Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [2/25, 21:46] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTING* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* (07037004285) *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽 Bismillahir rahmanir rahim Dukkan yabo ya tabbata ga Allah (S.W.A) da ya ba ni ikon shiga sabon wani littafin. Wannan littafin nayi shi dan fad'akarwa, nishad'antarwa, ilimantarwa da kuma du ba da halin da muke ciki a yanzu. Dafatan za ayi amfani da darasin dake ciki ayi watsi da abin da bai da kyau a littafin *Wannan shafin sadaukarwa ce ga duk wani mai son littafi na da kuma wanda su kai ta min Magana akan fitowar wannan littafin* *Nagode da kulawa sosai* *Har kullum ki na raina* *Mufida mu’azu* (Marubuciyar Auren dole) *Ba zan gaji da nuna kulawa ta gare ki saboda yadda kike ba ni k’warin gwiwa*, *ba abin da zan ce miki sai dai in ce Allah ya bar kauna kuma ya biya miki buk'atun ki* Tunatarwa: *Ko kasan/kinsan ina ake sanya zunuban mu yayin da muke sallah? Manzon Allah (S.A.W) ya ce: duk lokacin da bawa yake sallah ana sanya dukkan zunuban sa a wuyan sa da kafad’un sa, duk lokacin da yayi ruku’u ko sujada zunuban sa za su dinga fadowa kamar yadda ganye yake fadowa daga bishiya don haka mu tsawaita sujada da ruku’u domin zunuban mu su ragu. 1&2 Yau a garin Kaduna an tashi da matsanancin zafi kasancewar zafi ya fara shigo wa wanda yake hana mutum sakat, dawo wa ta daga makaranta kenan na cire uniform d’ina na fada toilet d'in dake jingine a d'aki na, ko side d'in Ummu ban shiga ba saboda zafin da ke son sa min wani ciwon, ko minti 5 ban d'auka ba na watsa ruwan sanyi kana na fito na zira 'yar t-shirt da wani simple skirt na nufi d'akin Ummu wanda na same ta zaune a 3 sitter rike da hisnul muslim a hannun ta tana nazari. Sallamar da nayi ne yasa ta katse karatun da take yi ta d'ago ta na kallo na tare da murmushi a fuskar ta, jikin ta naje na kwanta kasancewa ta mai son jiki duk da yaya Aminu ba ya so amma Ummu cewa take yi a k’yaleni ni ce auta kuma d’iya mace a gaban ta. "Ummu sannu da gida" "Yawwa Fatima an dawo? ya lesson d’in" Cikin shagwa ‘ba na ce "gaskiya Ummu na gaji da wannan lesson d'in waec da neco d’in nan, mutum ya dawo a gajiye gashi ba a tashi da wuri ga zafi yazo, a class mutum yaji kamar ya cire kayan jikin shi saboda zafi yanzu fa daga dawo wa ta sai da na watsa ruwa amma ji nake kamar ana kara min wani zafin, gaskiya ki yi ma yaya Aminu magana saboda shine d’an sa ido shi da wannan abokin nashi yaya Faruk, zan daina zuwa lesson d’in nan, yanzu ban da na school da nake attending kuma an kara sa ni a wani extra school ran weekend sai kace wata mango park" Dariya Ummu tasa tace "kai auta ina laifin wanda ya damu da ilimin ka ai in ba a gode mai ba bai ci kuma a kushe shi ba, kiyi hakuri ki k'arasa lesson din tunda kun kusa zana waec da neco d’in sai ki huta gaba d’aya tun da kinyi jamb kafin admission ya fito a fara zuwa jami’a Cikin jin dad'i na rungume Ummu ina murna ina cewa "wa ya ganni a jami’a? dariya Ummu tayi tace "auta kenan" sallamar yaya Khaleel ce ya katse mana hirar da muke yi Amsawa muka yi kana ya saki murmushi yace "auta me ake tattaunawa ne don na ga hirar ta muku dadi" Hararar wasa na mai tare da murgud’a baki nace "ba sai kaji ba kuma ni kadaina ce min auta saboda na girma kuma in k'awaye na suka ji dariya zasu min" Dariya yayi yace "to shikenan sister na daina tun da kin girma" Kallon Ummu yayi yace "yaya Faruk ya dawo yace in gaishe ki kafiin ya zo" Yalwata murmushin ta tayi tace "ikon Allah yaushe ya dawo" Amsa mata yayi da cewa "jiya ya sauka kin san ya kwana biyu bai zo Kaduna ba ya ‘boye a Abuja, kin san aikin sojoji sai a hankali ba sa samun hutu, nima na biya gidan ne in gaida momi mu ka hadu" Ummu juyowa tayi tana kallo na wadda tun san da naji an ambaci yaya Faruk nayi shiru kamar ba na d’akin tace "kin ji yayan ku ya dawo ki tashi ki je ki shirya mai abinci saboda nasan anan zai ci na dare" d’aure fuska nayi nace "gaskiya Ummu na gaji, kina gani yanzu na dawo daga makaranta sannan ki ce in dafa mishi abinci, ba ga iya talatu nan ba, basai ta dafa mai ba, yanzu yana zuwa ni zai fara sa wa ido da fad’a, indai ya dawo ban da sukuni a gidan nan, ya dinga d’akko laifi yana d’ora min ko banyi komai ba, Allah-Allah nake yi ya koma ga kuma takurawar yaya Aminu in yazo gaishe ku, ni ko ta ina a takure nake, na fara matse hawayen da ya fara zubo min Shi kuwa yaya Khaleel murmushi kawai yake yi saboda yasan halina na rashin shiri da yaya Faruk saboda yadda bai wasa a family, yafi yaya Aminu zafi ko dan kasancewar sa soja ne? oho! haka kuma abokai ne shi da yaya Aminu kasancewar su sa’annin juna, don haka ya matsa kusa da ni yace " oh Fatima miye abin kuka? kin san yaya Faruk baya cin abincin ‘yan aiki kuma ba ya d’aukan raini yanzu sai ya baki purnishment d’in da zaki kwana biyu kina jinyar kanki don ma na lura kamar ke yana raga mi ki kuma kin san indai yazo sai kin dafa abincin nan saboda shi yace a dinga barin ki kina dafa abinci, Ummu ta dinga hutawa kuma yana da gaskiya kinga kince kin girma, kwanan nan za a fara zancen auren ki kinga in kin je gidan mijin ki basai ki dinga dafa wa mijin ki kala kala abinci mai dad’i ba kinga anan ai yaya Faruk yayi taimako ya k'arasa maganar yana dariya. [2/25, 21:46] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTING* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* (07037004285) *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽 *Dedicated to Maimuna* (On top) *Marubuciyar*(‘yar shugaban kasa) *I really care 4 u*, *because u a so special to me* *QUESTION OF THE DAY* Wace mata ce a cikin matan manzon Allah (S.A.W) Allah ya ba ma Annabi Muhammad (S.A.W) umarni ya janye sakin da ya mata saboda ta kasance mai yawan azumi? 3&4 Mik'ewa na yi ba tare da na ce komai ba saboda in na biye ma yaya Khaleel sai ya sa ni kuka saboda in ya fara tsokana ta wani sa’in sai yaga nayi kuka yake kyale ni. Kitchen na nufa ina tunanin mai zan dafa mai wanda bazai d’au tym ba don ni a gaskiya ta mu bata zo d’aya da shi ba kasancewar yadda yake da zafi da fad’a ga salon mugunta duk ya iya shi, ko da yake ai ba a banza ba tunda soja ne dole yasan style na mugunta ga son girma kamar gyambo, duk da wani sa’in ya na ja na da wasa amma duk da haka na kasa sabawa dashi. Farfesun kayan ciki na dafa mai da soyayyar taliya na had'a da zob’o wanda yaji kayan had'i na ajiye akan dining table Tun da naci abinci na wuce d'aki na fara chat da friends d'ina don ina ganin ya fi min akan in zauna ayi hira da ni in dai yaya Faruk na nan. Ina chatting ina jin hirar su da yaya Khaleel da yaya Aminu da yazo gaishe da su Ummu kasancewar shi yayi aure, jefi- jefi nake jan tsaki saboda yadda na takura a d’akin, ban san tym d’in da na d'auka ba ina chatin sai tsayuwar mutum naji a baya na, ganin haka ne yasa na juyo don in ga wani gwanin ne ya tsaya a baya na ba tare da yayi sallama ba. Waigowar da zanyi na gan shi ya k'ure ni da ido fuskan nan ba alamar fara’a kamar an aiko mai da sak'on mutuwar shi cikin shigar shi ta wani lallausan yadi an mishi simple d’inki. Cikin karkarwar murya na jawo miyau da k’yar na had’iye ina addu’a a raina Allah yasa kar ya amshi wayar nan saboda ya hana ni chatting yace wai nayi yarinya da chat. "Ina wuni…yaya Faruk! ka dawo lafiya? Ci gaba yayi da kallo na ba tare da ya amsa gaisuwar da nayi mai ba illa hannun shi da ya mik’o min. A raina na ce "wannan yayan akwai rainin wayau to ni mai zan mik'a mai da ba zai iya min Magana ba, amma nasan maganin shi duk da nasan waya ta yake nufin in bashi. Juyawa nayi ina dube-dube kamar ina neman wani abu sannan na juyo na kalle shi nace "yaya me zan baka? Sai da ya gama shan k'amshin shi kana yace "au baki san me zaki bani ba koh? To mik’o min wayar ki tun da kin zama mai kunnen k’ashi, how many times did i warn you that i don’t want you to involve yourself in this social media amma baki ji ba? nasan matakin da zan d'auka a kanki don kin ga ina raga miki ne ki je ki tambayi Anisa za ta baki labari na don na ga alamar kin manta ni" Raina ne ya so ma ‘baci saboda ganin har yau yaya Faruk d’in nan kallon yara yake mana, in ban da haka ya za ace ina class d'in karshe a secondary amma yace wai ban kai in yi chat ba wanda yanzu kowa yasan harkar socialization ake yi amma shi kullum yafi son ya gan mu a local. Tsawar da ya min ce tasa hannu na yana rawa na mik'a mai hawaye na zuba a ido na. Ko da ya amshi wayar whatsapp d’ina ya fara bincika kasancewar ina online, ya d’au kusan 5 min yana latsa wayar kafin ya d’ago yana watsa min harara sannan yace "Teemah! ya ambaci suna na kasancewar wani sa'in haka ya ke kira na. d’ago wa nayi na kalle shi saboda yau ban san kalar muguntar da zai min ba, ni dai addu’a ta ita ce kar ya hana ni wayar saboda ta na min amfani, ga internet da nake research a ciki, ga chat d’in nan da nake k'aruwa dashi, ga online novels da na ke karanta wa yake sa ni nishad'i da kuma darusa da nake koya a ciki. Katse min tunani yayi da cewa "Fatima wai ba ki ji kiran da nayi miki bane? Ko zaki nuna min yanzu kin yi girman da baza a miki fad’a bane! Listen to me carefully! Teemah ba na so ina miki hukunci saboda wasu dalilai amma hakan bazai hana in kin yi laifi ki amshi purnishment ba, time without numbers na sha fad'a miki bana son kina wannan chat d’in nan saboda har yanzu ke yarinya ce tunda har yau baki gama secondary ba, yanzu k'aramar ki dake har kin san ki shiga groups d’in matan aure su na bud’e miki ido kina ganin posting d’in su na zaman aure, ki bari in time yazo da kaina zan ba Ku damar chat ke da Anisa because as now you are too small, yanzu ma Allah ne ya taimake ki, ban ga alamar kina chat da maza ba, da ke da waya sai in kinyi aure ko in siyo miki k’aramar nokia in ba ki, this should be the last time da zanyi warning dinki kina ji na koh? Gyad’a mai kai na yi saboda wani abu da ya tokare min a k’irji saboda har ga Allah yaya Faruk na matsa min, ni ban da damar yin abin da raina yake so kenan in dai yana gidan ko shi wa ya takura mai? in ban da ya mai dani wata mara class zai ce zai siyo min k’aramar nokia da haka in zauna ba wayar a hannu na mana, Shi wa ya san abin da yake yi a Abujar zai zo yana takura min, waye bai san sojoji da son mata ba zai zo yana takura min. Kamar yasan abin da nake cewa a raina yayi wani mayaudarin murmushi yace "ki gama zagi na a ranki lokacin ki ne kin ga kin girma ne da ai baki yi ba! kin san dai hali na" "Laifin ki na gaba shine mai ya hana ki kizo ki gaishe ni san da kika ji na shigo gidan ko ki na so ki nuna min yanzu kin wuce wannan level d’in don naga kanki na rawa. Rasa amsar bashi nayi don haka nace " ni banji shigowar ka ba shi yasa" ta‘be bakin shi yayi alamar bai yadda da abin da nace ba illa cewa da yayi "Teemah manya! Iya k'arshe yau Yaya Faruq ya kai ni saboda Magana d’aya sai ya wa ni ce na girma to da haka yake so nai ta zama don haka ban san lokacin da na d’ago kaina na watsa mai harara don kar ya gane sai na fara murza ido na alamar wani abu ya fad’a min a ido. re-action d’in da nayi yasa ya fara dariya saboda ko da can yasan ni da tsiwa da neman tsok’ana, bai ce min komai ba ya wurga min wayar akan gado na ya fita daga d'akin. Wata nannauyar ajiyar zuciya na saki saboda Allah ya raba ni da d’an ka’ida lafiya kuma ni jin dad’i na da bai tafi min da wayar ba, haka nayi ta zancen zuci har bacci ya dauke ni [2/25, 21:46] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITING* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽 Wannan shafin naku ne Sameena Aleeyou (Surukas)💞💞 Marubuciyar (Shak’uwa ce) Ina jinjina miki da irin talent d’in ki na rubutu Fatan alkhairi gare ki Ki na raina Jamila Sama’ila Yusuf 💖💖 Marubuciyar (A dalilin kane) Allah ya bar zumunci *Jinjina ga Hajara isa na amsar da ki ka bayar dadai na question of the day*. *Amsar ita ce nana Hafsa radiyal lahu anha* *Zanyi amfani da wannan shafin na gode wa masu kira na da kuma wanda suke min magana a pc chat, ba abin da zan ce muku sai godiya*, *pls zan jawo hankalin masu kira na ba akan novel ba ko sa da zumunci*, *duk wanda yasan dan wani nufi zai kira ni*, *ba na buk’ata saboda ba dan haka na sa numba na ba*, *saboda haka a kiyaye*, *ga masu cewa in turo musu ci gaban novel d’in*, *kuyi hakuri yanzu aka fara labarin* DARAJAR MUTUM DA CIKAR K’IMAR SA Ka da ka/ki damu da abin da ya wuce, don ba zai dawo ba. Ka da yau ta sha maka/ki kai, domin gobe ma rana ce. Yafe wa wanda ya cuce ka ni’ima ce. Tuna abin bak’in ciki da damuwa, wahala ce Manta alheri, butulci ne. 5&6 Washe gari na shirya cikin uniform d’ina na tafi makaranta, ko da aka tashi break, group muka yi a can k’arshen class d’in mu muna tattauna yadda graduation d’in mu zai kasance da kuma party d’in da za mu yi organizing. A raina neman mafita kawai nake yi domin nasan zai yi wuya ne a bar ni na je partin da ‘yan class d’in mu suka had’a tun bare in wannan mugun sojan na nan don wani sa’in gwara yaya Aminu ya fishi sauk’in kai da tausayi. Ashe kuwa za ayi drama da ni don yadda naci burin wannan graduation d’in da party d'in ina ganin ba abin da zai hana ni halartar shi sai wani ikon Allah amma ina jin duk hukuncin da yaya Faruk zai min sai naje sai dai in na dawo ya yanka ni k’arewar hukunci kenan. Muna cikin hirar ne sai ga Anisa (k’anwar yaya Faruk) ta shigo class d’in mu kasancewar school d’in mu d’aya da ita sai dai ita tana SS3B ni kuma ina A, bayan ta gaisa da ‘yan class d’in mu ta mik’o min hannu muka tafa, na kalle ta na ce "mutuniyar jiya ban gan ki online ba? Yamutsa fuska tayi kana ta ce " ina na ga tayin chat, yaya Faruk ya dawo gwara in kiyaye da in ja ma kaina ya k’ara fasa min waya ta" Kallon ta nayi da mamaki na ce "shi yaya Faruk d’in ne ya ta’ba fasa miki wayar? Harara ta tayi ta ce "ke wani sa’in sai ki dinga yin kamar baki san halin shi ba, fasa min ita yayi sai wani daddy ya k’ara siyo min". Dariya na fara yi na ce 'ki ce Allah ne ya taimake ni jiya nima yazo ya tarar da ni ina chat sai masifa da yayi ta min amma bai fasa wayar ba, nan na kwashe yadda muka yi dashi na fad’a mata. Kallo na tayi ta girgiza kai tace "ke Allah yana d’aura ki akan yaya Faruk, ni da yazo ya ganni ina chat wani mari da ya min ban san lokacin da na rungume shi ba, shi kanshi sai da yayi dariya don rashin tausayi ya d’auki wayar nan ya maka min ita da bango gashi a lokacin daddy bai dad’e da siyo mana ni dake ba, ranar in gaya miki ko abinci ban ci ba sai kuka da na dinga yi, momi ce ta dinga lallashi na tace za a siyo min sabuwa sannan na hak’ura" Ta na gama ba ni labarin na dinga mata dariya ina ce wa "gaskiya kina shan hukunci a gurin yaya Faruk" Dariyar da naci gaba da yi ne yasa ta d’aure fuska tana cewa "ke wani sa’in Fatima kamar zautacciya, yanzu miye abin dariya kuma in dai yaya Faruk ne ba wanda ya k’yale ke ma wataran zaki fad’a trap d’in shi ne" Na kalle ta na ta’be baki na ce "in Allah ya yarda ma bazan bari na fa’da tarkon shi ba, kar ya bani purnishiment d’in da zanyi fitsari a wando ban shirya ba" Dariya muka yi gaba d’aya ni da Anisa muka sake tafawa. Bell d’in da aka buga ne na koma wa class ya katse mana hirar da muke yi, mik’ewa Anisa tayi tace " in zaki tafi gida zan bi ki yau a can zan kwana na riga na fad’a wa momi" Cikin jin dad’i na ce "yau akwai chapter kenan amma gaskiya ni ba zan tsaya extra lesson d’in nan ba na gaji gida zan tafi" Anisa ta amsa min da ba komai sai mu tafi, in da rabon mu sha purnishment shi kenan in muka sami yaya Faruk a gidan" Duka na kai mata ina cewa "bakin ki ya sari d’anyan kashi, in ma purnishment d’in ne ai ke zaki fi shan wuya" Da sauri ta d’aga min hannu tana dariya ta fita daga class d’in saboda shigowar malamin physics. Ana buga bell na closing ba mu tsaya extra lesson d’in ba muka nufi gida tunda ba d’aukar mu za a zo yi ba. Ko da muka shiga cikin parlour, zancen yaya Faruk muka ci gaba da yi inda nake cewa "Allah ya taimake mu d'an sa ido baya nan, yanda ba na k’aunar mutuwa haka ba na k’aunar hutun yaya Faruk, don wani sa’in gwara yaya Aminu kana mishi dad’in baki zai kyale ka" Anisa ta kar’bi zancen da ce wa "yanzu ki duba ki gani, d’an gidan k’awayen mu ba a bari muje kullum muna gida sai kace wasu daddawar d’aka" Dariya muka yi naci gaba da ce wa 'k’yale su zan dawo da tsiwa ta, zamu fi daidaitawa, tun bare yaya Faruk d’in nan duk yafi matsa mana, haba takurawar tayi yawa" Mintsini na da Anisa tayi yasa na ce "miye haka! zaki wani mintsine ni, kin san ba na son a ta’ba min fata" Shirun da naji tayi ne yasa na kalle ta na ce " ke wai lafiya kika wani daskare a nan sai kace kakide" Still ba ta min magana ba don haka nace mata "sai kiyi ta tsayuwa har tsayuwa tazo ta same ki" Juyawar da zanyi kawai na ga mutum kwance a 3-Sitter yana danna remote kamar bai ji abin da muke cewa. Saboda k’arfin hali irin nawa na ce "yaya Faruk sannu da gida" sannan na juya da nufin tafiya duk da k’irji na da yake dukan uku-uku. "Teemah" ya kira ni cikin tsawa. Tsaya wa nayi ba tare da na amsa ba. "Ke da Anisa kuzo nan"ya fad'a cikin fushi. A cikin mu an rasa wanda zai fara k’arasa wa gurin shi saboda tsoro. " idan ku ka bari na k’ara muku magana sai kunyi fitsari a wando amma in kuna musu ku gwada ku gani" Da sauri muka k’arasa gurin shi saboda sanin halin muguntar shi. Shiru yayi kamar bazai yi magana ba can yace "zan yi maganin ku, na ga kuna tashen iskanci, zan sauke muku abin da ya ke kanku, ku yanzu har kunyi girman da zaku dinga zagin yayyin ku da gulmar su, ke Fatima har kina cewa zaki dawo da tsiwar ki, idan baki yi haka ba baki cika fitsararriya ba, dama naga kanki na rawa, zan dawo dake normal in cire miki abin da ke damun ki" Ya juya ga Anisa wacce sai zare ido take yi alamar tsoro ya ce "ke dan uban ki har da cewa ana takura muku kamar dadawar d’aka ko? to kun ja ma kanku dan ku da fita sai in makaranta zaku, idan ko na kuskura naga k’afar ku a waje sai na cire muku ‘kafa d’aya" *Hmmm readers nima kaina zan so in san wani hukunci yaya Faruk zai basu* *Ku biyo ‘yar mutan paki don jin yadda dramar zata k’are*. [2/25, 21:46] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽 *Wannan shafin na ku ne* *Batul Adam jattako* *Marubuciyar* (Dama ta) 💔💔💔 *Ina jin dad’in shawarar da kike bani da kuma kulawar ki gare ni, ba abin da zan ce miki sai godiya*. *Ban manta daku ba* *Mrs Mansoor* *Marubuciyar* (Munafukin miji) 💖💖💖 *Da* *Memcy Ata* *Marubuciyar* (Ni da yaya Farooq)💞💞💞 *Ina jin dad’in yadda kuke son wannan novel d’in* *Ana tare*.🤝🏽 *QUESTION OF THE DAY* Wani sahabi ne yake fad’in Magana tazo daidai da saukar wa a cikin Alkur’ani mai girma? 7&8 Murmushin mugunta yayi ya ce "by the count of three ku fara up & down" K’irgawa ya fara yi da 1…2….kafin yakai 3 har mun fara. Mun d’au kusan 15 min muna up & down amma yaya Faruk bai da alamar dakatar damu. Juyawa nayi na kalli Anisa da ta dage ba ta ko tsayawa, zufa sai zubo mata take yi ga k’afar ta sai rawar awilo take yi saboda gajiya. Duk da nima a gajiye nake amma hakan bai hana ni tausaya mata ba kasancewar yadda ba ta son purnishment. Rawar da k’afar ta taci gaba da yi ne yasa na kasa danne dariyar da take ci na, fashewa da dariya nayi ba tare da nasan dariyar zata fito ba. Mamaki ne ya kama yaya Faruk ganin dariyar da nayi amma bai ce min komai ba illah mik’ewar da yayi ya nufi inda chargers wire d’in mu suke ya zaro d’aya daga ciki ya nufi inda muke. Anisa ce ta fara kuka tana cewa "yaya Faruk don Allah kayi hakuri kar ka dake mu baza mu sake ba" Wuce ta yayi ya k’araso guri na ya zuba min d’aya a jiki, ina jin saukar bulalan na daka tsalle na hau kan kujera amma haka yaya Faruk ya biyo ni ya k’ara zuba min. Rawar a sosa mata na fara yi domin ko ta ina sosa jiki na nake yi, ji nake yi kamar an zuba min k’aik’ayi a jiki na. Rok’on shi na fara yi ina cewa "yaya dan girman Allah da darajar su momi da daddy da kuma darajar matar da zaka aura da kuma girman kakin sojan da kake sa wa kayi hakuri" Duk da ba ko wani lokaci yaya Faruk ke dariya ba amma a lokacin sai da yayi dariya sannan a lokaci d’aya ya d’aure fuska kamar bashi ba ne yayi dariya. Kallo na yayi kamar bazai yi magana ba can ya ce "uban wa kike wa dariya? ko kin ga mahaukaci ne a gurin nan" "ni ba da kai nake yi ba, Anisa nake ma dariya" na fad’a da alamar tsoro. 1-sitter ya samu ya zauna ya d’aura k’afar shi d’aya akan d’aya yana fuskantar mu. d’akin ya d’au shiru kamar ba mutane a ciki, sai da ya gama mulkin sa sannan ya kalle mu ya ce "zan tausaya muku na laifin da kuka yi, yanzu sai purnishment d’inku na surutun da kuka sa ni, saboda kun san surutu bai dame ni ba, ni ba irin ku bane in ta zuba kamar parrot" kuka muka fara yi muna bashi hak’uri saboda yadda k’afar mu ta gaji amma ko alamar tausaya mana bai yi ba illa juyowa da yayi ya ce "kuyi kneel down & raise your hand up, ku rufe idon ku, by the count of 2 ku fara" ai kafin ya fara k’irgawa muka yi kneel down, gwiwa ta kuwa ji nake kamar ba jiki na take ba saboda tsamin da tayi. Haka muka d’aga hannun mu muka rufe idon mu, a raina kuwa ban san sau nawa na ma yaya Faruk Allah ya isa ba saboda duk yadda ka ke neman mugu in kazo gurin shi, zance ya k’are. Duk da ido na a rufe yake hakan bai hana hawaye zubowa a ido na ba saboda rabon da a bamu irin wannan purnishment d’in ko a school har na manta. Mun d’au kusan 7 min a haka sannan muka ji sallamar yaya Khaleel, wani dad’i ne ya kama ni saboda nasan Allah ya kawo mai ceton mu saboda shi yaya Khaleel duk ya fisu hak’uri da wasa don in muna hira dashi kamar wani mate d’in mu muka maida shi. Yaya Faruk ne ya amsa mai sallamar da yayi, nufo inda yaya Faruk yake ya mik’a mishi hannu suka yi musabaha kana ya nemi kusa da kujerar da yake ya zauna "yaya sannu da gida? Yaya Khaleel ya fad’a. Ya amsa mai da "yawwa Khaleel, ya school d’in? "School lafiya lau" sannan ya juya ya kalle mu wanda duk mun galabaita saboda izayar da yaya Fauk ya mana kana ya juyo da kallon shi ga yaya Faruk yaci gaba da cewa "yaya Faruk ina neman alfarma a gurinka ka tausaya ma sisters duk da ban san laifin da suka yi ba na tabbata ba za su sake ba, ko saboda Anisa yaya ba ta jurar purnishment" Juyo wa yayi ya kalle shi yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai da ya gama shan k’amshin sa sannan ya ce "Anisa kawai ka sani da zaka ce ba ta son purnishment ko ita Fatima an fad’a maka ba ta gaji ba" Da mamaki Yaya Kalil ya kalle shi amma bai ce mai komai ba. "Stop" abin da yaya Faruk ya ce mana kenan. Kamar jira muke yi muka sauke hannun mu yayin da muka fara kuka. Ummu ce ta fito daga side d’inta ta nufo main parlour inda take jiyo kukan mu. Guri ta samu ta zauna ta kalli yaya Faruk inda take cewa "babban yaya kai da k’annen naka ne? hala wani laifin su ka yi" Ta juyo da kallon ta zuwa gare mu tana cewa "ku kuma ku rufe wa mutane baki, kun cika ma na gida da kukan ku" Yaya Faruk ne ya sanar da ita abin da muka yi. Mik’ewa tayi ta na ce wa "Anisa da Fatima ai kusan halin su d’aya, ga rawar kai da ya musu yawa, gwara da ka hukunta su, gobe ba za su sake ba" ta mik’e ta koma side d’in ta. Kallon mu yayi da wannanan murmushin na shi da ba ka cika gane me yake nufi ba sannan ya ce "zaku iya tafiya amma ku sani bayan sallar isha’i zan maku tambaya a note book d’in ku, idan ku ka kasa amsa wa, hmmm ya girgiza kai, ya ce ba sai na fa’da muku ba, ku ‘bace min daga nan" Tashi muka yi muka nufi d’aki, inda na mik’e da k’yar na shiga band’aki na d’auro alwala na shimfid’a sallaya kana na kalli Anisa wacce ta kwanta akan gado sai lumshe ido take yi alamar gajiya da kuma bacci da yake son d’aukar ta, "Anisa" na kira sunan ta. D’agowa tayi ta kalle ni ba tare da ta amsa ba illah idon ta da yayi ja. Cikin tausaya wa na ce ‘ki daure ki tashi kiyi sallah kin ga ma an kusa sallar magrib" Wani irin kuka ta fashe dashi mai ban tausayi tana cewa "Fatima bazan iya tashi ba, k’afa ta ciwo take min, pls ki kira min yaya Khaleel ya nemo mai gyaran targad’e" Duk da nima daure wa nake yi amma hakan bai hana ni yi dariya ba na ce "wane irin targad’e a na zaune k’alau, kawai tsabar up & down ne ya yi aiki a kan mu" Da k’yar na samu ta tashi ta d’auro alwala ni kuma na ta da sallah, ban san nima k’afa ta na ciwo ba sai da nazo yin ruku’u da sujada nan na gane ban da wayau. Bayan mun idar da sallah ne na d'akko ma na man zafi muka shafa a k’afar mu amma duk da haka ba mu daina jin ciwon k’afar ba. Yaya Khaleel ne ya shigo yana mana dariya yana cewa "wasu yau sun sha hukunci, wannan ko a barrack ne ai sai haka" ya sake fashe wa da dariya. Ganin yanayin da muke ciki yasa ya tsagaita da dariyar cikin tausaya wa ya ce "serious na tausaya muku amma ku ma kun san hali kuka k’i yin extra lesson bayan kun san yana gari, kuma ku ka dawo gida kuna gulmar su shi da yaya Aminu, pls ku dinga kiyaye abin da za a muku hukunci kun ji sisters" Da ma bai san haushin shi nake ji ba, ya ce wai yaya Faruk ya k’yale mu saboda Anisa, ni na zama on my own kenan, ba mai tausaya min. Hararar shi na dinga yi, in naga zamu had’a ido sai in wayance, ashe ya lura da abin da nake yi, don haka yayi murmushi ya ce "Fateemah kenan! na san fushi kike yi da ni saboda na ce a tausaya muku saboda Anisa, ko da ba na gurin ku ka yi deciding d’in dawo wa gida, nasan ke kika kawo shawarar" Shiru na mai saboda ni a yanzu abin da na fi buk’ata shine in ci abinci kuma in gasa k’afa ta da nake jin kamar ba a jiki na take ba. Anisa ce ta kalli yaya Khalil cikin galabaita tace "yaya Khalil pls kaje kace iya talatu ta kawo mana ruwan zafi a bowl da tsumma mu gasa k’afar mu ta tawo mana da abinci" Tausayin ta ne ya kama shi saboda yasan Fatima tafi ta dauriya da kuma tsiwa don haka ya mik’e ya nufi kitchen da kanshi ya d’aura ruwan a electric kettle sannan ya juyo ruwan a cikin d’an bowl da tsumma a hannun shi ya nufi d’akin. *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💕 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽 *Wannan shafin na ba ku shi ne kyauta ‘yan kainuwa Writers* *Allah ya bar mu tare*🤝🏽 *Anty Fauza*💕💕 *Ummy On top*💝💝 *Batul Adam Jatko*💖💖 *Aisha Machika*💗💗 *Sameena Aleeyou*💘💘 *Jamila Sama’ila Yusuf*💜💜 *Aisha Sada machika*💛💛 *Mrs Mansoor*💚💚 *Mom Hanan*🧡🧡 *Jiddah Wali*(cool)💓💓 *Fauxia MB*💗💗 *Halima MK*🖤🖤 *Wanda basu ji sunan su ba, mu had’u a next page, kuma ina yin ku sosai*. *Fatan alkhairi gare ku* *Xarah Auwal*💔💔 *Fadyla ingawa* *Amsar da ku ka bayar daidai ne na question of the day* *Amsar ita ce Sayyidina Umar* *Allah ya k’ara ilimi mai amfani* TUNATARWA Kar ka/ki raina matsayin wani saboda gaba. Kar ka/ki duba wanda ya fi ka/ki wadata, ka/ki tuna ka/kin fi wani. Kar ka/ki zamo cikin masu asarar rana guda ba tare da sunyi salatin Annabi (s.a.w) ba. Yi k’ok’ari ka yak’i shaid’an ta hanyar karanta alqur’ani domin kariya ne a gare mu. *Wannan 'yar nasiha ce a gare mu*👌🏼 9&10 Ko da yaya Khalil ya kawo mana ruwan, gasa k’afar mu muka yi muka k’ara d’aukar man zafi muka shafa kana muka hau gado dan mu kwanta mu wartsake gajiya kafin a kira magrib. Kallon mu kawai yaya Khalil yayi ya fita da alama tausayin mu yake yi, side d’in Ummu ya nufa ya same ta tana kallon tauraron d’an adam. Sallama yayi ya samu guri ya zauna a d’aya daga cikin kujerar dake girke a d’akin. Amsa masa tayi da murmushi a fuskar ta tana kallon shi "Khalil ya aka yi ne" Ummu ta fad’a. ya amsa mata da "Ba komai Ummu" ya ci gaba da cewa "Ummu pls ki sa akai wa su sisters abinci su ci, k’afar su ciwo take yi ga Anisa sai kuka take yi tana cewa tayi targad’e’" Dariya kawai Ummu tayi ta ce "wane irin targad’e, kawai dai ina jin k’afar su ce ta musu tsami, ai maganin su Kenan tun da su ba sa jin Magana, gobe ba za su sake ba". Mik'e wa tayi tana cewa "bari in je da kaina in kai musu yau su auta sun sha hukunci, ta fita tana dariya". kitchen ta nufa ta d’akko abinci a food flask da kwalin extotic mai sanyi da kofi ta nufi d’akin. Samun mu tayi har mun yi bacci, gefen gadon taje tana kiran sunan mu, da k’yar na bud’e ido saboda yadda na ji barcin bai sake ni ba. Ummu ce ta kalle ni tace "ya kamata ku tashi ku ci abinci magrib ta gabato yanzu zaku ji an kira sallah" Cikin shagwa’ba na ce "Ummu k’afa ta had yanzu ciwo take min ga Anisa ma har yau k’afar ta na mata ciwo" Ummu ta kalli Anisa wanda har yanzu bacci take yi tace "Fatima tashe ta" Duka na d’aka mata a jiki. Cikin firgita ta tashi tana cewa "dan Allah yaya Faruk kayi hakuri ba za mu sake ba" Mai zanyi in ba dariya ba, jin sautin dariya ta yasa ta tashi tana harara ta. Ummu ce ta ce "Ku tashi ku ci abinci, yanzu ai gashi kun yi baccin dole, sai da nace ma Fatima tayi hak’uri ta dinga wannan extra lesson d’in amma shine tayi kunnen k’ashi da Magana ta, ku kayi shawara ku ka dawo gida gashi nan kun ja ma kan ku hukunci, ku dinga kiyaye abin da za ayi muku hukunci kun ga yanzu kun girma" Amsa mata muka yi da "toh Ummu insha Allahu zamu kiyaye" Sakkowa muka yi muka ci abinci, Ummu na k’ara yi mana nasiha. Jin kiran sallar magrib ne yasa Ummu ta mik’e ta tafi side din ta, mu ma mik’e wa muka yi dan ba da farali. Ana sallar isha’i muka d’akko abincin mu a kitchen mu ka shigo dashi d’aki, anan muka ci abincin. Muna gama ci muka rufe k’ofar d’akin saboda kar mu had’u da yaya Faruk tun da yace in anyi sallar isha’i zai mana tambayoyi saboda mugunta. K’ofa muka ji ana knocking, cikin mu an rasa mai k'arfin halin da zai je ya bud’e k’ofar. Jin maganar yaya Khalil ce yasa Anisa ta mik’e taje ta bud’e k’ofar. Shigowa yayi ya zauna a kujerar dressing mirror d’ina ya na kallon mu, can ya katse shirun da cewa ‘yaya Faruk yace ku fito da note book d’in ku yana sauri ne. Kallon kallo muka dinga yi, Anisa kuwa har hawaye ya fara zubowa a idanun ta, ganin haka ne yasa yaya Khalil ya ce mata "haba Anisa miye abin kuka, ni nasan tambayoyin da zai muku baza ku kasa amsa wa ba, nasan sisters d’ina akwai k’ok’ari, ina so ku nuna mishi ku guraye ne". Jin yadda yaya Khalil yake fasa mana kai yasa muka samu k’arfin gwiwar tashi muka je muka d’akko littattafan mu. Yaya Khalil ne a gaba mu kuma muna bin bayan shi. Samun shi muka yi zaune yana daddana waya, mun d’au kusan 5 min a zaune ba tare da ya ce mana komai ba, sai da ya gama miskilancin sa sannan ya juyo ya kalle mu ya ce "sai yanzu ku ka gadamar fitowa bayan kunsan ina sauri ne zan tafi gida" Ganin neman wani hanyar yake nema da zai ci zalin mu yasa muka ce "kayi haku’ri yaya" Bai amsa mana ba illa mik’o mana hannun shi yayi alamar mu bashi note book d’in. Bud’e littafin yayi ya fara jefo mana tambayoyi, cikin ikon Allah muka amsa iya fahimtar mu. A gaskiya nasan mun burge yaya Faruk duk da bai fito ya fad’a ba amma ya nuna a fuskar shi. Ganin bai samu abin da zai ce mana ba ne ya fara borin kunya "Allah ya taimake ku kun amsa tambayoyin da na muku da yau sai kunyi kwanan zaune, dan jikin kune zai fad’a muku". Ya na gama fad’ar haka ya mik’e ya d’au key d’in motar shi ya bar gidan. Godiya muka yi ga Allah da ya ku’butar damu daga hukuncin yaya Faruk. Bayan fitar yaya Faruk ne muka kafa zancen shi, yaya Khalil ne ya fara mana dariya yana cewa "yau Allah ya taimake ku sisters, da baku amsa question d’in nan ba ina jin yau da yaya faruk ya ta’ba lafiyar jikin ku amma Allah ya taimake ku kun amsa tambayar". Cikin shagwa’ba nace "dama kaima yanzu yaya Khalil ba ka son mu, ashe so kake yi a dake mu, bari Abbu yazo sai na fad’a mai" Dariya ya fara yi yana cewa "sorry ‘yan k’anne na, ni ai naku ne har kullum, wasa nake muku" Nan hira ta ‘barke a tsakanin mu da yaya Khalil. ************************************************************ A can kuwa gidan su yaya Faruk kuwa, Momi ce da dadi zaune a falo suna hira, sallamar Yaya Faruk ce ta katse musu hirar da suke yi, momi ce ta amsa masa sallamar, zama yayi a k’asa yana cewa "wash na gaji! Momi da dadi sannun ku da hutawa" "Yawwa Faruk" dadi ya amsa masa. Dadi ne ya kalle shi cikin kulawa yace "daman ina neman ka Faruk, za muyi muhimmmiyar magana da kai. Jin haka yasa ya maida hankalin shi gaba d’aya gurin dadi don jin mai zai ce masa "Faruk a gaskiya bana jin dad’in zaman da kake yi ba iyali kusa da kai saboda shekarun ka ya kai a ce kana da yara 2 zuwa 3, ka kalli Aminu ka girme shi amma yaran shi biyu, nasan aure nufi ne na Allah amma kuma da sa kai, saboda haka kayi k’ok’ari ka fito da matar aure tun kan in yanke hukunci akan ka, na ga kai zaman bai dame ka ba, duk mutum kamalar sa ba ta gama cika sai ya ajiye iyali. Momi ce ta amshi zancen da cewa "ni kaina Alhaji zaman Faruk ya ishe ni, a ce mutum ya isa aure amma shi abin bai dame shi ba, sau nawa ina kiran shi ina mishi Magana amma bai d’au zancen nawa da mahimmanci ba, gwara kai da ka mai Magana wata k’ila zai fi jin maganar ka" Cikin ladabi Faruk yace "Momi da dadi kuyi hakuri insha Allahu na kusa fad’a muku wacce nake so, akwai wacce na dad’e nake so amma ita yarinyar ba ta sani ba, amma insha Allahu komai ya kusa zama daidai". Momi ce ta katse shi cikin fad’a tace "zancen banza kenan, yaushe za ka zauna kana son yarinya ka k’i fad’a mata, in ban da abin ka yaushe har ka fad’a ma ita yarinyar tasan kana son ta har kuka fahimci juna" Dadi ne ya katse ta da cewa "k’yale shi Hajiya, tun da yace a bashi lokaci, Allah yasa muji alheri" Ta amsa mai da "shikenan Alhaji na bar zancen, Allah ya za’ba mana mafi alkhairi". Dadi ne ya kalle shi yace "yaushe hutun naka zai k’are ne" Next week zan koma insha Allah saboda hutun da aka bani ya k’are" cewar Yaya Faruk. Nan suka ci gaba da hirar su cikin nishad’i. *HMM READERS A RAINA NACE DAMA AKWAI WADDA FARUK YAKE SO KUMA WACECE*? *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Ku ma ban manta da ku ba* *Miss Ayusha*💝💝 *Ummien Fauzan*💚💚 *Maimuna matar Abdoulaye AM*💞 *Ummu nabil*💜💜 *Hauwa A Usman*🧡🧡 *Sa’adatu Alkali*💙💙 *Mrs Makama*💓💓 *Mai Awara*💕💕 *Momyn Arfat*🖤🖤 *Nasiba Isma'il gawo*💔💔 *Sophiee*💘💘 *Balkin Fulani*💛💛 *Ana mugun tare* *Ina tare da ku*🤝🏽 *Sakina* (Tauraruwar mace group) *Badiyya daga kano* *Maman Abdullahi Adnan* *Saudat* *Hussaina* (facebook) *Da sauran wanda ban san su ba, kuma ina tare da ku* *Ina mik’a sak’on gaisuwa ta gare ku na yadda kuke son novel d’ina* *QUESTION OF THE DAY* Wani sahabi ne ya sadaukar da dukiyar shi da rak’uman shi a lokacin da manzon Allah (s.a.w) yake cewa "wa zai ba Allah rance, ya biya sa ranar tsayuwa? 11&12 Washe gari mun so mu makara kasancewar har yau ba mu wartsake gajiyar purnishment d’in da yaya Faruk ya sa mu ba. Yaya Khalil ne zai sauke mu a makaranta daga nan shi ma ya wuce School saboda yace akwai wani assignment da zasu yi submitting da safe. A hanyar tafiyar mu, yaya Khalil ne ke ta mana nasiha akan mu dinga kiyaye abin da zamu dinga ja ana bamu purnishment ko a dake mu saboda yanzu mun girma. Yaya Khalil ne ya kalli Anisa yana cewa "Anisa yau in zan dawo sai in tawo da mai gyaran targad’en dan na ga ma ‘kafar kamar tayi sauk’i" Dariya muka yi gaba d’aya saboda mun san yaya Khalil tsokanar ta yake yi. Cikin shagwa’ba tace "haba yaya Khalil! Har da kai ake tsokana ta, bari in na koma gida sai na fad’a ma momi saboda tace ya daina bamu irin wannan purnishment d’in…." Yaya Khalil ne ya katse ta da cewa "A’ah sister, ka da ki fad’a ma momi, yaya Faruk yana yin hakan ne dan taimakon ku da inganta ku, ba za ku gane haka ba sai nan gaba, kuma lesson d’in waec da neco da kuke gani, yana da matuk’ar mahimmanci a lokacin jarabawa, mutane ne basu gane ba" Amsa masa muka yi da "insha Allahu zamu kiyaye yaya Khalil" A raina kuwa addu’a nake yi Allah in ya tashi bani miji ya ba ni irin yaya Khalil saboda saukin halin shi dan duk matar da ta samu mai hali irn na yaya Khalil ta ji dad’i ba irin yaya Faruk ba, in ban da miskilanci da mugunta ba abin da ya ajiye. Har ya ajiye mu a school muna hira cikin farin ciki da nishad’i kamar kar mu rabu. Yau ma kamar kullum, in dai aka tashi break a school, ko ni in je class d’in su Anisa ko ita tazo class d’in mu. Yau ma hakan take saboda ni ce yau naje class d’in su. Samun ta nayi tana rubutu na zauna kusa da ita ina cewa "ke kuma me kike rubutawa ne tun d’azun gashi har an fita break baki gama ba" Amsa min tayi da "malamin maths ne ya ba mu classwork yace muyi mishi submitting kafin ayi closing, kin san shi da sa purnishment kamar yaya Faruk, na ma kusa gama wa" Kallon ta nayi cikin zolaya na ce "sister wata shawara na kawo mana, mai zai hana yau kar muyi lesson mu tafi gidan ku tun da nasan momi baza ta bari ya dake mu ba ko ya samu purnishment tun da kinga bayan lesson d’in school muna zuwa ran weekend, ba sai mu dinga d’an hutawa ba…." Ban k’arasa Magana ta ba Anisa ta zaro ido tana cewa "in kin ganni a lahira kai ni a kayi, ba inda zani, kina gani har yanzu k’afa ta ba ta daina min ciwo ba" Hararar ta nayi ina cewa "ke wani sa’in ba kiyi ba, kin cika tsoro, idan muna nuna muna tsoron shi haka zai dinga mana, kin ga gwara mu nuna mishi mun girma ba kamar yadda yake mana kallon yara ba" Anisa tace "ni fa ba inda zani, in kin ga na k’ara guduwa daga extra lesson to anyi closing d’in lesson d’in ne kuma kina dai ji Ummu da yaya Khalil suka mana fad’a akan haka shine zaki ce mu tafi kuma ai gaskiyar yaya Faruk ne da yake cewa ba mu girma ba, ni kam ban girma ba" Ai ban san lokacin da na fara dariya ba ina cewa "ke ce dai ba ki girma ba amma ni kam na girma, kina gani zamu yi graduation d’in gama secondary school, yanzu ai mun zama big girls" na ci gaba da dariya ta. Anisa ce ta harare ni cikin wasa ta ce "ke matsalar ki ba kya raina abin abin dariya (A raina nace kamar Fauxia mb ta Kainuwa writers) yanzu miye abin dariya, ai duk cikin girman ne, da yaya Faruk ya zuba miki wire a jikinki ki kace yaya Faruk dan girman Allah kayi hakuri, dan darajar momi da dadi da kuma darajar matar da zaka aura da kuma darajar kakin da kake sa wa" Dariya muka fara yi saboda ni sai a lokacin ne maganar ma ta ban dariya, cikin zolaya na ce ai gwara ni k’afa ta ba tayi rawar awilo ba kuma ni ba a tashe ni a barci na ce dan Allah yaya Faruk kayi hak’uri ba za mu sake ba" Dariya muka sake fashewa da ita tare da tafawa yayin da Anisa ke cewa "in k’afar ki ba tayi rawar awilo ba amma ai kinyi a sosa mata san da ya zuba miki bulala" dariya muka k’ara yi muna maida abin da ya faru jiya. Aisha k'awar mu ce ta nufo inda muke tana cewa "kuna jin dad’in ku, wannan hira haka da dariya fa" Murmushi nayi na ce "ko ke kika ji abin da ya faru sai kin yi dariya" nan na zayyane mata yanda muka yi da yaya Faruk, ita ma dariyar tayi inda muka ci gaba da hirar mu har aka buga k’ararrawa na koma wa class. Tun da yaya Faruk ya dawo ba ni da sukuni domin a takure nake, d’an chat d’innan da nake yi ba dama sai dai in yi shi a ‘boye, gashi ni ba inda nake zuwa, in dai yana gidan mu to ni ina d’aki saboda kiyaye abin da zai tanka min, ga wata tsurfa da ya fito da ita, in dai yana gidan sai ya tashe ni na dafa mai abinci ko yace wanda aka yi ba shi yake marmari ba ko yasa ni had’a drink. Wannan hutun yaya Faruk d’in ya zaman min bak’in hutu saboda ya hana ni sakat da jin dad’in rayuwa ta. Yau Allah ya amsa addu’a ta saboda jiya muna hira a falo naji Abbu yana fad’a ma Ummu yau yaya Faruk zi koma Abuja, dad’in da naji bai misaltuwa saboda nasan zan samu sauk’i na takurawar da ya min. Ina zaune a falo ina kalllan philliphine series film na (endless love), wani scene da aka nuno shi ya d’auki hankali na inda aka nuno jenny kwance a jikin johnny san da suka yi aure inda a asibiti aka tabbatar tana d’auke da blood cancer, yanda jenny yake lallashin ta yana kwantar mata da hankali yayin da ita kuma take kuka, wani scene aka k’ara nuna wa suna zauna a k’ark’ashin bishiya inda jenny ke kwance a jikin johnny yana ba ta caring duk saboda blood cancer da take d’auke dashi gashi likita ya tabbatar musu ta kusa mutuwa.A gaskiya film d’in ya d’auki hankali na ga tausayi kamar in yi kuka dan sai da naji k’walla ta tarun min a ido, don haka ne ko motsi ba na so nayi. Mai da hankali na nayi gun allon tv inda aka nuno jenny ta mutu a jikin johnny yana rungume da ita, hawaye ne yake zubo mai a idanun sa saboda kan ta mutu tace ya mata alk’awarin ba zai yi kuka ba. Saboda tausayin johnny da ya kama ni ban san lokacin da na fara kuka ba saboda ganin ya rabu da masoyiyar shi ta gaskiya wanda suka sadaukar ma junan su da soyayya tun suna yara har kawo yanzu da suka girma. Duk da ban san dad’in soyayya ba saboda ba na yin ta amma sai da naji wani feeling a raina saboda wannan shine soyayyar gaskiya, lallai wannan film d’in yaci sunan shi (endless love) Soyayyar yahudawa kenan ma bare a je ga wadda Annabin mu Muhammad (s.a.w) ya koyar damu. A raina na ce nima Allah ka bani wanda zai so ni tsakani da Allah da nuna mun caring da soyayya. K’amshi da ya cika d’akin ne yasa nayi saurin d’ago kaina don ganin wanda yake sanye da wannan turaren. Yaya Faruk ne cikin kakin shi na soja, fuskar nan a murtuke kamar bai san wata kalma wai ita dariya ba. kallo na yake yi kamar bai t’aba gani na ba, ganin abin nashi ba sauk’i yasa na sunkuyar da kaina k’asa. "Teemah" naji ya kira suna na. Cikin sanyin murya na amsa da "na’am yaya Faruk ina wuni" bai amsa gaisuwar ba illah ce min da yayi "me yasa ki kuka" shiru nayi saboda ban san amsar da zan bashi ba tsawa ya daka min mai firgitarwa yace "ba tambayar ki nake yi ba ko sai kin ji a jikin ki" "ba komai yaya Faruk" na fad’a cikin marairaicewar murya. Takowa yayi ya zauna kusa dani har muna jin numfashin junan mu, shiru falon ya d’auka kamar ba mutane a ciki, can ya kalle ni yace "Teemah kina soyayya ne? Tambayar shi ta ban mamaki saboda nasan ba na soyayya amma saboda kar in yi laifi sai na girgiza mishi kai alamar a’ah Ci gaba yayi da ce min "idan ba kya soyayya mai ya baki tausayi a wannan film d’in har ki ke masa kuka? tun d’azun na shigo amma ba ki lura da ni ba, kinyi concentrating akan film d’in, if you are not in love, why will you worry yourself in this movie at your age? Shiru na mishi saboda ni dai nasan ba na soyayya kuma nasan Abbu ma bazai bar ni ba har sai na shiga jami’a. Yaya Faruk kuwa duk da film d’in ya burge shi kuma ya tayar mai da tsohon mikin da ke cikin ranshi amma bai nuna ba illa wani sabon lamari da ya shiga ranshi.ci gaba da nazari yayi a cikin ran sa yana wani tunani na daban, ko da yake nesa ta zo kusa, ba ya son yin sake, yana bin komai ne a sannu. *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin naku ne ‘yan group d’in* *Tauraruwar Mace* *Mufy & Maryam A Paki fans* *Kainuwa Writers fans* *Khaleesat Haidar hausa novels* *Home of Hausa Novel* *Da sauran groups na facebook da whatsapp da ake posting d’in wannan novel d’in*. *Na gode da kulawar ku*.🤝🏽 *Na ji dad’in yadda wasu suka gwada nasu k’ok’arin na ba da amsar Question of the day, sai dai amsar ba Sayyidina Abubakar bane, amsar ita ce Sayyidina Usman bn Affan, shine wanda ya sadaukar da dukiyar sa da rak’uman sa a lokacin da Annabi Muhammad (s.a.w) yake cewa wa zai ba Allah rance ya biya sa ranar tsayuwa*! *Ina ba da hakuri* 🙏🙏 *sakamkon ji na shiru da akayi, hakan ya faru ne sakamakon wasu uzuri da suka taso min* *TUNATARWA* *Zamo mai yawan tuna mutuwa, hakan zai sa ka/ki cire kwad’ayin Duniya *Kar ka/ki raina matsayin wani saboda gaba. *In ka/kin samu dama kai aikin alkhairi da ita kafin ta kubce maka/ki *Yi k’ok’ari ka/ki yak’i shaid’an ta hanyar karanta Alkur’ani domin kariya ne a gare mu. Wannan ‘yar nasiha ce.👌🏼 13&14 Yaya Faruk ne ya d’ago ya kalle ni ganin zancen zucin da yak yi ba zai saman mai mafita ba. "Fatima" ya kira suna na cikin wata irin muryar da ban san shi da ita ba domin yau yaya Faru ya canza min na yadda yayi sanyi kamar bashi ba. Ya ci gaba da cewa "yau zan koma Abuja bakin aiki, ina so ki kiyaye da dokoki na da na fad’a miki a baya, yin hakan shi zai ku’butar dake daga hukunci na, idan na dawo naji ance kunyi wani abu ke da Anisa, hmmm ba sai na fad’i sauran ba dan ita ma na ja mata kunne don haka ku kiyaye". "Insha Allah zamu kiyaye" abin da na ce dashi kenan saboda a gaskiya yaya Faruk na shiga mun lamura na da yawa amma nasan ko na kai k’ara ba wanda zai goya min baya. d’agowar da zanyi mu ka had’a ido, nayi saurin sunkuyar da ido na saboda yau ni dai ban san me yake damun yaya Faruk ba. "Teemah" ya kira suna na. A raina nace ko kai ka rad’a min sunan sai haka, abu kad’an ya kira suna na. Wannan karan ban amsa kiran da yamin ba saboda duk a takure nake, shima naga alamar bai damu da in amsa kiran ba dan haka yaci gaba da cewa "as from today, ki daina sa irin wannan kayan kina zama dasu saboda kin fara girma kuma za a iya yin bak’i at any time ki na jina koh?. Kallon mamaki na bishi dashi na kuma kalli jikina saboda ni ban ga aibun shigar da nayi ba, wasu k’ananan kaya nasa doguwa sannan na d’aura top mai transparent wanda aka yi wa d’inkin kimono, lallai yau yaya Faruk da sabon salo yazo min dashi, in ban da haka miye gamin kifi da kaska, shi ba saurayi na ba kuma ba mijina ba bare ace ko kishi ne yake d’awainiya dashi da har zai kafa min wannan dokar ban da takurawar da yake min, ganin ba zan iya bin wannan dokar ba yasa nace "yaya Faruk ni ban ga aibun wannan shigar ba kuma ni ai naga daga ni sai ‘yan uwa na a cikin gidan shi yasa na sa kuma ma ai ban girma ba bare ace hukunci zai hau kaina" ran shi ne ya soma ‘baci ganin yadda nake so in fad’a mishi Magana a fakaice saboda ya gano Magana na fad’a mai na yadda yake ce mana ba mu girma ba shine yau na samu hanyar maida mai da martini don haka yace "ai daman baza ki ga aibun shigar ba tun da yanzu naga kina tashen rashin kunya sannan ga ci gaban da aka samu na kallon wannan philliphine d’in da kike yi, dan naga kamar sun fara sa ki a kan hanya shi yasa zaki ga baki yi wani laifi ba, da kike cewa baki girma ba ki koma play class nan zan san ke yarinya ce" a raina nace "kan ka ake ji, dama an ce gwano baya jin warin jikin sa, ya manta lokacin da yake cewa mu ba mu girma da yin chat ba dan yanzu na tuna mishi shine zai zama laifi" "Ummu na ciki ne? ya tambaye ni Amsa mishi nayi da ‘eh tana ciki" "kije ki ce mata nazo" ya fad’a yana danna wayar shi dake hannun shi. Mik’ewa nayi na nufi side d’in ta don fad’a mata zuwan yaya Faruk, yaya Faruk ne ya bi ni da kallo kana ya ta’be baki. Tun da na sanar da Ummu zuwan yaya Faruk nayi zama na a d’akin ta saboda nasan in dai na koma falon sai yaya Faruk ya nemi wani laifin ya d’ora min. Ni har tausaya wa matar da za ta auri yaya Faruk nake yi saboda fad’an shi, ko da yake irin su mata sun fi ladabtar dasu a cikin gida kaga kamar ba su bane suke masifa a waje. Maganar mu daina chat ma bai taso ba don yanzu nasa k’afa don ni ina k’aruwa a social media d’in nan, shi da yake wannan maganar yana nufin bai chat d’in ne ko duk salon takurawa ce. Haka na ci gaba da zancen yaya Faruk ni kad’ai a raina saboda a gaskiya ni dai tamu ba ta zo d’aya ba. Ummu ce ta nufo falon da fara’ar ta tana cewa "Faruk har an shirya za a tafi? Yaya Faruk murmushi yayi yana cewa "ina wuni Ummu, mun same ku lafiya? "lfy lau Faruk, za a tafi Kenan? Ummu ta fad’a Ya amsa mata da ‘’eh Ummu zan koma, hutun da aka bani ya k’are ga Ogan mu sai kira na yake yi akwai wani aiki da zamu je a garin Yobe na kwantar da tarzoma sai na samu sauk’in aiki na lek’o kadunan" "To Allah ya taimaka Faruk, ya baku sa’a a dukkan lamarin da kuka sa a gaba, Allah ya baku nasara, Faruk a ci gaba da rik’o da ibada don shine hanyar da za ta dinga taimakon ka" Ummu ta fad’a. Hakika yana jin dad’in addu’ar da Ummu ta ke mai kamar ita ta haife shi, shi yasa yake d’aukar ta kamar mahaifiyar shi kuma yake neman shawarar ta a al’amuran shi dan haka yace "Amin Ummu na gode" Kud’i ya ciro cikin wallet d’in shi ya matso kusa da Ummun ya ajiye yana cewa "Ummu gashi ba yawa a sa mana Albarka" Ummu tace "Faruk ba ka gajiya? To kaima Allah ya baku masu muku biyayya, Allah ya muku albarka" Cikin jin dad’i yake amsawa da "Amin Ummu" Kallon Ummu yayi yana cewa "Ummu pls a dinga lura da takun su Fatimah saboda naga kansu na rawa ga wannan chat d’in da suke yi, a sa ido saboda yanda ake samun ‘bata gari da marasa tarbiya ga mayaudaran samari duk a cikin wannan social media d’in, na dai kafa musu doka akan chat d’in, nasan idan suka ga ba na nan zasu iya ci gaba da yi" Murmushi Ummu tayi tace "kar ka damu Faruk, zan sa ido akan su" Nan ya mata sallama ya tafi yayin da Ummu ke mishi addu’ar nasara. ************************* WACECE FATIMA? Suna na Fatima, ni ‘ya ce a gurin Alhaji Ibrahim wagini motors, Hajiya Aisha ita ce mahaifiya ta. Asalin iyaye na ‘yan Katsina ne a k’aramar hukumar wagini wanda a yanzu mahaifin su Abbu ya dad’e da rasuwa sai Hajiya, mahifiyar su Abbu ce ke zaune a garin da ‘yan uwa, zama ne ya kawo su garin kaduna, yayi Degree d’in shi a ‘bangaren Business administration inda ya fad’a harkar kasuwanci na import & export na kayayyaki irin su atamfofi da su materials, haka zalika suna da kamfani shi da wan sa na saida motoci da suka bud’e mai suna ‘wagini motors’. Mu uku ne a gurin iyayen mu, yaya Aminu shine babba a gidan mu inda yayi Degree d’in shi akan information technology a ATBU Bauchi, yanzu haka yana aiki a ma’aikatar sadarwa na MTN dake kaduna, ya na zaune a kinkinau da matar shi da yaran sa guda biyu, Aisha ana ce mata Humaira sai namijin sunan sa Nabil. Daga yaya Aminu sai yaya Ibrahim wanda ya ci sunan mahaifin mu ake kiran sa Khalil, yanzu haka ya karatu a Kaduna State University, yana karantar pharmacy inda yake 400 level. Daga nan sai ni Auta inda yanzu na kusa kammala secondary school d’ina a Fenfield int’l scool dake wajen gwamna road. Ni dai fara ce amma ba can sosai ba, sannan ni tsaka tsaki ce saboda ni dai ba doguwa bace kuma ba gajera ba, ina da d’an manyan ido sannan ina da yalwar gashin gira da na kai, baki na d’an madaidaici, a tak’aice dai ni ina tsaka tsaki a masu kyau. Na taso cikin gata kasancewa ta ni kad’ai ce mace a gurin iyaye na amma hakan bai hana samun ingantacckenan tarbiyya ba. ba mu cika shiri da yaya Aminu ba saboda ganin wataran gidan wani zan je kuma ba kowa ne zai d’au shagwa’bar da nake yi ba duk da wani sa’in yana ja na da wasa amma hakan bai hana ni shakkar sa ba. Mutumina shine yaya Khalil saboda tamu tazo d’aya dashi saboda yadda yake zama muyi hira dashi sannan in yana da wata matsala ko shawara zai tunkare ni da ita ba tare da kowa ya ji ba, shi yasa Ummu da Abbu suka ce ba a jin kan mu, duk da sakewar da yake dani hakan bai sa na raina shi ba saboda Ummu tace ya bani ratar shekara kusan 3. Mahaifin mu sananne a wajen business d’in shi na siyar da kayayyaki da kuma gurin sai da motoci. Wannan shine tak’aitaccen tarihi na Wannan kenan [3/23, 13:02] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Ina mika gaisuwa ta ga* *Miss Marriam novels group* *Maejeeddarh Othman* (Home of Hausa novels group) *Ummi*(Kainuwa Writers fans) *Mhiz Tawerh* (nima ina yin ki sosai) *Fannata ta Annabi* (zinder) *Hussaina Paki*(‘yar garin mu) *Da sauran wanda ban samu damar anbata ba sabida yawan Ku* *Na gode da son da kuke ma novel d’in nan*🤝🏽 *Allah ina rok’on ka 🙏🏽🙏🏽🙏🏽 kabar mu da masoyan mu a du inda suke*, *ka nisanta mu da masu mana hassada da bak’in ciki da k’iyayya* *Wannan karan ban samu wanda suka ba da amsar question of the day na tambayar da nayi na cewa* *ya sunan bishiyar dake cikin aljanna*? *Amsar ita ce* *Jannatul kuldi* *Ina jin dad’in yadda kuke gwada hazak’ar ku*. *Allah ka k’ara mana ilimi mai amfani*. *Tunatarwa* Hak’uri ya kasu kasha uku 🤟🏼 * Hak’uri gurin yi ma Allah biyayya * Hak’uri saboda kiyaye dokokin Allah da sa'ba mishi * Hak’uri gurin jarrabawa Dukkan hak’uri yana tare da nasara, ya Allah ka bamu ikon hak’uri. 17&18 Ko da muka je gidan yaya Aminu, hira muka zauna muka yi da Anty jiddah kasancewar ta ita ma ‘yar hirar gashi tana da jan mutane kamar ba dangin mijin ta ba. Muna cikin hira da ita ne take ce mana "ina ko Faruk, kwana biyu bai lek’o mu ba, bari in munyi waya dashi zan ce mai kar ya bari azumi yazo bai yi aure ba, in ba haka ba, zamu ba dashi sadaka" Dariya muka yi gaba d’aya kana Anisa tace "ya koma Abuja, yana can yana fama da fad’an shi" Ni ce na k’ar’bi zancen da cewa "ai da su Momi za su taimaka su mishi aure saboda ina jin har da rashin auren ne yake sa shi wannan fad’an da yake yi, amma kuma ina tausayawa matar da za ta auri yaya Faruk saboda ba k’aramin hak’uri za ta yi da fad’an shi da miskilancin sa ba" Murmushi Anty Jiddah tayi kana tace "ni da zai bi shawarata da na za’bar mai kalar type d’in shi saboda ita yarinyar za ta iya dashi" Zaro ido nayi ina cewa "pls Anty kar ki fara, ki tausayawa ‘yar mutane, ki jik’anta in ba so kike ki sa yarinya ya aure ta, ta fara k’ashin wuya a rasa dalili ba alhalin yaya Faruk ne yake gasa mata gyad’a a hannu" Anisa ce ta kar’bi zancen da cewa "Anti in dai zai ji shawarar taki, pls ki masa magana saboda yayi auren nan nima in samu sakewa a gida saboda komai a takure nake yi kamar a gidan yari" ta k’arashe zancen kamar za ta yi kuka. Dariya muka fara yi saboda yadda take maganar, abin har ran ta haka yake. Haka muka ci gaba da hirar mu kamar wasu k’awaye. Sai da muka ci abinci sannan muka yi sallar la’asar, ba yadda ba tayi ba akan mu jira yaya Aminu ya dawo ya kaimu amma muka k’i, saboda in har muka jira shi ba lallai ya kaimu gidan k’awar mu ba amma yanzu tun da driver muke, ba mu da wata matsala. Sallama muka yi mata kana muka nufi gidan Aisha k'awar mu. Tun da muka je gidan muka dasa hira irin ta k’awaye, muna cikin hirar ne nake sanar dasu yanda muka yi da yaya Faruk ran da zai koma Abuja. Dariya suka yi gaba d’aya, ganin dariyar tasu kamar da manufa suke yasa na d’aure fuska kamar ba dani ake hirar ba. Anisa ce ta k’ara kallo na ta fashe da dariya tana cewa "wato Sister a yanzu na samo satar amsa a dramar da kuka yi da yaya Faruk da kuma dalilin da yasa ya hana mu chat da kuma takura mana da yake yi" Kamar ya? Na tambaye ta. Wani kallo ta min tana k’unshe dariyar da take bakin ta saboda yadda ta ga na d’aure fuska. Fatima! Zargi na ya fara hararo min cewa yaya Faruk son ki yake yi! Anisa ta fad’a. Dam! na ji k’irji na ya buga saboda yadda maganar ta zo min a bazata. Dariyar rainin hankali nayi sannan na k’ara d’aure fuska. "Anisa Kenan! ke a ganin ki mun dace da yaya Faruk? let me tell you something, na san yaya Faruk na da duk wani qualities da mace take buk’ata a gurin namiji, but to me, ba na daga cikin su saboda ke shaida ce na yadda tamu ba ta zo d’aya dashi ba, kuma ana yin aure ne idan jinin ku had’u da mutum ko ra’ayin ku amma ni duk a ciki, ba bu ko d’aya, So plss kar k’i k’ara bi na da irin wannan bak’ar fatan though shi yaya Faruk d’in ma bai ce yana so na ba kuma a yanayin girman kan shi, nasan bazai kula ni ba saboda har yau kallon yarinya yake min" Yanayin fuskar Anisa ce ta canza zuwa ‘bacin rai saboda maganar da na fad’a akan yaya Faruk bai mata dad'i ba kuma in da kara ai bai ci in fad’a mi shi haka ba don haka tace "Fatima ya kamata in zaki fad’i Magana ki tauna, kuma in da ka’ra bai kamata ki fad’i wannan maganar a gaba na ba saboda kar ki manta yaya na ne kuma zan ji zafin duk wanda ya zage shi a gaba na kuma duk wannan abun shi yaya Faruk bai sani ba, ni ce na ce ina zargin haka" Jiki na ne yayi sanyi saboda ban zata maganar za ta ‘bata mata rai ba don haka nace "Sorry Sister, ban san maganar zata miki zafi ba, but am sorry to say, ba na iya ‘boye abin da ke cikin raina ne" Duk wannan conversation d’in da muke yi, Aisha ba ta sa mana baki ba sai yanzu ne ta k’ar’bi zancen da cewa "Sisters ku bar wannan chapter d’in is not useful tun da shi yaya Faruk d’in bai fito ya fad’a ba, so plss dukkan ku kuyi hak’uri" Dariya muka yi gaba d’ayan mu amma a raina na k’udurta k’ara nisanta duk wani alak’a da za ta had’a ni da yaya Faruk, duk da a yanzu ma ba abin da ke had’a ni dashi sai takurawa da fad’a. Haka muka ci gaba da hirar mu kana muka canza akalar hirar tamu zuwa ga yadda jarabawar mu ta Waec da Neco take ta matso wa. Misalin biyar da rabi muka mik’e dan tafiya gida saboda Dadi na hanyar shi ta koma wa gida. Rako mu Aisha tayi har inda Driver d’in mu yake, sai da taga fitar mu daga gidan su sannan ta daina d’aga mana hannu. Ko da muka isa gida, toilet na fad’a na watsa ruwa saboda yadda ba na shiri da zafi yayin da Anisa ta fad’a gado tana lumshe ido San da na fito daga wankan, samun ta nayi tayi nisa a bacci. Duka na kai mata a jikinta ina hararar ta, a firgice ta mik’e tana murza idanu alamar magagin bacci. "Ke wai wace irin lazy ce, daga d’an fitar nan da muka yi shine kika wani baje kina bacci a zafin nan, kin wani saki baki sai kace wanda muka tafi a k’afa" nace da ita. Amsa min tayi da cewa "in ban yi bacci ba me zan yi, kina ganin tun d’azun muka fita, ai dole ka gaji" Simple English wears na sa, na juya ina kallon ta nace "yi ta barci ni kinga ma na bar maki d’akin" na fad’a ina fita daga d’akin. Ko da na fito parlour ba kowa, zama nayi a d’aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun dake k’awata parloun. Wani film naga ana haskawa a tashar Mbc Bollywood mai suna *Ramaiya vastavaiya* Hankali na ne ya tafi kan film d’in saboda ina son indian film especially love film din su. Yanda jarumin film d’in RIYA ya baro garin su ya tawo garin buduwarshi SONA duk da ba wani kud’i gare su ba, hasali ma ba a cikin gari suke zaune ba, ya taso a cikin daula, amma hakan bai dame shi ba illa ma hak’uri da ya dinga ba yayan Sona d’in akan ya barshi ya zauna tare dasu. Sharad’in da yayan Sons d'in ya gindaya ma jarumin ne ya ban mamaki, Saboda yayan yace zai ware mai fegi d’aya na gona ya nome hatsi kuma zai dinga wanke shanu amma duk ya yarda. Hmmm lallai na yarda india sun iya wahala akan so in ba haka ba yaushe zan yarda da wannan sharad’in. Sai naji jarumin ya burge ni saboda ina so in ga masoya nason junan su tsakani da Allah. Anisa ce tazo ta zauna kusa dani tana cewa "Fatimah! d’an ban labarin film d’in tun da ba a fara da ni ba’ Yamutsa fuska nayi ina cewa "pls Anisa don’t interrupt me, naga ke baki san yadda nake ji da lovers bane shi yasa zaki ce in baki labari alhalin ba gama film d’in nan aka yi ba". Ta’be baki tayi tana cewa "ke idan kina kallo sai ki maida film kamar gaske, wai da kike zancen lover’s kina soyayya ne da zaki san mahimmancin so? Anisa ta tambaye ni. Hararar ta nayi kana nace "in ma ina soyayyar ai kin fi kowa sani" Murmushi Anisa tayi kana ta ce "irin kune Fatimah in kuna so baku iya son abu kad’an ba" "Kan ki ake ji" na ba ta amsa a tak’aice. Ba wanda ya sake Magana a tsakanin mu, muka maida hankalin mu kan allon talabijin d’in muka ci gaba da kallo. Sai da film d’in ya k’are kana na juyo na kalli Anisa na ce "Sister dan Allah soyayyar Riya da Sona bai burge ki ba" Kallon mamaki take min sannan tace "sun burge ni, sai aka yi yaya? Ta k’arashe zancen cikin zolaya. Tsadadden murmushi kawai nayi ba tare da nace mata komai ba. Haka muka ci gaba da hirar film d’in, kiran sallar magrib ne yasa muka mik’e muka nufi d’aki don ba da farali. [3/23, 13:02] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *QUESTION OF THE DAY* *Menene sunan bishiyar da take a cikin Aljannah*? 15&16 *Ci gaban labarin* Dawowar Ummu d’akin shi ya tabbatar min da yaya Faruk ya tafi, harara ta tayi tana cewa "ke wai Fatima wani irin kunnen k’ashi gare ki? Ki na ji yayan kin a min sallama zai koma bakin aiki amma ko ki fito ki masa sallama". Cikin shagwa’ba na fara cewa ‘ai Ummu gwara da ya tafi! mutum ya bi ya matsa min kamar a kan sa nake zaune, ni dama yayi ta zama a can Abujan da naji dad’i. Murmushi kawai Ummu tayi kana tace "Allah ya shirye ki auta" Dariya kawai nayi na mik’e ina cewa ‘amin Ummu, bari inje in k’arasa kallon film d’in da na ke yi wannan masifaffen yaya Faruk yazo ya katse min kallo na. Film d’in na mayar na ci gaba da kallo na saboda yadda film d’in ya tsaya min a rai. Scene d’in karshe ne ya fi ba ni tausayi akan na baya, tun mutuwar Jenny, johnny ba ‘kara samun natsuwa ba. Kamar yadda suka yi wa juna alk’awari na cewa in sun mutu zasu had’u a wata duniyar, a cewar su a nan zasu ci gaba da rayuwar su. Johnny ne yake tafiya akan keke yana tunanin mutuwar Jenny, unfortunately kawai mota tazo ta bige shi wanda a take anan shima ya fad’i ya mutu. Lallai wannan soyayyar Johnny da Jenny ta kai a sa ma film d’in endless love. Ganin film d’in ya k’are yasa na mik’e na nufi d’aki ina raya wa a raina an ya yanzu za a iya samun wanda zasu so junan su kamar yadda Johnny da Jenny suka yi wa junan su. *ABUJA* (Birnin tarayya) Misalin k’arfe biyar na yamma, Yaya Faruk ne zaune yana sanye da farar vest a jikin sa da short nicker, a hannun shi rik’e yake da kwalin exotic. Idon shin a kan allon k’aton Tv d’in da ke girke a d’akin amma da alama hankalin shi ba akan kallon yake ba. Mafita yake nemar wa kan san a ganin in ba haka ba wankin hula zai kai shi dare, kuma hausawa na cewa A bari ya huce shi ke kawo rabon wani. A rayuwar shi baya son yin abu da gaggawa domin yana iya jawo da nasani. Yana cikin wannan tunanin ne yaji sallamar abokin shi Mus’ab, amsa masa sallamar yayi kana yazo ya zauna kusa dashi yana cewa "Allah yaja da ran Brigadier, ya aka yi ne, na ganka so cool?. Shiru yayi kamar bazai amsa mai ba, sai da yaja wata ajiyar zuciya kana y ace "Mus’ab ina tare da wata ‘yar matsala, zuwa na KD, Mom and Dad sun nuna min damuwar su akan rashin aure na, na samu na lalla’ba su akan su k’ara min time saboda ko ita yarinyar ban sanar mata da cewa ina son ta ba kuma kai kan ka kasan komai akai" Mus’ab ne ya kalle shi cikin kulawa yace "Farouk! For how long will you take you to tell that girl that you are in love with her, let me tell you Faruk, opportunity comes at once, so you have to face her that you really love her, ya kamata kayi amfani da damar ka kafin ta kufce maka saboda shi so ba a mishi haka, hausawa na cewa da zafi zafi ake bugan k’arfe, lokaci yayi da zaka fad’a mata saboda kar ta kamu da son wani ya zamana kana Son maso wani k’oshin wahala" Faruk cikin damuwa yace "the bad news that i don’t expect from her shine in na fad’a mata ina son ta tayi rejecting d’ina, Mus’ab ban san wani hali zan shiga ba saboda ta dad’e a cikin zuciya ta wanda zai min wuya in iya cire ta at once" Dariya Mus’ab yayi yana cewa "haba Bregadier! Kamar ba soja ba wanda ake turawa yak’i gari daban daban kuma kayi winning, kamar ba kai bane mata ke kawo kansu kana yarfa su, sai gashi akan yarinya d’aya duk ka bi ka damu kan ka" Murmushi kawai yayi saboda ganin yadda Mus’ab ya maida zancen wasa. Mus’ab ne ya mik’e ya mik’a mishi hannu don yin musabaha yana cewa "bari in k’arasa block d’in mu dan nasan tana nan tana jira na, sai k’orafi take min ka kwana biyu ba ka lek’o mu ba, ba ta san soyayya ce take d’awainiya dakai" Shima mik’e wa yayi dan ya taka mai yana cewa "ba laifin ka bane, laifin soyayya ce take son maida ni rago" Dariya suka yi gaba d’aya kana suka nufi bakin k’ofa dan ya taka mai. *KADUNA* Tun tafiyar yaya Faruk na samu sakewa yayin da na ci gaba da yin chat d’ina ba tare da fargaba ba duk da in Ummu ta gani tana min Magana ko tayi min barazanar za ta had’a ni da yaya Faruk in ya dawo. Yau ba mu da School kasancewar an bamu hutun ‘happy maulud’ na kwana biyu. Ganin haka ne yasa yau tun da safe na tambayi Abbu akan zan je gidan su Anisa in kwana, cewa yayi in sa diver ya kai ni. Misalin k’arfe sha d’aya na safe n agama shiri na saboda a yau nake so in munje mu rok’i Momi ta bar mu muje gidan k’awar mu Aisha na yadda take mana k’orafin ba ma zuwa sai dai ita tazo.. Ummu na tarar a falo tana kallon Manara Tv, na zo na zauna kusa da ita ina cewa "Ummu zan tafi sai na dawo’ In kinje kya gaishe da su Anisan da Hajiya Hajaran" Mik’ewa nayi ina cewa "zasu ji" Na nufi parking space inda driver yake jira na Knocking nayi ina jiran a zo a bud’e min, Anisa ce ta bud’e k’ofar tana gani na ta daka tsalle tana murna, nima na rungume ta muka nufi cikin falo. Momi ce ta sakko daga upstairs tana cewa "A dole ku cika min kunne ashe babbar k’awa ce a gidan" Dariya nayi ina cewa "Momi barka da hutawa" Cikin yalwatar fara’ar ta take amsa min da cewa "yawwa Fatima, ya mutanen gidan" "Lafiya lau sun ma ce a gaishe ku" na amsa mata Muna amsa wa’ Momi tace Hira muka fara yi da Momi kana muka nufi d’aki muka d’aura daga inda muka tsaya. Gaskiya ina jin dad’in zuwa gidan su yaya Faruk saboda yadda Momi ta ke so na, in naje rasa inda zata ajiye ni ta ke yi don murna kuma a gidan mun fi sakewa muyi abun da muke so saboda Momi ta ce a daina takura mana, da zarar munyi aure za mu daina abin da muke yi. Bayan sallar azahar ne muka je muka samu Momi akan zamu je gidan yaya Aminu daga nan zamu biya gidan k’awar mu. Fatan a dawo lafiya ta mana sannan ta gargad’e mu akan kar muyi yamma saboda kar Dadi yazo yayi fad’a. [3/23, 13:02] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin naku ne kyauta na yadda kuke son wannan novel d’in* *Tawakkaltu A Abdul* (Mhiz Tawerh) ❤❤❤❤❤❤ (Kince kin fi kowa son wannnan novel d’in) *Nafisa Khaleed* (bintu Khaleed) 💕💕💕💕💕💕 *Da sauran Wanda suke son wannan novel din*. *Ina gaishe ku*🤝🏽 *Question of the day* Wace mata ce a cikin matan manzon Allah (s.a.w) Allah ya d’aura auran ta a sama? 19&20 Da daddare bayan mun ci abinci dasu Dadi da Momi muka nufi d’akin mu, gado na hau ina cewa "Anisa akwai data a wayan ki? Kallo na tayi da alamar tambaya kana tace "me zaki yi da data yanzu kuma ni ban gan ki da littafi ba bare in ce ko browsing d’in assignment za ki yi" Wani gajeren tsaki na ja sannan nace "in zaki bani ki bani don kin ga waya na ba data shi yasa sai kin min tambayar rainin wayau? "Sorry Sis pls me za ki yi dashi saboda ina son in karanta wani novel ne da aka turo a wani group kuma na ji ance novel d’in yayi dad’i tun kan yaya ya hana mu chat" Anisa ta fad’a. "Wani abu zan duba a internet yanzu zan baki" na ba ta amsa.. Mik’o min wayar tayi kana ta tashi ta kunna d’an madaidaicin plasma tv dake jingine a bangon d’aki, ta d’akko remote ta zauna a rest chair dake d’akin tana canza channel. Kai tsaye whatsapp d’in ta na shiga na maida wayar silent saboda kar taji pinking d’in message. Wata bak’uwar number ce na ga an yi min sallama. Kai tsaye na amsa sallamar tare da tambayar "da wa nake magana" Sai da aka d’au kusan 3 min kafin aka min reply da cewa "uban wa ya baki izinin yin chat" A raina na ce wannan d’an rainin hankali ne da zai min wannan tambayar, sai na maida masa amsar "ba uban kowa ya bani izini ba illah ikon kaina" Sai aka k’ara turo min da cewa "kin san da wanda kike Magana kuwa" "ya za ayi in sani tun da ba duba nake yi bare in sani" na k’’ara da sa hoton keyboard moji na alamar murgud’a baki kana na tura text d’in. Sai da aka k’ara d’aukan kusan 4 min kafin a turo min message da cewa "hmmm Anisa sorry for yourself tun kan in dawo ki fara kuka da hawayen ki, tun da ban isa in ba ki command ki bi ba, yanzu kina ganin kin girma, idan na dawo zaki san da wanda kike chat, you will regret what you have done tun da ba kya jin magana stupid kawai" abin da aka rubuta a message d’in Kenan. Zaro ido nayi saboda sai a yanzu na gane da yaya Faruk nake chat saboda a chat d'in wata number yake using ba wacce muke da ita ba, duk da na tsorata amma hakan bazai hana in nuna mai har yanzu ban gane da wanda nake chat ba, amma a zuciya ta kuwa fargaba da tsoro ne suka cika ta saboda nasan abin da zai biyo baya idan ya dawo. Don haka sai na maida mishi amsa da cewa "pls wai da wa nake Magana ne? ka zo sai fad’a min Magana ka keyi son ranka, if you will not introduce yourself, I wanna block you" hannuna na rawa na tura saboda ina so in ga k’arshen dramar da muke yi ni da yaya Faruk. Message ya turo inda yake cewa "nasan kin gane ni, ki ke fad’a min magar da kika gadama, zaki iya blocking d’ina a yanzu amma ki tabbatar da in na dawo sai na canza miki kamanni, in baki yi wasa ba, abin da zan miki sai kin manta a wace duniyar ki ke dan sai na canza miki kamanni" Duk da na tsorata da message d’in da ya turo kuma har yau bai san ba Anisa ba ce amma haka na k’ara tura mai reply da cewa "Kan ka ake ji" Bai k’ara turo reply ba, dan haka naci gaba da chat d’in da nake yi da ‘yan class d’in mu da kuma ‘yan group d’in mu saboda group d’aya muke da Anisa. Vibrating d’in da wayar take yi ne yasa nayi saurin kallon screen d’in wayar. Sunan Yaya Faruk na gani a jikin screen d’in, da sauri na mik’a wa Anisa wayar ba tare da na ce mata komai ba. Ko kan ta d’auka, wayar ta k’atse, wani kiran ne ya sake shigowa a karo na biyu. Da sauri Anisa tayi receiving d’in kiran cikin ladabi saboda ganin sunan yaya Faruk a jikin screen d’in "Anisa kin zama ‘yar iska ko? ni kike fad’a wa maganar da kika gadama a chat! tun kan in dawo ki fara tausaya ma kan ki saboda ina jin sai na karairaya ki ko Momi ta kusan haifar wata ba ke ba dan ina jin sai an kira miki mai d’auri, dan abin da zan miki sai kin sha mamaki na, na ga alamar kin fara manta ni ne….. . Ai tun kan ya gama fad’ar maganar da yake yi Anisa ta fara kuka ta yi kneel down tana cewa cikin maganar kuka "wallahi yaya ba dani kayi chat ba, ka tausaya min, Fatimah ce ta ari waya ta tace zata yi browsing, ban san chat za ta shiga ba, ta sake fashewa da kuka a karo na biyu k…… "Wannan matsalar ki ce" abin da yace kenan ya katse wayar. Anisa ta sake fashewa da kuka tana cewa "wayyo Momi kizo ki cece ni! Fatima kin ja min! Duk da ta bani tausayi saboda ni kaina shaida ce akan muguntar yaya Faruk amma yanda take kuka ne ya ke bani haushi Dan yadda take kukan kamar yaya Faruk na gurin. Cikin jin haushi nace "Wai Sister miye abin kuka kamar wadda tayi wani babban laifi, kuma da kike wannan kukan ina ki ga yaya Faruk d’in, shi yasa wani sa’in kike ‘bata min rai saboda tsoron ki yayi yawa". Duk da kuka take yi amma bai hana ta d’agowa ta harare ni kana tace "tun da kin ja min ai dole kice haka". Dariya nayi kana na ce yanzu ya kike so ayi" na tambaye ta. "Ki kira shi ki ce da ke yayi chat ba dani ba, in kika yimin haka kin taimake ni" Anisa ta ba ni amsa. Zaro ido nayi sannan na ce "ki yi hak’uri kawai hukuncin ya hau kan ki tun da bai san dani yayi chat ba, kuma in dai yasan ni ce ina jin gunduwa gunduwa zai yi dani" na fad’a da alamar tsoro a fuska ta. Ganin yadda Anisa ta tayar da hankalin ta yasa na d’kko waya ta, na kalle ta cikin jin haushi na ce "dan Allah ki mana shiru, zan tura mishi text a waya ta in fad’a mishi ni ce nayi chat da wayar ki". Murmushine ya su’buce a fuskar ta kamar ba ita ke kuka ba, nima tsoro ne fal cikin raina saboda nasan duk san da ya diro garin nan, zan fuskanci hukunci mai tsanani a gurin shi. Haka kowa ya kwanta da tunanin mugancin yaya Faruk. Sai da nayi kwana biyu a gidan su Anisa kasancewar hutun yazo a tare da weekend sai ya zama kwana hud’u Kenan za mu huta sannan na tattara na koma gida ina mai jin dad’in hutun da nayi a gidan su Anisa saboda yadda nake sake wa a can ba tare da an sa min ido ba. Yau da yin jamb d’in mu kusan wata biyu kenan wanda yai daidai da zuwan jarabawar mu ta Waec. Dan haka ba ni da wani hutu illah karatu da na sa a gaba saboda yadda nake so in fito da grade mai kyau. Mun fara waec exam d’in ne da Practical d’in biology a watan may/june kana jarabawar ta ci gaba da gudana cikin nasara. Ran k’arshen exam d’in mu ka k’are da rubuta Islamic studies wanda daga nan muke sa ran samun nasara a sakamakon mu sai kuma Neco da za mu rubuta.. Ba mu samu wani hutu ba kasancewar waec da Neco ba nisa muka fara rubuta jarabawar Neco a watan June/July. Haka muka gama rubuta jarabawar cikin nasara da taimakon Allah. Bayan gama jarabawar mune muka fara tunanin yadda graduation d’in mu zai gudana saboda gaskiya mun shirya ma ranar. Yau kusan watan yaya Faruk uku da tafiya a Abuja wanda yayi daidai da ranar graduation d’in mu. Gaskiya naji dad’in wannan ranar saboda an yi hotuna na tarihi da ciye ciye, gashi an rausaya a ranar. Haka muka yi ta yin exchanging d’in numbers kamar kar a rabu, wasu har kuka suka yi saboda ganin an rabu Kenan kuma ba lallai a sake had’uwa ba, ni kaina sai da nayi hawaye, na kuma yarda da hausawa ke cewa sabo ake wa kuka. Haka nayi sallama da ‘yan class d’in mu muna masu missing d’in junan mu. A Washe gari ma akwai wani party da ‘yan class d’in mu suka had’a mana a wani hall amma ba za mu halarta ba saboda mun san a gida baza a ban mu ba. [3/23, 13:02] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin na ki ne* *Fauxia MB* *Ba za ki ji mutuwar sarki a baki na ba*, *na labarin Teema da yaya Faruk*, *kuma ni ban san wake yin makauniyar soyayya a cikin su ba*, *LOKACI NE da zai nuna hakan* *JINJINA GA* *Batul Adam A Jatko* (Damata) *Hauwa A Usman* (Wani Al’amari) *Ina taya ku murnar kammala novel d’in ku wanda yake d’auke da darasi*. *Na ya ba muku na yadda ku ka ja zaren labarin ku dan isar da sak’wanni ga mutane*. *Sai mun ji ku a new novels d’in ku*. *GAISUWA GA* *Ummu Fadlu* *Ameenatou* *Na amsar da ku ka bayar daidai a Question of the day na cewa A cikin matan manzon Allah (s.a.w) wanda Allah ya d’aura musu aure a sama ita ce Zainab bnt Jash*. *Allah ya k’ara ilimi mai amfani*. *Tunatarwa* Har kullum idan ka na so ka ci nasara a rayuwa, ka/ki fara wanke zuciyar ki kafin jikin ka/ki, kuma ka/ki wanke harshen ka/ki kafin hannun ka/ki, sannan ka/ki kyautata zato ga mutane. 21&22 Yau kwana biyu kenan da yin graduation d’in mu. Ina kwance akan gado ina karanta wani online novel mai suna ‘behind our love’ littafin ya min dad’i kuma marubuciyar tayi matuk’ar k’ok’ari a wajen salon rubutun na ta. Waya ta ce tayi k’ara wanda ya katse min karatun da nake yi, sunan Aisha friend da na gani a jikin screen d’ina shi yasa ni sakan murmushi D’auka nayi tare da cewa "Hi Aisha ykk? amsa min tayi da "normal! Kina gida ne? amsa mata da nayi "ina gida za ki zo ne?na tambaye ta. "yeah! Zan zo, naje school ne saboda hotunan da muka d’auka an wanke mana da kuma copy d’in video d’in, sai na zo" Aisha ta fad’a. "Ok sai kin zo" na ce da ita. Nan muka yi sallama da ita kana na ci gaba da karanta novel d’ina. Around one pm, sai ga Aisha tazo, nayi murnar zuwan ta dan haka ina kai ta side d’in Ummu suka gaisa muka wuce d’aki na. Nan muka dasa hirar makaranta kamar wanda muka dad’e ba mu had’u ba, a lokaci d’aya muna duba pictures d’in mu na graduation d’in mu wanda suka yi matuk’ar kyau. Aisha sai da takai kusan k’arfe uku sannan ta min sallama ta tafi tare da ma ta alk’awarin insha Allah ina nan zuwa saboda tace sai tazo sau nawa ban zo sau d’aya ba. Yaya Khalil ne yazo ya same ni a d’aki yana cewa "Sister me kike yi ne a d’aki naji ki shiru? "yawwa Yaya Khalil zo ka ga hotunan mu na graduation da video d’in da aka yi na event a ranar graduation d’in mu". Zama yayi ya kalli hotunan yana tambaya na wasu daga cikin ‘yan class d’in mu da ya ga mun d’auka tare, ni kuma ina mishi bayanin su, ya fara kallan video d’in ne ya duba wrist watch d’in shi ya na cewa "Sis bari in je parlour akwai wani program da zan kalla yanzu, in ya so kya ba ni labari duk da ban samu attending d’in graduation d’in ku ba saboda test da muke fama dashi" yaya Khalil ya fad’a. "Ok bros" na fad’a da alamar zolaya. Ficewa daga d’akin yayi yana cewa "that is my Sister". Gaskiya sai yanzu na ji dad’in graduation d’in mu saboda wasu abubuwan sai a kaset na ga sun burge ni. A cikin video d’in akwai wani dancing step da muka gabatar wanda namiji da mace za a sa masu cool music su fito su taka sannan wasu sai su sake shigo wa. A cikin wanda suka yi participating har da ni a ciki, ni da wani Kabir d’an class d’in mu a ka saka mana music d'in muka rausaya, step d’in da muka bayar ni kaina sai da ya burge ni. murmushi nayi sabo da ji nayi kamar mu k’ara yin graduation d’in. Jiki na ne ya bani kamar ana kallo na dan haka na juya na kalli saitin k’ofar dake d’akin. Wani irin razana da nayi ban san lokacin da jiki na ya fara rawa ba saboda wanda na gani, da kyar nake had’iye miyau a baki na saboda yanda naji mak’ogwaro na ya bushe. Yaya Faruk ne a tsaye da uniform d’in shi na soja, yau gani nake yi kamar yafi ko yaushe d’aure wa saboda yau har idon shi sai da naga ya kad’a saboda ‘bacin rai. Takowa ya fara yi cikin k’asaita yana tunkaro ni, matsa wa nayi kusa da gefen gado saboda ni yau tsoron shi nake ji, ga kuma laifin da na mishi a chatting. Hotunan da muka d’auka da ‘yan class d’in mu ya d’auka yana kalla, wasu na d’auka da mazan class d’in mu, wasu kuma ni da ‘yan matan class d’in mu. Cikin ‘bacin rai naga ya ajiye wanda na d’auka ni kad’ai da Wanda na d'auka da Anisa sai Wanda na d'auka da k'awaye na. Ya d’au sauran ya yaga. Wani ‘bacin rai ne ya kama ni ganin abin yaya Faruk ya wuce misali don ko a lokacin mulkin mallaka sai haka. cikin ‘bacin rai nace "yaya me yasa za ka yaga min bayan su kad’ai ne copies d’in da nake dashi". Lafiyayyen marin da naji a fuska ta shi yasa ni d’ago wa na kalle shi saboda ni dai a tunani na ban ga wata kalma da na fad’a mai da bai dace ba" Wani tsanar yaya Faruk ne ya kama ni a lokaci guda saboda ni a gani na tsantsan tsana yake nuna min. Cikin tsiwa na ce "yaya Faruk mai na maka ka mare ni! Wani marin na k’ara ji a fuska na wanda yafi na farkon zafi wanda yasa ni gigita. Wani abu na ji ya tok’are min k’irji wanda daga ji kasan na bak’in ciki ne da takaici don haka hawaye ne ya fara zubo min daga idanu na. Ganin in na ci gaba da mayar mai ni ce zan wahala saboda nasan yanzu sai ya jibge ni a banza. Cikin ‘bacin rai ya fara Magana yana cewa "wallahi Fatimah ki kiyaye ni! ina raga maki ne saboda wasu dalilai amma naga ke baki san haka ba! na ga kina tashen rashin kunya kuma kin san na tsani raini, ban da rashin kunyar da kika min a chatting sannan nazo naga video d’in ku na graduation d’in ku, kina rawa da wani d’an iskan classmate d’in ku alamar you a marture enough sannan kina d’aukan hoton da maza, sannan had kina da confidence d'in tambaya ta, you must be stupid". Yaci gaba da cewa " idan zan hukunta ki sai kin ce anya ni d’an uwan ki ne amma tun da kin fi so in fito miki ta haka zan aikata hakan gare ki dan naga alamar kin manta ni". Yana gama fad’in haka ya fita daga d’akin, ko kallon yaya Khalil bai yi ba da ke zaune a kujera a falo ya fice daga gidan dan ko sallama da Ummu bai yi ba. Bayan fitar shi ne na afka cikin tunani saboda ni a gaskiya ban ga laifi ko rashin kunyar da na mai ba da yake min wannan fad’an kamar ya ari baki, dama ni na lura yaya Faruk ba ya k’auna ta dan haka nima a yanzu na d’aura d’ammarar fito na fito dashi duk nasan bazan ci riba ba amma dole ne in nuna mai nima ban sa shi a ka ba. Hawaye ne yaci gaba da biyo min saboda har yau jin zuciya ta nake yi tana min zafi. Shigowar yaya Khalil ne yasa na d’ago na kalle shi da idanu na wanda suka yi ja saboda ‘bacin rai. Zuwa yayi ya zauna a guri na bai ce min komai ba illa kallo na da yake yi. fad’awa jikin shi nayi ina kuka saboda nasan shi zan fad’a wa damuwa ta kuma shine mai share min hawaye na. Cikin lallashi yake cewa "is ok Fatima! Ki daina kukan and tell me mai ya faru? tsakanin ki da yaya Faruk naga ya fita cikin fushi". Ci gaba nayi da kuka ina cewa "ni ban san mai nayi wa yaya Faruk ba ya tsane ni, abu kad’an sai ya kama min fad’a ko ya bani purnishment, kuma ba hali in fad’a saboda nasan ba mai ba ni gaskiya…" Katse ni yayi da cewa "keep that aside and tell me what is going on". Fad’a mishi komai nayi tun daga chatting d’in da muka yi da kuma yaga min hotuna da yayi da kuma abin da yace min. Shiru yaya Khalil yayi kamar ba zai ce komai ba, can ya kalle ni yace "Sister duk abin da yaya Faruk yake miki may be yana da dalilin yin shi saboda haka in ya dawo ki bashi hak’uri akan abin da kika ce mai a chatting da kuka bayar shi da kika yi akan me yasa ya mare ki, beside yaya Faruk zai iya hukunta kowa a family d’in nan. Cikin ‘bacin rai na ce "akan me zan bashi hak’uri bayan shi kullum burin shi ya takura min". Murmushi kawai yayi ya ce "do as i say Fatimah". Nodding d’in kaina nayi amma a zuciya ta na k’udurta cewa bazan bashi hak’uri ba saboda in sa’bawa ne ni aka yi wa laifi ba shi ba". Da haka muka bar zancen, muka ci gaba da wata hirar kamar ba abin da ke damu na. [3/23, 13:03] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin naku ne, ina godiya da yadda kuke bin wannan novel d’in*. *Ina muku fatan alkhairi gare ku*.🤝🏽 *Zinatu gatari* *Amina Samaru* *Mmn Shaheeda* *Rahmatu Jaafar* *Mom Affan* *Ikram 202* *Asiya Paki (‘yar garin mu)* *Meeynarh* *Question of the day* An tambayi manzon Allah (s.a.w) a cikin maza wa yafi so? Sunan wa annabi Muhammad (s.a.w) ya ambata? 23&24 Shi kuwa a ‘bangaren yaya Faruk, yana fita daga gidan ya fad’a cikin motar shi ya ba ta wuta. Ko da ya isa gida bai tsaya yin parking d’in motar a ma’adanar motoci ba ya fad’a cikin gida. Anisa ce zaune a parlour tana yanke fingers d’in ta da nail cutter a lokaci d’aya ta sa cool music tana saurara ta cikin home theater speaker d’in dake parlour. Sallama yayi a ciki-ciki wanda in dai ba ka lura da motsin bakin shi ba, ba za kace Magana yayi ba. Anisa wacce hankalin ta ke kan yanke fingers d’in ta, ba ta lura da shigowar shi ba sai takun tafiyar shi da taji a kusa da ita. D’agowa tayi ta kalle shi tare da lura da yanayin da yake ciki kamar yana cikin damuwa amma ba halin tambaya dan yanzu sai ya hau ta da fad’a. "Yaya sannu da zuwa" Anisa ta fad’a. Wani kallo da ya ma ta sai da gaban ta ya fad’i saboda tasan ruwa ba ya tsami banza. D’akin ya d’au shiru na ‘yan mintina kana yaya Faruk ya fara magana cikin fushi tare da cewa "Anisa bi ki ji san da nayi sallama ba ne ko ke ma za ki nuna min kin kawo k’arfin kan ki ne? Cikin sanyi murya tace ‘sorry yaya Faruk ban ji bane". D’akko min copies d’in hotunan da kuka yi ranar graduation d’in ku! Cikin mamaki tace "yana gurin Fatimah saboda d’azun ta kira ni tace friend d’in mu ta kawo mana". Ci gaba yayi da cewa "kuna ganin ku kun girma ko da har zaku d’auki hotuna da maza ko? har wani dancing step kuka yi saboda kuna tashen girma, bari in fad’a miki kiji, duk san da na gan ku da saurayi ko kuna zance, hmmm a ranar sunan ku sorry dan sai na kai ku kwata kun kamo kifin oga, ban da sauran purnishment da zan baku iri iri saboda kun ga ina k’yale ku shine kuke yin abin da kuke so". Ya ci gaba da cewa "yanzu ma saboda tsabar iskanci kina ji nayi sallama amma bi ki amsa min ba, wato ga d’an isa ko? ya kalle ta yana jiran amsa. Anisa ko da ta fad’a cikin tunani sabida a tunanin ta ba ta san me ya ‘bata mai rai da zai zo ya huce a kan ta kuma ya aka yi yasan sunyi hoto da ‘yan class d’in su? Ko dai ya je gidan su Fatimah ne! To in ban da abin yaya Faruq menene laifi dan sun d’au hoto da ‘yan class d’in su? Abin da ake yin shi na rana d’aya saboda tarihi. Tsawar da ya daka mata ita tasa ta yanke tunanin da take yi. "Kayi hak’uri yaya Faruk ban ji sallamar ka bane shi yasa" Anisa ta fad'a. Wani gajeran tsaki ya ja ba tare da yayi Magana ba, ya nufi side d’in shi. Tun tafiyar yaya Faruk d’aki, Anisa ke mamakin shi saboda ita dai a iya sanin ta ba ya shaye-shaye bare tace ko a buge yake, ita ko taba bata ga yana sha ba. To ko dai allurar sojan ce ta motsa? Wannan ne ba ta da amsar shi. Wani sa’in in ya zauna yana d’an jan ta da hira ba k’aramin dad’i take ji ba, saboda d’an uwa rabin jiki ne, hasali ma shi kad’ai ne wanda iyayen su suka haifa. Addu’ar ta shine Allah yasa yayi aure ko ya rage fad’an da yake yi. Yaya Faruk kuwa yana shiga d’aki ya fara kaiwa da komowa kamar wanda yake training. Sak’a da warwara yake yi duk akan mafita da yake nemar wa kan sa don in har bai d’au mataki ba yana ganin zai iya fad’a wa a cikin rami.. Marin da ya min ne yake mishi gizo a idanun shi kamar a time d’in ne ya mare ta. Hannun shi yakai ma naushi kamar shine ya mishi laifi. Zuciyar shi ce ta fara raya mishi akan cewa me yasa ya mare ta? hakan ba zai jawo ta k’ara jin haushin shi ba, tun da ita a tunanin ta yana matsa mata ne?. A fili yake fad’in "why? me yasa na mare ta? me yasa ban yi controlling d’in temper d’ina ba? duk wannan tambayoyi ne yake yi wa kanshi wanda ba su da amsa. Hannun shi ya d’aura a kanshi wanda yake faman yi mishi ciwo. Zuciyar shi ce yaji tana bashi command akan cewa yaje ya ba ta hak’uri ko ya samu sauk’in rad’ad’in da take mishi. Wata kuma zuciyar na ingiza shi akan cewa kar yaje, saboda hakan zai iya jawo wa ta raina shi wanda shi kuma ba ya fatan hakan ta kasance a gare shi saboda in akwai abin da ya tsana bai wuce raini da wulak’anci ba. Ganin bai samu mafita ba yasa ya tashi ya shiga wanka ko ya samu relief akan abin da yake damun shi. Bayan ya fito wanka ne ya d’akko t-shirt da jeans yasa, ya d’auki kwalin exotic a fridge kasancewar shine favourite drinks d’in shi dan haka ba ya rabo dashi a fridge, ya nufi garden d’in gidan. Sipping d’in exotic d’in yake yi a lokaci d’aya yana danna wayar dake hannun shi. Tunanin d’azun ne ya k’ara dawo mishi a karo na biyu akan cewa yaje ya ba Fatimah hak’uri ko da yana ganin hakan na nufin girman shi zai zube a gurin ta saboda yanayin rawar kanta da yaga tana fama dashi. *(Hmm to nima dai na k’osa in samo amsar a gurin yaya Faruk saboda zargi ne kala- kala a raina* *Amma dai bari in bishi sannu a hankali saboda nasan amsar na nan tafe)* Ganin tunanin bai da wani amfani a gare shi illah wani damuwar da zai k’ara mai, shi yasa ya tashi ya nufi side d’in Momi wacce ke zaune a 2-sitter rik’e da littafi da biro a hannun ta, da alama wani abu mai mahimmanci take yi. Yaya Faruk ne yayi sallama yazo ya zauna kusa da ita yana lumshe ido kamar wanda yake jin bacci. Amsa masa sallamar tayi kana ta maida hankalin ta gare shi. "Faruk! ta kira sunan shi. Cikin husky voice d’in shi ya amsa mata da "na'am Momi, Sannu da hutawa". Momi ce ta nazarce shi a cikin ‘yan mintuna sannan tace "Faruk! what is wrong with you". Amsa ma ta yayi da cewa "ba komai Momi, kawai dai ina jin stress ne ya min yawa". Murmushi Momi tayi kana tace "Faruk! yanda na lura akwai abin da yake damun ka, but it seems like you don’t want to tell me, any way bazan matsa maka ba tun da kana ganin ‘boyewar shine mafita a gare ka". "believe me Momi, i don’t have any problem, kawai dai ba na jin dad’in jiki na ne". Kallon shi kawai tayi saboda ba ta yarda da maganar shi ba amma bari ta bi dashi a hakan. Kasha magani ne? ta tambaye shi. "Eh na sha" ya ba ta amsa. Canza hirar yayi da cewa "Momi kayan sun k’araso ne? "Sun iso, yanzu ma lissafin da nake yi kenan saboda wasu za su kai garuruwa ne, na ga ma wannan karan an fi son less, next time sun zan sa a kawo min da yawa, dan ina ganin wannan zasu yi saurin k’arewa". Ci gaba suka yi da zancen business kana yaya Faruk ya mik’e da niyyar tafiya yana cewa "Momi bari in je in d’an kwanta". "Ka ci abinci ne? Momi ta tambaye shi. "No Momi i don’t feel like eating" ya amsa mata. "Daurewa za kayi kaci, saboda zama da yunwa ba dad’i, zan sa Anisa takai ma abincin side d’in ka" Momi ta fad’a. "Ok Mom" ya amsa mata sannan ya juya ya fita daga d’akin. Momi ce ta kira Anisa akan taje takai ma yaya Faruk abinci. Kitchen ta nufa ta d’akko abicin ta nufi d’akin. Samun shi tayi a kwance akan rest chair da alama akwai tunanin da yake yi, sabida ko sallamar da tayi bai amsa ba saoda yana cikin duniyar tunani. Ajiye food flask d’in tayi akan center table, ta nufi fridge ta d’akko mai swan water ta ajiye. Ganin duk wannan kai kawon da take yi a d’akin bai mata magana ba wanda ke nuni da yayi nisa a cikin tunani. Har ta juya da niyar barin d’akin, in yaso in ya gama tunanin ya ci abincin. Yanayin damuwar da taga yake ciki tun lokacin da ya shigo gidan yasa ta kasa samun peace of mind, dan haka ta matsa kusa dashi ta kira sunan sa a hankali amma bai amsa mata ba, ganin haka yasa ta rik’e mishi hannu. Da sauri ya d’ago kamar wanda ya tashi daga bacci yana kallon ta. Ganin haka ne yasa tace "yaya ga abincin nan in ji Momi wai kaci". "Ok" ya ba ta amsa a gajarce. Ta juya da nufin tafiya ta d’ago ta kalle shi kamar da abin da take son cewa. Kamar ya lura da yanayin ta ne yasa ya kira sunan ta. "Anisa zo nan". takowa tayi ta zauna a bakin gado. "Come close to me Anisa" abin da yace da ita kenan. Cikin sanyinta ta zauna kusa dashi. Hannun ta ya rik’e yana cewa "Anisa tell me what is in your mind, don’t be afraid, nasan akwai magana a bakin ki, so feel free". Kame-kame ta fara yi sannan tace "ba komai yaya, dama naga kamar akwai abin da yake damun ka ne, shi yasa na damu". Lallausan murmushi yayi ya ce "don’t worry my Sister, ba abin da yake damu na, but still i need your prayer because there is something that i want to archieve" Kallon shi kawai tayi ta gane he is serious of his word, dan haka tace "yaya i wish you success on what you want to archieve". Dad’in kalamenta yaji saboda yasan ko ba komai ya samu sauk’i a tunanin da yake yi. Haka ya dinga jan ta da hira wanda hakan ba k’aramin dad’i yayi wa Anisa ba, dan ta manta raban da ya zauna ya nuna mata caring d’in shi. Sallama ta mai ta tashi ta tafi tana mai fatan hakan ya dawwama a tsakanin su. [3/23, 13:03] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin naku ne*. *Mrs Makama* (Hijira) *Mom Hanan* (Mijin Aurenah) *Ummien Fauzan* (Tsananin Rabo) *Ummu Fatima* (Dija Qaya) *Khairaty* (Ya Sheikh) *Napheesa Isah Shehu* (Sanadin Maraici) *'yar mutan Paki na mik’a gaisuwar ta gare ku tare da yi muku fatan alkhairi*. *NA YABA MUKU* *Xarah Auwal* *Meeynarh* *Da sauran Wanda ban samu ambatar sunan su ba* *Kune ku ka bada amsar question of the day daidai*. *Allah ya k’ara ilimi mai amfani*. *Sunan wanda manzon Allah (s.a.w) ya ambata a lokacin da aka tambaye shi a cikin maza wa yafi so? Shine ya ba da amsar da cewa *‘sayyidina Abubakar radiyal lahu anhu shi yafi so a cikin maza’*. *Tunatarwa* Ka da ka damu da hassadar da mutum zai yi maka/ki, saboda wata ni’ima da Allah yayi maka/ki, idan ya baka/ki, babu mai k’wacewa. Wannan nasiha ce. Ka/ki ji tsoron yi ma mutane mummunan zato, ko da zaton naka/ki gaskiya ne, don zato shine mafi k’aryar a cikin zance. Wannan hadisi ne. 25&26 Bayan fitar Anisa daga d’akin, yaji ya samu relief a ranshi, ko ba komai ya ji dad’in addu’ar da ta mishi, yana yabawa da natsuwar ta. Abincin da Anisa ta kawo mai yaci, kana ya kunna tv yayin da ya kunna tauraron d’an adam, channel d’in Aljazeera yasa inda yake sauraran labarum da ke faruwa a k’asa daban-daban. Yanda ake faman fad’a a wasu k’asashen ne ya d'au hankalin shi, yayin da wasu k’asar suke fama da kashe-kashen da ake yi musu na kashe musu ‘yan uwa, mazajensu, matayen su ko ‘yaya ba tare da wani dalili ba. nuno wasu mutane aka yi suna kuka na yadda suke fama da yunwa da rashin muhalli duk a dalilin rashin zaman lafiya na k’asar. Hamdala yayi wa Allah da a k’asar mu ba a fama da irin wannan fad’ace-fad’acen, sai matsalar da ba za a rasa ba, na fama da matsalar (kidnapping) garkuwa da mutane da yanzu ya addabe k’asar tamu. Addu’a yayi akan Allah ya kawo mafita ya kuma zaunar da k’asar mu lafiya da sauran k’asashe baki d’aya. Kiran sallar la’asar ne yasa ya mik’e ya nufi masallaci, ko da ya dawo daga salllah bai shiga cikin gidan ba illah motar shi da ya shiga ya nufi haleems dan ya huta. Ko da ya isa gurin, ke’bantaccen guri ya samu ya zauna, yana kallon mutane da ke harkokin su. A wani ‘bangaren kuma, abokai zaka ga suna hutawa, wasu kuma masoya ne ke hutawa. Ido ya tsura ma wani saurayi da budurwa, kai daga gani masoyan gaskiya ne, in kai duba da yadda suke hirar su cikin nishad’i alamar ba abin da yake damun su. Yadda suke caring d’in junan su yasa yaji sun burge shi wanda shima yana fatan nan gaba ya samu irin haka ko ma fiye da haka. "Sai yaushe kenan? yaushe ne zai fito ya bayyana sirrin zuciyar shi da yake faman adana shi wanda yake ganin akwai lokacin da zai samu furta abin da ke ranshi? tambayar da yayi wa kansa kenan da yake buk’atar amsar a karan kanshi. (HMM YAYA FARUK KAR KAYI SAKE…. SAI KACE BA SOJA BA?) Yana cikin karanta wasik’ar jaki ne wata kyakkyawar yarinya tazo ta zauna a kusa dashi, ganin ko alamar kallon ta bai yi ba bare aje ga zai tanka ta. Ganin idan ta biye mai bai san da wata hallita a gurin ba, dan haka ta mishi sallama. Sanin darajar sallama yasa ya amsa mata, ya d’auke kan shi yana mai ci gaba da kallan wannan saurayi da budurwar. Lura da tayi bai san da zaman ta ba yasa tace "handsome naga kana zaune kai kad’ai ne shine naga ya dace in zo in taya ka hira". Yanda taga bai da alamar amsawa yasa tace "in ba damuwa zan iya samun numban ka". Wani malalacin kallo ya mata na alamar gargad’i amma hakan bai sa ta ji d’ar ba illah k’ara cewa da tayi "suna na Fatima amma ana kira na da Binafa, zan iya sanin sunan ka? ". Jin sunan da ta ambata yasa ya d’ago ya kalleta amma bai ce mata komai ba sai ma alamar tafiya da yayi saboda yadda yarinyar ta takura mai, gashi ya fito ne dan ya huta amma da alamar yarinyar ba za ta ba shi damar yin hakan ba. Mik’ewa ya yi da niyyar tafiya, saboda ya k’osa ya bar gurin duba da yadda yarinya ta takura mai. Cikin sauri ta k’araso gurin shi tana pleading d’in shi cikin shagwa’ba tare da cewa "plss handsome ba ka fad’a min sunan ka ba? idan ba damuwa can i have your phone number". Ganin yadda yarinyar ke da rawar kai, da alama irin sangartacciya ce yasa yace "I by name Bregadier Umar, but you can call me Faruk" ya juya da niyar ci gaba da tafiya. Motar shi ya shiga ya hango ta a glass d’in motar shi tana kallon shi, ya rufe motar da niyar tafiya yaga tana nokin d’in k’ofar motar, kamar kar ya kula ta sai yaga gwara su rabu lafiya da ita. Bu’de glass d’in motar yayi yana cewa "do you need my help? Karkatar da kai tayi alamar shagwa’ba tana cewa "pls Umar help me with your phone number, i want us to be friend! Tak’aitaccen murmushi yayi saboda yadda tayi Magana. numban ya d’auka ya ba ta ya ja motar a guje. Waving d’in hannu yaga tana mai da murmushi a fuskar ta. Direct gidan su Fatima ya wuce saboda yadda yaji zuciyar shi na azalzalar shi akan yaje. Parking d’in motar shi yayi ya nufi cikin gidan. Ko da ya shiga falon ba kowa a ciki, dan haka ya nufi side d’in Yaya Khalil. Samun shi yayi yana operating d’in laptop da wanda ke nuni da wani aikin yake yi. Sallama yayi ya nemi kusa dashi yana cewa "Bros ana aiki ne?" Amsa masa sallama yayi yana fad’ad’a fara’ar shi "sannu da zuwa yaya Faruk, ina wani research ne saboda akwai wani presentation da zamu yi a school" cewar yaya Khalil. "that is good, karatu sai an yi hak’uri sannan za a ci ribar abun bare in karatu yazo k’arshe sai a hankali" yaya Faruk ya fad’a. Yaya Khalil ne ya amsa mai da cewa "Gaskiya kam, system d’in karatu ya canza, ga lecturers d’in ba kowannan su bane masu tausaya wa student". "Allah ya kawo mana mafita kawai" cewar yaya Faruk. Amsa mai yayi da cewa "Amin". Zancen makaranta suka ci gaba dayi na yadda karatu ya koma a yanzu da matsalolin da ake fuskanta. Suna cikin hirar ne ya kalli yaya Khalil yace "ina Teemah ne? naje main parlour ban gan ta ba, ko har yanzu fushi take yi ne? Nasan ta fad’a maka yadda muka yi da ita, tun da kaine friend d’in su". Murmushi yaya Khalil yayi ba tare da yace komai ba. "Je ka kira min ita, kace ta same ni a garden" yaya Faruk yayi commanding d’in shi. Fita yayi daga d’akin ya nufi garden yana mai jiran zuwan ta. Ko da yaya Khalil ya je side d’in ta bai tarar da ita ba, dan haka ya nufi side d’in Ummu. Samun ta yayi kwance a jikin Ummu suna hira, da fara’ar shi ya k’arasa d’akin yana cewa "Assalamu alaikum in shigo ko in koma? Dan yau naga Ummu ta ware Khalil d’in ta tana gurin Autan ta". Ummu ce ta amsa sallamar tana cewa "kai ma kasan auta dangware shalele ce, ta gaban goshi ce, sai kayi kamu k’afa a gurin ta ka samu fada" cewar Ummu. Ni kuwa dake faman yamutsa fuska saboda nasan yaya Khalil yau da tsokana yazo. Kallo na yayi da alamar tsokana yace "Fatima ki tashi kije garden, yaya Faruk ne yazo yake neman ki". D’aure fuska nayi kamar ba dani ake maganar ba saboda har yanzu wani irin haushin yaya Faruk nake ji. Ganin ban da alamar tashi yasa ya kalle ni yana cewa "Sister ba ki ji abin da nace bane! Turo baki nayi kana nace "gaskiya yaya Khalil am sorry amma ba za ni ba, neman me yake min da har zai ce in same shi a garden banda marin da yamin bai ishe shi ba shine zai k’ara dawo wa ya d’aura a inda ya tsaya"ido na fal da hawaye. Duk wannan tak’addamar da muka fara yi da yaya Khalil, Ummu ba tace komai ba sai yanzu ta kalle ni tace "Fatima ki tashi kije tun kan in ‘bata miki rai, tun da ke ba kya jin magana" Cikin ‘bacin rai na mik’e na fita saboda yadda naji raina ya k’ara ‘baci na yadda ake ji da yaya Faruk a family, shi yasa yake yin duk yadda yaso ba tare da shakka ba, haka zalika ba a ganin laifin shi. A raina na k’udurta cewa yau duk abin da yazo dashi ina dai dai dashi saboda yadda naga ya takura min, beside kowa yana bin bayan shi, ba mai ganin laifin shi. Garden na nufa inda na same shi zaune akan kujera yana facing d’in wanda yake shigowa. Ko da na k’arasa ciki-ciki na masa sallama na nemi guri na zauna ba tare da k’ara cewa uffan ba. Motsin da bakin shi yayi ne ya tabbatar min da cewa sallamar ya amsa. Ta’be baki na nayi a raina ina cewa "miskili Kenan, kafi mahaukaci ban haushi, nima zan nuna maka gidan ka tarar". Jin shirun yayi yawa yasa raina ya k’ara ‘baci fiye da d’azun saboda ni a gani na duk salon wani cin fuska ne da kuma hanyar da zai ‘kara sa min wani ‘bacin rai, in ma hakan yake nufi bazan bashi fuskar ganin hakan a tare da ni ba bare ya samu wata damar na min yadda yake so. (HMM READERS NASAN KUMA ZAKU SO KUJI DALILIN DA YASA YAYA FARUK YA KIRA FATIMAH, TO NIMA HAKAN TAKE A GURI NA. KU BI NI SANNU A HANKALI DAN JIN SAURAN LABARIN) [3/24, 22:28] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Na sadaukar da wannan shafin gareki ‘yar mutan Nijar* (Dr Maimuna Matar Abdoulaye) *Marubuciyar* (Latifa) *Ki yi yadda kike so da shafin*. *Allah ya k’ara baki k’arfin gwiwa na taimakon al’umma* *Question of the day* Wace mata ce ta tara (9) a cikin matan manzon Allah (s.a.w)? menene asalin sunan ta da nick name d’in ta? 27&28 Cikin tattausan lafazi da jan hankali ya kira suna na "Fatimah" "Na’am" na amsa mai a tak’aice da kuma d’aure fuska saboda yadda na k’osa na bar gurin dan ni ban ga amfanin kiran da yayi min ba. "Fatima! Kina jin haushin marin da na miki ko? a tunanin ki kamar na tsane ki ko? "Dago wa nayi na kalle shi dan kamar yasan abin da ke cikin zuciya ta kenan amma ban da halin furta hakan. Kallo na yayi yaci gaba da cewa "Nasan kina ganin kamar ina takura miki ko? kuma ina interfere a personal life d’in ki wanda tuntuni na gane ba kya son hakan daga gare ni, duk a tunanin ki na samun liberty da human right da yake rud’arki". Fatima! Ina yi miki haka ne saboda future d’in ki as i take you like my blood sister, d’aya kuke da Anisa a guri na, ba zan ba ku freedom nayin socialization a matsayin ku na mata ba, any social life da kike gani da bature ya fito da tsarin fundamental human right yana da disadvantage, saboda a ciki akwai inda aka yi stating d’in cewa ‘you have the right to participate in any social activities you like’ kin ga kenan akwai illah babba a ce an ba d’an adam damar yin duk abin da ya ga dama ba tare da an tsawatar mai ba wanda a addinin mu, Annabin mu, Muhammas (s.a.w) ya fad’akar damu da cewa " idan baka jin kunya, ka aikata abin da kake so", na d’auke ki ne kamar Anisa da zan iya hukunta wa ba tare da fargaba ba, hakan yasa nake d’aukan action a kan ku, so i will not give you the opportunity to do what you like". A ‘bangare na kuwa wannan dogon bayanin da yake yi ne ya ishe ni, ji nake yi kamar in tashi in bar mai gurin. Cikin cool voice ya ce "Fatima am sorry da na mare ki, nima ba da san raina na miki shi ba, ke ki ka jawo hakan saboda yadda kika min magana ne ya ‘bata min rai, da kika tambaye ni dalilin da yasa na yaga miki hoto" 'Wonder shall never end" na furta hakan a raina, ko a mafarki ban ta’ba tunanin yaya Faruk zai furta wata kalma mai suna ‘Sorry’ a bakin shi ba, bare ni da yake d’auka na teenager. Gaskiya ne da hausawa ke cewa "in da ranka zaka sha kallo". Dad’i naji a raina yau yaya Faruk ya k’ask’antar da kanshi a kaina yana neman yafiya ta, da nayi tunanin ko wani salon ya canza da zai musguna min ko akwai wani shiri da yake yi a kaina yasa na magantu akan dad’in da naji nay a nemi yafiya ta. Ci gaba yayi da cewa "Fatima! Zan iya jurar komai amma ban da raini da wulak’anci, da fatan zaki kiyaye saboda as from now, ina so ki d’auke ni kamar Khalil da zaki iya fad’a wa damuwar ki da kuma neman shawara a gurin shi". Rasa a wace duniyar nake, wai yaya Faruk ne yake min Magana in a polite way da kuma neman mu shirya. Wani tunani ne yazo min akan cewa akwai dalilin da yasa yake neman mu shirya dan ruwa ba ya tsami banza. "Teemah" ya kira suna na da sanyin murya. Ban samu damar amsawa ba saboda yau mamaki ne ya cika ni, bin shi kawai nake yi da kallo dan ina so in tabbatar da cewa a buge yake ko a hankalin shi yake fad’an maganganun nan, duk da ban ga wata alama na yasha wani abu ba, yana fad’ar maganganun nan ne da gaske. Kallon da yaga ina bin shi dashi ne yasa yayi tak’aitaccen murmushi yana cewa "are you surprise? ki cire mamakin da kike yi dan na nemi yafiyar ki". Zuciya ta ce ke ingiza ni akan kar in yadda da dad’in bakin da zai min, saboda yana da dalilin yin hakan. Ganin ba zan ce mai komai ba yasa yace "Teemah! ba ki ce komai ba, ko ba ki yafe min ba? Satar kallon shi nayi na yadda yake magana yana wani lumshe ido kamar yana magana da budurwar shi. Duba da yadda nake son in bar gurin, hakan yasa nace "na yafe maka yaya Faruk kuma ni b aka min laifi ba". Wani murmushin jin dad’i yayi wanda hakan ya bayyana a fuskar shi. Lura da nayi da bai da alamar bani damar tafiya yasa na k’ara d’aure fuska kamar zan yi kuka saboda yadda na gaji da zama a gurin, kuma ni har yau ba wai na huce da abin da ya min bane. Tambaya na yayi akan wane course na yi applying kuma wani school nayi za’ba? A tak’aice na bashi amsa da cewa "computer science nayi applying kuma kaduna Polythecnic ne first choice d’in da na sa". K’arfin gwiwa ya dinga bani akan harkar karatu kasancewar sa mai son muyi karatu. Alamar da ya gani a fuska ta dake nuna na gaji yasa yace "Teemah za ki iya koma wa ciki, in kin je kya gaishe min da Ummu kice ina sauri ne amma zan shigo gobe mu gaisa". Ai kamar jira nake yi, nayi saurin mik’ewa ba tare da ce komai ba, na fara tafiya, "ka ji da shi" nace a raina duba da yadda yake ta fito da sabon salo kala-kala wanda shi yasan manufar shi. Jiki na ne ya bani cewa kamar yaya Faruk kallo na yake yi, juyawa nayi naga kafe ni da ido kamar wanda yaga sabuwar halitta. Harararshi nayi na d’auke kaina ina mamakin kallon me yaya Faruk yake min? amsar da ban sani ba kenan. shi kuwa yaya Faruk yaga san da na harare shi, sai murmushi yayi kawai kamar bai ga abin da nayi ba, yanda na kalle shi ma dariya ma na bashi. Ko da na shiga main falo, ban nemi kowa ba, na nufi side d’ina. Gefen gado na samu na zauna ina tunanin da gaske ne yaya Faruk yau ni ya nemi yafiya ta har yana neman mu shirya? Abu d’aya na yadda dashi shine zamu dinga gaisawa irin ta ‘yan uwan taka ba wai dan ban hak’ura ba, sai dn in ja ma kaina mutunci, tun da shi abu k’adan yake jira ya ‘bata wa mutum. Yaya Khalil ne ya shigo ya zauna kusa dani yana cewa "Sister ashe kin dawo? ina ta jiran ki a side d’in Ummu". Ta’be baki nayi nace "yanzu na shigo, shi yaya Faruk d’in nan ya wani tsare ni da wani dogon bayani, sai da ya gama mari na sannan zai lalla’bo wai na yafe mai sannan wai in ina da shawara in zo wajen shi, ni nasan akwai dalilin da yasa ya nemi yafiya ta amma ba wai ra’ayin kan shi bane". girgiza kai kawai yaya Khalil yayi, ya d’aura da cewa "Fatima! ba ki gama sanin waye yaya Faruk bane shi yasa, he is a simple and nice person ga wanda ya kiyaye dokokin shi, yana da dad’in zama, duk da sometimes miskili ne kuma yana da fad’a amma ba shi da wata matsala, tun da har ya nemi yafiyan ki ya kamata ki yafe mai saboda akwai laifin da muke wa ubangijin mu kuma in mun nemi yafiyar shi ya yafe mana, kar ki zama mai k’ullatar mutum idan ya miki laifi kin ji sister? D’aga mai kai nayi nace "ni ban k’ullace shi ba, na yafe mai, amma ni ba zan kai mishi damuwata ko in nemi shawarar shi ba". Dariya yayi yace "is ok Fatima, zo mu tafi side d’ina akwai research d’in da nake yi, kya taya ni hira". Fita yayi daga d’akin yayin da nake bin shi a baya. Yaya Faruk kuwa da ya shiga mota, tsintar kanshi yayi cikin farin cikin da bai misaltuwa, lokaci yayi da zai jawo Fatima jikin shi, ta daina mishi kallon mai son kanshi da kuma mulki. Lokaci-lokaci zaka ga ya saki wani lallausan murmushi. Ko da ya isa gida, d’akin Anisa ya wuce, samun ta yayi da wani novel tana karanta wa. Kusa da ita yaje ya zauna yana cewa "Anisa! Amsa masa tayi da cewa "sannu da zuwa yaya". Bai damu da ya amsa mata ba illah cigaba yayi da cewa "gobe in Allah ya kaimu around five p.m ku shirya zan kai ku outing Asaa pramise ku d’an yawata ku ga gari tun da kun ce ina takura muku kamar wasu daddawar d’aka shine naga gara in daina matsa muku" ya k’arasa maganar da wasa. Ita kanta Anisa abin ya ba ta mamaki wai yau yaya Faruk ke cewa su shirya zai kai su outing". Ita tun jiya zuwa yau taga ya canza mata, ya dawo so cool wanda ba ta san dalilin canzawar shi ba. Ita dai fatan ta shine Allah yasa ya d’aure a haka saboda ita ma tana son zama da shi suna hira kamar yadda wa da k’anwar shi suke yi. Yalwatar murmushin ta tayi dan kar ya gane ko tana mamaki ne tare da cewa "yaya mun gode sosai". Mik’ewa yayi ba tare da yace komai ba ya bar d’akin, a ranshi kuwa yaji dad’in yadda ta nuna farin cikin ta, shi yasa ma ya d’au alk’awarin zai jawo su jikin shi saboda su sake dashi. Cikin zak’uwa ta d’au wayar ta, tayi dialling d’in number Fatima. Daga d’ayan ‘bangaren, Fatima ce tayi receiving tana cewa "Anisa Hi". ‘how a you doing? Anisa ta tambaye ta "normal Anisa" na ba ta amsa. Anisa ce ta d’aura da cewa "gobe ki shirya zamu je outing". Da murna ta nace "da gaske Sister, waye zai kai mu? na tambaye ta. "Da gaske nake yi, ke dai ki shirya, around five za mu biyo mu d’auke ki, kuma kinsan abin mamaki? Anisa ta tambaye ni. Amsa mata nayi da cewa "ya za ayi in sani" na ba ta amsa. "To yaya Faruk ne zai kai mu" Anisa ta fad’a da murnar ta. D’if nayi kamar an d’auke wutar nefa dan har ga Allah ban so a ce shi zai kai mu ba duk kuwa da yadda nake son fitar, nasan in nace ba zani ba Anisa ba za ta ji dad’i ba amma da ba inda zani. Shirun da Anisa taji ne yasa tace "Fatima kina ji na kuwa" "ok Anisa, Allah ya kaimu sai kun zo" na fad’a da kasalalliyar murya Sallama muka yi na aje wayar yayin da nake tunanin wai miye dalilin yaya Faruk na canza wa a lokaci d’aya? Ganin ba mai bani wannan amsar yasa na watsar da tunanin. Ita kuwa Anisa tana ajiye wayar kiran yaya Khalil ne ya shigo. Tsadadden murmushi tayi kana ta danna received. "Assalamu alaikum lovely Sister" yaya Khalil ya fad’a. Amsa masa tayi da "wa’alaikumus salam yaya Khalil". "ya kike? Yasu Momi da daddy? ya tambaye ta. "Su na lafiya" ta bashi amsa a gajarce. "Anisa kwana biyu ba kya nema na, gashi yaya Faruk ya hana ku yin chat da mun dinga communicating" cewar yaya Khalil. Cikin shagwa’ba tace "plss yaya Khalil ka sa baki, naga kai na hannun daman shine, may be ya yarda mu fara chat d’in'. Dariya yayi sannan yaci gaba da cewa "ba ruwa na, so kike yasa ni up & down, in zo ina faman yi wa k’afa ta gashi ko in sa a nemo min mai gyaran targad’e". Kukan wasa ta fara mai saboda tasan ita yake tsokana. Hak’uri ya fara ba ta yana dariya kana suka ci gaba da hirar su sannan suka ya mata sallama. [3/27, 10:16] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* *EDIT BY* *MRS MANSOOR* *Wannan shafin naku na baku shi ne kyauta* *Aisha* (Auta Mama) *Maman Walida* *Fatima Arkilla* *Fatima Muh’d* *Maman Baffa* *Aisa* *Ina tare daku na yadda kuke bin wannan novel d’in* *TUKWICI GAREKU* *Xarah Auwal* *Aisha* (Auta Mama) *Ina muku fatan alkhairi na amsar da kuka bayar daidai a Question of the day da wanda suka yi k’ok’arin ba da tasu amsar*. *Amsar Question of the day shine, Sunan ta Ramlat ‘yar Abu sufyan, nick name d’in ta* (Ummu Habiba) *kuma itace ta tara* (9) *a cikin matan manzon Allah (s.a.w)*. *Allah ya bamu ikon yin amfani da ilimin mu ta hanyar da ta dace ya kuma* *k’ara mana ilimi mai amfani*. *TUNATARWA*: ka/ki zamo mai hak’uri, amma kar ka/ki yadda hak’urin ya jawo maka raini. Ka/ki zamo mai kyauta, amma kar ka/ki yadda kyautar ta jawo maka riya. Ka/ki zamo mai soyayya, amma kada ka/ki so wani daidai soyayyarka/ki ga Allah da Manzon sa. 29&30 Washegari da misalin k’arfe hud’u da rabi, yaya Faruk ne cikin shigar shi na wani lallausan yadi mai kalar sky blue, kayan sun matuk’ar dacewa da kalar jikinsa. Ta d’akin shi ya shiga side d’in Momi kasancewar akwai k’ofa a d’akin shi da zai iya shiga ba tare da ya fito ba. Samun ta yayi tana kallon tashar Manara Tv a tauraron d’an adam. Guri ya samu ya zauna kusa da ita kana ya gaishe ta. Amsa masa tayi tana mai maida gaba d’aya hankalin ta gareshi. "Ina za ka ne Faruk? na ga alamar kamar fita za ka yi’ Momi ta tambaye shi. "Momi za mu d’an fita outing ne dasu Anisa, daga nan zamu biya mu d’auki Fatima" cewar yaya Faruk. Fara’ar ta ce ta k’aru saboda yau taji dad’in yadda Faruk zai kai su gurin shak’atawa wanda a da ko zama yayi hira dasu bai dame shi ba. "ko kai fa Faruk, gwara ka dinga jawo k’annen ka a jiki ko sa cire tsoron da suke ma ka" "ba na jin dad’in yadda suke tsoron ka" cewar Momi. Murmushi yayi kana ya d’aura da cewa "Momi yaran ne naga suna tashen girma, dole sai ana nuna musu hanya, amma insha Allahu zan yi k’ok’arin jawo su jiki na, nima yanzu ba na jin dad’in yadda ba sa sakewa dani". "Momi ina Anisa ne? nace ta shirya around this time, amma naga tana so ta ‘bata min lokaci kuma tasan bana son jira" "Tana ciki bari in kira ta a waya" Momi ta fad’a. Kiran ta tayi akan tayi sauri yaya Faruk na jiran ta. Momi ce ta kalli yaya Faruk cike da kulawa ta kira sunan shi. "Umar" Saurin d’agowa yayi ya kalle ta saboda yasan duk abin da za ta fad’a mai mahimmanci ne tun da kira shi da Asalin sunan sa. Da sanyin murya ya amsa da "Na’am Momi". Sai da tayi shiru kamar ba za ta yi magana ba kana ta d’aura da cewa "Faruk! cikar mutum ya samu a rayuwa shine ya sami abokiyar zama, abin da nake nufi mata, idan mutm ya samu mace ta gari to ya cika rabin addinin sa". Kallon ta yayi ganin yadda take maganar yasan abin na damun ta. Ci gaba tayi da cewa "Faruk duk tak’amar mutum na kud’i, mulki, kyau, ilimi, nasaba da duk wani abu da mutum ya ke tunk’aho da shi, mutane ba sa ganin sa da wannan mutuncin har sai ya samu abokiyar zama sannan duk wa’innan abubuwan da na lissafo kana dasu bare ace baka da halin yin aure ne, babu yarinyar da zaka nema tayi rejecting d’in ka in har ka fad’a mata kana son ta". "wanccan hutun da ka dawo, ni da Dadin ka mun tuntu’be ka akan maganar aure amma sai wasu excuse kake kawo mana wanda ban gamsu da su ba, idan kana da matsala ne ka fad’a min sai a samu mafita tun da naga kai abun bai damun ka" "idan kuma idon ka har yau bai gama za’ba maka macen da ta dace dakai ba, ni ka bani za’bi, zan nemo maka a cikin familin ku ko nawa ko a k’awaye na". Cikin ladabi yaya Faruk ya fara Magana "Momi Plss ku k’ara hak’uri, nima nasan abin na damun ku, insha Allah nan ba dad’e wa ba zan gabatar muku da yarinyar da nake so, matsalar itace har yau ban furta ma yarinyar ina son ta ba dan ba ta dad’e da gama SSCE d’in ta ba shi yasa". Ranta ne ya fara ‘baci da yadda Faruk yake son raina musu hankali, dan haka ta fara Magana cikin ‘bacin rai "Faruk wai wacece yarinyar nan, da in an maka magana sai kace ba ka fad’a ma ta ba, what do you mean by that, kana nufin muyi ta jiran ka har sai ran da kayi niyya sannan za ka fad’a mata mu kuma muna zuba maka ido, kana nufin ba ka da confidence d’in da zaka tunkari yarinyar ne ka fad’a mata or what? Zuba mishi ido tayi cikin ‘bacin rai dan tana son jin wace amsa zai ba ta. "Momi pls take patient, insha Allah everything will be alright" yaya Faruk yayi maganar in a polite way. Za ta fara mai fad’a ta ga Anisa ta fito daga d’akin ta, dan haka fasa fad’ar abin da za ta ce tayi. Anisa ce ta tunkaro in da suke cikin shigar wata doguwar riga mai kalar bak’a, ta yafa d’an k’aramin mayafin rigar, takalmin da tasa wani flat shoe ne kalar white yayin da ta rataya side bag a hannun ta kalar white, gaskiya shigar ta amshe ta. Kusa da Momi ta nemi guri ta zauna yayin da ta d’aura kan ta a jikin kafad’ar Momi. "my dear you look so cute" Momi ta fad’a. Anisa kuwa sai murmushi take yi jin Momi tace tayi kyau. Yaya Faruk kuwa sai watsa mata wani harara yake yin da ta sa shi ya jira ta, dan shi ba abin da ya tsana irin jira. "za ki tashi mu tafi ko sai kin gama shagwa’bar, since i was waiting for you but you waste my time, instead of you to apologise amma kin zauna za ki fara shagwa’ba". A ranta kuwa cewa tayi "mai hali ba ya barin halin sa, gwara in bashi hak’uri mu rabu lafiya kar in ja ma kaina wani hukuncin". A hankali ta furta "sorry yaya Faruk". Ko sauraren ta bai yi ba illa mik’ewa da yayi yana ce wa "Momi sai mun dawo". Anisa kuwa waving d’in hannun ta tayi tare da cewa "Momi sai mun dawo, me zan tawo miki dashi? "Anything that is special" abin da Momi ta ce Kenan tana dariya. Ko da suka shiga motar, hira suke yi jefi-jefi kasancewar sa ba mai yawan san Magana ba. Parking yayi a k’ofar gidan su Fatima ba tare da ya shiga da motar ciki ba kasancewar yanzu za su shiga su fito su tafi. Ko da suka shiga ciki, kallon Anisa yayi akan cewa taje ta ce wa Ftima ta fito su tafi, shi kuma ya nufi d’akin Ummu in yaso sai ta shigo ta gaida Ummu. Samu na tayi a gaban dressing mirror ina sa jan baki a lip d’ina. "haba Fatima! ya kamata ace by now kin shirya, kin san yaya Faruk ba ya son jira". Hararar wasa na mata kana nace "yanzu ai ina jin wasa nake yi". Dariya tayi tace "koma dai me kike yi kiyi sauri kisa kayan mu tafi". Mik’ewa nayi na d’akko doguwar riga kalar ta Anisa, sai dai tawa an mata ado da golden colour a jiki na sa, nayi rolling da mayafin rigar, na rataya side bag kalar golden, na d’akko bak’in low past na sa. "Wow"! gaskiya naga wannan wankan, Fatima ba ki ga kyan da kika yi ba" Anisa ta fad’a. "Duk kyan da nayi ai ban kai yake ba" na ce da ita. "hmm haka dai kika ce Fatima, amma ko ki yadda ni dai kin min kyau". Anisa ce ta kalli Fatima ta ce "Fatima yaya Khalil nan kuwa? Kallon ta nayi na kya’be baki sannan na fara dariya a lokaci d’aya. "yana nan, yau ko kin manta hanyar d’akin shi ne in miki jagora". "to miye abin dariya daga tambaya, ko na fad’i abin da bai dace bane" Anisa ta fad’a tana ta’be baki. "ba komai Anisa, ke da yayan ki, ai ba zai zama laifi ba dan kin tambaye shi, gani nayi kawai kamar akwai wata a k’asa". " ke kika sani"cewar Anisa. Tare muka fito daga d’aki na inda Anisa ta kalle ni tace "bari in lek’a gurin yaya Khalil mu gaisa sai in shigo gun Ummu mu gaisa". Mamaki ta bani saboda yanzun nan ta gama ce min yaya Faruk na jiran mu amma gashi za ta tafi gurin yaya Khalil. "ke ma dai kin san sauran in kika dad’e, kya same ni a d’akin Ummu zan je in yi mata sallama" na fad’a. San da na shiga d’akin, samun ta nayi da yaya Faruk suna hira. sallama nayi na samu guri a can gefe na zauna na d’ago na kalle shi ganin yadda yayi wani so cool. "yaya Faruk ina wuni" na fad’a. Shirun da naji bai amsa ba yasa na yi tunanin ko miskilancin ne ya motsa, d’aga idanun da zan yi naga ya kafe ni da idanun shi alamar yayi nisa a kallo na. Ummu ce ta kira Sunan sa "Faruk! Kamar wanda ya tashi daga bacci ya d’ago ya kalli Ummu. "Ummu Magana kike yi ne" ya tambaya. "Dama Fatima ce take gaishe ka" ta fad’a. K’ara kallon ta yayi ya basar kamar bashi bane yake min kallon k’urilla. "oh! lafiya, ban ji ba ne" ya amsa a gajarce. Ta'be baki na nayi alamar kai ka Sani. Mik’ewa yayi kana yace "Momi bari mu tafi sai mun dawo, yamma tayi". "Sai kun dawo Faruk" Ummu ta fad’a. Ummu ce ta kalle ni tace "Ki tashi ku tafi ma na kar yayi ta jira, wai ina Anisa ne? "Tana d’akin Yaya Khalil, ta je su gaisa". Sallama nayi wa Ummu, na fita daga d’akin. A can ‘bangaren yaya Khalil kuwa, Anisa ce tayi sallama ta same shi kwance akan gado. Amsawa yayi kana ya mik’e ya zauna yana murmushi ganin shigar da tayi yadda ta amshe ta. "yaya Khalil ina wuni, barci kake yi ne halan". Wani had’ad’d’en murmushi yayi ya kalle ta "Sister sai ina haka, you look so beauty". "Tanx Bros, zamu d’an fita outing ne da yaya Faruk". "kai Anisa, shine ba gayyata, lallai kun zama ‘yan gatan yaya Faruk, ya baku purnishment ya Kuma d’auke ku outing, dad’in ya muku yawa" ya fad’a da alamar tsokana. "kai yaya Khalil, tun da abin ‘yar tsokana ce bari in tafi, dama na shigo ne mu gaisa". Dariya ya fara yi yana cewa "Sorry Anisa, ni ma in na samu time zan shirya ma na outing amma ni da ke zamu je outing d’in". Saurin juyowa tayi tace "kaima kasan ba zan iya tafiya ni kad’ai ba sai da Fatima". " Dama tsokanar ki nake yi, ai tare zan kai ku, muje in taka miki". ""a ka bar shi yaya Khalil, d’akin Ummu zan shiga mu gaisa, ina zuwa direct nan na tawo". "Muje dai na gaisa da yaya Faruk d’in". D’akin Ummu ta shiga suka gaisa a gurguje kana ta fito suka jera da yaya Khalil. Ita kuwa Fatima tun da fito, tsaya wa tayi a gefen motar, yayin da take pressing d’in wayar ta. Yaya Faruk da ke zaune a mazaunin driver, cool music ya kunna inda sautin ke tashi a hankali. Ganin Anisa da yaya Khalil sun a tawo wa yasa ya k’ara tamke fuska saboda yadda ta ‘bata mishi rai. Yaya Khalil ne ya k’arasa ya mik’a masa hannu suka yi musabaha kana ya gaishe shi. Amsawa yayi ya juya yana watsa wa Anisa banzan kallo. Cikin ta ne ya kad’a saboda tasan abin da kallon shi yake nufi na zata fuskanci hukunci a gurin shi. "Anisa kin raina ni ko? a gida haka ki ka ‘bata min time sannan yanzu ma kin k’ara ‘bata min time saboda kin ga na fara sakar miki fuska ko? Cikin rawar murya ta fara Magana "ya hak’uri, na je mun gaisa da yaya Khalil ne". "you are stupid! Sai an miki Magana ki fara ba da hak’uri". Ya juya da kallon shi zuwa ‘bangaren yaya Khalil yana cewa "kai ma har da laifin ka, kasan ba na son jira shine ka ja ta da hira ko? "Ayi hak’uri babban yaya, mun amsa laifin mu". Murmushi kawai yayi ya shiga cikin motar ya kunna. Ni kuwa dake gefe kamar ban san dramar da ake yi ba, sai aikin danna waya kawai nake yi. Hon d’in da yayi ne yasa muka yi saurin shiga back seat muka zauna. Wani irin kallo ya watsa mana kana yace "Uban wa kuka mai da driver da za ku zauna a baya". Anisa ce ke faman ta’ba ni alamar in koma gaba amma nayi biris kamar ba dani take yi ba. Jin tsawar da ya daka mana ne yasa Anisa ta fito da sauri ta na k’ok’arin bud’e gidan gaba. Jan motar yayi da k’arfi alamar ranshi a ‘bace yake ya bar layin. [4/1, 13:38] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin naku ne, masoyan yaya Faruk da Fatima* *Ina mik’a gaisuwa ta gare ku*. *Question of the day* A wace surah ce Allah (s.w.t) yayi Magana akan bashi kuma Ayah ta nawa ce? 31&32 Tun da muka fara tafiya, na lura da yadda yaya Faruk ya saita madubun gaban shi yake kallo na akai-akai, tun abin ba ya damu na har na fara takura da kallon da yake min. Shirun da yayi yawa ne a motar yasa na cire tsoron da nake ji na fara jan Anisa da hira saboda bazan iya zaman kurame ba, jefi-jefi yaya Faruk yana sa bakin shi a cikin hirar. Ko da muka isa gurin, wani ke’bantaccen guri yaya Faruk ya samar mana muka zauna yayin da ya je ya siyo mana ice cream da snacks muka fara ci. Yadda mutane ke harkar gaban su, ba ruwan kowa da kowa yasa naji gurin ya burge ni. Wasu suna ciye-ciye, can gefe kuwa gurin hutawa ne da mutane ne ke zaune, yayin da wasu ke wajen swimming pool suna wanka, kowa dai da abin da yake yi. Kujerar da na zauna tana opposide d’in yaya Faruk, yawan kallon da yake mun ne yasa na fara tsarguwa da kallon saboda ni ban ga dalilin kallon ba. Tambayar kaina nayi da cewa "ko dai shigar da nayi ne ba ta dace ba? ko kuma ban yi kyau bane? na tambayi kaina, ko ma dai menene shi ya sani saboda tun a mota na lura da yadda ya tsure ni da kallo a mota". Yaya Faruk ne ya fara da cewa "yau dai gashi na kawo ku outing, kun fita daga cikin layin wanda kuka ce ana takura ma wa ko? Shiru muka yi ba wanda ya amsa mishi. Ci gaba yayi da cewa "I know you will enjoy this place shi yasa na kawo ku nan, so in mun gama refreshing za ku iya zagayawa, ba na son hayaniya da mun zagaya ni da ku". A raina nace "ba ma buk’ata, dan in ka bimu takura mana za kayi". Mik’ewa muka yi muka fara zagaya gurin kana muka ya da zango a kujerun da aka ajiye da table a wajen swimming pool d’in dan hutawa ko refreshing, a gurin akwai kuma rest chair da aka ajiye musamman dan hutawa kafin ka fara wanka ko in ka gama wanka. Zama muka yi muna kallon yadda mutane ke wanka a ciki. Yaya Faruk yana can gefe kwance akan wata kujera ta hutawa yana sipping d’in hollandia, yana kallon duk abin da ke gudana a gurin. Wani handsome guy ne ya zo ya zauna a d’aya daga cikin kujerun da muke zaune ya mana sallama. Amsa masa muka yi muka d’auke kan mu. "Sannun ku da hutawa ‘yan mata" guy d’in ya fad’a. "yawwa sannun ka" Anisa ta amsa a tak’aice. "Suna na Aliyu, plsss in ba damuwa zan iya sanin sunan ku". Wannan karan ma ban yi Magana ba illah juyawa nayi ina kallon wani side kamar ba da mu yake yi ba. Anisa ce ta bashi amsa da cewa "ni suna na Anisa, ita kuma sunan ta Fatimah". "wow! Nice name, Anisa in ba damuwa ina son in yi Magana da Fatima, ina neman alfarmar ki na five min zuwa ten in ba damuwa". Murmushi tayi tace "ba matsala bari in baku guri". Mik’ewa tayi tace "Fatima bari in je can grass carpet d’in, kya same ni a can". Ni kuwa in ban da hararar ta ba abin da nake yi saboda yadda ta wani zauna tana bashi amsa. "Fatima! kamar yadda na fad’a muku ne, suna na Aliyu amma zaki iya ce min Haidar, tun da na zo gurin nan na ganki na ji na kamu da son ki, ina rok’on alfarma ki ba ni guri a zuciyar ki ko na samu shiga". Sake d’agowa nayi na kalleshi, ba laifi guy d’in bai da wani aibu amma a loakci d’aya na lura da yanayin shi kamar yana tashen samartaka ne da kud’i. A estimating ba zai wuce ishirin da takwas ba, a shekarun haihuwa. Murmushi nayi kana nace "Haidar na gode da son da kake min, but am sorry ni ba yanzu zan fara soyayya ba, karatu zan yi saboda ban dad’e da kammala Secondary school d’ina ba, kuma a gida ma ba za a bar ni ba" Lokaci d’aya fuskar shi ta nuna ya shiga cikin damuwa da abin da nace mai dan haka yace "duk da kin bani uzurin ki Fatima amma ina ganin wannan ba hujjar da zaki ce ba za kiyi accepting d’ina ba, ni zan iya jiranki ki fara high institution d’in". A raina kuwa cewa nayi "wannan daga gani zai yi naci, gwara in lalla’ba shi mu rabu lafiya". "kayi hak’uri Haidar, ba na son in yi deceiving d’in ka, shi yasa na fito na fad’a maka gaskiya, ina maka addu’ar Allah ya baka mai son ka da gaskiya". Yalwata murmushin shi yayi kana yace "gaskiya Fatima naji dad’in addu’ar da kika min duk da na gane kora da hali kike min, hakan yasa na gane ba k’aramin rashi nayi ba, duk da ba anshi tayin soyayya ta ba saboda na gano akwai wata baiwa da Allah ya miki, in ba damuwa zan iya samun phone number d’in ki mu dinga gaisawa tun da ba a bani damar nuna kalar soyayya ta gare ki ba, yanzu sai naje na lallashi zuciya ta, na ba ta hak’uri tun da an dasa mata ciwo". Ganin mafita d’aya ce a gare ni a gurin Haidar shine in bashi numba ta ko na samu ya rabu dani, dan haka na fad’a mishi numba ta. Kallo na yayi ya rausayar da kai yace "Fatima ki bani aron wayar ki in sa miki numba ta, kar in kira ki dinga ce wa waye? Ban gane mai Magana ba". Murmushi nayi saboda a yadda na karance shi yana da ban dariya. Waya ta na mik’a mai ba tare da nace komai ba. Duk wannan abun da yake faruwa yaya Faruk na kallon mu har zuwa san da na mik’a ma Haidar waya ta. Takun tafiya naji a kusa da mu, shi yasa ni d’aga kai dan ganin waye. Ido na ne ya had’u da na yaya Faruk wanda tsantsan ‘bacin rai ne kwance a fuskar shi. Ni in ba ido na yake min gizo ba, har wani ja na ga fuskar shi tayi, abun ka ga farin mutum, idon nan nashi ya kad’a ya koma kalar ja, jijiyoyin kanshi ko duk sun tashi. Wani irin rawa jiki na yakama yi da bugawa da k’irji na da yake yi saboda tsoron da ya kama ni a lokaci d’aya. "Wayyo! Naga ta kaina" na fad’i haka a raina. Sai faman zare ido nake yi kamar wacce tayi wa sarki k’arya. Ciikin izza ya amshi waya ta dake hannun Haidar ya maka ta a k’asa. Tun san da yaya Faruk ya fasa min waya naji wani k’unci ya ziyarce ni da kuma tsanar sa da naji ta ka’ra shiga min a cikin zuciya, in ban da zalunci akan me zai fasa min waya, ko yana tak’amar ba ni da k’arfin rama wa shi yasa ya aikata hakan ko kuma duk cikin k’iyayyar da yake min ce? me nayi wa yaya Faruk da yake min haka? tambayar da nake ta yi wa kaina kenan. Haidar kuwa bin shi yayi da kallo saboda ganin k’arfin halin wannan mutumin da bai san waye ba. "Malam akan me za ka amshi waya a hannu na sannan ka fasa ba tare da wani dalili ba, hasalima ni ba sanin ka nayi ba". Kallon rainin wayau ya mishi sannan yace "ba sai ka san ko ni waye ba da na aikata hakan, na isa ne shi yasa na aikata hakan dan nasan ba abin da zai faru". Haidar shima ran shi ne ya ‘baci da abin da wannan mutumin ya mai saboda rainin hankali "kai waye? me kake ji dashi da za ka aikata haka sannan kana fad’a wa mutum maganar da ka gadama". Da ‘bacin rai, yaya Fruk ya fara magana "gentle man you have to control your tongue, if not, you will face da consequences, sanin ni waye ba zai maka amfani ba saboda haka ka kula, lastly abin da zance maka shine ka fita hanyar k’anwa ta dan ba da irin kai ta dace ba saboda kaima naga har yau baka gama mallakar hankalin kan ka ba bare ka iya kula da wata ko ka bata caring irin na lovers, bayan haka ma she is a teenager, bazan bari a ‘bata mata tarbiyya ba, wannan shine gargad’in da zan maka in ka ji kenan". Wannan maganar da yaya Faruk yayi, shi ya ba Haidar amsar tambayar shi saboda ya gano suna da alak’a da Fatima. In a cool sound Haidar yace "Am sorry! Ban san cewa k’anwar ka bace kuma ni tsakani da Allah na ji ina son Fatima, kuma ni ba da niyyar cutar da ita nayi ba ko in yadaure ta ba kamar yadda kake nufi, sai anjiman ku". Bai jira jin amsar da yaya Faruk zai bashi ba ya bar gurin cikin fushi. Juyowa yayi cikin fushi ya fara Magana. "Fatima! ki kiyaye ni, kar ki bari in nuna miki true colours d’ina, ba za ki ji dad’i na ba, yanzu abin naki ya wuce na yin chat da hoto da mazan ‘yan class ya koma kin fara kula samari at your small age? Ana so a gina muku future d’in ku amma ke ba kya ganin haka, kina amfani da yadda rayuwa take tafiya wanda hakan matsala ce, let me warn you, duk san da na sake ganin kin kula wani, hmmm zaki fuskanci hukunci mai tsanani a guri na, ki tashi mu tafi gida". Duk wannan maganar da yake fad’a, kaina a sunkuye yake ina faman zubar da k’walla na takaici da bak’in ciki a lokaci d’aya. Wata tsawa da ya daka min ita tasa ni tashi ban yi niyya ba saboda har cikin kaina naji ta. Anisa kuwa dake kwance akan grass carpet can d’an nesa damu tana pressing d’in wayar, tun san da yaya Faruk ya baro gurin da yake ya k’araso gurin mu har san da ya fasa min wayar hankalin ta ya dawo kan mu. Abin da yake mata yawo a ranta shine "mai yasa yaya Faruk ya fasa ma Fatima waya kuma da alama ranshi ya matuk’ar ‘baci, ko ma dai menene ita a ganin ta wannan bai kai laifin da zai sa ya fasa mata waya duk da ita ma ya ta’ba fasa mata waya akan ya kama ta tana yin chat". Zuciyar ta ce ta ba ta amsa da cewa "yaya Faruk yayi hakan ne don ba yaso mu fara kula samari a yanzu wanda har yanzu kallon yara yake mana, yana so yaga mun maida hankalin mu a kan karatu". Jiki a sanyaye na mik’e na fara tafiya kamar mai fama da rashin lafiya saboda yadda a lokaci d’aya naji jiki na ya min duk a sanadin ‘bacin rai. Anisa da ba ta ji dad’in abin da ya faru ba yasa ta rasa mai za tace dan yadda Fatima ta hau dokin zuciya ba lallai ta saurare ta ba. A wani bakery ya tsaya ya siyan musu ice cream da snacks. Ko da muka shiga cikin motar ba wanda yake da k’arfin yin Magana saboda yadda ran mu yake a ‘bace. Jin shirun yayi yawa ne yasa ya kunna k’ira’ar sheikh Al Gamidi cikin suratul Rahaman, bin surar yake yi yana jin zuciyar shi na sa mun sauk’i. Gaskiya ne, duk wanda ya rik’e Alk’ur’ani, zai saman masa waraka da mafita a dukkan lamuran shi. Parking yayi a k’ofar gidan mu ba tare da ya shiga ciki ba. Fitowa nayi ba tare da nace komai ba, ko Anisa ban yi wa sallama ba, har yanzu abin da yaya Faruk ya min ya tsaya min a rai. Bayan fita na daga mota ya kalli Anisa wacce ta rasa abin da yake mata dad’i yace "Anisa d’au ledan nan ki kai ma Fatima, ki yi ma Ummu sallama sai ki fito mu tafi". Jiki a sanyaye ta fito daga motan ta nufi cikin gidan. Ko da ta shiga cikin main parlour, ba ta same ni a ciki ba, direct d’aki na ta wuce. Samu na tayi a zaune akan gado ina wani irin kuka mai ban tausayi. Anisa cikin sanyin jiki ta zo ta zauna kusa dani ta dafa kafad’a ta ta fara da cewa "Fatima! me yasa kike kuka alhalin kin san halin yaya Faruk, ko ni ban ji dad’in yadda ya fasa miki waya ba, though shi a ganin shi wannan ce hanyar da zai yi abiding d’in mu da kar mu kula samari". Cikin kuka na fara cewa "Anisa na gaji da abin da yaya Faruk yake min, tun ina iya daure wa har takai zuciya ta na ingiza ni akan in yi fito na fito dashi ko na samu freedom". "why? me yasa yake son takura min? me yasa yake interfere a cikin personal life d’ina? me yasa zai yaga min hoton da na d’auka da ‘yan class d’in mu yanzu gashi ya fasa min waya, me yasa ya takura min a cikin rayuwa ta… na k’arashe maganar. Anisa tace "wani hoto kuma ya yaga? "hoton mu ya yaga wanda muka d’auka da mazan class d’in mu". Anisa kuwa ba kalar tunanin da bai zo ma ta ba a ranta, a k’arshe dai ta dasa alamar tambayoyi akan abin da yasa duk Yaya Faruk yake aikata hakan. Kuka na ci gaba da yi ina k’ara jin haushin yaya Faruk a raina. Anisa kuwa in ban da hak’uri ba abin da take bani, k’arshe ma rok’o na tayi akan kar in fad’a ma su Ummu da Abbu, ita za ta fad’a wa Momi abin da ya faru kuma tasan za ta d’auki mataki akai sannan za ta sa yaya Faruk ya siyan min wata sabuwar waya. Yaya Khalil ne ya shigo cikin d’akin kana yace "Anisa kije yaya Faruk na jiran ki, ina tsarabar outing? Zaro ido tayi ta mik’e saboda ita ta manta yaya Faruk na jiran ta, yanda yake cikin ‘bacin ran nan, zai iya huce wa akan ta. Narai-narai tayi da ido alamar za tayi kuka. Yaya Khalil ne ya kalle ta da mamaki yace "ya akayi ne naga kamar za kiyi kuka? " tsoro nake ji yaya Khalil kar yaya Faruk ya ta’ba ni, in ya kama ni sai na gane kure na". Yanda tayi maganar yasa shi darawa, hango Fatima yayi sai faman shasshek’ar kuka take yi. Kallon Anisa yayi da alamar tambaya yace "Anisa me ya samu auta naga tana faman kuka". "ita da yaya Faruk ne" ta bashi amsa. Ta’be baki yayi yace "Auta ta yaya Faruk Kenan, ai fad’a a shirya". Anisa ce ta kalle ni tace "Plsss Fatima ki daina kuka, yaci ace kin saba da halin shi, ni zan tafi, sai na sake ‘bullo wa". Ganin ko amsa mata ban yi ba yasa ta gane har yanzu ina kan dokin zuciya, dan haka tayi murmushi ta bar d’akin. D’akin Ummu ta shiga ta mata sallama ta fito yayin da Yaya Khalil ya raka ta bakin gate, ta nufi inda Yaya Faruk yayi parking d'in mortar shi. *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin tukwici ne gare ku* *‘yan Facebook*, *mazan ku da Matan ku* *Ina yin ku sosai na yadda kuke son wannan novel d’in*. *KUN YI BAJINTA* *Meeynah* *Salmah* *Autan mama* (Aisha matar Abdul) *Kune kuka bayar da amsar daidai*. *Da sauran wad’an da suka yi k’ok’arin amsa tambayar Question of the day amsar da suka bayar akan wace Surah ce a cikin Alkur’ani aka yi Magana akan bashi kuma Ayah ta nawa ce, amsar itace Suratul Baqara a cikin Ayah ta 282, wasu sunyi k’ok’arin cewa Suratul Baqara*. *Allah ya albarkaci ilimin mu baki d’aya*. *K’ORAFI* *Na samu k’orafin ku da dama, wasu suna k’orafin in k’ara yawan typing, wasu kuma suna k’orafin ban a posting da wuri*. *Na gode da k’orafin ku kuma insha Allahu zan duba, amma yanayin rashin time yasa hakan ke faruwa da kuma wasu uzuri da za su iya tasowa*. *Da fatan za a min uzuri*. *Na gode*.🤝🏽🤝🏽 *TUNATARWA* Ka/ki zamo mai adalci, amma kar ka/ki ce sai ka iya wa kowa. Ka/ki zamo me neman na kai, amma ka da yakai ka/ki ga neman haram. Ka/ki zamo mai son iyalin ka/ki amma kada ka/ki yarda ka/ki shagala. 33&34 Ko da ta shiga motar, tarar da yaya Faruk tayi ya kifa kansa akan sitiyarin mota, sun d’au kusa minti biyar a haka kamar bai san da shigowar ta ba. Anisa kuwa in ban da addu’a ba abin da take yi saboda tasan me k’watar ta a gurin yaya Faruk sai Allah, tasan tun a gida take ‘bata mishi lokaci gashi yanzu ma yace ta shiga ta kai ma Fatima ledar shopping d’in da ya musu gashi ta da’de. D’ago kai yayi ya mata wani banzan kallo sannan ya d’aura da cewa 'uban me kika zauna yi a ciki bayan kin san ina jiran ki, ga driver kin samu ko? put in your mind sai kin fuskanci hukunci". "plsss yaya Faruk kayi hak’uri! Wlh ban je da niyar zama ba, Fatima na gani tana kuka shine na tsaya ba ta hak’uri". Jikin shi ne yayi sanyi saboda yasan shine silar da yasa Fatima kuka kuma shima yana ji a jikin sa bai kyauta wa Fatima ba amma sai ya dake ya fara Magana cikin fad’a da cewa "amma da kika tsaya ba ta hak’urin ina fatan kin had’a da goya ta, saboda ina ganin za ta fi jin lallashin da kike mata, ni kuma da kika maida d’an iska shine kika shanya ni ko? Ita dai ba ta k’ara ce mai komai ba illa sauraran fad’an da yake ta jero mata, fatan ta su isa gida ta fad’a wa Momi duk abin da ya faru, dan gaskiya abin ya tsaya mata a rai. A guje ya ja motar kamar wanda zai bar garin. parking d’in motar shi yayi a parking space, tsoron fito wa take yi kar yace ba ta jira ya fara fito wa ba. Tsawar da ya daka mata da cewa "uban me kika tsaya yi a ciki? ko sai na zo na fito dake ne! saboda rikicewa ba ta tsaya d’aukar ledar ba ta fito ta kwasa da gudu kamar wanda aka biyo ko murfin motar ba ta rufe ba. Gajeran tsaki yayi a lokacin da ya ga ta bar ledan a motar, ya d’auka ya rufe motar kana ya nufi side d’in shi ta k’ofar baya. Tana shiga cikin falon ta dinga sauke numfashi, tarad da Momi tayi zaune a falo. Momi ce ta kalle ta tare da cewa "ke kuma lafiya zaki shigo a guje kamar wanda aka biyo". Cikin basar da zance ta amsa da "ba komai Momi, sannu da gida". "yau an sha yawo kenan Anisa" cewar Momi. Kusa da ita taje ta zauna tana bata labarin gurin da suka je. Wayar tace tayi k’ara alamar kira ya shigo. Ganin sunan yaya Faruk yasa ta d’auke wuta kamar ba ita ke ba da labari ba. "ki same ni a d’aki na" abin da yaya Faruk yace kenan ya katse wayar. Cikin sanyin jiki ta mik’e tana cewa Momi "bari in je d’akin yaya Faruk ya na kira na". "Ok" momi ta amsa a gajarce. Samun shi tayi zaune akan rest chair, yana sanye da vest da three quarter. Sallama tayi ta shiga d’akin, ta nemi guri ta zauna. Amsa mata sallamar yayi kamar ba ya so. Taso wa yayi ya d’au d’an k’aramin cup dake ajiye akan fridge d’in shi ya kama hannun ta ba tare da yayi mata Magana ba. Bin shi kawai take yi ba tare da tasan in da za su je ba. K’ofar baya ya bud’e ya nufi wajen flowers d’in dake cikin gidan. Tambaya take ma kan ta "me za su yi anan da taga ya d’akko kofi ya kawo ta nan". Kallon ta yayi cikin d’aurewar fuska yace "je ki d’akko waccen bucket d’in na wajen tap d’in can". "dakko wa tayi tare da cewa "gashi yaya Faruk". Mik’a mata kofin yayi yace "wannan kofin da na baki shi zaki yi amfani ki cika min wannan bucket d’in, wannan shine purnishment d’in ki for today na ‘bata min time da kika yi". Saurin kallon k’aton bucket d’in tayi da kuma d’an k’aramin kofin da ke hannun ta, da ratar in da tap d’in yake da wajen bucket d’in. Tunanin ya za tayi ta cika wannan bucket d’in take yi da d’an k’aramin kofin nan? "za ki fara ko sai jikin ki ya fad’a miki, ba na son ‘bata lokaci". Hawaye ne ya fara ambaliya a fuskar ta. Kallon ta yayi yace "will u wipe your tears & start your work". Tap d’in ta nufa ta fara tarawa kana tazo ta juye a cikin wannan bucket d’in. Kujera ya samu ya zauna ya d’aura k’afa d’aya akan d’aya yana sauraren cool music a wayar shi. Haka Anisa ta dinga d’iban ruwa a cup tana juyewa a wannan bucket d’in. Momi kuwa da taji shirun yayi yawa yasa ta mik’e ta nufi side d’in yaya Faruk. Ko da ta shiga ba ta tarad dasu a ciki ba. Momi ce ta tambayi kan ta da cewa "ina suka tafi kuma". Ta glass window ta hango su a gurin flowers. Ta k’ofar d’akin yaya Faruk ta fito ba tare da ta koma side d’in ta ba. Anisa wacce saboda jeka ka dawo d’in da take yi yasa taji k’afar ta rik’e mata gashi ko rabin bucket d’in ba ta cika ba. Hawaye ne ke ta zuba a idon ta amma yaya Faruk bai da alamar tausaya mata, sai ma rausayar da kanshi da yake yi alamar yana jin dad’in music d’in da yasa. Momi ce ta k’araso da sauri tana cewa "me zan gani Faruk! me ta maka da zaka ba ta such kind of purnishment irin wannan daga dawowar ta". Cikin sanyi yayi magana "Sorry Mom, laifi ta min shi yasa". Anisa kuwa in ban da filling d’in bucket d’in ba abin da take yi, taji dad’i da Allah ya kawo Momi a lokacin, ko ba komai tasan yanzu zai kyale ta. Momi ta kalli Anisa cikin tausayawa tace "Anisa stop that work! Anisa da kamar jira take yi tayi saurin ajiye kofin ta tawo gurin Momi. Juyawa tayi ta kalli yaya Faruk cikin fad’a taci gaba da cewa "Faruk! am warning you amma ba ka ji, ka daina ba su irin wannan purnishment d’in saboda kasancewar su mata amma ka k’i ji, A wani dalilin za ka sa ta cika ruwa a wannan big bucket d’in da ‘dan k’aramin cup d’in, bayan kasan kan ta cika sai ta wahala, to ni ‘ya ta ba ta iya aikin wahala ba, ka kiyaye ni Faruk in ba haka ba zan sa’ba maka". "Sorry Mom" abin da yace kenan. A lokaci d’aya yana jin ‘bacin rai na yadda Momi za ta mishi fad’a a gaban k’anwar shi, salon ta raina shi. Hannun Anisa kawai Momi ta kama suka nufi side d’in su. A can ‘bangaren Fatima kuwa, yaya Khalil ne ya kalli Fatima wacce ke faman kuka yace "Wai Fatima me yaya Faruk ya miki ne haka da kike faman wannan kukan'. Fatima cikin shasshek’ar kuka tace "plss yaya Khalil, help me ask yaya Faruk what have i done to him da yake min irin wannan hukuncin? "tell me abin da ya miki" ya fad’a cikin hasala. Zayyane masa duk abin da ya faru tayi a outing d’in da suka fita. Shiru yayi yana kallon ta sannan yace "Fatima ba wai yaya Faruk bai yi laifi bane da ya fasa miki waya, ina so ki sani shi yaya Faruk matuk’ar ka kiyaye dokikin shi za ku zauna lafiya, yana son ci gaban ku na son ku ci gaba da ilimi shi yasa yake lura da takun ku, ku ke ganin kamar ya takura muku ne, tun da ya nuna ba ya son ku fara soyayya, ya kamata ace kin kiyaye dokokin". Kallon shi nayi da mamaki nace "are my not big da ba zan kula saurayi ba? infact ni ba ni na kira shi ba, after all ni ban yi accepting d’in shi ba, yaya Khalil mai yasa da yazo bai tambaye ni ba, sai ma fasa min waya da yayi". "Fatima! ya kamata ki d’auki yaya Faruk a matsayin wa a gare ki kamar yadda ni da yaya Aminu muke a gurin ki, duk abin da zai miki ki barshi a matsayin ke k’anwar shi ce kamar Anisa, kin fahimce ni ko? D’aga mishi kai tayi alamar eh. 'yawwa Auta, share hawayen ki, ni zan siyan miki irin taki ta da". Goge hawaye na nayi ina murmushi, sai naji na samu relief akan abin da ya faru. *************************** Momi kuwa direct d’akinta ta tafi da Anisa tana ci gaba da fad’a. Anisa wacce ta kwanta a jikin Momi sai faman ajiyar zuciya take sauke wa kamar wacce tayi gudu. "Mtsww" Momi ta ja wani gajeren tsaki. "Wai me kika mai ne ya baki wannan purnishment d’in? Momi ta tambaye ta. "Akan yace in kai wa Fatima ledar shopping d’in da ya mana cikin gida, shine da na shiga sai na tarar da ita tana kuka, ni kuma na tsaya ba ta hakk’uri ban fito da wuri ba, da na shiga mota shine yace sai ya bani purnishment" Anisa ta fad’a cikin shagwa’ba. "To ita Fatima me aka mata take kuka" Momi ta tambaya. Nan Anisa ta kwashe duk abin da ya faru ta fad’a wa Momi. Momi wanda ranta ya gama ‘baci da labarin da Anisa ta gama ba ta tace 'Akan wani dalili zai yaga mata hotuna ya kuma fasa mata waya saboda ta kula saurayi? Ni kaina na gaji da irin wannan abin da Faruk yake yi amma zanyi maganin shi, dole ne ya fito da mata yayi aure saboda ina ganin har da rashin aure yake sa shi yin wannan abubuwan, in ba haka ba zai gamu da ‘bacin rai na". "ina zuwa" abin da Momi tace wa Anisa kenan ta bar d’akin. Shi kuwa Faruk tun da ya shiga d’aki ya rasa me ke masa dad’i. "me yasa ban tsaya ta min bayani ba na fasa ma ta waya? Why? me yasa zuciya ta take ingiza ni akan d’aukan mataki akan ta? bai kamata ina taking action cikin zafin rai ba dan ba abin da zai jawo sai ‘bacin rai". Yana cikin wannan tunanin Momi ta shigo cikin ‘bacin rai. Kallon shi tayi ta kira sunan sa "Faruk" Saita kansa yayi ya amsa "Na’am Momi". "Faruk akan wani dalili ka yaga ma su Fatima hotunan graduation alhalin kasan na tarihi ne, hotunan ne suka d’auka bai dace ba ko ganin ra’ayin kanka ne yasa ka yaga? Sannan duk wannan bai ishe ka ba shine sai ka fasa mata waya akan ta had’u da wani a inda kuka je? ina so ka fad’a min dalilin ka na yin haka?. zuciyar shi ce ke umartar shi da ya fad’a mata dalilin shi nayin hakan amma yana ganin da sauran time, sabida haka yace "Momi kiyi hak’uri, yarinyar ce naga tana da rawar kai". "kid’an kai take dashi ba rawar kai ba, ka fita hanya ta Faruk, akan irin hukuncin da kake musu zan sa’ba maka, mata kowa yasan lalla’ba su ake yi, ni ba ina nufin kar ka hukunta su ba ne in suka yi laifi, ya zamana akwai lokacin hukunci da kuma wasa". Ci gaba yayi da cewa "yanzu abin da nake so dakai shine ka siya mata wata sabuwar wayar ka kai mata, sannan maganar mu ta d’azun akan maganar auren ka ba wai na manta bane, in Dadin ka yaga zai iya zira maka ido akan rashin auren ka to ni a zan iya ba, na baka nan da d’an wani lokaci kafin ka koma aiki in ba haka ba zan baka mamaki in za’ba maka". Ba ta jira jin cewar shi ba ta fita daga d’akin. Kan shi ya dafa wanda yake ji ya mishi nauyi. Kwantawa yayi akan gado yana kallan sama wanda ke nuni da ya fad’a tunani. "ya zama dole ya samar wa kanshi mafita a ‘bangare biyu, yanzu gashi Momi ta taso shi gaba akan zancen yarinyar da yake so bayan har yau bai furta wa yarinyar yana son ta ba, yanzu ya zai yi? Ya zamar mishi dole ya d’auki za’bi a d’aya a cikin biyu, ko dai ya fad’a ma yarinyar ko kuma Momi ta za’ba mishi yarinyar da ta mata kamar yadda take furta wa. Yau kwana biyu kenan rabon yaya Faruk da gidan mu, sai hakan ya min dad’i. Da yammaci ina zaune a wani ke’battaccen guri da akayi shi dan hutawa, inda aka ajiye kujeru da ta table, yayin da aka yi wata ‘yar bukka a sama. Pineapple-cocunut drinks ne a gaba na ina sipping a lokaci d’aya ina pressing d’in I-pad d’in yaya Khalil da ke hannu na. Jin shigowar mota yasa na d’aga kai na kalla dan ganin wanda zai shigo.. Ganin Motar yaya Faruk ce yasa na kau da kaina na ci gaba da abin da nake yi. Parking d’in motar shi yayi a parking space. Hango ni yayi a gurin shak’atawa yasa ya nufo gurin. Guri na naga ya na tawowa rike da wata leda a hannun shi, tamke fuska nayi dan ban san kuma da mai yazo ba. Sallama ya min ya nemi d’aya daga cikin kujerun ya zauna. In ban da amsa sallama dole ce da ban ga abin da zai sa ni in amsa mishi sallamar ba. Ciki-ciki na amsa sallamar kamar ba na so kana na gaishe shi wanda ko ni nasan ba lallai bane in ya ji gaisuwar da na mishi. Ga mamaki na sai naji ya amsa da "lfy lau Fatima, ya hak’uri da ni? A raina kuwa cewa nayi "ji wani tambayar rainin wayau da yake min, hak’uri da kai sai dole dan ba yadda mutum zai yi dakai ne, amma da sai na rama abin da kake min". Sanin ba zan bashi amsa ba yasa yayi murmushi. "Fatima" ya kira suna na a hankali. D’ago wa nayi na kalle shi ba tare da na amsa ba. Ci gaba yayi da cewa "nasan kina jin haushin abin da na miki ran da muka fita ko? kina d’auka na a mara adalci wanda yake k’ok’arin matsa miki, a guri na ba haka na d’auka ba, du kina miki haka ne ke da Anisa dan ganin yadda yanzu rayuwa ta koma, nasan nan gaba za ku gane hakan, za kuma kisan dalilin da yasa nake miki haka, anyway ga wata sabuwar waya na kawo miki, ina fatan za ki min uzuri akan wayar ki da na fasa". Mik’o min wayar yayi na k’i amsa saboda yadda zuciya ta ke tuno min san da ya fasa min d’ayar wayar inda a gani na ko zai yi amfani da wannan damar ne ya samu hanyar k’ara cusguna min. Wata zuciyar kuwa ingiza ni take yi akan in amsa tun da shi ya fasa min wayar. "Fatima, ba ki da wani za’bi da yafi ki amshi wayar nan, dan ba zan koma da ita ba" abin da yaya Faruk yace kenan. Ba ni da za’bi da ya wuce in amshi wayar dan nasan kafiyar shi. "Na gode" na furta mai a gajarce. "No need to thank me Teemah, komai zan iya miki ke da Anisa saboda ku k’anne na ne". "kamar gaske" abin da nace a raina kenan. Jin kiran sallar magrib yasa yaya Faruk ya mik’e da niyyar tafiya masallaci, ni kuma na koma cikin gida. Ko da na shiga d’aki, kwalin wayar na bud’e naga model d’in wayar Tecno K7, ko ba a fad’a min ba nasan babbar tawa ce saboda ni a da ina rik’e Tecno W4 ne. Dad’ i ne ya kama ni, ganin na samu promotion. Bayan sallar magrib ne na ji shigowar yaya Faruk da yaya Aminu, da alama had’uwa suka yi gurin shigowa. Zama na nayi a d’aki yayin da na jona sabuwar waya ta a charge. Ban fito ba sai da nayi sallar isha’i dan nasa yanzu Abbu zai fara tambaya ta. Zama nayi akan kujera ina jiran fitowar su, shigowar yaya Aminu da yaya Faruk ne ya katse min shirun da nayi. Guri su ka nema suka zauna yayin da yaya Aminu ya kalle ni. Da sauri nace "sannun ku da hutawa, ina wuni yaya Aminu" saboda nasan yanzu sai ya fara min fad’a dan shi ma kamar yaya Faruk yake, sai dai shi ya fi shi hak’uri. "wai dama kina cikin gidan nan tun d’azun amma ban ji motsin ki ba" yaya Aminu ya tambaye ni. "ina ciki, ina yin wani abu ne a ciki" na ba shi amsa. "yayi kyau"abin da yace kenan, ya juya ga yaya Faruk suka ci gaba da hira. Shi kuwa yaya Faruk tun san da yaya Aminu ya fara min Magana naga ya maida hankalin shi kaina, ko me yake so ya gano? Oho mishi. Ummu ce da Abbu suka zauna aka ci gaba da hirar dasu, duk hirar da suke yi sauraren su nake yi kamar ba na gurin ganin yaya Khalil ba ya nan, sai naji hirar ta ginshe ni. Ummu ce ta umarce ni da in d’akko food flask akan dinning a ci abincin a falo ba sai an koma kan dinning ba. Serving d’in kowa nayi na nemi guri na zauna nima na fara cin abincin. Muna cikin cin abincin ne yaya Kalil ya shigo parlour d’in yayi sallama. Amsa masa muka yi kana yazo kusa dani ya zauna. sannu da gida yayi wa Abbu da Ummu, ya gaisa da su yaya Aminu. Spoon d’in shi yasa a cikin abincin na muna ci muna hira k’asa k’asa. Bayan Abbu ya gama cin abincin ne ya kalli yaya Faruk ya kira sunan sa "Faruk". Tattaro hankalin shi yayi ya mik’a shi ga Abbu dan jin mai zai ce mai. Abbu ne yaci gaba da cewa "Lokaci yayi da ya kamata ace ka ajiye abokiyar zama, rayuwa ba za ta tafi ba sai da abokiyar zama, ya kamata ka bincika ka samo matar, kai kan ka za ka fi jin dad’in aikin ka da mu’amalar ka da mutane". Had’a ido muka yi a lokacin da Abbu yake mai magana, ganin kallon da yake min ne yasa na kau da fuska ta. Cikin ladabi yace "insha Allahu Abbu na kusa fito da matar da zan aura, akwai abin da ya tsayar dani ne shi yasa, amma a taya mu da addu’a". "Ana nan ana muku Faruk, Allah ya za’ba muku na gari da kai da ‘yan uwan ka". Abbu yace dashi. Yaya Faruk ne ya amsa "Amin Abbu" . Nan ita ma Ummu tayi ta mishi nasiha akan ya kamata ya fito da matar aure.. A raina kuwa cewa nayi "mutum ya girma amma yak’i yin aure ko mai yake jira? Gwara ma Allah yayi ya kawo mishi matar yayi auren ko ma samu sauk’i". Ummu ce da Abbu suka mik’e suka mana sallama, suka nufi side d’in su. Yaya Khalil ma sallama ya mana ya tafi d’akin shi saboda yace min yau bacci yake ji da wuri. Ya rage daga ni sai su yaya Aminu muka rage a falon. [4/6, 22:04] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin naki ne* *Nasiba Isma'il Uba* (marubuciyar Sanadin Aboki)💞 *My friend ina miki fatan alkhairi* *MUNA TARE*❤ *'yan Mufy & Maryam A Paki fans* *Maman Walida* *Auta mama*(Aisha) *Tawerh* *Hajara Tijjani* *Ramlerh* *Hauwa Hussaini* *Queen Aysha* *Maymoonah* *Fadeelah* *Barrister Teemah* *Har kullum ina tare daku ‘yan group d’ina da kuma son da kuke ma wannan novel d’in*. *Ba abin da zance daku sai godiya* *Sauran da baku ji sunan ku ba za mu had’u a next page*. *Tawerh ina miki fatan sauk'i, Allah ya baki lfy yasa kaffara ne* *Question of the Day* K’ofofin aljanna guda nawa ne? Lissafo sunayen su. 35&36 Maida hankali na nayi gaban allon Tv ina kallon tauraren d’an adam a tashar MBC Bollywood, jefi-jefi nake jin hirar tasu. Yaya Aminu ne naji yana cewa yaya Faruk "kai ma Soja ya kamata ace ka fito da matar aure, tun da iyayen mu sun nuna suna son kayi aure, in kuma baka fi son azumi in yazo a fara kad’a maka ganga ba" Murmushi kawai yayi kana yace "very soon insha Allahu zan gabatar da wanda nake so, kafin in koma aiki zan zo in same ka akwai maganar da nake so muyi" cewar yaya Faruk. "Ok sai kazo" ya bashi amsa. Yaya Aminu ya mik’e cikin wasa ya kalli yaya Faruk yana cewa "ni zan gudu, nasan madam nacan na jira na, kai ko k’arfe nawa zaka kai a waje ba matsala, ba mai tambayar ka". Shima mik’ewa yayi yace "nima tafiya zan yi". Sallama suka min suka tafi. Kasancewar yanzu ba ma zuwa ko ina tun da muka zana SSCE exam d’in mu, Abbu ne yasa yaya Khalil ya siyo mana form ni da Anisa a Al-Mannar Academy na shiga Mutawassid tun da mun yi saukar Al-qur’ani. Bayan mun cike form ne muka fara zuwa makarantar. Daddy form d’in computer training yasa yaya Faruk ya amso mana a Bintalya computer institute. Sai ya zamana yanzu ba mu da wani time, da mun dawo daga computer training, ba jimawa zamu tafi islamiyya, ba mu zamu dawo ba sai yamma. Yanzu tsakani na da yaya Faruk ba wani takurawa, ni gani nake yi neman shiri yake yi dani saboda yadda yake d’an ja na da wasa da kuma hira. Duk wannan abubuwan da yake yi ba wai na sake dashi bane saboda sanin hali. Yau ranar ta kasance ranar lahadi, yaya Faruk ne cikin shirin shi ya fito ya shiga side d’in Momi, bayan sun gaisa ne yake ce mata zai lek’a gidan yaya Aminu ne, fatan a dawo lafiya ta mai da sak’on gaisuwar ta ga Anty Jiddah da Humaira da Nabil. Kafin ya isa gidan sai da ya tsaya a wani super market, ya tsaya yayi wa su Humaira da Nabil shopping. Da isar shi gidan ya same su a falo da yaran suna kallo, su Humaira kuwa sai murna suke yi da ganin yaya Faruk saboda yadda yake kawo musu kayan zak’i da kayan wasa. Hannu ya mik’a wa yaya Aminu suka yi musabaha kana ya samu guri a d’aya daga cikin kujerun dake kewaye da falon ya zauna. Anty Jiddah ce ta gaishe shi tana tsokanar shi tana cewa "su Anisa ba su baka sak’o na ba? Ta’be baki yayi yace "wane irin sak’o ne". Dariya tayi ta d’aura da cewa "ce musu nayi su ce maka ka bani za’bi in za’bar maka mata tun da kai naga har yau ka k’i fito da wacce ta yi maka". Murmushi yayi yace "Madam kenan, ke kin san class d’ina yafi a ce za aza’bar min mata saboda ba ki ga yadda ‘yan mata ke so na ba a Kaduna da Abuja, infact nan ba dad’e wa ma zaki ga wacce nake so". "haka muke so Soja, gwara kayi zuciya kayi auren ko ka huta da gori" Anty Jiddah ta fad’a da alamar wasa. Yaya Aminu kuwa bai ce komai ba in banda dariya da yayi. Kayan motsa baki taje ta kawo mai ta ajiya ta nufi d’aki ta barsu dan su zanta. Nabil ne yaje kusa da yaya Faruk ya manne a jikin shi ya fara Maganar shi ta ‘yan koyo yace "Uncle Soja ina bindigar da kace ja ka ciyo min". Kunnen shi ya kama yace "sorry Nabil na manta ne amma in zan k’ara zuwa zan siyo maka". Tsalle Nabil ya fara yi yana cewa "yeh Uncle soja jai ciyo min bindiga". Humaira sai faman zun’bura baki take yi ganin ance za a siyo wa Nabil bindiga amma ita ba a ce za a siyo mata ‘yar baby ba (toys)" "zo nan Humaira" yaya Faruk ya kira ta cikin lallashi. "Me ya faru ne baby naga kina so kiyi kuka". Cikin shagwa’ba tace "ba kai bane kace zaka siyo wa Nabil bindiga, ni kuma ba kace zaka siyo min ‘yar baby ba (toys)". Dariya suka yi shi da yaya Aminu kana yace "ke ma zan siyo miki, an shi wannan ki kai ma Momi ta raba muku" Cikin murna ta amsa tana cewa "Uncle soja mun gode" ta tafi d’akin Anty jiddah da gudu. ganin haka ne yasa Nabil shima ya bi ta da gudu. 5 alive na kwali da Anty Jiddah ta kawo mai ya d’auka ya tsiyaya a glass cup ya sha, ya juya kallon shi zuwa gurin yaya Aminu yace "Aminu shawara nazo nema a gurin ka game da yarinyar da nake so". Yaya Aminu ya yalwata murmushin shi yace "Masha Allah ina jin ka, kace mun kusa yin suruka". Sai da ya numfasa kana yaci gaba da cewa "Aminu ba kowace yarinya bace na dad’e da fad’a wa tarkon son ta illah Fatima, bazan iya fad’a maka adadin son da nake mata ba, sai dai kawai in ce maka, I really love her". Da mamaki yaya Aminu yace "wace Fatiman kake nufi? Gajeren tsaki yayi kana yace "Akwai wata Fatima ce da ta wuce k’anwar ka". Dariya Aminu ya fara yi yana kallon yaya Faruk wanda ya tamke fuska ganin dariyar da Aminu yake mai. Wani dogon tsaki ya k’ara ja wanda yafi na farko yace "wai Aminu miye abin dariya, daga na fad’a maka sirrin zuciya ta, ka tasa ni sai dariya kake min kamar kaga wani mahaukaci". Tsayar da dariyar yayi yana cewa "Sorry Bregadier, my inlaw, abin ne da ban dariya da mamaki wai kai kake son Fatima, gashi kana da son girma, baka son raini, ita kuma Fatima ga rawar kai, amma soyayyar nan za ta ba da ma’ana, naji dad’i da Sister ta samu gwarzon namiji kamar ka, congrat". "Kai matsala na da kai Aminu, kana mai da zance mai mahimmanci wasa, nazo dan ka bani shawarar amma kana d’aukar zancen as a joke". "Ok sorry, joke aside, yanzu fad’a min shawarar da kake so in ba ka" yaya Aminu ya fad’a. "Kaga dai Fatima ba ta dad’e da kammala Secondary School ba, nan ba da jima wa ba admission zai fito su fara d’auka lectures, yanzu abin da yake damuna shine har yau ita Fatima ba ta san ina son ta ba, tsoron da nake ji shine kar in bari ta fara high institution ta had’u da wani su fara soyayya alhalin ni ina nan ina jiran ta, kar kuma in fad’a mata yanzu in katse mata karatu tasa soyayya a gaban ta? kai menene shawarar ka". Yaya Aminu in ban da bin shi da kallo ba abin da yake yi. mamaki yake yi wai Faruk ne ya zauna yana expressing d’in feeling d’in da yake ma Fatima, "lallai ya yarda Love is everything, you don’t have any choice to control yourself when you fall in love, ya kuma yarda da son da Faruk yake ma Fatima". "A shawara ta Faruk, ina ganin ka fad’a mata yanzu saboda tasan kana son ta da wuri, kaga ko nan gaba tasan da kai, ba za ta bari ta sa soyayyar wani a ranka ba, kasan A bari ya wuce shi ke kawo raban wani". Yaya Aminu ci gaba yayi da cewa 'yanzu kayi amfani da DAMAR KA ka k’ara jan ta a jikin ka na yadda SHAK’UWA CE za ta k’ullu a tsakanin ku, kaga daga nan sai ka nuna mata ZAZZAFAR K’AUNAR da kake mata, I know, she will not reject you, because you are one out of thousand". Wani murmushin dad’i yaya Faruk yayi saboda yadda yaji yaya Aminu ya bashi shawara da kuma yadda yake fasa mishi kai, hakan yasa ya k’ara samun k’arfin gwiwar tunkarar ta. Shawarwari yaya Aminu ya dinga ba wa yaya Faruk akan yadda zai shawo kan Fatima ba tare da wata matsala ba. Canza akalar hirar suka yi kana yaya Faruk yace ya kira mishi Anty Jiddah ya mata sallama ya tafi. Tun daga wannan time d’in ya zamana yaya Faruk na zuwa gidan mu yana ja na da hira, ga siyayya da yake min akai – akai, yanzu har dama ya bamu wai mu dinga yin chating, ga kira na da yake yi akai-akai. Ni ko mamakin mai ya canza yaya Faruk a lokaci d’aya nake yi, yadda ya dawo so cool da friendly damu. Yau da daddare ina zauna a d’aki ina buga game a waya ta, naji alamar shigowar war calling a waya ta. Sunan yaya Faruk na gani a jikin screen d’in yana yawo, d’auka nayi na amsa mishi sallamar da ya min. 'ki same ni a falo akwai maganar da za muyi" abin da yace min kenan ya katse wayar. Tunani na fara yi wace Magana ce zamuyi dashi da ba zai bari gobe ba sai da daddaren nan. Hijab kawai na d’aura akan night gown d’ina da zani akai na nufi falo. Samun shi nayi a falo shi da yaya Khalil suna hira. Guri na samu na zauna na gaishe shi. Ganin bai ce min komai ba yasa nace "gani yaya Faruk" Yaya Khalil ne ya mik’e yayi wa yaya Faruk sallama ya tafi side d’in shi. Shiru falon ya d’auka na d’an mintina kamar ba kowa a ciki. "TEEMAHHHH" Saurin d’ago kaina nayi saboda yadda naji yaya Faruk ya kira suna na wanda ya banbanta da sauran lokutan da yake kiran suna na. D’aga kai nayi na kalle shi ba tare da na amsa ba. Shiru yayi kamar mai tunanin abin da zai ce yake yi. "Fatima! ina so ki bani aron time d’in ki saboda maganar da nake so muyi a yanzu is ver important". Wannan wace Magana ce kuwa da yaya Faruk yake son fad’a min mai mahimmanci haka? nasan wannan tambayar ba ni da amsar ta sai dai in jira ya fad’a min ba. "Teemah, duk maganar da zan fad’a miki ki d’auke ta da mahimmancin saboda har cikin zuciya ta haka take, kar ki zata ko da wata manufa zan fad’a miki sai dan in fallasa abin da ya dad’e a cikin zuciya ta yana damu na". Duk da ban san wace Magana ba ce, sai naji gaba nay a fad’i duba da yadda yake amfani da cool sound wajen maganar. "Teemah! ba kowace Magana bace da ta wuce in ce miki INA SON KI FATIMAH, I know I am in love with you because my reality is finally better than my dreams". Gaba na ne ya fad’i na yadda maganar tazo min a bazata da firgita da nayi a lokaci guda wanda hakan ya kasa ‘boyuwa a fuska ta. "mai yaya Faruk yake nufi da wannan kalamen nashi, ko in ce tatsuniyar da za ayi ta a lokacin a gama, an ya yaya Faruk yana cikin hankalin shi da zai tunkare ni da wannan tsadaddiyar kalma mai wuyar furta wa? ya ma san wacce yake fad’a ma wannan kalmar" na tambayi kaina. Kamar ya san tambayar da nake yi wa kaina yace "Teemah, kar ki yi mamaki ko shakkar maganar da na fad’a miki, kar kuma ki d’auka da wani nufi a raina yasa na fad’a miki haka illah ina fallasa miki abin da ya dad’e a raina, duk wasu abubuwa da kika ga ina miki wanda kike d’auka a matsayin takurawa, ina miki shine dan ina kishin ki da kuma son da nake miki". Ci gaba yayi da cewa "Teemah! True love doesn’t have a happy ending because true love doesn’t have an end. My love 4 u has no end, farin ciki na shine samun Ki, there is only one happiness in this life, to love and be loved". Ni dai rasa a wani hali nake ciki, rasa wani hukunci zan yanke ma wannan maganar mai kama da labari shuni ya yi, na yadda namiji bai da kunya, tun da har yaya bai jin kunyar fad’a min abin dake ranshi ba, ya kuma manta abin da yamin a baya, duk ma ba wannan ba, zuciya ta ce tak’i marhabin da sak’on da yaya Faruk yazo mata dashi. Jin bance mai komai ba yasa yace "Fatima zan baki time kije ki yi tunani kafin in koma aiki saboda hutuna ya kusa k’are wa, dafatan zaki yi ma Magana ta duban basira". Ya mik’e yana duba wrist watch d’in shi yace "Gud night Teemah, na barki lafiya". Bai jira jin abin da zance ba ya tafi. [4/10, 20:51] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin naku ne* *Hussaina Ahmad da duk wanda ke group d’in Ni da yaya Farooq* *Ina muku fatan alkhairi* *Sak’on gaisuwa ta gare ku* *Sakina ilyas* *Sarah* *Umin kareemah* *Lubiee* *Fauxiya Masha Allah* *Doctor Maryash* *Ash, beely* *Aysha a* *Aeeshart* *Maman nabeel* *Hafsat m Goni* *Da duk wanda ke cikin group d’in Mufy & Maryam A Paki fans*. *Sauran wanda ba su ji sunan su ba, mu had’u a next page*. Wannan karan ba samu wanda ya kawo complete answer na question of the day, sai dai akwai wanda suka yi matuk’ar k’ok’ari irin su Meeynah Auta mama (Aisha) Xarah auwal Sulaiman Abdullahi (facebook) Amsar question of the day shine k’ofofin aljanna guda takwas ne (8) 1. Jannatul Firdausi 2. Jannatul Na’im 3. Jannatul Aliya 4. Jannatul Adnin 5. Jannatul Ma’awa 6. Jannatul Darul kuldi 7. Jannatul Ar-rayyan 8. Jannatul Darul salam Allah ka sa da mu daga cikin wannan k’ofofin. *Tunatarwa* Kar ka/ki bari fushi ya dinga ziyartar zuciyar ka/ki, saboda duk lokacin dab ka/ki yi fushi, shaid’an ne a cikin jinin jikin ka/ki da ruhin ka/ki. Wannan nasiha ce. Idan mutum yayi maka/ki abu mara kyau, ka/ki tuna da mai kyau da yayi maka/ki, saboda ko wane mutum yana da hali maii kyau, yans da mummuna. Wannan nasiha ce. 37&38 Tun da yaya Faruk ya tafi na ji ban da wani sukuni, jiki na a sanyaye na mik’e na nufi d’aki na. Akan gado na zauna ina tariyo maganganun da yaya Faruk ya zauna ya na fad’a min, kenan maganar Anisa ta zama gaske da tace yaya Faruk na matsa mana ne saboda ni, ya akayi tayi saurin gano cewa yaya Faruk so na yake yi amma ni ban gano haka ba. Har yanzu maganganun shi suna min yawo a zuciya ta, ban san kuma dalilin da yasa na kasa gasgata maganganun shi a raina ba duk da nasan har zuciyar shi yake fad’a min. Abin da bazan iya tantancewa ba shine ni dai a zuciya ta ba ta yi marhabun da maganar yaya Faruk ba, hakan na nufin kenan bana son shi? Wata zuciyar ce ta gargad’e ni da cewa "kar kiyi saurin yanke hukunci dan ba a yanzu bane zaki samo amsar ki". Ni kaina nasan yaya Faruk ya kai namiji da duk macen da ta ganshi za tayi fatan ya so ta, ya had’a duk abin da mace ke buk’ata, sannan ya na da ilimi, kud’i, kyau, duk da muna takun sak’a dashi, hakan ba zai hana fad’ar cewa yana da kyawawan halaye, matsalar shi ita ce fad’a da miskilanci. A ra’ayi na shine ba na ra’ayin namiji so rude, na fi buk’atar namiji friendly kamar yaya Khalil. Zuciya ta ce ta bani shawarar kar in fad’a ma Anisa wannan maganar, dan duk yadda takai ga complaining d’in abin da yaya Faruk ke mana, ba za taso in yi rejecting d’in shi ba, fad’a ma ta na nufin kamar maganar taje kunnen family ne. Shawara d’aya na yanke shine in yi watsi da maganar da yazo min in ci gaba da harka ta, in yaso in ya tambaye ni in ce ban gama shawara ba. Da wannan shawarar na samu mafita, na manta da wani batun yaya Faruk. WANENE YAYA FARUK? Yaya Faruk d’a ne ga Engineer Yusuf wagini, mahaifin shi ma’aikaci ne a NNPC dake marabar rido a kaduna, sannan yana da kamfanin sai da motoci da suka yi had’in gwiwa da k’anin shi Ibrahim. Mahaifin Faruk wa ne ga mahifin su Fatima. Mahaifyar shi Hajiya Rukaiyya ‘yar asalin cikin katsina ce, mahaifiyar shi business woman ce da take saro kaya daga Dubai take kawowa gida Nigeria. Yaya Faruk ya ci sunan kakan mu ne Umar, shi yasa ake kiran sa da Faruk. Mahaifin yaya Faruk shahararren mai kud’i ne. Yaya Faruk d’an kimanin shekara 32 kuma shine babba a family, ya ba ma yaya Aminu ratar shekara d’aya, sai suka taso kan su d’aya kuma abokai ne. Tun da aka haifi yaya Faruk sai da aka d’auki wasu shekaru sannan Momi ta sake haihuwa amma sai yaron bai zo da rai ba, daga nan sai da Momi ta sake d’iban wasu shekarun sannan ta haifi Anisa, dan har su Momi sun cire rai da sake haihuwa. Yaya Faruk tun yana k’arami yake da sha’awar aikin soja har yau da yake matsayin Bregadier. Yaya Faruk mutum ne wanda Magana bai dame shi ba, baya shiga abin da ba ruwan shi, akwai shi da miskilanci sannan ga wanda ya fahimce ci yana da dad’in zama da kuma kyauta, Shi mutum ne mai son zumunci. Yaya Faruk irin classic d’in mazan nan ne da ake ce musu one in town, yana da kyau wanda yake d’aukar hankalin ‘yan mata, kalar skin d’in shi normal fari ne wanda bai yi yawa can ba, gashi da dogon hanci, dogo ne amma ba can ba, yanayin jikin shi irin giant ne, yana da farin jinin ‘yan mata da kuma mutane, sai dai shi ‘yan matan ba sa gaban sa illah Fatima da yake ganin yayi gamdakatar da soyayyar ta. CI GABAN LABARIN A can ‘bangaren yaya Faruk kuwa tun da ya koma gida yaji ya samu relief a zuciyar shi, ko ba komai yau ya samu ya amayar da abin dake cikin zuciyar shi na wasu shekaru. Sai dai zuciyar shi ke kai kawo akan yanayin Fatima da ya fad’a mata maganar, bai ga wata alama na farin ciki ko bak’in ciki ba, yanzu ba zai iya yanke hukuncin cewa tayi na’am dashi ba ko akasin hakan. Idan Fatima tayi accepting d’in shi yasan ya samu farin cikin da ya dad’e yana buri, kenan idan tak’i accepting d’in shi yana nufin zai samu akasin farin ciki kenan, rasa Fatima a gurin shi yana nufin rasa jin dad’in shi ne, shi kan shi bai san lokacin da son Fatima ya mishi dabaibayi. Baya fatan hakan ta kasance gare shi saboda bai san halin da zai shiga ba in ya rasa ta. Yana cikin wannan tunanin ne wayar shi ta fara haske tana d’auke wa, hakan na nufin kira ne ya shigo wayar saboda a silent yasa ta. Sunan Ogan shi yaga yayi appearing a jikin screen d’in wayar. Da azama ya d’auka ya mik’a gaisuwa yana jiran jin abin da Ogan zai ce mai tun da ya kira shi a wannan lokacin. Sanar dashi yayi akan ya ajiye duk abin da yake yi ya tawo Abuja gobe, akwai wani aiki da za ayi kuma a ciki har dashi a ciki. Cikin ladabi ya amsa mishi da insha Allah yana nan tawo wa. Yana gama receiving d’in call d’in ya wurga wayar can gefen gado, ya dunk’ule hannun shi ya kai ma d’ayan hannun naushi kamar hannun ne ya masa laifi. Wani irin takaici ne ya kama shi a lokaci guda, yana ganin yanzu ne ya kamata ya jawo Fatima a jiki, su fahimci juna ta yadda za ta kamu da son shi, sai gashi rana tsaka ana neman shi a gurin aikin shi ba tare da ya samu ya fahimci juna da Fatima ba. Babbar matsalar shi shine na yadda zai tafi ba tare da ya tsaya yaji amsar shi a gurin Fatima ba, bai san wani lokaci aikin zai d’auke shi ba da zai sa ran dawowa don yaji amsar shi a gurin ta. Wata zuciyar ce ke ce mai "kar ka damu tun da har ka fallasa mata Sirrin zuciyar ka, ko wani lokaci zaka d’auka tasan da zancen ka". Da wannan k’arfin gwiwar ya samu ya tashi da niyyar zuwa gurin Momi dan ya fad’a mata maganar tafiyar shi. San da ya shiga d’akin, samun ta yayi zaune akan gado tana pressing d’in waya. Sallama yayi ya zauna awata round chair dake d’akin ya zauna. Amsa masa tayi tana nazarin shi ganin bas u dad’e da rabuwa ba a falo. ‘ya akayi ne Faruk’ Momi ta tambaye shi. Amsa mata yayi da cewa "Momi daman nazo in fad’a miki ne, gobe zan koma Abuja, yanzu aka kira ni akan wani aiki da za muje wani gari muyi, kuma ina daga cikin wanda za su jagoranci tafiyar". Kallon shi tayi saboda lura da tayi kamar bai shirya tafiya a goben ba, kamar kuma akwai abin da ke damun shi. "Allah ya taimaka ya ba ku sa’a akan aikin ku". Cikin jin dad’in addu’ar Momi ya amsa da "amin Momi". Shiru ne ya ratsa d’akin kamar ba wanda zai yi Magana a cikin su. Momi ce ta katse shirun da cewa "yanzu Faruk ya muke ciki game da maganar da nayi maka, kana nufin haka zaka tattara ka koma ba tare da ka tsayar min da kyakkyawan Magana ba" "Momi insha Allah in na dawo za ki ji duk yanda ake ciki, yanzu komai zai zo da sauk’i dan na riga na fad’a ma ita yarinyar ina son ta, na so ta ba ni amsa, sai ga tafiya ta taso ba shiri, abin ma duk na gida ne ai Momi". Cikin tuhuma Momi tace "wacece yarinyar? Murmushi yayi kana yace "in na dawo daga tafiya zan fad’a miki wace yarinya ce". Momi dad’i ne ya kama ta jin cewa ma yarinyar da yake so ‘yar gida ce duk da bai fad’a mata wace yarinya ba ce amma duk da haka taji dad’i. Addu’a ta shiga jera mishi tare da mishi fatan nasara akan aikin shi. Sallama ya mata ya koma side d’in shi yana ci gaba da tunanin masoyiyar shi. Washe gari ko da yaya Faruk yayi sallama da su Momi, gidan su Fatima ya wuce dan ya musu sallama. Ko da ya shiga main falo, bai samu kowa a ciki ba, wuce wa d’akin Ummu yayi, nan ma bai same ta ba. Jin motsin ta yayi a kitchen yasa ya nufi kitchen d’in. Fitowa tayi daga kitchen a lokacin shi kuma ya k’araso. Yalwataccen murmushi ta sakar mai tana cewa "Faruk ne! sannu da zuwa". Shima cikin murmushi ya gaishe ta tare da tambayar Abbu ko yana nan. Amsa mishi tayi da ya tafi gurin aiki. "Ummu da ma nazo in muku sallama ne zan koma gurin aiki, jiya Oga na ya kira ni, akwai wani aiki da ya taso kuma har dani ake buk’ata". "ikon Allah, tafiya ba shiri, to ubangiji Allah ya taimaka ya ba da sa’a". Amsa mata yayi da "Amin Ummu". "Ummu Khalil na nan ne" ya tambaye ta. "Ya tafi makaranta" Ummu ta ba shi amsa. Jim yayi kana yace "Fatima na nan ne? "Ba ta nan, Khalil ya d’auke ta zai kai su inda suke yin computer training, ina jin ma ai sun biya ta gidan ku sun d’auki Anisa, daga nan zai wuce makaranta". Har a ran shi bai ji dad’i ba da bai same ta ba, saboda yaso ya gan ta kafin ya tafi. Ummu ce tace "ban san da tafiyar ka ba, da na maka dambun naman nan da kake so, ko yanzu ma ba za a rasa ba, bari in d’ebo maka ka tafi dashi". "To Ummu, nagode, Allah ya saka da alkhairi". "Miye abin godiya Faruk, kaima ai kana kyautata mana, ka ga dan mun maka ai ba laifi, Allah dai ya k’ara bud’a muku". Amsa mata yayi da "Amin Ummu". Juyawa tayi ta koma kitchen dan ta d’ebo mishi danbun nama. Yana jin dad'in yadda Ummu ke bashi kulawa kamar d’an ta. Dawowa tayi d’auke da wani food flask a hannun ta wanda yake d’auke da dambun nama a ciki. Mik’a mishi tayi tace ‘in kaje ka samu guri ka juye saboda kar ya lalace. yayin da yayi ta jero mata godiya. Sallama yayi mata ya kama hanyar zuwa Abuja. Bayan na dawo ne, Ummuk ke fad’a min yaya Faruk yazo yin sallama saboda ana neman shi gurin aiki. Dad’i ne ya kama ni ganin ba mu had’u dashi ba, dan har yanzu ban samo amsar da zan ba shi ba. *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY AND WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *BAN MANTA DAKE BA*❤❤ *SHAK’UWA CE tasa ki ke raina my surukas (Sameena Aliyu) marubuciyar shak’uwa ce* *Ina miki fatan alkhairi a duk inda kike* *Dafatan za a ci gaba da amso mana primary & secondary data*.😝 _KINA RAINA_💝💝 _Mufida Mu’azu_ _(Marubuciyar Auren Dole)_ _Dearest friend, kamar yadda ba za ki manta ni ba, nima bazan manta dake ba_ _Har kullum muna tare ko ba novel_. _Ina taya ki murnar kammala littafin ki mai suna Auren Dole_ _Allah yasa an amfana da darasin dake ciki, an yi watsi da akasin haka_ _Sai mun ji ki a sabon novel d’in ki_. *My regard to you*🤝🏽 *Al-Mirah* *Screen play of hausa film*. *You are one of my fans, I appreciate it*. *I dedicated this page to you* *Sak’on fatan alkhairi gare ku* 💞💞 *Softie Deeja* *Hajara Tijjani* *Shatu Naseer* *Ruky wada ce* *Barrister Amal* *Maryam Muhd* *Classic lady* *Zaihash* *Fatima* *Zeisha* *Ummu Naeem* *Ummu sulaiman* *Ummie* *Humairah* *Hussainty* *Da duk wanda ke cikin group d’in Mufy & Maryam A Paki fans* *Question of the Day* Yaushe ne k’uraishawa suka jaddada sabunta gina ka’aba? Sannan akan me suka samu sa’bani? 39&40 Mun ci gaba da zuwa islamiyyar mu da computer training d’in mu cikin jin dad’i saboda ba mu da wani lokaci na zama a gida. Haka lokaci yaci gaba da tafiya inda kamar yau ne muka zana jarabawar SSCE, sai gashi Addmission a nan Kad Poly, sai dai ba course d’in computer science da na za’ba suka ba ni ba, sai suka canza suka bani Statistics, yayin da ita kuma Anisa suka ba ta course d’in da ta za’ba SLT (science & Laboratory technology). Mun yi waya da k’awar mu Aisha, take ce min sun ba ta computer science. Nan da nan muka je muka biya muka amshi acceptance letter, muka ci gaba da procedure na registration. Bayan gama registration d’in mu ne muka fara attending d’in lectures. Na yarda da aka ce rayuwar high institution rayuwa ce da za koyi darussa da dama, zaka had’u da na kirki da na banza, kowa da kalar rayuwar da yake gudanarwa ba tare da duka ko zagi ba, hakan yasa na kama kaina don guje wa irin bad groups d’in school. Ganin duk wani lecturer in ya shigo class d’in mu yake tsoratar damu akan mu dage kasantuwar yadda course d’in mu yake da wuya, shi yasa na ba da k’aimi wajen karatu dan ban son samun matsala a karatuna. _ABUJA_ Tun tawowar yaya Faruk bai zauna ba kasantuwar shirye shiryen tafiyar da za suyi zuwa garin Adamawa. Zaune yake akan three sitter, yana sanya da singlet d’in sojoji da short nicker na sojoji a jikin shi. Kayan sun matuk’ar yi masa kyau. Wayar shi ce ke ringing, wayar ce ta katse, wani kiran ya sake shigowa a karo na biyu. Ganin bak’uwar numba ce yasa ya ajiye wayar kasantuwar bai gane number ba, a ka’idar shi bai cika d’aukar number da bai sani ba. Jin wani kiran ya sake shigowa yasa ya ja tsaki ya d’auka saboda yadda mai kiran ya nace wa kiran "Assalamu alaikum" ya fad’a da cool voice d’in shi. "wa alaikas salam Bregadier Umar Faruk". Jin muryar mace ce yasa yayi shiru yana tunanin wacece saboda bai gane muryar ba. "plss da wa nake magana" ya tambaya. Cikin muryar shagwa’ba ta ce "nayi fushi Bregadier, tun da ba kayi saving number d’i na ba". Mtsww ya ja wa wani gajeran tsaki "hey! In za ki fad’a min wacece ke am waiting, in kuma ba ki shirya ba zan kashe waya ta" yayi maganar cikin fad’a. Ganin yadda yayi mata maganar yasa taji ba dad’i a ranta, don haka tace ‘Sorry Bregadier, if what i have said hurt you, Fatima Binafa ce da muka had’u a haleems". Shiru yayi kamar bai gane mai maganar ba kana yace "oh na gane, ya kike?". "Lfy lau" ta amsa a gajarce. Yadda yake mata Magana yasa jikin ta yayi sanyi don haka tace "da ma na kira ne mu gaisa" "to na gode, bye" abin da yace kenan ya katse wayar. Ya na ajiye wayar ya k’ara jan wani tsakin ganin yadda yarinyar take son matsa mishi, tun a haleems d’in ya gane take- taken ta. Shi yanzu tunanin Fatima yake yi saboda yadda ya d’aukantu da ta bashi amsar shi, amma ba hali tun da yanzu tafiya za suyi garin Adamawa kwantar da tarzomar da ake yi a garin, bai san ranar da za su dawo ba. Mus’ab ne yayi sallama ya shigo, ya nemi guri ya zauna. Amsa masa sallamar yayi yana murmushi. Mus’ab ne ya fara Magana da cewa "dole kayi murmushi, kasan abin da kayi baka kyauta ba, tuntuni nasa madam ta dafa abincin da kai, kace mana ga ka nan zuwa shine baka zo ba, yanzu sai ka tashi mu tafi". "Sorry Mus’ab, da na dawo sai naji ina buk’atar hutawa, shi yasa na zauna na huta". "Bregadier ba ka da hujjar k’ara kan ka a guri na, ka tashi mu tafi kawai". Mik’ewa yayi ya shiga d’aki ya canza shigar shi zuwa wani lallausan yadi sky blue ya fito. A K’afa suka k’arasa Block d’in su Mus’ab kasantuwar ba wani nisa a tsakanin su. Ko da suka shiga cikin falo d’in, samun su suka yi a zaune a falo. Bayan sun gaisa ne, matar Mus’ab mai suna Maryam ta ke mishi k’orafin ya guje su ba ya lek’o su. Murmushi yayi yace "ayi hak’uri Madam, kin san yanayin aikin mu ne sai a hankali". "an maka uzuri bregadier" Maryam ta fad’a tana dariya. Dining area su ka zarce inda aka jajjera abinci kala kala da drinks. Mus’ab ne da yaya Faruk suke cin abinci akan dinining table d’in, yayin da Maryam ke zaune a falo tana a falo rik’e da remote a hannun ta. "Nana! Nana" ta kira sunan ta. Wata ‘yar madaidaiciyar budurwar yarinya ce ta fito daga wani d’aki, kalar skin d’in ta irin chocolate colour d’in nan ne, sanye take da wata brown d’in atamfa a jikin ta, an mata six pieces gown, ta yane kanta da wani d’an karamin gyale a kanta, yarinyar ba za ta wuce shekara 20 zuwa 21 ba. Cikin natsuwa ta k’araso cikin falo d’in, yayin da ta amsa kiran da Maryam take mata. cikin siririyar muryar ta amsa "gani Anty Maryam" Kallon ta tayi tana cewa "na ji ki shiru ne ba ki fito ba, ki je kitchen na d’aura farfesun kayan ciki ki duba in yayi, sai ki zuba ma su yayan ki". Cikin siririyar muryar ta amsa "ina wani assignment ne kan mu koma school, lecturer bai da kirki, bari in je in duba". Gurin wucewa kitchen d’in ne ta lura da Mus’ab da yaya Faruk da suke zaune a dining area. Cikin ladabi ta gaishe da yaya Faruk kana ta wuce kitchen. Bayan shigar ta kitchen d’in ne ta sami wani food flask ta zubo farfesun a ciki, yayin da ta d’akko wasu glass plate biyu a hannun ta da serving spoon. In da suke zaune ta nufa cikin sanyin ta, serving d’in su tayi ta ajiye masu a gaban su. D’ago wa yaya Faruk yayi ya kalle ta yakau da fuska sannan ya juyar da kallon shi ga Mus’ab daka faman shan farfesun da Nana ta zuba musu. Mus’ab wannan kamar autar Hajiya ko? ya tambaya. Ta’be baki yayi kamar ba zai ce komai ba, can yace "yanzu Faruk kana nufin ba ka gane Nana ba?" Murmushi yayi yace "Am sorry Mus’ab, ba wai na manta ta bane, naga ta k’ara girma ne, kuma kasan na kwana biyu ban gan ta ba". "Ba wani nan, Nana in kin koma gida, ki fad’a ma Hajiya Faruk ya manta da autar ta". Murmushi tayi ba tace komai ba, ta koma falo in da Maryam ke zaune ta nemi guri ta zauna. Mus’ab ne ke fa’da ma yaya Faruk, Nana ta samu break ne a school, shine tazo taya Maryam zama kasancewar tana d’auke da juna biyu. "gaskiya ta kyauta, Allah ya sauki Madam lafiya". Mus’ab ya amsa da "amin". Bayan kammala cin abincin sune, suka dawo falo a ka fara hira. Jefi-Jefi yake sa bakin shi a cikin hirar kasancewar Magana bai dame shi ba. lura yayi da yadda ta maida hankali akan allon Tv kamar ba ta cikin d’akin. "Khadijah" yaya Faruk ya kira sunan ta. Amsa masa tayi cikin sweet voice d’in ta. "Me yasa ana hira ba ki ce komai ba" Murmushi Nana kawai tayi tace "ba komai" Maryam ce cikin wasa tace "ai halin ku d’aya, itama Magana ba ta dame ta ba". Ji yayi yarinyar ta burge shi kasantuwar sanyin ta da rashin maganar ta. "Ki ce ba tayo halin Mijin ki kamar parrot ba" cewar Yaya Faruk. Dariya Maryam tayi tace "nafi son haka, muyi ta hirar mu, amma kai Faruk zan so in ga matar da za ka aura, dan in ka auri mai Magana dole ka koya" Mik’ewa yayi yana duba wrist watch d’in shi yace "za ki gan ta ne Madam, duk wacce ta aure ni, dole ta rage Magana, ni zan tafi". Mus’ab ne yace "yanzu har za ka tafi ana hira mai dad’i, kai da kake gauro ba wanda za ka tarar a ciki". Murmushi yayi yace "akwai abin da zan je in k’arasa ne" Kallon Nana yayi yace "Khadija in koma gida kya gai da Hajiya ki ce sai nazo gaishe ta" "za taji" ta fad’a a gajarce. Juya kallon shi ga Maryam yayi yace "Madam sai anjima" "To sai anjima Faruk" ta amsa mishi. Tare su ka fito suna zantawa, Mus’ab ne ya kalli Faruk cikin zolaya yace "An bani sak’o in ba ka?" Kallon tuhuma ya mishi yace "wa ye ya baka sak’o? ya tambaye shi ganin yadda yayi maganar da tsokana. "Hafsa ce ta bani sak’o in ba ka"? "Wace Hafsa" ya tambaye shi. "Kai fa shegan sama ne, amma in ba haka ba Hafsa ce ba ka gane ba, yarinyar sir Bregadier General Ahmad ce, tace in ce maka wai mai ta maka ne ba ka kula ta a chat, idan ta kira ka ba ka d’auka, sannan in kuka had’u sai kayi kamar ba ka gan ta ba". "Baka ga yadda take maganar ba, ta bani tausayi". Ta’be baki yayi yace "ai sai tayi ta ba ka tausayi, tun farko ai sai da na ba ta hak’uri ta kama masu son ta, ko ta nemi wani, me zanyi da yarinyar da ba ta da kamun kai, ba ma haka ba ni ba ta min ba" ya fad’a yana yatsina fuska kamar itace a gaban shi. Cikin wasa Mus’ab yace "Kai mutumi na, tuntuni fa Hafsa take son ka, sai yanzu za kace ba ka son ta, bayan kasan tuntuni kai take jira, ka amsa query a gurin Bregadier General". Cikin hasala yace "in amsa query akan me? Tuntuni ai na fad’a mata tayi hak’uri ta kama dahir, as to me duk macen da ta bud’i baki tace tana so na, ina mata kallon wacce ba ta san darajar kanta ba, zan dinga mata kallon za ta iya fad’a ma ko wani namiji tana son shi, in tak’aice maka zancen, bana son in yi deceiving d’in yarinyar". Kallon shi kawai Mus’ab yake yi, sanin Faruk na fad’ar abin da ke ranshi ne kuma mai tsayawa akan Magana d’aya, don haka yace "na fahimce ka Faruk, amma shawarar da zan baka shine ka same ta ka ba ta hak’uri ta yadda za ta fahimta, kuma duk mutumin da yace yana son ka ai ya gama maka komai". "Zanyi k’ok’arin fahimtar da ita" ya fad’a cikin ko in kula da zancen. Mus’ab ne ya canza zancen da cewa "ya shirye shiryen tafiya Adamawa" Wani takaici ne ya kama shi ganin a sosa mishi inda ke mishi k’aik’ayi. "Kai dai bari Mus’ab, ai wannan tafiyar ji nake yi kamar in ce a min hak’uri ba za ni ba?" Da mamaki Mus’ab ya tambaye shi "saboda me?" "Mus’ab saboda ba ta bani amsar tana so na ko ba ta so na, yanzu duk wani abu da nake gudanarwa ina yi ne da rashin sanin madafar a wani matsayi nake, ina son ta, yanzu abin da yafi damuna shine ban san yaushe za mu dawo ba?" Mus’ab in ban da bin shi da kallo ba abin da yake yi, ya yarda so mai canza mutum, wai Faruk ne ya zauna yana doguwar Magana akan mace, lallai kam shi shaida ne akan mata ba su dame shi ba, amma yanzu gashi yana fad’an irin son da yake ma ‘yar uwar shi Fatima, ya yarda SO BABBAR CUTA ne". "Faruk ka ci gaba da addu’a akan Allah ya za’ba maka abin da yafi alkhairi, ba na so ya zamana son da kake yi ma Fatima ya koma *MAKAUNIYAR SOYAYYA*" "Ina yin addu’ar Mus’ab, kaima ina so ka taya ni". "Kar ka damu Faruk, Allah ya za’ba mana mafi alkhairi". "Amin" ya amsa yana duba agogo. Mus’ab bari in tafi, lokaci ya ja, sai mun had’u a Officer. Nan suka yi sallama, yayin da Mus’ab ya koma gida, shi kuma Faruk ya tafi Block d’in shi. *_KADUNA_* Yau ta kasance ranar Litinin, muna cikin class, mai mana Descriptve statistics 1 ne ya fita, bayan ya kwashe tsawon awa biyu yana mana lectures, sak’o ne ya iso gare mu cewa mai mana practical statistics ba zai samu shigo wa ba. Ganin muna da tsawon awa biyu free yasa k’awa ta Halima tace in zo muje mu bud’e folder a cikin asibitin poly mai suna "Shehu Muhammad Kangiwa Medical center" (SMKMC) dake cikin makarantar mu za ta ga likita. Ko da muka isa asibitin, record room muka je aka bud’e mana folder aka bamu "Tertiary Institution social health insurance programme" (Ti-ship) card da suka bamu da zamu dinga ganin likita wanda ke nuna mu ‘yan makaranta ne, ba za anshi kud’in mu a wajen amsar magani ba (pharmacy) da wajen d’iban jini (lab), za a dinga cirewa a cikin school fees d'in mu. Tambayar mu suka yi ko za mu ga likita ne a yanzu? Halima ce ta amsa musu da "eh" Ganin ta riga ta amsa musu yasa nayi tunanin in naje gurin likitan mai zan ce yana damuna tun da ni lafiya ta k’alau. Zuciya ta ce ta bani shawarar in naje in ce menstural pain nake fama dashi, in yaso in aka bani maganin sai in ajiye tun da ina fama da ciwon maran in period d’ina ya zo. D’aya daga cikin ma’aikatan ne ya katse min tunanin da nake yi da kiran suna na da yayi "Fatima Ibrahim" Amsawa nayi nace "gani" "Ki je room 2 ki jira" "Ok" na amsa a gajarce. Halima M Kabir suka tura ta room 3. Guri naje na samu a ‘bangaren room 2 d’in. Wanda ya fito shi zai kira sunan wanda zai shiga, haka aka yi har layi yazo kaina a ka kira ni. Knocking nayi a lokaci d’aya nayi sallama na shiga. Amsa min sallamar yayi ba tare da ya d’ago ya kalle ni ba. Rubutu na ga yayi a wata takarda mai kalar kwai, a jiki naga an sa Ti-ship Me yake damun ki? ya tambaye ni. "menstrual pain nake fama dashi" na bashi amsa. Ci gaba da tambaya ta yayi yadda menstrual pain d’in yake min. Rubutu ya fara yi akan wannan takarda. A lokaci d’aya na nazarci office d’in wanda ban da k’anshi baa bin da yake yi, wani hoton Doctor d’in na gani a cikin wani d’an k’aramin frame an jingine shi akan table d’in. "DR ABUBAKAR SADIQ MUHAMMAD" na ga an rubuta a jikin photo d’in. A nazarin da nayi matashi ne wanda ba zai wuce shekara 30 ba, fari ne amma bai kai farin yaya Faruk ba, matsakaici ne a jiki da kyau. A yadda nayi estimating ba zai kai tsawon yaya Faruk ba, sanye yake da lab coat na likitoci da medicated glass a fuskar shi. "hey! Student ko ba kya jina ne? "Sorry Dr, ban ji bane". Miye registration number d’in ki? Ya tambaye ni. "KPT/CST/18/5880" na bashi amsa Wani Department kike? "Department of Maths & statistics" D’ago kai yayi ya kalle ni kana yace "good course, ki ci gaba da k’ok’ari". Dad’i ne ya kama ni jin an yabi course din mu. "I will try my best" Wata ‘yar madaidaiciyar takarda ya mik’o min yace "gashi ki je pharmacy ki amshi magani, Allah ya k’ara sauki". Amsa masa nayi "amin Dr, na gode". Fad’a min yayi wacce zan kira next sannan na fita daga office d’in. Pharmacy na wuce na amshi magani, a can na had’u da Halima ita ma ta amshi na ta muka koma class. [4/15, 10:57] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 _Wannan shafin naku ne_ _Zainab Abdullahi_ (Abuja) _Kamar yadda kika ce ina burge ki, ke ma kina burge ni_. Fatima Bintu Kano (‘yar garin mu) _Hadiza Murtala_ (Maiduguri) _Yusra_ _Na gode da kulawar ku da kuma fatan alkhairi, na kuma ji dad’in yadda kuke son wannan novel d’in_. _Ni ma ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke._ *NUMBAR YABO* _Kamar yadda nake gabatar da shirin question of the day ne a cikin wannan novel d’in nawa, hakan yasa na fitar da wasu daga cikin shirin dan karrama su da ba su number yabo a cikin shirin_. _Sunayen wanda suka samu wannan karramawar sun had’a da_: *Aisha matar Abdul* (Auta mama) (Queen) *Xarah Auwal* (Ass Queen) *Meeynah* (Princess) *Insha Allah, akwai kyauta ta musamman ga wanda ta kasance ita ce ta farko zuwa na uku* *Wannan karan, Meeynah ita ce ta amsa duka tambayar, yayin da Aisha (Auta mama ta amsa d’aya daga cikin tambayar)* *Allah ya k’ara muku ilimi mai amfani da sauran d’aukacin musulmi baki d'aya*. *Amsar tambayar ita ce ‘A cikin shekara ta 35 ne, k’urayshawa suka jaddada sabunta gina ka’aba*. *K’urayshawa sun samu sa’bani ne akan d’aura dutsen hajarul aswad* . *TUNATARWA* _Ka/ki zamo mai neman ilimi, amma kar ka/ki yadda ya kai ka/ki ga girman kai_ _Ka/ki zamo mai Magana, amman kar ka/ki yadda ya kai ka/ki ga zalunci_ _Ka/ki zamo mai Magana, amma idan z aka/ki fad’i alkhairi_ _Ka/ki zamo mai k’arfi, amma kar ka/ki yadda ya kai ka/ki ga k’eta_ 41&42 Ko da muka koma class, mun tarar da citizenship har ya fara lectures, sai da ya barmu na tsawon minti 15 a waje, sannan ya fito ya tambaye mu ina muka je? Mun fad’a mishi daga asibiti muke sannan ya bar mu muka shiga kasancewar yana da sauk’in kai. Bayan mun yi closing ne, Halima ke tambaya ta, wai da naje ganin likita mai nace mai yake damu na? Dariya nayi nace "Tun da kin sa aka kai folder mu, na shirya k’aryar da zanyi in naje gurin likitan, ce mai nayi ciwon mara nake fama dashi, ya rubuta min magani, har yana ba ni shawara wai in dage, course d’in mu na da wahala". "Allah sarki, wasu likitocin ai na da kirki" cewar Halima. Amsar zancen nayi da cewa "gaskiya yadda na lura kamar bai da matsala, wasu likitocin ma in kaje gurin su, suyi ta maka fad’a har ka kasa fad’an me yake damun ka". Dariya Halima tayi tace "wlh kuwa, haka wasu likitocin suke". Ci gaba da hirar mu muka yi, muna cikin sakkowa daga upstairs ne, na hango motar yaya Khalil. Yau ina jin yaya Khalil bai da wani lectures ne da yawa, tun da ya samu zuwa d’aukan mu" na ce ma Halima. Halima da murmushi a fuskar ta tace "Ai ku ‘yan gatan yaya Khalil ne, ni kin ga yaya Jamal, idan ya dawo aiki, Maman mu tace yazo ya d’auke ni, sai yace wai an ci ka shagwa’ba ni, in dinga dawo wa da kaina. Dariya nayi nace "ki ce shima kamar yaya Faruk yake, shima fad’a kamar ya ari bakin wani, ga sa mutum purnishment". Haka muka ci gaba da conversation har muka k’araso in da motar yaya Khalil take, yaya Khalil ne da Anisa a cikin mota, gaisawa suka yi sannan ta tafi. Mun fara tafiya ne na ga yaya Khalil da Anisa suna hira k’asa- k’asa wanda ban san mai suke ce wa ba. Katse musu zancen da suke yi da cewa "wai yaya Khalil ban fa gane bane?" Murmushi yayi yace "da aka yi me sister?" "To na ga sai hira kuke yi k’asa-k’asa ba ku sa ni a ciki ba" Anisa ce tace "To ke Fatima tun da kika ga muna Magana a hankali ai ba a so ki ji zancen ne" ta k’arasa maganar tana murmushi. Cikin shagwa’ba nace "Yaya Khalil na ga so kuke ku had’e min kai da Anisa, in zama ni kad’ai" "Mu mun isa mu had’e miki kai, ke da kike da babban yaya soja" ya fad’a da alamar tsokana. Gintse fuska ta nayi saboda nasan yanzu yaya Khalil zai samu hanyar ci gaba da tsokana ta. Hirar mu muka ci gaba da yi cikin wasa da dariya har muka k’arasa unguwar su Anisa muka sauke ta kana muka nufi gida. Da daddare ina kwance a d’aki ina chating da friends d’ina naga wata sabuwar number an min Magana da ita. "Assalamu alaikum" abin da na ga an turo min. "wa alaikumus salam’ na tura reply. "Kin gane da wanda kike Magana? aka sake turo min. Reply na tura da cewa "ban gane ba gaskiya" Ki na Magana da Bregadier Umar Yusuf, yanzu ina fatan kin gane". Sai a lokacin na gane yaya Faruk ne, saboda ba da ordinary numban shi yake chat ba. "Oh yaya Faruk, sai yanzu na gane ka" "good, ya studies? ya tambaye ni. Amsa mishi nayi da cewa "karatu lafiya lau, ya aiki? "Aiki Alhamdulillah, yanzu ma muna shirye shiryen tafiya Adamawa ne wani aiki, a taya mu da addu’a". "To yaya Allah ya taimaka" "Amin". "Bari in bar ki haka ki huta tun da gobe ki na da lectures, ki kashe data d’in ki dare ya fara yi". Ba a lokacin nayi niyar sauka ba, saboda a group d’in mu na Statistics class rep d’in mu ya turo man da working d’in da function & geometry ya ba mu, ganin yadda yau ya min Magana ba tare da fad’a ba yasa na tura mishi reply "Ok yaya, yanzu zan sauka". "that is good, good night & have a sweet dream" abin da ya turo min kenan ya kasha data d’in shi. Ni ma kashe data na nayi ina mamakin yadda yaya Faruk yau ya zauna yana chating da ni, yanzu kam na yarda yaya Faruk yana so mu fara shiri dashi. But ban san me yasa na kasa samun peace of mind akan yaya Faruk ba, duk da ko a da d’in ba wai yana min wani abu ne da zai sa in tsane shi ba, sai dai fad’an da purnishment d’in da yake mana ne yasa nake jin haushin shi wanda nake ganin kamar ya tsane ni ne, amma zan yi k’ok’arin in ga na sake dashi a matsayin yaya d’an uwa na kuma yaya na. Da wannan tunanin na kwanta barci. A can ‘bangaren yaya Faruk kuwa, tun da ya gama waya da Teeman shi yaji wani farin ciki ya lullu’be shi, yanzu dai gashi ba wata hira suka yi irin ta masoya ba amma ya tsinci kanshi da jin dad’in haka, wai a hakan ma dan bai ji sirrin zuciyar ita Teeman ba, kenan idan ta amice dashi zai tsinci kanshi ne a birnin masoya wand aba kowa ne ke tsintar kanshi a ciki ba sai wanda suka aminta da junan su, in ko haka ne zai ci gaba da addu’ar Allah ya mallaka mishi Fatima saboda ita ce Farin cikin shi. Zai k’ara ba ta time kan ya tuntu’be ta akan ra’ayin ta game dashi. Da wannan tunanin barci ya d’auke shi. Tafiyar su yaya Faruk ta rage yau saura kwana biyu, kiran su aka yi a waya da akwai meeting da su Bregadier General da su Major General za ayi akan tafiyar, ko da suka halarci meeting d’in, an fad’a musu cewar an d’aga tafiyar ne zuwa next week sabida wasu dalilai. Da wannan damar yaya Faruk ya nemi permission akan yana so yaje Kaduna yayi 2 days. Sallama yayi Ma Mus’ab ya kamo hanyar zuwa Kaduna. Yana sauka ya shiga side d’in Momi ya gaishe ta, bayan sun gaisa ne take tambayar sa ba su yi tafiyar bane ta ganshi unexpected. Sanar da ita yayi an d’aga tafiyar zuwa next week, shi yasa yayi deciding d’in zuwa yayi 2 days a nan. Momi ta ji dad’in haka saboda tasan yaya Faruk mutum ne mai son iyayen shi da ‘yan uwan shi. Tashi yayi ya nufi side d’in shi ya watsa ruwa, fito wa yayi ya sami Anisa a falo tana karanta handout d’in ta, a gefen ta wani exercise book ne ta take jotting. Dad’i ne ya kama Anisa ganin ya kwana biyu bai zo ba, ba ta yi tsammanin ganin shi a wannan lokacin ba tun da Momi ta fad’a mata za su yi tafiya. Da fara’a tace "yaya sannu da zuwa". "yawwa Anisa, ya karatu". "Lfy lau yaya Faruk, amma gaskiya yaya karatun Polythecnic akwai wuya, gashi exam is approaching". Murmushi yayi yace "Anisa ko wani karatu da kike gani yana da wuyar shi both polythecnic & University, sai dai d’an banbabcin da ba za a rasa ba, ki dage sosai dan ki fito da grade mai kyau". "zan dage insha Allah". "yawwa my Sis". Jefi-jefi suka ci gaba da hirar, a gurin Anisa kuwa tana jin dad’in yadda yanzu yaya Faruk yake jan su a jiki ita da Fatima, ita ma ta na so ta ga yaya Faruk yana jan ta a jiki kamar yadda yaya Khalil ke jan su. Momi ce ta fito daga side d’inta ta k’araso falon ta zauna. Hira suka ci gaba da yi irin na happy Family, a ran Momi kuwa dad’i ne ya kama ta ganin yadda yaya Faruk ya fara rage miskilancin sa. Kasancewar yau ranar asabar, ba mu da lectures, hakan yasa na tashi da marmarin cin samosa da spring roll. Kitchen na shiga na duba dan in ga ko akwai duka kayan da nake buk’ata, samu nayi da akwai kayan had’in da zan buk’ata. Iya talatu na kira ta taya ni yanka cabbage da karas, ni kuma na ci gaba da sauran aikin, Saboda yadda yake da cin time, sai da na d’au lokaci kan na gama, ina gama wa na had’a ginger amma ban cika cittar ba saboda ka da yayi yaji sosai. Ina fito wa falon na tarar da su Abbu da Ummu da yaya Khalil da kuma yaya Faruk suna hira. Ja nayi na tsaya kamar wadda aka rik’e a gurin, ban yi zaton zuwan yaya Faruk a wannan lokacin ba. Yanzu idan ya turke ni akan in fad’a mishi matsayin shi a guri na, me zan ce mai? Ni kaina nasan ban da wannan amsar, da wannan tunanin na k’araso falo na nemi guri na zauna. Tun da na zauna yaya Faruk ya tsare ni da kallon shi wanda hakan yasa na tsargu. Gaishe shi nayi na mik’e na shiga kitchen na zubowa kowa a plate da wannan ginger wanda yayi sanyi a fridge. Ina lura da yaya Faruk da yana cin Samosa har wani lumshe ido yake yi, ko dad’i ya mai ne ban sani ba, ko da yake na lura lumshe ido a gurin shi kamar nature d’in shi ne. Mik’ewa nayi ganin time d’in zuwa islamiyya ya kusa duk da mun nemi excuse a makarantar ba kullum za mu dinga zuwa ba, saboda yanxu mun fara d’aukar lectures, ran sati da lahadi kad’ai Mu ke zuwa. Shiryawa nayi cikin Uniform d’ina, ina sa bak'ar socks ne naji waya ta tayi ringing. Sunan yaya Faruk na gani a jikin screen d’in yana yawo. Sai da na d’an yi jim kafin na d’auka saboda ban san me zai ce min ba. Sallama na yi bayan na d’auka, amsa min yayi kana yace "me kike yi ne ban ga kin dawo falo ba? "Ina shiryawa ne, time d’in makaranta ne yayi". "Ok har yau dama kuna zuwa ne? ya tambaya. "Eh muna zuwa, amma ran weekend kad’ai muke zuwa". "Hakan na da kyau, in kin gama ki fito in kai ki, ina waje". Amsa mishi na yi da "Toh". Ba haka na so ba, nasan in dai na shiga motar shi sai ya tambaye ni a inda muka kwana akan tayin soyayya shi wanda har yanzu na rasa me yasa na kasa samun mafita. Gun Ummu naje na fad’a mata cewa yaya Faruk ne zai kai ni. Kujera mai zaman banza na zauna, ina wasa da ‘yan yatsu na. Mun fara tafiya ne ya fara tambaya na game da karatuna, ina bashi amsa. cikin wasa yace ‘yan k’idaya kenan, kuna fama, dan naji an ce ku lissafin naku har motoci sai a saku ku k’irga sannan ku fitar da data saboda tsananin lissafi, in na samu time zan zo in kai ki barrack d’in mu ki k’irga mun yawan mutanen da ke shiga da fita". Dariya tayi tace "haba yaya Faruk, ina zan iya tsayawa k’irga motoci sai kace wata injin". "Gaskiya course d’in ku nasan akwai wuya amma ki dage, course d’in ku yana da amfani a ko ina, infact ku professional ne da ko ba aiki za a neme ku a ko ina, ko wani course da kike gani yana da challenges d’in shi, in ka mai da hankali, sai ki ga kin yi achieving goal d’in ki". "na gode yaya Faruk da shawarwarin ka". K’asaitaccen murmurshi yayi yace "Kar ki damu Teemah, you are my sister, it is my responsibility to give you advice at any time". Har raina naji dad’in shawarar da yaya Faruk ya bani, yanzu na k’ara yadda da zancen yaya Khalil da yake cewa yaya Faruk mutum ne mai dadin zama in ka fahimce shi, gaskiya a kwanakin nan ina jin dad’in yadda yake sake wa da mu. Ko da mu ka k’arasa gidan su Anisa, cewa yayi in yi sauri in shiga in kira ta, ba ya son jira. Sanin halin shi yasa ina shiga na tarar da Momi da k’awarta suna duba kayan da Momi ta saro, da fara’ar ta muka gaisa kana na gaishe da k’awar ta, bayan mun gaisa ne nake tambayar ta "Momi ina Anisa take?". "Tana d’aki, ina ganin ta shirya, ki shiga ki gani". D’akin na shiga na sameta ta shirya, ta tsaya sa powder. Hararar wasa na mata nace "ke matsalar ki cin time a gurin make up". "kin san Make up na son natsuwa, shi yasa nake tsayawa in yi shi a tsanake". "yanzu dai ba wannan ba, yau ba yaya Khalil bane ko Driver zai kaimu bare ki ‘bata musu time". Ci gaba tayi da Make up d’in ta tana cewa "To waye zai kai mu? "yaya Faruk ne zai kaimu, kin san kuwa ba ya son jira, kuma ke da zaki sa nik’ab, wani make up zaki tsaya yi" Anisa ba tayi wani mamaki ba, ta san yanzu yaya Faruk is a change person, ba abin mamaki ne dan yace zai kai su Makaranta. Tasan duk canzawar shi ba zai hana in ka mishi laifi ya zartar maka da hukunci ba, tasan yaya Faruk bai son jira dan ba ta manta da purnishment d’in da y aba ta ba kwanaki na filling d’in ruwa da k’aramin cup ba. Cikin sauri ta d’aura nik’ab d’in ta fito muka nufi motar shi. Wannan karan miskilanci ya motsa, tun da muka shiga motar ya kunna wa’azin Sheikh Yahaya Haifan yana saurare, mai taken Tsantseni, gaskiya ko ni da nkae sauraren wa’azin jiki na ne yayi sanyi saboda yadda Malamin ya kawo bayanai akan Tsantseni a rayuwar d’an adam, tambayar da nayi wa kaina a yanzu mutane nawa ne masu Tsantseni a duniyar nan, ko za a samu k’adan ne. Addu’a kawai nake yi akan Allah yasa mu dace, ya kuma ba mu ikon yin tsantseni akan duniya. Sauke mu yayi a wajen makaranta ya juya ya tafi. Ko da aka tashi ga Mamakin mu, shine yazo d’aukan mu. Lallai mun zama ‘yan gatan yaya Faruk kamar yadda yaya Khalil yake tsokanar mu. Wannan karan a mota ya ja mu da hira amma ba mai tsawo ba, tun da shi ba ma’abocin surutu bane. Sai da ya fara sauke Anisa a gida, sannan ya nufi gida da ni. Kallo na yayi yace "Teemah Samosan da kika yi da Spring roll ya min dad’i, in ba damuwa za ki min gobe in nazo?" ya tambaye ni. Duk da procedure d’in yin su Samosa da Spring roll yana da wuya, hakan ba zai hana in mishi ba, dan gaskiya nima yanzu na fara jin dad’in zama dashi. "Ok ba matsala, zuwa gobe insha Allah zan maka". Murmushi yayi yace "ki barshi wasa nake miki, amma in zan tafi sai ki min". "Lalacewa zai yi, sai dai in ran da zaka tafi in yi in ajiye a fridge, in yaso in kaje can ka soya" "Zan ba Maryam ta soya min in na koma, ni ina zan wani iya soya wa" A raina kuwa tambayar wacece Maryam nake yi, dan ba na tunanin abokiyar aikin shi ce. Kamar yasan abin da yake raina yace "Nasan zaki ji nace Maryam, matar aboki na ne Mus’ab, da muke Barrack d’aya" Shiru nayi ban ce mai komai ba tun da ba tambayar shi nayi ya min bayanin wacece ita ba, sun fi kusa koma wacece. Da haka muka k’arasa gida, ya ajiye ni a bakin gate ya juya motar shi ya tafi. [4/16, 12:31] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin na sadaukar dashi ne ga duk wanda yake cikin wata jarabta ko cikin wani hali* *Allah 🙏🏽🙏🏽🙏🏽na yi tawassali da sunayen ka da kyawawan ayukan mu, ka kawo mana mafita a al’amuran mu, ka bamu ikon cin dukkan jarabawar da ka mana*. *Alllah dan sunayen ka tsarkakakku, ya ubangijin Sammai da k’assai, ya Ubangijin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (s.a.w) Allah ka bi ya mana buk’atun mu na alkhairi* 🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽 _Plsss fans ina barar addu’ar ku akan wasu buk’atu nawa, Allah ya amsa min da sauran ‘yan uwan musulmai baki d’aya_ *Question of the Day* _A cikin matan manzon Allah s.a.w, wacece ta lurar da manzon Allah (s.a.w) game da wata dabara da zai jawo hankalin sahabban sa a ranar hudaibiyyah, kuma dabarar taci nasara sosai_ _Menene cikakken sunan ta?_ 43&44 Bayan na shiga d’aki ne, hirar da muka yi da yaya Faruk a cikin mota da kuma shawarwarin da ya din ga bani game da karatu ya dinga fad’o min a rai. A yanzu na sa a raina da cewa yaya Faruk ya samu wani matsayi a raina ta ‘bangaren zumunci, wata zuciyar kuma ta na ce min mai zai hana in bashi matsayin da yafi dacewa shine in amince da soyayyar shi, me yasa har yanzu zuciya ta ba ta anshi tayin shi ba? Wata zuciyar tawa kuwa shawara ta ba ni akan mu ci gaba da zumunci irin na ‘yan uwantaka. Da wannan sark’ak’en tunanin na tashi na nufi d’akin Ummu. Washegari ina zaune a falo, ina karanta wani online novel a cikin waya mai suna *Rayuwar yusra da Afshan*, wanda Maryam Ahmad Paki ta rubuta, labarin yayi touching d’ina na yadda soyayya ta canza ma Afshan hali, duk a dalilin soyayyar Muhsin da ta fad’a kuma mijin Yusra wacce ta rik’e ta kamar ‘yar uwarta ta jini, ba ta saka mata da komai ba sai soyayya da Mijin Yusra wanda take son shi kamar ranta, ko yaya labarin zai kasance a k’arshe? Gaskiya na yadda da marubuciyar da tace labarin Soyayya mai rud’ani da tausayi a cikin novel d’in, Shine na k’osa na ji k’arshen labarin. Sallamar yaya Faruk ne ya katse min karatun da nake yi. Amsa masa sallamar nayi da sassanyar murmushi na. Kusa dani yazo ya zauna, yana min kallon gefen ido. "yaya ina wuni" na gaishe shi. "lfy amma ba lau". ya amsa min Kallon shi nayi jin amsar da ya ba ni, a yanayin shi ban ga wani abu da yake damun shi ba. Shiru na yi ban k’ara cewa komai ba. Wani tsadadden murmushi yayi kana yace "Teemah ba ki tambaye ni me ya same ni". "yaya ai ni ban ga alamar ba ka da lafiya ba, na gan ka normal ne". Kallo na yayi sannan yace "Teemah, ni ko ke rashin lafiya?". Da sauri nace "Me yake damun ka?" Na fad’a da alamar tausayi. K’asaitaccen murmushi yayi yace "Ba irin ciwon da kike tunani bane, wannan daban ne, kuma ke ce maganin ciwon nawa". Gaba na ne ya fad’i, sai yanzu na gane mai yaya Faruk yake nufi, yana so ya d’akko min maganar da muka yi kwanaki ne akan amsar tayin soyayyar shi. Yanzu in ya tambaye ni mai zan ce mai? Gaskiya bazan iya fito wa direct in ce mai ban yi na’am dashi ba duk da matsayin da na ba shi a guri na. Katse min zancen zucin da nake yi yace "Teemah!" nasan kin gane me na ke nufi, ba komai ke damu na ba illah fama da ciwon son ki da ya min dabaibayi a zuciya ta wanda har yanzu ban san matsayi na a gurin ki ba, ina so ki bani amsa ta Teemah, dan zuciyata ta samu peace of mind". "An zo gurin".abin da na fad’a a raina kenan. Zuciya ta ce ke kai kawon me zan ce ma yaya Faruk a yanzu da zai yadda da hujja ta, dubara d’aya ce ta fad’o min akan in lalla’ba shi mu rabu lafiya. "yaya Faruk, kai ma kasa ba zan k’i ka ba, ko dan darajar ‘yan uwantaka dake tsakanin mu, ko a da damu ke samin misunderstanding rashin fahimtar juna ne, amma yanzu na gano kai mutum ne mai dad’in zama da dad’in mu’amala, sai dai ina neman alfarmar ka yaya ka k’ara min time, saboda kasan har yau ban gama sanin mecece soyayya ba" Tsura min ido yayi kamar yana so ya gano gaskiyar maganar da na fad’a mishi. Sunkuyar da kai na nayi dan gaskiya ba zan jure kallon da yaya Faruk yake min. "Fatima!" ya kira ni da wani irin salon maganar shi da ya banbanta da sauran lokuta. "Na’am yaya" Sai da yayi shiru kamar ba zai ce min komai ba, can ya d’ago ya kalle ni. "Teemah, zan iya k’ara ba ki time kamar yadda ki ka buk’ata, ina so duk san da na k’ara tambayar ki ya zama kin samo amsar". Ci gaba yayi da cewa "Teemah, ina son ki wanda ni kaina ban san adadin son da nake mi ki ba, ni mutum ne da ba na soyayya sai akan ki da na fara, akwai ‘yan mata da suke so na amma ni ke ki ka min, ba na so in yaudari mutum, dan haka Teemah ina rok’on ki kar ki yaudare ni, gwara tun wuri ki fito ki fad’a min abin da ke ranki, zai fi min sauki". Jiki na ne na ji yayi matuk’ar sanyi da maganganun da yaya Faruk ya fad’a min, yanzu gaskiya ba k’aramin girman yaya Faruk nake gani ba. "yaya insha Allah ba za ka same ni da aikata haka ba". Murmushin jin dad’i yayi wanda hakan ya nuna a fuskar shi. "Teemah, kinga kin sa na koyi surutu duk saboda son ki" ya fad’a da alamar wasa. Dariya nayi nace "Ni ba ruwa na yaya". Girgiza kai kawai yayi bai ce min komai ba. Haka muka ci gaba da zance jefi-jefi, yana k’ara jaddada min irin son da yake min. Tambaya na fara yi ma kaina "wai yaya Faruk wani irin so yake min haka? ni kaina na san ba ni da amsar amma alamu sun nuna ba k’aramin so yake min ba. Muna cikin haka ne, yaya Khalil yayi sallama ya shigo falon, ka sa ‘boye mamakin shi yayi ganin mu tare da yaya Faruk a kujera d’aya muna hira. Hannu ya mik’a mishi suka yi musabaha kana ya nemi guri ya zauna. Yaya Faruk ne ya kalle shi yace "Ashe ba ka nan, shi yasa ban ga motar ka ba" "Na d’an fita ne, naje gurin friend d’ina" yaya Khalil ya ba shi amsa. "Ok" yaya Faruk ya fad’a a gajarce. Ci gaba yayi da min Magana k’asa-k’asa yana fad’a min gobe zai koma Abuja, kar in manta in mishi Samosa da Spring roll d’in in ba Ummu ta ajiye mai, zai biyo ya amsa. Sauraren shi kawai nake yi ba tare da n ace komai ba saboda na ga yaya Khalil ya maida hankalin shi gare mu. Shi kuwa yaya Khalil kallo ya bi mu dashi ganin yadda mu ke Magana k’asa- k’asa, yana so ya tabbatar da zargin da zuciyar shi take yi akan mu. "Tun yaushe yaya Faruk da Fatima su ka shirya? An yaya babu wata alak’a tsakanin yaya Faruk da Fatima kuwa? Duk wannan tambayar da yake yi ma kanshi yasan ba mai ba shi amsar sai Faruk ko Fatima, shi kanshi yasan ba zai iya tunkarar yaya Faruk da wannan zancen ba, gwara dai ya tambayi Fatima. Kallan tsadadden wrist watch d’in shi yayi wanda ke d’aure a hannun shi, kallan time yayi ya juyo ya kanne min ido ya ce min cikin murya k’asa-k’asa "Teemah, zan tafi, nasan gobe in nazo ba zan same ki ba, mai za ki bani wanda zan dinga tuna wa dake" ya tsura min ido yana jiran ji mai zan ce mai, shi ko kunyar yaya Khalil ba ya ji. Murmushi nayi nace "yaya ni ban san me zan ba ka ba, amma dai zan maka addu’ar Allah ya kai ka lafiya, ya kuma baka nasara a aikin ka". Lumshe ido yayi saboda yadda yaji dad’in addu’ar da na mishi. "Na gode Teemah da wannan addu’ar taki, ko ita kad’ai ta wadatar dani". Had’a ido muka yi da yaya Khalil ya sakar min murmushi, saurin kau da ido na nayi dan nasan yau zan sha tsokana a gurin yaya Khalil. Mik’ewa yayi yace "Bari in shiga gurin Ummu mu gaisa, sai mun yi waya". "Ok sai mun yi waya" na ba shi amsa. Hannu yaje ya ba yaya Khalil suka yi musabaha yace "Khalil bari in lek’a gurin Ummu, gobe zan koma Abuja, may be ba ka nan, kana school". "Gaskiya may be ba za ka same ni ba, gobe da wuri nake so in shiga school". "Don’t mind, sai na dawo daga Abuja kenan". "Safe journey yaya Faruk" "Thanks Khalil" ya fad’a ya nufi d’akin Ummu. Samun ta yayi tana zaune tana muraja’ar Alk’ur’an, sanye da medicated glass a fuskar ta. Sallama yayi ya nemi k’asan carpet ya zauna kusa da ita. Amsa masa tayi da murmushi a fuskar ta. Gaisawa suka yi ta tambaye shi ya su Momi, Daddy da Anisa. Amsa mata yayi da suna nan lafiya. Ce wa tayi ya fad’a ma Momi tana nan shigowa wannan sati. Hira suka ci gaba dayi, a ciki hirar ne yace "Ummu gobe zan koma Abuja" "Da wuri haka Faruk, ni ina sha zaka yi mana kwanaki a Kaduna". "Ummu da kwana biyu na nemi permission zanyi saboda prospond d’in tafiyar mu da aka yi". "Allah dai ya taimaka, gwara da ka fad’a min da wuri, gobe sai in maka dambun naman ka tafi dashi". Yau tsintar kanshi yayi da kunyar Ummu duk da ba ta san me ke tsakanin shi da Fatima ba, yana mai k’ara ganin girman Ummu na yadda take nuna kulawar ta gare shi. "Ummu da kin barshi, saboda Fatima za ta min Samosa da Spring roll in tafi dashi, gobe zan biyo in amsa". Dad’i ne ya kama ta ganin ce wa Fatima ce za ta mishi Snacks ya tafi dashi, hakan na nuna yanzu sun shirya kenan. "Faruk ai Snacks daban, danbun nama daban, ka biyo gobe sai ka amshi duka". "Ummu na gode, Allah ya k’ara girma". "Amin Faruk, amma na sha ce maka in na maka abu ba godiya a tsakanin mu". "To Ummu bari in k’arasa gida" "Ka gaishe su" "Za su ji". Yana fito wa daga d’akin Ummu, d’aga mana hannu yayi ya fita daga falon. Yaya Khalil ne ya dawo kusa dani yana kallo na. Ni kaina kallon da yake min nasan akwai Magana a bakin shi, sai ban nuna mishi ba. Dariya nayi ganin yadda yake min kallon tuhuma yana murmushi. "yaya Khalil wai lafiya wannan kallon" Bai ba ni amsar tambaya ta ba, sai ce min yayi "Sister kun sa ni a confusion" "Ni da wa?" na tambaye shi. "Ke da yaya Faruk" "Da aka yi me?" Hararar wasa ya min yace "Fatima kinn gane abin da nake nufi, amma tun da kin nuna ba ki fahimta ba, bari in miki filla-filla". Ci gaba yayi da cewa "Fatima wai yaushe kuka had’e da yaya Faruk ban sani ba? na fara zargin ko akwai wata alak’a a tsakanin ku, sister tell me the truth". In akwai wanda ya cancanta yasan alak’ar mu da yaya Faruk bai wuce yaya Khalil da Anisa ba, sai dai kash, hakan ba zai yiwu ba, dan muddum yaya Khalil ya ji maganar nan kamar kowa yaji ne a family, hakan na nufin dole in amince da yaya Faruk duk da har yau zuciya ta ba taji wani alamu na kamuwa da son shi ba, ya zama min dole in bar maganar tsakanin ni da yaya Faruk duk da nasan duk daren dad’e wa dole a ji abin da ke tsakanin mu, ina fatan a lokacin na yanke hukunci tsakanin amincewa dashi ko akasin haka. Yaya Khalil ne ya katse min tunanin da nake yi. "Sister tunanin me kike yi ne?" "No ba tunani nake yi ba, ni ba abin da ke tsakanin mu ni dashi, kawai dai yanzu muna shiri ne, shi yasa ka ke ganin kamar akwai wata alak’a a tsakanin mu". Kallon tuhuma ya min yace "Kin tabbata abin da kika fad’a min gaskiya ne". "haka yake yaya Khalil". Girgiza kai kawai yayi amma ba dan ya yadda da abin da na fad’a mai ba. Tashi yayi yana cewa "bari in je gurin Ummu, na ga ban gan ta a falo ba". "Ni ma yanzu zan tashi in shirya, lokacin makaranta ya kusa". "Ok ki biya ma Anisa sai driver ya kai ku, akwai abin da zan yi ne yanzu, zan zo in d’auke ku in time d’in tashi yayi". "To shi kenan, sai kazo" na mik’e na tafi d’aki, shi kuma yaya Khalil ya tafi gurin Ummu. Kamar yadda yaya Khalil ya mana alk’awarin zuwa d’aukan mu idan aka tashi, hakan ce ta kasance, shi yazo d’aukar mu. A hanyar tafiyar mu muka ce ya biya damu bakery ya siya mana ice cream sannan yace mu za’bi abin da muke so. Beaf bread da pizza na d’auka, Anisa kuma ta d’auki Shawarma da sponge cake, shi kuma yaya Khalil ya d’auki meat pie da burger, gurin biya yaje ya biya sannan ya fara sauke ni a gida kafin ya tafi kai Anisa. Tun bayan sallar asuba, na fara had’in Samosa da Spring roll, sai da na tabbatar na gama, na d’auki had’in na sa a fridge, ko a lokacin har gari ya waye. Wanka na je na shiga, bayan na fito ne na shirya cikin cotton material kalar purple wanda ya sha d’inkin bit work, na d’akko gyale na light purple na yafa, na sa flat shoe, na rataya jaka ta side bag mai launin purple. Gaskiya ni kaina nasan kwaliyar ta amshe ni sosai. Fitowa nayi na tarar da Ummu da Abbu zaune a dining area suna kalaci, d’aya daga cikin kujerun dake zagaye da dining table d’in na nemi guri na zauna. "Abbu Ina kwana, Ummu an tashi lafiya?" "lfy lau Auta" Ummu ta amsa. Murmushi Abbu yayi yace "Fatima kin tashi lafiya?" "lafiya lau Abbu". Juyawa nayi ina tambayar Ummu "yaya Khalil bai tashi ba ne?" ‘"Ina jin bai tashi ba, dan ban ji motsin shi ba, ina jin bai da lectures d’in safe ne". Abbu ne ya kalle ni yace "Tun da na ga kin shirya, in kin gama break fast d’in ki same ni a falo, sai in yi dropping d’in ki, akwai in da na ke so in je da safen nan, tun da na ga Khalil bai tashi daga barci ba" Amsa masa nayi "To Abbu". Tashi yayi ya koma falo yana kallon labarai. Kallon Ummu nayi na ce "Ummu, in yaya Faruk yazo, Samosa da Spring roll na cikin fridge sai ki ba shi". Ummu murmushi tayi tace "Har kin yi kenan, gaskiya kin kyauta". "Tun bayan sallar asuba na fara yi saboda ina gudun kar in makara". Dariya Ummu tayi tace "Lallai kin yi k’ok’ari, Auta an shirya da yaya Faruk d’in ta kenan, ba sauran fad’a". Cikin shagwa’ba na turo baki nace ‘ko da shi yake ja, amma yanzu mun shirya". "Ai hakan yafi kyau Fatima" ta mik’e ta tafi falo. Bayan na gama ne naje na sanar da Abbu na gama, tashi yayi muka nufi parking space ya d’auki motar shi muka tafi. Sai da ya kai ni har department d’in mu ya sauke ni sannan ya tafi. Can ‘bangaren yaya Faruk bayan ya shirya ya tafi side Dadi, inda ya samu Momi a can. Yau Dadin bai samu zuwa aiki ba, kasancewar bai jin dad’in jikin shi. Gaishe su yayi suka amsa. Sun d’an ta’ba hira sannan ya mik’e da niyyar tafiya. Addu’a Dadi da Momi suka yi ta mishi da fatan nasara a tafiyar da za suyi. Kud’i ya ciro a wallet d’in shi ya ajiye ma ta. Tana matuk’ar son Faruk saboda son kyautata ma iyaye da ‘yan uwa, ga kyauta, fatan ta Allah yasa ya ci gaba da wannan halin nashi. Momi sai sa mishi albarka take yi irin wacce iyaye ke ma ‘ya’yan su. Sallama ya musu, ya nufi ma’ajiyar motoci, ya shiga ya nufi gidan mu. Ko da ya shiga falon, Iya Talatu ya samu a falo tana mopping, gaishe ta yayi ya tambaye ta "Ina Ummu take?" Amsa mishi tayi "Tana kitchen, ko in kira maka ita ne? "A’ah ki bar shi Iya Talatu, bari in k’arasa gurin ta". Kitchen d’in ya nufa ya same ta tana juye dambun naman da ta mishi a plastic mai d’an zurfi. "Sannu da aiki Ummu" "yawwa Faruk, ba dai har ka shirya ba ba?". "Yau da wuri nake so in tafi, akwai abin da zanyi ne in na koma". "Ka ga ko yanzu na gama dambun naman, bari in d’akko maka Snacks d’in da Fatima ta ma ka" Wani farin ciki ne ya kama shi a lokaci guda, ganin yadda Fatima ta tashi ta mishi snacks d’in kamar yadda tayi alk’awarin za ta mai, hakan na nuna kenan ta damu dashi. Bai san lokacin da murmushi ya su’buce mai Abuja D’akko mishi tayi ta samu d’an k’aramin basket ta jera mai a kai. Kud’i ya ciro a wallet ya ba ta. Ummu k’in amsa tayi tace "Haba Faruk, ni kam yau kayi hak’uri b azan amsa ba, tun kullum cikin ba mu ka ke yi, Allah dai ya k’ara bud’i". "Ummu plss ki amsa ba yawa". Murmushi tayi tace "Faruk ai ba raina wa nayi ba, wani lokacin na amsa, amma Allah a yanzu ba zan amsa ba". Bai son suna jayayya shi yasa ya hak’ura, amma ba haka yaso ba, yaso ta amsa. Sallama ya ma ta ya kana ya nufi Abuja. [4/20, 20:29] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan Shafin na ba ku shi ne kyauta* *Rabi’atu sk msh* (llileee) (Marubuciyar Haramtaccen zama) _Ummerherny Nerserllerh_ (Marubuciyar Da Aurena A Kanki) _Ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke, Allah ya bar zumunci_. _BA ABIN DA ZANCE MUKU SAI GODIYA_ *Hak’ik’a ina jin dad’in yadda kuke k’ok’arin ba da amsar kun a question of the day, ba da amsar ko ba daidai ba ne zai sa mutum ya k’aru, saboda shirin tambayoyin musulunci ne, ta hakan nima nake k’aruwa saboda nobody is perfect, ba wanda ya wuce kuskure* *Da fatan za a ci gaba da min gyara a cikin shirin, dan har yau nima d’aliba ce.* *Xarah Auwal*(Ass Queen) *Maman Walida* *Sakina iliyas* (Maman Khalil) *Ku ne ku ka ba da amsar daidai na question of the day, A matan manzon Allah (s.a.w) wacce ta lurar da manzon Allah (s.a.w) game da wata dabara da zai jawo hankalin sahabban sa a ranar hudaibiyyah, kuma dabarar taci nasara sosai itace Ummu Salma, cikakken sunan ta shine Ummu Salma Hindu ‘yar (bn) Umayyata.* *TUNATARWA* _* Ka/ ki zamo mai hikima, amma ka/ki yi amfani da hikimar ka/ki ba tare da ka/ki ‘batar da wasu ba_. _*Ka/ki zamo mai adalci, amma kar ka/ki ce sai ka/ki iya wa kowa_ _*Ka/ki zamo mai neman na kai, amma ka da ya kai ka/ki ga neman haram._ 45&46 Ko da ya isa Abuja, basket d’in da Ummu ta bashi ya ajiye a falo, bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito. Canza shigar shi yayi zuwa k’ananun kaya. Fridge ya wuce ya d’auki favourite d’in shi wato exotic da glass cup d’in da ke ajiye a saman fridge d’in. 1-sitter ya nemi guri ya zauna ya d’akko dambun naman da Ummu ta zuba mishi ya d’auka ya fara ci, a lokaci d’aya yana kora wa da wannan ruwan exotic din. Wayar shi da ke gefen shi ya d’auka yayi dialling d’in numban Mus’ab, bugu d’aya, ana biyu Mus’ab ya d’auka. "Asslamu alaikum Bregadier Faruk na Teemah" abin da Mus’ab ya fara fad’a kenan. Murmushi yayi don yasan Mus’ab so yake yi ya zolaye shi, amsa wa yayi "Wa’alaikumus salam, kana gida ne?". "ina gida, ba dai har ka dawo ba?". "eh na dawo, ina nan zuwa". "Ok sai kazo". Remote ya d’akko ya canza channel d’in zuwa tashar Aljazeera yana kallon labarai. Bayan ya gama abin da yake yi ne ya kasha tv d’in, ya d’auki wannan d’an basket d’in ya nufi block d’in Mus’ab. Sallama yayi ya nemi d’aya daga cikin kujerun ya zauna, gaba d’ayan su suna kallon wani hausa film mai suna *HAKK’IN RAI* wanda ake haskowa a tashar Arewa Tv. Maryam ce ta gaishe shi tana tambayar shi mutanen gida. Amsa mata yayi da duk suna lafiya. Nana ce cikin zazzak’ar muryar ta gaishe da yaya Faruk. D’ago kai yayi ya kalle ta wanda sai a lokacin ya lura da ita. Da fara’a a fuskar shi ya amsa mata yana cewa "ashe ba ki koma school ba?". "ban koma ba, sai next week". "Ok" ya amsa a gajarce. Yamutsa fuska yayi ya maida kallo shi ga Mus’ab yace "wai me kuke fahimta ne a hausa film, ni ban ga abin kallo ba, saboda a tunani na basa film mai ma’ana da wanda za a k’aru, sannan ba yin film akan al’adar su". Mus’ab ne ya cewa "Ni ma dan ba inda za ni ne, shi yasa na zauna ina kalla, kuma madam na so, dole in biye mata mu kalla". Maryam ce ta kar’bi zancen da cewa "Mu dai ba za mu k’i yaren mu da al’adar mu ba duk lalacewar su, kuma Hausa film d’in da kuke Magana, ai akwai masu ma’ana da kuma wanda suke nuni da al’adar su, kamar wannan film d’in da kuke gani da aka sa a Tv, ya ta’allak’a ne akan ku masu kaki, duk da ba duka aka taru aka zama d’aya ba, amma shi wannan d’an sandan saboda kwad’ayin kud’in da zai samu yasa ya d’auki wanda bai da laifi ya kai aka harbe shi, ya saki wanda yake da laifi saboda ya bashi kud’i, k’arshe kud’in shi bai mai amfani ba saboda rai da yakai aka kashe, kaga kenan *Hakk’in Rai* ba zai bar mutum ya samu kwanciyar hankali ba". Mus’ab ne ya kalle shi da alamar tsokana yace "mutumin ai ban zaci za ka dawo da wuri ba, ina sha ai Fatima za ta rik’e ka". Murmushi yayi yace "kaima kasan ba yadda zanyi ne na dawo, amma ni ban k’i in zauna gurin Teemah na ba". Maryam ce ta sa bakin ta a zancen nasu tace "wai Bregadier, kai nake jin kana maganar budurwa? Kai da kake cewa ‘yan mata ba sa gaban ka, amma ko wacece Fatiman nan, ta burge ni da ta kama zuciyar soja" ta k’arasa zancen tana dariya. Bai ce mata komai ba illa murmushi da yayi. Basket d’in da ke d’auke da snacks d’in ya ajiye a gaban Maryam yace "Madam in ba damuwa plsss ga Samosa nan da spring roll za ki taimaka ki soya min, Teemah nasa ta min a d’anyen shi, may be ma ya lalalce saboda naji tace yana da saurin lalacewa". Mus’ab cikin tsokana yace "ai ko ya lalace sai an soya kaci shi, tun daga hanun masoyiyar ka ya fito, ba zai maka komai ba illa k’ara maka son ta da zai yi". "kan ka ake ji, naga alamar ka maida ni wani kakan ka" yaya Faruk ya fad’a. Maryam ce ta bud’e food flask d’in taga bai yi komai ba, kallan Nana tayi tace "Nana d’auka kije kitchen ki soya mai, sai ki zubo mishi a plate yaci a nan". "To Anty Maryam" ta mik’e ta d’auki basket d’in ta nufi kitchen. Sai a lokacin ya d’aga kai ya k’ara kallon Nana, yana mamakin shirun ta yayi yawa, dan tun da aka fara maganar ba ta sa bakin ta ba, illah wayar ta da take pressing, bin ta yayi da kallo san da ta nufi kitchen, yana yabawa da natsuwar ta. Ko da ta shiga kitchen d’in, mai ta d’aura akan wuta, sai da yayi zafi sannan ta fara soya wa. Cikin ‘yan mintuna ta gama soyawa ta zuba a glass plate, ta had’o da ginger drink d’in da ke cikin fridge wanda sai k’anshin citta da lemun tsami da yake tashi. Tana zuwa ta ajiye a kusa dashi tace "yaya Faruk gashi". Da murmushi a fuskar shi yace "sannu da aiki khadijah, an sa ki aiki ko?" Fad’ad’a murmushin ta tayi tace "ba wani aiki yaya Faruk". D’aukar wayar ta tayi dake kujeran da ta tashi ta fara tafiya, da alama d’aki za ta tafi. Yaya Faruk ne ya kira sunan ta "Khadija". Juyowa tayi ta kalle shi da oily eyes d’inta ta amsa "Na’am yaya Faruk". "ya za ki tafi ba ki ci ba". Rasa me za tace mai tayi, dan haka tace "Samosa da spring roll bai cika damu na ba, na k’oshi ne yaya". Kallon ta yayi kawai yace "Ok, za ki iya tafiya". Kamar jira take yi, ta nufi d’aki ba tare da ta k’ara juyowa ba. Mus’ab ne yace "ko da mu ba a mana tayi ba, bazan yi zuciya ba, ci zan yi in ji ko gimbiyar hannun ta na da zak’i". Girgiza kai kawai yaya Faruk yayi saboda yasan in ya biye ma Mus’ab sai ya sa shi Magana don ya fi shi Magana. Yaya Faruk ne ya kalli Maryam yace "bismillah madam, zo ki d’ibi yanda zai ishe ki". Cikin wasa tace "da ba dan na k’oshi ba, da sai na ci naji, amma dai yanzu a min hak’uri soja, snacks d’in nan ba zai shiga ba". Shiru ya mata saboda yasan Maryam da tsokana kamar mijin ta, in ya biye musu sai sun sa shi Magana. Mus’ab ne ya d’auki d’aya yasa a bakin shi, lumshe ido yayi ya bud’e ya kalli Maryam da ta mai da hankalin ta ga tv. "Maryam! Mus’ab ya kira ta. Kallon shi tayi tace "ya aka yi ne Nurul k’albi". Cikin tsokana yace "gaskiya kar ayi ba ke, bud’e bakin ki in sa miki ki ji, snacks sai kace a bakery, kice dole mutumin ya rud’e akan ta". Dariya tayi tace "tun da naji ka yaba, to lallai Fatima ta ciri tuta". Bud’e baki tayi, Mus’ab ya d’auki samosa ya sa mata a baki. Taunawa ta fara yi a hankali tace "wow! Delicious, amma dai Faruk catering Fatima take karanta ko?". Ta’be baki yayi yace "Santi take karanta". Gaba d’ayan su suka sa dariya, saboda sun san rama tsokanar da suke mai yayi. Mik’e wa yayi yace "Ni kin ga tafiya ta, kai da matar ka kun tasa ni a gaba sai tsokana ta kuke yi akan Teemah, bari in na koma Kaduna sai na fad’a mata abin da kuke min". "Tuba muke yi na Teemah" Mus’ab ya fad’a yana dariya. Tafiya ya fara yi yana cewa "Maryam sai anjima". "To sai anjima Faruk". Mus’ab ne ya mik’e dan ya taka mai. Nana Khadija tun da ta shiga d’aki, ta fad’a kan gado, ta rasa abin da yake mata dad’i tun da taji an fara zancen Fatima, Me hakan ke nufi? Me yasa za taji haushi dan yaya Mus’ab da Anty Maryam suna tsokanar yaya Faruk akan Fatima? Mai yasa ba ta ci snacks d’in da ta soya ba, duk kuwa yadda take son Samosa da Spring roll? Hakan na nufin dan ya fito daga hannun Teemah ne kamar yadda ta ji yaya Faruk na kiran ta. Duk wannan tarin tambayoyin ba ta da amsar su. Mai yasa yaya Faruk ke burge ni? ta tambayi kan ta. Zuciyar ta ce ta ba ta amsa akan saboda yana da irin qualities d’in da kike so a gurin namiji, shi yasa kika ji yana burge ki... Ganin tunanin da ta fara bai da wani amfani yasa ta d’auki wayarta ta kunna cool music tana saurare, a haka bacci ya d’auke ta. *KADUNA* Karatun mu ya ci gaba da tafiya da dad’i da ba dad’i saboda matsalolin high institution da ba za a rasa ba. Yau sanye nake da cotton material kalar pink, yayin da nake sanye da white hijab & flat shoe, jakar dake hannu na kalar pink rik’e a hannu na. Magana na fara ma Halima wacce ta maida hankalin ta ga rubutun da take yi na ce "Halima bari in lek’a cikin asibiti, kwana biyu ba na jin dad’in jiki na". Tsayar da rubutun da take yi ta maida hankalin ta gare ni tace "Ayya Sorry Fatima, ki jira in k’arasa rubutun da nake yi sai in raka ki". "kar ki damu Halima, ki ci ga ba da rubutun ki, nima ba dad’e wa zanyi ba". "Sai kin dawo, Allah ya k’ara sauki". "Amin" na amsa mata kana na fita daga class d’in. Ko da na k’arasa asibitin, ba da kati na nayi a record room, ba a d’au wani lokaci ba naji an kira suna na, bayan naje ne ta tura ni room 5. Ko da na isa gurin, ba wasu mutane, dan haka ba a d’au lokaci ba aka kira suna na. Yau sanye yake da wani tsadadden yadi kalar ruwan madara sa’banin ran nan da na ganshi da shigar likitoci, yana sanye da d’an k’aramin medicated glass a fuskar shi, sai k’amshi dake tashi a room d’in. Zama nayi a kujerar da marasa lafiya ke zama, yau ma rubutu yake yi ba tare da ya d’ago ya kalle ni ba. Ganin bai ce min komai ba yasa nace "Ina wuni Dr". "lfy lau, me yake damun ki". Har a wannan lokacin bai d’ago ya kalle ni ba. "fever nake fama dashi kusan 1 week kenan". Sai a lokacin ya dakatar da rubutun da yake yi ya kalle ni. Kin ce kin kai kusan 1 week kenan kina fama da fever, bayan shi ba inda yake miki ciwo?" Ya tambaye ni. "gaskiya babu" na amsa masa a tak’aice. Hannun shi yasa a kan wuya na don jin yanayin temperature d’ina. Wani irin shock na ji san da ya ta’ba ni, ko dan shi ba muharrami na ba ne yasa naji haka? na tambayi kaina. Wata farar takarda yayi rubutu a jiki ya mik’o min yace "ga wannan takardar sai ki je lab a miki test duk da nafi tsammanin malaria ce ke damun ki, in kin yi test d’in sai ki kawo min result d’in in gani". "na gode Dr". "aikin mu ne, kar ki damu". Sallama na masa na tafi. Hakan ta kasance, washegari nayi sammakon zuwa aka d’ebi jini na a laboratory suka ce an jima in dawo, na tafi class, muna gama lectures na first period na koma. Da na amshi result d’in a laboratory na wuce na kai kati na a record room, tambayar su nayi Dr Abubakar nake son gani, sun fad’a min cewa yau sai da rana yake da aiki, dan haka na koma class da niyyar in in mun gama lectures kan in tafi gida sai in zo in ganshi. Muna gama lectures d’in na je na musu Magana kasantuwar sun d’auko folder na tun da safe, dan haka suka ce in wuce room 4 yau a nan zai ga patient. Ina zuwa ban samu mutane ba kasancewar rana ne, hakan yasa na wuce d’akin direct. Sallama nayi na nemi guri na zuna Amsa min yayi da murmushi a fuskar shi. "Fatima ko? ya tambaye ni. Mamaki ne ya kama ni yadda aka yi har ya rik’e suna na. Folder na ya d’akko ya ajiye a gaban shi, tambaya ta yayi na yi test d’in da ya ba ni? Mik’a masa takardar nayi nace "eh nayi". Sai da ya gama nazarin takardar sannan ya fara rubutu yace "Maleria ce ke damun ki, zan rubuta miki magani". Takadar ya mik’o min yace in amsa maganin a pharmacy. "Allah ya k’ara sauk’i student" "Amin Dr". Sallama na mishi na bar office d’in. Tun daga wannan lokacin in ban da lafiya ya zamana gurin shi nake zuwa ya duba ni, sai dai in ba ya nan ne nake ganin wani likitan. Lokaci na ta tafiya in da muka cinye zangon karatun mu na farko muka fara rubuta jarabawar mu ta farko. Muna chat da yaya Faruk amma ba sosai ba, kasancewar ya ce min in da suke ba network mai kyau. Duk san da muka had’u a chat yana k’ara jaddada min irin son da yake min. A can ‘bangaren yaya Faruk sai ya zama sun fara sabawa da Nana Khadijah kasancewar yana lek’a wa gidan su Mus’ab in kad’aici ya dame shi. Duk da in yaje ba wata hira suke yi ba kasancewar ita ma Magana ba ta dame ta ba amma yana yabawa da natsuwar ta da kamun kan ta. A haka har ran tafiyar su tazo suka tafi garin Adamawa. [4/21, 22:24] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin na sadaukar dashi ne ga masu son wannan novel d’in, masu min Magana ta pc, masu kira na daga wasu gari, ‘yan faceebook, ‘yan whatsapp, da duk group d’in da ake posting d’in wannan novel d’in da wanda na sani da wanda ban sani ba, na nesa da na kusa* *Ba abin da zance muku sai dai fatan alkhairi, Allah ya bar zumunci* *QUESTION OF THE DAY* _A halayen larabawa kafin musulunci, mai suka kasance suna bauta ma wa? saboda me yasa suke kasha ‘ya’yayensu?_ 47&48 Bayan gama jarabawar mu na zangon farko, aka bamu short break na hutun zangon. Muna zaune a gurin shak’atawa ni da Ummu muna hira, motar gidan su Anisa ce ta shigo. Bayan ta fito daga motar ne ta nufo in da muke tayi tana murmushi. Gaisawa suka yi da Ummu kana na gaishe ta, muka nufi main parlour. Kitchen na shiga na d’ebo drinks da snacks a d’an k’aramin tray da glass cup. Ajiyewa na yi gaban ta, na nemi guri na zauna. Da fara’ar ta tace "Fatima kwana biyu ba ki lek’o mu ba, tun da kun samu hutun first semester, in zan tafi sai mu tafi tare". "Bari in je ciki Momi, in za ki tafi sai mu tafi, Ummu kya fad’a ma Abbu in ya dawo". Mik’ewa nayi na nufi d’aki na don in basu guri. Da na shiga d’aki, kaya set 5 na d’iba na sa a jaka. Momi sun dad’e a falo suna hira kana ta kira ni muka tafi. Tun da naje gidan su Anisa muke hira, mu yi ta labarin ‘yan course d’in mu da rayuwar school life. Haka yaya Khalil ke zuwa mu zauna a parlour ko a garden muyi ta hira. Gaskiya ina jin dad’in yin hutu a gidan su Anisa. Kwana biyar nayi a gidan na koma gida. Mun koma school in da muka shiga zango na biyu, karatu ya k’ara zafi fiye da zangon farko, komawar mu da 2 Weeks result ya fito, GP d’ina yayi kyau, dad’in da naji shine ban da wani matsala na carry over ba, da muka had’u da Anisa ma ta fad’a min GP d’in ta yayi kyau. Mun yi nisa a zangon aka fara maganar siwes (Industrial training), tunani na fara yi inda zanyi siwes d’in. Zuciya ta ce ta ba ni shawarar in sa Asibitin school d’in mu dan lecturers d’in mu sun fad’a mana ana samun experience a can. Yau ta kasance ranar lahadi, yaya Khalil ne ya shirya cikin tsadadden yadi kalar ruwan k’asa, yadin ya matuk’ar yi masa kyau. Ta slice window na hango shi ya fito daga side d’in shi ya nufi parking space zai shiga mota. Da sauri na fito na k’arasa gurin shi ina cewa "yaya Khalil ina zaka ne? na ga wannan kwalliyar kamar gurin Anty na za ka, duk da ban san ko wacece ba". Ta’be baki yayi yace "Kin ga Auta ki bari in na dawo sai muyi maganar, in ba haka ba sai ki hana ni fita da maganar ki". Dariya nayi nace "kai yaya Khalil daga fad’ar gaskiya". Shi ma dariya yayi yace "To yanzu dai shi kenan sister, tun da kina so in samo miki Anty, zan bincika in gani, yanzu dai bari in tafi, sai na dawo". "Sai ka dawo yaya Khalil". Shiga motar yayi ya kunna ya bar gidan yana d’aga min hannu, d’aga mishi hannu nayi na koma cikin gida. Yana isa gidan, ya danna hon. Mai gadi ne yazo ya bud’e masa ya shiga da motar. Samun Anisa yayi a balcony d’in gidan, in da aka k’awata gurin da kujeru da tebur a can gefen gidan. Gurin ya k’arasa yana sakar mata tsadaddan murmushi, ya nemi guri ya zauna. Gaishe shi tayi ya amsa mata, tambayar ta yayi ko Momi na ciki?. Amsa masa tayi "Tana ciki". "Bari in shiga mu gaisa, yanzu zan dawo, yau akwai sabon labari da zan baki" ya fa’da da alamar wasa. "Sai ka fito". Tashi yayi ya nufi cikin falo d’in. Ko da ya shiga parlour d’in ba kowa sai k’arar tv dake aiki shi kad’ai a parlour d’in. Hango ta yayi tana sakkowa daga upstairs d’in dake parlour d’in. "Khalil yaushe ka shigo, maimakon ka hawo sama ina can". "shigowa na kenan". Momi, Ina wuni". Yaya Kalil ya gaishe ta. "lafiya lau, ya su Hajiya da Fatima". Momi ta amsa masa. "Suna nan lafiya". "Haule!" Momi ta fara kiran mai aikin ta. Cikin ladabi ta amsa ta tsuguna tana cewa "Gani Hajiya". "Drinks da ruwa da abinci za ki kawo ma Khalil". "Toh Hajiya" Haule ta amsa ma ta. Khalil ne yayi saurin kar’ban zancen da cewa "Momi ta bar shi kawai, zan koma gurin Anisa ne, tana can balcony". "Ba ayi haka ba, ke Haule je ki d’akko ki kai mishi can". "Toh Hajiya" Haule ta amsa cikin ladabi ta bar parlour d’in, ta nufi kitchen d’in. "Kace ba za ka zauna muyi hira ba, za ka tafi gurin mutuniyar ka" Momi ta fad'a "Ai zan dawo ciki Momi". "Sai dai na gan ka kawai, nasan sallama ce za ta shigo dakai, in ka had’u da Anisa ai sai Allah in kuka fara zancen ku". Dariya yayi ya bar falon, Momi kuwa neman guri tayi ta zauna. San da ya koma, samun ta yayi tayi playing ‘din wak’ar Rihana da tayi mai suna *if its love* bin wak’ar take yi a hankali kamar ita ta rera wak’ar. Murmushi yayi ganin yadda take bin baitin wak’ar, ita ma murmushi tayi tace "yaya ya aka yi ne? naga kana murmushi". Na ga ai kina son wannan wak’ar ne". "yaya Khalil ai ta iya wak’a ne" Haule ce ta k’araso ta ajiye tray d’in a kan table d’in, ta bar gurin. Kwalin chivita ya d’auka yayi shaking, sannan ya tsiyaya a glass cup d’in. Sai da ya fara sha kana ya ajiye yana kallon ta. "Anisa! ya kira sunan ta. Amsa masa tayi tana jiran ji mai zai ce ma ta. "Anisa zan bayyana miki abin da ke zuciya ta ne, ina so ki ba ni shawara". Ita dai bin shi take da kallo, saboda tasan in yaya Khalil zai yi Magana mai mahimmanci, manta wa yake da wani abu wai shi wasa, dan haka ta bashi dukkan hankalin ta. Ci gaba yayi da cewa "Anisa akwai yarinyar da na dad’e ina son ta, mun shak’u da ita, da farko ban d’auka cewa son ta nake yi ba, na d’auka *shak’uwa ce* sai daga baya na gane son ta nake yi, shine nake neman shawarar ki akan yadda zan tunkari yarinyar in fad’a mata". Wani abu ne taji ya tsaya ma ta a zuciyar ta, wanda ta rasa ko na menene, ba ta so yaya Khalil ya fahimci tana cikin wani hali. Cikin dauriya ta fara da cewa "Ina ganin yaya Khalil gwara ka fad’a ma yarinyar, barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa, kuma tun da kace kun shak’u da ya yarinyar ina ganin ba za ta k’i amsar tayin soyayyar ka ba, yaya Khalil ba wai zan yaba ka bane, amma ina ganin duk yarinyar da ka fito ka ambata mata kana son ta, za ta amince dakai, ka je ka fad’a mata". Wani irin murmushi dad’i yayi, saboda amsar da yake son gano wa, ya gano cikin sauki duba da re-action d’in Anisa d’in. "Anisa! Ya kira ta a karo na biyu. Wannan karan ba ta samu damar amsawa ba, ganin yadda ya zuba mata ido. Bai damu da amsawar ta ba yaci gaba da cewa "Anisa ba kowa bace yarinyar da nake nufi illah Anisa". Saurin kallon shi tayi tana jiran k’arin bayani. Lura da hakan da yayi yasa yace "Anisa ke nake nufi, ke nake so…., ina fatan za ki amshi tayin soyayya ta da na miki da hannu bibbiyu". Saurin rufe fuskar ta tayi da tafukan hannun ta. Cikin tsokana yace "Bari in tashi in tafi, tin da ba a amince da ni ba". Da sauri ta bud’e fuskar ta tace ‘kai yaya Khalil ni ban ce haka ba". "Kin amince kenan?". Sunkuyar da kan ta tayi tana murmushi kasancewar tana jin kunya ta fito tace mai ta amince. Duk da ya fahimci ta amince dashi, amma yana so ta fad’a da bakin ta saboda zai fi yin marhabun da hakan. Yaya Khalil bai bar gurin ba sai da ya samu amsar shi daga bakin Anisa na cewa ta amince da soyayyar shi. Nan ya dinga fad’a mata yadda yake son ta a zuciyar shi, hira suka ci gaba da yi kamar wanda suka dad’e a soyayya. Da zai tafi ne ya kalle ta yace "Kin san da zan tawo nan, sai Fatima ta tsare ni wai ina zani haka, kamar wanda zai je gurin budurwa, shine n ace mata tun da Anty take so zan samo mata, kinga yanzu in na koma sai in fad’a mata Antin da na mata". Cikin marairaicewa ta fara cewa "Plsss yaya Khalil kar ka fad’a mata, kasan Fatima tsokana ta za ta dinga yi". Dariya yayi yace "Shi kenan tun da ba kya son k’awar ki ta sani, ni nasan Fatima da kan ta za ta gano". "Ni ma ai zan fad’a mata, amma ba yanzu ba". "kunyar ta kike ji kenan, ko su Ummu da Momi ki ke jin kunya su ji". Shiru ta mishi ba tare da ta amsa mishi ba tare da ta ce mai komai ba. Girgiza kai kawai yayi ya sakar mata murmushi ya wuce cikin falo d’in. Cikin parlour d’in yaya Khalil ya koma yayi ma Momi sallama ya fito ya tafi. Fitowar da yayi suka had’u za ta shiga falo d’in, kallon junan su suka yi wanda ke nuni da sak’on da suka isar ma juna sannan ya mata sallama ya tafi. A school, Orientation na musamman aka mana akan Siwes da gurin da ya dace muyi siwes d’in mu. An bamu form mun yi filling, inda muka cike sunan mu, account number d’in mu, Bvn number d’in mu, sai sunan inda za muyi siwes d’in da address, daga k’arshe suka amshi form d’in. K’awancen mu na nan da Aisha amma ba mu cika had’uwa ba, kasantuwar department d’in mu ba d’aya ba, sannan akwai nisa tsakanin mu da department d’in su. Mun fara jarabawar mu na zangon na biyu wannan karan ma cikin nasara, inda aka raba mana takardar siwes inda za mu kai ayi accepting d’in mu, period of attachment d’in 4 month ne za muyi. Halima ce ta tambaye ni inda zanyi siwes d’ina, na fad’a mata a cikin asibitin school zan yi, jin hak ita ma tace bari tasa nan. Naji dad’i hakan da Halima tace nan za tayi, saboda zan so ace akwai wandda na sani a gurin da zanyi a ‘yan class d’in mu. Mun kai namu a asibitin school d’in mu, sun yi accepting d’in mu a d’aya daga cikin siwes student d’in su. Anisa ma jin cewa a cikin school zanyi siwes d’ina yasa ita ma takai takadar ta laboratory dake cikin asibitin. Bayan jarabawar mu da sati d’aya mu ka fara siwes d’in mu ni da Anisa da Halima a Shehu Muhammad kangiwa Medical Center dake cikin Polythecnic. Sanye nake da lapcoat, yayin da nasa farin baby hijab, hakan sai ya k’ara min kyau da shigar. Folder na d’auka zan kai office d’in Dr Abubakar Sadik da Dr Fatima. Sai da na fara zuwa office d’in Dr Fatima na kira sunan patients d’in da ke waje kana na shiga ciki muka gaisa da ita na ajiye mata folder. Gaskiya ina matuk’ar ganin girman Dr Fati kasancewar ta dattijuwa, mai son mutane, asibitin mutane na yabon halin ta ita da Dr Abubakar Sadik. Office d’in Dr Sadik na wuce na kira sunan wanda suke waje, na yi knocking d’in k’ofar. "Yes come in" abin da yace kenan. Sallama nayi na shiga ciki na ajiye mai folder, amsa min sallamar yayi. Gaisawa muka yi cikin wasa kasancewar shi ma na lura yana da wasa, amma shima na lura miskilin kanshi ne wani time d’in. Kallo na yayi yace "Fatima Zarah ko" Sai naji sunan ya min dad’i, ko hakan na da nasaba da dan ba a kira na da sunan ne? "yaushe kika fara Siwes a nan" ya tambaye ni. yau 1 week kenan da na fara, lokacin naji ance kai duty d’in safe kake dashi, ni kuma da duty na rana na fara". "Allah ya taimaka" yace min. Amsa masa nayi "Amin Dr" Kallon folder dake gaban shi yayi yace "Zarah, za ki rage folder d’in nan, ba zan samu ganin duka patient d’in ba, akwai inda zani". "Dr taimakawa za kayi tun da na riga na kawo". Cikin wasa yace "Sai dai in za ki zo ki taya ni". "Sai in taya ka Dr, in dai za ka nuna min yadda zanyi, amma kai zan nuna in patient suka zo kama ni na rubuta musu wrong medicine". Murmushi yayi yace "Kin dai min dad’in baki, zan duba su, amma plss kar a sake kawo folder daga wannan zan fita ne". "Insha Allah, za a kiyaye Dr". Sallama na mishi na bar office d’in. Yau kusan wata na uku a cikin asibitin, mun sa ba da mutane da dama, daga ciki har da patients da suke kawo katin su record room. Mun yi wani irin sabo da Dr na ban mamaki, mutane na mamakin yadda muka saba dashi kasancewar ba kowa ce mace yake kulawa ba. Yanzu haka muke chat dashi, wani time d’in ya kira ni mu gaisa kasancewar muna da number juna. Kusancin mu da Dr yasa na fara jin shi a raina, amma ban sa hakan a raina illah d’auka da nayi shak’uwar da muka y ice ta janyo haka Muna cikin yi siwes ne, result d’in mu ya fito. Naje na duba, wannan karan GP na ya k’aru fiye da firsr semester. A haka har mu ka cinye 4 month a asibitin na gama siwes d’ina muka yi sallama du da ba wai an rabu ba kenan, tun da zan ci gaba da shigowa in mu gaisa ko zan ga likita. Mun sami hutun 1 Week na siwes d’in mu kafin mu yi resuming mu shiga ND 2. Wannan karan Anisa ce tazo gidan mu da niyar yin kwana biyu. Tun da tazo na fahimci kamar akwai soyayya a tsakanin su da yaya Khalil, ganin yadda yanzu take jin kunyar Ummu, idan tana waya kalamen da suke maida wa junan su, da kiran ta da yake yi garden suna hirar su. Sai da na matsa ma ta ne ta fad’a min cewa suna soyayya, amma ba yanzu take so a ji a family ba. Hakan yasa na dinga tsokanar ta ina cewa "Anty na ta kaina, ni zan fara fad’a ma su Abbu da Daddy a bani goron albishir". Haka tayi ta rok’o na akan kar in fad’a musu kunya take ji. Da yaya Khalil ya shigo ina tsokanar shi nace "yanzu shine kamin Anty amma ban sani ba, kuka ‘boye min, nima zan rama". Dariya yayi yace "Sorry Fatima, laifin Anisa ne, da nace zan fad’a miki, cewa tayi ba yanzu ba wai da kan ta za ta fad’a miki". Hararar wasa na mata nace "Kin kyauta Anisa, yanzu ai gashi na sani, tun da ba kya so in Sani". D’aura fuska tayi kamar da gaske tacce "ke ni fa yanzu Antin ki ce, saboda haka sai ki yi biyayya". Duk’a wa nayi nace "Sorry Anti". Gaba d’aya muka yi dariya saboda yadda nayi maganar. Haka yaya Khalil ya zauna muka ci gaba da chapter kana ya mik’e ya fita. Kwana 2 da Anisa tayi naji sun burge ni saboda yadda suke gudanar da soyayyar su cikin so da k’auna. Tana gama kwana 2 ta koma gida. Har yau muna zuwa islamiyya ran weekend, yanzu haka muna jarabawar shiga JSS3. Mun koma school muka fara registration na shiga ND 2, yanzu karatu yafi zafi fiye da ND 1, yanzu ba ni da wani lokacin kaina sai na karatu. Yau Wednesday, mun fito ni da Halima daga MSSN da muke yi duk ran Wednesday, mun fara tafiya ne zamu je masallaci saboda lokacin sallah yayi. Waya ta ce tayi ruri alamar kira ya shigo Sunan wanda na gani ne a jikin screen d’in yasa na saki wani sansanyar murmushi sannan na d’auka. "Assalamu alaikum likita bokan turai". sautin dariyar shi naji yace "Zarah manya, ya kike, ya karatu?" "lfy lau Dr". "ya aiki, ya patents". "Aiki Alhamdulillah, patients kuma kullum cikin su muke". Ci gaba yayi da cewa "yanzu kina ina ne?" "Ina hanyar zuwa masallaci ne". "Ok yau k’arfe nawa za ku tashi daga School?". "Mun yi closing yau, lecturer da zai shigo mana bayan sallah ya bamu group work ne tun last week, saboda ba zai samu shigowa bay ace wanda ba su yi ba, su yi amfani da period d’in shi, gobe zai amsa, already mu mun riga munyi tun last week, yanzu in nayi sallah, zan biya SUG Hall ne, daga nan sai in wuce gida". "In ba zan takura miki ba, bayan sallah mu had’u a fanta fun tun da ba ki da lectures, akwai maganar da nake so mu yi". "Ok sai mun had’u". "Bye, take care" abin da yace kenan ya katse wayar. Bayan gama wayar mu ne na kalli Halima nace "kin san da wa muka yi waya?" Girgiza kaai tayi alamar ba ta sani ba. "Dr Sadik ne ya kira ni, wai yana so mu had’u a fanta fun". "ke dai taku tazo d’aya da shi, in kun had’u ki ce ina gaishe shi’. ‘zan fad’a mai insha Allah". Masallaci muka shiga muka yi sallah, bayan mun fito ne muka wuce cikin SUG Hall muka ci abinci, nan muka yi sallama da Halima ta wuce gida. Direct fanta fun na je na nemi guri na zauna ina jiran k’arasowar shi. [4/24, 21:59] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 _Wannan shafin naku ne ‘yan Kainuwa Writers fans na facebook da kuma fans 10 na whatsapp_ _Ina godiya da son da kuke ma wannan novel d’in, Allah ya bar zumunci_ _INA MUKU JINJINA TA MUSAMMAN_ *Meeynah (Princess of question of the day)* *Ramlah* *Fadeelah* *Kune ku ka ba da amsar tambayar daidai, Allah ya saka muku da alkhairi, ya biya muku buk’atun ku da sauran musulmai baki d’aya* *Amsar tambayan shine a halayen larabawa kafin musulunci shine sun kasance suna bauta ma gumaka, sannan suna kashe ‘ya’yayen su saboda tsoron/gudun talauci* _TSOKACI_ _A kwanakin baya, akwai wani tambaya da nasa a question of the day, in da na ce menene sunan bishiyar dake cikin aljannah? a next post d’ina sai nasa (jannatul Kuldi), to ina nufin bishiyar sunan ta shajaratul kuldi)_ _ganin yadda wasu suka min Magana ta pc akan cewa bishiyoyin dake cikin aljanna suna da yawa, wasu kuma suna challenging d’ina akan ba shajaratul kuldi bace_ _To ni dai har yau binciken da nayi da kuma fad’ar malamai ban samu akasin amsa ta ba_ _Amma ina rok’on duk wanda yake da cikakken amsar tambaya ta tare da hujja zai iya min Magana ta pc domin fahimtar dani, har yau ni d’aliba ce, kuma duk tambayar da nake rubutawa sai nayi bincike akai kafin nayi tambayar_ *TUNATARWA* _Allah yana jarabtar bawansa a lokacin da yaso, a kuma San da ya so_ _Allah ka bamu ikon cin dukkan jarabawar da za kayi mana_ 49&50 Kusan zaman minti biyar nayi ina jiran shi, sai ga motar Dr Sadik yayi parking d’in motar shi a gefen Fanta fun. Sanye yake cikin tsadadden yadi kalar white, kayan sun matuk’ar yi masa kyau, kasancewar Dr Sadik akwai d’aukan wanka, k’arasowa yayi da murmushi a fuskar shi. Kujerar dake opposite dani ya zauna yana ci gaba da sakar min sansanyar murmushin shi. Gaisawa muka yi cikin wasa da dariya kana ya bani hak’uri akan delay d’in da yayi. D’aya daga cikin ma’aikatan ya kira akan ya kawo mana drinks. Juyowa yayi ya tambaye ni yace "wani kala za a kawo miki Zarah?". Girgiza kai nayi nace "table water kad’ai ma ya isa". Kallo na yayi bai ce min komai ba yace wa ma’aikacin ya kawo table water guda biyu, ya had’o da fanta guda 2. Sipping yake yi kamar ba ya son shan fanta d’in. Wucewar kusan 2 minute, gurin ya d’au shiru ba tare da yace min komai ba. Shirun da naji yayi ne yasa na fara pressing d’in waya ta. "Zarah" naji ya kira ni cikin cool voice d’in shi. "Dr" nima na fad’a. Cikin tsadaddiyar muryar shi ya ci gaba da cewa "Zarah, na dad’e ina neman wacce ta dace da rayuwa ta, amma ban samu ba sai a yanzu, ni da kike gani Zarah, da ban yarda da wani soyayya ba bare in tsaya ‘bata lokaci na akai, yanzu ne nasan mahimmancin soyayya saboda na fad’a a cikin ta, ina kuma tunanin wacce nake so d’in za ta yarda ta amshi soyayya ta". Tsayawa yayi kamar ba zai ci gaba da Magana ba, can ya ci gaba da cewa "kar in ja ki da nisa, Zarah ke nake so…., I crown you the queen of my heart, so many reasons are there to love you, your cute smile, your sweet laugh, your innocence and your kind heart makes me love you… Wani irin fad’uwar gaba na ji a lokacin da ya sani saurin d’agowa na kalle shi. Wannan shine karo na biyu da aka zaunar dani aka fad’a min Kalmar soyayya. Tunano kalaman yaya Faruk nayi a lokacin da yake ce min _INA SON KI FATIMAH, I know I am in love with you because my reality is finally better than my dreams_ Gashi yanzu Dr ya zo min da wani sabon karatun wanda ban gama gane na farkon ba. Na so na fara warware matsalar yaya Faruk, hakan bai yiwu ba sai ga Dr ya k’ara zuwa min da wani al’amari mai wuyar fassaruwa. Idan nace ba na jin Dr a raina nayi k’arya, sai a yanzu da ya furta min yasa na tabbatar da cewa I am in love with Dr Sadik, sai dai yanzu ba ni da k’arfin amincewa kasancewar yaya Faruk bai san a wani babi yake ba. Dr ne ya katse min wasik’ar jakin da nake karantawa. "Zarah, I am a free person, duk yadda nake son mutum, in ya nuna bai amince ba, bazan matsa mishi ba, nasan so gamon jini ne, u are free to tell me if i am not your choice, zan fahimce ki".. Ajiyar zuciya na saki kana nace "Dr ka d’an bani time, zan fad’a maka ra’ayina game da kai". Ba tare da wata damuwa ba yace "Kar ki damu Zarah, na ba ki nan da gobe, ki yi shawara, zan kira ki in ji amsar ki, ko ki turo min text". Mik’e wa yayi yace "Zarah ni zan tafi, ki zo in sauke ki a gida". Shiru nayi ina tunanin kar yaya Khalil ko direban gidan su Anisa su zo d’auka ta ba su ganni ba. Wata dubara ce ta fad’o min na mik’e na bi shi cikin motar. Kasancewar yasan layin, gidan kawai na nuna mishi ya ajiye ni a bakin gate. Sallama muka yi ya ja motar shi ya tafi ya bar layin. Ina shiga parlour d’in ban ji motsin kowa ba, hakan yasa na wuce d’aki na watsa ruwa na canza shiga zuwa English wears, kitchen na wuce na d’ebi abinci a plate na nufi d’akin Ummu. Samun ta nayi tana gyara kayan ta a wardrope, sallama nayi na nemi guri na zauna. Ummu ce ta amsa tana cewa "Fatima an dawo?". "Na dawo Ummu, sannu da gida, san da na shigo ban sami kowa a parlour ba, shi yasa na wuce ciki na watsa ruwa" na ba ta amsa. "Ai kuna shawo rana, dole sai da watsa ruwa". Dariya nayi nace "Ummu karatu sai ka daure".. "Allah dai ya baku sa’a a karatun ku". Cikin jin dad’i nace "Amin Ummu". "Ummu aiki kike yi ne?" na tambaye ta. Amsa min tayi "mai wankin da guga ne ya kawo kayan, shine nake jera wa". "Ummu ki bari in na gama cin abinci sai in jera miki". "Ki barshi kawai Fatima, ke da kika dawo yanzu, ai na kusa gama wa". A haka muka ci gaba da hira da Ummu ina cin abinci. Bayan na gam cin abinci ne na d’auki plate d’in na tafi gurin sink na wanke. D’aki na wuce na kwanta akan gado, kalamen Dr ne suka fad’o min a rai *"Zarah ke nake so*., *I crown you the queen of my heart* Wani dad’i ne ya kama ni a lokacin, ji nake yi kamar yanzu yake fad’a min wannan tsadaddun kalmomin. D’aga kai sama nayi ina tunanin mafita. A wannan lokacin ina cikin tsaka mai wuya, ina buk’atar mai ba ni shawara, gashi ina da masu ba ni shawara, yaya Khalil da Anisa, amma ba ni da halin tunkarar su da wannan zancen, saboda duk inda suka ji cewa yaya Faruk na so na amma nayi rejecting d’in shi na za’bi Dr, ba mai ba ni shawarar in za’bi Dr, da alamu kuma zuciya ta baza ta k’i tayin Dr ba, dan alamu sun nuna son shi ya yi dabaibayi a zuciya ta, wannan shine hausawa suke cewa "Ga biki, amma babu zanin d’aurawa". Yaya Faruk da Dr Sadik na d’aura akan ma’auni, ko wanne na duba qualities d’in shi, sakamakon sai ya nuna min cewa yaya Faruk ya fi Dr qualities, hasalima ya fi shi kyau, son mutane, gashi kuma d’an uwana na jini, sa’banin Dr da mutane ke shakkar shi kasancewar sa miskili kuma bai damu da mutane ba "Me yasa zuciya ta tak’i amsar gayyatar sa da ya min na so? Menene aibun shi? Nayi k’ok’arin dasa son yaya Faruk a cikin raina amma hakan bai samu ba, Menene mafita?" na tambayi kaina. Zuciya ta ce tace min "mai zai hana ki amince da yaya Faruk saboda shi yafi cancanta ki so, in hakan ta kasance iyayen mu za su yi farin ciki da haka, ga k’arin zumunci da zai k’ullu a tsakanin su, hasalima shi yaya Faruk ne ya fara fad’a mi ki yana son ki, idan kika mai haka ba ki mishi adalci ba, kin sa yana ta jiran amsar ki, amma sai ki ka za’bi wani a kansa". Wata zuciyar kuma ce min take yi "Ba wani rashin adalci da kika masa, ko da yace yana son ki, ai baki ce kin amince ba, kuma shi so ba ruwan shi da ‘yan uwantaka, so yana zuwa ne a zuciyar mutum ba tare da yayi shawara dashi ba, ki bashi hak’uri kawai". Shawara ta biyu na d’auka saboda ina ganin ita ce mafita a gare ni. Zuciya tace ta bani shawarar in tura ma yaya Faruk text na ban hak’uri akan cewa yayi hak’uri dani, Allah shi ma ya bashi mai son sa. Wani tunani ne yazo min akan cewa in bari in ya dawo daga tafiyar da yayi yazo Kaduna sai in fad’a mishi, nasan zai fahimce ni, duk da nasan akwai ciwo, ba ni da yanda zanyi ne. Da yamma ina d’aki ina wani assignment naji yaya Khalil na kira na. Fitowa nayi na same su a falo, dashi da yaya Aminu suna hira. Gaishe da yaya Aminu nayi, kana nayi ma yaya Khalil sannu da gida. Yaya Khalil ne cikin tsokana yace "Fatima yau ina kika shiga ne a school, ni da Anisa muna ta neman ki a department d’in ku, gashi wayar ki is not reachable". "Yaya Khalil yau da kaina na dawo, ganin mun gama lectures da wuri". Yaya Aminu ne ya fara fad’a yana cewa "Tun da kun yi closing, ba sai ki nemi numban Khalil d’in ba ko Anisa, ki fad’a musu kin tafi, amma sai ki yi tafiyar ki su yi ta shan wahala, idan kika sake, za ki had’u dani". Cikin shagwa’ba nace "To ba kaina ne yake min ciwo ba". A raina nace 'yanzu na rabu da fad’an yaya Faruk, saura kai". Cikin tausayawa yaya Khalil yace "Ayya sorry sister, Allah ya k’ara sauki". "Amin na amsa". Yaya Aminu ne ya tashi ya nufi side d’in Ummu. Zama nayi muka ci gaba da hira kamar ba ni bace nace kaina na ciwo. Washe gari da daddare, kamar yadda Dr ya bani time, sai gashi ya kira waya ta. Ko kan in d’auka, wani special smile kawai nake yi. "Assalamu alaikum Dr" na fad’a. "wa’alaikis salam Zarah a cikin taurari". "dafatan kin wuni lafiya". "lafiya lau Dr, ya aiki?". "aiki alhamdulillahi, ya karatu". "karatu normal". Shiru muka yi na d’an mintuna kafin yaci gaba da Magana. "Zarah da fatan kin gama tunanin ki, yanzu amsar ki nake jira". Cikin jin kunya nace "Nima na amince, Dr nima ina son ka". "Wow! Zarah, I don’t know how to show my happiness to you, na ji dad’i, Allah ya barmu tare". "Amin Dr". Haka ya dinga ci gaba da fad’a min irin son da yake min, ban cika bashi amsa ba, kasancewar rashin sabo da hirar soyayya. Haka muka yi sallama muna masu shauk’in junan mu. Yau kusan watan yaya Faruk 5 rabon shi da Kaduna, yanzu ba mu cika had’uwa ba kasancewar ba network a inda suke. Sai dai wani lokacin Ummu tace ya kira yace a gaishe ni. A can ‘bangaran yaya Faruk kuwa, tun zuwan su garin Adamawa, basu da wani lokaci kansu, aikin da ya kawo su suke yi na kwantar da tozarmar da ke tsakanin Fulani da Iyamurai da aka samu sa’bani a tsakanin su, wanda hakan ya jawo asara da dama, ciki har da asarar rayuka. Bai da wani lokacin yin waya ko chat saboda rashin samun lokaci, wani lokacin in da suke zuwa akwai matsalar network a gurin, hakan yasa ba kullum yake kiran gida ba ko ya kira ni. Duk yadda suke tunanin rikicin mai sauki ne tsakanin Fulani da Iyamurai, abin ya wuce haka. Sun yi kusan wata uku a can Adamawa, sannan sak’o yazo musu cewa akwai wani course da za a tura su k’asar Uganda wanda za su iya d’aukan 3/4 month a can. Ko da suka dawo Abuja, bai samu damar zuwa Kaduna ya musu sallama ba saboda dawowar su kawai ake jira su tafi. Ko da ya kira Daddy ya fad’a mishi, fatan alkhairi ya mishi, amma yaso ganin shi ganin watannin da ya d’iba bai zo ba. San da ya sanar da Momi, fad’a ta fara yi akan wannan wani irin aiki ne? mutum ace rabon shi da gida kusan wata uku, sannan kuma yana dawowa an k’ara tura shi wata k’asar. Daddy ne ya dinga lallashin ta yana nuna mata aikin soja ya k’unshi haka, ta mishi addu’a da fatan nasara kawai. Haka kuwa Momi ta dinga mishi addu’a, ji take yi kamar taje ta ga d’an ta. Yanzu kusan wata 7 rabon shi da Kaduna, a wannan satin ne suke sa ran dawowa Abuja. Duk wannan watannin da yaya Faruk yayi a garin Adamawa da Uganda, bai manta dani ba, kullum ina cikin ransa, yana ganin yafi kowa k’osawar su dawo Abuja ya samu a basu hutu su je gida. Soyayyar mu da Dr ta zama wata irin soyayya da muke gudanar wa mai tafiyar da nishad’i, ba ko wani lokaci yake kira na ba, hakan bai damu na, saboda ina mishi uzurin yanayin aikin shi. Ba laifi Dr yana bani caring d’in da nake buk’ata a gurin lover d’ina, duk da wani lokacin ina ganin gazawar shi a ‘bangaren hakan, amma ina sa wa a raina cewa in muka yi aure, komai zai daidaita. Yau bayan mun tashi daga School ne, Ina cikin motar Dr Sadik muna hira, naji waya ta na ruri. Ganin Anisa ce yasa na d’aga da alamar tsokana nace "Matar yaya Khalil ya aka yi ne". Dariya tayi tace "Fatima Allah dai ya shirye ki, kina ina ne? gamu a department ni da Driver muna jiran ki". "Ok ki k’araso gaban department d’in mu, za ki ga wata mota ash colour a gurin, ina cikin motar". "Ke da waye a cikin motar" tayi saurin tambaya ta. "Idan kika zo kya gani" abin da nace da ita kenan na katse wayar. Ba a d’au wasu mintuna ba, sai gata ta k’araso motar. Ganin ta da nayi yasa na bud’e motar ina murmushi. "Anisa ga Dr Sadik ku gaisa" na fad’a. Kallo na tayi kamar za tayi Magana, sai kuma ta juya kallon ta zuwa ga Dr tace "Ina wuni Dr". "lfy lau Anisa, ya karatu". "lfy lau, ya aiki". "aiki alhamdulillah". Ita kuwa Anisa mamaki ne ya kama ta, saboda ita a sanin ta, Dr Sadik a asibitin school yake aiki, menene alak’ar shi da Fatima da zai biyo ta Department? duk da tasan sun yi Siwes a asibitin, kuma tasan sun saba da Fatima da Dr, yanzu to zuwan me yake yi gurin ta? Kamar nasan tunanin da take yi kenan nace "Anisa, wannan shine Dr Sadik, nasan kin gane shi, saboda yana aiki ne a cikin asibitin school, kuma shine my lover". Na juya kallo na ga Dr nace "Dr Sadik, wannan ita ce Anisa, k’awa ta kuma ‘yar uwa ta". Dr Sadik ne yace "Ina jin labarin ki Anisa gurin Zarah, ki ci gaba da kular min da ita, saboda ita special queen ce a guri na". Murmushi Anisa tayi tace "kar ka damu Dr". Sallama ta mana akan cewa tana jira na a mota. Dr Sadik ne ya min kallon da ke sani k’ara fad’awa tarkon son shi kana yace "Zarah, bari in tafi, tun da ga Anisa can na jiran ki". Fitowa nayi daga motar ina waving d’in hannu na. Anisa tun da ta koma mota take tunanin yaushe na had’u da Dr, me yasa ban fad’a mata ba? Wannan tunanin ta ci gaba dayi har na k’araso cikin motar. Mun fara tafiya ne Anisa ta kira suna na. "Fatimah! "Anty na ya aka yi ne" na fad’a da alamar tsokana. "Fatima wai yaushe ku ka fara soyayya da Dr Sadik ne? me ye dalilin ki na k’in fad’a min, bayan kin san ba ma ‘boye wa junan mu sirrin mu, ko da ki ka ga ban fad’a miki soyayya ta da yaya Khalil saboda ba na so yanzu Abbu da Daddy su fara tunkara ta da zancen, kin ga yanzu yaya Khalil sevice yake yi, na fi so sai ya gama service d’in, kin ga lokacin mun kusa gama Diplomar mu, amma ke wace hujja kike da ita? Gaskiya bazan ‘boye miki ba, ban ji dad’in abin da kika yi ba". Anisa ta fad’a da alamar damuwa. "Sorry Sis, ke ma kin san bazan k’i fad’a miki ba, kawai dai na ga ba mu dad’e dashi bane, shi yasa ban fad’a miki ba, kuma ina ganin nan gaba za ki iya cewa in hak’ura dashi". Da mamaki Anisa ta kalle ni tace "akan me zan ce ki rabu dashi Fatima, bayan na ga alamun kina son shi, kuma miye aibun shi da zan ce ki rabu dashi? kawai dai kin fad’i ra’ayin ki ne". A raina cewa nayi "da kinsan yaya Faruk ke so na kafin Dr, da ba ki ce haka ba, kuma ni nasan duk ran da kika san haka, ba za ki bani goyon baya ba akan Dr Sadik". Saboda mu rabu lafiya da ita yasa nace "yanzu dai ki yi hak’uri Anisa, na amsa laifi na". Murmushi tayi tace "kar ki damu Fatima, ke ai k’anwa tace tun da kina matsayin k’anwar miji, dole in hak’ura". Hannu na ba ta muka tafa, muka ci gaba da hira, ina k’ara ba ta labarin Dr Sadik. Bi na kawai take yi da kallo, tana jinjina irin son da nake yi ma Dr Sadik a d’an wannan lokacin da muka had’u dashi. Yanzu soyayyar mu muke sha da Dr Sadik ba tare da wata matsala ba, yawanci lokuta yana d’auka na mu jeostrich bakery ya min siyayya. Akwai lokacin da muka je Ostrich bakery d’in, na za’bar ma Anisa favourite snacks d’in ta da ice cream. Da na mik’a mata ledar take cewa "Fatima, maimakon ki bari in za mu koma gida sai mu shiga gurin, kin ga yanzu ice cream d’in ruwa zai yi". "Oh Sorry, ni da Dr Sadik ne muka je gurin ya siya mana". Anisa kuwa mamaki na take yin a yadda na fara canza halaye na daga had’uwa ta da Dr. "Fatimah, shawara zan baki, amma kar ki d’auka da wata manufa". "Ina jin ki Anisa". "Ki rage bin Dr Sadik yana fita dake, ba wai nace yana da matsala bane, hakan zai sa ya gane u a special, gwara ya siyo ya kawo miki, wani time d’in ki nuna mishi ba ki da buk’atar hakan". Wani irin kallo na bi ta dashi, saboda ni ban gane me take nufi da hakan ba? "yanzu ke nan nayi laifi dan mun je Ostrich bakery da Dr Sadik". "No Fatima, ba wai na ce kin yi laifi ba ne, ina fahimtar dake halin maza ne, ki iya takun ki, kuma ai nasan Ostrich bakery da poly ba nisa, tun da tsallaka titi ne, ina nuna miki yanayin high institution ne, kin ga sometimes yana zuwa department d’in ku, yanzu in wani wanda yasan ki, ya gan ki a gurin bakery d’in ya fad’a ma wani, za a iya canza muku manufa, yanzu duniyar nan mutum ake kiwo ba dabba ba, da fatan kin fahimce ni". Jiki na ne yayi sanyi da maganar da Anisa ta fad’a min, nima nasan gaskiya ta fad’a min. Don haka nace "Anisa na fahimce ki, zan kuma kiyaye". Yawwa k’anwata ta fad’a da alamar tsokana. Hararar wasa na mata muka canza hirar. Yanzu abin da yafi damu na shine yadda Dr Sadik ya matsa min akan yana so ya nemi izini gurin su Abbu, saboda yana so a san dashi a family d’in. Hak’uri na bashi akan yayi hak’uri ba yanzu zan bashi damar ya fara zuwa gidan mu zance ba, ba kuma yanzu zan gabatar dashi gurin su Abbu ba. Wannan kara da alama ba zai hak’ura ba, ganin yadda ya taso min cikin fad’a yace "Zarah, look, gwara ki fito ki fad’a min hujjar ki da ba kya so in fara zuwa gidan ku, na gaji da yadda kike kawo min excuse d’in ki in na miki magana, tell me what do you mean?". Cikin salon lallashi na fara bashi hakuri "Dr ka fahimce ni, nima na fi so ka zo gida akan department d’in da kake zuwa, insha Allah zan fad’a ma Ummu zancen ka, sai ta fad’a ma Abbu, in yaso sai ka fara zuwa, sorry Dr na" na fad’a kamar zan yi kuka. K’asaitaccen murmushi yayi yace "Na fahimce ki Zarah, sorry in na "ba ta miki rai". Girgiza kai nayi na ce "ya wuce Dr". A raina kuwa ban ji dad’in yadda ya min fad’a ba, ban san me yasa na kasa nuna mishi hakan a fuska ta ba, nasan ba komai yasa haka ba illa son da nake mai. Ci gaba yayi da ja na da hira, ina bashi amsa amma ba kamar yadda muke hira a lokuta da dama ba. Watak’ila fahimtar hakan da yayi ne yasa ya min sallama ya tafi. [4/29, 22:32] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 _Alhamdulillahi ala kulli hal_. *QUESTION OF THE DAY* _Qoramun(kogi) Aljannah guda nawa ne? lissafo sunayen su_ 51&52 Tun da na koma gida na rasa sukuni akan sa’banin da muka samu da Dr Sadik. Ni kaina nafi so yazo gida su Abbu da Ummu su san dashi, sai dai ba ni da wannan damar, tsora na shine idan wataran su ka had’u da yaya Aminu, zai iya fallasa sirrin da nake ‘boye wa tsakani na da yaya Faruk, hakan na nufin rashin amintar su da Dr Sadik kenan. Jiki na yana bani cewa yaya Aminu yasan abin da ke tsakanin mu da yaya Faruk, idan nayi duba da amincin su, ba sa ‘boye wa junan su sirrin su. Hakan na nufin dole in iya taku na dan ba na son kowa yasan tsakanin mu da yaya Faruk har sai ya dawo na bashi hak’uri, sannan in samu damar gabatar da Dr Sadik a matsayin wanda nake so. Ya kamata na nemo ma kaina mafita saboda kar Dr Sadik ya d’auka da wata manufa a guri na da na hana shi zuwa gidan mu. Kira ne ya shigo waya ta, mumban k’asar waje na gani, nasan ba kowa zai kira ni da wannan number ba sai yaya Faruk. Nayi mamakin ganin kiran shi a wannan time d’in kasancewar mun kwana biyu bai kira ni ba kuma ba mu had’u a chat ba. Jiki na a sanyaye na yi picking d’in call d’in. Sallama na mishi ya amsa. "Teemah na" abin da ya fad’a kenan. Ban amsa kiran da ya min ba illah cewa da nayi "yaya Faruk ina wuni, ya aiki". "lfy lau, ya su Ummu". "Suna nan lafiya". "Ya studies?" ya tambaye ni. "karatu alhamdulillah". "Nasan yanzu kun shiga ND 2 ko? ya tambaye ni. " Eh yaya har mun yi nisa". "To Allah ya taimaka". "Amin yaya Faruk". Teemah kin ji ni shiru ba na kiran ki, gashi ba ma had’uwa a chat, ba na samun zama ne, da ina sa ran a week d’in nan za mu dawo, amma ina ganin sai mun kai next month za mu dawo, nima na k’osa in dawo in ga kyakkyawar fuskar ‘yar k’anwa ta, in ga ko tayi missing d’ina". Murmushin jin dad’i nayi don a gaskiya, nasan yaya Faruk ya damu dani, alamomi da yawa sun nuna min hakan. "Allah ya dawo daku lafiya". "Amin Teemah nah, na gode da addu’ar ki, bari in barki haka, sai kin sake ji na". Sallama ya min ya katse wayar. A zuciya ta kuwa fargabar dawowar yaya Faruk nake yi, nasan cikin biyu za ayi d’aya, ko dai ya hak’ura dani idan na fad’a mishi ina da wanda nake so, ko kuma ya bijire ma buk’ata ta saboda ni kaina nasan yaya Faruk ba k’aramin so yake min ba. Yau ma kamar kullum, ni da Dr Sadik ne a cikin mota muna hira irin ta masoya, Tsayuwar Anisa muka gani a gaban mu tana murmushi. Gaisawa suka yi da Dr kana ta juya kallon ta gare ni tace "Tun da naga motar Dr, nasan kuna tare, shi yasa ban wahalar da kaina gurin kiran ki ba, na k’araso". "Kun gama lectures ne" na tambaye ta. "Eh mun gama, ni yanzu zan tafi gida, yau b azan tsaya jiran driver ba, tun da yaya Khalil ba ya gari". "Ok in kin je gida kya gaida su Momi da Dadi, ki ce ma Driver ba sai yazo ba, zan dawo da kaina". "Za su ji, zan fad’a mishi". Duk wannan zancen da suke yi, Dr bai sa musu baki ba, sai a yanzu yace "Anisa in ba damuwa, ina son yin Magana dake". Gaba d’aya maida kallon mu gare shi muka yi don sauraren mai ze ce. Murmushi tayi tace "Ba damuwa Dr ina jin ka". "A gida ba a barin ku kuna kula samari ne?" tambayar da ya Dr ya fara yi ma Anisa kenan. "Me ka gani Dr? ita ma ta jefa mishi wata tambayar ba tare da ta amsa mishi ba. "Naso ki amsa min tambayata ta farko, amma sai ki kamin halin ‘yan nijah ki ka sake jefa min tambaya akan wadda na miki, abin da yasa na tambaye ki shine yadda Zarah tak’i bani damar gabatar da kaina a gurin parents d’in ta, beside ni ba na son abin da zai zubar min da girma na, kin ga yawancin students sun san ni, so yanzu sai ki ga an fara wa mutum wata fassara ta daban, amma ita naga hakan kamar bai dame ta ba, ina so ki mata Magana, may be za ta fi d’aukar zancen ki da mahimmanci". Anisa kuwa tambayar da ta fara yi ma kan ta shine "Menene dalilin da yasa ba na son gabatar da Dr a gida? Duk kuwa lurar da tayi ina son shi". "kayi hak’uri Dr, zan mata Magana inshaAllah". Duk wannan maganar da suke yi ban ce komai ba, kamar ba na gurin. Anisa ce ta mana sallama ta tafi. Gaskiya yau Dr ya ‘bata min rai, ban so ya tunkari Anisa da wannan maganar ba, saboda ba na so Anisa tayi zargin ko ta kawo wani abu a ranta akan k’in gabatar da Dr da ban yi ba a gida. Bayan tafiyar Anisa ne na kalli Dr cikin damuwa na ce "Dr! D’agowa yayi ya kalle ni ba tare da ya amsa kiran da na mishi ba. Ban damu da amsawar shi ba naci gaba da cewa "Sadik, ban ji dad’i ba da ka fad’a ma Anisa halin da muke ciki, ba wai dan ban yi trusting d’in ta ba, na fi so in kammala wani shiri ne Kafin in tunkare su da zancen ka". Wayar shi yake pressing kamar ba dashi nake Magana ba, ga dukkan alamu, bai damu da yadda na nuna ‘bacin raina ba. "shiri? Wane irin shiri ne haka da zai hana ki gabatar dani a gidan ku". Ka k’ara hak’uri Sadik, komai ya kusa zuwa k’arshe". Wannan karan cikin ‘bacin rai ya fara Magana "look Zarah, ina ganin haka za mu ci gaba da tafiya, to bai da wani amfani, na baki yau ki yi tunani akan wannan maganar, in ba haka ba ni zan samar mana mafita". Wani irin sanyi jiki na yayi, yadda Dr yake fad’a min maganar da ranshi yake so, abin takaici shine na kasa nuna masa ‘bacin raina, duk kuwa da yadda maganar ta min zafi a raina. Sai kace ba Fatima ba da ba na bari a fad’a min mai zafi ba tare da na rama ba? Sai yanzu na yarda da Hausawa ke cewa *SO HANA GANIN LAIFI*. "Zan tafi" Dr Sadik ya fad’a. Jiki na kamar ba nawa ba, na fito daga motar. "Sai an jima" na fad’a a sanyaye. "Take care" ya fad’a a gajarce, kana ya figi motar a guje ya bar department d’in mu. Ko da muka class, jiki na duk a sanyaye yake, wanda yasa har Halima ta tambaye ni dalilin canzawa ta. Sanin ba ni da wani gamsashshiyar amsar da zan ba ta yasa, nace mata ba na jin dad’in jiki na ne. Cikin kulawa ta min fatan samun sauk’i. Ko da na koma gida, damuwa ce ta addabe ni ganin yau mun rabu da Dr Sadik cikin ‘bacin rai, babban abin da yafi d’aga min hankali shine yadda na ga Dr Sadik ya d’au zafi a yau. Haka nayi ta tunanin halin da Dr yake ciki a yanzu, ganin ba irin sallamar da muka saba yi dashi muka yi ba. A haka Ummu tazo ta same ni tana tambaya ta me yake damuna. Nasan Ummu na da saurin fahimtar halin da nake ciki yasa na yi murmushin da bai kai ciki ba, na ce mata ba na jin dad’in jiki na ne. Kallo na Ummu tayi kamar mai son gano wani abu, ganin haka ne yasa na tsargu na mik’e nace "Ummu bari in je in kwanta". "Allah ya k’ara sauk’i" Ummu ta fad’a tana bi na da kallo. Ni da na tafi d’aki da niyyar in samu hutu da tunanin dake addabar zuciya ta, sai gashi ina kwantawa barcin gaske ya d’auke ni. Ba ni na farka ba sai da naji Anisa ta d’aka min duka a jiki. A firgice na tashi ina waige-waige kamar wadda take neman wani abu. Anisa ce ta koma gefe tana ta kwasar dariya ganin yadda nayi. "Ba ki da abin yi ne yasa ki ke kwasar wannan dariyar". abin da nace mata kenan. Ban k’ara bi ta kanta ba, na wuce bathroom da niyyar yin alwala, ganin yadda lokacin sallah ya wuce ina bacci. Ko da na fito, samun ta nayi tana waya da yaya Khalil. Sallaya na shimfid’a na ta da sallah, har na idar da sallah ba ta gama wayar da take yi ba. Mik’ewa nayi da niyyar barin d’akin, saboda ban san lokacin da za ta gama wayar ba. Har na kusa kaiwa bakin k’ofa naji ta kira suna na. Juyowa nayi na kalle ta, katse wayar tayi ta ce "Fatima ki dawo ki zauna, akwai maganar da za muyi". Ban musa mata ba na dawo na zauna a gefen gado. "Ina jin ki" na ce da ita. Anisa ce ta ce "Fatima, ki yi hak’uri da abin da zance miki, wata k’ila maganar ba za ta miki dad’i ba". Anisa taci gaba da cewa "Fatima kin canza". Da sauri na katse ta "Kamar ya na canza?". "Fatima ki bari in gama maganar da zanyi sannan ki yi challenging d’ina, a da nasan ke ba kya ‘boye min komai naki, amma yanzu na lura ba kya son in san halin da kike ciki, ni bance ki dinga fad’a min komai naki ba, saboda ko wani mutum yana son sirri a rayuwar shi, yanzu na fara sa wa a raina cewa akwai abin da kike ‘boye min, na farko kin ga ba ki fad’a min alak’ar ki da Dr Sadik ba sai da Allah yayi naje department d’in ku, sannan ki ka fad’a min, da na miki Magana sai ki ka kawo min excuse d’in ki, na bar zancen, na biyu shine ban san hujjar ki ban a k’in ba Dr damar yazo gida su Abbu su san dashi, bayan nasan cewa in akwai dalilin ki nayin haka za ki fad’a min, shima ba ki fad’a min ba sai da Dr ya tare ni da zancen". Tsayawa tayi da min magana tana tunanin ko zan ce wani abu, amma ban yi Magana ba. "Fatima hakan ya tabbatar min kenan da abin da kike ‘boyewa wanda ba kya so in sani, in ba haka ba nasan ba za ki tsiri ‘boye-‘boye ba". Ban so Anisa ta d’au zancen a haka ba, duk abin da zan fad’a ma ta zai zama k’arya, tun da b azan fito in fad’a ma ta alak’a ta da yaya Faruk ba ne yasa na dakatar da Sadik zuwa gidan mu, ba kuma na so ta ci gaba da sa zargi a ranta. "Anisa ni fa ba ni da wani dalili da yasa ban ba Sadik damar zuwa gidan mu ba, kawai dai ina ganin kamar ba mu wani dad’e ba, shi yasa". "Wannan ba hujjah bace, in dai kin san ba wani dalili to ki barshi ya fara zuwa zancen a gida, instead of ya dinga zuwa department d’in ku, wasu su fara muku wata fassara ta daban". Anisa ta fad’a. Gaskiya ne da Hausawa ke cewa "Mai shawara aikin sa ba ya ‘baci" yanzu gashi d’an maganar nan da muka yi da Anisa yasa na samu relief akan tunanin da suka min dabaibayi, abin da yasa bazan nemi shawarar ta ba akan yaya Faruk da Dr Sadik, na san yayan ta za ta ba ni shawarar in za’ba, gwara dai in bar abin a raina har lokacin da komai zai zo k’arshe. "Insha Allahu zan fad’a mishi ya fara zuwa gidan" "hakan dai yafi". Narai-narai da ido nayi kamar zan yi kuka nace ‘Anisa ba zan ‘boye miki ba, ina son Dr Sadik, hakan yasa ba na so in ga na ‘ba ta mishi ranshi wanda zai jawo yayi fushi da ni, yanzu haka ban san me yake min dad’i ba saboda mun samu misunderstanding dashi akan wannan maganar, Anisa ki ba ni shawara". "Wannan wani irin so ne, Fatima take yi na Dr?" Anisa ta tambayi kanta. "Fatima, gaskiya ya kamata ki gane ke mace ce mai class, ba wai ina zuga ki ba ne, ina so kin san mace aka sani da jan aji, kar ki bari namiji ya gano irin son da kike mishi, hakan zai sa ya raina ki, ko ya samu damar juya ki, ba wai ina nufin kar ki nuna mishi irin son da kike mai ba, a harkar soyayya yana da kyau idan d’aya ya ‘ba ta ma d’aya rai yasan cewa shine da laifi, amma ba wai ya zamana mutum d’aya shi zai dinga amsar laifin da ba shi ya aikata ba, sorry to say Fatima, son da kike ma Dr ya fara wuce limit, saboda na ga hakan a tare da ke, ya kamata ki dawo hanya, ki kuma yi karatun ta natsu, ba komai nake guje miki ba, sai dan kar ki fad’a *MAKAUNIYAR SOYAYYA*, shawarar da zan ba ki shine ki tura mai text ko kira shi a waya akan cewa kin amince ya fara zuwa gida zancen, ina ganin zai daina fushin da yake yi dake ko Zarah" ta k’arashe zancen da alamar tsokana. Murmushi nayi saboda nasan tana tsokana ne da sunan da Sadik yake kira na. "Na gode da shawarar ki Anisa, ba abin da zance miki sai godiya, kuma zan yi k’ok’arin gyarawa". "Kar ki damu Fatima, matsalar ki, matsala ta ce". Hira muka ci gaba da yi da Anisa, sai wajen yamma sannan Anisa ta tashi ta tafi gida. Shawarar ta na d’auka na tura ma Sadik text akan cewa na amince ya fara zuwa gidan mu. Ran da ya fara zuwa gidan mu na gabatar dashi gurin Abbu, sun gaisa da Abbu cikin mutunta juna. Tun daga sannan jefi-jefi Dr Sadik yake zuwa gidan mu, mafi lokacin zuwan shi ran weekend. Haka muke ta gudanar da soyayyar mu da Dr Sadik. Yau bayan na dawo daga makaranta, Ummu ke sanar dani Hajiyan wagini (mahaifiyar su Abbu) tazo tana gidan su Anisa, murna da tsalle haka na dinga yi, saboda mun kwana biyu ba mu je wagini ba, ita kuma ta na dad’e wa, bata zo ba. Ko abincin ban tsaya ci ba, ina watsa ruwa na canza kaya na fito, na tafi shashin Ummu. "Sai ina?" Ummu ta tambaye ni. Dariya nayi nace "sai wajen waccen tsohuwar za ni, ba zan iya jiran ta tazo nan gidan ba, gwara in je in ganta". "In kin je kya gaishe su, in Abbun ku ya dawo za mu je mu mata sannu da zuwa". "To Ummu sai na dawo". "Sai kin dawo Auta". Saboda yadda na k’osa in kai gidan, ban tafi a k’asa ba, na tari keke napep na hau. Ina shiga gidan na same su a falo suna zaune. Sallama nayi da guda na fad’a jikin Hajiya na k’ank’ame ta. Anisa ce ta amsa sallamar ta na dariya. Sai a lokacin na lura da Momi dake zaune a d’aya daga cikin kujerun dake girke a falon, na gaishe ta. Amsa min tayi ta na murmushi. Ture ni daga jikin ta tayi tana dariya tace "Ja’ira za ki k’arasa ni ne, dama yanzu mu ka gama yi da Anisa". "Kai Hajiya mun yi missing d’in ki ne fa, shine za ki gwasale mu". "Ke raba ni da yaren nasaran nan naku, za ki wan ice kun yi misin ko musin d’ina ne oho miki". Dariya muka kwashe da ita ni da Anisa. "Ja’irai ni kuke ma dariya, bari iyayen ku su zo zan fad’a musu shak’iyancin da ku ke min". Anisa ce cikin dariya tace "Sorry Kakus, ba za mu sake ba". Yamutsa fuska tayi tace "Abin naku gaba yake yi, har da sauro ku ke had’a ni dashi". Sake fashe wa da dariya muka yi, ni kuwa har da rik’e ciki. Haka muka dinga wasa da dariya da Hajiyan wagini, sai da yamma na mik’e da niyyar tafiya. Momi ce tasa Driver ya maida ni gida. Da daddare su Abbu da Ummu da za su gaida Hajiyan wagini na sake bin su, saboda muna shiri da ita sosai. San da muka je gidan su Anisa, haka aka had’u a falon Dadi ana ta hira, da wasa da dariya. Sai wajen k’arfe tara na dare muka baro gidan. Hajiyan wagini sai da tayi kwana uku a gidan su Anisa sannan ta tawo gidan mu, tun da tazo na tare a d’akin ta, wani lokacin Anisa na zuwa a sha hira da ita. Yau ta kasance ranar jumma’ a, ba mu da wani lectures da yawa, hakan yasa na dawo gida da wuri. Ina dawo wa, na wuce d’akin Hajiyan wagini zaune akan carpet tana cin farfesun kaji. Zama nayi kusa da ita ina cewa "Kai Hajiyan wagini, an samu dad’i ko Magana ba a iya yi, tun da ba za a min tayi ba bari in wa kaina". Duk wannan maganar da nake yi Hajiyan wagini ba ta ce min komai ba, sai ma ci gaba da tayi da cin naman ta. Hannu na saka a cikin plate d’in na d’auki yanka d’aya daga ciki na sa a baki na. "gaskiya Hajiya dole ba za ki yi magana ba, wannan delicious haka". Harara ta tayi tace "wannan bature bai kyauta ba, a ce mutum yana d’an bahaushe gaba da baya, in zai yi Magana sai ya had’a da harshen nasara". "Kai Hajiyan wagini, yanzu zamani ya canza, mun riga da mun sa ba da wasu kalmomin da turanci, idan za muyi Magana sai mun had’a dashi". "wannan bature dai ya nace mutane". Dariya nayi nace "Hajiya kenan". Kallo na tayi tace "Ke Fatima kina da number Soja ki nemo min shi mu gaisa". A gaskiya bazan iya kiran yaya Faruk ba a gaban Hajiyan wagini, nasan za ta iya fahimtar wani abu, saboda nasan zai yi wuya in kira shi ba tare da ya fad’a min wata kalma da ta k’unshi so ba, ko in kira ta ya fad’a ma ta abin da ke tsakanin mu, nasan kuwa Hajiya sai tafi kowa murnar da wannan zancen, dan haka nace "Ba ni da ita, nima idan ya kira Abbu ko Ummu ne muke gaisawa". Hajiyan wagini ce ta ci gaba da cewa "Allah sarki Mai gida na nakai na, Allah ya dawo dakai lafiya ka fito da mata mu sha biki". Ganin Hajiya ta d’akko zancen yaya Faruk yasa na mik’e, don nasan ba ta gajiya da zancen shi. Tafiya na fara yi ina cewa "Ni dai bari in je in huta, yanzu in kika fara min maganar shi, ba gajiya za ki yi ba". "To ‘yar nema, da ma nasan ai ba zama za ki yi ba, tun da kin ji an ambaci wanda ba kwa shiri, dole ki tafi". "Ni dai kin ga tafiya ta Hajiya" na fice daga d’akin. Ran lahadi muna zaune ni da Dr a gurin shak’atar dake gidan mu, motar yaya Aminu ce na ga ta shigo gidan. Gaba na ne yayi wani irin buga wa, nasan idan har yaya Aminu yasan me ke tsakanin mu da yaya Faruk, ba k’aramin ‘bata min zai yi ba, ko ya fad’a ma su Abbu abin da ke tsakanin mu da yaya Faruk, nasan kuwa zan fuskanci hukunci gurin Abbu. Parking yayi a gurin parking space, Shi da Anty jidda ne da su Humaira da Nabil suka fito daga motar. Su Humaira ne da Nabil suka rugo da gudu gurin da muke, yayin da Anty Jiddah da yaya Aminu suka shige cikin gida. Bud’e musu hannu nayi suka fad’a jiki na suna dariya. Murmushi Dr Sadik yayi yace "wannan yaran waye Zarah" "yaran brother d’ina ne, yaya Aminu" na bashi amsa. "ku zo mu gaisa, ko sai Antin ku kawai ku ka sani". Humaira ce ta tawo gurin shi, shi kuwa Nabil k’ara mannewa yayi a jiki na, alamar ba za shi ba. San da Dr Sadik za tafi, kud’i ya bani a siya ma su Humaira su chocolate. Ko da na amshi kud’in, tunanin w azan ba tsakanin yaya Aminu da Anty Jidda nake yi, nasan dukkan su in suka sa tsakanina da Dr Sadik, ba za su yi wani murna da kyautar da ya yi musu ba, zuciya ta tafi kwanciya akan in ba Anti Jidda, nasan ita ba ta da wata matsala. Godiya na mishi, kana muka yi sallama ya shiga motar shi ya tafi, ni kuma na rik’e hannun su Nabil muka nufi cikin gida. Ina shiga cikin parlour d’in, na ga ba kowa, nasan ba za su wuce suna d’akin Hajiyan wagini ba, hakan yasa na nufi d’akin. Sallama na musu na nemi kusa da Anti Jiddah na zauna, na gaishe ta. Cikin Magana k’asa-k’asa tace "Fatima wanene wanda na gan ku a tare, ko da yake mu bar maganar, zan zo d’akin ki mu yi maganar, yanzu ki tashi ki je, yayan ki na neman ki, yace ki same shi a garden". Jiki na ne ya min nauyi, nasan kiran da yaya Aminu ya min na nufin zai min magana ne akan Dr Sadik, ko kuma akan yaya Faruk. Tashi nayi na nufi garden d’in don in ji mai yaya Aminu zai ce min. *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 _Allahumma innaka afuwun karimun tuhibbun afuwa fa afu anna, wagafirlana, warahamna, anta maulana fansurna alal qaumiz zalimin_ 🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽 *Wanda suka yi k’ok’arin ba da amsar question of the day su ne* *Meeynah (Princess of question of the day)* *Ramlah* *Allah ya saka muku da alkhairi da irin k’ok’arin da kuke yi* *Amsar tambayar ita ce: A cikin Aljannah akwai Qoramu (kogi) guda bakwai* Kogin ruwa Kogin Madara Kogin ruwan zuma Kogin ruwan giya (sharabun Tahoorun) Kogin Kafoor Kogin Zanjabeel Kogin Tasneem *TUNATARWA* _MAGANGANUN MANZO (S.A.W)_ _Yace_: _mafi girman Haske (ilimi)_ _Mafi girman duhu (jahilci)_ _Mafi girman kyauta (afuwa)_ _Mafi munin zance (K'arya)_ _Mafi kyawun zance (gaskiya)_ _Mafi kusantuwar al’amari (tashin alqiyama)_ _Ya ku muminai, mu yi amfani da lafiyar mu da lokacin mu da dukiyar mu kafin mutuwa tazo mana_ 53&54 San da na isa garden d’in, samun shi nayi a garden da jaridar Daily trust a hannun shi yana karantawa. Sallama na mishi kana na gaishe shi. Ciki-ciki ya amsa sallamar da na mishi da gaisuwar. Ci gaba yayi da karatun shi kamar bai san da tsayuwa ta a gurin ba. Ajiye jaridar yayi ya kalleni ya ce min "Fatima zauna ina da Magana da ke". Jiki na a sanyaye na nemi d’aya daga cikin kujerun na zauna. "Wane ne wannan da na gan ku a tare ya zo gurin ki?". Tambayar da ya fara jefo min kenan. "Sunan shi Dr Sadik" na bashi amsa. "Ba sunan shi na tambaya ba, me yazo yi gurin ki" ya k’ara jefo min wata tambayar. "A asibitin school d’in mu yake aiki, muna mutunci ne dashi tun lokacin da nayi Siwes a asibitin". Wani irin kallo ya min sannan yace "Duk mutuncin bai isa a makarantar ku ba, sai ya zo gidan ku?". Wannan karan ban bashi amsa ba saboda ban san me zan ce mai ba. Ganin haka yasa yaci gaba da cewa "Fatima na ga kan ki na rawa, zan yi mummunan sa’ba miki, in ma wani abun yak e kawo shi gidan nan ki fad’a mishi ki na da wanda yake son ki kuma shi za ki aura". Da sauri na d’ago na kalle shi jin har ya yanken hukuncin wai yaya Faruk zan aura. Ci gaba yayi da cewa "ko an fad’a miki ban san me ke tsakanin ki da Faruk ba ne? abin da yasa ki ka ga ban ma su Abbu Magana ba, saboda Faruk d’in yace min ya kusa dawowa, amma da tuntuni sun san da maganar, Na ga take-taken ki yana nufin ba ki amince da Faruk ba, wannan ne kuma ba ki isa ba, in kin k’aryata kuma ki gwada ki gani". Tashi yayi ya bar gurin ba tare da ya jira jin amsa ta ba. Wasu hawaye ne suka zubo min masu matuk’ar zafi, wanda ni kaina ban san dalilin zubar hawayen ba. Tun a yanzu kenan na fara fuskantar k’alubale game da soyayya ta da Dr Sadik a dalilin yaya Faruk, ina ga in su Ummu da Abbu in su ka ji gaskiyar maganar cewa Faruk ne ke so na? nasan ko me zan yi Abbu ba zai barni da Dr Sadik ba. Haka na jawo k’afa ta na shiga cikin gida. D’aki na wuce, na zauna akan kujerar dressing mirrow ina ci gaba da tunanin hanyar da zan bi in warware komai cikin sauk’i ba tare na ‘bata ma kowa rai ba. Addu’a ta d’aya ita ce Allah yasa yaya Faruk ya dawo in fad’a mishi abin da ke raina, nasan shi zai fi fahimta ta akn kowa, duk da nasan ba k’aramin matsala zan janyo a familin ba ganin yadda ake zaman mutunci da kuma zumunci, wannan ina gani shine mafita a gare ni. Shigowar Anti Jiddah ne yasa na k’ak’alo murmushin yak’e saboda ba na so ta gano halin da nake ciki. Gefen gado ta samu ta zauna tana bi na da kallo. "ya aka yi ne Fatima?" ta tambaye ni. "Ba komai Anti" na ba ta amsa. Ban son ta k’ara jefo min wata tambayar yasa na ce "Ina su Humaira ne?" "Suna gurin Hajiyan Wagini". Ku’din da Dr Sadik ya ba ni in basu na d’auka na mik’a mata. Bin kud’in tayi da kallo alamar tana buk’atar k’arin bayani. Dariya nayi nace "ki amsa mana Anti Jidda, sai in miki bayani". Murmushi tayi ta amshi kud’in tayi godiya. "Dr Sadik ne ya bani yace in ba Su Humaira da Nabil a sai musu chocolate". "Waye Dr Sadik? ta tambaye ni. "wanda ki ka ganni dashi d’azun" na bata amsa a gajarce. "Ko shine surukin mu?" ta fad’a da alamar tsokana. Wannan karan ban ba ta amsa ba, sai mumushi da nayi. Hakan yasa ta fahimta shirun da nayi me yake nufi. "Allah ya za’ba mafi alkhairi". "Amin Anty Jiddah". "Amma sai naji Dadin su Humaira kamar ya ce min Faruk ke son ki?" ta k’arashe maganar da min kallon tuhuma. Sanin Anty Jiddah ta riga tasan maganar, gwara in fito in fad’a mata abin da yake raina, wata k’ila ta samo min mafita. Don haka nace mata "Eh shi yace yana so na, amma ni ai har yanzu ban ce mai ina son shi ba, kuma ni maganar gaskiya Dr Sadik nake so". Kallon mamaki Anty Jiddah ta bi ni dashi, kamar ba za tace min komai ba, can ta d’aura da cewa "Fatima, nasan so daga Allah ne, shi yake sa ka wa mutum ba tare da yayi shawara dashi ba, amma wani lokacin mutum na iya sa son mutum a ranshi, ba wai nag a laifin kid an kin so Dr Sadik ba ne, sai dai ina duba miki wanda yafi dacewa da rayuwar ki, duk da ban san halin Dr Sadik ba, amma nasan ba wanda zai so ki da gaskiya ya kuma rik’e ki da amana irin Faruk, samun a Faruk a gurin ki ba k’aramin riba bace a gurin ki saboda yana duk wani qualities da mace za taso a gurin namiji, ba ki kyauta ma Faruk ba da tun farko ba ki fito kin fad’a mishi ya hak’ura ba, sai yanzu da ki ga kin samu wanda kike so, ni dai shawarar da zan baki shine ki rik’e Faruk a matsayin masoyin ki da kuma farin cikin su Ummu da za ki duba in har suka san da zancen nan. Ta ci gaba da cewa "mu dai muna bayan Faruk, ba za mu bari aka da Faruk a fagen soyayyar ba kamar yadda bai fad’i ba a fagen yak’i ba" ta k’arashe zancen tana dariya. Da alama ni zan sha k’asa, yanzu ma gashi Anty Jiddah tana bayan yaya Faruk, ga d’azun yaya Aminu y agama min fad’a akan shi, ina ga su Anisa da yaya Khalil, bare aje ga su Abbu da Ummu, nasan in da zan samu sassauci shine ta ‘bangaren Dadi, nasan ko Momi bayan d’an ta za ta bi. Cikin raunin murya na ci gaba da cewa "Anty Jiddah, tun kafin in had’u da Dr Sadik nake ta k’ok’arin in ga nasa son yaya Faruk a raina, amma hakan ya faskara, har yanzu ina ganin yaya Faruk a matsayin yaya ne a guri na, ba wai matsayin masoyi ba, ni ba zan iya nuna mishi ina son shi ba, alhalin ba haka yake a raina ba, hakan ya zama yaudara kuma daga baya zai ji haushi na akan haka, shi yasa na yanke shawarar in ya dawo in fito in fad’a mishi abin da yake raina game dashi". Da sauri Anti Jiddah ta katse ni da cewa "wace yaudara? ai Fatima kin riga kin yaudari Faruk, me yasa tun a lokacin da ya fad’a miki yana son ki ba ki fito kin fad’a mishi gaskiyar yayi hak’uri dake ba, sai yanzu da yayi nisa da son ki sannan za ki zo mishi da wannan maganar taki mara ma’ana, in har kika mishi haka ba ki mishi adalci ba". Tana gama fad’ar haka ta taso ta tawo guri na, dafa kafad’a ta tayi tace "Fatima, *KUSKURE D’AYA TAK*zai iya jawo miki danasani mara iyaka, ki yi nazari kafin ki yanke hukunci, ba ri in k’arasa gurin Ummu". Tana gama fad’ar haka ta bar d’akin. "Allah gani gare ka, ka kawo min komai da sauki" abin da na rok’a gurin Allah. Ban sake fito wa falo ba sai da Anty Jiddah za su tafi na fito in musu rakiya gurin motar su, yanda na lura yaya Aminu sai harara ta yake yi. Hajiyan Wagini sai da tayi kwana uku a gidan mu sannan ta koma gidan su Anisa wanda za ta tafi a washegarin ranar, ganin ranar da za ta tafi ya kasance ranar Friday yasa muka ce za mu bi ta, in yaso sai Driver yazo ya d’auke mu. Ran jumma’a ina dawowa daga school na had’a kaya na a d’an kit, na tafi gidan su Anisa, nayi ma Ummu sallama, dama mun riga munyi sallama da Abbu da safe. Ban wani dad’e a gidan ba, muka nufi hanyar Wagini. Tun da muka je Wagini, muka dinga zagaye ‘yan uwa, in mun dawo mu zauna da Hajiyan Wagini, d’an kwanakin da muka yi a garin kamar kar mu dawo. Kwanan mu biyu a garin, Dadi ya turo Driver yazo ya d’auke mu. Haka muka yi sallama da Hajiyan wagini muka dawo Kaduna garin gwamna. Yaya Khalil yana zuwa Kaduna lokaci-lokaci kasancewar a Jigawa yake yin service d’in shi. Yanzu soyayayyar yaya Khalil da Anisa ta mamaye dangi, kowa yasan da zancen, yanzu ni ake jira in wa Dr Aminu Magana ya turo da iyayen shi. Hausawa suka ce duk nisan gagri zai waye, hakan yake, domin a yau ne yaya Faruk ya dawo daga k’asar Uganda zuwa Birinin tarayya Abuja. Murnar shi ta koma ciki jin cewa sai sun k’ara sati d’aya a Abuja kafin a ba su damar zuwa gida. Waya yayi ma Dadi cewa sun dawo, amma ba zai samu zuwa ba sai next week, fatan alkhairi Dadi ya mishi kana suka yi sallama. Yau ya shirya da niyar zuwa gidan su Mus’ab saboda ya dad’e bai je ya gaida Hajiyan su ba. Block d’in su Mus’ab ya tafi. San da yaje ya na ta knocking amma ba a bud’e mishi ba. Wayar shi ya d’auka yayi dialling number d’in Mus’ab d’in. Ringing biyu tayi kafin a d’auka. "Assalamu alaikum, Allah ya ja da ran Bregadier na Teemah" abin da Mus’ab ya fara fad’a kenan. "wa’alaikumus salam, kana ina ne?" yaya Faruk ya tambaye shi. "Ina gida, ya aka yi ne?". K’aramin tsaki yayi kana yace "shine ina tsaye tuntuni ina knocking, kai da Maryam an rasa mai zuwa ya bud’e min". "Ka mana uzuri, ba ma falo ne, kuma kasan dai ma’aurata in aka zo aka ji shiru ana musu uzuri, gani nan zuwa in bud’e maka". Murmushi kawai yayi saboda yasan halin Mus’ab idan ya biye mai, sai ya yanko wani zancen na daban. Katse wayar yayi ya zauna a kujerar da ke balcony. Mus’ab ne cikin tsadadden yadi kalar ruwan toka, bud’e k’ofar yayi yana murmushi. "Tuba muke yi Bregadier Umar Faruk’ Mus’ab ya fad’a yana dariya. "Mus’ab ban san ran da za ka girma ba". "Ran da maryam ta haifo babyn ta ranar zan girma". Girgiza kai yaya Faruk yayi yace "Zuwa nayi ka raka ni wata unguwa". "In fita ina? kana ganin tsawon lokacin da muka d’iba ba ma nan, Maryam tayi missing d’ina, nima haka, sai dai ko zuwa anjima sai in zo mu tafi". "yanzu zaka raka ni ko in tafi?" yaya Faruk ya tambaye shi. "zan raka ka amma sai anjima, dan saboda kaine ma yasa na fito, ina jin yau ko sallah a d’aki zan yi". "Allah dai ya shirye ka Mus’ab, ka ga tafiya ta". Tafiya ya fara yi, Mus’ab ne ya bishi yana dariya yace "kai matsala ta da kai ba kasan wasa ba, zan raka ka, amma ka shigo ku gaisa da Maryam sai mu tafi". Kallon agogon shi yayi dake d’aure a hannun shi yace "ka bari in mun dawo, zan shigo mu gaisa". "Tun da ba z aka shiga ba, bari in shiga in fad’a mata". Shiga yayi ya fito suka shiga motar yaya Faruk suka tafi. A wani shopping mall ya tsaya yayi parking. Mus’ab ne ya bishi da kallo yace "yanzu dama shopping zaka kasa na bar Maryam ita kad’ai, kasan in ba dole ba, bazan fita ba". Yaya Faruk bai ce mai komai ba, sai ma rufe motar sa yayi ya shiga cikin Mall d’in. Tsadaddun turare ya siya ma Hajiyan su Mus’ab da Dadin su Mus’ab d’in, tuna wa da Nana da yayi yasa itama ya za’bar mata kalar na mata mai set, sai tsadaddun sabulai da su chocolate ya k’ara d’aukan mata. Ma’aikatan ne suka biyo shi da kayan ya bud’e musu bayan motar suka zuba a ciki. Mus’ab kuwa tambayar kan shi yake yi ina zasu da wannan kayan? Sanin halin Faruk na miskilanci, idan ya tambaye shi ba lallai ya amsa mishi ba, hakan yasa ya ja bakin shi yayi shiru. Unguwar su dake Maitama ya ga yaya Faruk ya shiga. A gate d’in gidan yayi hon mai gadi yazo ya bud’e mishi. Sai da yayi parking d’in motar shi a ma’adanar motoci sannan ya sakar ma Mus’ab murmushi yace " Mus’ab, dama gun Hajiyar ku za ka raka ni na gaishe su da kake ta min surutu a mota, sai ka fito mu shiga". "A gaishe ka Faruk, shine b aka fad’a min ba, ka tsaya ja min aji". "yanzu ba gashi na fad’a maka ba". Jerawa suka yi suna tafiya suna hira, har suka shiga shashin Hajiyan su Mus’ab. Mai aiki ce ke ta shawagin ta a falo tana ayyukan ta. Sallama suka yi suka nemi guri suka zauna. Amsa musu tayi tana gaishe su. "Baraka ina Hajiya take?" Mus’ab ya tambaye ta. "Tana sama, bari in je in kira ta". Katse ta yayi da cewa "No ki barshi kawai, bari in je da kaina". Kusan minti biyar sai gashi sun sakko da wata dattijuwar mata, sanye take da super exclusive wanda ak’alla kud’in ta zai kai dubu ishirin da wani abu zuwa talatin. Da fara’arta ta k’araso falo ta zauna a d’aya daga cikin luntsuma- luntsuman kujerun dake falon. "kace muna da babban bak’o, Faruk kaine a gidan?". Hajiyan Mus’ab ta fad’a da murmushi a fuskar ta. Cikin ladabi ya gaishe ta yana cewa "Ni ne Hajiya, mun same ku lafiya". " lau Faruk, yaushe rabon ka da gidan nan, da har nayi fushi" fad’a da alamar wasa. "A yi hak’uri Hajiya, ayyukan ne sai a hankali". Dariya tayi tace "haka kuke kai da Mus’ab, da an ta’ba ku sai kuce aiki ne ya ‘boye ku, Allah dai ya taimaka". "Amin Hajiya". Hajiyan su Mus’ab ce ta fara kiran Nana! Nana! Cikin natsuwarta ta sakko daga upstairs tana cewa "gani Hajiya". Turus tayi ta ja ta tsaya ganin yaya Faruk a gidan su, ganin ya dad’e basu had’u ba, gashi kuma material d’in da tasa linen ne kalar peach mai transparent ne. Cikin jin kunya ta k’araso ta gaishe da Mus’ab sannan ta juya ta gaishe da yaya Faruk. Hajiya ce tace "Nana je ki kawo masu abinci, snacks da drinks" "To Hajiya" ta amsa mata. Sai da ta koma sama ta yafo farin veil mai kauri sannan ta nufi kitchen. Mus’ab ne yace "Hajiya, Dady na nan ko? na ga motar shi, bari mu je mu gaisa dashi". "yana side d’in shi, abincin fa, ko sai kun dawo za ku ci?" "In ta kawo, ki ce ta kai mana side d’ina". Shopping d’in da yayi ya ajiye ma Hajiya a gaban ta yace "Hajiya gashi ba yawa ke da Dady, d’ayan ledar kuma na Khadijah ne". "Faruk har da hidima, Allah ya saka da alkhairi, mun gode". "Hajiya abin da ba yawa". "Mai yawan kenan, Allah ya muku albarka ya k’ara tsare ku daga mahassada da abokan gaban ku". "Amin Hajiya" suka amsa a tare. Side d’in Dadi suka nufa, samun shi suka yi yana karanta jaridar vanguard a hannun shi. Ganin su yasa ya ajiye jaridar akan center table, ya cire medicated glass d’in dake fuskar shi. Gaishe shi suka yi, ya amsa musu da fara’ar shi. Kirari ya fara musu na sojoji "Soja mazan fama, Soja marmari daga nesa, Soja birgimar hankaka, Soja ga ruwa ga yak’i". Ci gaba yayi da tambayar su yanayin aiki da kuma course d’in da aka tura su a k’asar Uganda. Labarin tafiyar suka dinga bashi da kuma nasarar da aka samu. Hira suka ci gaba da yi kamar wasu abokai. Sun d’an jima a ‘bangaren Dady sannan suka bar side d’in shi. D’akin Mus’ab na da suka shiga, a gyare yake kamar da mutum a ciki. Suna shiga yaya Faruk ya kishingid’a a 3- sitter yana lumshe ido. Dariya Mus’ab ya fara mai. Kallon ba ka da abin yi yaya Faruk yake mai. Ganin har yau yana ci gaba da dariyar k’asa-k’asa yasa yace "wai miye abin dariya, kai wani sa’in kamar wanda kayi gamo". "da kasan dariyar da nake yi da ba kace haka ba, ni nan tausaya maka nake yi na kad’aicin da ke damun ka, wannan lumshe idanun da kake yi na alamar gajiya ne, kaga da kana da aure, da an yi massage d’in ka shi kenan, amma kai na ga hakan ba ya damun ka" ya k’arashe maganar yana dariya. Shima yaya Faruk sai da ya dara a wannan lokacin yace "kai dai Mus’ab ban san lokacin da zaka daina wannan iskancin naka ba" "Ba wani zancen isakanci, maganar gaskiya ce". Sallamar Nana ce ta katse musu hirar da suke yi. Abincin da ta shigo dashi ne, da kuma wanda Baraka ta rik’o mata sauran drinks da snacks d’in suka ajiye akan center table d’in. Baraka ce ta fita daga d’akin yayin da Nana ta nemi guri ta zauna. Mus’ab ne ya nufi gurin tv ya kunna. Tambayar su tayi yanzu za su ci abincin? Mus’ab ne ya amsa mata da "Eh". Plate ta d’auka ta zuba ma yaya Faruk had’ad’d’iyar fried rice wanda taji hanta a ciki, a saman abincin kuma ta d’aura pepper chicken da coslow akai. A jiye mishi tayi, sannan ta d’akko swan da hollandia a gaban shi. "sannu da aiki Khadija, mun sa ki aiki ko?" yaya Faruk ya fad’a yana kallon ta. Murmushi kawai tayi tace "Ba wani aiki yaya Faruk". Mus’ab tayi serving sannan ta mik’e ta kalli yaya Faruk tace "Na ga kaya na gode yaya Faruk, Allah ya saka da alkhairi". Murmushi yayi yace "ya na gan ki a gida, ba ku da school ne?" yaya faruk ya tambaye ta. "muna dashi, yau test muka yi, tun around 11 na dawo". "Allah ya taimaka". "Amin". Yaya Mus’ab ne ya kar’bi zancen da cewa "kun kusa exams kenan, ina so in kun yi exams kije ki taya Maryam zama, kin ga ta kusa haihuwa". "Allah ya kaimu yaya Mus’ab" "Amin Nanan Hajiya" ya fad’a da alamar zolaya. Fita tayi daga falon, tana kara yaba wa da halin yaya Faruk, haka kawai take jin jinin su ya had’u. *SU WAYE MUS’AB DA NANA KHADIJAH?* Mus’ab d’a ne ga Alhaji Sa’id, daga shi sai Nana Khadija, su hud’u iyayen su suka haifa, Mahaifin su da mahaifiyar su Hajiya Safiya haifaffen ‘yan jigawa ne, zama ne ya kawo su garin Abuja, Mahaifin su fitaccen d’an siyasa ne, ya rik’e muk’ami da dama a harkar siyasa, yanzu yafi maida hankali a harkar business. Mus’ab shine d’a na biyu a gidan su, Soja ne da yake da matsayin Bregadier, yana da yaya mace Hajara da tayi aure, daga shi sai k’anin shi Usman, yanzu yana India yana karantar Medicine, daga shi sai Nana Khadija wanda a yanzu take karatu a University of Abuja, tana karantar English, yanzu haka tana level 2 a matakin karatu. Mus’ab da yaya Faruk sun had’u ne tun a makarantar sojoji, har ya zuwa yanzu da suke aiki a Abuja, sun kasance abokanan juna da ba sa ‘boye wa junan su matsalar su. A halayya sun banbanta domin yaya Faruk miskili ne, shi kuwa Mus’ab mutum ne mai wasa da dariya. Nana Khadijah kusan halin su d’aya da yaya Faruk, don itama Magana ba ta dame ta ba. *************************** Sai can yamma suka baro gidan su Mus’ab. Yau yaya Faruk shirya cikin shirin shi na zuwa Kaduna. Sai da ya biya ta gurin su Mus’ab suka ya d’auke shi kasancewar tare za su tawo Kaduna. Da rana suka sauka a Kaduna. Tun zuwan su gidan, kowa murna yake yi ganin yadda ya d’auki lokaci rabon shi da Kaduna. Abinci na musamman Momi ta shiga kitchen ita da Anisa suka shirya musu. Sai da suka shiga side d’in yaya Faruk suka watsa ruwa sannan suka canza shigar su zuwa k’ananun kaya suka fito falo. Momi ce ta zo ta zauna suka sake sabuwar gaisuwa, tana mai tambayar Mus’ab ya su Hajiyan su da Maryam. Amsa mata yayi da suna lafiya lau. Anisa ce ta jera musu abincin akan dining table, ta dawo falo ta fad’a musu ga abincin su nan akan dining. Yaya Faruk ne ya tashi yace ma Mus’ab yazo su je su ci abinci. Anisa ya kira tayi serving d’in su yayin da Mus’ab ke jan ta da hira. Bayan sun gama cin abinci ne suka dawo falo suka ci gaba da hira. Anisa ce ta zo ta zauna tana tambayar Mus’ab Anty Maryam, duk da ba sanin ta tayi ba, amma jin yaya Faruk na yawan fad’an ta yasa ta rik’e sunan ta, ta kuma san Matar Mus’ab ce duk da ya dad’e bai zo ba. Hira ce ta ‘barke tsakanin Mus’ab da Anisa, yaya Faruk kuwa bai cika sa musu baki ba. Wani kallo ya jefa ma Anisa, tuni ta sha jinin jikin ta saboda ta gane ya gaji da zaman ta a gurin shi yasa ya mata wannan kallon. Sallma tayi ma Mus’ab ta tafi d’akin ta. Bayan tafiyar tane ya kalli Mus’ab yace "kai wai ba ka gajiya da Magana ne, ka zauna kana ba ma k’aramar yarinya labari, salon ta raina ka". "Yanzu miye laifi dan na zauna mun yi hira, idan mutum bai yi hira da k’annen shi ba, da wa zai yi hira?" "Matsalar kace, ai sai ka zauna kayi ta hira da yara, in suka raina ka kai ka jiyo". "kace kai baka hira da Teemar ka saboda ka da ta raina ka, ko da yake a ‘bangaren soyayya ba yara, sai a ‘bangaren hira ne akwai yara ko". Shiru ya mishi ya maida hankalin shi ga allon talabijin. Mus’ab ne ya dinga trying d’in numban Maryam, amma wannan baturiyar sai ce mai take yi is not reachable at the moment, haka ya gwada na Nana shima duk amsar d’aya take bashi. K’aramin tsaki yaja ya kalli yaya Faruk da hankalin shi ke kan labarum da ake yi a tashar Aljazeera. "Faruk ba ni wayar ka in kira Maryam, ban san ko network bane ya hana kiran zuwa, bari in yi using da airtel numba d’inka in kira da ita, may be kiran yaje". Dialling d’in numban yayi duk da haka bai je ba, dan haka ya yanke hukuncin kiran Nana. "Assalamu alaikum" Nana ta fad’a bayan ta d’auka. "Wa alaikumus Salam Nana, Mus’ab ne, na kira Maryam ban same ta ba, kuma ni yanzu ina Kaduna, idan kin fito lectures ki je can ki kwana, sai ki tafi school daga nan, nima gobe zan dawo". "Zan je insha Allah, amma yaya Mus’ab wannan numban waye?" ta tambaya. "Numban Faruk ne" "ka ce ina gaishe shi". Sallama suka yi ya katse wayar. Mik’a mishi wayar yayi yana cewa "Nana tace tana gaishe ka". Murmushi yayi yace "Ina amsawa". Faruk wai yaushe zamu gidan Teemah ne, na ga sai ja min rai kake yi, gwara ka tashi mu tafi in ga sarauniyar da ta sace zuciyar soja, yanzu na san kammanin ta ya canza, tun da dad’e ban ganta ba". Sanin in dai bai tashi sun tafi gurin Fatima ba a yanzu, Mus’ab ba k'yale shi zai yi ba. D’aki ya shiga ya d’akko tsarabar da ya musu tun a k’asar Uganda, ware na Fatima yayi da na su Ummu da gidan su yaya Aminu. Kallon Mus’ab yayi yace "Tashi mu tafi". " sojan Teemah". Sai da suka fara biya wa gidan yaya Aminu, bai same shi ba yana gurin aiki, Anty Jiddah ya ba tsarabar da ya musu, suka ta’ba hira sannan suka yi sallama ya tafi gidan mu. Shi da Mus’ab suka shigo cikin parlour suka zauna, yaya Faruk ne ya tashi ya nufi d’akin Ummu. Samun ta yayi da Kur’ani a hannun ta tana muraja’a, guri ya samu ya zauna a k’asan carpet ya gaishe ta. Hira suka d’an ta’ba sannan ya sanar da ita da abokin shi Mus’ab suke. Tashi tayi suka koma falon. Gaisawa suka yi ta tambaye shi ya su Hajiyan su da Maryam? Amsa mata yayi suna lafiya kuma suna gaishe su. Da kanta ta tashi ta shiga kitchen ta samo musu abin motsa baki. Ta d’an jima a gurin su sannan ta tashi ta nufi d’akina don ta sanar dani zuwan yaya Faruk. San da tashigo, samu na tayi ina waya da Dr Sadik. Ganin ta ne yasa na katse wayar ina jiran jin me za tace min. Murmushi tayi tace "yayan ki ne ya dawo, gashi can a falo". Da murna ta nace yaushe yaya Khalil ya dawo, shine ba zai zo ya ganni ba?". "Faruk nake nufi ba Khalil ba". Wani irin fad’uwar gaba naji wanda ban san dalili, nasan hakan ba zai rasa nasaba da fusakantar shi da zan yi. Murmushin da bai kai ciki ba nayi nace "Ashe ya dawo, san da muka yi waya dashi yake ce min a satin nan zai shigo". "ki tashi kuje ku gaisa, shi da Abokin shi yazo" tana gama fad’ar haka ta bar d’akin. Tashi nayi na yafa gyale a saman kaina jiki na duk a mace. Sallama na musu na nemi guri na zauna. Tun da na zauna yaya Faruk ya tsura min ido kamar wanda ya fara gani na a yanzu. Gaishe da bak’on da na gani a falon sannan na juya na gaishe da yaya Faruk. "Da girman kujerar ki Sarauniya a gurin Bregadier Faruk, dafatan mun same ku lafiya" Mus’ab ya fad’a. Murmushi nayi nace "lafiya lau, ya aiki". "aiki alhamdulillah". Satar kallon yaya Faruk nayi ganin yadda yake wani lumshe ido, na lura lumshe ido ya zama d’abi’ar shi. "yaya Faruk sannu da zuwa, dafatan kun dawo lfy". "lfy lau Teemah". "Ina fatan kin yi missing d’ina kamar yadda nayi missing d'in ki". Saurin sunkuyar da kai na nayi ganin yadda ya fad’i maganar ba tare da yaji kunyar bak’on da suka zo tare ba. "Tun da ba za ki amsa bas hi kenan". "Fatima, wannan Abokina ne, sunan shi Mus’ab, muna tare ne a Abuja a barrack d’in mu, yana da mata sunan ta Maryam". "Sannu da zuwa yaya Mus’ab, ya Anty Maryam d’in". "Tana nan lafiya, tace in nazo in gaishe da gimbiyar Faruk". A hankali na furta "Ina amsawa". Mus’ab ne yaci gaba da cewa " gaskiya na yaba da natsuwar ki a yadda na ganki, ina fatan za ki rik’e mana sojan mu da kyau saboda yana matuk’ar son ki, kullum cikin maganar ki yake yi, duk wanda ki ka ga Faruk na so to ba k’aramin abu ba ne, dafatan za mu samu guri a gun ki". Shiru nayi na sunkuyar da kaina, a gaskiya ban san me zan ce ma yaya Mus’ab ba. "Amaryar tamu mai kunya ce". Yaya Faruk sai a yanzu Magana da cewa "Mus’ab kar ka cika ta da surutun ka, nasan in ka fara Magana ba ka gajiya". "au shigan mata za kayi, wa yaga sabon shiga". A yadda na lura yaya Mus’ab mai wasa da dariya ne. Haka yaya Mus’ab yaci gaba da ja na da hira kamar mun dad’e da sanin juna. Sun d’an jima a gidan mu sannan yace in sanar da Ummu za su tafi, in ya samu time gobe zai shigo. Ummu ce ta fito rik’e da wata leda a hannun ta tace "har za ku tafi Mus’ab, gashi ba a kai ma Maryam ba yawa". "Na gode Ummu, Allah ya saka da alkhairi". "Ummu mun gode". yaya Faruk ya fad’a. Kallo na yaya Faruk yayi yace "Fatima ki biyo ni gurin mota, zan baki sak’o". Bin su nayi har gurin inda yayi parking d’in motar shi. Ledoji ya fito dasu wanda alama ke nuna ba ta k’asar nan bace yace "ki duba, akwai na su Ummu, d’ayan ledan mai custume da sauran kayan su ne naki". Wani tausayin yaya Faruk ne ya kama ni a lokacin ganin tun da muka shirya yake cikin faranta min rai, amma ni gashi ina son saka mishi da sa’banin haka. "Na gode yaya Faruk". Yaya Mus’ab ne ya ciro kud’i a wallet d’in shi yace "Fatima gashi ba yawa, kya sa credit". Kallon yawan kud’in nayi da ake cewa in sa credit, k’in amsa nayi nace nagode. "Nawa ne ba za a amsa ba ko Fatima, sai na masoyi za a amsa". D’aga min kai yaya Faruk yayi alamar in amsa. Amsa nayi na mishi godiya. sallama na musu na koma gida ina yaba kirkin yaya Mus’ab. A hanya suna tafiya suna labarina, yayin da Mus’ab ke ci gaba da tsokanan yaya Faruk. Kwanan Mus’ab d’aya yayi sallama da su Momi, Momi ta had’a tsaraba tace a kai ma su Hajiya da Maryam, haka ya ma Anisa kyautar kud’i wai tasa credit. Godiya tayi ta mishi tana cewa a gaida Anty Maryam. Nan yaya Faruk ya raka shi gurin motar shi suka yi sallama. *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* _Masoya wannan littafin, ina ganin comment d’in ku, ba abin da zan ce muku sai godiya_ _Ina tare daku har kullum_ _Na baku wannan shafin kyauta_🤝🏽 *Rabbana atinah fid duniya, hasanatan, wafil akhirati hasanatan, wa qinna azaban nar*. *Rabbana alaika tawakkalna, wa ilaika anabna, wa ilaikal masir* *QUESTION OF THE DAY* _Wane gida ne Mafi raunin gida da aka ambata a cikin Alkur'ani mai girma?_ 55&56 Bayan ya raka Mus’ab gurin mota ne ya koma cikin gida ya wuce side d’in Momi. Guri ya nema ya zauna yana ba ta labarin tafiyar da suka yi garin Adamawa da irin nasarorin da suka samu, sannan yaci gaba da ba ta labarin course d’in da aka tura su k’asar Uganda. Murmushi kawai Momi ke yi jin ci gaban da d’an ta yake samu, tana alfahari da hakan. Kallon shi tayi tace "Alhamdulillah Faruk, kullum ina maka addu’ar Allah ya kare min kai, ya baka nasara a aikin ka, ina rok’on Allah ya ci gaba da tallafa maka a al’amuran ka". Cikin jin dad’in addu’ar da Momi ta mishi yace "Amin Momi". Ci gaba tayi da cewa "Bayan nan sai maganar mu ta gaba shine maganar da muka yi kafin tafiyar ka, to yanzu ina son ka tsayar min da Magana, wace yarinya ce kake so, in kuma har yanzu ba da tsayayyar Magana da ita sai ni in za’ba maka, kasan wannan karan ba zan d’aga maka k’afa ba". Wani irin yalwataccen murushi yayi sannan yace "Momi komai ya zo k’arshe tun da na dawo, ba kowace yarinya ce nake so ba illa Fatima". Momi cikin rashin fahimta tace "Wace Fatiman kake magana". "Fatiman gidan Abbu". Shiru tayi kamar mai nazari sannan tace "Dama ka fad’a mata kana son ta ne ko sai bayan da ka dawo ne ka fad’a mata?". "Tuntuni na fad’a mata, sai dai tace min in ba ta lokaci tayi tunani". Cikin farin ciki Momi tace "Masha Allah, gaskiya naji dad’in wannan zancen, Allah ya za’ba mana mafi alkhairi". "Amin ya Allah Momi" ya amsa mata. Amma a ran Momi tana juya zancen ne a ranta cewa yarinyar dama yarinyar da yake ta fad’ar yana so ita ce Fatima, amma zancen Dr Sadik da taji Anisa ta ce mata shi yake son ta fa, ko da yake mace da samari aka san ta, amma in haka ne mai zai sa Fatima ta tsaya sauraren Dr Sadik bayan tasan Faruk ne yake son ta? ganin ba za ta samo amsar ba yasa ta bar zancen a ranta. A ‘bangaren Nana kuwa tun bayan gama wayar ta da Mus’ab da suka yi, tayi saving d’in number yaya Faruk a wayar ta. Taso a ce sun gaisa da yaya Faruk, miskilancin ta ba zai ba ta damar yin hakan ba, duk da dai tace a gaishe shi, gaskiya tana yabawa da halin yaya Faruk. Da daddare ta kunna data d’in ta, cikin sa’a tana chat d’in ta ga ya hau online. Kamar ta share shi, amma wata zuciyar na umartar ta da ta mishi Magana. Sallama ta tura mishi. Sai da aka d’auki wasu ‘yan mintuna sannan ya turo mata reply da amsa sallamar. "ka gane mai magana" abin da ta sake tura mishi kenan. "No explain your self". Ya sake turo mata. Ba ta ji dad’in haka ba, tana ganin ya kamata ace yayi saving d’in numban ta ko dan wataran. "I by name Nana Khadija, a sister to Mus’ab". Wannan karan bai d’au tsawon lokaci ba ya dawo mata da reply. "Oh Nana, ya karatu? ya su Hajiya". " Lfy lau, ya su Momi? "Lfy lau, ki gaida Hajiya". "Za taji" "Gud night Khadija" "Ok gud night yaya Faruk". Suna gama wannan chat d’in yayi offline. Ni kuwa tun san da yaya Faruk da abokin shi suka tafi, na dawo cikin falo d’in na nuna mata kud’in da abokin yaya Faruk ya ba ni, da kuma tsarabar da yaya Faruk ya basu, sannan na bud’e tawa tsarabar da ya min. Gaskiya ko ni nasan yaya Faruk ba k’aramin kasha kud’i yayi ba, duba kalar kayayyakin da ya kawo min, ko ni a lokacin jiki na yayi sanyi da irin kasha kud’in da ya min, ko Ummu sai da ta jinjina tsarabar tana cewa yayi yawa, shi da ya tafi course zai tsaya kashe min wannan kud’in. A lokaci d’aya kuma sai addu’a take yi ma yaya Faruk akan Allah ya bashi ladan zumuncin da yake yi da kyautata musu. Ni dai ba ni da bakin Magana sai ma tattara kayan da nayi na tafi d’aki ina tunanin game d’in da za mu buga da yaya Faruk idan yazo gobe. Lallai akwai badak’ala tsakani na dashi, koma mai zai je ya dawo, gwara ayi ta tak’are don hausawa na cewa "shure- shure ba ya hana mutuwa, kuma duk nisan jifa k’asa zai sakko". Da wannan na samu k’arfin gwiwar ci gaba da harkoki na, ba tare da na bar fargabar da ke raina tayi tasiri a kaina ba. Washe gari kamar yadda yaya Faruk yace zai dawo, hakan kuwa aka yi. Ina zaune ina assignment naji rurin waya ta, ganin yaya Faruk ne na ji gaba na ya fad’i yau nake so na samar wa kaina mafita, amma na rasa me yasa nake jin kamar ban da wannan power d’in. D’auka na yi muka gaisa. "Ki same ni a gurin shak’atawa" yana gama fad’ar haka ya katse wayar. Tashi nayi na yafa veil a jiki na kasancewar rigar da nasa doguwar riga ne. Yau cikin k’ananun kaya yayi, blue d’in T-shirt ne da bak’in jeans. Sallama na mishi na samu guri na zauna. Irin wannan kallon ya min da yake sa ni tsarguwa ya min, a lokaci d’aya yana sakar min sihirtaccen kallo. Ganin kallon ba na k’are bane yasa na katse shi da cewa "yaya Faruk sannu da zuwa". "yawwa Teemah". Ci gaba yayi da cewa "Fatima kamar yadda kika ce in baki lokaci ki yi tunani, to na baki isasshhen lokacin da nasan ya isa kin zartar da hukunci game dani, ina kuma so ki fad’a min yadda kike ji na a zuciyar ki". Yau ga dama na samu da zan fad’a ma yaya Faruk sirrin zuciya ta, sai dai abin takaici, zuciya ta na gargad’i na da kar in fad’a mai, gwara in bari da kanshi ya fahimci hakan. "Amma anya in nayi haka na kyauta kuwa?". Gaskiya ban kyauta ba, amma ina ganin wannan shine damar da zan samu in yi amfani da ita ba tare da ran kowa ya ‘baci ba. Shawarar da na yanke shine in mishi tattausan lafazi, in yaso daga baya sai in fito in fad’a mishi. "Yaya Faruk duk wanda yace yana son ka ya gama maka komai, ba abin da zan baka da zan saka maka da wannan Kalmar, kai d’an uwa na ne, ba yadda za ayi in k’i ka, ba abin da zance sai dai in ce Allah ya za’ba mana mafi alkhairi" Hak’ik’a yaji dad’in wannan lafazin nawa, sai dai yaso ace na fito na fad’a mai cewa ina son shi, amma ya na ganin ko kunya ce ta hana ni fad’ar hakan, yasan da sannu zan fad’a mishi wannan Kalmar. "Na gode Teemah, insha Allah zan ci gaba da son ki, fatana ke ma ki so ni kamar yadda nake son ki" yaya Faruk ya fad’a min cike da jin dad’i. "Insha Allah" na bashi amsa a tak’aice. Da haka yaci gaba da furtar min kalamen soyayya zafafa. Bai d’au wani tsawon lokaci ba ya min sallama ya tafi da niyyar in an kwana biyu zai dawo. Tun daga wannan lokacin yaya Faruk yaci gaba da nuna min so, sai dai ba na bashi k’ofar da kowa zai fahimci hakan. Bayan dawowar yaya Faruk daga gidan mu, ya samu Momi ya fad’a mata yadda suka yi dani, Momi ta ji dad’in haka, saboda a gaskiya tamu tazo d’aya da ita, tana d’auka ta kamar Anisa. Daddy da ya dawo daga aiki Momi ke sanar dashi daddad’ar labarin game da yaya Faruk da ni. Daddy yayi farin cikin jin wannan labarin, don haka Daddy yace zai samu Abbu suyi maganar dashi. Da daddare yaya Faruk ne a falon Daddy, su na tattaunawa game da matsalolin da ake fuskanta a k’asar mu, da irin corruption da yayi yawa, fatan dai Allah ya daidaita komai. Daddy ne ya canza hirar da cewa "Faruk, na ji kyakkyawan labari a gurin Momin ku, ta fad’a min Fatima ita ce yarinyar da kake so, gaskiya naji dad’in hakan, kaga ga kuma Anisa da Khalil, gaskiya wannan had’in yayi, sai dai muce Allah ya tabbatar da alkhairi, Insha Allah zan samu Ibrahim da maganar". Lallai biri yayi kama da mutum, ya lura da kusancin da ke tsakanin Anisa da Khalil, yasan hakan za ta faru, ya ji dad’in haka saboda yasan Khalil kamilin mutum ne da ba shi da matsala, yayi murna da Anisa ta za’be shi a matsayin mijin aure. "Daddy na gode, duk yadda kuka yi da Abbu d’in shi kenan, in na dawo sai a tsayar da Magana ko Daddy, plsss amma Daddy ba na so ya d’au time". Dariya Dadi yayi yace "lallai Faruk kace da gaske kake son ‘yar tawa, kai da ake ta fama da kai akan maganar aure, kana kaucewa, yanzu da kan ka ke rok’on kar a ja time, to zan fad’a ma Abbun ka abin da kace, na fi so ne a had’a da na Anisa da Khalil, kaga service yake yi, na fi so sai mun samar mishi aiki, in hakan bai yiwu ba sai a fara naku". Murmushi yaya Faruk yayi yace "Allah ya kaimu Daddy". "Amin Faruk". Haka suka ci gaba da hirar su, kana yaya Faruk ya ma Daddy sallama ya tafi side d’in shi. Yau Daddy ne da Abbu a office d’in su dake Wagini motors suna tattaunawa game da bunk’asar da kamfanin yake samun ci gaba, da kuma irin nasarar da suke samu a harkar motocin su, sannan su ka gangaro yadda za su assasa kamfanin ya fi haka. Daddy ne ya canza akalar hirar da cewa "Ashe d’anka duk wannan delay d’in da yake yi game da maganar aure, Fatima yake so". "wace Fatiman?" Abbu ya tambaya. "Fatima k’anwar shi". Wani irin farin ciki ne ya kama Abbu, shi gani yake yi ma yafi kowa murnar da jin wannan labarin. Yana son halin Faruk, yana d’aukar shi kamar d’an da ya haifa da cikin saboda yadda yake masa ladabi da biyayya. Tabbas duk wanda ya samu suruki kamar Faruk yayi dace, don a wannan zamanin suna da wuyar samu. Cike da farin ciki ya ce "gaskiya yaya naji dad’in wannan maganar, kuma ko b aka fad’a min ba, kai mai zartar da hukunci ne akan su, saboda haka duk yadda kayi daidai ne". Dadi yaji dad’i yanda ya bar mishi wuk’a da nama, don haka yace mishi in yaya Faruk ya dawo daga Abuja za a tsayar da Magana. Abbu na dawowa ya sanar da Ummu halin da ake ciki, ai tsakanin Ummu da Abbu, cikin su an rasa wanda yafi murnar da wannan zancen. Ummu cewa take yi "Fatima ta samu miji na gari, wanda na dad’e ina mata addu’ar samun Kaman shi, Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kai mu lokacin". Abbu kuwa amsawa yake yi da "Amin Aisha". Kallon Ummu yayi yace "wani hanzari ba gudu ba Aisha, wannan Dr fa da yake zuwa gurin ta, har ta turo shi ya gaishe ni, shi kuma a me ta ajiye shi tun da tasan Faruk ke son ta". Ummu ce tace "Alhaji a kira ta a a ji ta bakin ta, ya kamata ta dakatar da wannan Dr d’in saboda yanzu maganar aure ce za ta shiga tsakanin ta da Faruk, in ban da ma wautar Auta, kana da wanda kuke soyayya sai kuma ka ci gaba da soyayya da wani. Dariya Abbu yayi yace "Kin san ‘yan matan zamani, su suna ganin tsayawa da samari fiye da d’aya shine cinyewa, yanzu dai tun da shi wannan daman ba wai ya turo iyayen shi ba ne, sai a wa Fatima Magana ta bashi hak’uri don ban a son tara samari". Abbu ne ya umarci Ummu da ta kira ni. Samu na tayi ina kallon wani indian film mai suna "Kabhi alvidana kehna" Gaskiya film d’in akwai tausayi ga soyayya. Ummu ce ta katse min kallon da cewa "Auta ana nan ana kallo ne". Cikin shagwa’ba na ce "To ya zanyi Ummu, yaya Khalil ba ya nan bare muyi hira, film d’in ne zai d’auke min kewa, ina so ran weekend in tambayi Abbu zan je gidan su Anisa, daga nan sai mu je gidan su Anty Jidda da Aisha". "Da ko kin yi zumunci". Ummu ce taci gaba da cewa "Ki je Abbun ku na kiran ki". "To Ummu" na amsa mata. Bayan Ummu na bi muka shiga falon Abbu. Kusa da Abbu naje na zauna a k’asar carpet. "Sannu da hutawa Abbu, Ummu tace kana kira na". "Yawwa Autan Ummu, ni nace Ummun ki ta kira min ke, saboda ina so muyi wata magana da ke akan wani labari da muka ji mai dad’i". Shiru nayi ina sauraron jin Abbu yace labari mai dad’i za muyi Magana, wannan wane labari ne? Abbu ne ya katse min tunanin da cewa "Fatima na ji dad’i dad’in labarin da na samu cewa Faruk shi yake son ki, hakan yasa nake alfahari da wannan familin namu, nasan Hajiyan mu in taji labarin nan za ta fi kowa da murnar haka, saboda haka ba abin da za mu ce sai dai Allah ya tabbatar mana da alkhairi, sai Magana ta gaba, game da wannan Dr da yake zuwa wajen ki, ina so ki fad’a mishi yanzu kina da wanda za ki aura, kin ga dam aba turo manyan shi yayi ba, in ban da wautar ki Auta, kin san kina da wanda kike so kuma ki ke tsayawa da wani, ban a son tara samari, yanzu in Faruk ya dawo za a tsayar da Magana". Wani irin takaici ne ya tokare ni da naji na kasa bud’ar baki na in yi Magana, gashi ina so in fad’a ma Abbu cewa ni Dr Sadik ne za’bi na, sai dai nasan ban da damar fad’an hakan, baa bin da yafi ‘bata min rai sai jin cewa wai in yaya Faruk ya dawo za a tsayar da Magana, akan me yasa yaya Faruk zai sanar da su Abbu bai nemi shawara ta ba. Abin da yasa ban fad’a mishi k’uduri na ba saboda ina son shawo kan matsalar ne a hankali, ashe ban san hakan zai jawo min matsala ba. Abbu ne ya kalli Ummu yace "Aisha ko akwai abin da zaki ce". "Ba abin da zance Alhaji, sai dai in ce Allah ya k’ara daidaita su, ke kuma Fatima ya kamata ki kula, ba yadda za ayi ki tauna taura biyu a lokaci guda, ki ba ma shi Dr Sadik d’in hak’uri, kar yaga kin yaudare shi, ki fito ki fad’a masa da wuri, ba ma kyau nema akan nema". Duk wannan maganar da Ummu ke yi kamar tana k’ara sa zuciya ta na zafi, da ina da hali da na tashi na bar gurin ba tare da sun sallame ni ba, amma nasan hakan ba zai yiwu ba. Abbu ne ya kalle ni yace "Fatima hakan ya miki ko, nasan in Faruk ya dawo lokacin kun yi exam, kin ga saura semester d’aya, sai a tsayar da bikin bayan kammala karatun ku". Shiru nayi ban ce komai ba, don lokaci wani irin zugi nake ji zuciya ta na k’ara yi. Ummu ce tayi dariya tace "Alhaji hakan ya mata tun da kaga tayi shiru, kasan yanzu auta ta girma". Dariya dukkan su suka yi kana Abbu yace "za ki iya tafiya Fatima, Allah ya miki albarka". "Amin Abbu" na amsa a tak’aice. Tun da na tashi na koma d’aki na, ko falo ban zauna naci gaba da kallon film d’in da nake yi ba, a lokacin ji nake yi komai ya fitar min a rai. Ina shiga d’aki na fad’a kan gado ina zubar da hawaye mai d’aci. Hawaye ne yaci gaba da zuba a ido na, ban damu da in goge ba saboda nasan ko na goge wasu ne za su ci gaba da zuba. Me yasa sai yanzu da nake ganin na kusa samun nasara akan wannan lamarin, sai gashi wata badak’alar ta shigo, yaya Faruk ya wargaza min target d’ina, ba abin da yafi d’aga min hankali sai jin cewa in yaya ya koma aiki ya dawo za a tsayar da maganar bikin mu, kenan hakan na nufin rabuwar mu da Dr Sadik ya zo kenan. Zuciya ta za ta iya hak’ura da Dr Sadik kuwa? "Ba za ta iya ba domin nayi nisa da son shi" zuciyata ta ba ni amsar hakan. Ya kamata in bi komai a sannu dan ganin na samu abin da nake so ba tare da ran su Abbu ya ‘baci ba. Fitowa in fad’a musu Dr Sadik nake so na nufin fuskantar hukunci daga kowane ‘bangare. "Allah ka kawo min mafita cikin sauk’i, ba ni da inda za ni na nemi shawara don nasan ba mai goyon baya na, Allah kai nake rok’o ka kawo min komai cikin sauk’i". Da wannan addu’ar na samu na tashi naje nayi sallar issha’i, ranar ko abincin dare ban tsaya na ci wani abun kirki ba. Ko shi a yanzu ya rasa inda na sa gaba, duk hirar da zai min ban cika tsayawa ina bashi cikakkiyar amsar da ta dace ba, sai dai in bishi da eh ko a’ah, in ya tambaye ni me ke damu na sai dai in ce mai ba komai, ga abin da ke damuna a raina shine yadda na kasa fitowa in fad’a mishi ina da wanda nake so ko zai k’yale ni in huta, amma abin haushin na kasa. Yaya Faruk bai d’auki hakan da wata manufa ba, sai ma uzuri da ya min akan cewa yanayin d’an adam yana tsintar kanshi da rashin walwala. Wannan time d’in yaya Faruk ya d’an dad’e a Kaduna, kusan 2 weeks yayi sannan ya koma Abuja. Duk wannan abin da ya faru bai sa naji na rage son Dr Sadik ba, sai ma wani k’ara son shi da nake ji a zuciya ta, matsala ta dashi shine yadda yake kawo min uzurin bai samun zama ko lokaci, kamar akan shi aka fara aikin likita, ni kaina yanzu na rage zuwa asibiti gurin shi in muna free ba mu da lectures, a wani lokaci sweet word d’in shi ke wanke duk wani laifi da ya min. Ko ya bani wani gift yanzu ba na nuna wa kasancewar na ga kowa a bayan yaya Faruk yake. Na kasa fitowa in ce mai ya dena zuwa gidan mu in na tuno da danbarwar da muka yi dashi akan haka, dubara ce tazo min nace mun kusa exams, yanzu ban da wani time, mu dinga had’uwa shi a school kawai sai bayan exams. Wannan lokacin bai min musu ba sai ma fatan alkhairi da ya min akan jarabawar da za mu fara. Da haka na samu Sadik ya daina zuwa gidan mu, sai dai mu had’u a school, ko yazo department d’in mu, ko ni in shiga asibiti in bai da aiki. Komawar yaya Faruk da kusan 3 weeks ne, Maryam ta haifo namiji. Tun da aka yi haihuwar Nana ta tare a gidan, ko School ne sai dai ta tafi ta nan ta dawo. Yaya Faruk ma yana shigowa ya d’auki yaro ayi hira dashi sannan ya tafi. Ko wani sa’in in ya dawo daga aiki sai ya kira Nana ta kawo mishi yaron ya d’auke shi kafin ya tafi block d’in shi. A wannan haihuwar Nana ta fara sakewa sosai da yaya Faruk duk da kasancewar su Miskilai, amma yanzu ba laifi suna hira. Ran suna aka rad’a ma yaron sunan Dadin su Mus’ab wato Sa’id amma suna kiran shi da Asim. Yaya Faruk siyayya yayi ta bajinta, kayan baby ya siyo masu yawa, sannan ya had’o da na mai jegon. Mus’ab kuwa rasa bakin godiya yayi, sai jinjina halin Faruk yake yi na kyauta kamar bai san ciwon kud’i ba in ya tashi kyauta, fatan shi Allah ya k’ara dank’on amincin su da yaya Faruk, saboda yaya Faruk aboki ne na kwarai. Yaya Khalil yana zuwa ya d’an yi kwanaki ya koma, ina kewar shi saboda shine abokin hira na. Soyayyar su suke gudanarwa shi da Anisa cikin kwanciyar hankali ba sa tare da kowace matsala, su sun sami goyon baya ko ta ina, ni kuwa yanzu ba ni da damar yin haka. Abin da ya bani mamaki shine yadda yaya Khalil bai min zancen yaya Faruk, hakan na nufin bai ji zancen ba ne, nasan yaya Khalil suna gaisawa da Sadik, amma in yaji kuma yaya Faruk yana so na, bayan shi zai bi, dama tuntuni yana bugar ciki na yaji ko akwai wata alak’a tsakani na da yaya Faruk in ace mai ba komai, ina ga yanzu in yaji zancen. Dole na ja baki na nayi shiru ban mishi maganar ba. Anisa ma ba ta min maganar ba, nasan cewa may be ba ta ji me ke wakana ba ne, nasan sai ta fi kowa zak’ewa akan maganar, in ba ta fi kowa ba, to ina jin ita ce a sawun gaba. "Kin manta da Hajiyan Wagini ne?’ wata zuciyar tace min. Nayi tuya na manta da albasa, Hajiyan Wagini ita ce ja gaba a ganin wannan auran ya gudana. Kenan ba ni da tsimi ba ni da dubara, sai yadda Allah ya zartar da hukuncin shi a kaina. Ko dai in fad’a ma Halima halin da nake ciki ne? ko kuma Aisha, duk wanda na fad’a ma wa a cikin su nasan za su bani shawara da kuma samar min mafita. A ‘yan class d’in mu, akwai k’awaye da nayi basu wuce 3 ba, Akwai Fauziyya, Salma sai Halima, duk a cikin su mun fi shak’uwa da Halima, shi yasa na yanke shawarar fad’a mata halin da nake ciki tun da itama in tana cikin matsala tana neman shawara ta. Da wannan shawarar nayi amfani bayan mun fito lectures muka samu guri muka zauna. Halima ce ta kalle ni cikin kulawa tace "Fatima ya aka yi ne, nag a kamar ki na cikin damuwa". Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke sannan nace "Ke dai bari Halima, ina cikin damuwa". "Me yake damun ki" Halima ta tambaye ni. Nan na zayyane mata duk abin da yake faruwa, har kawo yanzu da ake maganar in yaya Faruk ya dawo za ayi fixing d’in date d’in bikin mu. "Gakiya kina cikin rikici kuwa Fatima, ni dai a ‘bangare na ina goyon bayan ki, gwara ki auri wanda kike so, da a zo kuma ayi aure abu yak’i dad’i, mutane bas a gane halin da mutum yake ciki in ya fad’a tarkon soyayya, sai a dinga ganin laifin ka akan cewa kai ka d’aura ma kan ka, bayan ita soyayyar ba ta shawara da kai a lokacin da za ta shiga, ni dai shawarar da zan baki shine ki fito ki fad’a ma shi yaya Faruk d’in abin da yake ran ki, sannan ki samu su Abbu ki musu bayani, nasan za su fahimce ki, kuma shima yaya Faruk d’in in har son gaske yake miki ai zai so ki samu farin cikin ki, shi kuma ya fawwala ma Allah lamuran sa, sai ki ga Allah ya masa za’bi nagari". Sai a yau na samu wacce ta goyi baya na akan wannan maganar, hakan yasa na ji dad’in fad’a ma Halima da nayi, ko ba komai yanzu na samu mai bani shawara da share min hawaye na. Cikin murna da shawarar ta nace "Na gode Halima da wannan shawarar da kika bani, insha Allahu zan yi amfani da ita". "Ba komai Fatima, amfanin zaman taren kenan da kuma aminci". Ci gaba nayi da cewa "Kin san me? ban san ta yadda za ayi in je in fad’a ma su Abbu wai Sadik nake so ba, nasan wannan maganar da zan fad’a mishi zai iya sa wa yayi fushi dani shi da Ummu, za kuma su iya d’aukar mummnar mataki a kaina". "Ki bi komai a sannu ne Fatima, a hankali sai ki fad’a musu, nasan da yardar Allah za su yarda da za’bin ki". Haka muka zauna a gurin Halima na ci gaba da ba ni shawarwari. Sai da muka ga time d’in komawa class yayi sannan muka koma class. Lokaci na ta tafiya, sai gashi har mun fara rubuta exam. Kamar yadda muke jarabawar zango na d’aya a ND 2, sai ya zamana mun fi shan wuya akan sauran jarabawar. Fatan dai Allah ya taimake mu ya kuma ba mu sa’a a jarabawar mu. Bayan gama jarabawar mu naso muje Wagini mu d’an yi kwanaki tun da ba wani hutu mai yawa aka bamu ba, amma da na tuno da yanzu Hajiyan Wagini tasan abin da ke tsakani na da yaya Faruk, nasan idan na je matsa min za tayi akan maganar, shi yasa na hak’ura da zuwan. Hutun zangon da aka bamu ba wani mai yawa bane, shi yasa nayi tunanin zuwa gidan su Anty Jidda in yi kwana biyu a can. Yanzu ban cika son zuwa gidan su Anisa in kwana ba, saboda yanzu kulawar da Momi take ba ni tafi ta da, duk dama can tamu tazo d’aya, yanzu sai nake ji duk gidan ya fita kaina. Duk zuwan da nake yi Momi ba ta kawo min zancen yaya Faruk, ko tayi hakan ne dan kar in dinga jin kunyar ta ina jin. Ko a gidan yaya Aminu da na je yin kwana biyun, ban wani ji dad’in gidan ba saboda yadda yaya Aminu shi da Anty Jiddah suke zaunar dani sun aba ni shawarwari akan yaya Faruk, suna kuma k’ara jaddada min yadda yaya Faruk yake so na, bas u san duk wannan tunatarwar da suke min ba shi zai sa in canza k’udiri na, sai dai in ji su kawai, in da nake samun sauk’i ka ga dariya ta a gidan shine in su Humaira da Nabil muka had’u ina jan su da wasa, to nan za a ji magana ta. A daddafe nayi kwana biyu na koma gida. Mun koma zangon k’arshe a karatun mu, sai ya zamana duk wani hope namu yana kan wannan semester, tun da a shine muke sa ran final a karatun mu, don haka muka sake ba da himma dan ganin mun samu abun da muke so. Ina kwance da yamma a gado na lumshe ido na kamar mai yin bacci, a zahiri kuwa tanini ne ya dabaibayi ganin har yau ban samo wa kaina mafita ba, gashi kuma banyi amfani da shawarar da Halima ta bani ba, da yanzu komai ya zo k’arshe. K’arar sautin da ke tashi ne a waya ta na musamman da nasa a wayar yasa na gane Dr Sadik ne yake kira na. D’auka nayi cikin shagwa’ba nace "Hello, My Prince Sadik". "My Princess Zahra" shi ma ya fad’a. Ci gaba yayi da cewa "gani a wajen gidan ku, ki fito ki same ni". Duk da na ji dad’in zuwan shi sai da na ji fargaba, yanzu ban cika son yana zuwa ba tun da aka san me ke tsakani na da yaya Faruk, gashi Ummu da Abbu sun ja min kunne akan in dakatar dashi da zuwa, in fito in fad’a mishi yanzu ina da wanda zan aura. Dr Sadik ne ya katse ni da cewa "Ki na ji na kuwa Zahra". "Ina jin ka Dr, gani nan zuwa". Jiki na duk ba laka na sa Hijab d’ina na fito, samun Ummu nayi a falo tana zaune. Ganin Ummu a falo yasa na k’ara jin wata fargaba, duk da haka sai ban nuna hakan ba. Ummu ce ta kalle ni da alamar tambaya tace "Fatima ina za ki na gan ki da Hijab a jikin ki". Rasa abin da zance mata mayi. "Ke fa nake tambaya Fatima" ta sake jefo min wata tambayar. Cikin kame-kame nace "Dr ne yazo, shine zan je". Tuni fuskar Ummu ta canza zuwa ‘bacin rai tace "Dama Fatima ba ki fad’a mishi yanzu ki na da wanda za ki aura ba, kin fi son ki dinga ‘ba ta mishi lokacin shi, to ba na son irin haka, in kin je ki fad’a mishi gaskiyar magana ki na ji na ko?". "Zan fad’a mai Ummu" na fad’a da alamar rawar murya. "Yawwa Auta ta, je ki tun da yana jiran ki". Fita nayi amma duk ilahirin jiki na duk a mace yake, ganin tun a yanzu yadda Ummu ta fara min fad’a, ba abin da ke k’ara sakar min gwiwa in na ji ana maganar wai ina da wanda zan aura. Da haka na k’arasa na bud’e k’ofa na fita, na nufi inda yayi parking a waje. Bud’e min d’ayar k’ofar yayi alamar in shiga ta cikin motar shi. Ba na so ya fahimci halin da nake ciki yasa na aro murmushi na yafa a fuskata. Kallo na yayi yana sakin murmushi, a lokaci d’aya muna musanyar kallo ni dashi. "Zahra ta, sai ki ganni unexpected ko". "Na ji dad’i da ka min zuwan ba zatan, dan nayi missing d’in ka". Murmushi yayi yaci gaba da cewa "Zahra ina ganin lokaci yayi da zan turo su Daddy na gurin su Abbu ko, ya kamat by now a ce akwai wata magana mai k’arfi a tsakanin mu, are my right" ya tsura min ido yana jiran amsa ta. In akwai abin da nake jira, bai wuce a ce Sadik yace zai turo iyayen shi ba, sai gashi yau ya fad’a min amma ba ni da damar amincewa da hakan, tun da nasan abin da yake tafiya yanzu game da magana ta da yaya Faruk. "Are you with me Zahra" Sadik ya fad’a ganin yadda na yi shiru. Ajiyar zuciya na yi kana nace "gaskiya wannan shawara ce ka kawo, amma ina so ka d’an ba ni time, kaga ana so ne a had’a mu da yaya Khalil kuma yanzu service, idan ya dawo hutu sai in mishi magana a san yadda za ayi, sai in sanar dakai, ina hakan zai fi ko". "Hakan ma yayi, bari in k’arasa gida in huta". "Gaskiya kuna k’ok’ari, aikin likita ba hutu". Dariya yayi yace "Haka za mu daure mu ci gaba da yi, Allah ne zai ba mu ladan". "Allah ya taimaka" "Amin". Fito wa daga cikin motar nayi na jingina da window d’in motar. "Ya aka yi ne Zahra". "Ba komai Dr". Cikin tsokana yace "Ko kar in tafi ne?". "In da akwai hali sai in ce eh, amma ina so Sadik d’ina ya samu hutu, have a nice day". "Thanks Zahra". Sallama muka yi na bar jikin motar na nufi cikin gida, shi kuma Dr ya ja motar shi ya tafi. A daidai wannan lokacin kuma yaya Faruk ne ya shigo da motar shi cikin layin. Ganin ni ce na bar jikin motar yasa yayi tunanin waye a cikin motar na ke tare dashi, kau da wannan tunanin yayi ya k’araso gate d’in gidan mu. Horn yayi mai gadi yazo ya bud’e mai ya shiga. Sallama yayi ya shigo cikin falo d’in. Saurin d’ago kaina nayi don jin muryar mai yin sallama da ban tsammaci zuwan shi a wannan lokacin. Amsa mishi sallamar nayi ina mai sakin murmushin dole. Zuwa yayi ya zauna a kusa dani yana murmushi yace "Teemah, I miss you a lot". Maimakon in ba shi amsar da yake buk’ata, sai ma cewa nayi "Sannu da zuwa yaya Faruk". "Yawwa Teemah, ina Ummu take?". "Ta na ‘dakin ta". "Ok". Tashi nayi na d’akko mishi Table water da glass cup nazo na ajiye mai. "Teemah yaushe za ki k’ara min Samosa da Spring roll". A raina nace "Sai dai in maka dan darajar kai yaya na ne, kuma yanzu muna shiri, amma ba wai dan kana duba matsayin kai masoyi na ba ne". "Ran da kake buk’ata sai in maka" na bashi amsa a tak’aice. "Ok ran da nake so zan miki magana". "Teemah wa na gani yanzu a mota kin dawo daga wurin shi" ya fad’a da zafin rai kamar ba shine ya gama min magana da sanyin murya. Tsoro ne ya kama ni wanda in ka lura da ni sosai za ka iya gane hakan, amma sai na daure na ce "Oh wai Dr Sadik kake magana, a clinic d’in makarantar mu yake aiki, wani handout d’ina na manta dashi a office d’in shi, shine ya kawo min". "Ya aka yi yasan gidan ku?" ya sake jefo min wata tambayar. Nasan in ba kare kaina nayi ba, zan iya ja ma kaina, don haka na shirya k’aryar da zanyi nace "Ai a bayan layin mu yake, rannan ne ya ganni na fito daga gidan mu, shine ya tsaya muka gaisa yake tambaya na dama a nan layin nake, na ce mishi nan ne gidan mu, yau da na manta hand out d’ina shine ya kawo min". "Ya kamata ki kula, ina da kishi, ba na so wata mu’amala ta ci gaba da had’a ku in ba ta rashin lafiya ba da ya kama dole ki je in ba ki da lafiya, ki fad’a mishi ya daina zuwa gidan nan, dan ban ga amfanin haka ba". Wani irin haushin yaya Faruk ne ya kama ni a lokacin, ya wani tasa ni ya na ba ni command kamar wani uba na, shi a ganin shi yanzu yana da matsayi biyu a gare ni da na matsayin yaya a gare ni da kuma wanda ake tunanin shi zan aura. Ashe kuwa za muyi fito na fito dashi dan ban ga yadda zai ce in yanke huld’a ta ba da Dr. Ko da yake bai san me ke tsakanin mu dashi ba, shi yasa yace haka, amma duk da haka saurin nuna ‘bacin rai ba nawa bane, da sannu zai fahimci Dr Sadik shine yake mulkar birnin zuciya ta. Don haka cikin ladabi nace "Zan kiyaye yaya Faruk". Murmushin jin dad’i ya saki sannan yace "that is my Teemah". Ci gaba muka yi da hira amma ni duk zaman ya ishe ni, in na tuno yadda iyayen mu ke murna da wannan had’in sai in dinga jin raina yana ‘baci. Mik’ewa yayi yace "Bari in je gun Ummu mu gaisa". "Sai anjima yaya Faruk, nima d’aki zan shiga in yi karatu, akwai wani assignment da zan k’arasa". "Sai mun yi waya kenan". "Ok" na fad’a a tak’aice na tafi d’aki na. Shiga gurin Ummu yayi suka gaisa kana ya fito ya tafi. Yau kusan sati biyu kenan da zuwan yaya Faruk Kaduna, kasancewar ya fad’a min ya nemi hutu saboda yana so a gama komai akan maganar bikin mu dashi. Gani nake wannan matsalar shi, koma hutun wata nawa zai d’auka wannan matsalar. Yanzu had’uwar yaya Faruk da Dr Sadik kusan sau uku kenan, ban da wnada ya min gargad’i akan in yanke mu’amala dashi, tun yana tambaya ta ina mishi k’arya, har ta kai ya fara nuna min ‘bacin ran shi sosai. Yau ma hakan ta kasance, muna tare da Sadik a k’ofar gidan mu kasancewar yanzu ba ya shigowa harabar cikin gidan mu, sai ga motar yaya Faruk ta shigo layin. Wani irin tsoro ne ya kama ni da hakan ya nuna a fuska ta, nasan yau mai raba ni da yaya Faruk sai Allah. Cikin kulawa yace "Zahra me ya faru ne, naga yanayin ki ya canza". "Motar yaya Faruk ce na gani, kuma ya hana ni tsayawa zance". Wani irin kallo ya min na tuhuma sannan yace "Akan wani dalili zai hana ki". "Nima ban san dalilin shi nayin haka ba". "In ba rami me ya kawo zancen rami, haka kawai ba zai ha na ki tsayawa da wani ba, dole yana da dalilin shi nayi hakan, ya kamata ki gano da dalilin yin haka, in kuma kin san dalilin shi nayin haka sai ki fad’a min". Yanayin da ya min magana yasa nima na ji raina ya ‘baci dama ga kuma tsoron yaya Faruk da ya cika min rai, don haka nace "Ban gane me kake nufi da wannan maganganun n aka ba Sadik". "Za ki gane ne in ki ka gano dalilin". Ganin yadda Sadik yake fad’a min duk maganar da ya ga dama yasa nima na fita cikin motar ba tare da mun yi sallama ba, shi ma Sadik a lokacin ya ja motar shi ya tafi. A lokacin kuma yaya Faruk ya ajiye motar shi a bakin gate ba tare da ya shigo da motar ciki ba. Sauri nake in shiga cikin parlour saboda ba na so yaya Faruk ya tarad dani, dan nasan gamon mu dashi ba dad’i. Takun tafiyar shi da na ji yasa na k’ara saurin tafiya ta, don ba na so ya tsare ni da tuhumar shi. "Teemah! Ya kira suna na da wata irin murya da ta razanar da ni. Cak na tsaya da tafiyar da nake yi. _Ni kaina 'yar mutan Paki zan so jin yadda za ta kaya tsakanin Teemah da Faruk_ *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* _Wannan Shafin naku ne_ *Naga comment d’in ku a group daban-daban, hakan yasa naji dad’in yadda na ga kowa yana fad’ar ra’ayin shi game da fans d’in novel d’in*. *Election d’in fans da na sa akan novel d’in ina ganin yadda mutane suke za’ban fans d’in su, sai dai kamar na ga akwai partiality 😀 a wannan election d’in* *A next page zan fad’i wanda yafi yawan mabiya* *Na gode da yadda kuke bin wannan novel d’in sannu a hankali*🤝🏽 _GAISUWA GARE KI_ *Barrister Teemah* *Ina mik'a gaisuwa ta gare ki da irin k’ok’arin da kika yi na ba da amsar question of the day, Allah ya k’ara ilimi mai amfani* *Haka amsar take, mafi raunin gida da da aka ambata a cikin alkur’ani shine Gidan gizo-gizo* *TUNATARWA*: _Rayuwar Duniya tana k’unshe da abubuwa ak’alla tara_: _Farin ciki_ _Bak’in ciki_ _Had'uwa_ _Rabuwa_ _Samu_ _Rashi_ _Lafiya_ _Ciwo_ _Mutuwa_ _Annabi Muhammad (s.a.w) ya hore mu da muyi hak’uri da duk wanda muka yi karo dashi, domin ba zai dauwama ba, zai wuce_ _Allah ka k’ara mana hak’uri_ 57&58 Cikin takun k’asaita ya k’araso in da na tsaya, gaba na sai fad’uwa yake tun san da ya kira suna na. Wani irin kallo yake min da yake nuna yana cikin fushi. "Fatima miye had’in ki da wannan Dr da nake yawan ganin ki dashi?". "A clinic d’in makarantar mu yake aiki, shine yake biyo wa muna gaisawa". Wani banzan kallo ya k’ara watso min kana yace "Amma tun yaushe na ce miki ki rabu dashi, miye amfanin zuwa gurin ki da yake yi dan kawai yana duba lafiyar ki, in har ba yana da manufar shi ta yin haka ba, Fatima let me warn you for the last time, duk ran da na sake ganin ki dashi, two of you will face the consequences, kar ki ga dan ina son ki zai hana in kin shiga gona ta in hukunta ki, ya kamata ki gane ni mutum ne mai kishin abin da nake so, bare wacce nake sa ran zan aura, ki kiyaye". Yana gama fad’ar haka ya juya ya fita ba tare da ya shiga cikin gidan ba. Wata irin ajiyar zuciya mai k’arfi na saki don gaba d’aya a tsorace nake dashi, yau yaya Faruk na ga alamar idan da nayi wasa zai iya fasa min jiki ya bar ni da jinya. Haka na ja jiki na koma d’aki na ina addu’ar Allah ya kawo k’arshen wannan lamarin. Tun san da iyayen mu suka san da zancen yaya Faruk na rasa sukuni, gashi matsalar wadda nake tunanin za mu raba matsalar tawa dasu b azan iya fuskantar su ba. Rok’o na Allah ya d’aura ni akan su, ina ganin ko wani challenges zan iya fuskanta in dai akan Dr ne, shi nake so, ba kuma dan yafi yaya Faruk ba, hasalima yaya Faruk yafi shi komai. "Me yasa so ya zo min ta wannan sigar" Gashi na samu wanda nake so amma ba ni da kwanciyar hankali saboda wani Katanga da ta shiga tsakanin mu. Ga wani k’arin damuwar shine yadda Sadik yake tuhuma ta da wani zargin shi na daban, dan ma bai san halin da nake ciki ba game dashi na yadda ake so a raba mu, gashi yanzu yaya Faruk ya min gargad’i na k’arshe akan shi, na san kuwa zai iya d’aukar matakin da ya zo mai, ya kamata in kiyaye taku na don kar in fad’a trap d’in yaya Faruk ni da Sadik, ba k’aramin aikin shi ba ne yasa a kama Sadik a je a mishi horo ko shi ya d’au mataki da kanshi, ni kuwa b azan so abin da zai ta’ba min Dr ba. Ni ma yau yadda na ke ji na ba zan iya kiran Dr in bashi hak’uri ba dan yaga ina son shi sai ya dinga min fad’a ko ya fad’a min maganar da ya ga dama, kuma ban da halin rama wa. Don haka na share shi na tashi na ci gaba da harkoki na amma duk da haka tunani ne a raina kan matsalar da zan fuskanta nan gaba. Yaya Faruk tun da ya bar gidan mu ya koma gida cikin zafin rai. San da ya shiga main parlour d’in ya samu Anisa a parlour tana waya da yaya Khalil. Saurin katse wayar tayi ta mishi sannu da zuwa. "Ki same ni a side d’ina Anisa" yana gama fad’ar haka ya nufi side d’in shi. Yanayin shi da Anisa ta gani yasa ta ji ba dad’i a ran ta, da alamar akwai abin da yake damun shi. Tun da ya shiga d’akin ya rasa mai ke damun shi, ya rasa wani irin so yake ma Fatima haka da har yake jin wani irin kishin ta haka. Anisa ce ta shigo d’akin had’e da sallama. Ciki-ciki ya amsa mata. A ranta kuwa addu’a take ta jerowa saboda yau yanayin yaya Faruk ya sa ta a tunani. Cikin sanyin murya tace "yaya gani". Wani huci ya furzar sannan yace "Anisa waye Dr Sadik?". "A clinic d’in asibitin mu yake aiki". "Akwai wata alak’a ce a tsakanin sa da Fatima?" ya jefa mata wata tambayar. "Eh yaya Faruk akwai". Wani irin fad’uwar gaba yaji a lokaci d’aya idon shi ya kad’a ya canza kala. "Mecece alak’ar su d’in?". Anisa ta tambayi kan ta. Anisa ta fara mamakin tambayoyin da yaya Faruk yake jero mata, to me yasa yake son sanin alak’ar su? Wata irin tsawa ya daka mata da ta sa ta tsoro yace "ki bani amsar tambayar da na miki". Cikin rawar murya Anisa tace "Akwai alak’ar soyayya a tsakanin su". Wani irin kallo ya watsa mata kamar bai yarda da amsar da ta bashi ba. "Ita ma tana son shi? Ya k’ara tambayar ta. "Eh ta na son shi". "Tun yaushe suka fara soyayya". Wannan karan tambayoyin sun ma Anisa yawa, tana tunanin yaya Faruk bayan karatun sojan da yayi, ko ya had’a da aikin jarida ne a course d’in su, saboda wannan tambaya ta isa haka. "Anisa don’t let me come near you, in ba haka ba jikin ki zai fad’a miki, don iskanci sai in miki tambaya ki tsaya wani tunani". Anisa tana jin abin da yace da sauri ta ce "Ina ganin tun bayan gama siwes d’in mu ne". Shiru yaya Faruk yayi yana mamakin yadda Fatima ta maida shi k’aramin yaro, ta sa shi yaci gaba da son ta alhalin ta san ba ta san shi, baa bin da ya fi mishi ciwo shine yadda tayi amfani da damarta ta yaudare shi, dole ne ya hukunta ta daidai da laifin da ta mishi, kenan duk wannan lokacin da ya furta ma ta son shi ta d’auke shi a banza, ba ta tsaya a nan ba sai da ta had’a da son wani bayan shi bayan tasan tuntuni yake son ta, hakan na nuna sai bayan da ya furta mata yana son ta sannan ta fara soyayya da wannan Dr da kullum take mishi k’aryar ce wa suna gaisawa ne. "Me yasa wasu matan suke da yaudara ne?". Wannan tambayar ita ce ta ke mishi yawo a k'wak'walwar shi. Muryar shi ce a wannan lokacin tayi sanyi ya kalli Anisa yace "Anisa dake za a munafunce ni, a yaudare ni, ina tunanin ko kowa zai min haka, ban dake Anisa, saboda duk abin da na miki, ba ki da d’an uwan da ya wuce ni". Anisa ba ta fahimci inda maganganun yaya Faruk suka nufa fa. Kallon shi cikin rashin fahimta tace "yaya Faruk ni ban dani aka yaudare ka, hasalima ban fahimci mai kake nufi ba". Cikin ‘bacin rai yace "kina nufin ba ki san ina son Fatima tsawon lokaci ba, ko kina so ki fad’a min cewa Fatima ba ta fad’a miki ina son ta ba? shine ke kuma ki ka ba ta shawarar tayi soyayya da Dr saboda ni ba ki d’auke ni a matsayin yayan ki ba". Mutuwar tsaye Anisa tayi da jin wannan magangann da yaya Faruk yake fad’a. "Yaya Faruk yana son Fatima? tun yaushe kenan yake son ta? me yasa Fatima ba ta fad’a mata ba" duk wannan jerin tambayoyin da take dashi tasan ba wanda ya dace ya amsa mata sai Fatima. Tausayin yayan ta ne ya kama ta a lokaci guda ganin yadda a loakci d’aya yanayin shi ya canza. "Yaya Faruk ina son ka yarda da maganar da zan fad’a maka, wallahi tun da muke da Fatima ba ta ta’ba fad’a min kana son ta ba, yaya Faruk ya za ayi in goyi bayan bare bayan nasan d’an uwa na yana son ta, yaya Faruk ba ni da kowa da zan kalla a matsayin d’an uwa fiye da kai, ina so ka yarda da magana ta" Anisa ta fad’a da murya ta dake nuna alamun ta na son yin kuka. Ya d’an ji sanyi game da bayanin da Anisa ta mai, ya kuma yarda cewa ba ta san me ke tsakanin shi da Fatima ba. Nuni ya mata da zo ta zauna a inda take. Jikin ta ba k’wari ta tako ta zo ta zauna kusa dashi. Hannun ta ya rik’e ya fara ba ta labarin tun sa da ya fara so na, da kuma san da ya furta min yana so na. Bayan ya gama ba ta labarin ne ya d’aura da cewa "Anisa ina son Fatima wanda ni kaina ba zan ce miki ga lokacin da na fara son ta ba, na riga na mik’a mata yarda cewa Fatima za ta so ni duk kuwa da yadda a da take min kallon mak’iyin ta, sai gashi ta shammace ni a lokacin da ban yi zato ba". Anisa ce ta kalle shi cikin tausayi tace "yaya Faruk insha Allahu in dai Fatima rabon ka ce, sai ka aure ta kuma za ta so ka, in kuma ba rabon ka bace, duk son da kake mata sai ka ga Allah bai nufa kun yi aure ba, ka ci gaba da addu’ar neman za’bin Allah, nima zan taya ka da addu’a". Hak’ik’a ya ji dad’in maganganun Anisa da ta mishi. Murmushin da bai kai ciki ba ya sakar mata kana yace "Anisa na gode da shawarar ki, ina son maganar nan ki bar ta daga ni sai ke, ina so in ga iya gudun ruwan Fatima d’in, kafin in san matakin da ya kamata in yanke akan ta". "Ba zan fad’a ma kowa ba kamar yadda ka buk’ata, Allah kuma ya kawo mafita cikin sauk’i yaya". "Amin Anisa, nagode, za ki iya tafiya". Tashi tayi ta bar d’akin cike da mamakin wannan labarin da yaya Faruk ya ba ta. Tun da Anisa ta koma d’aki take juya maganar da suka yi da yaya Faruk. Sai a yanzu ta gano dalilin da yasa ban fito ta fad’a mata alak’ar su da Dr Sadik ba har lokaci da suka had’u dashi, da irin hujjojin da na kawo mata san da ta tambaye ni me yasa ban fad’a mata soyayyar mu da Dr ba, da kuma dalilin da yasa da farko na hana Dr zuwa gidan mu. A yadda ta ke jin ta tana ganin in ba tunkara ta tayi da tarin tambayoyin dake ranta ba za taji sauk’in tunanin da yake addabar ta. Abu d’aya ne zai hana ta tunkara ta, sai dan yadda yaya Faruk ya mata magana akan ta bar maganar daga shi sai ita. Yau kusan 2 days kenan rabon mu da mu had’u da Sadik ko ya kira ni a waya, daurewa kawai nake yi amma ni nasan yadda nake ji na rashin ganin junan mu. Da daddare sai ga kiran Dr ya shigo waya ta. Murna kamar in tashi in taka rawa, dama gashi nayi missing d’in ganin shi da zazzak’ar muryar shi. Hannu na har rawa yake wajen d’aukar wayar. "Assalamu alaikum Prince". "Wa alaikis salam". Shiru ne ya ziyarce mu, cikin mu an rasa wanda zai ci gaba da magana. Sadik ne ya katse shirun da cewa "Zarah kin min laifi ko ki kira ki ba ni hak’uri". Cikin shagwa’ba na ce "Wani laifi na maka Dr". "Au har kin manta kenan, yanzu dai ina son ki fad’a min kin gano dalilin da yasa shi wanna Faruk d’in yake hana ki tsayawa zance?" "Sadik ina so ka fahimta, yaya Faruk a matsayin yaya na yake, dole ni in bi abin da yace min, yaya Faruk yana da power a familin mu ya zartar ma kowa hukunci ba tare da an tuhume shi ba, try to get my point". Duk wannan bayanin da na mishi ba wai ya gamsu dasu ba ne, kawai dai zai bi ni a yadda ta ke so. Nan suka ci gaba da hira irin ta masoya. Washe gari ko da aka tashi School, Anisa suka biyo department d’in d’auka ta, na ga yanayin Anisa ya canza ba kamar yadda take ba, da na tambaye ta ko wani abu yake damun ta, sai tace min ba komai. Ganin yadda ta share ta d’akko wayar ta tana danna wa yasa nima nayi shiru, saboda nasan akwai wataran da za ka ga mutum bai jin dad’in jikin shi. Ni aka fara sauke wa sannan su ka tafi. Da daddare muna cikin waya da Dr naji alamar tsayuwar mutum a gaba na. Saurin d’ago kaina nayi don ganin wanda ke tsaye. Ido na ne yayi tozali da yaya Faruk. Ba yi tsammanin zuwan yaya faruk a wannan lokacin ba. Tsananin tsoron da nake ciki yasa na fara zufa duk kuwa da AC d’in dake d’aki na. Cikin murtukewar fuska ya kalle ni yace "Da wa kike waya". Halin da nake ciki a yanzu ba zai ba ni damar tsayawa yi mishi bayanin da wanda nake waya ba. "Ba ni wayar" ya fad’a cikin ba da umarni. Hannu na yana rawa na nik’a mishi wayar. Amsar wayar yayi ya shiga received call, last call wya duba ya ga an sa Prince Dr. Wani irin murmushin takaici yayi sannan yace "Fatima na sha tambayar ki, miye tsakanin ki da Dr Sadik kina ce min likitan ki ne, for the last time zan k’ara tambayar ki, miye tsakanin ki dashi". Shiru nayi na kasa cewa komai, miyau ma da k’yar nake iya had’iyar shi saboda tsoro. Cikin tsawa yaya Faruk yace "ki fad’a min abin da ke tsakanin ku". A karo na biyu ban ce komai sai ma k’ifta idanuwa na da nake yi. Wani gigitaccen mari naji a fuska ta da yasa ni rik’e kunci na. A lokaci d’aya na ji wani ‘bacin rai ya saukar min, tsoron da nake ji ya fita daga raina. Ina ganin yanzu ba zan jure cin kashin yaya Faruk ba, ban ga dalilin da zai dinga mari na ba. Hawayen takaici ne yake zubo min saboda yadda marin ya shige ni. Ina ganin lokaci yayi da zan daina ‘boye ma yaya Faruk alak’ar mu da Dr, tun da shi ya buk’aci in fad’a mai, gwara in daina tsoro in fad’a mishi gaskiyar maganar, ni kaina na gaji da ‘boyewa. Cikin rashin tsoro na ce "yaya Faruk, Dr Sadik shine wanda yake so na, ni ma nake matuk’ar son shi, ina ganin ba namijin da zan so sama dashi". Wani irin huci yaya Faruk yake yi, fuskar shi duk tayi ja kasancewar shi fari. Wani kallo yake mata na ba ki isa ba kana ya ce "Teemah kin yi kuskure da ki ka yaudare ni, ki kasa na ‘bata lokaci na akan ki, zan iya yin komai a kan ki in har mutum zai yi takara da ni a son ki, ya kamata ki gane hakan, kar ki bari in fito miki ta wata hanyar da kema za ki sha wuya, ba ki isa ki so wani ba, bayan ni ina son ki, ba ayi macen da za ta wulak’anta ni akan son ta ba". Ci gaba yayi da cewa "you are the only air i breathe, you are ticking in my heart like a little clock, I value our relationship more than you’ll ever know, you are the girl of my dreams, Fatima ashe ake duk ba haka ki ka d’auka ba a gurin ki, kin nuna min soyayya na zuwa a yananyi daban-daban". Ganin yaya Faruk da gaske yake akan furucin shi yasa zuciyata ta bani k’arfin gwiwar in k’alubalance shi ko zai bar ni nima na auri wanda nake so. "Yaya Faruk, sai dai kayi hak’uri, zuciyata tayi nisa a son Dr, kamar yadda ka ce ba ka san lokacin da ka fara so na ba, nima ban san lokacin da na fara son Sadik ba, yaya Faruk tun san da ka ce min ka na so na, nayi k’ok’arin sa son ka a zuciya ta, amma ban san me yasa zuciya ta tak’i amincewa dakai ba, har lokacin da na had’u da Dr muka fara soyayya, ba laifi na bane, laifin so ne, yaya Faruk ka fahimce ni". Wani irin rad’ad’i yake ji a zuciyar shi, yau wai shi Fatima take fad’a mai tana son wani bayan shi, ba tayi duba da tsawon lokacin da ya d’auka yana d’awainiya da son ta ba, yana ganin ya kamat ya d’auki mataki a kanta. Saukar wani mari na k’ara ji a fuska ta da ya fi na farkon zafi. Cikin k’unar rai yace "zan iya miki komai akan yaudara ta da kika yi, me yasa tun farko ba ki fad’a min in hak’ura ba, ki ka munafunce ni, sai da kika ga komai yazo gargara sannan za ki fad’a min, tun da abin na ki iskanci ne, zan ba ki mamaki". kuka na fara yi ina cewa "yaya Faruk ko mai za ka min, ba zan gaji da fad’a maka Dr nake so ba". Gani yake yi in dai ya ci gaba da tsayawa yana musayar yawu da ni, zai iya yin abin da zai jawo da na sani. Yanke hukunci yayi akan ya bar d’akin kawai. San da zai fita daga d'akin ne ya yi wurgi da wayar akan gado. Yana fita ya had’u da Ummu a falo, gaishe da ita yayi ya mata sallama ya tafi. Ganin yanayin shi yasa tayi tunanin akwai matsala, don haka ta tawo d’aki na. Samu na tayi ina kuka, ga ido na da ya yi ja. Ummu ce ta kira suna "Fatima" Cikin kuka na amsa mata. "Me yasa ki kuka?" "Ba komai Ummu". "Haka kawai ki ke kuka?" Wannan karan ban amsa mata tambayar ta ba, sai ma kuka na ci gaba dayi. Ran Ummu ne ya fara ‘baci, ganin ta tambaye ni nak’i ba ta amsa, gashi kuma sai kuka nake yi. Cikin fad’a tace "Tun da ba za ki amsa min ba, me ya had’a ki da Faruk na ga ya fita cikin fushi". "Fad’a muka yi". "Wani irin fad’a kuma?". "Sa’bani mu ka samu". "Akan me?" Shiru na k’ara yi. Tun da ba za ki fad’a min ba, sai ki yi tayi, in kukan zai miki magani" tana gama fad’ar haka ta fita daga d’akn. "Na ga ta kaina" Na furta hakan a bayyane. Yanzu ban san wani mataki yaya Faruk zai d’auka ba, ina jin yau allurer sojojin ta motsa ne, gwara da Allah yasa ya tafi, in ba haka ba ban san me zai min ba. Yaya Faruk yana fita ya shiga mota ya ja ta a guje. Karatun da yasa a motar shi ne yasa yaji ‘bacin ran da yake ciki ya ragu. Yana zuwa gida ya dinga danna ma mai gadi horn da k’arfi. Da gudu mai gadi yazo ya bud’e mishi yana mishi sannu da zuwa. Ko kallon shi bai yi ba saboda yadda yake jin zuciyar shi. Direct d’akin Daddy ya wuce. Abinci ya same shi ya na ci, kusa dashi yaje ya zauna. "Sannu da gida" yaya Faruk ya furta. Kallon shi Dadi yayi ya lura da akwai abin da ke damun Faruk d’in. "Yawwa Faruk". Ganin yadda Faruk d’in yayi shiru yasa Dadi yace mai "ya aka yi ne Faruk, na ga kamar kana tare da damuwa". Ba zai iya fad’a ma Dadin shi halin da yake ciki ba, don haka yace "Ba komai Dadi". Ba dan Dadi ya yarda ba yace "shi kenan tun da kace haka, kaci abinci ne?". "Yanzu na shigo gidan, ban ci ba". "Zo mu ci wannan da nake ci". Ji yake baa bin da zai iya ci ahalin yanzu, sabida haka yace ma Dadi "na k’ashi Dadi, ba na jin yunwa". "Me ka ci?" Dadi ya tambaye shi. "Ba komai". "Common, zo ka zauna mu ci, ya za ayi ka zauna da yunwa". Bai san musu dashi, shi yasa ya matso yasa d’ayan spoon d’in dake ajiye ya fara ci. Ji yake yi abinci bay a mishi taste a bakin shi saboda halin da yake ciki, bai fi spoon biyar yayi ba ya ajiye spoon d’in. Dadi ne ya kalle shi cikin kulawa yace "kana nufin ka k’oshi kenan?" "Eh Dadi". Dadi bai ce mai komai ba yaci gaba da cin abinci. Bayan ya gama cin abincin ne ya maida hankalin shi ga Faruk da ya fad’a cikin tunani. "Faruk alamu sun nuna kana cikin damuwa, but I don’t know why you d’ont whant to tell me" "Nothing is bordering me Dadi, ina tunanin nan da 2 days zan koma aiki, Dadi ina so ayi fixing d’in bikin mu da Fatima". Murmushi Dadi yayi yace "gobe za mu tsayar da Date d’in bikin, sai ka fara shiri". Murmushin yak’e yayi, duk da yaji dad’in maganar sa date d’in da za ayi, hakan bai say a samu peace of min ba. Suna wannan maganar ne, Momi ta shigo da flask a hannun ta. Ajiye flask d’in tayi kusa da Dadi da cup a hannun ta tace "wani sirri ake yi da ba za a jira ni in shigo ba" ta fad’a tana dariya. Dariya Dadi yayi yace "tsakanin mu ne, in tayi wari za ki ji". "Ina zaune nasan za a zo a fad’a min". Duk wannan maganar da ake yi, yaya Faruk bai ce komai ba, hankalin shi na wani guri. Momi ce ta zauna aka ci gaba da hira da ita, yaya Faruk ba wani dad’in zaman yake ji ba, tashi yayi ya musu sallama ya tafi sashin shi. Washe gari Dadi ya samu Abbu da maganar tsayar da lokacin biki, sun yanke nan da wata hud’u, lokacin mun gama Diploma d’in mu. San da Dadi ya dawo gida ya sanar da yaya Faruk, yaji dad’in labarin, sai dai shi yafi buk’atar in so shi, yana ganin soyayya ita tafi mahimmanci kafin a je ga zancen aure, sai dai ba yadda zai yi ne yasa ya buk’aci da a tsayar da lokacin bikin, fatan shi shine kafin lokacin, zan so shi. Ko sallama yaya Faruk bai min ba ya koma Abuja. Tun lokacin da yaya Faruk ya koma Abuja ya rage walwala, yanzu yafi so ya zauna shi kad’ai. Ya rasa yanda zai yi ya shawo kan Fatima, a da yana ganin abu mai sauk’i ne da zai iya jawo hankalin ta gare shi, sai dai a yanzu ya gane cewa nayi nisan da ba zan saurare shi ba, yanzu duk wayar da muke yi dashi, da fad’a muke k’are wa, gashi yanzu ya dawo da fad’an shi, abu kad’an ke sa shi hassala, ni kuma ba na jurar maganganun da yake fad’a min, hakan yasa ya rage kira na. Yau yana zaune a falon shi, yayi nisa a cikin tunanin da ya sa bar wa kanshi, Mus’ab ya shigo da sallama. Tunanin da yake yi yasa bai ji sallamar da Mus’ab ke mai ba. Tako wa yayi ya zauna kusa dashi. Dafa kafad’ar shi da Mus’ab yayi yasa ya dawo daga duniyar tunanin d yake yi ya saki ajiyar zuciya. Kallon shi kawai Mus’ab yake yi ganin tun san da ya dawo daga Kaduna yake cikin wannan halin. "Faruk, wai me ke damun kane?" Mus’ab ya tambaye shi. "Me ka gani?" Shima ya maida mishi tambaya. "Faruk, nasan ba kowace matsala za kai ta fad’a min, ina so ka dubi amincin mu da yarda da muka yi da juna, ka fad’a min matsalar ka, duk wani wanda yake tare dakai, yasan ka canza, plsss Faruk, ni kaina ba na jin dad’in ganin ka a wannan halin da kake ciki na tunani, hakan xai iya jawo maka wani ciwo ya kuma yi affecting d’in ka". Yasan ba wanda ya cancanta ya fad’a wa matsalar shi kamar Mus’ab, yasan zai iya taimakon shi da shawara, yana ganin fad’a mishi shine maslaha a gare shi, ko ba komai zai samu sauk’in tunanin da yake yi. "Mus’ab ina cikin matsala". Da sauri Mus’ab ya ce "Wace matsala Faruk". Nan Faruk ya sanar dashi halin da suke ciki shi da Fatima, da kuma matsalar da yake fuskanta a guri na. Tausayin Faruk ne ya kama Mus’ab a wannan lokacin, yasan Faruk bai san so ba sai a kaina, dole ne ya shiga wannan halin. Cikin tausayawa yace "gaskiya Fatima abin da ta maka ba ta kyauta ba, ko waye a ka ma haka dole ne ya shiga cikin tunani, a yadda ka bani labari na fahimci son da Fatima take ma wannan Dr d’in, irin son nan ne da ake cewa *Makauniyar Soyayya*". Faruk ne ya katse shi da cewa "Mecece Makauniyar Soyayya kuma?". Mus’ab ne ya bashi amsa da cewa "Makauniyar soyayya wata irin soyayya ce da mutum ya ke ma wanda yake tsananin so, irin wannan soyayyar ita ce mutum bai duba wanda ya dace yaso ba, bai duba aibun shi ko laifin shi, duk abin da zai yi/za tayi daidai ne a gurin shi/ta, mutum zai iya ‘bata wa da kowa akan wanda yake so, kuma duk a ganin shi/ta duk cikin soyayya ce saboda duk a ganin su a cikin soyayya ne saboda sun makance a so, wannan soyyar ita ce Makauniyar soyayya, kuma ita wannan soyayyar yawanci tana jawo danasani a lokacin da mutum ya hankalta". Faruk ya gamsu da bayanin da Mus’ab ya mai, ya kuma yarda da cewa irin wannan soyayyar nake yi. Mus’ab ne yaci gaba da cewa "shawarar da zan baka Faruk shine, ka ci gaba da addu’a akan Allah ya za’ba maka abin da yafi alkhairi a gare ka, sannan ka ci gaba da hak’uri da duk abin da za ta maka, shi so da maganar aure ya k’unshi k’alubale dama, sai dai kowa da irin yadda yake zuwa masa, nan gaba z aka ga ribar hak’urin naka, ina ganin komai zai zo da sauk’i tun da har anyi fixing d’in bikin ku". Ba k’aramin jin dad’in shawarwarin Mus’ab yayi ba, shi yasa yake jin dad’in kasancewa da Mus’ab a matsayin aboki. Da haka suka ci gaba da zanta wa akan matsalar, a haka Faruk yaji ya samu k’arfin gwiwa. Sallama Mus’ab ya mishi ya tafi. Yana kwance a d’aki yaji k’arar wayar shi, sai da aka sake kira sannan ya d’auki wayar. Sunan Binafa ya gani a jikin screen d’in wayar, kasancewar yayi saving d’in numbar ta tun da ta sake kiran shi. Sallama ya mata ta amsa masa. Sun d’an yi hira kafin Binafa ta d’aura da cewa "Umar, tun san da muka had’u Asaa pyramid, na ji na kamu da son ka, nayi k’ok’arin dannewa amma zuciyata ta gaza yin haka, hakan yasa na rasa walwala da sukuni, su Dad d’ina da Mom d’ina sun ta tambaya ta akan in fad’a musu matsala ta, ina ganin ko na fad’a musu bas u da maganin matsala ta sai kai, plss Umar ka tausaya ka bani masauki ko da yaya yake, zan yi farin ciki da haka". Sauraren ta yake na yadda take bayyana mishi yanda take son shi, ina ma a ce Teeman shi ce ke furta mishi wad’annan kalmomin, da bai san dad’in da zai ji ba, sai dai kash, ita ta riga tayi nisa da son wanin shi. Binafa ce ta katse shi da cewa "Bregadier kana ji na kuwa". "Ina jin ki Binafa, na gode da son da kike min, sai dai ina mai ba ki hak’uri Binafa, ina da wacce ta dabaibaye zuciya ta, sai dai ina miki addu’ar Allah ya kawo miki miji nagari". Kuka ta fara mishi tana k’ara fad’a mishi halin da take ciki a yanzu na son shi. Tausayin ta ne ya kama shi ganin yadda take mishi kuka, shima da yana da halin kuka da yayi ko ya samu sauk’i a ranshi. Me yasa so yake zuwa mutane mutane da launi daban-daban, ina ma bai fad’a cikin so ba, da bai tsinci kanshi a halin da yake ciki a yanzu ba. K’arar sautin kukan ta da ya ci gaba da ji a kunnen shi ne yasa ya tuna da waya yake yi. Lallashin ta yaci gaba dayi yana fad’a mata kalamai masu kwantar da hankali, da haka ya samu ya shawo kanta har ta hak’ura, kafin su yi sallama ta nemi alfarmarshi akan za taci gaba da kiran shi suna gaisawa sannan suka yi sallama da ita. Yau kusan wata d’aya kenan da gama service d’in yaya Khalil, tun da ya dawo ya fuskanci ina cikin matsala, idan ya tambaye ni sai in ce masa ba komai, tun yana tambaya na har ya gaji ya zuba min ido, sannan yayi mamakin wai yaya Faruk ke so na amma ban fad’a mai ba, ya sha gani na muna da waya da Dr, ya rasa in da na fuskanta, bayan dawowar shi yaji time d’in da aka yi fixing, ya rok’i alfarmar a k’ara mishi lokacin, in yaso a fara nawa bikin da yaya Faruk, daga baya ayi nasu. Komai yayi farko zai yi k’arshe, hakan ta kasance gare mu, mun rubuta final exam d’in mu mun yi graduation d’in mu, karatu da dad’i da wuya in aka gama shi, yanzu ba mu da wata sauran fargaba da ta rage mana game da harkar karatu. Bikin mu bai fi saura wata biyu ba sai ga yaya Faruk ya zo Kaduna. Hakan ya k’ara d’aga min hankali ganin yadda lokacin bikin mu yake matsowa, gashi har yau ban fad’a ma Dr Sadik halin da ake ciki ba. Kiran shi nayi a waya akan cewa in ba ya komai ya same ni a gida, akwai maganar da nake son mu tattauna dashi. San da ya k’araso ne ya kira ni a waya yana waje. Hijab na san a fito na wuce gurin Ummu na mata k’aryar cewa zan je gidan su Anisa in dawo yanzu. fatan a dawo lafiya ta min kana tace in gaishe da su Anisa da Momi. Ina fitowa na shiga motar nace mai ya tuk’a motar mu bar layin. Kallo na yayi da alamar tambaya, amma ganin yanayin da nake ciki yasa bai ce min komai ba ya ja motar mu ka bar layin. Sai da naga mun bar layin mun shiga wani layin sannan na ce ya tsaya a nan. Sai a lokacin naji zuciyata ta karye na fara kuka wanda nima ban san dalilin yin kukan nawa ba. Bi na yake yi da kallo ganin yadda nake kuka bil hakk’i yace "Wai Zarah me yake faruwa ne kike wannan kukan, ki fito ki fad’a min me ke faruwa dake ne". Cikin kuka nace "Sadik an kusa raba mu, za a sa almakashi a datse soyayyar da ke tsakanin mu, na kasa danne halin da nake ciki a yanzu, shi yasa na ga gwara in fito in fad’a maka halin da nake ciki a yanzu". "Ban gane me kike nufi ba, wai waye zai raba mu?" ya tambaye ni. "Sadik aure za a had’a ni da yaya Faruk, yanzu haka bikin bai fi saura wata biyu ba" Na k’arashe maganar cikin shashshek’ar kuka. Wani irin takaici ne ya kama shi jin wai an kusa bikin ta da Faruk, ba ta fad’a mishi ba, sai da ta ga komai ya rinca’be sannan za ta fad’a mishi. Shi yasa da tace mai Faruk d’in ya hana ta tsayawa zance yasa alamar question mark, yasan daman yana da dalilin yin haka, abin ta fi yi mishi ciwo a ranshi shine yadda a lokacin ya tambayeta ta nuna mishi ba wani abu dake tsakanin su. Cikin fad’a yace "Yanzu Zarah da kike wannan kukan miye amfanin shi, bayan sai da kika bari komai ya gama ‘baci sannan za ki fad’a min, gashi har ana maganar biki, yanzu mai ki ke so in yi akai". Cikin kuka nace "Dr dubarata ta k’are, plss ka samo mana mafita, wallahi in dai ba kai na aura ba zan shiga wani hali, lai zuciyata take so da muradi". Ganin yadda take kuka yaji duk jikin shi yayi sanyi, shi kanshi yasan Fatima na son shi. Cikin lallashi ya ce "Wipe your tears Zarah, ki ba ni hakalin ki muyi magana ta fahimta". Ina jin haka nayi saurin share hawayen dake fito wa daga fuska ta, na maida hankali na gare shi. "Zarah, kin yi kuskure da tun farko ba ki fad’a min me ke tsakanin ki da wannan yayan naki ba, duk yadda muke son junan mu, ba mu da wani power tun da har an yi fixing d’in bikin ku, ina ganin mafita a gare mu shine mu yi hak’uri da yadda k’addara tazo mana mu hak’ura da juna". Wani irin kallo na mishi na alamar tambaya akan abin da yace. Maganganun da Sadik ya fad’a sun k’ara sa ni a rud’ani ganin yadda yayi saurin mik’a wuya ga al’amarin, duk wani bijire wa da halin da nake ciki a yanzu duk akan shi ne, amma shi gashi a lokaci d’aya ya nuna ya hak’ura da ni. "Ban fahimci inda maganganun ka suka nufa ba, kana nufin har ka hak’ura dani, bayan duk fad’i tashin da nake yi duk a kan ka ne, Dr kar ka sa in fara zargin ko ba so na kake yi ba" Na fad’a cikin fushi. Cikin cool voice d’in shi da yake k’ara sace zuciya ta yace "try to understand me Zarah, maganar ba a son ki ma bai taso ba, ke kan ki kisan ina son ki, in har da ba na son ki, bazan tsaya ‘bata ma kaina time ba, kema kuma ba zan ‘bata miki lokacin ki ba, abin da yasa ki ka ga nace haka saboda na rasa wace hanya za mu bi mu shawo kan matsalar, yanzu gashi kin ce bai fi saura 2 month bikin ba". Sai yanzu na ji sauki a raina ganin shima Sadik ya nuna damuwar shi akan maganar, nasan yanzu zan samu relief a raina. Da haka muka ci gaba da tattaunawa akan matsalar, mun yi da Dr zai neme ni a waya mu samu mafita akan maganar. Fitowar da zan yi naga motar yaya Faruk ta shigo layin, da alama daga wani gurin yake tun da har ya biyo wannan layin. Shi kuwa yaya Faruk tun da ya ganni na fito a motar ya tabbatar da cewa tare muke da Dr. Kusa da motar Dr yazo yayi parking. Fitowa yayi daga cikin motar ya nufo inda nake, ni kuwa jiki na in banda rawa ba abin da yake yi, hakan da nayi ne yasa Dr ya lura da halin da nake ciki. Shima fito wa yayi daga side d’in driver ya kulle motar. Kallon kallo ake yi tsakanin yaya Faruk da Dr Sadik, da alama kowa da abin da yake sak’awa a zuciyar shi. *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *Wannan shafin sadaukar wa ce ga dukkan fans d’in Brigadier Faruk* *Lallai Faruk ya ciri tuta a wannan littafin da yafi kowa samun mabiya, ni kaina Bregadier Faruk na burge ni, kuma fans d’in sauran jaruman ina mik’a gaisuwa ta a gare ku, wani shafin kuma zai zama sadaukar wa gare ku* *Ina godiya ga dukkan d’aukacin masu bin wannan littafin* *Allah ya bar mu tare*🤝🏽🤝🏽🤝🏽 _A wannan shafin nake sanar da makaranta wannan littafin cewa na tsayar da wannan littafin har sai bayan sallah in Allah ya kaimu saboda kusantowar azumi_ _Allah muke rok’o yasa mu fara azumin nan cikin kwanciyar hankali, ni’ima, lafiya da wadata_ _Ya Allah kasa muna daga cikin wad’an da z aka ba ma aron rai da za mu ga wannan watan mai alfarma, idan kuma kwanan mu ya k’are kasa mu cika da Imani_ _Allah kasa mu fara azumin nan lafiya, mu gama shi lafiya_ 59&60 Yaya Faruk ne ya tako cikin takun k’asaita ya tawo gurin da nake, ni kuwa in ban da addu’a baa bin da nake yi a raina saboda ban san wani mataki zai d’auka a kaina ba. Hannu na ya rik’e cikin d’aurewar fuska, yana min wani irin kallon da ni kaina bazan iya fassara shi ba. Dr ne ya fara min wani hautsinannen kallo ganin hannu na a hannun yaya Faruk, hakan da na fahimta yasa na fara k’ok’arin k’wace hannu na amma ko alamar sake wa bai yi ba, ganin in na ci gaba da jan hannu n azan iya ja ma kaina ciwo yasa na hak’ura. Direct motar shi ya nufa dani ya zaunar dani a kujera mai zaman banza sannan ya kulle motar. Gurin motar Dr ya nufa wanda tun a lokacin da yaya Faruk ya rik’e hannu na yake kallo na. Wani irin murmushi yaya Faruk yayi ya ci za gefen le’ben shi, kana ya kalli Dr da wani irin d’aurewar fuska ya ce "Dr Sadik ko?" ya tambaye shi. Shiru Dr ya mishi bai bashi amsar tambayar da ya mishi ba, sai ma k’ara tamke fuskar shi da yayi. Yaya Faruk bai damu da rashin amsawar shi ba, ci gaba da yayi da maganar shi. "Warning nake so in maka, na ga alamar kamar ilimin addini bai gama wadatar ka ba, idan ba ka sani ba, ina so ka sani, ba kyau neman aure akan nema, hakan haramun ne kuma ya sa’ba ma addinin musulunci, ina so ka sani bikin mu da ita bai fi 2 month ba, ka fita harkar ta, idan kuma ka k’i… hmmmm" ya k’arashe maganar yana girgiza kai. "Duk wannan maganganun da kake yi kana nufin zai sa in tsorata ne, ko in ja baya da neman Zarah, hakan bai girgiza ni ba, sai ma k’ara min k’arfin gwiwa da yayi, abin da nake tutiya dashi shine Zarah tawa ce, tun da ni take so, ka ga ni ke da power akan ta". Jin wannan kalamen Dr yasa yaji wani irin ‘bacin rai ya ziyarce shi wanda yafi na da, yana ganin gwara ya koya ma Dr hankali yasan shi bat saran shi ba ne, don haka cikin fushi ya cakumo shi, Dr wanda ya ji hannun soja da kyar yake numfashi, har ya duk’ule hannun shi zai kai mishi naushi, ko me ya tuna ya sake shi ya bar gurin. Dr kuwa tun da ya samu yaya Faruk ya sake shi, ya shiga motar shi ya ja ta da gudu ya bar unguwar. Ni kuwa tun da na ga abin da yaya Faruk ya ma Dr, na ji kamar ni aka ma wa, tun da ni na janyo mishi hakan, kuka kawai na fara yi mai tsuma zuciya. Yaya Faruk na shiga cikin motar ya ji sautin kuka na ya cika mishi kunne, duk da kukan na ta’ba mishi zuciya hakan ba zai hana ya hukunta ni ba, gani yake yi in ya bar ni haka zan k’ara ganin lagon shi ne in raina shi. Wata irin juyowa yayi ya kalle ni da idon shi da ya canza launi, ya daka min wata irin tsawa da na ji kayan ciki na sun kad’a. "Fatima fitar min daga mota kafin in illata ki" ya fad’a cikin tsawa. Saboda tsoratar da nayi yasa na kasa bud’e k’ofar, sai rawa da jiki na yake yi. Tsawar da ya k’ara min ce yasa na fara k’ok’arin bud’e motar ko ta wani hali, ni dai in samu in fita daga motar, a yanayin yaya Faruk, in akwai abin da yafi illatawa, nasan zai iya. "Ki fita nace…" Ya k’arasa maganar yana buga hannun shi a sitiyarin motar. Ai ni ban ma san yadda aka yi na bud’e ba, ji na kawai nayi na fad’o daga motar, ban damu da buguwar da nayi ba na mik’e na fara tafiya da sauri ba tare da na juyo na kalli inda yaya Faruk yake ba. Haka na ci gaba da tafiya har na k’araso layin mu, jiki na kuwa sai ciwo yake min saboda fad’uwar da nayi lokacin da na bud’e motar. Lokacin da na kai gate d’in gidan mu, tsayawa nayi na goge hawayen da ke fuska ta nayi, ba na son kowa ya fahimci halin da nake ciki. Da yaya Khalil na had’u a gurin shak’atawa yana waya, gani na da yayi ne yasa ya katse wayar da yake yi tawo guri na. Cikin tsokana yace "matar Soja daga ina kike ina ta neman ki". Ban ce mai komai ba, nasan idan na bud’ e baki zan mishi magana, kuka ne zai fito. Ido ya tsura min yana kallon yanayi na. Hannu na ya kamo ya kai ni gurin shak’atawa ya zaunar dani akan jurera, shi ma kujerar dake kallo na ya zauna. "Fatima me ya same ki na ga idon ki yayi ja". "ciwo idon yake min". "Fatima nasan akwai abin da yake damun ki, tun dawowa ta daga service na lura da kin canza, da kina fad’a min damuwar ki, amma yanzu ban san me yasa kike so ki ‘boya min ba, baki san in na gan ki a damuwa ba, nima ina shiga damuwa, ki daure ki fad’a min kin ji Auta". Maimakon in fad’a mishi abin da ke damu na, sai ma kuka da na fara yi mai ban tausayi. Da ina da hali da na fad’a ma yaya Khalil damuwa ta kamar yadda ya buk’ata, nasan shi zai ba ni shawarar da ta dace da ni, amma a yanzu ina ganin ba bu wani amfanin fad’a mai tun da har na bar maganar ta kawo wannan lokacin da komai yazo k’arshe. Tun da na fara kukan yake kallo na, yadda ya lura ina da buk’atar yin kukan a yanayin da ya lura ina ciki, sai da ya bari na gama kukan sannan ya taso ya zo gun da nake. Farin handkerchief d’in shi yasa yana goge min hawaye, a lokaci d’aya yana girgiza min kai alamar kar in ci gaba da kukan. "Fatima wannan kukan da kika yi, shi ya tabbatar min da kina cikin damuwa, amma ba zan matsa miki ki fad’a min a yanzu ba, yanzu ki tafi d’akin ki huta, anjima zan zo in same ki muyi maganar". Tashi nayi na bar gurin, yayin da yaya Khalil ya bi ni da kallo yana k’issima abubuwa da yawa a ranshi. Yaya Khalil mik’e wa yayi ya shiga motar shi ya tafi gidan su Anisa. San da ya isa gidan, bai shiga ciki ba, parking yayi a harabar gidan ya kira wayar ta ya sanar da ita zuwan shi.. Ba a fi mintuna 5 ba sai ga shi ta fito cikin shigar material kalar milk, ta yafa k’aramin gyale a kanta. Da murmushi ta k’arasa side d’in kujera mai zaman banza tana murmushi. Shima murmushin yake sakar mata yana ci gaba da kallon ta ganin kayan yanda suka amshi jikin ta. "Sannu da zuwa yaya Khalil". "Yawwa Anisa, sannun ki gimbiya ta". Rufe ido tana dariya kana ta ce "kai yaya kana sa ni jin kunya". Shima Dariya yayi yace "Au kunya ta kike ji, gwara ki daina wannan kunyar taki, dan b azan yarda da haka ba". Sunkuyar da kai tayi tana ci gaba da murmushi. Hira suka ci gaba da yi kafin ya canza akalar zancen da cewa "Anisa dama akwai tambayar nake so in miki, ina so ki ba ni gaskiyar amsar". Mai da hankalin ta tayi gare shi tana sauraren shi. "Anisa me kika fahimta a yanzu game da Fatima, nasan tana cikin damuwa amma in na tambaye ta sai tace min ba komai, ina son in kin san wani abu ga me da halin da take ciki, plsss ki fad’a min, nasan ba za ta rasa fad’a miki ba". Ita kanta ba za ta iya cewa ga abin da yake damu na ba, tun da ban fito na fad’a mata ainihin matsalata ba, amma tasn duk wani halin da nake ciki, ba zai rasa nasaba akan magana ta da yaya Faruk ba, ba ta son a ce ta bakin ta za a ji komai, gwara ya gano me ke damuna da kanshi, don haka tace "gaskiya yaya Khalil ni ban san me yake damun Fatima ba, ni kaina na lura da canzawar ta, lura da nayi kamar ba ta son kowa yasan halin da take ciki, yasa nima ban matsa mata da tambaya ba, amma ni kaina ba na jin dad’in canzawar Fatima". "Shi kenan Anisa, insha Allahu zan gano ko ma me yake damun ta, ba ri in k’arasa gida, sai mun yi waya, ki gaida Momi". "Za taji, ka gaida Fatima da Ummu". Motar yayi wa key, yayin da Anisa ke d’aga mishi hannu. Yaya Faruk kuwa, tun san da na bar motar ya kwantar da kanshi a jikin sitiyari, wani irin zafi yake ji a k’irjin shi. "Me yasa Fatima take son d’aura mishi damuwa da hayaniya, idan bai wasa ba zai iya kamuwa da wani ciwon duk a dalilin son Fatima, So ya zamar mishi babbar cuta a gare shi tunda wacce yake so ba ta damu da halin da zai shiga ba". Sai da ya kusan kwashe mintuna 10 a gurin kafin ya ja motar ya nufi gida. Yana shiga gidan ya wuce side d’in shi ba tare da ya shiga side d’in Momi ba. Kwanciya yayi ya d’aga kan shi sama yana tunanin makomarshi a guri na, abin da yake k’ara d’aga mishi hankali bai wuce yadda bikin yake k’ara matsowa ba a lokaci d’aya kuma al’amura suna k’ara rinca’be wa. Da yana ganin matsalar mai sauk’i ce, sai yanzu yake ganin abin ya wuce tunanin shi. Yanzu wani mataki ya kamata ya d’auka? Wannan tunanin shi yafi mishi yawo a zuciyar shi. Momi ce ta fito daga kitchen ta kalli Anisa da take faman buga game a wayar ta. Kiran sunan ta Momi tayi ta amsa mata. "Anisa yayan ki bai shigo ba, na ga motar shi ya dawo, nasan halin shi ba lallai ba ne in yaci abinci, d’auki food flask d’in nan ki kai mai". "To Momi bari in je in kai mai". San da ta shiga d’akin, samun shi tayi yayi zurfi a cikin tunani. Tsayawa tayi tana kallon shi, yayin da wani irin tausayin shi yake k’ara mamaye zuciyar ta. A hankali ta k’arasa kan center table ta ajiye food flas d’in kana ta wuce gurin shi. Kusa dashi taje ta zauna tana kiran shi, amma ko alamar amsawa bai yi ba. Ganin hakan ne yasa ta rik’o hannu shi. D’ago kanshi yayi yana kallon ta. Sanin ba zai mata magana ba a halin da yake ciki yasa tace "yaya Faruk me yake damun ka, plsss yaya Faruk ka fad’a min ko nima zan ji sanyi a raina". Ta k’arashe maganar hawaye na zuba a idon ta. Yadda Anisa take damuwa da lumuran shi, yana ganin ba zai iya ‘boye mata komai ba. Don haka yace "Fatima ce matsala ta". Da sauri ta tare shi da cewa "Me ta maka yaya Faruk". Zayyane mata komai yayi na abun da ya faru yanzu tsakanin shi da ni. Wani irin haushi na ne ya kama Anisa, tana ganin lokaci yayi da ba za ta iya zuba ido yayan ta ya fad’a wani hali ba, za ta fito ta fad’a mata tasan me yake wakana. "Yaya Faruk, ina ganin wannan maganar ya kamata a ce su Dadi sun san halin da ake ciki, ka ga bikin ku na matsowa, in ba an shawo kan matsalar da wuri ba, komai zai iya rinca’be wa, barin wannan maganar zai iya jawo maka wata damuwar". "Kar ki damu Anisa, ni kaina ina tunain yin hakan, amma zan ci gaba da yin k’ok’ari na dan in ga komai ya zama normal, ba komai ba ne nake son in fad’a ma su Dadi su dinga ganin laifin Fatima, ina sa ran komai zai daidaita". Anisa jinjina irin son da yaya Faruk yake min ta ke yi, tasan idan ya rasa ni zai iya shiga wani hali, fatan ta Allah yasa komai ya daidai ta. Haka su ka ci gaba da tattaunawa akan matsalar. Sai da ta tabbatar yaci abinci kafin ta mishi sallama ta bar d’akin. Tana zuwa d’aki ta ga ba za ta iya jurar ganin halin da yaya Faruk yake ciki ba, shawara ta yanke akan taje ta nemi izinin zuwa gidan mu, tana ganin ta hakan ne za ta samu sassauci a yadda ta ke jin zuciyar ta. Da zuwan ta, ta fad’a ma Momi tana son zuwan gidan mu, Momi ta ba ta izinin zuwa. A lokacin da Anisa tazo gidan mu, ina d’aki na, ni kaina a lokacin ba zan ce ga abin da yake min dad’i. Gaisawa da Ummu na ji suna yi kafin ta shigo d’aki na. Da shigowarta ta nemi kujerar mirrow ta zauna tana kallo na. Cikin murmushi na ce "Ashe manya ne a gidan namu, Anisa ya su Momi?". "lfy lau" Ta ba ni amsa a tak’aice. Lura da yadda ta ke kallo na da kuma yadda ta amsa min yasa na zargi ko akwai wata a k’asa. "Fatima ina son mu yi wata magana da ke" Anisa ta fad’a. "Ina jin ki" Na ba ta amsa. Anisa cikin damuwa ta ce "Fatima ban ta’ba zaton hakan daga gare ki ba, tuntuni na lura da canzawar ki, ban san canzawar taki tana da alak’a da yaya Faruk ba, ban tsammaci za ki ‘boye min me ke tsakanin ki da yaya Faruk ba, Fatima yadda na d’auke ki, ashe ke ba haka ki ka d’auke ni ba, sai daga baya duk na samo amsar da nake buk’ata a gurin ki, shine kin min haka ne saboda kina ganin yaya Faruk d’an uwa na ne, zan goyi bayan shi, tabbas hakan ta ke a guri na, zan iya yin komai dan ganin yaya Faruk ya samu abin da yake buk’ata, ina gani ko da a ce yaya Faruk ba d’an uwan ki ba ne, ya ci a ce kin so shi saboda irin soyayyar da ya nu na miki na tsawon lokaci da ya d’auka yana rainon soyayyar ki, amma ke sai ki ka za’bi son zuciyar ki na ganin kin samu abin da kike so, ba tare da kin lura da halin da zai shiga ba, shawarar da zan ba ki shine yaya Faruk shi yafi dacewa dake ba Dr da kika d’aura ma so ba, wannan shawarar da nake baki ita, ina fad’a miki ne ba wai dan yaya Faruk yana matsayin d’an uwa na ne, sai don ina duba amincin da ke tsakanin mu dake, ko da yake nasan canzawar ki duk yana tattare ne da son da kike ma Dr, nasan za ki iya yin abin da yafi wanda ki ke yi, Dr shi ya janyo har ki ka canza, dan ni kaina nasan ba halin ki ba ne". Duk da nasan abin da Anisa ta ke fad’a min gaskiya ne, yau da alama Anisa na kai ta k’arshe ne tun da ta fito tana fad’a min wannan maganar, kasancewar ta ba ta da fad’a, amma hakan ba zai sa in mata shiru ba ganin yadda take ba ma Dr laifi a maganar. "Anisa ina ganin duk maganar da za ki yi, ki tsaya a iya kaina, Dr ba ruwan shi a wannan maganar, hasalima sai yau ne yasan me yake tsakani na da yaya Faruk". Wani irin murmushin takaici tayi sannan ta ce "Ai ke ba za ki ga laifin shi ba, tun da kin yi nisa a son shi, duk yadda za a fad’a miki gaskiya ba d’auka za ki yi ba, dan haka bazan ga laifin ki ba, abin da nake so in tunasar dake, yaya Faruk kamar matsayin miji yake a gurin ki, tunda duk an yi abin da musulunci ya tanada, shaidu ne kad’ai ba su shaida ba, ya kamata ki san da haka". Katse ta na yi da cewa "Ashe kin san ba a d’aura ba kenan, kin ga bai da damar hana ni kula Dr in ma shi ya turo ki". Cikin ‘bacin rai Anisa ta ce "Yaya Faruk bai san zan zo nan gidan ba, bare har ya umarce ni da na zo na miki magana, ke kanki kin San Yaya Faruk ba zai aikata haka ba, ni da kaina na ga ya dace na zo". "Anisa kar ki ga laifi na, ni kaina na rasa me yasa na kasa jin son yaya Faruk a raina, na san ya kuma cancanta da in so shi". Wani irin kallo Anisa ta min kana ta ce "Son zuciya shi ya jawo miki haka, ba wai zuciyar ki ce mai laifin ba, Fatima ina guje miki ranar danasani a lokacin da ba ta da amfani a gare ki, Makauniyar Soyayya da ki ke ma Dr shi zai jawo miki hakan". Kalamen Anisa sun min zafi, amma nasan ni ce mai laifi, ci gaba da tanka mata zai iya sa rai ya 'ba ci. Ci gaba tayi da cewa "In har Yaya Faruk ya shiga wani hali, ke ce sila, da ma ai kin ta'ba fad'a min shi ba ya cikin tsarin Wanda kike so ki aura" Anisa ta k'arashe maganar tana mai zubar hawaye. Kalamen ta sun sa jiki na yayi sanyi, nasan tun da ta fad'i hakan, ba zai rasa nasaba da halin da Yaya Faruk yake ciki a kaina. Ba abin da ya dace da nayi a lokacin da ya wuce nima in zubar da hawayen ko na samu sassauci a halin da nake ciki a yanzu. Duk wannan maganganun da suke yi Yaya Khalil yana bakin k'ofa yana jin me suke cewa, tun dawowar shi Ummu ta fad'a mai Anisa ta zo tana guri na, shi yasa ya taso ya tawo d'akin, wajen shiga d'akin ne yaji maganganun da Muke yi. Ganin shi kawai muka yi a d'akin ya shigo yana min wani irin kallo da bai sa ba yi min irin shi ba. Ganin irin kallon da yake min ne yasa jiki na ya k’ara sanyi, nasan yaya Khalil na ‘bata mishi rai, ba kasafai ka ke ganin ‘bacin ranshi ba, amma in ranshi ya ‘baci bai iya nuna fushin shi ba. Anisa da ta lura da shigowar yaya Khalil yasa ta mike’ tana goge hawayen ta da niyyar tafiya. Ta fara tafiya ne yaya Khalil ya kira ta cikin sanyin murya. Juyowa tayi ta kalle shi kafin ta ci gaba da tafiya, da alamar ba za ta tsaya ta saurari mai zai ce mata ba. Ci gaba yayi da kiran sunan ta, ko alamar juyowa ba tayi ba ta bar d’akin. Shi kanshi yaya Khalil yasan yau Anisa ran ta ya ‘baci, kuma ko waye aka ma d’an uwan shi haka, fushin da zai nuna kenan. Don haka ba zai matsa mata a yanzu ta saurare shi ba, yasan Anisa ba ta d’aukar abu da zafi, idan ta huce zai je ya lallashe ta. Yasan yanzu gurin Ummu za ta, yana da tabbacin ba za ta fad’a mata halin da ake ciki ba. Bayan fitar ta ne ya maida kallon shi gare ni. Cikin d’aurewar fuska ya kira suna na "Fatima". "Na’am yaya Khalil". "Fatima abin da kunne na ya ji min gaskiya ne cewa ba kya son yaya Faruk duk tsawon lokacin nan da aka d'auka?". Shiru na yi ban bashi amsa ba.. "Fatima kar ki bari raina ya ci gaba da ‘baci, zan miki abin da ba ki za ta ba, ki bani amsar da na tambaye ki". Yanzu idan na fito na ce mishi ba na son yaya Faruk, nasan na k’ara ma kaina wani laifin ne, gwara na mishi shiru. "Me kika mishi Fatima da har yake k’ok’arin shiga wani hali akan ki". Cikin kuka na ce "Yaya Khalil ni ba abin da na mishi, Anisa ce take ganin kamar laifi na ne". Watsa min harara yayi yace "Ba ma laifin ki bane ko? to laifin uban waye?" ya tambaye ni. "Laifin waye tun da kin ce ba naki ba ne". Ya sake jefo min tambayar. Kuka kawai na ke yin a yadda abu biyu suka had’un min, ga fushin yaya Khalil da yake yi da ni, ga kuma fad’an da yake min. Ci gaba yayi da cewa "Fatima kar ki bari mu sa’ba akan wannan maganar, ba za ki ji dad’in hakan a waje na, kar ki ga ina miki wasa, zan mugun sa’ba miki idan har hakan za ki ci gaba da yi, so ki ke yi ki tarwatsa mana zumuncin da muke yi mai dad’i, gashi yanzu ma Anisa ta fara d’aukar zafi akan abin da kike ma d’an uwan ta, ki dawo hanya, in ba haka ba kuma ni zan dawo dake, in ban da isakanci ya za ayi bikin ki ya kusa ki ci gaba da kula wani Dr, ke a haukar ki duk cikin so ne, to wannan ba so bane, shirme ki ke aikatawa, ya kamata ki fuskanci gaskiya ki so wanda yake son ki da gaskiya da amana, nasan son da shi Dr Sadik d’in yake miki ba zai kai na yaya Faruk ba". Rarrafo wa nayi na kama hannun shi ina ci gaba da kuka. Cikin kuka nake cewa "yaya Khalil dan Allah kayi hak’uri, kar kayi fushi da ni, kai kad’ai ne kake nuna damuwar ka a gare ni, kaima in ka juya min bay azan shiga wani hali, ni kaina na rasa yadda zan yi, ban san wani irin so nake ma Dr ba da na kasa hak’ura dashi, ina so ka taya ni da addu’a, ni kaina nasan ba na kyauta ma yaya Faruk"……. Ganin yadda nake kuka yasa yaji tausayi na ya kama shi, yasan duk wannan abubuwan da nake yi, sharrin so ne ya jawo hakan, amma ba zai yi saurin nuna tausayawar shi gare ni ba, yafi so in gano gaskiya in gyara. Mik’ewa yayi ya kalle ni yace "Fatima wannan kukan ba shi bane mafita gare ki, ki dawo hanyar da za ta fi miki shine ki nuna kulawar ki ga yaya Faruk sannan ki nuna mishi so, ina ganin wannan shine mafita a gare ki, gargad’i na k’arshe da zan miki shine in har ran Anisa ya ‘baci, to naki sai ya fi na ta ‘baci, dan ni nasan darajar soyayya, ba irin taki ta rashin madafa nake yi ba". Yana gama fad’ar haka ya bar d’akin, yayin da naci gaba da wani irin kuka mai ban tausayi. _Hmmmmm a min hak'uri da wannan ba yawa, sai bayan sallah in Allah ya kaimu za mu ci gaba da bin labarin Fatima_ _Anan nake ce mana Allah yasa ayi azumi lafiya_ _Allah ka yafe mana laifukan mu_ _'Yar mutan Paki na muku fatan alkhairi_ *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 _Wannan shafin naki ne namesake_. _Maryam Ibrahim Kusada_. _Ban san irin godiyar da zan miki ba na irin yadda kike nuna min so da nuna yabawar ki akan novel d’ina, abin da zance shine Allah ya bar zumunci ya kuma kai mu lokacin bikin ki_. _Ina miki fatan alkhairi_.🤝🏽 *INA SANE DAKU* _Fans d’in Nana Khadija, gaskiya kun nuna mata k’auna_. _Ana tare_. _Gaisuwa ta musamman gare ku_. *SAK’ON BARKA DA SALLAH* _Alhamdulillahi ala kulli hal_. _Yabo ya tabbata ga Allah (S.W.A) da yasa muka yi azumi lafiya muka gama shi lafiya, Allah muke rok’o ya amshi ibadun mu yasa muna da rabon ganin na wani shekarar_. _Anan ‘yar mutan Paki ke ma duk wani d’aukacin musulmi barka da sallah_. _Allah ka maimaita mana_ _Taqabbalal lahu minna wa minkum_ _Happy Sallah 2 all my fans_ *BAN HAK’URI* _Ina ba ma masoya wannan littafin hak’uri kan jinkirin da nayi wajen posting, sai a lokacin na k’ara tabbatarwa da wannan littafin yana da yawan mabiya da ni kaina ban san adadin su ba na yadda ake min magana ta Facebook, whatsapp, groups akan ci gaban novel d’in_. _Ba abin da zan ce muku sai godiya da fatan alkhairi_. _Ana tare har kullum_ 61-62 Tun san da Anisa ta fito daga d’aki na take faman goge hawaye, ba hawayen komai take zubarwa ba sai na tausayin halin da yaya Faruk zai shiga in ya rasa ni, a yadda ta gama karanta ta tasan nayi nisa a Makauniyar soyayyar Dr Sadik da zai yi wuya in amince da yaya Faruk, duk abin da ka ga yaya Faruk na nuna damuwar shi a kai to ba k’aramin so yake mai, gashi yanzu na nuna cewa Dr ne za’bi na, fatan ta shine Allah ya sassauta zuciya ta in amince da yaya Faruk dan samun farin cikin shi da kwanciyar hankalin shi. San da ta fito falon ba ta samu Ummu ba, hakan yasa ta nufi shashin ta dan yi mata sallama. Samun Ummu tayi akan kujera da minhajil muslim a hannun ta tana karanta wa. Sallama Anisa tayi kana ta nemi guri ta zauna akan carpet d’in dake shimfid’e a d’akin. Amsa mata Sallamar Ummu tayi kana ta rufe littafin dake hannun ta. Da fara’a Ummu ta kalle ta tace "ya aka yi ne Anisa". "Ba komai Ummu, zan koma gida ne". "Da wuri haka". Ummu ta sake tambayar ta. "Akwai abinda zanyi ne in na koma gidan". "To ina Fatiman?". "Tana d’aki, mun yi sallama da ita" Yanayin ta da Ummu ta gani ya nuna kamar akwai abin da ya had’a ta da ni, amma ganin ba ta fad’a mata ba yasa ba ta tambaye ta ba. "Khalil ne zai kai ki? Ummu ta sake tambayar ta. Cikin jin kunya Anisa ta amsa mata da cewa "A’ah ba shi zai kai ni ba". Ummu ce ta fara fad’a "Ban son shashanci, me yake yi da ba zai kai ki ba, kira min shi…". Da sauri Anisa ta kar’bi zancen da cewa "Ni na ce ya bar shi, yace in jira shi ya ci abinci yayi wanka, na ce kawai ya bar shi ya huta tun da yanzu ya shigo gidan". "To ai shi kenan, ki gaida su Hajiya" Nan suka yi sallama ta tafi. Shi kuwa Yaya Khalil na fito wa ya nufi shashin shi. Rasa me yake masa dad’i yayi, bai ta’ba tunanin zan makance akan soyayya irin wacce nake yi a yanzu ba, bai yi tsammanin in yaya Faruk ya min tayin soyayyar shi zan bijire mai ganin yanzu shak’uwa ta shiga tsakanin mu dashi a lokaci guda, ashe abin ba haka yake ba, hangen shi ne ya nuna mishi kamar ina son yaya Faruk, ashe yaya Faruk ne kad’ai yake d’awainiya da so na, ni ta Dr Sadik nake yi, da tun farko yasan yaya Faruk ne ya fara fad’a min yana so na kafin Dr, da bai nuna amince war shi ga Dr Sadik ba, da yasan yadda yayi ya raba mu dashi ta hanyar nasiha da lallashi da dubara, ko a yanzu lokaci bai k’ure mai ba, yana ganin zai iya juyo da hankali na in maida soyayya ta ga yaya Faruk dan shi yafi dacewa dani ba Dr Sadik ba. Ko a yanzu ya samu makamin da zai yi amfani dashi tun da yana fushi dani, yasan bazan juri ganin fushin shi ba, dole ne in zo in nemi afuwar shi, ta wannan hanyar zai yi amfani yaga ya karkatar da akalar tunani na zuwa ga yaya Faruk. Yanzu abin da yafi tsaya mishi a rai shine yadda Anisa ta nuna fushin ta, yasan ba k’aramin abu bane ya ‘bata mata rai kasancewar ta ba mai yawan fushi ba, zai bata time ta huce duk da yasan ba laifin shi ba ne, amma yasan yanzu laifi na zai iya shafar shi, shi bai ga laifin ta ba dan kowaye yaga ana ma d’an uwan sa haka iya nuna fushin da zai yi kenan. Haka yayi ta sa’ka da warware wa shi kad’ai. Tun san da yaya Khalil ya bar d’akin na ci da kuka na ba mai lallashi na, nasan na shiga tsaka mai wuya, wanda na ke sa ran zan samu sauk’i a gurin shi shima yayi fushi dani, ba abin da ke min yawo sai nasihar da ya min akan in nuna ma yaya Faruk so da kulawa, ni kaina nasan ya cancanci hakan daga guri na, "Me yasa ba zan ji shawarar da mutane suke ba ni ba akan yaya Faruk?" Na tambayi kaina. "Saboda zuciyar ki ba tayi marhabin da tayin soyayyar da yake miki ba, shi yasa ba ki d’au shawarar da mutane suke baki ba" zuciyata ta bani amsa. Yanzu gashi yaya Khalil yayi fushi dani mai tsanani wanda tun tasowa ta bai ta’ba nuna min ‘bacin ran shi irin haka ba, nasan yaya Faruk bai iya ‘bacin rai kasancewar sa mai hak’uri, abin da yafi shine in bari ya huce da ga fushin da yake yi sai in bashi hak’uri. Wata dabara ce ta fad’o min akan in fara kiran Anisa in ba ta hak’uri duk da nasan ba dole ba ne ta saurare ni, in na aikata hakan nasan zan yi saurin samun sassauci daga gurin yaya Khalil dan nasan yana d’aya daga cikin abin da yasa yayi fushi dani. Trying d’in numbar ta nayi amma ba ta shiga, hakan yasa na hak’ura da kiran ta. Ban san tsawon lokacin da na d’auka a zaune a d’akin ina karanta wasik’ar jaki, sai da na duba lokaci na ga ya ja. Ummu kuwa shirun da taji yayi yawa ne yasa ta taso ta tawo d’aki na. Tun da ta shigo d’akin ta lura da akwai abin da yake damu na ganin yadda na canza a lokaci guda, ga ido na da ya canza launi wanda hakan ke nuna da na ci kuka. Kiran suna na tayi cikin sanyin murya "Fatima". Sunkuyar da kaina nayi kana na amsa mata da "Na’am Ummu". "lafiya kika zauna ke kad’ai a d’aki har na tsawon lokaci ba ki fito ba" ta tambaye ni. "Ba ni da lafiya ne" Na ba ta amsa cikin rashin karsashi. "Me yake damun ki?" ta sake jefo min wata tambayar. Shiru nayi saboda ban san inda zan ce yana min ciwo ba. Shirun da taji nayi ne yasa tabbatar da akwai abin da yake damu na. "Me ya samu idon ki na ga kamar kin yi kuka" ta k’ara watso min tambaya. Cikin daburce wa na amsa mata da "Ba…komai" Na amsa mata a tak’aice. "Fatima! d’ago ki kalle ni" Ummu ta fad’a cikin bayar da umarni. A hankali na d’ago na kalle ta kana na sunkuyar da kaina k’asa. Kusa dani tazo ta zauna ta rik’e min hannu tana mai ci gaba da nazari na. Da tasausassar murya Ummu taci gaba da cewa "Fatima yanayin ki da na gani ya nuna min akwai abin da yake damun ki, tun kwanaki na lura da canzawar ki, shiru na miki dan in ga iya gudun ruwan ki, amma na lura abin naki gaba yake yi, kin san a duniya ba wanda yafi cancanta da ki fad’a ma damuwar ki irin ni, fad’a min me yake damun ki Auta ta kin ji" Ummu ta k’arasa maganar cikin lallashi. Nasan Ummu ba ta son gani na cikin damuwa, yanzu ita ma sai ki ga ta fi ni shiga damuwar. "Ina ma zan iya fad’a mata halin da nake ciki?". Zuciyata ce tayi saurin kwa’ba ta akan haka, nasan in akwai wanda ran su zai fi ‘baci akan tsakani na da yaya Faruk na bijire ma soyayyar shi bai wuce Ummu da Abbu ba, ya zamar min dole in ci gaba da taka tsantsan kar su fahimci akwai wata badak’alar a tsakanin mu dashi. Wata dubara ce tazo min akan in ce mata ba ni da lafiya, nasan shi kad’ai ne zai iya sa ta yadda da magana ta. "Ummu ni kaina ban san me yake damu na, kawai ba na jin dad’in jiki na ne" Na k’arasa maganar cikin rawar murya. Ummu ba wai ta yadda da maganar da na fad’a mata ba ne, ganin ban son fad’a mata abin da yake damu na yasa ta k’yale don ba ta son ta takura min, ko ni na fahimci hakan a fuskar ta. Murmushi tayi kawai ta ce "Shi kenan Auta tun da kin ce ba abin da yake damun ki, ki ci gaba da addu’a, Allah ya kawo miki sauk’i, Allah ya baki lafiya". "Amin Ummu". Mik’ewa Ummu tayi ta fara tafiya tana cewa "Ki daure ki fito falo, ba na son ki na zama a d’aki ke kad’ai". "Toh Ummu gani nan fito wa" na amsa mata. Ummu ba ta dad’e da fita ba na fito daga d’akin saboda ba na son ta tabbatar da akwai abin da yake damu na. A ‘bangaren yaya Faruk kuwa, tun san da Anisa ta bar d’akin ya yanke shawarar ya koma Abuja kawai, hakan zai sa ya fi samun relief akan damuwar da yake ciki, da wannan tunanin ya samu ya kwanta. Tuni bacci yayi awon gaba dashi, sai da ya kwashe kusan awa biyu yana bacci kafin ya tashi ya shiga band’aki ya watsa ruwa ko ya samu sauk’in da yake ji a jikin sa. Ba laifi san da ya watsa ruwan yaji dad’i a jikin sa, hakan yasa ya canza shigar shi zuwa farar jallabiya ya nufo side d’in Momi. Samun ta yayi a falo tana zaune, kusa da ita yazo ya zauna. Hira suka fara yi da Momi, a cikin hirar ne yake fad’a mata gobe zai koma Abuja. Mamaki ne ya kamata ganin bai dad’e da zuwa ba har zai koma, tafiya lokaci guda, ko ba komai yadda bikin shi yake matsowa ya d’an k’ara kwana biyu, ita a yadda ta lura kamar akwai abin da yake damun shi. Cikin kulawa tace "Faruk da wuri haka, yanzu na lura tafiyar bazata kake so ka dinga mana, sai dai kawai kace wa mutane gobe zaka tafi, kai ba a sanin rananr tafiyar ka, sai kace wanda ake kora" ta k’arasa maganar tana kallon shi. "Sorry Mommy, nima ban san da wuri zan koma ba, aiki ne ya taso aka kira ni, maganar shirye-shiryen biki duk mun gama magana da Daddy". "Nasan dama haka za kace aiki ne ya taso, dashi kake fake wa in kana son koma wa, anya Faruk ba abin da yake damun ka kuwa?". Murmushi yayi yace "Ba komai Momi, kawai dai yanayin aikin mu ne sai a hankali". "Allah ya taimake ku, ya baku nasara a aikin ku". "Amin Momi". Suna cikin hirar ne Anisa tayi sallama ta shigo. Amsa mata sallamar Momi tayi kana Anisa tazo kusa da Momi ta zauna. "yaya Faruk sannu da hutawa, Momi sannu da gida". "Yawwa Anisa har kin dawo, ya mutanen gidan, ya 'ya ta Fatima? Momi ta tambaye ta. "Suna nan lafiya, sun ce a gaishe ki". "Ina amsawa". Sai a lokacin yaya Faruk ya d’ago fuskar shi suka had’a ido da Anisa ya watsa mata harara. Kallon da ya mata na nuni da alamar tambayar me taje yi a gidan yau. Fahimtar hakan da tayi yasa tayi saurin sunkuyar da kanta. Zuciyar shi ce ke raya mishi Anisa ta je ta min magana ne saboda taga halin da ya shiga, wata zuciyar na k’aryata zargin shi. Tashi yayi ya nufi masallaci saboda kiran sallar da yaji ana kira yayin da Momi da Anisa suka mik’e dan ba da farali. Lokacin da na fito falon, Ummu kawai na samu a dining area a zaune tana cin abincin. Kitchen na wuce na zubo abincin na tawo da gorar ruwan faro na zo na zauna a d’aya daga cikin kujerun dining d’in. Tun da na yi lomar farko na ajiye cokalin saboda yadda ba ni da apatite a baki na kamar wacce tayi fama da rashin lafiya. Ummu na lura da yadda nake wasa da cokalin dake hannu na a cikin abincin. "Fatima ki ci abincin kin ji, za ki ji k’arfi a jikin ki tun da ba dad’in jikin ki kike yi ba, daurewa za kiyi". Ni sai a lokacin na tuna ma da nayi k’aryar ciwo, ya zama min dole in ci abincin dan kar Ummu ta jefo min tambayar da ban da amsar ta. Haka na dinga tsakurar abincin ina ci ba wai dan ina jin dad’in shi ba. Muna cikin cin abincin ne yaya Khalil yayi sallama. Amsa masa sallamar nayi, a lokaci d’aya ina addu’ar Allah ya sa yaya Khalil ya huce dan bai da wuyar sauka. Guri ya nema ya zauna kana ya ma Ummu sannu da gida ta amsa masa. Juyowa nayi da niyar yi mishi magana, yanayin fuskar shi da na gani ba annuri yasa na k’ara shan jinin jikina. Cikin dauriya na daure na ce "yaya Khalil sannu da zuwa". Maimakon ya amsa min sai ya maida hankalin shi kan wayar shi yana danne-danne. Jikin na ne yayi sanyi da abin da yaya Khalil ya min, hakan na nuni da bai huce da abin da na mishi ba kenan. Ummu ce ta ce "Khalil ba ka ji Fatima na maka sannu da zuwa ba ne ka mata shiru". Sai a lokacin ya dakatar da danna wayar da yake yi ya kalli Ummu ya ce "Oh dani take yi, ban ji ba ne". Dariya Ummu tayi ta ce "Ba na son shiririta Khalil, ya za ayi ace baka san kai Fatima take ma sannu da zuwa ba, kar kasa in muku dariya kai da mutuniyar taka". Shima dariya yayi ya ce "A min afuwa". Ummu ce ta kalle ni ta ce "Fatima jeki ki d’akko food flask a kitchen da plate, ki had’o mishi da maltina a fridge. Da sauri ya katse Ummu da cewa "No, ta bar shi kawai, bari in je in d’akko". Mik’ewa yayi ya nufi kitchen d’in. Ban san lokacin da hawaye ya zubo min, ba zan juri irin wannan hukuncin da yaya Khalil yake min ba, zan iya shiga wani hali da wannan salon da ya fito min dashi ta hanyar hukun ta ni, abin da yafi shine in je in bashi hak’uri ko da bai huce ba. Ganin Ummu na kallo na yasa na fara goge hawayen da ya zubo min. Ummu ba ta ce min komai ba, nasan ita ma tayi zargin akwai abin da ya had’a ni da yaya Khalil wanda ba ma so ta sani. Yaya Khalil ne ya dawo ya zauna ya fara cin abincin shi cikin walwala kamar ba shi ba ne ya gama d’aure fuska yanzu. Hira suke yi da Ummu, ni kuwa shiru nayi kamar ba na gurin, da na gaji da zaman ma tashi nayi na dawo falo na kunna Tv. Ido na akan allon Talabijin d’in yake, amma ni kaina idan aka tambaye ni akan me ake yi a Tv d’in ba zan iya fad’a ba. Tunani na kawai nake yi akan yadda lamura suke canza min. Bayan tafiya na ne Ummu ta kalli Khalil ta ce "Me ya had’a ka da Auta na ga tana maka magana ka share ta, sannan na ce ta zubo maka abinci kace ba ka so, to ba na son irin haka, da ka shiga kitchen har hawaye tayi, gwara ko me ta maka ka fito ka fad’a mata da wannan irin hukuncin da kake mata". Bai so Ummu tasan me yake faruwa, yasan sai ta fi ci nuna ‘bacin ranta akan hakan, shi yasa ba zai fad’a mata me ya had’a shi da ni ba, jin bayanin da Ummu tayi ya tabbatar da na fara nadamar abin da na yi, shi yasa ya min haka dan yasan zan ji zafi a raina. Murmushi yayi ya ce "Ummu ba abin da ya had’a ni da Autar ki, san da ta min sannu da zuwa ban ji bane ina faman danna waya, abinci kuwa da na ce ta bar shi na hutar da ita ne na ga tana cin abinci, ai ni da Fatima ba a jin kan mu" Ya k’arasa maganar yana dariya. Jin wannan amsar da yaya Khalil ya ba ta yasa ta ji dad’i, tasan ba abin da ya had’a ni dashi, dama zargi take yi. Tashi yayi ya bar falon, ko kallon in da nake bai yi ba. Lallai fushin da yaya Khalil yake yi da ni mai girma ne, dan bai ta’ba min irin hukunci haka ba. Sai da na bashi kusan minti goma da tafiya sannan na nufi sashin yaya Khalil. Dariya Ummu tayi san da ta ga na nufi side d’in yaya Khalil ta ce "Kun fi kusa, ai ku ba a jin kan ku". Yaya Khalil tun san da ya koma d’aki yake kiran Anisa, cikin sa’a ringing uku tayi ta d’auka. Sauke wata ajiyar zuciya yayi saboda yadda yake kiran ta tun san da ta bar gidan su amma ba ta d’auka ba, sai yanzu ya samu ta d’auka. Sallama ta mishi ya amsa mata cikin jin dad’in d’aukar wayar da tayi. Khalil ne ya ce "Tuba nake yi, duk da ban san laifin da nayi ba ake k’in d’aga waya ta" ya fad’a cikin wasa. Wata kunyar shi ce ta kama ta ganin yadda yayi ta kiran ta amma tayi biris. Cikin sanyin ta tace "Ka yi hakuri yaya Khalil". "Ba komai Sister, ni ke da ba da hak’uri, nasan ke aka yi wa laifi ke da yaya Faruk, kuma ko waye dole yayi kishin d’an uwan sa, ni ban ga laifin ki ba, sai dai laifin wani ba ya shafar wani Anisa, bai kamata ki yi fushi dani ba bayan kin san ba zan goyi bayan Fatima ba akan son zuciyar ta". Tasan abin da yaya Khalil ya fad’a gaskiya ne, sai a yanzu take ganin wautar ta na k’in tsayawa ta saurare shi da d’aukar wayar shi san da ya kira ta, a nan ta k’ara gode ma Allah da ya ba ta yaya Khalil a matsayin wanda za ta aura saboda irin halin shi mai sauk’in kai da fahimta. "Kayi hak’uri yaya Khalil na yi laifi, raina ne ya ‘ba ci a lokacin". "Ba komai Sister, ni dama na fahimci dalilin fushin ki". "Na gode yaya Khalil". "Kin wuce hakan a guri na, buri na ki kasance cikin farin ciki". Suna cikin hirar ne na shigo d’akin da sallama. Juyowa yaya Khalil yayi ya kalle ni kana ya kau da fuskar shi ya ci gaba da wayar da yake yi. Sai da na kwashe sama da minti goma a tsaye ba tare da yaya Khalil ya gama wayar da yake yi. Gajiyar da nayi da tsayuwa ne yasa na nemi gefen gadon shi na zauna. Sai da ya gama wayar ne ya juyo ya kalle ni cikin d’aurewar fuska kamar bashi ba ne ya gama kashe murya a waya. "Ina fatan lafiya dan na ga yanzu muka rabu dake a falo" Yaya Khalil ya fad’a cikin d’aure fuska. Cikin rashin karsashi na ce "Dama yaya Khalil na zo in ba ka hak’uri akan abin da ya faru". "Ni ai ba ni kika yi wa laifi ba, wanda kika yi ma laifi ya kamata ki je ki ba hak’uri ba ni ba, ina ganin za ki iya tafiya in wannan maganar ta kawo ki, ina da abin yi". Kuka na fashe dashi mai ratsa zuciya, kafad’ar shi na je na kwanta ina mai ci gaba da kukan da nake yi, nasan zan samu sauk’i a halin da nake ciki. Tausayi na ne ya kama yaya Khalil, bai so ya nuna min ya hak’ura da wuri, yafi so yaga mun daidaita da yaya Faruk. "Wannan kukan da kike yi bai da amfani Fatima, abin da yafi shine ki yi abin da ya kamata ki yi shine nuna ma yaya Faruk so, da kin aikata hakan ina ganin ba ki da sauran wata damuwa". Cikin kuka na ce "Zan kiyaye yaya Khalil, kayi hak’uri". Shima a lokacin zuciyar shi tayi rauni, ba zai juri ganin kuka na ba. Hawaye ya fara share min ya ce "Is ok Fatima, kukan ya isa haka, plsss ki daina abin da ba na so, ya kamata a ce yanzu kin san abin da ya dace dake ba bin son ranki ba, ya kamata ki kula ki gyara". "Toh! yaya zan gyara". Murmushi ya min yace "Shi kenan Auta, komai ya wuce". Dad’i ne ya kama ni ganin yaya Khalil ya daina fushi da ni. Hira muka ci gaba dayi da yaya Khalil kamar ba abin da ya faru tsakanin mu. Washe gari yaya Faruk ne ya zo gidan mu. Gaisawa suka yi da Ummu ya ma sallama akan cewa zai koma Abuja, add’ua ta mishi kamar yadda ta saba yi mishi in zai koma Abuja. San da ya shigo ina juyo maganar shi, tsoron fito wa nake yi nasan bai gama huce da fushin da yake yi dani. Kiran wayar shi ne ya shigo waya ta, ganin sunan shi a jikin screen d’in waya ta yasa gaba na ya fad’i. Cikin ladabi na gaishe shi, ya amsa min kamar ba ya so. "Ki same ni a waje ina jiran ki, kar ki ‘bata min lokaci" ya fad’a cikin bayar da umarni. "Gani nan zuwa" na bashi amsa a tak’aice. Hijab kawai na sa na fad’a ma Ummu yaya Faruk na kira na a waje kana na fita. Ko da na k’arasa inda motar shi take bai da alamar fito wa daga motar, knocking d’in glass d’in kofar nayi. Sai da ya gama jan ajin shi kafin ya fito daga motar. Gaishe shi nayi ya amsa min da k’yar. Sai da ya gama shan k’amshin shi kana ya ce "Yau zan koma, nasan za ki yi farin ciki da hakan, kar ki yi tunanin dan ba na nan za ki aikata abin da kike so, nasa a dinga lurar min da takun ki ko ba na nan, ki guji had’uwar mu in na kama ki da bijire ma umarni na, idan buk’atar wani abu ya taso kya iya ma Khalil magana ya amsar miki gurin Aminu, na bar mishi komai, ina k’ara gargad’in ki, ki kiyaye, ina fatan kin ji abin da na ce". "Na ji" na amsa a tak’aice. "Ki fad’a min in akwai abin da kike buk’ata akan hidimar bikin, ba na jin zan shigo Kaduna sai a satin bikin, in akwai event d’in da kika tsara sai ki fad’a min ko ki turo min ta waya, ni ba zai wuce walima da Dinner zan yi ba, nasan sauran friends d’ina ba za su rasa organizing d’in nasu event d’in ba". "Ba na buk’atar komai". "Wannan kuma ruwan ki, Sauri na ke yi ina so in biya ta gurin Aminu, maganar kayan akwati za mu yi waya dake sai ki fad’a min kalar kayan da kike so duk da Dadi ya ce in barshi zai min akwatin, nima zan had’o nawa sai a had’a". Lallai yaya Faruk ba k’aramin shirya ma bikin nan yayi ba yadda yake maganar abubuwan da za a gudanar a bikin, gashi yanzu Dadi ya ce zai yi akwati, nasan kuma ba k’aramin kud’i zai kashe a had’a akwatin, amma a haka yake cewa shima sai ya had’a nashi akwatin, nasan duk son da yake min ne ya jawo haka. Katse min tunani na yayi da cewa "Za ki iya koma wa ciki". "Allah ya kiyaye hanya" abin da na ce kenan na koma ciki. Hak’ika ya ji dad’in addu’ar da na mishi, sai da ya ga komawata ciki kana ya ja motar shi ya tafi. Bai zarce ko ina ba sai gurin aikin yaya Aminu, kiran shi yayi a waya akan ya k’araso kasancewar sun yi waya zai zo ya same shi. Yaya Aminu ne ya fito daga office d’in shi ya zo ya same shi a mota. Musabaha su kayi kafin su nemi guri su zauna a harabar company d’in. Tattauna wa suka yi game da yadda yaya Faruk yake so bikin ya gudana. San da yaya Khalil zai tafi ne ya nemi alfarma a gurin yaya Aminu akan yasa ido a kaina da lura da taku na da wanda nake mu’amala, ciki har da Dr Sadik. Yaya Aminu ya mishi alk’awarin zai sa ido a kaina. Da haka suka yi sallama dashi ya tafi. Zaman kad’aicin da yake damu na yasa na tambayi Abbu zuwa gidan su yaya Aminu in yi kwana biyu saboda yanzu yaya Khalil bai cika zama ba yana zuwa kamfanin su Abbu kafin ya fara aiki. Da k’yar na samu Abbu ya amince min kasantuwar yadda biki na ya matso kusa, ni ko a jiki na, gani nake yi kamar ba ni za ayi wa auren ba. Shirya wa ayi cikin wani less kalar ruwan madara, an mishi ratsi da kalar army green, d’inkin an min riga da skirt six pieces, gyale ma da takalmi da jaka duka ruwan madara na sa. Kwalliyar da nayi ba k’aramin amsar jiki na tayi ba. Sallama nayi ma Ummu na fito yaya Khalil shi zai sauke ni a gidan. Bayan mun k’arasa gidan ne yayi parking d’in motar shi a waje, muka jera a tare muka shiga gidan. Anty Jiddah muka samu a falo da su Humaira suna kallon cartoon. Lokacin da muka gaisa da ita ne take tsokanar shi da cewa ina ya bar Anisa muka zo ba tare da ita ba. Ba ta amsa yayi da cewa ba tasan za mu zo ba, da ta biyo mu. Sun d’an ta’ba hira da Anty Jiddah, yayi ma su Nabil da Humaira wasa kafin ya mana sallama ya tafi. Tun da na zo Anty Jiddah ke tsokana ta da amarya kin sha k’amshi. Fad’a min hakan da take yi sai in ji takaici ya kama ni. Nasihohi da jan hankali akan zamantakewar aure had’e da sirrin gyaran jiki duk sai da Anty Jiddah ta zauna ta koya min. Wasu littattafai ta bani in karanta mai suna Ki gyara da kan ki, Sinadarin Ma’aurata, Mu san kan mu Maza da Mata da sauran littattafan girki da ta k’ara had’a ni dasu duk da nima ba baya ba ce wajen iya girki. A cikin nasihar da take min ne cikin dubara take ta k’ara nuna min in yi hak’uri in yi ma yaya Faruk biyayya, ko ba komai shi d’an uwa na ne kuma wanda zai zama miji na. Ni dai kawai sauraren ta nake yi ba dan na ba nasihar ta mahimmanci ba, a wannan lokacin tunani duk yana gurin Dr ne da kwana biyu ba mu had’u ba, gashi ina son ganin shi amma ban san wace hanya zan yi amfani da ita ba wajen ganin shi, ina tsoron hukuncin da zan fuskanta a gurin yaya Faruk duk da nasan ba ya gari, nasan tun da yace ya sa a lura da taku na har zuciyar sa ya fad’a, matsalar dai ba ta wuce ban san wa ya sa ba. Lokacin da yaya Aminu ya dawo ya ganni yayi murna da zuwa na, haka muka zauna muna hira dashi. Yaya Aminu sai wata kulawa ta musamman yake ta bani, nasan hakan baya rasa nasaba da auran da ya ga zanyi, sai tambaya ta yake me nake so ya siya min. Har gajiya nayi da bashi amsar ban a buk’atar komai, da ya dame ni da tambaya ne nace mai komai yayi min ina so ba ni da za’bi. Da haka muka yi sallama dashi na wuce d’akin su Humaira. Wahegari bayan na taya Anty Jiddah aikace-aikacen gida ne nazo na zauna ina kallon wani indian film mai suna "Ok Jaoon". Kiran Dr ne ya shigo cikin waya ta. D’auka nayi yake sanar dani ya za ayi mu had’u, yana so muyi wata magana ne, ni kaina zan so mu had’u, sai dai hanyar da zan bi mu had’u ne zai zaman min wuya tun da mun gama makaranta, gashi ba inda nake zuwa. Sanin yaya Aminu ba ya nan yasa na kwatanta mishi gidan yaya Aminu na ce ya zo ya same ni a can. Ba a d’au wasu mintina ba sai ga kiran shi ya shigo yana sanar da ni ya k’araso. Tashi nayi na je na sanyo hijab, na wuce d’akin Anty Jiddah na mata k’aryar yaya Faruk ne ya ba ma wani abokin shi sak’o ya kawo min. A Gaban gidan yayi parking d’in motar shi. Ina zuwa ya bud’e min d’ayar k’ofar na shiga. Musayae kallo muka yi ni dashi, kowa da irin sak’on da yake so ya isar ma d’an uwan sa. Ni na katse shirun da cewa "Dr ina wuni, ya aiki". "lafiya lau Zarah". Shiru ne ya k’ara ratsa wa a tsakanin mu kafin Dr ya fara da cewa "Zarah ina ganin wannan had’uwar da muka yi dake ne nake son mu yanke decision, ban a son mu tsaya muna ‘bata wa kan mu lokaci, kin ga dai abin da yayan ki ko in ce masoyin ki ya min akan ya ganni dake, duk tak’amar shi ke zai aura, ina so yanzu ki fito ki fad’a min me kika yanke game da ni, in har kin za’bi auran shi to ni gwara in hak’ura duk da son da nake miki, in kuma ni kike so kamar yadda kike fad’a min ina so ki tabbatar min mu samo maslaha a yanzum lokaci na dad’e k’urewa ba mu nemar wa kan mu mafita ba". A tunani na zan iya hak’ura da Dr in auri yaya Faruk ko da ban jin son shi a raina, sai dan son da yake min da kuma ‘yan uwa na da suka nuna sun fi son in aure shi. Sai a yanzu nake ganin wauta ta na yanke hukuncin hak’urin auran yaya Faruk da zanyi, alhalin ga wanda zuciya ta take da muradi, take mishin son da ba zai misaltu ba, wanda son shi ya gama dabaibayi a cikin ta, kullum dashi take kwana tana tashi da tunanin sa. Yanzu maganar da Dr yazo min da ita tayi min tsauri, za’bin raina zan bi ko za’bin abin da ‘yan uwa na da iyaye na suke so zan bi? Ni kaina na gaji da wannan al’amarin da yak’i zuwa k’arshe, gwara ayi mai yiwuwa tsakanin yaya Faruk da Dr. "Anya kin ma yaya Faruk adalci? Duk irin son da yake nuna miki amma za ki za’bi son ran ki" abin da zuciya ta take fad’a min kenan. Wata zuciyar kuwa cewa take min "Ba wani maganar adalci, zan ba wa zuciya ta abin da take muradi". Sadik ne ya katse min tunanin da nake yi da cewa "Ke nake saurare Zarah, me kika yanke". Ya k’arasa maganar yana kallo na. Ajiyar zuciya na yi kana na ce "Dr kai kasan kai nake so, ni kaina ban san irin son da na ke maka maka ba, tuntuni nake neman hanyar da zan samar mana mafita dan mu samu mu ci ribar soyayyar mu ta hanyar yin aure amma na rasa, na bar maka komai Sadik, duk hukuncin da ka yanke ya yi min". Wani lalausan murmushi yayi yana jinjina irin son da na ke mishit un da har na bashi za’bi ya yanke hukunci ba tare da tunanin wani irin hukuncin zai yanke ba. "Kenan za ki iya hak’ura da auran Faruk d’in ki aure ni". ya fad’a yana min wani sihirtaccen kallo. Jim nayi ina tunanin irin hukuncin da zan fuskanta na k’in auran yaya Faruk alhalin komai ya zo k’arshe tun da bikin bai wuce wata d’aya da satittuka ya rage ayi bikin, idan na duba halin da zan shiga in na rasa Dr na gwammance in fuskanci kowane irin hukunci ne in dai za a barni da shi. Da wannan na samun k’arfin gwiwar amsa mishi ‘Zan hak’ura da auran shi in dai a kan ka ne". "Good, abu na gaba shine ya za ayi ki guje ma auran shi". Nan na tsaya tunanin hanyar da zan bi wajen ruguza auran amma ban samu ba, k’arshe dubarar da ta fad’o min shine in bar garin har bayan bikin, idan aka ga ba na nan za a hak’ura da auran, in yaso in komai ya lafa sai in dawo in ba su Abbu hak’uri da yaya Faruk hak’uri, in yaso sai a d’aura mana aure da Dr Sadik, wannan shawarar ce tayi tasiri a kaina. Fa’da ma Sadik nayi shawarar da na yanke, shi kan shi ya ba ni go ahead akan hakan, wannan ita kad’ai ce hanyar da za mu bi dan ganin mun cin ma burin mu. Shawarar da ya k’ara ba ni ita ce kar in nuna ma kowa komai a game da plan d’in da muka had’a, in ci gaba da shirye-shiryen bikin har lokacin da muka gay a kamata in yi tafiyar. Muna cikin wannan maganar ne motar yaya Aminu ta shigo layin, ban wani tsorata ba tun da ina cikin mota, nasan ko ya tambayi Anty Jiddah, za ta fad’a mishi k’aryar da nayi mata ne. Yaya Aminu na shiga falon ya nemi guri ya zauna, Anty Jiddah ce ta d’akko mishi abinci da driks ta kawo mai, ya fara cin abincin ne yake tambayar ta ina nake jin shiru ban fito na mishi sannu da zuwa. Sanar dashi tayi abokin yaya Faruk ne yazo kamar yadda na fad’a mata, dakatawa yayi da cin abincin yace mata bari ya lek’a ya ga ko waye. A lokacin ni kuma na fito daga motar ni da Dr muna ta kawo idea yadda komai zai tafi ba tare da an samu matsala ba, sauran dubarar mun barshi ne akan sai mun had’u a waya. Yaya Aminu shi kuma a lokacin ya fito ya tsaya a bakin gate yana kallon mu, juyawar da zanyi muka ha’da ido dashi. Sai a lokacin ya lura da san da ya dawo ya ga motar amma baisan ni ce a ciki ba. Sallama na yi ma Dr akan cewa zan koma gida yaya Aminu ya dawo, nan muka yi sallama dashi ya tafi. Ni duk a tunani na yaya Aminu bai ga fuskar Dr ba, shi yasa na fara tafiya ta cikin kwanciyar hankali ba tare da wata fargaba ba. Ganin ina tawowa yasa yayi saurin koma wa cikin gida. [6/28, 22:33] My Hapsy: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *INA SANE DAKU* _Masoya littafin SILAR KAYAN SALLAH, ina k’ara ba da ku hak’uri akan shirun da kuka ji ni na kwana biyu na rashin posting da wuri, hakan ya faru ne na yadda abubuwa suka yi min yawa, insha Allah zan muku typing d’in shi_. *QUESTION OF THE DAY* _Su wa K’urayshawa suka aika lokacin yana mushuriki a lokacin Sulhun Hudaibiyya, da yaga irin son da sahabbai suke ma (S.A.W) ya koma zuwa ga k’urayshawan yace musu ‘Ya ku mutane na, Wallahi hakika na bak’unci sarakuna, na bak’unci Kaisar da Kisra da Najjashi, wallahi ban ga wani sarki shugaba daya da mutanen sa suke girmama shi kamar yadda sahabban Muhammad suke yi ga Muhammadu ba_. 63-64 Yana shiga ya fara ma Anty Jiddah fad’a akan me yasa za ta bar ni in fita gurin Dr, bayan tasan an kusa biki na. Tabbatar mishi tayi da ba ta san shine yazo guri na ba, da ba ta barni na fita ba. A lokacin na shigo falon da sallama ta. Anty Jiddah ce ta amsa min ciki-ciki, da alama ita ma ranta a ‘bace yake. Yaya Aminu kuwa sai watso min banzan kallo yake yi. Hakan yasa jiki na yayi sanyi duk da ban san me nayi ba nayi k’arfin halin yi mishi sannu da gida. Maimakon ya amsa min sai ma nufo ni da yayi. Ban yi tunanin wani abu zai min ba shi yasa ban gudu ba. "Daga ina kike" yaya Aminu ya tambaye ni cikin d’aure fuska. "Abokin yaya Faruk ne yazo, shine ya turo shi guri na ya ba ni sak’o ya kawo min". Wani irin kallo ya watsa min mai nuna alamar tambaya kana ya ce "Ina sak’on da ya bayar". Cikin daburce wa na ce "ya… ce… zai…dawo…anjima…yana…sauri…ne…ya …bar…shi…a…". Ban gama fad’a mai abin da zan ce ya d’auke ni da wani lafiyayyen mari. Cikin fad’a ya ce "Uban wa za ki raina ma hankali, kina sha ban gane wannan Dr bane, za ki ce min abokin Faruk ne, ban fad’a miki ki rabu dashi kina da wanda zaki aura ba, yau ba gobe ba su Abbu za su ji wannan maganar, na gaji da rufa miki asiri, dama Faruk nasan hak’uri yake yi dake akan abin da kike mai saboda wannan Dr, tun da shi so ya rufe mai ido ba zai iya hukunta ki ba, yau za ki ji a jikin ki, kije ki d’akko jakar ki mu tafi gida". Kuka na fara yi ina bashi hak’uri akan yayi hak’uri kar ya fad’a ma su Abbu amma bai saurare ni ba. Ita kanta Anty Jiddah na ba ta haushi, amma ganin kukan da nake yi ne ya karyar mata da zuciya yasa ta fara ba yaya Aminu hak’uri akan ya min hak’uri, ko sauraren ta bai yi ba. Ganin ban da alamar tashi in d’akko kaya na yasa ya janyo hannu na ya kaini mota ya kulle ya shiga side d’in driver ya ja muka tafi. Muna zuwa gida ma ya rik’o hannu na kamar wacce ake ma jagora. Main parlour muka nufa yana ci gaba da min fad’a, yana d’aura laifin ga Dr, wanda ya ce in dai suka had’u sai ya ci mishi mutunci tun da shi yake hure min kunne. Jin yadda yake aibata Sadik yasa nayi k’arfin halin duk da tsoron dake raina nace Yaya Aminu ka daina ganin laifin Dr Sadik da ni, Allah ne ya jarrabe mu da son junan mu, abu ne mai wuya a ce lokaci guda in cire son shi…". Maganganun da yaji ina fad’a mai ne yasa shi harzuk’owa ya ficiko AV wire dake manne a jikin DVD ya fara zuga min ita a jiki na. Dukan da yake min ne yasa na sa kururuwa ina ta kuka, jin kuka na yasa Ummu da Abbu suka fito daga side d’in su suka nufo falon, shi kanshi yaya Khalil yana cikin d’akin shi yana jiyo ihu na, shima a lokaci d’aya suka shigo falon don ganin me yake faruwa. Yaya Khalil kuwa tun da ya ga dukan da yaya Aminu yake min ya zargi akwai abin da nayi wanda yasa na tunzura yaya Aminu yake min irin wannan dukan, shi yasa bai samu k’arfin zuwa ya cece ni duk kuwa da tausayin da na bashi. Dukan da suka ga yana min ne yasa Ummu ta daka mishi tsawa. "Aminu miye haka, wani irin laifi ta maka haka kake mata wannan dukan, so kake yi ka ji mata ciwo". Jin hakan da yaya Aminu yaji Ummu tayi magana yasa ya dakatar da dukan da yake min ya wurgar da AV d’in, sai faman huci yake yi. Sai a lokacin Abbu yayi magana ya ce "Ku same ni a falo na". Gaba d’ayan mu muka nufi falon Abbu, jiki na kuwa ba inda bai min rad’ad’i. Abbu ne ya kalli yaya Aminu ya ce "Aminu ban ji dad’in irin dukan da kayi ma Fatima ba kasancewar ta mace, kai babba ne, ka fi ta hankali". Cikin ladabi yaya Aminu ya ce "Kayi hak’uri Abbu, Ummu kema ki yi hak’uri". Abbu ne ya ce "Ba komai Aminu, dama ba laifi kayi ba, sai dai ina son kasan ita mace a hankali ake bin ta, yanzu fad’a min me tayi". Yaya Aminu ne ya nisa kana ya ce "Abbu akwai abin da yake faruwa wanda ban fad’a muku ba, ina sha matsalar k’arama ce da ni kaina zan iya shawo kan matsalar ba tare da na sanar daku ba, sai a yanzu nake ganin matsalar ta fi k’arfi na da ya zama dole in sanar daku ita…". Ummu ce ta katse shi da cewa "Wai wace matsala ce daka ke ta mana kwana-kwana, ka fito ka fad’a mana". Tun da naji yaya Aminu da gaske ya keyi fad’a musu zai yi, jiki na ya k’ara yin sanyi, ban san yadda za su d’auki maganar a gun su ba, hukuncin da za su yanke min shi yafi tsaya min a rai. Nan yaya Aminu ya gyara zama ya kwashe duk iya abin da ya sani tsakani na da yaya Faruk da kuma Dr Sadik, da abin da yanzu na fad’a mishi akan Dr. Shiru d’akin ya d’auka kamar ba kowa a ciki, kowa da irin abin da yake sak’awa a zuciyar sa game dani. Ni kuwa ina can a ra’be kamar wacce tayi ma sarki k’arya, ba abin da nake yi sai aikin k’ifta idanuwa da nake yi. Abbu ne ya ja gauron numfashi kafin ya juyo da kallon shi zuwa guri ni ya ce "Fatima, abin da Aminu ya fad’a min gaskiya ne?". Nasan ko wani abu nake sha bazan kalli idon Abbu in ce mai bana son yaya Faruk ba, na za’bi ba re akan shi, nasan abin da zai min sai ya fi na kowa muni ganin yadda ya d’auki yaya Faruk kamar yaya Aminu, shiru na a wannan lokacin sai ya fi min amfani. Ummu ce ta daka min tsawa ta ce "Ba dake ake magana ba Fatima kika yi wa mutane shiru, ko mu ma za ki fara gwada mana fitsarar da kika koya ne". Har yanzu na kasa bud’e baki na in yi magana sai hawaye da ya fara zuba a fuska ta. Tun san da abin nan ya faru, yaya Khalil bai yi magana ba sai bi na yake da ido. Abbu ne ya ci gaba da cewa "Fatima ke nake saurare". Ba ni da wata sauran dabara da ya wuce in fito in fad’a ma Abbu da Ummu abin da yake raina, watak’ila su duba uzuri na su fuskance ni su bar ni da wanda nake so, da wannan na samu karsashin yin magana. "Abbu kayi hak’uri, nima ba laifi na ba ne, nayi duk wani k’ok’ari akan in sa son yaya Faruk a raina don in faranta muku dashi kan shi yaya Faruk da ya nuna min soyayyar shi har ya zuwa yanzu da ake maganar bikin mu, amma zuciya ta tak’i amsar tayin siyayyar sa, zuciya ta tayi nisa a son Dr Sadik, Abbu da Ummu dan Allah ku tausaya min ku fahimtar da yaya Faruk, nasan zai fahimce ku…" Na k’arasa maganar cikin kuka. Abbu ne ya kalle ni ya ce "Ina sauraren ki Fatima, yanzu me kike so in miki". Ba tare da jin tsoron hukuncin da zai biyo daga baya ba na ce "Abbu so nake yi ka ba yaya Faruk hak’uri ya hak’uri ya hak’ura da aure na, Dr Sadik na ke so". Kowa a d’akin ni yake bi da kallo, a yadda na fahimci kallon da suke min yana nuni da ban san abin da nake yi ba. Ummu kuwa da ‘bacin ranta ya kasa ‘boyuwa tashi tayi tazo ta tsinka min kyawawan mari lafiyayyu guda biyu, wanda hakan ya haddasa min ganin taurari a fuska ta. Rabon da Ummu ta kai hannu ta a jikina na manta, bare har ya kai ga ta mare ni. Yau nasan ran Ummu ya ‘baci kasancewar ta mai hak’uri da sanyin hali, nasan za ta iya min abin da yafi haka in dai akan yaya Faruk ne. Cike da ‘bacin rai ta ce "In da nasan akan haka Aminu ya dake ki, da ko fito wa bazan yi ba har in mishi magana, Fatima ban ta’ba tunanin hakan daga gare ki ba, ki d’auka wannan maganganun da kike fad’a kamar guguwa ce dan in ta kad’a ta tafi ta riga ta tafi kenan, ci gaba da wannan maganganun zai iya sa ki fuskanci mummunan hukunci daga gare ni, ki kiyaye ni". Abbu ne ya katse ta daga fad’an da take min "Hajiya k’yale ta ki zo ki zauna". Ba ta musa mishi ba ta dawo gurin zamanta ta zauna ba tare da ta k’ara cewa wani abu ba. Kowa idan ka duba yanayin da yake ciki ransu a ‘bace yake. Abbu ne ya saki murmushin takaici wanda bai kai ciki ba ya ce "Na ji bayanin ki Fatima, ina so ki saurare abin da zan fad’a miki da kyau, wannan maganganun da kike fad’a min wai ba kya son Faruk kina da wanda kike so na d’auke shi shirme ne, Fatima abin da kike so a miki ba mai yiwuwa ba ne, ba na magana biyu, ba ni na had’a ki da Faruk ba bare ki ce za a miki auran dole, hasalima ba ki ta’ba nuna mana ba kya son shi ba sai yanzu da kika ga komai yazo k’arshe sannan za ki bijiro da wata magana mara amfani, ina so ki sani ko da basaid amincewar ki sai kin auri Faruk, ina so ki sani ba ki da wani miji bayan Faruk, zan iya nemar ma Faruk aure a ko ina ne bare ke mallakina, ba ki isa ki lalata mana zumuncin dake tsakani na da d’an uwana da kowa yake sha’awar mu ba wanda tun kan a san za a haife ki muke yin shi, sai ke a rana d’aya da kike so ki wargaza mana shi a lokaci guda, wannan su ne maganganun da zan fad’a miki, shawara ta rage naki, abu na k’arshe da zan fad’a miki shine ban yarda ki k’ara fita daga gidan nan ba sai in ni na umarce ki" Yana gama fad’ar haka ya mik’e ya shiga cikin bedroom d’in shi. Wani irin kuka na fashe dashi, a lokacin zuciya ta wani irin zafi take min da irin hukuncin da Abbu ya yanke a kaina. Ummu ce ta d’aura da cewa "Fatima kin bani mamaki, ina ganin ki yarinya mai hankali, ashe ban sani ba kin riga kin canza da yadda na sanki, ki rasa wanda zaki yi ma butulci sai Faruk wanda yake dazumunci da ganin girman manya, za ki nuna kin fifita wani a kanshi, tun yaushe Abbun ki ya raba ki da wannan Dr yace ki bashi hak’uri kina da wanda za ki aura, shine ki ke so ki nuna mishi bai isa dake ba, ki ka ci gaba da soyayya dashi, ko a fuska ki ka nuna ma Faruk wani abu sai nayi mugun sa’ba miki". Tana gama fad’ar haka ta bar gurin. Yaya Aminu mik’ewa yayi ya tafi, ko kallon in da nake bai yi ba. Ya rage daga ni sai yaya Khalil a falon, ina tunanin zai ce min wani abu, ga mamaki na bai ce min komai ba, a fuskar shi na gane shima bai ji dad’in abin da nayi ba. Tashi yayi ya koma side d’in shi, a raina ina k’ara mamakin canzawar yaya Khalil, in da a da ne yaga an min wannan dukan a gaban shi, ya dinga bani hak’uri kenan, amma yanzu ko magana bai yi min bare in sa ran zai ba ni hak’uri. Ganin ni kad’ai nayi saura yasa na tashi na tafi d’aki na dan in gasa jiki na, saboda ko ina a jiki na ba in da bai min ciwo. Tun daga wannan lokacin na rage fito wa falo, ba kuma wanda ya damu da fitowar tawa tun da fushi suke yi dani. Yaya Faruk na kira na a waya, sai dai hirar tamu ba ta yin wani armashi, saboda komai ya min magana sai na gadama nake bashi amsa, da ya tambaye ni dame-dame nake so ya sa min a akwati, k’in fad’a nayi, da ya matsa min ne nace duk abin da ranshi yake so, size d’ina kawai na fad’a mai, ba yadda bai yi ba akan mu tattauna akan bik’in, amma nak’i, ganin hakan da nake mai ne yasa yayi fushi ya rage kira na sai ya kama yake kira na. Nana Khadijah kuwa yanzu shak’uwar su sai k’ara gaba take yi da yaya Faruk, yanzu sukan zauna da ita yana jan ta hira, yawancin hirar tasu yana fad’a mata yadda yake so na, hakan yana ba ta mamaki ganin yaya Faruk miskili wanda bai damu da kula mata ba a yanda ta ji yaya Mus’ab na yawan fad’a sai take mamakin yadda yake fad’a mata yanda yake so na, lallai ta tabbatar da son da yake min ba k’aramin so ba ne, ba ta san bikin yaya Faruk ya kusa ba, sai da taje gidan su yaya Mus’ab ne taji suna maganar bikin da Anty Maryam, tun san da taji maganar bikin ta rasa yadda za ta fassara yadda take ji a ranta, ganin abin zai dame ta yasa ta watsar da tunanin da yake so ya zamar mata matsala. Lokacin da suka had’u da yaya Faruk ne take mishi fatan alkhairi a auran da zai yi, ta kuma mishi k’orafin me yasa bai fad’a mata bikin shi ya kusa ba, ya bata hak’uri akan mantawa yayi, shi kanshi yaya Faruk yana ganin mutuncin Nana Khadija saboda yadda ta d’auke shi kamar yayan ta, sannan natsuwar ta da kamun kanta da rashin hayaniyar ta na d’aya daga cikin abin da yasa yake ganin mutuncin ta, shima sai yake jin ta kamar k’anwar shi, ko su yaya Mus’ab da Anty Maryam suna mamakin yadda yake zama yana hira da ita duk da dukan su ba ma’abota surutu ba ne. Yau ina zaune a d’aki na kamar yadda na sabar ma kaina, yaya Khalil ne ya shigo da sallamar shi. Amsa mishi nayi na kau da fuska, saboda shima yanzu ya shiga cikin sahun wanda ba su damu dani ba. Murmushi kawai yayi ganin yadda nayi. "Fatima zuwa nayi in baki shawara a matsayina na d’an uwanki, wanda ya damu da damuwar ki, wanda kuma bai son ki sa kan ki a wani hali". Jin ban ce komai ba yasa yaci gaba da cewa "Fatima, abubuwan da kike yi sam bai kamata ba a matsayin ki na ‘ya mace, da nayi niyyar in zuba miki ido kamar yadda kike so a k’yale ki, sai na ga bazan iya ba, yanzu har kin manta sharad’in da na gindaya miki in dai kina so mu shirya shine ki so yaya Faruk, ko da yake na lura dake za ki iya ‘bata wa da kowa in dai akan Dr ne, tun da yanzu gashi kin za’bi ki zauna a d’aki ke kad’ai kina ganin in kika yi hakan za a gane kina fushi, to bari in fad’a miki ki ji, ki hak’ura da Dr Sadik tun da su Abbu da Ummu sun nuna sun fi son ki auri d’an uwan ki, ni da yaya Aminu ma mun fi son ki auri yaya Faruk d’in, me zai sa ba za ki duban hakan shi zai fi miki zama alkhairi tun da kowa shi yake so ki aura, duk abin da kika ga yawan mutane nak’i to ya kamata ka hak’ura dashi duk kuwa da son da kake mishi, zai iya yiwuwa abin ba alkhairi ba ne a gurin ka, ko da yake ke kin yi nisa a makauniyar soyayyar da ba za ki fahimci hakan ba, wannan shawarar ina baki ita ne a matsayina na yayan ki, nasan komin daren dad’e wa zaki tuna da shawarar da na baki, nasan a yanzu ba lallai ki d’auki hakan da mahimmanci ba, ki zauna ki yi karatun ta natsu ko dan gudun ‘bacin ran iyayen mu da kuma zumuncin mu da zaki ja ya samu rauni ta dalilin ki, ina fatan za ki yi amfani da shawarar da na baki, na barki lafiya" yana gama fad’ar haka ya bar d’akin ba tare da yaji nawa jawabin ba. Tabbas nasan duk abin da yaya Khalil ya fad’a gaskiya ne, ni kaina da zan iya amfani da shawarar da suke bani da na bi, sai dai matsalar zuciyata da ta riga ta daina d’aukar shawarar kowa a dalilin son Dr. Kasancewar takunkumin da Abbu yasa min na hana ni fita, ba k’aramin takura min yayi ba, yanzu ba ni da halin had’uwa da Dr sai dai a waya, na fad’a mishi duk halin da ake ciki, ya nuna min da kar in damu da duk abin da za’a min in dai zamu cin ma burin mu. Son da nake ma Sadik bai sa na hango illar abin da nake yi ba, ni ko da yaushe shine in kasance da son Dr a raina. Da wannan nake samun k’arfin gwiwa amma a maganar gaskiya halin da ‘yan gidan mu ke nuna min a yanzu na damu na, dan duk wanda yasan ni a da yasan na canza dan har wata ‘yar rama nayi. Duk wata kulawa da Ummu da su Abbu har ma da yaya Khalil suke nuna min a da, yanzu babu wannan. Gashi yanzu shirin mu da Anisa yaja baya, ba wani cika zuwa tayi ba tun san da tazo gidan mu muka samu sa’bani da ita akan maganar yaya Faruk, duk da ina kewar ta kasancewar yadda muka shak’u tun muna yara, hakan ba zai sa in rabu da burin zuciya ta dan in faranta mata, muna waya da ita jefi-jefi. Ranaku na ta wuce wa inda bikin mu ya kasance yau saura sati uku, a ranar kuma aka kawo akwatina Set biyu aka kawo, dana Abbu da ya had’a da na yaya Faruk, kowane set akwatuna uku ne da kit, haka ma na yaya Faruk, kowane set da kalar sa, kaya ne na gani na fad’a, akwatunan kad’ai abin kallo ne bare aje ga kayan dake ciki, baki ba zai iya fasalta kayan da ke ciki ba, sai dai gani da ido. A ranar ne na samu na rok’i Abbu akan ya barni in je gidan su Halima, jin inda zani yasa Abbu yasa yaya Khalil ya kaini ya d’akko ni. Ko da muka je gidan su Halima, da k’yar yaya Khalil na rok’e shi akan yaje ya dawo, da cewa yayi sai ya jira ni. Ina shiga muka gaisa da Maman su kana muka wuce d’akin ta. Hira muka dasa ta yaushe gamo, mai aikin su ce ta kawo min kayan abin sha da abinci. Ko kallon abincin ban yi ba saboda a halin damuwar da nake ciki, nafi buk’atar mai kwantar min da hankali akan wani abinci. Drinks kad’ai na d’auka na sha. Halima ce ta matsa min da tambayar dalilin ramar da nayi, ganin abokin kuka ake fad’a ma mutuwa yasa na kwashe komai na fad’a mata har ya zuwa yanzu halin da nake ciki. Halima ce ta numfasa kana ta ce "Gaskiya Fatima kina cikin wani hali, dole ne a tausaya ma halin da kike ciki, sai dai gaskiya ni ban goyi bayan ki akan ki tafi wani gurin ba, gwara ki ta ba su Abbu hak’uri akan su baki wanda kike so, ki ci gaba da nuna musu yadda kike jin Dr a ranki da halin da za ki iya shiga idan bashi kika aura ba, nasan za su fahimce ki, ko kuma kije ki samu Dadin su yaya Faruk d’in ki mishi bayani, nasan shi zai son farin cikin d’an shi dan ba zai so d’an shi ya auri wacce ba ta son shi, haka kuma ba zai so zumuncin su ya samu rauni saboda wannan auren ba". Girgiza mata kai nayi kana na ce "Halima ba wata dubarar da zan bi wadda ta fi min sauk’i shine in yi tafiyar, gurin da zani ba mai cutar wa bane, da kunya in tunkari Dadin su yaya Faruk da wannan maganar, gaskiya ba zan iya ba, Dadi da Momi sun nuna min soyayya, su Abbu ba za su saurare ni ba, dan ba ki ga yadda suka nuna ‘bacin ransu akan maganar nan ba ne, yaya Faruk ma ba zan iya tunkarar shi da wannan maganar ba dan ba zan so ya shiga wani hali sabo dani ba, kawai dai ki taya ni da addu’a, Allah yasa komai yazo cikin sauk’i". Cikin tausayawa Halima tace "Amin dai Fatima, insha Allahu zan dinga sa ki a addu’a ta". Da k’yar Halima ta tilasta min na ci abincin da mai aikin su ta kawo min, ba laifi na ci abincin dan na dad’e ban ci abinci mai yawa irin shi ba. Haka Halima taci gaba da bani shawarwari, hak’ik’a na ji dad’in shawarwarin da ta bani. Kiran yaya Khalil ne ya katse mana hirar da muke yi, sanar da ni yayi ya na k’ofar gida yana jira ma, sallama muka yi da ita, mun yi da ita akan sai mun had’u da ita ta waya. Ko da muka koma gida ban nuna musu komai ba, Falo nazo aka yi ta hira dani. A fuskar su kad’ai da na kalla na gane sun yi farin ciki da yadda na sake, da alama na hak’ura da k’udiri na. Jin dad’in hakan ne yasa bayan na koma d’aki Ummu ta shigo ta k’ara min nasiha tare da bani magungunan da za su gyara ni. Saboda ban son tayi fushi dani yasa na amshi magungunan nashi ba wai magungunan na da dad’i ba, hasalima wasu da nashi ji nake yi kamar in yi amai. Abbu ma ya kira ni ya k’ara min nasiha, na nunar mishi da ba komai na hak’ura. San da Ummu ta ce in zo in ga kayan akwati ban mata musu ba, dan bana son ta zargi ko har yanzu ban hak’ura ba, gaskiya iya had’uwa akwatunan nan ya burge ni, kai da gani kasan mai tsada ne, kayan ciki kuwa nasan kud’i yayi kuka, nasan ko Dadi da Momi kad’ai Allah kad’ai yasan kayan nawa suka zuba a ciki, bare har da na yaya Faruk da yace zai k’ara min. Ko ni idan na ce kayan bai min ba na fad’i son raina ne, gaskiya sun yi bajinta a akwatinan da aka kawo. Haka Ummu tasa mai gyaran jiki ta zo ta fara min gyaran jiki. Anisa ma tazo dan mu tattauna akan yadda bikin zai gudana, na sanar da ita da cewa ba wani event da zanyi sai walima, da ta matsa min ne na ce na bar mata wuk’a da nama, ta tsara duk yadda take so bikin ya gudana, hakan da na ce mata taji dad’i. Yau bikin mu ya rage saura kwana goma, sai shirye-shirye ake yi ko ta ina kasancewar abin na gida ne, a yau ne kuma muka shirya tafiyar da zanyi ni da Dr. Kayana na h’ada a irin jakar matafiya, na d’ebi abin da zan buk’ata. Sai da fito falo na ga ba kowa, dan gudun a sami matsala sai da na je d’akin Ummu na ga tana bacci, dama nasan Iya Talatu ba ta nan Ummu ta aike ta, haka na k’ara fita parking space na ga ba motar yaya Khalil, daman nasan Abbu baya nan. Da wannan na samu k’arfin gwiwa na d’akko jaka ta na fito cikin sand’a dan kar wani yaji takun tafiya ta. Cikin sa’a san da nazo bakin gate ba kowa, dan haka da sauri na bud’e k’ofar a hankali na fita. San da na fito daga gidan ne naji wasu hawaye sun zubo min masu zafi, zuciya ta na k’wa’ba ta akan abin da zan aikata ba mai kyau ba ne, zuciya ta na umarta ta da na koma, abin da nake shirin aikata wa zai iya janyo min fushi a gurin iyaye na da ‘yan uwa na, idan na tuna da in da za ni bai da wani matsala, zan dawo idan lokacin bikin ya wuce, da wannan na samu k’arfin gwiwar tafiya. Can bayan layin mu maka had’u da Dr kasancewar dashi zamu yi tafiyar. Ina zuwa ya bud’e min mota na shiga muka d’au hanyar barin garin. [6/30, 21:10] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* *FATAN ALKHAIRI* _Atika Bashir_ _Khadijat Ahmad_ _Murjanatu Bukhari_ _Ameenat Umar Abdullahi_ _Aisha Ibrahim_ _Da sauran fans na Kainuwa Writers Association na Facebook group_ _Amsar question of the day shine Urwatu bn Mas’ud As-Sakafiy (RA) shine wanda k’urayshawa suka aika lokacin yana mushiriki a lokacin Hudaibiyya_. 65-66 Muna fara tafiya na cire sim d’in dake waya ta nasa sabon sim d’in da Dr ya kawo min wanda zamu dinga waya dashi. Tun da muka d’auki hanya na kasa yin magana, in ban da hawayen da ke ta zubowa a ido na ba abin da nake yi, tunanin gida kawai nake yi da halin da zasu shiga idan suka san ba na nan, danasani na fara yi akan wannan shawarar da muka kawo na tafiya ta. Dr ne ya lura da halin da nake ciki ya fara lallashi na da kwantar min da hankali, hakan yasa na d’an saki jiki na duk da abin na damu na a raina. Ba mu sauka a ko ina ba sai a garin Wagini. Ni na dinga nuna ma Dr hanya har muka kai gidan Hajiyan Wagini. Bayan yayi parking ne ya kalle ni yace "Pls Zarah kar kisa kan ki a damuwa, ni kaina ba zan so in gan ki cikin damuwa ba, hakan da muka yi shine mafita a gare mu, kuma kin ga ba wani bak’on guri za ki zauna ba, gurin kakar ku ce, komai zai zama normal, za mu dinga waya, kin ga ba hali in dinga zuwa ina duba ki saboda kar a samu matsala amma in na samu sauk’in aikin zan yi k’ok’ari in lek’o ki, sai dai in nazo in fad’a miki in da za mu had’u don gudun samun matsala". Narai-narai nayi da ido, ji nake yi kamar in fashe da kuka saboda halin da nake ji na a yanzu. Girgiza min kai Sadik yayi alamar kar in yi kuka. Kasa daurewa nayi na fashe da wani irin kuka mai tsuma rai. Kallo na kawai Dr yake yi, da alama shima jikin shi yayi sanyi da halin da nake ciki. Cikin tattausan lafazi Dr ya fara magana "Zarah in har hankalin ki bai kwanta da wannan hukunci da muka yanke ba gwara in maida ke gida ki auri d’an uwan ki, ni sai in hak’ura, tun da muka tawo kike cikin wani yanayi har muka kawo, gashi kuma tun kan a je ko ina kin fara kuka, ba zan so ta dalili na ki shiga wani hali ba". Ina jin Sadik ya fara maganar sai ya hak’ura da ni in auri yaya Faruk tun da zan sa kaina a damuwa nayi saurin dawowa da natsuwa, nasan in har na koma gida ba abin da zai hana Abbu aura min yaya Faruk, hakan na nuna cewa nayi bankwana da Dr kenan. Murmushi na sakar ma Dr duk da iya le’be na ya tsaya na ce "Dr in na tuno halin da su Ummu za su shiga ne sai hankali na in ji ya tashi, zan yi k’ok’ari in ga na rage damuwa, fatana mu kasance a tare dakai". "Yawwa Zarah ina so in koma, kin ga yamma tayi, ba na son yin tafiyar dare". Jiki na ne ya k’ara yin sanyi na tafiyar da Dr zai yi, yanzu ganin shi zai min wuya tun da ban san lokacin da zai sake zuwa ba. Kamar ya san abin da nake tunani kenan ya ce "Haba Princess Zarah, don’t put yourself in worry, ai za mu dinga waya kuma insha Allah zan samu time in zo in duba ki". Wayar shi da ya fara ringing ne ya katse me mai maganar da yake yi, ya kalli Screen d’in wayar kafin ya juyo ga kallon shi gare ni ya ce "Zarah bari in k’arasa, Dr Kamal ne yake kira na, ina jin ana nema na a asibiti ne". Karyar da kai na nayi cikin muryar shagwa’ba na ce "Dr ka tsaya ko ruwa ne ka sha, yanzu in na shiga cikin gida sai Hajiyan Wagini ta tambayi waye ya kawo ni, in na ce direban gidan su Momi ne ya kawo ni, sai ta ce a kai mishi abinci da abin sha, kaga in har ka tafi zata iya d’ago ni, bari in shiga ciki in fito". Fita nayi daga motar na d’auki ‘yar jaka ta na shiga cikin gidan. Samun Hajiyan Wagini nayi zaune a falon ta. Ina sallama na fad’a jikin ta ina murna. Itama dariya ta fara yi ta amsa min sallamar tana cewa "Ja’ira d’aga ni kar ki k’arasa min k’afar tawa". K’ara lafewa nayi a jikin ta ina dariya na ce ‘Ke Hajiya dan ma kin samu na hau wannan k’afar taki, yaushe rabon da ki samu wanda ya hau". "Ai yanzu wannan k’afar tawa ta fi k’arfin ki, sai dai kuma ki bar ma ‘ya’yan ku da za ki haifa min ke da Soja marmari daga nesa, Allah sarki ina mai gidana na kaina, kwana biyu ba mu yi waya dashi ba…". Katse ta nayi da cewa "Kai Hajiya yanzu in kika fara zaro zancen nan ba tsayawa za ki yi ba, ni na manta da direba a waje, ko ruwa ban kai mai ba". "Au Allah sarki, Malam Lawal ne ya kawo ki, shine dan shashanci baki ce ya shigo mu gaisa ba, maza jeki ki ce ya shigo ciki, sai ki bud’e mai d’akin bak’i, akwai abinci a kitchen kije ki d’akko mai". Jin Hajiyan Wagini za ta iya gano wanda ya kawo ni in har na shigo dashi yasa na ce mata "Hajiya sauri yake yi, bai so ya yi tafiyar dare, ruwa kawai yace in kai mai ya sha". Ko iska zai bi k’arewar sauri da yake yi, ai dai ma gaisa ko’ tana gama fad’ar haka naga ta d’akko wani mayafi dake kan hannun kujerar ta. Jin Hajiyan Wagini za ta bod’e min yasa na ce mata "To bari in je in ce ya shigo ku gaisa Hajiyan mu ba sai kin fita ba, tun da k’afar taki ta zama a lalla’ba" Na k’arasa maganar da wasa. Ita ma cikin wasa Hajiyan Wagini ta ce "Ki yi addu’a ma k’afar ki tayi k’warin irin tawa". Kitchen na shiga na d’akko drinks da ruwa, na zuba a d’an madaidaicin tray na nufi k’ofar gida. Bud’e bayan k’ofar motar nayi na zauna, ganin haka yasa shima Dr ya fito daga gaban motar ya dawo baya. "Sorry Dr, na barka kai kad’ai ko" na fad’a cikin siririyar murya. Wani kallo ya jefo min mai isar da sak’wanni da dama ya ce "kar ki damu Zarah". Tsiyaya mishi ruwa nayi a glass cup na mik’a shi, amsa yayi ya sha kad’an ya ajiye yayin da ya d’auki Viju milk yana sipping. Mun d’an ta’ba hira dashi kana muka yi sallama da Dr ina d’aga mishi hannu shima yana d’aga min, tunanin kewar shi da zanyi kawai nake yi. Sai da naga tafiyar shi kafin na koma cikin gida. Hajiya ce ta kalle ni ta ce "Ina kuma Malam Lawal d’in na ga kin shigo ke kad’ai". "ya tafi, yace in gaishe ki". "Au yanzu sai da ya tafi bai shigo mun gaisa ba, ai shi kenan". Sanin in na zauna Hajiya ce zata dame ni da tambayoyin ta, shi yasa na wuce d’aki na barta a falo. A can ‘bangare su Ummu kuwa, bayan ta tashi daga bacci ne ta fito falo, ta dad’e a zaune ba ta ji motsi na ba, hakan yasa ta tashi ta tawo d’aki na dan ta duba ni. Ganin ba ta ganni ba yasa ta duba cikin band’aki na amma ba ta ganni ba, haka ta dinga duba ko ina a gidan ba ta ganni ba. Mamaki ne ya kama ta dan ita tasan ba muyi da ita zan fita ba. Fito wa tayi harabar gidan, sunan wanda yake musu gadi ta dinga kira. "Malam Musa! "Malam Musa! Jin kiran da Ummu ke mai ne yasa ya fito daga d’an d’akin shi dake can gefen gate ya tawo da gudu. "Hajiya gani" Malam Musa ya fad’a cikin ladabi. Ummu ce ta ce "Daman tambayar ka zanyi, ba ka ga fitar Fatima daga gidan nan ba, na tashi daga bacci ne na ga ban ganta ba". "Gaskiya ban ga fitar ta ba, ina jin ko lokacin da na shiga band’aki a lokacin ta fita". "Ba komai Malam Musa, za ka iya tafiya" tana gama fad’ar haka ta juya cikin falo. D’akko wayar ta tayi ta kira Anty Jiddah ta tambaye ta ko na zo gidan ta, nan Anty Jiddah ke sanar da ita ban zo ba. Haka Ummu ta kira Anisa ta k’ara tambayar ta ko na zo gidan, ita ma sanar da ita tayi ban zo ba. Duk inda Ummu take tunanin zanje, ta kira ta tambaya an tabbatar mata da ban zo ba. Gashi tana ta kiran numba ta ba ta shiga ba, ganin haka yasa Ummu ta kira Abbu ta sanar dashi halin da ake ciki. Ko minti ishirin ba a d’auka ba sai ga Abbu da yaya Khalil sun shigo a tare. Abbu ne ya kalli Ummu wanda hankalin ta ya fara tashi ya ce "Hajiya ya aka yi Fatima ta fita ba ki sani ba, kuma ba gidan k’awayenta ta tafi ba?" ya k’arasa maganar da tambayar ta. Ummu ce ta nisa ta ce "Na tashi daga bacci sai na ji ban ji motsin ta ba, na shiga d’akin ta ma ba ta nan, na kira gidan su Jiddah da Anisa ba taje can ba, har k’awar ta d’in nan Aisha ita ma na kira ta tace min ba ta je can ba, na kuma tambayi Malam Musa yace bai ga fitar ta ba, sai dai Khalil yaje gidan wannan k’awar ta Halima yaga ko can taje". Abbu ne ya kalli yaya Khalil ya ce "Khalil je ka gidan k’awar Fatiman ka ga ko tana can". "Toh Abbu, bari inje in gani" yaya Khalil ya amsa kana ya juya ya bar falon. Abbu ne ya nisa ya ce "Kar ki damu Hajiya, insha Allahu ba nisa tayi ba". Ummu ta ja gauron numfashi ta ce "Allah dai yasa Alhaji". "Amin". ya fad’a a tak’aice. ************************* Yaya Khalil ya je gidan su Halima ya tambaye ta ko na zo gidan, ita ma ta tabbatar mishi da ban zo ba. Ganin yanayin yaya Khalil yasa taji tausayin shi, tasan suna cikin wani hali gurin nema na, matsalar da aka samu shine ban fad’a mata inda za ni ba, dama tun farko ita ba ta bada goyon baya na wajen yin tafiyar nan ba, da haka suka yi sallama da yaya Khalil ya dawo gida jiki a sanyaye. Tun da na shiga d’akin Hajiyan Wagini na ajiye kaya na, cire kaya na nayi na shiga band’aki na watsa ruwa, na nemi kaya marasa nauyi nasa na fito na nufi kitchen na d’ebo abinci da ruwa na dawo falo. Zama nayi kusa da Hajiyan Wagini na fara cin abinci muna d’an yin hira da ita. Cikin hirar ne Hajiya ta kalle ni ta ce "Fatima lafiya na ganki a garin nan ke kad’ai alhalin bikin ki ya kusa, mu da muke shirin zuwa biki sai kuma in gan ki kinzo" ta k’arasa maganar tana kallo na. Ban so Hajiya ta fahimci plan d’ina da wuri, na fiso sai ta tashi tafiya Kaduna in bijire mata in k’i bin ta, zan fito in fad’a mata k’udiri na akan fasa auren yaya Faruk, nasan ba k’aramin rigima za mu yi da ita ba, zanyi duk iya yi na in shawo kanta akan tasa su Abbu su fasa auran mu. Murmushi nayi na ce "Hajiya zuwa fa nayi in miki sallama, shine kuma yanzu za ki tsare ni da tambayoyin ki, sai in ma yi zuciya in koma". Hajiya ce ta ce "Ka ji ni da ja’irar yarinya, to koma mana, ba dole in tambaye ki ba, na ganki kwatsam ke kad’ai kuma nasan a Kadunan ana can ana ta shirye-shirye". Shiru na mata taci gaba da maganganun ta, nasan ci gaba da tanka mata zai iya jawowa ta wargaza min shiri na, gwara in samu mu rabu da ita lafiya. Ina gama cin abincin na kai plate d’in kitchen, ban dawo falo ba na wuce cikin d’aki don muyi waya da Dr. Ido na ne yakai kan wayar Hajiyan Wagini, tashi nayi da sauri na sa ta a flight mode yadda in an kira za aji ta a kashe alhalin a kunne take, nasan za ta iya kiran Abbu ko Dadi taji dalilin zuwa na ko kuma su za su iya kiranta su tambaye ta ko na zo Waginin. Waya na zauna muka sha da Dr kamar kar mu rabu, lallai na yadda ba abin da yakai soyayya dad’i musamman in ka had’u da wanda kuke so junan ku, sanar dani yayi yana hanya, idan ya k’arasa Kadunan zai kira ni, sallama muka yi dashi akan sai ya kira ni. Yaya Khalil haka ya dawo ya sanar dasu cewa ban je gidan k’awa ta ba. Haka aka ci gaba da kira na amma ba a samu na, wayar a kashe take, Ummu najin haka ta soma kuka tana cewa "Oh ni Aisha, Allah kasa yarinyar nan ba wani gurin ta tafi ba". Abbu ne yaci gaba da lallashin Ummu akan ta daina kuka, a zuba ido a gani zuwa anjima, idan ban dawo ba sai a san matakin da za a d’auka. Su kansu idan ka ga gansu, kasan suna cikin wani hali na tashin hankali. Abu wasa-wasa sai gashi har dare ba a ganni ba, hakan yasa yaya Aminu wanda yazo gidan tun san da ya koma gida Anty Jiddah ta sanar dashi halin da ake ciki ya tawo gidan yace ko za a je a tambayi Dr ne ko yasan inda nake. Abbu ne ya hana yaya Aminu zuwa, yace in aka yi hakan ba a kyauta ma Dr ba, tunda ba a da tabbacin ko yasan inda nake, kuma hakan zai iya jawo wata matsala, ni ai ba yarinya ba ce, a dakata a gani ko zan dawo. Har dare ban dawo ba, shi kanshi Abbu ya rasa wace hanya zai bi ya shawo kan matsalar, gashi ya kasa d’aukar waya ya kira Dadi da Hajiyan Wagini ya fad’a masu halin da ake ciki, ganin dare yayi ne Abbu yasa kowa ya tafi ya kwanta, ko a ranar a nan yaya Aminu ya kwana, sai kiran Anty Jiddah yayi ya fad’a mata ba zai samu dawowa ba, a gidan su Ummu zai kwana. Haka kowa a ranar yayi kwanan k’unci da fargaba, ba wanda yayi barcin kirki a cikin su. Ummu kuwa da Abbu ba a san wanda yafi shiga tashin hankali ba, ba wanda ya rintsa a cikin su. Dukkan su tunanin su yazo d’aya akan cewa na gudu ne ba ‘bata nayi ba, shi yasa Abbu bai samu k’arfin gwiwar kai report police station ba. Washegari ne Abbu ya kira Dadi akan yana neman shi, wata ‘yar matsala ce ta taso. Ba a d’au wani lokaci ba sai ga Dadi ya zo gidan. Abbu ne yake sanar da Dadi ba a ganni ba, basa tunanin ‘bata nayi, sun fi tunanin guduwa nayi dan ra’ayin kaina. Tun da Dadi yaji wannan labarin ya dinga ma Ummu da Abbu fad’a akan ya hakan ta faru. Abbu na ganin babu wani dalili da zai ‘boye ma Dadi abin da yake faruwa tun da na riga na tona musu asiri, gwara ya fito ya fad’a mishi komai, hakan yasa bai ‘boye ma Dadi halin da ake ciki ba game da halin da muke ciki tsakani na da yaya Faruk da kuma Dr, har zuwa rashin gani na da ba ayi ba. Abbu ne ya d’aura da cewa "yaya ina neman afuwar ka akan ‘boye maka halin da ake ciki da nayi, ina ganin na isa da Fatima da zan ba ta umarni tabi, ashe abin ba haka yake ba, soyayyar wani ta fini mahimmanci a gurin ta da har ta za’be shi akan bin umarni na, A yau da a ce ina da wata ‘ya macen ban da Fatima da na ba Faruk ita, ina rok’on alfarma a gurin ka yaya kar ka hana ni, ina so in nuna ma Fatima ni na haife ta ba ita ta haife ni ba, zan aura mata aure da Faruk a rananr da aka tsara ba tare da an fasa ba, sai dai in ta mutu da auran shi a kanta, zan nuna wa Fatima ni ba irin uban nan ba ne da zasu bi son ransu su faranta ma ‘ya’yan su akan abin da suke so" ya k’arasa maganar cikin takaici. Dadi ne yaja gauron numfashi kana ya ce "Ibrahim ba ka kyauta min ba na ‘boye min halin da ake ciki na tsakanin Fatima da Faruk, dukkan su ‘ya’yan mu ne kuma ba za a tauye ma kowa hak’k’in shi dan mu faranta ma d’aya daga cikin su ba, ita soyayya Allah ne yake sa ta a zuciyar mutum, ba a tilasta wa d’an adam sai ya so wani, in Allah bai nufa yaso wanin ba zai ta’ba son shi ba duk kuwa da kusancin su, nasan Fatima ba ta kyauta ba da ta za’bi hanyar guduwa akan tana ganin shine maslaha a gare ta, da ni ta zo ta sama ta fad’a min halin da take ciki da abin bai kai ga haka ba, yanzu abin da yafi mahimmanci shine a samu a san inda Fatiman take, in yaso daga baya a samu mafita akan wannnan al’amarin. Abbu cikin ‘bacin rai yace "yaya kayi hak’uri da abin da zance, ni dai da kaina ba zan sha wahalar neman Fatima ba, bayan nasan guduwa tayi, taje duk inda zata tun da tana ganin hakan shi yafi mata". Ummu ce cikin kuka ta ce "Alhaji kayi hak’uri da abin da ya faru, yaro ne ka haife shi ba ka haifi halin shi ba, menene amfanin neman yarinyar da ba za tayi wa iyayen ta biyayya ba, abin da kake ji yana faruwa ko ka kalla a talabijin shine yau ‘yar ciki na ta aikata, abin da bai ta’ba faruwa a dangin mu ba amma ta sanadiyyar yarinyar da na haifa sai gashi ta aikata". Murmushi kawai Dadi yayi ya ce "Kar ki damu Aisha, komai zai zo da sauk’i insha Allah, ni zan koma, da yardar Allah za a ganta". Sallama ya ma su Ummu yayin da suka jera da Abbu suna ci gaba da tattauna matsalar, Dadi ne yake ta ba Abbu baki akan ya d’auki komai da sauk’i, kar ‘bacin rai yasa ya d’auki mummunan mataki. Yaya Faruk tun da ya koma Abuja ya ci gaba da ayyukan shi, sai dai matsalar da muke samu dashi na yawan fad’o mishi a rai, yana ganin komai ya kusa zuwa k’arshe tsakanin shi dani in har aka yi auren shi kenan, yasan wuyar ta ayi auran mu, yasan yadda zai yi ya shawo kaina in fad’a cikin zazzafar soyayyar shi, yana da hanyoyi da dama da zai bi da ni in kamu da son shi cikin sauk’i, da irin wannan tunanin yake jin sauk’i a ranshi. Yau yana zaune a falon yaya Muhsin suna hira, yayin da Nana Khadijah ke zaune a d’aya daga cikin kujerun dake falo tana karanta wani hausa novel mai suna *SANADIN KADDARA* tattauna wa suke yi akan yadda bikin zai gudana, hankalin ta ya kasu kashi biyu, d’aya yana ga littafin da take karantawa, d’ayan yana ga tattaunawar da su yaya Faruk ke yi akan bikin shi, ba tasan me yasa in dai aka yi maganar bikin yaya Faruk take jin wani iri a ranta ba, ta rasa yadda za ta fassara wannan lamarin da yake damun ta, ba kuma wanda take ganin za ta iya fad’a ma wa dan kar a canza mata manufar ta, ita dai abin da ta sani shine yanzu sun yi sabo da yaya Faruk wanda ita kanta take mamaki, sai dai a yanzu jikin ta nayin sanyi in ta tuno da auran da zai yi, tasan dole ne ta ja jikin ta daga gareshi a dalilin auran da zai yi. Yaya Faruk ne ya kira sunan ta "Khadijah! Kiran sunan ta da yaya Faruk yayi shi ya katse mata tunanin da take yi. "Na’am yaya Faruk" Nana ta amsa mishi cikin sanyin ta. "Ina fatan normal, naji kin yi shiru ne ba ki ce komai ba". Tsadadden Murmushi tayi kana ta ce "Ba komai yaya Faruk, novel d’in nan ne ya d’auke min hankali". "Ok hakan na da kyau" shima ya fad’a yana murmushi. Ta’be baki Mus’ab yaya ya ce "Kaima ai kasan wannan miskilar ba lallai ne kaji maganar ta ba, ko da yake naga ai taku tazo d’aya kuna hira, ko dan jirgin miskilancin tare ya d’ebo ku ya ajiye ku a airport d’aya ban sani ba". Dariya yaya Faruk yayi wanda hakan ya k’ara fito da kyawun shi ya ce "Kai fa Mus’ab iskancin ka yawa gare shi, yanzu ina ruwan ka a cikin maganr mu, ko kai na tambaya". Dariya shima Mus’ab yayi ya ce "Sorry Bregadier Faruk angon Fatima". Murmushi kawai yaya Faruk yayi bai ce komai ba. Wayar Mus’ab ce tayi k’ara alamar kira ya shigo. Bayan ya gama amsa kiran ne ya kalli yaya Faruk ya ce "Ka ga ina da appointment da Birgedier Aminu na manta, shine ya kira ni yana jira na, bari in je in dawo, pls ka jira ni". "Kawai dai ka same ni a Block d’ina tun da ban san time d’in da za ka dawo ba, idan muka gama hira da Khadija zan tafi" cewar yaya Faruk. "Ba matsala, sai mun had’u a can kenan". "Ok sai mun had’u" yaya Faruk ya amsa a tak’aice. Muhsin ya juya kallon shi ga Nana Khadijah ya ce "In Maryam ta tashi daga bacci, kya fad’a mata na d’an fita". "Sai ka dawo". Nan suka yi musabaha da yaya Faruk ya fita daga falon. Jefi-jefi suke yin hirar kasancewar su mara sa son surutu, lokaci d’aya kuma yaya Faruk na kara wayar shi a kunne da alama akwai wanda yake son kira bai samu ba. Gajeren tsaki ya ja kafin ya ajiye wayar shi a kan jikin shi. Shiru ne ya biyo baya kafin ya mik’e da niyar tafiya. Sallama ya mata ya fara tafiya. Kiran sunan shi da Nana tayi yasa shi juyowa. Itama tashi tayi ta tako tazo kusa dashi. Cikin marairaicewa ta ce "yaya Faruk what’s wrong". Cikin basarwa ya ce "Me kika gani". "Gani nayi yanayin ka ya canza a lokaci guda, kamar akwai abin da yake damun ka". Lallausan murmushi yayi ya ce "No don’t mind Khadijah, ba wani abu bane, just ina ta trying d’in number Teemah ne ya k’i shiga, sai a ce a kashe take, ni kuma ban cika son takura wa mutane in ce ai kai mata waya za mu yi waya da ita". Murmushi kawai tayi ta ce "Gaskiya amarya ba ta kyauta ma angon ta ba, tasan zai nema ta sai kuma ta kama ta kashe wayar" ta k’arasa maganar cikin zolaya. "lallai Khadija kin ga gadon barci na, yanzu ni ki ke tsokana". Dariya tayi ta ce "Sorry yaya Faruk, na ga Amaryar tamu ce za ta sa yayan mu a network". Girgiza kai kawai yayi ya mata sallama ya tafi. Yau kwana na biyu a Wagini, ina cikin d’aki ina waya da Dr. Jin Hajiya ta shigo tana sababi yasa nayi saurin yi yi mishi sallama. Cikin tsokana na ce "Hajiya wai ke da waye naji kina fad’a, wa ya ta’ba min ke". Cikin fad’a Hajiya ta ce "Ban sani ba, dan jakar uban ki, me kika sa min a waya ta na kasa kiran mutane, gashi kwana biyu kenan bamu yi waya da ‘ya’ya na ba, nasan haka kawai ba za su k’i kirana ba, sai dai in da dalili". Zagin da Hajiya ta min ne yasa na fara dariya. Ran Hajiyan Wagini ne ya k’ara ‘baci jin dariyar da nake mata ta ce "Au ‘yar jakar uba dariya ma na baki ko, ba zaki fad’a min me kika yi ma wayar nake ganin wani d’an jirgi a saman wayar ba, nasan ba wanda zai min aika-aikar nan sai ke". Kasa daure dariyar nayi saboda wani zagin da Hajiyan Wagini ta k’ara min. Ganin dariyar da nake mata yasa taci gaba da sababi ta ce "Ki yi dariyar ki da kyau, zan rama ne, dan ni da iyayen ki zan had’a ki, kwanciyar hankalin ki shine ki gyara min waya ta, ai nasan Soja sai yayi hak’uri dake, ko da yake shi ba ragon namiji ba ne" tana gama fad’ar haka ta fita daga d’akin tana ci gaba da fad’an ta. Ni kuwa cewa nayi "yaushe zan bar wayar ki a geneneral mode sanandin su Abbu su kira ki su tambaye ki, ki fad’a musu ina nan ko ke ki kira su". Dadi tun da ya bar gidan su Abbu tunani ne ya addabe shi, yanzu abin da yafi damun shi shine halin da yaya Faruk zai shiga idan ya riski wannan labarin, ga kuma rashin gani na da ba ayi ba, ya zama dole ya sanar da yaya Faruk halin da ake ciki dan barin kashi a ciki baya maganin yunwa, shi kanshi shaida ne da irin son da yaya Faruk yake yi min, ashe shi bai sani ba d’an shi son maso wani yake yi wanda yafi ciwo, da irin wannan tunanin yayi tayi har ya k’arasa gida. Samun Momi yayi da Anisa suna ta hira akan bikin, jikin shi ne ya k’ara sanyin ganin yadda kowa yake maganar yadda bikin zai kasance. Guri ya samu ya zauna yayin da Momi da Anisa suka mishi sannu da zuwa. Momi ce ta tashi ta nufi kitchen ta d’akko coconut juice wanda yaji madarar peak a ciki, k’anshi flavour ne kawai yake tashi a ciki. Tsiyaya mishi tayi a glass cup ta mik’a mishi. Amsa yayi ya sakar mata murmushi duk da damuwar da yake ciki amma ba lallai ne ka gane hakan a fuskar shi ba, kad’an ya sha ya ajiye ya maida kallon sa ga Momi ya ce "Rukaiyya ina so muyi wata magana dake, ina so ki yi wa maganar kyakkyawan fahimta". Jin haka ya sa ta tattara natsuwar ta ga Dadi dan jin mai zai fad’a mata. Anisa ce ta mik’e da niyar fita daga falon, Abbu ne ya dakatar da ita akan ta zauna. Dadi ne ya fara maganar da cewa "Rukaiyya kowani d’an adam da kike gani da k’addarar sa, Allah na iya jarabtar bayin sa ta hanyoyi da dama dan ya gwada imanin su yaga ko za su iya cinye jarabawar su, to hakan ce ta faru ga Faruk…". Momi ba ta gama jin zancen ba ta katse Dadi da cewa "Me ya same shi Alhaji, pls ka fad’a min abin da ya samu Faruk d’in". Dadi ne yaci gaba da cewa "Ba abin da ya sami lafiyar shi, sai dai wata jarrabawa da take niyar samun shi ko ma in ce ta same shi, nan Dadi ya sanar da Momi halin da ake ciki kamar yadda Abbu ya sanar dashi. Ran Momi ne yayi masifar ‘baci da abin da nayi, ita a ganin ta wannan wani rainin hankali ne aka zo musu dashi, sai da biki ya kusa za a ce na gudu kuma akwai wanda nake so, shi yasa tun san da Faruk ya fad’a mata yana so na ta yi mamaki dan tasan akwai wanda Anisa tace mata muna soyayya, abin da yasa ta bar maganar ganin Faruk bai fad’a mata wata matsala daga gare ni ba, ashe kuwa matsalar tana nan za ta ‘bullo. Cikin fad’a Momi ta ce "Alhaji lallai Fatima ta ci mutuncin mu, yanzu akan Faruk ta gudu dan ni ban kawo ‘bata tayi ba tun da ba kaza ba ce ita da za a ce a gida an zo an d’auke ta, duk yadda yake nuna mata so shine za ta saka mishi da haka a lokacin da bikin su bai wuce sati biyu ba, sakayyar da za ta mana kenan na irin son da muka nuna mata tamkar yarinyar da muka haifa da cikin mu haka muka d’auke ta, shine za ta nuna mana na butulci irin na d’an adam, me yasa tun farko ba ta fad’a bashi take so ba, da tuni ban bashi hak’uri ya hak’ura da ita ba, to tun da abin haka ne Anisa ma ta hak’ura da Khalil duk da shi na san bai da matsala, tun da k’anwar shi ta guji jinin ta itama me za tayi dashi". Ganin yadda ran Momi ya ‘baci yasa Dadi ya mata shiru, sai da ta gama fad’an sannan yaci gaba da cewa "Rukaiyya a matsayin ki na babba fushi bai kamace ki ba duk da nasan ke aka ‘bata mawa, maganar Anisa ta rabu da Khalil bai taso ba tun da su ba ruwan su a ciki, in za a ga mai laifi to bai wuce Fatima ba, laifin ta da na gani shine guduwar da tayi amma dan ta ce ba ta son Faruk ba laifi bane duk da ta wani ‘bangaren in aka duba yaci a ce ta so shi ko dan son da yake mata da kuma alak’ar zumunci dake tsakanin su, sai dai shi so ba ya duba wannan, ni yanzu abin nafi buk’ata shine a ga ita Fatiman". Momi ce tayi saurin katse shi da cewa "Anya Alhaji kana son Faruk kuwa, wato kai ba halin da d’an ka zai shiga ka ke tunani ba, kafi buk’atar dawowar Fatiman, yanzu duk yaudarar da yarinyar nan tayi ma Faruk duk ba abin duba wa bane". Murmushi Dadi yayi jin Momi na tambayar shi wai anya yana son Faruk kuwa. "Hajiya ina ganin tambayar ki ba ta buk’atar amsa na tambaya ta akan wai ina son Faruk kuwa, nasan za ki fi kowa sanin irin son da nake ma Faruk, kar ‘bacin rai yasa shaid’an yayi tasiri a zuciyar ki, duk wannan maganganun ba su ba ne maslaha a gare mu, sanar da Faruk shi yafi". Yana gama fad’ar haka ya d’akko wayar shi ya kira layin Faruk d’in, cikin sa’a ya samu numbar shi. Bayan ya d’auka ne Dadi ya umarce shi da yazo Kaduna yana neman shi, yaya Faruk ya amsa mishi da yana nan zuwa insha Allah. Ita kuwa Anisa mamaki ne ya kamata da jin abin da na aikata, ba ta zaci zan iya aikata kwatankwacin abin da na aika ta ba, tuni ta fara tausaya ma halin da yaya Faruk zai shiga, ita shaida ce a irin son da yake min. Itama ta k’udurce a ranta za ta rabu da yaya Khalil ko da Momi ba ta fad’i hakan ba duk kuwa da irin son da take mai saboda a dalilin k’anwar shi yayan ta zai shiga wani hali. Dadi ne ya kalli Momi ya ce "Kin dai ji munyi waya da Faruk d’in zai zo, ban ce ke ko Anisa ku kira shi a waya ku fad’a mishi abin da yake faruwa ba" yana gama fad’ar haka ya nufi side d’in shi. Momi cikin damuwa ta kalli Anisa ta ce "Anisa kin ji abin da Fatima tayi ko? amma kina gani Dadin ku bai ganin laifin ta, kema kina da laifin ki Anisa, nasan baza ki rasa sanin wani abu dake tsakanin Faruk da Fatiman amma ba ki fad’a min ba, da nasan matakin da zan d’auka da wuri, yanzu ai gashi har dake za a jefa d’an uwanki cikin wani hali" Momi ta k’arasa maganar cikin takaici. Ita kanta Anisa jikin ta yayi sanyi, tana ganin ba amfanin ‘boye ma Momi komai tun da yanzu tasan halin da ake ciki, dan haka ta zayyane ma Momi komai na tsakanin yaya Faruk dani, da irin matsalar da shi yaya Faruk yake fuskanta a guri na akan Dr Sadik, da kuma damuwar da yake shiga akan haka. Jin wannan labarin da Momi tayi ya k’ara sa mata ‘bacin rai akan wanda take ciki, nan Momi taci gaba da fad’an ta da irin matakin da za ta d’auka akan wannan al’amarin. [7/3, 23:16] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 *TA’AZIYYA* _Ina mik’a sak’on ta’aziyya ta ga family d’in Murjanatu Alhassan wacce Allah ya ma rasuwa a ‘Yar aduwa University a sanadiyar rashin lafiyan da tayi_. _Allah nake rok’o ya jik’an ki ya gafarta miki, Allah yasa aljanna ce makomar ki_. _San da naji labarin rasuwar ki ba k’aramin tashin hankali na shiga ba, nasan nayi rashi, ke k’awa ce ta gari da bazan mantaD dake ba_ 😭😭😭 _Ina mik’a sak’on ta’aziyya ta ga Hussaina wacce Allah yayi wa mijin ta rasuwa_. _Halima Mk ina k’ara mik’a sak’on ta’aziyyata gare ki na rasa mijin ki da kika yi_. _Allah nake rok’o ya jik’an su baki d’aya ya kyautata makwancin su, ya sa aljanna ce makomar su, Allah mu ma ka kyautata k’arshen mu_ _Ina rok’on duk wanda ya karanta wannan page d’in yasa su a addu’a_ *QUESTION OF THE DAY* _Wace surah ce take karantar da cewa duka abubuwan duniya suna da dangantaka da junansu, dangantaka bayyananna ko’boyayya, Kuma zumuntarsu na gudana gwargwadon dangantakarsu da juna_ 67-68 Su Abbu kuwa ba k’aramin fushi suka yi dani ba, yaya Khalil ma ya fisu shiga damuwa saboda yadda muka fi shak’uwa dashi, ba wani mai walwala a cikin su tun san da na bar gidan mu. Dadin su Faruk ya bada cigiya ta a kafafen yad’a labarai, sannan ya kai report police station amma har yanzu shiru ba wani bayani a kaina. Tsakanin Dadi da Abbu an rasa mai k’arfin gwiwar da zai iya tunkarar Hajiyan Wagini akan rashin gani na da ba ayi ba, tunanin fad’an da za tayi da halin da za ta shiga yasa suka ‘boye mata, sun barshi akan sai an ganni za a sanar mata da komai, a cikin su ba wanda tunanin shi ya kawo can zan tafi. Yau kwana biyu kenan da wayar da yaya Faruk suka yi da Dadi sai gashi a Kaduna. Tun san da Dadi ya kira shi yake tunanin dalilin kiran da Dadi ya mishi, yasan in akan biki ne zai sanar dashi a waya, ba sai yace yazo ba. Bayan ya huta ne Dadi ya kira shi side d’in shi. Samun shi yayi da Momi a zaune, alamun dake fuskar su na nuna kowa da abin dake damun shi. Sallama ya musu ya nemi guri ya zauna. Dadi ne yayi k’arfin halin amsa masa sallama. Cikin ladabi yaya Faruk ya ce "Gani Dadi". Dadi sai da saki ya gauron numfashi saboda tunanin abin da zai fad’a ma yaya Faruk ba mai dad’in ji ba ne kana ya kira sunan sa "Umar! Cikin sanyi ya amsa "Na’am Dadi". A ranshi kuwa jinjina abin da Dadi zai fad’a mishi mai matuk’ar mahimmanci ne tun da ya kira ainihin sunan shi. Dadi ne ya nisa kafin yaci gaba da cewa "Faruk, dalilin da yasa na ce kazo Kaduna shine akan wata k’addara da ta faru bayan tafiyar ka wanda yake da alak’a da kai, ka ga kenan ‘boye maka bai da wani fa’ida". Tun kan Dadi ya fad’a mishi maganar da yake son fad’a mai, yaji jikinshi yayi sanyi, yanzu jikin shi ya fara bashi ba abu mai dad’i Dadi zai fad’a mai ba. "Faruk abin da nake son fad’a maka shine yau kwana hud’u kenan ba a ga Fatima ba, ba a kuma san inda ta tafi ba, hakan kuma na da nasaba ne da auren da za a muku da kuma wanda take so shi wannan Dr d’in, ina son ka d’au hakan a matsayin jarabawar ka, shi Ibrahim saboda ranshi a ‘bace yake ya ce ko da ba ta dawo ba zai d’aura mata aure dakai, kuma ni na fahimci dan ya faranta maka zai yi, ni kaina nasan Ibrahim da Aisha suna nuna maka so kamar d’an da suka haifa,sun kansu yanzu suna cikin damuwa da abin da Fatima ta aikata, maganar a d’aura aure ba a ga Fatima bai taso ba, za a k’ara ‘bata Al’amarin ne, gwara in ta dawo a san yadda za ayi, ba na so ka sa wannan matsalar a ranka dan guje ma kamuwa da wata cutar, kayi hak’uri Faruk, nasan Fatima ba ta kyauta maka ba" ya k’arasa maganar cikin lallashi. Tun san da lokacin da Dadi ya fara labarta mishi wannan mummunan labarin kan shi yake a sunkuye ba tare da ya d’ago kai ba. Duk wannan maganganun da Dadi yake ma yaya Faruk ji yake kamar ana watsa mishi tafasasshen ruwan zafi ne a zuciyar shi, ran shi ba k’aramin ‘baci yayi da jin wannan labarin ba, jijiyoyin kanshi duk sun tashi, idanun shi duk sun canza launi zuwa ‘bacin rai, bai ta’ba kawo wa a ranshi wannan mummunan labarin Dadi zai sanar dashi, ji yake ina ma mafarki yake yi ya samu ya farkar daga wannan mummunan mafarkin wanda bai fatan ya k’ara yin irin shi, sai dai kash! Wannan mummunan labarin a zahiri Dadi yake sanar dashi, yau ya k’ara tabbatar da maganar da Hausawa ke cewa idan wani yak’i ka wani sai yaso ka, shi da ‘yan mata ke son shi yana ja musu aji, nan ya tuno da Binafa yadda take mishi magiya akan ya so ta saboda yadda ta kamu da son shi, ya samu ya ba ta hak’uri ta hak’ura da sauran ‘yan matan da suka fad’a mishi suna son shi bai kula su, sai gashi an samu a kanshi na gudu saboda kar na aure shi duk kuwa da irin son da ya nuna min amma ni ban ga hakan ba, na za’bi bare a kanshi, ba abin da yafi tsaya mishi a ranshi shine yadda na dinga mishi yawo da hankalin shi na k’in fitowa a fili na fad’a mishi ba na son shi da wuri, sai daga baya da ya sakankance da cewa ina son shi sannan na nuna mishi da ban yi na’am dashi ba, yanzu ba abin da yake mishi yawo a k’wak’walwar shi shine guduwar da nayi wanda ba a san inda na tafi ba, a yanzu yana ganin ba abin da zai fi mai sauk’i illah ya samar wa kanshi mafita kafin dawowa ta, shi kad’ai yasan matakin da zuciyar shi ke fad’a mishi ya d’auka akan wannan curkud’ad’d’en al’amarin, yana ganin ba wanda yafi cancanta da ya nemo ni dan zartar min da hukuncin da ranshi ke ayyana mishi da ya yanke wanda yake ganin shi kad’ai ne zai kawo k’arshen wannan abun da yake faruwa tsakani na dashi. Momi da Dadi jikin su ne ya k’ara yin sanyi ganin halin da yaya Faruk ya shiga tun a yanzu wanda ke nuna tsantsar tashin hankalin da yake ciki da kuma ‘bacin rai da ya mishi dabaibayi a lokaci guda. Falon ne ya d’auki shiru ba tare da kowa ya sake magana ba, kowa da irin tunanin da yake ayyanawa a ransa. Jin shirun da yayi yawa ne yasa Dadi ya kira sunan yaya Faruk cikin tattausan harshe. Yaya Faruk ne ya d’ago kan shi wanda yake mishi wani matsanancin ciwo, wani irin nauyi kan yake mishi saboda tsabar ciwon da yake yi mishi. "Come close to me my son" Dadi ya fad’a cikin lallashi. Ba abin da yaya Faruk yafi buk’ata a yanzu da ya wuce yaji shi a kwance ko ya samu sauk’in rad’ad’in da yake ji a zuciyar shi da kuma kan shi da yake mishi matsanancin ciwo. Ba tare da musu ba ya matso ya kwanta a jikin Dadi, a lokacin ne yaji wani irin zazzafan hawaye na fita daga idanun shi, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi kamar wanda yaci kuka ya k’oshi, k’arshe ma runtse idon shi yayi ko ya samu sauk’in halin da yake ciki, sai faman karanta *Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un* da *Allahumma ajirni fih musibatih, wa aklifni khairan minha* wannan addu’o’in su yake ta faman maimaitawa a cikin ranshi, a hankali yaji natsuwa ta fara shigar shi, ‘bacin ran da yake tare dashi ya fara raguwa. Momi na ganin halin da yaya Faruk ke ciki ita ma ta fara zubar da hawayen tausayin shi, tasan daman hakan za ta faru, yaushe rabon da ta ga hawayen yaya Faruk, amma yau a dalili na yaya Faruk na zubar da hawaye. Dadi na lura da hawayen da Momi ke yi, yasan dole ta shiga wannan halin in dai ta ga yaya Faruk a cikin wannan halin, shi kanshi kawai dauriya yake yi ba wai dana bun bai dame shi ba, a yanzu ba wanda yafi buk’atar lallashi sama da yaya Faruk. Dadi ba abin da yake faman yi sai shafa kan yaya Faruk yake yi kamar yadda ake lallashin k’ananun yara, a lokaci d’aya yana fad’a mishi sweet words masu kwantar da hankali. Jikin shi da yaji ya d’au zafi wanda hakan ke nuna zazza’bi ne ya kama shi mai zafi. Janyen jikin shi yayi daga jikin Dadi, hannun shi yasa ya rik’e kan shi wanda yake ji kamar zai tsage saboda ciwon da yake mai. Tashi yayi da niyar tafiya, ya fara tafiya kenan, hannun shi na dafe da kanshi, jirin da yaji yana d’ibar shi, nan ya fara tangad’i zai fad’i, da sauri Dadi ya taso dan ya rik’e shi kafin ya fad’i, ko kan Dadi ya k’arasa yaya Faruk ya fad’i a k’asa. Momi ce ta taso da gudu tana kuka tazo tana jijjiga yaya Faruk. Anisa ma wanda shigowar ta yayi daidai da fad’uwar yaya Farud da gudu ita ma ta k’araso gurin yaya Faruk wanda yake kwance a k’asa. Momi kuwa cikin kuka cewa take yi "Faruk ka tashi, ku kad’ai gare ni, daga kai sai Anisa, ku kad’ai Allah ya ba ni, kar ka mutu saboda ‘ya mace, idan ka mutu ban san halin da zan shi ga ba". Anisa ma cikin kuka ta kwanta a jikin yaya Faruk tana cewa "yaya Faruk dan girman Allah ka tashi, kai kad’ai ne d’an uwana da nake kalla na ji sanyi a raina, kar ka tafi ka barni da maraicin ka, rashin ka zai sa in shiga cikin wani mawuyacin hali, yaya Faruk kaji tausayin mu ka tashi dan Allah…" nan ta k’ara fashe wa da wani irin kuka. Cikin Momi da Dadi an rasa mai lallashin wani a cikin su. Dadi ne ya ta’ba yaya Faruk yaji yana motsi, hakan yasa ya fahimci suma yayi. Da sauri ya wuce gurin d’an k’aramin fridge d’in shi ya d’akko faro water mai sanyi yazo ya yayyafa mishi a jikin shi. Saukar ruwan da yaji a jikin shi yasa ya saki wata ajiyar zuciya. Dadi ne da Momi suka samu suka kama shi suka kai shi side d’in shi. Wayar shi Dadi ya d’akko ya kira family Dr d’in su ya fad’a mishi halin da yaya Faruk ke ciki. Ba a d’au wani tsawon lokaci ba sai ga Dr yazo da kayan aikin shi. Bayan gwaje-gwajen da Dr ya mai ne ya kalli Dadi ya ce "Alhaji a gwaje-gwajen da nayi na gano Faruk yana yawan tunani duba da yanda BP d’in shi ya hau, yawan tunanin da ya fara yi mishi yawa ne ya jawo mishi ciwon kai mai tsanani wanda hakan yasa temperature d’in jikin shi ya canza, ciwon kai da jirin ne ya hadassa mishi suma, sannan Alhaji pls a kiyaye fad’a mishi abin da zai sa ranshi ya ‘baci don kiyaye lafiyar shi, yanzu zan mishi allurar da zai sakko mai da zazza’bin, zan kuma sa mishi drip da yaji k’arfin jikin shi, sannan zan ba da maganin da za a bashi yasha, in da hali a barshi ya huta don a yanzu bai buk’atar hayaniya". "Za mu kiyaye insha Allah" Momi ta fad’a. Bayan ya mishi allura ne yasa mishi drip kana ya musu sallama suka fita da Dadi. Tun da aka sa ma yaya Faruk drip yake ta faman barci kasancewar har da allurar bacci Dr d’in yasa mai. Momi ce ta koma side d’inta dan dafa wa yaya Faruk abincin da zai ci in ya tashi. Anisa kuwa zama tayi a kusa dashi tana kallon yadda yaya Faruk ya koma a lokaci guda. Ba abin da take furta wa sai "Fatima why, me yasa za ki sa yaya Faruk a wannan halin da yake ciki" a lokaci d’aya hawaye na ci gaba da zubowa a idanun ta. Yaya Faruk sai da ya kwashe fiye da awa uku yana bacci kafin ya tashi daga baccin. A hankali ya dinga bud’e idon shi, Anisa ya gani a gefen shi tana rik’e da d’ayan hannun shi wanda ba a sa ma drip ba, yayin da hawaye ke zubowa a idanun ta. Ganin yaya Faruk ya farka yasa ta saki murmushi ta ce "yaya Faruk ka tashi, sannu ya jikin, yanzu ina yake maka ciwo, akwai abin da ka ke so ne, ko in kira Momi ne?". Jin wannan jerin tambayoyin da Anisa ke jero mishi yasa ya girgiza mata kai. K’ara rik’e hannun ta yayi yana kallon ta, idanun ta da ya gani ya canza kala ya tabbatar mishi da tayi kuka, hannun shi yasa yana goge mata hawayen. Kwanciyar da ya ji ya gaji da ita ne yasa a hankali ya tashi ya zauna. Da sauri Anisa ta kara mishi pillow a bayan shi ya jingina da gadon. Drip d’in da taga ya k’are ne yasa ta cire mishi ta koma ta zauna. "Me yasa ki kuka?" yaya Faruk ya tambaye ta. Kamar jira take yi ta k’ara sa wani kukan, cikin kukan take cewa ‘yaya Faruk dan Allah ka daina sa tunani ni a ranka, likita yace BP d’in ka ya hau kuma duk a dalilin tunani, plss ka cire tunanin Fatima a ranka". A hankali ya ce "Kar ki damu Anisa, komai ya kusan zuwa k’arshe insha Allahu, ki daina kuka kin ji my lovely sister". "Na daina yaya Faruk". Momi ce ta shigo da foodflask a hannun ta da flask. Ajiye wa tayi a kan centre table ta nufi yaya Faruk cikin fara’a ta ce "Ka tashi Faruk, sannu ya jikin". "Da sauk’i Momi". "To Allah ya k’ara sauk’i". "Amin Momi". Niyar mik’ewa yayi da niyar tashi amma har yau jikin shi ba k’arfi. Momi ce ta ce "Ina zaka kuma". Cikin muryar marasa lafiya ya ce "Ina so in je in watsa ruwa ne, jiki na ne nake jin shi ba k’arfi, ga shi ina so in yi sallah la’asar da ban yi ba". Cikin tausayawa Momi ta ce "Ka bari kaci abinci zaka ji dad’in jikin ka, in yaso sai ka watsa ruwan kayi sallah". "Bari in je in yi brush in dawo". "Ok" Momi ta amsa mishi. Tashi yayi a hankali yake takawa, da alama har yanzu bai gama jin k’arfin jikin shi ba. Band’aki ya shiga ya d’auraye fuskar shi kana yayi brush ya fito. Dawowa yayi ya jingina da gadon. Momi ce ta kalli Anisa tace "Je ki kan fridge ki d’akko plate da cup a zuba mishi ya ci". Anisa ce ta had’a mishi kakkauran Tea wanda yaji madara a ciki, d’ayan plate d’in kuma farfesun kayan cikin ne a ciki. Momi ce ta amshi tea d’in da plate d’in ta matsa kusa da yaya Faruk d’in. Tea d’in take bashi a baki wanda yake shan shi kamar mad’aci hakan yake jin shi a bakin shi, kad’an yasha tea d’in y ace ya k’oshi, ajiyewa Momi tayi ta fara bashi farfesun, yana shan farfesun ne ba wai dan yana jin taste d’in shi a bakin shi ba, sai don kar ran Momi ya ‘baci yasa yake sha. Dadi ne ya shigo d’akin yayi don ganin jikin yaya Faruk. Samun shi da yayi ya farka har yana d’an cin abinci yasa yaji dad’i a ranshi. A hankali ya k’araso gurin su yana Murmushi ya kalli yaya Faruk ya ce "Jiki yayi sauk’i kenan Faruk, Allah ya k’ara afuwa da sauk’i". Amsawa yayi da "Amin". Bayan ya gama cin abincin ne ya mik’e yaje ya watsa ruwa yayi alwala yazo ya rama sallolin da ake bin shi kana ya koma ya kwanta. Dadi ne ya kira su Abbu ya sanar dasu rashin lafiyar yaya Faruk. Da daddare sai gasu Abbu, Ummu da yaya Khalil sun zo duba shi. Jikin Ummu ne yayi sanyi ganin da Momi take amsa musu maganar su kamar ba ta so, tasan hakan bai rasa nasaba da halin da yaya Faruk yake ciki wanda a dalili na hakan ya faru dashi, ko waye aka yi wa d’anta haka dole ne ranta ba zai mata dad’i ba. Anisa kuwa tun bayan gaishe dasu da tayi ta tashi ta bar d’akin. Shi kanshi yaya Faruk bai ji dad’in yadda Momi tayi ma su Ummu, da yadda yaga Anisa na share yaya Khalil, yana ganin wannan abin da ya faru tsakanin shi da ni ne, bai kamata su ‘bullo da wannan matsalar ba duk da yasan dan saboda shi suke yin haka, suna jin haushin abin da na mishi. Yaya Khalil ne ya tashi ya bi ta d’akin ta amma ta k’i sauraren shi, a iya nazarin da yayi yasan ba abin da ya had’a shi da ita bare yace fushi take yi dashi, duk wasu kalamai na lallashi da ya kamata ya fad’a mata ta saurare shi amma tak’i, sai ma kuka da ta sa mishi. Jikin shi ne yayi sanyi da kukan da yaga Anisa ta na yi, shi kanshi yanzu dauriya ce yake yi irin ta namiji, gashi kuma Anisa na so ta d’aga mishi hankali da kukan ta. Cikin kukan take cewa "yaya Khalil ina rok’onka ka k’yale ni, ka barni na ji da halin da nake na halin da d’an uwa na yake ciki a yanzu wanda ‘yar uwarka ce silar shi shiga wannan halin, yaya Khalil tun da Fatima ta nuna ba ta son d’an uwa na to nima ina ganin babu wani fa’ida a ci gaba da soyayyar mu, nima ina kishin d’an uwa na kuma ina son sa, yaya Khalil ka fita na ce" ta k’arasa maganar cikin kuka. Sai yanzu yasan akan abin da yasa Anisa take k’in kula shi, tana mishi haka ne saboda ta rama abin da Fatima ta yi ma d’an uwan ta, yasan ko mai zai fad’a mata ba za ta saurare shi ba, abin da ya fi shine ya bari ta sakko, hakan zai fi sa su fi fahimtar junan su. Kallon ta kawai yayi ya girgiza kai ya fita daga d’akin. Yana fita ta sake fashewa da wani kukan, wannan lokacin akan abu biyu take kukan, na son yaya Khalil da ke d’awainiya da ita a cikin zuciyar da rashin yi mishi adalci na hukunta shi da laifin da ba nashi da kuma tausayin halin da yaya Faruk yake ciki. Haka su Ummu suka yi sallama da su Momi kowa da abin da yake damun shi a ranshi. Ranar haka yaya Faruk ya kwana da tunanin in da na tafi. Washegari jikin yaya Faruk yayi sauk’i dan ya samu ya fito falo ya zauna, ganin yadda kowa ke nuna mishi kulawa yasa ya saki jikin shi duk kuwa da yadda yake jin zafi a cikin zuciyar shi na abin da na mishi. Yaya Aminu ma yazo da Anty Jiddah sun zo sun duba shi, yaya Aminu haka ya ci gaba da kwantar mishi da hankali, ya nuna mishi shi kanshi halin da yake ciki na abin da na aikata. Sun d’an jima a gidan kana suka koma gurin Momi suka mata sallama suka tafi. Yau kwanan yaya Faruk biyu da zuwan shi Kaduna ya shirya zuwa Wagini gaishe ta, kiran ta da yayi a waya haka ma Dadi ya sanar dashi shima bai samun ta a wayar, hakan yasa ya shirya tafiyar. Fito wa yayi cikin shigar wani yadi mai laushi kalar ash, in ban da k’amshin turare da yake tashi ba abin da falon yake yi. Sallama yayi ma su Momi akan ya tafi Waginin, may be zai kwana a can ko ya dawo yau. Fatan a dawo lafiya suka mishi. Kasancewar ya sa wa motar speed yasa ya isa Wagini a da wuri. Hajiya na zaune a tsakar gida tana sauraren radio taji shigowar yaya Faruk. Sallama yayi yazo ya zauna kusa da ita akan tabarmar da take zaune. Amsa masa sallamar tayi da fara’a a fuskar ta. Hajiya ce ta ce "Maraba da mai gidana Soja na kaina, sannu da zuwa". "Yawwa Hajiya, mun same ku lafiya". "lafiya lau, ya aiki, ya wajen iyayen naka" "lafiyar su lau, suna gaishe ki". "Hajiya lafiya wai ba a samun wayar ki, su Dadi suna kiran ki ba sa samu, nima na kira ba ta shiga sai a ce min a kashe take". Hajiya dama kamar jira take yi ta fara fad’a "Rashin samu na da ake yi ba zai rasa nasaba da wannan ‘yar buhun ubar ba, ba yadda banyi da ita ta gyara min wayar nan amma yarinyar nan tak’i, idan na ce ta kira min ku a wayar sai ta ce ba ta shiga, haka na gaji na k’yale ta". Murmushi kawai yayi yace "Wai wace yarinyar ce ki ke magana Hajiya". "Au kai duk bayanin nan da nake yi ba ka gane wacce nake nufi ba, to amaryar ka nake nufi Fatima…". Da sauri ya katse da cewa "Wace Fatiman wai Hajiya". Hajiya ce ta mishi dak’uwa tace "Ungo naka, kaji ni da shak’iyin yaro, yau Fatiman ce ba ka gane ba". "Hajiya kina nufin Fatiman Abbu, dama tana nan ne". "Yau kwanan ta kusan shida kenan, na ji kana tambayar dama tana nan ne, kana nufin ba a san tana nan ba ne". "Tana ina ne Hajiya?". "Tana can cikin d’aki, hala tana can ta kunna kururuwar shed’an tana saurara, yarinya ba ta da aiki sai kunna wak’ok’in soyayya kamar a kanta aka fara". Bai tsaya sauraren abin jin bayanin da Hajiyan Wagini ta ke mishi ba ya mik’e ya nufi d’akin. Duk yadda na ‘bata mishi hakan ba zai hana shi jin dad’in tawowa ta nan Wagini ba, kowa tunanin shi bai kawo nan na tawo ba. Ni kuwa ina kwance akan gado, earpiece ne a kunne na ina sauraren wak’ar Hussaini Danko, sauraron wak’ar na ke yi sannu a hankali kamar ni na raira ta, mai taken _SOYAYYA TA_ Bin wak’ar na fara yi inda mai amshin take cewa _nima soyayya ta zan furta_ _ba a saka ni rana d’aya in yi gudun ka_, _so d’ammara nayi ko za ya saka min hauka_, _ko mutuwa nai zan so a dalilin son ka , _so ajiya nayi ranar shi tazo zan d’auka_, _idan tafiya nayi an ce da gwani amsar ka_, _nace kai na za’ba_, _har zuci bazan canza ba_, _ba kuma zan k’osa ba…_, _ni kaine burina ba a hana ni zuwa gurin ka_, _so ne jagora na shi ya dasa min k’imarka_, _amsar tambihi na je ka rabe min hujjar ka_, _ya zan yi in k’yale ka in ta zama a cikin cuta_, _so so soyay…_ Sauran baitin ne ya tsaya a iya baki na saboda idanuna da suka sauka akan wanda na gani a bakin k’ofa yana kallo na. A hankali ya tako ya k’araso inda nake ya tsaya yana ci gaba da kallo na, a yanayin shi bazan iya gane halin da yake ciki ba. Wata irin kunyar yaya Faruk ne ya kama ni da tsoron shi a lokaci guda, daskarewa nayi a zaune ba tare da na iya motsa ko da d’an yatsa na ba. Wani irin murmushi ya min wanda na kasa fasalta mai murmushin yake nufi a gurin shi. "Fatima kenan, ashe nan ki ka tawo a na ta neman ki a gida" ya k’arasa maganar yana min wani irin kallo. A halin da nake ciki na firgici ba zai bani damar in iya bud’e baki na in amsa wa yaya Faruk tambayar shi ba. A yadda na lura ma bai da buk’atar amsawa ta a yanzu. Ci gaba yayi da cewa "Fatima kamar yadda kike buk’atar in barki da masoyin ki wanda ku ke son junan ku ina ganin lokacin yayi, na yarda ke jaruma ce a soyayya da zaki iya fad’i tashi a kanta, in da kika ban kunya a soyayyar taki shine tsoron da kika sa a ranki har yakai ki ga barin iyayen ki wanda ki ka sa su a cikin halin damuwa, a matsayi kin a ‘ya mace ina ganin ba mutunci ki ba ne barin gari dan ba kowa yasan nan za ki zo ba, hakan da kika yi zai sa mutuncin ki ya zube a idanun mutane, anyway ba dogon zance zanyi dake ba illa in sanar dake *FATIMA NI UMAR FARUK NA HAK’URA DA AURAN KI, FATIMA NA HAK’URA DA SOYAYYAR KI DUK KUWA DA SON DA NA KE MIKI*. Sauri nayi na d’ago kaina na kalle shi, banyi zaton jin wannan kalamen daga bakin yaya Faruk ba sanin son da yaya Faruk yake min ban yi zaton zai yi saurin yanke hukunci irin wannan ba na hak’ura dani amma sanin halin yaya Faruk in ranshi ya ‘baci zai iya yanke kowane hukunci dan samar ma kanshi mafita yasa ya zartar da hukunci, bai duba halin da zai shiga ba, Kalamen da ya yi amfani dasu wajen yi min magana shi ya bi duk sassan jiki na ya katse min kuzari na da nake tare dashi a wannan lokacin. A lokacin wani irin tausayin yaya Faruk ne ya kama ni wanda ban san lokacin da hawaye ya fara sintiri a idanu na ba. Ci gaba yayi da cewa "Fatima ina da power da zan iya auran ki in kuma koya miki so na ko da ba kya so, ba wai wannan abin da kika aikata ne yasa naji tsoro na hak’ura da auran ki, sai dan ni ba mai son shiga rayuwar wani ba ne, ina son ba wa mutum right d’in shi ne a matsayin shi na d’an adam, kin fad’a min wannan Dr ki ke so ban d’au hakan a komai ba, sai yanzu da kika d’auki matakin fara guduwa daga gaban iyayen ki, na ji tsoron a matsayin ki na ‘ya mace kar ki je ki aikata wani abin da bai dace ba duk a dalilin aure na da zaki ko bayan anyi aure na da ke ki je ku ci gaba da soyayyar ku kuna cin amana ta, kin ga kenan zan iya d’aukan ko wai mataki da ya zo min idan hakan ta kasance, hakan yasa na fasa auren ki, Fatima nayi niyar nuna miki kuskuren ki na yaudara ta da kika min, da tozarta ni da kika yi niyar yi a lokacin da bikin mu bai kai sati biyu ba kika tawo nan da niyar guje ma aure na, na so in nuna miki ba kowane namiji ne ake yaudarar shi a zauna lafiya ba, sai dai k’udurin da nake dashi na miki hukuncin na fasa dan ke ‘yar uwa tace, hannun ka ba zai ru’be ba ka yanke ka yar, shi yasa zan barki da halin ki". Maganganun da yaya Faruk yayi amfani dasu wajen yi min magana sun min tsaurin da zuciya ta ba za ta iya amsar su ba, nasan maganganu ne yake fad’a min a k’aik’aice masu isar da sak’onnin da yake son isar wa wanda Hausawa ke cewa "kukan kurciya jawabi ne". Wani irin kuka na saka a lokacin, in ban da shasshek’ar kuka na da ya cika d’akin ba abin da ke tashi. Murmushin takaici yayi ya kalle ni ya ce "Fatima ba ki yi wa kan ki adalci ba da kike yin kuka alhalin ni ban miki wani abu ba, ina ganin in akwai wanda ya dace yayi kuka bai wuce ni ba saboda halin da kika sa ni a ciki, Fatima ni kukan zuciya nake yi wanda yafi na fili ciwo, ni a gani na murna ya kamata ki yi yau na cika miki burin kin a barin ki da wanda kike muradi". Ni dai ba abin da nake yi sai ci gaba da kuka na da nake yi, wannan maganganun da yaya Faruk yake fad’a min zai fi min sauk’i akan yasa bulala ya zane da wannan maganganun da yake fad’a min. Ganin Hajiyan Wagini kawai muka yi ta shigo cikin d’akin tana cewa "Haba Soja me kuma kayi ma amaryar taka, ko me ta maka ai kamata yayi kayi hak’uri da ita dan nasan dama ita ce da laifi, ni kaina tun da tazo take sa ni magana, dama ina jin haushin ta’ba min waya da tayi". Ci gaba nayi da kuka na ba tare da na tsagaita ba, hakan yasa Hajiyan Wagini ce ma yaya Faruk "Mai gida na wai me ka mata ne ta cika mana kunne da kuka". Wani irin banzan kallo ya watsa min kana ya kalli Hajiya ya ce "Hajiya kukan jin dad’i take yi dan ni ba abin da nayi mata". Hajiya cikin lallashi ta ce "Wai me aka miki ne ki ke kukan nan". Cikin kuka na ce "Hajiya dan girman Allah ki ba ma yaya Faruk hak’uri, na mishi laifi ne". "Me kika mishi?". Hajiya ta tambaye ni tana kallo na. Shiru nayi wannan karan ban bata amsa ba, hakan yasa Hajiya fusata ta fara fad’a tana cewa "Ka ga ja’iran yara, kowa sai tambayar shi nake yi me yake faruwa kun k’i fad’a min sai tamaula ku ke yi dani". Yaya Faruk ne ya rik’o hannun Hajiya ya ce "Hajiya mu je falo zan fad’a miki abin da yake faruwa" yana gama fad’ar haka suka bar d’akin. Samun guri yayi ya zauna ya zayyane ma Hajiyan Wagini abun da yake faruwa da hukuncin da ya yanke yanzu. Hajiyan Wagini na gama jin labarin ta sa kuka tana cewa "Yanzu dama abin da Fatima tayi kenan, shi yasa ta tawo nan, ba yadda ban yi ba akan ta fa’da min dalilin zuwan ta tak’i ta kuma d’au waya ta tayi min wani surkullen da ban da damar in kira mutane ko a kira ni, wannan wace irin hatsabibiyar yarinya ce, yaushe soyayyar zamani ta canza Fatima ta koma haka, to wallahi ba ta isa ba sai ta aure ka ko tana so ko ba ta so, anya Fatima tana da rabo kuwa a duiya tun da ta k’i ka, shi yasa ta ke kunna min wak’ar soyayya ni ina sha duk cikin son ka ne ashe wani barbad’ad’d’en take so ba kai ba". Duk da ranshi ba ya mishi dad’i amma hakan bai hana shi murmusa wa ba jin Hajiya na cewa wai anya Fatima na da rabo a duniya kuwa? Jin fad’an Hajiya yayi yawa yasa ya ce "Hajiya kar ranki ya ‘baci akan wannan maganar, ni na riga da na hak’ura da Fatima, kin ga kar a zo ayi abin da zumunci zai ‘baci". Wani kallo ta mai na anya kasan abin da ka ke fad’a kafin taci gaba da cewa "Anya Soja kana cikin hankalin ka kuwa, ko dai shi wannan Dr d’in da ka ce yana son ta ya maka wani surkulen da zaka hak’ura da Fatiman, in ba haka ba ya za ayi bikin ku bai wuce sati biyu ba kace ka hak’ura da ita, ina ganin ka gwarzon namiji ashe ba haka ba ne, ko da yake bazan yi mamaki ba tun da son da kake ma Fatiman ba zai barka ka d’au hukunci akan ta ba, abin kunya yarinyar da ka ga k’uruciyar ta amma wai shakkar ta ka ke yi, to in kai ka hak’ura ni ban hak’ura ba, ba wanda ya isa ya kawo min matsala a cikin iyali na in dai ina raye". Lallashin ta yaya Faruk ya fara yi amma kamar k’ara zuga ta ake yi, maimakon tayi shiru sai ma mik’e wa da tayi ta nufi d’akin da nake ciki. Tun san da suka fita suka bar ni na ci gaba da kuka na har na gaji, sai faman ajiyar zuciya na ke yi, ba kalar tunanin da bai zo min a raina ba a wannan lokacin. Fad’an Hajiya ne ya katse min tunanin da nake yi. "Sannu Fatima, na ji abin da kika aikata, bari in fad’a miki babu wanda ya isa ya lalata min zumuncin da yara na suka dad’e suna yi, a yadda soja yake fad’a min nima za ki iya fad’a min magana in dai akan wannan Dr ne, to ko ke Laila-Majnun ce k’arewar soyayya sai kin hak’ura da shi wannan shed’anin yaron da yake zuga ki, ke ba ki isa ki kunya ta ‘ya’ya na ba, ke in banda sharrin so ai kin san Soja yafi k’arfin ki a komai ma". Duk fad’an da Hajiyan Wagini take min kaina a sunkuye yake, nasan Hajiya za ta iya min abin da ya fi haka kasancewar duk cikin familin mu tafi son shi da shak’uwa dashi sannan sunan kakan mu ne wanda ya rasu, shi yasa duk wanda ya ta’ba yaya Faruk sai inda k’arfin ta sai ya k’are. Yaya Faruk ne ya shigo ya ga fad’an da Hajiyan Wagini ta ke min, magana ya mata a kan ta k’yale ni tun da ya hak’ura, jin hakan ya k’ara tunzura HajiyanWagini ta dawo da fad’an kanshi "Rufe min baki, na ga akan Fatima za ka iya dawowa Sallamame sai yadda tayi dakai, kai in ban da ba ka da zuciya har za ka iya sa bakin ka har ka bani hak’uri duk da abin da ta maka, to in kai kana tsoron ta ni ba tsoron ta nake ji ba". Duk wannan fad’an da Hajiya ke mai bai ce mata komai ba sai ma wayar shi da ya ciro yana daddanawa. Ganin wayar da yake dannawa yasa Hajiya ta ce "Yanzu Soja duk wannan fad’an da nake yi akan ka shine za ka bad’a min k’asa a ido, maimakon kaima ka nuna ‘bacin ranka ka taya ni yi mata fad’a sai ma wayar ka da ka d’akko kana dannawa, ai shi kenan" nan Hajiya ta k’ara sa wani kukan. Sanin rikicin Hajiyan Wagini yasa ya maida wayar shi gaban aljihun shi ya ce "Hajiya ki yi hak’uri, ban cika son d’aura ma kaina damuwa ba, likita ya min gargad’i akan haka saboda kiyaye lafiya ta kuma kin san ni ban cika son hayani ba". Wannan maganar da yaya Faruk ya fad’a ne yasa Hajiya yin shiru daga fad’an da yake min. Hajiya ce ta fara fita a falon, har ya fara tafiya kana ya juyo cikin d’aurewar fuska ya ce min "Ki shirya yau za mu koma Kaduna in kin gadama, in kuma za ki kira wannan Dr d’in ne ya zo ya d’auke ki ku tafi wani gurin, kina da damar yin haka, za’bin ya rage naki" yana gama fad’ar hakan ya bar d’akin. Samun Hajiya yayi akan zai koma Kaduna dani, Hajiya na jin haka ta ce itama da ita za a tafi a yi komai a gaban ta. Yaya Faruk bai mata musu ba ya ce ta shirya zuwa anjima za su tafi. Abinci Hajiya ta shirya ma yaya Faruk wanda na dafa. Tun da Hajiya ta zubo mishi abincin yaji bai marmarin shi dan yasan ni na dafa, ba yadda Hajiya ba tayi dashi ba akan yaci amma yak’i, sai ma ce mata da yayi bai jin dad’in bakin shi ne, ruwa kawai yasha da dambun naman da Hajiya ta kawo mai wanda ba ta rabo dashi yaci kad’an. Haka na zauna a d’aki ba tare da na fito ko falo ba, abincin da na dafa ma kasa fitowa nayi na ci, ko sallah a band’akin ciki nayi alwalata, na san in dai na kuskura na fito falo ba abin da zan fuskanta sai ‘bacin rai, fad’an Hajiya kawai ya ishe ni bare a je ga kallon da yaya Faruk yake min a yanzu, A yanzu ina ganin yaya Faruk ya dawo kamar yaya Faruk d’in da na sani a da, yanzu ga wani tsoron shi da ya sake shiga na a karo na biyu. San da za mu tafi yaya Faruk ne ya shigo d’akin ya ce in fito mu tafi. Ko da zan shiga motar tunani na fara yi akan gaba zan zauna ko a baya, had’a idon da muka yi da yaya Faruk ne ya watsa min wani banzan kallo yasa ba shiri na bud’e baya na shiga, Hajiya ma baya ta shiga yaya Faruk ya ja mu muka tafi. [7/8, 21:57] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* www.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa Writers Association *GAISUWAR TAKU CE* _Noorul-jannarh (Marubuciyar Detective Noor)_ _Maman Usy_ _Faeedaabdullahi1_ _Habiba Rabo_ _Hajiyar Allah_ _Surar da take karantar da cewa duka abubuwan duniya suna da dangantaka da junan su, dangantaka bayyananna ko ‘boyayya, kuma zumuntar sun a gudana gwargwadon dangantar su da juna ita ce Suratul Rum_ 69-70 Tun da muka d’auki hanya banyi magana ba, Hajiyan Wagini ce ke jan yaya Faruk da hira jefi-jefi, yanayin shi na nuna ba dad’in hirar yake ji ba, kawai dauriya yake yi, alamun shi na nuna kamar bai da lafiya. A haka muka ci gaba da tafiya, in ban da tunani ba abin da nake yi, Hajiya ita a dole fushi dani take yi shi yasa ba ta ja ni da hira ba. Muna shiga Kaduna yaya Faruk ya wuce da mu gidan Abbu, in ban da gaba na da yake fad’uwa, ba abin da yake yi, da ina da hali da na ce ma yaya Faruk kar ya kaini gidan mu, ya fara kaini gidan su duk da nasan ba lallai ba ne in samu tarba daga gurin su Momi da Anisa, nasan Dadi ba zai canza min a fuska ba, sai dai ya min fad’a akan abin da na aikata, nasan ko da ba a cikin hayyaci na nake ba, ban isa in nemi wannan alfarmar daga gurin yaya Faruk ba, yanayin fuskar shi kad’ai tsoro yake bani, ga wani kwarjini da min da ban tunanin zan iya mishi magana. Ina ganin yaya Faruk yayi horn, Malam Musa ne yazo ya bud’e mai gate d’in, nan na ji jiki na ya d’auki rawa, ga wani tsoro da fad’uwar gaba da had’u ya min dabaibayi a zuciya ta, duk wanda ya kalle ni a lokacin yasan ba na cikin natsuwa ta. Parking yayi a ma’ajiyar adana motoci kana ya bud’e ma Hajiyan Wagini mota ta fito daga ciki. Tafiya suka fara yi ba tare da sun damu da halin da nake ciki ba. Cikin rashin k’arfin jiki na bud’e motar na fito, a lokacin na ji wasu zafafan hawaye na zubo min, ni kaina a lokacin ba zan iya fad’ar dalilin hawayen nawa ba. Tsayawa na yi a jikin motar na kasa tafiya, jiki na ne ya min nauyi wanda ya haddasa min rashin k’arfin motsa k’afa ta. Yaya Faruk ne ya lura da rashin tawowa ta, hakan yasa ya juyo ya watsa min wani kallo mai isar da gargad’i. Ganin kallon da ya min yasa na ji tsoro ya k’ara shiga ta, ban san lokacin da na fara taka k’afa ta na fara tafiya ba, duk kuwa da yadda k’afa ta tayi min nauyi. Sallama su Hajiyan Wagini suka yi suka shiga cikin falo. Ummu ce ta amsa musu sallamar cikin walwala. Yaya Khalil ne ya gaishe su kana Ummu ta gaishe da Hajiyan Wagini. Yaya Faruk sun gaisa da Ummu cikin girmama wa. Ummu da yaya Khalil ne ta tare da tambayar shi ya k’arfin jikin shi. Amsa mata yayi da ya ji sauk’i. Sai a lokacin na tabbatar da zargi na akan rashin lafiyar yaya Faruk saboda yadda yanayin shi ya nuna hakan. Yaya Khalil ne cikin tsokana ya kalli Hajiyan wagini ya ce "Matar ke ce a garin mu, gwara da Allah ya kawo ki, dan nayi kewar ki". Cikin dariya Hajiya ta ce "Ja’iri ni matsa can, in da ka yi kewa ta ai da kaje in da nake". Dariya yayi yace "Hajiya ba lokaci ne shi yasa". "Ai na ga agogo ma a aiki" Hajiya ta fad’a cikin dariya. Suna cikin hirar ne Abbu ya fito daga shashen shi ya shigo main parlour. Murmushi ya saki lokacin da yaga Hajiya. Cikin farin ciki suka gaisa na irin tsakanin Uwa da d’anta. "Ina wuni Abbu" yaya Faruk ya furta cikin sanyin murya. "Lafiya lau Faruk, ya jikin naka". "Da sauk’i Abbu". "Allah ya k’ara sauk’i" Abbu ya fad’a cikin kulawa. "Amin Abbu". Hajiya ce ta ce "Wai Ibrahim me ya samu Sojan ne na ji kuna ta tambayar shi ya jiki, rashin lafiya yayi kenan sosai ban sani ba?". Abbu ya amsa mata da cewa "Yayi fama da rashin lafiya ne, amma yanzu da alama jikin da sauk’i". Juyowa tayi ta kalli yaya Faruk ta ce "Hala ciwon naka ba zai rasa nasaba da abin da Fatima ta maka ba ko, dan nasan har da dalilin ta kayi wannan rashin lafiyar, ai ba ta isa ta bijire ma wannan auren ba ta sa ka a wani hali, sai ta aure ka ko ba ta so, sai dai in mutuwa za tayi k’arewar rashin son ka kenan". "Hajiya, Allah ne ya d’aura min ciwo ba ruwan Fatima" yaya Faruk ya fad’a cikin sanyin murya. Cikin Hasala Hajiya ta ce "Ai dama haka za ka ce, tun da kai ba son laifin ta kake yi ba, ka riga ka makance a son ta". Sai a lokacin Hajiya ta kalli falon ta ga ba na ciki. Ni kuwa duk wannan abin da yake faruwa ina can jikin k’ofa a ra’be ba tare da na shigo ba, in ba ka lura da gurin ba, ba lallai kasan ina tsaye a gurin ba . Hajiya ce ta hango ni a tsaye a bakin kofa kana ta ce "Au Fatima can kika tsaya, ai dole ne ki kasa shigowa tun da ba ki da gaskiya" Hajiya ta fad’a. Duk wanda yake d’akin maida hankalin shi bakin k’ofa yayi jin Hajiya ta ambaci suna na, sai a lokacin suka lura da ni. Ummu tun da muka had’a ido da ita ta min wani kallo, hakan yasa na k’ara jin jiki na yayi sanyi. Falon ne ya d’auki shiru kamar ba kowa a ciki. Abbu ne ya kalli Hajiya, fuskar shi cike da ‘bacin rai ya ce "Hajiya ina kika samo wannan yarinyar". "Guri na ta tawo, ashe gudun hijira ta yi ta tawo guri tana ganin za ta samu tallafi na, sai da Soja yazo yake fad’a min ai ba a san da zuwan ta ba, Soja ya sanar dani halin da ake ciki, ni kuma na ce ta sha ruwan k’arya ta ce ba za ta auri Soja ba". Yaya Khalil ne ya mik’e ya tawo in da nake, saboda rashin kuzari a jiki na yasa na kasa motsawa. Hannu na ya rik’o ya shigo da ni cikin falon. Guri na samu na zauna a can gefe, ni kaina na tsargu da zama na a falon saboda laifin da nayi. Ummu wacce takaicin abin da na aikaita wanda dashi take kwana take tashi a ranta yasa ta taso ta fara duka na. Ba wanda ya hana Ummu duka na saboda haushin abin da na aikata, sai Hajiya ce ta wa Ummu magana akan ta daina duka na, addu’a ce magani ba duka ba. In ban da shashshek’ar kuka ba abin da nake yi, yau ni kaina nasan na daku a gurin Ummu. Abbu ko saboda ‘bacin ran dake damun shi kasa magana yayi, sai bi na yake yi da ido kawai. Kuka na naci gaba da yi ba mai lallashi na, nasan dama ba wanda zai kula ni tun da suna jin haushin abin da na yi, ni kaina nasan ban kyauta ba. Hajiya ce ta kau da shirun da cewa "Ibrahim ka kira min yayan ka ayi komai a gaban shi, dalilin zuwa na kenan, na ga alamar Fatima so take yi tayi fito na fito da kowa akan wannan maganar". Waya yayi ma Dadi ya sanar dashi zuwan Hajiyan Wagini da sak’on neman shi da take yi. Ba a d’au wani lokaci ba sai ga Dadi da Ummu da Anisa sun zo. Zama suka yi aka gaggaisa kafin Hajiya ta d’aura da cewa "Isuhu". Dadi cikin ladabi ya amsa "Na’am Hajiya". Hajiya ta ci gaba da cewa "Abin da yasa Na ce Ibrahim ya kira min kai shine akan maganar Soja da Fatima, naji k’udirin da Fatima take son aiwatarwa akan bijire ma auran, tun da ta na so ta nuna mana ita ‘yar zamani ce ta hanyar bijire maganar da aka riga aka gama ta, lokaci kawai ake jira, rana d’aya ta bad’a wa idon ta k’asa ta nuna bare yafi d’an uwanta, saboda haka na yanke hukunci Fatima ba ta isa ta auri wani ba in ba Soja ba". Dadi ne ya ce "Amma Hajiya….". Hajiya tayi saurin kar’ban maganar da cewa "Isuhu bana buk’atar jin wani bayani in dai ba goyon baya za ka bayar ba akan maganar auran". Falon ya d’auki shiru, kowa da irin tunanin da yake yi a ransa. Yaya Faruk ne ya nisa kana ya katse shirun da cewa "Hajiya ki yi hak’uri da hukuncin da na yanke kamar yadda na fad’a miki a baya, nasan kina son auran mu da Fatima, amma Allah bai k’addara ba, tun da Fatima ta nuna tana da wanda take so, ba ni take so ba, ina ganin Hajiya gwara a barta ta auri za’bin ranta dan guje ma wata matsalar da ka iya tasowa in aka yi auran, Hajiya bazan iya auran yarinya da ta mallaka ma wani zuciyar ta ba, ina neman afuwar ku, ni na hak’ura da auran Fatima" ya k’arasa maganar a hankali. Hajiya cikin fad’a ta ce "Wai kai Soja kana da hankali kuwa, akan ka faranta ma Fatima shine kai ka yarda ka sa kan ka a cikin damuwa, ita har ta isa ta ce ba ta son ka, to tayi k’arya dan bantan uban ta, ko kai ka hak’ura ni ban hak’ura ba, dole ne sai an yi wannan auran, sai dai in an yi auran ta d’au wuk’a ta yayyanka naman ka gunduwa-gunduwa saboda k’in ka da take yi". Abbu duk wannan maganganun da ake yi bai yi magana ba sai a yanzu ya kalli Hajiya ya ce "Hajiya ki kwantar da hankalin ki, ko da a ce kowa ya hak’ura da wannan auran ni sai na d’aura shi, Fatima ta sa min wani bak’in ciki a cikin zuciya ta da banyi zato ba, da nayi niyyar in zuba mata ido tayi duk abin da ta yanke ma kanta saboda yadda ta fifita saurayi akan mu iyayen ta, sai nayi wani tunanin akan in na k’yale ta hakan na nuna kamar ita ta haife mu kenan, saboda haka nima na ce Fatima ba ta da miji in ba Faruk ba in dai na isa da ita". Ba maganar da ta d’aga min hankali sama da ta Abbu, nasan yanzu ban da wata hanya da zan bi in samu in cimma muradina, hakan na nufin in rabu da Dr kenan. Hawaye ne ya fara zuba a idanu na, ni kaina na fara tausaya ma kaina halin da zan shiga matuk’ar ban samu Dr ba a matsayin miji. Yaya Faruk cikin sanyin jiki ya ce "Abbu na gode da kulawar ku gare ni, sai dai ina neman alfarma Abbu kayi hak’uri ku bar Fatima ta auri wanda take so, hakan zai fi wa kowa kwanciyar hankali akan a zo ayi abin da za ayi danasani daga baya". Ummu da Momi kuwa ba wanda ya samu k’arfin yin magana, kowa da abin da yake kissamawa a ranshi. Dadi cikin ladabi ya kalli Hajiya ya ce "Hajiya ba wai zan ja da maganar ki ba ne ko hukuncin da kika yanke, sai dai nima ina neman alfarmar ku akan ki duba wannan al’amarin, ku bari Fatima ta auri shi wannan Dr tun da har ta nuna shi take so, ni kaina zanyi farin ciki idan Fatima ta auri Faruk tunda duk d’aya ne a gurin mu, su duka ‘ya’yan mu ne, tun da auren yazo da tangard’a, hak’urin shi yafi". Haka Daddy yaci gaba da lallashin Hajiya da kawo mata hujjoji akan illar yin auran, da alama jikin Hajiya ya fara yin sanyin da maganganun da Dadi yake fad’a mata. D’aura zancen yayi da cewa "Hajiya ki yi hak’uri kar ki sa ma kan ki damuwa, mu yadda hakan Allah ya k’adar ta". Hajiya ce ta ce "Yanzu Isuhu kana nufin kenan dai Soja ya hak’ura da Fatiman, shi kenan tun da kana ganin hakan yafi, Allah shi ma ya kawo mishi ta gari wacce za taso shi" ta k’arasa maganar tare da fashewa da kuka. "Amin dai Hajiya, ki yi hak’uri Hajiya, mu rok’i Allah yasa hakan yasa shi yafi zama alkairi a gurin su" Dadi ya fad’a cikin sanyin murya. Da k’yar aka samu aka lallashi Hajiya tayi shiru. Momi wanda takaicin hukuncin abin da Dadi ya yanke yasa ta kalli Dadi ta ce "Yanzu Alhaji an ma yaron nan adalci kenan, kana ganin halin da ya shiga, shine yanzu za ka yanke wannan hukun…". Katse ta yayi da cewa "Rukaiyya ba na so ki sa bakin ki a cikin wannan maganar, hukuncin da kika ga na yanke, to ina fatan hakan ya sa yafi zama alkhairi da kuma samun maslaha ba tare da an shiga hakk’in wani ba a cikin su". Abbu ne ya kalli Dadi cikin taushin harshe ya ce "Kayi hak’uri yaya, ba wai zan yi jayayya da hukuncin da ka yanke ba ne, sai dai kamar yadda na fad’a a farko ban sauya ba, Fatima ba ta da wani miji sai Faruk". Cikin d’aure fuska Dadi yayi ya ce "Yanzu na gano hujjar ka Ibrahim, kana so ka nuna min ban da iko akan Fatima kenan tun da har zan zartar da hukunci akanta ka nuna k’in amincewar ka". Abbu cikin kwantar da murya ya ce "Kayi hak’uri yaya, ba haka nake nufi ba, Fatima ‘yar ka ce duniya da lahira, ka isa ka zartar da kowane hukunci akan ta, sai dai in aka yi haka ba a kyauta ma Faruk ba duk da shi ya ce ya hak’ura". Dadi k’ara tamke fuska yayi ya ce "Indai har na isa in yanke ma Fatima hukunci, na ba ta damar kawo shi wannan Dr da take so in d’aura musu aure". Abbu wanda bak’in ciki ya taru ya mishi dabaibayi a ranshi yasa ya kasa yi ma Dadi musu, shi kad’ai yasan halin da yake ciki a yanzu. Dadi ne ya ce "Ka bani wannan damar Ibrahim" ya k’arasa maganar da tambayar sa. Cikin takaici Abbu ya ce "Duk hukuncin da ka yanke daidai ne yaya". Dadi ne ya kalle ni ya ce "Fatimah!". "Na’am Dadi" na amsa a hankali. "D’ago ki kalle ni kin ji Fatimah". Kasa bin Umarnin shi nayi, wata kunyar Dadi ce ta kama ni, duk wannan abun da yake yi akai na dan ya samar min farin ciki ne, amma shine ni na bad’a ma ido na k’asa ta hanyar bijire ma auran d’anshi, ai da kunya in iya had’a ido dashi. Bai damu da d’agowa ta ba yaci gaba da cewa "Fatima, za mu baki za’bin ki na auran shi wannan Dr ba wai dan guduwar da kika yi yasa za muyi haka ba, za mu baki za’bin ki ne saboda ke ‘ya mace ce, bazan so a tauye miki hakk’in ki ba, saboda haka ki turo min shi Dr d’in mu yi magana dashi, sannan zan yi bincike akan shi". Wani irin dad’i ne mara fasaltuwa ya saukar min a lokacin jin cewa Dadi ya amince, nasan komai zai zo da sauk’i, sai dai a halin da nake ciki ba zai bani damar nuna farin ciki na a fili ba, sannan nasan duk wani bincike da zai yi akan Dr ba zai samu wani aibun shi ba, dan haka ban damu da binciken da zai yi akan shi ba. Ci gaba yayi da cewa ‘Fatima kin yi kuskure, ba ki kyauta ba akan abin da kika yi, ke mace ce, bai kamata akan d’a namiji ki bar gidan ku ki tafi wani gurin ba duk da gurin Hajiyar mu kika je, saboda ita mace abu kad’an ne yake zubar mata da mutunci a idanun mutane ba, kin ga hakan da kika yi kin sa iyayen ki da duk wani makusancin ki a cikin halin damuwa na rashin sanin in da kika tafi, da ni kika zo ki ka sama ki ka min bayani zan fahimce ki, bai kamata ki d’au zugar zuciyar ki ba ki aiwatar da k’udirin ki, yin hakan babban kuskure ne, kar ki sake makamancin haka kin ji Fatima". Kalamen da Dadi yayi amfani dasu wajen yi min nasiha ne yasa jiki na yayi sanyi, hak’ik’a Dadi mutum ne mai karamci, ba kowa ba ne zai iya nuna dattakun da yayi ba, k’aunar Dadi ce ta k’ara shiga raina na yadda ya d’auke ni kamar ‘yar shi, nima bazan gaji da d’aukar shi a matsayin mahaifi ba. Wasu zafafan hawaye ne suka fara ambaliya a idanu na. "Abbu na gode, insha Allah ba zan sake ba". "Yawwa Fatima haka ake so". Abbu da Ummu na kalla wanda yanayin su kad’ai ya nuna ba su ji dad’in hukuncin da Dadi ya yanke ba, ba yadda za suyi ne. A hankali na furta "Ummu da Abbu kuyi hak’uri akan abin da nayi, bazan sake ba". Cikin su ba wanda ya min magana, da alama har yau ba su sauka daga fushin da suke yi da ni ba. Sai a yanzu muka had’a ido da yaya Khalil, wani irin kallo yake watsa min mai nuna ‘bacin ran da yake ciki da takaici na da ya cika shi. Anisa ma kallo na kawai take yi na mamakin abin da nayi da kuma haushin abin da nayi. Abbu ne ya ce "Yaya na amince da wannan maganar saboda ka riga kasa baki, sai dai nima akwai wani sharad’i da zan gindaya ma Fatima, ina rok’on ka yaya da kar ka hana ni". Dadi ne kalle shi ya ce "Wani sharad’i ne wannan Ibrahim". Abbu ya juyo da kallon shi gare ni ya ce "Fatima kin ce dai Dr ki ke so ko?" ya k’arasa maganar yana jiran jin amsa ta. Shiru na yin a kasa bashi amsar tambayar da ya min. Tsawa ya daka min wacce ta razana ni ya ce "Ba dake nake yi ba kika min shiru". Cikin rawar murya na ce "Eh…Abbu". Takaici ne ya k’ara kama Abbun jin yadda ta amsa da ta amince amma sai bai nuna ba. Shiru yayi yana mamakin wai Fatima ce a gaban shi take son yin jayayya dashi saboda soyayya. "Good tun da kin ce Eh, ni ma na amince sai dai a bisa sharad’in duk wata matsala da za ta taso tsakanin ki da shi Dr d’in kar ki tunkaro nan gidan ko wajen ‘yan uwa na da sunan za ki kawo mana matsalar ki, idan kin amince shi kenan, kamar yadda aka sa lokacin bikin ba za a d’aga ba". Kowa a d’akin ni ya zuba ma ido dan jin amsar da zan bayar. Nima kaina wannan maganar ta min tsauri a guri na, yanzu za’bi ya rage gare ni. Abbu ne ya katse min tunani na da cewa "Ke na ke jira Fatima". "Na amince Abbu" na furta a hankali. Ido muka had’a da yaya Faruk, wani irin kallo ya watsa min da na fassara shi da kallon tsana yake min, idanun shi sun kad’a sun yi ja alamar ‘bacin rai, kallon ya ci gaba da jefo min dashi, hakan yasa na kasa jure kallon na sunkuyar da kaina. Hajiya ce ta fashe da kuka tace "Fatima ke wace irin shed’aniyar yarinya ce, yanzu mahaifin ki ya fad’a miki wannan maganar, amma saboda ke kin isa da kan ki, so ya riga ya rufe miki idanu, shine kika amince da sharad’in da ya fad’a miki, yanzu akan d’a namiji kika za’bi ki ‘ba ta wa mahaifin ki rai, Fatima ki gyara kuskuren ki tun kan ki zo ki fara nadama a lokacin da ba za tayi miki amfani ba". Abbu ne ya kalli Hajiyan Wagini ya ce "Hajiya ki k’yale ta tun da ta ga wannan hukuncin ya mata ai shi kenan". Yaya Faruk tashi yayi ya bar falon, a yadda yake jin zuciyar shi na k’issima mishi abubuwa marasa kyau akai na, yana ganin barin shi d’akin shi yafi, ko da yake cewa ya hak’ura da ni k’arfin hali kawai yake yi, ba wai dan zuciyar shi ta lafa da ciwon da take mai akan so na, sai dai ya k’udurta a ranshi ya hak’ura dani kamar yadda ya furta, zai ci gaba da rok’on Allah akan ya bashi juriyar hak’uri da ni. Zazza’bi ne yaji yana niyar kama shi, hakan yasa ya shiga motar shi ya tafi gida. Dadi ne ya kalle ni ya ce "Fatima sai ki fad’a ma Dr ina jiran shi". "To Dadi zan fad’a mai". Abbu ne ya kalle ni cike da ‘bacin rai ya ce "Zaman me ki ke yi tun da an miki abin da kike so, ina ganin sai ki tashi ki bamu guri ko". Jiki a sanyaye na tashi na tafi d’aki na. Yaya Khalil ma tashi yayi ya bar falon ya tafi shashin shi. Anisa ma bin shi tayi a baya ta nufi d’aki na. Su Dadi ne suka ci gaba da tattaunawa akan maganar, Dadi ne yaci gaba da ba kowa hak’uri akan hukuncin da ya yanke da kuma dalilin shi da yasa shi yin hakan, ba laifi su Abbu sun samu sauk’i akan halin da suke ciki. San da na shiga d’aki na nemi guri na zauna, na rasa abin da yake min dad’i a rayuwa ta, yau gashi an amince min in auri Dr, sai dai hanyar da aka bi gurin amince min ne yazo da akasi, hakan ya hana ni jin farin ciki a raina. Duk yadda nake so muyi aure da Dr, zan so da amincewar iyaye na, sai gashi da alama Ummu da Abbu ba su nuna farin cikin su da hakan ba, a yadda na lura ma a family d’in ba wanda yake bani goyon baya akan aure na da Dr. Zan so a ce na samu wanda ya fahimce ni akan son da nake ma Dr ba yana nufin ina k’in yaya Faruk ba ne, ina mishi so ne irin na ‘yan uwantaka, amma nasan hakan ba zai samu ba. Hawayen tausayin kaina ne ya zubo min a ido na masu zafi, yanzu nasan sai nayi hak’uri da abin da zan dinga gani a family akan za’ben Dr da nayi. Tuno da kallon da yaya Faruk yake min na ji na k’ara tausaya ma kaina, ban ga laifin shi ba dan ya nuna ‘bacin ranshi akan abin da na mai, da zai bani dama da na bashi hak’uri akan ya yafe min, dan nasan yana min kallo a matsayin wacce ta ci amanar shi, sai dai kash! Na san ba zan samu wannan damar a gurin shi ba. Hawaye ne ya ci gaba da zubowa a ido na, saboda halin da nake ciki ban damu da in goge su ba. Anisa ce ta yi sallama ta shigo d’akin, in b aka lura da motsin bakin ta ba baza kace magana tayi ba. Amsa mata sallamar nayi na sunkuyar da kaina, dan na san ba lallai ba ne ta min magana saboda haushi na da take ji. Kallo na take yi kamar wacce take son gano wani abu. Ido muka had’a ta watsa min harara, ban damu da hararar da ta min ba dan nasan tayi hakan ne cikin ‘bacin rai. "Fatima kenan, ina ganin zubar da hawaye ba naki ba ne a yanzu, ina ganin da tanadar hawayen kika yi ki ka ajiye dan akwai lokacin da zaki zubar da hawaye a lokacin da hakan ba zai miki amfani ba, yau kamata ya yi ya zama ranar farin ciki a gare ki tun da kin samu cikar burin ki, Fatima ba na zo in miki nasiha ba ne dan nasan ba d’auka za ki yi ba tun da kin yi nisa ba kya jin kira, Fatima sai kin yi nadamar abin da kika aikata duk daren dad’e wa, ki rubuta ki ajiye wannan maganar da na fad’a miki" Tun da ta fad’a min wannan zaffafan maganganun ba ta sake ce min komai ba, sai ma danna wayar ta da taci gaba da yi. Maganganun da Anisa ta fad’a min sun min zafi a cikin zuciya ta, sai dai ni kaina nayi mamaki da na kasa maida mata martanin maganganun da ta fad’a min, na alak’anta hakan da halin da nake ciki. Shiru d’akin ya d’auka kamar ba kowa a cikin, kowa da irin kalar tunanin da yake yi. K’arshe ma Anisa tashi tayi ta bar d’akin. Kiran Dr ne ya shigo cikin waya ta. Cikin sanyi jiki na d’auki wayar, mun d’au tsawon lokaci muna waya dashi kafin na sanar dashi halin da ake ciki da kiran da Dadi yake mai. Bayan gama tattaunawar su Dadi ne suka yi sallama suka tafi. A can ‘bangaren Dr kuwa tun san da na sanar dashi amincewar su Abbu yaji farin ciki ya kama shi, bai yi zaton amincewar su Abbu cikin sauk’i haka ba, lallai yarda da irin son da nake mai tun da har na iya jajircewa aka fasa aure na yaya Faruk. Gida ya wuce dan ya sanar da Dadi da Momi halin da ake ciki. San da ya shiga falon ne ya tarar da su Hanan da Farida suna kallo. Sannu da zuwa suka mishi kana ya tambaye su Momi. Sun sanar da shi tana d’aki. San da ya shiga d’akin ya same ta hakimce akan kujera. Guri ya samu ya zauna kana ya mata sannu da gida. Kallon shi tayi kana ta ce "Yau ba patients ne a asibiti na ga ka dawo gida da wuri". Murmushi yayi ya ce "lafiya lau Momi, dama mun yi waya da Zarah ne take sanar dani an ce in turo, kuma parent d’in ta sun ce ba za su d’aga bikin ba, shine nace bari in sanar daku". Momi ce ta ce "Au daman ba ka hak’ura da yarinyar nan, ina ce ka ce da d’an uwan ta za a had’a ta auran". "Eh Momi, Zaran ce ta nuna ni take so, shine shi d’an uwanta yace ya hak’ura". Ta’be baki Momi tayi kana ta ce ‘Ni tun farko nafi maka sha’awar Meemat yarinyar Hajiya Suwaiba amma ka na ce sai wannan yarinyar". Cikin shagwa’ba ya ce "Kai Momi, wannan Meemat d’in da ba ta da tarbiyya za ki ce in aura, ni nafi son Zarah ta". Momi ce taci gaba da cewa "Yanzu suna nufin a before two weeks suke nufin mu gama shirye-shiryen mu na biki, bayan kai kan ka kasan yadda muke so muyi organizing d’in bikin ka idan yazo, ina ganin sai an k’ara mana time dan ina bikin ka ya zama special…". Da sauri ya katse ta da cewa "Plss Momi don’t say that, da kyar fa aka shawo kan su suka yarda ita Zaran ta aure ni, yanzu idan aka nemi favour d’in su akan su k’ara mana time zai iya jawowa in rasa ta, tun da dai an fi k’arfin komai ina ganin a bi su a yadda suke so". ‘‘Ai shi kenan tun da ka na ce sai Zaran, in Dadin ku ya dawo zan sanar dashi halin da ake ciki". "Thanks Momi, bari in je in d’an huta" yana gama fad’ar haka ya fita daga d’akin. *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* www.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa Writers Association *SAK'ON GAISUWA* _Ba zan gaji da Mik’a godiya ta da fatan alkhairi ga masoya wannan Littafin, ban da abin ce muku na yadda ku ke bibiyar wannan labarin, fatana darasin da ke ciki Allah yasa ayi amfani dashi_ _'Yar Mutan Paki na marhabin da duk wanda yake bibiyar littattafai na_ *QUESTION OF THE DAY* _Ya sunan matar da ta d’auki takobi ta kare Manzon Allah (S.A.W) a lokacin da mazaje suka guje daga gare shi, akwai san da annabi ya ce mata "Tambaye ni abin da kike so? sai ta ce masa "Ina rok’on ka kasancewa mak’ociyar ka a Aljanna da son ka a duniya da son ka a lahira_ 71-72 *WANENE DR ABUBUAKAR SADIK MUHAMMAD?* Dr Sadik d’a ne ga Arc Alhaji Muhammad, haifaffen d’an garin Kaduna ne, mahaifin su shahararren d’an gwal ne, ya karanci ‘bangaren zane-zane, mahaifiyar su Haj Hauwa lecturer ce a Open University, su hud’u ne a gurin iyayen su. Dr Sadik suna zaune ne a Unguwar Dosa. Dr Sadik shi ne babba a gurin iyayen su, daga shi sai Hauwa (Hanan) wacce taci sunan mahaifiyar su, tana karanta Socio-logy, tana 300 level a Kasu, daga ita sai Farida da take 100 level a Open University, daga ita sai autan su Ahmad, yana primary 4 ne a school d’in su. Dr Sadik yayi karatun shi a ABU Zaria in da ya karanci medicine, yanzu haka yana aiki ne a cikin asibitin Kaduna Polythecnic, sannan yana aiki a wasu asibitocin idan buk’atar hakan ta taso. Gidan su Sadik wata irin rayuwa ake yi ta ‘yan boko da kuma ‘yanci, babu mai matsa ma wani akan abin da yake so, akwai freedom ta ‘bangaren iyayen, hakan yasa su ma yaren su ka taso da wannan d’abi’ar. A cikin su Farida ce ba ta cika d’aukan rayuwa da zafi ba, ba ta d’aura ma kanta social life ba, shi yasa su ke samun sa’bani da Hanan akan banbancin ra’ayin su. Duk da yadda mahiafin su ke basu ‘yancin yin duk abin da suke so, hakan bai hana wani lokacin in sun yi ba daidai ba ya musu fad’a. Dr mutum ne da bai cika son hayaniya ba sannan shi mai ji da kanshi ne, yana tafiyar da rayuwar shi akan turawa. Wannan shine tak’aitaccen tarihin Dr Sadik.. San da yaya Faruk ya koma gida, d’akin shi ya wuce ya kwanta, jin zuciyar shi yake yi tana mishi zafi, ga k’irjin shi da yake ji ya mishi nauyi, ya san hakan ba zai rasa nasaba da ciwon rabuwa da ni ba. Yana k’ok’arin yaga ya cire ni a ranshi, a yadda yake jin son ta a ranshi, yasan hakan ba mai sauk’i ba ne a gurin shi cire ni a lokaci d’aya a cikin zuciyar shi, zai ci gaba da add’u’a akan Allah yasa komai yazo mishi cikin sauk’i. Haka ya ci gaba da zama a d’akin, ciwon k’irjin na k’ara matsa mai, sai da ya d’auki lokaci kafin yaji k’irjin ya daina mishi ciwo. Tashi yayi ya watsa ruwa ya canza kayan jikin shi kana ya fito main parlour ya zauna ya kunna Tv dan ya rage ma kan shi tunani. A haka su Momi su ka dawo suka same shi, sun ji dad’in yadda su ka ganshi yana kallo, duk da idan kayi duba da yanayin shi kasan yana cikin damuwa, dauriya kawai yake yi. Zama suka yi suka dinga kwantar mishi da hankalali da mishi nasiha akan yarda da k’addara a duk yadda ta zo maka. Yaji dad’in yadda su Momi suke nuna mishi kulawa, ba sa son ganin cikin damuwa, shi yasa shima yake k’ok’arin ganin ya kwantar da hankalin shi dan kar yasa su cikin damuwa duk da kuwa yanda yake jin rad’ad’in abin da na mishi a zuciyar shi. Murmushi yayi ya ce "Zan yi amfani da shawarar ku Dadi da Momi, na gode da kulawar ku gare ni, addu’ar ku na ke buk’ata a ko wane lokaci, nasan ita ce nasara ta a dukkan lamura na". Tausayin yaya Faruk ne ya kama shi, sun san dauriya yake yi a matsayin shi na jarumtaccen namiji, amma abin na mishi ciwo a zuciyar shi. "Insha Allahu za mu ci gaba da maka addu’a Faruk, kullum kana cikin addu’ar mu, Allah biya maka buk’atun ka na alkhairi, ka dinga rage tunanin da kake yi ka ji Faruk, saboda gudun kamuwa da wata cutar, komai da ka ke gani muk’addari ne daga Allah" Dadi ya fad’a. "Amin Abbu na gode, zan kiyaye insha Allah". Momi ta ji dad’in yadda yaya Faruk yadda ya ke k’ok’arin ‘boye damuwar shi, hakan yasa ita ma taji damuwar da take ciki ta ragu. "Allah ya za’ba maka abin da yafi alkhairi Faruk" Momi ta fad’a. "Amin Momi" ya fad’a a hankali. Anisa kuwa in ban da murmushi ba abin da take yi ganin yaya Faruk bai sa damuwa akan abin da na mishi ba. Yaya Faruk ne ya kalli Anisa ya ce "Anisa ya aka yi ne, ko akwai abin da yake damun ki?" yaya Faruk ya tambaye ta. Murmushi ta mayar masa kana ta ce "Ba komai yaya Faruk". Haka suka zauna suka ci gaba da hira, wannan hirar da suka zauna suka yi tasa sun samu sauk’i na damuwar da suke ciki. Tun bayan tafiyar su Dadi na kasa fito wa falo, nasan ko na fito bazan samu tarba ba ta kowane ‘bangare, yaya Khalil ma nasan tun kan matsala ta da yaya Faruk muka rage shiri dashi, daman shi kad’ai wanda a ko wane lokaci nake tunanin samun sauk’i. Sallah kawai nake iya tashi in shiga band’aki in d’auro alwala in zo in yi sallah, ni kaina zaman ya ishe ni, ga yunwa da take addaba ta. Haka na wuni a d’aki ba tare da kowa ya lek’o ni ba, hakan ya k’ara sa ni cikin damuwa. Ganin zan cutu yasa nayi k’arfin halin fito wad an samar wa kaina abin da zan ci. Ina fito wa na tarar da Hajiyan Wagini da Momi da Khalil suna hira, fitowa ta da suka ga nayi ne yasa su ka bi ni da ido. Kitchen na wuce na d’ebo abinici na dawo d’aki na zauna na fara cin abinci na. Bayan na gama ci abinci ne na ci gaba da zama na a d’aki, duk kuwa da yadda na takura da zaman d’akin, ina ganin hakan shi yafi min akan fito wa ta. Ranar haka na zauna ni kad’ai a d’aki ba tare da kowa ya lek’o ni ya ga a wani hali nake ciki ba. Hajiyan Wagini ma nasan ba shigo wa za tayi ba tun da tana fushi dani. Yaya Aminu ma yazo saboda Abbu ya kira shi ya fad’a mishi na dawo, jin gurin Hajiyan Wagini na je yasa ya ji ya rage matakin da yayi niyar d’auka a kaina, yanda ya tashi a harzuk’e ya nufo d’aki na Abbu yasan har yau ranshi a ‘bace yake da abin da nayi. Abbu ne ya kira shi ya dawo ya zauna ya fad’a mishi halin da ake ciki, da kuma sharad’in da ya gindaya min na amince. Abbu ne ya ce ya k’yale ni tun da har na amince, ba buk’atar k’ara d’aukar mataki a kaina tun da na amince da sharad’in shi. Washegari ina jin su Ummu nayin Breakfast, amma na kasa fitowa, ba kuma wanda ya aiko akan in fito in yi breakfast. Nasan ‘bacin ran da nasa su ne yasa suka yi watsi da al’amari na, hakan kuwa ba k’aramin sa ni a damuwa zai yi ba. Ummu kuwa rashin fitowa ta ba k’aramin damun ta yayi ba, tana tsoron kar wani ciwo yazo ya kama ni, sai dai idan ta tuno abin da nayi sai taji takaici na ya kama ta. Tashi nayi na fito falon dan in gaishe dasu. Ko da na fito ba wanda ya d’ago ya kalle ni, a hankali na k’arasa inda suke. "Ina kwana Hajiyan Wagini". Hajiya wacce haushin abin da nayi bai sake ta ba ta fara fad’a da cewa "Ina ruwan ki da kwana na har da za ki gaishe ni, ni yanzu na yafe gaisuwar ki, na bar ma waccan fitsararren Dr da yake sa ki rashin jin magana duk ki dinga mishi". Wasu hawaye ne suka fara zubo min a idanuna, yadda Hajiyan Wagini ke min a yanzu kamar waccce ba ta san inda na fito ba, tun san da yaya Faruk ya je can Wagini ya fad’a mata abin da nayi take min fad’a, kamar ba ita ce muke wasa da dariya ba. Sauri na yi na goge hawayen da suke zubo min, a lokacin muka had’a ido da yaya Khalil yayi saurin kau da idon shi. A hankali na juya ga su Abbu da Ummu na ce "Barkan ku da Safiya Abbu da Ummu". A tak’aice suka amsa min da "Lafiya". Tun daga wannan amsawar da suka yi ba wanda ya sake kula ni. Jiki na ba k’wari na kalli yaya Khalil na ce "Yaya Khalil ina kwana". Duk yadda yake jin haushin abin da nayi ba zai iya jurar gani na a cikin wani yanayi ba, gashi a wajen su Ummu da Abbu ma duk fushi suke yi dani. Sakar fuskar shi yayi kad’an ya amsa min da cewa "Lafiya lau Fatima, ya kike?". Ganin yadda yaya Khalil ya amsa min yasa na d’an ji dad’i a raina. "lafiya lau yaya Khalil". Shima tun daga amsawar da yayi bai sake ce min komai ba, gajiya da zaman da nayi ne a falo ba tare da kowa ya kula ni ba yasa na tashi na koma d’aki. Hirar su na dinga jiyowa jefi-jefi. Haka suka gama breakfast kowa ya kama harkar gaban shi, falon shiru alamar ba kowa a ciki. Tashi na yi na d’akko kayan breakfast nayi kalaci a d’aki na, yayin da na ci gaba da zaman kad’aici. Ni kaina tunanin halin da na sa su Ummu na ‘bacin rai ya hana ni samun sukuni, dan haka zuciyata ta yi ta nusar dani akan in je in k’ara basu hak’uri ko na samu sassauci. Da wannan shawarar ta zuciya ta na samu k’arfin gwiwar tunkarar Ummu. Zuwa na yi na same ta a zaune a d’aki, da alama ita ma tayi zurfi a cikin tunanin da take yi ganin yadda tayi shiru. Tun da nayi sallama na nemi guri na zauna. Kallo na tayi ta amsa min sallamar ciki-ciki. Shiru ne ya ratsa falon kana na kalli Ummu da fuska da ta koma kalar tausayi na ce "Ummu dan Allah ki yi hak’uri ke da Abbu abin da na muku, nasan ban kyauta ba, bazan sake kamanta tafiya wani gurin ba tare da izinin ku ba". Duk wannan maganar da nayi Ummu bi na take yi da kallo, har yau takaici na ne ke cikin zuciyar ta. Shirun da na ji Ummu tayi ne ya k’ara sanyayar min da jiki. Can ta kau da shirun da cewa "Fatima ai ban zaci zaki iya zuwa k’i k’ara ba mu hak’uri ba a yadda yanzu ki ka canza halayen ki, kina yanke hukunci ne akan duk abin da zuciyar ki ta yanke miki ba tare da kin yi duban da hakan zai haifar miki ba, amma kar ki manta hausawa na cewa Son zuciya ‘bacin zuciya, duk wanda zai bari zuciyar shi ta dinga jagorantar shi yana tare da danasani, Fatima ban ta’ba tunanin za ki iya aikata abin da kika aikata ba na guduwa, wai yau ke Fatima akan d’a namiji kika za’bi tafiya wani guri dan guje ma auran da za a miki da d’an uwanki da bai wuce sauran kwanaki ba, me yasa tun farko ba ki nunar mishi da yayi hak’uri bashi kike so ba, sai da kika bari har ki ka had’u da wannan Dr sannan za ki fito da wata magana wai ba kya son Faruk, Fatima yadda na ke jin Faruk a raina kamar ni na haife shi haka nake jin shi saboda yadda nima ya d’auke ni kamar Mahaifiyar shi, yake k’okarin yi min biyayya da kyautata min, ta ya ba zan ji ciwon abin da kika yi mai ba, shi yasa ban ga laifin Hajiya Rukaiyya ba akan yadda ta d’auki zafi akan wannan maganar, ko ni ce aka yi ma d’a na haka dole zan ji zafi, tun da kin riga kin amince da sharad’in da Abbun ki ya gindaya miki shi kenan namu ido, sai dai ina so in tunasar dake wani abu da ba ki gama sani ba akan d’a namiji, duk yadda kika za’be shi dan ganin kin mik’a miki yardar shi, wataran zai iya baki kunya, ba kowane namiji ba ne yake sanin ka mishi halacci, sabida haka ni ba abin da kika min, wanda kika ma shine Faruk, tun da yace kuma ya hak’ura dake ina ganin magana ta riga ta k’are". Tana gama fad’ar haka ta tashi ta barni a zaune. Jiki a sanyaye na tashi na koma d’aki na tun da ban da wanda zan yi hira. Da yamma yaya Aminu ya kawo su Anty Jidda su gaishe da Hajiyan Wagini, ina ji tana tambayar ina nake aka ce mata ina d’aki. Tashi tayi ta tawo d’akin ta same ni kad’ai, kallo na kawai take yi kafin ta nemi guri ta zauna. Gaishe ta nayi ta amsa min cikin fara’a. Hira ta fara ja na dashi jefi-jefi kafin ta d’akko min zancen abin da nayi na tafiya wai gari ba tare da sanin su Abbu ba. Nasiha ta min sosai akan abin da na aikata bai kamata ba, tare da nuna min illar hakan da nayi. Ni kaina nasan ba kyauta ba, na kuma yi danasani akan haka. Ta d’an dad’e a d’aki na kafin ta fito falo suka ci gaba da hira da su Hajiyan Wagini. Abbu ma naje na same shi na k’ara bashi hak’uri akan abin da nayi, ya nuna min ‘bacin ranshi akan abin da na aikata, ya kuma nunar min da cewa shi yanzu ba ya fushi dani, tun da har na amince da sharad’in da ya gindaya min shi kenan. Jin hakan da nayi yasa na samu kwanciyar hankali tun da shi da Ummu sun ce ba sa fushi dani, ni a gani na wannan sharad’in da Abbu ya gindaya min ba wata matsala ba ce, ina ganin ba za mu samu wata matsala ba da har zai sa in zo gida in fad’a yadda muke son junan mu, ta ‘bangaren ‘yan uwan Dr ina ganin mai zai had’a ni dasu tun da ina gida na suna gidan su. Da wannan tunanin nake samun k’arfin gwiwa. Dr Sadik ya kira ni ya sanar da ni zai je gidan su Dadi akan neman da yake mai kasancewar ya ta’ba sauke ni a gidan, hakan ya min dad’i dan nasan komai ya kusan zuwa k’arshe. Sadik ya je ya samu Dadi inda ya mishi tarba mai kyau ba tare da ya nuna mishi wani abu a fuskar shi ba, ya mishi tambayoyi game da rayuwar shi, Sadik ya amsa mishi duk tambayoyin da Dadi ya mishi, ba laifi Dadi ya gamsu da amsoshin da ya bashi, dama ya riga ya sa an mishi bincike akan Sadik, ba a samu wani aibu ba akan labarin da aka mishi bincike, sai dai an sanar dashi gidan su irin rayuwar boko suke yin a ‘yanci, yana ganin wannan ba wata babbar matsala ba ce. Da haka su kayi sallama dashi akan ya turo iyayen shi a yi magana tun da bikin bai wuce sati biyu ba. Dr Sadik ya amsa mishi da in ya koma zai fad’a ma iyayen shi halin da ake ciki. Nan suka yi sallama ya tafi tare da jin dad’in yadda Dadi ya sakar mishi fuska. San da ya koma gida ya tarar da su Dadi a falo ana hira, guri ya nema ya zauna. Dadi ne ya kalle shi cikin kulawa yace "Sadik ya aka yi ne na ga kamar your mood shows that you a happy". Tsadadden murmushi yayi yace "Daga gurin parent d’in Zarah nake, sun ce in fad’a muku kuzo a gama maganar bikin mu da ita, tun da kwanakin da suke so a d’aura auren bai wuce two weeks ba". Dadi ne yayi murmushi ya ce "That is a good news, Momin ku ta fad’a min halin da ake ciki, insha Allah zan ma Uncle d’in ku na Abuja magana da Alhaji Hamza sai ka mana jagora gidan su ita yarinyar". Momi ce ta kalli Dadi ta ce "Amma in aka yi haka Alhaji ba a kyauta ba, yanzu kai Alhaji sai ka iya sanar da Alhaji Hamza yazo aje neman auren Sadik dashi alhalin kana ganin yadda Meema take son shi amma shi Sadik yak’i ba ta fuskar da za su yi soyayya, Hajiya Hadiza kullum cikin k’orafi take min akan Meema na son Sadik amma shi sai wahalar da ita yake yi, In ban da abin Sadik miye aibun ita Meema d’in da ba zai so ta ba, tana da kyan da duk namiji ya ganta zai so ta, gashi ta gama Degree d’in ta akan Economics, nasan yanzu in taji maganar auren da zai yi sai ta shiga cikin damuwa". Dr Sadik ne ya kalli Momin shi ya ce "Momi na fad’a miki am not interesting with that girl, yarinyar da ba ta da tarbiyya da sagarta ya mata yawa, she is not my type" yana gama fad’ar haka ya tamke fuska. Hanan ce ta kalli Dr Sadik cikin shagwa’ba ta ce "Haba yaya Sadik, miye laifin Meema da ka ke cewa she is not your type, Meema na so ka amma ban san me yasa yaya Sadik ba ka kula ta, ina ganin dan ba ka ga manyan mutanen da ke son ta ba, ko Momi…?" ta k’arashe maganar tana tambayar Momin su. Cikin tsawa Dr Sadik ya katse da cewa "Will you stop that rubbish explanation or else you will face the consequences". Tsawar da Dr Sadik ya ma Hanan ne yasa idon ta yayi narai-narai kamar me shirin yin kuka. Farida duk wannan maganganun da ake yi ba ta ce komai ba, ita ma a nata ra’ayin ba ta son Dr Sadik ya auri Meema saboda wayewar ta tayi yawa. Dadi cikin lallashi ya kalli Dr ya ce "Cool down Son, tun da ba ka son ta ina ganin shi kenan, ba za ma d’a na auren dole ba, ita Meeman ta hak’ura tun da Sadik d’in ba ya son ta". Dr Sadik ne ya tashi ya bar falon ya nufi side d’in shi. Dadi ya ci gaba da Momi fad’an akan ta daina matsa ma Dr akan sai ya so Meema, tun da yace yana da wacce yake so a k'yale shi. Dr Sadik ya kira ni ya fad’a min yadda suka yi da Dadin Faruk da yadda ya mishi tarba mai kyau, ni kaina na ji dad’in hakan dan nasan Dadi bai da matsala, ya sanar dani Dadin su na nan zuwa gurin Dadin Faruk akan maganar bikin. Yau ina zaune a falo ina kallon wani Nigerian film da aka sa a Afican Movie channel mai suna "My Affairs with Mother and Daughter" rabin hankali na yana ga kallon, rabin hankali na kuma yana ga tunanin halin da na tsinci kaina a yanzu. Tunanin yadda yaya Khalil ba ya shiga harka ta shi ya fi tsaya min a rai, Anisa daman nasan ba kula ni za tayi ba ganin yadda ta d’auki fushi, rabon da muyi waya da ita tun kan in tafi Wagini. Shawarar da na yanke shine in je in tunkari yaya Khalil in bashi hak’uri duk kuwa da fad’an da zai min, hakan zai sa in fi samun kwanciyar hankali. Tashi nayi na lek’a ta slice window na hango motar shi a parking space shaidar yana gida kenan. Side d’in shin a nufa nayi sallama. Amsa min yayi ya danna laptop d’in dake kan centre table. Tun da ya amsa min sallamar ya ci gaba da danna laptop d’in da yake yi ba tare da ya k’ara kallo na ba. A hankali na k’arasa inda yake na zauna. Shiru d’akin ya d’auka kamar ba kowa a ciki. Kau da shirun nayi da kiran sunan shi a hankali "Yaya Khalil gurin ka na zo". Har yanzu bai daina abin da yake yi ba na danna laptop d’in da yake yi ya ce "Ina jin ki". "yaya Khalil kayi hak’uri da abin da na aikata, nasan ban kyauta muku ba, nima kaina nayi danasanin abin da na aikata, plss yaya ka tausaya min ka yafe min" Na k’arasa maganar murya ta na rawa. Sai a lokacin ya d’ago ya kalle ni, shi kanshi yana tausaya min yadda yanzu kowa ba ya shiga harka ta da yadda nake takura kaina a d’aki ni kad’ai, sai dai in ya tuna tafiyar da nayi da kuma amincewar sharad’in Abbu da nayi a gaban mutane sai yaji ranshi ya k’ara ‘baci. "Fatima ni ba ki min laifi ba, in ma kin min bai wuce yadda kika tafi wani gari ba tare da Sanin su Abbu ba, ki ka sa mutane a cikin damuwa da tunani, Fatima ko ba a fad’a miki ba, ke kan ki kinsan ba ki kyauta ba, bayan da kika dawo kiyi k’ok’arin ki faranta ma su Abbu da cewa kin hak’ura za ki auri yaya Faruk, sai ba ki yi haka ba, sai ma amincewa da kika yi akan sharad’in da ya gindaya miki, Fatima akan ki an fara samun rashin fahimta a family, hakan kuma ya faru ne duk a dalilin abin da kika yi, yanzu Momi tana jin haushin abin da kika yi ma Yaya Faruk, gashi yanzu ma Anisa ba ta saurara ta duk a dalilin tana jin haushin abin da kika yi ma d’an uwan ta, kuma ni ban ga laifin ta, ki kwatanta misali akan ni aka yi ma haka, nasan kema irin matakin da za ki d’auka kenan, tun da ke ba kya jin nasiha da fad’a shi kenan Fatima zan zuba miki ido in ga iya gudun ruwan ki, tun da an amince miki da wanda kike so wanda duk akan shi ne kike aikata hakan ai ina ganin ba ki da sauran wata matsala". "Why me?" Na tambayi kaina. "Me yasa mutane ba za su fahimce ni ba? me yasa suke ganin laifi na dan zuciyata ta za’bi Dr a matsayin abokin rayuwar ta?". Wannan su ne tambayoyin da nayi ma kaina. Idanuna ne suka cika da hawaye na ce "Yaya Khalil kayi hak’uri akan laifin da Anisa ta d’aura a kan ka, nasan tayi haka ne akan jin haushin abin da nayi ma yaya Faruk, banyi haka dan in ‘bata ma kowa rai ba, sai dan ba ma zuciya ra abin da take so, in ma za ta ga laifi, ni ya dace ta ga laifi na". Murmushin yak’e yayi ya ce "Kar ki damu Fatima, Anisa ba irin ki ba ce, nasan duk yadda ta had’a dani wajen yin hukunci akan abin da kika yi ma yaya Faruk daga baya za ta fahimci abin da tayi bai dace ba, ita ba zuciyar ta ba ce take jagorar ta wajen aikata abu, ajizanci ne irin na d’an adam". Maganar yaya Khalil ta yi min zafi, nasan magana ce ya fad’a min a hankalce mai isar da sak’o. D’akin ne ya sake d’aukar shiru yayin da yaya Khalil ya ci gaba aikin da yake yi a laptop. Jiki na ba k’wari na tashi na bar d’akin, yaya Khalil ko bi na yayi da kallo na takaicin rashin gaskiya da na k’i yi da kuma tausayi na. Iyayen Dr Sadik sun je gurin Dadi akan maganar auren mu da Dr. Kasancewar Dadi ya amshi numbar Dadin su Sadik lokacin da ya yi kiran shi, shima Dr ya amshi numbar Dadin, hakan ne yasa Dadin su Sadik ya fad’a ma Dadi ranar da za su zo ayi maganar bikin. Ran da za su ne Dadi ya kira Abbu ya sanar dashi halin da ake ciki, hakan yasa Abbu ya shirya yaje dan yasan rashin zuwan shi zai sa Dadi ya mishi fad’a. Haka Dadi ya kira wani kawun su na Wagini suka mishi bayani, ba da ‘bata lokaci ba shima ya tawo Kaduna. Iyayen Dr Sadik sun je shi da Kawun Sadik d’in da Abokin shi Alhaji Hamza mahaifin Meema. A ‘bangare na kuwa Dadi da Abbu da Kawu Lawan ne suka tarbi iyayen su Dadi. Sun gaisa cikin mutunci da girmama juna kana su Dadin su Sadik suka nemar ma Dr Sadik aure na. An yi duk abin da ya dace na shari’a da Al’ada kana aka tsayar da bikin a ranar da aka sa na auren mu da yaya Faruk wanda yayi daidai da saura kwana 10 kenan. Sun ba da kud’in gaisuwar iyaye da kud’in sa rana, kana suka ba da Sadaki dubu d’ari. Haka suka rabu cikin mutunci. Abbu tun da ya dawo gida ya sanar da Ummu da Hajiyan Wagini da yaya Khali halin da ake ciki, San da yaya Aminu yazo ma Ummu ta sanar dashi tsayar da biki na da aka yi Dr. Hajiyan Wagini ko san da Abbu ya fad’a mata maganar biki na da aka tsayar da Dr sai da tayi kuka akan rashin auran yaya Faruk da na k’i, Ko su Abbu da Ummu sun fi son aure na da yaya Faruk, ganin hakan Allah ya k’adarta shi yasa suka hak’ura, sun barshi akan watak’ila Allah yayi ni ba matar yaya Faruk ba ce shi yasa hakan ya kasance. Abbu ya shawarci Hajiyan Wagini da Ummu da su maida ma yaya Faruk akwatunan shi, sun yi na’am da wannan shawarar tashi. Hakan yasa Abbu ya umarci yaya Khalil da ya kaisu Ummu gidan su Dadi a maida akwatunan. San da suka je gidan ba su tarar da Dadi ba, Momi suka sama. Yaya Khalil ne ya shigo da akwatunan. Bayan an gaisa ne Hajiya ta kalli Momi ta ce "Rukaiyya, ina so kuyi ma Ibrahim da Aisha fahimta mai kyau, Akwatunan Soja ne aka kawo mishi abun shi tun da auren bai nufa dashi ba, sabida ga kayan nan ku ajiye mishi abin shi, hakk’in shi ne". Momi duk da itama har yanzu ba ta daina jin haushin abin da nayi ma yaya Faruk ba, tana ganin bai kyautu su amshi kayan ba kasancewar duk d’aya ne. Cikin ladabi ta Hajiyan Wagini ta ce "Hajiya ina ganin da ba ku dawo da kayan nan ba, dawo da kayan bai da wata fa’ida, dan Faruk bai auri Fatima ba sai a dawo da akwatunan, ina ganin ko da Faruk bai auri Fatima ba, zai iya ma Fatima kyauta tun da k’anwar shi ce, Alhaji ma in ya dawo ya ga kayan fad’a zai yi". Ummu ce ta ce "Hajiya Rukaiya ki yi hak’uri ki bar kayan nan a gurin ki, rashin amsar kayan zai sa in za ta ko har yanzu kuna fushi da abin da Fatima ta yi ne". Hajiyan Wagini ta kar’bi zancen da cewa "Wannan gaskiya ne abin da Aisha ta fad’a, rashin amsar kayan kamar yana nufin ba ku huce da abin da Fatima ta yi ba, saboda haka in Isuhu ya dawo ki fad’a mishi ni na ce a bar kayan". Hira suka ci gaba da yi kafin suka yi sallama da Momi suka tafi. San da Dadi ya dawo Momi ta mishi bayanin dawo da kayan da su Ummu suka yi ya nuna ‘bacin ranshi akan me yasa su Ummu suka dawo da akwatunan, nan ya dinga ma Momi fad’an akan me yasa ta masa, haka ya kira Abbu ya nuna mishi rashin jin dad’in shi na dawo da akwatin da aka yi, sai da Abbu ya dinga bashi hak’uri kana Dadi ya hak’ura. Yaya Faruk ma da Momi ta sanar dashi dawo da akwatin da su Ummu suka yi ya nuna ‘bacin ranshi, dan shi a ganin shi tun da ya hak’ura da ni zai iya hak’ura da abin da ya min. Dr Sadik suna ta shirye-shiryen biki kasancewar shine wanda za a fara aurar wa a gidan su, kud’i kawai ake kashe wa tun da akwai wadatar 'ya'yan banki. Gidan su Sadik sun kawo akwatuna na gani na fad’a, daga gani an kasha kud’i wajen had’a akwatunan. Kasancewar gidan mu an riga an da an gama shirye-shirye tun kan bikin ya koma kan Dr, k’arashe kawai ya rage. Dr Sadik ya zo ya bani kud’in da zanyi hidimar biki da katunan da zan raba ma k’awaye na. Halima na kira na ba ma katin akan ta raba ma wanda ya dace, ita ma sai da ta min k’orafin tafiyar da nayi. Na kira Aisha na fad’a mata zancen bikin da ranar, ta tabbatar min da tana nan zuwa. Na so in je gidan su Anisa mu tattauna akan bikin, amma nasan ko a kaina aka saukar da rashin kunya da kunya in iya zuwa gidan su Anisa da wannan maganar, saboda haka na tura mata text akan in ta samu lokaci ta zo. Yaya Faruk ya kira Anisa ya mata fad’a akan shariyar da take ma yaya Khalil, ya nunar mata da laifin wani ba ya shafar wani, ya nunar mata in dan shi take mai haka ta daina dan shi Khalil bai mishi komai ba, ya k’ara nusar da ita halayen yaya Khalil nigari, hakan yasa Anisa tayi nadamar abin da tayi ma yaya Khalil duk da ‘bacin rai da kuma damuwa da halin da d’an uwan ta ke ciki yasa ta yin haka, ta ma yaya Faruk alk’awarin cewa in yaya Khalil ya zo za ta kula shi, za kuma ta bashi hak’uri akan abin da ta mishi. Yaya Faruk yaji dad’in wannan bayanin na Anisa. Yau biki na ya rage saura sati d’aya, yaya Faruk ne a d’akin shi yana tunanin da ya fara zaman mai jiki, duk yadda yake iya k’ok’arin shin a ganin ya daina tunani hakan ya gagara a gareshi, idan ya tuna ba shi zan aura ba hakan na k’ara sa shi a damuwa, yanzu yana ji yana gani zan auri wanda nake so bayan shi yafi cancanta da in so ganin yadda ya dad’e yana d’awainiya da so na, wannan su ne tunanin da ke addabar zuciyar yaya Faruk. Wani abu ya tsaya mishi a k’irjin shi, daga nan sai yaji k’irjin shi ya fara mishi ciwo, tun yana daurewa har ya k’arfin shi ya fara k’arewa. Haka ya kasance cikin wannan halin ba tare da wani yasan halin da yake ciki ba. Anisa ce ta shigo da food flask d’in abincin dake hannun ta, ganin halin da yaya Faruk ke ciki yasa ta saki food flask d’in abincin ya watse yayin da ta fita da gudu ta koma side d’in su Dadi. Cikin Kuka Anisa ta sanar da su Dadi halin da yaya Faruk ke ciki, gaba d’aya suka koma d’akin. Ganin halin da yaya Faruk ke ciki yasa Dadi ya kira family Doctor d’in su, bayan ya d’auka ne ya fad’a mishi halin da yaya Faruk yake ciki, umartar su yayi da su kawo shi asibiti saboda yanzu yana duba patients ne ba zai samu zuwa ba. Haka aka d’auki yaya Faruk aka tafi dashi asibitin da suke ganin likita, suna zuwa aka yi admitting d’in shi a wani special room. [7/22, 13:54] ‪+234 903 003 2630‬: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa Writers Association *FATAN ALKHAIRI* _Ina ma duk wani fans d’ina fatan alkhairi a duk inda yake, Allah ya bar zumunci da so_. _Amsar question of the day ita ce Nusaiba bintu Ka'ab Al Mazaniyya (RA), ita ce ta d’auki takobi ta kare Manzon Allah (S.A.W) a lokacin da mazaje suka guje daga gare shi, da kuma san da annabi ya ce mata "Tambaye ni abin da kike so?" Sai ta ce masa "Ina rok’on ka kasancewa mak’ociyar ka a Aljanna da son ka a duniya da son ka a lahira"_. 73-74 Dr ne yazo ya gwada BP d’in shi inda yaga ya hau sosai akan san da yazo gida ya duba shi, ya gano ba abin da ke damun yaya Faruk da ya wuce damuwa da tunani da ya sa ma kan shi, wanda hakan zai iya sa ya kamu da ciwon zuciya. Bayan ya gama gwaje-gwajen ne ya kalli su Dadi ya ce "Alhaji kamar yadda na fad’a muku ne a baya, Faruk yasa damuwa da tunani da damuwa a ranshi wanda hakan yasa ya kamu da hawan jini, yanzu a gwajin da na mishi BP d’in shi yayi high akan san da na zo na duba shi a gida, idan ya ci gaba da wannan tunanin da sa damuwa a ranshi zai iya kamuwa da ciwon zuciya, ya kamata a kiyaye abin da zai sa shi damuwa da tunani, insha Allahu zan d’aura shi akan magunguna". Jin wannan bayanin yasa jikin su Dadi ya k’ara sanyi da halin da yaya Faruk yake ciki, sun san duk wannan ciwon da yake fama dashi duk a sanadi na ne. Dady cikin dauriya ya kalli Dr d’in ya ce "Insha Allah za mu dinga kiyayewa, mun gode Dr". Hannu ya mik’a mishi suka yi musabaha kana ya musu sallama ya fita daga room d’in. Momi kuwa k’arin jin haushi na ne ya k’aru a zuciyar tar, ta san ni ce silar fad’awar yaya Faruk cikin wannan halin da yake ciki. Tasa a ranta cewa za ta taya yaya Faruk addu’a akan Allah ya kawo mishi sauk’i da mafita a cikin halin da yake ciki, Allah ya canza mishi da abin da yafi zama alkhairi gare shi, ya canza mishi da wacce tafi ni. A yanzu yadda take ganin na za’bi Dr Sadik akan yaya Faruk, ko da a ce na amimce da auran da yaya Faruk, ita ba za ta yarda ba, ba za ta yadda d’an ta ya dinga shiga wani hali ba akan mace. Dadi ma na cikin damuwa akan halin da yaya Faruk ke ciki, yasan duk abin da ya samu bawa dama rubutacce ne daga wajen ubangiji, dan haka zai dinga ma a yaya Faruk add’a akan Allah ya bashi wacce za ta so shi tsakani da Allah shi ma yaso ta. Dadi ne ya kira Abbu ya sanar dashi rashin lafiyar yaya Faruk. Cikin tashin hankali Abbu ya sanar da su Hajiya da Ummu halin da yaya Faruk ke ciki, Hajiya tun da taji rashi lafiyar yaya Faruk take kuka. Haka Abbu ya d’auke su ya kai su Asibitin, ko da suka je asibitin, kuka Hajiyan Wagini taci gaba dayi, sai da aka ce mata likita ya ce ba ya son hayaniya sannan ta daina kuka, ba abin da take mai sai addu’ar Allah ya bashi lafiya. Sai da yaya Faruk ya farka suka mishi ya jiki kana Abbu da Ummu suka dawo gida saboda Hajiyan Wagini ta ce ba inda za ta. Ni kaina san da naji labarin ciwon yaya Faruk sai da jiki na yayi sanyi, nasan duk a dalili na ne yake wannan rashin lafiyar, ni kaina bazan so ta dalili na yaya Faruk ya dinga kasancewa a cikin wannan halin ba, hakan yasa nima na shiga cikin damuwa, ji nayi ina son in je in ga halin da yaya Faruk d’in yake ciki. Washegari na ma Abbu magana akan in za su koma asibitin zan bi su, da farko Abbu cewa yayi ba zani ba, zuwan me zanyi tun da ni na ja mishi halin da yake ciki, ko so nake na je na k’ara sa mishi wani ciwon, miye amfanin zuwa na asibitin, har na cire ran zuwan asibitin tun da Abbu ya ce ba za ni ba, sai gashi da za su tafi Abbu ya sa Ummu ta kira ni. San da muka je asibitin su Momi da Dadi ne da su Anisa da Hajiyan Wagini a cikin d’akin da aka kwantar da yaya Faruk. Ni kaina yaya Faruk ya bani tausayi ganin yadda ya canza lokaci guda, da ga gani yana jin jiki. Dadi na gaisar da Momi da Hajiyan Wagini na gaisar tare da tambayar su ya jikin yaya Faruk. Dadi ne ya amsa min da fara’a a fuskar shi. Momi kuwa ba yabo ba fallasa ta amsa min kana ta d’auke fuskar ta. Hajiyan Wagini kuwa watsa min harara tayi kana ta ce "Uban me kika zo yi, duk wannan halin da ya shiga ba saboda ke ba ne, amma da yake rashin kunya gaba ki ka ba ta ba baya ba har ki ka iya tako k’afar ki da sunan kin zo duba shi". Sunkuyar da kaina na yi san da Hajiyan Wagini ta fara min fad’a, raina na min k’una na yadda a yanzu Hajiyan Wagini take kyara ta. Dadi ne ya ce "Hajiya a mata hak’uri". Ummu da Abbu kuwa ba su ce komai ba. Ranar haka kowa ya fita harka ta a cikin asibitin, sai hirar su suke yi ba tare da sun sa ni a cikin hirar su ba, hakan yasa nima na kama baki na ba tare da na tsoma baki na a cikin hirar ba, Dadi ne kad’ai ne ya kula ni a asibitin. Haka muka koma gida ina mai cike da jin haushin yadda aka min a asibiti. Yaya Mus’ab kuwa tun bayan tawowar yaya Faruk Kaduna bai kawo komai ba game da tawowar shi Kadunan ba, ya alak’anta tafiyar tashi ne da shirye-shiryen bikin shi da ya gabato, suna yawan waya dashi jefi-jefi, a wayar da suke yi dashi ne ya fahimci yaya Faruk yana cikin damuwa, ganin bai fad’a mishi ba shi yasa bai tambaye shi ba, yasan wani lokacin yaya Faruk yana da zurfin ciki, ba kowace matsala ba ce yake fito wa ya fad’a ba, sai dai a cikin kwana biyu idan ya kira wayar shi ba ta zuwa, hakan yasa yayi tunanin akwai abin da yake faruwa saboda yaya Faruk bai cika kashe wayar shi ba, sai da babban dalili. Yau cikin sa’a yana kira wayar ta shiga, Dadi ne ya d’auki wayar ya amsa kiran. Bayan sun gaisa ne yaya Mus’ab ke tambayar yaya Faruk, Dadi ne ya fad’a mishi rashin lafiyar yaya Faruk da kuma kwanciyar shi a asibiti. Yaya Mus’ab ya ma yaya Faruk fatan samun lafiya, ya sanar da Dadi in ya samu sauk’i a wajen aikin su zai zo ya duba shi, nan suka yi sallama da Dadi. Tun bayan gama wayar su yaya Mus’ab ke jinjina rashin lafiyar yaya Faruk, yasan duk abin da ya kwantar da yaya Faruk a gadon asibiti ba k’aramin abu ba ne. Khadija ma a ‘bangaren ta kwana biyun da ba su yi waya da yaya Faruk ba hakan yasa ta shiga damuwa, tun bayan tafiyar shi Kaduna ya kan kira ta su gaisa, ita ma tana k’ok’arin kiran shi su gaisa, sai dai a kwanan biyu da ba ta samun shi a waya yasa ta dinga tunanin rashin samun shi a waya da ba tayi, gashi tana son tambayar yaya Mus’ab ta ji dalilin da yasa ba ta samun shi a waya, sai wata zuciyar ta hana ta tambayar yaya Mus’ab d’in. Yau Nana suna zaune ne rik’e da Asim ita da Anty Maryam suna hira yaya Mus’ab ya fito daga bedroom ya zo ya zauna. Kallon shi Anty Maryam kana tace "Dadin Asim ya aka yi ne, na ga kamar akwai abin da yake damun ka". Nisawa yayi kana ya ce "Na kira wayar Faruk ne kwana biyu ba ta shiga, shine yau Allah ya taimaka na samu ta shiga, sai Dadin Faruk d’in ya d’auka yake sanar dani rashin lafiyar Faruk d’in har da kwanciya a asibiti yayi, nasan duk abin da ya kwantar da Faruk a gadon asibiti ba k’aramin abu ba ne, shine ki ka ga hankali na duk ya tashi, yanzu zan ta k’ok’arin neman permission a gurin aiki sai mu je mu duba shi" ya k’arasa maganar cikin damuwa. Anty Maryam cikin jimami ta ce "Allah sarki Faruk, gashi biki na ta gabato wa ga kuma rashin lafiya, Allah ya bashi lafiya, in ka nemi excuse a gurin aikin sai mu je can Kadunan mu duba shi". Nana da take ta faman yi ma Asim wasa ta tsayar da wasan da take mai tun san da taji yaya Mus’ab na fad’an rashin lafiyar yaya Faruk, ji tayi komai ya d’auke mata, ji tayi tana buk’atar ganin halin da yaya Faruk yake ciki, don haka ta ce "Yaya Mus’ab ni ma zani in za ku" ta fad’a a hankali. Kallon ta yayi kana ya ce "Ke Nana ban da abinki, kina zuwa School ina zaki, ki bari in mun je zan fad’a mishi kina gaida shi". "Toh yaya Mus’ab" ta fad’a a tak’aice, amma yanayin ta ya nuna ba haka taso ba. Hakan da Anty Maryam ta lura ne yasa ta ce ma yaya Mus’ab "Da ka k’yale ta mun je Kadunan da ita, tun da ta nuna tana son zuwa, kasan kuma Faruk mutumin ta ne". Murmushi yayi ya ce "Shi kenan, in za mu tafi sai mu tafi tare". Tashi yayi ya fita yayin da Anty Maryam suka ci gaba da tattaunawa akan rashin lafiyar yaya Faruk. Yaya Faruk sai da yayi kwana uku a asibiti sannan aka sallame shi, tare da gindaya mishi sharud’a akan yadda zai kula da lafiyar shi. Yaya Faruk yana k’ok’arin ganin ya kiyaye duk wani dokoki da likita ya gindaya mishi, hakan ne yasa bai cika son zama shi kad’ai ba saboda guje ma tunani, hakan yasa ya samu sauk’i akan damuwar da yake ciki. Yaya Mus’ab san da yayi requesting d’in permission aka bashi, ya shirya da su Anty Maryam da Nana suka tawo Kaduna. Nana kuwa wani irin dad’i ta ke ji za ta zo ta ga jikin yaya Faruk, tun san da taji labarin rashin lafiyar yaya Faruk ta rasa sukuni, sai yanzu da taga sun d’auki hanyar Kaduna, tasan yanzu hankalin ta zai kwanta. Kasancewar gudun da yaya Mus’ab yayi yasa suka shigo Kaduna a cikin d’an k’ank’anin lokaci. Yaya Faruk su na zaune a Main parlour suna hira da Anisa suka ji sallamar su yaya Mus’ab. Anisa ce ta amsa sallamar ta tashi ta bud’e musu k’ofa. Yaya Faruk ne yayi arba da su yaya Mus’ab, murmushi kawai yake yi ganin su yaya Mus’ab, bai yi mamakin ganin su ba, dan Dadi ya fad’a mishi cewa yaya Mus’ab ya kira wayar shi lokacin da aka kwantar dashi a asibiti, yasan yaya Mus’ab zai iya zuwa a ko wane lokaci. Nana kuwa tun da tayi arba da yaya Faruk wani farin ciki ya kamata ganin ya samu sauk’i, hakan yasa ta dinga sakar mishi murmushi. Anisa ma murmushi ta sakar musu tare da yi musu sannu da zuwa. "K’anwa ta har dake aka zo Kaduna kenan, sannu da zuwa" Yaya Faruk ya fad’a cikin fara’a. "Da ni aka zo yaya Faruk" Nana ta amsa mishi. Yaya Mus’ab ne cikin wasa ya ce "Da yake ai ita kad’ai ka gani, dole ka maida mu hoto ni da Maryam". Murmushi yaya Faruk yayi kana ya kalli Anty Maryam yace "Madam sannun ku da zuwa, kar mijin ki ya dame ni da k’orafin shi". Dariya Anty Maryam tayi ta ce "Ai gaskiya ya fad’a, ya ga ka manta da mu ne, sai ‘yar k’anwar ka gani". "To a min afuwa Madam, na amsa laifi na duk da nasan ba laifi nayi ba". "An maka afuwa Faruk" Anty Maryam ta fad’a cikin wasa. Gaba d’aya falon aka sa dariya. Kar'ban Asim yayi daga hannun Anty Maryam yana mishi wasa. Anisa tashi tayi ta je ta sanar da Momi zuwan su yaya Mus’ab kana ta wuce kitchen ta samo musu drinks da snacks kafin ta d’aura musu abinci. Gaisawa suka yi kana suka mishi ya jiki. Amsa musu yayi da ya ji sauki. Momi ce ta zo suka gaisa cikin walwala da sakin fuska. Bayan sun gaisa ne da tambayar ta ya mai jiki ta amshi Asim ta tafi dashi d’akin ta. Lokacin da Anisa ta gama girkin ne ta jera musu a dining table, zama suka yi suka ci ana d’an ta’ba hira. Bayan sun gama cin abincin ne, Anisa ta kai su Nana d’akin ta dan su huta, shi kuwa yaya Faruk ya tafi da yaya Mus’ab side d’in shi. Suna shiga d’akin yaya Mus’ab ya d’aure fuska kamar ba shi bane ya gama wasa da dariya a falo. Ganin haka yasa yaya Faruk murmusawa ya ce "Ya aka yi ne Mus’ab". In a serious talk yaya Mus’ab ya ce "To be serious Faruk, ban ji dad’in abin da ka min ba, tun bayan tafiyar ka na ke sa ran kiran ka saboda ganin yadda bikin ka ya matso amma ba ka kira kace min komai ba, ashe har ciwo kayi da yayi sanadiyar ka kwanciyar asibiti, da Dadi bai fad’a min ba bai zama lallai ka fad’a min ba, wai wani irin ciwo kayi ne har ka kwanta a asibiti, ga jikin ka nan ya nuna, dan har ‘yar rama kayi, Faruk na san duk ciwon da aka kwantar da kai ba k’aramin abu ba ne". "Abin da yasa ka ga ban kira ka game da maganar biki, ba bu buk’atar kiran ka akan wannan maganar saboda an fasa bikin mu ne da Fatima, kwantar da ni da aka yi a asibiti kuwa BP na ne ya hau" yana gama fad’ar haka ya fara danna wayar shi kamar ba shi yayi magana ba. Yadda yaya Faruk yayi maganar yasan ba wasa yake mai ba, yasan ma yaya Faruk zolaya ba halin shi ba ne. Wannan maganar da yaya Faruk ya fad’a main a fasa bikin shi ba k’aramin girigiza shi yayi ba, yasan ba k’aramin abu ba ne zai sa a fasa bikin ganin irin son da yake min. "An fasa bikin fa ka ce min Faruk, me yasa zaka hak’ura da Fatima bayan kasan halin da za ka shiga in dai ka rasa ta" yaya Khalil ya fad’a cikin damuwa. Murmushin takaici yaya Faruk yayi ya ce "Ban damu da halin da zan shiga ba Mus’ab, hukuncin da na yanke shi yafi min sauk’i da ni da Fatima akan halin da za ta iya jefa ni nan gaba saboda ta ga ina son ta". Tunani ne kala-kala ya addabi Mus’ab, wani irin laifi na mishi da zai sa ya fasa aure na bayan bikin ya kusa. Kamar yaya Faruk yasan tunanin da yake yi kenan ya ce "Nasan za kayi tunanin mai yasa na yanke wannan hukuncin, Mus’ab zan iya hak’ura da kowace mace in har ta nuna akwai wanda take so ko da kuwa son ta zai illata ni, hakan yasa na yanke hukuncin hak’ura da Fatima saboda yadda ta nuna za ta iya aikata komai in dai akan wanda take so ne, kai kan ka shaida ne halin da na shiga a baya duk a kan Fatima, a dalilin ta har na kamu da hawan jini, ka ga kuwa in ban hak’ura da Fatima ba za ta iya jawowa na fad’a cikin wani mawuyacin hali". Nan yaya Faruk ya warware mishi abun da ya faru har zuwa lokacin da ya hak’ura da ni da kuma halin da ya shiga. Ci gaba yayi da cewa "Mus’ab nasan na so Fatima, sai dai a yanzu na hak’ura da son ta, ban ce maka har yanzu ba sauran son Fatima a raina, sai dai zan yi iyakar k’ok’ari na in ga na ajiye son ta a gefe, zan ci gaba da addu’a akan Allah ya cire min son ta nima in samu sauk’i a cikin zuciya ta, zan yi abin da hausawa ke cewa in so cuta ne, hak’uri magani ne". Tausayin yaya Faruk ne ya dabaibaye yaya Mus’ab ta ko ina ya kama shi, ji yake yi da yana da halin da zai cire yaya Faruk daga halin da yake ciki da yayi, a maganganun da yaya Faruk yayi a yanzu ya fahimci cewar har yanzu yaya Faruk na so na, sai dai yana k’ok’arin danne son da yake min ne saboda ya samar wa kanshi mafita, shi kan shi yaya Mus’ab d’in ya ji haushin abin da na yi, ya kuma goyi bayan rabuwa dani da yaya Faruk yayi. Wani tunani ne ya fara wanzuwa a zuciyar shi, sai dai bai so yayi saurin yarda da wannan tunanin da yake zuwa mishi. Cikin tausayawa yaya Mus’ab ya ce "Faruk Allah ya za’ba maka abin da yafi alkhairi, Fatima tabbas ba ta kyauta ba, ina son ka d’auki hakan a matsayin jarrabawa, sannan ka sa a ranka wannan abin da ya faru cewa dama can Fatima ba rabon ka ba ce, ka ci gaba da addu’a da neman za’bin Allah a dukkan lamuran ka, insha Allahu komai zai zo maka da sauk’i, nima zan taya ka addu’a". Murmushin jin dad’i yayi kana ya ce "Na gode Mus’ab da shawarwarin ka, na gode da kulawar ka gare ni". "Ba komai Bregadier, zan iya yi maka komai dan taya ka samun farin cikin ka" yaya Mus’ab ya fad’a. Hira suka ci gaba da yi, yayin da yaya Mus’ab yaci gaba da kwantar mishi da hankali. Anisa kuwa suna can d’aki suna hira da Anty Maryam, jefi-jefi Nana nasa bakin ta a hirar, in ka gansu za kayi zaton sun dad’e da sanin juna. Da yammaci yaya Faruk ne da Nana suke zaune a farfajiyar gidan suna hira. Nana ce ta tsura ma yaya Faruk ido tana kallon shi, had’a ido suka yi tayi saurin sunkuyar da kai saboda kunyar da ta kama ta. Murmushi yaya Faruk yayi kawai, wannan kunyar na daga cikin abin da yasa Nana ke k’ara burge shi. "Yaya Faruk ba ka kai ni gurin Fatima na ganta ba" Khadija ta fad’a. "Me yasa kike son ganin ta?" yaya Faruk ya tambaye ta. "Ina son in ga amaryar ka ce wacce kake yawan ba ni labarin ta, shi yasa na ke son ganin ta". "Zan kai ki gurin ta ki ganta a matsayin ta na k’anwata amma ba a matsayin matar da zan aura ba, dan na da kwanaki za ta zama mallakin wani, kin ga ai ba amarya ta ba ce". D’ago wa tayi tana kallon shi saboda yadda maganar ta ba ta mamaki tare da girgiza ta, tasan a yadda yaya Faruk ke yawan ba ta labari akan irin son da yake min, yanzu kuma gashi yana fad’a mata ba shi zai aure ni ba, wani ne zai aure ni. Jikin ta ne yayi sanyi da jin wannan maganar da yaya Faruk ya fad’a mata, a hankali ta ce "Yaya Faruk me yasa za ka fasa auran ta ka bar ma wani ya aure ta duk da irin son da kake mata". Murmushin takaici yayi kana ya ce "Khadija Allah bai nufa daman mata ta ba ce, shi yasa a ka fasa auren dani, ki taya ni addu’a kin ji ‘yar k’anwa ta Allah ya za’ba min abin da yafi zama alkhairi a gare ni". "Insha Allah yaya Faruk zan taya ka da addu’a, Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi gare ka". "Amin Khadija, Na gode da addu’ar ki". Murmushi kawai tayi, amma a k’asan ranta tausayin yaya Faruk ne fal cikin ranta, a yanzu ta fahimci dalilin rashin lafiyar shi yana da nasaba da fasa auren shi da aka yi da ni, duk da bai fad’a mata dalilin fasa auren ba, ta alak’anta hakan ba daga ‘bangaren yaya Faruk ba ne ko kuma babban dalilin shi da yasa shi yin haka har ya bar ma wani ya aure ni duk kuwa da son da yake min. Haka suka ci gaba da hirar su cikin nishad’i. Kwana d’aya su yaya Mus’ab suka yi a gidan su yaya Faruk sannan suka koma Abuja, kafin su tafi sai da suka yi exchanging d’in numbobin wayar su da Anisa, a kwana d’ayan da suka yi har sun fara saba wa kamar wanda suka dad’e da sanin juna da su Nana da Anty Maryam, shi yasa da za su tafi sai da taji kewar su, su kansu su Anty Maryam sun ji dad’in yadda Momi da Anisa suka tarbe su, da za su tafi haka Dadi da Momi suka cika su da tsaraba. Haka suka tafi Abuja suna kewar junan su. Yau yaya Khalil ne ya je gidan su Anisa dan ya k’ara duba jikin yaya Faruk. Sai da ya fara shiga side d’in Momi suka gaisa tare da tambayar ta ya mai jiki sannan ya fito ya nufi side d’in yaya Faruk. Lokacin da ya shiga d’akin yaya Faruk na kishingid’e a resting chair yana kallon news d’in da ake watso wa a Afican Independent Television. Sallama ya mishi ya amsa mishi da fara’a a fuskar shi. Bayan yaya Khalil ya gaishe shi ne ya tambaye shi ya jikin shi. Amsa mishi yayi da ya ji sauk’i. Sun d’an ta’ba hira kana yaya Faruk ya d’aura da cewa "Khalil kayi hak’uri da abin da Anisa ta maka, nasan ba ta kyauta ba, in ban da abinta ta ya za ayi ta kama yin fushi dakai akan abin da ba ruwan ka a ciki, kasan yarinya ce sai a hankali, har yanzu da sauran k’uruciya a jikin ta, in har ta maka wani abu ka zo ka fad’a min, zan d’auki mataki a kanta". Murmushi yaya Khalil yayi kana ya ce "Ba komai yaya Faruk, ni ban yi fushi da Anisa ba, nasan duk abin da tayi tana da hujjar yin shi, nasan za ta sauka daga fushin da take yi da ni, Na gode yaya Faruk da kulawar ka gare ni". Suna cikin maganar ne sai ga Anisa ta shigo d’akin had’e da sallama. Amsa mata sallamar suka yi ta nemi guri ta zauna. Tun da ta gaishe da yaya Khalil ba ta k’ara bi ta kan shi ba, sai ma yaya Faruk da taci gaba da yi ma magana. Ganin irin kallon da yaya Faruk yake watso mata ne yasa tasha jinin jikin ta, tashi tayi ta bar d’akin. Yaya Khalil ya d’an jima a gurin yaya Faruk sannan ya mishi sallama ya fito. Main parlour ya dawo ya zauna inda ya tarar da Anisa da remote a hannun ta tana canza channel. Ko da ya nemi guri ya zauna ba ta juyo ta kalle shi ba, sai ma ci gaba da canza channel d’in da ta ke yi. Shiru ne ya ratsa falon kafin yaya Khalil ya kau da shirun da cewa "Anisa!" Jin kiran sunan ta da yayi ne yasa ta juyo ta kalle shi ba tare da ta amsa ba. Hakan ya ‘bata mishi rai, yana ganin wannan yana daga cikin salon raini ya kira ta kuma tana ji ta mishi shiru, dan haka cikin d’aurewar fuuska yace "Anisa nasan kin ji kiran sunan ki da nayi amma ki ka min shiru ko". Ganin yadda fuskar shi ta canza zuwa ga ‘bacin rai yasa taji jikin ta yayi sanyi, tasan ita ma ba ta kyauta ba, tasan yaya Khalil yana da hak’uri, sai dai duk ran da aka kaishi bango bai iya ‘bacin rai ba. "Kayi hak’uri yaya Khalil" Anisa ta fad’a cikin sanyin murya. Ci gaba yayi da cewa "Anisa zan iya jurar komai a gurin ki amma ban da raini, na zuba miki ido ne in ga iya gudun ruwan ki, sai na ga ke ba ki san haka ba, Anisa ina yabon kyawawan halayen ki, hakan yasa na ke k’ara jin son ki a cikin raina, sai dai lokaci d’aya kina so ki fito da wasu halaye da ba naki ba ta hanyar hukunta ni da laifin da ban aikata ba, ba yadda za ayi laifin wani ya shafi wani, abin da yasa na ke miki uzuri nasan ki na yin haka ne dan nuna jin haushin ki akan abin da Fatima ta ma yaya Faruk, ban hana ki nuna jin haushin ki ba ko d’auka wani mataki akan abin da Fatima tayi, sai dai ina ganin in kin tashi d’auakar matakin bai kamata ki sa ni a ciki ba, Anisa ke kan ki shaida ce akan yadda kowa ya nuna ‘bacin ranshi akan abin da Fatima ta yi, har yanzu Fatima ba ta wani sakewa a gida saboda yadda kowa yake nuna mata ‘bacin rai akan abin da tayi, ina ganin tun da har yaya Faruk ya ce ya hak’ura da ita, ya kamata kema ki hak’ura da wannan fushin da ki ke yi, ko ba komai Fatima ‘yar uwar ki ce kuma aminiyar ki ce tun kuna yara, ba wai ina fad’a miki da ki yafe ma Fatima dan ta na matsayin k’anwa ta ba, na fad’a miki hakan ne dan in nuna miki rik’o bai da amfani kuma ba shi da kyau a musulunci, saboda hakan zan barki ki yi tunanin akan maganar da na fad’a miki, duk hukuncin da kika yanke min, za ki iya kira na ki fad’a min, ko kuma in nazo sai ki fad’a min shawarar da kika yanke" yana gama fad’ar haka ya fita daga d’akin. Tun bayan fitar yaya Khalil daga d’akin ta rasa sukunin ta, tasan cewa yau ta kai yaya Khalil k’arshe, shi yasa ya nuna mata fushin shi, bai kamata ta dinga yanke mai hukunci akan abin da ba ruwan shi a kai, ko shi wanda take yi akan shi yace ya hak’ura, tasan in har ba taje ta ba yaya Khalil hak’uri ba, yaya Faruk zai iya yanke mata ko wani hukunci,ita kanta tana azabtuwa da irin hukuncin da ta ke ma yaya Khalil d’in, ya kamata ta je ta bashi hak’uri tun kan ya tafi, tasan in ya tashi yanke mata hukunci ita ce za ta sha wuya. Da sauri ta fito daga d’akin ta same shi har ya shiga motar shi. K’arasawa tayi gurin shi yayin da yake k’ok’arin kunna motar. Ganin yana k’ok’arin barin gurin yasa ta kira sunan shi "Yaya Khalil". "Ya aka yi ne?" ya fad’a cikin d’aurewar fuska. "Am sorry yaya Khalil, plss forgive me" ta fad’a a hankali. Kallon ta yayi ganin yadda ta marairaice fuska kamar mai shirin yin kuka, amma duk da haka sai ya nuna mata kuskuren ta, saboda gaba kar ta sake. "Kin gama maganar ki dan so nake yin a wuce gida, kuma ni ba hak’uri nace ki zo ki bani ba, cewa nayi ki shawarta da zuciyar ki, duk shawarar da ta baki sai ki fad’a min". Wannan karan kasa daurewa tayi, ba za ta juri fushin yaya Khalil ba, tasan ta ‘bata mishi, shi yasa yayi fushi da ita. Hawaye ne ya fara zubowa a idanun ta, tasan yaya Khalil ba zai juri ganin hawayen ta yana zuba ba, zai yafe mata laifin da ta mishi. "Yaya Khalil dan kayi hak’uri da abin da ya faru, nasan ban kyauta maka ba, amma insha Allah ba zan sake kamanta irin wannan laifin ba, kai kan ka shaida ne a irin son da nake maka, ba zan juri ganin fushin ka gare ni ba, plss yaya Khalil ka tausaya ma ‘yar kanwar ka". Ba zai juri ganin hawayen Anisa ba, yasan ta mishi laifi, tun da har ta gane kuskuren ta kuma ta bashi hak’uri ya kamata ya hak’ura, shi kanshi ba zai so su ci gaba da fushi da juna ba. K’asaitaccen murmushi ya sakar mata kana ya ce " Is ok my lovely sister & wife to be, komai ya riga ya wuce, amma pls ki kiyaye gaba, ba zan so mu dinga samun sa’bani da ‘yar k’anwata ba akan k’aramin abu, so wipe your tears & smile for me". Goge hawayen ta tayi, a lokaci d’aya tana sakar mishi da wani lallausan murmushi. Hira suka fara yi kamar ba su ba ne suka samu sa’bani, gashi har sun shirya kamar ba su. Sai da suka sha hirar su kana ya mata sallama ya tafi. Shirye- shiryen bikin mu ya ci gaba da gudana, yau bikin mu ya rage saura kwana biyu, ranar ne ya kasance henna design, ban wani shirya event ba kasancewar yadda bikin yazo min, bridal shower da walima kad’ai na shirya, Dr yaso ayi event masu yawa, nuna mishi na yi akan ba na son event d’in da yawa, saboda haka ne ya shirya Dinner kawai zai yi ta ‘bangaren shi. Abbu da Ummu duk sun min abin da ya dace akan bikin, Ummu ta bani magungunan da ake baiwa amare, sannan ta kawo mai gyaran jiki ta musamman dan ta min gyara na musamman. Yanzu ba laifi su Abbu ma suna zama mu d’an yi hira, hakan ya rage min damuwar da na ke ciki. Yaya Khalil ma yana tambaya na ko akwai abin da na ke buk’ata. Yaya Aminu ma yana kawo Anty Jiddah ta wuni, ita ma haka ta kawo min tsarabar magunguna na sha, har da turarurruka na tsugunnawa ta kawo min, sannan tana zaunar dani ta fad’a min dabarun zamantakewar aure, ina jin dad’in yadda Anty Jiddah take ba ni kulawar ta, hakan yasa na ke k’ara ganin girman ta da mutuncin ta. Momi da ita ake gudanar da shirye-shiryen bikin, yanzu ta rage fushin da take yi dani, in na gaishe ta cikin fara’a take amsa min. Anisa ma ta na zuwa a gudanar da shirye-shiryen bikin, sai dai ba ta sakin jikin ta wajen gudanar da shirye-shiryen. Hajiyan Wagini ce har yanzu ba ta huce ba, hakan yasa nima naji dad’in zaman ta a gidan su Anisa, sai dai idan tazo ne nake kauce ma had’uwar mu, dan in dai muka had’u sai tasan yadda tayi ta fad’a min maganar da ta ‘bata min rai. Aisha ma tun san da taji abin da ya faru na fasa aure na da yaya Faruk, ta nuna rashin jin dad’in ta. Gidan mu ya fara cika da ‘yan uwa da abokan arziki. Yau ne ya kasance za mu yi Bridal shower, shigar cot less nayi fari na doguwar riga, yayin da aka rubuta min *BRIDE TO BE* da farin rubutu wanda aka yi min crossing d’in shi akan rigar, nad’in da aka min na head kalar light silver aka min, takalmi ma kalar light silver na saka. Kwalliyar da nayi ba k’aramin amsa ta tayi ba. K’awaye na kuma shigar tommy skirt da polo suka yi. A farfajiyar gidan mu muka yi event d’in. Music kala-kala aka dinga playing a Bridal shower d’in. K’awaye na sun cashe a wannan ranar. Gaskiya Bridal shower d’in ya k’ayatar. A ranar ne dangin Dr Sadik suka zo suka sa ni a lalle tare da ba da kud’i mai yawa na sa lalle. Washegari ran juma’a ya kasance ranar d’aurin aure na, a ranar ne kuma zan yi walima. Da misalin k’arfe biyu na rana aka d’aura aure na ni Fatima Ibrahim Wagini da Dr Abubuakar Sadik Muhammad a k’ofar gidan mu. D’aurin auren da ya samu halartar manyan mutane daban- daban. Ina jin sanarwar an d’aura aure na samu kaina da wani irin fad’uwar gaba, yayin da hawaye suka zubo min a lokacin. Ni kaina ban san hawayen me nake yi ba, amma na alak’anta hakan da hawayen farin ciki ne nake yi ganin na auri wanda nake so da kuma k’alubalen da na fuskanta Kafin auren, nasan komai yazo k’arshe tun da Allah ya nufa na kasance matar Dr Sadik. Tsintar kaina nayi cikin farin ciki, damuwar da nake tare da ita na tsawon lokuta duk na ji ba bu ita a lokacin. Yau Allah ya cika min burin a da ya nufa na samu Dr a matsayin miji. Haka na ci gaba da gudanar da taron biki na cikin walwala, kowa ya ganni a lokacin yasan ina cikin farin ciki. Walima ma a farfajiyar gidan mu nayi, Malama Khadija Muhammad ce ta gabatar da muhadara mai taken _Zamantakewar aure a Musulunci_ Malamar tayi bayani akan yadda zaman aure ya kamata ya gudana a tsakanin miji da mata ta fuskar musulunci, malamar ta jawo hankalin mata yadda za su gudanar da rayuwar su a gidan aure. Haka dai Walimar ta k’ayatar kana aka tashi daga Walimar. Dr Sadik yazo da abokan shi mun d’auki hotuna, haka muka sha hotuna da su Anisa da Aisha da Halima da k’awaye na, yaya Khalil ma yazo mun yi hotuna dashi, wani mun d’auka ni dashi, wasu hotunan kuma mun d’auka har da Anisa a ciki. Yaya Faruk ya ba da gift da kyautar kud’i ya ba ma Momi ta kawo min, a ranar na samu labarin tun bayan d’aura auran mu ya tafi Abuja, na so mu had’u dashi in mishi godiya ko da ba zai amsa min ba. Hak’ik’a nasan yaya Faruk daban ne da har ya iya min kyauta ba tare da ya duba abin da ya faru a tsakanin mu ba. Hankali na bai tashi ba sai da naji an ce ga motoci can a waje na d’aukar amaryar sun zo, nan nemi farin cikin da nake ciki na rasa. Kuka na dinga yi san da aka kai ni gurin Abbu in mishi sallama, shi kanshi Abbu a lokacin na bashi tausayi, nasiha ya min akan zamantakewar aure tare da min fatan samun zaman lafiya a d’aki na. Nasan Abbu ya nuna min gata da so, in ban da matsalar aurena da yazo da matsala har Abbu yayi fushi dani, in ban da wannan matsalar Abbu bai cika nuna fushin shi gare ni ba. D’akin Ummu aka kai ni, muna shiga na fad’a jikin ta na ci gaba da kukan da na ke yi, ita kanta Ummu duk fushin da take yi dani, sai ta neme shi ta rasa, ganin irin kukan da nake yi ne yasa ita ma hawaye ya fara zuba a idon ta. "Fatima yau Allah ya nuna min ranar auren ki, ba abin da zan ce sai dai in ma Allah godiya da ya nuna min wannan ranar, Fatima aure ba abin wasa ba ne, kar ki dan kin auri wanda kike so ki yi zaton ko ba za ku samu sa’bani ba, aure zaman hak’uri ne, kowa da kike gani shi yake yi a d’akin shi, a yanzu ne da zama ya had’a ku za ki k’ara sanin halin shi yasan naki, dole ne ki kiyaye duk abin da ba yaso, yi nayi bari na bari, ki yi hak’uri da ‘yan uwanshi da iyayen shi, ki kyautata musu kamar yadda za ki kyauta mana, ki koyi hak’uri, juriya, kawaici, shi zai kai ki matakin samun zaman lafiya a d’akin ki, ki kula da tsafta, kissa, kwalliya, girki, wannan abubuwan da na lissafo miki da na ce ki kula suna da fad’i, shi yasa na baki su a dunk’ule, su ne za su k’ara miki daraja a gurin mijin ki, Auta ki yi hak’uri da duk halin da za ki tsinci kan ki a d’akin mijin ki, kin ga dai ke ki ka za’be shi a matsayin miji, saboda haka ki yi hak’uri kin ji Auta, Allah ya baku zaman lafiya". "Ummu ki yafe min duk laifin da na miki" Na fad’a cikin shashshek’ar kuka. "Na yafe miki Auta, tashi ki tafi kin ga ana jiran ki". K’ara shigewa jikin ta nayi na ci gaba da kuka na yayin da Ummu taci gaba da lallashi na. Da k’yar aka samu aka cire ni daga jikin Ummu ina kuka aka fita dani daga d’akin. San da muka fito farfajiyar gidan ne na hango yaya Khalil zaune a saman motar shi. Gurin yaya Khalil na wuce na kwanta a jikin shi ina ci gaba da kuka, shi kanshi daga gani dauriya kawai yake yin a tafiyar da zanyi. D’ago ni yayi yana girgiza min kai alamar in daina kukan, a lokaci d’aya kuma yana goge min hawaye. "Ki daina kuka kin ji Auta, ki zauna lafiya da Dr, in an kwana biyu zan zo in duba ki ko ba kya so" ya fad’a a hankali. Cikin kuka na ce "Ina so yaya Khalil". "Yawwa Fatima, yanzu ki tafi kin ga ana jiran ki, zan kira ki a waya". Maimakon in tafi sai ma sake fashewa nayi da wani kukan, hakan yasa ya rik’e min hannu, gurin Anty Zainab (k’anwar Ummu) ya kai ni ta rik’e min hannu. Juyawa yayi ya wuce side d’in shi, dan a yadda yake ji ba zai juri ganin tafiya ta ba. Allah Sarki yaya Khalil, duk a cikin gidan mu na fi shak’uwa dashi, abokin shawara na, mu yi fad’a mu yi wasa haka muke dashi, yau gashi a dalilin aure zan yi nesa dashi, sai kuma na zo gida ko shi ya kawo min ziyara. Kinkinau aka kai ni, nan Dr Sadik ya gina gidan shi. Gida ne mai matuk’ar burgewa ga duk wanda ya kalla, filawowin da aka zuba ne a gidan ya k’ara k’awata gidan. San da muka fito daga motan ne Anty Zainab ta fad’a min in zan shiga in shiga da k’afar dama. Lokacin da na zo shiga ban manta da abin da Anty Zainab ta fad’a min ba, haka ne yasa na k’ara da addu’a a raina na neman zaman lafiya a tsakani na da Dr Sadik. Falo biyu ne a had’e wanda za a iya shiga ta gaban gidan da kuma ta ta cikin gida, falo na biyu aka kai ni inda aka jera min kaya na.. Falon da aka kai ni ba k’aramun tsaruwa yayi ba, nan na k’ara ganin kayan alatun da Abbu ya zuba min. Bedroom aka wuce dani, nan ma ba k’aramin tsaruwa yayi ba. Ba abin da zan ce ma Abbu da Ummu sai godiya. Momi da Anty Zainab ce suka ci gaba da min nasiha akan zaman aure wanda yasa jiki na yayi sanyi. Sadik ne ya kira ni akan in shirya yanzu za a wuce Dinner, ga motoci nan ya kawo. Anty Zainab ce ta shirya ni cikin wani white gown d’in nan ce mai jan kasa, tana da adon silver a jikin flower d’in, a jikin rigar akwai duwatsu masu shining, head d’in da Anty Zainab ta d’aura min kalar golden, jakar da na rik’e irin wacce amarya ke rik’e wa ita ma kalar golden, haka ma takalmin da na saka, bayan na shirya ne ta sa min gyalen wanda yake zuwa had’e da kayan shima yana jan k’asa. Dr Kamal ne ya d’auke ni da Dr Sadik ya kai mu inda za a yi Dinner d’in. Hall d’in ya cika da ‘yan uwa na da da ‘yan uwan Dr Sadik. Bayan mun zauna a grin da aka ware mana na zaman Ango da Amarya kana aka fara gabatar da program of event. Mc ya umarci da mu fito fili mu taka rawa, abokan Dr Sadik da k’annen shi haka suka dinga mana lik'in kud'i, a ‘bangare na ma su Anisa da su Halima haka su ma suka dinga min lik'in kud'i. An ci an sha a gurin Dinner d’in, da haka taron ya tashi. Dr Kamal ne ya tsaya a gurin sai da kaji ya siya sannan ya tsaya ya siya Drinks kana ya wuce damu gida. Ina zuwa gida na wuce toilet na watsa ruwa saboda gajiyar da nayi kana na d’auro alwala. Wata had’ad’d’iyar night gown na sa na shafa humra kana na d’aura hijab na yi shafa’i da wuturi kasancewar sai da nayi sallar isha’i kafin mu tafi Dinner d’in. Bayan na idar ne na kwanta akan gado saboda wani irin barci da nake ji. Barci har ya fara d’auka na naji shigowar Dr Sadik d’akin. "Zarah ba dai har kin kwanta ba, ko abincin baki ci ba?" Dr ya fad’a a hankali. Cikin muryar barci na ce "Na gaji ne Dr, ga wani irin barci da nake ji shi yasa na kwanta". Wani irin kallo ya watsa min mai kashe sassan jiki ya ce " Ki sakko ki ci wani abun, kin san yunwar dare tana illah, in ban da abin ki ma Zarah ai yau ba ki da barci". Fahimtar in da maganar shi ta nufa yasa ta ce cikin shagwa’ba "Haba Dr, Allah kuwa bacci nake ji". Hannun shi ya mik’o min ya ce "Common, tashi ki ci wani abun, in ba haka ba sai in miki allura". Hannuna na mik’a mishi ya rik’e muka wuce side d’in shi. ‘Bangaren Dr ma ya had’u, yanda aka shirya side d’in kamar na wata amaryar duk da ba a zuba tarkace da yawa a falon ba, hakan bai hana falon tsaruwa ba, cikin bedroom d’in ma ya k’ayatar. Plate yasa na d’akko da cup, naman kazan yasa na zuba a plate. Saboda baccin da nake ji yasa ban wani ci naman sosai ba ga kuma rashin sabo, hakan yasa Dr ya dinga bani da kanshi, shagwa’be min yayi akan nima sai na bashi, haka na d’auka ina bashi yana ci, bayan mun gama ci ne ya tsiyaya min drinks d’in cup yana ba ni, ragowar naman na d’auka na kai frij na saka a ciki. Bayan mun gama cin naman ne yaje ya d’auro alwala, yana fitowa yasa ni naje na d’auro alwala. Sallah muka yi raka’a biyu kana ya kama kaina ya dinga jero addu’o’i akan Allah ya bamu zaman lafiya. Tashi nayi da niyar in koma side d’ina saboda baccin da nake ji kamar zan fad’i. Dr ne ya kalle ni ya ce Ina zaki ne Zarah". Amsa mishi nayi da cewa "Side d’ina zan koma in kwanta". Murmushi yayi ya ce "Ai baki da gurin kwanciya da ya wuci nan d’akin a kuma jikin mijin ki". Sunkuyar da kaina nayi ganin yadda Dr yake son sa ni jin kunya. "Zo mu je ki kwanta kin ji Zarah ta" ya fad’i hakan yana rik’e min hannu. Bin shi nayi na hau can k’arshen gado na kwanta. Murmushi kawai yayi ganin in da na kwanta a k’arshen gadon, gadon ya kwanta. Duk da baccin da nake ji kasa baccin nayi saboda Dr da ya hau gadon. "Zarah" Dr ya kira suna na. Shiru nayi kamar mai bacci, dan yau a tsorace nake da Dr. "Zarah nasan idon ki biyu ba ki yi baccin ba, pls come close to me" Dr ya fad’a a hankali. Saboda tsoron da nake ji yasa na kasa matsa wa kusa dashi, hakan yasa ya matso kusa dani ya kwantar dani a jikin shi. Lumshe ido nayi saboda yadda jiki na da na Dr suka had’u, ga kuma rashin sabo. A hankali ya fara magana da cewa "Alhamdulillah, All praise be to Allah, yau Zarah ke ce a matsayin mata ta, ban san yadda zan fasalta farin cikin da nake ciki ba, nasan ba wayau na ko dubarata ba ce yasa na mallake ki a matsayin mata ta, sai dai in ma Allah godiya akan ni’imar da ya min da ya bani ke a matsayin mata ta, ke fa Zarah wani farin ciki kike ciki akan wannan ranar". A hankali na bud’e ido na da na lumshe na ce "Dr farin cikin da nake ciki baki na ba zai iya furta wa ba, Dr ina maka so wanda ni kaina ban san lokacin da ya min wannan kamun ba, sai dai in gode ma Allah da ya cika min burina na same ka amatsayin miji, alfarmar da zan nema a gurin ka shine Dr ka so ni kamar yadda nake son ka, ka rik’e ni amana, yanzu kaine gata na". Murmushi yayi ya fara cire min hijabin da ke jiki na, yayin da ya fara shafa min kaina da yasha retouching. "Kar ki damu Zarah, am yours, u a mine". Haka muka ci gaba da musayar kalamai masu kwantar da hankali. A hankali Dr ya canza hirar da salon soyayyar shi, sak’onni yake aika ma ko wani sassa na jiki na. Dr ya nuna min tsantar so mai wuyar fasaltuwa had’e da kulawa a wannan daren. Ranar na k’ara tabbatar da babu abin da yafi dad’i fiye da kasancewa da wan da kake so. Haka muka raya wannan daren irin yadda masoya ke kasancewa a daren su na farko. Haka muka tsarkake jikin mu muka koma muka kwanta. Da asuba Dr ne ya tashi ya d’auro alwala ya tafi masallaci yayi sallah. Sai da ya dawo daga masallacin sannan ya zo yana hura min iska a kunne. A hankali na fara bud’e ido na, dan har yanzu bacci ne a cikin ido na. Muna had’a ido nayi sauri na rufe ido na saboda wata irin kunyar shi da nake ji a yanzu. Murmushi yayi ya ce "Kunya ta kike ji, Sorry princess Zarah na tashe ki, sallah za ki tashi ki yi, in kika yi sallar sai ki zo mu kwanta, nasan jiya ban barki kin kwanta da wuri ba". A hankali na tashi saboda yadda na ji kasala da ciwon jiki ya kama ni, ga zazza’bi da yake so ya rufe ni. Tashi nayi na shiga toilet na d’auro alwala na fito na ta da sallah. Bayan na idar ne na yi addu’o’i na dawo na kwanta. Dr ne ya janyo ni jikin shi, zafin da yaji jiki na yayi ne yasa ya ce "Oh God, Zarah ni na yi causing d’in wannan fever ko, sorry me yasa ba ki fad’a min ba". Lamo nayi a jikin shi ban ce mai komai ba. Kwantar da ni yayi ya je ya had’o ruwan allura, da k’yar na tsaya ya min saboda yadda ba na son allura. Koma wa bacci muka yi ni da Dr, ba mu tashi ba sai wajen k’arfe takwas na dare. Side d’ina na koma na yi wanka na saka atamfa super Holland d’inkin riga da skirt, simple make-up nayi. Momin su Dr ce ta aiko mana da breakfast, Farida ce ta kawo breakfast d’in, mun gaisa cikin mutunci, ba yadda banyi da ita ta zauna mu yi breakfast ta ce min sauri take yi tana da lectures d’in safe, alamun ta na nuna ba ta da hayaniya. Ragowar naman kazan da muka rage na je na yi warming d’in shi a Oven, dashi muka had’a muka yi breakfast. Bayan mun gama breakfast ne ya bani magani na pain relief na sha. Dr ne ya sanar dani zai je gidan su Momi ya gaishe ta. Bayan tafiyar shi ne na tashi na wanke kayan da muka yi breakfast kana na je na gyara side d’in Dr. Ranar haka na dinga bak’i daga ‘yan uwana da ‘yan uwan Dr, Anisa ma da Halima da Aisha sun zo, da yamma Aisha da Halima suka min sallama suka tafi. Su Momi da Anty Zainab sun k’ara gyara gidan. An kai ni gidan su Dr an gabatar dani a matsayin matar Dr, an nuna ni gurin ‘yan uwan Dr. Gidan su Dr ba k’aramin had’uwa yayi ba, kai da gani kasan kud’i ya zauna a gidan. San da za mu tafi ne Momi ta ba da kud’i masu yawa a ba ni. Muna dawowa na shiga wanka na canza shiga ta cikin wani tsadadden less. Gidan ya rage daga ni sai Anisa, itama rok’on ta nayi akan ta bari Dr ya dawo sai ta tafi. Dr na dawowa Anisa ta kira Driver yazo ya d’auke ta. Da za ta tafi ne naje na d’akko mata turare da wani material da kayan make-up a cikin akwati na, sai da na nuna ‘bacin raina sannan ta amsa. Raka ta nayi bakin k’ofa inda na ce mata "Anisa pls ki dinga zuwa kin ji, ki gaishe min da yaya Khalil". Ganin yadda na marairaice ne yasa ta ce min "In ina free zan dinga lek’o wa, zan Isar da sak'on ki ga Yaya Kalil". Da haka muka yi sallama da ita na koma ciki. Yau ma haka muka kasance cikin nuna ma junan mu zallar so da k’auna. Sai da muka d’auki sati d’aya ba inda Dr yake zuwa kasancewar an bashi hutu a gurin d’aki, ko ya fita ba ya dad’e wa yake dawowa. Hanan da Farida sun zo sun wuni, ganin Hanan ba ta wani sake jikin ta mun yi hira ba yasa muka dinga hira da Farida. Yau da daddare da za mu kwanta ne Dr ya d’akko ruwa a cup da wani pills ya mik’o min. Bin shi nayi da kallo nayi ina jiran k’arin bayani. Cikin shagwa’ba na ce "Dr ai yanzu ba in da yake min ciwo". Kallon da yake sa ni a cikin wani shauk’i ya min kana ya ce "Wannan ba pain relief ba ne, na family planning ne". Da sauri na kalle shi dan gasgata maganar shi, ya za ayi sati na d’aya a d’aki na ya ce in fara shan pills na family planning. "Ban gane ba Dr, ni me zan yi da pills d’in family planning da za ka bani na sha" Na tambaye shi. "Ina so ki fara shan pills d’in ne saboda ina so ki huta kafin ki d’auki ciki, ba na so ki sha wahala wajen laulayin nan, kin ga kuma ina so ki koma School ki had’a HND d’in ki, kin ga yanzu ki na samun ciki za ki haihu, hakan zai sa ki raba hankalin ki gida biyu wajen rainon baby da karatun ki, ki bari in kika yi nisa a karatun ki sai ki daina shan pills d’in". Kallon Dr kawai nake yi san da yake min wannan bayanin, ni a gani na ban ga dalilin da zan sha wani pills ba, hasalima ni tsoro nake ji yadda ake samun matsala wajen yin family planning. "Dr ina ganin ba sai mun yi family planning ba, ka ga wani lokacin yana zuwa da matsala, kuma ni ina ganin baby ba zai hana ni karatu ba, ina ganin a bar zancen family planning d’in nan, Sai ka ga ma Allah bai kawo cikin da wuri ba ko da ba ayi family planning d’in ba". Dr haka ya ci gaba da fahimtar dani akan in yi hak’uri in sha pills d’in amma na k’i, hakan yasa ranshi ya ‘baci ya ce in tashi in koma side d’ina. [7/24, 22:37] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa Writers Association *QUESTION OF THE DAY* _Wace surah ce take karantar da wajibcin tsare hakk’ok’in mutane, tsakaninsu, a ciniki da wasu mu’amalolin zamantakewa_. 75-76 Ina fita daga side d’in Dr na wuce side d’ina na zauna a kan gado. Tunani na ci gaba dayi akan pills d’in da Dr yake so in sha daga yin auren mu da sati d’aya, duk da hujjojin da ya bani bai gamsar dani ba da zai sa in fara shan maganin tsarin iyali ba tare da na jira na ga tsarin da Allah ya tsara min ba. Nasan Dr k’wararre ne a ‘bangaren aikin shi, ba zai bani pills d’in da zai zamar min illah ba amma ni a nawa ganin kamar yayi wuri in fara shan pills d’in family planning. Abin da yafi min yawo a raina shine akan wannan matsalar muka samu matsala da Dr, ban yi tunanin wannan matsalar zai sa Dr yayi fushi dani har yace in koma side d’ina. Ni ina da nawa dalilin na k’in ba Dr had’in kai wajen bijire ma shan pills d’in da yake so in sha in nayi duba da ko wata ban yi ba da yin aure amma yake so in sha pills, na sha samun labarin yadda wasu suke samun matsala a yayin da suka yi family planning, wasu ma dalilin daina haihuwar su kenan a yayin da suke so Allah ya basu yaran da sauran matsalolin da suke biyo baya a dalilin yin family planning d'in. Hujjar da Dr ya bani na cewa yana so in yi karatu na ba tare da matsala ba da kuma tausaya min laulayin ciki da zan yi idan na samu ciki shine hujjar shi akan in sha pills bai ishe ni hujjar da zan yi dogaro da ita wajen amince ma buk'atun shi. Haka na ci gaba sak’a da warwara akan samo mana mafita tsakani na Dr, dan ba na so wannan matsalar ta zama hanyar rusa mana farin cikin mu da muka fara gina wa a rayuwar auren mu. Zuciya ta ce ta dinga ba ni shawarar akan in amince da buk’atar da Dr yazo min dan nasan ba zai cutar dani ba. Da wannan na yanke shawarar akan gobe in Allah ya kaimu zan shaida ma Dr na amince da buk’atar shi. Haka na kwana cikin kad’aci saboda yadda na saba kwanciya a jikin Dr, ya min sabo da jikin shi. Washegari haka na tashi na had’a mana breakfast na jera a dinning table. D’akin Dr na wuce inda na same shi har yayi shirin shi na tafiya aiki kasancewa ranar zai koma aiki yana sa socks. Kallon-kallo muka yi ni dashi kana Dr ya kau da fuskar shi ya ci gaba da sa socks d’in shi. Murmushi na yi na k’arasa kusa dashi na zauna. "Good morning Dr" na fad’a. "Morning Zarah". "Dr fushi kake yi dani?" na fad’a cikin shagwa’ba. Tsadadden murmushin shi ya min kana ya shafa fuska ta ya ce "Me kika gani Zarah, ni ba fushi nake yi dake ba". Kwantawa nayi a kafad’ar shi yayin da na fara magana a hankali na ce "Dr kayi hak’uri akan abin da ya faru jiya da daddare, ba wai na k’i amincewa da buk’atar ka bane saboda nasan ba za ka ban abin da zai cutar dani ba, sai dai ina ganin kamar in na fara shan pills a yanzu yayi wuri sannan ina ganin wasu da suke samun matsala a dalilin yin family planning d’in su shi yasa ka ga na k’i amincewa, amma yanzu na amince da buk’atar ka dan nasan ba za ka mana abin da zai zamar mana matsala ba". Rungume ni yayi ya bani peck a goshi na saboda murnar amincewar da nayi. Hannu na ya rik’e yana murmushi ya ce "Zarah kin san ina son ki, ba zan yi abin da zai zamar mana matsala ba, pills d’in nan da za ki sha bai da matsala, kamar yadda na fad’a miki dalili na shine ya zama na mun yi planning yadda za mu tsara marriage life d’in mu, amma in har a cikin zuciyar ki ba ki amince ba shi kenan sai a bar shan pills d’in" ya k’arasa maganar yana kallo na. Murmushi na yi na ce "Na riga na amince Dr". "Thanks my lovely Zarah" ya fad’a cikin jin dad’i. Hannun shi na rik’e muka wuce dinning muka yi kalaci kana ya wuce gurin aikin shi. Tun daga wannan lokacin Dr ke bani pills na family planning ina sha. Zaman mu ya ci gaba da gudana cikin kulawa da so da k’auna, cikin d’an lokaci na canza nayi fresh, ga wani kyau da na k’ara. Yaya Faruk tun komawar shi Abuja yaci gaba da gudanar da aikin shi, yana k’ok’arin ganin ya cire duk wata damuwa da ka iya jawo mishi wata matsalar. Yanzu ba shi da wata sauran damuwa, aikin shi da ya k’ara sa wa a gaba, a yanzu ya k’ara nisanta kan shi da ‘yan mata dan gudun fad’a wa halin da ya shiga wanda har yanzu bai gama jin rad’ad’in abin a ran shi ba. Nana na iyakar k’ok’arin ta ganin ta cire ma yaya Faruk damuwar da yake ciki, duk da a yanzu ba wani alamu da ke nuna yana cikin wani hali na tunani ko damuwa, sai dai tausayin halin da ya shiga a dalilin abin da na mishi yasa tun san da suka je Kaduna ya fad’a mata fasawar auren shi da ni taji ta kasa samun natsuwa, ta sa a ranta za ta faranta ma yaya Faruk dan ya manta da abin da na mishi, a yadda ta d’auki yaya Faruk jin shi take yi kamar yaya Mus’ab, shi yasa take fad’i tashi akan ta ga yaya Faruk bai da wata damuwa, damuwar da Nana ke nuna wa akan shi yana sa yana k’ara ganin girmanta a idon shi. Nana ce ke zaune a falo ita da Hajiyar su suna hira, wayar ta ce tayi k’ara alamar kira ya shigo, tana jin k’arar wayar amma ta k’i d’agawa. Ganin ta k’i d’aukar wayar ne yasa Hajiya ta kalle ta tace "Nana ba kiran ki ake yi ba ne ki ka k’i d’aukar kiran". Cikin shagwa’ba ta ce "Hajiya Mukhtar ne fa yake kira". Kallon ta Hajiya tayi kana ta ce "Dan Mukhtar ne sai ki k’i d’aukar wayar, Nana me yasa kike haka ne, duk wanda yazo gurin ki sai kin ce bai miki ba, kullum fa k’ara girma kike yi, kuma ni ban ga aibun Mukhtar ba da ba kya son shi, yaro mai natsuwa da tarbiyya amma ke kin ce bai miki ba, ina laifin Wanda ya ce yana son ka". Marairaicewa tayi ta ce "Hajiya na fa bashi hak’uri tun san da ya fad’a min yana so na amma ya k’i ya hak’ura, ba na so in ci gaba da tsayawa dashi daga baya ya ga kamar na yaudare shi alhalin tun farko na bashi hak’uri ya hak’ura dani, ni kaina nasan Mukhtar bai da wata matsala ta a zo a gani, kawai dai ba na jin son shi ne, sauran kuma da suke zuwa guri na yawanci behaviours d’in su ne ba su min ba". Hajiya ce ta ce "Amma dai kin san yadda Dadin ku ya d’auki Mukhtar kamar d’an shi, kin san yadda amincin su yake da mahaifin shi Alhaji Ashiru, ni dai ba ruwa na in Dadin ku yaji abin da kike mai, ke ma kin san sai ran ki ya ‘baci". Suna cikin wannan maganar ne yaya Mus’ab ya shigo falon da sallamar shi. Gaisawa suka yi kana ya kalli Hajiya wacce taci gaba da yi ma Nana fad’a akan rashin kula samarin da take yi ya ce "Hajiya yau dai an ji kan ku ke da autar ki, tun da na ga sai fad’a ake mata". "Ba dole ka ji ni da Nana ba, na zuba mata ido amma ita ba tasan haka ba, yau in wannan yazo gurin ta tace bai mata ba yana da matsala kaza, gobe ma in wani yazo haka za tace, ga yaron nan Mukhtar da yake son ta shima ta ce bai mata ba, a cikin su ta kasa tsayar da wanda ya mata, ni na fara gajiya da irin halin Nana cewar Hajiya. Murmushi yaya Mus’ab yayi kana ya ce "Gaskiya Nana ba ki kyauta ba, duk ma su zuwa gurin ki a ce ba Wanda ya miki, ya kamata ki tsayar da wanda ya kwanta miki a ranki, ko Mukhtar da mahaifin shi yake da wani matsayi a garin nan ba na ganin yana wani abu da za a ce bai kamata ba, yana da natsuwa". Cikin sanyin ta tace "Ni fa yaya Mus’ab ba wai na ce Mukhtar yana da wata matsala ba ne, just kawai ba na jin son shi a raina ne". Murmushi yaya Mus’ab yayi ya ce "Hajiya ki k’yale ta tun da ta ce duk ba su mata ba, lokaci in yayi sai ki ka ga ta kawo miki surukin ki har gida ko Nana?" ya k’arasa maganar da wasa yana kallon ta. Murmushi tayi ta rufe fuskar ta alamar jin kunya. Hajiya ce ta kar’bi zancen da cewa "Ai shi kenan tun da kana goyon mata baya, Allah ya za’ba mana abin da yafi alkhari". Dukkan su suka amsa da Amin. Nan suka ci gaba da hira kana ya musu sallama ya tafi. Yau Yaya Faruk yana zaune a falon shi yana kallon wasan k’wallon k’afa da ake watsowa a tashar New world sport, idon shi ne ke kan talabajin d’in, amma hankalin shi na wani gurin. Sallamar da yaya Mus’ab yayi yaji shiru ne yasa ya shigo falon. Ko da ya shigo falon, yaya Faruk hankalin shi ba ya gurin bare yaji shigowar yaya Mus’ab. Dafa kafad’ar shin da yayi ne ya dawo dashi daga duninyar tunanin da ya tafi. Ganin yaya Mus’ab ne yasa ya saki murmushi tare da cewa "yaushe ka shigo ne?". Shima murmushin ya maida mai ya zauna a kujerar mai kallon ta yaya Faruk ya ce "Ai ba za kasan shigowata ba tun da kana duniyar tunani". Hararar shi yaya Faruk yayi cikin wasa kana ya ce "Ni na fad’a maka tunani nake yi, kawai dai hankali na yana kan ball d’in da ake buga wa a Tv ne". Dariya yaya Mus’ab yayi ya ce "Amma wannan ball d’in ta iya d’aukar hankali tun da har tasa nayi sallama ba kaji shigowa ta ba sai da na dafa ka sannan ka dawo daga duniyar wasan k’wallon da ake bugawa a Tv d’in". Wannan karan yaya Faruk bai ce komai ba sai ma murmushi da ya ci gaba da yi. "Faruk ni nasan tunani ka ke yi amma ba ka so ka fad’a min, duk wanda ya zo ya tarar da kai a halin da kake yasan kayi nisa ne a cikin tunani, plss Faruk ka rage tunanin da kake yi saboda samun inganci a lafiyar ka, nasan tunanin da ka ke yi ba zai rasa nasaba da Fatima ba" yaya Mus’ab ya fad’a cikin kulawa. Watsa mishi wani kallo yaya Faruk yayi ya d’aura da cewa "Kai fa Mus’ab sa idon ka yawa ne dashi, ni na ce maka tunanin Fatima nake yi, ba dama in yi shiru sai ya zama tunanin Fatima na ke yi". "In ma ba ka fad’a ba, yanayin ka ya nuna haka, ya kamata Faruk ka cire Fatima a ranka tun da tayi aure, nasan Fatima sai ta maka wuyar fita a zuciyar ka saboda son da kake mata, nasan abu ne mai ciwo gurin cire wanda kake so a cikin ran ka, sai ka ci gaba da dauriya da jajurcewa sannan za ka manta ta, tun san da abin nan ya faru Faruk ba ka dawo asalin Faruk d’in ka ba, ko gurin aiki duk ka canza, kai kan ka kasan da haka, dan Allah Faruk kayi k’ok’ari ka manta da komai, sai ka ga komai ya zama daidai" cewar yaya Mus’ab. Gauron numfashi yaya Faruk ya ja kana ya ce "Mus’ab na san Fatima tayi min nisa tun da a yanzu tana d’akin mijin ta tare da masoyin ta wanda suke son junan su, nasan ci gaba da tunanin ta a raina laifi ne babba tun da matar wani ce, kamar yadda na ce ne na hak’ura da Fatima to hakan yake a guri na, sai dai ba zan ‘boye maka ba Mus’ab, ban san me yasa zuciya ta wani lokacin take bijiro min da tunanin ta ba, ni kaina ina iya k’ok’arin ganin na manta da ita a zuciya ta dan ban ga amfanin tunanin ta da yake haifar min ba sai ‘bacin rai da kuma zunubi da nake d’aukar ma kaina". Ci gaba yayi da cewa "Plss Mus’ab ka taya ni da addu’a, ni kaina ba na so in dinga kasancewa a halin tunanin Fatima bayan nasan ta min nisa" ya k’arasa maganar cikin damuwa. Tausayin yaya Faruk ne ya kama yaya Mus’ab, yasan son da yaya Faruk yake min ba abu ne mai sauk’i da zai yi saurin cire ni a ranshi, yasan abu ne mai ciwo rabuwa da masoyi, ji yake yi kamar shine hakan ya faru dashi, dan ya d’auki yaya Faruk kamar d’an uwan shi ba wai aboki kad’ai ba. Yaya Mus’ab ne ya ce "Insha Allah Faruk zan ci gaba da taya ka addu’a akan Allah ya kawo maka sauk’in halin da kake ciki, sai dai hanya d’aya ce za ta kai ka ga manta Fatima cikin sauki tare da samun natsuwa". "Wace hanya ce wannan Mus’ab" yaya Faruk ya tambaya. "Ba ko wace hanya ba ce da ya wuce ka samu abokiyar rayuwa kayi aure, in dai ka bi wannan hanyar za ka samu maslaha a halin da kake ciki, dan aure yana kore damuwa yasa mutum cikin natsuwa" yayaMus’ab ya bashi amsa. "Mus’ab ba na ganin zan yi aure nan kusa, saboda a yanzu na k’ara d’aukar darasi akan ‘yan mata, ba ko wace mace ba ce za ta yi maka so tsakani da Allah, hakan yasa na ke kauce musu, sai gashi Allah ya jarabce ni da son ‘yar uwa ta Fatima, amma ba ta saka min da komai sai ‘bacin rai, kana ganin yanzu in na k’ara fad’a wa son wata yarinyar na san ita kuma wani salon za ta zo min dashi, zan dai ci gaba da addu’a akan Allah ya kawo min mafita sannan in lokacin aure yazo sai in yi" cewar yaya Faruk. Yaya Mus’ab ne ya ce "Faruk ya kamata ka gane kullum lokaci wuce wa yake yi, bai kamata ka ce ba yanzu za ka yi aure ba saboda abin da Fatima tayi maka, ba kowace mace ba ce mai irin halin Fatima, ita tayi hakan ne dan ganin ta samu cikar burin ta, shi yasa ta biyo ta wannan hanyar dan bijire ma auren ka, ka duba ‘yan mata na wa ne ke son ka amma kai ba su dame ka ba, ya kamata ka fuskanci rayuwar ka ta gaba shine ka samu kayi aure kamar yadda na fad’a maka, kai kan kasan su Dadi ba za su ji dad’i su ga ka k’i fitowa da matar aure ba". Shiru yayi kamar ba zai yi magana ba kana ya ce "Nasan duk abin da ka fad’a min gaskiya ne, sai dai a yanzu ban jin zan iya tsayawa in nemi wata yarinyar, sai dai in bari su Dadi ko Momi su za’ba min wacce suke so ko da ba na son ta zan iya hak’urin zama da duk wacce suka za’ba min dan in faranta musu". Kallon shi yaya Mus’ab ya yi saboda yadda yaya Faruk yake wannan maganar yasan har cikin zuciyar shi yake fad’ar wannan maganar, a yanzu yana ganin zai isar mishi da sak’on da zuciyar shi ke yawan bashi yana kore wannan tunanin daga ranshi, saboda yana ganin wannan hanyar ce kad’ai za ta fitar da yaya Faruk daga halin da yake ciki. "Idan ka bani dama ni zan za’bar maka wacce za ta dace da rayuwar ka" yaya Mus’ab ya fad’a yana ci gaba da kallon yaya Faruk dan ganin yadda zai kar’bi zancen. Wannan karan sai da yaya Mus’ab ya yi dariya dan yasan yaya Mus’ab akwai shi da son wasa, dan haka cikin wasa ya ce "Na baka wannan damar Bregadier Mus’ab Dadin Asim". Shima Mus’ab d’in dariya yayi kana ya ce "A ture maganar wasa Bregadier Faruk, maganar da na ke fad’a maka da gaske nake yi, na za’bar maka matar da za ta dace da kai, sai dai ban san kai ko za ka yi marhabin da ita ba a zuciyar ka". Ganin yadda Mus’ab d’in ya yi maganar yasan ba wasa yake mai ba, dan haka ya daure ya ce "Wace yarinya ce ka za’bar min". "Nana Khadija ita na za’bar maka, ita nake ganin za ta dace dakai, ta kuma taimaka wajen mantar da kai damuwar da kake ciki kasancewar yadda kuka shak’u da ita…". Duk da yaji abin da yaya Mus’ab d’in ya fad’a, amma sai zuciyar shi ke k’aryata mishi maganar da ya ji yaya Mus’ab d’in na fad’a, don haka ya katse shi da cewa "Wai wace Nana Khadijan?". Murmushi yaya Mus’ab yayi saboda yasan dama dole yaya Faruk ya shiga rud’u a yayin da ya fad’a mishi sirrin zuciyar shi. "Cool down Faruk, nasan ka gane Nana Khadijan da nake nufi, amma tun da ka na buk’atar k’arin bayani, Nana k’anwa ta nake nufi, ita na za’bar maka". Kallon shi kawai yaya Faruk yake yi ba tare da ya bud’e baki ya k’ara cewa komai ba saboda yadda maganar ta zo mishi a bazata da bai yi tsammanin ta ba, bai san a yadda zai d’auki maganar da yaya Mus’ab yazo mishi da ita ba. Shiru ne ya ratsa falon na wani lokaci kana yaya Faruk ya d’ago kanshi ya kalli yaya Mus’ab ya ce "Mus’ab nasan kana son ganin farin ciki na, ka damu da damuwa ta, son da muke ma junan mu daga Allah ne, amma ina ganin bai kamata dan kana son ganin farin ciki na ka yanke hukunci ba tare da kaji ra’ayin Nana ba, za ta iya yiwu tana da wanda su ke soyayya, kai kuma ka yanke hukunci dan ganin ka samar min da mafita, ba zan so in shiga hakk’in Khadija ba, ba zan so ta d’auke ni a mara adalci ba alhalin tana ganin girma na, ta na ba ni matsayin wa a gurin ta, ni ma k’anwa take a guri na, zan so ganin ci gaban ganin farin cikin ta". "Faruk kan in yanke wannan hukuncin sai da nayi nazari a kai, Nana tana da samari masu son ta, sai dai har yanzu ta kasa tsayar da hankalin ta wajen za’ben guda d’aya daga cikin su, hakan yasa Hajiya ta ke mata fad’a akan ta tsayar da miji tayi aure, nasan Nana ba za ta k’i bin umarni na ba in har na fad’a mata na za’bar mata miji, tasan ba zan zan mata za’ben tumun dare ba, shi ya sa ka ga na zartar da wannan huknci, nasan Nana ba za ta bijire ma umarni na ba, sai dai ko kaine Nanan ba ta kwanta maka a cikin ran ka ba, ko ba ta daga cikin tsarin matan da kake so". Wannan hujjojin da Mus’ab ya bashi ya k’ara d’aure shi da jijiyoyin jikin shi, yasan yaya Mus’ab na mishi haka ne dan ya samar mishi da farin ciki, sai dai har yanzu bai san a yadda zai d’auki maganar ba, shi dai yasan Nana na ya d’auke ta kamar k’anwar shi, sannan kyawawan halayen ta na daga cikin abin da yasa ya ke k’ara ganin k’imarta a idon shi, a yanzu ba zai yi saurin yanke hukunci game da ita ba, dan shi bai ta’ba kawo Nana a ranshi a matsayi na daban da ya wuce matsayin k’anwa da ya ba ta, duk da yaya Mus’ab ya fad’a mai cewa ba ta tsayar da gwanin ta ba, yana tsoron kar ya zamana a ranta ita ba ta ra’ayin shi, hakan zai zama da cutar wa kenan. Jin shirun da yaya Faruk yayi ne yasa Mus’ab ya katse shirun da cewa "Faruk kar ka duba kusanci mu ka cutar da kan ka, in har Nana ba ta maka ba ka fad’a min, ni zan fahimce ka". Mik’ewa yayi yaci gaba da cewa "Zan baka time kayi tunani akan wannan maganar, duk hukuncin da ka yanke akai ina marhabin dashi". Har ya zuwa wannan lokacin yaya Faruk ya kasa bud’ar baki yayi magana saboda a yanzu bai san wani hukunci zai yanke ba. Hannu yaya Mus’ab ya bashi suka yi musabaha kana ya mishi sallama ya tafi. A can ‘bangare na kuwa soyayyar mu muke ci gaba da sha ni da Dr, yanzu ba ni da wata sauran matsala ko damuwa a raina, shi yasa da ka ganni kasan ina cikin kwanciyar hankali da natsuwa. Yau Dr ne ya kira ni akan in shirya in ya dawo daga aiki za mu je mu gaishe da su Ummu da Momin shi. Murna ta bi ta cika ni saboda yau ce ranar da zan fara fita tun bayan aure na, ba irin rok’on da ban mishi ba akan ya kai ni gurin su Ummu amma sai ya ce in ba yanzu ba. Ko da ya dawo sai da ya ja min rai ganin yadda na k’osa mu tafi, sai da yaga zan mishi kuka sannan ya ce in zo mu tafi. Sai da ya tsaya a wani babban super market ya siya ma su Momin shi da Ummu turarruka masu tsada sannan muka tafi. Gidan mu muka fara zuwa, yana parking na fito da gudu na nufi side d’in yaya Khalil saboda na ga motar shi a parking space, ganin ba ya side d’in shi yasa na fito na nufi main Parlour. Sallama nayi na fad’a jikin Ummu na rungume ta ina murna, ita kan ta dariyar farin cikin gani na take yi. Ina sakin ta na wuce kusa da yaya Khalil na zauna ina murmushi. Shima murmushin yake maida min saboda murnar gani na da yayi. "Yau Auta ce a gidan namu" yaya Khalil ya fad’a cikin wasa. "Ni ce yaya Khalil, nayi missing d’in ku a lot, especially you Yaya Khalil" na fad’a cikin shagwa’ba. Murmushi yayi kana ya ce "Nima nayi missing d’in ki Fatima, gidan ya min fad’i da ba kya nan". Ummu ce ta kar’bi zancen da cewa "Au haka ma za ki ce Auta, kin fi missing d’in yayan ki akan mu ko, ai shi kenan". Dariya muka yi gaba d’aya na ce "Kema kin san Ummu dole ne in yi missing d’in ku ke da Abbu". "Ina wuni yaya Khalil na gaishe shi. "Lafiya lau Fatima" Yaya Khalil ya amsa min. "Ina wuni Ummu" "lafiya lau Fatima, ya mai gidan naki?" Ummu ta fad’a. Sai a lokacin na tuna da na bar Dr d’in a waje tun san da muka shigo gidan. "lafiya lau, tare muke ma dashi". Ummu ce ta ce "yanzu tare ku ke shine ki ka barshi a waje dan shashanci, tashi ki je ki shigo dashi". Tashi nayi na fita inda na same shi jingine a jikin mota. Da murmushi na k’arasa gurin shi na ce "Sorry Dr, murnar zuwa gida ne yasa na tafi ciki na barka". Shima murmushin yayi kana ya ce "Don’t mind Zarah, nasan murnar ganin su Ummu ne yasa ki ka manta da Dr d’in ki a waje, na miki uzuri". Turarrukan da ya siya ma su Ummu ya bani kana muka jera dashi har main parlour d’in. Sun gaisa da Ummu da yaya Khalil kana ya musu sallama akan zai je ya dawo sai ya kai ni gurin Momin shi. Mun sha hira da Ummu da yaya Khalil kamar kar mu rabu, sai dai har Dr yazo d’auka na Abbu bai dawo gida ba, na so mu had’u dashi yadda na kwana biyu ba mu had’u ba. Da za mu tafi ne na ba Ummu turaren, fuskarta ta nuna jin dad’in kyautar da muka yi musu. Haka na musu sallama muka tafi muna kewar juna. Gidan su muka wuce in da muka same su a falo suna hira. Bayan mun gaisa ne Farida ta cika gaban mu da kayan motsa baki. Ba laifi Momi ta tarbe ni, yawanci hirar dai ita da d’an ta suke yin ta ina sauraron su. Farida ce take ja na da hira jefi-jefi, ji nayi duk na takura kasancewa ta wannan shine zuwana na biyu da nayi, ga kuma rashin sabo da ban yi dasu ba. Muna zaunen ne a falo sai ga Hanan sun shigo da wata matashiyar yarinya. Shigar da suka yi ne ta d’aure min kai, in mutum ba yasan yaran hausawa ba ne bai zama lallai ya yarda ba, saboda wani irin English wears da suka sa da d’an wani k’aramin gyale da suka yafa a kansu. Abin da ya ban mamaki shine ganin ba wanda ya musu fad’a akan shigar da suka yi. Su biyun gurin in da Dr yake suka je suka zauna yayin da suka sa shi a tsakiyar su. Ni dai bin su da kallo kawai nake yi saboda mamakin su da ya kama ni. "Ina wuni yaya Sadik" Meema ta gaishe shi. Da murmushi ya amsa mata da cewa "Lafiya lau Meema, ya kike, ya su Mom". Cikin siririyar murya ta amsa masa "Su na nan lafiya lau yaya Sadik". Hanan ce ta kar’bi zancen da cewa "Ina wuni yaya Sadik". "lafiya lau Hanan, ya karatu?" ya tambaye ta. "Normal yaya Sadik" Hanan ta amsa mishi. "yaushe ka zo ne yaya Sadik" Meema ta tambaye shi. "Ba mu dad’e da zuwa ba ni da Zarah, ku gaisa da ita" Dr ya fad’a. Sai a lokacin hankalin su yakai guri na da nake zaune a d’aya daga cikin kujerun da suka k’awata falon. Kallo na yayi ya sakar min murmushi kana ya ce "Zarah ga Hanan da Meema". Murmushi na musu kana na ce "Sannun ku, Ina wunin ku". Hanan ce ta amsa min ba yabo ba fallasa da cewa "lafiya lau, ya kike". Ban ba ta amsa bad an gani nayi kamar tambayar rainin wayau ta min. Meema kuwa tun san da Dr ya ce mu gaisa ta tsura min ido tana kallo na, kallon da take min ne na rasa yadda zan fassara shi dan nasan irin kallon da take min yana d’auke da ma’anoni daban-daban. Yatsina fuska ta yi kana ta ce "Hi Zarah". Yadda ta amsa min gaisuwar ya min ciwo amma sai na share abin a raina kamar abin bai yi min ciwo ba. Momi ce ta ce "Har kun dawo kenan Meema, na ga ba ku dad’e ba". "Ice cream kawai muka je muka sha muka dawo gida" Meema ta fad’a. "Ok dama na ga kun yi saurin dawowa ne" cewar Momi. Wacce aka kira Meema na dinga tunanin ita wacece a gidan su Dr, a iya sani na Hanan da Farida sai Su ne k’annen shi mata, ita Meeman ce ban san ya suke da ita ba. Ba laifi Meema kyakkyawa ce, dan ba za ka kira ta mummuna ba, skin d’in ta so fresh, daga gani mayuka masu tsada take shafawa, sai dai a yanayin ta in ka kalle ta kasan rayuwar boko take yi ita da Hanan, shigar su kad’ai ta isa ta nuna maka haka, ganin yadda take shige ma Dr sai abin ya ‘bata min rai, na ga shi Dr hakan bai dame shi ba, sai dai kallon da Meema ta min ne yasa na dinga tunanin dalilin ta na yi min wannan kallon, ni dai a iya sani na yau ne muka fara had’uwa da ita, sai dai fuskarta ta nuna min ba tayi marhabin da ni ba. Hirar su suka ci gaba da yi suna dariyar su da Dr yayin da Momi kan sa bakin su a hirar. Jin ban sa baki na a hirar yasa Farida da Dr kan sako ni cikin hirar tasu, ganin hirar ba ta shafe ni ba yasa nayi shiru da baki na, sai dai in sun saka ni a hirar in yi murmushi. Mun d’an jima a gidan su Dr, da za mu tafi ne na ba Momi perfumes d’in da muka zo mata dashi kana muka yi musu sallama muka tafi. Haka muka koma gida raina bai min dad’i dan gaskiya yadda na ga Meema na shige ma Dr bai min dad’i ba. Yaya Faruk tun san da suka yi wannan maganar da yaya Mus’ab ya ke tunanin hukuncin da ya kamata ya yanke akan maganar amma ya kasa, gashi suna had’uwa da yaya Mus’ab a gurin aiki amma bai canza mishi fuska ba ko ya mishi magana akan hukuncin da ya yanke, yasan yaya Mus’ab ba zai mishi magana ba dan kar ya ga ya takura mishi, yasan ya zuba mishi ido ne ya ji hukuncin da zai yanke akan maganar, a yadda ya lura yaya Mus’ab bai fad’a ma Khadija maganar ba tun da ba ta sauya mishi ba, kuma har yanzu suna waya suna gaisawa. "Me yasa ba za ka amince da maganar da Mus’ab ya zo maka da ita ba ko dan shim aka faranta mishi?" zuciyar shi ta fad’a mishi haka. Shi kanshi yasan Mus’ab mai son shi ne tsakani da Allah tun da har yayi tunanin bashi k’anwar shi duk kuwa da masoyan da take dashi, yasan ba abin da ya kamata ya saka ma Mus’ab dashi shine ya amince da Khadija ko da kuwa bai jin son ta a ranshi. Har yanzu yana jin Nana a ranshi kamar k’anwar shi, tana bashi matsayi kamar na yayan ta, sannan tana nuna damuwar ta idan wani abu ya same shi, tana taya shi farin ciki idan abin alkhairi ya same shi, tun san da suka yi maganar nan da yaya Mus’ab har zuwa yanzu bai ji wani feeling na son ta daga zuciyar shi, sai dai zai iya ma Mus’ab komai dan yafi k’arfin komai a gurin shi. Yasan Nana yarinya ce da kowane namiji zai so ta saboda kyawawan halayen ta, sannan tana da kyau d’in da duk namijin da ya ganta zai iya kamuwa da son ta, ya sa ma ranshi zai auri Nana in har ta amince dashi, sannan ko su Momi in suka ji ya samu wacce zai aura za su ji dad'i a ransu, sannan za su yi murna idan su ka ji k'anwar Yaya Mus'ab zai aura za su yi farin ciki da hakan. Wannan tunanin da yayi ne ya yanke cewa zai tunkari yaya Mus’ab ya fad’a mishi ya amince da Nana. Da wannan shawarar ya samu k’arfin d’aukar wayar shi ya kira yaya Mus’ab akan in ya samu lokaci yana neman shi za su yi wata magana ne kana ya katse layin shi. Ba a wani jima ba sai ga yaya Mus’ab ya zo block d’in yaya Faruk. Bayan sun d’an ta’ba hira ne yaya Faruk ya fara da cewa "Mus’ab na kira ka ne akan maganar da ka zo min da ita kwanaki, nasan za kayi tunanin ko ban amshi zancen ka da mahimmanci ba ne shi yasa ban tuntu’be ka akan maganar ba, Mus’ab ko da a ce wata ka za’bar min in har ka yaba da tarbiyar ta da kamalar ta zan amshi maganar ka hannu bibbiyu bare Nana Khadija da take k’anwar ka, ko da ba ka fad’a min halin Nana ba ni shaida ne a zaman da nayi da ita akan kyawawan halayen ta da natsuwar ta, Mus’ab na amince da Nana, sai dai zan rok’i alfarma a gurin ka Mus’ab shine ka fad’a ma Khadija wannan maganar, in har ba ta amince ba kar ka matsa mata akan dole sai ta amince, ka fad’a min shawarar da ta yanke akan maganar, zan yi farin ciki idan ta amince, sannan ba zan ji haushin ta ba idan ba ta amince da ni ba". Murmushi yaya Mus’ab yayi kana ya ce "Kar ka damu Faruk, zan fad’a maka duk yadda muka yi da Nanan". Nan suka ci gaba da hirar su akan abin da ya shafi aikin su kana ya mishi sallama ya tafi. [7/29, 22:06] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa Writers Association *Gaisuwar ku ta daban ce a guri na ‘yan Kainuwa Writers* *Mrs Mansoor* _(Marubuciyar Munafukin Miji)_. *Fauxia MB* _(Marubuciyar Conel Akram)_ *Mrs Adam* _(Marubuciyar Mamaya)_ *Ummy Ontop* _(Marubuciyar Kishiya tace Silah)_. *Shatu* _(Marubuciyar Mai Rabo ka D’auka)_ *Hauwa A Usman* _(Marubuciyar Kaddara Tah)_ *Batul Adam Jatko* _(Marubuciyar Amfanin Soyayya)_ *Mrs Makama* _(Marubuciyar Ranar Baiko Na)_ *Maman Aysha* _(Halin Mutum Jarinsa)_ *Wanda ba su ji sunan su ba, su min hak'uri mu had'u a next page*. *Ana tare ko da yaushe*. _Amsar question of the day ita ce Suratul Mud’affifun, ita ce take karantar da wajibcin tsare hakk’ok’in mutane, tsakaninsu, a ciniki da wasu mu’amalolin zamantakewa_ *TUNATARWA*: _Wad'annan halayen guda uku lallai suna daga cikin halayen bayin Alah na k’warai, kuma wanda yayi rik’o dasu tabbas zai zama abin yabo a wajen Allah da bayin sa_. _Yin afuwa ga mutane_. _Biyan Bashi da ka samu iko_ _Karanta qul huwal lahu ahad_ _Allah kasa mu dace_ 77-78 Yaya Mus’ab da ya samu sauk’in aiki ne ya je gidan su dan jin ra’ayin Nana akan maganar da suka yi da Yaya Faruk. Lokacin da ya je bai sami Nana a gida ba tana school. Zama yayi suka ci gaba da hira, ba a wani d’au lokaci ba sai ga Nana ta dawo daga makarantar. Bayan sun gaisa ne ya ce ta same shi a side d’in shi in ta huta. Tana gama abin da za tayi ta nufi side d’in yaya Mus’ab d’in. Samun shi tayi yana kallon tashar Al- Jazeera ta nemi guri ta zauna. Yaya Mus’ab ne ya kalle ta ya ce "Nana nasan za ki yi ta tunanin dalilin kiran da nake miki da har na ce ki same ni a side d’ina ko?". Ci gaba yayi da cewa "Kiran mai matuk’ar mahimmanci ne da har ya sa na kira ki nan d’in dan nasan za ki fi sake wa ki fad’a min ra’ayin ki akan maganar da za mu yi, Nana maganar da za muyi akan Faruk ne, nasan kin san abin da ya faru da shi na fasawar bikin shi da aka yi, Nana Faruk yana cikin damuwa wanda yake buk’atar mai lallashin shi a kusa, Faruk yana da zurfin ciki, hakan yasa yake k’ok’arin ‘boye damuwar da yake ciki, Faruk aboki na ne da ya taimaka min a gurin aiki da sauran harkar rayuwa, shi yasa nayi tunanin wace hanya ce zan fitar da Faruk daga halin da yake ciki, dan haka ne na yi tunanin ba wacce za ta cire shi daga wannan halin da ya wuce ke saboda yadda kuka shak’u". D’ago kai tayi ta kalle shi kana ta ce "yaya Mus’ab ta wace hanya zan iya cire ma yaya Faruk damuwar da yake ciki, ina ganin in ma akwai hanyar bai wuce in ci gaba taya shi da addu’ar Allah yaye mishi damuwar da yake ciki, ya kuma za’ba mishi abin da yafi alkhairi a gare shi". Murmushi yaya Mus’ab yayi kana ya ce "Nana akwai hanyar da za ki bi wajen mantar da Faruk daga halin da yake ciki, hanyar kuwa ita ce ki aure shi". Da sauri Nana ta d’ago kai ta kalli yaya Mus’ab dan gasgata kunnuwan ta abin da suka ji mata da yadda maganar ta zo mata a bazata. Tasan tana jin yaya Faruk a ranta, tana jin wani irin feelings game dashi wanda ita kanta da farko ta danganta shi da had’uwar jini ne, sai daga baya da ta ci gaba da jin feeling d’in fiye da baya ta tabbatar ma kanta cewa wannan feeling d’in ya wuce had’uwar jini, sai dai ita kanta ta rasa a yadda za ta fassara shi. Tana damuwa a duk lokacin da ta ganshi yana cikin damuwa, haka tana cikin farin ciki idan ta ga yana cikin farin ciki, sai dai a yanzu ba za ta iya cewa farin ciki take yi ko jin haushi akan maganar da yaya Mus’ab ya zo mata da ita. Taso a ce da kanshi yaya Faruk yayi wannan tunanin akan ya aure ta ba wai shi yaya Mus’ab yayi tunanin haka ba, ita kan ta shaida ne a irin son da yaya Faruk yake min, tasan son da yake min zai wuya ya ma wata macen irin shi, yanzu in ta amince da auren shi ba tasan ko shi yaya Faruk zai yi farin ciki da hakan ba, za taso ta mallaki yaya Faruk a matsayin miji saboda yana da irin qualities da take so a gurin namiji, hasalima yaya Faruk irin mazan nan ne da duk wata mace idan tayi gamdakatar dashi a matsayin mijin ta za tayi murna, da ta tuna da dalilin shigar shi wannan damuwar bai wuce akan son ‘yar uwarshi yasa shi a wannan halin ba sai ta ji jikin ta yayi sanyi. Yaya Mus’ab ne ya katse mata tunanin da take yi ya ce "Nana ki fad’a min ra’ayin ki akan wannan maganar, in har ba kya son Faruk ba zan takura miki ba, shi kanshi Faruk d’in ba zai ji haushin k’in za’ban shi da kika yi ba, haka ba zai so in matsa miki akan ki amince dashi ba, sai dai in kika amince dashi kinyi taimako, dan za ki ba da taki gudunmawar wajen sa shi mantawa da damuwar da yake ciki, a dalilin wannan taimakon da kika yi sai ki ga Allah ya taimake ki a inda ba ki yi zato ba, kin ga kuma ga Hajiya ta fara miki fad’a akan rashin tsayawa da samari da kike yi, in kika amince da Faruk kin ga kin huta da fad’an Hajiya". Wannan tattausan kalamen da yaya Mus’ab ya fad’a mata yasa ta ji ta yi na’am da maganar da ya zo mata. "yaya Mus’ab ko da a ce ban san yaya Faruk ba ka bani shawarar in aure shi zan amince in aure shi, nasan duk wanda za ka za’ba min ya dace da ni ne, yana da halaye nagari, amma yaya Mus’ab shi yaya Faruk d’in ya amince zai aure ni ne, ba zan so muyi aure ba ya da ra’ayi na a ranshi, idan na fahimci hakan zan iya shiga wani halin". "Kar ki damu Nana, kafin in zo miki da wannan maganar sai da muka yi ta da yaya Faruk ya tabbatar min ya amince, nasan in da Faruk ba ya ra’ayin ki ba zai amince da maganar ba, abin da nake son ji a gurin ki shine in ji kin amince ko akasin haka". Cikin kunya ta rufe fuskar ta tace "Na amince yaya Mus’ab". Murmushin farin ciki yayi da jin amincewar da Nana tayi ya ce "Nana nagode da ba ki bani kunya ba, duk da nasan daman ba za ki bani kunyar ba, insha Allahu sai kin yhi farin ciki da kasancewar ki da Faruk, abin da zan ce miki shine ki yi hak’uri da yanayin Faruk a yanzu, a hankali sai ki ga komai ya zama normal". Haka yaya Mus’ab ya ci gaba da nuna mata fa’idar amincewa da yaya Faruk kana suka zarce da hira. Lokacin da suka had’u da yaya Faruk ne yake sanar dashi yanda suka yi da Nana. Jin ta amince da maganar yasa a ranshi ce wa zai aure ta ko da ba ya jin son ta a ranshi, yasan amincewar shi zai sa mutane da dama farin ciki, hasalima zai iya zama da Nana dan tana da wasu halaye da yake buk’ata a gurin matar da zai aura. Ya ma yaya Mus’ab godiya da irin wannan karamcin da ya mai. Tun san da yaya Mus’ab ya fad’a mai Nana ta amince yake tunanin yadda zai fara zuwa gurin Nana zance, hasalima shi har yanzu kallon k’anwa yake mata, sai dai yasan zuwan shi gurin ta shine da zai tabbatar da ya amince da ita, hakan ne zai sa shi yaya Mus’ab yasan ya amshi zancen hannu bibbiyu. A ‘bangare na kuwa zaman mu ya ci gaba da gudana cikin zaman lafiya da kulawa, tsakanin ni da Dr kowa k’ok’ari yake yi wajen faranta ma d’an uwan shi. Matsala ta da Dr bai wuce yawan hana ni zuwan gidan mu ko abin da ya dangancin family d’in mu, na sha tambayar shi dalilin shi nayin haka, sai ya ce min ba ya son ina yawan fita ne, hakan yasa na rage tambayar shi in ba abu ya kama ba. Yau ta kasance ranar weekend, ina zaune a falo ina kallon wani indian series film da ake watso wa a tashar GH one mai suna revenge. Knocking d’in da na ji ana yi ne ya katse min kallon da nake yi, tashi nayi in je in bud’e. Ina bud’e wa na ga su Farida ne da Meema, hanya na basu suka shigo kana na kulle k’ofar na dawo na zauna. Farida ce da Hanan su ka gaishe ni yayin da Meema ta d’aura k’afar ta d’aya akan d’aya tana yatsina fuska. Tashi nayi na d’akko musu drinks da snacks na ajiye musu. Meema ko kallan kayan da na kawo musu ba tayi ba sai ma wayar ta da ta d’akko tana dannawa. Yau cikin shigar transparent material suka yi, sai dai kowa kalar material d’in na sa daban. Hanan da Meema ne suke hirar su yayin da ni da Farida muke hira akan film d’in da ake yi a tashar GH one. Hanan ce ta kalle ni ta ce "Anty Zarah yaya Sadik na nan ne, in yana nan ki yi mana magana dashi". Amsa mata nayi da cewa "Eh yana nan, barci yake yi bari in taso muku shi". Tashi nayi na nufi d’akin da yake kwance na zauna kusa dashi. Hura mishi kunne na dinga yi har ya bud’e idon shi, kallo na yayi ya sakar min murmushi ya ce "my Zarah ya aka yi ne". Murmushin na mayar mishi kana na ce "Su Farida ne suka zo". "Ok ki ce musu gani nan zuwa, bari in d’an watsa ruwa" ya fad’a yana shafa fuska ta. "Sai ka fito" Na fad’a a tak’aice. Komawa nayi na sanar dasu yana zuwa kana na nufi kitchen dan in musu girki. Kuskus da kidney source na musu, bayan na gama ne na musu Banana milk shake. D’akko food flask d’in nayi da plates na kawo musu inda suke, na koma d’akko drinks d’in da na had’a musu da kofuna na ajiye musu. Ganin Farida ce kad’ai take cin abincin yasa na ce "Hanan ku ci abincin". "Na k’oshi ne" Hanan ta bani amsa a tak’aice. Farida ce ta kalli Meema wacce hankalin ta ke kan wata ta ce "Anty Meema in zuba miki abincin ne". Ta’be baki tayi kana ta ce "No ki barshi, ba na jin cin abincin ne". Raina ne na ji ya soma ‘baci yadda Meema ke min in muka had’u, a yadda na fara karantar Hanan ita ma na ga tana ji da kanta, ina ganin hakan ne yasa ma suka fi shiri da Meeman. Faridan ce ta kalle su ta ce "Anty Meema da Anty Hanan da kun zo kun ci ko kad’an ne, kun ga saboda zuwan mu ne ta tashi ta dafa" Meema cikin fad’a ta ce ma Farida "Mun ce ta mana girki ne da zaki ce saboda mu tayi girkin, ba ma jin ci ne ko dole ne sai mun ci, ba na son irin haka Farida". Hanan ce ta kar’bi zancen da cewa "Ke ma Meema ki k’yale ta, kin san Farida da neman suna". "Allah ya baku hak’uri" abin da Farida ta ce musu kenan. Duk wannan maganganun da suke yi du kina jin su amma sai nayi kamar ban ji su ba, ban yi zaton daga abin mutunci zai koma na tsiya ba, daman Meema tun a gidan su Dr na ga take-taken ta, za ko tasha mamaki na in dai haka za ta ci gaba da yin, dan ba zan juri rainin hankali ba, ita ma Hanan naga tafiyar su d’aya da Meeman, dole in yi taka tsantsan dasu. Falon ne ya d’auki shiru kamar ba kowa a ciki. Dr ne ya fito cikin shigar k’ananun kaya ya zo ya zauna kusa dani. Gaisawa suka yi kana suka ci gaba da hira. Hanan ce ta ce "Yaya Sadik Habeela za ka kaimu". Hararar ta yayi ya ce "Ku miye amfanin motar ku da ba zaku ba, sai ni zan kai ku". Marairaicewa Hanan tayi ta ce "yaya Sadik mun kwana biyu fa ba mu fita da kai ba, ka ga kai kana gurin aiki, mu kuma muna school, plsss yaya ka kaimu". Ni ce na ce "pls Dr ka kaisu". Murmushi yayi ya ce "Zan kaisu amma sai na ci abinci". Tashi nayi na nufi kitchen dan in zubo ma Dr abinci. Ko da na dawo sai na tarar da Meema kusa dashi suna hira. Wani irin takaici ne ya kama ni ganin Meema da Dr kusa da juna. Jiki a sanyaye na k’araso nayi serving d’in shin a koma kusa da Farida na zauna. Kallo na yayi ya ce "Zarah ki zo mu ci, ko ni kad’ai yau kike son in ci abincin". Murmushin yak’e na yi na ce "Na riga na ci nawa" Na bashi amsa a tak’aice. Bai ce komai ba yaci gaba da cin abincin shi. Meema ce cikin shagwa’ba ta kalli Dr ta ce "yaya Sadik zan ci abincin". Hararar ta yayi ya ce "Ba ga abincin can kusa da Farida ba an zubo muku, ki je ki zuba ki ci" Dr ya fad’a. Farida ce ta kar’bi maganar da cewa "Anty Meema ba yanzu ki gama cewa ba kya jin cin abincin, yanzu kuma kin ce za ki ci". Harara Meema ta watsa ma Farida kana ta ce "Ina ruwanki, da ban a jin cin abincin ne, yanzu nake jin ci, ko za ki hana ne". Farida shiru tayi ba ta ce mata komai ba. Dr ne ya kalli Meema ya ce '"Meema kin cika rigima, tun d’azun an kawo muku abincin kin k’i ci, sai yanzu da kika ga an zubo min za ki ce za ki ci". "yanzu ne fa na fara jin yunwar yaya Sadik" cewar Meema. "Ki je ki zuba wancan ki ci" Dr ya ba ta amsa a tak’aice. K’ara shagwa’be mai tayi ta ce 'Ni da kai zan ci yaya Faruk". Shiru ya mata bai ce mata komai ba, hakan yasa ta d’auki spoon ta fara ci a plate d’in da na zuba ma Dr. Ni dai ina zaune ina kallon ikon Allah, in raina yayi dubu to ya gama ‘baci, ji nake yi kamar in je in watsar da abincin ko na samu sauk’in ‘bacin ran da nake ji, abin da ya k’ara ‘bata min rai shine yadda Dr bai nuna damuwar shi ba akan abincin da Meema take ci dashi. Tambayar da nake ma kaina shine Meema tana da nufin ta yin haka, dan har yanzu ban san Meema wacece ita a gurin su Dr ba. Ganin in na ci gaba da zama ina ganin wannan takaicin raina ne zai ci gaba da ‘baci, hakanzai iya sa in kasa controlling d’in kaina, dan haka ne na tashi na nufi d’aki na kwanta. Dr ne ya shigo ya sanar dani za su fita. Tashi nayi muka fito tare dan muyi sallama dasu. Sallama na musu na raka su har bakin k’ofa. Ina kallo san da za su shiga mota, Meema ce ta shiga gaba. Dawowa nayi na zauna ina mamakin Meema, Dr kawai zan jira yazo ya min bayanin wacece ita a familin su, dan ina ganin bazan zuba ido tana min abin da ta ga dama ba. Sai can yamma Dr ya dawo tare da siyayyar da ya min na ice-cream da snacks d’in da ya siyo min. Ji nayi ba na marmarin abin da ya siyo min, saboda har yanzu ban daina jin haushin Meema ba a raina. Da daddare ina kwance a jikin Dr muna hira na kalle shi na ce "Dr dama akwai tambayar da nake so in maka". Kanne min ido yayi ya ce "You can go ahead Zarah". "Wai Meema ita ma ‘yar uwarku ce, na ga baka ta’ba bani labarin ta ba". Murmushi yayi ya ce "yarinyar abokin Dadi d’in mu ce, ta saba da ‘yan gidan mu sosai, in ba ma sani kayi ba zaka iya cewa ‘yar gidan mu ce dan yawanci tana gidan mu, mu ma mun saba da gidan su". Shiru nayi ina mamakin ashe ba abin da suka had’a ma take min wa'innan abubuwan, "to miye dalilin ta nayi min haka". Wannan dalilin ne ban sani ba. Kamar in ma Dr magana akan abin da Meema ke min sai na ga rashin dacewar hakan. Haka ya ci gaba da fad’a min amincin Dadin su da Dadin Meema ina sauraron shi kana muka tashi muka je muka kwanta. Yaya Faruk ya yanke cewa yau da yamma zai je gidan su Nana, dan haka ya fad’a ma yaya Mus’ab akan ya fad’a ma Nana yana nan zuwa. Tun da yaya Mus’ab ya kira Nana ya fad’a mata yaya Faruk na nan zuwa ta rasa sukuni. Tunani take yi akan da wane ido za ta kalli yaya Faruk a matsayin saurayin ta bayan ita kallon matsayin kallon kamar yayan ta haka take mishi, hasalima ita kunyar had’uwa take yi dashi tun san da yaya Mus’ab ya fad’a mata maganar, shi yasa ta dinga kauce ma had’uwar su. Da yamma yaya Faruk ne ya shirya cikin lallausan yadi kalar brown. Motar shi ya shiga ya ja, sai da ya tsaya a super market ya mata siyayya kana ya wuce gidan su Nana. Yana zuwa mai gadi ya bud’e mai ya shiga yayi parking a harabar gidan. Kiran ta yayi a waya ya sanar da ita zuwan shi. Fito wa tayi ta same shi a inda yayi parking d’in motar shi. Bayan sun gaisa ne ta bud’e musu side d’in yaya Mus’ab suka shiga. Sai da ta cika gaban shi da kayan motsa baki kana ta nemi guri ta zauna. Sun k’ara gaisawa ne kana yaya Faruk ya fara jan ta da hira. Kasa sakin jikin ta tayi ta bashi amsa saboda yadda a yanzu take jin kunyar shi. Shiru ne ya ratsa falon, sai k’arar AC da ke tashi a falon, kowa da kalar tunanin da yake yi. Shi yaya Faruk yana tunanin hanyar da zai bi wajen tambayarta ta amince za ta aure shi alhalin bai fad’a mata yana son ta ba, ita kuma Nana tunanin d take yi shine yadda za ta kalli yaya Faruk a matsayin saurayin ta. Yaya Faruk ne ya kau da shirun da cewa "Khadija nasan kin san dalilin zuwa na, Mus’ab ya fad’a min ki amince akan maganar da yazo miki da ita, amma duk da haka ina so in ji daga bakin ki cewa kin amince za ki aure ni, ba na so a shiga hakk’in ki, kar ki ji kunya ta, ki d’auka kamar da Mus’ab kike magana, zan fahimce ki?" ya tsura mata ido yana jiran jin amsar ta. Wata irin kunyar yaya Faruk take ji, duk wannan zaman a takure take. Sunkuyar da kanta tayi ta kasa d’agowa ta kalle shi ta bashi amsa. Shi kanshi yaya Faruk ya fahimci hakan, amma duk da haka ya ce "Khadija ina jiran amsar ki, ko ba ki amince ba". A hankali ta ce "Na amince yaya Faruk, Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi gare mu baki d’aya". Yaji dad’in addu’ar da ta musu, hakan yasa murmushi ya su’buce a fuskar shi ya ce "Good Khadija, na gode da kika amshe ni a matsayin wanda za ki aura, Khadija ina yabawa da kyawawan d’abi’un ki, natsuwar ki da hankalin ki, wannan halayen na daga cikin abin da namiji yake buk’ata a gurin duk macen da zai aura, ina so ki kalle mu a matsayin auren soyayya za mu yi, kar ki sa ma ran ki wasu tunani akan cewa a da ina da wacce nake so, daman Allah bai nufa Fatima mata ta ba ce shi yasa har ta auri wani, kin ga ni dake duk ba mu kawo ma kan mu hakan ba a baya, sai gashi Allah ya sauya lamarin wanda in Allah ya nufa za mu zama miji da mata, ina fatan kin fahimci bayani na". "Na fahimta yaya Faruk" Nana ta fad’a. Sun d’an ta’ba hira, yawanci duk hirar tasu yana tambayar ta ne akan School kana ya mata sallama ya tafi. Bayan Nana ta koma gida ne ta bud’e abin da yaya Faruk ya kawo mata, kayan make-up ne da tsadaddun turare, tayi farin ciki da kyautar da ya kawo mata, tasan wannan kyautar da ya mata na daga cikin alamun nuna kulawar shi gare ta. Tun daga wannan lokacin yaya Faruk yakan yi k’ok’arin kiran ta ko su had’u a chat, in ya samu lokaci yakan je gurin ta. Mu’amalar shi da Nana sai ta zamo abin burgewa dan suna ganin mutuncin junan su. San da yaya Mus’ab ya sanar da Hajiyar su da Dadin su halin da ake ciki sun yi farin ciki da jin wannan labarin, dan sun yaba da halayen yaya Faruk da kyawawan halayen shi, sun san Nana tayi dacen samun gwarzon namiji irin yaya Faruk. Zaman mu da Dr sai son barka, ba na tare da wata matsala sai wacce ba za a rasa ba tsakanin miji da mata. Anisa ta kan lek’o ni in tana free kasancewar ta samu D.E a Kasu, sun bata Microbiology. Abbu da Ummu sun zo da yaya Khalil, ranar haka na wuni cikin farin cikin ganin su da na yi. Dadin su Dr da Momin shi sun zo gidan mu. A cikin haka ne Dr ya sai min form na HND, nayi murna san da ya sanar min in kawo credential d’ina zai min applying d’in HND ne. Ba a wani d’au lokaci ba Admission ya fito na samu gurbin ci gaba da HND d’ina a nan Kaduna Polythecnic. Karatu na yana tafiya yadda nake so cikin nasara. Matsalar Meema sai abin da yayi gaba, sai dai ina k’ok’arin danne fushi na idan na ga tana nema na da fitina, a gefe kuma na ga Hanan tafiyar su d’aya da Meema, har yanzu kuma ban fad’a ma Dr abin da yake faruwa ba. Yau ranar ta kasance ranar weekend, ban dad’e da dawowa daga School ba kasancewar wani lecturer da ya ce mu zo ran sati. Dawowa ta kenan na kwanta a 3-sitter ina hutawa. Sallamar su Hanan na ji sun shigo kasacewar a bud’e na bar k’ofar. Jin sallamar su ne yasa na tashi na zauna ina murmushi. Farida ce da Hanan suka gaishe ni, Meema kuwa ko kallo ban ishe ta ba. Tashi nayi na kawo musu drinks. Meema ce ta ce "Hanan zo mu shiga kitchen in samu soft food in dafa, yau throughout ban ci komai ba". Hanan ce ta ce "Mu je toh". Nasan Meema abin da zan tanka mata take nema ba ta samu ba, shi yasa take nema na da fitina. Basu d’auki lokaci ba suka fito falon. Soyayyar taliya suka dafa da suka sa mata kayan lambu. Sun fara cin abincin ne suka kalli Farida suka ce tazo su ci ta ce ba ta ci. Haka suka gama cin abincin nan ba tare da sun d’auke ko da spoon ba, ni kuma nayi alk’awarin bazan d’auke komai ba, dan na ga abin nasu kullum gaba yake yi. Dr ne ya shigo falon kasancewar da zan tafi school shi yayi dropping d’ina yace min zai lek’a cikin asibiti akwai patient d’in da zai duba. Tun da ya shigo falon yaga yadda aka ‘bata shi ya d’aure fuska, ko da su Hanan suka gaishe shi a tak’aice ya amsa musu. Sannu da zuwa na mishi na kau da fuska ta kamar ban san abin da yake ma fushi ba, nima bai san raina a ‘bace yake ba. Lokacin da zai shiga side d’in shi ne ya min magana akan in same shi a ciki. Tashi nayi na bishi dan in ji mai zai ce min. Bayan tafiya ta ne Farida ta kalli su Hanan ta ce "Ya kamata Anty Hanan ku gyara falon nan, kun san yaya Sadik ba ya son k’azanta". Harara Meema ta watsa mata ta ce "Ba za a d’auke ba Farida, na ga kamar tsoron Zarah nan kike yi". Farida ce ta mata wani irin kallo kana ta ce "plss Anty Meema ba da ke nayi magana ba da za ki fara min fad’a, da Anty Hanan nake, da kike cewa ina tsoron Anty Zarah ai ba laifi ba ne, dan matar brother d’ina ce". Jin yadda Farida ita ma ta bud’e mata wuta ne yasa tayi shiru ba tare da ta k’ara cewa komai ba, in ban da faman hararar Farida ba abin da take yi. Ita kuwa Hanan danna wayar ta take yi ba tare da ta sa musu baki a maganar ba. Ina shiga d’akin na same shi yana rage kayan jikin shi. Kallon shi nayi na ce "Dr me zan dafa maka, ban dad’e da dawo wa daga school ba, ban d’aura komai ba". Maimakon ya bani amsa sai ce min yayi "Zarah akan me za ki bar falon da datti, kin san ba na son k’azanta, shine za ki bar falon a haka kuma kin san zan yi magana". "Ai ba ni na ‘bata ba, su Hanan da Meema ne suka ci abincin suka ‘bata gurin" nima na fad’a cikin d’aurewar fuska. "Da suka ‘bata ba sai ki gyara ba ko ki musu magana su gyara" cewar Dr. "Ina jin kafin su tafi za su gyara ne shi yasa ban yi musu magana ba" na fad’a. Bai k’ara ce min komai ba ya fita daga falon yayin da na nemi guri na zauna akan gadon. Yana zuwa ya daka musu tsawa yace "Shine kuka ci abinci ku ka bar gurin haka, kun san ban son k’azanta, da ku ka bar falon haka wa kuke nufin ya gyara muku, tun kan ranku ya ‘baci ku tashi ku gyara falon nan sannan ku wanke kayan da kuka ‘bata". Ba shiri su Meema suka mik’e suka fara gyara falon kana suka wanke kayan da suka ‘bata. Suna gamawa suka shiga mota suka tafi ba tare da sun min sallama ba. A ‘bangaren yaya Faruk sun fahimci juna da Nana, hakan yasa yaya Faruk ya kira su Dadi ya sanar dasu halin da ake ciki. Dadi da Momi sun ji dad’in wannan labarin, hakan ne yasa Dadi yace ma yaya Faruk ya sanar da Dadin su Nana d’in suna na zuwan Abujan da a tsayar da maganar bikin. Anisa ma da Momi take fad’a mata maganar ta ji dad’i da Allah ya musanya ma yaya Faruk da Nana, dan a kwana d’aya da tayi da ita ta fahimci rashin hayaniyar Nanan da natsuwar ta. Shima Abbu san da Dadi ya sanar da shi maganar yaya Faruk da Nana ya yi farin ciki da jin wannan maganar, hakan yasa suka tsayar da ranar da za su je Abujan. Ran weekend su Abbu da Dadi da Kawun wagini suka tafi Abuja. An musu tarba mai kyau da karamci, bayan sun gaisa ne su Abbu suka gabatar da abin da ya kawo su. Sun ba da kud’in gaisuwar iyaye kana suka tsayar da nan da sati biyu za su dawo a sa rana, haka suka rabu ana wasa da dariya. Sati biyu na cika su Abbu suka koma Abuja, an tsayar da biki nan da wata uku. Bayan dawowar su Abuja ne aka yanke shawarar had’a bikin su da su Anisa tun da yanzu yaya Khalil ya fara aiki a wani private Hospital inda suka bashi d'aya daga cikin pharmacist store. Ko wani ‘bangare shirye-shirye ake yi ba kama hannun yaro. Yaya Faruk bai samu zuwa Kaduna ba saboda yadda aiki ya tsare shi a Abuja, ya ce in ya samu sauk’in aiki zai zo, dan haka ta waya suke tattauna wa akan maganar bikin. Momi duk ta fi kowa murnar wannan auran da yaya Faruk zai yi, tana ganin hanyar fitar yaya Faruk ne yazo, ga kuma bikin auta Anisa da yazo a tare da yaya Faruk, dan haka shiri take yi ba na wasa ba. Sun yi da da Momi akan zai turo kud’i a had’a mishi kayan akwati tun da bashi da time, san da Momi ta sanar dashi akwatin da ya had’a min yana nan, ya sanar da ita a ajiye su, in yazo zai san yanda za ayi da kayan, a had’a wasu tun da wannan sun kwana biyu. Lokaci na ta tafiya yayin da biki ke ta matsowa. Yaya Faruk ya tambayi Nana in akwai event d’in da ta tsara ta fad’a mishi, ta nunan mishi da walima da kamu kawai za tayi, yayin da ‘bangaren shi abokan shi suka had’a mishi crossing of the sword. Yau biki ya rage sati biyu, dan haka ne yaya Faruk ya nemi excuse a gurin aiki ya tawo Kaduna. Momi tayi murnar ganin shi ganin yanzu bai da wata sauran damuwa, duk tasan har yanzu abin da ya faru ba mai sauk’in wuyar fice wa ba ne a rai. Lokacin da Momi take tambayar shi abubuwan da suka tsara ya sanar da ita, haka Momi ta dinga jero mishi event d’in da ta tsara. Sai dai yayi murmushi kawai, yasan Momi ta na so yayi aure, ga kuma abin da ya faru tsakani na dashi, dole yanzu ta nuna murnar ta. Ta nuna mishi akwatunan da ta had’a da wanda ita ma ta siya, shi kanshi yaya Faruk kayan sun burge shi ya kuma yaba. Yaya Faruk ya je gidan mu, su Abbu da Ummu sun yi murnar ganin shi, sun mishi fatan alkhairi a auran da zai yi tare da sa mishi albarka. Har kullum yana d’aukar su Abbu kamar iyayen shi, ba sa banbanta shi dasu yaya Aminu. Yaya Faruk yaje gidan yaya Aminu inda Anty Jiddah ta dinga tsokanar shi, sun tattauna da yaya Aminu akan yadda bikin zai kasance. Yaya Khalil ma ya had’a akwatuna na burgewa masu kyau da tsada. Yaya Khalil na yawan kira na yana fad’an min abubuwan da suka dangancin bikin. Nima na je gida san da muka yi waya da yaya Khalil yake fad’a min an sa biki, haka na kira Anisa ina ta tsokanar ta. Ba yadda ban yi da Dr akan ya barni in je gidan mu tun da bikin ya matso amma ya k’i yace sai bikin ya kusa. Haka na k’yale shi ba dan raina ya so ba, ina jiran a shiga satin bikin. An kai kayan akwati gidan su Nana, da su Ummu aka kai akwatin da su Anty Jiddah da k’anwar Momi Anty Fauziyya sai k’awar Momi. An basu tukwici na kai kayan da suka yi. San da su Ummu suka dawo ne ta kira ni a waya ta fad’a min fad’a akan rashin zuwan da ban yi ba, na ba ta hak’uri akan ranar mu na test a makaranta ne duk da ba gaskiya na fad’a mata ba, nasan idan ta ji Dr ne ya hana ni baza ta ji dad’i ba, ta fad’a min lokacin da za a kai kayan yaya Khalil, mun yi da ita akan insha Allahu zan zo ranar. Lokacin da Dr ya dawo nake fad’a mishi bai ce min komai ba, sai na d’auka ya amince min ne. Ana gobe za a kai kayan da daddare muna kwance da Dr nake k’ara fad’a mishi gobe zan je gida ba zan je school ba saboda ina son akai kaya dani. Wannan karan ma bai ce min komai ba, hakan ya ‘bata min rai saboda ban san ma’anar shirun shi ba. Da safe yana shirin tafiya aiki na ce "Dr jiya na tambaye ka zan je gidan mu ba ka ce min komai ba". "Ba za ki ba ne Zarah" ya fad’a min a tak’aice. Wani irin ‘bacin rai na ji ya ziyarce ni, lokaci d’aya na ji wasu hawaye sun tarun min a idanu na, na rasa manufar dalilin Dr na yi min haka, in sha’anin family d’in su ne da na mishi maganar shi zai kai ni ba tare da ya min musu ba, amma in dai abin da ya dangance ni ne sai ya dinga kakkaucewa, ina ganin wannan karan dole ne in k’waci ‘yanci na, ba zai yiwu ya dinga hana ni yin zumunci da ‘yan uwa na ba. "Akan me zai sa ba zan je ba Dr" na fad’a cikin ‘bacin rai. "Saboda ina da ikon hana ki zuwa ko ina, shine dalilin" ya bani amsa. Hawaye ne suka zubo min na share na ce "Dr in ka min haka ba ka min adalci ba, san da za akai akwatin yaya Faruk haka ka hani ni zuwa, yanzu ga na yaya Khalil za akai akwatin shi ka ce ba zani ba, ka kuma san yadda muke, da wani ido kake so in kalli su Ummu da mutane idan ban je ba, Dr ina so ka fad’a min dalilin ka da ba ka yawan bari na in je sha’anin family d’in mu alhalin ka na bari na ina zuwa na family d’in ka". "Ba sai na fad’a miki dalili ba" ya fad’a min a tak’aice. Yana gama fad’ar haka ya fita daga falo. Zama nayi a falon ganin yadda Dr ya min halin ko in kula da damuwa ta, bai damu da abin da hakan zai jawo min idan ban je ba. Wasu hawaye ne suka dinga zubo min na takaicin Dr. Zuciya ta ce take bani shawarar akan in shirya in je tun da na tambaye shi ya k’i bari na. Haka na tashi na shirya na kulle k’ofar na shiga motar da Dr ya siya min, ba ko wane lokaci nake hawa ba saboda hannu na bai gama k’wari ba. Ina zuwa gidan mu na ga ‘yan uwa, nan wani farin ciki ya ziyarce ni. Ban wani jima da zuwa ba aka tafi gidan su Anisa dan kai akwatunan. A raina ina fargabar zuwa saboda so d’aya muka zo da Dr muka gaishe su, ranar Dadi na nan, ban san yadda Momi wani kallo za ta min idan ta ga har dani aka kawo akwatin. Ga mamaki na san da muka je gidan haka Momi tayi ta nan-nan dani, haka ta dinga ja na a jiki, haka yasa na ji dad’i a raina, na san Momi ni mutuniyar ta ce, tun san da abin da ya faru tsakani na da yaya Faruk take fushi dani, yanzu na tabbatar da ta daina fushi dani. Haka na shiga d’akin Anisa ina tsokanar ta, zama nayi muka sha hira irin wacce muka kwana biyu ba mu yi irin ta ba. Sai da muka d’an jima kana muka tafi. Haka Momi ta ba su Anty tukwici na kayan akwatin da muka kawo. Muna koma wa gida na wuce side d’in yaya Khalil, nan na zauna muna ta tsara yadda bikin zai kasance kana muka zarce da hira. San da zan tafi gida ne muka had’u da yaya Aminu ya zo d’aukan Anty Jiddah, tsayawa nayi muka gaisa. Sallama na musu kana na shiga mota ta na ja. Sai da na fara tafiya ne fargaba ta kama ni dan yanzu nasan Dr ya dad’e da dawowa daga aiki, gashi ba yaso in kai yamma idan na fita, yanzu kuma gashi yamma tayi sosai. Da wannan tunanin na isa gida, ina shiga harabar gidan na ga motar shi a parkin space. Ganin k’ofar falon a bud’e yasa na shiga da sallama ta. Samun shi nayi a zaune yana kallon tashar Master Channel. Ciki-ciki ya amsa min sallamar da na yi mai. "Sannu da gida Dr". Bai amsa min ba sai ma tambaya da ya watso min "Daga ina kike?". Duk da nasan yasan in da naje bai hana ni amsa mishi da cewa "Daga gidan mu nake". "Good" ya fad’a a tak’aice. Ci gaba yayi da cewa "Amma ba na ce miki kar ki je ba". Duk da masan ban da gaskiya tun da na fita ba da izinin shi ba, hakan bazai hana ni in k’watar ma kaina ‘yanci ba. "Ka ce kar in je, amma na ga zuwa na yana da mahimmanci, shi yasa na je, amma kayi hak’uri fitar da nayi ba tare da izinin ka ba". Bai ce min komai ba ya tashi ya tafi side d’in shi. Ganin bai min magana ba yasa jiki na yayi sanyi na nufi d’aki na. Da daddare na shirya cikin shigar kayan bacci na nufi d’akin Dr. Samun shi nayi yana danna laptop. Duk da yaji shigowata amma hakan bai sa ya d’ago kanshi ya kalle ni ba. Kusa dashi na je na zauna na ce "Dr sannu da aiki". "Yawwa" ya amsa min a tak’aice. "Me kika zo yi?" ya tambaye ni. Tambayar ta ban mamaki da takaici tare da wani irin haushi da tasa na tsaya ina kallon shi, amma sai na danne fushi na ce "wannan wace irin tambaya ce Dr, za ka ce me na zo yi, kwanciya na zo yi". Cikin d’aurewar fuska ya ce "Ki tafi side d’in ki kije ki kwanta, a yanzu ba ni da buk’atar ki, in ina buk’atar ki zan nemi ki, tun da ni ban isa in baki umarni ki bi ba". Tsayawa nayi ina al’ajabin Dr tare da mamakin shi, duk da kunne na ya jiyo min abin da Dr ya fad’a min amma na kasa gasgata kunne na. Ina ganin akan fitar da nayi har ya kai ya zama wani laifi da har Dr zai hukunta ni irin hakan, bayan na bashi hak’uri akan laifin da na mishi duk da nasan akan gaskiya ta na aikata hakan. "Wai ni yau Dr yake cewa in tashi in bar mishi d’aki bai da buk’ata ta". Tashi nayi na fita daga d’akin. Tun kan in k’arasa side d’ina na fashe da wani irin kuka mai cin rai. Kwanciya nayi akan gado ina ci gaba da kuka, a lokaci d’aya ina mamakin Dr. Sai yanzu ne Kalmar na da aka fad’a min na cewa aure zaman hak’uri ne ya fad’o min, da ni a gani na in har kuna son junan ku ba wata matsala da ka iya zuwa ta muku dabaibayi a zaman ku, sai gashi tun ba a je ko ina ba na fara ganin dalilin da yasa ake cewa in yi hak’uri. Da k’yar na samu bacci ya d’auke ni saboda yadda nayi sabo da jikin Dr, ga kuma takaicin abin da ya min a lokaci d’aya. [8/5, 22:30] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa Writers Association *FATAN ALKHAIRI* *Khrty* _(Marubuciyar Ya Sheikh)_. *Maryam Bodinga* _(Maganin Biri, Karen Maguzawa)_. *Ummien Fauzan* _(Marubuciyar Bahijjah)_. *Mrs Xerks* _(Marubuciyar Sanadin Talauci)_. *Ummu Fatima* (Marubuciyar Dijah qaya)_. *Noorul huderh* _(Marubuciyar Detective Noor)_. *Mmn Rufaida* _(Marubuciyar Sanin Masoyi sai Allah)_. *QUESTION OF THE DAY* _Yi bayanin abin da suratul Bak’ara ta ke karantawar?_. 79-80 Washe gari haka na tashi na had’a mana breakfast, mamakin Dr ne har yanzu a raina. Ina zaune a dining ina breakfast Dr ya fito cikin shirin shi na tafiya aiki. Kujerar da ke kusa dani yazo ya zauna. A tak’aice na gaishe shi ya amsa min saboda har yanxu ban daina jin haushin abin da ya min ba. Kallo na yayi cikin wasa, ya ce "Zarah yau ba jira". Mamakin shi ne ya kama ni, kamar ba shi ba ne jiya da daddare ya gama ce min bai da buk’ata ta duk da hak’urin da na bashi, shine har ya manta abin da ya min, yake son ja na da wasa saboda ya d’auke ni a mara wayau. Ba tare da na d’ago na kalle shi ba na ce "Naga ba a da buk’ata ta shi yasa ban jira ka ba". Murmushi yayi kawai dan yasan magana na fad’a mishi. Breakfast na had’a mishi na ajiye a gaban shi. Lokaci na duba na ga na kusa yin latti, hakan yasa na tashi na je na d’akko jaka ta na fito falon. Samun shi nayi har gama breakfast d’in. Tare muka fito, saboda neman tsokana sai cewa yayi "Ki zo in sauke ki, dan na ga har yanzu hannun ki bai gama k’wari ba". "No ka barshi kawai, zan yi driving da kaina". Ban saurari mai ze ce min ba, na shiga motar na tafi. Da daddare ban yi gigin zuwa side d’in shi ba, dan ban manta maganar da ya fad’a min ba. Kwanciya ta nayi a side d’ina ni kad’ai, duk da tsoron da nake ji. Bud’e k’ofar da Dr yayi ne yasa na maida hankali na bakin k’ofar. Bulb d’in d’akin ya kunna. A kujerar dressing mirrow d’ina ya zauna yana kallo na. "Zarah ashe baki yi barci ba". cewar Dr. "Eh" na bashi amsa a tak’aice. "Na ji ki shiru ba ki zo ba, shi yasa na zo in ga ko lafiya". Kallon shi kawai na ke yi san da yake jero wannan bayanan, in ban da Dr ya maida ni yarinya, jiya ya gama ce min bai da buk’ata ta sannan yanzu yace min yaji shiru ban je gurin shi ba, saboda ni ban san darajar kaina na ‘ya mace ba da har zan bi shi ya koro ni, nima zan nuna mai ina da nawa matsayin a gurin shi. "Zarah na ji kin yi shiru" ya fad’a yana kallo na. "To me zance maka Dr" na fad’a. Mik’ewa yayi ya ce "Ok tun da ba ki da abin cewa ki tashi mu tafi side d’ina". Wani kallo na watsa mishi na alamar ka manta abin da ka fad’a min ne kana na ce "yanzu kana da buk’ata ta kenan, gashi ni kuma ba ni da buk’atar ka". Wani kallo ya watsa min na gargad’i kana ya ce "Zarah mu bar wannan maganar, laifi ni kika yi ma wa, ni ya kamata in yi fushi dake ba ke ya kamata ki ya fushi dani ba, tun da na bar maganar, ya kamata ke ma ki bar maganar, ba na son jan zance, ki zo mu tafi". Murmushin takaici na yi kana na ce "Tun da ka ce a bar maganar na bar ta, amma ni fa yau ba zan je side d’in ka ba". Kallo na yayi ya ga fuska ta a d’aure, yasan ba da wasa na fad’i maganar ba, ganin hakan ne yasa ya girgiza kai yayi murmushi. "Ya zan yi tun da gimbiya Zarah yau ta ja kambun ta, dole in yi yadda take so, bari in kwanta a nan d’in, ai duk d’aya ne" Dr ya fad’a cikin wasa. A hankali yadda ba zai ji ni ba na ce "Da dai ka koma side d’in ka da yafi, dan nima ban da buk’atar ka". "Me kika ce" ya tambaye ni. "Ban ce komai ba" na bashi amsa. Kwanciya ta nayi ba tare da na k’ara bin ta kanshi ba. Ina jin shi ya kashe bulba d’in, ya kunna dim light na gefen gadon. Gadon ya hau ya kwanta, dan neman magana ina jin shi ya matso kusa dani ya kwantar da kanshi a jiki na. Ina jin shi ya fara ta’be-ta’ben shi a jiki na ban ce mai komai ba. Sai da na ga ya canza salon da yake min ne yasa na fara k’ok’arin k’wace kaina. Matsawa nayi can gefe ina maida numfashi. A hankali Dr ya ce "Zarah me ya faru za ki min wannan hukuncin". "Ban da buk’atar abin da kake min ne, shi yasa" na fad’a. Kallo mai alamar tambaya ya watso min kana ya ce "Ban gane ba ki da buk’atar abin da nake miki ba, sai ki na da buk’atar hakan kenan sannan za ki bani hakk’i na". "Ni ban ce haka ba" na fad’a a tak’aice. "Kin ga Zarah, in ke baki da buk’ata, ni ina da ita, dole ne ki bani hakk’i na" cewar Dr. Wannan karan ban ce mai komai ba, sai ma kwanciya ta da nayi. Haka Dr ya matso ya fara yin yadda yake so yayi dani kasancewar nasan ko zan k’waci kai na wahala zan sha, dan d’azun ma da k’yar na k’waci kaina. Kuka na saka mishi, hakan yasa ya tsaya da abin da yake yi. Kallo na yayi ya ce "Zarah kukan me kike yi, dan zan amshi hakk’i na shine za ki sa min kuka, in dai dana bin da nake miki ne ba k’ya so, ni na hak’ura". Ci gaba da kuka nayi na ce "Dr ba akan wannan abi nda kake min nake kuka ba, duk da ka ce in bar maganar, but i can’t Dr, abin yana damu na a raina, plsss Dr ina so ka fad’a min dalilin da yasa ba ka so in je abin da ya danganci family d’in mu". Shiru yayi kana ya ce "Zarah, stop crying, i will tell you my reason, ba wai ba na so ki je abin da ya danganci family d’in ku ba ne, sai dan ina ganin kamar in kina yawan zuwa za a iya samun matsala dan na ga famiky d’in ku sun fi so ki auri d’an uwan ki, shi yasa na ke hana ki zuwa". "Dr wannan ba dalili ne da za ka dinga hana ni zuwa ba, Dr ina so in dinga zumunci da ‘yan uwa na, ina shiga cikin su, rashin zuwa na zai sa su ji haushin ka akan rashin bari na da ba kayi in suka fahimci kai ne ba ka bari na in je, ni kuma ba zan so a familin mu su ga laifin ka ba, bayan na baka trust akan cewa ba za ka bani kunya ba, sannan tunda aka yi auren mu ba wanda ya k’ara ta da wata magana akan rashin auran yaya Faruk da ban yi ba, yanzu ma kana gani bikin shi za a yi, ina ganin bai kamata ka kawo wannan tunanin a ranka ba". "Na fahimci kuskure na Zarah, zan kuma kiyaye kin ji my lovely Zarah, so wipe your tears and smile for me" ya fad’a yana sakar min tsadadden murmushi. Goge hawaye na nayi. "So smile for me" ya fad’a yana kallo na. Murmushi na sakar mai kana na kwanta a jikin shi. A wannan lokacin muka shirya ni da Dr. Ranar mun sha soyayya mai tsayawa a zuciya. A ‘bangaren yaya Faruk kuwa sai dai jiran ranar biki kawai yake yi dan ya gama shirye-shiryen shi. Nana tun ana saura sati d’aya suka fara gabatar da event d’in su kasancewar ta k’ara wasu event saboda yadda k’awayen ta suka matsa mata akan kamu da walima kad’ai sun yi musu kad’an, hakan yasa ta k’ara da Arabian night da bridal shower, yayin da Hajiyar su za tayi mothers day. Gyara na musamman aka yi ma Nana, wacce tayi mata gyaran ta k’ware a iya gyaran dan ko da yaya Faruk sai da ya ga ta k’ara mishi kyau, sai dai miskilancin sa bai bar shi ya fad’a mata hakan ba. Ita ma Anisa ta fara gudanar da event d’in ta. Duk da ina zuwa School hakan bai hana ni halartar duk event d’in da aka tsara ba, na ji dad’in yadda Dr bai hana ni zuwa event d’in ba dan ita ma Anisa sai da ta kwashe kwana biyar ana event na bikin. Ran Juma’a aka d’aura auran yaya Faruk da Nana Khadijah, bikin da ya samu halartar manya k’usoshi na Nigeria, dan ko ta wani’bangare abin sai san barka, ta ‘bangaren Yaya Faruk abokan shi sojoji da seniors d’in sa sun sami halartar bikin, Dadin shi kuwa manyan ‘yan kasuwa da ma’aikata sun halarci bikin, idan aka je ‘bangaren Dadin Nana kuwa ‘yan siyasa da wanda suka sauka da wanda suke kan mulki sun halarci bikin. Gaskiya wannan biki ya bar tarihi, dan shagalin da aka gabatar har kawo ranar bikin abin ba zai lissafu ba saboda yadda bikin ya k’ayatar. Bayan gama d’aurin aure ne aka zarce da Walima. Daga nan su Dadi suka dawo Kaduna aka d’aura auran yaya Khalil da Anisa. Taro dai haka ya ci gaba da gudana cikin jin dad’i da annashuwa, kowa ka gani kasan yana farin ciki da wannan ranar, dan biki ne da aka dad’e ba a yi irin shi a familin mu ba. San da na ga yaya Khalil ne ina ta tsokanar shi ran da yazo gidan su Anisa, da ya ce in kira ta na ce sai ya biya dan a yau Anisa tayi tsada, dariya ya min ya ce ko nawa ne zai iya biyan dan wannan ranar daban ce a gurin shi, sai da na gama ja mishi rai sannan na kira ta. Haka muka ta d’aukan hotuna, Hajiyan Wagini ma haka ta shigo hoton ana ta d’auka da ita kasancewar yanzu ta rage min fad’a, dan da tazo bikin tasa an kawo ta gida na. Haka Hajiyan Wagini ta sa kuka wai yau Allah ya nufe ta da ganin auren yaya Khalil da Anisa, ta gode ma Allah da ya nufa suka yi auran zumunci, ni da na k’i gashi Allah ya kawo wanda za su share mata hawaye, da k’yar aka samu Hajiyan Wagini tayi shiru. Sai da aka yi crossing of the Sword kana aka kawo Nana gidan ta da yaya Umar ya gina a sabon Kawo a Kaduna. Ban samu zuwa ba saboda ana shirye-shiryen kai Anisa, ina so akai amarya dani, da daddare sai muje dinner da Dr. Sai da aka kai Anisa gidan ta a unguwar rimi da Abbu ya gina ma yaya Khalil, ban koma gida ba sai da nayi sallar Magrib a gidan. Da zan tafi haka na dinga tsokanar Anisa, maimakon ta biye min sai kuka da tasa, tun ina mata dariya har sai da tasa nima na zubar da hawaye. Haka muka rabu da ita muna kewar junan mu, nasan soyayyar mu da Anisa daga Allah ne, ko mun yi fad’a za mu shirya, a tsakanin mu ba wanda yake iya dogon fushi da d’an uwan shi. Sai bayan isha’i ne muka shirya ni da Dr muka tafi inda za a gabatar da Dinner d’in. Ko da muka je an riga an fara event d’in. Hakan yasa muna shiga muka nemi guri muka zauna. Ana cikin gabatar da program of event d’in ne, MC ya kira ni a matsayin wacce za ta ba da tarihin amarya. Tashi nayi na je fara ba da tarihin amarya kana na k’ara da fad’an kyawawwan halayen ta, a k’arshe na k’ara da ba ma yaya Khalil amanar rik’e Anisa da amana, a k’arshe na yi ma wanda suka samu halartar dinner d’in fatan alkhairi, daga nan na ba ma Mc micro phone Na koma na zauna kusa da Dr. Haka aka ci gaba da gudanar da Dinner d’in. Ganin dare ya fara yi ne yasa muka tashi muka koma gida. Washe gari ma na je gidan Anisa, anan nake ji jiya bayan kawo amaryar, Momi ta had’a event WELCOME TO THE FAMILY in aka kawo Nana. Gaskiya Momi ba k’aramin tana ji ta yi ma bikin ba ganin tun da aka fara gudanar da bikin Momi ke ‘barin kud’i. Ban samu zuwa gidan Momi ba a ranar, hakan yasa ba mu had’u da Nana ba. Yaya Faruk kuwa yayi farin ciki da ganin wannan ranar mai tarihi, wacce take zuwa mutum sau d’aya a rana, ga kuma wanda Allah ya nufa da samun wannan damar. Ba abin da zai yi da ya wuce yayi ma Allah godiya na ganin wannan ranar da yayi. Da ma can Allah ya rubuta Nana ita za ta zama matar shi, hakan yasa wannan matsalar tazo bai aure ni ba duk kuwa da son da ya min. A yanzu ya sa ma ranshi zai zauna da Khadija a matsayi matar shi da ba ta kulawar da ta dace a matsayin ta na matar shi dan ita Allah ya nufa a matsayin matar shi. Kasancewar ba ran d’aurin auren zai je gidan shi ba, dan akwai ‘yan uwan Nanan wanda za su kwana, washe gari za su koma. Kafin yaya Faruk ya tafi gidan shi sai da yaje side d’in Dadi dan ya musu sallama. Cikin sa’a kuwa ya samu Momi a falon ita da Dadi. Sallama ya musu ya shigo kana ya zo kusa da Dadi ya zauna a k’asan carpet. Su biyun suka amsa mishi sallamar da yayi. "Barkan ku da hutawa" yaya Faruk ya fad’a. Dadi in ban da murmushi ba abin da yake yi. Momi kuwa farin ciki ne ya cika ta a ko ina wanda hakan yasa bakin ta ya kasa rufuwa. "Barka dai Faruk, har an shirya ne za a tafi gurin amarya, shi kenan yau Faruk zai bar mu" Dadi ya fad’a cikin wasa. Sunkuyar da kanshi yaya Faruk yayi yana murmushi. Dadi ne ya ce "Alhamdulillah, dukkan yabo ya tabbata ga Allah (S.W.A) da ya nuna min wannan rana da ya bani ikon aurar da kai da k’anwar ka Anisa, ban san yadda zan misalta farin cikin da nake ciki ba sai dai in yi ma Allah godiya, Faruk ina so ka rik’e matar ka da amana da gaskiya, ka da ka zalince ta domin Allah yana kallon ka, ita Allah ya za’bar maka a matsayin matar ka, kayi hak’uri da halayen ta, ka zama mai yi mata uzuri, hankalin maza da na mat aba d’aya ba ne, kaine a saman ta, kar ka dinga yawan mata fad’a, hakan zai sa ta dinga jin tsoron ka, Allah ubangiji ya baku zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba". Shi da Momi ne suka amsa da "Amin". Dadi ne ya kalli Momi ya ce "Hajiya ko kina da abin cewa". Momi ce ta ce "Duk abin da zan ce ka riga ka fad’a Alhaji, sai dai in ce Allah ya had’a kansu ya kuma tabbatar musu da zaman lafiya a rayuwar auren su". Haka yaya Faruk ya musu sallama ya tafi. Sai da ya biya gurin masu sai da kaji da drinks ya siya kana ya wuce gidan. San da yaje gidan shiru kasancewar ‘yan uwan ta sun koma Abuja. Side d’in ta ya shiga ya tarar ba ta falo, hakan ya tabbatar mishi da tana bedroom d’in ta. Lokacin da ya shiga d’akin, samun ta yayi a zaune akan bedroom ta sha kwalliyar ta. Sallamar da yayi ne yasa ta d’ago ta kalle shi. Had’a idon da suka yi ne yasa ta yi saurin sunkuyar da kanta. Murmushi yayi ya ce "Khadija kun ya ta kike ji ne". Ba ta bashi amsa ba illah murmushin da take yi. "Ina wuni" ta fad’a a hankali. "lafiya lau Khadija, ya taro". "Alhamdulillah". Shiru yayi kana ya ce "Kin ci abinci ne". "Eh Momi ta aiko da abincin". "Ok in za ki kwanta ki kashe bulb d’in d’akin ki, ni zan tafi in kwanta, ga nama nan ki ci ko ba yawa, nasan ba wani abincin kirki kika ci ga". "Na gode" ta bashi amsa a tak’aice. Fita yayi daga d’akin ya wuce side d’in shi. Jikin ta ne yayi sanyi jin cewa yaya Faruk ba a nan zai kwana ba, ita tsoro take ji dan side d’in ta shiru, sai dai tasan ba za ta iya ce mishi ya kwana a nan ba, dan ba taso ya d’auki maganar da wata manufa ta fad’a mishi. Wani tunani ne yazo mata akan cewa har yanzu yaya Faruk bai damu da it aba, saboda ba son ta a ranshi, in har da ya damu da ita ba yanda za ayi ya barta ta kwana ita kad’ai alhalin tana sabuwar amarya. Haka taci gaba da zancen zucin ta, ba ta san iya tsawon lokacin da ta d’auka tana tunani ba, da haka barci ya d’auke ta. Da asuba yaya Faruk yazo ya tashe ta tayi sallah kana ya wuce masalllaci. Da gari ya waye Nana ta tashi ta gyara side d’in ta duk da ba wani datti yayi ba, bayan ta gama ne taje ta yi wanka, tana fitowa ta zauna ta tsantsara kwalliyarta ta burgewa kana ta fito ta tafi kitchen ta d’aura musu breakfast. Tana cikin kitchen ne taji ana Knocking d’in k’ofar side d’in ta, zuwa tayi ta ga Momi ce ta aiko da Driver d’in su da kayan breakfast. Amsa tayi ta mishi godiya kana ta ce ya gaishe mata da Momi. Koma wa tayi ta kammala breakfast d’in da ta d’aura, bayan ta gama ne ta juye a food flask ta ajiye a Dinning table. Ganin har yanzu yaya Faruk bai fito daga side d’in shi ba ya sa ta fara tunanin ko taje ta sanar dashi ta gama had’a musu breakfast. Tashi tayi ta nufi side d’in shi, ganin k’ofar falon a bud’e yasa ta shiga da sallamar ta. Samun shi tayi da jallabiya a zaune yana kallo a Tv, hakan yasa ta kasa k’arasowa cikin falon. Amsa mata sallamar yayi ya maida kallon shi gare ta. Ganin yadda ta tsaya ta kasa shigowa ciki yasa ya ce "Khadija ki shigo mana ki ka tsaya a nan". K’arasowa tayi ta zauna nesa dashi kana ta ce "Ina kwana yaya Faruk". Da Murmushi a fuskar shi ya ce "Lafiya lau Khadija, kin tashi lafiya". "Lfy lau" ta amsa mishi a tak’aice. Shiru ne ya ratsa falon, in ban da sautin magana da ke fito wa a falon ba ka jin k’arar komai. Ganin shirun yayi yawa ne yasa yaya Faruk ya kau da shirun da cewa "Ya aka yi ne Khadijah". "Dama na zo in fad’a maka na had’a mana breakfast, Momi ma ta aiko mana da abinci" ta fad’a cikin sanyin murya. "Sannu da aiki, ki je ki yi breakfast d’in ki, ni sai anjima zan yi nawa in nayi wanka, ban cika yin breakfast da da wuri ba". "Toh" ta amsa mishi kana ta mik’e ta bar falon. Zama ta je tayi a dinning d’in, abincin da Momi ta aiko musu ta bud’e, Fankasau ne da vegetable soups wanda yaji naman kaza da naman sa a ciki, d’ayar food flask d’in farfesun kan sa ne a ciki, d’ayan kuma food flask d’in pepper cikin ne a ciki, duk cikin abin da Momi ta aiko musu sai taji ta fi marmarin fankasau, hakan yasa ta d’ebi kad’an taci kana ta had’a shayi a d’an k’aramin kofi tasha. Bayan ta gama ne breakfast d’in ne ta d’auki kayan da tayi amfani dasu ta je kitchen ta wanke. Tana gama wa ta ta dawo falo ta kunn Tv tana kallon tashar Joy Prime. Ba ta wani jima da zama ba sai ga yaya Faruk ya fito cikin shigar wani gezna shadda kalar light brown. Dinning ya wuce ya zauna, hakan yasa Nana ta mik’e taje ta yi serving d’in shi. Yadda take komai cikin natsuwa ne yasa yaji ta k’ara burge shi, komai in za tayi tana yin shi ne a natse. Bayan ya ta gama serving d’in shi ne ta tambaye shi ko akwai abun da yake buk’ata. Girgiza mata kai yayi alamar babu. Har za ta tafi ya kira sunan ta "Khadijah". Juyowa tayi ta kalle shi, tana jiran jin abin da zai fad’a mata. "Na gode" ya fad’a a hankali. Murmushi kawai tayi ta koma falon ta zauna taci gaba da kallo. Bayan ya gama breakfast d’in ne ya dawo ya zauna a falon yana danna wayar shi. Tashi tayi ta tafi dinning d’in ta d’auke kayan da ya ‘bata ta wanke kana ta dawo ta zauna. Hira ya fara jan ta jefi-jefi tana bashi amsa. Ya d’an jima da zama kana ya mik’e ya je side d’in shi ya fito. Kallon ta yayi ya ce "Khadija bari in je gidan Momi mu gaisa, in na fita sai ki kulle k’ofar, idan na dawo zan bud’e, akwai extra keys a hannu na". "Sai ka dawo yaya Faruk, ka gaida Momi da Dadi" Nana ta fad’a. Murmushi yayi ya ce "Za su ji". "Kar ki d’aura girki, Momi za ta aiko da abinci" cewar yaya Faruk. "Toh" Nana ta fad’a. "Me zan tawo miki dashi in zan dawo" yaya Faruk ya tambaye ta. "Ba komai" ta bashi amsa. Har ya fara tafiya ta kira sunan shi "yaya Faruk". Juyowa yayi ya na jiran jin abin da za ta fad’a mai. "Dama cewa zanyi ko za ka bud’e min side d’in ka in gyara ma". Yalwataccen murmushi ya sakar mata kana ya ce "Ki barshi Khadijah, bai yi wani datti ba, na riga na gyara, next time sai ki gyara min". "Toh" Nana ta fad’a. Fita yayi daga falon ya shiga motar shi, yana mai yabawa da halayen Khadija. Tashi tayi ta kulle k’ofar kana ta kashe kayan kallo ta tafi bedroom. Hajiyan su ta kira suka gaisa kana ta kira Anty Maryam suka sha hira, haka Anty Maryam ta ba ma yaya Mus’ab waya suka gaisa. Bayan ta gama wayar ne ta kwanta, ba a dad’e ba bacci ya d’auke ta. Sai can da yamma yaya Faruk ya dawo da kayan ciye-ciye da ya siyo, ya bata nata ya nufi side d’in shi. Sai da aka kira sallar magrib sannan taji alamar fitowar shi ya tafi masallaci, sai bayan sallar isha’i sannan ya dawo gidan. Side d’in ta ya shigo ya ganta a zaune a Dinning tana cin abinci. Kujerar da ke opposite d’in ta ya zauna. "Sannu da dawowa yaya Faruk" Nana ta fad’a. "Yawwa Khadija". "ya su Momi" Nana ta tambaya. "Suna nan lafiya, sun ce a gaishe ki" cewar yaya Faruk. Sanyayyen murmushi tayi kana ta ce "Ina amsawa". "yaya me zan zuba maka" Nana ta tambaye shi. Lumshe ido yayi kana ya ce "Ki zuba min duk abin da ranki ya miki". Bayan tayi serving d’in shi ne ta koma ta zauna. Jefi-jefi yake kallon ta ganin yadda ta kasa sakin jikin ta taci gaba da cin abincin, sai wasa da cokalin take yi. "Khadija ki ci abincin kar yayi sanyi" yaya Faruk ya fad’a. "Na k’oshi ne yaya Faruk" cewar Nana. Kallon abincin yayi ya ga ko rabi ba taci ba amma ta ce ta k’oshi, yasan zaman shi a gurin ne yasa ta takura. Bayan ya gama cin abincin ne ya ce "Khadija ki ci abincin, na ga ba wani abincin kirki ki ka ci ba". Yana gama fad’ar haka ya bar gurin ya koma falo ya zauna. Kwashe plate d’in tayi da cups ta kai kitchen ta wanke kana ta tafi bedroom d’in ta. Ya d’an jima a falon yana kallon action film kana ya mik’e ya shiga bedroom d’in Nana ya mata sallama ya tafi side d’in shi. Haka zaman su yaci gaba da gudana, idan yana gidan ya kan zauna su yi hirar duk da ba ma’abota surutu ba ne, zai tambaye ta ko akwai abin da take buk’ata, sannan in tayi girki zai zauna su ci, da daddare ya je ya mata sallama ya tafi side d’in shi. A ‘bangaren Nana ta rasa dalilin yaya Faruk na k’in kwana a d’akin ta a mastayin ta na sabuwar amarya, duk da yana k’ok’arin ba ta kulawa amma ba ta ganin hakan ya gamsar da ita, tasan ko wani ango wanda aka kawo mishi sabuwar amarya yana k’ok’arin ya ga ba ma amaryar shi lokacin shi wajen gudanar da tsaftatacciyar soyayya da amaryar shi, amma ita mai yasa yaya Faruk bai ba ta irin wannan soyayyar ba, ko hakan na nufin har yanzu ba ita ba ce za’bin shi da ba zai d’auke ta a matsayin amarya ba. Satin su uku a Kaduna yaya Faruk ya kai Nana gidan su Abbu da yaya Aminu da yaya Khalil suka gaisa kana ya wuce da ita gidan su Momi. Momi taji dad’in zuwan su, sai nan-nan take yi da Nana, ita kanta Nana taji dad’in yadda Momi ta nuna kulawar ta gare ta. Sai da daddare suka baro gidan su Momi suka musu sallama za su koma Abuja saboda hutun School d’in su Nana ya k’are wanda aka basu na k’arshen semester, shi ma yaya Faruk zai koma bakin aikin shi. Washe gari yaya Faruk ya d’auki Nana suka koma Abuja. Su Anisa da yaya Khalil sai cin amarcin su suke yi, yaya Khalil yana ba ma Anisa duk kulawar da ta dace. Ya kai ta gidan su Momi kana ya wuce da ita gidan su Abbu, a nan suka wuni, sai da daddare suka dawo gida. Yanzu kusan watan yaya Faruk d’aya da aure, har yanzu ba wani abu da ya shiga tsanin su na auratayya. Yau Nana tun da tashi take jin marar ta na mata ciwo, ta tabbatar da period d’in ta ne zai zo. Yanda take jin ciwo ba ta jin za ta iya tashi ta had’a musu breakfast. Hawaye ne kawai yake zuba a idon ta saboda yadda marar ta ke mata ciwo. Yaya Faruk ne ya shigo side d’in ta. Zama yayi a falon bai ji motsin ta ba. Idon shi ne yakai kan dining table ya ga ba komai a kai, hakan ya tabbatar mai da Nana ba ta had’a breakfast ba. Ya d’an jima a zaune amma har yanzu bai ji motsin ta ba. Tashi yayi ya nufi bedroom d’in ta. Ganin ta yayi a kan gado ta rik’e marar ta tana hawaye. Da sauri ya k’arasa gurin ta ya rik’o hannun ta. Bin ta yayi da ido yana ganin yadda ta ke rintse ido, da alama akwai abin da yake damun ta. "Khaldijah lafiya kike kuka" yaya Faruk ya tambaye ta cikin kulawa. "Mara ta ke min ciwo" cewar Nana. "Sannu, daman kina yin ciwon marar ne" ya sake jefo mata tambaya. D’aga mishi kai tayi alamar Eh. "Ki tashi ki yi wanka, bari in je in saman miki abin da zaki ci kafin mu tafi asibiti". A hankali ta tashi tana dafe da marar ta. Tausayin ta ne yaji ya kama shi saboda alamun su nuna marar ta matsa mata. Sai da yaga ta shiga ban d’aki kana ya fita daga d’akin. Ruwan tea yaje ya d’aura ya juye a flask. D’akin ya dawo ya ajiye flask d’in kana ya je ya d’akko milo da madara. Kakkauran Tea ya had’a mata ya mik’a mata. Kad’an tasha ta ajiye saboda yadda ba ta jin apatite a bakin ta. Ko breakfast bai yi ba ya ce ta fito su tafi. Wani private hospital suka je aka duba ta. Bayan ya gama gwaje-gwajen shi ne ya nemi yaya Faruk ya mishi bayani abin da yake damun Nana. Dr ne ya fara da cewa "Ba wata matsala ba ce ke damun matar ka illah ciwon mara da yawanci mata ke yi a lokacin da suke mensturation d’in su, ko wace mace da irin yadda ciwon yake mata, wasu suna shan wuya a lokacin da period d’in su ya zo musu, wasu za ka ga ba sa ciwon marar, ya danganta da halittar ta". Yaya Faruk ne ya k’ar’bi zanen dacewa "Dr akwai wani magani ne da yake tsayar da ciwon". "Akwai magunguna da allura da ke yi idan mace tana fama da ciwon marar, Wanda yawan shan Magungunan da allurar zai iya jawo wata matsalar in har ta zama addicted to it, za ta iya samun matsala a 'bangaren mahaifar ta ko dai ta wani 'bangaren, sai dai gaskiya abin da yafi magance wannan ciwo da ya wuce alak’a ta auratayya tsakanin miji da mata, in har namiji ya kusanci mace, za ta rabu da wannan matsalar". Dr ne yaci gaba da cewa "Yanzu zan rubuta magunguna sai ka biya pharmacy ka siya mata magunguna". "Na gode Dr" yaya Faruk ya fad’a. Hannu ya bashi suka yi musabaha kana ya je pharmacy ya siya magungunan, Nana ya d’auka suka tafi gida. Sai da ya tabbatar da tasha maganin ta sannan ya wuce side d’in shi. Zama yayi ya fara tunanin da likita ya mishi, kenan har da laifin shi wajen ciwon Nana, mai yasa bai sauk’e nauyin shi da Allah ya d’aura mai ba a matsayin shi na miji alhalin ita tana k’ok’arin ta wajen kyautata mishi, rasa abin da yake mishi dad’i yayi san da ya tuno halin da ya ga ta shiga san da take cikin ciwon, shawarar da yanke shine in har ta gama period d’in ta zai sauke nauyin da Allah ya d’aura mai. Rananr haka ya wuni a d’akin ta yana ba ta kulawa, da yaga ta motsa zai tambayaye ta ko ciwon ne. Sai da Nana tayi kwana biyar kafin mensturation d’in ta ya d’auke. Yaya Faruk da ya tabbatar da tayi tsarki yayi niyar kasancewa da Nana a yau. Da daddare har Nana ta kwanta taji sallamar yaya Faruk. Tashi tayi ta zauna ganin ya nemi gefen gado ya zauna. "Ba ki yi bacci ba Nana" yaya Faruk ya tambaye ta. "Eh ban riga nayi baccin ba" ta bashi amsa. Shiru yayi kafin ya d’aura da cewa "In ba damuwa ki same ni a side d’ina". Yana gama fad’ar haka ya tashi ya bar d’akin. Mamaki ne da tunani ya kama ta a lokaci guda, tambayar kanta ta fara yi mai za ta yi ma yaya Faruk in taje side d’in shi, tasan in abu yake da buk’ata zai fad’a mata, amma kawai ce mata yayi ta same shi a side d’in shi. Hijab ta d’aura akan sleeping dress d’in ta kana ta nufi side d’in yaya Faruk [8/11, 23:45] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa Writers Association *Amsar Question of the day ita ce Suratul Bak’ara tana karantar da kira zuwa ga addini da yadda ake ginin sabuwar al’umma daga mutane daban-daban na Jahiliyya*. *TUNATARWA*: _Ka/ki zamo mai magana, amma idan za ka/ ki fad’i ka/ki fad’i alkhairi_. _Ka/ki zamo mai adalci, amma kar ka/ki ce sai ka/kin iya ma kowa_. _Ka/ki so abin duniya, amma kar hakan yasa ka/ki mance da lahira_. 81-82 San da ta shiga ba ta ganshi a falon shi ba, hakan yasa ta nemi guri ta zauna. Ya d’an jima a zaune a d’akin bai ji shigowar Nana ba, hakan yasa ya fito da niyyar ya fito falo ya jira ta. Yana fitowa ya ganta zaune a falo. "Khadihah ya kika zauna a falo, ki zo mu shiga daga ciki" cewar yaya Faruk. Tashi tayi ta bi shi ba tare da ta ce komai ba. Gefen gado ta nemi guri ta zauna tana wasa da hannun ta da ke sanye da azurfa. Yanayin ta ya nuna a takure take da zaman. "Khadija ki shiga cikin bayi ki yi alwala" yaya Faruk ya fad’a. "Toh" ta amsa mishi. Bayin ta shiga ta d’auro alwala kana ta fito ta zauna. Tashi yayi suka yi sallar nafila raka’a biyu, bayan sun idar ne ya kama kanta ya dinga jero musu addu’o’i akan Allah ya basu zaman lafiya. K’aramin frij d’in da ke d’akin ya tashi ya d’akko musu fresh milk. Mik’a mata fresh milk d’in yayi ta amsa tare da cewa "Na gode". Murmushi kawai yayi ya nemi guri ya zauna. A hankali ta dinga sipping d’in fresh milk d’in, kad’an tasha ta ajiye sauran. Kallon ta yaya Faruk yayi, a ranshi yana yabawa da natsuwar ta, komai za tayi tana yin shi ne a natse, hakan yasa take k’ara burge shi. Tashi tayi ta d’auki ragowar fresh milk d’in ta maida cikin frij d’in. Kallon yaya Faruk tayi ta ce "yaya Faruk sai da safe". "Ina zaki tafi?" yaya Faruk ya tambaye ta a tak’aice. "Zan je in kwanta ne" ta bashi amsa. "Ba sai kin koma side d’in ki ba, ki yi kwanciyar ki a nan". Jim tayi kamar mai tunani, a lokaci d’aya kuma mamakin yaya Faruk take yi da y ace ta kwanta a d’akin shi, bayan yau kusan watan su d’aya da aure bai ta’ba gayyatar ta kwana a d’akin shi ba sai yau. Can k’arshen gado taje ta kwanta, yanayin kwanciyar ta kad'ai in ka kalla Kasan a takure take. Laptop d’in shi ya d’akko ya fara danna wa, ya d’an jima a zaune yana danna laptop d’in. Jefi-jefi yakan tsayar da danna laptop d’in da yake yi yana kallon Nana, ganin har yanzu ba tayi bacci ba, ga hijab da ta kwanta dashi yasa ya ce "Khadija ki cire hijab d’in nan, na ga kamar ya takura miki". In ban da ba ta son yi ma yaya Faruk musu, da ba za ta cire hijab d’in ba, dan za ta fi takure fiye da yanzu. Cire hijab d’in tayi ta linke shi ta ajiye a side bed. Ba ta wani jima da kwanciya ba bacci ya d’auke ta. Ganin tayi bacci ne yasa ya rage AC d’in da ke sanyaya d’akin, tashi yayi ya lullu’ba mata tattausan bargo. Sai da ya gama aikin da yake yi a cikin laptop ya kashe kana ya kashe bulb d’in d’akin, ya kunna dim light. Kwantawa yayi ya ci gaba da kallon Khadija da ke faman baccin ta, fuskar ta sai wani shek’i take yi kamar ba bacci take yi ba. Lokaci d’aya yaji tausayin ta ya kama shi na tsawan wata d’aya da ya d’auka ba tare da tasan miye aure ba, gashi ba ta ta’ba nuna mishi alamun jin haushin shi a fuskar ta ba, yasan abin na damun ta. Matsowa yayi kusa da ita, hannun shi ya kai kan fuskar ta, wani irin laushi yaji san da ya shafa fuskar ta, haka ya ci gaba da shafa fuskar ta har ya kai kan lips d’in ta, bai tsaya a nan ba ya fara shafa jikin ta. Lokaci d’aya ya ji ba abin da yake buk’ata illah ya kasance da Khadija. Kiss ya kai mata a goshin ta, a hankali ya gangaro zuwa le’ben ta ya manna mata kiss, a hankali yaya Faruk ya dinga sakar mata wani irin French kiss, haka yaya Faruk ya dinga aika mata kiss ko ta ina, lokaci d’aya yana shafa ta. Daga nan labari ya fara canzawa a gurin yaya Faruk. Ita kuwa Nana tun san da yaya Faruk ya fara shafata ta farka, sai dai ta k’i bud’e ido duk da tana tsoron abin da yaya Faruk yake mata, ga wani irin sak’o da yake aika marta da ya kashe mata jiki kasancewar wannan shine karo na farko da hakan ya kasance a tsakanin su. Haka yaya Faruk ya ci gaba da sarrafa Nana yanda yake so, sam ya manta da cewa budurwa ce kuma wannan shine karon ta na farko da hakan ya ta’ba kasancewa da ita. Ganin yadda yaya Faruk ya haukace mata yasa ta fara bashi hak’uri tana kuka, shi kuwa yaya Faruk duk wannan kukan da Nana take yi kamar k’ara ingiza shi take yi, tun tana kuka a hankali har kukan na ta ya fito fili, tsoron ta shine kar a ce allurer sojoji ce ta motsa zai sauke a kanta, da ko ta gama yawo, mutsu-mutsu ta fara yi ganin duk rok’on da tayi ma yaya Faruk bai san tana yi ba, tun tana ganin za ta iya jurewa har takai ga ko jikin ta ba ta iya motsawa, hawaye ne kawai yake zuba a idanun ta saboda gajiya da tayi da kuka. Yaya Faruk sai da ya sami natsuwa da ita kana ya ga aika-aikar da ya aikata mata. Kiran sunan ta yayi amma ba ta amsa mishi ba, sabod yadda bakin ta yayi nauyi ba ta jin za ta iya magana. Ga dai idon ta a bud’e tana kallon shi, in ban da hawaye da yake ci gaba da zuba a idanuwanta saboda wahalar da ta sha a hannun yaya Faruk. Tashi yayi ya shiga band’aki yayi wankan tsarki ya fito. Yadda ya bar Nana haka ya zo ya tarar da ita, hakan yasa ya tsorata. Da sauri ya hau gadon ya tallabo ta jikin shi. "Sorry Khadija, I don’t mean to hurt you, nasan ban kyauta miki ba da na tafiyar dake a haka, bazan sake ba kin ji". Ganin har yanzu ba ta ce mishi komai ba yasa ya ci gaba da cewa "Plsss Khadijah ki fad’a min in da yake miki ciwo, ko na ji miki ciwo ne?" ya k’arasa maganar da tambayar ta. Har yanzu dai Nana ba ta bud’e baki tayi mishi magana ba, duk da tana jin abin da ya fad’a mata. Tsoro ne ya k’ara kama yaya Faruk ganin re-action d’in Nana, kwantar da ita yayi ya sa mata pillow, tashi yayi ya d’ebo ruwa a bowl. Shafa mata ya dinga yi a fuskar ta, wata ajiyar zuciya ta sauke, hakan da tayi ne yasa hankalin shi ya fara kwanciya. Ajiye bowl d’in yayi ya dawo da kallon shi gare ta ya ce "Sannu Khadijah". Sunkuyar da kanta tayi ba tare da amsa mishi ba. "Za ki iya tashi ki yi wanka, ko in kai ki bayin" yaya Faruk ya tambaye ta. "Zan iya" ta fad’a cikin sanyin murya. A hankali ta sakko daga gadon, tafiya ta fara yi da niyar shiga band’akin, juwa ta fara d’ibar ta ganin ba wani k’arfi a jikin ta. Sauran kad’an ta fad’i yaya Faruk ya tashi ya rungumeta ta fad’a jikin shi. Kwantar da ita yayi akan gado yaje ya had’a mata ruwan d’umi kana ya dawo ya d’auke ta ya kai ta band’akin. Duk yadda ya so ya taimaka mata Nana ta k’i, hakan ya sa ya k’yale ta dan bai son takura mata. Dawowa yayi ya canza bedsheet d’in. Tausayin Nana ne ya dabaibaye zuciyar shi da dukkan sassan jikin shi, yasan ba k’aramin wahala ya ba ta ba, yasan Nana tayi k’ok’ari wajen jure ma buk’atun shi, wani irin feeling ya fara ji a zuciyar shi game da Nana, sai dai ba zai iya fassara wwani irin feeling ba ne. Lumshe idanun shi yayi ya fara tunano halin da suka kasance a awowin da suka wuce, tsintar kanshi yayi cikin wani irin farin ciki da annashuwa. Wani irin girma da matsayi ya k’ara ba ma Nana a zuciyar shi. Nana kuwa tun da ta gama abin da take yi a band’aki ta kasa fitowa saboda kunyar yaya Faruk da take ji. Ganin har yanzu ba ta fito daga band’aki ba yasa yaya Faruk ya tashi ya je yayi knocking d’in k’ofar. Bud’e k’ofar tayi ba tare da ta fito daga band’akin ba. Ganin ta yaya Faruk yayi ta jingina da tiles d’in da ke manne a jikin bangon bayin. Su na had’a ido tayi saurin sunkuyar da kanta. Murmushi kawai yayi ya shiga cikin band’akin ya rik’o hannun ta. Zaunar da ita yayi a gefen gado ya fita daga d’akin. Side d’in ta ya tafi ya d’akko mata wata night gown d’in kana ya dawo side d’in shi. Mik’a mata rigar yayi ta amsa. Kasa sa rigar tayi a gaban shi, hakan da ya fahimta ne yasa ya ce "Khadijah ki sa rigar". "Zan sa" ta bashi amsa a tak’aice. Tashi tayi ta koma band’akin tasa rigar, ta d’aura hijab d’inta a kai kana ta fito daga band’akin. Zama tayi a bakin gado ta sunkuyar da kanta, sam ba ta son su had’a ido dashi saboda wani irin kunyar shi da take ji. "Zo ki kwanta Khadijah" yaya Faruk ya fad’a cikin taushin murya. Kamar wadda take jiran a ba ta umarni, tashi tayi ta zo ta kwanta dan dama jikin ta ba k’arfi. Ba ta wni jima da kwantawa ba bacci ya d’auke ta. Yaya Faruk jefi-jefi ya kan kalle ta ya lumshe ido kana ya saki murmushi. Shi ma tashi yayi ya zo ya kwanta kusa da ita, nan bacci ya d’auke shi. Kiran sallar asuba ne yasa ya tashi ya nufi band’aki ya d’auro alwala, san da ya fito ya ga har yanzu Nana bacci take yi ba ta tashi ba, tunani ya fara yi ya tashe ta ko ya bari sai ya dawo daga masallaci, zuciyar shi tafi karkata akan ya tashe ta tayi sallar, in yaso in tayi sallar sai ta koma ta kwanta. Kunnen ta ya je yana hura wa, hakan da yaya Faruk ya ke mata ne yasa a hankali ta bud’e idanun ta. Tana ganin yaya Faruk kusa da ita tayi saurin rufe idanun ta, hakan da yaya Faruk ya ga tayi ne yasa shi sakin murmushi ganin tsakanin jiya da yau Nana kunyar shi take ji, ba ta son su had’a ido. A hankali ya ce "Ki tashi ki je ki yi sallah Khadijah an kira, zan je masallaci in dawo, in ki ka yi sallar sai ki kwanta". Duk wannan maganar da yaya Faruk yayi bai sa ta bud’e idanun ta ba, hakan ya sa ya mik’e da niyyar tafiya masallaci dana san abin da ya fad’a taji, kunya ce ba za ta bari ta bashi amsa ba. Bayan tafiyar shi masallacin ne ta tashi tayi sallar, bayan ta idar ne ta yi azkar d’in ta da addu’o’in ta kana ta tashi ta koma ta kwanta. San da yaya Faruk ya dawo daga masallacin ya tarar da ita ta koma baccin. Qur’ani ya d’auka ya koma falo ya zauna yana muraja’a, ya jima a zaune yana muraja’ar kana ya koma d’aki ya ajiye qur’anin. Kitchen ya nufa ya d’aura musu breakfast ya jera shi akan dinning table kana ya koma d’akin. Wanka ya shiga yayi kana ya fito ya shirya cikin wani tsadadden yadi. Har yanzu Nana ba ta tashi daga barcin da take yi ba, kusa da ita yaje ya zauna ya shafa fuskar ta, zafin da yaji ne yasa yayi saurin d’aura hanun shi a dokin wuyan ta, nan ma wani zafin yaji da yafi na fuskar ta, hakan ya tabbatar mishi da zazza’bi ne ya rufe ta. A hankali ya fara kiran sunan ta "Khadija". Bud’e idon ta tayi ta kalle shi kana ta lumshe idanun ta saboda yadda baccim bai ishe ta ba, ga kuma zazza’bi da ya rufe ta. "Kar ki koma baccin kin ji Khadijah, kwanciyar ta isa haka, na ji zafi a jikin ki ko ba ki da lafiya ne" ya k’arasa maganar yana kallon ta. D’aga mishi kai tayi alamar Eh. Tausayin ta ne ya k’ara kama shi dan yasan shi ya jawo mata wannan rashin lafiyar. Tashi yayi ya je ya had’a mata ruwan wanka kana ya rik’o hannun ta ya kai ta bayin. D’akin ta ya je ya d’akko mata wata doguwar riga na material da d’ankwali ya dawo ya ajiye mata akan gado. Falo ya fito ya zauna yana jiran ta, dan yasa in ta fito wanka ba za ta iya shiryawa a gaban shi ba. Nana na fito wa ta ta gogo jikin ta da d’an k’aramin tawul d’in da ke rataye a wata hanger ta musamman dan shanya tawul. Mai ta shafa ta d’auki rigar ta sa kana ta d’aura d’ankwalin ta fesa turaren da ta gani a gaban mirrow d’in shi had’in saudiyya. Fitowa daga d’akin tayi tana tafiya a hankali, daga gani har yanzu ba ta jin dad’in jikin ta. Nesa dashi ta zauna kana ta ce "Ina kwana yaya Faruk". Murmushi yayi kana ya amsa da cewa " lfy lau Khadija, ya jikin naki". "Da sauk’i" ta amsa mishi. "Yanzu ina ne yake miki ciwo?" yaya Faruk ya sake tambayar ta. "Ba inda yake min ciwo" ta amsa mishi. "Zo nan Khadijah" ya k’arasa maganar yana nuna kusa dashi. A kunya ce ta taso ta zauna kusa dashi. Hannun ta ya rik’o yana sakin wani tsadadden murmushi kana ya fara magana a hankali "Khadija na gode da kyautar da kika min mai mahimmancin, na gode da mallaka min kanki da kika yi, baki na ba zai iya fad’an farin cikin da nake ciki ba, duk yadda zan gode miki nasan yayi kad’an, ba abin da zan ce miki sai dai in ce na gode Khadijah, Allah ya saka miki da alkhairi ya miki albarka". Sunkuyar da kai tayi kana a hankali ta ce "Amin". Kwantar da kanta yayi akan kafad’ar shi, hannun shi ya kai kan dokin wuyan ta ya ji har yanzu da zafi a jikin ta. Kallon ta yayi ya ce "Khadijah kika ce ba in da yake miki ciwo, gashi na ta’ba jikin ki na ji da zazza’bi, taso mu je muyi breakfast sai in kai ki asibiti a duba ki". Hannun ta ya rik’e suka tafi dining suka zauna, da kanshi yayi serving d’in ta. Bayan sun gama breakfast d’in ne ya ce ta d’akko hijab (himar) d’in ta su je asibiti. Suna zuwa asibiti likita ya duba ta, magunguna da shawarwari likitan ya ba yaya akan nan gaba kar ya k’ara kwatanta ya da ya tafiyar da Nana kana suka ma Likitan sallama suka tafi. Tun da suka dawo gida yake tarairayar ta, motsi kad’an za tayi zai tambaye ta ina yake mata ciwo, ita kanta mamakin yaya Faruk take yi ganin yanda ya damu da halin da take ciki. Wayar shi ya d’auka ya kira yaya Mus’ab. Bayan ya d’auka ne suka gaisa kana yaya Faruk ya d’aura da cewa "Mus’ab in ba damuwa kasa Madam ta dafa mana da abinci zan zo in amsa". Yaya Mus’ab ne ya ce "Ina Nanan take da ba za ta dafa ba sai matata ta za a ce dafa abinci" ya fad’a da alamar tsokana. "Ba ta jin dad’i ne" ya amsa mishi a tak’aice. "Me yake damun ta" yaya Mus’ab ya sake tambayar shi. Sai da ya kalle ta ganin yadda ta marairaice fuska tana kwance a jikin shi. "Ina ruwan ka da sai ka ji abin da yake damun ta, tun da n ace maka ba ta da lafiya ba sai kayi mata addu’a ba, anya Mus’ab kai ba d’an jarida ba ne" shima yaya Faruk yay a amsa mishi cikin wasa. Dariya yaya Mus’ab yayi ya ce "Lallai Bregadier ka shigo cikin sahun manya, dole ka ce haka, kar ka manta kai k’ani na ne dan ka na auran k’anwa ta, ka ga dole ka min biyayya". Gaba d’ayan su suka sa dariya kana yaya Mus’ab ya ce "Bari in ma Maryam d’in magana, in ta gama girkin sai in kira ka a waya ka zo ka amsa, ka gaishe da Nanan". "Ok za ta ji, a gaishe min da Asim" yaya Faruk ya fad’a. Cikin wasa yaya Mus’ab ya ce "Au d’anka kad’ai za ka ce a gaisar, ba za ka ce in gaishe da Maryam ba ita da za ta muku girki, sai in fasa sa ta girkin". Murmushi yaya Faruk yayi kana ya ce "A gaishe ta". Dariya yaya Mus’ab yayi ya ce "Ko kai fa, har ka sa raina yayi sanyi". Girgiza kanshi yaya Faruk yayi yana jinjina yanda yaya Mus’ab yake da son tsokana. Sallama suka yi kana suka katse wayar. "Mus’ab na gaishe ki" yaya Faruk ya fad’a yana kallon ta. Tattausan murmushi tayi kana ta ce "Ina amsawa". Haka yaci gaba da jan ta da hira. Ranar haka yaya Faruk ya ba ma Nana lokacin shi tare da kulawar shi. Tun daga wannan ranar yaya Faruk suka d’aura rayuwar auran su cikin kulawa da tarairaya, duk wanda ya ga yanda zaman su yake gudana sai yayi sha’awa, yanda suke gudanar da zaman su kamar wanda suka dad’e a cikin soyayyar junan su. In ka yi duba da Nana da yaya Faruk kasan sun canza, har wani haske da fresh suka yi, saboda kwanciyar hankali da zaman lafiya da suke yi, ga kuma dad’in amarcin su da suke ci. Kusan watan su biyar da aure aka tura su yaya Faruk wani course a can k’asar Morocco na tsawon wata uku, har da yaya Mus’ab za su yi tafiyar. Lokacin da zasu yi tafiyar, haka Nana ta dinga ma yaya Faruk kuka, yaya Mus’ab sai tsokanar ta yake yi, shi kanshi yaya Faruk daurewa yake yi dan a yanzu yana jin Nana a duka sassan jikin shi, ga sabo da shak’uwa da suka k’ara yi, dad’in dad’awa ga jikin ta da zai yi missing, lallashin ta ya dinga yi tare da mata alk’awarin za su dinga waya, da k’yar yaya Faruk ya shawo kan Nana ta daina kukan. Sai da taga sun shiga mota sun bar harabar gidan kan ta koma cikin gida cike da kewa, sai a yanzu ne ta tabbatar da feeling d’in da take ji tun kafin su yi aure ba komai bane illah son yaya Faruk, a yanzu ta tabbatar da cewa son yaya Faruk ya gama ratsa duk wani sassan jikin ta da jijiyoyin ta. Duk da har yanzu ba ta san zuciyar yaya Faruk game da ita ba, tasan yadda yake kula da ita da ba ta kulawa ta musamman da kuma kyautata mata da yake yi tasan alamu ne na ya damu da ita, ita ko hakan da yake mata bak’aramin jin dad’i hakan yake sa ta ba, tasan nan gaba kad’an insha Allah tana sa ran cewa yaya Faruk zai so ta wanda a yanzu ba abin da take fata sama da hakan, tasan duk wani irin kyautata wa da zai mata zai biyo bayan soyayya ne, in har ta samu soyayyar yaya Faruk ba ta da sauran wata buk’ata a gurin shi, ko a yanzun da bai fito ya bayyana mata birnin zuciyar shi ba ta mishi uzuri akan halin da ya tsinci kan shi a dalilin soyayya wanda a k’arshe bai ci ribar soyayyar da yayi ba, dole ne yayi taka tsantsan dan guje ma faruwar hakan. Ranar haka Nana ta wuni tana tunanin yaya Faruk. Da daddare da tazo kwanciya wani irin kewar shi ce ta addabe ta saboda yadda ya saba mata da jikin shi, hakan yasa da k’yar bacci ya d’auke ta. Haka Nana taci gaba da zuwa makaranta, wani lokacin in suka yi waya da yaya Faruk tana fad’a mishi za ta gidan Anty Maryam da gidan Hajiyan su, bai cika han ta zuwa ba dan yasan ka’aici na damun ta. Yaya Aminu yazo da Anty Jiddah sun wuni kana suka juya Kaduna. Yaya Khalil ya kawo Anisa da Ummu, kwanan su d'aya suka koma Kaduna. Nana suna yawan waya da Momi suna gaisawa, Anisa ma na kiran ta koi ta ta kira ta, ko ta ina Nana ba ta da matsala, dan yaya Aminu ya kan zo Abujan yaji ko tana da wata damuwar ko dai wani abu da take buk’ata. Sai da yaya Faruk suka kwashe wata uku har da k’arin sati biyu a kai kana suka dawo gida Nigeria. Sai da suka fara zuwa office aka gabatar da liyafar da aka had’a musu na murnar dawowar su kana suka tafi gida. Nana da take ta faman harkokin ta, sam ba tasan a ranar yaya Faruk zai dawo ba, ko da suka yi waya dashi a jiya bai fad’a mata za su dawo ba, shi yasa ba ta kawo dawowar shi a wannan lokacin ba, duk da a lissafin ta tasan sun wuce lokacin da ya ce mata za suyi a k’asar Morocco da suka je. Tana zaune a falo tana kallon wani Nigerian series na Rahama Sadau mai suna *Shuga naija* da ake watsowa a tashar tauraron d’an adam. Knocking taji ana yi, hakan yasa ta maida hankalin ta bakin k’ofa tana tunanin ko wa yake yin knocking. Tashi tayi ta nufi k’ofar ta bud’e. Idon ta ne ya sauka akan yaya Faruk dake tsaye sanye da kakin shi, wani irin kyau ta ga yaya Faruk ya mata. "Ko dan sun jima ba su ga junan su ba ne?" ta tambayi kanta. Wata zuciyar tace mata daman yaya Faruk tun ainihi mai kyau ne, sai dai canjin guri da ya samu yasa k’yan shi ya k’ara fitowa. Yalwataccen murmushi ta sakar mai kana ta bashi hanya ya shigo cikin falon. Tun da ya had’a ido da Nana ya ji wani farin ciki ya lullu’be shi ko ta ina, sai a yanzu ne ya k’ara tabbatar da yayi missing d’in ta da ya gan ta. Wani irin tsadaddan kallo yake jifar ta dashi, a lokaci d’aya yana sakin wani lallausan murmushi. "Sannu da zuwa yaya Faruk" ta fad’a cikin sweet voice. "Yawwa Nana, amma haka ake wa miji sannu da zuwa in ya dawo daga tafiya" ya fad’a yana kallon ta. Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi ba tare da ta amsa mishi tambayar da yayi mata ba. Yasan tayi farin cikin ganin shi lura da farin cikin da ya lullu’be fuskar ta, sai dai yasan kunya ba za ta barta ta nuna mishi hakan ba. Hannun shi ya bud’e ya ce "Khadijah, come close to me". A hankali ta dinga takowa har ta k’araso kusa dashi. Hannayen shi yasa yayi hugging d’in ta. "I miss you Khadijah" yaya Faruk ya fad'a a hankali. Hannun ta ya rik'e har zuwa kan 2-sitter. "Nana ki fad'a min kin yi missing d'ina" ya k'arasa maganar yana kallon ta. Murmushi tayi ba tare da ta ce komai ba. A ranta kuwa cewa take yi yaya Faruk ni kad'ai nasan halin da na shiga San da ba ka nan, baki na ba zai iya fad'a maka yadda nayi missing d'in ka ba. "Ko ba ki yi missing d'ina ba" ya tambaye ta da alamar wasa. "Nayi missing d'inka yaya Faruk". Tashi yayi ya ce " Khadijah bari in je in kwanta, in an kira Sallah ki tashe ni". "Toh yaya Faruk". " yaya Faruk bari in sama maka abin da za ka ci, ban san yau za ka dawo ba". "No ki barshi Khadijah, mun ci abinci a office lokacin da muka dawo, sai da daddare zan ci" Side d'in shi ya nufa yayin da Nana ta wuce kitchen dan tayi ma Yaya Faruk girki. Ana gab da kiran sallah ta had'a mishi ruwan wanka kana ta je ta tashe shi daga barcin. Bayan yayi wanka ne ya wuce massalaci kasancewar an fara kiran sallah. Bai dawo ba sai da yayi sallar isha'i. Bayan sun ci abinci ne suka dawo Falo, labarin tafiya course d'in da suka je ya ba ta kana daga k'arshe ya ce su tashi su je su kwanta. Yau ma dai da suka kasance a tare sun nuna ma junan su sunyi missing d'in junan su. Bayan sati d'aya da dawowar yaya Faruk ya ce ma Nana su shirya su je Kaduna kasancewar ranar weekend ne, sai su dawo a washegarin ranar. Kwanan su d'aya a Kaduna suka dawo Abuja. Haka rayuwar auran su ta ci gaba da gudana. A ‘bangare na kuwa haka zaman mu ya ci gaba da gudana, yayin da na ci gaba da karatu na ba tare da wata matsala ba. Tsakani na da Meema abin gaba yake yin a rashin jituwa, gashi Hanan na lura tana goya mata baya akan abin da take min. Yanzu takai ba na jin zan juri abin da Meema ke min dan nasan in har na fad’a ma Dr ban san wani hukunci zai d’auka a kanta ba, ina ganin zan iya d’aukar mataki da kaina ba tare da na fad’a mishi ba. Yau ranar ta kasance ranar Friday, na dawo school da wuri. Kwanciya na je nayi saboda a gajiye na dawo. Ban wani jima a baccin ba na tashi. Wanka na shiga na yi na nemi simple dress na sa. Fitowa nayi da niyyar in je in d’aura girkin dare naji ana Knocking d’in k’ofa. Ina bud’ewa na ga su Meema ne da su Hanan. Hanya na basu ina musu sannu da zuwa. Farida ce kad’ai ta amsa min a cikin su. Drinks na je na kawo musu da snacks dan ban a rabo da yin snacks saboda zuwan bak’i. Hanan da Farida ne suka gaishe ni na amsa musu. Sai bayan mun gaisa ne Meema ta gaishe ni a wulak’ance, yanayin yadda ta gaishe ni haka nima na amsa mata, dan a yanzu ina ganin ba zan jure ma abin da Meema ke min ba. Zama nayi muka d’an ta’ba hira, gefe d’aya kuma hankali na yana kan wani shiri da ake gabatarwa a tashar Z Tv. Tashi nayi na je na d’aura girki kana na dawo da niyyar ci gaba da kallon shirin da ake yi a tashar. Samu nayi an canza channel d’in da nake kallo an sa wata channel d’in music, wak’ok’in da ake sa wa ba k’yan gani a channel d’in, Meema sai bin wak’ar take yi kamar ita ta rera wak’ar. Ganin remote a hannun Meema ya tabbatar min da ita ta canza channel d’in da nake kallo. Raina ne ya ‘baci da abin da Meema ta min amma sai na daure ban nuna hakan a fuska ta ba. Cikin taushin murya na ce "Meema d’an dawo min da channel d’in da nake kallo, ina son shirin da ake yi ne, na ga ma sun kusa gama wa, in aka gama sai ki dawo da channel d’in da kike kallo". Wani banzan kallo ta watsa min kana ta ce " Wannan nayi niyyar kallo, dan haka bazan canza ba". Kallon mamaki na bi ta dashi, ganin yadda take son nuna min mulkin mallaka ni da gida na. "Amma dai Meema kin san ni nake kallo kafin in bar gurin ko, dan na ce ki maida min channel d’in da nake kallo za ki ce ba za ki canza ba" na fad’a ina k’ok’arin controlling d’in fushi na. "Ba zan canza ba Zarah" ta fad’a ba tare da wata shakka ba. Ganin in na tsaya bin Meema a hankali za ta ci gaba da raina min hankali, dan haka na watsa mata harara na ce "Kin san dai gida na kika zo kika same ni, kin ga kenan baki da ikon nuna min isar ki a inda baki da ikon yin haka, dan haka dole ne a canza channel d’in nan dan ba ita nayi niyyar kalla ba". Kallon mamaki ta bi ni dashi ganin yadda na fad’a mata maganar da ba tayi zaton zan maida mata martanin maganar da na fad’a mata. Yatsina fuska tayi kana ta ce " Masu gida manya, amma ina jin shi gidan da kike tunk’ahon dashi, kema ba naki ba ne, na yaya Sadik ne, kin ga ina da ikon amfani da abin da yake nashi". Dariyar tura haushi nayi kana na ce "Ina ganin bakin ki bai fad’a miki gaskiya ba, ki kalli falon nan da kyau, komai da kika gani a falon nan daga gidan iyaye na aka kawo ni dashi, kin ga kenan ba ki da power da kayan nan side d’in, in iko kike so ki nuna min, ki je can side d’in shi Sadik d’in sai ki yi ikon ki a can, in ma side d’in a kulle yake ki zo in baki key d’in side d’in, in nayi niyya ma ko can d’in side d’in Dr d’in, zan iya nuna matsayina na matar gidan ba ke ‘yar d’osano ba". Kwalliya ta biya kud’in sabulu dan maganar da na maida ma Meema sun k’ona mata rai, in ka kalli fuskar ta zaka ga canzawar da tayi zuwa ‘bacin rai. "Ke Zarah har kin isa ki min gori dan na zo gidan yaya Sadik, kin san Dad d’ina yana da kud’in da zai iya siyan fiye da kayan da kike cika mana bakin an kawo ki dashi, in banda kin ci darajar yaya Sadik da sai kin yi danasanin maganar da kika fad’a min, da kike tunk’ahon ke matar gida ce, dan dai Allah bai nufa mun yi aure da yaya Sadik ba ne, da ba ki isa ki shigo cikin gidan nan ba" Meema ta fad'a cikin fushi. Mamakin furucin Meema nayi wai dan Allah bai nufa sun yi aure da Dr ba ne, da ban isa in shigo gidan ba, sai yanzu ne na san alak’ar Meema da Dr ba kamar yadda Dr ya fad’a min cewa yarinyar abokin baban su ce, kenan bayan wannan har da alak’ar soyayya a tsananin su, no wonder shi yasa take min abinda ta gadama, ashe kishi ne ke damun ta da kuma takaicin Dr bai aure ta ba. "Amma me yasa Dr bai fad’a min alak’ar su ba, dan me zai ‘boye min tsakanin su, me yasa bai aure ta ba?" duk wannan tambayoyin da nayi ma kaina nasan Dr ne ya kamata ya amsa min. Duk da kishin da ya turnik’e ni, ban bari Meema ta gani a fuska ta ba. Murmushin yak’e nayi na ce "wannan matsalar ki ce Meema, ko k’aruna ne Dad d’in ki k’arewar kud’i ba matsala ta ba ce dan ban ta’ba zuwa gidan ku maula ba bare ki goranta min, kuma me shi bay a fad’a sai dai a gani a jikin shi, kin san akwai masu kud’i, akwai muna masu kud’i, kin ga kenan za ki iya banbance a jerin da kuke, maganar alak’ar ki da Dr a da ba damuwa ta bace dan yanzu ni ce a matsayin matar shi, sai nayi niyyar bashi izini sannan zai k’ara, kin ga na zama zarah a cikin taurari, ba irin ki ba da ba ki kai matsayin da za a sa ki a jerin mata ba tun da har kika sa nuna kissar ki irin ta mata Dr ya aure ki". Tun san da muka fara musayar yawu da Meema, ba wanda yayi magana a cikin su Hanan da Farida, sai wannan karan ne Hanan ta sa bakin ta da cewa "Anty Zarah, bai kamata ki dinga fad’a ma Meema wa’innan maganganun ba, ita ma matsayin k’anwa take a gurin yaya Sadik, Allah ne bai nufa za su yi aure ba, da tana nan a matsayin matar shi". "Ya ishe ki Hanan, kar ki k’ara sa min bakin a cikin maganar nan, ki bari wacce nake yi dominta ta bani amsa da bakin ta, dan daman nasan bayan ta za ki bi" na fad’a cikin ‘bacin rai. Yatsina fuska Hanan tayi kanata ce "Dole in fad’i gaskiya in ya zama dole a fad’e ta". A yanzu ban da lokacin kula Hanan, na fi so in fara maganin Meema dan ita ce take so ta shiga harka ta, so nake in nuna mata nima ba kanwar lasa ba ce. Da alama na fara samun nasara akan Meema, dan tun da na bata amsar maganar da ta min take huci, a yanayin ta so take yi muyi wacce za muyi, nima kuma a shirye nake da duk wani abin da take ji dashi. Juyowar da zan yi dan mu ci gaba daga inda muka tsaya da Meema, ba zato naji saukar mari a fuskata. Meema ce ashe ta taso tazo in da nake lokacin da na juya ina ma Hanan magana. Cikin huci ta ce "Ke har kin isa ki fad’a min magana in k’yale ki, nawa kike, wanda suka fi ki ma basu isa bare ke, ke ko kallon banza mutum ya min sai yasan ya ta’bo ne bare ke har da zaki bud’e rubbush mouth d’in ki kina fad’a min maganar da tazo bakin ki, ina so in yi warning d’in ki, daga rana mai kamar ta yau, in har kika k’ara bud’ar bakin ki kika fad’a min maganar da ba ta min ba sai kin gane kuren ki, ke ko kallon banza kika min ranar sai kin yi danasani, ki rubuta ki ajiye sai na nuna miki yaya Sadik nawa ne, sai na aure shi….". Kan ta gama maganar da take yi ni tsinka mata kyawawan mari guda biyu wanda suka fi wanda ta min zafi. A yadda re-action d’in ta da tayi ya nuna marin ya shige ta dan har dafe kuncin ta tayi. Hannu ta d’aga da niyyar kai min wani marin, nayi saurin sa hannuna na rik’e hanun ta na watsar. "Kin yi kuskure Meema da kike tunanin in kika mare ni kamar kin ci bulus, ko a yanzu hannun ki yakai kan fuskata sai na miki mafiyin shi, in kuma kina musu ki gwada ki gani yadda za mu kwashi ‘yan kallo dake, ni da kike gani ba na barin ta kwana, ina k’yale ki ne dan darajar Dr da kuma matsayin kin girme ni, tun da na lura shekarun naki basu da amfani ki da komai ba sai koma baya da ya haifar miki, to ni kuma zan taka girma" na fad'a. Farida ce ta tashi tana bani hak’uri akan in yi shiru in k’yale Meema. Ganin yadda Farida ke bani hak’uri ne yasa na yi hanyar kitchen dan ni sai yanzu na tuna da abin da na d’aura. Ina cikin kitchen d’in ina jiyo maganganun da suke yi. Wani dogon tsak’i Hanan tayi kana ta ce "Ke dai Farida banza ce, kina kallo ta mari Meema, ban da maganganun da ta fad’a ma ta, shine har da ba ta hak’uri, maimakon ki ba ma ita Meeman hak’uri akan zarafin ta da Anty Zarah taci mata, shine kike ba ma ita Anty Zarah hak’uri dan neman gindin zama". Meema ce ta k’ar’bi zancen cikin masifa ta ce "Ki k’yale ta Hanan, na lura daman ita Farida tana bayan Zarah ne, sam Farida ba ta kishi na". Maida kallonta tayi ga Hanan ta ce " Can you imagine Hanan, wai ni yarinyar nan ta d’aga hannu ta mara, sai tayi danasanin marin da ta min, zan koya mata hankali". Hanan ce ta watsa mata harara ta ce "too late Meema, ai kin bani haushi da kika tsaya ta mare ki har two times ba tare da kin yi d’auki mataki ba, yanzu sai dai ki yi hak’uri kawai dan tayi winning akan ki". Farida ce ta ce " Abin da kuke yi bai kamata ba, in maganar gaskiya tazo a fad’a, Anty Meema you a the one that start causing this fighting, abin da yasa kika ji haushi dan ta rama abin da kika mata ne, kuma ni ban ga laifin ta ba, dan ko ni aka yi ma haka matakin da zan d’auka kenan". Gaba d’ayan su suka taso mata wai daman sun san baya na za ta bi. Meema ce ta ce su taso su tafi gida. Tashi suka yi suka fita daga falon ba tare da sun min sallama ba. Farida ce ta shigo kitchen d’in ta min sallama. [8/24, 22:20] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA* 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa Writers Association *HAPPY EID-EL KABIR* _Ina ma d’aukacin musulmai da fans d’ina barka da sallah_. _Allah muke rok’o ya maimata mana, yasa muna da rabon ganin na wata shekarar_. _‘yar mutan Paki na k’ara muku barka da sallah_. _Tak’abbalal lahu minna wa minkum_ 83-84 Ina jin tashin motar su na ja d’an k’aramin tsaki, takaicin Meema ne ya bi ya dame ni, nasan a yanzu za ta ji shakkar k’ara shiga gona ta tun da muka yi haka da ita. Jiran Dr kawai nake yi ya zo ya k’ara min bayanin Meema kamar yadda ya ‘boye min alak’ar su a baya, sai a yanzu da nake ji a bakin Hanan da Meema cewa akwai alak'ar soyayya a tsakanin su a da wacce ban san da ita ba. Shi kanshi haushin Dr d’in nake yi akan yadda ya ‘boye min alak’ar shi da Meema. Da haka na k’arasa girkin na fito kitchen na wuce d’aki na. Su Meema kuwa tun a hanyar su ta dawowa gida su da Meema da Hanan suke maganganun su akan abin da ya faru a gida na da suka zo, ita dai Farida kallon su take yi dan tasan in ta sa bakin ta fad’an kan ta zai dawo. Har suka k’arasa gida ba su daina maganar da suke yi ba a kaina. Momi suka samu a falo sanye da medicated glass a fuskar ta tana karanta jarida. Suna shiga falon Meema ta fad’a jikin Momi ta fara kuka. Hankalin Momi ne ya tashi ganin yadda Meema ke kuka. Tambayar su tayi me ya sami Meema take kuka. Hanan ce ta kwashe komai ta fad’a ma Momi abin da ya faru a tsakanin mu da Meema. Ran Momi ne ya ‘baci jin cewa na mari Meema. Wayarta ta d’akko ta kira Dr akan in ya tashi daga aiki yazo tana son ganin shi. Dr yana tashi daga aiki ya wuto gidan su. Samun su yayi a falo suna kallo, bayan sun gaisa ne ya tamaye su ina Momi. Fad’a masa suka yi tana d’akin ta. K’arasa wa d’akin ta yayi ya same ta resting chair, gaban ta kayan marmari ne a ajiye akan d’an k’aramin centre table tana ci. Sallama yayi ya nemi kusa da ita ya zauna. "Sannu da hutawa Momi" Dr ya fad’a. "yawwa" ta amsa mishi a tak’aice. Ci gaba tayi da cin fruit d’in ta ba tare da tayi magana ba. Kau da shirun yayi da cewa "Momi gani, naji kin kira ni a waya ki na nema na". Sai a lokacin ta maida hankalin shi gare ta tace " Magana nake so muyi akan matar ka". Kallon ta yayi yana jiran jin mai za ta ce a kaina. "Sadik!" Momi ta kira sunan shi. "Na’am Momi" ya amsa mata. Momi ce ta fara da cewa "Sadik tun farko na nuna maka sha’awar auran Meema amma ka ce kai sai Zarah kake so, ka fara kawo wasu hujjoji wanda ban gamsu dasu ba akan Meema da ka bayar, ban sani ba ko ita Zarah tafi saura mata ne da ka dage sai ita oho, let me go straight to the point in fad’a maka dalilin da yasa na kira ka, yau su Meema sun je gidan ka, matar ka ba ta ji kunyar kowa ba ta mari Meema, sannan daga Hanan ta yi mata magana ta fara mata fad’a, so ina so ka ja ma matar kunne akan ta fita harkar Meema, in ban da ka k’i ta da ita za ta zama matar ka, sannan kar ta k’ara kuskuren yi ma yara na fad’a dan ka san ko ni ba na matsa musu". Tun da Momi ta fara magana yayi shiru yana sauraren ta, dalilin da yasa na mari Meema yake yi, gashi yanzu Momi sai fad’a take yi, shima kan shi bai ji dad’in abin da nayi ba duk da bai san abin da ya had'a ni da Meema ba. "Amma Momi me ya had’a su da Meemam har ta mare ta" Dr ya tambayi Momi. Momi ce ta bashi amsa da cewa "Just akan ita Zarah ta kunna Tv tana kallo, so shine Meema ta d’au remote ta canza da ta ga Zarah ta bar falon, shine ita Zarah da ta dawo wai ta fara fad’a musu magana akan canza channel d’in da Meema tayi, har ta nace mata kayan ta ne, in suna so su nuna iko ne su je can side d’in ka, duk wannan bai ishe ta ba har da sa parent d’in Meema a ciki". Jin bayanin da Momi ta mishi ya k’ara ‘bata mishi rai, for what reason dan k’annen shi sun je gidan shi zan neme su da rigima, ba zai ti tolerating d’in abin da nayi ba. "Ki yi hak’uri Momi, zan mata magana in na koma, I d’ont expect that a gurin Zarah, zan d’au mataki akai". "That’s better" Momi ta fad’a. Canza akalar hirar Dr yayi, dan yasan Momi abu kad’an take jira ta fad’i aibu na tun da Dr ya k’i auran Meema. A nan Dr ya ci abincin dare, sai da yayi isha’i sannan ya bar gidan. Ranar Dr bai dawo da wuri ba sai wajejen bayan sallar isha’i sannan ya shigo gidan. Ina zaune a falo ina pressing d’in waya ta ya shigo da sallama, amsa mishi nayi kana na mishi sannu da zuwa, fuskar shi ba yabo ba fallasa, ya amsa min. Nima yadda na ke jin haushin shi yasa na k’ara d’aure fuska ta ba tare da na k’ara mishi magana ba. Side d’in shi ya wuce yayi wanka kana ya canza shigar shi cikin k’ananun kaya ya dawo side d’ina. Kujerar da ke kallo na ya zo ya zauna yana kallo na ba tare da ya min magana ba. "Dr ga abincin can a dinning, mu je in yi serving d’in ka, ko in kawo maka nan ne". "Ki bar shi na ci a gurin Momi" cewar Dr. Shiru nayi ban ce komai ba, sai ma ci gaba da pressing d’in waya ta da nake yi. "Zarah! Dr ya kira suna na. D’agowa nayi na kalle shi jin yanda ya kira suna na nace "Na’am Dr". Cikin d’aurewar fuska ya ce "Akan wani dalili yasa ki ka mari Meema har ki ka sako parent d’in ta a ciki, sannan dan Hanan ta miki magana ita ma kika had’a da ita, ba ki san Meema ta girme ki ba, ko da a ce ba ta girme ki ba ya kamata a ce ta ci daraja ta ko me ta miki, duk abin da ta miki ba sai ki bari in na dawo ba sai ki fad’a min in d’au mataki amma sai ki zauna ki na fad’a mata bak’ak’en maganganu, Zarah ba na son rigima, ba na so tun yanzu ki fara samun matsala da family na". Raina ne ya k’ara ‘baci da irin yadda ya je gidan su aka fad’a mishi gaskiya da k’arya kuma ya d’auka ba tare da ya ji ta baki na ba, ya tasa ni a gaba sai fad’a yake min ba tare da ya ji nawa bayanin ba. Shiru na mishi duk da yadda raina yake a ‘bace na daure ban mishi magana ba har ya gama fad’an shi. "Zahra kina ji ina miki magana shine kika min shiru, ko ke ba za ki yi laifi a miki fad’a ba" Dr ya fad’a cikin fushi. Cikin ‘bacin rai na ce "Me kake so in ce Dr, ina ganin duk abin da zan fad’a an riga an fad’a maka shi kuma ka yarda, ka ga kenan bayani na bai da wani amfani a gurin ka, in da hukuncin gaskiya ka ke so ka yanke ai sai nima ka tambaye ni abin da ya had’a ni da Meeman har na mare ta, amma da yake abin son kai ne ka yarda da maganar da k’annen ka suka fad’a maka akan abin da ya had'a ni da Meema". Wannan karan a hankali ya min magana ya ce "Me ya had’a ku da Meeman?". Kallon shi nayi na ce "Abin da suka fad’a maka shi ya had’a ni da ita, duk abubuwan da Meema take min ban ta’ba kai k’arar ta gurin ka ba saboda rugudun rigima, yanzu ga shi su sun fad'a maka ka yarda da maganar su, ni da ban da Wanda zai tare min ai sai dai in yi hak'uri da abin da suka fad'a maka". Ci gaba nayi da cewa " Ni ba ruwa na da girman ta tun da ita Meema ba ta ja girman ta ba..". Dr ne ya katse ni da cewa "Ya isa haka Zarah, plss ki dinga hak’uri da abin da Meema za ta miki, ba na son hayaniya". "A kan me zan yi hak’uri da ita ban da wanda nayi a farko, ko da yake ban ga laifin ka ba dan ka ce in yi hak’uri da ita tun da akwai alak’ar soyayya a tsakanin ku a da wanda ba ka fad’a min ba, sai a yau da nake ji a bakin su" Na k’arasa maganar ina jiran jin mai zai ce min. Shiru yayi bai ce min komai ba, sai ma bi na da ido da yake yi. Ci gaba nayi da cewa "Dr me yasa ka ‘boye min alak’ar ka da Meema bayan kasan duk daren dad’ewa zan ji mai ke tsakanin ku, shi yasa tun a farko nake tunanin wani irin laifi nayi ma Meema da take nema na da tashin hankali, ashe ni ce ban san abin da yake tafiya ba, soyayya ce a tsakanin ku a da wacce har ta so ta kai ku ga yin aure, Allah ne bai nufa ba, why Dr?". A wannan lokacin cikin lallashi yayi min magana da cewa "Zarah don’t put that in your mind akan tsakani ni na da Meema, kamar yadda na fad’a miki a baya cewa Meema yarinyar abokin Dad d’in mu ce, akwai aminci tsakanin su, ni ban d’auki Meema a matsayin lover d’i ta ba, na d’auke ta ne a matsayin sister d’ita kamar yadda na d’auki su Hanan, though akwai shak’uwa a tsakanin mu, Meema ita take so na, bai kamata ki ga laifi na ba dan ban fad’a miki wannan maganar ba, dan ni ban d’auke ta mai mahimmanci a guri na ba shi yasa ban fad'a miki ita ba, I hope kin gamsu da bayanin da nayi miki" ya k’arasa maganar yana jefo min shu’umin kallo da yake sanyayar min da jiki. Wani irin dad’i ne ya ziyarce ni a lokacin jin cewa shi Meema ita take son Dr, ba shi yake son ta ba, amma duk da haka ban gama samun natsuwa a zuciya ta ba in dai har Meema su na tare da Dr, nasan za ta iya yin duk wani dubarar ta taga ta jawo hankalin shi ya yarda ya aure ta, wannan shine babban fargaba ta. Tunano kalamen ta nayi na d’azun da take ce min Dr na ta ne, sai ta aure shi, ban san me Meema take nufi da wa’innan kalamen ta ba, gashi dai Dr ya min bayanin cewa ita take son shi ba shi yake son ta ba, menene ribar ta in ta aure shi bayan ta san ba son ta yake yi ba?. In har maganar da Meema ta fad’a akan sai ta auri Dr hakan yake a ranta ban san wani hali zan shiga ba nan gaba. Ban san lokacin da Dr ya taso ya dawo kusa dani ya zauna ba. Jin shi nayi ya tallabo fuska ta yana jefa min kallon da ke dawo dani cikin natsuwa ta. Cikin cool voice d’in shi ya ce "Zarah stop bordering your self, ba na so ki ci gaba da sa tunanin Meema a ranki, daga yanzu in har ta miki wani abun in na dawo ki fad’a min kin ji, ba na so ki na biye mata kuna samun misunderstanding a tsakanin ku, ina fatan kin fahimta". Murmushi na sakar mishi kana na ce "Na fahimce ka Dr, insha Allahu zan kiyaye". Shima murmushin ya mayar min ya ce " That’s what i want to hear from you". Cikin ‘yan mintuna sai gashi na daina jin haushin Dr, daman nasan har da kishi da yake damu na. A ranar sai da Dr ya koyar dani wani darasi a babin soyayya irin ta ma’aurata da suka damu da junan su. Tun bayar rigimar da muka yi da Meema, ban k’ara shiga harkar ta ba, duk yadda ta so in biye mata ba na kula ta, ita ma na lura a yanzu tana shakkar nema na da rigima, hakan yasa na k’udurta cewa zan danne duk abin da za ta min, dan ba na so in yi abin da zai ‘bata ma Dr rai. ****************************** A kwana a tashi ba wuya ga mai yawan rai. Sai gashi har na kammala HND d’ina nayi service. Har a wannan lokacin ba ni da ciki, a yadda na lura shi Dr hankalin shi bai tashi ba da rashin cikin da ban samu ba. Ni kuwa hankali na ne ya kasa kwanciya ganin ina neman shekara uku da aure amma har yanzu ban samu ciki ba. Gashi har Anisa ta haifi yarinyar ta mace wacce ta ci suna Amatur-Rahman. A ‘yan kwanakin sai na fara jin canje-canje a jiki na, zazza’bi da yawan kasala da ke damu na, ga wani fari da na k’ara yi. Yau muna kwance ni da Dr a gado, gani nayi ya tashi ya kunna bulb ya dawo ya zauna kusa dani yana kallo na. Hure mishi ido nayi na ce "Dr lafiya wannan kallon kuwa". "Ba komai, na ga wasu changes ne a jikin ki, na ga kuma kin k’ara min kyau da fari" Dr ya fad’a yana kanne min ido. K’ayataccen murmushi na sakar mishi kana na ce "Ni kaina Dr na rasa me yake damu na a ‘yan kwanakin nan, fever da kasala ke damu na, sannan ga haske da da na k’ara yi, ina jink o har da rashin lafiyar da nake yi ne yasa na k’ara haske oho". Tun da na fara maganar nan Dr ke bi na ido bai ce min komai ba har sai da na gama magana sannan ya d’aura da cewa "Zarah me yasa ba ki fad’a min ba ki da lafiya ba?". Marairaicewa nayi na kwanta a kafad’ar shi na ce " Yawanci sai ka tafi aiki nake jin zazza’bin da kasala, kan yamma sai ka ga na koma normal, shi yasa ban fad’a maka ba". "Bayan nan ba in da yake miki ciwo?" Dr ya tambaye ni. Shiru nayi kamar mai tunani kana na amsa mishi da cewa "Gaskiya babu, sai dai wani lokacin ina yin amai". Hannu na ya rik’e ya kalla kana ya maida kallon shi gare ni. "Yaushe rabon ki da ganin period d’in ki" Dr ya sake watso min tambaya. Amsa mishi nayi da cewa "Ina ganin almost 2 month kenan". "Ina zuwa" Dr ya fad’a a tak’aice. Tashi yayi ya je ya d’akko kayan gwaje-gwajen shi ya dawo ya zauna ya fara auna ni. Bayan ya gama gwajin shi ya ajiye kayan aiki a gefe. Jin bai ce min komai ba game da gwajin da ya min yasa na ce "Dr na ga ka gwada ni ba ka min bayanin abin da yake damu na ba". "A gwajin da na miki ban ga komai ba, amma zuwa gobe zan tafi da jinin ki da fitsarin ki sai a je dashi lab a ga me yake damun ki". "Allah ya kaimu goben" na fad’a. "Amin" ya amsa min a tak’aice. Washegari kuwa Dr ya tafi da jini na da fitsari asibiti dan a min gwaji. Tun a jiya da Dr da ya min gwaji ya gano ina da ciki, sai dai ba yaso zargin shi ya tabbata dan har yanzu bai shirya ma haihuwa ba, gani yake har yanzu suna da sauran lokaci kafin su haihu. San da yaje asibiti yasa an mishi gwaji a lab, sakamakon ya fito da cewa ina da cikin sati goma. Abin da yasa ya daina d’aura ni akan tsarin family planning saboda yadda nake mishi k’orafin rashin samun ciki na da kuma dad’ewar da nayi ban samu ciki ba sannan yana da tabbacin tsarin da ya d’aura ni akai zai yi wuya in samu ciki da wuri haka, sai gashi Allah yayi ikon shi ya bani ciki a lokacin da bai yi tsammani ba. Shawarar da ya yanke shine ba zai fad’a min ba dan shi bai shirya ma haihuwa ba, yasan in na sani ba k’aramin farin ciki zan nuna da jin labarin ba dan yadda a yanzu nake buk’atar samun ciki. Lokacin da zai tafi gida ne ya tawo da wasu pills da zai bani. Ko da ya dawo na mishi tarba ta musaman kana na kawo mishi abinci ya ci. Ganin bai ce min komai ba akan gwajin da yace in ya je asibiti za a min yasa na ce "Dr an yi gwajin kuwa, me yake damu na". "Oh kin ga na sha’afa in fad’a miki result d’in gwajin, daman nayi zaton Typhoid ke damun ki san da jiya na miki gwaji, yau d’in ma da aka yi gwajin a lab haka ya nuna hakan, ga magani na zo miki dashi, ki je ki d’ebo ruwa ki sha a gaba na dan nasan za ki iya mantawa ba ki sha ba tun da ke ba son shan magani kike yi ba" cewar Dr. Tashi nayi na je na d’ebo ruwa a cup na dawo na zauna a kusa dashi. Bani maganin yayi na sha da ruwa ina zuba mishi shagwa’ba shi kuma yana biye min. Ban fi mintuna 30 ba da shan maganin na ji marata ta fara min ciwo. Yatsina fuska na fara yi saboda yadda maran take neman takura min. Dr ne ya kalle ni ya ce "Ya akayi ne Zarah". "Mara ta ce naji ta fara min ciwo" na amsa mishi. Cikin kulawa ya fara min sannu. Tashi nayi da niyyar tafiya dan in je in kwanta ko zan samu relief akan ciwon da mara ta take min. "Ina zaki ne Zarah" Dr ya tambaye ni. Amsa mishi nayi da cewa "Zan je in kwanta ne, na ji marar tana so ta matsa min". Dr ne ya ce "Ayya, sannu Zaarah, jeki ki kwanta, za ki ji sauk’i in kika samu bacci". D’akina na wuce naje na kwanta. Abu kama wasa, tun ina jin ciwon marar a hankali har ciwon ya fara fin k’arfin tunani na. Tunanin abin da yasa min ciwon marar na fara yi, gashi ba period d’ina ba ne zai zo ba re in ce shi ne ya haddasa min ciwon marar tunanin. Tun ina iya daurewa har ta kai ga ba zan iya jure wa ba. Yanda nake jin ciwon ne yasa hawaye ya fara zubo min a idanu na. Rik’e mara ta nayi ina juye-juye a gado, a lokaci d’aya ina sai jero addu’o’i nake yi a raina ko zan samu sauk’in ciwon da nake ji. Gani nayi jini ya fara gangarowa ta k’afa na, har wani guda-guda ne ke biyo bayan jinin. Hankali na ne ya tashi ganin jini na gangaro wa. A iya tunani na wannan ba jinin mensturation ba ne saboda yadda yake zuba. Dr ne ya shigo d’akin ya same ni a halin da nake ciki. Da sauri ya k’araso ya d’ago ni. Jiki na ne ya saki saboda wahalar da na sha. Cikin rud’u Dr ya ce "Zarah me ya same ki haka ba ki kira ni ba". "Ciki na da Mara ta ciwo suke min Dr" na fad’a cikin galabaita. "Sannu Zarah, insha Allah za ki samu sauk’i kin ji" Dr ya fad’a cikin tausayawa. D’auka ta yayi ya shigar dani Ban d’aki. Sai da ya gyara ni kana ya kai ni side d’in shi ya bani taimakon da ya dace a matsayin shi na likita. Magunguna ya bani nasha kana ya min da allurar bacci. Cikin d’an lokaci k’ank’ani bacci yayi awon gaba dani. Sai da na kwashe sama da awa biyu sannan na farka daga baccin da nake yi. Dr na gani zaune a kusa dani, alamu na nuna yana jiran farka wa ta ne. Dr cikin tausayawa ya kalle ni ya ce "Sannu Zarah kin tashi, ina ne yake miki ciwo yanzu". Cikin sanyin murya na ce "Mara ta ce har yanzu take min ciwo". "Zai daina ne a hankali, bari in had’o miki tea ki sha" ya fad’a yana mik’ewa. Bayan fitar Dr ne na fara tunanin jinin da ya zuba a jiki na, sai dai abin da yake bani mamaki shine tun da na sha maganin da Dr ya bani na fara ciwon marar na da ciwon ciki, tambayar da na yi ma kaina shine me ya had’a maganin typhoid da zubar jini wanda ya haddasa min tsananin ciwon mara da ciwon ciki. Kau da wannan tunanin nayi a raina na barshi akan cewa may be maganin da Dr ya bani ya min k’arfi ne, shi ya haddasa min ciwon. Dr ne ya dawo ya zauna rik’e da cup d’in da had’o shayi a ciki wanda ya sha madara a ciki. A baki ya dinga bani, sai da yaga na sha ai yawa sannan ya k’yale ni. Haka Dr ya wuni ya na bani kulawa ta musamman. Waya yayi da Farida akan ta yi mi farfesun kayan ciki da girki ta kawo bani da lafiya. Wajen magrib sai ga Farida ta kawo farfesun da tayi da fried rice da ji hanta a ciki. Haka Dr ya matsa min na ci abinci duk da ban jin dad’in baki na. A kwana biyu na samu sauk’i, sai k’arfin jiki na ne bai dawo dai-dai ba Har a lokacin ban san ‘bari nayi ba. """""""""""""""""""""""""""""" Yau yaya Khalil ne yake zaune a falo d’auke da Amatur-Rahman a hannun shi. Anisa ce tazo ta zauna kusa dashi tana sakar mishi tattausan murmushi. Shima murmushin ya maida mata. "yaya Khalil sannu da hutawa, na barka kai kad’ai". "Kar ki damu k’anwa ta, nasan uzuri ne yasa kika barni ke kad’ai dan kin je ki mana delicious food d’in nan naki da yake sa ni santi". Fuskar tace ta yalwatu da annuri jin yadda yaya Khalil ke yaba mata. Mik’a mata Amatur-Rahman yayi wacce ta fara kuka. Amsar ta tayi ta fara jijjiga ta. Kallon ta yayi cikin tsokana ya ce "babyn nan wai rigimar wa tayi ne, ni dai nasan ban da rigima". Dariya tayi ta ce " Nima dai ban da rigima, ina jin rigimar Antyn ta tayi". Shima dariyar yayi ya ce "Wace Antyn ta d’in". Anisa ce ta ce "Kai wa kake tunanin nake nufi in ba Fatima ba". Yaya Khalil ne ya ce "Sai yanzu nima nasan in da tayo rigimar, amma a ‘bangaren kuka ke tayo dan ki fi Fatima saurin kuka, tsiwa ce dai Fatima ta fi ki". Murmushi Anisa tayi kana ta ce "Ina missing d’in Fatima, yaushe za ka kai ni gurin ta in wunin mata". "Ki bari ran weekend sai in kai ki" yaya Khalil ya fad’a. "Allah ya kaimu, amma yaya Khalil rashin haihuwar Fatima yana damu na, nasan haihuwa lokaci ne, sai in ga itama tana son haihuwa yanda take ma Amatur-Rahman in muka had’u, in na mata maganar sai ta nuna min ba ta damu ba, a yadda na fahimta ba taso a san ta damu ne, rashin haihuwar na damun ta" Anisa ta fad’a cikin nuna damuwar ta. Yaya Khalil ne ya ce "Allah ne bai kawo mata haihuwar ba, in lokaci yayi sai ki ga ta haihu, ki ci gaba da taya ta da addu’a, Allah ya kawo mata masu albarka". "Amin yaya Khalil, Allah ya amsa addu’ar mu" cewar Anisa. "Amin Anisa" yaya Khalil ya amsa mata. Da haka suka ci gaba da hirar su cikin so da kulawa. Bayan four month na sake jin canji a jiki na, wannan karan ban da zazza’bin da nake fama dashi da amai da nake yi, ga yawan bacci sannan ga kwad’ayi da yawan cin abinci da nake yi. Ni da kaina na fara zargin ko ciki ne dani saboda na ga wasu alamomi na masu ciki a guri na. Bayan Dr ya dawo ne na kai mishi ruwa yayi wanka kana ya fito ya shirya ya zo ya zauna akan dinning table naje nayi serving d’in shi dan ni na riga na ci nawa. Lokacin da ya gama cin abincin ne muka dawo falo ya zauna a kujera yana kallon tauraron d’an adam. Jikin shi nazo na kanta ya fara wasa da gashin kaina da na mishi gyara na musamman tare da turarurruka masu k’amshi na kai. Ban wani jima a jikin shi ba bacci ya fara d’auka na. Cikin kulawa Dr ya ce "Kwana biyu na ga alamar ba kya jin dad’i, ban san me yasa ki ke ‘boye min rashin lafiyar ki, ko kin manta mijin ki Dr ne". "Ni kaina Dr ba zan ce ga in da yake min ciwo ba, ina dai jin jiki na so weak da fever, ni abin da yafi matsa min Dr shine yawan baccin da nake yi da kuma cin abinci da nake ci akai-akai ga kwad’ayi" na fad’a cikin shagwa’ba. Tak’aitaccenn murmushi yayi kana ya ce "Kar ki damu, na zo miki da magani, bari in je in d’akko sai in baki ki sha". Side d’in shi ya je ya d’akko maganin ya dawo d’auke da ruwa a hannun shi. Maganin ya bani na sha, sai da ya bari maganin ya bi jiki na kana ya kwantar dani a jikin sa. Bacci ne ya d’auke ni saboda daman baccin nake ji. Cikin bacci naji ciwon mara ya ziyarce ni a lokaci guda. Ba shiri na farka daga nannauyan baccin da ya d’auke ni a jikin Dr. Tashi nayi na zauna ina rik’e mara ta tare da fad’in "Wash Allah! Mara ta". Kallo na Dr yayi kana ya ce "Ya kike jin ciwon maran". Kuka na fara yi saboda yadda nake ji na ce "Dr ba zan iya fasalta maka yadda nake jin ciwon marar ba, sai dai ina jin ciwon kamar na lokacin baya da nayi san da ka bani magani na sha, Dr ka taimake ni". Rik’o ni yayi ya fara lallashi na ganin yadda na rik’e mara ta da nake ji kamar za ta fashe saboda ciwo. D’auka ta Dr yayi da niyar kaini d’aki, jini ne ya fara gangarowa kamar wancan karan. Da sauri Dr ya k’arasa dani band’aki ya gyara ni, ko da muka fito daga band’aki jinin bai daina zuba ba. Duk wani taimako da Dr zai bani yayi iyakar k’okarin shi amma jinin bai tsaya ba, hakan yasa ya d’akko min hijab d’ina ya sa min. D’auka ta yayi ya sani a motar shi muka nufi kangiwa hospital inda yake aiki. Taimako na gaggawa aka bani tare da taimakon Dr, a k’arshe dai sai da aka min wankin ciki. Nan na tabbatar da cewa ‘bari nayi. Wajejen yamma Dr ya d’akko ni muka dawo gida. Ni kad’ai nasan yadda naji san da na tabbatar da cewa ‘bari nayi, na sa rai da wannan cikin da na samu dan a yanzu baabin da nake fata da ya wuce in haihu, sai gashi Allah yayi ikon shi a kaina. Tun da muka dawo gida nake faman kuka, duk lallashin da Dr ya min bai san a daina kukan ba, a yadda na fahimta shi Dr bai nuna damuwar shi akan ‘barin da nayi ba. Kallo na yayi ya ce "Wai Zarah kukan me kike yi ne haka, duk lallashin da na miki bai ishe ki ba, ko akwai inda yake miki ciwo ne" ya k’arasa maganar da tambaya ta. D’ago kaina nayi na kalle shi na ce "Dr yanzu laifi na kake gani dan nayi kuka, cikin da na dad’e ina burin in samu Allah ya bani a lokacin da ban yi tsammani ba, sai gashi Allah ya amshi kyautar da ya min amma ka ce ba zan yi kuka ba" na k’arasa maganar da k’ara sautin kuka na. Jawo ni jikin shi yayi ya ce "for God sake miye amfanin kukan nan da kike yi, ni ban ga abin d’aga hankali ba dan kin yi ‘bari ba, at any time Allah zai iya baki wani, ba na so ki dinga d’aga hankalin ki akan k’aramun abu". Janye jiki na nayi daga jikin shi na kalle shi cikin ‘bacin rai na ce "Dr miscarriage d’in ne k’aramin abu? In a gurin ka k’aramun abu ne, ni a babba na d’auke shi, daman na ga ba ka nuna damuwar ka akan ‘barin da nayi ba". "ya kamata ki fahimce ni Zarah, you have to take patient tun da haka ya faru, har wani dad’ewa muka yi da aure da za ki sa kan ki a damuwa dan kin yi miscarriage, mu d’auki k’addara tun da Allah yayi babyn mu ba zai rayu a womb d’in ki ba" Dr ya fad’a. Kasa ce mishi komai nayi saboda takiacin da maganar shi ta sa ni, nasan ci gaba da zama na a gurin ‘bacin rai da haushin abin da Dr yake fad’a min zai k’ara min matuk’ar Dr ba zai taya ni jimamin abin da ya same mu ba na miscarriage d’in da na samu ba. Tashi nayi na bar mishi gurin na wuce d’aki na. Ranar ma a d’akina nayi kwanciya ta dan har yanzu ban daina jin haushin rashin caring d’in da bai nuna min ba akan miscarriage d’in da nayi, ban san me yasa Dr bai son in haihu da wuri ba, ya d’auki halin turawa ya sa ma kanshi, dole ba zai nuna damuwar shi akan rashin haihuwa na ba. Ganin ban zo d’akin shi ba yasa ya biyo ni muka kwanta a d’aki na. Haka ya dinga fad’a min sweet words masu kwantar da hankali akan in cire damuwar da nayi akan miscarriage d’in da nayi. Duk wannan maganganun da ya fad’a min jin shi kawai nake yi, da na gaji da sauraren maganar da yake fad’a min na lumshe ido na kamar mai bacci, hakan yasa yayi shiru shi ma. Da haka bacci ya d’auke ni. Washe gari Dr ne ya ya turo Farida akan ta taya ni aiki kasancewar jiki na ba k’arfi. Momin Dr ce ta kira ni ta min ya jiki kasancewar Dr ya fad’a mata abin da ya same ni, ta ce in ta dawo daga aiki za ta zo ta gaishe ni, da haka muka yi sallama da ita. Na kira Ummu na fad’a mata nayi ‘bari, ta nuna jajantawar ta gare ni saboda ita ma a yadda na lura ta damu da rashin haihuwa ta, ba tason yi min magana ne dan kar ta d’aga min hankali. Da daddare Momi tazo da Hanan sun duba ni tare da jajanta min, ta kira Dadin Dr ta ba ni muka gaisa dashi shima ya min ya jiki kasancewar ba ya gari. Anisa ma da Anty Jiddah sun kira ni a waya sun min ya jiki. Cikin kwana biyu na samu sauk’in jiki na, hakan yasa na tashi na fara aikace-aikace na, na gyara d’aki na. Bayan na gama ne na tafi side d’in Dr na je fara mishi gyara. Ina cikin gyaran ne na tafi ‘bangaren wardrope d’in shi na fara jera mishi gogaggun kayan shi, a nan na ga wasu pills a cikin kwalin maganin ya ajiye su a cikin wardrope d’in. D’aukar maganin nayi na karanta amma ban gane ko na menenen, sai dai maganin yayi kala d’aya da wanda Dr ya bani. Maida wa nayi cikin wardrope d’in na ci gaba da aiki na. Zuciya ta ce take ta sa min tunani akan maganin nan, zuciya ta sai bani shawara take yi akan in yi bincike akan maganin saboda yadda sau biyu ya saukar min da ciwo da ciwon mara had’e da zubar jini wanda har ya kai ni ga zuwa asibiti. Iya tunani na, maganin da Dr ya bani ya min k’arfi a jiki na ne shi yasa na ke samu wannan matsalar. Ina gama aikin nayi hanyar fita, maganin ne ya k’ara fad’o min a rai na, hakan yasa na koma na bud’e wardrope na d’akko maganin. Zama nayi a bakin gado na bud’e data na sa sunan maganin a google. Bayani ne akan maganin da yawa suka nuno min a site d’in, hakan yasa na bud’e d’aya daga ciki. Bayanin da na gani akan maganin shi yayi barazanar d’auke numfashi na, sai da na d’auki tsawon mintuna biyar ban san a wani hali nake ciki ba. Da k’yar na jawo jarumta na ara ma kaina na dawo cikin natsuwa ta. Dan kar in gasgata zuciya ta yasa na k’ara shiga wani site d’in amma duk bayani d’aya yake zuwa min dashi. Abin da bayanin ke sanar dani cewa wannan maganin zubar da ciki ne da na gani a wardrope d'in Dr wanda yake bani a matayin maganin typhoid. Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo min daga idanu na. Abu d’aya ne yazo min a raina shine maganin da Dr ya bani ba typhoid ba ne kamar yadda ya ce min, maganin abortion Dr ya d’auka ya bani da hannun shi na amsa na sha da kaina saboda yardar da nayi mishi da soyayyar da ke tsakanin mu. "Me yasa Dr zai yaudare ni ta wannan hanyar, me yasa Dr zai raba ni da gudan jini na da nake son gani, me yasa Dr zai min sakayya ta irin wannan hanyar bayan yasan yadda nake so in samu ciki?" Na tambayi kaina. Zuciya ta ce ta bani amsa da cewa yayi hakan ne dan bai shirya ma haihuwa ba kamar yadda yake fad’a. Tunano lokutan da ya bani magani har sau biyu nayi, yanayin da na tsinci kaina a farkon maganin da Dr ya bani na zubar jini da ciwon mara kenan hakan na nufin miscarriage nayi kenan, hakan bai ishe shi ba sai da ya k’ara bani maganii a karo na biyu ya k’ara ‘barar min da ciki. "Ashe daman so na iya zuwa da cutarwa?" Tambayar da nayi ma kaina kenan. Tambayar da ya kamata a ce da kaina na gano amsar ta amma ban da halin yin haka saboda halin da nake ciki. Kenan shi yasa bai nuna damuwar shi akan halin da na shiga ba lokacin da nayi ‘bari. Wani irin ‘bacin rai ne na ji ya ziyarce ni a lokacin. "Inna lillahi wa inna ilaihir raji’iun" na dinga ambata a raina daboda in samu sauk’in halin da na ke ciki. Ba abin da a yanzu nake buk’ata da ya wuce dawowar Dr. A yadda nake jin zuciya ta zan iya fito na fito dashi dan ba zan bari ya nakasa min rayuwa ta ina kallon shi ba saboda tunanin shi ina son shi. [8/29, 21:10] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 ww.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa writers Association *Na Baku wannan shafin kyauta* _Hauwa_ _Safiya_ _Fateema_ _Maman Umar_ _Fadeela_ _Fatima M lawal_ _Ina godiya da yadda ku ke nuna ma wannan novel d’in one love_. _Y’ar mutan Paki na mik’a gaisuwar ta gare ku_. 85-86 Ban san lokacin da na d’auka a zaune ba a halin da nake ciki. Shigowar Dr d’akin ne yasa na d’aga kaina na watsa mishi wani kallo mai tattare da ‘bacin rai. Sallama ya yi ya k’araso cikin d’akin yana kallon irin kallon da nake watsa mishi. In ban da sanin darajar amsa sallama da nayi da ba zan amsa mishi sallamar ba. Ciki-ciki na amsa mishi sallamar da ya min. K’arasowa yayi ya zauna kusa dani ya sakar min mayaudarin murmushin shi ya ce "my Zarah jiki yayi normal kenan, tun da na shigo gidan na ga ya canza min, nasan aikin my Zarah ne, na je side d’in ki ban gan ki ba, ashe kina nan". Shiru na mishi kamar ba dani yake magana ba. Kallo na yayi ya ce "Zarah wai lafiya na ga mood d’in ki ya canza, ko har yanzu jikin ne". A karo na biyu na k’ara mishi shiru saboda ni kad’ai nasan ‘bacin ran da nake ciki. Matsowa yayi da niyyar hugging d’ina ya fara magana cikin wasa ya ce " Yau sarauta kike ji kenan, bari in ji wa ya ta’ba min Zarah ta". Ganin zai yi hugging d’ina yasa na mik’e cikin ‘bacin rai na ce "Dr kar ka ta’ba ni". Kallon mamaki ya min kana ya ce "Wai Zarah me yake faruwa ne?". "Abin da yake faruwa kake so ka sani Dr, yanzu ko zan fad’a amma abin da yake faruwar" na fad’a cikin fushi. D’akko maganin nayi na nuna mishi na ce "Menene wannan Dr, ina so ka yi min bayanin wannan maganin, menene shi kake bani a matsayin maganin typhoid". Mamakin ganin maganin yayi da har ya kasa magana, sai bi na da ido da yake yi. Ganin ba zai yi min bayanin maganin ba yasa na ce "Dr nasan daman ba za ka min bayanin maganin menene ba dan kasan ba ka da gaskiya, wannan maganin da ka ke hidden d’in shi a wardrope d’in ka na ganshi wanda kake bani a matsayin na typhoid, na gano maganin da kake ba ni maganin zubar da ciki ne, in kuma na fad’i akasin haka ka fad’a min". K’arfin hali Dr yayi ya ce "Ke Zarah wa ya fad’a miki wannan maganin abortion ne da kike d’aga ma kan ki hankali akai, dan ki yi miscarriage sai ki d’auki laifin ki d’aura a kaina". Cikin fad’a na fara da cewa "Ba wanda ya fad’a min cewa maganin abortion ka bani, jiki na ne ya bani hakan da kuma binciken da nayi na gano hakan, Dr in a tunanin ka ni ba likita ba ce, amma kasan akwai hanyoyi da zan iya bincike akan maganin kamar yadda na bincika a waya ta". D’akko waya ta nayi na bud’e site d’in da nayi browsing na mik’a ma Dr wayar na ce " In kana tunanin ni zan maka k’arya akan abin da na fad’a akan maganin da ka bani, na tabbata za ka yarda da bayanin internet dan na ga daman da turawa kake koyi shi ya sa har ka bani maganin da zai zubar min da cikin da na ke rok’on Allah ya bani…". Cikin tsawa Dr ya katse ni da cewa "Ya ishe ki Zarah! Enough! Na ga ina bin ki in a polite way ba ki sani ba, abin da kike zargi haka ne, maganin da na baki na abortion ne, nasan kina sane da cewa cikin da na zubar nawa ne ba na wani ba ko? ba ki da wani mataki da zaki d’auka akan hakan, haihuwa ce na ce ba yanzu nake so ki haihu ba, rayuwa ta ina mata planning ne da kike gani na, in lokacin da nake so ki haihu yayi zan bari ki haihu, dole ne ki bi instruction d’in magana ta tun da ni ne mijin ki". Ban san d’abi’ar Dr yayi nisa haka ba akan koyi da yahudu da har zai ce yana ma rayuwar shi planning bayan Allah shi yake tsara wa bawa rayuwar shi. " Dr ba zan ta’ba bin ka ba in dai akan wannan maganar nan ce, Dr babu da’a a gurin yi ma wani biyayya a gurin sa’ba wa mahalicci, dan haka ba zan maka biyayya ba wajen zubar da cikin da kake min, idan har ba ka son kyautar da Allah yayi maka ni ina so, a shirye nake na amshe shi hannu bibbiyu, wasu ma da kud’i suke neman Allah ya basu kyautar bai ba su ba sai mu da Allah ya ba mu ce ba za mu amsa hannu bibbiyu ba, da kake maganar kana ma kan ka planning, ina jin ka manta Allah shi yake tsara wa bawan shi rayuwar shi, A ce Allah yayi wa mutum kyauta ya ce ba yaso saboda ba a lokacin ya shirya ma amsar kyautar da Allah ya bashi ba bayan nan gaba bai san ko Allah zai k’ara bashi irin kyautar da ya mishi a farko, ko da yake kai na ga kayi nisa gurin koyi da yahudu, shi yasa ba za ka ga aibun abin da ka aikata ba". Saukar mari na ji a fuskata da yasa na razana saboda zafin marin da ya shige ni. Hawaye ne masu zafi suka fara zubo min a idanu na, halin da nake ciki a yanzu ba zai bar ni in goge hawayen ba dan a yanzu nafi buk’atar su ko na samu sassauci a halin da nake ciki. X Murmushin takaici nayi na ce "Dr dan ka mare ni ba komai ba ne tun da har ka iya d’aukar magani ka bani a matsayin maganin typhoid ka bani na sha alhalin maganin abortion kake bani nake sha, ashe shi yasa nake zubar da jini da ciwon mara a lokacin da ka bani maganin na sha, sau biyu kana d’aukar maganin kana bani ina sha, ko tausaya min halin da nake shiga idan na sha maganin ba kayi, tun da kake ba ni maganin ban kawo zaka iya d’aukar abin da zai cutar dani ba ka d’auka ka bani saboda yardar da na baka da soyayyar da nake maka, Dr ka riga kayi breaking d’in trust d’in da na maka, ina ganin a yanzu ba wanda ya rage na yardar dashi tun da wanda na yarda dashi ya ha’ince ni, Dr bazan ci gaba da zuba maka ido kana tafiyar min da rayuwa ta yanda kake so saboda tak’amar ka ina son ka". Kuka na fara yi wanda ke ta’ba zuciyar duk wani mai saurare, na durk’ushe a k’asa ina ci gaba da kukan. Cikin kukan na ce "Dr ban ta’ba tunanin haka daga gare ka ba, nasan auren soyayya muka yi da kai amma in ka min wani abin sai in yi tunanin ko ba ka so na ne, tun farkon auren mu ka kawo min maganar family planning kuma na yarda da tsarin ka saboda hujjojin da ka bani na cewa zan yi karatu ne kar in wahala shi yasa kake tausaya min, a raina ba na son yi family planning d’in, na biye maka ne saboda ba na son ‘bacin ranka, but why Dr kai ba zaka guji ‘bacin ran nawa ba?". Cikin shashshek’ar kuka na ci gaba da cewa "Dr ka fad’a min me yasa ba ka shirya mana haihuwa a yanzu ba bayan kasan kullum lokaci wucewa yake yi, Dr ka fad’a min ko ni ce ba ka so ka haihu dani". "If you succeed in cheating someone, don’t think that person is a fool, Realize that the person trusted you more than you deserve". Kallon Dr nayi da ido na da ya canza launi na ci gaba da cewa "but do you know what Dr? There will always be a soft spot in my heart for you, even when you’ve done wrong, even when you’ve let me down, even when you couldn’t care less, No any relationship can be survive without trust, but why did you break that trust Dr". Jikin Dr ne yayi sanyi da irin kukan da nake yi da maganganun da na fad’a mishi. Takowa yayi yazo gurin da nake durk’ushe ya tsugunna yana kallo na. "Am sorry my Zarah" Dr ya fad’a a hankali. "Dr ba na buk’atar wani ban hak’uri da ga gurin ka". Ina gama fad’ar haka na tashi na bar gurin. D’akina na tafi na ci gaba da kuka na, na rasa me yake min dad’i a raina. Ba na so muna samun sa’bani da Dr amma ban san dalilin shi da yake jawo abin da za mu samu sa’bani ba. Ashe gaskiyar mutane ne da suke cewa duk yadda aka kai ga yin soyayya a waje, idan aka yi aure sai dai a ci gaba da zaman hak’uri saboda hak’urin ne ke jan ragamar soyayya a zamantakewar auren wanda a yanzu nake ganin misali a kaina, a nan ne za ka k’ara sanin halin wanda ka aura wanda ba ka sani ba kafin ku yi aure. Abin da ban ta’ba zata daga gurin Dr ba shi yake min, abin da yafi damu na shine ba wanda zan iya fad’a wa matsala ta ya bani shawara saboda gudun kar a yi mana dariya in aka yi la’akari da soyayyar da muka yi da Dr kafin aure, Halima ce nake tunanin zan iya fad’a wa matsala ta saboda ita ce take bani shawarar da nake jin dad’i, yanzu in na fad’a mata za ta iya ma Dr wata fassara ko ta ga laifin shi akan abin da ya min, ni kuma ba zan so Halima ta ga laifin shi ba. Shawarar da na yanke shine in d’auki mataki na da kaina wanda Dr ba zai sake kamanta yi min haka ba, ko a yanzu na lura jikin shi yayi sanyi da abin da ya aikata min, nasan ba zan juri fushi da Dr ba saboda nima zan iya shiga wani hali na damuwa da tunani, sai dai dole ne in tursasa ma zuciya ta hukunta Dr idan ya min abin da bai kamata ba ta hanyar da ta dace. Haka na wuni a d’aki ni kad’ai, ba irin tunanin da bai zo min ba akan abin da Dr ya min. Ranar ko abinci ban d’aura ba saboda ba na jin zan iya yin girki a halin da nake ciki. Da daddare bayan nayi sallah ta ne na tashi na had’a shayi na sha da snacks kana na kwanta. Lumshe ido na nayi kamar mai bacci, duk wanda ya ganni a lokacin zai iya zaton bacci nake yi amma a zahiri ba bacci nake yi ba. Mafita kawai nake nenmar wa kaina ni da Dr dan duk son da nake mai ba zan bari ya nakasa min rayuwa ta hanyar bani pills d’in zubar da ciki wanda nan gaba za su iya shafar mahaifa ta, nasan nan gaba in hakan ta faru wata zai iya nemo wa ya aura a lokacin da yake da buk’atar haihuwa, ni kuma ya barni da danasani, shi yasa nake son d’aukar mataki tun yanzu. Shigowar Dr d’akin ne yasa nayi saurin bud’e ido na saboda ganin shi da nayi a d’aki na. Mamakin Dr ne ya mamaye sassan jiki na da har yayi jarumtar shigowa in da nake a yanzu. Lallai yau na tabbatar da namiji bai da kunya, in ban da haka ya za ayi ya ce har ya manta abin da ya had’a ni dashi d’azun. Ya d’auki magani ya bani na zubar da ciki, sannan in mishi magana maimakon ya lallashe ni sai ma mari na yayi da maganganu masu zafi da ya bi ni dashi, sannan yanzu da daddare ya zo inda nake da sunan zai kwanta dani, ai kuwa zan nuna ma Dr nasan darajar kaina. Saurin sakkowa nayi daga kan gado na tsaya ina kallon Dr na ce "Dr me ka zo yi a d’aki na?". Kai tsaye ya ce min " Kwanciya na zo yi tun da na ga yau kin guji side d’ina". Dr mamaki yake bani yadda yake da full confidence ko da yayi wa mutum laifi ne ba ya jin tunkarar wanda ya yi wa laifin, in ba haka ba ya Dr zai kalli ido na ya ce min ya zo ya kwanta ne kanshi tsaye. "Amma ba a d’akin nan za ka kwanta ba ko?" na k’arasa maganar da tambayar shi. "Ba ni da right ne in kwanta a duk in da nake so, ko ke ce kika sa dokar?" Dr ya fad’a. Ni ce na ce "Kana da damar kwanta wa a duk in da kake so saboda gidan ka ne, sai dai in har za ka kwanta a d’aki nan ni zan bar maka d’akin ka kwana kai d’aya dan ba zan kwanta da kai ba". Mamaki na ne ya kama Dr da har ya kasa magana sai bi na da ido da yake yi. Ganin Dr bai da alamar yi min magana yasa na ce " Dr kai nake jira". Ban san tunanin da yayi ba, fita kawai na ga yayi daga d’akin. Kulle k’ofa ta nayi na dawo na kwanta, sai da na jima ina tunani da neman mafita kafin bacci ya d’auke ni. Washe gari ma haka na tashi na had’a ma Dr breakfast d’in shi akan dinning kana na koma d’aki na kwanta. Sai da na ji fitar shi daga gidan kana na fito nayi aikace-aikace na kana na je na gyara ma Dr side d’in shi. Ko da Dr ya dawo daga aiki haka na tarbe shi ba yabo ba fallasa, duk yadda Dr yaso ya ga fara’a ta ban bashi wannan damar ba, duk wata hira da zai min sai dai in bi shi da "Eh ko a’ah", hakan ya tabbatar mishi da fushin da nayi dashi babba ne. Sai da muka yi kwana uku a wannan halin ni da Dr, ina mishi duk abin da ya dace a matsayina na matar shi, sai dai ba na bashi fuskar da za mu zauna mu yi hira dashi dan kar ya ga saurin sauka ta akan laifin da ya min sannan ban k’ara yarda mun kwana a d’aki d’aya ba dan ban ga amfanin kwanciyar mu a tare ba tun da bai shirya ma haihuwa a yanzu ba. Yau da daddare ina kwance cikin shigar kayan bacci kalar pink wanda ya amshi kalar jiki na. Dr ne ya shigo d’akin had’e da sallama. Amsa mishi sallamar nayi kana na d’auke ido na daga kallon shi. Gefen gado ya zo ya zauna yana kallo na kana ya ce " Zarah ina son mu yi magana ne" "Ina jin ka Dr" na bashi amsa a tak’aice. Dr ne ya ce "Zarah, ba na son in mun samu sa’bani mu dinga irin wannan zaman, ba na jin dad’in shi, ina ganin in komai ya wuce bai kamata a dawo dashi baya ba". Kallon shi nayi kana na ce "Wani abin na maka Dr? ina sauke duk wani hakk’i da ya rataya a kaina a matsayina na matar ka, ko akai wani abu da nake maka wanda ba ka jin dad’in shi?" Na k’arasa maganar da tambayar shi. "Zarah nasan na miki laifi kuma na baki hak’uri, ya kamata a ce kin yi hak’uri ki yafe min laifin da na miki, insha Allahu hakan ba za ta sake faruwa a tsakanin mu ba". Cikin lallashi ya ci gaba da cewa "Fatimah Zarah!" Yanda ya kira suna na ne yasa na ji sunan ya ratsa dukkan sassan jiki na saboda yadda sunan ya min dad’i a cikin raina da kuma yadda ya kira ni da cikakken suna na. Ji nake yi kamar in amsa kiran sunan na da yayi, sai dai yadda nake jin haushin abin da ya min ba zai bar ni damar amsa kiran suna na da yayi ba. Bai damu da rashin amsawa ta ba ya ci gaba da cewa "Zarah ki yi hak’uri, ni ma nayi realising d’in mistake d’ina, maganin da na baki ba yana nufin zan cutar dake ba ne, a wannan ‘bangaren ne muka samu sa’banin ra’ayi dake, ni ban ce ba zaki haihu ba, na so ne a ce nan gaba idan na samar miki aiki ki ka fara sai ki haihu, amma yanzu da zarar kin fara haihuwa hidima ce za ta k’arun miki na gida, ga hidimar office da na baby, amma tun da kin nuna you are ready to deliver a baby shi kenan, next time in kin samu ciki ba zan baki pills ba". Ci gaba yayi da cewa "I know how angry you are…& what you must be going through, so I hope, you know how sorry I am, for all that happens between us, please forgive me". "Sometimes a genuine apology, a simple hear felt " I' m ‘’Sorry’’ can change everything and start to mend the deepest wounds’’ am sorry for what I have done to you Zarah". Duk da naji dad’in yadda Dr ya bani hak’uri had’e da kalamai masu dad’i da kwantar da zuciya, hakan ba zai sa in yi saurin yarda dashi ba dan ban san ko zai iya ‘bullo min ta wata hanyar ba. A d'ayan b'angare na zuciya ta ina jin ba zan ci gaba da fushi da Dr ba saboda ni kaina a takure nake da irin zaman da muke yi dashi, ni kaina ba jin dad’in irin zama da muke yi nake yi ba, nayi hakan ne saboda Dr ya gane laifin da ya min mai girma ne a gurin shi yadda ba zai sake ba. A yanzu na ga alamar nadama a fuskar Dr wanda daman haka nake buk’ata, sai dai ina ganin akai wata hanyar da zan k’ara hukunta Dr cikin sauk’i da zai gane kuskuren shi. "Kin hak’ura Zarah?" Dr ya katse min tunanin da nake yi. "Ba komai Dr, komai ya wuce a guri na" na fad’a ina sakar mishi tsadadden kallo na. Murmushi ya sakar min kana ya ce "Na gode my Zarah". Nima murmushin na mayar mishi kana na ce "Don’t mind Dr". Hawa kan gadon yayi hugging d’ina. A haka Dr ya fara fad’a min tsadaddun kalmomin shi da suke sa ni natsuwa a duk lokacin da na saurare su. Canza hirar yayi da fara sakar min soft kiss ko ta ina a jiki na, yadda Dr yake min kai kasan yayi missing d’ina, ni kaina nasan nayi missing d’in Dr amma ba zan bashi wannan damar ba saboda ta wannan hanyar ce nake ganin ta rage min da zan k’ara amfani da ita wajen hukunta Dr akan abin da ya min duk da na hak’ura. Janye jiki na nayi daga jikin Dr na matsa gefe. Dr ne ya d’ago ya kalle ni a wahalce kana ya fara magana cikin sanyin murya ya ce "Zarah menene haka kike yi". Duk da na fahimci abin da yake nufi sai na nuna mishi ban fahimta ba na ce "Me nayi Dr". Dr ne ya ce " Ya za ki bari sai da muka yi nisa da faranta junan mu sannan sai ki janye jikin ki daga gare ni, miye amfanin abin da kika min kenan". Ni ce na ce "Dr ni ban ga abin da na maka ba, tuno wa nayi da planning d’in da ka tsara ma rayuwar mu, shi yasa ba zan bari ka kasance dani ba". A halin Dr yake ciki ba zai iya ci gaba da maganar da yake yi ba. Matsowa yayi ya had’a ni da jikin shi. Mutsu-mutsu na fara yi dan ganin na k'wace kaina daga rik’on da Dr ya min, amma da yake rik’on namiji daban ne na kasa, hakan yasa na sa mishi kuka na fara cewa " Dr ni ka sake ni, ba zan bari kayi amfani da ni ba sannan in na samu ciki ka ‘barar min, tun da ka ce ba ka shirya ma haihuwa ba ina ganin kasancewar mu a wajen tarayya da junan mu bai da wani amfani, ni zan jira duk lokacin da kake da buk’atar haihuwa sannan sai in baka jiki na amma ban da yanzu". A hankali ya sake ni ya sakko daga gadon. Idon shi ne ya canza launi, daga gani yana cikin halin buk’ata ta, ni kaina da na kalli yanayin shi nasan yana cikin wani hali, tausayin shi ne ya kama ni, sai dai ba na jin zan iya bashi wannan damar, nasan wannan hukuncin da na yi ma Dr shi zai kaini ga k’watar ma kaina ‘yanci na a gurin shi. "Zarah ba na baki hak’uri ba kika ce min kin hak’ura? Sai yanzu da kika ga ina da buk’atar ki shine za ki nuna min ba ki hak’ura ba, ba komai jikin ki ne, ba zan matsa miki ba" yana gama fad’ar haka ya bar d’akin. Yana fita na fara kuka saboda nima ba a son raina na mishi haka ba, ni kaina ba na son in ga na ‘bata mishi rai, sai dai a yanzu ya zama dole in bi wannan hanyar da in ta za ta kai ni ga samun cin nasara. Sai da na jima a wannan halin kafin na samu barci ya d’auke ni. Washe gari da Dr da ‘bacin rai ya tashi, ko da na gaishe shi da k’yar ya amsa min, breakfast d’in da na had’a mishi ko kallon shi bai yi ba ya wuce aiki. Haka da ya dawo side d’in shi ya wuce, sai da lokacin sallah yayi sannan ya fito ya tafi masallaci. Ko da na kwanta bacci kasa sukuni na yi saboda yau through out ban ga sakin fuska daga gurin Dr ba. Yakamata tun da ya gane laifin da ya min in hak’ura, gashi a maimakon mu samu sasanci a tsakanin mu na k’ara damula lamarin tun da jiya ban bashi kaina ba wanda a dalilin haka yake fushi dani. Tuno hukuncin da duk namijin da ya nemi matar shi ta hana shi nayi, hakan yasa hankali na ya k’ara tashi, nasan Allah ba zai kar’bi uzuri na ba akan hukuncin da nayi ma Dr na hana shi kaina. Hijab d’ina nasa da wani tsadadden flat shoe d'ina na nufi side d’in shi. Samun shi nayi a zaune yana danna laptop. K’arasa shigowa nayi had’e da sallama a baki na. Motsin da bakin shi yayi ne ya tabbatar min da amsa sallama ta yake yi. Kusa dashi na zo na zauna. Shiru ne ya ratsa d’akin kamar ba kowa a ciki. Dr ne ya kau da shirun da cewa "Ina fatan lafiya ko Zarah na gan ki a d’aki na a wannan lokacin". Kallon shi nayi jin yadda ya fad’a min maganar, nasan fushin abin da na mishi jiya ne yake so ya huce a yanzu. Marairaice fuskata na yi kana cikin shagwa’ba na ce " Dan ka gan ni a d’akin ka a wannan lokacin ai ba laifi ba ne Dr tun da d’akin my lovely husband d’ina ne na shigo". Dr ne ya ce "Laifi ne a guri na tun da jiya da naje d’akin ki kin haramta min kwana, kin ga kenan nima dan na tuhume ki da na ganki a wannan lokacin ai ba laifi ba ne". " I am sorry to say that sometimes matters of very small importance waste a good deal of precious time, by the long and repeated speeches and chicanery of gentleman who will not wholly throw off the lawyer even in congress, Am sorry Dr for what I have done to you yesterday, i will not repeat my mistake" Na fad’a cikin kwantar da murya da lallashi. Shiru yayi yana kallo na, da alama maganganun da nayi amfani dashi ya sanyayar masa da jiki akan fushin da yake yi dani. Hakan da na fahimta yasa na fad’a jikin shi na fara mishi kukan shagwa’ba. A hankali Dr ya fara lallashi na tare da goge min hawayen da ya fara zuba a idanu na yana cewa "Stop crying my Zarah". D’ago kaina nayi cikin marairaicewa na ce "Dr ka hak’ura da laifin da na maka jiya?". Murmushi ya sakar min kana ya ce " Na hak’ura Zarah, ba wanda ya wuce kuskure, but pls stop crying my baby". Saurin goge hawayena nayi, in a cool voice na ce "Na daina kukan Dr tun da ba ka so". "Shi yasa nake son ki my Zarah" Dr ya fad’a. Da wannan dubarar na samu na shawo kan Dr muka shirya. Haka zaman mu ya dawo normal da Dr kamar ba mu samu sa’bani a baya ba. Yau yaya Faru k ne suke zaune a falo da Nana suna kallon wani film da ake watsowa a tashar Joy prime na indian series mai suna Jansi Kirani. Wayar yaya Faruk ce tayi k’ara alamar kira ya shigo wayar shi. Ganin sunan wacce ke kirar shi yasa ya d’an saki murmushi kana ya d’auka. "Assalamu alaikum Binafa" yaya Faruk ya fad’a. Daga can ‘bangaren Binafa ce ta amsa mishi da "Wa alaikumus salam Bregadier Umar". Binafa ce ta ce "Bregadier ya kwana biyu ya kuma amarya". Juyawa yayi ya kalli ‘bangaren Nana da idon ta ke kanshi tun san da ya d’auki waya ya ambaci sunan Binafa hankalin ta ya dawo gurin shi. Had’a idon da suka yi ne yasa ya tayi saurin saukar da idanun ta k’asa. Murmushi ya sakar mata kana ya dawo kan hankalin shi ga wayar da yake yi da cewa "Lafiya lau Binafa". "Ai nayi fushi Bregadier tun da ba ka nema na, nayi zaton za ka dinga kira na mu gaisa amma sai ba ka kira ni ba, rabon da muyi waya da kai tun San da na kira ka kace min kayi aure". "Sorry Binafa ban samun time ne shi yasa, ya su Momy da Dad" yaya Faruk ya fad’a. Cikin shagwa’ba Binafa ta ce "Daman nasan haka za ka ce ba ka da time, su Mom da Dad suna nan lafiya". Mik’ewa Nana tayi da niyar barin falon saboda yadda ta fara jin ranta ya ‘baci akan wayar da yaya Faruk yake yi. Yaya Faruk ne ya sa d’ayan hannun shi ya r’ikota ta fad’a kan jikin shi. Binafa ce ta ce "Bregadier kasan dalilin kiran ka da nayi". "No sai kin fad’a" yaya Fruk ya ba ta amsa. "Na kira ka ne in faad’a maka biki na ya kusa" cewar Binafa. Yaya Faruk ne ya ce "Congrat Binafa, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya a tsakanin ku". "Na gode Umar da wannan addu’ar taka, my regard to ur groom" Binafa ta fad’a. "Don’t mind Binafa, a gaishe min da angon" cewar yaya Faruk. "Zai ji insha Allah" Binafa ta amsa mishi. "good bye Umar". "Take care". Katse wayar yayi ya juyo da kallo shi ga Nana wacce yanayin ta ya canza. A yadda ya fahimci yanayin ta, yasan kishi ne ke danun ta tun san da Binafa ta kira shi a waya,i dai yasan ba za ta iya mishi magana ba duk da ya ga yanayin ta ya canza. "Ya aka yi ne Khadija" Yaya Faruk ya fad’a yana kallon ta. Cikin sanyinta ta amsa mishi da cewa "Ba komai yaya Faruk". "Wayar da na amsa ce ta ‘bata miki rai ko?" yaya Faruk ya jefo mata tambaya. Girgiza mishi kai tayi alamar ba haka ba ne. Murmushi kawai yayi saboda ya san amsa wayar da yayi ne ya sa mood d’in ta ya canza, yasan ba taso ya fahimci hakan ne. Wannan halayen na Nana su suke k’ara mata martaba da daraja a idanun shi, shi kan shi a yanzu yasan da cewa ya fad’a tarkon son Nana, sai dai ba ya jin zai yi saurin furta mata Kalmar so a yanzu saboda har yanzu tabon da ke zuciyar shi bai gama warkewa ba. "Wacce muka yi waya da ita akwai mutunci a tsakani na da ita,, sunan ta Binafa, yanzu haka ta kira ne ta fad’a min za tayi aure, apart from that babu wani abu dake tsakanin mu, na ga k’anwa ta har ta fara kishin Binafan" yaya Faruk ya k’arsa maganar da wasa. Rufe fuskar ta tayi tana dariya. Murmushi yaya Faruk yayi ya ce "Ashe gaskiya na fad’a kenan tun da gashi kin rufe fuskar ki". Da sauri ta bud’e fuskar ta cikin shagwa’ba ta ce " Ni fa ba kishin ta nake yi ba yaya Faruk". "In ba kishin ta kike yi ba mai yasa mood d’in ki ya canza kuma sannan kika mik’e za ki bar gurin" cewar yaya Faruk. "Ba komai" Nana ta bashi amsa. Haka yaci gaba da tsokanar ta ita kuma tana biye mishi, haka suka ci gaba da hirar su cikin annashuwa. A ‘bangare na komai yana tafiya yadda nake so a zamantakewar mu da Dr, sai dai matsalar da na far fuskanta da Dr shine yadda a yanzu kusancin su yayi yawa da Dr. Idan na mishi magana sai ya nunar min da babu wani abu dake tsakanin su da ya wuce k’anwar shi ce sannan ga matsalar da ke damuna na rashin samun ciki da ban yi ba wanda har yanzu na lura Dr haka bai dame shi ba, abin ya fara damu na, gashi na rasa wanda zan fad’a ma wa in ji dad’i a raina. Ga yawan zuwan da Meeman da take yi, wani lokacin takan zo da Hanan ko ta zo ita kad’ai. A zuwan da take yi ne na fahimci closeness d’in su da Dr yayi yawa, ga waya da suke yi da ita. Yau ranar ta kasance ranar weekend ne, ina zaune ina kallon pix a wayan Dr yayin da shi yake d’aki yana bacci. Wasu hotuna ne suka d’auki hankali na a cikin wayar Dr wanda yasa na maida hankali na gurin hoto. Dr ne da Meema suka d’auki hoto a wani gurin shak’atawa, kayan da ke jikin Meema d’in wasu irin tsansparent English wears ne ta d’an yafa veil a jikin ta, hoton sun d’auka ne suna yiwa juna murmushi. Haka na ci gaba da kallon hotunan da Dr yayi da Meema a guri daban-daban. Yanayin yadda suka d’auki hotunan da suturar da ke jikin Meema shi ya fi b’ata min rai fiye da komai. Ina cikin wannan halin ne Dr ya shigo falon ya zo ya zauna kusa dani. Kasa daure wa nayi na kalli Dr cikin b’acin rai na ce "Dr me wannan hotunan suke yi a wayar ka". Kallon mamaki ya min kana ya ce "Ban gane me suke yi a waya na ba, nasan kin san wacece a jikin hoton, kin ga ba ki da buk’atar in miki bayanin ta". "Sanin ko wacece a jikin hoton yasa nake son sanin k’arin bayani akan wannan hotunan da kuka d’auka da suka sa’ba ma shari’a, shi nake so ka yi min bayani" na fad’a cikin fushi. "Yanzu dan na d’auki hoto da Meema shine ya zama abin tuhuma a wajen ki, kar ki bari kishi ya rufe miki ido Zarah" cewar Dr. Ni ce na ce "D’aukar hoton ka da Meema ba damuwa ta ba ce, sai dai yadda aka d’auki hoton ne da suturar da ita Meeman tasa ita ce abin tuhuma a gare ni dan a iya sani na Meema ba muharramar ka ba ce". Dr ne ya ce "Look Zarah mu bar wannan maganar, dan ban ga amfanin yin ta ba". Murmushin takaici nayi kana na ce "Dr dole ka ce in bar maganar nan saboda kasan ba ka da gaskiya, ina mamakin yadda a kullum in na tuhume ka akan Meema kake bani amsa kala d’aya akan cewa akwai shak’uwa a tsakanin ku sannan matsayin k’anwa take a gurin ka, Dr na gaji da yawo da hankalin da kake min na cewa Meema mutunci ke tsakanin ku". Wani irin kallo ya min kana ya ce e kike so in fad’a miki Zarah, kamar yadda na fad’a miki a farko ba wani abu da ke tsakani na da Meema period in kin yarda kenan, dan na gaji da miki bayani time without numbers akan tsakani na da Meema". Yana gama fad’ar haka ya d’auki wayar shi ya fita daga gidan. Zama nayi na fara kukan takaicin abin da Dr yake min wanda ban ta’ba zatan hakan daga gareshi ba, wai yau Dr da na nuna ma so yake min abubuwan da ya gadama dan yaga mun yi aure. Haka na gaji da kukan da nake yi na goge hawayena na tafi d’aki na. Tun daga wannan lokacin muka ci gaba da samun sa’bani da Dr akan Meema, duk na bi na canza, kai da ka kalle ni kasan akwai abin da yake damu na. [9/5, 11:53] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa writers Association *Fatan alkhairi gare ku* _Hajara Tijjani_ _Lubiee_ _Harira_ _Ummie_ _Maimunat Abba_ _Habiba Muhammad Rabo_ _Aysha Madugu_ _Zakiyya_ _Ina ganin comment d’in ku akan wannan littafin, ina yaba wa akan comments d'in Ku, ‘yar mutan Paki na muku fatan alkhairi a duk inda kuke da sauran masoya wannan littafin_. 87-88 Yau ranar ta kasance ranar Alhamis, ina zaune a falo ina karanta wani novel mai suna "Behind our love". Knocking d’in da naji ne yasa na tashi na bud’e k’ofar. Halima na gani a tsaye a bakin k'ofa. Rungume ta nayi cikin murnar ganin ta. Ita ma murnar take yi saboda mun kwana biyu ba mu had’u da ita ba. Hannu ta na rik’o muka dawo falo muka zauna. Hira muka fara yi kafin na tuna ban kawo mata abin motsa baki ba. Tashi nayi naje na kawo mata drinks da snacks a gaban ta kana muka ci gaba da hirar da muke yi. A cikin hirar da muke yi ne Halima ta kalle ni cikin kulawa ta ce "Wai Fatima kin yi rashin lafiya ne nag a kin canza, ko ciki kike dashi yasa kika canza". Murmushi nayi na ce "Ba ko d’aya a ciki". K’ara kallo na tayi kana ta ce " Serious speaking Fatima kin canza, yanayin ki ya nuna kamar akwai abin da yake damun ki". Tun da Halima ta tambaye ni abin da yake damu na naji ta ta’bo min abin da ya ke min k’aik’ayi a raina, a yanzu ba na jin zan ci gaba da adana abin da yake damu na saboda nasan fad’ar zai rage min halin damuwar da nake ciki. "Halima ba zan ‘boye miki abin da yake damu na ba tsakanina da Dr" na fad’a cikin sanyin murya. Halima bi na kawai take yi da kallo tana jiran jin abin da zan fad’a mata. "Halima tun da muka yi aure da Dr nake fuskantar problem ni da Dr in one way on the other, wanda yafi damu na a yanzu shine mu’amalar shi da Meema, duk yadda na nuna ‘bacin raina hakan bai sa komai ya canza ba, na rasa yadda zan yi Halima" na fad'a. "Wacece Meema kuma" Halima ta tambaye ni. Nan na bata labarin Meema har kawo yanzu da muke ci gaba da takun sak’a da Dr. Cikin tausayawa Halima ta ce "Gaskiya Dr bai kyauta ba, ban zaci hakan daga gare shi ba saboda yadda na ga kuna nuna ma junan ku soyayya kafin ku yi aure, sai dai shi namiji dama ya kan iya canza wa a ko wane lokaci, A b’angaren Meeman tun da kin nuna ba k’ya son tarayyar shi da ita Meeman ya kamata ya ja baya da ita, kinsan maza baka gane in da suka fuskanta, amma abin da nake so dake Fatima shine ki ci gaba da hak’uri, ki daina sa damuwa a ranki sannan ki daina yawan mishi magana akan ita Meeaman, tun da ya tabbatar miki da ba komai a tsakanin su ki yarda a hakan, insha Allah komai zai dawo normal, may be ma kishin ki ne yasa ki ka ga kamar akwai wata alak’a a tsakanin su da Meeman" Halima ta k’arasa maganar cikin tsokana. Ni ce na ce "Na gode da shawarwarin ki Halima". Tabbas na ji dad’i shawarar da Halima ta bani, ko ba komai na samu sauk’in damuwar da nake ciki. Haka Halima ta ci gaba da ba ni shawarwari wanda za su amfane ni kana muka ci gaba da hirar mu. Sai bayan la’asar sannan Halima ta tafi. B’angaren Meema kuwa tun da ta ga Dr na sakar nata fuska yasa ta fara zargin ko yanzu Dr ya fara son ta ne kamar yadda take son shi. Yanda take damun iyayen ta da maganar Dr yasa Mominta ta fara mata fad’a akan irin son da take ma Dr sannan ba ta ganin za ta bar Meeman ta auri mai Mata tun da bai aure ta a ta farko ba, da farko Momin ta fad’a ta fara mata akan ta hak’ura da Dr tun da ba shi ba ne autan maza sannan mai zai tayi da Dr tun da ya riga yayi aure, Dadin ta kuwa lallashin ta yake yi akan ta hak’ura da Dr ta za’bi d’aya daga cikin samarin ta masu son ta amma duk maganar da iyayen ta ke mata ta bayan kunnen ta take bi saboda tana gaanin Dr shi yafi dacewa akan ya zama Sanyin idaniyan ta sannan kuma mijin ta. Ba in da take samun goyon baya akan son da take ma Dr da ya wuce Hanan da Momin Dr. Kullum Meema ba ta da wani buri da ya wuce a ce Dr ya amshi tayin soyayyar da take mishi amma har yanzu ba ta kai ga cin nasara ba. Meema ce da Hanan zaune a Gurin shak’atawa dake harabar gidan su Dr. Zaune suke akan wasu kujeru da aka ke’bance na musamman dan hutawa, ko waccen su na rik’e da favourite drinks d’in su suna sha. Motar Dr ce ta danno kai cikin gidan. Parking yayi a parking space kana ya nufi cikin gidan ba tare da lura da su Hanan da ke zaune a gurin shak’atawar. Meema ce ta mik’e da niyyar barin gurin. Hanan ce ta kalle ta kan ta ce "Ina za ki Meema". "Yanzu zan je in dawo, ina son mu yi magana da yaya Sadik ne" Meema ta fad’a. Ta’be baki Hanan tayi kana ta ce "Ok sai kin dawo". Bayan tafiyar Meema ne Hanan ta ja d’an k’aramin tsaki saboda tun tana tausaya mta a irin son da take ma Dr yana share ta duk da d’inbin masoyan da Meema take dasu amma a yanzu Meema ta fara ba ta haushi akan yadda ta nace ma Dr alhalin shi ba ya son ta hasalima shi yayi aure, k’arin abin haushin shine har yanzu Dr bai nuna tausayawar shi ga Meema ba duk da irin son da take mishi, ba laifi yanzu su na shiri da Dr saboda ta rage wasu behaviours d’in ta da ba ya so, ita a ganin ta bai kamata Meema na wahalar da kanta ba akan Dr a yadda take, ita kanta za taso Dr ya auri Meema ko dan son da take mishi. San da Meema ta shiga falon ba kowa a ciki, hakan yasa ta nemi guri ta zauna tana jiran fitowar Dr. Ya d’an jima a ciki kafin ya fito daga side d’in Momi. Ganin Meema da yayi a zaune a falon yasa ya sakar mata murmushi. "Ina wuni Yaya Sadik" Meema ta fad’a cikin kwantar da murya. "Lafiya lau Meema, ya su Momi" cewar Dr. "Suna nan lafiya lau" Meema ta amsa mishi. "Yanzu kika zo ne?" Dr ya tambaye ta. Meema ce ta amsa da cewa "Na d’an jima da zuwa, muna wajen shak’atawa ne ni da Hanan". "Ok san da na shigo ban lura da ku ba, bari in tafi Meema, ki gaida su Dad". Har ya fara tafiya Meema ta kira sunan shi cikin marairaicewa. Juyowa yayi ya kalle ta kan ya ce " Ya aka yi ne Meema". "Dr ina so muyi wata magana dakai ne" cewar Meema. Murmushi yayi kana ya ce "Ina jin ki Meema". Meema ce ta ce "Dr me yasa ba ka so na?’". D’aure fuska yayi kamar ba shi ba ne ya gama sakar mata fuska ya ce " Look Meema, in dai akan wannan maganar ce ina ganin ba ki da buk’atar amsar ta, na riga na fad’a miki cewa ki yi hak’uri da ni, already yanzu ina da mata, na fad’a miki tun a baya na d’auke ki ne as a sister not a lover, zan iya miki duk abin da zan ma su Hanan, sannan za ki iya tambaya na duk abin da kike so zan miki shi, but ina so ki ajiiye maganar soyayya a tsakanin mu dan ki ga akan shi ne nake b'atawa dake". Hawaye ne ya fara zubowa a idanun ta kana ta ce "Yaya Sadik dan ka ga ina son ka shine kake min haka, ni kaina ban san tsawon lokacn da na d’auka ina jiran ka amshi tayin soyayya ta but you refuse, why yaya Sadik?, ka taimaka ka so ni sannan ka aure ni a matsayin matar ka, hakan ne zai sa in samu peace of mind na samu abin da nake so, yaya Sadik I don’t care about your wife in dai za ka aure ni zan zauna da ita". Tausayin ta ne ya kama shi da har yake jin kamar ya amince da buk’atar ta, sai dai yasan hakan ba zai yiwu a gare shi ba dan bai ra’ayin mata biyu sannan har yanzu bai jin son Meema a ranshi. Cikin sweet voice d’in shi ya ce " Sorry to say Meema, ki hak’ura da ni don ba na so in yi deceiving d’in ki, infact in da zan aure ki da tuntuni zan aure ki tun kafin in auri Zarah, a tsari na ba na ra’ayin mata biyu" yana gama fad’ar haka ya bar gurin. Kan kujera Meema ta fad’a ta fara kukan k’in amincewar Dr da bai yarda zai aure ta ba. Momi ke sakkowa daga upstairs ta hango Meema na kuka, hakan yasa ta k’arasa sakkowa da sauri ta k’araso gurin da Meema take. Kwantar da ita tayi a jikinta tana tambayar ta abin da ya same ta. Meema cikin kuka ta ce "Momi yaya Sadik ne". Da sauri Momi ta ce "Me ya miki". Nan Meema ta fad’a ma Momi yadda suka yi da Dr kana ta d’aura da cewa "Momi ki taimake ni in sami Dr a matsayin miji na, shi nake so, na kasa ba ma kowa wannan damar da na ba ma yaya Sadik amma duk da haka ya k’i so na, akan haka yasa Momi take ganin laifi na saboda yadda na dage sai yaya Sadik, Momi ki mishi magana ya aure ni, ni zan zauna da Zarah, plss Momi ki fad’a min ko ina yin wani abu ne da Dr ba ya so in daina" ta k’arasa maganar cikin shashshek’ar kuka. A yadda Momi take jin tausayin Meema tana ganin za ta iya mata ko wane taimako dan taga ta samu Dr a matsayin miji, ita ba ta ga wani aibun Meema ba da Dr yake fad’a tana dashi, dan kawai tana yin social life shine zai zama tana da aibu. Ba ta son takura ma yaranta, tafi son basu duk abin da suke so, amma wannan karan tana ganin za tayi ma Dr magana akan ya auri Meema ko dan zaman jiran shi da tayi tak’i auran kowa akan shi. Kukan da Meema shi ya dawo da Momi daga tunanin da ta fara yi. Cikin lallashi Momi ta ce "Is ok Meema, ki daina kukan hakan, zan san yadda zan yi ki samu Dr, ni kaina ina so ki auri Sadik". Cike da jin dad’i Meeme ta rungume Momi tana godiya. Hanan ce ta shigo falon ta nemi guri ta zauna tana kallon fuskar Meema da ta canza kala saboda kukan da tayi. Cikin tuhuma Hanan ta ce "Meema me yasa ki kuka?". Shiru tayi ba ta ba ta amsa ba, hakan yasa ta fahimci dalilin kukan ta. "Yaya Sadik ne ko?" Hanan ta tambaye ta. D’aga mata kai tayi alamar haka ne. Tsaki Husna tayi kana ta watsa mata harara ta ce "Wai ke Meema ba za ki hak’ura da yaya Sadik ba ne, sai ka ce shi kad’ai ne namiji, ga maza nan da suke son ki kala-kala amma ke kin nace sai shi, yanda kike da class ya kamata a ce kin hak’ura dashi tun da ya nuna ba yi da interest akan ki". Momi ce ta harari Hanan kana ta ce "Instead of ki lallashe ta Meema amma kin tsaya kina kara ‘bata mata rai, laifi ne dan Allah ya jarrabi mutum da soyayya". Hanan ce ta mik’e cikin shagwa’ba ta ce "Shi kenan Momi ai ga ta ga yaya Sadik d’in nan" tana gama fad’ar haka ta nufi d’akin ta. Yau Momi ce ta kira Dr akan ta na neman shi in ya taso daga aiki. Bayan tashi daga aiki ne ya wuce gidan Momi. Side d’in ta ya wuce direct ganin ba kowa a falon. A zaune ya same ta tana danna laptop sanye da medicated glass a fuskar ta. Guri ya nema ya zauna kana ya gaishe da Momi. Da murmushi a fuskar ta ta amsa mishi kana ta ajiye laptop d’in ta a gefen ta. "Ya aikin Sadik" Momi ta tambaye shi. Amsa mata yayi da cewa "Aiki alhamdulillah". "That’s good, Alla ya taimaka" Momi ta fad’a. "Amin Momi" cewar Sadik. Momi ce ta kalle shi cikin kulawa ta ce "Sadik magana nake so mu yi dake mai mahimmanci". Sadik ya fad’a "Ina jin ki Momi". Momi ce taci gaba da cewa "Akan Meema nake so muyi maganar". "Meema kuma Momi" Sadik ya tambaye ta. Gyad’a mishi kai tayi alamar Eh haka take nufi kana taci gaba da cewa "Gaskiya Sadik ba na jin dad’in yadda kake ma Meema, yarinyar nan tana son ka, tun kafin ka auri Zarah take son ka kana share ta till now ba ta daina son ka ba duk da tana da masu son ta, a lokacin da na maka maganar auren ta ka kawon wasu weak excuse which i was not satisfied dasu, na k’yaleka ka auri choice d’in ka saboda ba na son matsa maka, amma a yanzu ina so ka auri Meema ko dan darajar son da take maka, in ka min haka zan ji dad’i". "Amma Momi ni ba na ra’ayin mata biyu, beside Zarah ba za taji dad'in wannan labarin ba in har taji zan k’ara aure, sannan ni har yanzu Momi ina d’aukan Meema kamar su Hanan ne, sannan Momi kin san Meema akwai wasu behaviours na ta da ba na so, kar mu zo muyi aure da ita ana samun matsala a tsakanin mu da ita". Cikin fad’a Momi ta ce "Oh because of Zarah shi yasa ba za ka aure ta ba saboda ba ka so ranta ya ‘baci, I am tired of your complain about Meema, this time around sai ka auri Meema, I din’t care about her behaviours kamar yadda kake fad’a, in an yi auren you can change her the way you like, I am absolutely sure she will change since she love love you, ina so ka fara zuwa zance gurin ta dan ina so ayi bikin da wuri, this time around command nake baka ba request d’in ka nake yi ba". Rasa me yake masa dad’i Dr yayi jin cewa Momi ta ce command take bashi, a yadda Momi tayi maganar yasa da gaske take yi, zai yi wuya ta canza daga maganar da tayi. "Zan yi yadda kike so Momi, in dai auren Meema will make you happy zan aure ta" cewar Dr. Murmushi ne ya bayyana a fuskar Momi jin cewa Dr ya amince da buk’atar ta. Momi ce ta ce "Yawwa Sadik, nasan ba za ka ban kunya ba, nasan za ka amince da buk’ata ta, Meema na son ka Sadik, shi yasa nake son ka aure ta, in kuka yi aure sai ka ga a hankali son ta ya shiga zuciyar ka". A yadda yake jin zuciyar shi bay abo ba fallasa game da auren Meema da Momi take so yayi, ya sa ma ranshi zai auri Meema dan farin cikin Momi ba wai dan yana jin nan gaba zai iya son Meeman ba, yanzu abin da yafi damun shi shine in naji maganar auren yasa ba k’aramar matsala za mu samu dashi ba, dole ya bi komai a sannu dan guje ma faruwar wata matsala da ka iya zuwa a tsakanin mu. Kallon Momi yayi ya ce "Momi plss ina buk’atar ki d’an k’ara min time akan maganar". Momi ce ta ce "Kar ka damu Sadik, tun da har ka amince shi kenan, daman hakan na fi buk’ata daga gurin ka, sai dai ina so ka fara zuwa gurin Meema zance dan tasan ka amince za ka aure ta". "Zan yi k’ok’ari in je Momi" Dr ya fad’a. "Yawwa Sadik, Allah ya maka albarka" cewar Momi. "Amin Momi" Dr ya fad'a. Nan Dr ya canza maganar zuwa wata hirar dan ba yaso Momi ta ci gaba da mishi maganar Meema. Ya d’an jima a gurin Momi kafin ya mata sallama ya tafi. Bayan tafiyar shi ne Momi ta kira Meema ta sanar da ita yanda suka yi da Sadik akan amincewar auran ta da zai yi. Farin cikin da Meema ta shiga ba zai fasaltu ba jin cewa Dr zai aure ta, tsalle ta dinga yi kamar k’aramar yarinya taje ta rungume Mominta tana cewa "Momi Dr ya yarda zai aure ni". Ita kanta Mominta taji dad’in wannan labarin saboda yadda take son kwaciyar hankalin yarinyar ta. Tun da Meema taji Dr ya amince da auranta ta fara matsa mishi da waya akan yaushe zai fara zuwa zance gurin ta amma sai Dr ya basar da zance ko ya ce mata sai ya samu lokaci. Hakan ya fara d’aga mata hankali saboda tasan Dr na mata kora da hali ne saboda tayi fushi ta ce ta hak’ura da auran shi, tasa a ranta cewa za ta jure duk abin da zai mata in har zai aure ta, in yaso in aka yi auren sa yi wacce za suyi dashi dan ba za ta juri rainin hankali daga gurin shi ba dan ya ga tana son shi. Yau ma kiran shi tayi amma bai d’auka ba sai da ta kusan tsinkewa kan ya d’auka. "Ya aka yi ne Meema" Dr ya fad’a. Cikin kwantar da murya Meema ta ce "yaya Sadik na ji ka shiru, har yanzu ba ka zo ba". "Me zan miki in na zo" cewar Dr. Marairaicewa Meema tayi kamar za tayi kuka ta ce "Haba yaya Sadik, wannan wace irin tambaya ce za ka ce me za ka min in ka zo, aure fa za muyi, ya kamata a ce kana nuna caring d’in ka a kaina, amma ko kira na ba ka cika yi ba sai in ni na kira ka". " In na samu time zan zo" yana gama fad’ar haka ya katse wayar. Wani irin takaici ne ya kama Meema ganin irin wulak’ancin da Dr yake mata, in ban da so yaushe za ta jure wulak’ancin namiji ko waye shi kuwa, maza nawa take juyawa yadda take so. Yau ranar ta kasance ranar lahadi. Muna zaune a side d’in Dr muna kallo yain da nake kwance a jikin Dr shi kuma yana shafa min gashi na. Wayar shi ce tayi k’ara alamar kira ya shigo. D’aga wa yayi ya ga mai kiran kana ya ajiye wayar a gefen shi ba tare da ya d’auka ba. Ci gaba da k’ara wayar tayi amma hakan bai sa Dr ya d’auki wayar ba. Hakan yasa na kalle shi na ce "‘Dr kana ji sai kiran wayar ka ake yi…". Ban k’arasa maganar ba wani kiran ya sake shigowa. Picking d’in call d’in yayi kana yayi shiru. Ni dai ban ji me aka ce mai ba amma na ji dai ya amsa da cewa " Why are you disturbing me Meema, what do you want from me". Jin ya ambaci Meema na tabbatar da ita yake wayar. Kau da kaina nayi duk da raina da ya soma b’aci akan kiran da Meema ke ma Dr, ba na son yi mishi magana akan haka saboda kar ya d’auki hakan a matsayin kishi kamar yadda yake cewa in na mishi magana, sannan ina so in yi amfani da shawarar Halima akan kar in sa ma kaina komai ga me da alak’ar Dr da Meema. Tsawar da Dr yayi ma Meema ita ta dawo dani duniyar tunanin da na fad’a. "Will you keep that your mouth shut, kin bud’e min baki kina kuka, what have i done to you da kike min kuka". Ban ji mai ta ce mai ba, na dai jiyo shashshek’ar kukan ta. "Wannan matsalar ki ce Meema" Dr yana gama fad’ar haka ya katse wayar. Ni ko tun da na ji Dr na ma Meema fad’a na fara tunanin me ya had’a shi da ita, ganin ba abin da ya shafe ni ba ne yasa na ja baki na nayi shiru, ni hakan ma dad’i ya min dan yadda na ke jin haushin Meema akan yadda take ma Dr shishshigi ji nake yi kamar in kama ta da duka. Ko minti biyar ba ayi ba da wayar da Dr ya gama yi da Meema sai ga wani kiran ya shigo. Cikin ladabi ya d’auka ya ce "Momi good afternoon". "Afternoon Sadik" Momi ta amsa mishi a tak’aice. "Sadik ya muka yi da kai akan zuwa gurin Meema?" Momi ta tambaye shi. Shiru yayi ba tare da ya ba ta amsar tambayar da ta mishi ba. "Sadik ba ka ji tambayar da nayi maka ba" Momi ta sake watso mishi tambaya. "Zan je Momi, ban samu time ba ne" Sadik ya amsa mata. "To sannu agogo sarkin aiki, duk rashin time d’in ka ina so kayi squeezing d’in time ka je gurin ta, in ba haka ba you will see my bad side of me Sadik". "Sorry Mom" Dr ya fad’a. Momi ce ta ce "My last warning shine Meema ta fad’a min ba ka kiran ta sai ka gadama, sannan in ta kira ka sai ka fara mata fad’a, ba nason irin haka, kasan Meema ba ta son fad’a da tsawa, in ma wani abu ta maka ka mata magana in a polite way not rude, ina fatan ka fahimce ni". "Na fahimta Momi, zan kiyaye" Sadik ya fad’a. "Amma ita Meema ita tace ina mata fad’a in ta kira ni" Sadik ya tambayi Momi. "Ta fara gajiya ne da yadda kake mata, shi yasa ta kawo min k’arar ka, beside magana ta riga ta wuce’ Momi ta fad’a. Dr ne ya ce "Shi kenan Momi". "Ka gaishe da Zarah" cewar Momi. "Za taji" Dr ya amsa mata. Da haka suka yi sallama da Momi kana ya juyo da kallon shi gare ni ya sakar min murmushi. Tun da Dr ya fara waya da Momi na fahimci akan wata magana mai mahimmanci suke magana saboda amsar da Dr da na ji yana ba ta, sai dai hak’urin da Dr na ji yana ba ma Momi ne ya tabbatar min da wani laifi ya mata, a hasashe na a maganar da suke yi yana da alak’a da inda Momi take so Dr ya je bai je ba, gurin wacce Momi take so ya je ne ban sani ba, shi yasa yake ba ta hak’uri, sannan a maganar su na fahimci kamar har da maganar Meema take mishi, tambayar da na dinga juyawa a raina shine ina Momi take so Dr ya je?. Zuciya ta ce ta fara ayyana min wani tunani da yasa na fara sa wa a raina ko dai gun Meema Momi take so Dr yaje, to in akan Meema ne mai zai je ya Meema?. Saurin kau da wannan tunanin nayi dan nasan zuciya ta c eke son sa min wani tunani na daban, sannan maganar da Momi tayi da Dr a waya ba ta shafe ni ba tun da har Dr bai fad’a min akan abin da suka yi magana da Momi ba, hakan na nuna cewa maganar ba ta shafe ni ba. Dr ne ya katse ni da cewa "Zarah ya aka yi ne". Murmushi na mishi kana na ce " Ba komai Dr". "Momi na gaishe dake" Dr ya fad’a. Da fara’a a fuska ta na amsa da cewa "Ina amsawa". "Su Farida kwana biyu ba su zo ba ita da Hanan" na fad’a. Dr ne ya ce "School yayi zafi, nima sometimes in naje ba na samun su". Ni ce na ce "Allah ya taimaka". Lallausan murmushi ya min kana ya ce "Amin my Zarah". Kwantawa nayi a jikin shi muka yi fara gudanar da wata zazzafar soyayya mai wuyar fasalta wa. Da daddare Dr ne na ga ya canza wanka ya yayi shiga cikin wani lallausan yadi kalar madara. Ina zaune a falo na naga Dr ya fito yana ta baza k’amshi. Kusa da ni ya zo ya zauna yana sakar min murmushi. Kallon shi nayi na ce "Ina zaka Dr na ganka da key a hannun ka". "Zan je wata unguwa in dawo ne" cewar Dr. Kallon tuhuma na mishi kana na d’aure fuska na ce "Unguwa fa ka ce Dr, ka ga kuwa kyan da kayi shine za ka fita da shigar nan, salon ka fita mata su dinga kalle min kai". Dariya yayi yace " Kai Zarah, dad’i na dake kishi, kar ki damu ni naki ne, ba dad’e wa zanyi ba, yanzu zan je in dawo". Cikin shagwa’ba na ce "Gaskiya ni ban yarda ba Dr, sai dai ka je ka canza shigar da kayi ko ka hak’ura da fitar gaba d’aya". Da lallashi Dr ya ce "Kin ga Zarah na riga na shirya, ki yi hak’uri in je in dawo". "Na hak’ura, amma kar ka dad’e" na fad’a cikin shagwa’ba. Kiss ya kai min a goshi kana ya ce "Ba zan dad’e ba tun da my princess ta ce kar in dad’e". Murmushi na sakar mai had’e da jefa mishi wani kallo da Dr yake so in mishi irin shi. "Me zan tawo miki dashi" Dr ya tambaye ni. Amsa mishi nayi da cewa "Duk abin da ka ga ya maka". "Ni nasan abin da zan tawo miki dashi" cewar Dr. "Sai ka dawo" na fad’a. Dr ne ya amsa min da cewa "Ok sai na dawo". Tafiya ya fara yi yana waving d’in hannun shi, nima ina waving d’in hannun na. Kamar yadda Dr ya ce ba zai dad’e ba, ya cika alk’awari dan ya dawo da wuri, haka ya tawo min da kayan ciye-ciye da drinks had’e da snacks. A ‘bangare na kuwa ban san me ake ciki ba ga me da auran Meema da ya amince zai yi saboda bai min maganar Meeman ba. Ina iyaka k’ok’arina na ganin na toshe duk wace b’araka da za ta had’a ni da Dr. Wasa-wasa sai Dr ya tsiri fita da daddare, in na tambaye shi ina zai je sai ya ce min unguwa zai je. Yadda yake cin kwalliya in zai fita shi yasa na fara zargin ko dai gurin budurwa yake zuwa, sai dai ba ni da wata hujja da na ke da ita da zan yarda da cewa gurin budurwa yake zuwa. Kamar yau muna zaune na ga wayar shi na vibrating amma bai d'auka ba. Kallon shi nayi alamar tuhuma amma ban ce komai ba. K'aramin tsaki yayi kana ya mik'e da niyyar fita. "Ina zaka Dr?" Na tambaye shi. Zarah kin cika rigima, duk inda zan sai na fad'a miki kenan' ya fad'a da alamar wasa. D'aure fuska nayi na ce "Joke aside Dr, gaskiya fitar nan da ka fara yi da daddare ya fara damu na, wace unguwa ce ka ke zuwa da ba ta da suna, in na tambaye ka sai ka ce unguwa za ka, ai da baka yawan fitar nan, wai ina kake zuwa ne Dr?" Na k'arasa maganar da tambayar shi. Cikin kwantar da murya ya ce "Relax Zarah". " In ka fita tsoro nake ji, ni kad'ai a gida, sannan wace fita ce sai da daddare ake yin ta" na fad'a cikin marairaicewa kamar zan yi kuka. Dawowa yayi ya zauna kana ya fara lallashi na. Ranar sai da nasan yadda nayi na hana Dr fita. Tun lokacin da nuna b'acin raina akan fitar shi na samu ya daina fita. Kiran da Meema ta ke ma Dr ya wuce limit, a fahimtar da nayi shine yanzu bai cika son amsa kiran ta ba a gaba na, wani lokacin kuma zan ji yana k'asa-k'asa da murya in rasa me suke cewa. Hakan ba k'aramin b'ata min rai yake yi ba, bana so muyi ta samun sab'ani da Dr akan Meema. Yau Ni kad'ai ce a gidan Dr ya tafi gurin aiki. Knocking naji na tashi na bud'e k'ofar. Meema ce tsaye cikin wani tsadadden material da aka mata wani irin shegen d'inki. Fuskar ta sanye take da wani space da ya rufe rabin fuskar ta. Hanya na bata ta shigo ba tare da ta min magana ba. Nima guri na nema na zauna ba tare da na ce mata komai ba saboda yadda ba ta min sallama ba san da za ta shigo. "Hi Zarah ykk" cewar Meema. Wani banzan kallo na watsa mata kana na ce "normal". " Dr na nan ne?" Meema ta tambaye ni. "Gidan ai ba bak'on ki bane, za ki iya zuwa ki duba ki gani" na ba ta amsa. Wani tak'aitaccen murmushi tayi kana ta ce "Kar ki damu, in lokaci yayi da kaina zan je in duba ba sai kin fad'a min ba". Kallon ba ki san abin da kike fad'a ba na watsa mata kana na kau da kaina daga kallon ta. "Na zo ne in miki tuni akan maganar da muka yi dake na cewa sai na auri Dr, kar ki ga kamar tsoro ne yasa har yanzu ba ayi bikin mu dashi ba, lokaci ne zai nuna hakan a lokacin da kika ganni a matsayin amaryar ki, ina so ki kasance cikin shiri saboda a ko yaushe hakan na iya kasancewa". Raina ne ya fara b'aci da irin maganganun da Meema take fad'a min, sai dai ba na son in biye mata dan nasan nema rigima take yi dani, na d'auki maganganun ta kamar tatsuniya wanda ba za su faru ba, dan haka nayi saurin danne fushi na kana na sakar mata murmushin yak'e na ce "Allah ya kaimu lokacin". " Amin Zarah" ta fad'a tana pressing d'in wayar ta dake hannun ta. Mik'ewa tayi da niyyar tafiya kana ta kalle ni tace "Zarah na tafi, sai gani na biyu". "A sauka lafiya" na fad'a. Tun tafiyar Meema na fara nazari akan maganar ta, karo na biyu kenan tana min magana akan auren ta da Dr, ban san me ta shirya akan haka ba da take da tabbacin Dr zai aure ta, koma dai mai ta taka ba na jin zan iya zama da Meema a matsayin kishiya ta dan tun kan ta shigo take nema na da rigima, ina ga in anyi auren, ban san me za ta k'ullo min ba cewa Meeman ba ta fad'a mishi zuwan ta ba. *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 Maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa writers Association *Wannan shafin naku ne y'an Kainuwa Fans* _Aisha Mahmmud_. _Nafisa_. _Fatima Ibrahim_. _DeejahNah_. _Khadijah ashafura_. _Da sauran fans na kainuwa writers_. _Naji dadin ganin comment din ku, hakan ya fahimtar dani kuna bibibiiyar wannan labarin, ina muku fatan alkhairi a duk in da ku ke_. 89-90 Momi ta k'ara kiran Dr karo na biyu akan maganar shi da Meema. San da yaje gidan ne ya ba ta hak'uri akan ta k'ara mishi lokaci. Momi ta amince da rok'on shi akan k'arin lokacin da ya nema amma akan sharad'in Dadin su Dr zai je gurin Dadin Meema suyi magana akan bikin. Dr ya amince da hakan. Bayan Dadi ya dawo ne Momi ta sanar dashi halin da ake ciki. Da farko Dadi bai amince da maganar ba saboda yasan Dr ba ya son Meema da aure, jin cewa Dr ya amince yasa ya kira shi akan maganar ya kuma tabbatar mishi da amincewar shi. Ba a d'au lokaci ba Dadin su Dr ya nemi Dadin Meema akan maganar, sun yake nan ba da dad'ewa ba sai ayi fixing d'in bikin. Lokacin da Momi ta fad'a ma su Hanan maganar auren Meema da Dr Hanan ce kad'ai ta nuna jin dad'in ta amma ita Farida ba ta son Dr ya auri Meema saboda wayewar ta tayi yawa. Yanzu fitar Dr ya canza salo saboda yanzu in ya fita wani lokacin sai nayi bacci yake dawo wa, tun ina nuna b'acin raina har na dawo na zuba mishi ido ba dan raina ba ya b'aci ba, sai dan ba ni da yadda zan yi akan Dr. Hakan yasa damuwa ta fara min yawa, gashi har yanzu ban samu cikin da nake fatan samu ba. Tambayar Dr nayi akan zan je gidan Anisa, cikin sa'a ya bar ni. Shiryawa nayi na shiga mota ta na nufi gidan Yaya Khalil. San da naje gidan yaya Khalil ba ya nan. Zama nayi muka sha hira da Anisa yayin da Amatur-Rahman ke hannu na ina mata wasa. A cikin hirar ne Anisa ta kalle ni kana ta kira suna na da cewa "Fatima". D'agowa nayi na kalle ta ba tare da na amsa mata ba. " Me yake damun ki Fatima" Anisa ta tambaye ni. Kallon mamaki na mata kana na ce "Me kika gani Anisa?". " Naga abubuwa da dama a fuskar ki da nake so ki fad'a min" cewar Anisa. Cikin wasa na ce "Idon ki bai nuna miki gaskiya ba dan ba abin da yake damu na". Anisa ce ta ce "Fatima a ture maganar wasa, kin san na san ki ciki da waje, kar ki manta tun muna yara muke tare har zuwa yanzu, ina iya fahimta yanayin ki a kowane lokaci, yanayin ki ya nuna something is bordering you wanda ba kya so a sani, ba ma ni ba Fatima, duk wanda ya ganki yasan kina cikin damuwa, bazan matsa miki ki fad'a min damuwar ki ba, sai dai ina so ki rage ma kan ki tunani, sannan Fatima ki k'ara hak'uri a dukkan jarabawar da Allah zai miki, sai ki ga a dalilin wannan hak'urin da kika yi Allah ya biya miki buk'atun ki". A yanda na fahimci maganar Anisa tana min magana ne akan rashin samun cikin da ban yi ba, ba ta san bayan wannan ba akwai wata damuwar halin da Dr yasa ni a ciki da na rasa yadda zan b'ullo mishi akan fitar da yake yi, ina da tabbacin in har na fad'a ma Anisa za ta bani shawara wacce ta dace, sai dai nasan in Anisa taji wannan maganar za ta tuno min baya ne akan yadda a kullum nake yabon Dr da cewa ina da tabbaci a kanshi, gwara in danne matsala ta har lokacin da komai zai zama normal tsakani na da Dr. Murmushi nayi kana na ce "Na gode Anisa da shawarar ki gare ni". Ita ma Murmushin ta mayar min. Haka muka ci gaba da Hira har Yaya Khalil ya dawo muka gaisa dashi kana na musu sallama na tafi. Haka san da naje gidan Anty Jidderh ita ma haka ta tambaye ni me yake damu na, sai da na ce mata ba komai, girgiza kai kawai tayi alamar ba ta yarda da abin da na fad'a ba sannan ta canza wata hirar. A can b'angaren su Yaya Faruk kuwa Khadijah ce ke fama da rashin lafiya, hakan yasa yaya Faruk ya kaita asibiti, gwajin farko aka tabbatar mishi tana d'auke da ciki. Farin ciki kasa b'oyuwa yayi akan fuskar Dr jin wannan labarin. Tun a asibiti Yaya Faruk ya rungume ta yana murnar samun baby da za su yi. Ita kuwa Khadijah sai faman sunkuyar da kai take yi saboda kunya. Da suka dawo gida haka ya dinga tambayar ta ko akwai abin da take so ya mata. Motsi kad'an za tayi zai tambaye ta ko akwai inda yake mata ciwo ne. Ita abin har dariya yake ba ta ganin yadda Yaya Faruk yake mata. Kusa da ita Yaya Faruk ya zo ya zauna ya kwantar da ita akan cinyar shi. Cikin cool voice d'in shi ya ce "Khadijah kin sa ni a farin ciki, ban san da me zan saka miki ba, na da 'yan month za ki bani baby, ki fad'a min abin da kike so in miki ko miye shi in har bai fi k'arfi na ba zan miki shi". Wannan maganar da Yaya Faruk yayi yasa taji kamar ta ce mishi ya ce yana son ta, ita ta na ganin in ya fad'a mata wannan Kalmar ta ishe ta ba sai ya ba ta komai ba, saboda yadda take jin son Yaya Faruk a ranta ba tasan yadda za ta fasalta shi ba, tasan son Yaya Faruk ya gama dabaibayi a ranta da dukkan sassan jikin ta gaba d'aya. Yaya Faruk ne ya ce "Khadijah ba ki ce komai ba, ko ba kya so in miki kyauta ne kamar yadda za ki min babbar kyauta da baby da Allah ya bamu a cikin ki". "Duk abin da ka ga ya dace da ni Yaya Faruk " cewar Khadijah. Tsadadden Murmushi Yaya Faruk yayi kana a hankali ya ce "I Love you Khadijah......". Kallon mamaki Khadijah ta bi shi dashi saboda jin Kalmar da ba yayi tsammanin ta a yanzu ba a gurin Yaya Faruk. Lallai ta zama tauraruwa tun da har ta samu Kalmar da ta ke jira daga gurin gwarzon mijin ta. Ba tasan yadda za ta bayyana farin cikin da take ciki ba. Ba abin da za tayi da ya wuce tayi ma Allah godiya da ya ba ta miji d'aya tamkar da goma. D'aga mata gira yayi kana ya kanne mata ido ya ce " Are you surprise?". Murmushi kawai tayi kana ta girgiza mishi kai alamar a'ah. Hannun ta ya rik'e kana Yaya Faruk ya ce " I mean my word Khadijah, Ina son ki Khadijah kamar yadda kika ji na fad'a, ki daina mamakin jin wannan Kalmar daga guri na, kin cancanci haka a guri na, kina min duk abin da nake so, kina son ganin farin ciki na da nuna kulawar ki akan 'yan uwa na da duk abin da ya shafe ni, Khadijah zan iya miki komai dan na faranta miki saboda a kullum kike son faranta min". "Yaya Faruk na gode da yabawar ka gare ni, ba abin da zan ce maka sai dai Allah ya ci gaba da taimakon ka da yi maka jagora a dukkan lamarin ka". Murmushi yayi ya ce " Amin Khadijah" Cikin tsokana ya ce "Ni ba ki fad'a min kina so na ba Khadijah". Jikin shi ta k'ara shigewa a hankali ta ce " I love you Yaya Faruk very much". D'ago fuskar ta yayi ya ce "Really?". D'aga mishi kai tayi alamar Eh. Rungume ta yayi yana jin wani farin ciki na yawo a dukkan sassan jikin shi, a wani b'angaren yana gode ma Allah da ya kawo mishi Khadijah a rayuwar shi. San da su Yaya Mus'ab suka zo duba Nana haka Maryam ta dinga tsokanar shi yana biye mata. Dr ya sami Hutu a gurin aikin shi Wanda yayi daidai da shigar Khadijah next class, saboda haka ne aka basu hutu dan new student su fara registration d'in su. Ganin ita ma Khadijah na hutu ne yasa Yaya Faruk suka shirya suka tawo Kaduna dan su k'arasa hutun su a can. Yau da daddare in zaune a falo na kasa bacci saboda har yanzu ban ji motsin dawowar Dr ba, ga shiru da gidan yayi, in ban da mai gadi da yake can gefen shi, ba motsin kowa da nake ji. Jefi-Jefi na kan kalli agogo na goge hawayen da yake zubo min. Tagumi nayi ina tunanin rayuwa mai juya wa a ko wane lokaci, in ba haka ba mai nayi ma Dr da yake min sakayya irin wannan. Guraren k'arfe 10 na ji bud'e gate d'in da naji ne ya tabbatar min Dr ne ya dawo. Slice window na je na bud'e na hango Dr yayi parking d'in motar shi a parking space. Dawowa nayi na zauna ina jiran shigowar Dr. Bud'e k'ofar da yayi ne yasa na maida hankali na bakin k'ofar. Sallama yayi kana ya k'araso in da nake zaune ya zauna. Amsa mishi sallamar nayi ina bin shi da kallon tuhuma. " Ashe ba ki yi bacci ba Zarah" Dr ya fad'a. "Kana tunanin nayi bacci ne shi yasa ka dawo at this time Dr" na fad'a cikin b'acin rai. Dr ne ya ce "Sorry Zarah, a asibiti ne wani emergency work ya tashi, shi yasa ki ka ga ban dawo da wuri ba, da na so na kwana a can ne dan ban za ci za mu gama aikin da wuri haka ba". Murmushin takaici nayi ganin yadda Dr yake so ya raina min hankali wai daga gurin aiki yake. "Dr jiki na bai bani daga gurin aiki kake ba, na fi gamsuwa da ka je b'oyayyar unguwar da kake zuwa amma ba gurin aiki ba, a duk lokacin da wani important work ya taso maka ko aka kawo emergency patient ka na kira na a waya ka fad'a min ba za ka dawo da wuri ba, amma me yasa wannan karan ba ka kira ni ka fad'a min ba". Cikin kwantar da murya Dr ya ce "Believe me Zarah, daga asibiti nake, kin san aikin likita bai da specific time na kan shi". Kuka na fara yi mai tsuma rai na ce "Dr you have change, na fara gajiya da sababbin halayen da kake zuwa min dasu". Hawayen da yake zuba a idanu na ya fara goge min yasa lallashi na. Sweet words d'in da Dr ke fad'a min ne yasa na hak'ura na da ina kukan da nake yi. Ko da na tashi zan zubo mishi abinci cewa yayi in bar shi ya k'oshi, hakan ya tabbatar min da ba daga asibiti yake ba. Hannu na ya kama muka tafi side d'in shi muka kwanta. Washegari da daddare ina kwance a jikin Dr muna hira wayar shi ta fara ruri alamar kira ya shigo. Wayar tafi kusa dani, hakan yasa na sa hannu na d'auki wayar dan na mik'a mishi. Sunan Meema na gani a jikin screen d'in yana yawo. Mik'a mishi wayar nayi ba tare da na ce mishi komai ba. Amsar wayar yayi yaga sunan Meema ya ajiye wayar ba tare da ya d'auka ba. Tambayar da tazo min shine "Me yasa Dr ya k'i d'aukan wayar a gaba na". Jiki na yana bani akwai wata a k'asa da Dr ba ya so in sani. Na gaji da wannan rainin hankalin da Meema take min na kiran Dr a ko wane lokaci ta gadama, kiran da take mishi ko su Hanan ba za mishi irin shi. "Dr me yasa kak'i d'auka" Na watso mishi tambaya. "Meema ce, ta cika matsawa mutum" Dr ya amsa min. In a serious speaking na ce "Dr hak'uri na ya k'are akan kiran da Meema take maka, ban ga dalilin da za tayi ta kiran ka ba day and night, in wani abu take so ta fad'a maka me yasa ba za ta bari ku had'u ba, ka dakatar da ita ko kuma ka bari in ka fita sai kuyi ta wayar Ku a waje, I can't tolerate it anymore". Kallo Dr ya bi ni dashi kana ya ce " Zan mata magana". "That will be better" na fad'a. Ina gama fad'ar haka na tashi na bar gurin. Yau muna zaune da daddare aka kira Dr a waya ana neman shi a asibiti, an kawo wani patient emergency, hakan yasa ya tashi ya tafi. Sai bayan tafiyar shi ne na ga wayar shi a inda ya tashi. Hasken da naga wayar shi nayi ne yasa na tashi na d'akko wayar. Sunan Meema na gani a jikin screen d'in. Wani dogon tsaki nayi kana na ajiye wayar. Ba a jima ba sai ga text ya shigo na Meema. Kamar ka bud'e text d'in amma zuciya ta sai ingiza ni take yi akan in bud'e in ga mai ta turo mishi. Shiga inbox din nayi na fara cin karo da messages din Meema take turo ma Dr. Yawanci love messages ne da na greetings take turo mishi. Shiga sent message nayi ban ga wasu reply da Dr yayi ma Meema ba, sai dan kadan na greetings da ya mata reply da ta turo mishi. Ba wanda ya fi daga min hankali a cikin messages din sai wanda Meema ta turo ma Dr tana pleading din shi akan ya su ma Dad magana a yi fixing din bikin su tun da ya amince zai aure ta. Hannu na ne ya kama rawa da wasu hawaye masu zafi da suka fara zubo min a dalilin message d'in da na ga Meema ta turo mishi. Tambayar da na fara yi ma kaina shine Yaushe Dr ya amince da maganar auren Meema ni ban sani ba? Me yasa a kullum na tuhume shi akan Meema yake nuna min cewa babu wata alaka ta soyayya a tsakanin su da ta wuce brother and sister? Kenan Meema na da tabbacin cewa Dr zai aure ta shi yasa take kara jaddada min cewa sai ta auri Dr nake daukan hakan a matsayin wasa. Kenan duk wannan fitar da Dr yake yi gurin Meema yake zuwa ni ina nan a zaune ban sani ba, shi yasa in zai fita yake cin kwalliya sannan in na tambayeshi yace min wata unguwa zai je da na rasa sanin wace unguwa ce wannan. "Ashe ni ce suka maida mara wayau da suka b'ullo min ta haka". Kuka na fara yi mai cin rai da kona zuciya akan auran da Dr yake shirin yi da Meema. "Why Dr?" na fada a fili kamar Dr yana gurin. "Me yasa Dr zai min irin wannan mummunar sakayyar duk kuwa da irin son da nake mishi?". "Ashe laifi ne dan ka nuna ma namiji so da zai yi amfani da wannan damar yana maka abin da yake so?". Kalamen su Anty Jiddarh da Anisa da Aisha ne suka fara min yawo a kaina akan cewa in rage makauniyar soyayyar da nake nuna ma Dr dan wataran da ita zai yi amfani yam n abin da zai dade yana min ciwo. A lokacin ban dauki maganar su da mahimmanci ba saboda ina ganin suna adawa da auren na daDr ne, sai gashi Dr ya min abubuwa da dama da suke sa ni a cikin damuwa. Ciki kuwa har da pills din da ya bani wanda nake da tabbacin a dalilin shi ne har yanzu ban samu ciki ba duk da nasan haihuwa lokaci ce, amma saboda son Dr ya rufe min ido yasa na yi saurin manta abin da ya min da yafe mishi saboda nasan yana da dalilin yin hakan a kaina, sai gashi yana shirin sa zuciya ta da buga a dalilin auren da yake niyyar yi da Meema. Ni kaina ban san wani irin kishi nake ma Dr ba saboda nasan duk son shin e ya jawo min haka, ba na jin zan iya jure wa in ga Dr da wata a matsayin kishiya ta, ba zan iya jurar sharing din Dr da wata ya mace ba, kishin ma wai a ce da Meema da muke takun saka da ita. A wannan karan ina jin zamu iya fito na fito Dr akan auren da yake shirin yi ba tare da sani na ba, ni ya dauki pills ya bani, ga family planning da yasa nayi, gashi har yanzu ban sami ciki ba, sannan yana kokarin shigo da wata, nasan duk yadda Dr yake da tsarin turawa wataran zai ajiye wannan raayin ya bukaci haihuwa, idan ni kuma har lokacin ban samu haihuwa ba na san zai bukaci haihuwa daga gurin Meema, a lokacin ni kuma zan zama y'ar kallo. Da kyar na iya samu na tashi daga gurin na koma cikin daki na. Washe gari ko da na hada breakfast da kyar na iya daurewa na kai ruwan shayi baki na saboda yadda na ji baki na yana min daci, bacin rai ne kawai a tattare dani da haushin Dr da nake ji. A gefe guda kuma tsanar Meema ce ta ke yawo a raina saboda yadda take so ta yi ma rayuwa ta karan tsaye ta hanyar auren Dr. Da yamma sai ga Dr ya dawo daga aiki da faraar shi ya tare ni. Daurewa nayi na ari murmushi na tarbe shi duk da yadda nake jin zuciya ta na min zafi. Ba na son in yi saurin yanke hukunci sai na samu hujjar da zan gabatar mishi da ita, nasan yanzu in na mishi maganar zai iya musa min akan cewa ni ce nake zargin haka. Haka na daure na mishi duk abin da ya kamata, amma shi kanshi ya fahimci akwai abin da yake damuna da har sai da ya tambaye ni. Nunar mishi nayi da ba abin da yake damu na, kawai dai ina ji na so weak ne. Ranar na taki sa'a Dr bai fita ba, sai da ya d'auki kusan two weeks bai fita da daddare ba. Wata Ranar Talata Dr ya dawo aiki da wuri, ranar na ji sun yi waya da Momi, ban san dai maganar da suke yi ba, na ji dai yana ce mata bai samun lokaci ne amma in ya samu lokaci zai je. Da daddare wani irin bak'in ciki ne ya kama ni da wani irin kishin Dr da hakan ya nuna a fuska ta, tuni fuskata ta canza zuwa b'acin rai. Yau na shirya ma tunkarar Dr mu yi wacce za muyi dashi, ba zan juri d'aukar rainin hankalin da yake min. Kusa dani ya zo ya zauna, in ban da k'amshi ba abin da ke tashi. Jin zuciya ta nake tana tafarfasa, yanzu duk wannan kwalliya da wannan k'amshin duk Meema yayi ms wa. "Zarah ba ri in je gidan su Mema mu gaisa da su Dad, kwana biyu ban samu time na je ba" cewar Dr. Lallai yau na tabbatar da Dr ya maida ni k'aramar Yarinya mara wayau wacce ba tasan me duniya ke ciki, amma zan nuna mishi na wuce a raina min hankali, nasan me Duniya ke ciki. Cikin d'aura fuska na ce " Za ka gaida su Dadi ko za ka ga Meema". Murmushi yayi kana ya ce "In ban da abin ki Zarah, tun da gidan su zani kin san dole mu had'u da Meema". Mik'e wa yayi had'e da fad'in " Sai na dawo, i will not take long time". Ya kusa kai wa bakin k'ofa nayi saurin mik'ewa na sha gaban shi, fuskar nan tawa ba fara'a a cikin ta. Mamaki ne ya kama Dr ganin yanda na zo na tsaya a gaban shi ya ce "ya aka yi ne Zarah, zan fita kin zo kin tare min hanya". " Dr ban yarda da fitar nan da za ka yi ba, saboda haka ka fasa fitar nan da za kayi" na fad'a cikin d'aure fuska. "What do you mean Zarah da za ki ce in fasa fita?" Dr ya tambaye ni. "Yanda ka ji na fad'a haka nake nufi Dr" na fad'a. "Saboda me ba zan fita ba?" Dr ya sake tambaya ta. Kai na tsaye na ce "Saboda na gaji da yawo da hankalin da kake min da kuma mayar dani yarinya da kake yi wacce ba tasan abin da duniyar ke ciki ba". Ran Dr ne ya fara b'aci da yanda na ke mishi magana, dan haka shima cikin fad'a ya ce " Look Zarah, i don't want any trouble, bani hanya in wuce". Ni ce na ce na ce "Dr I mean what i said, yau ina son gane matsayina a gurin ka". Dr ne ya ce " Zarah wai me ya faru ne kike irin wannan maganar, pls ki ajiye wannan maganar da kike yi, ki bari in na je na dawo sai ki fad'a min me yake faruwa". "Ka na d'auka maganar da nake yi da wasa nake yi, wlh Dr fitar ka gidan nan na nufin neman rashin zaman lafiya a gidan nan, ko kana sha ban san abin da yake faruwa tsakanin ka da Meema kamar yadda a kullum kake son b'oye min me ke tsakanin ku, a duk lokacin da na maka tambaya akan Meema amsa d'aya ka ke bani cewa ba soyayya a tsakanin ku, ka d'auke ta ne a matsayin k'anwa, duk abin da aka yi shi a rashin gaskiya duk daren dad'ewa sai ya bayyana, na gano cewa fitar daren da kake yi gurin Meema kake zuwa a matsayin unguwa da ka ce min kana zuwa, ni kuma ka bar ni in maka jiran gida, to Dr in ba son Meema ka ke yi ba amma ai kana shirin auren ta ko?" Na k'arasa maganar da tambayar Dr. Mamaki ne ya kama Dr da har hakan ya nuna a fuskar shi. Bi na kawai yake da kallo saboda mamakin jin maganganun da na fad'a mishi. Jin bai bani amsa ta Ba yasa nayi murmushin takaici na ce "Me yasa kayi shiru Dr? kasan duk abin da na fad'a gaskiya ne, shi yasa ka kasa bud'e bakinka ka kare kan ka, Dr zan iya maka uzuri ko yafiya a duk abin da za ka min amma ba zan maka wannan alfarmar ba gurin yi min kishiya ba, kishiyar ma Meema wacce kasan ba ma shiri da ita". Nasan yau Dr yayi mamakin maganganun da na fad'a mishi, saboda a ko yaushe yana ganin zan iya hak'uri a duk abin da ya min. Cikin lallashi Dr ya ce " Zarah dole ki d'auki k'addara a yanda tazo domin auren Meema zan yi, abin da yasa ban fad'a mi ki ba saboda ba na so in d'aga miki hankali, amma tun da kin gano auren ta zan yi kin ga no need in k'ara b'oye mi ki". Meema nasan kina so na, dole ne kuma ki yi kishi na, wannan auren zan yi shi ne dan tausayin Meema da kuma umarnin da Momi ta bani akan in auri Meema, pls Zarah am sorry". Duk wannan maganganun da Dr yake yi kamar yana sa mashi yana caccaka min a cikin zuciya ta haka nake ji, wani irin b'acin rai na ke ji yana ziyarta ta a lokacin, wai ni Dr zai kalli ido na ya ce min zai auri Meema ne dan tausaya mata da yake yi da kuma umarni da Momin shi ta bashi akan ya auri Meema. Wasu hawaye ne suka fara zubo min ba tsayawa. Baki na ne ya kama rawa saboda kukan da yake son tawo min. Kallon takaici nayi ma Dr kana na ce "Me...kake...nufi...da...wannan maganar...da...ka...fad'a...min..cewa...za...ka...auri Meema...saboda...tausayin...ta...da...umarnin...Mom...". " Wannan Dalilin da na fad'a miki haka yake Zarah, apart from that ban da wani dalili da zai sa in auri Meema" Cewar Dr. "Kenan yanzu Dr auran Meema za kayi kenan..." Na k'arasa maganar da fashewa da kuka. "Ya zaman min dole in aure ta Zarah saboda umarni Mom ta bani" Dr ya fad'a. "Dr dama can kayi niyar auren ta, da kake cewa saboda Mom za ka aure ta, idan ba ka yi niyya ba Momi za ta maka dole ne" na fad'a cikin shashshek'ar kuka. Dr ne ya ce "Zarah ba zan iya musa wa Mom duk abin da ta buk'ace ni da nayi ba, shi yasa zan auri Meema". Dr ba ka isa ka auri Meemba, in kuma ka ce sai ka aure ta sai dai ka zab'a ko ni ko Meema". Tak'aitaccen murmushi Dr yayi ya ce " Zarah ke zab'i na ce, Meema kuma zabdamuwam ce, kin ga kenan dukkan ku zan zab'a". Dr daman akwai ranar da za ta zo ka min irin wannan sakayyar, duk irin soyayyar da na nuna maka da halaccin da na maka amma sakayyar da za ka min kenan, a dalilin kishin ka da son da na ke maka yasa zan Shiga wani hali idan ka auri Meema amma shine Dr kake fad'a min dukkan mu za ka za'ba, Dr kana kallon yadda tun kafin auren ka na samu matsala da iyaye na da y'an uwa na akan auran ka da nake son yi duk da d'an uwa na da yake matuk'ar so na amma na zab'e ka na k'i auren shi, a dalilin auren ka na shiga damuwa duk na jure saboda ina tunanin in na aure ka za ka maye min gurbi da farin cikin da na rasa a lokacin za ka kuma rik'e ni amana da yarda, ashe ni ce nake nawa wautar ban sani ba, sai gashi ka nuna min duk ba zan sami hakan a wajen ka ba" na k'arasa maganar da k'ara sautin kuka na. Zarah ba zan biye miki ba saboda ina son ki sai in k'i yi ma Momi biyayya?, da kike cewa kin zab'e ni akan d'an uwan ki ina ce saboda son da kike min ne, Zarah ni ban ce kar ki yi ma iyayen ki biyayya a kaina ba, nasan dai na ce ki nemar mana mafita akan yadda za mu mallaki junan mu, nasan tabbas Zarah kin nuna min so da ba kowace mace ba ce za ta iya nuna min ba tun da har kika zab'i farin ciki na akan ki bi umarnin iyayen ki, tabbas duk wacce tayi haka ta zama jaruma a soyayya, shi yasa nima ba zan yi irin kuskuren ki ba Zarah, dan haka ne ma yasa zan ma Momi biyayya in auri Meema domin yi wa iyaye biyayya nasa mutum ya samu farin ciki a rayuwar sa da ci gaban sa". Ji nayi kukan da na ke yi ya tsaya cak sakamakon maganganun da Dr ya fad'a min. jijiyoyin jiki na ke na ji sun daina aiki, jiki na yayi wani irin sanyi wanda ba na jin zan iya wani k'wak'k'waran motsi a gurin, ko idona na kasa motsa shi. Wani abu ne na ji ya tokare min makoshi. Yau ni Dr yake wa jirwaye mai kamar wanka akan k'in bin umarnin su Abbu da ban da ban yi ba duk da a dalilin shi yasa na k'i auran Yaya Faruk d'in da kuma shawarar shi da na bi dan in ga na mallake shi a matsayin miji, sai gashi wai yau ni Dr yake goranta mawa akan ban yi ma su Abbu biyayya ba, ban tab'a zaton Dr zai min wannan maganar ba, sai gashi yau a dalilin auren Meema Dr ya goranta min, ta yaya zanyi farin ciki da wannan auren da zai yi? Ko ina a jiki na rawa yake yi, durk'ushewa nayi a gurin na fashe da wani matsanancin kuka. Cikin kuka na ce "Dr na gode da tunasar dani abin da na manta a baya, wannan maganar da ka min ta sa na d'auki wani darasi na rayuwa, hakan da ka fad'a min yasa na gane kuskuren da nayi a baya, nasan ba komai ya ja min haka ba illah Makauniyar Soyayya da na nuna maka wanda daman irin ta take jawo wa mutum danasani, yau ni Dr kake goranta ma wa akan son da na nuna maka, na gode Dr..." Na k'arasa maganar cikin shak'ewar murya sakamakon kukan da ya tokare min a mak'oshi". Da k'yar na iya tashi na ja k'afa ta saboda nauyin da k'afa ta tayi min. Ina shiga d'aki na zauna a k'asan rug na saki wani kuka mai ban tausayi. Jin kaina nake yi kamar zai tsage saboda ciwon da yake min. Ban San tsawon lokacin da na d'auka ba a zaune ina kuka. Maganganun da Dr ya fad'a min su suke min yawo a k'wak'walwata. Sai a yanzu na gano kuskuren da nayi a baya wanda a da ban tab'a hango zai zaman min k'alubale ba, sai a yanzu na gano kuskuren da na tafka a baya da ban bi abin da su Ummu da Abbu da sauran mutane suke hango min ba. "Me ya hana ni yi musu biyayya in auri yaya Faruk ko sa da k'in shi zai iya ajalina?". "Me yasa ban faranta musu ransu ba a lokacin da suka buk'aci in musu abin da suke so duk da nasan ba za su tab'a zab'a min abin da zai cutar dani". "Me yasa duk son da iyaye na suka nuna min nima ban yi k'ok'ari na faranta musu da abin da suke so ba?". Duk wannan tambayoyin da nayi ma kaina nasan ba ni da buk'atar amsan su dan nayi wannan tunanin ne a lokacin da yake neman k'ure min. Nasan duk wannan misunderstanding din da muke samu da Dr har da rashin d'aukar magar su Abbu ya jawo min da hakk'in Yaya Faruk da ya nuna min soyayya ta gaskiya amma na k'i auren shi. Gashi yanzu ina fuskantar k'alubale a zamantakewar mu da Dr, ya kuma zaman min dole in yi hak'uri da duk abin da zai min ko zai fad'a min tun da ni na ce na ji na gani. Wannan abin da Dr ya min ya dasa jin haushin shi, na kuma sa ma raina a shirye nake da fuskantar duk wani hukunci sa da zai yanke min in dai akan maganar auren Meema ne, ba zan bari ya auri Meema ba, in kuwa har ya ce sai ya aure ta to hakan na nufin zaman lafiya a tsakanin mu ya k'are. Dole gobe Dr ya tsaya mu tsayar da mafita a tsakanin mu. Ranar nayi kukan da na dad'e ban yi irin shi ba. Ko sa da na kwanta ban yi baccin dad'i ba. Washegari da ciwon kai na tashi, gashi ba ni da magani a side d'ina, first aid box yana side d'in Dr. A yadda nake jin zuciya ta game da Dr ba na jin zan iya zuwa side d'in shi in d'auki magani in sha. Haka na ci gaba da kwanciya duk da ba bacci nake yi ba. Sai da na d'auki lokaci a kwance kana na tashi naje na dama kunun gyad'a na sha. Wanka na shiga nayi na nemi simple dress na sa, ko mai ban tsaya shafawa ba na koma na kwanta. Sallah kawai nake tashi na ke yi kana in koma in kwanta. Sai wajen yamma na ji kaina ya min sauk'i, tashi na yi na gyara gidan sannan na je na d'aura simple food. Ko da na gama girkin na ci, d'aki na koma na ci gaba tunani. Gaba d'aya na rasa abin da yake min dad'i a raina. Har zuwa dare ban k'ara fita falo ba. Dr ne yayi sallama ya shigo d'akin. Tun da ya shigo na zuba mishi ido ina kallon shi, ji nake yi kamar a yanzu ne yake fad'a min zafafan kalamen da ya fad'a min a jiya. Wasu hawaye ne naji suna k'ok'arin zubo min, saurin maida su nayi. Kusa dani ya zo ya zauna yana kallo na. Kau da kaina nayi na juya wani b'angaren saboda yadda naji raina na k'ara min zafi. Shiru ne ya ratsa d'akin kafin Dr yayi k'ok'arin kau da shirun da cewa "Zarah am sorry". Murmushin yak'e nayi na ce " Sorry for what Dr". Cikin sanyin murya Dr ya ce "Zarah I know i have hurt you, is a mistake". " Dr ni ba ka min komai ba, abin da ka fad'a min kamata yayi in gode maka saboda ka tunasar dani abin da na manta ne, saboda haka kar ka da mu" na fad'a. Duk yadda Dr yaso in tsaya mu fahimci juna ban saurare shi ba, haka ya gaji da zama ya tashi ya tafi side d'in shi. Tun daga wannan ranar muka fara samin sab'ani da Dr. Sai da muka kai kwana goma a haka kullum sab'anin mu gaba yake yi, duk yadda na nuna b'acin raina akan Dr ya janye maganar auran Meema amma Dr ban ga alamar janyewar shi ba, hakan yasa zaman mu yak'i dad'i. Duk na bi na canza kamar ba ni ba, ga rama da nayi a y'an kwanakin saboda rashin kwanciyar hankali. Yau ranar ta kasance ranar weekend, Dr na gida bai je aiki ba, a yau na shirya ma fuskantar Dr dan nima na gaji da irin zaman da muke yi. A side d'in shi na same shi yana danna waya. Can nesa dashi na zauna ina fuskantar shi. "Dr ina so in yi magana da kai ne" na fad'a kai tsaye. "Ina jin ki" ya ba ni amsa a tak'aice. Ni ce na ce "Ina so ka fad'a min me ka yayanke akan maganar da muka yi da kai akan Meema". Tsayar da danna wayar yayi kana ya d'ago ya kalle ni. "Amsar ba ta canza ba Zarah, zan auri Meema" cewar Dr. Cikin b'acin rai na ce "Dr wai dole ne sai ka auri Meema? to sai dai ka zab'i zama da Meema ko ni dan ni ba zan tab'a zama da ita ba, ba ma Meema ba, ba na jin zan yarda ka auri wata ka kawo min ita a matsayin kishiya bayan ni ka gama cuta ta, tun da ka bani pills d'in abortion da family planning da kasa nayi, gashi nan har yanzu ban sake samun ciki ba, ka na sha ban da hankali ne zan k'yale ka kayi aure alhalin ni ka nakasta min rayuwa dan a yanzu ban da tabbacin zan haihu ko ba zan haihu ba, nufin ka kayi aure nan gaba ka bukaci haihuwa amaryar ka ta haifa maka yara ni ina nan a zaune, impossible! dole mu ci gaba da zama ni da kai a haka, maganar wai za kayi wa Momi biyayya ka ajiye ta a gefe dan nima kai ka ja min na k'i yi wa iyaye na abin da suke so akan in auri Yaya Faruk na k'i bin maganar su, saboda son da nake maka yasa nayi haka". Shi ma cikin fad'a Dr ya ce " Zarah ni kike fad'a ma wannan maganar". A lokacin ina jin zan iya fad'a ma Dr duk maganar da ta fito daga baki na saboda yadda nake cikin b'acin rai. Ba tare da tsoro ko shakka ba na ce "Kai na ke fad'a ma wa Dr, a abin da na fad'a maka ka fad'a min wanda ba gaskiya ba". Wani banzan Kallo Dr ya jefo min kana ya ce " Tun da kin ce ni na jawo kika k'i yi ma iyayen ki biyayya ko in kawo miki hanya mafi sauk'i ne da za ki je ki auri d'an uwanki dan ki yi musu biyayya". Kai tsaye na ce "Za ka iya yin hakan Dr dan nima a yanzu zan so in share ma iyaye na hawayen da ban share musu a baya ba, nima zan so in gyara kuskuren da nayi a baya dan sa iyaye na farin ciki da ban sa su a baya ba da kuma guje ma gorin da ka min". Wani murmushi ya yi iya leb'e da na rasa ma'anar murmushi sannan ya ce " Zarah kar ki yi saurin cewa haka, nasan duk hukuncin da zan yanke ke za ki fi shiga wani hali dan son da kike min ba na wasa ba ne, kar ki zo daga baya kina danasani akan haka ". Murmushi mai cin rai nayi kana na ce " Dr duk hukuncin da za ka yanke min zan jura tun da dai nasan ba zan rasa raina ba" na fad'a. "Haka ki ka fad'a ko?" Dr ya watso min tambaya. Ba tare da nazari ko tunanin wani hukunci Dr zai yanke min ba na ce "of course haka na ce". "Ki je Zarah na sake ki saki d'aya..." Dr ya fad'a. Wani irin fad'uwar gaba ne na ji ya ziyarce ni a lokacin, k'irji na ne ke faman harba wa kamar zai fito, tun da Dr ya fad'a min kalmar saki na rasa a wace duniyar yake, ban tab'a tunanin wannan hukuncin Dr zai yanke min ba, a yanzu ina ganin lokaci yayi da zan hak'ura da Dr ko da shine autan maza, a yanzu na sa ma kaina juriya da hak'uri da Dr tun da zaman mu ya k'are dashi, yanzu babu wani sauran wata alak'a a tsakanin mu. Da k'yar na had'o kalmomi na fad'a ma Dr saboda juwar da ke naman d'auka ta. "Na gode da hallacin ka Dr, sakamakon *Makauniyar soyayyar* da na nuna maka ne ya jawo min haka da rashin d'aukar magana iyaye na ya jawo min, nasan na cancanci fiye da haka, mutane sun sha fad'a min illar makauniyar soyayyar da nake maka amma ban ji shawarar du ba saboda a lokacin ido na ya rufe da soyayyar ka sai a yanzu na gano illar son da na nuna maka dan shi ya sa ni a halin da nake ciki a yau, a yau na d'auki babban darasi a gurin ka na rayuwa, kuskuren da na aikata ba zan sake maimaita irin shi ba, sai dai kafin in tafi zan fad'a maka wata magana, duk wanda ya zalunci wani a zamantakewar mu Allah ya saka mishi". Ina gama fad'ar haka naje na fara had'a kaya na a trolik, sai a lokacin kuka yazo min mai k'arfi. dressing Mirrow na zauna na ci kuka na ba mai rarrashi na. Da k'yar na samu nayi controlling d'in kuka na ya tsaya saboda ba na fatan ci gaba da zama a gidan Dr, yanzu ganin gidan nake yi yamin bak'i, ji nake kamar a kan k'aya nake. Jiki a sanyaye na tashi na d'auki hijab na saka kana na jawo trolik d'in na fito. Ina fitowa wasu hawaye suka zubo min, saurin goge hawaye na nayi na nufi hanyar fita. Sai a lokacin na lura da Dr da yake zaune a falon. Saurin fita nayi daga falon na fita daga gidan. Ko motar da Dr ya siya min ban tsaya d'auka ba dan ba ta da amfani a gurin na. Kasancewar unguwar ta masu kud'i ce yasa ba wasu mutane a layin sai d'aid'aiku dake wuce a motar su, ga kuma yamma da tayi. K'arasowa bakin titi nayi na tsaya ko zan yi sa'a na samu abin hawa. Sai a lokacin sharad'in Abbu ya fad'a min a rai akan duk matsalar da za ta fad'a ni da Dr kar in tunkaro shi da maganar. Yanzu ina zani? Na tambayi kaina. Sai a yanzu na k'ara jin danasani ya k'ara shiga ta. "Wayyo Allah! Na ga ta kaina". Na d'an jima a tsaye kafin wata bak'ar mota ta tsaya a gaba na. Bud'e motar a kayi kana ya sakko da k'afafuwan shi waje sannan ya fito daga motar. Wanda na gani ya fito a motar ne yasa na ji kamar in ruga da gudu. _To ni kaina 'yar mutan paki zan so sanin waye a cikin motar dan ban da wannan amsar_. *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa writers Association _Masu kira na a waya ina Godiva, ba ni da abin ce muku sai dai fatan alkhairi, Sumayya Bala kema ina Godiva da yabawar ki gare ni_. _Wannan shafin na Baku shi kyauta ku yi yadda kuke so dashi_. 91-92 Yaya Faruk ne cikin wani tsadadden sky blue d’in yadi, daga ganin yadin kasan mai tsada ne. Gani nayi ya k’ara haske da k’iba, kana kallon shi kasan yana cikin kwanciyar hankali. Rabo na da ganin shi tun ran bud’ar kan su Anisa da muka had’u dashi a gidan mu, tun daga wannan had’uwar ba mu sake had’uwa dashi ba, sai yau da muka sake had’uwa dashi. Jikin motar shi ya jingina ya hard’e hannun shi. Ji nake yi kamar k’asa ta tsage in shige dan ban san me zan ce ma yaya Faruk idan ya tambaye ni inda zani da akwati. A takure nake da tsayuwar yaya Faruk a gurin. Nasan in ba ni na mishi magana ba bazai min ba dan haka na ce "Ina wuni yaya Faruk". "Lafiya" ya amsa min a tak’aice. Shiru yaya Faruk yayi kamar ba zai k’ara min magana ba kana ya ce min "Fatima ina zaki da yamman nan da akwati a hannun ki, na zo wucewa ce na ganki a tsaye, daga gidan Aminu nake". Sunkuyar da kaina nayi na rasa amsar da zan bashi dan gani nake yi ban da amsar tambayar da ya min. "Yanzu ina zan ce ma yaya Faruk zani bayan ni kaina ban san in da zani ba?" na tambayi kaina. "Ok tun da na ga alamar ba ki shirya tafiya ba ni bari in k’arasa gida, daman zan ce ki zo in rage miki hanya ne dan na ga yamma tayi, ki gaishe da mijin ki" cewar yaya Faruk. Yana gama fad’ar haka ya bud’e k’ofar motar ya shiga da niyar tafiya. Sanin zai iya tafiya gashi yamma tayi yasa na k’arasa bakin k’ofar motar na tsaya. Kamar bai san da tsayuwa ta a gurin ba ya sa ma motar key, hakan ya tabbatar min da bazai min magana ba. A hankali na kira sunan shi "Yaya Faruk". D’agowa yayi ya kalle ni jin na ambaci sunan shi amma bai min magana ba. "Kayi hak’uri in ka tafi ka bar ni a nan zan sha wuya kafin in sami abin hawa" na fad’a. Tab’e baki yaya Faruk yayi ya ce "wannan matsalar ki ce, da nace ki zo mu tafi ba tsayawa kika yi kina b’ata min lokaci ba, in na tafi kya samu abin hawa, in kuma za ki tafi d’in ne ki zo in sauke ki". Da sauri na d’auki trolik d’ina na zagaya na ajiye trolik d’in a bayan seat kana na zauna a kujera mai zaman banza ya ja motar muka tafi. Tun da muka fara tafiya ba wanda yayi magana a tsakanin mu. Can yaya Faruk ya kau da shirun da cewa "Ina zan sauke ki? Tunanin ina zan ce ya sauke ni na fara yi dan ni kaina nasan ko hauka nayi na tashi ba zan ce ya kaini gidan mu ba, to ko gidan yaya Aminu zan ce ya kai ni? shi ma ba mafita ba ne dan nasan yaya Aminu ba zai min da dad’i ba kuma mun riga mun bar hanyar gidan yaya Aminu d’in, in kuma na ce ya kai ni gidan yaya Khalil da wani ido zan kalli Anisa har na iya zama a gidan bayan na guji d’an uwanta a baya, haka in na ce zan je gidan Dadin su yaya Faruk lallai na cika mara kunya, idan kuma na ce za ni Wagini dare ya fara yi sannan sai na gwammaci ban je ba dan ni kaina nasan abin da Hajiyan Wagini za ta min ba zai min dad’i ba dan sai na gwammace ban je ba. "To yanzu ina zani?" Hawaye ne ya cika min idanu na saboda rasa mafita da nayi. Cikin fad’a yaya Faruk ya ce "Ke Fatima dan iskanci ina miki magana kina jina, in ba za ki fad’a min in da zan kai ki ba sai ki sauka dan ni ina da abin yi". "yaya Faruk ban san in da za ni ba" na fad’a murya ta na rawa. Saurin juyowa yayi ya kalle ni kana ya ce "kamar ya ba ki san in da za ki ba ki kasa na d’auke ki muna ta tafiya a mota, bari in kai ki gidan Abbu in kika tuno in da zaki sai ki tafi". Hanyar gidan su Abbu ya nufa, ganin hakan da nayi yasa na fara mishi kuka a mota ina rok’on shi kar ya kai ni gidan. Guri ya nema yayi parking kana ya kalle ni cikin d’aurewar fuska ya ce "look Fatima, ba zan d’auki iskancin da kike min ba, akan me za ki kama min kuka kina cewa kar in kai ki gidan su Abbu, to in ban kai ki nan ba ina zan kai ki, infact ni ban san inda zan kai ki ba, in kuma gidan ki za ki koma to muje in mayar da ke in yaso gobe sai ki je inda zaki, wai ina ma zaki at this time da akwati". Cikin kuka na ce "Dan Allah yaya Faruk kar ka kai ni gidan Abbu, ban san hukuncin da zai min ba in na fad’a mishi dalilin zuwa na". Duk da yanzu ba ya son wata alak’a ta k’ara had’a shi da ni in ban da gaisuwa amma ganin yadda na ke kuka yasan akwai abin da ya faru na ke so ya taimaka min kuma ko ba komai matsayin k’anwar shi na ke, shi babba ne bai kamata yace zai bi shawarar da zuciyar shi ke yanke mishi a kaina ba akan ya sauke ni duk ma matsalar da nake ciki ni ta shafa. Yaya Faruk ne ya ce "Yanzu ni me kike so in miki Fatima, sauri nake yi Khadijah na jira na a gida". Cikin shashshek’ar kuka na ce "Dan girman Allah yaya Faruk kar ka duba baya ka tausaya min, ko ma ina ne ka kai ni na yarda amma ban da gidan su Abbu. Ranshi ne ya k’ara ‘baci dan har yanzu bai gano abin da yake damu na ba, gashi na k’i fito wa in fad’a mishi abin da yake damu na. Cikin tsawa yaya Faruk ya ce "get out of my car, ko ma ina zaki ki je ba matsala ta ba ce". K’ara sautin kuka na nayi dan nasan in dai na fita daga motar nan ban da wata sauran dubara da ta rage min. "Yaya Faruk kai d’an uwa na ne, in ka tafi ka bar ni ban san in da zani ba, matsala muka samu da Dr yace in tafi gida, nasan zuwa na gida daidai yake da d’aukar ko wane mataki a gurin Abbu da Ummu tun da ni na yarda da sharad’in da ya fad’a min akan in na samu matsala da Dr ba ruwan shi na yarda, kai kan ka yaya Faruk shaida ne". Ci gaba nayi da kuka nayi na ce "Yaya Faruk nasan in za ka duba abin da na maka a baya ba za ka ta’ba taimaka min ba dan ni kaina nasan ban cancanci taimako daga gare ka ba, sai dai ina so ka min taimaka min saboda Allah da kuma matsayina na y’aruwar ka". Kallo na yayi ya kau da kanshi kana yayi shiru kamar mai nazari. Jiki na ne yayi sanyi da shirun da yaya Faruk yayi dan a tunani na ba zai taimaka min ba. "Za ki iya zama a gida na?" yaya Faruk ya katse min tunanin da nake yi. Cikin rawar murya na ce "Zan iya…yaya Faruk… indai har…zaka iya zama… dani". Bai k’ara ce min komai ba ya ja motar muka tafi. A wani had’ad’d’en gida na ga ya yi parking, horn yayi mai gadi ya bud’e mishi gate d’in ya shiga da motar shi. A parking space yayi parking kana ya fito daga motar. "Ki biyo ni" yaya Faruk ya fad’a yana ci gaba da tafiya. Jiki a sanyaye na fito na bud’e baya na d’auki trolik d’ina na bi shi a baya. Kusan a tare muka shiga cikin falo d’in saboda ya tsaya ya jira ni na k’araso. San da muka shiga ba kowa a falon. Sallamar da yaya Faruk yayi ne yasa Khadijah ta fito da sauri. Gurin yaya Faruk ya ta nufa da niyar hugging d’in shi, gani na da tayi ne yasa ta fasa tare da sakar min murmushi. Murmushi yaya Faruk fahimtar yayi abin da ya hana ta hugging d’in shi. Takowa yayi ya k’arasa gurin da take yayi hugging d’in ta ya rik’o mata hannu. "Sannu da zuwa yaya Faruk" Khadijah ta fad’a. "Yawwa my Khadijah, na bar ki ke kad’ai ko? ya fad’a yana sakar mata tattausan murmushi. Juyo da kallon ta tayi gare ni ta ce "Sannu da zuwa, k’araso ciki". Bin ta nayi na nemi d’aya daga cikin kujerun dake girke a falon na zauna. Kallon yaya Faruk tayi ta ce "yaya Faruk bak’uwa muka yi ne". Yaya Faruk ne ya ce "Fatima ce k’anwar Aminu da Khalil". Jin suna na da yaya Faruk ya ambata yasa Khadija tayi saurin juyo da kallon ta gare, sai a lokacin ta gane ni saboda sau d’aya muka had’u da ita lokacin da Anisa ta haihu. Ni kaina sai a ranar na k’ara ganin Khadijan yaya Faruk, ba laifi kyakkyawa ce, a kallon da na mata za mu iya zama mate da ita ko ta girme ni kad'an. "Khadijah ga Fatima nan za ta d’an zauna damu na somedays a nan gidan, ki kai ta d’aki ta huta". Jiki a sanyaye ta amsa mishi da "Toh". Tashi na yi ta kai ni wani d’aki da aka zuba kayan alatu a ciki, mutum in ba ya sani ba zai iya cewa na matar gidan ne saboda had’uwar shi. Band’aki ta nuna min in zan shiga in yi wanka. Khadijah tun da ta koma d’aki take tunanin zuwa na gidan nan, hankalin ta ba a kwance yake ba kawo ni da yaya Faruk yayi, a sanin ta ni matar aure ce amma mai zai sa in biyo yaya Faruk in zauna a gidan shi. Ko dai matsala na samu da miji na? tambayar da Khadijah tayi ma Kanta amma ba ta gasgata hakan a ranta ba. Shigowat yaya Faruk ne ya katse mata tunanin da take yi. Kusa da ita yazo ya zauna yana sakar mata lallausan murmushi. Ita ma mayar mishi da murmushin da yake mata tayi. Yanayin ta da ya gani yasan kamar akwai abin da yake damun ta, tun san da ya ya kawo ni gidan ya mata bayanin wacece ni ya lura yanayin ta ya canza amma yasan baza ta iya mishi magana akan me yasa ya kawo ni ba. Yaya Faruk ne ya ce "Khadijah ki yi hak’uri na kawo Fatima ba da izinin ki ba, matsala suka samu da mijin ta, in komai ya daidaita za ta koma gidan ta, akwai y’ar matsala ne shi yasa ban kai ta gidan Abbu da Dadi ba". Tak’aitaccen murmushi tayi kana ta ce "Ba komai yaya Faruk, Allah ya daidaita tsakanin su". "Amin my Khadija" yaya Faruk ya fad’a. Yaya Faruk ne ya canza hirar da cewa "Ya jikin naki, ina fatan ba abin da yake damun ki?". Nana ce ta ce "Jiki Alhamdulillah". "Akwai abin da kike so in siyo miki ne ko za ki ya cin abincin" yaya Faruk ya tambaye ta. "Momi ta aiko min da tuwan shinkafa miyar agushi kuma na ci sosai, abincin ya min dad’i" cewar Nana. Cikin tsokana ya ce "Ka ga y’ar gatan Momi". Tashi yaya Faruk yayi yace "Bari in je in watsa ruwa kafin a kira sallah". Ni kuwa tun da na shiga band’aki nayi wanka na d’auro alwala ta kasancewar na ga lokacin sallah yayi. Kaya na canza na ji kiran sallah, hakan yasan na shimfid’a sallaya na ta da sallah. Ko da na idar da sallah ban tashi daga sallayar ba. Ina zaune na ji kiran sallar isha’i na mik’e nayi sallar. Bayan na idar ne na tsaya yin lazimi kafin na mik’e na ajiye sallayar. Kan gado na koma na zauna na rafka tagumi, sakin da Dr ya min ne ya dawo min sabo. Kuka kawai na fara yi saboda sai a yanzu na fara jin zafin sakin da ya Dr ya min. Wai ni Dr ya saka? Duk irin fad’i tashi da nayi akan son shi amma bai saka min da komai ba sai kalma mafi muni wato saki. A yanzu mafitar da zan nemar wa kaina shine in cire Dr a raina, tun san da naji zai auri Meema da abubuwan da suka faru naji a yanzu zan iya sa ma kaina hak’uri in yi rayuwa ta ba tare dashi bad an soyayyar shi ba ta amfane ni da komai ba b’ace danasani da b’acin rai. Kaina na kifa akan cinya ta, kuka nake yi ba ji ba gani, duk wanda ya ganni a lokacin sai ya tausaya min. Sallamar da yaya Faruk yayi ne yasa nayi saurin shanye kukan da nake yi. D’ago kaina nayi muka had’a ido dashi. Yana jingine a bakin k’ofa ya hard’e hannun shi. Yaya Faruk ne ya ce "Ki fito falo mu ci abinci". Yana gama fad’ar haka ya fita daga d’akin ba tare da ya k’ara ce min komai ba. Jiki a sanyaye na tashi na shiga band’aki na wanko fuska ta kana na nufo falon. A kan dinning na same su suna zaune suna cin abinci. K’arasawa nayi na nemi guri na zauna. Nana ce tayi serving d’ina kana ta kalle ni da murmushi a fuskarta ta ce "Fatima ga abincin ki ci". Murmushi nayi kana na ce "Na gode". Kad’an na ci abincin na fara wasa da cokalin dake hannu na. Shi kuwa yaya Faruk kamar bai san da zama na a gurin ba. Sai ma feeding d’in Khadijah da yake yi ko kunya ta ba ya ji, hakan yasa duk naji zaman na takura. Mik’ewa nayi da niyyar barin gurin. Nana ce ta kalle ni cikin kulawa ta ce "Fatima ba dai har kin k’oshi ba, na ga ba ki wani ci abincin ba". "Na k’oshi ne" na fad’a. Kallon yaya Faruk tayi ta ce "Yaya Faruk ka mata magana ta zauna ta k’ara abincin". "Tun da ta ce ta k’oshi ki k’yale ta mana, tasan yanayin cikin ta" ya fad’a cikin halin ko in kula. Girgiza kai kawai Nana tayi ba ta k’ara cewa komai ba. Falo na koma na zauna ina jiyo maganar su k’asa-k’asa. A zahiri in ka ganni a lokacin za ka ce Tv nake kallo saboda yadda na k’ura ma tv ido amma hankali nag aba d’aya ba akan Tv yake bad an in ka tambaye ni me ake yi a Tv ba ni da amsar da zan bayar. Bayan sun gama cin abincin ne Nana ta tafi kichen kai plates d’in da aka yi amfani dashi ta wanke. Yaya Faruk ne yazo ya zauna can nesa dani yana pressing d’in wayar shi. Ko da Nana tazo falon kusa dani tazo ta zauna tana d’an ja na da hira duk da dukkan mu ba wai mun saba da juna ba ne. Duk wannan zaman da muka yi a falo yaya Faruk bai sa mana baki a maganar da muke yi ba. Na da’n jima a falon kafin na tashi na musu sallama na tafi d’akin da aka bani. Kwantawa nayi na rungume filo yayin da hawaye ke zubowa daga idanu na. Yau ni ce zan kwana a wani gurin ba tare da Dr ba saboda rabuwar da ta shiga tsakanin mu. Da k’yar na samu bacci ya d’auke ni mara dad’i mai cike da tunani da damuwa. Da asuba Nana ce tazo ta tashe ni nayi sallah. Bayan na idar ne na zauna na yi muraja’ar Alkur’an da na gani a gefen mirrow d’in dakin. Sai da gari yayi haske na fito falo inda na tarar da Nana tana jera kayan breakfast a dinning table. K’arasawa nayi muka gaisa da ita cikin fara’a kana na tambaye ta me zan taimaka mata. Cewa tayi in bar shi ta kusa k’arasawa ba sai na wahalar da kaina ba, da k’yar na samu ta yarsa na gyara falon da kitchen. Yau ma da aka zo yin breakfast haka Yaya Faruk ya dinga tarairayar Nana yana ba ta abinci a baki, motsi kad’an in tayi zai tambaye ta abin da yake damun ta. Nasan in na tashi na koma falo Nana ba za taji dad’i ba dan jiya ma ta nuna min rashin jin dad’in ta dana tashi ana cin abinci. Tun da muka had’a ido da Yaya Faruk nag a ya d’aure fuskar shi kamar ba shi ba ne yake sakar ma Nana murmushi yasa na sha jinin jiki na. Hakan yasa na yi saurin gama breakfast d’in dan in bar gurin. Ko da suka gama breakfast d’in Nana ce ta kwashe kayan ta nufi kitchen, hakan yasa na tashi da sauri na nufi kitchen d’in dan in taimaka mata. Tare muka yi wanke-wanken da ita duk da ba wani hira muke yi ba saboda rashin sabo amma yanda take sakar min fuska yasa naji ta kwanta min a rai dan na lura ba ruwan ta. Muna gama wa muka fito falon a tare. D’akin da na sauka na wuce yayin da ita kuma Nana ta wuce side d’in ta. Da rana ma tare muka yi girki da ita muka ci kasancewar yaya Faruk ya je gidan Momi. Da daddare ban yi gangancin zuwa dinning area ba dan nasan yaya Faruk ba kunya ta yake yi ba. Nana ce ta min magana akan in zo mu ci abinci na ce mata ba yanzun ba, sai zuwa anjima. Sai da naji falon yayi shiru sannan na fito falon na je na ci abincin. Washegari da daddare ina zaune a falo ni da Nana muna ta’ba hira. Yaya Faruk ne yazo ya zauna kusa da Khadijah. Cikin kulawa ya ce "Khadijah ba ki ci abinci ba, haka da rana kika ce min ba kya jin cin komai, yanzu fad'a min mai za ki ci kin ji" ya k'arasa maganar cikin lallashi. Cikin shagwab'a Nana ta ce "Yaya Faruk ba na jin cin komai ne, duk abin da naci sai in ji kamar zan yi amai". Sorry Khadijah daurewa za ki yi, wannan babyn na wahalar dake, in kika haife shi sai na bashi punishment tun da baya barin Momin shi taci abinci" ya k'arasa maganar da tsokana. "To ka bari zuwa gobe sai ka je gun Momi ka anso min d'an wake a gurin ta" cewar Nana. "Momi ma in taji ba ki ci abinci ba ni za ta yi wa fad'a dan tace masu ciki ba a so suna zama da yunwa, yanzu ki daure ki ci abincin, gobe sai in je gurin Momi d'in ta mi ki d'an waken". " To amma Yaya Faruk kad'an zan ci ko?" Nana ta fada. Murmushi yaya Faruk yayi kana ya d'aga mata kai alamar eh. Sai a lokacin na fahimci Khadijah ciki ne da ita a maganganun da na ji suna yi. Wani irin tausayin kaina ne ya kama ni na yanda jarrabawa ke samu na duk akan Dr. Cikin da nake ta burin samu a ko da yaushe sai ga Dr ya min Katanga da wannan hanyar tun da yanzu ba ma tare. "Ina zuwa" Yaya Faruk ya fad'a yana nufar dinning area. Abinci ya zubo a plate da spoon had'e da exotic ya dawo kusa da Nana ya zauna. Da lallashi ya dinga ba Nana abinci tana ci yayin da take zuba mishi shagwab'a kala-kala shi kuma yana biye mata. Hawaye ne ya tarun ma idanu sabida irin kulawar da naga Yaya Faruk ya ke ba ma Nana ba k'aramin burge ni suka yi ba yadda suke ba ma junan su kulawa. Ban tab'a tunanin Yaya Faruk sai iya nuna wa mace kulawa ba sai gashi na gani da ido na. Sallama na musu na tafi d'aki na fara kukan da ya zaman min abinci. Wannan kukan da nake yi ni kaina ban san dalilin yin shi ba. Da na gaji da kukan haka na goge hawaye na. A b'angaren Dr tun San da ya sake ni na fito na tafi ya tashi ya bar gidan. Gidan Momi ya je ya fad'a mata matsalar da muka samu dashi da kuma sakin da ya min. Momi ba ta wani nuna damuwar ta ba saboda yadda take d'aukin ya auri Meema. A cewar ta in yaso daga baya in yana da interest a kaina sai ya maida ni d'aki na. Haka Momi ta ci gaba da jawo hankalin shi akan ya yayi ma Dady magana a sa bikin da wuri, bai wani mata musu ba ya ce ya amince a tsayar da lokacin bikin. Sun yanke akan cewa in Dady ya dawo sai ayi fixing din date din bikin. A nan ya ci abincin dare kana ya musu sallama ya tafi. Lokacin da su Hanan suka ji labarin sakin abin bai musu dad'i ba tun bare Farida da muka fi sabawa da ita. Yau kwana na hud'u a gidan, ba abin da yake had'a ni da yaya Faruk in ba gaisuwa ba sai kuma wani dalili da ya zama dole ya min magana. Yaya Faruk ya dawo min ainihin Yaya Faruk na da da na sani, hakan yasa tsoron shi nake ji duk da ba wani abu da yake min na fad'a ko tsawa ba. Gurin Nana ce nake samun sauk'in damuwar da nake ciki saboda yadda take k'ok'arin ja na a jiki da kuma zama da take yi muna tab'a hira duk da na lura ita ma magana ba damun ta tayi ba kamar yaya Faruk. Ina zaune a d'akin nayi shiru ina tunanin da ya zame min jiki. Sallamar Yaya Faruk da yayi ne yasa na d'ago na kalle shi. Amsa mishi sallamar nayi na sunkuyar da kaina. Zama yayi a resting chair ya kalle ni. Kau da kanshi yayi shiru kamar ba zai yi magana ba. Sai da ya d'auki mintuna kafin ya kau da shirun da cewa "Fatima kin ce min matsala kika samu da mijin ki, gashi yau almost 4 days ban ji kin ce min ya neme ki ba akan ku sasanta, na so a ce an yi solving din matsalar ba tare da su Abbu sun ji ba, amma tun da bai neme ki ba dole ne in sanar dasu dan ba zai yiwu a b'oye musu ba, kin ga kuma nan 2-3 days za mu koma Abuja". Tun da na ji wannan maganar da yaya Faruk yayi hankali na ya tashi, nasan sauran b'oye-b'oye ba nawa ba ne, ya zama dole in fito in fad'a ma yaya Faruk gaskiyar maganar. Hawaye ne ya zubo min a idanu na nayi saurin sharewa. Cikin sanyin murya na ce " Yaya Faruk ba matsala muka samu ba kamar yadda na fad'a ma ka, saki na yayi". Da sauri ya d'ago ya kalle ni jin maganar da na fad'a. Shi ma da alama yayi mamakin sakin da Dr ya min ne. "Ya sake ki kika ce Fatima" yaya Faruk ya tambaye ni. D'aga mishi kai nayi alamar eh. Shiru ne ya ratsa d'akin, ni da yaya Faruk da tunanin da muke yi. Yaya Faruk ne ya kau da shirun da cewa "Allah ya kyauta, zan sami Abbu in mi shi magana, duk yadda ake ciki zan fad'a miki". " To yaya Faruk" na fad'a cikin sanyin murya. Tashi yayi ya fara tafiya da niyyar barin d'akin. "Yaya Faruk" na kira sunan shi. Juyowa yayi ya kalle ni ba tare da ya amsa min ba. Hawaye ne ya fara zubo min a idanu na, ban damu da in goge ba na ce "Yaya Faruk dan Allah ka yafe min abin da nayi maka a baya, nasan ban kyauta ba, sharrin so ya sa na kasa duba abin da ya dace dani, nasan na maka butulci, na yaudare ka, na b'ata maka, yaya Faruk nasan har da hakk'in ka yasa na tsinci kaina a halin da nake ciki, idan ba ka yafe min ba ba zan samu farin cikin da nake buk'ata ba". Kau da kanshi yayi daga kallo na. Lumshe idon shi yayi ya bud'e. Gani nayi idon shi ya canza kala Wanda ke nuna zallar b'acin rai da ya ziyarce shi a lokacin. Ganin shirun da ya min ne yasa na fashe da kuka na jawo gwiwowina na matso kusa dashi. Cikin kuka na ce " Yaya Faruk ka yafe min saboda Allah ba dan hali na ba, ka yafe min ko na samu farin cikin da nake buk'ata, ka yafe saboda girman zumunci dan Allah yaya Faruk... ". Wani irin tausayi na ne ya kama yaya Faruk, yasan wannan yafiyar da na ke nema a gurin shi har zuciya ta haka ya ke, ba zai dubi girman laifin da na mishi ba dan ta haka ne kawai zai iya yafe min. Zuciyar shi ce ke son dawo mishi da abin da na mishi a baya amma yayi saurin danne wa. Murmushin k'arfin hali yayi ya ce " Fatima ke y'ar uwa ta ce, na d'auke ki kamar Anisa, nasan kin min laifuka da dama Wanda in na tuna su suna k'ona min zuciya, Amma ba Wanda ya wuce kuskure, nasan kin yi hakan ne dan samar wa kan ki mafita ba tare da kin duba abin da zai haifar miki a gaba ba, na yafe miki Fatima, Allah ya yafe mana laifukan mu baki d'aya". Wani kukan na sake fashewa dashi mai ban tausayi na ce"Na gode yaya Faruk, bazan tab'a mantawa da karamcin ka gare ni ba". "Kar ki damu Fatima, ke k'anwa ta ce, yanzu ki daina kukan da kike yi ki je ki kwanta" cewar yaya Faruk. Da sauri na goge hawayena na tashi na koma kan gado na zauna. Fita yayi daga d'akin ba tare da ya k'ara ce min komai ba. [9/17, 10:27] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 Facebook: Kainuwa Writers Association www.maryamahmadpaki.blogspot.com *Wannan shafin tukwici ne gare ku* _Masoya wannan littafin ban san kuna da yawa haka ba, ban da abin da zan ce muku sai dai in muku fatan alkhairi, yanda kuke yabawa wannan littafin da d’aukan darasi da kuke yi a cikin littafin yasa nake jin dad’i, fata na a kullum labarin da nake rubutawa ya dinga fad’akarwa had’e da nishad’antarwa_. _Unique wife da Khadija Andija na ga comment d’in ku, ina godiya_ 93-94 Yaya Faruk d’akin Nana ya wuce ya same ta a gaban mirrow tana make-up. Jikin kafad’ar ta yaje ya kwanta yana sakar mata murmushi. Ita ma murmushin take mayar mi shi. Daidai saitin kunnen ta yaya Faruk ya ce "Kin yi kyau Khadijah". "Na gode yaya Faruk" Nana ta fad’a cikin siririyar murya. Yaya Faruk ne ya ce "Khadijah bari in je masallaci na ga lokaci ya kusa, daga nan zan biya gidan su Dad da Abbu". "Ka gaishe su yaya Faruk" cewar Nana. "Za su ji" yaya Faruk ya fad’a yana fita daga d’akin. Bayan yaya Faruk yayi sallar magrib ne ya wuce gidan Abbu. San da yaje gidan, Abbu da Ummu ya samu a falo suna zaune. Sallama ya musu kana ya shigo ya zauna akan rug kusa da Abbu. Da murmushi Abbu da Ummu suka amsa mishi sallamar. Bayan sun gaisa ne Ummu ta ce "Faruk ya wajen su Khadijah, tun da kuka zo Kaduna wannan karan sau d’aya ka kawo min ita, yaushe za ka k’ara kawo min d’iya ta". Murmushi yaya Faruk yayi ya ce "Gobe zan kawo miki ita Ummu dan ina jin nan da kwana biyu ko uku za mu koma Abuja". "Allah ya kaimu Faruk" Ummu ta fad’a ta amsa mishi. Dadi ne ya ce "yanzu nan 2 days kenan za ku koma Abujan". "Eh Abbu" yaya Faruk ya amsa. "Allah ya kaimu ya kuma ba da sa’a" cewar Abbu. Yaya Faruk ne ya amsa da cewa "Amin Abbu". Sun d’an tab’a hira kana yaya Faruk ya kalli Abbu ya ce "Abbu wata magana ce ke tafe dani akan Fatima". Abbu ne ya maida hankalin shi gurin yaya Faruk ya ce "Ina jin ka, Allah yasa ba wata matsala ba ce". Yau kwana na hud’u da zuwa gidan Aminu, a hanyata ta dawowa sai na ga Fatima a bakin titi tana tsaye, so shine sai na tsaya dan na rage mata hanya, bayan ta shiga motar ne nake tambayar ta inda zan kai ta sai take fad’a min sun sami matsala da mijin ta ne, sai yau da na sake tambayar ta take fad’a min cewa sakin ta yayi, yanzu haka ta na gida na". Ummu da tun da yaya Faruk ya fara magana ta tsura mishi ido, jin Kalmar sakin da ta ji yaya Faruk ya ambata ne yasa ta sunkuyar da kanta. Abbu shiru yayi kafin ya ja gauron numfashi ya kalli yaya Faruk ya ce " Ka ce yau kwana hud’u kenan". "Eh Abbu" yaya Faruk ya amsa. Yaya Faruk ne ya ci gaba da cewa "Abbu ina neman alfarma a gurin ka akan sharad'in da ka yanke mata kayi hak’uri ka janye….". Da sauri Abbu ya dakatar dashi cikin b’acin rai ya ce "Faruk kar ka ce za ka nemi wannan alfarmar a guri na dan ba zan iya maka ita ba, sharad’i ne na gindaya mata a matsayina na uban ta kuma ta yarda dashi, sai yanzu da aka samu matsala shi ne za ka ce in yi hak’uri, ai ko a lokacin da ta amince da sharad'in nasan har da k’uruciya ke damun ta da kuma Makauniyar soyayya da take ma wannan Dr d’in, nasan dole wata rana sai tayi nadamar amince wa sharad’ina da tayi dan iyaye ba abin wasa ba ne, kai kan ka Faruk ban san ba ka da hankali ba sai yau, yarinyar da ta k’i ka ta k’i bin shawarar iyayen ta, miye ba ka fuskanta ba a dalilin ta, shine za ka d’auke ta ka kai ta gidan ka, daman ai na fad’a mata in dai ta samu matsala da mijn ta kar ta doshi wani d’an uwa na da matsalar ta ko ta zo guri na, saboda haka kaima ina ba ka umarni ka je ka sallame ta, in ma za ta koma ma shi Dr da ta zab’a akan kowa wannan matsalar ta ce amma kar ta kuskura in ji ta je gurin family d’ina in ba haka ba kuwa za ta fuskanci mummunan hukunci daga gare ni". Yaya Faruk cikin ladabi ya ce "Abbu dan Allah ka janye wannan hukunci daka sa ma Fatima, ita kan ta tayi nadamar….". Abbu ne ya k’ara katse shi da cewa "Faruk kar ka bari raina ya b’aci akan maganar Fatima, ka dai ji abin da na fad’a maka, ka je ka sallame ta kafin ka koma Abuja dan ba kunya ne da ita ba za ta iya cewa za ta bi ka Abuja". Abbu na gama fad’ar haka ya tashi ya bar falon. Shiru ne ya ratsa falon, tsakanin Ummu da yaya Faruk ba wanda ya samu k’arfin yin magana. In ka kalli Ummu a lokacin ba za ka iya fad’ar halin da take ciki ba, sai dai kasan ta shiga damuwa a lokacin. Ummu ce ta ja wata nannauyar ajiyar zuciya ta ce "Faruk ka je ka sallame ta tun da ita ta yarda da sharad’in da Abbun ta ya fad’a mata, ita ta ja ma kanta duk abin da ya same ta, gashi nan tana k’aramar yarinya da ita ya mai da ta k’aramar bazawara, nasan in da kai ta aura da ba za ta fuskanci wannan k’alubalen ba duk da k’addara kowa ba ya kauce mata, ba irin nusar da Fatima da ban yi ba amma ta k’i jin magana ta saboda Makauniyar soyayya da ta d’aura ma kan ta, yanzu wani riba ta samu akan abin da ta yi, yau shekaru ba na nawa ban tab'a yaji ba amma sai gashi y'ar da na haifa an sake ta a cikin k'uruciyar ta ". Hawayen da ya zubo ma Ummu ne yasa tayi saurin goge hawayen da hannun ta. Jikin yaya Faruk ne yayi wani irin sanyi ganin yadda Ummu ta zubar da hawaye akan jin zafin sakin da Dr ya min da kuma rashin bin maganar su da ban yi ba. Yaya Faruk ne ya ce "Yanzu Ummu ina Fatima za ta in na ce ta fitar min daga gida? Laifi ne tayi kuma ta gano kuskuren ta ya kamata a tausaya mata, ko a lokacin har da k’uruciya da ke damun ta, na tabbata a yanzu ba za ta k’ara kwatatanta kuskuren da tayi ba, Ummu ki min alfarma in tafi da ita Abuja kafin komai ya daidaita". Cikin sanyin jiki Ummu ta ce "Faruk, Alhaji yayi fushi sosai da Fatima, idan har yaji ka tafi da Fatima Abuja kai ma laifin zai iya shafar ka, ka je kayi abin da ya ce, wannan sai ya zamar mata izina". "Toh Ummu" yaya Faruk ya fad’a. Sallama yayi ma Ummu ya fita daga gidan. Ko da yaya Faruk ya fito gidan su Dadi ya wuce. Sai da ya tsaya yayi sallar isha’i a masallacin da ke layin kana ya shiga cikin gidan. San da ya shiga falon ba kowa, hakan yasa ya wuce side d’in Dadi dan yasan suna can. Bayan sun gaisa ne yaya Faruk ya sanar da Dadi halin da ake ciki ga me da ni. Dadi bai ji dad’in hukuncin da Abbu ya yanke min ba dan haka ya kalli yaya Faruk ya ce "Gaskiya abin da mijin Fatima yayi bai kyauta ba duk da ban san me ya had’a su ba, shi ma Ibrahim d’in bai kyauta ba, tun lokacin da ya fad’a mata sharad’i nasan ran shi a b’ace yake zai iya janyewa daga baya, ashe shi da gaske ya ke yi, in ban da abin shi ai ba a biye ma yaro in ya b’ata maka, yanzu da ya ce kar ta je gurin family d’in shi ina yake so ta je? yanzu kai Faruk ya ka ke ganin za ayi, yanzu in na ce ka kawo ta nan a yadda ran Ibrahim ya b’aci zai iya turo Aminu ko Khalil su mata hukuncin da bai dace ba in ba na nan, ina so ka tafi da ita Abujan ta d’an yi kwana biyu a can, ita ma nasan Fatima yanzu hankalin ta ba a kwance yake ba, in yaso in Ibrahim d’in ya huce daga fushin da yake yi zan maka magana sai ka dawo da ita, nima zan ma Ibrahim d’in magana". Momi ce tayi saurin kallon Dadi ta ce "Haba Alhaji ya za ka ce Faruk ya tafi da Fatima Abujan, ka manta abin da ta mishi ne, dan ita ma Fatiman ba ta da kunya har ta iya zuwa gidan shi ta zauna sannan yanzu kuma Alhaji ka ce ya tafi da ita Abujan, ai ko ita matar tashi ba za ta ji dad’in wannan hukuncin ba, gwara ta zo nan ta zauna a gurin mu". Dadi ne ya ce " Hajiya ba laifi ba ne dan Faruk ya tafi da Fatima Abuja ta zauna a gurin shi, ai ba wani dad’ewa za tayi a can ba, ko me Fatima ta mishi matsayin y’ar uwar shi ta ke, ba zai dubi abin da ta mishi ya ce ba zai kyautata mata ba dan ta mishi laifi, zai kyautata mata ne dan girman zumunci, ita kan ta Fatiman nasan duk in da za ta zauna ba za ta sake ba saboda abin da ya faru da ita, amma in ta bar garin za ta samu relief d’in halin da take ciki dan rabuwa da miji ba k’aramin ciwo ba ne bare wanda ka ke so". "Shi kenan Alhaji, ni daman abin da nake ji kar ta bi su Abujan ne ita matar shi ta ga kamar an takura mata, ita ma Fatiman Allah ya daidaita tsakanin su da mijinta ta koma, ni kaina ban ji dad’in abin da Dr yayi ma Fatima ba, yarinya k’arama ya sake ta, Allah dai ya zab’a abin da yafi alkhairi". "Amin dai" Dadi ya amsa. Yaya Faruk ya d’an jima a gidan kana ya musu sallama ya tafi. Lokacin da yaya Faruk ya dawo gidan ba kowa a falon, hakan yasa ya wuce d’akin Nana in da ya same ta akan gado ta kwanta. Sallama yayi kana ya k’arasa gadon da take ya zauna a gefen ta. Nana wacce barci ya fara d’aukan ta ba ta san da zuwan shi ba. Kan ta ya fara shafa mata gashin kan ta da tayi parking d’in shi da ribbon. A hankali ya kira sunan ta a saitin kunnen ta had’e da hura mata iska. Jin sunan ta da yaya Faruk yake yi yasa ta bud’e idon ta da yake cike da bacci ta sakar mi shi murmushi. Fuskar ta ya shafa kana ya ce "Sleeping baby". "Sannu da zuwa yaya Faruk, ashe ka dawo, ban ji shigowar ka ba, ya su Momin da Ummu" Nana ta fad’a. "Suna nan lafiya lau, suna gaishe da ke, Yanzu na shigo na ga har kin fara bacci" cewar yaya Faruk. Nana ce ta ce "Tun da nayi sallah na fara jin baccin, shi yasa ina idar wa na kwanta". "Sorry na tashe ki, bari in je in watsa ruwa, ki koma baccin ki kin ji my Khadijah" yaya Faruk ya fad’a. Murmushi ta mishi kana ta ce "Abincin fa yaya Faruk". "kar ki damu na ci a gurin Momi" cewar yaya Faruk. "Sai da safe yaya Faruk, dan za ka iya dawowa ka tarar da nayi bacci" Nana ta fad’a. "Gud night dear" yana gama fad’ar haka ya manna mata peck a cheeks d’in ta kana ya fita daga d’akin. Su yaya Aminu da yaya Khalil kuwa ba su san abin da yake faruwa ba. Sai san da yaya Aminu da yaya Khalil suka je gidan Ummu take fad’a musu sakin da Dr ya min ba k’aramin girgiza su maganar tayi ba. Fad’a musu tayi yanda yaya Faruk suka yi da Abbu a kaina. Yaya Aminu bai wani jin haushin hukuncin da Abbu ya yanke min ba dan yana ganin duk abin da ya sameni ni na ja ma kaina duk da yasan har da k’addara. Yaya Khlalil kuwa tausayi na ne ya kama shi jin matakin da Abbu ya d’auka a kaina. A ganin shi ya kamata a tausaya min da abin da ya same ni. Da yana da hali da ya d’akko ni gidan shi na zauna kan Abbu ya sauka, sai dai yasan bai da halin yin haka saboda yadda Abbu yake fushi dani, hakan zai iya shafar shi in Abbu ya ji labarin shi ya d’auke ni. Dad’in da yaji shine yadda yaya Faruk bai yi fushi dani ba akan abin da na mishi, hakan ya k’ara tabbatar mishi da yaya Faruk daban ne a cikin mutane saboda halayen shi nagari, ba kowa ba ne zai iya yin abin da yaya Faruk d’in yayi. Washegari yaya Faruk ya d’auki Nana ya kai ta gidan Momi, Momi rasa in da za ta sa Nana tayi, haka ta cika da kayan k’walama irin na ma su ciki, bini-bini ta tambaye ta me take so a dafa mata. Ita Nana har kunyar Momi take yi, ba za ta iya fasalta farim cikin ta yadda Momi ke ba ta kulawa a matsayin ta na surukar ta, sun d’an jima a gidan kafin su ka musu sallama suka tafi. Next day ma haka yaya Faruk ya k’ara d’aukan Nana suka je gidan Anisa ganin yadda take mishi k’orafin wannan zuwan da suka yi bai kai ta ba. Ranar ma haka na zauna ni kad’ai a gidan, kad’aici ya same ni ga gidan shiru ba ka jin motsin komai. Haka na wuni a d’aki ni kad’ai, in ban da tunanin yadda rayuwa ta canza min ba abin da nake yi. Nasan a yanzu yaya Faruk ya riga ya fad’a ma Abbu abin da ya same ni, hankali na ba a kwance yake ba dan ban san wani hukunci ya tanadar min, gashi ban da damar tambayar yaya Faruk saboda yadda nake shakkar yi mishi magana ganin yadda bai sakar min fuska. Haka suka je Anisa ta musu tarba mai kyau, ba su sami yaya Khalid ba saboda yana wajen aiki. Ba su wani jima ba suka musu sallama suka tafi. Daga nan gidan su Ummu suka wuce, haka Ummu tayi ta nan-nan da ita, ita kanta Nana tana jin dad’in yaddda Ummu ke janyo ta jikin ta in ta zo gidan. Ko da Abbu ya dawo bayan sun gaisa ne ya kira yaya Faruk side d’in shi. Bayan yaya Faruk ya je kiran da Abbu ya mi shi ne ya ce "Faruk kayi abin da na sa ka?". Sunkuyar da kanshi yaya Faruk yayi cikin ladabi ya ce "Abbu kayi hak’uri, ba zan iya cewa Fatima ta bar gida na ba". Abbu cikin d’aurewar fuska yace "Ok ba za ka iya ba ko, that’s good, tun da kai ba za ka iya ba zan aiki Aminu ya je, dan in har na ta ka k’afa ta na je gidan kai da ita abin ba zai muku kyau ba tun da kaima ba za ka bi abin da na ce ba, ka fad’a mata na ce ta manta da sharad’in da muka yi da ita ne lokacin da ta zab’i shi Sadik d’in". "A yi hak’uri Abbu" yaya Faruk ya fad’a. "Zan hak’ura amma sai kayi abin da na ce" cewar yaya Faruk. Yaya Faruk ne ya ce "Abbu gobe insha Allah gobe za mu koma Abuja". Wannan karan Abbu cikin sakewar fuska ya ce "To Faruk Allah ya ba da sa’a ya taimake ku, amma Faruk ka tabbatar da kayi abin da na ce, akwai dalilina nayin haka, nasan ko ka ce ta bar maka gida Fatima ba za ta je gurin da bai dace ba, ina so ta k’ara fahimtar yanda rayuwa take da kuma kiyaye kwatatanta kuskuren da tayi a baya ta kuma gane mahimmancin bin maganar na gaba da ita da iyayen ta". "Toh Abbu" yaya Faruk ya amsa mishi amma ba wai dan zai iya kora ni daga gidan shi ba kamar yadda Abbu ya ce. Kud’i masu yawa Abbu ya ba ma yaya Faruk ya ba ma Nana, godiya yaya Faruk ya ma Abbu kana ya koma side d’in Ummu. Fad’a ma Ummu yayi kyautar da Abbu ya ma Nana ta nuna jin dad’in ta. Turaruwa masu tsada na jiki ta ba ma Nana da za su tafi. Haka Nana tayi ta godiya irin karamcin da su Ummu da Abbu suke mata. Ummu ce ta ce su gaishe mata da ni lokacin da za su tafi. Yaya Faruk yasan Ummu na daurewa ne amma tana cikin damuwa a kaina. San da suka dawo ne Nana ta shigo d’aki na ta sanar da ni dawowar su, sannan ta sanar da ni Ummu na gaishe da ni. Hakan ba k’aramin dad’i ya min ba jin Ummu ta ce a gaishe dani, nasan hakan na nuna ba ta fushi da abin da ya same ni duk da nasan ita ma sai taji haushin sakin da Dr ya min, Abbu ne fargaba ta dan ban san fushin da yake yi da ni ba. Da daddare yaya Faruk suna zaune da Nana a bedroom tana kwance akan cinyar shi. Yaya Faruk ne ya ce "Khadijah gobe za mu tafi Abuja da Fatima, a can za ta zauna kan komai ya dawo normal". Da sauri Nana ta tashi ta zauna ta kalli yaya Faruk. Cikin sanyin murya ta ce "yaya Faruk ba misunderstanding ka ce sun samu da mijin ta ba". Yaya Faruk ne ya ce "Haka ta fad’a min da farko, ashe divorcing d’in ta yayi, akwai dalilin da yasa ba zan kai ta gidan Abbu ba ne, nafi son komai sai ya dawo normal". Hawaye ne ya fara zubowa a idanun Nana. Mamaki ne ya kama yaya Faruk ganin yadda Nana ke zubar da hawaye saboda yace zai tafi dani Abuja, yasan hakan ba zai rasa nasaba da kishi ba, kallon ta kawai yake yi. "Me ya faru Khadijah kike hawaye, ko ba kya so in tafi da Fatima ne" yaya Faruk ya fad’a. Kuka ta fashe dashi ta fad’a jikin shi ta ce "yaya Faruk dole in yi kuka jin za ka tafi da Fatima, ka fad’a min sun rabu da mijin ta, nasan ita kake ma so tun a farko, yaya Faruk ka nuna ma Fatima so saboda ni kaina shaida ce akan haka, nasan in har kuna tare a ko wane lokaci son ta da ka danne zai iya taso maka at any time, hakan zai sa ka dawo da son ta sabo fil a zuciyar ka, ka ga kuwa hankali na ba zai kwanta ba, yaya Faruk ina son ka kuma ina kishin ka". D’ago da fuskar ta yayi yana goge mata hawayen fuskar ta. Cikin lallashi yaya Faruk ya ce "Pls Khadijah stop that crying, ki daina sa ma kanki wannan tunanin har ranki ya b’aci, kin ga you a pregnant, kar hakan ya shafi lafiyar babyn mu, tabbas nasan na so Fatima amma hakan ba zai sa dan ta rabu da mijin ta yasa in dawo da soyayyar da nake mata ba, tun san da Fatima ta nuna ba ni take so ba na sa ma kaina cewa na hak’ura da ita, ita kanta na fad’a mata cewa na hak’ura da ita tun a lokacin da ta fad’a min Dr take so, ba yanda za ayi in dawo da Fatima cikin rayuwa ta bayan na samu tabon da ta min a zuciya ta ya warke, ko ba haka ba ma ina dake yanzu ban da burin k’ara yin soyayya da wata y’a mace, ke kad’ai kin ishe ni, ina son ki Khadijah" ya k’arasa maganar da murmushi a fuskar shi. Jikin shi ta fad’a ya rungume ta tana cewa "Na gode yaya Faruk". Dariya yayi cikin tsokana ya ce "Ashe Khadijan tawa kishi ne da ita haka, ki ce sai nayi da gaske kar a bar ni na k’ara wata amarya". Rufe fuskar ta tayi tana dariya. Haka suka canza hirar ta su zuwa nuna ma junan su zallar so da kulawa had’e da tarairaiya. [9/21, 14:23] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 Facebook: Kainuwa Writers Association www.maryamahmadpaki.blogspot.com *Ya Allah kayi ma na maganin wad'annan musibobi da suka yi ma na katutu a Nigeria, kisan al'umma da akeyi, garkuwa da mutane, tsadar rayuwa da kuma talauci*. *JUMU'AT KAREEM* _TUNATARWA_: *QARYA DA ILLOLIN TA* _Qarya ita ce tushen laifuka kuma jagoran manyan kaba’irorin da d’an adam ke aikatawa_. _Qarya ita ke santa mutum yaci amanar d’an uwan sa ko abokin sa_. _Qarya ita ce tambarin dukkan munafukai domin it ace sinadarin da suke amfani da ita wajen had’a dukkan sharruka da qulle-qullen su_. _Qarya babu abin da yafi ta saurin zubar da mutunci da qimar mutum da zai aikata_. _Qarya tana nesanta baewa daga rahamar mahaliccin sa sannan ta kusanta shi zuwa ga gidan azaba_. _Ya Allah ka kiyaye mu daga yin Qarya ko yin furuci mara tushe, ka nuna mana hanyar gaskiya ka nisanta mu da yin Qarya_. 95 & 96 Washe gari bayan mun yi breakfast ne na je na wanke kayan da muka yi amfani dasu kana na zo na gyara falon. Bayan na gama ne na koma d’akin na ci gaba da zama na. Ji nake yi kamar in kira Anisa ko na samu sauk’in damuwar da nake yi. Kiran da ya shigo ne ya katse min zancen zucin da nake yi. Ga mamaki na Anisan ce ke kira na. A raina na ce kamar tasan ita nake tunanin kira. Da sauri nayi picking d’in call d’in ta. Bayan mun gaisa ne Anisa ta ce "Fatima ashe abin da ya faru kenan, Allah ya canza miki da mafi alkhairi". "Amin Anisa" na amsa mata. Anisa ce taci gaba da cewa "yaya Khalil ya ce min kina gidan yaya Faruk ko? gani nan zuwa". "Sai kin zo, ki gaishe min da Amatur-Rahman" na fad’a. "Za ta ji" ta Amsa min kana ta katse wayar. Ba a fi awa d’aya da rabi ba sai ga Anisa ta zo gidan yaya Faruk d’in. Maganar ta naji a falo suna gaisawa da yaya Faruk da Nana. Hakan yasa na fito falon na zauna kusa da Anisan. D’aukar Amatur-rahaman dake hannun ta nayi na fara mata wasa. Nana ce ta ce "Fatima sai yanzu muke ganin ki, ina jin da ba ki ji maganar Anisa ba baza ki fito ba". Murmushi kawai na yi ba tare da na ce komai ba. A raina nace "yaushe zan fito ba na samun sakewar fuska a gurin yaya Faruk, magana ba had’a ni take yi dashi ba in ba ta kama ba, in ban da gaisuwa ta da yake amsawa in na gaishe shi, sannan ga soyayyar da ya ke yi miki a gaba na wanda dole in haramta ma kaina zaman falon, ni gani na ke yi yaya Faruk kamar ma da gayya yake yin haka a gaba na". Tashi nayi daga falon na kalli Anisa na ce "In kin gama hirar ki same ni a d’aki". Ina gama fad’ar haka na wuce d’akin na ci gaba da yi ma Amatur-Rahman wasa. Jin yarinyar na ke yi har cikin zuciya ta, ba tunanin da ya fad’o min a lokacin shi ne yaushe nima zan ga d’an kaina? Wannan tunanin da nayi ne yasa hawaye ya tarun min a ido. Anisa ce ta shigo d’akin da sallama tana kallo na. Amsa mata sallamar nayi da murmushi a fuska ta. Kusa dani tazo ta zauna muka sake gaisawa kana na tambaye ta yaya Khalil ta ce yana gaishe ni. Anisa ce ta ce "Fatima ban ji dad’in abin da ya faru ba, nasan ko wane bawa ba ya guje ma k’addarar sa, kar ki sa abin a rai har ya dinga damun ki, nasan mutuwar aure akwai ciwo, shi destiny ba wanda ya isa ya kauce mishi, fata na Allah ya daidaita ku ki koma d’akin ki". Murmushin takaici nayi kana na ce "Anisa nasan duk abin da ya same ni k’addara ce, amma wani abin har da laifi na da ban d’auki shawarar ku ba a lokacin da kuke ba ni shawarar, Anisa ke shaida ce a irin son da na nuna ma Dr amma shi bai duba haka ba, sai yayi amfani da wannan damar yake min abin da ya gadama, Anisa kin sha fad’a min illar makauniyar soyayyar da nake nuna ma Dr da irin abin da zai haifar min nan gaba amma sai a lokacin na d’auka kamar a lokacin ba kya son tarayya ta da Dr d’in ne, sai gashi a yanzu na yarda da maganar da kuke fad’a min". Kuka na fashe dashi mai ratsa zuciyar mai saurare na ci gaba da magana cikin kuka na ce "Anisa wai ni Dr ya saka akan zai k’ara aure, yana fad’a min cewa shi zai yi ma Momin shi biyayya akan auren da take so yayi, har yana goranta min da cewa bai so yayi kuskuren da nayi na k’in bin maganar su Abbu, ina ma naji maganar ku a lokacin da kuke fad’a min gaskiya, Anisa nayi nadamar kuskure nah…" na k’arasa maganar da k’ara sautin kuka na. Ita ma Anisa hawaye ne ya zubo mata na tausayi na. Cikin sanyin murya Anisa ta ce "Fatima ki daina kuka, komai da kika ga ya same ki rubutacce ne, dama can Allah ya k’addara cewa Dr mijin ki ne, kuskuren da kika yi Fatima shine rashin bin maganar mutane da suka dinga baki, a lokacin idon ki ya rufe kika nuna ke sai Dr, a lokacin maimakon ki nemi zab’in Allah sai ki ka bi zab’in zuciyar ki". "Ni ma nayi nadama Anisa, a yanzu na gano cewa zab’in Allah shi yafi ba wai soyayya ba". Haka Anisa ta ci gaba da kwantar min da hankali. Yaya Khalil ne ya kira Anisa ya sanar da ita ya zo gidan yana falo, tare muka fito falon da ita. Samun su muka yi da yaya Faruk da Nana suna hira. Tun da na shigo falon yaya Khalil ke bi na da kallo. Gaishe shi nayi nayi ba tare na k’ara cewa komai ba. Hira aka ci gaba dayi ba tare da na saka baki na ba, duk hirar da suke yi ina sauraron su. Bai wani jima ba ya musu sallama ya fita. Anisa ce ta bi shi ta dawo ta sanar dani yaya Khalili na kira na. A harabar gidan na same shi yana jingine jikin motar shi. Jiki a sanyaye na k’arasa kusa dashi. Shiru ne ya ratsa a tsakanin mu kana na kau da shirun da cewa "yaya Khalil ya su Abbu da Ummu". "suna nan lafiya kau" yaya Khalil ya amsa min. Yaya Khalil ne ya ce "Fatima ashe abin da ya faru kenan, san da Ummu ta fad’a min sakin da Dr ya miki ba k’aramin tashin hankali na shiga ba, ban ji dad’in abin da ya faru ba, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a tsakanin ku, idan kuma da rabon ki koma sai Allah ya daidaita ku ki koma d’akin ki". Yaya Khalil ne ya ci gaba da cewa "Amma Fatima me kika mishi ya sake ki?" ya k’arasa maganar yana kallo na. Sunkuyar da kaina na yi yayin da hawaye ya tarun min a ido na ce "yaya Khalil baa bin da na mishi, kawai dai mun sami misunderstanding da shi ne akan auren da yake son k’arawa wanda a dalilin haka yasa muka rabu". "Fatima saboda zai k’ara aure ne yasa ki ka d’aga hankalin ki har ta kai kun sami matsala dashi ya sake ki, me yasa ba ki yi hak’uri ba tun da wanda zai aura ba akan ki zai ajiye ta ba, kin san kuma namiji mijin mace hud’u ne, why Sis" cewar yaya Khalil. "Yaya Khalil ba akan shi kad’ai muka samu matsala ba, Momin shi ce ke son yayi auren, dan na mishi magana shine ya ce min wai zai yi ma Momin shi biyayya, ba zai yi irin mistake d’in da nayi ba da ban ji maganar su Abbu ba…" na k’arasa maganar da fashewa da kuka. Cikin kukan na ci gaba da cewa "yaya Khalil su Abbu na fushi dani ko? nasan tafiyar nan da za ayi dani Abuja Abbu bai yarda in dawo gida ba ne, yaya Khalil I have ralised my mistake, ina so in nemi yafiyar su Abbu da Ummu, I have learnt a lesson". Tun da na fara maganar yaya Khalil yake kallo na, da gani yana ji tausayi na ne. Hannu na ya rik’e yana girgiza min kai. Jikin shi na fad’a na ci gaba da kukan, bai hana ni yin kukan ba dan yasan a hali da nake ciki a yanzu ina buk’atar yin kukan. Sai da ya ga nayi shiru ya d’ago ni da ga jikin shi. Cikin lallashi ya ce "Anisa komi da ya sami bawa rubutacce ne a gurin ubangiji, sai dai kamar yanda kika ce Dr ya ce miki shi zai yi ma Momin shi biyayya ba zai yi mistake d’in da kika yi ba kin ga anan darasi ne babba a gurin ki da ya kamata ki d’auki izinah, Fatima ko da su Abbu suka amince aka yi auren ki da Dr kin san wanda suke so ki aura amma saboda son da ya rufe miki ido yasa ba ki duba hakan ba, akan ki yarda da k’udurin sun a auran yaya Faruk shi yasa Abbu ya sa miki wannan sharad’in amma duk da haka Fatima sai ki ka amince da wannan sharad’in, Fatima ni da yaya Aminu sau nawa muka miki magana akan ki bi abin da su Abbu kike so but you reduce, sau nawa na nuna miki b’acin raina na kuma zaunar dake na miki fad’a akan abin da kike niyyar yi is not wright but still Fatima you did’nt take my advice, yanzu mai gari ya waya tun da shi wanda kika yi domin shi gashi shi yake miki gorin abin da kika yi at the end kuma ya sake ki sannan kuma zai bi umarnin Momi d’in shi ya auri wacce take so yau aura, kin ga ba ki yi gaining d’in komai ba". Cikin shashshek’ar kuka na ce "yaya Faruk I want to see Abbu & Ummu, ina so su yafe min, ba na so su ci gaba da fushi dani, I miss them". Yaya Khalil ne ya ce "Ki daina kuka Fatima, Abbu da Ummu ba fushi suke yi da ke ba, sai dai a yanzu dole su shiga damuwa jin abin da ya same ki, Fatima ko wani iyaye dole ya shiga damuwa idan aka yi divorcing d’in y’ar shi, Abbu yana cikin b’acin rai ne, nasan idan ya sauka zai ma yaya Faruk magana ya dawo dake, kar ki damu su Abbu za su yafe miki, ki daina sa ma kan ki damuwa Fatima, komai zai wuce, ban ji dad’in ganin ki haka ba, kowa ya kalle ki yasan ki na cikin damuwa, stop worrying your self kin ji my sis". "Toh yaya Khalil zan kiyaye" na fad’a cikin sanyin murya. Murmushi yayi yaya Khalil yayi kana ya ce "that is my Sister, so smile for me". Ban san lokacin da murmushi ya sakar min a fuska ta ba. Fuskar yaya Khalil ce ta k’ar yalwatuwa da murmushi ganin na yi murmushi. Kallon wrist watch d’in shi da ke hannun shi yayi kana ya ce min "Fatima zan koma gurin aiki, excuse na nema na fito, ki kira min Anisa sai in sauke ta a gida". "yaya Khalil ka gaishe min da su Ummu da Abbu da yaya Aminu da su Anty Jidderh" na fad’a a hankali. "Za su ji" yaya Khalil ya amsa min. Falon na koma na sanar da Anisa yaya Khalil na jiran ta. Sallama ta ma su Nana kana muka jera tana ci gaba da kwantar min da hankali. Sai da na ga sun shiga motar sun fara tafiya na musu waving d’in hannu na, su ma waving d’in su ka min. Koma wa nayi cikin d’akin ban sake fito wa ba. Wajen la’asar yaya Faruk ne ya shigo d’aki na. Yau ma kamar kullum fuskar nan tashi a d’aure take ya tsaya a gefe. Shiru ne ya ratsa a tsakanin mu kafin ya kau da shirun da cewa "Fatima za mu koma Abuja yanzu, ina so in ji saki nawa ya miki saboda akwai sakin da in aka yi shi in har ba kin gama iddah ba kina matsayin matar shi ce in dai ya maida ke a lokacin, za mu tafi dake Abuja ne na d’an wani lokaci. Ji nayi jiki na yayi wani irin sanyi, nasan tun da yaya Faruk ya ce zan bi su Abuja hakan na nufin cewa Abbu bai hak’ura ba da sharad’in da ya sa min, ji na ke yi kamar in ce ma yaya Faruk ba zan bi su ba, ko a nan d’in ma a takure nake saboda rashin sakewar fuskar yaya Faruk da kuma yanda wani lokacin suke gudanar da soyayya su a gaba na ba tare da jin kunya ba, Nana ce ma wani lokacin take nuna jin kunyar ta idan yaya Faruk yayi mata wani abin a gaba na. Sai dai nasan ba ni da mafita da ta wuce bin su d’in tun da nasan Abbu bai yarda da dawowa na gida ba tun da har na ji yaya Faruk bai fad’a min yadda suka yi da Abbu ba. Cikin sanyin jiki na ce "Saki d’aya ya min". "Kin ga kenan kina matsayin matar shi tun da ba ki gama iddah ba in har yace ya dawo dake, ki shirya kayanki". Yana gama fad’ar haka ya fita daga d’akin. Jiki a sanyaye na had’a kayana na zauna jiran su. San da za mu tafi Abujan ne Nana ta shigo ta min magana in fito mu tafi. Trolik d’ina na d’auka muka shiga mota muka nufi Abujan. Wajen magrib muka isa Abuja. Nana ce ta nuna min d’akin da zan zauna. Ina shiga d’aki na shiga band’aki na watsa ruwa. Kaya mara sa nauyi na sa ka. Ban fito d’akin ba sai da Nana ta zo ta min magana in zo mu ci abinci. Bayan mun gama cin abincin ne na koma d’akin da aka sauke ni. Ban jima da shiga d’akin ba na ji waya ta tana kuwwa. Ganin sunan Ummu da na yi ne yasa jiki na ya k’ara sanyi. Cikin sanyin murya na d’auka kana na gaishe ta. Amsa min tayi kana ta d’aura da cewa "Fatima kuna Abujan ne". "Eh Ummu" na amsa mata. Ummu ce ta ce "Fatima tun san da Faruk ya zo ya fad’a min mummunan labarin abin da ya same ki hankali na ya gaza kwanciya, na so a ce kina kusa dani a yanzu sai dai ba ni da halin yin haka a dalilin zafin da Abbun ku ya d’auka kuma ba kowa ya jawo hakan ba fa ce ke Fatima da kika yarda da sharad’in shi, yanzu ga avin da kika yi ya jawo miki, ke yanzu abin farin cikin ki ne a ce wannan mummunan k’addarar ta same ki amma ba kya gaban iyayen ki, abin da yasa hankali na ya kwanta shi ne nasan Faruk zai kula dake amma duk da haka ina so ki yi taka tsantsan saboda ba ki gama iddah ba, yanzu saki nawa shi Sadik d’in ya miki" Ummu ta k’arasa maganar da tambaya. "Saki d’aya ya min" na amsa mata. "Allah yasa hakan shi yafi miki alkhairi, in kuma da rabon ki koma gidan Dr Allah ya daidaita ku, ki kula Fatima, kin ga har yanzu ba ki fita iddar ki ba, yanzu shi Dr d’in yana cewa ya maida ki kin maidu, sannan ki zauna da Nana lafiya nasan ba ta da matsala, insha Allah ba wani dad’e wa za ki yi a Abujan ba, nasan Dadin ku zai mishi magana, yanzu ma dan yana kan k’udurin shi ne shi yasa bai yadda kin dawo gida ba, ki yi hak’uri kin ji Auta". Wani irin tausayin kaina da na Ummu ne ya kama ni a lokacin. Nasan Ummu ma na cikin damuwa akan sakin da Dr ya min, a maganar da ta min na fahimci haka. Ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Ummu ce ta katse ni cikin tashin hankali ta ce "Yanzu mi ye abin kuka daga magana". Cikin kuka na ce "Ummu ku yi hak’uri ku yafe min, ki neman min yafiya a gurin Abbu akan laifin da na muka a baya". "Ki daina kuka Fatima, na yafe miki, idan kika dawo Kadunan za mu yi magana, Abbun ki ma zai yafe miki". Cikin shashshek’ar kuka na ce "Na… gode…Ummu". "Ki gaida su Khadijan" Ummu na gama fad’ar haka ta katse wayar. Kuka na naci gaba wanda ni kaina ban san dalilin yin kuka na ba. Yau muna zaune a falo ni da Nana kasancewar ta je lectures ta dawo da wuri, yaya Faruk na wajen aiki. Anty Maryam ce ta shigo rik’e da hannun Asim. Gaisawa muka yi kana na tashi na d’akko mata drinks da snacks na ajiye mata na rik’e hannun Asim muka wuce d’aki na. Bayan tafiya ta ne su Nana suka ci gaba da hirar su. A cikin hirar ne Anty Maryam ta ce "Nana bak’uwa kuka yi ne, kin san tun da kuka dawo Kadunan ban samu shigowa ba, san da kuka shigo gurin mu kuma ba ku shigo da ita ba". "Fatima ce k’anwar yaya Faruk" na amsa mata. Da sauri Anty Maryam ta ce "Wai wace Fatiman kike magana?". Nana ce ta ce "Fatima dai da kika sani y’ar uwar yaya Faruk". "Tare kuka tawo da ita kenan?" Anty Maryam ta sake watso mata tambaya. "Eh tare muka tawo da ita" Nana ta fad’a. "Ina fatan lafiya dai kuka tawo da ita" Anty Maryam ta sake tambayar Nana. Nana ce ta ce "Sun rabu da mijin ta ne, shine yaya Faruk ya ce Dadin shi ya ce ya tawo da ita". "Kina nufin nan za taci gaba da zama kenan" cewar Anty Maryam. "yaya Faruk ya ce ba dad’ewa za tayi ba" Nana ta fad’a. Nana ta ci gaba da cewa cikin marairaicewa "Anty Maryam tun da yaya Faruk ya ce zai tawo da Fatima na rasa peace of mind d’ina duk ya tabbatar min da yanzu ba wata alak’a ta soyayya da zai k’ara shiga tsakanin su da ita amma hankali na gaza kwanciya, nasan in har yaya Faruk suna zama a guri d’aya da Fatima wataran dole ya ji son ta ya dawo mishi a cikin zuciyar shi ya ji yana sha’awar auren ta, Anty Maryam ke kan ki shaida ce a irin son da yaya Faruk ya ma Fatima, nasan har yanzu ba yanda za ayi ya ce ya rabu da son Fatiman a zuciyar shi, sai dai yana dannewa ne dana bin da ta mishi, kin ga in har yaya Faruk ya dawo da Fatima rayuwar shi ban san yanda zan yi ba in hakan ta kasance" ta k’arasa maganar cikin rawar murya. Anty Maryam tsura matai do tana kallon ta, ganin hawayen da ya tarun ma Nana a ido yasa tai tausayin ta ya kama ta, tasan Nana tana da hak’uri da kau da kai, tun da ta fito tayi magana abin na damun ta ne. Cikin lallashi Anty Maryam ta ce "ki yi hak’uri Nana kar ki sa damuwa a ranki, nasan dole hankalin ki ya tashi akan tawowa da Fatima da kuka yi, shawarar da zan baki shine kar ki sa ma zuciyar ki wani tunani daban tsakanin Fatima da Faruk, ina so ki ci gaba da zama da ita Fatiman lafiya, ina so ki yarda da maganar da shi Bregadier ya fad’a miki cewa ba wata alak’a da za ta had’a shi da Fatima, nasan tun da ya fad’a miki wannan maganar to hakan take a ranshi, ki ci gaba da hak’urin da na san ki dashi, kar ki bari shaid’an ya fara sa mi ki wani tunani na daban a ranki, duk abin da kika ga ya samu bawa to rubutacce ne daga wajen ubangiji". "Na gode Anty Maryam, insha Allah zan yi amfani da shawarar da ki ka ba ni" Nana ta fad’a cikin cool voice d’in ta. Murmushi Anty Maryam tayi kana ta ce "yawwa Nana, Allah ya k’ara ba ku zaman lafiya da Faruk d’in". Cikin fara’a ta amsa da "Amin Anty Maryam". Da haka suka canza hirar da suke yi, sai da Anty Maryam za ta tafi ne sannan Nana ta shigo d’akin da na ke ta amshi Asim a hannu na. Fitowa nayi muka yi sallama da ita. [9/23, 19:08] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com Facebook: Kainuwa Writers Association *TUNATARWA*: HIKIMA ZINARIYA!!! _Komai a duniya yana da mabud’i_. _Mabud’in ilimi shine tambaya_. _Mabud’in nasara hak’uri_. _Mabud’in arzik’i tsoron Allah_. _Mabud’in zaman lafiya adalci na gaskiya_. *Hattara da mabud’ai guda uku* _Fushi mabud’in azaba_. _Tsoro mabud’in fitina_. _Kwad’ayi mabud’in wahala_. 97 & 98 Tun daga wannan lokacin zama na yaci gaba da kasancewa a gidan yaya Faruka a Abuja. Sai dai zama na a Abuja ba wani ci gaba da na samu na raguwar damuwa ta sai ma k’arin damuwa da na samu saboda yanda zaman kad’aici yake damu na in Nana ta tafi makaranta, ga rashin sakewar fuskar yaya Faruk da ba na gani, in an ga walwala ta wani lokacin bai wuce gurin Nana ba, sai wani lokacin in Nana za ta je block d’in Anty Maryam ta kan nemi rakiyata. Ba laifi muna waya da yaya Khalil da Anty Jidderh da Ummu, yaya Aminu ma yak an kira ni, Anisa ma da Halima da Aisha muna waya dasu, Dadi da Momi sun kira ni sun jajanta min abin da ya faru, san da Dadii ya kira ni haka ya dinga kwantar min da hankali da min nasihohi masu ratsa zuk’ata, tabbas na ji dad’in maganganun Dadi da ya fad’a min. Zaman Abuja ya ishe ni, ji nake yi kamar in yi tsuntsuwa in ganni a gaban iyaye na, sai dai abin da yake k’ara sanyayar min da jiki shine duk wayar da muke yi da Ummu ban ji wani labari mai dad’i a gurin ta na cewa Abbu ya hak’ura da fushin da yake yi, nasan in har Abbu ya sauka daga fushin da yake yi zai nemi da in dawo gida. Duk wanda ya ganni a lokacin sai ya tausaya min, na yi bak’i na rame, da ka kalle ni kasan ina cikin damuwa, Na dawo so silent & cool. Tun ina mamakin rashin kiran wayar Dr da bai min ba har na daina dan nasa ma raina cewa a yanzu na daina d’aura ma kaina wani tunani a game da soyayyar Dr, nasan a yanzu ba ta ni yake yi ba, ta amaryar da yake shirin yi yake yi, na san cewa dole wataran sai Dr yayi nadamar abin da ya min dan ya ci amanar soyayyar da na mishi ta gaskiya. Haka na ci gaba da zama a gidan yaya Faruk, gashi a yanzu ina neman wata d’aya a gidan, kullum buri na shine in ji Ummu ta ce Abbu ya ce in dawo gida. Ganin har yanzu Yaya Faruk bai ce min komai ba ga me da komawa ta Kaduna amma har yanzu shiru, hakan yasa nayi shahadar tunkarar Yaya Faruk. Samun shi nayi a falo yana kallon wani American film. Tun da na gaishe shi ya amsa min ba Wanda ya sake magana a tsakanin mu. Ganin zaman ya ishe ni gashi ni American film d'in ba wani damu na yayi ba yasa na kau da shirun da cewa " Yaya Faruk in ban takura maka ba ina so muyi magana ne". "Ina jin ki" ya amsa min ba tare da ya daina kallon da yake yi ba. Nisawa nayi kana na ce "Yaya Faruk daman na ji shiru ne har yanzu ba ka min maganar komawa ta Kaduna ba kuma Yaya Faruk Sai na ga kamar zama na kamar ina takura mu ku ". Sai a lokacin ya d'ago ya kalle ni. Cikin d'aurewar fuska yace " Yanzu me kike so a miki da kika zauna kina min explanation, k'ofa a bud'e take in za ki koma Kadunan ne, in ban da ke stupid ce za ki zo kina ce min wai ko kin takura mana, dan uban ki ni ko Khadija ce muka ce kin takura mana ko kin ga wata alama ta an gaji dake ne?" ya k'arasa maganar yana kallo na. Hawaye ne ya tarun ma a ido, danasanin tunkarar Yaya Faruk nayi da wannan maganar, ga zagin da ya min ya min ciwo amma ba halin in nuna. Tsawa ya daka min ya ce "Ba da ke nake magana ba Fatima, ko Sai kin ji a jikin ki". Girgiza mi shi kai nayi alamar a'ah, dan nasan in na yi magana kula ne zai biyo baya. Yaya Faruk ya d'aura da cewa " Ke in ban da ba ki da kunya ba, ban yi tunanin za ki iya tunkara ta da maganar cewa wai kin ji shiru akan maganar komawar ki Kaduna, ko da yake tuntuni na fahimci kin canza dabi'un ki, saboda haka ba abin mamaki bane, in kinga kin koma Kaduna to Abbu ne ya ce in dawo da ke, ke in ban da baki da hankali ma Fatima, ni ina sha kin zo ne ki min magana akan in kira Abbu da Ummu in basu hak'uri amma shine za ki zo min da rubbish words d'in ki, in kin San zaman wani guri zai takura ki me yasa tun farko kika yarda da sharad'in Abbu, sai yanzu za ki zo kina min complain, in kika k'ara tunkara ta da wannan maganar sai jikin ki ya fad'a miki, kar kiyi zaton ko yanzu kin girma, a guri na har yanzu ke yarinya ce a guri na, dan haka ki tashi ki ba ni guri". Wani irin abu ne ya tsaya min a mak'oshi na d'acin maganganun da Yaya Faruk ya fad'a min, nasan duk maganar da Yaya Faruk ya fad'a min ni na jawo ma kaina. Gaba d'aya jiki na ba laka haka na tashi na koma d'aki na dasa kukan b'acin ran maganganun da Yaya Faruk ya fad'a min. Da na gaji da kukan ne na goge hawaye na. Ni kaina yanzu nasan kuka ya zama abin ci na dan yanzu abin kuka ba ya min yawa. Yau Dadi ne ya sami Abbu a office d’in su na Wagini motors. Bayan sun gaisa ne su ka tattauna akan b’angaren business d’in su, daga nan Dadi ne ya canza hirar da zuwa magana ta. Dadi ne ya ce "Ibrahim akwai maganar da na ke so mu yi". Abbu ne ya amsa masa da cewa "To yaya ina jin ka". "Ibrahim tun san da ka fad’a min an saki Fatima ban k’ara jin kayi maganar ta ba, na ji duk abin da ya faru da ka cewa Faruk wai Fatima ta bar gidan shi sannan kai kuma ba ka ce ta dawo gidan ka ba, abin da yasa ban ce ma Faruk ya kawo ta gida na ba saboda nasan in ta je Abujan za ta samu sauk’in damuwar da take ciki, da ka ce ta tafi to ina kake so ta je? San da ka sa ma Fatima sharad’in na d’auka saboda a lokacin ran ka a b’ace yake shi yasa, ashe kai da gaske ka ke yi, wannan hukuncin da ka yanke sam ba mafita ba ne, nasan Fatima tayi laifi a baya amma kuma ba wanda ya wuce kuskure, duk abin da ka ga ya samu mutum to Allah ya k’addara hakan zai same shi ko yaso ko yak’i, in dai Allah yace (kun) kasance to sai ya kasance, in ita Fatima yarinya ce da k’uruciya kai ai mahaifin ta ne, dole ka mata uzuri a matsayin ta na y’ar da ka haifa, nasan ita kan ta Fatiman sai tayi nadamar abin da ta aikata a baya sannan ba inda za ta ji dad’in zama fiye da gidan iyayen ta, nasan ita ma mahaifiyar ta d’in hankalin ta ba a kwance yake ba akan abin da ya sami Fatiman sannan gashi ba a gaban ta take ba, na zuba maka ido ne dan in ga iya gudun ruwan ka amma na ga kai ba ka da ranar sauka daga fushin da ka yi, hakan da ka yi ya nuna kamar ba ka yarda da k’addarar da za ta iya samun bawa a ko wani lokaci ba, saboda haka ina so Ibrahim ka amince da dawowar Fatima gidan ka sannan ka mata addu’ar Allah ya zab’a mata abin da yafi alkhairi sannan ka yafe mata kuskuren da tayi maka a baya". Nisawa Abbu yayi kana ya ce "yaya na yafe ma Fatima abin da ta min, na kuma gano kuskuren da nayi na cewa kar ta tunkare ni da matsalar ta in ta sami matsala da mijin ta, zan ma Faruk d’in magana ya dawo da ita". "yawwa Ibrahim hakan ya kamata ka yi, hak’uri ake yi da yara, Allah ya shirya mana zuri’ar mu baki d’aya" cewar Dadi. "Amin ya Allah" Abbu ya amsa. Da haka Dadi ya koma office d’in shi dan ci gaba da aikin shi. Ganin har yanzu Yaya Faruk bai ce min komai ba ga me da komawa ta Kaduna amma har yanzu shiru, hakan yasa nayi shahadar tunkarar Yaya Faruk. Samun shi nayi a falo yana Da A b’angaren Dr kuwa ya ci gaba da mu’amalar shi da zuwa ayyukan shi cikin kwanciyar hankali. Wani lokacin in ya ga tunani na zai kama shi sai yayi saurin kau da tunanin. Cikin d'an k'ank'anin lokaci aka sa bikin Dr da Meema. Wata d'aya kawai aka sa kasancewar ko wani b'angare a shirye su ke. Meema tun da taji an yi fixing d'in bikin su ta rasa in da za tasa kan ta saboda murna. Shirye-shirye da event suka dinga shirya ita da Hanan. A gurin Dr kuwa ba yabo ba fallasa haka game da shirye-shiryen bikin. Komai aka sa ma rana sai yazo dan a yau ne aka d'aura auren Meema da Dr. Wani b'angare a gidan Dr ya gyara ma Meema saboda gidan babba ne. Ko san da aka d'aura auren Dr bai yi wani farin ciki ba, yasan ya amince da auren ne saboda yayi ma Momin shi biyayya da kuma tausaya ma Meema da yake yi. Ran first night d'in su da ya kasance da Meema yayi mamakin samun ta a virgin da yayi saboda ganin yanda ta ke a waye, sai dai da difference is clear. Yafi jin dad'in kasancewa da ni akan Meema, yasan ni ta daban ce da baiwar da Allah ya min, yasan zai yi wuya ya samu iri na wajen faranta mi shi yanda yake so. Tun a nan ya fara missing d'ina, saurin kau da tunani na yayi a ran shi, a yanxu yana ganin bai da buk'atar yin tunani na tun da nuna ban damu dashi ba tun da ban ne me shi ba tun da muka rabu. A haka zaman su ya ci gaba da kasancewa, ba laifi Dr yana ba ma Meema Kula ita ma Meema tana k'ok'arin yin abin da Dr ya ke so da kauce ma abin da bai so. Da zama yaci gaba da gudana a tsakanin su ne zaman nasu ya fara canza salo. Matsalar da suka fara samu shine rashin son yin girki da Meema ba ta son yi saboda ba wani iya different foods tayi ba kasancewar tun tasowar ta ba ta shiga kitchen da niyyar yin girki har tafiyar ta turai karatu, ko a can tafi gane ma yin take away, sai in taso ne za ta yi simple food, ko da ta dawo gida Nigeria bai sa ta maida hankalin ta wajen koyan girki ba, abin da ta fi maida hankali shine dafa indomie da kuskus da dai irin simple food , sai dai ta ce ma Dr yaje restaurant ya musu take away, hakan ba k'aramin b'ata ma Dr rai yake yi ba kasancewar shi mai k'yank'yami ne, ba ya son cin abinci waje, hakan yasa wani lokacin yake zuwa gidan Momi yana cin abincin, ga fita da take yi without his permission, idan yayi mata magana sai tace mi shi tana da damar zuwa in da ta gadama dan ita ba matar kulle ba ce, ga yin shigar da ta gadama ko za ta fita ne ba tare da tayi la'akari da cewa a yanzu ita matar aure ce, gashi sometimes ba ta yarda dashi in zai yi love making da ita, sai dai in ita ta gadama, a tak'aice dai Meema nayi duk abin da ranta yake so. Kasancewar shima Dr d'an Human right ne da koyi da rayuwar turawa yasa bai cika damuwa da sa mata ido akan al'amuran ta ba, daga baya ne da yaga abin na ta ba na k'are ba ne yasa suka fara kai ruwa a tsakanin su. Wani lokacin in ya mata fad'a takan d'auka saboda son da take mi shi amma da an kwana biyu za ta dawo yin abin da ta gadama. Tun Dr na mata fad'a akan abin da take yi har ta kai ga yanzu tana maida mi shi magana dan ita a ganin ta ba za ta iya rayuwar takura ba. Wani lokacin in ya ma Momi complain akan halin Meema sai dai ta ba shi hak'uri dan tana ganin kamar yanakawo k'arar Meema ne dan ba choice d'in shi ba ce, daga baya da ta gano gaskiyar maganar da Dr yake fad'a mata akan Meema yasa ta ci gaba da bashi hak'uri had'e da kwantar mi shi da hankali. Dr ya fara shiga damuwa akan irin wannan zaman da suke yi da Meema. A lokacin ne ya fara danasanin rabuwa da yayi da ni, ga kewa ta dake addabar shi, hakan yasa damuwar ta mi shi yawa. Shi kan shi in ka ga Dr kasan ya canza in kayi duba da ramewar da yayi. Yau ranar ta kasance ranar lahadi, Dr yana gida yana hutawa yayin da Meema ke cikin d'aki. Meema ce ta fito cikin wani irin material mai tsada transparent kalar pink yayin da yafa d'an k'aramin veil a kan ta. Cikin takun k'asaita take tawowa, ba abin da kake ji sai k'arar takalmin ta, hakan yasa Dr ya d'ago ya kalle ta. Cikin murmushi ta zo ta zauna kusa dashi. D'aure fuska yayi yana ci gaba da kallon ta. "Ina za ki ne Meema na ga kin yi shirin fita?". Meema ta amsa mishi da cewa " Yau birthday d'in Leema, shine nake so in je". Da mamaki Dr ya kalle ta ya ce "At this tym za ki birthday, yanzu fa aka yi sallar magrib, shine kike shirin fita, wai da izinin wa za ki fita". "Haka aka yi fixing din tym d'in sannan kasan dai yanda mu ke da Leema, kasan ya kamata in halarci birthday d'in ta" Meema ta fad'a kai tsaye. " Ba za ki ba" Dr ya fad'a. Da sauri ta kalle shi ta ce "Because of what yaya Sadik za ka ce ba za ni ba". Dr ne ya ce " Saboda ni ke da iko da ke tun da ina matsayin mijin ki". "Amma Yaya Sadik kasan dai Leema ba za taji dad'i ba in ban yi attending ba saboda kasan she is my close friend" Meema ta fad'a cikin marairaicewa. "That's your business not mine" Dr ya fad'a cikin ko in kula. Wayar shi ya fara pressing ba tare da ya k'ara kula ta ba. Mik'ewa tsaye tayi cikin b'acin rai ta ce " Am sorry Dr, but i must attend that birthday, akan nayi aure sai ka ce ba zan dinga fita ba, am social yaya Sadik, so gaskiya ba zan juri takura ba, sai na dawo Yaya Sadik". Tana gama fad'ar haka ta nufi bakin k'ofa. Bin ta yayi da kallo har ta fita daga d'akin. Dafe kan shi yayi saboda a yanzu ba ya jin zai iya jurar abin da Meema ke mi shi. Nadamar rabuwa da ni ne ya fara d'awainiya dashi. A yanzu ya rasa mafitar da zai Samar wa kan shi. Tashi yayi ya d'auki key d'in motar shi ya bar gidan. A can b'angare na kuwa gashi ina Neman fin wata a Abuja amma har yanzu babu alamar komawa ta Kaduna. Tun san da Yaya Faruk ya fad'a min magana san da na mi shi magana ya fad'a min magana na k'ara shayin in k'ara tunkarar shi da maganar. Abbu ya kira yaya Faruk ya mi shi magana akan ya dawo dani Kaduna. Yau ina zaune a d'aki Nana ta shigo ta sanar da ni yaya Faruk na kira na. Bayan ta fita ne na biyo ta a baya. D'aya daga cikin kujerun na nemi guri na zauna. "Yaya Faruk sannu da hutawa" na fad'a. "Yawwa" ya fad'a a tak'aice. Ni ce na ce "Gani yaya Faruk". "A satin nan in na samu free time zan maida ke Kaduna, Abbu mun yi waya dashi ya ce in dawo da ke". " To yaya Faruk " na fad'a cikin sanyin murya. Shiru ne ya ratsa kafin yaya Faruk ya d'aura da cewa "Za ki iya tafiya". Tashi nayi na koma d'akin. Abubuwa biyu ne suka had'un min a lokacin, farin cikin komawa ta Kaduna da kuma fargabar had'uwa ta da Abbu. A satin yaya Faruk ya nemi excuse a gurin aiki. Ran da za mu tafi sai da na ji wani iri a raina saboda yanda muka saba da Nana. Naji dad'in zama da ita saboda yanda ta ke sakar min fuska duk da tasan alak'ar soyayya ta tab'a had'a ni da mijin ta, halayen Nana sun burge ni saboda yanda ba ruwan ta da shiga harkar abin da ba ruwan ta, gashi magana ba ta dame ta ba. Da za mu tafi haka ta had'o ni da tsaraba. Har gurin mota ta raka mu, sai da ta ga fitar mu sannan ta koma cikin gida. Tun da muka d'auki hanya ba Wanda ya kula d'an uwan shi har muka kawo Kaduna. K'ira'ar Sheikh Shureim kad'ai ke tashi a motar. Wannan tafiyar ba ta min dad'i ba saboda yanda shirun ya min yawa, shi yaya Faruk nasan daman magana ba damun shi tayi ba. Tun da muka doshi gidan mu gaba na ke fad'uwa har mu ka k'arasa cikin gida. Ko da muka isa parking space yaya Faruk ya riga ni fitowa. Jiki a sanyaye na fito na bi shi. San da na shiga samun yaya Faruk nayi suna gaisawa da Ummu. Sallama nayi Ummu ta amsa min. Tun da na shigo Ummu ta ke bi na da kallo. A lokacin ba abin da nake buk'ata da ya wuce in ji ni jikin Ummu. Jikin Ummu na fad'a na fashe da kuka. Ummu cikin lallashi ta fara shafa baya na tana cewa "Miye abin kuka". " Ummu am sorry, ki yafe min" na fad'a cikin kuka. "Ya isa haka Auta, ai na ce na yafe miki, ki je d'aki anjima za muyi maganar". Had'a ido muka yi dashi yayi saurin kau da fuskar shi. Tashi nayi na tafi d'aki na, d'akin da na d'auki shekaru ba na kwana a cikin shi sai gashi a yanzu na dawo da niyyar zama a cikin shi. Haka naci gaba da kuka na har bacci yayi awon gaba dani. Bayan tafiya ta d'aki ne Ummu ta dinga yi ma yaya Faruk godiya a bisa rik'e ni da yayi. Sun jima suna hira kafin ya mata sallama akan da daddare zai zo su gaisa da Abbu. Da daddare tun da naji dawowar Abbu na rasa sukuni. Ummu ce ta shigo ta min magana akan in fito in gaida Abbu. Jiki a sanyaye na fito daga d'akin na tsugunna nesa da Abbu. San da na gaishe da Abbu ba laifi ya amsa min ba yabo ba fallasa. Abbu ne ya d'aura da cewa "Fatima, a yanzu nasan kin fahimci mecece rayuwa da yanda rayuwa ka iya canzawa a kowane lokaci, nasan a yanzu ki d'auki darasi ko akan abin da shi Sadik d'in ya miki, Ni da Ummun ki wani irin so da kulawa da so ne ba mu nuna miki ba amma saboda soyayya kika zab'i faranta ran ki akan namu farin cikin, a gaban mutane Fatima nasa miki sharad'i dan ki janye k'udurin ki amma ba ki duba hakan ba kika ce kin amince da sharad'in da na sa miki, ko a lokacin raina ya b'aci da abin da kika yi amma saboda fushi na illah ne a gare ki yasa nayi saurin yafe miki a lokacin, yanzu kin ga sakayayyar da Makauniyar soyayya ta jawo miki, shi yasa San da Faruk ya zo min da maganar ki na ce mi shi kar ya kawo min ke tun da ke da kan ki kika yarda da sharad'in da na sa miki, ko a yanzu na ji ciwon rabuwar da kika yi da shi Sadik d'in". Maganganun Abbu ba k'aramin tab'a min zuciya yayi ba, nasan ban kyauta ma su Abbu ba. Kusa da Abbu na zo na tsugunna ina cewa " Abbu ka yafe min, na gano kuskure na, insha Allah ba zan k'ara kwatanta irin laifin da nayi ba..." Na k'arasa maganar da fashewa da kuka. Sunkuyar da kan shi Abbu yayi kana ya d'ago ya kalle ni ya ce " Na yafe miki Fatima". "Na gode Abbu" na fad'a cikin kuka. Ummu ce ta d'aura da cewa " Fatima ita Makauniyar soyayya da kike gani ba ta da amfani, ba abin da take jawowa fa ce danasani, duk soyayyar da idon ka zai rufe ba ka ji ba ka gani sannan ba ka duba me nan gaba za ta haifar maka sannan ba za ka ji shawarar da mutane suke ba ka akan ta ba, to wannan soyayya ba alkhairi ba ce, ina fatan kamar yanda kika fad'a cewa kin gano kuskuren ki hakan yake har cikin zuciyar ki, ina fatan kin d'auki maganar da ni da Abbun ki muka mi ki". "Na d'auka Ummu, insha Allah ba zan k'ara kwatanta irin laifin da na yi a baya ba" na fad'a. Haka Abbu da Ummu suka ci gaba da min fad'a da nasiha kafin daga bisani Abbu yace in tafi in kwanta. Tun daga wannan lokacin na samu sukuni a raina had'e da walwala saboda yanda na samu yafiyar iyaye na. Cikin ikon Allah sai gashi Allah ya cire min k'ulafuncin Dr a raina. Na cire ma raina tunanin shi dan guje ma kaina wata matsalar. A haka na ci gaba da zama a gidan mu. Lokacin da muka yi waya da Aisha take cewa za tazo gida na nake fad'a mata rabuwar da muka yi da Dr. Ta jajanta min kana ta ce min za tazo. Ba a d'au wasu lokaci ba sai gashi tazo. A hirar da muka yi da ita ne take fad'a min taji labarin Dr ya yi aure. San da ta fad'a min ban nuna damuwa ta ba duk da a lokacin sai da na ji b'acin rai a zuciya ta. Mun dad'e da ita muna hira kafin ta min sallama ta tafi. A haka lokaci ya dinga tafiya, sai gashi har na gama iddah ta, har lokacin Dr bai maida ni d'aki na ba. Hakan yasa Abbu yasa aka je gidan Dr aka d'ibo min kaya na. Tun bayan tawowa ta daga Abuja muna waya da Nana muna gaisawa da ita, San da ta kira ni ne take fad'a min sun rubuta final exam d'in su, ta had'a Degree d'in ta, na taya ta murna kana muka yi sallama. Yanzu ma Anisa tana final class d'in ta na Degree. Yau muna zaune da Abbu da Ummu muna hira da daddare bayan tafiyar su Yaya Aminu da Yaya Khalil. Bayan mun gama hirar ne Abbu ya kalle ni ya ce "Fatima tun da kin gama iddar ki, ina ganin ya kamata ki shirya ki je can Wagini gurin Hajiya, ina so in Neman miki aiki saboda ki rage zaman kad'aici, in an sami aikin zan sa Khalil ko Aminu su je so d'akko ki". Jin tafiya ta Wagini yasa jiki na ya k'ara sanyi, a yanda na fahimta in na tafi Wagini ban San ranar dawowa ta ba tun da Abbu yace sai ya Samar min aiki, babban fargabata shine yanda in naje Hajiya za ta tasa ni gaba akan rabuwa ta da Dr dan tun lokacin da ban auri yaya Faruk ba tasa ni a gaba, nasan in dai naje Wagini sai nayi hak'uri da Hajiya, a yanzu ban da kuma damar cewa Abbu ba na son zuwa Waginin ko dan kar in b'ata ma Abbu rai. " Allah ya kaimu Abbu" abin da na iya fad'a kenan. "Amin Fatima" cewar Abbu. Jiki a sanyaye na tashi na tafi d'aki. [10/2, 20:56] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com facebook: Kainuwa Writers Association _Ina mik’a sak’on gaisuwa ta da fatan alkhairi ga wanda suka kira ni a waya, da wanda suka min magana ta pc da groups akan rashin lafiyar da na yi_. _Ba abin da zan ce muku sai dai in muku godiya a bisa yadda ku ka nuna kulawar ku gare ni_. _Allah ya bar zumunci ya saka muku da mafificin alkhairi_. _Allah na ke rok’o gaba d’aya ya biya mana buk’atun mu na alkhairi ya kuma yaye mana damuwar mu_. _Allah ka zab’a mana abin da yafi zama alkhairi a gare mu_. *TUNATARWA*: *JAN HANKALI* *IDAN KA/KI AIKATA ABUBUWA UKU IMANIN KA/KI ZAI K’ARU:* 1. *Tilawar Alk’ur’ani*. 2. *K’iyamul- laili*. 3. *Azkar* *Za ka/ki fuskanci matsala a kabarin ka/ki idan ka/kika mutu da abu uku:* *Hakk’in wani* *Dabi’ar Annamimanci* *Hassada* *Abubuwa uku su na kau da Fushin Allah akan bayin sa* *Istigfari* *Tausaya ma wani* *Sadaka* *Ya Allah ka bamu ikon kiyayewa*🙏🏽 99-100 Tun da na koma d’aki nake tunanin tafiyar da za mu yi wagini, tunanin da ya tsaya min a rai shine yadda zaman mu zai kasan da Hajiyan wagini idan na je Waginin dan na san dole ne sai na toshe kunne na a duk abin da za ta fad’a min min, matsala ta ita ce ban san tsawon lokacin da zan d’auka a can ba, abin da na sa ma raina shine in yi hak’uri da duk abin da zan fuskanta a gurin Hajiyan wagini, da wannan tunanin na samu na ajiye tuanin tafiya ta Wagini. A na gobe za mu tafi Abbu ya kira ni ya sanar dani in had’a kaya na gobe za muyi tafiyar in had’a kaya na. Amsa mishi na yi da Allah ya kaimu kana na tashi na koma d’aki. Ummu ce ta shigo d’akin ta same ni bayan na koma. A yanayi na da ta kalla tasan ina cikin damuwa akan wannan tafiyar da za mu yi, ita kan ta na lura kamar Ummu tafi son in zauna kusa da ita, sai dai ba yanda za tayi ne. Ummu ce ta kira suna na "Fatima". Amsa mata nayi da cewa "Na’am Ummu". Ummu ce ta ce "Fatima ba na so ki sa damuwa akan wannan tafiyar da za ki yi, da nan da Wagini duk d’aya ne, ni kaina zan fi so ki zauna a nan d’in amma tun da Abbun ki ya ce za ki zauna a can ne Kafin ya sama mi ki aiki, nasan ko da aikin bai samu da wuri ba zai iya cewa ki dawo, ina so ki natsu Fatima dan ke ba yarinya ba ce, duk abin da kika ga ya samu bawa rubutacce ne daga gurin ubangiji, ba na so ki ci gaba da sa damuwa a ranki akan abin da ya faru da ke, idan kin je Waginin ba na so ki yi abin da Hajiyan Wagini za ta ce kin manta ko ki nuna b’acin ran ki akan wata magana da za ta fad’a miki, duk abin da Hajiyan wagini za ta fad’a mi ki ke kika ja ma kan ki tun da a farko kin k’i jikan ta, dole ne taji haushi, kowa yasan Hajiyan wagini mutuniyar ki ce a baya, tun kan abin da ya faru take fushi dake, ni ma kuma ban ga laifin ta ba, nasan idan ta huce za ku shirya ne, ita kan ta Hajiyan nasan in ta ji abin da ya same ki za ta sakko daga fushin da take yi, nasan daman tunanin zuwan ki wagini da kike yi kenan da kike yi kenan". "Insha Allah Ummu babu wata matsala" na fad’a. Murmushi Ummu tayi kana ta ce "yawwa Auta ta". Nima murmushin nayi. Da haka muka canza wata hirar. Washegari ni da Abbu muka d’auki hanyar Wagini. Wajen la’asar muka isa Wagini. Da zuwan mu Hajiya tarbe mu da abinci kala-kala kasancewar Abbu ya fad’a mata zuwan mu. Bayan mun huta ne Ummu ta kalle ni ta ce "Laila-Majnun ashe har da ke aka zo, ina kika bar Majnun d’in naki". Sunkuyar da kaina nayi ba tare da nayi magana ba. Maida kallon ta tayi gurin Abbu kana ta ce "Ibrahim ina fatan dai lafiya ko, tun da ka ce min kana nan zuwa da Fatima na ke ta tunanin Allah yasa lafiya". Abbu ne ya amsa mata da "Lafiya lau Hajiya, daman Fatima na kawo za ta zauna a nan ta kwana biyu kafin ta koma Kaduna". Hajiya ce ta amshi maganar da cewa "Ibrahim ban son shiririta, me ya faru da za ta zauna a nan, ina ta bar mijin na ta, ko shi mijin ne ya ce ta zo tayi hutu a nan". "Ko d’aya Hajiya, sun rabu da mijin ne, yau sama da wata uku kenan, shine na ce bari in kawo ta nan kan in samar mata aiki ta fara zuwa" cewar Abbu. Da sauri Hajiya ta ce "Yau na ji abin da ya fi k’arfi na, kana nufin wai shi mijin na ta ya sake ta, yanzu sakayyar da yaron nan zai mana kenan shi ne zai maida min jika k’aramar bazawara, duk irin son da yarinyar nan ta nuna mishi amma shine zai mata haka, soyayyar da Fatima ta nuna mishi ni ina jin in ba a irin wasan indian nan da nake jin labari ba na dad’e ban ga irin soyayyar haka ba, saboda shi tambad’ad’d’en yaro ne shine zai mata sakayya da butulci, amma wannan yaro ko watsatstse, yanzu da d’an uwan Soja ki kika aura ai da ba ki fuskanci haka ba amma ki ka na ce sai wannan Likitan, yanzu ba ga irin sakayar da ya saka mi ki da ita ba kenan, kema ai da laifin ki da kika na ce sai shi kika nuna mi shi makauniyar soyayya shi yasa zai mi ki sakayya da haka dan jakar uban ki, oh ni na ga abin da zan gani". Hajiya na gama maganar ta fashe da kuka. Da lallashi da k’yar Abbu ya samu tayi shiru. Ganin hakan yasa na tashi na shiga cikin d’akin Hajiyan Wagini dan nasan ci gaba da zama na a falon zai sa Hajiya ta ci gaba da min mitar ta. Wajejen k’arfe biyar Abbu ya d’auki hanyar komawa Kaduna. Ranar na sha mita a gurin Hajiyan wagini, ganin duk maganar da za ta min da ta danganci akan Dr ne ba na kula ta yasa ta gaji tayi shiru. Haka zama na ya ci gaba da gudana a Wagini tun ban saba da zaman garin ba har na zo na saba. Sai da na d’auki kusan Wata biyu a can kana Abbu ya turo yaya Khalil ya zo ya d’auke ni. Ran da zan tafi haka Hajiyan Wagini ta dinga kuka wai zan tafi in bar ta bayan ta saba zama dani. Ni kaina sai da nayi hawaye dan nima zaman garin ya min dad’i. Da haka muka yi sallama da Hajiya muka tafi. A hanya haka muka dinga hira da yaya Khalil a cikin mota har muka k’arasa Kaduna. Sati na d’aya da dawowa Abbu ya kai ni in da ya samar min aiki a Bureau of Statistics. Sai da suka min intetrview suka ce za su neme ni. Bayan kwana biyu da yin interview d’ina suka turo min message a Gmail d’ina sun d’auke ni aiki. Na yi murna da wannan aikin da na samu dan nasan zai d’ebe min kewa da tunani. Haka na fara suwa aiki na cikin kwanciyar hankali. Ban wani dad’e ba na saba da ma’aikatar gurin sannan ta b’angare na ina jin dad’in aikin. Cikin haka ita ma Anisa ta had’a Degree d’in ta. A yanzu baa bin da na sa a gaba na da ya wuce aikin da nake yi dan a yanzu ina ganin soyayya ta koya min darasi. A b’angaren Dr kuwa kullum zaman shi da Meema abin yak’i daidaituwa yayin da damuwar shi ke ci gaba da danasanin rabuwa da ni da yayi da kuma matsanancin so na da ke addabar shi. Yau ranar ta kasance ranar lahadi. Dr ne a zaune a gurin hutawa da aka k’eb’e a gidan. A kan table d’in drinks ne kusan kala uku a ajiye da d’an k’aramin kofi a ajiye. Wayar shi da ke hannu shi yake kallon wani pix d’ina da ke gallery d’in shi. Bai ji tafiyar Meema ba sai ganin ta yayi a gaban shi. Wani dogon tsaki ta ja kana ta d’aura da cewa "iska na wahalar da mai kayan kara, yanzu kai yaya Sadik ba ka da aiki da ya wuce ka tasa hoton tsohuwar matar ka a gaba kayi ta kallo, kasan kana son ta ka rabu da ita, in ban da abin ka yaya Sadik ga ni ka samu mai za kayi da wata banza wacce ba ta fi ni da komai ba, in son da take nuna maka ne ina ganin ai nafi ta son ka". Daman a cike yake da Meema ga kuma maganar da take fad’a mishi ba tare da ta tauna harshen ta ba dan haka tashi yayi ya tsinka mata mari wanda ya girgiza ta. Kuka ta fashe dashi tare da rik’e kuncin ta. Cikin kuka ta ce "Yaya Sadik you slap me". "Yes na mare ki ko za ki rama ne" Dr ya fad’a cikin hassala. Meema ce ta ce "Dan na fad’i gaskiya shine za ka mare ni, to yanzu na sa k’afar fad’a maka gaskiya, dan ba zan juri ganin kana kallon hoton wata y’ar iska ba a cikin gidan nan". Yanda Dr yake jin ran shi a b’ace yana ganin zai iya ma Meema hukuncin da bai kamata ba dan haka cikin tsawa ya ce "Meema you better leave this place or else I will teach you a lesson sannan da kike maganar Zarah in dai a waje na ne ta fi ki komai a guri na, son da na ke mata ba zan tab’a miki irin shi ba, son ta daban yake a cikin zuciya ta, ke in ban da darajar Momi da kika ci da kuma tausayin ki da nake yi da zan aure ki ne har za ki samu damar yi min rashin kunya". Ci gaba yayi da cewa "Meema ba ki san ni ba ne, k’yale ki kawai nake yi". Ganin yanda ran shi ya ke a b’ace yasa ya bar gurin dan yasan ci gaba da tsayuwar shi a gurin zai iya sa ya yanke ma Meema mummunan hukunci. Tun da ya bar gurin Meema ta bi shi da kallon mamaki. Washe gari Dr bayan ya dawo aiki ya wuce gidan Momi. Bayan sun gaisa ne Momi ta tambaye shi aiki kana suka ci gaba da hira. Cikin hirar ne Momi ta canza hirar da cewa "Sadik wai b aka da lafiya ne?". Amsa mata yayi da cewa "Me kika gani Momi". Cikin kulawa Momi ta ce "Sadik na ga ka canza ne ka rame, sai ka ce wanda yayi jinya, in da abin da yake damunka ka fad’a min". Murmushi yayi kana ya ce "Momi ba abin da yake damu na, in ma dai akwai abin da yake damu na bai wuce matsala ta da Meema ba, har yanzu zaman mu ya k’i zama normal da ita, sai tayi kamar ta canza sai ta dawo da halayen ta, gaskiya Momi na gaji da halayen Meema, sai a yanzu na ke k’ara danasanin rabuwa ta da Zarah dan ita ba haka take min ba, tana k’ok’arin duk abin da tasan zai sa ni farin ciki da kiyaye abin da ba na so sab’anin Meema da ban isa da ita ba, kullum ita tana nuna min tana da right na kan ta". Nisawa Momi tayi bayan ta gama jin bayanin Dr kana ta d’aura da cewa "Ka ci gaba da hak’uri Sadik, nasan Meema ba ta kyauta maka akan wasu abubuwa da take yi, amma idan ka ci gaba da hak’uri da ita da nusar da ita nasan za ta gyara tun da tana son ka, idan ba ta gyara ba zan tsawatar mata, mace sai da lallab’awa da lallashi ka ji ko Sadik". "To Momi zan yi yanda kike so amma in ta kai ni k’arshe zan ba ta mamaki" Dr ya fad’a. Shiru Momi ta yi ba ta k’ara cewa komai ba dan ita kanta ta gaji da k’arar da Dr yake kawowa akan Meema. Ci gaba da lallashin shi Momi tayi tare da nusar dashi akan kar yasa damuwa akan shi. Ya ji dad’in shawarwarin da Momi ta bashi dan ya samu relief akan damuwar da Meema take sa mai. Sai da ya ci abinci a gidan kana ya tafi dan yasan ba lallai ba ne in Meema tayi girki dan sai ta gadama take yi. Ko san da ya koma gida samun ta yayi a side d’inta tana hakimce yayin da music ke tashi a home theatre dake jone a wajen Tv d’in. Tun da ya shigo da sallama ta amsa mishi ciki-ciki kana ta d’auke kanta daga gurin shi ta ci gaba da bin wak’ar da ake yi. Mamaki ne ya cika shi na irin halin Meema yanda ba tasan ta tarbi miji in ya dawo ba ko ta amsar masa jaka ko wani abu in yana rik’e dashi a lokacin da ya dawo, sai dai in taso ne za tayi hugging d’in shin a welcoming d’in shi. Ganin ba kula shi za tayi ba yasa ya ce "Meema ba ki ganni ba ne". Juyowa tayi kana ta ce "Ni ko na gan ka yaya Sadik tun da ga ka a zaune kusa da ni". "Amma dan iskanci kin fi k’arfin ki min sannu da zuwa ko ki tarbe ni" cewar Dr. "Sorry yaya Sadik tun da ni ba wuya na yi laifi" Meema ta fad’a a yatsine. Jan tsaki Dr yayi ya mik’e ya bar gurin ba tare da ya k’ara cewa komai ba dan in da sabo ya saba da halin Meema. Bin shi tayi da kallo ta ja kana k’aramin tsaki kana ta ci gaba da bin wak’ar ba tare da wata damuwa ba. Washe gari ba laifi san da Dr ya dawo daga aiki ya samu tarba da kulawa a gurin Meema. Sai da ta raka shi har d’akin shi kana ta had’a mishi ruwan wanka sannan ta fito falo ta kunna wata wak’ar indian tana tik’ar rawa kamar a k’asar indian take. Bayan ya fito daga wanka ne ya nemi simple dress ya sa kana ya fito falo. Tsayawa yayi kawai yayi yana kallon ta ganin yanda take tafiyar da rawar kamar dan ita aka yi wak’ar. Ya kai kusan minti biyar a tsaye ba tare da Meema tasan da tsayuwar Dr a gurin ba. Extension wire ya je ya kashe kana cikin d’aurewar fuska y ace "Wai ke Meema wannan rawar da wak’e-wak’en da kike yi ba ya isar ki ne, atleast ya kamata a ce komai yana da time d’in shi". Turo baki tayi kana ta ce "Haba yaya Sadik ya ina cikin rawa na za ka zo ka kashe min, kasan I have the right to make myself entertain, so ni ban ga aibu ba a abin da nayi da kake complain". Yasan in ya ci gaba da biye ma Meema ranshi ne zai b’aci dan Meema tayi nisa a koyi da rayuwar turawa dan haka ya ce "Ni Meema ba na ce kin yi laifi ba ne amma ya kamata ki rage jin wak’e-wak’en nan dan ba abin da yake jawowa sai shaid’anu a cikin gida, ina fatan kin fahimce ni". Kusa dashi ta zo ta zauna ta ce "Na fahimta". Amma a cikin ran ta ba k’aramin haushin kashe mata wakar da take ji tayi ba. "Meema ina abinci na yunwa na ke ji" Dr ya fad’a. D’aure fuska tayi dan tasan yanzu nan za su sami matsala da Dr a rashin girkin da ba tayi ba ta ce "Ban yi girki ba yaya Sadik". "Saboda me yasa ba ki yi girkin ba" Dr ya tambaye ta. Meema ta amsa masa da cewa "Ina sha za ka biya gidan Momi ka ci ko restaurant ka ci shi yasa ban dafa ba, infact kasan ni girki ba favourite d’ina ba ne". Cikin b’acin rai ya ce "Wannan shine reason d’in ki da ba ki yi girki ba, kullum ni kuma sai in tafi gurin Momi ko restaurant in ci abinci alhalin ina da mata, impossible! Meema ina d’aga miki k’afa amma ba ki sani ba, sau nawa nake miki magana akan rashin yin girkin ki amma kin k’i canza wa, sai dai in na dawo in nemi drinks ko tea in sha idan ba ki yi girki ba saboda wata cutar ta kama ni, in ke ba ki damu da lafiyar ki ba ni na damu da tawa, Meema you better Know what you a doing beffer I show you the other side of me". Yana gama fad’ar haka ya mik’e ya shiga d’aki ya d’akko key d’in motar shi ya bar gidan. Ita kuwa Meema ba abin da ya dame ta akan fushin da Dr yayi dan tasa ma ranta cewa Dr ba zai matsa mata ba akan girki ba, ta aure shi ne dan tana son shi ba wai dan tazo ta maida kan ta baiwa a cikin gidan ba. Haka dai zaman gidan Dr ya ci gaba da gudana yau fari gobe tsumma. A b’ngare na kuwa ba ni da wata sauran damuwa dan ina k’ok’arin ganin na kiyaye duk wani tunani da zai dame ni. Cikin d’an lokaci sai gashi na canza na yi fresh ga kuma aiki na da nake zuwa. Haka lokaci ya ci gaba da tafiya. A cikin haka ne Nana ta haifi d’iyar ta mace. Tun da na ji labarin haihuwar Nana na k’ara tausaya ma kaina dan ni ban san lokacin da zan mallaki d’an kaina ba tun da yanzu ban a tare da Dr ga kuma planning d’in da nayi wanda ban san ko ta dalilin haka na sami matsala ba. A na gobe suna su Ummu da Anty Jidderh za su tafi Abuja dan haka nima na nemi excuse gurin aiki na muka tafi tare. Ita Anisa ta riga mu tafiya dan ita kwanan ta biyu da tafiya kenan. Tun da muka isa Abuja nayi arba da yarinyar na ji yarinya ta shiga raina. Ji na ke yi kamar ni na haife ta saboda son ta da ya shigar min rai. Yanzu duk wata haihuwar da za a yi a family sai na ji ina ma ni ce aka zo yi min murnar haihuwa. Nasan wannan tunanin da nake yi yana da alak’a da son ganin d’an kaina ganin yanda lokaci ke tafiya. Nasan yanzu yanda nake nemn kusan shekara da rabuwa ta da Dr ba zai yiwu in ci gaba da zama a haka ba, Abbu da Ummu nasan sun zuba min ido su ga iya gudun ruwa na. Ni kaina yanzu na ajiye maganar Dr a gefe tun da gashi ina neman shekara d'aya ba tare da yazo yayi biko na ba akan in koma gidan shi ni ma kuma ban damu da hakan ba dan nasan na fuskanci k’alubale a zaman mu. Fata na yanzu shine Allah ya zab’a min abin da yafi zama alkhairi a gare nib a wai son raina ba dan nag a illar Makauniyar Soyayya. Tun da muka zo na tare a d’akin Nana rik’e da babyn da aka haifa, sai dai in an zo barka ko za a ba babyn nono zan ba da ita. Su Anisa da Anry Jidderh sai tsokana ta suke yi wai in yi aure tun da baby nake so. Murmushi kawai nayi kawai nayi ba tare da nayi magana bad an ni a yanzu ban san wanda zan tsayar a matsayin miji na ba. Ranar Suna yarinya taci sunan Momi Rukaiyya ana kiran ta da Khairat. An yi k’ayatacciyar walima tare da kayan rabo na alfarma. Haka taron sunan ya watse sai dai mu ce Allah ya raya Khairat. Washe gari ta kasance ranar Asabar, a ranar ne su Ummu da Anty Jidderh da Anisa suka koma Kaduna. Ni kuma na ce sai ran litinin zan koma dan excuse d’in da na nema har da ranar litinin na nemi excuse. Yanda yaya Faruk na ga yana kula da Nana da khairat hakan ya k’ara burge ni, ko yana gurin aiki haka zai dinga kiran ta a waya yana tambayar ta ko akwai abin da take so ko in zai fita aikin. Idan yana gida kuwa baby na hannun shi. A kwana biyun da nayi wani tunani ne ya d’arsun min a zuciya ta wanda nasan ba abu ne mai yuwuwa ba. Tunanin da na fara sa ma raina shine ina ma yaya Faruk zai aure ni ya ajiye abin da na mi shi. Sai a yanzu nasan yaya Faruk shine irin mijin da ya dace in aura wanda zan samu dukkan kulawa kamar yanda yake ba Nana kulawa. Nasan in har na auri yaya Faruk nayi dace sannan nasan zan samu soyayyar shi kamar yanda ya nuna min a farko. Ni kaina a yanzu zan iya cewa ina jin yaya Faruk a raina tare da tunanin shi wanda ni kaina zan iya cewa son yaya Faruk ne ya fara shiga na a lokacin da ban yi tsammani ba. Sai dai yanzu abin da ya fi damuna shine yanda har yanzu yaya Faruk ya k’i sakar min fuskan shi bare mu zaun mu yi hira da shi irin na ya da k’anwar shi. Ran litinin na baro Abuja na dawo Kaduna tare da kewar Khairat a raina. Shi kuwa Dr damuwar da ya sa ma kan shi ya sa jinin shi yau, ko da yayi ma kan shi gwaji ya tabbatar da BP d’in shi ya hau amma hakan bai sa ya rage tunanin da yake yi ba. Yanzu tunanin da Dr yake yi shine yanda zai iya tunkara ta ya bani hak’uri in amince dashi ga wani irin so na da yake d’awainiya dashi wanda bai tab’a min irin shi ba sai a yanzu. yanzu lamarin Meema ya fara isar shi dan haka ba ko wane abu ba ne yake biye mata sai dai ya zuba ma ta ido ya ga iya gudun ruwan ta, sai dai in ta kai shi k’arshe ne yake tsawatar mata. Yanzu damuwar da yake ciki ta shafi har b’angaren aikin shi domin yawan patient d’in da yake duba wa a da a yanzu ba ya duba mutane da yawa, har gurin aikin abokan aikin shi sun san Dr ya canza a yanayin aikin shi saboda yanda a ka san shi da jajircewa da nuna k’ok’arin shi ta b’angaren aiki. Yau Meema ce zaune a falo tana kallon wani American film a lokaci d’aya tana pressing d’in wayar ta. Knocking d’in da aka yi bai sa ta tashi ta bud’e k’ofar ba sai ma ci gaba da kallon ta da take yi. Sai da aka yi knocking kusan uku sannan Meema ta tashi ta je ta bud’e k’ofar. Ganin su Hanan ne da Farida yasa ta d’an saki fuskarta ta ba su guri suka shigo. Bayan sun zauna ne Farida ta gaishe da Meema ta amsa ba yabo ba fallasa yayin da Hanan ta kau da kan ta ba tare da sun gaisa da Meema ba dan yanzu ba wani shiri su ke yi da Meeman ba. Sun kai minti goma a zaune ba tare da Meema ta kula su ba ko ta tashi ta d'akko musu abin motsa baki. Hanan Wanda ran ta ya fara b'aci da shariyar da Meema ta musu ta ce "Meema yanzu abin da kika yi kin kyauta kenan". Juyo da kallon ta tayi ga Hanan kana ta watsa mata harara ta ce " Me nayi da za ki ce na kyauta". Hanan ce ta ce "Yanzu mu zo gurin ki amma ki yi banza da mu kamar ba ki san da zaman mu a gurin ba, ina ganin ko da ba ki san mu ba muka zo gidan ki bai kamata ki mana irin wannan tarbar ba". Cikin fad'a Meema ta ce "Me kike so in muku Hanan, mun gaisa da Farida ke ko darajar gaisuwa ban samu a gurin ki ba amma kin fara k'orafi, Goya ku kike so in yi dan in nuna nayi farin cikin ganin ku ko me kike so in yi". Hanan ita ma cikin b'acin rai ta ce "Ban buk'aci Hakan a gare ki ba amma ki sani ba zan juri wulak'anci ba dan ke kan ki shaida ce akan haka". " To ki d'auki mataki mana Hanan ina ganin ai zai fi akan wannan surutun da kike yi, kin san dai ban son hayaniya" cewar Meema. "Ba yanzu zan d'auki mataki ba sai lokacin d'aukan matakin yayi" Hanan ta fad'a. Duk wannan maganganun da su Meema ke yi Farida ba ta tsoma bakin ta ba sai ma tab'e bakin ta da tayi ta ci gaba da danna wayar ta. Tasan a cikin su ba Wanda za ta ba wa hak'uri ya hak'ura hasalima sun fi kusa tun da k'awaye ne. Sai da ta ga hayaniyar su na ci gaba sannan ta sa baki. Da k'yar ta samu suka yi shiru. Haka falon ya d'auki shiru kamar ba mutane a ciki. Sun kai kusan minti sha biyar a zaune ba tare da Meema ta tashi ta d'akko musu abin sha ba, hakan yasa Farida ta tashi ta d'akko musu drinks a fridge. Ko kallon in da suke Meema ba ta sake yi ba. Sun kai kusan awa d'aya a zaune amma Meema ba ta da niyyar tashi ta kawo musu abinci dan haka cikin wasa Farida ta ce "Anty Meema yunwa fa na ke ji, me zan samu ne". "kitchen d'in ai ba bak'on ki ba ne, za ki iya tashi ki dafa, a yanzu ba Wanda ya isa ya tashe ni in je in muku girki dan ni ba baiwa ba ce, na ga kuma a gidan ba son yin girkin ku ke yi ba" Meema ta fad'a kai tsaye. Cikin Mamaki da amsar da Meema ta ba su ta ce "Anty Meema me ya kawo wannan maganar, daga wasa sai ki fad'a min wannan maganar, Allah ya baki hak'uri". Hanan ce ta k'arb'i maganar da cewa "For what reason za ki ba ta hak'uri bayan ita yakamata ta baki hak'uri akan maganganun da ta fad'a, da kike cewa ba ma girki amma ai ke kan ki kin san mun fi ki dan ba abincin da ba za mu iya dafawa ba, kin ga kenan mun fi ki". Nan Meema da Hanan suka ci gaba da musayar yawu. Da k'yar Farida ta samu Hanan ta tashi suka tafi gida. Ko da su ka koma gida Hanan ta fad'a ma Momi abin da ta musu. Ran Momi ya b'aci jin wulak'ancin da Meema ta ma su Hanan sai dai tayi k'ok'arin danne fushin ta dan ba ta son ta sa bakin ta tun da tsakanin su da su Hanan ne. Ita kan ta Momi sai yanzu ta gano abin da yasa Momi ke kauce ma auran Meema lokacin da ta ce ya aure ta. Yanzu ga shi nan sai matsaloli ke kunno kai. Fatan ta dai komai ya daidaita ya dawo normal. Ni kuwa ta b'angarena na shiga tsaka mai wuya a tunanin da na d'aura ma kaina wanda na ke ganin kamar iska ce ke wahalar da mai kayan kara dan nasan abu ne mai wahala Yaya Faruk ya dawo da ni rayuwar shi dan ni kaina nasan ban kyauta mishi ba da kuma kunya in iya tunkarar shi in ce yanzu Ina son shi ya aure ni. Wani lokacin ji nake yi kamar In kira shi in fad'a mishi Sirrin Zuciya ta ko da ba zai yi marhabin da magana ta ba. Nasan fad'an maganar zai sa in samu sauk'i a halin da na tsinci kaina a ciki. Wannan shine tunanin da a yanzu ya fi tsaya min a rai. Yau ranar ta kasance ranar lahadi ba ni da aiki. Zaune na ke a falo Ina kallon wani Nigerian series mai suna my kids & I. Muryar Wanda na ji yayi sallama yasa nayi saurin d'agowa dan ko a ina na ke muryar ba za ta b'ace min ba. Yaya Faruk ne cikin wani tsadadden yadi kalar sararin samaniya. Amsa mi shi nayi kana na k'ara yalwata fuska ta da murmushi. Nesa da ni ya nemi guri ya zauna. Gaishe shi nayi ya amsa min ba yabo ba fallasa. Tambayar shi nayi ya Nana da Khairat ya amsa min da su na nan lafiya. A raina na ce ko yaushe Yaya Faruk ya shigo Kaduna? Gaba na ne na ji yana fad'uwa saboda na sa ma raina cewa yau zan tunkari Yaya Faruk da maganar in ji ra'ayin shi a kaina. Wani b'angare na zuciya ta kuwa kwab'a ta take yi akan in bar maganar a raina dan zan iya fuskantar b'acin rai a gurin Yaya Faruk ko ya wofintar da buk'ata ta a gurin shi. Katse min tunani na yayi da cewa "Fatima ina Ummu". " Tana d'akin ta" na fad'a. Mik'ewa tsaye yayi ya nufi d'akin Ummu yayin da na bi shi da kallo. Tashi nayi na fita na tsaya in da Yaya Faruk yayi parking d'in motar shi dan in jira fitowar shi. Saman motar na hau ina ci gaba da tattauna yanda zan tunkari Yaya Faruk da wannan maganar kai tsaye. Na d'an jima a zaune kana Yaya Faruk ya fito ya nufi in da yayi parking d'in motar shi. Da sauri na sakko na tsaya ina jiran k'arasowar shi. Kallo ya bi ni dashi gani na a tsaye a gurin motar shi. "Lafiya Fatima na ga kin tsaya a nan, ko akwai abin da kike buk'ata ne" yaya Faruk ya fad'a. "Lafiya lau Yaya Faruk" na amsa mi shi. Bai k'ara ce min komai ba ya bud'e motar shi. Ganin tafiya zai yi yasa nayi saurin cewa "Yaya Faruk dan Allah ka ban 10 min ina son mu yi magana ne". D'aure fuskar shi yayi kana ya rufe motar ya zuba min ido yana kallo na. " Ina jin ki, amma ki tabbata maganar da za ki fad'a min ba zai wuce lokacin da ki ka d'iba ba saboda ina da abin yi". Sunkuyar da kaina nayi na rasa ta in da zan fara maganar. Shiru ne ya ratsa a tsakanin mu kafin Yaya Faruk ya kau da shirun da cewa "That means kenan ba ki da abin cewa tun da kika yi shiru". Cikin kame-kame na ce " Yaya Faruk daman ina so in k'ara ba ka hak'uri akan abin da ya faru a baya, nasan ban kyauta maka ba, amma a yanzu na gano kuskure na, dan Allah Yaya Faruk ka yafe min". Kallon mamaki ya bi ni dashi kana ya ce "Fatima in dai akan wannan maganar ce ta riga ta wuce a gurina tun da na ce na yafe miki sannan ni na ki min laifi ba tun da kin zab'i abin da zuciyar ki take so ne, in ma laifi ne bai wuce yanda tun farko ba ki fito kin fad'a min gaskiyar abin da ke zuciyar ki game da ni kika dinga b'ata min lokaci kina yaudara ta, beside ni komai ya wuce a guri na". " Na gode Yaya Faruk" na fad'a cikin sunkuyar da kai. "Za ki iya koma wa cikin" Yaya Faruk ya fad'a. Ganin in dai na bar nan gurin ba tare da na fallasa ma Yaya Faruk abin da ke damuna ba dan haka na ce "Yaya Faruk...daman... so na ke yi...in nemi...alfarma...a...gurin ka....". Yaya Faruk ya ce "Wace alfarma ce Fatima". Shiru nayi ban ce komai ba ina fargabar fad'a mai. " Kin yi shiru, wa ce alfarma ce kike nema a guri na, ki fad'a min in ji ko zan iya" cewar Yaya Faruk. Cikin k'arfin gwiwa na ce "Yaya Faruk ina Neman alfarmar ka aure ni saboda ina son ka.........". *Hmmmmmm Yau ake yin ta readers tsakanin Yaya Faruk da Fatima*. *Wannan amsar na gurin Fatima da Yaya Faruk*. *Ni kaina zan so in ji wni amsa Yaya Faruk zai ba ma Fatima* *'Yar mutan Paki na mu ku fatan alkhairi*. [10/8, 21:52] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com facebook: Kainuwa Writers Association *TUNATARWA*: *KADA MUBI HANYOYIN SHAIƊAN* _Shaiɗan shine farkon wanda ya fara fifita kansa akan waninsa_. _🌸Idan kaima ɗabi'arka/ki kenan to lallai kam kana/kina bin sahunsa a cikin mabiyansa_. _🌸Ya Allah kayi mana tsari da shaiɗan da ayyuka na shaiɗanu kuma ka ƙara tabbatar da zukatanmu akan yi maka biyayya_. 101-102 Wani irin murmushi yaya Faruk yayi da na kasa fassara mai murmushin shi yake nufi. Shiru yayi kamar ba zai yi magana ba kana ya ce "Fatima ina so ki maimaita abin da kika fad’a min yanzu". Kai tsaye na k’ara cewa "Yaya Faruk ina son ka". Lumshe idon shi yayi ya bud’e kana yayi y’ar dariya ya ce "Yanzu Fatima tun da ki na so na ya za ayi kenan". Cike da karsashi na ce "yaya Faruk so na ke yi ka amince da tayin soyayyar da na maka wanda na ke fatan ta kai mu ga yin aure, yaya Faruk kai ka dace da ka zama abokin rayuwa ta saboda halayen ka abin so ne ga duk wata y'a mace". Tun da na ke maganar yaya Faruk murmushi ya k’i b’ace wa a fuskar shi, hakan yasa na d’auka zai amince da ni dan nasan har yanzu yaya Faruk yana so na, abin da na mi shi a baya ne zai sa ya danne so na a cikin zuciyar shi. Lokaci d’aya yaya Faruk ya d’aure fuskar shi kamar ba shi ba ne ya gama sakin murmushi a yanzu. "Fatima kin san abin da kike fad’a kuwa, ina tunanin ba kya cikin hankali ko kuma kina tunanin mafarki kike yi, in ma mafarki kike yi ya kamata ki farka daga nannauyar mafarkin da kike yi saboda wanda yake gaban ki a tsaye a yanzu Faruk ne d’an uwan ki a tsaye a gaban ki wanda a da kika guje ma auren shi kika ce ba shi kike so ba". Jiki na ne ya fara yin sanyi jin maganar da yaya Faruk ya fad’a min amma duk da haka na sa ma kaina dauriya na ce "yaya Faruk nasan kaine a tsaye a gaba na, abin da na fad’a maka da gaske nake yi ba wasa ba, wannan maganar da na fad'a maka har cikin zuciya ta haka yake, yaya Faruk so na ke yi ka amince da ni mu yi aure". Wata irin tsawa yaya Faruk ya daka min da tasa na firgita kana ya kalle ni ya ce "Fatima enough of this rubbish, lallai yau na tabbatar da ba ki da kunya da har ki ka iya tunkara ta da wannan maganar ba tare da kin ji shakkar fad'a min wannan maganar ba, ko da yake miye abin kunya a gurin ki tun da a da ma kika iya fad’a min ba ni kike so ba kina da wanda ki ke so, ki shiga hankalin ki kafin in dawo da ke hankalin ki". Hawaye ne ya tarun min a idanu na dan jiki na ya fara ba ni cewa b azan samu nasara ba a gurin yaya Faruk. Wata Zuciyar ta ce min kar ki yi saurin karaya ki ci gaba da bashi hak’uri har ya amince dake tun da akwai son ki a zuciyar sa. "Yaya Faruk nasan na maka laifi a baya amma na gane kuskure na, nasan ka na duba abin da na maka a baya ne shi yasa ka ke ganin kamar da wasa na ke yi, yaya Faruk ka manta baya ka amin ce min ka kuma ci gaba da so na kamar yanda a da ka so ni, yaya Faruk nasan har yanzu kana so na, b’acin rai ne yasa ka ke k’ok’arin danne so na a ranka" na fad’a. Wani irin kallo ya watsa min kana ya ce "Fatima wannan iya tunanin ki kenan, tabbas na so ki a baya, son da ban tab’a tuanin zan ma wata y’a mace a rayuwa ta ba, na shiga wani hali duk a dalilin son ki amma tun lokacin da kika nun aba ni kike so ba na sa ma kaina hak’uri da ke, na fad’a miki wannan maganar san da na je Wagini kika fad’a min kina da wanda kike so, tun a lokacin na fara rok’on Allah akan ya zab’a min abin da yafi zama min alkhairi, cikin yardar Allah sai gashi komai ya zo min cikin sauki ya ba ni ikon hak’ura da ke ya kuma musanya min ke da Nana, ba abin da zan yi sai dai in gode ma Allah da ya bani Khadijah a matsayin matata saboda halayen ta nagari sannan a yanzu ba wanda na ke so sama da Khadijah, to ki sani har yanzu ban canza magana ta ba na cewa na hak’ura da ke, kema kan ki kina yaudarar kan ki ne da kike cewa kina so na, kin fad’i haka ne saboda yanzu kin rasa mijin ki kuma masoyin ki". Hawaye ne masu zafi suka fara zubo min a idanu na saboda tausayin kaina. Ban tab’a tunanin yaya Faruk zai k’i amincewa da ni ba saboda son da yake min sai ga shi lokaci d’aya ya nuna min cewa yanzu ba ni ba ce a zuciyar shi. Har zuciya ta nake son yaya Faruk a cikin raina. Sai dai abin takaici shi ne har yanzu ina jin son Dr a cikin zuciya ta ga kuma son yaya Faruk da ya shiga zuciya ta a lokaci d’aya. A raina a yanzu na fi son yaya Faruk ya aure ni ya zama shi ne abokin rayuwa ta saboda halayen shi. Cikin dauriya nace "Yaya Faruk zan iya auran ka ko da a yanzu ba bu so na a ranka, sannan ko da a ce Dr zai dawo kai zan zab’a saboda a yanzu zuciya ta tafi karkata zuwa gare ka". "Fatima ina son maganar nan ta tsaya a iya nan tsakani na da ke sannan ina so wannan maganar ta zama ita ce karo na k’arshe da za ki k’ara fad’a min magana makanmaciyar irin wannan maganar domin in dai wannan ita ce alfarmar da kike nema a guri na ba za ki tab’a samun ta ba, ina fatan kin fahimta" cewar yaya Faruk. D’aga mishi kaina nayi sakamakon yanda na ji kuka yana son zuwa min. Tun da yaya Faruk na ji ya fad’i cewa ya hak’ura da ni na ji jiki na yayi sanyi. Nasan yaya Faruk bay a magana biyu, he is a man of one word, maganar da ya fad’a min cewa ya hak’ura da ni nasan har zuciyar shi yake fad’a min maganar. Lokacin da ya fad’a min cewa ya hak’ura da ni a Wagini ban wani damu ba saboda a lokacin ina cikin mayen son Dr. Sai a yanzu da ya maimaita min cewa ya hak’ura da Hawaye ne kawai yake zubo min a idanu na. Yaya Faruk bai k’ara ce min komai ba ya shiga motar shi ya ja ya tafi ya bar ni a gurin. Jiki a sanyaye na bar gurin na koma d’aki na. Kuka na fara yi na rashin amsa tayi na da yaya Faruk yayi. Ban tab’a tunanin yaya Faruk zai yi watsi da maganar da na zo mishi ba duba da so na da yayi a baya, sai gashi ya ban mamaki gurin bijire ma buk’atata. "Me yasa yaya Faruk ba zai manta abin da na mishi a baya ba ya amince da tayin soyayyar da na mishi?". "Why yaya Faruk" na fad’a a fili. Hawaye ne kawai yake zubo min na rashin madafa dan nasan na rasa yaya Faruk sai dai in wani ikon Allah ne zai sa ya dawo daga baya ya amince min. Na d’au tsawon lokaci ina zaune a d’aki ba tare da na samar wa kaina mafita ba. Babbar matsala ta shine yanda a yanzu ba wanda zan iya tunkara da maganar nan dan ban san yanda kowa zai d’auki magana ta ba. Nasan kowa da yanda zai fassara magana ta da canza min ma’anar magana ta, in akwai wanda ya kamata in fad’a wa maganar nan bai wuce Anisa da yaya Khalil ba ko Anty Jiddah amma nasan ba zan iya ba saboda ni kaina nasan da kunya in iya tunkarar su da cewa ina son yaya Faruk. Ba lallai ba ne su yarda da maganar da na fad’a musu, saboda haka dole ne in bar maganar nan cikin zuciya ta tare da addu’ar Allah ya kawo min mafita a ciki. Da wannan tuanin na samu k’arfin gwiwa a cikin zuciya ta. A can b’angaren Dr kuwa tunanin da yasa ma kanshi kullum gaba yake yi. Yanzu ba abin da yafi damun shi da ya wuce ya zo guri na ya bani hak’uri akan abin da ya min sannan in amince mishi a karo na biyu. Tunanin yansa zai tunkare ni yake yi saboda yasan ba lallai in saurare shi ba duba da laifukan da ya min ga kuma matsalar Meema. Ga wani irin so na da yake k’aruwa a cikin zuciyar shi wanda ko a da bai jin makamancin yanda yake ji a yanzu. Wannan tunanin su suka hana Dr sukuni. Shi kan shi Dr yasan yawan tunanin da yake yi zai iya janyo mishi matsaloli dama wanda a yanzu in ya ma kanshi gwajin BP yana hawa, yasan kuma duk tuananin da yake yawan yi ne ya haifar mishi da haka. Yau Dr ne ya tashi bay a jin dad’in jikin shi, hakan yasa ko shirin zuwa aiki bai yi ba. Ya jima a kwance ba tare da Meema ta shigo d’akin ba kasancewar in ba tayi niyya ba a side d’in ta take kwana. Wayar shi da ke kusa dashi ya samu yayi dialling d’in numbar Meema. Sai da tayi ringing biyu tana katse wa kusan sau uku sannan ta d’auka. Sanar da ita yayi yana neman ta a side d’in shi. Meema sai da ta gama jan ajin ta sannan ta nufi side d’in Dr d’in. Samun shi tayi a kwance yana lullub’e da bargo. Da sauri ta k’arasa kusa dashi ta yaye bargon da ya lullub’a da shi. Wuyan shi ta tab’a taji zafi alamar zazzab’i ya kama shi. Cikin marairaicewa ta ce "Yaya Sadik me ya same ka na ji jikin ka da zafi, ko ba ka da lafiya ne?". Murmushi yayi kana ya d’aga mata kai alamar eh. "Ina ne yake maka ciwo" Meema ta tambaye shi. K’irji na ke min ciwo da kuma zazzab’i da ciwon kai’ Dr ya fad’a. Hannun shi ta rik’e kana ta ce "Sannu yaya Sadik, Allah ya baka lafiya, ko za mu je asibitin ku ne". Girgiza mata kai yayi kana ya ce "Kar ki damu Meema, akwai magunguna a guri na, ki je ki had’o min tea sannan sai in sha maganin". Mik’ewa tayi ta je ta had’o mishi tea ta kawo mi shi. A baki ta dinga ba shi har ya sha rabin kofi. Sai da ta ga yasha magani sannan ta fita daga d’akin. Tun da Meema ta fita daga d’akin ba ta sake koma wa ba sai can da rana, ko tunanin kawo mi shi abinci ba tayi ba. Da daddare ma sai da ya rok’eta ta dafa mi shi indomie sannan ta kawo mishi. Ko da ta kawo mishi indomie d’in ba ta dad’e ba kasancewar kiran da k’awar ta tayi yasa ta fita daga d’akin. San da ta gama wayar ba ta koma ba tayi kwanciyar ta. Washe gari jikin Dr ya sake rikicewa dan har ciwon yafi na jiya. Numfashin shi da k’yar yake fita saboda condition d’in da ya shiga. Yau ko tunanin kiran Meema bai yi ba saboda ba ya jin zai iya d’aga hannun shi ya d’auki wayar ya kira ta, gashi ko Momin shi bai ce Meema ta fad’a ma wa ba yasan da tazo. K’irjin shi ne yaji yana mishi wani irin ciwo da bai san yanda zai fassalta yanda yake ji ba. Meema kuwa sai ta gama abin da take yi ta feso wanka tayi shiga na wasu k’ananan kaya ta fesa turare kana ta wuce kitchen ta had’o mishi tea ta wuce side d’in shi. In ban da k’amshi ba abin da Meema ke yi. Tana shiga d’akin ta ga halin da Dr yake ciki. Sakin cup d’in tayi ganin yanda numfashin Dr yake wahalar fita. Rik’o shi tayi ta fashe da kuka tana girgiza shi. Dr yana jin kukan Meema amma ba zai iya magana ba saboda matsanancin halin da yake ciki. Meema cikin kuka kuwa cewa ta ke yi "Dr me ya same ka, ina sha jikin ka yayi sauk’i ashe jikin yayi worst, shi yasa jiya na ce mu tafi asibiti but you refuse, yanzu ji condition d’in da kake ciki". Da sauri ta fita daga d’akin tayi wa Mai gadi su magana ya taimaka mata suka sa Dr a cikin mota. Asibitin Kangiwa Hospital in da Dr yake aiki Meema ta kai shi. Suna zuwa aka k’arb’e shi aka kai shi special room dan ba shi kulawa ta musamman kasancewar Dr babban likita ne a asibitin ana ji dashi. Meema ta kira gidan su Dr ta fad’a musu halin da Dr yake ciki kana ta kira gidan su ta fad’a musu. San da Momi suka zo da su Dadi dasu Hanan kuka suka sa ganin halin da Dr yake ciki. Dadi ne yayi k’arfin halin kwantar musu da hankali. Ita kanta Meema jikin Mominta ta fad’a tana kuka ganin halin da Dr yake ciki. Lallashin ta Dadin ta da Momin ta suka dinga yi akan ta kwantar da hankalin ta Dr zai samu lafiya. Sai da aka kwashe awa d’aya akan Dr kafin aka samu nu numfashin shi ya daidaita. Ba a bari an shiga gurin shi ba sai da aka yi kusan awa biyu saboda ana so Dr ya huta. Abokin aikin shi kuma abokin shi Dr Kamal shi ya nemi ganin Dad office d’in shi. Jin haka yasa Momi ta tashi ta bi shi dan tasan duk wani bayani da Dr zai yi ba zai wuce akan ciwon da ke damun Dr ba. Bayan sun je office d’in Dr Kamal ne ya sake gaishe su. Dadi ne ya ce "Wai Me yake damun Sadik d’in ne". Dr Jamal ne yace "Gaskiya Dadi Dr Sadik yana cikin wani hali, a binciken da muka yi akan Dr mun gane damuwa ce tayi wa Sadik yawa wanda hakan yasa ya kamu da hawan jini, nasan kuma shi kan shi Dr yasan haka kasancewar shi Likita amma bai yi k’ok’arin kiyayewa ba, sannan a binciken da muka yi mun gano cewa Sadik yana fama da Ulcer wanda ta fara mishi cronic, yawan tunanin da yake yi da kuma ulcer da yake tare da ita ya kamu da ciwon zuciya saboda ita kan ta ulcer tana iya janyo heart deasease bare kuma ga tunanin da yake yi yayi worst". A tare Momi da Dadi suka ce "Ciwon zuciya!". Dr Kamal ya ce "Ku kwantar da hankalin ku, mun yi nasarar shawo matsalar kasancewar ba sosai ciwon ya tab’a zuciyar shi ba, za mu d’aura shi akan magani sannan in dai ya daina tunanin da yake yi komai zai dawo normal, sai dai yana da kyau ku mishi magana akan ya rage tunanin da yake yi da kuma k’ok’arin cin abinci a lokacin da ya dace". Momi kuwa kuka ta fara yi tana cewa "Wani irin tunani Sadik yake yi da har ya kamu da ciwon da yake neman barazana da rayuwar shi, yanzu ban da wannan ita ma Meema sai da ta ba da na ta gudunmawar wajen d’aura mishi wata lalurar na kamuwa da ulcer dan nasan rashin shin abincin da ba yayi ne ya sa ya kamu da wannan ulcer". Dr Kamal ne ya ce "Momi zai iya yiwu bai cin abinci yanda ya kamata ne ko kuma bai cin abincin akan lokaci, ita ulcer da kike gani mutum na iya samun ta ba sai lallai ba ya cin abinci ba, wata cuta ce mai zaman kanta da a yanzu d’aid’aikun mutane ne ba su da ita". Momi cikin kuka ta ce "Ni nasan Dr abinci bai dame shi ba amma matsalar yanzu ta b’angaren Meema ce, kuma wlh wannan karan ba zan laminta ba dan ba zan bari in rasa d’ana ba". Dadi ne cikin lallashi ya ce "Take it easy Hajiya, insha Allah Sadik zai samu lafiya, nasan za su bashi kulawarda ta dace, in ma ya samu sauk’i zan mishi visa yaje India ya k’ara ganin likita ta b’angaren cardiologist tun da su na da k’wararru ta wannan b’angaren". Haka dai suka ci gaba da tattaunawa da Dr Kamal kafin su mishi sallama su baro d’akin. Momi kuwa ita kad’ai tasan halin da take ciki na tashin hankali game da ciwon Dr sannan a gefe guda ga haushin Meema da take ji, tasan duk abin da ya samu Dr har da na ta contribution din saboda lack of caring d’inta akan Dr d’in. Wannan karan ta ci alwashi akan cewa ba za ta juri ganin halin da Dr yake ciki ba, dole ne ta d’auki mataki akan Meema d’in. San da suka koma d’akin Dr ya farka daga baccin da yake yi. Meema ce kusa dashi ta manne a jikin shi kamar za ta shige jikin shi. Hanan da Farida suna gefen shi. Momi ce da Dadi suka k’arasa kusa dashi suna mishi sannu. Ido kawai yake bin su ba tare da yayi magana ba. Har yanzu pulse d’in shi da sauri-sauri yake tafiya bai dawo normal ba. Dr ya sake shigowa ya duba shi kana ya bashi magunguna. Bai wani jima ba da shan maganin bacci ya sake d’aukan shi. Ranar dai haka Dr ya kasance cikin wannan halin. Meema tun bayan sallar la’asar ta musu sallama ta tafi gida. Sai bayan sallar magrib ta sake zuwa kasancewar ita tayi driving da kan ta. Ba ta wani jima a asibitin ba ta musu sallama ta tafi. Dadi ne yaso kwana dashi amma Dr Kamal ya ce ya bar shi shi zai kwana dashi. Haka su Dadi suka yi ma Dr sallama suka tafi tare da godiya a bisa jajircewar shi da yayi akan Dr. Washe gari ma haka mutane suka dinga zuwa duba Dr da abokanan Dadi da k’awayen Momi. Likitocin asibitin ma haka suka dinga shigowa suna gaishe shi. Sai da Dr yayi kwana uku a asibitin sannan aka sallame shi saboda matsawar da yayi akan a sallame shi. An bashi hutu a asibiti kasancewar har yanzu jikin na shi bai dawo normal ba. Yau kusan kwana biyu da dawowar Dr daga asibiti. Dr ne zaune a falon shi yana kallon news yayin da Meema ke chatting a wayar ta. Momi ce tayi sallama ta shigo cikin falon. Meema ce ta amsa mata kana ta ci gaba da danna wayar ta. Kusa da Dr Momi ta je ta zaune. Meema tun da ta gaishe da Momi ta tashi ta d’akko mata drinks ta ajiye ta nemi guri ta zauna ta ci gaba da pressing d’in wayar ta, a lokaci d’aya ta manna ear piece a kunnenta tana sauraren music. Dr ne ya gaishe da Momi kana ya jingina jikin shi a kafad’ar Momi. Cikin kulawa Momi ta kalle shi ta ce "Ya jikin na ka Sadik?". "Jiki alhamdullahi, na ji sauk’i Momi" Dr ya amsa mata. Murmushi tayi kana ta ce "Allah ya k’ara sauk’i, Dad d’in ka ya ce in gaishe ka da daddare zai zo ya duba ka, su Hanan ma suna gaishe ka, sun ce suna nan zuwa". Murmushi yayi ya ce "Ina amsawa Momi". Momi ce ta maida kallon ta ga Meema wacce hankalin ta yake kan waya da sauraren wak’ar da ke tashi ta cikin earpiece d’in ta. Mamakin Meema ne ya cika Momi yanda ta nuna ko in kula da ita. Momi ce ta kira sunan Meema amma ba ta ji ba saboda earpiece d’in da tasa ta toshe kunnan ta dashi wanda sautin wak’a ne kawai yake fitowa daga ciki. Sai da Momi tayi mata kira biyu amma still Meema ba taji kiran ba. Ran Dr ne ya b’aci dan haka cikin tsawa ya kira sunan ta. Da sauri ta maida hankalin ta gare shi saboda tsawar har cikin kunnen ta taji tare da cire earpiece d’in da ke kunnen ta. Cikin b’acin rai Dr ya ce "Meema ba ki ji Momi na mi ki magana ba ne". Cikin marairaicewa da shagwab’a ta ce "Ayya sorry Momi ban ji ba ne, kin san na sa earpiece a kunne na". Murmushin takaici Momi tayi a ranta tana k’ara mamakin halin Meema. Sai a yanzu ta k’ara tabbatar da dalilin da yasa Dr yake kushe halin Meeman da guje ma auren ta. Nisawa Momi tayi kana ta ce "Meema magana na ke so mu yi da ke". "To Momi ina jin ki" Meema ta fad’a. Momi ce ta ci gaba da cewa "Nasan kin san halin da Sadik ya shiga na rashin lafiyar da yake fama dashi, Dr Kamal ya mana bayanin cewa hypertension yake damun shi wanda har yaso ya tab’a heart d’in shi sannan bayan nan kuma Dr ya tabbatar mana da cewa yana da ulcer cronic, kin ga kenan lack of caring d’in ki har dashi ya asassa ciwon dake damun Sadik, Meema nasan irin zaman da kuke yi da Dr amma ba na so in sa baki na saboda ba na so in shiga harkar ma’aurata, abin da yasa kika ga na miki magana a yanzu saboda condition d’in da Sadik yake ciki yana buk’atar special caring da kwantar mishi da hankali in ba haka ba ciwon na shi zai iya yin worst fiye da haka, Meema nasan ulcer da ta sami Sadik rashin cin abinci ita ta janyo mishi wannan ciwon dan nasan ba ya samu ya ci abinci yanda ya kamata, kin ga situation d’in da yake ciki a yanzu bay a buk’atar tashin hankali da hayaniya, pls Meema ya kamata ki k’ara effort d’in ki wajen kula da hakk’in da ke kan ki, ni kaina ba na son in ga kuna samun misunderstanding a tsakanin ku, you Know Meema I take you as Hanan ba wai suruka ta ba, shi yasa kika har na zaunar dake na miki magana because I want you to change your behaviors". Meema tun da ta ji Momi ta fara wannan bayanin ta d’aure fuska. Sai da ta ba ri Momi ta gama maganar da take yi kana ta tab’e baki ta ce "For God sake Momi, ni miye laifi na akan ciwon yaya Sadik, shi ciwo yana iya samun mutum at any time sannan Momi ni ina ganin har da laifin yaya Sadik gurin samun wannan ciwon dan nasan duk tunanin da yake yi bai wuce akan ex-wife d’in shi ba sannan ni Momi I know I am trying my best wajen kula da yaya Sadik, shine dai ba ya ganin k’ok’ari na sannan wani lokacin in na mishi girki zai nuna min ba shi yake so ya ci ba, kin ga kenan Momi no need in dinga wahalar da kaina wajen yin girkin tun da ni dai wanda na iya shi zan mi shi, ke kan ki Momi kin san ko a gidan mu ba na shiga kitchen in yi girki sai dai in sa house maid ta min but tun da aka yi auren mu da Yaya Sadik nake k'ok'arin shiga kitchen because of his happiness amma Dr bai ganin haka, to kin ga Momi ba ni da laifi in any part". Momi kuwa bin Meema take yi da kallo da mamakin yanda ta zauna tana jero mata maganganu san ranta ba tare da ta ji kunyar ta ba. Mik'ewa Meema tayi kana ta kalli ta ce "Momi shi kenan ko zan iya tafiya, bacci nake ji zan je in kwanta" Murmushin takaici Momi tayi kana ta ce "Shi kenan Meema za ki iya tafiya". " OK Momi, ki gaida gida" tana gama fad'ar haka ta bar side d'in. Momi bin ta tayi da kallo har ta bar falon. Jiki a sanyaye Momi ta juyo da kallon ta ga Dr ta ce "Sadik ka ci gaba da hak'uri da Meema, ka daina tunanin Meema a ranka ko wani tunani na daban a ranka, ka ga dai yanzu ciwon da yake tare da kai ba ya son tunani, kai Likita ne kasan hakan, ka dinga k'ok'ari kana cin abinci yanda ya kamata, in Meeman ba tayi girki ba ka zo gida ka dinga ci ko kira su Hanan su kawo maka, pls Sadik ka dinga kiyayewa ba na son na rasa ka, na fi so in riga ka mutuwa". Hannun Momi ya rik'e yana murmushi ya ce " Kar ki damu Momi, zan dinga kiyayewa, kin san ita cuta Allah ne ya ke jarrabar bawa da ita a lokacin da ya so, ku ci gaba da taya in addu'a Momi ke da Dadi". "Za mu taya ka da addu'a Sadik, Allah ya baka lafiya" cewar Momi. "Amin Mom" Sadik ya fad'a. Momi ce ta canza maganar da cewa "Sadik ka fad'a min me yake damun ka, tunanin me ka sa a ranka da har ka ke da Bp sannan ga shi ciwon zuciya yana so ya kama ka". Ji yake yi kamar ya fad'a ma Momin shi tunani na da so na da a kullum yake addabar shi cikin zuciyarshi shi yake damun shi amma a yanzu yana ganin fad'ar mata hakan bai da fa'ida tun da bai riga ya tunkare ni da maganar ba. Dr ne ya ce "Momi kin San d'an Adam ba a raba shi da tunani sannan ga stress d'in aiki, kawai dai jarrabawa ce". "Allah ya kawo mafita ya yaye maka wannan ciwon" cewar Momi. "Amin Momi" Dr ya amsa. Sun jima da Momi tana ci gaba da kwantar mishi da hankali kana ta ce ya kira mata Meema suyi sallama. Ko da yaje side d'in Meema samun ta yayi tana bacci. Duk tashin ta da yayi bai sa ta tashi ba, da han haka ya koma ya sanar da Momi tana bacci. Raka Momi yayi wajen Motarta ta ja ta kana ya dawo side d'in shi. Dr sai da ya kwashe kusan two week a gida kafin ya koma aiki. Kullum burin shi bai wuce yanda zai tunkare ni ba saboda yasan wannan ita ce mafita a gurin shi na samun sauk'in halin da yake ciki. Sannan yana kasancewa cikin nadamar abin da ya min Wanda a ko yaushe yake ganin rashin kyautatawar shi gare ni. Matsalar shi a yanzu shine yanda in ya kira numba na ba ya zuwa, tunanin shi ko na daina amfani da numbar ne ko kuma layin ya sami matsala. Yana ganin in ya same ni a waya komai zai zo mishi da sauk'i wajen fuskanta ta. Yau ranar ta kasance ranar Juma'a. Dr ne zaune a bedroom d'in shi yana danna laptop d'in shi. Wani tunani ne yazo mi shi na cewa yau ya kamata ya tunkare ni mu fahimci juna ni dashi. Yasan yanda ya b'ata min rai abu ne mai wahala in tsaya in saurare shi a lokaci d'aya. Shi kan shi yasan ya min butulcin so Wanda a yanzu yake nadama a bisa abubuwan da suka faru a baya. Zuciyar shi ba abin da take sak'a mai da ya wuce bashi k'arfin gwiwa akan haka. Kashe laptop d'in yayi kana ya shiga band'aki ya watsa ruwa ya fito. K'ananun kaya ya sa kana ya feshe jikin shi da turare. A falon shi ya sami Meema kwance akan 3-sitter tana kallon Action film. K'amshin turaren Dr da taji ne yasa ta d'ago ta kalle shi. Kusa da ita yazo ya zauna yana sakar mata murmushi. Ita ma murmushin ne ya yalwatu a fuskar ta. Tashi tayi daga kwancen da take tayi matashi da cinyar shi. "Ki ce kina falo kina kallo kin barni ni kad'ai a bedroom" cewar Dr. Meema ce ta ce "Jiki na ne na ji shi so weak, na ga kuma aiki ka ke yi shi yasa ba na son takura maka". " Kin cika son jiki Meema, wani aiki kika yi da za ki ce kin gaji, bayan ga house maid nan na sa an kawo mini" Dr ya fad'a yana shafa fuskan ta. "Kai yaya Sadik nasan yanzu za ka fara k'orafi daga cewa na gaji" Meema ta fad'a cikin shagwab'a. "Is OK Meema, ba ri in je gidan Momi in dawo" Dr ya fad'a. Cikin marairaicewa Meema ta ce "Yanzu yaya Sadik fita za ka yi ka bar ni". "Yanzu zan je in dawo" Dr ya fad'a. "Ka tawo min da ice cream da baked chicken" Meema ta fad'a cikin shagwab'a. "OK zan tawo miki dashi, sai na dawo" Dr ya fad'a yana mik'ewa. Waving din hannun ta tayi kana ta koma ta kwanta. Dr kuwa yana fita gidan mu ya tawo. Tun a hanya yake jin gaban shi na fad'uwa saboda tunanin yanda zai tunkare ni. Har ya k'araso gidan yana tunanin yanda zai fuskance ni. Ya dad'e zaune a motar kana ya d'akko wayar shi yayi dialling din numba ta amma is not reachable. Hakan yasa ya fito daga motar ya yi knocking din gate din. Mai gadi ne yazo ya bud'e mai. Ganin Dr ne yasa cikin girmamawa ya gaishe shi saboda ya gane shi. Bud'e mishi k'ofar yayi ya shigo. Dr ne ya sanar dashi ya shiga ya sanar da ni nayi bak'o. Main parlour mai gadi ya yi sallama Ummu ta amsa mishi. Sanar da ita ana sallama da ni. Ni kuwa tun da na idar da sallar magrib ina zaune ina lazimi ban tashi daga sallayar ba har San da nayi sallar isha'i ina zaune. Ummu ce tayi sallama na amsa mata. Sanar da ni tayi na yi bak'o kana ta fita daga d'akin. Tun da Ummu ta sanar dani ana sallama da ni nake tunanin Wanda yake kira na a wannan lokaci. Mik'ewa nayi na fito dan ganin mai kira na. Ban gane wanene ba kasancewar ban k'arasa inda yake zaune a d'aya daga cikin kujerun dake gurin shak'atawa ba. K'arasawa nayi had'e da sallama ta. Juyowa yayi ya amsa min sallama ta had'e da murmushi a fuskar shi. Mamaki ne ya kama ni ganin Dr da nayi a lokacin wanda har hakan ya nuna a fuska ta. Wai Dr na ke gani a gaba na ko ido na ne yake min gizo?. Tabbatar da cewa shi d'in ne yasa na cire mamakin ganin shi da nayi. Gani nayi ya rame ya k'ara haske da alama kamar yayi fama da rashin lafiya. Tambayar da na fara yi wa kaina shine me ya kawo Dr gidan mu?. Ganin tambayar ba ta da wani amfani a guri na sai ma b'acin rai da hakan zai haddasa min yasa nayi saurin kawar da wannan tunanin a raina. "Fatima Zarah" Dr ya kira suna na. Ba tare da na mishi magana ba ko amsa kiran suna na da yayi na juya da niyyar komawa cikin gida dan ina ganin babu wani amfanin tsayawa in saurare bayanin abin da ya kawo shi gidan mu. Mik'ewa yayi ya kira suna na "Zarah". Ko alamar juyowa ban yi ba na ci gaba da tafiya ta na bar shi a gurin. Bi na yayi da kallo har na b'ace wa ganin shi yana nan a tsaye. Ganin tsayuwar ba ta da wani amfani a gare shi yasa ya fara tunanin tafiya. Yasan hakan daman za ta iya faruwa in har yazo waje na dan yasan raina a b'ace yake game dashi. Ya zama dole yayi hak'uri da duk abin da zan mishi. Fatan shi shine ya samu in saurare shi. Jiki a sanyaye Dr yayi ma mai gadi sallama ya bar gidan. [10/16, 19:54] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 www.maryamahmadpaki.blogspot.com facebook: Kainuwa Writers Association *TUNATARWA* *Magana Uku Ce Magabata Suke Yawan Maimaitawa:* *(1) Idan Ka/ki ka Gyara Sirrin ka/ki, Allah Zai Gyara Zahirinka/ki..* *(2) Idan Ka/ki ka Gyara Abinda Ke Tsakanin Ka Da Allah,, Allah Zai Gyara Abinda Ke Tsakaninka/ki Da Mutane!!* *(3) Idan Kuwa Ka/ ki ka Dage Wajen Neman Lahira,, Allah Zai Sawwake Maka/mi ki Samun Duniya.* *Allah Yasa Mudace Duniya Da Lahira!!* 103-104 Tun da Dr ya shiga mota yake mamaki na da tunanin yanda ban yi maraba dashi ba san da na gan shi. A tunanin shi in dai ya tako yazo inn da nake zan yafe mishi abin da ya min tare da manta komai da ya faru a tsakanin mu, sai gashi na bashi mamaki ban ma kula shi ba bare yayi zaton samun sassauci daga guri na. Yasan abin da ya min dole ne in kasance cikin fushi dashi tare da d’aukan dukkan matakin da na ga shi yafi dacewa wajen hukunta shi. Hakan ba zai dame shi ba in har zan yafe mishi in manta komai sannan mu k’ara dasa wata sabuwar soyayya da tafi ta da dad’i da gamsarwa dan a yanzu ne wani tsimin soyayya ta ke taso mishi a cikin zuciyar shi. Da wannan tunanin ya samu ya k’arasa gida. Side d’in shi ya wuce ba tare da ya shiga side d’in Meema ba. Bedroom d’in shi ya wuce dan a yanzu yafi so ya kad’aita shi kad'ai ko ya samu sassaucin yanda yake ji a zuciyar shi ga me da ni. Yana shiga ya samu Meema kwance akan royal bed d’in shi. Yayi mamakin ganin ta saboda ba ko wane lokaci ba ne take zuwa side d’in shi ta kwanta. Cire kayan shi yayi ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya fito. Motsin shi da Meema ta ji ne yasa ta bud’e idon ta cikin bacci ta ce "Yaya Faruk ashe ka dawo, ina ice cream d’in". Ran shi ne ya b’aci da tambar da Meema ta mi shi, daman ga yanayin yanda ya bar gurin na, dan haka yayi shiru kamar bai ji ta ba ya ci gaba da sa pyjams d’in shi. K’ara jefo mishi tambayar tayi da cewa "Yaya Faruk na ce ina ice cream d’in, tun d’azun na ke ta zaman jiran ka ba ka dawo ba, shi yasa ma ban ci komai ba". Wani banzan kallo ya watsa mata kana ya ce "don’t disturb me Meema ban siyo ba, ke ba ki san ki lura da yanayin da mutum yake ciki ba, za ki dame ni da shirmen maganar ki". Tab’e baki tayi kana cikin shagwab’a ta ce "yanzu yaya Sadik mi ye laifi na a nan dan na tambaye ka ko ka tawo min da ice cream d’in, since I was waiting for you amma na ga ba ka dawo ba, ban ci komai ba ina ta jiran dawowar ka, kasan ba na son heavy food da daddare". Ganin yanda Meema ke son takura mishi da surutun ta wanda ba abin da yafi buk’ata da ya wuce ya kasance shi kad’ai ko ya samu sauk’in yanda yake ji a zuciyar shi, hakan yasa cikin fad'a ya ce "Meema leave me alone, am not in a good mood, za ki iya koma wa side d’inki ki kwanta, a yanzu na fi buk’atar zama ni kad’ai, idan ina buk’atar ki zan zo in sa me ki ko in kira ki". Mamakin Dr ne ya kamata ganin da ga mishi magana ya fara mata fad’a, tasan fitar da yayi ne aka b’ata mishi rai shine yake son hucewa akan ta, k’arin takaicin ta shine yanda ya ce mata ta koma side d’in ta dan ya ga ta zo gurin shi. Cikin b’acin rai Meema ta sakko daga kan bed d’in ta fita daga d’akin ba tare da k’ara yin magana ba. Kwantawa yayi akan gadon yana kallon P O P dake saman ceiling d’in d’akin ya fad’a cikin kogin tunani. Tunanin yanda na nuna mishi halin ko in kula san da yazo gidan mu shine ya dinga mishi yawo a ran shi. Bai yi tunanin cewa in har ya taka k’afar shi ya zo in da na ke ba zan mishi haka ba saboda yasan irin son da nake mishi sai gashi na mishi bazata. A yanzu ba abin da yafi wahalar da shi irin soyayya ta da ke d’awainiya dashi a ko da yaushe. A yanzu ne ya tabbatar da irin zazzafar soyayyar da yake min wanda a da bai min irin ta ba. Tunanin yanda zai shawo kaina da irin soyayyar shi da yake saurin jawo hankali na yake yi. Haka ya ci gaba da sak’a da warwara yanda abin zai zo mishi da sauk’i ganin mun daidaita dashi ba tare da jan wani tsawon lokaci ba. A yanzu babban burin shi shine in amince mi shi mu k’ara dasa wata tsaftatacciyar soyayya wacce ba muyi ta a da ba. A shirye yake da ba da dukkan kulawar shi gare ni da min hallaci da soyayyar shi wanda bai min ita a da ba. Da wannan tuanin Dr ya samu bacci ya d’auke shi ba tare da ya shirya yin baccin a lokacin ba. A b’angare na kuwa tun san da na koma d’aki na fara mamakin zuwan Dr gidan mu wanda a yanzu sama da tsawon shekara d’aya da ya wuce bai neme ni ba ko ya tako ya zo gidan mu sai a yau da yayi niyyar yin haka. Tuananin abin da ya kawo shi gidan mu shi yafi d’awainiya da ni a cikin zuciya ta. Tunanin da na fi yarda dashi duk da ban tabbatar ba cewa Dr yazo gidan mu ne dan ya nemi sulhu a guri na mu daidaita saboda tak’amar ko wani lokaci yazo zan yi marhabin dashi. Sai dai in haka ne tunanin shi zan bashi mamaki domin zan nuna mishi cewa Fatiman da ya sani a da wacce ta nuna mishi makauniyar soyayya ba ita ba ce a yanzu. A yanzu na fito daga cikin duhun da a da nake ciki na soyayyar shi wanda ba na ji ba na gani amma a yanzu ina cikin haske ne domin a yanzu zan iya fuskantar shi da duk abin da yazo saboda na riga na ajiye soyayyar shi a gefe na zab’i hanyar da tafi dacewa da ni. Sai dai har yanzu nasan duk yanda Dr ya b’ata min ban daina jin son shi a raina ba. Nasan hakan ba ya rasa nasaba da sharrin so. Soyayyar da na nuna ma Dr a baya ita na fara tariyowa zuwa rayuwar auren mu da irin sakamakon da ya min da irin k’aunar da na nuna mishi ta hanyar yin min abubuwa da dama. Wanda yafi tsaya min a rai shine saki na da yayi wanda a yanzu na ke neman sama da shekara d’aya a gidan mu ba tare da Dr ya nuna damuwar shi akan hakan ba. Hawaye ne ya fara zubo min a idanu na d’aya na bin d’aya. Ban damu da in share ba saboda nasan shi kan shi hawayen rahama ne a gare ni. Tunanin da zuciya ta ke yawan yi shine daman Dr kuwa yana so na kamar yanda na ke son shi kuwa? Amsar da zuciya ta tafi karkata da ita shine Dr yana so na duba da yanda ya nuna min kulawar shi da irin soyayyar shi tun kafin in aure shi har zuwa rayuwar auren mu, sai dai nafi gamsuwa da cewa na fi son Dr akan son da yake min. A halin da ake ciki yanzu shine soyayyar yaya Faruk da take son hana ni sukuni ga kuma soyayyar Dr dake gefe d’aya a cikin zuciya ta. Sai dai a yanzu na fi marhabin da soyayyar yaya Faruk in har zan samu k’arb’uwa a wajen shi duba da yanda ya so ni a da sannan ga halayen shi nagari da su ka k’ara bayyanuwa a gare ni. Fata na shine in bar wa Allah zab’i ya zab’a min cikin yaya Faruk da Dr wanda zai fi zama akhairi a gare ni. Ina cikin wannan tunanin ne na ji sallamar Ummu ta shigo d’akin. Saurin goge hawaye na nayi kana na yalwata fuska ta da murmushi a fuska ta na amsa mata sallamar. Kallo na tayi ta zauna a gefen bed d’ina ta fuskance ni. "Fatima me ya same ki, tun da kika dawo kiran ki da aka yi a waje na lura da yanayin ki ya canza, shi yasa lokacin da kika dawo na ga kin wuce d’akin ki ban takura miki ba wajen sanin me ya faru". Shiru na yi ina sunkuyar da kaina kana ina wasa da y’an yatsun hannu na. Har lokacin hawaye ne ke k’ok’arin ci gaba da zubowa a idanu na. Ummu ce ta jefo min da tambaya "Fatima wanene ya aiko a ka kira ki a waje?". Cikin sanyin murya na ce "Dr Sadik ne". Kallo na Ummu tayi tana nazari na kafin ta d’aura da cewa "Kenan shi yasa yanayin ki ya canza ki ka zo d’aki kina tuani" Ummu ta fad’a. Amsa mata nayi da cewa "A’ah Ummu, ban ji dad’in jiki na ne". Girgiza kai Ummu kawai Ummu tayi ba tare da ta yarda da abin da na fad’a ba. Shiru Ummu tayi kana ta d’aura da cewa "Fatima ya dai kamata ki san abin da ya dace da ke dan shekaru sun ja, ya kamata ki tsaya ki natsu wajen tantance wanda ya kamata ki zab’a a matsayin mijin ki saboda ba na so ki k’ara kwatanta kuskuren da kika yi a baya sannan ki dage wajen mik’a wa Allah buk’atun ki Allah ya zab’a miki abin da yafi zama alkhairi a gare ki, nima zan ci gaba da taya ki da addu’a". "Na gode Ummu" na fad’a cikin sanyin murya. Mik’ewa Ummu tayi ta ce "Fatima ina so ki fahimci cewa duk abin da ya sami bawa rubutacce ne daga wajen ubangiji, kowane mutum da kike gani yana tare da k’addarar sa, duk abin da kika ga yayi farko ta yana da k’arshe, saboda haka ina so ki mik’a dukkan lamarin ki zuwa ga Allah subhanahu wata a’la akan ya saman miki mafita a rayuwar ki, ba na jin dad’in yanda wani lokacin na ke ganin ki cikin tunani, ni kaina hankali na ba ya kwanciya in na ganki a wannan halin, ya kamata ki daina sa ma kan ki damuwa kin ji ko auta ta" Ummu ta k’arasa maganar da wasa. "Zan kiyaye insha Allah Ummu" na fad’a. Murmushi Ummu tayi ta ce "Yawwa auta ta, haka na ke son ji, Allah ya kawo miki miji nagari". Murmushi nayi na sunkuyar da kaina kana na amsa da "Amin Ummu". Fita Ummu tayi daga d’akin. Bayan fitar Ummu ne na fara tunanin maganar da ta fad’a min. Nasan duk wannan maganar da Ummu take yi tana yin abin da hausawa ke cewa kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke iya gane wa, maganganun ta suna nuni da cewa kar in yi saurin amincewa da Dr duba da yanda ta faru a tsakanin mu, Ummu ba tasan nima a yanzu na ma kaina karatun ta natsu ba, a yanzu na dawo daga rakiyar makauniyar soyayya wacce ba za ta b’ille da ni hanyar da nake so ba sai dai ta bar ni a tashar nadama, a yanzu abin da na fi buk’ata shine duk wanda zan aura ya zama soyayya mai tsafta muka gina a tsakanin mu dan samun ribar soyayya ga duk wanda suka k’ulla ta a hanyar da ta dace. Ganin yanda tunani yake so ya takura min yasa na tashi na fito falo na kunna kallo dan in rage ma kaina tunanin da ke son addaba ta. Ina cikin kallo ne Ummu ta fito daga side d’in ta tazo ta zauna muka ci gaba da kallon kana mu tab’a hira jefi-jefi. Na ji dad’in kasancewa a wannan yanayin domin hakan ya cire min damuwar da nake ciki da tunanin da ke son takura min. Yau ranar ta kasance ranar Talata. Na dawo daga aiki na shigo da mota ta cikin layin mu na ga wata mota a gate d’in gidan mu wanda ban gane mai mamallakin motar ba. Kusa da motar na zo nati parking kasancewar ba hanyar da zan wuce. Ganin wanda ya fito daga motar ne yasa na bi shi da kallo dan ban yi tunanin zuwan shi a wannan lokacin ba duba da yanda muka rabu dashi. Dr ne na ga ya nufo mota ta. San da ya k’araso ne ya min nocking d’in k’ofar mota ta amma ban bud’e ba. D’aure fuska ta nayi ina jiran jin shi da me yazo. Sai da ya min nocking kusan sau 4 sannan nayi wining d’in glass d’in motar. . Sallama ya min na amsa mai kana ya d’aura da cewa "Fatima pls in ba damuwa ina so ki ara min time d’in ki muyi magana, d’azun na zo mai gadin ku yake fad’a min kin je gurin aiki, shi yasa ma na tambaye shi lokacin da za ki dawo aikin ya fad’a min". Tab’e baki na nayi na ce "Kash! Gashi kuma yanzu ban da time saboda yanzu na dawo daga aiki ina buk’atar hutawa, za ka iya dawowa next time in kana buk’ar hakan". Kallon mamaki Dr ya bi ni dashi saboda ba yi tunanin hakan daga gare ni ba. Ran shi ne ya b’aci da maganar da na mishi wanda hakan ya nuna a fuskar shi, sai dai yayi k’ok’arin controlling d’in fushin shi. "pls Zarah ko yaya ne ki bani time d’in ki, maganar da za mu yi da ke is very important a tsakanin mu, ba zan ja maganar tayi tsawo ba tun da kina buk’ar ki huta" Dr ya fad’a. "Ina ganin na riga na fad’a maka tun farko ban da time da zan tsaya sauraron ka a yanzu saboda ina buk’atar hutawa, maganar da ka ke yi wai maganar na da mahimmanci ina ganin a gurin ka ta ke da mahimmanci domin ni in dai ta b’angare na ne ba na buk’atar jin ta, in kuma maganar da mahimmanci a gurin ka kamar yanda ka fad’a za ka iya dawowa next time amma ba yau ba" cewa ta. Kallo Dr ya bi ni dashi kamar yau ya fara gani na, nasan hakan bai rasa nasaba da mamaki na. Nasan bai yi zaton zan mishi haka ba saboda yasan irin son da na ke mishi, sai gashi na bashi mamaki wajen fad’a mishi magana kai tsaye. San da yazo na k’i sauraron shi ya d’auka wannan hukuncin na tanazar mishi, sai gashi yau ma na zo da wani salo na kora da hali. Ganin Dr bai da niyyar matsawa daga gurin yasa na kunna karatun alk’ur’ani a cikin motar cikin suratul Rahaman kana na d’akko waya ta ina pressing. Nasan hakan ne kad’ai zai sa Dr ya tafi ba tare da mun yi musayar yawu dashi bad an nasan a cikin abin da Dr ya tsana shine shariya da k’yaliya. Ran Dr ya b’aci da abin da na mishi wanda hakan ya bayyana a fuskar shi sai dai yana k’ok’arin b’oyewa. Bai k’ara ce min komai ba ya girgiza kai kana ya tafi ya shiga cikin motar shi. A 360 ya ja motar ya bar layin. K’aramin tsaki nayi kana nayi wa mai gadi horn ya zo ya bud’e min na shiga da mota ta ciki. Ko da na shiga ciki ban yi realising abin da na wa Dr ba, a gani na Dr ya cancanci in mishi fiye da haka. Hakan ya tabbatar min da cewa a yanzu na dawo daga rakiyar makauniyar soyayya da na ke wa Dr. Nasan in da a da ne da yanzu ina nan cikin damuwa ganin na b’ata wa Dr rai amma a yanzu hakan bai dame ni ba duba da yanda a da na nuna mishi soyayya mara misaltuwa wanda ban ji ban gani. Yanzu na fi samun natsuwa a cikin zuciya ta saboda ajiye wahalalliyar soyayyar Dr da a da ta azabtar dani. Ranar haka na kasance cikin walwala dan nasan ko ba komai na b’ata wa Dr rai. Dr kuwa tun da ya fara driving yake tunanin abin da na mishi wanda bai za ci hakan daga gare ni ba. Soyayya ta dake wahalar dashi a yanzu ita take k’ok’arin cire mai duk wani walwalar shi da farin cikin shi. Wani irin so yake min da shi kanshi ba zai iya fasalta yanda yake ji na a zuciyar shi ba. A da yana ganin zai iya rayuwa ba tare da ni ba, sai a yanzu ne ya k’aryata zuciyar shi cewa ba zai iya ci gaba da gudanar da rayuwar shi ba tare da ni ba. Zuciyar shi ce ta fara harbawa da sauri-sauri a lokaci d’aya k’irjin shi ya ji ya fara mishi wani irin ciwo. Dafe k’irjin shi yayi ya rintse ido saboda yanda yake jin ciwon a cikin jikin shi. Jinginar da kanshi yayi a jikin sitiyari yana maida numfashi. Sai da ya d’auki lokaci kafin ya samu k’irjin ya lafa mishi amma har yanzu yana jin sauran ciwon. A haka ya samu ya ja motar har ya k’araso gida. Side d’in Meema ya shigo had’e da sallama ya zauna in da ya same ta a kujerar 2-sitter tana kwance tana buga game a wayar ta. Meema kuwa tun da ta amsa mishi sallamar ta mishi sannu ta maida hankalin ta akan game d’in da take bugawa ba tare da ta lura da yanayin da Dr yake ciki ba. Ciwon k’irjin ne ya k’ara dawowa Dr wanda ya fi lokacin da yake cikin mota. Yanda ya fara numfashi ne yasa Meema tayi saurin maida hankalin ta gare shi. Ganin halin da Dr yake ciki yasa ta yar da wayar da ke hannunta ta nufo gurin shi. Rik’e shi tayi tana tambayar shi in da yake mishi ciwo a lokaci d’aya tasa kuka mai ban tausayi. Dr bai samu damar yin magana ba saboda yanda yake ji a jikin shi. Da k’yar Dr ya samu ya bud’e baki ya fad’a ma Meema in da maganin shi yake a bedroom d’in shi. Da gudu Meema ta nufi bedroom d’in shi ta d’akko maganin ta bashi ya sha. Jingina yayi da kujerar da yake zaune yana maida numfashi a hankali. Bai wani jima da shan maganin ba ya fara jin bacci. Hakan yasa ya kwanta akan kujerar 3-sitter d’in da yake zaune. Meema ce ta zo ta zauna kusa dashi tana kallon shi. Wani irin tausayin shi ne ya kamata ganin yanda ciwon yake wahalar da Dr. Ji take yi kamar ta cire ciwon daga jikin shi ko ya samu sauk’in wahalar da yake sha. Hawaye ne ya fara zubowa a idanun ta na tausayin Dr. Hannun ta takai kanshi tana shafa mi shi a hankali. Haka Meema ta ci gaba da zama tana jiran tashin Dr. Dr sai da ya d’auki fiye da awa d’aya kana ya tashi daga baccin da yayi. A hankali ya bud’e idon shi yayi tozali da Meema kusa dashi. Mamaki ne ya kama shi ganin Meema kusa dashi. Hakan ya tabbatar mi shi da cewa tun san da ya fara bacci ta ke zaune a gurin. Shi kan shi yasan Meema na son shi sai dai al’adar yahudawa da take koyi dasu da wasu halayen ta na cewa tana da freedom d’in kanta ba ta cika bin abin da zai fad’a mata ba a matsayin shi na mijin tab da wasu hakk’ok’in ta da ba ta saukewa a matsayin ta na matar shi, wannan shine matsalar da suke fuskanta da ita Meeman. Shi kan shi wani lokacin tana bashi tausayi saboda son da take mishi, yana ji a ranshi zai iya ci gaba da zama da ita matuk’ar za ta gyara halayen ta ko dan darajar son da take mishi da kuma Momin shi. Yasan so d’aya ne tak ya kuma riga ya mallaka min, sai da ya na k’ok’arin ganin ya sa son Meema a ranshi ko yaya ne saboda yanda ta d’auki lokaci tana d’awainiya da son shi a cikin zuciyar ta kuma gashi yanzu tana matsayin matar shi ta sunna. Katse mi shi tunanin shi Meema tayi da cewa "Ka tashi yaya Sadik, ya jikin?". K’asaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskar shi ya ce "Na tashi Meema, naji sauk’i, thanks". "Thanks for what" Meema ta fad’a. "for your caring" Dr ya ba ta amsa. "you deserve more than that" cewar Meema. Murmushi yayi ya rungume ta kana ya rik’e mata hannu yana wasa dashi. A haka suka ci gaba da hira da Meema. Dr ne ya bata umarnin ta dafa mishi shayi wanda ya ji kayan k’amshi a ciki. Ba a d’au lokaci ba Meema ta dafa shayin ta kawo mishi ya sha. Ranar kam zaman su abin burgewa da ban sha'awa saboda yanda su ka tarairayi junan su. [10/21, 11:46] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 Facebook: Kainuwa writers Association www.maryamahmadpaki.blogspot.com *TUNATARWA* _Rayuwa haske ce_ _Mutuwa kuma aya ce_ _Arziki jarrabawa ne_. _Talauci kuwa misali ne_ _Hankali makaranta ne_ _Ilimi kuwa jagora ne_ _Jahilci kuwa duhu ne_ _Duniya gida ce_ Qabari daki ne_ _Allah ka sa mu dace_ 105 Ni kuwa ta b’angare na ban san halin da Dr yake ciki ba, gudanar da rayuwa ta nake cikin nishad’i ba tare da wata matsala ko damuwa ba. Matsala ta ba ta wuce yanda zan k’ara tunkarar yaya Faruk ba tun da ya min gargad’i akan in k’ara tunkarar shi da maganar ina son shi. Gashi ko na kira shi a waya bai cika d’auka ba sai ya gadama, in ma ya d’auka ba na iya sakewa in mishi magana saboda tsoro, sai dai in ce a gaida Khairat da maman ta. Tun san da Dr ya zo lokacin da na dawo daga aiki bai kuma zuwa ba, hakan yada nima na manta da batun shi dan ina sha ko ya ji haushin abin da na mishi ne. Yau ranar ta kasance ranar lahadi ba ni da aiki, hakan yasa na shirya dan in shiga kasuwa in siyo kayan make-up d’ina da suka yi k’asa. Ummu na je na fad’a ma wa kana na shiga mota ta na bar gidan. Kasuwa na shiga na yi siyayya ta kana na d’akko hanya na dawo gida. Tun da na shigo layin na ga motar Dr a gate d’in gidan mu. K’arasowa na yin a yi parking d’in mota ta a can gefe na fito na nufi hanyar shiga gidan mu. Da sauri Dr ya fito daga motar ya nufo in da na ke. Cikin sanyin murya ya min sallama na amsa mi shi. "Fatima gani na k’ara zuwa, ina fatan yau a free kike dan na ga yau ranar hutu ce, shi yasa na zo a yau". "Yau ma ka makaro saboda yanzu na dawo daga unguwa, za ka iya dawowa any time da ya maka". A yanzu Dr ya daina mamaki na saboda shi kan shi yasan sani da yayi a baya ba ni ba ce a yanzu. Cikin kwantar da murya ya ce "Zarah dan girman Allah ki daure ki saurare ni, nasan duk wannan abin da kike min kora da hali ne amma ba zan yi fushi ba in dai za ki tsaya ki saurare ni". Jin ya had’a ni da girman Allah yasa na ji jiki na yayi sanyi, dan haka na ce mishi mu shiga cikin gida. Gurin hutawa da aka keb'e a gidan mu muka zauna. Shiru ne ya ratsa a tsakanin mu kafin Dr ya kau da shirun da fara ba ni hak’uri akan abin da ya min a baya kana ya d’aura da cewa "Zarah ina son ki, duk abin da ya faru nasan laifi na ne na kuma amsa, rayuwa ta ba za ta ci gaba da tafiya daidai ba in ba ke, na shiga wani hali duk ta sanadin son ki, yanzu haka ina da hawan jin da kuma heart disease, nasan ba komai ya sa min wannan ciwon ba sai tunanin ki da nake yawan yi, pls Zarah ki manta baya ki yafe min mu koma rayuwar mu irin ta baya ta hayar amince min mu yi aure". D’agowa nayi na kalle shi jin ciwon da ya ambata yana tare dashi kuma duk ta sanadi na ya samu ciwon. Tausayin shi ne ya kama ni amma da na tuna halin da na shiga tun da na fara soyayya dashi har san da muka rabu yasa nayi saurin ajiye tausayin shi a gefe na dan a yanzu ba ni da buk’atar ci gaba da zama dashi, na fi buk’atar in auri d’an uwa na da ya nuna min so tun kafin in san miye so. Cikin d’aurewar fuska na ce "Dr na ji bayanin ka, sai dai a yanzu ba wani taimako da zan iya maka sai dai in ce Allah ya yaye maka lalurar da take damun ka saboda shi ya d’aura maka, maganar in amince maka ma ba ta taso ba saboda a yanzu na yi wa kaina fad’a, ba na so in k’ara maimaita makauniyar soyayyar da nayi a baya wacce tasa ni yin danansani, a yanzu na fi buk’atar in auri yaya Faruk d’an uwa na in dai zai amince da ni kamar yanda ka fad’a min in je in aure shi, Sadik kai kan ka shaida ne a irin son da na nuna maka, na nuna maka so da ba kowace mace ba ce za ta iya nuna maka kwatank’wacin shi, na samu matsala da iyaye na da y’an uwa na duk a dalilin son ka amma wai ni Dr ka ma gori akan ban ma iyaye na biyayya ba sannan ka had’a min da tukwici na saki akan in je in auri d’an uwa na, tun a lokacin na sa ma raina cewa Dr na hak’ura da kai". Hawaye ne ya zubo min masu zafi na yi saurin goge wa kana na ci gaba da cewa "Dr ka min abubuwa da dama Dr na shanye amma ba wanda ya fi bak’anta min rai irin sakayyar da ka min ta saki sannan ba ka k’ara waiwaiya ta ba sai a yanzu da kayi ra’ayin kan ka saboda kan tak’amar kai ka ke sarrafa zuciya ta yanda ka gadama, in wannan ne tunanin ka Dr ka riga ka makaro saboda Fatiman da ka sani a da ba ita ba ce a yanzu". Mik’e na kalli Dr wanda jikin shi yayi sanyi ya kasa magana na ce "ka gaida gida". Ina gama fad’ar haka na bar gurin yayin da Dr ya kifa kan shi akan table d’in da ke gurin. Da k’yar ya samu ya shiga motar shi ya ja ya tafi. Tun daga wannan lokacin Dr yake bibiya ta, ko ya zo gidan mu ba ko wane lokaci nake fita ba sai na gadama, kiran waya da text messages har abin ya fara damu na, yanzu ta kai har gurin aiki yana biyo ni yana rok'o na, duk wannan abin da Dr yake yi dai da na ji a raina cewa zan canza ra'ayi na in amince dashi ba dan har yanzu ban daina jin d'acin abin da ya min a baya ba sannan a yanzu na riga na sa ma raina cewa Yaya Faruk shine zab'i na. Duk da Yaya Faruk bai ba ni goyon baya akan maganar da na zo mishi da ita ba ina sa ma raina cewa zan iya auran shi a haka ko da a yanzu ya daina so na saboda nasan in har mu ka yi auren soyayya ta za ta dawo a gurin shi ba re ina da tabbacin cewa Yaya Faruk har yanzu yana so na sai dai abin da na mishi a baya ne yake k'ok'arin k'aryata zuciyar shi a kaina.. Ni kaina yawan takurawar da Dr yake min yasa hankali na ya fara tashi saboda ba na so wata alak'a ta soyayya ta k'ara had'a ni da Dr. Hakan yasa nake iyakar k'ok'ari na wajen ganin na ba shi fuskar da zai matsa min akan maganar soyayyar mu. Ga zawara da a yanzu suke son matsa min a gurin aikin mu ko ma su aikowa gidan mu, su ba na sa su a lissafi saboda bana ganin zan iya tsayar dasu a matsayin Wanda zan aura, hakan yasa na ke basu hak'uri a duk lokacin da d'aya daga cikin su ya tunkare ni da wata Kalmar soyayya. Babban tashin hankali na shine nasan Abbu na d'aga min k'afa ne kafin ya min maganar tsayar da miji gashi har yanzu ban San a babin da na ke da Yaya Faruk ba tun da babu wata tsayayyar magana da ta shiga a tsakanin mu. Wannan shine matsalar da na ke fuskanta a yanzu. Yau da daddare muna zaune a main parlour bayan mun gama cin abinci muna tab'a hira da su Abbu. Abbu ne ya canza hirar da kiran sunan. Amsa mishi nayi tare da maida hankali na gurin shi. Abbu ne ya ce "Fatima rayuwa tana tafiya da k'alubale sannan lokacin mu yana ta tafiya, nasan kin San cewa duk daren dad'ewa za ki sake wani auren tun da yanzu kin fi shekara d'aya a gida, abin da yasa kika ga ban miki maganar aure ba saboda ina so ki samu natsuwa, na zuba miki ido ne ina sha za ki kawo Wanda kika tsayar a matsayin miji Wanda za ki aura amma shiru, ke kan ki kinsan na d'aga mi ki k'afa ban mi ki maganar aure ba, kin San ni da Ummun ki ba za mu so ki ci gaba da zama ba tare da kin yi aure ba, ko wace mace darajar ta aure, A yanzu ke Musulunci ya ba damar ki zab'i wanda kika ga ya dace ya zama abokin rayuwar ki, ina so ki lura gurin zab'an Wanda ya dace da ke dan ba na so ki k'ara kwatanta kuskuren da kika yi a baya duk da k'addara ba Wanda ya isa ya kauce mata, saboda haka na ba ki nan da d'an lokaci ki tsayar da d'aya daga cikin masu nemanki da aure kin ji ko Fatimah". Gaba na ne kawai yake fad'uwa tun da Abbu ya fara maganar nan. Ba abin da ya fi d'aga min hankali shine nasan tun da Abbu yayi maganar nan nasan cewa daman irin wannan ranar na zuwa sai dai na so a ce Abbu ya min wannan maganar ne a lokacin da muka tsayar da magana da Yaya Faruk ya amince min. Nasan Abbu daUmmu za su yi murna da maganar, sai dai a yanzu ba ni da wani abin cewa tun da Yaya Faruk bai ba ni goyon baya akan haka ba gashi Abbu ya ba ni nan da d'an lokaci, hakan na nufin a ko wane lokaci zai iya tunkara ta ya ji wanda na tsayar. Abbu ne ya katse ni da cewa "Fatima kin ji abin da na ce ko?". Cikin sanyin murya na ce " Na ji Abbu, zan yi k'ok'ari in tsayar da d'aya daga cikin su". Murmushi Abbu yayi kana yace "Yawwa autar Ummu, haka nake son ji, Allah ya miki albarka ya zab'a miki wanda yafi zama alkhairi a gare ki". A hankali na amsa da "Amin Abbu". Juyawa yayi ya kalli Ummu wacce tun San da Abbu ya fara min magana ba ta ce komai ba ya ce "Aisha ko kina da abin cewa". "Ba ni da abin cewa dan nima zaman Fatima ya fara damu na, nafi so in ganta a d'akin mijin ta, tun da yanzu ka mata magana nasan za ta maida hankali wajen fitar da miji, Allah ya tabatar da alkhairi ga duk wanda za ta zab'a" cewar Ummu. Abbu ne ya amsa da "Amin Aisha". Abbu ne ya kalle ni ya ce " Fatima za ki iya tafiya". Sallama na musu na nufi d'aki na. Ina shiga na fad'a kan gado ina tunanin maganar da muka yi da Abbu. Hawaye ne ya fara zubo min wani na bin wani. Nasan hawayen da na ke zubarwa ba zai wuce akan rashin mafita da har yanzu ba na kasa samu akan Yaya Faruk ba, gashi Abbu ya k'ara min maganar da ta k'ara d'aga min hankali. Ganin in dai na zuba wa Yaya Faruk ido ba tare da na k'ara nuna jajurcewa ta akan maganar mu dashi ba wankin hula ne zai kai ni dare. Shawarar da na yanke shine gobe in Allah ya kaimu zan kira shi a waya da in k'ara tuna mishi maganar duk da gargad'in da ya min dan wannan ne kad'ai mafita a gare ni. Haka na ci gaba da sak'a da warwara kafin bacci ya d'auke ni. Washe gari sai da na duba lokacin da Yaya Faruk bai gida kana na kira shi. Da farko na d'auka cewa ba zai d'auka ba saboda kusan sau 4 wayar na shiga amma bai d'auka ba. A kira na biyar ne cikin sa'a ya d'auka. Tun da ya min sallama bai k'ara cewa komai ba. Bayan na gaishe shi ne na tambayi lafiyar Khairat da Nana ya amsa min a tak'aice. Shiru ne ya biyo bayan gaisuwar da muka yi. Hakan Yaya Faruk ya kau da shirun da cewa "ki gaida su Ummu ina da abin yi dan na ga ke ba ki da abin cewa". Sanin katse wayar zai yi yasa nayi saurin cewa "Pls Yaya Faruk kayi hak'uri kar ka kashe wayar, magana na ke so muyi in ban takura maka ba" na fad'a. Shiru yayi kamar ba zai min magana ba kana a dak'ile ya ce "Ina jin ki, amma ki tak'aita abin da za ki fad'a dan ina da aiki a gaba na". Ni ce na ce Cikin rawar murya na ce " Yaya Faruk... Akan... Maganar mu ta kwanaki ce....na ke so....in tuna maka". "Wace magana kenan" ya fad'a a tak'aice. Shiru nayi ina jin tsoron tuna mai saboda gargad'in da ya min akan maganar. "Ko ba ki ji tambayar da na miki ba ne" cewar Yaya Faruk. Cikin daburcewa na ce "Akan maganar da na maka...am..uhm...da na ce...ina sonka...uhm....ka....amince...ka ...uhmm...aure....n.....". Wata irin tsawa Yaya Faruk ya min wacce tasa na had'iye sauran maganar da nayi niyyar k'arasa fad'a. Cikin fad'a Yaya Faruk ya ce " Fatima kar ki bari mu had'u dan sai na ci ubanki da kyau, na lura har yanzu ba ki yi hankali ba, sai na hukunta ki da irin hukuncin da ya dace dake, kar ki yi tunanin kin girma, har yanzu kallon yarinya na ke miki, ban da tsabar iskanci har ki kira ni ki k'ara fad'a min maganar da na miki gargad'i akai saboda kin raina ni, duk San da kika bari na shigo Kaduna za ki gane kuren ki, ki kiyaye ni". Duk da na ji haushin maganganun da ya fad'a min sun b'ata min rai amma haka na daure na ci gaba da rok'on shi. Maganganun da yaci gaba da fad'a min ne yasa raina ya k'ara b'aci amma duk wannan bai sa na ji zan hak'ura da Yaya Faruk ba. A k'arshe da yaga zan matsa mishi katse wayar yayi. Kifa kaina nayi na fara kuka mai cin rai. Da na gaji da kukan ne na share hawaye na. Tunanin da na ke yi in har Yaya Faruk bai amince min ba wa zan tsayar a matsayin miji gashi Abbu ya bani lokaci ban kuma san lokacin da buk'aci amsa ta ba. Ba na jin zan iya amincewa da masu zuwa guri na dan ba ma fita nake yi ba bare har in duba wanda ya dace in tsayar. A zuciya ta ba na jin zan iya auran Dr ba wai dan ba na son shi ba, hasalima har yanzu da soyayyar shi a cikin raina sai dai ina k'ok'arin dannewa saboda guje ma kaina komawa gidan jiya ga yanzu yayi aure, ban san wace matsala kuma zan fuskanta ba. Fata na shi ne komai ya zo min cikin sauk'i yanda ba zan sami Matsala da Abbu ba. Ranar haka na wuni a d'aki na rasa abin da yake min dad'i sai da Ummu ta kira ni kana na fito. A can b'angaren Yaya Faruk kuwa tun da ya katse wayar da yake yi da ni ya ja k'aramin tsaki. Ran shi ne ya b'aci jin dalilin kiran da na mishi. B'acin ran da damuwar da ya shiga a baya shine na ke in dawo mishi dashi sabo. Matakin da zai d'auka a kaina ya fara yi dan ba yaso in dawo mishi da hannun agogo baya. Yana cikin wannan halin ne Yaya Mus'ab ya shigo cikin office din. Hannu ya mik'a ma yaya Faruk su ka yi musabaha kana ya nemi d'aya daga cikin kujerun da ke office d'in ya zauna. Yanayin shi da Yaya Mus'ab ya lura ne yasa ya ce "Faruk lfy kuwa na ga yanayin ka kamar kana cikin damuwa" cewar Yaya Mus'ab. Nazari ya fara yi akan ya fad'a ma Mus'ab abin da yake damun shi ko ya bar shi. Wata zuciyar ce ta ke mishi gargad'in kar ya fad'a mishi shi ko dan saboda Khadijah. Yasan Mus'ab mai fahimta ne amma in dai yaji maganar nan bai San yadda zai d'auki maganar ba saboda a yanzu k'anwar shi yake aure. Wata zuciyar shi kuwa k'arfafa mishi gwiwa take yi akan ya fad'a mai dan yasan zai bashi shawarar da ta dace. Mus'ab ne ya katse shi da tunanin da yake yi ya ce "Faruk ka fad'a min me ke damun ka". Nisawa Yaya Faruk yayi kana ya fad'a mishi abin da yake faruwa tsakani na dashi. Ga mamakin shi murmushi ya ga Yaya Mus'ab na yi. " Faruk wannan ba wata matsala ba ce, ina ganin yanzu ne Allah zai cika maka burin ka na samun Fatima cikin ruwan sanyi, tun da ita tayi maka maganar tana so ka aure ta ba matsala ba ce tun da har ta gane kuskuren ta, sannan kaima Allah ya dubi hak'urin da kayi shi yasa Fatima ta tunkare ka da maganar, nasan ba wacce za ka so sama da Fatima, ni dai ina ba ka shawarar ka amince". Bin shi da Kallo yayi kawai Yaya Faruk yayi har ya gama maganar. Dariya Yaya Mus'ab yayi ya ce "Ya a ka yi ne Bregadier na ji ka yi shiru, ko shawarar ce ba tayi maka ba". Tab'e baki Yaya Faruk yayi kana ya ce shawarar da ka fad'a ne naji ban gamsu da ita ba, shi yasa ka ga nayi shiru". Murmushi yaya Mus'ab yayi ya ce " Nasan za ka d'auki magana ta a shirme, wannan maganar da nake ma ka da gaske nake yi, nasan za ka yi zaton saboda Nana ba zan ba ka goyon ba Saboda tana matsayin k'anwa ta, Faruk zan so ka samu farin cikin da ka rasa a baya, ina so kaima ka d'and'ana gard'in soyayya da masoya suke sha, nasan har yanzu da son Fatima a ran ka, saboda haka feel free, ina da tabbacin Fatima ba za ta ba ka matsala ba". Murmushi Yaya Faruk yayi ya ce "Mus'ab a rayuwa komai na iya canza wa, a tunanin ka kana tunanin yanzu zan iya dawo da Fatima cikin rayuwa ta, kai kan ka shaida ne a akan abin da Fatima ta min, tun lokacin da ta nuna ba ta ra'ayina na sa ma raina cewa na hak'ura da ita, kasan ni kaifi d'aya ne ba na canza magana, soyayyar Khadijah kad'ai ta ishe ni, ina jin soyayyar ta a dukkan sassan jiki na, ban mata adalci ba idan na auri Fatima bayan halaccin da ta min, ko da zan k'ara aure ba Fatima zan aura ba". Yasan Yaya Faruk magana d'aya yake yi, yasan yanzu duk shawarar da zai bashi ba zai d'auka ba, gwara ya mishi shiru, yasan nan gaba zai nemi shawarar sa. Yaya Faruk ne ya canza hirar da maganar aikin su. Haka suka ci gaba da tattaunawa kana Yaya Mus'ab ya mishi sallama ya tafi. Yau ina zaune a falo na ji sallamar Anisa. Cikin murna na amsa mata. Zama tayi muka gaisa kana ta tafi gurin Ummu. Ta d'an jima a can gurin Ummu kana ta dawo falo muka ci gaba da hira. A k'arshe d'aki na muka wuce muka ci gaba da hirar Ji nake yi kamar in fad'a ma Anisa damuwa ta amma ina Shakkar fad'a mata, nasan Anisa za ta ba ni goyon baya akan maganar amma wata zuciyar na hana ni. Shawarar da na yanke shine kar in fad'a mata. Ranar haka mu ka wuni muna hira da Anisa. Sai da daddare Yaya Khalil yazo suka tafi.. Haka lokaci ya ci gaba da tafiya. Yau Dr ne da Momi suke hira a d'akin ta. Cikin hirar ne Momi ta kalle shi cikin kulawa ta ce "Sadik wai me yake damun ka ne, duk ka bi ka canza da yanda na san ka, duk Wanda ya kalle ka yasan kana cikin damuwa, ka kuma san ciwon da kake tare dashi ba ya buk'atar damuwa da tunani dan nasan ka fi ni sanin haka tun da kai Likita ne, ba sai na tsaya fad'a maka illar hakan ba, ina so ka fad'a min matsalar ka Sadik". Cikin damuwa Dr ya ce " Momi abin da yake damuna bai wuce akan Zarah ba, na je gurin ta time without numbers amma har yanzu ta k'i ta hak'ura, Momi na rasa yanda zanyi dan duk wata hanya da nasan zan bi in ga ta amince dani amma still har yanzu ba canji, a cewar ta d'an uwan ta za ta aura, Momi ina cikin damuwa ". Tausayin Dr ne ya kama ta, tasan son da yake min ba abu ne mai sauk'i da za ta ce ya hak'ura dani ba, ita kanta tana so d'an ta ya kasance cikin walwala da sukuni, hasalima a zaman da nayi da Dr ba ta ga wata matsala a tare dani ba, sai dai ba taso a kaina ya ci gaba da sa kan shi cikin damuwa. Cikin lallashi Momi ta ce " Sadik nasan kana son Zarah, ni kaina nasan yarinyar ba ta da matsala, ba na so kana sa ma kanka damuwa akan ta, ni kaina zan yi farin ciki idan ka k'ara auran ta a karo na biyu, amma tun da ta nuna yanzu ba ta da interest akan ka, tafi son d'an uwanta ina ganin ka hak'ura da ita". Cikin sanyin murya Dr ya ce "Momi bazan iya hak'ura da Zarah ba, ina son ta, zan shiga wani hali in na rasa ta, ki taya ni addu'a Momi". Jikin Momi ne yayi sanyi jin kalamen Dr, ita kan ta tana tausaya mishi halin da yake ciki, za ta taya shi addu'a Allah ya mallaka mishi ni ko ya samu kwanciyar hankalin da take buk'ata a gurin shi. Cikin taushin harshe Momi ta ci gaba da kwantar mishi da hankali da bashi k'arfin gwiwa akan zai same ni. Wannan shi ya k'arfafa ma Dr gwiwa har ya manta da damuwar da yake ciki. Yau bayan na dawo aiki ne na wuce gidan Anty Jiddah. Mun sha hira da ita kana nayi niyyar fad'a mata abin da yake damuna dan nasan za ta bani shawarar da ta dace. Zayyano mata halin da na ke ciki tsakanin Yaya Faruk da kuma takurawar da Dr yake min. Tun da na fara maganar Anty Jiddarh take kallo na har na k'arasa maganar. Anty Jiddarh ce ta ce " Fatima a bayanin da kika min ban ga laifin Faruk ba, duk Wanda aka ma irin abun da kika ma Faruk ba kowa ba ne zai yi saurin amincewa dake a lokacin da kika zo da irin buk'atar da kika zo ma Faruk da ita, ni kaina zan yi farin ciki idan Faruk ya aure ki saboda kun dace kuma za ki ji dad'in zama dashi, ta b'angaren Dr ina ganin ki rage abin da kike mi shi tun da ya gane kuskuren shi sannan a tsakanin Faruk da shi Dr d'in ba ki san Wanda Allah zai zab'a miki a matsayin miji ba, shawarar da zan baki ki dage da addu'a akan Allah ya zab'a miki abin da yafi alkhairi". "Na gode da shawarwarin ki Anty Jiddarh, insha Allah zan dage da addu'a" na fad'a. shawarwari Anty Jiddarh ta ci gaba da fad'a min Wanda hakan yasa ni farin ciki. Haka muka ci gaba da hira da ita har Yaya Aminu ya dawo kafin na musu sallama na tafi. Yau da yamma ina zaune a d'aki ina k'arasa wani aiki da na tawo dashi daga office. K'arar da waya ta tayi ne ya katse min aikin da na ke yi. Ganin sunan Dr ne a jikin screen d'in yasa na ja k'aramin tsaki na ci gaba da aikin da na ke yi. Sai da na ji wayar ta k'ara ringing sannan na d'auka. Bayan na d'auka ne yake sanar dani gashi a gidan mu yana jira na. Ko da na gama wayar dashi aikin da nake yi na ci gaba da yi. Sai da ya k'ara kira nan sannan na tashi na fita. A jikin motar shi na same shi yana tsaye. K'arasawa na yi na gaishe shi kana na yi shiru. Amsa min yayi da murmushi a fuskar shi. Yau ma dai kamar ko da yaushe rok'o na Dr yayi akan in amince dashi tare da k'ara fad'a min halin da yake ciki akan so na. Duk da a yanzu ina jin tausayin Dr amma hakan ba zai sa in amince dashi ba dan haka na k'ara fad'a mishi yayi hak'uri ni na hak'ura dashi. Yanayin shi ne na ga ya canza, alamu sun nuna bai ji dad'in rashin amincewa ta ba duk da ba wannan ba ne karo na farko da na fad'a mishi ya hak'ura dani. Bai ce min komai ya fara tafiya dan ya shiga mota. Yanayin yanda na ga yana tafiya na tabbatar da maganar ba k'aramar girgiza shi tayi, yanayin tafiyar shi na nuni da cewa kamar ba yi da lafiya. Haka da yaja motar da gudu ya danna wa mai gadi horn yazo ya bud'e mishi gate ni kuma na koma cikin gida. Dr kuwa haka ya dinga Jan motar da gudu har ya k'araso gida. Side d'in shi ya wuce ya kwanta. Zuciyar shi ce ke wani irin bugawa yayin da yaji kamar an tokare mishi k'irjin shi. Numfashi ya fara fitarwa mai wahala yayin da ya lumshe idon shi saboda wahalar da yake sha. Meema Wanda tun dawowar Dr taji shigowar shi side d'in shi. Tashi tayi ta nufi side d'in shi saboda yau bai wuni a gida ba tun da ya fita aiki. Tana shiga taga Dr a halin da yake ciki. Da gudu ta k'arasa gurin shi ta rik'o shi. Kuka Meema ta fara tana tausaya ma Dr halin da yake shiga. Ta rasa abin da yasa sai ya fita ya dawo yake shiga wannan halin. Dr Wanda hankalin shi ya fara barin jikin shi bai san me Meema ke ciki ba. Lokaci d'aya numfashin Dr ya d'auke. [10/23, 07:40] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞 🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀ *STORY & WRITTEN* *BY* *MARYAM AHMAD PAKI* *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽 Facebook: Kainuwa Writers Association www.maryamahmadpaki.blogspot.com _ALHAMDULILLAH_ _Kamar yanda na fad’a a cikin littafin nan cewa a last page d’in novel d’in nan zan fad’i wanda suka zo na 1-3 a cikin shirin Question of the day_. _Sannan kamar yanda na alk’arwanta cewa akwai kyauta ga wanda suka zamo 1-3 a cikin shirin_. _Ba abin da zan ce wa duk wanda suka ba da gudunmuwar su wajen ba da amsa tambayoyin question of the day sai dai in musu fatan alkhairi da addu’ar Allah ya saka musu da alkhairi ya kuma sa jannatul fidausi ta samo makoma a gare mu baki d'aya_. *Meeynah* _(Princess of question of the day 1st position)_ *Xarah Auwal* _(Ass queen of question of the day 2nd position)_ *Aisha Autar Mama* _(Queen of the question of the day 3rd position)_ _Sauran wanda su ma suka ba da gudunmawar su a cikin shirin sun had’a da_: _Hajarah Isah_ _Fadyla Ingawa_ _Ummu Fadlu_ _Ameenatou_ _Salmah _Maman Walida_ _Sakina Ilyas_ _Ramlah_ _Fadeelah_ _Br Teemah_ _Jazakumul lahu khairan bikum_. ⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇ LAST PAGE Jikin Meema ba in da ba ya rawa lokacin da ta lura Dr ba ya numfashi. Da k'yar ta samu ta kwantar da Dr akan pillow kana ta d'auki wayar ta cikin kuka ta kira Momi ta fad'a mata halin da ake ciki. Ba a d'au wani lokaci ba Momi ta tawo da Hanan suka zo gidan. Gaba d'ayan su kuka suka sa ganin halin da yake ciki saboda duk Wanda ya ga Dr a lokacin dole ne ya zaci ya mutu. D'aukan Dr suka yi suka sa shi a mota suka nufi Kangiwa hospital dashi. Sai da likitoci suka had'u akan Dr kafin su samu numfashin shi ya dawo kana aka jona ma Dr abin taimakawa numfashi(oxygen). Sai da Dr ya kwashe awa kusan uku sannan Dr ya dawo normal aka kai shi special room. An ba su Momi damar su shiga su duba shi amma su kiyaye yin hayaniya ko wata magana da za ta sa Dr ya koma cikin wani halin. Duk Wanda ya shiga ya duba Dr sai ya tausaya masa. Dr sai da ya kwashe kwana kusan 4 a kwance a asibiti. Sai dai tun san da Dr ya fara jin sauk'i yake ambatar suna na. Hakan yasa Momi ta fahimci akaina ya shiga wannan halin da yake ciki. Meema kuwa ranta ne ya b'aci da ain da Dr ya ke yi, gani take yi kamar wani salon cin fuska ne yake mata, hakan yasa ta rage zaman asibiti. Yau Momi ce da Dr a asibiti take tambayar shi abin da yasa shi cikin wannan halin. Hawaye ne ya fara zubowa Dr kana cikin sanyin murya Dr ya ce "Momi ke da Dadi nasan ba za ku so ku dinga gani na a cikin wannan halin da nake ciki ba, so Momi if you want to see my happiness ki je gun Zarah ki rok'ar min ita ta amince dani, ni nasan tana so na Momi, sai dai abin da na mata ne yasa take min haka, I love her Momi, nasan alhakin ta ne ya kama ni shi yasa Allah ya k'ara min sonta fiye da a lokacin baya, ni kaina nasan ban ma Zarah halacci ba, ban saka mata da irin sadaukar da ta min na soyayya ba, pls Mom pls help me, ina son ganin ta kusa dani". Jikin Momi ne yayi wani irin sanyi had'e da tausayin Dr. A shirye take taje ta rok'e ni in amince in auri Dr ko dan ceto rayuwar shi sannan ita kanta ta yaba min dan tasan ba ni da matsala hasalima Meeman da taso ya aura ita kanta yanzu ta fara dawowa daga rakiyar Meema saboda halayen ta. Rik'o hannun shi tayi ta sakar mishi murmushi ta ce " ka kwantar da hankalin ka Sadik, in dai Fatima rabon ka ce sai ka aure ta yardar Allah, yanzu a shirye nake na je na rok'eta ta amince ta aure ka, ni kaina yabawa da halin ta, ka sa ma ranka za ka samu Fatima in dai Allah ya nufa, ina da tabbacin har yanzu tana son ka za kuma ta amince, sai dai Sadik ba na so ina ganin ka a wannan halin, kasan ciwon da ke damun ka ba ya son damuwa, ka dinga kiyayewa dan samun ci gabanlafiyar ka, insha Allah zan je gidan su". Murmushi ne ya bayyana a fuskar Dr kana ya k'ara rik'o hannun Momi. A hankali ya ce "Momi na gode, Allah ya saka da alkhairi". Ita ma murmushin ta mayar mishi kana ta ce "you deserve more than that my Son". Haka Momi ta ci gaba da lallashin Dr ya kwantar da hankalin shi, suna cikin haka ne Dadin Dr ya shigo. shima dai kwantar mishi da hankali ya dinga yi. Haka suka dinga ririta Dr kamar wani k'aramin yaro. Yau Yaya Faruk ne ya tawo Kaduna dan ya gaishe da su Momi. Gidan su ya fara zuwa kana ya wuce gidan Yaya Aminu dan sun yi waya yana gida. Momin Dr da kanta tayi driving tazo gidan mu. Ina d'aki a kwance ina sauraran wa'azin Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa. Ina kwance na jiyo magana a main parlour amma ban maida hankali na gurin sanin wacce tazo ba. Ummu ce ta shigo ta kira ni. Tun da na shiga falon na yi tozali da Momin Dr. Mamakin zuwan ta nayi da tambayar kaina kar dai Dr ne ya turo ta. Murmushin Momin ne ya k'aru ganin na k'araso. A sanyaye na tsuguna na gaishe ta kana na nemi guri na zauna. Ummu ce ta kalle ni ta ce "Fatima ga Momin Abubakar nan, ta ce gurin ki tazo". Juyawa tayi gurin Momi ta ce "Hajiya bari in shiga ciki in Baku guri, in kun gama maganar Fatima ta kira ni". Momi ce ta ce "Haba ba zai kin je ko ina ba, ni nafi so ma in yi maganar a gaban ki" . Murmushi Ummu tayi ba ta ce komai ba. "Zarah alfarma nake nema a gurin ki, ina so ki yafe ma Sadik abubuwan da ya miki a baya duk da ban San mai ya miki ba, duk wanda kiga an nemi yafiyar shi to shi aka cuta, ina so ki yafe mishi saboda girman Allah da kuma darajata da na tako na zo dan na nemi yafiyar ki" Momi ta fad'a. Sunkuyar da kaina na yi ina wasa da zoben hannuna na ce "Momi ni Dr bai min komai ba, wanda ya min a baya ma na riga na yafe mishi". Fara'ar Momi ce ta k'ara linkuwa ganin yanda tayi saurin shawo kaina dan haka ta ce "Alfarma ta biyu da nake so ki min ina so ki amince ma Sadik ki aure shi, Sadik ya shiga wani hali a dalilin k'in amince mishi da kika yi, yanzu haka yana kwance a asibiti, ba Wanda yake ambata sai sunan ki, wannan alfarmar nake so ki min". Shiru nayi kamar bazan yi magana ba har sai da Ummu ta min magana. D'ago kaina nayi na kalli Momi kana na sunkuyar da kaina. Yanayin Momi ya sa jiki na yayi sanyi yanda take rok'o na, da alama halin da Dr yake ciki yayi tsanani. Zuciya ta ce na ji tana son yin rauni, saurin kau da hakan nayi a zuciya ta. "Fatima ina jin ki, ki fad'a min ra'ayin ka akan Dr d'in" Momi ta katse ni. "Momi ki ba wa Dr hak'uri, ni a yanzu ba na ra'ayin k'ara auren shi, akwai wanda nake so in aura, Allah yasa hakan yafi zama mana alkhairi" na fad'a. Momi cikin lallashi ta dinga rok'o na in tausaya ma Dr saboda gudun halin da zai shiga saboda rashin amincewa ta amma hakan bai sa na canza shawara ta ba. Ummu kuwa tun da muka fara maganar da Momi ba tasa bakin ta ba. Momi ganin ba ta samu nasarar shawo kaina ba yasa ta juya gurin Ummu. Hawaye ne ya fara zubowa a fuskar Momi ta ce ma Ummu "Hajiya ki taimaka ki sa baki Fatima ta tausaya ma Sadik, yanzu in ki ka ga halin da yake ciki sai kin tausaya mishi, ban san me zan fad'a mishi ba" Momi ta k'arasa maganar da fashewa da kuka. Tausayin Momi ne ya cika Ummu ganin babbar mace na kuka. Cikin tausayawa ta ce "Hajiya insha Allah komai zai zo da sauk'i, sai dai a yanzu ba zan matsa wa Fatima akan ta amince ta auri Sadik dan ban san dalilin da yasa tak'i amincewa dashi ba bayan a baya ita ita ta kawo shi a matsayin wanda za ta aura, in Fatima rabon Sadik ce, sai ki ga komai yazo da sauk'i ta aure shi, shi kuma Sadik Allah ya bashi lafiya, Allah ya daidaita lamarin". Hawaye ne ya ci gaba da zubowa a idon Momi tare da jinjina yanda za ta fuskanci Dr da wannan bayanin. A na cikin haka Yaya Faruk yayi sallama ya shigo. Gaishe da su Ummu da Momiyayi kana ya nemi guri ya zauna. Gaishe shi nayi ya amsa min a dak'ile. Sallama nayi ma Momi na koma d'aki na. Addu'a nake yi Allah yasa zuwan da yaya Faruk yasa yazo ne ya fad'a min ya amince da magana ta, da ban San farin cikin da zan yi ba. Bayan tafiya na Ummu taci gaba da fad'a ma Momi kalamai masu kwantar da hankali, har lokacin hawaye bai daina zubowa a fuskar ta ba. Duk maganganun nan da suke yi Yaya Faruk yana jin su. Momi ganin babu alamun samun nasara a zuwan ta yasa tayi musu sallama ta tafi. Bayan tafiyar ta ne Ummu ta mishi bayanin zuwan Momi gidan. "Allah ya zab'a abin da yafi alkhairi" Yaya Faruk ya fad'a. Sun d'an tab'a hira da Ummu kana ya mik'e ya shigo d'aki na. Mamakin ganin shi nayi domin ban yi zaton shigowar shi a lokacin ba. Hannun shi ya hard'e ya jingina da bangon d'akin yana kallo na. Sunkuyar da kaina nayi saboda tsoron hukuncin da zai min na ke yi na kiran shi da nayi a waya. "Fatima" ya kira suna na. A hankali na amsa mishi. Murmushi yayi ganin yanayi na da ya nuna a tsorace na ke kana ya ce "Fatima maganar da na ke so muyi ina so ki d'auke ta da mahimmanci, Fatima ke ce wacce na fara so kuma akan ki nasan dad'in soyayya da illar yin ta, Na so a ce tun farko ni kika fara aura ba wani ba amma sai Allah bai yi na hakan ma yasa na hak'ura da ke, Fatima na sha fad'a miki ina da kishin abin da na ke so, shi yasa ma ba na jin zan amince in aure ki dan nasan kin riga kin mallaka ma wani zuciyar ki da jikin ki ba ni ba, ko a yanzu da kike ik'irarin kina so na zan iya yarda da cewa wani abu nayi ya burge ki kike tunanin so na kike yi kuma nasan kina k'ok'arin ganin kin goge laifin da kika min a baya amma tsantsar so yana gurin tsohon mijin ki, shi kike ma wa, Fatima a yanzu bazan aure ki ba saboda ban yi ma Khadijah adalci ba wacce ta amince ta aure ni a lokacin da nake buk'atar wanda zai maye min gurbin ki, sannan na riga na sa ma zuciya ta hak'uri dake saboda misali ko na aure ki zuciyar ki na ga wani, saboda haka Fatima ki ajiye maganar soyayya da aure a tsakanin mu, ni kaina ba zan so a fara k'irga miki mazan da kika aura ba, gwara mu ci gaba da zama a matsayin y'an uwantaka kamar yanda kika nema a baya, sannan ina so ki tunkare ni da neman shawara in hakan ta taso ni kuma zan tsaya in saurare ki, A k'arshe ina so ki yi hak'uri ki koma gidan tsohon mijin ki tun da shima yana son ki, sannan ki tausaya ma halin da yake ciki da kuma rok'on da mahaifiyar shi tazo ta miki, ina fatan za ki d'auki shawarar da na baki". D'agowa nayi na kalle shi yayin da hawaye yake zuba a idanu na. Shi kenan na rasa Namiji d'aya tamkar da goma. Na rasa jajurtaccen namiji, mai kyawawan halaye da dad'in zama. Dole in hak'ura da Yaya Faruk tun da ya min wannan bayanin. Cikin rawar murya na ce "Na gode Yaya Faruk, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a tsakanin mu, ba abin da zan ce maka sai godiya". Murmushi yayi ya ce "Yawwa Fatima haka na ke son ji, yanzu ina so ki taso in kai ki asibitin ki fad'a ma shi Dr d'in kin amince za ki aure shi". Saurin d'agowa nayi na kalle shi na fara mutsu-mutsu da baki. Fahimtar da Yaya Faruk yayi ban son zuwa yasa ya ce "Fatima ba na son musu, ki taso mu tafi". Ba yanda na iya, haka na tashi nasa hijab muka fito a tare. Sai da muka je gun Ummu, Yaya Faruk ya fad'a mata za mu unguwa kana muka shiga mota muka tafi. Sai da muka fara tafiya ne Yaya Faruk ya tambaye ni wani asibiti a ka kwantar da Dr d'in. Duk da ban da tabbacin in da aka kwantar dashi, nasan ba zai wuce asibitin da yake aiki ba, hakan yasa na fad'a ma Yaya Faruk asibitin. Ko da muka shiga asibitin ba mu sha wahalar gane in da aka kwantar dashi ba kasancewar shi sanannen Dr a asibitin. A tare muka shiga room d'in da Yaya Faruk. Tun da muka had'a ido da Dr ya fara k'ok'arin sakkowa daga kan gadon. Wani irin tausayin shi ne ya kama ni ganin yanda ya canza a y'an kwanaki duk a sanadi na. Na k'ara tabbatar da cewa Dr ba k'aramin so yake min ba tun da ya shiga wannan halin. A yanzu nasan cewa soyayyar da Dr yake min tafi wacce na mishi a baya. Momi kuwa murna ce ta kama ta kamar ta tashi ta taka rawa. Meema kuwa dake can gefe tana danna waya ta d'ago ta zuba min wulak'antaccen kallo kana ta mik'e ta bar d'akin. Yaya Faruk ne ya tambayi jikin Dr kana ya mishi fatan samun sauk'i. Sallama ya musu kana ya sanar dani yana jira na a mota. Momi ma fita tayi daga d'akin ta barni daga ni sai Dr. Alamu ya dinga min akan in zo kusa dashi. Hakan yasa na k'arasa gefen gadon na zauna. "Fatima Zarah" Dr ya kira suna na cikin muryar rashin lafiya. Ban amsa kiran da ya min ba sai kallon shi da nayi. "Fatima ke na ke gani a gaba na kin zo duba ni, Zarah ban San wani irin farin ciki nake ciki ba na ganin ki da nayi a wannan lokacin, San da Momi ta dawo ta sanar dani kin k'i amincewa dani sai da likitoci suka taru akaina saboda numfashi na da ya d'auke, da k'yar aka samu numfashi na ya daidaita, ki tausaya min Zarah, ke ce farin ciki na kuma sanyin idaniya ta". A yanzu ina ganin ba abin da ya wuce da in amince da Dr tun da Yaya Faruk ya ce in hak'ura dashi na kuma fahimci hujjar shi nayin haka". Dr ne ya katse min tunanin da na fara da cewa " Kin amince Zarah za ki aure ni mu ci gaba da gudanar da soyayyar mu a rayuwar auren mu". "Na amince Sadik, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a gare mu" na fad'a. Cikin murna Dr ya dinga min godiya. Cikin y'an mintuna sai ga Dr a zaune yana hira dani kamar ba shi ne a kwance ba. Sanin Yaya Faruk ba ya son jira yasa na ma Dr sallama na fito. Dr ya so ya raka ni na hana shi kasancewar na lura jikin shi bai dawo normal ba. A waje na had'u da Momi na mata sallama. In da Yaya Faruk ya yi parking d'in motar shi na je na shiga muka tafi. A hanyar mu ta komawa gida ne Yaya Faruk ya kalle ni cikin tsokana ya ce "Ashe k'anwar tawa har yanzu tana son Dr d'in ta, gashi daga kai ki duba shi kin barni a zaune kuna can kuna hirar soyayya". Rufe fuska ta nayi ina dariya na ce " Yaya Faruk ba fa hirar soyayya muka yi ba fa". Murmushi yayi ya ci gaba da tuk'in shi yana jana da hira jefi-jefi. Ko da muka koma gida a Main parlour muka zauna muna ci gaba da hira dashi. Tun ban sake dashi ba har na sake muka ci gaba da hira. Ummu San da ta shigo falon ta ganmu da Yaya Faruk muna ba k'aramin jin dad'i ba ne ya bayyana a fuskarta ba. Haka Ummu ta zauna muka ci gaba da hirar da ita. Yaya Faruk ya jima a gidan mu kana ya mana sallama ya tafi saboda ya ce a yau yake son komawa Abuja. B’angaren Dr kuwa an samu ci gaba wajen samun lafiyar shi tun san da na je duba shi a asibiti. Hakan yasa ganin ya samu lafiya aka sallame shi tare da k’ara bashi hutun kwana biyu. Yanzu Dr hankalin shi ya kwanta ganin na amince zan aure shi. Kulawar da yake nuna min da gudun b’acin raina da yake yi yasa na ji na k’ara samun natsuwa da auren shi. Matsa min da Dr yake yi akan yana so ya turo gidan mu ayi maganar aure yasa na fara tunanin yanda zan tunkari Ummu da Abbu da maganar dan ban san yanda za su k’arb’i maganar ba. Ummu na fara sa ma na fad’a mata halin da ake ciki kana na d’aura mata da yanda muka yi da yaya Faruk. Ummu tayi mamakin maganar da na fad’a mata game da yanda muka yi da yaya Faruk, ba ta ji haushin yaya Faruk dan ya k’i aure na, tasan cewa ni na b’ata rawa ta da tsalle sannan ba kowa ba ne zai laminci abin da nayi daga baya ya amince ya aure ni ba, tun farko taso a ce shi na Aura amma Allah bai nufa ba, yanzun ma tasan Allah bai nufa zan zamo matar shi ba, fatan alkhairi ta min akan maganar mu da Dr kana ta ce za ta sanar da Abbu halin da ake ciki. San da Abbu ya dawo gida ne Ummu ta zayyane mishi halin da ake ciki. Shi kan shi yaso a ce karo na biyu yaya Faruk ne ya same ni a matsayin mata amma tun da yaya Faruk ya kawo dalilin na k’in aure na yana ganin bai kamata ya mishi magana akan ya aure ni ba tun da yanzu ba ya ra’ayi na yasan Allah ne bai nufa zan zamo matar shi ba. Fatan Allah yasa shi Dr d’in ya zamo wannan karan shine mijin da zan aura baa tare da wata matsala ta k’ara shiga tsakanin mu ba har ta kai ga rabuwa. Ummu yasa ta kira ni ya min nasiha tare da addu’ar Allah ya tabbatar mana alkhairi a tsakani na da Dr kana ya d’aura da cewa in fad’a ma Dr d’in ya turo. Ina fad’a ma Dr yanda muka yi da Abbu akan ya turo ya dinga murna. Ba a d’au wani lokaci ba Dr ya turo magabatan shi aka tsayar da biki nan da wata uku. Wannan karan na samu na samu natsuwa a alak’a ta da Dr ganin su Ummu da Abbu sun nuna amincewar su sannan su yaya Khalil da yaya Aminu da Anisa ma sun nuna amincewar su. San da Anty Jiddarh tazo na ke fad’a mata yanda muka yi da yaya Faruk da kuma halin da ake ciki tsakani na da Dr ita ma fatan alkhairi ta min. Meema kuwa tun san da taji aure na Dr ta tada hankalin ta da shi kanshi Dr d’in akan cewa ba ta amince ba. Tun Dr yana bin ta a hankali har tazo ya biye mata suna sa’in’sa da ita amma duk da haka Meema ba ta da alamar hak’ura. Dr da farko ya d’auka cewa za ta hak’ura ta daina ta da hankalin ta akan aure na da zai yi amma abin ya ci tura. Ganin yanda kullum suke cikin rikici da ita yasa ya je ya fad’a ma Momin ta, ita kanta Momin Meeman fad’a ta fara mishi akan aure na da zai yi. Ganin nan ma ba nasara yasa ya je ya fad’a ma Momin shi matsalar da su ke fuskan ta da Meema. Hak’uri Momi ta bashi tare da k’ara nuna mai ribbar hak’uri da yanda zai lallashi Meema d’in. Ta fad’a mishi in ta samu free time san da ba ta da aiki za ta zo gidan ta lallashi Meema d’in. Yaji dad’in yanda Momi ta bashi shawarwari kana ya mata sallama ya tafi. Ko da ya koma gida haka Meema ta dinga zuba mishi rashin mutunci wanda ta kai ya kasa controlling d’in zuciyar shi ya mare ta. Haka Meema ta dinga kuka tana fad’an duk maganar da tazo daga bakin ta. Jin yanda zuciyar shi ke mishi wani irin zafi da maganganun da Meema ke fad’a mishi yasa ya nufi side d’in shi dan yasan tsayuwar shi a gurin zai sa ya mata mummunan hukunci. Yau Momi ce ta zo gidan Dr. Side d’in Meema ta fara zuwa ta tarar da ba kowa a falon sai mai aiki. Mai aikin ce ta gaishe ta kana Momi ta ce ta kira matai ta. Sai da aka d’au lokaci kafin Meema ta fito. Tun da taga Momi ce ke kiranta ta k’ara d’aure fuska saboda yanzu haushin Momi take ji saboda tana ganin ta had’in bakin ta Dr zai aure ni. Sai da ta nemi guri ta zauna kana ta gaishe da Momi a dak’ile. Duk da Momi taji haushin yananyin yanda Meema ta gaishe ta amma sai ba ta nuna ba ta amsa mata da fara’a a fuskar ta. Nasiha da lallashin ta Momi ta dinga yi amma duk wannan mganar da Momi take yi kamar ba da ita take yi ba. Momi ce tasa Meema ta kira mata Dr kasancewar yana gida. Nasiha ta dinga musu gaba d’aya da nusar da su hak’uri da juna da kuma zaman lafiya a tsakanin su. Meema wacce ranta ya b’aci da wannan nasihar da Momi take musu ta ce "Momi ni fa in dai ba cewa kika yi yaya Sadik ya fasa auren nan ba to ina ganin no need of this advice, nasan kema son auran nan da yaya Sadik zai yi kike yi saboda kina son farin cikin d’an ki amma ni ba kya son nawa, ke kan ki Momi kin san irin son da yaya yake ma Zarah amma shine kike so ya auro ta ya had’a mu saboda in ta kwasar bak’in ciki, to ni dai bazan zauna da wata kishiya ba tun da gidan mu ma ban taso na ga kishiya ba saboda haka sai dai Dr ya hak’ura da wannan k’addararren auren da yake son yi" Momi da mamakin abin da Meema ta yi ya kama ta yasa ta kasa yin magana sai bin ta da tayi da kallon mamaki. Dr kuwa wanda ran shi ya gama b’aci da maganganun da Meema take fad’a ma Momin shi yasa ya daka mata tsawa ya ce "Ya ishe ki Meema, zan iya jurar komai amma ba zan lamunci ki fad’a wa Momi magana ba, ko da yake tarbiyya ba isan ki tayi ba". Wani banzan kallo ta watsa mishi kana ta ce "Ina fa tarbiyyar za ta ishe ni tun da ban je gidan ku an koya min ba, k’arya nayi ba da Momin aka had’a wannan munafuncin auren da za kayi bad an ta ga ni ba y’ar ta ba ce, in da Hanan ce ko Farida ai ba za ta bari a k’ara musu kishiya ba shine ni take so a min, in dai ana son kwanciyar hankali a gidan nan dole ne ka fasa auran nan in ba haka ba kuwa ka dinga gamuwa da b’acin rai, ko dan ka ga ina son ka shine za ka dinga wulak’anta ni, kai kan ka kasan ni y’ar gat ace gaba da baya saboda haka ba zan tsaya in ga za a yi disgracing d’ina ba". Dr saboda b’acin rai jikin shi har rawa yake yi ya mik’e da niyyar marin Meema amma fahimtar hakan da Momi tayi yasa ta hana shi marin ta. Cikin b’acin rai Dr ya ce "Meema tun da abin na ki ya wuce kaina ya fara koma wa kan Momi gwara in d’au mataki dan gaba ban san me za ki fad’a wa Momi ba dan haka ki je na sake saki d’aya in kin koyi tarbiyya da ilimin islamiyya may be in iya dawo dake". Momi ce ta daka mishi tsawa ta ce "Sadik a she ba ka da hankali ban sani ba, a gaba na za ka saki Meema, duk abin da ta fad’a ko tayi ba akan kishin ka da take yi bane yasa ta yi hakan, kai me yasa ba ka iya controlling d’in zuciyar ka ne idan ya b’aci, yanzu wace riba ka samu da ka sake ta". "Sorry Momi na yi kuskure, raina ne ya b’aci da maganganun da Meema take fad’a, I can’t tolerate it anymore". Meema kuwa mik’ewa tayi ta ja tsaki ba tare da ta ce komai ba duk da yanda take ji a zuciyar ta na sakin da Dr ya mata. Kayan ta taje ta had’o a trolik ta zo za ta wuce. Momi ce ta kira sunan ta amma ko alamar juyowa Meema ba ta da alamar yi. Tana fita ta shiga motarta ta ja ta bar gidan. Momi fad’a ta dinga ma Dr akan abin da yayi tare da bashi shawarar in an kwana biyu ya je gidan su Meema ya bata hak’uri ya dawo da ita. Ita kanta Momi ta dai fad’i hakan ne ganin yanda suke mutunci da amince da ke tsakanin su da gidan amma ba wai dan tana jin dad’in zama da Dr yake yi da Meema ba. Dr ya amsa mata da zai je gidan su Meema d’in amma ba dan haka yake a zuciyar shi ba. Haka Momi ta tashi ta tafi tare da mamakin halin Meema a ranta. Meema kuwa tun da ta je gida take kuka. Da Mominta ta tambaye ta dalilin kukanta ta fad’a mata gaskiya da k’arya. Ran Momin ne ya b’aci ta ce Meema ba za ta koma ba tun da Dr ba shi ba ne autan maza. Lokacin da Dadin ta ya dawo haka Momi ta zauna ta fad’a mishi abin da Meema ta fad’a mata. Da Dadi ya tambayi Meema ta k’ara tabbatar mishi da maganar. Dady ya tambayi ra’ayin ta game da komawar ta gidan Dr ta nuna ba ta ra’ayi, hakan yasa Dadi bai takura mata ba ya k’ayale ta. Lokaci na ta tafiya yayin da bikin mu ya rage saura sati d’aya. Duk wani shirye-shirye ta b’angare na da Dr komai ya kammala. Komai sabo Abbu ya min kamar wata budurwa. Ummu kuwa kayan gyaran jiki ta sa aka had’o min ana min da magunguna na gyara masu tsada ta dinga ba ni ina sha. Su yaya Aminu da Khalil ma ba a bar su a baya wajen kawo nasu gudunmawar. Hatta da su Anty Jiddarh da Anisa suma sun yi k’ok’ari ganin sun birge ni a bikin. Dadin su yaya Faruk ma ba k’aramar gudunmawa ya bayar a biki na ba, ita kanta Momi gudunmawar da ta bayar ba k’arama ba ce da turarurrukan wuta masu tsada. Hajiyan Wagini ma da tazo ta nuna farin cikin ta na auran da zan yi da Dr, nasan hakan ba ya rasa nasaba da ko yaya Faruk ya mata bayanin shi ya ce ya hak’ura da ni. Gaskiya ba abin da zan ce sai dai godiya dan na tabbar ni y’ar gata ce gaba da baya. Wannan karan ma akwatuna masu tsada shak’e da kaya ya min. Na jinjina irin soyayyar da Dr yake min. Yaya Faruk mu na yawan waya dashi tare da tambaya ta ko akwai abin da nake buk’ata. Ta account ya turo min da gudunmawar biki. Da na fad’a ma su Ummu su ma sun nuna jin dad’in su akan kyautar da yaya Faruk ya min. Dr yaso mu shirya event amma ban ba shi goyon baya ba ganin wannan ba shi bane auren mu na farko. Walima kawai da kamu na yarda zan yi. Tun da aka fara hidimar bikin da Halima da Aisha ake yi duk da sun yi aure haka suke k’ok’arin zuwa. Rana ba ta k’arya sai dai uwar d’iya ta ji kunya. Yau dai gashi Allah ya nufa an k’ara aure na da Dr Abubakar Sadik a karo na biyu. Sai dai in mana fatan Allah ya zaunar da mu lafiya. Bayan d’aurin auren ne yaya Faruk ya shigo ya min fatan alhkairi. Mun jima dashi yana min nasiha akan zamantakewar aure tare da kwad’aitar dani akan hak’uri a rayuwar aure. Ni kam ba abin da zan ce ma yaya Faruk sai dai in ce Allah ya saka mishi da alkhairi. Duk yanda na so Dr ya bari a d’aga tarewar amma ya k’i. Haka yasa aka shirya ranar za akai ni. Yau ma kamar aurena na farko sai da na ci kuka na san da za a tafi kaini na rabuwa da gida. Su Anty Jiddarh da Anisa sai tsokana ta suke yi. Lokacin da aka kai ni gidan Dr ne na ga Dr ya canza painting gidan tare da k’awata gidan. Haka kowa ya watse ya rage sai ni kad’ai. Ba su jima da tafiya ba Dr ya shigo gidan. Ranar Dr ya nuna mn wata irin soyayya wanda baki ba zai iya fad’a ba, ya shayar da ni soyayya mai wuyar mantawa, ya nuna min kalar soyayyar da yake min wanda har tausayi ya bani ganin yanda yake zubar da hawayen shi akan irin son da yake min Na sa ma raina cewa zan yi hak’uri da duk abin da Dr zai min tun da Allah ya nufi daman Dr shi zai zama mji na sannan zan yi iyakar k’ok’ari na ganin zaman mu bai samu wata tangard’a ba. Sai da muka kwashe sama da sati d’aya Dr yana nuna min kulawa da soyayya. Tun da na zo gidan na fahimci Meema ba ta gidan, ganin Dr bai min maganar ta ba yasa nima ban mishi maganar ta ba. Yau da muna zaune ne na ke tambayar shi wai Ina Meema, na ga tun da na zo ban gan ta ba. Amsa min yayi da tayi tafiya ne. Tun daga wannan lokacin ban k’ara tambayar shi Meema ba. Haka zaman mu ya ci gaba da gudana cikin so da zaman lafiya. Yanzu ban da wata sauran damuwa a zama na da Dr. Ina zuwa aiki na wanda muka yi da Dr tun kafin mu yi auren dashi akan zan koma aiki ya amince. Yanzu Hanan ba ni da sauran wata matsala da ita saboda yanda take ba ni matsayina na matar wanta, daman ita Farida ban da matsala da ita. Momi ma yanzu wata irin kulawa take bani ta musamman wanda da farko har na fara mamaki. Nima dai ina iyakar k’ok’ari na wajen ganin na kyautata musu. Yau Dr da yaje gidan Momin shi ne take mai magana akan dawo da Meema, ya amsa mata da zai je. A ra’ayin Dr ba ya sha’awar dawo da Meema amma ganin yanda Momi shi ke son ya dawo da ita da kuma duba irin son da Meeman ke mishi yasa zai dawo da ita. Lokacin da Dr ya je gidan su Meema ya shiga falon ba wanda yayi marhabin da zuwa dashi tsakanin Meema da Momin ta. Maimakon ya samu kalamai masu dad’i a gurin su sai sab’anin haka. Ba irin maganar da Meema ba ta fa’da mishi ta b’atanci ba. Haka ya baro gidan ran shi a b’ace. Ko da ya koma ya fad’a ma Momi yanda suka yi da Meeman ba ta ji dad’in haka ba. Ta tabbatar mishi da za su je da Dadin shi dan su ba Meeman hak’uri. Dr yasan zai yi wuya su Momi su shawo kan su Meema amma yafi son su je dan in ya hana ta za ta ga kamar ba ya son dawowa da ita ne. Momi sun je da Dadi gidan su Meema d’in da daddare. Dadin ta ya kira Meema ta sake tabbatar musu da cewa ita ba za ta koma gidan Dr ba tun da ya dawo dani, hasalima ta san ba son ta yake yi ba. Duk yanda Momi da Dadin Dr suka ba wa Meema hak’uri akan ta koma ta ce ba za ta koma ba. Hakan yasa jiki a sanyaye su ka tashi suka tafi ba tare da sun samu nasarar shawo kan Meema ba. Ko da Dr yaje gidan Momi ta fad’a msihi yanda suka yi da Meema bai nuna damuwa shi ba. Ni kuwa duk wannan abin da ke faruwa ban sani ba, sai da su Hanan suka zo suke fad’a min rabuwa suka yi da Dr d’in saboda aure na da zai yi. Ban ji dad’in abin da ya faru ba saboda ban so ta sanadiyyar aure na yasa suka sami sab’anin ba har suka rabu. Hakan yasa nima na tuno dalilin rabuwar mu da Dr lokacin da zai k’ara auren Meema ne. Lokacin da Dr ya dawo na mishi maganar rashin dad’i na akan rabuwa da suka yi da Meema. B’ata rai yayi ya dinga min fad’a akan in cire baki na akan Meema. Hakan yasa na sa ma kaina cewa ba zan k’ara mishi magana akan Meema ba tun da ba ya so. Ganin yanda yanayi na ya canza ne yasa Dr ya dinga ba ni hak’uri. Nuna mishi nayi ba fushi nayi ba kana ya saki ranshi muka ci gaba da hira. Yanzu aure na da Dr yana neman wata biyar amma har yanzu ban samu ciki ba. Hakan yasa hankalin Dr ya fara tashi saboda shi ma ba abin da yafi buk’ata da ya wuce ya ganni da ciki. Duk wani taimako da ya kamata Dr ya bani a matsayin shi na likita amma ba a samu nasara ba. Hakan yasa Dr ya fara danasanin family planning d’in da yasa nayi wanda a yanzu yake so in samu ciki amma Allah bai nufa ba. Ni kaina rashin samun ciki na tun lokacin zaman mu da Dr na farko har zuwa yanzu yana d’aga min hankali. Ganin yanda Dr yake d’aga hankalin shi ne yasa na ke danne damuwa ta. Haka Dr ya fara kai ni gurin k’wararrun likitoci suna duba ni. Sun tabbatar da cewa ba wata matsala da na ke tare da ita, lokaci ne kawai bai yi ba. Muna na cikin wata na shida ne muka fara gudanar da shirye-shiryen bikin Hanan da za ayi a watan. Duk wannan shirye-shiryen da ake yi ba jin dad’in jiki na nake yi ba saboda a kwanakin yanda nake fama da rashin lafiya a tsaitsaye. Yau ban da aiki saboda haka a gidan Momi na wuni saboda bridal shower da za ayi a washegari. Tun da nake kwanciya saboda zazzab’in da ya rufe ni. Hakan yasa Momi ta kira Dr ta fad’a mishi ba ni da lafiya. Ba a d’au lokaci ba sai ga Dr ya zo gidan. Haka ya shigo hankalin shi a tashe ya nufo kujerar da na ke kwance. Abokan wasan shi sai tsokanar shi suke yi yana rama wa. Kujerar da nake kwance ya zo ya zauna ya tab’a wuya na yaji yayi zafi. Hakan ya tabbatar da zazzab’i ne ya rufe ni. Zaunar da ni yayi ya nufi d’akin Momi ya d’akko jaka ta da veil d’ina ya dawo ya mik’a min. Momi ce ta tambaye shi ina za mu kuma bayan yana ganin ban da lafiya. Amsa mata yayi da gida zamu akwai allurar da zai min kuma bai tawo da ita ba. Cikin tausayawa aka dinga min sannu. Haka Dr ya rik’o hannu na muka shiga mota. Momi har wajen mota ta rako mu tana min sannu. Sai da taga mun fita daga gidan sannan koma ciki. Tun a hanya Dr yake tambaya ta in da yake min ciwo ban da fever d’in da ke damu na ce mai ba komai. Muna zuwa gida na nemi kujera na zauna. Shayi Dr ya je ya had’o min ya bani na sha. Ai ban gama shan shayin ba naji amai ya tawo min. Da gudu na tashi na nufi band’aki na dinga kwarara amai kamar zan amayar da kayan ciki na. Haka Dr ya rik’e ni sai da na gama aman. Wanke min fuska yayi ya rik’o ni ya kai ni bedroom ya kwantar dani. Allura ya min kana ya koma band’akin dan ya gyara. Ko da ya dawo ya tarar nayi bacci. Hakan yasa ya zauna a gefe na yana kallo na had’e da tausaya min. Washe gari ma haka na k’ara tashi da zazzab’in had’e da amai. Duk wani abu da na ci sai da na dawo dashi. Hakan yasa Dr ya fara zargin ko abin da muke nema ne ya samu. Gwada ni Dr yayi ya tabbatar da ina da shigar ciki na tsawon wata d’aya, shine yake wahalar da ni. Rungume ni Dr yayi cike da murna yana cewa "Zarah mu gode ma Allah, abin da muke nema ne ya samu, Allah ya amshi rok’on mu, you are preganant, am going to become a father, Alhamdulillah". Ni kaina wani irin farin ciki ne na ji ya kama ni da ban san yanda zan fasalta shi ba. "Ke ma Zarah kina farin cikin za ki zama Momi ko?" Dr ya tambaye ni. Hawaye ne ya fara zubo min a idanuna na d’aga mishi kai alamar eh. Kwantawa nayi a kafad’ar shi yayin da yake shafa min baya na. Duk yanda na so Dr ya bar ni in je gidan Momi saboda yau Bridal shower Dr ya k’i. Momi da ta kira shi tambayar shi jiki na da kuma dalilin da yasa ban zo ba. Shine yake fad’a mata dalilin ciwo na. Momi ta yi murna da jin wannan labarin na cikin da na samu. Hakan yasa Momi ta ce in zauna in huta ba sai na zo ba. Ranar haka Dr ya tare a kaina yana ba ni kulawa. Motsi kad’an zai tambaye ni abin da yake damu na. Haka dai aka yi bikin Hanan ina laulayi. Duk yanda Dr yaso in zauna a gida saboda yanayin jikina na k’i. An kai Hanan gidan ta da ke Unguwar sarki a Kaduna. Sai dai mu musu fatan Allah ya zaunar dasu lafiya. Ciki na yana da wata 9 na haifi d’ana namiji aka sa mishi suna Imran. Dr ya kashe min kud’i da baby a wannan haihuwar. Momi haka ta had’o min kaya da na baby a akwati shak’e da kaya. Dadin Imran kud’i ya aiko dashi ya ce a ba ni. Hanan ma haka ta kawo ma baby kaya masu tsada. Ummu da Abbu sun nuna bajintar su a haihuwar da na yi. Su yaya Aminu ma da yaya Khalil ba a barsu a baya ba. Yaya Faruk ma ya kawo Nana suna da sha tara ta arzik’i, ranar suka juya Abuja. Duk yanda Ummu taso in koma gida in yi wanka Dr ya k’i. Hakan yasa Momin shi ta ce in koma gidan ta nan ma hana wa yayi. Dole tasa suka ky’ale shi a ka turo wata y’ar uwar Ummu tazo ta zauna da ni. Haka muka ci gaba da kula da Imran. Yanda Dr yake nuna ma Imran kulawa yasa naji ya k’ara shiga raina. Ina da kusan wata biyar da haihuwa yaya Faruk ya tare a sabon gidan shi da ya gina a Abuja shi da abokin shi yaya Mus’ab. Arzik’in Yaya Faruk ya k’ara yalwata had’e da ci gaba da taimaka wa wajen ceto rayuwar al'umma da basu tsaro yanda ya kamata, hakan yasa ya ke samun lambar yabo da lambar yabo. Yanzu yaya na maida shi abokin shawara ta, Ba ni da sauran wata matsala tsakani na dashi. Wata rana ina zaune Dr ya dawo daga unguwar da ya fita. Bayan ya huta ne yake sanar da ni daga d’aurin auren Meema yake ta auri wani d’an abokin Dadin ta da yake aiki a NNPC. Shi ne na ke tambayar shi dalilin da yasa ya k’i dawo da ita yake fad’a min ta ce ba za ta iya zaman kishi da ni ba. Abin ya ban mamaki ganin irin son da Meema take ma Dr amma ta hak’ura dashi. Mamakin irin kishin ta nayi da har ta hak’ura da wanda ta ke so saboda kishi. Dr ne ya tabbatar min da cewa wanda ta aura yana matuk’ar son ta tun kafin shi ya aure ta, hakan yasa ta amince ta aure shi. Fatan zaman lafiya na musu ita da wanda ta aura. B’angaren Dr ma abin sai hamdala saboda samun d’aukaka da alkhairi da yake yi wajen taimaka wa al’ummar musulmai. Hakan yasa a ka k’ara mishi albashi mai tsoka. Yanzu ban da aikin da Dr yake yi har kasuwanci ya fara yi. Hakan yasa arzik’in shi kullum sai k’ara hab’b’aka yake yi. Ba abin da zan ce a zamantakewar auren mu da Dr sai godiya ga Allah subhanahu wata ala. Imran na da shekara d’aya da rabi na yaye shi. Na so tun da nayi arba’in mu je Abuja gurin yaya Faruk amma Dr ya hana ya ce sai Imran ya k’ara wayau. Sai bayan da na yaye shi ne na k’ara msihi maganar ya ce in bari ran weekend sai mu je. Hakan yasa na kira yaya Faruk na sanar dashi ranar zuwan mu ba. Ranar lahadi muka shirya muka tafi Abuja. Sai da muka tsaya a wani gurin siyar da kayan wasan yara muka siya ma Khairat kana muka k’arasa gidan yaya Faruk kasancewar ya fad’a mana sunan unguwar. Gaskiya gidan da yaya Faruk ya gina abin kallo ne saboda kud’in da aka kashe ma gidan. Mun samu tarba ta musamman gurin yaya Faruk da Nana. Khairat ta k’ara wayau sai gudun ta take yi ko ina. Mun kai kusan yamma kafin mu yi shirin koma wa. San da za mu tafi ne yaya Faruk ya ce mu shiga gidan yayan Nana mu gaisa da ita. Kud’i masu yawa yaya Faruk ya ba wa Imran. Kasancewar na san su lokacin da na yi zaman Abuja yasa san da muka shiga na zauna muka dinga hira. Dr ne ya ce mu tashi mu tafi kasancewar yamma tayi. Yaya Mus’ab ma haka ya ba wa Imran kud’i. Haka suka rako mu muka shiga gidan yaya Faruk muka shiga motar mu. Sai da suka ga tafiyar mu kana suka daina d’aga mana hannu. Bayan dawowar mu daga Abuja da kusan wata biyar muka tafi Makkah muka sauke farali kasancewar tun lokacin da na samu ciki yaso ya biya mana, ganin laulayin da nake yi yasa ya d’aga biyan zuwa wata shekarar. Mun je aikin hajji mun yi ibada kafin lokacin dawowar mu yayi muka dawo. Y’an sannu da zuwa haka suka dinga yi mana sannu da zuwa. Yanzu jikin Dr Alhamdulillah da sauk’i sai abin da ba za a rasa ba. Shi kan shi yasan ya samu sauk’i sosai dan BP d’in shi ya dad’e bai tashi ba da ulcer da yake fama dashi. Ko da ya je asibitin Barau Dikko b’angaren zuciya likitan ya tabbatar mishi da yana samun sauk’i ya kuma k’ara d’aura shi akan magani. Dr ya k’san a nemi hutu a gurin aiki kasancewar yana so ayi mishi check up a k’asar India. Dr ya mana booking d’in jirgin India saboda likitan zuciya (cardiologist) da yake so ya gani sannan za mu wuce k’asar saudiyya muyi Ummarah. Ana saura kwana biyu tafiyar mu muka je gidan Ummu da yaya Aminu da Momin Faruk muka musu sallama. Washe gari muka je gidan yaya Khalil da gidan Hanan da gidan Momin shi muka wuni a can Gurin Momi muka bar Imran saboda a cewar Dr wani bayan duba lafiyar shi da za mu har da honeymoon za mu k’ara yi a can Indian, ba zai so Imran ya takura mishi ba. Ranar da za mu tafi kasancewar jirgin safe za mu bi yasa Farida ta zo ta kai mu airport. San da aka kira sunan mu gurin shiga jirgi ne muka mik’e had’e da d’aga ma Farida hannu muka nufi jirgi. Farida ce ta dinga mana waving d’in hannu muna mata har muka shiga jirgi. Kujerar kusa dani Dr ya zauna yana rik’e da hannu na. A hankali Dr ya kalle ni ya sakar min tsadadden murmushi ya fara min magana a hankali. "Fatima Zarah!" Dr ya ambaci suna na. "Na am Dadin Imran" na amsa mishi. "Ina jin dad’in kasancewa da ke a ko da yaushe, duk wuya duk rintsi ina tare da ke, ina miki wani irin so da ban san yanda zan fasalta miki irin shi ba, zan so ki ci gaba da so na har k’arshen rayuwar ki". Murmushina na fad’ad’a shi na ce "Kar ka damu ni taka ce, nima ina son ka kuma zan ci gaba da son ka a ko wane yanayi". Rungume ni yayi ya fara min magana a kunne "Na gode Zarah tah! Allah yasa indian nan da za mu ki samo ma Imran k’anwa a can, dan ba k’aramin honeymoon za mu sha a can ba kafin mu tafi Ummarah daga can". Saurin rufe fuska ta nayi ina dariya. Wani zazzafan kiss ya kai min a kumatu na wanda yayi daidai da tashin jirgin mu sararin samaniya. Ni y’ar mutan Paki na ke cewa safe trip. Alhammdulillah! Anan na kawo kawo k’arshen wannan littafin mai suna *MAKAUNIYAR SOYAYYA* Laifukan da na yi Allah ya yafe min. Abin da na fad’a na alkhairi Allah yasa ya amfani jama’a. Fata na har kullum Allah yasa labarin da nake rubutawa ya amfani al’umma. Anan nake cewa sai mun k’ara had’uwa daku a cikin wani sabon littafi na mai suna…… Allah ka sa da mu da alkhairin sa baki d’aya. *GODIYA GARE KU MARUBUTA* Memcy Ata (Marubuciyar Ni da yaya Farooq) Fauxia MB (Marubuciyar Lokaci ne) Ummien Fauzan (Marubuciyar Bahijjah) Ummy Abdoul (Marubuciyar Jamaluddeen) Ina godiya da yanda kuke bin wannan labarin, da fatan da za ku ci gaba da suburbud’o mana labari masu ma’ana. *ANA TARE* Mrs Mansoor (Marubuciyar Munafukin miji) Batul Adam Jatko (Marubuciyar Amfanin soyayya) Mrs Adam (Marubuciyar Mamaya) Hauwa Usman (Marubuciyar Gadar zare) Noorul Jannerh (Marubuciyar Detective Noor) Ina jin dad’in yanda kuke nuna kulawar ku gare ni. *YABON GWANI YA ZAMA DOLE* Dole ne in jinjina muku marubutan Kainuwa Writers Association, kuna ba da gudunmawar ku wajen fad’akar da al’umma da nishad’antar dasu. *BA NI DA KAMAR KU* Y’an Mufy & Maryam A paki fans Ba wanda ya kai ku yawan comment akan wannan littafin da nuna kulawar Ku akan novel d'in. Da fatan za ku ci gaba da nuna kulawar ku gare ni. Nima y’ar mutan paki na tare da ku. [Mmn Walida, Sakina ilyas, Autar Mama, Fadeela, Hauwa Hussaini, Fadeela, Habiba Rabo, Br Teemah, Hauwa, Maimuna, Hauwaa, Hajara Tijjani, Maryam, Aysha, Safia, Ummie, Najerh, Siddiqa Dahiru, Hauwa j, Lubiee, Maman Aliko, Ramlah Salis Kabir, Maman Umar, ~Hauwa, Harira, Zakiyya, Aysha Umar gogo, Ummu Haneef] *BAN MANTA DA KU BA* Y’an Kainuwa Fans whatsapp da facebok Kuma ba abin da zan ce muku na irin yanda kuke nuna jin dad’in ku akan wannan novel d’in da yin comment d’in ku. [Xarah Auwal, Meeynarh, Asmau Madugu, Aisha Mahmud, Aisha Madugu, Eesha, Deejahnah, Khadija y’artuwalla, Fatima Arkilla, Rufaatu, Zinatu gatari, Fatima, Binafat, Fatima Ibrahim, Maman Sa’a, Maimunat Abba, Mrs Ahmad, Maryam Bello, Xee virus, Zainab Mas’ud, Maman Faruk, Ummi, Mom Affan, Amina Samaru, Rahma ja’afar, Maman Shahida, Maman Usy, Hajiyar Allah, Atika Bashir, Khadijah Ahmad, Murjanatu Bukhari, Faeedaabdullahi, Aisha Ibrahim, Ameenat Umar Abdulllahi] *GAISUWAR TA KU CE* Ina mik’a sak’on gaisuwa ta ga wannan groups d’in whatsapp da facebook yanda kuma ku ke yin comment akan wannan novel d’in. Tauraruwar Mace group Ni da yaya Farooq group Mrs Mansoor novels group Daily Hausa novels group Novels Villa group Da sauran groups d’in da ake posting d’in wannan novel d’i *DOLE NE IN TUNA DA KU* Ba ni da bakin godiya gare ku na yadda kuke son novel d'in nan da nuna k'aunar ku gare ni. Duk irin godiyar da zan nuna muku ina ganin tayi kad'an saboda yanda kuke tare dani. Fata na Allah ya ci gaba da had'a mu da masoyan mu a ko ina su ke. Wanda su ka kira ni daga wasu jahohin da Wanda suka min text da masu min magana ta Pc ba abin da zan ce muku sai godiya Mhiz Tawakkaltu Nafisa Khaleed (Bintu Khaleed) Fatima Sunusi Baraya (Unique wife) Badiyya Kano Mmm Abdullahi Adnan Saudat Hussaina (Facebook) Hussaina paki Fannata ta Annabi Asiya Paki Zainab Abdullahi (Abuja) Hussaina Ahmad Fatima Bintu Kano Hadiza Murtala YusraYusra Da sauran wanda ban samu rubuta sunan su ba saboda yawan ku. Da fatan za a min uzuri akan haka. Daga Taskar Marubuciyar Haka Amincin yake? Rayuwar Yusra da Afsahan Silar Kayan Sallah Makauniyar Soyayya Taku har kullum Maryam Ahmad paki na ke cewa Bissalam Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels