Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels Sanadin Boko 2-1 Posted by ANaM Dorayi on 05:26 PM, 18-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Duk gidan da na shiga kalmar iri daya ce,wato baya shigowa. da hanxari na nufi gidan su maman rahma,ita bata nan ma sai matar wansu tace min shadad bai xo ba, na dawogida na sake duba ko'ina, rijiya a datse da kwado, don haka ban kawo xaton ya fada ba. na dubi takalman shi da takardun makarantarshi da yake hm work, sai naji kuka ya kufce min. nayi-nayi,sannan na mike na sake fitowa, wata daga cikin makotana ta same ni tsaye kofar gida ina ta leke-leke,tace "kin ko gan shi? nace,"a'a." cikin muryar kuka tace "ikon Allah, to ke ina ki ka tafi ki ka bar shi? nace,bakin kasuwa naje, kuma nakan bar fa. tace da kin sani nan gidanmu ki ke turo shi in xa ki fita.kila fakonki aka yi kina fita aka xo aka dauke shi, na tsura mata ido. su wanene xa su dauke shi? tace, oho.mugu yana nuna kanshi? aka dauki babba ma bare yaro, ke dai wannan rayuwa tamu ba sai dai addu'a ba. nace,to su wanene xa su fake ni?ban jira amsa ba na juya cikin gidan,tamkar mai shirin daukan wani mataki.tace,kije ofishi 'yan sanda ki kai rahoto,ban juyo ba kuma ban tanka ba, a tsakar daki na zauna gwaraf,idanuna suna ta kai kawo guraran yin 'yan tsalle-tsallen shi, naji na fashe da kuka. hakika wadanda suka daukar min yaron nan ba su min adalci ba, don bani da wanda ya fishi duk fadin kano, naci kukana ma ishi, bani da mai bani hakuri, na share hawaye. abu tamkar wasa, sai gashi har anyi kiran sallar azahar,jikina a mace nayi sallah,ina zaune ina addu'a hawaye na bin kumatuna, sai naji sallamar maman su rahma,na amsa ba tare da na share hawayan ba. ta shigo tana cewa, hafsa kin ko ga maigidan nawa? sabon kuka ya kufce min, cikin muryar mai kuka nace wallahi har yanxun mama, tace na dawo kawai sai suke fada min wai kun xo neman shadad,hankakinki tashe. na ko ro mata wajibin duk abubuwan da suka faru, zama tayi rike da baki tana salati, tace lai finki ne in gidan mu yayi nisa ki rike hannun abunki kije dashi mana, angaya maki yanzu kaza batafi dan adam ba ne? Wlh sai kaza ko rago yayi yawanshi han kali kwace amma bil adam yana tafe ana cinikinsa, na sake fashewa da kuka, nace mama tunfa bai kai haka ba ina barinshi a gida, tace to yanxu me zaki fadawa dangin uban shi da iyayenki? Na mai maita kalmar dangin ibanshi? A cikin raina. Sallamar shi ne cikin murna ta ka tseni, anty na yau mun sha yawo da uncle dina, ya fado jikina, munje gurin wasa na hau doki da duniyar sama, mun sha ice cream, harma muka dau hoto. Ban bari ya sake cewa wani abuba na dagoshi na watsa mai wani irin mahaukacin mari, ya yanke da wani ihu sai ganin uncle din nashi mukayi a sukwane ya fado cikin gidan. Na han kadar dashi ya fadi na bishi da duka maman rahama tana a a-a a, ban tsaya ba ina dukanshi ina kuka. Shi kuwa uncle din nashi yana tsaye. Mama cikin jin haushi ta wanka min mari, tace ke ma haukaciyar ina ce? Za ki rufe dan wanan yaro da duka? Na dubeta ina kuka, mama wanan yaron yana jefani cikin damuwa, uban wanene yace yafita ba nanan saboda ya raina ni? Uncle din shi ya sa hannu ya dauke shi, yasa a kafada yana lalashi, shi kuwa sai tsala kuka yake. Cikin daurewar fuska yace, nasan haka zata faru, shi yasa ma na daukeshi ki san cewa kina kasada, ina sone kiji halin da zaki shiga in wani yai gaba dashi saka makon kasadar ki. Ya dubi maman rahama yace, mama don Allah ba kasada bane tatafi ta bar yaro shi daya, mai zai sa ba zata tafi dashi ba? Mamar rahama tace sakarya, nima yanzu na gama yimata fada, gwara da ka gwada mata hakan. Ni ko cikin takaici da masifa nace, ina ruwanka da shi? Menene hadinku da zaka zo ka dauke shi, shi shigi da kalata. Bai tankani ba, kilama bai fahimci hausar tawa ba. Mama tace jacan sakara, na shige daki bansani ba haushin daukar yaron nake ji ko farin cikin dawowarshi? Mama ina ji tana cewa kayi shuru. Kyale ta, kai kuma dana ka kyauta da kayi mata wanan ba razanar. Shi kuwa cikin hausarsu ta filani yola yake cewa, amma mama nikam banji dadin dukan nan da tayi mashi ba fa, da ma ni ta buga zanfi jin dadin hakan don nine na buga ya bude na tafi dashi. Na motsa ranta ne dan ta gane hakan na iya faruwa, in nace zan fada mata da baki bazata saurareni ba. Mama tace haka ne, ai hafsat shu‘uma ce, bayan yayi shuru, da kyar ya mikawa mama shi. Gashi mama, don Allah ki bata hakuri, na san cewa na taba ranta, amma fa kada ta sake dukan shi. Mama tace kada ka damu, gulmace ta sata dukanshi bakaga yanda ta haukace tana neman shi tana kuka ba. Yace Allah sarki! Ban san ko nawa ya ciro ba, naji dai yace mama ga wanan ki sai goro, sanan na jiyo murmushi yana cewa hafsat sai anjuma ko? Ban tamka ba mama ta shugo tana cewa, kinga harda kudi ya bani don Allah kiyi mashi godiya. Ta kwonto shadad a jikina, na turo baki nifa ban sanshi ba daga bikin rahama ya liki men. Wlh na rasa yanda zan yakice shi. Ta ce keko yarnan sai kace wace mujinta ya mutu da kurwarki? Nifa na tambayi rahama da lilin kin jama‘ar ki ta ke shai da mun tun rasuwar baban wanan yaro ne gashi kunyi zaman mutunci, to banda abinki hafsa itafa rayuwar duniya haka take kuma Allah ya fimu sanin abinda ya dace gare mu, don haka ki kula. Tan tahakiliki kila ya maye maki gurbin miji naki. Nace to na fada ne ba dan na amince ba sai don kada mama taga naki zancenta sanan ina son abar maganar cikin tarkace kayan zakin da ya sayowa shadad ne na ga hoton da suka dauka kala 3 sunyi kyau har wata zuciyar tace na yaga su sai kuma wata ta gargadeni da cewa mutumin nan bai cancaci haka a bayan idon sa ba. In kinyi masa a gaban idonsa yanzu sai ki mutunta hotonsa ko dan danki don haka sai na hakura na ajiye masa. Anfi saty banji duriyar shi ba hakan yayi min dadi shadad ne kanyi min zancen sa in na bala mashi harara sai yayi shuru don tun da na dakeshi yake dari dari da zancen uncle din sa. Nan na fahimci wani abu ga yaro shi yaro dan ja a jiki ne zagi duka baya gyara yaro janshi a jiki nuna mashi soyaya cusa mashi tsoron Allah yi mashi nasiha tare da bashi lbr magabata. Suna tai makawa gurin tarbiyya bana dukan shadad na fi yi masa duk abubuwan da na lisafa amma yau daya da na dukeshi duk ya shiga tai tayin sa. Kenan in baka yawan dukan yaro yafi tsoron dukan sannan ya fi jin magana. Wanan tunanin da nayi shiyaja na sake janshi a jiki, da dadare ya gama cin abinci yayi home work, nace ya bani lbr duk abinda ya faru a makarantar su. Nan zan tajin wane ya iya karatu wane ko an tada ya kasa, mun yi masa shem, nace kai fa ka kasa ko? Yace, ina yi anty, har antyn mu tace wai nine nafi kowa zan sake cin na 1 yanzu, nace to ka kara kokari har a islamiyya ka dage, yace uncle yace in na sake cin na 1 zai mun kyauta da ya so ko, uncle din shi sai na watsar da zancen. Nayi shuru ina tunanin yanda zanyi ga adashan da na kwasa gidan su maman rahama dubu 20 a hannuna kudin da naci burin inyi rigista da su, kuma ga kudin makarantar shadad, in ban da da ba cikin satyn nan zasu koro shi, kuma ni an kusa rufe rijista wata zuciya tace, tunda baki taba lattin biya ba kije ki nemi alfarmar suyi maki uziri, nan gaba sai ki basu. Don haka washegari naje naje nayi rigista ta, har kwana 4 ba sukori shadad ba, muna home work na ce wanan karon makarantar ku sunyi dagi amma gobe zanje in basu hakuri kada su koreka. Yayi caraf yace, anty an bani rasit wai na biya, ya tashi da gudu ya nufi ja karshi yana cewa, anty yau anyi kora ma, cikin mamaki na amshi rasit din ina dubawa, na shekara daya aka biya nace shadad wa ya biya maka kudin makaranta? Ya juya hannu tare da cewa ban sani ba. Da mamaki na kwana, da safe kuwa makarantarsu muka nufa kai tsaye bayan ya shiga aji ofishin mai karbar kudin makarantar, muka gaisa ta ganeni, nace shadad yazo da rasit wai an biya mashi kudin makaranta, wanda nasan ban kawo ba tace uncle dinshi bai fada maki zai biya ba? Na kasa magana, tace to shine ya zo ya biya na shekara 1. Sai sabuwar shekara zaki soma biya kudi. Da kyar na ce to shi kenan, na fita na nufi makaranta rai na a bace. Shi wanan habubakar din ba za ya fita hanyata ba kenan? Shi ma yana son dole sai ya cika burinsa a kai na. Tabdijan! Duk ranar da yasake gigin hada ido danine zan rufe idona ne in zage shi tas, yanda zai bar rayuwata ta huta. Abubakar lamido kyakyawan saurayi bafulatanin jahar adamawa dan yola, tuki yake cikin na tsuwa har ya isa gidansu tamgameme da ke bayan PZ, ya ajiye motar a mazaunin ta, sannan ya fito cikin takun na tsuwa ya nufi cikin gidan. Yan mata ne 2 a wadatacen palon duk kansu 1, sai dai in ka kali fuskarsu zaka gane daya tayi tsawon kafa ne, ta taras da yar uwarta. Suka amsa sallamarsa, karamar ta taso da sauri tana cewa (cikin harshen fillanci) sannu da dawowa hamma. Ya rumgumota gefen shi cikin harshen turanci ya ce mata. Yaya makaranta? Ta amsa da lafiya. Babar ta dubeshi da murmushi tare da mikewa tsaye dan girmama shi. Hamma sannu. Yace rukayya sannu da gida, ina dada tana ciki? Suka ce eh, tana ciki tare da baki. Ya nufi dakin shi, ummi tana rike da hahhun shi. Ya zauna bakin gado ya dubeta. Me kuka dafa? Tace tuwon semo da miyar kubewa danye. Je ki kawo mun shi kuma ya tube ya dan watsa ruwa ya tasa tuwon agabanshi amma ya kasa ci, tun lokacin da yaga hafsat ya ganeta daga muryarta duk da girman da tayi, bai sa ya kasa ganeta ba. Yana son sanin mai ya faru bayan da ya barta. Ina su innarta? Ina babanta? Me yasa ta canja daga mai tsananin wasa zuwa ma fadaciya? Me yasa ta canja daga mai son mutane zuwa me kin mutane? Mai yasa ta canja daga mai son tai mako zuwa mai kin tai mako? wata zuciyar tace ita kadaice zata baka wanan amsar. Tunanin ya katse lokacin lokacin da yaji hannun ummi a bayan shi, yasani ita ce dan suna mayukar shiri da ita. A hankali ya dago kai ya dubeta, ta tsura wa fiskarshi ido, tana da kishin yaransu kamar yanda aka san fulanin adamawa da yola nayi, da wuya kaji sunayin wani yare in ba nasu ba. Shi kuma abubakar ya fi mai da musu da turanci, haka ma abban su. Tace hamma me ya faru ne?Baka ci tuwonba kuma gashi kana ta tunani. Yayi dan murmushi tare da cewa ummi, me kika gani ne? Tace baka ci towon ba kuma gashi kana ta tunani. Yayi murmushi tare da cewa ummi kenan! Gajiya nayi yau, shiyasa kika ganni haka ya janyo tire ga banshi tare da cewa, zauna muci. Tace nikam na koshi, kaci sai in fitar da kayan, kuma bakin dada suntafi ta fito. Yace to. Ya dan tsa tsakala ya ture, ummi tace hmma ni sai nake kallon kamar ba gajiya bace, in mutun ya gaji in yayi wanka yana cin abin ci sosai, kafin yayi bacci gajiyar ta tafi. Ya dubeta ko? Tace, eh, yayi murmushi. To me ke damuna? Tace, ina kallon kamar tunani kakeyi ko? Yayi murmushi har dan sauti yafita, san nan yace to tunanin me? Ta juya hannunta tare da cewa oho. Ya lumshe ido. Ummi tana burgeshi yarinyar tana saurin fahimta shi yasa suke shiri yarinyar tana sonshi fiye da sauran yan uwanta shi ma yana yana son yarinyar, ta katse shi gashi kana sake yin wani tunanin? Yace tunaninki nake ummi, tace tunanina? To me nayi? Yace saurin fahimtar ki, tayi murmushi, to na gane cewa kana tunani kenan? Yace eh tace to tunanin me kakeyi? Ya mike zan fada maki amma yanzu muje wajen dada. Mahaifiyar tasu tana kokarin kashe TV din da rukayya ke kallo tare da yin fada cikin harshen fillanci. Na fada maki bana son yawan kallon nan, in kin gama rubutun to kije kicin kiyi min wanke-wanke. Zatayi magana sai ta fasa, saboda ganin hamma. Ta mike ta nufi kicin din. Da girmamawa ya gaida dadar su, ummi tace su ya findo sun tafi? Yace dama sune kuka ce min baki? Da na shiga mun gaisa ai, tace sune kuma saboda kaine suka zo. Anjuma zamu zauna da kai in babanku ya dawo. Ya dan ware ido, gurina? Ta nufi daki tana cewa in mun zauna zakaji, nima na gaji. Ummi ta dube shi, hamma ka zabi mata? Yace in na zaba kece zaki fara sani, ta ce zaku fara fada da dada kamar yanda kukeyi da abba. Nasani dada zatayi maka zancen aure ne, don lamido ya tarasu da baka nan kaje kano bikin abokin ka ya mai da hankali sosai gurin ta, suwa ya tara? Tace su faffa dukansu, harda fafa na abuja da abba da su gogo dukansu. Ya danyi di, tabbas ya kure kakan nasu, yau kwana 3 da dawowar shi amma ba wanda yace mashi komai? Yayi a jiyar xuciya me suka ce? Tace abba ya fada dada amma bata fada mana komai va, amma dai lalai saboda kai lamido ya hada taron, yace shi yasa tun da na dawo abba da dada suke daure min fuska har nayi zaton da na dade a kano ne musalin 9 wayar shi tayi kuka, yadaga ya duba afili yace abba. Tare da kalon hashim. Nawa zan tafi, abba na kira na. Ya dauki wayar cikin fillanci abba ke fada mashi yana jiransa, yace to gani nan. Yace nikam na boni hashim gara ka bonin, in kuma baka da lfy ne ka fada mana. Abubakar yayi dariya, kaima ka daina goyon baya na? Yace eh, na daina tunda har da iskanci, ace kaf dangi baka ga matar aure ba? Kowacce kace baka so mugashi har munyi yara. Abubakar yace, in nayi aure yan bibiyu zan haifa kaga sai in kamo ku. Ya daga murya yana cewa, shatu na tafi. Yace to ka gaida gida. Abubakar lamido shi ne da na farko a gurin ma haifiyar shi, hajiya fatima wada suke kira da (dada) da alhaji ibirahim lamido wanda suke kira abba. Duk wanda yake garin yola yasan lamido abubakar (family) saboda dukiyarsu da kuma akidarsu ta kin auran bare. Suna da yawa matuka, sam basa son su bada yayan su waje kokuma dan su ya auro, basu taba ba tun kaka da kakanni, haka suke har yau. Lamido yana da yaya kusan 30 da yankai, maza da mata. Matan sa 4 ne, kuma dukansu dangin shi ne alhaji ibrahim shi ne da na 3 gurin mahaifiyar su gogwal, wace itace matar farko, haka shine wanda ya fara yin kudi fiye da mahaifin su kafin kanansa su biyo baya. Lamido abubakar sarkine a wancan lokacin, mai fada aji, kafin ya sauka ya ba baban danshi sa‘a du maifin hashim. Lamido yanada tsutsuran ra‘ayi a kan auren waje, duk yayanshi maza saidai yace shirya kaje wajen wance yar baffanka ko yar gogonka, inko macece sai dai yace wane zai zo ki shirya ko jikokinsa haka ne abbukar su 7 ne gurin mahaifinsu,usman ke bin sa, sai umar, sai aiyu sai kasim, sanna rukayya sai auta hauwa'u, sunan gogwal ta ci suna ce mata ummi. shi ko abbukar sunan mahaifin lamido yaci, kakan babanshi kenan, shi yasa lamido ke san shi duk cikin jikokinsa yafi son baban shi abbukar kaf family hammam suke kiran abbukar don girmamawa. yana da wani irin kwarjini mai ban mamaki ga farin jini kowa na son shi, bugu da kari ya taso hannun shi sake, ma'ana yana da yawan kyauta. ya sanka bai sanka ba in yana da shi xa ya baka, shi yasa kawunan shi da goggonin sa su yafendon sa har su baffan shi kowa na son hama ya auri yarsa. su kan su yanmatan cikin family suna son sa, wasu har sun yi masa maganar, wasu sun aiko amma baice ma kowa kala ba. abbukar mutum ne da yake tsayiwa kan ra'ayinsa, a tsarinsa baya sha'awar macen da xata ce tana son shi, yafi son yaga mace da kansa yace yana sonta, matsalar shi duk cikar family bai ga wadda ta mishi ba, duk kuwa da kyawun yanmatan yana cikin maxan da kyau baya tsarin shi. a yanxu haka yana da (mastets digree) a fannin kasuwanci, yana jan kamfanonin abban su ne yayin da abban ke hutawa, tun kusan shekaru 7 bay, lamido ke zaba mishi yanmata yana cewa sai yayi master xaya yi aure. a tarihin gidan su shi ne da na farko wanda ya karya dokar lamido, ya ki yi aure a lokacin da ya bukata, bayan ya kammala karatu ya soma aiki.lamido ya kira shi yace mishi abbana, ina son ka shiga da kanka gidan baffanninka da ggonninka ka duba mata, in ma da xan zaba maka da kaina sai in ce kaje gidan baffanka na abj yaransa suna da kyau. Abubakar ya dubi kakansa, lamido nifa ba mai kyau nake so ba, kaikam sakarai ne saikace ba dan boko ba? Kowa yana son mace mai kyau, yace ban da ni, akwai wasu halaye danake son matata ta kasance dasu, a dan bani dama in tantance. Lamido yace to ubana, na baka wata 2 lokaci ishashe ya isheka kayi duk bin cikenka, abubakar yace na gode. Wata 2 har da saty 2 lanido yaji abubakar shuru, dan haka sai yasake aikowa ayi mashi kinran abubakar, wanda ya kasance cikin wanan kiran a kowanne lokacin. Abin da ya kudirta shine ba za ta taba kai kanshi gurin lamido ba, har sai lokacin da ya kirashi. Ba yan salan isha‘i ne ya sami lamido a gidan shi, cikin falonshi mai tsari irin na masu kudin da, duk da haryanzu a kwai kudin bai damu da canja tsarin falon ba, don ya masa. Ya zauna tare da gaida lamido, sannan ya sunkuyar da kai, lamido yace cikin yar tsokana, abba na nasan kana da kara ko da ka zaba mace ba zaka iya zuwa gabana ka fada ba. To dan matso ka fada mun gidan wa kaga matarka? Wacece tayi sa‘ar samun namijin duniya kamarka? Abubakar ya lumshe ido sanan ya sunkuyar da kai yace, gaskiya lamido saboda aiyuka bansamu zuwa ko ina ba. Fuskar lamido ya canja daga fara‘a zuwa daurewa. Sannan yace duk tsawon lokacin nan bakaje ka aiwatar da abinda muka zanta da kai ba, don baka dauki abun da muhim manci ba? Yace, a a yanayin aiki ne. Lamido yace yayi kyau yau wace rana? Abubakar yace alhamis, yace to gobe in an taso sallar juma‘a ka kira hashimu kuzo ina nemanku. Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 2-2 Posted by ANaM Dorayi on 05:46 AM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Abubakar yace to. Lamido yace tashi kaje, bai amsa sai anjuman da abubakar yace masa ba. Duk da abubakar na sane yaku ma dawo gida daga ofis, bayan salar juma‘a sai ya kishin gida har dan bacci ya soma daukar shi, sannan yaki kiran hashim ya fada mashi kamar daga sama sai yaji an doki kafadar sa, ya bude ido yaga hashim tsaye, yace har ka iso? Hashim yace na iso ina? Ka fada min ne? Yanzu lamido ya kira wayata yace ya yajimu shuru. Nace me yafaru? Yace baka famun yana neman mu ba. Na kareka nace ka fada min, nace na mantal yace ya bamu minti 20. Abubakar yace kanme zakayi karya? Kawai kace masa ban fada maka ba. Hashim yace tashi dai muje, amma bari ka canja kaya, ya bude duriwar manyan kaya ya ciro masa shadda waganbari bowa mai kalan sararin samaniya. Hula baka minister, ta kalmi baki, yace tashi dan Allah fadan lamido bashi da kyau, tunda in ya tashi sai ya fara cin uban iyayen mu kafin ya dawo kan mu. Abubakar ya soma sa kaya yana cewa, ni nifa kasan Allah? Eh inji hashim, babu mai min auren dole. Sai irin matar da tai min, mace 1 nakeso a rayuwata, kuma sai na zabi duk wadda ta hada duk irin halayen da nake son don bana son inyi mata 2 ko 3, 1 nan ta isheni. Hashim yayi dariya, sanan yace niko har na hango wace zan kara da ita fatana Allah karyasa lamido yace wajenta zamuje. Abubakar ya dube shi kana nufin wai lamido zai ce min in je gurin wata ne? Hashin yace kaima ka sani, domin in baka manta ba juma‘a kamar haka yace kasameni muje gunsa, mukaje yace muwuce wirin shatu. Kana nufin munfika biyaya ne? Kada ka manta mahaifiyar ka da a haifin ka yar mace da dan namiji suke, kuma suma hadin ne. Abubakar yace duk ina sane, hasim kanayi kamar baka san ABUBAAR SADDIK ba, zaku sha mamakin zuri‘ata tashi muje Hashim ya mike tare da ajiye kwalbar turaren da ya kara fesawa a mazauninta. Duk suna zaune gaban Lamido, wanda fuskarsa ke take, yace Hashimu kuje gidan Baffanku Adamu, 'yan matan gidan guda biyu ne, ka zabi daya da kanka ina jiranku bayan sallar isha'I". Hashim yace to, mun gode. Sai mun dawo. Suna mota Hashim na tuki, Abubakar yana ta son tuna 'yan matan gidan Baffa Adamu. Anya ya san su ma? Hashim ya katse masa tunani da cewa, "Kai duk ruwan idonka saika zabi daya daga cikin yaran gidan Baffa Adamu." Abubakar yace ba dole bane su min. Hashim yace Allah yasa kada ka canki wadda nake hari." Tsaki Abubakar yaja, sannan yace tun kana yaro zaka tara ma kanka gajiya, ka hada mata suyi ta maka rigima kullum kuna fada Lamido, gashi kai ba dama ka saki wata duk danginka irin gidan Yaya Sule gida sai kace sansanin yaki." Hashim yayi dariya harda dukan sitiyari, sannan ya ce ni nan sai na gaji Lamido hudu nan sai na hada, Allah ya taimaka inji Abubakar. A kofar falon suka yi sallama, Yadikko ta amsa tare da bude kofar, ganin su Abubakar ta fadada fara'arta, tana masu sannu da zuwa cikin harshen fillanci. Sun zauna a falon suka gaisheta, ta amsa tare da tambayar mutanen gida, suka ce lafiya, cikin hanzari ta nufi dakin 'yan matanta guda biyu, tace Maimuna ga baki can falo su Hamma ne ku kai masu abin sha. Jamila ta mike da hanzari, haka ita ma Maimuna kowacce tana fatan gurinta yazo. Tun fitowar su ya tsaida hankalinsa gurinsu, tabbas da don kyau zaiyi aure da ya zaba, amma ba ra'ayinsa kenan ba. Cikin yanga Maimuna ta gaishe su, yayin da Jimila keta rawar kai gami da tsuga surutu. Maimuna kam tun daga gaisuwa ta ciro waya tana ta yin abinda bai sani ba, chattin ne ko game. Hashim yayi kasa da muya yace wacce tayi? Kafin Abubakar ya bada amsa, Jamila tace Hamma don Allah inga wayar ka. Ba tare da ya bata wayar ba ya mike. Hashim tashi lokacin sallah yayi, ya dube su ku kira ta muyi sallama. Maimuna ta dube su har zaku tafi? Ko ruwan kai Hamma baka sha ba. Yace zan sha wata rana, yau kam na gode. Yadikko suka jero da Jamila nan dai suka yi masu sallama, a hanya ne Hashim yake ta damun shi da son jin wacce ya zaba, yace ni fa babu wadda tayi min. Hashim yace don me? Ga Jamila, Abubakar yace bana som mace mai yawan surutu da rawar kai, gami da bincike, wannan ya nuna in na aureta zata dinga daukar wayata tana min bincike ko kuma tana min bincike a daki. Ya ce, Maimuna fa? Ita ma a'a ban cika son mace mai shiru sosai ba, sai yawan danna waya, hankalina bazai kwanta ba, domin zata iya share ni tayi ta mu'amularta da waya. Hashim yace, tab, to wallahi bada ni za a gurin Lamido an jima ban don haka kaje ka masa bayani. Abubakar yace tare zamu je, zaka ga kamar bazan iya yi masa magana ba ko? Hum, bari mujem suna gaban Lamido duk sun yi shiru, shi kanshi Abubakar yana jin zuciyar shi na rawa, tamkar bazai iya bayani ba. Amma ya daure yace babu wadda ya zaba, ya kawo dalilansa. Lamido ya tsura masa ido, zuciyarsa na zargin Abubakar nason kawo masa sabon salo ne cikin zuri'a, amma sai ya danne yace naji. Hashim tun daga gobe Asabar har zuwa rana irin ta yau, ku zaga duk zuri'ar mu Abbab ya zabi wacce yake so in na Yola basuyi ba ku tafi har Adamawa, kai har 'yan Kaduna da Abuja da Kano kuje ya zaba. Tsahon sati biyu na baku, ina jiran amsa. Abubakar yace to mu gode sai dai a duba yanayi ayyukan mu. Lamido yace wannan ya rage naku, ku zaku cire lokacin da kuka ga zai dace ba tare da kun shiga lokacin aikin ku ba, ku tashi kuje. Sun ajiye bayan isha zasu dinga bin dangin kila a dace. Sati guda suna zagaye gidajen dangi, amma ko ina sai Abubakar yace bata yi ba, wannan yace kazama, wannan yace zatayi rowa, wannan yace ta cika yawo. Hashim yace to muje gidan mu ga kanne na, su kuma yace basa jin magana, irin su daya da Rukayya kanwata. Hashim yace haka ne amma fa bazaka samu mace dari bisa dari da irin halin da kake so ba, su dama da kashin hakarkari akayi su kaga kenan a karkace suke, in ka dage cewa zaka mikar dasu sai su karye. Abibakar yace, look bance maka dama ba, amma irin matar da nake so nasan zan samu. Hashim yace kasan me zamu yi? Tunda yau goma ga watan daya, saura kwana biyar ayi family meeting mu jira ranar in kowa yazo sai ka duba Abubakar yace Allah ya kaimu Duk shekara suke yin mitin na zuri'ar su, suna yin taron ne a gidan tsohon wato Lamido, suna tattauna matsalolin 'ya'yansu da su kansu a taron, duk wata kowanne mai matsala yana fada ta kudi ko ta wani abin da yake suna da asusun da suke tara kudi duk wata. Sai a dauka ayi maganin matsalar da shi, tunda kuma ba duk dangin bane masu kudi, sai dai masu kudin sunfi talakawan yawa. Tun ana gobe taron ake kada shanaye biyu saboda yawansu, Lamido ke bada su, yayin da wasu daga cikin manyan 'ya'yan zasu yi ta kawo kulolin abinci manya kala daban daban, yan nesa irin su Abuja Kaduna tun Juma'a suke dauko hanya. Dada ta shiga dakin bayan ya amsa sallamarta, ta ta ganshi kwance cikin bargo kasancewar lokacin sanyi ne tace, ka tashi fa Abban ku fa ya tafi dasu Ummi da Aliyu da Kasim. Usman da Umar kuwa na tabbata yanzun sun tafi da iyalansu. Shiri yayi tsaf cikin kayan alfarma, in ka ganshi zaka yi zato cewa sarki ne, shi da Dada ne kadai. Gidan ya cika makil, filin da aka saba yin taron tuni an shirya shi da kujeru, gurin zaman iyaye daban, na 'ya'ya daban haka ma na jikoki. Dole su baka sha'awa, yanmata da samari ga sunan, wasu dama anan suke hada kansu shikenan, Lamido hakan na daga cikin abinda yake sashi jin dadi a taron, gurin su Hashin Abubakar ya nufa, a gabaki dayan tsararrakin sa babu wanda bashi da yara........ har saitin su usman da umar duk sunyi aure, hatta usuma da umar suna da matansu matar usman tana da tsohon ciki, ta usuman kuwa tana da danyen goyo, dukansu suna aiki ne a kar kashin abubakar don mutun ne mai adalci, kansu umma a hade yake. Hashim ya soma yi mashi tsiyar cewa ya makaranta, salisu yace ba dole yayi maka ba, tun da bashi da mai tashin sa. Sani yayi tsagal yace, azumin nan mai zuwa sai munyi mashi kidan tazuru, yace zakuyi ku gama. Hashm ya turo mashi kujera zauna dai dai nan ka samu damar kalon yan mata gasunan iyaka gininka. Ya zauna tare da cewa ku tayani duba, sun bude taro da adu‘a kamar yanda suka saba, sannan aka gabatar da marasa lafiya dan ayi masu adu‘a sannan sauran abubuwan suka ci gaba. Daf da karshene wanin baffan su mai suna yusuf yace ya kamata kafin a tashi daga taron nan a saka ranar abubakar, dan kowa ya san lokacin, duk iyayen sun amince da hakan. Lamido ma yayi na‘am. Abubakar dai zuface ta rufeshi, yayin da a bokan wasa suka ta masa dariya. Sukuwa yan mata kowace tana son taga wacece mai rabon nan. Shi kuwa tuni taron ya gundire shi. Anci ansha samari sun sami yan mata wasu kuma sunyi kari, amma abubakar duk basuyi masa ba. Hashim yace gasu khalisat yayan baffa na abuja, yace wadan nan yaran masu salon tsiya, barni kawai. Kamar daga sama yaji lamido na kiran shi tacikin abin magana, Hashim yace to kaifa kila yau ta yan tatsuniya za a yi maka, irin na 'ya'yan sarakunan nan ace mata su jeru namiji yaje ya zabo. Abubakar ya mike ya mufi gurin Lamido, yace ina so yanzun nan ka shiga cikin 'yan matan nan yanzu ka fitar da mata ka, nasa ranar auren ka wata biyar daya ga watan. In kayi lissafi zai zama wata hudu da kwana goma sha biyar kenan, kafin lokacin kun fahimci juna." Nan da nan dangi suka sheda suka shiga murna, shi kuwa gurin zaman shi ya koma. Hashim yace tashi mu duba, yace dan Allah ka bar ni ka ji." Haka taron ya tashi ba tare da Abubakar ya zabi mata ba, hakan ya kona ran mahaifansa da Lamido, daga bisani kakarsa Gogwal kodai bashi da lafiya ne? A bincike shi, sun tsare shi ya ce shi kam lafiyar shi lau, amma bai samu kawai mai irin halayen da yake so bane. Cikin bacin rai Lamido ya ce sun zura masa ido amma ya sani rana baza a daga ba ko ya sami mata ko bai samu ba, in lokacin yayi zasu daura aure da duk wadda suka ga dama. Abubakar kuwa ko a jikinsa, cikin hakan ne bikin abokinsa Sagir ya taso a Kano, yaje yayi arba da yarinyar da ya santa a Kaduna lokacin da yaje (Bautar Kasa), tana talla mai yawan wasa, kusa shekaru goma baya. Yana son sanin abubuwa game da yarinyar kuma yana jin wani abu a ranshi game da ita, sai dai abin tambaya ta tara halayen da yake so matar shi ta kasance? Ya iso gida daga gida Hashim, gaban iyayan nashi ya zauna a kasa, Abban ya dube shi yau in ni na haife ka ina son ka fada min nufin ka damu. Dada tace dazun su Yafendon shi da suka zo dukan su kowa na cewa yazo ya sasanta da 'yar gidanta, na ce masu dai kun sanshi in ya yarda shike nan, amma fa ni bazan maku alkwarin ko ya yarda ba. Don haka ka fitar da mata kada ka hada ni da 'yan uwana, Abba yace yama fada mana nufin shi kawai, in yana da wata matsala ne sai ya kawo uzurin sa muji, in ko lafiyar shi lau to raini ne da walakanci, baka jin kunya kannan ka duk sunyi aure cikin dangi ko ina lbarinka ake, fada min nufinka." Ya danyi dim don yasan abinda zai fada yanzu zaya girgiza su. Dada kayi magana mana. Ya dan numfasa yace, naga wadda nake so." Abba yace, ko kai fa, fada min wacece yanzu na sanar da Lamido ta waya." Yace tana Kano." Suka hada baki gurin cewa, Kano? 'Yar gidan Goggonka Furera?" Ya ce a'a ba dangin mu bace. Suna hada baki gurin cewa, ba dangi ba? Eh, ya dago ya dube su, ba zato sai yaji saukar mari gefe da gefe, sannan ta rufe shi da duka. Sunkuyar da kai kawai yayi tayi ta dukan shi. Abban su kuwa sunkuyar da kai yayi ba tare da yace Dada ta daina dukansa ba, har sai da ta bar shi don kanta. Cikin tashin hankali take cewa ba zaka jawo mim abin fada a cikin dangi ba, kai ne mutum na farko da zai kawo matsala a zuri'ar mu? Tur! Ba dani za a yi ba, ta fice daga falon rai bace, yana nan zaune Abba yace kasan dai kazo da abin da bazai yuwu ba ko? to ka cire wannan tunanin a ranka in dai kana so kaci gaba da zama danmu. ya mike shima ya fita dàga falon, Abubakar yana zaune cikin halin da baza yace gashi ba, yafi awa daya saññañ ya fito ya tafi dakinsa. washe gari sam iyayen basu amsa gaisuwar sa ba, wannan lamari ne mai girma. Ya zama dole ya faranta ran iyayan sa, yasan idan tasu ne zai iya shawo kan su, tsoron lamido da sauran dangi suke yi. Shi kuma yana so ya kawo karshen wanan auran, domin wasu na cutuwa, an hada su da wadanda basu so. Sannan ko mai mace zatayi wa namiji ko shi yayi mata babu rabuwa, yasan ba wai haramun bane auran zumuncin, to amma yanda zuri‘arsu suka dauke shi tamkar ibada, shine yake son su gane auren bare ma ba haramun bane. Akan gadon shi yake ta juyi tare da neman mafita, ya kalli agogo 11 a fili ya furta Allah yasa hashim bai yi bacci ba, ya daga wayar sa yasa a kunne, bayan ya laluba num hashim din. Tayi kuka har ta katse ba‘a dauka ba, don haka ya ajiye wayar yana miyar hashim har yayi bacci sai kace mace. Kusan minti 30 wayarshi ta soma ruri, ganin sunan hashim ya daga da wuri,ya soma korafi ka cika baci kamar mace. Hashim yace ina tare da iyalina ban san tayi ringin ba, duk da tana kusa dani in ka fahimce ni ka kira lokacin ina duniyar ma‘aurata, bana tare da ku. Abubkar yace ban tam bayeka ba, sannan Allah dai ya tsine ma mai tona asirin iyalansa, don haka sai kai hattara. Kasanan dalilin kiran da nayi maka? Hashim yace sai ka fada? Abubakar ya gyara kwanciya sannan yace, kila kaji mamakin cewa wadda nake so ba a cikin zuri‘armu take ba ko? me kake son fada mun? Hashim ya mike ya nufi falo dan kada matarshi shatu taji abin da zasu tau tauna. Kada kace zaka shugo da bidi‘a cikin zuru‘ar anan, kasan hakan zai jamaka matsala kai da mahaifin ka? Abubakar yace haba hashim kai fa ba jahili bane, abinda kake kira bidi‘a ba haramun bane. To auren zumunci sunna ne? Ka fada mun a matan monzon Allah wacece yar uwarsa ko a kwai bata wuce guda 1 ba, kuma duk matansa yan kabilar sa ne?Dashi fa muke koyi, don haka matar da aura ina nufin ba haushiya ce, ina zoton ma ba zawara ce, kaga kenan zanyi sunna. Hashim yayi tsaki, wannan karan bana tare da kai, matsawar baka canja tunani ba. Me hausa sukafi yaren mu na fulani? Kyau ko asali? Abubakar yace look! Hashim ka fahim ceni sosai, ba al‘ada ce a gabana ba, addini nake son awa agabana, yarenmu suna da kyau da asali da kuma tarbiyya, amma ban ga wadda tatara irin halin da nake so ba. Ok inji hashim. Ita wannan ta tara duk abin da kakeso? Abubakar ya tashi zaune, ba zan saniba sai dai na ga 1 daga ciki, saura sai ta bani dama mun zanta. Hashin yace kana nufin baku taba zantawa ba? Abubakar yace ni ke sonta, ita bata san inayi ba, domin bata so in kusanto ta, na dai taba sanin ta da. Hashim dan Allah ka natsu, ina so ka taimaka mun yanda zan shawo kanta, zanfi tsayuwa kan ra‘ayi na inna tuna wanda nakeyi dan ita, ta san ina yi. Hashim yace, abinda zai fi kaje ka fada mata nufinka, ka ce mata kana sonta kuma zaka aure ta, na san zata girmama zan cenka don matan da suka san abin da suke yi, suna girmama zancen aure. In dai ba wani ya riga ba. Abubakar yace ta tsani maza, ina zaton namiji yayi mata laifi. Hashim yace kaje, in baku sasanta ba ka sanar da ni, sai mu koma tare. Kai dai kasan yan da zakayi mahaifanka kada su shiga fushin lamido. Yace zan ga me zanyi. Sukayi sallama. Arana ta 3 ce daada ta shigo dakin shi, da wowarshi kenan daga office, tace ka sauya ra‘ayin ka ne ko kanan kan bakanka? Ya kwantar da murya. Dada kiyi hakuri, wlh wace nake son aura musulma ce mai tarbiyya. Tace amsa kawai zaka bani, ba. Tace amsa kawai zaka bani, bana son dogon turanci, ya ce to duk yanda kuke so haka zanyi, tace uhm! Isa da kai kaje ka cire mata a dangi, ta tausasa murya, da zakaji tawa ma, ka sami lamido ka fada mashi ya zabo maka. Na tabbata zaka wanke lefukan da kowa ke ganin ka dashi. Muma zaka ciremu a zargin da lamido ke mana, na san baka sami lbr mitin din da lamido ya kira su abban kuba ko? Ya dube ta, na sami labari sai dai ban san abun da aka tau tau na ba, duk da nasan dan ni akayi shi. Tace to ya tara yayan shi maza ya sanar dasu cewa bai yafe ba duk wanda ya bari dan sa ya kawo bakon lamari a cikin zuri‘armu ba, yace za‘a yanke mumunan mataki a kanshi da yayan ta hanyan yanke zumunci da su Zaharaddeen Shomar whatsapp. 08168575100 Sanadin Boko 2-3 Posted by ANaM Dorayi on 07:34 AM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Abubakar yayi shuru, yayin da jikinshi yayi sanyi lakwas. Al‘amarin mai girma ne, yace dada kada ki damu, zanje gurin lamido amma ina so ku daina fushi dani. Tace to mu dama fushin mu don kaki bin abin da muke so ne, da kabi shi kenan mun huce. Yace to zanyi duk me kuke so. Har zuciyar shi ya san ya amsa ne kawai, amma ba dan zai je wajen lamido da batun a zaba mashi mata ba, zai jene da batun wanda yake so amma sai yaje kano ya dawo. Tun dare ya shaida wa mahaifan nasa cewa zai shiga lagos a gobe, don tau taunawa da wasu abokan kasuwan cin sa a bisa wata cinikayya da zasu yi. Sukayi masa adu‘a da safe karfe 9 ya hau jirgin kano. Sai da ya huta a masaukin shi sannan ya daga waya ya kira layin sagir yace yana kamo don Allah ya kawo masa mota. ******* ******* ***** Tun dare zazzabin shi ya tsananta, kwana mukayi babu bacci, gashi bani da ko parasitamol bani da kudin saya cikin yan satitikan tsananin babu ta dameni, jiya ko girki banyi ba. Da dadare garin rogo muka sha muka kwanta, jikin sa ya tsanata sosai da safe har da safe har ta kai numfashin sa na futa dai dai. Nace ka bari dai in watsa ruwa sai mutafi asibiti tunda kan da kati, ko da bani da na mota, ina saka hijab na lura ya mike idanun sa sun kafe hakoransa suna datsewa, dukda ban san suma ba tabbas suma ne wannan. Cikin matsanancin tsoro da firgici na sunkuce shi da gudu nayi waje ina fadin innalilahi wa inna ilaihir raju‘un! Kamar daga sama na ganshi tsaye jikin mota, da gudu na nufeshi ina cewa, ya mutu! Ya mutu!! Da sauri ya karbe shi yasa a mota bai jirani ba ya figi mota kamar dama abinda yake jira kenan. Na koma cikin gida ina zagaya ina kai kawo, kusan awa 3 sannan naji tsayiwar mota da gudu na fita, shi kadai ne ya fita fiskar shi mur tuk, ko bai fada ba nasan shadad ya cika.da gudu na juya cikin gida ina kuka, hakika nayi rashi. Na zube kan katifa nayi kuka na gode Allah, sai nace Allah yasa mai cetona ne. Ina fitowa sai nagan shi jingine a bango, na daure nace ka daukosh bari naje na fadawa su maman rahama. Yace ki ce musu me? Ya rasu mana, yace inji wa? Na kara matsawa kusa dashi me kake nufi? Yace ya far fado nazo ne in kaiki gurin shi. Likita yace typort ne ya kamashi da kyau. So, yanzu in kin gama kukan ki shirya ki dauki duk wani abu da zaku bukata a can. Yan kayan shi kawai na diba, sai nawa guda 2, da daudumar sallah da alkur‘ani. Na fito yace kin dauki komai? Na ce eh. Amma kafin muwuce bari na sanar da maman rahama, kada suji shuru. Yace to ina jiranki a mota. Sai da na kule gida sannan naje. Asibitin kudi ne mai tsari dakin mu kadai ne har da kayan kalo ga na‘ura mai sanyaya daki da taruwa. Na kafe shadad da idanu, duk ya rame yanata bacci. Hawaye sai sauka suke a idanuna, yace min yana zuwa. Bayan fitarshi likita yazo muka gaisa, ya tambayi mai jiki nace da sauki, yace bai tashi ba ko? Nace eh yace to idan ya tashi ki bashi abinci ko da ruwan tea ne, sai ki bashi magungunan shi an siyo? Nace banga ta kardar maganin ba ai, yace tana hannun baban shi, yace dan Allah kada kiyi masa wasa da magani, nace to. Yana fita na soma tinanin ina zan sami kudi? Gashi ko abincin da zan bashi bani dashi in ya tashi. Nace oh Allah na gode maka a wanan hali da kasa ni, Allah ina mai naiman sauki a gareka. na dauki wayata na kira Rahama na fada mata muna asibiti an kwantar da shadad, tace taji gurin Abubakar, gasu nan zuwa dashi da sagir ma. Kusan minti 25 da yin maganar mu sai gasu. Rahama ce gaba dauke da katon kwando da kulolin abinci da filas na ruwa zafi, Abubakar da Sagir suka shigo da ledoji. Ya nufi yar durowan da ke gefen gadon ya jera kalolin jus ne da ruwa. Sannan sai magun gunan shadad ne ya zuba su a wani kwando dake jikin gadon, kila an tanade shi ne dan zuba maganin dama. Sagir ya koma ya shiga da dadduma mai girma, ya shinfida ta can gefe suna fiskantar gadon, rahama ta dauko kwandon ta zuba musu da fadukan shinkafa da kayan lambu, sai farfesun kifi. Ta zo ta daukar musu ruwa tana cewa bari na sashi a fridge saboda naji babu sanyi. Ni dai sai bisu nayi da idanu. Rahama ta dube ni, bari in sa mana, nace zuba dai dai cikin ki. Abubakar wanda ya zauna saiti na da na dago fiska sai mu hada ido, na daure fiska Rahama ta sani ni magana 1 nake yi shiyasa bata matsa min ba, ta zuba nata ta juyo kujera kusa dani, ina bakin gado ne ta soma ci. Ya kurbi ruwa me yasa ba zaki ciba? Na dan tsuke fuska, sannan na dube shi haka kawai. Ya kali kofar shigowa, kamar mai nazari. Can ya sake duba na, amma ba don kin karya ba, kuma ba don baki jin yunwa ba?ban karya ba kuma ni bance bana jin yunwa ba. Rahama ta ce, Alhaji abubakar dama ka barta, domin duk abinda tace tana nufin hakan. Abubakar ya dubi Rahama, yace kina nufin bata karyawa? Rahama tace a a ina nufin duk maganar da ta fada ba zata canja ba, shi ne dalilin da yasa kaga da tace ba zata ci ba, ban matsa mata ba. Ya ce ok. Duk kamshi ya cika dakin sagir da Abubakar kasa kasa suke hirarsu. Wayata ta shiga ruri, nayi tsam tare da son in tashi taro da son inhasashi ko wanene, ina dubawa sai naga number super markert din mu. Gabana ya fadi, sam na manta da wani aiki. Ida nuna suka kai kan Abubakar, ya kafe ni da ido da alama yana so yasan wanene ya kirani? Nikam a zatona manaja ne, na daga da sanyin jiki. Ba muryar shi ba ce, nace ishak ne ko musa? Yace ishaq ne yace munjiki shuru ne kuma manaja yace baki ce bazaki zo da yanma ba, tun dazu yace kina zuwa ki sameshi ofis. Ya numfasa yace ranshi fa ya baci, wai shi kin soma isarsa. Nace ishaq don Allah kace yayi min uziri, yaro nane ba lafiya duk na rudene shiyasa ban tuna da aikin ba, yanzu haka muna asibitin anbashi gado. Yace to kikirashi ki fada mishi, dan kada ya gane nine na kiraki. Nace to na gode. Na dafe goshi na, Rahama tace ya akayi? Kin san cewa na manta da batun aiki? Shine Ishak ya kirani. Na shiga dan na wayata ina son in duba account dina, duk da nasan bani da kudi, ko ina ziro ziro, nashi gshi bani da kudin ma da zan kira manaja sai in na sa. Rahama ta ce ga wayata ki kira shi, na harare ta kina hauka ne, zan kira wani namiji da wayar ki, bayan kinyi aure? Ta ce to menene, ba da nima Ogana ne ba? Nace sam, da kika ce, ki tuna mijinki har canza maki layi yayi don kada mutane su dinga kiranki, kuma hakan yayi daidai, don ya nuna kishin ki. Yanzu sai na kira Manaja? Alhalin yanzu baki da wata alaka dashi?, tace to naji. Sagir wanda bansan suna jina ba, yace a to fada mata gaskiya. Na dube su, idanun Abubakar su suka sa na sunkuyar da kaina.Yace, "ga wayata ki kira, na girgiza kai, ka barshi na gode, ya shiga danna lambobi, ban sani ba sai naji yana cewa Manaja yarinyar nan Hafsa tana da uzuri, don haka bazata samin zuwa aiki ba sai bayan wani lokaci da bazata iya cewa gashi ba, don haka tana son uzuri.Na tsura masa ido, a raina ina cewa ji mutum zaya balgace min aiki na, bayan dan shiru kadan da yayi sai yace, to shike nan. Ya dube ni "menene na zare min ido? Ya yarda, nace na gode. Amma ba haka ya kamata ka tambaya ba saboda shugabanane a gun aiki. Ya ce yanzun nayi laifi kenan, na girgiza kai alamar a'a, sannan nakai dubana ga Shadad.Sai bayan munyi Azahar sannan ya farka, naba bashi tea. Abubakar ya bashi magani, naji dadin yanda ya bashi don ni idan na bashi kuka da su amai yake yi, amma shikam ya bashi cikin lallashi kuma yasha. Amma sai yace masa Uncle bazaka kara guduwa kabarni ba, ya ce eh amma sai kasha magani. Cikin rawar jiki yasha, na kanyi al'ajabin irin son da Shadad yake yiwa Abubakar, domin ba shine mutum na farko da ya fara masa magana ba, bai taba zuwa gurin kowa ba sai shi.Sun fita sai ni da Rahama na kasa rike abin da ke ciki na nace, Rahama wai me wannan abokin mijin naki yake nufi da ni ne? Ta ce baki tambaye shi ba? Na harare ta in ya bani amsa zan zo ina tambayarki ne? Na jima ina tambayar sa bai bani amsa ba nifa gaskiya bana son shishigin nan ki fada masa. Ta ce ke me ya hana ki fada masa, ta gyra zama Hafsat ki nutsu da kyau ki lura. Abubakar yana nemanki da alkhairi ne, koda bai fada min ba nasan kila sonki yake. Na dubeta da wani irin kallo cike da masifa nace sona? Don Allah ki daina wannan sabon, in har yayi kuskuren furta min kalmar so ai sai yayi nadamar yin hakan.Tace maida wukar, tambayar ki zanyi. Cikin harara nace, ina jinki, ta ce kina nufin laifin Munir ya shfi sauran maza? Tsakani da Allah zaki bani amsa, na ce kusan haka ne, ta ce kina dai da ilimin addinin musulunci, ance laifin wani yana shafar wani? Na ce baya shafa amma na dade ina ji a bakin iyaye na cewa maza ba yan goyo bane maza rigar kaya ne, maza basu da tabbas, maza mugun ice da dai sauran sunayen da ake kiran su da su, da ban yarda ba sai gashi namijin yayi min, don haka ni layi guda na ajiye su. Zaharaddeen Shomar whatsapp. ,08168575100 Sanadin Boko 2-5 Posted by ANaM Dorayi on 03:15 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO "Amma wanda ya bada wannan shawara ya kyauta, dan kai da Fadi kun dace, kuma ina zaton tana da wasu irin halaye da kake so." Ya ce, "Na rasa dalilinku na cewa mun dacen." Ya ce, "Ya kake son nayi da Hafsatu?" Hashim ya ce, "Kun daidaita?" Abubakar ya ce, "Akwai alamun nasara. Abba ne ya sani na dawo da gaggawa, saboda wasu takardu. Sati na sama zan koma ko da kwana daya ne, daga nan in mun daidaita zan kai ka ka ganta. Amma ka shirya anjima zamu je gurin Lamido." Hashi ya ce, "In dai kan yarinyar da zaka shigo da ita cikin zuri'armu ne zaka masa to ka tafi kai daya ba zan je ba." Abubakar ya ce, "Na rasa me yasa kuke tsoron Lamido haka, shi ba dodo ba ba komai ba, ni Allah kadai nake tsoron na sabawa ba mutum ba, zan je kuma zaka ji sakamako." Har ya fita Hashim ya ce, "To yaushe zamu je wajen Fadin?" Tsaki Abubakar yayi sannan ya yi gaba. Lamido ya tarbe shi cikin fara'a, ya ce, "Ubana ka iya zabe, domin ko da ni ka bari to da wuya na zaba maka irin wannan Babban kamu, lallai kun dace." Abubakar ya sunkuyar da kai cikin daure fuska ya ce, "Ni fa ba nine na ce ina son Fadi ba." Ya ce, "Duk wanda ya hada ku yayi maka gata." Abubakar ya ce, "Ni wadda na zaba daban, bana son Fadi." Ya ce, "To kila ka gaji takwaranka Mahaifina kenan, tarihi ya nuna mana duk cikin zuri'ar nan shine mutun daya taba auren mata 2 lokaci daya. Fada min wadda ka zaba ita ma yau akai mintinta, rana daya duk a sa su a lalle." Abubakar ya yi shiru, Lamido ya ce, "Duba, taso ka matso nan, ka fada min wadda kake so." Abubakar ya matso, ya dubi Lamido, "Wata yarinya ce a Kano, sunanta Hafsatu, bata daya daga cikin zuri'armu....." Wani wawan mari Lamido ya sakar masa da bayan hannu, ya mike tsaye cikin fada mai tsanani yana cewa, "Tir da kai, ba zaka surka mana Zuri'a ba, tunda muka taso zumunci iyayenmu suke yi, don haka muma ba zamu daina ba har bayanmu, don kana takama da boko, bokon banzanka, na yi tunanin shine yasa kake zagaye-zagaye, kana juyamu kamar waina (masa), to kaje da Iyayenka zan yi, don ina girmamaka saboda sunan Ubana, zan ajiye uban a gefe in kamata inci mutuncinka, baka wuce duka ba a gurina, FITA!!!!! Abubakar ya tashi ya fita. Kafin wani lokaci ya kira dukkan manyan 'ya'yanshi ta waya ya fada musu yana nemansu gobe da safe. Abban Abubakar yana jin kiran ya sha jinin jikinshi kan batun Hamma ne, domin Dada ta fada masa komai game da abin da Abubakar ya ce. Ummi ta shigo dakin yana ta sintirin kai kawo, ta ce, "Hamma!!!" Ya dubeta ta ce, "Ka ja surutu cikin dangi, ko a Makaranta surutunka 'yan uwa suke yi, wai ka canja hali yanzu baka da biyayya, ni kam ka yarda da Fadin mana." Abubakar ya kama hannun Ummi ya rike kam, "Tun farko ina rokon Allah ya bani macen da nake so, zuciyata ta san da Fadima, amma ta kama son Hafsa ranar da na fara ganinta, nasan kema zaki so ta Ummi." Ummi ta ce, "Hamma ina son duk abinda kaima kake so, sai dai bana son matsalar dangi, zaka yi kallon halin da su Dada zasu shiga, tunda kace Lamido yana nemansu." Ya ce, "Ki taya ni addu'a, so baya barin mutum ya ji tsoro, ni da kaina na fadawa Lamido batun Hafsa, jikina yana bani zan yi nasara, kullum cikin mafarkin Hafsa nake." Ummi ta ce, "Allah ya amsa." Lamido ya mike yana kai kawo a tsakanin 'ya'yansa wadanda suke zaune akan kafet. Dukkansu manyan mutane ne masu fada aji, domin wannan yana wane wannan ne a kudi. Ya dubi Mahaifin Abubakar ya ce, "Ibrahim dauki wayarka ka kira min danka Abubakar." Nan take Abba ya aikata haka, shima Abubakar nan take ya bar komai ya nufi gidan Lamido. Abubakar gabansa ya fadi ganin daya yiwa Iyayanshi kamar masu neman gafara. Dakin yayi tsit sai karar agogo, jiki a sanyaye shima ya zube tare da sunkuyar da kai, sai dai duk da haka bai ji a zuciyarshi cewa zai canja daga batun son Hafsa ba. Lamido ya ce, "Abubakar!!!" Cikin zafin rai ya ambaci sunan. Abubakar ya dago da kai ya dube shi, Lamido ya nuna su ya ce, "Su waye wadannan?" Abubakar ya kalle su ya ce, "Iyayena ne." Ya ce, "Da kyau." Ya ce, "To ina son ka fada musu abinda ka fada min jiya." Abubakar ya sake dubansu gabanshi na faduwa, musamman da suka hada ido da Baffa Magaji, Lamido ya ce, "Ka fada musu nace." Abubakar ya kasa magana. Ya ce, "OHO!!! ni ka raina kenan da ka zo ka same ni kafada min saboda ba nine na haifeka ba?" Baffa Magaji ya ce, "Ka yi magana mana, wane ne sa'anka a nan?" Abubakar ya ce, "Dama kan batun yarinyar da nake so ne, wadda ba 'yar cikin zuri'armu ba." Dukkansu suka hada baki gurin tambayarshi, "Me ka ce?" Illa Babanshi da ya sunkuyar da kai cikin matsanancin takaici. Baffa Magaji ya ce, "Kai ko Shaidanin yaro ne, zaka kawo mana sabon al'amari cikin zuri'a." Lamido ya daga ma Baffa Magaji hannu, sannan ya ce, "Ban taraku kwanakin baya ba na gaya muku cewar kar wani daga cikin 'ya'yayenku ya kawo mana wani sabon al'amari a cikin zuri'armu ba?" Duk suka ce hakane. Ya ce, "To lokacin ina zargin Abubakar zai aikata haka, gashi zatona ya zama gaskiya. Don haka yanzu kai Ibrahim tunda ka kasa tankwasa danka ba ka iya bashi tarbiyya ba, ina son ta bakin ka kafin kuji ta bakina." Abba ya nisa ya ce, "Lamido Allah ya huci zuciyarka, na jima ina fama da Abubakar akan wannan matsalar, sam ya ki bin umurnina, don haka ina son 'yan uwa da suke zaune ku zama shaida, daga yau na cire shi daga cikin 'ya'yana. Ina son Lamido ya cire shi daga cikin zuri'armu don girman Allah. Baffa Sa'adu ya ce, "Ina rokon alfarma gurin Lamido, da ya ba Abubakar dama muji uzurinsa kafin a yanke masa hukunci." Lamido ya ce, "Gashi ga ku." Baffa Sa'adu mai rike da sarauta a yanzun wato Mahaifin Hashim ya dubi Abubakar ya ce, "Dana fada mana dalilinka na son ka saki layin da ka same mu a kai?" Cikin karfin hali ya ce, "Baffa duk ciki ban samu mace mai irin halayen da kamannin da nake so ba." Abba ya ce, "Ka ji ko? In ba rainin wayo ba ace duk zuri'armu masu kyau da ilmi da tarbiyya amma ace ya rasa matar aure? Sai ya je yayo mana rore-rore?" Baffa Magaji ya ce, "Muna jin shi ai, ya fada mana irin matar da yake so muji dame yake takama." Abubakar ya ce da su Baffa, "Bana son macen da an kalleta za'a san kyakykyawa ce, nafi son baka kuma zuri'armu kusan duk kyawawa ne farare, game da batun halaye kuma, nafi son mace da bata cika wayewa ba, sai wadda bata cika buri ba, mai ilmi duka 2, mai tarbiyya da hankali da natsuwa, sannan kuma 'yar talakawa wadda za taji magana ta, ta girmama Iyayena da duk wani nawa, mai tsoron Allah a duk inda take, mai hangen na kasa da ita ba na sama da ita ba, wadda bata da rawar kai. Baffa kada ku yi zaton na raina tarbiyyar 'yan matan zuri'armu, ko ba za'a samu mai irin wannan hali a cikinsu ba, a'a za'a samu matsalar daya ce, ina son na auri wadda nake so kuma take so na, ba wacce take sona ni kuma bana sonta ba, Manzon Rahama ya hana auren dole, don yana da illoli, bana son a cikin zuri'armu akwai dayawa wadanda zaman hakuri da biyayya kawai suke yi, alhali babu biyayya ga abokin zamansu, hatta dan sabawa mahalicci." Baffa Magaji ya taso ya ce, "Wato auren zumuncin ne sabawa Mahalicci? To sarkin iya magana fada mana inda aka ce ya haramta?" Abubakar ya gyara zama, "Aure bautar Ubangiji ne, a duk lokacin da aka hada Ma'aurata dan dole ba so da kauna, to ba zasu yi wannan bautar ba yadda Ubangiji ya ce, maimakon lada sai kaga zunubi ya samu. Mu dauki misali da gidan Yaya Saleh, duk family ba wanda bai san tashin hankalin da suke ciki kullum ba, banda kuma sauran dangi da ba'a sani ba." Baffa Magaji ya ce, "Lallai Abubakar, boko ya sa ka fitsare idanunka, kana rigima damu saboda aurenka." Abba ya ce, "Duk wannan zantukan naka basu isa su zama hujja ba, tunda ba littafin da yai hani ga auren zumunci." Lamido ya ce, "Ikon Allah!!! Ashe tun ina da rai zan samu wani a zuri'armu da zaya kalubatanceni akan al'adarmu? Dole ne na dauki mataki, in ko ba haka ba in na mutu zumuncinmu rushewa zai yi." Abubakar ya ce, "Ku yafe ni, ba zan zama sanadiyyar rushe zumuncinmu ba, haske na zo mana da shi cikin zuri'a, ku kwatanta dani zaku gane nufina nan gaba. Ma'ana ku barni na auri bare." Baffa Sa'idu ya ce, "Abubakar mene ne dalilinka na cewa ba zaka auri mace mai kyau ba? Alhalin shine burin duk wani namiji." Ya kalli Abba, "Da ban san yin wannan batun ba, amma yanzu ya zama dole na fada, dalilai 2 ne suka sa nace ba zan auri mace dan kyau ba. Na 1 Yaya Mansur in baku manta ba lokacin da aka ce ya nemi Waslia bai ki ba, ya ce ko ba komai ai tana da kyau, da suka yi hadari fuskarta ta lalace, har yau ba wanda bai san irin wulakancin da yake mata ba. Abu na 2, lokaci mai tsawo daya gabata. (Abba ka yafe min abinda zan fada, ina dan yaro lokacin kun dan samu hargitsi da Dada, na ji kace mata abu 2 ne suka sa kake zaune da ita, na farko biyayya ga Lamido, na 2 dan kyanta da take da shi. Ta yiwu ka manta, kayi min afuwa ban so na fada ba) A lokacin in zaka tuna ina karami amma raina yayi matukar baci kwarai, da muka je Makaranta nake fadawa Hashim sai ya ce Ai shi jiya ya ji Dadarsu tana fadawa Abbansu zaman hakuri kawai take yi da Abbansu, don ita ba shi take so ba, daga lokacin na kudurce a raina bazan taba aure ba, sai wadda nake so take sona. Ina son iyayena ku taimake ni, ku duba hujjojina, in kunki ni zan hakura in yi biyayya amma har abada ba zanyi farin ciki ba. Duk jikinsu yayi sanyi, kuma sun tabbata kowannensu yanada shigen wanan matsalar ko shi bai son matar ko ita bata son shi, amma wanda suka hada kansu su suna zaune lfy. Baffa sa‘adu yace, ina rokon lamido yayi mashi izini yatafi, mukuma munyi shawara. Lamido yace, ya iya tafiya. Abubakar ya mike cike da kwarin guiwa ya fita. yasan adu‘a bata faduwa, don tashi yake tun 2 dare ko 3 yana fadawa Allah matsalar shi. Lamido ya dubesu daya-bayan-daya, kuna nufin kun amince da batun sa? Baffa jume yace, a a sai yanda kace. Baffa sa‘adu yace, da zai yuwu hujjojinsa sun isa a duba lamarin, koda a gaban kotu ne. Amma in zancena ya bata ran lamodo aimun afuwa. Lamido yace ban gamsu ba har yanzun, biyayya muke bukata kuma kuje kuci gaba da shirin biki duk suka watse, kowa zuciya cike da nazari. Da dare ya sake zuwa gidan Baffa sa'adu don ya lura shi mai saukin kaine, kuma zai iya taimaka masa har yaga ya ci nasaram ya ce Baba na zo ne naji ko kun gamsu da bayanin bayan tafiyata? Baffa ya ce, Lamido bazai taba amincewa ba, ni kaina na cutu da wannan hadin da ake yi tsahon lokaci, sai da na sake Aure sannan na sami nutsuwa. Dalilin musgunawar da mai dakina take min duk dan ranta baya son auren mu. Aure na da Bilki ita ma 'yar dangi ce amma ni na ganta na ce ina sonta, ta yarda. Daga kanta ne na gane aure kina so ina so shine aure, in mace tana sonka tana kaunarka da ka sami matsala zata fara tausayinka, zata yi komai don ta faranta ranka. Amma in mace bata kaunarka, Abubakar akwai matsala babba. Ni yanzun shawara daya zan baka, ka gwada. Kaje ka sami Limamin Masallacin Juma'a kasan aminin Lamido ne ko?" Abubakar ya ce eh, ya ce to kaje ka same shi kayi masa bayani da neman tainakonsa, kila a dace. Kasan mu 'ya'yansa ne bamu da wani karfin tankwara shi, ga rikicin tsufa. Muna son mu lallaba shi ne har mu rabu lafiya. Abubakar ya ce za shi. Sai da kafa ta dauke sannan ya shiga gida. Don yana tsoron haduwar shi da mahaifinshi. Yana maida kofa ana turowa, sai da gaban shi ya fadi, zaton shi Dada ce, amma ai yaga Ummi ranta a bace. Ya matsa ta shiga, ya dubi agogo sha biyu ta gota, ya ce Ummi kina menene baki bacci ba? Ta zauna "Hamma ka janye auren kan nan mana, Dada ta yini kuka, hawayenta ba sauki bane a wajenka." Ta zamo ta durkusa, "ka dubi Allah kayi hakuri ka yarda cewa haka Allah ya so ganin zuri'armu. Ya kama ta, "Tashi Ummi Dada da Abba zasu fahimce ni da zarar komai ya daidaita, kije ki kwanta, fata na daya ki taya ni fada ma Allah shine kadai mai maganin matsalata. Baffa Sa'adu ya bani dama ta karshe, idan har na gwada bata yi ba, na dauki alkawarin cewa na hakura." Ta ce "zanci gaba da yi maka addu'a," Ta fita. daga sallah asubahi bai dawo ba saboda tsoron haduwa da mahaifansa, gidan Hashim ya karya duk da ruwan tea ne ya sha. Yayi wa hashim bayani, hashim yace, sannu namiji. Kayi kokari, zan rakaka gurin liman. Bayan la‘asar suka sami liman agida, sun gaisheshi sannan suka gabatar da kansu, yayi murna da jin jikokin amininshi ne, daga nan suka kora mashi jawabin komai. Liman yace, to zan ganshi in Allah yaso zamu tautauna batun, in kuma ya sausauta ra‘ayinsa to akan nada kyau, don nasha yunkurin in fada mashi wanan al‘adar tayi tsuri, musanman in yana bani lbr matsalar gidan yayansa ko wasu daga jikoki wadanda basa zaune lfy. Amma nakan fasa in na tuna yanda ya dauki lamarin. To yanzu tunda dama tasamu zanyi kokari in nusar dashi. Sukayi godiya sannan suka tafi. Duk aranarce dai liman yayi tattaki zuwa gurin lamido, sunyi murna da ganin juna, duk da cewa ko yaushe suna haduwa. Sun gaisa sannan liman ya soma da cewa, aminina gurinka nazo da batu mai matukar muhinmanci, duk dacewa batun nawa ba zaiyi maka dadi ba. Amma inaso kakali lamarin ta fiska 2, addini da kuma zamani. Ni da kai dukanmu musulmai ne, muna koyi ne da manzon tsira (s a w) addini ya amince muzabawa yayanmu maza na kwarai amma bai yarda muyi musu auran dole ba. Idan muka dubi fiskar zamani zamuga cewa, mubar yayanmu suyi auren so da kauna, zaifi bamu kwanciyar hankali. Lamido yace, oho! Abubakar ya kawo maka karata kenan? Liman yace a a yazone yanemi da in rokyaka ka amince, yayi aure da wada yake so, wai shin ma wane dalili yasa ku rike wanan al‘adar sai kace bauta? Lamido ya ce iyaye da kakaninmu suna gudun hada iri da wani ne saboda kada mu gauraya da mugun iri. Liman yayi dariya sannan ya ce, da kai dani da bature da balarabe da igbo da hausa da duk wani yare daga mutum daya muke shine Annabi Adamu Alaihissalan. Sannan Manzon Rahma ya fada mana Musulmi 'yan uwan Musulmi ne. Lamido ya ce, amma nasha ji daga bakin ka kana cewa mai yanke zumunci ba zaya shiga Aljanna ba, wata rana kace ba mai shiga Aljanna sai mai sada Zumunta. Liman ya ce to ai ba ana nufin ka kamo wannan ka ce sai sunyi aure ne zumunta ba. Abinda ake nufi shine Ziyara, kwana biyu ka dade baka ga dan uwanka ba, shirya kaje ku gaisa kuyi zumunci, wannan shine sada zumunta. Yanke zumunta kuwa shine kace wane baya zuwa, don haka nima na gaji da binshi bazan je ba, kowa ya zauna a inda yake. Shine yanke zumunta, don haka ka sassauta ra'ayinka ka tafi dashi daidai da zamani. Sannan daidai da turbar addinin Musulunci, cewa aka yi in zaku yi aure ku nema wa 'ya'yanku Uwa ta gari. Sannan ana auren mace saboda abubuwa guda hudu, asalinta, kyawunta, kudinta da Addininta, Manzo SAW ya ce na hore ku da ma'abociayar Addini, don haka shawara anan sai ku duba, suwaye iyayenta? Kuma wanne irin hali gareta? In mai Addini ce shike nan. Ku hakure ku cebakomai saikuga ci gaba, ku cire 'yar wani dangin kusa ta cikin naku shine karuwa, shine zumunci dangin ku sun zama 'yan uwa da danginta, kuma ko bayan ranta zaku yi ta zumunci da danginta. Liman ya dinga bashi misalai tare da Hadisai zuwa Ayoyi, har jiki Lamido yayi sanyi, ya ce to zai gana da 'ya'yanshi, in yaso za a bincika aji asallinta. Amma fa sai dai in ya yarda ya hada mata biyu, domin baza a fasa Fadi ba. Liman ya ce, "Wannan ba laifi ba ne." Lamido ya kuma tara 'ya'yansa ya gaya musu cewa, sakamakon zuwan da Liman ya yi yayi masa bayanai da dama akan wannan lamari, dan haka ya nada Baffa sa'adu da su binciko masa 'yar wane ne? Sannan ya ce da Abba in yaje gida ya turo masa Abubakar. Ko da Abba ya dawo gida bai samu Abubakar ba, sannan duk wayoyinsa a kashe suke, ya kira Hashim yake gaya masa in ya ga Abubakar ya fada masa Lamido yana neman sa. Tare suka je gurin Lamido ya ce, "Hakika kana da sa'a, zan amince da auren in naji cewa Iyayenta masu mutunci ne, itama 'yar mutunci ce. Sannan kuma in ka yarda ka hadasu 2 ka auri Fadi itama. Sannan ita yarinyar tunda bakuwa ce anan gida na zaka kawota mu zauna da ita muga irin nata dabi'un." Har zai ce wani abu sai Hashim ya zungure shi, sannan ya ce ya amince. Lamido ya ce, "Shi bashi da baki ne sai kai?" Sannan Abubakar ya ce, "Na amince." Lamido ya ce, "To sai kuje, in mun shawarta lokacin da za'a je zaka ji."Farin ciki gurin Abubakar baya misaltuwa, ya isa gidansu da karfin gwiwa. Dada tana zaune suna hirarsu da Rukayya, ya zube gabanta yana neman gafararta, sun ji komai daga bakin Abba, sai dai ta ce, "Shawara daya zan baka, kada ka yi rawar jiki akan bakuwar da zaka kawo cikinmu, ka nuna kamar kafi son 'yar uwarka a kanta, ka tashi mun yafe maka. Ka samu Abba ka bashi hakuri, sannan ka samu Hashim ku je gurin Fadi." Ya ce, "To." Ummi cikin murna ta ce, "Ni kam in zaka Kano zan bika muje na ga Hafsat." Ya ce, "To, Amma sai na fara zuwa in na dawo sai muje tare."shi da Hashim suka nufi gidan Goggo Jami, sun jero ita da Fadi zasu fita, hannun Fadi rike da makullin mota, sai ga Abubakar. Suka tsaya Goggo da fara'a ta ce su shiga. Fadi ta musu sannu da zuwa, suka gaisa sannan Goggo ta koma ciki tasa a kawo musu abin sha duk da cewa da safe ne. Fadi ta gaishe su, Hashim ne ya ce, "To Fadima, kin san dai dalilin zuwanmu tunda magana ta yi nisa, yanzun ma yana kan hanyar tafiya ne muka biyo. In ya dawo zamu zo zuwa na musamman." Ta ce, "OH, zashi gurin KISHIYATA ko? In kaje ka gaidata." Ta mike, "Nima zan je office ne." Suka mike suma, Abubakar bai yi magana ba, Hashim ne ma ya mata sallama. Suna hanya inda Hashim zaya kai shi filin jirgi don zuwa Kano. Ya ce, "Kuna ta fadin Fadi nada mutunci, dubi irin tarbar da tayi mana." Hashim ya ce, "Kishi ne, taga kowa a family ita daya ake aure, amma ita su 2, dole ta damu." Abubakar ya ce, .... zaharaddeen Shomar what's app 08168575100 Sanadin Boko 2-6 Posted by ANaM Dorayi on 11:25 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO "Ummi fa dole ta tsani auren Fadi, saboda ita bata da kirki, da ace ina da yanda zan yi to ba zan auri Fadin ba." Hashim ya ce, "Na kula ai da zaka yiwa Lamido musu ne, shiya sa nayi saurin amsawa." Haka suka yita hira har ya kaishi filin jirgi, yau dai da farin ciki ya nufi Kano, kuma baya jin zai samu matsala da Hafsat. Tunda bawan Allah nan ya tafi na kasa sukuni, ga rigimar Shadad yana Aunty Uncle fa? Tun ina cijewa har ta ni da kiran layin wayarsa, amma abin takaici ana fada min yana kashe. Daga bisani nayiwa kaina fada na watsar da lamarinsa. Shadad ya murmure ya koma makaranta nima na koma bakin aiki na. Na yi mamakin Manaja da bai ce min kala ba, su Ishak ma sai mamaki suke yi, na kuma ci gaba da zuwa makarantata. Tun mun horu da shan garin rogo, yanzun ma shi na jika ma a matsayin abincin dare. Na shimfida mana tabarma a tsakar gidan kasancewar lokacin zafi ne ga Kano akwai zafi. Muna cikin sha naji bugun gida, na tashi naje na tambaya wanene? Muryar da ban tsammace ta a lokacin ba ce. Ya ce ni ne Sadeek, jiki yana bari na bude, ta re da haska wayata, na ce "Sannu da zuwa, shigo." Ya shigo Shadad har yana faduwa garin gudu yana fadin "Uncle." Uncle ya daga shi sama, na kakkabe masa tabarma ya zauna.nakawo masa ruwa, nazauna ina cewa ina yini? Yace lfy, ya jikin shadad? Nace ya sami sauki. Don ya latsani yaji ko na damu dashi yace, shine tun da natafi ko flashig nace ai bakamin sallama ba,kuma wayar taka ai akashe take. Yayi murmushi, yau naga canji anty. Kina ta min fara‘a yau ba daure fuska ba harara, why? Nace ina sa ran zan sami lbr mutumin kirki a gurinka, wanda ya taimakeni tsawon lokaci da ya wuce, mutumin da ya fara gina karatuna, yace meyasa kike tsamanin samun lbr sa gurina? Nace, kun dibi kama, sannan kayi mun batun da yayi min a lokacin baya, wato na buga kudi, yace, fada mun yanda kukayi dashi, na kalmashe kafa. Na zaiyana mushi yanda mukayi da shi, yayi dariya. Banyi mamaki ba lokacin da yace, wai hafsat me na kara ne kika kasa ganeni. Alhalin ni kuwa tun lokacin da muka daukeki zuwa wajen buki rahama da sagir na ganeki, duk da da yarinyace kwarai kuma siririya, in kina yar gala-gala takar yar siririyar kafar ta karye. Nace dama kaine? Sunanka abubakar sadeek? Nce wallahi ban ganeka ba, idanunka dai in nakala sai inga kamar na taba ganinka, kai gaskiya fa tunda muka hadu kake taimako na, na gode Allah ya saka maka da mafificin Alkairi. Sannan ina so ka yafemun rashin kunya da rainin da nayi ta maka bisa rashin sani. Yace, nifa bakiyi min komai ba, asalima burgeni kikayi, ya kali kofin gari bance ki daina shan gari ba? Nace shi muke dashi, yace ina indomie da na sai muku? Ace ba ajiya ka bani ba? In zan kwana ban ci ba ba zan taba abin wani ba, yace naku ne fa, banaso muyi jayaya yasa nace maki nawa ne. shadad yace uncle bakace ka daina guduwa ka barni ba? Yace, tafiyar gaugawa ce ta sameni. Ya dube ni yace wannan zuwan na musan man dan ke, duk da zuwan da na dun gayi abaya suma dan kene, ki shirya gobe zamu tauna muhimmin zantuka zan shigo, nace to. Ya mike ki dafa ma shadad indomie, zakaci ko? Shadad yace eh, yace to ni zan tafi kada kayi rigima, zan zo da safe in kaika school. Yace, to uncle, suka rakashi bakin kofa sannan suka rufe gidan suka dawo. Tun da na kwanta bayan nayi shafa‘i da wuturi na kasa bacci. Tunanina wacce irin magana zamuyi? Nasani ba zaya wuce zai yi mun batun bayan rabuwa ba, domin nasan zaya iya cewa zai mai dani gida. Niko anawa ganin lokacin komawata gida baiyi ba, duk da ina ceke da son kannena, da yaya umar, harma da shi babanmu. Inna kuwa ita nafi son gani, ina so kafin na hadu da ita sai na zama wani abu a SANADIN BOKO. Zan wanke laifina zanyi abun da na kasa a baya, a fili nace banyiwa inna adalci ba, Allah kada ka dauki raina sai ka hadani da ita na roke ta gafara. Kuka ya kwace min, da dakina zaiyi magana da zaice yasani lokacin kuka na kenan.ringin din wayata ne ya ka tseni, na dauka ina kalon numbobin, nayi mamakin yanda na hadace numbobin shi aranar da na fara ganin shi. Nayi salama muryarsa kasa-kasa bani son ya fahimci nayi kuka, ya amsa kin soma baci ko? Nace a a yanzunan na gama shafa‘i da wutiri, yace shadad fa? Nace yayi bacci shi tuni. duk mukayi shiru har saida na duba naga wayar na kunne, nace kana jina? Yace ina jin ki, muryarki nake son ji ki min hira. Nace wace irin hira? Yace ko wace, ina jinki. Me kakeso mu tautana gobe? Yace wannan sai gani gaki, nace to Allah ya kaimu, yace amin. Yauwa, ummi tace in gaisheki, bansam me yasa naji faduwar gaba ba, nace wacece haka? Yace kanwata, itace autarmu. Nace to ina amsawa. Ya akayi ta sanni? Yace, duk dangina sun sanki, labarina ka basu? Yace, eh, to me kace masu? Yace, zan fada maki shi gobe. Nace, to wai meyasa ka damu da ni tun farkon ganina ina yariya kake ta taimako na? Yace kila Allah yayi nine kawai don in taimakonki, kila watarana kayi min gori, shiyasa bana karbar taimakon maza, ko kasa in saka maka da wani abu wanda bani da izini a kansa. Yace, me kike nufi? Yaci gaba, kada ki damu kanki, ni bakince rance nake baki ba, zaki biya ni, nace dame zan biyaka? Naci gaba da cewa, kai baka cikin wadanda zasu cuceni, kai na daukeka yayana ciki 1. Yace a a kada ki dora min dutsin da zai shiga tsakanin halas da halas, nace kamar yaya? Yace sai dai nazo gobe, yace kiyi bacci dani a ranki zakiyi mafarki innazo kifada min, goog night. Ya kashe wayar. Nayi shuru ina so in tono abubuwan da mika tau tauna, amma na kasa, illa kalmarshi ta karshe da yace kada nashiga tsakanin halas da halas, dan kawai nace shi yaya nane na daukeshi uwa daya uba daya? Kamar yanda na saba duk bayan sallah asubahi sainayi azakar, haka da magariba. Yanzuma na gama namike na cika bokiti daruwa na nufi wanka. Da nafito nazo na tashi shadad, yana bude ido nace mashi adu‘ar tashi daga bacci kada ka manta. Nan take ya karanta. Na sunkuce shi sai bayi, nai masa wanka nasashi yayi alwala, na zura mashi jallabiyar sa mai gajran hannu wanda na sai masadon yin sallah. Nace to maza yi sallah kuma kayi adu‘a yace to. Na koma na dauko sabulun da mukayi wanka dama na wankine nazo na wanke muna kayanmu, cikin raina ina mitar kayan shadad duk sun kode inna sami kudi zan sai mai wasu. Tsaf na shiryashi cikin kayan makaranta na dafa mashi indomie, na share ko ina gyara. 7 da rabi na gama komai, sai kurum naji bugun gida, nazaci dan a daidaitana ne sai da na bude naga Abubakar tsaf cikin riga da wando blue jeans, riga baka. Takalminshi sau ciki bakake, sumarshi tanata sheki baka wuluk. Kamshin turaren jikin shi ya cika gurin, ya shigo shadad ya kwaso da gudu ya nufo shi. Sama ya dagashi yana cewa, serious student, har ka shirya? Nace, bari nayi maka shin fida. Yace a a zo mu kaishi tukunna. Na saka hijabi muka fita, muna direshi a makaranta yace min shifa yunwa yakeji, nace to yanzu yaya za‘ayi? Mukoma gida inmaka indomie. Yace an ta cin abu 1 kenan? Muje gurin abinci nikam yau masa zanci, nace nifa bana son abin siya, nafi son komai inyishi da kaina, yace zakiyi min masa? Muje kasiya lokaci ya kure.a zatona in yasiya gidanmu zamuwuce, sai naga mutum ya nufi wata hanyar, masaukin sa ya kaimu na dube shi gaskiya sadeek ba zan shiga hotel ba, babu mutunci gareni matsawar aka gani cikin nan. Yace nafiki kishin hakan, ba dan dani bane zamu shiga nan ba zan aminbe ki shiga ba. Muka shiga daki tamkar a gidanka. Ya zauna wai muci waina, nace a a ba zanci ba. Yayi nace ni bana cin masa, nama karya fa. Yace ban yarda ba kice dai kina jin kunyata, nace nifa na kosa inji maganar da zamuyi, inada kagara. Yace, bari in gama. Sai da ya koshi ya dora da ruwan shayi da yasa aka kawo masa, sannan yace to kafin inyi maganata, zanyi maki tambaya 1 rak! Nace to, kina da aure? Nace a a, yace to gaskiyar magana ba wata kwana ko dogon turanci, ina sonki zan aureki nan da yan watannin da basufi 2 ba....da sauri na mike saboda zantukan da naji suna yawo a kwanyata, na nuna shi, kana sona? Ni kake so? Na bubuga kirjina, yace com down my hafsy, ki tsaya mu fahimci juna. Jikina ya soma bari, jin ya ambaceni da hafsy, sunan da munnir ke kirana dashi, da ina son sunan aman yanzun in da sunan da na tsana to shine. Nace, nina sani, dole dawainiyar da kayi ka nemi ka fanshe, to karya ne kakeyi ba kai bane wannan bawan Allah mai tai mako don Allah, kaima cutata kake sonyi. Da gudu na nufi hanyar fita ban san ya akayi ba kawai na tsince shi gaba na yayi key din kofar. Yace, ki saurare ni, bana nufinki da komai sai Alkairi, nace bana so. Jikina kake bukata. Tsaki yaja ya koma ya zauna yana kallona, na jingina da kofar ina kuka, har na gama bai hanani ba. Yanata dan ne dannen wayar shi, nagaji nace ka bude mun kofa, yace in kinga kin fita anan to kin saurare ni, kuma amsar cewa kina sona zaki aure ni, nace bana sonka. Yayi murmushi, karya kike kina sona, haushi ya kara kamani, nace ni bana sonka, Allah ka bude mun kofa in tafi abina.Maimakon amsa da naga ya mike ya nufi gadonsa ya cire rigarsa da farar singileti, ya hau gadon ya kwanta, kauda kaina nayi ina tura baki, ina cewa indai sai nace ina son ka sai dai mu shekara a haka. Wasa wasa har lokacin sallah yayi, ina kallon shi lokacin na gaji da tsayuwana tsuguna, yayo alwalar shi ya tada sallah. Nazo kan gadon na dinga neman key har ya idar ban gani ba, na koma inda nake, ya kira wayar Sagir wai don Allah ya fadawa Rahma karfe biyu taje makarantar su Shadad ta dauko shi ta tafi dashi gidansu, mu munyi tafiya. Ya dube ni, ki shiga kiyi sallah, na ce in naki fa? Ya ce ki gamu da Allah. Ya fada kan gadon shi ya ci gaba da bacci. Ina ta neman makullin ina sanda, amma Allah baibani ikon ganin sa ba, don haka naje nayo alwala nayi sallah. Ina zaune ina tunanin anya kuwa wannan dan tahalikin cutata zaiyi? Amma bari ya tashi na gwada yi masa dabara duk da naga shima kar yake kallo na, amma da macucci ne da tuni ya aika abinda zuciyarsa take so. Daf da la'asar ya farka, ya shiga bayin nake zaton ruwa ya watso da naga ya jima kuma ya shiga da wasu kayan, ya fito yayi sallah, sannan ya ce nifa ina jin yunwa. Na hada rai na ce to ni ina ruwana, ya ce ke mijinki yana jin yunwa zaki ce ina ruwanki? Na ce ni dai ka bude ni in tafi. Ya kira waya wai a kawo masa jalof din shinkafa da farfesun koda. Ya dube ni me zaki ci? Na ce nidai burin in bar nan, ya share ni. A raina na kudurce ana kawo masa abincin zan fice koda tsiya, amma ana danna kararrawar kofar sai naga ya zuge gilas din window yayima ma'aikacin magana ya amsa, ya zauna yana ci yana waya da Hashim cikin fillanci jifa jifa yakan sako hausa, anan ne na gane zancena yake yi, lokacin da yake cewa Allah Hashin in zamu shekara anan sai randa ta saurare ni zata fita, ya sake juyowa ya ci gaba da fillanci. Ni kuwa nayi zugum kamar wacce take neman gafara, ganin yamma tana kara yi bansan abinda zai biyo baya ba idan dare yayi, don haka na ce bari na saurare shi, kafi sannan bari na gwada dabarata ko da lalata yake sona. Sai da ya gama wayar na ce to naji zan saurare ka, amma banda yau. Don yau ina azumi ne, in ma jiki na kake so ka bari gobe zan baka. Ya dube ni da sauri, jikinki? Ina jikin kin yake? Ya ja tsaki banga jiki anan ba, ni ke nake so, zatinki na ke so ba jikin ki ba, kin tsaya kina zabga min karya wai kina azumi. Ki tsaya muyi magana shine mafita, amma har wani jiki kike dashi? Na ce in ba jikina ba me kake so? Ya ce halayenki da ke kanki nake so, inna sauraroka, yi batunka. Ya ce tashi ki matso nan dan bazan iya daga murya ba kamar fada. Na dan matsa ya ce bana bukatar sai kince kina sona, na riga naga sona a idon ki, fada min inda su Baba suke in tura magabata na, nayi shiru, tunani nake ga garin zuwa amma babu zanin daurawa, lallai zanso haka sai dai nasa in Abubakar yaji labarina bazai aure ni ba. Sannan in shi ya yarda iyayen shi baza su yarda ba. To ni da na shigo duniya ma yaya za'ayi mutum mai mutunci ya aure ni? Yanzun ma ina zan san inda iyaye na suke? Tunda nasan ba gidan kanshi yake ba, gidan haya ne kila yanzun ya tashi... "Ba ki bani amsa ba." Ya katse ni. Na ce ni fa kaga ka kyale ni, bazan aure ka ba, ya ce nasan kina tunanin ki fada min kin taba aure kada in ce bana son bazawara, to kin min kuma zan aure ki a haka. Shike nan? Takaici ya sa wasu hawaye zubo min, nace a raina da na taba aure me zai hana ni fada?" Ya ce ki fada min damuwarki bana son kuka. Na ce, ina rokon wata alfarma a gurinka, don Allah ka zauna a matsayin yayana, mai bani shawara in bukatar hakan ta taso, ka zam mai min fada a duk lokacin da nayi ba daidai ba, na dube shi in nayi abin duka ma ka doke ni....." Na fashe da kuka tare da sa kaina cikin hajabi. Ya zo ya tsuguna a gabana, ban sani ba sai da naji muryarsa dab dani. Abin zaifi armashi idan kika amince na zama mijinki majibancin lamuranki, mai saki cikin farn ciki, mai kare lafiyarki da mutuncinki, hanyar shiga aljannar ki. Hafsat ina so da kaunarki, ki amince. Wallahi nasha alwashin zama dake har karshen rayuwata, bazan sake ki ba yanda mijinki na baya yayi, zan rike danki tamkar ni na haife shi." Na dago ina kallon shi, shi zatonshi na taba aure mijina ne ya sake ni, ina ma ace haka ne? Da tuni nayi magana. Na ce kayi hakuri duk ba wannan bane, don Allah ka kyale ni kawai yanda ka ganni." Shima shiru yayi. Can ya ce. "To naji, yanzun ki fada min inda mahaifanki suke kawai." Na ce ban sani ba, wallahi ban san inda suke ba. Ya ce to shike nan share hawayen naki in maida ke gida. A cikin mota ni dashi kowa tunanin shi daban. Motar tsit kamar babu kowa a ciki. Shi a tunaninshi kila bayan nayi aure baban Shadad ya sake ni nabar gida, kila Iyayena suna son in koma gidan mijina ni kuma naki. Ni kuma tunani na shine zanso matuka Abubakar ya zama mijina, don wannan gata ne Allah yayi min in dai na same shi a matsayin miji. Amma nasan da wahala in zai ji labarina ya aure ni. Ya tsaya kofar gidan mu jikin sa sanyaye, ya kifa kanshi a sitiyarin mota. Na bude kofar motar tare da cewa sai anjima. Ya zaro wayata daga aljihunsa na baya ya mika minn ni na manta ma ina da wata waya, na karba jiki babu kwari na shiga gidan sukuku, nayi sallolina na zauna cikin tagumi , Allah nake roko ya zaba min mafi alkhairi. Misalin karfe takwas suka shigo shi da Shadad, yau har cikin dakina ya shigo, Shadad ya zauna a jikina shi kuma ya tsaya da leda a hannun shi. Ya ajiye min ledar. "Kici wani abu zan kira wayarki anjima. Gobe da safe zan wuce kila na biyo." Sai naji har raina bana son tafiyar tashi, sai dai bani da izinin hana shi. Na bude ledar kaza ce da madara mai sanyi, rabona da cin kaza tun lokacin Hajiya Hindu Likita, Allah ka yafe mata har in gushe bazan daina mata addu'a ba. Na ci na koshi, Shadad dama da guntun baccin shi ya shigo, yana zuwa yayi bacci. Nayi shafa'I da wuturi na kwanta. Sam bana jin bacci zuciyata ce ma take ta azazzala ta tare da fada min bazata juri Abubakar ya subuce mata ba gara ma in san abin yi. Na kosa ya kira ni, sai gurin sha daya da rabi lokacin na debe tsammani da kiran sai ga wayata na ruri. Na daga da sauri don marmarin jin muryarshi. A tare muka yi sallama, sannan muka kara hada baki gurin amsawa. Ya ce kin fara bacci ne? Na ce a'a" ya ce ki fada min tsakani da Allah ki kasa bacci saboda menene?" Na ce bazan iya ce maka ga dalili ba." Yayi shiru, can yace sona ne ya hanaki bacci kamar yanda sonki ya hana ni. Muna son juna mezai hana ki bani hadin kai muyi aure? Duk abinda kike so zan maki Don Allah ki tainake ni Hafsat." Muryata can kasa, jikina yayi lukwi nayi juyi zuwa ruf da ciki. Sannan na ce in nace ba jin wani abu mai kama da so a tare dakai, hakika nayi karya. Sai dai in na saki jiki zuciyata tazame da sonka, a karshe zan sha wahala, duk ranar da kasan who I am. Ya ce ki fada min komai, bazan taba gudar ki ba, don kin sami wata matsala ko kina da matsala da iyayenki zan fahimce ki sosai. Na ce zan fi so in kabar batun aurena, ya ce in yi yaya da sonki to?" Na ce hakuri mana, nima hakuri zanyi." Ya ce amma da gaske kina sona? In na duba wasu abubuwa zan iya yarda cewa ina sonka, kai kadai ne kasa ni in manta alkawarin da na dauka na cin mutuncin duk wani namiji da yayi min kallo fiye da daya. Kaine kake sani inyi abinda ban niya ba. Ya ce har kin sani naji sanyi a zuciyata, don Allah ki taimaka muyi aure. Gidan mu an matsa min in fito da mata, yanzun haka an bani lokaci." Na ce dama baka da mata? Ya ce ina da mata, na ce to bazan taba auren ka ba don na san wata rana zata yi min gori. Da saure ya ce bani da mata wasa nake maki. Na ce duk da haka kayi auren ka ni bazan iya aurar ka ba, hirar mu daga jayayya sai zance soyayya, tare da magiya. Abin al'ajabi sai na jiyo kiran sallar farko. Na ce, "Sadeek kaji abinda naji kuwa? Ya ce me? Na ce, kiran Sallah fa." Ya dubi agogo yanzun nan fa muka fara magana, na ce shi ne nima na gani, to zaka shigo kafin ka tafi? Ya ce bazan shigo ba, kuma bazan sake zuwa kano ba tunda kince baza ki aure ni ba, kin kuma ki fada min dalili. Bance komai ba har lokacin da yace min sai wata rana, ya kuma kashe wayar shi. Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 2-7 Posted by ANaM Dorayi on 11:27 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Munir ya dubi mahaifiyar shi, fuskar shi babu walwala. Ta ce ya akayi? Ya mika mata takardar hannun shi, sakamako ne na gwaji ya amso, da sauri ta mike tsaye HIV? Subhanallah! Muje wani asibitin, ya ce Momy tun daga Dubai suka fada min ban yarda ba, sai da nazo nan na sake yi har kashi biyu, ta dauki waya jiki na bari ta kira Dady a waya. Kuka ta saka masa tana fadin Munir yana da kanjamau. Shima Munir din kuka ya saka, a sukwane Dady ya baro ofishinsa zuwa gida, ganin su cikin halin damuwa harda kannan shi, sai hankalin Dady ya kara tashi. Ya ce ku kwantar da Hankalin ku zan shirya mana zuwa America za a duba shi." Momy ta ce, zan fi son haka. Shi kadai ne ya rage min yanzun tunda yayanshi suka yi fada suka kashe kansu a Maleshiya, yanzun kuma a ce shima yana da kanjamau?" Cikin kankanin lokaci suka shrya suka tafi. Sai dai kash! Can ma sun tabbatar yana dauke da ita. Sai dai sun basu wasu maganguna cewa ya dinga sha, sannan idan sun zo nan ma ya dinga shansu. Jiki babu kwari suka dawo. Sannu a hankali ya hakura ya cigaba da zuwa aikin sa, yana shan magani. Sai dai koda yaushe yana zargin mahaifansa sune suka ja masa wannan halin, SANADIN BOKO. Da sun bari yayi aure ya tabbata baza ya zama daya daga cikin masu neman mata ba, gashi yayyanshi sun mutu su biyu. Shi kuma ga halin da yake ciki. Ya hadu da wata yarinya 'yar mutunci, Usataziyya a rufe cikin hijabi da nikabi, ya ce yana sonta. Tuni ya fara zuwa shira. Yarinya mai suna Nanah A'isha ta amince dashi, sam bai fada mata yana da ciwo ba, kuma ya gama sheke ayarshi, kuma yanzun 'yar mutunci yake son ya aura don cuta. Iyayenshi ma basu nuna masa abinda zaiyi bai dace ba, sai ma suka shiga lamarin suka yi dumu dumu suka yi ta barin kudi aka sa bikin. Wani daga cikin abokan Munir yayi mata text ta waya wai Munir yana da kanjamau, ko ya fada mata? In kuma bai fada mata ba to ta sani yanzun. In kuma tana musu to ta gayyace shi suje ayi gwajin jini. Nanah ta firgita kuma ta sanar da mahaifanta. Sune suka nemi Munir da ya zo suje ayi gwaji, nan da nan ya zuke daga nan kuma sai ya samu Nanah yana borin kunya, wai ya fasa tunda iyaynta basu yarda dashi ba. Ta ce to menene don sunce muyi gwaji, ai ba sai ta mummunar hanya ba ake dauka, ko malamai sunce ba laifi bane don anyi gwaji. Ya ce shi ya hakura, ta ce Allah ya hada kowa da rabonsa. Gida uku yana neman aure amma ana dagaoshi, bakin cikinsa ya karu. Dole ya koma wajen tsohuwar budurwarshi wadda suke rigima suna zargin junan su. A nashi tunanin ita ce ta sak mishi, ita ma tana tunani shi ya saka mata. Ya ce mata suyi aure kawai tunda suna shan magani, ta amince nan dai iyayen su suka shiga barin kudi tunda duk suna dashi. A yawon amarcin su ne suka je America aka duba su in da Likita ya tabbatar masu zasu iya zama indai suna shan magani, sai dai yana gani da wuya su sami haihuwa. Su basu damu ba, amma da suka zo gida Momy ta damu. Ta fadawa Dady cewa ita yanzun ba za ta samu jika ba a wurin yaranta maza? Ya ce kada ta damu, tunda ga 'ya'yanta mata. Haka suka ci gaba da zama shi da matar shi a unguwar Kinkinau. Sai dai kullum yana cike da bakin cikin ciwonshi, wanda yake danganta shi da iyayenshi duk SANADIN BOKO. *************** Baba ya dubi Umar ya ce, "Tunda ka yi aure ka kwashe kannanka baka son zuwa duba ni, gashi bani da lafiyar da zan fita nema. Ya ce "wallahi Baba bana son zuwa ne in ban sami dan abinda zan riko muku ba, yaran nan kuwa na kwashe su ne dan kuji saukin kudin haya. Nima can kasan buga buga ce kawai. Bus din tawa kwanan nan kudi kawai take ci kullum sai nayi gyara, Allah ya taimaka. Umar ya ciro dubu daya ya bashi tare da cewa "Ga wannan sannan ga doya nan" ya ce na gode Allah ya saka da alkhairi" Baba ta shigo ta ce, "Mun gode Umar Allah ya ba da lada." Har ya mike zai fita, ya ce Umar zomana" Ya dawo ya zauna. Baba ya yukura, Babah ta kama shi ta sa mishi filo a bango ya jingina. Ya dube shi dakyau. "Umar wai har yanzun babu labarinHafsatu ne?" Umar ya daure fuska, shi kam in karatune wannan tambayar to ya jima da haddace ta. Babah ta ce "Malam kai ne fa da kanka ka kore su, ba dole suyi nisan kiwo ba? Gara ma innar su sunsan inda take, amma Hafsa yanzun wayamasan tana mace ko a raye oho. Umar ya mike tare da cewa, "In da rabon ganawa za a gana." Baba ya ce, "Umar ina cike da nadamar abinda na aikata. Hakika ina zaton nine na yiwa Hafsa baki har kaddara ta fada mata, da ina mata addu'a da bata shiga wannan halin ba, ko dai zaka sa cigiya ne? Umar dai gani yau Baba yafi kullum rudewa akan batun Hafsat, sai ya lallaba shi da cewa. "To Baba, za a cigita kada ka damu" ya ce to Umar, a cigita. Allah yasa a dace." Tabbas tun bayan rabuwar shi da innar su Hafsat yaga matsaloli kala kala, ga ciwo ya sa shi a gaba, wai suga ya kwanta a asibiti har sau biyu. Umar ne ke ta fama dashi, don ma Allah ya taimaka Innar su ta sa shi ya saida mashin din ta cika masa ya sai Bus ya diban lodin kasuwa daga Rigasa. na dama ta shige shi yanzu tun da ya rasa matar shi fatansa ya samu yar. Cikin haka ne umar yaga yar uwar inna mai suna murja a wata ziyara da ya kai munanfashi. Yace yana sonta itama ta amince, nan aka kare komai inda aka sha buki,tare da dan madaidai cin gidan da ya kama mai daki 3 don haka ya kawo kannan shi zuwa gidan. Tun baba yana dan fita har ta kai baya iya fita din ma, ga ka‘idojin abinci, gashi ba kudi. Yanzu baba bashi da burin da ya wuce yaga hafsat, shikam umar ya kance bai san inda zaije yaga hafsat ba, domin yayi bakin cikin abin da ya faru. Kuma hafsat itace silar rabuwar iyayen su, shi sam bai ga laifin baba ba, tun da dai dai gwargwadon ilimi ta samu, sun dage sai tayi jami‘a, to ga abinda ya biyo baya yanzun. ************** Haka inna anata ban garen tana zaune lafiya gidan mijinta, da yayan taguda 2. Kuma duk sanda umar yazo takan tambaye shi ko ya sami labarin hafsat. Yace, inna ki daina batun hafsat, babu inda za‘aje nemanta. Ita tasan inda muke, inda muna ranta kamar yanda take ranmu da tuni tazo koda zamu kashetane. Kum inna ya kamata ki sauwaka ma kanki batun ta, dubi yanda tabaki kunya, ta zubar da kimanki ta kashe aurenki, dan kawai kin tsaya mata ta sami gishirin zamani, wato ilimi. Ta miki sakamako da haka. Inna tace, ina zaton kadarace ta fadawa hafsat, yanzu da tatafi ba asaniba ko tana raye ko tana a ma ce, kilama ta mutu gurin haihuwa. Umar yace, to muyi adu‘a kawai Allah ya yafe mata. Inna tace, amin. Amma nafi dora laifin kaina. Don da lokacin da mahaifinku yace bayaso tayi boko da na hakura da yanxu ban bar yaya na ba. Da yanzu bata gudu ba. Umar yace duk mu bar wanan ga kadara, Allah shine mafi sanin da lilin da hakan ta faru,tsakaninta da mijinta akwai mutiny's juna, haka nan ya yansa ta hada da nata yayan ta sunguma. ********* Abubakar ya dawo gida cike da rashin kwarin gwiwa. Cikin kwanakin duk ya canja ba kwanciyar hankali. Ummi ita ce ta fara gano haka acikin gidan su, ta dunga matsa mashi da son jin matsalar shi. Yace, kinyi kan kanta da in fahimtar dake halin da nake ciki. Tace zan gane hmma. Yace nida hafsat muna son juna, sai dai a kwai wani dalilin da take ganin zai hana mu aure wanda ban san dalilin ba. Kiyi shuru da bakinki kada wani a gidan nan yaji wannan zancen. Ummi tace, hmma ina tunanin zaka iya shawo kan kowace matsala da zata hanaka auren anty hafsa. Tunda ka iya shawo kan lamido ya yarda ka aure ta. Abinda ko iyayenmu ba zasu iya kwatanta hakan ba. Kai sadauki ne, kana da nasara a kan duk abinda kasa a gaba.ina ji ajikina zaka auri anty hafsa. Dadin kalaman ummi sun karfafa mishi gwiwa sosai, har ya bata kyautar wayar da take ta nacin ya bata. Da yace sai ta gama secondary. Amma yana bukatar ya kara natsuwa kafin yagane ta in da zai shawo kan matsalar. Ko da ya fada ma Hashim cewa hafsat taki, tace ba zata aure shi ba saboda wasu dalilai nata. Hashim yace, kada ka damu zamuje tare kuma zata yarda. Amma yanzu abinda nafi so ka nutsu, iyayanmu su san ka karbi fadi. Dan haka yau dadadare zamuje zance. Daga ofis super market ya wuce inda ya siyo kayan shafe-shafe da tande-tande dan suyi tsaraba. Lokacin da fadi ta nufo su abubakar, ya zuba mata ido. Gaskiya tana da kyau, sai dai baya jinta a rai kamar hafsa. Ta zauna suka gaisa, tace ya dawo lfy? Yace lafiya lau. Hashim yace, mun zone dama mu dan gaisa. Amma yanzu bari in matsa ku zanta ke da yallabai. Abubakar yace kaje ina, kamar dai zamu shekara? Bai saurari Abubakar ba, ya fita. Fadi tace, don baka sona shi ne zaka ce wai sai kace zaku shekara? Ni to ina son ka. Ya dube ta kin ji abakina cewa bana sonki? Tace, banji ba, amma naji yanda kaita kokarin doje ma aurana. Ni kam ko wane lokaci nayi sallah ina fada ma Allah cewa ya bani kai amatsayin miji na, gashi ya amsa. Ranar da aka kawo mintin bai kon mu da sa rana ban iya bacci ba don murna, gani nake daga bacci ya debe ni zan farka in ga cewa ba gaskiya bane. Zugun abubakar yayi yana kalon kasa, wannan al‘adar tana cikin al‘adun da ya tsana a mata. Ba wai haramun bane mace tace tana son namiji, amma a kalla kijira ya fara furtawa. Shi yasa yake son hafsa, don tana da kamun kai. Shi a nashi ra‘ayin in dai mace zata fito tace tana son namiji ba mijinta ba, ko kuma shine yazo da da‘awar son shi gurinta ta amsa mashi ba. To wannan bata cika mace ba a nashi ra‘ayin.........ta katse shi. Na san waccen yarinyar da kake nema ta kano din tafi ni kyau ne ko? Ya dago kai, please ki muyi maganar da ta shafeni da ke, bana so kina saka hafsat. Tayi dan diM, can tace shi kenan. Yanzu wane shiri zamuyi? Ya kamata bukinmu yazo da sababin salo na burgewa acikin zuri‘ar mu. Yace, ko? Tace, sosai kuwa. Yace, to ki rubuta duk abinda kikeson ayi, in yaso in nazo zan gani. Ya mike zan tafi gida, ga yar tsaraba nan. Ya nuna mata lader. Cikin doki tace, amma na gode. To yanzu har zaka tafi bamuyi wata fira ba sosai. Wani lokacin in nazo zan dade. Ta rako shi har bakin gate in da hashim yake tsaye da jamilu yayan fadi. Suka gaisa da jamilu, inda ya shiga jin jina masa da cewa ya gode da wanan jahadin da yayi a gurin lamido, inda ya samo musu yanci. Abubakar yace au! Kai ma kayi farin ciki ne? Jamilu yace, ba dole ba, don yarinyar da nagani zuciyata ta so ba yar zuri‘ar mu bace. Son yarinyar ya shige ni a kudu muka hadu da ita lokacin da muka je (N Y S C) Allah ya shi maka albarka bayan bukinka zanyi maganar tawa. Abubakar yace Allah ya taimaka, mu kam bari mu tafi. sati 2 tsakani da zuwan shi kano, lamido ya kirashi to kasan lokaci yana gabatowa, don ha sai kafadi inda iyayen yarinyar nan suke saboda aje a kammala da su suma. Zufa ce ta soma tsatsafo ma Abubakar, amma sai yace, am.....dama mahaifinta yayi tafiya ne shi yasa. Amma idan ya dawo sai in fada muku saboda ya riga ma ya san da maganar, kuma su a shirye suke. Lamodo yace, to cike da damuwa ya fito, dole ne ya koma kano gobe sai sai ya takurawa hafsa don yasan abinda take ikirari zai hana auren su. Ya kira phone din hashim yace, ka shirya gobe juma‘a zamu shiga kano, sai mujuyo ranar sunday. Hashim yace, to ******* Nikam tun ranar da abubakar ya tafi na shiga halin kunci da damuwa. Na rasa dan ragowar farin cikin da ke tare dani. Ina zuwa makaranta da gurin aiki, amma bana iya cin wani abu. Ban amince ina son abubakar ba sai yanzu. Har shadad yafini hakurin rashinsa, duk da cewa sun shaku matuka. In nayi kamar in kira lanbobin da ya bani sai in fasa. Nace, kai gara in koyi yanda zanyiwa kaina fada, in hori zuciyata ta saba da rashin sa kada in zurma da yawa in kamu da ciwon zuciya a banza. Don nasan babu mai hankali da zaya aureni. Kai akwai daran da na rabashi ina kuka. Ba zance irin kukan da na saba bane, wannan kukan son abubakar ne. Yau satin mu 2 rabon mu dashi. Ina zuwa ne cikin aji, duk da hankalina yana gurin malamin amma har yayi ya gama ba zance ga kalma 1 da yake fadi ba. Tunanin Abubakar sadeek kawai nake yi. Na san abaya na so munnir amma ban shiga irin wannan ma tsanancin halin ba. Wani irin abubuwa nake ji game dashi, waddanda ba zan iya fasrasu ba. Kenan da ba son mannir nayi ba. Kenan da shirme nakeyi. Ya rintace tasa nake ganin kamar son shi nake. Karshe ya cuceni, shima dama ba sona yake yi ba sha‘awa ce. Gashi dalilin abin da yayi min yasa na rasa abubakar sadeeek. har aka watse cikin aji ban sani ba. Da yake ni ba kawa ko aboki gareni a makaranta ba, babu wanda ya kulani. Kasancewar ko yaushe cikin daure fuska nake, masu son kulani ma tuni sun watsar dani, saboda rashin fuska. Ringing din wayata ne ya dawo dani daga tunanin da nayi zurfi acikin sa. Jikina lakwas na dauka. Nasan rahama ce, tunjiya take min nacin inje tana nemana, ba tare da na duba fuskar wayar ba na kaita kunnena. Muryar da tayi min sallama ce tasa naji na watsake. Bansan na mike tsaye ba, ina cewa. Wa‘alaikumus-salam. Yace, ina kike ne? Sai na samu kaina da wani jan aji, ina tambayar wanene? Da sauri yace, kina nufin baki ganeni ba ko? Nace, eh. Yace, good! Ki fada min inda kike sai inzo in sameki. Nace, ban gane kowanene ba ya za‘yi in fadi inda nake? Sai kurum ya kashe wayar shi. Take naji haushin kaina, mutumin da nake son gani ruwa a jallo amma yanzu na tsaya salo. Da sauri na fita na nufi gida, ko in biya in dauki shadad wai ina zaton yana kofar gidanmu. Ganin bashi na juya da sanyin jiki na nufi makarantar su shadad na daukoshi muka nufo gida. Hashim ya kali sagir yace, kaima kazo muje mu 3 don mu sami galabarta. Sagir yace, nifa shaknar hafsat nake ji, gashi tana bani girma kada taga zamu matsa mata. Rahama tace, ka daure kuje, kila ganin idonka ta sausauta. Abubakar yace, nifa hafsat nasani tana sona. Dalilin da take fadin cewa ba zai bari muyi aure ba shine nake son ji. Sagir yace, to ku tashi muje. Suka mike yana mitan cewa dan miskilanci irin na hafsa waima nine bata gane ba yau. Hashim yace, kai dai wannan abu yayi maka ciwo. Kasani ko kila bata gane kadin bane? Sagir yace, wannan yanuna kai kadai kake sonta, ita bata sonka kamar yanda kake zato. Abubakar yace tabbas tana sona, amma ku muje dai. Misalin karfe 8 na dare, Shadad ya yi barci, muna kan tabarma a tsakar gida, ni kuwa lokacin zuciyata ta kekashen idanuna sun bushe ina ta tunanin ina cewa, "Ya Allah, dama haka so yake?" Na tashi zaune, na mike tsaye, na jingina da bango duk banji dadi ba dai, zuciyata tana tuhumata da cewa nice na bar dama ta, me yasa na nuna ban gane shi ba? Sai kuma wata zuciyar tace ki daina saka kanki cikin matsala, ba zai aureki ba, keda kika yi cikin shege?!!! Na koma na kwanta, hawaye na sintiri a idona daga gefen idona zuwa kumatuna, so matsala ne, dama ban san Abubakar ba, dama ban zo Kano ba, dama ban je bikin Rahma ba. Bugun kofar ne ya sani na dawo cikin hayyacina, da sauri na mike cike da fatan shine, ba tare da na saka takalmi ba na nufi kofa, ban bukaci na san waye ba na bude kofa. Ganin shi tsaye ya sa na sauke wata nannauyar akiyar zuciya, sai kuma Miskilanci ya motsa na ce, "Daga ina? Ka canja ne ba kace ba zaka kara zuwa ba?" "Au korata kike? To shike nan bari na koma." Da sauri na ce, "Ni bance ba, ai ance bakonka Annabinka, ka iya shigowa." Ya ce, "Zaki ji da gulmarki. Hashim ku shigo." Na shimfida musu tabarma suka zauna, shi kuma ya zauna kan tabarma ta kusa da Shadad yana shafa masa kai, na kawo musu ruwa cikin jug, na nemi kujera 'yar tsuguno na zauna. Na gaishe su suka amsa, sai dai shi daya kafe ni da ido yana kallona, duk da ba wuta sai hasken farin wata, ya ce, "Ni ba zaki gaidani ba?" Na kalleshi irin hararar masoya, na maida kaina kasa. Ya ce, "Shine na kiraki dazu wai kike cewa baki gane ni ba." Shiru nai ban tanka ba Ya ce, "Ka gani ko Hashim ta gane ni." Sagir yayi dariya, "Kila bata gane ka din ba." Abubakar ya ce, "Bani aron hankalinki nan. Shi yasa na kwaso abokaina dan su zama shaida, da farko ina sonki, kuma ki ban amsa. Ta dago ta ce Abubakar bana sonka, ba aibu bane dan kince baki sona, in yaso sai sonki ya zama ajalina, amma daga yau idan har kinki amince min ba zaki kara ganina ba koda cikin mafarkine. Gabana ke faduwa, na ce, "To ai ban ce bana sonka ba." Hashim ya ce, "Pls Hafsa, magana daya zamu yi tunda kina da hankali tin taba aure bai kamata mu tsaya muna wasa da hankulan juna ba." Abubakar ya ce, "Magana daya ce Malama, kina sona?" Kalma daya ce da Hashim ya fada ta dagan hankali, wai na taba aure? Inama na taba auren ai da bazan damu ba, sam banji maganar da Abubakar yake min ba, su duk sun dauka aure nayi na haihu, to tun kan na samu matsala gwara na rabu da shi, sai dai sonsa ya zama ajalina, na ma rabu da iyayena ballantana shi? Tsawar da ya dakamin ita ta dawo dani daga tunanin da nake ya ce, "Kin maidani dan iska ne ina magana kin min shiru?" Hashim ya ce, "Ki yi magana mana Hafsa." Muryata ta soma rawa irinta masu kuka, "Lallai ina son ka har ba zan iya kwatanta son da nake maka ba. ..... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 2-08 Posted by ANaM Dorayi on 11:28 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Domin sonka ya shigeni ne a lokacin da nake tunani na ha'ka dogon rami na saka so a ciki na rufe shi, ina fatan kowa ya mutu ya huta. Amma abin bakin ciki sai da ya fito har ya zo ya kama ni, a bisa adalci Abubakar bai cancanta na zam matarka ba, matsayinka na kamili, kada ka so kaji dalili ko ka matsa min na fada maka." Na kifa kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka irin wanda yake sa jiki motsi, gidan ya yi tsit, gidan shiru kamar ba mutane.Abubakar ya ce, "Malama ki nutsu ki fiddamu daga tunani." Hashim ya ce, "Baiwar Allah ki nutsu ki mana bayanin komai, da kin san irin son da wannan bawan na Allah yake miki hakika da baki masa haka ba, ni abokinsa ne kuma dan'uwansa ne na jini, Mahaifina wan Mahaifinsa ne, tare muka taso kamar 'yan 2, ya san sirrina haka na san nashi, tunda muke da shi ban taba jin ya ce yana son 'yan matan da suke nacin sonsa ba, na kosa na ganki mai sa'a." Na dube shi na ce, "Ina son sa, kuma ina matukar farin ciki ace na samu mutum kamar Abubakar ya zama Uban 'ya'yana, amma kash!!!" "Amma kash me?" Sagir ya ce, "Dan Allah ki daure ki fada mana Insha Allahu za'a samu mafita." Na mike tsaye, "Ba wai ka aureni ba, da zarar ka ji matsalar, sirri ne zan fada muku." Na yi shiru, na yi ajiyar zuciya cikin kudurin gaya musu, "Amma ina so na gaya maka Abubakar ina sonka, kuma duk lokacin da ka tuno da ni ka tuna cewar na soka, zan ci gaba da sonka har karshen rayuwata." Na kalli Hashim na ce, "Za ka so dan'uwanka ya auri karuwa? Wadda ta bar gidan iyayenta saboda cikin shegen da tayi? Ta shiga duniya tana zaman kanta?" Abubakar ya mike zumbur ya ce, "Cikin in, in, wa? Wa kenan kina nufin ke karuwa ce? Cikin shege kika yi kika haifi Shaddad?" Na ce, "Kwarai kuwa, ciki nayi." Ban ankara ba naji saukar mari wanda idanuwana suka daina gani na wucin gadi, ya ce, "Tur da haihuwarki, kin cuceni da kika bar ni na fada son ki, Allah ya isa!" Ya fice fuuu!!! Sagir da Hashim suka bishi. Shadad ya farka a gigice sakamakon kukan da na fasa, na zauna kasa ragwab, ya zo ya fado jikina muna kuka tare da ina fadin "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha." Mun yi kuka ya ishemu, amma har daga bisan Shadad ya yi bacci, ni kuwa tuni zazzabi ya rufeni hakanan hawayen idanuna bai kafe ba, abin da nake tsoro kenan rabuwa da Abubakar gashi nan kuwa, Ya Allah! Ya ma aka yi na fada masa zancen a baibai? Kafin safe ko motsi na kasa yi don zazzabi da ciwon kai, Ga fuskata ta kumbura sumtum saboda marin da Abubakar yayi min, ga kuma kukan da nayi, haka muka kawan gidan ko sakata ban iya samu na sa ba saboda azabar ciwo. Da asuba da kyar na iya tashi nai alwala, a zaune na yi Sallah, Shadad ma Sallah kawai yayi dan ba zan iya yi masa wanka ba, har 8 ina kudundune ban san me zai biyo baya ba. Shin Abubakar zai iya rabuwa da Hafsat? Ko Munnir yana sane da cikin da yayiwa Hafsay? Baba fa da bangaren Inna kuwa suna ganin Hafsa? Duk amsar tambayoyin nan Sae kun biyo mu a littafi na 3 Godiya gareku Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels