Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [6/23, 12:43 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written by_ _jiddah S mapi_ _Follow me on wattpad_ jiddahpretty Hi guys this is my first story hope I will have your maximum co-op ration ❤️ *NOTE:* Banyi wannan littafin sabida wani ko wata ba, labarin kirkirrarre ne sabida haka akula sosai. _dedicated to fateemahsardauna_ Page 1&2 "Haba Ahmad meyasa bazaka dauki kaddara ba, kasani fa kowani dan Adam da irin tasa kaddarar, na wani yafi na wani amma Sam kai baka dauki kaddaraba. Nan naga Wanda aka kirada suna Ahmad ya dago kanshi, yana hawaye fuskarshi tayi ja, buɗe baki yayi yanason yin magana amma ya kas, sai kuka yake kamar wata mace, hadda shesheka dakyar ya iya cewa "Haba Habeeb ya bazanyi kuka ba, bacin kai kasan abinda yake damuna, idan Banyi kukaba me zanyi?" Yaƙare maganar cikin sanyin murya. Gyara zama Habeeb yayi haɗe da cewa. "Addu'a ya kamata kayi Ahmad, domin itace abinda yakamata kowani musulmi yayi, a lokacin daya samu kanshi cikin yanayi na kunci." "Ya isa haka Habeeb, ka ƙyaleni naji da abinda yake damuna, bawai ka cikani da surutunka ba, sanin kanka ne nayi babban rashi a rayuwata, rashin daba zan taɓa mantawa ba, tunda narasa FATEEMAH narasa komai, na wulaƙantata, na ƙuntata mata, nayi mata abinda bazata taɓa mantawa daniba, Ina zanga Fateemah? Ina zanji labarinta? tana raye ko Tana mace?" Ɗan jinkirtawa da maganan yayi, kana ya cigaba da cewa. "Idan Tana raye Ya Allah Ka bayyana min ita, idan kuma tamutu Allah Ka kai haske kabarinta!!" Ya ƙarashe maganan yana wani irin gunjin kuka. Awannan lokacin har Habeeb ba'a barshi abaya ba, duk dauriyanshi shima seda yayi hawaye, yana me tausayawa abokinnashi. *** *** "Wai Ina kike ne BINTU? kiyi sauri dan Allah kinsanfa mommy Tana jiranmu a mota." "Ina zuwa Sis HABEEBA, gyalena nake dubawa ban gani ba." Naji wata siririyar murya Tana fada. "Kiɗauki nawa a wardrobe mana bintu." Habeeba tafaɗi haka cikin yanayi na ƙosawa. "Okay nama dauka ae ganinan." Beentu tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin yafa gyalen ajikinta. "Okay dama koban ce kidauka ba zaki dauka kenan?" Habeeba tafaɗa tana ɗan kallon gefen da Beentun take. Nan naga Beentu na sauƙowa daga kan step, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa. Farace sol doguwa siririya, tana da manya manyan idanu, bakinta dan karami, ƙoƙarin gyara gyallen take, tayadda zai zauna akanta. Cewa tayi "Haba My Hussaina, Kinsan fa bama haka dake, kuma naga kema ay kinasa abuna ko my sis?" "Da ma ay haka zakice, kullum se kinwa mutum laifi kizo kina mishi sanyin murya, to yanzu de muje kinga Mom nata kirana, kusan 6 missed calls tayi min" Habeeba tafaɗi haka tana mai duban wayarta dake riƙe a hanunta. "Okay to muje" Cewar Beentu. A tare suka fito daga falon suna sauri. _see me next page_ ✍️🏻 *Jidderh S Mapi* [6/23, 12:43 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story written by_ Jiddah S mapi _dedicated to fateemahsardauna_ _wattpad jiddahpretty_ Page 3&4 Suna fita daga falon habeeba ta kwalawa driver Kira yace gani hajiya tace Ina mommy yace ay hajiya ta dade da tafiya tace bazata iya jiranku ba idan kun gama ku sameta agidan abinci ok to kaimu driver yace to nan suka shiga motar suka tafi bayan driver yayi parking naga sun shiga wani waje me kyau Wanda naga ma'aikata da uniform suna rabawa mutane abinci wasu kuma suna dafawa Wasu na wanke plates daga gani de wannan gidan abinci ne Wanda yayi suna agarin ADAMAWA Ina daga kaina naga an rubuta HASSY and HUSSY'S KITCHEN suna fita a motar idanun mutane suka dawo kansu Ana tacewa kaga 'yan biyun hajiya bada kunku asare Kuje gida kuce yafadi habeeba ce kadai me cewa sannunku Samarai barka da war haka ita kuma bintu sai murmushi take nan naga sun nufo wata kykkyawar mata wacce zatakai shekara 40 habeeba tafada kan cinyar matar Tace mommy shine kikayi tafiyarki kika barmu matar da aka Kira da mommy naga tayi murmushi nan naga tsananin kamanta da habeeba tace ba dole natafi ba Kun tsaya kunata shirme kuma kunsan yau ranar biyan ma'aikata ne Mommy ai bintu ce ta tsayar damu kinsan yanayinta dayin Abu kamar karkashi Aa karki sake kizagammin ya zo maya my bintu kizauna anan Bintu tayi murmushi tace mom inason yau zanyi stew da kaima Mom tace Haba bintu yazaki gajiyar da kanki kizauna kihuta kinji my bintu Aa mom kibari zanyi Toshikenan bazan hanakiba jekiyi Ahmad dama nayi niyan tafiya yau amma bazan iya tafiya nabarka awannan yanayin ba Nagode habeeb Allah yabarmin kai dan Allah habeeb ko bayan na mutu idan kasamu my teemah dan Allah ka aureta sabida kai Kadai nayadda dakai Kai Kadai nasan zaka riketa da amana tinda kasan bakar wuyar datasha kasan na zalinceta naci amana dan Allah kayimin wannan alkawarin🙏🏻 _see me next page_ [6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written by Jiddah s mapi _dedicated To fateemahsardauna_ _wattpad_ Jiddahpretty Page 5&6 Ahmad kadaina irin wadannan maganganun Banajin dadinsu Sam meyasa kake maganar mutuwa bayan bakaga fateemahn kaba Ahmad insha Allah Bazaka mutu ba seka ga fateema Ka nemi yafiyanta Sannan ku Gina rayuwa me kyau Kuma inada tabbacin fateemah zata yafe maka Habeeb bana tinanin my teemah Zata yafemin koda bayan raina ne Habeeb babu abinda yake damina kamar yanda mommy tadau Zancennan da zafi ka duba kagani Yau kusan shekara daya ban sa mommy a idona ba Yazanyi da rayuwa ta ya karashe maganan yana me hawaye Abin tausayi Habeeb kam ba bakin magana Shi mamaki ma abun yake bashi wai ace yau Ahmad ne yake kuka yana fada mishi damuwanshi Shida magana ma be dameshi ba Gsky dayana da yanda ze taimaka mishi daya yayi Amma shi besan ma ta ina ze fara ba Allah ka gaggauta kawo mana karshen Matsalarnan Ameen *BINTU* Mommy wai meyasa bintu take zubar mana da class ne Kiduba fa yanzu wajen masu aiki zataje suyi tare Gsky mom abinda takeyi bata kyautawa wannan aji down ne😏 Habeeba kibi rayuwa a hankali Ita duniya a hankali ake binta Wanda batazo bama Tana jiranshi bale muda muke cikinta Ni gsky mom kina daurewa bintu gindi dama nasan Niba sona kike ba Bawai bana sonki bane beebah babu Wanda ze haifi da Yakishi sede idan kaddara ne mom tafada idonta yana cika da hawaye A hankali tajuya kanta yanda bintu bazata ganta ba ta goge idonta Bintu kuwa iyayen son aiki tanata girki suna dan hira da ma aikatan Dan ita ba ma'abociyar son magana bace Cikin hiranne wata Wanda suka dan saba da bintu Take tambayan bintu Friend dama inason inyi miki wata tambaya Ok nabeela inajinki Amma Allah yasa ranki baze baci ba Aa ba komai yi maganarki ok Dama inason tambayanki tum bayau ba Hajiyace ta haifeki!!!? Haba nabeela wannan wace irin magana ce yazakimin wannan tambayar? Bacin kinsan mu 'yan biyune nice babba Gsky bintu ba kowane ze yadda ba Duba da irin yanayinki Kiga beebah mana Tana Kama da hajiya Amma ke Sam babu abinda yahadaki da hajiya ta kamanni ko hali gsky akwai abun dubawa anan What are you saying nabeela!!!? Cewar mom Wanda tin farkon maganarsu takejinsu Ta taso tambayar bintu kota gama hadin? See me next page _Wattpad_ Jiddahpretty [6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written_by Jiddah S mapi _dedicated to fateemahsardauna_ Page 7&8 A take suka juyo ganin yadda mommy tayi maganan da karfi Nan take jikin nabeelah yayi sanyi ganin yadda yananayin mommy yacanza a lokaci kankani Haba nabeelah wannan wace irin magana ce meyasa kike son sa shakku a zuciyar 'Yar da Nina haifeta a cikina? shin bakida labarin Akwai 'yan biyun da Sam basa Kama da juna?" "meyasa ku mutane Bakwa gane abune yanzu da ace bani na haifi bintu ba dazaki hada abinda Baza'a taba cewa ke kika hada ba" saikuma tsaya "Gsky bana son irin wannan tambayar" Kai daga yau ma kada nakara ganinki da bintu Dan nan gaba bansan mezaki ce mata ba "Kiyi hakuri hajiya in Allah ya yadda hakan bazata Kara faruwa ba...." inji Nabeela "Banason dogon magana nabeela nariga nagama magana" hajiya ta mayar mata "Bintu wuce mutafi" Tafada cikin bacin rai "To mommy" cewar bintu wacce tinda mommy tafara fada ta Sunkuyar da kai saida zasu tafi ne takuma ɗaga kai tadubi Nabila wacce duk kunyar momy ya isheta *AHMAD* Dakyar habeeb yasamu ya lallabashi yai shiru "Ahmad gobe idan Allah yakaimu kafin in tafi dan Allah inason muje asibiti Aduba lfyrka dubi yadda karame" inji Habeeb "Aa base naje asibiti ba maganin cutana bana asibi bane Maganin cutana my teemah ne idan nasameta zan warke insha Allah" inji Ahmad "Toshikenan yanzu de ka kwanta kahuta sannan karage damuwa saboda zata haddasa maka cuta" inji Habeeb "Nima Bari nakira agida nafada musu na shaida bazan samu dawowa ba sai gobe" Mommy na isowa wajen Beebah tasamu sit nata ta zauna rai ɓace Beebah bataga fuskar tambaya ba Sai takarasa wajen Bintu tace "Bintu yanaga ran mommy a bace" "babu komai sis" inji Bintu saboda tasan idan Beebah taji maganarnan bazata ɗauka da sauki "Yazakice min ba komi bayan gashi ranta a matukar ɓace" "Nace miki ba komai ke meyasa kin fiye naci ne? Inji Bintu "Ko zaki dake nine to?" cewar Beebah "Nibance zan dake kiba dan haka kimatsa min anan" Bintu ta mayar mata "Zaki fara ko beebah meyasa bakya girmama tane tagirmeki fa" inji mommy Beebah ta zumburo baki tana kunkuni wai datayi magana sai ace ta girmeta abinda baifi ƴan mintuna ba "Yanzu de kutashi mutafi gida sabida yau yayanku ze dawo" cewar mommy "Yee mommy dagaske kik?"cewar beebah "Dama nataba miki karyane?" Nan wayan mommy yafara ringing "Yawwa ga shima yana Kira" amsawa tayi takara a kunnenta "Hello my son yakake? ok se gobe? Amma meyasa yau bazaka dawo ba? Ok to Allah yakaimu goben" saikuma ta kashe wayar "Kunga yayan nakuma yace se gobe ze dawo" mommy tafaɗa musu "Kai amma naji haushi mommy" cewar beebah Mommy tace "Yau da gobe duk dayane beebah kawai muyi addu'a Allah yakawo shi lafiya" "Ameen" cewar bintu _See me next page_ _wattpad_ Jiddahpretty [6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story by_ jiddah S mapi _dedicated to fateemah sardauna_ Page 9&10 Washe gari bayan sun gama breakfast ne, Habeeb yake cewa Ahmad "To kaga ni yau zan tafi kuma bazan dawo nan dawuri ba" Saboda wannan zuwanma dakyar mommy tabarni. Acewarta bataso nayi nesa da ita Dan Allah Ahmad kada kasa tinani a ranka Sannan kuma karka gaji da Zuwa gidanku neman tuba a wajen Mommynka "Aa Habeeb bazan iya zuwa inda mom take ba gsky" Sabida mom idan taganni bacin ranta karuwa yake Har Tana barazanar Zata tsinemin idan harna sake zuwa inda take Ba tareda Fateemah ba Kai innalillahi wa'inna ilaihiraji'un abun haryana kai da hakane Ahmad Wlh Habeeb shiyasa kaga damuwan sunyi min yawa narasa yanda zanyi Yanzu ma tafiyar da zakayi banso ba Koba komai kana debemin kewa. Amma yana iya, idan kaje ka gaida mommy Da kannan ka duka Nagode Allah yabar zumunci Habeeb yace Ameen Ahmad yace "Kashirya nakaika airport karkayi missing flight" Ok Bintu kinga yau broh ze dawo "Kizo mushiga kitchen dakanmu muhada mishi delicious" Bintu tace "Ok sis karki sami damuwa muje" Suka tashi suka shiga kitchen suna ta hira Mommy Tana kallonsu Tana Mejin farin ciki a zuciyarta tace "Allah yasake hada kanku my twins" *AHMAD* Tafiya suke a mota suna hira shida Habeeb. Nan Habeeb yake kara jaddada masa akan yakula da kanshi yadaina yawan tinani. Ahmad yace "kaga karka dameni tin jiya kana ta maimaitamin kalma daya kamar karatu" Ohh "dama nasan bazaka taba canza haliba Ahmad" Eh naji bazan canza ba Dahaka har suka isa airport *BINTU* Bintu kuwa anata aiki a kitchen bebba se surutu take zubawa. Banda eh, aa, to, Ba abinda Bintu take cewa har suka gama hada frid rice da kaji Bintu tahada sobo me cucumber Mommy tace "yanzu natura driver yaje dauko shi a airport Wai ya karaso" Yeeeee mommy "Aida kin fadamin da tare zamu tafi dashi" Kai Beebah kin fiye gaggawa Haba mommy "yabazanyi gaggawa ba yaufa kusan 2weeks ban ganshi ba sede waya" Bintu kuma murmushi kawai tayi Horn sukaji abakin gate Nan Beebah tafita da gudu Tana oyoyo yaya oyoyo Kafin driver yagama parking harta fara Bubbuga motan Seda yafito da sauri yana oyoyo my sis Nan ta rungumeshi kamkam Tana murna Yace ina dayarki? Tana falo itada mommy Ok mushiga daga ciki Suna tafiya Tana rike da waist nashi har suka shiga falon. Tana cewa "yaya kadauko tsaraban toh" Mushiga de tukun kinsan tsarabarki ta daban ce. Mommy tace "oyoyo my son sannu da zuwa nan itama ta rungumeshi tana murna" Bintu ta tsaya Tana tayi mishi murmushi Yace "kekam meyasa bazaki Waye ba Bintu" kullum kina cikin rashin sabo da mutum. Cheww Allah yakyauta halinnan naki. Kina gani fa 'yar uwarki tazo tayi min oyoyo Amma ke kina tsaye Daga nanne Bintu taje ta rungumeshi Yahada su duka uku ya rungume sunata murna "Ahmad yana komawa gida ya kwanta agado yana tinanin mommynshi da kanwarshi" Wai yau shine Kanwarshi wanda yafi so aduniya take gudunshi? "Yau shine mommynshi take ikirarin tsine mishi" "Idan yatuna rayuwarshi na da se yayi kuka" *WANENE AHMAD*? AHMAD KABEER yarone awajen alhaji kabeer. Alh kabeer shahararren dan kasuwane "Wanda yayi suna a duniya" Alhaji kabeer de dan asalin garin adamawa ne Shi asalin fulani ne Wanda yafara harkar kasuwanci tin yana saurayi Allah kuma ya buda "mishi sabida yanda yake da kyauta da taimakon talakawa" Alh kabeer yabude gidan marayu tin yana saurayi, sabida yadda Allah yasa mishi tausayin marayu a zuciyarshi. Dan hakane har yaki yin aure " dan yana gudun kar ya auri matar dazata hanashi taimakon marayu" Iyayenshi ne suka nema mishi aure Agidan marayu Wanda shiya bude da kanshi Acewarsu zatafi jin tausayin marayu 'yan uwanta "Inda suka nema mishi wata kyakkyawar yarinya me Suna mariya" "Ba matsala a auren mariya da alhaji kabeer sabida mariya Yarinyar kirkice" Bayan shekara hudu Allah be kawo musu haihuwa ba Har abun yafara damin mariya Inda alhaji kabeer yake cemata "karki damu mariya haihuwa na Allah ne" "Idan ma Allah be bamu b! Baga gidan marayu ba, semu dau daya murike kaman mu muka haifa Mariya tace "haba Alhaji kasan fa akwai banbanci tsakanin ɗa da kuma ɗan riko" Aa mariya ɗa na kowa Ne! Ganin yahau matsifane mariya tayi shiru "To dahakane har Allah yakawo ranar haihuwanta inda aka sha shagali akayi murna" Akasawa yaro sunan baban alhaji kabeer wato AHMAD. Ahmad de yasamu gata dan kota ina anaji dashi "Ahmad kyakkyawa ne" Fari Ne shi, dogo, da dogon hanci, ga karamin baki, Atakaicede shi yayi kama da larabawa. Sede kuma matsalar shi nada yawa Yanada girman kai sosai Ga kallon banza "Ga zama da abokan banza" Wasu abubuwan dayake yi abokai ne suke zigashi "Sai yayi ta tsula rashin kunya son ranshi" Dafarko yasamu daurin gindi awajen iyayenshi Se daga baya abun yafara damunsu *bayan wasu shekaru* "Dahakane har allah yasake basu haihuwa" "Yarinya taci sunan wacce take kula da gidan marayu na mahaifinsu wato FAREEDAH" Fareeda de kykkyawa ce tana Kama da Ahmad sosai. "Sannan kuma tinda aka haifi fareeda Ahmad yakara bude sabon rashin kunya" Shi adole yana da kanwa Bayan haihuwar fareeda fareeda ne Alhaji kabeer yafara diban yaranshi suna zuwa gidan marayu kai tallafi. Acewarshi idan sun girma suma zasu taimaki marayu. "Ranar farko dasukaje gidan marayun" Ahmad yasa fararen kaya masu kyau yanata Hada rai danshi beso zuwa ba. "Bayan an tara yara ana raba musu kudi ne" Alhaji kabeer yahango wata kyakkyawar yarinya. "Tana zaune a gefe tana kallonsu tana murmushi" Alhaji Kabeer yaɗan tsaya da rabiyar yana kallonta. Se ya yafito ta da hannu yace zo! Yarinyan ta tashi a hankali tana tafiya Harta iso su, seta durkusa tace gani. "Alhaji Kabeer yayi mamakin wannan yarinya batafi shekara goma ba" Amma take da natsuwa haka gata dakyau. Shi kuma Ahmad se harara yake tayi wai ana bata mishi lokaci Alhaji yace "ya sunanki?" Ahankali tace "sunana Fateemah" ✍️🗒️ *JIDDAH S MAPI* [6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by Jiddah S mapi _dedicated to walidation S mapi_ Wattpad Jiddahpretty Page 11&12 Wow nice name inji Fareedah, Gsky Daddy yarinyannan kyakkyawa ce, gata fara ga ido wow. Daddy yace meyasa ana raba kudi amma baki zo kin karɓa ba? Tace "banada bukatar kudinne shiyasa, duk abunda nake so mama tana bani. "To ay zaki iya ajiye kudin sabida watarana cewar Fareedah" Shi kuma Ahmad se duba agogo yake yanata tsaki, ba abun yacewa Daddy ze tafi ba, se harara yake ta bankawa yarinyan. Gani yake kamar ita take kara delaying nasu. Daddy ya ciro kudi masu yawa ya bawa yarinyan, ta girgiza kai tace "aa nagode abawa sauran" Kikarɓa ni na baki ay, a hankali tasa hanu ta karba tace"nagode Allah yasaka da alheri" Ameen ************* Tin daga wannan rana idan daddy yaje gidan marayu sai yace a kira mishi Fateemah yadau kudi yabata. To fa dahaka suka saba da Fareedah sosai watarana ma Fareedah takan zuwa gidab Marayun suyi ta hira da Fateemah, har yazama idan Fareedah bataje taga Fateemah! ba batajin dadi a ranta, sunyi muguwar shakuwa da Fateemah.. Ta ɓangaren Ahmad kuma yana dada lalacewa sabida abokai dayake tare dasu, mutane suna yawan kawowa Alh Kabeer karan Ahmad amma baya taɓa yadda se yace suyi hakuri yaranta ne daya girma ze daina. Abun yana taɓa zuciyar Mariya taya za'ace yarinta bacin yaro yakai shekara 29 ina maganan yarinta anan? yauma kamar kullum Alh Kabeer ne da yaranshi zasuje gidan marayu, yayinda Fareedah take ta rokon mom tashirya suje taga kawarta kuma Bestyn ta. To Fareedah naji tashi muje yawwa Mom ko kefah A hanyarsu tazuwa gidan marayu ne Alh kabeer yake tambayan Ahmad "Wai kai son yaushe ne zakayi Aure? Ahmad yahada fuska yana hararan Fareedah wai ana tambayanshi Aure a idon yarinya karama. Ba tambayanka nake ba?. Am daddy insha Allah very soon zan kawo muku matar dazan Aura. Mommy tace "udan ma be kawo ba mu sai mu nema mishi"Fareedah tace "yess mommy nizan nema mishi ma dakaina. Daya juya ya banka mata harara tayi tsitt Bayan sun shiga gidan marayu ne Fareedah tafara neman Fateemah a inda tasaba ganinta amma bata ganta ba! Ta tambayi wasu yara su biyu suna wasa tace"ina Fateema? " Sukace Fateemah batada lafiya tanata kuka tin ɗazu taki amata allura. A wana ɗaki take? cewar Fareedah cikin tashin hankali tayi tambayar? muje nakaiki cewar wata yarinya Suna shiga dakin taga Fateemah tana ta kuka tana rawan sanyi Da gudu tafita tana kiran mommy! Mommy naganin Fareedah ta fito da gudu, tafara tambaya lafiya? Fareedah batayi magana ba se nuna daki take! Mommy tace kiyi magana, dakyar tace Fateemah, wace Fateeman? Cewar Daddy..... Nan suka shiga dakin da gudu. Suna zuwa sukaga Fateemah bata motsi nan Fareedah ta tsala ihu Mommy tace kira yayanki awaje Fareedah ta taso da gudu tana kiran yaya yaya Ya dago kanshi yace ke me haka? Kinata kiran sunana kamar wani sa'anki "Yaya wai kaje inji mommy" Yaja wata doguwar tsaki yace muje Suna zuwa Daddy yace oya Ahmad dauke ta dawuri mutafi asibiti😳 Haba Daddy kaduba fa farin kayane ajikina ta yaya zan fara daukanta? Dubi jikinta fa duk datti....... Zaka dauketa ne ko sai ranka ya ɓaci cewar daddy. A hankali yaɗauketa yana yatsina fuska Yariketa kamar kashi ya ɗauka sai yayi sauri sauri ya wurgata a motar da iya karfinshi. Har saida kanta ya bugu Daddy yace shiga mutafi, dakyar yadaure yashiga yanata kunkuni. Ita kuma Fareedah sai kuka take tana kiran sunan Fateema tana cewa ta tashi karta mutu A haka har suka iso specialist hospital. Suna zuwa ba ɓata lokaci aka karbesu Likitoci suka shiga ciki da ita, Ahmad yace dama daddy inason naje wani waje na karɓi sako, babu inda zaka kana gani mun kawo yarinya ba lafiya rai a hanun Allah kace zaka tafi, baka da imani ne? Ahmad ya haɗa rai yasamu waje ya zauna yanata kunkuni me haɗi na da ita da za'a hanani yin uzirina akanta? Yarinya kucaka ma da ita Suna cikin zama wata nurse ta fito tace doctor yana magana dakai. Alh kabeer yace to, nan yashiga ciki, doctor yace kaine baban yarinyan daka kawo? Alhkabeer yace eh nine Ok amma kasan da ciwon dayake daminta? Yace Aa Doctor yagyara zama yace Alh rayuwar 'yarka tana cikin matsala "Ka taɓa zama da ita ka tambayi matsalarta? Daddy yace Aa Tofa akwai babbar matsala! Am sorry to say, 'yarka tana dauke da ciwon zuciya wanda idan har aka barta cikin tunani tayi nisa zata iya rasa ranta a ko wani lokaci. ✍️🗒️ *JIDDAH S MAPI* [6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story written by_ Jiddah S mapi _dedicated to my lovly sister @walidation_ _✅ote me on_ _wattpad Jiddahpretty_ Page 15&16 Da kyar Fareedah ta janye Fateemah zuwa gefen hanya ta kwantar da ita tace "ki zauna anan bara naje na kama mana Napep" A haka ta kama musu Napep ta rike Fateemah suka shiga se gida. Shi kuma Ahmad yana jan motarsa ya wuce carwash yace a wanke mishi ita, Alh Kabeer kuwa da mariya suna zuwa gidan marayu yacewa mama yanason magana da ita, Tace "ok ba komai ina jinka Alh" Yace dama so nake na ɗauke Fateemah na ɗan wani lokaci idan ba matsala, Mama tace ba komai Alh. Ay duk an zama ɗaya, Da haka suka tafi gida. *************** Shakuwa me tsanani ta shiga tsakanin Fareedah da Fateemah, Dan Fareedah sosai takeson Fateemah har cikin Ranta komai za'a siya mata zatace sai an siyawa Fateemah. Shi kuma Ahmad a duniya babu abinda yatsani gani kamar Fateemah, kwata kwata Allah be haɗa jininsu da ita ba, Ko abinci Fateemah ta dafa baya ci idan har ya san ita tadafa. Yauma kamar kullum Fateemah ce take goge goge a falo, tana kan goge TV ne taji ance mata "ke baki da hankali ne ko kin taɓa ganin inda ake goge TV da tsumma? Koda shike ba laifinki bane laifin iyayenki ne dasuka haifeki a titi, daga baya suka yadda ki" Nasan da agaban iyayen ki kike, dakin iya goge TV. Wawiyar banza. Tunda Fateemah take a rayuwarta ba'a taɓa faɗa mata maganan daya ɓata mata rai irin ta yau ba, Ahmad ne farko yafara kiranta da shegiya. A hankali ta ɗago kanta tace "kayi hakuri zan gyara insha Allah " Ai kuwa yaja tsaki ya fita a ɗakin yanaji kamar ya shaketa ta mutu kawai. Wato yarinyannan duk abunda za'ayi mata bazatayi kuka ba, saide tayi tabada hakuri kamar marokiya, sai nayi maganinta ay. Ita kuma Fateemah yana fita tasa kuka me cin rai, Tana cikin kuka ne taji muryan Fareedah tana, Besty ina kike? Ta share hawayenta tace "gani nan" Fareedah ta rungumeta tace "meya sameki naga kamar kinyi kuka? tace "Aa babu komai kaina ke ciwo" Ayya sorry kinsha magani? Eh nasha, Ok muje ɗaki to ki kwanta. Da daren ranan Fateemah takasa bacci, data rufe ido sai tana tuna maganganun Ahmad na ɗazu. _ba laifinki bane_ _Laifin iyayenki ne_ _Dasuka haifeki a titi_ Wato ni shegiyace? A titi aka haifeni? To ina iyayena suke!? Meyasa suka yadda ni? Shine tambayoyin data kasa amsawa kanta, Data kara tunawa seta fashe da kuka, Jikinta yafara zafi, tana kokarin ta tsaida kukan amma ta kasa. Da haka har tafara tari, jikinta yafara rawa taja bargo ta lulluɓa jikinta amma har yanzu tana jin sanyi. Tana cikin wannan halinne Fareedah ta tashi zatayi fitsari, Taga Fateemah acikin bargo jikinta yana rawa gashi fuskanta yayi ja, A razane ta iso wajenta tana tambayanta meya faru Fateemah ba bakin magana se ido kawai, Ta fita da gudu taje ɗakin mommy ta kirata, A tare sukazo da mommy, Mommy tana ganin halin da Fateemah take ciki tace akira mata Alhaji, Ai kuwa Alh Kabeer yana zuwa yace aje akira Ahmad yazo su tafi Asibiti. Fareedah ce taje kiranshi tana zuwa tayi knocking yace "yes waye? " Tace Yaya Fareedah ce, Yace me kikeso? Tace "Daddy ne yace nakiraka" Daddy kuma? Meya faru? Nima ban sani ba! Ok ina zuwa, Ahmad yana zuwa Daddy yace "oya ɗauke ta da wuri mu tafi Asibiti kar dare yayi sosai. 😳Daddy wani Asibiti? Dama wani Asibiti muke zuwa? Inji Daddy Daddy Ai yanzu dare yayi abari sai gobe mana da safe.... Kai Ahmad baka da hankali ne? Ko baka ganin halin da take ciki? Ko da Fareedah ce zakace abari sai gobe? Yayi shiru dan besan me zecewa Daddy ba ganin yahau 90, A haka badan yaso ba ya ɗauketa yakaita mota, Ji yake kamar ya shaketa tamutu ko ze huta ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written by_ Jiddah S mapi _dedicated to my lovly sister_ @walidation Page 13&14 "Alh 'yarka tana cikin matsala" zai fi maka sauki ka kirata ka lallaɓata, ta faɗa maka meke damunta, sabida hakki ne a kanka. To fa nan Daddy yafara share zufa, yanason yace ba 'yarshi bace, amma yana tsoron kar likitan yace mishi makaryaci. "Yace toh doctor nagode" yanzu ya ake ciki? Doctor yace "a halin yanzu de an ɗaura mata ruwa, saura na rubuta muku magungunan da zaku saya" Ahmad kuwa abokanshi sunata kiranshi awaya, yana ta tsaki wannan wani irin abune? Bamu santa ba! Ba dangi ba! Ba 'yan uwa ba! Amma ahanani yin komai chewww.... Yasake jan wani dogon tsaki ganin ana sake kiranshi. "Dan Allah karka dame ni Bash, ka kyaleni na huta wannan wana irin Bala'i ne?" naji da matsalar Da Daddy yasani yau ne ko da naka? Ɗittt ya kashe wayar. Zo nan my son! "To" Yawwa dama zuwa zakayi ka siyo magunguna acikin asibitin, to Daddy ya karɓi papern yana tafiya yana tsaki. Fareedah kuwa takasa zama, da zarar taga likita yana wucewa sai tace doctor ya jikinnata? tin suna amsawa har sukayi shiru ***************** Da ahmad yakawo maganin suka ɗunguma gaba ɗaya suka shiga ɗakin, suna shiga suka tarar da Fateemah ta farfaɗo, Fareedah tayi gudu ta rungumeta. "Ita kuma Fateemah ta lumshe ido" Ahmad kuwa yau kamar ido ya faɗo tsabar harara *nace oho de* Ya jikin naki inji Daddy a hankali tace "da sauki" tom Allah yakara sauki tace "Ameen" Daddy Yace idan kika ɗan samu sauki bazaki je gidan marayu ba gida zamu wuce, tnx Daddy gaskiya nima nafison taje gidanmu zamufi kula da ita. A take Ahmad ya ɗago kanshi yana kallon Daddy, yace "Daddy wani gida zata wuce? " Wani gida kake ciki? Cewar Daddy, nan yai shiru yana kallonsu. ************* Washe gari bayan an sallamesu ne daddy yace "Ahmad ka kaisu gida ni zan wuce gidan marayu nafaɗawa mamansu nacan bazata koma ba sai ta samu sauki", to Daddy. Mommy tace "Alhj tunda ga Fareedah me ze hana su tafi tare mu kuma muje gidan marayun tare", ok ba matsala ay Ahmad kaisu gida, to Daddy Da kyar Fateemah take tafiya, sabida tanajin jiki. Fareedah ce ta riketa har suka shiga motan a hankali. Bayan sun ɗau hanya suna tafiya ne "Fateemah tafarajin Amai, A hankali tace inajin Amai! Fareedah tace yaya kayi hakuri ka tsaya tanajin Amai, yai shiru kamar bai jita ba, ta sake cewa "yaya Amai takeji", nanma shiru ba amsa sema kara gudu dayake. Nan Fateemah tafara sheka Amai kamar ba gobe, tofah nan yaja birki ya tsaya. Yace "fitah" sukayi shiru dan Fateemah ta galabaita, ya sake cewa "nace kufita" Fareedah tace "haba yaya baka ganin Amai take ne kabari mana tagama". Zaku fitane ko sai na Ɓata muku rai, ya daka musu tsawa!!. Fateemah tafara yunkurin tashi Amma ina ba dama, da kyar Fareedah ta riketa suka fita, suna fita a motar Fateemah ta faɗi dan bata da karfi ko kaɗan. Haka yana gani yaja motarsa yabar wajen _wattpad_ Jiddahpretty ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:46 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *jiddah S mapi* _Dedicated to my lovely sister walidation_ ✅ote me on wattpad *Jiddahpretty* Page 17&18 "Suna shiga cikin Asibiti Likitocin sukayi kansu da gudu suka karɓe ta sai Emergency Room", Daddy kuwa hankalinshi duk a tashe yanata zagaye Asibitin. Azuciyarshi yana tunanin to me ya tadawa Fateemah ciwon tane haka, Dahaka har likita yafito daga ɗakin yacewa Daddy yana buƙatar magana dashi, Daddy yace to. "Bayan yashiga ɗakinne likita yace mishi Alh idan har kanada daman dazaka Aurar da 'yarka to kayi mata Aure, kaga idan har agidan miji take bazata rinƙa yin wasu tinani barkatai dahar ciwonta zai tashi ba. Daddy yayi shiru yana tinani, se daga baya yace to nagode Doctor. Doctor yace "yau zamu sallameku sabida anyi mata Allura ansa mata drip idan ya kare zaku iya tafiya" Bayan an sallamesu ne suka koma gida, Daddy ya kira Hajiya Mariya yayi mata bayanin abinda Doctor yace, Yace "Mariya bakya ganin kawai mu haɗa Auren Fateemah da Ahmad? Tunda mun yadda da tarbiyanta, To Alhaji ne dai banƙi ta taka ba Amma baka tinanin karmu shiga haƙƙin yarinya marainiya, Kaga Ahmad shi bawani isashen hankali ne dashi ba kar muzo muyi abinda zai damemu, Haba Mariya shi Ahmad ɗin ba haifanshi akayi ba? Tunda haifanshi akayi ai munada iko dashi. To Alh Allah yasanya Alkhairi cewar Hajiya Mariya. Dahaka Daddy yasanya ranan Auren Fateemah da Ahmad, suma kansu basu sani ba! ******************** Akwana atashi ba wuya a wajen Allah yau ne Ranan juma'a wanda yayi daidai da yanda Alhaji Kabeer yasa ranan Auren Fateemah da Ahmad, Fareedah da Fateemah sai ganin mutane suke suna shiga gidan suna ta guɗa. Fareedah ta tambayi Mommy meyake faruwa mommy tace ba komai, Shi kuma Ahmad yana wajen Abokansa sunata shashancinsu, inda suketa shaye shayensu, Bayan juma'a aka ɗaura Auren Fateemah da Ahmad, akan sadaki dubu Hamsin wanda Alh Kabeer ne yabiya, Se dare Ahmad yadawo gida, Daddy ya kira wayanshi yace "kasameni a falo" Daddy yacewa Hajiya mariya takira mishi Fateemah da Fareedah, Bayan sun hallara a falonne, Alh Kabeer yayi gyaran murya yace "Da farko dai nasan yau zakuyi mamakin yanda mutane suketa zirga zirga agidannan, to yau Aure aka ɗaura, Auren Fateemah da Ahmad". A razane Ahmad yaɗago kanshi yana kallon Daddy, Ya buɗa baki zaiyi magana Daddy ya ɗaga hannu yace "Banason jin komai daga bakinka kuma babbar kuskuren da zaka aikatamin shine sakin Fateemah ko wulaƙanta ta" Sannan kuma daga gobe zata tare zuwa side naka, Idan naga yanayin zamanku ba matsala kuma idan kun fahimci junanku saiku koma gidanka na jambutu, Yace zaku iya tafiya. "Tofah dahaka suka wuce ɗaki kowa jikinshi a mace, Ita kuma Fareedah murna take kamar me, suna shiga ɗakin ta rungume Fateemah tana ta tsalle, ita kuma Fateemah shiru kawai tayi ta rasa me zatayi, Dahaka Fareedah tafara haɗa mata kayanta tana cewa gobe a ɗakin yaya zaki kwana kai ammafa i will miss you, Fateemah shiru tayi batayi magana ba tana ganin anya bazataje wajen Daddy tace a raba Aurennan ba? , Kai idan tayi haka kuma batayi daidai ba domin sunyi mata halacci" Azuciyar Ahmad kuwa yanata kulla salon muguntar daze yiwa yarinyan, Lalle zakici ubanki Ai nagodewa Allah ma dayasa babu Wanda yasani acikin abokai na dako nasha kunya, Ina yaro dani ace nayi Aure ay Akwai raini. "Haka Fateemah da Ahmad suka fara rayuwa, Inda Ahmad yake mugun takura Fateemah, idan dare yayi sai yayi ta sata tsallen kwaɗo kuma yace idan ta faɗa saiya kasheta, Haka Fateemah tayi ta hakuri dashi idan Fareedah tashigo saita saki fuska tayi ta dariya idan suna hira, Amma da zarar taji muryar Ahmad tofa zuciyarta tafara tsinkewa kenan" "Dahaka Fateemah tayi ta hakuri da Ahmad wulakancin yau daban na gobe daban haka zatayi ta hakuri dashi, babban abinda yafi daminta dashi shine shaye shaye dayakeyi, tanason tafaɗa ma Fareedah amma tana mugun tsoronshi dan yace mata idan ta kuskura tafaɗa wa iyayenshi yana shan abu saiya kasheta!" Me karatu Fateemah tasha wahala a wajen Ahmad fiye da misali. Yauma kamar kullum Ahmad ne yashigo gidan A buge yana tafiya yana tangaɗi, Fateemah kuwa tana kitchen tana itada Fareedah suna girki, Kawai se sukaji karan buga kofa Fareedah tayi sauri zata je taduba ko menene, Fateemah tayi saurin katseta. Tace ki bari zanje naduba dan ita tasan halin Ahmad may be yaje yasha abune yadawo, Tana leƙa ɗakinshi taga ya kwanta rub da ciki. Ai kuwa tarufeshi a, Dataje kitche tacewa Fareedah ay ba kowa. "Tofah har dare Fateemah kwata kwata ta manta da ta rufe Ahmad a ɗaki, haka Har tayi abincin dare ta ci tayi wanka ta kwanta har bacci yafara ɗaukanta, amma taji zuciyanta yanata tsinkewa tarinka cewa astaghfurullah! Shi kuma Ahmad lokacin da ya dawo hankalinshi yayi wanka yanason yaje club amma me yana buɗe kofan yaji gumm! Ya rasa yanda zeyi gashi yanajin yunwa kuma ana ta kiranshi awaya club yacika saura shi kawai ake jira, Yadinga buga kofan yana kiran sunanta amma shiru. Haka ya zauna yana tuna abinda zeyi mata yau idan ta buɗe kofan, Wato raini yafara shiga takaninsu kenan! tana zaune kawai ta tuna yau Ahmad be zageta ba anya lafiya kawai seta tashi tafita tace bara na lekashi nagani, Tana zuwa taga kofanshi a rufe, taɗan buga ƙofan kaɗan. Kamar jira yake yace waye tayi shiru, yace oya open the door Sai alokacin ta tuna abundance yafaru da rana😳ta zaro manya manyan idanunta tace kayi hakuri zan buɗe na mantaka ne wallahi, Cabɗi ni ta manta? ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *jiddah S mapi* _Dedicated to my lovely daughter AFRAH_ _✅ote me on wattpad Jiddahpretty_ Page 19&20 "Yace taɓɗi ni ta manta lalle zataci ubanta, ai kuwa da gudu Fateemah taje taɗau malullin ɗakin tazo ta baɗeshi" Tana buɗewa taji mari tass, dan ubanki ni kika manta! Gidan ubanki ne? Dazaki rufeni kice kin manta yau sena nuna miki kuskurenki! Ya rike hanunta da karfi yana janta Yabi ta kofan baya da ita ya buɗe motarshi yasata aciki, yafita da gudu acikin gidan, "Yana gudu tanata bashi hakuri shi kuma hakurin datake bashi yana kara bashi haushi" Dahaka har ya iso wani gida, Tangameme me Ƙaton get yayi parking, Yafita agidan da kanshi ya buɗe get ɗin yashiga cikin gidan yace mata fita! Tafara cewa dan Allah kayi hakuri wallahi mantawa nayi. Yau zakisan kin manta ni! Haka ya ɗauke ta a motan Ya fita da ita Yana ɗaukan ta be ajeta ako ina ba se a wani bedroom wanda ya kayatu da abubuwan kyale kyale, Haka tana gani yafara yayyaga kayan jikinta tana bashi hakuri amma ina. Haka Ahmad yayiwa Fateemah fyaɗe (eh mana ai wannan fyaɗe ne), Haka Ahmad ya ɗauki Fateemah A sume yasata a mota ya kama hanya, Saida yayi tafiya me nisa kadin ya tsaya ya buɗe motar yana daga ciki ya cillar da ita waje yaja motarsa ya tafi. **************** "Bayan Ahmad yakoma gidane ya fara wani tinani me ze faɗawa Daddy idan ya tambiyeshi ina Fateemah, kai anya bazan koma in ɗaukota ba! Kodai nabarta ne! *(Nace duk kai kaɗai)*" Haka yayi wanka ya kwanta yayi baccinshi, Washe gari da safe Fareedah tazo ɗakin dan takirawa Mommy Fateemah, Tana zuwa tayi knocking, yace waye? tace Fareedah ce yace mene ne? Tace mommy ce take kiran Fateemah! Dumm yaji zuciyarshi ta buga, Kije ina zuwa tace toh, Yana zuwa ɗakin mommy yace "inakwana mommy" Tace lafiya ina Fateemahn? Yace Fareedah fita ki bamu waje, Fareedah tafita yasamu bakin gado ya zauna, Yace Mommy wato yarinyannan ta rainani ne jiy ta kulleni a ɗaki har dare wai ta manta ni, Shine me? Inji mommy, Yace shine itama nakaita inda za'a manta da ita! kana hauka ne ko ka fara shaye shaye ne? Yayi shiru, Ina ka kaita? Yace bayan gari, Ji kake tass tass tass Mommy ta wanke shi da mari har sau uku, kayi hauka ko? Yayi shiru ba magana nake maka ba? Shiru har yanzu, Tashi ya tashi Tace muje, Yashiga gaba suka fita! Suna fita yaga Fareedah a kwance lub abakin kofa kamar ba Rai, Da gudu Mommy taje wajenta tana kiran sunanta amma shiru, mommy ta kwala ihu tana kiran sunanta, shi kuma Ahmad ya rikece yarasa me zeyi. "Suna cikin haka Daddy ya sauko da sauri yana tambayan meyake faruwa? Mommy tace mishi Fareedah ce ta suma! Yace wa Ahmad kawo ruwa. Ahmad yatashi da gudu ya ɗebo ruwa aka Zuba mata a hankali tafara buɗe idonta tace ina Fateemah? Da alama taji duk maganganunsu, Ahmad yayi shiru Daddy yace wace Fateemah? Mommy tace Fateemah ce Ahmad yaje ya yadda ita!" Daddy yace what are you saying Mariya? Mom tace katambiyeshi kaji mana wai ta kulleshi a ɗaki shine yarama, Daddy ya ɗago idonshi yana kallon Ahmad Yace me nakeji, Yayi shiru, Daddy yace tashi muje suka ɗunguma duka suka shiga mota. Ahmad yajasu suka tafi sunata tafiya sukaga wajen yayi nisa mommy tana ta Addu'a a ranta, Har suka iso bayan gari kafin yatsaya, Daddy yace ananne? Ahmad yace eh ok ina take yayi shiru, Mommy kuwa tazuba ma wani dutse ido Taga kamar jini ne akai, tacewa Alhj kalli can, Daddy yana kallo yaga jini ne awajen! Suna zuwa sukaga jini dayawa akan dutsen harya fara bushewa, Daddy yace Wannan jininfa? Ahmad yayi shiru Daddy have ba tambayanka Nake ba? Daddy Nina ban Sani ba! Tass Daddy ya wankeshi da Mari. Ina kakai 'yar mutane? Inji Mommy yayi shiru... Ba tambayanka ake ba? "Shikamma yarasa ya zeyi idan yayi magana su mareshi yayi shiru suyi ta tambayanshi ya rasa ya zaiyi" "Suna cikin dubawa sukaga wani mutum yana zaune dagacan gefe, Daddy yaƙarasa wajen mutumin yace mishi, bawan Allah bakaga wata yarinya Acan Akwance ba? Tsohon yacewa Daddy, eh ai ɗazu wasu mutane sunzo sun ɗauki wani gawa acan kuma a yadda nagani gawan kamar mace ne........." Ai kafin yaƙarasa Daddy yafaɗi awajen, da gudu suka ƙaraso wajen suna tambayan tsohon meya faru? Yayi musu bayanin komai, kafin yakarasa zancanshi ai Fareedah ma tayi ƙasa, mutumin yarasa meyake faruwa. Mommy tadinga zabga ihu shikuma Ahmad atake jikinshi yafara rawa da ƙyar suka ɗaukesu zuwa Asibiti ************** Tun daga wannan rana Alh Kabeer yazama bashi da lafiya harya kasance jikin yayi tsanani hawan jini yake daminshi, Ɓangaren Fareedah ma bawani lafiyane da ita ba tazama shiru bata da yawan magana. Shikuma Ahmad yarasa meyake mishi daɗi Abu kamar wasa gashi yazama gaske, shima yazama shiru shiru dama gashi miskili. Alh Kabeer jiki yayi tsanani yana jinya sosai, yau kam jikinma yafi na kullum an kaishi Asibiti rai yayi halinshi saide muce Allah yagafarta mishi da duk musulman da suka mutu "Ameen" ✍️🗒️ *jiddah S Mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _Story/written by_ Jiddah S MAPI _dedicated to my daughter Afrah_ _✅ote me on wattpad Jiddahpretty_ Page 21&22 "Tun daga Wannan ranan Hajiya Mariya tadaina yiwa Ahmad magana, Fareedah ma ba magana take mishi ba ko yayi musu magana ɗauke kai kawai suke Abun duniya yayi mishi yawa ya rasa ina zesa kanshi shi fa a Azuciyarshi yanaji bata mutu ba! Haka yazama kamar wani mahaukaci duk inda yaji ance Fateemah saiya juya yaga meshi, abokansa sun kasa gane kanshi baya zuwa club yadaina bin mata ko ankirashi awaya baya ɗauka sai shaye shaye yake kamar mahaukaci" Akwai wata rana daya kira Fareedah yace tazo tasaya mishi magani Fareedah batayi magana ba sai yaga kamar ta rainashi ne haka yarike Fareedah yayi ta dukan ta. Mommy tana dawowa taga Fareedah jiki a fashe tace meya sameki? Fareedah tace Ahmad ne ya daketa! Mommy tafita a ɗakin taje ta sameshi a kwance kan gado, mommy tace Ahmad bazaka kashe 'yar mutane ka kashe mahaifinka sannan kazo ka kashe Ƙanwarka ba, baka isa ba kayi kaɗan Katashi kabar gidannan cikin minti goma idan kasake dawowa saina tsine maka Albarka!!!Ahmad yabuɗe baki zaiyi magana amma Mommy tace idan ya kuskura yayi magana Allah ya isanta haka ya tattara kayanshi yabar gidan. Ahmad ya rame bashi da tinani saina Fateemah a halin yanzu yafara tuninin yana son Fateemah ne idan ya tuna da hakurinta da juriya, Sai yayi ta kuka kamar me, haka Habeeb yazo ya tarar dashi haka, Yace meya sameka Ahmad yayi mishi bayanin duk abinda yafaru. ********** *cigaban labari* "Yaune ranar zagayowar haihuwan Bintu da Beebah an haɗa party wanda kawayensu na makaranta dayawa suka hallara, inda Bintu da Beebah suka sa anko na skirt pink da top black suka ɗaura kai da black na ɗankwali, Faɗin yanda sukayi kyau ɓata lokaci ne domin yau 'yan biyun Mommy sunyi mugun kyau kamar asace a gudu, kawayensu kuma sunsa dogon riga baki sunyi kyau suma sosai an yanka cake ansa waƙa a speaker Inda Beebah tayi ta dansewa ita da ƙawayensu Bintu sai video kawai take yi musu tana dariya." Habeeb kuwa ya kira Beebah yace mata sweet sis ki hau watsapp kituramin hotonan da kukayi yau zansa a status ɗina tom broh bari na buɗe Data.... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written By *jiddah S MAPI* _dedicated to my daughter AFRAH_ _follow ne on wattpad Jiddahpretty_ Page 23&24 "Beebah ta buɗe data ta turawa Habeeb hotonan su da videos ɗin dasukayi, habeeb yana ganin videon yace mata wow sweet sis kunyi kyau gaskiya tace thank you broh, Se mangariba dab suka gama partynsu suka raka duk ƙawayensu kowacce tashiga motarta suka tafi, Bintu ce ta kwashe musu gift dasuka samu daga wajen ƙawayensu tashiga musu falon mommy dashi". Ahmad yau ya tashi da tsananin ciqon kai inda yayi ta birgima yana riƙe da kanshi, dakyar yasamu yasha magani yaɗan samu sauƙi, ya zauna a gefen gado yana tinani azuciyarshi yace "da ace my teemah tana nan data bani magani da kanta nasha, komai nayi mata zatayi hakuri dani wayyo my teemah ina kike dan Allah ki bayyana min kanki nasan kina raye baki mutu ba! Ki fito dan Allah naganki zan nuna miki soyayyar dabaki taɓa jin labarinshi ba ko a Novel. Haka ya karashe tunanin shi ya tashi ya shiga wanka, bayan yafito daga wankane yashafa mayukanshi masu kamshi ya taje gashin kanshi me laushi kamar na indiyawa, ya buɗe wardrobe nashi yaɗauko wani riga pink colour da bakin wando ya ɗauko picap baki yasa ya dubi kanshi a madubi yaga ya rame sai de yayi fari sosai, a hankali ya rufe idonshi yace oh god help me out. "Habeeb bashi da damuwan daya wuce damuwar abokinshi Ahmad, kullum idan ya zauna sai yayi tagumi yana tinanin ta ina zai fara taimakawa Ahmad, har Mommy tagano yanayin shi da daddare suna zaune a falo suna kallo, Bintu tana ɗan danne danne awaya ita kuma Bebbah ta kwantar da kanta akan cinyar Habeeb tana mishi rigima wai sai yayi mata tsifa, Mommy tace Habeeb inason in tambayeka wani Abu mana? Yace to Mom ina jinki Mommy tace meya sameka ne naga tin ranan daka dawo daga Kaduna kashiga damuwa ko wani Abunne yasamu Ahmad? " Habeeb yace gaskiya mom Ahmad yana cikin matsala nan yafara faɗa mata duk abunda ya faru Amma ya ɓoye mata yanda Ahmad ya yar da Fateemah, Ba Mommy ba har 'yan biyu saida sukayi hawayen tausayin Ahmad, Mommy tace yanzu shi Ahmad ɗin yana ina? Habeeb yace yanzu de yana gidanshi acikin kadunan Amna yace min bazai iya zama a Kaduna ba gaskiya ze tafi Dubai yayi zamanshi acan, Mommy tace to yayi Aure mana wata kila idan ita Hajiya Mariyan taji zata yafe mishi, Habeeb yace gaskiya mom Ahmad A halin yanzu ko yayi Aure to matar daya Auran agaskiya GANGAR JIKINSA TA AURA dan zuciyar Ahmad tana wajen Fateemah mommy tayi shiru tana tunani...... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S mapi* _dedicated to Eeshart💕_ *🌈KAINUWA WRITTERS ASSOCIATION* _{united We stand and succed; our ambition is to Entertain & motivate the mind of readers}_ *WATTPAD* @Jiddahpretty Page 25&26 "Bayan wasu lokutane Mommy ta ɗago kanta tace da yayi Aure dayafi dai Habeeb wata kila ta yafe mishi idan taga yayi Auren, musamman idan yaje mata da jika, (toh fa kunji mommy da zance) Habeeb yace ok mommy baradai nagwada yi mishi maganan ko zai yadda, to Amma mommy idan ya yadda wa zai Aura sabida kinsan bashi da budurwa! Mom tayi shiru daga baya ta nisa tace ga Habeeba saina bashi ita ya Aura! Habeeba tayi shiru atake zuciyarta ta tsinke!!! To Shikenan mom bara zanyi mishi maganan anjima inji Habeeb " Ahmad yana kwance ciwon ciki ya dameshi yasha magani ma ba sauki da kyar ya ɗau wayarshi yakira abokinshi Bash, Hello Bash dan Allah kana inane? Bash yace kanada matsala ne? Ahmad yace eh akwai matsala ok kana wani club ne? Bash bana club Ina gidana na anguwar sarki kazo ka sameni ok, Bayan wasu mintuna saiga Bash. "Bash yana shiga ɗakin yaga Ahmad a kwance yanata murkususu, ya ƙarata ɗakin da gudu yana tambayan Ahmad meya faru? Ahmad baya iya ko magana sai rike maranshi dayake, Meya sameka A hankali yace cikina! Bash yayi shiru yana tinani can yace "Haba gaye meyasa zaka cutar da kanka ga 'yammata a club kala kala ya zaka zauna da ciwon ciki kamar mace? Haba mana gaye karka bada ni mana" Aa Bash nadaina bazan sake kusantar wata mace ba a duniya, na riga nayi Alkawari idan ba my Teemah ba saide ciwon cikin yakasheni, to Amma ai saika ɗan sha ko kwalba ɗayane inji Bash, Ahmad yace nasha nasha banga anfaninshi ba sai ma ƙaramin cuta dayake, to Shikenan saika kashe kanka. Yanzu me kake so Nayi maka? Ahmad yace mommy zaka kiramin awayarka inason naji muryarta dana Fareedah, Bash yayi shiru dan ya tuna Mommy tahanashi tafiya da Ahmad idan tagansu tarema hararanshi takeyi Mommy taki jininshi, amma bari dai ya gwada. Yacewa Ahmad bani numbanta Ahmad yamishi nuni da wayarshi Bash ya ɗauko wayar yaɗau numban Mommy yakira ta, da farko kamar baza'a ɗaga kiranba sai daga baya aka ɗaga. mommy tace hello, ba'ayi magana ba! Tanata hello hello anyi shiru, Bash yakasa magana, sai can yace hello momsy ya gida? Mommy tayi shiru tsabar taƙaici tarasa me zatace mishi, dan tagane muryanshi, azuciyarta tace wannan Bash ɗin da kanshi kamar sandan mopping sainayi maganinshi, Tace meke tafe dakai? Yace am dama momsy Ahmad ne..... Mommy tace dakata banason shashanci komai Ahmad yayi a duniyarnan dasa hannunku aciki sabida ku abokanshi ne, ku kuke bashi shawara mara kyau, mom tafashe da kuka tace Allah ya isa tsakanina daku Bashir, kun ɓatawa ɗana rayuwa nabarku dashi nikam na yafe Ahmad duniya da lahira, kuma idan kasake kirana to hukuma ne zasu rabamu dakai. Mommy takashe wayar tana kuka me cin rai. "Bash yayi shiru yana kallon Ahmad, wanda yake ta kukan dana sani, Yace haba gaye ya zaka tsaya kana kuka akan maganar tsohuwa kasanfa tsofinnan surutun bala'i ne dasu ka manta kawai kaɗansha ko kwalba ɗaya ne, idan babu kuma a frij ɗin zan iya saya maka da kuɗina" *note* (ana cewa aboki baya ɓata aboki, wannan magana ba gaskiya bace wani abokin ma ze iya kashe ko nawa ne dan ganin kaima ka ɓata rayuwarka kun zama daidai akiyaye abokai da bakai ba gindi ko kawayen dabasu da natsuwa Allah yatsaremu Ameen🙏) Ahmad yace Aa akwai a frij ɗaukomin kwalba ɗaya, da Bash yaga Ahmad ya shanye kwalban giya me tsada ɗaya sai ya ƙara ɗauko waniyabashi haka Ahmad yayi ta ɗurawa har bacci yaɗaukeshi. Da Bash yaga Ahmad yayi bacci saiya fita a ɗakin yakira numban wata yace hello polinah kina inane? Ok kizo anguwar sarki yanzu kisame ni yabata numban gidan. Polinah wata sheɗaniyar yarinya ce wanda ta ƙware a bariki, sau da dama Bash yanayiwa Ahmad tallanta amma yaki, itama polinah tanason Ahmad sosai kamar ranta, yau ta samu dama. ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:48 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _Story/written by_ *jiddah S Mapi* _Dedicated to my lovly friend *ELHAM*_ *KAINUWA WRITTERS ASSOCIATION* {United we stand and succed, our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} Page 27&28 "Bayan wasu mintuna Bash yaji ƙaran tsaiwar motar polina, ya tashi ya fita a falon yaje yaƙaraso da polina cikin ɗakin, polina Big girl ce ko ta ina ta haɗu tana da shape wanda ake kira cocacola shape, Tana shiga ɗakin tahango Ahmad kwance agado yana bacci Alaman ya sha abu sosai, Bash yacewa polina Babe nasan ke kaɗai zakiyi mishi maganin abinda yake daminshi, polina tace that way i love you Bash kai kaɗai kake gane damuwata har kayi mini magani, kuma zanyi mishi magani yanzu yanzu ma kuwa kai dai kawai ka jiramu a falo, Bash yace nabarku lafiya ita kuma polina ko kunya babu tafara kwaɓe kayan jikinta, jikinta har rawa yake" Ɓangaren Mommy kuma tinda Bash yakirata taji hankalinta yatashi, idan Ahmad yamutu ya zanyi? Nayi rashin mahaifinshi, yanzu kuma in rasa shi? Kai anya kuwa abin zaiyi? Baradai nakira Bashir ɗin na tambayeshi awana gida Ahmad yake, ay hanunka baze taɓa ruɓewa ka yanke ka yar ba, duk maganannan Azuciyarta takeyi, sai kawai taɗau waya takira Bash, tace kai Bashir awana gida Ahmad yake? Bash yace a gidanshi na unguwar sarki, Mommy takashe wayar taɗau hijabinta da makullin motarta tayi gaba. "Bash yana gama wayar yatafi siyan musu abinci a restorant, Polina kuwa tana bedroom ita da Ahmad sunata aikata masha'arsu duk da Ahmad ba'a hankalinshi yake ba" Mommy gidan Ahmad ta nufa tayi parking na motarta awaje, Tanata sallama ba'a amsaba tarinƙa kiran Bashir taji shiru, atake taji zuciyarta ta buga saita shiga cikin falon, tana sallama babu wanda ya amsa tace Allah yasa lafiya, takama hanya zata tafi taji muryan mace ƙasa ƙasa tana cewa i love you so much my Ahmad, tafara addu'a aranta kawai saita kama banyan bedroom, Ahmad kuma alokacin yafara dawowa hankalinshi yafara kiran sunan polina polina mom taji muryan Ahmad yana cewa polina Ita kuma polina tana cewa Ahmad I love you so much, da polina da taga Ahmad yana son yadawo hankalinshi, saita haɗa bakinsu wuri ɗaya, alokacin mommy ta buɗe kofa, sai kawai taga Ahmad da mace kwance kan gado ba kaya bakinsu ahaɗe ay kawai saita zube awajen.... Muje zuwa ✍🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:48 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *jiddah S Mapi* _Dedicated to All my fans💋_ *WATTPAD* Jiddahpretty Page 29&30 "Polina tana ganin mutum ta buɗe ƙofa kuma ta faɗi kasa take, sai kawai tadiro akan gadon ta tsala ihu, Alokacin Bash yadawo daga siyan abinci yaji ihun polina amma shi yazata iskanci ne kawai" Polina takara zabga ihu tana cewa azo ataimaketa, Bash yatashi da sauri yaje bedroom ɗin, yaga mom akwance ƙasa kamar ba rai, ai da gudu yaje frij ya ɗauko ruwan sanyi yazo wajen datake kwance. *BINTU* "Bintu ce kwance akan gado tana chatting awayarta kirar samsung, yayinda Beebah take kwance agefenta tana bacci., Bintu ce tanaɗawa Beebah duka tace ke tashi kiga nayi saurayi sabo Haɗaɗɗe, Beebah ta tashi tana matsifa Waike bakida hankali ne Bintu? ya mutum yana bacci zaki tadashi? Bintu tace ke dallah tashi kiga wani saurayin dana haɗu dashi a IG. Beebah ta tashi tana tsaki". Bintu tace kalleshi fa gayen ya haɗu wallahi yashiga raina lokaci ɗaya. Beebah taga hoton gayen ya haɗu gashi kamar ɗan india, atake taji zuciyanta ya buga, Sai kawai tayi tsaki ta tashi tabar ɗakin Bintu kuwa tayi shiru tana mamakin halin 'yar uwar tata. ******************* "Bash ya zubawa Mommy ruwan sanyi ahankali tasauke ajiyar zuciya, tafara buɗe idonta tana salati. polina kuwa sai rarraba ido take, Ahmad kuma baya hayyacinshi amma yaji an fara lasa mishi zuma kuma an daina, kawai saiya fara kiran sunan Polina a hankali, dayaji shiru saiya tashi akan gadon yana dafa bango har ya iso inda polina take ita dasu mom. polina tace my Ahmad sai kawai Ahmad ya rungumeta yafara shafa jikinta, polina tanajin haka tafara biye mishi a idon mommy, mommy kuwa tana ganin Ahmad abuge yana neman mace a idonta takara sumewa awajen". Bashir yatsaya sokoko yana ganin ikon Allah, yakara zubawa mommy ruwa afuska tana farfaɗowa tacewa Bash yakaita Asibiti, da kyar take iya tafiya harta shiga motarta tabawa Bash makulli suka ɗau hanyar Asibiti. Suna zuwa Asibitin Doctor yagwadata yace "gaskiya Hajiya am sorry to say kinada hawan jini wanda yayi chronic ajikinki idan har kikasa damuwa aranki zaki iya rasa rayuwarki!" Mommy tace nagode Doctor insha Allah zan kiyaye. "Alokacin da Ahmad yadawo hankalinshi sai yaga Bash bayanan amma yaji karan ruwa a toilet, kuma yasan Bash bazeyi wanka ahalin yanzu ba sai dai idan 'yammata yakawo. Yana wannan tunanin yaji karan buɗe kofa a hankali yaɗago kanshi yana kallon kofan, nan yaga polina tana fitowa daga ita sai towel, taƙaraso kan gadon tana yauki, tace "well done my Ahmad gaskiya yau ka jiyar dani daɗi sosai" Ahmad yayi shiru yasan polina ba karamar karuwa bace ba abunda bazata iya ba gara yayi maganinta tunda wuri. "Yatashi akan gadon kamar be damuba yaje wajen kayanshi yacire belt" Polina tana son tamaida kayanta taji duka kamar tayi hauka tsabar zafi Ahmad yadinga watsa mata Belt tana ihu, Dataji zafi yakai zafi ta kwasa da gudu tayi hanyar waje, Ahmad yasa mata ƙafa tafaɗi ya taka ruwan cikinta sai kawai ta suma yaje frij yaɗauko ruwan sanyi me ƙanƙara yazo ya buɗe marfin goran yana tsaye yafara watsa mata ruwan, ta buɗe idonta da karfi tana ihu yakara watsa mata belt yace kimin shiru. Ubanwa yakiraki? Tace Bash ne, yace me kikamin? Tayi shiru ya kara watsa mata belt, dataji azaba saita fara faɗa mishi duk abunda yafaru, Ahmad yanajin haka ya haukace da dukan polina idan taji azaba saita suma idan yawatsa mata ruwan sanyi ta farfaɗo yakara fara dukanta, da kyar polina taja jikinta tafita agidan. "Yana ganin tafita yaɗau makullin mota yanufi hanyan gidan Mommy, Yana zuwa yayi parking a kofan gidan domin yasan ko yayi horn megadi baze buɗeba dan Mommy tahana" Yana fita a motanshi yaga motar mommy ma ta tsaya abakin kofar, sai kawai ya daƙe ze wuce cikin gidan, yasa kafarshi na dama kenan yana shirin sa nahagu acikin gidan yaji muryan Mommy tana cewa "idan ka kara taku ɗaya daga inda kake kashiga gidannan Allah yatsine maka Albarka!!! Ahmad yatsaya da ƙafa ɗaya asama ɗaya akasa, ya kasa sauke ɗayan kafarshi..... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:48 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *WATTPAD* Jiddahpretty *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Page 31&32 "Ahmad yakasa juyawa, mommy tace Ahmad ta sanadin baƙin cikinka mahaifinka ya mutu, ka kashe 'yar mutane yarinya me hankali, sannan nima yanzu naje an gwadani ance inada hawan jini, kaga saura ni idan ka kasheni, saika kashe Fareedah ko? To baka isaba, kayi kaɗan bazaka kasheni ba! Ahmad idan ka kara taka gidannan Saina tsine maka! Kafice kabar anguwannan ma gaba ɗaya banson ganinka, Ahmad ya durkusa akasa ya rike kafan mommy yana rokon gafara". Mommy ta tureshi tashiga gida tana me taƙaicin Ahmad, Haka Ahmad yatafi gida yana kuka kamar ranshi yafita, Yana zuwa gida ya buɗe frij ya ɗauko kwalban giya yafara sha kamar ba gobe. *HABEEB* Habeeb tin ranan daya bar gidan Ahmad yashiga bincike kullum yana hanyan gidan marayu yana tambayansu ko akwai wacce aka tsinta? Domin shi jikinshi yana bashi Fateemah bata mutu ba! Ko Mommy batasan yana bincike ba haka ze shirya yace ze tafi makaranta Amma yana fita ze tafi nemawa Ahmad Fateemah, karatunshi yaɓaci baya attending na class, yazama busy wajen nemawa abokinshi matarsa. Duk da shima yanada nashi damuwan amma yana ganin damuwan Ahmad yafi nashi. "Yau takama ranar juma'a babbar rana Habeeb ne yayi shiri yacewa mom ze koma makaranta mommy dasu Beebah suka haɗa mishi kayanshi, suka rakashi wajen motarshi yatafi" Habeeb gidan Ahmad yanufa A Kaduna yana zuwa yatarar da Ahmad yana bacci Alamun yashawu, haka ya zauna yayi musu girki ya zuba a flask yashiga toilet yayi wanka yayi alwala, yana sallah Ahmad yatashi daga bacci, yace wow suprise Habeeb agidana yau kai naji daɗi, shima yatashi yashiga toilet yayi wanka yayi alwala yazo ya tada sallah, bayan sun idar da sallah ne Habeeb yakalli Ahmad yace "Ahmad kayi min alkawarin bazaka kara shan abu ba! amma nazo naganka a buge meyasa? Ahmad yayi shiru, Habeeb yace tambayarka fa nake? "Ahmad yace Habeeb bazaka ganemin bane, haka yabashi labarin duk abinda yafaru, Habeeb shiru yayi dan Ahmad yamugun bashi tausayi, yaƙarasa dacewa Habeeb mommy ta tsane ni! Gara nayi ta shan giyar ina neman matan ko zanji sauki a raina. Aa Ahmad karkace haka shan giya ko neman mata baya ragewa mutum baƙin ciki da damuwa karatun kur'ani shine idan kayi zaka samu sauki aranka." *BINTU* Bintu sunyi nisa a soyayyarsu da saurayin data haɗu dashi a IG a halin yanzu har maganan aure yafarayi mata, inda tace mishi yashigo gidansu asanshi tukunna. Yace mata insha Allah zai shigo ayi magana. Beebah idan taga Bintu tana chat da mutumin sai taji ranta yana ɓaci tarasa meyasa Gashi kuma Bintu kullum suna tare awaya. Yau suna zaune afalo da mommy, Bintu tacewa Beebah zokiga hotunan my Abdul kinga yanda yayi kyau, Beebah tamatsa kusa da ita tana kallon hoton, taja tsaki tace "kiga yanda yake dariya kamar ɗan tsintuwa yasamu gidan masu kuɗi"... Afirgice Mommy taɗago kanta tana kallon Beebah..... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* *dedicated to my Eeshart❤️* *WATTPAD* Jiddahpretty *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Page 35&36 "Tana zuwa ɗakin tashaƙo wuyar Beebah ta rinƙa zabga mata belt tana huci, Beebah taji wuya sai zazzare ido take ihunma takasa" Suna cikin haka Mommy tashigo ɗakin, taga Beebah a hannun Bintu sai zare ido take, ita kuma Bintu sai huci take tana zaneta, Mommy tayi saurin shiga ɗakin tana ƙoƙarin kwatan Beebah Amma takasa, Dataga Beebah tana jujjuya idanu Alaman zata suma, tafita a ɗakin da gudu tana ihu takira Baba me gadi da driver. Tace kuzo zata kasheta ranta yaɓaci dama haka take idan ranta yaɓaci, da gudu suka shiga ɗakin, sukayi kan Bintu suna ƙwatan Beebah Amma ina Rikon da Bintu tayi mata bana wasaba! "Da kyar da suɗin goshi suka ƙwaci Beebah, ai kuwa tanajin an saketa ta kwasa da gudu tayi cikin toilet ta kulle ƙofar" _Ahmad_ Ajmad ne yake tambayar Habeeb meyake faruwa awayar? Habeeb yace wallahi Ahmad narasa ganewa Bintu wani irin zuciya ne da ita idan ranta yaɓaci, tanada hakuri sosai Amma idan ranta ya ɓaci ba'a gane kanta, yanzu fa dukan Beebah takeyi kamar 'yarta, Ahmad yace ay dama haka me hakuri yake idan ranshi yaɓaci ba kyau, saidai kuyi ta mata Addu'a....... Kafin yakarasa yaji wayarshi tana kara, daya duba saiyaga sunan Abdul ne, yayi dariya yaɗau wayar, yace "hello dude ya kake?" ɗayan bangaren akace lafiya ya jikinnaka? Ahmad Yace da sauki, Albishirinka? Ahmad yace goro, nasamu matar Aure anan Adamawa, Ahmad yace kai banason ƙarya, yace wallahi nake faɗa maka kuma Aurenta zanyi insha Allah. kaima ina maka Addu'a kullum Allah yabayyana maka Fateemahnka idan har tana raye, idan kuma bata raye Allah ya musanya maka da mafi Alkhairi, Ameen cewar Ahmad cikin sanyin murya yayi maganar sukayi sallama. "Abdul abokin Ahmad ne yakasance me bashi shawara ako da yaushe, bayason damuwar Ahmad ko kaɗan, sannan yana taƙaicin yaga Ahmad yana tafiya da Abokanan banza, shima yana daga cikin masu bincikowa Ahmad Fateemahn shi". _Bintu_ Bintu takicin abinci taki yiwa kowa magana agidan, har na tsawon kwana biyu, abun yadami Mommy sosai yau ta tarasu a falon ta tanason ta sasantasu, zaman dasukeyin baya mata daɗi ko kaɗan. kuma haka akayi dan Bintu ta sakko Beebah kuwa tabata hakuri komai yawuce. Yau friday Bintu ce ta dami Abdul sai yazo gidansu, shikuma Abdul yana gudun wulaƙancin Beebah yace mata gaskiya yau bazan zoba Babyna, tace mishi dan me? Yace babu, tace idan badan wulaƙancin da Beebah tayi maka ba nasan bazaka ki zuwa ba! Yace mata Aa wallahi bahaka bane, tace to kazo, da Abdul yaga ta nace yace mata to zanzo Amma sai bayan juma'a tace tom. Haka akayi kuwa bayan juma'a saiga Abful yazo, yayi kyau yasa brown na shadda da hula brown yayi kyau sosai, Bintu kuwa tasa Abaya pink da gyallenshi tasa flat shoe pink tayi kyau kamar asace a gudu. Tana zuwa wajenshi yaji ƙamshin turarenta a hankali ya lumshe idonshi, ya buɗe yace "Tsarki ya tabbata ga ubangijin dayayi wannan halitta" Bintu tayi dariya har kumatunta ya lotsa tace godiya nake masoyina. Abdul yayi dariya yace ranki ya daɗe dolene yau nayi snapping naki ko ɗayane Bintu tarufe fuskanta tace banason hoto, Abdul yayi yayi ta ɓuɗe fuskanta taƙi, ahaka ya ɗauketa hoton ta rufe fuskanta da hanunta, tana dariya. Haka sukaci gaba da hirarsu cikin farin ciki, suna cikin hiranne Abdul yanata dariya, dan Bintu yau tana ta bashi labarai, kawai saiga Beebah tazo wucewa, da Alama mommy ce ta aiketa. Bintu tayi shiru zuciyarta tana bugawa tana tsoron kar Beebah ta wulaƙanta Abdul irin na rancan. Beebah tana isowa wajensu ta tsunkuya har ƙasa tace "ina wuni yaya Abdul".... ✍🗒️ *jiddah S Mapi* [6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!*🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *dedicated to my love ❤️* *WATTPAD* Jiddahpretty *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Page 33&34 "A firgice mommy taɗago kanta tana kallon Beebah tace ke Beebah bakida hankali ne? Ya 'yar uwarki tana nuna miki saurayinta zaki faɗi maganan banza akanshi? Idan nakarajin irin wannan maganan daga bakinki saina ɓata miki rai tashi kibani waje" Beebah tafita a ɗakin, mommy tace kiyi hakuri Hassana na kinga 'yar uwar taki batada hali me kyau, bani hoton nashi nagani, Binta tace to saita nunawa Mommy hoton mommy tace kaii amma gaskiya sirikinan ya haɗu masha Allah ya sunanshi? Abdul inji Bintu, masha Allah Babban suna Allah yabarku tare, kuma Allah ya nunamin ranar Aurenku Ameen. _Ahmad_ Habeeb ne yasashi agaba yayi ta mishi nasiha, Ahmad yace nagode Habeeb Allah yabar zumunci. _HABEEB_ "Habeeb kuwa acikin zuciyarshi yana tunanin yafaɗawa Ahmad damuwarshi amma yana tsoron kar ayi mishi mumunan fahimta, azuciyarshi yace kai garadai nafaɗa mishi ko zai nema min mafita, Wani abu yace mishi Aa karka faɗa ka riƙe sirrinka, ba lalle bane kowa yayi maka kyakkyawan zato" Yana cikin tunanin yaji an dafashi, Ahmad ne yace "abokina kasan bana ɓoye maka komai a rayuwata? Habeeb yace eh, to kaima banason ka ɓoyemin komai inason kafaɗamin damuwarka, na lura tin Wancan zuwannaka kana ɓoyemin wani abu" Habeeb yace babu komai Ahmad dama wata 'yar matsalace agida amma in Allah ya yadda za'ayi solving nasu very soon. To Allah yasa Ameen _Bintu_ Yau ce ranan dasukayi da Abdul zaizo wajenta dan haka tasha wanka tasa atamfa ja da jar gyale sai jar takalmi tayi makeup, idan kaganta kamar kasace ka gudu. Abdul yazo gidansu Bintu anyi mishi tarba me kyau, Bintu ta ajeshi a babbar falo suna hira sai Abdul yace "Babe tinda nazo banga twins nakiba ki kirata mana mu gaisa". Bintu tace tom, saita ɗau waya takira Beebah tace kiseni a falon Mom, Beebah tace ok Jim kaɗan saiga Beeba tasha doguwar rigar material ja itama jar gyale tasa, tana zuwa falon ta tsaya akan Bintu tace gani, Bintu tace Abdul ne yakeso ku gaisa, tace to bagani ba! Bintu tayi shiru Abdul yace ya kike ƙanwata? Beebah tace Aa niba ƙanwar ka bace ni ƙanwar Habeeb ce, Abdul yayi dariya yace toya kike ƙanwar Habeeb? Tace lafiya "Yace ok saiya cire kuɗi yace gashi ko ƙanwar Habeeb, Beebah tace Aa ai gidanmu ba'a yunwar kuɗi. Ta juya tayi tafiyarta Bintu tayi shiru tarasa yazatayi, Abdul yace karki damu my dear nasan yaranta ne yake daminta karkiji komai. A rayuwar Bintu ba abinda tatsana kamar wulaƙanci haka suka ƙarashe hiransu da Abdul tarakashi wajen motarshi tace mishi sai yaushe Kenan yace gaskiya ba rana Babe, tace dan Allah kayi hakuri da abinda twins nawa tayi maka yace ba komai babe, haka sukayi sallama yatafi tana ɗaga mishi hannu. Tajuya tashiga cikin gida ta samu Beebah kwance suna waya da Habeeb, tana zuwa ta wupce wayar ahanun Beebah Tace "bakida hankali Ko? to yau zan koya miki hankali har Zaki wulaƙanta Abdul kuma kinsan shi zan Aura? Beebah tace bani wayata! Baza'abada ba! Ki ƙwace Beebah tafara ƙwatar Wayar suka kwashe da dambe! _HABEEB_ Habeeb suna waya da Beebah yaji duk Abinda sukeyi yanatayi Musu magana su daina amma ina sai ihun Beebah yakeji alamun tana dakuwa, aranshi yace me hakuri fushinshi babu kyau! Beebah bakaramin duka takesha ba awajen Bintu, gashi bakinta baya shiru, tana ta zagin Abdul, da Bintu taga Beebah ba shiru zatayi ba saita fita falo ta tsinƙa sucket na TV tashiga ɗakin da gudu... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* _pls share🙏🏻_ [6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* *dedicated to my love❤️* *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 37&38 "Abdul ya saki baki yana kallon Beebah a Azuciyarshi yace wataƙila ma sabon salon iskancine takoya zatayi mishi, taƙara cewa ina wuni yaya Abdul, Abdul yace lafiya kanwar Habeeb ya kike ya gida? Tace lafiya lau yaya, Yace ina zuwa haka? Beebah tace Mommy ce ta aikeni G.R.A zan kai aika, yace ok dama nima tafiya zanyi me zai hana na sauƙe ki acan? Tace tom nagode, Abdul sukayi sallama da Bintu yashiga motar Beebah ma tashiga suka tafi" A hanya Abdul yake tambayar Beebah yace "ƙanwar Habeeb meyasa kika sauya alokaci ƙanƙani? " Beebah tanason tayi mishi rashin mutunci Amma tana tsoron karya faɗawa Bintu takara shan dukan mutuwa. Tace mishi babu komai yace "ok" yaje ya ajeta a G.R.A yayi tafiyarsa. _Ahmad_ "A kwana biyun da Habeeb yazo wajenshi yaɗan samu sauƙin abunda yake daminshi, Amma har yanzu bai dawo daidai ba, yau yaɗan buɗe data yace bazi yaɗan ganin Abunda yake tafiya a social media, yana buɗe datan yaɗan aje wayar sabida messages ɗin sugama shigowa, bayan wasu 'yan mintuna yaɗauki wayar yana duba messages na abokai da kuma 'yan uwanshi saiya shiga message na Abdul wanda yaga hotone yatura mishi, yana buɗewa yaga hoton wata faran yarinya doguwa tsiririya ta rufe fuskanta tana dariya da Alama batason hotonne aka ɗauketa, Duk yanda yaso yaga fuskarta yakasa" Yabuɗe voice chat ɗin da Abdul yayi mishi yaji Abdul yace "dude ga hoton matana danake Auran" Ahmad yayi mishi reply da Allah yasa ka Aureta dude, yatura mishi. _Bintu_ "A duniya ba abinda takeso sama da Mommy dakuma Abdul yanzu har maganan Aure yashiga, domin Abdul yaturo iyayenshi anyi magana, ansa rana, wata biyu masu zuwa, idan an ɗaura Aure kuma a kaduna zasu zauna". ************* "Yau Da daddare mommy tashiga ɗakin Habeeb Tanason tambayarshi maganin ciwon kai, Amma me? Tana zuwa ɗakin taga Habeeb yarungume hoto yana kuka Kamar ƙaramin yaro, be maji shigowarta ba! "A hankali tajuya tafita a ɗakin ta tsaya a window tana leƙanshi, sai kuka yake harda sheshsheƙah, yana kukan yatashi yaje wajen kayanshi, ya ɗauko wani frame pink colour me kyau yasa hoton aciki ya buɗe kayanshi yasa frame ɗin ya fesawa kayan turare ya juya yashiga toilet". Mommy tana tsaye tana kallon ikon Allah, nan ta tuna wata rana datazo takamashi yana kallon hoto, yana ganinta yayi sauri ya ɓoye hoton abayanshi, Mommy tagaza ganewa Habeeb wani irin mutum ne? Idan tace ya kawo matar daze Aura sai yace mata "A GIDANMU TAKE" tarasa gane me kalman yake nufi. Amma koba komai yau saitaga hoton dayake ɓoyewa ko ta halin ƙaƙa! Tajuya tayi tafiyarta takoma falo. Habeeb yana shiga toilet ya wanke fuskarshi yayi alwala yazo yayi sallah, yana idarwa yatafi falon mommy yana zuwa yatarar da ita da 'yan biyunta suna hira, yafara murmushi yace kaga Mommy da 'yan biyunta, mommy tace eh wallahi Habeeb Amma meya sameka naga kamar kayi kuka? Habeeb yace wallahi mommy yau bacci nayi tayi, Mommy tace ok. "Da safe Mommy takira Habeeb awaya tace yazo falo zata aikeshi, Habeeb yana zuwa Mommy tace GRA zakaje ka karɓomin saƙo yace tom Mommy, Habeeb yana fita agidan Mommy taje ɗakinshi ta buɗe kayanshi daidai inda taga jiya ya ajiye hoton, Tana ganin hoton ta ɗauka ta tafi ɗakinta dashi, tana zuwa ɗaki ta buɗe frame ɗin. Ta ɗauko hoton tana gani. Amma me? Tana kallon hoton jikinta yafara rawa hanunta yakasa rike hoton kawai sai hoton yafaɗi. itama tabi bayan hoton a sume... *Share, vote and comment🙏🏻* ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to My love_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _jiddah S mapi_ Page 39&40 "Mommy takai minti talatin Asume, kafin Beebah tashigo falon tana sallama taga Mommy Akwance ƙasa ba Alamun numfashi, Ta tsala ihu tana kiran Bintu, dagudu Bintu tashigo ɗakin ganin Mommy asume tayi gudu taje frij ta ɗauko ruwa suka shafa mata afuska" A hankali tasauke Ajiyar zuciya, tafara buɗe idanunta. Ganin Beebah da Bintu tsaye akanta cirko cirko, tafara Addu'an Allah yasa basuga hotonba. Tajuya tana dube duben inda hoton yake Amma bata ganiba, ta rikice tana neman hoton can taga hoton Agaban Bintu daidai ƙafarta, Bintu kuma bata lura da hoton ba burinsu suji me ya sumar da mom? Mommy dataga Alaman basuga hoton ba tayi sauri ta kwanta rub da ciki akan hoton tana cewa wayyo cikina! Tafara ja da cikinta har ta iso wajen gado tatura hoton babu wanda yagani. Bintu da Beebah suka rinƙayi mata sannu harta samu tayi bacci, Beebah ce takira Habeeb tace mishi "yaya mommy ba lafiya harta suma" Habeeb yace meya sameta? Tace babu komai muma dai haka muka shigo muka ganta a sume, yace "ok" ina izuwa. Habeeb yana zuwa yaga mommy akwance tana bacci yafara tambayan Bintu meya sameta? Bintu cikin sanyin murya tace nima dai haka nazo naganta a sume! Amma naji tana cewa cikinta ne yake ciwo! Yayi shiru yana kallonta yace "ok". Habeeb yazauna awajen mommy harta tashi daga bacci, tana tashi tacewa "yaushe kadawo?" Yace mommy ay tin Ɗazu nadawo tace ok cikin sanyin murya tace inason kaje kasiyaminmagani yanzu yanzu basai kawani canza kaya ba! Yace tom mommy, yatashi yafita mommy ta tsunkuya taɗau hoton a ƙarƙashin gado Kana tasa a frame ɗin ta ɓoye a rigarta tabi bayanshi. Tana fita taganshi yana ƙoƙarin buɗe ɗakinshi, da sauri ta ƙarasa wajenshi tace kai Habeeb mezakayi kuma a ɗaki bayan kasan banida lafiya harda suma? Amaimakon kayi sauri kasiyomin magani? Habeeb yayi mamakin yanda mommy takeson korashi amma be kawo komai aranshi ba!. Yace mata mommy kuɗi zan ɗauka sabida kuɗin hanuna yakare, Mommy tace kaje ɗakina kacire acikin jaka, yace tom Mommy. Saida Habeeb yabar gidan kafin Mommy tashiga ɗakin ta ajiye hoton yanda tagani ta gyara wajen kamar ba'a taɓa komai ba. Harda fesa turare. *_Ahmad_* Tin bayan tafiyan Habeeb yashiga damuwa kamar da dama acikin abokananshi daga Habeeb sai Abdul ne kaɗai suke kwantar mishi da hankali saɓanin Bash dayake bashi giya yasha kuma yakawo mishi mata. *_Bintu_* Bintu kuwa da Abdul soyayya tayi nisa idan Abdul beji muryan Bintu ba To ranan akwai tashin hankali. ****************** "Bayan wata ɗaya da sati uku, wanda yayi daidai da kawo kayan lefen Bintu Daza'ayi ayau juma'a, gidansu Bintu ne yau ake shirye shiryen karɓar kaya, inda Mommy tayi namijim ƙoƙari wajen ganinta ƙayata abun, Abinci musamman akayi daga gidan Abincin Mommy, yayinda aka dafa abubuwa masu daɗi da ban sha'awa aka zuba a take-away, drinks kuma ba'a magana mommy tayi ordernsu kamar ba gobe. (Azuciyana nace wannanma ba ranar Auren ba) An kawo kaya komai yayi daidai inda akayiwa Bintu kaya nagani nafaɗa, kowa yasa Albarka anyi mata fatan Alkhairi. Abdul ne yabijirowa Bintu da maganar pre-wedding pics, Bintu taje sama ta sakko kasa tace bazatayi ba! Hakan ya fusata Abdul har yayi fishi da ita kota kirashi baya ɗaukan kira. Abun yadami Bintu, tasamu Beebah tayi mata bayanin duk abinda yafaru, Beebah tace Abu me sauƙi basai kitura mishi text kice kin yadda zakiyi ba, Idan yazo saimu tafi tare inyaso sai ayi dani. Thats my sisterluv inji Bintu tabawa Beebah hannu suka tafa tace hakan kuwa za'ayi.. _✅ote, comment, and share pls_ ✍️🗒️ *_jiddah S Mapi_* [6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my love_ *WATTPAD* Jiddahpretty *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Page 41&42 " hakan kuwa akayi data turawa Abdul message aranan yazo suka ɗibi kaya sai wajen ɗaukan hoto, Dasukaje ɗaukan hoto akace Bintu tashirya, Bintu tace itafa bazatayi wani hoto ba sabida bidi'a ne, amma ayi da Beebah tinda su 'yan biyu ne, Da farko Abdul yaki amma dayaga Bintu ta nace kawai saiya amince suka ɗau hotunan" Beebah kamar itace Amaryan dagaske, tayi kyau bana wasa ba, Sunyi hotuna kala-kala ciki harda wanda Beebah tariƙe wuyan Abdul, da wanda yaɗan sunkuyo daidai wuyarta, sunyi kyau matuƙa fiye da tsammani. "Ahmad yana kwance akan gado yana ɗan chat da Abokinshi Habeeb, sai kawai yaji karan message. daya duba message ɗin saiyaga Abdul ne yatura mishi hotona, daya buɗe hotonan saiyaga Abdul da wata fine girl, sunyi kyau sosai, Yacewa Abdul gaskiya kunyi kyau Amaryar taka kyakkyawa Allah yabada zaman lafiya. "Ameen" cewar Abdul. _Bintu_ Ita kuwa Bintu dilki akeyi mata lagadan ba ajalan ba, Beebah ma tace sai tayi dilkin tare suke dilkin sunyi kyau bana wasa ba, idan kagansu kamar larabawa. *************** "Lokaci yaja kwanaki sun wuce, kamar yadda akasa date na Auren Bintu Da Abdul hakan kuwa akayi yau Alhamis, za'ayi kamu, a wetline dake cikin garin Adamawa" Bintu da Beebah anko sukayi sunsa doguwar rigan material jaa ne yalƙi sunyi makeup idan kaga Bintu zakace ba 'yar nan kasan bace kamar balarabiya Ƙawayensu kuwa sunsa Pink na dogayen riga plane material sun ɗaura kansu da baƙaken ɗan kwali, Abun ba'a magana. Hall ɗin da aka kama musu an ƙayatashi da kayan kyale kyale, Wajen yayi kyau, Abokan Ango sunsa baƙin shadda dayaji zubi Abun saidai kawai ayi shiru. Can nahango Beebah da Bintu suna musu, Bintu ce tace ita bazata iya zama acikin mutane ba! Beebah kuwa tace ay bata isaba! suna cikin musune Bintu dataga sun dameta sai kawai tajuya tafita a hall ɗin, daidai lokacin da MC. Yafara cewa ana neman amarya afili. Gashi Bintu tafita, ƙawaye sai juye juye suke sun rasa ya zasuyi,gashi MC. Yanata kiran Amarya, da Beebah taga haka sai kawai tafara tafiya Zuwa wajen Ango tana shiga tsakiya zata wuce taji MC. Yana cewa atafawa Amarya. "kawai sai taji wajen ya ƙaure da tafi, Abdul yana zaune yana kallon ikon Allah yarasa meyake faruwa, MC. Yace ana neman Ango afili" Abdul ne yatashi jiki amace yana Zuwa wajen MC. Yanaso yace ai ba ita bace Amaryar Amma yana zuwa daidai tsakiyan fili yaji ance atafawa Ango da Amaryarsa waje ya kaure da tafi ana ihu. MC. Yace Anaso ango yayi rawa da Amaryarsa rawa irinna nuna farin ciki da farko dai ango yakama hanun Amaryar tashi su shigo tsakiyar fili yanda baƙi zasugansu da kyau... _Ahmad_ Ahmad kuwa sauri yake ya isa garin Adamawa sabida Abdul yadameshi da kira, gudu yake akan kwalta kamar zai tashi sama, yana duba agogonshi yana kara spirit. _Bintu_ Bintu kuwa tana fita a hall ɗin napep takama ta tafi gida dan tafara jin kanta yana ciwo. Tana zuwa gida tawuce zata shiga ɗakin mommy taga mutane dayawa, kawai saita juya tawuce ɗakin Habeeb. Amma me? Tana shiga ɗakin Habeeb taganshi yarungume hoto yana kuka kamar ƙaramin yaro. Tayi sauri ta karata cikin ɗakin tana me kiran yaya Habeeb yaya Habeeb meya sameka kake kuka? Habeeb ne yayi saurin ɓoye hoton yana share hawayrnshe. Yace Bintu na meya dawo dake gida ana tsaka dayin kamunki? Yaya ni wallahi banason wannan hayaniyar ne tana sani ciwon kai. yaya meya sameka kake kuka? Kuma hoton waye ka ɓoye abayanka? Habeeb yayi shiru can yace Babu komai Bintu na, wannan wani sirri ne nawa dana ɓoye bana so kowa yasani harsai ranan da Allah yakarɓi rayuwata, Bintu tace yaya meyasa kake irin waɗannan maganganun yau fa ranar murna ce sanin kanka ne nice farkon da mommy tafara Aurarwa agidannan. be kamata ka zauna acikin baƙin ciki ranar Aurena ba! Kamata Ai farin ciki zakayi, Habeeb yace to Bintu insha Allah zan daina damuwa". yanzu ina kika bar su Beebah da Abdul? Bintu ta shagwaɓe fuska tace "suna wajen kamu". _Hall_ "Abdul da Beebah ba sun rasa yanda zasuyi haka suka daure suka shiga fili sunata caskalewa, Abdul yariƙe hanun Beebah suna rawa kamar 'yan india, Abokansa kuma suna watsa kuɗi kamar ba gobe. _Ahmad_ 3:30pm cif yashigo garin Adamawa, bai tsaya ko inaba Sai a babban hotel na garin, yana zuwa yabiya kuɗin ɗaki aka bashi key yawuce, yana shiga cikin ɗakin ya ajiye kayanshi akan gadon yabuɗe toilet yashiga yayi wanka, yana fitowa daga wanka yashafa lotion da turaren jiki me kamshi, yataje suman kanshi, ya ɗauko wata baƙar shadda me kyau wanda tasha adon jaa ajiki, yasa jan hula, yaɗauko jan Agogo da takalmi jaa yasa, idan kaga Ahmad zakace balarabe ne, kamar asace a gudu yayi kyau har yafi kyau kyau awannan rana. "yayi sauri yaɗau makullin mota yabuɗe ɗakin yafita, Yana fita harabar hotel ɗin kallo yakoma sama, kowa idonshi akan Ahmad, wani dagacan gefe yace inama ace nine wannan. Jin hakaAhmad yajuya yace mishi bawan Allah ka godewa Allah aduk inda ya ajiyeka, ni nan dakasan matsalata da bazakaso ace kasanni bama balle ace kaine ni". Yana gama faɗan haka yajuya yayi tafiyarshi, wajen parking na motoci yanufa, yana zuwa yashiga baƙar motarshi kirar land-rover. ya tada motarshi yanufi hanyan wetline wajen kamu. Yana zuwa yayi parking yashiga cikin hall. Dashigarshi hall ɗin kallo yakoma sama, kowa yana kallonshi maza da mata. "MC ne yace ga babban abokin ango atafa mishi, waje ya kaure da tafi, ana ihu MC. yace muna neman amarya da ango dakuma babban abokin ango afili" Beebah tinda ta ɗaura idonta akan Ahmad taji zuciyanta ya buga, gayen ya birgeta infact wankanshi ne yafi tafiya da imaninta, MC. Ne yasake cewa muna jirnku, Ahmad ne yafara fitowa kowa sai kallonshi yake, nan Beebah da Abdul suka shigo, Beebah tana shiga fili tawuce wajen Ahmad tana rawa da jikinta kamar wata 'yar india, Ganin haka Ahmad yafara rawa shima yana watsa mata kuɗi, mutane sai tafi sukeyi musu. "Abdul kuma yatsaya afili kamar gunki yana kallon ikon Allah, yama rasa me zeyi? Sai juye juye yake yana dariyan dole" Beebah kuwa tazage afili kamar ibada sai juya jikinta take kamar hawainiya, Da Ahmad yaga yanda take rawa. Azuciyarshi yace wannan wace irin Amarya ce?... _✅ote, comment and share pls🙏🏻_ ✍️🗒️ *_Jiddah S Mapi_* [6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S mapi_ Page 43&44 "A zuciyar Ahmad yace ay Amarya ko bata da kunya, ranar Aurenta tana ɗan jin kunyar mutane Amma ita ta zage sai tiƙa rawa taje agaban Abokan Ango? Kai wannan abu da alamar tambay" Beebah kuwa acikin zuciyarta tance kai wannan gayen ya haɗu ana gama kamu zan tambayi numban wayarshi, duk nan yafisu wanka, duk maganar dasuke acikin zuciyarsu be hanasu taka rawa a filin ba, har MC yace to mun gode Allah yasakawa amarya da ango dakuma babban abokin ango. Haka suka juya suka tafi, an gama kamu dab mangariba kowa ya watse. Ahmad ne yacewa ango yanason yabishi hotel ɗin daya sauka sabida sunada magana me muhimmanci, Abdul yashiga motarshi suka wuce Hotel. _Bintu_ Bintu tace ita wallahi daga kamu ba abinda za'a karayi a Aurenta na bidi'a. Washe gari ranar jumma'a ranar da za'a ɗaura Auren Abdul Muhammad da Bintu Umar, shirye shirye ake na musamman, kawayen mommy sunzo daga wani gari 'yan wanka ne kuma hajiyoyi ne. Bintu kuwa tasa leshi jaa me kyau tayi makeup kamar asace agudu, Beebah ma ba'a barta ba wajen kyau, kawayensu ma sunyi kyau sosai. Kawayen mommy suma leshi suka ɗinka garin mata dashi, idan kashiga gidan saika raina kanka. 2:30pm cif aka ɗaura auren Bintu da Abdul akan sadaki dubu ɗari lagadan ba ajalan ba, Anyi Aure an kammala komai da mangariba abokan ango sukazo su ɗauki amaryarsu. Tofa nan akeyinta Habeeb dayaga za'a tafi da Bintu yadinga suma kamar me farfaɗiya, har mutanen wajen suka fara mamaki, mommy ce tacewa Bintu takoma gida, Beebah ce tazama amaryan karya taje tashiga mota aka tafi da ita, bayan mutane sun watse ne mommy takira Habeeb cikin ɗakinta da Bintu ta ajiyesu, mommy ce tace Habeeb? Yace na'am tasake cewa Habeeb? Habeeb yace na'am Mommy tasake cewa Habeeb? Yace na'am, Mommy tace sau nawa nakira sunanka? Yace sau uku, mommy tace tom nataɓa kiran sunanka sau uku? Yace Aa tace inason kafaɗamin gaskiya. Meye a tsakaninka da Bintu?.. Habeeb yayi shiru sai kawai yafara kuka, mommy tace ba kuka natambayeka kayi ba, idan har nina haifeka kafaɗamin Abinda yake ranka? Habeeb yace Mommy inasonta ne!!! Kuma Aurenta nakeso nayi!!! Tass tass tass kakeji Bintu ce taɗago ta dallawa Habeeb mari tana huci... Bakada hankali ne yaya? Ko kafara shaye shaye ne? Ko ka sami taɓin hankaline? Ko bakasan ciki ɗaya muka fito dakai bane? Duk waɗannan tambayoyin tana yinsu ne cikin hawaye.. Yaya kai mahaukaci ne bakada hankali, sai yau na tabbatar da haka kanka ya taɓu. Ke Bintu kece me taɓin hankali bani ba! Kece kanki yasami matsala bani ba! Ina matsayin yayanki zaki kirani mahaukaci? Kece mahaukaciya! Yana magana yana hawaye, Kinsan iron son danake miki? Kinsan baƙin cikin danake ji idan naganki da saurayi? Kinsan yaya nake kwana acikin kwanakinnan da Auranki ya iso? Kinsan yanda nakeji kamar na kashe Abdul idan naganku tare? Duk nasan baki sani ba. "Mommy ce ta tsaya awajen ba bakin Magana sai zazzare ido datakeyi kamar wata taɓaɓɓiya, idan wannan yana magana tajuya ta kalleshi idan wannan yanayi ta juya ta kalleshi tarasa ya zatayi da duniyarta tarasa ina zatasa kanta ayau, jitake kamar ta tara kayanta tabar gidan kafin su fara mata tambayoyi, juyawa tayi zata bar musu ɗakin taga mutum akwance kasa ba alamar numfashi! Beebah ce kwance kasa, wanda ta daɗe da dawowa ta dalilin faɗa dasukayi da Abdul bayan ankaita gidanshi ta tsigeleshi tayi gaba abinta, tana dawowa shine ta tarar da abinda yafi karfin kunnenta. Jin kalaman Habeeb yasa tafaɗi ta suma! Mommy ta tsala ihu ta iso wajen da Beebah take kwance ƙasa!... _✅ote comment and share pls_ ✍️ *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *WATTPAD* _Jiddah S Mapi_ Page 45&46 "Mommy ce tayi kan Beebah dagudu tana ihu, ganin haka yasa Bintu tayi sauri ta ɗauko goran swan a frij tazo aka shafawa Beebah afuska, a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana buɗe idonta tafara tambayan Habeeb, yaya me naji kana cewa? Kamar naji kace kanason Hassana kuma da Aure? Kamanta mu 'yan biyu ne da ita? Ko ka manta ciki ɗaya muka fito da ita? Allah yasa dai wasa kake, duk tabayoyin datake mishi tanayine cikin hawaye sannan ta Zubawa Habeeb ido, Mommy tayi shiru tanayi wa Habeeb kallon tuhuma. Da Habeeb yaga duk shi suke kallo, ciki kuwa hadda Bintu, sai kawai yafara kame kame, yajuya yafita a ɗakin. _Ango_ Abokansa ne suke ta zagin Abu wai an raina musu hankali, yaza'ayi ranar Aure a nemi Amarya arasa, Abdul yatsaya yakasa yin komai sai gyara gari yake tin ɗazu da goge zufa, Yakira numban Bintu yafi sau 20 ba'a ɗaga ba! Azuciyarshi yace kodai yaudarana dama takeda niyan yi? Ahmad ne yadafa kafaɗan Habeeb yace "kadaina tunani dude" insha Allah gobe Zamuje gidansu Amaryar tafaɗa mana meyake faruwa, domin kasan lamarin Aure yanzu, kowa yana kokarin yaga an ɓata, Abdul ne yace "Haba Ahmad kana gani fa yarinyannan tadinga wulaƙanta ni a idon duniya, Aure wasane? Hakafa ranan kamu ta tafi tabar wajen saida ɗayar 'yan biyunta tazauna awajen, yanzu kowa yazata Beebah ce Matata!... Wani irin magana ne kake faɗa dude? Kana nufin wannan ba itace kake Aura ba? Kuma ai naga pre-wedding pics ɗin da ita akai. Abdul ne yayi mishi bayanin duk abinda akayi, Ahmad yayi shiru yana tunani can yace "Amma Abdul ka tabka kuskure Babbah! Meya kaika ɗaukan hoto da 'yan biyun wacce kake Aura kuma kace Ba itace matarka ba! Kana ganin mutane baza suyi maka mumunan fahimta ba? agaskiya ka aikata Babban kuskure! Abdul yace "hakika Ahmad na aikata kuskure to amma tayaya zan wanke wannan kuskuren danayi"? Ahmad yace mafita ɗayane garemu shine kaje gobe ka ɗauko matarka koma muje tare, kacewa kanwarta ta ɗauko duk kayan da kukayi hotunan dashi saimu tafi tare dukanmu huɗu, Ita matarka saitasa kayan da wancan tasa ranar dazakuyi hoton koda shike ai su 'yan biyu ne, bazasu rasa kaya kala ɗaya ba, Idan munje wajen ɗaukan hoton, ni saina ɗauka da Beebah kai kuma ka ɗauka da matarka, sannan muɗauka dukanmu huɗu, kaga zamu juya kan mutane, ba kowa ne zai gano bakin zaren ba, idan aka tambayeka saikace ai Bintu itace matarka! Abdul wani sanyi yaji azuciyarshi, yacewa Ahmad to insha Allah haka za'ayi, nagode da wannan shawarar. Suka sallami abokanansu suka basu hakuri, kowa yawatse. _washe gari_ Ahmad ne da Habeeb suka buga wanka, sunsa anko gaba ɗayansu shadda ne fari da zubin baƙi, sukasa hula baƙi da takalmi baƙi sai agogo baƙi, bakaramin kyau sukayi ba, suka shiga motar Ahmad baƙi, suka ɗau hanya sai gidansu Bintu. Suna zuwa Abdul ne yashiga daga ciki dan Ahmad yace shi baze shiga ba! Yana jiransu awaje, Abdul yana shiga ya gaida mommy afalo, mommy take bashi hakuri tace kayi hakuri Abdul wata 'yar matsala aka samu, shiyasa kaga ba'a kai maka Bintu ba! Abdul yace ba komai, mommy ce ta tashi afalon taje takira Bintu aɗakinsu, Bintu ce ta tashi tasa dogon riga, gaba ɗaya ta rame tin jiya take cikin kuka da tinani tarasa meyake mata daɗi. Goga powder tayiwa fuskarta tasa baƙin kwalli acikin Idonta tayafa baƙin gyale, ta fesa turare ajikinta masu kamshi, tasa flat shoe, duk abinda takeyi Beebah na kallonta tace ko zamuje ku gaisa ne? Beebah tace no, tace dan Allah muje, Beebah data tuna dukan rannan saita diro akan gadon tace bari nasa hijab sai naje mu gaisa. "Suna zuwa falon Beebah tafara tsayawa abaya baya dan tasan rashin kunyan datai tamishi jiya, shi kuma saiya basar yace ya kike kanwar Habeeb? Beebah tace lafiya ya gajiya? Yace babu, Abdul ne yayi gyaran murya yace amm Hassana da Hussaina? Sukace na'am yace wata alfarma nazo nema awajenku, duk da Bintu yanzu ita matatace amma dole na nemi alfarma, Sukace ba matsala kafaɗa muji in Zamu iya, Yace dama inason ku ɗibo kaya waɗanda kukayi anko, da wanda mukayi pre-wedding pics dashi, yanzu zamuje ayi sabon hoton sabida wancan akwai matsala" "Bintu ce tace ita bazatayi hoto ba! Abdul yadinga haɗata da Allah taki, da Abdul yafusata yace look Bintu karkiga dan inasonki kice zaki wulaƙanta ni, yanzu miji nake awajenki umarni nake baki kitashi ki ɗebo kayanki zamuje ayi sabon hoto! Yafaɗa cikin fushi. Bintu ce tahaɗa rai ta tashi tashiga ɗaki ta ɗebo kayan dana Beebah, Beebah ce takarɓi kayan ta tafi sawa a mota, ita kuma Bintu tashiga cikin ɗakin mommy domin sanar da ita. _Ahmad_ Shikuma ya zauna yanata jiransu amma har yanzu basu fito ba! Ganin haka yasa yajuya kanshi yadaina kallon kofar gidansu Bintun, dayaji karar buɗe kofar saiya juya yaga Beebah ce takesa kayansu aciki, tace ina wuni? Yace lafiya, daga cewa lafiya be kara komai akaiba kuma be sake juya bayanshi ba, yayi readyn jan mota idan sun fito. Beebah ce tashiga cikin motar tazauna tana kallon side view na Ahmad. Abdul da Bintu Kuwa sunata rigiman fitowa. Bintu tace sai Abdul ne zai fara fitowa shikuma Abdul yana tsoron kada yashiga gaba ta gudu, shima yace sai ita zata fara fita. Da kyar Bintu tayadda tafara fitowa rai aɓace taje ta buɗe motar tashiga wajen da Beebah take. Shikuma Ahmad ko juyawa ya kallesu baiyi ba, yana ganin Abdul yashiga, ko gama rufe marfin motan baiyi ba! Yaja motar cikin fishi yafara watsa gudu akan titi.... _✅ote, comment and share pls🙏🏻_ ✍️🗒 *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my Facebook fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 47&48 "Ahmad gudu yake akan titi kamar zai tashi sama, Abdul ne yayi mishi magana yace, haba Dude wannan wani irin gudu kakeyi? Baka tsoron muyi hatsari? Ko kuma mu bugu da bishiya? Shiru Ahmad yayi mishi, ganin haka yasa Abdul yaja bakinshi yayi shiru, sabida yasan halin abokinnashi" Bintu kuwa acikin zuciyarta haushin wanda yake tuka motar takeji, mutuminnan wani irin mugu ne? Yana gani muna cikin motar amma yake irin wannan gudun? Duk yanda akayi wannan baisan darajar mutum ba, mugu azzalimi, duk acikin zuciyarta take wannan maganar. Beebah kuwa duk gudun da akeyi batama saniba sabida hankalinta duk ta tattarashi akan Ahmad, gayen yamatuƙar tafiya da imaninta, Haka har sukayi parking awani waje me kyau, saman wajen an rubuta "Adamawa special photos" Ahmad yanayin parking ya buɗe motar yafita ko juya bayanshi baiyi ba, yana fita su Bintu ma suka fito, dukansu suka shiga cikin ɗakin da ake ɗaukan hoto, suna zuwa sukayiwa me hoton bayanin yanda akayi, yace musu ba matsala za'asan yanda za'ayi. Duk maganar dasukeyi Ahmad ya sunkuyar da kanshi baya kallon kowa, har suka shirya dukansu, Bintu da Beebah sunsa anko na riga da skirt atamfa suka ɗaura kansu, sunyi kyau bana wasa ba, Me hotone yafara ɗaukansu hoto, dukansu, idan An ɗauka ɗaya saisu janza kaya. An ɗauki Beebah da Ahmad tarike wuyanshi, sai kuma akace za'a ɗauki Bintu da Ahmad. Ahmad yana zaune akan kujera tunda aka fara ɗaukan hoton bai ɗaga kanshi yakallesu ba, saidai yakalli me ɗaukan hoton, Bintu ce zasu ɗau hoto da Ahmad sai me hoton yace saikin rike wuyanshi idan har kunaso kar mutane sugane, Bintu ce taɗan sunkuyo kaɗan tarike wuyan Ahmad, jikinsu ne yayi shocking atake! Bintu tasake shi da sauri tayi baya, shima Ahmad yaji wani shocking ajikinshi harya kusa faɗowa kasa. "Me hoton ne yace ku muke jirafa". Bintu ta iso wajen jiki amace tarike wuyan Ahmad aka ɗaukesu hoto, ana gama ɗauka suka tara kayansu aka tura musu hotunan awaya. A hanyansu ne nakomawa gida motarsu tasamu matsala, Ahmad ne yace duk su fito, Beebah uwar kauɗi itace tafara fitowa daga motar, sai Abdul yabi bayanta, sai Bintu ce karshe, Ahmad ne yace wata tabamu ɗankwalinta mana zamusa awani waje. Beebah ce tahaɗa face alamun koza'a kasheta bazata bada ba! Bintu ce tacire ɗan kwalin kanta ta mika mishi tace gashi. Ahmad Azuciyarshi yace ashe tanada hakuri bara kawai mu gaisa da ita, ɗago kanshi yayi dan su gaisa saiyaga ta sunkuyar da kanta tana gyara gyellen ta, sai kawai yaɗauke kai, ita kuma tana Gama gyaran gyalle tajuya zata kalleshi taga ya ɗauke, saita basar, Ahmad kuma tin ɗazu addu'a yake acikin zuciyarshi domin tin jiya yakejin tsinkewar zuciya. Bintu ce ta ɗago kanta tanason yiwa Beebah magana daidai lokacin Ahmad ma yaɗago kanshi. Suna haɗa ido, Bintu tafara jujjuya ido alamun akwai matsala, Ahmad ne yafara ja da baya yana nuna Bintu, ita kuma Bintu ta tsala ihu tace "ku taimakeni zai kashe ni" Abdul ne yariketa da karfi yana tambayanta meya faru? Ta juya da karfi tafara gudu akan titi tana ihun ataimaketa, Abdul da Beebah ma suka rufa mata baya suna binta da gudu, Ahmad kuma ya bushe awajen sai nuna waje ɗaya yake da yatsa! Gudu take Akan titi bata lura da yanda motoci suke wucewa. Abdul da Beebah sai binta suke suna kiran sunanta Bintu!!! Bintu!!! Bintuu!!! daidai wani dutse bintu tafaɗi kasa sabida ta gaji, tana faɗuwa kanta ya bugu da dutse atake kan yafara jini, Daidai lokacin Abdul da Beebah suka iso wajen, suna zuwa Abdul ya ɗauketa yatare Napep yace Asibitin specialist, suka shiga me Napep yakaisu. Suna zuwa aka karɓi Bintu akayi Emergency Room da ita. _Ahmad_ Shikuma Ahmad yakai minti talatin hanunshi asama yana nuna waje ɗaya, bakinshi kuma yana rawa kamar mejin sanyi, saida yaɗan fara dawowa natsuwarshi kafin ya buɗe mota yakama hanyan Kaduna, ko waiwayar Adamawa be karayi ba! "Abdul ne yaje gidansu Bintu yafaɗawa mommy abinda yake faruwa, aruɗe mommy tafito tashiga motar suka nufi Asibitin". _Bintu_ Bata dawo hankalinta ba har yanzu likitocine akanta, Beebah kuwa sai kuka take kamar ranta zai fita, Azuciyarta kuma tana Addu'an Allah yasa ba Aljanu bane suka shafi Bintu, Domin ita tana matsifar tsoron me Aljanu. _Ahmad_ Allah Allah yake yakarasa garin Kaduna, yama rasa me zai fara tinani a halin yanzu? Fateemahn shi yagani ko kuma idonshi ne yake mishi gizo? To Amma idan Fateemah ce ai zatayi mishi magana, to amma ita wannan tagudu, anya itace Fateemahn shi? Kodai kamane kawai? Komadai menene idan naɗauko Mommy da Fareedah zasu san komai, Yanata magana shi kaɗai kamar taɓaɓɓe, idan yatuna yanda tarike wuyanshi sai yayi murmushi.... ✍️🗒 *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* *Dedicated to my love* *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 49&50 "Mommy suna zuwa Asibiti Beebah ta taso tazo wajenta, mom ce ta tambayeta meya sami Bintu? Beebah tace wallahi mom nima ban sani ba, Amma inada tabbacin Aljanu ne suka shafeta! Mom tace ke Beebah banason iskanci, kifaɗamin meya sameta ko kodai wani Abun Abdul yayi mata? Beebah tace wallahi mommy ba abinda aka mata kawai tana ganin Abokin Abdul damukaje ɗaukan hoto dashi tafara ihu wai ataimaketa zai kasheta" Mommy tace ina yake Abokinnashi? Mom tun lokacin data fara ihu yatsaya awajen yana nunata ko magana beyi ba To mukuma munbita, mun barshi awajen, Zuciyar mommy ce tayi matsifar tsinkewa!!! Atake ta tsunkuya dan wani hajijiya takeji, Tacewa Beebah kiramin Abdul yakaini inda kukabar mutumin, Beebah ce tace tom mommy lafiya? Mommy tadaka mata tsawa! Kiramin Abdul nace, Beebah ce tabar wajen da sauri dan ganin yanayin mommy. _Ahmad_ Gudu yake akan hanya, burinshi kawai ya iso KD dan jiyake kamar ba mai amotar, dayaga motar bata mishi gudu sai kawai yaɗau waya yakira Habeeb, yace mishi dan Allah ka nemamin jirgi yanzunnan, Habeeb ne yace ok kasameni a Airport, Ahmad yajuya motarshi yakoma Adamawa zuwa Airport, Yana zuwa yatarar da Habeeb harya karɓa mishi pass, Yamika mishi hannu suka gaisa, Yace yau ba surutu sauri nake, Habeeb abun yabashi mamaki taya za'ayi Ahmad yayi sauri haka? Duk yanda akayi akwai matsala. Mangariba cif yashiga garin KD, Yana sauka a Airport yafita da sauri yatari Napep, Yawuce sai gidan Mommynshi, Yana zuwa me gadi yahanashi shiga, Yarokeshi, megadin yace bazan yadda na rasa aikina ba Ahmad! Hajiya tace duk ranan dakazo nabuɗe maka kofa abakin Aikina, Amma Alfarma ɗaya zanyi maka Shine kazauna anan yanzu Fareedah zatazo dan hajiya ta aiketa, Idan tadawo saika faɗa mata sakonka.. Be gama magana ba, saiga motar Fareedah ta kunno kai, Tana ganin Ahmad ta ɗauke kanta tana kokarin shiga gida, Ahmad ne yayi mata Alama da hannu, yahaɗa hannunshi waje ɗaya Alaman yana neman Alfarma, Hakika Fareedah taji tausayin Ahmad yau, ganin duk yanda yabi ya rame yayi baƙi kamar bashi ba! Saita buɗe mishi ɗayar kofar tayi mishi Alama dayazo, Ahmad ne yasauke ajiyar zuciya, Yatashi yaje yashiga motar, Yana shiga megadi yabuɗe mata get tawuce ciki, Acikin gida ta tarar da mommy tana zaune tayi tagumi kamar kullum. Tana fita amotar tabuɗewa Ahmad shima yafito. Mommy kamar daga sama taga Ahmad acikin gidanta kuma amotar Fareedah, Tashi tayi ta iso inda suke, Tana zuwa ta fesawa Fareedah mari har guda uku, kana tace "Fareedah bakida hankaline? Kokin manta me nace miki? Ko kin fini son Ahmad ɗinne? " Fareedah tayi shiru. Ahmad ne duk jikinshi yayi sanyi, Har yayi dana sanin zuwa, Yatsuguna kasa zai fara magana mommy tace idan kasake kace uffan Allah ya isa! Fita kabarmin gida, Ahmad ne yafara kuka yace "Mommy nayadda zan fita nabar miki gidanki, Amma ina neman wata Alfarma? " Mommy tace "Banason jin komai daga Bakinka Ahmad kaficemin agida" Wannan karon Fareedah ma tasa baki a rokon mommy, Fareedah kuka Ahmad kuka, Kuma dukansu a tsunkuye suke, Mommy ce taga sun mugun bata tausayi, sai kawai itama tafashe da kuka ta tsunkuya tarike hanunsu ta ɗagasu ta rungume, Ahmad yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, Rabonshi dayaji ɗumin jikin mommy tin lokacin da Daddy yarasu, Sun kai minti talatin ahaka kafin mommy tace kafaɗamin abinda yake daminka Ahmad? Ahmad ne yace "Mommy naga Bintu a Adamawa" Mommy ce tayi saurin rufe bakinshi da hannunta, Tace shiiii banason karya, karkayimin karya don kanason in soka, Ahmad yace mommy na rantse da Allah Bintu nagani, harda goshin sallahn ta Mommy tayi shiru, taya za'ace wanda yamutu ya dawo? Kodai Ahmad yasamu taɓin Hankali ne sanadin shaye shaye? Can tace idan har da gaske kake gobe zamuje Adamawan in tabbatar, Idan naje kuma naga karya kakemin, tofa bani bakai Ahmad, Yace mommy nayadda idan ba ita bace Karki kara yimin magana Kuma nima bazan sake zuwa inda kike ba! Fareedah tazama shaida. Mommy tayadda da sharuɗanshi sukasa niyyan gobe da safe zasu tafi Adamawa. ****** Mommy sunje wajen dasu Beebah sukabar Ahmad Amma basu ganshi ba! Mommy taruɗe tafita a hayyacinta, Da kyar suka kama hanya suka tafi Asibiti, Suna zuwa daidai Lokacin Bintu ta farfaɗo. Amma wani ikon Allah sai kallonsu take kamar bata sansu ba! Idan sunyi mata magana saita fara kuka, Likita ne yace sun duba sunga ba wani matsala zasu iya tafiya gida. Suna zuwa gida mommy takira Habeeb ɗakinta, Tacewa Habeeb "gobe zamubar garinnan" Kakiramin Abdul yazo muyi magana. Habeeb ya ruɗe yace, Mommy meyasa zamubar garinnan? bayan nanne mahaifarmu? Mommy tace banason dogon surutu Habeeb kayi Abinda na umarceka. Habeeb yayi shiru, can yace kuma Mommy kikace gobe? Mommy tace da Asuba ma kuwa... _✅ote, comment and share pls_ ✍️🗒️ *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 51&52 "Washe gari" Mommy ce tacewa su Beebah sushiga mota zasu koma Gombe, Beebah tace "yanzu mommy kina ganin idan muka bar garinnan ba damuwa? Kituna fa mun saba da mutane anan, Bakya tunanin muje can mushiga wata rayuwa? " Mommy ce ta dakatar da ita da hannu tace "Beebah bakisan damuwan dazamu shiga anan idan har muka Zauna yafi nacan bakoh? " Beebah ce tace "Mommy wace irin damuwa zamu shiga? Kodan Bintu bata buɗi baki tayi magana bane haryanzu? Mommy kika sani ko iskokai ne suka shafeta?" Mommy ce tacewa Beebah wannan maganar taki ɓatamin lokaci kawai kike, Kishiga mota kawai mutafi. Beebah ce tashiga motar badan taso ba! Bwyan sun shiga mota gaba ɗayansu, Driver yaɗauki hanyar barin garin Adamawa, Beebah kuka takeyi sabida ko sallama basuyi da kawayenta ba, Mommy ce take bata hakuri tana lallashinta har tayi shiru. _Ahmad_ Suna idar da sallahn Asuba suka kama hanyan Adamawa, Amma mommy tace subi flight na safe, Suna zuwa Airport, daidai lokacin da aka fara sanarwa ashirya jirgi zai tashi, Daidai lokacin Ahmad ya tuna cewar ya manta wayarshi agida. Kuma bai kashe ba! Yacewa Mommy "mom inason in koma gida na manta wayana" Mommy tace haba Ahmad baka ganin jirgi zai tashi yanzu ne? Yace mommy matsalar ay wayar ba'a kashe ba! Za'ayi ta kirana aji switch off, Mommy tace kodai karya kayimin ne Ahmad? Yace haba mommy taya za'ayi nayi miki karya, Mutafi ma kawai, Haka suka shiga jirgi sukayi tafiyarsu. _Adamawa_ Sauri suke suga sun bar gari yola, daidai zasu fita a fire away from yola, Habeeb yacewa mommy, "Mom munyi babban mantuwa" Mommy tace me muka manta? Yace mommy mun manta da Abdul, baizo yabamu takaddan sakin Bintu ba! Mommy kar mubar garinnan da Aure akanta, Mommy tace hakane fa kuma, yanzu kiramin shi awaya ka tambayeshi ina yake, Habeeb yaciro waya yakira Abdul, Yacewa Abdul ina kake? Abdul yace ina Airport, Habeeb yace me kakeyi a Airport? Ina jiransu Ahmad ne yau zasuzo, ok gashima sun karaso. Ok idan kaɗaukesu kasamemu a fire away mana akwai wata muhimmiyar magana dazamuyi, Abdul yace to bari sai nazo. Ba'a daɗe dayin wayar Abdul da Habeeb ba, saiga su Ahmad sun karaso, Abdul ne yaɗaukesu amotershi, yace musu suyi hakuri zasu biya ta Fire away kafin su dawo Su Ahmad sukace ba komai, Ahmad ne yacewa Abdul idan mun dawo gidansu Bintu zaka kaimu, Abdul yayi mamaki sosai, ganin Ahmad dasu mom nashi sunzo wai yakaisu gidansu Bintu, Gashi abunda yafaru jiya. Sai kawai ya kawar da zancen. _Bintu_ Ita tarasa waɗannan wasu mutane ne? Tin jiya a asibiti sukeyi mata magana, Ita bata sansu ba! Hasali ma tanason ta tambayesu meya kawota nan? Wannan wani gari ne? Amma takasa Tambaya, Dataga sun shiga mota zasu tafi wani gari, azuciyarta tace Alhmdllh zasu kaini garina, may be ma satoni sukayi, Da Wannan tinani taji karan tsaiwar mota. Tana juya baya taga wani mutum yafito daga wajen zaman driver, Daga baya taga an buɗewa wata Mezata gani? Sai taga mommy tafito a motar, daga baya saiga Fareedah. Bubbuga motar datake ciki tafara Alamun tanason tafita. _Not Edited_ _✅ote & comment pls_ ✍️🗒️ *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *WATTPAD* _Jiddah S Mapi_ Page 53&54 "Habeeb ne yaga alamunta, dasauri yabuɗe mata marfin motar tafita. Sai gani sukai Bintu ta tashi dagudu taje tarungume wata kyakkyawar mata da 'yarta, Bintu kuma acikin zuciyarta daɗi takeji tunda gasu mommy da Fareedah, tana ganin mommy tana hawaye tafara tambayanta mommy meya faru kike kuka? Ko Daddy ne ba lafiya? Alamun mamaki ne yabayyana afuskar su Mommy da Fareedah, Har Ahmad ba'a barshi abaya ba! Wajen mamakin tambayoyin da Bintu take. Basu tashi jin mamaki ba, saida Bintu tace "Mommy waɗancan mutanen satoni sukayi ko? Allah yataimakeni dannaji yana waya da wani wai a filin jirgi, dabaku zo dawuri ba, dasunana gawa!!! " Wannan maganar ya girgiza mommy [6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my Eeshart much love habibty❤️_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *WATTPAD* Jiddah S Mapi Page 55&56 "Bintu kuka tafara kamar ba gobe, ita gaskiya batason Ahmad bata kaunarshi, idan ta tuna zagin dayai tamata lokacin datake gidansu sai taji ta tsaneshi, Hasalima tsoron shi takeji, wanda yayi niyan kasheka Amma kayadda kaci gaba da zama dashi? Wata zuciyar tace mata karkiyi haka, ta sanadin ki babansu yarasu idan kikace bakya sonshi ai kinyi butulci. Kiduba irin son da kanwarshi take miki" Mommy tace ke muke sauraro, Duk ɗakin sunyi shiru bakajin komai sai kukan Bintu, Ta ɓangaren Ahmad kuma ji yake kamar yaje ya rungumeta! Ya tsani yaga tana hawaye zafi yakeji acikin ranshi. Bintu tace "bazan iyaba!!!" wlh Mommy bazan iyaba!!!! Ahmad ne yafara ɗaga hanunshi sama alaman zaiyi roko, Mommy ta dakatar dashi. Mommynsu Habeeb ne tace "menene bazaki iyaba Bintu?" Bintu tace "bazan iya musu daku ba!" Alhamdulillah inji duk mutanen ɗakin, Ahmad ne yace mommy inada magana, Mommy tace muna jinka. Yace mommy inason kuzama shaida Kamfanina na takalma da jakunkuna nabarwa Fateemah halak malak yazama nata! Sannan akwai gidajena dake G.R.A a Kd guda biyu wanda nayi niyan zamu zauna da Fateemah aciki, sannan idan Fareedah tayi Aure zasu zauna da mijinta a ɗayan Yanzu ma haka Za'ayi, shikuma Abdul zan siya mishi gida agefen namu duk muzauna tare! Mommy tayi murna sosai sannan Habeeb da Abdul sunyi godiya sosai Su Ahmad kuma sunce gobe zasu koma, yayinda akasa ranan Aurensu Abdul da Beebah, Habeeb da Fareedah, sannan Ahmad da Bintu sati mai zuwa idan Allah yakaimu ****** yau akeyin ta! yaune ranan ɗaurin Auran su Abdul da Beebah, Habeeb da Fareedah! Amare sunyi kyau sabida sunyi dilki Idan kagansu kamar daga kasashen larabawa! Musamman Bintu data zama kamar 'yar india. Yau za'ayi lunching Amare dukka uku sunsa Dogayen riguna pink color me yalki da bakin roses suka ɗaura kansu, Me yi musu makeup na musamman aka ɗauko inda ta fesa musu kwalliya kamar ba gobe! Idan kaga waɗannnan Amaren zakace babu Amaren dasuka kaisu kyau. "Babban hall aka kama musu, inda akayi decoration na wajen da kayan ƙyaleƙyale na zamani, Kujeru uku me zaman mutum bibbiyu akayiwa kwalliya irinna gidan sarauta! _Ahmad, Habeeb da Abdul_ Suma ba'a barsu abaya ba wajen kyau, Sunsa Fararen shadda me ɗauke da zibin baƙi ajiki, Takalmi baƙi sukasa, sai agogo ma baƙi da bakaken hula. Subhanallah!!! Idan kaje kaga yanda aka tsara wajen da ƙawayen Amare da Abokanan ango da Amaren da angwayen, Sai ka raina kanka! Abinci kuma kamar ba dafawa akai ba! Drinks kuma babu kalan wanda babu, Amare sun zauna akan kujerun da aka kayata dominsu, Da angwayensu. Kuyi imagine yanda Amaren da angwayennan zasu bada light Awajen. An jera kawaye kamar cinnaka sunyi layi dukkansu da anko, dogayen rigane marun color sukayi anko sun ɗaura kai da peach na roses. Sumafa ba'a barsu abaya ba! Wajen kyau. Beebah ce taga ba'a kira Amare ba har yanzu gashi kawaye sai caskalewa suke afili, Sai kawai tamike Abdul yasan hali,, yasan mezatayi Yarike hanunta ta janye hanunta tafara tafiya tan rawa. Daidai lokacin aka sake wakan "Ahmad shanawa" Me taken agirgiza baya baya a karkaɗa ayi kamas Beebah ce tafara girgiza jikinta tana rawa kamar ba Amarya ba! Kowa ya juya yana kallonta rawa take tana juya jiki kamar hawainiya. Da Abdul yaga yanda take girgiza jikinta sai ya tashi shima yabi bayanta, Suka fara rawa atare dama Abdul ma ba daganan ba! MC. Yakira Amaren dukkansu da angwayen suka shiga fili. Ahmad yarike hannun Bintu. Sune agaba! Suna shiga tsakiya Bintu ta wapce hanunta tafita! Ahmad yatsaya yana kallon ikon Allah. Bintu kuwa acikin Zuciyarta idan ta tuna abinda Ahmad yayi mata sai taji ta tsaneshi, Batason Ahmad!!! Ta tsaneshi Amma bazata iya musu da mutanen dasuka taimaketa ba! Da yanzu tana gidan marayu, batasan ya rayuwarta zai kasance ba! Tana cikin tinani taga Ahmad ya iso wajenta, A hankali ya tsunkuya ya rike hannayenta duka biyu. Ya sassauta murya Yanda ba wanda zaiji daga ita sai shi Yace "Wifey meyasa kikemin haka? Kodai baki yafe min bane? Kisani fa Allah ma muna mishi laifi ya yafe bale mutum ɗan Adam, Dan Allah na roke ki, ki taimakawa rayuwata Kece farin cikina Rabona danaji farin ciki acikin rayuwata tin ranan da wancan abun yafaru, Daga ranan Na daina ganin haske a rayuwata, ki tausayamin my Teemah. Inasonki!!! Inasonki!!! Inasonki!!! I love you with all my heart, Zan iya rasa rayuwata idan kika gujeni. My teema inason ki manta komai mu gina sabon rayuwa, Wallahi idan kika gujeni bazan taɓa gane hankalina ba! Yafaɗa cikin hawaye. Bintu dataga yana mata kuka gashi mutane sunata kallonsu, saita fara kokarin tayar dashi. Shi kuma yazauna akasa yaki tashi sai hawaye dayake kamar Amarya, Ganin haka yasa Bintu tace "na yafe maka duk abinda kamin, kuma bazan taɓa manta halaccin da iyayenka suka min ba! Ahmad na yafe maka duniya da lahira" Ahmad ne yafara dariya kuma yana hawayen farin ciki. MC. Ne yafara magana yace "ana neman duk Amaren da ango a fili, suzo su nuna mana farin cikin Dasuke ciki ayau. Ahmad ne yarike hanun Bintu, Habeeb yarike Hanun Fareedah, Abdul kuma yarike hanun Beebah, Tafiya suke suna ɗan rawa, yayinda mutane suka sa tafi suna ihu. Wakar biki yayi biki akasa musu, inda suka fara rawa Amma banda Bintu data tsaya tana dariya. Ahmad dayaga zata badashi afili, sai ya rike kwankwason ta yafara rawa, Bintu kamar kasa ya tsage tashige tsabar kunya. Tafara kokarin cire hanunshi ajikinta Amma ina yaki saima kara janyota jikinshi dayake. Dataga haka saita fara kuka tana tureshi. Ahmad ne ya rungumeta afilin yasa bakinshi daidai kunnenta yace "Haba wifey mutane fa suna kallonmu ki daina kukannan kinji wifey" Tafi sukaji anayi musu, Ahmad yasaketa! Taga ba kowa afili daga ita sai shi su Beebah sun tafi! Dj ne yasake musu wakan Romantic, Bintu kamar gunki sai juye juye tafara, Ahmad ne yarike kwankwasonta yana rawa da ita. Dj yace atafa musu Akasa tafi Awajen. Dahaka har aka gama lunching kowa yashiga motan mijinshi aka wuce dasu gidansu Beebah. Suna zuwa Bintu ko cire takalmi batayi ba! Ta kwanta akan gado tana nishin gajiya, Beebah ce tace "dama ya lafiyar kura bale takama zawo" Bintu tace yanzu nice kuran Beebah? Nafa lura kin fara rainani a 'yan kwanakinnan, dan kinga zakiyi Aure ko? To bara nafaɗa miki har yanzu ke yarinyace awajena ehen. Fareedah tace "wayaga Babba kema ai ba Auran kikayi ba! Tare dai zamusan komai" Bintu tace wannan magana taki tafi karfina! Kinga namayi bacci, Dukka suka kwashe da dariya. _Ahmad_ Jinshi yake kamar wani sabon halitta, suna zuwa gida yakwanta akan gado yafara tunanin wai yau Fateemarshi ce tazama mallakinshi? Yanzu gobe war haka suna tare da ita amatsayin mata da miji, Can't wait to see yafaɗa da murya. Habeeb dake gefe yace "Wai me kake faɗa ne Ahmad?" Wallahi ina ganin kamar karya ne wai gobe nida my Teemah a ɗaki ɗaya kan gado ɗaya? Can't wait to see wallahi cewar Ahmad, Habeeb ne yaji zuciyarshi tabuga!!! Yanzu gobe Bintu a ɗakin Ahmad zata kwana? Kuma kan gado ɗaya? Dasauri yafara faɗin Astaghfurullah Ashe yanzu ita matar wani ne. Ahmad ne yaga yanayin shi yace "lafiya Habeeb?" Habeeb yace lafiya lau ba komai Kai dai kafiye zumuɗi, Ahmad yace ba dole nayi zumuɗi ba! Rabona fa da mace tun muna tare da Bash. Habeeb ne yayi dariya yatashi yashiga toilet da niyan Alwala. Beebah ce tacewa su Bintu ku baza kuyi sallah bane? Bintu tace nifa bana sallah tin jiya! Fareedah ma tace ita sai jibi zata fara. Ita kuma Beebah yau period nata yazo! (Tofa kunga Amare da period ranan biki) *Washe gari* Mommyn Habeeb da Mommynsu Ahmad ne suka tarasu babvan falo, Sukayi musu nasiha me tsima zuciya. Daga karshe Mommyn Beebah takira dukka Amaren a ɗakinta, tayi musu nasiha irin na zaman Aure Sannan ta basu wasu sirrikan yanda zasubi da mazajensu. Ta ɗauko wasu turare acikin jakanta, tace "ga wannan ku tabbatar sai idan zaku kwanta kafin ku shafa kada ku kuskura kushafa idan zaku fita anguwa" Turaren matan Aure ne! Sukace "to" Suna fita bayan kofa Beebah ta makale ta buɗe turaren tashafa kafin ta rufe tafita. Taje tasamu kowa yahaɗa kayanshi, musu suke, wai mommynsu Ahmad tace a motar haya zata tafi bazata bi motar mijin kowa ba! Sunyi sunyi tabisu amotar Ahmad taki, Haka suka hakura, kowacce tashiga motar mijinta Suka ɗau hanyar Kaduna garin gomna. Bintu ce take kukan rabuwa da mommy acikin motar, Ahmad juyawa yake yana kallon yanda tarufe ido tana zuba kuka kamar karamar yarinya. A hankali yarike hanunta me laushi da tsantsi yafara wasa dashi, Ta sauke ajiyar zuciya jin hanunshi cikin nata yana murzawa! "Beebah kuwa uwar kauɗi, tana shiga Abdul yazuba mata ido Yana kallonta, jin kamshin turaren data shafa yasashi lumshe ido. Tazauna agefenshi kamar mutuniyar kirki, Yace matso! Tayi shiru tana kallonshi, gashi Idonshi arufe amna yana mata magana. Yasake cewa matso mana A hankali ta matso wajenshi Yarike hanunta yace "wani irin turare kika shafa?" Tace "turare nane" Yace ban yadda ba! Kifaɗamin gaskiya, Tace gaskiya nafaɗa maka, Yace "ok". "Fareedah kuma tana shiga motar Ta sunkutar da kanta tana wasa da yatsun hannunta, Habeeb yace "kisaki jikinki ni mijinki ne" ✍️🗒️ *Jidda S Mapi* [6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *WATTPAD* Jiddah S Mapi *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Godiya dubu ga masoyana masu bibiyar littafin Agidanmu Take!!! Banso labarin tazo muku a short story ba! Amma ya na iya Haka Allah yatsara, nagode da nuna soyayyarku gareni, banyi tsammanin first Novel ɗina zan samu masoya har haka ba! Sai gashi Allah yasa nasamu, alhmdllh ina godiya gareshi sannan ina godiya gareku* *Special thanks to mrs sardauna bazan manta dake ba!* *godiya ga Eeshart tnx for your comment i really appreciate* *Bazan manta dakai ba! Aliyu Ibrahim* *Much love to my Sister walidation S Mapi* *Ina miƙa gaisuwata da kuma godiyata ga ɗaukakin jama'ar kungiyar KAINUWA dashen Allah* *kuna raina kanne na! Walidation S Mapi da Hafsat Ibrahim Khalil* *Godiya ga ɗaukakin jama'ar group na Agidanmu Take!!! Bazan manta da kuba!* Page 57&58 🔚🔚🔚🔚 "Fareedah taɗan saki jiki kaɗan da Habeeb, ahanyansu nazuwa kaduna ansha love amota musamman Beebah data rikita ɗan mutane da turare, Bayan sun iso ne kowa yafito amotar a gajiye kamar an dakesu. Ahmad ne yanunawa Habeeb wasu gidaje tsararru kerarru haɗaɗɗu, guda uku yace "Habeeb kazaɓi gida ɗaya acikin waɗannnan" Habeeb yace "kowannema nagode basai nazaɓa ba! Allah yasaka da alkhairi sannan yabar zumunci" Ahmad yace "Ameen" To tinda gidan uku be kuma ajere komai naciki kala ɗaya ne nizan zauna a tsakiya tinda nine karami Dukka suka kwashe da dariya Habeeb ne yarike hanun matarshi yace sai kun karaso. Ahmad yace daɗin Abin dai baza'aci fuskarmu ba! Kowama yanada tashi. Duka suka wuce gidansu, Bayan sun idar da sallan mangariba da isha ne Ahmad yaɗauki wayarshi yakira su Habeeb da Abdul yace idan ba matsala yanason zasuyi magana agidanshi dukkansu da matansu, Sukace ba komai. Jim kaɗan saigasu sunzo suka zauna a babban falon da yake mallakin Bintu ne da Ahmad, Bayan sun zauna Habeeb yabuɗe musu da Addu'a. Ahmad ne yayi gyaran murya yace "da farko ina godiya ga Allah me kowa me komai wanda shine yayi sanadin taruwanmu anan, Sannan ina mika godiya ga Abokaina Kuma Aminaina Wato Habeeb da Abdul, hakika kunmin inuwa wanda ba kowa bane zai iya yiwa abokinshi Awannan zamanin" Ahmad yatsunkuyar da kanshi yafara hawaye yace "Habeeb kasan irin wahalar danayi a neman Fateemah kuma kaima ka tayani nemanta alokacin danake cikin taahin hankali, Sai wani ikpn Allah ashe Fateema A gidanku take!!! Bamu sani ba! Matar da Allah yarubuta zata zama matarka ashe A GIDANMU TAKE!!! nasan kanason Fateema Habeeb Amma Allah bai rubuta kai zaka Aureta ba! Matar da Allah ya rubuta zaka Aureta A GIDANMU TAKE!!! Habeeb ne yace "kayi hakuri Ahmad kadaina kuka komai yawuce kamar yanda matar dakake nema A GIDANMU TAKE!!! haka zalika matar danakeso yanzu A gidanku take!!! Ikon Allah kenan". Abdul ne yace "godiya yakamata muyiwa Allah daya nuna mana wannan rana ba kuka ba!" Ahmad ne yace "ku yafeni dukkanku nasan nashiga hakkin ku" Habeeb yace kadaina irin wannan maganar Ahmad komai yawuce. Muyi addu'a dai kawai Allah yajikan Daddy yasa mutuwarshi shiyafi Alkhairi mukuma idan namu yazo Allah yasa mucika da imani "Ameen" cewar duk mutanen falon. Kasancewar Amaren duk suna off hakan yasa mazajen duk suka hakura dasu, Banda Ahmad da saida ya yayi wasa da Fateemah Bintu. Bayan sati ɗaya, Ahmad ne naji yana yiwa matarshi sannu duk ya rikice, Dana leka ɗakin sai naga Fateemah Bintu kwance akan gado ba alamar motsi gashin kanta abarbaje, Naga Ahmad yashiga toilet nabishi naga ruwan zafi yahaɗa Bahon wanka, Naga yadawo Dali yaɗau 'yar mutane yayi hanyan toilet da ita, nikuma kasancewar ban kai age ɗin dazan san me sukayi ba! Yasa na ɗauki biro na da takadda na naɗaukan rohoto nayi waje sai gidan Habeeb. Ina zuwa naga Fareedah kwance akan cinyarshi tana zuba shagwaɓa kamar wata baby shikuma yazage sai biye mata yake, nace to abun nakun na yarane, nayi gaba sai gidan Abdul da Beebah uwar kauɗi. Ina zuwa naji abunda yafi karfina! Beebah ce take cewa Abdul "Baby anya ba ciki ne dani ba? Kaduba kaga yanda nake Amai fa" Abdul dayake rungume da ita yace "Allah yasa cikine, da bawanda zai kaini Farin ciki" Nayi gaba nace bada niba. *********** _Bayan wasu shekaru_ Gidan Ahmad ne naga wasu kyawawan yara suna wasa su biyu mace ce dakuma namiji farare kamar Auduga. Ahmad ne kwance atsakiyarsu yana cakulinsu sunata dariya, Sai naga wata kyakkyawar mata tashigo tace "Hubbie wai ina su mommyy karama sukaje ne? Tin ɗazufa suka fita wai wasa" Daga baya naji wata mace tace "Ai mommy karama A GIDANMU TAKE!!! Tin dazu suna wasa dasu Daddy karami" Juyawar dazanyi sai naga Polina da hijabi. Ashe wai Bash ya shiryu dayaga Ahmad ya gyara halinshi, Polina ma ta musulunta tayi Istibra'i sannan Bash wanda yanzu ake kira da Bashir ya Aureta! Suna zaman lafiya harta haifa mishi yara 'yan biyu Haneef da Haneefah. Suma suna zaune ne agefen gidansu Ahmad wanda shi Ahmad dakanshi ne yasaya musu. Ahmad ne yace to Alhamdulillah yanzu dai kinji inda suke, Tinda itama ga 'yarta tin ɗazu A GIDANMU TAKE!!! Alhamdulillah!!! Alhamdulillah!!! Alhamdulillah!!! Nan nakawo karshen littafina me suna A gidanmu take!!! Kuskuren danayi ko tuntuɓen harshe Allah yagafarta mani. Saimun haɗu a littafina na gaba me taken MAKAUNIYA CE!!! *special thanks to WALIDATION S MAPI sisi forever* ✍️🗒️ *Jiddah S Mapi* Taku ce 👍🏻 Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels