Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels ๏ปฟ[11:20pm, 19/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘บ *NWA* NA *Princess Amrah* Da *Rabiatu sk msh* *~hannu biyu writers~* Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mad`aukakin sarki, tsira da aminci su k`ara tabbata ga shugaban mu annabi Muhammad (SAW) tare da alayen sa. Kamar yanda muka fara rubata wannan littafin, muna fatan mu k`arisa shi cikin aminci da yardar Allah mad`aukakin sarki, muna fatan abun da muke son isarwa ya isa ga d`aukacin al'ummah musulmai har ma da wanda ba musulmai ba. Wannan labarin k`irkirarre ne k`agagge ne munyi shi ne akan illar zuwa party, da duk wurin da addinin musulunci yayi hani dashi, ba munyi shi don cin zarafin wani ko wata bane, munyi ne domin nuna illar abun. Abstract (shimfid`a). Labari ne mai ku`nshe da wasu bayin Allah da suka mayar da zuwa party tamkar ruwan shan su, sukan fita a kowane lokaci ba tare da sanin iyayen su ba, sai dai kuma daga baya zasu had`u da rikicin rayuwa suyi dana sani a lokacin da bashi da amfani. Allah ya shiryar damu bisa hanya madaidaiciya, Allah kuma ya bamu ikon d`aukar abunda zamu karanta a ciki. But idan kin San kina da tsoro kar ki karanta shi. (Lol..๐Ÿ˜Š) Page 1โƒฃ K`arfe 8:00AM. Kwance take kan lallausan gadon ta na royal bed, wayar ta na jikin chaji amma still tana latsar ta, zumbur ta mik`e cike da murna tana fad`in "yesss! Am glad to hear that woooo" komawa tayi ta kwanta taci gaba da charting d`in ta. Wani kyakkyawan yaro ne ya shigo d`akin cikin shagwab`a yace "yaya Afnan momy is calling youh", Cikin haushi tace "am coming", "Buh yaya Afnan the momy said...", katse yaron tayi "Affan tell her that am coming now", tafiya yayi yana waigen ko ta taho har yabar d`akin bata tafi ba, aikin charting kawai take. Jin shiru Afnan batazo ba yasa momy sake tura Affan, a bakin k`ofa suka had`u tace "sai ka tafi ai uban gulma gani a hanya". Bakin shi tunzure ya tafi tana biye dashi a baya. "Afnan wai bazakije islamiya bane tun d`azu Affan ya shirya yana jiran ki amma kin k`i fitowa?", "momy banda lafiya fa" Afnan ta fad`a cikin shagwab`a. "Me ya same ki?" "Momy mp ne fa", "Eyyah sorie, kije ki kwanta ki huta, hope kin sha magani" "Yeah momy nasha" "Ok Allah baki lafiya, Affan kaje kacewa driver ya kai ka kawai, kace wa malamin su Afnan wai bazata samu zuwa ba may be da yamma idan ta samu sauk`i taxo". Kitchen ya nufa ya d`auki launch box nashi ya nufi mota. Dakin ta ta koma taci gaba da charting d`in ta. A fili tace "kawai abi a damu mutun da wata islamiya, da yamman ma barin je ba birthday party'n Kerry zanje". "Arewa Stars kun jini shiru wlh momy ne ta kira ni wai sai na tafi islamiya". D`aya daga cikin members na group d`in Arewa Stars tace "hhhh tou ya kika ce da ita?" Afnan ta mayar mata da "nace mata mp pain ke damu na". Wani namiji ya turo da "lol...Afnan bakya ji fa, yanzu dai ku fidda mana colour`n da zamu saka anjima", Sally tace "ai an riga da an fitar, ash, pink and black ne zaa saka, har na kira wanda zai mana decoration na sanar dashi colour d`in", Haka dai sukaci gaba da hirarrakin su cike da nishad`i da munanan k`udurin abubuwan da zasu aikata a wurin birthday party`n Kerry. A rikice ta fito daga d`akin ta dan duk a kayan ta bata da colour d`in da zasu saka, "Afnan lafiya?" Momy ta fad`a tana kallon ta. "Lafiya lau momy, maganar practical materials d`in mu ne, malamin yace daga ranar monday za`a rufe sayar wa", "Tou Afnan yau fa Saturday, kina tunanin idan kinje yau zaki samu ne? Kuma ma ai naga duka fa jiya kikace ya fad`a maku ku siya", "Momy tun fa last week ya fad`a nice dai ban sani ba sai jiya". "Ok akwai kud`i hannun ki ko sai na baki?", "Momy sai kin k`aro min dan ban san ko nawa zan kashe ba kar suyi min short", "Ok ki bud`e side drawer na ki d`auki yanda zai ishe ki". Cikin murna ta nufi d`akin, kud`i sosai ta d`auka sannan ta fito. "Zaki iya driving ko sai Abu ya dawo ya kaiki?", "Zan iya momy" ta fad`a tare da d`aukan key ta fita waje, a daidai parking space d`in babban gidan su taje, wata benz cement colour ta bud`e ta shiga. Bata zarce ko ina ba sai gidan su Feenah. Bayan ta gaishe da maman Feenah suka shiga d`an k`aramin d`akin ta. "Ina fatan kina sane da birthday party`n kerry yau ne, kuma nasan baki da colour`n kayan da za`a saka, shine nazo d`aukan ki muje na siya miki", "Eyyah Afnan nikam yau barin je wannan party`n ba, wanda naje a baya ma ina rok`on Allah ya yafe min dan zunubi ne babba muke kwasar wa kan mu, kuma ga k`arya da muke yiwa iyayen mu kawai dan muje wurin sab`on Allah, gaskiya ki tafi kawai bana so". Cikin takaici Afnan ta mik`e tsaye "haka kika fad`a ko? Aikuwa yanzun nan zanje na sanar da umma`n ki abubuwan da kikayi a baya, kuma wallahi harda k`ari zan miki nasan dole zata yarda", Marairaicewa Feenah tayi dan tasan halin umman ta, k`aramin aikin tane ma ta hana ta zuwa har skul d`in ta da ko ina ma, sosai ummanta ke tsaron ta. Ganin Feenah tayi zurfi a tunani yasa Afnan ta fara cewa "sai kisan abunda zaki fad`awa umman ki dan ki kare kanki". Cikin takaici Feenah tace "kiyi hak`uri Afnan kar ki fad`a mata, na yarda zanje". Murmushin mugunta Afnan tayi tace "oya lets go". Hijabin ta har k`asa ta sako, a d`an madaidaicin parlor`n su suka tayar da umma`n ta, "ummah zan raka Afnan gidan su Maryam khalil amma bazamu dad`e ba". "Ok a dawo lafiya, ki gaishe min da hajiya Zainab, kiyi saurin dawowa ki tafi tahfiz k`arfe sha biyu". "Insha Allahu momy barin dad`e ba". Daga nan kuma suka kama hanyar AA BOUTIQUE don sayen k`ananan kayan da zasu saka. ยฉAmrah and Rerbee'art novels Admins ONLINE HAUSA READERS๐Ÿ“š [11:29pm, 19/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page2โƒฃ Nan suka hau dudduba kalar kayan da zasu saka, Afnan ce taci karo da wata had`ad`d`iyar top gown hot pink sai torches d`in black kad`an kad`an, baki d`aya k`irjin rigar a bud`e yake da wasu hudojin da aka k`awata su da zanen manyan flowers, bayan rigar yafi gaban ta tsawo da kad`an, hannun ta ma d`aya dogo d`aya gajere ne, gata da shape sosai irin wadda take fidda zahirin coca cola shape na mace, (niko Amrah nace wannan kyan ta masu aure su same ta, ai ranar babu oga ba zuwa office..lol). Bayan ta tabbatar da rigar ta burge ta ne suka hau dubama Feenat nata, "nidai Afnan pls bana son mai tallan jikin nan, asamar min mai rufe tsiraici", Cikin fushi Afnan tace "wallahi duk wadda aka samu ita zaki d`auka kuma dole ki saka ta", Shiru Feenat tayi taci gaba da bin bayan Afnan suna kewaye boutique d`in, da k`yar suka samu wata gown ash da torches d`in pink, gown ce ta mutunci mai A shape, zata iya sauka har k`asa, tana da turtle neck da dogon hannu. Sosai Feenat taji dad`in wannan rigar, dan tasan zata iya sakata ba tare da taji komai ba. Side d`in jewelries suka koma, nan naga k`aryar fashion sark`a da `yan kunne da abun hannu, komai na AA BOUTIQUE kyau gare shi, nan Afnan ta zab`i wata siririyar chain mai kyau, Feenat ma irin shi ta zab`a, kud`in suka biya sannan suka koma mota dan nufar gida. Cike da damuwa Feenat ta kalli Afnan tace "yanzu Afnan wace k`arya zan ma Ummah anjima idan zan fito?" "Oho miki, sai kisan abunda zaki fad`a mata, nidai k`arfe biyar na yamma zanzo d`aukar ki, ki tabbatar kin shirya by then", Tun daga nan kuma sukayi shiru su duka har akazo k`ofar gidan su Feenat. Afnan da kanta ta fitar ma Feenat da kayan ta daga leda, cikin in ina Feenat tace "Afnan ki tafi da kayan nan idan mun tafi can zan saka, dan yanzu Ummah zata iya cewa in bata ta gani kuma nasan halin ta zata iya fahimtar wani abu", Bata ce mata komai ba sai jinjina kanta da tayi, daga nan taja motar ta sai gida. *K`arfe 1:00pm* *~Gidan su Ruky.~* "Momy ta samu fa, yau ma akwai wani casun", Wadda ta kira da momy tayi mirmushi tace "kedai Ruky bakya gajiya da casu, kullun baki nan baki can, duk inda ake wani biki ko party kina can ko? Yau kuma wane casu ne akeyi?" "Momy birthday party`n Kerry ne fa za`ayi kuma mune best friends nata, idan bamuje ba waye zaije?" Momy tace "ehh kuma fa gaskiyan ki, to amma ki k`ure kwalliya dan nasan yau akwai wankan gayu, so nake auta ta tafi kowa yin kyau a wurin, kiyi chajin iphone d`in ki sosai yanda zaki d`auko pictures da yawa", Can naji wata murya zazzak`a daga bakin k`ofa tana fad`in "haba momy, wai yaushe zaku tuba ga Allah ne ki daina d`ora Ruk`ayya akan wannan munanan halayen? Ku baku ma tsoron mutuwar ku? Koda yaushe fa mutuwa zata iya riskar ku dan ita bata alerting mutun kafin tazo", Cikin takaici momy tace "ke Rumaysa wai ina ruwan ki ne? Ni tunda na gane ke ba wayayyiya bace kinga ina saka ki a irin wannan harkokin ne? tou wallahi kul dinki, kar ki kuma jefo mana wannan shegen bakin naki idan muna maganar mu". Rumaysah tayi shiru daga nan bata kuma fad`in komai ba, sai dai kuma har a ranta tana tir da Allawadan halin mahaifiyar ta da k`anwar ta Rukayya, mahaifin su yana kabari amma su suna nan basu ta yi mashi addu`ah sai munanan d`abiu, da wannan tunanin ta shiga d`akin ta cike da tsanar halayyar su. Da tafiyar ta kuwa suka hau shewa da k`arfi, momy tace "k`arfe nawa ne party`n?" "K`arfe biyar na yamma ne momy, amma kuma nasan ba lallai ne a fara shi a lokacin ba ana iya akai dare", "A ina zakuyi" "Momy nima ban sani ba, suna so suyi suprising namu ne, Sally ce kawai tasan inda za`ayi dan har ma ta tura wanda zayyi mana decoration ina tunanin ma har an gama", "Tou yayi daidai `yata, ya maganar dressing fa?", "Pink, black and ash ne za`ayi kuma ina dasu ai da banda shi momy da tun d`azu na mimi magana", "Ok yayi daidai autah nah, Allah kaimu anjimar, sai ki tafi da mota ta dan bana so kowa ya kara ki a tashi dan kar a miki wulak`anci", Tafi sukayi da junan su, Ruky tace "das my momy, saisa nake sonki always". ยฉAmrah and Rerbeeart novels, [11:35pm, 19/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* *~hannu biyu writers~* Page3โƒฃ *Karfe 1:30pm* *~Gidan su Iby.~* "Yaya Mukhtar dan Allah zaka bani aron motar ka anjima?", "Me zakayi da ita?" Yayan nashi ya fad`a yana latsar system nashi. "Yaya zanje wani wuri ne?" "Shi wurin baya da suna ne?" "yana da suna yaya, ganin abokina zanje", "Ganin abokin ka kuma shine bazaka iya d`aukar mashin d`in ka kaje ba dole sai a mota?", yayan nasa ya fad`a a lokacin da ya dawo da kallon shi ga Iby. "yaya wai me yasa kake min haka ne? Yaya na yana da kud`i ina alfahari da hakan amma kuma baya kyautata min, me yasa yaya bazaka so aga k`anin ka da manyan harkoki bane wai?", Cikin mamaki Mukhtar ya kalli Iby yace "au! Ashe abun ma hakane, tou tunda hakane ma bazan bayar ba, kaje ka nemi loud speaker kayi shela akan nak`i ara maka mota ta kuma bayan ina da motocin da yawa, sai inga idan akwai wanda ya isa yamin wani abu", Tashi Iby yayi yana gunguni can k`asa k`asa, "Me kake fad`i!?" Mukhtar ya fad`a a hayak`e. "B..b...bance komai bafa yaya" ya fad`a in tammered. *Karfe 2:30pm* *~Gidan su Shareef da Shareefat.~* Shareefat ce kwance kan doguwar kujera ta rasa abunda yake mata dad`i dan tunanin rashin kayan da zasu saka wurin party`n kerry, alamar tafiya taji tayi saurin duba ko waye, ganin Shareef ne yasata ajiye nannauyan ajiyar zuciya tare da fad`in "Reesha dama ina jiran zuwan ka", "Menene?" Ya fad`a yana kallon ta, "Mubar area`n nan dan kar mamy taji mu", Barin parlor`n sukayi suka koma can kusa da gate d`in gidan, "reesha dama in fad`a maka wallahi banda kayan sakawa anjima, nasan kuma kai kana dasu, ya za`ayi dan Allah", Dariya yayi sosai yanayi yana nuna ta da yatsa, sai da yayi mai isarshi lokacin har Shareefat ta k`ule, "Tou Reeshat ni yanzu me zan miki? Kije kiyi aro kawai", K`ara b`ata fuska tayi tace "ai wallahi inda akwai inda zanyi aron da nayi, dan bazan yarda kowa da anko ni banda shi ba", Shareef yace "kar ki damu zan nemo miki shi yanzu, amma fa ban iya zab`e ba zakiyi hakuri da duk wadda na siyo miki?", Kallon shi tayi sosai tace "kai Reesha ka tafi dani dan Allah", Zaro ido yayi yace "idan na fita dake yanzu anjima idan zamu fita k`aryar me zan ma mamy? Kedai kiyi hak`uri kawai zan duba miki mai kyau, kuma koya take indai kalar ta hau ai shikenan", "Ehh haka ne kuma, Reesha, pls nidai mai kyau nake so", da wannan maganar Shareef ya tafi, shareefat kuma ta koma cikin gida. Amrah and Rerbeeart sk novels Admins ONLINE HAUSA READERS๐Ÿ“š [11:45pm, 19/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* *~hannu biyu writers~* Page4โƒฃ Haka dai gidajen su *Arewa stars* d`in suka kasance, kowa ya nemi kalar kayan da da suka zab`i sakawa a birthday party`n kerry d`aya daga cikin members na *Arewa Stars,* murna fal a zukatan su, sun d`au dogon lokaci suna tsumayen wannan ranar duk da yawan party da suke amma na kerry ya banbanta saboda asalin ta ba tashin Nigeria bace a America ta tashi, tasan duk wani salo na wayewa da gayu, sannan kuma iyayen tama suna bakin k`ok`arin su ganin sun mata duk abunda take so, yanzu ma haka bata k`asar ta tafi Dubai inda za`a d`inka mata rigar da zata saka yau wurin birthday party`n ta kuma a yanzu suke sa ran isowar ta saboda gashi rana har tayi. *K`arfe 3:20pm* yayi daidai da dirar jirgin su Kerry a babbar airport d`in aminu Kano dake cikin jihar kano, jikin ta har rawa yake taga ta fito daga jirgin dan bata san tsawon lokacin da zasu d`auka a mota basu isa katsina ba, gashi kuma bata son African time a harkar ta. Da sauri ta fito daga jirgin ta fara hangen inda zata ga Dad nata, da sa`a kuwa can ta hange shi sanye da suit black and white yana kalle kallen ta inda zaiga fitowar tilon `yar sa. Da gudu ta iso gaban shi tare da hugging nashi sosai kamar mata ta rungumi mijin ta, "Welcome back my daughter" Dad d`in nata ya fad`a bayan ta sake shi yana mata murmushi. "Thank you Dad, amma ya kamata muyi sauri Dad, kaga time is going friends d`ina har sun fara shiri I know", "Ok lets go dear" ya fad`a suka kama hanyar fita. Gaban parking area naga sun nufi wata had`ad`d`iyar corolla s fara tas, tun daga nesa ya latsa remote motar ta bud`e kanta, gaban motar Kerry ta zauna bayan ta zauna ya rufe mata k`ofar sannan shima ya shiga ya rufe tashi k`ofar. Da k`arfi yaja motar jin autar shi tace suyi sauri su isa katsina. "I missed youh so much my Dad, tafiyar kwana biyar amma ji nake kamar nayi one year ban ganku ba", "Muma munyi kewar ki my Kerry, musamman ma Mum inki kamar zata min kuka wai sai ta biki, sai da nata bata baki sannan ta hak`ura" "Dad pls ka k`ara gudun nan bai fa ishe ni ba" Gudun ya k`ara sosai kamar mai shirin tashi sama, ba dan komai ba sai dan yaga ya farantama Kerry rai. *Karfe 4:34pm* A wannan lokaci ne su Kerry suka iso garin Katsina, sai a lokacin kuma ta kunna wayar ta, nan taci karo da sak`onni sosai na *Arewa Stars* wanda suka neme ta a waya basu same taba, suna son jin kota dawo dan kar suita wahalar shiri bayan kuma bata dawo ba. Data ta kunna ta shiga watsapp, *Arewa Stars* taci karo dashi a farko, nan taci karo da conversations da yawa duk suna magana ne akan jin ta shiru da akayi bayan kuma sun gama plans d`in komai da zai wakana a gurin. Guntun murmushi tayi sannan ta rubuta "Kar ku damu *Arewa Stars Allah ya min dawowa kuci gaba da shirin ku daga inda kuka tsaya, birthday party na dole sai anyi shi babu gudu ba ja da baya.* Nan suka hau replying na dad`in da sukaji, sauka tayi daga watsapp d`in ta kira Deezee makeover akan tana son ganin ta yanzu sannan ta shiga wanka. bata wani b`ata lokaci ba sai gata ta fito daga wankan. Trolly bag d`in da ta dawo dashi ta bud`e ta ciro wata riga, "shantalin uwar nan kai" sis Rabi`ah ta fad`a a lokacin data kalli rigar, ni kam uwar gayyar kasa fad`in komai nayi saboda tsantsar kyawun ta. Doguwar riga ce irin mai bin jikin nan, an tsaga gefe gefen ta, complete pink ce rigar arm less, an k`awata ta da wasu irin manyan stones masu walk`iya tamkar zinari, wuyan ta kuma V neck ne inda aka zagaye shi da sirfani da stones a jiki, a daidai k`irjin rigar kuma anyi wani rubutu da stones din an rubuta *"AM PLUS 1",* Sannan aka zagaye rubutun da zanen flower daya k`ara k`awata rubutun, daga bayan rigar tayi nan ma naga an rubuta *"IT`S KERRY"* shima an k`awata shi kamar yanda akayi ma na gaban, "tir k`ashi!" Kawai na iya furtawa, ba komai na fad`a maku akan kyawun rigar ba, idan nace sai na zayyane maku yanda take duka tou za`a ci 10 pages ne, just close your eyes ku hango yanda rigar take (lol..). Da gudu wata budurwa ta shigo wadda da ganin ta an san `yar aiki ce, fad`i k`asa tayi cike da girmamawa kanta sunkuye alamar tana son yin magana amma sai an bata izini sannan zatayi. "Go on" kerry ta fad`a cike da raini. "Ma You have a visitor", "Let her in" ta fad`a a tak`aice. Kamar yanda ta shigo d`in haka ta fita, tsaki Kerry tayi a bayyane wanda yayi daidai da shigowar Deezee. Amrah and Rerbee`art sk novels [11:54pm, 19/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* *~hannu biyu writers~* Page5โƒฃ Har k`asa Deezee ta duk`a ta gaishe da kerry, "Thank you" kawai ta fad`a tare da zama bakin gado. "Can I start?" Kerry ta tambaye ta cikin ladabi kamar tana magana da babarta. "Yes you can, ina son makeover na kirki wanda baki tab`a yiwa kowa ko mai kama dashi ba, zan baki naira dubu hamsin idan kika min na kirki, pink, ash and black ne za`a had`a", deezee lashe money๐Ÿ˜œ tuni ta fara rawar jiki da fara`a taji zancen kud`i, "fara saka kayan dan kar ayi kuma wurin sakawa a b`ata wani abu", "Good idea" kerry ta fad`a tare da zira had`ad`d`iyar rigar a jikin ta. Nan suka hau makeup baji ba gani, abunka ga mutun kyakkyawa dama, babu kwalliyar ma tayi kyau ina ga Deezee makeover ta mata. *Karfe 4:45pm* *~Gidan su Afnan.~* Bayan ta gama kwalliyar ta duka ta saka kayan ta d`aura after dress akai, nan fa ta fara tunanin yanda zata fita, gashi kuma ta fad`awa Momy bata da lafiya d`azu, D`aukar wayar ta tayi ta kira MD, bugu d`aya kuwa ya d`aga, "MD ba kanta fa" ta fad`a bayan ta koma kan gadon ta. "Me ya faru ne `yan mata?", "Na rasa kalar k`aryar da zanyi in bar gida fa, gashi nama momy k`aryan banda lafiya da safe dan kar inje islamiyaโ€ž ka bani idea pls". Shiru yayi na wani lokaci kafin yace "to fa! Bari zan kira ki yanzu". Tsinke wayar yayi ya fara tunanin kalar k`aryar da Afnan zatama momy, "yess" ya fad`a a lokacin da wani tunani yazo masa, kiran wayar ta yayi ringing d`aya ta d`auka, "MB ya?" Ta fad`a rud`e. "Idan kinyi kwalliya ki goge ta, ki nemi after dress ki d`ora hijabi a kanta, ki k`irk`iri kukan k`arya sosai kice baban su Esee ya mutu, yanzu aka kira ki aka fad`a miki shine kike so kje, idan tayi insisting zata biki jana`izar sai kisan yanda zakiyi ki hana ta", sosai taji dad`in wannan shawarar, "saisa nake sonka MD, a duk *Arewa Stars* kafi kowa brain mai kyau", daga nan ta tsinke wayar tana mai jn dad`in shawarar da MD ya bata. *karfe 4:50pm* *~Gidan su Feenat.~* Ummah ce zaune akan sallayar ta tunda ta gama sallar la`asar take zaune tana ta lazumi, a hankali Feenat ta fito cike da tsoro ta duka har k`asa, ta kasa fad`in komai jikin ta sai rawa yake, har a ranta tayi nadamar shigar ta group d`in *Arewa stars* sai dai kuma duk wanda ya shiga baya fita kuma tasan haka, tausayin ummanta take sosai yanda take k|ok`arin tarbiyyantar da ita ba dare ba rana. Ganin Feenat ta zauna kusa da ita kuma tayi shiru yasa ta ajiye casbahar hannun ta tace "Safeena ya akayi ne? Knzo kin tasa ni gaba kuma kin kasa fad`in komai", Da k`yar ta iya furta "ummah d`azu bayan tafiyar Afnan ta koma gida ne ta kira ni wai an kwantar da momy`n ta asibiti, bata da lafiya sosai dan aiki ma za`a mata gobe,shine nake son naje ganin ta", "Ashsha kuwa abu bayyi dad`i ba, ya kamata kam ki hanzarta ki gano ta, ki gaishe min da ita sosai" ta ciro d`ari uku daga jikar ta ta mik`ama Feenat tace "ki sai mata kayan marmari da wannan ki kai mata, wannan d`ari biyun kuma sai ki hau napep dashi" ta sake mik`a mata wasu kud`in. Wasu irin hawaye suka fara ma Feenat ambaliya, sosai ta k`ara jin tausayin ummanta, me yasa ta zab`i wannan rayuwar fiye da farin cikin ummanta? Tunanin da take kenan a ranta, "Tou ki daina kukan mana Feenat insha Allahu zata samu lafiya, ki tafi ki kula da kanki kiji tsoron Allah kuma", duk lokacin da Feenat zata tafi wani wuri ko makaranta ne sai ummanta tace mata taji tsoron Allah, takan yawan tuno da wannan maganar a duk lokacin da zata je wani party. Amrah and Rerbee`art sk novels [12:00am, 20/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page6โƒฃ *Karfe 4:56pm* *~Gidan su Afnan.~* Tuni Afnan ta k`wak`ulo hawayen dole tana mitsitstsikar ido kamar da gaske, ba wuya kuwa idon ta yayi jajir, da gudu ta fita parlor tana kiran "momy! Momy!!", Momy`n na daga d`akin ta tace "gani a d`aki na Afnan, lafiya!?" "Ba lafiya ba momy" ta k`ariso d`akin tana ta sauke ajiyar zuciya kamar da gaske. Momy tace "lafiya? Me ya faru?" "Momy baban su Ihsan Abdallah ne ya rasu yanzun nan ta kira ni, bama a kawo gawar sa ba wai sai gobe da yake hatsarin jirgin sama ne sukayi", Momy ta dafe k`irjin ta tace "mun shiga uku! Allah sarki na tausaya masu, yanzu shikenan sun zama marayu, in ko haka ne barin saka hijabi na sai mu tafi tare", Saurin katse ta Afnan tayi tace "noo momy ki zauna kawai tunda ba`a kawo gawar saba, nasan sai zuwa gobe za`ayi jana`izar shi kinga sai kije goben, yanzu zanje inta bata hak`uri dan nasan yanzu tana can tana kuka", "To ba damuwa Afnan, Allah ya mashi rahama, idan ta kama ma sai ki kwana acan tunda mutuwa ta kauda komai", Sosai Afnan taji dad`i amma a zahiri ta nunar da wannan mutuwar ta tab`a ta sosai. *Karfe 4:58pm* *~Gudan su Ruky.~* "Mamy har na shirya kin ganni nayi kyau?", Ruky ta fad`a tana wani jujjuyawa a gaban Mamy`n su. "Kinyi kyau sosai auta na, ina mai tabbatar miki da yau sai kinfi kowa haskawa a gurin, su o'e da ba`a waye ba kuma a haka za`a k`are fad`in Allah yace annabi yace kamar kansu farau musulunci" ta k`arisa maganar tana kallon Rumaysah, itakam ko a jikin ta, dan tasan duk da tsanar da mamy ke gwada mata saboda bata halayen banza bazai hana ta samun mijin kirki ba, kullun tana ma mamy da k`anwar ta addu`ar shiriya dan wannan hanyar da suka d`auka hanyar kirki sam ba hanyar kirki bace. Key`n motar mamy ta d`auka sannan ta fice, nan ta kira Triple A ya fad`a mata a inda za`ayi. *Karfe 4:59pm* *~Gidan su Iby.~* har a wannan lokacin Iby na zaune ya rasa yanda zayyi ya d`auki d`aya daga cikin motar yayan sa, ganin yake girma ya fad`i idan ya hau mashin ya tafi, barin kuma a dam d`in Ajiwa za`ayi party`n ba cikin gari ba, sand`a yayi a hankali ya shiga d`akin Mukhtar, ya samu baya nan tunda ya tafi masallaci bai dawo ba, makullin camry CE ya d`auka cike da murna ya tafi. * *Karfe 5:15pm.* *_~AJIWA DAM~_* A daidai wannan lokaci ne kowa ya hallara a bakin ruwan ajiwa, an k`awata gefen ruwan da kyakyawan decoration, abunda yafi komai kyau a wurin shine yanda kowa ya saka kaya ash, pink and black, ga wani sauti da yake tashi a hankali a hankali, Kerry uwar birthday kuma tana cikin mota bata fito ba har sai DJ ya gano wak`ar da zata shigo da ita. Muje zuwa (inji Asea Bashir), This is just the beggining. Amrah nd Rerbeeart sk novels. [5:09pm, 20/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page7โƒฃ Wak`ar *broken angel* aka saka a lokacin shigowar Kerry, cike da k`asaita ta fito daga motar ita da saurayin ta Triple A, hannun su sak`ale da juna suna wani taku kamar basa son taka k`asa, Ihu duka wurin aka d`auka take suka fara fiddo wayoyi suna snapping nasu, tafi kake ji sosai wurin da k`arfi, kai da kagan su kasan suna cike da farin ciki tsantsar shi, banda Feenat data ware kanta gefe cike da haushin zuwan ta wurin. *karfe 6:30pm* A lokacin ne za`a yanka cake, nan aka hau tafin yanda Triple A ya kama hannun Kerry ya d`ora akan cake d`in, hotuna sosai suke d`aukar su kuma a lokacin ne hotunan sukafi yin kyau saboda rana ta fad`i hasken flash lights yafi fita da kyau. Sautin kiran sallar magrib ne yake fita kad`an kad`an daga wani masallaci nesa da dam d`in, da alamar dai can cikin garin Ajiwa yake. Feenat ce zaune tana tunanin yanda za`ayi tayi sallah, can wata dabara ta fad`o mata, a bakin wani famfo taje tayi alwala ta bud`e handbag d`inta ta zaro hijabin ta ta saka, can daga gefe inda ba`a jin kid`an ta koma tayi sallar ta sannan ta dawo cikin mutanen. *k`arfe 7:30pm* Cashewar su suke sosai kowanen su ya kama partner d`in shi, a hankali na fara jiyo wani sauti mai had`e da wani irin kuka_kuka kamar kukan shanuwa ko alade, sukam da yake sunyi nisa a casun su har yanzu basu fara jin shi ba, tun sautin yana fitowa kad`an kad`an har ya fara yawaita, sautin wak`a na fita daban sannan na wancan kuka kukan ma yana fita daban, sai kuma yanda kururuwar take k`ara tashi sosai. Feenat ce keta bige hannun MD dake faman shafar gabanta har yana k`ok`arin kai hannu cikin rigar ta, kunnen ta ta kasa sosai dan yanda sautin abun yake fita har ya fara yin yawa, ido ta fara zarowa ๐Ÿ˜ณ tana kasa kunnuwan ta cike da tsoro da fargaba, da k`arfi ta buge ma MD hannun shi wanda yasa shi dawowa hayyacin sa, Da sauri ya koma wurin Reeshat dake rawa ita da MC, rungumo ta yayi ta baya ya fara shafar ta a hankali, nan sukaci gaba da romancing juna cike da jindad`i. Itakam Feenat sosai hankalin ta ya tashi, nan ta fara tunanin to wannan kururuwar ta mecece? K`ok`arin magana take masu amma muryar ta bata fita saboda sautin wak`ar dake tashi. "Na shiga uku ni Safeenat! Wannan k`arar ta mecece? Kar dai namun daji ne zasu cinye mu" ni kuwa Amrah nace in namun daji ne ma ai da abun yazo da sauk`i saboda akwai hanyoyi da yawa zaku iya guduwa. Sosai wannan k`arar take k`ara yawaita, a hankali sautin speakers d`in ya fara canjawa yana komawa irin wancan sautin na kuka, Reesha ne yace "oh common! Dj wannan kukan daka kunna mana fa? Abeg ka canja shi mana, abu kamar kukan jaki", Sally dake rungume da Reesha tayi dariya tace "wuce jaki ma wannan". Amrah and Rerbeeart sk novels [5:22pm, 20/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page8โƒฃ Sautin ne ya k`ara d`aguwa sosai, Dj`n ma hankalin shi ya soma tashi, shidai a iya sanin shi bashi da wannan sautin a duk wak`ok`in shi, k`ok`arin wucewa ya fara yi amma d`if! Wayar ta d`auke, dvd d`in ta mutu, ga hasken fitilar duka ya mutu, sai wannan sautin da yake ta k`ara yawaita. Feenat jiki sai rawa yake, ta ambaci sunan Allah amma sam ta kasa, ga wani irin mugun duhu daya mamye wurin, Dj ma hankali ya k`ara tashi, Sally tace "mun shiga uku! Wa ya kashe mana hasken?", Reesha yace "kila dai cikin samarin nan ne wani ya kashe ta, shegu maza! Iskanci yayi dad`i kenan", Cike da tsoro da rawar murya Sally tace "wannan ba kashe shi akayi ba, kaji sautin da yake tashi fa, na shiga uku ni Saleemah" sai hawaye sharrrr a kumatun ta. Wata irin k`ara da k`arfi speakers d`in sukayi wanda yasa lokaci daya kowa ya dawo hayyacin sa, tsoro duk ya kama su, wani irin iska mai had`e da guguwa ya fara tashi, Kerry uwar birthday tuni hawaye sun cka mata ido, wayar ta take ta nema amma ta rasa inda take, ita dai tasan akan table ta ajiye ta a lokacin da zasu yanka cake amma kuma yanxu ta duba nan babu ita, can daga nesa ta hango hasken ta alamar ana kira saboda wannan muguwar k`arar bazata bari k`arar waya ta fita ba, hannun ta ta zira zata d`auko amma sai taga wayar ta k`ara yin gaba kamar anja ta, k`ara zira hannu tayi amma wayar ta k`ara tafiya, binta taci gaba dayi ana jan wayar har saida tayi nisa sosai ta fara fita daga cikin mutane, har tabar baki d`aya area`n da suke party. Ihu dukkanin su suke, daga mai kiran dady sai mai kiran momy amma babu mai kiran sunan Allah, sannu sannu kukan nan ya k`ara yawaita, da suna jin murya d`aya ne amma yanzu ya zama muryoyi da yawa babu adadi. "Tashin hankali" na fad`a a raina, tuni biro na ya kufce ya fad`i tsananin tsoro da fargaba, ban san a ina yake ba dole sai Sis ta siyo min wani. Muje zuwa, ba`a fara komai ba yanzu za'a fara inji Amrah. Amrah and Rabeeart sk novels, [8:02pm, 21/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page9โƒฃ *'Karfe 9:00pm* *_AJIWA DAM_* Iya rud'ewa da kid'ima yau *AREWA STARS* sunyi ta, kuka suke su duka 19 d'in banda Kerry da tabi wayar ta, hankali tashe Feenat ta ringa kiran "Ummah! Ummah!! Ummana kizo ki taimake ni, alhakin ki ne Ummana, kullun k'ok'arin ki ganin kin bani kyakkyawar tarbiyya amma bana d'auka, ina watsi da duk tarbiyyar da kike bani, yau gashi nan muna ganin abunda muke shukawa", sosai take kuka duk ta fita hayyacin ta. A hankali guguwar nan ta fara isowa inda suke, k'ura ce mai had'e da wasu irin k'ananan halittu wanda bazasu iya misaltuwa ba, da yawan gaske suke ta zuwa wurin su, ga wannan kukan mai muryoyi da yawa shima yana ta k'ara yawaita, ga kuma duhu shima babu wanda ke iya ganin ko tafin hannun sa. Wurin Eseeee k'warin suka nufa da mamaki naga sun k'adaddabe ta baki d'aya kamar yanda zuma kema mutun idan ta kama shi. Sosai take kuwwa tana ta k'ok'arin murje su daga jikin ta amma sai k'aruwa suke, da mamaki wannan halittun suka ringa shigewa a cikin fatar Esee suna yawo ciki kamar wani bororo, har cikin kanta suka shiga suna mata yawo akai, banda soshe soshe babu abunda take, take gashin kanta ya fara kakkaryewa yana fita har sai da baki d'ayan shi ya fita kanta ya koma swal, in banda yawon wannan halittun dake cikin kan. Fatar jikin ta ta fara zagwanyewa tana barin tsokar ta baki d'aya kamar wadda ta k'one, kamar gari haka fatar ta ringa murmusa a k'asa, take Esee ta fad'i wurin bata a hayyacin ta. Reesha da Sally kam har yanzu basu saki junan su ba, cike suke da tsoro da fargabar wannan al'amarin, Can suka ji wannan halittun sun dawo kan su, yanda suka ma Esee suma haka suka masu kuma har a lokacin suna manne da juna basu rabu ba hannun Reesha a cikn rigar Sally kan k'irjin ta. Fad'i sukayi a tare suma basa a hayyacin su. Da wata irin dariya da k'arfi naji wata muryar da tunda babata ta haifeni ban tab'a jin ko makamanciyar ta ba, Wannan k'warin ne suka hau dunk'ulewa guri d'aya, d'aya na cin d'aya har suka zama guda d'aya babbar halittar da babu halitta mai girman ta a duk doron k'asar mu ta Nigeria. Nan ta hau jijjigar jikin ta saboda duk inda bai gama had'ewa ba ya had'e. Idon ta ma jaa ne tamkar garwashi wanda hasken idon kawai ake iya gani a duk fad'in filin. Afnan ce b'oye a bayan wani katako wanda jikin shi duk k'usoshi ne ta lafe jikin ta sai rawa yake, da k'arfi taji an buga ta jikin k'usoshin duk suka caccake ta, take jini ya fara ambaliya daga jikin ta, tun daga nan itama ta fita hankalin ta da alama suma tayi, bata kuma sanin abunda yake wakana ba. Nan ma wata dariyar ta kuma yi da k'arfi wadda tafi waccan ma tsanani. Ruky wadda tuni ta sume tsananin tsoro da tashin hankali da k'arfi halittar nan ta d'auki Ruky ta d'aga ta sama ta nanata k'asa, take kuwa Ruky ta farfad'o, sake d'aga ta sama tayi ta jefar sai kan wani dutse, take jini ya fara ambaliya daga kanta itama ta sake sumewa. Dj da Mc kuwa had'a su tayi da karfi ta matse su sai ga hannun Dj ya b'ullo ta bayan Mc, hannun Mc kuma ya b'ullo ta cikin Dj, wulwula su taci gaba dayi sannan ta jefar dasu daidai kan dutsen da ta jefar da Ruky, take suma suka sume. Dariya mai had'e da sautin kuka ta fasa lokaci d'aya, wanda yasa sauran da bata kashe ba suka k'ara tsorata da ita, dan cikin su har da wanda ya saki zawayi daga zaune akwai, a ransu kuwa banda dana sani babu abunda sukeyi, ni kuma Amrah nace maganin irin ku kenan, wata k'ila wasu idan suka ji labarin ku koda halin su ne zasu daina, basu san aron lokaci bane Allah ya basu amma sun kasa ganewa, yau gashi sun had'u da daidai dasu, muje zuwa dai inji ni Amrah. Amrah and Rerbee'art sk novels [8:14pm, 21/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page1โƒฃ0โƒฃ Bari mu koma b'angaren gidajen su. *Karfe 10:30pm* *~Gidan su Feenat.~* Ummah ce zaune tayi tagumi baki d'ayan hankalin ta a tashe yake, ita dai tasan a duk inda Feenat take ya kamata by now ta dawo gida, "to ko dai jikin maman Afnan d'in ne ya rikice?" Ta fad'a a ranta, "To inko hakane ai ya kamata Safeena ta kira ni a waya ta sanar dani in ma acan zata kwana, amma gashi har dare yayi babu ita babu kiranta kuma", Wayar ta ciro nan ta hau neman lambar Feenat tana ta ringing amma bata d'aga ba, a hankali ta soma jiyo k'arar ta daga d'akin Feenat alamar can ta barta, "to kenan anan ta bar ta kome?", D'an guntun tsaki tayi tare da komawa ta kishingid'a ko zataji zuwan Feenat dan har a lokacim bata rufe gida ba. Jin shiru har sha d'aya ta kusa yasa tace "bari dai in tashi in tafi gidan su Afnan d'in sai a fad'a min asibitin da maman take, wata k'ila dai babu lafiya", Hijabin ta ta zira a hargitse ta rufe gidan da makulli ta fita. Da sa'a kuwa tana zuwa bakin titi ta samu napep babu kowa, bata koyi ciniki ba ta hau ta kwatanta inda zai kaita. *Karfe 10:49pm* *~Gidan su Afnan.~* Momy ce zaune ta rungume Affan dake ta bacci abin sa hankali kwance, ita kuwa tv kawai ta tsura ma ido tana kallon NTA wai a nufin ta ko za'a fad'i cewa wani jirgi yayi had'ari amma har yanzu babu, canjawa tayi ta kai AIT amma nan ma babu, tab'e bakin ta tayi tace "wata k'ila har an gwada ban gani ba, Allah dai yayi ma duk musulman cikin jirgin rasuwa, wanda suke raye kuma Allah ya basu lafiya, nayi zaune har Alhaji ya kwanta ya barni da wannan rigimammen", D'aukar Affan tayi ta d'ora a kafad'ar ta sannan ta kashe kallon, Daidai zata kashe wutar parlor'n ne yayi daidai da shigowar Umman Feenat. Cikn mamaki Ummah ta gaishe da momy, momy ma amsawa tayi da mamaki dan sam bata wayi Ummah ba, "Ina zuwa dan Allah" momy ta fad'a tare da nufar d'akin Affan ta kwantar dashi sannan ta dawo. Zama tayi tace "baiwar Allah lafiya dai a cikin wannan daren?", Ajiyar zuciya ummah ta sauke sannan tace "to ko dai ba inda nake son zuwan bane nazo? Ni inda zanje fa mai gidan bata da lafiya tana asibiti, kuma tun a waje mai gadi yace min wai me nan gidan lafiyar ta lau", Momy tace "Allah sarki! Gaskiya ba nan bane sai dai ko makwaftan mu, ya sunan mai gidan da kike neman?", "Ban san sunan su ba gaskiya, sai dai nasan sunan 'yar Afnan Abbas tana da k'ane kuma Affan, maman ta bata da lafiya ne 'yata ta tafi ganin ta, amma gashi har yanxu bata koma gida ba shine nake son jin ko lafiya?, amma babu komai nagode barin ci gaba da bincike ko Allah zaisa in dace", ta fad'i hakan ne tare da mik'ewa tsaye tana neman fita. Cikin mamaki Momy ke kallon Ummah, baki a sake da 'kyar ta iya furta "b..b..b..baiwar Allah ai nan ne gidan su Afnan Abbas, kuma nice mahaifiyar Afnan, sai dai kuma ni lafiya ta k'alau babu abunda ya same ni", Da sauri Ummah ta dawo ta zauna tana kallon momy, "kina nufin 'Yata Safeenah Al-hassan ba nan tazo ba kenan?", "Gaskiya ba nan tazo ba, k'ila dai wani wurin zataje shine ta miki k'aryan zatazo gani na", "Hajiya dan Allah ki kira min Afnan in tambaye ta ko tana da masaniyar inda Safeenah ta tafi" ummah ta fad'a tashin hankali k'arara a fuskar ta, momy cike da tausayin Ummah tace "sai yanzu na gane ki ashe kece maman Feenat, kin san kolacin da muka had'u last speech and prizes given d'in su ban kalle ki sosai bane, wallahi Afnan bata nan taje gidan rasuwa ne", Ummah tayi salati ta rufe idon ta tana matsar hawaye, "to ina Safeenah taje? yaushe Safeenah ta koyi wannan halin? Kenan k'arya tamin? Allah yasa dai ba maza tabi ba suka sace min ita" wasu zafafan hawaye sukaci gaba da bin ta. Momy kuwa a ranta cewa take "kai! Allah ya shiryi yaran yanzu, k'ila ma yawon iskancin ta xata tafi shine ta ma uwarta k'aryar banda lafiya, kuma ta rasa wanda zata ce baida lafiya sai ni", Dady'n Afnan ne ya fito yana fad'in "maman Afnan lafiya kuwa?", yana fad'in haka yana kallon Ummah cike da mamakin yanda tazo gidan su cikin wannan daren dan shi tsoro ma ta bashi. Momy bata bashi amsa ba sakamakon sallamar da sukaji, maigadi ne ya shigo yana fad'in "yallab'ai wani bawan Allah ne yaxo, da ganin shi dai babban mutum ne yace wai sunan shi Alhaji Abdallah, wai baban Ihsan ne k'awar Afnan, wai yana son ganin ka", Dady yace "Alhaji Abdallan da akace yayi hatsarin jirgi ya rasu!? Kace masa ya shigo". Tir k'ashi! Kallon sis R. Nayi cike da k'aguwa da shigowar Alhaji Abdallah, muje zuwa dai sis R. Ta fad'a, sai kuma gobe zakuji posting d'in mu insha Allah. Amrah and Rerbee'art sk novels [11:36pm, 23/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page1โƒฃ1โƒฃ Ba'a jima ba kuwa sai ga maigadi tafe Alhaji Abdallah a bayan shi, A kid'ime Dady ya mik'a mashi hannu suka gaisa tare da cewa "bismillah ga wurin zama", Alhaji Abdallah ya zauna sannan yace "nazo ne dama inji ko lafiya tun da yamma Ihsan ta baro gida tace nan zata zo wai Afnan bata da lafiya, kuma gashi har yanzu bata koma gida ba" Ido bud'e momy ta kalle shi cike da mamaki tace "Alhaji ai muma nan tun yamma Afnan tabar gidan nan wai kayi accident da jirgin sama ka rasu", Salati Alhaji Abdallah yayi a bayyane yana mamaki, a ranshi yace "kenan Ihsan bata zo nan ba?", Momy tace "innalillahi wa inna ilaihi rajiun! k'arya Afnan tamin kenan dama ba can zataje ba?", Ummah dai na tsaye cikin tashin hankali tana sauraren su, sun jima d'akin babu wanda ya kuma cewa wani abu kowa da abunda yake sak'awa a ransa, sai daga baya ummah tace "in kuwa hakane tou duk inda yaran nan suke suna tare, babu mamakin ko wani wurin sukaje shine suka tsara mana k'arairayi mu kuma muka yarda, Allah dai yasa lafiya suke". Dady yace "wannan hakane baiwar Allah! Tou ina yaran nan sukaje ne?", Alhaji Abdallah yace "nima tunanin da nake kenan, wai yara k'anana har sun san su had'a mana k'arya idan zasu tafi, kuma ni wallahi bana kullen Ihsan sosai, inda ma ace ina mata tsanani ne da sai ince banga laifin ta ba". Dady cikin tashin hankali yace "barin tafi Office yanzu nasan Sajent Musa yau night gare shi, inspector Bala ma kamar night ne saboda sanda na baro office lokacin yaje, barin hanzarta in tafi", Alhaji Abdallah yace "na manta ashe tare nake da DSP, ai da sauk'i ma kenan, sai mu tafi tare". Wayar Dady ce ta d'auki k'ara, dubawar da zayyi yaga Inspector Ashir ne, d'aga kiran yayi tare da fad'in "akwai magama inspector, gani nan zuwa Station d'in yanzu", "Yallab'ai nan ma dai akwai matsala, mutun biyu sukazo wai suna so a masu cigiyar yaran su sun fita tun yamma basu dawo ba, d'ayan ma wai twins ne yaran", inspector'n ya fad'a cike da girmamawa. Dady ya kalli Alhaji Abdallah sannan yaci gaba da fad"in "same case da zai kawo ni station d'in, ka jira ni yanzu zan taho" yana kaiwa nan ya kashe wayar tare da d'aukar key'n mota ya fita, Alhaji abdallah ma ya mara masa baya. Basu jima a hanya ba suka isa station d'in, cikin hanzari Dady ya nufi office d'in Inspector Ashir ya samu mutun biyu dattijai zauna sai raba ido suke kamar sunyi k'arya an turke su (lol..). Bayan inspector Ashir ya saaraa ma Dady sannan yace "yallab'ai kamar yanda na fad'a maka to ga mutanen nan, amma dai kaji daga bakin su", D'aya daga cikin su yace "sunana Alhaji Ma'aruf, yara na 'yan biyu Shareef da Shareefat ne suka bat'a", Cikin mamaki Dady yace "b'ata? Garin ya hakan ta faru?" Alhaji Ma'aruf yace "d'azu ne da yamma lokacin da bana nan Shareef yaje wurin Mamin su yace wai zasu je wata gaisuwar rasuwa baban classmate d'in su ya rasu, to da naji su shiru shine na gano inda sukace sunje d'in da k'yar da wahala ma na gane gidan, naje sun shaida min su babu wanda ya rasu a gidan su, suma 'Yar su ta fita tun yamma bata dawo ba, duk gidajen dangi da nake tunanin yaran nan zasuje naje amma ban same su ba, ga lambobin wayar su bata shiga, hankali na ya tashi sosai shine nazo nan ko da wani abu da za'a iya yi min". nannauyan ajiyar zuciya Dady ya sauke, gaban shi ya k'ara fad'uwa yayin da bugun xuciyar shi yake tafiya da sauri sauri, ya jima a haka kafin yace "to kai fa bawan Allah me ya faru?" D'ayan mutumin yace "nifa tawa 'yar gidan mahaifiya ta tace min zataje ta duba ta wai ta dad'e bata je ba, nikau har da dad'i naji ta kula min da uwa, jn ta shiru har dare yayi bata dawo ba yasa na kira ta amma tak'i shiga, na kira mahaifiya ta tace min ai Nuratu bataje inda take ba, hankali na ya tashi sosai, nayi iya bincike na amma ban same ta ba, shine na yanke hukuncin zuwa nan nasan insha Allahu zakuyi bakin k'ok'arin ku". Alhaji Abdallah in banda kallon su babu abun da yake yi, to wai miye dalilin da yasa yara matasa suka b'ata a lokaci d'aya? Kuma same case ne kowa k'arya yayi kafin yabar gida? Tambayar da yakewa kansa kenan wadda yasan bata da amsa har sai lokacin da aka gano yaran. Dady ya gyara murya yace "abunda ya kawo ku nima shine muhimmin abunda ya fito dani a wannan lokacin nida bawan Allah'n nan.." nan ya basu labarin duk abunda ya sani har Ummah dake gidan su akan b'atar 'yar ta itama. Alhaji Ma'aruf yace "tabbas yaran nan aduk inda suke suna tare, baza'a tab'a kiran wannan da coincidence ba saboda abu ne wanda yake a bayyane, fatan mu dai Allah yasa a duk inda suke suna lafiya", Alhaji Bashir (Baban Nuratu) yace "ai sai asan abunyi ba wai mu tsaya anan muna magana ba, ko gidajen radio ne sai mu fara xuwa kafin gari ya waye asan abunyi". Da wannan maganar suka rantaya su duka hud'un a cikin motar Dady, basu zarce ko ina ba sai VISION FM, nan suka bada sanarwar b'atan yara matasa wanda dukan su babu wanda ya wuce shekaru 16-17 ba. Amrah and Rerbee'art sk novels, Admins ONLINE HAUSA READERS๐Ÿ“š [11:43pm, 23/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page1โƒฃ2โƒฃ K'arfe 11:05pm *~AJIWA DAM~* Wani irin haske ne mai had'e da guguwa mai k'arfi ya haskaka wurin, Feenat dake gefe makure har ta sik'e da kuka tana ganin hasken ta saki ajiyar zuciya dan wani sanyi sanyi taji a ranta, d'aga kanta da zatayi taga yanda akayi kaca kaca da *AREWA STARS* kamar wasu dabbobi, Can kuma hasken ya canja launi izuwa red colour, Md da Reeshat dake gefen ruwa suna kallon ikon Allah bayan hasken ya b'ullo sukaji alamar motsi ata inda suke, cike da tashin hankali Reeshat ta k'adaddabe Md gabanta sai dukan uku uku yake, bata ankara ba taji anja gashin ta dataima mayen gyara sama ana ta wulu wulu dashi, sosai take jin zafi dan dama a ranar tayi sabuwar relaxer, sai da tayi sama sosai da ita sannan ta jefar a bakin wani k'arfe da akebi ta jikin shi idan za'a shiga ruwa, take ta sume bayan ta sai zubar da jini yake. Md ma ta up side down ta d'auke shi da k'arfi ta jefar a jikin Reeshat, shima sumewar yayi inda k'afar shi d'aya ta cire tun daga cinyar shi sai zubar jini take, cinyar daban ta fad'a a cikin ruwa sai sauran gangar jikin ne a jikin Reeshat. Nuratu, Shamow da Sady sun dunk'ule junan su suna kallon yanda wannan halittar take wuji wuji da Md da Reeshat saboda har a lokacin wannan jan hasken bai mutu ba, hankalin su tashe dan sun san dole suma sai anzo kansu, babu mai iya yiwa d'an uwan sa magana a cikin su sai faman rawar lab'b'a suke, ga wata irin zufa na keto masu duk da sanyi sanyin ruwan Dam d'in dake akwai amma bai hana masu jin zafi ba. A hankali wani irin ruwa ya ringa saukowa a daidai inda suke, ruwa ne bak'i k'irin tamkar ruwan kwata ga wari da yake yi, Da mamaki a duk inda ya d'iga na jikin su sai yayi wani irin bororo kamar masu gyambo, haka yaita sauka a jikin su har saida yayi masu kaca kaca da jiki kamar wanda suka k'ok'k'one, A had'e ta jefo masu wani d'an k'aramin dutse wanda baki d'ayan su ya had'a ya sumar dasu a lokaci d'aya basu kuma sanin kome yake wakana ba. Dariya ta kuma fashewa da ita da k'arfin gaske har sai da itacen wurin suka ringa girgiza da kansu, k'yallayen da akayi decoration dasu kuwa da kansu suka ringa yayyagewa, speakers da generator kuwa rugurgujewa suka ringayi kamar yanda ake rugurguza dunk'ulallen gishiri ko maggi, Ta dad'e tana dariyar kafin ta d'aure fuska wasu irin blue ruwa suka ringa kwaranya daga idanuwan ta wanda da alama ruwan hawaye ne, Girgiza kanta tayi taci gaba da waigawa gabas da yamma bata ga kowa ba, ta diba kudu inda taci karo da Samir wanda ya gama kid'imewa amma shi a zaton shi ya tsira saboda a wani lungu ne ya lab'e inda matuk'ar baka san yana wurin ba to bazaka ganshi ba, amma da mamaki wannan halittar ta zira dogon hannun ta ta cafko shi a tafin hannun ta, bakn ta takai a cikn wandon shi sai ga kayan marmarin sa (lol..) a bakin ta had'e da jini sai zirara yake, Tofar dashi tayi sannan ta jefar da Samir wanda a lokacin har ya sume tsabar azaba da tayi masa yawa. K'arfe 11:30pm *~kerry~* tayi tafiya mai nisa har sai da ta sik'e da tafiyar ta nemi wuri ta zauna sai haki take, hankalin ta tashe sai nishin gajiya take, A hankali ta fara jin hayaniya a kunnen ta wadda ta k'ara tsorata ta, k'ara kasa kunnenta tayi taji k'arar tana k'ara yawaita, "Oh Dad help me!" Kawai take fad'a, Da k'arfi halittar ta jawo ta da hannu ta rik'e ta da tafin hannun ta, wata shu'umar dariya tayi wadda ita kad'ai tasan ma'anar ta sannan ta busa ma Kerry iska da bakin ta adaidai kanta sannan ta jefar da ita, take Kerry ta sume itama. bakin Dam d'in ta koma ta kalli Arewa nan taga Feenat takure sai rawar jiki take, Hannun ta tasa ta jawo ta ta rik'e ta, a hankali Feenat ta fara furta *"AU'DHU BI KALIMATULLAHI TAAMMAAT MIN SHARRI MA KHALAKA, BISMILLAHILLADHI LA YADHURRU MA'ASMIHI SHAI'UN FIL ARDI WALA FISSAMA'I WAHUWAS SAMI'UL ALEEM"* Amrah and Rerbee'art sk novels, [8:20pm, 27/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page1โƒฃ3โƒฃ Wata irin k'ara ta saki da k'arfin gaske tare da yin wulli da Feenat can nesa da ita, Wannan blue hawayen ne yaci gaba da kwaranya daga idonta, tsantsar damuwa ce k'arara a yamutsatssiyar fuskar ta, A razane ta koma inda ta jefar da Feenat ta sake d'aukar ta ta matse ta tam a hannun ta, tsananin girmanta yasa kamar bata rik'e komai a hannun ta ba, Sosai Feenat ke kuka, a wannan karen ma sai ta kasa yin ko addu'ar ma, a nan ne ta samu damar dunk'ule ta wuri d'aya ta nad'e ta kamar gammon kifi, ta d'aga ta zata jefa a cikin ruwa saboda yanda ta b'ata mata rai, duk cikin su babu wanda yayi k'ok'arin hana ta abunda take yi sai Feenat, hakan yasa kawai ta yanke hukuncin ta jefar da ita a cikin ruwa yanda tasan babu ita babu fita saboda girman ruwan bama za'a gane akwai mutun a ciki ba, Daidai ta d'aga ta zata jefar kenan Feenat ta sake bud'e baki tace *"LA HAULA WALA K'UWWATA ILLAA BILLAH, U'I'DHU KUMAA BI KALIMATULLAHI TAAMMAAT WA MIN KULLI SHAID'AANIN WA HAAMMAAT WA MIN KULLI AININ LAAMMAAT, ASTAGHFIRULLAHI WA ATUBU ILAIK, YA ALLAH NASANI NI MAI LAIFI CE, INA NEMAN GAFARAR KA YA ALLAH, ALLAH KAI KAD'AI KAKE DA IKON TSERATAR DANI DAGA WANNAN AL'AMARIN, ALLAH NA ROK'E KA DA SUNAYEN KA TSARKAKAKKU, KA CECE NI DAGA K'ANGIN DA NAKE CIKI",* Tana kaiwa nan tayi shiru sai wasu zafafan hawaye dake fita daga idon ta, kawai ta barma Allah al'amarinta ne dan tasan shine kawai zai iya fitar da ita, bata da k'arfi ko wata dabara sai Allah. Da mamaki sai ga wannan halittar ta ajiye Feenat k'asa a hankali tana sauke ajiyar xuciya, Sumbatar ta tayi a goshi wanda yayi daidai da saukar hawayen ta akan fuskar Feenat, Da sauri Feenat ta d'ago kanta ta kalle ta tace "yake wannan halitta, nasani mu masu laifi ne ga Allah kuma laifin da muka aikata ne yake bibiyar mu, ina so ki bud'e bakin ki ki fad'a min abunda muka miki saboda mu rok'i gafarar ki" jiki na rawa tayi maganar bayan ta sunkuyar da kanta k'asa saboda halittar fuskar tama kanta abun tsoro ce, just imagine halittu da yawa su dunk'ule su zama guda d'aya, ya girmanta zai kasance? Kanta ta gyad'a alamar baxata fad'i komai ba, Feenat tace "dan Allah idan kina jina kuma zaki iya magana tou ki fad'a min, wannan ishara ce ga wasu mutanen masu hali irin namu, zan so naji komenene saboda gaba". Wata irin k'ara ta saki da k'arfi wadda ta k'ara gigita Feenat, hatta da ruwan dam d'in sai da ya canja launi, itatuwan gurin kuwa ganyen su suka ringa cirewa da kansu suna fad'uwa k'asa, jijjiga kanta ta hau yi baki na rawa tana k'ok'arin yin magana amma ta kasa, Da k'yar ta iya bud'e baki zatayi magana kenan sai ga wani irin ruwa yana fita daga bakin ta, wannan ruwan da yake fita shi ya hana ta fad'in komai amma da alama tana son yin maganar babu hali ne, Hanya ta nuna ma feenat da hannun ta da alama tana nufin ta tafi ne, amma Feenat tak'i tafiya sai kad'a mata kai take tana hawaye, "Bazan iya tafiya in bar 'yan uwana anan ba, bazan tafi ba har sai kin fad'a min abunda muka miki", Itama kan taci gaba da kad'a mata tana yunk'urin magana ta kasa, Dogon tunani Feenat ta tafi a wani lokaci tun kafin ta shiga group d'in *AREWA STARS,* Wata rana suna zaune da Ummah tana mata karatu, bayan sun gama ne take bata k'issoshi ciki har da na aljanu a ciki, anan ne ummah ta shaida mata da cewa duk ranar da taji zahirin muryar aljani tou sai ta kurumce, haka kuma duk ranar da kikaga aljani da idon ki sai kin makance ko kuma ki haukace", Saurin zabura tayi tare da fad'in "bama sai kinyi magana ba amma ki sani nayi nadama, nayi nadamar sanin *AREWA STARS* ina mai baki hak'uri idan akwai abunda muka miki wanda ba daidai ba, zan tafi gida zan shaidama iyayen mu dan suzo su tafi da gawarwakin wanda suka mutu, wanda sukaji rauni kuma a kaisu asibiti" tana kaiwa nan ta kama hanyar tafiya k'afarta babu takalmi kanta ko d'ankwali babu. Tayi tafiya mai nisa kafin ta isa bakin titi, mutane ne sosai wurin tamkar da rana ne saboda wani mai sai da shayi daya tada gen, daga gefen shi kuma wani mai tsire ne shima da tashi tawagar, ganin haka yasa feenat tayi hamdala tare da k'arisowa inda suke. Suna ganin ta kuwa suka hau daddarewa, su a tunanin su mahaukaciya ce, sallamah tama sauran da basu gudu ba amma suka k'i amsa mata, "Dan Allah ku taimake ni wallahi ni ba mahaukaciya bace ina buk'atar taimakon ku ne", Da sauri wani yace "dama kin tab'a jin inda mahaukaci yacewa kansa mahaukaci ne? Ki gafara ki bamu wuri dallah can kn kore mana mutane daga majalisa", Kuka ta b'arke dashi sosai tare da tafiya a ranta tana tunani "banga laifin ku ba saboda nayi kama da mahaukatan, duk abunda muka shuka shine muke girbewa, ya Allah mun azabtu hakanan, Allah ka sassauta min". Wata mota ta gani irin babbar nan (j5) an sako dabbobi a ciki, hannu tasa ta tsaida ita ta tsaya, driver'n ne ya lek'o ta window saboda ta gefen shi take yace "malama lafiya?", "Lafiya k'alau malan, dan Allah idan cikin katsina kayi ina neman taimako ne ka taimaka ka tafi dani ka sauke ni ko bakin roundabout d'in farko ne" Mamaki k'arara a fuskar shi yace "ke amma kin raina min hankali, a cikin tsohon daren nan zakice na taimake ki, wata k'ila ma ke aljana ce, ke ban yarda dake bama inga k'afarki" ya fad'a yana nuna k'afar da yatsa. "Wallahi malan kaga k'afa ta ni mutun ce" ta fad'a tare da nuna mashi k'afar tana kuka. "Katsina zanje, amma kinga motar duk dabbobi ne daga kasuwar Mai_adua nake nayi dare, sai idan kin yarda zaki shiga cikin su to", Da sauri tace "wallahi na amince", Bud'e mata yayi ta shige cikin su tsamo tsamo, sauk'in ta d'aya ma dare ne akwai duhu duk sunyi bacci. A cikin kashi da fitsarin su ta kwanta tana sauke ajiyar xuciya. Amrah and Rerbeeart sk novels, Admns ONLINE HAUSA READERS๐Ÿ“š [8:29pm, 27/09/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page1โƒฃ4โƒฃ Nan da nan kuwa suka isa katsina, cike da tausayi yace mata "baiwar Allah!" Amma ina, tayi nisa da baccin ta, Sake kiranta yayi "ki tashi mun iso katsina ki fad'a min wace unguwa zan kaiki?" Nan ma shiru. Parking yayi da motar ya fito ya zagayo ta bayan inda take kwance cikin dabbobin ya bubbuga ta a hankali ta bud'e idon ta da suka kumbure sosai, "Nace mun iso katsina ina zan kaiki?", Tunani ta farayi inda zata je, nan ta yanke shawarar kawai ta fara zuwa gida wurin Ummanta, Har ta bud'e baki zata fad'i haka kuma ta tuna da Ummah zata iya yi mata komai idan taje, ta fara zuwa ko gidan su Afnan ne yanda koda sunje gida daga baya baxata mata komai ba a gaban iyayen AFnan, "Goruba road zanje wurin kalamu waheed shopping mall", Fita yayi ya koma gaban motar yaja ta sai goruba road. *K'arfe 12:30am.* A daidai k'ofar gidan su Afnan aka dire Feenat, a hargitse tama mai motar godiya tare da shigewa gidan duk ta daburce, Kai tsaye cikin gidan ta dosa, securites d'in suka nemi hana ta shiga d'aya daga cikin su ne yace "k'awar Afnan ce fa, kuma kun san ana case na b'atar su Afnan, ku barta ta shiga wata k'ila tana da masaniya ma". "Shiga" ogan nasu yace mata, da sauri kuwa ta shiga jiki sai rawa yake mata, tashin hankali k'arara a fuskar ta. Sallamah tayi murya na rawa ta shiga cikin parlor'n, Hankalin tane ya dad'a tashi yanda taga manyan mutane zazzaune sunyi tagumi har da masu yin kuka, daga gefe kuwa Ummah ce da momy suna ta faman kuka babu mai rarrashin wani, Daga can k'arshen kujerun kuma mami (maman Ruky) ce tayi tagumi ta zurfafa a tunani. Sai da tayi sallamah har sau uku amma babu wanda yaji ta saboda duniyar tunanin da suka lula, Ata hud'un ce duka suka amsa mata a tare, Kasantuwar duka mazan basu san ta ba yasa suka bita da kallo dan yanda take a rikice kamar mahaukaciya. Da sauri Ummah ta d'ago kanta daga kukan da take, cikin hanzari ta isa inda Feenat take ta rungume ta da k'arfi tana sauke ajiyar zuciya, Wani sabon kukan taci gaba dayi tana mai tausayin ummanta, lokaci d'aya tabi ta xube kamar ba ita ba. Momy ma tasowa tayi da k'yar ta iya fad'in "Safeenah! Ina kika baro min Afnan? ina fatan kuna tare da ita", Sakin ummah tayi ta koma ta rungume Momy tana ta faman ajiyar xuciya ta kasa fad'in komai, Dady jin haka yasa ya tabbatar da itace k'awar Afnan, mik'ewa yayi ya isa inda take tare da fad'in "Safeenah kiyi hak'uri ki daina kukan nan ki mana bayanin inda yaran nan suke" Nan ma shiru tayi dan bata san ta inda zata fara ba, Alhaji Abdallah yace "ki taimaka mana kiyi shiru kiyi bayanin inda suke, idan basa raye ne ko gawar su muna da buk'atar gani dan mu sallace su" Da sauri Alhaji Ma'aruf yace "haba Alhaji Abdallah! Ya zaka ringa fad'in haka? Insha Allahu yaran mu basu rasu ba, suna lafiya aduk inda suke". Ummah ta share hawayen ta tace "Safeenah ki kwantar da hankalin ki ki mana bayani kinji?", Mami ce ta taso daga kan kujerar da take tace "duk wannan bashi zaisa tayi bayani ba, idan kun kula ai a rikice take, ya kamata a bata lokaci ta samu tayi wanka taci abinci ko zata samu natsuwa", Momy tace "hakane kam, muje kiyi wanka idan ana binki bashin salloli ma sai kiyi". D'akin Afnan momy ta kaita, da k'yar ta iya yin wanka tayi alwala, koda ta fito har momy ta fiddo mata wata doguwar riga ta Afnan, cif ta mata a jiki kuwa sannan ta kama yin sallar isha dan itace kawai a kanta, Da gamawar ta tayi shafa'i da wutri, ta rok'i Allah gafara sosai sannan ta fita parlor da hijabin a jikin ta. Ta samu iyayen sun kasa zaune sun kasa tsaye, kowa yana tunanin inda yaron shi yake, Da fitowar ta duk suka mik'e idon kowa a kanta, kowa cike da son jin inda yaron shi yake. Zama tayi akan carpet d'in dake tsakiyar parlor'n, wani sabon kuka taji amma a haka ta daure ta fara fad'in "Da farko ina mai neman gafarar ku a bisa k'arya da muka maku baki d'ayan mu, birthday'n k'awar mu Kerry ne yau sai sa muka shirya maku k'arairayi domin mu samu kubar mu mu fita, Sai gashi Allah ya gwada mana iyakar shi, ya nuna mana mummunan aikin da muka aikata tun a duniya duk da yake wannan bashi ne na farko ba". Cike da k'osawa Alhaji Abdallah yace "go to the staright point, ina yaran suke yanzu!?" Cikn rawar murya tace "suna *Ajiwa dam,* but am sorry to say, duk basa cikin hayyacin su, tayi kaca kaca dasu dan bana sa ran akwai rayayyu a cikin su" tana kaiwa nan tayi shiru sanadiyyar salatin da suka d'auka duka d'akin. Alhaji Ma'aruf ne yayi k'arfin halin cewa "wacece ita!? Wacece ta mana kaca kaca da yara? Wallahi sai nayi ajalinta matuk'ar ta kashe min yara, yara na 'yan biyu su kenan na mallaka fa, wallahi sai ta raina kanta, zata san ta tab'a iyalin Alhaji Ma'aruf Sale, ku tashi mu tafi wurin ta ni zan maku maganin koma wacece ita, ko ubanwa ya haife ta a fad'in k'asar nan sai ta raina kanta" yana kaiwa nan ya fice sauran ma suka mara masa baya, Ganin za'a tafi abar su yasa Ummah da Feenat ma suka bi bayan su. Amrah and Rerbeeart sk novels, *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page1โƒฃ5โƒฃ *NOTE:-* *kuyi hak'uri na rashin jin mu kwana biyu, hakan ya faru ne na rashin isasshen time, tests nake sosai ga kuma exam muna facing, am in need of your prayers fans, love youh all.* ************** A mota d'aya suka d'unguma suka tafi, sai momy, ummah, mami da kuma Feenat driver ya tafi dasu, Sosai suke gudu nan da nan sai gasu a Ajiwa, a bakin dam d'in sukaje tare da barin fitilun gurin a kunne saboda duhun dake akwai. Sosai suka razana ganin yaran su a babbaje k'asa kamar marasa gata, Wasun su kuka kawai suke dan babu alamar rai a tare dasu musamman ma wanda suka hango can gefen ruwa babu k'afa d'aya. Feenat kuwa jikin ta sai rawa yake dan kar wannan halittar ta dawo dan tana matuk'ar tsoron ta, ta k'ank'ame ummanta sosai tana kuka tana k'ara tuno da yanda aka ringa illata mata abokai. Alhaji Ma'aruf yaci gaba da dube duben inda zai hango yaran shi, daga can nesa ya hangi Reeshat k'ank'ame da MD duk kansu babu alamar numfashi, wata irin k'ara ya saki cike da tashin hankali, da k'arfi yace "idan ba tsoro ba ki fito mana! Wallahi sai na kashe ki in har yara na suka mutu, ki bayyana kanki inji wanene ubanki a k'asar nan!" Yana kaiwa nan yaci gaba da kukan shi kamar k'aramin yaro. Su kuwa sauran suka hau bincikar yaran su, Nan da nan kowa ya gano yaron shi amma fa duk kanwar ja ce saboda babu alamar rayuwa a tare dasu. Sauran da babu iyayen su kuwa nan aka barsu babu galihu, A hankali suka fara jin wata k'ara mai had'e da guguwa tana dosowa inda suke, Sosai hankulan su suka tashi musamman yanda sukaji k'arar tana k'ara tinkaro su, ga wani irin haske daya bayyana a wurin, Cike da tashin hankali suke kallon al'amarin, Feenat kuka sosai take tace "ummah gata nan, ta dawo zata kashe ni, dan Allah kice mata tayi hak'uri ta koma" Ummah ta rungume ta tace "ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu babu abunda zata miki, kici gaba da addu'ah kawai kar ki daina, kar kuma tsoro ya hana ki yi kinji?", Kai kawai ta gyad'a mata idon ta kyam akan guguwar dake nan dunk'ulewa wuri d'aya. Dady ya rungume momy yana fad'in "mun shiga uku! Ga Afnan bata numfashi kuma ga wannan al'amarin, mu gudu kawai mu kai 'yar mu asibiti dan tabbatar da ko tana da rai", Cikin tashin hankali momy tace "insha Allahu ma tana raye, Alhaji ban san ya zanyi ba idan na rasa Afnan, itace 'yar budurwar da nake tak'ama da ita gashi mahaifata ta lalace" ta k'ara fashewa da kuka. Dady yace "ki daina kukan nan kina k'ara tayar min da hankali ne, mu tafi abun mu kawai tunda dama da mota ta muka zo", Daidai sunbi hanya zasu tafi kenan wannan guguwar ta tare su, da k'arfi iska ya ringa dawo dasu cikin mutane, duk k'ok'arin da suke na tafiya amma dawo dasu iskan yakeyi, ga Afnan dauk'e a hannun Dady, momy kuma ta rik'e shi tam saboda tsabar tsoro, tunda uwar data haife ta bata tab'a shiga tashin hankali irin wannan ba, Dole basu dan yanda zasuyi suka tsaya cikin mutanen, shi kanshi Dady'n k'arfin hali ne kawai ya hana shi yin kuka, Dan kuwa Alhaji Bashir yanayin daya ga Nuratun shi ciki dole shima ya shiga tashin hankalin, kuka yake sosai kamar k'aramin yaro, ga wata irin k'ara data sa babu mai jin wani idan yayi magana. A hankali guguwar ta dunk'ule wuri d'aya inda ta koma wasu irin k'anana k'ananan halittu bak'ak'e wulik, exact abunda ya faru a baya yanxu ma shine, haka suka ringa cin junan su har suka zama babbar halitta guda d'aya. Feenat na gani ta tabbatar da wannan halittar ce, nan da nan hankalin ta ya k'ara tashi tana k'ara tuno baya, "tou wai ma me ya dawo dani bayan ta sallame ni? Babu fa wanda yace mu bisu mune kawai mukayi niyya" maganar data ringayi a ranta kenan. Da k'arfi halittar tayi wata irin k'ara wadda sai da komai na wurin ya jijjiga, mutanen wurin kuwa wasu suka ringayin sama da k'asa, basu samu daidaituwa ba har sai da ta tsaya da wannan k'arar ta fuskance su baki d'aya tana k'ok'arin yin magana. Amrah and Rerbee'art sk novels, [4:45pm, 2/10/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page1โƒฃ6โƒฃ Da sauri Ummah ta k'ara matsawa inda take tace "dan Allah kar kiyi magana", Duka hankulan su suka dawo kan Ummah suna mamakin dalilin da yasa ta hana halittar yin magana, A tsorace Feenat tace "nasan dalilin hana ta magana Ummah, amma kuma ya zama dole tayi magana domin sanin musabbabin abubuwan data mana". Duk kanin su kallon Ummah da Feenat suke, babu wanda ya iya yin magana saboda yanda suke cike da tsoro, tun da suke a rayuwa basu tab'a ganin halitta mai girman ta ba, ko a frictions films basu tab'a gani ba, amma sai gasu yau a gaban ta bayan ta illata masu yara. Ummah ta juyo gare su tace "tabbas idan muka bari ta mana magana duk kan mu muna cikin hatsari, duk da bani da tabbas amma wannan aljana ce, ta b'oye halittar ta ne saboda matuk'ar muka ga zahirin ta tou no more us, da zarar muka bari tayi magana har mukaji muryar ta komai zai iya samun mu, saboda jin zahirin muryar ta zai iya saka mu kurumce ko ma mu haukace baki d'aya, ina mai bada shawara da indai magana kuke son yi da ita tou mu rok'e ta ta shiga jikin d'aya daga cikin mu sai ta mana bayanin komai". Kallon Ummah suke sosai saboda furucin ta, Alhaji Ma'aruf daya gama tsurewa yace "indai har sai ta shiga jiki na tou sai dai ta tafi bamu son jin bayanin kuma mun yafe mata", Dady ma bayan ya ajiye Afnan yace "ai wallahi na yafe, mu dai dan Allah kiyi hak'uri ki tafi kawai, ki bar mu mu koma gidajen mu dare nayi sannan kuma bamu san ya lafiyar yaran mu ba", bayan ya miyar da kallon sa ga halittar. Momy ta d'aga kai alamar maganar da Dady yayi gaskiya ne. Alhaji Abdallah yace "bai kamata mu tafi haka kawai ba, mu dai daure ta shiga jikin wanin mu, kunga tanan ma zamu iya samu ta warkar mana da yaran mu data illata", Mami cikin kuka tace "kayya! Babu maganar warkarwa a halin yanzu, kaga fa yanda tamin da yarinya, Ruky na ta baro gida lafiya lau amma yanzu jita fa, *Allah ya wadaren zuwa party ma baki d'ayan shi"* ta k'ara fashewa da kuka. Ummah ta sauke ajiyar zuciya tace "ni nasan bazata iya shiga jiki na ba, amma barin gani", ta koma close to halittan babu alamar tsoro a tare da ita. Sunkuyawa tayi har k'asa tace "idan zaki iya shiga jiki na ki shiga, ki shige ni dan ki masu bayanin komai". Wata irin k'ara ta kuma saki bakin ta a bud'e kamar zata had'iye Ummah, hakan bai sa Ummah taji tsoro ta matsa ba, sai ma cewa da tayi "ke nake jira". Kai tahau girgizawa har a lokacin bata rufe bakin ba, wannan blue hawayen sukaci gaba da kwaranya daga idon ta, a hankali ta soma ja da baya kanta sunkuye k'asa tana girgixa kanta. Mik'ewa Ummah tayi tsaye tace "kun gani! Na fad'a maku bazata tab'a iya shiga jiki na ba, abunda yasa kukaga nace ta shiga d'in nasan wasun ku zasuce k'arya nake kawia dai ina tsoro ne, tou kun gani da idon ku, bazata tab'a koda shafa na ba, haka kuma ina da tabbacin baxata iya shigar Feenat ba, saisa ma kuka ga ita kad'ai ta koma gida ba tare da ta mata wani abu ba". Kai sukaci gaba da jinjinawa alamar sun gamsu da duk kalaman Ummah, Dady yace "tou yanzu miye mafita? Nidai a zahirin gaskiya ina tsoron ta shige ni dan kar tak'i fita, tou wai ma baiwar Allah me yasa ta kasa shiga jikin ki da 'yar ki mu kuma kike tunanin zata iya shigar mu?". Ummah ta ce "ba wai ina da tabbacin zata iya shigar ku bane, ina dai tunanin zata iya d'in ne, akwai wasu abubuwan wanda muka rik'a nida Safeenah wanda ina da tabbacin babu wani abun cutarwa da xai iya cutar damu har sai idan Allah yayi nufin sa akan mu". *Amrah nd Rerbee'art sk novels๐Ÿ“š* [4:54pm, 2/10/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page1โƒฃ7โƒฃ Dady yace "menene wannan abun da kuka rik'a baiwar Allah?" Ummah tace ba wani abune mai wahala ba, wasu kalmomi ne wanda baku kad'ai ba hatta da *Amrah and Rabiatu sk Fans* idan suka rik'e su zasu kub'uta daga duk wani aljani namiji ko mace, kai baki d'ayar al-umman musulmai ma nake maka magana. Kalmomin sune:- *LA-ILAHA ILLA-LLAHU WAHDAHU LAA SHARIKALAHU LAHUL-MULKU WA LAHUL-HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KAD'IR* so d'ari ko wace safiya, sai kuma *A'UDHU BI KALIMATULLAHI TAAMMAAT MIN SHARRI MA KHALAK* itama sau d'ari a yini, sai *AYATUL KURSIYYU, BISMILLAHILLADHI LA YA DHIRRU MA'ASMIHI SHAI'UN FIL-ARDI WALA FISSAMA'I WAHUWAS-SAMI'UL ALEEM, U'IDHI KUMA BI KALIMATULLAHI TAAMMAAT WAMIN KULLI SHAID'ANIN WA HAAMMAT WA MIN KULLU AININ-LAAMAT, FALAQ, NAS DA IKHLAS K'AFA UKU UKU* a kowace safiya, idan mutun yana da yara ma yana masu tou insha Allahu babu abunda zai same sa, hatta da sihiri ko kambun baka yana da wuya ya kama mutun matuk'ar ya rik'i wannan adhkar d'in, sune na rik'a kuma koda wace safiya sai munyi su tare da Safeenah inayi tana amsawa kafin ta fita ko ina, kuma kuma inda zaku rik'e su am sure babu abunda zai iya cutar daku". Dady yace "tabbas wannan wani babban makami ne kuka rik'a, kuma muma insha Allahu daka yanzu mun rik'e su kenan", (ina fatan masu karatu ma zasu rik'e su saboda suna da muhimmanci a rayuwar mu, musamman ma a wannan lokacin da kana baccin ka wasu na maka nasari, Allah yasa mu dace ameen). Ummah tace "tou yanzu ya kukace? A barta ta tafi ko kuwa akwai wanda zai bari ta shiga jikin sa? Nasan dole tana da maganganu a bakin ta, sannan zamuyi da wajewa in har ta shiga jikin mutun zata fita, idan ba haka ba kuma komai na mata ita taja, ina da babban malamin da zai iya salwantar da rayuwar ta, malam Mu'awuya *(na cikin JINNUL_ ASHIQ)* Zai iya da ita, barin ma nasan bazatayi haka ba". Alhaji Abdallah yace "babu komai ni ta shiga jiki na, a adhkar d'in da baiwar Allah'n nan ta bamu na rik'e su sosai, kuma nasan koda ta zauna a jikina baxata dawwama ba saboda zan kasance mai yawan yin su insha Allahu". Dad'i sukaji su duka, Ummah da Alhaji Abdallah suka k'ara matsawa kusa da wannan halittar tace "ga wanda zaki shiga nan, amma ina fatan bazaki cutar dashi ba" kai kawai ta d'aga masu tare da b'acewa b'at daga wurin. Su duka sai da suka tsorata, har umman ma yanzu ta tsorata, Bayan 'yan seconds Alhaji abdallah ya fasa wata irin k'ara da k'arfi kamar ba mutun yayi ta ba, nan ya hau jijjikar jikin sa hawaye na fita daga idon sa. Sun dad'e a haka babu wanda ya iya furta komai kafin ya bud'e baki yace "yaran ku sun illata min duka iyali na (family na), tun daga mamana, babana, yarana uku da miji na, wasu sun mutu a dalilin haihaye su da suka ringayi, babana ya tsufa sosai da mamana, hakan yasa basu da wani k'arfi sosai abu kad'an yana iya yaji masu ciwo, sun mutu baki d'ayan su, sai yaro na d'aya jinjirin da na haifa yau kwana biyu shima ya mutu, miji na da sauran yara na biyu sun ji ciwo sosai. Bayan nan kuma a inda na zauna ina karb'ar gaisuwar mutane ma basu barni ba, sai da suka k'ara kashe min wasu mutanen wasu kuma suka gudu, taya kuke tunanin zan k'yale su? Ni ba muguwa bace saboda bani da ra'ayin shiga bil-adama, Feenat kuwa tafi k'arfi na, a lokacin dana d'auke ta da nufin yi mata wani abu kawai na kasa, kuma ma inda ace na mata wani abun da na cuce tane saboda babu abunda tamin, gefen su take tana dana sanin xuwa wurin da tayi, hakan yasa na bata izinin ta tafi gida, tun kafin ta tafi ta buk'aci na mata bayanin dalilin da yasa na masu haka amma na kasa saboda bana son taji murya na a zahiri, yaran ku kuma babu wanda na kashe sai dai duk sun raunana sosai, zasu farfad'o koba yanxu ba, ku kwashe su ku tafi dasu sannan ku masu gargad'in kar su sake zuwa wurin *party,* koda wani sukaji xaije tou su hane sa da xuwa, ni abun da na masu mai sauk'i ne, na tabbatar da inda wasu ne a cikin jinnu har kashe su zasu iya yi, gashi kuma duk cikin su babu mai neman kariya daga Allah". *Amrah and Rerbee'art sk novels๐Ÿ“š* [5:03pm, 2/10/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page1โƒฃ8โƒฃ Tayi shiru kafin taci gaba da "akwai abubuwa da dama da mu jinnu bama son su, matuk'ar bil-adama suka rik'e su tou komai muguntar aljani bazai iya ma mutun komai ba, kamar abubuwan da matar nan ta lissafa maku, bayan su kuma akwai yawan amfani da man hulba, bamu son warin shi sosai, sannan kuma akwai miski, shima idan bil-adama yana amfani dashi babu abunda jinnu zasu iya masa, yin addu'ah kafin shiga ban d'aki yana makantar mana da idanuwa, akwai su dai da dama wanda idan na tsaya lissafo su zaku iya kwana anan. Kai kuma bawan Allah" tayi nuni da inda Alhaji ma'aruf yake da yatsa tace "ka kiyaye ni! Zan maimata maka cewa ni ba muguwa bace, inda ace ni muguwa ce da ko gawar yaranka bazaka tayar anan ba, kana tak'ama da kud'i kud'in banza gareka! Sai kuje yanzu kud'in ka su warkar maka dasu ai, na haukatar da uwar birthday d'in saboda itace silar komai, sannan kuma ita da saurayin tane suka kashe min iyaye, saurayin nata ma na haukatar dashi, tunda iyayen su masu kud'i ne sai su neman masu magani, bana buk'atar ku sake nema na saboda na gama daku" tana kaiwa nan Alhaji Abdallah yayi atishawa da k'arfi had'e da yin hamma. Koda na duba naga duk jikin su a sanyaye yake har dai Alhaji Ma'aruf da hawaye ke kwaranya daka idon sa, fatan shi dai Allah yasa yaran sa zasu mik'e da k'afafun su. Dady da momy dai kuka ne kawai aikin su, sun tasa Afnan gaba da har yanzu bata da alamar tashi, baccin ta fad'a masu cewa bata kashe su ba da sunce Afnan bata da rai. Bayanin komai suka ma Alhaji Abdallah, wurin 'yar sa ya koma ya d'aura ta akan cinyar sa yana fad'in "why Ihsan? Mesa kika zab'i wannan rayuwar? Mesa kika d'aukarwa kanki wata tarbiyyar da ban sanki da ita ba? Gashi yanzu kin jawa kanki, ga yanda Allah ya maku, wannan ishara ce ga duk masu hali irin naku, musamman matasan yanzu da suka miyar da *party* tamkar ruwan shan su, suma iyayen su k'arya a kowane lokaci kawai dan su tafi *party,* ga yanda tayi dasu *A YINI D'AYA* ta gama da rayuwar su" yaci gaba da kuka sosai yana jijjiga ta. Haka Dady ma ya ringa jijjigar Afnan wai a nufin shi ko zata farka amma babu ko alama, Momy da kuka ya gama cin k'arfin ta tace "Afnan ki rasa irin k'aryar da zaki mana sai ta mutuwa? Ki danganta mahaifin k'awarki da rasuwa? Kenan dama ciwon k'arya kike min a lokacin da nace miki ki tafi islamiya? K'arya kike min da kikace zakije school d'in ku siyen kayan practical? Fita *party* kawai kuke zuwa Afnan? Haka kike so yaran ki su miki Afnan? Na gama yarda dake har abada, na gama yarda da duk abunda zaki fad'a min, ina fatan Allah ya gwada min ranar da kema 'yar ki zata miki haka, bana fatan Affan yayi koyi da mugun halink..." Bata k'arisa maganar ba sanadiyyar toshe mata baki da Ummah tayi tana fad'in "kar ki mata baki Hajiya, kefa uwa ce kuma duk bakin da kuka mata zai iya binta, dan Allah kar b'acin rai yasa ki fad'in munanan kalmai akan 'yarki da kika haifa". Cikin kuka Momy tace "dole ne yasa ni fad'in haka, Afnan taci amana ta taci amanar mahaifin ta, ni a kowane lokaci ina tink'aho da ina bama 'yata tarbiyya mai kyau, ina alfahari da yanda nake basu tarbiyya ita da k'anin ta, ashe duk a banza, tana jefar dasu ne a cikin gida kafin ta fita, aikuwa kinma kanki, 'yar secondary School d'in da kike shekarar k'arshen ma bazaki k'arisa taba aure zan miki, mu koma gida wallahi sai kin fitar da miji, idan ma baki dashi zan kai hoton ki masallaci mai so yazo zan basa sadakar ki" A hankali Afnan ta fara bud'e idon ta, tana d'ora shi akan Momy da sauri ta rufe tana rewinding d'in abubuwan da suka faru tun daga k'aryar da tayi kafin ta baro gida, casun da sukayi da kuma yanda wannan halittar ta ringa yi dasu, wasu zafafan hawaye suka ringa kwaranya daga idon ta, "tou me ya kawo su Momy nan? Ya akayi suka san muna nan? Me ma ya same ni naji jiki na duk babu dad'i?" Maganar xuci ce tayi amma bata san ta fito zahiri ba. *Amrah and Rerbee'art sk novels๐Ÿ“š* [10:42am, 13/10/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page 19-22 "Lokacin tonuwar asirin ku ne yayi" momy ta fad'a tare da watsa mata wani mugun kallo. Duka wurin shiru kake ji babu mai magana in banda sautin kukan Afnan dake tashi, Da k'yar ta iya furta "momy sharrin shaid'an ne dan Allah kiyi..." Bata gama maganar ba sanadiyyar tsawa da ta yi mata da k'arfi dolen ta tayi shiru. Nan iyayen suka hau harhad'a su wuri d'aya suna k'ara tausaya masu musamman ma Md da cinyar shi ta fita daga gangar jikin sa baki d'aya duk jini ya gama b'ata shi. Alhaji Ma'aruf ne yayi waya a asibiti yace a kawo masu mota, ya kwatanta masu inda suke sannan ya kashe wayar yaci gaba da kukan shi, babban tashin hankalin shi bai wuce yanda yaga jikin Reesha duk ya zagwanye ba, babu fata kwatakwata a jikin kamar ya k'one, ga kanshi babu ko alamar gashi yayi fari fat. Reeshat ma can jikin k'arfen shiga ruwan ya gano ta jikin ta duk ya fashe har a lokacin jini bai daina zuba ba, kuka kawai yake yi kamar k'aramin yaro. Ba'a wani jima ba sai ga Ambulance taxo, take a ka fara saka su a cikin motar baki d'ayan su sannan aka tayar suka tafi, suma iyayen bin bayan su sukayi a motocin da suka xo ciki. Nan da nan sai gasu bakin Federal medical center, ciki suka shige basu zarce ko ina ba sai accident and emergency. ******** An dudduba su sosai dan manyan likitoci aka kira dan su duba su amma babu nasarah, Duk wanda ya kamata ama d'inki anyi amma wurin baya d'inkuwa, da zarar an d'inke sai ya dare, su kansu likitocin abun ya d'aure masu kai. Md kuwa duk iya k'ok'arin su sunyi amma abu yaci tura, sun samu sun tsayar da jinin dake fita daga jikin shi amma cinyar baxata tab'a komawa a jikin sa ba, shikenan ya zama gurgu. Nuratu, Shamow da Sally kuwa in banda wari babu abun da sukeyi, idan aka fasa maruran jikin su sai wani ruwa mai yauk'i ya ringa fitowa, sai kuma marurun ya koma yanda yake. Sosai suka tsorata da wannan al'amarin, ga wasun su har yanxu basu farfad'o ba amma kuma suna jin alamar suna numfashi kad'an kad'an. Samir kuwa nashi yafi na kowa illah shikenan yanxu ta raba shi da mazakuntar sa, babu shi babu aure, haka likitocin suka ringa fita dan basu da yanda zasuyi masu. Da sauri Dady ya tari wani likita yace "Dr. Ya ake ciki? Ina fatan an samu nasarah" Kai kawai ya kad'a masa yace "sai dai mu jira zuwa safe in sha Allahu zasu farfad'o, wasu sun farfad'o a cikin su wasu kuma shiru ne, mun samu anyi d'inki amma ya ringa daddarewa, Alhaji akwai al'ajabi a wannan abun, mesa d'inki zaina warwarewa idan anyi shi?", Dady yace "shikrnan Dr. Mun gode sosai sai goben". Momy kuwa ta koma gida saboda har asubah ta kusa gashi kuma Affan shi kad'ai ne a gida. Ummah da Feenat ma sun koma gida da nufin sai da safe zasu dawo. *Gidan su Kerry* *4:56am* Har a lokacin iyayen Kerry sun kasa bacci, babban tashin hankalin ma yanda suke ta neman number d'inta amma yak'i shiga, daga farko tana ta ringing ne ba'a d'auka ba, daga baya kuma sai ma suka daina samun ta kwata kwata. Mom d'in ta banda kuka babu abunda take yi, shima Dad d'in k'arfin hali ne kawai baya so matar shi taga yayi kuka hankalin ta zai k'ara tashi, Ko sanda suke America Kerry bata tab'a kwana wani wuri ba, duk inda taje komai dare bata kwana acan sai ta dawo gida, kuma idan taga alamar xatayi dare sosai ma tana kiran su ta shaida masu zatayi dare sosai dan kar hankalin su ya tashi, wannan dalilin ne yasa suka k'ara rikicewa ganin har asubah ta gabato amma babu ita. K'arfe shida na safe iyayen suka tattaru a asibitin, wanda suka farfad'o d'in su suka bayar da adress d'in sauran ciki kuwa har da na Kerry, Dady, Alhaji Ma'aruf da Alhaji Abdallah suka ringa bin addresses d'in suna sanar wa iyayen yaran, a rikice suka ringa tafiya asibitin suma. Gidan su Kerry ne k'arshe saboda shine wajen gari, horn Dady yayi sai ga mai gadi ya bud'e masu gate suka shiga daga ciki, umurni suka masa da ya shiga yayo sallama da mai gidan. Koda ya shiga ya samu Mom kwance a cinyar Dad kamar zautacciya sai sumbatu take tana kiran Kerry, Cikin girmamawa yace "Oga kayi bak'i", Da sauri Mom ta tashi daga jikin shi tana share hawayen ta, "Je kace gashi nan zuwa" Tafiya yayi inda Mom kuma ta mik'e tace "mu tafi tare, may be ko maganar Kerry ne". Fita sukayi hannun ta rik'e dana Dad saboda wani jiri jiri da take gani kamar zata fad'i tsabar kukan da tasha. Hannu Dad ya mimmik'a masu suka gaggaisa, "Ince dai ko lafiya" Dad ya fad'a yana kallon Alhaji Ma'aruf. "Ehh tou, lafiya ba lafiya ba, wata magana ce muke tafe da ita" Alhaji Ma'aruf ya fad'a. "Duk kan mu sai dai mu taru muyi hak'uri mu mik'awa Allah al'amarin sa.." Dady bai gama maganar ba Mom tayi saurin katse sa da cewa "kar dai kace min 'yata Kareemah wani abu ya same ta" cike da firgici idon ta kan Dady. "Duka yaran mu da suka je wurin Party'n ne suka had'u da wahalar rayuwa, sun tab'o ma kansu *JINNU* ne, so kun san su kuma basa yafiya sai sun d'auki fansa, indai aka tab'a su, yanzu dai maganar da nake maku suna asibiti su duka yaran, wasu sun farfad'o wasu kuma har yanzu shiru ne, shine muka karb'o address na wanda basu tashin ba dan mu sanar dasu saboda mun san hankalin iyayen su ba a kwance yake ba, yara tun jiya sun bar gidajen su amma shiru basu dawo ba dole hankali zai tashi". Tuni wani kukan ya kufce ma Mom, da k'yar ta iya furta "ai dama na fad'a maka haka, ni nasan kerry ba lafiya ba, bata tab'a zuwa wani wuri ta kwana ba" taci gaba da kuka jikin ta sai rawa yake. (Inda zaku san akwai k'arancin ilimin addini har yanzu fa daga Dad har Mom d'in babu wanda ya ambaci sunan Allah). Tasu motar suka shiga suma take suka rankaya sai FMC. Nidai Amrah biye nake dasu dan ganin yanda iyayen kerry zasuyi idan suka samu labarin 'yar su ta haukace, gasu da jahilci kuma jahilin mutun bai iya d'aukar k'addara ba. Muje zuwa dai. *Amrah nd Rerbee'art sk novels๐Ÿ“š* [10:54am, 13/10/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page 23-25 D'aya bayan d'aya suka ringa farkawa duk kansu da hawaye bushe a fuskokin su ga wani irin rad'ad'in ciwo dake damun su. A daidai isowar su Dad d'akin ne yayi daidai da farkawar Kerry, Da k'arfi ta fasa wani irin ihu wanda sai da duka d'akin ya amsa, take kuma ta k'yalk'yale da dariya tana kallon su. Gadon da take kai ta fara lilawa da k'arfi kamar zata karya shi, zanin dake shimfid'e jiki ma ta cire ta nannad'e shi ta jefa shi sai kan Mom d'in ta da k'arfi. Kayan jikin ta kuwa tuni ta fara k'ok'arin cire rigar amma saboda yanda ta kama ta sosai yasa ta kasa cirewa, ganin ta kasa cirewa yasa ta fashe da kuka wanda babu ko alamar hawaye, can kuma ta k'ara fashewa da dariya mahaukaciya dai sak. Hankalin Mom da Dad ya k'ara tashi sosai ganin abunda ke faruwa, da an ganta an san bata da hankali, gashin kanta duk tayi tuzu tuzu dashi lokaci d'aya kamannin ta suka soma sauyawa, Da sauri Mom ta fara k'ok'arin nufar inda take amma ta bud'e baki tace "idan kikaxo min nan sai na kashe ki, ni ban sanku ba" ta b'ata fuska kamar da gaske bata san sun ba. Duka hankali ya koma kan su, ganin yarinya mai gata wurin iyaye ga abun da ya same ta yasa Afnan fashewa da wani irin kuka mai tsuma zukata. Ana cikin haka ne sai ga wani likita ya shigo, Cike da damuwa yace "ina iyayen yaran nan da suka had'e wuri d'aya?"(Mc da Dj), Da sauri suka ce "gamu", "Tou gaskiya munyi bakin k'ok'arin mu dan ganin mun raba su amma abun yaci tira, mafita d'aya ce nake tunanin in har akayi tou za'a samu solution d'in abun", Da sauri sukace "mecece mafitar likita?" "Ina ganin dole sai dai a raya d'aya d'aya kuma ya mutu saboda yanda aka matse su da k'arfi yasa komai nasu ya had'e, har xuciyar su ma ta had'e ta zama amfani d'aya take yi, idan ba haka ba kuma sai dai suci gaba da rayuwa a haka har lokacin da wani zai mutu cikin su sannan a raba", Malan Liman (mahaifin Dj) yace "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Yaron yau kenan! Ka haife shi baka haifi halin sa ba, kullun nasiha ta d'aya da yaron nan akan yaji tsoron Allah saboda a kowane lokaci mutuwa zata iya riskar mutun, ashe abun da yake aikatawa kenan, ishara ce Allah ya nuna masu tun a duniya, kuma ma Allah yana son su da rahama tun da har haka ta kasnace, da baya son su da rahama da haka zai barsu suci gaba da aikata alfasha har sanda mutuwar su zata zo, kuma ishara ce ga sauran al'ummah masu halin iri nasu". Alhaji Amiru (mahaifin Mc) yace "ka daina wannan maganar malan, yanzu miye abun yi?". Likita yace "kuje kuyi shawara a tsakanin ku, duk yanda kuka yi zaku iya samu na Office d'in shine na biyu daga gefen dama idan kun fita daga nan" yana kaiwa nan ya fice hannun shi rik'e da takardu. Sautin kuka kawai kake ji a cikin d'akin, iyayen kerry kuwa sai kallon ta sukeyi kamar ba ita ba, a rud'e mom tace "Alhaji wannan ba 'yata bace, sun canja min 'ya wallahi, ni yarinya ta lafiya lau ta baro gida babu abun da ya same ta, saboda me za'a ce min wai itace wannan? Ban yarda ba sun dai siyar min da yarinya shine suka musanya min ita da wannan, 'yata bazata tab'a cewa zata kashe ni ba" wasu zafafan hawaye sukaci gaba da ambaliya daga fuskar ta. Dad yace "haba Mom Kerry! Mesa zaki fad'i haka? Baki ji abun da sukace ya samu yaran bane? Bafa ita kad'ai ta samu matsala ba, yanzu kika ji wani likita yana bayani akan abun da ya samu wasu daga cikin yaran, kiyi hak'uri ki daina kuka, ko birnin sin (China) ne zan kai Kareemah indai zata samu lafiya, ki daina kukan nan bana so kina yin sa", Cikin damuwa tace "inda gaske ne ita waccan mesa babu abunda ya same ta?" Tayi nuni da Feenat dake zaune kusa da ummanta. "Nace ki daina maganar nan fa, kiyi shiru mana Kerry zata samu lafiya" (duk maganar da zasuyi basa ambaton sunan Allah). Shiru d'akin yayi cike da damuwa Dady yace "tou wai ma menene asalin k'ungiyar nan tasu ne?", Alhaji Abdallah yace "nima dai tambayar da nake wa kaina kenan, su wannan yaran har sun san wai su fitar da wata k'ungiya a tsakanin su" Feenat tace "yanzu kuwa zan baku labarin asalin k'ungiyar *AREWA STARS* da dalilin bud'e ta da kuma shugabannin k'ungiyar". Hankalin kowa ya koma kan Feenat dake share 'yar k'wallar data soma fito mata, Hankali na ya tashi dana duba naga ruwan biro na ya k'are gashi kuma ina son d'auko wa fans rahoton komai, da sauri nacewa sis R. "Sis kije ki siyo min pen yanxu dan kar labari ya wuce mu", Fuskar ta ta b'ata tace "ke sis Amrah kin san fa biro tayi tsada yanzu, gaskiya sai kin kawo kud'i na gaji da siye da kud'i na", D'an murmushi na mata nace "ki karb'o bashi zan baki kud'in idan mun koma gida". Murmushi tayi sannan ta nufi hanyar shago domin siyo biro d'in. Ku biyo mu idan mun siya wata zaku jimu insha Allahu. (lol..) *Amrah nd Rerbeeart sk novels๐Ÿ“š* [5:18pm, 16/10/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page 26-30 "Asalin k'ungiyar ta samo tushiya ne tun muna zana jarabawar jss, Shareef da Shareefat wanda suke twince ne masu k'aunar junan su da had'in kai tsakanin su. Tare ake kawo su makaranta kuma tare ake zuwa d'aukar su, duk abunda Shareef ya samu baya cin shi sai ya kawo ma Shareefat haka itama take. Ni kuma k'awata d'aya wato Afnan, duk da nake marainiya baba na ya rasu tun ina k'ank'anuwa ta hakan bai hana mahaifiya ta kaini wannan babbar private School d'in ba mai suna *SALDEFI INTERNATIONAL SCHOOL,* duk yaron da zaka gani a makarantar to d'an masu hali ne in banda ni da rufin asiri ne kawai kuma mahaifiya ta tana so na samu ilimi mai kyau. Afnan na k'auna ta sosai nima kuma ina k'aunar ta, har gidan su an sanni nima kuma gidan mu an santa. Sai dai kuma akwai banbancin halayyya tsakani na da ita saboda ita tana da son huld'a da mazan class d'in mu, tana yawan yi min fad'a wai na kasa in waye har yanzu gashi ina da kyau maza na son yi min magana amma bana basu fuska, sai dai kawai na mata murmushi idan ta fad'i haka. Kwatsam wata ranar da zamu kammala zana jarabawar jss muna zaune da Afnan akan window sai ga wani yaro yaxo kusa damu, hannu ya bata suka tafa kamar yanda suka saba ni kuwa na b'ata fuska tamkar ban tab'a dariya ba. "Wai Afnan wannan k'awar taki bata dariya ne ita?", Kallon ta ta juyo gare ni tace "Feenat wai? Tana yi mana me ka gani?", "Kawai dai yanayin ta na gani haka, amma ya kamata ta saki jiki damu tunda dai duk ana tare" ya k'arisa maganar da kanne mata ido d'aya. Shareef da Shareefat ne tafe hannun ta rik'e a nashi suka gitta ta inda muke, da sauri Afnan tace ma yaron "nikam Shamow dama ina son tambayar ka akan wancan yaran da suka wuce?", "Wai Shareef da Shareefat kike nufi?", "Ban san sunan su ba, amma pls ina so ka bani labarin daka sani game dasu, haka kawai yaran suna burge ni da alamar saurayi da budurwa ne" Saurin dafe bakin shi yayi yana k'ok'arin yin dariya "inji wa ya fad'a miki haka? Twince ne fa, ke baki ga komai nasu iri d'aya bane? Yaran gidan former Minister'n petroleum ne Alhaji Ma'aruf Sale, yaran 'yan gata ne da kike ganin su, suna k'aunar junan su sosai, kamar yanda kika gansun can to haka suke ko a class, koda yake ba class d'in mu d'aya dake ba saisa baki san su sosai ba har kike fad'in haka, babu malamin daya isa ko fad'a yayi ma d'ayan su, idan kuwa wani malami yayi kuskuren haka tou ranar baxai kwana a makarantar ba sai an kore shi, kowa yana tsoron tinkarar su da sunan magana saboda ko murmushi basu yi sai ga junan su, nima tun farkon zuwan su makarantar nan nake son masu magana amma hakan bata yiwuwa saboda sun fi k'arfi na, akwai wani yaro d'an ss2 daya ma macen magana wai yana son ta wallhi baki ga yanda yaron ya wulak'anta ba sai da ya bani tausayi, saisa kawai na hak'ura na k'yale su, ni wallahi tsoron su ma nake". Dariya Afnan ta k'yalk'yale da ita tana tafa hannu "amma dai ka bani kunya guy, kai yanxu duk tak'amar da k'wambon amma ka kasa tinkarar wasu, ni kuwa wallahi sai na masu magana sai dai duk abun da zai faru ya faru, kowa yana ji da nashi ai, su idan uban su former minister ne ni nawa Commissioner of police ne, bari ma ka gani" mik'ewa tayi da sauri ta bi bayan su tana k'ok'arin shiga gaban su, nima nabi bayan su jiki na sai rawa yake dan bana so wani abu ya samu Afnan. "Hi" Afnan ta fad'a bayan ta shiga gaban su. "Hello" Reesha ya miyar mata da amsa, "Am Afnan by name", tare da sakin d'an murmushi. Kallon banza suka watsa mata kafin macen tace "and so?", "I just want you 2 to be my friends, ina yawan ganin ku a School d'in nan kuma kuna burge ni, and I decided kawai na maku magana yau, babana shine commissioner of police a halin yanxu", Da sauri Shareef ya sakar mata fuska jin ko waye mahaifin ta yace "am Shareef and Shix Shareefat, nyc to meet you", "Nyc to meet you too dear, pls ko zan iya zama frnd d'in ku in ba damuwa?", Shareefat tace "why not? You can dear" Murmushi Afnan ta masu tare da mik'awa Shareef hannu suka gaisa sannan ta mik'a ma Shareefat, nan ta masu introducing d'ina da Shamow take suka hau hira kamar dama sun saba. Haka muka kasance mu biyar har lokacin da mukayi hutun jss, Afnan na zuwa gidan mu nima ina zuwa nasu, duk da talaucin mu bai sa ta raina mu ba, tana yawan bani labarin Reesha da Reeshat kamar yanda ta miyar masu da suna. Haka ta k'agara hutun mu ya k'are saboda sabuwar rayuwa da take burin yi idan mun koma, Shamow kuwa shi yayi naming namu da *5 STARS* saboda yanzu mun had'e kan mu sosai kamar mun dad'e da sanin junan mu. *Amrah nd Rerbee'art sk novels๐Ÿ“š* [5:25pm, 16/10/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page 31-33 Ranar da muka koma hutu kuwa munyi farin ciki saboda a class d'aya aka had'e mu, Shamow ya kawo wata Friend d'in shi Nuratu yace "shix my frnd wai tana da sha'awar kasnacewa a cikin mu ne, shine nace zan kawo ta ku gani", Reesha yace "tou muna da dokoki sai idan ta aminta dasu sannan zata shiga cikin mu" Da sauri ta d'aga kanta tana kallon shi, "K'ungiyar mu duk wanda ya shiga cikin ta zai mana alk'awarin bazai tab'a fita ba har sai lokacin da mutun zayyi aure, sannan kuma duk lokacin da muka yanke hukunci a abu babu wanda ya isa yace a'a, zamu ringa tallafawa junan mu idan wani yana buk'atar taimako, idan wani zayyi *BIRTHDAY* dole mu had'a kai mu faranta masa rai, kin yarda?", "Ehh na yarda wallahi na amince" "Good, miye Sunanki?", "Sunana Nuratu Abdullahi", "Kinyi register daga yanxu kin shiga cikin mu". Nidai haka nan nake cikin k'ungiyar ba wai dan ina so ba sai dan bana so na b'atawa Afnan rai dan naga itace silar k'ungiyar. Shamow yaji dad'i sosai yace "tou amma ya kama ta mu canja suna ko?" "Ehh ya kamata gaskiya" Reeshat ta fad'a. "Why not mu saka *AREWA STARS?* wato taurarin arewa", Reesha ya bayar da shawara. Tafa hannu duka mukayi saboda sunan yayi dad'i sosai. ******* Haka mukaita k'ara yawa har lokacin da muka kai mutun 15, daga nan Reesha yace a rufe shigar da mutane haka nan saboda idan mukayi yawa sosai abun bazayyi dad'i ba za'ayi ta samun sab'ani. Hakan kuwa mukayi bamu k'ara d'aukar kowa ba duk da akwai mutun uku da sukayi requesting amma akayi rejected nasu. Wata rana English teacher'n mu ya shigo shine first period ya fara lesson mu kuwa muna baya muna meeting akan *Birthday* d'in Iby dake gabatowa, wani taku muka fara jiyowa na takalmi tun daga farkon class, a tare muka d'aga kai mukayi duba ga wata kyakkyawar budurwa sanye da sabbin uniforms d'in ta, skirt d'in ta ko guiwar ta bai rufe ba sai d'an hijabi akan wuyan ta, hannun ta na jan wani d'an trolley bag k'arami irin wanda ake saka littattafan makaranta. Duka hankalin 'yan class d'in ya koma gare ta saboda wani kallon raini da take watsa ma kowa, Baki ta tab'e tare da zare dark glasses d'in dake idon ta tace "excuse" Shi kanshi malamin sai da ya tsorata da ita, dan daga ganin wannan ba xatayi kunya ba, nan ta hau yi masa bayani cikin British English nata cewa Principal ya gwada nata nan class d'in yace taxo, sosai turancin yarinyar ya burge shi, take ya gwada mata baya yace ta zauna acan saboda duk gaban a cike yake, bayan kuwa mune kad'ai saboda kowa yana tsoron mu a class d'in yasa babu mai iya tinkarar wurin mu ya zauna. *Amrah nd Rerbee'art sk novels๐Ÿ“š* [12:31pm, 20/10/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page 34-35 *We Dedicated this page to ```Pharty KK``` you always pray for me, tanks alot for the caring, Amrah loves youh much๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜* A yatsine ta ringa kallon mu tana jira mu matsa mata wuri ta zauna, kallon raini mu duka muka bita dashi kamar yanda ita ma shi take mana, har a lokacin English teacher'n mu bai daina kallon ta ba, ganin mun k'i bata wuri yasa yace "hey! Two of you let her sit down mana, shix a new commer fa you have to welcome her", Da sauri Afnan ta kalle shi tana k'ok'arin yin magana ya d'ora yatsun shi akan lab'b'an sa da nufin baya so tayi magana, gunguni ta hau yi tare da matsawa ta shige jikin Shamow da shima ya kasa kauda kallon shi daga kan Kerry. Bayyanannen tsaki tayi tare da harar Afnan sannan ta zauna teacher yaci gaba da lesson d'in shi daga inda ya tsaya. Da mamaki sai ga Kerry ta fiddo iphone 6s+ tana latsa, duk kan mu mun tsorata da ganin wayar saboda zuwan wayar kenan Nigeria, ban tab'a kallon ta a zahiri ba sai yanxu. Bayan an tashi break fast duk aka fita aka barmu zaune muna ta surutu, itama Kerry d'in bata fita ba sai latsar wayar ta take yi, yaron da muka aika ya siyo mana moi-moi ne ya shigo ya same mu "naje wai yau ba'a kawo moi-moi ba sai dai fried rice" tsawa Reesha ya daka masa tare da fad'in "ba ance daga Crispy ake kawo ta ba? na baka enough money ka hau mashin ka siyo mana mana? Ko so kake har a dawo bamu ci abinci ba?" Da sauri yaron ya fita dan yana tsananin tsoron Reesha, dama saboda aike yasa aka d'auko masu hayar shi kullun yake zuwa makarantar baban su yana biyan shi albashi duk wata. har a lokacin Kerry bata daina latsar waya ba, kira ta latsa bayan an d'auka ne tace "mom ba'a kawo min breakfast bafa" a shagwab'ance. Ban san me aka fad'a ba daga d'aya b'angaren sai naji tace "ok mom am waiting" ta tsinke wayar. Banda kallon ta babu abunda muke yi, daga ganin yarinyar big gal ce, Afnan dai kallon raini kawai take aika mata, ni kam burge ni ma tayi saboda shix very classic, ga kyau da komai ta had'a. Kafin d'an aiken mu ya dawo aka kira Kerry a waya ta d'auka "yes" tayi shiru daga nan kafin ta kuma cewa "a kawo min mana ina class, ka tambayi Principal yasan inda ya gwada min na shiga ai, ni bazan iya fitowa ba" ta tsinke wayar taci gaba da latse latsen ta. Da rawar jiki principal ya shigo hannyn shi rik'e da basket had'ad'd'en gaske, har k'asa ya duk'a sannan ya mik'awa Kerry shi, "keep it there" ta fad'a tare da nuna masa d'an nesa da ita. Ajiyewa yayi sannan ya fita yana d'an waigen ta. Da k'arfi muka d'auki shewa muna kallon shi, a kunyace ya fita ba tare daya sake waiwayowa ba. ******** Haka dai mukaci gaba da rayuwa da Kerry ba tare da mun san ko sunan ta ko tasan namu ba, ko k'ala baya had'a mu da ita, babban abunda ya bani mamaki bai wuce yanda take da sharp brain ba, so da yawa idan ana lesson hankalin ta baya ma wurin malamin amma da zarar ya tambaye ta sai ta bashi answer, su kansu malaman suna mamakin k'walwa irin tata. Wani lokacin har Iby yana cewa zayyi mata magana amma sai Afnan ta hana shi. Gata da yawan waya da maza, kullun aka tashi daga skul sai tayi AP da namiji kuma manyan yara take tarayya dasu. Da haka har muka kammala SS 1 zamu shiga SS 2, bayan an dawo hutu ne muka fara ganin sauyi daga Kerry, saboda kullun tazo sai ta bimu one by one ta bamu hannu mun gaisa har da su Iby kamar yanda taga muna yi dasu. Wani lokacin har fira take k'ok'arin jana dashi saboda ta kula duk na fisu sauk'in hali. Bayan sati biyu da dawowa hutu ne ta tare ni wai tana so ta shiga group d'in mu, dana fad'awa su Reesha yace "ai an riga da an rufe shiga k'ungiyar mu, wasu ma suna so amma mun hana su shiga" Iby ya katse shi da cewa "kai guy yarinyar nan fa big gal ce, wallahi tunda ta yarda duk wani jiji da kanta ta nemi mu saka ta is good kawai a saka ta d'in, sauran wanda suka nema mutun hud'u ne ko uku suma sai a saka su, kaga mun cika 20 kenan daga nan sai mu rufe d'aukar kowa, koya kuka ce?" Mu duka muka had'a baki mukace "hakan yayi" Reesha yace "to shikenan ayi hakan" Washe gari na shaida ma Kerry komai, taji dad'i sosai ta kuma bayyana min hakan, bayan anyi break tayi introducing kanta a wurin mu muma muka mata namu, tun daga nan ta shiga cikin mu har ya zamo kamar ma itake leading namu, har Reesha sai abunda Kerry ta fad'a yake ji saboda kusan komai itace take mana, idan wani party za'ayi itake d'aukar nauyin komai na party'n, ko abinci muka daina siye sai ita take siya mana. Wani lokacin ma idan muka rasa idea'n k'aryar da zamuyi a gida mu fita itace take fad'a mana yanda zamuyi dan duk ta fimu k'walwa. Haka rayuwar mu taci gaba da kasancewa, amma a koda yaushe ina yawan neman gafarar Allah saboda ina cin amanar ummanah, duk lokacin da zan fita sai tace min inji tsoron Allah, haka kuma aduk lokacin da na mata k'arya naje wani wuri nakan tuno da furucin ta, lokaci d'aya naji bana son rayuwar da nake ciki, na tsani kaina a doron k'asa. Wannan fitar da mukayi ta k'arshe ma sai da nace baxanje ba amma Afnan tace inhar banje ba sai ta tona min asirin abubuwan da nake yi a wurin ummanah, tsananin tsoron ummah da nake yasa na bata hak'uri banda yanda zanyi dole sai da na bisu, wannan shine asalin k'ungiyar *AREWA STARS"* Ta k'arisa maganar tana kuka sosai cike da nadama. *Amrah nd Rerbeeart sk novels๐Ÿ“š* [1:06pm, 20/10/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page 36-40 Duka iyayen sunyi shiru sun ma rasa abunda zasu fad'a, yaran kuwa in banda kuka babu abun da suke yi ga azabar ciwo da ta addabe su, ga DJ da MC ance baza'a iya raba su ba dole sai d'aya ya rasa rayuwar sa. MD ma shike nan ya rasa k'afar sa d'aya ya zama gurgu. _(Allah sarki! Haka rayuwar take, ba'a gama halittar d'an adam ba har sai lokacin daya kwanta damar sa, wallahi wannan rayuwar abun tsoro ce, yanzu zaka ganka da lafiya kuma yanxu xaka iya rasa ta, yanxu kike da k'afa yanzu Allah yana iya yin yanda yaso da k'afar, haka kuma zaki ganki lafiya lau da idon ki Allah zai iya sawa ki rasa idon a lokaci d'aya, wallahi ko wannan ya ishe mu ishara akan muji tsoron Allah, mutuwa bata alerting idan zataxo, wallahi wannan labarin dana rubuta kusan abubuwan da suke faruwa kenan da gaske, muna fita daga gidaje ama iyaye k'aryar xa'aje wani wuri amma inda za'aje d'in daban yake, shin bamu gudun Allah ya zare mana rayuwar mu a inda mukaje d'in? Kar ku manta cewa manzon tsira Allah ya k'ara masa aminci yace "za'a tada mumini akan abunda ya mutu yana aikatawa" shin zamuso a tashe mu muna aikata alfasha? Duk abunda muke aikatawa fa Allah yana ganin mu, idan a tunanin mu ai mun ma iyayen mu k'arya bazasu tab'a gane wa ba tou ko mun manta cewa akwai RAQIB DA ATIB? wanda ranar k'iyama zasu bada shaidar abunda duk muka aikata, mun manta cewa k'afafuwan mu zasu bada labarin inda muka taka mukaje dasu? Mun manta cewa hannuwan mu zasu bada labarin abun da muka tab'a dasu? Mun manta da cewa bakin mu zai bada labarin abunda aka fad'i dashi ko akayi dashi? Mun manta da cewa ido zai bada labarin abun da aka kalla dashi? Mun manta da cewa ba'ayiwa Allah dabarah, baki d'aya rayuwar yanzu tarbiyyar yaran mu ta tab'arb'are, na kirkin mu k'alilan ne, wallahi muji tsoron Allah, mu dage yiwa kan mu da iyalan mu adduo'i'n shiriya, wallahi zaman kabari kanshi abun tsoro ne, zaman kad'aici kenan, barin ace tsayuwar k'iyama, ranar da wayon ka da dabarar ka bazai amfane ka da komai ba, ranar da uwa da uba ba tamu suke ba kowa ta kan sa yake, Ya Allah kasa mu cika da imani, Allah ka shiryar mana da duk wanda suka b'ata)._ Da kuka da komai Dad da Mom suna ji suna gani aka d'auki Kerry bayan an d'ad'd'aure ta aka nufi psychiatric (asibitin mahaukata) da ita. ```Bayan wata daya.``` Duk wata k'asa da suke tunanin idan sun kai Kerry zata samu lafiya sunje amma abun babu sauk'i, kud'i kawai suke kashewa amma abu yaci turah, daga k'arshe dai haka suka hak'ura suka dawo da ita Nigeria a asibitin mahaukata saboda xama da ita bazai tab'a yiwuwa ba, duka take sosai ga surutai marasa ma'ana da take yi tana fad'in "ai duk laifin ku ne, kune baku bani tarbiyyar kirki ba, inda kun kula dani da tarbiyyar kirki ai da komai bai same ni ba" sai kuma ta fashe da kuka, hakan yasa kawai suka hak'ura suka miyar da ita asibitin. Su kuwa su Afnan abu babu sauk'i, ciwon ana magani amma kamar bayi ake ba, kulkun k'ara rub'ewa yake yana wari, Momy tace ta fiddo miji a mata aure amma duk a samarin ta wanda tama magana a waya da murna zasu amince, amma da zarar sunxo sukaga yanda take ga wari tana yi sai su tafi bazata sake ganin su ba, kullun cikin damuwa take. Samir kuwa ya warke sosai dan shi kad'ai ne ma ya warke, amma abun haushi da takaici shine bashi da mazakunta, bazai tab'a auruwa ba har abada, in ma yayi auren babu macen da zata iya zama dashi. *Amrah nd Rerbee'art sk novels* ๐Ÿ’€ *A YINI 'DAYA* ๐Ÿ’€ ๐Ÿ‘น๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€๐Ÿ‘น ๐Ÿ‘บ *ยฎNWA* *Na Princess Amrah* *Da Rabiatu sk msh* Page 36 *```KARSHE```* ๐Ÿ’“๐Ÿ’“๐Ÿ’“ haka dai rayuwar taci gaba da tab'arb'are masu, raunukan su sai k'ara rub'ewa suke abun k'yama da tausayi, Ummy banda wari babu abunda takeyi, ko Mamin ta ta daina shiga d'akin da take, in ma abinci zata kai mata sai dai ta ajiye daga bakin k'ofa ta rarraho ta d'auka. Afnan kuwa Momy ta aika da hoton ta masallatai ayi tallar ta, nan da nan kuwa aka fara rububin ta, amma da mamaki duk wanda yazo yaga fuskar ta da yanda take sai ya tafiyar sa. Kamar kullum Momy ce zaune ta buga tagumi ta tsurawa Afnan ido tana kallon ta cike da tausayi, sallamah akayi Momy tayi saurin amsawa tana kallon mai shigowa, Dady ne ta gani hannun shi rik'e da Affan sanye da Uniforms alamar daga makaranta ya d'auko shi, "Oyoyo momy na" ya fad'a tare da isowa wurin Momy. "Sannu da dawowa Alhaji" ta fad'a bayan ta rungume Affan a cinyar ta tana cire masa safar k'afa. "Momy wai yaushe Yaya Afnan zata warke ne?", D'an murmushin yak'e ta mashi kafin tace "insha Allahu zata samu lafiya yaro na, ka ringa saka ta a addu'ah kaji?", Kai ya d'aga cike da tausayin 'yar uwar sa. "Assalamu alaikum" akayi sallamah, Dady ya amsa da "wa alaikumussalam, Mati ya akayi ne?", "Yallab'ai kayi bak'o", "Bak'o? Waye ne?", "Wani gurgu ne yallab'ai, yace ayi masa sallamah da kai", "Gurgu? To kace ina zuwa". Kallon shi ya miyar ga Momy yace "Maman Afnan barin fita inga mai nema na". Bayan ya fita ya samu wani gurgu ne ya mik'a masa hannu suka gaisa, "Bawan Allah meke tafe da kai?" Dady ya fad'a yana kallon gurgun mai ido d'aya. "Sunana Sani, dama yallab'ai naga wani hoto ne a masallacin da nake aiki, so ina da ra'ayin auren yarinyar indai babu damuwa" Shiru Dady yayi ya k'are masa kallo sosai sannan yace "ehh to! Nidai a wuri na babu damuwa, amma ka shigo mu shiga ciki idan yarinyar taji tana son ka sai ayi binciken komai sannan a d'aura aure". Murmushi yayi sannan yabi bayan Dady daya fara shigewa cikin gida. Bayan sun shiga ciki ya gaishe da Momy cikin girmamawa itama ta amsa masa da sakin fuska. Dady yayi ma Momy bayanin abunda yake tafe dashi kai tsaye momy ta goyi bayan abun, Afnan ma dake kwance take ta amince dashi duk da yanda yake d'in. ***** Shirye shirye sosai suka kankama na bikin Sani gurgu da Afnan, duk da ba wani abu za'ayi ba walima ce kawai za'ayi. Ranar jumu'ah aka d'aura auren su amarya ta tare a babban gidan ta da Dady'n ta ya mallaka mata ita da mijin ta. Feenat kuwa taci gaba da zuwa makarantar ta har sun fara zana jarabawar k'arshe ta sakandire. Kerry kuma har yanzu abun shiru babu sauk'i, gashi kuma sun k'i zuwa wurin malamai duk da shawarar hakan da ake basu. *AREWA STARS* dai a haka suka k'are da tab'arb'ararriyar rayuwa, wannan ishara ce ga masu hali irin nasu, masu yawan zuwa party ba tare da iyayen su sun sani ba, ina fatan wannan gajeren labarin zai zama fad'akarwa ga al'ummah musulmai har ma da wanda ba musulman ba. ALHAMDULILLAH!!! Duk abunda yayi farko zayyi k'arshe, muna godiya ga Allah mai kowa mai komai da ya bamu ikon kammala wannan labarin namu, kurakuran dake cikin labarin Allah ya yafe mana,inda muka yi daidai kuma Allah ya bamu ladar. Muna godiya ga masoyan mu da suka bibiyi labarin har ya kaiga k'arshe irin su:- ```Rukayya Auwal,``` ```Faty KK``` ```Husnah Ibrahim,``` ```Aysha Khalil,``` ```Amman Suraj``` Da da da da, lissafo ku ba abune mai sauk'i ba, sai dai muce muna k'aunar ku akoda yaushe, kuci gaba da kasancewa damu a littattafan mu na gaba. Jinjina, fatan alkhairi, godiya su tabbata ga K'ungiya mai albarka *```NAGARTA WRITERS ASSOCIATION```* Allah ya bar zumunci ya k'ara had'a kawunan mu amin. ```ZARAH~B~B``` *godiya da jinjina mai tarin yawa a gare ki, kin nuna mana soyayya kuma kina kan nuna mana ita, Allah yabar mu tare ya k'ara miki baseerah.* All groups members and admins na group d'in da muke muna gaishe ku, tsayawa lissafo ku ba abune mai sauk'i ba, sai dai mu maku godiya da bibiyar labarinmu da kukayi. 'Yan uwan mu writers muna godiya a gare ku, Allah ya raba mu da sharrin mahassada da mak'iya. Amrah and Rabi'atu sk novels group mun gaishe ku da babbar murya, Allah ya barmu tare ameen. Kuci gaba da kasnacewa dani Amrah a cikin novel d'ina mai suna *UMMU HAYDAR* idan na kammala exam insha Allahu. Amratu A Mashi and Rabiatu Sk msh AKA Amrah da Rerbee'art ke cewa mu huta lafiya. Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels