Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels 3/4/24, 7:51 PM - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more. 3/7/24, 9:03 AM - my lovely sister: ❤‍🩹 *WAYE SHI?*❤‍🩹 *MARUBUCIYAR LITTAFIN* *1:-RAYUWAR ZAINAB* *2:-RASHIN MAHAIFIYA* *3:-YARIMA ASLAM* *YANZU KUMA GAMU ƊAUKE DA SABON LITTAFI MAI SUNA WAYE SHI ?* *STORY&WRITTING* *BY* *ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR*💪 *ROYAL STAR🌟}* *FREE BOOK* 📚📖. *Littafi mai d'auke da soyayya,Sadaukarwa,tausayi,ilimantarwa,har ma da nishad'antarwa,*faɗa karwa*ku dai ku biyo garkuwar taku* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* 🅿️..........1⃣↔2⃣. *BISIMILLAHI RAHMANU RAHIM DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI MAƊAUKAKIN SARKI WANDA YA BANI IKO NA KAMMALA LITTAFINA MAI SUNA YAREEMA ASLAM SANNAN YA BANI IKO YAU NA KAWO MUKU SABON LITTAFINA MAI SUNA WAYE SHI ? INA FATAN ZAKU BIYONI DAN JIN SAƘON DANA ZO DASHI A WANNAN LITTAFIN.* ______________ A fusace wata matashiyar budurwa ta bazata wuce shekaru sha shida a duniya ba ta ɓalle murfin wata mota ƙirar bogati ta fito jikinta sanye da uniform doguwar rigace ta ɗan wuce guiwowin ta sai doguwar safa fuskata glass ne wanda ya tufe rabin fuskar tata hakan ne bai bani damar kallonta sosai ba cikin tsawa ta ce" Safwan, Safwan" kaf ma'aikatan gidan sai da suka tsaya da abinda suke suka jeru a layi sukayi ƙasa da kai kallon su tayi ta cikin baƙin glass ɗin ta ce " ina Safwan" ta faɗa a tsiwace cike da rashin kunya shiru sukayi cikin ransu suna faɗin yau Safwan ya taɓo wannan jarababbiyar yarinyar mun shiga ku tsawar data daka musu ce tasa sukayi saurin cewa a tare" Ranki ya daɗe tunda ya tafi kaiki makaranta bai dawo ba" shiru tayi kafin ta ce " idan ya dawo a sanar dashi inason ganinsa da gaggawa", da "toh ranki ya daɗe" suka amsa mata juyawa tayi ta nufi part Ammi. Tana zaune tana danna wayar ta taga shigowar Safna cikin fara,a ta ce "daughter kin dawo" fara,ar ta ce ta koma saboda zare glass ɗin datayi ganin idon Safna taf da hawaye ka mota tayi ta zaunar daita ta ce " daughter keda waye" cikin tsananin ɓacin rai ta ce "Ammi meyake ɗaukan kansa? waye shi ? menene taƙamarsa? aiki fa yake yiwa mahaifina yana biyansa amma sam baya respecting ɗina yau Ammi ƙin zuwa yayi ya ɗaukeni sai wani friend ɗina me Abdul yaga ina tafiya a ƙafa ya ragemin hanya ya kawoni har gida Ammi ya tozartani yau ƙawayena suka dinga yimin dariya wai ina tafiyar ƙafa Ammi bazai yuwu ba damar da Abba ya bashi tayi yawa dole fa yasan waye shi a gidan nan ba kowa bane face maƙasƙanci mai yimana aiki sannan ya dinga driving ɗina duk inda nake so naje" ta ƙasara cikin cije laɓa alamun zuciyar ta ba ƙaramin zafi take mata ba numfashi Ammi ta sauke kafin ta ce " kiyi haƙuri daughter kinsan Abbanki yanzu kina masa magana faɗa zaiyi miki dan na lura yaron ya asirce shi sam baya ganin girman kowa a gidan nan banda Alhaji ba wanda ya isa yayi masa magana yabi musamman ma ni daya maidani karkatacciyar kukar sa yafi raina ni akan kowa dan ni ban isa ma ince yamin abu ba ni wallahi ma tsoro yake ban" tsabar ɓacin rai Safna takasa magana miƙewa tayi ta nufi part ɗinta wurgi tayi da jakar hannunta sannan ta cire uniform ɗinta ta shiga wanka shower ta sakar ma kanta ko taji sanyi a ranta tafi minti talatin a toilet ɗin kafin tayi wanka ta fito gaban dressing mirrow ta nufa mayuka ta shafa a jikinta kala-kala bata buƙatar yin kwalliya dan haka lipstick kawai ta goga sannan ta bar gurin ta nufi wadrobe ɗinta riga da wando ta ɗauko wanda jins ne armey colour sai t-shirt ɗinsa ribom ta ɗauka ta ɗaure gashin kanta masha Allah tayi bala'in haɗuwa Safna kyakkyawa ce sosai kana ganinta kaga bafulatanar asali tanada tsayin hanci sosai da idanuwa fara ce saidai ba irin farin nan ba mai ɗaukan ido farinta yana sirki da ja ba ruwan ta da ɗaukan mayafi ko hijabi a haka ta tafi palourn gidan kamar yanda tayi tsammani ba kowa dining ta nufa ta fara buɗe warmers ɗin abinci duk abinda akayi be birgeta ba dan haka kichine ta shiga tayi farfesun naman kai wanda yaji kayan ƙamshi bayan ta kammala ta zuba wanda zata iya ci ta bar kichine ɗin zama tayi taci dan yunwa takeji bayan ta kammala ɗakinta ta koma ta sakeyin brush sannan ta ɗau littafin ta tanufi garden ɗin gidan domin tayi karatu kasancewar suna da C.A test ɗin english gobe duk rashin ji irin na Safna bata wasa da karatu sam tayi nisa cikin karatun ta taji alamun zaman mutum a kusa daita a hankali ta buɗe idonta ta sauke su akansa fuskar nan tasa a haɗe kamar kullum ranta ne ya ƙara ɓaci cikin masifa ta kalleshi da niyyar ta balbalesa da masifa saidai wannan kwarjin da ƙwayar idonsa suke mata yasa ta kasa cikin dakewa ta ɗauke idonta a kansa kafin ta ce " Mallam mene matsalar ka danine wai? na fahimci ganin kanka kake kai ɗaya dani koh saboda kawai Abbana ya baka dama koh to ya kamata ka dinga tuna waye kai, kai ba kowa bane face ɗan aikin mu ƙasƙantacce kuna driver na tuni idonsa sun kaɗa sunyi jawur tunda yake ba wanda ya taɓa gaya masa baƙaƙen magana irin haka sai wannan tatsitsiyar yarinyar tabbas yasan idan yayi yunƙurin hukun tata kashe ta kawai zaiyi dan haka yayi ƙasa da kansa yana ƙoƙarin danne zuciyar sa ita kuma ganin bai ce komai ba yasa ta cigaba "yau baka zo ka ɗaukeni a school ba kasani a albashinka na wannan watan" wata razananniyar tsawa daya daka mata ce tasa tayi wata irin gigicewa nuna ta yi yayi da yatsa ya ce "ke kin isa ki zauna kina gaya min magana kamar haka, kishiga hankalin ki karkiga kina yiwa sauran ma,aikata rashin kunya suna ƙyale ki Safwan ba irin su bane ni ba sakarai ne ba da zaki dinga gayamin kowace irin magana ina zuba miki ido ba dan haka ki shiga hankalinki" ta tsorata da yanayin sa amma hakan bai sa tayi shiru ba dan haka ta ce "ba tsoranka zanji ba fa dole in gaya maka matsayin ka tunda naga mantawa kakeyi kana ganinka a ɗan masu gida" tana faɗa ta zuba da gudu saboda tasan idan har ya riƙeta na lahira saiya fita jin daɗi. Shikuwa dafe kansa yayi yana mamakin rashin kunya irin na Safna ko za,a kasheta sai tayi dole sai na saita ta sai tagane ba kowa ake yiwa rashin kunya ba dole saina koyawa yarinyar nan girmama manya ta kowa ne hali. shima barin garden ɗin yayi ya nufi ɗakin dayake nasa a gidan kan gado ya faɗa har yanzu zuciyar sa tafarfasa takeyi. *KASH LAIFIN DAƊI ƘAREWA KUDAI KU BIYONI YANZU MUKA FARA* https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU domin shiga wanna group ɗin namu mai albarka mata zallah pls ba namiji *INA GODIYA A GAREKU MASOYANA* *#ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}* 3/7/24, 9:03 AM - my lovely sister: ❤‍🩹 *WAYE SHI?*❤‍🩹 *MARUBUCIYAR LITTAFIN* *1:-RAYUWAR ZAINAB* *2:-RASHIN MAHAIFIYA* *3:-YARIMA ASLAM* *YANZU KUMA GAMU ƊAUKE DA SABON LITTAFI MAI SUNA WAYE SHI ?* *STORY&WRITTING* *BY* *ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR*💪 *ROYAL STAR🌟}* *FREE BOOK* 📚📖. *Littafi mai d'auke da soyayya,Sadaukarwa,tausayi,ilimantarwa,har ma da nishad'antarwa,*faɗa karwa*ku dai ku biyo garkuwar taku* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* 🅿️..........3️⃣↔4️⃣. *BISIMILLAHI RAHMANU RAHIM DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI MAƊAUKAKIN SARKI WANDA YA BANI IKO NA KAMMALA LITTAFINA MAI SUNA YAREEMA ASLAM SANNAN YA BANI IKO YAU NA KAWO MUKU SABON LITTAFINA MAI SUNA WAYE SHI ? INA FATAN ZAKU BIYONI DAN JIN SAƘON DANA ZO DASHI A WANNAN LITTAFIN.* ______________Miƙewa yayi ya shiga toilet ɗin ɗakin nasa yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya na gwanjo kamar yanda ya saba gani yayi ba zai iya zama a ɗakin ba don ransa a ɓace yake kan maganganun da Safna tayi masa ɗazu fitowa yayi harabar gidan wajan Baba me gani ya zauna suna taɓa hira wayar sa ce tayi ringing ya zira hannu ya ɗauko ta a aljihunsa Nokia ce duk an nannaɗeta da kyauro ɗagawa yayi banji me akace masa daga ɗaya ɓangaren naji ya ce "to ganinan yanzu" miƙewa yayi ya cewa me gadi " Baba zan ɗan fita sai na dawo" ya ce "to yaro Allah ya kiyaye hanya" amsawa yayi da Ameen sannan ya fice daga gidan wasu motoci naga ya nufa a ƙalla zasuyi guda takwas duk kalarsu ɗaya baƙaƙene wulik sai guda ɗaya data banbanta dasu ita kuma fara ce motocin sunyi bala'in haɗuwa kafin ya ƙara wani soja ya buɗe masa ƙofar farar motar shiga yayi ya zauna kafin a hankali motocin suka fara tafiya suna barin layin kai tsaye Nasarawa G.R.A suka nufa wani katafaren gida naga sun nufa yanayin haɗuwar gidan zai bawa mai karatu mamaki gaba ɗaya unguwar babu gida mai kyan sa a parking space ɗin gidan sukayi parking duk guard ɗin da suke cikin motocin suka fito suka ƙame kowanne hannunsa riƙe da bindiga a hankali motar dayake ciki ta buɗe yana fitowa suka sara masa kallon su yayi ya ce "ina marshal Abbas?" a tare suka amsa da yafita tare da Amstron zasuyi binciken da muka fara" ya ce "ok bari in shiga in shirya zamuje wannan cafe ɗin da matar oga ke yawan zuwa" suka amsa da "toh yallaɓai" juyawa yayi ya nufi part ɗinsa falon gidan ya shiga ,yanayin haɗuwar falon sai baka sha,awa kujeru ne masu tsananin kyau a ciki blue da adon golden sai kuma ƙatuwar t v bango wadda take bango guda sai firish dake ajiye a gefe sai dining space da an wadata falon da fulawowi ba wani tarkace a falon alamu sun nuna gidan shi kaɗai yake rayuwa a gidan. bedroom ɗinsa ya shiga ai ban ida zama ƴar ƙauye ba saida nayi karo da bedroom ɗin komai na ɗakin na glass ne har ƙofofin hatta gadon na glass ne saidai kuma irin glass ɗin nan ne da ni ban taɓa ganin irinsa ba dan kamar katako haka yake abinda zai birgeka yana nufar hanyar bedroom ɗin ƙofar ta buɗe da kanta ba tare daya taɓata ba kyan bedroom ɗin yafi na falon sosai toilet ɗin ɗakin naga ya nufa yana tun karar ƙofar itama ta buɗe nidai na daki baki ina kallon ikon Allah zama nayi na cigaba da kallon ɗakin bayan kamar mintina biyar ya fito dreesing mirrow ya nufa zama yayi ya shafa mayuka kala-kala sumar nan tasa daya barbazata ya gyara masha Allah idan akace maka shine saurayin daya shigo gidan nan ba zaka yarda ba wadrove ɗinsa ya nufa wata tsadaddiyar shadda ya ɗauko golden colour yasa innalillahi aljan kenan balarabe zallah daka ganshi kasan ba bahaushe bane S G S funtua kenan matashin saurayi da duniya take alfahari dashi sojane wanda tantirai suke shakkarsa ana an batar sunanshi zakaga mai laifi yana zufa alamar tsoro ta bayyana akan fuskarsa cikin sauri yake fitowa dan yamma tafarayi kai tsaye cafe ɗin suka nufa yaran sa ne suka fita sukayi zagaye kafin su dawo suka ce" yallaɓai bamu ga alama komai ba" ya ce "ok ku maidani gida" suka amsa masa sannan suka shiga motocin su suka tafi a jere gwanin sha,awa bayan sun isa cikin sauri ya cire kayan ya maida kayan daya cire sannan ya barbaza sumar kansa ya dankwafa hula tashi kafiye naci wani abu naga ya shafa nan take farin nan nasa ya disha she ya canza kama cikin sauri ya shiga mota suka maidashi gidan aikin nasa. Ita kuwa goguwar tunda ta zura da gudu bata tsaya ko ina ba sai a part ɗinta numfashi kawai take saukewa har yanzu a tsorace take dan yanayin data ganshi daya riƙeta data kaɗe so take ta ɗauko littafin ta data manta a garden ɗin amma tsoro ya hanata shahada tayi ta fito saɗaf-saɗaf ta nufi garden ɗin tana ɗaukan littafin ta kuma kwasa da gudu ta bar gurin........ *KASH LAIFIN DAƊI ƘAREWA KUDAI KU BIYONI* *INA GODIYA A GAREKU MASOYANA* *#ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}* 3/7/24, 9:03 AM - my lovely sister: ❤‍🩹 *WAYE SHI?*❤‍🩹 *MARUBUCIYAR LITTAFIN* *1:-RAYUWAR ZAINAB* *2:-RASHIN MAHAIFIYA* *3:-YARIMA ASLAM* *YANZU KUMA GAMU ƊAUKE DA SABON LITTAFI MAI SUNA WAYE SHI ?* *STORY&WRITTING* *BY* *ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR*💪 *ROYAL STAR🌟}* *FREE BOOK* 📚📖. *Littafi mai d'auke da soyayya,Sadaukarwa,tausayi,ilimantarwa,har ma da nishad'antarwa,*faɗa karwa*ku dai ku biyo garkuwar taku* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* 🅿️..........5️⃣↔6️⃣. *BISIMILLAHI RAHMANU RAHIM DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI MAƊAUKAKIN SARKI WANDA YA BANI IKO NA KAMMALA LITTAFINA MAI SUNA YAREEMA ASLAM SANNAN YA BANI IKO YAU NA KAWO MUKU SABON LITTAFINA MAI SUNA WAYE SHI ? INA FATAN ZAKU BIYONI DAN JIN SAƘON DANA ZO DASHI A WANNAN LITTAFIN.* ______________Numfashi ta sauke da taga ta ɗau littafin a ɗakinta ta cigaba da karatun washe gari bayan ta shirya kasa fitowa tayi saboda tsoron haɗuwa dashi gashi test ɗin english ɗin ce farko shahada tayi ta fito kamar yanda tayi tsammani yana tsaye a bakin mota idon sa a lumshe kanta a ƙasa ta ƙara gurin don yau ɗin tunda ta tashi batajin ɗaɗi sosai tana ƙarasowa ya buɗe idon sa ga mamakin ta sai taji ya ce" good morning madam" kasa amsawa tayi amma hankalinta ya kwanta ganin ba abinda zai mata buɗe motar tayi ta shiga shima mazaunin driver ya zauna kafin yaja motar a hankali ya bar harabar gidan har sukaje school ɗin ba wanda yayi magana sai da zata sauka taji ya ce "sorry madam" ɗan satar kallonsa tayi sannan ta wuce ba tare data ce masa cikanka ba shi mamaki ma take bashi yau anya kuwa lafiyar ta ƙalau yasan halin Safna koda tana tsoron ka sai ta maka tsiwa da rashin kunya koda kuwa zaka kasheta amma ga mamakin sa yau sai yaga ta koma so silent sai yaji sam baiji daɗin hakan a ransa ba. Kai tsaye daga nan gidan sa ya wuce don akwai binciken dayake so sun gabatar kirane ya shigo wayar sa ɗagawa yayi yana faɗin "hello bross ka sameni a gidana" bai jira me za,a ce ba ya katse kiran ya cigaba da driving ɗinsa. a gidan ya samu marshal Abbas har ya rigashi zuwa gaisawa sukayi sanna ya ce "amma kana kusa dama naga ka rigani zuwa" ya ce "dama na taho kira nayi inji kana nan gidan ko kuwa kana gidan aikin naka" ya ƙarashe cikin zolaya" murmushi S G S funtua yayi ya ce "yanzu nakai ƴar rigimar makaranta dama kuma ina son haɗuwa da kai". ƙarasawa sukayi cikin falon gidan suka zauna a kan luntsuman mun kujerun dake ciki suna fuskan tar juna ɗan tsaki Abbas yayi ya ce "duk girman gidan nan wai babu mace in mutum yazo ku lemo babu mai kawo masa" harara SGS funtuan ya watsa masa ya ce "to kai tunaninka ko aure nayi mata zata dinga yimaka wahala ne" Abba ya taɓe baki ya ce "ai mu matan mu sayi maka" shiru yayi bai tanka masa ba. Ganin hakan yasa Abbas cewa " boss dole fa musan abinyi akan wannan matsafin a kowace rana sai an samu sassan jikin mutane biyar ko shida duk an cire musu wasu sassa na jikinsu sannan yana amfani da ƙananan yara ma wajan tsafinsa shiyasa ɓatan ƙananan yara shiyasa ɓatan ƙananan yara yanzu ya yawaita a ƙasar nan" wani irin huci SGS ɗin ya furzar zuciyar sa na ƙara hasala ya ce " Marshal bazai yuwu mu zuba ido mu cigaba da kallo ba tabbas hajiya Aisha tana da masaniyar komai Amma oga yaƙi bari ayi komai saboda matar shi ce dole musan mafita ta hanyarta ne kawai zamu samu bayani akan sa har mu iya kawo ƙarshen sa amma dole muma buƙatar mace a aikin mu wacca zamu sa ta shiga jikin hajiya Aisha ta dinga kawo mana bayani" shima Abbas ɗin nufashi ya sauke ya ce "hakane amma dole sai munyi taka tsantsan dan duk wanda ya ce zaiyi bincike akan mutumin nan rasa rayuwar sa yakeyi" murmushi SGS ɗin yayi ya ce" banda abinka marshal Abbas dama ai aikin soja aikin saida raine ko a kasheka ko ka kashe" ya ce "hakane bosss bari inje naga madam sai kira take" ya ce "ohk zamuyi magana anjima" sallama suka ƙarayi sannan Abbas ya tafi shi kuma SGS ya kwanta zuciyar sa fall tunane-tuanen wannan binciken da suka sa a gaba. "Mimi Mimi"wata tsohuwace fara soll daga ganinta duniya ta zauna mata take ta raɗa mata kira haɗe fuska Mimin tayi cikin ɓacin rai ta ce "wai nikam granny wannan kiran da kikemun kamar nayi miki sata fa" hararar ta tsohuwar tayi ta ce "yarinya sai baƙin halin jaraba dama keda Safiyanu bansan wayafi wani baƙin rai ba wallahi" sai kuma ta fara share hawaye" Allah sarki jikina Allah yasa ka dawo garemu ka sauke wannan fushin zuciyar taka mahaifin naka yayi nadama da kansa ya faɗamun amma kai ko ajikin ka kama manta da rayuwar mu Allah ubangiji ka kar kato mana da hankalin sa gida" sambatu ta cigaba dayi tana goge hawaye Mimi da haushin tsohuwar ya cikata kasancewar ta hanata yin chart ɗinta da friend ɗinta tsaki ta buga ta ce " ni wallahi granny kin isheni bari in bar miki ɗakin" kuka granny ɗin ta fashe dashi tana faɗin" ja'irar yarinya mara kunya rashin kunya zaki mun"...... *KASH LAIFIN DAƊI ƘAREWA KUDAI KU BIYONI* *INA GODIYA A GAREKU MASOYANA* *#ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}* 3/7/24, 9:03 AM - my lovely sister: ❤‍🩹 *WAYE SHI?*❤‍🩹 *MARUBUCIYAR LITTAFIN* *1:-RAYUWAR ZAINAB* *2:-RASHIN MAHAIFIYA* *3:-YARIMA ASLAM* *YANZU KUMA GAMU ƊAUKE DA SABON LITTAFI MAI SUNA WAYE SHI ?* *STORY&WRITTING* *BY* *ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR*💪 *ROYAL STAR🌟}* *FREE BOOK* 📚📖. *Littafi mai d'auke da soyayya,Sadaukarwa,tausayi,ilimantarwa,har ma da nishad'antarwa,*faɗa karwa*ku dai ku biyo garkuwar taku* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* 🅿️..........7⃣↔8⃣. *BISIMILLAHI RAHMANU RAHIM DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI MAƊAUKAKIN SARKI WANDA YA BANI IKO NA KAMMALA LITTAFINA MAI SUNA YAREEMA ASLAM SANNAN YA BANI IKO YAU NA KAWO MUKU SABON LITTAFINA MAI SUNA WAYE SHI ? INA FATAN ZAKU BIYONI DAN JIN SAƘON DANA ZO DASHI A WANNAN LITTAFIN.* ______________Nihla ce taji kukan Ammi ta shigo ɗakin da gudu tunda taga Anty Mimi ta juya ta fita dan tasan faɗa sukayi dan indai zasu zauna guri guda sai sunyi miƙewa Mimi tayi ta fita a ɗakin tsohuwar dan amsa kiran daya shigo wayar ta. Wata hamshaƙiyar hajiya ce zaune gefen ta ƴan mata ne guda biyu dukkansu jikin su sanye da ƙananan riguna wanda basu wuce gwiwoyin su ba kana ganinsu kaga cikakkun ƴan bariki dukkan su suna manne a jikin hajiyar suna shafata yayin da ita kuma take lumshe ido tana amsa kira a wayar ta sallamar commender Halima ce ta karaɗe falon da sauri hajiyar ta ture ƴan matan ta saka hijabi sannan ta bada izinin shigowa fuskar Halima ɗauke da murmushi ta ce "ranki ya daɗe" ɗan taɓe baki Hajiya Aisha tayi ta ce "dame kika zo waye ya aikoki" cikin sigar yaudara Halima ta ce "alkhairi ne ya kawoni gunki amma fa idan kin ban haɗin kai" gaba ɗaya hajiya Aisha ta maida kallonta kan Halima dan bata wasa da yaran mijin nata bata doguwar magana dasu amma yau kuma har Halimcy ce tazo take mata magana a haka cikin haɗe rai ta ce "ina sauraren ki" kujera Halimcyn ta samu ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ita dai Hajiya Aisha kallon ta kawai take kallon ta Halimcy tayi kafin ta ce"Hajiya Aisha taimako ne ya kawoni garunki akwai binciken da ake a kanki kuma ana zargin kina haɗe da matsafin nan jagus sannan kuma kina less mijinki yasan da cewa kina tare da jagus amma bai san kina harkar lesbian ba kina ɓoye wannan harkar saboda bakyason a sani amma ni kuma nasan komai da kikeyi inason ki nutsu kiji inason in taimake kine amma in kikayi ƙoƙarin cutar dani wallahi zaki gani kafin nazo gurinki akwai wacca na sanar wa komai akanki har bidiyonki na tura mata na sanar daita da zarar kin cutar dani ta watsa a social media zan zauna a gunki zaki zama ƙawata ta hakane kawai zasu kuɓuta ni kuma zan dinga basu bayanan ƙarya akanki har na goge zargin da suke miki amma dole zakina biyana duk wata sannan idan kikayi ƙoƙarin sanar da wani ta ƙaremiki don asiri baya cina kuma baya cin wanda suke bincike a kanki idan kina mamaki ki gwada yanzu". gaba ɗaya gumi ya gama wanke wa hajiya Aisha fuska karo na farko kenan data tsorata a rayuwar ta rufe ido tayi ta fara karanta wasu ɗalasuman tsafi amma me ko gezau halimcy ba tayi ba dan haka saita sallama ta ce "yanzu ya kike so ayi maganar ki zama ƙawata bata taso ba saboda kamar cin Amanar ƙungiyar mu ne amma san dinga biyanki kaso me tsoka" SGS Funtua da ke sauraron su ta na'urar dake maƙale a kunnen halimcyn ya ce "ki ƙara ƙoƙari dole ta yarda ki zama ƙawarta ta hakan me kawai zamu samu bayanai akan ta" haɗe fuska halimcyn tayi ta ce "ok na fahimci bakya buƙatar taimakona kinga tafiya ta" da sauri hajiya Aisha ta ce " tsaya dan Allah karki min haka na amince da buƙatar ki amma da sharaɗin matuƙar kikaci amanata sai naga bayanki" duk da halimcy ta tsorata hakan bai hana ta yin murmushi ba ta ce "kema haka" sannan ta fice a gidan". Cikin farinciki SGS Funtua ya ce "good job halimcy amma fa ki kula kar ki bari aga wata alama ta cewar mu kikewa aiki" ta ce "insha Allah yallaɓai zan iya bada rayuwata akan ceton Al,umma" ya ce "good za muyi magana anjima" ta ce "godiya nake yallaɓai" sannan suka katse kiran a gaggauce ya shirya ya bar gidan dan yamma tayi hakan ne yasa bai ƙarasa binciken da yake ba. Zaune take ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya chart take da ƙawayen ta sai wani ya mutsa fuska takeyi shigowar sa harabar gidan ne yasa ta ɗago idanuwan su ya haɗu da na juna harara ta galla masa sannan ta murguɗa masa baki sakin baki Safwan yayi danshi rashin junyar Safna har mamaki take bashi yarinyar daya girme mata sosai batafi sa,ar ƴar autar su ba Nihla amma sai shegiyar rashin kunya haɗe fuska yayi ya tunkaro ta ai kafin ya ƙaraso gurin ta zuba da gudu har tana zubar da lemon dayake akan ɗan table ɗin dake gaban ta abin har yaso ya bashi dariya tsoron yarinyar yayi yawa amma kuma bata fasa rashin kunya........ *KASH LAIFIN DAƊI ƘAREWA KUDAI KU BIYONI* *INA GODIYA A GAREKU MASOYANA* *#ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}* 3/7/24, 9:03 AM - my lovely sister: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU ❤‍🩹 *WAYE SHI?*❤‍🩹 *MARUBUCIYAR LITTAFIN* *1:-RAYUWAR ZAINAB* *2:-RASHIN MAHAIFIYA* *3:-YARIMA ASLAM* *YANZU KUMA GAMU ƊAUKE DA SABON LITTAFI MAI SUNA WAYE SHI ?* *STORY&WRITTING* *BY* *ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR*💪 *ROYAL STAR🌟}* *FREE BOOK* 📚📖. *Littafi mai d'auke da soyayya,Sadaukarwa,tausayi,ilimantarwa,har ma da nishad'antarwa,*faɗa karwa*ku dai ku biyo garkuwar taku* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* 🅿️..........9️⃣↔🔟. BISIMILLAHI RAHMANU RAHIM DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI MAƊAUKAKIN SARKI WANDA YA BANI IKO NA KAMMALA LITTAFINA MAI SUNA YAREEMA ASLAM SANNAN YA BANI IKO YAU NA KAWO MUKU SABON LITTAFINA MAI SUNA WAYE SHI ? INA FATAN ZAKU BIYONI DAN JIN SAƘON DANA ZO DASHI A WANNAN LITTAFIN. ______________Murmushi yayi ya nufi part ɗin sa a ransa yana faɗin ina sonki amanata bayan ya shiga ɗakin kiran Abbas ne ya shigo wayar tasa ɗaga kiran yayi da sallama ɗauke a bakin sa amsawa Abbas ɗin yayi yana faɗin "ranka ya daɗe na samu labarin hajiya Aisha tayi bukin ɗin jirgi zuwa senigal gobe" zumbur ya miƙe daga kashin giɗar da yayi ya ce "mene dalilin zuwan nata ka nemo minshi kafin tafiyar ta" ya faɗi haka yana yanke kiran dafa kasan yayi ya rasa ina zaisa ransa yaji daɗi kewar mahaifiyar shi ta kama shi yasan daya na kusa daita damuwar sa zatayi sauƙi gashi wadda da ta maye masa gurbinta ta rasu hawayen daya gangaro masa ya goge ya ce "meyasa daddy meyasa ni baka sona kamar sauran tunda ka haifeni baka nuna min so kamar sauran na samu duk wani abu na more rayuwa amma na kasa samun mai maye min gurbin Mommah na wadda tamin haka ta rasu Allah sarki Mommy insha Allah zan riƙe miki amanar ƴar ki Safna kamar yanda kika riƙeni nima. "Granny wai meyasa baki son zaman lafiya ne ke kullum kin fiso a dinga tashin hankali a gidan nan kawai kin kira daddyn mu sai faɗa kike masa akan ɗansa bai fiki son sa ba aka faɗa miki" Mimi ce ke maganar cikin ɓacin rai dajin haushin abinda kakar tasu tayi ma mahaifin su a gaban yara ita kuwa tsohuwar sakin baki tayi tana kallon ikon " kin gama nace kin gama mara kunya ni yarinyar nan narasa ubanwa kikayo a rashin kunya mahaifiyar ki ba haka take ba haka mahaifin ki amma shima Safiyanu tun yana ƙarami bayaji ko kaɗan kuma bari in gaya miki wallahi yarinya nafi ƙarfin ki fasa miki baki zanyi ni zaki yiwa rashin kunya" ta ƙarasa tare da fashewa da kuka tsaki Mimin tayi ta fice daga part ɗin ita kuwa granny kayan ta ta fara haɗawa tace wallahi sai na bar gidan nan Aliyu tun kan ƴaƴan ka su fara yimin duka Mommah ce ta shigo taga abinda tsohuwar take haƙuri ta samo bata tana rarrashin ta ta ƙyar ta haƙura tana faɗin " anci darajar ki da tafiya ta zanyi" zama Mommah tayi tana tayata hira har ta sake. tunda ya ɗauko ta zai kaita makaranta ya fahimci akwai abinda ke damunta tayi shiru yau ba tsiwa sam sai yaji ransa ba daɗi har suka iso makarantar bata sani ba ta tafi kogin tunani cewa yayi " ranki ya dade mun zo" cikin sanyi jiki ta buɗe murfin motar zata fita muryar sa taji yana faɗin "sorry madam" ɗan satar kallon sa tayi ta fice daga motar haka kurin yaji shima duk ransa ya 'baci dan baya san ganinta a damuwa tafi kyau in tana tsiwa da rashin kunya... *WACECE SAFNA* *KASH LAIFIN DAƊI ƘAREWA KUDAI KU BIYONI* *INA GODIYA A GAREKU MASOYANA* *#ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}* 3/7/24, 9:03 AM - my lovely sister: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU ❤‍🩹 *WAYE SHI?*❤‍🩹 *MARUBUCIYAR LITTAFIN* *1:-RAYUWAR ZAINAB* *2:-RASHIN MAHAIFIYA* *3:-YARIMA ASLAM* *YANZU KUMA GAMU ƊAUKE DA SABON LITTAFI MAI SUNA WAYE SHI ?* *STORY&WRITTING* *BY* *ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR*💪 *ROYAL STAR🌟}* *FREE BOOK* 📚📖. *Littafi mai d'auke da soyayya,Sadaukarwa,tausayi,ilimantarwa,har ma da nishad'antarwa,*faɗa karwa*ku dai ku biyo garkuwar taku* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* 🅿️..........1️⃣1️⃣↔1️⃣2⃣. BISIMILLAHI RAHMANU RAHIM DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI MAƊAUKAKIN SARKI WANDA YA BANI IKO NA KAMMALA LITTAFINA MAI SUNA YAREEMA ASLAM SANNAN YA BANI IKO YAU NA KAWO MUKU SABON LITTAFINA MAI SUNA WAYE SHI ? INA FATAN ZAKU BIYONI DAN JIN SAƘON DANA ZO DASHI A WANNAN LITTAFIN. ______________Safna ƴace guda ɗaya tilo ga babban ɗan kasuwar nan mai suna Alhaji Abubakar matawalle ɗan kasuwane wanda yai shura a jahar mu ta kanon dabo Nigeria matar sa ɗaya mai suna Maryama, yana zaune lafiya da matar sa shekarar su goma da aure ko ɓatan wata bata taɓayi ba hakan yasa dangin mijin nata suka sako ta gaba da gori rashin asali dana haihuwa sam bata sakewa a gidan mijin nata koda yaushe yaran su da manyan su suna kan hanyar gidan gashi in suka zo suyi ta 'bata mata gidan haka take haƙuri saboda bata da kowa sai mijin nata ana haka suka haɗashi aure da ƴar uwar sa bazawara ce kuma tayi haihuwa biyu a gidan data baro dan haka suka ce tunda ita ba juya bace tazo ta haifa masa ƴaƴa abun mamakin kuma shine tunda akayi auren shekarar Amaryar tasa bakwai ba haihuwa dan haka sai duk surutun da suke sukayi shiru kuma sai da tasan yanda tayi tasa suka dena musu suntiri a gida dan ta lura in tayi wasa irin na Maryama zasuyi mata itada kishiyar ta sam basu da matsala suna zaune lafiya sun haɗa kansu yanzu Maryama ta samu natsuwa sosai a gidan mijinta dan Amaryar tata irin matan nan ne goggagu sam bata ɗaukan raini ita kawai duniya ce gaban ta business ɗinta take gari-gari ana haka Maryama ta samu ciki murna a wajan Alhaji matawalle ba,a magana haka Saratu dan ita ko a jikinta dan dama ita ba haihuwa ce a gaban ta a lokacin Safwan shekarar sa ɗaya da fara aiki a gidan kuma tun zuwansa Allah bai haɗa jinin sa da Amaryar Alhaji ba wato Saratu amma shida Mommy ya ɗauke ta kamar mahaifiyar sa. Tare da Safwan ake rainon cikin dan in ya fita haka zai siyo ma Mommy su ɗata yalo da sauransu takan ce indai mace na haifa Safwan zan baka ita matsayin mata indai inada rai har mijinta saida ta faɗawa lokacin da cikinta ya isa haihuwa bata iya aikin komai wataran safwan ke mata har Allah ya sauketa lafiya yarinyar taci sunan mahaifiyar Alhaji matawalle ana kiranta da Safna cewar Mommy zata masa takwara sanda yarinyar ta fara wayo ta shaƙu Safwan sosai duk inda taji muryar sa ta sani in bai ɗauketa ba ta dinga kuka kenan shekarar safna biyar a duniya Allah yayi wa Mommy rasuwa sakamakon ciwon ciki datayi na dare ɗaya amma duk da tana cikin ciwo saida ta nana tawa mijin nata cewar indai Safna ta girma ya taimaka ta cika mata burin ta ya aurawa Safwan ita tasan zai riƙe mata Amanar ɗiyar tata sannan shima Safwan ɗin ta bashi amanar ƴar tata. Mutuwar ta daki Safwan da Matawalle sosai nan riƙon Safna ya koma hannun Saratu wato Ammi kasancewar tana son yarinyar yasa take gatan tata kamar ƴarta amma sam bata yarda Safwan ya ɗauke ta tun yarinyar na kuka in ta ganshi har ta haƙura haka shima tun yana damuwa har ya haƙura sanda yarinyar ta girma gaba ɗaya sai halayen ta suka koma na Ammi har ma ta fita dan indai rashin kunya ne da rashin girmama manya kuma da izza Safna ta haɗashi kaf gidan Safwan kaɗai take shakka dan shi sam baya sake mata fuska amma sauran ma'aikatan gidan duk ta raina su ta dinga sasu aiki kenan sam ta tsani talaka a rayuwar ta dan a cewar ta duk ƙazamai ne wannan hali na Safna yana damun mahaifin ta danshi mutum ne mai son jama'a ga kyauta. wannan shine labarin jarumar tamu a taƙaice *CIGABAN LABARI* *KASH LAIFIN DAƊI ƘAREWA KUDAI KU BIYONI* *INA GODIYA A GAREKU MASOYANA* *#ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}* 3/7/24, 9:04 AM - my lovely sister: ❤‍🩹 *WAYE SHI*❤‍🩹 *NA ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}* 🅿️➡️1️⃣3️⃣ ______________Yau tunda suka taho motar tayi tsit ita Safna ta ƙurawa gefan titi ido har suka iso makarantar bata sani ba, bai san abinda yake damunta ba amma sai yaji ransa duk babu daɗi dan bubbuga kujerar da take zaune yayi a hankali ta ɗago tsintar kansa yayi yana faɗin "Madam meyake damunki?" bata kulashi ba duk da dama ya tsammaci hakan. Jakarta ta ɗauka zata fita yakuma faɗin "sorry Madam" still dai bata kulashi ba ta juya ta nufi ajinsu juya motar tasa yayi zuciyar shi sam babu daɗi, kiran Abbas ne ya shigo wayar tasa ɗagawa yayi yana faɗin "Abbas ya ake ciki kasamo wani evidence ne ?" a ɗaya ɓangaren cikin rashin jin daɗi Abbas ɗim ya ce " boss har yanzu shiru dai ni bama wannan ne yasa na kiraka ba dan Allah Safwan ka daure kazo funtua kodan saboda mahaifiyar ka....." cikin tsawa Safwan ɗin ke faɗin " wait Abbas na gaya maka babu ruwan ka da abinda ya shafi tsakanina da iyayena ka tsaya iya matsayin ka wannan ba matsalar ka bace" ya ƙarasa yana katse kiran jingina kansa yayi akan sitiyarin motar zuciyar sa na tafarfasa nan da nan idanun sa suka kaɗa sukayi jawur zuciyar sa sai tafarfasa takeyi bai san meyasa Abbas keson fama masa ciwon daya daɗe a zuciyar shi ba why Abbas why meyasa bazaka barni na zauna lafiya ba bana son zancen gidan bana so ya ƙarasa yana dukan sitiyarin a hankali ya lumshe ido rayuwar sa ta baya ta fara dawo masa tana tuna masa WAYE SHI. Safwan Asalin ɗan garin Funtua ne mahaifinsa Alhaji Habib Funtua ɗan kasuwane wanda ba,a iya nigeria yayi suna ba a ɗaukacin duniya baki ɗaya Alhaji Habib mutun ne mai zafin rai da zuciya gashi sam baya son talakawa bashida taimako sam tsakanin sa da talaka yayi masa aiki ya biyashi Mami itace matar sa ta farko suna da yara shida Anty Suraiyya wadda take aure a kaduna itace babba tana kula da companyn Abbun nasu nacan sai Anty Shukura ita kuma tana aure a Abuja kuma itama ita take kula da companyn mahaifin nata sai Anty Saudat a lagos sai Samira ita kuma a gombe sai Safwan sannan Mimi ƴar auta duka matan suna kula companyn mahaifin su kasancewar duk ƴaƴan shi sunyi ilimi mai zurfi Safwan shine kaɗai ɗansa na Namiji saidai shi kuma Safwan sam babu abinda ya rage a halin Mahaifiyar su na son taimako da son jama,a sannan tun yana ƙarami bashida burin daya wuce ya zama soja. Kowa a gidan nasu yasan da hakan shekarun sa sha shida a duniya ya kammala secondary kasancewar sa yaro mai matuƙar hazaƙa a lokacin me ya sanar da mahaifin sa ƙudirin sa nason aikin soja amma sai ya ce sam bai yarda ba business zai karanta kamar sauran ƴan uwan sa ya kula masa da babban companyn sa dake kano ya roƙi mahaifin nasa kan ya barshi yayi aikin sa saboda bashida wani interest akan business ɗin amma yaƙi sanin halin mahaifin nasa yasa ya haƙura Turkey aka turashi karatu amma me saiya juya akalar karatun nasa zuwa taraining ɗin sojoji a wata babbar makarantar ko yarda sojoji anan Turkey ɗin shekara biyu yayi yana training sannan ya fito da babban muƙami a makarantar sojojin kowa yana son Safwan saboda yanayin maida hankalin sa shiyasa suka so su riƙeshi anan ya musu aiki yaƙi yarda saboda shima ya bautawa ƙasar sa sanda ya dawo Nigeria bada sanin mahaifin shi ya dawo ba kasancewar course ɗin shekara shida aka tura shi mahaifiyar shi kawai tasan da hakan. dan haka sai ya wuce gidan sa na kano yake aikin sa acan a ƙananan shekarun sa da basu wuce ashirin ba ya taka matsayi da dama wanda duniya take alfahari dashi ba iya ƙasar sa ba SGS FUNTUA kenan ɓoyayyen matashin daya ɓoyewa duniya kamannin sa saidai aikin sa tantirai suna tsoron sa dan ko sunanshi aka faɗa a gaban mai laifi saiya razana. a shekaru shidan nan ya taka matsayi da dama sannan yasamu kyaututtuka iri-iri cikin lokaci ƙanƙani yazama matashi mai kuɗi. KASH KU BIYONI. NGD DA ƘAUNAR DA KUKA NUNA MIN INA NEMAN AFUWA MA RASHIN POSTING DA MAYI KWANA BIYU INSHA ALLAH DAKA YANZU MUN DAWO POSTING BABU KAMA HANNUN YARO NGD Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* TAKU ZAINAB KABIR JAEN GARKUWAR ROYAL STAR 3/7/24, 9:04 AM - my lovely sister: ❤‍🩹 *WAYE SHI*❤‍🩹 *NA ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}* 🅿️➡️1️⃣4️⃣. ______________Ranar daya cika shekara shida da tafiya karatu Walima mahaifin sa ya haɗa masa ta tarbar sa da kuma murnar damƙa ma ɗan nasa companyn sa yaran sa gaba ɗaya sun zo daga gidajen auren su kowa burin sa ya ganshi saɓanin mahaifiyar sa da zuciyar ta take cike da tsoron hukuncin da zai yiwa ɗan nata inya gane yana aikin soja suna zazzaune a palourn suka fara jiyo jiniyar motoci mamaki ne ya kama dukkannin su suna mamakin waye yazo haka da jiniya gaba ɗaya suka fito harabar gidan dan ganin wane baƙon sukayi. shi kuwa Safwan tunda suka shigo gidan zuciyar shi ke tsananin bugawa har motocin su suka gama parking wani security ɗin nasa ne ya zagayo ya buɗe masa ƙofar motar a hankali ya zuro ƙafafun sa kafin ya gama fitowa gaba ɗaya haɗaɗɗan matashi ne ya bayyana jikin sa sanye da kakin sojoji kansa babu hula saidai sumar kansa dake a kwance luff tasha gyara tayi masa kyau sosai baƙin glass ne a fuskar sa fari ne soll irin farin nan da babu sirkin ja a ciki cikeda da dakewa ya fara takowa a hankali ya nufi wajan da mahaifin sa dake tsaye yayi mutuwar tsaye ganin abinda ya gigitashi da sauri Safwan ya tafi zai rungume shi cikin wata iriyar tsawa ya dakatar dashi "dakata karka taɓani Safwan ni zaka tozarta ni zaka kunyata a idon duniya" cikin sanyin muryar ya ce "sorry Abbu" wanke shi da mari yayi yana faɗin "baka isaba wallahi baka isa ka tozartani ba wallahi kaje ka barmun gida babu ni babu kai na cireka a ƴaƴana banida wani ɗa namiji a yanzu" zubewa yayi kan gwiwoyin sa yana bawa mahaifin nasa haƙuri amma cikin zafin rai ya tureshi daga riƙon daya yiwa ƙafar tasa. Idanun Safwan ɗin sun kaɗa sunyi jawur ganin irin tozarcin da mahaifin sa keyi masa a gaban security ɗin nasa kasa tashi yayi a gurin cikin wata tsawar yaji mahaifin nashi na cewa " zaka fita ko sai na sa an fitar da kai ta ƙarfine eyeee?" a hankali ya tashi ya hau jikin sa a matuƙar sanyaye da sauri Mamin sa ta biyoshi tana faɗin ka dakata yarona dan Allah karka tafi ka zauna tare damu ta ƙarasa cikin kuka shi kanshi Safwan ya kasa daurewa ganin hawayen mahaifiyar tashi shima hawaye kawai yakeyi kamar ba soja ba cikin zafin rai mahaifin nasa yace "Halima indai kika ƙara taku ɗaya daga inda kike a bakin auren ki na yanke duka igiyoyin auren dake kanki" cak ta tsaya ta durƙushe a gurin tana kuka sauran yaran nata suma sunayi da matuƙar sauri Safwan ya shiga mota suka bar gidan zuciyar shi na masa ƙuna tsanar mahaifin shi da halayen shi suka rufe kai tsaye gidan sa na kano ya koma inda yake zaune a kwana kin nan damuwa tayi masa yawa kewan mahaifiyar shi da halin daya bar ta a ciki sun lulluɓashi dan haka ya yanke shawarar ya nemi aiki a wani gidan ko ya rage damuwa in yana ganin sa tare da mutane shine ya nemi aiki a wajan Alhaji matawalle kuma yaci sa,a ya ɗauke shi a matsayin driver sai dai sam baya baiyyana asalin sa ya buɗe company kala-kala a na kula masa dasu ya tara dukiya dashi kansa bai san yawan su ba dan a yanzu companyn sa yana na biyu a manyan companys na Nigeria daga na mahifinsa sai nasa kasancewar ya samu ma,aikata masu amana suna kula masa da dukiya sosai shi kuma yama cigaba da aikin sa na soja duk da dai ba wanda yasan asalin mai companyn nasa kawai dai kowa yasan SSG Company. wannan shine asalin abinda yasa jarumin namu ya fara aikin driver. WANNAN KENAN. cigaban labari..... ku biyoni dan jin yanda zata kaya ngd Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* 3/7/24, 9:04 AM - my lovely sister: ❤‍🩹 *WAYE SHI*❤‍🩹 *NA ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}* 🅿️➡️1️⃣5️⃣. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* _____________A hankali yaja motar shi yafara driving a hankali duk zuciyar shi babu daɗi sam baya son tuna abinda Mahaifin nashi yayi masa ya kamata ko yaya ya masa uziri a hankali ya koma gidan zuciyar sa babu daɗi sam kansa yana matuƙar sara masa idanun sa sunyi jawur a haka ya ƙarasa gida kan ƴar katifar sa dake gidan ya kwanta bacci kuwa nan da nan ya ɗauke shi bai farka ba sai gab da za,a tashi su Safna dan haka da cikin hanzari ya tashi ya fito makarantar tasu ya nufa yana zuwa ana tashin su hango su yayi su uku sun fito suna taho wa inda ake ɗaukan ɗaliban zuba mata ido yayi kawai saiya tsinci kansa da sakin wani tattausan murmushi a hankali ta ƙaraso gaban motar ta buɗe murfin ta shiga sai dai ko kallan sa batayi ba shima bai damu da hakan ba suka kamo hanyar gida. yau ta kama weekend tun safe Safna take shan aiki saida ta gyara ko ina tsaff sannan tayi wanka ta shirya cikin wani material maroon colour da adon milk wanda akayi misa ɗinki doguwar riga harabar gidan tafi to wayar tace tayi ringing ɗaga kiran tayi tana cewa "baby tun ɗazu fa nake jiranka" a ɗaya ɓangaren shima Mahbub ɗin yace "sorry princess ina bakin gate ɗin gidan ku" cikeda murna ta ce "are you serious darling" murmushi yayi yana faɗin "yess of course yanzu ma zaki ganni" yana faɗin hakan motar sa ta shigo gate ɗin gidan duk abinda sukeyi akan idon Safwan ne dake zaune ɗan nesa dasu kaɗan. mamaki ne ya cika zuciyar sa yaushe Safna ta fara kula samari kuma waye ma Saurayin da take kulawa mamakin sa ne ya katse sanda yaga managern companyn sa Mahbub ya fito a mota ransa ne ya ɓaci matuƙa me yarinyar nan take nufi bazai yuwu ba ya faɗa cikin zuciyar sa ransa kam duk inda yake yayi dubu ya ɓaci yana kallon su suka isa garden sai wani shagwaɓa take zuba masa da suka isa wajan zaman garden ɗin yana kallo Safnan ta jawowa Mahbub ɗin kujera ya zauna cikin wani baƙin kishi ya taso daga inda yake ransa a matuƙar ɓace sam ya ma manta matsayin sa a gidan wajan su ya nufa gadan-gadan suka suna zaune suna shan soyayyar su bama su lura dashi ba Mahbub ne idon sa ya sauka akan SGS ya nufo gurin s, zumbur ya miƙe zuciyar shi tana tsananin bugawa ita kuma Safna mamaki ne ya kamata ganin Mahbub ɗin ya zabura har yana taka ta bai sani ba. Shi kuma SGS kafin ya ƙaraso hankalin ya dawo jikin sa da sauri ya dai-dai ta natsuwar sa ya ƙarasa ya miƙa ma Mahbub hannu yana faɗin "barka da zuwa ranka ya daɗe" sanin waye Safwan ɗin da yanda yake ƙoƙarin ɓoye kansa kansa yasa shima Mahbub ɗin sakin murmushi yana faɗin "barkan mu dai kana lafiya" ya ce "Alhamdulillah" haushi ne ya kama Safna ta ce " baby wa kake cewa ranka ya daɗe wai driver nawa bana son irin haka fa" murmushi Mahbub ɗin yayi mata a zuciyar sa yana faɗin baki da hankali baki san dawar garin ba a fili kuma ya ce "oh baby Sorry bazan ƙara ba", kallon Safwan Safna tayi cikin tsiwa da rashin kunya tana faɗin "kamin tsaye aka ka kauce ka bani guri zanyi magana da mijina" ji yayi kamar ta soka masa wuta da tace mijinta amma saiya dake ya ce "to ranki ya daɗe" a fakaice kuma yayi Mahbub in kiya da ya bashi minti biyu yana jiran sa a waje sannan ya bar gurin...... Wannan kenan. Kudai ku biyoni. Taku ako da yaushe Zainab kabir jaen GARKUWAR ROYAL STAR 3/7/24, 9:04 AM - my lovely sister: ❤‍🩹 *WAYE SHI*❤‍🩹 *NA ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* 🅿️➡️1️⃣6️⃣. ______________Ko minti ɗaya Mahbub kasayi yayi a gurin saboda son cika umarnin ubangidan nasa yana barin gurin shima ya miƙe yana faɗin "Beb saƙon gaggawa daga office ana jirana zan dawo next week insha Allah" bai jira amsar ta ba ya bar gurin a ranta taji ba daɗi sosai amma sai tayi masa uziri da kiran daga office ne a waje ya taradda Safwan ɗin buɗe gaba motar yayi ya shiga sannan yayi masa umarni da su tafi har suka fita a unguwar ba wanda ya ƙara cewa ƙala sai can Safwan yaja numfashi ya ce "menene haɗin ka da Safna?", ɗan sosa kai Mahbub ɗin yayi kafin ya ce"ranka ya daɗe she's my girlfriend" ɗan kallon sa yayi kafin ya ce "auren ta zakayi?" ƙasa da kai yayi kafin ya ce "No Oga ai na kusa aure ma da yarinyar ancul ɗin mu auren family za,a mun" cikin ɓacin rai Safwan ɗin ya ce "kenan yaudarar ta kake?" ƙasa da kansa yayi saboda ya fahimci ran ogan nasa ya ɓaci. Shi kuma Safwan cikin faɗa ya ce "kar na ƙara ganinka a gurin ta as from today babu kai babu ita" cikin ladabi ya ce "insha Allah oga". Dai-dai lokacin suka iso ƙofar gidan Safwan ɗin sauke sa yayi shi kuma ya tafi. To tundaga ranar Safna bata ƙara jin Mahbub ba ko wayar sa ta kira sai dai ta ƙaraci ringing ɗinta ba,a ɗaga ba in tayi masa text message ma ba zai mata reply ba ta damu ƙwari kafin daga baya ta watsar da lamarin sa dan yanzu tayi wani sabon saurayin Ameer ɗan gidan ministan kuɗi yaron bayaji yana wasa da ƙudi sosai class ɗin su ɗaya ya daɗe da cewa yana sonta amma bata yarda sun fara soyayya ba sai yanzu. exam ta ƙarato su Safna sunyi busy da yawa kasancewar jarabawar da zasu zana itace shaidar su ta kammala Secondry wato Neco da waec karatu suke babu ji babu gani domin son su samu nasara duk da a ɓangare ɗaya sam bataji daɗin zana jarabawar don ba zata dinga ganin sahibin nata ba koda yaushe. To sun zana jarabawa lafiya kuma sakamako yayi kyau sosai yanzu Safna babu abinda tasa gaba sai soyayyar ta Ameer dan daddy ya ce bazata fara karatu ba sai tayi aure yanzu Ameer har gidan yake zuwa kuma koda yaushe akan idon Safwan ne abun yana ɓata masa rai sosai dan yana ganin wannan zubar da mutunci ne yasa Safna kula wannan yaron da, da kaɗan zai girmeta a ransa ya ce dole inyi wani abu ya kamata inyi gaggawar auren yarinyar nan tun kan yaran nan su ɓata mata tarbiyya dan haka ya samu Alhaji da maganar yaji daɗi sosai ya ce " dama Safwan jira nake naji kayi magana nima nayi tunanin ya kamata a cika alƙawarin mahaifiyar ta tunda yanzu ta gama makarantar ta amma safwan ya kamata ace zuwa yanzu ka sanar mana da iyayen ka" sosa kai yayi ya ce "Alhaji iyayena ne zasu neman mun aure gidan nan ni asalina ɗan ƙauyen funtua ne nazo birni ne neman kuɗi sai Allah ya haɗa ni da kai daddy zanje ƙauye in turo magabata na" ya ce "Allah sarki to shikenan sai ka turo sun bama lokaci da yawa za,asa ba ai" ya ce "to daddy". Safwan da kansa yaje dangin mahaifin sa wanda mahaifinsa ya wulaƙanta dan yana ganin su talakawa ne ya wofantar dasu Safwan ɗin ya gina musu rayuwa ya taimake su yaje ya faɗama yayyen mahaifin nasa duk abinda ke faruwa kuma ya sanar dasu idan sunje neman auren kar su sake su faɗi asalin mahaifin sa. . Sunji daɗi sosai kuma a satin sukazo nemar wa ɗan nasu auren Safna Alhaji matawalle ya karramasu sosai kuma anan akasa ranar biki wata huɗu a cewar sa baya buƙatar komai daga hannun Safwan ɗin sai sadaki. ita kuwa goguwar sam batasan abinda ke faruwa ba tana can tana shan soyayyar ta da Ameer ɗinta sai da biki ya rage wata biyu sannan mahaifin nata ya sanar daita a gigice cikin tsananin tashin hankali take faɗin "daddy wallahi bana sonsa bana ƙaunar sa bazan iya zama dashi ba wallahi daddy bazan iya ba" cikin tsananin ɓacin rai Alhaji matawallen ya ce "Safna indai har na isa dake ki amince da auren nan idan kuma ban isa dake ba kije na zare hannuna akanki" hankalin ta ya matuƙar tashi dajin kalaman mahaifin nata cikin kuka ta ce "daddy kayi haƙuri na amince wallahi na amince" ɗan sassau towa yayi yamata nasiha sannan ta bar gurin tunda ta shiga ɗakinta kuka take yanzu ita Safna za,a haɗa aure da wannan matsiyacin da bai da komai drivern ta inalillahi wainna ilaihi raju'un shine kawai abinda take maimatawa biki ya rage wata ɗaya aka kawo lefe a cewar Safwan zaiyi wa Safna komai na aure da akeyi akwatuna biyu ne sai dai kayan cikin duk masu araha ne atomfofi shidane duk ledoji sai wasu dogayen riguna na gwanjo guda biyu sai takalmi da jaka masu araha guda biyu sai ƴan kayan kwalliya wanda ba, a rasa ba sanda safna taga lefan jitayi kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu. Sam bata yarda su haɗu da Safwan dan gaba ɗaya bata son ganin sa wata irin tsanar sa ce ta mamaye mata zuciya sai da biki ya rage sati ɗaya suka haɗu gaba ɗaya ta rame tayi baƙi duk gayun nan yanzu batayi gaba ɗaya tausayin ganin ta a haka ne ya kamashi sai yaji zuciyar sa sam ba daɗi kuɗi ya bata dubu biyar ya ce in akwai abinda zatayi wani murmushin baƙin ciki ta saki ta ce " bawan Allah kana tunanin akwai wani abu da zanyi a wannan auren naka ina kayi kaɗan ai wallahi babu abinda zanyi kuma ka ɗebe kuɗin ka bana buƙata dan ni ɗin kasan ba matsiyaciya bace"...... Wannan kenan kudai ku biyo ni dan jin yadda zata kaya. ayi haƙuri da rashin posting ɗin da bamayi kwana biyu insha Allah daganan zuwa azumi zamuyi ƙoƙari muga munyi abinda mukayi. Na gode da irin kulawar ku gareni inajin daɗin yanda kuka nuna dauwar ku akan wannan littafi. Wannan littafin na sadaukar dashi ga duk wani member dake cikin group ɗinnan. SANNAN INA MIƘA GODIYATA A GAREKI ƳAR UWA KUMA ƘAWA AMINIYA A GARENI SISTER MUKARAMMA BISA YANDA KIKE ƘARAMUN ƘWARIN GWIWA DA KUMA KULAWA NA GODE SOSAI ALLAH YA BAR ƘAUNA YA KUMA BAR ZUMUNCI NA SADAUKAR DA LITTAFIN NAN GAREKI KACO KAM. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU TAKU AKO YAUSHE GARKUWAR ROYAL STAR . Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels