya ɗaura a damtsen hannunsa. Ya kwashi wayoyinsa ya dau key ɗin Mota ya fice daga gidan ko Hafsat bai yiwa Sallama ba. Gudu yake shararawa sosai akan titi, cikin 1 hour ya ƙarasa inda Neehal take da taimakon abun da ke ɗaure a hannunsa wanda shi yake masa pointing hanyoyin da zai bi zuwa inda Neehal take. Ya yi parking a gabanta inda wayarta take yashe a ƙasa wanda da sim ɗin ciki ya iya gano inda take. Ya fito cikin sauri yana kiran sunanta. Ta buɗe ido da ƙyar ta ƙura masa ido amma ko hannunta ta kasa d'agawa, ta kai maƙura a galabaita. Dan ma lokacin ƙarshen damuna ne ba'a rana mai zafi sosai, amma rashin cin abinci da ƙishirwa su suka taimaka gurin galabaitar ta_ta over. Ameen ya tsugunna a gabanta tare da riƙe hannunta, yana sakin ajiyar zuciyar farinciki ya ce. "Miemerh wa ya kawo ki nan?" Ta girgiza masa kai tana son ta yi magana amma ta kasa. Da ƙyar ta iya cewa "Ya..ya..!" Ya ce "Na'am, I'm here with you." Ta yi luuu da idanunta ta lumshe su, daga gan bata ƙara sanin inda kanta yake ba ta sume. Ameen ya ciccib'e ta fahimtar da ya yi ta suma ya kai ta cikin Mota ya kwantar da ita a bayan Motar. Shi kuma ya shiga gaba ya ja motar a guje suka bar gurin bayan ya dauko mata wayarta dake yashe a ƙasa. Ya so ya yi binciken abun da yake neman sanin gaskiyar sa, amma halin da Neehal take ciki yasa ba zai iya tsayawa ba, ya ji jikinta da zafi sosai alamun akwai zazzaɓi a jikinta. 50 minutes ce ta kai su gidan Mama, a ƙofar part ɗin Mama ya yi parking ya fito ya ɗauko ta, har lokacin tana nan kamar yadda ya ɗauko ta. Babu kowa a falon ƙasa sai su Dije dake kitchen suna girki, su Mama tunda suka hau sama yin Sallah ba su sakkowa ba. A kan carpet ɗin Parlour'n ya shimfid'e ta. Ya zauna a gurin kanta yana kallon kumburarriyar fuskarta da ta ci kuka ta k'oshi, ta yi jajawur kamar ka latsa jini ya fito. Zulai ce ta fito daga kitchen ta ci karo da su, ta zaro ido waje cikin tsananin kaɗuwa, da gudu ta yi hanyar steps ta hau upstairs ta sanar da su Mama dake zaune jigum_jigum a Parlour'n sama Ameen ya dawo da Neehal. A tare suka taho cikin sauri dan tabbatarwa. Mama ta ƙaraso da gudu ta rungume Neehal a jikinta tare da sakin kuka ta ce. "Alhamdulillah, Allah na gode maka daka dawo mun da d'iyata." Su Aunty A'isha kuwa har rige_rigen tambayar Ameen inda ya gan ta suke. Shi dai bai ce komai ba, dan abun da yake damun sa ya fi ƙarfin sa. Yana kallon su suka gama murnar bayyanar Neehal da godiya ga Allah, sai ya ji daɗi ko ba komai ya saka Mama da ahalinta farinciki. Hajiya sai shafa kan Neehal da har lokacin bata farfaɗo ba take. Mama ta dubi Ameen ta ce. "A ina ka gan ta?" Ya lumshe idonsa ya buɗe ya ce. "Ban san sunan gurin ba, amma is looks like Bush ko kuma sabuwar unguwa, amma dai wajen gari ne ba cikin mutane ba, na yi amfani da sim ɗin da mu kai waya da ita ne na yi tracked." Aunty Sadiya ta ce. "Ita ta kira ka?" Ya ce. "No." Sannan ya ba su labarin wayar da suka yi da Neehal da yadda ya ɗauko ta. Hajiya ta ce. "Allah ya yi da rabon shan ruwanta a gaba, dan wataƙila ƴan yankan kai ne suka sace ta Addu'a ta ci su suka yarda da ita." Aunty A'isha ta ce. "Ko ma su waye Allah ya toni asirinsu." Mama ta ce. "Amin." sannan ta dubi Ameen ta ce. "Kira Dad ka faɗa masa, bawan Allah nan ko ruwa bai sa a cikinsa ba ya fita." Ameen ya zaro wayarsa ya yi dialing Numbern Daddy amma bata shiga ba. "Mama ta ce. "Lafiya kuwa yake, kar ya je ya sawa kansa wata matsalar fa saboda damuwa, tun d'azu nake kiran shi nima amma bata shiga." Aunty Sadiya ta ce. "Ina ya ce miki zai je?" Mama ta ce. "Hospital's ya duba wai ko Neehal accident ta yi an kai ta can." Aunty Sadiya ta jinjina kai kawai. Ameen ya miƙe ya ce zai je ya yi Sallah, Mama ta ce Ya sanar da Abba an ga Neehal yana masallaci tunda ya tafi Sallah bai dawo ba. Sai a lokacin su Mama suka fara damuwa da halin da Neehal take ciki, murna fa ta koma ciki. Mama duk ta ruɗe ta shiga jijjiga ta. Aunty Sadiya ta ɗebo ruwa mai sanyi a fridge ta cire hijabin jikin Neehal ta shiga shafa mata ruwan a fuska zuwa wuyanta. Cikin ikon Allah ta sauke dogon numfashi tare da buɗe idonta, suka haɗa ido da Mama. Mama shafa fuskarta ta ce. "Sannu Daughter." Neehal bata iya amsa mata ba sai mayar da idon ta yi ta rufe. Gaba-ɗaya suka sauke ajiyar zuciya. Ta yi luf a jikin Mama cikin sakanni baccin wahala ya ɗauke ta. Dije ta ɗauko filo Mama ta kwantar da kanta akai. Nan fa suka shiga kiraye_kirayen mutane suna sanar musu an ga Neehal. Haneefah mai kuka hankali ya kwanta, dan ita Mama ta fara kira ta sanarwa saboda halin damuwar da ta shiga. Duk bayan mintuna sai Neehal ta zabura a cikin bacci tana faɗin, "Me nay muku kuke son cutar da ni? Karku ɓata mun rayuwa dan Allah, ni marainiya ce." "Mama! Mama! ki zo ki ceci ni karki bari su keta mun haddi za su ɓata mun rayuwa." Ko kuma ta ce. "Harda kai ake ƙoƙarin cutar da ni? Me yasa kake cikin azzaluman nan?" Kalaman da take yi kenan wanda ya tayar da hankalin su Mama matuƙa." Aunty A'isha ta ɗora kanta akan cinyarta ta shiga tofa mata addu'a, Aunty Sadiya kuma towel ta sakawa a ruwa tana matsa mata a jikinta saboda yanda jikin nata ya yi zafi zau." Mama kuka take tana faɗin "Na shiga uku, fyaɗe aka so yi mata kenan, they want to rape my daughter? Su waye waɗannan azzaluman? Ku duba mun yarinya kar na je sun cutar mun da ita." Aunty Sadiya ta ce. "Insha Allahu babu abun da su kay mata." Hajiya ta ce. "To waye take cewa harda kai a ciki? Kenan ta ga idon sani a cikin waɗanda suke ƙoƙarin yi mata fyaɗen?" Aunty A'isha ta ce. "Nima abun da na fahimta kenan, mu jira ta tashi sai mu ji ƙarin bayani daga bakinta." Sai bayan La'asar Neehal ta farka, ta buɗe idonta ta sauke su akan Aunty A'isha dake zaune a kusa da kanta. Aunty A'isha ta kama hannunta ta ce. "Sannu Neehal!" Ta gyaɗa mata kai a hankali tare da ƙoƙarin tashi. Aunty A'isha ta taimaka mata ta tashi zaune. A hankali ta ce. "Aunty zan sha ruwa." Aunty A'isha ta miƙo mata ruwan da aka tanada already saboda ita, ta karɓa ta sha sosai sannan ta shiga sauke ajiyar zuciya. Mama ta ce. "Daughter kin tashi? Sannu, ina ne yake miki ciwo a jikinki yanzu?" Ta nuna mata kanta da ƙirjinta. Mama ta ce. "Sannu kin ji, Allah ya sauwaqe." Cikin dashashshiyar murya ta ce. "Amin, zan yi wanka Mama." Mama ta taso ta kamata ta miƙe tsaye dak'yar tana yatsina fuska gami da taune lips ɗinta. A hankali suke tafiya Mama na riƙe da ita har suka hau upstairs. Bedroom ɗinta Mama ta kai ta rage kayan jikinta ta shiga toilet ta yi wanka ta fito, sai ta ji jikin nata ya yi mata daɗi. Ta zira doguwar riga mara nauyi ta saka hijabi ta yi Sallar Azhar da la'asar dake kanta. Kafin ta idar su Mama sun shigo ɗakin dukan su. Tana idarwa suka shiga yi mata sannu. Mama ta dawo kusa da ita ta janyo ta jikinta, Neehal ta saki ajiyar zuciya a hankali ta ce. "Mama ina Yaya da Daddy?" Mama ta shafa fuskarta ta ce. "Ameen tunda ya kawo ki bai dawo ba, Har Hafsat ma ta zo ta tafi, ta ce ba ya jin daɗi ne, Dad kuma tun d'azu wayarsa bata shiga, sai yanzu ba jimawa ya kira ni ya ce yana hanyar zuwa gida." Neehal ta gyaɗa kanta kawai bata ce komai ba. Mama ta cigaba da magana. "Sadik ya zo shi da Abbansa d'azu, Ahmad ma ya kira ni wai zai taho yanzu na ce masa ai an gan ki ma, amma ya ce cikin week ɗin nan Insha Allahu zai zo." Hajiya dake jan carbi ta ce. "Ai mutane suna ta zuwa ko ta ina jaje da taya mu murna, sai abun kuka ya sameka kake gane mai k'aunarka." Aunty Sadiya ta ce. "Haka ne kam." Aunty A'isha ta kawo wa Neehal tea ɗin data haɗa mata a cup ta ce. "Ta so ki sha." Neehal ta girgiza mata kai alamun baza ta sha ba. Mama ta ce. "Ki daure ki sha ko kaɗan ne, na san babu abun da kika ci tun jiya." Kamar zata yi kuka ta ce. "Ƙirjina ciwo yake mun, ba zan iya sha ba." Cikin damuwa Mama ta ce. "Tsoro nake Neehal kar su saka miki ciwon zuciya da wannan tashin hankalin da suke jefe ci a jiki." Aunty A'isha ta ce. "Insha Allahu haka baza ta faru ba, ta daure dai ta sha tea ɗin zata ji daɗi." Neehal ta bar jikin Mama ta ɗauki cup ɗin ta kafa a baki ta runtse ido ta k'ukk'uta tana jin sa kamar ruwan mad'aci, da ƙyar take iya had'iyewa, bata son tay musu musu ne kawai. Ta ajiye cup ɗin tana jin kamar zata yi amai saboda yanda tea ɗin yake mata juyi a cikinta. Cikin ikon Allah kuma sai ya zauna bata yi aman nasa ba. Aunty Sadiya ta ce. "Neehal ki faɗa mana yanda aka yi aka sace ki da kuma abun da ya faru. Neehal ta runtse ido kamar bata son tuno wani abu ta fara ba su labari turyan_turyan tun daga farko har ƙarshe. Salati suka saka gaba-d'ayan su cikin d'imuwa da al'ajabin wannan al'amari. Mama tana hawaye ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, wacce irin ƙungiya ce wannan kuma? A ina suke a ina suka san ki?" Hajiya ta ce. "Ai wannan daga ji matsafa ne masu shan jinin mutane." Aunty A'isha tana kuka ta ce. "Wai me mutane suka ɗauki wannan duniyar nan ne? Me yasa suke manta cewar za su mutu su koma ga mahaliccin su? Rayuwar duniya fa tamkar kifta ido ne ka buɗe zaka neme ka ka rasa a cikinta? Me yasa muke manta kwanciyar kabari da azabar Ubangiji?" Aunty Sadiya ta ce. "Ke da Allah ya nufa da rahama ya baki imanin tunanin abun da kika faɗa, su kam waɗannan mutanen sam babu haka a ransu, duniyar kawai suke nema suna ganin kamar ba za su mutu ba." Hajiya ta ce. "Hasbunallahu'wani'imal'wakil, Astagfirullah wa'atubu ilaihi, Allah ka kashe mu cikin imani da kai, wannan wacce irin rayuwa muke ciki? da mutane suke neman duniya su manta da k'iyama." Mama ta ce. "Yanzu duk wannan abubuwan da suke faruwa da Neehal saboda wannan banzan ƙudirin nasu ne, Allah ya fi su kuma shi zai mana maganinsu." Ita dai Neehal hawaye kawai take, domin ita kaɗai ta san me yake damunta." Aunty Sadiya ta dafa ƙafaɗarta ta ce. "Neehal! Wa kika gani a cikin waɗanda suke son cutar da ke wanda kika sani?" A tsorace Neehal ta kalle ta, Aunty Sadiya ta gyaɗa mata kai alamun tabbatarwa. Ta girgiza kai cikin tsoro ta ce. "Ban san kowa ba a cikin su, ban taɓa ganin su ba dukan su sai yau." Aunty Sadiya ta ce. "Nutsu Neehal ki faɗa mana, kina da sama da wanda ya fi mu ne a duniyar nan? Muna son mu kawo ƙarshen matsalar ki ne." Neehal ta saci kallon Mama ta ce. "Da gaske ban san kowa ba." Aunty A'isha ta kama hannunta ta ce. "Haba Neehal, dama akwai abun da zaki ɓoye mana a cikin duniyar nan, d'azu kina bacci kina zabura kina cewa harda kai a cikin wanda za'a cutar da ni, ki faɗa mana wanene?" Neehal ta saka kuka ta ce. "Babu kowa fa." Hajiya ta ce. "Ka ji yarinya da iskancin banza, rayuwarki fa ake son taimakawa." Aunty Sadiya ta ce. "Say it Neehal, ina son tabbatar da zargi na ne." Mama da gabanta ke dukan tara_tara cikin sanyin murya ta ce. "Please Neehal ki faɗa mana, ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru, ko da wata bazaranar su kay miki sai abun da Ubangiji ya rubuta sannan zai faru da ke." Neehal ta ƙurawa Mama ido a ranta tana cewa. 'Ba zan iya faɗa muku wanda na gani a matsayin wanda zai keta mun haddi ba saboda ke Mama, karamcinki da halaccinki a gare ni ba zai bar ni in faɗi abun da zai saka zuciyarki ta buga ba Mama, ba zan iya ba, ba zan iya faɗar wannan mummunan baƙin labarin ba. Na yiwa kaina alƙawarin wannan maganar da ita zan mutu a cikin cikina, ba zan iya faɗawa kowa ba.' Mama ta riƙe hab'ar Neehal ta saka idanunta a cikin nata na ce. "Idan har kin ɗauke ni uwa ki faɗa mana Neehal, gabana sai faɗuwa yake dan Allah ki faɗa." 'Matar data riƙe ni riqon gaskiya da amana ba tare da mun haɗa wata dangantaka ta jini da ita ba, ta nuna mun k'auna fiye ɗan data haifa a cikinta, take fifita farincikina akan nata, take shiga damuwa a duk lokacin da na shiga, ɗan da ta haifa a cikinta bai jefa ta cikin damuwa ba sai ni, ta yaya zata ce in mata abu in ƙi yi? Ta riga ta ɗaure ni da jijiyoyin jikina, amma ina fata abun da zan sanar musu ya zama maganata ta biyun ƙarshe a duniya, ya Allah kasa ina faɗa ka nufe ni da yin kalmar shahada, daga nan ka ɗauki raina, dan ba zan iya jurar ganin Mama cikin tashin hankali ba.' Neehal ta faɗi haka a ranta. Aunty Sadiya ta bubbuga ƙafaɗarta ta ce. "Neehal please Talk, kin bar mu cikin zullumi da fargabar zuci." Neehal ta runtse idanta da ƙarfi cikin rawar murya kamar yadda zuciyarta da jikinta suke rawa ta ce. "Da..da... Daddy!..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *6️⃣9️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* .........Cikin matuƙar gigita Mama ta saki fuskar Neehal da ƙarfi ta kalli Aunty Sadiya tana so ta yi magana amma ta kasa. Gaba-ɗaya suka waro Ido waje kamar zai faɗo ƙasa amma aka rasa mai magana a cikinsu. Kuka mai tsananin taɓa zuciya Neehal ta fashe da shi, tana jin anya kuwa ta yiwa kanta adalci data faɗawa Mama wannan maganar? Sai ta ji dama ta ƙi faɗa, ta san dole za su haqura su ƙyale ta da tambayar, amma ta riga ta furta bakin alqalami ya bushe. Aunty A'isha ta runtse idanta tana karanto Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un a fili. Sannan ta samu yar nutsuwa ta dubi Neehal ta ce. "Neehal! Wanne Daddy'n kike nufi?" Mama ta shiga girgiza kai ta ce. "Sadiya da gaske Neehal sunan Daddy ta ambata ba kunnena bai ji mun dai-dai ba?" Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. "Shi ta ce." Mama ta dafa gado da hannunta ɗaya tana ambato duk addu'ar da ta zo bakinta jin kanta na wani irin juyawa. Sai a lokacin Hajiya data ƙame baki buɗe ta iya magana, ta dubi Neehal ta ce. "Ƙarya ne, wannan abun sharri ne ba Muhammadu kika gani ba, wani ne ya yi kama da shi saboda yana son ya k'ulla masa sharri, na san Muhammadu ba zai taɓa aikata hakan ba." Aunty Sadiya ta miƙe tsaye ta ce. "Ba ƙarya ba ne, ba kuma wani ne ya yi kama da shi ba, shine da kansa, kuma na daɗe da gano hakan." Aunty A'isha ta ce. "Subhallahi, Sadiya kin san wa ake magana akai kuwa? Gen. Fa, mijin Yaya Fateemah mahaifin Ameen." Aunty Sadiya ta ce. "Shi ɗin fa." Mama tana numfashi da ƙyar ta ce. "Sadiya, kina nufin Muhammad Tafida dama shine wanda kike zargi akan al'amuran Neehal?" Aunty Sadiya ta dafe kanta na wasu sakanni sannan ta tsugunna ta ɗora hannunta akan ƙafaɗar Mama wadda jikinta yake rawa ta ce. "Na yi mamaki a yadda na san ki mutum ce ke mai saurin fahimtar abu amma kika kasa gane wasu sauye_sauye a tattare da Yaya Tafida. Abu na farko da yasa na fara dasa zargina a kansa shine, a yanda yake sanannen mutum mai kuɗi wanda ya san manyan ƙasar nan da yan siyasa amma ace ana aikatawa Neehal wannan abubuwan ya kasa binciko masu aikata hakan a matsayin sa na babban soja. Talaka mara gata shi yake shan wahala a shari'a a ƙasar nan, amma ban da irin su Yaya Tafida, a yanda yake tun lokacin da akay kisan Jameel a rana ɗaya idan ya so sai yasa an gano masa waɗanda suka yi kisan, amma bai yi hakan ba. Kuma tunda aka fara abun nan ban taɓa jin ya ce yau yana yin wani bincike akan abun ba ko kuma yasa a yi masa. Secondary kuma, idan ban manta ba Yaya Tafida ya yi shekara bakwai da yin retired, Amma kullum sai ya fita tun safe sai dare yake dawowa. Ina yake zuwa? Kin taɓa tambayar sa akan haka? Idan baki manta ba farko dana fara zargin sa na taɓa tambayar ki cikin hikima ina yake zuwa yanzu shi da ya yi retired? Kika ce mun gurin kasuwancinsa yake zuwa dubawa sai kuma Mall ɗinsa da yake lek'awa time to time. Kuma ɗan wannan abun ba zai saka mutum ya wuni a waje ba, tunda daga kasuwancin har Mall ɗin nasa akwai masu kula da su, babu abun da zai yi idan ya je, ko kina tunanin zai je ya zauna a cikin yaransa ne? Abu na uku kuma Yaushe rabon da ki ga wani abokinsa ya zo gidan nan alhalin kuma kafin ya shiga wannan ƙungiyar suna zuwa sosai? Duk da ba a gidan nan nake kwana ba amma na san wannan kuma na sa an bincika mun. Tun daga lokacin dana fara zargin sa na saka ido sosai akan duk wani motsinsa, amma da yake shi ma da shirinsa yake tafe na sha bak'ar wahala kafin na gano wasu abubuwan, su ma ba sukai cikakkiyar hujjar da zan iya cewa direct shi ba ne, shi yasa ban bayyana ba. Sannan sai labarin abun da ya faru da Neehal a gidan Ameen, shi ma ya ƙara tabbatar mun da zargi na. Na girgiza ba kaɗan ba a lokacin dana gane da saka hannu Yaya Tafida a duk abubuwan da suke faruwa da Neehal, domin ban taɓa zaton haka daga gare shi ba, Yaya Tafida mutumin kirki ne kowa ya san da haka, na yi mamaki matuƙa da yakasance dan cikin ƙungiyar matsafa duk da ban san ta yanda aka yi ya shiga ba amma na san tabbas ba'a san ran shi ba ne ƙaddarar sa ce ta zo a haka. Lokuta da dama ina kulle kaina a ɗaki in yi kukan takaici da baƙin cikin wannan al'amari, gami da tausayin ku ke da Ameen da Neehal da shi kan shi Yaya Tafidan, idan zaki lura har gidan nan na rage zuwa, saboda watarana kar na yi subutar baki na faɗa miki wannan mummunan labarin, ko kuma mu haɗu da Yaya Tafida in kasa jurewa in masa wata maganar da zai gane na san abun da yake. Dalilin da yasa kullum al'amarin Neehal yake ƙara tab'arb'arewa tare da ƙara yin gaba saboda wanda yake aikata abun da shi a ake zama a tattauna akan matsalar da kuma hanyoyin da za'a magance abun yana cikin mu, the way da zamu kawo mafita duk ya sani, shi kuma sai ya canza salo yanda zai ƙara kawar da tunanin mu daga kan abun. Shi yasa muka kasa samun mafita al'amarin ya ƙi ci ya ƙi ƙarewa, sai yanzu da ita kanta Neehal ɗin Allah ya nuna mata shi da idonta. Kuma muna fata Insha Allahu ƙarshen abun ne ya zo." Mama ta runtse ido ta buɗe numfashinta na kaiwa da komowa da sauri da sauri ta ce. "Tabbas biri ya yi kama da mutum Sadiya, sai yanzu da kikai waɗannan maganganun sannan wasu abubuwan suke dawo mun kwanyata. Ku san shekaru goma sha biyu kenan da nake lura Tafida kamar baya cikin nutsuwarsa, sai yay ta yin wasu irin abubuwa amma ban taɓa kawo komai a raina ba. Sannan kuma lokuta da dama ana kiransa a waya sai ya dinga ƙin d'agawa a gabana, ko kuma ya d'aga ya ce yana zuwa zai kira daga baya. Na raba shi da *Kabir Ginyau* saboda ba mutumin k'warai ba ne, amma na lura bai rabu da shi ba, duk da ya ce mun ba mu'amala suke yi kamar ta da ba, gaisawa kawai suke. Sannan kuma lokacin da aka sace Sadik tun a wurin d'aurin Aure Usman ya ce a ɗaurawa Neehal Aure da wani amma ya ce a'a, bayan iyayen Sadik sun ce ba zai auri Neehal ba na same shi a ɗaki ni da shi na ce masa zan aurawa Ameen Neehal mu huta da wannan tashin hankalin, amma ya dinga kawo mun wasu hujjoji da suka akan hakan har na haqura na bar al'amarin, ashe duk kansa yakewa tanadi, ashe da Mushirinki miji nake zaune, me yasa ka aikata haka Tafida? Why? Why? Ko ɗan ɗanka guda ɗaya tilo a duniya bai kamata ka aikata wannan mummunan laifin ba, bai kamata ka ɓata masa suna a Duniya ba. Ka cuce ni ka cuci Ameen, am sorry Ameen ban maka zaɓin Uba na gari ba." Mama ta ƙarashe zancen cikin sark'ewar numfashi. Aunty Sadiya ta shiga bubbuga bayan ta a hankali tana maimaita mata sunan Allah. Kuka sosai Aunty A'isha da Hajiya suke yi, dan wannan abun ba ƙaramin girgiza zuciyoyinsu ya yi ba. Neehal ta kama hannun Mama tana kuka amma bata ce komai ba, so take tay mata magana amma ta kasa. Mama ta damk'e hannunta cikin dashashshiyar murya ta ce. "Ki yi haquri Neehal, duk wannan abun da ya faru nina jawo miki, da na barki a hannun A'isha ta riƙe ki da ƙila haka baza ta faru da ke ba." Neehal ta girgiza mata kai tare da rungume ta ta ƙara fashewa da kuka. A hargitse Daddy ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi cikin matuƙar tashin hankalin da Mama zata iya cewa tunda suka yi aure bata taɓa ganin shi a cikin irinsa ba, Abba na biye da shi a baya shi ma cikin tashin hankali yana tambayar shi abun da yake faruwa ya gan shi duk a birkice. Mama ta janye jikinta daga jikin na Neehal ta miƙe tsaye cikin sauri, ta nuna shi da hannunta cikin muryarta dake fita da ƙyar saboda tsantsar damuwa ta ce. "Me ya kawo ka inda muke, ko ka zo ka ƙara mana wani ciwon zuciyar ne akan wanda ka saka mana ni da marainiyar Allah da bata ji ba bata gani ba? Ko kuma ka zo ne ka aiwatar da mummunan nufinka a kanta a gaban mu?" Daddy ya ƙaraso kusa da ita ya kama hannunta kamar zai yi kuka ya ce. "Dan Allah Fateemah ki tsaya ki saurare ni in miki bayani, na san a yanzu ji kike kamar ki kashe ni saboda tsana, amma dan Allah ki tsaya ki ji mai zan faɗa miki, wallahi ba laifina ba ne nima babu yadda zan yi ne." Mama ta fizge hannunta ta ce. "Muhammad ko ganin ka bana k'aunar yi balle na ji wannan muryar taka mai ƙara mun k'una da baƙin ciki a cikin raina, dan Allah ka fice daga ɗakin nan ko kuma ni in fita in bar maka gidanka. Ka ba ni mamaki kuma ka bani kunya, ashe dama ba dan Allah kake riƙon Neehal ba? Yanzu duk abubuwan da suke faruwa da ita kai ne sanadi?" Daddy ya ƙara riƙe hannunta ya ce. "Please Doctor, ki mun wannan alfamar ki tsaya ki saurare ni in miki bayani, ko da wannan zata kasance alfarma ta ƙarshe da zaki mun a rayuwata. Please and please, ni kaina a yau na ji tsani kaina da rayuwata." Mama ta kuma k'wace hannunta ta ce. "Bayanin me zaka mun Tafiya? Bayanin kai ka kashe Jameel da Anwar ko kuma bayanin kana riƙon Neehal ne saboda ka lalata rayuwarta? Ko kuma bayanin da zai ƙara tabbatar mana kana cikin ƙungiyar matsafa kai ɗan shan jini ne?" Abba dake bakin ƙofa yana kallon su cikin tsananin mamaki ya ce. "Subhallahi, Fateemah me kike faɗa haka? Kin san kuwa mai kike cewa? Mijinki ne fa General Muhammad Tafida a gabanki ba wani ba." Mama tana hawaye ta ce. "Na sani Yaya, Na sani." Sai ta mayar da duban ta ga Daddy ta ce. "Ka cuce ni, ka cuce ni Muhammad, ka ɓata wayonka, ka ɓata rawarka da tsalle, yanzu duk damuwa da k'aunar da kake nunawa Neehal duk na Ƙarya ne? pretended kawai kake yi saboda kar mu gano mummunan nufinka a kanta? Muhammad why? Me yasa? Mai Ubangiji ya rage ka da shi a rayuwar nan da ka zaɓi saɓa masa da laifin da ba ya yafewa? *Shirka* fa muham......" Kasa ƙarasa abun da take son faɗa ta yi saboda numfashinta da ba ya fita sosai, sai haki take jikinta na wani irin ƙyarma. Daddy ya yi ƙoƙarin riƙe ta ta yi baya da sauri kamar zata faɗi, da sauri Aunty Sadiya ta tashi ta riƙe ta, ta zaunar da ita a bakin gado. Cikin kuka Hajiya ta ce. "Na shiga uku ni Zainabu, wannan wacce irin masifa ce, Allah ka farkar da ni idan mafarki nake." Aunty A'isha ta dubi Mama cikin sanyin murya ta ce. "Ki yi haquri mu saurari Yaya Tafida mu ji me yake tafe da shi, ki bi komai a sannu dan Allah, kar wani mummunan ciwon ya kama ki." Mama zata yi magana amma ta kasa, sai jujjuya kanta kawai take. Abba ya ce. "Ni fa ƙara saka ni a cikin duhu kuke, dan Allah ku fahimtar da ni abun da yake faruwa." Aunty A'isha ta ce masa. "Ka zauna yanzu zamu ji komai daga bakin Yaya Tafida." Abba ya ƙaraso ya zauna akan carpet cikin tsananin al'ajabin wannan murdadden al'amarin. Aunty A'isha ta mayar da duban ta ga Daddy dake ta yiwa Mama sannu cikin tsananin tashin hankali, ta ce masa. "Ka zauna ka yi mana bayanin muna sauraren ka." Daddy ya sauke nannuyar ajiyar zuciya ya goge gumin da ke ta tsalala a fuskarsa sannan ya zauna shi ma ya fara magana kamar haka. Shekaru goma sha uku da suka wuce baya Abokaina Alhaji Karbir Ginyau da Alhaji Idris suka dame ni akan na shiga harkar siyasa, tunda ina da kuɗi kuma na san manyan mutanen ƙasar nan gani General na sojoji mulki ba zai mun wahala ba. Na nuna musu ni bana son harkar siyasa ko kaɗan kuma ba zan yi ba. Alhaji Kabir abokina ne tun samartaka, zan iya kiran shi ma da aminina. Sai dai halayyar mu k'wata_k'wata ba iri ɗaya ba ce, shi mutum ne mai matuƙar son abun duniya dan zai iya yin komai akan kuɗi, sannan yana harkar bin matan banza. Ina faɗa masa gaskiya a kodayaushe a matsayinsa na abokina amma ko kaɗan ba ya ɗauka. Yakan ce mun idan mutum bai shana ba a gidan duniya mai zai yi? Da na ga ba zai taɓa dena halinsa ba sai na koma bin shi da addu'ar fatan shiriya idan mai shiryuwar ne. Kabir ya dinga mun naci da magiya akan in shiga siyasa harkar akwai samu sosai a cikinta. Na nuna masa ni fa ba zan yi ba, amma ya ishe ni da naci da magiya, har na amince masa zan yi amma na ce sai na yi shawara da iyalina. Na tuntubi Fateemah da maganar, da farko ƙin amincewa ta yi sai daga baya na lallaɓa ta ta yarda da ƙyar ta amince in yi siyasar, bayan ta kafa mun sharad'an yin komai cikin gaskiya da tsoron Allah. Zuwa lokacin nima ina son yin siyasar sosai, Kabir ya ƙwadaita mun yanda ake samun Alkhairi a cikin ta. Ban fara siyasa daga matakin ƙasa ba sai na fito takarar shugaban ƙasa. Na saka kuɗi na mai yawa na siyi Form ɗin takara. A hankali na fara tara mabiya da magoya baya, na samu waɗanda suka daɗe a cikin siyasar ake damawa da su suka d'aga hannuna. Tunda na fara harkar sai na fara shiga busy, yau mu ne nan garin gobe mu ne can. Wannan dalilin yasa Fateemah ta ƙara tsanar harkar, har ta fara mun zancen ko zan haqura in daina. A lokacin ni kuma abun ya shiga raina sosai gaskiya, sai na lallaɓa ta na ce mata da zarar komai ya dai-dai ta zan koma normal kamar da. Ana haka Kabir ya ce mun harkar siyasa fa dole sai an haɗa da taimakon malamai. Ban kawo komai a raina ba nake ba shi kuɗi a matsayin wanda za'a kaiwa malamai suke yin addu'a. A lokacin ni akaran kaina na san idan aka yi Elections ba zan taɓa winning ba, amma sai na saka a raina komai dan dagiya ne wani lokacin zan iya cin zaɓen. Sai na dage da taimakawa jama'a da takalawa, ta hanyar samar da maguda nan ruwa a wuraren da ba su da ruwa, da kuma gina masallatai a ƙauyuka. A hankali sunana ya fara baza ƙasar nan, mutane suka san ni sosai. Watarana ranar da ba zan taɓa iya mantawa da ita ba a rayuwata, ranar baƙin ciki ranar da tsautsayi yasa na faɗa cikin k'azamar ƙungiyar da babu komai a cikinta sai shirka da tsantsar rashin imani. Alhaji Kabir ya zo ya same ni har office ɗina ya ce mun, yanzu na fara yin masoya sosai a ƙasar nan, zata iya yiyuwa in ci zaɓe, dan haka in zo mu je zai kai ni wani guri da za'ai mun aikin da zai saka in ci zaɓen, dan siyasar yanzu dole sai da haka. Na ce masa in dai gurin kaucewa hanya ne baza ni ba, ni babu wanda zan kaiwa kukana sai Allah shi zan roƙa da shi na dogara. Kabir ya dinga nuna mun ba wani abu ba ne ai wannan is common thing, in ma ban yi yanzu ba sai na yi watarana, dan indai na ce kwanciya zan yi a siyasa zan ga kwanciya, za ai komai babu ni. Nan dai ya dinga saka mun san abun a raina yana mun huɗubar banza har kalamansa suka yi tasiri a kaina, sheɗan ya dinga zuga ni tare da ƙawata mun daɗin mulki da cigaban rayuwa da zan samu in har na haye kujerar mulkin shugabancin ƙasar nan. Ni har ga Allah na bi Kabir da niyyar zai kai ni wurin wani malamin, irin malaman soron nan ko masu duba, amma ko kaɗan boka da masu tsibbu ba su zo raina a matsayin wanda Kabir zai kai ni gurin su ba. Amma me? Mun yi tafiya ta kai ta awa uku kafin mu tsaya a wani tangamemen gida dake can wajen gari, babu gida gabansa babu gida bayansa, shi kaɗai a gurin. Muna zuwa ƙofar gidan na ji gabana ya faɗi, na dubi Kabir da ya gaji da mitata da nake ta yi masa tunda na ga muna ta tafiya ta ƙi ƙarewa na ce masa. "Ina ka kawo ni Kabir?" Ba tare da ya kalle ni ba ya ce. "Inda na ce zan kawo ka mana." Daga haka ya buɗe Motar ya fita, nima ban da zaɓi sai bin bayan nasa. Ya k'wank'wasa ƙofar gate ɗin gidan, mintuna kaɗan wani ɗan tsoho ya zo ya buɗe mana, suka yi maganar da ni ban ji me suke cewa ba sannan Kabir ya shige gidan. Na tsaya na ƙi shiga saboda yanda gabana yake ta faɗuwa sosai, sai hasbunallahu'wani'imal'wakil nake maimaita a cikin raina. Kabir ya juyo ganin ban bi shi ba ya ce in shigo mana. Na ƙara tambayar sa Kabir wai inane nan ka kawo Ni? Ni fa hankalina ya ƙi kwanciya da gurin nan, gaskiya gida zan koma. Ya ce, ka zo mu je ka gani mana, haba ka cika garaje matsalata da kai, mu ci wannan uwar tafiyar sannan ta tashi a banza, wannan abun da taimakon ka zan yi ba kaina zan yiwa ba. Na yi tsaki sannan na bi bayan shi. Wani dogon lungu ne a cikin gidan, nan muka bi mu kaita tafiya sannan na ga mun shiga wani ƙaton Parlour, wanda babu komai a cikin sa sai wasu irin abubuwa marasa kyan gani a rarrataye, na shiga bin Parlour'n da kallo tsigar jikina na tashi. Kabir ya buɗe wata ƙofa dake falon ya shiga tare da yi mun alamar in biyo bayan shi. Ban musa ba na bi shi na shiga nima, abun da na tarar a ɗakin ba ƙaramin daga mun hankali ya yi ba ya kuma girgiza tunanina, har na yi tunanin ko mafarki nake. Wata mace hakimce akan kujera ta mulki tsirara haihuwar uwarta, kanta babu gashi a aske yake tal kamar Namiji. Ta ɗaura wani jan k'yalle a hannunta da ƙafarta. Sai zazzare idanu take yi. Gabanta kuma wani tulu ne na zinare wasu k'artan maza guda biyu suma ba kayan kirki a jikinsu suna tsiyayo mata wani jan abu mai kauri a cup tana ƙarba ta sha. A fili na ce A'uzubill...... Amma kafin na ƙarasa na ji an buge mun bakina, na juya dan ganin waye amma ban ga kowa ba. Kabir ya tsugunna yay sujjada ga matar nan wanda hakan ya ƙara tayar mun da hankali. Na sunkuya na d'ago shi cikin fusata na sharara masa mari na ce. Kabir gurin matsafa masu shan jini ka kawo ni gurin mushirikai? To rashin imanina bai kai haka ba, neman duniya ta ba zai saka in ɓata har haka ba. Na juya na fice daga ɗakin cikin tsananin fusata da baƙin ciki ina Allah wadaran halin Kabir. Tafiya nake kamar zan tashi sama ina haɗa hanya har na kai bakin gate ɗin gidan, na dubi mai gadin gidan a fusace na ce masa ya buɗen ƙofa. Amma kafin ya yi wani yunƙiri sai gani na na yi a ɗakin dana bar Kabir da wannan matar yanda na bar su. Na shiga rarraba ido cikin tsananin al'ajabi ina bin ɗakin da kallo tare da tunanin da yanda aka yi na iya dawowa ɗakin cikin kiftawar ido ni da nake a bakin gate. Na bi su da kallo kamar yadda suka tsaya cak suna kallo na su ma, na buɗe baki da niyyar magana ko addu'a amma na ji na kasa. Sai na juya da sauri na ƙara ficewa daga ɗakin, wannan karon da gudu na ƙarasa gate ɗin gidan. Amma nan ma kafin kiftawar ido na ƙara ganin an mayar da ni wannan ɗakin. Sai da muka yi haka har sau uku, ni na ƙi haqura in tsaya a ɗakin kamar yadda suke so, su kuma sun ƙi bari na in fita daga gidan, sai na kai bakin gate sannan su ƙara dawo da ni cikin ɗakin. A na ukun ne matar nan ta shek'e da wata mahaukaciyar dariya tana duba na, ni kuma inata aikin zazzare idanu da numfarfashi. Sai da ta yi dariyarta mai isarta ta gama sannan ta murtuke fuska kamar an aiko mata da saqon mutuwa ta fara magana cikin amon murya da faɗin.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *7️⃣0️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ......."Barka da zuwa Muhammad Tafida, ƙungiya na farin ciki da kasancewar ka a cikinta. A kodayaushe muna san irinku masu tsantsar riƙo da addini a cikin mu, domin mu mun fi son mu ɓata shiryayyu su koma ɓatattu, wannan shine burinmu akodayaushe." Sannan ta dubi Kabir ta ce masa. "Aikinka yana kyau mai jan kai bawan mai jan kai, a yau za'a ƙara maka matsayi a cikin wannan ƙungiya, sakamakon kawo mana wannan babban mutum cikinta da ka yi. Markus da Jamus suna alfahari da kai." Na dubi Kabir na dube ta ba tare da na gane inda maganganunta suka dosa ba. Ina son na yi magana amma na kasa koda motsa labbana ne balle na iya sarrafa harshena. Na yi ƙoƙarin juyawa na fice daga ɗakin kamar yadda na yiyyi d'azu amma na kasa, daga nan ma ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi na ganni kwance akan wani irin gado ɗan ƙarami, babu komai a jikina sai jan k'yalle ɗaure a hannuna da kaina da ƙafata. Na yunƙura na tashi sai na ga mutane mata da maza kusan hamsin zagaye da gadon da nake, dukkanin su tsirara haihuwar uwarsu sai ɗan jan k'yallen nan kamar na jikina. Suna watsa mun wani jan abu ajikina wanda na fahimci jini ne, suna kuma yin wani abu da bakinsu kamar wak'a amma da wani irin yare irin nasu na matsafa. Na gaza yin komai sai bin su da ido, Kabir kawai na gane a cikinsu sai wannan ƙatuwar matar dake facing ɗina tana mun wani irin kallo. Sun daɗe suna yin abubuwan su akaina, su shaƙa mun hayak'in wannan, su fesa mun wancan su watsa mun wannan, haka dai sukay ta yi. Sai na ji gaba-ɗaya jikina kamar ba nawa ba, kamar an canza ni, na ji zuciyata da ƙwaƙwalwata kamar ba su taɓa sanin abu a cikin duniyar nan ba sai waɗannan mutanen. A tak'aice dai a ranar na zamto member na wannan ƙungiyar ba dan son raina ba sai sanadiyyar la'anannen abokina, kuma duk abun da suka saka ni in yi bana musu nake yi. Ni ban sani ba ashe har mun kwana a gidan, wannan farkawar da na yi ma tsakar dare ne. Sai washegari da hantsi sannan aka bani kayana na saka muka baro gidan ni da kabir, bayan Sarauniya kamar yadda na ji suna kiran wannan ƙatuwar matar ta kafa mun sharad'an zuwa kullum wannan gidan ana aikin ƙungiya tare da ni. Ta tabbatar mun babu abun da zan nema a duniyar nan in rasa komai girman buƙata_ta da burina zan samu, sannan kuma dole duk aikin da ƙungiya ta saka ni in yi shi komai wahalarsa, kuɗi kuwa idan suna bautawa mutum sai sun bauta mun a duniyar nan saboda yawan kuɗin da zan yi. Ta kuma raɗa mun suna jaririntah, sauran ƴan ƙungiya kuma suna kira na autan ƙungiya. Jikina kamar ba nawa ba muka taho gida ni da Kabir dake ta murmushin farinciki da jin daɗi. Ni dai kawai kallon sa nake ina jin kaina ya mun wani irin nauyi kamar duka mutanen duniyar a kaina suke. Sai da muka shigo cikin gari sannan na fara dawowa nutsuwata, hankalina ya fara dawowa jikina. A fili na ce. "Shikenan na zama matsafi ɗan shan jini kenan?" Na yi tambayar cikin tsananin mamaki da al'ajabi. Kabir ya tuntsure da dariya ya ce. "Harkar akwai samu na gidana, zaka yi bala'in kuɗi nake faɗa maka mutumina, na san inna faɗa maka gaskiya tun kafin mu zo baza ka taɓa amincewa ka biyo ba, shi yasa kawai na kawo ka. Na daɗe ina son saka a cikin wannan harkar dan na san ƙungiya tana buƙatar irinku masu tsoron Allah." Ban san lokacin da nay masa wata muguwar shak'a ba, ya yi saurin taka burki. Ina huci na ce masa, "ka cuce ni Kabir ka cuci rayuwata, yanzu mai zan ce da Ubangiji na da kuma iyalina akan wannan mummunar harkar daka saka ni a cikin ta? Mene ribarka na mun hakan Kabir? Wanne laifi nay maka a rayuwar nan ka zaɓi sanya ni cikin wannan mummunar harkar? Wacce irin tsana kai mun har haka? Dan wannan ba k'auna ba ce." Ya k'wace jikinsa dak'yar daga shaƙar da nay masa yana mayar da numfashi ya ce. "Aikin gama ya riga ya gama, duk wani hargagi da zakai baza ka taɓa fita daga cikin ƙungiyar nan ba har abada, ƙungiya ce da in aka shiga ba'a fita, sai dai in mutuwa ka yi." A hasale na ce masa ƙarya yake, kuma zai sha mamakina, ni da ƙara zuwa wannan gidan har abada. Anan muka rabu da Kabir baram_baram ya fice ya bar mun Motata ina girmama rashin imani da son duniya irin na Kabir, ko kaɗan ban taɓa sanin yana wannan harkar ba, dan ban yi zaton son duniyar tasa har ya kai haka ba. Bayan na koma gida na tarar da Fateemah duk ta tayar da hankalinta akan rashin dawowata gida jiya. Tana gani na ta saka kuka ta ce. Indai har ina son zama da ita daga ranar in bar siyasa, ta gaji da wannan bala'in yawa_yawan, ga wani mummunan mafarki da ta yi a daren jiya a kaina. Na tabbatar mata daga ranar na bar siyasa har abada, dama ko bata faɗa ba na yi niyyar dainawa saboda a sanadinta na faɗa wannan mummunar harka. Saboda tana cikin murnar gani na bata lura da canjin yanayin da nake ciki ba. Amma tay ta tambaya ta inda na je na kwana, na sanar mata wani ƙauye muka je campaign motarmu ta lalace mana a hanya. Tay ta mun wani irin kallo kamar bata yarda da abun da na ce mata. First maganar data fara fitowa daga bakinta a lokacin in rabu da Kabir Ginyau domin ba mutumin arzik'i ba ne, bata son alaƙa ta da shi, dan ta san duk inda na je tare muka je da shi. Na ce mata Insha Allahu na rabu da shi kenan. Daren ranar ban iya runtsawa ba saboda tsananin damuwa, na yi dana sanin, sanin Kabir a rayuwata babu adadi. Na yi kuka, na yi kaico da rayuwata, na tsani kaina, na dinga addu'ar Ubangiji ya ɗauki raina a daren in huta, da dai in cigaba da rayuwa a matsayin ɗan shan jini. Washegari safiya tana yi na ji hankalina gaba-d'aya ya yi gurin matsafan nan, na ji kamar zan mutu idan ban je gurinsu ba. Lokacin ina aiki ban yi retired ba, na shirya da zummar zuwa gurin aiki na fita, ina fita na kira Kabir na ce ya zo ya kai ni gidan jiya dan ba zan iya gane hanya ba. Kabir ya zo ya dinga mun dariya yana faɗin dama ya ce ba zan taɓa iya fita ba daga ƙungiya ba da kaina zan koma, to sun riga sun gama tsaface ni na zama na su. Tun daga wannan rana idan ban je gidan nan ba yau to gobe zan je. Amma ko sau ɗaya ban taɓa kwana a can ba, duk da kowanne member akwai ranar kwanansa a gidan, dan an fi yin aiki cikin tsakiyar dare. Ni kaɗai ne bana kwana saboda ban san me zan faɗawa Fateemah ba idan na je na kwanan, ina zan ce mata ina zuwa? Sarauniyar ƙungiya tana matuƙar sona a cewarta, hakan yasa ko da an ce a yi abu na ƙi yi bata iya hukunta ni, saɓanin sauran members da babu wanda yake iya yi mata musu. Ni kuma ina sane nake ƙin yi wani abun idan ta umarce ni, saboda ta yi zuciya ta kashe ni. Dan wallahi ina cikin ƙungiyar ne kawai amma bana so, ni kaɗai na san baƙin cikin da nake ciki a sanadiyyar kasancewa ta a cikin wannan ƙungiya, kodayaushe cikin yiwa Kabir Allah ya isa nake, tunda shi ya jefani a cikin wannan iftila'in, kuma har abada ba zan yafe masa ba. Babu abun da ake aikatawa a cikin wannan ƙungiyar face zallar rashin imani da shirka da tsantsar tsafi. Zaku sha mamaki idan kuka ji manya da wasu daga cikin masu mulki a ƙasar nan wanda ake musu kallon mutanen kirki amma suna cikin wannan ƙungiya. Lokaci ɗaya na sauya daga aihin Muhammad Tafida na, na koma wani daban, na watsar da duk abokaina saboda tsoron kar su gano mummunar hanyar dana faɗa, ƴan ƙungiyar nan su suka zama aminaina da su kaɗai nake hulɗa. Dole ne ko kuma in ce sharad'i ne na wannan ƙungiya, duk wanda yake cikinta sai ya yi tarayya da ƴarsa ta cikinsa budurwa, idan kuma macece ta yi da ɗanta saurayi wannan tilas ne ga kowa. Amma naga su members ɗin ƙungiyar kamar hakan ba ya damun su, daɗi ma suke ji da murnar hakan, wasu ma ba ƴaƴa ɗaya suke ɓatawa ba, in sun kai goma ƴan'matan da samarin duk sai sun ɓata su, wasu ƴaƴan ma sanadiyyar hakan suke rasa ransu. Iyayen kuma su fi kowa nuna damuwa da zak'ewa akan al'amarin a idon duniya. Wanda ba shi da yar ko ɗan ne kawai ake masa uzuri, amma za'a ba shi wani aikin a madadin wannan ya yi, ko lalata ƙananan yara mata da maza, ko kuma wani babban saɓon ga Ubangiji. Nima hakan ce ta kasance da ni, bani da ƴa mace dan haka aka bani aikin ɓata ƙananan yara mata ta hanyar yi musu fyaɗe. Kai tsaye na ce ba zan iya ba, duk da ina cikin wannan ƙungiya amma imanina bai tafi duka daga cikin zuciyata ba. Manyan ƙungiya suka mun caaa aka da masifar dole sai na yi, ai ba fin su na yi ba da za'a saka ni abu ina ƙin yi, amma Sarauniya ta tsawatar musu ta ce su rabu da ni, ta san ya zata yi da ni. Haka na cigaba da rayuwa cikin takatsantsan da ɓoye abun da nake aikatawa, dan babu wata alama da zata nuna maka ina wannan mummunar harkar idan ka gan ni, ba ma ni kaɗai ba, duka yan ƙungiyar idan suka fito cikin gari haka ne, ko iyalanmu ba su isa sun gane ba. Na karb'i riƙon Neehal a lokacin da Fateemah ta zo mun da shi gidana saboda Allah ba dan wani abu ba, kuma Allah ne shaidata akan hakan. Tun kafin nan dama ta saba zuwa mana hutu tun iyayenta suna da rai, haka kawai na ji ina son yarinyar tamkar ƴar cikina dana haifa haka nake kallon ta. Da zuciya ɗaya nake riqonta kuma nake yi mata komai. Watarana lokacin Neehal ta kusa shekara da dawowa hannunmu gaba-d'aya da zama Kabir ya zo gidana. Ban shigar da shi ciki ba saboda bana son Fateemah ta san muna tare sai muka zaune a farfajiyar gidan. Muna zaune sai ga Neehal an dauko ta daga makaranta ta dawo, tana hango ni ta taho da gudu ta rungume ni kamar yadda ta saba, nay mata Welcome sannan ta gaishe da Kabir ta wuce cikin gida. Kabir ya bita da kallo sannan ya dube ni ya ce wannan yarinyar fa? Na haɗe rai dan na san halinsa da maitar mace komai ƙanƙantarta nay masa bayanin yanda take a gurina. Ya jinjina kai bai ce komai ba, ashe shi ya k'udurce abun a ransa, washegari muna zuwa ƙungiya ya ce ai ina da 'ya mace budurwa ƙarya nake na ce ban da ita. Cikin mamaki na ce musu da gaske ban da ƴa mace ta cikina, ɗana ɗaya ne tal a duniya kuma namiji ne, kuma Kabir ya fi kowa sanin haka. Kabir ya bayar da labarin ganin da yaywa Neehal jiya a gidana. Sarauniya ta yi bincike a ƙwaryar tsafinta sai ga fuskar Neehal ta bayyana. Ta dube ni ta ce. Tunda ni nake ciyar da Neehal nake shayar da ita nake tufatar da ita kamar ƴar cikina take a yanzu, dan haka ƙungiya tana buƙatar budurcinta. Na ce gaskiya ba zan iya cutar da ƴar amana ba marainiyar Allah. A fusace Sarauniya ta ce mun. Dole in yi, in ba haka ba su kashe iyalina su kashe ni kuma sannan wani a cikin ƙungiya ya karb'i budurcin Neehal ɗin. Hankalina idan ya yi dubu ya tashi a ranar, dan na san duk abun da sarauniya ta faɗa zata iya aikata fiye da hakan ma. Ba zan so in rasa matata da ɗana ba, kuma ba zan so a ɓata rayuwar Neehal ba. Dan haka na yanke wata shawara, na nuna musu na amince zan yi abun da suke so, amma a lokacin Neehal ta yi yarinta su ɗan bari ta ƙara girma. Da ƙyar suka amince da abun da na faɗa, dan a cewar su wanda ba su kaita ba ma ana musu fyaɗen. Na dawo gida hankali a tashe cikin rashin sanin mafita, ni ba'a abun in ce Fateemah ta mayar da Neehal gurin ƴan'uwanta ba dan tserayar da rayuwarta ba, ta ce mun akan me? Na dai ƙudurce a raina komai zai faru sai dai ya faru amma ba zan taɓa haikewa Neehal ba har abada, gwara na rasa raina dana aikata wannan abun kunyar. Ni babban tashin hankalina da suka ce ko ban aikata mata da kaina ba wani zai aikata mata. Ban taɓa sanin ina son Neehal sosai ba sai a wannan lokacin, Na saka ido sosai akanta saboda na san tsaf zasu iya ɓullo mata ta wata hanyar, musamman Kabir da kodayaushe cikin zancen ta yake. Haka shekaru suka shud'e ina ƙara bawa ƙungiya excuse akan Neehal, na rasa me yasa su kuma suka damu da ita over, kodayaushe cikin yi mun nacin in yi in far mata suke, wai hakan ba ƙaramin cigaba zai ƙarawa ƙungiya ba, yarinyar ta musamman ce gashi nima ban taɓa yiwa ƙungiya irin wannan aikin ba shi yasa suka damu da abun. Lokacin da na yi released soyayyar Neehal da Jameel sai na ce ya turo a yi auransu idan dagaske yake, Fateemah ta ce, na bari ta ɗan yi karatu mana tunda time ɗin candy kawai ta yi. Amma na ce a'a, dan so nake kawai na aurar da ita na huta da fargaba a kanta, a ganina idan ta yi aure ai dole su haqura da batun. Ban san a inda Kabir ya samu labarin Engage ɗinsu ba dan ban faɗa masa ba saboda bana son ya sani. Amma sai tsintar maganar na yi a ƙungiya, aka dinga zazzaga mun masifa wai ina son cin amanar ƙungiya ne, na ce musu danginta ne suke son aurar da ita ba ni ba ne. Sai suka ce to duk yadda za'a yi a yi a fasa batun bikin nan, ko kuma in karɓo musu abun da suke so kafin lokacin bikin. Na amsa musu kawai amma ban aiwatar ba. Wallahi ban san ya aka yi ba, ban kuma san ta yanda aka kashe Jameel ba, kuma bani da masaniya a lokacin da suka shirya kisan. Sai da aka yi sannan nake ji a ƙungiya Kabir ne ya shirya komai. Sarauniya ta tabbatar mun da cewar haka zasu yi ta yiwa duk wanda zai auri Neehal, tunda ni taurin kai gare ni na ƙi yi musu abun da suke so. Manyan ƙungiya sun so hukuntani amma Sarauniya ta hana, ni kaina ina mamakin yanda Sarauniya bata iya hukunta ni duk laifin da zan yi, ita da bata da tausayi da imani ko kaɗan. Duk uwar bautar da kake mata kana mata laifi na rana ɗaya zata rufe idonta ta azabtar da kai. Abun da ya taimake ni akan Neehal ƙa'ida ne kowa shi zai yi amfani da ƴarsa, wani ba zai taɓa replace ɗinsa ba a ƙungiya, wannan dalilin ne yasa ba'a bawa wani damar keta wa Neehal haddi ba sai ni. Ban taɓa tunanin zasu kuma kashe Anwar ba a lokacin dana bashi auran Neehal, na yarda Ubangiji ne ke rayawa da kashewa rayuwar kowa a hannunsa take, dan haka sai kwanan mutum ya ƙare zai mutu. Ga dukkan alamu ba su samu labarin auren Neehal da Anwar da wuri ba sai gab da za'a kawo lefen ta, wallahi shi ma kamar kisan Jameel ban san sanda aka shirya kisan aka kashe shi ba. A lokacin hankalina yay matuƙar tashi domin na san idan aka cigaba da tafiya a haka akwai matsala, tunda dole hankalin mutane zai dawo kan abun, za'a fara zargin lallai da wata a ƙasa. Na rasa ya zan yi, na rasa hanyar neman mafita. Challenges da barazanar dana samu a ƙungiya baza su faɗu ba akan wannan al'amarin, wai ina ta raina musu hankali shekara da shekaru na ƙi yin abu. Ni kuma na ƙudurce a raina gara na mutu dana aikatawa Neehal wannan mummunan abun. Lokacin da Fateemah ta zo mun da batun tattaunawar da suka yi da su Sadiya akan suna zargin da akwai wanda yake aikata kisan su Anwar hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin na san tabbas idan tafiya ta yi tafiya asirina zai iya tonuwa. Ban tabbatar da hakan ba sai lokacin auransu da Sadik. Domin ƙungiya ba su san da bikin ba sakamakon ɓoye zancen bikin da kay sai da ya zo daf sannan aka bayyana, ana i gobe d'aurin Aure cikin dare sun tura a kashe Sadik aka tarar baya nan an sace shi. Hankalin ƙungiya ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin sun gane da alamun akwai wanda yake bibiyar al'amuransu kenan, nima hankalina ya tashi ba kaɗan ba dan bana son asirina ya tonu duniya ta san halin da nake ciki. Duk zuwa masallacin da na ce ina yi mu yi karatu ba can nake zuwa ba, gidan ƙungiya nake zuwa mu kwana muna bincike dan gano waye yake bibiyar al'amuranmu amma har yau mun kasa ganowa. Gidan da aka kai Neehal nan nake zuwa kullum muna aikin ƙungiya tun bayan dawowar mu Kano da zama. Wancan ɗayan gidan sai idan za'ai gagarumin aiki nake zuwan sa. Da Sadiya take cewa akwai wanda take zargi bayan an sace Sadik ko kaɗan ban yi tunanin ni take zargi ba, dan duk wata kafa ko alama da zata saka ayi zargi na akan al'amarin Neehal na toshe ta, duk binciken mutum bai isa ya gane ina cikin wannan mummunar harkar ba, dan takatsantsan nake bana wasa ba. Lokacin dana bawa Neehal Mota na saka yarana suna bin bayanta duk inda zata je, saboda kaɗan daga sharrin yan ƙungiya su saka a sace ta su tsare ta, su kira ni su ce dole sai na aikata abun da suke so a gaban su. Ni kuma idan su kay hakan bani da wata sauran mafita dole na aikata. Allah ya taimaka ya dubi maraicinta ba su yi hakan ba sai a wannan karon. Wallahi ban san time ɗin da suka shirya sace Neehal ba, sai bayan sun ɗauke tan nake sani. Kuma wannan duk shirin Kabir ne, shi yake shirya komai akan Neehal. Sarauniya kuma ta yi farinciki da hakan har da ƙarin matsayi tay masa na yanda duk wata hanyar mugunta ya san ta. Suka kuma shirya gagarumin shagali dan murnar mallakar BUDURCIN NEEHAL. Abun da suka daɗe suna fata da burin samu, domin bincikensu ya tabbatar musu ba ƙaramin cigaba ƙungiya zata samu ba idan member ɗin cikinta ya mallaki Neehal. Sun riga sun saka ni a tasku da tsaka mai wuya, dole na je na aikata abun da suke so, domin sun ce idan ma ban yi ba zasu saka wani ya yi, kuma bayan sun mata fyaɗen zasu kashe ta, su yanka ta su sha jininta. Shi yasa na amince za ni amma har ga Allah ba dan na aikata ɗin ba ne, sai dan na fito da ita daga wannan gidan, in yaso ni su kashe ni a matsayin hukuncin fitar da itan da na yi. Taimakon ta da Sagir ya yi ma nina saka shi, na san dole zata tambaye shi dalilin da yasa ya taimake ta, sai na ce masa ya ce mata saboda Ameen ya taimake ta idan ta tambaye shi." Daddy ya yi shiru yana mayar da numfashi, ɗakin ya yi tsit kamar babu halitta a ciki. Ya fara hawaye sannan ya cigaba da magana cikin raunin murya. "Wallahi bani da niyyar cutar da Neehal a rayuwata, ku yarda da ni. Tamkar ƴar cikina haka na ɗauke ta. Da ace ina son cutar da ita da tuni na yi abun da suke so an wuce gurin, tunda ina da opportunities ɗin hakan da dama. A gidana take kwana take tashi, zan iya yin komai da ita a duk sanda naso ba tare da an gane ni na yi ba, ko kuma na saka a sace mun ita in yi duk abun da nake so da ita a wani gurin sannan in dawo da ita ba tare da an gane nina aikata hakan ba. Amma kuma sai ban yi ba saboda ba zan iya ba, ba zan iya cutar da ita ba. Lokacin da ta je gidan Ameen ni na je gidan na fesa mata abu a fuska, a lokacin na gaji da ƙwarzabar da ƙungiya take mun gami da barazanar kashe iyalina akan ƙin yi musu abun da suka umarce ni, a lokacin na saduda kawai zan aikata ɗin. Amma ina zuwa sai na kasa aikatawa saboda wasu dalilai, na farko idan har na yi rape ɗinta a gidan Ameen za'a ce shi ne ya aikata, domin babu wanda zai yarda ba shi ba ne, tunda babu alamar da zata nuna wani ya shigo gidan daga waje, Nima na yi amfani da spare keys ɗin kowacce ƙofa dake gidan na gurina kasancewar gidan nawa ne na mallakawa Ameen. Kuma ta ƙofar baya na shiga balle mai gadi ko wani ya ga lokacin dana shiga, shi yasa na fasa dan ba zan iya bari a k'ullawa ɗana sharri ta sanadiyya ta ba. Na biyu kuma wani tsoron Allah ne ya dirar mun a zuciyata a lokacin, na ji ba zan iya farantawa ƙungiyar mutane ƴan'uwana na sabawa Ubangijin da ya halicce ni da laifika biyu ba, laifin zina da kuma laifin cutar da ita, na ji kawai koma me zai faru sai dai ya faru amma ba zan iya ba, sai kawai na fasa na fice na bar gidan. A lokacin ni addu'a nay ta yi dama ƙin aikatawar tawa yasa su kashe ni, amma ba su yi hakan ba sai faɗa da fatar baki kawai da sukay mun. A ranar har na je na dawo Fateemah bata san na fita ba, sakamakon maganin bacci dana zuba mata a lemo ta sha. Kuma ranar da wuri na kwanta na nuna mata a gajiye nake bacci zan yi, ina ganin bacci ya ɗauke ta na tashi na fice. A yau na ɗauka Sarauniya zata fille kaina ne saboda tsananin takaici da baƙin ciki, domin ba ƙaramin buri ta ci ba na mallakar BUDURCIN NEEHAL. Amma sai naga ba tay hakan ba, ta ce zamana a cikin ƙungiya ba ƙaramin cigaba yake ƙarawa ƙungiya ba, dan haka baza ta so su rasa ni a cikinta ba, sannan kuma tana sona ba zata iya cutar da ni ba, amma duk da haka sai ta hukunta ni, hukunci mai tsanani, kuma dole sai na aikata abun da suke so akan Neehal baza su haqura ba. Ban san dame zata hukunta ni ba dan bata faɗa ba. Amma ina fatan dama ta kashe ni in huta da wannan asararriyar bak'ar rayuwar da nake mara amfani. Wannan shine gaskiyar abun da yake faruwa." Sai ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro. A fili Abba ya shiga maimaita "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." Cikin tsananin tashin hankalin jin halin da ɗan'uwansa yake ciki. Neehal ta ƙara volume ɗin kukanta kamar yadda Hajiya ta fashe da matsanancin kuka. Mama ta sunkuyar da kanta ƙasa tana ganin wasu taurari na gilmawa ta cikin idonta, daga baya kuma ta daina ganin komai sai duhu dulum na wasu sakanni. Ta yi tunanin bayanin da Daddy zai yi zai ƙaryata abun da Neehal ta faɗa da kuma zargin da Aunty Sadiya take masa ne, ya ce ba shi Neehal ta gani ba wani mai kama da shi ne, ko kuma sharri akai masa kamar yadda Hajiya ta faɗa. Amma sai ta ji saɓanin hakan, sai ma amsa laifinsa da ya yi, ya tabbatar musu yana cikin ƙungiyar matsafa shi ɗan shan jini ne. Ta shiga tambayar kanta anya kuwa ba mafarki take ba? Anya mijinta adalin miji mutumin kirki zai aikata haka? Ko a mafarki bata taɓa tunanin zata faɗa irin wannan jarrabawar ba, bata taɓa tunanin ƙaddara irin wannan zata riske su ba. Muhammad ɗinta mijinta Mahaifin Ameen shine a cikin wannan mummunar harkar? Zuciyarta ta kasa yarda da wannan al'amarin, yay mata girma baza ta iya ɗauka ba. Ta d'ago kanta ta zubawa Daddy jajayen idanunta da suka rine saboda tashin hankali, ta yi gyaran murya cikin ƙarfin hali saboda muryarta da take a shak'e, cikin dauriyar ciwon da take ji a cikin zuciyarta ta ce masa. "Wannan labarin ƙaryar daka zauna ka tsara shi da kukan munafurcin da kake ba zai saka in yarda da kai ko ina yafe maka ba Muhammad, cuta ce ka riga daka cuce ni babu yanda zan yi. Wallahi da ba dan kai ka faɗa mun wannan maganar da bakinka ba da ba zan taɓa yarda ba inda wani ne ya faɗa mun, ko da kuwa Hajiya ce data tsugunna ta haife ni ta faɗa ba zan yarda ba, dan na maka kyakkyawar shaidar kai mutumin kirki ne. Ka bani mamaki Muhammad, ace shekara da shekaru da matsafi mashayin jini nake rayuwa." Daddy ya matso ya kama ƙafafunta ya ce. "Allah ne shaidata akan duk abubuwan dana faɗa muku shine gaskiyar al'amarin, dan Allah Fateemah ki yarda da ni, ki karɓi hakan a matsayin ƙaddara kamar yadda na ɗauka wannan ita ce *ƙaddarata* a rayuwata." Mama ta watsa masa wani kallo ta ce. "Ƙaddara ko son zuciyarka? Komai ɗan Adam ya aikata sai ya ce ƙaddara ce, saboda ita ƙaddarar ba'a ganin ta bare ta kare kanta ko? Wannan labarin naka shirya shi kawai ka yi ka faɗa mana. Ban da haka ta yaya kana cikin ƙungiya za'a shirya yanda za'a kashe ƴaƴan mutane amma ka ce baka sani ba? Ta yaya hakan zata kasance?" Daddy ya ce. "Wallahi bana sanin lokacin da suke shiryawar, na fi tunanin cikin dare ne da bana zuwa gidan suke shiryawa." Mama ta ce. "Me yasa ka san dalilin da yasa aka kashe su Jameel amma ka bar Sadik ya nemi Auran Neehal? Ko dan ba ɗanka ba ne ko an kashe shi baka da asara?" Daddy ya ce. "Babu yanda zan yi ne Fateemah, bani da mafita, ko so kike in ce miki Neehal baza tay Aure ba? Ki ce mun akan wanne dalilin in rasa amsar baki? Wacce fassara zaku mun idan na faɗi haka? Wallahi ko Anwar da Jameel dana san za'a kashe su a ranar dana fara ganin su da Neehal zan aura musu ita ba tare da duniya ta sani ba, balle har ƙungiya ta ji su ɗauki matarsu su tafi ba tare da an yi taron bikin komai ba, kinga da tuni na huta da wannan fargabar, da duk abubuwan da suka faru da Neehal ba su faru ba." Mama ta runtse idanta cikin matsananciyar damuwa ta ce. "Muhammad ka taɓa shan jinin mutum ɗan'uwanka? ka taɓa yin tsafi ta shirka da kanka?" Daddy ya shiga girgiza kai ya ce. "Fateemah tsafi gaskiyar mai shi, wallahi ba yin kaina ba ne tsaface ni suka yi, idan na je gidan duk abubuwan da nake yi ba'a cikin hayyacina nake ba." Hawaye suka fara shatata daga idon Mama, cikin muryar kuka ta ce. "Fatana da addu'a ta ɗaya ne, Allah yasa kana yin Sallah da azumi Muhammad? Allah yasa baka sadaukar da su saboda san duniya ba?" Daddy ya ce. "Ban daina Sallah ba balle azumi kema zaki bayar da shaidan hakan." Mama ta buɗe idonta tare da dafe ƙirjinta ta ce. "Na san babu yadda za'a yi ace ana Sallah a gidan matsafa, a ina kake yin Sallar?" Daddy ya ce. "Idan na dawo da yamma nake haɗawa na yi, asuba da isha'i kuma ina yin su akan lokaci, Magriba ma wani lokacin inna dawo da wuri ina yin ta akan lokaci." Mama ta girgiza kai cikin takaici ta ce. "Da azumi a bakinka kana zuwa gurin shirka mene makomar azumin naka?" Daddy ya ce. "Bana zuwa gidan da azumi, hutu nake ɗauka." Mama ta yi murmushi mai ciwo ta ce. "Da kuɗin tsafi da shan jini kake ciyar da mu ka tufatar da mu?" Daddy ya ce. "Wallahi ban taɓa ciyar da ku da haram ba, ni akaran kaina ban taɓa cin kuɗin ƙungiyar nan ba, dan na san haram ba ƙaramin bala'i ba ce a jikin ɗan Adam. Fateemah kin san ina da kuɗi tun asalina, Baffa ya rasu ya bar mana kadarori da tarin dukiya, and then my salary is more than 1.5 kin san wannan kuma already, ina business ina da Mall a Abuja da Kano, waɗannan sun isa na ciyar daku nay muku komai na buƙatar rayuwa ba tare da k'azaman kuɗin ƙungiya ba. Ke tsarkakakkiya ce Fateemah, ba zan taɓa yi miki algus da kazanta a rayuwarki ba. Wallahi Fateemah baki san tarin yawan nadamar dake cikin zuciyata ba ne, ina jin dama ban taɓa sanin Kabir ba a rayuwata, dama ban faɗa harkar siyasa ba, da ana dawo da abun da ya wuce baya dana dawo da rayuwata na cire wannan dattin da ya ɓata mun tsaftatacciyar rayuwata." Mama ta sauke ajiyar zuciya bata kuma cewa komai ba. Ta mayar da idanunta ta lumshe tana jin yanda zuciyarta take bugawa da sauri da sauri gami da wani irin zafi da take mata kamar ana gasa mata nama a cikin ta. Daddy ya bar jikinta ya koma gaban Neehal, ya d'ago kanta yana hawaye ya ce. Ki yafe mun Daughter ni ne sanadin saka miki baƙin ciki a rayuwarki, dan Allah ki yafe mun ko zan samu sauƙin azabar Ubangiji idan na mutu." Neehal ta girgiza kai ta ce. "Babu abun da kai mun Daddy sai tarin Alkhairi, ka riƙe ni ba tare da ƙyara ko zangwama ko hantara ba a gidanka, ka bani tarbiyya ka bani ci da sha da sutura, ka bani ilimin addini dana boko ka samar mun aikin yi. Abun da ƴan'uwana na jini wanda Ubangiji ya ɗora musu hak'k'in hakan ba su mun ba, amma duk kai ka yi mun. You Are still my father Daddy, kai na sani a matsayin ubana a duniyar nan, wannan abun da ya faru ƙaddararmu ce gaba-d'ayan mu, amma kai ma ba laifinka ba ne." Sai ta faɗa jikinsa tana ƙara fashewa da kuka mai ban tausayi tare da faɗin. "You are still my father Daddy." Daddy ya rungume ta yana kuka sosai ya ce. "I'm Bad father for you Neehal, mahaifinki shine wanda ya yarda aka kashe shi saboda ganin ya kare mutuncinki da martabar ki, ni kuma ni ne nake ƙoƙarin raba ki da su, I'm not good fasher for you, please forgive me Daughter!." Aunty A'isha ta lumshe idonta hawayen tausayinsu na zuba daga cikin idanun nata, sun bata tausayi ba kaɗan ba, wannan wacce irin ƙaddara ce, gaskiya Kabir ya cuci Daddy, Amma Allah zai masa sakayya. Aunty Sadiya ma duk taurin zuciyarta sai da ta yi kuka. Abba ya jinjina kai ya ce. "Na rasa da sunan da zan kira wannan baƙin al'amarin, Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un. Yanzu Muhammad kai da na sani mai riƙo da addini kai ne a cikin ƙungiyar matsafa fiye da shekara goma? Ya assamadu kasa mu yi kyakkyawan ƙarshe." Turo ƙofar ɗakin da aka yi yasa suka juya gaba-d'aya suna kallon ƙofar, Neehal ta bar jikin Daddy da sauri. Zulai ce ta fara shigowa sai kuma wasu mutum uku masu sanye da suit a jikinsu. Ɗaya daga cikin su ya yi sallama, babu wanda ya iya amsa masa. Bai damu ba ya ɗauko i.d card a aljihun rigarsa ya nuna musu tare da faɗin. "Ku yi haquri mun shigo muku har bedroom ba da izinin ku ba, mu ma ba'a son ranmu ba ne, mun yi ta knocking baku ji mu ba shiyasa muka shigo. Jami'ai ne mu daga hukumar S.S ta ƙasa." Ya kalli Daddy sannan ya cigaba da magana da faɗin. "Mun zo ne for arrest you bisa umarnin ɗanka Major col. Al'ameen Muhammad Tafida, akan laifin da in mun je office zaka ji." Abba ya waro ido cikin tashin hankali amma bai yi magana ba. Daddy ya yi murmushi sannan ya goge hawayen fuskarsa ya tashi ta haɗa tafukan hannayensa ya yi tafi sau uku sannan ya ce. "Wannan ya tabbatar mun da zargin da nake na Ameen ne ke bibiyar wannan al'amarin, sannan kuma shi ya saka a ɗauke Sadik saboda ya tseratar da rayuwar shi. Ko yanzu na faɗi na mutu zan yi farinciki ban yi asarar haihuwar ɗa ɗaya tamkar da dubu ba, na bar ɗan da ƙasa da duniya zata yi alfahari da shi. Duk ɗan da ya kama ubansa da laifi sannan bai yi ƙasa a gwiwa ba ya sanar da hukuma domin a kama shi a hukunta shi hakan ya tabbatar ba zai ƙyale duk wanda ya kama da laifi ba kowa ye. Lallai Ameen ya cika jami'in tsaro na gari wanda ƙasar mu take buƙatar irin su. I'm proud of that, zan mutu da farincikin haka." Daddy ya dubi su Mama ya ce. "Zan iya ce muku sai watarana, domin ka'idar wannan ƙungiyar da nake ciki ne duk wanda ya fallasa sirrin su ga wasu sai an kashe shi, ni kuma na baku labarinta yanzu, dan haka a daren yau zasu tsotse jinina sai dai a wayi gari aga gawata, dan haka ina neman yafiyar ku gaba-d'aya akan baƙin ciki da damuwar dana saka ku a ciki." Ya ƙarasa gaban Mama ya yi kneel dawn ya ce. "Ki nema mun yafiya a gurin gwarzon ɗana Ameen." sannan ya matsar da bakinsa daf da kunnenta cikin raɗa ya ce. "Ina neman alfarmar ki aurawa Ameen Neehal, domin tun kafin ta yi candy ya sanar mun yana son ta, nina nuna masa ba zan ba shi ita ba saboda wani dalilina. Dan Allah ki mun wannan Alfarmar, koda zata kasance alfarma ta ƙarshe da zaki mun a rayuwarki." Daga haka ya miƙe ya fice daga ɗakin cikin sauri ba tare da kuma kallon kowa ba, mutanen nan suka mara masa baya da sauri. Su Aunty sun shiga cikin tashin hankali ba kaɗan ba da jin furucin Daddy na wai ƴan ƙungiyar su zasu kashe shi, kuka Neehal ta fashe da shi mai ƙarfi tana kiran sunan Daddy. Hajiya kuwa gaba-d'aya bata cikin hayyacinta ta ma daina fahimtar abun da yake faruwa, Aunty A'isha ma kuka take sosai. Abba ya tashi da sauri ya bi bayan su Daddy. Mama ta miƙe tsaye tare da dafa bango ta ce. "Ina wayata in kira Ameen, na san yana can cikin damuwa da baƙin cikin abun da ubansa ya aikata na son zuciya da son duniya, ku kira mun ɗana in ji a halin da yake ciki, kar zuciyarsa ta buga saboda baƙin ciki. Dan Allah ku kirawo mun shi in ji lafiyarsa." Sai ta tsugunna ta fara laluben wayarta a ƙasan ɗakin cikin fitar hayyaci, ta samu ta ɗauko wayar amma sai wayar ta zubce daga hannunta ta faɗi saboda rawar da jikinta yake yi. Ta miƙe tsaye tana jin kamar ana wujijjigata a cikin iska saboda juyawar da kanta yake mata. Lokaci ɗaya ta ji numfashinta ya tsaya cak, idanunta sun daina ganin komai sai duhu, a hankali ta yi baya luuu ta faɗi ƙasa babu alamar numfashi a jikinta..........✍️ *To masoya makaranta littafin Neehal, anan zamu dakata sai bayan Sallah idan mai kowa mai komai ya kai mu zamu cigaba da yardar Allah. Allah yasa muga wannan wata na Ramadan lafiya, Allah ya karb'i ibadun da zamu yi yasa muna cikin 'yantattun bayinsa da zai ƴanta a cikin wannan wata mai albarka. Allah ya bawa dukkan Musulmi lafiyar yin ibada, Amin ya Allah.🙏* *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *7️⃣2️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ..........Cikin dare Mama ta farka, Aunty Sadiya da idanunta biyu har lokacin ta tasa ta a gaba ta tashi da sauri ta kira likita, ya zo ya ƙara duba jikin Maman, Alhamdulillah an samu numfashinta ya daidaita yana fita da kyau, hakan yasa suka cire mata Oxygen ɗin suka yi mata allurar bacci dan ta ƙara samun relief. Sai a lokacin Aunty Sadiya ta ji ta samu nutsuwar zuciya ganin Maman tana numfashi normal. Da Asuba Mama ta kuma farkawa, alhamdulillah ta farka cikin nutsuwarta, kanta ne kawai ta ji yay mata nauyi da ƙirjinta da har yanzu take jin ciwo a cikin zuciyarta. Ta shiga bin inda take da kallo abubuwan da suka faru na dawo mata cikin kwanyarta. Ta runtse ido saboda wani ɗaci da ta ji ya ƙaru a cikin zuciyarta akan na da. Ƙoƙarin tashi zaune ta yi cikin ƙarfin hali da na zuciya duk da yanda take jin jikinta kamar ba nata ba. Jin motsinta Aunty Sadiya dake kan darduma ta juyo ta kalli gadon da take da sauri, miƙewa ta yi ta ƙarasa gaban gadon tana faɗin. "Sannu Yaya." Mama ta gyaɗa mata kai cikin dauriya tana ƙoƙarin tashi zaune, da sauri Aunty Sadiya ta taimaka mata ta tashi sannan ta saka mata pillow a bayanta. Kanta ta dafe da hannunta tana sassauke numfashi cikin muryar dake fita da ƙyar ta ce. "Sadiya ina Neehal da Ameen?" Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. "Suna gida, anjima kaɗan idan gari ya waye zasu zo." Ta gyaɗa mata kai sannan ta ce. "Suna lafiya dai ko?" Aunty Sadiya ta ce. "Lafiya k'alau, jiya har wajen ɗaya na dare Ameen yana nan, na san nan da anjima zaki gan shi ya dawo." Mama ta lumshe idonta ta ce. "Hajiya fa?" Aunty Sadiya ta ce. "Suna tare da Ya A'isha da Neehal." Mama bata kuma magana ba sai hannunta data ɗora a kan ƙirjinta. Aunty Sadiya ta ce. "Sannu, Ya jikin naki? Bari na Doctor ya ce mun in kin tashi na kira shi." Mama ta girgiza mata kai, sannan ta d'ago a hankali ta cire drip ɗin hannunta. A hankali ta ce. "Taimaka mun mu je toilet na yi alwala." Aunty Sadiya ta ce. "Haba Yaya baki da lafiya fa, ki bari idan likita ya duba ki sai ki je, na san yanzu ko tafiya baza ki iya yi ba." Mama ta girgiza kai ta ce. "Zan iya Sadiya, ki bari na fara yin Sallar tukunna." Aunty Sadiya bata kuma magana ba ta kama ta, ta sauko daga kan gadon ta raka ta toilet. Ita kanta Maman ta san ƙarfin hali ne kawai irin nata, amma ba ƙaramin jiri take ji ba, tafiyar ma duk da Aunty Sadiya ta riƙe ta amma jinta take kamar zata faɗi. A zaune ta yi sallolin dake kanta da ƙyar, bayan ta idar Aunty Sadiya ta taimaka mata ta koma kan gadon ta kwanta. Sai a lokacin ta fita ta kira likita ya zo ya ƙara dudduba jikin Maman tare da yi mata faɗan ta rage tunane_tunane. Ya cewa Aunty Sadiya ta bata magungunan da ya rubuta mata jiya idan an siyo, amma ta fara shan koda tea ne first. Bayan fitarsa Aunty Sadiya ta dubi Mama ta ce. "Bari na yiwa Ya A'isha waya ta kawo ruwan zafi da kayan tea, jiya ba ma cikin nutsuwarmu babu abun da muka taho da shi, magungunan ma Yaya Rufa'i (Mijin Aunty A'isha) ne ya siyo su da ya zo, ya ce ba zai yiyu ki farka kuma ba'a siyo ba." Mama ta jinjina mata kai kawai, amma bata jin zata iya saka wani abu a bakinta da sunan ci ko sha. Aunty Sadiya ta ce. "Dan Allah Yaya ki bar wannan tunanin, kin ji dai abun da Doctor ya ce, jininki ya hau sosai a cikin yini ɗaya kacal, inaga kuma kin ɗore da tunanin na kwanaki da yawa? Kuma kin san hakan already a matsayin ki na babbar Likita." Mama ta buɗe idonta da suka yi kamar na masu shaye_shaye saboda cuta ta ce. "Ta yaya Zuciyata zata bar tunani alhalin an riga an dasa mata baƙin ciki, Sadiya Muhammad fa, Yaya Tafida mijina ne a cikin ƙungiyar matsafa, me...." Sai numfashinta ya sark'e ta fara tari, hakan yasa ta kasa ƙarasa abun da take son faɗa. A ruɗe Aunty Sadiya ta ce. "Dan Allah Yaya ki bar wannan maganar, mu yanzu ta lafiyarki muke, kin ga karki ƙarawa kanki wani ciwon akan wanda yake damun ki already." Mama ta samu tarin ya lafa mata, cikin dashashshiyar murya ta ce. "Tunani ya zama dole Sadiya, dole in yi tunanin rayuwata ni da ɗana yanda zata kasance mana a gaba babu Muhammad, da kuma yanda baƙin fenti ya barwa rayuwarmu zai mana illa." Aunty Sadiya ta ce. "Insha Allahu zaku cigaba da rayuwarku tare da Yaya Tafida cikin kwanciyar hankali." Mama ta juyo idanunta a kanta ta ce. "Ta yaya? Ko kin manta abun da ya faɗa kafin su tafi na sharad'in ƙungiyar su?" Aunty Sadiya ta ce. "Ban manta ba, dan nima jiya da zullumun abun na kwana, amma kuma a yanzu na san babu abun da ya faru da shi, saboda da wani abu ya faru da tuni mun samu labari." Mama ta ce. "Idan ma ƴan ƙungiyar basu kashe shi ba ai hukuma baza ta taɓa barin shi ba, dole ne a yanke masa hukunci dai-dai da abun da suke aikatawa." Aunty Sadiya ta ce. "Ni kuma bana tunanin hakan, domin idan kika duba labarin da Yaya Tafida ya bamu gaba-d'aya ba'a cikin son ransa yake zaune a cikin wannan ƙungiyar ba, tun asali saka shi aka yi ba bisa yardar shi ba, hasalima tsaface shi akai yanda ba zai iya barin cikin ta ba." Mama ta ce. "Hmmmm, ke kika san wannan Sadiya, amma su hukuma basu san haka ba, kuma na shiga ban ɗauka ba bata fitar da b'arawo." Aunty Sadiya ta ce. "Haka ne, amma Insha Allahu Ubangiji zai fitar da shi, tunda ya ga zuciyarsa." Mama ta girgiza kanta kawai cikin takaici, tana jin dama Ubangiji ya karb'i ranta kafin zuwan wannan mummunar ranar. Aunty Sadiya ta cigaba da magana. "Yaya Fateemah a da na fiki takaici da baƙin cikin halin Yaya Tafida, har ji na yi na tsatse shi bana son ganin sa, amma a jiya tsanar ta juye zuwa tsantsar tausayi. Na tabbata duk halin damuwa da baƙin cikin da muke ciki ya fi mu, domin shi abun a kansa yake faruwa. Yaya Fateemah akwai ciwo ba ƙarami ba kana aikata abu a rayuwarka amma kuma zuciyarka bata son abun da kake aikatawar, irin wannan abun ba ƙaramin ciwo ne da shi a zuciyar ɗan Adam ba." Mama zata yi magana suka ga an turo ƙofar ɗakin an shigo. Aunty A'isha ce hannunta ɗauke da tea flaks da leda. Mama ta bita da kallon mamaki ganin har ta zo cikin mintuna ƙalilan bayan yi mata waya. Ta ƙaraso cikin ɗakin suka gaisa da Aunty Sadiya bayan ta ajiye kayan hannunta, sannan ta ƙarasa bakin gado ta zauna a wajen kan Mama, ta yi mata ya ya jiki bayan sun gaisa. Mama ta ce. "A'isha har kin fito kin zo a safiyar nan?" Aunty A'isha ta kalli Aunty Sadiya ta ce. "Dama ina cikin asibitin nan gurin Neehal." A razane Mama ta ce "Gurin Neehal kuma? Mai ya same ta?" Tana ƙoƙarin tashi ta yi maganar. Aunty A'isha ta taimaka mata ta tashi zaune sannan ta ce. "Ba wani abu ba ne, suma ta yi, lokacin muna ƙoƙarin kawo ki asibiti, shine muka haɗo ku duka muka kawo, amma yanzu jikin nata alhamdulillah da sauƙi, nama tashe ta ta yi Sallah, ina jin allurar da akai mata ce bata sake ta ba sai ta koma baccin, amma zuwa anjima ma muna saka ran su bata sallama." Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Allah sarki Daughter, Allah ya nuna mun ƙarshen wannan jarrabawar taki." Aunty A'isha ta ce. "Insha Allahu komai ya zo ƙarshe." Mama ta ce. "Allah yasa, ina Hajiya fa?" Aunty A'isha ta ce. "Tana can gurin Neehal, ina komawa zaki gan ta, ta zo, dan dake ta kwana a cikin ranta, ta tafi gida ma jiya ta dawo yau ƙi ta yi ta ce anan zata kwana." Jinjina kai kawai ta yi tare da lumshe idonta. Aunty A'isha bata jima ba ta tafi, ta ɗauki wata Nurse a waje suka tafi tare zata dawo tare da Hajiya. Hajiya data zo taga yanda Mama ta rame ta zabge sai ta saka kuka, da ƙyar Aunty Sadiya ta lallame ta ta bar kukan. Ƙarfe bakwai saura na safe Ameen ya shigo ɗakin. Lokacin bacci ya fara fizgar Mama sakamakon Magungunanta da ta sha. Hajiya ta bar ɗakin ta koma wajen Neehal saboda Aunty A'isha data je gida dan ɗebo musu abubuwan buƙata na amfani. Aunty Sadiya ta amsa sallamar da ya yi tana kallon sa ganin yanda shima ya fita hayyacinsa a kwana ɗaya, kana ganin sa kaga wanda yake cikin damuwa. Ya gaishe ta, tare da tambayar ta jikin Mama. Kamar Maman ta ji sai ta buɗe idonta dake cike da bacci tana kallon sa. Ya ƙarasa bakin gadon ya zauna tare da kama hannunta yana tambayar ta jikin ta cikin tsananin kulawa. Ta amsa masa da sauƙi. Ya sauke ajiyar zuciya tare da damk'e hannunta a cikin nasa. Duk da baccin da Mama take ji amma haka ta daure ta tashi zaune tana ciccize leb'e, domin tana buƙatar tattaunawa da ɗanta a halin yanzu. Ta yi gyaran murya haɗe da ɗan tari ta ce. "Ameen, ka ji abun da Dad yake yi ko?" Taune lip ɗinsa ya yi da ƙarfi tare da sakin numfashi alamun maganar ta taɓa masa zuciya ba kaɗan ba. A hankali ya ce. "Na daɗe ina zargin shi Mum, a jiya kuma na tabbatar." Mama ta ce. "Amma mai yasa baka taɓa faɗa mun ba Ameen? Kuma ta yaya ka gane?" Ya ƙara taune lip ɗinsa sannan ya ce. "Na ɓoye miki ne saboda ban tabbatar ba, bana son na faɗi abun da ba shi ba ne. Ta yanda aka yi na gane kuwa tun lokacin da Miemerh ta zo gidana time ɗin da Hafsah ta samu miscarriage aka shigo gidan dan cutar da ita, a vantlation ɗin ɗakin da take na ga wani ƙaramin card, kuma na Daddy ne. A lokacin na shiga ruɗu ba kaɗan ba, amma duk da haka ko kusa ban yi tunanin shi ba ne, na yi tunanin dai wani wanda ya san shi ne ko a cikin abokansa. Sai dai daga baya dana zauna na yi dogon nazarin ta yanda aka shigo gidan an yi amfani da keys ɗin gidan ne, kuma Daddy ne kaɗai yake da su. Tun daga sannan na fara saka ido akan dukkan al'amuransa tare da zurfaffen bincike akan duk waɗanda yake mu'amala da su. A lokacin bana zargin sa, na fi zargin wanda yake mu'amala da su ne suke son cutar da shi ta hanyar Neehal. Sai dai duk yanda naso gano komai hakan ya gagara duk da bani kaɗai nake aikin ba, ni da wasu Freind's ɗina ne da suke aiki a hukumar SS ta ƙasa. Ba ƙaramin shiri ne da su Daddy ba na ɓoye dukkan sirrinsu, ta yanda ko kana bibiyar su baza ka iya gano su da wuri ba. Daga baya ne wata dabara ta zo mun, lokacin da za'a yi bikin Miemerh da Sadik sai na saka a dinga bibiyar mun al'amarin shi, cikin ikon Allah kuwa haƙana ya cimma ruwa, domin kuwa na yi nasarar gane ana bibiyar rayuwarsa musamman lokacin da aka shiga satin bikin. Da kaina na yi badda kama na dinga bibiyar masu bibiyar rayuwar tasa, ana i gobe za'a sace shi na yi nasarar sace na'urar ɗaya daga cikin masu bibiyar tasa. Lokacin da zai tafi gurin kamu ne, a gurin kamun suka b'uya a wani waje amma sun kakkasu kowa da kafar da ya samu ya buyan. Da wannan damar na shammaci ɗaya daga cikinsu na shak'a masa powder bacci, ko 2 minutes bai yi ba ya langwab'e. Na lalabo aljihunsa na ɗauki wannan na'ura dana lura kowa a cikinsu yana da ita. Da ita na gane dukkan shirinsu akan kashe Sadik ana i gobe d'aurin Auren sa, hankalina ya tashi ba kaɗan ba, daga nan muka ƙara duk'ufa akan bincikar al'amarin. Nina tura yarana suka ɗauke Sadik a lokacin da su kuma suke daf da zuwa kashe shi. A lokacin ne kuma na gane da hannun Daddy a cikin al'amarin, ta yanda ya gigice da ɓatan Sadik ɗin. Da kuma yanda a cikin week ɗin kullum sai ya fita da daddare, ba ya fita da Mota amma yana yin ƴar tafiya daga sai a zo an ɗauke shi a Mota, ina yin ƙoƙarin bin su a baya a daren a kullum idan aka ɗauke shi, amma tafiya kaɗan sai in ga sun ɓace mun bat in neme su in rasa. A jiya bayan na ɗauko Meimerh daga gurin nan na yi tracked Numbers ɗin Daddy, gaba-ɗaya location ɗin da suke nuna mun nesa kaɗan ne da gurin da na ɗauko Meimerh, hakan ya tabbatar mun da zargi na. Dad yana dawowa gida officer Gobir ya kira ni ya sanar mun kamar yadda na ce masa, ni kuma na kira hukumar SS nan da muke aikin tare na ce su je su tafi da shi su tuhume shi." Ya yi shiru na wasu sakanni yana sauke numfashi idonsa sun kada sun yi jajur. Cikin wata irin murya ya cigaba da magana. "Na yi takaici da baƙin cikin ganin ranar jiya a rayuwata, na ji dama Ubangiji ya ɗauki raina in huta da kunyar duniya a lokacin da halin Dad ya bayyana ga mutanen cikinta, na yi fata da roqon Ubangiji ya ɗauki rana babu a dadi, na yi fatan ace mafarki nake zan farka. Ban taɓa tunanin koda Dad zai yi wannan harkar za'a haɗa baki da shi a cutar da rayuwar Miemerh ba, tare da kisan Mutanen da basu ji ba, ba su gani ba. Na ji kamar in kashe kaina a lokacin da na yi realised Mahaifina matsafi ne, Mahaifina ɗan ƙungiyar asiri ne masu shan jinin......." Sai ya kasa ƙarasawa numfashinsa ya fara wata irin fizga, hawaye kawai Mama take yi tunda ya fara magana. Hannunta na rawa ta kwantar da kansa akan ƙafaɗarta saboda ganin abun da ta manta rabon da ta gani a tattare da shi, baza ma ita tuna ranar data ganin ba wato hawaye. Dama abun da take gudu kenan damuwar ɗanta, ta san duk duniya babu wanda zai kaishi baƙin ciki da takaicin halin Daddy, ko ita baza ta fi shi ba tunda ita mijinta ne, a duk lokacin data so zata iya sauya miji a rayuwarta, amma shi kuma fa? Mahaifinsa ne, abun da ba'a taɓa iya sauyawa a rayuwa, kuma paint ɗin abun da Daddy ya yi shi zai ta bibiya har ƴaƴa da jikokinsa. Ta ɗora hannunta akan lallausar sumar kansa tana shafawa cikin alamun rarrashi, ɗayan hannun kuma tana goge masa hawayen fuskarsa duk da itama hawayen take yi. Aunty Sadiya dake kallon su ta lumshe idonta cikin ƙoƙarin mayar da hawayen tausayinsu da ya cika mata ido. Sun yi 5 minutes a haka sannan Mama ta d'aga kanshi daga jikinta, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya share mata hawayen fuskarta ita ma. Murmushin ƙarfin hali Mama ta yi tare da kissing hannun nasa. Cikin sanyin murya sosai ta ce. "Ka yi haquri Ameen, ƙaddara ce Ubangiji ya ɗora mana, shi ma Dad ba son ransa ba ne ƙaddararsa ce a haka. Ka rage wannan damuwar da nake gani a cikin idanunka, kar wani ciwon ya kama mun kai, bana son in rasa ku kai da Neehal, tunda na tabbatar na rasa Daddy har abada. Sannan ina maka godiya da jinjina akan yanda ka sadaukar da lokacin ka gami da lafiyarka akan kare rayuwar marainiyar Allah, Na gode sosai Allah ya biya ka da Aljannah." Ta ƙarashe zancen da shafar kuncinsa. Ya sauke numfashi tare da gyaɗa mata kai, ya motsa labbansa a hankali ya ce. "Amin." Aunty Sadiya ta dube shi ta ce. "Ameen ka rage jin zafin Daddy a cikin ranka, domin shi ma ba laifinsa ba ne hakan ta kasance da shi, hasalima jefa shi cikin wannan harkar ba bisa son ransa da yardarsa ba." Ameen ya kalle ta cikin alamun tambaya amma bai ce komai ba. Aunty Sadiya ta jinjina kai sannan ta bashi kaf labarin da Daddy ya ba su. Ya lumshe idonsa yana sakin ajiyar zuciya, ko ba komai ya ji daɗi da ya kasance mahaifinsa ba bisa son ransa ya faɗa wannan mummunar harkar ba, amma kuma hakan ba zai saka a ce ba shi da laifi ba shi ma. Ya buɗe idonsa ya ce. "Duk da haka Dad ba zai taɓa fita daga cikin wannan case ɗin ba, domin case ne babba ba ƙarami ba, kuma a idon mutane da hukuma duk ɗaya yake da sauran ƴan ƙungiyar, tunda duk abun da suke aikatawa shi ma yana yi kuma a cikinsu yake." Aunty Sadiya ta ce. "Jikina ya bani Insha Allahu zai fita, ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne." Mama ta ce. "Ameen ka kira Abokinka waɗanda suka tafi shi ka ji yana lafiya, saboda jiya kafin ya tafi ya ce ƴan ƙungiyar zasu iya kashe shi saboda labarin su da ya sanar mana." Aunty Sadiya ta yi ɗan murmushi a ranta ta ce. 'Ashe har yanzu tsohuwar zumar tana nan." Ameen bai yi musu ba ya ɗauki wayarsa ya kira abokin nasa kamar yadda Mama ta ce amma bai d'aga ba. Ya dube ta ya ce. "Daga nan can zan je, duk halin da ake ciki zan sanar muku." Mama ta ce. "Allah yasa mu ji Alkhairi." Suka amsa da Amin, sai dai shi Ameen ko kaɗan ba ya ji a ransa Daddy zai fita daga cikin wannan case ɗin. Har ya tashi zai tafi Mama ta tsayar da shi, ya koma ya zauna dan jin mai zata faɗa masa. Mama ta ce. "Ameen dama kana son Neehal tuntuni mai yasa baka taɓa sanar mun ba?" Ya yi shiru na wasu sakanni kansa a ƙasa sannan ya ce. "Na yi zaton baza ki amince mun ba, shi yasa na fara faɗawa Dad domin ya shawo mun kanki, shi kuma ya ce mun in bar maganar ba zai bani ita ba,ban kuma san dalilinsa na yi hakan ba, shi yasa kawai na haqura." Mama ta ce. "Me zai saka in ƙi amince maka Son? Komai kake so a duniyar nan idan ina da shi zan baka, da ka faɗa mun da abu ɗaya zai saka bazan baka ita ba, idan ita ta ce baka so." Ya yi shiru bai ce komai ba. Mama ta ce. "Tashi ka je, Allah ya yi maka albarka, ya jib'anci al'amuranka ya shirya ka." Ya yi murmushi cikin jin daɗin addu'arta ya ce. "Amin Mum, Allah ya ƙara sauƙi." Mama ta yi murmushi ta ce. "Ameen, ka biya ka duba Neehal ɗin kafin ka wuce." Ya amsa mata sannan suka yi sallama da Aunty Sadiya ta yi masa kwatancen inda aka kwantar da Neehal ya tafi, yana jin zuciyarsa na masa sanyi kasancewa da ya yi da Mama, sai ya ji wani kaso na cikin damuwarsa na yayewa. Har lokacin da ya je dakin Neehal bata tashi ba baccinta take. Suka gaisa da Hajiya ta shiga tambayar sa ko shi ma cutar yake ne duk ya yi wani iri. Bai bi takan ta ba ya ƙarasa bakin gadon da Neehal take ya tsaya yana kallon ta, zuciyarsa na k'issima masa abubuwa da yawa a kanta. Ya yi kusan 10 minutes sannan ya yiwa Hajiya sallama ya tafi. Sai da sha ɗaya ta wuce sannan Neehal ta tashi daga baccin. Toilet kawai take je ta yi uzurinta ta kuskure baki ta fito ta cewa Aunty A'isha ta kai ta gurin Mama. Aunty A'isha ta ce ta bari a basu sallama mana, amma ta ƙi yarda harda kukanta, ganin haka yasa Aunty A'ishan ta raka ta. Suna shiga ɗakin ta tafi da gudu ta rungume Mama dake kwance idanunta a lumshe. Mama ta buɗe ido ta ce. "Daughter, Ya jikin naki?" Cikin sanyin murya tana duban yanda Maman ta zabge lokaci ɗaya ta ce. "Da sauqi Mama, ya naki?" Mama ta ce. "Alhamdulillah." Sai kuma ta fara kuka. Aunty Sadiya ta ce mata. "Kukan na mene ne kuma Neehal?" Bata yi magana ta cigaba da kukanta. Mama ta ce. "Me ya faru?" Cikin kuka ta ce. "Ki yi haquri Mama, na san ni ce sanadin wannan ciwon naki, saboda......." Cikin sauri Mama ta katse ta da faɗin. "Wanne irin shirme ne wannan Neehal, bana hana ki irin waɗannan maganganun ba, ciwo Ubangiji ne ke ɗora shi kuma shi ya ɗora mun. Ki bar kukan hakan kin ji ƴar albarka, ke ba lafiya karki ƙarawa kanki wani ciwon." Ta gyaɗa mata kai tana share hawayenta. A ranar aka sallami Neehal duk da dama already ta sallami kanta, sai magungunanta da zata cigaba da sha. Ranar haka aka dinga zuwa duba Mama, ƴan'uwa da abokan arzik'i ko ta ina, ana kuma yi musu murnar bayyanar Neehal. Da yawan mutane sun ɗauka damuwar ɓatan Neehal ce ta sakawa Mama ciwo har ta kwanta a asibiti. Kwanan Mama huɗu aka sallame ta daga asibitin, Alhamdulillahi jikin nata ya yi sauƙi, amma cikin zuciyarta cike take fal da damuwar abun da mijinta ya aikata da zullumin makomar rayuwarsa, duk da dai har yanzu abun da ya faɗa na sharad'in ƙungiyarsu akan kisan duk wanda ya fallasa sirrinsu har yanzu bai tabbata a kansa ba. Su Uncle Ahmad da Abba da Uncle Mahmud suna ta cuku_cuku akan case ɗin Daddy, amma abun ya ci tura ko damar ganin sa basu taɓa samun yi ba. Ameen kuwa ya yi busy suna ta aikin ganin sun kamo sauran ƴan ƙungiyarsu Daddy. Duk inda Daddy yake tunanin za'a ga wani daga cikin ƴan ƙungiyar an je duk ba'a same su ba, gaba-d'aya sun ɓace bat tamkar aljanu, da alama su ma suna can suna shirin ko ta kwana akan farautar su da suka fahimci ana yi. Babu wanda yasan halin da Daddy yake ciki sai ƴan'uwa na jiki_jiki da ya zama dole, ko ƴan dubiya sun tambaye shi idan an zo su Mama sukan san abun da zasu faɗa na rashin ganin shi da ba'a yi ba, wanda zai saka baza a yi tunanin ko da akwai wata matsalar ba.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *7️⃣1️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* *Barkanmu da Sallah, fatan an yi Sallah lafiya? Allah ya maimaita mana, Amin.* .........Aunty Sadiya ta yi kanta tana kiran sunanta tare da jijjigata. Neehal ta faɗa jikinta ta rungume ta tana faɗin. "Please Mama wake up, karki mutu ki bar ni, dan Allah Mama ki tashi karki tafi ki bar ni., Mama! Mama!..." Aunty A'isha ta zo ta janye ta tare da rungume ta, ta shiga rarrashinta cikin dauriya. Dan itama hankalinta ba a ƙaramin tashe yake ba na ganin halin da Maman take ciki, ta umarci Zulai dake tsaye ta ɗauko ruwa mai sanyi a shafawa Maman ko Allah zai sa ta farfaɗo. Hajiya kuwa bata motsa ba, dan bata jin idan ta tashi ƙafafunta zasu iya ɗaukar gangar jikinta balle har su yi tafiya, sai salati take yi tare da duk addu'ar da ta zo bakinta cikin matuƙar gigita na wannan mummunan al'amarin. Aunty Sadiya ta bar jikin Mama ta ɗauko wayarta ta shiga kiran Numbern Ameen, tana shiga amma ba ya ɗauka. Aunty Sadiya ta karɓi ruwan da Zulai ta kawo ta fara shafawa Mama a fuska, amma ko alamar zata motsa ba su gani ba. Hankali a tashe suka ɗauke ta sukay Mota dan kai ta asibiti. Ganin yanda aka ɗauki Mama kamar gawa ya ƙara tayar da hankalin Neehal, stress ɗin sun mata yawa, ga tashin hankalin tafiyar da aka yi da Daddy ga halin da Mama take ciki ga kuma dunbin damuwar dake cunkushe a cikin zuciyarta, hakan yasa ta sume itama. Sai daukar ta aka yi aka haɗa da Mama aka kai su asibitin. *AFTER TWO HOURS* *HOSPITAL* A hankali Neehal ta buɗe idonta tana kallon saman ɗakin da take na wasu sakanni, sannan ta juyo da kanta gefen damanta domin fahimtar gurin take. Aunty A'isha dake zaune a kujerar gaban gadon marasa lafiya ta rafka tagumi ta sauke ajiyar zuciya tare da tashi tsaye cikin sauri ta ƙarasa kusa da Neehal ta kama hannunta ta ce. "Sannu Neehal, kin tashi? Bari a kira Doctor." Neehal ta d'aga mata kanta dak'yar, tana so ta tambaye ta ina Mama amma kuma ta kasa motsa bakinta da niyyar magana, ga wani irin ciwon kai da kanta ke yi mata. Aunty A'isha ta fice daga ɗakin, Hajiya dake zaune akan sallaya ta taso ta shiga yiwa Neehal sannu, Neehal ta gyaɗa mata kai kawai tare da mayar da idanunta ta lumshe. Har lokacin tana jin nauyin da ƙirjinta da yay mata gami da zafin zuciya. Bayan mintuna kaɗan Aunty A'isha suka dawo tare da wani likita, ya dudduba Neehal ɗin tare da yi mata ƴan tambayoyi, ta amsa masa da kai kawai ta nuna masa kanta da ƙirjinta a matsayin inda yake yi mata ciwo. Ya cire mata drip ɗin hannunta sannan ya cewa Aunty A'isha ta bata magungunan da suka siyo mata, amma su bata ko da tea ne ta fara sha. Zai je ya haɗo allura ya dawo yay mata. Sukay masa godiya shi kuma yay mata addu'ar samun sauƙi. Aunty A'isha ta taimaka mata ta tashi zaune ta kuskure mata baki, sannan ta haɗa mata tea ɗin ta bata ta sha. Da ƙyar Neehal take had'iye tea ɗin saboda ɗacin da take jin yay mata a bakinta, kaɗan ta sha ta ɗauke kanta. Aunty A'isha ta bata magungunanta ta sha sannan ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Ta dubi Aunty A'isha cikin muryar marasa lafiya ta ce. "Ina Mama?" Aunty A'isha ta ce. "Tana Emergency na asibitin nan sun bata gado, amma jikin nata da sauƙi yanzu." K'walla ta taru a idon Neehal, kamar zata yi kuka ta ce. "Ina son na gan ta." Aunty A'isha ta ce. "Gurin da take ba'a bari a shiga, kin ga Hajiya ma tun d'azu take naci sun hana ta shiga, sun ce sai ta farfaɗo za'a samu ganin ta, amma Sadiya tana gurin, da zarar ta farfaɗo zata kira mu ta sanar mana." Neehal ta fara hawaye amma bata ce komai ba. Aunty A'isha ta ce. "Mene abun kuka kuma ke da baki da lafiya? Ki kwantar da hankalinki zata samu lafiya Insha Allah, karki saka damuwa a ranki ki ƙarawa kanki ciwo." Neehal ta gyaɗa mata kai sannan a hankali ta ce. "Ƙarfe nawa? Ina son na yi Sallah Aunty." Aunty ta ce. "Ƙarfe tara na dare, mu je in kaiki toilet ki yi alwala ko in kawo miki ruwan nan ki yi idan baza ki iya tafiya ba?" Ta taune lip ɗinta sannan ta ce. "Zan iya zuwa toilet ɗin." Aunty A'isha ta taimaka mata ta tashi da ƙyar ta kai ta toilet ɗin ta yi tsarki sannan ta ɗauro alwala suka dawo ɗakin ta yi Sallar Magriba da isha'in dake kanta a zaune. ************** Ameen tun bayan da ya kawo Neehal gida ya koma gidansa ya kulle kansa a ɗaki ya cigaba da binkicen da yake hankalinsa a matuƙar tashe. Gabansa na faɗuwa ƙirjinsa na dokawa a million saboda fargaba. Baya son abun da yake zargi ya tabbata. Yana jin Hafsah tana ta yi masa knocking amma bai bi ta kanta ba, Sallar la'asar ce kawai ta fitar da shi daga gidan zuwa masallaci, yana dawowa ya koma ɗakin ya ƙara rufe kansa. Wannan karon sai da ya yi wanka saboda uwar zufar da yake haɗawa. Bayan ya fito ya ɗauki wayarsa ya kira wani suna magana yana lallatsa laptop ɗinsa, da alama tare suke aikin da wanda yake wayar da shi. Bayan wasu mintuna yana cikin aikin lokaci ɗaya ya yarda wayar hannunsa da system ɗin gabansa a matuƙar gigice. Ya shiga bubbuga hannunsa akan goshinsa yana maimaita kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un a fili. Ya miƙe tsaye idanunsa a lumshe, wani irin jiri ya ji ya kwashe shi hakan yasa ya yi saurin dafe hannayensa a jikin bango, ƙirjinsa na d'agawa saboda yanda zuciyarsa take bugawa. Ya daɗe a haka kafin ya zame ya zauna a ƙasa hannunsa dafe da ƙirjinsa, idanunsa sun yi ja jajur. Cikin wata irin murya dake nuni da tsantsar tashin hankali yake faɗin. "Ya Allah...! Dad why? Why?" Yana jin wayarsa tana ringing amma ko kallon inda take bai yi ba. Sai da ya ga Magriba tana ƙoƙarin yi sannan ya lallaɓa ya tashi da ƙyar ya ɗauki wayarsa ya kira wani abokinsa jami'in SS, ba tare da tunanin komai ba ya sanar masa da buƙatarsa tare da ƙudirinsa akan Daddy. Sannan ya koma ya kwanta akan gado ruf da ciki, yana son ya ɗauki system ɗinsa ya cigaba da duba abu amma ya san ko ya ɗauka babu abun da zai gane a cikinta, balle har ya fahimci wani abu. Duk wani bincike da zai yi akan al'amarin Neehal ya yi kuma ya gano komai duk abun da yake son gani, sai dai ya yi da na sanin yin binciken, da ya san abun da zai binciko kenan da tun farko bai fara binciken ba. Duk yanda mutum yake tunanin tashin hankalin da Ameen yake ciki ya wuce nan, mahaifi fa! Mahaifinsa wanda yake matsayin uban Neehal a yanzu amma shine da aikata mata wannan abubuwan? A matsayinsa na babban jami'in tsaron ƙasa mai ƙoƙarin ganin ƙasar sa ta gyaru tare da kama duk wani ɓata gari amma shine da kansa a cikin ɓata garin. Shine dalilin da ya saka kenan ya hana shi Auran Neehal ashe yana da wata manufar ne a kanta? Tambayar da yake ta yiwa kansa wanda ba shi da mai ba shi amsa me yasa Daddy ya shiga wannan ƙungiyar? Wanne irin rud'in shaid'an ɗin ne da huɗubar mummunar zuciya suka ɗebe shi ya faɗa cikin halaka ta duniya da lahira? Babban tashin hankalinsa ɗaya halin da Mama zata shiga idan ta ji Daddy ne ke aikata duk waɗannan abubuwan. Ya zata ji? Ya duniya zata ɗauki maganar? Wata zuciyar tasa kuma ta kasa yarda cewa Mahaifinsa ne da wannan ɗanyen aikin, tana ta faɗa masa ya sake bincike may be gaskiya ta bayyana, wataƙila wani ne ya shiryawa Dad ɗin haka, ko kuma wasu abokan nasa suke wannan harkar yake bin su amma shi ba ya yi? Ko ko ko.......Babu abun da bai kissima a ransa ba dangane da wannan harkar da Daddy yake yi. Ya fara bibiyar al'amarin Neehal ne tun lokacin da aka biyo ta har cikin gidansa, ada baya ɗaukar abubuwan da suke faruwa da wata manufar, ya yi zaton daga Allah ne kawai, sai lokacin zuciyarsa ta fara yi masa kokwanton tabbas da wata a ƙasa. A yau ya ji duniyar tay masa zafin da bata taɓa yi masa irinsa ba a rayuwarsa, ya ji ya tsani kansa da Daddy, bai san da idon da zai kalli Mama da Neehal ba, a ce Mahaifinsa wanda Neehal takewa kallon Uba a gare ta shi yake aikata mata haka? Tsananin tashin hankali da damuwar da Ameen ya shiga a yau baza ta faɗu ba. Har bayan Sallar isha'i yana kwance a inda yake cikin mawuyacin halin damuwa, zuciyarsa na k'issima masa abubuwa mara sa kyau a kansa, harda wacce ta bashi shawarar ya kashe kansa saboda damuwa da tsananin takaici da kunyar duniya. A hankali ya fara dawowa cikin nutsuwarsa da taimakon Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un da yay ta maimaita a cikin ransa. Hakan yasa ya iya tashi dariyar cikin k'unar zuci, bai bi takan wayarsa da ake ta kira ba da bugun ƙofar da Hafsat take masa ya shiga toilet ya ƙara watsawa jikinsa da ya ɗauki zafi ruwa tare da dauro alwala. Ya fito ya xora jallabiya ya tayar da Sallar Magriba da isha'i dake kanshi. A kowacce sujjada yana roƙon Allah yasa mafarki yake ba gaske ba ne abin da binciken sa ya nuna masa, tare da roƙon ya farkar da shi cikin gaggawa, ko kuma idan ma gaske ne Allah yasa ba Daddy ba ne, wani ne daban gaskiya zata bayyana a gaba....... Aunty Sadiya tana tsaye a bakin window'n ɗakin da Mama take tana lek'enta cikin tsananin tausayawa, Maman na kwance akan gadon ƙaramin ɗakin da take ita kaɗai an saka mata robar numfashi (Oxygen) a hancinta. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe idonta ta buɗe sannan ta yi baya ta zauna akan kujera tana sauke numfashi cikin yanayin tsantsar damuwa. Wayarta dake hannunta ta latsa, hakan ya yi dai-dai da shigowar kiran mijinta cikin wayar Barrister Ahmad. Ta d'aga tare da karawa a kunne gami da sallama, bayan ya amsa mata cikin taushin murya ya ce. "Haleemah ya jikin Yaya Fateemah da Neehal?" Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. "Da sauqi Habibi, naga Ya A'isha ta mun text ta ce Neehal ta farfaɗo, Yaya Fateemah kuma gata nan a kwance har yanzu dai shiru." Uncle Ahmad ya ce. "Masha Allah, itama Yayan Insha Allahu zata farko cikin k'oshin lafiya, damuwar data riske ta lokaci ɗaya ne yasa ta cikin wannan halin." Aunty Sadiya ta ce. "Allah yasa." Uncle Ahmad ya nisa ya ce. "Komai zai wuce Insha Allah, gobe da sassafe nima zan taho Kanon sai mu je can inda Yaya Tafida yake mu san ya za'a yi da case ɗin." Aunty Sadiya ta ce. "Ɗazun nan Yaya Hamza (Abba) ya bar asibitin nan, kuma daga can inda aka tafi da Daddy yake, ya ce sun ƙi bari ma ya gan shi, sun ma ƙi saurarar shi balle a yi magana." Uncle Ahmad ya ce. "Kin san case ɗin nan ba ƙaramin case ba ne, musamman ma da bamu san evidence ɗin da Ameen ya ba su ba, amma Insha Allahu zamu yi iya yin mu wajen ganin Yaya Tafida ya fito, su kuma sauran ƴan ƙungiyar an kama su." Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. "Barrister kana ganin Yaya Tafida zai iya fita daga cikin case ɗin nan kuwa? Su kuma sauran ƴan ƙungiyar a iya kama su?" Uncle Ahmad ya ce. "Insha Allah Habibty, babu abun da ya fi ƙarfin Ubangiji, bincike kuma shi zai bayyana gaskiya." Aunty Sadiya ta ce. "Haka ne." Uncle Ahmad ya ce. "Ameen ɗin ya zo asibitin kuwa?" Ta ce. "Ina ta kiran wayarsa ba ya pick." Ya ce. "Allah yasa dai lafiya yake, ki cigaba da kiran sa, Insha Allahu za'a yi sa'a ya ɗauka." Aunty Sadiya ta ce. "Toh." Daga haka suka yi sallama ta katse wayar. Layin Ameen ta kira. Har lokacin yana zaune akan sallaya hannunsa dafe da kansa. Yana jin kira ya shigo cikin wayarsa, kamar ya share sai kuma ya yi wani tunani, ya san definitely cikin kiran da ake ta yi masa baza a rasa na Mama ba, rashin ɗaukar mata waya kuma zai ƙara saka ta a cikin damuwa, hakan yasa ya miƙe da sauri ya ɗauko wayar a inda ya yasar da ita cikin tsananin dauriya saboda wani irin juyawa da kansa yake masa. Ganin Aunty Sadiya ce yasa ya ɗaga wayar ya saka ta a handsfree amma bai ce komai ba. Cikin sauri Aunty Sadiya ta ce. "Ameen ina ka shiga ne yau?" Shiru ya yi bai bata amsa ba. Ta kuma cewa. "Kana lafiya Ameen? Ka yi magana mana." Ya runtse idonsa numfashinsa na fita da sauri da sauri cikin matuƙar sanyin murya ya ce. "I'm fine." Aunty Sadiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Masha Allah." Cikin matuƙar damuwa ya ce. "Ina Mum?" Ta ce. "Muna tare da ita, tun d'azu take kiran ka tana son magana da kai amma baka pick call ɗin." Ajiyar zuciyar shi ma ya sauke ya ce. "Zan zo yanzu in gan ta." Aunty Sadiya ta ce. "Ba ma gida, muna Hospital." A ruɗe ya ce. "What? Kuna me? Waye ba shi da lafiya?" Aunty Sadiya ta ce. "Neehal ce bata jin daɗi." Ya taune lip ɗinsa da ƙarfi sannan ya ce. "Wanne asibitin kuke?" Ta ce. "Nasarawa." Ya ce. "Okay gani nan zuwa." Bai jira amsarta ba ya katse kiran. Mukullin Mota kawai ya laluba ya buɗe ɗakin ya fita. A falo ya tarar da Hafsat zaune idanunta sun yi jajur alamun ta ci kuka ta k'oshi, ta bi shi da kallo zuciyarta fal kishi. Ya ɗan tsaya yana kallon ta. Miƙewa ta yi ta tako gabansa tana kallon sa cikin firgicin ganin yanda ya fice daga hayyacinsa a yini ɗaya. Ta fashe da kuka a hankali cikin kukan ta ce. "Meke damun ka Al'ameen da ka yi wannan ramar lokaci ɗaya? Tun d'azu ka rufe kanka a ɗaki ka bar ni cikin zullumi da damuwa, ka san kuma dole hankalina zai tashi." Lumshe idonsa ya yi cikin k'unar zuci, ya san bai kyauta mata ba tunda bata da masaniyar abun da yake faruwa balle tay masa uzuri akan halin da yake ciki. Bai ce komai ba ya kama hannunta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ya shiga share mata hawayen fuskarta. Ta kwace hannunta tare da faɗawa jikinsa ta rungume shi. A hankali ya kai hannunsa ya ɗan bubbuga bayanta alamun rarrashi, kafin ya zare ta daga jikinsa ya zaunar da ita akan kujera ya fice daga falon ba tare ya yi magana ba. Ta bi shi da kallo cikin tsananin takaici, a tunaninta duk wannan halin da yake ciki saboda Neehal ne, wutar kishi da tsanar Neehal ne ke ƙara ruruwa a cikin ranta. Ita kam wannan shegiyar yarinyar ta zame mata ƙarfen ƙafa a tsakaninta da mijinta, amma zata yi maganin abun, dole ne ta yiwa tufkar hanci tun kafin dare yay mata ta zo tana kuka da idanunta. Ikon Allah ne kawai ya kai Ameen asibitin dan baya cikin nutsuwarsa ko kaɗan. Aunty Sadiya ya kira ta faɗa masa section ɗin da suke. Ya buɗe Mota da ƙyar ya fito yana jin jikinsa kamar ba nasa ba saboda damuwa. Cikin kulawa da tausayawa Aunty Sadiya ta tarb'e shi, kama hannunsa ta yi ta zaunar da shi sannan ita ma ta zauna. A hankali ta ce. "Ameen! Ka ga yanda ka koma kuwa? Kamar wanda ya yi jinyar shekara guda, ga jikinka na ji shi ya yi wani irin zafi." Lumshe idonsa ya yi bai ce komai ba. Cikin tausayawa Aunty Sadiya ta ce. "Ka yi haquri Ameen, haka rayuwa take cike da kalubale da jarrabawa, damuwa baza ta taɓa maka maganin abun da ke damun ka ba sai dai addu'a." Gyaɗa mata kai ya yi a hankali sannan ya motsa labbansa da ƙyar ya ce. "Ina Mum da Miemerh?" Aunty Sadiya ta ce. "Neehal tana cikin asibitin nan amma ba'a nan wajen ba, Ya A'isha da Hajiya suna tare da ita, Yaya Fateemah kuma tana cikin ɗakin nan." Ta ƙarashe zancen da nuna masa ɗakin da Mama take. Cikin mamaki ya buɗe idonsa yana kallon ɗakin bugun zuciyarsa ƙaruwa. Aunty Sadiya ta ce. "Damuwar data same ta lokacin ɗaya ce yasa har ta suma, amma zuwa yanzu Doctors sun shawo kan matsalar har ta samu bacci, bana son ka ƙara tayar da hankalinka akan tashin hankalin da kake ciki already, shi yasa da muka yi waya ban sanar maka ba." Bai jira jin ƙarashen zancen Aunty Sadiyan ba ya miƙe ya nufi ɗakin cikin sauri. Ya ƙarasa gaban gadon da take ya ƙura mata ido, cikin zuciyarsa yana jera mata addu'ar samun lafiya. Yayin da tashin hankali da damuwar da yake ciki ya ninku ganin halin da Mama take ciki. Ya san ya rasa Daddy a rayuwarsa dan hukuma baza ta taɓa barin shi ba, koda ba'a kashe shi ba zai ƙare rayuwarsa a prison ne, amma ba zai so ya rasa Mama ba Mace mafi soyuwa a gare sa, Mahaifiyarsa mai tarin alkhairi ga duk wanda ya rabe ta. Ya ɗora hannunsa akan nata a hankali tare da lumshe idonsa da suka yi jajur yana kukan zuci. Daddy bai musu adalci ba, me yasa ya faɗa wannan mummunar harkar da har su koma ga mahaliccinsu tabon abun da ya aikata ba zai bar rayuwarsu ba? Haka ya zauna a gaban Mama yana ta tunane_tunane wanda yake ƙara masa radad'i da k'uncin zuciya. Da wanne ido zai kalli Neehal da ƴan'uwanta? Da wanne ido zai kalli Mama da nata ƴan'uwan? Da wanne ido zai kalli mutanen duniya da dangin Daddy akan abun da Dad ɗin ya aikata? Kunyar kowa yake ji har shi karan kansa, ji yake tamkar shi ya aikata wannan abun kunyar. Wani Doctor ne ya shigo ɗakin yasa shi dole ya fita, dan farko ma faɗa ya kama akan shiga ɗakin da ya yi, Aunty Sadiya ta bashi haquri ta ce ɗanta ne ya zo ganin ta. Ganin yanayin Ameen Aunty Sadiya ta shiga kwantar masa da hankali cikin kalamai masu taushi, da ƙyar ta lallaɓa shi ya koma gida wajen ɗaya saura na dare, dan da cewa ya yi a nan zai kwana, Aunty Sadiya ta ce ya baro Hafsat ita kaɗai ya koma gobe da safe sai ya dawo. Bai je yaga jikin Neehal ba saboda dare da ya yi, idan ya dawo da safen ya je ya duba ta. Bayan Neehal ta idar da sallolin ta, ta koma kan gado ta kwanta, ba jimawa likitan ya dawo yay mata allurar bacci. Sai dai tashin hankali da damuwar da take ciki ya hana baccin zuwar mata, ko alamun shi bata ji. Ta lumshe idonta dai kawai ta fara tunane_tunane. Rayuwarta ta fara tunowa tun tana ƙarama lokacin iyayenta suna raye, bata iya tuno komai a lokacin sai fuskokinsu da wasu moment ɗinta tare da su kaɗan. Ta tuna yanda Aunty A'isha take bata labarin irin tarin k'aunar da mahaifinta yake mata, ta tuna farkon dawowarta hannunsu Mama da irin riqon gaskiya da amana da sukay mata, gami da tarin k'aunar da suke nuna mata. Mama ta nuna mata son da ko ɗan data haifa albarka, lokuta da dama tana danne farincikinta dana ɗanta domin nata farincikin. Ta tuna wasu lokutan baya lokacin tana ƙarama hankali bai gama isar ta ba, yanda take ɓatawa Ameen abubuwan amfaninsa tana sane, shi kuma babu haquri zuciya a kusa, yana ɗan maketa ta kwanta tay ta birgima tana ihu a ƙasa, Mama ta zo ta ɗauke ta, ta rarrashe ta, shi kuma tay masa faɗa ta ce ya daina dukar mata yarinya ƙarama, yay mata faɗa ko nasiha mana idan ta yi masa abu ba wai duka ba. Sai sun koma ɗaki sannan ita kuma Maman tay mata faɗan ta daina taɓa masa abubuwa. Ta tuna wata rana lokacin tana Jss Mama ta aike ta ta kira shi, ta tarar yana toilet yana wanka, ga laptop ɗinsa a ajiye akan bedside drower a kunne. Ta zauna ta dinga lallatsa masa tay masa barna ba kaɗan ba ta tay masa delete ɗin some important documents ɗinsa. Ranar ta gane Allah ɗaya ne a gurinsa dan tsallen ƙwado ya saka ta, wuni ta yi ranar kuka ƙafa ta ƙi takuwa. Yayin da Mama ta kusa cinye shi ɗanye da masifa. Hakan da Mama take yi ba wai tana yi dan ta saka ta raina Ameen ɗin ba ne, hasali ma bata yi masa faɗa koda wasa a gabanta sai dai wanda Allah ya yi ta ji ko ta gani, kuma kodayaushe cikin nuna mata ta girmama shi take, ita Maman tana yi masa haka ne dan tsoron kar su cutar da marainiyar Allah. Mama ta yi mata tarbiyya irin wacce ake fatan kowacce uwa ta yiwa ƴaƴanta, ta nuna mata respect ɗin na gaba da ita ko waye ne. Hakan yasa ko yaya mutum ya girme mata take girmama shi. Ta tuna Daddy da tarin k'aunar da ya nuna mata a duniyar nan, Daddy ko faɗa baya mata sai dai nasiha, a duk lokacin da zai mata magana cikin fara'a da zolaya yake mata, ko me take so a duniyar nan yana yi mata shi idan bai fi ƙarfin shi ba kuma abun ba mara kyau ba ne. Ko laifi ta yiwa Mama ta san inta kamata zata yabawa aya zaƙinta gurin Daddy take gudawa ta buya, shi kuma ya bawa Mama haquri ita kuma yay mata faɗan har ta kuma. Tun tana ƙaramarta Mama ta koyar da ita yawaita karatun Alkur'ani da azkar da yin nafilfili wanda zuwa yanzu sun zamar mata jiki, uwa uba ibadah da nusar da ita son lahira fiye da duniya. Ita kuma me zata ce da waɗannan bayin Allah a rayuwarta? Sun zame mata garkuwa, bango, jigo da duk wani abun tunk'aho a rayuwa. Komai za su yi baza ta taɓa ganin baƙin su ba a idonta. Wannan abun da ya faru ta san ƙaddara ce Allah ya ɗora musu su duka. Ta tuna yanda dangin mahaifinta dana mahaifiyarta suka banzartar da ita, k'anin mahaifiyarta uwa ɗaya ya kasa yi mata riqon tsakani da Allah, saboda a ganinsa wahala zata zamar masa. Yanzu gashi da bata hannun nasa ya zama abun tausayi, dan ganin da tay masa lokacin bikinsu da Sadik ya zama kamar wani almajiri, duk ya fita hayyacinsa duniya ta fara koya masa hankali. Ta tuna ƙaddarar rayuwarta da yanda al'amura suka dinga tafiyar mata, ashe ƙaddarar ba ta_ta ba ce ita kaɗai, ta shafi mutane masu girma da daraja mafi soyuwa a gare ta, wadda duk matsayin da ta kai a rayuwar nan su ne sanadi. 'Ya Allah ka fitar da Daddy daga cikin wannan al'amarin, Allah ka yafe masa dukkan abun da ya aikata maka ka shirya shi ya bar wannan mummunar hanyar, Allah ka saka masa akan sanya shi cikin wannan harka ba tare da yardarsa ba da bara_gurbin abokinsa ya yi sanadin shigar sa. Allah ka tashi kafaɗun Mama ka bata lafiya da ikon cinye wannan jarabawar daka ɗora mana.' Ta faɗi haka a zuci tana zubar da hawaye. "Yaya..." Ta faɗa can ƙasan mak'oshi, ko yana ina ko a wanne halin yake ciki yanzu sai Allah. Da tunanin Ameen da halin da yake ciki allurar da akay mata ta yi aiki a jikinta bacci ya ɗauke ta wajen ƙarfe uku na dare.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *7️⃣3️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* ...........Washegarin da aka sallamo Mama ya kama Ranar Lahadi. Da safe su Maman suka hallara a part ɗin Mama a Falon sama dan tattaunawa akan al'amarin Daddy. Uncle Mahmud, uncle Ahmad, Kawu Musa, Abba da Mama. Kawu Musa da bai san abun da ya faru da Daddy ba sai a yanzu Abba ya sanar masa da komai. Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa cikin tsananin d'imuwa. A ruɗe ya ce. "Subhallahi, wanne irin mugun aboki Alhaji yake tarayya da shi? gaskiya ya cika cikakken mara imani, matsiyaci ne na ƙarshe amma." Abba ya ce. "Ai Ginyau ba ƙaramar cuta ya yi mana ba, dan ya yi sanadiyar ɓacin sunan zuri'armu." Mama ta ce. "Hmm, idan bera da sata daddawa ma da wari, da a ce Yaya Tafidan bai bi shi ba ai bai isa ya ɗauke shi ya kai shi ba, ko kuma yana zaune a gida ya saka shi a cikin ƙungiyar ba." Kawu Musa ya ce. "Kar ki ce haka Hajiya, babu ta yanda za'a yi dan mutum ya ce maka ka zo ku je wani guri ka yi tunanin a wannan mummunar hanyar zai saka ka, ko da zai kaika gurin irin waɗannan mutanen baza ka taɓa kawowa a ranka saka a cikinsu za'a yi ba, kuma idan har gaskiya ne abun da Alhaji Tafida ya faɗa to duk abun da ya aikata a cikin wannan ƙungiya ba'a hayyacinsa ya yi ba, tunda tsaface shi suka yi. Duk abun da ya aikata na saɓon Allah alhakin yana kan waɗanda suka saka shi a ciki ko a gurin Ubangiji, domin ba shi da yanda zai yi ne a dole yake aikatawa, kuma shi ma ya ce abun yana damun sa. Dan haka yanzu dole mu san yanda za'a yi ya fito daga hannun hukuma sannan kuma ya bar cikin wannan ƙungiyar. Ita kuma Neehal wannan abubuwan da suka dinga samun ta sanadiyyar shi Alhaji Tafidan ba laifin kowa ba ne sai mu danginta, domin da mun riƙe ta a hannunmu babu ta yanda za'a yi wannan al'amarin yakasance a gare ta. Watsi da ZUMUNCI da gudun wahala na ƴan'uwan mahaifinta da mahaifiyarta duk shi ya janyo mata, banda haka ta yaya har za'a ce yayar kishiyar mahaifiyarka ce zata riƙe ka banda ma da mutunci sosai a tsakani, alhalin da danginka a raye. Su suna can sun saki baki tunda yarinya ba'a hannunsu take ba babu ruwansu da wahalarta koma me zai faru da ita ya faru basu da asara. Bacin su kuma wahalar da mahaifinta ya yi da su." Uncle Mahmud ya ce. "Malam Musa da zancenka gaskiya, amma duk da haka Ubangiji ne ya ƙaddara mata hakan zata faru da ita." Kawu Musa ya ce. "Haka ne, amma komai yana da sanadi a rayuwa, rashin ZUMUNCI ba ƙaramin abu ba ne, wanda bai yi shi a duniya ba fa aka ce zai yi shi a wuta. Yanzu da ace tana hannunmu mu danginta da Alhaji Tafida ya faɗa wannan harkar ai baza su ce ya je har inda take ya cutar da ita ba, tunda kamar yadda suka faɗa ba shi yake ciyar da ita ba da sauransu." Abba ya ce. "Haka ne Malam Musa zancenka dutse, na fahimci abun da kake nufi da maganar ka da kuma abun da kake son faɗa. Mutane ne yanzu sun mayar da zumunci na ganin ido da kuɗi, zumuncin Allah amma ba'a son yin sa, kuma an mayar da hakan kamar ba komai ba." Kawu Musa ya ce. "Ƴar guda ɗaya tal a duniya amma su kasa riƙe ta, bacin tarin Alkhairin da mahaifinta yay musu da yana raye. Amma kuma da yake Allah mai ƙudura ne ba ka ga yanda su Salisun suka koma ba yanzu gaba-d'ayansu. (Ƴaƴan Baffa, wanda ya riƙe Umma da Abba.) Sun zama abun tausayi, abun da zasu ci ma gagarar su yake yi, ita ɗin da suka so ta tagayyara gashi Ubangiji sai d'aga ta yake, wannan ƙaddarar data same ta ma Insha Allahu komai ya zo ƙarshe, kuma da ma rayuwar mumuni dole sai da jarrabawa. Wallahi idan kuka ga halin matsin rayuwar da Umar yake ciki sai kun tausaya masa, kuma shi ma duk alhakin marainiyar Allah da ya zalunta ne ya fara kama shi." Mama ta jinjina kai ta ce. "Na gani tabbas, lokacin bikin Neehal da Sadik kamar ba shi ba, har wani tsufan dole ya yi." Kawu Musa ya ce. "Ba dole ba, zaluntar Maraya ai ba wasa ba ne, ga kuma watsi da ZUMUNCIN Allah." Uncle Ahmad ya ce. "Mutanen duniyar nan sai addu'a, ita dai wannan yarinya Allah yasa iya wahalarta kenan duniya da lahira, Allah ya bata miji na gari da zai riƙe ta da amana." Gaba-ɗaya suka amsa da "Amin ya Allah." Sannan suka koma hirar Daddy da yanda za'a yi ya fito, inda suka k'ark'are akan matsayar za su nemi abokin Ameen waɗanda suka tafi da Daddy dan su san ya za'a ɓullo wa abun. Neehal tana kwance a ɗakinta tana tunanin rayuwa da bata rabo da shi Mama ta shigo ɗakin. Ta tashi zaune tana amsa sallamar da ta yi. Mama ta zauna a gefenta ta ce. "Neehal ban ga kin fito kin ci abinci ba." Kamar zata yi kuka ta ce. "Mama bana jin yunwa ne, wai yaushe Daddy zai dawo?" Mama ta ce. "Ban sani ba Neehal." Ta fara hawaye ta ce. "Mama dan Allah ki cewa su Abba kar su bari a kashe shi, ko kuma su cewa Yaya yasa waɗanda suka kama shi su sake shi." Mama ta ce. "Al'amarin ba ƙarami ba ne Neehal, ke dai ki tay masa addu'a kin ji." Neehal ta d'aga mata kai. Mama ta ce. "To share hawayen mu je ki ci abinci, ai ba zai yiyu ki zauna da yunwa ba." Bayan Azhar sai ga Mommy'n Hameedah fakal_fakal ta zo gidan, duk zaman da Mama ta yi a asibiti bata zo ba sai yau, yauma dan ta ji labarin abun da ya faru da Daddy ne a wajen Kawunsu k'anin mahaifinsu. Ta zo tay ta ƴan koke_kokenta akan abun da ya samu Daddy tare da borin kunyar abun da suka yiwa Neehal na mutuwa da samarinta suke yi. Daga Mama har Neehal babu wanda ya kula ta, sai da ta gaji dan kanta ta yi shiru. Da yamma Ahmad ya zo gidan. Lokacin Neehal bacci ma take Mama ta tashe ta. Tunda ta sakko ya ƙura mata ido ganin yanda ta rame ta ƙara haske, idanunta duk sun jeme alamun suna shan kuka. Ta zauna a ƙasa nesa da shi a hankali ta ce. "Ina yini?" Ya ce. "Lafiya k'alau Princess ya jiki? Ashe Mama ma bata da lafiya?" Ta ce. "Da sauqi, ita ma Maman ta ji sauƙi Alhamdulillah." Ya ce. "Masha Allah, Allah ya ƙara afuwa, wallahi ban sani ba ai da tuni na zo. Su Ummi suna muku ya jiki." Ta ce. "Amin, ba komai, muna amsawa, ina Yarana?" Ya ce. "Yaranki suna nan k'alau, kullum sai rigimar zasu gurin Aunty suke yi." Ta yi murmushi kawai. Ya gyara zama sosai cikin kulawa ya ce. "Princess bacin rashin lafiya akwai wani abu da yake damun ki, dan Allah ba dan ni ba ki rage saka samuwa a cikin ranki, ki miƙawa Allah dukkan alamuranki shi zai shige miki gaba, amma damuwa bata haifar da komai sai matsala, Please Princess ki mun wannan alfamar." Gyaɗa masa kai Neehal ta yi cikin gamsuwa tare da yi masa godiya. Ya ɗan jima a gidan suna hira, anan yake sanar mata next week za kai kayan lefensa, tay masa fatan Alkhairi tare da fatan zaman lafiya a rayuwar auransu. Bayan Magriba su Abba suka gana da Kamal abokin Ameen, suka faɗa masa buƙatarsu da labarin da Daddy ya ba su na shigar sa cikin ƙungiyar. Ya jinjina abun sosai ya kuma yi musu alƙawarin zai yi iya yinsa na ganin hakan ya yiyu duk da hakan da matuƙar wahala, dan case ɗin ya bar hannunsu yana gun manyansu. Daɗin abun da ba'a fito da zancen ba ga al'ummar gari ba, amma dai ya ce su dage da addu'a. Da daddare bayan isha'i Neehal tana kwance a falon ƙasa suna chatting da Haneefah Ameen ya shigo falon, ko sallamarsa bata ji ba sai k'amshin turarensa. Saurin kifa wayar ta yi a ƙirjinta tare da lumshe idonta kamar mai bacci, dan haushin shi take ji akan kama Daddy da ya saka a yi, a ganin ta ya kamata ya yi bincike kafin ya yi saurin zartar da hukunci. Shi kuwa tsayawa ya yi yana kallon ta, ta turo baki domin tana jin idanunsa na yawo a jikinta, tsawon three minutes yana kallon ta sannan ya wuce sama. Ta buɗe ido jin takun sa akan steps tana kallon bayansa. Tana ganin ya haye ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta shige ɗakin su Dije dan kar ya fito su ƙara haɗuwa. Washegari da safe ta je school ta dubo result ɗinsu da aka kafe musu tun week ɗin da ya wuce. Alhamdulillah kamar kodayaushe ya yi kyau successfully. Sai a lokacin ta ji haushin rashin apply ɗin N.Y.S.C da bata yi ba, a lokacin classmates ɗinta suna ta yi ita kuma ta ƙi yi saboda auranta da Sadeek, dan ba zai yiyu daga yin aure ta fara da bautar ƙasa ba. Shine Mama ta ce ta bari sai next year ta yi. A cikin week ɗin nan ta fara bucking karɓar result ɗinta. Sati biyu da sallamo Mama bayan cuku_cuku da shan gwabarmaya su Abba suka samu aka fito da Daddy, dan ma Daddy'n na manya mutane ne a ƙasar shi yasa abun ya ɗan zo musu da sauƙi, amma duk da haka sun sha wahala ba kaɗan ba. Ana i gobe ranar ne kuma jami'an tsaro suka yi nasarar k'one gidan tsafin ƙungiya bisa jagoranci Daddy. Bisa Ikon Allah sai abun da ya zo da tsautsayi ashe duka ƴan ƙungiyar suna cikin gidan suna meeting akan yanda za su yi Daddy ya zo hannunsu a wannan lokacin, tunda Sarauniya ta hana a kashe shi, su kuma jami'an tsaro basu san suna cikin gidan ba, gidan kawai suka zo da niyyar k'onewa aka haɗa da su. Sai da wutar ta mutu sannan aka dinga zak'ulu k'onannun gawarwakinsu. Jami'an tsaro ba su so haka ba, sun so su kama su a hannu. Amma al'ummar gari da labarin ya bazu kowa cewa yake yi gwara haka, dan halin ƙasar nan tsaf za'a kama su a tsare kuma a ƙi yi musu hukuncin komai a yi ta jan abun har a manta da maganar, musamman da ya kasance da wasu daga cikin manyan ƙasa a cikin ƙungiyar. Ranar ƙasar nan da kewaye rud'ewa aka yi da zancen kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Daddy ya yi kuka sosai tare da ƙara godewa Allah da ya bar shi da imaninsa, shigarsa cikin ƙungiyar nan bai ruɗe shi yasa ya manta da Ubangiji ba, ya kuma gode masa akan fitar da shi da ya yi, domin yasan wannan ikonsa ne kawai da rahamarsa yasa ya cece shi. Ranar ji ya yi tamkar an sauke masa wani abu mai nauyi a cikin zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa, ya ji jikinsa da kansa yay masa wasai kamar wanda ya tashi daga doguwar cuta, nutsuwarsa ta dawo cikin jikinsa. Ya ƙudure a ransa yanzu bautar Allah da istigfari kawai zai duk'ufa yi akan abubuwan da ya aikata, duk da bayin kansa ba ne amma ba zai dogara da hakan ya ƙi tunatarwa Allah ba. Bayan ya fito daga wanka ya shirya ya ci lafiyayyen abincin da Mama tay masa da sassayan lemo wanda rabon da ya ci ya manta saboda rashin kwanciyar hankali. Gashi duk ya rame ya yi duhu sakamakon tsaren shin da aka yi. Su Abba sun zo ana ta ƙara jajanta abun tare da murnar kub'utar da shi da Allah ya yi, domin sun san ba iyawarsu da dabararsu ba ce Ubangiji ne ya dubi zuciyar Daddy ya tseratar da shi bai mutu yana aikata wannan mummunan saɓon ba. Abba ya dubi Daddy ya ce. "Toh Alhamdulillah, Masha Allah, komai ya yi farko yana da ƙarshe, Muhammad wannan ita ce taka jarrabawar kai kuma, fatanmu Allah kar ya kuma maimaita mana irin wannan musifa ga zuri'armu da ma dukkan Musulmi baki ɗaya, wannan kuma ya isa ya zama izna ga ƴan baya akan mu'amala da abokai wanda bana gari ba ne. Dan shi aboki kullum burinshi ya ɗora ka akan hanyar da yake, musamman in bata ta gari ba ce." Daddy ya ce. "Gaskiya ne, ai na yi dana sanin sanin Kabir Ginyau a rayuwata, shi yasa Fateemah tun farko kamar ta sani ta dinga ƙoƙarin raba ni da shi, Allah ya yi dai wannan abun sai ya faru. Amma kuma sanadin haka gashi an yi nasarar kawar da mugun iri daga doran duniya, an rage masu saɓon Allah." Abba ya ce. "Allah ya kyauta, ya cigaba da tonawa masu irin wannan munanan d'abi'un asiri." Suka amsa da Amin. Dai-dai lokacin Ameen ya shigo falon. Daddy ya tashi da sauri ya tarye shi tare da rungume shi yana murmushi ya ce. "Da fatan yanzu zuciyar gwarzon ɗana ta yi fari da mahaifinsa akan baƙin da ta yi a da?" Ameen ya yi murmushi cikin wasa ya ce. "Kamar da saura dai Dad." Daddy ya marairaice fuska, gaba-d'aya Falon suka saka dariya. Neehal kam ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murnar Allah ya fito mata da Dad ɗinta lafiya. Sai Hamdala ga Ubangiji take. Alhamdulillah rayuwar gidan Mama ta koma kamar da ita da Daddy wanda a da ta fitar da ran samun hakan. Suna fatan kuma matsala ta ƙare musu haka daga su har Neehal. Hankalin ƴan'uwa ya kwanta akan problem ɗin Neehal tunda an gano bakin zaren har ma an yi maganin abun, yanzu sai fatan Allah ya kawo miji na gari ta yi auranta. Bayan sati biyu wanda ya kama farkon watan maulud aka yi bikin Ahmad wanda har yanzu bai san an fasa Auran Neehal da Sadik ba, dan Neehal ce masa ta yi d'aga bikin aka yi. Neehal ta je ta yi kwana uku da ita aka sha biki aka rak'ashe. Ƴan'uwan Ahmad sun nuna mata k'auna, kowa ya zo Ummi ta nuna masa ita ta ce ga Aunty'n su Afrah wadda ta tsince su ta riƙe su. Ranar D'aurin Aure da Mama da Daddy suka je ta biyo su suka dawo gida tare. A daren ranar ta ci kukan da bata san dalilinsa ba, ta ji dai kawai tana jin ba daɗi akan Auran da Ahmad ya yi, amma ta daure bata bari kowa ya fuskanci halin da take ciki ba. Ta koma bakin aikinta wanda aka ƙara mata girma bayan karɓar result ɗinta da ta yi. Ameen bai yi magana ba akan yana son Neehal ko wani abu makamancin haka, ko nuna alamar hakan ma bai yi ba. Mama kuma ta zuba masa ido ta ga iya gudun ruwansa da ƙarshen muskilancinsa. Da Daddy yay mata zancen ta ce masa kar ya kuma balle Ameen ɗin ya ji, sai ya zo da kansa ya ce yana son abun, tunda bai isa tay masa tallar ƴarta kota ba shi ita a bagas ba. Daddy ya yi dariya kawai. Mama ta dage da yiwa Neehal addu'ar samun miji na gari tare da neman zaɓin Allah mafi Alkhairi a gare ta. Ita ma ta ce mata ta dage da yin addu'ar hakan...........✍️ _*Ga Barka da Sallah nan har 3 pages, sai dai ni ban ji nawa ba har yanzu.😒😥*_ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *7️⃣4️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ .........Yau ta kama ranar Asabar, da yamma Mama da Daddy suna zaune a falon ƙasa na part ɗin Mama suna hira door beil ta yi ƙara. Neehal bata nan ta je gidan Haneefah tun Azhar. Daddy ya tashi ya je buɗe ƙofar. Kawu Musa ya gani, da fara'a ya tarb'e shi tare da yi masa iso zuwa cikin falon. Ya shigo ya zauna a kujerar dake fuskantar wadda Mama take, Daddy kuma ya koma ya zauna a gefenta. Cikin girmamawa da muntuntuwa Kawu Musa suka gaisa da Mama. Zulai ta shigo falon ta kawo masa drinks a cikin plate tare da gaishe shi. Bayan ya ɗan kurb'i juice ɗin ya dubi Daddy ya ce. "Na ji daɗi dana same ka a gida, dan har na yi tunanin baka nan sai Hajiya kawai." Daddy ya ce. "Ai yanzu yawanci da yamma ina gida, da rana ne nake ɗan fita idan ta kama." Kawu Musa ya ce. "Allah sarki, dama wata magana ce mai muhimmanci ke tafe da ni." Mama ta bayar da duka hankalinta a kansa, Daddy ya ce. "Toh muna sauraren ka Malam Musa." Malam Musa ya gyara zama ya ce. "Jiya da yamma Ameen ya zo ya same ni har gida mun gaisa, to na zata zuwan nasa kamar na kodayaushe ne da yake zuwa lokaci zuwa lokaci muna gaisawa, sai dai bayan mun gama gaisawar na fuskanci akwai magana a bakinsa sai ce masa, Aminullah kamar akwai magana a bakinka, meke tafe da kai ne? Sai ya sunkuyar da kai ya faɗa mun abun da ke ransa, wato yana son Auran NEEHAL. Shine na ce to bazan yi ƙasa a gwiwa ba yau na taho ƙafa_ƙafa domin sanar da ku wannan abun farincikin, tunda ya ce mun bai sanar muku ba." Ya ƙarashe zancen cikin murmushin farinciki wanda ke nuni da yana jin daɗin al'amarin sosai. Mama ta kalli Daddy wanda shi ma yake murmushin sannan ta jinjina kai ta mayar da kallonta ga Kawu Musa cikin mamaki ta ce. "Lallai na gaishe da Ameen na jinjinawa halinsa, wato dan ya san idan ya zo ya same ni bazan amince ba ko kuma Dad ɗinsa shi yasa ya je ya same ka, saboda bashi da kunya ba zai faɗa da bakinsa ba sai dai ya turo ka, to bazan amince ba duk da haka." Kawu Musa ya yi ƴar dariya sannan ya ce. "To ai wannan shine ƙa'ida, abun da ya yi shine dai-dai, idan kana son yarinya ka je ka samu magabatanta ba wai ka je kai ta hure mata kunne kana cika ta da surutun kawai ba." Daddy ya ce. "Faɗa mata dai, ita tafi son ya zo su yi ta ja masa aji ana ƴank'wana shi." Kawu Musa yana dariya ya ce. "Ai ɗan nawa ba irin waɗannan mazan da ake yiwa haka ba ne." Ganin sun mayar da abun wasa cikin seriously Mama ta ce. "Koma yaya ɗan naku yake dole ya ajiye duk wani ji da kai ya zo ya nemi yarda da amincewar yarinya, domin bazan yi mata Aure ba tare dana tabbatar tana so ko bata so ba." Kawu Musa ya yi murmushi ya ce. "Haba Hajiya, abu na gida abu tuwona maina ai bama buƙatar wani jan abubuwa, yarinyar nan tunda Ubangiji ya kawo mata ƙarshen matsalarta burinmu yanzu kawai mu gan ta a ɗakin mijinta, hankalinmu sai ya fi kwanciya." Daddy ya ce. "Wannan gaskiya ne Malam Musa." Mama ta ce. "Nima ban ƙi ta taku ba, hasalima abun da na kasa da addu'a a gaba kenan Allah ya kawo mata miji na gari ta yi auranta. To amma dan Ameen ya ce yana son ta baza mu amince masa ba ba tare da mun ji ra'ayin yarinya ba, idan bata so duk sonmu da abun dole mu haqura." Kawu Musa ya ce. "Wannan ai duk ba wata matsala ba ce Hajiya, yaron nan kowa ya san halinsa ba shi da wani aibu, kowanne iyaye zasu so ƴarsu ta yi dacen miji da kamar Ameen yaron kirki. Ni dai dan Allah ina nema masa wannan alfarmar a gurinku, domin a ganina koda bata son shi idan aka yi auran zata so shi, za su fuskanci juna, bare ma Insha Allahu na san baza ta ƙi ba. Mu dai kawai mu bi su da addu'ar Allah yasawa abun albarka ya ba su zaman lafiya." Daddy ya ce. "Amin Amin, mun gode sosai Malam Musa, Allah ya bar zumunci." Ya ce. "Amin, amma mune da godiya akodayaushe Alhaji, Allah ya raya zuri'a ya ƙara buɗi." Mama ta sauke numfashi ta ce. "Amin, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Malam Musa ya ce. "Amin, shine kawai dama, ina Neehal ɗin ne ban ga gilmawarta ba ko tana gurin aiki?" Mama ta ce. "Ta je gidan ƙawarta ne, yau ai Asabar bata da aiki." Malam Musa ya ce. "To Allah ya taimaka, ni zan wuce sai na kuma dawowa, duk abun da ake ciki sai ku sanar mun a waya." Mama ta ce. "To ka gaida gida da mutanen gidan, mun gode sosai fa, Allah ya bar zumunci." Ya ce "Gida zai ji." Tare da miƙewa, Daddy ya tashi ya bi bayansa dan raka shi. Bayan ya dawo Mama ta ce masa. "Ni fa Gen. bana son mu tursasa Neehal akan Auran Ameen, kuma ka san indai muka faɗa mata baza taɓa ƙi ba, ni kuma bazan so hakan ba gaskiya." Daddy ya yi murmushi ya ce. "Bana jin zata ƙi Ameen Fateemah, a yanda Neehal abubuwa suka faru a baya akan aurarrakinta da Allah bai nufa an yi ba tana buƙatar ace ta samu miji na gari wanda baza ta yi kuka da shi ba ko bayan ba ma raye, ke kika haifi Ameen kin fi kowa sanin halinsa, Ameen ba shi da wata matsala da zata saka a hana shi Aure." Mama ta ce. "Hmmm, in aura masa ƴa ya cinye mun ita da masifa da faɗa." Daddy ya yi murmushi ya ce. "Wannan kuma aiba a ƙasa ya ɗauka ba gurinki ya gado, kuma tunda yana k'aunarta ai bazai mata ba. Kin ga Fateemah kamar yadda Malam Musa ya ce mu bi al'amarin nan kawai da addu'a, idan Alkhairi ne Allah ya tabbatar mana, Insha Allahu watarana sai mun yi alfahari da farincikin auransu." Mama ta ce. "Allah yasa." Sai kuma ta shiga mitar Ameen dan ya san baza ta iya cewa Malam Musa a'a ba shine ya turo musu shi, zai zo ya same ta ne har inda take." Daddy dai dariya kawai yake yi mata, zuciyarsa wasai, domin babban burinsa a yanzu Ameen ya auri Neehal, domin ya san bazai taɓa wulaqanta ta ba, ya yarda da ɗansa da irin tarbiyyar da yay masa. Ita kuma Mama anata ɓangaren tana son abun domin idan ya kasance sai ta fi kowa farinciki, amma gani take kamar tursasa Neehal zasu yi, ita kuma baza ta so hakan ba. Sai bayan Magriba Neehal ta dawo gida. Direct ɗakin Mama ta wuce, ta faɗa jikinta cikin shagwab'arta ta ce. "Wash Mama na gaji sosai." Mama ta ce. "Wani aikin kika yi ne?" Ta ce. "Driving mana." Mama ta ce. "Daga gidan Haneefah zuwa nan shine zai saka ki gaji saboda lalacinki." Ta turo baki bata ce komai ba. Mama ta ce. "Ki je ki ci abinci ki huta bayan isha'i Dad yana son ganinki." Ta ɗan waro Ido ta ce. "Lafiya Mama?" Dan haka kawai ta ji gabanta ya faɗi. Mama ta ce. "Ba wani abu ba ne tambayar ki kawai zai yi." Ta yi shiru a ranta tana kissima abubuwa da dama, ko kaɗan maganar aure bata zo cikin zuciyarta ba a matsayin abun da Daddy zai yi mata magana akai ba. Ta bar jikin Mama ta tashi ta ɗauki jakarta jikinta duk a sanyaye, Mama ta bi ta da kallo har ta fice. Kayan jikinta ta rage sannan ta shiga toilet ta watsa ruwa ta fito. Ta zira doguwar riga sannan ta ɗauko laptop ɗinta ta zauna ta shiga lallatsawa. Har aka yi sallar isha'i bata tashi ba, da yake tana fashin Sallah ne. Sai wajen tara saura ta kashe system ɗin ta tashi, ta san yanzu Daddy'n ya dawo. Ta zira hijabi ta fice daga ɗakin ta nufi part ɗin Daddy. A dinning area ta same su suna dinner. Da fara'a Daddy ya ce. "Daughter sai yanzu? Na ɗauka ko bacci ya ɗauke ki ma." Ta ce. "A'a Daddy, aiki na ɗan rage." Dad ya ce. "Toh Masha Allah, Allah ya taimaka ya yi albarka Daughter." Cikin jin daɗin addu'arsa a gare ta da baya gajiya da yi mata a kodayaushe ta ce. "Amin Daddyna." Mama ta dube ta, ta ce. "Ki zauna ki zuba abinci ki ci." Bata yi musu ba ta ja kujerar kusa da Mama ta zauna ta zuba abincin ta yi Bismillah ta fara ci cikin nutsuwa. Bayan sun gama cin abincin Neehal ta tattara kayan da suka bata ta wanke a kitchen ɗin part ɗin Daddy'n. Sannan ta koma Parlour'n sa ta zauna a ƙasan kujerar da yake kai. Cikin girmamawa ta ce. "Daddy gani, Mama ta ce kana son magana da ni." Daddy ya gyaɗa kai tare da duban ta cikin sanyin murya ya ce. "Ina son in tambaye ki ne Daughter kuma dan Allah ki faɗa mun gaskiya." Gabanta na fad'uwa ta ce. "Insha Allahu Daddy, indai na sani zan sanar maka." Daddy ya ce. "Yawwa d'iyar kirki, tambayar da zan miki akwai wanda kike so ne yanzu? Ma'ana akwai wanda kuke mu'amala ta soyayya wanda kike da burin aurar shi?" Neehal ta yi ƙasa da kanta cikin jin kunya, tun bayan rabuwar su da Sadik bata ƙara saurarar wani ɗa namiji da sunan soyayya ba, mutum ɗaya ne ma ya nuna yana son ta, a gurin aikinsu yake kuma dama shi ya daɗe yana nuna yana son nata, ita ce kawai bai yi mata ba. Daddy ya ce. "Kin yi shiru Daughter." Ta sauke numfashi cikin ladabi ta ce. "Babu kowa Daddy." Daddy ya ce. "Kin tabbata?" Ta gyaɗa masa kai. Cikin murmushi ya ce. "Toh Alhamdulillah, dama Yayanki Al'ameen ne ya zo mana da maganar yana son auranki, mun yi farinciki da jin daɗin hakan sosai, amincewarki kawai muke jira mu fara shirye-shiryen biki." Ai wata irin muguwar fad'uwar gaba ce ta riski Neehal, saboda tsabar firgicin da zuciyarta ta shiga fitar jininta har ƙara gudu ya yi. Tun daga sunan Yayanki Al'ameen yana son auranki da Daddy ya faɗa bata ƙara fuskantar sauran abun da yake cewa ba. 'Yaya fa, Yayana fa? Impossible, gaskiya ban ji dai-dai ba, ba shi Daddy yake nufi ba.' Ta faɗi haka a ranta. Mama dake nazartar yanayinta ganin yanda ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa sai ta girgiza kai, dama ta san za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Daddy ya cigaba da magana. "Idan ba kya so Daughter ki faɗa babu mai miki dole, sai mu yi fatan Allah yasa haka shi yafi Alkhairi, ya kawo miki wani na gari." Ta d'ago kanta a hankali cikin ƙoƙarin son mayar da k'wallar data tarar mata a ido cikin rawar murya ta ce. "Daddy ban gane wanne Al'ameen ɗin kake nufi ba?" Dad ya ce. "Ameen dai na gidan nan." Sai ta ƙurawa fuskar Daddy ido kamar shine Ameen ɗin, ta san mafarki take yi babu ta yadda za'a yi a ce ta auri Yayanta, ta shiga addu'a da fatan Allah ya farkar da ita daga wannan rudad'd'en mafarkin da take. Muryar Daddy data ji yana faɗin. "Daughter!" Shi ya dawo da ita cikin nutsuwarta, ta tabbatar gaske ne ba mafarkin ba. Ta sauke numfashi sannan ta ce. "Na'am Daddy." Ya ce. "Karki saka kanki a cikin damuwa, it's your life no body will force you ki yi abun da bakya so kin ji. Yanzu ki tashi ki je ki nutsu ki yi tunanin abun da kike ganin ba zaki takura ba a rayuwarki, abun da yafi miki dai-dai zuciyarki tafi samun nutsuwa a kansa, da safe sai ki faɗawa Mamanki abun da kika yanke." Kamar wadda k'wai ya fashewa a ciki haka ta miƙe da ƙyar ko sallama bata yi musu ba ta fice daga falon. Mama da bata ce k'ala ba ta bita da kallo. Bayan ta fice ta sauke numfashi ta ce. "Dama na san haka zata faru Gen. Jibi yanda yarinyar nan ta firgice daka faɗa mata zancen nan, na san yanzu zuwa zata yi ta tayar da hankalinta tay ta tunani." Daddy ya ce. "Nima na san dole zata kaɗu da jin wannan batun, amma wannan ba abun tayar da hankali ba ne Fateemah, I assure you sai kin fi kowa murna da farinciki da Auran Neehal da Ameen bayan Auran Insha Allah. A kullum burinki da addu'arki Allah ya bawa yarinyar miji na gari wanda zai riƙe ta da amana ya samar mata da farinciki a rayuwarta, Ameen rainonki ne bani da haufi a kansa da waɗannan abubuwan kuma kema kin sani." Mama ta ce. "Duk na san wannan, kuma ni bacin Neehal ma ina duba Matarsa Hafsat, dududu yaushe aka yi auransu har da zai ƙara Aure, yarinyar nan baza ta ji daɗi ba." Daddy ya yi murmushi ya ce. "Wato kina taya ƴarki kishi kenan?" Mama ta ce. "Ba zancen kishi ba ne gaskiya ce." Daddy ya ce. "Wannan ai duk ba wata matsala ba ce, tunda Ubangiji ne ya ce a auri mata har huɗu idan mutum yana da halin yi zai kuma yi adalci a tsakaninsu, addu'a kawai zamu yi Allah ya haɗa kansu, shi kuma Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakaninsu." Mama ta ce. "Haka ne, Amin, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Da jan ƙafa Neehal ta ƙarasa part ɗin Mama ta shige ɗakinta ta faɗa kan gado, da ƙyar ta iya zare hijabin jikinta saboda uban gumin da take haɗawa. Yaya fa, mijin Hafsah da bata k'aunarta shi su Daddy suke son aura mata, dan ita bata yarda Ameen ne ya ce yana son ta ba tafi tunanin kawai Daddy ya faɗa ne. Ita fa a tsarin rayuwarta sam bata son Auren mai mata, mai matar ma kuma Yayanta mijin Hafsat. Yaya masifaffe ta dinga yi masa magana idan sun yi Auran yana share ta. Ta turo baki kamar yana ganin ta tana hango yanda yake tsare gidan nan nasa. A fili ta ce. "Impossible, tunda Daddy ya ce sai na amince to zan ce masa ban amince ba kawai a bar zancen." Da wannan kalaman ta sauke ajiyar zuciya ta ji zuciyarta ta samu nutsuwa har ta samu k'warin gwiwar miƙewa ta rage kayan jikinta ta kashe light ɗin ɗakin ta kwanta. Sai dai me? Tana kwanciya wata zuciyar ta ce mata. 'Kina da hankali kuwa Neehal? Ɗan Mama da Daddy na cikinsu zaki iya kallon idonsu ki ce musu ba kya son shi baza ki iya auran shi ba? Mama da Daddy fa? Wanda ko wani suka kawo miki ba ɗansu ba bai kamata ki bijire musu ba.' Sai ta tashi zaune cikin sauri ta faɗin Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un. Ita dai gaskiya baza ta iya Auran Ameen ba, ta yaya zata iya kallonsa a matsayin mijinta? Ya zaman Auran nasu zai kasance? Sai ta fara hawaye cikin rashin mafita. Idan har ta bijirewa Daddy ta san bata yiwa kanta adalci ba, duniya ma sai ta zage ta, ita karan kanta ma zata ga baƙin kanta. To amma ita da wani ma suka kawo mata ba Ameen ba da sai ta amince, amma ita dai baza ta iya Auran Ameen ba, Yayanta ne fa. Ta yi 1 hour tana tunanin mafita amma ta kasa samowa, gashi Daddy ya ce da safe Mama zata tambaye ta abun da ta yanke a game da maganar. Wayarta ta lalubo bisa shawarar zuciyarta da ta bata na ta nemi shawarar wani, time ta fara dubawa ta ga sha ɗaya saura, to wa ma zata kira? Tambayar da yiwa kanta kenan. Dama Mama ce abokiyar shawararta, idan kuma ba ita ba sai Haneefah, Haneefah kuma zuwa yanzu ta san ta yi bacci, ko ma bata yi bacci ba ya yi dare ta kira ta a yanzu. Sauran waɗanda zata iya shawara da su kuma a duniya wanda ta san za su faɗa mata gaskiya da abun da zata yi na dai-dai sai Aunty Sadiya da Aunty A'isha. Su kuma Mama ƴar'uwarsu ce, ta yaya zata yi wannan zancen da su? Ta yi tunanin kaf danginta babu wanda zata iya kira dan ya bata shawara, wa ma ta shak'u da shi da zai bata time ɗinsa su yi magana? "Uncle Usman." Zuciyarta ta bata amsa, tabbas shi kadai ne zai bata shawara ya faɗa mata abun da zata yi na dai-dai. Ta latsa wayar ta lalubo Numbern sa ta yi dialing, duk da wata zuciyar na ce mata kar ta kira shi, ƙila yanzun haka yana tare da iyalinsa, amma duk da haka bata fasa kiran nasa ba because she is in needing solution. Bai ɗauki kiran ba har wayar ta katse. Dafe kanta ta yi hawaye na cigaba da zuba daga idanunta, fuskar Ameen kawai take hangowa a cukule, tana son ta hango shi as her husband amma ta kasa, ko dan ta yiwa Mama da Daddy biyayya sau ɗaya tak a rayuwarta akan abun da suke so wanda ita bata so, idan ta tuna tsantsar farincikin data gani a fuskar Daddy a d'azu da yake mata maganar sai ta yi tunanin ya zai ji idan ta ƙi amincewa, duk farincikin nan zai daina shi ne fa. To amma ita yanda zaman nasu zai kasance da Ameen a matsayin MATA da MIJI kawai take tunani, kuma matsalarta ba iya Ameen ba ne kaɗai har da Hafsat..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *7️⃣6️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ..........Idanunta suka sauka akan kyakkyawar kamilalliyar fuskarsa mai cike da kwarjini, ta yi ƙoƙarin ɗauke kallon ta daga fuskarsa amma ta kasa. Wani irin kallo yake mata wanda yasa ta ji wani irin abu yana yawo a cikin jinin jikinta, kamar yadda zuciyarta take bugawa da ƙarfi. Kallon sa take yi yau as husband to be not as brother before, tunanin hakan yasa ta ji gabanta ya yi wani irin mugun faɗuwa, ya sakar mata wani murmushi wanda zata iya cewa ba'a taɓa murmushin da ya kayatar da ita kamar shi ba. Ta lumshe idonta da sauri wani baƙon abu yana cika zuciyarta a kansa, like kunya ko tsoro. Ta yi baya da sauri tare da buɗe ido tana ɗan turo baki gaba, zuciyarta ta bata shawarar ta zura da gudu ta koma ɗakinta, har sai ya bar gidan sai ta fito. Ta juya cikin sauri amma ko ɗaga ƙafarta bata yi ba ya kamo hannunta, ta juyo kamar zata yi kuka dan abun da take ji a game shi ƙara yawa yake yana neman hautsina mata zuciya, kuma bata taɓa jin hakan a gare shi ba a rayuwarta sai yau. Ta saci kallon fuskarsa ta ga ya haɗe rai kamar ba shi ya yi murmushi yanzu ba, ya tsatstsare ta da kyawawan idanuwansa wanda suke ƙara mata yawan abun da take ji a kansa a cikin zuciyarta. Murya ƙasa_ƙasa ya ce. "Can't you great me?" Ta shiga girgiza kai tsoronsa na ƙaruwa a ranta, cikin rawar murya ta ce. "Ina yini?" Bai ce komai sai kallon fuskarta da yake yi kamar mai neman wani important thing a fuskar. Ta yi ƙasa da kanta a ranta tana addu'ar Allah yasa Mama ta fito ko ta samu ya bar ta. Tana ji ya saki ajiyar zuciya a hankali sannan ya sakar mata hannu without saying anything ya nufi ɗakin Mama. Ta bi bayan shi da kallo tare da murgud'a baki, ganin kamar zai jiyo ta buɗe ƙofa ta fice da gudu. Ya juyo jin ƙarar buga ƙofa, ya girgiza kai kawai tare da yin murmushi sannan ya shige ɗakin Mama. Mama tana shirya gogaggun kayanta a wardrobe ya shigo ɗakin da sallama. Ta amsa masa ba tare da juyo ta kalle shi ba. Ya zauna akan bedside drower tare da gaishe ta. Ta amsa masa tana rufe wardrobe ɗin sannan ta ƙaraso ta zauna a bakin gado. Tana duban sa cike da kulawa ta ce. "Ya su Hafsah?" Ya ce. "Lafiya k'alau." Mama ta ce. "Dafatan dai lafiya, tun ranar Friday rabon ka da gidan nan." Ya ce. "Lafiya k'alau Mum, weekend ɗin nan ban fita ba a gida nake wuni." Mama ta ce. "Okay." Sun taɓa hira kaɗan wadda majority akan aiki ne sannan ya yi mata sallama ya tafi. Bata yi masa zancen Neehal ba shi ma bai yi mata ba. Neehal kuwa tunda ta sauka ƙasa tana sauke numfashi ta shige ɗakin su Dije, ko abincin ma bata je ta ɗebo ba saboda tana tsoron kar Ameen ya sakko su ƙara haɗuwa, sai da ta ga fitarsa ta window'n ɗakin su Dije sannan ta fito. Da daddare Mama ta yi mata zancen Ameen akan jin ra'ayinta, dan Kawu Musa yau wayarsa biyu akan jin inda maganar ta kwana. Shiru ta yi ƙirjinta na luguden bugu. Mama dake kallon ta cikin nazari ta ce. "Neehal, ki kalle ni as your Mother ba mahaifiyar Ameen, ki faɗa mun abun da yake ranki kamar yadda kike faɗa mun a kodayaushe kin ji ƴar albarkata." Ta gyaɗa kai a hankali sannan ta ce. "Na amince." Mama ta ce. "Kin amince da me?" Ta kwantar da kanta a ƙafaɗar Mama ta ce. "Kin sani fa." Mama tana murmushi ta shiga shafa bayanta ta ce. "Da gaske Daughter maganar da kike faɗa mun tun daga zuciyarki take, bana son ki yi abun da ba kya so, in ba kya so you are free to say, no body will force you." Ta ƙara shigewa jikin Mama ta rufe fuskarta da hannunta ta ce. "Allah da gaske nake Mama." Mama ta faɗaɗa fara'a akan kyakkyawar fuskarta cikin tsokana ta ce. "Kina son Ameen ɗin kenan?" Da sauri ta cusa fuskarta ta ɓoye a jikin Mama tare da turo baki gaba. Mama ta shafa kanta cikin tsananin farincikin data manta rabon da ta yi kamarsa ta ce. "Masha Allah Neehal, Allah ya yi miki albarka ya inganta rayuwarki, ya baki ƴaƴa masu ladabi da biyayya kamar ki, Allah ya baku zaman lafiya yasa haka shi ya fi Alkhairi." Ta amsa da Amin a cikin zuciyarta. Ba ta kallon fuskar Mama amma a muryarta kaɗai tana jin irin farincikin da take ciki, kuma duk saboda ta amince da Auran Ameen ne, ina ga Daddy? Shi wanne irin farinciki zai ji idan ya ji wannan batun? Su saunawa suka saka ta a cikin farinciki a rayuwarsu? Babu adadi. Kenan data ƙi amincewa haka zasu ji babu daɗi a cikin ransu? Gwara da Allah yasa bata yi wannan gatobarar ba. Ta san bata son Auren Ameen ko kaɗan a cikin ranta, amma ta yiwa kanta alƙawari zata danne ta daure ko a fuska baza ta bari a gane ba, zata saka a ranta Allah ya yi Ameen ne mijinta, zata karb'i Auransa hannu bibbiyu idan Ubangiji ya yi hakan ta kasance. Amma tana mamaki da girmama abun a cikin zuciyarta ba kaɗan ba, YAYANTA MIJINTA, ko a mafarki bata taɓa tunanin hakan zata iya faru ba, ita mantawa ma take akwai aure a tsakaninsu da Ameen. As blood brother desame mother desame father take kallon shi. Wasu hawaye da bata san kona mene ba ta ji suna rige_rigen gudu akan kuncinta daga cikin idonta. Ta ƙara rungume Mama tare da fara kuka a hankali. Mama ta shiga bubbuga bayanta tare da faɗin. "Kunan na mene ne?" Ta ja majina bata ce komai ba. Mama ta d'ago da kanta tana kallon yanda take kukan ta ce. "Mene ne wai?" Ta girgiza mata kai kawai. Mama ta ce. "Iskanci ne kenan?" Cikin kukan ta ce. "Bana son na bar ki ne Mama." Mama ta yi murmushi tana jin tausayinta na cika mata zuciya, ta shiga share mata hawayen fuskarta tana faɗin. "Wa ya ce miki zaki bar ni dan kin yi Aure? Duk sanda kike son gani na zaki zo ki ganni ai." Cikin shagwab'a ta ce. "Ke baza ki zo ki dinga gani na ba?" Mama ta yi murmushi ta ce. "Zan zo mana, Amarya tun kafin a yi Aure har an fara zancen zuwa gida." Ta cusa kanta a jikin Mama cikin tsananin jin kunya. Mama ta ƙara rungume ta a jikinta tana jin tsananin farinciki a ranta, tabbas kamar yadda Daddy ya faɗa bata jin akwai wanda zai kai ta farinciki idan wannan al'amarin ya kasance. Bayan Daddy ya dawo Mama ta sanar masa yanda suka yi da Neehal. Farincikin da ya nuna ba zai misaltu ba, ya kira Neehal ta zo part ɗinsa wadda gaba-d'aya yanzu ta ji tana jin kunyarsa, ya dinga saka mata albarka tare da tarin addu'oi, har da tambayarta me take so ya yi mata a rayuwar nan wanda zata ji daɗi? Ta ce masa babu komai ai ita ya gama yi mata komai a rayuwa. Ta kasa tantance tsakanin shi da Mama wa ya fi wani farinciki da amincewarta. Da daddaren Ameen ya kuma dawowa gidan, Neehal tana falon ƙasa tana kallon wani series firlm ɗin India da take matuƙar so, bata ji sallamarsa ba sai k'amshinsa ne ya sanar mata da zuwan sa. Ai kuwa da sauri ta miƙe ta nufi upstairs, ya bi ta da kallo kawai yana sakin wani munafukin murmushi. A balcony suka ci karo da Mama, garin saurin da take har da tuntube ta yi. Mama ta ce. "Subhallahi, ki dinga kallon gabanki mana kina tafiya a hankali, kuma lafiyarki kuwa na gan ki kamar a firgice?" Tana sassauke numfashi ta ce. "Babu komai." Tare da shigewa falo. Mama ta tab'e baki ta sauka ƙasa abinta. Ta tarar Ameen ya zauna har lokacin bai bar murmushin da yake yi ba, ta yi masa wani kallo sannan ta zauna a kujerar dake facing ɗinsa. Suka ƙara gaisawa sannan Mama ta ce masa. "Ya na ga ka dawo?" Ya kama haɓa da hannunsa ɗaya ya ce. "Oh Mum, dan na dawo gidanmu laifi ne?" Mama ta ce. "Baka da gaskiya ne shi yasa na tambaya." Ya waro ido ya ce. "Rashin gaskiya kuma Mum?" Mama ta ce. "Ka fi ni sanin me ka yi ai." Ya yi murmushi ya ce. "I don't know fa." Mama ta ƙara ta tab'e baki ta ce. "Ai baza ka taɓa sani ba, wannan muskilancin naka yana k'ona mun rai, ka turo a sanar mana abu kuma ka san an sanar manan and still you can't say anything about it." Ya shafa kansa yana murmushi sosai ya ce. "Mum, what do you want me to say?" Mama ta ce. "Abun da ka je ka faɗa a zo a faɗa mana." Ya yi shiru still yana murmushi bai ce komai ba. Mama ta shiga mitar abun da yake ranta, harda ce masa alfarma ta yi kawai ta ba shi Neehal amma ba dan halinsa ba, babu yanda zata yi da Kawu Musa ne kawai. Shi dai murmushi kawai yake yi. Daga baya kuma ta koma yi masa faɗa da faɗin. "Ga Neehal nan Ameen, idan Allah ya yi auranku na baka amanarta, ka riƙe ta da amana dan Allah, ka ga yarinyar nan bata da kowa sai Allah, marainiyar Allah ce, idan ka zalunce ta Ubangiji bazai bar ka ba." Ji ya yi jikinsa ya yi sanyi, soyayyar Neehal da k'aunarta gami da tausayinta na ƙara narkar masa da zuciya. Daga nan part ɗin Daddy ya je wanda dama shi ya kira shi yana son ganin sa, shi ma faɗa da nasiha ya yi masa duk akan ya riƙe Neehal da amana ne. Neehal kam bata kuma fitowa ba tunda ta shige ɗaki dan bata san ta fito su haɗu kar ta je bai tafi ba. Wani irin tsoronsa da kunyarsa Ubangiji ya ɗoro mata tun daga lokacin data fara tursasawa zuciyarta karɓar sa a matsayin mijin da zata aura. A daren Daddy bai jira komai ba ya kira Abba da wasu cousins ɗinsa ya sanar musu abun da yake faruwa, ya kuma faɗa musu a cikin week ɗin nan yake son akai kuɗin Auren Neehal gidan kawunta. Mama ta ce masa saurin me yake har haka? Ya ce mata baza ta gane yanda yake d'okin abun ba ne, a yanzu ba shi da wani sauran buri a rayuwarsa bayan ya ga Auran Neehal da Ameen..... Kamar yadda ya faɗa ranar Asabar wanda ya kama kwana biyar da yin maganar da yamma suka kai kuɗin na gani ina so gidan Kawu Musa. Ranar Neehal ji ta yi gaba-d'aya kamar ba ita ba, ita ce yau aka karb'i kuɗin Auranta da Ameen? Sai ta dinga jin abun kamar a mafarki, ta tabbata dai Auransu za'a yi da Ameen, ɓoye kanta ta yi a ɗaki ta ci kuka ta k'oshi. Su Daddy ba su baro gidan Kawu Musa ba sai da aka tsayar da lokacin biki wata uku masu zuwa, a haka ma da ƙyar Kawu Musa ya yarda, ya ce abun tunda duk na gida ne no need a ja lokaci, in san ransa ne bai ƙi a yi bikin a cikin two weeks masu zuwa ba. Da Daddy ya zo yana faɗawa Mama ta ce, ta san wannan duk shirin Ameen ne, shi yake zuwa yana zubawa Kawu Musa sintiri akan maganar bikin. A ranar bayan Magriba Ameen ya zo gidan kamar kullum, sai dai tun daga ranar da Neehal ta zura masa da gudu bai kuma ganin ta ba, dan b'uya take yi a ɗaki, ana yin Magriba zata shige ɗakinta ta kulle dan ta san shine time ɗin zuwansa gidan, bata fitowa har sai ta tabbatar ya tafi. Shi kuwa yana sane da ita da duk b'uyan da take, kuma ya san duk saboda shi ne, ƙyale ta kawai ya yi ya ga iya gudun ruwanta dan ya san akwai ranar ƙin dillanci. A ranar Mama ta ce masa ya sanar da Hafsat maganar bikin, ya amsa mata duk da bai so hakan ba, da ya so sai abun ya matso daf sannan ya sanar mata, amma yaya zai yi tunda Mama ta bayar da umarni dole ya bi. Bayan isha'i ya koma gidansa, ya tarar da Hafsat Hakimce a falon ƙasa ta ci uwar kwalliya ta tarb'arsa..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *7️⃣5️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ .........Ta ja gwauron numfashi ta sauke tana ƙoƙarin komawa ta kwanta wayarta ta fara vibrate alamar shigowar kira. Ta ɗauki wayar ta duba wake kiran nata, ganin Uncle Usman ne ta sauke ajiyar zuciya a hankali tare da picking kiran ta kara a kunnenta. Cikin muryar dake nuni da damuwa tay masa sallama, ya amsa mata. Ta ce. "Uncle an wuni lafiya?" Ya ce. "Lafiya k'alau Neehal, dafatan kina lafiya?" Ta sauke numfashi ta ce. "Lafiya k'alau Uncle." Uncle Usman ya ce. "Masha Allah, naga kiran ki, ina wanka ne kika kira ni, Allah yasa dai lafiya dan na ji muryarki wani iri kuma kira a daren nan." Idonta ya ciko da k'walla, ta daure ta ce. "Dole ce tasa na kira ka yanzu Uncle, da na so na bari sai da safe amma ina buƙatar magana da kai urgently." Uncle Usman ya ce. "To! Allah yasa lafiya dai?" Ta ce. "Lafiya k'alau, kawai shawararka nake nema akan wani al'amari, Allah yasa bazan takura ka ko Aunty ba?" Uncle Usman ya ce. "Haba babu komai Daughter, Aunty'n ki ta yi bacci ma ita." Neehal ta gyara zama ta bawa Uncle Usman labarin duk yanda suka yi da su Daddy, ta kuma faɗa masa ita bata son Auren. Uncle Usman ya sauke numfashi ya ce. "Mene abun damuwa anan Neehal? Ai wannan abun farinciki ne mu a gurinmu ba kaɗan ba, Ameen mutumin kirki ne, iyayensa ma haka kuma kin fi kowa sanin hakan." Ta ce. "Na sani Uncle, amma Yaya fa, ni dai baza iya auransa ba Allah." Uncle Usman ya yi murmushi ya ce. "Mene da Yayan?" Ta turo baki tana hawaye ta ce. "Kai ma ka san halinsa, kuma yana da mata fa." Ta ƙarashe maganar hawaye na zuba daga idonta. Uncle Usman ya yi ƴar dariya sannan ya ce. "Ina ruwanki da matarsa, zamanta daban naki daban." Ta yi shiru bata ce komai ba. Cikin serious ya cigaba da magana. "Neehal, zan faɗa miki gaskiya a matsayina na uba a gare ki, ki cire wani abu mara kyau na Ameen daga cikin zuciyarki, alkhairinsa da na iyayensa a gare ki zaki duba, ki tuna ajiye komai nasa da ya yi ya ɓata lokacinsa da energy ɗinsa dan ganin ya samo miki mafita a rayuwarki, abun da ya yi saboda ke aiki ne na siyar da rai amma duk da haka sai da ya yi duk dan saboda ya ga ya cire ki daga cikin damuwar rayuwar da kike ciki. Alkhairin iyayensa a gare ki kuma ba zai fadu ba saboda tarin yawansu, ki tuna barazana da Daddy ya fuskanta saboda ke, amma duk dan ganin bai ɓata miki rayuwa ko ya bari an ɓata miki ba ya zaɓi duk wata barazana da abun da za'ai masa, kuma duk saboda ke." Cikin tsananin mamaki ta ce. "Uncle a ina ka san wannan labarin?" Uncle Usman ya ce. "Aunty A'isha ce ta kira ni ta sanar mun tun lokacin da abun ya faru, har ma na kira Daddy da Mama na jajanta musu." Ta jinjina kai kawai. Uncle Usman ya ce. "Ki ajiye duk waɗan can abubuwan dana lissafa miki, ki duba Ameen ɗin shi karan kansa, mene ne aibunsa daza ki ƙi shi? Ɗan Adam tara yake bai cika goma ba Neehal, ki yi addu'a kawai Allah ya tabbatar muku da Alkhairi ya kau da fitina a tsakaninku, amma ta yaya ma zaki ce baza ki amince ba, ko a fuska karki bari ki nuna damuwar da za su gane bakya so, ɗansu ne fa Neehal na cikinsu, ko da basu furta ba amma baza su taɓa jin daɗi ba idan kika ƙi ɗansu, muma baza mu ji daɗi ba." Nasiha sosai Uncle Usman yay mata. Ba dan ranta ya so ba ta ce masa ta amince, zata cewa su Maman ta amince. Yay murna sosai ya dinga saka mata albarka. Sai ɗaya suka gama wayar, ta tashi ta shiga toilet ta canza pad ta dawo ta kwanta. Babu bacci ko d'igo a idonta, idan ta tuna gobe fa tana cewa Mama ta amince shikenan kamar yadda Daddy ya ce za'a fara shirye-shiryen bikinsu sai ta ji hawaye sun zob'o mata, shikenan zata zama Matar Yayanta Ameen shi kuma Mijinta? Idan ta tuna ba son ta yake ba sai ta ji hankalinta ya ƙara tashi, ko kuma idan ta tuno Hafsat da dama can ba k'aunarta take ba, ina ga ta aure mata miji? Amma duk da haka dole zata amince kamar yadda Uncle Usman ya ce mata, Mama da Daddy basu cancanci butulci daga gare ta ba. Ta sha kuka sosai kafin bacci ya ɗauke ta ba tare data sani ba. Da safe da ta tashi idanunta jajur duk sun kumbura haka ma fuskarta saboda kukan da ta sha, ta shiga toilet ta yi wanka ta dinga dirzar fuskar saboda ta ware, bayan ta fito ta shirya harda ƴar kwalliyarta ta rambad'a kwalli duk dan kar Mama ta gane ta yi kuka. Ƙarfe takwas da ƴan mintuna ta fito ta sauka ƙasa. Ta tarar da Mama a kitchen tana haɗa breakfast. Ta tsaya a bakin ƙofa ta ce. "Barka da safiya Mama." Mama ta juyo ta ce. "Yawwa, kin tashi lafiya?" Ta ce. "Lafiya k'alau Mama." Mama ta ce. "Masha Allah." Tana bin ta da kallo. Ta kirkiro murmushi ta ce. "Bari in taya ki aikin Mama." Mama bata ce komai ba, ta ƙaraso suka ci-gaba da aikin tare. Dauriya kawai take yi amma ita kaɗai ta san halin da zuciyarta take ciki, gabanta sai faɗuwa yake saboda tunanin kar Mama ta tambaye ta abun da ta yanke akan maganar Auran Ameen. Allah ya taimake ta har suka gama aikin Mama bata ce mata ko ƙala ba. Tare suka yi breakfast da Maman, sai bayan sun gama ta tashi zata tafi Mama ta ce ta koma ta zauna. Ƙirjinta na luguden bugu ta koma ta zauna, dan ta san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi. Mama ta kalle ta na sakanni sannan cikin sanyin murya ta ce. "Kuka kika yi jiya da daddare ko Neehal?" Ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da girgiza mata kai. Mama ta ce. "Hmmm, Neehal bazan taɓa yi miki dole akan abun da ba kya so ba, haka ma Dad ɗinki, ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa, indai ba kya son Auren Ameen babu mai yi miki dole." Ta d'ago da kanta a hankali tana danne kukan da yake ƙoƙarin kufce mata ta ce. "Da gaske fa Mama ban yi kuka ko na damu ba." Mama ta ce. "Any way dai, ni dai abun da zan faɗa miki karki saka damuwa a ranki, i know You very well, kuma karki tursasawa zuciyarki karɓar abun da ba kya so, rayuwarki ce bata wani ba karki cuci kanki, ki yi abun da zuciyarki bata so." Ta yi shiru bata ce komai ba. Mama ta ce. "Yanzu zaki gidan Sadiyan ne? Har ta kira ni a waya tana kin taho, kamar aka ce mata a hanya kika kwana, ita da bata jira." Ta yi murmushi ta ce. "Auntynah kenan, she missed me that is why." Mama ta ce. "Ki je ki gaishe da Daddy sai ki tafi, make sure kin dawo gidan nan before Asr, zamu je shopping kin sani." Ta miƙe ta ce "Insha Allah." Kafin sha ɗaya ta je gidan Aunty Sadiya. Aunty Sadiya ta tarb'e ta cikin farinciki tare da tsokanar ta da wata sabon gani. Bayan sun gama gaggaisawa suna cikin hira Aunty Sadiya ta ce mata. "What going on Neehal naga kamar kina cikin damuwa?" Ta girgiza kai a hankali tana jin damuwar zuciyarta na ƙaruwa ta ce. "Babu komai Aunty." Aunty Sadiya ta ce. "Baki iya ƙarya ba Neehal, shi yasa kina yi ake gano ki, faɗa mun mene ne? Yanayin ki ya nuna cikin damuwa" Ta yi shiru k'walla na cika idanunta. Aunty Sadiya ta yi ɗan murmushi saboda ta san dawar garin, Mama ta kira su ta faɗa musu komai ita da Aunty A'isha tun jiyan. Cikin lallami ta ce. "Kin yi shiru Neehal." Ba tare data d'ago ba ta ce. "Aunty ban san me zan ce miki ba ne." Aunty Sadiya ta ce. "Abun da yake damunki zaki faɗa mun." Ta turo baki ta ce. "Daddy ne ya ce wai Yaya zan aura." Murmushi Aunty Sadiya ta yi ta ce. "Kamar ya? Wanne Yayan?" Ta ce. "Yayana fa, Aunty ki duba abun nan, ta yaya zan iya Auran Yaya?" Ta yi maganar cikin marairaicewa. "Ta yadda kowacce mace take Auran mijinta mana." Cewar Aunty Sadiya tana dariya. Ta fara hawaye ta ce. "Aunty kin san halin Yaya fa, Ni tsoron shi nake, kuma kuma.... Yana da matarshi fa." Aunty Sadiya ta ce. "Rigimammiya, wannan rigimar taki ai sai Ameen ɗin." Bata ce komai ba sai cinno baki data ƙara yi. Aunty Sadiya ta gyara zama tare da dafa ƙafaɗarta, seriously ta ce. "Neehal! Bai kamata Auran Ameen ya dame ki ba ko kuma ya saka ki cikin damuwa ba, kin san Ameen kin san komai nasa fiye da kowacce mace da zai aura a duniya, haka kema ya san komai naki. You know Ameen is a good person, ke zaki faɗi hakan ga wasu ma. To mene abun damuwa dan kin aure shi, mu kanmu sai mun fi jin daɗi da farincikin hakan, hankalinmu sai yafi kwanciya, bamu da fargabar yanda mijinki zai riƙe mana ke ko kuma fargabar wanne irin ƴan'uwan miji zaki haɗu da su. Batun matarsa kuma ba'a kanta zaki zauna ba ita ma ba'a kanki zata zauna ba, hasalima kowaccen ku gidanta daban." Ta ɓata fuska ta ce. "Ai ita yake so, ni ba ya so na." Aunty Sadiya ta danne dariyar dake ƙoƙarin k'wace mata dan ta gano mutuniyar tata har da kishi a lamarin nata ta ce. "Wa ya faɗa miki? Yana son ki mana, in ma ba ya son ki sai ki koya masa son naki, sai ka ce ba rainon Yaya Fateemah ba?" Ta juya ido ta ce. "Ai nima bana son shi." Wannan karon Aunty Sadiya kasa danne dariyarta ta yi saboda yanda Neehal ɗin ta yi maganar. Ta ɗan dara sannan ta ce. "Allah ya shirya ki Neehal." Nasiha ita ma Aunty Sadiya ta yi mata tare da ƙara nuna mata qualities ɗin Ameen, kamar dai yanda Uncle Usman ya faɗa mata jiya, a ƙarshe dai ita ma ta ce ta dage da addu'a kawai tare da neman zaɓin Allah. Wajen ƙarfe uku ta koma gida, ana yin la'asar suka fita shopping ita da Mama, sai daf da Magriba suka dawo. Bayan Magriba ɗaya daga cikin staff ɗin gidan ya zo ya cewa Mama ta yi baƙo. Ta ce masa ya je ya shigo da shi part ɗinta. Baƙon yana zaune a falon ƙasa ta sauko, mamaki gami da fara'a suka bayyana akan fuskarta ganin Alhaji ne Uban gidan Abban Neehal. Cikin murya mai cike da fara'a ta ce. "Alhaji kai ne a gidan namu yau? Sannu da zuwa." Alhaji Ali ya yi murmushi yana riƙe da sandar dake taimaka masa gurin tafiya ya ce. "Ni ne Hajiya, da fatan mun same ku lafiya?" Mama ta zauna akan carpet ta ce. "Lafiya k'alau Alhaji, da fatan an zo lafiya? Ya hanya? Ya Iyali? Ya ƙafa?" Alhaji Ali ya ce. "Alhamdulillah, komai lafiya k'alau, ƙafa gata nan sai godiyar Ubangiji, a satin nan ma muka dawo daga Saudiyya na je ganin likita." Mama ta ce. "Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi, ƙafar tana yin sauki dai ko?" Ya ce. "Alhamdulillah, ana samun cigaba." Mama ta ce. "Haka ake so, wancan satin nake yiwa Neehal maganar ya kamata ta je ta gaishe ka, sai A'isha ta ce mun itama kwanaki ita ma ta yi zancen hakan a zuciyarta, ta tambaya kuma aka ce baka gari. Ashe kun dawo, Alhaji ka zo da kanka maimakon ka yi waya mu mu zo kai da ba lafiyar ƙafa ba." Ya yi murmushi ya ce. "Ai wannan shine lafiyar, zumunci shine lafiyar ƙafa, babu komai." Mama ta ce. "Haka ne, Allah ya saka da Alkhairi, na ji daɗi kuwa sosai, bari na kira Neehal ɗin ku gaisa." Ya ce. "Toh, Maigidan baya nan ne?" Mama tana miƙewa ta ce. "Yana nan masallacin jikin gida, bari na kira shi a waya na sanar masa zuwanka." Alhaji ya ce. "To babu laifi." Sai da Mama ta fara lek'awa ɗakin su Dije ta je su kawowa baƙo abinci sannan ta hau sama ta kira Neehal. Neehal ta sakko da murnarta dan tana k'aunar mutumin a rayuwarta, ta gaishe shi cikin ladabi, ya amsa sannan ya shiga tsokanarta da ina surukinsa? Yaushe zata kai masa shi su gaisa? Ita dai murmushi kawai take kanta a ƙasa. Sai isha'i Alhaji Ali ya tafi, da yake Daddy ya dawo suna ta hira. Wajen tara da rabi na dare Neehal tana shirin kwanciya saboda ƴar gajiyar fitar da ta yi dake jikinta, kuma tana son ta tashi da wuri gobe fitar safe zata yi zuwa aiki. Mama ta shigo ɗakin, ta kunna light ta ce. "Ko har kin yi bacci ne?" Neehal ta ce. "A'a, ina dai shirin kwanciya." Mama ta zauna a bakin gado ta ce. "Kin ci abinci kuwa?" Ta ce. "Na ci." Mama ta yi shiru kawai tana kallon ta, ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa gabanta na fad'uwa." Mama ta sauke numfashi ta ce. "Shikenan ki yi baccinki, dama zuwa na yi in duba ki." Ta ce. "Toh Manana sai da safe." Mama ta ce. "Allah ya kai mu." Tare da miƙewa ta fice. Neehal ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da lumshe idonta, ta yi tunanin Mama zancen Ameen ta zo yi mata. Ta tashi ta sakawa ƙofar ɗakin key tare da kashe light sannan ta koma ta kwanta. Washegari kafin 8 ta fita, bata dawo gidan ba sai da 2 ta wuce. Bayan ta yi wanka ta fito daga ɗakinta zata sauka ƙasa ta ɗibi abinci ta ci kamar yadda Mama ta umarce ta, tana buɗe ƙofar falon sama da nufin fita suka yi karo da mutum zai shigo. Ta d'ago kanta da sauri bugun zuciyarta na sauyawa saboda k'amshinsa da ya sanar mata da ko waye tun kafin ta kalli fuskarsa......✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *7️⃣6️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ..........Idanunta suka sauka akan kyakkyawar kamilalliyar fuskarsa mai cike da kwarjini, ta yi ƙoƙarin ɗauke kallon ta daga fuskarsa amma ta kasa. Wani irin kallo yake mata wanda yasa ta ji wani irin abu yana yawo a cikin jinin jikinta, kamar yadda zuciyarta take bugawa da ƙarfi. Kallon sa take yi yau as husband to be not as brother before, tunanin hakan yasa ta ji gabanta ya yi wani irin mugun faɗuwa, ya sakar mata wani murmushi wanda zata iya cewa ba'a taɓa murmushin da ya kayatar da ita kamar shi ba. Ta lumshe idonta da sauri wani baƙon abu yana cika zuciyarta a kansa, like kunya ko tsoro. Ta yi baya da sauri tare da buɗe ido tana ɗan turo baki gaba, zuciyarta ta bata shawarar ta zura da gudu ta koma ɗakinta, har sai ya bar gidan sai ta fito. Ta juya cikin sauri amma ko ɗaga ƙafarta bata yi ba ya kamo hannunta, ta juyo kamar zata yi kuka dan abun da take ji a game shi ƙara yawa yake yana neman hautsina mata zuciya, kuma bata taɓa jin hakan a gare shi ba a rayuwarta sai yau. Ta saci kallon fuskarsa ta ga ya haɗe rai kamar ba shi ya yi murmushi yanzu ba, ya tsatstsare ta da kyawawan idanuwansa wanda suke ƙara mata yawan abun da take ji a kansa a cikin zuciyarta. Murya ƙasa_ƙasa ya ce. "Can't you great me?" Ta shiga girgiza kai tsoronsa na ƙaruwa a ranta, cikin rawar murya ta ce. "Ina yini?" Bai ce komai sai kallon fuskarta da yake yi kamar mai neman wani important thing a fuskar. Ta yi ƙasa da kanta a ranta tana addu'ar Allah yasa Mama ta fito ko ta samu ya bar ta. Tana ji ya saki ajiyar zuciya a hankali sannan ya sakar mata hannu without saying anything ya nufi ɗakin Mama. Ta bi bayan shi da kallo tare da murgud'a baki, ganin kamar zai jiyo ta buɗe ƙofa ta fice da gudu. Ya juyo jin ƙarar buga ƙofa, ya girgiza kai kawai tare da yin murmushi sannan ya shige ɗakin Mama. Mama tana shirya gogaggun kayanta a wardrobe ya shigo ɗakin da sallama. Ta amsa masa ba tare da juyo ta kalle shi ba. Ya zauna akan bedside drower tare da gaishe ta. Ta amsa masa tana rufe wardrobe ɗin sannan ta ƙaraso ta zauna a bakin gado. Tana duban sa cike da kulawa ta ce. "Ya su Hafsah?" Ya ce. "Lafiya k'alau." Mama ta ce. "Dafatan dai lafiya, tun ranar Friday rabon ka da gidan nan." Ya ce. "Lafiya k'alau Mum, weekend ɗin nan ban fita ba a gida nake wuni." Mama ta ce. "Okay." Sun taɓa hira kaɗan wadda majority akan aiki ne sannan ya yi mata sallama ya tafi. Bata yi masa zancen Neehal ba shi ma bai yi mata ba. Neehal kuwa tunda ta sauka ƙasa tana sauke numfashi ta shige ɗakin su Dije, ko abincin ma bata je ta ɗebo ba saboda tana tsoron kar Ameen ya sakko su ƙara haɗuwa, sai da ta ga fitarsa ta window'n ɗakin su Dije sannan ta fito. Da daddare Mama ta yi mata zancen Ameen akan jin ra'ayinta, dan Kawu Musa yau wayarsa biyu akan jin inda maganar ta kwana. Shiru ta yi ƙirjinta na luguden bugu. Mama dake kallon ta cikin nazari ta ce. "Neehal, ki kalle ni as your Mother ba mahaifiyar Ameen, ki faɗa mun abun da yake ranki kamar yadda kike faɗa mun a kodayaushe kin ji ƴar albarkata." Ta gyaɗa kai a hankali sannan ta ce. "Na amince." Mama ta ce. "Kin amince da me?" Ta kwantar da kanta a ƙafaɗar Mama ta ce. "Kin sani fa." Mama tana murmushi ta shiga shafa bayanta ta ce. "Da gaske Daughter maganar da kike faɗa mun tun daga zuciyarki take, bana son ki yi abun da ba kya so, in ba kya so you are free to say, no body will force you." Ta ƙara shigewa jikin Mama ta rufe fuskarta da hannunta ta ce. "Allah da gaske nake Mama." Mama ta faɗaɗa fara'a akan kyakkyawar fuskarta cikin tsokana ta ce. "Kina son Ameen ɗin kenan?" Da sauri ta cusa fuskarta ta ɓoye a jikin Mama tare da turo baki gaba. Mama ta shafa kanta cikin tsananin farincikin data manta rabon da ta yi kamarsa ta ce. "Masha Allah Neehal, Allah ya yi miki albarka ya inganta rayuwarki, ya baki ƴaƴa masu ladabi da biyayya kamar ki, Allah ya baku zaman lafiya yasa haka shi ya fi Alkhairi." Ta amsa da Amin a cikin zuciyarta. Ba ta kallon fuskar Mama amma a muryarta kaɗai tana jin irin farincikin da take ciki, kuma duk saboda ta amince da Auran Ameen ne, ina ga Daddy? Shi wanne irin farinciki zai ji idan ya ji wannan batun? Su saunawa suka saka ta a cikin farinciki a rayuwarsu? Babu adadi. Kenan data ƙi amincewa haka zasu ji babu daɗi a cikin ransu? Gwara da Allah yasa bata yi wannan gatobarar ba. Ta san bata son Auren Ameen ko kaɗan a cikin ranta, amma ta yiwa kanta alƙawari zata danne ta daure ko a fuska baza ta bari a gane ba, zata saka a ranta Allah ya yi Ameen ne mijinta, zata karb'i Auransa hannu bibbiyu idan Ubangiji ya yi hakan ta kasance. Amma tana mamaki da girmama abun a cikin zuciyarta ba kaɗan ba, YAYANTA MIJINTA, ko a mafarki bata taɓa tunanin hakan zata iya faru ba, ita mantawa ma take akwai aure a tsakaninsu da Ameen. As blood brother desame mother desame father take kallon shi. Wasu hawaye da bata san kona mene ba ta ji suna rige_rigen gudu akan kuncinta daga cikin idonta. Ta ƙara rungume Mama tare da fara kuka a hankali. Mama ta shiga bubbuga bayanta tare da faɗin. "Kunan na mene ne?" Ta ja majina bata ce komai ba. Mama ta d'ago da kanta tana kallon yanda take kukan ta ce. "Mene ne wai?" Ta girgiza mata kai kawai. Mama ta ce. "Iskanci ne kenan?" Cikin kukan ta ce. "Bana son na bar ki ne Mama." Mama ta yi murmushi tana jin tausayinta na cika mata zuciya, ta shiga share mata hawayen fuskarta tana faɗin. "Wa ya ce miki zaki bar ni dan kin yi Aure? Duk sanda kike son gani na zaki zo ki ganni ai." Cikin shagwab'a ta ce. "Ke baza ki zo ki dinga gani na ba?" Mama ta yi murmushi ta ce. "Zan zo mana, Amarya tun kafin a yi Aure har an fara zancen zuwa gida." Ta cusa kanta a jikin Mama cikin tsananin jin kunya. Mama ta ƙara rungume ta a jikinta tana jin tsananin farinciki a ranta, tabbas kamar yadda Daddy ya faɗa bata jin akwai wanda zai kai ta farinciki idan wannan al'amarin ya kasance. Bayan Daddy ya dawo Mama ta sanar masa yanda suka yi da Neehal. Farincikin da ya nuna ba zai misaltu ba, ya kira Neehal ta zo part ɗinsa wadda gaba-d'aya yanzu ta ji tana jin kunyarsa, ya dinga saka mata albarka tare da tarin addu'oi, har da tambayarta me take so ya yi mata a rayuwar nan wanda zata ji daɗi? Ta ce masa babu komai ai ita ya gama yi mata komai a rayuwa. Ta kasa tantance tsakanin shi da Mama wa ya fi wani farinciki da amincewarta. Da daddaren Ameen ya kuma dawowa gidan, Neehal tana falon ƙasa tana kallon wani series firlm ɗin India da take matuƙar so, bata ji sallamarsa ba sai k'amshinsa ne ya sanar mata da zuwan sa. Ai kuwa da sauri ta miƙe ta nufi upstairs, ya bi ta da kallo kawai yana sakin wani munafukin murmushi. A balcony suka ci karo da Mama, garin saurin da take har da tuntube ta yi. Mama ta ce. "Subhallahi, ki dinga kallon gabanki mana kina tafiya a hankali, kuma lafiyarki kuwa na gan ki kamar a firgice?" Tana sassauke numfashi ta ce. "Babu komai." Tare da shigewa falo. Mama ta tab'e baki ta sauka ƙasa abinta. Ta tarar Ameen ya zauna har lokacin bai bar murmushin da yake yi ba, ta yi masa wani kallo sannan ta zauna a kujerar dake facing ɗinsa. Suka ƙara gaisawa sannan Mama ta ce masa. "Ya na ga ka dawo?" Ya kama haɓa da hannunsa ɗaya ya ce. "Oh Mum, dan na dawo gidanmu laifi ne?" Mama ta ce. "Baka da gaskiya ne shi yasa na tambaya." Ya waro ido ya ce. "Rashin gaskiya kuma Mum?" Mama ta ce. "Ka fi ni sanin me ka yi ai." Ya yi murmushi ya ce. "I don't know fa." Mama ta ƙara ta tab'e baki ta ce. "Ai baza ka taɓa sani ba, wannan muskilancin naka yana k'ona mun rai, ka turo a sanar mana abu kuma ka san an sanar manan and still you can't say anything about it." Ya shafa kansa yana murmushi sosai ya ce. "Mum, what do you want me to say?" Mama ta ce. "Abun da ka je ka faɗa a zo a faɗa mana." Ya yi shiru still yana murmushi bai ce komai ba. Mama ta shiga mitar abun da yake ranta, harda ce masa alfarma ta yi kawai ta ba shi Neehal amma ba dan halinsa ba, babu yanda zata yi da Kawu Musa ne kawai. Shi dai murmushi kawai yake yi. Daga baya kuma ta koma yi masa faɗa da faɗin. "Ga Neehal nan Ameen, idan Allah ya yi auranku na baka amanarta, ka riƙe ta da amana dan Allah, ka ga yarinyar nan bata da kowa sai Allah, marainiyar Allah ce, idan ka zalunce ta Ubangiji bazai bar ka ba." Ji ya yi jikinsa ya yi sanyi, soyayyar Neehal da k'aunarta gami da tausayinta na ƙara narkar masa da zuciya. Daga nan part ɗin Daddy ya je wanda dama shi ya kira shi yana son ganin sa, shi ma faɗa da nasiha ya yi masa duk akan ya riƙe Neehal da amana ne. Neehal kam bata kuma fitowa ba tunda ta shige ɗaki dan bata san ta fito su haɗu kar ta je bai tafi ba. Wani irin tsoronsa da kunyarsa Ubangiji ya ɗoro mata tun daga lokacin data fara tursasawa zuciyarta karɓar sa a matsayin mijin da zata aura. A daren Daddy bai jira komai ba ya kira Abba da wasu cousins ɗinsa ya sanar musu abun da yake faruwa, ya kuma faɗa musu a cikin week ɗin nan yake son akai kuɗin Auren Neehal gidan kawunta. Mama ta ce masa saurin me yake har haka? Ya ce mata baza ta gane yanda yake d'okin abun ba ne, a yanzu ba shi da wani sauran buri a rayuwarsa bayan ya ga Auran Neehal da Ameen..... Kamar yadda ya faɗa ranar Asabar wanda ya kama kwana biyar da yin maganar da yamma suka kai kuɗin na gani ina so gidan Kawu Musa. Ranar Neehal ji ta yi gaba-d'aya kamar ba ita ba, ita ce yau aka karb'i kuɗin Auranta da Ameen? Sai ta dinga jin abun kamar a mafarki, ta tabbata dai Auransu za'a yi da Ameen, ɓoye kanta ta yi a ɗaki ta ci kuka ta k'oshi. Su Daddy ba su baro gidan Kawu Musa ba sai da aka tsayar da lokacin biki wata uku masu zuwa, a haka ma da ƙyar Kawu Musa ya yarda, ya ce abun tunda duk na gida ne no need a ja lokaci, in san ransa ne bai ƙi a yi bikin a cikin two weeks masu zuwa ba. Da Daddy ya zo yana faɗawa Mama ta ce, ta san wannan duk shirin Ameen ne, shi yake zuwa yana zubawa Kawu Musa sintiri akan maganar bikin. A ranar bayan Magriba Ameen ya zo gidan kamar kullum, sai dai tun daga ranar da Neehal ta zura masa da gudu bai kuma ganin ta ba, dan b'uya take yi a ɗaki, ana yin Magriba zata shige ɗakinta ta kulle dan ta san shine time ɗin zuwansa gidan, bata fitowa har sai ta tabbatar ya tafi. Shi kuwa yana sane da ita da duk b'uyan da take, kuma ya san duk saboda shi ne, ƙyale ta kawai ya yi ya ga iya gudun ruwanta dan ya san akwai ranar ƙin dillanci. A ranar Mama ta ce masa ya sanar da Hafsat maganar bikin, ya amsa mata duk da bai so hakan ba, da ya so sai abun ya matso daf sannan ya sanar mata, amma yaya zai yi tunda Mama ta bayar da umarni dole ya bi. Bayan isha'i ya koma gidansa, ya tarar da Hafsat Hakimce a falon ƙasa ta ci uwar kwalliya ta tarb'arsa..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *7️⃣8️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ..........Ranar Friday da yamma wanda ya kama bikin Neehal saura 4 weeks cif, tana zaune a ɗakin Mama suna hira dawowarta kenan daga gidan Alhaji Ali da ta je ta gaishe shi. Wayarta dake kan cinyarta ta fara ringing, ta ɗauka ta duba, ganin Sadik ne yake kiranta ta waro Ido cikin mamaki, duk da ta yi loosed wayoyinta a gidan ƙungiya amma Daddy yana fitowa ya siya mata sabbi dal guda biyu, ita kuma ta yi welcome back na Sims ɗinta. Amma da yake a email take sarving Numbers ɗinta tana ɗora shi akan wayar numbobinta suka dawo, that is why Numbern Sadik ta fito a wayarta with saved tunda bata goge ta ba ko bayan sun rabu. Ta d'aga tare yin sallama cikin sanyin muryarta. Sadik ya amsa mata tare da faɗin. "Neehal kwana dubu kin manta da Yayanki ko? Ko ɗan kira na mu gaisa ma ba kya yi." Ta ɗan murmusa ta ce. "Ka yi haquri Ya Sadik dan Allah, na san bani da bakin da zan kare kaina a gurinka." Ya ce. "Shikenan ya zan yi tunda kin ce Allah amma da ban yi niyyar haqura ba." Ta ce. "Toh Na gode, ya su Maamah da Batul?" Ya ce. "Suna nan k'alau, ya Mama da Daddy?" Ta ce. "Duk suna lafiya." Ya ce. "Masha Allah, ki gaishe su Please." Ta ce. "Za su ji Insha Allah." Ya ce. "Na manta lefin naki biyu ne ma a gurina, ashe bikinki ya taho amma babu labari Neehal?" Cikin mamaki ta ce. "A ina ka ji Ya Sadik?" Ya ce. "Zancen duniya yana b'uya ne? Amma dai Neehal baki kyauta mun ba da baki faɗa mun ba sai da abun ya zo daf nake ji." Ta ce. "To ka yi haquri, wannan ma na karb'i laifina." Ya ce. "Na ƙi yin haqurin." Ta shagwab'e ta ce. "Haba Yayana ni ce fa, ka haqura Please." Ya sauke numfashi ya ce. "Shikenan na haqura, Insha Allahu a cikin satin nan zan zo in gaishe da Mama." Ta ce. "Toh Shikenan sai ka shigo, Allah ya kawo ka lafiya." Ya ce. "Amin, sai anjima." Sai ta ji kamar ta tambaye shi yaushe ne nasa bikin, amma dai ta fasa ta ce. "Allah ya kai mu." Tare da katse wayar. Ta kalli Mama da hankalinta yake kan wayarta tana latsawa, can ƙasan ranta moment ɗin soyayyarsu da Sadik yana dawo mata. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ta ce. "Mama Ya Sadik ne ya kira ni, ya ce yana gaishe ki." Mama ta ce. "Ina amsawa." Da daddare kamar haɗin baki sai ga kiran Ahmad ya shigo wayarta. Sai da gabanta ya faɗi saboda rabon da su yi waya da shi tun satin bikinsa da ya yi mata ban gajiya. Ta d'aga tare da ɗan bata fuska kamar yana ganin ta. Ya yi mata sallama ta amsa can ƙasan mak'oshi. Cikin taushin murya ya ce. "Princess!" Ta lumshe ido a hankali ta ce. "Na'am Uncle." Ya ce. "How are you?" Ta ce. "Lafiya k'alau." Ya ce. "Uhm, me Ahmad ya yi aka daina kula shi? babu kira babu magana a chat, sai dai in na je gidan Ummi ta ce mun kun yi waya da yaranki." Ta turo baki bata ce komai ba, a ranta tana cewa. 'Kai da ka yi auranka ka manta da ni amma kai kake mun complain.' Ya ce. "Hello, Princess." Ta ce. "Na'am." Ya ce. "Why are you silent?" Ta ce. "Nothing, Ka yi haquri Uncle." Ya ce. "No prob, na ji wani labari a gurin Ummi." Ta ce. "Labarin me?" Ya ce. "Na auranki mana." Ta yi shiru bata ce komai ba. Ya ce. "Hmm, dole ki yi shiru tunda ke ma kin san baki kyauta ba, yanzu Princess ace za'a yi bikinki amma You can't tell me, sai da Mama ta kira Ummi ta faɗa mata sannan nake ji a gurinta." Yanda yake maganar ta gane ya ji haushi sosai, kamar zata yi kuka ta ce. "Ka yi haquri Uncle." Ya ce. "No, ai I'm not your Uncle right? Shi yasa baki faɗa mun bikinki ba" A shagwab'e ta ce. "You Are." Ya ce. "To me yasa baki faɗa mun ba." Ta ce. "Babu komai fa da gaske, I'm sorry." Ya ce. "Ba zan haqura ba, dan na san da ban kira ki ba yanzu baza ki kira ni ba." Ta ce. "Zan kira ka mana." Ya ce. "Eh zaki kira ni, amma sai nan da kamar 2 weeks haka ki ce na kawo miki twins ko?" Ta yi murmushi ta ce. "To yanzu tunda ka kira ni ai shikenan my Uncle sai ka yi haquri." Ya ce. "Na haqura, amma duk da haka I will punish you, punishment ɗin kuma shine bazan kawo miki twins ba." Ta ce. "Tab', aikuwa da kiranka zan yi inta maka kuka." Ya yi murmushi mai sauti ya ce. "Zaki iya ai, cry cry Baby." Ta ce. "Yanzu na girma na daina kukan ai." Ya ce. "Na san baki daina ba, zaki dai ki daina." Ta ce. "Ya Auntynah?" Ya ce. "She is fine." Ta ce. "My regard please." Sun daɗe suna hira da shi wadda ta saka su duka su biyun a cikin nishad'i, sai da ta ga goma ta wuce sannan ta yi masa sallama ta kashe wayar ganin ba shi da niyyar barin wayar, ta rungume wayar a ƙirjinta tana jin tsohon tsumin Ahmad na ƙoƙarin tasowa daga cikin zuciyarta, she missed him alot in her life. Ta lumshe idonta da ya ciko da k'walla. Shi kuwa Ahmad bin wayar ya yi da kallo bayan ta kashe kamar zai gan ta a cikin screen ɗin wayar, har yanzu yana son Neehal babu yadda zai yi ne kawai tunda ƙaddara ta raba su. Ya lumshe idonsa yana hango ta a cikin zuciyarsa tana murmushinta mai kyau, ba ya jin akwai macen da zai kalla a duniyar nan ya ga kyawunta kamar yadda nake ganin na Neehal. Ya buɗe ido a hankali yana sauke numfashi sannan ya tashi ya nufi ɗakin da Matarsa take bacci, wadda take fama da laulayin ɗan ƙaramin cikinsa. Washegari da safe sai ga Aunty Hauwa matar Uncle Umar ta zo gidan Mama, da tarkadu na kadarorin Neehal da littafi dake ɗauke da record ɗin duk wata dukiya ta Neehal da inda take da yanda ake juya ta. Mama ta yi mata godiya sosai tare da d'unbin Alkhairi. Ta sanarwa Neehal Uncle Umar ba shi da lafiya, cutar hawan jini na damun shi. Mama ta cewa Neehal ta shirya su koma tare da Aunty Hauwa ta dubo jikin nasa. Bayan sun je Neehal tana ganin shi ita sarkin kuka sai da ta yi kuka saboda yanayin jikin nasa da halin da yake ciki. Shi ma kukan ya saka cikin numfarfashi yana roƙon ta gafara akan zaluntar da ya yi a rayuwa. Ta ce ita ta yafe masa dama kuma bata riƙe shi a ranta ba. Ta kira Mama ta sanar mata halin da ake ciki, Mama ta ce ta saka shi a Mota su kay shi asibiti zata je asibitin yanzu ita ma. Suna zuwa aka bashi gado, zuwan su ba jimawa Mama ta ƙarasa asibitin, ita ta biya dukkan wani charges da akay musu. Washegari Sunday da daddare aka kay lefen Neehal gidan Kawu Musa, a daren Kawu Musa yasa aka juyo da kayan zuwa gidan Mama ya ce ai nanne gidan iyayen Neehal mene sai sun wahalar da kansu sun kay gidansa. Kaya masu kyau da tsada na gani na faɗa sune a cikin lefen Neehal, ba ƙaramin tatsar Ameen kuɗi su Aunty su kay ba, dan ma kusan rabin kuɗin Daddy ne ya bayar. Akwatuna goma sha biyar ne cif manya masu tsada, su kansu abun kallo ne. Banda wasu abubuwan da aka zubo a cikin Basket ɗin kaba da kuma wasu manyan jakunkunan leda guda biyu. Washegari misalin ƙarfe biyu na rana Ameen ya koma gidansa daga gurin aiki, bai shiga cikin gidan ba sai ya kira mai gadi da mai bawa flowers ruwa ya ce musu su shigar masa da akwatunan Hafsat na kayan faɗar kishiya dake cikin Motarsa. Suka amsa masa shi kuma ya shige ciki. Hafsat tana bedroom ɗinta tana shiryawa, fitowarta kenan daga wanka ta ji shigowar Motarsa gidan, a gaggauce take shiryawa dan kar ya shigo bata kammala shirinta ba. Bayan ya hau upstairs ɗin ma bai shiga ɗakin nata ba sai ya zauna a falo yana jiran su mai_gadi su shigo da kayan. Suna kammala shigowa da shi ba jimawa sai ga Hafsat ta fito cikin shirinta tana ta zabga murmushi. Ameen ya d'ago daga danna wayarsa da yake ya kalle ta. Turus ta tsaya murmushin fuskarta na ɗaukewa, da tsantsar mamaki take bin kayan da kallo, set na akwatuna mai shida sai ƙatuwar jakar leda guda ɗaya. Ta dube shi cikin mamaki ta ce. "Baby wannan kayan fa, na wa ye?" A dake ya ce. "Naki ne, na faɗar kishiya ake cewa ko?" Ta tsaya kawai kamar status tana kallon shi na wasu sakanni, sannan kamar wata sabuwar kamu ta ce. "Wasa kake yi Baby, na san na wani ne ya kawo maka ajiya shine kake mun wasa." Ta ƙarashe zancen tana nufar kayan. Ya yi ɗan murmushi ya ce. "My dearest wife uwar gidan Ameen, babu maganar wasa anan, aure zan yi nan da three weeks da kwanaki, so waɗannan kayan naki ne, and kuma ki faɗi me kike so na canza miki a gidan nan, kafin lokacin bikin sai a canza." Ta saki baki tana kallon shi ganin yanda yake maganar babu alamar wasa a fuskarka. Wata irin bugawa ta ji ƙirjinta ya yi mata. Cikin raunin murya ta ce. "Dan Allah da gaske Al'ameen Aure zaka ƙara? Baka ce mun ka fasa ba?" Ya yi mata wani kallo bai ce komai ba. Sai kuma ya miƙe ya yi ƙoƙarin janyo ta jikinsa ya rarrashe ta ganin ta fara hawaye. Ta yi baya cikin sauri a tsawace ta ce masa. "Karka kuskura ka taɓa ni, munafuki kawai macuci azzalumi." Sai kuma ta fashe da kuka. Ya tsaya kawai yana kallon ta cikin mamaki da ɓacin ran sunayen data kira shi da su. Ta juya ta shige ɗakinta da gudu tana kuka. Ya lumshe idonsa ya buɗe sannan ya ɗauki mukullin Motarsa dake kan kujerar da ya zauna ya juya ya fice daga gidan. Ba ya son ya cigaba da zama a gidan Hafsah ta yi masa abun da ba zai jure ba, ya ɗauki hukunci a kanta a zo a samu matsala. Yana fita Hafsat ta fito daga ɗaki kamar mahaukaciya tana kuka ta shiga bubbud'e akwatunan tana cilli da kayan ciki a tsakiyar falon. Tana yi tana faɗin. "Wallahi Ameen baka isa ba, ka yi kaɗan ka yi mini kishiya, zan ga ta yanda za'a yi auran nan ina raye." Sai da ta gama watsar da fiye da rabin kayan sannan ta sauka ƙasa a matuƙar fusace ta shiga kitchen, su Harirah suka bi ta da kallon mamaki ganin ta a haka babu maraba da mahaukaciya yanda take huci tana zazzaro ido. Taɓarya ta lalubo ta ɗauko ta fito falon ta fara faffasa abubuwa, ai da gudu su Harirah suka yi ɗakinsu suka banko ƙofa. Harirah ta dubi Baraka ta ce. "Mun shiga uku, Hajiya ko ta haukace ne?" Baraka ta ce. "Ko kuma dai ta tayar da aljanu ba, dan wannan aikin sai dai su." Dai-dai lokacin Hafsah ta rantab'awa show glass taɓarya, ji kake tassss gurin da ta dokawa taɓaryar ya yi ƙasa a dagargaje. Ai cikin rige_rigen gudu su Harirah har faɗuwa suke suka banka toilet suka rufo cikin tsoro tare da fargabar har Hafsat ta gama da falon ta dawo kansu. Duk wani abun fasawa a falon sai da Hafsat ta yi masa illa, sannan ta hau sama ta yiwa na saman ma. Tana zuba uban gumi da haki ta zaɓi jaka ta zira takalmi ta yi gidansu tana kuka. Su Harirah dai suna toilet rungume da bango ba su san ma ta fice ba, suna tsoron kar su fito aljanun su haɗa da su. Sai zazzare ido suke cikinsu na ƙugi. Hafsah ce zaune a falon gidansu tana ta rusa kuka, tunda ta je gidan kusan minti talatin kukan kawai take yi, Mom har ta gaji da tambayar ta abun da ya faru. A harzuk'e Mom ta ce. "Daughter wai ba tambayarki nake yi abun da ya faru ba, kin taho a hargitse kamar wata korarriya kin zo sai kuka kike mun kin ƙi yin magana." Ta ɗan tsayar da kukan ta ce. "Mom ashe Ameen yaudarata ya yi bai fasa Auran da ya ce zai yi ba." Mom ta ce. "Kamar yaya kenan?" Cikin kuka ta ce. "D'azu ya kawo mun wasu tsinannun kaya wai kayan faɗar kishiya, wai saura 3 weeks bikinsa." Sai ta kuma fashewa da kuka. Mom ta ce. "Kan uban nan, lallai ma yaron nan ɗan iska ne, mu zai yiwa haka? To wallahi bai isa ba, zai zo gidan ya same ni ne, sai dai ya zaɓa ko ke ko auran da zai ƙara. Ki daina kukan nan haka da'alla, har wani shid'ewa kike kamar wadda aka cewa na mutu, yanzu zan kira Alhaji in sanar masa halin da ake ciki, dan yana dawowa ya san matakin ɗauka cikin gaggawa. Shi kuma mara kunyar zai zo ya same ni har inda nake, na san zai kwaso jiki zalalo_zalalo ya zo biko, anan zan masa wankin babban bargo in ci masa mutunci. Yaro da ana ganin ka kamar na Allah ashe ka ce na shaid'an ne kai, banda ƙaddara mai zai haɗaki aure da wannan ai kin fi ƙarfin ajin shi." Ita dai Hafsah kukanta kawai take yi, bata ma saurarar sababin Mom. Ameen bai koma gidansa sai bayan Magriba, a lokacin ya ga aika_aikar da Hafsah ta yi. Da farko gani ya yi kamar ba Falon gidansa da ya saba gani ba ne kodayaushe tsaf, ya tsaya yana kallon Falon kamar wanda aka yi yaƙi a cikinsa cikin mamaki. Ya tsallake abubuwan ya haura sama dan jin ba'asin faruwar hakan a gurin Hafsah. Sai ya tarar falon saman ya ci uban na ƙasa a haukacewa. Yanda aka yi da kayan da ya kawowa Hafsah shi ya tabbatar masa gaba-ɗaya wannan aikin nata ne. Ransa ya yi matuƙar ɓaci ba kaɗan ba, saboda kawai ya ce zai ƙara Aure? Mene matsalar mata da ƙara Auren Namiji ne? Ubangiji ne fa ya halatta a yi, da wannan haukan ba gwara ki dage da Sallah kina addu'a da kai kukanki gurin mai duka akan Allah ya baki kishiyar ta gari ba, idan mai sharri ce ki roƙi sharrin ya ƙare a kanta ke kuma ya tsare ki daga sharrin. Amma sai sabon jahilci da hauka zaki tsiro. Cikin tsantsar ɓacin rai ya nufi ɗakinsa ya yi wanka ya fito. Kamar yadda ya zata bata gidan, ya sauka ƙasa ya tarar su Harirah wanda jin shigowarsa yasa suka fito falon, amma duk da haka a tsorace suke. Fuska a cukule ya ba su umarnin gyara gidan sannan ya fice. A gurin gyaran ne su Harirah suka gane dawar garin, wato dalilin da yasa Hafsah ta yi wannan haukan. Saura sati biyu biki Mama ta ɗauko mai gyaran jikin data gyarawa Neehal lokacin bikinsu da Sadik ta fara yi mata. Haramar biki fa ta ɗauka sosai, Daddy ya ƙara gyara gidan Mama, duk wani furniture's dake part ɗinta an canza shi an saka sabo, haka ma cotton's da carpet's. Ga contributions da Mama take samu ko ta ina, haka ma Neehal ɗin. A lokacin ne Neehal ta fara nuna damuwarta ta fara k'unci da koke_koke irin wanda ta yi lokacin bikinsu da Sadik, ganin dai da gaske auran nata za'a yi, tafiya zata yi ta bar Mamanta. Ameen ma shirye-shiryen bikinsa kawai yake yi ya ajiye batun wata Hafsat a gefe, ya ce idan ta gaji da zaman gidan nasu ta dawo, dan shi dai ko zata shekara ba zai je wani biko ba. Mama bata san Hafsat ta yi yaji ba dan bai faɗa mata ba, Daddy ma haka. Kuma ko kaɗan ba ya nuna alamar bata gidan nasa. Wannan karon Mama ta ce babu abun da za'a yi na events, Ranar d'aurin Aure kawai zata yi yini da daddare a miƙa Amarya gidanta. Haneefah da sauran mate ɗinsu na Familyn su Mama ba su so hakan ba, sai dai ita Neehal hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, dan bata son taro ko kaɗan. Aunty Sadiya dai ta ce sai sun yi Kamu ranar Alhamis ko a gida ne an kira masu kiɗan ƙwarya sun buga musu sun jajige baza'a yi biki lami ba. Tun ranar Sunday wanda ya kama saura kwana biyar d'aurin Aure Ahmad ya kawo twins, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Neehal ba. Ya kuma bata kuɗi masu kauri a matsayin gudunmawa, wanda sai da ya ɓata rai sannan ta karɓa. Uncle Usman ma ranar ya sauka shi da iyalansa. Ana i jibi biki gidan ya ɗinke da jama'a, dangin Mama dana Daddy da kuma na Neehal, wannan karon sun mata kara babu laifi sun zazzo, wasu ma bata san su ba sai an faɗa mata dangantakarta da su take ganewa, Kawu Musa ne duk ya yi musu tilas suka zo, da kansa ya je har Gabasawan ya kai musu abun gayyata. Matan Ƴaƴan Baffa ma sun zo da ƴaƴansu. Ranar aka yarfawa Neehal ƙunshi a fararen hannunta da ƙafarta, ƙunshin ya yi matuƙar kyau akan fatarta data sha gyara bana wasa ba. Sai walwali take tana hasakawa, ga wani k'amshi mai daɗin gaske dake tashi a jikinta. Ita akaran kanta ta san ta sauya, dan wannan gyaran jikin har ya fi wancan da aka yi mata kyau. Sai ta tsaya a gaban mudubi ta yi ta kallon kanta tana murmushi ita kaɗai..........✍️ *Wanga novel yaushe zaka ƙare ne?🤔😰* *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *7️⃣9️⃣* Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR* *Call 08066268951*131*4#* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ..........A safiyar ranar Hafsat tana zaune a ɗakinta na gidansu abun duniya duk ya ishe ta, tunda ta zo gidan bata da aiki sai kuka, duk ta rame ta lalace ko abinci sai uwar ta yi yaƙi da ita take tsakura ta ɗan ci. Tana son Ameen kuma baza ta so su rabu ba, amma kuma baza ta iya jure kallon sa da wata macen ba. Gashi kuma Mom ta k'wace duk wayoyinta wai saboda kar ta kira Ameen ta zubar musu da kima a wajensa dan ta san halinta, shi kuma ya ƙi kiran ta balle ya zo, gashi Dad ɗinta baya nan yana London. Abin da yake ƙara d'aga mata hankali idan ta tuna Ameen yana can yana shirin bikinsa da wata ita ya banzatar da ita, ita yanzu burinta ɗaya a duniya ta san wa Ameen zai aura, ta ga me matar ta fita da yasa Ameen ɗin zai aure ta, ƴar waye a ina kuma take? Kamar amsar tambayarta ta ji an turo ƙofar ɗakin, ta d'aga kanta da sauri tana share hawayen fuskarta. Wata ƙawarta ce mai suna Jalilah ta shigo Mom na biye da ita a baya. Ba tare da ƙawarta_ta ta damu da yanayin da ta gan ta a ciki ba ta ce. "Hafsy wannan ba mijinki ba ne Ameen?" Tana miƙa mata wayar hannunta ta yi maganar. Hafsah ta karɓa tare da ƙurawa screen ɗin wayar ido. Katin d'aurin Auren Ameen da Neehal ne irin wanda ake yi a yanzu a waya a saka wak'a, amma ita ba wannan ne damuwarta ba, sunan wadda ta gani a matsayin amaryar shi yasa zuciyarta bugawa da ƙarfi. FATEEMAH MUHAMMAD TAFIDA (NEEHAL). Ta murza idonta a tunaninta idon ne ya ganar mata ba dai-dai ba, amma still dai abun da ta gani shi ta ƙara gani. Wata uwar ƙara ta saki tare da sakin wayar, Jalilah ta yi saurin tare abarta cikin tsoron kar ta faɗi ta fashe. Hafsat ta miƙe tsaye jikinta na bari cikin tashin hankali ta ce. "Mom, kin ga abun da na gani kuwa? Neehal Ameen zai aura, yarinyar da Mamansa take riƙo." Mom ta ce. "Na gani nima Daughter, auran cin amana zai yi." Cikin ƙaraji Hafsat ta ce. "Ameen why? Me na yi maka? Ka rasa dawa zaka haɗa ni kishi sai da wannan aljanar yarinyar, yarinyar dana tsana." Sai ta fashe da kuka ta ce. "Munafuki, komai ya ce Neehal Neehal ashe son ta yake yi, yarinyar ta ƙi auruwa shine shi zai aure ta, in ma wani mugun abun ne da ita ya shafe mu kenan? (Hafsah bata san me ya faru ba akan case ɗin Daddy da Neehal, da yake an ɓoye abun ne babu wanda ya ji sai wanda ƴan'uwa na jiki.) Jalilah ta ce. "Na daɗe da ganin wannan videon tun last week, ina ta kiran wayarki bata shiga, a online ma bana ganin ki kwata_kwata. Shine na ce bari dai na je gidanki na tabbatar da gaske mijin naki ne zai yi aure, na je kuma na tarar bakya nan sai masu aiki, suka ce mun kina gida." Hafsah ta haɗa kanta da jikin wardrobe tana kuka sosai, tashin hankalinta ya ninku akan na da, Neehal fa, yarinyar data tsana a duniya tun kafin ta gan ta, ita Ameen zai aura, ashe dama son ta yake? Ko kuma ta ce soyayya suke? Da ƙyar Mom da Jalilah suka rarrashe ta. Mom ta kira ƙanwarta Safiya suka haɗu suka zauna suna zagin Ameen da Neehal har Mama ba su ƙyale ba suka dinga cewa ita ce munafuka ita ta haɗa komai. Aunty Safiya ta kwantarwa da Hafsat hankali ta ce ta bar komai a hannunta, ta yi mata alƙawarin Ameen sai ya zo har inda take yana kuka da idonsa tare da begging ɗinta, wannan aure da zai yi kuma sunansa matacce. Da daddare Neehal tana zaune a cikin ƴan'mata suna ta tsokanarta, wannan ta ce mata daga jibi shikenan zata shiga daga ciki. Su Haneefah ne sakaran sharri, harda cewa yanda ta sha gyaran jikin nan ta yi kyau Allah yasa kar ta zautar musu da Yaya. Ita dai idanunta a lumshe tana tunanin abun da ya dame ta bata su take ba. Damuwarta yanda rayuwar Auranta zata kasance, tana yawan jin ana cewa kowanne Aure yana da tasa matsalar da kuma k'alubale, to ita ko wacce matsalar zata je ta tarar sai Allah? Ta sauke numfashi tana tuna yanayin mijin da zata aura da yanda Auran nasu ya kasance, zuciyarta ta kasa hasaso mata yanda rayuwar auren nasu zata kasance, ga kuma wani ƙarin matsalar kishiya, ta riga ta san Hafsat bata son ta tun a da ballantana kuma yanzu. Ta sauke ajiyar zuciya tana jin zuciyarta babu daɗi ga tarin fargaba a cikinta. Muryar Aunty A'isha ta ji a kanta tana kiran sunanta. Ta buɗe ido tare da amsawa. Aunty ta ce. "Tunanin me kike yi haka inata magana baki ji ba? Ga hayaniya ta cika ɗakin amma ke baki ma san ana yi ba." Cikin sanyin murya ta ce. "Babu komai Aunty." Aunty ta ce. "Koma da akwai ki yi addu'a, addu'a makamin mumuni ce, ba wai ki zauna ki yi ta tunani ba." Ta ce. "Insha Allah Aunty." Aunty ta ce. "Yawwa, tashi mu je part ɗin Daddy Umma na son ganin ki." Ta miƙe ba tare da yi magana ba suka fice. A falo suka yi kicibus da Hajiya, ta dubi Neehal ta ce. "Ke wai ya kike abu da sanyin jiki ne kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki? Ko baki da lafiya ne?" Neehal ta turo baki bata ce komai ba. Aunty ta yi murmushi ta ce. "Mood ɗin amarci ne kawai." Hajiya ta ce. "Mudun amarcin me? Ki zage jiki ki dinga abu cikin kazar_kazar da annashuwa mana, kin wani cukele fuska kamar waccan uwar taki Saratu da bata k'aunar fara'a. Wai ina Aminun ne? Tunda na zo ban gan shi ba, ko ɗan zancen nan ma shi ba ya zuwa ne?" Aunty ta yi murmushi ta ce. "Hajiya gida fal da baƙi ina zaki gan shi?" Hajiya ta tab'e baki ta ce. "Bai ga damar zuwan ba ne, amma Aminu ai ba wata kunya ya cika ba." Aunty ta kama hannun Neehal suka yi gaba. Umma kaɗai suka tarar a Extra room ɗin dake part ɗin Abba. Neehal ta zauna a ƙasan gado Aunty ta juya ta fita. Faɗa da nasiha sosai Umma ta yiwa Neehal akan zamantakewar aure, ta nusar da ita abubuwan da ba'a so a zaman aure da kuma wanda ake so, ta nuna mata mahimmancin tsafta, addu'a, iya sarrafa girki, ladabi da biyayya da iya kula da miji a rayuwar aure. Sai kuma uwa uba haquri, wanda mutane da dama tun kafin Umman suke ta faɗa mata aure ɗan haquri ne, sai ta yi haquri. Mama ma ta zo ta ɗora mata da nata faɗan. Washegari aka yi Kamu kamar yadda su Aunty Sadiya suka shirya, a harabar gidan Maman aka yi decoration mai kyau na gurin zaman amarya, aka jera fararen kujerun roba na zaman baƙi. K'wararrun masu kiɗan ƙwarya suka zo suka buga kiɗa manyan mata suka cashe, an ci an sha an yi bidiri, kuɗi kamar tsinto shi ake yanda family da k'awayen Mama suka dinga zuba lik'i, Mama ta yi kyau sosai, ta sha kiɗan uwar amarya uwar ango a gurin masu kiɗan ƙwarya. Neehal ma ta yi kyau sosai ta sha make up, tsoffi suka feshe ta da turaruka aka kamata (Kamun amarya). Gidan ya cika ya yi mak'il da jama'a. Amarya dai dauriya kawai take amma k'iris take jira ta fashe da kuka, halin da zuciyarta take ciki ba zai misaltu ba, ita kaɗai ta san me take ji. Ga jama'a sun hana ta sakat da ɗaukar hotuna. Bayan Sallar isha'i Mama suna falon Daddy ita da su Aunty, cikin ɓacin rai da takaici ta dube su ta ce. "Wai ashe Hafsah bata gidan Ameen ta yi yaji?" Aunty A'isha ta ce. "Yaji kuma kamar ya?" Mama ta ce. "D'azu Doctor Rahina wadda muka yi aiki da ita a asibiti take faɗa mun, ashe ƙanwarta ƙawar ƙanwar mahaifiyar Hafsat ɗin ce." Aunty Sadiya ta ce. "To akan me ta yi yajin? Ko dan zai ƙara Aure ne?" Mama ta ce. "Hmm, ina zan sani, amma Ameen bai taɓa faɗa mun, a yanda Rahinan take faɗa mun zata yi sati uku fa a gida." Aunty Sadiya ta ce. "Subhallahi, wannan abu bai yi daɗi ba, amma bari na kira Ameen ɗin na ji asalin maganar." Ta kira shi bai d'aga ba. Mama ta ce. "Gaskiya Ameen bai kyauta mun ba, akan me zai bar yarinya ta daɗe a gida haka? Shi yasa shekaran jiya da nake tambayar sa zata yi taro ya ce mun ta ce baza ta yi ba, ashe yasan tsiyar da ya shuka kenan." Aunty A'isha ta ce. "Baki san me ta yi masa ba Yaya, kar ki ga laifinsa." Mama ta ce. "Koma me ta yi masa dai ai haquri ake tunda a da bata taɓa yi masa ba, yanzun ma da dalili ai, duk matar da za'a yi mata kishiya ai sai an yi haquri da ita." Ta miƙe tana faɗin. "Zai zo ya same ni ne." Ta shiga ɗakin Daddy ta tarar da Neehal ta zubawa hannunta da ya sha ƙunshi ido tana kalla. A zahiri zaka yi tunanin hannun take kallo, amma a badini tunani take, tunani take daga gobe fa shikenan ta zama matar Ameen, wataƙila ma i yanzu an kaita gidansa. Mama ta ce. "Kina nan ashe inata neman ki ki ci abinci." Ta sauke numfashi tare yin ƙasa da kanta hawaye ya zubo daga idonta. Mama ta ce. "Kukan ne dai Neehal? Allah ya nuna mun ranar da zaki daina wannan kukan naki." Kamar zuga ta Maman ta yi sai hawaye sharr kamar an buɗe fanfo. Mama ta ƙarasa ta zauna a gefenta tare da janyo ta jikinta ta ce. "To ya isa haka kukan, ki yi shiru kar kanki ya yi ciwo." Maimakon ta yi shirun sai ta ƙara fashewa da kuka tana shigewa jikin Maman. Mama ta shiga bubbuga bayanta cikin danne zuciyarta, dan itama idan ta tuno few days idan ta tashi baza ta ga gilmawarta a gidan ba sai ta ji babu daɗi a ranta. Ganin ta ƙi yin shiru ta d'ago fuskarta ta ce. "Haba Neehal ki yi shiru haka mana, ko a akwai wani abun da yake damunki?" Ta girgiza kai cikin kuka ta ce. "Ni bana son barin ki Mama." Mama ta ce. "Oh Neehal rigima, sau nawa zan faɗa miki dan kin yi aure hakan ba yana nufin kin barni ba ne, kuma ai haka rayuwar take tunda aure ya zama dole, kowa da haka yake sabawa, ki yi haquri kin ji." Ta ƙarashe zancen tana share mata hawaye. Mama ta ce. "Ina nan ina murna na kusa samun ƴan jikoki daga gurin autata, ita kuma tana damun kanta." Neehal ta rufe fuskarta da hannunta tare da juyawa Mama baya. Mama ta yi murmushi ta miƙe ta kama hannunta ta ce. "Mu je ki ci abinci, na san baki ci ba."........ Yau kam bacci rabi da rabi Neehal ta yi, ƙarshe ma sai tashi ta yi ta ɗauro alwala ta shiga yin nafilfili tana roƙon Allah ya kawo musu komai cikin sauƙi a rayuwar Auransu. Washegari ranar D'aurin Aure, gida ya ƙara ɗinkewa da jama'a maza da mata. Sai ƙarfe biyu za'a d'aura auren a babban masallacin juma'a na unguwar. Da safe su Ummi suka zo harda matar Ahmad Khadijah da Ahmad ɗin. Neehal bata taɓa tunanin shi kanshi zai zo ba balle matarsa, Khadijan kuwa mai kirki da faran_faran ba ruwanta ta shiga cikin su Haneefah ana ta hira da ita. Batul ƙanwar Sadik ma wajen sha biyu na rana ta zo, ta ce su Maamah ma suna hanya. Sai da Neehal ta gan ta sannan ta tuna da kuɗin da Sadik ya turo mata ta account a matsayin gudunmawa ta manta bata faɗawa Mama ba, sai a lokacin ta faɗa mata, Mama ta ce zata kira shi bayan biki ta yi masa godiya. Tsoro da fargabar Neehal yau ya fi na kullum, dan da mutum zai yi close da ita sosai zai iya jin yanda zuciyarta take bugawa da sauri da sauri. Ta dai daure tunda garin Allah ya waye yau bata yi kuka ba, amma ta kasa cin komai dak'yar ta iya shan ruwan tea kaɗan. Ita da Haneefah da wata Freind ɗinta Zee suka je aka yi mata make up. Ta yi kyau sosai ta fito tsaf a amaryata sai baza k'amshi take. Ƙarfe biyu na rana kamar yadda aka tsara Ubangiji ya nufa aka ɗaura Auren AL'AMEEN MUHAMMAD TAFIDA da FATEEMAH MUHAMMAD GABASAWA. A lokacin Neehal ba su jima da dawowa daga gurin kwalliya ba, ta ji Aunty Sadiya tana an ɗaura, yanzu Uncle Ahmad ya kira ta ya faɗa mata. Bugun zuciyarta ne ya ƙaru ta ji ta a cikin wani irin yanayi da bazai misaltu ba, shikenan ta zama matar Aure matar Ameen. Ta lumshe idonta tana sauraren yanda zuciyarta take bugawa. "Finally an ɗaura, yarinya ta zama matar Aure..." Ta ji muryar Haneefah cikin dariya a kanta tana faɗar haka. Duk yanda taso mayar da hawayen idonta kasawa ta yi sai da suka zubo. Wajen ƙarfe uku na rana suna part ɗin Ameen na gidan da yake anan ƴan'mata da k'awayen Amarya suka tare tunda aka fara bikin. Afrah ta zo da murnarta ta ɗane jikin Neehal da fara'arta ta ce. "Aunty Uncle ya zo, ya yi kyau sosai." Amrah ta ce. "Aunty wai shine Ango ke kuma Amarya?" Wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarci Neehal, ta san yanzu za'a ce ta zo su je a yi musu hoto tare da shi, ita kuma gaskiya bata san da idon da zata kalle shi a matsayin Mijinta ba, wani irin feeling na daman take ji a kansa, kunyarsa da tsoronsa sun ƙara cika zuciyarta. Ta janye Afrah daga jikinta da sauri ta miƙe ta shige toilet duk da bata da abun yi a toilet ɗin. Tana ji Aunty Sadiya ta shigo tana neman ta amma ta ƙi fitowa har ta gaji ta fice. Mutun sama da biyar sun shigo neman ta sai a ce musu tana toilet, ita kuma ta ƙi fitowa dan ta san dalilin kiran nata, sai haqura aka yi aka ƙyale ta. Aka cigaba da shagalin biki cikin nishad'i da farin ciki. Hada_hadar mutane yasa Neehal ta ɗan saki ranta, dan da biki ya yi biki ko lokacin Kaɗaita bata samu ba, daga a gaisa da wannan sai a gaisa da wancan. Ga k'awayenta da ƴan gurin aikinsu sun zo mata sosai. Sai can yamma da Aunty A'isha ta zo ta jata part ɗin Daddy zata yi wanka a kaita gidanta ta fara kuka sosai, tana kukan ta yi wanka aka taimaka mata ta shirya. Zuwa lokacin har an fara ɗibar mutane ƴan kai Amarya. Ta zauna a gefen gadon Daddy tana ta kuka a cikin mayafi. Daddy ne da kansa zai kai ta gidanta, ya shigo ya tarar da ita tana kuka su Aunty suna aikin ban baki da ƙara yi mata ƴan nasihohi. Mama kuwa dama ko ɗakin bata tunkara ba, dan ta san idan Neehal ta gan ta kukan da zata yi sai Allah. Shi ma Daddy zama ya yi ya ƙara ɗora mata da nasiha akan zaman aure. Sai bayan ya gama yi mata faɗan za'a fita da ita Mama ta shigo ɗakin. Neehal ta tashi da sauri ta rungume ta tare da ƙara volume ɗin kukanta, duk dauriyar Mama sai da zuciyarta ta karye ta yi hawaye. Da ƙyar Daddy ya janye Neehal daga jikinta ya kama hannunta suka fice tana gunjin kuka. Gidan Neehal babu nisa sosai, anan cikin Nasarawan ne unguwar badawa. Kafin a ƙarasa da ita wasu har sun fara dawowa. Har ɗakinta har kan gadonta Daddy ya kai ta bayan ya ce ta shiga da ƙafar dama tare da yin Bismillah. Gidanta ya yi kyau ya tsaru sosai, madaidaici ne ba ƙato sosai ba, amma an ƙawata shi da kayan ado da alatu dan har ya fi gidan Hafsat kyau da tsaruwa. Mama da Daddy kuma sun zuba mata kaya na alfarma, kowa sai Masha Allah da sam barka yake. Daddy ya kama hannunta a cikin nasa ya shiga yi musu addu'ar fatan Alkhairi da zaman lafiya a zaman auransu. Mutanen ɗakin na amsawa da Ameen, abun gwanin burgewa. Bayan ya gama ya ɗan bubbuga bayanta ya ce. "Kukan ya isa haka Daughter, ki yi haquri kin ji." Ta zame daga kan gadon ta durk'usa a ƙasa ta rungume ƙafafunsa tana kuka sosai ta ce. "Na gode, na gode, na gode sosai Daddy, Allah ya biya ku da Aljannah maɗaukakiya, Allah ya saka muku da Alkhairi kai da Mama, bani da bakin godiya a gare ku." Cikin karayar zuci Daddy ya ce. "Amin Daughter, Allah ya sanya miki albarka ya baki ƴaƴa masu albarka." Ya ƙarashe zancen tare da d'ago ta ya mayar da ita kan gadon ya zaunar. Ta riƙe hannunshi gam tana hawaye, da ƙyar ya samu ya zare hannunsa ya fice yana jin zuciyarsa babu daɗi sosai. Haneefah ta ajiyewa Neehal ƙaramar jakar akwatin da aka zubo mata kayan da zata yi amfani da su a kusa da ita, tana hawaye ita ma, domin Neehal ta bawa mutanen ɗakin tausayi sosai. Aunty Sadiya ta zo ta rungume ta tana rarrashinta. Da wayo da dabara su Aunty da su Haneefah suka samu suka bar gidan, aka bar ta ita kaɗai k'wal daga ita sai halinta..........✍️ *Ban yi editi ba, a yi haquri da typing errors.* *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _*By*_ _*Zeey Kumurya*_ *8️⃣0️⃣* ..........Kamar yadda yau ta kasance ranar farin ciki ga su Mama da duk wani masoyinsu haka ta kasance rana mafi muni da baƙin ciki a gurin Hafsah. Daren jiya ko bacci bata iya yi ba saboda wani abu da yay mata cunkus a cikin zuciya. Tunda ta tashi yau da safe kuwa take ta aikin kuka, ta ƙi ci ta ƙi shan komai. Da rana ta samu Mom ta bata ɗaya daga cikin wayoyinta daƙyar, jikinta har rawa yake yi gurin azarɓaɓi da zumuɗin shiga yanar gizo, aiko cikin lokacin ƙanƙani ta ci karo da abun da take nema. Pics ɗin Neehal kala_kala tun daga na ranar kamu har na ranar ɗaurin Aure wanda bai jima da sauka ba ta yi katari da shi, sai kuma na Ameen a gurin ɗaurin Aure, wasu shi kaɗai wasu kuma da jama'a yana ta murmurshinsa mai kyau wanda ya tabbatar mata yana cikin tsananin farin ciki. Ya yi kyau sosai cikin milk ɗin dakakkiyar shadda ya sha babbar riga wadda ta ci aiki mai kyau. Bata san lokacin data yarda wayar ta_ta ba tare da kurma wani uban ihu, shikenan Ameen ya zama nasu su biyu, yau ita ce da kishiya? Abar da bata taɓa kawo ta ba a cikin rayuwarta ko a mafarki da sunan za'ai mata, gaskiya Ameen ya cuce ta, zata iya cewa tunda ta zo duniya bata taɓa ganin ranar baƙin ciki irin wannan ba, ita ƴar gata ce bata taɓa neman abu ta rasa a rayuwarta ba, kome take so iyayenta suna yi mata. Ameen ne mutum na farko da ya fara bata ciwon kai a rayuwarta, yanzu kuma yana ƙoƙarin saka mata na zuciya. Ihun data kurma ya yi dai-dai da shigowar Aunty Jamila cikin falon wadda zuwanta gidan kenan, Aunty Jamila ta ƙarasa gare ta da sauri cikin damuwa ta ce. "Subhanallahi, Hafsah lafiya? Me ya faru?" Cikin kuka ta ce. "Aunty na kaɗe har ganyena, ta tabbata Ameen ya ƙara aure ya mun kishiya, na shiga uku ni Hafsat." Aunty Jamila ta zauna a gefenta ta ce. "Haba Hafsah, dan an yi miki kishiyar kike wannan kukan da ihun? Me hakan zai haifar miki? A kanki aka fara kishiyar ne? Ko kanki farau ne? Kishiya ai abokiyar zama ce ba abar tashin hankali ba, da har zaki zauna kina wannan abun." Hafsah ta ce. "Aunty ce mun fa ya yi ya fasa auren, ashe munafiki bai fasa ba." Aunty Jamila ta kama haɓa ta ce. "Hafsah! Mijin naki kike cewa munafiki dan ya ƙara aure sunnar ma'aiki da Ubangiji ya halatta masa ya yi? To akul kar na ƙara jin kin kuma jifan mijinki da wannan kalmar." Hafsah ta yi shiru a ranta tana takaicin yanda bata kula kowa a familyn Ameen da matan abokansa, may be da suna hulɗa da wani ko wata zata samu labarin bikin tun kafin lokaci ya ƙure, may be da ta yi ƙoƙarin hana yin auren, amma yanzu lokaci ya ƙure mata tunda an yi an gama, amma duk da haka baza ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen bin duk abun da Aunty Safiyya ta ce mata ba dan ganin auran Neehal da Ameen ya zama matacce........ Neehal tana zaune naɗe cikin mayafi tana kukanta ta ji ana sallar ishai, ta miƙe daƙyar saboda kanta dake mugun sara mata ta yi ta_ta Sallar da yake tana da alwalarta. Sai a lokacin ta ɗaga kanta ta shiga bin madaidaicin ɗakin da take ciki da kallo, ya matuƙar yi mata kyau da burgewa. Ta lumshe idonta a hankali tana jin ta kamar mai cuta, bata fi ten minutes da idar da sallar ba ta ji ƙarar buɗe ƙofa daga waje, tana can tana tunanin da ya aure ta ko shigowar Mota gidan bata ji ba, ta miƙe da sauri ƙirjinta na tsananta bugu ta koma kan gadon ta zauna ta ƙudundune jikinta guri guda da mayafin jikinta. A hankali ta ji an turo ƙofar ɗakin da take, gabanta ya yanke ya faɗi, sallamarsa cikin kamilalliyar muryarsa da kuma daddaɗan ƙamshinsa suka ziyarci hancinta a lokaci ɗaya. Ya tsaya a jikin ƙofa bayan ya mayar ya rufe tare da harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallon ta, hakan ba ƙaramin ƙarawa Neehal saurin bugun zuciyarta ya yi ba. Ya tako a hankali ya ƙaraso bakin gadon tare da tsugunnawa a gabanta, fuskarsa na fitar da wani irin annuri gami da sihirtaccen murmushi. A hankali ya saka hannun damansa ya shiga ƙoƙarin buɗe fuskarta, jin hakan ita kuma ta ƙara ƙanƙame mayafinta a jikinta, kukan data daina na ƴan mintunan da suka gabata ya dawo sabo ta hanyar fara zubar hawaye daga idonta, jikinta har ƴar rawa ya fara saboda tsoro da fargaba, duk guje masan da take yau gashi daga ita sai shi a gida ɗaya a ɗaki ɗaya, sai dai ita ba wannan ne ya fi damunta ba, damuwarta yanzu ya zo mata ne a matsayin miji, kuma bata san irin zama da rayuwar da ya shirya musu ba. Ya yi nasarar yaye mayafin, fuskarta da ta yi jajur saboda kuka ta bayyana, saboda tsorata a ƙoƙarinta na ƙara riƙe mayafin bata san ma hanyar da zai cire cikin sauƙi ta samar masa. A hankali ya kama hannunta dake kan cinyarta ya riƙe tare da sakin wata sassanyar ajiyar zuciya, ƙamshin jikinta ya fara tasiri a gare sa, riƙe hannunta da ya yi ya zo mata a bazata har ƴar zabura ta yi tare da ƙara yin ƙasa da kanta. Ya damƙe hannun nata sosai a cikin nasa jin tana ƙoƙarin zare shi, cikin wata sassanyar murya mai daɗin amo mai kama da raɗa ya ce. "Welcome home my bride." Ta turo baki a hankali maganarsa na yi mata yawo a cikin zuciyarta da kwanyarta, kalmar *my Bride* ɗin da ya furta ta fi komai bata mamaki, da kuma yanda ya yi mata magana cikin sanyi da wani irin salo. Ya yi murmushi mai sauti tare da kai ɗayan hannun nasa ya ɗago haɓarta, ta yi saurin lumshe idonta tana jin zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito saboda bugu, yanayin da take jin kanta da zuciyarta ba zai misaltu ba, ita kanta ta kasa tantance yanayin da take ciki, kafin ya shigo ta san tsoro da fargabar ganinsa da kasancewar da za su yi a gida ɗaya take, amma yanzu da ya shigo inda take yake tsugunne a gabanta sai ta ji wani baƙon al'amari a game da shi a cikin zuciyarta. Tana jin yanda ya ƙurawa fuskarta ido yana kallon ta ko kiftawa babu a jikinta, sai ta ji ita ma zuciyarta tana azalzalarta da ta buɗe idonta ta kalle shi, duk yanda ta so bijirewa daga umarnin zuciyarta amma zuciyar ta ƙi bata goyon baya, bata ma san lokacin data buɗe kumburarrun idonta da suka ci kuka suka ƙoshi ba ta zuba su akan kyakkyawar fuskarsa da gangar jikinsa a lokaci ɗaya, amma bata bari sun haɗa ido ba. Sanye yake cikin wani tsadadden yadi milk colour, kansa sanye da hula, duk da bai fiya sakawa ba amma ta yi masa kyau sosai. Yanda ya kafe ta da ido yasa ta kallon nasa idon ita ma, hakan ya ƙara mata jin abun da take ji a cikin ranta, ta yi saurin janye nata idon saboda wasu abubuwa da take gani suna shiga nata idon daga nasa masu kaifi suna ƙoƙarin fasa mata zuciya. Ta lumshe idonta a hankali hawaye ya zubo daga cikinsu tare da ƙoƙarin cire hannunsa daga kan fuskarta saboda yanda ta ga yana yi mata wani irin kallo da ya kashe mata jiki. Ya shafi kuncinta cikin sanyin murya ya ce. "Cry cry baby, kukan barin gidan Mama ne ko na zuwa gidan Ameen?" Ta turo baki tare da cire hannunsa daga fuskarta, amma ko 2 second ba'a yi ba ta ji hannun nasa a gefen wuyanta yana shafawa cikin wani irin salo, hakan yasa ta ji tsigar jikinta ta fara tashi, wani abu da bata san ko mene ma yana yawo a cikin jikinta, kawai sai ta saka kuka tare da ja baya, yanayin da zuciyarta da gangar jikinta suke ciki bazai misaltu ba, ta rasa ya zata yi, ta rasa ina zata saka kanta. A hankali ya ce. "God! Kukan dai miemerh, Please ki daina kukan nan, na ji jikinki da zafi kar zazzaɓi ya rufe ki, kuma na san wannan kukan da kika sha kanki sai ya miki ciwo." Cikin shagwabarta ta ce. "Ni bacci nake ji." Ya ɗan yi murmushi sannan ya miƙe ya ce. "Ni kuma na hana ki ko? To ki bar kukan haka, indai ni ne na tashi, amma kafin ki kwanta ya kamata ki ci wani abu ki sha magani." Ta turo baki ta ce. "Ni na ƙoshi bacci kawai zan yi." Bai ce komai ya matsa daf da ita sannan ya ɗora goshinsa akan nata ya ɗora hannunsa a ƙirjinta saitin zuciyarta ya ce. "Wannan bugun zuciyar duk na tsoron mene ne?" Ta ja wani gwauron numfashi ta sauke tana jin abun da bata taɓa ji ba a tsahon rayuwarta a dalilin kusancin da suka samu, ga ƙamshinsa dake ƙarawa zuciyarta hauhawar yanayin da take ciki. Ta runtse idonta numfashinta na fita da sauri da sauri. Ya janye fuskarsa daga ta_ta, yana kallon tsoro ɓaro_ɓaro akan fuskarta_ta, ajiyar zuciya ya saki a hankali tare da jan gwauron numfashi. Ta ƙara jan mayafinta ta lullub'e jikinta. Ya yi murmushi kawai wanda ya kasa b'acewa daga fuskarsa tunda ya shigo ɗakin sannan ya juya ya fice. Ta sauke ajiyar zuciya tare buɗe fuskarta ta bi ƙofa da kallo, a ranta tana mamakinsa yanda yake mata magana da wasu abubuwan. Bayan kamar 15 minutes ya dawo ɗakin, saurin rufe idonta ta yi tana keɓe fuska, ya ajiye ledodin hannunsa sannan ya juya ya ƙara fita, bai jima ba ya dawo hannunsa ɗauke da tire da glass cup da fork. Ya d'auko kaza ɗaya dake cikin ɗaya daga cikin ledodi biyun da ya ajiye ya saka a cikin tiren sannan ya kalle ta ya ce. "Oya come and eat." Ta mak'e kafaɗa alamar a'a. Ya miƙe ya ce. "Okay, idan baki sauko ba kin san dai baza ki gagare ni ɗauka ba ko?" Jin haka yasa ta buɗe idonta da sauri tare da ja baya, kamar zata yi kuka ta ce. "Ni fa Yaya na ƙoshi Allah." Ya kalle ta na wasu sakanni ba tare da ya yi magana ba ya tunkari gadon, da sauri ta sauko tana cize lip saboda ciwon kai idonta cike fal da hawaye. Ta zauna a gaban tiren tana turo baki gaba. Ya dawo ya zauna shi ma a kusa da ita, ba tare da ya yi magana ba ya saka fork ya gutsiro naman ya kai bakinta, ta kawar da kanta gefe, ya saka hannu ya juyo da fuskarta tare da haɗe da rai yana yi mata kallon warning. Ganin babu wasa a fuskarsa ta buɗe bakinta ya saka mata tare da fara hawaye. A kausashe ya ce mata. "Ki haɗiye mun wannan kukan naki, karki bari hawaye ya ƙara zubowa daga idonki." Ba shiri ta haɗiye kukan amma cikin ranta ji take kamar ta fasa ihu. Duk yanda take ɓata fuska da turo baki bai saka ya daina ya bata ba sai da ya tabbatar ta ƙoshi, ita kanta ta san tana jin yunwa, amma yanda take jin kanta na sara mata babu abun da take buƙata a yanzu sama da bacci. Fresh milk ɗin da ya zo da ita a ɗayar leda ya d'auko ya tsiyaya ya bata, ta kurb'i kaɗan ta ajiye, yay mata wani kallo alamar ta d'auka ta ƙara sha. Ta saka kuka ta ce. "Yaya cikina fa zai fashe." Ya yi murmushi tare da kai hannu saitin cikin ya ce. "Mu ji ta inda zai fashe ɗin." Ta ture hannun nasa tana cigaba da kukan nata. Ya janyo ta jikinsa a hankali tare da kwantar kanta akan kafaɗarsa ya ce. "Kuka, kuka dai Miemerh? I know baki ci wani abincin kirki ba yau saboda hada_hada, ta yaya zan barki ki kwana da yunwa? ko so kike Mamanki ta sab'ar mun? Baki san warning ɗin data ja mun a kanki ba ne shi yasa." Ta yi shiru bata ce komai ba sai ƙoƙarin tashi da ta yi daga jikinsa, bai hana ta ba har ta miƙe ta haye kan gado. Tana ƙoƙarin kwanciya ya miƙe ya ce. "Ta so mu je ki ga gidan naki kafin ki yi bacci." Ba musu ta miƙe ta ja mayafinta ta yafa ta sauko daga kan gadon saboda ita ma bata so daga cin abincinta ta kwanta ba, shima kuma nasa nufin kenan." Ya kama hannunta ta k'wace, ya ƙara riƙewa, ta kalli fuskarsa ya harare ta, ta ɗauke idonta da sauri tare turo baki. Ko ina a gidan sai da ya kai ta ya nuna mata, tsarin gidan ya yi mata kyau sosai kuma ya burge ta. Sannan ya raka ta, ta koma nata ɗakin. Suna shiga ta nufi kan gado. Ya ce. "Kin yi Sallah ne?" Ta gyaɗa masa kai. Ya ce. "Wanka fa?" Ta ce. "Na yi shi ma." Ya ce. "Ki sake wani, sai ki fi jin daɗin baccin." Bai jira amsarta ba ya d'auki tiren da ta ci kaza da sauran kayan gurin ya juya ya fice. Ta turo baki ta yi kwanciyarta. Mintuna kaɗan sai gashi ya dawo ɗakin, bai ce mata komai ba ya shige toilet hannunsa ɗauke da soap da soso, ya ajiye su sannan ya kunna mata heater. Ya fito yana duban ta ya ce. "Ki tashi ki yi wankan kar bacci ya ɗauke ki." Ta tashi tana babbata fuska ta shiga toilet ɗin. Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juya ya fita..........✍️ _*I'm sorry, na san kuna ta jirana, tun rana na yi typing amma network ya ban matsala, sai yanzu na samu ya yi. Thank you so much masoyan Neehal, ina jin daɗin yanda kuke k'aunar book ɗin nan, masu mun magana a PC da masu kirana da masu magana a group suna cikiya ta ina godiya sosai da kulawa, alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke masoyana na.😘🥰😍*_ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _*By*_ _*Zeey Kumurya*_ *8️⃣1️⃣* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ..........Tana mita a ranta an saka ta wanka alhalin bata dad'e da yi ba sai ka ce wata kwad'uwa ta yi wankan ta gama. Sai kuma ta ji jikinta ya yi mata daɗi, ta ɗauki zanin data cire ta d'aura ta yafa d'ankwalin kayan akanta ta fito. Ganin baya nan ta saki sassanyar ajiyar zuciya tare yin sauri ta ƙarasa ta yi locked ƙofa. Ta dawo ta zauna a bakin gado ta janyo jakar da Haneefa ta ajiye mata ta buɗe dan duba abun da zata sakawa jikinta mara nauyi dan baza ta iya bacci da atamfa ba. Wasu kayan bacci ta fara cin karo da su riga da wando, rigar idan ta saka ta ko cibiya baza ta rufe mata ba, wandon kuwa ba shi da maraba da pant, ga kayan sharara, ta ɗaga su a hannunta tana kallon su cikin takaici, bata ma san time ɗin da Haneefah ta sako mata su ba, watsar da su ta yi a gefe tana jan tsaki. A fili ta ce. "Wa ake tunanin zai saka wannan kayan? Ba dai Neehal ba." Ta cigaba da duba jakar, Allah ya taimake ta ta samo wata doguwar rigar bacci mai ɗan santsi. Ta ajiye ta a gefe sannan ta mayar da kayan data fito da su ta yi zipping jakar ta rufe. Cikin sauri ta zira rigar ta ɗaura zanin jikinta akai, sannan ta tashi ta kashe light ɗin ɗakin ta kwanta tare da lumshe idonta. A ranta tana mamakin yau ita ce zata yi bacci akan gadon gidan Aurenta, ta ƙara yarda komai yana da lokaci a rayuwa. Bacci ya ɗan fara fizgarta kamar a mafarki ta ji ya buɗe ƙofa ya shigo, ta buɗe idonta da sauri gabanta na faduwa amma bata motsa ba. Ya kunna light hakan yasa ta yi saurin mayar da idonta ta rufe. Da alama shi ma wanka ya yi, dan ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya ash colour. Ya ƙaraso bakin gadon ya zauna tare da ɗora hannunsa a goshinta ya ce. "Jikinki da zafi har yanzu, ki tashi ki sha magani." Ta ƙudundune jikinta guri ɗaya tare da buɗe idonta kaɗan ta ce. "Bacci nake ji, idan na yi bacci zan ji ni normal." Bai ce komai ba ya tashi ya fita ba tare da ya kashe mata light ɗin ba, ta bishi da kallo sannan ta lumshe ido ta koma baccin dake cin ta. Ya ɗan jima sannan ya dawo ɗauke da sabon duvet, ya lullub'a mata a jikinta sannan ya je ya rufe ƙofa ya dawo ya kashe light ya kunna bedside lamp. A hankali ya hau kan gadon ya kwanta ya shiga cikin bargon tare da janyo ta jikinsa, ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da lumshe idonsa yana ƙara cusa fuskarsa a jikinta dan sosai ƙamshin jikinta ya yi masa daɗi tare yin tasiri a gare sa. Ta motsa tare da buɗe idonta a tsorace saboda yadda ya ƙwaƙume ta a jikinsa, dama baccin ba wani nisa ya yi ba. Ta zare jikinta da sauri ƙirjinta na dokawa a million ta tashi zaune tana keɓe fuska kamar zata yi kuka. Ya ɗan ɗago yana kallon fuskarta ta cikin ɗan hasken bedside lamp, shi dariya ma ta bashi yanda ta yi da fuska kamar wadda ta ga dodo ko fatalwa saboda tsoro. Ya kama hannunta a hankali ya ce. "What happening?" A shagwabe ta ce. "Bacci fa nake ji sosai, dan Allah Yaya ka koma ɗakinka ni bazan iya bacci kana nan ba." Ya janyo ta gaba-d'aya ta faɗa jikinsa ya saka hannunsa ya matse ta, yana jin yanda jikinta yake rawa saboda tsoro. Ɗayan hannun nasa ya kai kanta ya shiga shafa gyararren gashin kanta slowly. Dai-dai kunnanta ya kai bakinsa ya ce. "Relax, babu abun da zan miki." Ta buɗe baki zata yi magana ya hana ta ta hanyar ɗora finger ɗinsa akan lips ɗinta ya ce. "Shiiiii.....Just sleep." Ta turo baki tare da lumshe idonta tana sakin ajiyar zuciya a hankali. Mamakin Ameen take ba kaɗan ba, ko kaɗan bata yi tunanin zai kalli ɗakin da take ba ma a yau a yanda yake nuna mata a baya balle har ya shigo su kwana tare, shi yasa babu fargaban hakan ko kaɗan a ranta, amma yanzu ya dasa mata fargabar, sai faman mammatse jikinta take guri ɗaya kamar wacce take kwance kan a ƙaya, a matuƙar tsorace take sai faman jan numfashi take tana saukewa. Saboda tarin gajiya da ciwon kai da baccin dake kanta cikin mintuna ƙalilan bacci ya kuma ɗauke ta ba tare data sani ba. Ajiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta, ya ɗan rabata da jikinsa tare da gyara mata kwanciyarta, ta wani dunk'ule jiki kamar dafaffiyar kaza. Ya tsurawa fuskarta ido yana sakin murmushi shi kaɗai, yanda yake jin kansa a yau ba zai misaltu ba, sosai yake cikin farin ciki da nishad'i gami da annashuwa. Ya saka finger ɗinsa guda ɗaya yana zagaye lips ɗinta da shi, zabura ta yi amma bata farka ba, ya ƙara yin murmushi ganin gaba-d'ayanta a tsorace take. Imagine yanda bata jin daɗin jikinta a yanzu ya yi mata wani abu, ya san idan bata fasa masa kunne da ihunta ba to sai an jiyo kukanta a mak'wabta. Yanda take uwar raki, ko yaya ciwo yake ta yi ta kuka kenan, ina kuma ga ya yi mata abun da ya san dole sai ta ji jiki. Bai san tsawon lokacin da ya ɗauka yana kallon ta tare shafa kanta zuwa fuskarta ba cikin shauƙi, a haka dai bacci ya ɗauke shi. Da asuba kusan makara suka yi saboda dukkan su da tarin gajiya a jikinsu. Ameen ne ya fara tashi lokacin har an shiga Sallah, ya tashe ta sannan ya shiga toilet ya yi alwala a gaggauce ya tafi masallaci. Daƙyar ta iya tashi dan ji ta yi kamar ta koma ta cigaba da baccin, dan bai ishe ta ba. Ta dai cize ta tashi ta shiga toilet ta yo alwalar ta fito ta ɗauko hijabi a cikin jakar kayanta ta zira ta tayar da Sallah. Bayan ta idar ta ɗauko wayarta a cikin hand bang ɗinta ta yi karatun Alkur'ani tare da azkar ɗin safe, Alhamdulillah ta ji sauƙin jikin nata da ciwon kan sosai. Har gari ya fara haske bai dawo daga Masallacin ba, ta miƙe ta yi locked ƙofa sannan ta kwanta ta koma baccinta. Bata jima da kwanciya ba ya dawo gidan, duk abun da ya san zata buƙata na toilet ya kwaso ya kawo mata, sannan ya cire jallabiyar jikinsa ya hau kan gadon ya jawo ta jikinsa suka cigaba da baccin tare. Wannan karon ta riga shi tashi. Ta buɗe idonta a hankali ta sauke su akan kyakkyawar fuskarsa, baccinsa yake yi hankali kwance. Ta zame jikinta daga nasa a hankali ta tashi zaune, a lokacin ta gane babu riga a jikinsa, ta ƙurawa faffaɗan ƙirjinsa dake ɗauke da farar fata da kwantaccen ƙananun gashi ido. Sai ta ji kamar ta kai hannu ta shafa su amma sai ta kasa. Jin ta take kamar a mafarki, wai yau ita ce kwance gado ɗaya da yayanta akan ƙirjinsa? Abun har yanzu bai daina bata mamaki ba. Ta yunkura da nufin ta sauka ta ji ya riƙo ta, ta kalli fuskarsa da sauri ta ga still idanunsa a rufe suke. Ta yi ƙoƙarin k'wace jikinta ya buɗe idanunsa dake lumshe saboda bacci ya ce. "Where are you going?" Ta yi ƙasa da kanta cikin kunya a ranta tana addu'ar Allah yasa bai san ta tsaya kallon shi ba. A hankali ta ce. "Toilet." Ya jawo ta jikinsa ya ce. "Me zaki yi?" Ta yi shiru tana rarraba ido cikin tsoro kamar ace kyat ta ruga da gudu. Ya shafi saman idonta ya ce. "Matsoraciya." Sannan ya sake ta. Ta ɓata fuska tare da sakin ajiyar zuciya ta sauka daga gadon. Tana mitar abubuwan da yake mata a ranta, fargaba fal a cikin ranta na kar abun ya wuce haka. Sai ta fara tambayar kanta 'anya kuwa Yayanta data sani a da shine na yanzu? Wannan kamar ba Yayanta ba an canza mata wani' ga abubuwan da yake mata ko kunya ba ya ji, ko dama haka mazan suke ba su da kunya ne? Ta yi mamakin ganin sabon toothpaste da brush da robar jower jel da takarcen sabulan wanke toilet na ruwa, sai kuma sabbun towels guda biyu an yi hanging ɗin su a cikin toilet ɗin. Brush kawai ta yi ta fito, tana son yin wanka amma bata san a yaya zata iya fitowa idan ta yi wankan yana ɗakin ba, sai kawai ta yi fitsari ta wanke toilet ɗin duk da babu dattin komai a cikinsa ta fito. Ta tarar baya ɗakin ya fita sai mayen ƙamshinsa mai kama guri, gaba-d'aya ya gama ɗakin. Cikin murna ta koma cikin toilet ɗin ta yi wanka tana addu'ar Allah kar ya dawo da shi ɗakin har sai ta gama shiryawa. Adduarta ta karɓu kuwa, har ta gama ta fito ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa bai dawo ba, tana cikin d'aura ɗankwali ya shigo ɗakin da sallama, ta amsa masa ba tare da ta juya ta kalle shi ba. Ya tsaya a kanta yana kallon ta har ta ƙarasa ɗaurin nata. Cikin sanyin murya ta ce "Ina kwana?" Bai amsa ba sai tsugunnawa da ya yi a gabanta tare da lek'a fuskarta ya ce. "Kwalliyar ce ba'a son in gani ake boye mun?" Ta rufe fuskarta da hannunta zuciyarta ta fara bugun da take yi mata a duk lokacin da suka yi over close. Ya cire hannun nata ya matsar da fuskarsa daf da tata ya ce. "Wai wannan wacce irin kunya ce da ta ƙi ƙarewa? Ko sai na yi maganinta ne?" Ta shagwab'e fuska tare da turo baki gaba. Ya ƙurawa lips ɗin nata ido, a hankali kuma ya ɗora nasa soft lips ɗin akan nata, bata yi aune ba ta ji ya haɗe bakunansu guri guda ya shiga bata hot kiss. Abun ya zo mata a bazata hakan yasa lokaci ɗaya jikinta ya d'auki rawa, gaba-d'aya ta ƙara firgicewa da al'amarin sa, amma duk da haka sai da sak'onsa ya ratsa dukkan jikinta, ta dinga jin wani irin abu tun daga kanta har tafin ƙafarta yana yawo a cikin jininta. Yanda yake kissing ɗin nata kamar zai cinye mata baki shi yake ƙara tsorata ta, ta yi ƙoƙarin k'wace kanta amma ta kasa, ƙara jawo ta jikinsa ma ya yi alamun ba shi da niyyar bari. Ƙarar knocking ƙofar parlour ce tasa ya sake ta a hankali yana sauke numfashi gami da ajiyar zuciya. Runtse idonta ta yi tana jin kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya, ita kam ta ga ta kanta Ameen zai kashe ta da wannan abubuwan da yake mata. A kasalance ya tashi ya fita daga ɗakin idanunsa har sun fara sauya kala. Ta buɗe idonta a hankali tana jin lips ɗinta kamar har yanzu suna cikin bakinsa, ta kai hannu ta shafa lips ɗin nata tare da lumshe idonta, tana jin jikinta kamar ba nata ba. A hankali ta tashi ta ɗauko wayarta ta duba time, ƙarfe goma sha ɗaya saura na safe ta gani. Gyaran ɗakin ta shiga yi bayan ta gama ta fita da niyyar gyara falo suka ci karo da Ameen. Ya kama hannunta ya ce. "Mu je mu yi breakfast Mamanki ta kawo mana abinci." Ta yi ƙasa da kanta kewar Mama na ƙara cika mata zuciya, cikin sanyin murya ta ce. "Waya kawo breakfast ɗin?" Ya shafi kuncinta ya ce. "One of our soldiers staff." Bata kuma magana ba ya ja hannunta suka ƙarasa tsakiyar falon inda abincin yake akan Centre Carpet. Har ya d'auko plates da cups da spoons da kayan tea duk ya ajiye a gurin, tana mamakin yanda yake ɗauko mata duk abun da ya san zata buƙata in time tun kafin ta yi yunk'urin ɗaukowar, Shi da a gida komai sai dai a ɗauko masa yana daga zaune. A ranta ta ce. 'Ko Matarsa yakewa hakan shi yasa itama yake mata.' Haka kawai ta ji gabanta ya fadi tunowa da ta yi da Hafsat..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _*By*_ _*Zeey Kumurya*_ *8️⃣3️⃣* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ .........Saurin yin ƙasa da kanta ta yi daga kallon sa tare da amsa masa sallamarsa. Ya ajiye ledodin hannunsa a gaban gadon sannan ya zauna a kusa da ita. Ba tare data kalle shi ba ta ce. "Sannu da zuwa." Ya amsa mata a can ƙasan mak'oshi, sannan cikin kulawa ya ce. "Kin ci abinci?" Ta ce. "Eh." Ya ce. "Na dare fa nake nufi bana rana ba." Ta girgiza masa kai alamar a'a. Ya ce. "Okay sakko mu ci wannan." Ya yi maganar yana nuna ledodin gabansu. Ta ce. "Akwai sauran abincin da Mama ta kawo fa." Ya ce. "Mu je ki bani na kaiwa mai gadi sai mu ci wannan ɗin." Ta miƙe ba tare da ta yi magana ba ya bi bayanta. Abincin duka ta juye masa sannan ta ɗauko plates da cup da spoon kamar yadda ta ga ya yi jiya. Sai a lokacin ta tuna data tashi yau da safe ba ta ga ragowar kazar jiya ba. Ta kai kayan ɗakinta ta zauna jiransa, mintuna kaɗan ya dawo, ya zauna a ƙasan gado ya janyo ledar kazar ya ce. "Me kike jira baki fara ci ba?" Ta nuna masa kansa da hannunta, tana ƙoƙarin sarving ɗinsu ya katse ta da faɗin. "I forgot something." Ta kalle shi da alamun tambaya, ya ce. "Je ki yi alwala." Ta ce. "Na yi Sallah fa." Ya ce. "Wata zamu sake." Ba tare da tunanin komai ba ta je ta yo alwalar, kafin ta fito har ya shimfid'a musu darduma. Ya miƙe bayan ta saka hijabinta ya ja su suka yi Sallah raka'a biyu, ya dad'e yana yi musu addu'ar zaman lafiya da wanzuwar farin ciki a rayuwar auransu a cikin sujjadarsu ta ƙarshe. Bayan sun idar ya kama kanta ya yi mata addu'a kamar yadda ma'aiki (S. A. W) ya koyar da mu ga sabbun ma'aurata, sannan ya umarce ta data yi masa shi ma kamar yadda ya yi mata. Bata yi musu ba ta yi masan, ya ce su je su ci kazar. Tare suka ci amma wannan karon bai bata a baki ba, ko taɓa ta bai yi ba bai nuna alamar ma zai yi hakan ba, hakan yasa ta ji daɗi amma duk da haka a takure take jin ta, masifar tsoron da take ji a ɗazu ne dai ya ɗan ragu tun da ta ga bai yi mata komai ba tunda ya shigo ɗakin. Bayan sun gama tana tattare kayan ta ce. "Jiya ya ka yi da ragowar kazar nan?" Ya ce. "Tun a daren na kaiwa mai gadi." Ta gyaɗa masa kai sannan ta fice da kayan. Sai da ta dauraye su sannan ta komo ɗaki, ta tarar ya fita baya ɗakin. Ajiyar zuciya ta saki ta jin daɗi sannan ta rufe ƙofar ɗakin, toilet ta shiga ta yi ƴan uzurarrikanta, ta fito ta cire kayan jikinta ta saka wani riga da wando masu taushi na bacci, ta mitsitsika humra a jikinta kamar yadda mai gyaran jikin da ta yi mata ta ce tana yi duk dare sannan ta kashe light ɗin ɗakin ta kwanta ba tare da ta kunna bedside lamp ba. Bacci take ji sosai, ta bararraje akan gado tana murna a ranta zata yi baccinta cikin kwanciyar hankali babu fargaba da tsoron komai a ranta. Sai dai ko 5 minutes ba ta yi da kwanciyar ba ya turo ƙofa ya shigo, a lokacin bacci ya ɗan fara ɗaukar ta. Ta buɗe idonta a hankali gabanta na fad'uwa. Kunna torchlight ɗin wayarsa ya yi ganin ɗakin da duhu, ta yi saurin runtse idonta tana addu'ar Allah yasa idan ya ga bacci take ya k'yale ya koma ɗakinsa. Shi kam dama abun da yake so kenan, so yake ta saki jikinta sai ta sakankance sai ya dawo ɗakin. Ya ɗan tsaya yana haska ta sannan ya hau kan gadon ya yaye bargon data rufe jikinta da shi. Tana jin shi ta ƙi motsawa duk dan ya yi tunanin bacci take. Ya haske fuskarta yana murmushi cikin sanyin murya ya ce. "I know you are not sleeping." Ta buɗe idonta kaɗan tana kare fuskarta da hannunta bata ce komai ba. Ya matsar da wayar daga saitin fuskarta sannan ya matsa jikinta ya saka hannunsa akan lallausan gashinta ya fara shafawa a hankali. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali tare da lumshe ido saboda yanda ƙamshinsa yake ratsa k'ofofin hancinta, a shagwab'e ta ce. "Yaya I want to sleep." Ya ajiye wayar hannunsa sannan ya ɗauki kanta ya ɗora akan cinyarsa, cikin wata irin murya da idan da za'a ce mata Yayan nata yana da ita baza ta yarda ba ya ce. "Ni kuma tunanin ki da san kasancewa dake ya hana ni bacci *Baby love*." Saboda tsananin mamaki bata san lokacin data buɗe idonta cikin sauri ta kalle shi ba, dan tabbatar da abun da ta ji ba kunnenta ne ya jiye mata ba dai-dai ba. Ya ja kumatunta tare da kashe mata ido ya ce. "It's so amazing ba?" Ta yi shiru kawai tana kallon shi. Ya yi murmushi, sannan ya rank'wafar da fuskarsa daf da ta_ta, cikin murya mai kama da rada ya ce. "Na san zaki yi mamaki idan na ce miki am in love with you tun lokacin da ban san menene so ba, ban ma san me kalmar son take nufi ba, lokacin kina only 5 years a duniya da muka zo gidanku da Mama kika zo kina mun ihu a cikin kunnena. Tun ranar tunanin ki yake manne a cikin raina, da shi nake kwana nake tashi. Sometimes sai in zauna ni kaɗai idanuna a lumshe ina hango ki a cikin raina kina yiwa Aunty shagwab'a ko kuma kina surutunki ko kuka da tsalle_tsallenki, sai in ji ina son na kuma ganinki, a lokacin ban gane ma'anar hakan ba sai daga baya na fahimta. Duk yanda zan miki bayanin yanda soyayyiyar ki ta azabtar dani baza ki gane ba Miemerh, amma dai na sha wahala. Bayan Allah ya yiwa su Abba rasuwa kin dawo hannunsu Mum da zama bazan iya kwatanta miki farin cikin da na ji ba a wannan lokacin, na tabbata ko Mum bata kai ni farin ciki da hakan ba, tunda ko ba komai idan na zo gida duk weekend zan gan ki in ji daɗi a raina. Dalilin da yasa ban bayyana miki soyayyata a gare ki ba a lokacin da ya dace, da na yiwa Daddy maganar ina sonki sai ya nuna mun in bar maganar dan bazai bani ke ba, ban kuma san dalilinsa na faɗar hakan ba har yau. Na haqura da maganar ko Mum ban faɗawa ba, ba kuma wai dan na daina son ki ba ne, ko kaɗan soyayyar ki bata ragu ba a cikin zuciyata sai ma ƙaruwa da take yi, saboda in yiwa Dad biyayya ne kawai na haqura." Ya yi shiru na wasu sakanni yana goga mata sajen fuskarsa a kuncinta sannan ya cigaba da magana. "FATEEMAH....! I LOVE YOU WITH ALL MY HEART, I LOVE YOU MORE THAN WORD CAN EXPLAIN, I LOVE YOU MORE AND MORE NEEHAL." Ta lumshe idonta tana jin ta kamar a cikin gajimare saboda wani irin shauk'i from no where da yake mamaye dukkan zuciyarta, an sha faɗa mata kalaman soyayya babu adadi a rayuwarta, an furta kalmar *i love You* babu adadi, amma bata taɓa jin waɗanda suka yi tasirin da wanda Yayanta yake faɗa mata a yanzu ba a cikin zuciyarta. Kalamansa sun ratsa dukkan zuciya da gangar jikinta. Ta ji kamar ta ce ya cigaba da yi mata kalaman kar ya daina. Hannunsa ta ji yana dawo a sassan jikinta cikin wani irin salo da yasa ta ji kamar jinin jikinta zai tsinke ya tsiyaye. Ya ƙara yin ƙasa muryarsa bakinsa akan kunnenta ya ce. "Baki ba zai iya faɗar irin tarin k'aunar ki dake cikin raina ba saboda yawanta, but i want to show you ta yadda zaki gamsu ki tabbatar da abun da nake faɗa miki." Ya ja numfashi tare da lumshe idonsa ya ɗora bakinsa akan nata, a tare suka saki wasu tagwayen sanyayan ajiyar zuciya. Cikin lokaci ƙanƙani Ameen ya juye mata daga wanda ta sani zuwa wani daban, sarrafa ta yake cikin wani irin salo mai tsayawa a rai da wuyar mantawa cikin k'warewa da nutsuwa. Da farko sak'onnin nasa sun fara tasiri a kanta, daga baya da ta ga yana ƙoƙarin kaiwa ga abun da take matuƙar tsoron faruwarsa sai ta fara ƙoƙarin k'watar kanta tare da saka masa kuka, amma ina bai gane wannan yaren ba, inda yake son zuwa kawai yake hanqoro. Bata ƙara firgicewa da al'amarinsa ba sai da ta ji yana karanta addu'ar data san mana'arta da dalilin da yasa ake yin ta, ta fara ture shi tana dukan duk inda hannunta ya kai a jikinsa a ƙoƙarinta na son ya k'yale ta amma bai ma san tana yi ba, burinsa kawai yakai inda ransa yake da murad'in zuwa. Duk yadda Haneefah ta dinga kwatanta mata wahalar abun ta ji fiye da hakan, sai da ta yi tunanin baza ta farka ta gan ta a duniya ba saboda azabar da ta sha, Mama da Daddy da duk sunan wanda ya zo bakinta sun sha kira da neman agajinsu, kuka kam har sai da muryarta ta dashe saboda yin sa......... Bayan komai ya lafa tana kwance a ƙirjinsa ya yi mata kyakkyawar runguma kamar zai mayar da ita ciki, idanunsa a lumshe ya cusa kansa a cikin gashin kanta yana shaƙar ƙamshin gashin, hannunsa ɗaya yana kan gadon bayanta yana shafawa a hankali cikin sigar rarrashi. Ita kuma ban da hawaye da sakin ajiyar zuciya babu abun take. Jikinta gaba-d'aya ciwo yake mata, ko ɗan yatsanta bata tunanin zata iya d'agawa. Sassauta riqon da ya yi mata ya yi ya ɗago fuskarta cikin tsananin tausayinta da k'aunar ta ya ce. "Please Miemerh ki bar kukan nan haka, zaki ƙarawa kanki wani ciwon fa." Ta cinno masa baki kamar zata yarda shi a ƙasa ta bar jikinsa cikin dauriya tare da juya masa baya tana ƙara ƙanƙame bargo a jikinta ta cigaba da kukanta. Ya yi murmushi kawai sannan ya tashi zaune, yau jin zuciyarsa yake fess tamkar wani baƙin ciki bai taɓa wanzuwa a cikinta ba saboda farin cikin da ya cika ta, yanda yake jin kansa cikin nishad'i da annashuwa ba zai misaltu ba. Jallabiyarsa ya lalubo ya zira a jikinsa sannan ya miƙe ya kunna light ya shiga toilet, bayan wasu mintuna ya fito ya hau kan gadon ya kama bargon jikinta da nufin ya yaye shi. Ta ƙanƙame bargon idanunta a runtse tana ƙara volume ɗin kukanta, ita kaɗai ta san azabar da take ji a cikin jikinta, jin cikinta take kamar an yi mata yasa, ƙafafuwanta kuwa kamar ba'a jikinta suke ba, ƙasanta kamar an jajjaga mata attaruhu a gurin saboda radad'in da yake mata. Ya rank'wafa ya ce. "Baby wanka zan miki fa." Ta ture fuskarsa da hannunta ta ƙara juya masa baya, wata irin kunyarsa ce ta ninku a cikin zuciyarta akan wadda take ji a da. Bata ankara ba sai ji ta yi ya ɗauke ta cak ita da bargon. Ƴar ƙara ta saki saboda ji ta yi kamar ya fama mata ciwon jikinta, ya rungume tsam yana rarrashinta sannan ya miƙe da ita a jikinsa ya kai ta toilet ya ajiye ta a cikin tub bayan ya zare bargon jikinta. Zabura ta yi ta ruk'unk'ume shi kamar zata janyo shi cikin tub ɗin saboda azabar data ji tana ratsa ta a sakamakon jin ta da ta yi a cikin ruwan zafi. Ya riƙe ta ya mayar da ita cikin ruwan ganin tana ƙoƙarin miƙewa. Sannu kawai yake jera mata cikin kulawa da soyayya, ita kuma sai taɓara take zuba masa, sai dai ta ƙi bari ta buɗe idonta ta kalle shi. Sai da ruwan ya huce sannan ya fita ya bar ta dan ta yi wankan tsarki. Ya dawo ɗakin ya cire zanin gadon ya sake wani sannan ya fice daga ɗakin ya je ɗakinsa ya yi wanka ya dawo. Ta ji sauƙin radad'in da gurin yake mata sanadiyyar ratsa ta da ruwan zafin ya yi. Bayan ta yi wankan, ta fito daga cikin tub ɗin daƙyar, a lokacin ya dawo toilet ɗin. tsugunnawa ta yi da sauri tana dunk'ule jikinta guri guda tare da fashewa da kuka. Ya dafe kansa a ransa yana faɗin 'Yau fa sai Allah Neehal da kuka, dama yaya lafiyar kura bare kuma ya taɓo ta.' Towel ya ɗauko ya ɗaura mata duk da daƙyar ta bar shi ya ɗaura matan wai ita bazai ga jikinta ba, sannan ya lullub'e mata kanta da wani ya ɗauko ta suka fito ya kwantar da ita ya shiga tsane mata kanta da towel. Sai da ruwan gashin nata ya ɗan tsana sannan ya kwanta ya janyo ta jikinsa ya ce. "Please Baby ki bar kukan nan mana, ko so kike zuciyata ta fashe ne?" Cikin kuka ta ce. Ni ka kai ni gurin Mama mutuwa zan yi." Ya shafi pink lips ɗinta ya ce. "Wai gurin da zafi ne sosai?" Shiru ta yi masa a ranta tana cewa. 'Dan ba jikinka ba ne ai.' Ya kai hannu ƙasan mararta ya ce. "Mu ji ya gurin yake." Ture hannun ta yi da sauri ta matse ƙafafuwanta. Ya ƙara rungume ta a jikinsa ya ce. "Gani fa zan yi ko da ciwo a gurin." Ta fashe da kuka sosai ganin shi nishad'in shi ma yake ita ya bar ta da jin azaba a jikinta, Cikin kuka ta ce. "Kuma sai na haɗa ka da Mama." Yana dariya ƙasa_ƙasa ya ce. "Me zaki ce mata ƴar gidan Mama?" Shiru ta yi masa ta cigaba da kukanta, ya yi murmushi sannan ya shiga rarrashinta, cikin lokaci ƙanƙani bacci ya dauke ta. Ajiyar zuciya ya sauke tare da gyara mata kwanciya. Ya shiryawa dukkan wata rigimarta dan ya san dole ya sha ta a wannan stage ɗin tunda ya siya da kuɗinsa. Ya lumshe idonsa d'umin jikinta na ratsa shi yana saukar masa da nutsuwa, bai san sanda shi ma baccin ya yi awun gaba da shi ba.......✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _*By*_ _*Zeey Kumurya*_ *8️⃣2️⃣* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ .........Da kansa ya haɗa mata tea cikin cup, ya zuba mata Irish da soyayyiyar waina ƙwai a cikin plate, ya ɗora bread a kai bayan ya shafa mata jam a jikinsa. Kallonsa kawai take yanda yake yin komai cikin natsuwa, ta dunk'ule jikinta guri guda gaba-d'aya ta kasa sakewa. Ya ɗago ya kalle ta fuska a sake ya nuna mata cinyarsa tare yi mata alamar ta je ta zauna akai. Ta waro ido tare da ɗauke kanta kamar bata gane me yake nufi ba. Ya matso kusa da ita a hankali ya daga ta cak ya ɗora ta akan cinyar tasa. Ta fara mutsu_mutsu tare da ƙoƙarin sauka daga jikinsa, ya riƙe ta sosai tare da juyo da fuskarta ya zuba mata narkakkun idanunsa a cikin nata, ba shiri ta lumshe nata idon ƙirjinta ya fara bugun da ya saba. Ya shafi gashin girarta tare da ƙara gyara mata a jikinsa. Gaba-d'aya sai ta rikice ta fara ƙoƙarin yi masa kuka, ko da wasa ta ƙi buɗe idonta saboda tsoron kar su ido. A hankali ya cusa kansa a wuyanta yana shaƙar ni'imtaccen ƙamshin jikinta. 'Ya Allah, wannan bawan naka zai kashe ni da raina, wannan abun kunyar har ina?' Ta faɗi haka a ranta. Rawar da jikinta ya fara yi ne yasa ya ɗago da kansa daga jikinta, murya ƙasa ƙasa ya ce. "Ni fa bana son wannan tsoron da kunyar sun ishe ni haka." Ta tura masa baki tare da ɓata fuska. Ya ce. "Okay, I know how I treat you tsoro da kunyar su tafi." Ya karashe zancen tare da kai hannunsa bayanta ya fara jan zip ɗin rigarta ƙasa. Saboda dimauta bata san sanda ta ƙanƙame shi ba tare da sakin kuka, sosai ta rikice, al'amarin Ameen ya girmewa kwanyarta. Ya tsaya da abun da yake yi yana murmushi ya ja karan hancinta bai ce komai ba. Juyar da ita ya yi yana faɗin. "Let us eat first, sai mu fi samun full energy." Ta zame ta sauka daga jikinsa da sauri tare da ƙoƙarin tashi, a nufinta ta ruga da gudu ta koma ɗaki. Ya kama hannunta tare da mayar da ita ta zauna akan cinyarsa. Ya ɗora kansa akan kafaɗarta yana kallon gefen fuskarta ya ce. "Common, wai wannan abun da kike yi na mene ne? Wannan Ameen ɗin fa ba Yayanki ba ne Mijinki ne?" Ta marairaice fuska ta ce. "Ni dai dan Allah ka barni in zauna a ƙasa." Ya ce. "Yanzu a sama kike?" Ta yi shiru tana ƙara marairaice fuska, shi bai san me take ji a jikinta ba da zuciyarta idan ya taɓa amma yay ta nanik'ar ta. Ya kama hannayenta da suka sha jan ƙunshi yana kallo, a hankali ya kai hannun bakinsa ya yi kissing sannan ya ce. "I like this." Ita dai ji take kamar ta fasa ihu, kunyarsa take ji sosai kamar zata hallaka ta, amma shi ta ga kamar bai san da wata aba kunya ba. Ya ɗauko cup ɗin da ya haɗa tea ya kai bakinta, ba musu ta buɗe bakin ta fara sha saboda so take su yi su gama ya sake ta ta huta, ita kam baza ta iya da wannan abun kunyar ba. Tea ɗin har ya fara hucewa amma haka take sha saboda a ganinta sake ƙara haɗa wani ma sabon wastern time ne da ƙara yawan kasancewarsu tare. Shi ya ciyar da ita amma shi bai ci komai ba, kamar ta share sai kuma zuciyarta ta kasa haquri da hakan. Kanta a ƙasa ta ce. "Kai baka ci ba." Ya yi shiru kamar bai ji ta ba. Ta ɗan ɗago kanta ta ce. "Yaya baka ci abincin ba." Ya shafi lips ɗinta ya ce. "Kina son in ci ne?" Da sauri ta gyaɗa masa kai. Ya ce. "To bani in ci."Bata kuma magana ba ta janyo cup ta haɗa masa sabon tea sannan ta zuba masa komai na gurin a cikin plate. Ta zame daga jikinsa ta zauna a ƙasa, ta gyara zip ɗin rigarta da ya fara zuge mata. Ta janyo kayan zuwa gabansa. Ya tallafe fuskarsa da hannunsa yana kallon kayan break ɗin ya ce. "What is this?" Ta ce. "Ci zaka yi." Ya ce. "Sai dai ki bani." Ta rufe fuskarta da hannunta kamar wadda ta yi sab'o tana girgiza masa kai. Ya ce. "To ɗauke abinki daga gabana." Ta cire hannun kamar zata yi kuka ta ce. "Dan Allah Yaya ka ci , ni dai bazan iya baka ba." Bai ce komai ba ya janyo ta jikinsa sannan ya fara cin abincin. Sai ta ji daɗi a ranta har da sakin ajiyar zuciya. Tana jikinsa har ya gama sannan ta samu ya sake ta. Tattara kayan gurin ta yi ta kai kitchen ta tsaya wanke su. Kafin ta gama har ya shiga dakinsa ya d'auko laptop ya dawo falon yana lallatsawa. Data fito har ta fara murna zata sarara babu takurarsa tunda yana aiki, ta yi hanyar balcony zata shiga ɗakinta ta ji ya ce. "Come here." Ta ɓata fuska sosai kamar zata fashe da kuka, ta ƙarasa inda yake tana k'unk'uni a cikin ranta. Ya zaunar da ita a gefensa tare da kwantar da kanta akan kafaɗarsa ya cigaba da aikinsa. Ta ce. "Yaya Mama fa zan kira." Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Not now." Ta turo baki wanda ya zame mata jiki, yana jin ta sai mutsu_mutsu take, she is totally uncomfortable, bata da damar tashi ne kawai. Ya yi ɗan murmushi tare saka hannunsa ɗaya ya shiga shafa bayanta, a ransa yana faɗin dole ya yi maganin rashin sakin jikin nan nata da shi tare da cire mata kunya da tsoronsa soon. Sai da aka kira Sallar Azhar ya ajiye system ɗin, lokacin har ta yi bacci a jikinsa. Kamar kar ya tashe ta amma dai ya tashe tan dan ta yi Sallah. Ta buɗe idonta kaɗan, ya shafi saman idon ya ce. "Lokacin Sallah ya yi, idan kin yi Sallar sai ki koma baccin." Ta gyaɗa masa kai kawai. Ya taɓa goshinta ya ce. "Ya jikin naki da kan?" Ta ce. "Sun yi sauƙi." Ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi." Sannan ya kama hannunta suka miƙe dan yin alwala. Bata koma baccin ba bayan ta idar da sallar kamar yadda faɗa. Gyaran gidan ta shiga yi duk da babu wani datti a cikinsa, cikin 1 hour ta gyara ko ina, ta kunne burner ta saka turaren wuta ƙamshi ya bud'ad'e gidan. Ameen bai dawo ba har 2 ta wuce, hakan ya yi mata daɗi ba kaɗan ba, dan ita al'amarin sa ya daina bata mamaki sai tsoro, sai tambayar kanta take 'dama haka auren yake miji ya yi ta manne maka kamar wani cingum.' Wayarta ta ɗauko ta kunna data ta shiga WhatsApp. Ko gama shigowa messages ba su yi ba ya buɗe ƙofa ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Ta amsa masa tare da ajiye wayar hannunta ta miƙe ta ce. "Sannu da zuwa." Ya ce. "Yawwa, ki shiga daki za'a shigo da kaya ne." Ta juyo ta nufi ɗakin. Slindern gas ne ya yi repiling sai kuma cartoons ɗin lemuka da ruwa wasu samari guda biyu suka shigo da su. Bayan sun tafi ya shiga ɗakinta ya tarar da ita a kwance. Ya tsaya a bakin gadon ya ce. "Baccin kenan?" Ta tashi zaune ta ce. "Yanzu zan yi, gyaran gida na tsaya yi." Ya miƙa mata hannunsa ya ce. "Taso mu je ki ga wani abu." Bata yi musu ba ta sakko ya kama hannun nata suka fita, suna fita falo ta ga babu wayarta a inda ta ajiye. Ta kalle shi ta ce. "Yaya wayata ban gani ba." Ya ce. "Ni na ɗauka, i want check something." Bata kuma magana ba suka shiga kitchen. Lemukan suka sassaka a cikin fridge sannan Ameen ya kunna shi ya fice. Ita kuma tsayawa ta yi tana ƙara ƙarewa kitchen ɗin kallo, ya yi mata kyau sosai bata gajiya da kallonsa, dama ita a rayuwarta tana k'aunar kitchen. Ta fita falon ta tarar da shi kwance akan doguwar kujera ya kunna TV. A hankali ta ce masa. "Su Aunty sun ce za su zo kuma har yanzu na ji shiru." Ya kalle ta ya ce. "So?" Ta ce. "Ka bani wayar in kira su in ji me ya tsayar da su, sannan in yi magana da Mama." Ya miƙa mata hannunsa, ba musu ta taho ta kama amma fa a tsorace take da shi. Ya zaunar da ita a gabansa bai ce komai ba. Ta ɓata fuska zata fara shagwab'arta suka ji ƙarar shigowar Mota gidan. Da murna ta ce. "Ga su nan ma insha Allah." Ya mintsine ta a hannu ya ce. "So kike su zo saboda in rabu da ke ko? Ai ba kwana zasu yi ba zasu tafi ne." Ta sosa inda ya mintsine tan tana cinno baki gaba, dalle mata bakin ya yi ta keɓe fuska zata fara sana'ar tata. Knocking ɗin ƙofa ne ya hana ta yin abun da ta yi niyya. Ta tashi da sauri cikin murna, yana kiran ta ma bata ji ba. Da Haneefah ta fara cin karo bayan ta buɗe ƙofar. Ta doka tsalle ta rungume ta. Aunty Sadiya dake bayanta ta ce. "To kayar da ita ki yi muku asarar babyn." Ta saki Haneefan tana murmushi ta ce. "Da kuwa Ya faruq ya yi ƙasa ƙasa da ni a garin nan." Haneefah dai bata ce komai ba sai bin ta da kallo take tana murmurshin munafurci. Ta basu hanya suka shige, sai a lokacin ta ga Hameedah da Aunty Hauwa da Matar Uncle Usman. Ta yi mamakin ganin Hameedah amma bata nuna ba. Ameen ya tashi zaune yana yi musu sannu da zuwa. Aunty Sadiya ta shiga tsokanarsa, ya yi murmushi kawai ya ƙi biye mata. Haneefah sai kunshe dariya take, ya harare ta sannan ya gaishe da su Aunty Hauwa, Hameedah ta gaishe shi ya amsa mata ba tare da ya kalle ta ba sannan ya miƙe ya fice. Kaya aka shiga shigowa da su falon, kayan abinci da kayan lefen Neehal da kayan sawanta na gida, sai manyan robobi dake ɗauke da cincin, dubulan da alkaki. Neehal ta buɗe store aka zuba mata kayan abincin, kayan lefen kuma su Aunty suka shigar mata da su daki. Bayan sun gama shigar da kayan ta kawo musu drinks sannan ta ɗauko plates ta zuba musu abincin da suka zo da shi a ƙatuwar warmer. Ta dubi Aunty ta ce. "Ina Mama da Aunty A'isha da Hajiya?" Aunty Sadiya ta ce. "Suna nan ƙalau, daa da Ya A'ishan ma zamu zo ta ce mu taho kawai ta zo daga baya, Hajiya ma har ta shirya Ya Fateemah ta hana ta zuwa." Neehal ta ce. "Kai Mama, ita bata zo ba shine zata hana ta zuwa, ina twins ɗina?" Aunty Sadiya ta ce. "Sun tafi gidan Mamy ai tun jiya da daddare." Ta ce. "Okay." Barinsu ta yi su suna cin abinci ta shiga ɗakinta, Haneefah da gulma da tsegumi ke cin ta ta biyo bayanta. Cikin tsokana ta ce. "Ka ga amaryar Yayanta, um'um." Sai ta saka dariya ta ce. "Ɗan bani labarin daren jiya mana." Neehal ta harare ta, ta ce. "Da kin sani ai shi kika tambaya tunda kin tarar da shi a gidan." Haneefah ta ce. "Na san ma babu abun da ya faru tunda na gan ki ragal, Yaya ya daga ƙafa kenan." Neehal ta ce. "Ke kika sani dai." Haneefah ta ce. "Ke dai zaki sani, yarinya zaki gane kuranki ne." Bata kula ta ba, ita kuma Haneefah ta cigaba da tsokanarta tana zuzuta mata wahalar abun." Da abun ya ishe ta sai ta keɓe fuska kamar zata yi kuka. Haneefah ta kyalkyale da dariya ta ce. "Ki adana kukanki zuwa dare yarinya zai fi miki amfani a lokacin." Da Neehal ta ga abun nata iskanci ne kawai da tsokana sai ta fice ta bar mata ɗakin. Har bayan laasar suna gidan anata hira, Hameedah sai shishshigewa Neehal take. Ita da Matar Uncle Usman suka jerawa Neehal kayan sakawarta a cikin wardrobe. Bayan sun gama kintsa mata gidan tsaf suna shirin tafiya Aunty Sadiya ta ja Neehal daki, ƴar nasiha ta ƙara yi mata akan zaman aure sannan ta bata wasu magunguna ta ce ta dinga sha kafin ta kwanta. Neehal ta karɓa a kunya ce, ta mik'o mata wani abu a leda ta ce. "Ga hand dryer nan, tun ranar da za mu zo jere na manta ban taho da ita ba, na san zaki buƙace ta sosai a yanzu." Neehal ta karɓa ta ciro ta a kwalinta ta gani tare da yi mata godiya. Aunty Sadiya ta miƙe tana faɗin. "Ki dinga shiga ruwan zafi akai_akai, na san ki da shegen son jiki duk zafin da zaki ji idan kin shiga ki daure na ɗan lokaci kaɗan ne, amma zaki ji daɗin jikinki sosai." A kunyace ta amsa mata da "Toh." Amma ko kaɗan bata tunanin abun da suke nufi zai faru tsakaninta da Yayanta nan kusa. Ganin da gaske tafiya zasu yi Neehal ta marairaice ta ce. "Dan Allah ku bari sai dare sai ku tafi, in kuka tafi fa ni kaɗai zan zauna a gidan." Haneefah ta ce. "Zabuwa uwar tsoro, na ga da mai gadi a gidan." Aunty Hauwa ta ce. "In mun kai daren ma idan zamu tafi haka zaki ce." Ta yi ƙwalƙwal da ido kamar zata yi kuka, Aunty Sadiya ta tallab'a ta sannan suka tafi Haneefah na yi mata dariya. Sai da ta ga fitar su daga gidan sannan ta koma ciki daga rakiyar da ta yi musu. Tana shiga falon ta zauna tana hawaye, sosai take kewar gida da su Mama, gashi ya ɗauke mata waya bare ta kira Maman ta ji muryarta ko zata ji daɗi. A haka Ameen ya dawo ya same ta. Ya zauna a kusa da ita ya janyo ta jikinsa ya ce. "Su Aunty sun tafi sai kuka kuma?" Ta kwantar da kanta a ƙirjinsa ta ƙara volume ɗin kukan nata. Ya shiga bubbuga bayanta cikin rarrashi ya ce. "Sorry, bari na miki Mama amma sai kin yi kin bar kukan." Da sauri ta haɗiye kukan ta ce. "Na daina." Tana share hawayenta. Ya taya goge hawayen sannan ya ɗauko wayarsa a aljihunsa ya yi dialling numbern Maman, Neehal kamar ta k'waci wayar dan zumuɗi da ƙaguwa. Mama tana ɗakin Daddy tana haɗawa su Ummin Ahmad kayan biki, sun zo yi mata sallama ne gobe da sassafe za su wuce kiran Ameen ya shigo wayarta. Ta ɗauko ta ɗaga tare da yin sallama. Ameen ya amsa mata sannan suka gaisa ya yi mata godiyar kayan garar da aka kawo. Ya kalli Neehal wadda kaɗan ya rage ta fashe masa da kuka saboda ya ƙi bata wayar ya ce. "Ƴar rigimarki ce take son ta yi magana da ke." Mama ta yi murmushi ta ce. "To bata wayar mana, ko sai ka gama ja mun ran ƴa tukunna." Ya miƙawa Neehal wayar yana murmushi. Ta karɓa da sauri a hankali ta ce. "Mamana." Mama ta ce. "Na'am Daughter, ya kike?" Ta ce. "Lafiya kalau, ina Daddy?" Mama ta ce. "Yana nan ƙalau, ya baƙunta? Da fatan babu matsalar komai dai?" Ta ce. "Alhamdulillah babu komai Mama sai kewarku da nake." Sai kuma ta ɓata fuska ta fara hawaye ta ce. "Mama shine yau baki kira ni ba tun safe, yanzu ma sai da na kira ki." Mama ta ce. "Ki yi haquri Neehal, kin san har yanzu da baƙi a gidan ban samu zama ba." Ta ce. "Shikenan to." Suka cigaba da magana tana zubawa Mama shagwab'a. Ameen ya k'wace wayarsa ya yiwa Mama sallama ya kashe kiran. Ta turo masa baki. Ya tsaya kawai yana kallon ta, ta yi masa kyau ba kaɗan ba, gaba-d'aya ta sauya masa saboda dad'ewar da ya yi bai gan ta ba kafin biki, abun da ya fi komai ɗaukar hankalinsa a gare ta daddaɗan ƙamshin dake tashi a jikinta, jiya kawai dauriya ya yi amma ba ƙaramin tasiri ƙamshin ya yi a gare shi ba. A hankali ya saka fuskarsa a wajen wuyanta yana sakin sassanyar ajiyar zuciya, ya lumshe ido yana shaƙar ni'imtaccen ƙamshinta. Dif ta yi ta ƙi motsi saboda razana, numfashi kawai take saukewa a hankali, sosai gabanta yake fad'uwa tsoro ya cika mata zuciya. Ya ɗago kansa ya zubawa ƙirjinta ido yana kallon yanda yake d'agawa da komawa saboda bugun da zuciyarta take yi da sauri da sauri. A hankali ya kai hannunsa kan ƙirjin nata, ta yi saurin ture hannun nasa gami da fuskarsa a lokaci ɗaya. Ya janyo ta da sauri ya haɗe bakinsu guri guda ya fara kissing ɗinta..... Kiran Sallar Magriba ne ya cece ta daga hannunsa, ta tashi da sauri tana mayar da numfashi ta yi ɗakinta ta kulle ba tare da ta kalli side ɗin da yake ba. Ta jingina bayanta da ƙofa tana sakin ajiyar zuciya. Tana jin shi ya buɗe tashi ƙofar ɗakin ya shiga. Daƙyar ta iya jan ƙafarta ta ƙarasa ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta yi Sallah. Bayan ta idar ta koma toilet ta yi wanka saboda yanda take jin jikinta wani iri. Har aka yi isha'i bata ji shigowar Ameen gidan ba, ta zauna a bakin gado ta rafka tagumi maganganun Haneefah na yawo a kwanyarta, ta san wani abun ba haka ba ne Haneefan ta faɗa ne kawai, amma wani abun data faɗa kuma gaskiya ne. Hakan ya ƙara tsorata ta, ga abubuwan da Ameen ɗin yake mata su ma suna ƙara firgita ta, ita bata son wannan abun gaskiya tsoro take ji sosai. Gashi wannan Ameen ɗin ba wanda ta sani ba ne a da, new Ameen ne a gurinta. Ta lumshe ido tana tunanin sabbin abubuwa a gare ta da yake mata. A hankali ta ji an turo ƙofar ɗakin an shigo, ta buɗe idonta suka sauka a kansa yana ƙarasowa ciki bayan ya yi sallama hannunsa ɗauke da ledodi guda biyu..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _*By*_ _*Zeey Kumurya*_ *8️⃣4️⃣* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ...........Ya riga ta tashi da asuba, da ya tashe ta Sallah daƙyar ta tashi saboda baccin dake kanta, shi ya kaita toilet ta yi alwala saboda ƙin tafiya ta yi, wai ita tsoro take ji kar ta yi tafiya ciwon da take ji a jikinta ya ƙaru. Ya zira mata doguwar riga da hijabi cikin lallab'awa yana ta yi mata sannu ita kuma tana ta yi masa shagwab'a da rakin ciwon da jikinta yake mata. Bayan ya shimfid'a mata darduma ya fita zuwa masallaci. A tsaye ta yi Sallah amma ba ƙaramar dauriya ta yi ba, dan har jiri_jiri take ji yana k'wasarta. Tana idarwa ta cire hijibin jikinta ta koma gado ta kwanta, ko 2 minutes bata yi da kwanciyar ba bacci ya ɗauke ta. Bayan ya dawo ya yi mamaki da ya tarar har ta yi bacci, niyyarsa idan ya dawo ya haɗa mata tea ta sha sannan ya bata magani. Ac'n ɗakin ya kunna bayan ya yaye bargon data rufa ya ga yanda take haɗa gumi. Jallabiyar jikinsa ya cire ya kwanta tare da janyo ta jikinsa, ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙara lafewa a jikinsa. Kyakkyawar Fuskarta ya zubawa ido yana jin yanda k'aunarta take ƙara mayaye ko wanne gurbi na zuciyarsa. Bambancinsu dake bayyane na zahiri ita da Hafsah yake aunawa a cikin zuciyarsa. Hafsat tana da kyawunta dai-dai gwargwado, amma Neehal ta fi ta kyawun fuska dana jiki kuma ta fita tsaho da cikar gashi, Tsayi kawai Hafsat zata ɗara Neehal shi ma da kaɗan, hasken fata kuma dukkanninsu Farare ne, sai dai kowacce kalarta daban. Ɓangaren tarbiyya da addini kuwa ko hanya Hafsat ba su haɗa da Neehal ba, Hafsat Sallah ma akan lokaci sai ya zanzare mata take yi, balle kuma su azkar da karatun Alqur'ani zai cewa bai fi sau a ƙirga yaga tana yi ba a zaman auransu. Neehal kuwa ya san perfect ce a wannan fannin. Batun iya girki ma baza a haɗa Neehal da Hafsah ba ko kaɗan, Hafsat tana yi ne kawai dan gudun ɓacin ransa, kuma rabi da kwata Ƴan aiki ne suke yi, zai iya cewa ita taya su kawai take yi dan kar a ce bata yi ba. Batun tsafta ma Neehal ta ɗara Hafsat, musamman tsaftar muhalli, jikinta ne dai bata barin shi da ƙazanta, ta wannan fannin kam zai yabe ta, dan ƴar gayu ce sosai Hafsat. Amma gayun nata har ya yi yawa ya koma iyayi da firirita. Duk da haka baza ta nunawa Neehal gayun ba, amma nata ya fi na Neehal fitowa dan ita over acting take yi masa. Ya sauke numfashi tare da lumshe ido ya fara shafa fuskar Neehal a ransa yana yiwa Allah godiya da ya mallaka masa ita a lokacin da ya gama fitar da rai da samunta. Jin ta ɗan motsa yasa ya buɗe idonsa, sai ya ga ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba cikin baccin. Ya shafi lips ɗin nata tare da ɗan murmusawa, ya lura hakan ya zamar mata jiki saboda tsabar shagwab'arta. Ya yi mata light kiss sannan ya lumshe idonsa hannayensa zagaye da bayanta, a haka bacci mai daɗi ya ɗauke shi. Ta riga shi tashi da safe, ta yi wajen 5 minutes da farkawa amma ta ƙi koda buɗe idonta ne balle ta yi ƙoƙarin tashi. Ciwon da jikinta yake mata har yanzu yana nan, Ciwon kai ne dai ta samu sauƙin shi. A hankali ta buɗe kumburarrun idanunta da suka canza kala saboda kukan da ta sha a daren jiya. Ta yi ƙoƙarin tashi ta ji ta gam a jikinsa ya riƙe ta. ɓata fuska fuska ta yi, tana son tashi kuma tana tsoron kar ya farka. A hankali dai ta lallab'a ta tashi zaune tana taune lips ɗinta saboda yanda take jin jikinta. Fuskarsa ta zubawa ido da saman cikinsa zuwa ƙirjinsa da ya bayyana sakamakon tashi zaunen da ta yi bargon da suka lullub'a ya yi ƙasa. Kalamansa na jiya da ya faɗa mata ne suke dawowa cikin kunnenta kamar a yanzu yake faɗa mata. Ta lumshe ido tana tuna yanda ya kira sunayenta guda biyu na gaskiya dana inkiya. Abun da bata taɓa ji ya faɗa ba, sai ta ji sunan ya yi daɗi a cikin muryarsa, ta ji kamar babu wanda ya iya faɗar sunanayen nata sai shi. Wani murmushi ne ya kufce mata ba tare data shirya masa ba. Wani baƙon al'amari ne yake riskar zuciyarta a game da yayan nata. Ta buɗe idonta tana kallon kyakkyawar fuskarsa, ji ta yi kamar ta kai hannu ta shafi kyakkyawan sajen fuskarsa ko kwantaccen gashin ƙirjinsa mai sheƙi wanda hasken farar fatarsa ya ƙara fito da baƙinsa. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta yunk'ura da nufin ta fice daga cikin bargon ta sauka daga kan gadon. Caraf ta ji ya riqo qugunta, ta juyo a tsorace ta kalle shi. A hankali ya buɗe idonsa dake cike da bacci, cikin muryarsa data ɗan sirka sakamakon baccin da ya yi ya ce. "Kina tunanin zan iya cigaba da bacci ne bakya tare da ni?" Kawar da fuskarta ta yi gefe bata ce komai ba. Ya ɗan ɗago kansa ya ce. "Ina zaki in kin tashi?" Ta girgiza masa kai alamun babu ko'ina. Ya janyo ta sai gata zaune akan ruwan cikinsa. Cikin shagwab'a ta ce. "Aushh!" Ya shafi fuskarta ya ce. "Sorry Dear, ciwon ne har yanzu ko?" Ta yi ƙasa da kanta ta ƙi cewa komai, ita fa kunyarsa take ji sosai kamar zata nitse, amma ta lura shi ko a jikinsa. Ya ɗago kanta ta yi saurin runtse idonta tare da saka hannayenta ta rufe fuskarta. Ya yi murmushi ya ce. "Open your eyes please." Mak'e masa kafaɗa ta yi. Ya ce. "Okay, in hana ni ganin fuskarki sai in kalli other part ai." Ya ƙarashe maganar idanunsa akan ƙirjinta. Ko ba'a faɗa mata ta san inda yake nufi zai kalla, hakan yasa ta yi saurin kwanciya akan ƙirjinsa tana keɓe fuska. Ya ƙara yin murmushi tare da ɗora hannunsa akan bayanta ya fara shafawa slowly. Luf ta yi a jikinsa tana shaƙar daddaɗan ƙamshinsa da take masifar so a rayuwarta. Kamar mai rad'a ya ce. "Ya jikin naki?" A shagwab'e ta ce. "Da sauƙi." Ya ce. "Bari na ga gurin, kar na je da rauni sosai." Saurin tashi ta yi daga jikinsa ta fara hawaye ta ce. "Ni ba sai ka gani ba." Bai kula ta ya tashi zaune sosai ya kwantar da ita, tana mammatse ƙafa da kuka ya duba ya ga babu raunin da ya yi tunani. Rungume ta ya yi yana aikin rarrashi, daƙyar ya samu ta yi shiru ta bar kukan. Amma fa ko da wasa ta ƙi bari su haɗa ido. Cikin tsokana ya ce. "Babu rauni a gurin dan haka bari na ƙara." Ya rank'wafa jikinta kamar gaske. Ta fashe da kuka jikinta har rawa ya fara saboda tsorata, ta ɗauka da gaske yake. Ya lakuci hancinta ya ce. "Raguwa kawai." Ta tura masa baki. Yana tsokanarta ya tashi ya fice daga ɗakin dan samar mata abun da zata ci. Ta samu ita ma ta tashi ta shiga toilet tana tafiya daƙyar, wanka ta yi tare da ƙara gasa jikinta. Tana fitowa ta shirya cikin sauri dan kar ya dawo ya same ta ba kaya. Wani yadi ta saka maroon colour ɗinkin riga da skirt, ya yi mata kyau sosai ta yi ɗaurin ɗankwalinta simple sannan ta shiga ƙoƙarin gyara ɗakin. Tana cikin jera pillows akan gado ya dawo hannunsa ɗauke da ƙaramin tea flaks da cups da spoons. Ya ajiye kayan a ƙasa sannan ya ce. "Wa ya aike ki aiki ke da ba lafiya ba?" Ta ɗago ta ce. "Mene aikin a nan?" Tsayawa ya yi yana kallon ta dan ta yi masa kyau ba kaɗan ba, a hankali ya taka zuwa inda take ya rungume ta ya ce. "You look so beautiful Baby love." Sannan ya yi kissing check ɗinta ya sake ta ganin har ta fara keɓe fuska. Ya juya ya fita ita kuma ta cigaba da abun da take tana sakin ajiyar zuciya. Bai jima ba ya dawo da kayan su Madara da milo da ledar magunguna a hannunsa. Ya zauna akan Carpet ɗin bakin gado ya fara haɗa mata tea ɗin. Ta dube shi ta ce. "Yaya share ɗakin fa zan yi." Ba tare da ya dube ta ya ce. "Ki bar shi ki zo ki sha tea." Bata ce komai ba ta ƙaraso ta zauna a gefensa. Ya miƙa mata tea ɗin ta karɓa dan ba karya tana jin yunwa. Sai da kusa shanyewa ta ajiye cup ɗin. Yana kallon ta ya ce. Ki ƙara mana. Ta ce. "Na ƙoshi." Bai ce komai ba ya janyo ledar magungunan da ya shigo da ita ya fara fito da su. Ya miƙa mata bottle water ya ce. "Bari na b'aro miki magungunan." Ta kalli maganin ƙwayar dake gabanshi kusan kala biyar tana yatsina fuska ta ce. "Yaya duk ni zan sha magungunan nan?" Ya ce. "Eh." Ta ce. "Na mene?" Ya ce. "Akwai na ciwon jiki dana rage zugi dana zazzaɓi." Ta ɓata fuska ta ce. "Ni fa lafiya ƙalau." Ya ce. "I knew." Kamar zata yi kuka ta ce. "Da gaske fa." Duk da ita ma tasan ba hakan ba ne dauriya kawai take, amma ita kaɗai ta san me take ji a jikinta. Ya miƙa mata maganin ta ƙi karɓa, ta ce. "Kai fa ba doctor ba ne Yaya." Ya kalle ta yana murmushi ya ce. "Amma ai ɗan Doctor ne ko?" Ta turo baki ta ce. "Nima ai ƴarta ce." Ya janyo ta jikinsa ya ce. "Dama waya ce ba ke ƴarta ba ce? Wa ma ya isa ya faɗa." Shi ya bata maganin tana bab'b'ata fuska kamar zata yi kuka ta haɗiye. Ya kwantar da ita cikin mintuna kaɗan ta yi bacci, saboda harda maganin da yake saka a bacci a cikin wanda ya bata. Bayan ya kwashe kayan ya kai kitchen ya dawo ya yi karatun Alqur'anin da bai samu ya yi ba bayan Sallar Asuba kamar yadda ya saba kullum. Ƙarfe goma da mintuna Mama ta turo aka kawo musu breakfast, ya ɗiba ya ci sannan ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya. Falo ya koma ya kira abokansa da suke ta yi masa missed call tun jiya, abun da ya guda shi suka dinga yi masa wato shak'iyanci, wai saboda ya yi amarya ya b'uya kwana biyu ko d'uriyarsa ba'a ji. Sai da 12 na rana ta wuce sannan Neehal ta tashi, Alhamdulillah jikin nata ya yi mata sauƙi sosai, ciwon jikin da zugin da take ji duk sun tafi sai kaɗan. Jikinta ne kawai take jin shi fayau babu k'wari. Abincin da Mama ta kawo ya haɗa mata ta ci sannan ya fita Masallaci dan yin Sallar Azhar. Ita kuma ta shiga gyaran gidan, bayan ta gama ta yi Sallah sannan ta dawo falo ta kunna kallo dan ta gaji da kwanciya, shi kuma bai dawo ba dama ya ce mata zai biya ta wani guri kafin ya dawo. A tunaninta gidansa zai je gurin Hafsat dan ita har yanzu bata san Hafsan ta yi yaji tana gidansu ba, tunda babu wanda ya sanar mata.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _*By*_ _*Zeey Kumurya*_ *8️⃣5️⃣* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ .........Misalin ƙarfe biyu Ameen ya je gidan Mama, kamar ba gidan ne kwana biyu da suka wuce a cike fal da jama'a ba duk an fashe. Zulai da Dije ya tarar suna aiki ƙasa, sai wasu cousin's sister ɗin Dad su uku a zaune suna hira, da yake su sai jibi za su wuce dan ba'a ƙasar nan suke zaune ba. Yana shiga suka fara tsokanar shi, ya zauna suka gaisa yana murmushi sannan ya tashi ya nufi sama. Aunty A'isha da Amira da Ammi matar Uncle Mahmud ya tarar suna gyara a parlour'n. Bayan sun gaisa Aunty ta ce. "Yanzu muke shirin zuwa gidan naka ni da Amirah da Maryam." Ya ce. "To ya naga ko shiryawa baku yi ba?" Aunty ta ce. "Muna ƙarasa aikin nan zamu shirya mu tafi." Ya gyaɗa kai kawai sannan ya nufi ɗakin Mama. Mama tana haɗa kayan da ta yi fitar biki da su Aunty Sadiya tana taya ta ya shigo ɗakin da sallama. Suka amsa masa tare da kallon sa. Aunty Sadiya ta ce. "Ango ka sha ƙamshi, shine ka baro mun d'iyar tawa ita kaɗai a gida." Murmushi kawai ya yi bai ce komai ba ya zauna tare da gaishe su. Yana kallon Mama ya ce. "Mum gajiyar bikin ce naga ko murnar gani na bakya yi?" Mama ta harare shi ta ce. "Ka san abun da ka yi mun ai." Ya langwabe kai ya ce. "Yau kuma me na yi?" Aunty Sadiya ta yi murmushi ta ce. "Zai wuce akan maganar Hafsah ne." Da ɗan mamaki ya ce. "Hafsah kuma?" Mama ta ce. "Ka yi mamaki da muka sani ko? Tunda kai baka sanar mana ba, yanzu Ameen abun da ka yi ka kyauta kenan?" Ya sunkuyar da kansa bai ce komai ba. Mama ta cigaba da yi masa faɗa, bata san me ya faru ba amma gaba-d'aya ta ɗora masa laifi." Ganin yanda ta ɗauki zafi sai ya sanar musu da abun da ya faru ranar da ya kaiwa Hafsat kayan faɗar kishiya. Aunty Sadiya ta yi salati ta ce. "Gaskiya Hafsah bata kyauta ba, amma ta ɓata wayonta da wauta, tun yaushe aka daina irin wannan kishin, ina ganin ta wayayyiya ashe sakarya ce." Mama ta ce. "Duk da haka da ka bita gidan nasu, ko kuma ka zo ka faɗa mana sai a sasanta ba sai maganar ta yi nisa ba, yanzu iyayenta baza su ji daɗi ba a ce tafi wata a gida amma ka ƙi zuwa, za su ga kamar wulaqanci ne." Ya sauke numfashi ya ce. "Ita fa ta tafi da kanta Mum ba da iznini na ba." Mama ta ce. "Duk dai da haka, haquri zaka yi, abun da haquri bai bayar ba rashin sa ma bazai bayar ba." Ya ce. "Shikenan Mum insha Allahu zan je gidan nasu." Mama ta ce. "Yaushe?" Ya ce. "I will select the day." Mama ta ce. "Shikenan, Allah ya yi muku albarka ya kau da fitina a tsakaninku, Allah ya haɗa maka kansu, kai kuma ka zamto mai adalci a tsakaninsu, Allah ya baka ikon hakan kai ma." Ya ce. "Amin, insha Allah." Mama ta ce. "Tun ɗazu na yi girki gashi har rana ta yi ba'a kai muku ba, zaka tafi da shi ko su A'isha su tafi da shi?" Ya ce. "Daga nan ba gidan zan koma ba direct, zan biya can gidan Hafsah na ɗauko abu." Mama ta ce. "Yanzu gidan babu kowa kenan a cikinsa?" Ya ce. "Daa da masu aikinta, last week na je su je gida kawai idan ta dawo sa dawo, mai gadi ne kawai a gidan." Aunty Sadiya ta ce. "Allah ya kyauta." Mama ta ce. "Ya Neehal ɗin? I'm trying her number bata shiga." Ameen ya ce. "May be network ne, idan na koma zan kira ki sai na haɗa ku." Mama ta ce. "Toh, ta ce ma tabar ɗayar wayarta a nan gidan, in zaka tafi sai ka tafin mata da ita." Ya ce. "Okay, Ina tsohuwar gidan nan ne?" Mama ta nuna Aunty Sadiya ta ce. "Sai dai in wannan uwar taka ce tsohuwa amma ba tawa ba." Aunty Sadiya ta yi murmushi ta ce. "Hajiya tana ɗakin Neehal na da tana bacci." Ameen ya ce. "Aikin kenan." Harararsa Mama ta yi, ya yi murmushi. Ƙarfe Uku da ƴan mintuna Neehal tana ɗaki tana drying gashinta data manta tun safe bata yi ba su Aunty A'isha suka zo. Ta yi packing gashin ta d'aura ɗankwali ta fita parlour. Murna kamar ta kashe ta da ta ga su ne. Suka zauna suka ci abincin da suka zo da shi tare suna ta hira. Ana yin Sallar la'asar Aunty ta ce za su tafi. Neehal ta dinga roƙon ta kar su tafi su ƙara zama, harda hawayenta su Amira na yi mata dariya. Daƙyar Aunty ta yarda suka kai ƙarfe biyar a gidan. Kwana biyun nan Hafsat ta yi su ne cikin k'unci tamkar tana cikin k'abari, idan ka gan ta sai ka ɗauka cuta ta yi duk ta lalace ta yi duhu. Yau tun safe ta je ta tasa mahaifiyarta a gaba da kuka, wai ta bar ta ta koma gidanta ita ta gaji da zaman nan, ta san halin Ameen bazai taɓa zuwa ba. Mom ta yi shiru bata ce komai ba, ita kanta al'amarin ya fara isarta, abun kunya ne a gurinta k'awayenta su san ƴarta ta yi yaji, kuma indai aka cigaba da tafiya a haka dole wataran su sani, gashi Ameen ya wuce duk inda take tunani, bata taɓa zaton za'a kawo har i yanzu bai zo ba, ta tabbatar da maganar Hafsah na cewa Ameen ya wuce duk inda suke tunani kuma ba ya ɗaukar raini da wulaqanci. Ta dubi Hafsat cikin tausayawa ta ce. "Ki yi haquri Daughter mu jira babanki ya dawo, ya ce wani aiki ne ya tsayar da shi amma insha Allahu next week zai dawo, idan ya dawo sai ya je ya samu mahaifin shi Ameen ɗin su yi maganar." Hafsat ta gyaɗa mata kai ta ce. "To Mom ina son na je gidan Aunty Safiyya na yi kwana biyu, na gaji da zaman nan haka." Mom ta ce. "Indai hakan zai saka ki ji daɗi to ki shirya anjima driver ya kai ki, kuma ki saki jikinki dan Allah kina cin abinci ko kya yi kyan gani ki ɗan ciko, idan shi Ameen ɗin ma ya gan ki a haka ai sai ya raina ki, ya ce saboda shi kika damu kanki haka." Ita dai Hafsah bata ce komai ba, koma a yaya Ameen zai gan ta bata damu ba, ita dai fatanta Allah ya dai-daita su ta koma gidanta, babban abun da yake bak'anta mata rai idan ta tuna yana can tare da wannan shegiyar yarinyar data tsana, sai ta ji wani baƙin ciki ya cika mata zuciya, kamar zata haɗi zuciyar ta mutu. Bayan ta je gidan Aunty Safiyya ta ɗauki wayarta a b'oye ta kira Ameen tunda ita Mom ta ƙara k'wace wayartata, sai dai har wayar ta yi ringing ta gama bai ɗauka ba, dama ta yi tunanin hakan. Ta ji daɗin zuwanta gidan Aunty Safiyya, saboda yanda ta daɗa kwantar mata da hankali, ta ce tana nan tana shiri na musamman wanda zai saka dole Ameen ya zo da kukansa yana roqonta ta koma gidansa, lokaci kawai take jira a gama aikin. Kafin Magriba Ameen ya dawo gida, lokacin Neehal tana zaune a falo tana karatun Alkur'ani kaɗaici ya ishe ta. Ya tsaya yana kallon ta bayan ya yi sallama yana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake tashi a cikin parlour'n. Sai da ta kai aya sannan ta rufe Alkur'anin ta ajiye ta ɗago tare da amsa masa sallamar. Ya sakar mata murmushi sannan ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta yana kallon ta kamar zai lashe ta. Ƙasa ta yi da kanta cikin sanyin murya ta ce. "Sannu da zuwa." Ya ɓata fuska ya ce. "Haka aka welcoming ɗin miji dama?" Ta ɗan kalle shi ta ce. "To ya ake yi?" Ya ce. "Special hug and kiss to him." Ta waro ido sai kuma ta yi saurin rufe fuskarta da hannunta. Ya yi murmushi a ransa yana ƙara hasko wani bambancin na Hafsat da Neehal wato kunya, Hafsat ko a ranar da aka kawo ta gidansa bata nuna kunya ba sam, hasalima da ya je ko irin kukan nan na amare bata yi, babu alamun ma ta yi dan idonta ragal da shi. Ya rungume ta a hankali cikin kulawa da k'auna ya ce. "I missed you so much baby love." Ta yi shiru tana shaƙar ƙamshinsa tare da sakin ajiyar zuciya a hankali, tana jin wani abu yana yawo a cikin zuciyarta game da shi, kenan ita ma she missed him? Ya kama hannunta yana ɗan murzawa ya ce. "Have you eaten food?" Ta gyaɗa masa kai ta ce. "Kai fa?" Ya ce. "Na ci a gidan Mum." Ɗago kanta ta yi daga ƙirjinsa tare da ɓata fuska ta ce. "Shine ka je gidan Mama baka tafi da ni ba?" Ya shafa kanta ya ce. "Kin taɓa ganin amarya ta fita kwana biyu da kaita inba wata lalurar ba?" Ta girgiza masa kai. Ya ce. "To kin gani, idan an kwana biyu sai na kaiki ko?" Ta gyaɗa masa kai sannan ta ce. "Ina wayata? Ko baka gama checking ɗin ba ne?" Ya gyaɗa mata kai yana shafa kuncinta. Ta ce. "To ka bani, ina son na kira Family and Friends na yi musu ban gajiya." Ya ce. "Alright, Mum ma ta bani ɗayar wayarki da kika manta a gida." Ya zaro ta a aljihunsa ya miƙa mata. Ta karɓa ta ce. "Contacts ɗina duk suna cikin ɗayar ai." Ya ce, "To bari na ɗauko miki." Ya sake ta ya miƙe ya shiga ɗakinsa ya d'auko mata wayar ya kawo mata. Ya zauna ya ce. "Ki bari a yi Sallah sai ki kikkira su." Ta ce. "Toh." Ya janyo ta jikinsa ya shiga aika mata da saqonninsa masu rikitarwa, sai da aka kira Sallar Magriba sannan ta samu ya k'yale ta. Bayan an yi Sallah ta shiga kiran wayar, Daddy ta fara kira sannan Mama sannan Haneefah. Da suka gama waya da Haneefah sai ta kira Ummin su Ahmad, suka gaisa ta yi mata ya suka je gida da bangajiyar biki gami da godiya sannan ta ce ta bawa Zahra wayar. Bayan ta bata sun gaisa ta ce. "Shine kuka tafi ba ku zo ba, aida ko twins kun kawo mun, amma sai tafiyar ku na ji kawai ko sallama babu." Zahra ta ce. "Ki yi haquri, wallahi sai da na ce zamu zo washegarin da aka kaiki Ummi ta hana, na ce a kawo miki twins to shi ma Yaya ya hana ya ce sa zo miki wani lokacin." Neehal ta ce. "Shikenan ina twins ɗin nawa?" Zahra ta ce. "Suna gidan Yaya." Neehal ta ce. "Ki gaishe mun da su sosai, ko kuma ki turo mun ma numbern Aunty Khadijan sai na kira ta mu gaisa da su." Zahra ta ce. "Toh shikenan zan tura miki." Daga haka suka yi sallama ta katse kiran. Ta cigaba da kiran friends ɗinta da abokanan aikinta tana yi musu ban gajiya, har Batul k'anwar Sadik ma sai da ta kira. Ta yi mamakin yanda katin wayarta ya ishe ta wannan kiraye_kirayen, sai bayan ta gama ta duba ta ga ashe Ameen ne ya tura mata credit daga account ɗinsa. Har bayan isha'i Ameen bai dawo ba. Ta yi wankanta ta shirya cikin wasu riga da wando masu kyau, wandon irin mai buɗewan nan ne ta ƙasa, ta saka hula pink colour a kanta da yake kwalliyar jikin kayan pink colour ce, ta yi kyau sosai. Ta zauna a falo tana kallo sai baza ƙamshi take. Tara saura Ameen ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama. Ta kalle shi cikin wani irin salo ta juya masa ido tare da amsa masa sallamarsa cikin karyar da murya. Sandarewa ya yi yana kallon ta dan salon nata ya shige shi ba kaɗan ba. Bata motsa ba sai ido data zuba masa tana murmushi. Ya ƙaraso a hankali ya ajiye ledodin hannunsa ya rungume ta tare da sakin ajiyar zuciya. Ita ma ajiyar zuciyar ta sauke ta ɗan shafa kansa ta ce. "Welcome Yayana." Ya lumshe idonsa yana ƙara shigar da ita jikinsa tare da shaƙar ƙamshinta da ya fara saukar masa da kasala. Ta ɗan ture shi ta ce. "Daga zuwanka zakai mun syqueising ɗin kaya." Ya buɗe idonsa yana sauke numfashi ya ce. "Kin yi kyau sosai baby, ina son wannan ƙamshin naki." Ya ƙarashe zancen yana shafa kwantaccen gashin gaban goshinta. Ta ɗan murmusa ta ce. "Thank you." Sannan ta bar jikinsa ta tashi ta nufi fridge. Ya bi ta da kallo. Ruwa ta tsiyayo masa mai sanyi a cikin glass cup ta kawo masa, ya karɓa tare da yi mata godiya ya shanye. Ya janyo ta ya ɗora ta akan cinyarsa sannan ya buɗe ledodin da ya shigo da su, ice-cream ne da choculates da wafer da popcorn a ciki, abubuwan da ya san tana matuƙar son su sosai. A baki ya bata komai ta ci, shi kuma ya sha ice-cream kawai. Ta tattare sauran ta ajiye a fridge bayan sun gama. Ya Ɗauke ta cak ya kai ta ɗakinsa ya dire akan gado shi kuma ya shige toilet. Murmushi ta yi ta tashi ta fice ta koma ɗakinta ta kwanta. After 20 minutes ya biyo bayanta, ya shirya cikin wasu white ɗin kayan bacci. Ya hau kan gadon ya yaye bargon data lullub'a ya ce. "Da kika gudo nan ɗin bazan iya zuwa ba ne."Cikin marairaicewa ta ce. "Ni fa Yaya bacci nake ji, ka koma ɗakinka." Ya ɗora hannunsa a kan cikinta ya ce. "I can't." Ɓata fuska ta yi bata kuma magana ba, Ƙasa ya yi da hannun nasa a jikinta ya ce. "Ya jikin naki? I hope kin warke?" Kamar zata yi kuka tsoro ƙarara akan fuskarta ta ce. "Ni ban warke ba." Ya kwanta tare da janyo ta jikinsa ya ce. "Kar ki mun kuka, babu abun da zan miki, I just want to sleep with you." Ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido ta saka hannayenta ta zagaye bayansa da su kamar yadda ta ji ya yi mata..........✍️ ```Ban yi edit ba.``` *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _*By*_ _*Zeey Kumurya*_ *8️⃣6️⃣* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️* Jameey yar'mutan kankia *Promo* *Promo* *Promo* Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake. #300-sau biyu a rana #500 -sau ukku a rana #700 -sau hudu a rana Kiyi man wanann number magana danjin ynda zaki biya 08160508316 .........Cikin one week Ameen ya koyawa Neehal son sa da k'aunarsa, wata shak'uwa ce ta ƙara shiga tsakaninsu mai ƙarfin gaske, a yanda suke jin junansu a zuk'atan su ko 1 second basa son su yi ba tare da junansu ba. Ameen ƙarshe ne a iya soyayya da kula da tattali da tarairayar mace. Through out yana gida manne da Baby love ɗinsa suna zuba k'auna, Sallah ce kawai take fitar da shi zuwa Masallaci, sai kuma idan ta yi baƙi, dan kusan kullum a cikin Family ko friends ɗinta wasu sai sun zo mata, Haneefah ma ta zo ta wunar mata. Neehal ta yarda ta kuma gasgata cewa Ameen ba ƙaramin so yake mata, kwata_kwata yanzu babu wannan miskilancin bare haɗe rai. Ita ce ma take ɗan taɓa masa idan class ɗin ya motso mata. Neehal an samu abun da ake so tay ta zuba masa shagwab'a yana lallab'a ta. Sai dai har yanzu bata daina jin kunyarsa ba, tana dai ɗan daurewa ta ƙoƙarta ta nuna masa soyayya dan ta lura yana jin daɗin hakan sosai. Za su wuni tare manne da juna sai dare ya yi ta gudu ɗaki ta kulle, shi kuma ya yi amfani da spare key ya buɗe ɗakin ya bita ya nuna mata bai san wannan zancen ba, tay ta bab'b'ata fuska tana rigima amma duk da haka sai ya yi abun da take gudun, idan ya gama sai ya shiga aikin rarrashi. Yau asabar, wanda ya kama kwana takwas da tarewar Neehal. Misalin ƙarfe goma sha biyu na rana tana tsaye a kitchen tana aikin girkin rana. Sanye take cikin wani straight skirt Black colour mai tsaga a baya, sai riga mai ƙaramin hannu light Brown, irin roban nan ce mai bin jiki, ta kama jikinta sosai. Kanta babu ɗankwali sai bana data saka kalar rigar jikinta, ta yi parking ɗin gashinta sai sheƙi yake ya sha oil na man kitso mai ƙamshi. Sauri take yi ta kammala aikin nata kar Ameen ya tashi daga baccin data bar shi yana yi, tun bayan kwana uku da Mama ta daina kawo musu abinci ita take girkinta. Idan zata yi girkin kodayaushe Ameen yana manne a jikinta, duk inda ta ɗora ƙafarta nan zai saka tashi, in ta yi complain ya ce taya ta aikin yake yi, alhalin ba haka ba ne delay ma yake ja mata a aikin nata, abun da zata yi shi in one hour sai ta yi kusan 2 hours. Tana aikin tana tunanin a ka'ida fa jiya Ameen zai bar gidanta ya koma gidan Hafsah, amma sai ta ga ya ƙara kwana. Ta yi ta mamakin abun amma dai bata yi masa magana ba, yau ma kuma ta ga bashi da alamar zuwa gidan Hafsan. Amma ta ƙudurce a ranta zata yi masa magana anjima akan hakan. Ƙamshin turaren Ameen ta ji ya cika mata hanci da kuma sign na ana kallon ta, ta juya da sauri ta gan shi tsaye yana kallon ta, jikinsa sanye da single da threequarter wando. Bata ce masa komai ba ta juya ta cigaba da aikinta. Ya ƙarasa inda take a hankali ya rungume ta, ta baya tare da sakin ajiyar zuciya. Ta lumshe ido ta buɗe ta juya tana kallon shi tare da ɓata fuska ta lakuce masa hanci ta ce. "Wa ya ce ka tashi yanzu?" Ya langwab'ar kai ya ce. "Saboda kin tashi mana." Ta ɗan ture shi ta ce. "Ka koma baccinka ka bar ni in yi aikina." Ya jingina da jikin cabinet bai ce komai ba, sai kalar tausayi da ya yi da fuskarsa kamar sabon maraya. Ta juya ta cigaba da aikinta tana murmushi ƙasa_ƙasa. After 5 minutes ta juyo ta ce masa. "Ya da shiru kuma?" Ya ɓata fuska kamar wani yaro tare da ɗauke kai. Ta ƙarasa jikinsa ta saka hannayenta duka ta zagaye wuyansa ta ce. "Wa ya taɓa mun Yayana a tsakar ranar nan?" Bai kalle ta ba shi a dole fushi yake ya ce. "Ke ce mana, na zo zan taya ki aiki kin gwale ni." Ta kwanta a jikinsa ta ce. "Ka taya ni aiki ko ka ƙara mun wani aikin?" Ya zagaye bayanta da hannunsa ya ce. "Duk a cikin tayin aikin ne ai." Ta ɗago daga jikinsa ta ce. "To mu je a taya nin." Ya yi murmushi yana bin ta da kallo. Ta juya masa ido. Ya ƙara janyo ta jikinsa ya ce. "Ko dai barin aikin nan zamu yi ne mu je mu yi wani." Cikin shagwab'a ta ce. "Um,um Yaya baƙi fa zamu yi, sai sun zo bamu tanadar musu komai ba." Ya kwantar da kansa akan kafaɗarta bai ce komai ba. A haka ta cigaba da aikin yana jikinta kamar kullum. Sai da aka kira Sallar Azhar sannan ta samu ya bar ta ya tafi masallaci. Bayan sun ci abinci sun yi wanka sun shirya suna zaune a parlour akan kujera 2 seater suna game a wayar Neehal aka yi knocking ƙofar parlour. Neehal ta bar jikinsa tana dariya ta yi masa gwalo sannan ta tashi cikin sauri dan kar ya cafko ta, ta nufi ƙofa. Haka take yi masa kodayaushe idan ta yi baƙi, ya yi murmushi tare da yi mata alamar zan kama ki ne. Kamar yadda ta zata Salma ce wadda ta raka ta gidansu Sadik ita da sistern ta. Neehal ta ce. "Sannunku da zuwa, amma fa na yi fushi sai yanzu zaku zo?" Salma ta ce. "Ki yi haquri, sai da muka yi girki ne." Neehal ta ba su hanya suka wuce sannan ta mayar da ƙofar ta rufe. Suka gaisa da Ameen cikin mutuntawa da fara'a sannan ya tashi ya shige ɗakinsa. Neehal bata zauna ba sai da ta kawo musu drinks da abinci da kayan snacks ɗin gararta. Suka ƙara gaisawa sannan Salma ta ce. "Amarya kin sha ƙamshi, kin ga yanda kika yi kyau kuwa? Anya kuwa idan Mama ta gan ki zata gane ki?" Murmushi kawai Neehal ta yi dan ita akaran kanta ta san cikin one week ɗin nan ta sauya. Sai bayan Magriba su Salma suka tafi, saurayin Salman ne ya zo ɗaukar su, har bakin Motarsa ta raka su. Ga mamakinta sai ta ga Sadik ne. Ta riƙe haɓa tana kallon sa cikin tsananin mamaki, shi kuma ya shiga tsokanarta da amarsu ta Ango yana murmushi. Ta dubi Salma zata yi k'orafi Salman ta yi saurin ce mata. "Bari na yi ki gani da idonki dama." Suka yi dariya gaba-d'aya sannan ta yi musu fatan Alkhairi suka yi sallama ta koma cikin gida, a ranta tana jin daɗin haɗewar Salma da Sadik . Da daddare suna shan fruits a falo ta dubi Ameen cikin nutsuwa ta ce. "Wai Yaya ba tun jiya ya kamata ka koma gidan Aunty Hafsah da kwana ba ne? Ya ɗago ya kalle ta bai ce komai ba amma fuskarsa ta sauya. Sai ta ji babu daɗi gabanta har fad'uwa ya yi saboda ta dad'e bata gan shi a cikin irin wannan yanayin ba. Sai ya daina shan fruits ɗin ma, ita ma ganin haka sai ta daina sha. Tana shirin tattare sauran yay mata wani kallo data san mana'ar shi, dole ta koma ta cigaba da sha. Sai da suka kwanta ta ga har lokacin ransa a b'ace yake sannan ta bashi haquri har da hawayenta. Ya rungume ta ya nuna mata komai ya wuce amma kar ta sake yi masa maganar. Abun ya bata mamaki ba kaɗan ba. Ta dinga tambayar kanta me zai saka Ameen ɗin ya yi haka? Washegari da murna ta tashi dan Ameen ya gaji da rigimar da take masa na son ganin Mama ya ce zai kaita bayan Magriba ta gan ta. Da yamma tana aiki a kitchen ya shigo kitchen ɗin ya tsaya a kusa da ita. Ta dube shi tare da turo baki ta ce. "Kallon kenan?" Ya ce. "Na gaji da watching TV na zo kallon ki." Ta ɓata fuska ta ce. "Dan Allah Yaya ka barni in yi aikin nan, yanda ka koyi cin nan idan ban yi maka abinci ba me zaka ci?" Ya ce. "Au acici ma na zama?" Ta ce. "Eh mana, da ai baka cin abinci sosai." Ya ce. "A da ɗin ma Soyayyar ki da damuwar rashin mallakar ki ya saka hakan, yanzu kuma na same ki bani da wata sauran damuwa." Ta yi murmushi kawai. Ya kwanta a jikinta yana sakin ajiyar zuciya. Cikin shagwab'a ta ce. "Allah Yaya kana takura mun fa a gidan nan, zan haɗa ka da Mama fa." Ya ce. "Ke ce kike yin kyau ai ki yi ta ƙamshi mai daɗi, duk ki saka in zauce." Ta yi murmushi kawai ta cigaba da aikinta. Bayan Magriba kamar yadda ya alƙawarta suka je gidan Mama. Murna da zumuɗin Neehal suka kasa b'oyuwa. Dije ce ta buɗe musu ƙofa, cikin murna ta rungume ta suka gaisa sannan ta shige ciki tana ƙwalawa Mama kira. Girgiza kai kawai Ameen ya yi ya zauna a falon ƙasa. A ɗakin Mama ta tatar da ita akan darduma tana jan carbi, faɗawa jikinta ta yi ta rungume ta. Mama ta shafa kanta cikin farin cikin ganin ta, ta ce. "Yau Amarya ce a gidan namu?" Ta rufe fuskarta da hannunta tana dariya. Mama ta ce. "Ina Ameen ɗin?" Ta ce. "Yana falon ƙasa, ina yini Mamana." Mama ta ce. "Lafiya ƙalau." Tare da bin ta da kallo ganin yadda ta ƙara kyau ta murje alamun tana cikin kwanciyar hankali. Ta ɓata fuska ta ce. "I missed you so much my Mum." Mama ta ce. "Nima haka Daughter, kwana biyu gidan ya mun faɗi Ni kaɗai, babu mai zuwa ya ɗane mun jiki, sometimes da shagwab'a sometimes da murna." Ta yi murmushi ta ce. "Ina Daddy?" Mama ta ce. "Yana masallaci, kin san sai an yi isha'i yake shigowa." Neehal ta gyaɗa mata kai sannan ta ce. "Mama yanzu wa ya ke yi miki girki?" Mama ta yi murmushi ta ce. "Ni nake abuna mana." Ta marairaice fuska ta ce. "Kullum kuma, ni bana son kina wahala." Mama ta ce. "Mene abun wahala? Kin fi so in jibge inta zama babu ɗan motsa jiki." Ta girgiza kai. Mama ta ce. "Ki bari In kin haifi Baby girl sai ki bani ita in ta girma sai ta dinga yi mun girkin." B'oye fuskarta ta yi a jikin Mama tana murmushi. A haka Ameen ya shigo ya same su. Bayan Daddy ya dawo ta je part ɗinsa, ya yi farinciki sosai da ganin ta da yanayin data gan ta a ciki. Ta zauna suna ta shan hirarsu. Shi kuma Ameen yana can Mama ta saka shi a gaba tana yi masa faɗan ƙin zuwa gidan su Hafsah. Tana mitar suka je part ɗin Daddy, shi dai Ameen bai ce mata komai ba. Suna zama ta dubi Daddy ta ce. "Ka yi masa magana ya je gidansu yarinyar nan tunda ni ya ƙi jin tawa maganar." Daddy ya ce. "Ba ƙi ya yi ba nina sani, baki san dalilinsa na ƙin zuwan ba, shi yasa kika ga ni ban shiga cikin maganar ba." Mama ta ce. "Babu wani dalili, kullum sai dai ya dinga ce mun zai je zai je amma ya ƙi zuwa, ita rayuwa ai komai ɗan haquri ne, dama haka zaman tare yake zo mu zauna zo mu saɓa. Amma yarinya ta kusa wata biyu a gida ka ƙi zuwa, sai yaushe kenan zaka je?" Ya ɗago cikin sanyin murya ya ce. "Ki yi haquri Mum, insha Allahu gobe da yamma zan je." Mama ta ce. "Yanzu na ji batu, ko kai fa, Allah ya kai mu goben lafiya." Suka amsa da Amin. Sai a yanzu Neehal ta gano bakin zaren, dalilin da yasa ba ya zuwa gidan Hafsah ashe yaji ta yi, ita fa ta ce ko waya bata taɓa ganin sun yi ba, kuma bai taɓa ce mata zai je gidan ba. Sai ta ji babu daɗi a ranta tausayin Hafsan ya kamata. Mama ta kawo abinci nan part ɗin Daddyn, Neehal ce kawai ta ci kaɗan shi Ameen ko ruwa bai sha ba. Tana gamawa ya ce ta taso su tafi. Ɓata fuska ta yi ta ce. "Ni anan zan kwana." Bai ce mata komai ba ya yiwa su Mama sallama ya tashi ya fice. Har ta fara murna Mama ta ce. "Mu je in baki abun da zan baki ku wuce kar ya yi ta jiran ki." Ta shagwab'e fuska ta ce. "Mama ya bar ni kwanan fa." Mama ta ce. "Banga alama ba." Daddy ya yi murmushi ya ce. "Ki yi haquri Daughter ki je ku tafi, idan an kwana biyu sai ki zo ki kwanan." Ta gyaɗa masa kai sannan ta yi masa sallama suka fice da Mama. Ameen yana cikin Mota ya hango ta tana tahowa fuskar nan a keɓe, ya yi murmushi dama ya san Mama baza ta taɓa barin ta kwana ba. Ta buɗe Motar ta shiga ta ƙi kallon inda yake, ya kalle ta ya ga harda hawayenta. Ya matso ya kama hannunta ya ce. "Fasa kwanan kika yi?" Ta turo baki ta ce. "Mama ce ta koro ni, kuma kai ma ka ƙi tafiya, daka tafi ai zata barni in kwanan." Ya janyo ta jikinsa ya ce. "Tunda Mama ta koro mu sai mu tafi namu gidan mu ma." Ya kashe mata ido tare da rad'a mata wata magana a cikin kunnenta. Fuskarta ta yi saurin rufewa da hannunta tana murmushi ta ƙara cusa kanta a ƙirjinsa.........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* *8️⃣7️⃣* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* Washegari tun safe Mama ta kira Ameen ta ƙara yi masa tuni akan zuwansa gidansu Hafsah. Da yamma ya shirya cikin manyan kaya light blue ɗin shadda. Neehal tana fesa masa turare ta ce. "Ka yi kyau fa sosai Yayana." Ya yi murmushi ya ce. "Duk wannan shiryanin da kike yi fa ba sai saka in fasa zuwa zancen da na yi niyya ba." Ita ma murmurshin ta yi ta ɗauko agogon da zai saka ta fara saka masa ta ce. "Ai bazan so ma ka fasa zuwa ba, ni me iya raka ka zancen ne ma." Ya janyo ta ya zaunar akan cinyarsa ya ce. "Kar fa ta yi miki duka budurwar tawa, ta ce dan iyayi kin rako saurayinta zance." Ta juya masa ido ta ce. "Idan ta san me take yi she will never do that." Ya yi murmushi tare da sauke ta ya miƙe tsaye ya kwashi wayoyinsa. Har bakin Mota ta raka shi ta yi masa addu'a, sai da rungume ta sannan ya shiga Motar ya tafi. Haka kawai ta ji zuciyarta babu daɗi bayan fitarsa dan ta san gurin Hafsat zai je. Wani abu wanda ta tabbatar kishi ne ya tokare mata a ƙirji. Ganin abun na neman yin yawa sai ta kunna karatun Alkur'ani a speaker, tana saurara tana kuma bi a hankali. Cikin mintuna ƙalilan Ameen ya ƙarasa gidansu Hafsah. Ya yi horn mai gadi ya buɗe masa tangamemen gate ɗin gidan. Ya shiga ya ƙarasa parking space ya yi parking, a ransa yana tunanin ko yaya zai ga Hafsah da irin tarb'ar daza ta yi masa. Har yanzu haushin abun da ta yi masa bai bar cikin ransa ba, dan Mama kawai ya zo wannan bikon. A hankali ya fito daga cikin Motar cikin takunsa na nutsuwa da ƙasaita mai ɗaukar hankali. Ɗaya daga cikin yaran gidan ya aika domin ya yi masa iso. A ɓangaren Hafsah tun ranar data je gidan Aunty Safiyya bata dawo ba sai jiya, shi ma dan saboda yau da daddare Dad ɗinta zai dawo ne. A yau kuma Aunty Safiyya ta zo ta kawo mata magunguna da zata yi amfani da su wanda zai saka Ameen ya zo gare ta. Tun a yau ɗin ta fara amfani da magungunan, ta sha na sha ta turara jiki dana turarawa suka binne na binnewa. Aunty Safiyya ta tabbatar mata da a cikin kwanakin nan Ameen zai zo, dan aikin malamin da ya bayar da magungunan tamkar yankan wuqa yake. Aunty Safiyya ta ɗora mata da huɗubar banza ta rashin mutunci da jan ajin da zata yiwa Ameen idan ya zo. Suna zaune a main parlour'n part ɗin Mom suna hira, masu aiki nata kaiwa da komowa suna shiryawa mai gidan delicious ɗin tarb'ar shi. Wanda Ameen ya turo ya shigo cikin girmamawa ya sanar musu da zuwan Ameen. Da sauri Hafsat ta kalli mahaifiyarta ta kalli Aunty Safiyya. Mom ta ce ta bayar da umarnin a je a shigo da Ameen ɗin. Aunty Safiyya ta ce. "Kin ga aikin Malam ko Hafsat? Zaki ga yanda zai rud'e yana roqonki ki zo ku tafi, ke kuma ki ja class ɗinki ki gaggasa masa maganganun da na ce miki." Hafsah da farin ciki ya cika mata zuciya saboda zuwan Ameen ta ce. "Insha Allahu Aunty, abun da kika ce babu fashi." Mom ta miƙe ta ce. "Bari na shiga ciki kafin ya shigo in fito in yi masa wankin babban bargo nima." Aunty Safiyya ta miƙe ta bi bayanta. After 3 minutes Ameen ya shigo parlour'n bakinsa ɗauke da sallama. Lokaci ɗaya daddaɗan ƙamshinsa ya cika parlour'n, Hafsah ta lumshe idonta tana jin yanda ta yi missing ƙamshin over a cikin ranta, Sai dai kuma ta ji ƙamshin nasa ya ɗan sauya ya sirka da wani, wanda ko tantama bata yi na Neehal ne, dan is like humra ta mata. Ta buɗe idonta tare da haɗe rai wani zafi ya ziyarci zuciyarta data tuna zuwa yanzu fa ya haɗa jiki fa da wannan yarinyar. Ko kallon inda yake bata yi ba balle ta amsa masa sallamarsa. Idanunta suna kan TV. Kansa ya yiwa mazauni a kujerar dake facing ɗin tata, ya shiga bin ta da kallo cikin mamakin yanda ta share shi. Ya danne zuciyarsa ya ce. "Hafsah Ya kike?" Ta juyo ta yi masa wani mugun kallo gami da harara ta murgud'a masa baki. Sandarewa Ameen ya yi saboda tsananin mamaki ya tambayar kansa abun da take nufi da hakan, ita da yi masa laifi ita ce kuma da yin fushi lallai akwaita da ƙarfin hali. Hafsah da duk zaton ta aikin Malam ne ya yi aiki ga Ameen har ya zo gidansu a yau ta miƙe cikin tsiwa da rashin kunya ta ce. "Ameen me ya kawo ka inda nake? Baka yi auranka ba ka wofantar da ni saboda butulci da rashin tabbas irin naku na maza? Sai yau zaka kwaso jiki ka zo gurina, ni kuma ga sauna sai na washe maka baki na bi ka ko?" Ran Ameen ya fara ɓaci amma bai ce komai ba sai kallon ta kawai yake. Hafsah da zigar Aunty Safiyya take yawo a cikin kanta ta ce. "Ka tashi ga ƙofa nan ka koma inda ka fito, ni Hafsat na gama Auranka har abada Ameen, kuma ina roqon ka da Allah ka sauwaqe mun ƙaddararre Auran ka, dan bazan iya zama da kishiya ba." Ran Ameen fa ya kai matuƙar ɓaci, a fusace ya buɗe baki zai yiwa Hafsah magana sai kuma ya fasa ya shiga furzar da zazzafan huci. Hafsat ta tab'e bakinta ta ce. "Idan ka cika dan Halak cikin Fateemah da Muhammad in ga takarar sakina a yau ba'a gobe ba." Cikin matuƙar fusata Ameen ya miƙe tsaye yana jifan ta da wani irin kallo, idanunsa har sun fara sirkawa zuwa ja saboda tsananin ɓacin rai. Ya yi ɗan taku ya ƙarasa gaban Hafsah ya ce. "Hafsat kin san me kike faɗa kuwa? Kina cikin hankalinki kuwa? Ni kike faɗawa haka?" Kafin Hafsah ta yi magana muryar Mom ta karad'e parlour'n da faɗin. "Sannu Ameen, na ce sannunka." Duk da yanayin ɓacin rai da yake ciki amma haka ya tsugunna ya shiga ƙoƙarin gaishe ta. Ɗaga masa hannu ta yi ta ce. "Riƙe gaisuwarka bana buƙata, yanzu kai Ameen dan baka da kunya ka iya takowa ka zo cikin gidan nan bayan wulaqanci da tozarcin da ka yi mata, ka yi mata kishiya sannan kuma ta taho gida ka ƙi biyo bayanta saboda gaka ishashshe ko? Ka fi ƙarfin zuwa biko. To bari ka ji in faɗa maka in baka sani ba ka sani, ƴata ta fi ƙarfin wulaqancin ɗa Namiji wallahi, me kake da shi? Me kake t'akama da shi? Abun takaicin ma ka rasa da wa zaka haɗa ta kishi sai da yarinyar da asalinta ubanta ba kowa ba ne, ƴar matsiyata da matsiyatan danginta suka kasa riqe ta." Aunty Safiyya dake bayanta ta tari numfashinta tana turo d'auri gaban goshi ta ce. "To ai Yaaya abun duk shiri ne, shiryawa aka yi, wannan munafukar uwar tasa ce ta shirya komai." Da sauri Ameen ya miƙe idanunsa sun yi jajur, ba zai iya jurar wannan cin mutuncin ba, abun ya bar kansa ya koma kan Baby love ɗinsa amma duk bai ishe su sai sun haɗa da mahaifiyarsa? Ba ƙaramin danne zuciyarsa ya yi ba na ƙin mayar musu da martani, ya juya kawai ya fice daga parlour'n ransa a matuƙar k'ololowar ɓaci. Bayan fitarsa a tsorace Hafsat ta ce. "Na shiga uku Aunty, maganin nan fa kamar bai yi masa aiki ba, ina jiran na ga ya yi kneeling a gabana yana bani haquri tare da bagging ɗina sai na ga ya tashi kamar zai dake ni." Ita ma Aunty Safiyya jikinta ya yi sanyi. Amma cikin ƙarfin hali ta ce. "Ya yi masa mana, ke baki lura ba da yanayinsa ba ne? Shegiyar tattaurar zuciyarsa ce ta saka bai nuna ba, amma muna nan dake abun zai cijo sa ne zaki ga ya dawo ni na faɗa miki, ke dai ki cigaba da yin yadda na ce miki kar ki yi kuskure." Hafsat ta koma ta zauna tana sakin ajiyar zuciya, ita dai tsoronta ɗaya kar ta rasa Ameen. Tun bayan fitar Ameen ba jimawa Neehal tana zaune ta ji cikinta na ɗan juya mata kaɗan_kaɗan, ko kusa bata yi tunanin period zata yi ba, sai da cikin ya ɗan murɗa mata ta ji abu ya fara fita daga jikinta sannan ta yi realising. Mamaki ne ya kamata ganin yau sau ɗaya a rayuwarta tunda ta fara period ya zo mata ba tare da ta sha wahala ba. Ta miƙe ta shiga ɗakinta ta kimtsa kanta sannan ta kwanta akan gadon dan ba normal take jin ta ba, cikin ya ɗaure mata kamar kodayaushe idan tana period. Ikon Allah ne ya kawo Ameen gida lafiya dan saboda ɓacin rai ko ganin gabansa sosai baya yi. Neehal ta yi murmushi jin shigowar motarsa, duk da bacci ya fara fizgarta amma ta yage shi ta miƙe dan tarb'ar mijinta, zuciyarta cike fal da tsokanar sa da zata yi. A falo suka ci karo, ta tsaya turus tana kallon shi kamar wani mayunwacin zaki yanda yake huci. Cikin mamakin yanayinsa ta ce masa. "Sannu da zuwa." Bai ko kalli inda take ba ya tura ƙofar ɗakinsa ya shiga ya banko ƙofar da ƙarfi. Cikin fad'uwar gaban ganin yanayin da ya shigo ta bi bayan shi, amma tana tura ƙofar sai ta ji ta kulle. Ta tsaya tana kallon ƙofar kamar zata gan shi a jikin ƙofar sannan ta juya ta bar gurin zuciyarta babu daɗi. Zama ta yi akan kujera tare da yin tagumi da hannu bibbiyu tana tambayar kanta me ya ɓata masa rai haka? Tashi ta yi ta ƙara komawa bakin ƙofar ɗakin nasa ta shiga yin knocking amma ta ji bai buɗe mata ba. Sai ta ji haushi ta koma ɗakinta ta kwanta, ita ba ita ta yi masa laifi ba amma shine zai yi mata haka, tana yi masa magana ya share ta ya shiga ɗaki ya kulle, ta bubbuga masa ƙofa kuma yana ji ya ƙi buɗewa. Shi kuwa Ameen yana shiga ɗakin ya cire rigar jikinsa ya cillar akan gado sannan ya ɗauki remote ya karo AC, dan ji yake gaba-d'aya jikinsa da zuciyna yi masa wani irin zafi suke masa, kwanciya ya yi rigingine ya lumshe idonsa tare da dafa kansa da yake yi masa ciwo saboda hayaniyar su Hafsat. Kalamanta dana Aunty Safiyya ne suke yi masa kuwwa a cikin kunne, Hafsat har ta yi tsaurin idon da zata ce masa idan ya cika ɗan Halak ta kira sunan iyayensa na ainihi ta ce ya sake ta? ita kuma k'anwar uwarta mai kama da Ngozi ta cewa Mama munafuka! Lallai zai shayar da su ruwan mamaki, wannan shine karo na uku da Hafsah ta yi masa Manyan laifuka a rayuwar Auransu. Kiran Sallar Magriba ne ya tashe shi dan dole ya yi alwala ya fita. Sai da ya kalli ɗakin Neehal sannan ya fice, a ransa yana addu'ar Allah yasa bata yi kuka ba. Ita tana can ma bacci ya ɗauke ta. Sai bayan isha'i ya dawo gidan, lokacin zuciyarsa ta fara sanyi sakamakon Sallah da zikirin da ya yi. Ya buɗe fridge ɗin parlour ya d'auko ruwa mai sanyi ya sha, ajiyar zuciya ya sauke ya nufi ɗakin Neehal. Lokacin bata jima da tashi daga bacci ba, ta shiga toilet ta fito kenan tana zaune a bakin gado tana latsa wayarta. Ya tura ƙofa ya shigo tare yin sallama, ba tare data kalle shi ba ta amsa masa. Ya tsaya a jikin ƙofa yana kallon ta, ta ɗan ɗago ta kalle shi ta tura masa baki sannan ta mayar da idonta kan wayarta. Ya yi murmushi sannan ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta, hannayensa duka biyu ya ɗora akan cinyarta, yana kallon fuskarta ya ce. "Baby yau babu magana." Ta ja numfashi duk wani haushin sa da take ji yana barin zuciyarta, ajiye wayar ta yi ta ɗora hannunta akan lallausar sumar kansa ta shiga shafawa bata ce komai ba. Ya kwantar da kansa akan cinyarta tare da saka hannunsa ya zagaye k'ugunta yana shaƙar daddaɗan ƙamshinta. Duk wani ɓacin rai da su Hafsat suka saka masa yana kallon kyakkyawar fuskarta ya ji ya gushe, yanzu kuma da kansa ke jikinta sai ya manta da shi ma gaba-d'aya. Ta ture kan nasa ta ce. "Bani da lafiya fa." Da sauri ya ɗago kansa ya ce. "Subhanallahi, da gaske baby baki da lafiya? mene ne yake damunki?" Ganin yanda ya yi maganar a rud'e sai ta ƙara narkewa ta ce. "Ciwon ciki na yi, kuma ka dawo ina maka magana ka ƙi kula ni." Ya tashi ya hau kan gadon ya janyo ta jikinsa cikin damuwa ya ce. "I'm sorry My love, raina a b'ace yake time ɗin ne, bana son na zauna kusa da nake kar na yi miki tsawa ko abun da baza ki ji daɗi ba akan laifin da ba ke kika mun ba." Ya kai hannu kan cikinta ya ce. "Yanzu ya jikin naki? Allah yasa dai baki sha wahala ba irin wadda kike sa?" Ta bar jikinsa ta koma ta kwanta akan gadon ta ce. "Sosai ma, kamar zan mutu." Dafe kansa ya yi ya ce. "Ya Salam! Sannu Baby, ko za mu je asibiti ne?" Ta ce. "Ya daina ai yanzu." Ya bi ta ya kwanta shi ma cikin jimami da damuwa yana ta jera mata sannu da riri tata, ita kuma tana zuba masa taɓara. Daga baya kuma sai ta saka masa dariya. Ya tsaya yana kallon ta ya ce. "What's funny?" Tana shafa sajen fuskarsa ta ce. "Wasa fa nake maka ban wani sha wahala ba." Ya sauke ajiyar zuciya tare jan karan hancinta ya ce. "Shine da zaki ɗaga mun hankali ko?" Ta ce "To ka yi haquri bazan kuma ba." Ya saka idanunsa a cikin nata ya ce. "Wai ciwon cikin ma na mene ne?" Ta yi murmurshin mugunta ta ce. "Kamar ya?" Ya ce. "Kin fini sani ai." Ta rufe fuskarta da hannunta tana dariya. Ya ɓata fuska ya ce. "Me yasa abun nan zai mun haka?" Juya masa baya ta yi cikin jin kunya. Ya juyo da ita da hannunsa ya kai hannun ya danna mata ciki. Ta kwabe fuska ta ce. "Ouch! Da zafi fa." Ya rungume ta ya ce. "Sorry, dannawa na yi dan ya yi ya zube da wuri." Ta yi murmushi ta ce. "In ka yi haquri ma is just 12 days ne zai tafi." Ya waro ido ya ce. "Ko 120 days ba, I already knew the days, is just 2 to 3." Ta ɓata fuska ta ce. "Dama saka mun ido kake yi?" Ya ce. "No, the way da kike acting ne ake ganewa, baki da aiki sai kwanciya kamar ruwa, ga taɓara da raki." Ta juya masa ido ta ce. "Yanzu na daina to." Bai kuma magana sai langwab'e kai da ya yi yana kallon ta. Ta san me yasa ya yi hakan, gwalo ta yi masa tana dariya ƙasa_ƙasa. Ya zira hannunsa a cikin rigarta ya ce. "Idan babu can ai da akwai nan." Ta zaro hannun nasa ta yi kalar tausayi ta ce. "Mu je mu ci abinci yunwa nake ji." Yana bin ta da wani irin kallo da idanunsa da suka fara sauya kala ya ce. "No let me take this first." Zata yi magana ya hana ta, ta hanyar haɗe bakunansu guri guda. Ta lumshe idonta a hankali tare da saka hannayenta duka a kansa tana shafa gashin kansa zuwa bayan wuyansa........ Washegari da yamma Ameen ya je gidan Mama, bai b'oye musu komai ba ita da Daddy na daga cin mutuncin da su Hafsat suka yi masa ba. Cikin tsananin mamaki Mama ta ce. "Yanzu Ameen Hafsan ce ta faɗa maka haka?" Ya gyaɗa mata kai zuciyarsa na yi masa k'una. Daddy ya ce. "To ai ni Mahaifinta ya kira ki ɗazu da safe, ya ce mun jiya_jiya ya dawo daga ƙasar ya tarar da wannan abun mara daɗin ji, amma a yanda muka yi magana da shi gaskiya ga dukkan alamu ba shi da masaniyar wannan cin mutuncin da suka yi." Mama ta ce. "Allah ya kyauta." Sannan ta dubi Ameen cikin lallami ta ce. "Ka yi haquri, Ni na tursasaka ka je, ban taɓa tunanin za'a yi haka ba." Ya ce. "Babu komai Mum kansu suka yiwa ai." Daddy ya ce. "Ban da abunku na mata mutumin da ya zo sulhu gurinku me ne na tsayawa na neman fitina da shi kuma?" Mama ta ce. "Shaid'an ne kawai, ka yi haquri Ameen tunda bata taɓa yi maka makamancin wannan laifin ba, karka yanke hukunci da baza mu ji daɗi ba dukanmu." Ya furzar da iska daga bakinsa ya ce. "Ta taɓa mun Mum, lokacin data yi barin ciki abortion ta yi ba miscarriage ba, and kuma suka je ita da k'anwar mahaifiyarta aka juya mata mahaifa wai ita bata shirya haihuwa yanzu ba." A tare Mama da Daddy suka kama salati cikin tsananin kad'uwa. Mama ta ce. "Ikon Allah, ko na ce shirme, wani yana nema wani yana gudu, shi Ubangiji ai ba'a yi masa wayo, Allah yasa mu dace." Haka suka cigaba da tattauna maganar Mama sai tausar Ameen take, ita bata son ya ce zai rabu da Hafsat. Dan yanda take hango zallar ɓacin rai a cikin idanunsa ta san zai iya aikata komai. Shi kuma Ameen wani irin d'aci yake ji a cikin zuciyarsa, ji yake tamkar a yanzu ne Hafsat ta b'arar masa da gudan jininsa. A lokacin ji ya yi kamar ya sake ta saboda tsabar baƙin ciki, amma ya taushi zuciyarsa ya haqura. By now kuma ta kai shi bango, dan haka dole ya yi mata abun da zai saka ta dawo cikin nutsuwarta da hankalinta, ta gane ba tsoronta yake ji ba kawaici ne kawai irin nasa yake yi mata. Daga gidan Mama gidansu ya wuce direct, ya tsaya a bakin gate daga waje ya ɗauko Joter da Pen ya rubuta abun da zuciyarsa ta bashi umarni. Bayan ya gama ya karanta sannan ya ninke takardar, horn ya danna mai gadi ya buɗe ƙaramar ƙofar gidan ya lek'o dan ganin waye, Ameen ya fita daga cikin Motar ya ƙarasa ya bashi papern ya ce ya bawa Hafsat sannan ya juya ya shige cikin Motarsa ya bata wuta ya bar layin, ya bar mai gadi da bin sa da kallo riƙe da takarda a hannu baki a sake..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* _*⚡NEEHAL⚡*_ _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *8️⃣8️⃣* ..........Hafsat tana zaune a ɗakinta tana tunanin Ameen data mayar da shi sana'arta, tun safe take tsammanin zuwansa dan jiya kusan kwana ta yi tana bankad'a magani da turara jikinta. Ɗaya daga cikin masu aikin gidansu ta yi knocking ƙofar ɗakinta, ta bayar da umarnin a shigo. Cikin ladabi Mai aikin ta sanar mata saqo aka bayar aka kawo mata ɗan aiken yana falo. Jikin Hafsat ya bata saqon daga gurin Ameen yake amma mai makon ta yi farinciki sai ta ji gabanta ya faɗi. Miƙewa ta yi suka fito tare da Mai aikin, a main parlour ta tarar da Mom da Aunty Jamila wadda ta zo yiwa Dad sannu da zuwa. Mai gadi dake tsaye ya risina ya gaishe ta sannan ya miƙa mata takardar tare da shaida mata in ji Ameen. Ta karɓa fuskarta da alamun mamaki. Duban Mum ta yi ta ce. "Kin ga wai takarda ce in ji Ameen." Mom ta ce. "Lallai Yaron nan, ya cika shegen miskilancin tsiya, may be ta ban haquri ce ya yo, dan girman kai ba zai zo ya bayar da bakinsa ba sai dai ya rubuto miki a takarda." Hafsah bata kuma magana ba ta buɗe takardar ta fara karantawa. Aunty Jamila dai kallo reaction ɗinta kawai take yi. Wani uban ihu Hafsat ta kurma da ya saka su Mom toshe kunnuwansu ba shiri. Lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya sauya gumi ya fara tsatstsafo mata. Ta nufi mahaifiyarta a gigice tana nuna mata takardar da hannunta dake faman karkawa kamar yadda duk jikinta yake yi. Cikin rawar Muryar ta ce. "Mo..Mom..wai ya sake ni, saki ya rubuto mun, Mom ki duba ko idona ne bai gane mun dai-dai ba." Sai ta fashe da kuka. A razane Mom ta karb'i takardar ta duba. Aunty Jamila innalillahi..... kawai take maimaita cikin tsananin al'alabi. Durk'ushewa Hafsat ta yi ta shiga zunduma ihu tana faɗin. "Ameen kar ki yi mun haka Please, ka san ina son ka bazan iya rayuwa babu kai ba, Please ka ce mun wannan takardar bakai ka rubuta ta ba, wani ne ya copy note ɗinka ya rubuta dan ya raba mu. Na shiga uku...." Wani uban ashar Mom ta lailaya ta miƙe tana faɗin. "Lallai wannan yaron ya cika cikakken butulu, shegen yaro ni zai tozarta a idon duniya ya mayar mun da Ƴa ƙaramar bazawara? Lallai zai gane kuren sa a ƙasar nan, sai ya san ya taɓo mu wallahi." Aunty Jamila dake karanta takardar sakin da Mom ta yada a ƙasa ta ce mata. "A'a Yaya mu bi komai a sannu, ai saki ɗaya ne ma, insha Allahu za'a dai-daita su." Mom ta yi mata wani mugun kallo sannan ta juya ta ɗauki wayarta, jikinta na tsuma ta kira Aunty Safiyya ta ce ta zo gida yanzu_yanzu tana son ganin ta. Aunty Jamila ta koma kusa da Hafsah wadda haukan lokaci ɗaya ya kama ta, janyo ta jikinta ta yi ta shiga rarrashinta tana faɗa mata ta kasance musulmar k'warai mana mai yarda da ƙaddararta a duk yanda ta zo mata. Hafsah ko fahimtar abun da take cewa bata yi balle ta saurara. Mom da take jin kamar ta zunduma ihun ita ma irin na Hafsah ko zata ji daɗi a cikin ranta ta yi k'wafa sannan ta latsa wayarta ta lalubo numbern Mama ta yi dialing. Mama tana toilet a lokacin tana alwalar Sallar Magriba kiran ya shigo, ta ƙarasa alwalar ta fito sannan ta yi picking cikin mamakin ganin mai kiran nata, dan kiran farko har ya katse wani ya ƙara shigowa. Mama ta yi mata sallama. Mom bata bi ta kan sallamar ba ta ce. "Hajiya Fateemah kin aura wa ɗanki ƴarki ni kuma ya sakar mun tawa." Cikin shock Mama ta ce. "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, Ameen ɗin? Yaushe?" Mom ta ce. "Ki riƙe sallallaminki zai miki amfani wani lokacin ba'a nan ba, munafurcin banza munafurcin wofi, amma ki sani wallahi Ameen sai ya san ni ya wulaqanta." Ta ja tsaki sannan ta katse kiran. Aunty Jamila ta dube ta, ta ce. "Haba Yaya, ya zaki kira........" A zazafe Mom ta katse ta, ɗaga mata hannu ta yi ta ce. "Dahalla Jamila saurara mun, bana son wani dogon jawabinki na banza, ko dan ba ƴarki aka saka ba ne." Girgiza kai kawai Aunty Jamila ta yi. Mama kuwa bin wayar ta yi da kallo bayan ta katse, ta zauna a bakin gado tana jin zuciyarta babu daɗi sosai akan sakin Hafsah da Ameen ya yi, ba ta ji daɗin kalaman mahaifiyar Hafsah ba, amma duk da haka ta fi jin zafin sakin Hafsah da Ameen ya yi. Numbern sa ta lalubo ta yi dialing, komawarsa gida kenan ya tarar Neehal tana bacci a falo, da alama bata ma san lokacin da baccin ya ɗauke ta ba. Ya ɗaga wayar ya kara a kunne. Mama ta ce masa "Ameen where are you?" Ya ce. "Ina gida." Ta ce. "To ka zo yanzu ina son ganin ka." Ya ce. "Gani nan insha Allah." Ɗakinsa ya shiga ya yo alwala ya fito ya fice ba tare da ya tashi Neehal ba, tunda ya san ba Sallah zata yi ba. Zaune yake a gaban Mama yana sauraren faɗan da take yi masa. Ta ce. "Ban ji daɗi ba ko kaɗan Ameen, gaskiya baka kyauta ba, duk tausar kan dana dinga yi jiya amma sai da ka aikata wannan d'anyen aikin? Bana son ka kasance cikin mazan da dan sun samu wata matar su rabu da wadda suke tare da ita." Cikin ladabi ya ce. "Mum ba haka ba ne kema kin sani, dan na samu Neehal haka kawai bazan rabu da Hafsah ba, halinta ne ya janyo mata. Kuma ina son hakan ya zama kamar jan kunne a gare ta. Mama ta sauke numfashi ta ce. "Saki nawa ka yi mata?" A hankali ya ce. "Ɗaya ne." Mama ta ce. "Shikenan, Allah ya dai-daita ku, ya kiyaye faruwar hakan a gaba." Ya amsa da Amin sannan ya tashi ya yi mata sallama ya tafi. Har kusan isha'i su Hafsat suna falo, mahaifiyarta na faman kumfar baki Aunty Safiyya data zo gidan tana taya ta, Hafsat kuma tana ta aikin kuka. Ko sallar Magriba ba su yi ba, ba su ma da niyyar yi, Aunty Jamila ce kawai ta yi. A haka mahaifin Hafsah ya shigo ya same su, ya zauna tare da tambayar ba'asi. Mom ta kora masa bayani, ta ƙara da faɗin. "Yanzu Alhaji sai ka san matakin da zaka ɗauka ga Ameen da iyayensa na wulaqanta maka ƴa da suka yi." Dad ya haɗe rai ya ce. "Hafsah 'yata ce wadda nake k'aunarta kamar raina, bana jin bayan iyayena akwai abun da nake so a duniyar nan sama da ita. Na san halinta na san abun da zata yi, haka na san mijinta Ameen yaron kirki ne shi da iyayensa, ya samu ingantacciyar tarbiyyar da nake da tabbacin bai saki Hafsat haka kawai ba tare da wani dalili ba, face ta yi masa wani abun. Dan haka i will never blame him akan abun da ya yi, balle har na ɗauki wani mataki kuma ban bawa kowa ikon ɗauka ba. Ban da ma hauka daga mutum ya saki mace sai a ce za'a ɗauki mataki a kansa? Duk matan duniya da ake sakin su fa? Ko ma ba haka Ameen ya wuce matakin da za'a ce za'a ɗauki wani mataki a kansa, irin matakin da kuke nufi na a wulaqanta shi ko something like that." Ya nuna Mun da hannu ya ce. "Wannan ya ishe ki ishara, a da idan ina faɗa miki ɓata Hafsah kike yi ba gata kike yi mata ba sai kina ganin kamar k'arya ne, yau gashi nan ta yi aure Mijinta ya kasa ɗaukar halayenta ya sako ta. Ba fina son ta kika yi ba Amina, kuma nima ina nuna mata gata dai-dai gwargwado, amma ba irin naki ba, naki ya yi yawa. Kasancewar ni ba mazauni ba ne kullum ina tafe neman halak ɗina shi yasa tarbiyyar da kika yiwa Hafsah ta fi tasiri a gare ta akan tawa. Amma yanzu tunda ta dawo gidan, zan yi iya yina wajen ganin na gyara rayuwarta, duk da an ce ice tun yana d'anye ake iya tank'wara shi." Ya mayar da kallonsa ga Aunty Jamila ya ce. "Idan zaki tafi gidanki ki tafi da Hafsan ta yi zaman iddarta a can, domin ki koya mata ilimin zaman duniya da kuma yanda zata samu lahirarta, da rayuwar zaman Aure da haqqokinsa dan ganin ta gina rayuwarta ko dan gaba. Sannan kuma duk lokacin da Ameen ya zo domin mayar da ita ɗakinsa zan yi masa maraba in kuma bashi ita." Yana gama faɗin hakan ya miƙe ya nufi sashensa. Gaba-d'aya suka bi shi da kallo baki a sake, Aunty Jamila ce kawai ta ji daɗin maganganunsa ta kuma yaba masa. Mom ta saka kuka tare da surutan shiga tsakaninsu aka yi da Daddyn Hafsah, amma da ba zai faɗi haka ba. Bayan Daddy ya dawo gida Mama ta sanar masa da abun da ya faru, ya ji ba daɗi shi ma amma ya ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Sai bayan isha'i Ameen ya koma gida, ya tarar da Neehal ta shirya tana jiransa ya zo su fita, kamar yadda ya ce zasu je gidan wani abokinsa. Wanka ya yi sharp_sharp ya shirya suka tafi. Satin nan da aka shiga gaba-d'aya kullum sai sun fita bayan Magriba, ya kai ta gidan wani daga cikin abokansa daga nan su biya su sha ice-cream cikin soyayya da k'aunar junansu. Ameen ya manta da Hafsat da babinta a cikin ransa, kula da tarairayar Matarsa kawai ya saka a gaba. Neehal tana son ta ji inda aka kwana a zancen komen Hafsah amma tana jin tsoron ta tambaye shi, tunda ya ce karta ƙara yi masa maganar data danganci Hafsah. Ranar yana bacci suka yi waya da Aunty Sadiya take sanar mata Ameen ya saki Hafsah, yanda sakin ya daki zuciyar Neehal ba zai misaltu ba, har hawaye sai da ta yi, ta ji a ranta Ameen bai kyauta ba. Suna gama waya da Aunty Sadiya ta kira Mama ta dinga roqon ta akan ta saka Ameen ya dawo da Hafsah. Mama ta ce mata, ita ma burinta da fatanta kenan, bari ta yi Ameen ɗin ya gana hucewa sai a san abin yi. Ranar Ameen kasa gane kanta ya yi, ta ƙi kula shi ta dinga yi masa k'unci. Ya rarrashe ta ya lallab'a ta amma duk a banza, sai haqura ya yi ya k'yale ta, daga baya kuma da karan kanta ta saki ranta suka koma normal. Yau Monday wanda ya kama kwana goma sha bakwai da Auran Neehal da Ameen. Da safe yana shiryawa zai tafi aiki da yake hutun 2 weeks aka bashi. Neehal tana tsaye tana kallon sa ta yi kalar tausayi da fuskarta kamar zata yi kuka. Ya ƙarasa saka talalmin ƙafarsa sannan ya ɗago ya kalle ta. Hannunsa ya miƙa mata ta ɗora nata akai a hankali. Ya riƙe hannun tare da janyo ta jikinsa ya zaunar da ita akan cinyarsa ya ce. "Mene ne." Ta ɓata fuska ta ce. "Ni bana son ka fita." Shafa bayanta ya shiga yi a hankali ya ce. "Ki yi haquri Baby, bazan dad'e ba fa zan dawo." Ta ce. "Ai na san baza ka dawo da wurin ba." Ganin tana shiri fara hawaye ya ce. "To ko in tafi dake ne?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. Ya yi murmushi sannan ya sauke ta ya miƙe. Tun jiya da yake shirye-shiryen zuwa aiki yau take haka, jikinta gaba-d'aya ya yi sanyi, a yanda take jin sa yanzu a cikin zuciyarta bata k'aunar abun da zai rabata da shi ko na awa ɗaya ne balle na awanni. Ya ɗauki briefcase ɗinsa suka fita ta yi masa rakiya zuwa bakin ƙofar parlour. Ya ɗan tsaya yana kallon ta sannan ya kama fuskarta da hannunsa ya ce. "I will miss you Darling." Ƙasa ta yi da kanta bata ce komai ba. Rungume ta ya yi ya ce. "Please Baby ki saki ranki, idan na tafi kina haka ai babu abun da zan iya ko na je gurin aikin, ko kuma in zauna in fasa zuwa ne?" Ta girgiza masa kai tare da d'agowa ta yi masa murmushi ta ce. "Ka je Yayana, ya za'ai ka ƙi zuwa aiki? Allah ya kiyaye hanya ya kare mun kai." Murmurshin ya yi shi ma ya ce. "Amin, thank you so much dear, ko ke fa, harna ji daɗi." Ta bar jikinsa ta ce. "Ka tafi kar ka yi late." Ya ce. "Shikenan Baby, karfa ki damar mun kanki ki yi ta tunani, ina ƙarasawa office zan kira ki." Ta ce. "Insha Allah Yaya, Allah ya kaika lafiya." Ya ce. "Amin." Sannan ya yi mata pick a kuncinta ya fice tana ɗaga masa hannu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tsakanin Ameen da Neehal cikin kwanciyar hankali da farinciki da tattali gami da kula da juna. Duk wanda ya zo gidansu sai sun burge shi sun ba shi sha'awa, zamansu gwanin sha'awa. Bayan sati biyu ita ma Neehal hutunta ya ƙare na gurin aiki da yake wata ɗaya aka bata. Ameen ya ce bai san zancen ba baza ta koma wani aiki ba, aikin ma na Jarida na gidan TV wanda ya dace da wanda bai dace ba ya kalle masa mata. Neehal har da Kukanta dan tana matuƙar k'aunar aikinta amma ya yi biris ya ƙi yarda, sai da ta kira Mama ta faɗa mata sannan ita kuma ta kira shi ta yi masa magana akan hakan, dole ba don son ransa ya yarda ta koma aikin, amma ta sha sharad'ai da dokoki, duk da yawan hijaban lefenta haka ya ƙara jibgo mata wasu dogaye har ƙasa da socks na ƙafa ya ce da su zata na fita. Ita dariya ma ya bata dan ita ma tafi son tana saka hijabin akan mayafi. Ranar data koma bayan ta dawo ya tasa ta a gaba da mita kamar zai yi kuka, wai ta yi kyau sosai da ya kalli labaran data gabatar, yanzu ya san wasu ma da suka kalla sun yaba kyawunta. Rarrashinsa ta yi da abun da ta son yana matuƙar so, da haka ta samu ya bar yi mata mitar. Bayan wata ɗaya wanda ya kama wata biyu da Auransu suka je Gombe aka sha shagalin bikin Ameerah ƴar gidan Uncle Mahmud. Duk wanda ya ga Neehal a bikin sai ya tanka kyawun da ta yi da irin canzawar da ta yi. Ta ƙara haske da ƙiba abun ta. Hajiya sai faman nan_nan take da ita tana cewa ciki gare ta, ita kuma sai ta ɓata fuska ta ce bata da komai ita. Ana shagalin biki amma suna manne da Ameen kodayaushe a waya. Har tsokanarta ake yi ana ce mata Cingam ne ita da shi. Daf da za su je bikin Ahmad ya kawo mata twins sun yi mata kwana biyu. A bikin ne labarin mutuwar Hafsat ya bazu a dangin su Mama, sakamakon rashin zuwanta bikin, daga masu cewa Allah ya raka taki gona sai masu cewa Allah yasa haka shi Alkhairi. Bayan sun dawo daga Gomben sai zancen Hajiya ya zamto gaskiya, dan tunda suka dawo Neehal bata da aiki sai bacci, sai ta ɗora girki tana shiga d'aki ko ba da niyyar bacci ba sai ta kwanta ta yi bacci. Ga shegen kwad'ayi da ƙin cin abinci, ita dai ta wuni tana taunar abu a bakinta shine kwanciyar hankali. Daga ita har Ameen ba su gane ciki ne da ita ba, saboda bata laulayi kwata_kwata, ciye_ciye ne kawai da Bacci. Shi Ameen ya ɗauka zirga-zirgar zuwa gurin aiki ne take sanya mata gajiya take wannan baccin, ciye_ciye kuma dama ya san gwana ce ita a wannan fannin duk da na yanzu ya yi yawa, amma duk da haka bai kawo komai a ransa ba..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡ NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *8️⃣9️⃣* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* ..........Yau ya kama weekend, ranar Sunday da rana Ameen yana parlour yana operating laptop, Neehal kuma tana d'aki tana aikin bacci. A hankali ta buɗe idonta dake cike da bacci, baccin bai ishe ta ba yunwace ta tashe ta. Miƙewa ta yi ta shiga toilet ta wanke bakinta tare da d'auraye fuskarta ta fito. Ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali ta lek'a kamar mara gaskiya, ganin Ameen zaune akan kujera yana aiki sai ta saki ajiyar zuciya ta mayar da ƙofar ta rufe ta koma ciki. Wardrobe ɗinta ta buɗe ta lalubo choculates ɗinta a inda ta b'oye su ta zauna a ƙasa ta fara sha tana lumshe idanu saboda daɗin dake ratsa ta. Sauri take yi ta yi ta shanye kar Ameen ya shigo ya gan ta, dan ya hana ta shan zaƙi saboda yanda ta mayar da su sweets abincinta, ba dare ba rana a ƴan kwanakin nan. Shi yasa ta koma sha a b'oye, kullum idan ta je gurin aiki sai ta bayar an siyo mata da yawa sai ta zo ta b'oye in ba ya gidan ta yi ta shan abin ta. Sai da choculate ɗin ta ishe ta sannan ta mayar da sauran ma'ajiyarta ta goge bakinta da tissue ta fita parlour. Tunda ta fito ya ji ƙamshinta ya ɗago yake kallon ta, a gefensa ta tsaya tare da shagwab'e fuska. Ya saka hannunsa ya janyo ta ya ɗora ta akan cinyarsa. Ajiyar zuciya suka sauke a tare. Ya shafa fuskarta ya ce. "Har kin tashi daga baccin?" Gyaɗa masa kai ta yi. Ya ce. "Mene ne kuma ya faru Babyn Yaya?" Ta saka hannayenta ta zagaye bayansa ta ce. "Masara nake son ci dafaffiya." Ya ce. "Masara kuma Baby? a ina za'a samo ta?" Kamar zata yi kuka ta ce. "Koma a ina ne, ni dai ita nake son ci." Ajiyar zuciya ya sauke tare girgiza kai ya ce. "Bari na kira a kawo miki." Ta ce. "A'a ni dai ka je da kanka, ka taho mun da gyaɗa mai gishiri da kwakumeti." Tsayawa kawai ya yi yana kallon ta, ta fara yi masa shagwab'a. Ya rungume ta ya ce. "Yanzu dai kin ga aiki nake yi Baby ba sai na fita ba, ki bari na bayar a siyo miki, ni duk waɗan nan abubuwan ma ban san inda zan samo miki su ba." Ta ce. "Ni na sani mu je tare." Zai kuma magana ta fara yunk'urin kuka. Ya ce. "Shikenan bari na ɗan ƙarasa wani abu sai mu je." Ta turo baki alamun ba haka taso ba amma bata yi magana ba. A hankali ya kai hannu ya shafi cikinta ya ce. "Rigimarki da kwad'ayin da kika koya yanzu da yawan bacci ina tunanin fa na yi ajiya ne." Ta tura hannunsa bata ce komai ba ta lumshe idonta. Ya shafi saman idon yana murmushi, yana fatan a ce hasashen ya zama gaskiya. Kafin ya gama abun da ya ce zai ƙarasa har ta yi bacci a jikinsa. Bayan ya gama ya tashe ta dan su je su siyo abubuwan da ta ce, ɓata fuska ta yi ta ce. "Mafarki fa nake yi Yaya ina cin masarata ka tashe ni." Ya ce. "I'm sorry, yanzu ai zamu je mu siyo ki ci a reality ba'a mafarki ba." Ga mamakin Ameen ta san ko ina da ake siyar da abubuwan data lissafa, suka je ya siya mata har da ƙarawa da wasu abubuwan. Sai da ya biya ta restaurant ya siyi abincin da zai ci, duk da ta ce masa zata iya girki idan sun koma gida, ya ce mata ya hutashshe ta, dan ya san girkin nan daƙyar zai yiyu. A daren yau kuma sai jikinta ya yi zafi zazzaɓi ya rufe ta, ko baccin kirki ba su yi ba. Washegari da sassafe kuwa suka shirya sai asibiti, dan ya ce ya kai ta gurin Mama ta ƙi yarda. Bayan an yi mata gwaje_gwaje da test aka tabbatar tana da shigar ciki na 7 weeks. Murnar da Ameen ya nuna ba zata faɗu ba, ya yi sujjada tare da yin godiya ga Ubangiji. Neehal kuwa sai kunya amma ita ma a cikin ranta farin ciki ne fal. Bayan sun dawo daga asibitin ya kwantar da ita akan gado ya ce. "Ki kwanta ki huta Baby zan je in yi gyaran gida, ko me kike so ki kira ni in miki karki wahalar mun da kanki da Small Babyna." Ta shafa sumar kansa ta ce. "Aikin fa? Baza ka je ba?" Ya ce. "Baki da lafiya ina na ga ta zuwa aiki Baby." Ta ce. "Na warware fa, zan iya yin komai." Ya ce. "No, ko toilet zaki shiga just call me in zo in ɗauke ki in kaiki, kar ki yi tafiya ki wahala." Ta yi murmushi kawai. Ya yi kissing goshinta da cikinta sannan ya fita. Yana fita ta miƙe ta je ta tsaya a gaban mudubi ta ɗaga rigar jikinta tana kallon cikin, murmurshin farinciki ɗauke akan fuskarta. Jin abun take kamar a mafarki, ita ce da ciki very soon da yardar Allah she will be come a Mother. A haka Ameen ya shigo ya same ta, cikin tsokana ya ce. "Wasa kike masa ne?" Saurin rufe cikin ta yi ta rufe fuskarta da hannunta. Ya ƙaraso ya rungume ta yana dariya ƙasa_ƙasa. B'oye fuskarta ta yi a ƙirjinsa tana murmushi. Ya jata suka faɗa kan gado ya ce. "Bari na duba lafiyar Babyn." Ya fara ƙoƙarin cire mata riga. Ta marairaice ta ce. "Bani da lafiya fa." Shi ma marairaicewar ya yi ya ce. "Nima haka." Ta ja karan hancinsa da ƙarfi bata ce komai ba........ Sosai Ameen yake kula da tattalin Neehal, dan sai yanzu kuma ta fara laulayi, idan ta ci abun da bai yi mata ko ta shak'i ƙamshinsa sai amai, ga zazzaɓi daren da take kwana da shi kullum. Kwad'ayi kuwa da bacci sai abun da ya yi gaba, shi yasa duk abun da Ameen ya gani a hanya ko bata ce masa tana so ba sai ya siyo mata, wani ta ci wani ta ƙi ci. A haka take lallab'awa take zuwa aiki, duk da ya hana ta ya ce ta ɗauki hutu ta ce masa ita bata son zaman gidan, ta fi son tana fita tunda ba wani jin jiki take sosai ba. Amma idan ta je gurin aikin ba wani abun arzik'i take yi ba rabi da rabi bacci ne, a yi ta tsokanar ta kuwa a gurin aikin, sai dai ta yi murmushi kawai cikin jin kunya. Ta ƙi barin Ameen ya faɗawa su Mama tana da ciki, wai ita kunya take ji. Ya yi dariya ya ce. "Indai Mum ce gani ɗaya zata yi miki ta gane, kin sani ke ma." Jin haka sai ta ƙi zuwa gidan Maman, sai dai kullum cikin faɗar tana son ganin Maman take, idan suka yi waya tay ta yi mata mitar ta ƙi zuwa gidanta. Ranar wata Sunday Daddy ya cewa Mama ta shirya ta je ta gano Neehal ɗin ta ga gidanta tunda bata taɓa zuwa ba. Ai kuwa ranar Neehal murna kamar me, ta shiga kitchen ta yiwa Mama abubuwa na tarb'ar ta. Sai yamma Maman ta je gidan. Neehal ta tafi da gudu ta rungume ta, Ameen ya bi ta da wani kallo data san ko na mene ne, juya masa ido ta yi tana murmushi. Mama ta zauna suka gaggaisa tana bin Neehal da ido, Neehal ta tashi ta je ta kawo mata abinci da drinks. Mama dai kallon ta kawai take yi tana noticing ɗinta, ta lura da yanda take yin komai a sanyaye da kuma yanda jikinta ya d'ashe ta yi wani irin haske. Ta yi sarving Mama ta koma kusa da ita ta zauna tana ta yi mata hira. Can ta kalli Ameen ta turo baki ta ce. "Mamana ta zo shine baza ka ba mu guri mu yi sirri ba?" Harararta ya yi bai ce komai ba. Ta kwanta a jikin Mama tana ɓata fuska. Kafin Mama ta tafi ta shiga ɗaki dan yin fitsari, bayan ta yi fitsarin ta fito daga toilet sai ta kwanta akan gado, duk yanda ta so daurewa kar ta yi bacci amma ina baccin ya ce bai san wannan zancen ba, saboda rabon ta da yi tun safe, tana kitchen tana ta aiki. Mama ganin shida saura ta yi ta dubi Ameen ta ce. "Ina Neehal ɗin ne? Tafiya zan yi fa." Ya ce. "Tun yanzu?" Mama ta ce. "Tunda na zo na gan ku mai zan zauna yi kuma." Ya miƙe ya shiga ɗakin Neehal, mamaki ne ya kama shi ganin ta kwance tana baccinta hankali kwance. Ya juya ya fita ya ce wa Mama. "Kin ga Mum daga shigar ta har bacci ya ɗauke ta." Mama ta ce. "Bacci kuma?" Ya gyaɗa mata kai. Tashi Mama ta yi ta shiga ɗakin ta zauna a gefen Neehal, tafin hannunta ta kama ta dudduba sannan ta kalli Ameen dake tsaye a bakin ƙofa ta ce. "Wani abu yana damunta ne ko ta yi rashin lafiya?" Ameen ya ce. "Tana yin zazzaɓin dare dai, amma yanzu da sauƙi tana shan magani." Mama ta ce. "Kun je asibiti?" Ya ce. "Eh." Mama ta ce. "Me aka ce yana damunta?" Ya shafa gashin kansa tare da yin ƙasa da kansa ya ce. "She is pregnant." Mama ta mayar da kallon ta ga Neehal cikin tsananin farin ciki ta shafi fuskarta ta ce. "Allah ya sauke ki lafiya Daughter, ya baku lafiya ke da unborn." Can ƙasan mak'oshi Ameen ya amsa da Amin. Dama Mama tun zuwansu Gombe data ga yanayin Neehal ɗin ta fuskanta. Ta miƙe ta fita Ameen ya bi bayanta dan yi mata rakiya, suna tafe tana ƙara faɗa masa yanda zai kula da Neehal da abubuwan da zata yi da wanda baza ta yi ba, tana kuma tambayar sa abubuwan da Neehal ɗin take yi. Sai daf da Magriba Neehal ta tashi, ta dinga yiwa Ameen mita akan ƙin tashinta da ya yi da Mama zata tafi, shi dai bai ce mata komai ba har ta gaji ta haqura, kiran Maman ta yi ta ji ya ta koma gida, Mama ta sanar mata lafiya ƙalau, sannan ta faffaɗa mata addu'oin da zata dinga yi a matsayinta na mai juna biyu, cikin jin kunya take amsa mata. Suna gama wayar ta juyo zata yiwa Ameen complain ya yi saurin cewa. "Bani na faɗa mata ba, ita ta gane da kanta, ai dama na faɗa miki." Ta yi murmushi kawai a ranta tana hasaso irin farin cikin da Mama ta yi da ta ji labarin cikin. Bata ƙara nutsewa da jin kunya ba sai da Daddy ya kira ta ya yi mata ya jiki, dan ta san definitely Mama ta sanar masa da batun cikin jikinta. A ɓangaren Hafsah kuwa kamar yadda Dad ɗinta ya faɗa a ranar ta bi Aunty Jamila zuwa gidanta tana gunjin kuka. Saboda kuka da damuwar data saka kanta a ciki har jinyar kwana biyu ta kwanta. Bayan ta warware Aunty Jamila ta fara koyar da ita abubuwa kamar yadda Dad ya buƙata daga gare ta, da farko bata mayar da hankali akan abubuwan ba sai dai ta zauna ta yi ta koke_koke da tunane_tunane. Daga baya cikin dabara Aunty Jamila ta ce mata idan bata gyara dabi'unta ta koyi zaman rayuwar duniya ba babu ta yanda za'a yi Ameen ya mayar da ita, sannan ta fara mayar da hankali. Ta kan addini Aunty Jamila ta fara yi mata dan sai ya gyaru sauran abubuwan za su gyaru. Wata yarinya ƴar mak'otansu Aunty Jamila ta ɗauko take yiwa Hafsan karatun addini, za su yi ƙarin Alqur'ani da sauran littatafai. Ita kuma Aunty Jamila sai ta ƙara mata da bayanin wasu abubuwan akan addinin. Sannan kuma idan zata yi girki tare suke yi, dan Hafsan tana gani tana koya. A hankali Hafsah ta fara sakin jikinta zaman gidan Aunty Jamila ya fara yi mata daɗi, ta kuma mayar da hankali akan karatun da ake yi mata. Sai dai fa kullum da tunanin Ameen take kwana take tashi a ranta. Lokuta da dama tana zama tay ta tunanin zaman Auransu, babu shakka ita akaran kanta ta san Ameen ya yi haquri da ita, a kodayaushe idan ta yi masa laifi uzuri yake mata ya dinga nusar da ita aibun abun da ta yi masa, sannan yana iyakar ƙoƙarinsa wajen ganin ta gyara addinta ta ko yi ilimin addinin, ta kan tuna lokacin data zubar masa da ciki, da farko fushi ya yi mai tsananin gaske da ita, daga baya kuma ya koma yi mata nasiha da nuna mata girman lefin da ta aikata ga Ubangiji. A lokacin gani take kamar rashin wayewa ne yasa ya kasa fuskantar abun da take nufi na ta yi ƙanƙanta da fara tara ƴaƴa a yanzu, sai yanzu da ilimi ya fara ratsa ta sannan ta gane ashe ita ce mara wayewar da kuma tarin duhun jahilci a kanta. Ranar suna zaune lokacin an yi wata biyu da sakinta take bawa Aunty Jamila labarin magungunan da Aunty Safiyya ta dinga kawo mata a matsayin su ne za su janyo da hankalin Ameen gare ta. Aunty Jamila ta yi salati ta ce. "Yanzu ita Safiyya an girma ma amma bata bar halin yarinta ba na bin Malam tsibbu? To Allah ya shirya ta yasa ta gane gaskiya. Ita kuma Yaya tana kallo bata yi magana ba?" Hafsah ta ce. "Bata ce komai ba." Aunty Jamila ta ce. "Dama ita Yaya haka take, duk abun da zaka yi bata k'wabar ka, na dai-dai ko na rashin daidai. Ke kuma wannan ya ishe ki izna, ki gane komai na Allah ne, ɓata wayonki da kika yi kika bi ɓata shi yasa Ubangiji ya barku da halinku, da a ce Sallah kika dage da ita da addu'a kamar yadda kika dage da yin amfani da magungunan nan da watak'ila al'amarin bai kai har haka ba, amma da kika kasa tsayar da Allah a al'amarinki kin ga illar hakan ai, tunda maganin bai yi aikin komai ba. Mutane su yi ta asarar kuɗaɗen su saboda jahilci suna zuwa gurin wani mutum ɗan'uwansu wai da sunan shi zai biya musu buƙata, ya baku maganin k'arya da wofi ya ci kuɗinku a banza, ga kuma tarin zunubi a gurin Ubangiji, dan shirka ba ƙaramar masifa ba ce, Allah ya raba mu da ita." Hafsah ta gyaɗa kai ta ce. "Amin Aunty na gode da tunatarwarki a gare ni. Amma Aunty kullum sai na saka ran ganin Ameen, ko ya turo wani nasa, ko ya kira ni amma shiru har na kusa gama iddata." Cikin tausayinta Aunty Jamila ta ce. "Ki ƙara haquri Hafsah kin ji, komai rubutacce ne a gurin Ubangiji, ki fawwala masa komai, idan ya nufa akwai sauran zamanku da Ameen a gaba sai ki ga kin koma, idan kuwa iya zaman kenan sai ki yi haquri, Allah ya kawo miki wani na gari." Gyaɗa mata kai Hafsah ta yi a hankali jikinta duk ya yi sanyi akan Ameen, ta san tunda ya samu mace kamar Neehal zai yi wahala ya ƙara waiwayar ta a cikin rayuwarsa..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *⚡NEEHAL⚡* _By_ _Zeey Kumurya_ *9️⃣0️⃣* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* ```I DEDICATED ALL THIS NOBEL TO MY LOVELY MOTHER, ONE IN THE BILLIONS, ONE LIKE NO OTHER, SUPER WOMAN, *HAJIYA FATIMA KUMURYA* ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA MAI AMFANI, AMEEN.``` *SPECIAL THANKS TO* *Abubakar Ak saraki,* *Muhammad Kareem,* *Mu'az,* *S deen and* *Yareema.* *Mutanen kirki kenan wanda basa gajiyawa da yin share, Allah ya saka muku da Alkhairinsa.* .........Rayuwa na tafiyarwa su Neehal yadda ya kamata cikin kwanciyar hankali da farinciki. Sosai Ameen yake k'aunar cikin jikinta tun kafin ya fito duniya, da daddare idan sun kwanta haka zai ta shafa cikin yana magana shi kaɗai, wai magana yake yi da ɗansa, wataran har ta yi bacci ta bar shi yana ta faman latsa mata ciki, da safe ma haka yana tashi zai ɗora daga inda ya tsaya wai gaisawa suke yi. Ita dai sai dai tay ta yi masa dariya, in ta gaji kuma ta ture hannunsa daga jikinta. Cikin Neehal ya shiga wata na uku lokacin farkon azumin watan Ramadan Haneefah ta haifi ƴarta mace mai kama da ita sak. Murna gurin Neehal ko ita ta haihu sai haka, ranar da ta je Barka daƙyar take bari a ɗauki yarinyar, tana hannunta ta rungume ta sai kallon ta take. Mommyn Haneefah ta yi ta mata dariya tana cewa in da rai ita ma kamar yau ne zata haifa, da yake gida aka mayar da Haneefan. Duk da azumi ne kuma ga laulayin da take fama da shi amma zuwanta uku kafin ranar suna. Ranar suna yarinya ta ci sunan Mommyn Haneefah Maryam, Haneefah ta ce Neehal za'ana ce mata. Neehal ta ji daɗin wannan karar da Haneefah ta yi mata sosai, kayan barka sosai Ameen ya siyawa takwararsu da ita kanta Haneefan, ita ma Neehal ta ƙara da nata kayan. Ba'a yi taron suna ba kasancewar azumi ne. Wataranar Laraba Neehal tana kitchen tana girki da yamma ta ji ana knocking ɗin ƙofar parlour. Ta goge hannunta ta fito ta nufi ƙofar, lokacin cikinta ya fito ɗan wata shida, ya yi mata das a jikinta abun sha'awa, yanzu an bar laulayi. Sai da ta tambayi waye? Sannan ta buɗe ƙofar. Ɗaya cikin yaran gidan ne masu bawa flowers ruwa da yi mata aike. Bayan ya gaishe ta ya ce. "Hajiya wasu baƙi ne suka zo wai suna san ganin ki." Neehal ta ce. "Baƙi kuma? Maza ko Mata?" Ya ce. "Maza ne dattijai haka kamar almajirai." Neehal ta ce. "Kuma suka ce Ni suke son gani?" Ya ce. "Eh, dan sun ce daga can gidan Hajiya babba (Mama) aka turo su." Neehal ta ce. "Okay ka ce su shigo." Ta juya ta koma ba tare da rufe ƙofar ba a ranta tana Mamakin baƙin da aka ce ta yi, ɗakinta ta shiga ta ɗauko hijabi ta zira akan doguwar rigar abayar dake jikinta. Ta duba time ta ga biyar ta wuce lokacin dawowar Ameen gida ya kusa. Jin ƙarar turo ƙofa yasa ta fita parlour'n. Maza ta gani su biyu kamar yadda yaron gidan ya ce mata dattijai ne kuma kamar almajiran, tabbas ta san fuskokinsu amma ta kasa tuno inda ta san sun. A kan Carpet ta zauna tana bin su da kallo, su kuma sai aikin kalle_kalle suke a parlour'n suna baza ido a lungu da sak'o na cikinsa. Cikin girmamawa ta ce musu. "Sannunku da zuwa." Suka amsa da "Yawwa." Tare da dawo da kallon su gare ta. Ta ce. "Ina yininku?" Suka amsa mata sannan ɗaya daga cikinsu ya gyara zama ya ce. "Ikon Allah, Neehal ke ce kika zama haka? Girman ɗan Mutum babu wahala." Ta yi murmushi kawai. Ya cigaba da magana cikin sanyin murya. "Ga dukkan alamu baki shaida mu ba, amma hakan ba'abun mamaki ba ne bisa ga yadda muka wofintar da rayuwarki duk da kasancewar muna gari guda dake, Neehal Salisu ne da kuma Sani ƴaƴan Baffa mariki'n mahaifanki." Da mugun mamaki Neehal ta ɗago tana kallon su tare da tambayar kanta abun da ya hana ta gane su. Zuciyarta ta bata amsa da cewa 'Tsufan da suka yi mana' wanda ya wuce yawan shekarunsu a duniya, kuma ta manta rabon da ta gan su a, duk da Kawu Musa ya ce sun zo bikinta, amma da yake cikin hada_hada ake bata gan su ba. Cikin tsananin mamaki ta ce. "Kawu Sani da Kawu Salisu?" Kawu Sani ya gyaɗa mata kai. Ruwan hawaye fal cikin idonsa ya ce. "Mu ne Neehal, abun ya baki mamaki ko? Na ganinmu da kika yi a gidanki, mun zo ne mu roqe ki gafara akan abun da muka yi miki ko ma samu sassaucin k'uncin rayuwar da muka shiga, mahaifinki ya riqe mu tamkar ƴan'uwansa da suke ciki ɗaya a lokacin da yana raye haka ma mahaifiyarki, mahaifinki shine komai namu, ya yi mana komai a rayuwar nan, amma saboda butulci da wani tunanin banza da wofi muka wofantar dake ƴarsa ƙwaya ɗaya tal a duniya, muka yarda zumunci muka kasa riqe ki saboda muna gudun wahalar d'awainiya dake. Amma da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne sai gashi Allah ya ɗaukaka ki, mu kuma ya bar mu da iyawar mu, dan Allah Neehal ki yafe mana, wallahi muna cikin tsananin k'uncin rayuwa. Abun da zamu kai bakinmu ma gagarar mu yake, karayar arzik'i Ubangiji ya ɗoro mana lokaci ɗaya, hatta da muhallin da muke rayuwa a cikinsa ba mu tsira da shi ba, yanzu a wani rubab'b'en gidan haya muke tare da iyalanmu, shi ma wani bawan Allah ne ya ji k'an mu ya biya mana kuɗin shekara ɗaya....." Sai ya fashe da kuka. Neehal Sarkin kuka har ta fara hawaye, ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Kawu ni ba ku yi mun komai ba dama, ko kun mun na yafe muku." Kawu Salisu yana matsar ƙwalla ya ce. "Kayya Neehal, ba iya wannan ne cutar da muka yi miki ba, Mahaifinki kafin ya rasu ya ranta mana wasu kuɗaɗe masu kauri da muka buƙata daga gare shi dan mu ƙara jarinmu, amma bayan rasuwarsa saboda son zuciya irin tamu muka ƙi kawo kuɗin a haɗa a raba muku haqqinku ku iyalansa, muka riqe saboda mun san ba mu da gadonsa, muna baƙin cikin a ce ba mu ci komai ba daga cikin dukiyarsa. Dan Allah ki yafe mana Neehal ko za mu samu sassauci a gurin Ubangiji bayan mutuwar mu." Neehal ta ce. "Na yafe muku Kawu, dan Allah ku bar waɗan nan maganganun komai ya wuce." Bata jira cewar su ba ta miƙe ta kawo musu drinks masu sanyi, ai ko bi takan cups ɗin data kawo ta ajiye musu ba su yi ba suka buɗe robar suka shiga kuk'k'uta. Kitchen ta koma ta ƙarasa girkin da take, ta zubo musu a cikin tire ta kawo musu. Shi ma ba su bi takan spoons ba suka saka hannu duk da tururin da abincin yake suka shiga zabga lauma, kana ganinsu ka ga wanda suke tattare da yunwa. Cikin mintunan da ba su fi biyar ba suka share abincin, suka fara sakin gyatsa. Neehal dai kallon su kawai take cike da tausayawa. Suna wanke hannu suka miƙe za su tafi suna zabga mata godiya, ɗakinta ta shiga ta tattaro duka kuɗin dake hannunta ta fito ta miƙa musu ta ce. "Kawu ga wannan a yi cefene, ku yi haquri bani da enough cash ɗin kuɗi a hannuna, amma insha Allahu cikin week ɗin nan zan zo har gida, sai ku bani address ɗin gidan." Ai kamar za su yi mata sujjada saboda murna da godiya, ita abun ma kunya ya bata. Sai da suka bata address ɗin sannan suka tafi. Tattare kayan gurin ta yi ta kai kitchen jikinta a sanyaye, ta dawo ta gyara gurin ta ƙara fesa room freshener a ɗakin. Hijabin jikinta ta cire ta zauna akan kujera ta fara tunanin rayuwa da yanda al'amuran cikinta suke wakana. Ta tuna su Kawu Salisu a da sanin data yi musu ƴan gayu ne masu ji da kansu, amma ƙarshe ga yanda Ubangiji ya yi da su, ba su da maraba da almajirai gashi duk sun tsofe. Ta tuna Uncle Umar da yanda shi ma rayuwa ta juya masa baya, ga ƴarsa Iman ta haifa masa ɗan gaba da Fatiha, Aunty Fauziyya kuwa ta koma kamar zautacciya saboda tension ɗin rayuwar da take ciki. Ta nuna a baya yanda duk suke jin daɗin rayuwarsu suke yin abun da suka ga dama, a lokacin ba sa tunanin akwai lokacin da zai zo da zasu girbi ABIN DA SUKA SHUKA, shi yasa aka ce a rayuwa ka yi mai kyau sai ka ga mai kyau a gaba. Allah yasa mu dace, Amin. A haka Ameen ya dawo ya same ta. Ta ɗaga kai a hankali ta kalle shi tare da amsa masa sallamarsa. Ajiye kayan hannunsa ya yi ya tsaya yana murmushi, ta gane mai yake nufi amma sai ta kasa motsawa balle ta tashi ta yi masa abun da yake jira. Ya ƙaraso inda take ya tsugunna a gabanta yana kallon fuskarta ya ce. "What happened Baby?" Ta lumshe idonta kawai bata ce komai ba. With so worry ya ce. "Oh My God, Baby me ya faru? Ko baki da lafiya ne?" Ya shiga tattab'a wuyanta da fuskarta. Girgiza masa kai kawai ta yi. Ya kama hannunta ya ce. "Please Baby tell me abun da ya faru, hankalina ya fara tashi da ganin yanayinki, ko wani abu ya faru da bana nan?" Ta buɗe idonta tana kallon fuskarsa, damuwa ta hango ƙarara a cikinta, sai ta ji tausayinsa ya cika mata zuciya, daga dawowarsa ta saka shi cikin damuwa, haka yake ko yaya ya ga ta ɗan canza yanzu zai rud'e ya yi ta tambayar ta abun da yake damun ta, in ya gan ta a cikin damuwa kuwa rasa inda zai saka kansa ya ji daɗi yake. Hannu ta kai ta fara shafa fuskarsa ta ce. "Babu komai fa Mijina, kewar ka ce kawai take damu na." Ya saki ajiyar zuciya a hankali yana kallon cikin idonta ya ce. "Kin tabbata? Dan Allah idan wani abu yana damun ki Baby ki faɗa mun." Ta ce. "Da gaske fa Dear babu komai." Ya shafi cikinta ya ce. "Sorry My Boy, da na ƙi kula welcoming ɗinka, rigarmar Mamanka ta saka, yau ka hana ta bacci ka rama mana, Daddy missed you too." Murmushi ta yi tana jin yanda yake shafa cikin nata a dukkan jikinta, ta shafi lallausar sumar kansa ta ce. "Dama can ai ba baccin ake bari na in yi ba." Ya ce. "Ban da sharri dai Baby." Sannan ya yi kissing cikin nata, lumshe idonta ta yi tana sauke numfashi. Ya miƙe ya koma kusa da ita ya zauna ya janyo ta jikinsa ya ce. "Baby! Akwai abun da yake damunki wallahi, dan Allah ki faɗa mun, ganin ki a haka yasa gaba-d'aya na rasa nutsuwata." Ta saka hannunta ta rungume shi sosai tana shaƙar ƙamshinsa tare da sakin ajiyar zuciya, tabbas akwai abun da yake damun ta, kuma ba komai ba ne face yanda ta ga su Kawu Sani da halin matsin rayuwar da suka ce mata suna ciki, amma bata san ta ina zata fara faɗa masa ba. Ta fara shafa kafaɗarsa da hannunta ɗaya ta ce. "Da gaske yaya babu komai, Just I'm not in the mood." Ya ce. "Sorry, bari na yi wanka sai mu fita, na san zaki jin daɗin hakan, ina kike son mu je? Gidan Mama ko gidan Aunty ko gidan Aunty Sadiya ko gidansu little Neehal ko gidan Kawu ko wani gurin daban?" Ta ce. "Gidan Mama, daga nan sai mu biya inga namesake ɗina sannan mu je mu sha ice-cream, Gobe sai mu je gidansu Auntyn." Ya shafi kuncinta ya ce. "An gama Gimbiya Sarautar Mata." Ta ce. "Sarautar Ameen dai." Ya ɗago ta ya ce. "Me kika ce?" Ta yi dariya kawai. Ya ce. "Ni ban taɓa jin kin faɗi sunana ba sai yau, ƙara faɗa mu ji ko kin iya." Kafaɗa ta mak'e masa. Ya ce. "Shikenan mu je in yi waka." Ya miƙar da ita sannan shi ma ya miƙe suka shiga ɗakinsa. Ta taimakonta ya cire kayan jikinsa, ya ɗaura towel a k'ugu Sannan ya fara ƙoƙarin cire mata abayar jikinta. Ta riƙe hannunsa tana ɓata fuska dan ta san me yake nufi ta ce. "Ni fa ban jima da yin wankana ba." Ya langwab'e kai ya ce. "Yanzu kuma taya ni zaki yi." Cikin shagwab'a ta ce. "Ai na san ba iya wankan zaka tsaya ba, sai ka saka ni jik'a gashina da yamman nan." Bai ce komai ba ya cire mata abayar, ya janyo ta jikinsa ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ce. "To ai ke ce Baby kullum ƙara kyau kike da......." Saurin rufe masa baki ta yi dan ta san me zai ce. Murmusawa ya yi ya ɗauke ta cak ya nufi toilet da ita.......Suna hanyar zuwa gidan Mama ne take sanar masa da zuwan su Kawu Salisu, anan ya gane dalilin damuwartata. Washegari ya tambaye ta address ɗin su Kawu Salisu, ta faɗa masa ba tare da tunanin komai ba. Yana fita ya aika yaransa suka siyo kayan abinci masu yawa ya haɗa musu da kuɗi ya ba su address ɗin su Kawu Sani ya ce sukai musu, bai faɗa mata ba sai daga baya take jin labari wataran ta kai musu ziyara suke faɗa mata, su ma suka ce bai ce a ce in ji shi ba, yaran da suka kawo kayan ne suka kwatanta musu shi anan suka gane shi ne. Haka rayuwa ta yi ta tafiya, kwanaki na shud'ewa. Mama ta yi nacin Ameen ya mayar da Hafsah amma ya ƙi, ya ce idan ya dawo da ita ya san ba zai yi adalci a tsakanin su da Neehal ba, dan haka gara bai kwasarwa kansa zunubi ba, dan shi a yanzu babu gurbin wata ƴa mace a cikin zuciyarsa, Neehal ta kanainaye ko ina, dama can tun fil azal ita ce a ciki, ya Auri Hafsat ne kawai saboda matsawar da Mama ta yi masa a time ɗin akan ya yi Aure. Ita ma Neehal ɗin tana yawan yi masa maganar ya mayar da Hafsat ɗin ɗakinta, amma duk sanda ta yi masa maganar basa kwashewa ta daɗi, dan fushi yake yi sosai ya ce dama ya san ba son sa take yi ba. Daƙyar take samu ta lallab'a shi ya sauko. Lokacin da cikin Neehal ya shiga wata tara idan mutum ya gan ta sai ya tausaya mata saboda girman cikin, ƙafafuwanta duk sun kumbubbura. Hana ta aikin komai Ameen ya yi, shi yake komai na gidan kafin ya fita, daga baya kuma Aunty A'isha ta turo musu Maryam ɗinta take taya ta zama da aikace_aikace. E.d.d ɗinta saura one week Mama ta je ta ɗauko ta, ta dawo da ita gida. Ameen bai so haka ba amma babu yadda zai yi, sai dai kusan raba dare yake a gidan kafin ya tafi, a hakan ma sai Mama ta kora shi. Neehal tay ta yi masa dariya. Zuwa wannan lokacin Hafsah ta tabbatar Ameen ba zai taɓa dawowa gare ta ba, ta yi kuka ta yi dana sani mara iyaka, daga baya ta haqura ba dan ta daina son shi ba, sai dai fa har a yanzu tsanar Neehal na nan a cikin ranta, musamman da take ganin kamar ita ce silar rabuwar su da Ameen. An yi bikin Hameedah da wani abokin aikinta mai Mata da yake nacin son ta, a da ta ƙi shi sai da taga bata da kowa sai shi sannan ta amince masa, Tunda Ameen ɗin da take nacin so baya ta ita. Neehal bata je bikin ba saboda time ɗin ta yi nauyi sosai. Matar Ahmad ma ta haifi ɗanta Namiji watanni uku da suka wuce, su Afrah an yi k'ani sai murna, yanzu ma kullum cikin murna suke Auntinsu ta kusa ƙara haifo musu new Baby........ Ranar wata Alhamis cikin dare Neehal ta fara jin ciwo a jikinta, kusan kwana uku kenan tana jin jikin nata babu daɗi, amma ciwon na yau ya fi na kullum. Tun tana yi tana daurewa har ta fara nurk'ususu tare da salati, Mama take Sallah ta sallame ta yi kanta. Ganin Haihuwa ce ta kira Daddy a waya ta sanar masa, cikin hanzari ya baro part ɗinsa suka ɗauke ta da su kai asibiti da ita bayan Mama ta ɗauki duk abun da ake buƙata, Asibitin Nasarawa suka je inda Maman take aiki, dama a can take yin awu. Haka kawai Ameen ya ji ya kasa bacci a daren ranar, sai tashi ya yi ya yo alwala ya shiga yin Sallah. Mama da kanta ta karb'i haihuwar Neehal, sai kusan asuba Allah ya sauke ta lafiya ta santalo Ƴaƴanta Maza guda biyu masu tsananin kama da mahaifinsu. Ba tare an goge musu jiki ba Mama ta rungume su idonta cike da ƙwallar farinciki, sannan ta ɗorawa Neehal su duka akan cinyarta. Neehal tana kallon su ta ji gaba-d'aya zafin wahalar labour da ta sha ta gushe daga cikin zuciyarta, wata zazzafar k'aunar yaran ta maye gurbin su. Mama ta lek'a ta faɗawa Daddy ta ce ya kira Ameen ya sanar masa. Kiran sa Daddy ya yi ya ce masa ya zo suna asibiti Neehal ta haihu, ba tare da ya faɗa masa abun da ta haifa ba. Ga mamakin Ameen sai ya ji hankalinsa ya tashi, mukullin Motor kawai ya ɗauka ya fice cikin sauri. Sam zuciyarsa bata ta Babyn da ka haifa tana ga Neehal, so yake kawai ya gan ta ya ga halin data ciki, ya ga lafiyar jikinta. Neehal tana kwance a ɗakin hutun da aka kaita ita kaɗai, Mama da Daddy suna can tare da Babies ɗin. Ameen ya shigo ɗakin kamar an jefo shi, ya ƙarasa gaban gadon ya kama hannunta yana kiran sunanta cikin damuwa. Bacci ya fara ɗaukar ta hakan yasa daƙyar ta iya buɗe idonta ta kalle shi. Ya ce. "Baby kina lafiya? Ya jikin naki? Mene yake miki ciwo yanzu? Kin sha wahala ko? Sannu Allah ya yi miki albarka." Ta ɗaga hannunta a hankali tana murmushi ta shafi sajen fuskarsa ta ce. "Yaya me yasa baka zo ba, ina ta kiran ka ina son na gan ka." Ya ƙanƙame hannunta a cikin nasa ya ce. "Ban sani ba ne Baby, ban san kina labour ba wallahi, da sai na zo mun yi tare, Mum bata faɗa mun ba." Ta ɗora hannunsa akan cikinta cikin shagwab'a ta ce. "Na sha wahala fa sosai Yaya, haihuwa akwai wahala, ni bazan kuma ba, karka kuma mun ciki ka ji." Ya kwantar da kansa akan ƙirjinta ya ce. "Sorry Baby, Allah ya saka miki da gidan Aljannah, sannu kin ji, yanzu ina ne yake miki ciwo?" Ta ce. "Duka jikina da kaina, more especially cikina." Kamar wanda aka tsikara ya ɗago kansa ya ce. "Sannu Allah ya baki lafiya, insha Allahu zaki samu lafiya soon." Ta gyaɗa masa kai. Ya shiga shafa cikinta ya ce. "Ina Babyn da kika haifa? Mece ce ko Namiji?" Kamar amsar tambayarsa sai ga Mama ta shigo ɗakin rungume da Baby, ya miƙe da sauri ya karb'e shi, Mama ta ce. "Ka jira ai in baka ko?" Ya yi murmushi tare da sakin wata kakkafar ajiyar zuciya, rungume yaron ya yi kam a ƙirjinsa cikin tsananin farin ciki. Ya koma ya zauna a gaban Neehal ya zubawa yaron ido kamar zai cinye shi yana murmushi, cikin ransa kuma yana godiya ga Allah. Mama ta miƙa masa dabino da Zamzam ta ce. "Ka tauna ka ba shi tare da ruwan, ka kuma yi masa addu'a ba kallo kawai ba." Neehal ta yi murmushi, Ameen ya yi kamar yadda Mama ta ce. Ya ɗago ya kalle ta ya ce. "Mum me yasa baki kira ni ba da tana labour?" Mama ta ce. "In ka zo me zaka yi?" Ya ce. "Addu'a mana." Mama ta ce. "Yanzu dai tunda ta sauka lafiya shikenan." Shigowar Daddy dake ɗauke da ɗayan Babyn ne ya hana shi magana. Ya saki baki yana kallon sa, Daddy ya ƙaraso ya miƙa masa Babyn yana murmushi ya ce. "Ga Al_hussain nan." Waro ido Ameen ya yi ya ce. "Dad! Twins ta haifa?" Sai kuma ya juya ya kalli Mama. Ta gyaɗa masa kai tana murmushi. Matsar da na hannunsa ya yi Daddy ya ɗora masa ɗayan akan cinyarsa, ya haɗa su duka ya rungume cikin tsananin farin cikin da bazai misaltu ba, yana ƙara godiya ga Allah da wannan baiwar da ya yi masa." Ya yi mintuna uku a haka sannan ya miƙa wa Daddy Al_hassan ya yiwa Al_hussain addu'a kamar yadda ya yiwa Al_hassan. Ya sunkuya dai-dai fuskar Neehal ya ce. "Thanks You so much Darling, ban san me zan ce miki ba saboda tsananin farin ciki, Allah ya yi miki albarka ya raya mana su, ya sa mu zamto ababen alfahari a gare mu." Idanunta a lumshe ta amsa da Amin cikin jin kunyar su Mama. Ya ɗago yana ɗan jijiiga yaron dake ta mulmul da baki saboda dabino da Zamzam da aka saka a bakin. Mama ta ce, "Tunda ba ki yi baccin ba tashi ki gwada feeding ɗinsu." Ta buɗe ido a hankali tare da tashi zaune tana yamutsa fuska. Ameen ya yi saurin saka mata pillow a bayanta ta jingina da shi sannan ya ɗora mata yaron akan cinyarta. Ƙurawa kyakkyawar fuskarsa ido ta yi tana jin duk duniya babu abun da take so kamar shi da ɗan'uwansa a yanzu, wani irin feeling take ji a kansu wanda baki bazai iya faɗa ba, wannan ita ce soyayyar ɗa da Uwa data ji ana faɗa kenan. Daddy ya miƙawa Ameen ɗayan ya fita dan zuwa Masallaci jin an fara kiran assalatu, Mama ta mara masa baya dan akwai abun da zata yi a office ɗinta yanzu. Ameen ya zauna a kusa da Neehal bayan fitar su yana murmushi ya ce. "Ki bashi mana." Ba tare data ɗauke idonta daga kan ɗanta ba ta ce. "Me?" Ya ce, "Abincinsu mana." Ta yi murmushi tare da zuge zip ɗin rigarta ta ciro Brest ɗin ta ɗan raba bakin yaron ta saka masa a hankali. Kamar bazai sha ba sai kuma ya fara zuk'a, ta ɓata fuska tare da runtse ido. Ameen da ya kura mata ido ya ce. "What?" Ta ce. "Zafi na ji." Ya matsa jikinta sosai ya ce. "Sorry." Ta shafa kuncin yaron hannunsa ta ce. "Kamarku ɗaya da su." Ya ce. "Eh mana, ai saboda na fi ki son su ne." Ta ɓata fuska bata ce komai ba. Gyara Babyn hannunsa ya yi ya rungume ta, kwantar da kanta ta yi akan kafaɗarsa idanunta akan yaranta, jin abun take kamar a mafarki, yau ita ce da ƴaƴa har biyu, gaskiya ikon Allah ya wuce gaban komai a rayuwa. A haka Mama ta turo ƙofa ta same su, saurin barin jikin Ameen ta yi tana ƙara yin ƙasa da kanta. Mama ta dube shi ta ce. "Baza ka yi Sallar ba ne kai?" Ya shafa kansa bai ce komai ba, ya miƙa mata yaron ya fita, ta bi shi da kallo sannan ta mayar da kallon ga Neehal ta ce. "Ruwan Nonon ya zo kenan?" Neehal ta ce. "Ban sani ba, yana dai ta tsotsa." Mama ta ɗauke shi ta saka mata ɗayan ta ce. "Shi ma bashi ya sha, idan ma bai zo ba sosai nan gaba zai zo." Kafin ƙarfe goma na safe Mama ta rubuta musu sallama tunda lafiya ƙalau take ita da Babies ɗin. Da daddare Neehal tana zaune akan gado a ɗakin Mama ita da Ameen ya ce mata. "Baby Wanne suna za'a saka musu ne?" Ta ce. "Duk wanda kake so Yaya." Ya shafi kan na hannunsa ya ce. "Wannan tunda shine Babba a saka masa Muhammad, Sunan Ma'aiki S.A.W, mun kuma yiwa Daddy da Abba takwara." Sannan ya shafi kan na hannunta ya ce. "Wannan kuwa Abubakar Sadik." Ta yi murmushi ta ce. "Masha Allah, sunaye masu daɗi da asali, Allah ya raya su ya saka su biyo hali da dabi'un masu sunan." Ya ce. "Amin, me za'a na ce musu?" Ta yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce. "Sudais da Shureim." Ya ce. "Masha Allah, Allah yasa su kasance masu karatun Alqur'ani kamar masu sunan." Ta ce. "Amin." Suka cigaba da hirar su wadda gaba-d'aya akan yaran ne, idan ka ga yanda suke yiwa yaran sai ka rasa waye ya fi son yaran a cikinsu..... Tunda aka yi haihuwar kullum gidan cikin baƙi ƴan zuwa barka yake, Twins da Mamansu gwanin sha'awa kodayaushe tsaf_tsaf da su an shirya su cikin kaya masu kyau da tsada suna ta tashin ƙamshi. Da safe kafin Ameen ya tafi aiki yake zuwa sai kuma bayan Magriba idan ya dawo, idan ya ɗauki yaran nan daƙyar ake karɓar su daga hannunsa, Neehal kawai yake bawa su ta daɗin rai, ita ma wai dan saboda feeding ɗinsu ne. Saura kwana uku suna Hajiya ta zo, tunda ta zo ta sakawa Ameen ido, bai isa ya shiga sun zauna da Neehal a ɗaki ba sai ta fara mita tana cewa "Jego dai take yi Manne mata." Shi kuma yana sane sai yay ta yin wasu abubuwan yana ƙara kunna ta. Neehal tay ta yi musu dariya. Ana i gobe suna Ahmad ya zo ya ga Babies shi da twins, waɗanda farin ciki ya kusa kashe su saboda Aunty ta haifo musu k'anne guda biyu, kowa da nasa a cewarsu. Kayan Barka sosai Daddy ya siyawa yaran bayan wanda Ameen ya siya already tun kafin a haife su, ga waɗanda mutane suke ta kawowa, sai kayan suka yi yawa sosai Masha Allah. Ranar Suna aka sha shagali a gidan Mama, an yi komai cikin bajinta da wadata. Mai Jego ta sha kyau ita da Babies ɗinta har ma da Angon ƙarnin. Neehal ta cigaba da zama a gidan Mama, shi Ameen ya ɗauka da an yi suna zata koma, Mama ta ce sai bayan ta yi arba'in. Yau Asabar wanda ya kama wata guda cif da haihuwar Neehal. Tana zaune a parlour ita kaɗai tana chatting a wayarta ta ci kwalliya ta yi kyau sosai sai tashin daddaɗan ƙamshi take. Ameen ne ya shigo parlour'n da sallama. Ta ɗaga kai ta kalle shi cikin mamakin ganin sa a dai-dai wannan lokacin, kasancewar time ɗin tsakiyar rana ne bai fi ya zuwa a irin time ɗin ba. Ta gyara zama tare da yi masa sannu da zuwa tana murmushi. Ya zauna a gefen ta yana kallon ta bai ce komai ba. Hannunsa ɗaya ta kama ta ce. "Ya dai?" Ya langwab'ar da kai ya ce. "Baby kullum ƙara kyau kike hankalinki kwance, but me ko bacci bana iyawa saboda rashin ki." Ta ce. "Who told you? Ina missing ɗinka sosai fa Yaya." Ya ce. "Ba wani nan, ni ban gani ba." Ta ce. "Me zan yi ka yarda to?" Ya ce. "Ki cewa Mum kin gaji ke gidanki zaki koma." Ta yi murmushi sosai bata ce komai ba. Ya ɓata fuska ya ce. "Oh dariya ma kike ko?" Ta kwanta a jikinsa tare da rungume shi ta ce. "No, kai ma ka san bazan iya faɗawa Mama haka ba, kuma idan ka yi haquri kwanaki kaɗan suka rage in koma." Ya ce. "Kafin lokacin na gama jiga ta kenan?" Tana yi masa tafiyar tsutsa a bayan kunne ta ce. "Tunda ka daure na baya zaka daure na gaba ma." Ya saka hannayensa ya zagaye bayanta cikin marairaicewa ya ce. "Ni dai ki sakawa Mama kuka ta bar ki mu tafi gidanmu, wankan ya isa haka." Ta ce. "Ka yi haquri Yayana Please mu ƙarasa sauran kwanakin." Banza ya yi mata ya ɓata fuska sosai. Ta kai finger ɗinta ta fara zagaye lips ɗinsa da shi tana faɗa masa wata magana a cikin kunnensa, ya lumshe idonsa tare da yin murmushi ya ce. "Ina Twins love?" Ta ce. "Suna gurin su Aunty Dije sun goya su." Ya ce. "Ke kullum sai dai a goya miki su, ke bakya goya su?" Ta ce. "Ban iya ba ni." Ya ce. "In mun koma gidanmu fa?" Ta ce. "Ai zaka na goya mun su ko?" Ya ja karan hancinta ya ce. "Sai dai ke in na goya ki." Ta ce. "Tom Yayana, su sai su yi ta kwanciyar su kawai." Wani kallo yay mata da ya saka ta yi dariya. Tashi ta yi ta karb'o Sudais Zulai ta biyo ta da Shureim, Ameen ya karb'i Shureim ɗin, wasa ya fara yi masa yana ɗan ɗaga shi. Ya ce. "Baby kin ga yana mun dariya." Ta ce, "Shureim ɗin ko? Yaushe ya iya dariyar?" Ya ce. "Gashi nan kuma." Ta ce. "Na gani ai." Ya ɗago ya dube ta ya ce, Wai ina Mum ne?" Ta ce. "Bacci take yi, jiya Sudais bai bar ta ta yi baccin kirki ba." Ya ce. "Kamarya?" Ta ce. "Kukan dare ya yi ta yi, ni kuma na kai mata shi ta rarrashe shi, tunda ni na yi na yi ya ƙi yin shiru." Ameen ya shafi fuskar yaron ya ce. "Ka daina kukan dare kana hana Mum da Baby bacci, dan wannan Mum ɗin taka raguwa ce, wataran in ka ƙi yin shiru taya ka kukan zata yi." Ta tura masa baki ba ta ce komai ba. Ya kalli lips ɗin da suke zuba k'yalli ya ce. "I want it." Ƙara tura masa su ta yi, ya matso da fuskarsa a hankali ya ɗora nasa akai..... Daƙyar ta samu ya cika ta, shi ma dan Shureim ya fara kuka ne. Ya dungure masa kai sannan ya miƙa mata shi, ta yi murmushi tare da bashi Sudais sannan ta fara feeding ɗinsa. Ƙura nata mata ido ya yi, kallon shi tare da saka hannunta ta kwantar da kansa akan kafaɗarta. Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido yana shaƙar daddaɗan ƙamshinta........Kwanan su Neehal Arba'in da biyu ta koma gidanta ita da Dije domin tana taya ta rainon su Sudais, lokacin sati ɗaya da yin bikin Salma da Sadik. Sabon shafin soyayya Neehal suka buɗe ita da Ameen bayan ta koma wadda tafi ma ta farkon Auransu. Ranar Anniversary ɗinsu Ameen ya yi celebrate ɗinta sosai, kyaututtuka masu tarin yawa ya yi mata na k'auna tare da nuna mata tsantsar soyayya. Washegari kuma suka tafi yawon shak'atawa zuwa other countries su da twins ɗinsu wanda suka yi wayo sosai kamar ba ƴan wata biyu da kwanaki ba.......... *AFTER FIVE YEARS.* Katafaren parlour ne babba mai ɗauke da duk wani abun ƙawata parlour a cikinsa, ƙamshi mai daɗi ne ke tashi a cikin parlour'n. Wasu yara ne ƙanana guda biyu kaɗai a cikin parlour'n Mace da Namiji waɗanda baza su wuce shekara uku ba. Macen tana zaune a kan kujera ta keɓe fuska kamar zata yi kuka. Namijin kuma yana zaune a kan Carpet yana playing game. Hanif da Haneefah kenan second born ɗin su Neehal. Turo ƙofar parlour'n aka yi aka shigo, gaba-d'aya yaran suka kalli bakin ƙofar. Ameen ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Da gudu Haneef ya tashi ya je ya rungume ƙafafunsa, Ameen ya ɗaga shi sama ya shilla sannan ya sauke shi ya kamo hannunsa suka ƙaraso cikin parlour'n. A gaban Haneefah ya tsaya ya ce. "Wa ya taɓa mun Hany Baby ɗita?" Yarinyar mai kama da uwarta exactly ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba ta ce. "Ba Mommy ce ta koro mu downstairs ba, kuma ta ce baza ta ƙara kai mu gidansu Yaya Afrah da gidansu Yaya Neehal da gidan Mama gurinsu Ya Sudais ba." Ameen ya yi murmushi ya ce. "Rashin ji kuka yi mata ko?" Ta ce. "Hanif ne ya barbaza mata kayan kwalliyarta." Hanif ya yi saurin cewa. "Allah Abbu ita ta ce in zo in taya ta kwalliya irin wadda Mommy take yi." Ameen ya ce. "How many times I told you ku daina yiwa Mummy rashin ji kuna saka ta magana saboda bata lafiya?" Haneefah ta ce. "Sorry Abbu mun daina." Ameen ya ɗauke ta ya ce. "Yawwa yaran albarka, ku zo mu je mu bawa Mummy haquri." Ya kama hannun Hanif suka nufi upstairs. A k'aton bedroom ɗin Neehal suka tarar da ita tsaye a gaban mudubi tana gyara kayan dake kan shi. Ta juyo a hankali ta kalle su sau ɗaya ta ɗauke kanta. Suka ƙarasa kusa da ita, Ameen ya ce "Mummy mun zo bayar da haquri." Ta kalle shi ta ce. "Bazan haqura ba yau kar ma ku ɓata bakinku." Haneefah data fi Hanif surutu ta marairaice fuska ta ce. "Please Mummy we are sorry." Harararta ta yi ta ce. "Kin fi kowa iya rashin ji da bakin bayar da haquri." Ameen ya ce. "Yanzu dai Please Mummy forgive us." Neehal ta ce. "Shikenan, amma kar ku kuma." Yaran suka rungume ta suna murna. Haneefah ta ce. "Mummy yanzu zaki kai mu gidansu Yaya Afrah da Yaya Neehal da gidan Mama ko?" Haneef ya ce. "Da gidansu Abul (Ɗan Sadik da Salma) ko Mummy?" Neehal ta ce. "Insha Allah." Ameen ya zaro choculates daga cikin aljihunsa ya ba su sannan ya ce. "A je a parlour asha ban da ɓata jiki da rashin ji." Da gudu suka fice, Neehal ta bi su da kallo a ranta tana jinjina rashin jin su, shi yasa Mama su Sudais ne ƴan wajenta, yanzu ma suna gidanta za su yi mata weekend, su Haneef kuwa ana kai mata su take tattaro su da kayansu ta bayar a dawo da su, dan baza ta iya ciwon bakin bari_bari ba. Ameen ya janyo ta jikinsa ya ce. "Me ya faru ne Babyn Baby?" Ta shagwab'e fuska ta ce. "Kai ne mana, daga fita Masallaci tun ɗazu sai yanzu zaka dawo." Ya kama hannunta suka ƙarasa ya zauna a bakin gado ya zaunar da ita akan cinyarsa ya kwantar da kansa akan kafaɗarta ya ce. "I'm sorry Baby love, mun tsaya da Barrister ne, amma ke ma kin san duk inda nake my heart is with you." Ta yi murmusa tare da shafar sumar kansa bata ce komai ba. Cikinta dake ɗauke da Unborn ɗan wata huɗu ya shafa ya ce. "My Unborn Twins, Abbu missed you." Neehal ta ɓata fuska ta ce. "Na ce maka bazan ƙara haifar twins ba insha Allah, da su Haneef zan ji ko da su in na haife su?" Ya ce. "To ba tare muke rainon ba?" Ta ja kunnen shi ta ce. "Kaima ai rainon naka nake yi." Ya yi murmushi ya ce. "Exactly ƴar Aljannah, yanzu ma a zo a ji da ni." Ta kwantar da kanta a jikinsa ta ce. "Dole ne ma ai, I love You so much Nurul qalbi." Ya ƙara rungume ta tsam kamar zai mayar da ita ciki, cikin wani irin yanayi da ƙamshin jikinta ya jefa shi a ciki ya ce. "Love You too My Baby." Tare da ɗago fuskarta ya haɗe bakinsu guri guda cikin tsananin shauk'i..........✍️ _*Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah. Komai nisan dare gari zai waye, komai nisan jifa ƙasa zai dawo, sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a je ba. Yau 02/06/2022 Ubangiji Mai girma da ɗaukaka ya nufa na kammala wannan book ɗin nawa mai suna NEEHAL, Kuskuren da na yi a cikinsa Allah ya yafe mun, abun da na faɗa dai-dai Allah ya haɗa mu a ladan. Da fatan za'a ɗauki darussan dake cikin labarin, a yi kuma watsi da abubuwan cikinsa marasa kyau. Masoya masu bibiyar littafin Neehal tun daga farko har kawo yau ina godiya tare da yi muku fatan Alkhairi, alkhairin Allah ya kai muku har gadon baccinku. Ina roqon wanda na ɓatawa a cikin wannan tafiyar ya yafe mun, domin ɗan Adam ajizi ne. Waɗanda suke ganin kamar ban yi musu dai-dai ba a cikin labarin su yi haquri haka na tsara labarin tun farko, Na gode Na gode Na gode sosai MASOYA, Allah ya bar k'auna. Sai mun haɗu a sabon Nobel ɗina nan ba da jimawa ba da yardar Allah. NEEHAL, AMEEN AND MAMA they will miss you😍🥰.*_ *DOMIN GYARA KO SHARHI AKAN LITTAFIN NEEHAL, Contact Me.* 👇 *09047871750* *By* *Zeey Kumurya* Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels