Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels ๏ปฟ[: TA ME GARI* NA khadija usman *BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM* 1โƒฃ Na rantse da Allah bazan yadda ba sai an biyani nikana tun kin isa ma wlh kika sake kika je kika fadawa innata yaseen sai kinci ubanki cewar dije dake kara tattake garin dake zube a kasa kuma an barar din duk ranar da kika qara cemin dijan gala tame gari tuwon gidanku ma zanje in barar wlh su Shatu dake gefe suna kallo ba damar suyi magana dije taci uwarsu dan haka sukayi gum ko yi hakurin sun kasa fada hafsi kuwa sai rizgar kukanta takeyi dan tasan yau idan taje gida kashinta ya bushe gurin delu dan saita mata dukan mutuwa kuma tasata nemo mata wani garin koda ta tuna ai saita kara bare baki dije ce ta kalleta tace wai ke uwar me nayi miki da kiketa min wannan kukan danma ban faffasa miki baki ba hegiya me idon gyada shatu ce ta karaso kusa da ita tace kin san delu dukanta zatayi idan taje gida kin san dai ba imani ne da ita ba shuru dije tayi na dan wani lokaci kamar wadda ta tuna wani abun sannan kuma tace toh kinga ke kika jawo wa kanki tunda kika tsoka ne ni amma kiyi haquri kinji tahi nasan yadda zamuyi amma sai kin bani hakuri da sauri hafsi tace yi haquri dan Allah toh naji ya sunana Anti dije wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta dan tana masifar son sunan nan na 'yan binni dan haka da sauri tacewa hafsi taso muje gidanmu in baki dawar ki kara kaiwa nikan da sauri hafsi ta mike dan tasan ko yanzu takai nikan sai ta ci ubanta dan ta jima dan haka da sauri suka je gidansu dije koda suka je dije bata boyewa inna saudi komai ba aikuwa ta basu dawa suka kai nika har gida dije suka raka hafsi aikuwa delu kamar ta ari baki taita jarabar ta dayake 'yan dukan basa kusa sun dai samu rabon zagi amma bata daki hafsi ba ******** mota ce kirar honda Accord LC ta shigo cikin garin Gawo kasancewar rashin kyawun hanyar ga kuma da alama wanda ke cikin motar yasha tafiya mutum biyu ne ciki matasan samari kyawawa daka gansu kaga wadanda hutu da nera suka zauna a wajen tuki yakeyi kamar wanda aka yiwa dole kafin ya waiga ya kalli dayan yace cikin kasalalliyar muryarsa Habeeb wlh nagaji dayawa na matsu mu qarasa cikin garin nan in yada zango kan gadon tsohon nan wanda aka kira da habeeb yayi murmushi kafin yace hmm kaima kenan bare kuma ni dana sha tafiya kwana nan gashi yau ma son ganin wannan me ran karfen yasa na biyoka hmmm kai dai bari ai wannan tsohon inaga rokon Allah yakeyi mana shiyasa bama iya daukar lokaci bamu ganshi ba ko daddy ma fa kullum shi batun shi baba malam kusan koyaushe yana kan hanya toh Allah yaja da kwana dai Ameen ya Allah kam bala'i ta fada yayin da taga motar na kokarin shigewa alamar ma na ciki besan me yayi ba giginyar dake hannunta ta dauka ta saita glass din motar ta wurga cikin sa'a kuwa ta daki glass din side driver sannan taje ta hada da bakin habeeb wanda yagama amsawa da ameen yanzu wani wawan birki ya taka tare da kiran ya Allah sbd ganin abun da yayi kamar a mafarki dubansa yakai inda habeeb yake yaga nan da nan bakinsa ya haye ya wani kumbura kamar bakin jaba ga kuma jini na zuba yaso yayi dariya harga Allah amma ba hali dole ya ambaci kalmar subahanallah ya fara kokarin bude motar ya fito danya zagaya gurin habeeb dan shi har yanzu baisan ta inda abin yafaru ba amma dai kawai yaga wulgawar abu tsaye take ta rike kugu da hannu daya dayan kuma wata katuwar giginyar ce datafi ta farko girma kwalliyar fuskarta kawai yagani yaji gabansa ya fadi dan wlh babu tantama wannan aljana ce wa'innahu sulaimanu wa'innahu bismillahir rahmanir raheem ya fara ambata cike da tsoro da faduwar gaba domin dai babu tantama wannan aljana ce duba da yanayin ta gata fara sol saika ce zabiya ga kuma uban bakin kwalli data shafa a bakin nan kamar 'yar auta ga jagira cinku ta hade da kwallin dataja hawayen masoyi jikinsa ne ya hau kyarma inda ita kuma dije take ta fahimci meyake nufi aikuwa a zuciyarta tace anzo gurin harara taci gaba da wurga masa tanata juya ido inda shikuma hakan ke kara firgita shi cikin karkarwar jiki ya qarasa inda habeeb yake ya sunkuyar da kansa kasa sakamakon nauyin daya yi masa sbd giginyar ta bugi kansa ga haqorinsa guda daya daya fita ga bakin ya kumbura yayi tsayi kamar shantu cikin rawar jiki Nasir yakarasa inda yake ya bude murfin motar yana me karanta duk addu'ar data zo bakinsa dago kansa yayi ya dubeshi jin yanata kwarara addu'a sai ya fahimci lallai gamo sukayi domin ya hango aljanar tsaye da irin tasu giginyar ta Aljanu tanata juya ido duk da jirin dayake ji hakan bai hanashi rudewa ba shima ya kama kokarin fitowar nan suka kankame juna shida nasir wanda har kwalla yafara yi dan tsoro musamman duba da yayi da yanayin gurin babu komai sai tarin bishiyoyi da besan kona meye ba amma dai yasan harda na kuka kuma sune gidan aljanu cikin wata irin murya da malkwada harshe dije tace ku bil adama daga ina wani irin fitsari ne ya kufcewa naseer shiko habeeb ji yayi kamar ya suma dan kanshi saida ya amsa ko bakwa ji ne ina tambayarku? cikin in i na nasir yace yi....yi..ha.k..uri.daga Abuja Abuja wlh muka zo shine aka ce dan kunzo daga binni kubi takan 'ya'yana suna tsaka da yin wasan su wato sbd kun raina mu ko ah ah wlh ba...bahaka bane wlh ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba dan girman Allah kiyi haquri wlh bamu sani ba toh naji zan hakura amma sai dai kubar abin hawanku anan ku qarasa da kafarku inda zaku ko kuma ni inkai ku ah ah wlh mun gode suka fada a tare zamu karasa da kafarmu ina ke ina wahala akanmu hahahahahaha tayi dariya sannan tace saini dije uwar aljanu ku wuce amma fa bazan kyaleku ba duba da yadda kuka raunata 'ya'yana yanzu haka suna bangon duniya wajen me magani dan haka sai naje naga yadda jikinsu yake tukunna kafin in san wanne hukunci zanyi muku kuuuuu cikin nasir yayi wata kara dan girman Allah kiyi hakuri wlh bamu san dasu bane ina mu ina aikata haka muna sane toh naji ku tashi ku tafi gobe kuzo ku dauke wannan motar amma ba yau ba to toh toh mun yadda wlh sam habeeb yakasa tafiya yayin da naseer ne ya kamashi da kyar yasaba a kafada ya miki hanya bako waiwaye harda hadawa da dan gudu bako waiwaye tunda dije taga haka ta zube a gurin tanata dariya harda hawaye a irin wannan yanayin su shatu suka qaraso suka risketa nan suka shiga tambayarta sam kin fada musu tayi gashi ba damar su matsa ta dankari banza dan karfi ne da ita kamar yaki inji su duk ta fisu karfi sai da tayi me isarta kafin ta mike tace mu tafi hafsi ce tayi karfin halin tambayarta ina gyadar da kika samo ? ban sani ba tafada tana harararta ai kuwa tayi gum suka ci gaba dactafiya da zarara ta tuno yadda bakin habeeb ya koma da kuma yadda taga Naseer yayi fitsari saita kuma kyalkyalewa da dariya sudai su hafsi nasu ido amma ba damar tambaya sai uwar gayyar ta so bada labari dakanta ***** tafiya yakeyi ya hada zufa ga habeeb na cikin wani hali da taimakon Allah da taimakon wasu matasa daya sansu a gidan baba malam suka qarasa da shi gida ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* 2โƒฃ *ina neman afuwarku sakamakon jina shuru da kukayi a littafina ZARGI NE SILA Insha Allahu shima zan karasa muku shi nan kusa uzuri ne yasha kaina* ba karamin tashin hankali baba malam ya shiga ba ganin halin dasu habeeb suka shigo cikin rudewa ya shiga tambayarsu lfy ko hadari sukayi sam naseer baya cikin nutsuwarsa abinda kawai yake iya fada shine gamo mukayi malam aljana wlh aljana ce subahanallah!!! malam ya fada kafin ya ce aje a kirawo muntari me chemist don ya duba habeeb domin yaga yana jin jiki da alama bayan an gama masa duk abinda yakamata ayi masa harda allura malam kuwa rubutu yayi musu tare da tofa musu addu'oi sbd dukansu sun firgice daga baya suka samu bacci su duka kowa yanata al'ajabin abun wai aljana toh ko a ina suka ganta oho **** da wakarta ta shigo tana rerawa inda ko sallama batayi ba ta shigo innah dake zaune tana dama fura tace kai kai dije nidai naga ranar da zakiyi hankali wlh ace da girmanki amma kina abu kamar wata karamar yarinya ni wai makarantar Allan ma anya idan na turaki kina zuwa kuwa ? turo baki tayi gaba sannan tace ina zuwa mana toh ba'a can na iya karatun sallah ba kuma dai bari in fada miki tsakani da Allah ina zuwa in labe wani lokacin bayan ajin su mairo ta gidan me gari in ta kallonsu ana koya musu karatun arna haba inna saudi ta rike tace oh ni saude nagamu da ja'irar yarinya wato duk hanaki din danayi wato baki jiba ko saida kika dinga zuwa Allah ya shirye ki Ameen dan kuwa yanzu ma a shirye nake kamar carbi kasa magana inna tayi a ranta tana jinjina kiriniya irinta dije tarasa dalili ko dan taga ita kadai ce ohoo haka dai taci gaba da damun furarta ita ko dije ta shiga cikin daki ta kwanta a cewarta saitayi bacci kuma kada a tasheta tana kwanciya ta tuna da abinda yafaru dazu aikuwa ta sheke da dariya wadda saida inna ta taso ta lekata taganta sai dariya takeyi harda rike ciki girgiza kai kawai tayi ta saki labulen dan ita lamarin dije sai addu,a wani lokacin idan tayi abu kamar me aljanu *Asalin labarin* Malam muhammadu dan asalin jigawa ne yanada mata hudu da tarin yara matarsa ta fari nada yara shidda maza ta biyu kuwa yaranta tara bakawai mata biyu maza ta ukun nada yara biyu duk maza sai Amaryarsa dake da yara goma sha daya tara maxa biyu mata Alhmdlh gidan akwai zaman lfy da hadin kai domin ya gina gidansa da zaman lfy dazumunci mariya itace matarsa ta uku itace keda yara biyu inusa da Auwalu duk cikin matan sa tafi hakuri da kawaici hakan yasa yaranta suma sukayi sanyun hali irin nata sam basu da hayanikuma dukansu manoma ne sosai yayin da dukansu sukai aure kuma barakallah dukansu suna nan da rai malam inusa nada mata daya wato saude Allah be azurtasu da haihuwa ba tsawon lokaci sai daga baya suka fara samu amma kuma yaran wabi sukeyi saida tayi haihuwa hudu haka kafin daga baya tasamu cikin dijee cikin hukuncin Allah kuma ita ta rayu khadija ta taso yarinya kyakkyawa fara ce sol irin fararen nan ne sosai sai dai fa batajin magana duk wata tsokana da caskale ta kware akai dan haka yara sa'anninta ke tsoronta inda har suka samata suna bata sani ba wato uwar mazga๐Ÿคฃ a cikin 'ya'yan malam muhammadu dayawa daga cikinsu sun sami cigaban rayuwa inda sukayi karatun boko wasu sun sami aiki a birni wasu kuwa kasuwanci yakaisu kuma cikin ikon Allah ansami daukaka da wadata inda malam muhammadu yake da matansa suke samun kulawa a yanzu haka shine matsayin me gari wanda su habeeb 'ya'ya ne ga dansa babba wato khamis dake aiki a abuja sam basu dade da dawowa daga U.S ba inda suka shafe shekara goma sha biyu a can dan a can sukayi karatun su na secondry har zuwa jami'a indadukan su suka karanci fannin likiktanci shi habeeh ganygoicial shi kuma Naseer consultant ne yanzu haka satinsu biyu da dawowa shine suketa zaga dangi dan suna son kauye basu da kyama sam *cigaban labari* uwar mazga nata sharar bacci cikin baccin ma mafarkin su habeeb tayita yi wai har da zawo naseer yayi aikuwa take ta qara rushewa da dariya wadda ta qara jawo hankalin inna ganin da tayi tanata bacci ba ruwanta yasata tashinta dan itafa ta gama gasgata aljanu ne da dije ***** inna saudi ce ta fito dauke da kwarya cike da fura inda dije dake zaune gefen babanta yana cin tuwo tanata zuba mishi surutu inna saudi tace malam na fito bari inyi sauri inje in dawo inga jikin nasu dije taso muje ki rakani dan dare ne yanzu yafi mu tafi mu biyu ah ah ni ba inda zani ai munyi fada da baba malam shiyasa jiya da hafsi tace min dijangala tame gari na barar mata da gari ni yanzu nayi yaji saiya zo biko dariya sukayi dukansu inda malam inusa yace yi tafiyarki kinji kyale wannan uwar rigimar ai bama saika ce ba ni nayi gaba saina dawo a dawo lfy innata Allah yasa tasa kai ta fice gyara zamanta tayi tace baba wai ni waye beda lfy ne a gidan me gari ? yayyenki ne na abuja wai gamo sukayi da aljana a hanyar su ta shigowa gar......ai be qarasa ba yaga ta mike ta suri takalma tana bari inje in raka inna sai na dawo ta zura da gudu tabarsshi da sakin baki kafin daga baya yayi murmushi yace Allah ya shiryamin ke dije ta **** bata riski inna a hanya ba dan ba hanyar datayi tsammani tabi ba kusan a tare suka isa amma innah sam bata ganta ba ta shige gidan bayan sun gaisa da surikanta ta shiga bangaren mai gari ta gaisheshi tare da su habeeb wadanda suka warware amma kumburin bakin habeeb na nan idan nasir ya kalle shi saiya qara fashewa da dariya iya kuluwa habeeb ya kulu jiyakeyi inda ba aljana bace tayi musu haka ba wlh da mutum ne bema san me zaiyi masa ba a haka inna ta musu sallama tana dada jajanta abin kafin ta miqe tayi musu sallama ta fita a kofar gida ta riski me gari zaune bisa kujerar sa ta tsoffi ta lababa ta shige gidan indayana kallonta amma ya qyaleta dan yasan halin mutuniyar tunda bataso kulashi ba toh gara ya kyaleta dakin kakarta ta je ta gaisheta da sauran matan gidan sunata tsokanarta malam yaje biko kenan lababawa tayi ta dauki kwalli cikin kayan kwalliyar dake cikin wani karamin kwando kafin tace goggo habi ance anyi baki a gidan nan suna ina ? suna can sashen malam dan basuji dadi ba kam dan gamo sukayi. zaro idoo tayi๐Ÿ˜ณgamo fa a ina? can tsallaken lawoli dan sai dazu jibrin yaje ya dauko motar su ma dan can suka barta oh Allah ya kiyaye gaba bari naje in gansu toh maxa kam dan dare yafara yi kizo ki tafi gida in kuma nan kwana to ah ah niba zan kwana a nan ba oh dai ke kika sani sai da ta tsaya lungun bangaren ta zazzana kwalli ta fito aljanar sak๐Ÿ‘นkafin ta nufi dakin datake jiyo maganar su da alama waya daya yakeyi daga cikinsu cikin sanda ta qarasa qofar dakin cikin sa'a tana zuwa ana kawo wuta inda haske ya gauraye dakin baki daya kasancewar habeeb ya juya bayane yana shan fura da kyar da dabara sbd bakinsa shi kuma nasir yana waya hankalinsa be kawo inda take ba shiyasa basu ga tsayawaer ta ba Angaishe ku fitinannun bil adama masu kunnen kashi.... [16/12, 11:39] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ * *vote* *comment* *share* [16/12, 11:39] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* na khadija usman 5โƒฃ cikin kwanaki kadan aka gamawa dije komai na makarantar ta arabi da boko kasancewar Alhaji khamis ba mazauni bane yasa dije ke fuskantar rashin jin dadin zama ga dukka mutanen gidan dan su nasir ba qaramar wahala suke bata ba saukinta daya bangaren masu aiki take shiyasa take dan samun rangwame duk tayi sanyi da dana sanin zuwa binni sam inbanda karatu ba abinda tamaida hankali akai dawowarta kenan daga makaranta ta shiga tayi wanka dan dama bata son kazanta duk shakiyancinta man basira me aiki take shafawa duk da vaseline ne amma bawani duhu datayi koba komai cimar kauye da ta birni akwai banbanci kuma ga A.C dake ratsata daga school har gida dan makaranta me tsada aka sata kasancewar tayi primary daga nan inna tace bazata yadda taci gaba da karatun arna ba shiyasa ta hakura su kuma anan suka sata a J S S 3 bada jimawa ba jasu zana juinior waec kuma alhmdllh tana fahimta sosai ko yanzu data gama shafa mai niyya tayi tadanyi kwalliyarta amma data tuna in tayi anan za'a yi mata dariya hakan yasa tafasa yi tunda bata iya ta 'yan birni ba har yanzu dan kayan kwalliyarta tun na gida ne fitowarta yayi dai dai da fitowar habeeb wanda ya zuwa yanzu yasa an mayar masa da hakorin roba a inda yasamu gibi baza'a taba ganewa ba tafiya yakeyi yana waya da alama hirar ta soyayya ce duba da yadda yaketa lumshe ido tare da karya murya fitowa tayi zuwa kitchen dan tadau abincinta sanye take da riga da sicket na atamfa se yawo takeyi cikinsu kusa. dinkin kauye sam bata lura dashi ba har saida takawo kusa dashi kamshin hadadden turarensa na indunusia ya bugi hancinta wuceshi tayi ta shige tadauko abincin ta dai dai tazo fitowa sukayi karo miyar agushi ce da tuwon shinkafa duk ta hada a kwano daya hakan yasa malmalar tuwon tayi kasa yayin da miyar tasauka jikin farar T.Shirt din dake jikinsa ta gangara kasa aikuwa take ya saki wata 'yar qara sakamakon miyar nada dan zafi dan kun san manyan coolers na riqe zafi sosai dan ja haya tayi kadan a dan tsorace dan sam bata bukatar wani abu ya hadata da wadan nan azzaluman dan haka kawai ma in sun so wahalar da ita sukeyi suyita cewa tayi musu kukan aljanu ko wani abun in takiyi su daketa bare kuma yanzu data tabbatar tayi laifi ai bata gama tunani ba taji saukar tagwayen marin dasai da kanta ya bugu da fredge din dake wurin wata qara tasaki wadda mamy ahigowarta kenan ita da naair da wata budurwa wadda bata santa ba nasir jaye da troly koda suka shigo suka ga meya faru iyakar kuluwa mamy ta kulu yayin da naseer ya fara bala'i yana qara fadin ya tsani yarinyar nan shiko habeeb tunda ya mareta huci kawai yakeyi yayin da yake qara jin tsanar yarinyar har cikin ransa budurwar dake tsaye ce ta yamutsa fuska tare da fadin mamy pls where did u get dis poolish basterd girl? hamm yusra she's from Alhaji's village !!amma gaskiya kinyi sake mamy dubi fa da abincin da zata cinye amma dai daddy yaqara yawan abincin gidan ko dan kin san mutanen qauye da ci basu san wani mentaining ba burinsu kawai ciki yadauka musamman tuwo basa masa wasa bare anga farin tuwo tsaki habeeb yaja kafin yace ai zataci ubanta wlh yau bazata ci abinci a gidan nan ba nasir ne yayi caraf da cewa iya yau kawai ai wlh sai jibi kafin taci wlh ni kwana uku ma yakamata tayi dan ubanta intaji wuya dakanta zata koma kauye ai shegiya me siffar 'yan ruwa dariya duka suka sa banda habeeb da ya qara hambareta ya juya ya fice nan suka gama mata tujara kafin suka barta a gurin bayan mamy tasa basira ta kwashe tuwon daya zube ta kuma tabbatar kar abawa dije abincin dare a gurin suka barta tanata kuka yayin da tayi me isarta data tuna innarta da baffanta can kuwa saita yi shuru ta furta a fili ina dalili zan zauna ana cutar dani yaseen bazan yadda ba gara in koma dijeta ta da dije masifa dije bala,i dije annoba jahannama ga fasinja uwar mazga bari inga wato kai kace yau bazanci abinci ba yau toh wlh kaine bazaka cishi ba har sai gobe kajawa kanka kai kuma uban 'yan mugunta kace bazanci ba har sai jibi toh kaima sai jibin kaci ku kuwa masu cewa sai nan da kwana uku toh kuwa sai lokacin zakuci dukanku dariya tayi ta mike tana taba inda ya mareta ta jinjina kai ta tashi ta shiga dakinta kudin da daddy yabawata last week yace inta tashi siyen wani abun basaita tambaya ba dan haka ta boye su bata ma siye komai ba su ta je tadauko ta fito zuwa farfajiyar gidan gurin bala driver ta nufa inda yana ganinta ya shiga washe baki qarasawa tayi cikin sakin fuska ta duqa har kasa ta gaisheshi ya amsa cike da jin dadi kafi. tace dama aikoni akayi yace toh toh ya akayi? gashi hajiya tace kasiyo mata maganin kashi wane irin maganin kashi kuma? eh wai bakuwar nan ce dasuka zo tare yau kwananta goma batayi kashi ba shine tace a siyo mata wanda zaisa tayi sannan wai da maganin na wanda in an yaye yaro ake bashi dan yayi bacci wai yaye za'a kawo mata yau shine tace a siyo mata shi toh kaao kudin amma ina su Alhaji karami ai su suke shigo da magani gidan in ana buqata wai mantawa sukayi shiyasa tace yasiyo sachet goma sha biyu biyu dan a ajiye sbd gaba toh yafada tare da miqewa ya tafi dan akwai wani pharmacy nan bayan layin guri tasamu tazauna dan ta jirashi har ya dawo hhhhhhhh mudai je zuwa waitng your's comments [16/12, 11:39] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* NA khadija usman *gaskiya naga soyayya yau Alhmdllh naga sakonninku masoya wannan buk din banyi niyyar posting yau ba amma gashi nayi muku kyauta sadaukarwa ga dukkan masoya dijangala ta me gari* ๐Ÿ˜˜ 3โƒฃ wata irin bugawa kirjinsu yayi a tare inda nasir ya bude baki da niyyar yin ihu tace kanamin ihu bakinka zai tsaya a haka har abada gum yayi banda zufa ba abinda ke ketowa ita ko se raba ido takeyi a dole aljana habeeb dake zaune bakinsa fal da fura dan yakasa hadiyewa karasawa tayi cikin dakin yayin da dukansu yau saida sukayi fitsari dariya ce fal cikin dije amma takasa yi ta gintse kallon kwaryar gaban habeeb tayi taganta cike da fura tab wadda duk iya shansu basu isa su shanye ta ba bare ma taga 'yan binni kadan suke cin abinci ko a film in an nuno hmmm tace a zuciyarta ta furta yau zakusha azabatul ula kallon su tayi taga yadda suke makyarkyata tace wato bakwajin magana ko ? ko a cikin bil'adaman naga ku takadirai ne kun takamin yara sunacan sun sami gocewar kashi a tsakiyar kansu amma ku kuna nan kuna shan fura ba ruwanku ko sannan danace kada ku dauki abin hawanku sai gobe shine kuka tura jibirila dan me gari ya dauko ko sbd kun raina izayar jinni toh tunda yarana suna halin jinya yanzu kuma bari in kwantar daku dan mai maganinsu ya fadamin yace sai sunyi shekara dari uku da saba'in kafin su warke abin takaicin ma gasu 'yan biyu ne ko yayesu banyi ba duk jarirai ne basu wuce shekara dari da ashirin ba gashi kunja musu jinya tun suna rarrafe dan haka tunda kuma ku biyu ne yanzu zan yi muku abinda kukayi musu kashin tsakiyar kanku zan malkwadar yadda zakuyi jinya tare wayyo Allah nadan girman Allah kiyi haquri wlh wlh bamu san da yaranki a gurinba dan ya rasulillahi manzon Allah sallallahu alaihi wasallam dan binta 'yar ma'aikin Allah nanfa suka shiga rokarta duk da dai shi nasiri a iya bincikensa besan da wani kashi a tsakiyar kai ba amma ba mamaki a halittar aljanu akwai shi su kuma ta tsinka musu jijiyar kai yau sun shiga uku shi wlh da yasan haka ne wlh da be zo kauyen nan ba shiyasa mamy bata son su zo a fannin habeeb ma haka kukan zuci yakeyi yayin daya saki baki furar ta zubo dan iya tashin hankali yana ciki a rayuwarsa ba abinda ya ke tsoro irin aljani yau saiga shi garin tukin ganganci irin na naseer yaje ya tsokano musu su kunji fa sharri readers๐Ÿคฃ katse musu tunani tayi ta hanyar ce musu zanyi muku afuwa amma da sharadi da sauri sukace mun amince wlh ko meye mun yadda mudai ki dena zuwa mana toh in kun yadda zaku shanye furar nan duka yanzu ๐Ÿ˜ณzaro ido sukayi waje tare da fashewa da kuka musamman nasir da a duniya ba abinda ya tsana irin fura cikin marairai ce fuska da kuka ya hada hannunsa biyu yace dan girman Allah kiyi hakuri wlh bana shsn fura danasha amai zanyi ke zan iya kwanciya ciwo ma oh to to tunda baka shan fura bari a sake maka hukunci zan daure cikinka kadaina kashi da fitsari tsawon shekara goma zan kanne maka ido daya zan toshe maka kofar hanci daya da rabin bakinka zan...... ya isa dan Allah kiyi hakuri wlh zan sha kafin tayi wata magana tuni sun fara shan furar inda suka dinga kokawa da ludayi a cewarta basa sha sosai zata kawo musu irin tasu ta aljanu aikuwa suka bada himma sosai inda suketa sha cikinsu ya cika dam gashi furar ko rabi batayi ba dan su a ganinsu ma kamar qarata akeyi bata ankara ba kawai taga sun fashe da kuka a tare abinda yabata dariya kenan wai babba da kuka abinda bata taba gani ba sai a talabijin dan haka batasan lokacin data kama dariya ba su suna kuka ita tana dariya gashi dai furar nan shanta suke motsi taji alamar za'a shigo gurin ganin sun duka suna kallon fura suna kuka yasata saurin barin gurin ta labe bayan dakin dan wani lungu ta fara dirje bakin fuskarta da sallama malam ya shigo gurin turus yayi ganin su sai gunjin kuka sukeyi suna shan fura subahanallah ya fada yana me kiran sunan su jin muryar malam yasasu dagowa suna fadin yauwa malam aljana wlh tana dakin nan sun rude gaba daya yayin da itako tana jin suna aljana ta dira ta katanga tayi dakin kakarta tana fadin ni nayi gida dan nama fasa zuwa gaida bakin saida safe nazo au da duk kina ina ja'irar yarinya nama aza kinyi gida toh ban tafi ba sai yanzu nayi niyya ehee mificin hannunta tajefo mata ta kauce tana dariya ta fice daga gidan sosai naseer ke amai ya galabaita matuka inda hankalin malam yatashi sosai dan shima habeeb zazzabi ya rufeshi ba shiri malam yasa aka dauko mota aka nufi asibitin cikin gari dasu dan basu taimako dan shi lamarin yana bashi mamaki wai aljana kuma duka su biyu ke ganinta saida aka sa musu drip dukansu aka musu allurai kafin suka yi bacci amma a dan wannan lokacin duk sun rame ******** tunda abin nan yafaru bata qara zuwa gidan malam megari ba dan ita tama manta da wasu baki yau kusan kwana hudu kenan tadai ga innarta na yawan zuwa gidan me gari yau da wuri ta tashi ta share gidan tsaf duk da shekararta sha hudu yanzu amma tana aiki sosai sai dai in bata so ba yau dinma dan tanason ta bi su sadiya cikin gari dan zasuje gidan yayar sadiyar ne dan haka takevtaya inna aiki dan karta hanata **** a gajiye suke likis sbd tafiyar kasa da suka sha dan haka tasamu gefen hanya ta zauna tana mayar da numfashi kamar wadda tayi gudu cikin tsananin gajiya ta dubi sadiya tace yaseen bazan iya qarasawa gida a kafa ba wannan ai sai in mutu kafin inkai to ai laifinki ne dije an bamu darinmu ta ihemu mu hau mahin kika tahi kikace a rabeta kowa ya kahe nahi to gahinan ai sawun mu ya fada mana dan ni wlh ji nakeyi kamar ba a jikina kafafuna suke ba toh ni uwarku ce da in nace kuyi abu he kunyi a wane dalili toh wlh duk wadda taqaramin harri banyi abu ba tace nayi hena mazgeta hegu kawai .gum sukayi sun san sauran dan duk wadda tace kala yanzu uwar mazga zata kaddamar musu kunga ku tahi mu tare me mahin ya kaimu gida to ina kudin ? cewar shatu ku zo kuji dabarar dana shirya duk suka hada ka wunansu guri daya kome suka ce oho naga dai sun rushe da dariya sannan suka mike suka fara tarar dan mashin sun tari mashin yakai goma ba wanda ya tsaya sai daga baya wani saurayi ya tsaya yace ina zaku ne 'yammata? nan Gawo nawa? toh ku bada nera sittin tunda ku uku ne ah ah malam cewar dije uku hamsin in yayi maka dariya abin yabashi wai uku hamsin dan haka yace to ku hau nan suka dane mashin dukansu sannu har suka iso cikin gawo dai dai gidan me gari inda dan wani tudu yake suka ce masa ya isa ya tsaya yanata zuba musu surutu sukuwa wannan ta kalli wannan ta kalli wannan da haka kuwa sai yaga hafsi da shatu sun kwasa a guje dije ta yunkura yayi caraf ya riketa aikuwa dan da nan kallo yadawo garesu inda yara suka fara taruwa harda 'yan manya manya kan kace me guri ya cika dam tuni lbr ya isko gidan megari yana zaune dasu habeeb dake shirin komawa gida gobe dan Alhmdllh sun sami sauki dan megari yayita amso musu taimako maganin iska kuwa da tsari duk anyi musu shi suna zaune suna tattaunawa akan gidajen da basu je ba yau zuwa gobe zasu je na kusa kusa na nesa kuma sai sun kuma dawowa ana haka aka zo aka fadawa me gari wai ga dije can tayi sata an kamata cikin sauri ya mike duk da jikin tsufa amma kalmar tayi muni sata!!!sata fa toh meta sata ? ganin yadda maganar ta shigeshi yasa su habeeb tambayar sa wacece dije? kanwarku ce diyar gurin inusa ku tashi muje duka suka miki suka bi shi koda suka iso gurin sun iske dandazon mutane an taru koda akaga me gari kowa ya ratse yabashi hanya ya isa gurin inda yaga dije tsaye me mashin ya rike mata hijabi itako ko a jikinta tanata gwagwiyar goruba rasa ma me zai ce yayi inda ya qarasa yana fadin malam dan Allah sakarta mana wlh baba bazan saketa ba sai an biyani kudina nawa ne kudin naka? naira hamsin ne yanzu kai da duk akan nera hamsin katarawa mutane wannan jama'ar toh ai hakkina ne naga kuma akan sana'ata ne toh garin yaya kudi ya hadaku? nan yakwashe komai yafada masa aljihu ya laluba ya ciro nera dari yabashi yace yabar canjin sannan yasaki dije malam yakama hannunta suka nufi cikin gida su habeeb sam basu lura ba dan suna waya ne da mumy sai da suka gama suka juya suka hango bayan me gari rike da hannun wata yarinya ze shiga gida nan suka nufi gidan suma tsaye ya tadda matansa da sauran ahlin gidan duk tsaitsaiye suna jimamin abin nan yabasu labarin ainihin abinda yafaru kowa ya kalli dije wadda har yanzu bata cewa kowa kanzil ba tanata dai cin goribarta ana haka su naseer suka shigo kasancewar dije ta juya baya nan suka tambayu meya faru nan malam ya shiga sanar dasu cikin zolaya habeeb yace tab ashe kuwa yau sai na bawa budurwar kauye kashi dai dai nan dije ta juyo akayi ko sa'a tasha kwalliyar nan sai dai yau jambaki tasaka kanta kile sabanin baya wani uban ihu naseer yasaki inda shima habeeb ya karba suka fara fadin gata nan itace suka kwasa da gudu sai dakin inna dudu suka rufo mamaki ne yakama kowa yayin da dije ta zube a gurin tanata dariya ganin haka malam ya dauka shedananta ne dan haka be bi ta kanta ba ya nufi dakin da suka rufe anyi anyi su bude sunki dije ce ta taso tazo dai dai kofar windo ta leka tace in baku bude kofar nan ba saina kwakule muku idanu da sauri suka taso suka hau kokawar bude kofa tun daga nan malam ya fahimci karatun suna budewa dije ta kara fashewa da dariya zasuyi ihu me gari ya buga musu tsawa yace dama wannan ce aljanar datake tsorata ku? eh itace wlh itace shi kanshi me garin yaso yin dariya ganin yadda duk jikinsu ke kyarma to ai itace kanwarku diyar babanku inusa a shakiyancin dije nasan zata aikata fiye da haka dimmm sukayi gaba dayansu inda suka kai dubansu ga dije wadda ta dallaro harshe tare da yimusu gwalo tace ni ba aljanah bace gyadata kuka takemin ta zube ina shirin in tsince naji fitsari na juya inyi koda na juyo naga kun takemin ita shine nayi maganinku tunda tafara magana zuciyar mazan tahau lugude musamman. habeeb da yayi asarar hakorinsa guda na kasa saboda abin wayyo Allah muje zuwa readers yawan comments yawan page [16/12, 11:40] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* na khadija usman 6โƒฃ *wannan shafin sadaukarwa ne ga dukkan member's na khadija fans novels hakika naga ruwan comments da kuma masu bina pc nagode sosai Allah yabar kauna* ta jima zaune kafin daga baya taji alamun dawowarshi mika mata yayi tare da canjin tace ya rike canjin ta karbi maganin a bakar leda ta shiga cikin gidan tunani ta shiga yi shin wai ta inama zata fara ne wai wazata fara yiwa illa habeeb,nasir,mamy,ko uwar mugaye yusra ah ah takan ya habeeb zan fara tunda shi yafara min mugunta mikewa tayi ta shiga kitchen cikin sa'a ta riski basira na zuba coffee cikin cups kallonta tayi tace sannu da aiki Anty na murmushi basira tayi yayin data kamo hannun ta cike da tausayawar abinda aka mata dazu tace sannu dije kiyi haquri da abinda ke faruwa gidan nan ki dinga taka tsantsan da hajiya dan wlh batada imani suna iya hanaki abincin kwana ukun dasuka ce dan haka kada kidamu zan dinga boye miki a daki da zarar kin tashi ci zan nuna miki inda zan dinga ajiye miki dariya dije tayi kafin tace kada ki damu Anty ai daga yau har zuwa kwanakin da suka dibar min zanci abinda raina ke so ke dai kawai kisa ido kiyi kallo nice fa dije wlh a kauyenmu anno ba ake cemin duk gidan dana leqa saina sasu jinya dan haka sai sun san nice sukawa haka da naso in canza amma naga basu san kara ba gara ayi gwari gwari mamaki ne yakama basira inda take kallon dije daketa zaro zance ba wakafi ba aya duk da take qaramar yarinya dan ita a ganinta bazata wuce shekara sha biyar ba amma ta iya tsara zance kamar redio amma kuma in akayi la'akari da dabara irin ta mutanen kauye wannan ba komai bane farantin data dora kofunan akai ta dauka da niyyar fita dije tace ina zaki kuma Aunty ? wadan can 'yan sudan din zan kaiwa shayi wai da yamman nan kin san su ah ah kawo inkai musu ki huta ai kinyi aiki kin gaji naga ma kamar bacci kikeji dan haka jeki kwanta ki dan huta zan qarasa aikin kije ki toh kadafa kije suyi miki wata muguntar kuma ah ah ba komai ai haquri zan basu kada ki damu mika mata tray din tayi ta fita dai dai wani dan corridor ta labe ta fito da ledar daga jikinta ta bude juya maganin tayita yi dan ta rasa na bacci dana kashi kawai shahada tayi ta babbala sachet daya a cikin biyun ta juye cikin daya kofin dayan na hannunta ta fara barewa shima da alama kam wannan shine na baccin tafada a bayanne dan naga shi inna ta siyawa Ahmadu lokacin data daukoshi yaye shima duka guda goma ta juye ta dinga juyawa har duka suka narke kafin ta mike ta boye sauran a wani loko inta dawo ta dauka ta nufi part dinsu ta dan jima a tsaye kafin daga haya tayi knoking shigo kawai basira taji ance murda handle din kofar tayi ta kunna kai parlon da sallamar ta habeeb zaune daga shi sai boxer da singlet yana zaune yana duba system dinshi da alama wani aikin yakeyi me muhimmanci duba da yadda yamaida hankalinshi gaha daya ga abinda ke gabanshi shiko naseer jallabiya ce a jikinshi yana zaune yana danna waya da alama charting yakeyi naseer ne ya amsa sallamarta inda ya dago idonsa tare da wurga mata harara uban me yakawoki dakin nan ? um dama itace batajin dadi shine tace in taimaka in kawo muku tsaki yaja kafin ya maida hankali ga wayarshi qarasawa tayi ta durkusa ta ajiye cup daya a gabanshi sannan ta nufi gurin habeeb shima ta ajiye masa nashi shi kam ko kallonta beyi ba dan haka ta mike ta nufi hanyar fita har takai kofa taji muryarsa yana fadin idan naqara ganinki a dakin nan wlh saina lahira yafiki jin dadi shegiya me siffar aljanu nunar rana kawai itadai bude kofar tayi tay ficewarta inda shi kuma ya jawo coffee dinsa yafara sha jiyayi na yau yafi na kullum dadi dan wani kamshi da dan zaki zaki yayi dan haka ya dinga sirba baji ba gani shima naseer haka yayita sheqe abinshi inda shi kuma beji wani canji ba hamma yake tayi baji ba gani yayin da yafara ganin uku uku dan haka ya mike ya nufi bedroom yana tangadi kamar dan maye sam yarasa wannan wane irin bacci ne yazo mai lokaci daya naseer daya bishi da kallo yana ambatar lfy dai bros naganka ka sauya cikin murya irin ta wanda bacci yakama sosai yace lfy qalau kawai bacci nakeji bari in dan matse duk da naga yamma tayi ok a tashi lfy bai bashi amsa ba ya shige ciki kawai shi ko yaci gaba da abinda yakeyi yana cikin haka kusan minti talatin yaji cikinsa yayi wata irin murdawa da ya dan share amma daga baya yaji bazai iya ba dan kamar ba haya yakeji dan haka ya mike ya shiga toilet din dake falon yana ko shiga yafara antayo abinsa rai fesss itako dije tana fita kicin ta koma ta tarar da basira harta koma daki freidge ta bude ta fara kwashe lemukan ciki kamar wadda aka sa guda biyu kawai ta bari ta dauko su ta bude tare da zuzzuba wannan maganin kashin aciki kowanne sachet daya daya kana ta mayar ta rufe alamar motsin tafiya taji cikin sauri ta rufe friedge din ta tashi ta nufi cabinet tajawo filet ta kama daurayewa kamar me wanke wanke mamy ce ta shigo kitchen din tana kiran sunan basira ganin dije a tsaye tana aiki yasata tambayar ina basira ta shiga? batajin dadi ne shine nake tayata kanta ke ciwo ta sha magani ta kwanta wani wawan kallo mami ta watsa mata kafin tace hmmm ai dama aikin shiyafi dacewa dake a gidan nan maza ki daukomin lemo a friedge ki kawo mana dinning muna jira zamuci abinci toh ta amsa ita kuma mamy ta juya ta fita dariya dije ta fara yi tare da fadin komai kuke so zanyi muku amma ni da lfyr ku zan fanshe lemukan ta diba ta nufi falon inda ta iske mamy da yusra har sun fara cin abincin ajiye lemon tayi da niyyar juyawa taji yusrah tace ke aljana me siffar tumatur uban waye zai zuba miki lemon toh dawowa tayi ta bude ta zubawa kowa ita gwara ma da suka ce ta zuba musu din dan da sun taba murfin da da kansu zasu gane an bude lemo a zuciyarta tana jinjina kalar muguntar da zata yiwa yusrah dan da Alama tata saita fi ta kowa barin gurin tayi da sauri ta nufi dakinsu inda su hajiya aka baje koma aka dankari abinci da drinks. kasancewar lemon da sanyi kuma na roba ne shiyasa suka kusa shanye su dan kadan suka bari sun dan jima suna hira kafin mamy taji cikinta ya murda alamar tanajin bayan gida mikewa tayi ta shiga bedroom dinta ta afka toilet ita ko yusra ta dan jima kafin itama taji yanayin na hajiyar itama ta mike ta shige dakin inda ta afka toilet tafara zabga nata tutun ******* shi kam naseer abin ba'a magana domin kuwa ya zuwa yanzu ya tabbatar cikinsa yadan rikice dan haka ya dinga zarya zuwa toilet abun mashi har bashi tsoro yakeyi duba da yadda yaketa zaryar toilet ga muntar sa harya fara zafi bangaren habeeb kuwa baccinsa yakeyi kamar wani matacce bangaren su hajiya kuwa abin fa ya ci tura inda suketa zaryar zuwa toilet ganin abin yana neman wuce gona da iri yasata lalubar wayar habeeb dan ya zo yakawo mata magani ta kira yakai sau biyar be daga ba hakan yasa ta kira number naseer shima din shuru domin yana toilet ya na ta zabga abin tana kokarin kara kira yusra ta shigo dafe da cikinta tana dukawa mamy na bude baki da niyyar tambayarta taga ta kwasa da gudu tayi toilet din dakin itama cikinta sake murdawa yayi inda ta tashi da niyyar shiga toilet din taji shi gam a bame koda ta dan yunkura tana rawar disko irin ta wanda kashi inya matsi mutum taji kawai ya zubo mata ku biyoni *vote* *comments* *khady ce*โœ [16/12, 11:40] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TA ME GARI NA khadija usman 7โƒฃ wayyo Allah cikina mamy ta fada tare da dukan kofar toilet din cike da maseefa takama fadin wai ke yusra uwar me kikeyi a bandaki har yanzu ko kashin danko ne ai ya ci ace kin gama to waima ina na dakin da kike shine sai kin taho nan a wahalce yusrah ta bude kofar toilet din kafin daga bisani tasa hannunta ta toshe hancinta kafin tace mamy wlh gudawa nakeyi dazu kam da dan dama dama amma yanzu kamar ruwa nake yinta ni tsoro ma nakeji kar inje ko amai da gudawa zanyi cikin mamy ne yayi wata qara bata san lokacin data buge yusrah ba ta afka toilet itako yusrah bin wajen da mamy ta tsaya tayi da kallo tare da fadin mamy kema gudawar kk yi ashe? ****** kwance take kan katifa amma tunaninta nacan gurin masu zawon gidan dan haka ta mike ta fita zuwa falon akan idonta yusra ta fito tana tfy a dudduke kuma a botsare ta kuma dafe ciki kallonta dije tayi kafin tace sannu anty harara ta wurga mata tare da fadin dan uwarki ciwo kikaga inayi da zaki cemin sannu kuri tayi da ido takama dariya kasa kasa sannan tace ah ah dana ganki haka ne saina ga kinyi kama da masu ciwon zawo amma kiyi haquri tsaki tayi kafin taja qafa ta bar gurin inda dije na ganin ta shige ta kife a gurin tana dariya saida tayi me isarta kafin ta mike ta nufi kitchen tana shiga ta bude drower ta fito da bucket din da ake zuba kaji idan an soya ta zauna zaman dirshin tare da dauko lemo jin alamun ya huce ba sanyi yasata tunawa da ita ta kwashe su dazu ashe tsaki tayi ta mike ta nufi friedge din falo ta dauko exotic me sanyi ta zauna ta fara yagar naman tana shan lemo kuma saida taji kamar cikinta ze fashe kafin ta mike da kyar tana hamdala har tazo fita a kicin din ko me ta tuna kuma oho? sai naga ta juyo ta shiga store ruwa ta dauko carton daya ta nufi friedge dasu duka ta bude ta dura maganin nan a cikin kowacce gorar ruwa kafin ta jera su a friedge dan tasan suna cikin wannan halin bazasu buqaci lemo ba sai dai ruwa saida ta gama shirya su ta miqe tabar kitchen din takoma daki ****** sam yakasa gane meya rikita cikinsa haka lokaci daya dan ya zuwa yanzu yayi bayan gida sau ba adadi dan haka da himma ya qarasa inda wayarsa take ya dauka danya kira docter yusif abokinsa yakawo mishi magani ganin missed calls din mamy yasashi fara kiranta amma bata daga ba yasan bazai wuce zancen aiken datace zatayi masa ba shi kuwa a wannan yanayin dayake ciki ba inda zai iya zuwa dan haka jin bata dauka ba yasa shi kuma be sake kira ba dan haka ya kira doctor yusif yana dagawa yasanar dashi abinda zai kawo masa ya kashe wayar minti talatin sannan doctor yusif ya iso direct part dinsu ya nufa yana zuwa lokacin naseer yana fitowa kenan daga toilet yana ganinshi ya mika masa hannu pls bani maganin nan kada in mutu dariya yusif yayi kafin yace lallai abin nan yadameka sosai so gashi ko karba yayi kafin yace pls dan bani ruwa a friedge din nan yana dubawa yace ba ruwa sai lemo kai pls kaje cikin gida ka daukomin pls fita yayi yaje kitchen yadauko yana fitowa yaga mamy ta fito ta nufi dakin da yusra take mamy ina yini? juyowa tayi ganin yusif a tsaye yasata hamdala tare da fadin lfy qalau ya aiki ? lfy qalau alhmdllh abokinka kuwa yana nan dan nakira wayasu duka basu dauka ba eh yana nan bejin dadi ne wai subahanallah meke damunsa ? wlh wai zawo yakeyi yanzu haka wani abun yaci kin sanshi sarkin ciye ciye a waje sai yanzu tayi tunanin irin cimakar dasuka ta ci kuma duk laifin yusra ne ita tasa sai an siyo gashi nan taja musu shegiya gashi yanzu taja musu rudewar ciki jin cikinta ya dan juya yasata fadin am kanaji yusif inka shiga wajen nasa ka kawowa yusra maganin itama tasha dan itama cikinta ya dan birkice ok mamy ya fada tare da juyawa ya nufi hanyar fita ka danyi sauri dan Allah insha Allah yanzu zan dawo be wani jima ba sai gashi yadawo aikuw a da sauri mamy ta nufi kitchen tadauko gorar ruwa tun a can ta bude maganin tasha dasauri ta nufi dakin yusrah ta bata itama tasha ******** toh fa abu kamar wasa gida ya kacame da 'yan zawo abincin da basira tayi ba wanda ya kalleshi se dije da duk abinda su mamy ke ciki ta sani hankalinta kwance ta zage ta dirki abincinta ****** washe gari sai wajen qarfe goma yatashi da kyar ya iya bude idonsa domin nauyin dasukai masa jikinsa yakeji wani iri duk ba kwari haka ya lallaba ya tashi ya shiga toilet dan yayi wanka yayi sallar magrib wanda shi a tunanisa bai jima yana baccin ba ganin toilet din kaca kaca yasa ranshi ya baci shin wane dan iskan ne yayi haka da wurin yana cikin haka yaji an turo qofar da qarfi koda ya duba naseer ne baiko bi ta kanshi ba ya sabule wando ya fara nishi harda 'yan hawaye domin yazuwa yanzu gudawar ma taki zuwa sai majina toh inama yaci abincin dazai narke yazama kashi tun jiya yake yin abu daya ina yaga lokacin zaman cin abinci gara ma ruwa danshi yana sha sosai maganin da yusuf ya kawo masa kuwa duk ya shanye su amma a banza ga mamy ma ya kirata tace mishi itama hakan take amma tasan be rasa nasaba da ciye ciyen da yusra tasa sukai tayi tsakanin jiya da yau ya tsinewa yusra tare da ja mata Allah ya isa yafi sau nawa zuba masa ido habeeb yayi ganin yadda yaketa faman nishi harda 'yar kwalla ga uwar zufa dayakeyi kuma inba abin ya girmama ba yasan ba yadda za'ayi naseer ya iya irin wannan lalurar a gabansa dan haka hankalinsa tashe ya nufi gurinsa yana fadin sannu bros meke damunka haka? nishi yayi kafin yabashi. labarin cimar da sukayi jiya inda ya fada mishi su mamy ma nacan na fama subahanallahi ai ban sani ba meyasa baku fadamin ba duk da halin dayake ciki saida ya fella masa harara kafin yace ta ina za'a sanar dakai ka kwanta bacci kamar gawa kasan ko tashi nawa nayi maka amma bakaji ba ya Allah wlh ni kaina ban san wane irin bacci nayi ba me nauyi haka yanzu haka wlh be isheni ba kaga malam nidai dan girman Allah taimaka kasamin drip kar ruwan jikina su ida qarewa jini ya biyo baya toh ai abari dai inyi wanka in rama sallolin da ake bina ko toh yi maza kayi naseer yafada tare da mikewa yayi tsarki ya fita yana dafa bango ****** hankalin habeeb ba qaramin tashi yayi ba domin kuwa gidan duk na 'yan gudawa ne dole ya kwashe su duka ya nufi hospital dinsu dasu domin dole asa musu drip da sauran allurai wannan kashi sai kace annoba itako dije komai akeyi akan idonta inda taketa dariya basira ta kalleta tace ke wai lafiyarki kuwa? wlh qalau nake kawai murna nakeyi ina cikin farin ciki su da sun dauka in ta zama suna dimata kamar jaka ina kallonsu wlh kadanma suka gani daga yanzu duk wanda ya qara yimun wani abu na mugunta saina sa shi rawar nanaye๐Ÿ˜‚ kallonta baseera tayi cike da mamakin maganar ta tace kina nufin kece silar rashin lafiyar 'yan gidan nan? sosai ma kuwa Aunty ai baki sani ba ma wlh kadan suka gani tunda suka sa nadawo dijeta ta ainihi kallonta kawai basira takeyi tare da yaba qoqari da muguntar yarinyar dole itama tayi hankali da ita dan kar wataran tasata rawar nanayen itama๐Ÿคฃ miqewa dije tayi ta tafi ta bude friedge ganin babu sauran ruwa ko guda daya yasata qara fashewa da dariya harda kwalla kafin tace sai ni dije uwar mazga ba'a min ba ma nayi bare anyimin ***** kwanan su mamy biyu a asibiti duk sun rame inda gudawar ta tsaya cikin ikon Allah yusracan dada ramewa hakora sun bayyana daddy dake zaune gefen gadon da mamy ke kwance yana ta fadan meyasa suka ci abinda sukaci waje wasu basa inganta tsaftar kayansu gashi nan sun jama kansu ai nan yagama me isar shi kafin daga baya ya shiga dawai niyar kula dasu kwanansu biyu a asibiti ana musu karin ruwa kafin aka sallamosu zuwa gida koda basira ta gabatar musu da abinci cewa sukayi basa ci kayan fruit kawai suka dinga sha dan sunyi losing Apetti basu jin dadin komai itako dije rai fesss domin makarantart ake tafiya hankali kwance yauma shigowarta kenan ta hange su mugaye a zaune cikin garden su uku sanye take cikin unifoam dinta riga da wando da farin hijab qarami tana shirin shigewa taji muryar naseer na fadin ke Aljana dan ubanki baki iya gaisuwa bane ? qarasawa tayi inda suke daya bayan daya ta gaishesu ba wanda ya amsa sai baqon da suke tare dashi mikewa tayi da niyyar tfy naseer yajawota ya zuba mata rankwashi aka sai da ta danyi kara bata san sanda ta furta kaci bashi a fili ba...... mu kara wuta ku biyo ni *vote* *comment* *Alqalamin khadiy* โœ [16/12, 11:40] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* 4โƒฃ *dole in faranta muku masoyan ta me gari* *jinjina agareku da godiya me tarin yawa masoya na kamar* *JATTAKO NOVELS FANS* *SADNAF NOVEL FANS* *KHADIJA NOVEL FANS* *HAJJAJOH NOVEL FANS* *da duk sauran groups din da ban ambace su ba kuna raina* **** jikin habeeb har rawa yakeyi sbd tsananin bacin rai haka ma ga Naseer sunma rasa me zasu ce ganin yanayin da suke ciki yasa me gari rike hannunsu tare da cewa dije ta tafi gida aikuwa ko kafin ta fita saida ta qara musu gwalo kowanne a cikinsu ji yakeyi idan ya riketa zai iya shaketa har saita mutu malam ne ya shiga tausarsu da naseeha da nuna musu halin kuruciya ne dan kawai tanada kuruciya sai akace tayi wa mutane halin dabbobi cewar naseer kallonsa habeeb yayi kafin yace ai wannan yama wuce halin dabbobi ai sai na jakuna da tumaki irin na kauyen nan ma sosai ran me gari ya sosu ganin yadda kiri kiri suketa zagin dije bama hakan yafi bata mishi rai ba irin yadda yaketa tausar su amma suna ta nuna kiyayyar su gareta inda har suke fadin baxasu je gidan su ba sam kenan hakan na nufin zasu tsiro da lalacewar zumuncin gidansa hmmm lallai dole yasan abinyi dan haka baxata taba sabuwa ba tashi yayi ya barsu anan sunata mita suka fasa fitar ma ko ina ***** kwana megari yayi yana saqa da warwara kafin daga baya ya cimma matsaya tunda asuba a masallaci da suka hadu da yaransa da jikoki gurin yun sallah ya tsayar da malam inusa yace yana son magana dashi cike da ladabi ya amsa ya tsugunna gyaran murya yayi kafin yace kasamu labarin abinda yafaru tsakanin yaran nan nawajen khamisu da dije? eh nasamu lbr gurin su ayuba jiya da dare har na bata kashi ma sosai toh Alhmdllh amma banso ka daketa ba sai dai nagama yanke wani hukunci wanda ban sani ba ko zai yimaku dadi a matsayinku na iyayen khadija insha Allahu baba duk abinda ka yanke nasan me kyau ne bazai cutar damu ba masha Allah Allah yayi maka albarka Ameen dama bawani hukunci na yanke ba illa na turata birni can gidan shi kamisu din inyaso tasamu ilimin zamani itama sannan su fahimci junansu da zumunci me karko dan iya jiya da suka san juna naga alamar gurbin kiyayya a idon yaran sbd kuruciya shiyasa nake son ta zauna gidansu nasan zata samu rayuwa me kyau kuma zata nutsu domin inka duba kiriniya irin ta dije abin se addu'a jimm yayi kafin ya nisa yace toh baba malam badamuwa Allah yasa haka yafi alkhairi sai dai mahaifiyar ita dijen sbd kasan gidansu sun tashi da akidar kin karatun boko shiyasa ko yanzu ta hana dijen tayi kada ka damu inka koma kace ina nemanta zanyi mata bayani da kaina insha Allah nasan zata fahimceni dan tanada saukin hali hakane nan yayiwa mahaifinsa sallama ya nufi gidan zuciyarsa cike da damuwa dan yana son dije kuma gashi a halin dije kauye ma ya aka kare bare binni kawai ba yadda zaiyi ne akan umarnin mahaifinsu ba karamin fama malam yasha ba kafin inna saudi ta fahimceshi inda daga baya ya yi mata nasiha nan ya fada mata yau zasu tafi dan harda shi koda aka fadawa dije abin mamaki murna ta dinga yi dan tana son rayuwar binni da kuma karatun boko dan haka ta shiga hada kayanta inda innarta ta dinga kallonta zuciyarta na tunanin inda 'yarta zata rayu gidan hajiya zahida macen dake kyamar mutane ko zuwa sukayi saita nuna a fili daga baya ma tace ta daina zuwa kuma kamar abin magani duk abinda ta ce ya zauna a gun Alhaji khamis 'yan tafiya sun shirya tsaf yayin da ba wanda yasan da tafiyar dije har saida aka zo tfy sannan akaga da malam za'aje kowa yayi mamaki zuciyar su habeeb kamar ta buga akan dole suka yi shuru dije ta shige mota ita da malam akaita daga musu hannu inda kawayenta keta murna da kuma kewar uwar mazga yayin da dayawan mutane ke murnar ala raka taki gona *DIJE A BIRNI* tunda suka shigo garin abuja ta zuro kai ta glass tana leke kamar zata fado yayin da malam keta murmushi yana tsokanarta ita kota kansa bata bi ba kallonta kawai takeyi sukuwa mazaje bakin ciki kamar ya kashe su da gayya nasir ya qara daga glass ai kuwa saida dije tayi kara dasauri malam yace lfy ? bakomai baba malam bari zan rama zaki rama me? kai dai ka bari kawai kasan bana cin bashi ba'acin nawa dole in anci nawa sai an biya toh Allah ya kyauta Ameen sun karaso gidan Alhaji khamis aljannar duniya inda cikin sa'a suka riskeshi kuwa ba karamin farin ciki yayi ba ganin dan tsohonshi a gidanshi kasancewar matar gidan ta fita shiyasa basu sameta ba nan bada bata lokaci ba me gari ya sanar da dansa komai da dalilin kawo dije kwarai ya nuna jin dadinsa inda nan take me gari ya nuna baxai kwana bazai koma dole aka sa drivrr ya mayar dashi ranar ******* me aikin gidan Alhaji ya kira ya ce tasa dije tayi wanka sannan ta bata abinci kafin hajiya ta dawo koda hajiya ta dawo ba karamar rigima aka kwasa ba dan saida Alhaji yayi mata jan ido kafin ta yadda da zaman dije a gidan kuyi managed yanzu aka fara zaman dije a binni yafi na kauye cakwakiya [16/12, 11:40] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TA ME GARI NA KHADEEJA USMAN 8โƒฃ bana karanta littafin kowa a yanzu bayan *FAHIMTA,KUKAN KURCIYA,ZAINABU Sune littatafan danake karantawa a halin yanzu dan haka ina son ayimin adalci koda anji labarina yayi kama da na wasu littafan da ake rubutawa yanzu dan Allah ina son ayimin adalci domin wlh nawa sakon danake son isarwa daban ko kadan bazan saci fasahar wasu ba zanyi amfani da tawa basirar da Allah yabani sbd da haka ina rokonku daku tayani da Addu'ar Allah yabani ikon faranta muku masoya ta me gari wannan shafin nakine 'yar uwa rabin jiki fadimatuzzahra'u (mamy)fateema maman fateema (ihsan)ina sonki da kewarki ************* me kika ce ya fada tare da kara kamo kunnenta ya murda da qarfi qara tasaki tare da matso kwallar wahala cikin kuka tace wlh bance komai ba shegiya aljana aike sunan daya kamata asa miki kenan me siffar 'yan ruwa ya cikata tare da fadin bacema mutane da gani kamar jira take kuwa ta kwashi jakarta ta zura da gudu tayi cikin gida doctor yusif ne ya kalle shi tare da fadin wai kai man wane irin mugu ne ? kawai kasa yarinya a gaba sai wahalar da ita kukeyi sai kace ba qanwarku ba haba dan Allah hakan ba kyau zaisa ta raina ku ai kallon gefen ido habeeb yayi musu wanda shi tunda aka fara abun ma baice qala ba dan shi duniya babu abinda ya tsana irin yarinyar shiyasa ko zancenta baya son ayi ganin irin diban dayakeyi masa ne yasashi fadin kai kuma meye ka tsare mutane da idonka irin na aljanun ainihi hmmm kawai yace tare da maida kansa zuwa abinda yakeyi naseer ne yace da kasan abinda yarinyar nan tayi mana wlh da kokai inta gaisheka baza ka ko kalleta ba bare ka amsa toh me tayi muku har haka kuna ganin ta 'yar karama da ita ta yaya har zatay muku wanni abinda zaisa ku takurata haka umm kai kake mata kallon qarama shegiyar me rai ce da kk ganinta nan ya kwashe komai na zuwansu kauye ya fada masa yusuf dan dariya har da fadawo daga saman kujerar dayake kai yayi inda duka su biyun suka kulu habeeb tashi kawai yayi yabar gurin ya shige cikin gida shi ko naseer qumewa yayi yai banza da yusuf yanaji yanata mai magana ya kyaleshi dan haka ya mike yayi masa sallama yace ya tafi da harara ya rakashi yana fadin inka tafi kada ka dawo wata dariyar ya kumayi tare da fadin dole ai in dawo bil adama. ******* tana shiga gidan direct dakin su ta wuce ta wurgar da jakar tare da cire hijabin ta zauna gefen katifa tana sharar kwalla tabbas yaxamar mata wajibi tabar gidan nan don me zata zauna aita cin zalinta kullum sai an sami wanda zaiyi mata wata muguntar indai anga taji dadi toh fa daddy na nan dan shine kawai ke nuna mata tsantsar soyayya da kulawa a cewarsa yaji dadin bashi ita da baba malam yayi sbd bashida diya mace toh itafa iyayenta ita kadai suka haifa yanzu tasan suna can suna kewarta kamar yadda take kewarsu wasu hawayen ne suka qara biyo kuncinta domin tunawa da tayi da yanzu suna can suna fama ita da innah akan rikicinta tana cikin haka baseera ta shigo dakin dauke da flate shake da jellop rice da pure water dan shine ruwansu da hajiya tace su dinga sha yanzu yanzu ma ta hango shigowar dijen ne ta windon kicin shiyasa ta biyota da abincin dan ita dai Allah ya jarabceta da son yarinyar nan ganinta da tayi tana kuka yasata qarasawa kusa da ita tana tambayarta lfy khadija? fadawa tayi jikinta tare da fadin nagaji Anty gida nake son komawa ina son ganin innata nagaji da zama da muguntar da akeyimin a gidan nan babu gurin wanda nake jin dadi daga gurinki saina gurin daddy in yana gari ni gara nakoma kauye yafimin akan zaman nan din yanzu na tsani birnin bana so hannu tasa ta share mata hawaye tare da fadin ah ah kadeeja dena kuka mana kin manta ke kika cemin so kikeyi kiyi karatu kizama lawyer ki dinga taimakon mutane da iyayenki ba?ke fa kika cemin so kikeyi innarki da baffanki su dawo birni ki gina musu katon gida innarki ta dena daka baffa yabar zuwa gona kenan kin fasa?haba dijangala ta me gari kin san dai bayan wuya se dadi wata rana se labari duk irin cin zalinki da sukeyi wata rana zasu dena ke da zaki girma ki zama hajiya ga gida ga babbar mota ku biyo layi keda me garinki kinsa shi a gaba eye kuma ma idan kince zaki tafi ni ki barni dawa?ai kafata kafarki domin ni dake yanzu mutu ka raba dan haka bana son in kara jin kin sami damuwa akan mutannan kiyi haquri kinji duk me haquri natare da riba tashi maza kici abincinki kada ya huce maganganun basira sunyi tasiri a zuciyar dije shiyasa ta dan kwantar da hankalinta amma fa wlh ta quduri aniyar duk wanda yayi mata saita rama bakomai zata haqura ba abincin taci kafin ta tashi tayi wanka inda basira keta bata labaran ban dariya har ta warware gaba daya ******* haka rayuwa taci gaba da tafiya yayin da dije keta fuskantar muzgunawa itako tanata musu kalolin mugunta amma har yanzu basu dagota ba duk da ya zuwa yanzu ta qara girma kyanta na fulanin asali yaqara bayyana yayin da makerin budurci na nan na kera dije yayin data hadu da qawaye 'ya'yan masu kudi 'yan gayu duk a gunsu take koyar duk wani abu first class yanzu batada aiki sai karatu koda yaushe tana daki ko kicin tana taya baseera aiki sam dijen yanzu ta canza babu wata hayaniya taxama so cool ba yawan surutu su kansu mutan gidan wuyar haduwa sukeyi kasancewar batada amfani a wajensu yasa basu wani damu da rashin ganinta ba ya zuwa yanzu me gari yazo yakai sau hudu kuma ganinta dayakeyi ta canza yasashi jin dadi da kwanciyar hankalin qara barinta gidan kawun nata ****** a dai dai wannan lokacin ana shirye shiryen auran matasan gidan yayin da naseer zai auri yusrah 'yar qanwar mamy shi kuma habeeb zai auri sajida diyar abokin daddy ce babanta ambasserddor ne sajida yarinya ce fist class maqura ce gurin wayewa tanada ilimi sosai amma bata aiki kusan sa'ar habeeb ce dan da kadan ya girme mata amma kasancewar shi namiji ne me son classic lady kuma dayake batada wani girman jiki shiyasa yaji ya kamu da sonta inda suke zuba soyayya ta bugawa a jarida yau bikin saura sati uku anata hidimar gyara gidan shiyasa kowa yake busy yusrah kam a gidan mamy take domin mahaifiyarta sun rabu da mahaifinta tun tana qarama maman ta kuma wani auren amma a saudiyya suke zaune da mijin kuma mahaifin yusrah ya hanata 'yarsa gashi kuma matar dayake aure batada kirki hakan yasa yusrah gudowa gidan mamy inda kusan nan ta qarasa girmanta ****** yusrah ce zaune da kawayenta a main parlor suna ta tsara yadda hidimar bikin zai kasance dije ce ta fito sanye da riga da wando indian design kanta babu dankwali sai yalolon gashinta da bashida cika sai matuqar tsawo datasa band ta kama shi ta kuma tufke jelar tayi gammo da ita tun zuwan daddy wancan lokacin ta karbi kudi a gurinsa ta siyo kayan sawa masu kyau da tsada dan ya fada mata komai take so ta tambayeshi kada taji tsoro shiyasa yanzu batada matsala da duk wasu kayan kyale kyale ga qawarta rufaida Aliyu na sayo masu sosai dan itama yarinyar akwai son daukar wanka kuma babanta yanada kudi sosai gashi tanada yayye maza itace kuma auta shiyasa take fantamawa kitchen ta nufa domin dauko ruwa dan ya zuwa yanzu ta sauqaqawa kanta shan pure water itama faro take sha kamar kowa na gidan tana daf da shiga ta ji yusra tace keeeee da kamar ta share sai kuma taga be dace ba dan tasan da ita take dan haka saita tsaya tare da juyowa ta kura mata idanunta masu kama dana mejin bacci wata kawar yusra ce wow yusrah ina kuka samu wannan kyakkyawar baturiya zance ko balarabiya ne ma oho me aikin mu ce me aiki? kalisat ta tambaya tare da juya lamarin son kudi irin na iyayen yarinyar wannan a yanzu ai jari ce ko tace kadara amma fa hadari ce ga duk gidan da sukayi gangancin daukarta aiki yanzu a ganinta bazata wuce shekara sha bakwai amma dubi yadda take ina ga takai ashirin kuma yusrah ce ta katse mata tunaninta ta hanyar cewa ke me kike so a kawo miki ? hmmm ni indomie ma ya isa me dan yaji pls juyawa tayi ga sauran kawayenta tace ku kuma fa dayar tace ita kunun aya take so dayar kuma wai jellop din macaroni d kifi sai drinks ko wanne ita kuwa yusrah cewa tayi farfesun kayan cikin rago take so ta kuma hada mata zobo murmushi dije tayi kafin tace iya wannan sun isa ko kuna buqatar wasu abubuwan tsawa yusra ta daka mata tare da fadin kijini da munafukar yarinya ina ruwanki da sun ishemu ko basu ishemu ba ai mun san abinda muke buqata shiyasa muka fada miki iya su din dayalla wuce kibawa mutane wuri kiyi abinda nasaki Allah ya huci zuciyarki Aunty ta juya ta shiga kitchen tana shiga kamar abun arziki duk abinda suka lissafa ba abinda bata hada ba kuma harta gama Anty basirra bata shigo ba sai da ta jera komai akan wani qaton tray kafin ta nufi parlon yusrah na ganinta ta qara hade fuska wai ita oga tsugunnawa tayi tare da fadin gashi anty nagama nan ta shiga ajiye wa kowa abinda ya buqata tana gamawa tayi hanyar fita waje yusrah ta rakata da harara kasancewar an dan fara hada hadar biki mamy sun tafi dubai hado lefe shiyasa gidan shuru kharleesart ce ta fara dibar indomie din domin taci da zafinta domin kuwa yadda ta ganta a ido ga kamshi tanayi tasan zatayi testing tana sawa a bakinta da sauri ta dawo da ita domin wani tsinnanen yaji ne wa nda yake barazanar dauke harshenta kallonta yusra tayi dai dai takai spoon din hanta bakinta da dukan kuzarinta da sauri ta fito da ita domin wani dan iskan daci dataji ga shi ba alamun maggi ko wasu kayan dandano a ciki shukrah wadda itama dai dai nan ta bude fillet dinta ta diba takai bakinta wani kafirin tsami daya kashe mata haqora tayi saurin hadiyewa maryam kam tana kai kofin kunun aya taji wani mugun gishiri daya kusa dauke mata fatar harshe miqewa yusrah tayi ta shiga dandana abincin kowa jin abinda taji da sauri ta furzar cike da bacin rai ta miqe da niyyar fita ta jawo dije ta kime ta son ranta dan yau bata san ma kalar dukan dazatayi mata ba watakil saita sumar da ita a yadda takejin zuciyarta alamar bude falon taji anyi kuma an mayar an rufe ta cikin labule cike da masifa ta nufo gun ta yaye labulen wata razananniyar qara tayi sakamakon ganin dije idanunta a wurqile ta wani markwade harshe hannunta rike da wata zabgegiyar bulalar ice ga kuma wuqar da ake sara qashi da ita nufo ta tayi ita kuma ta fara ja baya sauran ma duk miqewa sukayi cike da tsoro kowacce na neman maboya gidan ubanwa zaku ? dije ta fada da wata malkwadaddiyar murya jikinsu ne yahau kyarma suka qanqame juna suna shirin yin ihu tace duk wanda yayimin ihu a cikinku saina tsaga bakinsa da wannan wuqar ta daga wuqar hannunta qanqame juna suka qarayi suna kuka barinma yusra data qame guri daya dan ita tsoron me aljanu takeyi sosai ubanwa yasa kusa godiyarmu aiki saboda bama so ta wahala muka girka muku irin girkinmu kuma kuce bazaku ci ba ke harda tashi da tafiya kice zaki kamota ki daka ko ta nuna yusarah baki na rawa kamar mejin sanyi tace wa..ll..a...hi ah ah bulalar hannunta ta daga ta zuba mata zatayi ihu tace kul kikamin kuka inba haka ba zan sa 'dana yazo ya yini yana dukanki da bulalar qarfe kama bakinta tayi ta rike tana mutsu mutsu tsananin azabar bulalar daya shigeta ba'amagana jikinta yasaba da hutu gashi yau an daketa da bulalar aljanu wai a hakan ma danta roba ce inaga ansa mata ta qarfe dan haka ta qara gum da bakinta meye nufinku musha wahalar girka muku abincin kuce bazaku ci ba ko me? mu din banza cewar maryam wlh zamu ci yanzun nan zamu ci ko? da sauri suka shiga girgiza kai eh eh wlh mu mun isa musaku wahalar banza toh kuyi maza kowacce taci abinda tasa a dafa mata inba haka ba saina sa aljani duna yaxo yayi muku durar kabaki toh toh munji zamu ci wlh kuyi haquri bayin Allah kowacce ci takeyi tana kuka duk harshensu ya amsa ga zufa gashi basa son ko kallon fuskar ta ai dama dagani kasan wannan kyan ba'a banza ba harda hadin aljanu saida suka cinye komai tass bnda kuka da majina da dallo harshe ba abinda sukeyi sunata budar baki sannan ta miqe tace daga yau ko kallon banza kuka karawa godiyarmu wlh saina ci ubanku kuma naji kun fadawa wani wannan abinda yafaru duk saina biki gidajenku ni kadai nasan mezan muku ku tashi ku fita waje zan tafi inbar godiyata tayi bacci da gudu suka nufi qofa harshe a waje baki bude kamar irin mayu suna fita suka zube gurin shukrah data sha kunu aya me gishiri amai kawai takeyi itada yusrah suko su kaleesart banda kartawa ba abinda cikinsu keyi alamar y yamutse kenan suna fita ta rushe da dariya tare da hada kwanukan ta nufi kicin tana fadin shegun banza wlh kadan kuka gani dan na fuskanci saina gyara muku zama tana wanke kwanukan data bata tana dariya a haka harta gama ta fita ta dauki ruwanta ta koma daki har yanzu dai basira bacci takeyi Allah sarki kodan yawan aikin datakeyi ne sukuwa suna nan zaune duksun baza baki sun baje a gurin banda kuka da kakari da nishi ba abinda sukeyi motar su naseer ta kunno kai *alqalamin shady*โœ *vote* *comments* *with* 08066364077 [16/12, 11:41] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TA ME GARI NA KHADIJA USMAN 9โƒฃ narasa bakin da zan godewa masoya wannan littafin sai dai ince Allahu yabar qauna yaqara bani kwarin gwiwar faranta muku ko yaushe ๐Ÿ˜˜ ****** ko gama parkin habeeb beyi ba naseer ya balle murfin motar ya nufi gurin su da sauri yana tambayar lfy meya faru meya sameku naga duk kun shanya baki a iska? yusra da bakinta ya kacame da daci ne ko bauri ji takeyi bakin duk ya dade itace tayi qarfin halin ce mishi abinci mukaci me yajin bala'i kallonta yayi duba na rainin hankali kafin yace wannan wane irin rashin sanin ciwon kai ne ta yaya zaku je kuci abunda kuka san zai yi muku illah yanzu dan Allah dube ku kunyi wani zugwi zugwi daku kamar mayunwatan 'yan boko haram dayalla ku tashi ku shiga ciki kada kai su maryam suka shiga yi tare da fadin ah ah mudai basai mun shiga ba dan Allah dai ka taimaka ka bamu maganin wankin ciki pls habeeb ne ya qaraso gurin yana tambayar sa lfy ? nan ya sanar dashi wai yaji suka sha fada yayi musu sosai akan illar da yaji keyi kafin yace su shiga ciki kafin yakawo musu magani dan kar yajin da suka sha yayi effected dinsu dan yaga sunsha da yawa shiko naseer fada yayita yiwa yusrah duk yadda yaso su khaleesart su shiga parlor ki sukayi har sai da habeeb yakawo musu maganin suka tafi ita ko yusrah da sanda ta shiga ta wuce dakinta inda ta fada toilet tanata brush kamar zata qarar da kamfanin makilin sai yunkurin amai takeyi dan ji takeyi gaba daya makogoronta kamar ya qone ๐Ÿคฃ ****** tun daga wannan rana wani kallon rashin mutunci ko na raini be qara shiga tsakanin dije da yusrah ba har saida mamy ta dawo zuwa lokacin daddy na nan domin shirye shiryen biki kudi sosai dije ta karba gurin daddy dan yin siyayyar nata kayan bikin a cewarta tunda ba'asa da ita a anko ba baruwanta nata zatayi rufaida da husna qawayenta sune suka tafi siyayyar tare kudi sosai suka kashe dan har ciko sukayi mata tare da qara mata wata siyayyar direct shagon wani me yi musu dinki rufaida ta kaisu suka kai kafin suka wuce gida duk sun gaji suna sauketa suka wuce ita kuma ta nufo gate din gidan ta qaramar kofa ta shiga inda tana shiga ta iske su yusrah da qawayenta tare da naseer sai abokansa da alama suna tattauna harkar bikin ne ta so ta wuce su amma ganin yadda yusra ke binta da harara yasata yin kwana ta nufi gurin da suke cike da takunta na 'yammatan zamani wadan da inuwar budurcin bata dade da sauka bisa kansu ba riga da siket ne na wani blue din material a jikinta wanda aka yiwa ado da kyalkyali na yellow din flowers dan haka tasa takalmin me matsakaicin tsini tare da siririn mayafinta yello kanta babu dankwali hakan ne ya qara bayyanar da yalwataccen gashin kanta dayasha gyara yanata walqiya da dan murmushi akan fuskarta ta nufo gurin su inda hankalin Amir abokin naseer ke kanta wow so beautifull bros ya dan daki kafadar naseer do u look what i see? dagowa naseer yayi domin ganin me Amir ke kodawa haka ganin wadda ke nufo su ne yasashi sakin sirirn tsaki tare da juyawa yaci gaba da maganarsa dasu maryam duk abinda yayi dije ta lura dan haka ta qara fadada murmushinta ita ko yusrah baqaramin dadi taji ba da yadda naseer din yayi cikin siririyar muryarta tayi musu sallama da sauri qawayen yusra suka amsa tare da wage baki kamar ze yage dan fara'ar da suketa yimata hakama abokan ango dukansu kamar masu tallar makilin a ranta tace ikon Allah sukuma wadan nan haka Allah ya hallice su babu aji bare aje maganar jansa cikin salon karya harshe tace barkanku da hutawa Aunti's dina har rige rigen amsawa sukeyi cikin sakin fuska ykk qanwar mu ya kuma shirye shiryen biki? all is fine so ya gajiya da yawace yawace ? duk alhmdllh toh fatan dai yayana be barku kunata dibar kura a bakin zannuwa ba cike da rashin fahimtar maganar ta suka juya suka kalleta nup kada ku damu bawai ina nufin wani abu bane naga kun zubamin ido kamar zaku hadiyeni ina nufin fatan dai yana cika muku jaka da tsaba ko dan nasan halin yaya naseer badai mammako ba sai yanzu yadago ido ya dubeta tare da sakar mata harara amma sai yaga ta waske tare da fadin sannunku abokan ango ykk? lfy beauty cewar Amir dayafi kowa zakewa yayi kyau tafada kafin taci gaba fatan dai kuna cikawa 'yammatan jakunkunansu ko dan nasan halin samarin yanzu duk 'yan kamus ne dariya Amir yayi tare da gyara tsayuwarsa danya qara burgeta yace ah ah qanwarmu ai mu ba irin wadanda kk sani bane mun bude bakin aljihu basu da matsalar komai hmm au hakane ? ta tambaya tare da yatsina fuska sosai ma kuwa ai gasu nan indai ba butulci zasuyi mana ba sun san mun bude bakin aljihu sunata kwasa hakan yayi kyau abokin ango dan wahalar banza๐Ÿ˜‚ta fada tare da qoqarin barin gurin yake kawai Ameer yakeyi bakin ma yaki rufuwa dariya ce ko kuma murmushi duk ya rasa tayi itako ta sa kai da nufin barin gurin sai kuma ta dawo ganin yadda yusra ke yi mata wani kallon raini tare da naseer dake harararta gaban naseer taje ta dan rusuna tare da fadin gani yaya? ubanwa ya kiraki ? ubana mana ta fada tare da qifqifta ido kasan ance babban wa magajin uba kaga ko ai kai ubana ne ko? rasa me zaice mata yayi sai yusrah datayi qarfin halin fadin ke wai wannan wane irin iskanci ne haka anan kinga sa'anninki ne miqewa tayi tare da fadin ah ah wlh ko daya daga sa'annin baffana sai yayyena sai kuma wadanda ban sanma a wanne mataki zan ajiye su ba dan nasan da sunyi aure da wuri da ko a haihuwar raquma nice auta cikin 'ya'yansu tana gama fadar haka ta qara gaba tabar kowa shaye da mamakinta kwafa yusra tayi tana jinjina rashin mutuncin dazata yiwa yarinyar danta lura tashen balaga takeji ****** tun daga wannan lokacin babu wanda ta kuma haduwa dashi kowa yana cikin hidimar biki inda suketa shirye shirye **** rana bata karya yau saura kwana biyu daurin aure yayin da mutanen qauyen gawo suka iso dije ce ta sama musu masauki danta lura indai ta hajiya mamy ne sai dai su wulaqanta dije tasa ran zuwan innarta amma sai taga ba'a zo da ita ba har kuka sai da tayi nan aka shiga rarrashinta ita da basira suka shiga dawainiya da mutanen inda daga baya ta bar baseera ta tafi dansu rufaida nata jiranta dan suje qunshi tunda batada waya da sauri ta fita ta bar gidan tana zuwa kuwa ta tarar suna jiranta nan suka shiga mota suka tafi sunata mata mita dan rufaida akwai son biki kai kace bikin yayanta za'ayi anyi musu qunshi ja da baki tare da gyaran jiki barakallah masha Allah sunyi kyau sosai matuqa sai dare suka dawo gidan duk wanda yaga dije a cikin mutanen kauye saida ya yabata masu taya iyayenta murna nayi masu hassada a zuciya nayi ranar akayi kamun yusrah inda aka gabatar da komai cikin wadata **** yau ake dinner dan haka kowa yake burin qure wanka sauri takeyi ta qarasa part din da 'yan garinsu suka sauka dan zasu je gurin makeup da sukayi booking sam bata lura da shi ba hakan yasa ta dan bugeshi kadan wata irin angaza yayi mata kafin tayi wani yunkuri yakai hannu da niyyar marinta cikin sauri ta kauce a hasale yafara magana ke wace irin mahaukaciya ce iye dan ubanki bakya ganin gabanki in kina tafiya kamar budurwar qauye au ashe fa banyi kuren harshe ba itace wato ke kin girma ko shine rannan harda yiwa mutane rashin kunya ke ga 'yar birni wai tsaya ma duk wannan saurin da rawar jikin da kikeyi duk na menene? idan ma na zuwa gun dinner ne wlh kiyi saurin fasawa dan wlh naga qafarki a gurin saina ci ubanki saina babbala ki gurin manyan mata ne wato classic lady ba irinku wadanda ko dadewa da yayeku ba,ayi ba wuce ki bani guri shegiya me siffar aljanu kalamansa sunyi mata zafi matuka ta so yin kuka amma saita ga meye nata nayin kuka a wanne dalili hmmmmm kawai tace tare da qarawa gaba taje tayi abinda zatayi ta fito tana fita still ta hadu da yusrh daqawayenta suma da alama fita zasuyi dan su shirya tagansu da akwati yauwa ke zonan dan uwarki kin kula su tayi tasa kai da niyyar ficewa wani sauri yusrah tayi tare da fadin ke ina miki magana kina jina nasan duk wannan rawar kan da rawar kafar da kikeyi danki fita bazai wuce dan kije gun dinner bane to wlh kk sake naga kafarki a gurin nan sai kinci kut........dan gurin manyan guys ne da big girls ba cakuri cici irinki indai ba tsintar bottle din da akasha drinks zaki tsinta ba wucewarta tayi batare data tsaya qara jin me yusran zata ce ba tana fita ta shiga tunanin maganganun su duka biyun wato suna nufin ita batakai wadda zata je bikinsu ba?suna nufin ajinta yayi low dayawa da har zesa takasa taka gurin?juya maganar ta shigayi cikin ranta ta jima tana saqa da warwara kafin daga baya tasami mafita murmushi tai tare da yin kwafa a fili ta furta big guys classic lady's a kafta๐Ÿ˜œ ****** shiri sosai kowanne bangare keyi musamman bangaren amaren dan ko wacce so takeyi taga ta burge ta bada kala cikin taron dan haka kowacce ke babban shiri dije ce ta shigo gidan direct part din mamy ta nufa dake upstairs tasan su yusra na can na shiryawa a zaune ta same su ana shirin fara yiwa yusrah kwalliya da sallamarta tashiga dakin wasu sun amsa wasu kuwa suna sabgar gabansu da qarasawa tayi inda yusrah ke zaune tanata hura hanci tace sannu Anty meye kuma ? ta fada tare da hararart ba komai dama zuwa nayi in baki haquri akan abubuwan da suka faru a nasan nayi miki laifi kiyi haquri nasan idan bamu samu lokaci yau na rokeki ba nasan bazan samu wata damar ba kuma pls aunty kiyafemin kada kai yusra ta shiga yi tare da girgiza kafa nasan dai badan Allah kika rokeni ba nasan bazai wuce dan kije gurin dinner dinnan bane kuma wlh bazaki ba kinji na rantse dan haka wuce ki tafi munafuka lah wlh Aunty bahaka bane ka.....naji ta katseta fice kawai nan duk ba sa'anninki qara matsowa tayih arda fadawa jikinta aunty na zanyi missing dinki sosai finciketa tayi tana fadin zan ciuwarkifa ina wasa dake ne sim sim ta juya ta fita yayin da wasu daga cikin qawayen yusrah ke mata fadan rashin kyautawar datayi duk tayi banza dasu tana fita ta saki dariya tare da fadin woa ni dije wato ke kin saki baki in baki haquri kedin banza waya ta fito da ita ta shiga dannawa ganin akwai password a jiki yasata buga tsaki ta bar gurin direct part din mazan gidan ta nufa duk da tasan zuwa yau ya cika da baki dan tasan dole akwai masu zuwa daga nesa koda ta isa mamaki tayi dan ba kowa tura qofar tayi a hankali ta shiga 'yar magana ta jiyo daga bedroom taji muryar naseer na fadin ai ni inaga daga yau nayi musu sallama shiyasa gara in kwashe su tun yanzu inkai su can tunda yanzunma dole saina dauki kayan dazansa ba gara inyi me gaba daya ba habeeb yace gaskiya ka kawo shawara me kyau nima bari nabi sahunka kawai na huta sadaf sadaf ta dinga yi inda ta hangi wayarsa da wallet ajiye saman center table...... toh ko me dije ke shirin yi ? na gaji typing akwai wahala inyi ma ba comments๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ gara na rage *vote* *comments* *with* 08066364077 daga alqalamin khadyโœ [16/12, 11:41] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TA ME GARI NA khadeeja usman ๐Ÿ”Ÿ wow gaskiya naga dije nada masoya dayawa inta ballo muku ruwa ba ruwana๐Ÿคทโ€โ™€wato tana wuta kuna binta da fetur ko ๐Ÿคฃ sai da ta duba wayar ta tabbatar tashi ce sannan ta dauka tayi saurin fita labewa tayi jikin wani corridor kafin ta danna wayar wani irin farin ciki taji ganin babu security nan nake ta shiga neman number yusra my sweet wife taga ansa da sauri ta shiga gurin rubuta sako gajeren sako ta rubuta tayi sending ma wayar yusrah saida ta tabbatar ta ya shigo kafin tayi delete dinsa a wayar naseer cikin sanda ta koma ta mayar da wayar har yanzu be fito ba dan haka tayi saurin ajiyewa ta fita dakin su yusrah ta nufa tare da sallama kamar dazu an farawa yusrah kwalliya dan haka ta nutsu amma ganin dije yasata fadin uban me yakawo ki kuma ? qarasawa tayi ta lababa ta ajiye wayar kafin tace dama yaya naseer ne ze fita yace inzo in fada miki wai ki duba wayarki ya turo miki sako to naji maza bacemin da gani sim sim ta fice tana dariyar mugunta wayarta ta laluba ta duba sai taga sakon nashi kuwa slm sweety na pls abin nan an qara lokacin zuwanmu sai zuwa 11 wai sbd akwai wata qaramar walimar da aka shirya mana mu da qawayenku so bana son ki gaji dan haka ki jira dakaina zanzo daukarki nida big bros da bridge dinsa amma qawayenki su shirya suyi gaba kada ki kirani yanzu ina busy in nazo akwai magana murmushi tayi bayan tagama karantawa tare da fadawa kawayenta su kam shewa suka sa suka shiga yimata tsiya kallon meyin makeup din tayi tace a bari sai zuwa anjima dan kar ayi ta baci ****** dije ke bawa rufaida dasu husna lbarin abinda yafaru sun san halin mutuniyar dan ko a school in malami yayi mata abu saita san hanyar dazata rama dan haka koda tagaya musu ihu suka shiga yi tare da dada qarawa wutar fetur nan ta shiga fada musu plan dinta **** masha Allah tabarakallahu ahsanul khalikeen iya kyau dije tayi kyau matuqa inda ta dauki wankan wata arniyan gawun ta red din material tare da ash din head gaskiya koni dana ganta na yaba dan tayi kyau sosai ta fito tamkar amaryar sai baza kamshi takeyi duk sunyi kyau sosai inda suka fito daga gurin suka shiga mota dan yanzu kusan 8:45 da alama an kusa farawa dan haka cikin sauri dije ta dubi rufaida tace muyi sauri mu qarasa dan Allah kada kwabata tayi ruwa dariya husna tayi tace hmm yau fa akwai cakwakiya dan haka qara wuta kinji duk suka sa dariya kafin suka nufi gida dan nesa kadan rufaida tayi parking kafin suka maida duban nasu ga qofar gidan inda sukaga anata tururuwar shiga mota can suka hango qawayen yusra nata shiga mota sbd kusan kowacce nada motar kanta yasa kowaccensu bata bi takan abokan ango ba suka shiga motocinsu sukayi gaba a cewarsu sa dan caccashe kafin zuwan amaren daga yusra sai wata friend dinta da me makeup aka bari sbd ma kada wasu su dameta yasata kashe wayarta har sai time din daya fada mata ya kusa saita bude tasan kuma bayada number wata qawarta badan hakan ba ma ita da kunnawa sai gobe suna kallon kowa a hankali guri yagama watsewa sannan suka hango motar da za'a dauki amarya ta nufo gurin ganin yadda motar tasha ado da fulawoyi da balow dole ya burgeka da sauri dije ta kalli rufaida tace now is our time murmushi rufaida tayi kafin ta bude murfin motar ta fito ta nufi gurin waccan motar naseer an hakimce a baya sanye cikin ash colour din shadda datasha aiki bakar hula yasa akansa sai yayi wani kyau da kwarjini ango kenan number yusrah yaketa kokarin kira amma anata ce mishi a kashe har ranshi yadan fara soyuwa rufaida ce ta karaso wurin tare da dan kwankwasa glass din tace Assalamu alaikum angonmu dan sakin fuska yayi wai shi a dole yau ranar farin ciki ce a gareshi be kamata yayi fushi ba kafin ya amsa dan yasan bazai wuce daya ce daga cikin qawayen yusra ba dan yasanta da shegen shige shige ga yawan qawaye dan haka yace ya akayi ne ina amarya ta? dariya tayi kafin tace amaryarka na nan qalau sai dai zuwan nawa ma nata ne ita ta aiko ni da saqo na jima tasaye lnata jiranka gashi kowa ya watse an barni ni kadai inata jira in isar da sakon masoya murmushi yayi kafin yace toh fa sakon me? nasan baka sanni ba ni cousin sister muke da Aunty yusra ta bangaren abbanta to kasan dangi kowa da nasu al'adan mu a namu yau ranar dinner dangi ne zasu wuce da amarya inya so kaima ka tafi daban sai anje gurin saiku hadu ku shiga tare ikon Allah yafada tare da zaro ido dan abin ya dan sosa Ranchdan haka yace a wanne yare kenan ai a ganina kafi kowa sanin kowacce yare ce yusra tunda gashi har zaka aureta ganin yadda tabashi amsa ya tabbatar da dangin mahaifin yusrah 'yan kwamus ne gara yabisu sannu kada suce zasu hana auren gaba daya๐Ÿคฃ toh yanzu meye abinyi kenan? abinyi mu wuce kawai dan kar aita jiranmu dan sun dan jima da tafiya ok come in yafada murfin gaba ta balle ta shiga driver yaja suka tafi dije na ganin dun tafi tacewa husna yessss da alama plan dina yayi aiki ja mu tafi kawai husna kallon dije ta shiga yi tare da fadin wlh khadija in aka kaiki gidan kishiya ta shiga uku daga ita har mijin sbd annoba ce ni ko ta fada cikin hade rai nidai bance ba kima ce mana ni ina ruwana kawai abinda nasani duk wanda yayi min abinda raina beso ba wlh sai ya san yayi min Allah ya shirya Ameen taja mota suka tafi bawata hirar arziqi tsakaninsu ganin in tayi wasa itama dije na iya shirya mata nata rashin mutuncin yasata sakin rai ta dinga janta da hira har saida taga ta warware๐Ÿคฃ *uwar mazga kenan*๐Ÿ˜‚ ****** guri yayi guri ya hadu iya haduwa tun dazu su habeeb da amaryarsa suka hallara qawayen amarya har sun gaji da tiqar rawa inda dangi da 'yan uwa kowa ya matsu a fara abinda ya tara su kowa ya gaji abokan naseer se kiransa sukeyi a waya inda yaketa ce musu gashi nan zuwa suna hanya habeeb ma se kiransa yakeyi da duk wani na kusa amma se yace suna hanya kowa ya gaji M.C murya harta fara dashewa dan yadda yaketa cigiyar amarya da angon ๐Ÿคฃ **** suna qarasowa gurin driver na gama parking rufaida ta bude ta fita a cewarta zata wai zata sanar da zuwansu yusrah ta fito daga inda aka boyeta saisu shiga kuji fa kamar wata kayan sata๐Ÿคฃ motarsu dije na isowa suka faka daga wajen guest in din kafin daga baya suka shigo suka yi parkin amma basu fito ba saida ta kusa minti talatin kafin ta dawo gurin ranta a bace ta bude motar ta shiga ganinta da yayi haka ne yasashi tambayar ta ya'akyi ne qanwarmu ? hmm wlh nida Aunty yusra ne waina sanar da ita wane colaur din kaya kasa na fada mata shine wai ita wlh tasan bakayi kyau wai ai daga kalar dressing din dakayi sai qawayenta da sauran danginmu suce baka waye ba suyita mata dariya dan haka ita inje in sanar maka kaje ka sake dressing tunda tafara kora masa jawabi ransa in yayi dubu ta ba wandabe baci ba dan haka cikin bacin rai yafara fadin ita din banza tasan nawa na kashe ai wlh ko namiji ya ganni yasan dai shigata tayi amma shine tayimin wulaqanci oh kawai dai tace cin mutunci ta shiryamin a gurin amma wllh zata gane kurenta gurin ma baxani ba haba yaya kamar ya bazaka ba bayan.... katseta yayi tare da fadin ubanme zan shiga inyi wazan burge a gurin bayan wadda nayi dominta ta kushe tun kafin ma tagani hakane amma ai be kamata ka koma ba gurin fa duk kai ake jira mu nemi mafita kawai wace irin mafita data wuce kawai in sanar da bros suyi abinda zasuyi kawai ni banda ni gaskiya bata kyauta ba amma inaga yakamata kaima ka qona mata rai kamar yadda tayi maka hmm ta yaya? ta hanyar aron amarya aron amarya kuma kamar ya kenan? zan shiga ciki ne in duba wadda naga kayanku sun zo d same colaur ko sunyi shige kawai mu qara tsarata ku shiga gurin nasan dole zataji haushi amma tunda ita tace kalar kayan daka sa beyi mata ba ai kaga koma mezai faru daga baya ai kasata taji ba dadi kamar yadda taso kaji kunya yana shirin bata amsa yajiyo muryar m.c nakara cigiyarsu sai kuma ga kiran habeeb ya shigo yasan kwanan zancen dan haka yace kinga je ki nemo kawai in yaso ran kowa yabaci dai dai nan dije ta bude mota suka fito alhmdllh cewar rufaida kallonta yayi dan besan meta gani ba gama raba gardama nan kallonsa ya mayar gun dayaga tana kallo masha Allah ya furta ganin yadda siririyar farar yarinya take da kyau na ban mamaki da jan hankali kasancewar dare ne se hasken fitilu ga kuma makeup din datasha ecxatily amarya yasa shi qara kwadaituwa da kawai ya shiga da ita be damu ba dako qawar amar yar bros ce ko qanwarta shi dai kawai yasamu ya fita kunyar abonkansa da suka zo masa daga wata uwa duniya yasan duk wadda yaga yarinyar nan ai yasan ya kece raini dan tafi yusra komai qiba kawai yusrazata nuna mata shima kuma sai yanayinta ya amshi jikin nata kinga je kiyi yadda ya dace kawai kinji sister nagode da saurinta ta isa gun su dije da suka nufi gurin shiga holl din kamar gaske tayi musu sallama tana aarasa wa ta shiga labarta musu komai suka dinga dariya kuwa zuwa can takamo hannun dije suka nufo gurin motar da naseer ke ciki tunda suka nufo gurin ya shiga gyara zaman hula da kafadar rigar sa suna zuwa rufaida ta leka ta glass tace ya fito yana fitowa ta damka hannun dije a hannunsa dukansu saida sukaji tsikar jikinsu ta tashi turare ta fito dashi a hand bag dinta masu kyau da tsada ta shiga feshe su dashi inda take kamshin ya hadu da nasu na jikin yabada wani sassanyan kamshin daban ko tunanin wacece beyi ba illa ma wani nishadi dayaji nan rufaida tace bari taje ta sanar da zuwansu tana shiga holl din ta qarasa ta sanar da m.c isowar daya amaryar da angonta take kuwa yasa aka canza kida guri ya kacame da murnar isowarsu wasu daga qawayen yusra suka mike tare da abokan ango dan taro amarya da angon nata suna shigowa gurin aka hau tafi da sowa yayin da waqar Abdul d one ke tashi ta lale amarya da ango habeeb da amaryarsa qura musu ido sukayi yayin da kowanne kishi yacika zuciyarshi dan ita dai amaryar habeeb ta kure wanka so takeyi taga tafi amaryar qanin mijin nata bada kala amma gashi ko kusa ma babu hadi shi kuwa habeeb ganin yadda qanin nasa da amaryarsa suka fito suka haska gurin yasa yadanji haushi saida suka nufo gurin yaga ashe ba yusra bace to kodai wata me makeuo din ce ta shigo da ake canzawa mutum halitta yasan naseer da son kece raini anya kuwa? hat suka qaraso mazauninsu kafin kowa ya dan nutsu inda nan fa qawayen yusra da dangi aka shiga mamakin to ina yusra dan ko makaho indai yasan yura yasan dai wannan ba ita bace nan fa aka shiga cece kuce ganin lokaci ya fara qurewa yasa aka shiga hada hadar abinda ya tara yana son kallon yarinyar amma yana jin nauyin yin hakan ganin abokai da qawaye nata zuwa suna pic dasu yasashi satar kallonta dai dai tayi murmushi damm yaji kirjinsa yayi dije!!dije!!dije? ya shiga ambata a zuciyarsa ganin ya ganeta yasa suna hada ido tayi masa killer smile tare da kanne ido daya saurin kawar da kansa yayi tare da fadin how this comes? bai samu amsa ba yaji m.c na gayyatar su a filin rawa jiki ba kwari ya miqe suka fita shi kanshi habeeb se yanzu ya gane yarinyar nan ya shiga mamakin ya akayi haka suna filin rawa anata musu liki da sun hada ido da naseer saita saki murmushi can ta dan qara matsawa jikinshi kafin ta rada mishi a kunne ya kaga 'yar yayen kaga yadda ko su classic lady's din sukayi mubaya'a ko rada mta shima yayi a kunne wlh zaki ci ubanki kuwa murmushi tayi kafin tace ani bana ikata laifi sain shirya karbar hukuncinsa gani yadda sukeyi suka burge mutane dayawa aka shiga daukarsu pictures da videos ** yusrah tana ganin lokacin daya fada ya kusa ta ce ayi mata makeup din tare da munna wayarta tana budewa kira na shigowa ta duba ko shine sai taga khaleesart ce da sauri ta daga dan tasan zancen be wuce suce suna jiransu ba hello qawata ya akayi? kina ina? ina gida mana ina jiran naseer ya zo mu wuce wane naseer kuma ai sede ki nemi wani nan ta fada mata abinda ke faruwa a haukace ta miqe ta na fadin ni naseer zaiyiwa haka ni zaka wulaqanta narantse da Allah yau sai anyi uwar watsi ko ta kan me makeup bata biba ta suri mayafinta da key din mota qawarta da suke tare ganin yadda ta fita yasa suka bita..... ina ganin comments dinku kuna burgeni naji dadi sosai da masu kirana da masu min text nagode *vote* *comments* *with 08066364077* *Alqalamin khadyโœ [16/12, 11:41] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* NA KHADIJA USMAN 1โƒฃ1โƒฃ *wannan shafin na sadaukar dashi ga dukkan member's na khadeeja fans novels na yaba kwarai da comments dinku dan haka ma nace daga yanzu ku kadai ne zaku sami tame gari* bayan an dan gama caccashewa ne kowa ya koma gurin zamansa yayin da wadanda suka san yusrah naseer zai aura da suka ga ba itace a gurin dinner din ba sun cika fam da mamaki wasu suka barje haushinsu akan kudinsu suka dinga bazawa naseer liki dan a ganinsu yusrah ce ta shirya rashin mutunci musamman dangin babanta amma dangin mamanta a cike suke danma dayawansu basu san wace ce dije ba ana haka aka sanar da amarya da ango su yanka cake su habeeb ne suka fa ra inda yaba amaryarsa itama ta bashi cikin gogewa da kwarewa sannan aka zo kan su dije da nata gogan ๐Ÿ˜œ shiya fara yankawa ya wawuro tabkeke ya nufi bakinta cike da mugunta ta gane nufinsa dan haka ta shirya tare da bude dukkan bakinta ya tura mata nan take aka dauki tafi raf...raf..raf...sannan itama ta mika hannu da niyyar dauko wanda zata bashi dan mitsitsi ta yanko tare da nufar bakinsa ya so yaki bude bakin amma ganin dayayi ido yayi yawa akansu ga pic anata dauka ga masu video coverage hakan yasa ya dan bude bakin kadan ga mamakinsa sai gani yayi tasa masa a hankali dan gefen bakinsa ne ya baci da cake din be ankara ba yaji takawo bakinta saitin gurin ta ziro harshenta ta lashe tare da dora masa kiss a bakinsa qamewa yayi kamar gunki guri kuwa ya kaure da hayaniya da tafi wasu ko da suka san yusrah zai aura suka shiga rattaba nasu luguden leben shi kanshi naseer din cike yake da tararradi domin yasan yanada tarin 'yan qalu bale daga abokansa zuwa friends dinsa amma yasan ai laifin yusrah ne tunda ita taso dizga shi gara ma da akayi hakan dan ya fita kunya amma fa ba abinda zai hanashi cin uwar yarinyar nan ansa taken nigeria a gurin wanda shi ke nuna taro ya tashi ko kafin naseer ya ankara ya nemi dije sama ko kasa ya rasa itako wata 'yar loko tasamu ta labe ta ta cire daurin kanta ta lababa ta sirnane zuwa gurin motarsu tana zuwa ta bude ta shige baya sai ganin su rufaida tayi sunata raba idanu kallonsu tayi tare da fadin ku kuma lfy naga kunata muzurai? hmm ai dole muyi cewar husna ke kin san yadda kirjina ke bugawa kuwa haka kawai kija amana shegen duka ji fa abinda kikayi khadeeja bakiji yadda wasu dangin amaryar ke fadin sai sunci ubanki shiyasa muka silale dan da kin dada bata lokaci wlh guduwa zamuyi rufaida tace ai gara ke ni ai idona idon naseer shaqeni zaiyi a dau gawata bare kuma yusra kai dayalla can matsoratan banza ni wlh dana san ma haka zakuyita min da ni kadai zanyi aikina kun san zan iya ina ruwana da duk hukuncin da zasuyi min nasan dai duk wanda yayimin cikinsu wlh sai in hana daukar amaryar ma gaba daya ko inyi abinda zaisa 'yan bikin kowa ya......bata qarasa ba suka ga shigowar motar yusrah a miliyan ko kwakkwaran parkin bata gama yiba ta bude ta fito ta nufi qofar holl din da gudu tuni mutane sun fara fitowa ta kutsa kai ta cikin su inda tana shiga tafara ruwan ashar tare da ball da duk abinda tayi kacibis dashi hange takeyi taga inda zata ga tsinnanun maciya amana amma bata gansu ba riqeta aka shiga yi inda ta dinga ihu da zage zage nan ta shiga sanar da danginta da qawayenta masu ganin laifinta sakon da naseer ya tura mata na karta shirya da wuri wato hakan na nufin yanzu ya tafi da dije gurin professional walimar daya ce an shirya musu wlh saiya san yayi mata haka duk saita ci kut.....๐Ÿ™Šsu haka aka rirriketa ana mata fada amma tayi banza dasu ta dinga rashin mutuncinta shiko naseer tuni suka fice da sauran abokan shi kuma su habeeb tuni ya saita shima da tashi amaryar naseer na kallon zuwan yusrah amma ya qyaleta kowa yagama fitowa inda kowa ya shiga abin hawansa inda kowa yakama gabansa kusan su dije ne karshen fita dan duk su rufaida a tsorace suke ji sukeyi bazasu iya driven ba inda dije ta cika fam gashi bata iya driven sosai ba shiyasa ganin suna neman bata rai yasata fadin na rantse da Allah cikinku kowacce bashi taci kuma seta biya ah ah khadeeja rufa mana asiri wlh ba haka bane kada kija mana wani bala'in to tsayuwar me mukeyi ku wuce mu tafi mana jiki ba kwari suka ja motar suka nufi gida a hanya dije tace kunga ku wuce dani gidanku kawai mukwana can dan ni gobe ma kauye nayi๐Ÿ˜ƒ bikin fa? wanne biki ai inba so nakeyi a hada da jana'izar gawata ba gara in gudu qauye harsai jarababbun nan sun bar gidan daga baya in dawo dan in suka san gaskiyar abinda yafaru inaga naman jikina zasuyita yanka har sai sunga nakai takarda๐Ÿ˜‹ dariya suka sa tare da fadin ashe khadija tanada tsoro hmm ai tsoro halak ne haka kawai a taba lfy ta a jawa me sona asara mijin dazan aura duk yaga tabo a jikina me yafi raina?gara in san nayi koba komai tsawon shekara uku danayi banga innata ba zan fanshe a haka har suka qaraso gidan su rufaida suna shiga sukayi wanka sukayi sallah tare da cin abinci suka kwanta bacci ***** gida fa ya kacame inda mamy ta kira naseer cikin bacin rai tace tana son ganinshi bai wani jima ba yazo yana shiga dakinta ya iske yusrah kamar mahaukaciya fuskar nan ta hade da majina da hawaye idanunta duk sun kumbura alamar tasha kuka cikin ladabi ya gaisheda mamy ko amsawa batayi ba ta shiga tambayarsa dalilin daya sa ya aikata abinda ya aikata bayani ya shiga yi mata inda nan take yusrah ta karyata tare da fadin wlh qarya ne mamy kinga text din fa dayamin karba mamy tayi ta karanta tare da fadin ubanwa to ya tura wannan saqon ? karba yayi ya duba yakaranta yaga number sa ce kuwa cike da mamaki ya kalli mamy yace na rantse da Allah wlh wlh bani na tura sakon nan ba tabbas number ta ce amma banida masaniya akanshi amma mamy ai itama ta turamin wata cousin sister dinta tace wai dreesing dina beyi ba saina dawo na sake wani caraf ta amshe da fadin wlh qarya ne ni babu wanda na aika nan aka shiga musu ganin haka yasa mamy daka musu tsawa tare da fadin kai ban son iskanci ya akayi ka hadu da dije a gurin to be boye komai ba ya fadawa mamy nisawa tayi kafin tace amma wannan anyi shegiyar muguwar yarinya yanzu nagane bakin zaren cikinku akwai wanda yayi mata wani abun tayi maku ramuwar gayya kenan nan kowa ya shiga fadin abinda yafadawa dije akan zuwa gun dinner din koda naji yanzu naji batu amma ko wannan uwarta ta haifi fitina da kanta zako tasan tayimin haka wlh saita gane batada wayo nan ta gama fadin duk abinda zata fada suma kowannensu a zuciyarsa ya gama kiyasta hukunci. dazai yima dije niko nace to ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta๐Ÿ™Š ******* washe garin ranar asabar aka daura auren habeeb khamis da sajida A lawan tare da na yusrah Abubakar da angonta naseer khamis duk akan sadaki dubu dari dari inda dinbin jama'a suka shaida duk dangin kauye maza sunzo harda ko mahaifin dije da megari ansha yinin biki inda karfe takwas aka dauki amare zuwa gidajensu dake wuse zone 2 gidan yayi matukar kyau tare suka gina shi gate daya ne amma kowacce part dinta daban babu kuma abinda aka banbanta wajen ginin konai iri dayane har aka gama shagalin biki ba wanda yaga idon dije duk masu son ganinta kuwa sai washe garin ranar ta dira a gidan koda ta iso 'yan garinsu nata shirye shiryen komawa kauye dan haka itama ta hada kayanta suna can falon baki ta iske su bakaramin dadin ganin mahaifinta tayi ba inda shima yaji dadin ganin tilon 'yar tasa ganin yadda ta canza tayi kyau ga kuma nutsuwa shima a bangaren me gari dadin yaji inda ya shiga sa musu albarka koda tace zata bisu bawanda yayi hanzarin hanata dan ta yi kokari dan haka koda aka tashi tafiya da ita aka shiga mota sai bayan ta shiga ne mami ta ganta inda ta ciji yatsa takira daddy akan meyasa za'a tafi da dije yace zata ganin gida ne duk yadda taso ya hana bata samu shiga ba a ranta tace zaki daw ki sameni su dije an dau hanya yayin da zumudi da farin cikin dokin ganin innarta yasa take gani. kamar motar bata gudu tayi bacci ta tashi yafi sau nawa kafin a isa sai kusan yamma suka iso gida zo kuga murna gurin dije *WELCOME BACK TO VILLAGE DIJE* *vote* *comments* *with 08066364077* insha Allah indai nasami lokaci zaku jini zuwa dare [16/12, 11:41] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* NA khadija usman 1โƒฃ3โƒฃ *rawa da girgiza zanyi gabanku in jujjuya๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ zanyi muku albishir comments dinku na burgeni๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ* *gaskiya naga soyayya a zahiri da badini jinjina gareku masoyana nasan soyayyar tame gari ce ta shafeni ina matuqar godiya gareku Allah yabar qauna* *sadnaf ina tayaki murnar samun lfy Allah ya qaremu da lfy da duk musulmin Allah baki daya,Aunty safiyya huguma kema ina miki fatan samun lfy me dorewa Allah yasa anyi aikin a sa'a* **** kallonsu dije tayi taga yadda jikinsu ke makyarkyata ita abunma sai ya bata dariya dole saida ta dan murmusa kafin ta maida kallon ta garesu tace na kira waya azo a tafi daku sbd haka ku tashi mu tafi dan bana son jira magiya suka shiga yi kuka wi wi dan inna mairo harda fyace majina suna wlh ba laifinta bane hansai ce shima din hamidan duk akan hansai suka dora laifin ganin da tayu duk suna son zamewa su barta ciki yasata sakin kuka tare da fadin munafiki wlh qarya ne duk da laifinsu suma kuma ni yauhe ma nasa ku quntatawa 'yar mutane bakai ka gani ka auro ta ba ko nice inna da dole innace kayi abu se kayi ? ah ah hansai kiji tsoron Allah ki fadi gaskiya wlh 'yan sanda basuda imani ko kadan kikkilemu zasuyi ko digon jininmu baza'a samu ba sbd haka ki karbi laifinki kawai a tafi dake ni a barni da dana se 'yata hafsy ta qarasa maganar tana miqa hannu da dafa kan hafsy data maqure guri guda tana kallon ikon Allah kunga duk nagaji da surutu sbd haka kutashi mu tafi kawai ta fada tana me qoqarin mikewa hansai ce ta miqe da kyar ta kalli dije kafin ta kaikaice ta ce ke dayalla gafara can dan kinga ma ana lallabaki wlh dukanku ina iya hadawa inci uwarku ba inda zani hukumar hegiya dan haka kin dade baki ce su shigo din su tafi dani ba ganin yadda taketa bala'i da kumfar baki yasa fa zuciyar dije bugawa daram dararam dam dan ita kanta tasan idan ta bari wannan me kama sa jinsin ordisay din ta damketa to fa wlh saita ci kut......๐Ÿ™Š gara ta lallaba ta zame dan taga alamar wannan kaddarar hafsy ce koba kamai ta tayata da addu'a kawai ๐Ÿคฃ ganin da hansai tayi kamar dije ta tsorata da ita yasata qara sakin sababi duk da itama qarfin halin ne dan wlh da za'a tsaga kirjinta tsab zuciyarta zata fado ta fito kallon tsaf dije tayi mata ta lura da sababin da takeyi na iya baki ne a ranta tace kin gama yawo yarinya amma a fili saita ce keeeeeee!!!!! shutup your magout maout ina magana kinayi kin san wacece hukuma kuwa ?kinyi lafuffuka da dama kuma masu girma ciki harda na zagin hukuma dan haka dole ki karbi hukuncinki tare da masu mara miki baya dan haka kuna batamin lokaci pls ku wuce muje hamidan ne yace yanzu dai ranki ya dade laifin waye ya shafeni ni? oho dai koma laifin waye ai kai ka sani ni ba ruwana danme zaka auro yarinya ka maidata baiwa suma iyayenta saina sa an tafi dasu tunda basu kula da yarinyarsu suka dauka duka bata kinga ranki ya dade wlh wlh laifin duk na hansai ne ko inna? eh wlh itace da anyi abu saita ce zata zane mutum kota zaune shi sbd haka muke yi mata biyayya duba da yanayin hallitar da Allah yayi mata oh yanzu nagano bakin zaren kana namiji matarka kw juyaka kenan to waye mijin cikinku? nine wlh amma a suna toh yanzu ka zabi daya shin zaka barta matsayin mijin ko kuma zaka dawo mikin in yaso a dai daita? wlh zan koma cikakken namiji ma toh masha Allah wane mataki zaka dauka yanzu? sakinta zanyi dama ta isheni wlh nisawa tayi taga dai ba kyau raba sunnar ma'aiki kuma ta lura da yadda hansai jikinta yayi sanyi daga jin an ambaci kalmar saki saita bata tausayi tace to yanzu zanyi muku wani adalci guda daya zan rufa muku asiri kowa yazauna muyi magana zama sukayi duka inda su kansu suke mamakin yadda suke bin maganar yarinyar kodan fa hukuma ba sauki ganin su nutsu yasata zame gilashin idonta abin mamaki ji nayi su dije an afka wa'azi gadan gadan ta shiga yi musu nasiha da taushin murya Allah kenan duk cikinsu nutsuwa sukayi sunaji inda duk jikinsu yayi sanyi saida ta gama kafin tabi kowa tanaa fada masa laifinsa tare da sanar dasu inta kaisu abuja irin hukuncin da za'a musu amma yanzu in sunji nasiha zata san yadda zatayi a kyalesu amma fa daga wannan lokacin zasu yawaita kawo ziyara qauyen kuma kowannw lokaci suna iya zuwa da sauri suka amsa sun yadda inda daga baya dije tace ta sallamesu su tashi su fita wai zata yiwa hafsy gwajin cutar caskalaxation ๐Ÿคฃ duk suka miqe suka fita jiki ba kwari sun jima da hafsy tana yimata nasiha akan rayuwa kafin ta bata abinda tazo mata dashi tace zata tafi amma kafin ta koma abuja zata dawo sai dai kada ta bari su rainata itama kuma kada ta raina kowanne cikinsu a haka sukayi sallama hafsy harda kuka tanama dije godiya sai yamma ta dawo gida babu wanda ta fadawa abinda tayi washe garin ranar tasamu zuwa gidan su shatu ita kam ba laifi da sauki abin in akayi la'akari da auren kauye dama an san dole sai anyi wannan bautar ******** haka kwanaki suka dinga tafiya inda hutun dije ya qare daddy ya kira yace ta dawo gida koda me gari yafada mata bata so ba amma dole ta fara shirye shiryen komawa duk cikinsu ita da iyayenta suna kewar tafiyar tata ******** to bari mu leqa gidan amare kuma anyi taro lfy kowa ya kama gabansa yayin da aka bar angwaye da amarensu kasancewar kowa auren soyayya sukayi yasa suke cikin farin cikk da walwala da kulawa da juna naseer da yusra kam kullum addu'arsu Allah yakawo dije domin sun zauna sun tattauna akan abinda ya faru sun gama gano itac silar komai dan haka kowa ya qudiri aniyar yimata nasa salon rashin mutuncn toh fa zama ya fara zama domin yau kusan sati biyu da aurensu kullum daga gidan mamy ake kawo musu abinci su duka inda suka saki jiki suke shan amarci sosai ba ruwansu a bangaren habeeb ma abin maliyan luqwi domin yasamu yadda yake so sajida ta kware a fannin soyayya macece me tsananin kissa da kisisina irin su ne matan daba boka ba malam amma karfar baka kadai ta wadatar suyiwa mutum kwaf daya duk irin yadda ta lura msmy na ji da yusra hakan yasa ta qara jawota jikinta itama domin ta lura yusrah da sauranta har yanzu ****** yau dije ta shirya dawowa iyayenta sunyi mata nasiha matuka daddy ne ya turo aka dauketa sai birnin tarayya๐Ÿš— kusan magarib suka iso gidan direct dakin su ta nufa bata bi takan mamy ba dan tasan ko ta dawo ko bata dawo ba gurin mamy duk daya ne dan haka dokin ganin basira kawai takeyi koda basira ta ganta kuwa rungumeta tayi suka shiga murnar ganin juna sai da tayi wanka tayi sallah kafin taci abinci sam basu samu haduwa da kowa na gidan ba dan ita harga Allah tama manta da wata cakwakiyar data tafi ta bari *vote* *comment* *with 08066364077* *Alqalamin khady*โœ [16/12, 11:41] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* NA Khadija usman 1โƒฃ2โƒฃ ba qaramin farin ciki innah tayi ba da ganin dije ta canza tayi kyau ta wuce ma tunanin yadda take so ta zama ita kanta dijen tayi farin cikin ganin innah inda suka bude shafin hira danma yamma ce zabbi inna tasa aka yankawa dije ta kwashi gara kuwa inda ko da wasa bata sanar da innah zaman da takeyi a binni ba itama innar ganin canzawar dijen yasa tabar tunanin da takeyi a baya na ko dijen na cikin wahala sai bayan isha'i suka sami zama da iyayenta inda sukaita taba hirar yaushe gamo nan dije ta dubi innah tace wai ni innah ina ko su hafsy da shatu ai sunyi aure tun tuni sai dai kam ita hafsy abun ba dadi dan dan yayar delu ne ya aureta kin san ko gurin delu ba dadi take ji ba dan haka koda yaron ya nuna yana so duk da ba yaron kwarai ne ba ta ce dole sai anyi gashi dama yanada wata matar yanzu in kinga hafsy sai kin tausaya mata wlh ga wahalar miji gata kishiya abun ba'a magana wlh gwanin ban tausayi tsayawa tayi da cin abincin da takeyi kafin tace Allah sarki hafsy wlh na tausaya mata aure a qarancin shekarunta haka ai an cuceta inna ce ta kalle ta tare da fadin to me kike nufi ? bata isa auren bane ko kuwa? wlh inna in kikaga irin yadda nake tausayawa wadanda ake yiwa aure da wuri sai kinyi mamaki musamman yanzu da naje nayi rayuwa cikin wayayyun mutane bazaki fahimci ana cutar yaranmu na karkara ba sai kinga yadda in sun tashi haihuwa suke shan wahala yanzu ba da bane amma har yanzu kunki ku gane ni yanzu ma a abuja waye zai kalleni bare ma har yazomin da maganar aure ai gani zaiyi nayi masa qanqanta inna ce ta riqe haba tana kallon ikon Allah tare da jin kalaman dije wadda ta dage sai zuba sharhi takeyi can ta nisa tace au ke nan ma kina nufin baki isa aure ba kenan? wlh ban isa ba a birni dai kam musamman 'yan boko gani zasuyi anyi min auren wuri dube ni fa duka nawa nake um gaskiya na ganki fa gashi nan kirji ba komai hmm inna kenan to wlh akan 'yammatan abuja ni ko kirgar dangi ban fara ba mutanen da zaki ga nonuwansu kamar jarka ai me qananan halitta ce zaki gansu kamar kaina ke dije ke dije kiji tsoron Allah to a baro ake tura musu shi ko hmm ai inna yanzu duk yadda na fasalta miki bazaki yadda ba kawai mubar maganar wace unguwa hafsy take? tana can alqaleri insha Allahu gobe ko zanje ai nasan ma gidan yayar delun idan naje sai a rakani ai bama saikin sha wahala ba a cikin gidan suke toh Allah yasa ma in gane danni yanzu kananun hanyoyin nan duk na manta su duk da duhun dake dakin be hana inna wurga mata harara ba tare da fadin ai dayake can a sama kike yawo wlh kuwa kamar kin sani ga hanyoyi nan kamar filin ball ka kure iya tafiyarka kamar zaka bangon duniya ganin inta biyewa dije zatai ciwon baki yasata sauya akalar hirar tare da fadin ya zaman naki yake to a gidan kawun naki ince dai babu wata matsala ai innah in ana batun matsala ma karki dinga kawota gidan nan mutanen kwarai ne sosai zamana dasu kamar ma hadiye juna yanda kika ga talaka da kudi ko ince miki buhari da talaka sosai suke kula dani ke tsakani da Allah bakiga yadda suke kula dani ba nima kuma ina binsu sau da qafa to Alhmdllh naji dadi sosai ashe zahida ta canza hali wlh kullum da tunaninki nake kwana nake tashi ina tsoron kada kema kidau dabi'ar arna tunda kinje ansaki makarantarsu inna kenan ke har yanzu baki bar maganar arnan nan ba wai waya fada miki karatun boko na arna ne kawai dan ka je ka koyi ilimi sai a ce maka arne ai ku tuni kunyi nisa bakwajin kira dan haka ni ya isheni haka kije ke kika sani kiyita yi ba ruwana amma ai zaki samin albarka dai? albarka ai kullum sata nakeyi toh nagode innata suna tsaka da hirar baffa ya shigo aka shiga yi dashi saida suka raba dare kafin kowa ya kwanta asuba tagari ******* tunda safe dije ta karade gari duk gidan data san yakamata ta shiga ta shiga a gidan me gari ta yada zango inda suka kwashi hirar su da mutan gida aka sha drama duk wanda yaga dije sai yayi mamakin ta kasancewar ta canza inba an fada maka ance dije bace da wuya ka ganeta ta zama 'yar gayu komai ya canza bata samu zuwa gidan hafsy a ranar ba sai washe gari tunda safe ta shirya cikin riga da siket na atamfa kasancewar an fara sanyi yasa ta dora wata babbar rigar sanyi a saman dressing dinta qaramin mayafi ta yafa tare da sa hill dinta baki tare da hand bag data zuba wasu 'yan kayan da zata kaiwa hafsy ta fito ta tarar da inna na gyaran masarar da za'ayi tuwo yau sannu da aiki innah yauwa me shigar 'yan duniya yanzu ke duk kin dauki dabi'ar mutanen nan dubi.......bata bari ta qarasa ba ta qarasa jikinta da rungumeta tare da fadin pls inna ya isa tare dakai mata kiss a kumatu tana dariya ta saketa ta nufi hanyar fita saina dawo inna oh ni saudatu na shiga uku yanzu kuma wannan dabi'ar wace iri ce ita babba dake da cizo a kumatu wato shi cizon ma yanzu an banbanta shi dana binni dana kauye me makon nayi miki magana ki cijeni da haqori saiki turamin baki ki dunguremin kumatu Allah ya shiryamin ke dije **** dan mashin din daya sauketa ta tsaya bawa kudi yara tuni sun zagaye ta yayin da wasu matan da 'ya'yansu suka kai musu rahoton baquwar baturiyar da akayi yasa suka fara tururuwar leqowa ta katanga ganin ta nufi gidan ladidi me kosai ne yara suka qara duruwa a qofar gidan da sallama ta shiga gidan inda ta iske bakowa a tsakar gidan qara sallamar tayi kafin taji an amsa daga can ciki hafsy ce ta fito sanye cikin riga da zani na atamfa duk sun kode iya hannun rigar kadai ya isa ayi maka rafar kasan riga harda tattara๐Ÿคฃ duk ta wani cakude tayi kalar tausayi ganin bakuwar dake. tsaye ne yasata kafeta da ido gani takeyi kamar tasan fuskar amma zaiyi wuya ma dan tana ganin a talavijin ne dan haka dai ta dan saki rai tace sannu baiwar Allah itako dije tunda ta ganta tausayinta ya kamata ji takeyi kamar tayi kuka duk nawa suke ita da hafsy yanzu fa suke shekara sha bakwai amma in suka jera kana iya rantsewa ta haifi dije ganinta a haka ya raunana zuciyar dije sosai ganin cewar bata ganeta ba yasata yin murmushi tare da fadin *dijan gala tame gari ba auren talaka ba talaka noma da sassabe* hafsy najin dije ta fadi haka ta saki wata dariya tare da farin ciki tayo cikin dije da niyyar ta rungumeta sai kuma ta fasa ta shiga kallonta tana fadin dagaske kece dije?kece kika zama haka ? anya kuwa? rungumeta dije tayi kafin ta fashe da kuka nice hafsy meyasa kika fasa rungumata ko baki son rabata ne ? ah ah dije indai kece dijeta dana sani kuma uwar mazga me bani kashi bazan ki rabar jikinki ba illa dai kada in shafa miki datti kin ganki kuwa dije tabbas Allah na sonki ji yadda rayuwa ta sauya miki ni kuwa dubeni duk na tsofe banda bauta da wahala a hannun uwar miji da kuma kishiya da shi mijin kanshi ba abinda nake tsinta dubi yadda kika koma kamar ba'a duniya kike rayuwa ba wlh dije nayi miki murnar tafiyarki binni dama nice nasamu koda kwatan abinda kika samu ne ta karasa maganar tana kuka dena fadar haka hafsy Allah na sonki bai kuma manta dake ba ba kuma dan na fiki bane nima yasa nazama haka ki yadda da kaddarar ki kizama mai juriya da haquri har ki samu kici jarabawar ki yanzu dai muje dakin ki tukun dakin ta suka shiga sai kace dakin tsohuwa qaramin gadon qarfe ne shima duk ya tsufa dakin ko kyan gani babu sallaya ta shimfidawa dije a gurin ta zauna inda suka shiga hira sunata nishadi tare da tuna baya dije na lura da yadda hafsy keta mutsu mutsu dan haka ta tambayeta lfy? dan marairaicewa tayi tare da fadin wlh dije narasa yadda zanyi ne abincin dazan sama miki naketa tunani yanzu gashi yadda kike din nan da wuya ki iya shan ruwan gidan dan na rijiya ne kada ki damu hafsy maza samo yaro yasama mana abinda zamu ci jiki ba kwari ta mike ta fita neman yaro inda bata sha wahalar samu ba kuwa dan sun cika qofar gidan suna jiran baturiya ta fito su qara kallonta dubu daya dije t bawa yaran tace su siyo taliya sai kayan miya da maggi aikuwa da gudu suka karba sai kace a mota suka tafi sai gashi da wuri sun dawo dari tabasu tace su raba aIkuwa murna ba' a magana tashi hafsy tayi ta hura wuta sunada ice fitowa tayi sukayi girkin tare har suka gama kuwa cikin mutanen gidan ba wanda ya dawo ranar hafsy ta barge haushin yunwar kwana da kwanaki kuwa dan ta debi girki daman ga mutumin kauye da son taliya kallonta dije ke yi cike da tausayawa kafin ta tambayeta matsalarta duk yanayin zaman da takeyi a gidan da kowa saida ta fada mata aikuwa take dije ta danna wata uwar ashar tsumi ya motsa nan ta shiga zazzaga bala'i kallonta hafsy tayi taga yadda ta rikede lokaci daya ta koma dijengala dinta ta da 'yar takife jahannama ga fasinja uwar suburbuda da mazga sai da tayi me isarta kafin ta nisa tace ina 'yan gidan suka tafi? shi yana bakin kasuwa ita kuma kihiyar tawa da innarsa sun tafi suna can gidan su abokiyar zaman nawa dan kinsan duk gidan nan tsoron ta sukeyi har hi me gidan hi yasa ma inna ke binta kamar ita ta haifi dan girgiza kai dije tayi tare da fadin hukuncin ta kanta zai fara kenan? dafe kirji hafsy tayi tare da fadin na higa uku dije wane hukunci kum?kaddai kicemin har yanzu muguntarki na nan nidai rufamin asiri wlh karsu rama akaina dayalla rufawa mutane baki kin san ni idan na tashi rama abu to da basira nake amfani an fada miki gaba duka zan afka musu ni nasan me zanyi musu uwar ita kishiyar taki zanci wlh ni ba ruwanaa ke dije rufawa kanki asiri wlh wannan inta tauheki ko qafarki baza'a gani ba ruhehiya ce hi yasa ma fa ita kanta inna da hi hamidan din ke tsoronta dan mullikekiyar katuwa ce ance aljanu ne suka hura mata iska wai data hararesu kallonta dije tayi tare da fadin ke hafsy a ina taga aljanin da har zata hararesu ? ance tun tana qarama kafin dije tace wani abu suka tsinkayo muryar hamidan na fadin iskancin banza da wofi wace shegiyar ce ta shigomin gida tasan kuma inna da hansai basa nan har aka taramin yara a qofar gidan yana fada ya qaraso dakin tunda hafsy tajishi jikinta ya kama rawa ta dinga kallon dije tana yarfa hannu ita kuwa dijen ko'a jikinta illah zuge jakarta da tayi ta lalubo siririn farin glass dinta ta manna a fuskarta tare da qara gyara zamanta yaye dan yalolon labulen dakin yayi tare da fadin nace wace hegiyar ce ta higar min gida bada izini na ba cikin rawar murya hafsy tace am dama.....da...ma um...daga...kinga barshi in gabatar masa da kaina daga abuja nake ma'ana birnin tarayya nasan kasan sunan garin ina daya daga cikin hukumar farin kaya ta 'yan sanda masu bincike inda muke bi kauyuka muna bincika yadda suke gudanar da zamantakewar aurensu hakika mun kuma samu yadda mukayi tsammani dan gashi nan mun gani a gidanka sbd haka yanzu basai nayi wani bincike ba zan kira waya jami'anmu na 'yan sanda masu sa kaki suzo su tafi dakai mun same ka dai lafuffuka da dama duba da yadda na riski matarka duk da bata cemin komai ba ta rufa maka asiri amma banga alamar kana kula da ita ba ji yadda dakinta yake ji suturar jikinta gashi tun zuwana na aunata naga bata ci tana qoshi koma taci ta koshin bata samun me kyau dan haka zamu tafi dakai can ofishin 'yan sanda mafi kusa kafin gobe a wuce dakai abuja daga nan sai musan abinyi dakai hukuncin daurin rai da rai ko kuma daurin shekara hamsin tunda tafara maganar hantar cikinsa ta kada jikinsa yafara mazari *kun san ance shege na kauye sai tsoron 'yan sanda* ๐Ÿ˜‚ gurfanawa yayi a gurin tare da fadin wlh wlh ranki ya dade alqu'arn idan da laifina a ciki in mutu a tsaye yaseen laifin hansai ne da innah qara hade rai tayi tace au wato ma kanada wasu matan kenan? ah ah guda daya ce kuma itama kaddara tasa na aureta ko hafsy? nidai ban sani ba cewar hafsy da tayi zuru tana kallon dije ikon Allah tare da yabawa da basirar ta ah ah hafsy duk wanda yaga yanayin zamana da hansai yasan kaddara ta hada auranmu amma wlh bada son rai ba ranki ya dade in kina yiwa Allah kiyi haquri wlh ban san an fara wannan binciken ba oh wato sbd shi zaka daina kenan kafin yabata amsa sallamar su inna ta karade gidan tare da sababi ganinsa da hansai tayi a bakin kofar hafsy yasata tahowa gadan gadan kofar dakin tare da fadin munafiki uwar me kuma kakeyi a anan alama yakeyi mata da hannu yi shuru yana mata nuni da cikin dakin uwar miye a cikin dakin da kake nunamin mutuwa tayi ko me inaga dai cewar inna da itama ta nufo dakin gadan gadan suka qaraso ya kauce ya basu guri koda dije taga hansai duk rashin tsoronta saida ta ji gabanta ya fadi wata narkekiya ce duk da batasa yawan shekaru amma kam akwai kiba ganin dije da sukayi a hakimce gata 'yar gayu yasasu dan rage sauti tare da kallon hamidan wacece ita kuma wannan din? hukuma ya fada kamar me rada daga garin su baba buhari take nan ya kwashe duk bayanan da dije tayi masa ya fada musu cike da rawar jiki harda rusunawasuka gaida dije suma nasu sharhin ta rattabo musu aikuwa nan duk jiki ya hau tsima suka shiga bata haquri ganin duk sun rude yasa tace su fita zatayi waya duk suka miqe suka fita suna makyarkyata hansai ce karshen fita dan da kyar ta mike bayanta dije tabi da kallo a ranta tace jar ubancan wannan duwawun ai sai inyi matakala dasu in zan hau katanga suna fita ta kalli hafsy tace y kikaga ni jinjina kai tayi dan ta kasa magana tasan dije ta ballo musu ruwa magana tafara yi kamar me waya cikin daga murya ok sir,yes sir su ta dinga fadi kafin daga baya ta ce su shigo ta gama duk sunyi tsiru tsuru a gabanta se raba ido sukeyi naso naqarasa muku banida carji afuwan *vote*, *comments* *with 08066364077* *Alqalamin khady* โœ [16/12, 11:41] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TA ME GARI NA khadija usman 1โƒฃ4โƒฃ tun sassafe ta shirya ta tafi makaranta a can suka hadu da su rufaida aka shiga hirar yaushe gamo tare da tambayarta yadda tabaro mutanen gida bayan ta dawo a parlo ta iske mamy zaune ita da wata hajiya saudat qawarta tana duba wasu kaya da sallama ta shigo parlon ta tsugunna ta gaishesu cikin fara'a hajiya saudat ta amsa amma ita ko mamy ciki ciki ta amsa dan har yanzu tana kule da yarinyar tarasa wane mataki yakamata ya dauka akanta amma kawai bari ta turata gidan su naseer tasan acan su zasuci ubanta ba ruwanta koda abu ya biyo baya sunfi kusa am kinaji na cewar mamy dije da har ta mike ta fuskanci da ita take dan haka tace eh mamy maza idan kin shiga ki shirya ki fito kizo habu ya kaiki gidan yayyenki ku gaisa da su kije kiga amare tunda kin gudu bakije kinga gida ba koh ? ta karasa maganar tana murmushin mugunta tunda dije taga mamy na murmushi tasan akwai abinda ta shirya mata dan haka cikin ranta tace dena gaigaye mamy nima da shirina zan tafi gudun bacin rana amma a fili saita ce to bari inje in shirya yauwa to yi sauri kinji dije dariya ma abin yaso bata a iya shekarin datayi a gidan nan tana iya cewa bata taba samun dariya ko magana irin haka ba a gurin mamy amma yau sai gashi wai ita take yashewa baki dan kawai tasan inma taje ubanta zataci da sauri ta shirya ta fadawa basira inda zata sannan ta debi guzurinta a 'yar qaramar hand bag dinta ta fito saye da doguwar riga arebian gown cofee colour inda ta sanar da mamy ta fito wasu kaya ta bata tace ta kaiwa yusra zata kirata a waya tarasa dalilin daya sa mamy harda wani farin ciki takeyi dan ta turata gidan a ranta tace wlh kome zai faru sai dai raba biyu kowa yaji jiki suna tafiya ita da baba habu driver sun zo dai dai wani store tace dan Allah ya tsaya tana zuwa ba musu ya tsaya ta shiga gutin ba jimawa ta fito tace su tafi yaja mota kuwa suna tafe suna hira har suka qaraso gidan tabbas gida yayi kyau matuka babu makusa inda cikin sanyin jiki ta fito ta nufi bangaren dama dan bata san ya tsarin gidan yake ba tana zuwa bakin parlourn ta shiga kwankwasawa an dan jima kafin taji ance yes come in murda handle din kofar tayi ta shiga parlourn tabbas ya hadu iya haduwa ba qarya inda ta shiga da sallama dauke a bakinta ga mamakinta sai gani tayi yusra na washe baki tare da fadin oyoyo sister ta taso da niyyar rungumeta qamewa tayi a gurin tana kallon ikon Allah murmushi yusrah tayi tare da qarasawa ta rungume dije itama dijen ganin yadda tayin yasata itama yin hakan ta dan jima a haka kafin ta saketa ta kamo hannunta tare da fadin qaraso ki zauna ya gajiyar tafiya ance shekaran jiya kika dawo kinyi gudun hijirar gashi kin dawo kin same mu ya mutan gidan duk lfy suke dai ko? ita dai dije yake kawai takeyi dan tasan wlh wannan faran faran din da dalili hmmm koma meye ai zan gani bari na biki yadda kk so sakin jiki tayi suka shiga hira tamkar ba yusran data sani ba amma dije ta tabbatar da dalilin yin hakan aikuwa suna tsaka da hira taga wayar yusra tayi qara dauka tayi tare da barin falon ta shige bedroom dinta takai wajen minti 30 kafin ta fito ta sake neman guri ta zauna tare da fadin me za'a kawo miki sister ban dai yi girki ba nasan ze biyo da take away so something with drinks duk akwai su ba matsala um um ba abinda zan sha ga sakonki inji mamy ta miqa mata ledar hannunta karba tayi tare da fadin tnx yusrah ce ta kara kallon dije kafin tace naga kinki sakin jikinki ki manta da komai kawai kinji no ba haka bane tashi ma zanyi in tafi naga yamma tayi kije ina? cewar yusrah a dan hade rai gida mana kinga bamuyi da baba habu ya zo ya daukeni ba gara in tashi da wuri dan taxi zan shiga ah ah wlh bazai ma yiyu ba kizo gidan nan baki hadu da yayanki ba ai bazai ma sabu ba nasan ya kusa dawowa kawai ki jirashi ta karasa maganar tana murmushin da ita kadai tasan dalilin yinshi tsaf dije ta karanceta a ranta tace hmm kin girmeni amma baki fini wayo ba tabbas in kuka min abinda ban gamsu dashi ba toh naku salon muguntar da zanyi muku saiya ci uwar wannan a fili kuwa cewa tayi ok to bari in leka bangaren ya habeeb ko ok ba matsala muje in rakaki miqewa tayi ta suka fita part din sajida zaune suka sameta sanye cikin riga da wando three quater sai wata 'yar mitsitsiyar riga wadda da kadan ta rufe cibiyarta kanta yasha qananan kitso jikin nan sai kamshi ke tashi sajida bata da kyau kwarai amma akwai wanka domin irin matan nan ne masu son komai suga sune a farko shiyasa komai nata yake kan gaba ko cikin friends dinta da fara'arta ta tarbesu amma ta rasa dalili tun ranar da ta tambayi habeeb meye alaqar su da dije ya fada mata da ganinta da tayi gurin dinner taji sam bata ra'ayinta ko da ta ganta yanzu gabanta saida ya fadi amma sbd halinta na 'yan duniya kuma goggiyar 'yan boko yasata sakin fuska nan ta karbi dije hannu bibbiyu abinci me rai da motsi takawowa dije inda ta bude ciki taci t koshi dan dama yunwa takeji tunda dawowarta kenan daga skull mami ta tunkudota nan ba laifi amaryar habeeb ta iya girki amma dai gaskiya basu dace ba cewar dije dan wannan ai kusan sa'arsa ce sun dan taba hira kafin suka tashi suka koma part din yusrah inda suna shiga yusra ta shige ciki tace ma dije tana zuwa miqewa tayi itama ta shiga toilet din dake parlour ta dauro alwala tazo tayi sallar la'asar bayan ta idar ne ta koma kan kujera ta kama kallon wani film da ake haskawa a bollywood film din yatafi da hankalinta hakan yasa sam bataji tsayuwar mota a gidan ba illa jin sallamarshi kawai da taji yayi amsawa tayi ga mamakinta shima din cikin sakin fuska ya shiga fadin ah ah mutanen kauye yaushe aka dawo? kallon mamaki tayi masa tare da fadin shekaran jiya to an dawo lfy? lfy qalau suna gaisheku hmmm muna amsawa ok bari na shiga ciki in dan watsa ruwa shiru tayu bata bashi amsa ba a ranta tace kinga dije anya kuwa bazaki tashi ki gudu ba ba mamaki mutanen nan shirya yankaki suka yi dan kin san dai ko giyar wake kika sha bamai yimiki dariya irin wannan amma da ganin yadda suka miki kin san da mugunta a zuciyarsu dan haka tunda qafafunki ki tashi ki fece kafin a karya miki su miqewa tayi ta nufi qofa harta daga labulen ta tsinkayi muryar yusra na fadin ina kuma zaki? am dama zan tafi ne tunda ya dawo cikin hade rai tace mamy bata fada miki cewar sai kinyi kwana biyu zaki koma ba zaro ido tayi tare da fadin kwana biyu fa a nan gidan? eh ko bazaki zauna ba? to amma ai ban taho da kaya ba kuma ma skull dina fa? iyeeeh lallai yarinya wato skull dinki da yaushe kika fara bokon yau she ma ministry tasan da zamanki shine zaki fadamun makaranta to bari ma kiji da ke kin dauka abinda kikamin kisha a banza wlh duk duniya bawanda ya isa ya hana inci ubanki ba duka ba zagi amma zaman prison zakiyi a gidan nan na tsawon kwana biyu cikin awa biyu kika barar min da burin danaci a bikina toh ke cikin kwana biyu sai duk wanda ya ganki ya tausaya miki dan haka kada ki kuskura ki fita a gidan nan dan dama an sanar da me gadi kada yabari ki fita kirjin dije fa ya shiga lugude inda takeji kamar ta arta bata san tanadin da sukai mata ba tasan ma makaman yakin su sunfi nata dan haka ta yunkura da niyyar artawa taji ya riketa haba classic lady ina zaki kuma ai kinzo gida kuma sai jibi ya fada tare da hade rai mutsu mutsun kwacewa takeyi inda ya riqe hannun da karfi riqo bana wasa ba hakan yasata sakin qara don jinda tayi yana barazanar ballata wurgi yayi da ita gefen kujera inda saida kanta ya dan bugu kafin ya dauketa da wani wawan marin dayasa ta ganin star wata qarar ta saki yayi saurin aza hannunshi a saman bakin shi alamar tayi mishi shuru kasa shirun tayi inda nan ya shiga fyadarta yusra na gefe tana dariyar mugunta saida ya gama canzawa dije hallitar fata abinka da fari duk jikin sai yayi ja yayi rudu rudu kafin ya kyaleta ya zauna yana maida numfashi cikin daurewar fuska yace dan uwarki ubanwa yasa kiyi min abinda kikaimin shiru tayi in banda shasshekekar kuka ba abinda takeyi da alama dije akwai zuciya yusar ce ta taso cikin daga murya dan uwarki ba magana akeyi miki ba ta karasa maganar cikin daka tsawa uwarki ce๐Ÿ˜  sukaji ta ce ๐Ÿ™Š cikin zaro ido kusan a tare suka fadi me kikace cikin jan kuka da majina tace cewa nayu uwarki ce kuma wlh tunda kuka taba mana godiyarmu duk sai kunci ubanku kallon kallo aka shiga yi shi naseer yana nazari da tunanin rainin hankalin yarinya itako yusra ta tuna da yadda suka kwashe kwanakin baya amma kuma kai ai da gani wannan ba irin wadan can bace dan haka a hasale tayo kan dije da niyyar dukanta wata irin zabura dije tayi kayo cikin yusra ganin da yusra tayi dije tayo kanta yasata sakin ihu tayi bayan naseer ke ni zaki yiwa iskanci cewar naseer wlh zan babbala ki itako dije ko'a jikknta ta nufosu tana qara barw baki miqa hannu yayi da niyyar riqota aikuwa tayi caraf da hannun a bakinta ta dankara masa cizo kuma gam ta rike hannun qara ya saki wadda tasa yusra saurin barin gurin ta ruga da gudu tayi bayan kujera duk yadda yaso ta saki hannun ki tayi saida taga jini yana bin yatsansa besan sadda yakai mata mangari ba aikuwa zafin da taji ne yasata tashi ta dane bayansa ta shiga yakushinsa tako ina baji ba gani cizo duk ta dabaibayeshi ga azabar da hannunsa keyi ga jini nabin yatsan dan ta dauke mai fatar koma cinyewa tayi oho waya sani duk yadda yaso yaraba dije da jikknsa abu ya faskara gashj tana kuka tana yakushinsa duk ta damalmale masa jiki ta hada masa jini da majina cikkn daga murya ya kira sunan yusra sakamakon wani dankareren cizon da dije ta mallara masa a kunne hakan yasa shi finci kota da iya qarfinsa ta fada kan kujerar da yusra ta labe a bayanta riqe da waya jikinta na makyarkyata tana son yin kira takasa nemo number ma ido biyu sukayi da dije aikuwa ta kwalla wata qara wadda duk gidan ya amsa kanta dije tayi ta cakumeta aikuwa yusra memakon ta tabuka wani abun sai kawai ta bude baki ta shiga kurma ihu nan ko dije ta fara caskala ta itama harda rabon nata cizon a kumatu ganin tana shirin kashe masa mata yayo kanta ai kafin ya qaraso ta saki dije ta qara nufarsa ba shiri shima ya juya dan ko kadan bazai so ta qara dane shi ba yarinya kamar mayya sai shan jini takeyi habeeb na zaune a parlour shida sajida suka tsinkayi ihun yusrah da sauri suka taso suka nufo part din suna zuwa suka shiga kokarin budewa dan lokacin da naseer ya kamo dije da niyyar duka yusrah ce harda rufe kofa dan haka suka shiga bugawa yana fadin nasir nasir lfy bude mana yusra ce ta nufi kofar danta bude dije tasha gabanta tanata kada kai tana bude baki naseer ko nacan yasa tissue yanata qoqarin goge jinin dake bin hannunsa da bayan kunnansa fuskarsa kuwa tuni duk ta hade tayi burdin burdin dan tasha yakushi da dabara yasamu ya qaraso ya bude kofar ya salam meya faru haka naganku a wannan yanayin ? kafin yabada amsa yaji kukan dije daga cikin parlourn leqawa yayi aikuwa ya ganta ta fara jifa da duk abinda ke falon tanayi tana kuka tambayar nasir yayi meke faruwa nan ya sanar masa dalili gurin dije ya nufa inda take kokarin jefo da wani fishers dishuis ya riqeta gam tare da hadata da jikinsa ya rungume ta tsam ya shiga yi mata addu'o'i a kunne dije na jinsa tayi luf tare da qara gyara kwanciyar kanta a kirjinsa dukansu sai suka tsinci kansu cikin yanayi me wuyar fassarawa dije kam sai sauke ajiyar zuciya takeyi tare da qara shakar daddadan kamshi turaren dake jikinshi har take taji wani bacci na shirin kwasheta jin shirun da sukayi ne yasa naseer leqowa dan duk su yusra da sajida gayyar tsorone hakan yasa suka kame a waje yanayin daya gansu ciki duba da yadda yaga habeeb ya wani rufe ido bakinsa saitin kunnen dije gashi kuma ita ta wani lafe a jikinshi duk radadin da ilahirin jikinshi keyi mishi sai yaji ya dena ji yayin da yaji zuciyarsa tayi masa wani irin zafi dan me zai rungumeta haka to me hakan ke nufi jin shirun da matan sukayi ne yasa su dan shirin leqowa dan da alama abun ya lafa tunda sunji shiru aikuwa suna leqowa idon su yasauka akan abinda naseer ya kurewa gani daram dammmmmm gaban sajida yayi dubs da yadda taga mijinta rungume da wata mace bata san lokacin datayi kansu ba tana zuwa tajanye dije daga jikinsa dije najin an jata tayi saurin qara langabewa ta zube a gurin shi kuwa bude idonsa yayi a hankali ai kuwa ya saukesu cikin na sajida data kafeshi da ido ckin tuhuma waigawa yayi ya kalli inda dije ta sheme kafin ya maida dubansa ga naseer yace sai ku maidata gida tunda kun rama yana gama fadar haka ya juya ya fice a dole sajida ta bishi itama............ *vote* *comment* *with 08066364077* *Alqalamin khady*โœ [16/12, 11:41] โ€ช+234 806 493 3819โ€ฌ: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TA ME GARI 1โƒฃ5โƒฃ team dijeee kuna qarawa wutar nan fetur sai dai fa kuma hmmm a dai yi shuru yanzu muci gaba da gashi ga masu tambayar littafin daga farko masu kirana da masu yimin mgn ta pc pls ku taimaka ku dinga tambaya a group dina in baki ciki kiyi min magana zan tura link kiyi join nasan mutan gidana akwai karrama bako da kin tambaya zasu hau tururuwar tura miki dan akwai su da karamci ๐Ÿ‘ ina mugu mugun ji daku member's na khadeeja fans novels๐Ÿ˜˜ ****** ita kam yusra ko ta kan dije dake kwance bata qara biba ta lallaba ta shige daki shima naseer din binta yayi inda ba shiri dole ya dauki emergency care box suka nufi part din habeeb yayi musu dressing kafin suka dawo ind take kwance har yanzu tana nan yadda suka barta itako dije bacci ne ma yadauketa a gurin sai sauke ajiyar zuciya takeyi cikin baccin koda suka shigo suka risketa a hakan naseer ya kalli yusra yace ke jeki tasheta ta tafi gida wani kallo tayi masa kafin tace kai ka tasheta mana ah ah naga dai ai ke yafi cancanta daki tasheta tunda ke kika sa aka kawo miki ita hmm lallai to ai sai kayi duba cikin ni dakai wayafi wani shan jiki kaga kenan wanda yafi wahala shine yafi matsuwa da a barshi ya huta ni zaka danawa tarko inje in tabata tayimin yadda ta yi maka ka ganka kuwa?ta fada tare da sakin dariya kulewa naseer yayi kafin yace ban ganni ba amma na ganki ki duba gefen bakinki da kuma kumatunki ga dankwalelen cycle nan an zana miki na musamman dan haka ki wuce kije ki tasheta ta bar gidan nan ina zaman zamana ke da mamy kunja an rudamin jiki yanzu ta ina zan doshi zuba ruwa duk yarinya tabi ta yage mutane sai kace kura nk ina zargin ma a garin nan akwai damusoshi alamu sun nuna cikinsu ta girma ga kuma 'ya'yan aljanu nidai wannan yarinyar ba qaramar jaraba baba malam ya jefo mana ba kaga ni wlh duk ba wannan ba yanzu dai ka samo min maganin da zansha wlh ji nakeyi fuskata duk ta daure hararar ta yayi kafin yace toh duk azabar da kk ji bata kai ya wadda nake ji ba suna tsaka da maganar dije tayi juyi tare da yin miqa alamar zata tashi da gudu suka kwasa suna rige rigen shiga daki wajen shiga dakin ma yusra ta riga shiga inda tana shiga dai dai naseer ya kawo kai danya kutsa ai kuwa ji kk yi bamm tare da wani sauti qummmm goshinsa ya daki qofar ko zafin daya ji baibi ta kai ba ya danna qofar ya qarasa sa key din kafin ya jingina bayansa da kofar suka shiga maida numfashi kamar wadanda suka yi gudu ko wani aikin wahala jin goshinsa yayi kololo ne yasashi sa hannu ya taba yaji zafi kuwa kallon yusra yayi dake zaune gefen gado tana mayar da numfashi kafin yace kinga maza ki kira mamy ta turo a kwashi yarinyar nan da sauri ko ta dauki wayarsa ta shiga kiran layin mamy tana dagawa yusra tace yauwa mamy pls ki turo a dauki yarinyar nsn pls jin hakan da mamy tayi yasata fadin baku kuka ce a barta tayi kwana biyu ba meye kuma na cewa ta dawo yau ko har kun gama huce fushin naku ne? ai gara kawai ta tafi din inba haka ba...fizge wayar naseer yayi tare da fadin hello mamy au kana kusa ashe ya akayi ne naji kunce a turo a dauketa yau ince ko kaci ubanta dai ko yasan halin mamy inya fada mata abinda ya faru zata iya sasu daukar wani matakin shi kuma a nashi tunanin ya lura duk lokacin da ya yima yarinyar wani abu toh sai yaga shi yafi cutuwa qara maimaita tambayar tayi hakan ya katse mishi tunanin dayake yi ko baka jina? tun yaushe ma ai ba qaramar lallasata nayi ba i hp dai daddy ma baya nan dan ban son ya ganta a wannan yanayin gashi kuma yusra kinsan ta da rigima tace lallai saita koma yau dan wai kada inyi kisan kai ganin yadda na lugwiguita mata jiki ah to indai haka ne gara ta dawo din dan daddy'n ku yana nan kada kuma ya ganta yace meya sameta ta fada mishi gaskiya kasan shi fa akan yarinyar nan kamar wanda aka sihirce dan haka inaga kawai ku barta ta qara kwana kafin nan ta dan murmure sai ta dawo bayan ya tafi ni kuma in barje nawa haushin no mamy ai duk hukuncin daya kamata ayi mata zan gama yi mata kedai barni da ita kawai amma dai ki turo a dauketa din kawai tunda kun matsa dai to ka kawota mana kaga ma saika san abinda zaka fadima daddy'n naku ka fadi wani laifin tayi ka hukuntata nikam yadda nake din nan ina zan iya fita ki ganni ya fada a zuciyarsa ya naji kayi shuru naga ne zaiyi wuya in samu lokaci dan inada meeting karfe 8 din nan na dare gashi zai daukemu lokaci kuma kinga ni inama zan sami time har inkawo ta kawai dai ki turo din inya so kisan me zaki fadawa daddy inya ganta ko kuma kawai ma ki hana haduwar ta so ok to hakan yayi bani yusra mika mata wayar yayi suka qara magana ta kashe wayar ****** shi kuwa habeeb ba qaramin fama yasha ba kafin sajida ta fahimceshi saida yasha aikin rarrashi tare da fada mata kalaman da suka kwantar mata da hankali kafin suka koma normal **** ita ko dije koda ta farka ganin wai hartayi baccin gaske daga na qarya ganin yadda suka kwasa da gudu dazun duk tana kallonsu jin duk jikinta na ciwo ga kuma fatarta data tashi inda naseer ya daketa tunawa da abinda tayi musu kuma yasata sakin dariya tare da fadi a fili ta furta wlh tunda kuka yimin haka sau kun sani wato ni kuka kawo ga jaka kuyita dimata har kwana biyu hhhhhh bakusan dije bane na gwada muku kalata ta fuskar rahma kunki fahimta yanzu aka fara game din let's see who's d winner between us dakin dake pacing dinta ta nufa koda ta shiga hakan ya nuna mata bedroom din yusra ne dan haka kanta tsaye ta nufi toilet din dakin heater ta kunna har ruwan yayi dumi kafin ta fara yin wanka tanayi tana wash tare da matsar kwalla tana kuma ayyana irin fansar da zata dauka akan su niko nace dije banda kuma kisan kai ๐Ÿคฃ ta jima sosai kafin ta gama ta dauro alwala tana fitowa ta bude wardrope ta shiga neman kaya sai kace dakinta tasan duk kayan yusra sun mata yawa duk da ba wai sosai ba dan haka ta shiga neman ko doguwar riga ce cikin sa'a ta samu kasancewar rigar nada madauri saitayi mata dai dai bayan tayi sallah ta fito farlon inda ta hango mutan gidan nata zuro kai ta qofa suna leqe duk tana lura dasu ta share su ta zo parlour ta zauna tare da dora kafa daya kan daya ta shiga tunanin meya kamata tayi musu ne ma ba ta jima ba ta tsinkayi bugub qofar falon tare da sallama kwarai ta dau murya ta baba habu driver ce amsawa tayi tare da fadin ana zuwa su kuwa mutan gidan sunaji aka fara takaddama nasir yace yusra ta fita ita tace shi ya fita kowa yaqi fitowa cikin hasala yace wlh dai kinji kunya wai wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar tasa ki kasa fita dan tsoro mun dai ji kunya ni da kai idan kai ka kirani babba akanta amma akanmu fa nida ita ai kaine kai kuma yakamata ka fita ka sallameta tunda kaine me gidan ni kam bazan je ba dan ko yanzu ban gama jin zafin ciwon jikina ba haka kawai yarinya ta zo ta qaramin wani ciwon kana gani ma dan raini harda samin kaya ni inka fita ma kaja mata kunne ta ciremin kaya wlh ko inzo inci mata uwa bude qofar gayi tare da fadin zo ki je da kanki ki fada mata zuwa da kai ai yafi sako maza zo ya fada yana me nuna mata hanya wlh ba inda zani dan ba sunana saratu ba zan iya zuciya in shake yarinya har saita mutu kaga ko maganin kada ayi kar a fara wuce ka sallameta tabar min gida yaso ya qara magana amma ya qyale yasan halin yusra akwai rai ni gara ya koma mata nasir din kada taga damar sa cikin hade rai ya fito tare da nufo inda dije ke zaune ko kallonta beyi ba ya wuceta ya nufi qofar falon bayan ya bude suka gaisa da baba habu kafin yace bari ya kira dijen ta fito su tafi yana shirin shiga sukayi kacibis da ita ke maza inda abinda zaki dauka dauko ki wuce gida to tace tare da rabashi ta wuce a ranshi yace wannan duk wanda ya aureki ya aurarwa kansa masifa da kudinsa bakin mota ta nufa shi kuma yana ganin haka ya koma ciki tana qarasawa bakin motar ta dubi baba habu tace baba dan Allah inda hali aromin wayarka in kira daddy mika mata yayi yana washe baki bayan ya matso number Alhajin flashing tayi inda daddy na zaune yana cin abinci yaga shigowar kiran habu driver kuma yasan ya tafi dauko khadija hajiya ta fada masa dan haka yssan ba mamaki akwai magana shiyasa ya yi dialling number muryar dije yaji dan haka cikin sauri yace lfy diyata? lfy qalau daddy dama naga baba ne yazo daukata kuma ni gaskiya daman um....dama...kinga fadi kawai kanki tsaye khadija me kk bukata dama cewa zanyi munyi magana ne da Aunty yusra da ita matar yaya habeeb shine suka ce in dawo nan da zama toh shine nace su fada maka wai bazasu iya ba shine nace ni bari na fada maka dadi daddy yaji dan haka cikin sakin fuska yace kaji su to ai wannan ba matsala bane duk dayane ai naji dadi kwarai to nagode daddy gobe abawa baba habu yakawomin unifoam dina zan wuce school in mun taso sai in biyo in dauki kayana toh badamuwa Allah yayi muku albarka ameen daddy ta kashe wayar tare da miqawa baba habu tace ya tafi kawai ita ko ta juya ta koma cikin gidan tana shiga falon ta tarar da su zaune jin bude kofar suka jiyo suna ganin dije kusan a tare suka furta lfy?me kika dawo yi kuma bata tamka musu ba saita fara kokarin zama saida ta zauna kafin tace naji kunce kuna son nayi muku kwana biyu ne shine nace bari in zauna din yafi kada in tafi kuga rashin kyautawata ko mamy tayi fada mun shiga uku๐Ÿ™†โ€โ™€ ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ *vote* *comments* *with 08066364077* *Alqalamin khadyโœ* ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* 1โƒฃ6โƒฃ *ina neman afuwan mutane pls dan Allah ku dinga min adalci nasan masoya basa yawa kuma daukaka daga Allah take ina iyakar kokarina wajen ganin na faranta ran kowacce a cikin masoya na idan kun tambayeni littafin daga farko ko wani page din ban tura muku ba kuyi min uzuri kun san jiki da jini kuma inada abin yi amma nake sadaukar da lokacina dan nishadin ku duk wadda take son littafin tayi magana group nasan zata samu pls afuwan dan Allah na kuma gode da soyayyarku gareni Allah ya bar kauna ya qara zumunci* *** kut......in kin isa Allah ya tsinen ai wlh bazan zauna da 'yar jagaliya a gidana ba cewar yusra ta fada tana huci shima nasir cikin hade rai yace ke ina wasa dake ne ?wlh tun muna mu kadai ki tashi ki tafi gida waye zai yadda ibola ta zauna masa a gida har kwana biyu ko ki tashi wlh ko in babbala ki a kwasheki a kaiki gani sukayi ta miqe yusra da dama tun tuni ta miqe tsaye ta riqe kugu ganin dije tayo kanta yasata kwasa da gudu tayi bayan naseer wanda shima ganin dijen ta miqe ya danji wani abu a zuciyarsa amma fa gara ya nuna mata shima namiji ne dan haka saiya dake ya tsaya yana fadin ke yusra meye haka ban son iskanci saida ta qaraso gabansa kafin ta kalleshi ido cikin ido shiko kawar da kai yayi domin shi in yana kallon idonta sai yaga kamar idon mage bare yanzu daya qara tabbatarwa kansa yarinyar nan ruwa biyu ce wato mutum aljan๐Ÿ˜‚dan haka be son hada ido da ita kada yaje ko maguzawan ne akanta arnan farko su nuna masa basu san hasken addini ba tsinkayar muryarta yayi tana fadin haba yayana yanzu kawai dan nace zan kwana biyu gidan ka kk korata bayan kuma tun farko ku kuka nemi da in zo inyi kwana biyu a wajenku ai ko ba komai nayi muku haka dan zumunci amma tunda bakwaso shikenan jin kalaman datayi yasashi sauke a jiyar zuciya domin yasan yanzu zata ce zata tafi amma me ? sai ji yayi tace tunda na fuskanci baka son in zauna gidanku hakan na nufin tun yanzu zumuncinmu zai samu rauni kuma nasan megari bazaiji dadi ba bare iyayenmu dan haka na yanke shawarar zamana a gidan nan har sai ranar da nayi aure ๐Ÿ˜ณ me? la'ilahaillah anta subahanaka inni kuntu minazalimin a'uzubillahi minasshaidanir rajim ka manta baka hada da ayatul kursiyyu ba cewar yusra dake bayan naseer wanda keta kwarara addu'o'i kawai dan dije tace zata zauna a gidansu itako dije dariya ma abin yabata cikin zuciyarta tace ikon Allah sai kallo ganin yaki yin shuru banda ruwan dala'ilai ba abinda yakeyi hakan yasa dije fadin haba ya naseer meye naga kanata addu'a ko wani abun ne yafaru ? kinga khadija dan girman Allah da ma'aikinsa na rokeki ki taimaka ki koma gida kinji to wai sbd me? ta tamvaya yasan sha'anin jinni be zama lallai yarinyar tasan meta aikata musu ba kuma baya son tasani dindan haka saiya waske yace kawai kinga mamy nada hawan jini ga shi ma yau mura take fama da ita matsananciya ina ma zargin limoniya gareta kinga gara kije ki zauna kusa da ita nasan zaki taimaka mata da wasu abubuwan hakane kam yakamata in koma yauwa qanwata ya fada a dan raunane yusrah ma harda gyada kai tare da fadin wlh kam gara kije dan tayi kewarki toh shikenan ta fada tare da fadin ni zan wuce toh saida safe Allah ya tsare ya kiyaye a sauka lfy qofar falon ta nufa har ta isa sai kuma ta tsaya ta juyo yake sukayi mata tare da wiving din hannu ita wlh dariya ma suka bata dan haka saida ta dara tare da fadin lah ya naseer meya sameku ne a fuska kaida aunty yusra naga duk kunji ciwo saurin kallon juna sukayi kafin daga baya suka hada baki wajen fadin Accident subahanallah accident kuma?da kura ko kuma da kare dan wannan ai naga ciwon kamar bada mota ko wani qarfe akayi shi ba ko da biri mukayi fada naseer ya fada yana yashe baki .biri kuma a ina? ai da yake akwai shi a nan gidan toh shine ina masa wasa ya yakusheni yusra ma haka .wow gaskiya wlh har kunsa nafasa tafiya sbd wlh ina son biri dama .wayyyoooo ๐Ÿคฃ dan girman Allah ki tafi kawai gobe zan kawo miki shi ah ah nidai ina son ganinshi wlh ai nasa an kasheshi what ? kisa fa? akan me? .sabd yaji mana ciwo har haka saina lura gaba gaba zai iya daukar rai ma amma ko wannan biri sai kace ba dan nigeria ba ah ah dan boko haram ne au dama dabbobi ma suna zama 'yan ta'adda ai.....kaga dan Allah ka barta ta tafi dare yanayi kuma gashi taxi zata shiga Allah ya kaiki lfy sister cewar yusrah dake tahowa danta dan tura dije au ni kinga ma fa na manta wlh aunty ashe fa baba habu ya tafi ko yanzu ya zanyi to ni dije ta fada tare da rike haba .akwai abinyi kawai kinga bari nadauko miki kudi kishiga taxi tunda baki da su ko ah ah barsu kawai inaga inada su a jakata zasu isheni zuwa gida to a gaida su daddy zasu ji tace tana qoqarin fita tana ficewa kuwa yusra ta rufe qofar tare da sauke ajiyar zuciya haka shima naseer din bakin gate ta nufa gurin me gadin gidan inda ta samu guri tazauna suka shiga hira kamar sun san juna tun da can gumi fa ta hadu da anka nan kayan zance ya hadu sukaita zubawa kuwa kafin daga baya taji qarar mota a waje koda suka leqa baba habu ta gani da kayanta a akwati kin kim kim musa me gadi ne ya karbi kayan tace ya tafi kawai nan ya juya ya musu saida safe ganin dare nayi ne yasata miqewa tare da fadin toh baba musa zan shiga ciki saida safe ko toh hajiya mu kwana lfy Allah yasa ta fada tare da jan trolly dinta harta nufi part din su yusrah kuma saita fasa ta tsaya ta danyi jimm kafin ta juya akalarta zuwa part din su habeeb tana zuwa ta shiga knoking a hankali a daidai wannan lokacin suna zaune suna hira tare da dan taba kallo jin ana buga kofar yasa shi fadin waye a hankali shiru tayi sai da ya qara maimaitawa kafin tace nice jin muryar mace yasa sajida saurin miqewa ta nufi kofar tana fadin kece wa? khadija!! bude qofar tayi sukayi ido hudu da dije inda gaban sajida ya yanke yafadi ganinta da tayi da jaka dirkekiya lfy ? ta tambayeta cikin dan hade rai kallonta dije tayi ganin yadda tayi mata tambayar yasata itama hade nata ran kafin tace lfy lau mana ta karasa maganar tana me kutsa kai palon sai yanzu ya dago ya dubesu shima ganin dije da jaka yasashi mamaki tare da fadin ke lfy naganki da jaka haka kamar me shirin barin gari guri ta samu ta zauna tare da fadin lfy lau wlh nadauka daddy ya kiraka yayi maka bayani ai shine yace in zauna inyi kwana biyu anan nama shirya zan tafi sai gashi yasa an aikomin da kaya na toh da zanje part din ya naseer sai naga kaine babba kada kaga ban kyauta ba gara in zauna anan ko hmmm haka tunda yace haka be qara fadin komai ba illa juyawa da yayi ya kalli sajida dake tsaye kikam ta zuba musu ido maida kallonsa yayi ga tv din itama sajida ganin haka yasata samun guri tazauna dan nesa dashi sun jima a haka banda karar tv babu abinda kk ji a falon itako dije duk jikinta ciwo yake mata gashi tana jin yunwa ga bacci data fara ji gyaran murya tayi kafin tace am yaya nace ba kallonta ya juyi yayi jin yadda take son yin magana dashi lallai ma yarinyar nan yafada a ranshi itako ko'a jikinta tace wai azumi kukeyi ne a gidan nan? cikin rashin fahimtar magsnarta yace kamar ya ban gane ba kina nufin na nafila ko me? ah ah na dare nake nufi naga ne ko ruwa ba'a bani ba ga yunwa da nakeji kamar hanjina zai tsinke toh naga kada inyi nauyin baki tunda ni bana azumin gara a in magantu kada in cuci kaina binta yayi da kallo wanda tarasa na meye shi kanshi ya kasa tantancewa ko kala be ceba taga ya miqe tare da daukar wayarsa ya nufi dakinsa ganin hakan datayi yasata fadin to ko masauki a tausaya a bani ai ko tunda abincin bazai samu ba nazo gidan economic masu auna ci da ciyar da wani rasa me zai ce yayi kaji yarinya sai kace irin kurege shi sam be son yawan magana bare wasa dan haka cikin dan hade rai yace ki tambayi matar gidan mana ai itace da gidan yana gama fadar hakan ya shige daki sajida data tsaya kallon ikon Allah tare da nazari inda daga karshe taji dadin yadda habeeb din yai sannan tasaki ranta tare da fadin oh khadija baki abin magana ga gajen haquri tashi muje in nuna miki inda zaki sauka ok ta fada tare da mikewa dakinta dayan takaita inda tace ta zauna a kawo mata abinci ah ah ni ai a gidan nan nafi qarfin a kawomin kice dai in tashi in dibarwa kaina kawai in hidimtawa kaina kada kizo inga laifinki kin san hausawa sunce mu dangin miji ba'a iya mana kallonta sajida tayi tare da nazarin yarinyar wannan yarinyar fitinanniya ce ta qarshe amma zanyi maganinki ta fada a ranta........ naso inyi muku yafiv haka amma kaina ciwo yakeyi bacci๐Ÿ˜š *vote* *comments*[3/14, 9:18 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TA ME GARI 1โƒฃ7โƒฃ nayi adungure na wulwula na heqo na mazgo gaisuwa ta tare da jinjina ga dukkan masoya ta me gari tare da jinjinar ban girma ga members na khadija. fans novels 1 da khadija fans novels 2 ina ganin comments dinku gaskiya kuna yin dije da yawa ๐Ÿ˜˜ miqewa tayi ta tabi bayan sajida wadda ke ganin ikon Allah ganin da gaske take bin nata zatayi yasata juyowa tare da fadin haba qanwarmu ai kya tsaya inyi dawainiya dake ko iya na yau ne ko a matsayinki na bakuwa kamar yadda kk fada dakatawa dije tayi tare da fadin ah ah matar yaya bawai fa wani dalili yasa nace ki bari in nemawa kaina d'a'amin ba kawai sai dan kin san iyawa mutum sai Allah kuma gashi naga bakisan da zuwana ba kada in saki wahala kije kawai ki kula da mijinki dan naga alamar ke yake jira bakin ciki ya cika masa zuciya kije ki rarrasheshi kallonta sajida tayi tare da fadin wane irin bakin ciki kuma ? ah bakin cikin zuwana mana shin wai be baki labarin abinda ke tsakaninmu ba? dammmm gaban sajida ya fadi cikin karfin hali tace meye tsakanin kun ? ah lallai da sauran ku tunda har yanzu be fada miki ainihin sahihin abinda ya hadani dashi ba zuciyar sajida fa tafara cunkushewa jin yarinyar na ambatar wai alaqa tsakaninta da habeeb shin me hakan ke nufi?wace alaqa ce kuma?to ko dai ya so yarinyar ne ?kai no habeeb dake son babbar mace wadda ta iya tattali irinta me zaiyi da wannan berar wadda inba kayan fitina da jaraba ba ba abinda ta ginu akai dan haka cikin dan hade rai tace ai ke yakamata ki sanar min alaqar ba shi ba kallonta dije tayi ta nazarci matar tun dazu ta karance ta akwai kishi dan haka saita kiyasta a ranta kawai inta yi mata wani rashin kyautarwa wlh ta hakan zata azabtar da ita itako sajida haushin yarinyar ta tsinci kanta da ji dan sai yanzu ma taga meye dalilinta na tsayawa ta biye mata yarinyar da bata wuce sa'ar kausar ba autar su dan haka saita sa kai da niyyar ficewa daga dakin muryar dije taji na fadin .yauwa Aunty jeki bashi haquri ni bawani dadewa zanyi ba zan koma gida amma dan Allah a dan taimaka a qara yawan abincin gidan kar ayi la'akari da girman mutum shi ci ba'a nan yake ba kada ki ganni siririya wlh rainon kauye ce dan haka a taimaka kada a tauye ma cikina hakkinsa kuma kada ki manta kice masa ya baki labarin zuwansu qauye last ko ta kanta sajida bata bi ba tasa kai ta fice itama ta fito sajida na kokarin shiga dakinta ta tsinkayi muryar dije na fadin aunty inane madafa? kamar ya ? ashe fa matar yaya 'yar gayu ce na manta wlh i mean kitchen? nuni sajida tayi mata da hannu inda tai shigewarta daki tana shiga dije ta kwashe da dariya tare da qarasawa kitchen din ruwan tea kawai ta hada tasha dan duk jikinta ciwo yakeyi har yanzu musamman gurin da nasir ya riqeta a nan ta shanye shayin ta gama ta koma masaukinta tare da bude jakarta ba kayan bacci ciki dan haka ta kwanta abinta a haka da kayan yusra๐Ÿคฃ tana shiga dakin ta sameshi gaban mirrow yana fesa body spray a dan hade rai ta qarasa ta karba ta shiga fesa masa duk yana lura da yanayinta kasancewar ta mace me iya tattali da soyayya sajida ta waye kwarai ta san hanyoyin mallakar miji cikin sauki ba boka ba mallam tasan kissa kala kala hakan yasa ta mamaye zuciyar habeeb domin shi dama dan son rayuwa ne kuma saiya samu me tarairayarsa duk yadda yake da jin kai da miskilanci to fa a gaban sajida tamkar yaron goye yake kuma yana iyajin zai iya mata komai a rayuwa dan haka koda yaga yanayinta yasan akwai damuwa damuwar kuma bazata wuce akan zuwan dije ba dan yasan sajida akwai kishi dan haka saida yabari sun gama shirin kwanciya kafin ya jawota jikinsa cikin salon tasa soyayyar ya shiga fadin what's wrong with my princess ? uhmm ? shuru tayi kafin zuwa can yaji tace mece sahihiyar alaqarka da khadija? cike da mamakin tambayar datayi mishi yace kamar ya ban fahimta ba inaga ai kinfi kowa sanin matsayinta a gurinmu ko? hmmm amma ai tace in tambayeka ainihin sahihiyar alaqar dake tsakaninku wai a kauye shine nake son jin ko akwai wata a qasa ne murmushi yayi a zuciyarsa tare da fadin lallai yarinyar nan bala'i ce ko ince annoba ifritu wato tayi nazarin hallayar sajida harta zurma ta ita kuma duk da girmanta da shekarunta ta kasa fahimta wannan akwai shegiyar yarinya wato so takeyi ya bata labarin abinda tayi musu a qauye abinda ya barshi a sirri baya fatan matarsa tasan abin kunyar daya faru shine take son fallaso shi ai wlh gobe korata zaiyi gidan nasir suje can su karata tunda su sun saba wristilling da ita jin yayi shuru ne yasata fadin kayi shuru baka bani amsa ba oh baby matsala wlh wlh kinji na rantse miki wlh babu wata alaqa tsakanin mu in ba matsayinta na qanwa garemu ba ke ni wlh banma santa ba sai zuwan da mukayi time din da muka dawo nigeria daga nan tsohon nan ya hadomu da ita shine silar zamanta a gidanmu so banda wannan alaqar banga wata ba amma ban san dalilinki na tambayata ba hmm ai dole in tamvaya ganin yadda kayi mata dazu a gidan naseer kuma gashi yanzu ta dawo nan amm.......shiiiiiii ya fada tare da dora yatsan shi a saman lips dinta haba baby ya kk son maidani baya ne me kk tunani namijin dake da mace kamarki shine zai iya hango wata to kisani wlh inda ana ciro zuciya to dana ciro mikitawa kinga yadda nake sonki nake ji dake ke wlh ni ko wacce mace kallon 'yan daudu nake musu kuma ma in zaki hadani da wata ina laifin ma ki hadani da ta kwarai saiki hadani da hambirin hayam wlh kin cuce ni kin san yadda na tsani yarinyar ma kuwa wlh sbd daddy yasa nake raga mata kuma bana son raini shiyasa kika ga ban. fiya shiga shirgin kowa ba sai naki ke kadai keda habeeb kisawa ranki ko'a lahira bazan miki kishiya ba bare gidan duniya da sai naga wadda taimin zan aura dai ko ? to duk ba wadda tayimin sai fadimatuz zahra'u sajida,batula,Aliya,kamila,sharifa,zakiyya.....zai ci gaba ta katse shi ta hanyar mannewa da jikinshi tare da aika masa da rikitattun sakonnin da suka sa ya kasa qarasa wa ya shiga maida martani ita ko ta dage wajen ganin ta biyashi tukwicin kalamansa masu tsadar gaske a wajenta nan suka lula duniyar masoya Asuba ta gari ******* ana kiran sallar asuba a kunnen dije koda ta farka tayi sallah ta yi addu'ointa kamar yadda ta saba kafin daga baya ta miqe ta afka kitchen break fast me rai da motsi ta hada sannan ta jera saman dinning kafin ta koma daki wanka tayi tare da shiryawa cikin unifoam dinta sannan ta fito saman dinning ta nufa ta fara karyawa amma bataji alamar mutan gidan sun shirya fitowa ba gashi har kusan 7:15 sai da ta gama karyawa tsaf kafin ta miqe ta nufi dakin dataga sun shiga jiya kwankwasawa ta shiga yi ya akayi ne waye ? taji muryar sajida na fadi au to bakuwar gidan ce naga shuru ne me gidan be fito masallaci ba shine nace bara in sanar muku ana shirin tada sallah ya gaggauta koya samu jam'i don kin san sallah in rana ta fito ba kyau gara a yita da duhun asuba bude qofar sajida tayi tare da kallon dije jin abinda ta fada mata wato dai so takeyi tace basa tashin asuba kenan shine ta fada a fakai ce ganin ta cikin shirin makaranta yasata fadin to tasalla munji mun tashi ai a bari mu gama kimtsawa sai mu fito ko? ah ah in dan ta dije anty ku koma bacci nidai kiramin me gidan a sallameni in tafi naga zan makara gyaran murya yayi daga bayan sajida shirye yake tsaf cikin kayan suit ash colour sunyi masa kyau matuqa cikin hade rai yace lfy nake jin hayaniya lfy qalau yaya dama zuwa nsyi ince na shirya zan tafi school toh a dawo lfy to wa zai kaini? au dama baki taho da me kaiki din ba yayi maganar yana me fitowa a dakin sajida ta biyo shi suka nufi waje inda suka bar dije tsaye da sakin baki ganin da gaske fita zasuyi gashi dai bataga ya karya ba oh yanzu nagane ta fada a zuciyarta wato sbd ni aka ki yin abin kari a gidan nan hhhhh tayi dariya kadan ashe kuwa akwai kura dan wlh ko da bala'i sai naci na qoshi tana ta sambatun ta har suka fice bata sani ba saida taji alamar rufe kofar kafin ta juya a hankali tabi bayansu .direct gurin motar sa ya nufa yana zuwa ya bude mazauninsa ya shiga inda yabar murfin bude sajida ta tsaya riqe da murfin suna maganar su ta masoya tana fitowa ko ta kansu bata bi ba ta nufi part din nasir ta shiga kwankwasawa nasir da suke tsaye suma suna bankwaba da juna yaji ana buga kofa yayi saurin sakin yusra ya nufi kofar yana fadin sai mun dawo dan yana kyautata zaton habeeb ne dan ya fada masa in zai wuce asibiti zai wuce dashi dan yanason yaga likitan fata dan yadda kura ta yayyageshi๐Ÿคฃa cewarsa yana bude kofa sukayi ido biyu da dije .besan lokacin daya furta la'ilahailla anta subahanaka inni kuntu minazzalimin lfy me ya kawoki da sassafen nan ? ganin yadda yayi yasa dije kusan sakin fitsari dan dariyar data guntse yusra da tana dab da shiga daki taji yayi wannan addu'a yasata dawowa dan taga meya gani aikuwa itama na ganin dije tace ya salam meye kuma kika manta ai da kin fadawa mamy ta kira waya ai sai a aika miki shi ai badaga gida nake ba anan na kwana cikin hada baki sua ce a ina din? a gidan y habeeb sauke ajiyar zuciya sukayi kusan a tare kafin nasir yace Alhmdllh qanwarmu sarkin hankali ai gara da kk kwana a can ni yanzu ma kinga abuja zamu tafi ni da yusra dan haka basai kin zo mana sallama ba in zaki tafi ki gaisheda su mamy tsarabar ki insha Allah daban take in mun dawo yana fadar haka ya juya ya koma suka kullo kofa harda sa key dariya dije tasa kafin ta gaji ta mike ta nufo inda su habeeb suke wadanda duk abinda ke faruwa suna kallo sai dai basu san me suke fada ba sun dai ga komawar nasir da dariyar da dije tayi tana qarasowa bata ce qala ba ta bude murfin baya ta shige ta qame ta kalli window cike da mamaki a fuskar kowannensu sajida ta bude baki zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar daga hannu kafin cikin hade rai ya juya yace ke dan ubanki bakida hankali ne meye na shiga motar mutane uban waye drivern ki? cikin marairaice fuska tace kayi haquri yaya wlh dama tsayuwar da mukayi da yaya nasir ne yace in fada maka wai daddy yace ka ajiyeni a school daga can zan wuce gida ma nafasa zaman jin ta ambaci tafiya yasa sajida saurin fadin ai kawai ba komai sweety ka ajiyeta din inaga shi nasir din yafasa fitar tunda kaga ya koma watakil dan yaga za'a fita da jerry dinsa ce jin sarauniya tayi magana yasashi fadin ok kawai sallama sukayi inda ya fita daga gidan be ko bi takan naseer ba kasancewar yasan school din tasu direct can ya nufa da ita yana tsayawa ta bude ta fita tare da fadin saina dawo yaya .ki dawo ina? gidan ka mana ai ni naga wuri ......... *Alqalamin khady*โœ [3/14, 9:34 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* NA khadeeja usman 1โƒฃ8โƒฃ *ina matuqar godiya da addu'arku gareni Alhmdllh nasami sauki tare da kuzari da karsashin ci gaba da suburbudo da sambado tare da sheko muku ta me gari uwar mazga hakika kuna dadamin qwarin gwiwa ta yadda nake jin zan iya yini zungur ina muku typing amma sbd halin yanayi zan bawa kaina haquri inyi muku na 'dan lokaci zakufi jin dadin sa๐Ÿ˜‚* tana gama fadar haka ta juya ta shige makaranta ta barshi da sakin baki inda ya shiga fadi a fili wlh bazan yadda ki zauna min a gida ba bari kawai in kira daddy ince masa ki koma can kuma sai yace kai nasan halin yarinyar nan yanzu haka bazata koma bs kawai fadamin tayi dan inyi haushi sbd ta mayar dani kare hmm zanyi maganinta haka yayita tuki yana sambatu da masifar ba gaira ba dalili har ya isa asibitinsu yana zuwa ba jimawa ya fara aiki itako dije tana shiga cikin makaranta direct office din principal ta wuce ta sanar dashi daga yanzu a dinga biyawa daukarta da motar makaranta ta fada musu inda ta koma dayake dama a cikin bill din makarantar harda kudin transport suke hadawa sai dai in ka so kasa a kawo danka amma su ba ruwansu shi yasa koda dije ta fada ba'a samu matsala ba tana fitowa ta nufi class nan suka hade dasu rufaida aka shiga hira kafin malami ya shigo suka fara lesson **** Amarya kenan kin ganki kuwa yadda kika canza kinyi wani kyau dake kamar wata black american dariya sajida tayi kafin tace ke laila wlh banda sharri wlh ba maganar sharri fadamin meye sirrin ne me habeeb ke baki kulawa da soyayya ta fada tare da yin fari da ido shegiya qawata kodai to har an sama mana baby ne baby fa kika ce tun yanzu ?ai sai mun shekara kafin inyi ciki ke yadda habeeb yake dan son rayuwa yanzu in nayi ciki ai sai a hankali shima kanshi yafi son mu huta ai tafawa sukayi tare da fadin kusha sha'aninku bird loves naso inga habeeb ranar aurenku inga bakin nan sai gashi ina malesia na tsinkayi lbrn bikin gashi ba halin in dawo sbd wani uzuri .hakane kam Allah be nufa dake za'ayi ba yanzu gashi kinzo har gida ai bari in tashi in sama miki abinci ko me kike so ta tambayeta tana qoqarin miqewa komai ma kin san ni banida zabi ok ta fada tare da kokarin miqewa ta shiga kitchen da sallamarta ta shiga falon inda ta iske laila hakimce da remote tana canza tasha batare data juyo ba ta amsa sallamar har saida ta ji dije nayi mata ina yini kafin ta maido da dubanta gun wani kallo tabi dije dashi ta amsa gaisuwar a yatsine ko ba'a fada mata ba tasan wannan qanwar habeeb ce domin kuwa tana kallonta ta hango kamar su sai dai kawai ta fi shi haske dan ita fara ce sosai hmm tab di lallai akwai aiki wato har an fara kawo 'yan leken asiri lallai sajida batada hankali ita ina zata yadda da a kawo mata wata dangin miji ai ko kawowa za'ayi gara a ce ta dauko a danginta balle wannan yarinyar da gani idonta feke yake tund dije ta lura da kallon da matar ke binta dashi taga kuma ta lula duniyar tunani kawai saita qarawa wutar ta mai tayi shigewarta dakin data kwana jiya laila na tsaka da tunani sajida ta fito hannunta dauke da jallop din makaroni daya sha kayan vegetables da busashshen kifi sai kamshi yakeyi qarasowa tayi kusa da ita taja mata dan qaramin center table din dake gefen kujera ta ajiye mata abincin tare da komawa ta qaro mata ruwa da lemo ta na ajiyewa ta zauna ita kuma laila ta sauke gwouron numfashi tare da fara cin abincin saida ta gama tsab kafin ta kalli sajida tace qawata wani abu nagani a gidanki daya dagamin hankali .cikin razana sajida tace me kk gani ? wata yarinya nagani yanzu ta dawo da alama kanwar mijinki ce naga daga makaranta ta dawo sajida ina tunaninki ina iliminki da wayewarki suka tafi tun yaushe aka daina yayin 'yar zaman daki wannan budurwar yarinyar ai kawota kawai akayi ta hanaku sakewa inba haka ba su dai ba ci suka rasa ba ba sha ba bare ace sun takura ne suka kawota nan dan haka wlh kisan abinyi ke banda ma uwarsu daya ubansu daya ai da sai ince ko kawota ma akayi ta gama gane miki sirri karshe ta aure miki miji rasssss gaban sajida ya fadi tare da nazarin maganar laila ganin yadda duk yanayinta ya fara canzawa yasa laila qara dogon sharhi aikuwa nan sajida ta fada mata tsakanin habeeb da dije da dangantakarsu ai kuwa nan laila ta dinga kwarara wa sajida ruwan zuga tare da fadi mata illar zama da dangin miji dan mijinki na babba sai a kawota nan a kaita gidan naseer mana nan sajida ta fada mata yadda suka kwashe dasu naseer tab iskancin banza ajanun banza aljanun wofi mu za'a gwadawa aljani ni danayi gadonsu dari ba daya ne akan kakata data mutu suka dawo kaina dan dama tun tanada rai munfi da ita shiyasa koda ta mutu suka ce ni suke so wlh duk qaryar rashin mutunci takeyi yarinya qarama da kicifi tun yanzu ganin yadda laila ta dage tanata zazzaga masifa ne yasa sajida fara lallaminta domin da alama akwai aljanun fa a nan dan yadda ta fara daga murya itako dije tunda ta shiga daki tayi wanka ta canza kaya ta nufo falon domin nemawa kanta da'amin inji ta saita tsinkayi maganar da laila keyi saida ta gama ji tsab har takai lokacin da sajida ke rarrashinta babu wanda ya lura da fitowarta direct kitchen ta nufa tana shiga ta shiga gyara duk wani abu da sajida ta bata tare da dora nata girkin kasancewar kitchen din rufe yake hakan yasa basuji kamshin girkin ba bare kuma girkin na mugaye ne dama dirka dirkan kulolin data gani ta dauka ta juye a ciki shinkafa ce fara sai miya datayi leqowa tayi falon inda ta gansu laila har yanzu tanata ma sajida famfo qara lababawa tayi ta dauko abincin cikin sanda ta ajiye saman dinning din kafin ta koma kitchen din ta gyara sji fes kamar ba'ayi amfani dashi ba kafin ta kuma lababawowa ta shige dakinta tare da mayar da unifaom dinta sannan ta fito da rarrafe ta zagaya bayan kujera ta labe jin kamar qofa tayi motsi yasa su saurin waigawa sajida da zuciyarta ke kusa dan sai ysnzu ma ta tuna da yarinyar cewa tayi gida zata tafi to uban me ya dawo da ita bari ta tashi taci uwarta kawai inya so ta kadata ta koma gidan su nasir suje can su qaraci gayyar rashin hankalinsu can inma kashe su aljanun zasuyi su kashe su sai me nan ta miqe laila ta dafa mata baya suka nufi dakin suna zuwa suka tura qofar ga. mamakinsu bakowa toilet sajida ta nufa ta shiga fadin ke khadija !! khadija!! jin shuru yasata tura qofar ta leqa bakowa cike da mamaki ta juyo ta dubi laila tace kika cemun ta dawo kuma? ban gane nace miki ta dawo ba to karya zanyi miki ko me? ta fada cikin hade rai to kuma gashi bata nan duk da nasan munyi magana da habeen da safe cewa gida zata wuce toh nidai naga yarinya ta shigo kuma da unifaom fara ce siririya ko tabbas itace amma ai muna falon ko dai kafin in fito ta fice baki lura ba wlh ba wani fita datayi dan tana shigowa kina fitowa sai dai in wani salon munafircin ne na qannen miji kinga irin abinda nake fada miki ba nan fa suka shiga neman dije gani duk sun leqa basu ganta ba yasa sajida fara zargin kodai aljanun laila ne suka fada mata qarya gashi ba damar tace ah ah tasan halin laila yanzu sai su hau sama ganin basu ganta ba duka cike da mamaki suka fito suna tunanin ina ta shiga itako dije tun shigarsu dakin ta miqe ta koma kitchen nan ta hau safa da marwa na shirya kaya a saman dinning duk wani ruwa da kalar lemo saida ta hada a gurin saisa ya cika tab da kayan ciye ciye kafin tayi saurin fita zuwa qofar falon ta cake tana jiransu fito tana daga tsaye taji alamar sun dawo falon dan haka ta turo kofar ta shigo da sallamarta tare da nuna alamun gajiya a tare da ita kallonta suka shiga yi musamman laila da taga yadda ta shigo din itako sajida ta shiga karyata maganar laila dan duk wanda yaga dije a wannan lokacin yasan dawowarta kenan basu gama tunanin na sukaji dije ta buga tsalle tare da fadin yehhhh dan dunga yaushe kuka karaso bayan saida nace ku bari mu taho tare ashe kun sato hanya kun taho lah ashe akuyatu ta fanshe ni dan tayi muku girki dukansu juyawa sukayi suka kalli inda take magana ganin gima giman kuloli ga dinning din cike da kaya yasa sajida sakin qara tare da nufar bayan kujera dan ta buya itama laila ta mara mata baya habeeb ne ya shigo dauke da sallama a bakinsa inda yana shigowa yaga dije tsaye na fadin aunty laila taso ga dan kutungayya wannan aljanin dake saki yawan munafurci yana son ku gaisa da kyar ya mayar da kofar ya rufe inda ya saki baki yana kallon sajida data leqo kai jiki na karkarwa ganin hakan da yayi yasa shi fahimtar yarinyar nan ce yanzu hska tayi musu wani abun dan yasan iskancinta ai kuwa yau saita ci ubanta daga yau bazata qara ba nufarta yayi gadan gadan da niyyar cafkarta ya nadeta kawai sai gani yayi tayi gurin dinning tana fadin kada ki damu darwanatu ai kowa zai ci abincin nan waya isa kiyi girki aki ci duk ds nasan duk kayan 'yan gidan ne ah ah kada ku damu basai kun kawo naku ba ku barmu da namu kalar kutttt habeeb ya hadiyi wani yawu dan sai yanzu yakai dubansa ga saman dinning dinsu wanda yaga dirka dirkan kuloli ga kuma kayan ciye ciye nan tab akai dubansa yakai ga sajida wadda ya zuwa yanzu banda rawa ba abinda jikinta keyi cikin rada ya shiga tambayarta abinda ya faru hankali ta fada mishi duk abinda tasani da yadda laila ta fada mata dawowar dije da kuma yadda ta duba basu ganta ba jin murysr dije sukayi na fadin ah ah ai basai kun dauko su ba dukansu yanzu zasu taho muci gaba daya ai kada ku damu dukansu na jin haka suka juya da niyyar kwasa da gudu amma me? kafin su kai ga fita suna rige rige da gwara kawuna dije tayi caraf ta riqe habeeb wani ihu ya saki dan in baku manta ba na fada muku habeeb akwai tsoro dariya dije takeyi iya yinta ta kuma riqe habeeb wanda ya kama ihu iya yinsa tare da karanta ayatul kursiyyu a fili naseer da yusra ne suka fito daga part dinsu jin ihun naseer ganin laila da sajida sun rukunkume juna suna rawar dari a bakin falon yasasu qarasawa tare da tambayarsu lfy duk sun kasa magana inda naseer yayi ta maza shida musa me gadi da shima ya karasso yanzu jin ihun me gidan suna shiga suka ga dije zaune dirshan a gaban habeeb ta riqe masa maka kam tana dariya harda kwalla shiko ya bude baki yana ihu da addu'a naseer yasan kwanan zancen dan haka ya kasa qarasawa sai musa ne ya qarasa koda ya isa nan ya tsugunna ya fara bawa dije haquri domin yasan wannan aikin na jinni ne kallon sa tayi tace nice dai dijen da ka sani ga dai aljanun can akan dinning suna walima kallon gurin duk sukayi suka ga abinda ke kai kowa yafara zufa yana neman hanyar fecewa inda habeeb najin muryar musa ya shiga magiyar yace ta sakeshi zan sakeka amma su dan dukununu sunce yau sai mun tayasu murnar zagayowar haihuwar dan autan su dan haka dole kowa na gidan nan ya zo yaci abin cin can nan aka shiga kallon kallo su kuwa matan na waje tuni suka sheqa pary din yusra suka kulle inda sajida ta dubi laila tace kin gani ko gashi nan harda irin na kanki sunzo min gida ina zaman zamana gashi kinsa sun kawo ziyara kin san suna binki meyasa kika zomin bayan kin san ni dul lamarin iska tsoronshi nakeyi cikin kuka laila tace wlh ni banida aljanu ki dena jamin jaraba kada suji su dafemin ina na kan naki dari ba dayan ? ai sun barni tun da aka yayeni wayyo ni wlh gida zan tafi tunda abin harya kai haka baxan kara zuwa gidanki ba ashe har uwar aljanu kk aje a gida duk kansu tsorace suke sunata kukan nadama wai๐Ÿคฃ su kuwa mazan nacan dije fa tace sai kowa yaci abincin nan kafin su dan dukununu su bar gidan nan jin in ba'aci bazasu tafi ba yasa habeeb saurin amsa duk zasu ci shidai tunda ta sakeshi a gaba tasasu suka nufi dinning inda musa jikinsa ke bala'in rawa hakama naseer suna qarasawa sukaja kujera da niyyar zama dije ce ta da karfi tace ya naseer ka jefar da tunguji ba ruwana da sauri ya ja da baya tare da kwalla kara habeeb da yake kokarin zama ji yayi tace shikenan ya zauna akan iya tsibbanatu qara yayi tare da zamewa qasa ji kakeyi kwal ya kwale da gefen table din yayin da qugunsa yayi qara....... *Alqalamin khady* TA ME GARI na khadeeja usman 1โƒฃ9โƒฃ naji rokonku masoya amma kuyi haquri bazan iya yi muku typing sau biyu a rana ba ku tuna fa dukanmu matane munada uzuri a gabanmu karantawa ba wahala cikin qanqanin lokaci zaka gama amma typing akwai wahala ina son nishadinku shiyasa na ke bada lokacina nake muku typing fatana kuyi haquri mu qarasa da yadda muka fara idan nasami dama zan iya yi muku fiye da biyun ma a rana wata azaba yaji amma ba halin yin ihu ya zuwa yanzu dan duk a rude yake ganin yanayin da duk suke ciki yasa dije cewa lah sannunku kunga fa yanzu sun fara fushi gara ku tashi a gaggauta walimar nan su kama gabansu kaga dan dukununu kuyu haquri ku debo naku kujerun ku basu wannan su zauna ta fada tare da qara gyara zaman kujerun gurin cikinsu duk wanda ka kalli fuskarsa kasan kadan yake jira ace arrr ya arta dan haka cikin himma suka fara qoqarin zama a dan dosane itama dijen zama tayi ta kame guri daya tare da fadin toh ku zuzxuba mana arwanatu ๐Ÿ˜ณ sukayi sunata raba idanu jin ta ambaci a zuba abincin kowanne yana kissima yadda zai kwashi wannan girkin na aljanu itako dije ta kame tana kallon kowa a ranta banda dariya ba abinda takeyi can kuma sai ta miqe zumbur kamar wadda ta tuna wani abun suma miqewar sukayi dan su yanzu duk wani motsin yarinyar tsoro yake basu ganin duk sun miqe ne suma yasata fadin ina kuma zakuje? binki zamuyi cewar naseer da kyar ai nima ba tafiya zanyi ba zanje ne na kirawo matanku suzo su taya autaress murna suma yauwa Alhmdllh dan Allah kirawo su din cewar habeeb da ya zuwa yanzu ya dora laifin faruwar komai akan sajida dan a bayanin data masa ya fuskanci bakuwarta ce silar komai toh ku koma ku zauna mana in kirasu duk komawa sukayi suka zauna inda ita kuma tasa kai ta fice a falon ta nufi part din su yusrah dan tasan suna can tana fita naseer ya kalli habeeb cikin marairaicewar fuska kamar zaiyi kuka yace bros nifa wlh lamarin yarinyar nan tsoro yake bani wannan wace irin masifa ce tunda muka fara ganin yarinyar nan bamu taba wanyewa lfy ba wannan ai ita ce da tauraruwa me wutsiya gani yayi habeeb da musa nata mishi alama daya yi shuru sai daga baya ya fahimci me suke nufi ganin musa nayi masa nuni da saman dinning hannu yasa da sauri ya kama bakinsa kamar qaramin yaro suka shiga raba ido๐Ÿคฃ tana zuwa part din ta shiga kwankwasawa laila da sajida da suke jiran tsammanin warabbuka sukayi saurin nufo kofar dan sun san yazuwa yanzu komai ya kamalla barin ma laila data matsu tabar gidan dan ita yusra ta shige daki ta kulle kanta ta shiga kiran wayar mamy amma bata daga ba da sauri sajida ta bude kofar batare da tambayar waye ba aikuwa sukayi ido biyu da dije da gudu ta nufi ciki inda suka fara rige rigen tserewa ita da laila amma dije ta shigo tana fadin meye haka aunty ? jin tace Aunty kuma cikin muryarta ya dan sa sajida tsayawa amma ita kam laila tayi bayan kujera tanata rarrafawa dan ta samu ts fece jiki na rawa sajida ta tattaro karfin halin daya rage mata tace ya...ya...akayi ina su habeeb kallonta dije tayi kafin tace ban gane ina su yaya habeeb ba gasu can a part dinki yayi baki yace in fada miki wai in kin gama gudun tsoron kizo ku gaisa kuri tayi tana kallon dije jin cewar har habeeb yace ta zo yasata yin tunanin komai ya zama normal ba mamaki malamai ya kirawo ai gara ayiwa gidan addu'a gaba daya da alama komai ya lafa dan taga yarinyar ta warware dan haka cikin dan qarfin hali ta maze tace toh jeki ina zuwa ok ta fada tare da fadin ina Aunty yusrah itama yakamata taje a gaisa da ita dan bakin daga family dinmu ne na qauye toh bari na kirata tana ciki cewar sajida data juya ta nufi dakin da yusra ta kulle tana zuwa ta shiga buga qofar yusra dake can bayan gado manne da waya ta qanqame jiki tanata faman kiran wayar mamy wadda sai yanzu ta samu ta dauka tana dagawa kuwa yusra ta shiga fadin pls mamy kizo ki taimakemu wlh jaraba da annoba kika kawo mana ashe cikin kwana daya datayi a cikin biyun da kkk ce tasa kowa yasan da zamanta mamy pls n'd pls kizo ki dauketa ta koma gidan ni nayafe mata duniya da lahira jin da mamy tayi yusra na kuka yasata fadin calm dawn mana yusrah ki ci ubanta mana karfinki tafi ko kuwa shi naseer din tafi qarfinshi ne iye bazaki gane ba mamy duk yadda na fada miki nidai dan girman Allah kizo ki dauketa .to amma ai naji tace wa daddy'n ku ku kukace ta zauna tayi muku kwana biyu dan haka ma nabar maganar dawowar tata wlh mamy na rantse da Allah bani bace wall.....kinga ya isa wai meya ke faruwa ne kk kuka haka dukanki takeyi ko yankar naman jikinki wlh mamy ni gara ma ta dakeni da masifar da nake gani nidai mamy kizo ki dauketa dan Allah suna tsaka da maganar ta tsinkayi bugun kofa aikuwa ta fashe da kuka tare da fadin kin ji ta ko mamy dan Allah kiyi sauri kixo jin haka da mamy tayi yasata saurin kashe wayar ta miqe dan ta sanar da daddy su taho jin taki budewa ne yasa sajida yi mata magana saida taji muryar sajida kafin ta bude tana leqo kai tace ya ake ciki dan juyawa sajida tayi bayanta taga dije bata hangota nan ta sanar da yusra sakon da dije ta sanar mata tab wlh ba inda zani ah to ni ina ruwana kiyi zamanki kin san dai ba mamaki malamai ne suka zo daga kauyensu dan inaga sun san da zaman lalurar ta inaga shiyasa sukayi addu'a muma gara muje kar abin ya shafe mu bayan sun tafi tunda abin har yakai ga ana min girki da walima a gida ai ni nafi kowa shiga uku sun dan jajja kafin yusra ta yadda ta fito da kyar laila ta fito a bayan kujera suka bi bayan dije kamar abin magani amma ganin ko'a jikinta yasa su yadda da almatsutsan sun sauka ya zuwa yanzu koda suka qarasa part din nan aka shiga kallon kallo kowa ya kasa shiga sai da dije ta juyo ta kalle su tace ya haka ku shiga mana laila ce tace ah ah ni daga nan ma wucewa zanyi ki mikomin jakata da takalmi in kin shiga Allah ya bada zaman lfy ai wlh baki isaba sai dai ki shiga ki dauka in kin matsu wace matsuwa nayi ai ba dole a mota fa nike kinga bari in tafi a haka na turo daga baya a karbar min dije ce ta kalleta tace haba aunty ta ya zaki shiga mota a haka ba takalmi me yayi zafi haka ? ai ni sai yanzu na tuna ma ashe bada takalmi nazo ba suna mota har jakar sakin baki sajida tayi tana kallon laila da duk ta birkice kamar ba itace daxu ke ruwan bala'I ba dan haka cikin quluwa tace ah ah tsirara kika shigo gidan ba takalmi ne kadai baki zo dashi ba amma ai karki manta mukullin motar na ciki ko? innalillahi wa'inna ilaihir raji'un cewar laila a fili ba yadda ta iya dole suka tura qofar suka shiga suna shiga suka hangi mazan tsaye kamar ace arr su arta ita ko dije suna shiga ta mayar da qofa ta rufe tare da fadin sannunku da zuwa ku qarasa ayi walimar daku ku kadai ake jira nan fa guri ya hautsine zasu sa ihu tace lah aunty kada kuyi ihu wlh kunayi zasu sa bakinku ya qara girma nan fa jikin kowa yahau makyar kyata kasancewar dinning din kujeru takwas ne nan tajawa kowa daya ya zauna duk wanda ka kalla matsar kwalla yakeyi inda duk suka dubi kayan dake gurin wanda suka kalli kwalbar carbont din dake gurin gaba daya sai idanunsu yake musu gizo suke ganin kamar jini ne๐Ÿคฃ kunji fa sharri๐Ÿ˜œ bude kular tayi ta leqa 'yar mitsitsiyar shinkafar dake can kasan kular ta hango dan dama fa iya wadda zata iya ci kawai ta dafa jaraba ce tasata zubawa cikin wannan kular lahhhh amma ko baku kyauta ba akuyatu ai bani kadai nace muku ku ragemun ba suma fa duk zasuci irin girkin ku amma shine kuka rage iya cikina ta fada tare da dan hararar kujerar daba kowa jin ta ambaci an cinye abinci sai ita kadai aka ragewa yasa kowannensu hamdala a zuciyarsa juyowa tayi ta kallesu taga duk sun kafeta da ido dariya taso kwace mata amma ta danne tace toh kunga har sun gama cin nasu abincin kunyi jinkiri amma ai ga kayan drinks nan kuci ni bari inci wanda suka ragemin din nan ta shiga kokarin zuba shinkafar harta gama ta fara ci cikinsu ba wanda ya motsa bare ya dauki wani abun shi kam musa ji yakeyi dazai samu dama da inya fece bamai sake ganinsa tunda aikin gadin ba dole bane itakam dije tanata cin abincin ta hankali kwance su kuwa sai muzurai sukeyi sai da ta gama tasha ruwa kafin ta juyo ta kallesu tace sunce tunda baku cin irin wannan bari su kawo muku irin nasu da sauri aka shiga rubibin daukar abin ci inda saboda tsabar sharri habeeb daya dauki apple wai jinta yayi kamar goribar data bushe wai kawai dan ta aljanu ce๐Ÿคฃ kowa a gurin yana shan abu kamar magani kuma yana kuka itako dije sai surutun ta takeyi ita kadai hakan ke qara firgita su sukuwa suka shiga 'yammatan hawaye su mamy na qarasowa suka shiga yin horn jin shuru ba'a bude ba yasa habu fitowa ya bude gate din da kanshi ya shiga da motar mamy cikin tashin hankali ta bude murfin motar ta fito ita da daddy wanda suka nufi part din da basu san ko na waye a ciki ba suka shiga bugawa jin ana buga kofar da dan karfi ga alamar magana yasa su naseer qara rudewa dan duk a tunanisu ko abincin da suka ki cine abubuwan suka gayyato wasu dan haka suka qara kidimewa tare da qoqarin tura duk abinda ke hannunsu baki dije ce ta miqe ta nufo kofar a ranta tana fadin wane me tsautsayin ne kuma tana bude qofar taga su daddy mamy na qoqarin tureta ta shiga tana fadin suna ina?me kk yi musu jin muryar mamy ne yasa yusra da su naseer bude murya suka sa kuka....... *kai kai naso inci gaba amma....* *vote* *comments* *with 08066364077* *Alqalamin khady*โœ [3/14, 9:42 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* NA Khadija usman 2โƒฃ0โƒฃ *A gaskiya mutane basuyi mana adalci ba duk da nasan masu qarancin ilimi da tunani ne sukayi abinda sukayi kowa fa da ra'ayinsa duk wadda taga bazata iya novels kyauta ba ra'ayinta ne ban kuma ga laifinta ba haka mu da mukaga zamuyi kyauta muma ra'ayinmu ne dan haka bai kamata ayita magana daya ba har takai ga anyi mana rubdugu ana zagin iyayenmu gaba daya dan girman Allah ina rokonku ku dinga mana adalci reader's ku duba irin wahala da westing time din da muke yi duk dan mu faranta muku ina rokon afuwar duk wanda magana ta ta batawa rai๐Ÿ™* cikin rudewa da tashin hankali mamy ke fadin ya salam me zan gani haka me yake faruwa ta fada tare da qarasawa cikin falon ta nufi inda su yusra suke daddy ne ya shigo shima inda dije na ganinsa ta shiga yimasa sannu da zuwa cikin nuna farin cikin ganinshi ta fara fadin oyoyo daddy gwamma da kuka zo wlh kunzo a dai dai sai ayi tare daku daddy ne ya dubi sauran mutane yaga yadda fuskokin su suke amma kuma yaga dije qalau da alamun farin ciki a tare da ita ga kuma mamy data azalzaleshi cewar ba lfy gidan yaran ya taso suje dan haka ya juya ya kalli inda mamy take tana tambayar yusra dake ta kuka me ke faruwa caraf dije tayi tace ai wlh daddy ban san haka nake da farin jini ba sai yau kai wlh naga soyayya kasan fa yau na cika shekara goma sha bakwai to ni nama manta sai dazu na tuna shine nake fadawa yaya shine fa yace wai dole sai anyi qaramar walima toh shine fa aka dan hada kayan sha wai kafin su shiryamin bikin birthday din wai shine fa Aunty yusra tace bata yadda ba a gidan ta za'a shirya party din shine itama aunty sajida tace ah ah sai dai ayi anan toh shine fa aketa rigimar yanxu haka ashe har kun samu labari duk qamewa sukayi jin abinda dije ta karkace baki tana fadi yayin da yusra ta tsaida kukanta dan bataga amfanin yinsa ba ya zuwa yanzu kutmelesi lallai wannan yarinyar kashesu zatayi kawai itako mamy jin abinda dije tace ya qara bata ranta wato ma har rigima yaranta keyi dan kawai su shiryama wannan me kama da mutanen boyen party lallai ma wato dai inta fahimta saude da yunusa ba qaramin shiri sukayi ba kafin su turo yarinyar nan duba da yadda komai yake tafiya game da yarinyar daga kan daddy yanzu har gashi yaranta ma zasu fara dawainiya da ita kamar ba su ne suke nuna tsanar yarinyar ba a fili a bar ma tasu to matansu fa ji yusra yanda take kuka ashe ma akan wannan ne take cewa ta zo yarinyar zata kashe su to sbd kawai ba'ayi iskancin tuna ranar haihuwar bane a gidan su ko kuwa? lallai yazama dole ta dauki mataki dan wannan yarinyar daga ganinta ba alkhairi bace daddy ne yace kai amma yaran nan kun fiya shiririta wlh kai yanzu habeeb harda kai da girmanka akayi wannan abin dakai habeeb da tun dazu yayi zugum yanata raba ido sbd tsoron Allah yayi masa yawa yama rasa gane inda batun ya dosa sai da ya ji muryar daddy na fadin wlh dai in an girma asan an girma yanzu dai kun ajiye iyali dukanku ba yara bane yanzu gashi ina zaman zmana kun tasoni akan wani shirme naku dukansu shuru sukayi suka shiga rarraba idanu domin kuwa ba halin suce qarya ne ba haka bane aljanun dake wurin suyi kulin kulifita dasu suce sun qaryata uwar dakinsu dan haka kowa ya shiga mirgina kai da raba ido ita kam laila fatanta bai wuce ta bar gidan ba dije ce ta katse wa kowa tunanisa inda tace cikin 'yar shagwaba daddy ku taso kuma ayi daku ah ah ni bada ni ba cewar daddy wannan aikin ku ne na yara a dai bani ruwa ya isheni miqewa dije tayi ta dauko masa gorar ruwa ta dauki cup ta zuba masa inda ya karba yana kaiwa baki da niyyar sha yaji naseer na fadin kada kasha daddy pls sauke kofin yayi kafin yace sbd me ? kafin ya bashi amsa dije tace sbd tunanisa akwai sanyi ne to babu wani sanyi ka dauka ka fini son daddy din ne dazan bashi ruwan dazai cutar dashi kaga ya naseer wlh ba ruwana idan ka hadu da fushin......hmmm bari dai inyi shuru ta qarasa maganar tare da kashe masa ido tana dariya kasa kasa ganin yadda tayi ne yasashi yin gum da bakinsa mamy dake gefe duk tana lura da yadda komai ke faruwa ganin hakan yasata sakin ranta tare da fadin oh wato daddy'n ku kadai kuka sani ni ko tayi ma ba'aminba to ba damuwa godiya nake ah ah mamy wlh ba haka bane cewar habeeb munga kamar a koshe kike ba kya buqata au dama ana gane mutum ya qoshi da ruwa kenan? ah ah no ba haka bane barii inje in kawo miki wani ya fada yana qoqarin mikewa duk tana hankalce dashi hakan yasa ta shiga nazarin tabbas akwai abinda ke faruwa boye mata sukayi dole ne kuma ta bincika dan haka saita maxe tare da fadin no shi wannan ba nasha bane ai duk sunyi expire cewar sajida dasai yanzu tayi magana tun shigowarsu duk mamy ta karanci halin da kowa ke ciki expire kuma duk kayan gurin eh wlh habeeb ya fada da sauri musa ne ya mike tare da fadin to ni fa zan koma bakin aiki wanda a ransa ya ayyana yana fita hada kayansa zaiyi yayi kauye bai ko jira amsar kowa ba yasa kai ya fita aikuwa yana fita dije tabi bayansa yana gab da shiga daki yaji ta kira sunansa aikuwa da gudu ya afka dakin be ko tsaya rufewa ba jiki na rawa daga labulen dakin tayi ta tsaya daga waje kafin ta dan leqo kanta tace nasan ya zuwa yanzu so kk yi ka bar gidan nan ko to wlh kasake ka bar aiki a gidan nan ko kasa kafarka ka fita sainasa inna arwanatu ta shanye mun qafafunka da hannaye inga ta inda zaka moru inka musa ka tafi din tana gama fadar hakan ta juya ta koma cikin gida musa kuwa kuka ya shiga yi harda sharbar majina ganin hakan bazai fishsheshi ba ya miqe ya dauki buta ya daura alwala ya samu guri ya zauna a cewarsa gara ya dinga zama cikin tsarki da alwala shina kariya ce nan ya shiga karanta ayatul kursiyyu tana shiga ta tarar da daddy ya mike yana fadin tafiya zaiyi dan ita mamy tace ya wuce sai anyi murnar da ita jiki na rawa laila ma ta miqe ta dibi kayanta dan tasami hanyar kubuta ba wanda taiwa sallama ta fice daddy har yakai bakin kofa ya tsinkayi muryar habeeb na fadin am daddy dama maganar khadija ne dakatawa daddy yayi tare da juyowa dauke da murmushi akan fuskar sa yace ai kada ka damu tayimin bayanin komai nan da can ai duk dayane da sauri habeeb yace daddy baka fahimceni bane ina nufin batun....caraf dije tace wai batun zuwa makaranta ta ai nayima principal bayani kada ka damu nace a dinga zuwa daukata da sauri naseer yace a dinga zuwa daukarki kamar ya? eh ai kasancewar na dawo nan da zama shine naga ba sai anyi wahalar daukar min driver ba kawai su dinga daukata da motar ina gidan wa kk dawo da zama suka fada da bayyanar tashin hankalin maganarta a fuskokinsu har suna hada baki sai dai in gidan naseer cewar habeeb ah ah gidanka dai naka dai jin suna neman kwafsa mata yasa ta fadin kai brothers meye haka in dai dan nice kada ku bata ranku ina gidan kowa zan iya yini nan in kwana can ko kuma in dinga kwana daddaya ko bibbiyu dan haka daddy kada ka damu bari in bika in kwaso sauran kayana daya kamata tana gama fadar haka ta fice tayi wajen mota daddy kuwa juyawa yayi yace to sarakan rigima ni ba ruwana gata nan ta raba muku rigima ai yasa kai ya fici yabarsu duk da bugun zuciya mamy da duk abinda akeyi bata ce qala ba saida daddy ya fita kafin ta kalle su tace su zauna kowa ya zauna ta dan jima kafin tafara magana tace ina son sanin abinda ke faruwa a gidan nan tsakanin jiya da yau dan idona ya ganmun wasu ina son qarin bayani dukansu suka shiga rattaba mata bayani kuwa jinjina kai ta shiga yi tare da naxari zuwa can ta nisa tace idan na fahimta wannan yarinyar annoba ce kenan a gida na nasan aninda zanyi badai tace zata dawo nan ba da zama to yau zan fada muku abinda zakuyi mata tasan ta dawo da zaman kamar yadda ta buqata nan ta shiga yi musu bayanin tare da fada musu matakinda zasu dauka dazai sa sai dije ta koma kauye da qafarta ta fada tare dayin kwafa ta miqe tayi musu sallama ta fito su habeeb suka biyota inda ta shiga motar habeeb danya maidata gida itako dije koda sukataho ita da daddy ta sanar dashi tana son yasai mata waya koda qarama ce dan su dinga gaisawa tunda yanzu sun danyi nisa ba musu kuwa suka shiga wani shagon saida waya ya siya mata qarama dai dai ita a cewarsa saita gama secondry kafin yasai mata babba harda layi yasai mata kafin suka wuce gida suna zuwa kuwa ta shiga hada kayanta baseera tayi kewar rabuwarsu amma ta tausayawa su habeeb da zasu zauna da dije komai nata saida ta hada tsab aka loda a mota ta ta shiga ita da habu driver ta nufi gidan su habeeb....... ........... *wlh drmar nan fa yanzu aka fara kudai ku biyoni* *Alqalamin khady*โœ[3/14, 9:45 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* NA Khadija usman 2โƒฃ1โƒฃ *A gaskiya banida bakin da zan gode muku masoya ta me gari a duk inda kk ina matuqar alfahari daku ngd sosai Allah ya qara qauna da zumunci luv u all๐Ÿ˜˜* suna qarasawa gidan habu ya shiga fito mata da kayanta inda ta tsaya tunanin to ina zata dosa gidan habeeb ko na naseer ?kai gidan ya habeeb ya kamata in fara zama tukun musa sai sim sim yakeyi tare da ladabi dashi aka dinga jidi kayan dije zuwa qofar part din habeeb kasancrwar magariba tayi yasa suna gama ajiye mata kayan suka juya shida habu dan yin sallah ita ko dije ta shiga knoking ta jima tana bugawa amma shiru kk ji ba'a bude ba tun dije nayin bugun marmari harta koma yin na qarfi amma still shuru jin ba ada niyyar budewa yasata juyawa ta nufi part din naseer canma bugun ta shiga yi still ba wanda ya bude ta jima anan din ma nan fa ran 'yammata ya fara baci wato ni zasuyi wa haka ko? to ko basa nan ne ta fada a zuciyarta tabbas da alama basa dan da suna nan tasan bazasu ki budewa ba kodan abinda ya faru dazu da wannan tunanin ta nemi guri ta zauna jin ana sallar magariba yasata miqewa ta nufi bakin gate gurin musa ta dauki buta tayi alwala bata ko tambayeshi mutanen gidan na ciki ba ta koma can gefe ta shimfida dankwalinta ta tada sallah tana tayarwa taji ana danna horn musa ya bude habeeb ne ya shigo aikuwa yana gama parking ya fito ya nufi part dinsa a kofar yaga kayan dije murmushi ya sake tare da fiddo wayarsa ya kira sajida tana dagawa yace zo ki bude nadawo zuwa can sai gata ta bude masa ya shiga suka mayar da kofa suka rufe saida ta idar da sallarta a nutse kafin ta miqe ta nufi part din ta kuma bugawa shima still banza akayi da ita ta gaji da bugu sannan ta nufi gun musa take tambayarshi ko matan gidan basa nan ne nan yake shaida mata duk suna ciki zamewa tayi ta zauna a ranta tace au wato ni za'ayiwa wulakanci dan na nuna ina son zama hhhh tayi dariya kadan kafin tace yaseen zaku san kunyi min haka nasan duk dan in koma gida ne to wlh ko kasheni zakuyi ba inda zani shi dai musa nashi ido dan yanzu hirar ma dayake yi da ita ji yayi bazai iyaba dan haka yana kallon ta tanata dariya ita kadai be ce kala ba zuwa can ma ya shige dakinsa ya banko bayan ya rufe gate din kamar yadda ya saba ita ko dije ko 'a jikinta saima tunanin data shiga yi na inda ya kamata ta kwana ta jima zaune a gurin har aka kira sallar isha'i ta miqe tayi kafin ta kuma zama tana neman mafita zuwa can ta miqe ta nufi gurin kayanta jakarta ta zuge ta fito da wayar da daddy ya siya mata gashi bata sata carji amma ai da akwai na ciki bari ta kunna ta yi amfani da ita haka to wai ma uwar me zakiyi da ita din ta fadawa kanta a hasale (niko nace su dije za'a huce haushi akan waya ne) ba kaiii ya salam ta fada a fili nan ta shiga kakkanta sauran kayan tana jansu gefe guda harta gama duk ranta a bace yake kawai tuna irin saqar rashin mtuncin da zatayi musu tasan sun shirya mata hakan ne dukansu an fada musu ita tana jin tsorone wlh nan zata kwana tasan kafin gari ya waye ta yi mafarkin irin abinda zata musu da wannan tunanin ta shiga neman abinda zata shimfida ta kwanta ganin bazata samu ba yasata dauko dankwalayenta da siket dinta dan batada zani ta shiga shimfidawa har ya danyi tudu yadda zata kwanta hijab babba ta dauka ta kwanta ta rufe ko ina na jikinta *niko nace haba dije sai kace mayya ki koma gida mana*๐Ÿคฃ ****" su kuwa su naseer shawarar mamy suka dauka ita tace suyi mata hakan tasan idan taga basu bude ba dole ta koma gida ai dan haka duk bugun da takeyi suna jinta sun san itace dan tun zuwansu da habu sun ganta itama sajida habeeb cewa yayi ta bari inya dawo zai kirata saita bude masa kawai dan haka duk sun saki jiki ya zuwa yanzu dije ta koma dan sun san dai duk ifritancin ta bazata kwana farfajiyar gidan nan ba ita kadai koda kuwa ita ce aljanar da kanta *** dije fa dare yayi baccin nan fa ba dadi dan sanyin kasan tiles din ga kuma sauro duk da ta rufe ko ina na jikinta amma sai ta ji kamar suna bula hijabin suna cizonta ga kukansu daya dameta duk ta rasa abinyi oh ni dije na shiga uku ta fada tana me sosa qafarta dataji kamar sauro ya cije ta wlh da da inda zan samu turmi na rantse da Allah da saina dauko shi cikin daren nan na shiga daka koda shinkafa ce inya so kowa kada ya rintsa ta kiyasta kalolin mugunta a ranta sunkai kala hamsin a haka tayita saka da warwara tana ja musu Allah ya isa tare da tunanin me zatayi musu gobe ta huce kuma wlh ko da bala'i saita kwana cikin gidan nan tanata wannan saqar zucin bacci ya kwasheta har akayi sallah bata sani ba sai da sanyin asuba ya kadata kafin ta tashi taga gari har yayi haske salati tayi tare da miqa ta miqe ta nufi dakin musa tana zuwa ta tarar da buta bakin kofar dauka tayi tazagaya cikin flower tayi fitsari kafin ta dawo tayi alwala sai da tayi sallah ta fara shirin zuwa school duk da yunwar da take ji gashi ko wanka batayi ba jiya da dare bare kuma yanzu haka dai ta kimtsa dan tana gudun makara kasancewar yanzu suna S.S.3 ne suna ta shirye shiryen fara S.S.C.E gashi kuma dama dije bata wasa da karatu duk iskancinta dan haka ta shirya ta kankanta kayanta a gefe harta ta juya da niyyar tafiya kuma sai ta tsaya jimmm dariya naga tayi kafin ta juya ta koma gurin ta nemi guri ta zauna ta shiga fadin wlh na ma fasa zuwa school din in na tafi ai nabar baya da kura kenan hhhhh ta saki dariya kafin naga ta miqe ta ciro waayarta ta kunna time ta duba taga 7:10 dan haka tasan duk inda masu gidan suke ya zuwa yanzu sunata shirye shiryen zuwa office dan haka ta miqe ta shiga zagaye a gidan ko me take nema ohoo ta jima tana zagaye gidan kafin daga baya ta taga wata igiiya daure daga bayan dakinda alama ta shanya ce dan haka ta je ta fara kokari. kuntowa tasha wuya kafin ta kunce ai kuwa tana zuwa ta shiga dariya tare da nazarin ta ina zata fara qofar ta kalla aikuwa nan ta shiga neman salon da zatayi qaramar jakarta ta bude ta dauko kifiyar tsifa nan ta shiga turawa guri. mukullin ta jima tana malqwayawa hada cije baki kuwa har saida taji wani abu yayi 'yar qara kafin ta zare kibiyar wadda ita kanta dan wahalar da aka bata saida ta malkwaye danma irin me kwarin nan ce ta kusa saida ta tabbatar ta gama lalata inda makuli zai iya shiga kafin ta fara neman dabarar daure kofar wata irin dauri tayima kofar na fitar hankali wanda ita kanta in ance ta fadi ta inda ta fara bazata iya ba tana gamawa ta koma part din naseer shima yadda tayiwa habeeb din haka tayi musu duk ta hada zufa sai da ta kammala kafi. ta tsaya ta riqe kugu ta shiga fadin yau sai inga yadda zaku bi ku fito wlh sai kun san na kwana a waje naga me zuwa ya bude ku ta fada tana haki kamar me shirin yin dambe **** su kuwa dukansu suna ciki suna shiri dan yau sunada meeting da zasuyi dan haka sukayi waya akan kowa ya shirya cikin lokaci sam sun manta ma da wata aba dijeee *da babu gara ba dadi manage pls* *Alqalamin khadyโœ* [3/14, 9:48 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TA ME GARI NA khadeeja usman 2โƒฃ2โƒฃ kai kai kai gaskiya na fuskanci mutane ma sunfi son dije dani zan fa koma 'yar adawarta dan na fuskanci hmmmm bari dai kawai nayi shuru bazan gaji da nuna farin cikina ga daukakin masoya tame gari ba a kullum ina ganin sakonni tare da kira ban san adadi ba ngd da addu'oinku gareni ina matuqar sonku tare da ji daku **** luv birds suna manne da juna suna sallama an rako miji suna qarasawa bakin qofar falon sajida aka shige gaba ana kwarkwasa aka zira key dan a bude ji tayi yaqi shiga shiko habeeb dayake ganin kamar tana hakan ne dan qara salon jan hankalinsa yasashi fadin pls baby aimun afuwa a barni haka kin san sauri nakeyi cike da salo wai ita irin baby din nan tace wlh ba haka bane sweety key din ne yaqi shiga ban san dalili ba qarasawa yayi ya karbi key din ya shiga zurawa ganin da gaske fa yaqi shiga yasa shi qara azama amma still dai haka haka ma a bangaren su naseer suna can suna kokawar bude qofa amma taqi buduwa dije na tsaye tana jin ki..ki..ki ..ki anata dannar kofa jin sun jima sunayi tasan ya zuwa yanzu duk sun wahala ransu ya baci dan haka ta qarasa jikin qofar tare da kwankwasawa da sauri habeeb yace waye ?dan ya matsu ya fita ni ce nan cewar dije hasbunallahu wa'nimala wakeel ya fada a fili wannan jaraba har ina wato yarinyar nan dawowa tayi kenan kamar tasan meyake fada a zuciyarsa sai ji yayi tace ina nan dama ba inda naje anan na kwana badai ni kuka sa na kwana a waje ba to naji ni na kwana a waje cikin duhu da sanyi da sauro to ku kuma ku yini cikin haske da A.C ga fanka ba sauro bare kuda kuzauna kuyita kallon juna ta qarashe maganarta tare da yin dariya tace wlh kuma naga wanda zai bude ku muddin ina nan a haka zaku tabbata ni naji ina nan zan dinga kwana a nan waje ku kuma kuyi zamanku cikin gidanku ai yafi jikin window suka dawo habeeb yayi slide dinsa tare da leqowa yafara mata magana cikin bacin rai dan ya zuwa yanzu yafara tunzura da lamarin yarinyar gara kawai yafara cin ubanta inya so kome zai faru ya faru ba aljanu ba ko kukar bulukiya ce akanta be shafeshi ba keeee dan ubanki ni sa'an wasanki ne ya fada yana me nunata da yatsa ta ciki ah ah kai ba sa'an wasana bane dan inaga lokacin da aka haifeni ma kai ka zama saurayi da ace ma anyi auren wuri da an ajje kamata kai ya fada tare da dukan qarfen dake tsakiyar jikin window wlh idan baki zo kin bude qofar nan ba wlh wlh kinji na rantse sainayi miki abinda iyayenki bazasu gane ki ba dan zan manta da komai inci uwarki yatsina fuska tayi tare da fadin iyayenmu bazasu gane mu ba dai dan yaseen sai dai a qona gidan nan ta fada tare da juyawa ta nufi part din su naseer wai ta leqo su suma tana zuwa suma ta kwankwasa suma haka ta rattaba musu bayani sai dai sabanin habeeb shi naseer hakuri ya shiga bata tare da rokon ta budesu ya shiga sanar mata meeting garesu kuma wlh in basu halarta ba zasu sami matsala tunani tayi taga ko ba komai bai kamata tayi musu haka ba coz wannan fannin da ban amma kuma sai dai naseer yafi habeeb dan shi ya karaya da wuri ya bada kai bori ya hau dan haka nan ta shiga kici kicin kunce igiyar amma ta kasa tana tsaka da haka ta hango habeeb ya nufo gurin da take gadan gadan cike da mamakin yadda akayi ya fito ta kwasa a guje tayi hanyar gate ya so binta amma ya kasa dan shi bazai iya gudu ba sam duba da yadda yaga ta zura a guje kamar iska na qara mata gudun kwafa yayi tare da qarasawa bakin kofar su habeeb da suma suke ta leqe ta window kamar maguna cikin dan zafi yace kai kuma dayalla malam saika bude ta kitchen ka fito sam naseer ya ma manta da wata qofa ta baya ta cikin kitchen sai yanzu sim sim ya juya ya nemo key din ya bude ya fito yana fiwo ko kallonsa habeeb beyi ba ya juya ya nufi bakin motarshi shima ganin hakan yasa be tamka mishi ba ya shiga tashi motar shima suka fita ita ko dije cikin sa'a tana fitowa daga gidan ta ga motar makarantar su aikuwa ta afka aka wulla da ita *** sam yarasa mafita game da lamarin dije yarinyar da gani kasan batada lfy duba da yanayin kiriniyarta da fitina gashi yanzu inya ce ta koma gida daddy zaiga kamar da wani abu ko ma yaga laifin mamy duba da yadda mamy ke nuna kin dangin daddy to yanzu meye mafita? yana tsaka da wannan tunanin naseer ya turo kofar office din tare da sallama amsawa yayi tare da yi masa nuni daya zauna suyi magana zaman yayi duk da shima yana son suyi magana dashi dan ita ta kawo shi amma bari ya fara jin tashi bayani ya shiga koro mishi akan dije nan yake tambayarshi meye mafita ,? wlh nima maganar dana zo da ita kenan gaskiya ya ksmata asan abinyi ni a ganina tunda dai yarinyar nan irin naci ce dangin laquwa kawai mu haqura ta zauna din kamar yadda ta nuna ta na son zaman tare damu sai dai mu kiyaye bata mata rai tare da duk wani abinda mukasan zai sa sabani tsakaninmu tunda dai kaga ita dangin ifritai ce da an tabata sai mutum yaji jiki mu samu mu gagganda mu aurar da ita cikin qankanin lokaci dan na fuskanci batada wani wayo kaga saimu dan sami wani galmashuran mu hadata dashi mu lallabata cikin salama a rabu lfy Ajiyar zuciya habeeb ya sauke tare da fadin to ai duk ba wannan ba a ina zata zauna ? dan ni gaskiya zamanta zai kawomin matsala da sweety na duba da yadda yarinyar ke da rawar kai ita kuma sweety na ga kishi kuma ma ni bana son harkar hayaniya wlh ni ko kallon yarinyar nayi gabana faduwa yakeyi kada taje taci gaba da gayyato aljanun nan suna watanda da kayan gidana dan kaga ko na jiya fa maimakon suzo da nasu to nawa fa duk suka nakasa jimmmmm naseer yayi ya shiga nazarin maganar habeeb lallai fa akwai matsala to ammaai ko su aljanun in ka lallabasu basa cutarwa a cewarsa dan haka ya nisa yace wannan ba matsala bane saita zauna inda nake ko? Alright indai kaga ba wata matsala ai shikenan amma wlh yarinyar nan ko yau dana kamata inaga saina kusa kasheta dariya naseer yayi yace ka kusa kasheta ita kuma ta kasheka gaba daya ba ko kuma tasa ka kukan.....bari dai nayi shuru ya fada yana rufe baki tare da dariya qasa qasa to dadin abin dai kowa yanada abin fadi gaskiya ne amma na wani yafi na wani ba naseer ya fada yana qoqarin miqewa dan tafiya shima miqewar yayi yana fadin na sa an kira me gyaran doors din nan inaga ya zuwa yanzu an gyara ok ya fada tare da sa kai suka fice gaba daya ***** itako dije sam ta manta ma da tsiyar data shuka sai da aka kusa tashinsu ta tuna dan haka ta shiga tunanin mafita kawai in koma gida ince wa daddy nafasa zaman nan shi yafi min alkhairi dan wlh wannan me siffar mugun dawan ya rikeni kwanana ga kare yaje ma yayimin rauni a zo aurena a ragemin farashi to wai ke dije yaushe kika fara tsoro ne kece fa uwar mazga jahannama ga fasinja dije Annoba fitinatu cewar wani bangare na zuciyarta ke banza da ne nake amsa wannan sunan amma yanzu tunda na fara shan ruwan alwalar la,asar naji nafara sanyi ita kadai take ta surutunta a zuciyarta har aka tashi ta shiga motar komawa gida jikinta a sanyaye ta jima zaune a unguwar nesa da gidan taki shiga kamar abin dole danma suna ci suna koshi a makarantar amma da yau taci ubanta da yunwa duk da tunanin matakin da habeeb zai dauka a kanta ya hanata sakewa taci abincin *niko nake su dije anyi laushi ne*๐Ÿ˜‚ tana nan zaune har magariba ta gabato ta hango dawowar su habeeb nan ta shiga neman mafita zuwa can kuwa ta saki murmushi dan tunawa da tayi da wata dabara qafar wandonta ta shiga nadewa duka biyu zuwa gwiwa ta bubbuda qafafu ta gyara saiti shi kuwa musa ya wangale gate motocin na shiga yayin da matan masu gidan kowacce ta fito dan tarbar mijinta anci kwalliya dan tarbar miji suna gama shigewa musa ya fara qoqarin maida gate aikuwa dije ta kwaso a guje ta nufo ciki yana gaf da ida rufewa ta afko kamar an jefota tana fadin ku gudu gasu nan ku gudu ku gudu ai musa be ko tsaya qarasa turawa ba ya afka dakinsa ya banko ji kake garam su kuwa mata anata kwarkwasa sun nufo parking space inda mazajensu suka parka suna qoqarin fitowa sukaga ahigowar dije na fadin ku gudu gasu nan ganin yadda take a sukwane yasa naseer da yusra kwasa suma a guje inda sajida ta juya itama da niyyar guduwar shims habeeb haka ji kakeyi kummmm kawunansu ya hadu yayin da hancin habeeb ya fashe jini ya fara biyowa itako sajida bakinta ya bige shima har da jini amma ko ta kan juna basu bi ba suka shiga rige rigen tserewa yayin da ita uwar gayyar tuni ta shige parlor ta tsaya tana mayar sa numfashi a wannan yanayin suka shigo suna kokarin danna kofar da aka gyara dazu suka aa key nan habeeb ya sunkuya tare da safe kai jin jini na bin gefen hancinshi ita ko sajida sai yanzu taji zafi kamar kada ta taba aikuwa taji baki yayi suntum dan da nan jambakin datasa ya hade da jini da maiko abin saiya qarawa bakinta style ๐Ÿ˜‚ sun jima haka kowa na mayar da numfashi kafin dije ta dago ta dubi sajida taga yadda lokaci daya halittar bakinta ta sauya aikuwa duk yadda taso hadiye dariyarta kasawa tayi sai da ta dara dariyar da takeyi ne yasa habeeb dagowa dan tambayarta me takewa dariya ai kuwa shima yayi tozali da bakin sajida da ya samu qarin armashin kwalliya..... *wayyo cikina* ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ *na kasa qarasawa* * *Alqalamin khady*โœ [3/14, 9:52 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TA ME GARI NA khadija usman 2โƒฃ3โƒฃ shi kanshi duk yadda yaso ya maze kasawa yayi duba da yadda yaga bakin sajida lokaci daya ya koma kamar na jaba sam yama manta da ciwon nashi nan shima ya shiga dariya sajida kuwa ta zubawa sarautar Allah ido ganin duk su biyun shi da dije sai babbaka dariya sukeyi hakan yasa tayi tsammanin ko abinda ya biyo dijen ne ya shige jikinsu dan haka saita fara ja baya tana neman hanyar shafcewa cikin dariyar harda rike ciki ya nunata da yatsa ya na fadin kin ganki kuwa sweety kin kalli yadda bakinki ya koma kuwa ? tabawa tayi da hannunta taji yayi suntum sai yanzu na fuskanci meyake yiwa dariya itako dije cikin dariyar ta juya kallonta ga habeeb tace wlh yaya kaima bakaga hancinka ba har ya malkwade shafawa yayi shima ya danji zafi sai yanzu ya dan nutsu kafin ya rike kansa ya samu guri ya zauna tunawa da yayi da gudun da suka sheko to ko uban me ya koro yarinyar oho cikin wannan yanayin ya dago da kyar yace ke su waye suka biyo ki ne? tsayar da dariyar tayi kafin tace ba fa wasu bane qawaye na ne na skull shine mukace ayi rige rigen zuwa gida to shine fa na sheqo a guje....... dukansu sakin baki sukayi suna kallonta inda zuciyar su ta shiga sama da kasa kowannensu yama rasa abin cewa tana gama fadar haka kuwa ta juya tayi cikin daki tana dariya dukansu sun kasa magana sajida da ya zuwa yanzu takejin kamar ta shake yarinyar ta mutu kowa ya huta takeji wannan jaraba har ina yanzu duk wannan gudun famfalakin data sa su ashe shirmenta ne na banza da wofi dama ga haushinta da take ji tun safe tama rasa hukuncin daya kamata tayi mata haka shima habeeb ransa ya gama dagulewa wato ma duk wannan gudun data sa su ashe kawai na iskanci ne yanzu dubi yadda ta mayar masa da bakin mata tamkar na jaba duk soyayyar da aka kwadaita masa yau amma yarinyar nan tayi masa bakin cikinta tunda ta yaya zai fuskanci wannan bakin na sajida a haka itama sajida a nata bangaren hakan take domin yau ta kudiri aniyar shayar da shi soyayya ta musamman amma sai gashi wannan matsiyaciyar yarinyar ta bata masu shiri ji yadda hancin mijinta ya wani maude abin haushin ma ga gobe yusuf zai zo da matarsa yanzu haka zasu zo su gansu sun canza kamanni kai wannan yarinyar Allah ya hadata da marurun rayuwa wannan jaraba har ina ga yadda ta kwaso a guje wlh ita ta dauka ma 'yan boko haram ne suka shigo anguwar ashe wai shirmenta ne gashi dai ta zama budurwa amma ba hankali tana tsaka da wannan tunanin taji muryar habeeb cikin dariya yana fadin sweety duk tunanina ne hakan ya fada yana me qara kunshe dariya iya kuluwa ta kulu amma itama data kalleshi taga yadda hancinsa ya wani bude yayi dirimm dashi ai saita fara dariyar itama ganin tana kallonsa tana dariya yaga yadda bakinta yakeyi shima sai dariya haka suka dinga yi sam sun manta da dije wadda tun da ta shiga daki itama ta zube ta fara tata dariyar ganin yadda lokaci daya halittar mutan gidan ta canza gashi ta kubuta daga hukuncin laifin dazu sai da tayi me isarta ta miqe ta shiga toilet tayi wanka ta canza kaya kafin ta fito falon koda ta fito bata iske kowa falon ba da alama sun shige ciki dan haka kai tsaye ta bude kofar ta fita ta shiga jido kayanta tana kaiwa dakin datake kwana sai da ta gama tsab kafin ta duba saman dinning taga an shirya shi tsaf da abinci mai rai da motsi komawa tayi tayi sallar magrib inda ta zauna tana karatun kur'ani har aka kira isha'i tayi kafin ta miqe ta fito falon bata iske kowa ba nan ma da alama masu gidan basu da niyyar fitowa dan haka ta zauna ta fara harraka abincinta sai da taci ta koshi sannan ta kai plates din data bata kitchen ta dauraye su kafin ta koma falon ta zauna kenan kuma saita mike ta fice daga part din gaba daya su kuwa masu gidan suna can cikin daki zazzabi ne ya rufe sajida yayin dashi ma gwaskan kansa ke masa ciwo ko yunwar ma ba ji sukeyi ba dan sajida ta rasa bakin cin abincin ji takeyi ya zuwa yanzu kamar bakinta ba'a fuskarta yake ba dan haka da kyar sukayi sallah suka kwanta aka shiga zaman kurame part din su naseer ta nufa tana zuwa ta shiga bubbugawa a wannan lokacin suna zaune a falo sunyi jugum suna jiran ko ta kwana jin ana buga kofar yasasu kallon juna amma kowa ya kasa motsawa nuni naseer ya shiga yiwa yusra data je ta duba waye hararsa tayi tare da maqe kafada alamun taki din bata rai yayi wai shi me gida ya zare ido alamun ta tashi amma taki jin anata bugawa ya lallaba ya miqe cikin sanda ita ma yusra ta mike ta qarasa daga bakin bedroom dinta a cewarta idan abun gudun ne saita shige daga nan kamar barawo yazo sata haka naseer ya dinga sanda kafin cikin murya me kamar rada ya ce waye? ni ce cewar dije jin muryar dije yasashi fadin lfy dai ko? eh lfy ta bashi amsa tare da fadin fatan dai duk kuma lfy kuke bai bata amsa ba illa sauke ajiyar zuciya da yayi tare da bude kofar ya ko ganta tsaye murmushi ta sakar masa tare da rabashi ta shiga ciki ya mayar da kofar ya rufe amma besa key ba saboda tsaro inji shi yusra dake can kurya tana kallon duk abinda ke faruwa har dije ta samu guri ta zauna kafin ta dan dawo falon tana yake nan dije ta gaisheta dukansu suna son su tambayeta meya faru dazu suna jin tsoro dan haka sukayi gum ganin babu me niyyar magana yasa dije takalo hira daga um sai um um haka aka dinga hirar itako dije da ba gajiya takeyi ba ta dinga digo da hira ganin da sukayi batada niyyar shuru yasa duk suka bingire suka shiga baccin karya ganin datayi sunyi bacci yasata miqewa ta fice batako tashe su ba su kuwa masu baccin karya ashe na gaske harya sacesu basu sani ba karshe dai nan suka kwana **** tun asuba da dije ta tashi tayi sallah bata koma bacci ba wardrope ta bude ta shiga jera kayanta ciki tunda ita batasan da maganar zamanta gidan naseer ba dan haka ta shirya kayanta tsaf komai ta ajiye inda zata buqata dakin yayi kyau matuka data qara gyarashi kasancewar yau friday yasa take son shiga school da wuri dan da wuri suke tashi ta fuskanci 'yan gidan basa tashin asuba a cewarta dan haka ta ce bari ta samawa kanta abin kari ta wuce abinta ga mamakinta koda ta fito saita iske saman dinning da kayan jiya karasawa tayi ta bubbude taga yadda ta barshi jiya haka yake to ko me ya hanasu cin abinci oho ita harta manta ma da abinda ya faru jiya dan haka saita shiga kitchen dan samawa kanta abinda zata ci harta yi niyyar yin nata ita kadai sai kuma taga rashin dacewar hakan duk da batasan dalilin yin hakan da sukayi ba amma dai tasan ba haka kawai bane dube dube ta shiga yi ganin botikin gyada da tayi yasata fasa dafa tea ta dama kunun gyada cikin qankanin lokaci ta gyara wake tare da markada shi ta soya kosai lafiyayye ta fito falon dashi ta kwashe kayan sama ta mayar kitchen ganin abincin ba abinda yayi yasa ta juyeshi ta sa a friedge tana fitowa ta ga sajida ta fito da alama bata jin dadi ganin yanayinta cikin kulawa dije ta shiga gaisheta ta so ta shareta amma saita amsa da kyar itako dije bata kawo komai ba ta dauka ko ciwon ne ya jiki aunty dije ta kara fada hararar ta tayi qasa qasa bata ko amsa ba ta nufi kitchen dan sama musu abinda zasu ci dan da yunwa suka tashi ganin da dije tayi ta nufi kitchen yasata fadin Aunty ga abin kari na hada mana gaba daya naga kamar bakyajin dadi jim tayi kamar ta shareta sai kuma ta tuna da masifaffiyar yunwar da suke ji dan haka cikin hade rai bako walwala ta dawo ta nufi dinning sai yanzu ta lura da ba abinda ta dafa jiya da yamma amma bata damu ba ta juya ta nufi daki bata wani jima ba saiga shi sun fito ita da habeeb dukansu yau inka gansu babu wata walwala a tare dasu gaisheshi dije tayi ya amsa ba yabo ba fallasa itako dije a ranta tace dama kun saki ranku dan indai nice tunda na ce zan zauna a gidan nan ko naman jikina zaku na yanka saina zauna din kujera taja ta zauna nan ta zuba kunun ta a cup ta dibi kosai a plate bata ko kalli inda suke ba ta fara afkawa cikinta bakaramin dadi yaji ba ganin kunun gyada da kosai yana son kunu sosai kowanne iri hakama kosai itama sajida tsintar kanta tayi da son cin kosan wanda ada sam bata ko son jin sunansa bare ace taci zuzzuba musu tayi nan suka shiga aikawa kasa da hanci ba qaramin dadi sukaji ba su duka dan haka ko bakinsu ba'aji dije ce ta cinye nata kosan ta miqa hannu da niyyar debowa cikin kula danta qara taga wayammm binsu tayi da ido inda ta kalli plate din gaban kowa taga shi habeeb saura uku ita kuma sajida sauran daya bata ko tsaya wata wata ba ta dauke nsu gaba daya cikin sauri suka kalleta amma ko'a jikinta taci mayar gabanta ta zauna ta fara ci habeeb ne yayi qarfin halin fadin ke wannan wane irin iskanci ne mu sa''aninki ne ? ah ah amma kuyi haquri naga ne ai ana barwa qarami dan ragowa ko zai bukaci kari to ku kuma naga kamar bakusan babba da yaro ba gashi ni ban koshi ba kuma ciki be san ayi masa kara ba musamman cikin kauye tunda ya riga ya saba da hatsi shiyasa na yi muku haka amma idan baku koshi ba ai naga akwai duk kayan hadin a gidan ni da ba manomiya ba kuma ban nemo na kawo ba bare ace zan hana kaga sai chair lady ta shiga ta qara maku wani tana gama fadar haka ta miqe ta shiga dakinta danta shirya ta wuce school dukansu binta sukayi da ido sajida data gama kuluwa tace wai ni dear tsoron yarinyar nan kk yi ko kuma me? ta yaya kana gani yarinya tanawa mutane rashin mutumcin dataga dama amma ka kyaleta to ke me zai hana ki dauki mataki ya fada yana me kokarin mikewa dan barin gurin au hakama zakace ko? to shikenan zan kuwa dauki matakin kamar yadda kace amma wlh matakin dazan dauka baxai yiwa kowa dadi ba dan ni ba ruwana da wata alakar dake tsakaninku ko kuma ran daddy'nku da zai baci wlh baxai yiyu ba ni ban haihu ba amma a fara kawomin jidalin dangin miji tun yanzu duka yaushe mukayi auren da har za'a wani kawomin wata watanma dangin dangarera inda ma qanwarka ce uwa daya uba daya amma cousin wlh ma an raina min hankali ta tafi gidan naseer mana ko dole sai nan yarinya sai jaraba da fitina baki kamar reza tunda ta diro gidan nan narasa kwanciyar hankali daga ni har sauran jama'ar gidan amma kun kasa daukar mataki ji yadda ka tsaya qanwar cikinka tana fada ma magana to wlh yau zanyi maganin abun ta fada tare da kokarin miqewa shi kuwa habeeb da tunda ta fara magana ransa ya fara baci tsaye yayi ya zuba mata ido itako dije ta fito kenan da niyyar tafiya ta ji sajida na sababi tsayawa tayi tana kallonta har zuwa lokacin data mike ta nufo ta gadan gadan tana kumfar baki a inda dije take bata ko matsa ba ganin sajida ta nufota yasata fadin um um Aunty um um fa ina tausaya miki wlh kada ki qaraso sajida da masifa ta rufewa ido ko jinta bata nuna tayi ba sai qara nufota takeyi yayin da dije tana daga inda take tafara dariyar mugunta abinda yabawa habeeb mamaki da tsoro kenan........ *sai kun dinga hakuri da duk yadda kuka samu duk yadda naso in samu lokaci fiye da haka baya samuwa* *Alqalamin khady*โœ [3/15, 6:29 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* NA khadija usman 2โƒฃ4โƒฃ *har kullum bakina bazai gaji ba haka alkalamina bazai gaza ba wajen nuna godiyata ga daukakin masoya na wlh banida bakin dazan gode muku dashi bisa addu'ar da kukeyimin ina rokon Allah yaqara bani ikon faranta muku Allah yasa ko bayan nagama muku ta me gari kuci gaba da bibbiyata tare da nunamin soyayya fiye da yanzu ina mugu mugun sonku fiye da yadda kuke son ta me gari* ๐Ÿ˜˜ gadan gadan ta nufo dije ita ko sai murmushi takeyi tana tsaye kyam cikin shirin zuwa makaranta ganin da habeeb yayi dije na dariya tana kuma tsaye tana jiran karasowar sajida babu ko alamun tsoro a tare da ita bare tasa niyyar guduwa hakan yasa yasan akwai abinda ta shirya dan haka cikin daka tsawa yace keeeee!!!!sajida bana son shashanci me kk shirin yi haka ? tsayawa tayi cike da jin zafinsa ta juyo tace mataki zan dauka tunda kai ka kasa ta yaya zan zauna qaramar qanwata tana min iskanci wannan wace irin jaraba ce tunda yarinya tazo ta hanani sakewa ni da gidana sannan kai ka zuba mata ido tamkar kana tsoronta to gara na kawo qarshen wannan rashin mutuncin nata wlh nagaji ko ta bar gidan nan ko kuma wlh a fita da ita da ambulance ido dije ta zaro๐Ÿ˜ณambulance fa kk ce Aunty na shiga uku kice dukan jinya zakimin to amma bakomai da sauki tunda bana mutuwa bane ko banza na mori zaman jinya dan naga in anje dubiya mutum yana tara abin arziki gashi ko ba komai ka dada samun kulawa gurin dangi dan haka kada ki damu zo ki daki iya yinki har ki gaji amma fa ki lura gurin bugun kada ki dakeni inda zanji zafin da hankalina zai fita in fama miki ciwo naga bai gama sabewa ba ni nama fasa zuwa makarantar zo ki jibgi rabonki yau hau ce ta hauni rawa zuciyar sajida ta shiga yi jin furucin yarinyar anya kuwa wannan yarinyar ba jinsin shedan bace kai gaskiya da sake lahaulawala quwwata illahbillah Allah ka rabamu da wannan jaraba shima habeeb a nasa bangaren haka ya shiga zancen zuci duk yadda akayi wannan yarinyar jinsin aljanu ce duba ma da yadda take da kyau ga farinta sak na aljanun sannan ga shegen rashin ji shiyasa ma take ita kadai gun iyayenta dama ance aljanu kishi garesu shiyasa ta hana iyayen haifar jinsin bil adama gashi yanzu ta zo ta addabe su su iyayen nata nacan suna cikin kwanciyar hankali ita kuma tana nan tana gasa su muryar ta suka tsinkaya tana fadin Aunty tunanin me kk yi kada ma kice na tauye miki haqqinki gurin yin dukan ban barki kinyi yanda ranki ke so ba bari kawai in tube ki zabi inda yayi miki ki daka amma dan Allah ki dan daki gurin nama nama dan kin dai ga yadda nake ba wani naman kirki ne dani ba tana gama fadar haka suka ga ta shiga kokawar cire hijabi tana qoqarin cire jakar bayanta basu tsinke da lamarin ba sai da sukaga ta shiga kiciniyar daga riga da alamar zata cire ke meye haka kikeyi bakida hankali ne ya fada a dan hasale rasss nake yaya kai dai kawai ka tsaya kasha kallo in zaka iya gara kabarta ta huce haushinta amma dan Allah ko da na suma ban samu nasarar ganin yadda aka fita dani aka sani a mota ba ko kuma ganin wanda ya daukeni ba ku taimaka ku dauki hoto ku ajiyemin sannan a sanar da masu zuwa dubiya musamman daga kauye in sun tashi riko abin dubiya su biyo da zabi da kaji kuma danyi kada a yanka ko a soya a kawowa aunty tayimin dahuwar 'yan birni inci in more sannan dan Allah aunty ki lura gurin dukan kada ki taba fuskata ki daki iya jiki sbd kar bakina ya nakasa ya hanani cin abincin daren yau sai dai in sha kunu da safe *oh su dije jaraba wato magana ta fada musu a fakaice* ๐Ÿ˜ ci gaba tayi da kokarin daga rigar wai ita a dole cirewa zatayi wanda inda cirewar gaske ne da tuni ta cire amma yanzu daga ta kama can sai ta kama nan ganin da sajida tayi yarinyar na kokarin yin tsirara gaban mijinta kun santa kuma da kishi haksn yasa bata san lokacin data kama hannunsa ba tajashi sukayi ciki tana ambatar ta shiga uku ba tana shiga dakin tasa key ta zauna gefen gado ta dafe kanta shima din habeeb zaman yayi dukansu aka rasa me magana itako dije tana ganin yadda sajida tayi ta saki rigarta ta kama dariya tare da daukar jakarta da hijabinta ta nufi waje tana dariya tana fadin waya gaya miki da cirewar zanyi yadda zamani ya koma yanzu maza da mata duk suna iya ma mutum fyade inje ku nakasani ke da mijinki kunga araha yanzu ba gashi na kubuta ba dan wannan me qirar mazan inda ta riqeni wlh baxan sake moruwa ba inaga sai dai na koma kauye a cikin wannan yanayin ta qaraso bakin gate yadda yake tun jiya haka yake wato hakan ya nuna musa be fito ba tun jiya daya shiga kenan sai yanzu ta tuna abinda ya faru nan ma dariyar ta kuma yi taso leqa musa amma sai ta tsinkayi horn din motar makarantar su dan haka da sauri ta fita ta shiga suka wuce **** ni fa gaskiya bazan iya ba wlh wannan jaraba har ina yarinya kamar 'yar shedan na fuskanci wata rana in tana gidan nan saita sa anzo an dau gawar mu daga Aljanu sai shaidanu duk sun cika mana gida nidai wlh asan yadda za'ayi tunda ta fara maganar yake kallonta harta gaji tayi shuru dan jim yayi kafin yace to yanzu ya kk so ayi korarta zanyi ko kuma me? bance dole ka koreta ba amma ta koma gidan naseer tunda ai ba kai kadai bane dan uwanta kina ganin komawarta can din shine mafita ? kada fa ki manta gida daya muke kuma ina son ki fuskanci wani abu game da yarinyar na fuskanci duk abinda ta lura mutum baya so to shi tafi yi yanzu kinga ai shi naseer be nuna mata abinda nake nuna mata kamar dana nuna bana son zamanta a nan amma kinga ai nan din ta dawo so inaga mafita daya ce mu lallaba ta har a hankali zansa ta bar gidan amma ki duba fa yadda taketa samu yin accident muna daga gida wuta bazata bi da khadija ba sai dai ruwa ruwan ma na sanyi dan ya zuwa yanzu na fuskanci yarinyar batada hankali shiru tayi tana nazarin maganar sa zuwa can cikin sanyin murya da marairaicewa tace amma honey ni ba zaman nata ba kaga fa cousins kuke da ita ina jin tsoron kayi mata wani kallo ba matsayin qanwa ba siririn tsaki yaja tare da fadin kinji matsalarki ai ke kishi yanzu ke ni me zanyi da wannan figigiyar yarinyar kamar kazar mayu wadda inda nayi auren wuri dana haifeta ko ke kanki kin san inda kinyi aure on time da yanzu kinada kamarta dan haka ban son shirmen banza mafita muke nema yanzu bana son shashanci shikenan zanyi kokarin danne zuciyata amma pls cikin qanqanin lokaci mu san abinyi tabar gidan nan insha Allah dan na fiki matsuwa da hakan ah ah wlh nafika eh to yanzu kam kin fini tunda dubi yadda aka haramta miki sa jambakin safe ba ya qarasa maganar yana kunshe dariya ganin yadda ta kalli madubi ta bata rai yasa shi matsowa kusa da ita ya fara aikin rarrashi ****** koda dije ta dawo daga makaranta direct part din yusra ta nufa ita kadai ta iske zaune a falo tana kallo harga Allah batayi murnar ganin dije ba duk da zaman kadaicin ya dameta dan me gidan ya fita masallaci ita kuma sajida batada wani sakewar fuska inba gaban mijinta ba nan fa sbd kissa kamar ta hadiyeka amma da zarar an barku ku kadai zata cukule dan haka bata fiya shiga inda take ba yake kawai take yiwa dije bayan ta zauna ta gaisheta suna a haka dije ta miqe tace bari ta koma part din sajida har bakin kofa yusrah ta rakota ita ko dije abin ma mamaki yake bata ganin yadda inta je guri tace zata tafi ake murnar tafiyarta fiye da murnar zuwanta koda ta shiga falon da sallama dauke a bakinta ta iske sajida zaune ita da wata mata da yara biyu cikin sakin fuska suka amsa mata su duka qarasawa tayi harda dan rissinawa ta gaida matar ta amsa mata cike da fara'a nan ta juya ta gaida sajida itama da fara'a a fuskarta ta amsa mata karo na farko kenan a zamanta a gidan shigewa tayi daki tana zuwa ta cire kagan makaranta ta shiga toilet danyin wanka da alwalawa dan gabatar da sallah tana shiga Amina ta kalli sajida tace Amarya wannan qanwarki ce halan na ganta kyakkyawa da ita masha Allah ga hankali murmushi sajida tayi a ranta tace me hankali a gwiwa dai amma a zahiri tace eh qanwata ce tunda qanwar oga ce kai gaskiya na gaba da hankalinta wlh anan take da zama kenan? eh sajida ta fada a takaice suna tsaka da haka dije ta fito sanye da doguwar riga ta atamfa kanta ko dankwali babu ta qaraso gurinsu tana hamma tare da fadin Aunty wlh yunwa nakeji kije ga abinci can saman dinning tayi mata nuni da hannu juyawa dije tayi a ranta tana yaba acting irin na sajida wato dan taga bakuwa shine take nuna kamar ba komai tsakaninsu hmmm to bari itama ta biye mata gara taci ta koshi kafin ta fuskanci qalu balen gaba tana tsaka da cin abinci su habeeb suka shigo su dua ukun habeeb,naseer,sai doctor yusif suna shigowa suka zauna naseer ya cire waya ya kira yusrah ba jimawa kuwa saigata tazo nan fa aka shiga hirar yaushe gamo itakam dije saida ta tabbatar ta koshi kafin ta qaraso falon ta shiga gaishesu dukansu suka amsa cikin sakin fuska juyawa tayi taja yaran sukayi cikin dakinta ta shiga yi musu wasa sai da akayi sallar la'asar kafin su yusuf suka fara shirin tafiya suna harrakawa dije ta gito da yaran kallonta doctor yusif yayi kafin yace Auntyn yara kun gaji da wasan kenan da har muna shirin bar miki su murmushi tayi kafin tace to ai ni koda an barmin ina so wlh to tunda kina so ki bisu gidansu kiyi kwana biyu cewar sajida aikuwa Amina tayi caraf tace wlh kuwa da naji dadi dan dama in Abban Anwar ya fita rasa 'yan hira nakeyi kinga sai kiyi mana weekend ko sister me zai hana ai ko cewa kk yi ta dinga zuwa duk week tana muku weekend bakuda matsala dan haka ke jeki shirya ki zo ku tafi cewar habeeb mamaki ne ya cika zuciyar dije ganin yadda ake ta tallarta dan haka saita maxe tayi kamar bata ji su ba naseer ne me fadin ai khadija batada matsala akwai dadin zama dan haka Allah ya taimaka haka sukaita tunzura har saida Amina ta dameta ta dauko kayanta kala biyu ita kam taga ikon Allah yau koda suka zo shiga mota har rige rigen bude mata mazan da matan keyi koda ta shiga ta zauna da sauri suka rufe ji kk yi bammmm ita abin nasu ma dariya ya fara bata dan haka saita bude motar da niyyar fitowa cikin hada baki suka tambaye ta ina zaki kuma? kallonsu tayi daya bayan daya kafin tace mantuwa nayi zan koma in dauko da sauri habeeb yace wa sajida matso ta fada miki abinda zaki dauko mata basaita fito ba idanma yana nesa ne to ki fada mata sai ta dauko akwatin in kin dauka saita mayar kada ki samu damuwa 'yar qanwarmu.......... *Allah ya raka taki gona dije* ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ *Alkalamin khady* โœ [3/15, 6:30 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* NA khadija usman 2โƒฃ5โƒฃ ita dije abinma dariya yabata ganin da gaske sukeyi yasata fadin ah ah a barshi ma nafasa daukar yauwa 'yar albarka kuje kawai yusuf Allah ya kiyaye sai munyi waya cewar habeeb shikam yusuf dariya yaketa yi ciki ciki dan yasan wannan tunkuda dijen da sukeyi wlh ba banza ba haka yaja motar sa suka fita mutan gidan nata daga musu hannu kamar dangi sunzo rakiyar mutum zashi saudiya๐Ÿคฃ suna ganin sun fice a gidan duka suka ce Alhmdllh Allah ya raka taki gona ameen inji matan nan kowa yayi nasa wuri da matarsa ****** saida ya biya ya dan yi musu siyayya kafin suka wuce gidan ba karamin mamaki dije tayi ba ganin haduwa da tsari irin na gidan doctor yusuf lamarin bai qara rikitata ba saida suka shiga palon gidan gaskiya masha Allah ya hadu iya haduwa suna shiga ita da yaran suka qarasa saman kujerar suna tsalle ita kuma ta qarasa a hanki ta zame qasa dan ta zauna yayin da taga doctor yusuf yayi wuf ya shige daki tare da ledar daya yo musu siyayyar da ita yana shigewa kuwa ta tsinkayi muryar wata dattijuwa na fadin to to andawo jaraba ta dawo da yau bakina shuru gidan tsit na yi bacci na cike da annushuwa da mafarki me dadi amma yanzu daga dawowarku har kun ajiye shaida ina shi yusuf din yake naga duk na ganku amma shi ban ganshi ba ince dai ba wani abun ya siyo kuka munafunce ni aka shige dashi ciki ba ko? ikon Allah cewar dije data tsaya tana kallon sababi jin dije tace ikon Allah yasata juyawa gurin sai yanzu ta lura da ita to ita kuma wannan sadakan yallan daga ina iyayen kwashe kwashe? yusuf ne ya fito cikin fara'a yace qanwar su habeeb ce ta zo mana weekend washe baki tayi tare da fadin ah ah Allah sarki nako ga kama kamar an tsaga kara kice ke 'yar gida ce ai na dauka kina daya daga cikin irin kare arzikinka ta fada tana me wurgawa Amina harara Amina wadda idan da sabo ya zuwa yanzu ta saba da halin hajiya hauwa dan haka ta qara dukar dakai sbd bata son tayi wani motsin kirki yanzu a qarewa iyayenta sababben zagin yau da kullum tun da ta auri yusuf take cikin wannan halin da hajiya hauwa wadda mahaifiya ce ga yusuf din a cewarta bata so ya auri 'yar talaka ba wadda zasu qarar da arzikinsa gara ya auri 'yar masu kudi to da yake da rabo gashi harda yara biyu haka kawai ta tattara kayanta ta dawo gidan da zama kullum bata bacci har sai taga shigowar yusuf kuma ta tabbatar be shigo da komai ba da kanta take kulle qofar falon ta rike key din a gurinta da asuba ta zo ta bude wai duk dan kar aje ko ya boye abinda ya siyo a mota saita yi bacci ya dauko iya kyautatawa yusuf nayi mata duk wani jin dadi ya dauke mata shi amma sam bata gani taki barinshi ya sarara su biyu ne yaranta daga shi sai qanwarsa farida wadda yanzu haka tana aure a kd ne bata fiya zuwa ba sbd batajin dadin yadda mahaifiyarsu keyi gashi amina nada kirki sosai to ku haka ake bakuwa kusata ta zauna qasa ta fada tana me karasawa inda dije take zaune tashi kinji ai daga ganinki ke jinin arxiki ce kin saba da hutu ji fatarki ina ke ina zama a kasa tashi ki zauna kinji duk inda yayi miki ki zauna ki mike kafa ai tunda jinin su habibu ce ke bakida matsala dan yaran kirki ne sun san mutunci ita dai dije ta kasa magana haka hajiya ta dinga tantadinta harta gaji aka kira sallar magrib kowa ya kama gabansa Amina ta kai dije dakin da zata zauna bayan tayi sallah ne tana zaune kan dadduma Amina ta shigo dakin da sallamarta dauke da faranti a hannunta amsawa tayi tare da qara gaisheta ta amsa cike da fara'a kafin ta ajiye ta nemi guri ta zauna tace ya bakunta .sunkuyar da kai dije tayi kafin tace Alhmdllh nan da can ai duk dayane to Allah yasa haka kika dauka harga zuciyarki wlh dagaske nake Aunty ina yaran ne? kin san suyi jaganiya yauban gaji ina musu wanka har sunyi bacci toh da wuri haka ? wlh kuwa ga abinci nan kici sai dai kiyi haquri da abinda kk gani ban sani ba ko baki saba da cin irinshi ba kiyi haquri tun safe kafin mu fita hajiya tasa aka dafa amma dayake kin zo da kafar dama nasan gobe za'a canza insha Allah yauwa Aunty dama abinda ya dan dameni nake tunanisa yanzu kenan meyasa kika zauna tana ci miki mutunci haka duk da ban sanki ba ban san halinki ba amma na yaba miki Allah inda nice ko hmmm da tuni an wuce gurin kallonta Amina tayi tare da yin 'dan murmushi kafin tace kuruciya kenan ai ko kece khadija ba abinda zakiyi illah hakuri ko dan albarkacin kina auren danta sannan ko ba komai nasan wata rana sai labari tayi duk yadda take so nasan wata rana in ance tayimin ba bazatayi ba tabdijam wlh Aunty baki sani ba ne irin wadannan tsoffin zeyi wuya subar mutum ya sarara gasu da shegen tsawon rai yanzu wannan saita iya qara hamsin ko ma fiye nan gaba dariya Amina tayi tace kai khadija to ya za'a gansu kuwa lokacin ai qanqancewa sukeyi kiga sunata komawa kamar masu cutar tamowa qarshe sai dai kiga ana sasu a baro in kuma sunada gata ne zakiga ana turasu a keken nan na jarirai da suke koyon zama kai khadija๐Ÿ˜‚ Allah kuwa Aunty halan baki taba gani ba? ah ah Allah bai taba gwadamin ba to kuwa kiyi addu'a sosai dan ga alama nan a gidanki dariya Amina tayi tana qoqarin mikewa tace ni dai ci abincin kafin in dawo musha hira to tana dai bari ayi hirar ko? ai na fada miki ke da sa'a kika zo gidan tunda har fada tayi wai laifinmu ne da bamu kirata munce zamu taho dake ba gashi yanzu munja mikk cin tazarce dan haka kada ki damu ke din da hajiya kun jone murmushi dije tayi a ranta tana kissima yadda zata saita hajiya Amina na fita dije ta jawo farantin gabanta din ta bude wake da shinkafa ne mai da yaji ai kuwa dije dadi taji maimakon taji haushi dan ta dade marabinta da ci a ranta tace inba ma dai abin da izgili ba ai wake da shinkafa abin marmari ne dan dai kawai anyi hakan ne da mugunta sai da taci ta koshi sannan tayi sallar isha'i tana tsaka da sallar taji an turo kofar dakin au to ana nan ana gaida ubangiji kenan to Allah ya amsa ta nemi guri tazauna saida dije ta gama addu'ointa kafin ta juyo tayi mamaki ganin hajiya zaune amma saita maze ta shiga gaisheta cike da fara'a ta shiga amsawa kafin daga baya ta fara zubawa dije surutu ganin da dije tayi tasamu abokiyar yi yau yasata cire hijabin datayi sallah ta gyara zama kallonta hajiya tayi kafin tace Allah me halitta kenan yanzu ke wannan farin nske baya damunki ji beki fa waima da dare kenan ina ga rana au dama fari yana damun mutum sai kace na Allah ya isa eh mana kin ganki kuwa nifa inba idona ne yakemin gizo bahar wani yellow yellow naga kinayi ko ma dai harda shawara farin nan naki ah ah ba shawara bace ai da kin lura da kyau da zakiga kwayayen lantarkin da aka jona min suna kawo wuta๐Ÿ˜  rike baki tayi tare da nuna al'ajabi tace wuta kuma a jikin mutum yarinya? eh mana ai zamani ne yazo da hakan ke kanki nasan da'a zamaninku akwai wannan fasahar to wlh da ke za'a fara gwadawa a kanki ah ah wallahi daina jamin jafa'i tunda Allah ya tseratar dani oh ni hauwa'u yanzu har takai ga bature yayo wayar da za'a jona jikin mutum to meye amfaninta ga amfaninta nan kin gani irinku masu gani suki kyalewa yake haskawa hanya yanzu ba gashi har kinga yadda fatata take haske ba uhmmm lallai lamarin babba ne ta fada tana me rike haba itako dije kuluwa tayi cewar da tayi farinta da kuma shawara ke damunta shiyasa ta matsu ta tashi ta tafi ganin taki tafiya saima qara malkwado wani zancen takeyi yasa dije miqewa ta shiga toilet batare datace da ita ko kala ba wanka tayo ta fito daure da towel a jikinta aikuwa caraf sai ji tayi tace oh ni 'yasu ke ko wannan yarinyar kina cin abinci kuwa ? ji kashin wuya kamar a zuba tiyar hatsi ai in kinji ci daya ma kenan ni ko ke cin abinci wannan kashin wuyan nawa da kika gani wani sirri ne bari ma in fada miki daya a ciki ko wanka da kikaga nayi yanzu bada sabulu nayi ba dan ni sabulu na najikina ๐Ÿ˜ณ jikinki kamar ya? ai sbd ramar tawa da tayi yawa wata rana ina wanka lokacin an siyo mana wani sabulun wanka girmansa yakai kwanan sha to shine fa ina cikin wanka dashi na nemeshi na rasa nayita nema ban gani ba hae na haqura nace bari nayi da ruwa kawai ina zuba ruwan naga kumfa na tashi shine fa na fara lalube koda na duba sai naga ashe lokacin da nake murzawa ya subuce ya fada cikin kashin wutan nan nawa da kika magantu akan shi to da nayi niyyar in dauko shi kawai sai nace bari in barshi na huta idan na tashi yin wanka ba saina sha wahalar murza sabulu ba qarya kikeyi dan uwarki ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ taji hajiya ta fada ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ *managed pls* *Alqalamin khady* โœ [3/15, 6:31 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* NA khadija usman 2โƒฃ6โƒฃ *ina jinjina gareku khadija fans novels 1,2,da kuma 3 tare da tame gari fans da kuma hausa novel 1,2,3 da zama na amana 2 Facebook gaskiya na yaba sosai da comments dinku ina kuma godiya da addu'arku gareni kamar yadda kukemin kuma Allah ya biya muku bukatunku* *bazan manta daku ba kuna raina kuma ina ganin comments dinku gaskiya ina godiya Allah yabar kauna* *jattako novels fns* *sadnaf novels fns* *zauren mai dambu group* *Hikayar marubuta* *online writters groups* *Arewa novels fans* *da duk wadanda ban fade su ba suna raina wlh ina kuma mugu mugun ji da ku* ah abin harda zagi kuma hajiya babba ai dole in zage ki ke yanzu inba kin rainan wayo ba ta yaya zaki cemin wai sabulu ya bace a jikinki ko da dan mitsili ne bare kuma girman kwanon sha anya ma kuwa kinsan kwanon sha kuwa? a haifeni a kauye kice ban san kwanon sha ba hajiya ni ko na sanshi kawai ki yadda da maganar da na fada miki na rantse da Allah bazan yadda ba dan ko'a tarihi ban taba jin makamancin abinda kk fadamin ba sai kace sabulun aljanu *yauwa anzo wurin dije ta fada a zuciyarta* au to wai da ke kin dauka sabulun na mutane ne? to amma ai ke kikace wanda ake siyo muku na kuwa san babanki ne ke siyowa ko kuma ai mutum ne shi ko kuwa kina son kicemin yasan dandalin aljanu acan ya siyo muku to da nace miki ana siyo mana ai bakiji nace miki ga wanda ya siyo ba ko? eh kuma fa hakane amma ke inba karyar jaraba ba a ina kikaga aljanun da har zasu siya miki sabulu murmushi dije tayi kafin ta nufi kofa ta murza mata key ta dawo ta rufo toilet ma sannan ta fara leqe leqe kamar munafuka hajiya ta bita da kallo kafin tace ke wai uwar me kk leqawa haka sai zagaya ni kk yi kamar kin kama akuyar mayu shiiiiii dije ta dora hannunta a saman bakinta ina zuwa kedai saida ta gama 'yan dube dubenta kafin ta kalli hajiya tace wani sirri zan fada miki bana son kowa yaji shiyasa sirri kuma? wane irin sirri duk ke 'yar nan duk duniya ki rasa abokin da zakiyi sirri dashi sai ni anya ba yankani kike shirin yi ba kuwa dan ni wlh inda abinda nake tsoro yanzu bai wuce mutuwa ba in kin san abinda zaki aikata min kenan gara ki sanar dani dan manzo kai hajiya wlh kin fiya tsoro to dama maganar da kk takalo ce ta Aljanu kin ganni nan to inada su sunkai miliyan daya a kaina innalillahi wa'innailaihir raji'un miliyan daya fa kika ce ?to ni dai ko a mazahabar jama'u ban taba jin kan mutum ya dau Aljani fiye da dari ba daya ba shima cikon na darin danna mutuwa ne shiyasa amma ke kice har miliyan daya sai dai in kece aljanar da kanta to Alhmdllh tunda kin fahimta shikenan na fahimci me ?ba dai da gaske ke din aljanar bace? eh ah'ah rabi mutum rabi aljan nake ๐Ÿ˜ณke 'yar nan fadamin gaskiya in san abinyi tun wuri ai gaskiyar kenan abinda yasa ma kikaga na tsaya haka sbd naga yadda kika karbeni ni shiyasa ni bana cutarwa da kike ganina ina rayuwata ne cikin bil'adama amma ina azabtar da duk wanda yake kuntatawa jama'a su kuwa masu shiga tsakanin masoya ko ma'aurata kashe su nakeyi gaba daya masu gani ba kyalewa kuwa kamar masu tanka halittata su kam bakin nake murgudewa in tsiyayar da idanunsu ta yadda bazasu moru ba sannan in......... wayooo na shiga uku hajiya ta fada da karfi yusuf da Amina da tun dazu suka zo da niyyar susha hira da dije suna dab da shiga suka tsinkayi hirar hajiya da dije akan sabulu suka tsaya suji yadda zata kaya ai tunda sukaji dije tacewa hajiya ita aljana mutum.ce yusuf ya tuna da yadda naseer ya basu labari dije tayi musu aikuwa nan ya kama dariya Amina ta kalleshi kasa kasa take tambayarsa janta falo yayi ya fara bata labari kafin yace nasan ta fuskanci halin da muke ciki shiyasa ta bullo mata ta wannan hanyar marairaice fuska Amina tayi kamar zatayi kuka tace haba Abban Anwar baka tunanin hakan ya cutar da ita kaga fa tsohuwa ce in jininta ya hau fa? hakanma bazai faru ba nidai kawai fatana Allah yasa wannan yarinyar ta zama silar shiryuwar hajiya ta barmu mu zauna lfy kinga ni tashi mu zaga ta bayan window musha kallo kinji my choice jiki ba kwari ta mike ya kalleta yace haba mana ki saki jikinki pls kin san dai hajiya mahaifiyata ce bazan so abinda zai cutar da ita ba ko nasan halin yarinyar a sai dai ta firgitata kamar yadda ta firgita wadancan kartin tunawa tayi da labarin daya bata aikuwa ta kama dariya suna tsaka da haka suka jiyo ihun hajiya da gudu suka fita suka zaga ta window suka danyi slide dinsa kadan suka kama kallo ni fa ki daina min ihu me nayi miki ? kinga dan Allah yake muminar aljana kiyi haquri daga ganinki hwlh anga me afuwa wlh ban aikata ba duk abinda kika ga inayi ciwon sanyi ne yake tabani badan ma kar ince ki tambayi yusuf ba nasan bai sani ba da nace ki tambayeshi to tun ina budurwa na hadu da matsalar sanyin kwakwalwa inya bugani sai inta abu irin na marasa hankali ni dama tunda na ganki nasanke ba mutum bace amma da naga kuna yanayi da su habibu saina yadda ashe ke mutum aljan ce nasan suma basu sani ba amma ina rokonki da kada ki kasheni inada marayu kinga ni ke kula dasu gashi...... to wai laifin me kikayine da zan kashe ki? nasan nayi kuma kema nasan kin sani kawai kina son kiyimin kisan rashin imani ne bayan kin murgudemin baki kin tsiyayarmin da idanu ki tausayamin ki duba tsufacda furfurata ki duba qananun yarana au har yanzu kina haihuwa dama? ah ah yusufa da farida mana in an hada da irin shekarunki ai kinga su jarirai ne ko? hakane ina zuwa kaya ta ciro tasa dan sanyi takeji kafin ta dawo ta zauna akan bedside drower ta dora data kan daya kafin tace hajiya cike da rawar baki ta amsa ya zuwa yanzu tayi zaman dirshan bisa tiles na'am ranki ya dade me haskrn sallah dan naga ke din musulma ce ko a cikin aljanun kinada imani bakya wasa da ibada duk naji yanzu dai ki fadamin dalilinki na hana yaranki sakewa da iyalansa kika zo kika takura musu kika...... kinga duk basai kin fada ba nasan kin sansu wlh sharrin ciwon sanhi ne kamar yadda na fada miki amma ina nan ina neman magani oh kenan shi kesa kike aikata abinda kikeyi ? sosaima kuwa ni tsorona ma kada yasa in aikata kisan kai gara in nemi magani tunda wuri ai indai magani ne kin gama samu dan ni har maganin dayafi nashi ma ina bayarwa cikin hajiya ne yace quuuuuuu cikin sauri ta yamutsa fuska tace ah ah bama sai kin bayar ba dayake na karbi wani ina kan aiki dashi yau ma wa'adin zai cika nasan gobe na warke to shikenan naji amma yanzu dole ki karbi hukuncinki na yin katsalan dan da tanka halittar Allah da kuma shiga shirgin daba naki ba haba yallabiya kiyi haquri sharrin shaidan ne da kuma.... ganin da dije tayi duk hajiya ta hada zufa duk da sanyin A.C dake dakin ga kuma fanka saita bata tausayi dan haka ta rage abinda tayi niyyar yimata sbd gudun kada taje jinin tsohuwa ya hau ta shiga uku garin gyara ayi barna shikenannaji tunda kin bada haquri kuma kin smu maganin cutar dake damunki ba matsala zan kyaleki amma daga yau kullum da dare zan dinga kwana gidan nan sannan da rana zan ding zuwa zagaye batare da kowa yasani ba inga halin da ake ciki idan naga baki warke ba sai in dora da nawa maganin wlh nama sn zan warke sannan kada ki sake inji in fadawa kowa ni ba cikakkiyar mutum bace dan ba wanda yasani wace ni ai ni banida wannan subutar bakin nifa banda yanzu magana ma bata dameni ba ta fada tana me marairaice fuska sai da dije ta dan yi murmushi ganin yadda ta danyin ita ko hajiya da qarfinta ta yunkura tace Allah ya baku haquri ni zan tafi dan wlh bacci nakeji kije ina ai ke tare zamu kwana dake da waya kawoki? wlh dama zuwa nayi in shiga bandaki tsautsayi ya ritsa dani oh dama anan kike shiga toilet din dakinki babu ne ko me? kaddara wlh kaddarar haduwa da ke tkawoni ko kafin dije ta bata amsa har takai bakin kofa dije na shirin yin magana taga tsohuwa ta bude kofa ta sheqa da gudu ba ko waiwaye aikuwa nan ta fada saman gado ta dinga dariya su yusuf ma dariyar suka shiga yi suka zagayo koda suka shigo dakin dije nata dariya saida yusuf yace sannu da gama rikitamin uwa bata daina driyar ba gnin hakan yasa amina tace kaga mu gudu fa kar a ritsa damu ko na gasken sunzo nan suka juta suka fita har sun wuce yusuf ya nufi dakin hajiya yana zuwa ya tura yatji shi bame gam ya kwankwasa amma shiru kk ji dariya yayi a fili yace Allah yasa ki gyara Ameen *Alqalamin khady* โœ [3/15, 6:32 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TA ME GARI NA khadeeja usman 2โƒฃ7โƒฃ up up up irin wannan cigiya haka masoya tame gari lallai dije tasha jaje to an nemota da kyar tace a gaisheda masoyanta dan haka ina muku fatan alkhairi tare da jinjina da miqa godiyata gareku masoya ta me gari masu yimin magana ban samun amsa musu da wuri suyimin uzuri ba lallai dan an gani online ya zamana ina kan whatsapp bane ta yiyu wani uzurin nakeyi amma naji wasu masu abar a kusa sun fadamin magana amma banji haushi ba nasan so ne ya kawo hakan amma kuyi haquri jin da hajiya tayi ana buga kofar yasata saurin shigewa toilet ta rufo har saida taji bugun ya lafa ta jima a cikin toilet din jin da tayi an daina bugun yasata dan bude qofar ta ziro kai kasancewar a tsorace take sai taji kamar muryar dije na fadin ku bita bandakin ku kamota ai kuwa da sauri ta fito ta fara qoqarin shiga cikin wardrope din amma kasancewar ba irin wadda mutum zai iya shiga bace abu ya gagara ganin hakan yasa ta tura kanta kasan gado tare da jan ciki harta shige duk wani motsi da zatayi gani takeyi dije na kallonta yayin data dinga karanto duk wata aya data sani kai harda hadisai gashi ba damar tayi juyi haka ta kwana a gurin batare da tayi baccin kirki ba har aka kira sallar asuba a kunnenta kafin ta zamo ta fito ta shiga toilet da kyar tayo alwala aikuwa tunda tahau sallaya taketa jera salloli tare da addu'ar Allah ya kareta daga sharrin jinni๐Ÿคฃ ita ko dije saida tayi me isarta kafin ta miqe ta dauro alwala ta haye gado ta kwanta cikin zuciyarta tace oh ni dije ina karya da aljanu ina cin uban mutane Allah yasa dai basa ganina bakuma sa jina kada su zo daukar fansa tana wannan tunanin ko itama taji kamar motsi a dakin aikuwa da sauri taja bargo ta rufe har kanta ta fara karanta ayatul kursiyu ni ko nace su dije ashe ana....... ๐Ÿ™Š ***** washe gari yusuf na dawowa daga masallaci gari ya danyi haske dan dabi'arsa ce inyaje sallar asuba baya dawowa sai gari ya waye tarr yana shigowa ya riski hajiya a falo da gima giman jakunkunanta cike da mamaki ya karasa gabanta ya duka ya shiga gaisheta ga mamakinsa amsawa tayi cike da fara'a kafin tace kun tashi lfy dai ko ? duk lfy kalau am ya naga wadan nan jakunkunan kuma na miye? nawa ne dama na yanke shawarar komawa gidana jira nakeyi ma ka shigo ince kasa a gyara shi yanzu dan nasan yayi kura a zuciyarshi yace lallai khadija kin iya saiti amma a fili saiya marairaice fuska yace haba hajiya me yayi zafi haka laifin me muka miki da har zaki ce zaki bar gidan nan lokaci daya kuma da gaggawa haka idan munyi miki laifi ne ai saiki fada mana mu gyara inma ita Aminan ce tayi miki wani abu ai saiki fadamin in dauki mataki a kanta dan baxan lamunci a bata miki ba kafin ya gama rufe baki sukaji budewar kofa Amina ce ta fito sanye da dogon hijab dinta tare da carbi a hannunta fitowarta yayi dai dai da fitowar dije itama kusan a tare suka qaraso falon suna zuwa Amina ta gaisheda hajiya ta amsa cike da sakin fuska sabanin da dasaita samu rabon zagi koda dije ta karaso gurin kowa ta shiga gaidashi koda ta zo kan hajiya ta gaisheta sam kin amsawa tayi sai dai ta maido mata da gaisuwar itako dije ta ci gaba da gaisheta jin ta kuma maido mata yasa tace hajiya aini ya kamata in gaisheki ranki ya dade dukansu kallonta sukayi ganin yadda ta ke duddukar dakai itako dije tace haba hajiya meye abin ranki ya dade anan dan Allah ki bari kada kisa su yaya su zaneni duka fa kikace wane mutum ai ba wanda ya isa ya tabaki ya kwana lfy inaaaaaa ai kinfi karfin kowa ganin yadda takeyi yasa dije saurin dakatar da ita ta hanya fadin wadannan jakunkunan fa baki akayi a gidan? yusuf ne yace inafa baki a rigimar hajiya ce a motsa wai ita dole saita koma ainihin gidanta data fara zama kiji fa kawai rana tsaka tace zata tafi ai dole mu binciki kanmu ko mu tambayi dalili dan ni bazan taba yarda ta tafi ta barmu ba bayan kowa a gidan nan yasaba da ita aikuwa dole in tafi in barku ko kuna so ko bakwa so dama can lalura tasa na zauna daku ba komai ba dan in kula da yadda zamanku zai gudana insa muku ido kasan ku yara farkon aure sai ana lura daku dan kun fiya rawar kai yanzu kuwa naga kunyi hankali ai gara in tattara in koma inda nafi wayo ko haba hajiya gaskiya ni ban goyi bayan ki tafi ki barni ba in su Anwar suka tafi school ni da wa zan dinga zama yana debemin kewa cewar Amina haba 'yar albarka ai zaki saba da sannu kinji kada ki damu zan dinga zuwa lokaci zuwa lokaci ina duba ku ai kallonta dije tayi kafin tace au kice ma kin tafi baki tafi ba kenan tunda zaki dinga zuwa ah ah ina nufin su in sun sami dama su dinga zuwa dubani ni me zanzo nayi a gidan yara kuma dukansu saida sukayi dariya kasa kasa a haka suka tsinkayi muryarta tana fadin ke Amina maza tashi ki dora abin kari mana kada abar bakuwa da yunwa a ranta tace duk da nasan ya zuwa yanzu Allah kadai yasan irin abincin data dibga taci na mutane taci nasu na aljanu amma a fili taci gaba da cewa ki debe duk abinda yakamata a girka kinji harda farfesun kajin nan duk ayi kada su lalace toh Amina ta amsa tare da mikewa ta nufi kitcheen a ranta tana hamdala tare da godewa khadija data zama silar ganin wannan ranar a gurinta tana shiga ta shiga hada kayan break masu rai da motsi irin wanda yakamata ace wanda ya taka matsayi irin na yusuf ana ci a gidansa tana tsaka da aikin dije ta shigo da sallamar ta ta qarasa inda take ah ah haba ranki ya dade ke da kanki a kitchen kuma dariya dije tayi kafin tace kai Aunty kema kin zama hajiyar kenan ba dole ba irin wannan aiki da kikayi shekara da shekaru muna zaune da mata yau kinsa zata bar gida rana tsaka au to tunda bakya son ta tafi bari inje in dakatar da ita ai ba matsala ni na isa wlh ta tafi na dinga zuwa gaisheta ai kedai Allah yayi miki albarka wlh kin gamamin komai duk da cewa uwar miji uwa ce amma ita tata matsalar tasa na gundura da zamanta yanzu kuma Allah yakawomin mafita kice wai ta zauna ai sai dai kice in shirya yin rakiya dariya dije tayi kafin tace ai na dauka kin fi son zaman nata ne da sai ince tasha zamanta kawai ta qarasa maganar tana dariya itama Amina dariya tayi nan dije ta kama mata aikin suka gama sunata hirar hajiya akan abinda yafaru jiya yau kam gida ko yara sun san ya canza inda kowa yaci yasha cikin nishadi bayan an gama ne yusuf yasa wani yaronsa yace yaje yasa a gyara gidan hajiya aikuwa cikin qankanin lokaci aka gama komai ya kira ya sanar masa an gama .saida yadan qara sayen wasu abubuwan aka dan kwaskware gidan abinka da masu abin cikin qanqanin lokaci aka gyara ko ina fess tunda dama bawani komai gidan keda ba kawai kura ce koda aka tashi tafiya hajiya kuka ta fara yi a ranta tana ta jama dije Allah ya isa data rabata da kujerar ta ta mulkin mallaka a gidan danta wadda bata tashi yin ritaya yanzu ba amma ko wannan ko'a cikin aljanun ta cika marar imani nan dai ta dinga sharbar majina har gida aka rakata yayin ita da dije ke zaune a bayan mota ko motsin kirki hajiya ta kasa har suka isa sam ba wani farin ciki a fuskar hajiya hakan yasa dije rabawa ta bayanta ta rada mata a kunne naga alamar cutar sanyin nan bata rabu dake har yanzu dan haka zan kawo miki magani anjima kuma wlh kada ki sake inga kafarki kwana kusa kin koma gidan nan duk abinda kike buqata ki kira ki sanar za'a kawo miki in na bukaci kije zanzo cikin dare in sanar mikk kije naga yanzu kina ta kuka nasan kukan da kikeyi ko na miye ki kiyaye gyada kai hajiya ta shiga yi a hankali tace naji ranki ya dade yusuf da duk abinda dije keyi yana lura da ita dan haka ya saki murmushi a ranshi yace khadija hooo duk wanda ya aureki zaisha fama haka suka gama zama a gidan hajiya bayan yusuf ya kira wata qanwar hajiya akan ta zo su zauna tare sannan yasa a nemo musu mai aikin da zata dinga kula da gidan tare da me gadi nan sukayi musu sallama bayan ya vasu kudi tare da sanar dasu gobe zai dawo in Allah ya yarda haka hajiya tanaji tana gani suka fice zuciyarta kamar ra fashe amma ba halin bayyanawa tana tsoron mutum aljan ***** yau kwanan dije biyu a gidan yusuf kuma yaune zata koma gida yayin da kallo daya zakayi ma masu gidan ya zuwa yanzu ka tabbatar suna cikin nutsuwa tunda akayi sallar la'asar dije ta shirya ta zo ta kame a falo masu gidan ne suka fito suna dariya da alama hirar tayi musu dadi ganin dije da sukayi a zaune yasa su fadin ah ah ranki ya dade dan yanzu sunan da suke fada mata kenan tunda sukaji a bakin hajiya me zamu gani haka kamar an gaji damu? murmushi tayi. kafin tace ba batun gajiya illa dai inason in koma ne dan nayi kewar mutanen gidan hmm kajita sai kace ba ita tacemin nan da can duk daya ne ba cewar Amina bar ma ta wannan su wadanda take cewa tayi kewar tasu tunda tazo ko waya basuyimin ba sabanin da da kullum sai munyi waya da safe kinga alama ta nuna su basuyi kewarki ba kamar yadda kike cewa ke kinyi ta su to ya za'ayi su kira kuce sunyi rashin kunya inaga shiyasa suka ki kira ah ah ko dai ko dai?? ko dai me ? ko dai an gwada musu irin na hajiyata ne shiyasa suka shiga taitatayinsu dariya tayi kafin tace ina ni ina yiwa ysyyena haka kunga ni duk ba wannan ba gida nake so na kuma gama shiryawa a zo a kaini ko in hau taxi rufa mana asiri ai mu bazamu yadda mu batawa mumina rai ba haba wane mu tashi maxa ki kimtsa in maida ke salin alin ni nagama shiryawa ina yarana muyi sallama nofal na bacci Anwar kuma yana gidan hajiya ko kin manta ok hakane to bari mu mike mu saita hanya ta fada tana kokarin miqewa Amina tace ta jirata inda tshiga ciki ba jimawa ta fito dauke da leda a hannunta ta damkawa dije da farko kin karba tayi saida Aminar ta nuna rashin jin dadinta sannan ta karba fayi godiya har bakin mota ta raka su inda dije ta kame kyam a baya ba yadda basu yiba ta hau gaba tace ita tafi jin dadin zaman baya dole suka haqura suka kyaleta a hanya ya tsaya ya qara mata siyayya inda suka nufi gida koda suka iso yamma ta danyi kasancewar yau weekend duk bamai zuwa aiki yasa mutan gidan suka zo garden suka zauna duka suna hira ana nishadi gabansu kayan fruit ne sai lemuka da ruwa inda duka suke hira ana babbaka dariya sam sun ma msnta da wata wai ita dije tunda kowa ya warke๐Ÿคฃ horn din da suka jiyo ne daga bakin gate yasa suka maida hankalinsu gurin inda sukaga motar yusuf ta danno kai kasancewar gilashin gaban a bude yake yasa ba'a suka ga ba kowa ciki sabanin na baya dayake a rufe๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TAME GARI* NA khadeeja usman 2โƒฃ8โƒฃ kasancewar bayan motar a rufe yake yasa basu ga dije ba har yusuf yayi parking kafin ya fito ya zagaya ya budewa dije data kame kam kai kace wata hajiya ce innalillahi wa'inna ilaihir raji'un sukaji naseer ya fada habeeb da sajida da hankalinsu bai kai ga dije ba suka ce meya faru kk wannan salati Annoba ta dawo cewar yusra habeeb daya gutsuri apple kenan tsayawa yayi shi bai hadiye ba kuma bai fito da ita ba duk sun kasa motsawa sallamar dije ce ta farkar dasu inda ta shiga fadin Assalamu alaikum my brothers n'd sisters gaskiya nayi missing dinku duk da naga ku kamar bakwa farin ciki da dawowata ma dan naga fuskokinku kamar wadanda aka aikoma da mutuwa waya isa yace baya farin ciki da dawowarki cewar naseer yana yake ko ba haka ba duka gyada kai sukayi amma banda sajida data hade rai sosai ganin hakan da dije tayi yasa itama ko kallonta batayi ba ta nemi guri ta zauna yusuf ne ya miqa musu hannu suka shiga gaisawa bayan ya samu guri ya zauna kafin yace to ga kayan aro nan na dawo muku dashi kada ace na riketa waya ce da kadawo da abinda aka ara maka din ? ai da nan da can duk dayane daka barta ma a can din ba matsala da sai a biyota da kayanta khadija ai tafi karfin a bada aronta sai dai kyautarta kawai cewar habeeb daya qarasa hadiye apple din bakinsa dayaji tazamar masa kamar dutse ah ah so kukeyi matanku su yankomin sammaci suce na dauke musu 'yar qanwarsu babu ruwana wallahi indai mune bakada matsala ai munada kakkyawar fahimta da mazajenmu komai suka yanke bama musawa cewar yusra au hakane to tunda hakane bari inyi farin ciki dan na lura bazan sha wuya gun dauketa gaba daya ba cike da rashin fahimtar maganar tashi habeeb yace kamar ya gaba daya kuma ai dole zatayi aure ko? ah to idan kuma ya kasance nine zan aureta din fa dammm kirjin habeeb ya buga domin jin furucin da yusuf din yayi ji yayi zuciyarsa tayi masa zafi cikin dan zafi yace ita kuma Aminan ka kai ta ina ? sajida da sai yanzu tayi magana tace tana nan a gidan nasa ku maza kunya ce daku in kun tashi kara aure ah ah Aunty na ai a aure ba batun kunya kuma kin san Amina batada matsala a wannan fannin ba Aunty ba cewa zakayi mama habeeb ya qara fada a dan hasale kai gwafdede dakai ka kalli sajida kace mata Aunty ko kunya baka jiba dariya yusuf yayi kafin yace to banda abinka yaya ai ko yusra yanzu Aunty zan dinga kiranta bare kuma sajida datake matar babban yaya inka so ka kirani da baba malam karewar yaya kaga bana son iskanci malam kabar wannan shirmen naka ita wannan yarinyar duka nawa take da zaka kama fadar irin wadannan maganganun a gabanta so kk yi ta raina mutane kawai du du du me khadija ta sani cikin week din nan zasu fara zana S.S.C.E fa amma kk wani maganar aure a gabanta haba malam ai sai kaja ta raina mutane duk abin nan da akeyi sai ka rantse da Allah dije bata gurin tana zaune abinta ta dauki lemon bawo tana sha jin sun 'danyi shuru da dramer tasu yasa ta tunawa da wayarta da daddy ya siya mata wadda ita taso ta dauka ranar da zata tafi gidan yusuf bata samu dama ba dan haka tana tunawa ta mike dan shiga ciki ta fara tafiya ta tsinkayi muryar yusuf yace kayanki fa princess? batare data daina tafiyar ba kuma bata juyo ba tace biyoni dasu pls ta shige ciki abinta girmanki ya wuce haka ai ya fada yana me kokarin barin gurin suka hada ido da naseer dake ta masa ruwan harara au to yaya laifin me kuma nayi ake min wannan harara haka ? baka kirana da abinda yafi yaya ka wani tsaya kanata sakin magana gaban yarinya salon kasa ta raina mutane banda abinka meye abin raini a ciki a gara ayi komai a gabanku a matsayinku na manyan yayye nifa inka ce yayan nan ji nakeyi kamar in kurma ihu wlh inba iskanci ba ina ni ina kai banda ma zamani daba ruwan abota da shekaru ai da sai ince kai sai dai kayi abota da qanin daddy ai ba komai koma dai sa'an daddy ne soyayya bata tsufa dan haka bari kuga in tashi nabi ta kada ran 'yammata ya baci yana gama fadar haka ya juya ya nufi motar ya bude ya fito da ledar ya nufi part din habeeb da mugun sauri habeeb yasha gabanshi yace ina zaka malam? kaji ka yaya da wata tambaya gurin princess mana in kai mata kayanta haka kawai zan barka ka shiga ciki ka sameta a matsayinta na wadda ba muharamarka ba kallonsa yusuf ya shiga yi yana murmushi kafin yace haba yaya kamar baka san halina ba wannan wane irin magana kk yi naga fa tun kafin ayi nisa kafara adawa anya kuwa zaka iya min jagora gurin daddy ? habeeb da inda akwai kalmar data ke qona masa rai to bata wuce yace masa yayan nan ba dan haka cikin hade rai yace in kana iyawa ka kawo in shigar mata dashi kai kuma ka koma gida maza su hajiya na jiranka kasan dai abinda zai biyo baya inka dade au ni wlh kama tunamin wace hajiya kuma ai kai wannan matsalar ta kau akwai lbr sai mun zauna yanzu dai bari muyi sallama da princess tukunna sauran bayani gobe zan sameka a office sallama dawa? ai wlh in kaga ka kara ganinta to ba yauba sai wani lokacin kuma dan na lura dakai nema kk yi ka hargitsa mata kwakwalwa ka hanata karatu kememe ya hana yusuf shiga gidan inda karshe yabashi kayan yayi musu sallama wadd matan ne kawai suka amsa masa amma mazan banza suka mishi ya shiga motarshi yana murmushi yabar gidan naseer da sai yanzu ya lura da kallon da yusra keyi masa yace ke kuma meye kk tsareni da ido kamar wadda ta warke daga cutar makanta yaja tsaki yayi part dinsu cike da mamakinsa ta mara mishi baya .hakama sajida da duk abinda mijinta keyi tana kallonsa har yanda ya karbi kayan ko kafin ta iso inda yake harya shige ciki itama ta mara masa baya yana shiga ya iske dije zaune tana daddana waya cike da bacin rai yace keee ubanwa ya baki waya ? dagowa tayi ta dubeshi a hankali ta mayar da kanta ga abinda takeyi a wayar tace mishi to dai yaya a dinga saita harshe in an tashi tambaya dan kasan ni fa amsa nake bayarwa dai dai da yadda aka tambayeni yana shirin yin magana sajida ta shigo ta kafesu da ido kallon da take mishi ya qara tunzura shi yace wato yusuf ne ya siya miki waya ko? ke har kin kai namiji ya baki abu ki karba ko nawa kike duka da zaki rike waya yanzu duk iskancin da kikeyi ina kyaleki ne badan ina jin tsoronki ba sai dan gani nakeyi wannan jikin naki idan na tashi dukanki babbalaki zanyi dan haka ki mikomin wayar nan in mayar masa da abarsa tun kafin ranki ya baci ko kallonsa batayi ba ta shiga kallon wayar datayi dialling har akayi picking kafin cikin sanyin muryarta ta furta barka da wannan lokacin my daddy shuru ta danyi alamun ana magana daga daya bangaren murmushi ta saki kafin tace kowa lfy shine ma yace yana son magana dakai tana fadar haka ta mika masa wayar cikin bacin rai yace uban waye ? ubanka ne yaji an fada daga cikin wayar take yadauki murya cikin rawar hannu ya karba kafin cikin girmamawa ya shiga gaida daddy naji kana tambayar uban waye shine nace ubanka ne yanzu ka gane ai ko? ah ah wlh daddy ba haka bane ina tambayarta wanda ya siya mata waya ne to shine..... ai duk ana nan dai dan ni na siya mata wlh habeeb kasake naji wani abu marar dadi ya faru game da zaman yarinyar nan a gidan nan saina saba maka da har naji dadi ganin yadda kuke kula da ita amma yanzu na lura tunda mahaifiyarku ta fara kawomin korafe korafe nasan saita zuga ku kunyi abinda be dace ba to wlh ku kiyayeni wannan karan daga ku har ita zan saba muku insha Allah daddy ba abinda zai faru Allah yasa Allah kuma yayi muku albarka Ameen ina ita khadijan baban bata wayar wulla mata yayi kan cinyarta ta karba inda tasa wayar a kunne suka gama da daddy sannan ta kashe harararta habeeb yayi kafin ya jefa mata ledar gurin yusuf yace ga kayan da kk rokeshi nan kwadayayyiya kallon ledar tayi kafin ta miqe ta shiga tattara abinda ya zubo cike da rashin damuwa da maganar shi kafin ta tattara ta dauka sannan tace ai kaima yaya kasan ba halina bane roko dan haka ka daure ka dingamin shaidar kwarai ni kunga nayi nan inje inyi waya da my choice tana fada ta juya abinta ta barshi da sakin baki my choice? ya maimaita kalmar sajida ce tace nifa ban gane nufinka ba habeeb naga duk ka wani hargitse ba dole na hargitse ba kina jin abinda 'dan iskan can ke cewa to sai me ?ni banga wani abu a maganar da yayi ba in yarinya taga tana sonshi ba shikenan ba bakaji yace matarshi bata da matsala ba ashe kema bakida hankali yarinya karama kamar khadija za'a yiwa aure duka nawa take ? eh lallai fa qaramar yarinya amma ai duk ga kayan more mace nan a tattare da ita kuma nawa akayiwa auren da basu kaita ba suka zauna harda haihuwa ai shiyasa kuwa suke gamuwa da yoyon fitsari kinga ni ban son shashanci ki kyaleni kawai dan na lura kema jirgi daya ya kwaso ku yana fadar haka ya shige daki bammm ya bugo kofa yayin da ta zauna sharaf kan kujera ta shiga tunani to me hakan ke nufi ? wata zuciyar ta saka mata mugun tunani wata kuma ta bata me kyau daga karshe dai tace kai gaskiyarshi fa duka nawa yarinyar take da har za ai batun wata soyayya bare ma nasan habeeb dina bayada wannan tunanin da nakeyi bari inje in rarrashi abina ta fada tana me miqewa ta shiga daki ***** sannu a hankali rayuwa ke tafiya yayin da su dije suke zana jarrabawarsu cikin sauqi da kwanciyar hankali zamanta gidan su habeeb kadaran kadahan babu wata sakin fuska gurin sajida da shi kanshi me gidan har gara naseer ma amma ko ita yusra wani lokacin cin magani takeyi yayin da itako dije bata ko kula da yadda takwe mata iyakarta inta iske naseer a gida suyita hirar su inda zaita tsokanota tana bashi labarin kauye yana dariya abin har mamaki yake bata yadda ya canza mata lokaci daya yauma ta fito kenan da niyyar komawa part din su habeeb din inda ta jima gurin su yusra suna hira dan ba laifi yau itama yusran ta saki jiki da ita sun danyi hira tana shiga parlon taji hayaniya inda ta shiga da sallama duka juyowa sukayi suka bita da wani kallon rainin hankali kafin suka kwashe da dariya ganin yadda suka mata yasa tayi niyyar shigewa amma saita tsinkayi muryar wata na cewa .ah lallai su Aunty kun iya kiwo ji yadda kashi ya fara tofon tsoka anji jar miya an nuna anyi jajir an baro su inna a kauye yanzu hakama an manta dasu sai irin haka ta faru an kira sunansu ake tunawa dasu dukansu suka sa shewa tare da fadin gaskiyarki kuwa kausar fada mata dai anzo zaman tsegumi sai tsula tsiya akeyi wlh ni Aunty da ace kin fadamin tunda wuri da tuni nayi miki maganin wannan matsalar sajida da sai yanzu ta tanka tace hmm ku barni dan Allah ni da abinda ke damuna kuje can ku qarata ta fada tare da miqewa tayi cikin dakinta af kinga ko na fada muku harda laifin Aunty ji fa yadda tayi ba dole yarinyar ta raina ta ba wlh yau sai mun gyara miki zama ke sai ma kin bar gidan nan dan uwarki zo nan dije data zuba musu ido ta tsaya tana nazarin ta inda zata fara bata gama tunanin ba taji an jawota kiiiiii har an dangwarar da ita zauna dan uwarki yau wlh sai kin san bamuda mutunci kuriii dije tayi musu da ido daya bayan daya kafin tace to wai ku in tambayeku me kuke shirin yimin ne kuma me nayi muku? au tambaya ma kk yi kinga mimi kawai kaddamar mata saita fahimta dariya dije ta farayi harda rike cike ganin hakan yasan duk suka bita da kallo inda kausar dayake itace qarama tace kutmelesi au dariya ma kikeyi a fusake tayo kan dije ta shiga kai mata duka duk da dije najin dukan amma dariya kawai takeyi ganin haka yasa kausar dakatawa ta kalli mimi tace anya kuwa yarinyar nan nada lfy kuwa? ci gaba mana ko kin gaji cewar dije da har yanzu dariyar takeyi *vote* *,comments* *Alqalamin khady* โœ[3/15, 6:37 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* na khadija usman 2โƒฃ9โƒฃ Au wato ma baki daku ba ne shiyasa kk cewa aci gaba cewar kausar data taso nan tayi kan dije ta shiga tillikar ta itama duk da dije najin zafin dukan iya ji amma taurin zuciya yasa banda dariya babu abinda takeyi ganin hakan yasa su dakatawa suna kallonta tare da mayar da numfashi dan abinka da jinin hutu har sun gaji itako dije harga Allah jikinta ya amshi duk sakonnin da suka aika mata ganin duk sun gaji sun tsaya yasa tace badai har kun gaji da yakin sunkurun ba? au bakinki be mutu ba kenan to bari ki gani in sa nawa hannun muci uwarki a zo a tattara ki a mayar dake kauye a welbarro ah ah kinga dakata cewar dije naga abin naku zalunci ya shigo ciki abin taron dangi ne ni da gidan dan uwana amma an kafamin kahon zuqa kawai sbd nazo na zauna kamar akan uwar wani nake zaune ke dan uwarki mu kk zagi ? nidai bana son sharri bakiji na zageku ba amma in kunce hakan toh nafada din ta qarasa maganar tana murguda baki tare da gyara tsayuwarta ta coge tana yatsina fuska dan wlh fa ta daku a ranta tace shegu a haka kamar basuda kwari a she nama ya ratsasu da dan sauransu gashi suna shirin halakani ai na fuskanci sai mun dirje bakin yarinyar nan yadda baxata samu bakin rashin kunyar nan ba rufe mana kofa mu lakadi shegiya yadda batada maceci da sauri mimi ta nufi kofa tasa mata key ta zare ta taho dashi a hannunta kinga kausar rufe Aunty ta waje dan na lura itama bazata barmu muyi yadda muke soba tana iya hanamu maganin wannan shegiyar dije dake tsaye taga kausar ta nufi dakin sajida saida ta zura kai ta ciki taga sajidar bata nan da alama tana toilet dan taji karar ruwa aikuwa ta zaro key din ta fito dashi ta waje ta rufe ta dawo falon a take zuciyar dije ta shiga lugude a ranta tace kinga dije ko ba komai sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma wadannan kitika kitikan da suka koshi da madara gasu nan kamar shanu ki lababa ki tsere to ai kuma sun rufe kofa ya kenan lura da sukayi dije kamar ta tsorata yasa su kara kaimin nufota tare da narka mata na maguzawa dakewa dije tayi amma jikinta da zuciyarta kamar sa fado kasa dan rawa ko kafin mimi ta karaso tace mata kinga balama dakata nifa ba koriyar ciyawar da kk saba ci bace naga kin nufoni gadan gadan kina tande baki dabbar mayu ai bata karasa ba taji saukar wani shu'umin marin data rasa daga ina yazo bata gama tantancewa ba ta fulanin ta motsa jin ana neman sata jinyar dole aikuwa tayi kan mimi a sukwane cikin sa'a kuwa ta dami gashin kanta dayake kalba ce akayi mata da Attact iya qarfinta ta rike tare da cizgawa wata kara mimi ta saki wadda tasa su kausar nufo dije da dukkan karfinta ta tunkuda mimi da kanta ya daki karamin center table din dake gurin aikuwa take kai ya fashe ganin jini yasa ta sakin wata karar a karo na biyu kausar na ganin hakan tayo cikin dije yayin da humaira tayi gurin mimi data bare baki tana kuka tare da shafo jinin a hannunta wanda wannan shine karo na farko a rayuwarta data taba jin ciwo da jini haka tattaro dukkan karfinta tayi itama suka kacame aikuwa nan dije ta nuna ita rainon kauye ce dan kuwa tuni ta samu lagon kausar kasancewar ita basu saba da irin wadan nan wahalhalunba da iyakar karfinta dije ta kama nonon kausar ta murde itama karar tayi nan ta shiga neman hanyar kwatar kai amma ina dije dan mugunta harda cije lebe takeyi jin da kausar tayi dije na shirin kasheta kuma ba mafita yasata gartsawa dije cizo a hannu ai kuwa jin zafin cizon yasa dije qara himma bata san lokacin data gwara kan kausar da plasman dake manne jikin t.v stand ba ji kakeyi kwararats ta sheqo kasa ta tsage nan fa ihu ya hadu biyu ita kanta dijen daba damar kukan ne da tayi dan ta dan sha jiki su kuwa duk sun bude baki suna ihu humaira dataga abinda ya faru da wadanda suka fita tsageranci ai take jikinta ya hau bari dan dama duk burga ce sun fita kwaliti sai yanzu hankalinta yakai ga bugun kofar da akeyi haggu da dama ma'ana dakin sajida da kuma kofar falon duk ta rude ta rasa inda zata nufa ga ihun wadan nan na kwancen ita kuma dije tayi mata zuru masifa na cinta jira takeyi tasamu nama kawai yanayinta ya kara tsorata humaira duk da tabi ta rude aikuwa nan ta fara kokarin guduwa dije ta rufa mata baya tana fadin ai ba inda zaki dan uwarki yau ko ni ko ku badai kunce sai anyi yakin badar yau a gidan nan ba to sai munga karshen shi muga wakeda nasara nan ta yi cikinta da himma ganin hakan yasa humaira daukar duk wani abu data gani ta jefawa dije ita kuma tana gocewa wani yaje yasamu frame din dake manne a falon sai dai kaji rassss sun sheqo kasa au to ai sai ki fadamin zakka kk son ku fitar shiyasa zakuyi mana barna a gidan duk da ban san nawa kk fasawa ba yayana ya siya ko ku kuka kawo 'yar uwarku dashi to bari na tayaki nan fa ta nufi dinning duk coolers din dake kai sai da ta dinga saita humaira dasu tana jifanta aikuwa kan kace me falo ya kacame da yayi kaca kaca cikin zafi humaira tayo cikin dije bisa ga shawarar zuciyarta data bata akan cewa ta ci uban dije kawai yadda take lange langen nan suma su kausar rashin zuciyane yasa haka aikuwa tana zuwa dije tayi mata na 'yan wristelling ta kai mata wani wawan naushi amma fa bada hannunta ba da ludayin miyar da ita kanta humaira bata lura dashi ba ba shiri baki yayi tsartuwa aikuwa nan dije bata bata wata damar kuka ba sbd mugunta duk inda tasan saitin kashi ne saita buga harda goshi duk inda ta buga sai dai kaji yace kwalll ai kuwa saita saki dariya sbd zalunci gwiwar ta saita ta bada kwalll ai kuwa humaira ta bude dukkan muryarta tana ihu tana kiran wayyooo Aunty ki zo ki taimakemu wai bakuda imani ne bamai taimakon mu a hannun kinfi 'yan boko haram rashin imani ta fada tana me qara rushewa da kuka itako dije dariya ta shiga tana fadin muje zuwa mana ai yanzu aka fara ni yaseen ko rabin gajiya ban tashi yiba kawai muci gaba da kaftawa yau nayi muku alqawarin sai kunga kalar mazgar da baku taba gani ba sajida da hankalinta ke mugun tashe ta kira habeeb yace mata yana kan hanya amma shuru gashi sai ihun 'yan uwanta take jiyowa wanda take addu'ar Allah yasa yarinyar bada mutanenta ta hada su ba suke caskala su dan tasan ita da an tabata sai sun kawo ziyara ita fargabarta ma abin ya tsaya iya wadanda suka jawo kar su ce a gidan zasu kwana yau an taba musu hantar su layin habeeb ta kuma kira nan ya shaida mata gashi nan shida naseer sun kusa zuwa tunawa tayi da spare keys din dake cikin lokarta nan ta shiga dubawa ta dauko na dakinta ta bude amma sai me ? sam takasa fitowa illah ziro kai datayi kadan batare da sun lura ba nan ta hango su kwance sunata wai wai tare da reto da jiki kamar suna takaraa makarantar allo ga dije nan kamar uwarsu tasa sun kama bakinsu da hannunsu amma fuskar nan tasu a kwabe sunata digar hawayen azaba jin ana buga kofar ne sosai yasa sajida fitowa da kyar ta nufi kofar kamar ta tashi sama dan karma dije ta ankare da ita dan ita masifar yarinyar tsoro yake bata dije ko tana lura da ita ta shareta dan ita kanta ta matsu a zo a rabata da wadannan kartin banzan a cewarta da bataga amfaninsu ba inda itace kamarsu ai aikin soja zata shiga dan jikinsu kalar wannan aikin ne amma sai gashi taga alama ko aikin office ma ba alamunsa anan koda ta qarasa ta bude kofar taga ba key jiki dole ba yadda zatayi ta juyo falon kamar tasan yadda akayi nan ta shiga duba kan kujera ko kala batace ba kamar munafuka sim sim ta ganshi ta dauka ta bude kofar su ukune tsaye habeeb naseer da yusrah sai musa dake tsaye daga can bayansu wanda da za'ace arrrr yanzu zai sheka dan ya kudirarwa ransa baxai kuma shiga gidan nan ba matukar yaji ana sautin neman taimako da sauri suka shigo inda sukayi cirko cirko ganin su mimi zaune suna reto da kawuna ga ciwuka ga falo daya hadu ya hade wadda ita kanta sajida sai yanzu ta lura da barnar da akayi ya Allah habeeb ya fada kafin ya kalle su cikin bacin rai yace kaii uban mu ya faru haka naganku kamar kunyi Accident dubi yadda kuka mayarmin gida tamkar na mahaukata anya kunada hankali kuwa? sai yanzu suka farga da shigowar su aikuwa da sauri suka rarrafa suka bude baki cikin kuka kausar tace wlh yaya ku gaggauta fita da wannan yarinyar a gidan nan dan wlh batada hankali wlh bakaken aljanu gareta da alama sannan suna sata hauka wlh yaya zata iya kashe ku wata rana cikin rawar murya yusra tace to ku wane tsautsayi yakaiku fada da ita kuma ke Aunty sajida ai laifinki ne meyasa baki sanar dasu fada da aljani ba dadi cikin bacin rai tace su basuda hankali ai daka fara fada ka kalli fuskar wanda kk yi dashi kasani in mutum ne in ma aljani ne kuma nace musu baruwana suka ki ji gashi ban sunjawa kansu ai an zuqe musu jini dan da ganin yadda suke yanzu sai an musu karin jini to ku meya kaiku taba da transfomer ana ruwan sama ?cewar naseer wlh kaddara kasan ance me rabon shan duka bayajin kwaba ni babban takai cina na ji yadda aka sauyanin halitta duk da ban kalli madubi ba amma dana shafa goshina wlh naji kamar ma ba fuskata ba dan sai naji kamar ta Dila wlh in kince dila kinyiwa kanki zabe me kyau bakiga yadda kika koma ba sai kace fukar bahaguwar bakar rakuma cewar naseer daya fada yana kunshe dariyarsa wayyo ni na shiga uku wayyo Allah yanzu ni dan banida gata babu wanda ya duba yadda nake ba wanda ya saurareni sai 'yan uwanku kuke ta tasu cewar dije data dora hannu aka ta baje baki tana ihu wadda ihunta yayi dai dai da shigowar mamy wadda tashigo a sukwane jin ihun sakamakon kiranta da yusrah tayi a waya cikin tashin hankali lokacin da basu san abinda ke faruwa ba sai ihu da sukaji.......... *Alqalamin khady* โœ [3/15, 10:47 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TA ME GARI* na khadija usman 3โƒฃ0โƒฃ Au wato ma baki daku ba ne shiyasa kk cewa aci gaba cewar kausar data taso nan tayi kan dije ta shiga tillikar ta itama duk da dije najin zafin dukan iya ji amma taurin zuciya yasa banda dariya babu abinda takeyi ganin hakan yasa su dakatawa suna kallonta tare da mayar da numfashi dan abinka da jinin hutu har sun gaji itako dije harga Allah jikinta ya amshi duk sakonnin da suka aika mata ganin duk sun gaji sun tsaya yasa tace badai har kun gaji da yakin sunkurun ba? au bakinki be mutu ba kenan to bari ki gani in sa nawa hannun muci uwarki a zo a tattara ki a mayar dake kauye a welbarro ah ah kinga dakata cewar dije naga abin naku zalunci ya shigo ciki abin taron dangi ne ni da gidan dan uwana amma an kafamin kahon zuqa kawai sbd nazo na zauna kamar akan uwar wani nake zaune ke dan uwarki mu kk zagi ? nidai bana son sharri bakiji na zageku ba amma in kunce hakan toh nafada din ta qarasa maganar tana murguda baki tare da gyara tsayuwarta ta coge tana yatsina fuska dan wlh fa ta daku a ranta tace shegu a haka kamar basuda kwari a she nama ya ratsasu da dan sauransu gashi suna shirin halakani ai na fuskanci sai mun dirje bakin yarinyar nan yadda baxata samu bakin rashin kunyar nan ba rufe mana kofa mu lakadi shegiya yadda batada maceci da sauri mimi ta nufi kofa tasa mata key ta zare ta taho dashi a hannunta kinga kausar rufe Aunty ta waje dan na lura itama bazata barmu muyi yadda muke soba tana iya hanamu maganin wannan shegiyar dije dake tsaye taga kausar ta nufi dakin sajida saida ta zura kai ta ciki taga sajidar bata nan da alama tana toilet dan taji karar ruwa aikuwa ta zaro key din ta fito dashi ta waje ta rufe ta dawo falon a take zuciyar dije ta shiga lugude a ranta tace kinga dije ko ba komai sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma wadannan kitika kitikan da suka koshi da madara gasu nan kamar shanu ki lababa ki tsere to ai kuma sun rufe kofa ya kenan lura da sukayi dije kamar ta tsorata yasa su kara kaimin nufota tare da narka mata na maguzawa dakewa dije tayi amma jikinta da zuciyarta kamar sa fado kasa dan rawa ko kafin mimi ta karaso tace mata kinga balama dakata nifa ba koriyar ciyawar da kk saba ci bace naga kin nufoni gadan gadan kina tande baki dabbar mayu ai bata karasa ba taji saukar wani shu'umin marin data rasa daga ina yazo bata gama tantancewa ba ta fulanin ta motsa jin ana neman sata jinyar dole aikuwa tayi kan mimi a sukwane cikin sa'a kuwa ta dami gashin kanta dayake kalba ce akayi mata da Attact iya qarfinta ta rike tare da cizgawa wata kara mimi ta saki wadda tasa su kausar nufo dije da dukkan karfinta ta tunkuda mimi da kanta ya daki karamin center table din dake gurin aikuwa take kai ya fashe ganin jini yasa ta sakin wata karar a karo na biyu kausar na ganin hakan tayo cikin dije yayin da humaira tayi gurin mimi data bare baki tana kuka tare da shafo jinin a hannunta wanda wannan shine karo na farko a rayuwarta data taba jin ciwo da jini haka tattaro dukkan karfinta tayi itama suka kacame aikuwa nan dije ta nuna ita rainon kauye ce dan kuwa tuni ta samu lagon kausar kasancewar ita basu saba da irin wadan nan wahalhalunba da iyakar karfinta dije ta kama nonon kausar ta murde itama karar tayi nan ta shiga neman hanyar kwatar kai amma ina dije dan mugunta harda cije lebe takeyi jin da kausar tayi dije na shirin kasheta kuma ba mafita yasata gartsawa dije cizo a hannu ai kuwa jin zafin cizon yasa dije qara himma bata san lokacin data gwara kan kausar da plasman dake manne jikin t.v stand ba ji kakeyi kwararats ta sheqo kasa ta tsage nan fa ihu ya hadu biyu ita kanta dijen daba damar kukan ne da tayi dan ta dan sha jiki su kuwa duk sun bude baki suna ihu humaira dataga abinda ya faru da wadanda suka fita tsageranci ai take jikinta ya hau bari dan dama duk burga ce sun fita kwaliti sai yanzu hankalinta yakai ga bugun kofar da akeyi haggu da dama ma'ana dakin sajida da kuma kofar falon duk ta rude ta rasa inda zata nufa ga ihun wadan nan na kwancen ita kuma dije tayi mata zuru masifa na cinta jira takeyi tasamu nama kawai yanayinta ya kara tsorata humaira duk da tabi ta rude aikuwa nan ta fara kokarin guduwa dije ta rufa mata baya tana fadin ai ba inda zaki dan uwarki yau ko ni ko ku badai kunce sai anyi yakin badar yau a gidan nan ba to sai munga karshen shi muga wakeda nasara nan ta yi cikinta da himma ganin hakan yasa humaira daukar duk wani abu data gani ta jefawa dije ita kuma tana gocewa wani yaje yasamu frame din dake manne a falon sai dai kaji rassss sun sheqo kasa au to ai sai ki fadamin zakka kk son ku fitar shiyasa zakuyi mana barna a gidan duk da ban san nawa kk fasawa ba yayana ya siya ko ku kuka kawo 'yar uwarku dashi to bari na tayaki nan fa ta nufi dinning duk coolers din dake kai sai da ta dinga saita humaira dasu tana jifanta aikuwa kan kace me falo ya kacame da yayi kaca kaca cikin zafi humaira tayo cikin dije bisa ga shawarar zuciyarta data bata akan cewa ta ci uban dije kawai yadda take lange langen nan suma su kausar rashin zuciyane yasa haka aikuwa tana zuwa dije tayi mata na 'yan wristelling ta kai mata wani wawan naushi amma fa bada hannunta ba da ludayin miyar da ita kanta humaira bata lura dashi ba ba shiri baki yayi tsartuwa aikuwa nan dije bata bata wata damar kuka ba sbd mugunta duk inda tasan saitin kashi ne saita buga harda goshi duk inda ta buga sai dai kaji yace kwalll ai kuwa saita saki dariya sbd zalunci gwiwar ta saita ta bada kwalll ai kuwa humaira ta bude dukkan muryarta tana ihu tana kiran wayyooo Aunty ki zo ki taimakemu wai bakuda imani ne bamai taimakon mu a hannun kinfi 'yan boko haram rashin imani ta fada tana me qara rushewa da kuka itako dije dariya ta shiga tana fadin muje zuwa mana ai yanzu aka fara ni yaseen ko rabin gajiya ban tashi yiba kawai muci gaba da kaftawa yau nayi muku alqawarin sai kunga kalar mazgar da baku taba gani ba sajida da hankalinta ke mugun tashe ta kira habeeb yace mata yana kan hanya amma shuru gashi sai ihun 'yan uwanta take jiyowa wanda take addu'ar Allah yasa yarinyar bada mutanenta ta hada su ba suke caskala su dan tasan ita da an tabata sai sun kawo ziyara ita fargabarta ma abin ya tsaya iya wadanda suka jawo kar su ce a gidan zasu kwana yau an taba musu hantar su layin habeeb ta kuma kira nan ya shaida mata gashi nan shida naseer sun kusa zuwa tunawa tayi da spare keys din dake cikin lokarta nan ta shiga dubawa ta dauko na dakinta ta bude amma sai me ? sam takasa fitowa illah ziro kai datayi kadan batare da sun lura ba nan ta hango su kwance sunata wai wai tare da reto da jiki kamar suna takaraa makarantar allo ga dije nan kamar uwarsu tasa sun kama bakinsu da hannunsu amma fuskar nan tasu a kwabe sunata digar hawayen azaba jin ana buga kofar ne sosai yasa sajida fitowa da kyar ta nufi kofar kamar ta tashi sama dan karma dije ta ankare da ita dan ita masifar yarinyar tsoro yake bata dije ko tana lura da ita ta shareta dan ita kanta ta matsu a zo a rabata da wadannan kartin banzan a cewarta da bataga amfaninsu ba inda itace kamarsu ai aikin soja zata shiga dan jikinsu kalar wannan aikin ne amma sai gashi taga alama ko aikin office ma ba alamunsa anan koda ta qarasa ta bude kofar taga ba key jiki dole ba yadda zatayi ta juyo falon kamar tasan yadda akayi nan ta shiga duba kan kujera ko kala batace ba kamar munafuka sim sim ta ganshi ta dauka ta bude kofar su ukune tsaye habeeb naseer da yusrah sai musa dake tsaye daga can bayansu wanda da za'ace arrrr yanzu zai sheka dan ya kudirarwa ransa baxai kuma shiga gidan nan ba matukar yaji ana sautin neman taimako da sauri suka shigo inda sukayi cirko cirko ganin su mimi zaune suna reto da kawuna ga ciwuka ga falo daya hadu ya hade wadda ita kanta sajida sai yanzu ta lura da barnar da akayi ya Allah habeeb ya fada kafin ya kalle su cikin bacin rai yace kaii uban mu ya faru haka naganku kamar kunyi Accident dubi yadda kuka mayarmin gida tamkar na mahaukata anya kunada hankali kuwa? sai yanzu suka farga da shigowar su aikuwa da sauri suka rarrafa suka bude baki cikin kuka kausar tace wlh yaya ku gaggauta fita da wannan yarinyar a gidan nan dan wlh batada hankali wlh bakaken aljanu gareta da alama sannan suna sata hauka wlh yaya zata iya kashe ku wata rana cikin rawar murya yusra tace to ku wane tsautsayi yakaiku fada da ita kuma ke Aunty sajida ai laifinki ne meyasa baki sanar dasu fada da aljani ba dadi cikin bacin rai tace su basuda hankali ai daka fara fada ka kalli fuskar wanda kk yi dashi kasani in mutum ne in ma aljani ne kuma nace musu baruwana suka ki ji gashi ban sunjawa kansu ai an zuqe musu jini dan da ganin yadda suke yanzu sai an musu karin jini to ku meya kaiku taba da transfomer ana ruwan sama ?cewar naseer wlh kaddara kasan ance me rabon shan duka bayajin kwaba ni babban takai cina na ji yadda aka sauyanin halitta duk da ban kalli madubi ba amma dana shafa goshina wlh naji kamar ma ba fuskata ba dan sai naji kamar ta Dila wlh in kince dila kinyiwa kanki zabe me kyau bakiga yadda kika koma ba sai kace fukar bahaguwar bakar rakuma cewar naseer daya fada yana kunshe dariyarsa wayyo ni na shiga uku wayyo Allah yanzu ni dan banida gata babu wanda ya duba yadda nake ba wanda ya saurareni sai 'yan uwanku kuke ta tasu cewar dije data dora hannu aka ta baje baki tana ihu wadda ihunta yayi dai dai da shigowar mamy wadda tashigo a sukwane jin ihun sakamakon kiranta da yusrah tayi a waya cikin tashin hankali lokacin da basu san abinda ke faruwa ba sai ihu da sukaji.......... *vote* *comments* *Alqalamin khady* โœ [3/15, 11:07 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TAME GARI* NA khadija usman 3โƒฃ1โƒฃ Ah ah wlh basai kin fasa ba ki tafi kawai duk lokacin da muka so ganinki ma zo ko? suka tambayi matan eh wlh Allah ya tsare ya kiyaye hanya Ameen ta fada jiki a sanyaye kamar wadda kwai ya fashewa taja qafa tana tafe tana waiwayensu mamy kuwa nata raka su da harara saitayi tafiya kadan sai ta tsaya su kuma sai kaji sunce ya akayi ? saita ce kewar ku ce wlh ji nakeyi kamar in fasa tafiyar san ba yadda zanyi ne aikuwa dole ki tafi tunda mamy ta bukaci hakan dan ba yadda za'ayi ta yanke hukunci ki ketare cewar habeeb to banda abinka yaya ai bafa cewa nayi bazan je ba cewa fa nayi ina jin kewarku kamar in fasa tafiya ke ni dayalla wuce muje kun tsayamin surutun banza cewar mamy dije na ji tana gani aka nausa mota aka nufi gidan daddy *welcome back home dijeee* ******* ba karamin jin dadi basira tayi na ganin dije ba aikuwa nan aka shiga hirar yaushe gamo danma jikin dije yayi tsami tana bukatar hutu dan haka bakin a mace yake tun asubar fari mamy ta iso dakin dasu dije suke tace dije ta fito ita zatayi aikin gidan nan yanzu ga mamakin mamy sai gani tayi dije tayi tsalle tare da fadin Allahu akhbar kallonta tayi ta dan ja baya tare da fadin ke dan ubanki meye na jamin farkon kalmar kiran sallah ? wallahi farin ciki ne mamy kai kedai Allah ya biyaki yayi miki duk abinda kk da niyyar yimin ba amin ba dan ubanki kajimin shegiyar yarinya da muguwar addu'a ke kin san me nake shirin yi miki ne? ai shiyasa kema na roka miki irinshi bari dai kawai kiga yadda za'ayi gara in fara aikin nan da wuri kar in makara dan ni yau ina cikin farin ciki yau zamu gama exam dinmu ma'ana yau zamuyi candy kinga ko yau ranar farin ciki ce murmushin mugunta mamy tayi a ranta tace Alhmdllh wato yau kuke da last paper zako kici ubanki basai kin je ba naga ta inda zaki bi ki bar gidan nan kamar dije ta shiga zuciyarta tasan me take ayyanawa sai ji mamy tayi dije tace ni dai bari nayi ayyukan da aka sani tun wuri dan kar aimin sagegeduwar zuwa kafin mamy tayi wata magana har dije tahau karkade kujerun falon kwafa tayi ta shige dakinta dan komawa bacci dan dama tsabar tijarar data sawa ranta ne yasata tashin asuba yau dan daddy baya nan amma data tuna yau saita kuntatawa yarinyar saita nemi guri ta zauna tana jiran dijen ta gama tazo ta fada mata nan ta cicci uwarta ta hanata kuma zuwa makarantar tana shigewa dije tayi wurgi da filon kujerar ta kama dariya tare da rike kugu a fili tace lallai ma mamy yadda nazo birni nasaba da rayuwar hutu iya dan zaman da nayi na waye ta yaya kike tunanin zan maida kaina irin aikatau to miye ribar zamana a birnin kenan to ba abinda zanyi iyakata dake idan banyi ba ki narkeni ko ki zagi iyayena kin dade bakiyi duka biyun ba ni jikin nan ya saba da wahala dan haka a kafta kawai ta fada tana me shigewa dakinsu tana zuwa wanka tayi tare da shiryawa cikin sauri sauri tana gamawa ta nufi kitchen gun baseera dake kokarin hada abin kari ganin bata gama ba yasa dije ta sungumi katon biredi tare da exotic tasa a jaka ta fita da sauri tana fadin saita dawo a sukwane ta fice a falon ta nufi dakin su habu driver da suke dan baccin safe nan ta tasheshi yayi mamaki ganin ta shirya da wuri yau dan duka time din 6:47am hajiya yau da wuri zamu fita kenan kowa yasan kin dawo eh kasan da ai nasaba bi makwabta ina gaishesu to shine naga a da din ina makara shine nace yanzu bari in dinga sammako ko zan gama da wuri yau ta karasa maganar tana harararsa ganin hakan da yayi yasa shi gane baka ta fada mishi dan haka ba shiri ya mike ya fito da mota ta shige suka tafi shuru shuru mamy ta gaji dan haka ta fito tana fitowa kuwa taga falon yadda ta barshi cike da mamaki da bacin rai ta nufi dakin amma taga wayam kitchen ta nufa tana zuwa kuwa taga basira ita kadai nan ta shiga tambayarta dije ta sanar mata ta tafi makaranta wata uwar ashar ta narka kafin ta shiga bala'i da fadin in dije ta dawo saita ci ubanta badan ma tana son ta koya mata darasin da ko wani taji yace zaizo birni saita hanashi ba to da yau saita kadata kauye uban kowa ya huta amma yanzun ma zataci ubanta ne. *** a makaranta kuwa dije sun fito exam inda daukaki daliban ke farin ciki da murnar kammala karatun su na secondry kasancewar makarantar yaran masu kudi ne yawanci dan haka wasu dayawa a cikinsu sun hada party hakama malaman sun hada musu party wanda sam dije ta ma manta da batun ga daddy baida masaniyar hakan shima ganin da dije tayi anata shirye shirye dan harda iyayen yara yasa ta kalli rufaida cikin marairaice fuska kamar zatayi kuka tace ni fa besty banyi shirin komai ba wlh ko daddy ban fadawa ba gashi kuma kin san shi kadai ne zai iya zomin kuma ko wasu kaya ban zo dasu ba wlh sharp na manta wlh gashi na dana bom a gida bare in koma in dauko kaya yanzu ya zanyi kenan? kinga kwantar da hankalinki ki kira daddy ki fada masa kawai batun kaya kuma ai har yanzu da sauran time abinda sai after 4 za'a fara yanzu kuma 12 fa muje gida cikin kayana ki duba inda wanda yayi miki saiki sa tunda kinga ba anko mukayi ba bare ace za'a samu matsala ko ? eh kuma hakane ngd nan tasa hannu ta dauko wayarta dake cikin aljihun wandonta ta shiga kiran daddy yana dagawa taji yace ina taya 'yata murnar kammala karatunta na matakin secondry dariya tayi tare da fadin nagode daddy ashe kanada labari? eh principal dinku ta sanar dani kuma sunyi min text suna invite dina zuwa bikin graduation din da za'ayi to bazan samu zuwa ba amma na kira yayyenki nace cikinsu wanda yasami dama yazo miki amma nikam ayimun uzuri kinji ko 'yar daddy cike da farin ciki ta amsa da bakomai inda suna qare wayar suka nufi gidansu rufaida a can suka gama shirinsu sai 4:15pm sannan suka iso gurin inda suka iske an fara gabatar da abinda ya tara iya kyau 'yammatan sunyi kyau yayin da aka fara gabatar da sunayen hazikan dalibi inda aka shiga kiran sunayensu tare da basu kyaututtuka a fannin boko da arabic kiran da akayiwa dije ne yasa na farga da mutanen dake wurin inda ita bata ko lura ba tasa kai ta isa gurin itace daliba mafi kokari da kwazo a makarantar duk iya shege da kiriniya irin nata akwai kokari hakan yasa tasamu kyaututtukan da ita kanta tayi mamaki mamaki ne yakamata hango habeeb datayi kame kan kujera ya zuba mata ido inda bayan an sallameta ta fito da niyyar wucewa idonta ya sauka kan naseer dake can gefe shima da alama ma besan da zuwan habeeb gurin ba tabe baki tayi a ranta tace nasan dan daddy kuka zo anyi muku dole amma bari na qarasa in gaishesu dan na lura iya kwana dayan da nayi bana gidan su har wata kiba sunyi *nayi ne kawai dan in faranta muku amma raina bace yake so kuyi hakuri da wannan kuma* *Alqalamin khady* โœ [3/15, 11:10 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TAME GARI* NA khadija usman 3โƒฃ2โƒฃ da fara'arta ta karasa inda naseer ke zaune wanda tun kafin ta karaso ya shiga sakar mata murmushin daya bata mamaki domin dai tasan wannan murmushin na murnar ta bar musu gidan su ne tana zuwa ta shiga gaisheshi inda ya amsa tare da fadin ina taya qanwata murnar kammala karatunta matakin na farko nagode yayana ta fada tare da cewa ina su Aunty yusra fatan tana lfy ? lafiya kalau tace a gaisheki tana miki murna nagode sosai ina amsawa shiru yayi kafin daga baya yace ashe dai qanwar tamu tanada kokari har haka kice za'a je dake murmushi tayi batare da tace komai ba shima shirun yayi ganin haka yasa dije tace bari taje zasuyi pic da kawayenta da malamai nan ta juya ta barshi a gurin yabi bayanta da kallo yana hangota cikin kawayenta sunata pic da kuma malamai a haka aka gama komai kowa ya watse amma daga naseer har habeeb ba wanda yasan d'an uwansa ya ziyarci gurin sai dab da magariba sannan kowa ya watse su dije gidan su rufaida suka wuce inda saida dije tayi sallah harda yin wanka kafin taci abinci sai wajen karfe takwas ta tafi gida da sanda ta shiga cikin sa'a ba kowa a falon dan haka direct dakinsu ta wuce ta ajiye kayan data shigo dasu nan suka dan taba hira dan ta gaji dayawa ba dadewa bacci ya kwasheta ******************** sannu sannu su dije sun dan kwana biyu da kare makaranta ana jiran result sam taki yadda su hadu da mamy abinda dije bata sani ba ko mamy na lura da ita tanata saka da warwarar yadda zata bullo mata ne ta kadata kauye kowa ya huta cikin hikima batare da daddy ya gane ba **** bikin rufaida ake shirin yi duk da kasancewar mahaifinta dan boko amma baya bawa 'ya'yansa mata damar karatun gaba da secondry har sai kinyi aure hakan yasa rufaida ta fidda miji ansa rana suna son junansu su dije ne kirjin biki anata rawar kafa da shirye shiryen abubuwan da zasuyi tare da kayan da zasu saka dan haka take jiran daddy ya dawo ya bata kudi yau friday daddy ya shigo gari sai bayan isha'i yana zaune a falo yana kallon news mamy na zaune tana masa hira jefi jefi dije tayi sallama ta iso falon da fara'a daddy ya amsa tare da fadin ah ah lovely daughter kina lfy? saida ta zauna daga gefen kafafun sa kafin ta fara gaisheshi ya amsa tare da yi mata murna da kuma tambayarta ya yaga ta dawo gida ko ta gaji da zaman gidan yayan nata ne murmushi tayi batare data bashi amsa ba ta sadda kai kasa mamy da idonta kamar zai fado sbd hararar datake aika mata amma dije tayi kamar bata bata gani tambayoyi daddy ya shiga yi mata akan zamanta a gidan yayanta inda dije ta karkace ta dinga antayi mala malan karya harda mai fuka fukai akan wai yadda suke kula da ita daddy nata fara'a da jin dadi a ranshi dan yana son 'yan uwanshi sosai amma hajiya karima sam bata maraba da duk wanda ya fito daga tsatson Alhajin daga kauye a baya tasami nasara da dama wajwn biye biyen malamai amma yanzu tarasa dalili ko tayi aikin baiyi yadda take so sun jima suna hira dije nason sanar dashi tana bukatar kudi amma tanajin nauyi dan haka take ta nuku nuku yana lura da ita dan haka yace daughter ko kina bukatar wani abun ne? sadda kai ta karayi tace am dama bikin rufaida za'ayi saura sati biyu shine zamuyi shirye shirye to ba matsala gobe sai a baki kije ki sayi abinda kk bukata ko? muryar mamy sukaji tana fadin ah kice munada shagali ai kada ka damu Alhaji basaika bata komai ba wannan aikin ai nawa ne dole in hada 'yata tafi ta kowa akwai wasu kaya da hajiya ma'u ta kawo sai a kaita ta zaba sauran abubuwan kuma na bata kudi ta siya ko cike da jin dadin maganarta daddy yace to ni an hutar dani ma kenan amma na bada wani abun a rage ai ai Alhaji basaika bada komai ba ni duk zanyi komai dan yarinyar nada kirki sosai dije da tunda mamy tayi magana ta dago ta kalleta ta fahimci abinda take shirin aikata mata amma ba damar tayi magana haka jiki ba kwari ta mike tayi musu saida safe yayin da mamy ta bita da kallon sai kin raina kanki ****** shuru shuru har daddy ya gama abinda zaiyi ya tafi dije bata ji an qara mata maganar kudi ba sai bayan ya tafi mamy ta kirata ta shiga zaginta tare da sanar da ita indai tana raye to baxata kara bari taci kudin daddy ba sannan in tana son kanta da arziki ta tattara kayanta ta koma kauye bakaramin damuwa dije ta shiga ba jin muguntar da mamy ta shirya mata yanzu ina mafita? ba yadda za'ayi dai ta sanar da rufaida dan tana mata kokari akan komai yanzu kuma bikinta za'ayi yakamata ta taka rawar gani to yanzu yazatayi kenan ? tunani ta shiga yi kafin daga baya tasami mafita tsalle ta buga tare da fadin yessss sai ni dijen.mai gari nawa baseera dake zaune tana linke kayanta ta dago ta kalleta tace yadai lafiyarki kuwa ?ko sunzo ne in san nayi? dariya dije tayi kafin tace kedai bari kawai wata tsiya zan tsula wlh a gidan nan sakin baki baseera tayi kafin tace ke khadija tsiyar me kuma?dan Allah kada tarihi ya maimaita kansa ki hada harda ni dariya dije tayi kafin tace wallahi ni har kin tunamin ma dan sam na manta da wannan lokacin dan a cikin shika shikan ta'addancin danayi bana sa wannan a ciki saboda kankantar sa yanzu ke khadija wannan ne karami to shi babban ya yake kenan? ki tambayi su yaya habeeb zasu baki labari zaro ido tayi kafin tace rufamin asiri nidai dan girman Allah ki rufamin asiri kada ki hada dani ai ke kada ki damu ko inawa kowa wlh banda ke Aunty na mamana badan kin haife ni ba ta karasa maganar tana dariya haka suka dinga hirarsu cikin nishadi kwanciyar hanksli amma zuciyar dije nacan na saka da warwara **** dare yayi dan kusan qarfe daya da wani abu ake nema kasancewar zafi akeyi sosai duk da A.c dake kunne da fanka hakan bai hana mamy jin zafi ba a cewarta dan haka ta fito falo ta dan kishingida har bacci mai nauyi ya dauketa dije da saboda abinda ke ranta baccinma ta kasa yi saboda haka ta fito cikin sanda dan sam bata lura da mamy ba saida taji munshari Alhmdllh ta fada a ranta inda direct ta nufi dakin mamy kai tsaye ta shiga bincike ko'ina inda tana bude wata hand bag din mamy tayi tozali da kudi rafar 'yan dubu dubu dariya tayi inda ta dauki dauri biyu tasa kai ta fice tana dariya a ranta tana kissima dramer da za'ayi gobe *niko nace su dije an fara 'dan hali ne ko kuma me?* ๐Ÿค” **** tunda asuba da dije tayi sallah ta fito falo ta zauna tare da tsintsiya a hannunta da mofa dake cikim bucket da ruwa tana nan zaune dataji kamar motsi saita mike da saur ta fara shara a haka har mamy ta fito shirye cikin shiga ta alfarma da alama fita zatayi tunda dije ta ji motsi ta mike ta fara shara tanayi tana sharar kwallah kamar wadda aka cewa ubanta ya mutu mamy ce ta kalleta cike da mamaki ganin yadda kwalla wata ke bin wata tace ke kuma uban me yasameki kike shara kina kuka kamar wadda aka sa dole banza dije tayi da ita taci gaba da yadda takeyi duk da ta dan soma gajiya ke ba magana nake miki ba ban son iskanci fa wallahi zan ci ubanki kijini da 'yar iskar yarinya batare da dije ta dago ba ta ce kema zaifi miki kyau ki fara kuka tun yanzu dan ni na kusa gama nawa cikin rashin fahimtar maganarta tace ban gane ba kin kusa mutuwa mamy shiyasa nake kuka kijini da 'yar buta...........uba ubanki ne ke kashewa da zaki kalleni kice na kusa mutuwa to a ina kika sani juya baya dije tayi ta ciro hakoran robar data siyo masu kamar na horo na wasan yara tasa wanda tun jiya taso tsorata mamy dashi da dare amma data samu kudin dataje nema kawai saita fasa ta barta ta huta yau sa gamu to ko ke mayya ce wallahi kinyi kadan kice zan mutu yau kujini da shegiya kin juya min baya kamar allo juyo ki kalleni ki fadamin mana in daki bakinki sai hakoranki sun zube jiyowa dije tayi sukayi ido hudu da mamy wata razananniyar kara mamy tasaki yayin data yadda jakarta ta nufi daki amma ina dije ta cimmata ta rike mata kafa runtse ido mamy tayi ta shiga ihu iya karfinta yayin da dije tayi saurin cire abin dan ta sami damar yin magana tace ki ciremin hokaran mana ko kin fasa? *zan yi kokari. yi muku posting kullum.yanzu ku kara hakuri typing akwai wahala wallahi* *Alqalamin khady* โœ [3/15, 11:18 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TAME GARI* NA khadija usman 3โƒฃ3โƒฃ innalillahi cewar mamy ta fada da karfinta baseera da taji ihun mamy ta leqo amma ganin dije a tsaye ga mamy ta kure da bango yasa ta fahimci dije ta fara aikinta kamar yadda tace dan haka ta sakada daga gefe tana kallon yadda za'a kwashe su kuwa su habu driver da me gadi sun jiyo ihu amma basuda tabbacin daga inda ya fito dan haka suka baza kunne dan jin inda zai qara fitowa jin shuru ba'a kuma yi ba yasa suka qara maida hankali ga hirarsu in banda rawa babu abinda jikin mamy keyi yayin da take ta tuna da mafarkan datake yawan yi akan dije ashe yarinyar dama garken aljanu ne akanta shiyasa ta addabi rayuwar kowa kenan duk irin tsarin datake sha na mayu da aljanu gashi beyi aiki akan wannan yarinyar ba yau abin yazo kanta sam takasa dagowa ta kalli dije itako dije hakan ne ya qara bata dama ta kara maqe murya ita ala dole jinsin aljanu (niko nace dije ina tausaya miki ranar da dubunki ta cika aka ramfo ki) kince zaki ciremin hakora to ki tashi ki fara aikinki mana dan kin san sai kin nemo katafila wajen babbago shi to kada ki bata shekaru kinayi gara ki fara da wuri zan tausaya miki in rangwanta miki albarkacin kina matsayin uwa ga masoyiyar mu dan haka bari nasa a kawo miki kayan aiki irin namu zasu sauqaqa miki duk da bai zama lallai ki iya daga wasu daga ciki ba amma zan taimaka miki dan cikar burinki wallahi ni banida wani buri a rayuwata cewar mamy baki na rawa idonta rufe ta hada hannu biyu gaban dije ni da kike ganina tun ina qaramata burina bai wuce inyi aure in haifi yara biyu ba kuma Allah ya cikamin bayan wannan yanzu banida wani kuma ah ah kinada shi mana wallahi banida shi karima kina fa dashi ranku ya dade dan daga jin muryar nan wlh kunfi dubu dan haka ku yadda banida shi munce kinada shi kariiimaaaa dije ta fada cikin 'dan daga murya ai mamy bata san lokacin data tuma a kasa ba tayi rufda ciki ta saki kuka wanda in bata manta ba ko kar tayi karya da saita ce marabinta da kuka tun na amarci ๐Ÿ˜‚amma yau gata tsofai tsofai da ita an sata kuka wayyo ita karima muryar dije taji tana fadin bama son musu a iya binciken da nayi mun gano kinada manyan buruka a rayuwarki ciki harda korar uwar dakinmu daga gidan nan ni din banza ni na isa in raba hanta da jini ai khadija tafi kowa cancanta da zama a gidan nan ni duk duniya akwai yarinyar danake so irin ta karya muka yi miki kenan? wallahi ko uban ubana bai isa yace kuna qarya ba kuda a halittar ku sam baku san wani abu wai shi karya ba ta yaya zance kuna qarya ai ban isa ba takarasa maganar tana me jan majina da matso hawaye to tunda kin san haka meyasa kike shiga shirgin daba naki ba mun so mu sauqaqa miki shiyasa muka sa ta koma gidan 'ya'yanki amma kika san yadda kikayi kika dawo da ita nan wannan ma bai isheko ba wato saida kk hana mai gidan biya mata bukatar data tambaya alhalin ke bayi mata zakiyi ba wallahi yaseen kwarankwasa kinji na rantse ba laifina bane dawowar ta gidan nan wlh sharrin yarana ne dan dama shi habeeb tun yana shan nono na fuskanci baida son mutane shi kuwa naseer tsegumi to yawan tsegumin su yasa nace ta dawo gida kuma kinga abin Allah saiya hadasu da munafukan mata wlh ba yin kaina bane su suka dinga zuga mazan to dama abu ya tadda hali musamman naseer da yusra sarakan munafurci su suka qara iza wutar duk da nasan gaskiya nasan khadija batada fitina to sbd bana son sunanta ya baci shiyasa naje na taho da ita kuma batun Alhaji danace kada ya bata kudi wlh ni nayi niyyar yimata komai da take bukata dan yanzu haka ma can nayi inda zan gwangwajeta da kaya na alfarma inda nake son tafi amaryar ma haduwa da tsari dan kun san khadija ba baya ba wajen kyau sannan ga....... ya isa haka amma kin makaro dan yanzu haka har su akuyatu wadanda muke cousins da su sun dauki wani abu a jakarki yanzu zasu tafi suyi sadaka da su domin almajiran mu sun cika kofar gidan nan cikin mamy ne yabada kuuuu wata muguwar gudawa ta taso mata jin wai an kwashi kudi a jakarta za'a rabawa almajiran aljanu wayyo ta shiga uku bata ankare ba ko taji ta jika wandonta da dan karamin zawo jin dan doyi da dije tayi yasata fadin warin me nakeji haka ta fada tana toshe hancinta mamy data tabbatar bako tantama zawi tayi yasata fadin wlh inaga jaba ce ko beraye sukayi tusa a store duk da zuciyarta na rawa ta fadi hakan dan tasan sun gama sanin me tayi amma bari tayi karyar kare kai Allah yasa kada su gano muryar dije ta tsinkaya tana fadin wato zawo kk yi kenan ba laifi ai abin yabada kala tusar bera data jaba ta hade da zawonki to yanzu kinga ance akwai sauran almajirai kusan miliyan uku basu samu sadakar ba kuma sunce suna nan ba inda zasu suma sai an basu dan haka yanzu muna neman izininki ki bamu wannan da hannunki muje a basu a basu hakuri mamy dake duke wani kuka ta fashe dashi dan a rayuwarta ita mace ce me son kudi ta yaya zata iya rabawa aljanu sama da miliyan uku kudi to ai ko bil'adama ne batada wannan zarafin bare jinnu har yanzu kanta duke yake ta kasa kallon dije dan wannan hakoran data gani tun farko sun razana ta dan girman Allah kuyi hakuri wallahi banida wannan arzikin to ba dama kince uwar dakinmu zaki je ki siyawa kaya ba to ki bayar dasu ayi sadakatu jariya banda abinku bskwaso uwar dakin naku tafi ta kowa ne ? mu kk tambaya? ni na isa in tambayeku wlh subutad baki nayi to munji mu dawo kan maganar mu kince ke kina son khadija to meyasa bakya son dangin.mijinki ? waye yace bana sonsu mutanen kirki irin wannan ai ni nafi kowa sa'ar dangin miji ko ince 'yan uwa ma kin fada ba dai dai ba cewar dije data gaji da tsayuwa ta zagaya ta zauna kan kujera mamh datake jiyo.muryar dan nesa da ita yasa ta kara hautsinewa dan duk a tuninta wani salon ne to kin san kina sonsu meyasa bakya zuwa inda suke kullum.kk kyamarsu sannan kina..... wallahi a cikin satin nan nake shirin zuwa dan dama can ina tunanin farraku akayi mana tsakaninmu amma yanzu ya karye ga dukkan alamu to munji amma bamu yarda ba tana shirin sake magana sukaji ana kwankwasa kofa da sauri dije tace kinyi baki 'ya'yanki sunzo gaisheki mu zamu wuce mu barki da uwar dakinmu ama anjima zamu dawo ta mike ta nufi kofa ta bude duk da zuciyarta na raya mata tayi sakin layi datace yaran mamy ne bayan batada tabbas su din ne kuwa inda cikin sakin fuska ta basu guri suka wuce ta shiga gaishesu mamy data mike tana ta kokarin kintsa fuska da son shiga daki don wanke jikinta taga shigowar su habeeb take ta kara yadda da lamarin tana gab da shigewa dakin ta tsinkayi muryar habeeb yana fadin ah ah mamy lfy kuwa naganki haka? hmmm kai dai bari kawai ta fada tana me kallon inda dije ke zaune wadda ta dago ta kalleta tace lah mamy meya sameki haka nima fa yanzu na lura ? apolo nakeyi ta fada tana me tafiya da baya da baya dan karsuga shatin kashin dake jikinta ikon Allah cewar naseer *Alqalamin khady* โœ [3/15, 11:19 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TAME GARI* NA khadija usman 3โƒฃ4โƒฃ *domin ku kawai masoya tame gari nayi kewarku kwana biyu wlh abin ne sai a hankali ina fatan zaku kara hakuri fiye da yadda nasanku,sannan masu bina pc suna tambayar buk din dan Allah kuyi haquri wlh banida time din tsayawa inta turashi abin ne dayawa kuma kullum abin daduwa hakeyi Alhmdllh ina sonku fiye da yadda kk son tame gari* a polo mamy ? tun yaushe? kai ni bana son jarabar magana ku jirani ina zuwa ta fada tana me afkawa daki tana shiga ta rufe kofar nan ta shiga tsinewa aljanun dije albarka tare da fargabar bata san ko nawa suka dauka a jakarta ba suka bawa musakan aljanu to inma ba son zuciya irin na jinni ba su da suna iya zuwa banki su dibi wanda ransu ke so amma wai su tsaya dibar nata dan su rabawa wasu dan salon mugunta da anyi magana yanzu haka suce basa cin haram ta jima tsaye tana tsinewa dijen tare da ninkin tsanar ta a zuciyarta ji tayi kamar an taba qofar ai a sukwane ta afka toilet tana shiga ta fada a fili Allah ya isa tsakanina daku wannan wace irin jaraba ce yanzu wato dama yarinyar nan iyayenta sun san tanada fasinjoji shiyasa suka kadota nan shi yasa ashe yaran nan suka dinga rokata in zo in dauketa ashe su kadai suka san azabatul ular da suka sha ni gashi an ganamin azabatunna'ura banji ba ban gani ba kawai dan na hana abata kudi to wlh da sake gurin malam zan tafi ya bani tsarin kar tasan kar inzo ingama da shegu zaki gane kurenki ne tanayi tana wanke kashin jikinta yanzu dubi kiga marabina da inyi kashi a wando tun na yaye amma yau kiri kiri an sani nayi Allah ya isa wlh da haka harta gama ta kimtsa jikinta cikin dan hade rai ta nufo falon dan tama fasa fitar kuma yanzu tunda aljanun sun sauka uwar yarinyar zataci inya so ko sun dawo tabasu hakuri duk da bata fatan su dawo din dan wannan hakoran data gani in batayi qarya ba zata iya cewa sunyi hauren giwa *kai mamy a rage ta gobe* ๐Ÿคฃ karasowar ta falon yayi dai dai da shigewar dije dakin su inda su habeeb suka duka suka gaida mahaifiyar su cikin girmawa ta amsa tana me tambayarsu lafiyar matansu duk suna lafiya suka amsa yayin data lura da yanayin naseer yana ta fara'a kamar mai tallan hokorin maka cikin kulawa tace naseer ya akayi naganka kamar cikin farin ciki kara fadada fara'arsa yayi inda ya shiga sunkwiyar dakai sannan yafara magana am dama jiya ne yusra tayi zazzabi to shine nayi mata test sai naga tana da juna biyu wajen 3months kai dan Allah dagaske kk wannan maganar wlh kuwa mamy dagaske kai Alhmdllh amma naji dadi wlh yanzu ya jikin nata? ai tasamu sauki sai abinda ba'a rasa ba to ka kula da ita sosai ko inxo in daukota ta dawo nan da zama kai gaskiya nayi farin ciki ni karima yau zan dauki jikana kun san ance abin cikim kwan yafi kwan dadi kai kuma fa bawani labari ne? ta tambayi habeeb wanda ada sam baya bukatar matarsa ta haihu yanzu amma yarasa dalili tunda naseer ya fada mishi matar shi nada shigar ciki shima yaji yana son hakan sai kuma yaga mamy ma ta nuna farin cikinta shima dan haka zai so yaga yadda zatayi idan yace sajida nada ciki tunanin me kk yi ne ? mamy ta katseshi am ni dai mamy tukunna dai a tayamu da addu'a tunda kinga auren bawani dadewa yayi ba da har za'ace an damu kaci gidanku auren naku ne be dade ba auren yanzu da wata tara cikin na goma an haihu amma ku gaku nan kuna neman tasamma shekara amma kacemun wai baku dade ba kai dai ka biyewa tsarinku na 'yan zamani dakai da wannan guzumar matar taka da kun hakura ma kun gwada yin daysn ka tabbatar ko tana haihuwar in kwayayen basu bi jinin al'ada ba dan wannan dadewar ba aure ai ba fa'ida bane yanzu dai kagani akan kannenka zasu samu qaruwa su barku abin haushi kunaji kuna gani sun zama su uku sun sami ribar aure ku kuwa kuna nan kuna kayan kashi kuna dada tsufa ba gara kuyi me dalili ba haka ta dinga zazzaga masifa har ta gaji tayi shuru inda daga karshe suka ce zasu tafi kiri kiri tace ya tsaya tayima yusrah wani abun ya tafi mata dashi tasan masu ciki da kwadayi haka suka zauna zaman jira habeeb kam ya cika iya cika ya kudurta a ransa insha Allah daga yau zai fara bita har sai sajida tasami ciki ๐Ÿ˜‚ sun jima zaune kafin mamy ta fito dauke da basket da kuloli niki niki tace kuma batace abawa ci ki kasayar ba nan suka mata sallama suka tafi tana qara jaddadawa naseer ya kula da yusra ******************* ba yadda mamy ta iya haka ta cire kudi ta sayawa dije duk abinda ta alqawarta wa su arwanatu bayan ta dawo ta kira dije ta bata dije na tafiya ta kife a gurin ta fashe da kuka tana ta tsinewa su akuyatu itako dije rai fesss hidamarta ta shiga yi inda mamy ta shirya ta tafi kauye da kyar tayi kwana daya ta dawo bakaramin mamaki sukayi ba da ganinta duk da ta dan taba halin amma ba kamar da ba su dije biki yayi biki inda aka sha shagali anan wani abokin angon ya ga dije ya nuna yana sonta kasancewar bata taba soyayya ba bakuma ta da niyyar yi yssa ta bashi hakuri amma ya nace dole tabashi number ta wai su dinga gaisawa tsabar nacinsa yasa dije ta bashi number bayan biki anyi an tashi lfy sai muce Allah yabada zaman lfy Ameen ***** tun ranar daya zo mata da batun son su haihu tashiga tashin hankali matuka domin dama bafa wai ra'ayinta bane kin son haihuwar ba illah gwajin datayi kafin aure an tabbatar mata mshaifarta batada kwarin da zata dau ciki ta rasa yadda zatayi ta sanar da habeeb gashi tana mugun sonshi shiyasa tayi amfani da kissa ta nuna masa bata son su haihu da wuri su mori rayuwar su tayi hakan ne dan idan ya fara mata maganar haihuwa ta nuna masa shan maganin datakeyi yayi mata illa tasan zai tausaya mata tunda dashi akaji dadin to amma me ga wata sabuwa wai ya na son su haihu tayi karairaiyar tayi kissar tayi amfani da yaudararrun kalamai amma ina taga sam wannan.lokacin sunki aiki to ina mafita? laila ita ta fado.mata a rai da sauri ta dauki wayarta ta kirata saida ta kusa tsinkewa sannan ta dauka bayan sun gaisa ta sanar da ita tanason ganinta wa? ni? a gidanki? bama nida hankali kenan kin manta artabun da akayi kenan ke dayalla tabar gidan wannan an rufe shafinta kedai kizo kawai wlh ina son ganinki um.um.fa ina tsoron 'yan walimar nan na gidanki ko suna nan har yanzu basu gama ba ke ban son iskanci suna nan har yanzu muke zaune lfy kedai ki shigo dan Allah to shikenan zan shigo anjima ok.sai kinzo nan ta yanke wayar tare da qara fadawa duniyar tunani ko zata samu mafita *** sai da ta gama jin bayaninta kafin ta dago ta kalleta wlh sajida kina bani mamaki wani lokacin wai duk ina basirarki take tafiya ne?duk ina kissa da kisisinar dana sanki dasu nasan ke ba boka ba malam amma Allah yayi miki baiwar sanin hanyoyin sarrafa d'a namiji shin shi dan wannan matalar ne zata gagareki magance ta hmmm laila kenan baxaki fahimta ba wannan karon habeeb bakiga yadda ya nunamin ba ina shawo kanshi akan.komai cikin sauki amma wannan karon abin yaki to ai wannan.me sauki ne ki nuna masa kawai kin amince ku daina tsarin iyalin amma ai yasan Allah ke bayarwa kuma lokacin daya so inyaga baki samu ba sai ki nuna masa illar maganin ne yasa haka ummmm hakane amma ko kin manta habeeb likita ne likitan ma na mata ina gudun kada yayi bincike ya gano karshe abin ya kwabe .. to ke tsayawa zakiyi harya gani din ko kinaji kina gani zaki tsaya yayi miki gwajin ai family doctor dinku zaki tasamma ya baki bake result ki nuna masa inya so yayita baki magani kina banka ina gudun ranar da zai san bana haihuwa yayimun kishiya wannan abar ita nake tsoro ke dan Allah ma kibar wannan zancen ai kishiya keda ita sai a lahira kawai dai kibi shawarar dana baki inaga ita ce mafita hakanr to Allah yasa mu dace Ameen ta fada tana me qoqarin mikewa bari nakawo miki ruwa mun tsaya zance ban.baki abinci ba ***** yawan nacin sa da kiran dayake mata yasa ta fara saurar sa ishaq mutum.ne mai sauqin kai da kuma barkwanci wasa da dariya itako dije ga son zance da haka ya siyeta ta fara biye masa a waya suna shan hirar su kullum sai sun raba dare duk yadda ya so tabashi dama yazo gidan su ki tayi hakan yasa nan.ma kullum yake mata magiya amma sam taki yarda itako mamy tarasa hanyar dazatabi dan ta kuntatawa dije tabar gidan ta tsani ganinta amma taga alamar yarinyar tazo kenan koda yadda Alhaji ke nunawa sai dai aure ai kuwa in kin san wata baki san wata ba ta fada a zuciyarta wani tunani tayi nan ta saki murmushi kafin tace a fili ta yaro kyau take bata karko daga ke har fasinjojin naki nasan inda zan jefa ku sai abi wani sarkin kuma muma mu huta mun yadda kwallon mangwaro *muje zuwa kudai reader's dramer yanzu aka fara fatana ku kara hakuri* *Alqalamin khady* โœ [3/15, 11:19 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TAME GARI NA khadija usman 3โƒฃ5โƒฃ Alhamdulillah,naga sakon ku masoya tame gari,masu kirana ma duk ina godiya Allah ya kara kauna ya barmu tare Ameen yau tun safe mamy tasa ake gyaran gidan, hakan ya tabbatarwa da dije daddy na nan shigowa gari kenan,dan haka itama ta shiga nata shirin,dan tana son sanar dashi batun zuwanta gida dan ya zuwa yanzu yakamata ace taje taga iyayenta dan tayi kewarsu. Shigowar dare daddy yayi,dan haka basu samu damar haduwa da dije ba sai da safe wajen yin break fast,wanda yau mamy da kanta takira dijen sai wani nan-nan takeyi da dije da wata fara'a inda abin ya dinga bawa dijen mamaki,shi kuwa daddy dadi yadinga ji, ganin yadda mamy yanzu take nuna tsantsar kulawarta akan danginsa,sabanin da datake nuna tsanarsu k'arara da kyama,hakan gasa dayaga yadda take yiwa dije da kuma sanar dashi datayi wancan lokacin zataje kauye sai ya ji ya k'ara sonta,tare da k'ara bata wani matsayi a zuciyarsa.Cikin fara'a ya amsa gaisuwar da dije ke yi masa, haka ma mamy,yayin da dijen ta fara aikawa cikinta d'a'amin ba kama hannun yaro,dan dama dije fannin girki ba wasa. ko da suka gama daddy ya koma falo shi da mamy suka zauna,itama dije na karewa ta taso ta iso falon ta zauna kasa daga gefen daddy ta shiga sanar dashi batun zuwanta kauye,cikin fara'a da jin dadin maganar tata yace "kai beautifull daughter amma naji dad'i wlh" dan nima kin tunamin da zumunci ai tafiyar dani za'a yita,dan haka ki fara shiri zuwa next week saimu tafi gaba d'aya, zanyiwa yayyenki magana sai su shirya har matansu a tafi gaba d'aya. cikin farin ciki dije ta amsa da to daddy nagode Allah ya kara girma. Ameen daughter,sai a fara shirin zuwa ganin maigari ko? mamy da tunda suka fara maganar taji yace dukansu zasu kauye taji ranta ya baci ta dago kaitare da fadin"haba Alhaji ! ya zaka ce a tafi gaba d'aya bayan na fada maka lalurar da yaran can ke fama da ita,kasan kuma bai kamata ace suyi doguwar tafiya ba yanzu. Au hakane fa kema kin kawo uzuri,wannan ai bawata matsala bace, su mazan sai a tafi dasu, tunda dama su zuwan yake kamar wajibi a gurinsu dama dai dan matan nasu suje suga tushen mu ne. To wai zuwan yazama dole ne ?naga ita khadija yazamarwa dole tunda ita ce tushenta can kowa nata nacan,banda ma dai son zuciya da kwadayi irin na mutanen kauye,ta yaya zan haifi 'ya kwaya daya tal a duniya sannan in bari tayi nesa dani,to amma mutanenmu musamman na kauye sun baci da shegen son abin duniya da mutumin kauye da noma da kiwo a ka sansu, amma yanzu sun sawa ransu wai suma sai sunyi boko,to bokon da suk........ya isheki karima!! cewar daddy cikin daga murya,wallahil azeem ki kiyayeni cin mutuncin naki ya isheni,da na dauka kin shiryu kin daina ashe tuban muzuru kikayi,ni banma yadda da zuwanki da kikayi garin ba kwanan baya ,nasan akwai abinda ya kaiki,ina so ki shiga hankalinkk ko da na barki a baya kina abinda kika ga dama to ba tsoronki nakeji ba,kyaleki nakeyi kawai dan a zauna lafiya,amma ke na lura kinki ki fahimci hakan to wallahi ki kiyayeni kinji na fada miki.Fada sosai daddy ya shiga yi inda yake shiga bata nan yake fita ba,da farko Dije taji haushin maganganun mamy amma daga baya dataji yadda daddy ya fara sababi saita dan ji sanyi. Mamy kuwa lakwas tayi dan batayi tunanin daddy zaiyi mata magana haka ba,kallonta ta mayar ga Dije suna ko hada ido Dije ta zaro mata su tare da dan wurkila su,sai mamy taga kamar abubuwan ne,ji tayi gabanta ya fadi dan haka tayi saurin kawar da kanta tare da fadin nashiga uku a zuciyarta,tsam ta mike ta nufi part dinta,daddy ma kwafa yayi ya nufi part dinsa shima aka bar Dije na muzurai ganin haka yasa itama ta mike tayi nata gurin ranta fari kal sbd batun tafiyarta kauye. ***************** Tun ranar data furta masa ta amince ta daina shan duk wasu kwayoyin haihuwa ya saki ranshi, inda ya dad'a dagewa tare da bata kulawa sosai ko yaushe yana manne da ita wai duk dan ta samu ciki,ita kuwa sai ta kara narke masa,soyayya sosai suke sha abinsu. Sosai Naseer ke bawa yusra kulawa, dan har aiyukan gida shike tayata, tunda tun farko sun hada baki da sajida sunce basa son masu aiki. **** Ko da daddy ya kirasu ya sanar dasu batun tafiya kauye duk ransu bai so ba,amma dole suka amsa masa,dukan su kamar abin hadin baki da suka fadawa matan cewa sukayi sai sun bisu,shi Habeeb bai wani damu ba da sajida tace zata bishi,amma shi Naseer lallaba yusra ya shiga yi inda fafur taki amincewa tace ita saita je tunda ba laulalayi takeyi ba dole tasa ya hakura aka shirya tafiyar da ita. ****** Gobe Alhamis ranar ta kama ranar tafiyarsu dan haka, daddy yace su shirya da wuri,ko da dare yayi dije kasa bacci tayi dan murna inda Ishaq ya kirata a waya,koda ta fada mishi batun tafiyar da zatayi gobe,sosai ya nuna mata rashin jin dadin sanar dashi da wuri da batayi ba inda ya dinga rokonta akan ta amince ya zo da safe suyi sallama amma taki amincewa dole ya hakura. Washe gari da sassafe kuwa sai ga su Habeeb dukansu,ko da daddy ya gansu da matansu bai tambayi dalilin su na tafiya dasu ba. Zuciyar mamy cunkushe take fa tsantsar bakin ciki daka kalleta zaka san tana cikin zunzurutun bacin rai dan ba yadda zatayi ne kawai ta hakura dan yanzu lamarin daddy yafi karfinta da alama sakin hannu ya kamata. *(niko nace dama ana sakin hannu ne a bangaren asiri,haba mamy)* ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ kowa ya shirya dan haka suka fito gaba daya dan shiga motoci. Daddy ne ya kalli Habeeb yace, amma dai kun san ba zaku debi motoci haka mu tafi dasu ba kamar zamu taron siyasa.Dan haka ku da matanku ku shiga mota daya muma saimu shiga daya. to daddy suka amsa cike da ladabi. yadda yace din hakan sukayi dan haka suka shiga suka saita hanya sai garin jigawa kauyen gawo. *A sauka lfy* *vote* *comments* *with* *Alqalamin khady* [3/15, 11:20 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ TAME GARI NA khadija usman 3โƒฃ6โƒฃ *Alhamdillah gaskiya ban san da bakin da zan godewa masoyana ba,hakika naga ainihin sahihiyar soyayya naga zallar so fiye da yadda dije ke son mazga ina alfahari daku da godiya gareku tare da addu'ar Allah yabar kauna ya kara zumunci ya sa zumuncin da soyayyar su dore har abada ameen* sai kusan la'asar suka shigo garin,inda gida ya kacame da murnar zuwansu,mai gari kuwa abin ba'a magana,ba karamin farin ciki yayi ba na ganin daddy gaba daya da iyalansa,nan da nan aka shiga hidima dasu. itako Dije ko da aka iso babu wanda ya lura da sulalewarta sai gida,sai da mai gari yace wai ina tawaje na ne?sannan suka lura da bata nan,dariya yayi dan ya tabbatar ta tafi gidane. da gudunta ta shiga gidan tana kwalawa inna kira,wadda tun isowar su labari ya isko ta cewar gasu Dije nan aikuwa tsantsar farin cikinta ya kasa boyuwa dan tayi kewar 'yar ta sosai. tana zuwa ta fada jikin Inna, inda ita kanta Innar ta debe kunya ta rungumeta,sosai Dije ke kukan farin cikin jin dumin mahaifiyar ta, suna tsaka da haka baba Inusa ya shigo dan ya samu labarin isowar su yanzu ma daga gidan mai gari yake yayi wa su daddy sannu da zuwa,ya nufo gida dan jin cewa diyarsa tana can domin shima yayi kewar ganin tilon 'yar sa,ba karamin farin cikin ganin Dije yayi ba domin gani yayi ta canza masa tayi masa girma a ido,tabbas ya yaba da kokarin yayan nasa wajen rikon diyar tasa. Ko da Dije ta ganshi ba karamin jin dadin ganin mahaifin nata tayi ba da sauri ta taso ta isa gabanshi ta tsugunna ta shiga gaisheshi cikin girmamawa da fara'a,amsawa ya shiga yi tare da tambayarta bayan rabuwa. Daga nan kuma suka shiga hirar bayan rabuwa,sosai suka shiga hira ta shiga taya Inna aiki dan baba yasa an yanka kaji da zabbi dan ayi farfesu a kuma soyawa baki,fura Dije ke damawa dataji nono sosai. magariba aka kira,hakan yasa baba mikewa dan tafiya masallaci,yana fita itama Dije ta daura alwalar ta shiga daki ta bar Inna na karasa aikin,itama tana gamawa tayi alwalar ta shiga yin sallar. *** ********** *** Baba suke jira ya shigo dan ya samo yara su kai kayan nan gidan mai gari. suna zaune har akayi sallar isha'i sannan baba ya shigo nan yake sanar musu cewa maigari yace su mamy sunce nan zasu sauka ita da matan su Habeeb dan haka a gyara musu guri. Tunda Dije taji haka tasan shirin mamy ne tasan kuma tayi haka ne kawai dan cin zarafi,ba bata lokaci kuwa suka mike ita da Inna suka kara gyara dakinta na da,sun gama kenan sun dawo sun zauna sukaji sallamar su tare da Haruna dan gurin baba zakariyya da wasu yaran dauke da akwatunan su niki-niki,bayan sun gama shigo da kayan ne su mamy suka iso da su yusrah wadanda dukan su sai yatsina sukeyi dan dama zani ce ta tadda muje su da mamy sam ba sa son mutane indai ba nasu ba basa kuma son rayuwar kauye duk da yadda sukayi tsammanin kauyen ya kasance sunga sabanin hakan amma a cewar su kauye kauye ne. Ganin kamar a gajiye suke yasa mamy shimfida musu tabarma babba nan suka zauna duk da garin da sanyi kasancewar lokacin sanyi ne,Dije ce ta fara yi musu magana kamar abin dole suka dinga amsa mata a daddakile Sam bata wani damu ba dan dama ta saba da hakan,ita kuwa Inna sam sai taji ba dadi ganin yadda sukayin hakan na nufin kenan 'yarta a haka take rayuwa?kai ba haka bane watakil gajiyar mota ce da wannan tunanin ta barwa ranta suka shiga gaisawa ba yabo ba fallasa,bayan an kawo musu abin tabawar da ak tana dar musu duk da ba wanda ya kula da farko amma ita yusrah abinka dame ciki,tana shakar kamshin dabgen dahuwar daddawar da naman kajin nan yasha tuni yawunta ya guda ,ta jawo kwano kuwa ta shiga dandanawa an taji zakwai,dan ji tayi kamar a duniya bata taba jin test irin wannan ba ai nan da nan ta shiga korawa cikinta jawabi,ganin yadda take cin ne yasa su mamy suma suka dan fara tabawa,sai gashi su mamy an manta a gaban surukai ne sun sheke abinda ke cikin kwanon yusrah kam harda sudi kamar taga makerin kwanon. Ganin sanyi yafara yawa yasa Inna tace su shiga ciki,bayan sun shiga sunyi mamakin ganin yadda aka gyara dakin duk da gadon karfe ne amma da katifa sai wata katifar a qasa wadda aka sawa zanin gado nan mamy ta zauna su kuwa suka gefen gadon suka zauna. Wanka Dije tayi tasa riga da wando na bacci tare da hijabi ta fito taga inna nata kokarin kankanta kaya tana kokarin shiga kicin,sannu da kokari innata ta karasa tare da karbar kwanukan ta shiga dasu kicin din ta fito ta tadda Innar tana nade tabarmar da suka tashi,shima karasawa tayi ta karbi nadin tabarmar ta nade kafin ta kaita daki ta fito inda Innar ta kalleta tace sannu Dije,ashe yanzu kinyi hankali da son aiki,ai na dauka zaman birni ya bata ki kema dan naji ance matan birni basa son aiki, dariya Dije tayi kafin tace, kai! inna waya fada miki matan birni basa son aiki? Au har sai an fadamin,mutanen da zaka gansu jiki lukwi-lukwi kamar bawon kwai,ai da kin gani kin san basa wani aikin wahala,yanzu ke baga shi nan ba wa zai ce asalinki nan ne,jibi yadda kika zama kamar ma ba 'yar kasar nan ba,gaba daya kin canza kamar wadda bata cin tuwo,duk da dama su mutanen birni sun maida cin tuwo kauyanci. Kai! Inna ashe gaskiya ne maganar mutane,da suke cewa ke na gado a zance,gashi nan tun dazu kike ta zuba zance ba commer ba fullstop. Na shiga uku! sunan su waye kuma hakan? inna ta fada harda dan dafe kirji Dariya Dije ta gumtse kafin tace, "au kina nufin yanzu baki san su ba Inna?" Ta ina zan san su bayan daga jin sunan kin san sunan manyan arna ne. Ke meya kaiki mu'amulla dasu?,wato duk jan kunnenki danayi bakiji ba ko Dije? Hmmm! Inna kenan wallahi dan ma bakiga ita commer din ba har wata 'yar lankwasa ta yi. Saboda tsabar kafurcin ko kuma saboda me? Inna ta jefo tambayar a guje,wadda tasa dole Dije saida tayi dariyar da take boyewa. Au dariya ma kikeyi kenan ko?,saboda duk kin koyi dabi'unsu,ba dan ma tun kina shan nono nake yawan maimaita miki kalmar shahada ba tare da karanta miki bisimillah, kulhuwallahu ,falaki da nasi,tare da duk wasu addu'oin tsari, kice da yanzu sun dulmiyar min dake,dan daga jin sunayensu musamman ma na dayar kin san sun koshi da ruwan kafurci,daga ji kin san gadonsa sukayi bawai haye bane. Au dama ana taka hayen addini Inna? ke da baki sani ba? Ah ah ni ban taba sani ba kam. To kamar yadda suke gudowa daga addininsu na kafurci su dawo namu na muslunci,haka suke fita daga nasu su koma wani dai na dangin arnar dan jahilci wai su sun tuba,to wallahi bari kiji in fada miki ki gaggauta rabuwadasu tun wuri,dan bazan yadda ayimun sakiyar daba ruwa ba,zan kuma cire kunya inyiwa karima magana dan suma da laifinsu da basa sa miki,ido har suka bari kike mu'amulla da dirka-dirkan arna. ganin da Dije tayi Inna ta dage tanata fada iyakar iyawarta yasa ta yin gum da bakinta tace, yakamata Inna a dora ruwan zafi dan nasan sai sunyi wanka kafin suyi bacci. tana ci gaba da fadan ta mike ta hura wuta ta dora ruwan kafin ta dawo kan Dije taci gaba dayi mata fada akan su cammer da fullstop akan ta rabu dasu. Tare da Innar suka shiga dakin,inda suka iske su zaune suna hira,amma jin shigowarsu yasa su yin shuri,mamy harda jan dan guntun tsaki wanda duka tsakanin Dije da Inna ba wanda baiji ba,amma sai suka share suka nemi guri suka zauna. Sake gaishesu Inna tayi kafin tace, Naji ance da ku duka zaku zo harda matan su mai sunan malam,amma naga daya ce tasami zuwa ciki ko dayar tayi nauyi ne? cikin rashin fahimtar tambayar ta ta mamy ta ce, kamar ya kenan? Naga ne harda kanwar ki ku ka zo wannan ta kwancen dan naga kun dan yi kama da ita, ta nuna sajida dake kwance saman gadon karfen. Ita kanta mamy tasan duk wanda yaga Sajida yasan ba sa'ar auren Habeeb bace ,amma saita maze ta ce,ai wannan ita ce matar mai sunan malam din,wannan kuma matar Naseer ce duk ta nuna su. Ikon Allah!! cewar Innah kice yaro ya raya sunnah yayi koyi da Annabin rahma,yafara da bazawara,to Allah ya sanya alkhairi ya bada zuriyya dayyiba. Duk yadda Dije ta so hadiye dariyarta kasawa tayi haka ma yusrah,itako mamy kunya taji yayin da uwar gayyar ko ta cika fam,tama rasa kalar rashin mutuncin da zata yiwa tsohuwar nan. Itako uwar gayyar inna bata ma san ana yiba,nan taci gaba da sheko addu'a har baba ya shigo ya sake gaishesu ya juya zuwa daki Inna ta tashi ta bishi. Tana fita Sajida ta kalli Mamy tace, ina son yin wanka amma naga gidan kamar ba toilet ya za'ayi kenan?,dan wallahi bazan iya kwana haka ba. Injiwa yace miki ba toilet!,ai wai a haka akwai shi,ai mudai kaddara ta auremu da aka jawomu wannan kauyen ga shegen sanyi,gara ku ma mazajenku sunce ku kuka matsa sai sun taho daku,ni da nasan dawan garin tuntuni, ai ni aka matsawa sai na zo, ta karasa maganar tana kallon inda Dije ke zaune ta wurga mata harara. Dije yi tayi kamar bata san tanayi ba saima ta mike d niyyar barin dakin taji mamy tace, "sai ki hada mata ruwan wanka dan tayi ko" bata tanka ba ta fice tadauki bokiti ta zuba ruwan zafi ta surka, har ta dauka kuma ta ajiye ta kara kandamo ruwan zafi ta kara tasa hannunta taji zafi rau,dariyar mugunta ta saki ta dauki ruwan faki bandaki ta dawo ta leka dakin tace takai mata. Sai da ta gama yangarta kafin ta mike ta dauki duk abinda zata bukata ta fito Dije tayi mata jagora har bakin bandakin. Cike da kyankani take kallon gurin inda ta leqa da sauri ta dawo harda toshe hanci,hakan ne ya kara kular da Dije dan tasan dai bandakinsu sumunte yake ,kuma wanke yake fess,dan inna akwai tsabta itaka dai ace baida rufi,ganin datayi ko kallonta Dije batayi ba yasa ta shiga,ta dan jima kafin ta cire kayanta tana ta neman gurin rataye wa ta rasa,dole ta dora saman katanga inda ta dawo ta tsaya tana tunanin yadda zata iya wanka a irin wannan wurin,dan tunda take a rayuwarta wannan shine karo na farko data taba zuwa kauye kuma ta taba shiga irin wannan bandakin. Itako Dije dake tsaye sajida na aje kayanta ta zura hannu ta kwashe su dan dama tsayuwar datakeyi kenan,tasa kai ta nufi hanyar waje tana fadin zaki gane bakida wayo wato ni zaki rainawa muhallin iyaye ko,tana zuwa zaure ta watsa kayan saman wani buhu dake jingine a gurin itama bata san kona miye ba ta fice tayi gidan maigari tana fadin ni acan ma zan kwana. ****** Gajiya tayi da tsayuwa ga sanyi dake busata ga kyankyani datake ji tasa hannu danta fara wankan,da sauri ta dauke jinshi tayi da mugun zafi kuma dama ita duk sanyi bata fiya son ruwa mai zafi ba. Mikewa tayi da niyyar dauko kayanta tasa ta fita ta sanar da wannan shwgiyar yarinyar ta kara mata ruwa amma kuma sai me? wayam ta gani babu kaya babu alamar su. *Hegiya dije a nzo gidan naku ma saikin nuna hali,to fa!!!* *vote* *comments* *with* *Alqalamin khady* โœ [3/15, 11:23 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TAME GARI* NA khadija usman 3โƒฃ7โƒฃ *A koda yaushe bazan gaji da bawa masu bina pc akan in tura musu tame gari hakuri ba,wallahi banida time din wannan kuyi hakuri abin ne dayawa kunada yawa sosai kuma kowa da wanda yake so,ya kk so inyi ina iyakar kokarina wajen ganin na saurari kowa,amma duk da haka ban tsallake zagi da cin zarafi ba a gurin wasu,amma nagode sosai kuma ni yanzu ba abinda zai batamun rai insha Allah yadda nafara littafin nan tunda ni nayi niyya to saina karasa shi da yardar mai duka dan haka ina mugu mugun sonki all tame gari fans* ๐Ÿ˜˜ __________________ Qara dubawa tayi sosai ko kayan sun zube kasa ne,amma taga wayam ga sanyi daya fara kodar ta yana shiga jikinta,to ya kenan? ko tantama batayi tasan kayan baya suka fada,to ya zatayi kenan,yankewa kanta tayi kawai tayi wankan inta gama ta leko intaga wannan me siffar aljanun tace ta miko mata kayan,in kuma bataga kowa ba tayi shahada ta dauko da kanta,da wannan tunanin ta qara sa hannu cikin ruwan dan ta fara wankan,yana nan dai da zafin sa ga sanyi da iska nata busowa abu ya hadar mata goma da ashirin. Wani dutse data gani ajiye gefe ta dan raba ta zauna akai,tana jiran ruwan ya huce tayi wankan,ta jima a zaune jin sanyi na niyyar illata ta yasa ta matso da ruwan ta dinga diba kadan-kadan tana watsawa tana gantsarewa tare da rutse ido. ****** Tana fita direct gidan maigari tayi tana zuwa kuwa gida ya amsa kuwwar zuwanta inda aka shiga hirar yaushe gamo ,har maigari suka shigo shida su Habeeb suna biye dashi nan suka zauna aka dasa sabuwar hira. Ganin dare nayi ne yasa maigari cewa Dije "ke tawajena!! anan zaki kwana ne?,dan naga dare yafara yi. Ai kaima kasan dole in kwana a gidanka,shekara ta nawa marabin da in kwana, kaga kuwa dole in barje haushina. Ja'ira baki abin magana,to su 'yan gidan naku ai cewa sukayi inda kike nan zasu zauna to kuma gashi kin gudo kin barsu ya kenan? To ai nayau ne kawai yanzun ma inada dalilin kwanan anan, dan haka ka kwantar da hankalinka gobe tun da asuba zan koma. Miye abin tashin hankalin acikin kwanan naki uwar magana!!! cewar Baba Habiba matar maigari uwar gida, to ai naga duk kamar bakwa farin ciki da kwanan da nace zanyi ne,duk da mun jima bamuga juna ba. to ai kece Dije ba'a kewarki wlh duk inda kika zauna sai an so ki karawa motarki mai, saboda addabar mutune da kike yi da rashin jin ki,ai ni naga kokarin wannan yaron (Daddy)da sauran mutanen gidan da suka iya zama dake har tsawon wannan lokacin banji ance kin sabauta wani ba. Inji wa ya fada miki bata sabauta wani ba ? cewar Naseer dasai yanzu yayi magana,shi kuwa Habeeb nacan yanata dannar waya ,Sajida yake kira amma bata daga ba,jira yakeyi data daga ya tashi ya basu wuri danshi baya son yawan surutu. Au ta gwada muku halin kenan ya cewar Baba. kallon Dije Naseer yayi yaga yadda ta tsareshi da ido saiya tuno duk artabun da akayi da su abaya,ya so kora jawabi amma ya waske yace, Ai Baba ba karamin dadin zama ke da khadija ba,yarinya ba ruwanta salaha da ita nutsatstsiya,ga hakuri da sanin ya kamata ga....... ai tun a nan yakamata ka tsaya dan in jikina duk kunne ne ban yadda ba tunda naji ka ambaci kalmar hakuri nasan kadai fada ne kawai ammaina Dije take da hakuri,yarinyar da tun tana goye ko kallonta kayi indai bai gamsar da ita ba saita rama,bare kuma data fara tasawa,dan haka sai dai ka fadawa wasu halin Djje badai ni ba, dan duk wanda ya kwana da sanin haihuwar Dije a garin nan,to yasan da zamanta,dan in tana guri bata buya...... managed pls *vote* *comments* *with* *Alqalamin khady* โœ [3/15, 11:24 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TAME GARI* NA khadeeja usman 3โƒฃ8โƒฃ ___________________ Haka hirar tasu takasance,inda Naseer ya dage ya dinga yabon Dije na dole,dan gudun kar tarihi ya maimaita kansa. Shiko Habeeb kiran dayake yiwa Sajida ne bata dauka yasa ransa baci, "ko ina tabar wayar oho" ganin dare nayi yasa ya mike yacewa Naseer, "toh sarkin zance! inka gama ka iya tasowa mu tafi,dan ni nagaji da jin wannan hirar taku" ya karasa maganar yana kokarin fita daga dakin. Oh ni 'yasu!! kai dai wannan hali naka baiyi ba wallahi,ace mutum kullum fuska tamke,ji dan uwanka ya tsaya anata hira dashi rai rai rai, amma kai sai wani ciccin magani kakeyi,ka manta lokacin da ka fada komar Dije kenan kazo kanata karkarwa harda su sume-sume,amma yanzu ka gyare ka karo wulakanci,to wallahi in bakayi wasa ba tarihi zai maimaita kanshi,ni dai ba ruwana,naso ma ace kataho da taka matar amma saboda tsabar rowar mu ganta sai shi Nasiru ne ya taho da tasa,kai ban san meya hanaka ka taho da takan ba ko muni ne yayi mata yawa da alama mun fita. Jin batun da baba tayi ne yasa Dije tunawa da tabargazar da Inna tayi dazu,dan haka cikin boye dariyarta tace, Ke baba!! har mata nawa kike so ya taho miki dasu,ko kin fara magagin tsufa ne,dan naga har gaisawa kunyi da ita fa sosai. Wallahi karya kikemun! nadai gaisa da matar Naseeru,sai ita Karima,sai wannan sangamar kanwar tata,sai kuma ke,toh bayan ku indai ba karya ake son nayi ba,to ni banga kowa ba. Dariya Dije tayi,kafin ta juya ta kalli fuskar Habeeb taga yadda yayi kicin kicin gashi bakin kofa,shi bai fita ba,shi bai dawo ba ya tsaya yana jin cin zarafin da Inna keyi wa matarsa,wadda ya zuwa yanzu abin yafara damunshi,dan kusan duk wanda yaga Sajida saiya nuna basu dace ba,duk da tana da daukar wanka amma shekarunta sun kasa boyuwa saboda girman jiki. "Ai inna wannan da kika kira da sangama itace matar tashi" Rike haba baba tayi! kafin tace," Ikon Allah!! ku fa mutanen birni baruwanku da girma ko tsufan mace,inba haka ba kai ina kai ina wannan matar kusan sa'ar mahaifiyarka,abinma ba dacewa wallahi,to amma ya za'ayi ance matar mutum kabarinsa Allah dai yabada zaman lafiya,Ameen. Sakai yayi ya fice ransa a dan bace,inda Dije da Naseer suka kwashe da dariya wadda har saida ya juyo sautinta ransa ya kuma baci,fuuuuu ya fice yayi side din baba malam. Naseer wani zaman ya kumayi aka sha hira dashi sosai,har saida baba ta bingire, nan shi da Dije suka dinga kaftawa kamar wasu abokan wasa ko wasu sa'anni,ganin da yayi Dije batada niyyar gajiya yasashi cemata zai je ya kwanta nan yayi mata sallama ya fice yana hamma. ********* In ana sandarewa ya zuwa yanzu to fa ta sandare domin haduwa hakoranta sukeyi gaf gaf saboda wani mugun sanyin datake ji,dan haka ta lallaba ta karaso kofar bayin ta zuro kai dan jin inba kowa ta zagaya ta kwashi kayanta tasa,ganin ba kowa yasata saurin fitowa tana gab da gama fitowar taji motsi ana rufe gida,da mugun sauri ta koma ciki inda garin shigewa harda goge hannu tayi,tana dan lekowa taga baba ne ya dawo ya shige daki,ta goge 'yar kwallar wahalar data farayi da dana sanin zuwa kauye ta kara zuro kafa da niyyar fitowa taga inna ta fito rike da buta,nan ma ta koma da sauri,jin kamar motsi a bayin yasa Inna tasan da mutum a ciki dan haka ta koma ciki. Ganin abin bana wasa ba yasa ta fashewa da kuka dan ita a rayuwarta bata san wahala ba sam,ganin kukan bazai fissheta ba yasa ta mike a guje ta fito ta zaga cikin sauri ta shiga neman kayan amma bata gansu ba. wayyo ni Sajida ta fada fili tare da sakin marayan kuka,to ko dai Aljanu ne suma a wannan gidan yasa suka kwashe mata kaya,tunawa da tayi da cakwakiyar su da Dije a Abuja yasa ta tabbatarwa da kanta ba ko tantama su ne suka kwashe mata kayanta,jin sanyin naci gaba da suburbudar ta yasa taja kafa ta koma bayin dan ta yankewa kanta kawai ta kwana nan amma ko gobe wallahi gida tayi. Tana shiga ta samu gefen dutsen nan tazauna ta tallafe haba ta fara marayan kuka. Inna ce ta kara fitowa ta nufo bandakin tazo dab da shiga taji sasshekar kuka,ta tsaya jim!! taji daga bayan gidan kukan ke fita dan haka ta ce , Da mutum? jin ana magana a waje yasa Sajida saurin cewa Eh!! lafiya kuma naji kina kuka 'yar nan? Shuru tayi tana tunani ta fada ko tayi shuru,um kada inje in fada su bini suci ubana gara kawai in waske dan haka cikin shakewar murya tace , Dama mantawa nayi ban taho da kayan da zanyi amfani dasu ba in na gama wanka. Shine kuma kike kuka?to bari a karbo miki,ai magana zakiyi ba ki tsaya kina kuka ba,haka Inna ta juya tana juya lamari irin na 'ya'yan birni,yanxu inba tabara da iskanci ba ya za'ayi gundumemiyar mace kamar wannan ta tsaya yin kuka kawai saboda kaya,bata da baki ne da bazata iya kwalawa mutane kira ba,kuma me meyi laifin na jikinta da ta shiga dasu ai da saita dauro ta fito inta shiga saita canza,amma dan sanabe wai sai an canza wasu. Ta jima tana sallama amma shuru,sai dag can taji mamy ta amsa cikin muryar bacci. ko da ta fada mata abinda sajida ke bukata,sai da tayi jim tare da yada magana kafin ta hau laluben inda zata ga kayan amma bata gani ba,dole tace yusra ta bada nata,sai da ta gama tata yatsinar kafin ta fiddo da towel da hijabi ta ajiye gefen gadon ta juya tayi kwanciyarta,nan Inna ta matso ta dauka ta fice ta kaiwa sajida Da kyar ta dawo dakin dan yadda jikinta ke rawa,inda hankalin mamy yayi matukar tashi ganin yanayin datake ciki,dasauri ta kamata ta shiga tambayarta abinda ya sameta cikin kankanin lokaci haka,sam takasa magana illa rawar sanyin datakeyi wadda mamy cikin hanzari tajawo waya ta shiga kiran layin Habeeb, wanda shi a dai dai wannan lokacin yana kwance rigingine yayi pillow da hannuwansa,yana tunanin maganar mutane akan matarshi,to miye aibun ta,meye dan ya auri age mate dinsa? kai mutane munafunci yay musu yawa wallahi inkayi wasa sai sun hanaka rawar gaban hantsi. Yana jin kira na shigowa yasan itace ke kiransa dan taga missed calls dinsa,sai da kiran ya katse wani ya kara shigowa kafin ya mika hannu ya dauka amma saiya ga kiran mamy ne,dan haka da sauri yayi picking tare da sallama . ko amsawa batayi ba ta fada mishi Sajida ba lafiya, tambayarta yayi mike damunta tace mishi zazzabi ne me zafi yanzu yanzu ya kamata. cewa yayi yana zuwa,dan haka ya mike ya fice ya shiga neman Haruna danya rakashi cikin gari yasamo mata magani. Shi kanshi yayi mamakin ganin yanayin datake ciki,to kodai ciki gareta ya fada a zuciyarshi,daga wannan tunanin ya tsinci kanshi da tsantsar farin ciki wadda ya kasa boyewa har saida ya murmusa tare da shafo sumar kanshi,nan ya tasheta yasa tasha magani,bashi yabar gidan ba sai da yaga tasamu bacci,inda lura da yanayin sa yasa mamy ta fahimci ciwon dadi ne kenan dan haka ita ma ta kwantar da nata hankalin ta kwanta abinta duk suka fasa wankan. ************** Washe gari ma da zazzabin ta tashi inda koda Dije tazo ta gaishesu duk kin amsawa sukayi, duk yana cikin plan din mamy wadda take ganin in suka nunawa dije haka a gaban iyayenta zasu fahimci komai su hanata komawa su yadda kwallon mangwaro su huta da kuda. Itako Dije nunawa tayiabin bai dameta ba ta dinga dan waskewa,da dama ita ko basuyi haka ba batada niyyar komawa yanzu dan haka ta barsu subata harbin iska, ****** kwanansu biyu a garin mamy ta ballo da ruwa inda sunje gidan maigari gaba dayansu ta tasa daddy a gaba tace sai sun koma gida ita bazata iya ci gaba da zama a wanban kauyen nasu ba,babu abinda ya kara bawa daddy mamaki da haushi illa tattaro sajida da yusra da mamy tayi kuma babu kunya suka nuna masa suma. sun gajiba zasu iya zama a kauyen ba har kwanakin da sukayi niyya su cika ba. sawa yayi aka kira masa su Habeeb inda a gabansu yace matan su maimaita abinda suka ce,ai kuwa ba kunya sajida ta zage ta dinga rattaba bayanin cin fuska harda cewa wai mayu sun kamata daga zuwa,ganin da Habeeb yayi ta zake dayawa tana ta cin mutuncin asalinshi yasa ya daka mata tsawa ransa matukar bace. Daddy ne ya daga masa hannu alamun ya kyaleta,aikuwa taci gaba,har saida takai inda take son tsayawa kafin ta tsaya. Tana idarwa mamy ta amshe nan itama tayi me isarta bawanda ya tamka,harta gaji tayi shuru. Itako yusra ta kanta takeyi dan laulayin da takeyi shiyasa tayi shuru bata ce komai ba ta tsaya tan sauraren su itadai kawai ta masu ta ganta a gida. murmushin takaici Daddy yayi kafin ya kalli mamy yace, "yanzu Karima duk wannan cin mutuncin da kikeyi saboda kawai kinzo kauye ne? ai bawai batun nazo kauye bane,ni fa a rayuwata natsani kauye kai ni bama kauye ba duk wani jinin talaka wallahi,saboda shi talaka kullum burinshi yaga mai kudi ya wulakanta saboda tsananin hassada da...... ya isa haka!! daddy ya dakatae da ita Amma ai kin san ko ni wanene kika aureni kuma kin san asalin inda dangina suke ko? Ai kai ka daina danganta kanka da wadan nan mutanen dan kai Allah yayi maka sutura,inba ma basu barka haka ba waye zai samu ya kubuta daga wannan masifar ta zaman kauye ta dawo kuma wai ko da sunan ziyara. Hmmmm!!! hakane naji nakuma gode sosai,amma kisani wallahi ban yadda ki koma gidaba dukanku har sai kwanakin dana dibar mana ya cika. Gangan ma kenan!! ai wallahi bazan kara yadda na kwana da 'ya'yan mutane ba su macemun anan in shiga uku,tafiya kam kamar da kasa,kai da aka binne cibiyarka anan ka zauna har kwanakin su cika saika dawo,Dan haka ku tashi mu tafi tun kafin rana tayi mana. Mikewa sukayi duka suka nufi kofar fita Daddy baiko ce musu kala ba. Har sun kai bakin kofa suka Tsinkayi muryar Habeeb ya kira sunan Sajida yace, Indai nine mijinki ban yadda kibar garin nan batare da izinina ba kuma sai kwanakin da mukayi niyya sun cika. shima Naseer haka ya fadawa yusrah. To ni a matsayina na uwarku na basu izinin su wuce mu tafi in kuma ban isa ba sai inji labari,kafin fa juya ta kalli su sajida tace, In kuma a cikinku akwai mai zama banyiwa kowa dole ba kuna iya zamanku. Ai wallahi mamh in kin ganni a lahira kaini akayi cewar Sajida,dan ni da kara zuwa wannan kauyen har abada dan haka muje kawai mamy karsu karasa kasheni. suna gab da fita daddy yace,kin kyauta Karima amma wannan lokackn zan nuna miki ko ni waye kuje Allah ya kiyaye hanya amma wallahi zan shayar dake mamakin da baki taba tsammani ba........ *vote* *comments* *with* *Alkalamin khady* [3/15, 11:26 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASSO..*๐Ÿ‡ณ (palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA khadeeja usman 3โƒฃ9โƒฃ Zaune yake gaban baba maigari yana yi masa bayani,inda baba malam din ya tattara nutsuwarsa gaba daya ga zancen dan nasa,tare da tunani mai zurfi akan abinda yake shirin aikatawa,dan haka yayi shuru yana saurarensa har saida yakai aya,kafin ya sauke goron numfashi yayi jim kadan yana nazari. Tabbas maganar dansa gaskiya ce,gaba ake ji ba baya ba,domin karima tana so matuka ta tarwatsa musu zumunci yaransu masu tasowa,gashi maganganun ta sunyi tsauri,bata jin kunyar nuna kyamar ko waye indai dan kauye ne ko talaka,yayi tunanin abin zai tsaya iya kanta ne sai gashi tasa harda surukanta wanda suma sun dauki wannan mummunar akidar ta kin mutanen kauye da kyamar talaka,tabbas inya barta wannan abin yayi tasiri,"toh fa tabarbarewar zumunci za'a samu a zuriyarsa",wadda baya fatan hakan. maganar daddy ce ta fargar dashi ga tunanin daya tafi,inda daddy ke cewa,inka amince baba ina son ayi abinda na fada abi shawarata dan wannan lokacin nayi rantsuwa wallahi saina nuna mata kalata da bata taba gani ba. Ka kara hakuri khamis, dan dukka rayuwar hakuri akeyi musamman sha'anin mata,sai dai ni kaina wannan lokacin abinda tayi ya taba zuciyata,amma hukuncin daka yanke kana ganin baiyi tsauri ba akan su? Baba ai wannan hukuncin shine dai- dai dasu,shine zai sa su shiga taitayinsu. To kayi shawara da yaran naka ko? Banyi ba baba! Amma nasan babu wanda zaiyi mun musu a cikinsu. To shikenan!! mu bari zuwa anjima mu tattauna da sauran 'yan uwanka sai muji yadda za'ayi ko? Toh baba!! Allah yasaka da alkhairi. Ameen! Allah yayi muku albarka baki daya. Ameen nan yayi masa sallama ya fice dan gaisawa da jama'ar dake jiransa a waje. su kuwa su mamy,ba wanda suka wa sallama ko kallon arziki haka suka hada kayansu suka tafi bayan sun gama cin mutunci da yadda maganganu wai an kama su za'a cinye su an kawo su garken mayu. _____*********______ Zaune take gefen gadon Innah suna hira ita da Zainab diyar wajen baba bala kanin mahaifin ta,inda zainab din keta yaba kyan da Dije tayi tare da sanar da ita irin surutun datake sha a kauyen na wai taki aure ta tsaya karatun boko. Dagowa Dije tayi ta kalleta kafin tace, "kin san Allah ne yaso mutanen garin nan ban karasa wayo na anan ba", da wallahi duk saina sa su ciwon baki,dan kut.....nafasa, Ah ah!! da kin karasa ai. Ai na auna na auno na kuma hango ba amfanin karasawar ne,amma inba gulma da shegen tsegumi irin na mutanen kauye ba,meye laifin karatun boko,kuma ma duka nawa muke da har za'a damu dan bamuyi aure ba,su je su ga inda uwayen mata suke,wadana suke cikin jin dadi ga nera ta zauna,gasu bul-bul dasu kamar kajin gidan gona,amma ba mashin shini,sun gama cika har sun fashe. kamar dai matar yaya Habeebu kenan ko? dan ni nayi mamakin da aka ce wai itace amaryar sa. Dariya Dije tayi kafin tace, To me kika gani game da wannan,badan kar kice nayi miki karya ba wallahi da sai ince miki akwai iyayenta a kasa. kinga basai kin karasa ba dan wallahi nasan halinki Dije da karyar masifa,duk uwar data haifi kamar wannan.matar ai ta kusa cizon kasa. kinga fa abinda ke hadani dake da can kenan shiyasa nake kilarki,dan karyata ni da kikeyi,sai ki bari kije ki ganewa idonki wata rana. Ah ah ni wallahi bada ni ba,kina kallon cin mutuncin da shegun nan sukayi mana,ai naga kokarin zamanki tare dasu da banga alamun targade ko karaya a tare dake ba,saima wani fresh da kikayi. hmmmm!! kedai abar kaza cikin gashinta,kin san dai halin Dije kowa yayi mata saita rama,to hakan ce ta dinga faruwa shiyasa nasami sa'ida,amma wallahi da in kun ganni sai kun dauka a jejin sambisa nayi rayuwa. Shegiya!! kice kinji abar, hmm kedai kawai mubar maganar,bari intashi mu wuce kawai kar rana tayi. A tsakar gida suka iske Innah tana gyaran shinkafa,inda sukayi mata sallama suka fice ta bisu da Addu'ar Allah ya tsare a kuma gaishe mata ita. **** wannan karon ma kamar wancan lokacin yara baibaye su sukayi har suka sallami mai mashin suka nufi kofar gidan, da sallama suka shiga inda suka iske Hansai jingim zaune tana bakacen geron da daalama surfawa tayi. har wani murgudewa tayi garin amsa sallamar da kuma ido biyu da tayi da jami'ar tsaronsu wato Dije. cikin sauri bakinta har yana hardewa ta shiga kwadawa Inna Haule kira,aikuwa sai gata nan itama a sukwane jin kiran da Hansai ke mata,tana zazzaga masifa da ya zuwa yanzu ita ke mulkin dan haka ta taho tana fadin,"ke wai lafiya kike ta kwalamin kira kamar naci bashi", Turus tayi ganin jami'ar tsaron su tsaye ta harde hannuwa. washe baki ta shiga yi inda ta fara fadin, marhaban lale! yau kice kun kewayo sannunku da zuwa,ai ko yaushe munata tsimayi da sa idon yaushe zaku bullo ashe zuwan bazata kukeyi,kai amma munji dadin ziyarar nan wallahi,ke Hansai maza tashi ki dauko musu tabarma mana da ruwan sha, Ganin yadda ta yunkura da kyar dan ta mike,Dije a ranta ta furta Astagafirullah!!! Allah mai halittar bawa yanda ya so yanzu kalli ko hannun ta kawai yayi ni gaba daya,ganin kafin ta mike din ma wani sabon jidalin ne yasa Dije fadin, Ina ita Dayar abokiya zaman tata take? Allah sarki!! Ai sun tafi neman kudi ita da mijinta yanzu haka suna legas,tun bayan haihuwarta, Allah sarki! ashe harta haihu kenan? eh tasamu diyarta mace ansa mata suna Hadiza. washe baki Dije tayi cikin nuna farin ciki tace kai amma Allah ya raya,yaushe zasu dawo? ai basu jima da tafiya ba dan dama da Hansai ya fara tafiya daga baya ya dawo da ita data cika kwanakin ta saiya dauki Hafsy din. nan Dije ta kara sabin sharhi da sabbin dokoki kafin tayi musu sallama suka ce zasu koma har kaji madu rai Inna haule tasa aka kama guda biyu d sauran tsarabun kauye ta bawa su Dije a cewarta da ta fada komar 'yan sanda gara tayi kyautar shiga daka kayi kuka. ************** Yau jumma'a dan haka tun safe maigari ya tattara iyalinsa gaba daya manyan yaransa ya kira ya sanar dasu abinda ke faruwa,tare da kuma bukatar da dan uwansu yazo da ita,dukan su sun amince sun bada goyon baya, Amma baba Inusa ya dan jimanta abun a ransa amma daya tuna zumunci abu ne mai girma sai kawai yayi addu'a. Ana idar da sllar juma'a daruruwan mutane suka shaida daurin Auren zuriyar gidan mai gari. KHADIJA INUSA DA HABEEB KHAMIS ZAINAB KABIRU DA NASEER KHAMIS Tare da mai gayya mai aiki madugu uban tafiya. ALHAJI KHAMIS (Daddy) da Zarkwadediyar amaryarsa,tsohuwar budurwarsa wadda yaso aure tun farko Allah baiyi ba wato MARYAMA diya ga kanwar maigari amma ita yanxu da sanin ta da amincewar ta dan tun zuwan su Daddy daya ganta tazo gidan mai gari aka sanar masa mijinta ya rasu gashi dama bata taba haihuwa ba,to fa sai tsohuwar soyayya ta motsa nan aka shiga tuna baya sai kuma lamari yazo akan gaba. *tabbbbbb......Alkur'an ba ruwana dan akwai bom* *vote* *comments* *with* *Alqalamin khady* [3/15, 11:27 PM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASSO...๐Ÿ‡ณ (palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA Khadeeja usman 4โƒฃ0โƒฃ Tuni labari ya iso gari cewar,an daura auren Daddy da kuma yaranshi,abinka da kauye,nan da nan magana ta bazu,masu sa albarka nayi,masu tsegumi nayi. kasancewar ana idar da sallah kuma cikin masallaci aka daura auren, yasa su Habeeb dake nesa daga waje suke jin kamar kunnensu gizo yayi musu jin kamar an ambaci sunayen su wajen daura auren. Suna nan tsaye suka hango fitowar su Daddy da maigari anata mika musu hannu tare da yi musu Allah ya sanya alkhairi inda sukaita washe baki,da alamun farkn ciki a fuskar su,suka nhfo inda su Habeeb din suke,wadanda suma ya zuwa yanzu sauran 'yan uwa nata zuwa suna basu hannu,tare da ce musu Allah yasanya alkhairi,lamarin daya kara daure musu kai kenan har su Daddy suka iso inda suna zuwa suka tasa su gaba batare da dogon bayani ba zuwa gida,dukan su ji sukayi jikinsu yayi sanyi toh me yake faruwa? yanzu haka inka bibbiya aure aka daura a gidan Daddy zaisa suyi alheri shine ya kirasu.Da wannan tunanin suka karasa gidan. Nan ma suna shiga gida yadau guda da fadin ga angwaye nan,inda sauran mata da abokan wasa suka shiga tsokanar su,lamarin daya kara sasu yin yake dan badai murmushi ba. Jan su baba malam yayi zuwa bangaren shi,inda suna zuwa suka samu guri suka zube yarab dan ba wani mai kwari cikinsu,duk da basu tabbatar da abinda suke zargi ba. Bayan baba malam gayi gyaran murya nan ya shig rattabo musu bayanin komai game da abinda suka ji kuma suka gani yanzu,inda ya dinga musu sharhin da sam bama sa fahimtar shi har ya kare batunsa Daddy ya shigo ya karbe,nan din shima ya fada musu dalilinsa nayin hakan,ganin kowannensu baice komai ba yasa Daddy yakalle su yace, "Naji kunyi shuru", ko baku karbi hukuncin danayi yanke muku ba? ko baku yadda da zabin nawa ba? Nan ma shurun sukayi har saida ya kara magana. Mun Amince Daddy Allah yasa haka shine mafi alkhairi! Ameen!! Allah yayi muku albarka ya albarkaci zuriyarku baki daya,yasa kuyi alfahari da wannan auren ko bayan ba mu. kai kayi alfahari da Auren Khadija,kai ma kayi da taka matar zainabu! Ameen suka amsa nan maigari da Daddy suka fice suka barsu zaune an rasa ma me cewa kanzil kowanne zuciyarsa cike da tunani barkatai. wani abu suka tuna lokaci daya ksmar kowa yasan abinda ke zuciyar kowa kawai sai suka saki dariya inda suka kalli juna suka kuma hade rai. Wallahi ni dai an cuce ni,dan ni a tsarin rayuwata ban shirya qara aure yanzu ba,cewar Naseer. Wai kai aka cuta ko ni? ni da a tsarina ba auren mace fiye da daya,ai gara kai kana da niyyar karawa wata rana ni kuwa fa?kai ni duk bama wannan ba a ma rasa wadda za'a hadani da ita sai Khadija kawai dan tsabar ci baya,yarin yar da bata cikakken bacci kullum Aljanu na bisa kanta,so akeyi nima tazo gidana ta haifamin irinta masu fitinar tsiya,to wa ma zan nunawa wannan tatsitsiyar yarinyar ince wai mata ta ce! ni wannan ma ba shine abin ji ba shiyas kaga nayi dariya dazu,yadda gidanmu zai kama da wuta,idan su mamy suka sami labarin abinda ya faru,ni wallahi da za'aimun gata da sakin yarinyar nan zanyi salin alin batare da ankai ruwa rana ba. Kana sakinta ni kuma sai ince a bani ita a bar Zainab din,dan wallahi gara khadija sau dubu akan Zainab,kai ba fa kaga kafafunta ba wallahi sunyi nawa,gata baka,kai ni wallahi ni aka fi cuta,khadija kuwa nasanta nasan halinta sai in lallaba ta muyi zamanmu hankali kwance wallahi magani ma zan nemar mata. Ji yayi ransa ya baci da kalaman Naseer,dan haka cikin dan zafi yace, kai wane irin mahaukaci ne? matar tawa kake fadin wadan nan maganganun akanta? ah to ya kake son ince? kai tunda baka so ba sai ayi furfure ba,Wallahi ni da gudu zan amshe ta,kai ni fa da ni aka bawa ita bazanyi wani bakin ciki sosai ba duk da ban shirya ba,amma ya zanyi ance kaddara ta riga fata,ya karasa maganar kamar zai fashe da kuka. Hmmm!!!! lallai Naseer kayi nisa ya fada yana me mikewa ya cire rigarshi ya fada saman gadon yayi rufda ciki,tare da lumshe idonsa,ya rasa dalili sam baya jin bakin cikin yin auren da akayi mishi,amma kuma baya farin ciki,tunanin khadija ya fara yi zamansu da duk wata dramar da aka dinga kwasa a zuciyarsa ya furta,ashe ba'ayi komai ba tukun dramar na nan gaba. Shiko Naseer tunanin kafafun Zajnab kawai yakeyi,wai ya zaiyi inya tashi sai mata takalmi.? ๐Ÿค” *Ni ko nake lallai kowa da abinda ya dame shi* *ga wannan ku dan taba dan naji dadin comments dinku akan page din jiya,ku dai tanaji ruwan kashe wuta dan har yanzu fa Dije bata da labari ,bare kuma uwayen gayya 'yan birni,masu brush da kwandala* *vote* *comments* *with* *Alqalamin khady* โœ[3/18, 8:02 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿ‡ณ (palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* 4โƒฃ1โƒฃ Da gudunta ta shigo dakin,inda ta iske Dije kwance rashe-rashe saman gadon Innah,tana waya da Ishaq. Ganin yadda ta shigo din yasa Dijen dagowa ta kalleta,batare data kashe wayar ba tace, ke kuma lfy malam kika shigowa mutane a haukace haka ? ina tsaka da soyayya ta zaki katsemun jin dadinta!!! Au kice zani ce ta tadda muje bari kawai inyi shuru da bakina tunda abin nema ne duka ya samu,kin san da jikon da akayi tun da can kenan! ban fahimci abunda kike magana akai ba? wata ce ta zageni ko tayi gulmata inje in kaddamar mata maxa fadamun da sauri kar hawan ruwana ya tashi", Sha kuruminki ni nadauka ma kin samu labari amma naga alamar baki san da zancen ba,to albishirinki!! Goro fari kal! meye tukwicin? "nabaki dan mutum da uwarsa" masha Allah to karkarde kunnuwanki kisha labari. ke ni in zaki fadamun abu ki fadamun in bazaki fadamun ba ki kara gaba ki barni insha luv dina da rabin raina. gyara zama tayi,kafin tace, .Allah yayiwa maigari albarka Allah ya ja da kwana. Ameen Dije ta amsa dan ta matsu taji meya ke faruwa. kin san tun ranar dana fara ganin su yaya Naseer naji duk duniya ba namijin danake so saishi,amma saboda nasan ya wuce ajina dan ba abinda zaiyi da 'yar kauye da kuma hango halin mamansa da nayi yasa na cirewa raina wannan banzan tunanin,ban san ma ina sonsa ba har yanzu saida naji yayi aure kuma naga matarsa yanzu ,har ga Allah naji kishinta matuka,amma ganin wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa yasa nacire abun a raina. to cikin ikon Allah da kuma yardar sa yau gashi Allah ya amshi rokona ya cika min burina,tsoho mai ran karfe yayi abinda zan ta yimasa addu'a har karshen rayuwata. Ke ni fadamin meya faru ne nagaji dajin soki burutsun ki. kafin ta bata amsa suka tsinkayi muryar Inna tana magana cikin kuka tana fadin, Wallahi bazai yiyu ba malam,sai dai ince kayi hakuri wannan lokacin,nasan ban taba sabawa umarninka ba amma wannan lokacin dole inyi magana,ta yaya ma hakan zai yiyu! duk da yarinyar nan bata fito ta fada mana irin zaman datayi a birni ba,amma ai munada hankali,kuma zuwan su ya nuna ya kuma tabbatar da batayi zaman wani jin dadi a can ba,nasan halin Dije da shegen kafiya da taurin kai,shiyasa ta zauna,duk a bar majjjjjjjjjj ta wannan ta yaya kake tunanin Dije zata iya zaman kishi da wannan matar wadda ko ni uwar ta ban isa ba,yakamata a dinga mun adalci,Dije ita kadai Allah ya bani duk wani hukunci da kuke yankewa a kanta ban taba magana akai ba,amma wannan lokacin ina ganin anyi abinda bai dace ba gaskiya,dan dalilinku bai kai dalilin da zaku hada su aure ba alhalin kun san ba son junansu sukeyijjjj ba,kai yau ko Dije tacemun tana son yaron nan wallahi bazan bari ta aure shi ba dan bata isa yin kishi da wannan guzumar matar ba,indai ba so kuke a kawomin gawar ta ba wata rana..ta karasa magabar tana me sharbejjj majina. tunda ta fara maganar ya kafeta da ido yana saurararta har takai aya,shuru yayi yana nazarin maganar ta tabbas yasan saude mace ce mai hakuri da kawaici ga dukkan lamuranta,yasan malam na yanke hukunci akan kowa kuma ya zauna babu mai muds masa dan haka akanshi baza'a fara ba,shi kanshi yasan wannan hadin da akayi akwai cakwakiya cikinsa amma ba yadda zaiyi dole yayi biyayya dan yasan dashi da iyalinshi duk karkashin hukuncin baba maigari suke komai ya zartar dole su aminta dan haka cikin tausasa murya ya shiga kwantarwa da Inna hankali,amma ina sam bata fahimtarj shi,ganin hakan yasashi daga muryar shima tare da fada mata inta matsu taje tasami maigari da kanta tayi masa bayani,wadda yasan da kamar wuya hakan ya yiyu,amma ga mamakinsa sai ji yayi tace inkamun izini zanje in samu baba!, a dawo lafiya ya fada wanda yakai kallonsa ga bakin kofar inda yayi ido biyu da Dije da hawaye shabe -shabe,kureshi tayi da ido kafin daga baya ta karasa gurin Innah ta fada jikinta suka fashe da kuka. tabbas ya tausayawa iyalin nasa sai dai shima ba yadda zaiyi da hukuncin mahaifinsa dan ya tabbar dalilin sa na yanke wannan hukuncin yana da karfi sosai,kuma bai isa ya musa masa ba kawai abinda yafi ya lallaba su ya rarrashe su tare da yiwa tilon 'yar sa addu'ar Allah ya basu zaman lafiya ya kuma kareta dan haka cikin tausasa murya ya shiga yi musu magana. Nana Khadija!! "ya kira sunan ta a tausashe", cikin dashewar murya ta amsa masa. nasan ya zuwa yanzu kinji duk abinda yake faruwa ko? kai ta gyada masa alamar eh! to Alhmdllh,ina son ki kasance me yimana biyayya akan hukuncin da mahaifina ya yanke akanku gaba daya wadda kin san bake kadai aka yiwa haka ba ku hudu ne,kuma duka kowa ba'ayi shawara dashi ba illa mu iyayenku,munyi hakan ne dan mun san mun isa daku kuma zakuyi mana biyayya,kada kisawa zuciyarki tunanin wani abu yazo yadameki kisawa ranki auren nan alkhairi ne ko da bakwa son junanku sannu a hankali zaku koya na rokeki da girman Allah,ki daure ki karbi hukuncin da mahaifina ya zartar a kanku kiyi mini wannan alfarmar ki.....ya isah baba dan Allah kabar rokona haka!, Dije ta katseshi cikin kuka. Wallahi baba na yadda na amince da duk hukuncin da kuka yanke nayi muku alkawarin duk runtsi duk wuya bazan baku kunya ba ta karasa maganar tana fashewa da wani kuka mai cin rai. to kukan na miye khadija? nasan bazai rasa nasaba da kinada wanda kike so ba,ina son kiyi hakuri naso a rayuwa nabaki damar ki zabawa kanki mijin da kike so amma hakan bai yiyu ba amma nasan haka ALLAH ya kaddara wani baya auren matar wani Allah yasa muyi alfahari da auren ku Ameen. jikin Innah a sanyaye ta furta,kaddara ta riga fata babu yadda zamuyi,zanci gaba da tayaki da addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a rayuwarki. Ameen ! ko ke fa,abinda yakamata ki fada kenan tun tuni,yanzu bari naje nayi sallar la'asar naji an kira sallah,ya mike ya fita. yana fita Innah ta dubi Dije cikin karaya tace, Wallahi Dije ina jiye mike zaman kishi da koda sa'arki ce bare wadda ta haifeki ma da gani,ikon Allah kenan ni uwarki banyi zama da kishiya ba gashi ke zaki je kiyi. kada ki damu Innah"wallahi lafiya zamu zauna indai nice bazaki ji wat baraka daga gareni ba insha,Allah hmmm!! yaro man kaza" bazaki fahimta ba yanzu kawai Allah yasa alkhairi. a zuciyarta ta amsa da Ameen,kafin ta zame ta kwanta kan cinyar Innah jin wani zazzabin gaggawa na shirin kamata. ******* Washe gari tunda sassafe Daddy yabar jigawa ya nufi Abuja inda yana isa ya iske mamy da surukanta baje a falo suna ta ciye-ciye,da fara'arsa yayi sallama ya shiga falon. sunyi mamakin ganinsa a wannan lokacin,amma suka basar tare da amsa sallamar tasa suka shiga gaisheshi,nan ma cikin sakin fuska ya amsa kafin ya haye samansa mamy tabi bayansa tana fadin shima yaji ba dadi ya gudo. tana shiga ta iske shi yana kokarin cire babbar rigarsa,dan haka ta karasa tana fadin sannu da zuwa,ashe kana hanya babu ko labari. Wallahi kuwa naso in kira kuma saina fasa nace kawai sai dai ku ganni. Ai na dauka sai nan da kwanakin daka diba zaka dawo din? Eh to da naso hakan amma wani uzurin gaggawa ya tasomin. kaga Alhaji kawai bawata kwana-kwana kace dai kaima kauyen ta isheka,dan dama nasan karfin hali kawai kayi dan kar a ce ka guji asalinka,gashi da kaga uwar bari ai kadawo. yaji zafin maganganunta ji gayi kamar ya fada mata abinda ke faruwa amma sai ya daure yabari akwai lokaci dan haka yayi murmushi yace, Ina mutum ina gudun tushensa da asalinsa kawai dai na fada miki uzuri ya tasaoni bagashi su wadancan yaran naki da basu da abin yin ba suna can na baro su ba. wayake ta wadan can shashashun,ai sai suyita zama tunda basu san ciwon kansu ba,ga matansu nan a nan duk lokacin da suka gaji suka dawo su kwashi abinsu. ai kuwa yakamata su ci gaba da zama kusa dake sa fi samun kulawa. A ina zan ajiye su? ai wannan ba matsala bane gidan nan nawa danace miki na siya a hannun minister kin san girman sa yasa nace bazan zauna ciki ba dan yayi shi danshi da family dinshi ne gaba daya dan su zauna sai Allah ya aiko masa da wannan kaddarar dole ya said shi,to basai mu koma can gaba daya ba. Dagaske kake Alhaji ko da wasa? Dagasken gaske kuwa! Ammq ko da nafi kowa farin ciki,da burina ya cika ace nice a wannan gidan. kada ki damu burinki kamar ya gama cika kawai ki fara shirye-shirye nan da sati ma inaga zaku tare. kaga Alhaji bari kaga inyiwa yaran nan albishir batako tsaya taji mai zaice ba ta fita da sauri ya rakata da dariyar mugunta. cikin kankanin lokaci aka shiga kwaskware gida kasancewar dama a kimtse yake feni kawai akayiwa ko wanne part,tsarin gidan yayi kyau da tsari cikin kankanin lokaci komai yayi neat kasancewar nera tayi kuka inda su kansu surukan mamy sunji dadin komawar su wannan tamfatsetsen gidan kowacce sai kai ha kara girma,yayin da kowanne bangare ke kokarin yin barin nera dan burgewa da gwangwaje yaran nasu. shiko Daddy dakansa ya sayi furnitures masu kyau da tsada duk part din nan hudu aka sa na mamy dana amaryarsa iri daya sak komai yasa,hakama na Dije da zainab bai banbanta komai ba suma har colour. sai da ya tabbatar a cikin kwanakin daya diba konai ga kammala kafin ya rufe dukannin parts din su Dije,ko da su mamy sukaje ganin nasu kusan sumewa sukayi dan dadi. shi ko Daddy ko mamy bai sanarwa ba ya kama hanyar jigawa. **** Tunda aka daura auren basu hadu da junan su ba,Dije ko har yanzu zazzabi ke damunta ko da maigari ya tambayi baba yunusa ina Dijen nan yake sanar mishi halin da take ciki. Habeeb yasa aka kira ya fada mishi halin da matarsa ke ciki yace yaje ya dubata..... *managed pls* *with* *Alkalamin khady* โœ [3/18, 8:06 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS...* ๐Ÿฎ (Place of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 4โƒฃ3โƒฃ *Hakika kowanne bawa da irin tasa jarrabawar,ni tawa yawan lalura ne,Amma wasu sun kasa fahimta ta,babu yadda za'ayi kalau lafiya inki Yi miku posting,ni nayi niyya na Fara rubuta muku tame gari ban San cewa Zan Kai har haka ban gama ba,Dan Allah ku dinga Mana uzuri mu writer's maganganu ku masu kaifi agaremu su ke Kara sa zuciyarmu rauni Dan Muna ganin Muna iya kokarin mu Amma ku kuna fada Mana ba dadi,babu dole duk wadda taga tagaji da bibiyar buk din to ta sawwakawa kanta da karantawa.* *Sannan bazan gaji da rokon masu bina pc suna Neman buk din suyi min uzuri Dan Allah,masu min magana bana samun damar dubawa Suma suyi hakuri duk Ina sane daku Kuma Ina matukar godiya.* **** ************** **** Tana kwance saman gadon Inna ta kudundune sbd sanyin da takeji,muryarsa ta tsinkaya Yana gaida Inna,wadda ke amsawa cikin Jin kunya da nauyinsa,kasa tashi yayi daga tsugunnon da yayi,bare ya tambayi Ina take,lura da yanayin sa da Inna tayi yasata fadin, "ka shiga Tana ciki". Dafarko yi yayi Kamar baiji ba,sai da ya Dan jima kafin ya mike ya nufi dakin inna. A ciki ciki yayi sallama wadda indai ba kunnen maciji ne dakai ba bazaka taba Jin abinda yace ba. Samun guri yayi ya tsaya,yayin da ita Kuma taji alamar shigowar mutum,hakan yasata kokarin yaye bargon data rufa dashi,sai dai kafin ta yaye din bayyanar kamshin turarensa ya sanar Mata da ko waye din tsaye . Komawa tayi ta lafe yayin da shi Kuma ya Kara gyara tsayuwarshi bashida niyyar yin magana. Jin da yayi tsayuwar ta isheshi yasashi fadin, Ke ni na gaji da tsayuwa ki tashi mu tafi asibiti,nasan kina jina likimon Munafunci kikayi. Da ta so ta kyaleshi Amma saita kasa Dan hi tayi in Bata tofa albarkacin bakinta ba to zata iya shiga wani yanayi. Dan haka cikin muryarta ta marasa lafiya tace. "So na dauka tabarya ka hadiya,shiyasa ban tausaya wa tsayuwar da kayi ba", [3/18, 8:07 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (Place of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 4โƒฃ4โƒฃ *Kuyi hakuri nasami miss number ne a page din daya gabata amma fatan zaku fahimce ni* Itama yusrah jiri-jiri ta Fara gani,hakan yasa ta nemi guri ta duka tare da dafe kanta datake ji lokaci daya Yana Mata wani mugun ciwo. Shi kuwa Daddy Yana Gama musu jagora tare da Nuna musu kowanne sashi na bangaren amaryar sa wayarsa ta Fara ruri alamun Ana Kiran sa,hakan yasa ya fito ya nufo wajen,sai da ya gama wayar sannan ya nufo wajen daya hangi su mamy Amma ya Nuna Bai gansu ba Dan ya Kara kuntata musu Dan yasan ya zuwa yanzu sun shiga kidima da wani yanayi na kasa tantance meya ke faruwa.Yana fitowa ya hange su kuwa yashe a kasa,ita ko yusra h tana duke,cikin ko in Kula ya karasa inda suke,duk da yaga halin da suke ciki Amma ya Nuna Kamar Bai damu ba,Daya daga cikin direbansa ya Kira,cikin kankanin lokaci kuwa sai gashi Nan ya Kira su Habeeb yace suzo su taimaka asa uwarsu da matansu a mota akaisu asibiti. Dukansu hankalinsu ya tashi ganin halin da suke ciki,musamman Naseer Daya san Yusrah nadauke da ciki Kuma yaga halin datake ciki,babu Bata lokaci suka sasu a mota suka nufi asibiti dasu,shi ko Daddy baiko bi ta kansu ba Dan ya San ya zuwa yanzu abinda ke damunsu kishi ne,Kuma burinsa ya cika,Dan haka Ya fito da waya ya Kira Hajiya baturiya yace Mata ya maganar da sukayi fatan komai ya kammala. Amsa Masa tayi da an Gama komai ya zuwa yanzu dama jiran wayar sa takeyi. Shikenan zuwa goben sai ayi komai ko? Shikenan Allah yakaimu Ameen! Nan sukayi sallama ya Kira restaurant din dayayi order abinci cewar su kawo yanzu,aikuwa ba Bata lokaci sai gashi sun kawo abinci Mai Rai dai lafiya,Nan fa mutanenmu suka shiga kwasar gara da harrakawa. *********** Itama yusrah kafin a karasa asibitin ta karasa sumewar hakan yasa ko da suka Isa duka daki Daya aka Basu tare dayi musu taimakon gaggawa kasanceawar tun suna hanya suka Kira Yusuf dayake Yana asibitin suna zuwa kuwa aka antaya wa su Hajiya mamy zurkudediyar alluran bacci,bayan an Gama musu duk abinda ya kamata an tabbatar sun farfado. Suna asibitin Daddy ya Kira su yace su zo Yana son ganinsu. Sun Dan jima kafin su zo suna zuwa yajasu part din mamy. Bayan sun zauna ne yaga sun nutsu yayi gyaran murya tare da Yin addu'oi na musamman sannan yafara magana. Nasan a matsayinku na 'ya'ya agareni nayi muku abinda ku kuke ganin ban kyauta muku ba,duk da cikinku babu Wanda ya nunamin hakan baiyi Masa dadi ba sai dai nasan kunyi shuru ne Dan kuyimin biyayya,Alhamdulillah naji dadi Kuma nayi farin ciki da Allah yabani yara masu biyayya "Allah yayi muku albarka". Ameen!! Suka amsa gaba daya Sannan Daddy yaci gaba,kuyi hakuri da auren Dana daura muku batare Dana tambayi Ra'ayin Daya daga cikinku,ko kuna da ra'ayin Kara aure ko bakuda shi,to banayi hakan bane Dan wani abu,ko dan na Bata ran matanku da mahaifiyarku ,sai dai nayi ne Dan gyara da duba duk abinda zai je ya dawo Nan gaba idan nabari abinda matanku da mahaifiyarku sukayi yaci gaba da faruwa,shiya sa nadauki wannan matakin,to Amma Ina son ku sani,Kamar yadda ban nemi izininku ba nadaura muku aure,haka Suma yaran da aka daura muku auren dasu babu wadda aka nemi Jin ra'ayinta Kuma suka amince,to dukanku munji dadi da kukayi mana biyayya Allah yasa yadda kukayi mana Allah yabaku masu Yi muku Kuma. Ina son Kamar yadda kuka mini biyayya ku rike amanar da Allah ya Baku ku Kula da matanku,kuyi adalci tsakaninsu,ku tabbatar kunyi adalci dan gudun tashi da shanyayyen barin jiki ranar gobe kiyama,ku rike amanar da kuka dauka kuyi kokarin sauke nauyin dake rataye a wuyanku,Allah yayi muku albarka ya albarkaci aurenku da zuriyarku baki Daya,Ameen!! Nan yaci gaba dayi musu nasiha Mai ratsa jiki da zuciya,sai da ya gama kafin ya shiga sanar musu plan din daya shirya akan su mamy har sai sun gane kuskurensu,Nan ya fada musu shirin dayayi gobe,dukansu sunji sun Kuma gamsu Dan haka ya fada musu plan dinsa na farko Daya shirya. Kuyi managed *Alkalamin khady* โœ [3/18, 8:07 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (Place of the excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA khadeeja usman 4โƒฃ6โƒฃ Kamarya!! Na kwantar da hankalina,bayan Ina ganin gayyar mutanen garinku a gidana,wato bayan wannan kodaddiyar Mai zubin mayun,harda Karin mutum biyu aka samu,no wonder,ashe shiyasa na dinga mafarkai kaje gidan marayu da sansanin 'yan gudun hijira ka debo mutane ka kawo su gidan nan,Ashe wannan gayyar ne suka bugo Mana sammako,ni wannan rashin son 'ya'ya irin na saude da inusa ban San Ina zasu kaishi ba,inba haka ba 'yar kwaya Daya ku gagara riketa,duk nasan kwadayi ke dawainiya da su,shine wato Dan sunga ita ta samu gurin Zama shine harda tattago wasu da hadota dasu,to wallahi Sam bazan lamunta ba dole su tattara su koma inda suka fito a yau basai gobe ba.Ta karasa maganar tana wani huci,idonta na kan mama mariya dake hakimce kan kujera,Jin maganganun da mamy ke Fadi yasata harde kafa Daya kan daya. Duk abinda ta fada baisa Daddy ya Nuna Mata bacin ransa ba ko kadan,Dan yasan abinda zataji yanzu shine zai daga hankalinta,ya wargaza nutsuwarta,dan haka cikin sanyin murya ya Fara Mata magana. Haba uwar gidana,me yayi zafi haka,kada fa ki Manta kece sarauniyar gidan gaba Daya Kuma shugaba a cikin gidan,ai irin wannan Bai Dace da tauraruwa Kuma lantarkin gida ba,Dan haka kiyi hakuri kizo kisamu guri ki zauna kiji me zan fada muku. Wani sanyi taji a ranta,Wanda yasata sakin karamin murmushi ya lura da hakan,ita ko a zuciyarta tana ayyana idan har Zama suka zo yi to kuwa saita maida su kamar bayi,Dan duk masu aikin gidan sallamar su zatayi,daga mazan har matan Kai har maigadi ma,da wannan tunanin ta karasa ta zauna tana karkada kafa da hura hanci,Nan surukan suka shiga gaisheta,sabanin yusrah data mike ta fada jikinta tare da sakin kuka Mai sauti. Cikin kidima ta shiga tambayrta me aka Mata ? Cikin kuka ta Fara fadin wallahi mamy kice Masa ya sakeni,Dan wallahi bazan Kara Zama dashi ba,mugune Azzalumi Wanda Bai San kima da darajar soyayya ba,wallahi na tsaneshi,idan har Bai sakeni ba wallahi zan kashe shi daga shi har matsiyaciyar yarinyar. Ban gane ba? Wace yarinya ce wannan da take Neman tarwatsamin farin cikin yarana? Nuna Zainab yusrah tayi da hannunta. Au! Au! Kice ku naku shirin na musamman ne,wato da tuggu da makirci Kika iso gidan,shine daga zuwanki yau Kika Fara shiga tsakanin Mata da miji ko? To wallahi baki Isa ba,inma uwarki ce ta kitsa Miki daga wannan bakin kauyen naku to kisani zaman maraya Dana karkara akwai bambamci,to Wai ma uwar me Kika kulla da har yaran da suke masifar son junansu kamar Laila da majnun suka samu sabani,har take cewa ya saketa? Mamy Wai aurenta yayi. Ke bana son iskanci wanne irin aure Kuma?to kodai kema kin shiga tarzomar mafarkin ne kamar yadda nayi? Sajida dake zaune take Jin tamkar zuciyarta zata tsake ta fito,Dan ji takeyi duk wani abu da zasu ji to ko Rabin abinda takeji bazai kaiba,Amma sanin abinda ta shiryawa zuciyarta yasa ta danne tare da sakin murmushin dayafi kuka ciwo tace,tabbas mamy ba mafarki yusrah tayi ba gaskiya ne cewar duk mazajenmu sun Kara aure kamar yadda Habeeb yayi mun bayani, sakamakon rashin Jin maganar su da mukayi muka baro kauye Wanda sai yanzu nakejin tabbas bamu kyauta ba,abinda mukayi am........ Ke dayalla dakata ni bama na fahimtar ki sosai,shin mazajen naku ne suka Kara auren batare da ni mahaifiyar su na sani ba ? Shin Kuna nufin kucemin Kuma daga kauye suka dauko matan nasu? Kai wallahi karya ne. Wallahi mamy gaskiya ne abinda Anty ta fada Dan Dana yiwa Naseer magana Akan inbai sakeni ba saina fada Miki sai yace ai harda kema anyi Miki Wai ina kyautata zaton ma itace wannan zaune kusa da Daddy. Wayyo! Wayyo! Na shiga uku ni karima,kishiya da girmana Hamisu da gaske ne abinda suke fada? Ka fadamin inji ni aka yiwa kishiya,? Kishiya ma daga kauye? Wallahi bazai yiyu ba,nasan shirin mahaifinka ne,Dan ya tozarta ni,ni da zuri'ata,wallahi Bai Isa ba saina warware wannan mugun kullin da akaimun,yanzu na fahimci abinda ya faru,Amma yanzu zanyi maganin abun,Ina son yanzu ba sai andau lokaci ba Kai Habeeb da Naseer a matsayina na uwar data haifeku,ku warware wannan tsinannen auren yanzu ku sakar musu yaran su kafin nima nasan abinyi akan tawa,ta karasa maganar tana huci. Dukansu kallon juna suka tsaya yi,yayin da shi Kuma Daddy ya tsaya Yana kallon mamy Dan yayi tsammanin fiye da hakan ma daga gareta,Saida maganganun data fada akan mahaifinsa sun Bata ransa Amma shi yasan matakin dauka yanzu. Magana nake muku cikin tsawa ta fada,wadda dukan su su hudun suka shiga yanayin damuwa shikam Naseer a yanzu ji yakeyi daya saki Zainab gara tace ya saki yusra Dan ko zagin data Masa ya Isa ya saketa,shi kuwa Habeeb duk da baijin wani son Dijen a ransa Amma baijin ya tsani auren ko ita kanta,Kuma shi a tsarin shi ma babu saki ko da wa ya aura,Dan haka duk sukayi shuru. Wallahi idan har baku sake su ba yanzu-yanzu na rantse da Allah saina tsine muku... Ke kuma ki sani adadin sakin da sukayi kema adadin naki kenan! Cewar daddy Daya Mike cikin bacin Rai,yasan inda a abinda mamy ta tsana Bai wuce ace tabar gidansa ba,matar da ko 'yan uwanta Bata son zuwa wajensu,Dan haka ta girziza da jin furucinsa Wanda yasata saurin dagowa ta kalleshi. Yes! nasan kinji abinda nace, Yanzu Alhaji kana nufin idan yaran Nan suka saki wadannan 'yan kauyen Nima sakina zakayi? Tabbas kuwa sakin ma uku!! Idan Kuma na janye fa? Aurenki na Nan. Shikenan na janye furucina Amma Kai kana ganin kayimun adalci? Kayiwa yaran adalci? Wannan ke kike ganin haka Dan haka na sallami kowa ku tashi ki tafi maganar da naso yi ayita wani lokacin,kuje Allah yayi muku albarka..... *Alkalamin khady* โœ [3/18, 8:08 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASSO..* ๐Ÿฎ (Place of the excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA *Khadeeja usman* 4โƒฃ7โƒฃ Sam yusrah kin yadda tayi ta koma dakinta,inda mamy ta goya Mata baya tace tayi zamanta har saita Gama aiwatar da shirin datake yi akansu.Shiko Daddy Yana lura dasu Amma ya zuba musu ido yace gara ma ayi hakan an samu ragin wata fitinar. Kishi sosai mamy ke nunawa mama mariya yayin da tayi dibar Karen mahaukaciya da ita ta watsar,hakan ya Kara kuntata zuciyar mamy aikuwa ta kudurta aranta saita sake sabon shiri,Dan wallahi dole saita kada wadan Nan kauyawan rigarsu. ****"****"**** Tun sassafe ta tashi ta Dora musu abin Kari kasancewar ta kwararriya wajen iya girki,Dan haka ta shirya musu lafiyayyen break fast,bayan ta Gama jerawa a dinning ta koma tayi shirinta cikin kwalliyarta kamar a baya,sai ka rantse kace ba abinda ke damunta Nan kuwa damuwar dake tattare da zuciyarta ta zarce ta kowa a gidan,kawai dai ita kadai ta barwa kanta sanin abinda ta kudurtawa zuciyarta. Saida ya shirya tsaf cikin shigarsa ta shirin fita office kafin suka hallara a falon,kujera taja Masa ya zauna kafin ta saki murmushi tace! Bari na Kira amaryarka ko? Dagowa yayi ya kalleta da kyawawan fararen idanunsa,danshi harga Allah yama Manta da wata amaryarsa da aka kakaba masa baice da ita komai ba ya mayar da idanunsa kan karamin cup din dake gabansa,kafin yace! Ki zauna kawai Bari naje na kirata,ah ah wannan ai bamai yiyuwa bane ta Yaya zan wahalar da ango kawai kasha zamanka zan Kira Maka kanwar tawa da Kaina,shikenan!! Kawai ya furta ita Kuma ta juya ta fice a falon a zuciyarta tana dariyar mugunta domin wannan shine plan dinta na farko Wanda zata Fara rikita kwakwalwar Mai gidan dashi. Shikuwa bayanta yabi da kallo harta fice ta nufi bangaren Dije a zuciyarsa Yana mamakin canzawarta Dan yayi mamaki kwarai sanin halinta da yayi akan kishinsa to Amma ba mamaki dama ance wasu matan zaka ga sunada zafin kishi kafin ayi musu Amma da zarar anyi shikenan sai kaga sun bada Kai bori ya hau,gashi ko ya tabbatar dama Bata wani Bata lokacinta ba danshi bayan ita baya ganin wata mace Dan sajida ta daban ce a gurinshi tana Kula dashi matuka iyakar iyawarta to Mai zaisa yace zai Mata wata kishiya! Da ire-iren wannan tunanin ya tsaya jiran dawowarta. Itako burinta Bai wuce taga fuskar wadda aka kakaba wa mijinta ba,Dan ko ranar da sukaje gun Daddy Bata wani kalleta sosai ba Dan hankalinta ba'a kanta yake ba,gashi kuma an cewa su tafi ita ta Fara fita da zumbulelen hijabi ko kafin su fito har sun hangota ta shige. Batare da tayi sallama ko knoking ba ta Danna Kai falon,tsayawa tayi tana karewa Falon kallo yadda ya tsaru tamkar a kasar turai ga kamshi dake tashi ta ko Ina,ba laifi ta yaba da tsabtar amaryar da miji Bai damu da ita ba,Kai tsaye ta nufi bedroom din Dan tana kyautata zaton Nan ne kasancewar komai tsarin ginin irin nata ne,Kai tsaye ta turn kofar ta shiga,inda ta iske Dijen tsaye gaban mirrow sanye da riga da wando na Pakistan Amma wandon pencil ne sai rigar Mai umbrella kanta take tajewa tana son sa ribbons taji alamar bude kofarta,a zatonta ko Zainab ce harta juyo zata aza Mata masifa sai tayi ido hudu da sajida,cike da mamakin meya kawo yarinyar dakin amaryar Habeeb,inma dai ita ta jawota Dan shishshigi da Nuna son dangin miji ko kasancewar ta 'yar kauyensu ,to wannan dai annoba ce daban take da sauran mutane. Duk da Dijen ta dan ji zafin shigo Mata daki da tayi bako sallama(kaji su Dije Koda yashe ma tasan dadin auren๐Ÿ˜œ) Amma saita share tare da fadin,lah!! Aunty kece da kanki? Um nice Ina Mai dakin take? Dije gani tayi kamar ta Raina Mata hankali Dan haka tace,tana wanka' wani abun ne a fada Mata inta fito? Eh! kice Mata muna jiranta wajen yin bareak fast. Ok to zan fada mata Harta juya sai Dije tace Aunty harda ni? Gaskiya ban San dake aka zo ba Dan haka banyi dake ba sai dai ki leka side din Naseer tunda 'yar uwarku ce ko Kya samu saura. Hakane can bama iya saura ba ko sabo za'a dafa min tunda duk tsatso Daya muka fito an San darajar hatsi da tsaba. Taso tankawa yarinyar saita tuna a dakin wa take karta rainata inta fito Dan haka ta juya abinta ta fice Tana fita Dije tace! Shegiya Mai siffar samudawa wato ni Zaki rainawa hankali Wai a nufinki bakisan wadda aka daurawa aure wancan rafkakhan din mijin naki aure da ita ba, ni naci uwar rainin wayo,haka tayi ta masifa harta gama shiryawa sannan ta fita. Tana zuwa ta tarar da su zaune da alama amaryar suke jira,batare da Bata lokaci ba taja kujerar dake fuskantar ta Habeeb ta zauna,wani kallo sajida ta watsa Mata tana shirin yimata magana Habeeb ya rigata,ta hanyar fadin,ke wannan wane irin iskanci ne! Ke dama gaki ga yadda kike Kai fall fasinjoji Zaki tashi ki fitowa mutane ba dankwali! Ai a tunanina ba laifi bane Dan mace ta nunuwa mijinta baiwar da Allah yayi Mata,Kuma ma Ina laifin wannan kwalliyar tawa ai Kai da gani kasan dama Dan irinka sabon ango akayi ta. Kwata-kwata rasa abin cewa yayi,itako sajida wani sabon tashin hanline ya risketa sakamakon Jin Wai Dije itace Amaryar Habeeb,wannan karon duk yadda taso kissa tayi aiki Ina!! abin yaki yiyuwa sakamakon Jin zuciyarta da tayi tana Mata suya da Kuma tunawa da tayi da wasu abubuwan da suka faru a baya,Wanda alamu sun Nuna karara Habeeb nason yarinyar Amma Koda tayi Masa magana ya kanainayeta da dadin baki irin nasu na maza,shiyasa a lokacin ko tayi tunanin wani abun sai ta tuna yadda yake santa da Kuma yadda yake Nuna Mata baida ra'ayin yin Mata biyu,hakan yasa ta sakankance ta yadda dashi Ashe kwaf Daya yake shirin yi mata! Wayyo ita kanta Ina zata San kanta.Duk yadda taso ta danne abun kin yiyuwa yayi,Dan haka cikin bacin rai tafar magana, Me nake shirin gani Habeeb? Ko ince nake shirin ji? Kana nufin Khadija ka aura? lallai namiji buhun Kaya ! Namiji buhun barkono! Namiji bishiyar lalle ko ince iccen magarya,wallahi ka cuceni ka rasa da wadda zaka hadani sai da wannan yar tatsitsiyar yarinyar Kai ko kunya ma bakaji ba,duk yadda nake Kula da kai Dame na rageka? Tunda ta Fara maganar ya kafeta da ido,yayin da Dije ta Nuna ko a jikinta ta Fara aikawa cikinta abinda yake bukata,sai da taji ta koshi kafin ta dago ta dube su sannan taja kujerar baya da niyyar barin gurin,sai ta tsinkayi muryar sajida na fadin wallahi sai dai ka zaba ko ni ko ita Dan bazan iya kishi da kanwar kankwata ba,wannan ma ai raini ne Kai ko kunya bakaji ka tunkari wannan ficikar yarinyar a matsayin miji. Zancen yaushe kuma! Wallahi Aunty kada ki yadda kawai ki bashi zabi ko ke ko ni din,Nima zanga ko inada matsayi a zuciyarsa ko banda,sai dai fa kafin ki yanke hukunci kiyi tunani Dan zawarci a wannan shekarun naki hmmm nayi shuru tasa Kai ta fice tana dariya. *Pls.ku Kara hakuri* *Alkalamin khady* โœ[3/18, 8:08 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (place of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 4โƒฃ8โƒฃ Tana Jin sajida nata balla ruwan bala'i tana cusa Mata ashar,Amma ta share ta fice abinta,shikuwa gogan Yana zaune ya zuba wa sajida ido kawai,ganin yadda taketa kumfar baki ,Saida yaga takai aya kafin yace, Idan ni na aureta banji kunya ba,ke ai gashinan kin tsaya kina cacar baki da 'yar ficikar yarinyar da Kika raina,Kuma in baki Manta ba da kike cewa na zabi Daya ko ita ko ke! Shin kin Manta ita din zabin mahaifina ce? Kin San kuwa babu yadda za'ayi Dan uwana ya karbi zabin da aka mana,ni saboda nine fitsararre bijirarre ince bana so! To ai Koda hakan zata kasance sai dai na sakeku ku duka biyun in zauna hakan ba mace. Habeeb!! Ashe dama zaka iya rabuwa Dani? Ashe dama duk fadar da kake yi kana cewa aurenmu ba saki ba yaji kishiya har abada ashe duk karya ce,sai yanzu nake gane kuskuren Dana tafka,da girmana da shekaru na ka binne ni a Bai bai,kasa na yadda da dukkan yaudararrun kalamanka,na Manta da cewa ku maza ba'a baku amana,shikenan naji na Kuma amince bazaka iya rabuwa da ita ba kasancewarta zabin mahaifinka,amma ni dole ka rabu dani,Kuma wallahi bazan zauna zawarci da cikinka dake jikina ba,zuwa zanyi na tunkudar dashi tunda ubanshi Bai damu dashi ba sam,. Tunda ta ambaci tanada ciki ya nemi nutsuwarsa ya rasa,da mugun sauri ya ture kujerar dayake Kai ya karaso inda take tana matsar kwalla,kokarin Kama hannunta yake Amma taki yadda,be barta ba har Saida ya samu nasarar rike hannun nata kafin ya kura Mata ido nadan wani lokaci,duk da taki dagowa ta kalleshi,amma hakan baisa ya kauda idonsa daga gareta ba,Jin yaki cewa komai yasata dago kanta sukayi ido hudu dashi,ta so ta janye idonta Amma takasa,hakan yasa suka kurawa juna ido na Dan wani lokaci. Shine ya Fara magana ta hanyar fadin,yanzu ashe Zaki iya rabuwa Dani? Dama Zaki iya salwantar da jinina dake jikinki saboda kin da kikemin? Ashe bakya Sona? Kisan Kai fa kike shirin yi! Da sauri ta dago ta kalleshi,yes!! Kisan Kai Mana Kuma harna mutum biyu,domin muddin Kika zubar da abinda ke cikinki wallahi Nima mutuwa zanyi,a da bana son kisami ciki da wuri,Amma daga baya sai Allah ya jarrabeni da son haihuwar,wallahi Ina son baby fiye da kaina,Ina son Inga na haihu dake saboda kinada matsayi mafi girma a gurina,Yana Gama fadar haka ya jawota ya rungume ta tsam a jikinshi,ya shiga bubbuga bayanta alamar rarrashi,kafin yafara Rada Mata a kunne,haba masoyiyar my kifin gwangwani,ki kwantar da hankalinki,ai babu wata macen data Isa ta kamoki bare harta zarta ki,waccan ni wallahi badan kin tuna da ita ba da ni nama Manta da zamanta Kuma kema shaida ce,kiyimin adalci! Tabbas maganganun sa sunyi matukar tasiri Dan haka ta saki jikinta ta Kuma Kara yadda da duk abinda ya fada mata, Rakoshi tayi zuwa parking space har Saida taga fitar shi kafin ta dawo da tunanin nemawa kanta mafita,Dan Zama guri Daya da wannan aljanar tsautsayi ne ai! To wazata Kira suyi shawara ,kawai gida yakamata taje,tana shiga ta dau waya ta kirashi ta shiga sanar Masa zata gida, Meyasa baki fadamin tun Ina gida ba sai yanzu? Wallahi ji nayi gidan yayimin zafi Ina son zuwa ganin ummana zuwa gobe sai in dawo. Me yasa har sai gobe? Saboda Ina son haduwa da Daddy kasan kuwa baya dawowa sai dare dole sai dai in kwana. Amma kin San ban iya bacci nikadai ba ko?ya kike so nayi? Hakuri zakayi sweet husby yau Daya dai! Shekenan ki gaishe su ki kulamin da kanki da Kuma baby na. Ok don't mind bye! Ok bye!! Tana kashewa Jakarta kawai ta dauka da key din mota ta fice. ****** Tun fitar ta Dije ta gani domin tana gurin mama mariya Nan ta yini,ganin yamma tayi batada shirin komawa bangarenta yasa mama mariya tambayarta bazata tafi taje tayiwa mijinta girki ba sannan ta kimtsa kanta! Bata fuska Dije tayi tare da fadin to ni girkin me zanyi Masa bayan ma Bai damu Dani ba! Ni tunda aka kawoni yaune fa kawai magana ta hadani dashi [3/18, 8:08 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (Place of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 4โƒฃ9โƒฃ Kina nufin kicemun har yanzu baku tsaya kun fahimci junanku ba? "To mama ya zanyi Masa! ni zan jawoshi kome" nifa wallahi dama wannan auren nayi biyayya ne kawai amma wallahi bana sonshi inada Wanda nake so!,kawai kunyar Daddy tasa na amince. To ai kin gama magana tunda har ya kasance kin amince din Dan Daddy'n naku,to bara kiji ki tsaya ki nutsu ki kwantar da hankalinki kibar duk wani sakarci ki kula da mijinki inba haka ba kina gani kishiya zata Miki fintinkau,ki Zama 'yar kallo,bare ke da kikeda wannan kishiyar uwar Mata ai ko ni keda ita saina girgiza bare ke 'yar tsakuwar Nan... "Dariya Dije tayi sannan tace to ai kinada mamy" Kuma kinsan a haife ta haifi Anty sajida. Rabu da wannan wayake ta Tata! Ai bata Kai wannan gogewa da Zama 'yar zamani ba,yanzu dai duk mubar wannan maganar wallahi indai baku tsada hankalinku kun tsaya kun fahimci junanku ba! To ko zan sanar wa da Alhajin inya so ayita ta kare asan abinyi a raba auren kowa ya huta. Duk da harga zuciyarta Bata Jin son Habeeb Amma da mama mariya ta ambaci a raba auren Saida gabanta ya fadi,taji kuma bata bukatar hakan,Dan haka saita marairaice fuska kamar me shirin yi kuka, Ni fa ba haka nace Ina son a raba auren ba kawai dai...sai Kuma tayi shuru. Yo ai ba fada kukayi ba Amma kun Nuna cewa ku din 'yan zamani ne ai Dan haka gara ayita ta kare! Ni dai gaskiya bana son a maidani karamar bazawara,asa 'yan maza su koma yimin Dan Kira gara koma meyi inyi. Yauwa ko ke fa,ki zage damtse ki kwaci mijinki hannun kishiyarki bawai ki rabasu ba ah ah kowa tasa ta fishsheshi ki kafa gwamnatinki kema! To ta Yaya? Au kijini da sakarcin banza! Duk hudubar da aka dinga nanata muku da za'a kawoku ta tashi a banza kenan? Bakiga 'yar uwarki yadda tayi maliyan lukwi abinta ita da mijinta ba, to Bari kiji..... Nan ta shiga zayyanowa Dije abubuwa masu matukar muhimmanci da tasiri a rayuwar aure,Nan Dije fa ta nutsu ta shiga hadda da bita. Bari in tashi in tafi In Fara tun yau wallahi Dan ca zanyi a raba kwana,Dariya mama mariya tayi a ranta tana jinjina rashin kunya irin ta diyan zamani inba haka ba,taya Dije har tasan wani raba kwana. To naji uwar mata kafin ki tafin jirani Ina zuwa! Cewar mama mariya data nufi dakinta. Fitowa tayi dauke da kofi a hannunta ta mikawa Dije tace maza shanye shi. Karba tayi takai bakinta inda tana dandanawa tayi saurin dauke cup din tare da fadin,wallahi mama ba dadi, Ai dama bance Miki da Dadi ba Dan haka shanye shi maza inkuma so kikeyi kishiyarki ta fiki to Dan bakisan shirinta ba. Ai kafin mama ta rufe baki Dije ta kafa Kai ta kusa zuke abinda ke ciki. Dariya ce ta kwacewa mama Dan a yadda ta fuskanta Dije nada Dan banzan kishi tsabagen shirme da jaraba ne yasa bazaka gane ba Amma ta hango fa akwai cakwakiya. Tana gama Sha mama ta Bata wani turare tace ungo wannan shafawa zakiyi shi Kuma a gabanki Yana gyara gaban mace matuka da kuma sa kamshi karba tayi ta mike tare da fadin to mama sai na dawo. Kul!! Naga kin dawomin Nan Dan Nima babanku yau Nan yake. Dariya Dije tayi tace Kai mama bako kunya! Kinci gidanku keda kunyar ni maza wuce kiyi uzurin gabanki. Dije na fitowa ta shiga part din Zainab,Nan ma wasu Dalasiman ta shiga biya Mata tare da dada koya Mata wasu darrusan,ganin so suke su cike Mata kwakwalwa yasa ta mike ta fice tayi nata wurin. **********"""********* Tsaye na Hango Dije a kicin anata faman girke-girke hada wannan Gama wannan harta gama duk abinda ranta yake so,Bata San takamaimen yanzu lokacin dawowarshi ba amma dai Bari ta jera komai akan tsari,hakan tayi sannan ta shige daki ta cire kayanta tare da daura towel ta afka toilet,wanka ta santalo kafin tazo ta sallara kwalliya,sosai tayi masifar kyau,rasa kayan da zata Sa tayi saita tuna da akwatunansu na lefe da Daddy ya Basu jiya,budewa tayi ta shiga duba kayan ciki,Kaya ne masu kyau da Kuma tsada,Dan haka hannunta ya sauka kan wata Arebian gown maroon colour,zarota tayi ba qaramin kyau rigar tayi Mata ba Dan haka tasa undies tare da zura rigar,kuma cikin ikon Allah kamar an gwada da ita tayi mata dass a jikinta tana kokarin Kara gyara kanta taji alamun horn,lekawa tayi ta window aikuwa taga shine ke dawowa da Naseer,da sauri ta Kara murza powder tare da Kara fesa turare ganin karfe shida harda 'yan mintina,dankwalin rigar na hannunta tayi saurin fita falonta Dan hakan na cikin karatun da aka koyar da ita. Sallama sukayi da juna inda kowa yayi nasa wuri, Direct part din sajida ya nufa inda Yana zuwa ya murda kofar jinta yayi a rufe gam,Nan ya shiga knoking Nan ma shuru,tsaki yayi kafin ya fito da wayarshi ya shiga Kiran layinta,shuru Bata daga ba har yayi Mata missed call kusan biyar dole ya hakura ya mayar da wayar aljihunsa Yana me Kara Jan wani tsakin dayafi na farko,tabbas ya gaji ga yunwa gashi Yana son yayi wanka ya zaiyi to? Ko part din mamy zaije to ai fishi takeyi dasu har yanzu ya salam! Ya furta a hankali dole ya koma office kenan yayi wanka yasamawa kansa abinda zaici duk da wannan tunanin da yayi baisa ya tafin ba saima jingina da yayi da bayan kofar. Duk abinda yakeyi tana kallonshi,zuciyata na raya Mata shin taje ta sameshi din Kota share,tunawa da tayi inta ci gaba da rayuwa dashi a haka itace Bata da riba danshi yanada matarshi,hakan yasa ta mike ta fito kamar Mara gaskiya ta tunkaro gurin dayake, kasancewar idanunsa lumshe suke Kuma flat sheos ne a kafarta shiyasa Sam Bai ji takunta. Jin wani daddadan kamshin turare daya had da sassanyar iskar dake bugawa yasashi bude idonshi a hankali,fess ya saukesu akan 'yar kyakkyawar farar yarinyar,duk yadda kauda idonsa akanta kasawa yayi illah ma wani Abu dayaji Yana fuzgarshi zuwa gareta,Yana tsaka da tunanin yaji muryarta tana fadin sannu da zuwa Yaya! Kasa amsawa yayi Dan ji yayi wannan kamar ba Dijen Daya sani ba fitinanniya,Mai tsiwa da jarabar tsiya.nan ma Bai Gama tunanin ba yaji ta Mika hannu tare da sabule jakar dake sakale a kafadarshi,tare da Kama hannunsa zuwa bangarenta,kamar wani soko haka ya bita zugwi- zugwi har suka karasa ta murza kofar suka shiga,wani sassanyan dadin kamshi ya ziyarce shi, tabbas sajida nada tsabta da kokarin gyara amma duk da haka yau sai yake ganin gyaran da akayiwa wannan falon na musamman ne Dan marabi shi da shigowa tun ranar da suka taho dasu Dije daga kauye. Ka zauna Mana Yaya! Bari na hada Maka ruwan wanka nasan ka gaji, Kafin ya Bata amsa harta shige zuwa bedroom dinta ta fada toilet ta hada Masa ruwan wanka Fitowa tayi tare da fadin kana iya shiga Dan an gama Kai kadai ruwan ke jira. Tabbas Yana bukatar yin wanka Dan haka be musa ba ya mike ya shige,ji yayi ruwan ma na want kamshi na musamman, murmushi yayi tare da fadin Nan su Dije anyi hankali kenan Ashe yarinya za'a dake kema sannan ya fada kwamin wankan ya shiga cuda daudarsa. Koda ya fito daure da towel dinta Sam ya Manta kayansa na bangaren sajida gashi Bata dawo ba yasan hakan baya rasa nasaba da abinda ya faru dazu kaiii Mata sarakan kishi,rasa man dazai shafa yayi kawai sai yayi amfani da nata,bisa dole ya mayar da wandon jikinshi Dan ba yadda zaiyi Amma iya singlet kawai ya saka ya kasa mayar da waccan rigar, .Zama yayi a gefen gadon inda Yana zaman yaji ta bude kofar ta shigo da sallama,amsawa yayi Dan haka yaji tace! Yaya ga abinci can na jiranka,Sam ba damar Jan aji Dan yunwa fa Yana jinta Dan tun safe marabinshi da abinci Baiyi Mata magana ba ya mike tana gaba Yana biye da ita,suna Isa Dinning ta shiga zuba masa,sosai yaci abinci Dan yayi Masa Dadi,Yana gamawa yaji ana Kiran sallar magrib dole ya mike ya koma dakin yasa rigarshi tare da yin alwala ya fita masallaci. Itama Alwalar tayi tayi sallah ganin Bai shigo ba har isha'i yasa ta mike tayi wanakanta tare da daura alwala ta shirya cikin rigarta ta barci,wani barci takeji sosai Dan tayi tunanin ko Sajida ta dawo ne shiyasa taji shuru.ko kadan Bata damu ba Dan dama abinka da ban Saba ba. Shi kuwa bayan anyi sallar ishi'i ya jima a masallaci Yana addu'oin kafin ya fito ya nufo gidan. Tsaya wa yayi a wajen ya Kara Kiran number sajida still Bata daga ba hakan yasa ranshi ya Fara baci,ya jima a wajen jin sanyi na Neman lahantashi yashi nufar cikin gidan,ya jima tsaye bakin kofa Yana tunanin shiga zuwa can ya tura kofar ya shiga,yaji dadin rashin ganinta a falon Dan haka ya rage kayan jikinshi Dan be Saba kwanciya da Kaya ba,ya rage daga shi sai boxer,kwanciya yayi saman three seeter sai dai me? Wani zazzafan sanyi yakeji Wanda tun Yana daurewa ya kasa,ga wata fitinanniya sha'awa data gallabesa kasancewar shi mutum ne Mai yawan bukata lokacin sanyi Dan sajida ma tasan halinsa hakan yasa koyaushe suke manne da juna Amma duk da tasan da haka yau tasa kafarta ta barshi bayan Bata sanar dashi kwana zatayi ba Kuma ta na sane da halin dazai shiga a Daren Nan ganin sanyin naci gaba da ratsa shi Dan karya jawa kansa matsala yasa ya mike ya nufi dayan bedroom dinta,a rufe ya jishi ruf Wanda hakan yasa yayi tsammanin ko Tana ciki ne sai yaji dadin hakan ya nufi Daya bedroom din ya murda kofar,bude ya jishi Dan haka yasa Kai ya shige kasancewar ta kashe wutar dakin sai dim night shiyasa Bai wani lura da ita ba har Saida ya fada saman gadon yaji ya taba abu Koda ya juya Saiya ganta kwance tanata sharar baccinta,mikewa yayi ya kunna wutar dakin take yayi tozali da yaloluwar rigar baccinta data bi jikinta ta lafe,sauri yayi ya kashe wutar tare da jawo pillow ya jefar bisa kafet ya kwanta Amma me? Tunanin yadda ya ganta yasa shi cikin wani yanayin na tsananin bukatuwa Dan haka ya Kara runtse idonshi. Duk yadda yaso yayi bacci kasawa yayi,ganin alamun kamar tanada nauyin bacci yasashi mikewa Dan zuwa ya rungumeta ko yaji saukin abinda yakeji. Yana hawa saman gadon ya jawota jikinshi inda ta bude idonta,jinta a bakon gurin da Bata Saba kasancewa a gurin ba yasa ta fara kokarin fasa ihu,ji tayi ya hade bakinsu guri guda Wanda yasa ihunta saurin komawa ta shiga zaro ido. Abu wasa wasa Nan fa su Habeeb aka haukace sosai ya shiga sarrafata inda duk wata gangar jikinta ta mutu ga Kuma tsabar tsorata da tayi da ganin yadda yake yi mata abinda Bata taba tunanin anayi wa wata mace ba,tana tsaka da wannan tunanin taji Yana ambatar addu'ar saduwa da iyali inda yadawo da ita daga duniyar tunanin data afka sakamakon Jin sa da tayi Yana kokarin jefa kwallo a raga. *Goal* ๐Ÿคฃ *Ba ruwana yaseen team tame gari ku da sajida* *Alkalamin khady* โœ [3/18, 8:09 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (Place of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* Na Khadeeja Usman 5โƒฃ0โƒฃ *Oh ni Dijee !! wannan ruwan comments haka ai saiku sa sajida ta yankomin sammaci,to dai Alhamdulillah naji Dadi kwarai Kuma Ina godiya ga addu'oinku gareni luv all* ๐Ÿ˜˜ Sam ya rasa nutsuwarsa tare da dukkan wani tunaninshi, domin ya tsinci kanshi a sabuwar duniyar da beyi tunanin zai iya zuwa gurin ba tabbas wannan shi ake Kira da Dan hakin daka Raina! Sosai ya samu nutsuwa wadda sai bayan ya gamsu sosai,sannan ya tuna da tabargazar da yayi,shasshekar kukanta kawai yakeji Yana ratsa kunnuwansa,inda ya laluba a hankali ya dauki boxer dinshi ya nufi toilet,Saida ya tsarkake jikinshi kafin ya fito Yana zuwa ya kunna light din dakin take ya Hango ta saman gadon ta lullube har fuskarta da bedsheet da alama Kuma kuka takeyi,duk da ya yaba da jarumtar ta Dan baiyi tunanin ta iya daukar Koda Rabin abinda yayi Mata bane,sai gashi ta bashi mamaki,shafo gefen wuyansa yayi gurin data rattaba Masa yakushi,Sam baiji zafin gurin ba sai yanzu yake Dan ji,rasa yadda zaiyi ya Fara Mata magana yayi Dan dole ne yasan sai yayi rarrashi Amma ta Yaya? Ta Ina zai Fara? Shi tsoron shi ma Daya kada yaje ta tayar Masa da wadan Nan jiga jigan aljanun nata.Ganin kamar tana rawar sanyi ne yasashi saurin karasawa inda take ya bude bargon,dagowa tayi da kumburarrun idanunwanta ta kalleshi,sai Kuma ta fashe da kuka Mai sauti,dafe Kai yayi tare da fadin ya Allah! Kafin ya juya tare da matsawa daf da ita ya bude baki da niyyar yimata magana ta katseshi ta hanyar fadin,kaga Dan Allah nidai na rokeka a matsayin ka na likita Mai ceton rai ka taimaka ka ceci rayuwata ka mayar min da kafafuna ka dinke min kamar yadda ka rabani dasu,dama nasan baka kaunata Amma ban taba tunanin kiyayyar da kakemun takai hakaba,kowacce amarya ai ance sai an sayi bakinta sannan an Bata kaza da lemo a baki,an rarrasheta sannan a lallabata tayi bacci, Amma Kai dubi abinda kayi mun kawai Dan tsabar tsagwaron kiyayya jibi yadda ka raba kwankwasona da kuguna ,kanaji na Ina cewa zaka yagani amma kayi banza Dani har Saida kayimun fyade,to wallahi kada kaga kana Dan uwana sai na cire kunya na murje idona na kaika Kara human right Dan wannan zaluncin daka aikata min,ai kowa ya ganka yaji abinda kayimin mamaki ma za'ayi da ban mutu ba,to sai Allah yasa inada tsawon rai! Ta karashe maganar tare da rushewa da kuka. Duk yadda yaso ya maze kasawa yayi Saida ya juya bayansa ya dinga dariyar maganganunta har Saida yayi Mai isarsa mafin ya juyo ya kalleta tare da fadin,naji nayi laifi amma ayi hakuri sai dai in kin duba ai ba auren soyayya mukayi ba shi yasa na biyo Miki ta wannan sigar ba kaza ba lemo ban San cewa kinajin yunwa ba dan naga kin debi girki shiyasa. Kaga ni ba surutu nake bukata ba yanzu so nakeyi kawai kayimin taimakon gaggawa ka jona min cinyoyina daka cire wayyo ni miskina wayyo ni Innata da babana. Kinga ya Isa Bari naga ta Ina zan fara tukun,sam Bata hanashi ba haka ya yaye Mata bargon,ba laifi gaskiya ya danyi barna Dan haka baice Mata komai ba ya mike ya nufi toilet ruwan zafi ya hada kafin ya dawo ya kinkimeta su Dije Banda matsar hawaye ba abinda akayi a haka harya shiga da ita toilet din ba wani jira ya sata cikin ruwan wata karamar Kara tayi taso mikewa Amma ya dannata tare da fadin, sorry baby...ki tsaya ruwan zai taimaka Miki kafafun su hade,haka ya dinga canza Mata ruwa har sau uku dayaga ta Dan saki jikinta a cikin ruwan Nan ya Dan fito ya barta,zuwa can ya koma ya tarar tana gyangyadi,tashinta yayi tare da sata ta tsarkake jikinta yaso kamota Amma ta buge Masa hannu ganin ta samu,kawai dai tana dingisawa harta karasa bakin gadon da kanshi ya yaye zanin gadon ya shimfida wani sannan yace ta kwanta,Shima kwanciyar yayi ya dauka ma zata hanashi Amma yaga ta juya baya ba jimawa duka bacci ya sheke su.....! ********************** Tunda ta Isa gidan ta korawa mahaifiyarta jawabin duk abinda ya faru,harta gama Bata katseta ba Saida takai aya sannan ta numfasa tace,yanzu ke dan abin kunya ta Yaya kikayi sakaci da kula da miji har yayo Miki kishiya? Wallahi mummy ban gaza ta ko Ina ba Ina iyakar kokarina tako wane fanni,ni abinda ma yafi konamin Rai Wai ya rasa wadda zai auro sai wannan yarinyar khadeeja. Amma ai kince auren Hadi ne ko? Eh hadasu akayi Nan ta bata labarin abinda ya faru zuwansu kauye. Ahaf kice laifinki ne,Ina ke Ina biyewa uwar miji! Kina kallon itama a dosane take amma Kika biye Mata Kika jawa kanki to gashinan anyi muku ruwan kishiyoyi ai hukunci mafi Muni a gurin mace. Ina duk Abubuwan Dana koya Miki? Ina dabarun Zama da mijin Dana koyar dake tare da kissa kala-kala? Ai nace Miki bayan miji ki Kama 'yan uwansa Koda su sun Nuna basa sonki to ke ki Nuna kina sonsu sosai Koda ba hakanne cikin zuciyarka ba,yanzu da Kika kwaso kafa Kika taho yaji kikayo akan kishiya ko me? Ah ah mummy zuwa nayi dai daukar wani karatun. Ai na dauka yaji kikayo ince kin Fara yankawa kanki tikitin zawarci kenan,Dan in Kika dawo gidan nan ai na shiga uku ga kannenki uku gabana ba mashinshina,gara kiyi me yiyuwa ki kadata tayi gaba ta ruwan sanyi kici gaba da murza kambunki har abada. To mummy naji,amma wallahi ji nakeyi zuciyata kamar zata fashe, Yo ai dama kishin kenan Kuma banda abinki ai in kinbi a sannu kece a sama Dan kema kanki shaidace Kuma na koyar dake karatun,tunda nawa akayomin cikin ruwan sanyi nake korasu inda suka fito Dan haka kema kibi abin sannu a hankali zakiyi nasara,yanzu kawai ki kwana anan Dan akwai hadin da zansa ai miki zuwa gobe saiki koma. To wata sabuwa Kuma mummy,nafa cemai cikine Dani! Au to sai me? Karya fa nakeyi! Ai na sani amma kisan yadda zakiyi cikin ya zube. As dole mummy Dan wallahi nasan da wuri zai ganoni garama in San abinyi,Kinga wannan duk ba damuwa bane za'san yadda za'ayi. Da yamma suna zaune taga Yana kiranta taso dauka amma mamanta ta hanata,haka ma Kiran dare dole taki dauka Dan Kar plan dinsu ya rushe. *********************** Washe gari kiri-kiri yaki zuwa gun aiki ya tsaya kula da Dije uwar rigima,wadda har yanzu fa take kan bakanta na saita Kai kararsa, Sam duk yadda taso ta fita taje sashen mama mariya hanata yayi ya kasa ya tsare hatta da gyaran gidan duka shi yayi har girki sai lallabata yakeyi akan taci danshi gani yakeyi in ya barta ta fita din tona Mai asiri zatayi inda zatasa girmansa ya zube Kuma ya dinga Jin kunya,bashi ya fita ba har sai da aka Kira sallar la'asar Dan azahar ma gida yayi ta. Yana dawowa daga salla yayi niyyar shiga ya dauko key din motarsa ya tafi gidansu sajida ya karbo keys din part dinta tunda ya lura iskanci takeji,duk lokacin dataga dama ta dawo,Yana shirin hawa compound din yaji alamar bude get Koda ya waiga motar sajida ce Dan haka ya tsaya tare da kafeta da ido,Sam Bai motsa daga inda yake ba harta bude motar ta fito,cike da yauki da yanga tare da shaking din body ta nufo inda yake,daure fuska yayi Amma tana karasowa ta rungumeshi sam baiyi niyyar maida martani ba amma saita kasheshi da salonta, kasancewar shi ya juya bayane ita fuskantar bangaren Dije yasa ta hango Dijen na kokarin jawo kofar Sam Bata tsaya Bata lokaci ba Dan bawani tazara ne dasu ba Dan haka ta Fara kissing dinshi tako Ina tana fadin yayi hakuri tare da jaddada Masa yadda tayi missing dinshi. Tana ganin Dije ta iso daf dasu ta Fara fadin,haba hubby na ai basaika fadamin yadda kayi missing Dina ba ni kaina nasan yadda nasaba kula dakai nasan jiya baka samu yin bacci ba Dan ba gurin kwana watakil ma a mota ka kwana kayimin afuwa kaji mijina yau zan biyaka bashi. Washhh sukaji ance dasauri ya rabu da jikin sajida ya nufi gurin data Dan durkushe alamun tanajin wani Abu A rude ya shiga tambayrta meya faru? Shagwabe fuska tayi tare da langabar dakai tana fadin au tambaya ta ma kakey! Bayan kafi kowa sanin abinda ka aikata nasan zaka dawo shiyasa zan gudu gun mama mariya Dan har yanzu bacci nakeji tunda baka barni nayi jiya ba sannan ga gurin daka.....๐Ÿ™Šzafi yakemin inaga fami nayi shine yakemun zafi muje ka dubamin kaji...... Tashin hankali Wanda ba'a samasa Rana. *Team sajida gareku* *Alkalamin khady* โœ [3/18, 8:10 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (Place of the excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 5โƒฃ1โƒฃ Wani irin buguwa zuciyar sajida tayi sakamakon ji da ganin abinda Dijen tayi,ji takeyi kamar taje ta watsa musu fetur ta kyasta musu ashana su Kone kowa ya huta...Bata Kara tsinkewa da lamarin ba Saida ta tsinkayi muryarsa Yana fadin, Waike wace irin raguwar yarinya ce ne me jarabar rakin tsiya,daga Dan yin tuntube shine Zaki dami mutane da kananan koke-koke Yana maganar Yana satar kallon inda sajida take tsaye,wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke Daya kasance ba abinda take zargi ne ya faru ba,Jin ajiyar zuciyar da tayi wadda tasa duka Saida suka juya suka kalleta. Wani bakin ciki ne ya ziyarci zuciyar Dije wato ma baya son matarsa tasan wani abu ya faru tsakaninsu,to wallahi yau zasu San da Dije suke zaune,har ni zasu rainawa wayo Dan sunga sun girmeni,nida da nawa wayon aka haifeni ba Wanda ya koyamin. Ji sukayi ta fashe da kuka yayin da Sajida da sauri ta karaso inda take,a nata salon kissar ta Nuna kulawa da Dijen yadda zai Kara yadda da ita hakan yasata rike kafar tare da fadin sannu ! Garin Yaya hakan ta faru? Faduwa Kika yi kenan! Kema Khadija ki daina wani shirmen yanzu baki San kin girma bane. Nasani Mana ta fada cikin kuka,tunda duk wadda aka riga aka yiwa fyade ai ta gama girma,yanzu Aunty kema dama haka Yaya yake Miki? Kuma Kika yadda kike zaune dashi baki kaishi Kara ba! Ita Sajida a tunaninta Habeeb ba mamaki dukan Dije yayi Dan dama can tasan basa shiri bare an bashi ita bada son ranshi ba,Dan haka. Harda Kara langabar dakai tare da karkace baki cikin salonta na manyan Mata da Kuma son yiwa Dije dabarar da zata Sa ta tsorata da Habeeb ta gudu tabar gidan,kallon Habeeb tayi tare da zuge Jakarta ta Ciro key ta Mika Masa tace,naga tun kayan jiya ne a jikinka yakamata kaje kayi wanka Bari na Rakata da kaina kada ka damu. Karba yayi yayi saurin barin wurin,Dan bayason Dije ta furta wani abu akan daransu na jiya Amma yaga ta waske ai kamar bazata fada ba. Yana shigewa Sajida ta dawo da kallonta ga Dije Dan Fara shirya Mata hanyar tserewa,ita kuwa Dije a zuciyarta ta furta dama kin bishi yafi Miki Dan Kar nake kallonki Amma a fuska saita Kara Zama kalar tausayi tare da fadin,wai Dan Allah Aunty kema haka Yaya yake yi Miki dama? Murmushi Sajida tayi tare da fadin ah ah! Ni Bai taba buguna ba ko zagina,kema din Dan baya sonki ne, Kuma kin San kiyayyar da namiji bata gushewa shiyasa gara ma tun wuri kice Masa ya rabu dake Dan wata Rana illata ki zaiyi. Gani Dijen ta nutsu harda yin tagumi yasa sajida dada kaimi gurin yi Mata famfo Bata katseta ba har Saida ta Gama sannan Dijen ta numfasa tace. Lallai ma yayan Nan ni din ce zaice baya so! To ko wallahi sai dai ya kasheni a zo a fita da gawata,ai aurena dashi mutu ka raba,ni haka nake duk inda ba'a sona to nafi makalewa a Nan inta kuntatawa Wanda baya son ganina kullum insa Saiya kalli Koda inuwata ce,Kuma ma yasan baya Sona jiya fa Aunty kaza da lemummuka ya siyomin,ya dinga bani a baki harna koshi,yasa mukayi sallah Kuma yace gado Daya zamu kwana,shine fa kawai Aunty ya rabamin cinyata ya.....ke!!!! Wata iriyar tsawar da sajida ta daka mata,itako Dije ko a jikinta tana shirin ci gaba taga Sajidar ta nufi sashenta da gudu kamar wata mahaukaciya. Dariya Dije tayi tare da fadin,har ni Zaki nunawa bariki to ni Dan uwarki Allah ne ya nufi bazan Zama karuwar kowa ba saita mijina Dan tun ranar da aka haifeni na Fara shafawa kaina jambaki da hoda,ban taba magana da Mata ba sai bayan an yaye ni Amma da Ina Shan nono kuwa maza kadai nake yadda dasu da Kuma saurarar maganarsu Dan in haddace hanyar mallakar su. Mikewa tayi tana Dan dingisawar ta nufi part din mama mariya,tana ganinta tasan Mai afkuwa ta afku,Bata wani tsaya saurararta ba ta tashi ta shiga dakinta zuwa can ta Kira Dijen ta Isa dakin,Direct toilet ta jata inda ta tarar ta hada wani ruwa cikin baho tace ma Dijen ta shiga,Nan ta fada Mata muhimmancin ruwan,ba laifi sosai taji dadin ruwan ga wani kamshi dayakeyi,bayan ta fito maman ke Mata sannu,abin mamaki Wai yau Dije ce da Jin kunya saiga Dije tana sinne Kai haka dai taki komawa bangarenta tayi zamanta Nan bayan magrib saiga Zainab itama ta shigo Nan aka zauna akaita kwasar Hira. Tana Isa falon saita ja burki ta tsaya,ta jima tsaye kafin ta saki murmushi,ta jinjina Kai ya zuwa yanzu ta fuskanci Dije dama baki ne bawani wayo gareta ba to Bari tayi amfani da rashin wayon nata ta cimma muradinta,cikinta ta shafa tare da ambatar Kaine makami na,sannan ta tura kofar dakin,tsaye yake gaban mirrow Yana balle botir din rigarshi,ta bayanshi ta karasa ta rungume shi tana fadin nayi missing Dinka dear na. Dan murmushi yayi tare da fadin Nima hakan. Ban yadda ba! Juyowa yayi ya fuskanceta tare da fadin saboda me? Saboda kanada amarya. Shiru yayi Mata Bai Bata amsa ba hakan ya Kara tabbatar Mara da gaskiya maganar yarinyar. Ji yayi tace Amma kasan sai kayi Mata sati Daya ko? A matsayinta na amarya Kuma budurwa! Eh nasani Dan haka nafara daga jiya! Yana fadar hakan ya juya ya fice Dan dama masallaci zai fita ko Alwalar Baiyi ba yace inyaje masallaci yayi. Me hakan ke nufi kenan? Ya daina Sona ne? Kaiii ba hakan bane! To koma dai Yaya ne zan bashi satin ranar kwana na takwas din kuwa! Hmmmm Nan ta saki murmushin da ita kadai tasan manufar yinsa. Shikuwa ana idar da sallar isha'i ya shigo ya dauki key din mota ya fita,gasassun kaji yasiyo tare da fresh milk Mai sanyi sai kayan fruit duk da suna da su Amma sai yakejin kamar wannan na musamman ne wani botique ya nufa yasayi kananan Kaya tare da biyawa shopping mall Nan mama wasu kananan abubuwan da zai bukata ya siya sannan ya nufo gidan Yana tunanin dramer su ta jiya da Dije,Daya tuno wani Abu Kuma sai Inga yayi dariya shi kadai... *Dan farin cikinku kawai nayi muku typing yau Dan haka kuyi managed* *Alkalamin khady* โœ [3/18, 8:10 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ ( Place of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 5โƒฃ2โƒฃ *Hakika babu babban jin Dadi sama da Allah ya hadaka da masoya,inama ace wannan soyayyar da kuke nunamin ta kasance har abada ko bayan nadaina rubuta novels da zanji Dadi da alfaharin samun masoya kamarku,Allah yabar zumunci tare da soyayya madawamiya Ameen!* *Wannan shafin sadaukarwa ne ga dukkan masoya littafin tame gari* ________________________ Koda ya shigo gidan direct bangaren Sajida ya nufa,ga mamakinsa zaune ya isketa saman stool na madubi,kusan zai iya cewa ma tunda ya fita a haka take,ko kadan bataji shigowar sa ba har Saida yazo gabanta sannan ta ankara da shigowarsa, murmushin karfin Hali ta kago Dan ita a dole batason yaga gazawarta tako wanne fanni.tsugunnawa yayi gabanta tare da dafa cinyoyinta hakan yasa taji wani irin Abu da Kuma hatsabibin kishinsa ya taso Mata Amma sai ta danne. Meya faru ne my princess? Damuwa ko? Dariyar karfin Hali tayi tare da girgiza Masa Kai alamar bakomai. To duk tunanin na meye? har ba'asan da shigowata ba? Ba tunanin da nakeyi illah kawai.....sai Kuma tayi shuru. Kawai me? Uhmm!! Fadamin inaji. Kawai ba komai sai tunanin rabuwa da zanyi dakai na tsawon kwanaki har bakwai bama kwana tare! Ah ah! Kinyi mantuwa kwana shida dai, amma Ina son ki sani Nima fa bada son Raina hakan zaya kasance ba,domin kin riga da kin San kece sarauniyar mata,soyayyarki ta riga ta ginu a zuciyata kin ginata da tubali Mai karkon da babu wata Diya macen data Isa ta shigo cikin zuciyata,abinda Kika ga nayi nayi shine saboda soyayya Dan in nunawa mahaifina ya iya haihuwa zan yi Masa biyayya kamar yadda Dan uwana yayi,sannan kin San dole Koda bazanyi komai da ita ba ya kasance na shiga dakinta na sauke hakkin ko da kwana ne,Dan haka Ina son ki Kara sawa a zuciyarki,ni Habeeb naki ne kedai duk wadda ma ta shigo sai dai ta Zama 'yar karere. Duk da taji dadin maganganun nashi,Amma hakan Bai hanata daukarshi ta kaishi mazaunin maza munafukai ba,tanada wannan matsayin a gurinsa Amma ya iya kwana da wata,Amma saboda Munafunci irin na da namiji a yadda ta fuskanta nunawa ma yakeyi beyi komai ba,bayan yarinyar ta sanar da ita komai ya faru ,abinda yasa ta bi dashi yadda yake so kawai Dan ta isar da kudirinta dake zuciyarta,inba haka ba da tuni tayi dibar Karen mahaukaciya dashi ta watsar. Ya jima zaune gurinta tare da Mika Mata sakonnin soyayya, daga baya ya mike tare da Bata ledar Daya shigo da ita,karba tayi jiki a sanyaye Dan ita harga Allah ganin abin takeyi kamar a mafarki Wai ita akawa kishiya, bata Kara tsinkewa dashi ba Saida taji ya jawota jikinshi be ya manna Mata kiss a goshi kafin ya juya da niyyar tafiya,duk yadda taso ta daure Saida zuciyarta ta karye taji hawaye ya zubo,Sam Bai lura ba Dan ya riga Kuma hankalin yayi inda Dije. Yana fita ta kifa Kai tasanya kuka har Saida tayi me isarta bacci ya kwasheta ko wankan data Saba yi batayi ba. ******"****** Fitowarta daga wanka ta tsaya Rama sallar isha'i da Bata samu tayi ba abangaren mama mariya,Hira tayi musu Dadi,ta idar da sallar ta dawo gaban mirrow ta zauna Dan shafa Mai, tunanin abinda Naseer yayi dazu a gabansu ita da mama mariya bako kunya takeyi,haka kawai sai taji moment din ya burge ta,yanayin tsari da soyayyar da sukeyi kamar ba auren Hadi ba, tunawa da tayi da nata mijin da aka hadata dashi tayi,gashi gabjeje ga shegiyar mugunta, kai gaskiya ni akafi kwara,duk da Habeeb yafi Naseer kyau nesa ba kusa ba gashi handsome man,Amma muguntarsa ta jiya kawai Daya nunamin ita tasa nasan wannan halin nasa a bangaren dangin uwa ya daukoshi,Dan mu kaf family dinmu bamai wannan halin( Niko nace um- um fa Dije a dai dinga Sara ana duba bakin gatari Kuma dama ai jaba batajin warin jikinta๐Ÿ˜€).Tana gama shafa Mai ta mike ta dauki kayan baccinta tasa itafa wallahi har yanzu a tattale take jinta,duk mutum yabi ya mayar Dani kamar wadda akayiwa shayi. Tana tsaka da masifarta ita kadai taji an turo kofar an shigo,ganin shine yasata dafe kirji tare da ambatar Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,me Kuma ya kawoka daki na? Ta fada kamar fizgo maganar daga bakinta. Karasowa yayi tare da ajjiye ledojin Daya shigo dasu,kamar bazai Bata amsa ba sai Kuma taji yace,mutum da gidansa dama ana Masa iyakar shiga duk inda yaso Kuma a lokacin Daya so ne? Ni bance ba Amma... Amma me? Ai naga kanada Mata a dai dai wannan lokacin Bai Dace kazo inda nake ba. Meyasa jiya baki Fadi hakan ba. Dan nasan Bata Nan ne shiyasa nabarka ka kwana. To yanzun ma ki kaddara Bata Nan din shiyasa nazo in Kara kwana. Na shiga uku! Wayyo ni uwata wayyo ubana,shikenan a shirya yin jana'izata gobe Dan wallahi nasan ajali ke kirana kwanana ne suka Kare. Ai da sauki ma tunda har kina tunanin Zaki Kara kaiwa gobe. Ai ba hakan nake nufi ba,nasan tun Daren yau zan mutu,inyi kwanan keso,ni babban tashin hankalina ance duk akan abinda ka mutu akai a haka za'a tasheka. Um lallai to ai saiki godewa Allah Daya kasance Zaki tashi kina me raya sunna ne. Yana Gama fadar hakan ya bude ledar Daya shigo da ita ya dauko towel ya farke ledar yasabashi a kafadarsa tare da shigewa toilet yabarta Nan zaune tana sharar kwalla. Koda ya fito zaune yasameta ta hada kai da gwiwa tanata kuka,hakan yabashi dariya Amma ya Gama abinda yakeyi yasa kayan baccinshi,ko kadan bataji lokacin Daya fita ba illah dai taji budewar kofa da hanzari ta mike danta rufe kofarta Amma sai ganinshi tayi dauke da plate da cup duk ashe dawowa ma yayi,mayar da kanta tayi yadda yake,taci gaba da kukanta. Kamshin kazar ne ya bugi hancinta,ta gefen ido ta Dan karkace tana satar kallon jar gashin kazar tare da Dan hadiyar miyau.sam Bata ji motsin hayowarsa saman gadon ba sai jinsa tayi ya jawota jikinsa,tana shirin kebe baki sai jin bakinsa tayi cikin nata,ya Dan jima Yana kissing dinta Saida ya tabbatar ya kashe Mata jiki,sannan yace, Tashi muyo alwala muyi sallah ko! To ai ni nayi sallata. Ai wannan ta musamman ce zamuyi,Kuma bake kikace jiya kowanne ango da amarya sai sunyi sallah ba Kuma ango ya lallaba amarya taci kaza ba yasata tayi ba,shiyasa nadauki nasiharki ai yau. Batace komai ba kuwa ta mike ta nufi toilet Tayo alwala ta fito,Shima shiga yayi yayo tasa,yanayi Yana tunanin Wai meke damunsa ne haka? Shine yake yiwa Dije haka to kodai aljanun nata ne suka sashi yakeyin duk wadan Nan abubuwan to koma dai menene shi gaba takaishi Dan ya dandani wata irin Zuma Mai zakin gaske a bagassss. Bayan sunyi sallah Nan ya dafa kanta yayi Mata duk addu'oin da suka kamata sannan bayan ya Gama ya jawo filet din da kazar ke ciki,jawota yayi jikinshi Nan ya shiga Bata a hankali,su Dije tun ana Kara har ta zage ta Debi kazarta son ranta Don dama ta fadawa su rufaida itafa duk lokacin da tayi aure saita sheke kazar amarcinta Dan haka Saida tajita ta koshi,sannan ta kauda Kai,madarar ya Bata Nan ma fa Sha tayi Saida ta koshi sannan Shima yaci yasha. Bayan sun wanke hannunsu tare da yin brush,ya juyo ya kalleta tare da fadin, Sai Kuma in lallaba ki kiyi bacci ko? Gyada Kai tayi kamar karamar yarinya alamar eh! Abin dariya ta bashi Nan ya daukota tare da dorata kan gado Shima ya kwanta a bayanta yaja musu bargo ya rufesu,shafata ya rinka to yana fadin yi bacci amarya. Ita abinma mamaki yake Bata Wai yau itace kwance da Yaya Habeeb gado Daya matsayin miji da Mata,tana tsaka da wannan tunanin taji hannunshi cikin rigarta. Kokarin rike hannun tayi,taji ya Rada Mata a kunne pls bana iya bacci har sainayi hakan,in Kika Bari nayi to saima na rigaki bacci. Tanaji yawo da hannunsa cikin jikinta yayin da cikin kankanin lokaci ya kashe Mata jiki,ji tayi labari fa ya Fara canza salo..... *Yau Kuma kome Dije zatace an cire Mata oho?* *Alkalamin khady* โœ[7/8, 9:10 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (Place of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 5โƒฃ3โƒฃ *A gaskiya Raina yafara baci zuciyata ta Fara tafarfasa sakamakon maganganun wasu marasa kan gadon,ni Naga dama na sadaukar da lokacina nake yi muku TAME GARI Dan nishadantar daku,Amma wasu dayake hankali da iya magana yayi musu yawa sai su nemi su zageka a banza kawai Dan sunyi maka magana baka samu damar dubawa ba,Dame zamuji? Hidimar gida Kota yaranmu ko ta megida gurin aiki,Amma duk da haka muke kokarin ganin mun faranta muku,dalilin hakan yasa marubuta da yawa suka mayar da littafin su na kudi,Dan a ganinsu gara ayi musu zagi me dalili amma mu da mukaga bazamu iya siyarwar ba addu'ar ku muke bukata mu mune banzaye kenan da bamu San ciwon kanmu ba kenan ko? Shikenan Inaga daga TAME GARI bazan Kara rubuta book ba.* Duk magiyar datake yimasa baiji ba har Saida ya samu nutsuwa sannan ya saurarara Mata,inda ya mirgina gefe Yana sauke numfashi,Yana Jin kukanta Yana son yin rarrashi Yana tunanin yau Kuma abinda za'a ce ya aikata,jin tana dada sautin kukan ne yasashi matsawa jikinta tare da jawota ya rungume ta tsam a jikinsa,duk yadda taso ta kwace kasawa tayi hakan yasa cikin muryar kuka tafara fadin, Ni ka rabu dani ka sakeni,wallahi Yaya ban taba sanin dagaske baka Sona Kuma ka tsaneni ba sai tsakanin jiya da yau, kowacce amarya in an kaita gidan mijinta zaka ganta da safe ta tashi tana fara'a da walwala,amma ni sai dai a ganni da kumburarrun idanu da talalliyar kafa,ban taba sanin Kai sarkin mugaye bane sai yau,a yadda nakeji yanzu nasan ka kara rabani da dukkan albarkatun dake dauke da sinadaran jikina,Ina da tabbacin yanzu banida wani vitamin a tare Dani,wallahi indai haka ake auren kiyayya to masu Zama har su haifi yara da mutum Kuma duk a baya sonsu mahaukata ne,ni yanzu dubi yadda kake Neman mayar Dani misakar karfi da yaji wato sai dai a dinga turani a wheel chair,me yasa bazaka gwada karfinka a kan waccan bultuwar matar taka ba sai a kaina ni kadai,ko Dan kasan ita sai dai kuyi Kare jini biri jini,to wallahi Nima sai ka San kayimun hakan Dan sai na.....da sauri ya rufe Mata bakin,Dan baya fatan ramuwar Dije a rayuwarsa,rarrashinta ya shiga Yi tare da sanar da ita wannan fa shine auren,kuma kowacce da haka ta saba. Bawani wayo da zakamin ,Dan ni da nawa wayon aka haifeni,suna Shan wannan wahalar suke haihuwa,wallahi ban yarda ba. To Banda abinki ai daga baya Dadi gareshi na farko ne Dana biyu keda zafi,Amma daga Nan duk sai Dadi. Yaseen in jikina duk kunnene ban yarda ba,meye abin dadin a wannan abin,nidai yauma na Kuma rokonka Dan Allah katashi ka dinke ni tun kafin gurin yayi tsami. "To Bari nagani ko nayi Miki filla-filla din" Ba musu kuwa ta bude Masa Dan ita a dole fa anyi Mata daga-daga. Shi Kam a ranshi har yanzu Yana jinjina rashin wayon yarinyar a wannan fannin Dan shidai yasanta da shegen kaudi da jaraba sai dai Daya tuna ance duk fa wayon amarya sai ansha manta,Dan haka yaci gaba da duba Mata gurin Dan yaga Koda gaske yaji Mata ciwon kamar yadda ta fada,Sam ba wani alamar ciwo,sai dai yasan dole taji zafi,Amma Dan ya bita yadda take so sai yace, Gaskiya Kam kin ji jiki,Bari ayi Miki taimakon gaggawa,sake gasata yayi inda Nan ma Saida aka Sha daga ya dinga lallabata kafin gari ya waye yabata magani. ********************* Tun asuba Daya fita masallaci Bai dawo ba Saida gari yai haske,Yana shigowa bangaren sajida ya nufa domin duba lafiyar yata kwana,tunda ya shiga suka hada ido ya tabbatar batayi baccin kirki ba Dan haka yakarasa gareta Yana tambayarta meya hanata bacci jiya? Duk yadda taso ta boye damuwarta kasawa tayi kawai saita sa Masa kuka,jawota yayi jikinshi cikin rudewa yake tambayarta matsalarta,ji yayi tace, Ba wani Abu bane illah marata dake min ciwo ga Kuma Aman Dana kwana inayi,cike da rudewa ya shiga fadin,meyasa baki sanar Dani ba kinsan bake kadai bace Kika Bari Kika kwana da ciwo kin San matsalar da hakan zai haifar kuwa? Insha Allah bawata matsala nabaka damar cin amarcinka ne Dan Kar in dameku,ta fada tana Mai kallon fuskarsa dan taga yadda zaiyi. Murmushi taga yayi tare da shafa sajen shi ko me ya tuna oho! Wani bakin cikin ne ya ziyarci birnin zuciyarta,inda tama rasa abinyi,zuwa can tunanin maganarsu da mahaifiyarta ya fado mata,am hubby dama cewa nayi me zai Hana mu hada girki,kaga yanzu Kuna tsaka da cin amarcinku Bai kamata amarya ta dinga girki ba kawai ni a ganina duk wadda tayi girki a dinga zuwa ana ci a part dinta ko ya kace? Kada Kai yayi tabbas tayi tunani Mai kyau,Dan haka ya amsa da shikenan wannan ma wani abune dazai Kara taimaka muku da zaman lafiya,Amma kin San da farko kin tsoratani ranar da naji kinata kunduma ashar kamar jinsin maguzawa. Hmmmm! Ai tsorata nayi ne kasan yarinyar taka akwai ruwan kwankwamai,shiyasa Wai nayi riga kafi karta yo cikinmu kasan iskoki Inka Nuna musu kaima kwallo ne sai suyi laushi. "Dariya yayi tare da Jan hancinta yace Mata me wayo" Wani bakin cikin ne ya tokare mata makoshi,wato ma Mata me wayo bama yarinya me wayo ba,Amma haka ta daure Nan tafara Mika Masa sakon barka da safiya bashi ta barshi ya fita ba sai wajen karfe Daya, kasancewar yace yadau hutun zuwa gurin aiki,Koda ya leka part din Dije Bai ganta ba yasan tana bangaren mama mariya Dan haka ya wuce masallaci. ****** Sannu sannu har Habeeb yagama satinsa gurin Dije Wanda kullum sai ya kashe arna saba'in Wanda tun tanajin zafi harta dawo tafara Jin dadin dayake fada Mata ana ji,jinta ta dinga yi kamar wata uwar Mata ta dinga jinta tamkar ba ita ba,Abu Daya ke Bata mamaki dashi,da dare zai saki jiki da ita ya zame Mata kamar wani rakumi da akala,Amma da zarar da gari ya waye sai taga Yana wani ciccin magani,sai dai Kuma taga Yana murmushi shi kadai,yau zaibar dakinta dan haka jinta takeyi kamar an Mata albishir da gidan aljanna,duk wani aikinta tayi shi ta Gama da wuri ta nufi part din Zainab suka shiga hirar su da suka Saba. * **"******""******"*** Mamy ce zaune da ita da yusrah da cikinta ya zuwa yanzu ya fito,zaune suke suna Shan iska yayin da kowa da abinda ke ranshi,ita yusra harga Allah tafara gajiya da zaman da takeyi dan ta lura Naseer baida niyyar zuwa su tattauna matsalar su ta lura waccan 'yar kauyen ta Gama dashi yanzu ko ta Tata bayayi,illa dai tana ganin sakonshi kullum na ya baby'n shi tare da kudi dayake Mata transfer a account dinta lokaci zuwa lokaci. Itama mamy a nata bangaren tunanin yadda Daddy ya sauya Mata take,Sam yanzu Bai wani tsayawa ya saurareta inma taje mishi da masifa Saiya tattara yabar Mata dakin gaba Daya baya ce Mata ko kala,gashi taje gurin malam yace yayi Mata aiki Amma bataga want canji ba Dan duka cikinsu har yaran nata ba Wanda taga yanada niyyar rabuwa da matar kakabe din da aka kakaba musu. Suna tsaka da wannan tunanin ta hango fitowar Daddy da mama mariya suna tafe suna dariya yayin da hular Daddy ke sanye Akan mama mariya,mamy batasan sanda ta mike tayiwa gabansu tsinke ba lokacin har sun Isa gaban motarshi tana mishi a dawo lafiya,shi Kuma Yana shirin Kiran driver,muryar mamy sukaji tana fadin,me zan gani Alhaji wannan wace irin badala ce in an girma ai asan an girma,Amma Banda haka ta Yaya gotai -gotai daki zaka wani biyewa wannan kilakin ga 'ya'ya ga surukai kawai ki wani fito anata maka wata karairaiya.yana shirin yin magana yaji mama mariya tace, Banda abinki Karima kokin Manta kowacce mace karuwar mijinta ce,sannan kinsan ita soyayya Bata tsufa yaddar da kikayi Kika Bari taki ta tsufa ita tasa aka kawo Miki tsohuwar Zuma Kuma gata tashin kauye,kin San Kuma fa rainon birini da kauye akwai banbanci,Kuma maganar yara da kikeyi ai gara muyi su gani suga yadda ake kula da miji Dan Kar suyi sakaci sai sun tsufa a dakko musu tsohuwar soyayya. Mamy na shirin yin magana Daddy ya dakatar da ita ta hanyar fadin,kinga Karima bana son kananun surutu ni kunga tafiyata sai na dawo ya karasa maganar Yana me shigewa bayan motar da driver ya bude Masa Dan ya karaso. Yana tafiya itama mama mariya ta juya tana karkadawa mamy kugu ta shige ta barta da baki sake. ******* Yau su uwar gida sajida an karbi girki anata kaiwa da komowa,sai da ta kammala tayi wankan tare da cancada kwalliya,Koda ya dawo daga masallaci ya biya bangaren Dije danya sanar da ita Yana ta fito suci abinci,Bata musa ba ta taso ta fito Dan dama ta rasa me zata dafa har tana tunanin taje gurin mama mariya taci,sanye take cikin doguwar riga kirar buba Mara nauyi,ya rigata shiga har ya zauna sannan ta rufa Masa baya,a saman dinning table iske su Dan haka itama tayiwa gurin tsinke.Da fara'a sajida ta shiga tsokanarta ya amarci,saita tsinci kanta da kunyar amsa Mata kawai sai tayi murmushi,duka sajida ce tayi serving dinsu jellop din macaroni ce da taji kayan vegetables da busasshen kifi, kowa yaci dai-dai cikinsa inda bayan sun kammala Dije na shirin barin falon ya Kira sunanta tare da umartar ta dawo ta zauna,dawowar tayi inda ya bita da kallo Yana ganin tayi Masa wani irin kyau tare da wani kwarjini,sai yaganta kamar ba khadijan Daya sani ba wannan ta Zama nutsattsiya Kuma me kunya. Bayan duk sun zauna ya shiga Yi musu nasiha tare da rokon su zauna lafiya,kamar yadda kowanne magidancin kwarai ke fatan iyalinsa su kasance,Nan yace su rabawa kansu kwana,wani dum sajida taji Amma saita ce Inaga kwana biyu yayi ko? Ok ba matsala hakan yayi Miki khadeeja? "Ya tambayeta Yana kallonta" Eh yayi! Ta fada tana mikewa tayi musu Saida safe ta fice. Inda yabi bayanta da kallo Yana Jin wani Abu na fizgarshi,harta fice baibar kallon kofar ba wadda har Saida sajida ta gaji ta zungureshi ya juyo suka hada ido sai Kuma yaji kunya...... *Alkalamin khady* โœ ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA khadeeja Usman 5โƒฃ4โƒฃ Kamar yadda suka tsara din kwana biyu yayi a dakin sajida,wadda tayi shiri sosai tare da Kara Masa wasu salon Dan tafiyar da nutsuwarsa,tabbas ba laifi gaskiya yaji dadin hakan,sai dai fa ya kasa manata yadda Dije take duk da bata bashi wata gudummawar wajen aiwatar da abin,amma yayi mamakin Jin abinda yaji daga gareta. Sai dai ta tsawon kwana biyun Nan Sam sajida Bata bashi wata dama ko kofar zuwa gurin Dijen ba. Duk da ya rasa dalilin dayasa kwana biyun yake kwana da tunaninta,Dan yau ma yaso ya leka yaga yadda take amma Sam yakasa samun wannan sukunin,Dan ya lura Sajida wata sabuwar jaraba ta koyo kwana biyun Nan,da kyar badan yayi niyya ba ya shirya ya koma bakin aiki. ********* Wajen 5pm o'clock ya shigo gidan,tunda Mai gadi bude Masa kofa ya hango shigerwata part din Naseer,bayan ya Gama parking ya Dan jima zaune ko zaiga fitowarta,yakai kusan 15 minutes Amma yaji shuru,Jin hakan yasa ya bude murfin motar ya fito,yaso Wucewa Amma sai yaji ya kasa dnn haka ya nufi sashen.Zai iya cewa duk tsawon zamansu da sukayi yauce rana ta farko daya taba shiga bangaren kanin nashi. Murda handle kofar yayi yasa Kai tare da 'yar siririyar murya yayi sallama wadda ba lallai kaji meya ce ba,ita Kam kamar Mai kunnen maciji Sarai taji Kuma azatonta Naseer ne ya shigo Dan haka ta dago da niyyar tsokanar shi,tunda yanzu suna 'yar hakan. Ganinshi jingine jikin kofar ya harde hannu a kirjinshi yasa ta kafeshi da idanunta,Wanda shi Kuma kallon da yaga tana yi mishi yasashi Jin wani iri,ta wani fannin kasala ta wani bangaren Kuma tsoro,danshi fa Banda Yana danne zuciyarsa ko da tazo mishi da wani tunanin akan Dije da tuni ya yadda ita din aljana ce ko Kuma danginsu,Dan har yanzu Bai Manta gwagwarmayar da sukasha da aljanun yarinyar ba kamar tasan tunanin dayake saita janye idanunta daga kanshi,Dan yanzu wata irin kunyarshi take ji,Dan haka ta Kama wasa da yatsanta,hannunta ya zubawa ido Wanda yasha lalle ja Amma yazama maroon hakan ya Kara haskaka shi kan farar fatarta,dukansu kowa da abinda sakawa Kuma yakasa motsawa daga inda yake,muryar Zainab ce ta katsesu inda take fadin, "Wai ni ko matar yayanmu Anya bamu Samu karuwa ba kuwa? Irin wannan kwadayi haka Ina zaman zamana kin wani zo kin tadani to gashi Nan ba farfesun hanji ba kici na tumbi ma Amma kisani gaskiya iya kwana biyun Nan na gaji gara ma ki dinga yi da kanki ki barni Nima inji da kula da nawa sabgogin mijin tunda....maganarta ta makale ganin Habeeb da tayi tsaye bakin kofa. Murmushi ya sakar Mata itama ta shiga gaisheshi tare da ajiye plet din hanjin a gaban Dije wadda ta sunkuyar da Kai takasa dagowa,ga mamakinsu gani sukayi ya juya ya fice kawai. Duka Dije ta kaiwa Zainab cikin sa'a ta kauce tare da fadin,lallai yarinya kin iya bada Kaya irin wannan bin bini haka! Kinga ni tashi kibi mijinki kada kisa ya Kuma dawomin a matsayinsa na surikina,kada ku hanani daukar wankan la'asar na tarbar mijina gashi Nan kina gani naki mijin harya gudo. Wani dukan Dije ta Kara Kai Mata tare da fadin,wallahi zee zan Miki rashin mutunci,baki San kin bani haushi ba kin Sa naji kunya gaban sa,sai ya daukeni mayya ma ai. To sai me! Ai shi yasaki maitar naga. To abokin sharrinki ya mutu,duka-duka yaushe ma nasan nayi auren,har kike min maganar wani ciki,bakiji ance uwar gida ce keda ciki ba ni Ina naga wani kwarin daukarshi. Kinga ni ba surutu ba tashi maza kije ki tarbi mijinki,da alama Yana bukatarki tunda har gashi ya biyoki,haka Zainab ta Kama Dije da farantin Hanjinta har waje,wadda ita Dijenma abin Dariya ya dinga bata.Wasa-wasa har Saida Zainab ta kawota bakin kofarta suna tafiya tana Kara fada Mata abubuwan da zata yi Dan ta Zama the best a zuciyar mijinta. Koda ta shiga Bata iskeshi ba,Zama tayi taci Hanjinta ta koshi sannan ta mike ta nufi kitchen a gaggauce tayi musu jellop din cous-cous Dan lokaci ya kure kunun Aya ta hada ta sa firji,Koda ta Gama anyi magrib Bata tsaya wanka ba Saida ta yi sallar magriba sannan tayi Koda ta fito ana kiran isha'i Dan haka ta shafa Mai tare da saka rigar data ware Dan yin sallah tayi sallarta,bayan ta idar ne ta shirya cikin wasu riga da siket English wear marasa nauyi light makeup tayi kasancewar ta me son yin kwalliya,ta fuskanci baya son shigowa gida sai yayi sallar isha'i Dan haka Zama tayi a Palo tare da kunna TV ta kamo tashar Arewa24 tana kallon shirin dadin kowa,Bata jima da Zama ba taji alamar shigowarshi,Saida ya karaso Falon sannan cikin cool voice tace mishi sannu da zuwa,amsawa yayi a hankali sai dai ya kafeta da idonsa Wanda yasa ta Kara sunkuyar da kanta kasa. Shi kuwa ganinta yayi tayi wani masifar kyau kodai mutanen sunzo ne๐Ÿคฃ. Sam Bata San barinsa wajen ba illa jin Kara rufo kofar shi dataji. Ya Dan jima sannan ya fito sanye da jallabiya da alama wanka yayi,Shima zaman yayi ya maida hankalinshi ga kallon,yaji muryarta tana fadin, Nan za'a kawo ma abincin ko dinning zaka ci? Shuru yayi da kamar bazai amsa harta fidda ran amsawarshi daga baya taji yace muje inci acan din Kar in Bata Miki guri ko. Batayi magana ba ta mike ta nufi dinning area din kusan lokaci Daya suka Isa . Bayan sun Gama cin abin cin sun dawo falo Basu jima da Zama ba bacci ya dauketa batare da saninta ba Wanda sai wajen asuba data farka ta ganta kwance saman jikinshi a kan gado sai taji kunya,a ranta ta furtaa Allah yasa Bai ganni Ina shararar da miyan bacci ba. *********** Sannu sannu rayuwa na tafiya haka ta kasance a gidan Habeeb,inda yanzu kusan watan Dije uku da Fara kwanan Habeeb dakinta,sai dai a wannan zaman Dije ta Fara fahimtar halayyar Sajida,domin ta fahimceta a gaban Habeeb wani salo take nunawa na musamman tare da kulawa akan Dijen,sabanin inya fita da farko tana tsayawa taita Mata tambaya ya tsakaninsu da Habeeb,da taga Dijen ta ramfo ta takan Gaya Mata abubuwan da zasu hanata bacci,sai kawai ta canza lale dataga ya fita Nan fa zata hau zazzaga wa Dije kudirinta tare da fada Mata tun wuri ta tattara ta bar gidan inba haka ba sai tayi data sani. Sam Dije Bata kulata ba Kuma ta fadawa kowa ba ***** Yau ma fitarsa kenan Sajidar ta iskota har bangarenta,ta shiga zaginta tare da fadin inta Isa ta fito wallahi saita babbala ta,Kuma saita dauje Mata baki tasan Habeeb ko an fada Masa bazai yadda ba. Ita Kam Dije yanzu Bata Tata take ba ta kanta takeyi Dan wani irin kasala takeji kwana biyu,ita mamaki ma take Bata wato ita Kuma nata salon kenan.sam bata zaci haka daga gun Sajidar ba ganinta wayayyiya amma Kuma yanzu ta birkice gaba Daya. Yau Kam kin tafiya tayi ta dinga surfawa Dije zagi,wadanda har Saida sukasa Dijen zuge gilashin windo ta mayar Mata da martani.hakan ya kara harzukata tayitayi har ta gaji ta koma bangarenta. Da daddare bayan Habeeb ya dawo,Bata ko Bari yaci abinci ba kasancewar dakin Dije yake ta shigo falon ta zauna,Dan yanzu ace duk wadda keda girki a ci abinci bangarenta. Bayan sunci sun koshi yasa wadda ita dole tasa ta ci ga mamakin Dije gani tayi Sajida ta rike ciki tare da fadin wayyo Allah na shiga uku dear pls ku taimakeni kanwata wayyo zan mutu marata.......... Mamaki ne ya Kama su duka cikin tashin hankali duka suka nufota,rurrufe ido kawai takeyi tare da Kara ambatar wayyo marar ta cikin rudewa ya ciccibeta Dije ma hijabi ta dauko ta rufa musu baya suka nufi asibiti. Suna zuwa babu Bata lokaci ya shiga duba matsalar Bai gama gani ba yaga jini na biyowa ta kasanta dai dai Nan Kuma bincikensa ya Nuna Masa lallai Sajida maganin zubar da ciki Tasha. Innalillahi wa'innailahir raji'un! Kawai yake furtawa to meya hada sajida da maganin zubar da ciki,jikin bangon dakin ya jingina Wanda ya ya Fara wasu hawaye a fili ya furta why? Sajida? Meyasa Kika aikata hakan abinda ya zuwa yanzu nake lissafin zuwansa duniya. Jin shirun yayi yawa yasa Dije bude dakin ta shiga,yanayin data ga Sajidan ciki ya daga Mata hankali ganin jini na biyowa kafarta,tana juyawa taga Habeeb na kuka,cike da mamaki da Kuma firgici tace. Meya faru? Yaya meya sameta haka ? Ka duba halin datake ciki ka taimaka Mata Mana! Khadeeja sajida ta cuceni,Sam Bata kyautamin ba,cikina,jinina,mafarkina,shi ta zubar min. Subanallahi Dije ta furta. Garin Yaya? Ban sani ba Nima Ashe dama Bata Sona? Ah ah Yaya jeka taimaketa Dan Allah she's need your help pls! Ko kallonta beyi yasa Kai ya fice . Jin maganarsu takeyi kamar a mafarki,Dan haka ta Mika hannu ta shafo zaninta Jin da gaske jinin ne ke binta tare da wani azababben wani ciwon Mara Daya taso Mata lokaci Daya wata Kara ta saki ta sumeeeeee........ Wohoho! Ku biyoni Dan Jin ya hakan ta kasance dama hausawa sunce in zaka Gina Ramin mugunta ginashi dai dai Dan watakil Kai zaka fada๐Ÿ˜œ *Insha Allah Zaku dinga jina kullum zan Gama muku kafin axumi.* *Alkalamin khady* โœ [7/8, 9:10 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA khadeeja Usman 5โƒฃ4โƒฃ Kamar yadda suka tsara din kwana biyu yayi a dakin sajida,wadda tayi shiri sosai tare da Kara Masa wasu salon Dan tafiyar da nutsuwarsa,tabbas ba laifi gaskiya yaji dadin hakan,sai dai fa ya kasa manata yadda Dije take duk da bata bashi wata gudummawar wajen aiwatar da abin,amma yayi mamakin Jin abinda yaji daga gareta. Sai dai ta tsawon kwana biyun Nan Sam sajida Bata bashi wata dama ko kofar zuwa gurin Dijen ba. Duk da ya rasa dalilin dayasa kwana biyun yake kwana da tunaninta,Dan yau ma yaso ya leka yaga yadda take amma Sam yakasa samun wannan sukunin,Dan ya lura Sajida wata sabuwar jaraba ta koyo kwana biyun Nan,da kyar badan yayi niyya ba ya shirya ya koma bakin aiki. ********* Wajen 5pm o'clock ya shigo gidan,tunda Mai gadi bude Masa kofa ya hango shigerwata part din Naseer,bayan ya Gama parking ya Dan jima zaune ko zaiga fitowarta,yakai kusan 15 minutes Amma yaji shuru,Jin hakan yasa ya bude murfin motar ya fito,yaso Wucewa Amma sai yaji ya kasa dnn haka ya nufi sashen.Zai iya cewa duk tsawon zamansu da sukayi yauce rana ta farko daya taba shiga bangaren kanin nashi. Murda handle kofar yayi yasa Kai tare da 'yar siririyar murya yayi sallama wadda ba lallai kaji meya ce ba,ita Kam kamar Mai kunnen maciji Sarai taji Kuma azatonta Naseer ne ya shigo Dan haka ta dago da niyyar tsokanar shi,tunda yanzu suna 'yar hakan. Ganinshi jingine jikin kofar ya harde hannu a kirjinshi yasa ta kafeshi da idanunta,Wanda shi Kuma kallon da yaga tana yi mishi yasashi Jin wani iri,ta wani fannin kasala ta wani bangaren Kuma tsoro,danshi fa Banda Yana danne zuciyarsa ko da tazo mishi da wani tunanin akan Dije da tuni ya yadda ita din aljana ce ko Kuma danginsu,Dan har yanzu Bai Manta gwagwarmayar da sukasha da aljanun yarinyar ba kamar tasan tunanin dayake saita janye idanunta daga kanshi,Dan yanzu wata irin kunyarshi take ji,Dan haka ta Kama wasa da yatsanta,hannunta ya zubawa ido Wanda yasha lalle ja Amma yazama maroon hakan ya Kara haskaka shi kan farar fatarta,dukansu kowa da abinda sakawa Kuma yakasa motsawa daga inda yake,muryar Zainab ce ta katsesu inda take fadin, "Wai ni ko matar yayanmu Anya bamu Samu karuwa ba kuwa? Irin wannan kwadayi haka Ina zaman zamana kin wani zo kin tadani to gashi Nan ba farfesun hanji ba kici na tumbi ma Amma kisani gaskiya iya kwana biyun Nan na gaji gara ma ki dinga yi da kanki ki barni Nima inji da kula da nawa sabgogin mijin tunda....maganarta ta makale ganin Habeeb da tayi tsaye bakin kofa. Murmushi ya sakar Mata itama ta shiga gaisheshi tare da ajiye plet din hanjin a gaban Dije wadda ta sunkuyar da Kai takasa dagowa,ga mamakinsu gani sukayi ya juya ya fice kawai. Duka Dije ta kaiwa Zainab cikin sa'a ta kauce tare da fadin,lallai yarinya kin iya bada Kaya irin wannan bin bini haka! Kinga ni tashi kibi mijinki kada kisa ya Kuma dawomin a matsayinsa na surikina,kada ku hanani daukar wankan la'asar na tarbar mijina gashi Nan kina gani naki mijin harya gudo. Wani dukan Dije ta Kara Kai Mata tare da fadin,wallahi zee zan Miki rashin mutunci,baki San kin bani haushi ba kin Sa naji kunya gaban sa,sai ya daukeni mayya ma ai. To sai me! Ai shi yasaki maitar naga. To abokin sharrinki ya mutu,duka-duka yaushe ma nasan nayi auren,har kike min maganar wani ciki,bakiji ance uwar gida ce keda ciki ba ni Ina naga wani kwarin daukarshi. Kinga ni ba surutu ba tashi maza kije ki tarbi mijinki,da alama Yana bukatarki tunda har gashi ya biyoki,haka Zainab ta Kama Dije da farantin Hanjinta har waje,wadda ita Dijenma abin Dariya ya dinga bata.Wasa-wasa har Saida Zainab ta kawota bakin kofarta suna tafiya tana Kara fada Mata abubuwan da zata yi Dan ta Zama the best a zuciyar mijinta. Koda ta shiga Bata iskeshi ba,Zama tayi taci Hanjinta ta koshi sannan ta mike ta nufi kitchen a gaggauce tayi musu jellop din cous-cous Dan lokaci ya kure kunun Aya ta hada ta sa firji,Koda ta Gama anyi magrib Bata tsaya wanka ba Saida ta yi sallar magriba sannan tayi Koda ta fito ana kiran isha'i Dan haka ta shafa Mai tare da saka rigar data ware Dan yin sallah tayi sallarta,bayan ta idar ne ta shirya cikin wasu riga da siket English wear marasa nauyi light makeup tayi kasancewar ta me son yin kwalliya,ta fuskanci baya son shigowa gida sai yayi sallar isha'i Dan haka Zama tayi a Palo tare da kunna TV ta kamo tashar Arewa24 tana kallon shirin dadin kowa,Bata jima da Zama ba taji alamar shigowarshi,Saida ya karaso Falon sannan cikin cool voice tace mishi sannu da zuwa,amsawa yayi a hankali sai dai ya kafeta da idonsa Wanda yasa ta Kara sunkuyar da kanta kasa. Shi kuwa ganinta yayi tayi wani masifar kyau kodai mutanen sunzo ne๐Ÿคฃ. Sam Bata San barinsa wajen ba illa jin Kara rufo kofar shi dataji. Ya Dan jima sannan ya fito sanye da jallabiya da alama wanka yayi,Shima zaman yayi ya maida hankalinshi ga kallon,yaji muryarta tana fadin, Nan za'a kawo ma abincin ko dinning zaka ci? Shuru yayi da kamar bazai amsa harta fidda ran amsawarshi daga baya taji yace muje inci acan din Kar in Bata Miki guri ko. Batayi magana ba ta mike ta nufi dinning area din kusan lokaci Daya suka Isa . Bayan sun Gama cin abin cin sun dawo falo Basu jima da Zama ba bacci ya dauketa batare da saninta ba Wanda sai wajen asuba data farka ta ganta kwance saman jikinshi a kan gado sai taji kunya,a ranta ta furtaa Allah yasa Bai ganni Ina shararar da miyan bacci ba. *********** Sannu sannu rayuwa na tafiya haka ta kasance a gidan Habeeb,inda yanzu kusan watan Dije uku da Fara kwanan Habeeb dakinta,sai dai a wannan zaman Dije ta Fara fahimtar halayyar Sajida,domin ta fahimceta a gaban Habeeb wani salo take nunawa na musamman tare da kulawa akan Dijen,sabanin inya fita da farko tana tsayawa taita Mata tambaya ya tsakaninsu da Habeeb,da taga Dijen ta ramfo ta takan Gaya Mata abubuwan da zasu hanata bacci,sai kawai ta canza lale dataga ya fita Nan fa zata hau zazzaga wa Dije kudirinta tare da fada Mata tun wuri ta tattara ta bar gidan inba haka ba sai tayi data sani. Sam Dije Bata kulata ba Kuma ta fadawa kowa ba ***** Yau ma fitarsa kenan Sajidar ta iskota har bangarenta,ta shiga zaginta tare da fadin inta Isa ta fito wallahi saita babbala ta,Kuma saita dauje Mata baki tasan Habeeb ko an fada Masa bazai yadda ba. Ita Kam Dije yanzu Bata Tata take ba ta kanta takeyi Dan wani irin kasala takeji kwana biyu,ita mamaki ma take Bata wato ita Kuma nata salon kenan.sam bata zaci haka daga gun Sajidar ba ganinta wayayyiya amma Kuma yanzu ta birkice gaba Daya. Yau Kam kin tafiya tayi ta dinga surfawa Dije zagi,wadanda har Saida sukasa Dijen zuge gilashin windo ta mayar Mata da martani.hakan ya kara harzukata tayitayi har ta gaji ta koma bangarenta. Da daddare bayan Habeeb ya dawo,Bata ko Bari yaci abinci ba kasancewar dakin Dije yake ta shigo falon ta zauna,Dan yanzu ace duk wadda keda girki a ci abinci bangarenta. Bayan sunci sun koshi yasa wadda ita dole tasa ta ci ga mamakin Dije gani tayi Sajida ta rike ciki tare da fadin wayyo Allah na shiga uku dear pls ku taimakeni kanwata wayyo zan mutu marata.......... Mamaki ne ya Kama su duka cikin tashin hankali duka suka nufota,rurrufe ido kawai takeyi tare da Kara ambatar wayyo marar ta cikin rudewa ya ciccibeta Dije ma hijabi ta dauko ta rufa musu baya suka nufi asibiti. Suna zuwa babu Bata lokaci ya shiga duba matsalar Bai gama gani ba yaga jini na biyowa ta kasanta dai dai Nan Kuma bincikensa ya Nuna Masa lallai Sajida maganin zubar da ciki Tasha. Innalillahi wa'innailahir raji'un! Kawai yake furtawa to meya hada sajida da maganin zubar da ciki,jikin bangon dakin ya jingina Wanda ya ya Fara wasu hawaye a fili ya furta why? Sajida? Meyasa Kika aikata hakan abinda ya zuwa yanzu nake lissafin zuwansa duniya. Jin shirun yayi yawa yasa Dije bude dakin ta shiga,yanayin data ga Sajidan ciki ya daga Mata hankali ganin jini na biyowa kafarta,tana juyawa taga Habeeb na kuka,cike da mamaki da Kuma firgici tace. Meya faru? Yaya meya sameta haka ? Ka duba halin datake ciki ka taimaka Mata Mana! Khadeeja sajida ta cuceni,Sam Bata kyautamin ba,cikina,jinina,mafarkina,shi ta zubar min. Subanallahi Dije ta furta. Garin Yaya? Ban sani ba Nima Ashe dama Bata Sona? Ah ah Yaya jeka taimaketa Dan Allah she's need your help pls! Ko kallonta beyi yasa Kai ya fice . Jin maganarsu takeyi kamar a mafarki,Dan haka ta Mika hannu ta shafo zaninta Jin da gaske jinin ne ke binta tare da wani azababben wani ciwon Mara Daya taso Mata lokaci Daya wata Kara ta saki ta sumeeeeee........ Wohoho! Ku biyoni Dan Jin ya hakan ta kasance dama hausawa sunce in zaka Gina Ramin mugunta ginashi dai dai Dan watakil Kai zaka fada๐Ÿ˜œ *Insha Allah Zaku dinga jina kullum zan Gama muku kafin axumi.* *Alkalamin khady* โœ [7/8, 9:10 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (Palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA khadeeja Usman 5โƒฃ5โƒฃ Cike da tashin hankali Dije ta fito daga dakin,kacibis sukayi da Naseer Wanda yaga lokacin da suka fito daga gida,ya lura kamar ba lafiya ba,hakan yasa ya biyo sahun su,cikin rudewa Dije ta shiga fadin, " Pls Yaya Naseer ka taimaki Anty sajida, ban San meya sameta ba,Amma tana bukatar taimako" Bai wani tsaya tambayarta Ina Habeeb ba ya nufi dakin dayaga ta fito,itama binsa tayi da gaggawa. Koda ya shiga ya isketa cikin wannan yanayin tabbas ya razana shima,Dan haka wayarsa ya daga ya Kira doctor yusuf yasanar dashi abinda ke faruwa. Bayan zuwan doctor yusuf din, Fita Dije tayi ta jingina da kofar tare da kuka,tana tunanin to meya Sami Sajida haka? Kusan mintuna talatin suka dauka kafin suka samu jinin ya tsaya,kowannensu cike da mamakin abinda suka gani,sai dai shi Naseer ya tahallaka faruwar hakan ga Dan uwansa,Dan yasanshi Sarai tun farko yace shi a ra'ayinshi bayason matarshi ta haihu da wuri,to Amma ai ya sanar dashi kwanaki cewa Sajida nada ciki,Kuma ga dukkan alama yayi matukar farin ciki da faruwar hakan Wanda a lokacin shi kanshi Naseer din har Saida yayi mamaki,aikuwa ya Zama dole yaje yaji dalilin faruwar lamarin dandai a yadda gwajinsu ya Nuna musu Sajida maganin zubar da ciki tasha. ****** Ba Wanda Habeeb ya sanarwa Sajida na asibiti daga Iyayenta har nashi,Wanda su Naseer sun dauka ya fada shiyasa Basu wani damu ba ganin wai ba Wanda yazo tunda dare ne,shi Naseer gida ya wuce ya bar su a asibitin Dan yaso magana da Habeeb Amma yanayin Daya ganshi shiya tabbatar mishi akwai damuwa,shiyasa ya kyaleshi. Shima Habeeb din hakan take a gurinshi,inda yaja hannun Dije wadda keta rokonshi akan yabarta ta kwana a asibitin Amma ko kulata beyi ba,ya sata mota suka tafi gida. ***** Tun asuba Dije data tashi Bata koma bacci ba ta tsaya ta gyara ko'ina tare da yin abincin da zasu asibiti dashi,Sam takasa gane matsalar dake faruwa, domin tana ganin jiya Habeeb kwana yayi beyi bacci ba, duk juyin datayi saita ganshi tsaye ko zaune Yana safa da marwa har aka Kira sallar asuba yayi alwala ya fita masallaci,acan Suka hadu gaba dayansu har Daddy Nan Daddy yaji Naseer na tambayar Habeeb ya jikin sajida. Amsa masa yayi da cewar, " da sauki" "Assha" cewar daddy! "Meya sameta?" "Dan zazzabi ne Daddy Amma taji sauki" "To Allah ya bata lafiya" "Ameen! Direct asibitin ya wuce Dan so yakeyi yaji ta Yaya hakan ta faru,sai dai Koda ya Isa ya tarar an Kuma Mata allurar bacci,wadda sai Nan da kusan awa Daya zata saketa,kujera yaja ya zauna ya zuba Mata ido Yana Mata kallon tuhuma. Itako Dije Jin shuru Bai dawo ba yasa ta tabbatar da ya tafi asibitin,Dan haka ta shirya itama ta dauki abincin da zata Kai a basket ta shiga part din mama mariya ta sanar Mata, kasancewar Daddy na part din mamy ne,yasa mama mariya ta kirashi a waya ta sanar dashi,yayi mamaki kwarai da Jin Wai asibiti Sajida ta kwana Amma Habeeb Bai fada Masa ba dazu a masallaci,nan yace to suyi gaba ita da Dijen shima gasu nan zuwa. Hakan ko akayi habu driver suka sa ya kaisu. Suna Isa direct dakin suka nufa. Yana Nan zaune yaga ta Fara motsawa alamun zata farka,sannu a hankali yaga ta bude idanunta fes,sannan ta fara kalle-kalle,har idonta ya sauka akansa,so takeyi ta tashi Amma sai taji jikinta yayi Mata wani iri,ba kwari. A hankali yayo tattaki ya iso bakin gadon a tunanin ta taimaka mata zaiyi ta tashi sai Jin maganar sa tayi Yana fadin, "Dama Sajida Ashe bakya Sona?" "Ashe duk cewar da kikeyi kinfi kowa kaunata,da son ganina cikin farin ciki Ashe karya kike yi?" "Laifin me na aikata Miki da kika zabi salwantar da gudan jini na,farin cikina a yanzu Wanda na tahallaka dukkan burikana akansa!" "Meya hadaki da maganin zubar da ciki? In bakya son haihuwar ai saiki sanar Dani,ni Kuma zan durkusa na rokeki ki fadi ko nawa zan biyaki harki haifamin shi,Amma sai da Kika bari nasawa raina nima na kusa Zama uba sannan Kika Sha abinda yayi sanadiyar zubewar cikina, wallahi kin cuceni bazan ta......" Sallamar su Daddy da su mama mariya da sun Dan jima da yawa amma dayake Daddy ya kirata yace suma suna hanya shine suka tsaya jiransu Dan su shiga tare.... *Toh fa! Ana wata ga wata,ku biyoni Dan Jin ta Yaya kaddara ta sauya lamarin Sajida har reshe ya juye da mujiya* *Alkalamin khady* โœ ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* (Palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA khadeeja Usman 5โƒฃ6โƒฃ *Kuyi hakuri na rashin jina da bakuyi ba jiya,mun Sami matsalar wuta ne,Kuma ko yauma charji na kadan ne zanyi muku abinda ya samu* **************** "Wai me kake Fadi ne Habee?" "har yanzu nakasa fahimtar inda zancenka ya dosa".Kana nufin kicemun ni ke dauke da ciki! Cikin ma Kuma na haihuwa to ta Yaya hakan zata kasance? Kowa a gurin shuru yayi Yana sauraren maganarta,Wanda Habeeb yaso yin shuru ne Dan kada suji komai,Amma ganin tana neman Raina Masa hankali yasa shi fadin, "Kada ki daukeni marar hankali Mana" ni Zaki kalla ki dinga tambayar wai kinada ciki ko bakida shi! Bayan kin fi kowa sanin ta'asar da Kika aikatamin,to wallahi ki sani bakiyi a banza ba duk irin son da nake yiwa mace,in har ta Nuna Bata son hada jini dani to babu abinda zai hanani tsanarta Nima sann...... Daddy ne ya dakatar dashi ta hanyar fadin, Wai me ke faruwa ne,kun tsaya kunata wasu maganganu marasa tushe,ku sanar damu meke faruwa? Ga mamakin su gani sukayi Habeeb ya fashe da kuka tare da fadin, "Daddy, sajida ta cuceni,cikina ta zubar! Innalillahi wa'innailahir raji'un! Kowa ya shiga Fadi a dakin,inda hakan yayi dai dai da sallamar su Naseer shida Zainab. Runtse ido Sajida tayi tana me tunanin ta yadda hakan ya faru. *MAFARIN LAMARIN* Tun lokacin da suka yanke wannan shawarar ita da laila,sannan da dataje gida ta fada wa mamanta Nan suka yanke shawarar abinda suke ganin zai fisshe su family doctor dinsu suka Kira suka yiwa bayanin komai,batare da Bata lokaci ba ya sanar dasu hanyoyin da zasu bi. Magunguna ya bawa Sajida yace matukar tana shansu zasu canza ta,sannan zasu sata kiba Susa tayi fresh,inda har kowa zaiyi tunanin tanada ciki sannan idan mijin yace zaiyi Mata scanning kada ta yarsa,ta taho asibitin su zai San yanda zaiyi mata,haka dai yayita Basu shawarwarin da zasu bi. To bayan sun dawo ne Kuma maman tace ta tafi gida kafin ta yanke abinda zai biyo baya. Kasancewar cikin magungunan da doctor ya Bata harda na daukewar al'ada hakan yasa tsarinta ya tafi yadda take so. *Allahu akhbar*! Allah Mai yadda yaso da al'amarin bawansa,cikin wannan yanayin Allah yayi ikonsa sajida tasami ciki batare da saninta ba,Wanda kowa ya fidda Mata Rai da samun haihuwa,sai dai ba'a cire Rai da rahmar Allah. Duk yadda suka so tsarin yabi baiyi aiki ba,hakan yasa Sajida sauya salon kishinta akan Dije,in Habeeb na Nan faram-faram,in kuwa ya fita sai ta hau zagin Dije,Wai duk Dan ta tamka mata,saita kamata ta buga inyaso ita Kuma ta kwanata laga-laga tace Dije ta gayyato aljanunta sun ta naushin cikinta har cikin ya zube,sai ta Kira mamanta a kaita asibitin su inda family doctor dinsu ke aiki,to ganin Dije taki kulata yasa ta sanar da Mamanta,shine ta Bata maganai tace duk ranar girkin Dije ta zuba a cikin lemon da zata Sha,inya so in sun zo cin abinci saita Sha da zarar Tasha din kada ta Nuna komai saita dawo bangarenta saita Kira wayar maman inyaso saita zo su kaita asibitin su,daga baya su Kira Habeeb suce cikin dare abin ya faru,Kuma an tabbatar abincin dataci na karshe a shi aka sa Mata maganin zubar da ciki, daga Nan za'a zargi Dije sai yayi waje road da ita. Shiyasa ranar da Dije tayi girkin ta shiga wanka tazo ta saka kwayar cikin karamin cup,tadan sakada ta yadda baza'a ganta ba,to bayan sun zauna cin abin cin ta jawo kofin ta zuba,inda a tunaninta ko ta Sha tunda batada komai ba abinda zai faru da ita Wannan shine Mafarin lamarin. Pls ba nida charji ne *Alkalamin khady* โœ [7/8, 9:11 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (Palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA khadeeja Usman 5โƒฃ5โƒฃ Cike da tashin hankali Dije ta fito daga dakin,kacibis sukayi da Naseer Wanda yaga lokacin da suka fito daga gida,ya lura kamar ba lafiya ba,hakan yasa ya biyo sahun su,cikin rudewa Dije ta shiga fadin, " Pls Yaya Naseer ka taimaki Anty sajida, ban San meya sameta ba,Amma tana bukatar taimako" Bai wani tsaya tambayarta Ina Habeeb ba ya nufi dakin dayaga ta fito,itama binsa tayi da gaggawa. Koda ya shiga ya isketa cikin wannan yanayin tabbas ya razana shima,Dan haka wayarsa ya daga ya Kira doctor yusuf yasanar dashi abinda ke faruwa. Bayan zuwan doctor yusuf din, Fita Dije tayi ta jingina da kofar tare da kuka,tana tunanin to meya Sami Sajida haka? Kusan mintuna talatin suka dauka kafin suka samu jinin ya tsaya,kowannensu cike da mamakin abinda suka gani,sai dai shi Naseer ya tahallaka faruwar hakan ga Dan uwansa,Dan yasanshi Sarai tun farko yace shi a ra'ayinshi bayason matarshi ta haihu da wuri,to Amma ai ya sanar dashi kwanaki cewa Sajida nada ciki,Kuma ga dukkan alama yayi matukar farin ciki da faruwar hakan Wanda a lokacin shi kanshi Naseer din har Saida yayi mamaki,aikuwa ya Zama dole yaje yaji dalilin faruwar lamarin dandai a yadda gwajinsu ya Nuna musu Sajida maganin zubar da ciki tasha. ****** Ba Wanda Habeeb ya sanarwa Sajida na asibiti daga Iyayenta har nashi,Wanda su Naseer sun dauka ya fada shiyasa Basu wani damu ba ganin wai ba Wanda yazo tunda dare ne,shi Naseer gida ya wuce ya bar su a asibitin Dan yaso magana da Habeeb Amma yanayin Daya ganshi shiya tabbatar mishi akwai damuwa,shiyasa ya kyaleshi. Shima Habeeb din hakan take a gurinshi,inda yaja hannun Dije wadda keta rokonshi akan yabarta ta kwana a asibitin Amma ko kulata beyi ba,ya sata mota suka tafi gida. ***** Tun asuba Dije data tashi Bata koma bacci ba ta tsaya ta gyara ko'ina tare da yin abincin da zasu asibiti dashi,Sam takasa gane matsalar dake faruwa, domin tana ganin jiya Habeeb kwana yayi beyi bacci ba, duk juyin datayi saita ganshi tsaye ko zaune Yana safa da marwa har aka Kira sallar asuba yayi alwala ya fita masallaci,acan Suka hadu gaba dayansu har Daddy Nan Daddy yaji Naseer na tambayar Habeeb ya jikin sajida. Amsa masa yayi da cewar, " da sauki" "Assha" cewar daddy! "Meya sameta?" "Dan zazzabi ne Daddy Amma taji sauki" "To Allah ya bata lafiya" "Ameen! Direct asibitin ya wuce Dan so yakeyi yaji ta Yaya hakan ta faru,sai dai Koda ya Isa ya tarar an Kuma Mata allurar bacci,wadda sai Nan da kusan awa Daya zata saketa,kujera yaja ya zauna ya zuba Mata ido Yana Mata kallon tuhuma. Itako Dije Jin shuru Bai dawo ba yasa ta tabbatar da ya tafi asibitin,Dan haka ta shirya itama ta dauki abincin da zata Kai a basket ta shiga part din mama mariya ta sanar Mata, kasancewar Daddy na part din mamy ne,yasa mama mariya ta kirashi a waya ta sanar dashi,yayi mamaki kwarai da Jin Wai asibiti Sajida ta kwana Amma Habeeb Bai fada Masa ba dazu a masallaci,nan yace to suyi gaba ita da Dijen shima gasu nan zuwa. Hakan ko akayi habu driver suka sa ya kaisu. Suna Isa direct dakin suka nufa. Yana Nan zaune yaga ta Fara motsawa alamun zata farka,sannu a hankali yaga ta bude idanunta fes,sannan ta fara kalle-kalle,har idonta ya sauka akansa,so takeyi ta tashi Amma sai taji jikinta yayi Mata wani iri,ba kwari. A hankali yayo tattaki ya iso bakin gadon a tunanin ta taimaka mata zaiyi ta tashi sai Jin maganar sa tayi Yana fadin, "Dama Sajida Ashe bakya Sona?" "Ashe duk cewar da kikeyi kinfi kowa kaunata,da son ganina cikin farin ciki Ashe karya kike yi?" "Laifin me na aikata Miki da kika zabi salwantar da gudan jini na,farin cikina a yanzu Wanda na tahallaka dukkan burikana akansa!" "Meya hadaki da maganin zubar da ciki? In bakya son haihuwar ai saiki sanar Dani,ni Kuma zan durkusa na rokeki ki fadi ko nawa zan biyaki harki haifamin shi,Amma sai da Kika bari nasawa raina nima na kusa Zama uba sannan Kika Sha abinda yayi sanadiyar zubewar cikina, wallahi kin cuceni bazan ta......" Sallamar su Daddy da su mama mariya da sun Dan jima da yawa amma dayake Daddy ya kirata yace suma suna hanya shine suka tsaya jiransu Dan su shiga tare.... *Toh fa! Ana wata ga wata,ku biyoni Dan Jin ta Yaya kaddara ta sauya lamarin Sajida har reshe ya juye da mujiya* *Alkalamin khady* โœ ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* (Palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA khadeeja Usman 5โƒฃ6โƒฃ *Kuyi hakuri na rashin jina da bakuyi ba jiya,mun Sami matsalar wuta ne,Kuma ko yauma charji na kadan ne zanyi muku abinda ya samu* **************** "Wai me kake Fadi ne Habee?" "har yanzu nakasa fahimtar inda zancenka ya dosa".Kana nufin kicemun ni ke dauke da ciki! Cikin ma Kuma na haihuwa to ta Yaya hakan zata kasance? Kowa a gurin shuru yayi Yana sauraren maganarta,Wanda Habeeb yaso yin shuru ne Dan kada suji komai,Amma ganin tana neman Raina Masa hankali yasa shi fadin, "Kada ki daukeni marar hankali Mana" ni Zaki kalla ki dinga tambayar wai kinada ciki ko bakida shi! Bayan kin fi kowa sanin ta'asar da Kika aikatamin,to wallahi ki sani bakiyi a banza ba duk irin son da nake yiwa mace,in har ta Nuna Bata son hada jini dani to babu abinda zai hanani tsanarta Nima sann...... Daddy ne ya dakatar dashi ta hanyar fadin, Wai me ke faruwa ne,kun tsaya kunata wasu maganganu marasa tushe,ku sanar damu meke faruwa? Ga mamakin su gani sukayi Habeeb ya fashe da kuka tare da fadin, "Daddy, sajida ta cuceni,cikina ta zubar! Innalillahi wa'innailahir raji'un! Kowa ya shiga Fadi a dakin,inda hakan yayi dai dai da sallamar su Naseer shida Zainab. Runtse ido Sajida tayi tana me tunanin ta yadda hakan ya faru. *MAFARIN LAMARIN* Tun lokacin da suka yanke wannan shawarar ita da laila,sannan da dataje gida ta fada wa mamanta Nan suka yanke shawarar abinda suke ganin zai fisshe su family doctor dinsu suka Kira suka yiwa bayanin komai,batare da Bata lokaci ba ya sanar dasu hanyoyin da zasu bi. Magunguna ya bawa Sajida yace matukar tana shansu zasu canza ta,sannan zasu sata kiba Susa tayi fresh,inda har kowa zaiyi tunanin tanada ciki sannan idan mijin yace zaiyi Mata scanning kada ta yarsa,ta taho asibitin su zai San yanda zaiyi mata,haka dai yayita Basu shawarwarin da zasu bi. To bayan sun dawo ne Kuma maman tace ta tafi gida kafin ta yanke abinda zai biyo baya. Kasancewar cikin magungunan da doctor ya Bata harda na daukewar al'ada hakan yasa tsarinta ya tafi yadda take so. *Allahu akhbar*! Allah Mai yadda yaso da al'amarin bawansa,cikin wannan yanayin Allah yayi ikonsa sajida tasami ciki batare da saninta ba,Wanda kowa ya fidda Mata Rai da samun haihuwa,sai dai ba'a cire Rai da rahmar Allah. Duk yadda suka so tsarin yabi baiyi aiki ba,hakan yasa Sajida sauya salon kishinta akan Dije,in Habeeb na Nan faram-faram,in kuwa ya fita sai ta hau zagin Dije,Wai duk Dan ta tamka mata,saita kamata ta buga inyaso ita Kuma ta kwanata laga-laga tace Dije ta gayyato aljanunta sun ta naushin cikinta har cikin ya zube,sai ta Kira mamanta a kaita asibitin su inda family doctor dinsu ke aiki,to ganin Dije taki kulata yasa ta sanar da Mamanta,shine ta Bata maganai tace duk ranar girkin Dije ta zuba a cikin lemon da zata Sha,inya so in sun zo cin abinci saita Sha da zarar Tasha din kada ta Nuna komai saita dawo bangarenta saita Kira wayar maman inyaso saita zo su kaita asibitin su,daga baya su Kira Habeeb suce cikin dare abin ya faru,Kuma an tabbatar abincin dataci na karshe a shi aka sa Mata maganin zubar da ciki, daga Nan za'a zargi Dije sai yayi waje road da ita. Shiyasa ranar da Dije tayi girkin ta shiga wanka tazo ta saka kwayar cikin karamin cup,tadan sakada ta yadda baza'a ganta ba,to bayan sun zauna cin abin cin ta jawo kofin ta zuba,inda a tunaninta ko ta Sha tunda batada komai ba abinda zai faru da ita Wannan shine Mafarin lamarin. Pls ba nida charji ne *Alkalamin khady* โœ [7/9, 8:53 AM] El~hajj: [7/9, 8:48 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* (Palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* na Khadeeja Usman 5โƒฃ7โƒฃ Hawaye ke bin gefen idonta,idan har da gaske ne cewar ciki ta samu ya zube lallai ta tafka babban kuskure,amma Kuma har yanzu zuciyarta Bata karaya ba akan kudirinta na fitar da Dije,Dan haka runtse idonta tayi tana Jin maganar Daddy Yana fadin, "Haba 'yata",me ya kaiki aikata wannan danyen aiki haka?,haihuwa ai rahma ce amma kike gudunta Dan wani shirme naku na diyan zamani. Caraf mamy ta karbe da fadin,"wannan ai ba shirme bane,ganganci ne,inba haka ba kin samu ma kin taki sa'a a wannan yawan shekarun naki kin Sami haihuwar shine Kika salwantar,oh! Ni Karima,shi dai Kam Habeeb baiyi sa'ar aure ba,daga guzuma sai 'yar kauye! Ta karasa maganar tana kallon inda Dije take tare da wurga Mata harara. Ita ko Dije tun lokacin dataji Habeeb ya Fadi cewar Wai Sajida ciki ta zubar abin ya daure Mata Kai,Dan gani takeyi ko shege ne ita dai bazata iya zubar da ciki ba,bare Kuma Mai tushe da tsantsar asali. Gurin dai bawanda ya Kara cewa komai,yayin da Daddy ya Kira Habeeb da Naseer zuwa waje,nasiha ya shiga yi musu,sannan ya umarci Naseer Daya dawo da yusrah Dan zaman ya Isa haka,sannan shi Kuma Habeeb ya shiga tausar sa da bashi hakuri akan abinda Sajida ta aikata masa,tare da ce masa kada yace zai wani dauki mataki,ya fawwalawa Allah komai,Daman haka ya kaddara Masa.Jin Daddy kawai yakeyi amma gani yakeyi babu macen da zata aikata Masa wannan laifin ya kyaleta. Kiran mahaifiyar Sajida yayi ya sanar Mata Sajidan ba lafiya tana asibiti,cikin tashin hankali ta bazamo kuwa. Koda ta karaso zuwa lokacin duk su mamy sun tafi,sai shi Daya tsaya jiranta,Koda ta iso ta kirashi ya sanar da ita number dakin da Sajida take,wadda har yanzu zuciyarta ta kasa nutsuwa,Banda kuka ba abinda takeyi,shiko ko kallonta beyi ba.Koda maman ta iso bayan ya gaisheta mikewa yayi tare da ce Mata," to ni zan wuce,amma Ina son idan Sajida taji dama ku wuce da ita gida saina nemeta". "Ban gane saika nemeta ba,yimin bayani inji dalla-dalla",say Kai yayi ya nufi kofa tare da fadin tayi Miki bayani da bakinta Yana Gama fadar hakan ya fice. Sajida kuka Mai sauti ta saki inda maman ta shiga tambayarta meya faru?, Cikin kuka ta labarta Mata komai,salati ta shiga yi tare da fadin,lallai munyi kuskuren da bazai gyaru ba. "Ah ah mummy kada kice haka ,dole zai gyaru kinji fa abinda yace Wai in tafi gidanmu wayyo na shiga uku,cewa fa yayi Wai har Saiya nemeni,yaushe kenan? "Kinga yanzu ba lokacin wannan maganar bane,ni dai abinda nake so dake,Koda wasa kada ki sake ki fadawa abbanki gaskiyar abinda ya faru,kinji ko? Daga baya zamu San abinyi. ************ Tunda abun Nan ya faru,Sam ya rage walwala,Dan ko abinci ya rage ci,dama can be wani fiya yin dariya ba sai abin yazo ya Kara haduwa,tun abun baya damun Dine har ya Fara damunta,Abu Daya tasani da zarar dare yayi tofa lokacin zaiyi Fara"a Dan ta fuskanta ta wannan fannin bashida aji,har zuwa asuba zaita lallabata,Amma da gari ya waye magana ma wahala ma takemai. Yau Kam takai makura,ta Kuma Gama sawa zuciyarta bazata bashi hadin Kai ba,hakan ko akayi,Koda ta Gama girkinta ta gyara ko ina,rigarta ta dauko Fara ce iyakarta cinyarta,gata shara shara kusan komai na jikinta ana gani,tarasa dalilin da yanzu inta Sa bra take damunta,sannan taga yanzu duk kayanta na dinki sunyi Mata kadan to kodai sai yanzu tayi cikar daki. Haka dai ta shirya ta feshe jikinta da turare,tunda ya shigo daya daga cikin bedroom din ya shiga yayi wanka Wanda a yanzu ya mayar dashi nashi,bayan ya fito falo ya jima zaune Yana jiran fitowarta Amma yaji shuru!,Jin yunwa na nukurkusarsa yasa shi zuwa dinning da kanshi yayi serving din kanshi,bayan yaci ya koshi ya dawo yaci gaba da kallonshi,kallon yakeyi Amma hankalinshi na gareta na tunanin meya hanata fitowa? Kashe kallon yayi kafin yaje ya tura kofar dakin, kudundune ya hangota can tsakiyar gado ta lullube jikinta,a hankali ya karasa ya yaye bargon,sai ganinta yayi tana rawar sanyi,da sauri ya jawota jikinshi Yana tambayarta meyake damunta?, Kuka tasa Masa tare da fadin banida lafiya,kullum da zazzabi nake kwana,Amma na fuskanci Kai bama ka fahimta kwata-kwata, tunda Naga duk halin da nake ciki saika San yadda kayi ka kashe arna saba'in babu ko tausayin ka kyale wasu ko zasu muslinta,Kai ni wallahi duk ba wannan yafi damuna ba ma kafa duba ka gani,yawan yin da kakeyi ka toshemin kofar mahaifata,gashi Nan kaja na daina period kusan wata uku ban ganshi ba,ni tsorona ma kada Inje ko ka mayar Dani dunkunkuma,wadda Bata period kwata-kwata,ga yawan tashi da zuciyata keyi nidai Allah yasa ba wani ciwon ne Dani ba,gashi kafafuna ma suna min ciwo,ban sani ba ko skills sells ce ma Dani Bata Nuna ba har sai yanzu.. .... *Gaskiya Naga korafin marubuta da yawa akan rashin comments,babban abin bakin ciki sai dai kaji ance tnx,babu sharhi ta yadda marubuci zai samu kwarin gwiwar ci gaba da suburbudo muku ci gaba,pls readers ku gyara gaskiya.* ๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„ *Alkalamin khady* โœ [7/9, 8:49 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..* ๐Ÿฎ (*_palace of excitation n'd pleasant writer's_*) *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 5โƒฃ8โƒฃ *Alhamdulillih! Alhamdulillih 'yan uwana musulmi Ina yiwa kowa barka da sallah fatan anyi Sallah lfy Allah Mai kowa Mai komai ya maimaita Mana yasa mukasance cikin bayin da aka 'yanta a cikin wannan wata Mai Albarka ameen* ____''''""""Am back""""""___ Tunda ta Fara maganar ya zuba Mata ido Yana nazarinta,so yakeyi ya gasgata hasashensa Amma Kuma Yana kokwanto,ganin da tayi ya tsareta da ido baice komai ba yasata sakin kuka Mai sauti tare da fadin, "Ai dama nasan ba abinda zakayimin,tunda Kai baka iya wani rarrashin mace ba sai da dare ko Kuma kwayoyin halittarka sun rikece da Rana ba,Nan fa zanji murya marar 'ya'ya na fita Amma muddin ba hakance ta tashi ba to baka ko yin dariya,shikenan naji na yadda baka Sona ka aureni Amma Nima kasan bana sonka ai to basai kawai mu dangana ba mu bawa zuciyoyinmu hakuri ba mu rungumi kaddara, kowacce mace kaje gidanta kaga mijinta Yana Nan Nan da ita Amma Ni ban San ya zan auna mizanin tsanar da kamun ba a rayuwa ta, shikenan naji Amma Dan Allah Ni ka taimaka ka dubamin mahaifa ta kaga meyasa na daina al'ada tsawon wata uku,ta karasa maganar tana me shasshekar kuka". Kamar bazaiyi magana ba sai Kuma zuwa can taji yace, "Bayan rashin ganin period din naki sai kuma me"? "Wallahi ko kamshi naji wani lokacin sai zuciyata ta tashi,sannan ga zazzabi,Ni babban tashin hankalinma sai inji Ina yawan son kana.....sai Kuma tayi shuru. "Ina me?ki karasa Mana. Shuru tayi tare da Kara kudundune kanta cikin bargon Dan har wani jiri-jiri take ji. Jin da yayi batada alamar amsa Masa yasashi fahimtar abinda take nufi, ganin halin da take ciki yasashi mikewa ya fita Dan sama Mata magani. Itako tanajin fitarshi ta saki marayan kuka a fili ta furta "wayyo Ni innata! Kinga abinda wancan tsohon ya jawomin gashi Ni garin son inyi biyayya In burge gashi na kawo kaina makasa yanzu hakama mutuwa ta ce ta kawo jiki,na shiga uku ta karasa maganar tana Kara matso hawayen da daka gani kasan dole aka musu suke fitowa,tana cikin wannan yanayin taji ya bude Kofa ya shigo dauke da cup a hannunsa da ruwa,Yana karasowa ya hau gadon ya tasota ya tallafota,bige hannunsa tayi tana fadin Ni ka rabu Dani tunda baka Sona ka Dade da tanadar geron sadakar bakwai Dina. "Waye yace Miki bana sonki"? "Wallahi Ina sonki sosai matukar so tun ba yanzu ba Dan haka ki daina cewa bana sonki". "Da gaske kana Sona Yaya"? Sosaima kuwa! Dan haka Kisha magani yanzu zuwa dasafe sai muje asibiti. Duk da Bata son magani Amma kalamansa sunsa ta karba batare dako darr ba ta antaya tare da korawa da ruwa. Bata wani jima da Sha ba bacci ya kwasheta,ya jima zaune yana kallonta Yana murmushi,tare da nazarin abinda yake son tabbatarwa kansa,inko har hakane lallai ya godewa Allah Mai kyauta da kari,tunawa da yayi da abinda Sajida tayi Masa yasashi Jin ransa ya baci Dan haka ya mike ya shige toilet ya sakarma kansa shower.... *** *** Tun ranar da suka koma gida ta shiga tsananin damuwa domin kuwa ko abinci Bata ci Banda kuka ba abinda takeyi,mahaifinta yayi rarrashi harya gaji domin shi baisan ainihin abinda ke faruwa ba,illah kawai sunce Masa Habeeb yayi tafiya ne shine tasa damuwa a ranta danya tafi da amaryarsa.Hakuri ya shiga bata tare da nasihohi da haka har tafiya ta kamashi ya bar kasar. Yauwa kamar kullum tana zaune a dakinta duk ta bi ta rame ta fita hayyacinta,mahaifiyar ta ce ta shigo dauke da faranti a hannunta abinci ne da ruwa tare da lemo Mai sanyi,Saida ta ajiye ta Sami guri ta zauna sannan ta kalli sajida data gyara zamanta tare da sunkuyar dakai. Cikin bacin Rai mahaifiyar ta ta Fara magana, wato ke bakyajin magana ko? Kin bi kinsa tunanin banza da wofi a zuciyarki Akan wani banza namiji,yanzu ke a haka kike son mu tunkari abinda ke gabanmu,kin San ko Ni kaina inajin takaicin abinda ya faru Dan koba komai in waiga in kalleku zagada zagada keda kannenki gabana ai dole gabana ya dinga faduwa,tunda kin samu kin auru ai bazan Bari inyi gangancin da Zaki fito ba,ba boka ba malam Amma wallahi Saiya shigo hannu Dan haka ki kwantar da hankalinki ki samu ki murmure mu tunkari yakin Dan muyi nasara. Sosai taji dadin maganganun mahaifiyarta Dan haka ta saki ranta taci abinci tare da kudirewa ranta saita Rama abinda Habeeb yayi mata.,tunda ya kasa Mata uzuri. **** ***** Tayi cikin farin cikin komawarta dakinta,da farko Naseer shareta ya shiga yi,Saida ta dinga kwantar da Kai tana bashi hakuri, albarkacin cikin jikinta ya shiga tausaya Mata kasancewar cikinta ya tsufa sosai suna jiran hukuncin ubangiji ne, Zamansu da Zainab kadaran kadaham babu Mai shiga shirgin wani in Naseer baya Nan Amma in Yana Nan saika rantse da Allah ba Wanda ya fisu hadin Kai,hakan yasa hankalinshi ya kwanta har wata Yar kiba yayi. ***** Tun sassafe yasa ta shirya suka wuce asibiti,sawa yayi akayi Mata duk wani gwaje_gwajen Daya Dace,inda result ya tabbatar tana dauke da ciki,sai dai akwai maleria fever dake damunta,sosai yayi farin cikin kasancewar cikin dan haka ya kasa boyewa,ko kadan Bai fada Mata ba illah lura datayi Yana cikin farin ciki sosai. A zuciyarta ta furta to kodai farin ciki yakeyi da ciwon nata ne! Dan haka cikin kulawa ta kalleshi tare da fadin, "Wai Ni me yake damuna ne da akamin test? Murmushi taga yayi abinda ya dada kular da ita kenan Dan haka tace au ciwon nawa ma abin dariya ne kenan? Ah ah abin farin ciki dai. Na shiga uku Yaya dama ana farin ciki da ciwon mutum? Sosai ma kuwa ya Bata amsa tare da mayar da hankalinshi ga tukin da yakeyi, Ji yayi tasa Masa kuka tare da fadin ai Ni dama nasan wallahi karya kakemin da kacemin Wai kana Sona Ashe kiyayyata dakai har takai haka! Ina ciwo kana murna shikenan Nan ta fashe da kuka. Baiyi Mata magana ba har suka karaso gida suna zuwa,ko Gama parking baiyi ba ta bude murfin ta fita,Yana Gama parking din yabi bayanta Dan yasan wannan chakwakiyar dole ya warwareta. *Alkalamin khady* โœ [7/9, 8:59 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASS..*๐Ÿฎ (*_palace of excitation n'd pleasant writer's*_ *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 5โƒฃ9โƒฃ Koda ya karaso ya tarar da ita harta karasa daki tana zaune saman kujera tana kuka,shuru yayi yayin Daya zuba mata idanu,sannan ya zuba hannu a aljihu,ya jima tsaye a haka,ganin kukan nata yayi yawa zai iya sata ciwon Kai Wanda hakan matsala ne ga rayuwarta yasa shi matsawa kusa da ita ya zauna tare da dagota, "Haba my lovely sister,meye abin kuka Kuma? Uhmmm fadamin kinji! Ya karasa maganar Yana jawota jikinshi. "Bawani your lovely sister ,kawai ka kirani da your hated sister,ai na fahimci komai yanzu wallahi baka Sona tunda har kake murna da ciwona". "Ai ciwon naki ne na Dadi ne shiyasa". Kara fashewa tayi da kukan,wato dama ana ciwon dadi? "Sosai ma kuwa". "To ta Yaya"? "Yauwa to bara kiji yadda hakan ke faruwa,Amma saikin share hawayenki,kinji ko my.... Share hawayen ta shiga Yi harda gyara zama,to na daina kukan ta fada a Dan shawagwabe,yanayin yadda tayi maganar Saida tasa tsikar jikinshi tashi,Dan haka sosai ya jawota jikinshi ya mannata Nan ya cire Mata gyalen data yafa ya ajiye a gefe,dankwalin ma cirewa yayi Nan ya shiga shafa gashin kanta ,sosai yanayin yayi musu Dadi su duka,hakan har ya shagaltar dasu da mantawa da batun bayanin ciwo,sosai ya shiga shafata yayin da yake bin ko'ina na jikinta yana kunna light,tuni suka birkice inda ya kinkimi abarsa suka antaya bedroom din su,Saida suka tabbatar sun samawa kansu nutsuwa,sannan kowa yaje ya tsarkake jikinshi. Ba wani jimawa zazzabi ya rufeta,hakan yasa ya tuna da maleria da akace tana damunta,wadda yasan dole sai anyi treated dinta,fita yayi ha hado Mata tea Mai kauri,Saida ya tabbatar ya Dan huce sannan ya tasheta ya dinga Bata a baki,ko Gama Sha batayi ba ko ta shiga kwara amai,Saida ta amayar da duk abinda ta Dan Sha sannan ya kamata yakaita toilet ya wanke Mata jikinta ya daukota kamar wata babydoll,sosai tayi mamakin ganin ya zage Yana gyara gurin batare dako kyankyani ba,Saida yaga gurin ya koma neat kamar ba abinda ya faru sannan ya dawo yaci gaba da Bata sauran tea din,anyi sa'a batayi Aman ba,tana Gama Sha ya Bata magani Nan ne ma tasoyin gaddama Saida ya lallabata sannan ta karba Tasha. Ji yayi tace,"baka fadamin dalilin dayasa ake murnar ciwon mutum ba". "Ai na dauka kin Manta ne kin hakura da ji". "Ah ah! Ni ban hakura ba Ina son ji Dan Karin ilimi, Kumatunta ya Kama yaja tare da fadin,"yarinya me wayo". "Amma ai kin San me ake nufi da aure ko"? "Ah ah! Ni ban sani ba". "Toh naji baki sani ba,Amma ai kin San burin kowacce mace in tayi aure ta haihu ko?Amma ban San ko ke bakya so ba". "Kan balastin! Injiwa yace maka bana so! Ga kawata can rufaida saboda Bata haihu ba har yanzu uwar mijinta ta tsaneta, wallahi nafi son na haihu,kawai dai Dan nasan Kai bakason ka haihu Dani ne shiyasa bakamin yadda akeyi a Sami ciki. "To ya akeyi a Sami cikin? A bazata taji tambayar Amma saita maze tace Nima ban sani ba Amma nasan da kanamin yadda kayiwa anty ai Nima Dana Sami ciki. Shafa gefen fuskarshi yayi tare da sakin murmushi,sannan yace," to yanzu idan nace Miki kinada ciki to ya zakiyi? Zaro ido tayi tare da fadin,"ta Yaya ma hakan zata kasance? "Ta yadda nake bi da ke,shiyasa Kika ga Ina murna da rashin lafiyarki,domin na tabbatar nayi ajiya anan ya karasa maganar Yana shafa cikinta,. Rasa me zatayi tayi,farin ciki ne kome ohoo,illah sinke kanta da tayi Wai ita kunya,jawota ya karayi jikinshi,tare da fadin kin gamsu yanzu Ina Miki abinda ake samun ciki,kin San dai bazai yiyu inyi Miki filla-filla a banza ba ko?,Kara rukunkumeshi tayi tana boye fuskarta sosai ya shiga shafata har baccin Daya zame Mata na gado ya saceta. Kulawa sosai take samu daga gareshi da soyayya inda har take mamakinsa da yadda taga yanayi,Dan wani lokacin sai tayi da gaske yake fita aiki kullum rokonshi ta kula Masa da baby'n Shi. ******* Yau Yusrah ta tashi da nakuda kasancewar tun safe aka kaita asibiti,Amma Bata haihu ba sai wajen karfe Daya, alhamdulillih ta haihu lafiya tasami da namiji,sosai kowa ke murna tare da Nuna farin ciki, Naseer baki yaki rufuwa hakama Zainab,wadda itama take dauke da nata Dan matashin cikin,kusan zance kowa yayi farin ciki da samun haihuwar inda mamy da Daddy sosai suka Nuna murnansu,sai washe gari aka sallami su bayan an tabbatar da lafiyar su,daga baby har Mai jego, direct mamy ta wuce da ita part dinta inda sam hakan baiyiwa Naseer Dadi ba. Kwana biyu da haihuwa da safe su mamy na zaune itada da yusrah da wasu danginsu,yayin da Dije da Zainab keta kiciniyar aiki duk da mamy nata yada musu magana,itร  Kam Dije dama dauriya kawai takeyi Dan zazzabi takeji. Sallama suka ji inda suka juya gaba dayansu Dan Jin muryar Mai sallama,Sajida ce da mamanta,bayan sun zauna a mutunce su Zainab suka gaishesu inda ga mamakin su sukaga sun amsa cikin sakin fuska,har kasa sajida ta tsugunna ta gaida mamy,inda ta amsa ba yabo ba fallasa Dan haushinta da takeji na zubar da cikin da tayi,Basu nuna sun damu ba Nan suka yi Mata barka,sun dau lokaci shuru zuwa can maman sajida ta Miko medium akwatin da suka shigo da ita shakare da kayan baby,sosai fuskar mamy ta shakare da farin ciki,Nan fa ta Fara Saida tikitin godiya,kallon juna sukayi,suka kyafta ido sannan maman sajida ta Fara magana. "Haba hajiya ai wannan ba komai bane yiwa Kai ne,Kuma ko ita Sajida ai Dan kaddara ta gifta ne wadda Saida muka fita da ita waje likita ya tabbatar Mana da cewa a I wani magani aka zuba Mata na gargajiya Mai hadarin gaske a lemo Tasha,shi Kuma Habeeb Bai wani tsaya dogon bincike ba ya yanke hukunci Wanda yasan yanZu duniya ta lalace kana tare da makiyinka ma baka sani ba,to yanzu dai Alhamdulillih ta Sami sauki likita ya tabbatar Mana da hakan,Dan haka yanzu ma zuwan namu da biyu ne,munzo ne bisa umarnin Mai gidan yace a karbo takardar Dan tasamu tayi aure zaman haka bashida amfani dan gashi Nan Dan ganinta da akeyi a gidan yasa an Fara tururuwar zuwa yanzu ma Dan gidan president ne ya makale. Haba hajiya wane Kuma batun saki,Dan Allah bar wannan maganar,ai gara ya zauna da ita da ya zauna da dangin kauye,kada ki damu,yanzu ma ba inda zata tayi zamanta dakinta,Ni Dama nasan makarmashiya aka shirya,to abin ya karye naci dubu sai ceto,zai dawo ma ya sameni Kinga ki tafi kawai ki barta,ki bawa Alhajin hakuri. "Ai da nace gara a rabun zaifi"! Dan Allah daina batun rabuwar Nan kedai,haka sukaita ja inja har suka cimma matsaya Wanda dama burin su Sajida kenan,Koda ta tashi tafiya kudi masu yawa ta mikawa yusrah tace inji Alhajin yace kafin yazo,bayan Sajida ta rakota Nan suka kwashe da dariya sannan tace mummy aikin ki na kyau wallahi,kedai Bari badai mun shiga next level ba saisun gwammace kida da karatu,kedai kibi abubuwan Dana fada miki.,insha Allah kuwa mummy,Nan suka yi sallama ta shiga mota driver yaja suka tafi. Ko part din mamy Bata koma ba ta nufi part dinta cike da farin ciki. Itama Dije dayake tana ta kanta rarrafawa tayi ta nufi nata bangaren Dan sosai mamy ke fada Mata magana wadda kawai ta kyale ne Dan halin da take ciki Amma yaseen saita Rama inta warke.... *Alkalamin khady* โœ [7/9, 9:00 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASSO...* ๐Ÿฎ (palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* Na Khadeeja Usman 6โƒฃ0โƒฃ Yau Bai samu damar dawowa da wuri ba, kasancewar yayiwa wani aiki a asibiti,Sam Bai kula da sashen sajida bude yake ba,Dan haka direct part din Dije ya nufa kamar yadda ya saba.Yana shiga Bai taddata a falo ba Dan haka ya kutsa Kai cikin daki,kwance ya hangota saman bed ta kudundune da alamun tanajin sanyi,hakan ya tabbatar Masa da zazzabin ne ta dawo Mata,tilasta Mata yayi dole suka tafi asibiti a Daren ko hutawa baiyi ba,allurar paracetamol yayi Mata Dan yasan Bata son shanshi,sannan ya daura Mata ruwa,sai wajen 12 suka dawo gidan,inda ya cika da tsananin mamakin ganin part din sajida da wuta,karasawa yayi da ita dakin ya hada Mata ruwa Mai zafi tayi wanka,abincin Daya gani saman dinning yaje ya debo abinci a plate,Saida ya tilasta Mata sannan taci kadan,Dan gudun kada tayi amai yasa ya kyaleta,magani ya Bata Tasha sannan yasa ta kwanta, Saida ya tabbatar tayi bacci sannan ya mike ya nufi part din Sajida Dan yaga waye ya kunna wutar dakin. Yana shiga ya iske falon gyare tsab dashi yanata tashin kamshi,Sam Bai lura da ita ba sai muryarta ya tsinkaya tana fadin "you're welcome my man",Yana shirin yin magana yaji ta rungumeshi,janyeta yayi daga jikinshi cikin daure fuska yace, "Ke waya baki izinin dawowa?" Ba cewa nayi ki zauna har saina nemeki ba! Ya fada as husky voice.Sosai ta marairaice fuska cikin salonta na kwarkwasa ta Fara fadin, "Haba nurul hayati,kana tunanin duk abinda ya faru ban fika Jin ciwo ba,nice fa zanfi kowa cutuwa,Kuma wallahi ni Koda na Sha maganin da zummar maganin ciwon Mara Nasha,ban San cewa hakan zata kasance ba,nayi mamaki da ka kasa fahimtata,ta karasa maganar tare da sakin kuka,duk da Yana Jin haushinta,Amma sai yayi nazarin maganar ta tabbas ta yiyu abinda ta fada ya Zama gaskiya,Dan haka ya kalleta a fili yace, "Amma ai cewa nayi saina nemeki ko? Waya ba ki izinin dawowa?. "Kayi hakuri my wallahi na kasa samun nutsuwa da rashinka kusa Dani Sam bazan iya rayuwa babu Kai kusa dani ba kayimin uzuri mijina ka yafemin,sosai take kuka ta rungumeshi,hakan yasa tausayinta kwarai,bayanta ya shiga shafawa alamar rarrashi. "To ya Isa haka kukan kinji,ya fada yana bubbuga bayanta alamar rarrashi,Kara lafewa tayi tana sauke ajiyar zuciya,Dan batama yi tunanin shawo kanshi zai zo Mata da sauki haka ba.Hannunsa ta Kama ta nufi bedroom dashi,ruwan wanka ta hada masa,Saida ta taya shi wankan sannan itama ta sake yi,sannan suka fito, kasancewar dare yayi sosai yasa Bai ci abincin data tanadar Masa ba saboda bayacin abincin dare late,bayan sun Gama ne tunaninsa ya koma ga Dije ya shiga tunanin koya jikin nata?,duk abinda yakeyi tana lura dashi,Dan haka ta shiga Masa salon iri-iri Wanda ya shagaltar ta dashi harya Manta da batun Dije.Sosai ta Nuna Masa tayi kewarsa inda shi ma da kanshi ya Nuna hakan,sunsha soyayya sosai inda daga Nan sai bacci Kuma Wanda har yasa su makara. Tunda asuba ta farka taga bata ganshi ba,sai tayi tunanin masallaci yaje,Dan haka tana yin sallah ta Kuma komawa bacci,sai wajen goma ta tashi shima da kyar,Dan yanzu sosai take morewa bacci,Koda ta tashi yau ba zazzabi sai dai Dan rashin kwarin jiki da batada,tana shirin Fara gyara gidan taji sallamar Zainab,sosai taji dadin shigowarta,Dan haka ta yakar hakora, tambayarta tayi jikinta sannan tace, "Dama zuwa nayi inga yadda Kika kwana da jikin,Dan nasan tunda waccan me kirar samudawan ta dawo yau ana can ana kashe arna"โ€ฆ Sai a lokacin Dije ma ta tuna da dawowar sajida Dan Sam tama Manta, murmushi tayi tare da tunawa da lallai Kam Bata ganin Habeeb,tunda gimbiya ta dawo. Kallon Zainab tayi tare da fadin, "ke yarinya ba dole yayi rawar kafa ba,first love dinshi ce fa! Ni wallahi nama Manta da ta dawo,nasan Yana can ana ta kashe shi da luv shiya sa,Dan haka Ni Bari in tashi in samama kaina abinda zan afawa zumbili na".Tare suka shiga kitchen din sukayi girki Mai sauki,sunayi suna hira, har suka Gama,bayan sun Kare ne sun ci sun koshi sannan Zainab ta gyara Mata gidan,Dan Dije kasa tashi tayi sai bacci,Sam batayi wani tunanin Habeeb ba. ***** Kwana biyu cif ya kwashe batare da yasata a idonshi ba,duk yadda yaso zuwa dubata sai tasan salon da tayi Masa ta shagaltar dashi,yau ta Kama girkinta ne,Dan haka yaketa zumudi ya tashi aiki,sosai ya fahimci Sajida shiyasa yau ya kudiri niyyar sai magrib ma zai koma gidan,yasan duk bala'i dai lokacinta ya fita. Saida yayi sallah sannan ya dawo,Yana shiga ya isketa zaune saman sallaya ta idar da sallah tana addu'a,wanka ya shiga Dan haka tana idarwa ta Mike ta zauna saman gadon tana jiran fitowarshi,ya Dan jima sannan ya fito,da kallo ya bita,sai yaga kwana biyun dabai ganta ba harta Kara mishi girma da Kuma kyau, murmushi ta sakar Masa,shima ya mayar Mata da martani,Sam baiyi tunanin bazatayi fushi dashi ba sabanin hakan Daya gani,itako Dije anata bangaren Bata ga abin fushi ba Dan ta dauka haka akeyi in kanada kishiya har sai kwananka zakaga miji,sosai suka Nuna sunyi kewar juna,inda Nan da Nan suka suka shiga aikawa juna sakonnin soyayya.Bayan sun Sami nutsuwa ne suka Kara yin wanka,kwance take jikinshi tanata Mai korafin jikinta ciwo,cikin salon shagaba.Babu ko knocking sukaji ana Murda kofar alamun ana so a shigo. Janyeta yayi daga jikinshi yaje ya bude kofar batare ma Daya tambayi waye ba,Sajida ce tsaye sanye cikin Riga da wando theree quarter,Bata Bari yasamu damar tambayarta meya kawota ba,illah rabawa datayi ta gefenshi ta shige,sakin kofar yayi ya juyo tare da fadin, "Ke malama lafiya Zaki shigowa mutane daki Kai tsaye haka!" Farrrr tayi da ido itako Dije kallon ikon Allah ta tsaya yi,Dan wata dariya ce tazo Mata,wadda takasa danneta,ganin hakan yasa Sajida nufar inda Habeeb yake Dan ta kunsawa Dije bakin ciki,sakalo hannunta tayi a wuyansa tare da kashe murya,Wanda shi Habeeb tsabar bakin ciki ma ya hanashi ko motsi,cikin wani salo tafara furta, "Haba my man! Shine ka barni cikin kewar ka,kasan na Saba da Jin dumin jikinka, musamman kwana biyun Nan,ka nunamin Inada muhimmanci a rayuwarka,kasa na yadda nafi kowacce mace kamar yadda ka fada,Dan haka.......Bata karasa ba sukaga hasken flash,dukansu waigawa sukayi,sukaga Dije tsaye rike da wayar Habeeb tana musu hoto,Yana shirin yimata magana yaji tace, "Dan Allah tsaya Yaya sauran Daya,gani nayi kunyi min Kama da wata tunkiya da ragon Inna da nake wasa dasu lokacin Ina karama,sai Naga Anty Sajida sakkkk tunkiyar wallahi.....๐Ÿ™Š Comments with *Alkalamin khady* โœ [7/9, 9:00 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASSO..* ๐Ÿฎ ( _palace of excitation n'd pleasant writer's_) *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 6โƒฃ1โƒฃ Sakin baki Habeeb yayi Yana kallon Dije,dan yama rasa abinyi,itako Sajida iyakar Shaka ta shaka,.Basu ankare ba suka ga ta nufo su tana fadin,"yaya kudan gyara muyi ๐Ÿคณ selfie Yaya saika Dora a secren server din wayarka kowa yaga matanka.Cikin zafin nama Habeeb ya mika hannu da niyyar wafce wayar, aikuwa sai gani yayi ta kwasa a guje zuwa falo,Sajida da tun dazu ta rabu da jikin Habeeb tsabar takaici kamewa tayi a gurin,shi kuwa rufa Mata baya yayi,zagaye falon suka kamayi,inda daga karshe ya cafke ta,ya shiga kokarin kwace wayar,boyeta tayi a jikinta, hakan yasa ya matseta tare da kokarin lalubar wayar,har suka fada saman kujera,mutsu-mutsu ta shiga yi,ya rasa yadda zaiyi da ita,Dan haka yafara Mata cakulkuli,dariya take yi sosai tana gaggantsarewa,shi kuwa hakan datakeyi ya Fara jefa shi cikin wani yanayi,sosai take shigewa jikinshi,Wanda hakan ya Kara canza akalar lamarin,Wanda yasa suka Manta da batun waya suka shiga romancing din juna. Cikin wannan yanayin Sajida ta iske su, Wanda tsabar bakin ciki Bata San lokacin da taji hawaye na zubo Mata ba,Dan haka ta nufi kofar fita,cike da Dana sanin zuwanta part din,gaskiya wannan plan din na mummy Sam ba basira a ciki,gara Nima nasake taku,wallahi saina ci uban yarinyar nan,haka ta karasa bangarenta tana ta sakawa da kwancewa,tare da kudirewa ranta saita ci uban Dije. Su kuwa tsuntsaye sosai suka shagala,inda suka kasa jurewa har Saida suka Isa babbar head quarter,sosai suka samu nutsuwa,sannan suka yi wanka,magani Dije Tasha yayi Mata allura Nan ta zube a jikinshi tanata mishi shagwaba,shi ko duk yabi ya sukurkuce Mata Dan a rayuwa Yana son mace Mai shagwaba,Dan haka ya kyaleta suka ta shan shagalinsu har bacci ya dauke Dije. ******* Yau Akayi sunan Yusrah,inda yaro yaci sunan Daddy wato,(Khamees) suna kiransa da sudais,sosai akayi shagali,kowa yayi rawar gani,domin kuwa yaro yaga gata,su mamy da Daddy sun yi rawar gani hakama Habeeb,bare Kuma angon karni.Sosai su Dije suka dau wanka,ansha pic kala-kala,sai muce Allah ya Raya sudais. ***** Yau kwana biyu da yin suna, Alhamdulillih! Jikin Dije ta Dan ji dadin shi ko Dan treatment din data Samu kwana biyu,zata iya cewa tun ranar da Sajida ta shigo part dinta basu Kara haduwa ba,sai ranar suna, tasan abinda tayi matan Nan ne yasa ta yin shuru kwana biyu,Kuma dama tana sane tayi hakan,gobe ma ta Kuma. Tana zaune ita kadai,taji duk zaman ya dameta,gashi mama mariya Bata Nan,Dan taje gida wani biki da akeyi,Wanda su kansu su Dijen su so zuwa Amma kememe mazajen suka hanasu,ganin ta gaji da zaman ita kadai gashi Sha biyu ne yanzu na rana,Dan haka ta yanke shawarar tafiya gurin Zainab Dan ta Dan rage lokaci,fitowarta kenan tana shirin rufe kofa ta tsinkayo tahowar Sajida ta nufota,dakatawa tayi da rufe kofar inda dai-dai Nan ta karaso,tana isowa Dije tace, "Ah Aunty,kece mu shiga Mana",duk da tasan da akwai abinda ya kawota,Amma ganin Bata Nuna ba yasa itama ta bita hakan,ba yabo ba fallasa suka shiga,inda Sajida tana shiga gadan- gadan ta nufi gaban T.V din dake manne a bango,ga mamakin Dije gani tayi Sajida ta fito da muciya daga jikinta tahau farfasa kayan wajen,duk abinda takeyi Dije na kallonta Bata Kuma yi yunkurin hanata ba,Saida ta tabbatar ta fasa duk wani abu datasan zai fashe,sannan ta tako zuwa gaban Dije,wani shu'umin murmushi ta sakarma Dije kafin ta juya tace,kinyi kuskure khadeeja,Habeeb na Sajida ne ita kadai,naso kin bar gidan Nan salin alin tun kan na Nuna Miki kalata,Amma Naga bakyajin magana,kin samu guri kin mike kafafu,to ki sani kishi da mace kamar Ni ba abune Mai sauki ba,Dan haka ki jira abinda zai biyo baya,tana Gama fadar hakan ta juya ta fice,yayin databar Dije tsaye da tsabar takaicin barnar da tayi mata. Zama tayi saman kujera,tare da dafe kanta,yayin da takejin wani tukukin bakin ciki na taso Mata,bawai na komai ba,sai na barnar da Sajida tayi Mata,amma babu komai wallahi zata San tayi. Ji tayi an turo kofar da sauri,yayin data tashi a firgice tana kallon kofar,Habeeb ne sai Sajida a bayanshi,gani tayi Yana Binta da kallo,inda ita Kuma ta maida kallonta ga Sajida,gani tayi ta sakar Mata murmushi,a ranta tace,hmmmm! Na fuskanci baki sanni banne har yanzu kalata Daya Kika sani Bari na Nuna Miki na biyun,Habeeb na shirin yin magana,yaji Dije tace, "Haba Dan Allah Aunty! Yanzu Saida Kika fada Masa duk abinda ya faru? Kin San halinsa yanzu hankalinshi zai tashi,shiyasa nace kada ki fada Masa Dan nasan halin sa yanzu zai damu,Ni Kuma bana son ganinshi cikin damuwa,kin San masu irin lalurar mu in ta taso barna mukeyi,Ni yanzu babbar damuwata ma Bai wuce tunanin wace barna zasu sani nayi Nan gaba ba,gashi bani kadai ba,Kar su sa mafarki da burin mijina ya zube,amma Dan Allah Yaya kodaa sun taso kaga nafara barna,kada ayi kokarin hanani Dan nasan bazasu cutar Dani ba,ke Kuma Aunty pls Dan Allah kidaina sanar da Yaya irin wannan lamarin,Kinga mijin mu ne ya fita nema,Bai kamata mu dinga daga Masa hankali ba, yakamata mu dinga Masa addu'ane a duk lokacin da ya fita,Dan haka Yaya ka kwantar da hankalinka ba abinda ya faru banji ciwo ba garin fashe-fashen Ina lafiya baby'nka ma lafiya yake,takร rasa makaganar tana Kama hannun Habeeb tare da dorawa saman cikinta ta shiga yawo dashi....... Dan Allah ku Kara hakuri,Ni kaina na Matsu na Gama muku book din Nan wallahi. *Alkalamin khady* โœ [7/9, 9:02 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ AWESOME WRITER'S ASSO.. ( place of excitation n'd pleasant writer's) TAME GARI NA Khadeeja Usman 6โƒฃ2โƒฃ Sosai ta shiga tashin hankali da Jin kalaman Dije na karshe,Wanda tsananin firgita da jinsu yasa mamaki da Kuma takaicin maganganun yarinyar na farko suka bace a kwakwalwarta,kalaman Habeeb ne suka dawo da ita daga duniyar tashin hankalin data fada,ji tayi Yana fadin, "Haba baby! Meyasa haka? Nidai zan iya jurar komai a wannan larurar taki,Amma bazan juri salwantar unborn dina ba,Dan haka ya Zama wajibi muje gurin masu magani Dan a rabaki dasu,Dan Kar wataran su cutarmin dake". Shigewa tayi jikinsa,inda cikin sigar shagawa tace, "Ah ah my Yaya! Kada ka Kara furta cewa zaka rabani da su,Dan idan sukaji ka wallahi sai wani bakai ba,Dan kasan dai fada da aljani ba Dadi,kawai dai sukan sauke fushinsu ne akan abinda ya Bata musu,Amma ka taba gani sun cutar Dani"? Yana shirin yin magana,ta Dora yatsanta saman bakinsa shhhhhh....alamun yayi shuru,kada kace komai Yaya,Dan maganar daka fada dazu na batun rabani dasu ma,sun ruga da sunji komai,Dan haka sai nayi yaki wajen Basu hakuri.Tunda yaji ta furta haka ya wani canja kalar fuskarshi ya koma kalar tausayi,tare da fadin Dan Allah baby ki Basu hakuri wallahi nasan karonmu dasu ba Dadi,bisa kuskure na furta kalaman rabaku,ban San tare aka haifeku ba,wallahi ban son tuna ba......" Katseshi tayi ta hanyar fadin, "kada ka damu yaya,ai Kai na jikina ne yanzu bakada matsala dasu,Dan sun Riga da sun sanka,sun San matsayinka a gurina,Nidai tunanina kawai wannan barnan ya za'ayi a gyarata? Tayi maganar cikin sigar tambaaya. "Baby wannan duk ba wata matsala bace kada ki damu,yau za'a canza wasu insha Allah, bari ma na Kira wasu collogue na wani company da suka shirya Mana office dinmu su zo suga yadda za'a Kara tsara wurin kinji,fatana Allah yabaki lafiya. "Ameen yayana!Dije ta fada tana me kashewa Sajida ido Daya,wadda ya zuwa yanzu Sam Bata fahimtar wani abu da sukayi, maganar cikin Dije ita ta tsaya Mata arai,dawowar tunaninta, shine yayi dai-dai da kashe Mata ido Daya da Dije tayi,gani sukayi ta juya ta fice tare da fashewa da kuka.Dukan su basusan dalilin kukan ba,ita dai Dije abinda ta bari, tana kukan ne Dan ganin batayi nasara ba,duk da batasan me ta fadawa Habeeb ba,illah dai tayi farin cikin kashe gobarar datayi duk da batasan mafarin tashin ta ba. Ajiyar zuciya ta sauke,tare da fadin, "Yayana pls kaje kaji matsalar Aunty,kaga ta fita tana kuka,ta karasa maganar tana shafar gefen fuskarshi,Kama hannun nata yayi ya sumbata kafin yace, "Ki kula da kanki kada ki taka kwalba,zan Kira yanzu zansa a gyara. ******** Yana shiga ya isketa tana kuka,ya jima tsaye sannan ya karasa saman kujerar,tallafo ta yayi zuwa jikinshi,amma me? Saita shiga zamewa,tare da buge hannunshi,cike da mamakin abinda tayi mishi ya tsaya Yana kallonta.A nata bangaren kuwa,tsananin takaici da wata irin tsanar shi taji ya ratsa zuciyarta,gani takeyi yaci amanarta,tunda har yayiwa Dije ciki,gani takeyi ya daina sonta kwata-kwata,Dan haka ta Kara tsananta kukanta,shiko yama rasa me zai ce Mata,Dan haka ya zuba Mata ido kawai Yana kallonta. Itako saka kawai takeyi da warwara Dan batasan ma abinda zata yi ba tukun,duk wani abu data kulla akan yarinyar Saiya warware,ta dauka Kiran Habeeb da tayi ta fada Masa cewar yazo ga Dije Nan aljanunta sun tashi harta farfasa kayan dakinta,ta dauka zatayi nasara Habeeb ya Kora Dije gida,tunda yasan wahalar da suka Sha a gidan da ita,Amma Kuma sai labari yasha bambam ta tonowa kanta abinda zai iya zamar Mata ciwon zuciya. Ganin taki daina kukan ne,Kuma taki bashi damar jin matsalarta, yasashi tashi ya fita Dan Yin abinda ke gabansa. Yana fita ta Kara fashewa da kuka,tare da daukar waya ta Kira mahaifiyar ta,tana dayawa cikin kuka tafara fadin, "Na shiga uku mummy! Na mutu, wallahi mummy I will die, she's pregnant mummy"! Cikin sanyin murya tace, "Kinga ki nutsu kiyimin bayanin abinda ke faruwa,Dan ban fahimci inda maganar taki ta dosa ba? Cikin Kuka ta labartawa mahaifiyar ta abinda yake faruwa. Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace, "Sajida abinda zance dake yanzu shine,kawai kiyi hakuri,kiyi naki 'yan dabarun,Dan wallahi Ni kaina Ina cikin matsala,Dan mahaifinku Ashe ya Dade da yin aure a boye ban sani ba,duk tafiye tafiyen dayake cewa yanayi Ashe suna tare,jiya da daddare sai gashi ya dawo tare da matar harda yara hudu Kuma duk maza,Ni gashi duk taronku Mata Allah ya bani,Kuma ke kadai nasamu Kika auru,Dan haka kiji da kashe taki wutar nima inyi kokarin neman ruwan kashe tawa,tana kaiwa Nan ta kashe wayar. Wani kukan takara dasawa zuwa can ta mike,tare da share hawayen ta,tabbas zata dau mataki,babu macen data Isa ta haihu da Habeeb,tunda ta tabbatar yanzu ba ita ba haihuwa,yanzu wazai Bata shawarar? Wa take dashi yanzu,Dan ita Sam Bata wani damu da Jin auren mahaifinsu ba,Dan dama ai yasaba,Banda abin mummy ma meye na wani kishi!( Niko nace hmmmm sajida ai shi kishi ba ruwanshi da tsufa... Fata dai ayi Mai hankali da tsafta.) Haka ta gaji ta mike ta shiga nemarwa kanta mafita. ******* Tunda safe take leke ta window tana Allah-Allah Habeeb ya fita,Dan yau dakin sajida yake,sai wajen karfe goma sannan taga ya fito,cikin shigarshi ta manyan kaya dinkin zamani,yayi Mata matukar kyau,sai dai fa yau bataga Yar kadaferiรฑ anzo yin rakiya ba,ko lfy oho musu! Ita dai burinta ya fitan,sai da taga megadi ya bude Masa kofa ya fita itama ta koma ta Kara kimtsawa. ๐Ÿ˜ณ Karamar jaka trolly Naga Dije ta jawo,kome zatayi da ita oho? Direct part din Sajida ta nufa,tana zuwa ta tura kofar,zaune ta ganta kan kujera ta Dora kafa Daya kan Daya tana yin breakfast,Jin an bude Kofa yasata maida hankalinta ga kofar Dan a tunaninta ma Laila ce da sukayi zata zo yanzu. Kallon Dije tayi data Sha dogon hijabi har kasa,sannan ta tsaya Mata a ka ta rike kugu da duka hannunta biyu sai wani zare Mata ido takeyi,cikin ko in kula tace "malama ke Kuma lfy? Kika zo kikayi ma mutane tsaye a ka". Hmmm "lafiyar kenan! Dama zuwa nayi na Dan taba kuruciya,Dan na kwana biyu ban tuna baya ba". "Kamar Yaya kenan? "Kada ki damu, zuba ido kiyi kallo,gani tayi Dije ta cire hijabin jikinta,ai da sauri Sajida ta mike,ganin Dije saye da biri da wando Kuma tied,Bata Kara sarewa ba Saida taga Dije ta zuge jakar data shigo da ita,muciya ce da tabaryar karfe,ludayin Miya pock,da duk wani abu mai kalar makami,Dan haka ta mike da sauri tayi bayan kujera tana fadin,na shiga uku,yau Yan daba ne suka hauro,tana tsaka da haka taji karar bude Kofa,Laila ce ta shigo ta mayar da kofa ta rufe harda sa key,Wai Dan Kar wani ya shigo asami akasi yaji sirrin da zasu Tattauna akai,da takun kasaita ta karaso falon wadda sai yanzu idonta ya sauka akan Dije dake tsugunne tana fidda kayan aiki. Waigawa tayi ta hango Sajida make bayan kujera,alama Sajida take Mata da Dije,hakan yasa ta dau haske,inda take cikinta yabada kuuuuuuuu ...Dan Bata Manta karon wancan lokacin ba,kamar barauniya a hankali ta zame takalmin kafarta ta lallaba Sadaf Sadaf ta nufi mabuyar sajida. Duk abinda sukeyi Dije na kallonsu Amma ta share,tabaryar da muciya ta dauka,inda ta shiga aiki kamar yadda sajida tayi Mata,sosai tayi barna itama har Saida ta gaji,su kuwa su Sajida da zarar sunji karar fashewar abu sai su Kara curewa waje Daya. Zama tayi tana maida numfashi,sannan ta Fara magana tana fadin,yanzu aiki ya kammala saura yiwa bil'adama bille, Jin abinda tace yasa su Sajida rudewa da neman mabuyar datafi ta inda suke,kansu ne ya hadu ji kake kummmmmm, kowacce hannunta tasa ta toshe bakinta tare da matso kwallar azaba,a cikin wannan halin Sajida tayiwa Laila alamar ta Bata wayarta,da kyar ta lalubo ta cikin hand bag ta Mika Mata, number Habeeb tasaka ta shiga kiranshi cikin rudewa,Kira wajen biyar tayi Masa amma Bai dauka ba Nan ta Kara tsinkayo muryar Dije tana fadin yauwa Bari mu tashi mu Fara aiki Dan mu kammala da wuri,saboda yau zamuyiwa Mai martaba gyaran fuska......... *Alkalamin khady* โœ [7/9, 9:03 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASSO....* ( _Palace of excitation n'd pleasant writer's_) *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 6โƒฃ3โƒฃ Banda zufa ba abinda ke karyo musu gaba dayansu,wayar ta sake Kira tare da fadin "Dan Allah ka dauka Mana",tana Fadi tana yarfa hannu,harta Kiran ya Kara yankewa Bai dauka ba,Nan suka Kara jiyo muryar Dije tana fadin, "Wai Kuna inane,Akuyatu"?kuyi sauri ku Kira su aunty arwanatu,da Yaya lugudanatu,ke nama Manta in ki biya ku taho da tumakatu 'yar sarkin wanzamai,da kawu kwaya-kwaya Dan Naga yafi iya irin na zamani,ku iso da wuri Dan Allah Kar Mai martaba ya gaji da jira ya Fara tsinke gashinshi da hannunshi. Sosai cikin sajida ya bada wani sauti,ji kake kuuuuuuuu.....kallonta takai ga Laila taga yadda ta hada zufa ga wani marayan kuka da takeyi,tasa hannunta ta toshe bakinta,da sauri Sajida ta Kara Danna lambar Habeeb Allah Allah takeyi ya dauka. Shikuwa Habeeb silent yasa wayarsa ya shiga wata tearter ne,kuma koda ya fito ya Manta Bai maidata normal ba,sai zuwa can ya tuna ya daukota,Yana daukowa Kiran sajida na katsewa, kasancewar bayada number,yasa shi niyyar sharewa,Amma Kuma Saiya ga missed calls Kuma da number,hakan yasa shi tunanin Kiran number yaji ko waye,Yana Kira kuwa yaji muryar sajida cikin tashin hankali tana fadin, "Please Habeeb come and help us,wlh zata kashemu,Wai bille zatayi mana,Dan Allah ka taimaka kazo Yan......Bai ko karasa Jin abinda take fadiba yaji wayar ta yanke.Cikin kidima ya fito a office,kacibis sukayi da Naseer ya shiga tambayarshi lfy?,Sam yakasa bashi amsa illah fada mishi da yakeyi sun zo...sun kawo ziyara,cike da rashin fahimtar idan maganar sa ta dosa ya kalleshi Dan neman Karin bayani,Amma Ina! Har yakai parking space ya shiga mota,cike da mamaki yabi bayanshi shima a tashi motar, kasancewar ba Wanda yasan abinda ke faruwa a gidan hakan yasa kowa dayaji irin horn din da ake bugawa hankalinsu ya tashi,duk suka firfito suka tsaya Jin Mai zai faru. Direct part din Sajida suka ga Habeeb ya nufa a guje,kowa Saiya rufa Masa baya,gani sukayi ya tsaya cakkkk....kome ya tuna oho? Baya yayi sannan ya jawo Naseer ya tura shi gaba tare da fadin, "Please bros ka taimaka ka shiga wallahi mutanen khadeeja ne suka tashi sun rutsa Sajida a ciki,ban San meke faruwa ba,Dan tunanina kada Susa tayi abinda zai Kai ga salwantar abinda ke cikinta,kaga ba ita kadai ba......katseshi yayi ta hanyar fadin, "Ai wallahi Inka ganni a lahira kaini akayi,ka Manta irin azabar da muka Sha,sannan kakemin maganar Wai in shiga to Kai me zai Hana ka shiga tunda matarka ce a sunfi saninka a kaina".... "Ba Wai batun haka bane,kaga Kai ka fini abin Nan shine nace,me zai hana Kai din ka shiga Inya so in kaga abinda ke wakana saika kiramu" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka. "Anki shiga din' nace Anki shiga din,wato Kai kaki Ni ka turani,toh Baga su mamy ba,su shiga Mana Dan ban San a yanayin daka iya riskarsu ba,Dan haka su da suke mata,Kuma manyanmu,su Fara shiga kawai mugani. "Dan uwarka bazan shiga ba,Ni nace yaje ya auro irin aljanu,aiga 'yar uwarta Nan ita ta shigan Mana,sai Ni ko,salon a je a hada Dani tunda kun gaji da ganina to alkur'an ba inda zani,Jin muryar su mamy na tashi yasa su Sajida bare baki tare da sakin ihu.Sosai Habeeb ya Kara kidimewa,inda ya nufi kofar kamar gaske,Yana tabawa yajita Gam,Dan haka ya shiga murzawa, Muryar Dije ya jiyo tana fadin,an Gama ranka ya Dade za'a hada harda na wajenma,ai da gudu Habeeb ya kwasa ya nufi bakin gate su mamy ma duka suka rufa Masa baya,suna kaiwa Nan suka tsaya maida numfashi,mamy ce cikin mayar da numfashi ta shiga tambayarshi meya sa shi gudu,? Shima cikin haki yace, cewa sukayi Wai a hada damu". Dafe kirji mamy tayi tare da fadin, "Me za'a hada damu din? "Nima ban sani ba,Amma Inaga salon azabar su ne na aljanu". "Oh ni karima na shiga uku Wai ma waya tabosu ne?" "Wallahi mama Inaga sajida ce Dan ga motar kawarta nana da alama tare suka jangwalo su". To basai abin ya Kare akansu ba mu miye namu a ciki,cewar yusra dake kokarin sauke Sudais tana mikawa Naseer, Zainab ce tace ai kun San lamarin iska,su kan me uwa da wabi sukeyi.Haka dai suka tsaya curko curko,ganin hakan yasa baba Mai gadi ya karaso tare da tambayar su meke faruwa,sosai suka Masa bayani,inda ya tayasu jimami tare da fadin akwai shawara in kun amince,me zai Hana maza fade ta muji. " Dama nace Mai zai Hana a kirawo irin malaman Nan masu rukiya! Kwarai kuwa ka kawo shawara cewar mamy Bari na Kira malam buba,ai ko tsayawa batayi taji me zasu ce ba ta matsawa malam buba Kira,Yana dayawa ta sanar dashi ya zo gidanta ba lafiya zai cire aljanu,Nan yace Mata Yana zuwa. Sadaf Sadaf suka dinga tafiya kamar barayi,har suka karasa bakin kofar,suna zuwa da kyar Habeeb ya Dan matsa ta gefen window Wai ko zai gano wani abu,Amma ba halin ganin Dan ko Ina a rufe yake ruf, su kuwa su Sajida,suna can Banda kuka ba abinda ba sukeyi, musamman da sukaji Dije na cewa a hada Dana wajen ai duk sai suka Kara karaya. Itako Dije Saida ta tabbatar ta huta sannan ta yunkura tare da fadin,Yaya gurguwa tashi muje mu Fara kaddamar da aikinmu,tana mikewa ta shagide kafa da mere baki ta dauko lafciciyar wukar Nan ta cikin set din wukake,wato ta Sara Kashi,ta nufi bayan kujerar,Sajida data Dan zuro Kai Wai taga ya ake ciki taga Dije a haka ai saita mike tayi tsalle saman kujera,hakama laila,Nan suka shiga zagaya falon,itako Dije dada karkacewa ma takeyi tana fadin,haba bil-adam ku tsaya Mana ayi muku komai cikin sauki,na yantse a hankayi janyi muku,Kuma bajan bayi jininku ya juba a kasha ba duk Jan lashe.....wata uwar sufa Sajida tayi Saida hannunta ya bugu,Amma Bata ko tsaya Jin zafin da taji ba ta nufi kofa Allah ya Bata sa'a ta murza key ta bude,tana fitowa su Kuma saiga su mamy da malam buba............ ๐Ÿค” To fa me zai faru kuma gaba! Ga malam ga aljanun Dije ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ *NIDAI BA RUWANA YASEEN* *ALKALAMIN KHADY* โœ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ AWESOME WRITER'S ASSO.. ( Palace of excitation n'd pleasant writer's) TAME GARI NA khadeeja Usman hakika duk inda masoyi yake yanada Dadi,masoyana kune abin alfaharina, khadeeja novel fans daga 1 har zuwa 10 na yaba da kokarin comments dinku,da sauran group din da nake ciki,Ina alfahari da dukan masoya tame gari nagode sosai masoyana ๐Ÿ˜˜ 6โƒฃ4โƒฃ Yana gaba su mamy na binsa a baya kamar barayi,itako Dije sunata faman zagaye ita da Laila a falon,Dan cewa tayi an Kara musu karfin hukunci yanzu Kam harda aski za'a musu,umarni ne daga Mai martaba. Ganin shigowar su mamy,yasa Laila wage baki iya karfinta tana ihu,tana Kiran azo a taimaka Mata,Wanda sai a wannan lokacin Dije ta ankare da jama'ar da suka hallara a falon.Ji tayi ance malam gata Nan cewar mamy tana Nuna Dije,itako Dije ganin haka yasata sulalewa kasa tare da rufe ido Wai ita ta Suma. Shi kuwa malam tunda ya kyalla ido yaga Dije Fara tas da ita,gashi tayi 'yar kubul- kubul,fatar ta sai sheki takeyi,saboda jaririn cikin dake jikinta,hakan yasashi lasar baki kamar tsohon maye, musamman Daya Kai duba zuwa kirjinta ganin yadda yake cike. Juyowa yayi ya fuskanci su mamy tare da fadin,"gaskiya Hajiya lamarin yarinyar Nan babba ne,domin aljanun dake kanta sunada mugun yawa,Dan wallahi bazan boye muku ba 'yan daba ne akanta,Kuma 'yan daban ma rukakku,masu zukar wiwi. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,yanzu dama a aljanu akwai 'yan daba?"cewar mamy. "Sosai ma kuwa hajiya,Kuma su matsalar su 'yan Sara suka ne,dan haka sai anyi da gaske kafin a fidda su daga jikinta,Dan haka sai kunyi hakuri kun Dan fita daga waje,Dan ba karamin artabu zamusha dasu ba",ya karasa maganar Yana gyara babbar rigarshi,tare da Kara Saba jakarshi a kafada. Mamy ce tafara ja baya,tare da kallon sauran,Nan kowa yayi hanyar waje, Banda Habeeb Daya kafe,yace ayi komai a gabansa,Saida mamy ta janye shi tare da fadin inshi yagaji da rayuwa,to su suna sonsa a raye,badan ya so ba yabi su suka fita,bayan malam yabada umarnin a kulle kofar ta waje har Saiya bada umarnin a bude tukunna,aikuwa hakan akayi,duk suka fita yayin da shi Kuma ya sauke jakarshi ya nufi inda Dije ke kwance. Tsaye yayi bisa kanta Yana me Kara Kare Mata kallo,Wanda hakan da yayi yasa Dije Dan bude ido Daya,karaf idonta ya sauka kan fuskarshi Yana lashe baki,ji tayi kamar ta tashi ta zura a guje,domin tasan yau asirinta ya Gama tonuwa.Tana tsaka da wannan tunanin taji hannun mutum a jikinta Yana shafata,tare da fadin,"gaskiya Hajiya kin biyani,yau can kwashi gara Danni dama nafi son irin wadannan iskar masu bugar da mutum,yanzu Dana Shaka Mata hodar Nan zansha budirina,inta dibar lamari,Ina Jan lokaci irin wannan yarinya haka.....jar fata kamar baturiya. Tunda Dije taji ya Fadi haka ta ramfo shi,wato irin malaman Nan ne masu fakewa da rukiya suna cutar da yaran mutane,to ko yau zakasan ka kawo kanka,Dan lamarin a kanka zai Kare,ta fada cikin zuciyarta.Shikuwa malam buba,tuni ya juya ga jakarshi ya hau lalubo hankachif din dazai Shaka Mata,daukoshi yayi tare da sakin murmushi sannan ya dauko wani ruwa a 'yar Karamar kwalba,Wanda zai Shaka Mata ta farfado bayan ya Gama biyan bukatarshi....sai dai me?Yana juyowa yaga Dije tsaye rike da kugu tanata rarraba ido,yadda yaga tana zare idon yadan tsorata,Amma yasan duk wannan abinda takeyi Daya samu nasarar Shaka Mata,to batada katabus,nufota yafara yi,amma saiyaga itama tana matsoshi,hakan yasa yaja ya tsaya zuciyarshi na bugawa kadan kadan,Amma ya dake,gani yayi gadan-gadan take tunkaroshi tana yake hakora tare da dariya kyal-kyal-kyal,jikinsa ne yadan Fara rawa kadan,itako Dije abinda take so kenan,aikuwa saita birkice tana biyoshi shikuwa ya shiga ja baya,aikuwa sai gani yayi Dije ta kwasa da gudu ta Fara zagaya falon,inda tayiwa inda ta ajiye makaman yakinta tsinke,muciya ta dauko tare da wannan wukar,ganin ta nufo shi da gaske,yasashi wage baki ya shiga karanta ayatul kursiyyu da karfi,ji yayi tayi รงaraf ta cafke taci gaba da karantawa,aikuwa guri ya Kara kacamewa,sosai jikinsa yahau Bari,itako Dije Kara lankwashe baki tayi tare da fadin,"bakai malami Mai fitar da aljanu ba! To yau kaina zan fitar maka da naka,wato ka fake da Allah kana zaluntar iyaye kana lalata musu yara ko?,to daga yau bazaka Kuma ba,Dan billen danayi niyar yi musu Kai zanyiwa shi. Zubewa yayi a kasa bisa gwiwoyinsa,Yana fadin,"Dan girman Allah kiyi hakuri,wallahi ban San cewa ku gawurtattu bane ba da ko kusa bazan Fara zuwa ba". "Karya kakeyi ka sani,tunda har kasan cewa mu 'yan daba ne,to kawai gara na farde cikinka yau musha jini,sannan muyi soye da namanka". "Dan girman Allah kiyi hakuri, wallahi ba laifina bane Hajiya ce ta kirani". "Ai nasan ita ta kiraka,Amma meyasa data kirakan bakace bazaka zoba,to ka sani,yau din Nan basai gobe ba zan kaddamar maka,Dan saina rabaka da duk wata gaba ta jikinka". Ba Kuka yake ba,amma yanayin dayake ciki garama ace kukan yakeyi,Dan haka ya shiga rokon Dije,magiya sosai ya shiga yi Mata ita kuwa tana Kara fada Masa nau'ikan azabar da zatayi Masa,Saida taga ya Fara fitar da kwalla,sannan ta bashi umarnin ya mike tsaye,Yana mikewa tace yayi rawa,tsayawa yayi Yana tunanin ta yadda zai Fara,Dan marabinshi da yin rawa tun Yana yaro,Dan haka yanzu baiko San ta Ina zai Fara ba, kasancewar ya jima Yana rokonta harya hada zufa,shiyasa ya cire hularshi ya ajiye gefe,aikuwa Dije tayi ido hudu da rantal din kansa,take muguntar ta Kara motsawa,Yana tsaka da tunanin taya zai Fara rawa,gara kawai ya saita hanya ya fece,aikuwa sai ji yayi kwallllll akansa,Dije ta kwala Masa muciya akansa,ji yayi dukan ya ratsa dukkan jikinshi Dan ji yayi kanshi ma kamar ba'a jikinshi yake ba,Yana so yayi ihu ba halin yi,saboda Kar a jiyo malam na kuka. "Zakayi rawar ko bazaka yiba"? "Zanyi wallahi,zanyi" ya fada Yana me gyara babbar rigarshi,Nan ya shiga rawa babu kida,haka yaita tikar tawa abin ba fasali,itako Dije Dan dariya harda faduwa kasa. ******** Jin shuru yasa kowa tunanin ko lfy?, Shikuwa Habeeb Sam hankalinshi ya kasa kwanciya,Dan shi bai yadda ace malami ya nemi a barshi ya kebance da Mara lfy shi kadai ba,Dan haka kawai ya nufi kofar,yanaji mamy na kiranshi Amma yayi shuru har Saida ya bude kofar,dai dai malam yayi wata irin malkwada da Dije tasashi yayi,Wai a cewarta rawar 'yan Indiya ce,a indiyan ma 'yan Tamil Nadu keyi irinta...... *Alkalamin khady* โœ*AWESOME WRITER'S ASSO..* (palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* NA KHADEEJA USMAN 6โƒฃ6โƒฃ Sakin baki yayi ya tsaya Yana kallon ikon Allah,yayin da Da malam ya takarkare Yana tikar rawa Yana wani lankwashewa,Sam yama Manta da wata Dije agun ya shagala da kallonsa yanata malkwaya gashi Kuma Yana kuka,yana tsaka da yin rawar kawai yaga ya zube tare da fashewa da kuka,sannan ya kalli Dije yace,"wallahi sai dai in kasheni zakuyi ku kasheni Dan na gaji,Ni ba Dan oroso ba,Amma an maidani Dan cashiya,wallahi na gaji,Dan girman Allah kiyi hakuri wallahi na tuba,ban San cewa ku hatsabibai bane,da ba abinda zai sa da aka aikamin goron gayyata inzo",ya karasa maganar Yana fyaรงe majina da gefen rigarshi. Wani juyi Dije tayi,ta dira gaban malam,Wanda yasa Habeeb antayawa a 360 ya Isa gareta ya rikota,fadawa tayi jikinsa,inda ta rufe idonta da suketa faman Marmar,Wanda badan Habeeb a rude yake ba,daya fuskanci halin da take ciki na likimo,Amma shi kanshi a tsorace yake,Dan jikinshi Banda rawa ba abinda yakeyi,Dan In ba Dan Kar ace yayi karya ba, da Saiya ce wani irin nauyi yaji ta Kara,(Niko nace Kai Habeeb Banda zuki ta malle๐Ÿ˜‚),yasan hakan Bai rasa nasaba da aljanun dake kanta a yanzu. Shikuwa malam ganin Dije ta zube,aikuwa ya suri jakarsa ya antaya a guje,su mamy dake labe bakin kofa suna son shiga suna Jin tsoro,sai ji sukayi rakacam,malam yayi ciki dasu,kafin suyi wani yunkuri suka tsinkayi muryar malam Yana cewa,"kada kuga laifina wallahi aljanun 'yan daba ne,da 'yan rawar solo,kudai kuyi ta kanku,nikam nayi Nan.mamy ce tayi kokarin mikewa,tare da shafa gefen bakinta inda taji Yana Dan Mata zafi,jini ta lakato aikuwa ta maida kallonta ga Sauran,ganin goshin yusra tayi alamar hakora gashi shima ya dan fashe,cikin hasala tace"ke Kuma waya cijeki? "Mamy ba kece Kika kafamin hakora ba". Dafe kirji tayi tare da fadin,"Ni Kuma Yusrah?kada kimin sharri,kinaji malam yace aljanun 'yan daba ne,waya sani ko su suka Miki aik.....Bata karasa ba,ta hangi Sajida da Laila ana kiciniyar tashi,Dan Suma ragas sukayi,suka Fadi,cikin rashin sa'a Sajida ta fada kan Laila,gashi su Sajida Abu ba kadan ba๐Ÿ™Š,ita Laila dukta kuje,itako Sajida tana kyautata zaton tayi targade a yatsanta na kafa,Dan taji lokacin da yayi Kara,hakan yasa ta gagara tashi daga kan Laila,wadda nauyi ya isheta take ta kokarin tunkudeta,ganin hakan dasu mamy sukayi,yasa su karasawa suka hadu ita da yusrah suka janye Sajida da kyar,itako Zainab da Naseer suna gefe,Banda dariya ba abinda sukeyi,ganin su mamy sunja gefe sun tsaya sunata haki,cikin hasala mamy ta juyo tace," ku Kuma uwar me kukeyiwa Dariya? Naseer ne cikin Kara guntse dariyarsa yace,"babu komai mamy kawai dai dariyar ce tazo Mana lokaci daya". "Eh lallai nagani ai,Kuma Naga rashin mutunci irin na riqaqqun aljanu,wato abinma harda Nuna bambamci,da sanayya,Kai da suka San kana auren irin godiyar tasu,wato sai suka rabu da Kai da matarka,da Suka rarako malam shine mu suka hada damu,to wallahi ko zasu daddatsani Allah ya isanmu bamu yafe ba"..... zata Kara magana yusra ta toshe Mata baki,tana fadin,"Bari mamy,kada ki Kara jawo Mana jaraba,bamu fita daga wata ba mu afka wata,Nidai ki cireni a Allah ya isan Dan na Dade da yafewa". Ganin tsayiwar bazata fisshesu ba yasasu Kara sadadawa,suka Dan tura kofar,Dan suga meke wakana a ciki,suna lekawa suka hango Dije kwance,shame-shame a jikin Habeeb,yanata tofa mata addu'a,ganin alamun kamar aljanun sun sauka yasa suka Dan Fara shiga a layi kamar masu neman aiki๐Ÿ™‰. Ganin barnar da Dije tayi yasa mamy fadin,"kan ubancan,ai wallahi wadannan sunci uwar 'yan daba, directly a kirasu da 'yan ta'adda wannan barna haka? Sai kace dangin bera lallai dole mu dauki matakan tsaro a gidan Nan Dan abin Naga ba sauki.Duk abinda sukeyi Dije na jinsu,Jin addu'ar ta Gama ratsata a cewarta,yasa tayin wata katuwar Mika da doguwar hamma,[8/24, 11:21 AM] +234 814 016 5919: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *AWESOME WRITER'S ASSO...* (Palace of excitation n'd pleasant writer's) *TAME GARI* Na Khadeeja Usman 6โƒฃ7โƒฃ Dukansu zabura sukayi tare da Kara ja baya,ganin tana kokarin mikewa, harta mike tare da bin falon da kallo ita a zuwan Bata San meya faru ba.ganin tana ta raba idanu yasa Habeeb fadin,"sannu kinji lovely sis". Can kasan makoshi ta furta yauwa,sannan ta shiga tambayar meya faru? Bawanda ya Bata amsa illah wani kallon tsoro data ga suna Binta dashi,hakan yasa a zuciyarta ta furta,lallaia yau da malamin gaske aka kawomin da karyata ta Kare,duk da Banga wannan tsoron a idanunsu ba,yanzu kuwa ji yadda suke want girmama Ni,kamar cikinsu duk nice babba!tana tsaka da tunanin taji ya riko hannunta,tare da fadin,"zo muje kiyi wanka ki gasa jikinki,fatan dai ba inda Kika ji rauni ko?. Gyada mishi Kai tayi tare da kwabe fuska,cikin salon shagwaba tace,"banji ciwo ba my lovely bro sai dai jikina dakemin ciwo,sannan kaina ma musamman keyata da Kuma goshi na"ta karasa maganar tana matsar ido,duk a salonta nason matso hawaye sai dai sunki zuwa. "Ya Salam! Ya furta tare da cewa"to yanzu ya za'ayi kenan? Asibiti zamu wuce in dubaki? "Ah ah,Nidai ka daukeni ta fada tana Kara narkewa. Hakan kuwa akayi,ya shiga nannade hannun rigarshi kamar zaiyi dambe da kato ya sunkuceta,yayin da yabar mutanen Falon da kallon juna.Naseer na ganin hakan yasa Kai ya fice Zainab ta Mara Mai baya,ganin hakan yasa itama yusrah tabi mijinta Nan akabar mamy tsaye dasu Sajida,tsaki mamy tayi itama tasa Kai ta fice Dan tsananin takaicin data Shaka inta tsaya tace zatayi magana,to fa kuka zatayi.Tana fita Laila ta kalli sajida da kunajjen goshi tace, "Gaskiya kawata bazan Kara zuwa gidanki ba,Dan na fuskanci ajali ke kirana Inna sake na amsa Kira na uku, wannan wace irin jarababbiyar yarinya ce,ko ince hatsabibiya,Nidai shawarar da zan baki,kawai ki rungumi kaddara,ki zauna da mijinki da ita kanta kishiya ki lfy,kowa ya iya biya allonsa ai Saiya wanke,Nidai Kinga tafiya ta Dan wlh ban sayu ba baza'a nakasa Ni a banza ba,asa na Kara yin kwantai,ko kafin Sajida ta ankare har takai bakin kofa,hakan yasa tayi saurin Binta danta cimmata,Amma ko kafin takai ga cimmata harta fice,hakan yasata dafe kanta,tare da laluben gurin zama ta zauna tare da kallon dakin taga yadda Dije ta haukata Mata shi, sannan ga muguwar barnar da tayi Mata,tabbas dole ta nemawa kanta mafita,dolene taje gida gun mummy ta Bata shawara. Ita kuwa Dije suna shiga,Bai zame ko Ina da ita ba sai toilet,ruwan dumi ya hada Mata sannan yace tayi wankan Yana zuwa,ba musu kuwa tace dashi to,Dan gara Daya fita din,saboda duk sanda yace suyi wanka tare,wata kunyarshi takeji. Koda ta Gama wankan ta fito zaune ta sameshi kan sofa rike da cup a hannunsa ga magani Kuma a gefe,tuni annurin fuskarta ya kauce ganin maganin datayi,Yana lura da ita Amma ya hade Rai,Dan yasan idan ya sakar Mata fuska,to fa zata kawo Masa wargi,itama hakan data gani yasa ta mayar da takkuban musun datayi niyya,tana yamutsa fuska ta karbi maganin Tasha,bayan ta Gama Sha din baice da ita komai ba,ya Nuna Mata alamar ta kwanta ta huta, hakan kuwa akayi ba musu ta kwanta Dan dama duk ta gaji wallahi. ******* Yau kusan sati da faruwar abun,wato tashin aljanun Dije,sai Kuma yau Sajida tasamu zuwa gida.Da sallamar ta ta shiga falon,ga mamakin ta saita iske duk ahlin nata zaune,hakan yasata karasawa tare da kafe wadda tagani zaune kusa da Daddy'n ta da ido,bayan ta karasa ta zauna ta shiga gaida iyayenta,Nan yake gabatar Mata da sabuwar amaryarsa,Sam bataji komai dangane da hakan ba,illah ma fatan alkhairi datayi musu,Wanda hakan datayi ya mugun bakanta ran mahaifiyar ta,sai Aiko Mata da kantin harara takeyi. Sai kusan azahar suka Sami kebewa da mahaifiyarta inda suna shiga dakin ta zayyana Mata duk abinda ke faruwa.kallonta tayi shekeke,tare da fadin to yanzu da Kika kwaso jiki Kika taho uwar me zanyi miki?,yanzu ke Dan bakida hankali na fada Miki halin da nake ciki shine Kika kwaso jiki rabe-rabe Kika zo mu jera nida ke,ace wace uwar su waye 'ya'yan,yanzu dubi kannenki su uku muna Nan zaune dasu kullum daga Mai karya yazo sai Mai karairayi,shin ke ko hakan bazai sa ki maida hankali da kwatar 'yancinki gidan mijinki? To Nidai yanzu ba abinda zanyi Miki Dan dama ance gaba da gabanta,Dan wannan da ubanki ya auro nata salon na karuwan Tasha ne,Dan haka kiyi ta kanki inyi ta tawa,kowa tasa ta fissheshi,tunda ke har yanzu kin tsaya yarinya karama tana wasa da hankalinku,haka mummy tayita zazzaga abinda ke ranta Dan haka Sajida Bata wani Sami wata mafita ba,tayi musu sallama tabar gidan. ******* Zama fa yanzu ya canza salo,domin duk wata hanya da Sajida tabi Akan Dije tofa Bata bullewa,hakan yasa tabi duk ta rame ta Kara baki,domin taki kwantar da hankalinta ta fahimci ainihin zaman kishi na islama,itako Dije hankali kwance take rainon cikinta yayin da take samun kulawa tako wanna bangaren,Dan mamy ma tana Dan kula da ita duk da tace ita badan ita takeyi ba,Dan jikanta takeyi,itakam Dije ko'a jikinta. Yau tana zaune a dakinta taji zaman ya isheta,Dan haka ta mike ta nufi compound danta Dan taka,Sajida ta hango ta....... *Alkalamin khady* โœ [8/24, 11:22 AM] +234 814 016 5919: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 6โƒฃ8โƒฃ *Alhamdulillah barka da sallah ga dukkan daukakin musulmi,farin cikin riskar wannan Rana cikin koshin lafiya yasani yi muku typing,har abada bazan taba manatawa da ku ba masoya tame gari sakamakon addu'oinku gareni,Ina matukar godiya da farin cikin sadaukar da wannan page din gareku masoyana,BARKA DA SALLAH* SAJIDA ta hango zaune ta zuba uban tagumi,da sauri ta karasa inda take har tana hardewa,(Niko nace Dije tafi a hankali meye na gaggawa),harta Isa gurin Sajidar Bata San ta Isa ba da alama tayi nisa cikin tunani.Dan tafi tayi Wanda yasa Sajida Dan firgita,ganin Dije a tsaye a kanta ga katon ciki yasata sakin tsaki,itako Dije yi tayi kamar Bata ji me tayi ba,Dan haka taja Daya kujerar dake fuskantar Sajida, kasancewar da alama gurin anyi shi ne da alama Dan hutawar masu gidan,ganin ta zauna yasa ta kallon Sajida tare da fadin, "Aunty waye ya rasu"? Kallonta tayi da mamaki bayyane a fuskarta itama ta jefo Mata Tata tambayar, "Waye yace Miki anyi mutuwa"? "Ah ah ba Wanda ya fadamin,kawai Naga kin zuba tagumi ne,Kuma sai fuskarki ta Nuna alamun kamar an Aiko Miki da sakon mutuwar ne". Wani tsakin Sajida ta Kara ja,Dan takaici ko amsa Bata bawa Dije ba ta mike tabar ta a gurin. Itako Dije saman kujerar da Sajida ta tashi ta mike kafarta,tare da taba baki ta furta a fili ke Kika sani. Ta jima a gurin taji zaman ya gundureta ta mike tayi bangaren mama mariya,can ta karasa yininta kasancewar yau ba itace da girki ba yasa ta share guri tayi zamanta. Itako Sajida tana shiga bangarenta ta dinga Kai kawo tana nemarwa kanta mafita,Dan harga Allah baxata iya jurar zafin da take ji a zuciyarta ba,zuwa can ta samo maganin damuwarta tare da yin murmushi a fili ta furta,yarinya kin Gama yawo. ******* Tunda Sajida ta karbi girki zata Iya cewa Bata sashi a idonta ba,duk da dokar Daya kafa ta haduwa a ci abinci gaba Daya,Amma ganin cewa yanzu Bata damu da cin abinci ba tafi ga kayan marmari dana kwadayi yasa baya takura Mata taci din sai dai yayi ta siyo duk abinda take so din,amma yau tsawon kwana biyu Sam Bata ganshi ba,Bai shigo dubata ba,Kuma ta tabbatar lafiya yake Dan tana hango fitarshi da dawowar shi. Tana tsaka da tunanin meye matsalar taji ya turo kofar ya shigo.Dago Kai tayi ta kalleshi tare da kokarin mikewa Dan zuwa Yi mishi sannu kamar yadda ta Saba,Amma sai gani tayi ya wuceta yanemi guri ya zauna,sororo tayi ta bishi da kallo Amma sai taga ya basar da ita,karasawa tayi inda yake ta zauna kusa dashi sosai,Bai Nuna kulawar komai ba,hakan yasa cikin sanyi ta furta, "Ina kwana! Lafiya ya amsa a takaice. Ganin shurun yayi yawa ita Kuma Bata Saba da hakan ba,Dan ita in ana zaune mutum biyu Bata son taji anyi shuru batare da ana motsa baki ba,Dan haka ta katse shirun tare da fadin, "Wai lafiya kake my lovely bros,Naganka ba yanayin da na Saba ganinka ba, Allah yasa bani na Bata maka Rai ba? Hmmm kawai yace tare da kokarin mikewa ya kalleta ido cikin ido,sannan yakai hannunsa ya tadata tsaye ya tsugunna ya sumbaci cikinta,sannan ya juya ya nufi hanyar fita,har yaje bakin kofa sannan ya tsaya baiko juyo ba yace ki sameni a bangaren Sajida yanzun Nan bana son Bata lokaci,Yana Gama fadar hakan ya juya ya fice. Itako tsaye tayi cike da mamakin sa,da kamar baxata ba sai Kuma kawai tashiga daki,hijabi ta dauko ta fito ta nufi part din Sajida. Koda ta kafin ta shiga ta tsaya tayi knoking daga can suka Bata izinin shiga batare da sun tambayi waye ba, zaune ta iske su a falo manne da juna,yanayin data gansu taji wani Abu a ranta,Amma saita danne ta zauna a daya daga cikin kujerun falon,tana Zama ta shiga gaishesu,Sajida ta amsa Mata da kyar tana ci gaba da shafo sajen dake kwance gefen fuskar Habeeb. Shuru ne ya biyo baya na Dan lokaci,Banda karar TV ba abinda ke tashi. Muryar Habeeb ta tsinkaya ya Kira sunanta, Khadeeja! Daga yanayin Daya kirata ta Dan fuskanci kamar ransa a bace yake,Dan haka ta amsa Masa da na'am,tare da Kara tattara nutsuwarta. Magana yaci gaba dayi Yana kallonta,tunda na aureki na taba ce Miki bana son matata? Cike da mamakin maganar sa wadda tazo Mata a bazata ta tsareshi da ido. "Ba kallona Zaki tsaya yiba,amsa nake bukata. Cikin sanyi ta amsa masa da ah ah! "Na taba fada Miki wani sirrin kwanciyar dake tsakanin mu da ita?" Ah ah! "Koda tsautsayi ya faru a baya na taba ce Miki bana sonta? Nanma da ah ah ta amsa mishi,sbd tafara Jin zuciyarta nayi Mata nauyi da kalaman sa dayake jifanta dasu. "To meyasa Kika goranta Mata,tare da ce Mata Ni na sanar dake ba sonta nake ba auramin ita akayi dole,sannan banajin dadin mu,amular aure da ita,sannan kikayi Mata gorin haihuwa? Kalamansa taji tamkar saukar guduma,Dan haka ta rutse ido tare da budesu tar Akan Sajida,wadda ta watso Mata wani kallo tare da murmushin mugunta,Wanda Nan take Dije ta baro jirgin,Dan haka tayi kokarin danne zuciyarta tare da mayar da kallonta gareshi.murmushin karfin Hali tayi tare da Kara kallon Sajida ta kashe Mata ido Daya,Wanda yasa ta rasa ma'anar wannan kallon,cikin dakiya ta da kwarin gwiwa ta silalo kasa tare da zubewa saman gwiwoyinta ta Fara magana cikin rawar murya irin ta me son yin kuka tace, "Allah ya huci zuciyar saraki,ranka ya Dade banyi hakan da nufin Bata maka raiba,illah mun Sami misunderstanding ne ranar,sai tace min ai ka sanar da ita duk yadda akayi aurenmu,matsama akayi ka aureni,sannan Kai baka sameni a budurwa ba,kadaiyi hakuri ne ka rufamin asiri Wai Dan Ina matsayin 'yar uwarka,sannan Kai cikin Nan ma kaddara tasa aka sameshi,Amma da da yadda zakayi da tuni an barar dashi,kawai Dan baka farga da wuri bane Saida ya girma,hakan data fadamin ne yasa naji zafi shine nima na fada Mata,nace duk abinda ka fada akaina,to duk ka fadesu a kanta,Amma Dan Allah kayi hakuri ka yafemin,bawai na fada ne Dan in Bata maka Rai ba,na fada ne saboda Jin zafin maganganun da akace sun fito daga bakin Wanda nake ganin girma da mutuncinshi fiye da kowa a duniya. Bata tsaya lura da yanayin da suke ciki ba ta juya ga Sajida,tare da fadin, "Ke Kuma Aunty na dauka kin hakura tun a ranar ai,Ashe baki hakura ba,da nasan Zaki fadawa Yaya dana Kara baki hakuri,Amma yanzu Ina me Kara baki hakuri,mu zauna lfy,mu rufawa kanmu asiri da mijinmu,Kinga shi ya fita nemowa,kamata yayi mu da muke gida mu daina shirme,mu bishi da addu'ar Allah ya bashi abinda ya fita nema,ya Kuma tsare Mana shi,Dan Haka Ina dada rokonki gafara akan abinda na fada miki,tana kaiwa Nan ta mike tsaye tare da kallonsu tace nabarku lfy,fatan za'a yafi juna,ta juya ta fice tana dariya ita kadai,Dan ta fuskanci Sajida bom ta hada mata,amma tayi maganinta gobe ta Kuma,shi Kuma zaizo ya sameni ne. Shikuwa Habeeb tun farkon da Dije ta tsugunna bada hakuri,yaga hankalinta,ransa ne ya baci Jin Wai Ashe ma Sajidar ce ta Fara Mata Gori,Kuma ma ta Bata hakuri Ashe,Amma tasa shi yake shrin CI mata mutunci,gaskiya Allah yasoshi,ji yarinya Mai hankali,har tasan ta roki a yafe Mata sannan a zauna lfy. Cikin bacin Rai ya Juyo ya kalli inda Sajida take zaune,wadda tayi mutuwar zaune,domin kuwa ta kurawa inda Dije ta tashi ido bako kiftawa..... *Dominku masoya tame gari,ku Kara hakuri,komai nisan jifa* *Alkalamin khady*โœ [8/24, 11:23 AM] +234 814 016 5919: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *TAME GARI* NA Khadeeja Usman 7โƒฃ0โƒฃ *_To ai hikenan_* Ganin da mama mariya tayi Dije nata bazgo zance harda cewa gwanda da ita Bata haihu ba yasata,karasawa gabanta,tana fadin"haba manyan mata, haihuwar kike yiwa wannan Abu Dan sakarcin banza! Yanzu fa Kika fara..... "Na Fara me? Ciwon ko me? Ai kuwa indai abinda nakeji yanzu na Fara ji ma toko wlh mutuwa zanyi kawai Dan Allah ki kiramin innata".Ta karasa da kyar tana Kara rushewa da kuka. "Ni ba nakudar nake nufin yanzu Kika Fara ba,haihuwar nake nufi Wanda zaiyi dozin biyu ne daga Daya Yana ihu inaga sauran Kuma!,Dan Allah kiyi shuru ki dinga addu'a kinji yi dauriya,ba'ason mace da raki". "Naji,zanyi dauriyar, amma Ni bazan Kuma haihuwa ba,wallahi Kuma idan na samu na haye,duk shegen Daya Dakar mun da sai munyi shari'a dashi,ashe dama haka akeji,wayyo Allah Bari dai in karasa saukar Nan kawai,bude murya tayi tahau karanta ayar da duk tazo bakinta,harda su hadisin da annabi sallallahu alaihi wasallam yace abi uwa sau uku kafin yace abi uba sau daya,. Juya fuskarta tayi ga Habeeb,inda ta ganshi tsaye Yana kokarin daura Mata wani ruwan,Sam bazaka iya bambamce halin dayake ciki ba,tabbas duk Dan da baibi uwarsa ba sai dai muyi Masa fatan shiriya. Muryarta ya tsinkaya tana fadin,"lallai manzo yayi gaskiya,Daya ce a fifita uwa akan uba,Yaya kana Jin abinda nake ji kuwa? Tabbas na amince ka Kara aure Dan Ni nabarwa kowacce mace Kai,tazo taita haihuwa Ni na yafe,kawo kunnenka kaji Yaya in bar maka wasiy.....maganar ce ta makale sakamakon wani nishi Daya taso Masa,wata katuwar kabbara tayi tare da nishi Mai karfi,saiga baby ya fado take ya tsanyare da kuka,Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da fadin Alhamdillah! Kasancewar daga shi sai mama mariya a dakin,Dan yace shi zai karbi haihuwar matarshi,mamy da Daddy na can reception suna jiran tsammani,shiya duba baby'n yaga baby girl kyakkyawa da ita,Dan a take ya hango tsantsar kamarta da mahaifiyarta,ji yayi soyayyar yarinyar data mahaifiyarta na ratsa dukkan sassan jikinsa,kayan asibitin da suke bayarwa aka sawa jaririyar sannan aka gyara Dije wadda ya zuwa yanzu ba baka sai kunne,Banda haushin Habeeb ba abinda takeji,shi kuwa murnar ganin ta sauka lfy ya duba yaga Kuma batada matsala yasa yayi Mata 'yan allurai danta huta,ya makale baby babu ko kunya,Saida mama mariya tace yakaiwa su mamy ita,ita Kuma Bari taje gida tayi duk abinda ya kamata ta kawo. Cewa yayi ta barshi kawai Dan Nan da awa Daya zata farka saisu tafi gida. Haka dai ta sanar dashi dole ta koma gidan ta hada mata abunda zata bukata sa sameta acan, Sosai mamy ta Nuna farin cikin haihuwar Wanda har Saida kowa yayi mamaki,ta rike yarinya Kam da kyar tabawa Daddy ya ganta yayi Mata addu,a. Kamar yadda yace ko ba'afi awa dayan ba ta farka,tea ya hada mata Mai kauri ya Mika Mata,Wanda badan tanajin yunwa ba acewarta bazata karba ba Dan gani takeyi duk shi yaja Mata ta wahala,shi kuwa Yana sane da take takenta ya kyaleta,Saida ya tabbatar ta shanye sannan ya hau shirye-shiryen tafiyarsu gida. Koda suka iso gida kulawa sosai aka bawa Dije,yayin da mama mariya tace ta dawo bangarenta,tako ji dadin hakan,bayan sun Isa ko wanka sosai na gargajiya akayiwa Dije,yayin da Habeeb ke fadan Wai meyasa aka Mata wanka,fada mamy tahau yi masa tana cewa su meya samesu da aka musu,ganin anfi karfinshi yasa shi yin shuru,dama ga haushin an maidata bangaren mama mariya Suna zaune da dare tana cin tuwon dawa miyar kuka da taji naman rago da manshanu,ga yajin daddawa,gefe Kuma katon mug ne cike da kunun gyada,ga farfesun Naman Kai an Sata a gaba Wai dole Sata cinye duka,tana Jin dadin tuwon sosai,suka ji sallamar ta,cikin sanyi ta shigo ta nemi wuri ta zauna,amsa Mata sukayi suma,Nan ta shiga yiwa Dije sannu da jiki da Kuma barka,itama amsawa tayi,baby'n Zainab ta Miko Mata,ga mamakinta sai gani sukayi tana kallon baby'n tana share Karamar kwalla,ta jima anan kafin ta tashi ta tafi,duka suka bita da kallo kowa da abinda yake sakawa a ransa. Tana shiga bangarenta dirent dakinta ta wuce ta fada kan gado,kuka ta fashe dashi tare da mugun tausayin kanta,taso ace itace ta haihu da Habeeb ko Dan soyayyar datake tsakaninsu,me yasa ta biyewa rudin shaidan da zuciya,ta tabbata da yanzu itace ta haifi wannan cikin da ita da kanta tayi sanadiyar barewarsa,to waima a zamanta da khadeeja da kishin data Nuna Mai ta tsinta? Haka taita kuka har Habeeb ya dawo ya risketa,sosai ta bashi tausayi,Dan rashin haihuwa babbar jarabta ce,rarrashin ta ya hau yi,Saida ya tabbatar ta samu nutsuwa,sannan ya shiga yayi wanka itama tayi suka kwanta. ***** Ana gobe suna duk 'yan garinsu Dije suka zo,dama Bata San ran zuwan innarta ba,Amma harda matan Mai gari. Ranar suna yarinya taci sunan Inna wato (saudat) Amma sun Mata lakabi da( Sukaina). Sosai akayi shagali sai dai muci Allah yakaimu na 'yan baya wato su Zainab. Kwana biyu da suna akace za'a tafi da Dije gida,aikuwa fur Habeeb yaki amincewa,saima yabar gidan,ana fadawa Daddy yace a tafi da ita Bai dawo ba sai dare,yasan dai dole 'yan tafiyar sun tafi yanzu,Amma Yana zuwa Daddy yayi Masa albishir din an tafi da Dije. Da izininsa,sosai ransa ya baci har yayi fushi. Ganin fushin ba inda zai kaishi yasa dole ya sakko Kodan kada ya shiga hakkin Sajida wadda a yanzu take bashi tausayi,Dan duk tayi laushi lubus. ****** Cikin kwanciyar hankali take wankanka inda take shan gyara tako Ina take Shan gyara,Saida tayi wata uku sannan ta dawo,kafin ko ta dawo Habeeb duk sati sau biyu yake zuwa. Tabbas zaman su yanzu ya sauya domin Zama sukeyi na mutunta juna Dan yanzu duk wani shiririta dukansu sun watsar,yayin da Sukaina tayi wayo matuka,kusan ma Rabin kulawarta Yana gurin Sajida ne,Habeeb na kokarin kwatanta adalci sosai a tsakaninsu,Dan ko wacce yanzu da nata matsayin a zuciyarsa. *5 years letter* ******* Zaune suke a falo gaba dayansu yayin da Suke Hira cikin Jin Dadi, kasancewar yanzu Habeeb yayi musu babban gida shima Naseer yayi nasa da matansa Kuma duka Alhamdillah kowanne bangare ana samun zaman lfy. Duk sun maida hankalinsu ga kallo,yayin da Dije ke zaune a kasan capet tana bawa Nihal wato jaririn data Kara Haifa nono suka jiyo karar fashewar Abu daga kicin,dukan su mikewa sukayi suka nufi kicin din,suna zuwa suka ga Sukaina ce ta baro da kofuna daga saman cabinet bayan ta taka kujera kome zata dauko,oho? Ganin fuskar Dije da tayi yasata firgita dan tasan ummin nata Bata Mata da sauki kawai saita kakkafe ido tare da karkace baki ta langabe Kai,ganin hakan cikin tashin hankali habeeb ya Isa gareta da sauri ya rungumeta,ya shiga Kiran sunanta,itako sai fa far take da ido,dakinta ya nufa da ita,inda yana shiga ya sauketa saman gadonta cikin rudewa da rashin sanin abinyi,ji yayi ta kyalkyale da dariya,tare da kashe Masa ido Daya, "Sorry Daddy! I do all this because of ummi she didn't beat me yap" ta Kara kashe Masa ido,Dije da shigowarsu kenan cikin kidima ai sai suka tsaya Jin abinda yarinyar tace,a fili Dije ta furta tabbas tarihi zai maimaita kansa....... *TAMMAT BIHAMDULLAH* Anan na kawo karshen wannan littafin na *TAME GARI* Ina rokon Allah yagafartamin kuskuren da nayi a ciki,abinda nayi dai dai Allah ya bani ladansa. Ina Matukar Mika godiyata ga masoyana na nesa dana kusa ina farin cikin kasancewar kaunarku gareni,insha Allah Nan bada dadewa ba inhar Allah ya sauke Ni lfy zaku jini a sabon littafina Mai dauke da nishadantarwa fiye ma data me gari,na barku lfy. *Alkalamin khady* โœ Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels