Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels [11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *ABU BILAL!!!* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *_______________________ ______________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation All thanks to Allah SWT for the privilege to start this book,special greetings to my siblings ,cousins and My lvly fans that have waited so long for Majidadi,and now am back da wani saban salon,I know u will luv it,cos I am in luv with it too,ABU BILAL daban yake da saura.😘😍😀 FREE PAGES PAGE 1 Tafiya takeyi da sassarfa ,idanuwanta dake sanye cikin farin medical glasses ɗinta wanda yake tamkar na gayu ya kuma ƙawata fuskarta takai dubanta ga tsadaddiyar Agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta,ɗan zaro dara-daran kyawawan idanuwanta tayi tana kallon lokaci da alamu ta makara sosai.kayan jikinta na kalla dan ganin irin saurin da takeyi sanye take cikin uniform blue wando da hijab doguwa har ƙasa mai hannu sai farin ɗankwali wanda duk yarda ta janyoshi be hana gashin kanta bayyana ba,wanda yake kwance lub a goshinta harya kusa haɗewa da giranta,a kafaɗarta kuma irin jikkarnan ta goyo da mata ke yayine saƙale ta saka hannu ɗaya ta bar ɗaya yana yawo a bayanta.Halimatu Doguwace daidai misali bata da ƙiba ko kaɗan sai dai kuma jikinta ko ina a ciccike yake bata da irin farin nan sai dai tana da matuƙar kyau komai nata kamar ita tayi kanta,Halimatu bazata wuce shekara sha bakwai ba.A daidai bakin layin ta tsaya tace "washh Allah Khadija wallahi na gaji"ta ƙare maganar tana kallon Khadija dake tsaye ta haɗe fuska.juyo idanuwa Khadija tayi tace"Malama idan zakizo mu wuce kizo,haka kawai kin samu latti da wannan shiriritar taki".rausayar da kai Halima tayi tare da shagwaɓe fuska ta wuce gaba kawai.bin bayanta Khadija tayi tana mita kamar zata ari baki.dafe kai Halima tayi tace"billahil azeem kin dameni!!,zamu raba hanya yanzu ku...".kasa ƙarasa maganar tayi tana kallon gefenta.zaune yake akan farar kujerar roba yayi ɗaya kan ɗaya duk da yana zaune bazaisa ka kasa gane cewar shi dogo bane ba,yana da faffaɗan ƙirji,chocolate colour ne,in da fuskarsa ke ɗauke da daradaran idanuwa ga gashin girarsa baƙi siɗik kamar wanda yayi jagira,yana da dogon hanci mai ɗaukar hankali ga ƙaramin bakinsa dake ɗauke da laɓɓa masu tudu sunyi kamar browni kamar lite pink.yana da matsakaicin gemu sai gashin baki in da gefen fuskarsa ke da ɗan siririn saje kaɗan har zuwa saitin kunnensa,gashin kansa gwanin burgewa baƙi siɗik yasha aski sai ɗaukar ido yake yi.sanye yake da wando fari 3 quater sai farar T-shirt ,idanuwansa a lumshe ga hannunsa ɗaya ya ɗaga yana shafa sumar kanshi fuskarnan ɗaure babu alamar wasa a tattare da ita ABU BILAL kenan.wani irin ƙwalalo ido Khadija tayi ganin yarda Halimatu ta saki baki tana ƙarewa ABU BILAL kallo,hakan kuma yayi daidai daya soma buɗe lumsassun idanuwansa jin ido na yawo a jikinsa carab idanuwansa suka faɗa cikin na Halima da azabar ƙarfi ta rumtse idanuwanta tana ja da baya yayin da zuciyarta ta harba da masifar ƙarfi.wani irin fizga Khadija tayi mata suna barin wurin da sauri wani irin kallo Khadija tayi mata da masifa tace"kinyi hauka ne?,meke damunki haka?,kina so ki janyo mana bala'in da kab danginmu baxasu iya kare mu ba?,ni dai ki rufamun asiri yarda kike zuwa unguwar nan lafiya toki koma gidanku lafiya kin daiga ta silata kike shigowa unguwar nan".galala haka Halima kebin Khadija da kallo wanda ko kaɗan ta kasa fahimtar abunda take cewa.har lokacin gabanta be daina faɗuwa ba da ƙyar ta haɗo magana can cikin maƙoshi tace"waye shi?".Harara Khadija ta xabga mata tace"ban sani ba,kuma ni daga yau ki riƙa wucewa islamiyyan kawai na sameki a can".siririn tsaki Halima ta saki tace"banxa masifaffiya kawai"ta fizge hannunta tana shigewa cikin islamiyyan ,duka yinin ranar a haka Halimatu tayi shi gaba ɗaya bata fahimtar komai babu abunda ta koya a makarantar duk tayi kamar wata marar lafiya,gaba ɗaya Khadija na lura da ita amma haka ta share dan bata son tado maganar ɗazu.tunda aka tashi islamiyyan bakin islamiyyan yake cike da ɗalibai da gudu yaron ya ƙaraso gaban Halimatu ya janyo hannunta yace"Aunty dan Allah ki gyaramun"ya ƙare maganar yana kallon takalmar ƙafarsa da zaren su ya warware,juyowa tayi tana kallon yaron kyakyawa dashi yarone ɗan kimanin shekara biyar a duniya sosai uniform ɗin islamiyyar suka yi matuƙar amsarshi ,murmushi ta sakar mashi ta shafa kanshi tare da duƙawa tace"to brother".ɗaure masa igiyar takalmin tayi kafin yace"thank u".da murmushi a fuskarta tace"what's your name?".hannu yasa ya shafi sumar kansa ya furta"BILAL ALIYU".kafin tayi magana taga zaratan maza su biyu sun janye hannun Bilal daga jikinta a tsorace taja baya da sauri kamar zata faɗi ganin su ya matuƙar tsoratata babu annuri ko kaɗan a tattare dasu.numfashi Khadija ta mayar tare da ɗago Halima daga ɗuƙen da take cikin sanyin murya tace"Sadiya why all this?,please na roƙeƙi karki janyo wani abun daba shi bane".a daddafe suka wuce gida,tunda suka tunkaro in da tabar wannan mutumin na ɗazu take kallon wurin kamar idanuwanta zasu faɗo sai dai babu kowa a wurin,lokaci ɗaya taji ko kaɗan bata jin daɗin jikinta,haka a saɓule sukayi sallama da Khadija ita kuma ta kama hanyar gida tana tafiya da tunanuka iri iri a ranta.a matuƙar razane take bin jikinta da kallo wanda aka malale mata shi sharkab da ruwan kwata duka jikinta ya ɓaci har a saman glasses ɗinta ji tayi ranta ya matuƙae ɓaci da azamar sauri ta rufawa motar baya har in da sukayi parking ta tsaya tana ƙarewa Drivern motan kallo cike da masifa tace"ka kallah yarda ka ɓata ni da ruwan ƙazanta,ko dabba kayiwa haka aika tsaya kaga lafiyarta balle kuma mutun".a fusace ya ɓalle marfin motar ya fito yana binta da mugun kallo yace"anje an ɓata zan zuba maki tafi a wurin nan wallahi".tuni idanuwan Sadiya sun sauya kala a hassale tace"wallahi ko da wasa balle a gaske,duk wani abun da kake ji dashi to nawa yafi ƙarfin naka,idan kuma kana ganin wasa toka gwada,wanda besan darajar Ɗan adam ba kawai".sosai zuciyar Jagwado ta ɓaci dajin furucin yarinya ƙara a kansa hannu ya ɗaga zai kifa mata mari,ganin Abu Bilal ya buɗe murfin mota ya fito a hankali cikin takun ƙasaita ya ɗaga masa hannu sosai sautin muryarsa ya daki dodon kunnenta in da da ƙyar ya iya furta "kiyi...haƙu...ri"ya ƙare maganar da nisa a tsakani ya juya ya shige gaban gidan da suke tsaye.wani irin daskarewa a wurin Sadiya tayi tana bin wannan mutumi da kallo tuni taji duk wani ɓacin ranta ya gushe a haka ta juya ta nufi hanyar unguwarsu da babu nisa sosai tsakaninta da wannan...daidai ƙofar wani tanƙameman gate naga ta tsaya ,hannunta tasa tare da tura ƙofar masu gadin dake wurin su biyu suka miƙe da sauri sanye da uniform suna mata sannu da zuwa,fara'a faɗaɗe fuskarta tace"ina wuninku,nikam nace a daina tashi mun haka ku ɗin ai tamkar iyaye kuke a gareni".cike da jin daɗi da irin karramawa da dattako irin na Sadiya suke mata fatan alkhairi.tana ta ansa addu'ar da suke mata kafin ta nufi main Entrance na gidan.Sai lokacin na samu damar ƙarewa gidan kallo wani irin tanƙameman gida ne wanda zaka iyakiransa gari guda tsayawa faɗin tsaruwar gidan ɓata lokaci ne dan ko rade's ɗin dake parking lot abun kallo ne.ko ina ga masu aikin gidan nan sai shawagi sukeyi suna kuma yiwa Sadiya sannu da zuwa tana ansawa murmushi faɗaɗe a fuskarta ,masha Allah shine abunda na faɗa lokacin data shiga parlon aljannar duniya kenan babu wasu tarkace a parlon sai dai ya tsaru iya tsaruwa daga cikinsa ne kuma ya rabu har ɓangarori ukku.ɓangaten dama naga ta shiga tun a parlon ta soma kwaɗa sallama tare da kiran "Amma!,Ammana!!".wata farar dattijuwar mata ta fito cikin shiga ta alfarma fuskarta ɗauke da murmushi kallo ɗaya zaka mata ka hango tsantsar kamarta da Halimatus sadiya."ƴar albarka sannu da dawowa,ya akai na ga jikinki haka?"Amma ta faɗa.cike da soyayyar mahaifiyar tata ta langwaɓar da kai gefe tace"Ammana ruwa ne aka watsamun a hanya,amma yanzu zan gyara jikina "ta ƙare maganar tana tura ɗaya daga cikin ƙofofi ukku dake parlon.da alama kuma nan ne bedroom ɗinta,ɗakin ya tsaru komai na cikinsa royal blue ne ko ina ɗakin gyare yake tsab sai zuba ƙamshi yakeyi ,jakkar dake rataye kafaɗarta ta ajiye a ma'ajinta sannan kai tsaye ta wuce toilet,uniform ɗin ta soma cirewa sai da ta saka su a injin wanki ta wanke tas har inner's ɗin jikinta sannan ta sanyasu a wurin shanya dake toilet ɗin,sannan ta ƙarasa ciki ta soma sakarwa kanta shawa.da ƙarfi ta runtse idonta ganin wannan saurayin na ɗazu yana mata gizau babu abunda take gani sai siffarsa da kuma kunnenta dake tariyo mata dadaɗar muryarsa,a daddafe ta samu tayi wankan ta fito ɗaure da towel sai ƙamshin daɗaɗan sabulan wankanta takeyi kai tsaye gaban mirror taje ta busar da yalwataccen gashin kanta wanda yake baje har tsakiyar bayanta sannan ta shafa lotion da sauri sauri ,doguwar riga na kanti ta saka fara ƙal da ita ta feshe jikinta da turaruka masu daɗi sannan ta janyo agogonta ta saka ta kuma saka glasses ɗin idanuwanta taja veil ɗinta black tayo waje. ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE VOTE COMMENTS SHARE FISABILLAH [11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *ABU BILAL!!!* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *_______________________ ______________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation FREE PAGES PAGE 2 kai tsaye parlo ta fito tana kallon wayar hammunta ƙirar samsung kusan cin karo sukayi da sauri taja baya tana ƙarewa Faruq kallo tun daga sama har zuwa ga fuskarsa dake ɗauke da faffaɗan murmushi,murmushin itama ta saki tace"Yaya Faruq yaushe ka dawo ne?".far yayi da idanuwa yana buɗe hannayensa yace"lokacin da little Ammiena ta manta dani note(Faruq yaron yayar Daddyn Sadiya ce wacce ta rasu,su biyu iyayensu suka haifa sanadin hakan Daddy ya sakawa ƴarsa Halimatus sadiya).murmushi tayi tace"ni dai ban manta da Yaya ba Allah".matsa masa tayi ya wuce ciki wurin Amma yayin da Halimatu ta fito main parlo na gidan tana kallon Hajiya mama dake hakimce akan chair hannunta ɗauke da remote tana canza tasha.duƙawa Sadiya tayi tace"Mama barka da gida".sakin fuska Hajiya Mama tayi kamar ba ita bace ke ɓata rai yanzu tace"a'a ƴar albarka an taso daga tahfeez ɗin kenan?".Gyaɗa kai Sadiya tayi alamar eh tana ɗago kanta tana kallon Daddy da shigowarsa gidan kenan fuskarta ɗauke da murmushi ta ruga tana karɓar jikkar hannunshi tace"Daddyna barka da dawowa".shafa kanta yayi yana janta a jikinshi cike da soyayyarta yace"lafiya qlau little,ya Tahfeez?".cikin sanyin murya tace "Alhmdllh".wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Hajiya Mama ganin Daddy ya janyo Halimatu jikinsa ji tayi kamar zuciyarta tayi zallo ta hito saboda tsananin kishin ita bata taɓa haihuwa a gidan ba,kuma Sadiya ita kaɗai ce ƴarsa duk duniya.a fili kuma sai ta saki murmushi tace"Daddyn Sadiya barka da dawowa,ya aikin?".cike da murmushi yace"lafiya qlau Hajiyar Halimatu ,ya fama da ƴar rigimar tawa?".nan ma dariyar tayi tace"ai kasan yau ana Tahfeez rigiman da sauƙi yanzu dai ake shirin farata"dukansu dariya suka saka kafin ta karɓi jikkar hannun Halimatu ita da Daddy suna wucewa babban part na cikin parlon. Ɓangaren Abu bilal kuwa yana shiga madaidaicin gidan nasu ya soma halbar da bucket ɗin daya ci karo dashi a hanya,saurin miƙewa tsaye Mama tayi tana gyara kashin ɗaurin ɗankwalinta tana ƙarewa Abu bilal kallo wanda ta taso ne da masifa taji uban waye ya halba mata bokiti,wata dariya Datti ya saki yace"su Uwani masifa to ba ni ɗin da kika raina bane,masu gidan ne da kansu,sai naga kinyi shiru kamar ruwa ya ciki".ƙanƙance ido Mama Uwani tayi tace"to ai ina da gaskiya tunda bakai ka sayar mun bucket ɗin ba".ko kallonsu Abu bilal beyi ba ya wuce zai shiga part ɗinsa da gudu Bilal ya rugo tare da rungume Abbansa daga baya.wani irin lumshe idanuwa Sudeis yayi yana jin abun har cikin ransa yasan duk duniya yaron shi tilo ɗaya ke iya yi masa haka,fuskarsa kada ran kada han ya juyo tare da ɗaga yaron sama ,dariya sosai Bilal ya saki yana cewa Abbana"welcome".dawo dashi yayi akan ƙirjinsa tare da sunbatar goshinsa yace"thank u".shiru yayi alamar yana son sake wata maganar,fahimtar hakan da Bilal yayi duk da ƙananun shekarunsa yasan halin Abbansa tsab yasa yace"Tahfeez alhmdllh,nayi karatu da yawa,Abba yau har Aunty nayi a scul"."amma nan nan ka shigo mu ka fara iskewa ko sallamar bamu samu arziƙinta ba bare kuma gaisuwa,Allah na gani Aliyu halinka sai kai,haka kawai kaita cutar mu".rufe ido da ƙarfi Sudeis yayi yana kuma taunar lips ɗinsa kamar zai huda kafin ya juyo da runannnun idanuwansa yana watsawa Datti harara,ganin yana yin idanuwansa yasa Mama uwani shigewa ɗakinta da sauri tana kyarmar jiki.ba shiri Datti ya kwashi silifas ɗinsa yana niyar yin waje kusan cin karo sukayi da Aunty Aysha wacce tasha ado na alfarma daka ganta kasan hutu ya gama ratsata, kallo ɗaya zaka mata kaga tsantsar kamarta da Sudeis fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa shigowa tace"a'a ba kanta Kawu guduwa da silifas a hannu?,da alama yau ka taɓo ɗan rigimar taka kenan?".wiƙi wiƙi yayi da ido yana washe baki dan yasan yau kam yayi arziƙi bashi ba zuwa maula.ƙwafa yayi yace"kedai bari Aysha ,cutar dani kawai Aliyu ya gama yi,Allah yasan ko kallon banza ban taɓa yi masa ba".sauke Bilal Sudeis yayi bece komai ba ya wuce part ɗinsa yana ɓalle buttons na gaban rigarsa.ɗakine madaidaici parlo ne ɗauke da kujeru da kayan kallo komai na ɗakin fari ne tas gyare yake tsab sai zuba masifar ƙamshi yake yi,kai tsaye bedroom ya shiga nan ma ɗakine madaidaici ɗauke da gado da wadrobe da miro komai tsab,toilet ya shiga ya cire wandon jeans na jikinshi ya soma sakarwa kansa shawa ya ɗauki lokaci a toilet ɗin kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa ga ƙarami yana goge kansa da shi,ƙarar wayarsa yasa ya fito parlo kallon Aunty Aysha yayi ya ɗauke kai ya kwashi tsaɗaɗɗun wayoyinsa ya koma bedroom.kallonsa tayi ta girgiza kai ta juyo tana sauraran surutun da Bilal ke zuba mata tana murmushi tana ɓare masa chololate ɗin data masa tsaraba.kai tsaye gaban mirrow yaje ya shafa lotion ɗinsa yayi ya feshe jikinshi da ɗaɗɗan turarensa masu masifar ƙamshi sannan ya buɗe wadrobe ɗinshi boxer ya ɗauko da singlet ya saka sannan ya saka crexy trouser ya saka T-shirt blue colour,agogon gucci ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa kafin ya tako a hankali zuwa parlon cikin ɗaya daga cikin kujerun ya xauna yana kallon Aunty Aysha ciki ciki yace"sannu".ko kaɗan batayi mamakin yarda yayi mata ba tasan halinsa sarai nan ma yayi abun arziƙi daya ce mata sannu,juyowa tayi ta kallesa tace"Sadauki Aliyu ni na rasa me wa'ancan tarkacen yaran keyi a ƙofar gidan nan,Aliyu kallo ɗaya xa'a maka ai maka kallon ɗan daba ɗan shaye-shaye wannan wacce irin rayuwe kake yi?,ka koma gida Aliyu ka ƙi ,kabar zuwa aiki ni na rasa meye matsalanka,to ka sani yau nazo ɗaukan Bilal ne,baxan iya bari ya taso yana ganin mahaifinsa a cikin irin wannan bauɗaɗɗiyar rayuwar ba".sosai maganar ɗauke Bilal ya daki zuciyarsa duk tsawon maganar da takeyi sai yanzu ya ɗago yana ƙare mata kallo.tabbatar masa tayi tace"yes,yau zan ɗauki Bilal ko kana so ko baka so,ace yaro ko islamiyyah yaje wa'ancan ne zasu je ku ɗauko shi?".lumshe ido yayi ya rasa abun cewa da ƙyar ya iya haɗo kalaman"Aunty no..kada..ki"shiru yayi ya kasa ƙarasawa yana jin bugun xuciyarsa na tsananta,shareshi tayi ta wuce bedroom ɗinsa akwati ta ɗakko ta soma saka kayan Bilal a ciki tas ta kwashe komai niƙi niƙi ta fito da akwatin parlo ,shikam Abu bilal kasa cewa komai yayi illah kallonta da yakeyi,janyo hannun Bilal tayi tace"ka fito da akwatin xanje mu gaisa da Mama Uwani sannan mu wuce.bata jira cewarsa ba ta wuce ɗakin Mama Uwani.da sallama a bakinta ta shiga ɗakin ,ansa sallamar Mama uwani tayi tace"a'a Aysha ce,sannu da zuwa".da yauwa Aunty Aysha ta ansa ta ƙarasa shiga tana janye da hannun Bilal a saman tabarmar da Mama uwani ta shimfiɗa mata ta xauna bayan sun gaisa tace"Mama nazo tafiya da Bilal ne".zaro ido Mama tayi tace kice mana yau gidan ba lafiya kawai muyi ta kanmu,ɗauke Bilal a gidan nan ai tamkar kafa wani tashin hankali ne".dariya sosai Aunty Aysha ta saki tace"lallai yaukam akwai rigima ku ƙyalesa yayi ya gama"miƙewa tayi ta buɗe jakkarta ta ibo kuɗi masu yawa taba Mama uwani tayi mata sallama,sosai tayi mata godiya sannan ta rakota ƙofar ɗaki.tsaye Aunty Aysha ta hango Sudeis ya jingina bayansa a bango ya lumshe idanuwansa ga hannuwansa rumgume a ƙirji.matsowa tayi kusa dashi tasa hannu ta janyoshi tace"haba autan Mamy ka daina ɓata ranka,kaga ba nisa ne tsakanina da kai ba ko yaushe idan kaso zaka iya zuwa kaga Bilal,kayi haƙuri zanyi hakan ne duk dan tarbiyarsa ta gyaru".shagwaɓe fuska yayi tare da langwaɓar da kai kamar wani ƙaramin yaro shafa kansa tayi tace"am sorry my lovely bro"..murmushi ya sakar mata wanda yayi matuƙar ƙawata fuskarsa.sama ya ɗaga Bilal yana shafa kansa suka fito waje,a nan suka samu Datti yana ta kwashewa su Jagwado albarka san ranshi,miƙewa yayi da sauri yana gyara hular kanshi yana matsowa kusa da Aunty Aysha,a lokacin har an saka akwatin Bilal a motar da tazo dashi.kuɗi da yawa ta bawa Dattiya sannan tayi masa sallama kafin ma ta idasa maganarta yayi gaba abunsa tunda ya kwashi kuɗi,zagayawa gefen motar yayi ya durƙusa ya kama hannuwan Bilal yana kallonsa karo na farko da naga yayi magana mai tsayi yace"Allah yayi maka albarka,ka kula da karatu sosai ,ka zauna wurin Aunty xanzo ko yaushe ina ganinka kaji".ido cikin ido Bilal ke kallon Abbansa can yace"Abba zaka riƙa kawo mun chocolate ɗina a gidan Aunty ko?".gyaɗa masa kai yayi.sannan yaci gaba da cewa "to Abu Bilal na gode"ya faɗa tare da rungume Abban nasa,shima rungumesa yayi yana jin zuciyarsa na zafi a haka ya cireshi daga jikinshi ya sakashi mota ya rufe,har motar ta ɓace Bilal na ɗaga masa hannu.juyawa kawai yayi ya koma cikin gidan,kai tsaye bedroom ya shige ya faɗa saman bed tare da rumtse idanuwansa abubuwa da yawa suna dawo masa a kai. ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE. VOTE COMMENTS SHARE [11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *ABU BILAL!!!* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *_______________________ ______________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation FREE PAGES PAGE 3 Ko kaɗan a daren Abu bilal kasa runtsawa yayi gaba ɗaya tunaninsa da komai nasa ya gama birkicewa,ganin abun bamai ƙarewa bane yasa ya tashi ya ɗauro alwala ya soma sallah,wannan yana ɗaya daga cikin nagartan halayansa duk tsanani be manta da sallah ba da kuma azumin alhamis da litinin ,haka zalika yaransa ko me sukeyi basa bari lokacin sallah ya wuce su.sai bayan yayi sallahn asuba ya samu bacci mai nauyi ya ɗauke shi akan sallayar.Tun sassafe Karima ta fito tsakar gidan ta soma share-share(Karima ƴar mama uwani ce).bayan ta gama ta tattaro wanke wanke tana wanke wa,kamar yarda ta saba duk kullun tana gamawa ta ɗaurawa Mama uwani girkin wainan da takeyi na siyarsa,a hankali gidan ya soma tara mutane masu siyan waina,hayaniyarsu ce ta tashi Abu bilal daga bacci wanda dama shi duk irin nauyin baccin da yakeyi motsi kaɗan kan iya tashin shi,wani siririn tsaki ya saki saboda ya tsani wannan sa'an ta Mama Uwani babu abunda suka rasa amma ko kaɗan ta kasa haƙura da wannan sana'ar,zura jallabiya yayi ya fito fuskarnan murtuke sai ɗacin rai yakeyi saurin duƙar da kai Karima tayi ganin irin mugun kallon da yake jefarta dashi,da sauri ta miƙe tayi baya,ji kakeyi gidan yayi tsit gaba ɗaya masu siyan wainan sunyi shiru a tunaninsu yabar gidan tun da sukaga su Jagwado basa ƙofar gida.wiƙi wiƙi da ido Datti yayi sana baya baya yana faman boye rigar dake jikinshi dan rigar Abu bilal ɗince an mashi shanya jiya ya ɗauke yace"Allah ya soni dama Uwani tace in ɗauka in gwada muga ko zaiyi mun kyau,banni dai ban taɓa satar maka kaya ba,ah tau Allah na tuba me akayi akayi wani kayan Sude can bare shi Sude ɗin".wani irin mugun kallo Abu bilal ya jefesa dashi kafin ya halbar da ƙatuwar robar da Karima ta gama zuba ruwa ciki,tuni su Jagwado suka shigo a guje suka kora masu siyan waina,ƙafa yasa ya halbar da ƙullun wainan.da sauri Mama uwani ta miƙe tace"Amma Dattiya kaji tsoron Allah ni nasan kama ɗauki kayanshi bare nace kasa ko xai maka kyau?".ganin da gaske Abu Bilal ƴan ɓannar yake ji sai ɓarin kaya yake yi yasa ta dauke roban kuɗinta tayi ɗaki a guje tana danna kuba.Karime dake rakuɓe ya dakawa tsawar da yasa ta soma sakin ƙara da ƙarfin gaske tace"Yaya Aliyu na tuba wallahi bazan sake fita nayi dare ba".wani kyakyawan mari ya sakar mata wanda yayi sanadiyar dauke jinta da ganinta na mintoci kafin da ƙyar ta fizgo baki da niyar yin ihu ,suman tsaye tayi lokacin da Rambo(karen Abu bilal)yayo kanta yana sinsinanta,a guje Jagwado yazo ya shiga tsakaninsu ya riƙe Rambo yace"Allah ya huci zuciyar mai gida,hakan bazata sake faruwa ba insha Allahu".da kausashiyar murya ya kalleta yace"kin san sauran ai".ya wuce ɗaki yana hararar Dattiya dake laɓe bakin kofa yana niyar sakin fitsari a wando.yana shiga ɗakin towel ya ɗauka ya wuce toilet yin wanka.minti 40 yayi ya gama shiryawa tsab cikin ƙananan kaya kamar kullun yau kam harda p-cap ya murza a kansa sai tashin masifar ƙamshi yakeyi duka kayan jikinsa dark blue ne dama Abu bilal ba daga baya ba wurin saka takalmi sau ciki,sosai ya fito ɗan gaye dashi yana kuma ɗaukar hankali.jin ƙamshin turarensa ya fara tunkaro waje yasa Karima yin saurin ɗauraye robar dake hannunta tayi saurin lafewa bayan kitchen tana raba idanu,wani irin taji lokacin da taga ya fito,ƙura masa ido tayi kamar zata zazzago idanuwanta.tsaye yayi bakin ɗakinshi babu kowa a tsakar gidan kuma ta gyara ko ina tsab.ƙwafa yayi yace"zan kwakwale idanuwanki masu kama dana mayu".da sauri Karima tayi saurin yin ƙasa da kanta tana jin kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito dan masifar tsoro,tasan ko be ganta ba yana gane idanuwa a kansa,kai tsaye waje ya fita in da ya iske yaransa a wurin miƙewa sukayi suna musabaha dashi kafin ya zauna kan kujera tare dayin ɗaya kan ɗaya ya kuma lumshe idanuwansa.Aguje Halima ta fito tana saka Ahlari a jakar dake rataye a kafaɗanta saurin riƙeta Amma tayi tace"Little ae baki makara ba bare kuma kiyi mani wayau ki fita baki karya ba".wani irin kwaɓe fuska tayi kamar zata saki kuka tace "wallahi Amma basan karin nan nake ba,ki barni dan Allah".zaro ido Hajiya Mama tayi tace"haba Sadiya babbar budurwa Tahfeez fa zakije ina amfanin fita baki ci abinci ba,yanzu tau bara na haɗa maki a lunch box".kyawawan idanuwanta ta lumshe kafin ta waresu tace"to Mama".cike da tsananin soyayyah Faruq ya kalleta yace"ƴan mata yau ni zan ajiyeki a school gaskiya".raurau tayi da ido kafin ta zagaya da sauri wurin Daddy ta saƙalo hannuwanta akan wuyanshi ta kwantar da kanta a kafaɗanshi cikin turo baki tace"Daddyna ka gaya masa ni nafi son zuwa Tahfeez a ƙafa,ƙwaɗayin ladan nake yi".murmushi Daddy yayi ya shafo kan ƴar tasa yace"dandai kince lada Ammina amma ko ni basan fitanki a ƙafa nake yi ba,kinsan yanzu duniyan ta lalace".juya idanuwa tayi kamar mai tunanin wani abu can tace"to Daddy kuyi mani addu'a zanje lafiya na dawo lafiya da yardar Allah".murmushi Hajiya Mama tayi tace"insha Allah kuwa,zoki wuce kada kiyi latti kinji".karɓar box ɗin tayi cike da ladabi ta dan durƙusa tace"na gode Mamana"kafin ta wuce tace"sai anjimanku kafin in dawo yau ayimun abun daɗi".ta fita tana kwashe hijabinta sama tana gyara riƙon box ɗinta.sake baki Amma tayi tace"naga ranar da Sadiya zata girma,kwatakwata yarinyar can bata da wayau sai shirme,kuji yarda ta fita tana yaye hijabi,duk ta wani sakalce a gari".murmushi Daddy yayi yace"ni dai a barmun Ammina tayi abunda take so,komai lokaci ne insha Allah zata daina data ƙara girma".cikin natsuwa take tafiya tana kallon littafin dake hannunta tana gyara haddanta,hankalinta kwance tana tafiya harta ƙaraso ƙofar gidan su Khadija,a daidai soron gidan ta samu Khadija tsaye da alamu fitowarta kenan itama da shiga irin ta Sadiya,washe baki Halima tayi tace"to ki fito muje dan ni nan ba tsayawa zanyi ba".murmushi Khadija tayi tace"a lallai yau dan an fito da wuri ba ae dole kice haka,ni wuce muje".a haka suka jero suna tafiya.yauma Halima ce side din da su Abu bilal suke zaune.ganin unguwar ƙwalam ba kowa yasa Khadija zaro ido shaf ta manta da yaune lahadin ƙarshen wata kuma yaune yaran Abu bilal ke gyara unguwa kuma babu wanda ya isa ya fito bare ya biyo ta hanyan.tsayawa sukayi da sauri ganin su Jagwado sun tsaya a gabansu,ras ras haka gaban Khadija ya bada sauti yayin da Halima kam ko a jikinta dan tsab ta gane Jagwado shine wanda ya watsa mata ruwan kwata a jiki.littafin dake hannunta ta rufe ta kwashe Hijab dinta ta saka littafin a jakka,cikin rawar baki Khadija tace"dan Allah kuyi haƙuri wallahi na manta shiyasa na janyota muka biyo ta nan hanyar"gaba ɗayansu juyowa sukayi suna ƙarewa Halima kallo wanda ko kaɗan bata san me sukeyi ba gaba ɗaya ta zuba kyawawan idanuwan ta ƙure Abu bilal da ido ko kiftawa bata yi.idanuwansa a lumshe kamar ko yaushe cikin kausasshiyar murya yace"bar kallona"ko kaɗan taƙi dainawa saima lumshe ido da tayi lokacin da raji daddaɗar sautin muryarsa ta sauka a dodon kunnenta.wata uwar tsawa Jagwado ya daka mata wacce tasa ta juyo da azabar ƙarfi cikin hassala itama tace"dallah malam kabar mun tsawa tun da kai ba uban.."kasa ƙarasa maganar tayi ganin Abu bilal tsaye a gabanta yana jefarta da mugun fusataccen kallo.har ƙasa Khadija ta duƙa tace"Abu bilal dan girman Allah kayi haƙuri baƙuwace anan,insha Allah ba zata sake kallonka ba ko yiwa yaranka rashin kunya"cikin sauri Khadija ta janyo Hijab ɗin Halima tace"ki basu haƙuri".sakin baki Halima tayi kafin tace"tabɗi,wallahi bazan bashi ba,ko ba shine ba jiya ya watsa mun ruwan kwa.."saurin saka hannu tayi ta rufe bakinta ta kuma fashe da kuka saboda ɗallin da Abu bilal yayi mata a baki fuska ɗaure yace"uwar rashin kunya".ƙasa tayi da kai tana rusa ihu tare da bubbuga ƙafafuwanta tanayin baya baya tana cewa"Allah sai na gayawa Daddy,dama kaima mugune irin wancan"ta ƙare maganar tana nuna Jagwado da hannu.wani uban haushi ne ya turnuƙe zuciyar Abu bilal cikin cool voice yace"bara na maki duka sai ki kawo kaka ba Daddy ba".wani irin zaro ido tayi zuciyarta na bugawa da ƙarfi ta yarda box din hannunta ta fasa wata gigitacciyar ƙara wanda sai da Abu bilal ya rufe kunnuwansa ya kuma rumtse ido da ƙarfi,sannan Halima ta sheƙa a guje har tana ture shi.ƙwafa yayi yana kallon gudun da takeyi wanda taƙi biyu xaiyi ya kamata ya juyo yacewa Khadija"bar nan".har ƙyarmar jiki takeyi ta miƙe zata bar wurin a tsawace Jagwado yace"your box".kwashe box ɗin tayi itama ta runtuma a guje tana godewa Allah daya sa basu faɗa tarkon Abu bilal ba.a hanya ta samu Sadiya,tana ganinta ta ƙalƙale da dariya harda riƙe ciki .wani uban harara Khadija ta jefa mata tace"kici gaba tabbas wata rana bazaki dara ba in dai akan Abu bilal ne,dan baki san waye shi ba shiyasa sakarcinki yake sawa kike neman cutar da rayuwarki a banza,ina mai tabbatar maki kuma Mugun da kika kirashi tabbas zai maki aikin mugunta".wani irin lumshe ido Halima tayi tace"wow nice name Abu bilal"sai kuma ta saki ƙayataccen murmushi.tsaki Khadija taja ta wuce warta cikin islamiyya har lokacin gabanta be daina dakan ukku ukku ba. ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE. VOTE COMMENTS SHARE [11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *ABU BILAL!!!* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *_______________________ ______________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation FREE PAGES PAGE 7 ```Start``` ```patronizing``` ```ABU BILAL``` luvly ```fans Ta hanyar wannan account din 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337. Lumshe ido Halimatu tayi kamar mai bacci sai kuma ta ware idanuwanta akan fuskar Khadija tace"ni bance maki am in luv with him ba,just dai i want to be with him that's all".Dafe kai Khadija tayi tace"lallai kam kice tashin hankali na dunfaromu kuwa,wannan mutumin kina tunani yana da feelings akan wani abu wai soyayyah?,to bari kiji Abu bilal besan meye tausayi ko soyayyah ba,a duk duniyar nan ina ga yaronsa da yayarsa kawai yake tausayi yake kuma ɗagawa,ina tunanin idan kika fahimci waye Abu bilal kece mace ta farko da zaki fara nisanta kanki dashi".wani irin faɗuwa gaban Halimatu yayi sai kawai ta share tace"ashema yana da feelings tunda har yana iya aure ya haifi yaro".ƙwafa Khadija tayi tace"ina dai faɗa maki idan ma son shi kika fara to kiyi gaggawan cirewa dan a duniya babu wanda ya tsana sama da mutun yace yana son shi".fari da ido Halima tayi tace"what ever".suna a haka Faruq yayi ƙwanƙwasa ƙofan jin tace"yes come in "yasa yace"Faruq ne".dariya khadija tayi tace"eh Yaya ka shigo".tura ƙofan ɗakin yayi ya shiga bakinsa da sallama kai tsaye gaban Sadiya ya duƙa yace"Ammina sannu,how is your body"ƙasa tayi da kanta tace"Alhmdllh".kallonta yayi kafin yace"ina kike jin pain ".lumshe ido tayi tace"no where,dama fever ne".gyaɗa kai yayi kafin ya miƙa mata Drugs ɗin hannunshi yace"kisha yanzu and at the night kuma".a hankali ta furta thank u.murmushi yayi kafin ya juyo yace"Khadija ya gida da Ummi?".sakin baki tayi tana dariya tace"haba Yaya Faruq ni da ka manta ko ina existing ma a room ɗin nan,saboda ƴar rigima ba lafiya".murmushi ya saki yace"ba haka bane,kinsan dai Ammin tawa uwar raki ce ae".murmushin itama tayi tace"haka ne kam,su Ummi suna lafiya,ai kwana biyu baka leƙa ba".shafa kansa yayi zuwa gemunsa yace"when i'm less busy zan shigo na gaishe ta"daga haka ya miƙe ya fita yana janyo masu ƙofan.nannauyar ajiyar zuciya Khadija ta sauke tace"ke ga namiji daya ansa sunansa namiji mai nagarta amma ki wani maƙalewa wani".cikin rashin fahimtar in da zancen nata ya dosa tace"who's that".harara Khadija ta zabga mata tace "zaki cemun baki san Yaya Faruq yana sonki bane?".a bazata tambayar yazo mata ta wani ƙwalalo ido tace"haba mana is just your imagination he's my Yaya fa,mu duka Amma ne fa ta rainemu".Dariya zancenta yaso bawa Khadija tace"ai naga dukanku ita ta haifesu kuma babu aure a tsakaninku"."kinga Khadija i can never imagine dating Yaya Faruq,please let's call up the chapter".Halima ta faɗa. Shiru Khadija tayi bata kuma cewa komai ba ta miƙe tsaye tana cewa"malama tashi ki raka ni".miƙewa Halima tayi tana janyo long hijab ɗinta mai hannu ta saka tace "muje".a jere suka fito a babban parlo suka samu Daddy da Amma suna kallon news.Har ƙasa Khadija ta duƙa ta gaishe da Daddy shima cikin sakin fuska ya ansa yana saka mata albarka 10k ya bata yace ta gaishe da su Ummi.langwaɓar da kai Halima tayi tace"let me escort her".jinjina kai Daddy yayi yace"a kula da hanya".da to suka ansa kafin tayiwa Amma sallama ta fito,a jere suka fita daga gidan.har sun soma tafiya daidai ƙofar gidan Aunty Aysha Halima taci burki tare da kallon Khadija tace"ki rakani nan mana,2days ban shiga wurin Aunty Aysha ba".kallonta Khadija tayi tace"amma baxamu daɗe ba gaskiya bana son magriba yamun a hanya".ta ƙare maganar suna tura ƙofan gate ɗin gidan.da gate man suka fara gaisawa da yake yasan Halima ya barsu suka wuce ciki,babu lefi shima gidan yana da girma ,suka tura main entarance na main parlo bakinsu ɗauke da sallama.tsaye yake ya juya baya yana zuba ruwa a mug,sanye yake da ƙananan kaya kamar kullun yayi sagging trouser ɗinsa har kana iya hango farin boxer ɗin dake jikinsa,duk yarda sukeyin sallaman hakan besa ya juyo ba sai da Aunty Aysha ta fito daga kitchen tace"kai dai Aliyu naga ranar da zaka bar wannan mishkilancin naka ace sallama ma anayi ba zaka iya buɗe baki ka ansa ba".juyowa yayi yana kafeta da ido bece komai ba nan idonsa ya safka akan Halima da yake janyo hijab ɗinta daga jikin door,murmushi Aunty Aysha ta saki tace"haba Halima ai nayi fushi gaskiya,yaushe rabonki da gidan nan saboda Allah,ko jiya kina tahfeez na leƙa na gaishe dasu Amma".da fara'arta itama ta ƙaraso cikin parlon tana cewa"wallahi Aunty school ne baya bari".ta ƙarashe maganan suna zama karab idanuwanta suka sarƙe cikin na Abu bilal wanda yake kai Mug ɗin ruwan sanyi bakinsa wata uwar harara ya afka mata ,da sauri tayi ƙasa da kanta tana cewa"Aunty ina su Nahnah?".juyawa tayi tace "ae kinsan da yake mun ƙara yawa gidan na tabbata Bilal da Khalifa sun janye mun ƴar auta suna baya ana hawa keke".Sai lokacin Khadija taga Abu bilal zaro ido tayi tana addu'ar Allah yasa kada Halima ta ganshi.miƙewa Aunty Aysha tayi tace"bara a kawo maku ruwa".ruwa da lemu ta ɗauro a ƙaramin tray ta kawo masu tare dasu Bilal dake biye da ita.da gudu Bilal yazo ya faɗa jikin Halima yace"la Aunty ni kika zo nema a gidan mu?,kinga Abbana taso muje ki gaishe shi".ya ƙare maganar yana jan hannun Halima dake kallon fuskarshi da murmushi sai a lokacin ne taga tsantsar kamar Bilal da Abu Bilal."ka santa ne"Aunty Aysha ta tambaya.Nahnah dake lafe jikin Halima tace"eh Momy ita ce Auntyn da yake baki labari ta tahfeez".juyowa tayi tana kallon Abu Bilal tace"Aliyu yauga Auntyn Bilal ka gani sai ku gaisa".wani irin haɗe fuska yayi yana kallon Aunty Aysha data tsare shi da ido.cikin ƙasa da kai Halima tace"ina wuni".tana kuma maimaita sunan Aliyu a ranta.yana tafiya yace"lafiya" .yayi hanyar waje wani irin haushi ya turnuƙe zuciyar Khadija kawai tace"to zamu wuce"."da wuri haka kuma".Aunty Aysha ta faɗa.miƙewa Halima tayi tace"dama rakiya zan mata na biyo,insha Allah zan shigo ai".itama Aunty Ayshan miƙewa tayi tana jan hannun Bilal daya maƙalewa Halima tana cewa"to Allah ya kaimu,sai kin shigo".da ƙyar ta janye Bilal daga wurinta sannan suka fita Khadija sai masifa takeyi dan khadija badai faɗa ba.banza Halima ta mata har suka rabu kafin ta dawo gida zuciyarta cike da tambayoyi iri iri.Ɓangaren Hajiya Mama kam duƙe suke a gaban wani ƙaton mutumi baƙi ƙirin dashi sai mazurai yake yi cikin murya marar daɗin saurara yace"me kike so ayiwa yarinyar?".nisawa Hajiya Mama tayi tace"boka ina so a turawa yarinyar baƙaƙen aljannun da zasu hanata zama lafiya,wanda zasu rikita mata rayuwa wani lokacin ma ayi tunanin mayyah ce ko kuma ta haukace,so nakeyi idan suka tashi a kamota can dawa,kuma duk wanda ya kusanceta da sunan so ko tausayinta to ya mutu ya zama kuma ace ita ake tunanin tana kisan".jinjina kai Bokan yayi yace" zaki biya million 1,aikinki an gama da batun shi yanzu haka suna niyyar shiga jikinta,sai dai duk ƙarshen wata xaki basu jinin baƙaƙen dabbobi wannan dalilin ne zaisa duk tsanani su kasance tare da ita".wata irin murmushi ya suɓucewa Hajiya Mama tana jin damuwanta yazo ƙarshe ta buɗe jakkarta ta kwaso kuɗin ta jibgesu gaban Bokan sannan ta tashi suka bar kan dutsen ita da Hajiya talatu.daidai Halima zata shiga gida taji wani irin masifar sanyi na ratsa duka sassan jikinta ga tsigar jikinta data mimmiƙe gaba ɗaya,lokaci ɗaya kuma taji ta daina jin sanyi .gate ɗin gidansu ta buɗe ta shige. ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE VOTE COMMETS SHARE DAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING.. [11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *ABU BILAL!!!* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *_______________________ ______________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation FREE PAGES PAGE 4 Zagaye ɗaki Hajiya mama takeyi tana faman ture ɗaurin ɗankwalin da tayi na shadda,ciza hannu tayi tana zancen zuci da kuma tunanin maganarsu ta jiya tana kuma zancen zuci,lokaci ɗaya tayi na'am da abunda zuciyarta ta saƙa mata,waya ta ɗakko tare da danna wa lambar aminiyarta kira bugu ɗaya ta ɗaga bakin ta da faɗin"kaga uwar mugai,kaga Hajiya Jamila mata ga Alhaji Abubakar amarya shalele,angulu bata jewar banza,yau kuma da wacce akazo?,me aka ƙunso mana?".murmushi Hajiya Mama ta saki tace "wallahi talatu kinsan kan tsiya"ta ƙare maganar tana muskutawa da gyara zama sosai ,sannan taci gaba da cewa "nifa na gama yanke hukunci,yarda ban taɓa haihuwa a gidan nan ba,bana kuma iya bawa mutanan nan Lamis wallahi,shi kaɗai Allah ya bani wannan dalilin yasa na gama tunanina tsab na yanke shawarar basu ƴar mijina Halimatu".wata muguwar dariya Hajiya Talatu ta saki tace"gaskiya kin ƙware a fannin mugunta,kina ganin Alhaji Abubakar bazai gigice ba idan ya rasa Halimatu?,kifa tuna yayi tsawon shekaru be samu haihuwa ba sai daga baya ya samu Halima kuma ke shaida ce lokacin da yazo neman aurenki sai da ya baki tabbacin in dai kika so Halima to babu abunda bazai gagare sa yayi maki ba in dai a duniyar nan ne".tsuka Hajiya Mama taja tace"to sai meye daga wannan?,ni meya ruwana in ma mutuwa xaiyi ya mutu a raba gado a bani wannan uwar dukiyar daya tara in kwashi kasona in yi gaba,ko da Halimatu ranshi ce sai dai yayi haƙuri dan na gama yanke shawara ita zan bada,kuma ni kinsan basan shegiyar yarinyar nan nake ba mai kama da aljannu,ko kaɗan ita da uwarta bana ƙaunar ganinsu bare kuma naji tausayin su,bayan na gama da ita zan juyo takan uwar ne ae itama ".dariya sosai suka saka kafin Hajiya Talatu tace"hakan yayi,kuma wannan itace hanya mafi sauƙi da zaki kawar da maƙiyanki ba tare da kowa ya sani ba,yanzu idan dare yayi sai ki sanar kawai"da haka sukayi sallama kowa da abunda yake saƙawa a ranshi.tunda suka tashi tahfeez babu wanda yasan dawowanta kai tsaye ɗakinta ta shiga tare da faɗawa akan bed tare da lumshe idanuwanta dake niyyar canza launi,zanen surarshi kawai take gani tana mata yawo da yarda bakinsa ke motsawa yana magana,wani irin ƙayataccen murmushi ta saki tana kuma sauke tagwayen ajiyar zuciya tana jin yarda zuciyarta ke bugawa da tsananin tunaninsa tun daga jiya zuwa yau bata da sukuni sai faman tunanin Abu bilal,ganin duhun magriba ya taho yasa ta miƙe ta shiga toilet sai lokacin ta cire Unifoam tayi wanka kafin ta ɗauro alwala ta fito,cikin sauri ta shirya cikin riga da siket na material kafin ta kabbara sallah tunda ta gama sallahn bata tashi ba sai da akayi sallan isha sannan ta miƙe tana tattara kayan da tayi sallah kafin ta wuce gaban mirrow dan gyara jikinta.."wai ni kan ina Halima?,tun ɗazu banji alamun shigowarta gidan nan ba bare kuma motsinta"Hajiya Mama take tambaya.nisawa Amma tayi tace"ina jin shigowarta kuwa kinsan ƴar taki halinta sai ita wani lokacin shiyasa nima na shareta".gyara zama Faruq yayi yace"wayyo Ammanmu mun tuba ae da sai ki duba mana ita".ya ƙare maganar yana langwaɓe kai kamar zaiyi kuka.jinjina kai Amma tayi tace"Lallai ma Umar tunda an gaya maka nima bani da aikin yi ne ,tayi ta gama zata fito ta same mu ne".murmushi ya saki wanda ya ƙara fito da ainahin kyawun shi.Umar faruq irin mazan nan ne masu tsayi da kuma kaurin jiki sai dai ba sosai can ba,fari ne tas yayin da fuskarsa ke ɗauke da daradaran fararan idanuwa ga bakinshi gwanin kyau red,yana da saje da kuma gemu da gashin baki ga gashin kanshi baƙi sidiƙ kamar na larabawa.Ɗaga kanshi yayi yana dubanta tana tahowa cikin natsuwa tallabar kumatunsa yayi duka biyu yana kafeta da idanuwa ko kibtawa baya son yi.kai tsaye itama kusa dashi tazo ta zauna tana cewa"Yaya lafiya".taɓe baki yayi sannan yace"hala yau gidan lefi akayi maki kenan?".turo ɗan karamin bakinta tayi kafin tace"ko ɗaya fitan ne bana ji".dariya Hajiya Mama tayi tace"banga lefinki ba ƴar gado,kinga duk yau Daddynki yana waje can bukka shima haka ya faɗa mana".da sauri ta miƙe tana yin hanyar waje tana faɗin"ashe Daddy yana gidan shine ko a sanar da ni".miƙewa Amma tayi tana yin hanyar kitchen tana cewa"aifa shikenan,shima Daddyn ya gama sukuni ae".miƙewa Faruq yayi ya rufa mata baya.kai tsaye gate ɗin gidan ta buɗe babu kowa a wajen shiru sai hasken fitulin da suka ƙawata unguwar fita tayi tare da rufe gidan tana ƙoƙarin shiga ɗayan gate ɗin dake jikin nasu in da nan ne wurin shaƙatawar Daddy kuma suke kiransa bukka saboda gaba ɗaya wurin rufin bukka ne ƴar yayi wurin ya ƙawatu matuƙa.ko kaɗan bata kallon gabanta take tafiyarta burinta kawai taga Daddy ji tayi ta faɗa wa abu.cikin wani irin masifar tsoro da zaro ido taɗanyi baya tana niyar kurma ihu.saurin saka hannunsa yayi ya rufe mata baki yana kuma dallah mata harara cikin tsawa yace"ki rufe mun baki a wajen".wani irin ruɗewa ta kuma yi ko kaɗan bata ɗauki muryarsa ba saboda tsananin tsoron da take ciki tuni hawaye sun soma zarya akan kumatunta ta soma kyarma.kallo ɗaya yayi mata ya ganeta ras tsaki yaja tare da murɗe mata kunne yace"ke saurareni kona faffala maki mari".carab kunnuwanta kamar a mafarki suka amsa sautin daddan muryarsa dib dib haka ƙirjinta ya buga da masifar ƙarfi,a hankali ta soma buɗe daradaran idanuwanta wanda suka soma sauya launi tana ƙarewa fuskarsa kallo.wani irin haɗe fuska yayi yace"nifa bansan kallo".kunyace ta kamata tayi ƙasa da kanta yayinda murmushi ke suɓuce mata wanda batayi niya ba.cikin sanyin murya tace"Ayyah Hamma ka bani tsoro ".matsawa yayi daga kusa da ita yayi wucewarsa da sauri ta juyo tana bin bayansa da kallo .daidai nan Faruq ya ƙaraso tsareta yayi da idon tuhuma shima yana bin bayan Abu bilal da kallo kafin yace"waye shi?".taɓe baki tayi tare da buɗe hannuwa alamar bata sani ba tace"na bigeshi ne kawai".jinjina kai yayi kafin yayi gaba tabi bayansa a nan suka samu Daddy kishin kiɗe yana karatun jarida.kai tsaye matsawa tayi kusa dashi ta lafe a jikinsa tana tunanin me ya kawo Abu bilal unguwarsu.kallonta Daddy yayi ganin tayi shiru yasa ya shafo kanta yace"Ammina kina lafiya dai ko?".gyaɗa kai tayi alamar eh,sai wurin 9 suka koma gida shima dan gobe monday yasan Halima zataje school.da tunanin Abu bilal bacci ya ɗauketa.Ɓangaren Abu bilal kuwa yana shiga gida ya samu duka ƴan gidan zaune a tabarma.da sauri Karima ta miƙe tana masa sannu da zuwa beko kalli in da take ba ya ansa da "lafiya"zaiyi wucewarsa.Dattiya dake kwance ya ɗago yace"yanzu Sude sai dai kazo ka wuceni ko gaisuwar arxiƙi babu?",tsakani da Allah baka kyauta mun ba,ni mema na haɗa da kai banda tsoron Allah,nan nan Uwani ta gama kwashe maka karama amma na murje ido ina yayyafim ruwan bala'i"wani irin zabura Mama Uwani tayi tace"wallahi Dattiya kaji tsoron Allah ka canza Hali,ina ce kaine ka fara maganar Aliyun".wiƙi wiƙi da ido haka Dattiya yayi sai kuma yaja gefen babbar riga yana matsar ƙwallah tare da faɗin"shi dai ai Allah yana gani,kuma ba azalimin kowa bane,waye wani Sude can Allah na tuba bare da girmana na zauna ina gulmarshi".ihun da Karima ta saki ne yasa su duka miƙewa kowa yana raba ido a guje tayi ɗaki tana danna kuba,Mama Uwani ma tayi ɗakinta da gudu,kafin Dattiya yayi aure tuni Rambo ya iso kusa dashi yana niyar cabkar ƙafarsa wani irin tsalle yayi ya kama katanga ya afka gidan Malan Audu ya faɗa a bisa tuƙwanan ruwan labara yana ihu iya ƙarfinsa,Abu bilal kam ko a jikinsa ya buɗe ɗakinsa ya shigewarsa.a guje Malan Audu ya fito yana salati tare da kama Dattiya yana miƙar dashi tsaye yana cewa"kai kuwa lafiya ?".fizge rigarsa yayi daga hannun Malan Audu yace"da lafiya ka ganni haka?,wancan mugun yaron ne ya sako mana alkaba'i a gida,amma ka barni da Sude nasan tsiyar dazan ƙullah mashi,Allah zaiga tsiya zaiga Dattiya ma ba daga baya ba mun daɗe a duniya ana damawa damu.Malan Audu da yake aminin Dattiya ne komai suke ƙullawa tare suke yi ya bushe da dariya yace"kai kake raga masa dama,da gida na yake aeda tuni wani labarin akeyi ba wannan ba,haka kawai yaro ya zauna a gari yana cutar mu?".jinjina kai Labara tayi tace"wallahi kudai kiyayi kanku,bakin rijiya ba dai wurin gaɗan makaho bane,Aliyu Sudais dai ba daga baya ba duka zai iya daku".wani irin hayayyaƙo mata da sukayi yasa tayi saurin shigewa ɗaki tana sharesu.Dare ya raba tsakiya misalin ƙarfe 2:30am daidai agogo ta nuna a lokacin ne kuma na hango Hajiya mama lulluɓe cikin shigar jan kaya da baƙi tayi wani iri babu kyan kallo wani baƙin kasko ne a hannunta a haka ta haɗa wuta a ɗakinta tana ƴan sirkullenta,wani ƙaton mutun mai kama da siffar da babu kyan kallo ya bayyana yana wani irin ɓaɓɓaka dariya yana cewa"lokacin sadaukarwarki yayi,dole ne kiyi sadaukarwa dole ne ki bada jini ,dole ne ki bada rai Jamila".cikin rashin tsoro da kuma ƙwarewa a harkan ta kwashe da dariyan itama cikin rashin wani tunani tace"na bada Halimatus sadiya ƴar mijina,yarinya mafi soyu akab ahalinmu".wani irin dariya ya saki hayaƙi yana fitowa daga bakinsa yana faɗin"zaɓi mai ƙyau,dodo zaiyi alfahari dake Jamila ci gaba da ɗaukaka ya samu rayuwarki,kin bada sabon jini"da ƙarfi ya soma ƙwala kiran Halimatus sadiya,Halimatus sadiya,Halimatus sadiya"sai da ya faɗa haka har sau ukku sannan ya ɓace ɓat tare da duk wani abun da Hajiya Mama ta haɗa a wurin.wani irin firgigit Halima ta miƙe tsaye yayinda idanuwanta ke a rufe babu alamar ta farka daga baccin da takeyi ɓat ta ɓace daga dakin babu ita babu alamunta . ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE VOTE COMMENTS SHARE [11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *ABU BILAL!!!* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *_______________________ ______________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation FREE PAGES PAGE 5 Zagaye wurin yake da mutane iri iri kowa irin shigarsu ɗaya watau ɓaƙi da ja,wutace keci a tsakiyar babban filin da suke zagaye dashi kowa da abunda yakeyi ,wani ƙaton mutun ne zaune ba kyan gani fuskar nan murtuƙe babu alamun annuri a tattare da ita ya riƙe wata ƙatuwar sanda mai zanan maciji.a daidai tsakiyar mutanan wanda ƙaton mutumin da ya ɗauko Halima ya bayyana,haka itama Haliman ta bayyana har lokacin idanuwanta a rufe suke alamar tana bacci,nuna ta yayi da wannan sandar ta hannunsa tuni ta faɗi akan gwaiwowinta tana layi kamar wacce tasha wani abu.wata iriyar dariya suka fashe da ita,yayin da wata mata mai suna Dosun ta taho riƙe da ƙwarya cikinta ɗauke da wani baƙin ruwa kai tsaye gaban Halima tazo ta ɗago kanta ta saka mata ƙwaryar a baki tsab ta ɗure mata fiye da rabin ruwan kuma ta shanye sauran kuma ta wanko mata tun daga kanta har ƙafafunta.wata irin miƙa Halima tayi tuni xufa ya fara keto mata ,a hankali ta soma buɗe dara-daran idanuwanta wanda suka soma riƙiɗewa ,cikin rashin kuzari ta soma kallon in da take tana kuma jin ihu kala kala a wurin,a kan fuskar wannan ƙaton mutumin ta sauke idanuwanta da sauri tayi baya tana furta"innalillahi wa'inna ialaihir raju'un".sosai muryarta ta shiga kunnuwansa ya rufe ido da ƙarfi ya kuma miƙe zumbur.Halima batayi aune ba taji sirinji a cikin damtsen hannunta ana jan jininta wani irin zafi da daɗaɗin azaban allurar ya shigeta lokaci ɗaya,runtse ido tayi hawaye yana kawo mata ta miƙe tsaye da sauri tana furta"ke lafiya".ko kallonta Dosun bata yi ba tayi gaba da jinin Halima data ɗauka.raba ido Halima ta fara tana kuma karanto duk wata addu'a data zo bakinta ganin wannan mutumin na doso in da take tsaye,kuma sai lokacin ta buɗe idanuwanta da kyau tana ƙarewa in da take tsaye da kallo ba ƙaramin tsoro ya shigeta ba.zagayeta Oga Sam yakeyi kamar zai cinyeta ɗanya haka yake zuro harshe.cikin muryar kuka tace"dan Allah kada ka cutar da ni,kaji tsoron Allah,ni ban sanku ba,in lefi nayi maku dan Allah kuyi haƙuri".wata uwar dariya suka saki gaba ɗayansu wanda ke iya gane abunda take faɗa.cikin hausa marar ɗaɗi da kuma murya marar ɗaɗin ji Oga sam yace"kin damemu da magana a nan wajen".wani wuƙa mai sheƙi da kaifi taga ya bayyana a hannunsa ya ɗaga da niyar caka mata.wani irin ƙwalalo ido tayi ta soma karanta ayatul kursiyyu da duka iya ƙarfinta da sautin muryarta.tuni hannunsa ya soma rawa yana ƙarewa kyakyawan fuskarta kallo wanda a yanzu ta riƙiɗe ta koma ja saboda tsananin tashin hankalin data tsinci kanta a ciki.Ɗan jim yayi kafin yaja baya xuwa wani ɗaki cikin sauri yawancin mutanan dake wurin suka rufa masa baya.ganin duk wanda ake buƙata ya shigo yasa ya fara magana yace"wannan yarinyar xai mana wahala mu iya kasheta da sauƙi,kuma tabbas idan muka takura akan hakan xata mana ɓannar da shekaru da dama aka mana irinta ko kuma in ce ta xarce wacce aka mana ma,wanan dalilin yasa na yanke shawarar mexai hana itama mu janyota a ƙungiyar nan,kafin idan ta gama mana amfani a lokacin babu Allah a bakinta sai mu kasheta kuma daga yanzu lokaci zuwa lokaci xata kasance cikin tsananin azaba da tsoratarta wannan shine hukuncin da xamu mata na kasa kasheta da mukayi a yanzu".babu wanda yaja da maganar tasa lokaci ɗaya dukkansu suka haɗa hannuwa suna karanta wani abu marar ɗadi da yin mubaya'a akan hukuncin da ogan nasu ya yanke.yarda sautin muryarsu ke fita haka hajijiya ke juyar da Halima kanta na matuƙar sarawa da masifar ƙarfi,lokaci ɗaya cikinta ya wani murɗa ta zube a wurin a kakkafe tana kyarmar sanyi wani irin azaba ne ke ziyartarta yayin da ta gara rolling a cikin ƙasar wurin kamar wacce take zagaye wurin.wani irin kukan wahala ta saki lokacin da take jin saukar wani ruwa a jikinta kamar ana yayyafa mata wuta,ga masifar wari,haka tana ji tana gani suka kuma ɗura mata wanan ruwan cikin nishin wahala ta sulale wurin wani wahalallan bacci nayin gaba da ita.nunata Oga Sam yayi da wannan sandar ta hannunshi tuni ta ɓace bat kamar ba'a taɓa kawota wurin ba.dukansu suka fashe da tsananin dariyan mugunta.a cikin daren kuma Talatu ta kirawo Hajiya Mama ta zayyane mata abunda ya faru da kuma hukuncin da Oga Sam ya yanke,a razane ta miƙe zaune tace"ina ce dai bata san wanda ya kawota wurin ba?".dariya Talatu tayi tace"kwantar da hankali ina zata samu damar sani bayan ciwan azaba daya sakata gaba,ae ina mai tabbatar maki ko ni da naje wurin bazata taɓa ganeni ba bare kuma ke".wata sanyayyar ajiyar zuciya Hajiya Mama ta sauke tace"wallahi har naji sanyi,ai ni ƙara ma aita gara mun ƴar iskar ta fitini kowa ta zama anno ba kafin tabar duniya,anjima kizo zaki rakani kan dutse can bicci insa a ƙara ingizowa shegiya abunda xai mun maganinta dan wallahi ni nafi kishi da ita akan uwarta ma".dariya sosai suka saka kafin suka yi sallama da rabuwa akan cewa da azahar zasu je bicci.tun da wuri Daddy yayi kari suka fita office shi da Faruq ko ganin Little be tsaya yi ba saboda kiran daya samu na gaggawa.kallon agogo Amma tayi a lokacin ne kuma agogo ta buga ƙarfe 8:00 daidai na safe,sallamar Iro Driver ta katse mata tunaninta ya matso ya rinsina a gabanta ya gaisheta cike da girmamawa ta ansa kafin yace"Hajiya Babban ,Ammin masu gida yau baxata je makaranta bane?".miƙewa tayi tace"nima yanzu xan shiga na dubota naga shirun yayi yawa ka jirani kaɗan".ta ƙare maganar tana nufan part ɗinta.kai tsaye ɗakin Halima ta tura.hangota tayi lulleɓe akan bed sallama tayi ta shiga ɗakin gefan bed din ta zauna tana yaye duvet ɗin da tayi rufa dashi,daga ita sai ƴar ƙaramar riga kallo ɗaya Amma tayi mata ta gane kwata kwata baccin baya yi mata daɗi ga wata wahalalliyar ajiyar zuciya da take saukewa lokaci zuwa lokaci,idonta ta mayar akan jijiyar kanta dake halbawa da ƙarfi gasu kuma sun fito ruɗu-ruɗu kamar wa'anda aka xana.hannunta na rawa takai akan dokin wuyanta da sauri ta janye jin yayi matuƙar zafi.bubbugata tayi tana cewa"Sadiya,Sadiya".wata irin miƙa Halima ta saki kafin lokaci ɗaya ta wara dara-daran idanuwanta wanda suka kaɗa suka zama jajir,brown ɗin ciki kuma ya juye ya koma baƙi-ƙirin.da ƙarfi Amma ta rufe idonta tana cewa"Hasbunallahu wani'imal wakil".sannan ta buɗe idonta cike da firgici tace"Sadiya meke damunki haka?,kinga idonki kuwa?,ko kinyi kuka ne?,amma kuma ko kuka baya riƙiɗar da idon ki haka,baki da lafiya ne?".a ruɗe Amma duka ke jero mata wanan tambayoyi,ɗago ido Halima tayi tana kallon Amma wanda a lokacin kuma tsab idonta ya koma fari ƙal da brown ɗinshi sai dai ƙallin hawaye dake kwance tab a idon ji tayi baƙinta yayi masifar nauyi ta kasa furta abunda ke ranta sai kawai ta tsinci kanta da cewa"Amma zazzaɓi nake kuma nasha Drugs".cike da al-ajabi Amma kebin idon Halima da kallo can dai tace"to Allah ya sawaƙe ki samu ki tashi ki watsa ruwa sai ko tea ne kishi sai ki ƙara shan maganin".da to kawai ta ansa kafin Amma ta fita taja mata ƙofar ɗakin.zumbur ta miƙe zaune,red haka eyes ball ɗinta yayi kamar wanda ya kawo danja kuma ya ɗauke glass cup ɗin data kallah ya faɗo daga table ya fashe a wurin.saurin runtse ido tayi kafin idonta ya dawo daidai sannan ta miƙe ta shiga toilet ji tayi jikinta wasai kamar ba ita ta tashi tana ciwan kai ba,wanka tayi tayo alwala dan har lokacin batayi sallan asuba ba,da ƙyar tayi sallan wacce babu natsuwa a cikinta sannan ta saka riga da siket na atamfa kasa murxa komai tayi sai turaren data fesa ta ɗaura ɗan kwalinta ta faɗa kan bed take wani baccin ya kuma shureta wanda take yinshi cike da mafarkai iri iri mararsa daɗi. ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE. VOTE COMMENTS SHARE DAN GIRMAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING [11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *ABU BILAL!!!* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *_______________________ ______________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation `Start``` ```patronizing``` ```ABU BILAL``` luvly ```fans Ta hanyar wannan account din 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337. FREE PAGES PAGE 8 A hankali ta tura Gidan ta shiga babu kowa alamar kowa ya tafi masallaci yasa ta wuce ciki kai tsaye.kafin ta ƙarasa shiga Hajiya Mama ta shigo gidan Lamis na miye da ita tsayawa Halima tayi tanawa Hajiya Mama sannu da dawowa,da fara'arta ta ansa tana cewa "kai Alhmdllh jiki yayi kyau,Allah ya ƙara lafiya"da ameen Halima ta ansa tana mayar da kallonta ga Lamis daya ƙureta da muggan idamuwansa ko kibtawa baya yi,ƙasa tayi da kai tace"Yaya Lamis ina wuni".fuska ya saki yace"lafiya qlau tauraruwar mata,ya jikin naki?".da Alhmdllh ta ansa tana wucewa ciki ya bita da kallo.Harara Hajiya Mama ta jefa masa tace"kallon duk na uban menene?,wallahi Lamis ka kiyayeni kama ɗauke idonka daga kan Halima dan bama zan yarda da wannan ba".ajiyar zuciya ya sauke yace"to Mama akwai wata matsala ne dan naso Halima?,naga kuna shiri kuma zamanku lafiya"."rufemun baki ban yarda ba ban kuma amince ba,karma kasa wa kanka wannan alaƙan" ta ƙare maganar tana wucewa cikin.da kallo ya bita kafin ya bi bayanta yana murmushi.Lamis yaro ɗaya tilo ga Hajiya Mama duk duniya shine kawai take matuƙar so bata kuma iya cutarwa.Lamis irin maxan nan ne masu barƙwanci da son mutane ko kaɗan bashi da wani hali da zaka kushe.yana da matsakaicin kyau.har suka wuce part ɗin Hajiya Mama yana kallon Halima data fito daga kitchen ya daɗe rabon daya ganta saboda karatun daya fita ƙasar waje,duka kwanan shi biyu da dawowa kuma sai lokacin ya ganta.zama Hajiya Mama tayi tana kallon shi,saurin sunkuyar da kai yayi ya kasa cewa komai.taɓe bakinta tayi tace"ya Kawun naka".murmushi yayi yace"yana lafiya".miƙewa tayi tace" bara na kawo maka abinci".cikin cool voice ɗinsa yace"am not hungry".dawowa tayi ta zauna tace"kai ka sani ai".shiru bece mata komai ba kafin ya miƙe yace"bara na gaishe da Amma".taɓe baki tayi bata ce komai ba,daga haka ya fita ya shiga part ɗin Amma bakinsa ɗauke da sallama.Amma ce zaune da Faruq suna fira.da fara'a Amma ta ansa tace"lallai mutanan turai an sauka kenan,kai munyi ta barka karatu ya kammalu".da murmushi fuskarsa yace"barka da dare Amma,na sameku lafiya"."lafiya Alhmdllh "ta ansa kafin yaba Faruq hannu suka gaisa fuska sake."Ammi,Little maza kizo ki kawo wa Yayanki abinci duk da nasan always he's full".ɗan shafa kansa yayi yana murmushi yace"yau dai zanci abincin Ammana tau".fitowa Halima tayi ta wuce kitchen ta haɗo masa abinci a tray tazo ta duƙa har ƙasa ta ajiye tace"kuma duka zaka cinye".cikin alamun sun saba yace"daina kula ni,bayan ɗazu kin nuna kamar baki sanni bama,ko murnar dawowa na baki yi ba".zama tayi tana kama kunnenta tace"Allah nayi murna kawai dai ɗazu ima jin jikin duk sai a hankali ne".dungure mata kai Faruq yayi yace"what ever ai kinyi murna Yaya Lamis ya dawo".dariya suka saka duka Lamis yace"Allah ya ɗayyi ba Ummaruje abunda nake so ta fahimta kenan".tsuke fuska Faruq yayi yace"har gobe ba zaka daina ɓata mun suna ba Lamis".dariya kawai yayi yana safkowa dancin abincin da Halima ke zuba mashi.haka suka sha fira sai wurin 9pm ya tafi zuciyarsa cike da tunani kala kala.ko da yazo kwanciya fir bacci yaƙi zo masa babu abunda yake gani sai fuskar Halima da ganin bacci ba xai zo ba yasa ya tashi ya ɗauro alawala ya soma sallah...tun sassafe ta tashi ta soma shirin makaranta bata tsaya ɓata lokaci ba ta shirya cikin trouser ash colour sai riga iyakarta gwaiwanta mai tsaga daga 2sides ɗinta kalar milk sai ƙaramin himar sosai kayan suka mata kyau white socks ta saka da black toms ta saɓo ƙatuwan school back ɗinta itama black ta fito tana saka eyes glasses dinta tana Kuma kallon black watch ɗin dake daure a tsintsiyar hannunta,kai tsaye dining ta nufa in da ta samu ƴan gidan gaba ɗaya a zaune,side hug tayiwa Daddy dake zaune tace"Good morning sir",shafo kanta yayi yace"morning my little how is your body?".tace"alhmdllh" sannan ta juya ta gaishe da Hajiya Mama dake saka masu chips a plate,itama da fara'a ta ansa sanan ta gaishe da Amma da Yaya Faruq tana zama a chair ta kusa da Daddy,tea kawai tasha tana niyar miƙewa Daddy ya riƙeta yace"a'a little kici chips please yau na kawo maki tsaraban chocolate".ae ba shiri ta koma ta zauna tana ɗaukar fork tace"ai dole naci,dama Yaya Lamis yace yamun tsaraban Chocolate".ta ƙasan ido Hajiya Mama ke kallonta tana ayyana wani abu a zuciyarta.sauri sauri taci chips ɗin kafin ta miƙe da sauri tana duƙawa gaban Daddy ,ya gane nufinta dan haka ya ɗaura hannunsa a kanta yace"Allah yayi maki albarka ya kuma bada ilimi mai amfani".cikin jin daɗi ta ansa da "ameen ameen yh rabb"kafin tayi masu sallama tana cewa"Ammana kimun addu'a na tafi".ganin time be wuce ba yasa suka biya suka tafi da Khadija dan ita a napeep take tafiya school ɗinma Daddyne ya sakata saboda mahaifinta bamai ƙarfi bane.tunda suka shiga school ta fara jin yana yinta na canzawa kamar kanta zaiyi ciwo jin beyi ɗin ba yasa ta share ta soma harkokin gabanta har sukayi break tanajin ba daɗi,tana ta zaune akan seat Khadija ta kalleta tace"ki tashi muje muyi break".cikin rashin son yin magana tace"i'm full".kallonta khadija tayi tace"da kika ci mene zaki ce wani kin ƙoshi".tuni idanuwanta sun soma canza launi cikin ƙasa da murya tace"please leave me alone"saurin miƙewa Khadija tayi tsaye tana kallon yarda lokaci ɗaya idanuwan Halima da muryarta suka sauya.kiran da Uncle ɗinsu ya turo yana mata yasa ta fita tana tunanin meke faruwa haka da Halima.wani irin zumbur Halima ta miƙe tana jujjuya kai da gudu tayi hanyar waje ba tare da tasan in da ta dosa ba.da gudu Zahra tayi office ɗin Uncle walle danta gayawa Khadija.a hankali yake tafiya cike da natsuwa hannuwansa zube cikin aljihun wandon jeans dake jikinsa yana tsotsar lips ɗinsa kamar ya samu sweet fitowarsa kenan daga primary sections yazo ya siyawa Bilal textbooks . da ƙarfi ta bankesa tana niyar wucewa saurin riƙeta yayi ya fizgota da baya yace"ke baki gani ne".ganin fuskar Halima yasa ya waro idanuwa yace"again everywere you".dafe kai tayi da ƙarfin gaske ta kwarara wani uban ihu ta tafi zata faɗi , wani ƙaton stone ya gani wanda map ɗin school ɗinsu ke sama yasa yayi saurin tarbota ta faɗo jikinshi gudun kada ta faɗawa stone ɗin.a daidai lokacin kuma Khadija da sauran class mates ɗinsu da tearcher's suka ƙaraso wurin.dafe kai Uncle walle yayi yace"heee oh my God Halima,Halima".wani irin kuka Khadija ta saki ta duƙa tana girgixa Halima tana kiran sunanta.tsaki Abu bilal yaja dan ko kaɗan baya son hayaniya.xame jikinsa yayi daga nata ya miƙe xai tafi da sauri principal na secondry ya riƙesa yace"please your'e muslim help us and solve tha problem".taune lips ɗinsa yayi da ƙarfi kamar zai huda ya shafi gashin kanshi ya duƙa ya sunkuci Halima yace"i will take her home".ba yarda Khadija bata so ta bisu ba amma sam aka hana sai dai suka tafi da Uncle Walle.a motar Abu bilal suka tafi gidan sai da Uncle Walle ya nuna masa gidan kafin yayi horn gateman ya leko ganin besan motan ba yasa yace"daga ina?,wa ake nema?".wani siririn tsaki Abu bilal yaja kafin yace"ƴar mai gidan aka kawo".da sauri ya buɗe gate ɗin ,Shikam ya danna hancin motarsa ciki bai ƙarasa parking lot ba ya kashe motan ya fito baya ya zagayo ya ɗauko Halima wanda har lokacin take kwance tamkar gawa,kamar ya ɗauki baby haka ya rungumota ya nufi main entrance na gidan ya fara danna bell ɗin gidan.Amma dake kitchen tace"Aysha kije ki duba waye a ƙofa".da to Aysha ta ansa tana ajiye bowl ɗin hannunta ta fito zuwa ƙofan tana buɗewa ta zaro ido da ƙarfi tace"Yaya Halima".ae da gudu ta koma kitchen bakinta na rawa tace"Amma,Amma Yaya Halima come and see her".kallonta Amma keyi ganin taƙi natsuwa yasa Amma tace"bana son sakarci idan ba zaki natsu kiyi magana ba kije ki cire uniform ɗinki kixo ki wanke mun cavage ɗin nan".haɗiye yawu tayi da ƙyar tace"wallahi Amma Yaya ce aka kawo ".ajiye knife ɗin hannunta tayi ta fito parlon ta nufi ƙofa Aysha na biye da ita.wani irin sororo Amma ta tsaya tana kallon Abu bilal da ƙyar ta iya lalubo magana tace"subhanallah ku shigo".ciki Abu bilal ya shiga yana daura Halima akan ɗaya daga cikin royal chairs na parlon.tamkar gawa haka ya ajiyeta kafin ya kalli Amma yace"barka da gida"yana ɗan risinawa."barka me yake faruwa ne?".shiru Abu bilal yayi ya kasa cewa komai sai Uncle walle ya shigo ya mata bayani,ajiyar zuciya ta sauke tace"na gode ƙwarai,Allah yayi maka albarka".murmushinsa mai kyau yayi yace"ameen,ameen Allah ya bata lafiya ya faɗa yana fita daga parlon.sai da ya fita da uncle walle sannan ya wuce gida. ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE VOTE COMMENTS SHARE DAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING [11/13, 23:34] Jordan: 11 Jan hannun Halima Khadija tayi tace"ki wuce muje class,Allah yaji kanta yayi mata rahma lokacinta ne yayi".wasu zafafan hawaye ne ke kawowa a idon Halima tana Kuma tuna mafarkin da tayi a jiya,jiki ba ƙwari tabi bayan Khadija suka wuce class.duk yinin ranar haka ta wuni sukuku ko kaɗan bata jin daɗin jikinta.zaune take a parlo sanye take da riga da siket na shadda ɗinkin yayi matuƙar yi mata kyau ga ɗaurinta irin zahra buharin nan tayi eye glasses ɗinta data saka ya kuma masifar yi mata kyau.a hankali ya turo ƙofan ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ya ƙaraso cikin parlon ,bowl ɗin naman dake hannunta ta ajiye tace"Yaya sannu da zuwa".shafa kansa yayi zuwa sajensa ya ƙwaiƙwayi muryanta yace"lafiya qlau Matar Yaya".langwaɓar da kai Halima tayi tace"ayyah Hamma Lamis ni sunan nan yana mun nauyi sosai".zama yayi daga ɗaya daga cikin chairs ɗin yace"owk soon zaki daina,to ke baki da saurayi ne?".dariya ta saki tana saka hannunta ta rufe fuskarta,ƙura mata ido yayi yana kallon zanan jan lallan daya ƙawata yatsunta yace"bana da ansa kenan?".Abu bilal ya faɗo mata a rai murmushi kawai tayi tace"am too young for that ae,kaifa kana da budurwa?".ɗage gira ɗaya sama yayi yace"akwai dai wacce nake so amma bata ma san ina sonta ba".zaro daradarn idanuwanta tayi da alamun mamaki tace"Yaya As in how?".shiru yayi can yace"forget about that"."yanzu Lamis ashe tun ɗazu ka shigo gidan ka barni ina fa faman jiranka?"Hajiya Mama ta faɗa.sosai kai yayi yana yin ƙasa da kai Halima tace"ai Hajiya ya kusa awa a wurin nan".waro ido yayi ya ɗauki pillow na chair ya jefa mata yace"halan na fara wasa da ke?".daidai nan kuma Faruq ya shigo da ido ya kafesu ya kasa cewa komai kawai gently ya wuce room ɗinsa ba tare daya tankawa kowa a parlon ba.miƙewa Lamis yayi yace"sorry hajiyata bazan kuma barinki kina jira ba,muje na ƙarɓi saƙon".girgiza kai Hajiya Mama tayi ta wuce part ɗinta."maxa tashi ki kaiwa Yayanki lunch ɗinsa".Amma ta faɗa .turo baki Halima tayi tace"Amma why not Aysha".riƙe da baki haka Amma tabi Halima da kallo tace"owk Ma ae bara mu zauna kawai kici gaba da bamu umarni".saurin miƙewa Halima tayi bata ce komai ba ta wuce kitchen ta haɗa komai a cikin tray ta ɗauko ta nufi ɗakin Faruq.knocking ta fara yi kafin yace"come in".da sallama ta shiga a bakinta ,kafin ta ɗago idanuwa tana kallonsa sanye yake cikin 3quater ash colour sai t-shirt black sosai yayi kyau sai fiyar da sanyayyan ƙamshi yakeyi,a daya daga 2 chair dake bedroom ɗin ya zauna yana crosing legs ɗinsa.ta ƙaraso ta janyo table ta ɗaura tray ɗin tace "Yaya your lunch".lumshe idanuwa yayi yana jin soyayyarta na kuma fizgarsa yace"meye tsakaninki da Lamis?".a bazata tambayar yazo mata turo baki tayi tana kallonsa kafin tace"nothing".kafeta yayi da idanuwa amma ya kasa cewa komai ganin ya soma latsa wayarsa yasa tayi ficewarta ya bita da kallo.a wurin Hajiya Mama kuwa Lamis ta tsare da ido tana cewa"Amma ina ga Muhammad tambayarka nayi ko?".ƙasa ya kuma yi da kansa yace"Hajiya nothing".wani uban harara ta jefa masa tace"wallahi kada ka kuskura naji wani abu tsakaninka da ita beside zama tare da ita ma i don't want it balle kuma wani relation ya shiga".ajiyar zuciya Lamis ya sauke yana jan gemunsa yace"i see nothing bad in it Hajiya".kamar Hajiya Mama zata fasa ihu a hassale tace"Muhammad get out".jim yaɗanyi kafin yace"kiyi hakuri "ya tashi yabar ɗakin.rarumar waya tayi tana dannawa Hajiya Talatu waya bugu ɗaya ta ɗauka kafin tace wani abu Hajiya Mama tace"ki ganemun yaron nan yana niyar janyo mun bala'in da yafi ƴarfina talatu".daga ɗayan ɓangaren Hajiya Talatu tace"what's wrong".cikin tsananin tashin hankali Hajiya Mama tace"Muhammad Lamis mana,ga dukkan alamu yana son yarinyar nan Halima,and everytime day and hour idan yazo yana maƙale da ita".Hajiya Talatu dake kwance ta miƙe da sauri tace"sam wannan ba mai yiwuwa bane,kin daisan abunda kenan,aike kika haifesa ki nuna masa bakya so ki rabasu ko ta ƙarfin tsiya mana".ajiyar zuciya Hajiya Mama ta saki tace"aini kaina ya ƙulle nama rasa abunyi Talatu"."dole kam asan abunyi in ba kina so ki rasa yaronki bane".sun tattauna sosai kafin sukayi sallama."wannan tsayuwan a kaina na menene kuma?".zamewa yayi ya zauna yace"ina Bilal?".shiru Aunty Aysha ta masa sunkuyar da kansa ƙasa yayi yace"kada ki gaya mun kin basu yarona"."idan an basu Bilal aiya cancanta yaje yaga ƴan uwansa ne,ni yanzu ba wannan ba gobe zakaje airport ka ɗauko Abban Khalifa at 9".ɗago kansa yayi yana kallon Bilal dake cewa "oyoyo Abu bilal"da gudu yaron ya rugo ya faɗa a cikin Abban nashi ya rungumesa da ƙarfi.shima Abu bilal ɗim rungume Bilal yayi a jikinsa sosai yana jin wani irin sanyi a ransa shafa kansa yayi kafin yace"Allah yayi maka albarka".murguɗa baki Halima tayi tace"ai dai muma an saka mana albarkan".ɗago kai yayi yana kallonta yana ƙisisifa irin rainin da tayi masa shi sai yanzu ma ya ganta danshi idonsa ya rufe Bilal kawai yake kallo.zama tayi kusa da Aunty Aysha tana cewa"to waishi kullun sai yazo gidan nan ne".dariya Aunty Aysha tayi tace"yaronsa yake zuwa gani Halima kinsan soyayyar uba da ɗa".zazzaro ido Halima tayi tace"ni dai kibar cewa Bilal yaronsa ne,ni nan nazo ki bani kayansa ne yamun kwana"."bazashi ba,he's going with me".miƙewa tayi tace"Allah bazai bika ba".ƙwafa yayi yace"da yake ke kika haifa mun shi"."ya isa haka,ba rigima nace kuyi ba ni na rasa meke shiga kanku abarmun Bilal ban fara talla dashi ba".langwaɓar da kai Abu bilal yayi yace"even weekend's bazai mun ba?"."eh bazai je ba".cup ɗin dake kusa dashi ya ɗauka ya jefa mata da ƙarfi Allah yaso silver cup ne.kallon cup ɗin kawai tayi ya canza direction da idonta dake blinking da red colour,kallo ɗaya ya mata a lokacin ya gane ba ita bace hakan yasa yaja sirirn tsaki ya miƙe yana jan hannun Bilal,carab tayi da hannun shi tace"no".da kallon Mamaki Karima ta bisu tana kallon yarda Halima ta tare Abu bilal wanda tun shigowarta gidan take kallon yarda take masa,karasowa wurin Karima tayi tace"yau naji ikon Allah,mutun da ɗansa amma ki hanasa fita dashi?,a ƙauyenku haka ake yi?".ƙoƙarin juyowa Halima keyi ta kalli Karima .cikin cool voice yace"Haleemah".tun daga maɗigar kanta har zuwa tafin kafarta sai da taji kiran sunan for the firt time daya fara kiran sunanta ji tayi kamar babu wanda ya iya kiran sunanta sai shi duk da bata cikin hayyacin amma sai da taji kiran har ranta,shikam yayi hakan ne gudun kada ta kalli fuskar Karima.tsura masa idanuwa tayi .shikam cikin sanyin murya yace"ke kibar wajen nan kafin na ɓallaki da gulma".wasu hawaye ne suka kawo idon Karima tayi ɗakin Aunty Aysha.sakin hanun Bilal yayi be kuma cewa komai ba ya raɓa ta gefanta ya wuce.riƙe hannun Bilal tayi da kyau kafin ta dawo ta zauna a hannunta Bilal yayi bacci kafin da ƙyar Aunty Aysha ta mayar da ita gida lokacin har an gama sallan isha'i.sai lokacin Aunty Aysha ta samu damar shiga ɗakin da Karima take har lokacin kuka ta samu tana yi muryarta harta disashe.cike da tausayawa ta zauna gefanta tare da kama hannuwanta ta juyo da ita tana fuskantar ta tace"alamu sun nuna kishi ƙarara a tattare da ke Karima,na daɗe ina karantarki akan Sudais sai dai ban gazgata ba sai yau".ƙasa Karima tayi da kai tana goge hawayen dake kawowa idonta cikin dishewan murya tace"nima bansan ya akayi hakan ta faru da ni ba Aunty,nima tsintar kaina nayi a haka,na kasa cireshi a raina".cike da tausayawa Aunty Aysha ta kalleta tace"nasan kinsan waye Aliyu da halinsa kuma,bazan iya cewa komai ba sai dai in ce ki dage da addu'a hakan shine kaɗai mafita insha Allah komai zai zo da sauƙi idan da rai da rabo sai kiga Allah yayi nasa ikon akanku".babu laifi hankalinta yaɗan kwanta da maganganun Aunty Aysha sosai ta lallasheta kafin sukaji sallaman Jagwaɗo yazo tafiya da ita gida.a haka ta bisa suka koma gida,da sallama bakinta ta shiga gidan da sauri Dattiya ya ɓoye kwanon kifin dake gabansa cikin babbar riga yana raba idanu yace"ni dai banji daɗi ba,ace a gidanka ma baka da sirri kome kake yi sai kawai kaji an shigo ba enscuse(excuse),to ni dai ba komai nake ci ba,ahtau yo ba komai nake ci ba bare kuma a ƙwalalo maka ido ɗan abunda zaka saka a bakin salati ya gagareka a gidanka"."kai dai bakaji daɗi ba wallahi Dattiya ina kaga bakin salatin?,ko kuma bakin shiga abunda babu ruwanka ba,wai ƴarka ta cikinka ita kake wa rowar kifi".wani salati Dattiya ya saki hawaye ya kawowa idonsa yace"amma Uwani kin cuceni,meye wani kifi?,me akayi akayi wani kifi,yanzu Karimen kike cewa ina wa rowa,Allah ne kaɗai zai shiga tsakanina da ke gaskiya,ko in haɗa kayana in bar maki gidan ko na huta da baƙin cikin da kike so ya kashe ni".Dariya sosai Jagwado ya saki yace"aiko Kawu zan baka wurin kwana ma".tsuke baki Dattiya yayi yace"kai tafi can mai cin haram,duk wannan jikin naka ai kayan Allah ya isa ka tara".dariya Jagwado ya kuma saki yayi hanyar waje abunshi. ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337. [11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇 *ABU BILAL!!!* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *_______________________ ______________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ```Start``` ```patronizing``` ```ABU BILAL``` luvly ```fans Ta hanyar wannan account din 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337. FREE PAGES PAGE 9 Ƙarasowa Amma tayi cikin parlon tana ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin dake a tattare da ita,zama tayi tare da kamo hannun Halima she's spechless tama rasa abun yi tana a haka Halima ta saki wata uwar ƙara ta fara fizge-fizge,Faruq da shigowansa kenan gidan ɗaukan wasu files daya ajiye ya shigo gidan da sauri yana ƙarasowa cikin parlon ya kuma ci karo da Halima dake ƙoƙarin barin parlon a guje,saurin riƙota yayi yace"ke lafiya?,subhanallah me yake damunki haka?".kokoyi suka soma yi tana neman ƙwatar kanta,da iya ƙarfinsa ya riƙeta da ƙarfi yana gizgizata yana cewa"wannan wacce irin ƙaddara ce kuma,spirit a jikin Halimana"ya ƙare maganar cike da rauni.tsaye Lamis ya tsaya yana ƙare masu kallo kafin yace"me yake damunta haka"wanda shigowarsa kenan.cikin muryar tashin hankali Faruq yace"may be spirit".waro ido Lamis yayi ganin tana neman tafi ƙarfin Faruq sai kururuwar ihu take yi wanda tuni ta jefar da himar ɗin kanta tattausan gashin kanta ɗuka ya baje a jikinta har fuskarta baka gani,sai da sukayi da gaske kafin suka iya sakata cikin wani ɗaki da ke anan parlon da sauri Lamis ya rufe ƙofan da key yana jingina da wurin.da sauri Hajiya Mama ta fito tana cewa "me yake faruwa ne?,ina wanka nake jiyo ihun little".har lokacin Amma tana ta tsaye ta kasa yin ƙwaƙwaran motsi.Faruq da damuwa ya gama dabaibayeshi ne ya faɗawa Hajiya Mama abunda ke faruwa,kafin tayi magana taga yarda Halima ke buga door ɗin ɗakin da take kulle tana jijjigawa iya ƙarfin,ƙaran fashe-fashe suka soma ji,a matuƙar tsorace Lamis yace"kada fa ta jiwa kanta ciwo".kallon ƙasan ido Hajiya Mama ta bisa dashi cikin hikima tace"to idan kuma aka buɗeta ta gudu fa?,ko kuma maƙota suka taran mana fa?".kafin kowa yayi yunƙuri Lamis ya buɗe ɗakin ya faɗa jin ƙarar Mirrow alamun ta fashe shi.hakan kuwa akayi dan hannuwanta duk jini har ɗiga yake yi.kusurwar ɗakin take nunawa tana jefa duk abunda ya tari gabanta ,,,wata dariya Dosun ta kwashe da ita wanda Halima kaɗai take iya jiyo dariyar da iya ganin Dosun,jinin Halima dake ɗiga ta lakuce ta ɓace bat.wani irin juyewa hannuwan Halima sukayi gaba ɗaya ta fara murmurɗewa tana niyar zubewa,saurin riƙota Lamis yayi zufa na zubo masa yana furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un yana kuma kiran sunanta.a hannunsa ta ƙarasa sandarewa ta koma kamar an nannaɗeta.wasu hawaye ne masu ɗumi suka soma zarya a fuskar Amma ganin ƴarta ɗaya tilo yacce take shan wahala waya ta ɗauka tana kiran Daddy ta daɗe kafin ya ɗauka bakinsa ɗauke da sallama,ansa sallamar tayi a sanyaye tace"Daddy kazo gida Little ba lafiya an dawo da ita daga scul".bece komai ba ya kashe wayan yana kwashe keys ɗinshi ya fito da sauri dan yasan da abun da sauƙi Amma ba zata taɓa kiransa ba musamman data kasance mace mai kawaici da haƙuri da kawar da kai ga komai..a katifan ɗakin Lamis ya kwantar da ita.Faruq kam ya gama daskarewa ƙwaƙwaran motsi ma ya kasa yi daga in da yake tsaye sai zufan dake zubo masa suna a haka Daddy ya shigo parlon ganinsu cirko-cirko yayi saurin shigewa ɗakin da yaga suna kallo,kai tsaye gaban katifan yazo yana duƙawa ya soma kiran sunan Halima tare da janyota jikinshi,ganin halin da take ciki yasa ya dafe kai yana jin matsanan ciyar damuwa na taso masa yace"what's wrong Aminatu"ya faɗa yana kallon Amma.cikin sanyin murya tace"i don't know kawai ance ta faɗi a school ne"."ina ga kamar iska ne fa"Hajiya Mama ta faɗa.kallonta kawai Daddy yayi kafin ya dawo da kallonsa ga Halima dake motsi.ido cikin ido Daddy ya kalleta in da idonta sun koma red ,eyes ball ɗin kuma suka koma black saurin janye idonsa yayi saboda jin wani abu na ratsa shi ,kaya suka soma zubowa na fashewa na fashewa duk abunda ta kallah sai ya lalace a time ɗin kafin ta sake sakin ƙara ta faɗi wani wahalallan bacci yayi gaba da ita.ɓoyayyan ajiyan zuciya Daddy ya sauke yana cewa"alhmdllh ta samu bacci,kafin ta farka sai musan abun yi"ya ƙare maganar yana miƙewa zuwa parlo...tsaye ya tsaya cak yana kallon Mami dake zaune cikin shiga ta alfarma kai da ka ganta kasan naira ta gama jiƙata,tsantsar kamarsu ta bayyana dan zakayi tunanin Mamy kaki tayi ta ajiye Aliyu,janye idonsa yayi kai tsaye ya nufi hanyar part ɗinshi.da sauri tace"Aliyu,Aliyu Sudais"cak ya tsaya ba tare daya juyo ba cikin kausasshiyar yace"nan ma kinzo ku ƙarasa kasheni da baƙin ciki ne?"..salati Dattiya ya saki yace"dan ƙari,kaji irinta,meye wani wai Sude Allah na tuba,to dai yau kin ganewa idonki irin halin da muke ciki,a kullun mune mararsa mutunci a idon Sude,tunda cin arziƙi mukazo dole muyi biyayyah,ahtau cin arziƙi mana in da ba haka b...."saurin haɗiye maganarsa yayi yana ja da baya ganin irin mugun kallon da Abu bilal ke jefa masa.miƙewa Mamy tayi ta ƙaraso bayanshi tasa hannu ta juyo shi yana fuskantarta,ko kaɗan kasa haɗa ido yayi da ita yayi ƙasa da kanshi yana jin zuciyarsa na zafi kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito."ka kalleni Aliyu,ka kalleni sai ka gayamun ni mahaifiyarka nazo na ƙarasa kasheka da baƙin ciki,meyasa kai ba zaka ɗauki ƙaddara ba?,meyasa kai bazaka miƙa lamuranka ga Allah yayi maka sakayyah ba?,Aliyu ka haƙura ka daina neman Hajiya Jamila dan nasan ba abu bane mai sauƙi ka iya samunta ba,ita ɗin tamkar alkaba'i take duk in da ta nufa to tamkar annoba ce ta bayyana Aliyu".ji yayi zuciyarsa ta buga da matuƙar ƙarfi wata irin zuciya ta ciyosa a kausasahe yace"i don't care ko da zai zama abu na ƙarshe da zanyi a rayuwata sai na nemota,meya kawoki wurina bayan yace ya cire ni a yaransa inyi nesa dashi har abada,kuma kuma yace ku nesanta da ni?".murmushin da yafi kuka ciwo Mami tayi tace"ka taɓa ganin in da aka raba uwa da ɗanta?,Aliyu ka shirya mu koma gida".da sauri ya zame hannunsa daga riƙon da Mami tayi masa yace"never,this will never happen"saurin yin shiru yayi yana danne saitin zuciyarsa da ƙarfi.girgixa kai Mami tayi tace"tunda kai bazaka koma ba zanje wurin Aysha na ɗauki Bilal aishi baka isa ka rabasa da kowa nasa ba".kallon Mami yakeyi kamar idanuwansa zasu faɗo kafin yace"Billah yau da ace bake mahaifiyata ce tsaye kike gayamun wannan ba to da bana tantama mutunanin ko waye ya ƙara awa ɗaya da kansa a gangar jikinsa ba,yarda nabar ku haka zalika Bilal ya barku har abada,kuma duk wanda yayi gigin ɗaukar Bilal zuwa wannan gidan ko waye tabbas zaiga mummunan abun da zai faru dashi wanda bazai manta da Abu bilal ba har abada".sakin baki Karima tayi tana tunanin ashe Abu bilal yana magana har haka?,tunda suke tsawon shekaru ko Mami tazo bata taɓa jin yayi magana haka ba.katse shirun Mamy tayi tace"to ni zan ɗauka idan yaso sai ka kashe ni ni".saurin zubewa yayi ƙasa akan gwaiwowinsa ya haɗa hannayensa duka biyun cikin rawan murya yace"kada kimun haka,kada ku ƙarasa kashe ni da raina,kada ku ɗauki farin cikina zuwa gida mafi muni da ƙyama a rayuwata,ina roƙonki da girman Allah kada ki taɓa mun yaro kuma kema kiyi haƙuri ki daina zuwa wurina".dafe kai Mamy tayi tace"Aliyu baka son ganina ne?,ko ka samu wacce ta fini ne?"ta ƙare tambayar a tsorace,idamuwansa da suka sauya launi ya lumshe yace"ko kusa Mamy,har abada bani da wacce ta fiki".hawayen dake ƙoƙarin zubo mata ta mayar tace"ƙaddara ta riga fata Aliyu,ka yafe mun ka daina ganin laifina a abunda ya faru,na zaɓi nayi hakan ne dana rasa ka bazan iya jurar ganin gawarka ba Aliyu,ka yafe mun"ta ƙare maganar kuka na ƙwace mata ta ɗauki bag ɗinta ta fice gidan da sauri.anan in da yake duƙe yabi bayanta da kallo yana jin zuciyarsa na barazanar tarwatsewa da ƙyar ya iya miƙewa ya shige ɗakinshi yana jin kanshi na sarawa.tuni fuskar Karima ta jiƙe jagab da ruwan hawaye hankalinta a matuƙar tashe ga tsantsar tausayin Abu bilal daya rufeta ta faɗa ɗaki itama tana sakin kuka mai cin rai. ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE VOTE COMMENT SHARE DAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING [11/13, 23:34] Jordan: 14 Cikin wani firgici Jagwado yayi kansu girgiza Abu bilal yakeyi yana kiran sunansa ganin wannan ba zata yiba ya sunkuce ya saka shi mota yayi asibiti dashi.wani kukan ne ya kwacewa Karima haka ma Dattiya ya ɗaura hannu saman kai"yace Allah kaji ƙaina ka tadamun kafaɗun Sude,wake gare ni in ba Sude ba,shi ne da daɗi da ba daɗi yana nan tare da ni,komai shi yake mun yo Allah na tuba in ba Sude ɗin ba sai wa"ya ƙare maganar yana bin hanyar waje yana ƙwala Malan Audu kira yana goge hawaye da majina da gefan babbar rigarshi.kama Karima Mama uwani tayi tana lallashinta da bata baki. 2hour's. A hankali ya soma buɗe idanuwansa yana ƙarewa ɗakin da yake kallo dafe kansa yayi yana son tuno abunda ya faru amma sam ya kasa tuna komai,a hankali ya miƙe zaune a daidai lokacin ne kuma Jagwado ya turo ƙofan ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da leda da alama abinci ya siyo masu.kallonsa Abu bilal yayi yace"what i my doing here?".nusawa Jagwado yayi yace"how is your body?".tsura masa ido yayi kafin yace"Alhmdllh".yaye cotains ɗin window yayi yana kallon yacce garin yayi duhu safko wa yayi yana cewa"tsawon yaushe nake nan?".a taƙaice Jagwado yace"since azahar".waro ido yayi yace"u mean i missed asir and also magrib?".gyaɗa kai Jagwado yayi alamar eh,hakan yasa ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya fito ya samu harya shimfiɗa masa prayer mat,nan ya rama sallolin da aka biyo shi ,kaɗan yaɗanci jullub rice ɗin da naman kaza yasha ruwza ya ture plate ɗin yace"i'm full then i want to go home".ba yarda Jagwado beyi dashi akan ya haƙura safiya yayi ba amma sam ya ƙiya ba arziki akayi discharging ɗinsu suka koma gida.. Since 10 Khadija tazo gidan duba Halima suna ta zaune parlo Khadija tace"yaushe zaki koma islamiyyah?".shiru ta ɗanyi kafin tace"soon,kuma nifa ina da damuwa".gyara zama sosai Khadija tayi tace"what's the case?".lumshe dara daran idanuwanta tayi tana gyara zaman eye glasses ɗinta tace"i want to know him Khadija,jiya naji abunda ya ɗaure mun kai,hankalina ya tashi ina tashi daga raɗaɗin ciwo kunnuwana suka jiyomun munanan kalamai da ake faɗawa Yaya Aliyu,babban matsalan ma shine da Daddy yace har abada baya son sake ganin Yaya Aliyu bare kuma yagan na kulasa,kinsan halinsa as if he don't care ya kama gabansa,nikan na kasa bacci am deep in love with him Khadija,bazan iya rabuwa dashi ba,ina so nasan waye,na kuma san a ina Daddy ya san shi".ta ƙare maganar cike da rauni.ajiyar zuciya Khadija ta sauke tace"duk da kinsan bana yin Abu bilal amma bazanga laifin zuciyarki ba danta so shi,sai dai ina ƙara gaya maki shi ɗin ba kalanki bane,kuma tunda kikaji Daddy yayi magana a kai tau tabbas akwai wani abu a ƙasa wanda mu basu sani ba,kamata yayi ki fara tambayan Amma idan kikaji daga gareta sai asan abun yi wanda duk da haka bana koyon bayan kiso Ɗan daba kuma drinker".runtse ido Halima tayi da ƙarfi tana jin zafin maganganun Khadija akan Abu bilal,sai wurin 12 kafin Khajija ta tafi,a kuma gate ne Halima ta haɗu da Lamis daya shigo gidan yanzu fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙaraso kusa da ita yace"hy cuttie me kike yi a gate?"."na raka Khadija ƙofan gate ne "ta faɗa itama cikin sakin fuska .juyawa yayi in da fararen kujeru suke wurin ya ƙawatu ba lefi yace "muje can zamuyi magana".bin bayansa tayi suka xauna suna fuskantar juna kafin yace"cuttie yaushe zakiyi aure?".waro ido tayi sai kuma ta saki dariya tace"kaima babba bakayi ba,bare kuma ni da ban ƙarasa secondry bama ina SS 2 nefa".lumshe idonsa yayi yana jin sautin bugun zuciyarsa yace"to kinga ni ina so nayi aure nan da 1year amma in wacce nake so ta yarda".cikin jin daɗi tace"nasan zata yarda ma,ka kalleka so handsome ga ilimi mafi abunda yafi ma gaka da addini to me mace zata nema kuma?".murmushinsa mai kyau yayi yace"ae so ba ruwansa da wannan".ɗan jim yayi kafin ga kama hannuwanta ya riƙe yana kallonta,saurin yin ƙasa da kai tayi tana jin wani iri a tattare da ita,sosai ya riƙe hannun kafin yace"Halima kece wacce nake so ,kuma nake burin aura,please karkice No ki dubeni ki yarda da soyayyata a gareki".ras ras haka ƙirjin Halima ya bada sauti saurin ɗago idanuwanta tayi tana kallonsa wanda har hawaye sun soma kwanciya saurin zare hannunta tayi daga riƙon daya yi mata a firgice tayi cikin gida da gudu tana haki bata ma san abun yi ba.runtse ido Lamis yayi tare da shafa fuskan shi kafin ya tashi ya shiga cikin gidan.jan hannunshi kawai Hajiya Mama tayi kai tsaye ta wuce dashi bedroom ɗinta tana danna key tace"uban meye kake gayawa yarinyar can?".shiru yayi mata a tsawace tace"Muhammad ina magana".lumshe ido yayi a rayuwansa besan meye ƙarya ba bare kuma yayiwa Hajiyan shi cikin dakiya yace"nace ina sonta kuma zan aureta ne".daskarewa Hajiya Mama tayi a wurin kafin a fusace taci kwalar Lamis tana girgizashi da ƙarfi tace"a gaskiya baka da hankali,kana ganin irin ciwan da takeyi mahaukaciyar zaka aura mai kwana kango?,mai lashe kurwar mutane?,anya Lamis kana da cikakken hankali kuwa?".kallonta kawai yake yana nazartar yanayinta yace"idan kuma ƴarki ce kema zaki so a samu wanda zai taimake ta ,i don't care ko zan mutu a hanyar taimako "."ka rufemun baki sakarai kawai,idan kai ka sallama ni baxan taɓa yarda da hakan ba,your the only son i have,i can't imaging halin dazan shiga idan na rasaka bam shirya ma wannan ba,ban yarda ba ban kuma amince ba in dai ina da rai hakan bazara taɓa faruwa ba Lamis i mean it".kallonta kawai yakeyi kafin yace"Hajiya do u know something about Halima's condition?,kina yi kamar kinsan komai a kanta".saurin sakin sa tayi tana dabur bur cewa"tace am ...au...kana zargina ne kenan Lamis?".shafa gemonsa yayi yace"ko ɗaya".be jira cewarta ba ya fice daga ɗakin.hannu kawai Hajiya Mama ta ɗaura a kai tama rasa abunyi motsin kirki ta kasa yi kawai saita fashe da kuka tana roƙon Allah ya tsare mata Lamis tana kuma kudiri niyar shiga malamai dan a raba mata Lamis da Halima. Cikin natsuwa ta shiga parlon Amma ganin babu kowa yasa ta wuce bedroom ɗinta ta tura ƙofan bakinta ɗauke da sallama,a gaban mirrow taga Amma tana fesa turare,gefan bed taje ta zauna kafin cikin sanyin murya tace"Amma".sai da ta gama shafa turaren ta ajiyesa in da ya dace kafin ta juyo tazo gefan bed din itama ta zauna tace"menene?".ƙasa Halima tayi da kai ta kasa cewa komai sai hawayenta da take ƙoƙarin mayarwa."meye hakan kuma?,idan baki shirya magana ba ga hanya zaki sakani gaba kina mun kuka".ɗagowa tayi ta kallah Amma tace"Ammana dan Allah da girman manzonsa ki gaya mun waye Yaya Aliyu?,a ina Daddy ya sanshi?,wani abun ya taɓa haɗa su ne?".kallonta kawai Amma tayi tana nazartar yanayinta kafin tace"babu wani alaƙa tsakanin Daddy da Sudais,sanin waye sh kuma bazai amfaneki ba,kawai kiyi biyayyah ga abunda Daddynki ya saka kiyi".ta ƙare maganar tana ƙoƙarin miƙewa.saurin riƙeta Halima tayi tace"Amma ki taimaka mun,ina da tarin tambayoyi a tattare da ni,bazan samu sukuni ba har sai nasan waye Yaya Aliyu meyasa Daddyna baya sonshi,ki taimake ni ki faɗa mun Amma hakan zaisa nayi farin ciki na kuma warware tantamar dake raina".ƙura mata ido Amma tayi tace"kima dai san idan son Sudais kikeyi kiyi saurin ciresa a ranki dan hakan bazai haifar maki da ɗa mai ido ba".gayaɗa kai kawai Halima ta iyayi tana ƙure Amma da ido,nisawa tayi kafin tace" shekarun baya da suka wuce,shekara sha bakwai baya lokacin ina da tsohon ciki ki abun ya faru"....waiwaye adon tafiya,tuna baya. 17 YEARS BACK WAYE ABU BILAL!!! ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337. [11/13, 23:34] Jordan: 13 Tun rasuwar Junaid Halima bata ƙara kwanciyan hankali ba,bata so ko kaɗan wani abun ɓacin rai na haɗata da wani dan tsab tasan ciwanta sai dai abunda bata sani ba shine har wanda ya sota ma zai iya kasancewa cikin wannan tarkon,ko kaɗan bata son zama cikin mutane sai dai sam yanzu ta mayar da wannan kangon wurin zamanta kamar walƙiya haka take ɓacewa ta bayyana a cikinsa yanxu abun ya kawo har saman bishiyar kuka takan zauna ko kuma sai dare ta tafi kan kuka ta kwana can sai safiya ta dawo.girgiza kai Amma tayi tace"yanzu waye kake tunanin zai iya shiga kangon can ya fito da Halima?,ko kaɗan fa ƙofan ta rufe babu mai iya shiga"ta ƙare maganar hawayenta na ƙara zubowa.shafa kai Daddy yayi yana jin matsanancin tashin hankali na kuma ruskarsa yace"gashi Imam baya gari,kuma duka wayoyinsa a kashe,yanzu ki koma gida insha Allah za'asan abunyi a kai".kamar marar lakka haka Amma ta wuce cikin gida tana yi tana waiwayen baƙin kangon da Halima take ciki,yau kwananta biyu kuma taƙi fitowa duk wanda yaje da niyar shigo to baxai ga ƙofa ba kuma bazai iya dira katangan ba.cikin tashin hankali Aunty Aysha ke gayawa Abu bilal abunda ke faruwa taci gaba da cewa"babban tashin hankalin shine ba'asan wanne hali take ciki ba,gata mace gaskiya iskan nan yana wahalar da yarinyar nan" taɓe baki Abu bilal yayi yace"Allah ya kyauta"kai tsaye hanyar waje yayi yana fita kuma kangon ya dosa ko ɗar beyi ba,addu'o'i yake karantawa a ranshi har ya isa bakin kangon,tsaye ya tsaya yana ƙarewa kangon kallo,kallonsa kawai Faruq da Lamis suka tsaya yi sun gagara cewa komai Daddy kam ya shiga gida ɗauko phone's ɗinsa dan yasan abunyi.lumshe ido Abu bilal yayi bayan ya gama addu'o'insa yace"bismillah"yana kuma saka kai jikin bangon.a take suka ga ƙofan ta buɗe ya wuce ciki da izinin ubangiji.saurin rife hancinsa yayi saboda wani azabar wari daya daki hancinsa kalle-kalle ya soma yi a wani ɗaki da babu kowa a ciki sai kwanuka wasu da jini wasu kuma wani irin bakin ruwa me yauƙi,kamar a film haka yake ganin giccin mutane a wurin ƙwafa yayi ya kuma ambaton sunan Allah yace"Haleemah"shiru ba'a ansa ba sai ɓaɓɓakewa da mugun dariyan da akayi,sama ya ɗaga kansa yana hango Halima acan saman ƙaton bishiyan kuka,duk tayi wani hiri hiri ta gama sauyawa da halitta,addu'a ya riƙayi yana tofawa a saman kamar an jefota haka ta faɗo kafin ta iso ƙasa yayi saurin saka hannuwansa ya tareta ta faɗo a ƙirjinsa,wani irin bangajesa tayi ta tsaya tsaye akan manyan ƴan yatsunta na ƙafa tana wani irin gurnani.kallon ikon Allah yakeyi kafin ya fizgota ya matse mata babban yatsanta na hannun dama ,cikin wani irin sauti tace"ka sakeni,ka sakeni nace".ta wani juyo tana ƙwalalo masa muggan idanuwanta da suka fito kamar ƙwan fitila."ku fita daga jikinta,idan ba haka ba kuma zan ƙonaku yanzun nan,kuma ina gargaɗinku da kada ku cutar da wani itama ku barta ta huta haka".wata irin dariya Halima ta saki tana cewa"bazamu iya barin jikinta ba ".murza hannun nata yayi da ƙarfi aiko ta saki ƙara tana tafiya luuu zata faɗa akan ƙayoyin dake wurin.saurin tarbota yayi kafin ya rungumota kamar baby ya fito da ita daga cikin kangon.wani irin ajiyar zuciya Faruq da Lamis suka sauke a tare suna kuma mayar da kallonsu ga jikinta da yayi duƙu-duƙu gashin kanta duk a baje gaba ɗaya ta sauya launi.shikam Abu bilal ko kallonsu beyi ba ya fara tafiya suka rufa masa baya.har cikin gidan ya shiga da ita a parlo ya tsaya yana shimfiɗar da ita akan carpet.wata uwar ƙara Hajiya Mama ta saki tana cewa"Daddy ku fito ku gani,Daddy Amma".kusan a tare Amma da Daddy suka fito , da gudu Hajiya Mama tayi ɗaki dan a matuƙar tsorace take,da sauri Abu bilal ya ɗago yana bin bayan Hajiya Mama da kallo saboda jin muryarta a kunnensa,sai dai be samu ganin fuskanta ba.Aysha dake rakuɓe tana kuka ita ta taso da sauri Mamanta ma na take mata baya.ƙarasowa cikin parlon Daddy yayi yana maida kallonsa ga Abu bilal wanda ya ɗago daga duƙen da yake,kallo sukeyiwa juna ido cikin ido kafin cikin rawar murya Daddy yace"Aliyu kaine?,meya kawo ka gidana?".cikin kausasshiyar murya yana haɗa yatsunsa suna ƙara yace"get out of my hause wannan karon ya zama karo na ƙarshe da ƙafarka zata kuma shigowa gidana balle harka ɗauki kazamin hannunka ka ɗaurashi akan ƴata".da sauri Amma ta shiga gaban Daddy tace"haba Abubakar kai baka ganin irin taimakon da yayi mana?,ko last time shine wanda ya dawo da ita gida data faɗi a school,kome yayi maka ya kamata kayi haƙuri".wani tsaki Daddy yaja cikin ɗaga murya yace"wai ke baki gane shi bane?,it's Aliyu yaron Alhaji Ahmad ,why can't you look at his face very well Amina ".juyowa Amma tayi tsoro ya nuna ƙarara a fuskarta tabbas ranar firgici da tsoro ya hanata kallon fuskar Aliyu da kyau haka yauma sai da Daddy ya nusar da ita kafin ta ganeshi rabon data saka shi ido tun tana da tsohon cikin Halima 17years kenan.bakinta na rawa tace"Sudais".ƙasa Sudais yayi da kai don tun ranar daya zo gidan na farko ya gane Amma sai dai ganin bata ganeshi ba yasa ya share kawai,kuma yasan Aunty Aysha bata san Amma ba sakamakon ba'a gidansu ta tashi ba ko da tayi aure a london take zaune sai tsakanin nan ne ta dawo Nigeria da zama.cikin kausasshiyar murya Daddy yace"dama ashe shine wanda ya taɓa zuwa mun gida kuma baki gayamun ba,Aliyu idan ka kuma shigo mun gida hukuma ce zata rabani da kai and i mean it wallahi".cikin dakiya Aliyu yace"to Allah ya bada iko Daddy,babu wani abun da zai firgita ni tunda har a baya na rayu" .cikin muryar kuka Amma tace"please you people should stop that,komai ya faru ya faru ne a ta dalilin kuskure,kuma kai Daddy kasan an cuci Aliyu da yawa ko don taimakon da yakewa ƴarka bazaisa ku tausaya masa ba"."karki sake min irin wannan maganan,mashayin ,ɗan daban,wanda ya keta haƙƙin Allah,ya aikata saɓo mafi muni wanda ko a zamanin dabbibu banga ana haka ba".runtse ido Aliyu yayi da ƙarfi kafin ya waresu harsun soma canza launi dan tsananin ɓacin rai kasa furta komai yayi ya juya zai fita,ji yayi an riƙo hannunsa,tsaye ya tsaya cak ba tare daya juyo ba yaji sautin muryarta tana cewa"Yaya Sudais" wata uwar tsawa Daddy ya daka mata wanda tunda take a rayuwarta be taɓa mata tsawa irin haka ba.jikinta na ƙyarma tayi sauri ta lafe bayan Lamis dake kusa da ita."kada na kuma ganin kin danganta kanki da Aliyu,har abada babu ke babu shi,idan kuma kika saɓa zakiga irin abunda zai faru da ni da ke a gidan nan Halima".girgiza kai Abu bilal yayi ransa a matuƙar ɓace ya fice daga parlon dan har ji yakeyi bashi gani.hawayen dake zubowa idonta ta goge tana maimaita sunan da Daddy ya kirata dashi wanda tasan a iya rayuwarta xata iya ƙirga sau nawa Daddy ya kirata da Halima.kama hannunta Faruq yayi kai tsaye ya wuce da ita bedroom ɗinta yana lallashinta akan kada ta ɓata ranta baya so kanta yayi ciwo.binsu Amma tayi a ɗakin kafin ta kama Halima zuwa toilet ita da kanta tanwanke mata kai ta wanke ƴarta tas ganin babu wani kuzarin kirki a jikinta,kallonta takeyi yarda tayi masifar rama duk ta zabge a zaman kwana biyu kawai,doguwan riga marar nauyi red ta bata ta saka kafin ta gyara mata kanta.Faruq ne yayi sallama ya shigo ɗakin da mug ɗin tea mai kauri ya zauna yana bata tea ɗin a baki,ganin haka Amma ta wuce part ɗinta tana tuna rayuwar baya data wuce.sai da ta shanye tea ɗin kafin ya bata farfesun ƴan ciki da yaji kayan yaji sai da ya tabbatar ta ƙoshi kafin ya taimaka mata ta kwanta yayi mata addu'a ya shafa mata sannan ya rufeta da duvet ya fita.ikon Allah ne kawai ya mayar da Abu bilal gida ko kaɗan be kula karaɗin Dattiya ba ya faɗa ɗaki ya saka key yana ji zuciyarsa kamar ta fasa ƙirjinsa ta fito saboda tsananin xafin da take masa,naushi ya kaiwa bango ya soma ɓarar da duk abunda yazo gabansa yana fitar da wani nishi marar daɗin ji.a guje Karima tazo ƙofar ɗakin tana bugawa da ƙarfi cikin muryar kuka take cewa"Yaya dan Allah kayi haƙuri ka buɗe,yaya kada ka illata kanka,dan Allah ka buɗe".ta ƙare maganar tana jijjiga door ɗin ɗakin.ganin bashi da niyar buɗewa yasa da gudu tayi waje babu ko hijab a jikinta cikin sa'a kam taci karo da Jagwado wanda zuwansa kenan cikin kuka tace"Abu bilal ne,Abu bilal ne".be jira jin me zata ce ba ya tureta yayi cikin gidan da gudu.itama ta rufa masa baya ganin ɗakin a kulle yasa ya fito da key's ɗinsa ya buɗe ɗakin dan shi kaɗai keda key ɗin ɗakin Abu bilal.a daidai lokacin ne kuma Abu bilal ya dafe kansa da ƙarfi yana ganin ɗakin na jujjuyawa dashi ya tafi luuu zai faɗi,da matuƙar ƙarfi Karima tayi tsalle cikin ɗakin ya faɗo a jikinta suka faɗi tare .lokacin da Jagwado ya ɗagoshi a sume yake . ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE. 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337. [11/13, 23:34] Jordan: 12 Kamar ana mintsininta haka takeji a baccin a matuƙar razane ta farka daga bacin babu kowa a parlon dama bacci ne yaɗan ɗauketa kai tsaye hanyar waje tayi,babu kowa a farfajiyar alamun duka maza masu aikin gidan sun wuce masallaci don yin sallar la'asar gate ta ɓuɗe tana ci gaba da tafiya.fitowarsa kenan daga gidan Aunty Aysha sauri yakeyi ya tafi masallaci dan shigowarsa unguwar kenan da ido ya bita ganin ko shoe babu a ƙafarta balle kuma hijab wanda tunda ya santa be taɓa ganinta ko da veil a waje ba sai hijab saɓanin rana daya da dare ya ganta ta fito a haka.taɓe baki yayi duk da yana da yaƙinin ba ita bace ba yayi wucewarsa masallaci gudun kada ya rasa jam'i.minti 10 da faruwan hakan ya fito daga masallaci gaya mutane tsaye a ƙofar gidan su Halima,shafa kai Faruq yayi yace"tabbas da kowa ya tafi sallah ta fito,abun tashin hankalin ma ba'asan ina ta nufa ba".ta gefansu ya raɓa ya wuce ko kallonsu beyi ba.da gudu Khalifa ya shiga gida yana cewa"Ummi,Ummi Yaya Halima ta ɓata ba'a ganta ba".dungure masa kai tayi tace"liar,ka dai san ba kyau ƙarya"."wallahi Ummi da gaske nake ga Uncle Faruq can a waje ma".kallonta ta mayar ga Abu bilal dake shigowa gidan hankalinsa kwance tace"Aliyu wai da gaske ne".tsura mata idanuwa yayi yace"what"."wai Halima ta ɓace"ta ƙarashe maganar tana ajiye bucket ɗin sock's na yara data wanke.taɓe baki yayi yace"i think so".kafin ya kuma magana ta zare hijab ɗinta dake ajiye a parlo data gama sallah tayi waje hankalinta a matuƙar tashe dasu Faruq ta fara cin karo cikin tashin hankali tace"Faruq anga Haliman?,ina taje? yanzu khalifa ke gayamun".kasa magana yayi sai dai Lamis yace"a'a of to now ba wanda yasan in da take ma"."innalillahi wa'inna ilaihir raju'un "ta faɗa tana shihewa gidansu Halima a tsaitsaye ta samu su Amma wanda tsantsar tashin hankli ya gama bayyana a jikin Amma.nisawa Imam yayi yace"tabbas ba zata wuce cikin wani wurin ba a kusa da gida ,iskan jikinta ne suka fitar da ita ,kada ku damu insha Allah data dawo daidai zata dawo gida".zufa Daddy ya goge yana cewa"hasbunallahu wani'imal wakeel,Allah ka tsare mun ƴata a duk in da take"gaba ɗaya ya gama rikicewa duk addu'ar data zo bakinsa ita kawai yake yi kafin ya taso ya dawo gida a ƙofar gida ya zauna shi da su Faruq suna jiran tsammani.Junaid matashin yaro kuma yaron maƙwabcinsu yazo da sauri gaban Daddy ya duƙa yace"Daddy ga Halima a kangon can".be ƙarasa rufe baki ba dukansu suka miƙe tsaye suna hango tsohon kangon da yake nuna masu wanda tsawon shekaru babu wanda yake gigin zuwa wurin duk shuko kin kuka ne wurin da abubuwa iri iri.kai tsaye wurin suka nufa kowa da abunda yake ayyanawa a ranshi.Halima kam kwance take a cikin kangon sai juye-juye takeyi kamar macijiya gaba ɗaya duk ta jiwa kanta ciwo ga azabar ciwo dake cinta.Oga sam ne ke zagayeta yana yayyafa mata baƙin ruwa mai masifar wari.jin ruwan takeyi tamkar zubar wuta a jikinta gaba ɗaya ta banban ƙare ta gama sauya launi duka jikinta a juye yake yayin da idanuwanta suka koma kamar garwashin wuta .tsaitsaye sukayi ƙofar kangon jin irin ihun dake fitowa daga ciki da sauri Junaid,Lamis da Faruq suka kutsa kai cikin kangon Junaid ne ya fara ƙarasawa ya ɗagota carab idonsu ya haɗu ido cikin ido,bismillah Lamis yayi ya ɗagata tsaye yana janyota waje tana tirjewa babu abunda take kallo sai fuskar Junaid hannu tasa da ƙarfi ta ingije Junaid yayi baya xai faɗi Faruq yayi saurin taro shi"yace what's that?,saboda ya taimaketa tana mace kun kawota wurin ƙazantar nan?".ko kula Faruq bata yi ba suna fitowa waje ta langwaɓe alamar ta sume,akan idon Abu bilal Lamis ya ɗakkota .wani irin tsuka yaja yana buga ƙofa da ƙarfi,saurin kallonsa Aunty Aysha tayi wanda isowarta ƙofar kenan cikin zafin zuciya yace"waye shi daya ɗaukota?".riƙe baki tayi tana ƙare masa kallo tsantsar kishi ta gani ƙarara a idonsa sharewa tayi tace"kana da damuwa da wannan ne,ina kana ganinta ta wuce ae,yanzu ake faɗa wai ka ganta,shine baka tsayar da ita ba?".taɓe baki yayi yace"did i send her?".wani haushi ne ya kama zuciyar Aunty Aysha kamar ta fashe da ihu haka ta ture Abu bilal ta wuce ciki dan tun ɗazu Abban Khalifa ya dawo.da Hajiya Mama Lamis ya fara cin karo.wani irin kwalalo ido tayi tace"Lamis ka haukace ne?"daburburcewa tayi ta kasa komai tana tunanin abunda zaije ya dawo.a saman carpet ya shimfiɗar da Halima ya soma cicire mata ƙayoyin da gashinta ya kwaso,sosai sukayiwa Junaid godiya kafin ya tafi gida.kusan awa ɗaya tana wanan baccin kafin ta miƙe tana faɗin Junaid da iya ƙarfinta riƙeta sosai Faruq yayi ya soma tofa mata addu'o'i kafin ta fara natsuwa.kamar saukar aradu haka suke yin mutuwar Junaid a cikin unguwar.kafin sallar magrib tuni ko ina ya ɗauka cewar Junaid ya mutu.tsurawa Hannuwanta ido tayi tana tuna mafarkin da tayi wai tana shaƙare Junaid wani wahalallan kuka ta saki tana rungume Amma da ƙarfi ,itama Amman riƙeta tayi cikin muryar kuka Halima tace"Amamana na kashe shi,wallahi ni na kashe shi,me yasa ya taimake ni?,me yasa yazo kusa da ni?".ta ƙare maganar kuka na ƙwace mata,saurin rife mata baki Amma tayi tace"kada na ƙara jin irin wannan,bake kika kashe shi ba kiyi masa addu'a dama lokacinsa ne yayi kinji".kuuuu haka cikin Hajiya Mama ya juya ga zufa dake karyo mata fizgar hannun Lamis tayi ta wuce bedroom ɗinta dashi tare da danna key cikin hassala tace"shin wai ni ko dai Amina(Amma) ta haifa mun kai ne,ita Haliman ƙanwar uwarka ce nace?,ka duba halin da ake ciki kowa ya gagara ɗaukota sai kai sallamamme,na rasa ina hankalinka da tunaninka suka tafi Lamis,kai baka ganin duk wanda yaje da niyar taimaka mata sai ta kashe shi?".tsurawa Hajiya Mama ido yayi cike da alamomin tambaya ya ɗaure da ƙyar yace"in dai zan mutu akan taimakon Halima a shirye nake na bada rayuwata ta,kuma ba ita ta kashe Junaid ba kwanansa ne kawai suka ƙare,idan bamu taimake ta ba waye xai taimaketa a wannan halin".hannu Hajiya Mama ta ɗaura saman kai ta sauke tace"yauni maga abunda ya isheni ni jamila,to bari kaji lai kaɗai na mallaka ban kuma shirya rasaka ba".murmushin takaici yayi yace"in dai baki cutar da Ɗan kowa ba toki kwantar da hankalinki babu abunda xai samu Muhammad Lamis"."ban gane wannan tambayar ba Lamis?,kana xargine akan condition ɗin Halima".shafo gemonsa yayi yace"a'a wai magana nayi kawai".rasa abun cewa tayi kafin ta nuna masa hanya tace"maza ka tafi gida wallahi idan na safko parlo na sameka ranka zaiyi matuƙar ɓaci Muhammad,zan saɓa maka ".shiru yayi kafin yace"to sai anjima",ya fice daga gidan.Faruq kam yana parlon Amma yana ta kallon Halima dake xaune taci kuka harta gaji har muryarta ta fara disashewa i zuwa yanzu kam wani mugun tsoron wani ya kusance tako ya taimake takeyi ta gama firgita da duk abunda ta gani a mafarki ta to tabbas tana buɗe ido dashi zata fara cin karo,hawaye ne suka kawo idonta ga zuciyarta tana bugawa da ƙarfi,hannu tasa tana janye eye glasses ɗinta tana share hawayen idonta."kiyi hakuri,bana son kukan nan"shine abunda Faruq ya faɗa.girgiza kai tayi tace"kowa in yi haƙuri yake faɗa mun,tabbas baku san abunda nakeji a zuciyata bane,baku san me yake faruwa bane shiyasa har kuke da bakin bani hakuri"."duk tsanani yana tare da sauki Ammina kiyi hakuri komai xaizo da sauki,kuma hakuri shi yake kawo nasara". ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337. [11/13, 23:34] Jordan: 15 Nisawa Amma tayi tace"Sudais ya kasance yaro mafi soyuwa a wurin mahaifansa watau Alhaji Ahmad da Hajiya Maryam yaransu huɗu Aysha itace babba sai Aliyu sai kuma ƙannensa ƴan biyu watau Khaleel da Khaleem,Alhaji Ahmad kuwa ya kasance Aminin Mahaifinki tun yarinta suke tare kuma shima babban ɗan kasuwa,yaso Aliyu ya biyosa shima yayi kasuwanci sai dai Aliyu tunda ya tafi waje karatun Architecture ya daɗe bai dawo ba a kuma can ne ya samu aiki,yayin da ni ban taɓa ganin ƴarsu Aysha ba tunda aka haifeta Hajiya Maryam ta bawa ƙanwarta marigayiya Hajiya Aysha ita,a can ta girma a can kuma tayi aure,Aliyu ya taso cikin gata da soyayyah da kulawa sai dai ya kasance mishkiline na gaske wanda ko iyayensa sai sunyi da gaske yake iya buɗa baki yayi magana,wannan son da suke masa yasa suka lallaɓashi ya dawo gida nan Nageria in da aka buɗe masa Company ɗinsa yana harkar zane zane,a kuma lokacin ne Hajiya Maryam ta haifi yaranta ƴan biyu maza watau Khaleel da Khaleem yara masu matuƙar kama da juna kuma ya zamana duk duniya babu abunda Aliyu yake so sama da Khaleel da Khaleem duk in da zaije yana tare dasu kowa ya sanshi yasan twins ɗinsa rainonsu gaba ɗaya shi yayi".nisawa Amma tayi ta kurɓi ruwa dake kusa da ita sannan taci gaba da cewa"a kuma daidai wannan lokacin ne Hajiya Maryam ta buƙaci da Aliyu yayi aure,hankalinsa yayi matuƙar tashi saboda shi bashi ma kula ƴan mata bare kuma yace ga wacce yake so,kasancewar kusancin iyayenku maza yasa ni da Hajiya Maryam muka zama aminai komai a tare mukeyi sai dai ni matsalar dake damuna a lokacin shine da na samu ciki sai ya ɓare sai bayan su Khaleem sunyi wayau aka samu cikin dana samu ya tsaya har yakai matakin haihuwa,ina dab da zan haihu kuma Hajiya Maryam tazo mun da shawaran tana so taga Aliyu yayi aure tunda ita Aysha ta daɗe dayin aure,sai dai uwar riƙonta ta rasu kuma tabar ƴarta mace mai suna RUMANA rumana kyakyawa ce ajin farko son kowa ƙin wanda ya rasa gata da haƙuri da kuma kawaici hakan yasa na bawa Hajiya Maryam shawarar mexai hana su haɗa auren Rumana da Aliyu,sosai tayi na'am da shawarar tace kuma xata turomun Aliyu tunda taga ɗan gida na ne sai na masa bayani,hakan akayi tunda na masa magana bai musa ba haka ya yarda akayi auren duk da ba Son Rumana yakeyi ba a lokacin.bayan aurensu da Sati ɗaya kuma na haifi ɗana namiji lafiyayye yaci suna Ahmad watau sunan Abban Aliyu kenan".zaro ido Halima tayi tana kallon Amma kafin cikin rawar murya tace"shine wanda naga pic ɗinsa ɗakin Daddy na tambaya waye aka cemun na ajiye kawai?".gyaɗa mata kai Amma tayi tace"eh shine,kuma yayanki uwa ɗaya uba ɗaya"."Amma meyasa kuka ɓoye mun?,kuma yana ina?".girgixa kai Amma tayi tana ƙoƙarin mayar da hawayenta tace"saboda faɗan hakan yana tada wani tsohon ciwo da kuma mumunan tabo ga dukkan ahalin guda biyu".shiru Halima tayi amma ta kasa fahimtar me Amma ke nufi da hakan.ci gaba Amma tayi da cewa"bayan na gama wankan Ahmad mahaifinki ya samu wata kwangila da zaiyi shekaru a ƙasar waje,bamu so rabuwa da juna ba saboda zamana da Ahalin Hajiya Maryam yana mun daɗi mun zama tamkar wanda muka fito ciki ɗaya,gadan gadan tafiya ta kama saboda shaƙuwar dake tsakanin su Khaleem da Ahmad yasa suka roƙemu damu bar masu Ahmad har Allah ya dawo damu lafiya,tabbas na firgita dajin wannan magana ganin shi kaɗai Allah ya bani amma Hajiya maryam tafi ƙarfin komai a wurina a nan take na mallaka mata Ahmad kuma muka tafi muka bar mata shi,sai dai ta waya mu gaisa.shekarar Ahmad huɗu su Khaleem kuma 6 daga lokacin ne kuma mumunar ƙaddara ta fara faɗawa a wannan family mai cike da soyayyar juna da aminci da zaman lafiya,kuma har lokacin bamu dawo ba ko ziyara bamu taɓa zuwa ba,Hajiya Maryam ta kirani tana gayamun cewa Alhaji Ahmad zaiyi aure,ni kaina na shiga ruɗu amma haka na daure ban nuna mata ba ina bata baki da haƙuri wata biyu aka yi auren Alhaji Ahmad da wata wai Hajiya Jamila wanda harta gama zamanta a gidan ban taɓa ganin ko da hoton ta ba.a lokacin kuma komai ya daidaita tsakanin Rumana da Aliyu yana matuƙar son matarsa yana kuma riritata baya son abunda zai taɓa mashi ita.bayan wata biyar da Auren Hajiya Jamila komai ya canza a gidan,Alhaji Ahmad bayajin maganar kowa sai tata,kuma sai abunda tayi a gidan be isa ya tsallaka koda kara ta gindaya ba,kuma ta shiga ta fita ta raba shi da Aliyu sai da yakai ko da kallo Alhaji Ahmad baya son ganin Aliyu bare kuma ya raɓesa,hakan ya dasa muguwar gaba tsakanin Aliyu da Hajiya Jamila wanda ita hassada da ƙyashi yasa bata son Aliyu kullun burinta bai wuce taga ya faɗi ba,haka naita bawa Hajiya Maryam Hakuri dan bana so tabar gidan uban ƴaƴanta,a kuma lokacin ne Rumana ta kamu da wani matsanan cin ciwo ta koma kamar mahaukaciya ta zaune,sai dai a kullun idan ciwon ya tashi a ɗaɗɗaureta da sarƙa a kuma rufeta a ɗaki,dan xataita yagar fatar jikinta ne tana kuma neman illata kanta,wannan al-amari ba karamin girgiza wannan ahalin yayi ba,anyi magani anyi har an gaji,wanan abun kuma shine farkon fara tarwatsa rayuwar Aliyu duk yabi ya susuce ya lallace baya bacci be da kwanciyar hankali saboda ciwan Rumana,har lokacin shekararsu goma sha biyu da aure amma ko ɓari Rumana bata taɓa yi ba,kuma duk ciwanta besa Aliyu ya rabu da ita ba ko kuma ya ƙara aure,haka yake xama ya bata abinci tana t dukansa tana yakushinsa amma be fasa kula da ita ba,gaba ɗaya ma ya tattara yabar zuwa aiki sai kula da Rumana.a wannan lokacin ne kuma Hajiya jamila da Aliyu sukayi wani gagarumin faɗa saboda ya kamata tana zuba magani a abincin Rumana,ya shiga tashin hankali wanda yakai har ya mari Hajiya Jamila ita kuma tayi amfani da wannn daman tayi masa alƙawarin zai biya marin daya mata ko ta wacce hanya".shiru Amma tayi tana share hawayen daya ƙi tsayawa a idonta tana kallon Halima tace"a cikin wannan yanayin kuma na haifeki kikaci sunan Ammin Faruq wanda itama a lokacin ne ta rasu riƙon Faruq ya dawo hannuna aka dangin mahaifinsa suka kai mana shi har Amerika,a wannan yanayin ne Aliyu ya fita dasu Ahmad ,a yarda yace ya barsu a mota kafin ya dawo ya samu babu Khaleel ,khaleem da kuma Ahmad,yayi ruɗewa iya ruɗewa in da a wurin suka bashi tabbacin wata mata ce tazo ta tafi da yaran,yacce suka kwatanta masa surarta lokaci ɗaya zuciyarsa tayi na'am da Hajiya Jamila ce,gida ya dawo yana tuhumarta ita kuma tace bata san anyi ba don duk ranar be fita ba,a kuma cikin ɗakinsa aka tsinci kayan su Khaleem ɗuk jini da wasu irin abubuwa da suke bada tabbacin Aliyu ya faɗa kungiyar asiri ne,sosai hankalin kowa ya tashi da ƙyar Abba ya kira Daddy yake gaya mana mutuwar su Khaleem da kuma Ahmad,ya girgiza sosai amma sai ya ɓoyemun yaƙi sanar da ni case ɗin dake faruwa kuma ya hanani yin waya da kowa.sam Aliyu ya birkice yaƙi ansar laifinsa ya kuma ɗauki alƙawarin ɗaukar mataki akan Hajiya Jamila ,a wannan lokacin kuma wani tashin hankalin ya doso kai in da Abba da kanshi ya kama Hajiya Jamila tana ihu a ɗaki ga Aliyu kwance kwance a ɗakin akan gadonta yayin da take fitar da jini tana ihun Aliyu yayi mata faɗe".wani irin miƙewa Halima tayi da sauri tace"be yiwuwa,wannan ba gaskiya bane,Yaya Aliyu bazai taɓa aikata haka ba ".ta ƙare maganar hawaye na zubowa a idonta.girgiza kai Amma tayi ta kasa tsayar da hawayenta tace"Ayyah Halima ki daina saurin yanke hukunci haka,mahaifiyar data haifesa ita da kanta ta bada shedan Aliyu yayiwa Hajiya Jamila fyaɗe".daskarewa a wurin Halima tayi ga tsananin tsoro daya bayyana ƙarara a idonta da ƙyar ta haɗiyi wayu mai masifar ɗaci cikin rawan murya tace"yaya za'ayi uwar data duƙa ta haifi ɗanta wanda tafi kowa yarda da ɗanta ta bada wannan ƙazamar shaidan ga ɗan data haifa da cikinta,anya Mamy itace mahaifiyar Yaya Sudais kuwa?". ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAMYAWAN ƘARSHE 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337. [11/13, 23:34] Jordan: 16 Kallonta kawai Amma tayi tace"wannan kuma ko waye ya kallah yasan gaskiya,kuma da bata tabbatar da hakan ba da bata bada shaida ba".wasu hawayen ne suka kawo idon Halima ta kasa cewa komai kafin Amma taci gaba da cewa"a lokacin ne Abba ya kira Daddynki yana sanar masa da baƙin ganin da yayi"haka Daddynki ya kwasa ya tafi gidan amma ba abunda ya canza dan Abba yayi matuƙar fushi a nan ne yake faɗin ya rabu da Aliyu har abada kuma ya ciresa daga cikin ƴaƴansa ko da mutuwa yayi kada Aliyu yazo kan gawarsa kuma duk abunda yasan ya masa toya tattaro ya dawo masa dashi".ko kaɗan Daddy be nuna beji daɗi ba dan shima ya yarda ɗari bisa ɗari Aliyu ya aikata hakan saboda lura da shaidu da kuma yarda Hajiya Maryam ta bada shaida da kanta akan ɗanta,shima cikin fushi ya yayiwa Aliyu faɗa da wulaƙanci sosai ya kuma yi ala wadai da irin halin da Aliyu ya canza kuma a nan ne ya yarda Aliyu ya shiga ƙungiyar Asiri,shima yace bashi ba Aliyu kuma bazai yafe masa ran ɗansa daya salwantar ba,a takaice dai haka suka kori Aliyu da matarsa Rumana wacce take cikin halin ciwo,Allah kadai yasan yarda suka rayu bayan shekaru kuma akaji labarin Rumana ta samu ciki kuma a lokacin Aliyu yana zaune da Dattiya tsohon mai gadin da Hajiya Jamila tasa aka kora ,yanzu kuma bazan iya ce maki ga in da Dattiya yake ba,a wata majiyar wai Hajiya Jamila ta tari Aliyu ta faɗa masa lallai yayi hankali da kansa wannan duk yana daga cikin sakamakon marin daya yi mata ne kuma ya jira abunda zai faru na gaba,bayan ta dawo ne kuma Abba ya saketa duk wani asirin data masa ya warware,.a lokacin Daddynki yaso ya ganta yaji meya haɗa su amma sam Abba ya hana yace ba amfani kawai ya barta shi bazai iya ci gaba da zama da ita bane,wannan takaicin sakin yasa ranar da Rumana ta haihu ko tashi daga in da take bata yi ba Hajiya Jamila ta shigo ta kasheta har lahira ga yaro jariri kuma,a nan ne kuma Aliyu ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani saboda tsaban rikicewan da yayi ,daga wannan lokacin kuma babu wanda ya kuma jin labarin Hajiya Jamila har gobe kam,amma kuma Aliyu yana da ƙudirun nemanta a ko wanne yanayi ko da hakan zai zama abu na ƙarshe da zai aikata a rayuwarsa,mu kuma tun daga wannan lokacin alaƙar mu taja baya zan iya ce maki rabon dana ga wani cikinsu harna manta,Ammi kinji iya abunda na sani a rayuwar Aliyu,sanin gaskiyar wannan al-amari kuma sai Allah sai kuma wanda yayi fatanmu dai Allah ya bayyana gaskiya kowa ya gane matsayarsa".kuka sosai Halima ta fashe dashi gaba ɗaya ta gama rikicewa,idanuwanta sunyi jajir tace"Amma har raina ban yarda Yaya Aliyu zai iya haka ba,duk iya halinsa na fahimci yana da kirki ga addini sai dai ban musa shaye-shayen da yake ba shima wannan kuma na ɗauka duk ƙunci ne yasa ya faɗa wannan harkar amma ki yarda yana da zuciya mai kyau".murmushin da yafi kuka ciwo Amma tayi tace"nasan waye Aliyu ,kuma Aliyu a da babban malami ne yana da matuƙar ilimi na boko dana addini,fatanmu dai muyita yi masa addu'a har Allah ya bayyanar da gaskiya".kasa cewa komai Halima tayi ta miƙe ta fito tana share hawayen dake kuma zubo mata.tsayawa Faruq yayi yana ɓata fuska yana kallon yarda idonta ya canza launi alamun taci kuka sosai,langwaɓar da kai yayi yace"meyasa kike son wahalar da kanki haka?,dan Allah kiji tausayinmu Ammina,ki sani kece farin cikinmu a gidan nan,kuma kinsan yawan ɓacin ranki abunda zai iya janyowa".murmushin ƙarfin hali tayi tana cewa"na daina Yayana".murmushinsa mai kyau yayi kafin ya jata suka zauna yana mata fira har yaga taɗan sake tana dariya kafin ya tafi ya barta.. Ɗuƙe take ta rasa abunda ke mata daɗi yau kimanin kwana biyar kenan bata saka Abu bilal a ido ba bare kuma taji daga garesa kusan kullun sai ta shiga gidan Aunty Aysha amma bata ganinsa kuma kota tambayeta itama sai tace kwana biyu bata ganshi ba.miƙewa tayi tana jan Hijab ɗinta ta leƙo parlo ganin babu kowa yasa ta fita da sauri a gate kam babu wanda ya tareta ta fice daga gidan,gidan Aunty Aysha ta shiga da sauri ta ƙarasa ciki tana kallon motar Abu bilal a parking lot ,har tuntuɓe takeyi wurin saurin ta shiga,cak ta tsaya tana ƙare masa kallo wanda shi ɗinma ita yake kallo kamar yau ya soma ganinta,gani tayi yayi rama sosai da alama yana cikin damuwa.ƙasa tayi da kanta,sai lokacin shima ɗauke idonsa daga kallonta ya wuce kan chair ya zauna beko kulata ba,cikin parlon ta dawo daidai gabansa ta tsaya cikin rawar murya hawaye na kawowa idonta tace"Yaya ina ka tafi na daina ganinka?".banxa yayi mata ko kallonta beyi ba bare kuma tasa ran zai bata ansa,zama tayi a gabansa tana tanƙwashe ƙafafunta tace"dan Allah ka gaya mun Yaya".wani irin ɗaure fuska yayi kamar an saukar masa da mutuwa yace"i'm not your Yaya".wani irin haushi ya kama Khadija da shigowanta parlon kenan ta kalli Halima tace"malama tashi muje gida dallah"ko kallonta Halima batayi ba saima saurin miƙewa da tayi ganin Abu bilal yabi hanyar fita cikin ɗaga sauti tace"i know who you are".cak ya tsaya tare da lumshe idanuwansa da suka fara sauya launi ya juyo yana kallon Halima yace"then what?,everything you hear about me just believe it babu wanda bani nayi ba,duka ba zargi bane sai kuma me kike so ki sani bayan wannan?".wani irin kuka mai cin rai Halima ta saki da matuƙar ƙarfi ya runtse idonsa danji yayi sautin kukanta har cikin ƙwaƙwawalwar kansa ya rasa wanne irin yanayi ne yake ji a kanta a lokutan nan,cikin muryar kuka tace"wallahi bazan taɓa yarda ba,tabbas akwai wani abu a ƙasa ba zaka taɓa aikata irin haka ba".wani tsaki yaja afin ya tureta daga gabansa ya wuce abunsa.a nan wurin ta duƙe tana sakin wani kukan da gudu Bilal ya iso wurinta ya duƙa tare da tallabar fuskarta yace"Aunty,ki daina kukan bana so,ki daina zance wa Abba ya daina maki faɗa ina sanki kinji,duk wanda nake so Abbana yana sanshi ".sosai ta riƙe Bilal a jikinta amma ta kasa cewa komai bare ta tsaida hawayen idonta,hannu yasa yana goge mata hawayen fuskarta yana nuna mata alamun tayi dariya,murmushi ta ƙirƙira tana ƙoƙarin miƙewa.Khadija kam ta cika tayi faful a wurin ƙiris take jira ta fashe,jan hannun Halima tayi fuuu suka fice Bilal na binsu da kallo.ta baya Abu bilal ya hango fitarsu wani iska mai zafi ya furzar ya kuma duƙar da kansa yana sauraron bugun zuciyarsa.har cikin bedroom Khadija taja Halima kafin ta sakar mata hannu tace"watau bakiji kashedin Daddy ba kenan?,Halima me kika gani ga Ɗan daba da kika maƙale masa har kina zubar da girmanki da hawayenki a gabansa?,meye ya shiga kanki ne?".wani kallo take bin Khadija dashi kafin tace"kada ki sake ce masa Ɗan daba,nace bana so,ko daban yake yi aike be maki ba".sakin baki Khadija tayi tana kallonta kafin tace"koma me zakice karesa da kikeyi be isa yasa a daina masa wannan kallon ba tunda ya aikata,kuma ki sani bazan taɓa baki goyon bayan kiso Sudais ba har abada".tsuka Halima taja kafin tace"dama ban roƙa ba"ta ƙare maganar tana buɗe ƙofa ta fice daga ɗakin bin bayanta Khadija tayi a daidai ƙofa suka ci karo da Lamis,wani irin faɗuwa gaban Halima yayi ta koma da baya tanayin ƙasa da kai. ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337. [11/13, 23:34] Jordan: 17 Dedicated this page to Balkis Adam Bello Khadija kam da wani irin kallo tabi Lamis mai wuyar fassaruwa,murmushi yayi yana cewa"sarkin ɓoyo yau kin fito kenan".cewar Lamis,kasa cewa komai Halima tayi kafin Khadija tace"ai kwanan nan Yaya sauyi kala-kala ma ka ganshi".harara Halima ta bita dashi kafin tayi ƙasa da kai tace"ina yini Yaya Lamis",da lafiya lau ya ansa yace"muje kuga wani abu".be jira cewarsu ba yayi gaba suka bisa baya a chair ya zauna yana ɗauko wani ƙaramin box ya miƙawa Halima sannan ya ciro agogo mai kyau ya miƙawa Khadija yace"ga naki ƙawarmu,bansan zamu haɗu ba aeda kema an maki naki na daban"murmushi kawai tayi tace"na gode kwarai Yaya hakanma ae yayi".baki Halima ta turo kafin tace"thanks".kallonta kawai yayi kafin ya janye kallonsa daga gareta.miƙewa Khadija tayi tace"muje ki rakani tau".murguɗa baki Halima tayi yace"wallahi baza ni ba".sakin baki Khadija tayi,murmushi kawai Lamis yayi yace"muje na ajiyeki ƙawarmu".dariya tayi tana cewa"kinga na samu rakiyan da yafi naki".gwalo kawai tayi mata ta wuce ɗakinta,a haka suka fita a motar Lamis,tunda suka tafi babu mai cewa komai can Lamis yayi breaking silent ɗin da yace"Khadijatau ya kike da ƙawar taki?",ɗan murmushi tayi tace"Yaya ina lafiya,Halima sarkin rigima ma tana lafiya".kansa ya shafa yana cewa"bari ta jiki nikan in ce bansan anyi bama".dariyan itama tayi tana faɗin "tuba nake" a haka har suka ƙarasa gidan su Khadija,10k ya bata amma da ƙyar ya samu ta ƙarɓa sannan ya juya ya tafi abunsa....shiru yake yana shafa kansa yayinda idanuwansa suke lumshe a hankali ya ware su wanda harsun canza launi ,iska ya furzar yana cewa"wai me yake damuna yanzu?",ina so na ganta".ya faɗa yana miƙewa tsaye key ɗin motarsa ya ɗauka yana fita yayinda zuciyarsa ke masifar azazzalarta da masifan son Halima tabbas yasan son Halima ya shammaceshi yayi masa mugun kamu shi kansa bazai iya faɗin taya hakan ya faru ba,burinsa kawai ya kasance da ita,duk wani motsin da zaiyi sai ta faɗo masa a rai,ɗaura kansa yayi akan sitiyari cikin sanyin murya yace"sonki yana azabtar da ni Halimana".tuno rigimarta yayi lokaci ɗaya ya saki ƙayataccen murmushi ya kuma dannawa motan shi key ya nufi unguwar su Halima.a waje yayi parking daidai ƙofar gidan Aunty Aysha kafin ya fito zai shiga gidan kamar kullun sanye yake da wando jeans ash colour sai t-shirt black colour mai dogon hannu sosai yayi matuƙar kyau sai fitar da sihirtaccen ƙamshi yake yi ga tsadaddiyan agogon gucci ɗaure a tsintsiyar hannunsa,cover's black ne a ƙafarsa sai sheƙi sukeyi ,a hankali ya tura ƙofar gidan Aunty Aysha ya shiga sai da yaje ƙofan parlo sannan yayi sallama da gudu Khalifa ya rugo ya rungumesa yana cewa"oyoyo Uncle".ɗaga yaron yayi sama yana shafa kansa kafin yace"ina Bilal?".ɗan shiru yayi kafin yace"yaje gano aunty Halima ,kuma Umma bata sani ba yace kada na gaya".lumshe idanuwansa yayi lokaci ɗaya yaji zuciyarasa ta buga da ƙarfi ga wani irin tsinkewan zuciya lokaci ɗaya,dafe kansa yayi da yaji ya matuƙar sara mashi yayi saurin sauke Khalifa ya juya zai fito da sauri,riƙesa Aunty Ayaha tayi tace"Sudais lafiya kuwa?" shiru yayi kafin yace"Bilal,zan kira sa".be jira cewarta ba ya fice da sauri,hijab ta saka itama ta bi bayansa dan kwata kwata bata yarda da yanayinsa ba tasan dole akwai abunda ke damunsa.zaune Halima take akan bene sai jujjuya kai takeyi tana jin ansa kuwwar ihun da kuma maganar da ake gaya mata,Bilal kam yana ta tsaye gabanta yana riƙe da hannunta yana jijigawa yana cewa"Aunty ki buɗe idonki don Allah,nifa ke nazo gani ko Umma bata sani ba"ya karashe maganar kamar zaiyi kuka.a hankali ta soma buɗe dara-daran idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir kamar gauta lokaci ɗaya suka juye,zumbur ta miƙe tana rufe kunnanta da ƙarfi ga wani irin rikitaccen ihun data saki,raɗau haka Abu bilal yaji dodon kunnansa ya ɗaukar masa ihun Halima wani irin bugawa ƙirjinsa ya kuma yi ya tura gate ɗin gidan da sauri ya shigo ,Daddy,Amma da fitowarsu kenan dan jin ihun Halima yasa Daddy saurin ɗaga hannu yana cewa"ka sani hukuma ce zata fita da kai a gidan nan Aliyu,tabbas yau sai kayi dana sanin da baka taɓa yi ba a rayuwanka".ko kaɗan Abu bilal be gane abunda Daddy yake faɗa burinsa kawai yakai ga in da su Halima suke dan ya gama gane meke faruwa da wata irin murya da azabar ƙarfi ya furta"Bilal,Bilal".juyowa Bilal yayi yana ɗagawa Abu bilal hannu yana cewa"Abbana,ina sanka sosai,da fatan kazo man da Chocolate,Aunty Halima ma zata sha tunda ina santa zan sammata ko Abu bilal?".runtse ido da ƙarfi Abu bilal yayi yana cewa"no,no Hale..ee...ma,kada kimun haka".a kuma daidai lokacin ne Halima ta saki ihu tana saka hannu ta bangazo Bilal daga kan bene da azabar ƙarfi.da wani irin zafin nama Abu bilal ya ture Daddy dake gabansa yana cewa"a'a".ya ruga wajen a guje,sai dai kash kafin ya ƙarasa Bilal ya kai ƙasa idanuwansa a buɗe yana kallon Abu bilal ga hannunsa ya ɗaya yana miƙawa mahaifin nasa,shima Abu bilal ɗin hannu ya miƙa da niyar kamo na Bilal amma hannun Bilal ya riga nasa zuwa ƙasa,akan gwaiwowinsa ya faɗa yana kallon yarda jini ke malala daga cikin kan Bilal wanda ya fashe,daskarewa yayi a wurin wata irin kyarma na kwace masa ya kasa ƙwaƙwaran motsi a wurin da masifar ƙarfi ya rungumi Bilal wanda idanuwansa suke buɗe akan fuskar Abu bilal ,wasu hawaye ne suka zubowa Bilal kafin a hankali idanuwansa suka rufe ruf,Daddyma tsaye ya tsaya cak Aunty Aysha kam numfashinta ke niyar ɗauƙewa ta saki ƙara.a hankali Abu bilal ya soma ɗaga rinanun idanuwansa wanda i zuwa yanzu baya fahimtar komai miyan bakinsa ya ƙafe,kamar a mafarki haka yaga Halima kamar an jefota daga bene ta nufo ƙasa itama,wani irin ƙarfij hali yazo masa yayi saurin miƙewa ya tarota ta faɗo akan hannayensa,tana kuma sandarewa alamar ta some.da gudu Daddy ya karaso yana janyeta daga jikin Abu bilal yana jefa masa wani kallo mai wuyar fassaruwa.shikan kamar marar lakka haka ya faɗi a gaban Bilal,kuka yake son yi amma sam yaƙi zo masa ji yayi kansa na jujjuyawa kamar juwa na katantanwa da shi,da gudu Amma ta karaso tana janye Bilal daga jikinsa tana sakin kuka mai cin rai tana faɗin"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un "a guje Faruq ya karaso wurin yana ansar Bilal daga hannun Amma yayi ɗakinsa dashi dan basa taimakon gaggawa,dishi dishi haka Abu bilal ke gani ko kaɗan ya kasa furta komai sai bin jinin Bilal dake malale a wurin yake da kallo kamar wani dolo,da ƙyar ya iya tattaro sauran yawun dake bakinsa masu masifar ɗaci ya haɗiye da ƙyar yana lumshe idanuwansa yasa hannuwa ya shafi fuskarsa.a rikice Faruq ke duba Bilal kasancewar yana da kayan aiki a gida amma sam Bilal yaƙi ko da motsawa a nan kuma ya tabbatar da cewa Bilal ya mutu,in da ya ajiyeshi kam gaba ɗaya wurin ya ɓaci da jiki,ji yayi kafafunsa sunyi sanyi kamar ba zasu iya ɗaukarsa ba,jan zani yayi ya lulluɓe gawar Bilal yana cewa"Allah ya karɓi baƙuncinka Bilal".kafin jiki a sanyaye ya fito parlo,tsai tsaye ya gansu Aunty Aysha sai kuka takeyi kamar zata shiɗe ,Amma ma kukan takeyi Daddy ne zaune a chair yasa Halima a gaba sai kallonta yake wanda har lokacin bata farfaɗo ba,kallonsa ya mayar ga Abu bilal dake tsaye a jikin bango ya lumshe idanuwansa yana kallon sama ,jijiyoyin kansa sun fito radau raɗau kamar an zana su kallo ɗaya zaki masa kiga tsantsar tashin hankali ƙarara a tattare dashi.cikin rashin ƙwarim gwaiwa Faruq ya ƙarasa gabansa yana dafa kafaɗarsa.a hankali ya buɗe idanuwansa yana kallon fuskar Faruq dake nuna tsantsar karaya lokaci ɗaya,idonsa ya mayar ga ash ɗin wandonsa wanda duk jinin Bilal ya ɓata,jan hannunsa kawai Faruq yayi zuwa cikin ɗakin da Gawar Bilal take a rufe,har gaban gadon Faruq ya kaisa yana bubbuga kafaɗunsa.wani irin tsinkewa gabansa yayi zuciyarsa ta harba da masifar ƙarfi hannu na ƙyarma yasa ya yaye zanin da aka rufe gawar Bilal da ita. ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA ƘYAƘYAWAN ƘARSHE 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337. [11/13, 23:34] Jordan: 18 Baya Sudais yayi saurin yi kamar zai faɗi tarosa Faruq yayi ,kasa cewa komai yayi gaba ɗaya ya koma batun-butumi zamewa yayi daga jikin Faruq ya zauna a chair tare da dafe kansa da duka hannu biyu,a daidai lokacin ne kuma Halima ta farka daga mugun mafarkin da takeyi tana raba ido,ƙoƙari takeyi ta tuna abunda ya faru amma ta kasa,ganin su Amma na kuka yasa ta yunƙura da ƙyar tana kuma kallonsu,safko ƙafanta tayi tana binsu da kallo kafin ta hango Faruq a ɗaki,miƙewa tayi kai tsaye ta nufi ɗakin jiki ba ƙwari,kamar marar gaskiya haka ta ƙarasa shiga ɗakin.saurin runtse ido tayi tana jin zuciyarta kamar zata fasa ƙirjinta ta fito saboda ganin gawar Bilal da tayi ,mayar da kallonta tayi ga Abu bilal dake duƙe har lokacin gabansa ta duƙa tare da ɗaura hannuwanta a kan jikin shi,cikin dishewar murya tace"Yaya talk to me,is'n't you talking".ɗagowa yayi yana kallonta hawayen dake maƙale a idanuwansa suna safkowa akan fuskarshi,ba ƙaramin tsorata tayi ganin hawaye a idon Abu bilal,idasa zama kawai tayi tana fitar da numfashi a hankali..lokaci ɗaya mutuwar Bilal ta zagaye ko ina kasancewar yaro ne na mutane ga fara'a .miƙewa Abu bilal yayi yana barin ɗakin da Gawan Bilal take,da Dattiya yaci karo a gate da Mama uwani da Karima ,kuka wewe haka Dattiya yakeyi yana sharar majina yana ganin Abu bilal ya kuma rushewa da wani sabon kuka yace"wallahi wannan yarinyan ta cucemu,Allah sai ya saka mana,dole yanzu mu wuce da ita chazi ofis idan na yarda Allah ya tsinan,meye wani Halima ?,a'a kaini raba ni dole ta biya Dilalu".ta gefansu Abu bilal ya raɓa ya wuce karima ta bisa da kallo hawaye na safkowa idonta ganin yarda lokaci ɗaya ya gama fita a hayyacin shi.ciki suka ƙarasa wani irin ƙwalalo ido Dattiya yayi yace"kul ba ruwana,meye wani gidan Alhaji Abu,wanda dasa hannunsa aka kore ni ina galantiyo a titi,tona tabbata da gangan ƴarsa ta kashe wannan yaro Dilalu,alqur'an hukuma ce zata rabamu,ni ba ruwana".kallonsa duk mutanan ɗakin suke yi a haka su Mamy suka ƙaraso harda Abba babu wanda yake komai har aka gama shirya Bilal .raba ido kawai Halima takeyi ta makure jikin bango .a haka aka shigo aka ɗauki Bilal zuwa waje dan yiwa gawansa sallah.babu wanda yaga fitar Halima sai dai aka jiyo muryarta da ƙarfin gaske tana kiran"Yaya Aliyuuu".daga duƙen da yake yayi saurin miƙewa ganin yarda ta fito babu ko hijab bare hula,tana hangosa tayi kansa da gudu tare da shaƙareshi tace"Yaya kace su dawo mana da Bilal ɗinmu Allah be mutu ba,kana kallo zasu tafi maka da ɗanka"kuka ya ƙwace mata ta kasa ƙarasa abunda take son faɗa,sosai ya kamata ya riƙe amma ya kasa cewa komai,gaba ɗaya ya nemi kalamai a bakinsa ya rasa .Lamis ne ya ƙaraso yana janyota luuu ta tafi ta sume a jikin Abu bilal,miƙawa Lamis ita yayi yana saurin juyawa ganin Abba da Daddy sunyo in da suke.haka Lamis ya ɗauketa ya wuce da ita cikin gida kafin ya fito aka sallaci Bilal aka tafi dashi maƙwancinsa(Allah kayi mana kyakyawan ƙarshe).kowa ya watse a wurin sai Abu bilal dake duƙe a gaban kabarin,wasu hawaye masu ɗumi suka zubo masa yana taɓa kabarin cikin cushewan murya yace"Allah ya jikanka Bilal,ka tafi ka barni,bana da wani farin ciki ko sauran amfani a duniya bilal haka na rasa Rumana kaima gashi yau na rasaka,hasbunallahu wani'imal wakeel".dafa kafaɗunsa Lamis yayi yana ɗagosa kasa kasa cewa komai yayi sai hannunsa da yaja,bin bayansu Faruq yayi shima he's restless a haka suka dawo gida.a cike unguwan take ta ko ina da maza manya da yara harda mata ko wannensu hannunshi ɗauke da muggan makakai kowa da abunda yake faɗa.da ƙyar suka kutsa zuwa gaban gate ɗin gidan Daddy.cikin rashin fahimta Faruq ya zaro ido yace"ban gane me kuke nufi ba".a fusace ɗaya daga cikin mazan yace"abunda kaji an faɗa dai,dole a fito mana da Halima muma mu kasheta mu rama abunda take yi mana,dama itace ta kashe Junaid ta kuma kashe Zahra ƴar gidan saneta jiya da dare ta kashe Habu da Lawali daga sun ganta tana bakin kango ita da wasu la'annanun irinta yanzu kuma sai ace ta kashe Bilal yaro bawan Allah ,wallahi mun gaji da shiru ana cutar damu".sakin hannun Abu bilal Lamis yayi da sauri ya shige cikin gidan kafin su lura.a dabarbarce yace"Amma ina Halima" Amma da suke tsaitsaye suna jin bala'in da ake waje ta nuna masa Halima da aka kwantar kan chair har lokacin bata farfaɗo ba,be jira cewarsu ba ya sunkuceta ya fito parlon rufa masa baya sukayi da gudu ya fice ta gate ɗin baya ya fice da Halima daga gidan.wata nannauyar ajiyar zuciya Amma ta sauke ganin sai da aka fita da Halima sannan mazan nan suka samu karfin buɗe gate ɗin gidan suka shigo cikin compound ɗin,sai kuma ga ƴan sanda da sojoji sun iso wurin ,take wurin ya hargitse sai da aka yi halbi sama sannan aka samu rangwame aka kora maza a waje Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels